______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈💎 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ _______________★★★________________ ______________°°°°°_____________ *__GABATARWA__* Bismillahir Rahmanir Raheem. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mamallakin Ranar sakamako, tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu kuma masoyin mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, da iyalen shi da Sahabban shi, da duk wanda suka bi shi zuwa ranar sakamako. Ina ƙara gode wa Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi Mai suna “BABBAN GIDA” ina roƙon shi da ya bani ikon gamawa lafiya ya kuma yafe min kuskuren da na tafka cikin labarin yasa ƴan uwa su amfana da shi. Ameeeen. Labari ne ƙirƙirarre, haka nan sunayen cikin shi ma ba a yi su dan cin mutuncin wasu ba, sai dai duk wanda wani ɓangare na littafin yayi daidai da rayuwar su sai su gyara kuskuren su da suka fahimta daga ciki. DIAMOND LADY 💎 *___SHIMFIƊA___* Littafi ne mai ɗauke da soyayya, cin amana, rashin tausayi, gwagwarmaya ƴan uwan taka, cakwakiya da kuma zanen ƙaddara. *___GARGAƊI___* Babban gida littafin mallaki na ne, ina da haƙƙi a kan shi saboda haka ban amince a karanta min shi zuwa audio ba sai da izini na, ban Amince wasu su haɗa min document ɗin shi ba. Takun farko garaɓasa ne, haka na biyu (ƙarshe) ya kasance na kyauta shima. . Comments ɗin ku kawai nake buƙata...domin shine ƙarfin guiwa tah. *____SADAUKARWA____* Dukka littafin Babban gida sadaukarwa ne gare ki Aishatu Usman (Baby). Tabbas kin kasance ta musamman gare ni. Bazan taɓa mantawa da alkhairin ki gare Ni ba. Allah ya cika miki burukan ki baki ɗaya ya bar ƙauna💋 _____________°°°°°______________ ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝔒𝔲𝔪 ℨ𝔞𝔦𝔫𝔞𝔟🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣1️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin _babban gida_. Ina ƙaunar ku loadi loadi. Ku ci gaba da kasancewa da alƙalamin DIAMOND LADY 💎🤟 tare da comments. Barkan ku da Sallah. SHARE AND COMMENT PLEASE _______________★★★________________ Misalin ƙarfe goma sha ɗaya ne na safe (11:00am) yayin da hasken rana ya fito yayi ƙwal kasancewar yanayi ne irin na zafi da wuri rana take haskaka. Ihun da naji yasa na nufi gidan domin ɗauko report. Gida madaidaici ginin block, sai ƙofar ƙarfe me jan paint Wanda tsabagen dukan da ruwa ke mishi ya koma brown saboda tsatsa. Mutane ne zaune a ƴar rumfar dake jikin gidan wacce aka kafa ta daidai bishiyar yandi dake wajen. Gabaɗaya kallo ɗaya zaka yi wa mutanen ka tabbatar ba na kirki bane don kuwa siffar su na ainihin bayyana ɗabi'ar su ta shaye_shaye ga kuma ihu da hayaniya da suke alamun wani musu ake bugawa. Kai tsaye cikin gidan na nufa domin ganin su waye ke ihu, abun mamaki wata kyakkyawar mata ce wacce bazata wuce 32_34years ba tare da yarinyar ƴar kimanin shekaru 10years. Jibgar su mutumin yake yi wanda kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar ba kan shi ɗaya ba kuma da gani mahaifin yarinyar ne wato mijin matar. Ba ko ƙaƙƙautawa kamar wanda aka bawa contract ɗin hakan yayin da Mamah babu abun da take sai hawaye. Ita kuwa Zahrah bakin ta bai mutu ba yayin da shima yaƙi dakatar da dukan da yake mata. “Wallahi ba zamu taɓa yafe maka ba, mugu kawai azzalumi” Cike da mamakin ta mutumin wanda ba zai wuce shekaru 45years ba yake duban yarinyar baki buɗe. Ina da sabo ai ya saba da rashin kunyar Zahrah sai dai bai yi tsammanin ta kai har haka ba. Yanzu tsofai tsofai da shi ko kunyar shi ba zata ji ba take zazzaga mishi rashin kunya. (Ni Ko na ce ina tsufa a nan, bayan ko mutuncin kanka baka kama ba) Ganin shirun nasa yayi yawa yasa ta goge hawayen da ke kan fuskar ta tana watsa wa mutumin kallon banza “Wallahi Kawu ba zaka taɓa shiga aljanna ba in dai baka tuba ba, haka kawai bamu maka laifin komai ba ka kama jibgar mu, wallahi Allah sai ya saka mana...” Bata kai ga ƙarasa abun da tayi niyyar faɗa ba taji an hanɓare mata baki, ba tayi mamaki ba saboda haka halin mamah yake sai kace damo, Gashi dai babu laifin da suka yi wa kawu yake dukan su, amma ta kasa yin komai, ita da take ƙoƙarin yi kuma an hanata.. wannan ai shi ne a dake ka a hana ka kuka. “Ke Zahrah me yasa kam baki da hankali? Eyeh!! Ɗan uwan ubanki ne fa kike zagi” Ta faɗa tare da jan hannun Zahrah zuwa ɗakin ta. Shi kuwa Kawu tsabagen mamakin Zahrah da ya cika shi bai iya taɓuka komai ba har sai da suka shige ciki sannan ya samu damar ficewa daga gidan yana mai nufar dabar su dake ƙofar gida ranshi a ɓace. Hawaye na kawai ke zuba idon Zahrah yayin da Mamah ta ɗan murmusa tana jin takaicin irin halin da ta sanya kanta. A hankali ta fara magana cikin sassanyar murya wacce ke ɗauke da zallar sarewa.. “Haba Zahrah! Wai sai yaushe ne zaki sauya ɗabi'un ki?” Ta ƙarasa tare da bin ta da kallon tuhuma. Tura ɗan ƙaramin bakin ta Zahrah tayi sannan ta kalli Mamah “Haba Mamah manah, wai sai yaushe ne zaki samu ƴanci a cikin gidan nan! Kin san dai Kawu ba ƙaunar mu yake yi ba kuma don meh zai ke dukan mu kamar wasu bayin sa, Ni wallahi Mamah ba zan ƙyale shi yayi ta zaluntar ki ba! Shine kawai. Ta ƙarasa tana gurmuɗa bakin ta tamkar tana gaban Kawu. Jikin Mamah kuwa sanyi yayi da maganar Zahrah, Zahrah dai yarinya ce amma in ta zari magana ko wani babban iyakaci sai dai ba zata zuba mata ido ta lalata mata aure ba. Sam Zahrah bata da haƙuri ko na misƙala zarratin ammah ta ɗauki aniyar sauya ta da yardar Allah. Bayan sun gama kukan su ne Mamah ta ƙara jan hankalin Zahrah kan rashin kirki da take tafkawa. “zahrah'u ke har yanzu yarinya ce, ammah zan ci gaba da nuna Miki hanya saboda gaba, idan babu Ni zaki sha matuƙar wahala” Zahrah da gabaɗaya ta ƙosa da zantukan Mamah yasa ta gyaɗa kai sannan ta miƙe ta nufi ƙofa. “mamah nikam na tafi can gidan su Amira wasa na” Mama dai da addu'a ta bi ɗiyar tata sannan ta tashi don ta kammala wankau ɗin da aka Kawo Mata zuwa yamma kuma zata wuce kasuwa. ★★★★★★ Ɓangaren kawu kuwa cikin fushi ya nufi dabar dake ƙofae gidan shi kamar an aika mishi da saƙon mutuwa. Mutanen da ke zaune a dabar kuwa da wata mahaukaciyar dariya suka kece suna tafa hannaye.....kallon banza da Kawu ya watsa musu yana muzurai kamar wani dodo yasa suka tsagaita. “Haba Ale Idrisu, kar ka bamu kunya Manah! Kai da kace yanzu zaka fatattako su har waje ya naga kai ka dawo” Faɗin Baba Mola kenan wanda shima mazaunin dabar ne kuma ɗaya daga cikin tawagar Ale Idrisu. Kallon shi Ale Idrisu yayi sannan ya sauƙe murya ƙasa saboda kada sauran tawagar su ji yace “wallahi wannan tsinanniyar yarinyar ce da ke hana ni rawar gaban hantsi, ammah zan ci ubanta ne shegiya” Dariya Baba Mola yayi sannan ya dubi abokin shi Ale Kabir kafin yace “kada ka damu aboki na, shawara ɗaya kawai zaka bi domin samun muradin ka!” Cike da ƙaruwar Ale Idrisu ke kallon Baba Mola Wanda ke wani lumshe idanuwa tamkar mai jin bacci yana washe bakin shi da ya koma baki tsabar zuƙar sigari da yayi mishi kanta. “Na faɗa maka yarinyar nan kawai ka samu ka haɗa ta ka kai ta gidan mata, tun yanzu inda ta saba da can kaga shikenan, ko ka manta da alƙawarin da kayi wa shugaba ne?” Zaro idon shi yayi nan da nan alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskar shi. Hakan yayi daidai da fitowar Zahrah zuwa gidan su ƙawar ta. Kallon banza ta bi su da shi tana tofar da yawu irin taga kashi ɗin nan ta wuce. Shi kuwa Kawu ganin ta sai ya ɗaure fuska yana ƙara maida hankalin sa ga Baba Mola. Ɗan baƙi ne ya juyo ya kalli uban gidan sa bayan wucewar Zahrah yana wani lashe baki tamkar maye. “Yah oga nifah nayi kamun yarinyar nan, kyakkyawa ce son kowah, ah nidai zan jira nan da shekara biyu zuwa uku kawai ka wullo min ita” Ya ƙarasa yana tanɗe baki. Kallon baka da hankali Kawu ya wulla wa ɗan baƙi. “Lallai ɗan baƙi baka da hankali, in kai ina yarinyar da ko shekaru goma bata wuce ba! Wai ma an ce maka duk rashin son ta da nake zan baka ita ne, Toh ita ɗin mallakin ɗan masu kuɗi ne kuma jari ce a gare ni! Saboda haka ka kauda idon ka a kanta tuntuni ka riga kasan da hakan koh?” Ya faɗa yana cije leɓen shi sannan ya maida hankalin shi ga Baba Mola suka ci gaba da maganar su. Ɓangaren Zahrah tunda ta wuce dabar su Kawu ta fara ɗan gudun ta tana tsalle tsalle irin na yara da ta saba yi har ta zo wajen wasu yara da suke wasa waɗanda su ma ba zasu wuce sa'annin ta ba. Wani daga cikin yaran ne ya watso mata ƙasa ai kuwa bata yi wata wata ba ta cakumo shi ta fara narka kamar ɗan ta. Wani tsoho ne yazo wucewa ya fara raba faɗan ammah Zahrah ta ƙi sakin Yaron nan. Duka kawai take kai mishi yayin da yayi la'asar har abun tausayi. Tsoho kuwa da yaga yarinyar ta fi ƙarfin shi yasa ya koma gefe yana jiran ko Allah zai kawo wani matashi.. Cikin motar shi yake ƙirar Mercedes Benz Mai tinted glass ya shawo corner ɗin. Ganin yarinya ƙarama ta kama yaro sai jibgar sa take gashi ya kasa tsinana komai alamun ya jima a hannunta ya sa shi yin parking. Cikin takun sa na ƙasaita ya fito. Ba tare da ya ce komai ba ya nufi wajen da yarinyar take su kuma sauran yara sai kallon su suke saboda suma tsoron yarinyar suke kada su je garin rabiya ta dawokansu. Hannun ta ya riƙe tare da jan ta gefe ammah ina Zahrah ta yi wani kukan kura zata ƙwace, jin ƙoƙarin ta na kwacewa yasa yayi murmushi sannan ya juyo da ita tana fuskantar shi. “ke bari Manah!” abun da kawai ya faɗa sannan ya ɗago yaron da ke kwance a ƙasa jikin sa kaca kaca da ƙasa. Bata yi yunƙurin sake kamo yaron ba saboda irin kwarjini da yayi mata sai ta ja gefe tana saita numfashin ta. Yaro kuwa ganin an ƙwallon e shi ai gidan su kawai ya nufa ba tare da yace komai ba. Ishaq kenan, ɗa ɗaya ga Cancellor wanda ya kammala karatun shi na mass communication yanzu haka next month zai wuce America for his masters. Kallon ta yayi lokaci ɗaya yaji yarinyar ta burge shi, yana so yaga mace jaruma, wacce bata bari a gano raunin ta. Murmushi yayi mata sannan yace “ƴan mata ya sunan ki” Zahrah kuwa tayi tunanin zai dake ta ne amma jim tambayar da yasa ta ce “Zahrah” Yace “wow! Nice name" duk da cewa bata San meh yace ba da turanci kawai sai tayi murmushi har dimple ɗin ya ya lotsa. Ishaq kuwa samun kan shi yayi da zuba mata ido sannan yace “which class are you now, yau Monday Mai ya hana ki zuwa makaranta?” Lokaci ɗaya yanayin Zahrah ya sauya gashi yayi mata turanci kuma bata so ya gane cewa bata iya ba. Can tace “ai ba a yin komai a makarantar ma, shi yasa bamu zuwa yanzu ma gidan su Amira zanje” “waye ce amirah?” “ƙawa ta ce” “toh muke na kai ki sai kike nuna min hanya” Kafaɗa ta maƙe alamun ba zata je ba, ko kaɗan Mamah ta hana ta kwaɗayi balle har shiga motar ƴan gayu, inaaaa ba zata shiga ba. “tsoro na kike ji Zahrah? Sunkuyar da kanta tayi sannan tace “a'ah” Cike da kulawa ya tsuguno daidai yadda tsayin su zai daidaita ya kamo hannun ta “kin ga cutie ki ɗauke Ni matsayin yayan ki, kada ki ji tsoro na bazan cutar da ke ba” Cike da gamsuwa ta kaɗa kanta sannan yayi murmushi yace “good! Taho mu tafi" Bin bayan shi tayi sannan ya buɗe mata seat ɗin mai zaman banza, bayan ta shiga ya rufe sannan suka fara tafiya tana nuna mishi hanya. “cutie kika ce baa komai a makarantar, wa ce kike zuwa?” “bamu da nisa da makarantar, primaryn gwamnati ne" Zaro ido Ishaq yayi sannan yace “kina so na sauya miki makaranta?" Tuni ta ɗaga kai abun ka da yarinya babu hankali. Shi kuwa murmushi yayi sannan yace “alright zan saka ki wata makarantar ammah sai kin daina faɗa irin wannan da na tarar kina yi..." Bata jira ya ƙarasa faɗin abun da ke ranshi ba tace “na yadda, na ma daina daga yau” “shikenan zaki raka Ni gurin baban ki ai?” “aah Baba na ya rasu, sai dai Kawu na da Mamah na, kuma Kawu ba so na yake yi ba kullum sai ya duka mu Ni da Mamah na” Cike da mamaki Ishaq ke kallon Zahrah sannan yace “shikenan sai ki raka Ni wurin naman naki" a daidai nan suka iso gidan su amirah sannan yayi parking. Kallon ta yayi sannan yace “cutie yaushe zaki koma gida?” “sai da Yamamah zan wuce kasuwa taya Mamah aiki" “shikenan zan zo da yamma kin ji, sai muje wurin Mamah ɗin" Daga haka ta fice da gudu ta nufi gidan su Amira ko godia bata mishi ba. Ya dade kafin ya ja motar shi ya tafi yana mamakin zantukan Zahrah, kuma yayi niyyar tallafawa rayuwar ta. KO DAI ISHAQ SON ZAHRAH YAKE? TOH IN SON TA YAKE YA ZAA YI DA KAWU? KO MAMAH ZATA AMINCE? MENENE ALAƘAR KAWU DA MAMAH? Duka amsoshin ku na cikin littafin *_Babban gida_* Yanzu ma aka fara! Ku ci gaba da bibiyar alƙalami na don nishaɗantuwa, ilimantuwa da kuma samun faɗakarwa. COMMENTS ƊIN KU NA DA MATUƘAR AMFANI DOMIN SHINE ƙWARIN GUIWA TA DIAMOND LADY ce💎🤟 ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈💎 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣2️⃣ Wannan shafi naki ne masoyiya AISHA MB (MHIZ ISHA) marubuyar littafin _aljanar ruwa ce_ Thanks a lot for ur selfless actions friend, loads of love🤩😘 Barka da Sallah SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Anyi sallar azahar kenan sai ga Yaya Ishaq ya zo kamar dai yadda ya faɗa, ya rasa ma ta yaya zai kira cutie ɗin tazo. Wani yaro ne yazo wulgawa ai kuwa da sauri ya dakatar da shi. “kai yaro zo” ba tare da musu ba yaron ya je wurin yaya Ishaq Ɗan kallon yaron yayi sannan yace “ka ɗan shiga gidan nan kace Zahrah ta zo inji yaya ta” Ba musu yaron ya buɗe ƙofar gidan sannan ya shiga ɗauke da sallama a bakin shi. “Salamu Alekum” Maamahn Amira da ke shara ita ta amsa masa tana mai dakatawa da sharar don jin neh yaron yazo yi “wai Zahrah tazo in ji yayan ta a waje” Bai jira amsar da maamah zata bashi ba ya fice abun da. Yayah Ishaq kuwa har kuɗi ya bawa yaro. Maamah ce ta ƙwala kiran amirah da suka wuce can filin bayan gidan suna wasan su. Jin shiru basu amsa ba yasa ta wuce a fusace “ke ƴar karuwai ki fito yana jiran ki a waje” Cike damamaki take kallon mamah. Shin meh yasa ake danganta ta da karuwanci?, Menene laifin ta da za'a ke mata hakan? tunawa da sabon yayan ta Ishaq da tayi, ai kuwa da gudu ta fita tana yi wa amirah sai da safe. Tana ganin yaya Ishaq ta ɓare baki kamar gonar auduga yayin da shima yake jin ta ajikin shi. Babu abun da yake yi sai aika mata da saƙon murmushi. “cutie, kin ce zaki kai Ni wurin Mamah koh?” Zaro ido Zahrah tayi kamar wata munafika. Shi kuwa yaya Ishaq jin. Shiru yasa ya ƙara kallon ta tare da faɗin “cutieeee...” Ɗan tunani tayi da ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwar ta sannan tace “toh yaya muje” “yauwah cutien yaya.” A hankali yake driving ɗin yayin da hankalinsa kwacakwam ya dawo gare ta. “cutie mai Mamah take ji a kasuwa da yamma” Ɗagowa tayi da har zata yi shiru wata zuciyar tace ki faɗa masa wataƙila sanadiyyar haƙa sai ya samar muku sauƙi daga muguntar Kawu. “mamah fah masa take soyawa a kasuwar kasan saboda meh?” Kai ya girgiza kamar wani yaro yayin da ta marakraice fuska “idan taje tayi Masar ne take samun kuɗi, sauran Masar kuma muna ci da daddare saboda Kawu baya bata kuɗin abinci, sai dai shi ya shigo da ledar abubuwan sa da tsire da irin lemon jarkar man ammah baya taɓa ko sanmana..” can ta ɗan yi shiru “kuma da kuɗin Masar Mamah take min kayan sallah, sannan tana wankin gidan Cancellor ma saboda ta samu kuɗi” Jikin yaya Ishaq sanyi yayi jin irin wata rayuwa. Yana nanata wa a ranshi wai baya basu abinci. Kai anya wasu mazan ko zasu shiga aljanna? Ka auro mata ka rabata da gidan su ammah ba zaka iya ciyar ta ba? Haba maza ai kuwa zan taimakawa waɗannan ahaki ko meh zai faru. Zahrah kuwa da taji shirun yayi yawa sai ta ɗan taɓo fuskar shi “ka fasa zuwa ganin Mamah koh?” Jijjiga kai yayi sannan yace “aah cutie, zanje naga mamah” Isar su kasuwa keda wuya suka fito, Zahrah ce gaba sai yaya Ishaq da ke bin bayan ta. Directly rumfar da Mamah ke ƙosai ta nufa. “Mamah ga sabon yayah nah” Mamah da ta ke kwashe Masar da ta soyu ta ɗago ɗan bata fahimci meh Zahrah ke faɗi ba. “ya Hajiya Balaaba ɗin” Ɗan yamutsa fuska tayi da ta tuna wulaƙancin da maamah ɗin tayi mata sannan tace “lafiyar ta ƙakau, tace a gaishe da ke” murmushi Mamah tayi sannan ta zuba masa uku a plate ɗin roba sannan tace “ga Masar nan kici,, nadan baki ci komai ba” Amsa tayi ta ajiye sannan tace “mamah ga sabon yaya nahiyar yazo gaishe ki” sai a lokacin Mamah ta lura da yaya Ishaq dake tsaye harɗe da hannayen shi a ƙirji. Shi kam hankalin shi baya kan shi, in ba da kallon su Mamah babu abun da yake yi. Gyaran murya Mamah tayi, sai lokacin ya ɗan miƙe da kyau sannan ya nufi rumfar Masar. Duƙawa yayi ya gaida Mamah cike da girmamawa. “ina wuni Mamah, ya aikin” “lafiya ƙalau ” kawai Mamah tace fuskar ta na ainihin bayyana mamaki da kuma kuɗin da ta shiga, idan bata yi ƙarya ba ai wannnan yaron gidan Cancellor ne. Ganin yanayin Mamah yasa yaya Ishaq ya murmusa.. “mamah nimah ki ɗauke Ni kamar ɗan ki, ki ɗauke Ni kamar yadda na ke jin ƙanwa ta Zahrah a jiki na, bani da niyyar cutarwa a gare ku sai dai ina don tallafa wa rayuwar ku.” Murmushi mamah tayi “babu komai yaron nan ammah kai ɗin waye, kuma a ina kaga zahrah.” “mamah Ni ɗa ne a wajen Cancellor sannan kuma na haɗu da Zahrah ne hanyar tafiyar ta zuwa gidan su Amira ƙawar ta” Tun daga farko har kaita gidan su amirah da yayi ya labarta wa Mamah. Salallami ta fara “shikenan Ita dai Zahrah ba zata taɓa sauya halin ta ba kenan, toh Allah dai ya shirya” Murmushi yaya Ishaq yayi sannan ya matso cikin rumfar, gefen matackn da take ajiye soyayyiyar masa yayi sannan ya kwashe ledodin,, duk wanda yazo siya da kan shi yake zuba musu har lokacin maghrib yayi. Masallacin da ke cikin kasuwar yaje yayi Sallah ya dawo. A lokacin Mamah har ta gama haɗa kayan suyar ta zasu dawo gida. Ƙarasawa yayi ya ce “mamah a kwaso kayan sai mu tafi.” Ƙasa musu mamah tayi kawai ta umarci Lauwali almajirin dake taimaka mata da su wuce. Har wajen motar suka nufa sannan ya jera kayayyakin suka wuce ɗiiiiiiiiiii sai gidan Kawu. Mamah kam lumshe ido tayi yayin da zuciyar ta ta karye, tunanin when last tashiga mota take yi tun ranar da aka kawo ta gidan masoyin ta Abdulkarim Kuru. Lokacin da ta cire tsammanin wahala a rayuwar ta sai gashi yanzu ɗan uwan masoyin ta na gasa mata aya a hannu. Suna isowa Lauwali ya ciro kayan ya shigar da su gida, abun mamaki lokacin dabar su Kawu babu kowa sai Aminu Aljan. Basu mishi magana ba suka kutsa cikin gidan. Bayan sun ajiye komai Mamah ta shimfiɗa wa yaya Ishaq sallaya ya zauna sannan ita ma taje tayi sallah. Mutuniyar kuwa kwantawa taje tayi. Har Mamah ta idar da Sallah bata ga giftawar Zahrah ba yasa ta ƙwala mata kira “zahrah, Zahrah fito ki je ki siyo wa Ishaq ruwa gidan su Badi'ah.” Zahrah da bacci ya ɗan fara kwashe ta ta turo baki gaba sannan ta fito. Mamah sake baki tayi tana kallon ta ganin ko Sallah bata yi ba. Harara ta ɗan yi mata sannan tace “wuce kije kiyi sallah” Juyawa Zahrah tayi tana ɓata fuska kamar wainar fulawa sannan taje tayi alwala don yin Sallah. Lauwali kuwa ya gama wanke kayayyakin kamar yadda ya saba yayi ma Mamah sai da safe. Yaya Ishaq ne ya ƙira shi bayan yazo ya zaro 5k a aljihun shi ya bashi. Godia sosai Lauwali yayi sannan ya wuce. Zahrah na idar da Sallah ta fito, gefen yaya Ishaq ta zauna sai wani tura baki gaba take yi kamar wani pipe😄. Harara Mamah ta maka mata kafin ta ce “tashi kije gidan su Badi'a ki siyo masa ruwa da lemo.. ba musu ta miƙe duk da cewa bata don zuwa gidan. Badi'a Sa'ar ta ce ammah basa shiri ko kaɗan saboda yadda suke treating nata. Gaba ɗaya unguwar babu wanda ke kyautata musu inda ka cire gidan Cancellor sai kuma Ammin Badi'a, ita dai bata tsangwamar su ammah bata shiga sabgar su. Bayan ta siyo ta kawo gaban shi ta ajiye, Mamah ta zubo mishi Masar a plate sannan ya fara ci ba tare da jin ƙyamar su ba. Ita ma Mamah tace tare da Zahrah. Bayan sun gama ci yaya Ishaq ya sanar da Mamah ƙudurin shi na maida Zahrah private school da ke kusa da su. Mamah tayi farin ciki sosai har da kukan ta zai aikin godiya take rabza wa Ishaq, shi kuwa duk kunya ta cika shi. Da haka yayi musu sallama ya wuce zuwa gida zuciyar shi wasai. ★★★★★ Sai wajen ƙarfe sha biyu na dare (12:00pm) Kawu ya dawo, su kuwa lokacin sun riga da sun rufe gidan. Bugawa yake ta yi babu ƙaƙƙautawa sai kututtuma ashar yake yi. Sama sama mamah ta jiyo ƙarar buga ƙofa,, a zabure ta miƙe zuwa hanyar waje. “dan abu ta kazar ubanki ki kizo ki buɗe min ƙofar nan inda ba haka ba in na shigo sai na lahira ya fiki jin daɗi. Jinjina kan ta tayi kafin taa nufi ƙofar. Tana buɗe ƙofar ko ya banko ta har sai da ta buge kan Mamah. Layi ya shigo yana yi alamun yayi mankas abun shi. Mamah kuwa cikin zuciyar ta tana Allah wadaran wannan miji nata. Ƙunshi ledar hannun shi ya ya ƙara ƙanƙamewa kamar za'a ƙwace mishi daga hannun shi. A haka ya nufi ɗakin shi cikin tangaɗi har ya isa bakin ƙofa.. juyowa yayi ya kalli Mamah before ya shige ya na banko ƙofar. Hawayen da ke zuba kan fuskar ta ta gode haɗi da wucewa nata ɗakin. Ba ita ta ta kwanta ba sai da ta yi alwala ta fara jera nafila tana roƙon Ubangiji ya kawo mata ɗauki. _______________**********_______________ Ina kuke bayin Allah masu buƙata! Ina waɗanda ke cikin damuwa, ina waɗanda suke buƙatar neman wani zaɓi wurin Ubangiji. Toh ga damah nan wacce take guarantee. Manzon ALLAH صلي الله عليه وسلم yana cewa:- “idan dare ya wuce tsakiya ALLAH ( Subhanahu wata'ala ) yana sauƙowa zuwa saman duniya sai ya ringa cewa:- ( shin akwai mai neman gafara a gafarta masa ? ) yana ta fadar hakan har zuwa ketowar alfijir. ( saheeh musleem ) Saboda haka duk wata damuwa da kike da ita, don't hesitate to ask Allah, baya gajiya da amsa buƙatun bayin sa. Ki tashi kiyi sallah, koda raka'āt biyu ne sun wadatar ki roƙi Ubangiji kina mai yaƙini da shi, sai kiga ya amsa miki. Kina cikin damuwa? Matsalar gidan aure ko kuma jarrabawar rayuwa, toh kada ki kuskura ki cire yaƙini a addu'a. YA hayyu~ya~Qayyum!! Kayi gafara agaremu da iyayanmu da 'yan uwanmu da masoyan mu da sauran al'ummar musulmai. KO YA ZATA KAYA? WANE NE KAWU?ME ALAKAR SHI DA ZAHRA?, MEH YASA YAKE CUTAR DA ITA? YA KUKE TUNANIN ZATA KAYA IDAN KAWU YA FAHIMCI CEWA WANI NA ƘOƘARIN TAIMAKAWA MAMAH? AMSOSHIN KU NA NAN TAFe, BA A FARA LABARIN BA HAR SAI MUN JE BABBAN GIDA. KU CI GABA DA KASANCE WA DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY DOMIN NISHAƊANTUWA DA KUMA ILIMANTUWA. COMMENTS ƊIN KU KAWAI NAKE SO DON SHINE ƙWARIN GUIWA TA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎🤟 Oum Zainab ce! ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙱 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈💎 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰0️⃣3️⃣ Shafin ku ne ƙawaye na ZAINAB SHEHU UMAR ( ZEELY) SA'ADATU LAMARA ZULKHAIRAT (Matar mijinta) RABI'ATU ABDULLAHI HASSAN (matar Ɗan jagade) FATIMA AHMAD ABDULLAHI (Fatima anatomy) Ina ƙaunar ku saboda Allah Barkan ku da Sallah SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Sassafiya Mamah ta tashi da aikace-aikacen gida. Sai around 8:00am Zahrah ta fito tana miƙa “oooooooooooh” Mamah ce ta kalle ta sannan ta kawar da kai. Wurin Mamah ta taho “ina kwana Mamah" “lafiya ƙalau Zahrah kije kiyi wanka sai ki siyo manah ƙosai da koko gidan Mati." Da “toh Zahrah ta amsa tana wucewa banɗaki. Bucket ta cika da ruwa sannan ta shiga toilet ɗin. Wanka tayi ta fito. Rigar ta ƴan kanti wacce ta ɗan ji jiki ta saka kafin ta shafa mai. Tana gamawa ta janyo hijabin ta da saman shi ya ɗan koɗe saboda dukan rana. Fitowa tayi ta cewa Mamah “kawo kuɗin” miƙa mata 500Naira tayi sannan tace “ki siyo bread 🍞 Babba guda ɗaya da canjin. “toh" Daga haka ta fita zuwa gidan Mati da ke kan kwanar layin su. Tana fita ƙofar gidan su nan a cike kamar wadda za'a yi taro sun cika rumfar wasu kuma har da kan dandamalin da ke jikin gidan sai ihu suke suna buga uban shewa da gani kaga tataccun ƴan iska. Kallo ɗaya tayi musu ta kau da kanta gefe haɗi da tsaki. Aljan ne ya hango ta sai wani fara washe baki “ƴar oga! Ina zaki haka da sassafe" Bata yi tunani da ita yake ba shi yasa ko kallo bai samu daga gare ta ba. Su kuwa sauran ƴan dabar suka saka ihu nan suka fara tsokalar Aljan. Da ɗan gudu ta isa gidan sannan ta bada kuɗin ta haɗi da miƙa jug ɗin roba da ta zo da shi. Ana sallamar ta ta amsa bread wajen Bala Mai shayi daga nan ta wuce gida. Kamar dai ɗazu wurin a cike yake ammah haka ta wuce abun ta saboda gargaɗin Mamah kan kada ta kuskura ta ce zata kula wani a dabar. A ɗakin mamah suka karya, Bayan sun karya Mamah ta ɗauƙo wasu kuɗaɗe daga aljihun doguwar rigar da ke jikin ta. Kuɗin zasu kai 15k. Da mamaki Zahrah ke kallon kuɗin, duk da bata da wayo sosai ammah ta san wannan kuɗin da yawa suke “mamah kuɗin menene wannan?” “yayan ki Ishaq na da kirki sosai, ya bamu ne mu ƙara a jarin masa” Ko rufe baki Mamah bata yi ba taga ana shigowa da kayan abinci, shinkafa, taliya, macaroni, indomie da mai har da manja. Mamaki ne a fuskar su har lokacin da aka ce “a ina za'a ajiye su?” Nuna musu ƙofar ɗakin ta tayi don kuwa nan ne wajen da zasu rabauta daga hannun Kawu. Suna gama shiga da su suka fita. Mamah bata bar mamaki ba ammah tayi shiru abun ta. Sai wajen 11:00am Kawu ya banko ƙofar ɗakin shi fuskar nan duk yawun bacci alamun ko sallar asuba bai yi ba. Wata shegiyar miƙa da yayi abun takaici Mamah dai jinjina kai tayi tana roƙon Allah ya shirya Yunusa.. Wani kallon banza ya watsowa Mamah sannan yace “ke ɗan ubanki shine jiya kina ji ina buga gida kika ƙi buɗe min? Gidan na ubanki ne? Nace na ubanki ne gidan?” Mamah dai bata kula shi ba ta ci gaba da yi wa Zahrah bayanin yadda zasu sauya kasuwancin nasu. Sheƙa Kawu yayi hakan yasa ya kawo wa Mamah wani uban duka. Caraf Zahrah ta tare ai kuwa sai a tsakiyar kanta wanda yayi sanadiyar faɗuwar ta ƙasa sumammiya. A firgice mamah ta yo kanta tana jijjiga ta ammah shiru. Hakan bai ishi Kawu ba sai da ya ƙara kawowa Mamah wani dukan. Bata damu ba saboda hankalin ta da ya matuƙar tashi kada taje ta rasa ɗiyar ta. Ba tare da ya damu ba ya fice zuwa dabar tasu. Wani ihu suka sa suka fara yi mishi kirari “Takawar ka lafiya Yunusa BabanMutuwa, kayi yadda kaso da uban kowa, ita kanta mutuwar tsoron ka take, kaga sarki mai cikakken iko” Dariya yayi jin yadda ake fasa mishi kayi nan da nan majalisa ta fara, ana shan sigari ana gulma tare da kututgumo ashar. Authubillah! ★★★★★★★★ Ta ɗauki kimanin mintuna 20 kafin Zahrah ta ja dogon numfashi wanda lokaci ɗaya ta saki wani irin ihu. Mutanen da ke waje kan su sun tsorata bare kuma Mamah dake kusa da Zahrah, wasu faratu ne zaƙo zaƙo suka fara fitowa daga hannun ta sannan ƙwayar idon ta ta juya baka ganin komai sai farin idon da ya sauya zuwa blue colour ga wani girma da jikin ta ya ƙara tamkar wata aljana da ta fito filin daga. Mamah ko rasa yadda zata yi da ita tayi, banda ɓari babu abun da jikin ta ke yi. Miƙewa tsaye Zahrah tayi tana nufar hanyar waje, Mamah bata yi ƙoƙarin riƙe ta ba saboda ita kanta a tsorace take. Hakan yayi daidai da shigowar Kawu cikin gidan. Zaro idanuwa yayi cikin kiɗima ya fara ja da baya da niyyar guduwa.. Kirif!! Ƙofa ta rufe kanta yayin da halittar dake gaban shi ta sheƙe da wata dariya maras daɗin ji. “Hahhhhhhhhh_hhhhhhhhh_hhhhhhhhhhh” dariyar da bata tsaya ba sai bayan minti 10. Kawu kuwa duk rashin tsoro irin nashi yau yaji, ai ance faɗa da aljani ba daɗi.... gabaɗaya zufa ce ke ketowa a jikin shi, bata yi mishi komai ba kawai hannun ta ta ɗaga sama lokaci ɗaya Kawu ma ya ɗago bisa iska. Gefe ta wulla kawu kafin ta ƙara daga shi can sama a wannan karon, wani irin jujjuya shi take wanda hannun ta ne ke famar yin wannan aiki ɗin, bugawar da tayi mishi sai da ƙasa ta jijjiga, tuni ƴan majalisa suka watse duk da basu san daga ina bane hakan. Ko motsi Kawu baya yi hakan yasa ta busa mishi iskar bakin ta daga wurin da take. A wahalce yaja wani dogon numfashi. Bai zata ba bai nufa ba sai ka cinnaku sun kewaye shi, cizo ta ko ina yi masa suke. Babu abinda yake banda susa da kururuwa. Duk abinda ke faruwa Mamah ta kasa cewa komai. Sai can ta samu bakin magana “zahrah don Allah kiyi haƙuri ki bar shi haka ai yaji jiki” “hhhhhh_hhhhh" bayan wani lokaci tayi shiru sannan ta juyo tana fuskantar Mamah Cikin haɗe fuska take magana “Madina! Wannan ba Zahrah bace nice!” ta faɗa cikin Muryar ta maras daɗin saurara.. Jikin Mamah ne ya fara tsuma hakan yasa Zahrah hura wa Kawu iska, nan da nan cinnakun suka ɓace ɓat! Jikin shi kuwa duk ya kumbura, ga uban ciwon da yake masa. Banzan kallo halittar ta watsa mishi sannan tace “Idrisu BabanMutuwa!" A tsorace Kawu ya ɗaga sannan ya maida kan sa ƙasa “ka saurare Ni da kyau! Ka gama naka mulkin yanzu lokaci na ne! Ka daɗe kana cutar da mahaifiya ta da bata taɓa zaluntar ka ba!” A lokacin mamah ta zube a ƙasa sumammiya. Duk wannan na daga cikin shirin halittar. “Idrisu Ni na san ka! Ka cutar da rayuwar mu, baka san cewa na san kai ne ka kashe mahaifi naba koh?, Kai ne ka hana Mamah komawa ga dangin ta ta hanyar sihiri koh? Toh wallahi ka kuskura ka ƙara wani kuskure kan hakan zan tona asiri har ƙwayoyin da kake siyarwa” Kawu dai an rasa bakin magana,kai kawai yake jijjigawa. “magana zaka yi ba jijjiga kai kamar gwaje ba” “eh na daina wallahi na daina” Daga haka ta ɗaga hannun ta lokaci ɗaya shima ya tashi bata direshi ko ina ba sai cikin ɗakin sa. Tana fitowa ta ɗaga Mamah ma ta kai ta kan katifar ta. Daga nan ta hura mata iska ita kuma ta faɗi ƙasa kamar matacciya.. Numfashi Mamah ta sauƙe lokaci ɗaya kuma ta tuna meh yake faruwa. Tana juyo wa taga Zahrah kwance kamar gawa.. A hankali ta nufo ganin kamar bata motsi yasa Mamah saurin ɗebo ruwa a cup, addu'ah ta tofa ciki sannan ta shafa mata a fuska. Numfashin da Zahrah ta ja yasa Mamah jin sanyi cikin ranta. A hankali ta fara buɗe idanuwan ta tana mai tuna abun da ya faru. “Sannu Zahrah, ina ne yake miki ciwo?” ta faɗa a kiɗimce “mamah kai na” “sannu yi haƙuri bari na je na siyo miki magani, ki jira Ni kada ki fita kinji..” Hijabin ta ta janyo ta fito, karo suka ci da ya Ishaq ƙofar gida ba tare da yan shi bane ta gota zata wuce. Cike da mamaki yace “mamah meh ke faruwa?” sai a lokacin Mamah ta ɗago “zan siyo paracetamol me a nan chemist zahrah ce ba lafiya.” “subhanallah, toh ki koma ciki bari na shigo Mu kai ta asibiti.” Da kan shi ya ɗauko Zahrah ya saka ta a mota. Babu ƙaƙƙautawa suka isa asibiti. A&E (Accident and Emergency) aka nufa da Zahrah. Taimakon da ta samu daga wurin likitoci yasa ta ɗan ware. Sai wajen 5:00pm aka sallame su ammah kafin nan Doctor ya nemi magana da namijin saboda matar kam duk a ruɗe take. Bayan sun shiga office ɗin doctor, a hankali doctor ɗin ya kalli yaya Ishaq “bawan Allah garin ya kuka bar ƙanwar taka damuwa ta mata yawa, yarinya ƙarama a ce BP nata na elevating haka tun yazo, gaskiya da matsala ko ma meh take so ya kamata Ku bata” A sanyaye yaya Ishaq yace “in sha Allah doctor za'a kiyaye” Daga haka ya fito. Da kanshi ya ƙara ɗaukan Zahrah suka nufi mota har suka isa babu wanda yayi magana. Bayan sun isa Mamah da kanta ta wanki Zahrah da ruwa mai zafi sannan ta haɗa mata tea Mai kauri da sauran kayayyakin da Ishaq ya siyo musu. Bayan sallar maghrib yaya Ishaq ya fita sallah sannan Mamah ma tayi. Kallon Zahrah tayi tace “zaki iya sallar?" Kai ta gyada a hankali Mamah ta taimaka mata tayi alwala a zaune sannan tayi sallar ma a zaune. Bayan yaya Ishaq ya dawo Mamah ta shiga kitchen don girka abinci, ya rage iya yaya Ishaq ne da Zahrah. Kallon ta yayi yace “cutie, meh ke damun ki haka kike sa damuwa a ranki” “babu komai yaya Ishaq, meh ka gani?” Wani kallo ya watsa mata “baki yadda Ni ɗan uwan ki baneh da ba zaki iya sharing damuwar ki da Ni ba ko?” Jijjiga kai tayi tace “aah yaya babu komai fah, Ni mah ban San meh ya same Ni ba kawai dai Kawu ya zo dukan Mamah shine na tare, daga nan ban san ina nake ba”. Shiru yayi yana nazarin wannan kawun da take faɗa, yana don ganin shi gaskiya. “shikenan cutie, ki huta kafin Mamah ta gama girki” Bayan sun ci dinner tukun na Yaya Ishaq ya tafi. TOH FAH, YA RAI ZA'A KAYA, YAU KAWU ANJI JIKI WURIN ALJANU KO kAWU ZAI SAUYA HALI? Duk cikin babban gida. BA'A FARA WASAN BA, JUST FOLLOW MY INK THE DIAMOND BHATOOL💎🤟 LIKE AND SHARE ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡BABBAN GIDA🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕽0️⃣ 4️⃣ Ina matuƙar godiya masoya na! Wannan PAGE ɗin naku ne. Allah ya bar ƙauna. Much love 😘😘😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Har zuwa lokacin nan Kawu bai fito ba, ganin haka yasa Mamah zuwa ƙofar ɗakin ta leƙa. Suna haɗa ido ya galla mata harara hakan yasa ta fito waje babu shiri. Sai bayan sun shiga ɗaki Kawu ya fito. Jikin sa yayi ruɗu ruɗu kamar wadda aka yi ma bulala. A hankali ya lallaɓa ya fice. Kai tsaye gidan Aminiyar shi jummai Rubber ya nufa. Masu gadi sanin shi da suka yi da irin yadda yake alaƙa da uwarɗakin su yasa suka buɗe mishi. Ba tare da ya kula su ba ya wuce zuwa cikin gidan. Zaune take daga ita sai wani matsiyacin shiru wanda da shi Gara babu, sai kuma bra. Fara ce sol, jibgegiya. Can ƙarshen parlourn wasu ƴan mata ne da ba zasu wuce 23years ba tsirara haihuwar uwar su sai masha'ar su suke yi (authubillah). Ko kunya babu haka suke ta abun su basu daina ba har sai da Jummai Rubber ta Basu umarnin fita zasu yi magana da baƙo.. A haka suka fice yayin da Rubber ta zubawa Kawu ido tana nazartar shi. “Takawar ka lafiya gwarzo jarumi, ka daki kowa ko zagi kowa, ko mutuwa tsoron ka take ji” Murmushi yayi da jin kirarin Rubber sannan ya maida hankalin sa gare ta. “Rubber magana mai muyi” Dariyar shaƙiyyanci ta saka sannan tayi shiru “ai in na ganka idrisu na san magana ta kawo ka, ina jin ka” “yau wani mummunan abu ya faru da ni” Nan ya kwashe drama ɗin su da Zahrah ta bata. Ita kanta abun ya girgiza ta in dai har kuwa da gaske ne akwai matsala. “ni babbar samuwa ta ma bata wuce sanin Ni na kashe baban ta ba, ga kuma sanin ƙwayoyin da nake miki safara” Cikin kwantar da hankali Rubber tace “Kaga kada ka wani damu, shawara ɗaya ce zan baka idan ka bita to zaka wuce wannan step ɗin” Cike da ƙaguwa ya kalli Rubber sannan ya rungume ta (nace oh ita ɗin ma matar shi ne kam?) Cikin kunnen shi ta faɗa mishi wata magana wanda duk gulma ta ban jiyo meh suke faɗa ba sai ji nayi yace “gaskiya Rubber me ta daban ce” Murmushi tayi sannan ta manna mishi peck a kumatu daga nan wasan ya sauya salo (Authubillah) Sai da suka gama suka yi wanka tare. A nan ya suka ci abinci kafin ya nemi wani ɗaki ya shiga. Wata ƴar Siriyar budurwa ce ta shiga ɗakin Bayan shi, jikin ta babu wasu kayan arziƙi haka ta shiga tana wani karairaya kamar macijiya. Tare da Kawu suka kwana suna sheƙe ayar su Ni kuwa nace (Allah ya shirye su). ★★★★★★★★ Alhamdulillah! Cikin ikon Allah jikin Zahrah yayi sauƙi, da safe Mamah da kanta tayi musu girki, bayan sun karya Mamah ta kai mata ruwan zafi toilet tayi wanka! Ba'a daɗe ba yaya Ishaq yazo. Tayi murnar ganin yayan ta sosai shima yaji daɗin ganin jikin da sauƙi.. Gaisawa suka yi da Mamah cike da girmamawa. Ya Ishaq yace “cutien yaya jiki yayi sauƙi koh" Cike da jin daɗi tace “eh yaya na warke” Cike da zolaya ya ce “ai na yi zaton da safe zan zo cin jallof ne” Ya faɗa yana kanne mata ido. Cike da shagwaɓa tace “kai yayah! Ai sai ka riga Ni mutuwa ma” “ni rufa min asiri! Damah so kike na mutu ko” “aah yaya" ta faɗa tana zare ido “alright in kin ji sauƙi zuwa gobe sai na kai ki makarantar koh?” cike da farin ciki tayi hugging nashi tightly “na Gode Yaya Ishaq Allah ya ƙara maka buɗi ya faranta maka” “ameen cutie, to same Ni kafin ki karya ni ko” Ɗan tura baki tayi ta matsa gefe. Haka suka yini suna shan hirar su har azahar, sallah yaya Ishaq yayi kafin ya dawo Mamah ta haɗa mishi nashi abincin. Ita kuma Zahrah ana rikici ita wallahi ba zata ci abinci ba ta ƙoshi Da ƙyar da siɗin goshi ya lallaɓa ta suka ci tare, bayan sun gama yake sanar da Mamah batun makarantar da zai saka Zahrah yayin da ta ke ta sharɓar bacci abun ta. “wacce makaranta da ɗin take zuwa Mamah" “nan makarantar gwamnati ne bayan inji mai wando” “ammah ta gama primary ai” “eh yanzu haka sun shiga jss 1 ne” “ohk shikenan goben zamu je sai a gama mata shirye shiryen saboda nimah sati mai zuwa zan bar ƙasar” Da mamaki Mamah ke kallon Ishaq “ina kuma zaka je” “mamah zan je nayi masters ɗinah be, zan kammala biyan kuɗin jss ɗin ta, nasan zan shigo bayan shekara uku ko biyu” Duk da cewa basu wani saba ba ammah Mamah tana jin Ishaq a jikin ta tamkar yaron da ta haifa. “toh Allah dai ya bada abun da za'a ke nema ɗin” “Ameen Mamah bari zan wuce nikam, sai goben” “toh Ishaq sai ka dawo, ka gaida gida, Allah ya saka maka da alkhairi” “Amin” yace yana ficewa daga gidan. Majalisar Kawu kuwa yau babu wanda ya zauna tun bayan jijjigar da suka ji anyi duk suka tsorata. Shima Kawu yana can yana sheƙe ayar sa gidan Rubber. Da yammah jikin Zahrah ya warke, tace wa Mamah bari ta ɗan zagaya unguwar don Allah Bata hana ta ba ko ba komai jikin ta zai ƙara ƙarfi ai ina ta zagaya. Wanka tayi ta fita tana ƴar waƙar ta har ta zo ƙarshen layin su, wata ƴar ajin su Lawisa Musa ta gani. Kamar wasu manya suka ɗan fara taɗi abun su “ah Zahrah Abdulkarim dama a unguwar nan kike?” Da mamaki Zahrah ta kalli Lawisa “kar ki raina min wayo mana Lawisa, ina banda uban ƙarya zaki ce baki san nan layin nake ba” Sanin halin ta da Lawisa tayi yasa ta yi shiru kafin tace “sorry ƙawa ta, na shafa'a ne, toh ya gida” Farr da ido tayi tace “lafiya ƙalau" “jiya an zo duba masu fashi, Man Labour ya ɗauki sunan ku ammah ke Amira ta ce wai baki da lafiya da gaske ne” “eh wallahi Lawisa, jiya har asibiti aka kwantar da Ni" Cike da tausayawa Lawisa tace “Allah ya sauwaƙe Zahrah Abdulkarim, bari na wuce gida nikam, aika na Umma ta tayi” Daga haka suka yi sallama. Zahrah ta juyo saboda duk ta gaji ƴar tafiyar da tayi. A ƙofar gida suka ji karo da Kawu, ko kallon arziƙi bai samu ba daga wajen ta. Duk da cewa yana tsananin shakkar ta ammah hakan ba hana shi dakewa ba don da wuya ka gano tsoron Kawu. “ke don ubanki baki iya gaisuwa ba neh?” Cikin halin ko ina kula tace “mutanen kirki masu daraja mutane su ake gaishe wa” ta faɗa tana gurmuɗa baki. Shaye da mamaki ta tafi ta bar shi, ya rasa meh yake masa daɗin haka nan lokaci ɗaya yayi wata shu'umar dariya “shawarar Rubber zata yi aiki kwanan nan inda ba haka ba zasu ruguza min buri na, kai!!! Basu isa ba, dole na dakatar da su. Dole. Sallahr maghrib suka yi, sannan isha', ana kiran ishà Kawu ya fice ta uwar shayibu. Bayan sun yi dinner suka ɗan yi hirar su. “mamah" Zahrah ta ambaci sunan ta “na'am Zahrah, menene?” “mamah yanzu haka zamu ci gaba da zama a gidan nan?, Wallahi Mamah Ni na gaji da rayuwar gidan nan, dubu fa duk mutane gudun mu suke yi saboda wannan banzan mijin naki” “ke Zahrah! Ki kiyaye kalaman ki, kar ki manta ɗan uwan mahaifin ki ne shiɗin kuma miji na! Bana kuma son jin wannan zancen kinji ko” Takaici duk ya cika ta tace “shikenan Mamah, toh Ni ki kai Ni wajen wata ƴar uwar ki manah! Ni tunda muke baki taɓa kai Ni wajen su ba” Ba tayi mamakin jin hakan daga Zahrah ba, tun bata kai haka ba take cewa su gudu gidan su Mamah ammah sai tace iyayen ta sun mutu. Daga nan Zahrah bata kuma cewa komai ba tun da Mamah tayi shiru. Ɓangaren Mamah lokaci ɗaya tsohon ciwon ta ya dawo sabo. Abun da take ƙoƙarin binne wa kullum kenan, sam bata so a dawo mata da zancen ko kaɗan. Bata manta ranar da ta rabu da iyayen ta, shekaru 14years kenan! Lokacin da ta yi kunnen uwar shegu da ahalin ta! Gashi yanzu tana don zuwa gare su ammah ta kasa!! “Ya Allah" kawai ta samu damar furta wa. Har wajen 2:00am bata yi bacci ba, yanke shawarar yin Sallah tayi ko zata ji sauƙi. Tana cikin sallar bugun gidan ya dira kunnuwan ta, bata katse sallar ba sai da tayi raka'āt biyu tukun nah ta fito. Ƙoƙarin ta buɗe mishi sai dai abun haushi yau ma a buge ya shigo da ƙunshi ledar sa a hannu. Bangare ta yayi ya shigo ciki. Bayan ta rufe ƙofar itama tayi ciki tana takaicin banzan hali irin na idrisu. Ganin ya tsaya be shiga ɗaki ba ta ɗan taɓe baki ta wuce zata shiga ɗakin ta. Jawo ta yayi ta faɗo jikin shi, cikin zafin Nama ta fizge jikin ta. Cikin Muryar ƴan maye yace “haƙƙi na zaki bani Madina" cike da takaici ta wuce zata shiga ɗakin ta ya ƙara jawo ta da ƙarfi. ɗakin ya cilla ta ya rufi kirif. “Wallahi baka isa ba idrisu! Da ni zaka yi mu'amala kana cikin maye?” “toh meyeh....na..ga...naga....ke mata...ta...ce” “haƙƙin mata nawa ka sauƙe da zaka ce ina baka haƙƙin ka? Wallahi ba abun da zai haɗani shimfiɗa da ƙazami irin ka” Cikin maye ya janyo dorinar da ya saba dukan ta da ita ya fara jibgar ta, ihu take ammah Kawu bai daina dukan ta ba kamar an aiko wahayi gare shi ne. Duka sosai yake mata da shi kan sa sai da yaji jiki, tun tana ihu har ta daina. Duk budurin da ake yi Zahrah bacci ta take sha. Maƙwafta na jin ihu ya wuce misali suka fara fitowa. Ammin Badi'a ce da mijin ta suka zo, ƙwanƙwasa ƙofar da suke yi shi ya tada Zahrah daga bacci. Jin babu Mamah a gefen ta yasa ta fito. A tsakar gidan ta tarar da ita yashe sai wani irin sauti take fitar wa ga Kawu kuma tsaye kanta da dorinar sa. Bai lura da Zahrah ba sai da tazo wurin, ba tare da ta kula shi ba ta kwanta jikin Mamah tana sake wani kuka mai tsuma zuciya. Jin ba a daina buga ƙofa ba yasa ta je zata buɗe, tsawa ya buga mata “keeee....” bata kula shi ba ta wuce ta buɗe. Ganin Ammin Badi'a da mijin ta abun ya bata mamaki. Shigowa suka yi, Ammi ta riƙe hannun Zahrah suka shige. Kawu bai jira wata wata ba ya fizgo Zahrah daga hannun Ammi. Dukan ta ya fara nan da nan tayi wani tsalle ta gudo bayan Ammi. “Wallahi Kawu baka isa ba! Uban me Mamah tayi maka zaka mata irin wannan dukan, wallahi bazan taɓa yafe maka ba wani abu ya same ta. Meh yasa? MEH yasa nace MEH yasa Kawu? Ka cutar da rayuwar mu iya cutarwa, tabbas sakayyar Ubangiji tana jiran ka. Allah ya isa” Daga haka ta kece da wani irin kuka mai ban tausayi. Jikin Mamah ta dawo ta na jijjiga ta “ki tashi Mamah! Kada ki mutu, in kin mutu bashi da asara nice zan shiga maraici, Mamah ki tashiiiii" Ta ƙarasa cikin ƙaraji. Abban Badi'a ne ya umarci Ammi da ta taya Mamah ta kai ta ɗaki sannan ta bata taimakon da ya dace. Zahrah gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta in ban da suruce suruce babu abun da take “ke ma Mamah nace miki mu tafi wurin dangin ki kin ƙi toh ai dole muyi ta Fuskantar Matsala. Allah ya isa tsakanin mu da kai Kawu. Sai Allah ya saka manah. MU HAƊU GOBE DUK YADDA AKA YI AKWAI WANI ƁOYAYYEN AL'AMARI MUJE ZUWA DON BA'A FARA WASAN BA SAI MUN JE BABBAN GIDA. CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY....TARE DA ZABGA COMMENTS. DIAMOND BHATOOL 💎🤟 ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰0️⃣5️⃣ Ina ƙaunar ki Qawa ta AISHA USMAN (Baby) namecy. Allah ya kula min da ke a ko ina ya cika miki burin ki. Much ƙauna ƙawa ta ta kaina.. wannan shafi dai naki ne tawan....🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Ammi ce ta taimakawa Mamah ta kwantar da ita, sannan ta hango thermoflask Allah ya so akwai ruwa a ciki, a ɗan baho ta haɗa tayi mata tapid sponging. Mamah kuwa kuka kawai take yi. Ta rasa meh yake mata daɗi, Ammi kuwa sai aikin lallashi take tana danasanin abinda mutanen unguwar ke yi wa Mamah duk da cewa ita bata ciki. ”Tabbas matar nan na buƙatar taimako kuma zan taimaka mata iya iyawa ta.” Ɓangaren Zahrah kuwa Abban Badi'a ne ya riƙe hannun ta suka fita zuwa gidan shi yana Allah wadai da irin halin Idrisu. Tare da fatan Allah ya saka wa iyalen shi da abun da yake musu. Asubar fari hankalin ta ya dawo jikin ta, ganin ta a ɗakin ƴan gayu yasa ta zaro ido waje. Tunani ta fara MEH ya kawo ta nan sai ta tuna abun da ya faru daren jiya. “Toh asibiti aka kawo Ni kenan” Ƙafar mutum da taji a kan tata yasa ta duba, “Badi'ah, MEH nake yi a gidan su kumah? Oh ashe jiya Ammin su ne suka taimaki Mamah” Banɗaki ta nufa wanda yake cikin ɗakin tana mamakin gayu irin nasu Badi'a hala shi yasa ko a islamiyya bata kula Ni saboda gidan masu kuɗi take. Duk cikin ranta take zance. A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin ta nufi waje. Cikin sanɗa ta ke tafiyar kamar wata ɓarauniya. “Zahrah ina zaki je asubahi haka” Abba ne ya dakatar da ita lokacin dawowarsa kenan daga masjid. Sunkuyar da kan ta tayi kafin tace “ina kwana" Murmushi yayi “lafiya ƙalau Zahrah, ki koma kiyi sallah in gari ya waye sai ki koma" Bata yi mishi musu ba saboda kwarjininsa. Wucewa tayi simi simi kamar ƙadangare ta koma. Alwala tayi sannan ta ɗan taɓa Badi'a. Itama tashi tayi ta shiga toilet Tana mamakin meh wannan maras kunyar take yi a gidan su. Sai da ta jira fitowar Badi'a cikin sanyin murya tace “ki ɗan bani hijab nayi sallah” Bata ce mata komai ba ta buɗe wardrobe ta janyo hijab ta miƙa mata. Buzu buzu tayi sallar Badi'a na mamakin yadda take yi. Sai da ta idar ta ce mata ai ba haka ake sallah ba. Duk rashin mutunci irin na Zahrah sai ta ce toh koyamin. Sai wajen ƙarfe 6:10am ta koma gida. Abun mamaki gidan tas.. ɗakin Mamah ta shiga. Abun mamaki kwance taga Mamah. Kusa da ita ta zauna can tace “mamah” Cike da don manta abun da ya faru tace “zahrah! Kiyi wanka da wuri kafin Ishaq yazo." Sarai ta gano Mamah shi yasa tayi shiru abun ta. Wanka tayi ta fito, a ɗakin ta tarar da Ammi zaune gefen Mamah tana bata abinci, haka kawai ta tsinci kanta da farin ciki maras misaltuwa. “ina kwana Ammi" “lpia ƙalau Zahrah, ki saka kayan sai ki je ki ɗebo abincin.” Tana shirya wa ta ɗebo abinci taci sai lokacin Ammi ta wuce gida. Mamah kuwa godia tayi ta shaƙa mata. Da misalin ƙarfe 9:49am yaya Ishaq ya zo gida. Sun gaisa da Mamah kamar ko yaushe cikin sakin fuska. Basu ɓata lokaci ba suka nufi wata private school Mai kyan gaske. Makarantar ta matuƙar burge Zahrah kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa.. ALMUNAUWARA ACADEMY Yara ne ke wasa gwanin ban sha'awa, wasu bisa lilo Wanda da gani nursery students be. Wasu kuma ta wani ɓangaren waɗanda uniform ɗin su ya bambanta da na sauran wasu na guje guje wasu kuma suna wasanni mabanbanta. Biye take da yaya Ishaq yayin da zuciyar ta ke mata wani irin sanyi. Yau ita ce a cikin ALMUNAUWARA ACADEMY, “makarantar su Badi'ah fah kenan.” Ta faɗa tana sake wani irin ƙayataccen murmushi. Daidai wani building suka nufa wanda da alamu shine staff room. Wani room Wanda aka manna signboard jiki ɗauke da “ADMIN" yaya Ishaq yayi knocking, izinin shiga ya samu suka shiga tare. Sai da ta gaida mutumin kafin ta zauna kamar yadda taga yaya Ishaq ya zauna. “Mallam Muhammad, Barka da safiya” yaya Ishaq ya faɗa tare da miƙa wa mutumin hannu. “barka mutumi na, wannan ce yarinyar da muka yi magana da kai kenan" “eh ita ce” Wasu takardu ya fitar ya miƙa wa yaya Ishaq. Bayan ya kammala cike su ya ɗauko books cikin wani bag ya miƙa mata. Haka dai aka gama komai a ranar aka bata uniform ɗin ta set II, farin ciki wurin Zahrah ba'a magana. “ki jira Ni waje zan yi magana da malamin ku” Ko amsawa bata yi ba ta fice zuwa jikin motar yaya Ishaq ɗin. “Yauwah Man Please Please ka sanya wa yarinyar nan ido, ina so tayi karatu sosai” “Alright I'll in Sha Allah” Daga haka suka yi sallama. Direct gida ya yi dropping ɗin ta. “ki shiga zan shigo gobe na miƙa ki, ki gaida Mamah" “toh yaya Allah ya kiyaye hanya”. Kar kuso ku ga murna wurin iya Zahrah! Duk sai wani rawar kai take, Mamah kuwa kallon ta kawai take tana ganin ikon Allah. Yayin da wani ɓangare na zuciyar ta ke tausayawa yarinyar Tata. Da yamma yaya Ishaq yazo. Sabbin sandals da socks da wata school bag ya kawo mata. yayi mata ƙarin bayani a kan makarantar sannan ya ja hankalin ta kan ta maida hankali. “cutie na!" Ɗagowa tayi ta kalle shi “ki dage da karatu kinji, ina so ki zama wata abu a rayuwa, ki zama abar alfahari gare mu baki ɗaya. Banda wasa, karatu kika je ba wasa ba, ki saboda haka ki maida hankalin ki ga karatun. Banda kula maza babu ruwan ki da su.... sannan banda faɗa. Kin gane ko?” “eh na gane, in Sha Allah zanyi karatu da yawa" Murmushi yayi yace “Alright in naji labarin kinyi faɗa, hmmm” Sallama yayi wa mama ya wuce shima don ya fara preparations na tafiyar shi London don yin masters ɗin shi. Haka kawai yake jin faɗywar gaba ko dan kawai sabon da suka yi da cutien shi ne ko kuwa, “only God knows” ya faɗa can ƙasan maƙoshi. Washegari tun 6:30 ta gama shirin ta. Kayan sun matuƙar ƙarɓan ta tamkar ɗin ita aka yi, Coffee brown trouser be sai Brown coloured hijab da riga. Sun matuƙar haska kyakkyawar fuskar ta tamkar wata sarauniya. Horn ɗin da taji ne yasa ta ruga a guje zuwa waje. Ko sallama bata yi wa Mamah ba ta fice abun ta. Tun daga nesa yake hango ta tana tahowa. Ɗan lumshe idanuwan shi yayi ƙasan maƙoshi ya furta. “She look so breathtaking, tabarakallah”. Tana zuwa ta buɗe motar ta shiga “ina kwana yaya Ishaq" Cike da zolaya yace “lafiya ƙalau zumuɗa, live kin daɗe da shirya wa.? Ehnn” Fuskar ta ta rufe da hijabi tana turo baki “kai fahimta kace na shirya da wuri” “shine kika biye min?, Damah dai zumuɗin kike yi faɗa min gaskiya cutie" ya faɗa yana ɗaga mata gira.. A haka suka isa sannan ya ja hankalin ta kan tayi karatu in yazo ɗaukar ta zata biya mishi. “bye” Hannu ta ɗaya mishi sannan ta juya ta shiga. A lokacin ne students da dama ke zuwa. Kai tsaye ita ma shiga tayiba tare da nuna bata san school ɗin ba. Unfortunately wani staff ya ganta. Da gani bai jin Hausa ma “hey!” ya faɗa yana nuna ta da yatsa. Wurin da yake ta nufa sannan tace good morning" “morning, are u new here?” It's da bata san ma me yace ba kawai sai ta ɗan tura baki da ta tuna da new na yace sai tace “yes” “ohk which class?” Wannan kam da yake ta sani caraf tace “jss one” Da hannu ya mata alamar ta shiga wannan class ɗin “go and keep your bag there” Kai ta gyaɗa kamar ta ji meh yace. (Nace zaki sani in ya gano baki jin turanci duk buge kike yi😂) Yaji daɗin yadda suka yi da malamin kawai sai taji tana son ita ma ta ƙware a turancin nan wallahi. a hankali ta shiga class ɗin babu kowa, kawai sai ta ajiye Baga ɗin ta a front seat ta fita. Hanyar ta ta fitowa taga Badi'a na tunkaro ajin kawai sai taji tana don jiranta.. “Zahrah a makarantar nan aka saka ki" kai kawai Zahrah ta gyaɗa. Badi'a ta ja hannun Zahrah suka shiga cikin class ɗin, dropping bag ɗin ta tayi ta ɗauko ta Zahrah da ta ajiye a left sided front seat zuwa middle raw daga nan suka fita tare. Bayan anyi assembly suka dawo class. First period Basu English ne, gashi malamin bashi da kirki duk tsoron shi suke. Yana shigowa suka miƙa gabaɗaya “good morning sir” “morning how's the weekend?” “fine sir" “ohk have ur seats" Lesson plan ɗin shi ya ɗauko daga nan ya buƙaci marker daga wurin class rep. Bayan ya bashi ya rubuta TENSES sannan ya juyo “good morning once again, our topic of discussion today is TENSES. Is there anyone who'll tell us something about tenses?" Shiru class ɗin yayi babu alamar motsi tamkar ruwa ya cinye su. Jin shirun su yasa ya yi pointing Badi'a, “Badi'ah Kabir Umar, please say something” shiru tayi tare da sunkuyar kanta. “Alright, the girl next to Badi'a say something" Bata san ma da ita yake ba saboda ba jin turancin take yi ba. Zaro ido ƴan class ɗin suka fara jin taƙi tashi. Zata jawo musu bala'i wurin Uncle Hashim. Badi'a ce ta ɗan buge ta hakan yasa ta yi tunani ko so take ta faɗa mata MEH abun yake nufi. (Ku ji Zahrah, ke da baki san komai ba ke zata tambaya?😂) Uncle Hashim da ya fusata cikin tsawa yace “you should get out of the class now” still shiru ita ina ta san ma da ita yake. Zaman ta tayi ta ci gaba da jin abun da ake. Ganin duka class sun zubo mata ido yasa ta galla musu harara. Fita uncle ɗin yayi hakan ya baiwa ƴan clsss ɗin damar mata magana, wasu na zagin ta wasu kuma na cewa tayi sauri ta fita. “Zshrah kina ji yana miki magana kika yi banza da shi ko?, Baya wasa ki fita in ba haka ba zaki ji a jikin ki" Badi'a ta faɗa tana ɗago hannun Zahrah alamun ta fita waje. Ƙememe Zahrah tayi tace “toh Ni na san da Ni yake ne" Ku ji ikon Allah fah😂 Wannan shine ZAHRAH'S FIRST DAY AT SCHOOL MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA TSAKANIN ZAHRAH DA KUMA UNCLE HASHIM SHIN MAKARANTAR NAN KUWA TA DACE DA ƳAR KAWU? JUST FOLLOW MY INK AND COMMENT & SHARE ITZ DIAMOND LADY💎🤟 Oum Zainab ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊 ️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣6️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Uncle Hisham har ya dawo class ɗin Zahrah na zaune kamar ba da ita ake yi ba. Fita ya ƙara yi sai Gashi tare da uncle Suraj (Mr Mugu as hey said). Uncle Suraj na zuwa students suka miƙe suna gaishe shi. Ba tare da ya amsa ba yace su zauna. Kallon su yayi fuskar nan ɗaure kamar fuskar shanu “Among U who's the stupid girl that refused to obey Hashim's order? Ya faɗa in a husky voice nashi. Zare idon kowa ya fara. Ƙasa ƙasa Badi'a tace “Zahrah don Allah ki tashi ki tsaya in ba haka ba in ƴan aji ne suka nuna ki sai ya miki shegen duka, don Allah ki tashi” Banza Zahrah tayi mata kamar ba da ita ake magana ba. abu fah yayi abu, Zahrah ba dai taurin kai ba. Duka su biyun sun tunzura,, hakan yasa suka wuce principal's office. Sanar da shi komai suka yi sannan ya ce su ƙyale ta, shi kuma uncle Hashim ya ci gaba da darasin shi after break za'a nemo yarinyar. Ba don uncle Suraj ya so ba haka ya haƙura ammah tabbas yarinyar nan zata ci ƙwal ubanta. Bayan uncle Hashim ya gama clsss ɗin yace lallai Zahrah taje principal's office yanzu. Bata ma San meh yake nufi ba ta dai ji principal kenan ƙarar ta ya kai. Hmm. Bin bayan shi tayi har suka isa, sai bayan ya shiga ta shiga, Gaida principal ɗin tayi da turanci, ya amsa mata. Kneel down ya saka ta a gefe yayin da uncle Hashim ke zaune kan kujera.. “What's that your name miss?” principal ya tambaye ta. “Ohoh wannan ai na sanshi” ta faɗa cikin ranta. “Zahrah Abdulkarim Kuru.” daga haka tayi shiru. Kamar wanda ya gano bata jin turanci sai ya dawo mata magana da Hausa. “malamah Zahrah MEH yasa malam ya baki umarni kika ƙi bi?" Kanta ta sunkuyar ƙasa “mallam Ni ban san da Ni yake ba, kuma ban ji MEH yace ba” Kallon baki da wayo ya mata “kina nufin duk maganar da nayi baki ji ba, ƙarya kike” sai a lokacin ta fahimci ashe ya iya Hausa ma kuma shine da tayi shirin bai yi mata ba. “Wallahi ban ji ba, Ni bana gane turanci da Hausa kayi min ai zan gane, kayi haƙuri” Haƙurin da ta faɗa yasa ya sauƙo “meh yasa to baki jin turancin?” “makarantar gwamnati nayi makaman namu ma ba iyawa suka yi ba kuma yau na fara zuwa nan ɗin” Nan da nan suka sake suna ta hira shi dai PC kallon su kawai yake. “kina don ki koyi Turancin ko kuwa” “ina so sosai, sai dai ban san yadda zanyi ba” “shike nan kada ki damu zan na koya miki kullum ko abu biyu ne, lokacin break kike zama a aji zan ke zuwa. Cikin murna tace “na gode Mallam” “tashi ki koma class". Haka suka yi second period ammah lokacin uncle ɗin su bai tayar da ita ba. Lokacin da aka tashi kuwa tana fita taga motar yaya Ishaq, da sauri ta ƙarasa ta shiga. “ƴan makaranta, hope kin ji daɗin makarantar” ɗan yamutsa fuska tayi kafin tace “ga ta nan dai, Ni kam yau abun kunya dai nayi" Zaro ido yayi jin tace abun kunya “faɗa kika yi ko cutie" “aah Yaya, wani malami ne yake ta min turanci Ni kuwa ban san meh yake cewa ba ashe wai cewa yayi na tashi na amsa tambaya.” MEH yaya Ishaq zai yi in ba dariya ba. Ɓata ran da tayi yasa ya tsagaita. “toh ya kika yi kuma?” Ɗan bakin ta ta turo “ Ni zama na nayi ban kula shi ba shine yace na fita, Ni wallahi ban san da Ni yake ba” “ya zane ki kenan?” “aah ai ban fita ba saboda ban san da Ni yake ba, shine ya ƙira wani mai fuskar shanu ko dariya da baya yi” “sai kuma shi mai fuskar shanun ya zane ki?” “aah shima cewa yayi na fita to ban san duk a kaina ake ba Ni kuwa nayi zama na, duk sai suka fita tare, shine malamin ya dawo ya ci gaba da darasin, Ni ban ma gane ba” “shikenan kada ki damu zaki koyi Turanci fiye da malamin in kika sa kanki, mu bi na siya miki wani littafi ki gani” Girgiza kai tayi sannan tace “baka tambaye Ni ya aka ƙare ba ai" “ina jin ki ai” Shine da ya gama yace muje office ɗin wani ina ga dai headmaster be" Dariya yaya Ishaq ya saka yace “kai cutie babu headmaster a secondary School sai dai principal" Ranta ta haɗe tamau “toh ai Ni ba sani nayi ba” “shikenan ina jinki, principal ɗin ya duka ki kenan” “aah shi da Hausa ya min magana shine na ce masa Ni ban fahimci da Ni yake ba kuma bana jin turanci, malamin kuwa yaji tausayi na yace zai je koya min” Murmushi yayi daidai isowar su wani bookshop. “ki jira Ni ina zuwa” Ɗauke da littafai a hannun sa ya fito “yauwah karɓi waɗannan cutie, ki riƙe su da iya su zaki ita turanci, sannan ki ƙara maida hankali, duk abun da baki gane ba ki tambaya kinji kar kiji kunyar kowa” “toh" Ita kaɗai ta shiga gidan shi kuma ya juya. Duk wainar da ake soyawa Kawu bai sani ba. Bayan ta ci abinci kawai sai taji sha'awar zuwa islamiyya. Wanka tayi ta fito. Ganin yadda uniform ɗin suka cakushe saboda rashin ya sa ta ɓata fuska. “ke kuma lafiya?” Mamah ta tambaye ta Kayan ta nuna mata sai wani tura baki take yi “kiga kaya na kamar daga bakin kura aka amso su” “toh ki shiga gidan su Badi'a ki goge mana kafin lokacin" da kamar bazata je ba sai wata zuciyar ta ce kije. Sai da tayi nadamar zuwa islamiyya dan kuwa Ustaz Jamil sai da yaci ubanta kan fashi, kuma ya sata duk haddar da yake Binta sai ta biya. Tun daga ranar kuwa tayi alƙawarin ba zata ƙara zuwa islamiyya ba ko za'a kashe ta, ammah da ta koma gida Mamah tace ai dole sai taje. Tsabagen bakin ciki kamar tayi kuka. Haka rayuwar Zahrah ta kasance, cikin satin nan kuwa tayi mummunan sabo da ƙawar ta Badi'a yau in suna gidan Mamah to gobe suna gidan su Badi'a. Ranar Asabat da yammah yaya Ishaq ya zo don yi wa su Mamah sallama. Mamah kam har da kukan ta saboda yace ba lallai ya dawo ba sai bayan shekara biyu ko uku. Uwar gayya Zahrah kuka kamar zata mutu, “haba cutie, meneneh kuma abun kukan? Ba dai zamu na waya da sabuwar wayar Mamah ba?, Toh kiyi shiru kinji, idan ma kin dage a school in na dawo sai mu tafi tare kema ki shiga jirgi" Jin yace jirgi nan da nan ta goge hawayen fuskar ta “shikenan yaya zan dage kuma zaka yi alfahari da ni” Murmushi yayi mata sannan yace zo muje ki raka Ni siyayya.. Shopping mall suka je ya siyo mata kayayyaki da mayuka da sauran su. Sandals talkalma duk ya siya mata a cewar shi ko baya nan ba sai ta siya ba. Daga haka suka dawo gida cikin farin ciki. Ranar tare suka yi dinner, sai wajen 9:45pm ya tafi cike da kewar cutie ita ma cutie ya bar ta da kewa. Ko ba komai soyayyar mahaifi da ta rasa tana samun ta wurin yaya Ishaq ga kuma sabuwar ƙawar ta da kuma Ammi har da Abba. Hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba tunda Kawu yanzu ko ya zage ta ba kula shi take ba. Ƙarfe goma da rabi suka fara shirye-shiryen kwanciya kawai suka ji an banko ƙofar ɗakin.. shaye da mamaki Mamah ke duban Kawu da ya shigo fuskar shi ɗaure kamr kumburarriyar fulawa. Zahrah ko ko kallon yadda yake bata yi ba. Duban Mamah yayi yana wani cika yana batsewa.. “ke Madina, ina so ki share gidan nan gobe tatas kina ji ko?” Caraf Zahrah tace “toh kaga gidan cikin datti ne da zaka yi magana?” Banu yadda ya iya da Zahrah kawai ya ci gaba da muzuran shi “ni dai na faɗa miki, ɗaki na mah a ciro komai na cikin shi don kuwa gobe dalleliyar amarya ta zata zo gidan nan” Zaro ido Zahrah tayi lokaci ɗaya yanayin fuskar Mamah ya sauya. Bata ce mishi ƙala ba har ya gama surfa bayanan shi ya fice fuu Kamar Mahaukaci. Daren Mamah bata samu ta rintsa ba, ba wai saboda kishi ba aah sai don bata san waye Kawu zai auro ba. Washegari tun safiya Mamah ta cika umarnin Baba, da kanta ta gyara gidan tsab gudun kada taƙi yi ma ya ci mata mutunci gaban baƙin amaryar. Dawowar Zahrah daga school ta kafa rikici ita ala dole ba zata je islamiyya ba tunda za'a yi baƙi a gidan. “haba Zahrah, yanzu inda kin zauna uban meyeh zaki yi a gidan” Fuskar ta a kwaɓe take kallon Mamah “mamah naga yau za'a kawo amaryar Kawu, Mamah ina tsoro su zo bana nan nasan ko sun miki abu ba zaki rama ba ammah idan ina nan zan tare miki” ta ƙarashe da Muryar tausayi. “ke yarinya ce Zahrah, idan sun yi min ma a banza suka yi tunda ba kula su zan yi ba, maza tashi ki tafi makaranta.” Ganin da gaske Mamah so take ta hana ta zama kawai ta ɓare baki ɓaaaaaa sai ihu “wallahi Mamah in na fita ba zan dawo ba, tsayawa zanyi mota ta buge ni shikenan ai koh” ta fice a guje. Mamah da ta rasa abun yi sai tabi bayan ta tana ƙwalla ƙira “zahrah, Zahrah ki dawo shikenan na yadda" duk da ta ji me Mamah tace tayi burus ta ƙara wa bujen ta iska, Mamah na biye da ita har suka kawo ƙofar gida tukun ta juyo. Marakraice fuska Mamah tayi hakan yasa ta dawo ta rungume ta duka su biyun suka fashe da kuka mai ban tausayi. Sai zuwa yamma tawagar amarya suka zo, ihu da shewa ba'a magana. Sai da suka gama jere suka fito tsakar gida su ka fara zage zage. “Munafika uwar kishi tayi luƙus a ɗaki” Wata daga cikin matan tayi caraf “kin san damah ba zata fito ba ai. Irin matan nan fah sai Saudatu ta dage, don kuwa ko meh kika musu ba zasu ji haushi ba” Ɗayar matar da ta fara magana tace “toh ai babu zuciya kin sani, shi yasa tayi shiru” Hannu suka tafa suna sake guɗa da shewa irin nan matan barikin nan. “ƙawa ta baki da dama, wallahi gaskiya ne maganar ki, kin san ance bata da dangi, kamar ma Idrisun tsinto ta yayi” “Toh Allah dai ya kiyaye, ammah dole Saudatu ta dage” “ke dai lantana kawai ki bari" ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰0️⃣7️⃣ Wannan shafi sadaukarwa ne gare ku masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ A kunnen Zahrah suka faɗi komai yasa ta ce “Mamah bari naje banɗaki na dawo” Mamah bata ce komai ba saboda bata ji MEH suka ce ba. Zahrah na fita ta Banka musu wani bazan kallo mai ɗauke da ƙasƙanci da tsana kafin ta ja wani tsaki “Mtsssss....daɗin ta ma gidan aka zo ana same ta” Matar da ɗazu aka ƙira da lantana ce ta zaro idon ganin yarinya ƙarama na mata rasar kunya. A fusace ta yo man Zahrah babu shiri ta goje, wani ice ta gani a gefen ta tayi saurin rarumar shi” Lantana Bata haƙura ba ta ƙara biyo Zahrah ai kuwa bata aune ba taji ice a bayan ta. Ƙarar da tayi ne yasa Mamah da sauran ƴan kawo amarya fitowa. Tunda ta jinka mata icen ta ja gefe tana sauƙe numfashi, lantana kuwa zube wa ƙasa tayi tsabar azabar da bayan ta yake yi. A hankali Mamah ta tako saboda ta taimakawa Lantana. Hannu ta miƙa mata cike da ƙuluwa ta doke hannun Mamah ta miƙe. Still ta ƙara yin kan Zahrah a fusace “yau mai hana Ni cin bura uban yarinyar nan shima sai naci uban sa” Babu alamar tsoro a tattare da ita sai karkaɗa jiki take. A hanzarce Mamah ta taho zata ja hannun Zahrah. Ɗaya daga cikin ƴan kawo amarya kuwa ta bangaje Mamah. Abu ƙarami dai ya dawo babba. Don kuwa Zahrah janye Mamah tayi zuwa ɗakin ta. Jawo ƙofar tayi ta fito ta fara by bubbuga musu icen nan, ance Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi ammah wannan karon naga ikon Allah. Hayaniyar da ta kaurece ga kuma ihun matan ya jawo hankalin ƴan unguwar. Tuni gida ya cika ana ta tambayar ba'asi da ƙyar Ammi ta lallashi Zahrah suka wuce ɗakin Ammi. Labarin ya matuƙar ɓata ran Ammin. Saboda haka ta ja hannayen su duka biyun suka bar gidan. Dare na yi aka kawo amarya tare da ƙawayen ta wanda shigar su kaɗai kaga kaga ƴan jagaliya, guɗa ce kawai ke tashi sai uban habaici da ake gabzawa wanda wacce suke yi wa bata ma san suna yi ba. Damah tuntuni labari ya isa kunnen Saudatu Kwalba, shi yasa ta tattaro duk ƙawayen ta da niyyar sai sun ci uban uwa da ƴar, sai dai babu yadda zasu yi takaici ya cika su ganin babu kowa a ɗakin, kenan har sun gudu?. Ai kuwa dabara ta zo wa Aunty Amarya kan in ango ya shigo ta haɗa shi da matar. Ai kuwa ta samu na nasarar hakan. Ran kawu ba ƙaramin ɓaci yayi ba “zasu dawo gidan su same Ni ai" Su Kawu an ci amarci an gaji da amarci. Kwana biyu su Mamah basu dawo ba nan fah Kawu yasa sha jinin jikin sa. “Fatan na Allah yasa dai ba aikin da nayi bane ya ɓaci, idan kuwa haka ne toh akwai matsala!” “kai bazai yiwu ba!!! Inaaaah! Madina wallahi bayan barki ba!, Dole mu rayu tare kuma dole kiyi rayuwar ƙasƙaci!. Yanzu dai ina da zaɓi ɗaya ne, dole na fita ko ina na zaga saboda na nemo su!, Ina sun tafi fa komai ya lalace, duk burin da naci zasu ruguje!!! Zan nemo ku duk yadda kuka je ne”. Ɓangaren yaya Ishaq kuwa ya keta hazo tare da kewar ƙanwar shi. Wasa wasa sai da su Mamah suka shafe sati guda a gidan Ammi tukun na suka haɗo domin dawowa, Ammi ta bawa Mamah kayayyakin sakawa nata, na Badi'a kuma ta bawa Zahrah. Zuciyar su wasai suka dawo abun su. Lokacin da suka dawo Saudatu Kwalba na zaune akan shimfiɗar tabarma da tayi, gefen ta kuma ƙawar ta ce Asabe Bala'i sai hira suke yi. Ɗauke da sallama su Zahrah suka shiga, Asabe ce ta ɗago tare da mamakin da ke bayyane akan fuskar ta sai kuma ta sauƙar da kan ta ƙasa. Ƙasa ƙasa gudun kada baƙin su ji ta tace “ke Kwalba waɗannan su waye” “ina kuwa zan san su waye” ta juyo wurin su Mamah. Ganin sun tunkari ɗakin kishiyar yasa ta miƙe zuwa wajen su. Cike da hatsabibancin ta irin na ƴan Iskan matan bariki ta wani riƙe kunkumi. “baiwar Allah uban meh zaki yi kin shigo gidan miji na ba izini kin dashi ɗaki kumah?” Murmushi mamah ta cilla mata wanda yasa zuciyar ta ƙara tafasa. “kut!!!! Ina miki magana, toh don Ubanki jawo hannun ƴar ku mai zubin aljanun nan ki fita min gida” “a'ah!, Shi mai gidan bai faɗa miki cewa mata biyu gare shi ba?” Amsar da mamah ta bata ne ya tabbatar mata da cewa ita ce Madina matar Idrisu. Lokaci ɗaya ta shiga ruɗu. Mamah kuwa ta ciro key ta buɗe ɗaki suka shige ita da Zahrah. Mamaki ya matuƙar kama Saudatu har sai da Asabe ta zo ta ja ta suka wuce ɗaki.. “ke Bala'i ammah idrisu ya raina Ni, irin wannan yaudara haka” “wai MEH ya faru ne?" “ke da kike gani wannan tsuleliyar matar da kika gani da yarinya mai shegen kyau kamar ɗiyar Mayu matar sa ce fah!!” Shaye da mamaki Asabe ke kallon ƙawar ta. “lallai in dai haka ne toh bamu ga ta zama ba” “ai kuwa, yanzu meyeh abun yi?” “rabu da ita kawai, zan bata shekara biyu zuwa uku ta sarara sannan na aika ta lahira shikenan, ɗiyar ta kuma ta zama jaka ta” “Ammah Kwalba bakya tunanin a samu matsala kafin lokacin da kika bata?” “A'ah Bala'i, ba a so a fahimci komai game da mutuwar ta, yanzu haka zan aika a kawo min Bibalo ta dawo waje na da zama ko dan saboda cikar buri na. Idan Bibalo ta dawo nan kinga ai Sa'ar yarinyar ce, xan sa take cin zalin ta kuma na hana ayi magana har baƙin ciki ya kama uwar, daga ƙarshe cikin shekaru ukun da na ɗebar mata ciwon damuwa yayi mata mummunan kamu, sai na sa boka Bulebule ya ƙarasa min ita, daga nan kuma ɗiyar ta ta zama tawa, sai yadda nayi” Dariya suka kwashe da ita suna tafa hannu “kai ƙawa ta baki da dama!, Ƙwaƙwalwar ki tana mugun ja” “ke dai ki bari, ko kin manta suna na ne ‘kwalba’?” “hhhhhh haka ne fah, shiyasa nake daɗa ƙaunar ki” (TOH KUN JI FA KUDIRIN AMARYAR KAWU, KO YA ZA'A KAYA? Ɓangaren Mamah kuwa suna shiga ta ƙara kaɗe ɗakin ta, ta gyara zaman kayan abincin su da kyau, sai lokacin ta tuna yau da Ishaq ya tafi. Addu'a da fatan alkhairi tayi ta jera masa. Daga nan suka yi zaman su a ɗakin.. “zahrah” jin mamah ta ambaci sunan ta yasa gaban ta faɗuwa don ta San in tayi mata irin kiran nan toh abun is serious. “na'am Mamah ta” “kina ji na koh” “eh Mamah ina jin ki” “ko da wasa ban amince kiyi wa matar kawun ki tsiwa ba, kinga idan kika yi mata zaki jawo mana kawun ki ne shiga rayuwar mu, don Allah Zahrah ki mata biyayya kin ji" Cikin sanyin jiki ta ce “toh mamah naji ammah wallahi idan ta shiga harƙa ta ba zan ƙyale ta ba” “zahrah kenan! Ba zaki taɓa sauya wa ba, baki tunanin gaba ne kam? Yanzu in aka ce bana nan rai yayi halin sa gashi kuma baki da kowa a duniyar nan fah? Su ɗin dai sune dolen ki a lokacin, kuma baki da wanda suka fisu, ya kamata zuwa yanzu ac kinyi koyi da hali na” “haba Mamah Allah ma ya sauwaƙe, Ni zan riga ki mutuwa ma kuma mamah ai ko kin mutu akwai ahalin ki, shiyasa nake cewa Ni ki haɗa Ni da su ko da ace ke ba zaki je gare su ba” Lokaci ɗaya yanayin Mamah y sauya, abun da take ji a ƙirjin ta Allah kaɗai ya sani, hawaye ne kawai ke zuba daga idon ta. Nan hankalin Zahrah ya tashi don. Ko kaɗan bata son ɓacin ran Mamah. “mamah ta don Allah kiyi haƙuri Ni nayi miki laifi ko" Jijjiga kai tayi don a halin yanzu ko kaɗan ba zata iya magana ba. “shikenan kiyi haƙuri ba zan ƙara tambayar ki ahalin ki ba tunda na fahimci ba kyaso, kiyi shiru haka don Allah” ta ƙarasa itama hawaye na zuba daga idanuwan ta yayin da take goge wa Mamah nata hawayen. Da ƙyar Mamah tayi shiru sannan ta kamo hannun Zahrah ta ƙanƙame cikin nata tamkar za'a ƙwace mata ita. “ɗiya ta Zahrah, ba wai bana so ki san ahali na baneh sai dai kawai in anyi maganar ina shiga wani yanayi, kada ki damu wata rana da yardar Allah zaki gan su har ki rayu da su” “shikenan Mamah na ta kaina na daina ba zan ƙara tambayar ki ba, to yi murmushi muga" Ta faɗa tana lakuce kumatun Mamah. Nan da nan kuwa suka ware suka ci gaba da hidimar su. Wajen azahar Ammi ta aiko Badi'ah da basket ɗin abinci ta kawowa Mamah. Sun daɗe suna hira da ƙawar tata kafin ta tafi. Suka ci abincin su kafin su fitar da kayan Masar Mamah su ka ƙara tsaftace su. Da yamma Mamah ta wuce kasuwa wurin kasuwancin ta, alhamdulillah yau kam da wuri ta gama har aka zo ana neman masa. Da taimakon Lauwali suka dawo. Bayan ta sallame shi ya tafi. Duk abun da yake faruwa akan idon amaryar Kawu, jira kawai take mai gidan ya dawo ta zuba mishi yasha. Ana yin Sallah sai ga Badi'ah da basket ɗin abinci, Mamah ta amsa tayi godiya sannan ta bata wancan na ranan because it's already washed. Badi'a na shirin fita taji an riƙe kafaɗarta, a tsorace ta ɗago ɗin ganin waye. Murmushi mai ɗauke da ma'anoni ta ke zuba mata. “ƴan mata nace waye yake aiko ki kawo abinci?” tun da ga nan ta harbo matar, “kenan wannan ce auntyn Zahrah, tab, tallai akwai matsala dole na sanar da Ammi" jin bata bata amsa ba yasa ta ƙara maimaita mata “ƴan mata wai waye ke aiko ki kawo abinci ne” “nimah ban sani ba, sake Ni na tafi gidan kada a neme ni” “kenan ba aiko ki ake yi ba” “eh Ni nake kawowa da kaina, sake Ni" Banu yadda Saudatu ta iya ta sake Badi'a, a tsorace ta isa gida. “Ammi Ammi Ammi!” “kai Badi'a irin wannan ƙira haka ba ƙaƙƙautawa?” ta faɗa yayin da take fitowa daga bedroom ɗin ta. “Ammi wallahi amaryar gidan su Zahrah abun tsoro ce, kamar ƙaruwa take. Ammi har tsayar da Ni tayi tana tambaya ta wai wa yake aiko Ni na kawo abinci” “subhanallah sai kika ce mata MEH?” “cewa nayi Ni nake Aiko kaina manah" “yauwah good girl, u're very clever daughter, Allah yayi miki albarka” “Amin ameen Ammi na” Kawu bai shigo gida ba sai wajen 11:00pm na dare, yana shigowa kuwa ya fara washe baki yana nufar ɗakin amaryar shi. Lokacin tayi shirin ta ta zaba kwalliya tamkar zata fita yawon bariki. Da sauri Kawu ya nufi yadda take. Peck tayi mishi haɗi da hugging nashi “sannu da dawowa mai gida na“ Cike da ɗauki yace “yace sannu amarya ta abar ƙauna ta” Ɗan sake shi tayi, “oyah muje kayi wanka kaji” ba musu Kawu ya biyo ta suka fito da yake toilet ɗin su a waje yake. Cike da ƙwarewa a harƙar barki ta kama hannun shi ta raka shi bayan yayi wanka suka dawo tare ta taya sanya kaya. Abincin da Rubber ta aiko musu da yammah ta zuba mishi, bayan yaci yayi hani'an tukun ya ɗago yana kallon amaryar. “ko wannan matar ko ta dawo” Cikin halin ko ina kula tace “wace mata kenan?” “ina nufin wannan banzar mai ɗakin can” Ita kuwa jin ya ambaci matar shi da banza farin ciki ya mamaye zuciyar ta, cike da murnar samun nasara a Oman ɗin ta tace “eh toh wata jemammiyar mata da yarinya dai sun shigo lokacin ƙawa ta Asabe tana nan, ai ka santa?” Cike da ƙaguwa yace “eh na san Asabe ƙawar ki” “toh matar tana shigowa ita da yarinyar ta suka yo kan mu suna tambayar wacce ce daga cikin mu amarya. Da Asabe ta nuna musu Ni sai suka kwashe da dariya, duk fushi da rashin mutunci irin namu kasa mata magana nayi ina jin ta riga da ta asirce Ni ne” Ta faɗa tana sakin kukan munafurci. Shi kuma sai lallaɓa ta yake kamar wata uwar sa. “yi haƙuri amarya ta ki faɗa min me ke faruwa manah, tabbas duk wanda ya taɓa min ke zai ga fushi ne” Ɗan guntun hawayen ta ta goge ta ci gaba da fuskantar shi “kawai matar sai ta rufe mu da zagi, a nan ta kora Asabe sannan ta juyo kaina, yarinyar da suka shigo tare ita ma ta ɗaurabkan yadda matar ta tsaya sai zagi na suke wai Ni karuwa ce, abun babu daɗi” ta ci gaba da kukan munafurci nata. “shine na basu haƙuri da ƙyar suka haƙura kuma sun ce idan na faɗa maka sai ta min shegen duka. Daga haka ta juya ta nufi ɗakin gefen can naga ta buɗe, sai a lokacin na gane ita ce matar ka da kuma ƴar ka” GA FA WANI SALO DA AMARYAR KAWU TA FARA MUJE ZUWA, BA'A FARA WASAN BA. KUYI COMMENTS DA YAWA DON SHINE ƙWARIN GUIWA TA. ITZ DIAMOND LADY 💎 Oum Zainab ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲 0️⃣8️⃣ Bazan manta da ke ba ƙawa ta Murjanatu Abdulwahab Yusuf, ina matuƙar ƙaunar ki saboda Allah. Na gode da ƙaunar ki gare Ni. Ubangiji ya ƙaunace ki. SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Ran Kawu idan yayi dubu toh duk ya ɓaci a fusace ya fita daga ɗakin amarya yayin da ta daka tsalle saboda murnar cin nasara. Yana isa ko sallama bai yi ba ya fara buga ƙofar ɗakin yayi shaye da mamaki maka ta buɗe Bata aune ba kawai taji sauƙar mari s fuskar ta. Bata tsaya ba kawai ita ma ta rama. Mamaki ne ya kama Kawu wai yau shi Madina ta mara don ya mare ta, gaskiya akwai matsala. A kasalance ya koma ɗakin amarya yana huci.. “mai gida ba dukan ta kayi ba koh, bana so ko kaɗan taji haushi na” Murmushin yaƙe yayi “shikenan mata ta damah warning na kashe mata” “yauwah mai gida ammah gobe ya kamata ace an raba mana girki da kuma kwana ko” Shaye da mamaki yake kallon ta kafin yace “ai nikam kullum ina nan, MEH zanyi da waccar matar kuma” “aahmai gida ba za'a yi haka ba, zata ga kamar ina zaluntar ta ne” nan kuwa cikin ranta daɗi take ji. “aah mu bar zancen nan, Ni anan zan je kwana” “shikenan tunda ka ce haka” ta ɗanyi shiru sannan ta ci gaba. “sai batun girki, ai yanzu tunda ta dawo sai a raba“ “ke dai zan ke baki ki girka, ita dama can ita take ciyar da kan ta da ɗiyar ta” Daga haka ya miƙe zuwa gado, su basabun ba Kawu an samu gadin banza. Ita kuwa amarya farin ciki ne fal ranta. Mamah kuwa tunda ta rama marin da Kawu yayi mata ta fara jin wani sanyi a ranta, kullin da take yawan ji a ƙirjin ta sai taji kamar ya ragu....ɗaki ta koma tayi alwala sannan ta fara jera nafilfilu daga nan bacci ya ɗauke ta. Washegari da wuri suka tashi, Zahrah ta shirya cikin uniform ɗin ta sannan ta zauna jiran Badi'a, ba'a jima ba ta shigo hannun ta ɗauke da basket, “mamah Ina kwana" “lafiya ƙalau Badi'a ya su Ammi?” “suna lafiya, ga breakfast in ji Ammi Zahrah ki samu ki shirya kafin Abba ya gama breakfast” “toh Allah ya amfana, ki gaishe da Ammi” “toh" sannan ta juya zuwa gida. Chips ta zuba a plate ta fara ci, tana gamawa tayi brush ta fito. Sai da ta shiga ta gaida Ammi suka fito ita da Badi'a don jiran Abba. Abba na fitowa suka gaida shi sannan suka tafi sai school. Rayuwar school tana yi wa Zahrah daɗi a halin yanzu don kuwa cikin sati da ƴan kwanaki ta fara gane darasi sosai, uncle Hashim na yin iyakar iyawar shi wajen ganin Zahrah ta na koyon abubuwa. Alhamdulillah, da yake ƙwaƙwalwar ta na ja tuni tayi nisa. Ga kuma Badi'a ita ma ba'a barta a baya ba wurin taimaka mata. Yau suna da English, uncle Hashim ya shigo yayi delivering class ɗin shi kuma kowa ya gane daidai gwargwado. Bayan ya fita aka yi sauran three classes ɗin daga nan aka tashe su. Kamar kullum.ya Abba ne ya zo ɗaukar su, suka gaida shi. Bayan su isa gida kowa ta wuce gidan su. Zahrah na shiga taci karo da amaryar Kawu na girki, ɗauke kanta tayi don ita ba mai shiga abun da ba'a sanya ta baneh. Kamar daga sama taji Muryar matar “ƴata babu gaisawa ne?” Harara Zahrah ta cilla mata tare da nufar hanyar ɗakin Mamah. Murmushin mugunta amaryar Kawu tayi sannan ta ci gaba da girkin ta. Wanka tayi sannan ta ɗauko uniform ɗin ta na islamiyya ta zura..Mamah na fitowa daga bayi daidai isowar Badi'a da abinci ita ma cikin shirin ta na islamiyya. Sannu Mamah tayi mata ta amshi abincin. Zahrah na gama ci ta ɗauki jakar ta ta fice, da yake islamiyya ba wani nisa sosai daga gidan su yasa suka taka da ƙafa. An samu sauyi sosai don yanzu Zahrah tana maida hankalin ta ga karatun ta na islamiyya, kuma hadda sosai take bayar wa. Bayan sun dawo daga islamiyya wanka kwai tayi ta sauya kaya sannan tayi wanki. Tana gamawa ta fice zuwa kasuwa wurin Mamah. Sai bayan maghrib suka dawo. A daren suka wanke kayayyakin amfanin su kafin suyi dinner da aka aiko daga gidan Ammi. Haka rayuwa ta ci gaba a gidan Kawu, babu abun da ya taɓa haɗa Baba Amarya da Mamah har suka shafe watanni uku a gidan sai dai a ɓangaren baba amarya kullum akwai abun da take ƙunsawa kuma har yanzu Kawu baya ciyar da Mamah da Zahrah. A irin wannan lokacin ne su Zahrah suka fara exams, Alhamdulillah an gama kuma sakamako yayi kyau, Badi'ah Kabir Umar ita ce first sai Umar Yusuf sai kuma Zahrah Abdulkarim Kuru. Farin ciki kamar suyi yaya Abba yayi musu kyauta ta Musamman kuma lokacin Hutu Badi'a da Zahrah suka tafi Jos gidan yayar Ammi. Hajiya Barira yayar Ammi ce, uwar su ɗaya uban su ɗaya. Tana da yara huɗu, yaya Affan, Aunty Fadila, Aunty Aisha sai ƙaramar su Khady.. sun samu tarba ta musamman daga wurin Hajiya da kuma yaranta.. Yaya Affan baya nan yana Cyprus, a can yake karatu, Aunty Fadila da Aunty Aisha su kuma sun gama secondary sun fara karatu a ATBU ammah an saka auren su tare. Khady kuwa sa'ar su ce, yarinya mai ɗan karen kinibibi da rashin ji, rayuwar su a Jos tayi musu daɗi, sai da suka shafe sati biyu suka dawo Bauchi. Abun mamaki duk budurin nan Kawu bai san Zahrah baya nan ba, abinci kuwa kullum sai Ammi ta shigo da kanta ta kawo. Baba Amarya abun na ci mata tuwo a ƙwarya saboda haka tun da Kawu ya dawo take mishi kuka wai ita ta gaji. “nikam na ganiii zan bar gidan nan don har ga Allah bazan iya rayuwa cikin sa ba” “yi haƙuri amarya ta meh aka yi miki har kika gaji da gidan” Share ƙwallar idon ta tayi tace “Wannan matar taka bata son zaman lafiya, haka kawai sai ta turo yarinyar ta mai zubin Mayun nan tayi ta zagi na, yarinyar nan har da zubar min girkin da nayi maka wai kowa ya rasa tunda su baka basu, nikam tsiro nake kada wata rana baka nan su yanka Ni" Rungume ta yayi jikin shi “aah ki bar Ni da su, zan hukunta su kuma ba zasu ƙara shiga rayuwar ki ba, ke da gidan ki ai ina kin ce na kora su sai na kaɗa su. “uhm uhm ka bar su zasu ce nayi musu munafurci an kore su, Ni ina son zaman lafiya tare da su, suna bani tausayi” “shikenan zan bar su ammah zan gargaɗe su akan ki don baza su takura miki ba a Cikin gidan ki, Yanzu dai zubo min abinci naci” Bayan yaci abinci yayi wanka ya nufi ɗakin mamah. Ta idar da Sallah a lokacin tana tasbihi ya shigo bata ko kalle shi ba ta ci gaba da tasbihin ta. “keeee Madina, kwana biyu ina ɗaga miki ƙafa daga ke har shegiyar ƴar ki zaku takura wa amarya ta. Kar ki ga nayi sanyi kiyi tunanin tsoron ki nake ji, wallahi daga ke har ita Zahrah zan azabtar da kuma fiye da tunanin ku akan mata ta” Daga haka ya fice a fusace, a tsanake Mamah ta bishi da ido har ya fice. Ta girgiza kanta sannan ta maida hankalin ta kan karatun Alkur'ani da ta fara. Ranar da su Zahrah suka dawo sun dawo da goma sha tara ta arziƙi daga Jos.... kayayyakin sawa da makamantansu duk sun samu ga kuɗin da aka basu. Mamah tayi farin cikin dawowar Zahrah gida don kuwa kullum sai tayi kuka ina ta tuna ta. Sun koma makaranta lafiya tare da ƙara maida hankalin su a karatun su both ALMUNAUWARA da kuma IMAM MAKIK. Zahrah ta zamo zakara don yanzu ana matuƙar ji da ita cikin school ɗin su. Sam bata shiga sabgar kowa in ba ƙawar ta Badi'a ba, ammah duk wanda ya shiga sabgar ta toh ya shiga sabgar ta bata ƙyale wa. Ɓangaren Mamah ta ci gaba da suyar Masar ta a kasuwa, kuɗin kuwa tana adana shi saboda gaba, don a halin yanzu babu abunda ta nema ta rasa, abinci za'a kawo tun daga breakfast, lunch har dinner daga gidan Ammi. Sun ɗauke su tamkar jinin su hakan yasa damuwar Mamah ta ragu uwa uba yanzu babu wata alaƙa tsakanin ta da Kawu, sai ya share watanni biyu basu haɗu ba hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba lokaci ɗaya daga ita har Zahrah suka murmure jiki ya ƙara kyau. Bana amarya ma dai bata shiga sabgar su saboda bata samu damar hakan ba ammah ƙudurin ta yana nan dangane da su. Tufafi ma dai basu rasa ba saboda Abban Badi'a yana siya musu, school fees kuwa already Yaya Ishaq ya biya mata har kammala junior studies nata. Wasu lokutan in ta zauna ita kaɗai babu abun da ke faɗo mata sai yaya Ishaq wanda a halin yanzu bata san ya yake ba, ko yana lafiya ko akasin haka. Takan yi mishi fatan alkhairi domin kasancewar shi haske cikin rayuwar ta, sanadiyar shi yanzu ta samu wayewa fiye da da, addu'a kuwa kullum cikin sallolin ta bata mantawa da yaya Ishaq tare da fatan Allah ya dawo da shi lafiya. Bahaushe yace sannu sannu asarar mai rai yanzu haka Zahrah sun kammala jss 1 ɗin su, sakamako mai kyau mai haskaka wa kowa mamaki yake yadda Zahrah Kuru ta zama popular cikin school ɗin duk da cewa lokacin da tazo makarantar she's nothing but a stupid girl. An now she shines everywhere gata dai yarinya ce ammah akwai ƙwaƙwalwar manya. Hakan yasa ta samu farin jini da ɗaukaka kama daga ƴaƴan uwanta students, seniors ɗin ta, teachers na baa barsu baya ba hakan duk da taimakon uncle Hashim da kuma Aminiyar ta Badi'a. WANNAN KENAN TEAM ZAHRAH KUYI FARIN CIKI MUTUNIYAR KU TA DAGE FAH KO INA YAYA ISHAQ HAR YAU BAI NEMI CUTIEN SHI BA? HAJIYA BABS AMARYA FA TANA NAN TANA SHIRI, KO ZATA CI NASARA. KU BIYO NI TARE DA ALƘALAMI NA DON JIN YADDA ZATA KAYA. BA'A FARA WASAN BA HAR YANZU. DIAMOND LADY 💎🤟 CE (Oum Zainab) ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 0️⃣9️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Yau rana ce ta musamman da aka ware a cikin makarantar ALMUNAUWARA ACADEMY kamar yadda ya kasance cikin tarihin makarantar duk shekara akan gudanar da bikin yaye ɗalibai -speech and prize giving day-. Ko ina na makarantar ya ƙawatu kasancewar makarantar ta ƴaƴan masu hannu da shuni ne. A nan aka fara gabatar da programs da ke a agenda na taron. Cikin programs ɗin akwai drama show da wasu students zasu gabatar. Drama ɗin an shirya ta ne only to motivate the students. Cikin lokaci MC ya sanar da agenda na gaba, wanda shine drama show. Wani curtain da ya kasance tamkar decoration naga an yaye. Babu abun da ya bayyana sai herarrun seats da aƙalla zasu kai 30 daga can baya. Ta gaba ɓangaren hagu akwai evidence box sai kuma ta can tsakiya kujeru biyu da kuma tables biyu. Ɗaya ɓangaren by the right hand side wasu kujeru ne dake facing waɗannan seats sai kuma can jikin bango babban table da wata lallausar kujera. Haka wajen ya tsaru, babu ɓata lokaci jama'a suka fara shigowa suna zama a waɗannan seats ɗin. Badi'a ce da kuma khalid suka shigo cikin kayan lawyers ɗauke da files a hannun su. Suna zama sai ga Umar ya shigo ya tsaya near the evidence box. Maryam kuma ta zauna a seat ɗin dake facing mutanen by the right hand side. Onportunately sai ga Zahrah well dressed in judge's dress, ga kuma wasu sanye da kayan police na biye da ita. A hankali ta ke takowa har ta iso seat ɗin da aka tanada domin ta. Kowa a lokacin ya miƙe har sai da ta zauna sannan ɗaya daga cikin police ɗin ya miƙa mata files da sauran abubuwa gaban ta. Ba tare da ɓata lokaci ba ta ciro glasses 👓 ɗin ta ta sanya, nace MASHA ARRAHMAN, Files ɗin ta fara buɗe wa sannan ta umarci Muhammad da ya karanto cases da suke da shi. Cikin harshen turanci ya fara magana a nutse.. "Case na farko: Ana zargin Mallam Uba Idi da safarar ƴan mata da kuma miyagun ƙwayoyi tare da lalata wata ƴarinya da tazo Companyn shi neman aiki wacce a halin yanzu ta mutu. Case na biyu: Ɓarayi guda uku, Dauda, Muhammadu, Idris da shiga gidan wani attajiri don satar daga ƙarshe har ta kai ga kashe mutumin da ahalin sa" Daga haka ya ɗan rusuna sannan ya zauna. Zahrah da ta make ta ce “su waye lauyoyi” Badi'a ce ta fara tashi haɗe da rusunawa “Suna na Barr.. Badi'a Kabir, nice lauyan Wanda yayi ƙara” sannan ta rusuna ta zauna. Khalid ma ya miƙe “I'm Barr. Khalid Umar, I'm for defense counsel" daga haka ya rusuna. Cike da ƙwarewa suka yi zaman nan tamkar dai a court ɗin gaske suke gudanar da shari'ar sannan aka yanke wa masu laifi hukunci daidai da laifin su. Daga nan aka sauƙe curtain. Manyan baƙin mu appreciated the drama sannan sun bada kyaututtuka da dama wa waɗanda suka yi wasan, yayin da wasu suka ware kyauta ta Musamman ga Justice Zahrah Kuru wacce ta matuƙar burge mutane da damah. Haka aka ci gaba da gabatar da programs har aka kammala. Daga nan aka fara raba prizes. Zahrah ta karɓi prizes sosai ita da Badi'a. Irin prizes ɗin da ta karɓa yasa a wajen wakili Governor ya Bata kyautar garin kuɗi har 100k haka sauran jama'ah suka yi ta mata kyaututtuka na ban mamaki. Anyi taro lafiya an gama lafiya. Lokacin tashi Abba yazo ya ɗauke su sai gida. Mamah da Ammi sun yi matukar alfahari da ƴaƴan nasu ammah duk wannan sha'ani da ake yi Kawu da amarya babu wanda ya sani. Shaye shayen Kawu kuwa sai abunda ya ƙaru...dabar su ma ta dawo tamkar dai da yanzu kuwa har shiga cikin gidan suke yi saboda samun dama daga Bana amarya. Ranar Monday suka je makaranta. Principal ne ya aiko a ƙira mishi Zahrah Kuru. A tsorace ta fito daga class ɗin su ta nufi office ɗin principal da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga bayan ya bata umarnin hakan “good morning sir" “morning Zahrah, how's studies?” “Alhamdulillah sir. I was informed that u want to see me” Ba tare da ya bata amsa ba ya ɗaya phone ɗin shi ya kara a kunne, bayan few seconds aka yi picking. “Assalamu Alykum" baa jin meh ake cewa daga ɗaya ɓangaren daga bisani ya miƙa mata wayar. Ba tare da ta san wanene ba cikin Muryar ta mai daɗin sauraro tayi sallama. A lokacin kuma principal ya fita daga office ɗin. Jin Muryar cutien shi ya sake wani murmushi mai ɗan sauti “wa alykumussalam cutien yaya” Bata san lokacin da ta cilla wani ihu ba saboda farin ciki sai kuma hawaye sharrrr “aah cutien yaya kuka kike yi? Toh shikenan lemme hang off the call and I won't call again” Da sauri ta share hawayen ta kamar tana gaban shi “i'm sorry yaya Ishaq, kukan farin ciki ne, ina kwana ya karatun" “Alhamdulillah cutie, ya Mamah?” “lafiyae ta ƙalau, kusan kullum sai tayi jajen ka” “Ayyah ki gaishe ta zan aiko muku saƙo in Sha Allah” “toh Yaya mun gode, i thought har ka manta da mu" “ni ina na isa na manta da ƙanwa ta!, Rufa min asiri kullum cikin kewar ku nake" Murmushi mai ɗan sauti tayi daga ɗaya ɓangaren yace “ba wannan ba dai cutie, jiya naji abun alkhairi da kika yi, kuma na gani. Ina alfahari da ke ƙanwa ta, ki ƙara dagewa Please” “in sha Allah yaya” “shikenan sai anjima, damah I called only to complement on your performance and I'm proud of you zahrah" “thank you yayah, bye” Daga haka ƙiran ya katse. Principal ne ya shigo tare da uncle Hashim da uncle Suraj. A nan kowa ya yabe ta tare da faɗin irin alkhairin da makarantar ta samu sanadiyyar drama show ɗin su, Governor daga baya da kanshi ya aiko wa makarantar saƙo kuɗaɗe masu yawa haka manyan mutane suka bada kuɗaɗe su mah. She's totally speechless on how victorious she's, and she promised to do better than this. Daga ƙarshe yace ta turo baban ta domin karɓa mata kyaututtukan da ta samu, in ta fita ta kira mishi Badi'a. “ohk sir" daga haka ta fice zuwa class. Badi'a ma same message aka yi passing mata. Finally they decided to send Abba, don ita ko karen huka ne ya cije ta ba zata taɓa turo Kawu matsayin wani nata ba. Toh me mah ya kai ta? Mutumin da bai san ci ko shan ta ita da mahaifiyar ta ba a matsayin shi na wadda hakƙin su ke a wuyan shi, bai don ko da lafiyar su da rashin ta ba. Inaaaah ba zata taɓa ba ko da kuwa alkhairi zai wuce ta ne. Haka har lokacin tashi suka koma gida daga nan suka tafi islamiyya. Bayan sun dawo kowa ya wuce gidan su. ★★★★★★★ Tafiya suke ita da Asabe Bala'i cikin wani ƙungurmin daji wanda ke da matuƙar duhun tsiya suna tafiya suna sare ice saboda irin bishiyoyi masu canopy ɗin an ne a ciki. Sunyi tafiyar da ta kai kimanin 2hours kafin su iso wajen wani old building Wanda ke zagaye da wasu bishiyoyi masu baƙaƙen leaves. Daidai ƙofar wajen suka nufa. Tsawa aka buga musu “kai!!! ba'a shigowa nan da ƙafar damah! Ku fice” A tsorace dukan su suka juyo don irin yadda Muryar ta kasance maras daɗin sauraro da kuma mugun tsoratarwa... “zaku iya shigowa yanzu ammah kada ku kuskura ku shigo min da ƙafafun dama” A ruɗe suka shiga kamar dole. Wani irin gini ne maras kyawun fasali, jikin ginin baƙi ƙirin ga wasu ƙwari baƙaƙe dake yawo jikin ginin, duhu ne ya mamaye wajen lokacin ɗaya suka rasa inda da zasu sanya kansu yayin da suka ji wata guguwa ta tashi, rumtse idanuwan su suka yi sannan suka ji iskar ta janye su zuwa wani sashe. Lokaci ɗaya haske ya bayyana a wajen, suna buɗe idanuwan su suka gansu zube gaban wani mutum mummuna.. Idan nace muni to fah munin ya wuce misali, fuskar shi ne baƙa ƙirin ta yamutse ga uban gashin kai kamar na wata baindiya sai dai nashi babu alamun gyara, gemun shi ya kai saitin guiwar shi Tsayin sa kuwa ba'a magana haka girman jikin sa ya wuce misali. Sam ba shi da daɗin gani. Dariyar shi ce ta ƙara tsoratar da su suka fara zazzare idanuwan su kamar waɗanda suka yi wa sarki ƙarya. “Hhhhhhh.....Saudatu Kwalba tare da ƙawar ta Asabe Bala'i. Hhhhh...hhhhhhh.....barkan ku da zuwa fadar Bulebule Bokan kowa hhhhhhh....hhhhhhh....” “mun go....de...ran....ka..shi...daɗe....” Lokaci ɗaya ya haɗe fuskar shi ya fara duban su. “Kwalba kin zo akan kishiyar ki ko?" Cike da mamaki ta ɗan kalli boka Bulebule. “kin zo ne akan ta mutu ammah ba yanzu ba sai nan da shekara biyu sannan ki mallake mijin ki da kuma ƴar ɗan uwan sa zahrah” “eh haka ne ranka shi daɗe ka taimaka min” “shikenan kada ki damu" Wata ƙwarya ce ta bayyana a gaban shi, cikin ta ya fara surkulle yana furta wasu maganganu. Can ya buga kwaryar nan da nan ta ɓace “Akwai matsala! Matar nan ba zata mutu ba sai dai zanyi miki wani aiki da zata haukace, idan ta haukace ita da kanta zata fara jinya sai ta gudu ta bar gidan. Ita kuma ɗiyar ta zaki mallake ta ammah akwai babbar matsala don kuwa akwai manya manyan sheɗanu a tattare da ita wanda Ni kaina tsoron taɓo su nake. Mijin ki ki sa a ranki kin mallake shi. Hhhhh....hhhhhhh...hhhhhhh..” “yauwah ranka shi daɗe na gode sai kuma kuɗin aikin" Dariya yayi sannan yace “bulebule baya karɓar kuɗi kasafai sai dai ladan aiki da zaki bashi wanda ya kasance mai sauƙi. Zaki zauna a tare da ni na kwana biyu, zan yi amfani da ke sau biyar” Ba tare da ta damu ba tace “shikenan ranka shi daɗe na gode” “ke Asabe zaki iya tafiya ita sai nan da kwana biyu ammah in kina so zaki iya zama zan baki ɗaki kema anan” “shikenan ranka shi daɗe zan kwana a nan ɗin” (Authubillah!!! Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yace :duk wanda yake wurin ɗan duba, ko kuma boka, kuma ya aminta da abun da ɗan duban ya faɗa masa toh haƙiƙa ya kauracewa abun da aka sauƙin min” Mata muji tsoron Allah mu sani mutuwa tana nan tana jiran mu, MEH yasa in muna da bukata bazamu riƙa wurin Allah ba? Shi fah in ka roƙe shi zai amsa maka kuma baya gori dan ya baki. Saboda haka ki kiyaye in son mallake mijin ki toh ki kyautata masa da haka zaki sace zuciyar sa kai har ma da ta dangin sa matsawar kina kyautata musu. Allah ya tsare). ★★★★★★★ Abba da kan shi ya amso musu kyaututtukan su. Cike da farin ciki ya dawo yana nunawa Ammi. Sunyi farin ciki da nasarar yaran musamman Zahrah da ta kasance babu mai tsaya mata damah. Sai da yammah dab da dawowar su daga islamiyya suka wuce zuwa gidan Mamah. Tabarma ta shimfiɗa musu “sannun ku da zuwa maraba lale” “sannun mu Maman zahrah” Bayan sun zauna ta ɗebo musu ruwa. Ba tare da nuna ƙyama ba Ammi ta kurɓi ruwan. “ina wunin ku ina gajiya” “lafiya ƙalau Maman Zahrah" “ya hidima kumah, Allah dai ya saka muku da alkhairi Abban Badi'a" “amin babu komai Maman Zahrah ai yiwa kai ne," Murmushi mamah tayi. Abba ya gyara murya sannan ya fara magana “toh kamar dai yadda kika ganmu a nan mun zo ne don taya ki murna bisa nasarar da Zahrah ke samu a makarantar su ta boko. Shekaranjiya anyi tarin yaye ɗalibai a makarantar tasu, toh a nan ta samu kyaututtuka da dama, akwai kuɗaɗen ta kimanin Naira Dubu ɗari biyu (200k) Wanda ta samu daga wurin manyan mutane a faɗin jahar da kuma wajen ta. Saboda haka ne ma na amso musu saƙon ita da ƴar waje na Badi'a.” Cike da farin ciki Mamah tace “madallah Allah ya saka da alkhairi Allah yasa mai amfani ne” Ammi ta amsa da “Ameen” “toh saboda haka ne nake ganin MEH zai hana kije ki buɗe account sai a zuba miki kuɗin a ciki” girgiza kai mama tayi “Aah Abban Badi'a ba za'a yi haka ba, kawai ka riƙe kuɗin a wajen ka ina ga zaifi. Idan a waje na ne zai iya salwanta a banza ammah idan a wajen ka ɗin ne kamar zai fi. In yaso in an tashi amfani da shi sai ayi nan gaba" Abba bai Musa da shawarar Mamah ba haka Ammi. Girman ta kuwa a idon su ya ƙara ƙaruwa. Daga nan suka yi sallama suka wuce gida. TOH GA FA BABA AMARYA DA KUMA TUGGUN TA GA MAMAH DA ƊIYAR TA GA KUMA YA ISHAQ SHIMA ASHE YANA NAN. KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY DON JIN YADDA ZATA KAYA COMMENTS DIN KU KAWAI NAKE SO SABODA SHINE ƙWARIN GUIWA TA. DIAMOND LADY CE 💎🤟 Oum Zainab. ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣0️⃣ Bazan manta da ku ba ƴan uwa na kuma rabin jiki na Aminatouh Adamu Hassan (Dr. Meenal) Sa'adatu Adamu Hassan (Shaheedah) A'ishah Saleh Uthman da kuma Safiyya Saleh Uthman (Autar Umma) SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau daɗi gobe akasin haka. Tun ranar da BABA AMARYA ta dawo daga wurin boka Bulebule komai ya sauya a gidan nan. Cikin sati guda ta fara shimfiɗawa Kawu sarautar mulkin ta a gidan, tana cewa abu har rawar ƙafa yake don yayi mata. Wannan shine mafarin zancen. Zaune take akan taburmar da ta shimfiɗa yayin da Kawu ke mata tausa a tsakar gidan. “mai gida tashi ka ɗaura mana sanwar nan manah don Ni na riga da na gaji” Da sauri ya miƙe kamar mai cika umarnin mahaifiyar sa ya fara haɗa ice cikin murhu. Ba don komai ta sashi ba sai don kawai haka tayi ra'ayi. Da ƙyar wutar nan ta kama ammah haka tace ya daure yayi musu girkin nan. Tun bai wuce 11:20am aka fara girkin ba har 1:00pm da ɗori ba a saka shinkafa ba. Lokacin da Zahrah ta dawo daga school tayi arba da Kawu na girki. Shewa ta buga sannan tayi hanyar ɗakin Mamah tana dariya. Batayi tsammani ba sai jin Muryar shi tayi yana ƙwalla mata ƙira.. “Zahra'u zahrah'u”.....babu alamun zata tsaya ballantana na ta amsa ta wuce ciki abun ta. Kamar yayi kuka haka ya tasa tukunya da murhu a gaba, gashi babu yadda ya iya tunda gimbiya ce ta bashi girkin. Ana cikin haka Badi'a tayi sallama da basket ɗin abinci a hannun ta, a hanzarce ya miƙa ya zo gaban ta yana miƙa mata hannu. “ɗan matsa zan wuce” “kawo na shiga da shi” da ƙyar Badi'a ta danne dariyar da ta kama ta sannan tace “gyara na wuce ko sai na yi wa bodyguards ɗina magana” kasancewar bai san ta ba kuma yaga ƴar gayu yasa yayi tunanin da gaske ne. Direct ɗakin Mamah ta miƙa abincin sannan ta fita. Kawu da ya gama galabaita ga rana, ga zafi ga hayaƙi in Banda zufa babu abun da ke ketowa daga jikin shi. Bana amarya kuwa ta tsare ina bai dafa ba ko ta dafa ba zai ci ba don ba bashi zata yi ba. “kiyi haƙuri kizo ki amshi girkin nan, Ni babu abunda zan iya wallahi yanzu haka na wahala” Hararar shi tayi ta gatsina hanci tukun tace “ita waccar ta ɗakin uban meh take yi a gidan da bazara dafa ba, maza je ka taso ta” Zungui zungui babu kunya ya ja ƙaton kanshi zuwa ɗakin Mamah. Lokacin kuwa sun zuba fried rice da kuma papper meat da aka kawo daga gidan Ammi suna ci. Yawun Kawu duk ya tsinke ammah ya dake. “madina ki fito in ji amarya kiyi girki” Idan gini na magana toh, Mamah ko kallon shi bata yi ba gashi yanzu duk jin zuciyar sa yake yi a mace ba zai ma iya dukan ta ba. Ya fi 10minutes yana jira ko zata fito ammah shiru, hakan yasa ya ja dogon kafar shi ya koma wajen bana amarya. Marairaice mata fuska yayi “don Allah gimbiya kiyi haƙuri ki zo ki ƙarasa, gaba ɗaya sun ƙi kula Ni su ma. (Nace ah su Kawu anyi luƙus kenan” Harara ta ƙara banka mishi “toh ita ɗin uwar ka ce da ba zaka ce ta fito ba, koma kace ta fito” haka ya ƙara komawa kamar ɗan ta. “tace wai ki fito" banza Mamah ta ƙara yi mishi. Babu yadda ya iya ya ƙara dawowa. Wasa wasa abinci har 3:00pm ba'a zuba shinkafa ba. Da ya gaji kawai ya fice shagon gyaran babur da yake ya zauna Allah ya taimake shi wani ya kawo gyara sannan ya samu ya ci abinci. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, duk shekara sai lashe kyaututtuka masu yawa daga makaranta da kuma wajen makaranta. Yanzu har su Zahrah suka shiga aji uku (jss 3) kwacakwam hankalin su ya koma kan karatun su, gashi Badi'a na shirin yin sauƙa saboda damah can tayi wa Zahrah nisa. An samu sauyi cikin gidan Kawu sosai don kuwa yanzu Kawu ya zama dolo, babu abun da ya isa yayi sai da umarnin baba amarya. Ya bi ya rame har abun tausayi ammah hakan bai taɓa zuciyar Zahrah ba. Yaya Ishaq har yau shiru babu shi, sai dai wasu lokutan ya kan kira wani staff ya haɗa shi da Zahrah. Su Zahrah an girma,duk ƙiriniya irin ta Zahrah yanzu babu, ko dan ance zama da maɗaukin kanwa wai shi ke kawo farin Kai. Toh Zahrah ma dai ta sauya. Ga wani irin kyau da take yi yanzu wanda ake kira da ƙyalƙyalin ƴan matanci....ta ko ina Zahrah batada makusa. Idan kyan fuska ne toh Zahrah ƙarshe ce, kana ganin ta kaga fuskar Mamah kamar anyi copy sai dai Mamah da yake wahala ta dafar da ita yasa Zahrah ta fita haske sosai. Uwa uba wani rashin don magana da Zahrah ta ɗauko abun mamaki idan har kaga tana magana toh an taɓo ta ne. Hakan ba ƙaramin ƙara mata kwarjini a idon ƙawayen ta yayi ba don kuwa kowa shakkar ta yake. Zahrah ce zaune a class yayin da mates ɗin ta suka kewaye ta tana kwatanta musu yadda ake solving wani equation a maths, da ƙyar suka samu suka fitar da amsar. Bayan sun gama ne ta ci gaba da koya musu sauran abubuwan da suka kamata. Aikin su kenan kullum a school yanzu idan sun je saboda an ma daina shiga clsss ɗin su. A lokacin exams kuwa Zahra ta nutsu ta rubuta abun ta. Bayan an kammala aka sallame su har sai result ya fito za'a neme su don yin registration na senior class, ranar sunyi kuka iya kuka saboda wasu ba a nan zasu ci gaba da karatu ba. Zahrah na ɗaya daga cikin waɗanda suka cire tsammanin dawowa ALMUNAUWARA don ci gaba da karatu duba da sponsor nata baya nan kuma babu alamun zai dawo, kuɗin kuma yafi ƙarfin mahaifiyar ta. “Dole zan koma government school ne na sani ammah Alhamdulillah for these three good years I've learned a lot” Da haka ta lallaɓa zuciyar ta tare da fauwalsws Ubangiji komai. Yanzu iya islamiyya suke zuwa. Zahrah ta maida hankalinta sosai kan karatun addinin ta, wanda ya kawo sauyi mai kyau cikin rayuwar ta. Rayuwar ta haskaka sosai, a da Zahrah bata iya riƙe bakin ta duk maganar da ta zo mata ko a waye kwaɓa mata take yi ammah yanzu Alhamdulillah an samu great improvement don kuwa a rana maganganun Zahrah ƙirgaggu ne, sanadiyyar islamiyya yanzu Kawu yana cin arziƙin gaisuwa daga gare ta, haka baba amarya ma idan ta ganta takan gaishe ta. Sana'ar Mamah ta ja baya sakamakon jinya da take yawan yi yanzu sauƙin ta ma suna samun abinci ko da yaushe ga kuma kyakkyawar kulawa daga sabon ahalin su. Jinya abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, an je asibiti abu yaƙi yiwuwa. Duk san ɗin da za'a yi sai ya nuna normal hankalin Zahrah duk ya tashi. Damuwa ce fal a ranta ga wata dama da ta fara yi. Fahimtar haka da Ammi tayi yasa ta yanke wata shawara ita da mai gidan ta. “Ni wallahi Abban Badi'a abun ya ɗaure mun kai, mutum mai lafiya lokaci ɗaya sai jinya, duk da cewa ba abun mamaki baneh kaɗan daga hikimar Ubangiji ammah jinyar Maman Zahrah akwai sa hannu astaghfirullah, a ce duk wani investigation da aka yi sai ya nuna normal bayan kuma gata nan tana jin jiki” “ni kaina nayi tunanin hakan, ita wannan mata gaskiya tana ganin jarrabawar rayuwa, kiga fa mijin ko sau ɗaya ban taɓa ganin an zo da shi ba” “wallahi kuwa Ni haushi yake bani daga shi har amaryar tasa mai zubin karuwai. Wallahi haƙƙin Madina da ɗiyarta kaɗai ya ishe shi, da sannu zai fahimci hakan tun anan duniya. “Allah zai saka musu kam” “Ammah Ni ina da wata shawara fah, ko za'a gwada ISLAMIC medicine me?" “shawara Mai kyau sai mu gwada ai.” Tun da aka fara ISLAMIC medicine ta ɗan fara samun sauƙi, sai dai yanzu ta fara wasu irin surutai musamman ina tana bacci. Wani lokacin Zahrah sai dai ta zauna tayi ta sharar kukan ta daga ƙarshe ta ɗaura da yiwa Mamah addu'a. Yau da safe Zahrah na zaune gefen Mamah yayin da take bacci kawai taji Muryar Mamah na magana. “Tabbas na riga na cuci rayuwa ta da na gudu na bar dangi na wanda bana jin har abada zan ƙara ganin su, Alhaji Baba da kuma Hajjaty ina roƙon ku yafe min bana jin zan iso gare ku mutuwa zata riske ni.... Nan da nan jikin Mamah ya ji ƙera da zufa sai wani karkarwa take yi. Addu'a ta tofa mata nan da nan taci gaba da bacci ta. “Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari game da rayuwar Mamah na, ya Ubangiji kafi kowa sanin ɓoyayyen al'amari da kuma bayyananne, ya Rabb! Ka bawa mahaifiya ta lafiya ka kuma bani ikon haɗa ta da dangin ta” ta ƙarasa hawaye na zubowa daga idanuwan ta. Kwanci tashi asarar mai rai Mamah ta shafe wata guda tana jinyar da aka gagara gano wace iri ce, a lokacin kuma baba amarya ta fara shiga tana gaishe ta kullum. Ita dai Zahrah bata kawo komai a ranta ba don yanzu babu laifi suna gaisuwar mutunci da BABA AMARYA ɗin. Ana cikin haka result ɗin su ya fito, a ranar kuwa suka dukufa zuwa school bisa tursasawar Ammi. “Zahrah ki tashi kije ki shirya a can tare da Badi'a kuje school za'a buɗe muku result” cikin fuskar dake bayyana tsantsar damuwa tace “Ammi don Allah ki barni na zauna a nan tare da Mamah, Badi'a sai ta duba min" “Aah Zahrah tashi zaki yi ku tafi, ina nan zan kuka da mamah” Babu yadda ya iya ta wuce gidan Ammi a can suka shirya suka shiga adaidaita saboda Abba ya tafi Kaduna. Suna isa ganin classmates ɗin su Zahrah ta ɗan ware, ihun murna suka yi da suka hango Zahrah da Badi'a. Da gudu suka rungume su tamkar zasu faɗi ƙasa. Murya uncle Hashim me ta dakatar da su “Hey! Are You alright?” waskewa suka yi suka ce “yes sir” Yace “Alright You guys should FOLLOW me to the computer library so that your results will be checked” Yana tafe suna bin bayan shi har suka iso. Ɗaya bayan ɗaya ake dubawa kuma Alhamdulillah duk duk sun samu abun da ake so na tafiya senior class. Badi'a ce second to the last, Tana fitowa tayi hugging Zahrah “best frightful and colourful result” Tsalle Zahrah tayi “Alhamdulillah, bari na dubo nawa ki jira ni” Kamar yadda Badi'a ta fito da gudu haka Zahrah ta fito da gudu “Awful and marvelous result" Farin ciki tamkar su yi yaya. ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣1️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Bayan an duba wa kowa PC ya haɗa musu assembly. “Good day to you all our graduating junior students, you indeed deserved to be honored because you all perform well an fantastic.” Tap tap tap sukafara tafi “The most amazing part of your success is that three students from this school were honored with money 💰.” Tap tap tap “I'll like to see Mayam Muhammad on the stage” M² ta fito a natse, “the state's board of junior secondary School examination awarded 100k to you for your wonderful performance and this school specifically honored you scholarship in to the senior class.” Nan da nan ihu ya kacame sai tafi Tap tap tap A hankali ta koma tana murmushi. “Badi'ah Kabir Umar, shi also perform wonderfully in this exams the board awarded 300k to you, congratulations Badi'a, and to you also the school management awarded a scholarship to you in to the senior class” Ihu ta ka ina da ƙyar suka yi shiru. “The champion, Zahrah Abdulkarim Kuru being the overall best student to write this JSSE in this state at large was awarded the sum total of 500k and sane, management of the school awarded a scholarship to you" Murna ta ko ina sai da PC ya tsawatar musu suka yi shiru. “Congratulations to you all, I hope you'll improve and do better next, Maryam, Badi'a, Zahrah see me in my office" Daga haka kowa ya watse yana farin ciki bayan an raba musu admission letter nasu da deadline na registration ɗin. Zahrah tafi kowa yin farin ciki ko babu komai Ubangiji ya kawo mata mafita. A office ɗin PC aka ɗauki pictures nasu aka ce su turo iyayen su gobe before a sallame su. Daga haka suka wuce. Abba, Mamah ammi duk sunyi farin ciki. Alhamdulillah jikin Mamah yayi sauƙi kwanan nan saboda amfani da magungunan ISLAMIC da take yi. Yayin da suka fara sabawa da baba amarya. Da yake babu registration bana, on their resumption day sassafe suka fice don yanzu Abba ya samar masu driver da zai ke kula da zuwan su da komawar su. Direct old ss1 suka nufa. Around 7:30 kuwa sauran students suka fara zuwa, da yawa sun dawo ammah wasu sun sauya school ne wasu kuma barin gari zasu yi. Bayan anyi assembly Uncle John who's the only Christian cikin staff ɗin su ya fara shigowa. “good morning sir” “morning, sit down” Bayan sun zauna ya fara yi musu bayani cikin harshen turanci. “Ina yi muku Barka da shiga ajin senior. Fatan zaku ƙara maida hankula ku ga karatun ku. Shi wannan aji da kuke gani na senior mataki ne daga cikin matakan rayuwa, idan kika tafka kuskure cikin sa yana iya wargaza ƙaddarar rayuwar ki. Saboda haka ku nutsu ku san MEH kuke yi” Nan ya ci gaba da bayani wanda a fakaice career guidance ya Basu. Cike da zumuɗi da farin ciki bayan ficewar Uncle John suka fara magana. Zainab Sani tace “Ni fah da kuke gani tun ba yau ba na riga na ware abun da zan karanta nan gaba. A rayuwa ta ina matuƙar ƙaunar yadda Nurses ke kula da maras lafiya. The way they show their concern, care and love to their patients drove me to like the profession” Idanuwan su suka zuba mata yayin da ta ci gaba da bayani. “kun san MEH, yadda suke salwantar da lokacin su don kula da patients, Baku gani doctors zuwa kawai suke na wani lokaci su tafi, ammah Nurses suna yin 8hrs suna kula da patients da zarar wata ta tafi wata zata zo saboda kada abar patient a haka. Da wannan profession ɗin zaki samu lada da yawa, sai ki samu aljanna sanadiyyar su” Kowa ya gamsu da bayanin Zainab. Ɗan gyara zama Zahrah tayi tace “Babban buri na a duniya bai wuce na zama cikakkiyar alƙaki wato judge mai cikakken iko ba. Ina so naga ko yaya mai laifi yake an hukunta shi. Akwai wani babban rabo a rayuwa ta da yasa nake don ganin duk mai laifi ya karɓi hukunci daidai da laifin shi.” Shiru kowa yayi yana nazarin Zahrah. Sun daɗe suna ta maganganu game da career nasu. Har lokacin tashi yayi Duk malamin da ya shigo maganar da yake yi musu kenan tare da basu shawarari kan yadda zasu yi karatun su successfully. Bayan Zahrah ta koma gida ta tarar da jikin Mamah babu daɗi. Ina banda kuka babu abun da take yi tana roƙon Ubangiji da ya bawa Mamah lafiya. “mamah tah! Ke kaɗai ke gare ni bayan Allah. Don Allah Mamah na ki tashi ko kaɗan bana son rasa ki.” Cikin bacci taji kukan Zahrah ita ma lokaci ɗaya hankalin ta ya tashi. Cikin Muryar ciwo ta kamo hannun Zahrah “Ɗiya ta! Ki sani kowanne rai sai ya ɗanɗani mutuwa, dole ko ban mutu yanzu ba zan mutu nan gaba. Addu'ar ki kawai nake buƙata Zahrah! Ke kaɗai Allah ya bani kuma ina da burin zuwa ga ahali na sai dai na kasa. Amma ke bazan so ki ci gaba da rayuwa tare da wannan maras imanin ba ko da kuwa bayan raina ne. Yanzu ki tashi ki shirya ki tafi islamiyya" Maganganun Mamah sunyi matuƙar tasiri a zuciyar Zahrah, gyara mata shimfiɗa tayi ta zuba abinci a plate sannan tayi feeding Mamah. Sai da ta bata ruwa ta tabbatar ya tsirga kafin ta kwantar da ita. A gaggauce ta samu ta shirya gashi lokaci ya kusa ƙurewa. Sallama tayi wa Mamah ta wuce gidan Ammi. Ammi kaɗai ta tarar a parlourn zaune tana kallo. Da sallama ta shiga sannan ta zauna jikin ƙafar Ammin. Cikin Muryar ta mai sanyi tace “Ammi ina yini” Murmushi Ammi tayi tana yabawa da nutsuwa irin ta Zahrah wacce lokaci ɗaya ta zo ba tare da tsammani ba tamkar wahayi. “lafiya lau zahran Mamah, ya jikin mamah” “da sauƙi” “toh Allah ya ƙara sauƙi, Badi'a Badi'a ki fito manah tun ɗazu Zahrah ke famar jiranki” Daga room ɗin ta ta ce “sorry zahrahty gani nan zuwa” Bayan Badi'a ta zo suka wuce islamiyya. Yau gabaɗaya Ustaz ya kasa fahimtar Zahrah, fuskar ta ɗauke take da zunzurutun damuwa. Zuwan ma kawai tayi ne ba wai ɗin taso ba. Gani take kamar ina ta bar Mamah mutuwa zata zo ta ɗauke ta. “Zahrah! Zahrah!! Zahrah” bakin shi uku ammah bata amsa ba. Babu alamun ma ta san MEH ake ko a Ina take. Badi'a na taɓa ta ta zabura sai wani zare ido take yi. “zahrah baki da lafiya ne yau gabaɗaya hankalin ki baya kan aji. Baki na yafi uku ammah baki san ina yi ba" Cike da basarwa ta ce “lafiya ƙalau Ustaz kawai tunani ne yayi min yawa.” “Zahrah tunani meh kike yi haka ƴar ƙarama da ke da zai sa ki shiga irin wannan yanayin?” Bata yi tsammanin jin irin wannan tambayar ba daga Ustaz shiyasa kawai tace tunani take yi. Murmushin da iyakar shi fuska ne tayi sannan tace “laaaaa Ustaz ba fah wani tunani nake yi ba kawai duniyar ne ban jin daɗin ta” “toh Allah ya sauqaqa Zahrah ammah ki rage tunani” daga haka ya wuce. Badi'a dake nazartar ƙawar ta tunda suka fito daga gida gashi yanzu fararen idanuwan ta sun yi jazur da su. “Zahrah, gaba ɗaya yau tunda muka fito nake nazartar ki, anything wrong?” “just nothing” ƙura mata ido Badi'a tayi kafin tace “ƙarya kike Zahrah akwai, kawai dai ban kai matakin ki faɗa min baneh na gode” Ta faɗa cike da fushi. Kamo ta Zahrah tayi kafin tayi murmushi “yi haƙuri ƙawa tah, kin kai har kin wuce ki ji damuwa ta. Ba komai ke damu na ba in banda rashin lafiyar Mamah, yau da na dawo abun yayi worst, kin ga yadda Mamah ke shan wahala, Badi'a bazan iya jurewa ba bazan iya jurar ganin Mamah a haka ba” Ta faɗa ƙwalla na zubowa daga cikin idanun ta. Cikin sigar rarrashi Badi'a tace “Zahrah ke musulma ce kuma kinyi imani da Allah da sauran rukunai na imani?” Gyaɗa kai Zahrah tayi don kuwa maganar ma kawai tana yin ta ne ba don tana so ba. “kin sani kowanne bawa da kalar tashi ƙaddarar, khairan ta zo ko akasin haka dole ka rungume ta a matsayin ka na mai imani. Jinyar Mamah na daga cikin jarrabawar ku ke da ita, Zahrah addu'a kawai ita ce mafita, ki ƙara akan yadda kike yi nimah nan ina yi miki haka Ammi na da Abba na” Maganar Badi'a sun rage mata damuwar da take ji sosai. Murmushi Zahrah tayi ta riƙo hannun Badi'a “ƙawaye iri iri ne ammah tawa ƙawar ta musamman ce, ban san wani aiki mai kyau nayi Wa Ubangiji ba da ya azurta Ni da ke da kuma ahalin ki, duk wuya duk rintsi ina ƙaunar ki. Allah ya saka muku da alkhairi ke da Ammi da kuma Abba”. Ci gaba da tafiya suka yi hannun su riƙe da na juna kamar wanda aka yi attempting raba su. Sai da suka iso suka yi sallama kowa ta wuce gida. Tana komawa ta wanke uniform ɗin ta ta dawo gefen Mamah ta zauna. Mamah da ke bacci bata ma san Zahrah ta dawo ba. Ganin bacci take yasa zahah ɗauko Quran ɗin ta tana rerawa. Kamar daga sama taji tarin Mamah. Ajiye Quran ɗin tayi ta matso wajen ta tana shafa bayan ta. “Sannu Mamah na sannu, na kawo miki ruwa" Kai ta gyaɗa. Zahrah ta bata ruwa sannan ta ci gaba da karatun ta. Lokaci ɗaya kuma tayi shiru yayinda ta faɗa duniyar tunani. “Kawu ko sau ɗaya bai taɓa leƙowa don duba jikin mamah ba talkless of yace zai kai ta asibiti. Anya kuwa Kawu mijin Mamah ne?, Toh idan mijin ta ne ma ba na tunanin auren soyayya suka yi. Dubi rayuwa ta fah! Shin ko don Ni ƴar yarinya Mamah ta cancanci kyautatawa daga Kawu idan ma ace tayi masa wani laifi ne a da. Allah Sarki Mamah nah, in Sha Allah Ni zan zama gatan ki, zan kula dake har lokacin da zaki samu lafiya zan kuma ƙwata mana ƴancin mu da zarar na samu damar hakan. Bani da burin da ya wuce na zama cikakkiyar alƙali, Kawu sai na karɓawa mahaifiya ta haƙƙin ta daga wurin mutumin da tunda na tashi ban taɓa ganin ya yi mata alkhairi ba kullum cikin musguna mata yake. Ina son haɗuwa da ahalin Mamah sannan ina son haɗuwar ta da ahalin ta, nasan su ma zasu yi farin ciki” “nayi alƙawari Mamah nah kinda kuwa haɗa ki da ahalin ki shine abu na ƙarshe da zan yi tabbas zan so cimma shi” Ganin tunanin babu yadda zai kai ta gashi maghrib ta gabato. Tashi tayi ta matso kusan Mamah, Ɗan taɓa ta tayi a hankali, “mamah lokacin sallah yayi, bari na kawo miki baho kiyi alwalar, ina zaki iya?” Ɗaukowa baho tayi da ruwa tayi wa Mamah alwala daga nan ta sanya mata hijab a jikin ta ta juyar da ita ta fuskanci alƙibla sannan tace. “kiyi sallar mamah” duk da raɗaɗin jinya hakan bai sa ta yin farin ciki ba, wai yau Zahrah da kanta take cewa tayi sallah, Zahrah da bata don sallah a da. Alhamdulillah. Ita ma alwalar tayi tayi sallar ta ta roƙi Allah ya bawa Mamah lafiya. Sauran masa da miyar rana ta ɗauko taci bayan yaci ta ɗauko Quran ɗin ta taci gaba da koyon hadda. Haddar ta ta koya tana gamawa ta rufe Quran ɗin ta ɗanyi addu'oin ta waɗanda yawanci roƙawa mamah lafiya take wurin Ubangiji. Lokacin ishà ma da kanta ta taimaka wa Mamah tayi sannan ita ma tayi. Tana idarwa taji sallamar Ammi da kuma Badi'a,amsa musu tayi cikin sassanyar muryar ta. “Wa alykumussalam, Ammi sannu da zuwa” “yauwah sannu Zahrah” “ku zauna manah,” Zama Ammi tayi bakin bed ɗin kusa da Mamah. Cike da kulawa tace “ys jikin madinar?” “da sauƙi ammi” “Zahrahty ya jikin Mamah? Badi'a ta faɗa fuskar ta ɗauke da damuwa. “da sauƙi Alhamdulillah” “Allah ya ƙara sauƙi” “zahraj tashi ki ɗan zuba mata abincin nan ta ɗan ci ko kaɗan ne ko ta samu ƙarfin jiki” Ammi ta faɗa tana nuna mata basket ɗin da Badi'a ta ajiye gefen ta. “Ammi ai bata iya cin abincin, ɗazu ma ƙin ci tayi sai Ni na cinye shi da na dawo” ta faɗa tamkar zata yi kuka. Shikenan zubo ki miƙo Ni zan bata la'alla taci. Zahrah ta zuba abinci ta kawo kusan Ammi ta ajiye, a hankali Ammi ta ɗan taɓa mamar.. “madinah ya ƙarfin jikin?” Da ƙyar ta amsa “da sauki” “toh Allah ya ƙara sauƙi, ga abinci ki ɗan tashi ki ci ko zaki ji ƙarfin jikin ki” Ta faɗa tare da ɗago mamahn. A hankali take feeding ɗin ta, wani abun har da yunwa ta ɗan ci da ɗan yawa kafin ta janye kanta gefe alamun ta ƙoshi. Bata kwantar da ita ba sai da ta tabbatar abincin ya tsarga. A nan suka zauna har 10:00pm suka wuce. Damuwa ta taru tayi wa Zahrah yawa, da ƙyar bacci ya ɗauke ta bayan ta rufo musu ɗakin da addu'a. ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣2️⃣ Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘 SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Kamar daga sama ta jiyo Muryar Mamah na ƙiran sunan ta. “Zahrah, Zahrah zahrah” ta faɗa tana lalumowa ko zata ji ta. A firgice ta tashi jin kamar mafarki take. “mamah” ta matso daga da Mamah dake zaune, “kunna haske” cike da mamaki take kallon Mamah. “mamah ke kike magana haka, Alhamdulillah Alhamdulillah” Rufe mata baki tayi sannan ta fara magana ƙasa ƙasa yadda babu wadda zai ji su “ki kunna haske, zan nuna miki abu ne” Lalumowa hasken tayi ta kunna sannan ta zuba wa Mamah ido. Da ƙyar ta miƙe ta nufi wata ƴar adakar ƙarfe dake ɗakin, ɗan murɗa wasu abu dake jiki kamar zobe tayi sannan adakar ta buɗe. Wata haka da ta sha ƙura ta gani ta ɗauko sannan ta rufe adakar. A hankali take takowa dan kuwa ba wani ƙarfin jikin ta take ji ba. Zahrah da mamaki yayi kusan kashe ta ga wani tsoro da ya shige ta lokaci ɗaya. Ta ma rasa wane irin tunani zata yi. Ta tuna taji ana cewa idan mutum yan jinyar ajali toh yakan samu sauƙi daf da mutuwar shi. Saurin kawar da wannan tunani tayi jin an dafa kafaɗarta. “Zahrah!", Ta ambaci sunan cikin raunananniyar murya yayin da Zahrah ta kasa amsawa sai ma wani firgici da ya mamaye ta. “Zahrah! Ke kaɗai Allah ya bani, kuma bana so ki ci gaba da wannan rayuwar idan aka ce babu Ni. Ina ji a jiki na bazan yi tsawon rai ba, sai dai yanzu naji wani ƙarin guiwa na tunkarar ki da batun ahali na. Tun ba yau ba kina tunkara ta da maganar ina basarwa saboda yadda nake jin wani mololo ya tare min zuciya da zarar an yi min tambayar. Yau bana jin abun shiyasa nake don sanar da ke Ni wacece, ban ce ki ci gaba da zama cikin gidan nan ba saboda babu rayuwa mai daɗi cikin shi. Ina da rai ma baki samun kulawa daga wajen kowa sai Ni yin idan babu Ni ban san ya zaki ji ba. Ammah a matsayi na na mahaifiyar ki kuma mai ƙaunar ki,ko da bayan raina ne bazan zo ki bar cikin gidan nan ba saboda shi ɗin tamkar gidan mahaifin ki yake. Ammah idan kika ji ba zaki iya ba ko kin takura da hakan, ko kuma anci gaba da tauye hakkin ki toh ki nemi ahali na. Wannan jakar da kike gani mallaki na ne kuma ita ce motar da zata sada ki da dangi na, zan damƙa ta a hannun ki da zarar na sanar da ke labari na, kuma zan so ki adana ta kamar yadda nima na adana ta.” Ɗan dakata wa Mamah tayi da bayanin tare da ƙanƙame hannun Zahrah cikin nata yayin da hawaye ke zubowa daga cikin idanun ta, ga kuma alamun gajiyawa a tare da ita. Ganin hakan yasa Zahrah share nata hawayen. Cikin ranta kuwa tunani take “kamata yayi ace nayi farin ciki da wannan daren, kamata yayi ace naji murnar da ban taɓa ji ba a wannan daren saboda tsantsar tarihin da zai buga cikin rayuwa ta. Daren da zan samu abun da na daɗe ina fatan samu tun ina ƴar ƙarama ta, abun da tambayar da ke sa mahaifiya ta tayi fushi da ni gashi kuma zata bani shi a yau. Ammah meh yasa Ni bana jin naji wannan labari da na daɗe ina son ji?, Labarin da zai kasance makullin baƙin ciki na?” “Tabbas ina don sanin tarihin ki Mamah, ina son sani idan nace bana so toh nayi ƙarya. Ammah Mamah ba a irin wannan lokacin ba. Ina don ki sanar da Ni labarin ki ne a lokacin da in naji zanyi farin ciki, a yanzu baki da lafiya kuma bamu da kowa sai Allah, sai kuma bayin sa Ammi da Abba da ya aiko cikin rayuwar mu. Zan so ki Dakata da faɗin labarin nan zuwa wani lokaci” Itama Mamah ɓangaren ta tunani kawai take yi game da rayuwar ta, yarintar ta, tasawar ta i zuwa auren ta da masoyin ta Abdulkarim Kuru. Haihuwar ɗiyar ta Zahrah, da mutuwar ba zata da mijin ta yayi, auren ta da Kawu da kuma irin baƙar izayar da ya gasa mata ita da yarinyar ta. Shiru shiru babu wanda yayi magana cikin su, Mamah na jiran amsa daga ZAHRAH kan ta fara bata labari yayin da Zahrah ta kurma cikin duniyar tunani. Mamah da ta gaji da zama ne ta ɗan kishingiɗa, hannun ta dake cikin na Zahrah ne ya zame wannan shine dalilin farkawar su duka biyun daga duniyar da suka faɗa ta tunani. Bubbuga ƙofar da suka daɗe basu ji anyi ba ya sa suka miƙe tsaye a tare. Har Mamah ta miƙe zata buɗe ƙofar Zahrah tayi saurin dakatar da ita. “aah Mamah, na san bai wuce Kawu baneh kuma ba zaki buɗe masa ba" bata yi mamakin jin maganar Zahrah ba hakan yasa ta zauna bakin bed Babu musu. Jikin ƙafar ta Zahrah ta zauna tare da kwantar da kan ta kan cinyar Mamah. A hankali ta ɗago ta kalli idon Mamah sannan ta kawar da nata gefe. “mamah ba haka kawai yasa na tsani Kawu ba sai don rashin nuna ƙaunar shi gare ki a matsayin ki ta iyalin shi. Ba ma wannan ba tunda kika kwanta bai taɓa tako ƙafar sa don ya duba jikin ki ba balle yace yau a kai ki asibiti ko ya karɓi takardar magani yace zai siyo ba bayan kuma Ni da kaina na sanar da shi baki da lafiya.” Tabbas abun da Zahrah ta faɗa bata ga laifin ta ba ko kaɗan at least ya kamata ko sau ɗaya ace ya zo ya duba ta ɗin. Gyangyaɗin da Zahrah ta fara ne yasa Mamah cewa ta dawo su kwanta gobe da kammala maganar su. Ba musu Zahrah ta kwanta jikin Mamah nan da nan bacci mai daɗi yayi awun gaba da su. Safiya ta gari. Ba su suka tashi ba sai da gari ya fara wayewa Mamah ce ta fara tashi ɗauke da addu'ah a bakin ta. A hankali ta sauƙo ta fita, ɗan watsa ruwa tayi a jikin ta ta haɗo da alwala sannan ta yi sallah. Bayan ta isar da Sallah ta yi azkar ɗin ta. Miƙewa tayi don tashin Zahrah tayi arba da jakar nan, a kasalance ta ɗauke ta ta jefa ta cikin wardrobe ɗin kayan ta dake sama can. Bayan ta tashi Zahrah ta ɗan fara kaɗe ɗakin. Tana yin Sallah ta gaida Mamah “ina kwana mamah” “lafiya zahrah” “ya kwanan jikin?" “Alhamdulillah, yi maza ki tashi kiyi wanka kada ki makara" “toh" tace tana miƙewa, ninke sallayar tayi sannan taje tayo wanka. Uniform ɗin ta ta manta ba'a goge yake ba, a hanzarce ta shiga gidan Ammi ta goge lokacin Badi'ah ta tashi. Sanya uniform ɗin ta tayi tana gamawa Mamah ta zubo mata jallof ɗin taliyar da ta musu, ita dai Zahrah mamaki take don rabin ta da cin girkin Mamah tun kwanaki basu fi biyu ba bayan kwantar da ita da aka yi a asibiti yau kuma ta tsiro girki. Bayan ta ci abincin tana santi ta wanko hannun ta tayi brush daga nan ta zari school bag ɗin ta da kuma hijab ta zura ta fito. A bakin ƙofa suka ci karo da Badi'a ita ma ta shirya tsab” “har kin shirya kenan, bari na miƙa wa Mamah sai mu wuce" ba tare da ta amsa mata ba tayi waje. Tana miƙa wa tayi wa Mamah ya jikin ta fito, driver ne ya kai su school sai dai yau Zahrah tamkar ba ita ba, tunani ya addabe ta. Babu abun da ya tsaya mata a rai irin hirar su ta jiya tare da Mamah. Hirar da ta tsaya mata cikin zuciyar ta. “meh Mamah take nufi kenan,idan na fahimta akwai ɓoyayyen al'amari dangane da ita, bana son rasa Mamah don ita ɗin numfashi na ne, ammah cikin maganganun ta na jiya naji zuciya ta na karye wa” Other heart ɗin ta tace “haba Zahrah, damah ai yanzu kam kin kai ki san tarihin mamar ki” “ƙwarai to ammah bana so rada ta ai” “duk da haka dai ya kamata ki saurare MEH Mamah zata sanar da ke, la'allah ƙarshen zaman ku da azzalumin kawun ki yayi” “ai kuwa dai, nimah na ga hakan” Haka tayi ta magana da zuciyar ta har uncle Hashim ya shigo. Dukkan students suka miƙe suna gaida shi, sai dai Zahrah hankalin ta baya ma ajin, bata san wainar da ake toyawa ba. Bai yi mata magana ba ya basu umarnin zama, har ya fara clsss ɗin bata san MEH ake ba sai da Badi'a ta buge ta. Firgita ta waro ido tana kallon Badi'a. “ke wai tunanin meh kike yi ne?” “banu komai” Ƙasa ƙasa ta harare ta tace “kina nan kina tunani har uncle Hashim ya shigo kina zauna muka gaida shi kuma kice ba tunanin komai kike yi ba?, U better concentrate” daga haka ta zunguri ƙeyar ta. Daf da lokacin closing PC ya sa aka kira Maryam, Badi'a da kumah Zahrah zuwa staff room. “ba komai ne ya sa na kira ki ba sai don na sanar da ku cewa yanzu ba sai anjima ba zaku tafi Jos zaku yi representing school ɗin nan a wani programs so nayi magana da iyayen ku akan tafiyar. Yanzu ku ɗauko school Bags ɗin ku ku ajiye su a nan. Tare zaku tafi da Academic officer da kuma Hashim. Please Behave well” Suka haɗa baki suka ce “ohk sir” Ɗauko bags ɗin su suka yi suka ajiye. Lokacin Academic officer ya ce su fito. Abun mamaki PC ya tsayar da su. “ku zo” Zuwa suka yi ya miƙa musu sabbin uniform da gani goge su aka yi saboda ɗumin dake jiki. “ku tafi da wannan, ina zaku tafi wajen sai ku sanya.” Bayan sun amsa suka koma daga nan motar su ta tashi sai Jos. RACAS FOUNDATION COLLEGE, old airport jos, plateau suka nufa. Ɗan zagayawa A. Officer yayi da su sannan suka koma zuwa destination da aka basu don sai da safe za'a yi competition ɗin. Abinci mai rai da lafiya yayi order, bags uku ya aiki musu suma suka ɗauki two bags. Bayan sun ci abinci sun kora da drink suka yi sallah. Hutawa suka kwanta suka yi, ba su suka tashi ba sai 4:12pm, suna tashi suka watsa ruwa suka maida kayan su sannan suka yi sallah. Knocking door ɗin aka yi, Badi'a ta buɗe, Academic officer ne yace su zo. Wani ɗan cool down area suka samu suka zauna. Yayi musu bayani akan programs ɗin da kuma wanda kowa zai yi participating. Daga nan ya ƙara haska musu hanya tare da taimakon uncle Hashim, bayan an kwatanta wa kowa nashi A. Officer ya ce “ toh bari a gwada kowa Muga yadda zai yi” Maryam zata yi representing school ɗin ne a junior spelling challenge and pronounciation yayin da Badi'a zata yi essay writing sai kuma Zahrah impromptu speech. Marya aka fara gwada wa and Alhamdulillah she's done it well. Tayi da kyau har sun saka rai kan spelling challenge nasu.. Badi'a ma ya bata piece of paper sannan ya bata topics. Within short period of time ta kammala, he's impressed by the way she answer the question, ita ma aka dasa alamun nasara a tattare da ita. When it turns to Zahrah, a topic is given to her also, and tayi yadda ya kamata, her confidence, gentleness, the way she speaks like she's from Elizabeth's palace. Bayan sun kammala ya ƙara gyara musu kowa aka faɗa nata corrections nata, and they all master it. Da yake lokacin sallah ya gabato kai tsaye komawa suka yi suka yi alwala suka yi sallah. After they prayed suka ce su gwada playing Qur'anic trick, Zaki janyo ayah sai ki zaɓi ɗaya cikin su ta faɗi wani surah take, idan ta canka daidai sai ta karanto cigaban. Haka suka yi tayi har lokacin ishà. Alwala suka yi suka watso ruwa sannan suka jona sallah, suna idarwa bayan azkar suka Fara hirarrakin su. Few minutes da fara hirarrakin su aka yi nocking, abincin su aka kawo musu sai lokacin duka tuna a na rana da aka kawo akwai extra bag da basu taɓa ba. Ɗauko ta suka yi kads ayi asara suka fara cin ta. Bayan sun ci suka buɗe Bags ɗin daren, chips ne sai egg sauce da kuma milk drink. Bayan sun cinye tas suka ci gaba da hirar su. Ba su suka kwanta ba sai around 10:00pm. Safiya mai albarka marvelous squad. Cikin baccin ta tayi mafarkin Mamah. Sai ga ta nan kusa da ita suna wata magana, bayan sun gama maganar sai Mamah ta damƙa mata wata haka wacce bata san ta miye ba tare da gargaɗin ta kada ta buɗe ta kwana kusa. Bayan ta karɓa sai Mamah ta ɓace ɓat, tana ɓacewa sai Zahrah ta fara kuka tana neman taimako, wai sai ga baba amarya ta fito tana sheƙa mata dariya can kuma ta ɓata rai. A zabure ta miƙe gani gari har ya waye. Ɗaya bayan ɗaya ta tayar da su suka yi sallah, sannan kowacce ta shiga tayi wanka. Suna fitowa suka shafa cream ɗin da suka ga ajiye gaban dressing mirror dake room ɗin. Around 7:00am aka kawo breakfast, suna ci suka yi brush suka fara Sanya uniform saboda za'a fara program ɗin ne by 9:00am and suna so su je da wuri. “Zahrah wannan kam daidai ɗin ki ne ke zaku saka” Badi'a ta faɗa tana miƙo mata wata bujen riga. Zumɓura baki tayi ta harare ta. “u're out of your mind actually Ni zan saka wannan burgujejiyar rigar?” Gira Maryam ta ɗaga mata wanda yasa ta cilla mata ita. “ke maryam ke ce uwar mata cikin mu ke zaki saka ta” “wannan rigar nimah bazan saka ta ba sai dai na mayar da tsohuwa ta” Dariya suka kwashe da ita sannan Badi'a ta tsagaita ta ce “wa yaga new plus old which is equivalent to mark reduction” ta ci gaba da dariyar ta. Maryam ta ƙulu iya ƙuluwa kafin tace “shikenan na haƙura zan sa ammah dai kun min wayo ne. Gwalo Zahrah tayi mata sannan tace “don't wear it if u like Mamah baby😂” Jin sunan da Zahrah ta ƙura ta yasa ta wulla rigar. Suna cikin haka aka yi knocking su a guje Maryam ta janyo rigar ta saka tana hararar Zahrah yayin da Zahrah ke tayi mata dariya. “if u're ready we can go” A nutse suka fito suka bi bayan shi zuwa motar su. Daga nan motar su ta lula sai RUCHAS FOUNDATION COLLEGE. TOH, MU KASANCE GOBE DA KU DON JIN WACECE MAMAH DA KUMA DALILIN ZAMAN TA TARE DA KAWU? ME KUKE TUNANI ZAHRAH ZATA YI BAYAN SANIN ASALIN MAMAH SHIN ZASU CI COMPETITION ƊIN NE KO KUWA? DUK CIKIN LITTAFIN BABBAN GIDA KU CI GABA DA SAMBAƊO MIN COMMENTS REMEMBER FILIN BADA SHAWARA DA KARƁAR ƘORAFI A BUƊE YAKE ITZ DIAMOND LADY 💎 Oum Zainab ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣3️⃣ kada ku mance gabaɗaya littafin sadaukarwa ne gare ku AISHATU USMAN (Baby Unah) sai dai gashi sai ranar da pages ɗin nake ba tare da sanin ki ba ammah na san ke ɗin mai fahimta ce ai... Haka wannan shafin ma dai sadaukarwa ne gare ku A'ISHAH MB (Baby Isha) marubuciyar littafin Rayuwa da macijiya Pinky darling marubuciyar littafin SO FAIZA ALMUSTAPHA (Fa'eeh BG) marubuciyar littafin a mafarki na santa. I guys mean a lot to me, so much love u....Allah ya ƙara muku hazaƙa da zaƙin hannu. SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Suna isa suka yi parking motar su. A lokacin ba'a wani zo da yawa ba saboda sai 9:00am za'a fara. A nutse suka shiga cikin ƙatoton ball ɗin da aka jere shi da kujeru fiye da dubu biyu. High table already well set kawai mutanen ake jira. Front seat suka samu suka zauna duk da cewa wurin is meant specifically for audience, suka ci gaba da gwada yadda zasu yi har aka fara zuwa. The first person to come wani Black timid balded man ya zo wurin su bayan sun gaida shi ya amsa sannan ya tambaye su su waye su. Cikin nutsuwa Maryam tayi mishi bayanin cewa sun zo representing school nasu ne, ya tambayi wani school suka faɗa mishi nan ya rubuta a paper dake hannun shi daga nan yace su tashi nan wurin isa not meant for them, bayan shi suka bi ya nuna musu wurin da aka wani don participants a nan suka zauna. Tun daga lokacin aka fara zuwa, people from various schools da wasu ma ba a Jos ɗin suke ba, baƙi duk suna ta zuwa kowa sai wuri yake samu Abun ku da Nigeria iyayen african time sai wajen 9:15am aka daina shigowa alamun kowa ya kammala zuwa. Ba tare da ɓata lokaci ba MC ya fara gabatar da programs ɗin da za'a yi tare da welcoming address na manyan baƙi da kuma shuwagabannin taron. Everything is well set so ba a ɓsta lokaci ba aka fara. Schools fiye da hamsin ne suka halarci taron, aka fara da Spelling challenge and pronounciation. Ɗaya bayan ɗaya aka ƙira partipants na kowanne school suka samu wurin da aka tanada don shi wannan program ɗin. Bayan sanar da su cewa duk wanda ya zaɓa number, bayan yayi spelling ba daidai ba za'a yi withdrawing nashi daga masu participating. First round aka cire 39 schools second round baa cire kowa ba, third round aka cire 20 schools sai kuma fourth round aka cire 15 schools ya rage saura 5 partipants representing 5 schools. Da ƙyar aka cire biyu aka bar biyu, Maryam kaɗai sai wata Christian suka rage, sun fafsta sosai kafin daga ƙarshe aka cire wannan ɗayar.....Nan da nan aka saka tafi raf raf su Academic officer da uncle Hashim Baki har kunne student ɗin su won the Trump. Sara ɗin ta na da ta koma ta zauna kusa da sauran ƴan uwanta, ba'a wani ɓata lokaci ba aka shiga essay writing, Abu da rubutu time kawai aka basu daga nan aka basu question papers. Within an hour suka kammala kowa yayi submitting, Babu wanda ya San Mai nasara a wannan ammah kowa na fatan kasancewa mai nasara. Daga nan kuma Badi'a ma ta dawo wurin ta. Hayaniyar da aka fara ne yasa mu ya roƙi mutane da suyi shiru, bayan an yi shiru tamkar babu kowa aka yi introducing last program Wanda duka ya fi tsayi a ciki, sai dai za'a iya ɗaukar four good hours tukunna a kammala. Shima aka kira partipants ɗin suka fito. Bayan sun fito aka faɗa musu dokokin su da kuma Marks awarded to each step. Successfully aka fara kuma duk Waɗanda suka yi they performed well. Mutum 20 ne suka yi daga nan aka tsayar da taron aka je break na 2hours. Sallah suka yi a wani nearest mosque sannan suka samu wuri suka zauna, suna zaune uncle Hashim ya kawo musu abinci, a wurin suka ci sannan suka koma hall ɗin lokacin kuwa babu kowa a ciki. Bayan cikar lokacin mutumin ɗazu wasu the first to enter, ya ƙara ɗaukar sunan school nasu. Bayan kowa ya dawo aka ci gaba da impromptu speech. Zahrah was second to the last to be in the stage. Cike da nutsuwar ta wacce mutane ke ganin kinibibi ne da kuma yanga sai dai haka abin yake a jikin ta ta wuce ta ɗauki paper ɗin ta miƙa kamar yadda sauran suke yi, abun magana aka miƙa mata a lokacin da ake karanta mata topic nata. Yana kammalawa ta juyo ta fuskanci shuwagabannin, a nutse cikin Muryar ta mai ɗaukar hankali tare da turancin ta wanda mutane da dama ke cewa kinibibi ne da ƙaryata ta fara gaida su mataki zuwa mataki har ta isa ga audience. Tafi ne kawai ke tashi a ball ɗin duk da cewa mutane da dama sunyi saidai wannan ya kasance daban, everything with her is unique, her approach, Grammer and pronounciation was different uwa uba kuma voice nata da take magana da shi cike da gayu da kuma ƙwarewa. Ci gaba da zubo turancin ta tayi wanda Ni reporter dai ban samu ikon haddacewa ba balle na karanto manah, Allah i know is tayi fiye da duk wanda suka yi, babu wanda zai ji bai yaba ba sai ɗan hassada. Abun mamaki sauran na baya basa concluding time ke cika ammah Zahrah sai da ta kammala komai gashi tayi bayani yadda ya kamata, tana gamawa kuma lokacin ta na cika. Hakan ba ƙaramin burge mutane yayi ba, babu wanda Zahrah bata tafi da imanin shi ba sai ɗan baƙin ciki. Gashi dai mostly ba Hausawa bane partipants ɗin kuma kamata yayi ace sun yi fiye da ita musamman da ya kasance ita ɗin ba ta samu Foundation mai kyau ba ammah duk ta wanke su. Mutum na ƙarshe na gamawa aka fita hutun rabin hour din cire sakamako da kuma haɗa gifts. Basu bar halal ɗin ba saboda babu wani abu da zasu yi in sun fita ɗin. Cold and chill drink aka miƙa musu daga malaman su suka sha abun su sannan suka fara ɗan hiran abun. “kai Zahrah, kin matuƙar ƙayatar fah, wallahi babu wanda ya kai ki yi, Ni har na baki winner na category naku” Hararar wasa tayi wa Maryam “kinji fah su chairlady of the occasion, sai ki ga kuma Ni da kike tsammani bana cikin masu nasarar.” Caraf Badi'a tace “Allah ma ya tsare ai kin basu a jikin su, ke kam Maryam naki ma a bayyane yake, nice dai cikin duhu" “nothing but succes from Allah in Sha Allah” Zahrah ta rufe musu baki da hakan. Bayan lokacin hutu ya ƙare still dai su kaɗan ne a hall ɗin sai lokacin aka fara shigowa, mutumin na ya ƙara ɗaukar sunan school nasu ya wuce. Within few minutes kowa ya dawo don jin sakamako. Ashe duk abun da ake an watsa shi duniya, ta channels da dama sun ɗaura live ne saboda yadda COMPETITION ɗin ya sanu, gashi ana samun kuɗi sosai in mutum yayi winning. Chairman na taron sai da yayi dogon bayani gamsasshe tukun ya bada space wa shugaban alƙalan COMPETITION ɗin. A natse ya fara magana,ya fara da gaisuwa da kuma ƙarfafawa partipants baki ɗaya guiwa kan cewa duk sun yi ƙoƙari. Daga nan ya fara faɗin result. Dummmmm gaban kowa ya faɗi saboda kowa zai so ace school nasu tayi nasara. “let's start with the first category, that is spelling challenge and pronounciation. The first and the winner of this category goes to ALMUNAUWARA ACADEMY Bauchi, in person of Maryam Aminullah. You can come forward and receive you gift. Bayan ta amso ta juya ya ƙara cewa miss Maryam in addition to the gift, Senator Umar Bukola awarded 100thousand Naira to you. You can have it now” A natse ta amso envelope ɗin ta juyo bayan pictures da aka ɗauka. “To the second category, the best essay writer of the year award goes to ALMUNAUWARA ACADEMY Bauchi, in person of Badi'a Kabir Umar. Here goes the best essay writer of the year from same school, congratulations ALMUNAUWARA ACADEMY. Your gift and award is here.” Itama har ta juya zata dawo yace “i'm not done with you Miss Badi'a, a another gift of 100thousand naira from sir Umar Bukola was added, come forward and get it" Bayan ta amsa ta dawo yayi shiru, sai bayan tafi da ihu ya kafa ya ci gaba. “A lady from Elizabeth's palace here won the yeae's impromptu speech with the required Marks without skipping any. You're indeed an angel Miss Zahrah Abdulkarim Kuru from the glorious ALMUNAUWARA ACADEMY Bauchi. This shows to us that ALMUNAUWARA ACADEMY promote and produce capacitive intelligent and amazing students, Zahrah Abdulkarim come forward” A nutse ta ƙarasa ta amshi aware ɗin da gift ɗin ta ta juyo. Muryar shi ce ta dakatar da ita “Miss Zahrah again received 100k cash from sir Umar Bukola, in addition to this members of the high table have the sum total of 200k for you miss Zahrah ” A nutse ta amso su ta dawo, ihu hali ɗin ya saka da ƙyar aka yi shiru Zahrah na dawowa seat ɗin ta tayi hugging colleagues nata kowa ya taya kowa murna daga nan shiru ya biyo baya. Ci gaba da magana yayi “Again we've the year's award to the glorious ALMUNAUWARA ACADEMY, participants from the school should come forward” Ƙyas ƙyas ƙaran camera kawai kake ji na tashi bayan sun amsa sun koma zaman su kenan aka ƙara ƙira.. “people of time, people that have respect for time, being the first to arrive to the hall, the first one resume after the first break and the last to resume after the last break. Your award and gift is ready, ALMUNAUWARA ACADEMY again won this award. Congratulations ALMUNAUWARA ACADEMY" Su uku suka amsa sannan suka dawo. Bayan sun dawo aka fara fita, da taimakon Academic officer da uncle Hashim suka kwashe gifts da award nasu zuwa mota daga nan kuma suka koma wurin da suke. Bayan sunyi sallah suka yi wanka suka ci abinci sannan suka ɗan huta. Sallar maghrib suka yi daga nan suka ƙara yasuwa saboda gajiya. Basu koma ba a ranar saboda haka bayan dinner suka kwanta. Early morning suka naushi motar su sai Bauchi. School suka fara isa, daga nan suka ajiye gifts da sauran abubuwa kowacce aka mayar da ita gida. Tana shiga ta tarar da Mamah tana zabga amai a ƙofar ɗakin da gani ma ta jigata da ƙyar take ƙaƙarin kana ganin ta ka ga gajiya da rauni . Da gudu ta rugo tana isowa gurin Mamah, duk wahalar da take ji lokaci ɗaya ta ɓace ɓat, rungume ta tayi ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. “mamah tun yaushe ne baki da lafiya” Cike da ƙarfin hali Mamah tace “taimaka na wanke baki na zamani koma ɗaki...” A hankali ta sake ta ta miƙe don ɗebo ruwan, tana kuskure bakin ta ta taimaka mata suka isa ɗaki... bisa gado ta kwantar da ita daga nan ta fito ta tsaftace wajen. Ganin basket ɗin gidan Ammi ya tabbatar mata da abinci aka aiko, tsakura tayi ta isa gefen Mamah, da ƙyar ta ɗan ci 3spoons sannan ta koma, ita ma ci tayi ta dawo gefen Mamah ta kwanta. Bata aune ba baccin gajiya yayi wuff da ita, cikin baccin ta ji mama ta ƙanƙame ta firgit ta farka ta juyo gare ta. “mamah kina son wani abu ne” “a'ah ta amsa tana kaɗa kanta. Daga nan suka ƙara kwanciya basu daɗe da kwantawar ba ta ƙara ƙanƙame ta. Wannan karon tana farka wa taji Muryar Mamah a kunnen ta. “tashi Zahrah zamu yi magana" da sauri Zahrah ta miƙe tana fuskantar Mamah “mamah menene kike don faɗi haka?” “zahrah bani da lokaci isasshe ya zama dole na sanar da ke Ni ɗin wacece saboda ina jin kamar ana ka na zaafita da Ni wajene. Bata kawo komai ranta ba tace “mamah babu abun da zai faru” “buɗe wardrobe ki hau kan kujera zaku ga jakar da na ɗauki daren ranar ki fito min da ita kinji?” Ba tare da ta amsa ba ta ɗauko jakar tana miƙowa Mamah. “aah Zahrah ki riƙe a hannun ki ban kuma amince ki buɗe ta ba har sai ranar da kika ji zama gidan kawun ki ya ishe ki ko kuma lokacin da wanin su yayi ƙoƙarin Cutar da rayuwar ki” ta ɗan yi shiru yayin da zuciyar Zahrah ta riga ta karye da bayanin Mamah. MU HAƊU GOBE, KADA KU MANCE COMMENTS ƊIN KU SHINE ƙWARIN GUIWA TA! INA ƘAUNAT KU SOSAI. ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣4️⃣ SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ FLASH BACK ABATCHA ESTATE ABUJA Tun daga titin da zai sada ka da ABATCHA ESTATE zaka tabbatar wa kanka wuri na musamman zaka dosa. Ga kuma wani ƙaton signboard da ke ɗauke da ABATCHA ESTATE make a roundabout. Wani makeken Black gare ne wanda tunda nake ban taɓa ganin irin shi ba ko da kuwa cikin manya manyan estates dake birnin Abuja. ABATCHA ESTATE kenan. Hamshaƙin ESTATE da in dai kana rayuwa cikin birnin Abuja ne toh ka sanshi sai dai ba kasafai zaka samu labarin wadda ya taɓa shigan shi. ESTATE ne da ya tsaru iya tsaruwa, an kashe kuɗi sosai wurin gina shi. Uwa uba ba kowa ake bari ya shiga ESTATE ɗin ba don kuwa hardly kaga wani bare ya je, sun keɓe kansu kuma ba sa mu'amala da Barr in ba larura ba, a cewar su iya su sun ishi kansu rayuwa. Wasu manya manyan guards ne wanda girman su kaɗai ka gani hankalin ka sai ya tashi, tsaye suke bakin gate ɗin fuskokinsu su tamkar ta shanu, babu fara'a ko kuma alamun ta. Ga wasu irin khaki da suka sanya mai colourn Blue. Da ƙyar na samu hanya don na shiga in ɗauko report. “masha Allah” Naira tayi kuka cikin wannan ESTATE, wani titi na ƙara miƙewa yayin da nayi arba da wani haɗaɗɗen mansion Wanda Kai tsaye zan iya cewa fada ce ta wani mai sarauta. ABATCHA ESTATE, Ainihin sunan mamallakin wannan ESTATE shine Mohammad Abatcha, haifaffen garin Birnin Gwari ne dake jihar Kaduna. Ammah asalin iyayen su Fulani ne na ƙasar Niger. Alhaji Kabir Abatcha da kuma matar shi Sa'adatu Fulani ne usul daga garin Birnin Gwari dake jahar Kaduna. Kiwo ita ce ainihin sana'ar su kuma sunyi auren zumunci ne da Sa'adatu.Bayan haihuwar ɗan su na fari wanda yaci sunan kakan da ABATCHA shine dalilin sayar da shanun su suka dawo cikin Kaduna da zama. Bayan tattaunawa ta musamman tsakanin su suka yanke shawarar fara sayar da babur da kuma keke. Alhamdulillah cikin ikon Allah Allah ya buɗa musu sosai sai dai tunda suka haifi ABATCHA Allah bai ƙara basu wani ɗan ba. ABATCHA ya taso ne ciki gata, kulawa ga uba soyayyar iyaye. Tun yana ƙarami Allah yayi masa farin jini da saboda tsantsar kyau da yake da shi irin na dukkanin asalin nan. Yayi karatun primary ɗin da ba kamar iyayen shi ba da suka yi iya karatun Allo. Bayan ya kammala secondary school ɗin shi kuma ya fara karatu a ATBU, mechanical engineering yayi saboda yana son ci gaba da kula da kasuwancin mahaifinsa wanda a yanzu ya bunƙasa sosai. A lokacin da yake karatun ne suka haɗu da Karima ɗiyar Abokin Baban sa ne wanda kasuwanci ya kai shi Kaduna. Duk da cewa iyayen sun so ya koma tushe ne yayi aure basu ƙi ba kasancewar mahaifin Karima aboki ne na kusa ga baban sa. Ba'a daɗe ba kuwa aka yi musu aure. Bayan auren su da watanni kaɗan Baffa ya damƙar da kasuwancin da hannun ɗan shi, a lokacin kuma suka koma Birnin Gwari da zama a cewar su zasu fi samun nutsuwa. Abun ka da zamani yayi wa kasuwancin sa register da “ABATCHA AUTOMOBILES”. Lokaci ƙalilan Allah ya sa albarka ciki kafin kace meh wuri ya sanu ga kuma uban ci gaba da aka samu. A lokacin ne kuma Hajjaty matar Alhaji Baba ta samu cikin farko zo kuga ɗauki wajen su da kuma iyayen su. Bayan wata tara ta haife ɗan ta mai suna Abubakar. Kyakkyawa da shi kamar mahaifinsa ga kuma farin jini da yaron ke da shi. Bayan shekara biyu da haihuwar shi ta ƙaro ɗanta mai suna Umar, daga nan Uthman sai kuma Aliyu wanda shine ƙarami cikin maza.Daga nan Hajjaty bata ƙara haihuwa ba. Dukkan yaran sun tashi cikin kulawa da kuma gata, ahali ya ginu gashi suna matuƙar jin daɗin rayuwar su. A lokacin da Aliyu yake Aji biyar na primary Alhaji Baba ya ƙara aure. Basu wani damu da auren shi ba kasancewar basu sanya damuwar wasu a ran su. Amarya Khadijatu bata yi dogon zango ba Allah yayi mata rasuwa. Babban ɗan ta Muhammad mai sunan Baffa sai ƙaramin Yusuf. Bayan haihuwar Yusuf ne Allah yayi mata rasuwa, to da yake lokacin ita ma Hajjaty cikin ta ya kusa haihuwa kawai aka yi inducing labour ta haife shi kafin lokacin. Wannan karon mace ta samu saboda irin farin cikin zuwan yarinyar suka saka mata suna Madina. Madina da Yusuf duka Hajjaty da kanta ta shayar da su cike da so da ƙauna. Madina ta ga gata fiye da kowa cikin gidan, gatar kuwa ta ko'ina tun daga wurin babban yayan su Abubakar har zuwa kan yayanta Yusuf ga kuma soyayyar iya duka kasancewar ta ƴaƴan ɗaya tilo da suke da. Madina tayi karatun Addini MASHA Allah haka boko ba'a barta a baya ba. Tun tana ƙaramar ta bata da ƙirininya da rashin ji irin na yara. Bayan ta gama secondary Yaya Abubakar ya samar mata admission a nan KASU. Wasa wasa tana karatu sosai har ta cinye semester ta farko. Kowa yayi farin ciki da ita sosai. Daga nan ne kuma ƙaddara ta sauya mata salo haɗuwar ta da Abdulkarim Kuru wanda shi ma ɗalibi ne cikin makarantar sai dai shi yana dab da gamawa. Soyayya suke yi mai cike da kulawa yayin da shi Abdulkarim iyayen sa Allah yayi musu rasuwa tun yana yaro. Ya taso ne a gidan ɗan uwan mahaifiyar sa wanda rayuwarsa tare da su babu abunda yake tsinta sai wahala musamman wurin matar gidan da kuma yaron ta Idrisu. Haka ya daure ya ci gaba da zama tare da su har suka kammala primary. Tun lokacin kuma ya fara neman sana'ar hannu don tallafawa kan sa. Sai dai kash, ko da yayi ya damu ƴan kuɗaɗen sa sai umman idrisu ta ƙwace ta bawa ɗan ta gashi kuma shi babu aikin da yake yi sai zama a dabar ƴan shalli tun yana yaron sa. Bayan ya kammala secondary bai sa ran ci gaba da karatu ba saboda mahaifin idrisu ma Allah yayi masa rasuwa,hakan yasa tun lokacin ya fara sana'o'in hannu, dako, garuwa da sauran su babu wanda bai yi ba sai dai kuɗin duka a gindin ummah ya ke ƙarewa, ko kaɗan bata tausayin sa gashi da shi yake cefane a gidan ammah abincin gidan babu rabon shi. Haka ya ci gaba da rayuwa bayan wani lokaci wata rana suka haɗu ad abokin sa na primary wanda yanzu baban sa shine chairman na yankin su, da taimakon abokin ya samu damar tafiya jami'a ammah baban abokin ya zaɓa masa KASU saboda kada yake mantawa da shi. Tare da abokin sa Bello gadauji suka ci gaba da karatun su kuma Alhamdulillah Abdulkarim na samun ci gaba sosa yana kuma samun nasara. A shekarar shi ta ƙarshe ne suka haɗu da Madina Abatcha ɗiyar hamshaƙin attajjirin da babu kamar sa cikin Kaduna state da kewaye. Da farko ya ji tsoron alaƙar su ammahdaga baya suka ware suna zabga soyayya. Ranar da Madina ta tunkari Hajjaty da maganar aure take so bata kula ta ba sai ma cewa da tayi ta samu yayan ta Abubakar wanda yanzu yaron sa na da Shekara biyu a duniya. Tunkarar yayan ta da tayi ya jawo babbar matsala don kuwa cewa yayi ba ta isa tayi aure yanzu ba kuma ko zata yi sai dai shi da kan shi ya samar mata miji ko daga dangin Hajjaty ne. Kuka sosai Madina tayi bayan jin bayanin yayan nata gashi kuma Hajjaty da Alhaji Baba sun ƙi saka baki. Ana cikin haka Abdulkarim ya kammala karatun sa sai dai bai samu aikin yi ba. Basu rabu ba har bayan komawar sa gida. A nan yake sanar da baban Bello maganar Madina. Kwantar masa da hankali yayi daga nan ya wuce don gaida umman su. A lokacin ya tarar da mummunan abu don kuwa idrisu shaye shaye yake ba kuma ƙafar yaro, ga kuma bin ƴaƴan unguwa yana lalata su tun iyaye na kai ƙara har suka gaji suka fauwalala Allah komai. Ɓoyayyen batu ma ashe har boka gare shi wanda yake rufe masa bakin iyayen yara. Idrisu yayi baƙin ciki sosai gani ɗan uwan sa cikin rahama gashi kuma wai har karatu yayi. Wurin Bokan shi kai tsaye ya nufa bayan yayi masa aiki kan cewa Abdulkarim ba zai taɓa samun aiki ba ya dawo. Shiru shiru babu aikin yi gashi kuma tsakani da Allah shi yana ƙaunar Madina kuma auren ta yake so yayi. Aikin hannu ya fara yana zama a matsayin yaron shago ma wani ɗan kasuwa cikin haka da idrisu ya gano ya haɗa masa ramin mugunta har aka kore shi. Yanke shawarar neman auren Madina yayi dai dai iyayen ta sun ce aah saboda sun riga sun mata zaɓi. Madina tayi kuka sosai kamar ba gobe har rashin lafiya tayi ammah yayun ta suka ƙi amincewa da batun ta. Ana cikin haka sheɗan yayi mata huɗuba ai kuwa ta hau tayi daram. A hankali ta fara haɗa kayayyakin ta masu muhimmanci wuri ɗaya, sarƙoƙin ta da kuma abubuwan ta masu tsada duk ta haɗa su wuri ɗaya sai dai bata san ta yaya zata fita da su ba. Shawara ce ta faɗo mata ai kuwa tayi na'am da ita. Dare nayi tazo ta fito da su a hankali ta zuba cikin motar ta da take fita school da ita, bayan ta gama ta kwanta tayi bacci kamar bata da wata damuwa. Da safe ta shirya kamar dai zata wuce school tayi wa Hajjaty sallama sannan ta ja motar ta. Maimakon ta wuce school sai ta nufi hanyar garin Bauchi. Sai bayan azahar ta isa tana isa ta samu wani restaurant ta ci abinci daga nan ta shiga cikin gari neman habibyn ta wanda tasha wahala kafin samun sa. Bayan ta sanar da shi ƙudurin ta da kuma dalilin guduwar ta ne ya fara lallamin ta akan ta koma gida ammah fit ta ƙi daga ƙarshe ta e wallahi in Basu je anyi musu aure ba to zata sheƙe kanta. Babu yadda ya iya ya sanar da baban Bello da ya so yin jayayya shima daga ƙarshe ya yadda. Sati na zagayowa aka ɗaura auren su tare da masoyin ta Abdulkarim, sai dai shi ko gida bashi da shi, cikin sarƙoƙin ta masu daraja ta bada ɗaya aka siyar, da kuɗin ya sayi gida ɗan madaidaici, two bedroom apartment with one parlour sai kuma kitchen da toilet. Sauran kuɗin kuma ta sashi ya nemo jarin kayan shago tunda akwai jikin gidan su ya zuba. Sannu a hankali suka shimfiɗa rayuwar su mai cike da soyayya da kulawa. Wasu lokutan Madina kan shiga ɗaki ta sha kuka ta fito ammah ta ɗauki alwashin ba zata raba auren ta da masoyin ta ba, su kuma familyn ta suje ita ma ta yafe su. Duk wannan waina da ake toyawa idrisu bai sani ba sai ranar yazo wucewa ya e bari ya tsaya ya siya sigari. Yana shiga yaga Abdulkarim a shagon, tun daga lokacin ya wuce wurin Bokan sa. A lokacin Bokan ya sanar da shi ai shagon Abdulkarim ɗin ne kuma yana da mata ma, har da juna a jikin ta. Cike da hassada yace boka ya durƙushe kasuwancin kowa ya rasa kuma shima ya kashe masa shi. Boka yace gaskiya shi duk hatsabibancin sa baya kisa sai dai ina shi da kan sa ya kashe shi tunda ɗan uwan sa ne. Ana cikin haka fah kasuwanci ya fara ja baya, kafin shekara shago ya zama fankayau. Shawara ta bashi kan su sayar da gidan su nemi wanda bai kai wannan ba. Bayan sun sayar suka koma wata unguwar a haka ahaka bar ta haihu.....yarinya kyakkyawa ta haifa wacce kowa ya gani sai ya yaba don kuwa bata bar komai na Madina ba. Ranar suna yarinya ta ci sunan Fatima Zahrah sunan mahaifiyar Abdulkarim taci. Sannu sannu yarinya ta fara wayo gashi sai ƙara kyau take yi. A haka suka ci gaba da rayuwa har zuwa lokacin bata san wani idrisu ba ballantana shirin sa. Kwatsam wata rana mai baƙin tarihi wacce ta kasance katanga tsakani ta da masoyin ta Abdulkarim. A ranar ne aka samu gawar sa a kusa da wani gidan mai an yi mishi kisan wulaƙanci, Madina tayi kuka sosai har sai da aka kwantar da ita a asibiti. Bayan taji sauƙi aka sallamo ta. Kai tsaye gidan ta aka wuce da ita da taimako mamar Bello. Bayan ta gama takabar ta ne ta yanke shawarar komawa gida saboda wanda ta gudo domin shi ya tafi ya barta. A ranar da ta gama shirye shiryen ta ne aka ce ana sallama da ita a waje. Bayan ta fita ta tarar da shi cikin wani koɗaɗɗen yadin sa da yaji jiki. Suka gaida ta tambaye shi ko shi waye yace ai shi ɗan uwa ne ga marigayi idan ba zata damu ba shi yana so ya aure ta ne. Cikin zuciyar ta kuwa wani tsoron mutumin ne ya ɗarsu lokaci ɗaya ta amince da batun sa aka ɗaura musu aure. Cikin gidan ta na da ta tare sai dai tun da ta shiga gidan farin cikin ta ya ƙare. Farkon auren ya kan kyautata mata, abinci haka baya mata shamaki da shi. Bayan watanni kaɗan da auren salon shi ya sauya, a kowacce rana sai ya jibgi Madina tamkar dai mahaifin ta haka ya mayar da ita, yarinyar ta Zahrah baya ƙyale ta, akan idon ta yake jibgar ɗiyar ta ta sai dai babu yadda ta iya saboda mugun tsoron shi da take ji. Shan giya da sauran kayan maye babu abun da ya bari sai ƙaruwa ma da yayi gashi bata da ikon hana shi, a na haka ya fara kafa majalisar matasa irin shi masu zaman kashe wando haka zasu yi ta busa hayaƙi a ƙofar gidan. Ranar da ta yijarumta ta tunkare shi da maganar majalisa sai da yayi mata dukan Kawo wuƙa, a lokacin Zahrah bata haura shekara biyu a duniya ba haka ita ma tayi ta kuka ganin irin dukan da ake wa mahaifiyar ta. Tun daga wannan rana yarinyar ta sanya tsanar kawun ta a cikin ranta har zuwa girman ta. Abinci da yake hana su daga gidan mamar Bello ake kawo musu, su ma bayan wani lokaci suka tarkata komatsen su suka koma Birnin Abuja da zama, hakan ba ƙaramin tayar da hankalin Madina yayi ba, takan ji ina ma ta gudu ta koma ga iyayen ta sai dai duk lokacin da tayi yunƙurin hakan sai ta gwammace bata yi ba, rashin lafiya ce zata kamata ga wani abu da zai tsaya mata a ƙirji kamar dutse. Hakan yasa ta fauwala lamurran ta ga Allah ta bar batun guduwa..... Yanke shawarar sayar da wata sarƙar ta tayi bayan ta siyar ta siyo kayan suya kama daga tanda, bahuna plates na roba da sauran su ta fara soya Masar siyarwa sai dai ba'a kai ko ina ba mutanen unguwar suka daina siya dalilin mijin ta idrisu. Ganin yunwa zata iya yi musu illa ita da ɗiyar ta yasa ta fara soya Masar a kasuwa wanda hakan ya zama maslaha gare ta. Bayan Zahrah ta kai shekarun shiga makaranta ta sanya ta a makarantar gwamnati, Zahrah ta tashi da rashin haƙuri da kuma masifa ga rashin kallon mutuncin manya, tun tana ƙarama tsanar kawun ta ta ɗarsu a ranta shiyasa ta ƙudurta a ranta duk ranar da tayi ƙarfi sai ta ramawa Mamah dukan ta da yake yi. Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah har Zahrah ta shiga primary school wanda Mamah ke ɗawainiya da komai nata kama daga sutura zuwa karatun ta da kuma cikin ta. Sam yarinyar ta tsani maza, a tunanin ta duk maza haka suke mugage marasa tausayi shiyasa ta ɗauki aniyar kare kanta daga kowanne irin farmaki namiji zai kawo gare ta, faɗa da maza baya damunta kuma koyaushe takan yi ƙoƙarin ganin tayi nasara kan su. A kullum burin Zahrah bai wuce ta zama alƙali ba saboda take kulle duk wani mai laifi. ★★★★★ ______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️ ﷽ PROLOGUE 𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣5️⃣ SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________ Zahrah yarinya ce ƙarama sai dai Allah ya bata kaifin basira tamkar wata babba. Kukan da take yi ta tsayar jin kiran Sallah yayin da Mamah ta rungume ta kamar za'a ɗauke mata ita. “Zahrah ta! Ke ɗin ta musamman ce kuma inada yaƙini akan ki, zaki iya ɗaukar fansar mahaifin ki ta hanyar da ta dace koda kuwa bayan Ni bana nan domin ina ji a jiki na zama na da ke ƙaiyadadde ne.” Zame jikn ta tayi a hankali sannan ta share hawayen ta yayin da ta mayar da hannayen ta bisa kafaɗar Mamah. “Na ɗauki wannan alƙawarin Mamah tah! Nayi miki rantsuwa da wanda rai na ke hannun shi duk wanda na kama da laifin raba mahaifi na da rayuwar shi bazan ƙyake shi ba, dole doka ta hau kanshi kamar kowa.” Murmushin yaƙe Mamah tayi ta ƙara rungumo Zahrah jikin ta. “na yadda dake ɗiya ta, Ni na kasa ɗaukar fansar masoyi na ammah nasan ke zaki ɗau fansar mahaifin ki. Fatan nasara takasance dake a kowanne yanayi.” Da ƙyar suka tashi suka yi sallah musamman Zahrah da ke fama da gajiya shiyasa ta ce yau ba zata je islamiyya ba, abinci Mamah ta girka bayan sun ci suka kwanta don su huta. Yinin ranar Zahrah a sukwane tayi shi ga wata fargaba da take ji. Zuciyar ta wani irin bugu take yi innalillahi wa inna ilayhi rajiuun kawai take maimaitawa. Bayan Badi'a ta kawo abinci kamar kallum Zahrah ta amsa suka ɗan yi taɗin su kafin ta wuce. Serving nasu tayi a plate ɗaya ita da Mamah daga nan suka zauna suna ƴan zantukan su. Ita dai yau Zahrah cike take da mamakin Mamah, yadda yau take ta ɓarin magana kamar mota maras birki, tun daga taɗin family nata har zuwa kan rayuwar ta gidan Abban Zahrah. Daga ƙarshe da ta ɗauki hakan a matsayin kewa tayi wa Mamah yawa shiyasa take maganar. Bayan sallar isha'suka yi addu'a kamar kullum suka kwanta bacci. Bacci mai uban nauyi ne ya kwashe Zahrah. ★★★★★★★ Tafe take cikin wani baƙin daji mai ɗauke da duhun gaske, babu alamar akwai halitta cikin shi. Ta jima tana tafiya tare da fatan Allah ya haɗa ta da wani wanda zai taimaka mata ta koma gidan kwatsam ta fara jiyo sauti daga can nesa. Yanke shawarar zuwa guriin sautin tayi tare sa fatan Allah yasa mutane ne. The more ta yi tafiya the more sautin ke ƙaruwa. Tayi doguwar tafiya kafin ta kusanto wurin sautin sai dai alamu sun nuna cewa sautin ba na mutane bane....gurnanin da take ji ne tare da wata mahaukaciyar dariya mai ɗan karen sauti da amo maras daɗi yasa ta ɗan ji tsoro daga ƙarshe kuma ta yanke shawarar ƙarasawa. Bata kai ga ƙarasawar ba taji ƙasa na wata irin girgiza wanda hakan tayi sanadiyar faɗuwar ta ƙasa, da ta tayi ƙoƙarin tashi sai ta koma saboda girgizar ƙara ƙamari take yi. duk ƙoƙarin ta na tashi tsaye ya gagara hakan yasa ta kwanta tare da runtse idanuwan ta tana miƙa wuya Wasu munanan halittu ta gani masu munin gaske, kayuwan su manya manyan wanda ke ɗauke da ƙaho biyu, na hagu jibgege na dama kuma ɗan ƙarami. Fuskar su ja jawur da ita ga idon su ɗaɗɗaya ne manya manya marasa daɗin kallo. Baƙin su kuwa ya kai faɗin randa Wanda ke ɗauke da wasu gabza gabza haƙora da suke da launin shuɗi. Gangar jikin su irin ta mutum ce sak ga kyan fata da suke da shi sai dai bakin su da yake a wangale yana zubar da wani kore da jan jini suke ƙara wangalewa. Ta riga ta saddaƙar cewa tata ta ƙare hakan yasa ta ƙara runtse idanuwan ta tare da karanto wasu addu'oin tsari. A hankali halittun suka matso daf da ita suka ɗaga ta....basu ajiye ta ba sai cikin wani cage Wanda ke ɗauke da wasu mutane kusan biyar.....ana cikin wannan abu sai ga wata mahaukaciya ta bayyana gaban cage ɗin, jikin ta duƙu duƙu ga wasu kayayyakin ta da suka ji jiki. A hankali mahaukaciyar ta jawo ƙofar cafke ɗin tana motsa bakin kamar mai karanta wani abu. Tana gama buɗe ƙofar ta jawo su ɗaya bayan ɗaya daga ƙarshe ta janyo Zahrah ta faɗo jikin ta. Bata kai ga gane fuskar waye ba taji kiran sallar asuba, ɗauke da addu'ah a bakin ta tayi miƙa. Mintuna kamar 10 ta kwashe tana nazarin mafarkin da tayi tare da hasaso ko meh yake nufi. Kan ta ne ya fara juyawa hakan yasa ta buɗe idanuwan ta da suke lumshe. A hankali ta shashima gefen ta ta gano ta ina Mamah take sai dai babu kowa gurin. Ƙafar ta ta sanyo ƙasa yayin da ta ware idanuwan ta. A hankali ta fita don gabatar da alwala tunanin ta Mamah na banɗaki, ganin ƙofar a buɗe yasa zuciyar ta bugawa sai tayi saurin kawar da abun da zuciyar ta ke shirin shirya mata ta hanyar ɗiban ruwa a buta, sai da ta gama ɗiba ta shiga bayi bayan ta fito tayi alwala ta koma ɗaki don yin Sallah. Tana idarwa bata iya ko yin azkar ba bacci yayi awun gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai wajen 8:12am sanadin mummunan mafarki da ta ƙara yi na wannan mahaukaciyar. A sukwane ta miƙe tsaye sai dai ƙara kallon gado da tayi sai taga still babu mamah. Zuciyar ta ne tayi wani irin bugu har sai da ta kusa faɗuwa. A hankali ta duba wurin da Mamah ke sallar asuba ko yaushe taga wayam kuma babu sallaya shimfiɗe. Mamaki ne ya cika ta yau ko ina Mamah ta tafi?. Bayan ta fito tayi wanka ta dawo still Babu Mamah babu alamar ta hakan yasa ta tsorata da lamarin. Kaya kawai ta sanya ta nufi gidan su Badi'a ko can Mamah ta nufa sassafe. Karo suka ci da Abba ya fito daga part ɗin shi, a natse ta kalle shi tare da sunkuyar da kanta ƙasa. “ina kwana abba” “lafiya kau Zahran Mamah ya Maman ki?” Tsoro tambayar ta bata, wane irin ya Mamah bayan kuma nan ta zo. Kawar da abun da zuciyar ta ke saƙawa tayi tare da faɗin “lafiyar ta ƙalau” “toh madallah” daga haka ya wuce ita ma Zahrah ta shiga part ɗin Ammi. Breakfast ta tarar Badi'a da Ammi nayi wanda hakan yasa zuciyar ta yin wani mummunan bugu, a daidai lokacin ta faɗi ƙasa a yashe. Cike da ruɗewa Ammi da Badi'a suka yi kan Zahrah. Tunani meh za'a fara yi mata Ammi tayi cikin ruɗu tace “badi'ah kawo ruwa masu sanyi” Da gudu Badi'a ta nufi fridge ta ɗauko ruwa. Har Ammi ta gama yayyafawa Zahrah wannan ruwan babu alamun numfashi a tattare da ita. Kuka Ammi take yi kamar ranta zai fita haka Badi'a, gashi ƙwaƙwalwar ta duk ta toshe ta ma rasa MEH zata yi. A cikin wannan yanayin Abba ya shigo ganin suna kuka yasa shi ƙarasowa yadda suke da sauri. “Lafiya kuke kuka haka” kasa magana suka yi hakan yasa ya kai kallon sa ga wurin da idanuwan su ke. Ganin Zahrah da suka gaisa tare cikin mintuna marasa yawa yasa ya matso “meh ya samu zahrah?" Badi'a da ta shiɗe tace “Abbah Zahrah ta mutu, shikenan ta mutu kuma babu abun da aka yi mata” A hankali Abba ya kai hannun shi ya riƙo hannun ta, jin akwai pulse yasa ya ɗago Zahrah da sauri. “ku biyo baya na” Cikin hanzari ya fita da Zahrah direct parking. Space ya nufa ya kwantar da ita, Ammi da Badi'a suka shiga. Kai tsaye Northern Specialist hospital ya nufa da ita. Ba a ɓata lokaci ba aka karɓe ta saboda yanayin da aka zo da ita. Cikin aƙalla 30minutes aka taro numfashin Zahrah da taimakon doctors da kuma Nurses. Daga nan aka saka mata line na N/A sannan aka yi mata antidepressants injection tuni bacci yayi awun gaba da ita. Ganin doctors na fitowa yasa Ammi saurin nufar su “ehm Please ta tashi ko? Zahrah bata mutu ba ko yauwah ku faɗa min meh ke damun zahrah” Ganin yadda ta bi ta ruɗe yasa doctor murmusawa have “she's Alright now, ammah tana buƙatar hutu, so zuwa jimawa za'a ɗauke ta daga nan a mayar da ita paediatric medical ward sai ku duba ta” Jijjiga kai ammi tayi ba tare da ta fahimci dogon bayanin shi ba tunda yace she's alright. Reception suka koma suka zauna suna ta addu'ar fatan sauƙi wa Zahrah. Sai a lokacin Ammi ta tuna basu bi sun sanar da Mamah ba can tace ba sai an sanar da ita ba kawai saboda kada a ɗaga mata hankali bayan ba cikakkiyar lafiya gare ta ba. Har wajen azahar shiru hakan yasa Ammi komawa A&E wadda ɗin, karo suka ci da doctor ɗin da yayi mata bayani. “ehm doctor Bata tashi ba har yanzu?” “eh yanzu dai a je a nemo mata abun da zata ci zuwa jimawa zata iya farkawa anytime” “ok” daga nan Ammi suka koma suka yi girki suka dawo. Har yamma Zahrah bata tashi ba, hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba shine Mamah ta yanke hukuncin sanar da Mamah kada ta ji Zahrah shiru. Abba na gida kawai ta ƙira shi tace ya aika yaro ya sanar da Mamah Zahrah na asibiti ammah ba sai ta zo ba da an sallamo ta zasu dawo. Cikin sauri Mamah ta yi picking call ɗin da ke shigowa wayar ta. “Eh ina ji” Ta ɗaya ɓangaren kuma ban ji MEH aka ce ba. A zabure ta miƙe tsaye “ban gane ba.....tooooh ko zaka sa a tambayi amaryar gidan ko tana kwance ba lafiya ne ita ma?.....ohk ina jira” Daga haka ta dawo ta zauna. Wasa wasa maghrib tayi kuma Zahrah dai bata farka ba, kuma Abba bai ƙira Ammi ba. Yanke shawarar barin Badi'a tayi in yaso in Zahrah ta tashi kafin su dawo ma ita tana nan. Tana isa bayan tayi girki ta nufi gidan Mamah, ɗakin Mamah ta nufa kai tsaye tare da sallama a bakin ta. Jin shiru babu amsa wa tasa ta shiga da sauri tunanin ta ko Mamah na bayan gida ne. Shiga tayi ta ɗan zauna saboda ta jira ta. Jira shiru shiru Mamah bata fito ba gashi Ammi na son wucewa asibiti. Kai tsaye ta nufi hanyar banɗakin. “da mutum ne a ciki?” Sai da Ammi ta maimaita sau biyar ammah shiru ita ma nan da nan zuciyar ta buga wani irin tsoro ya kama ta. Ganin jiran ba shi da amfani yasa Ammi ta shawarar tambayar baba amarya ko ta ga fitar ta. Wani kallon banza Baba amarya ta wulla wa Ammi tare da jan tsaki ta koma ɗaki bayan jin ƙudirin Ammi. Cikin ruɗu Ammi ta fice zuwa gida, ta sanar da abba kafin yace ta wuce babu damuwa wata ƙila Mamah gidan wasu ƴan uwan su ta tafi. Har lokacin da Ammi ta koma ba'a sauyawa Zahrah waje ba saboda har lokacin bata farka ba. Allah Sarki ƙauna Badi'a kam kasa cin komai tayi sai kuka ta ke yi “kiyi haƙuri kiyi wa Zahrah addu'a idan kina kukan babu abun da zai miki sai dai kema ki fara ciwon kai.” Kai ta gyaɗa tace “toh mamah” “oyah zo ki ci abinci” babu musu ta ƙarasa Mamah tayi serving nata, ta ɗauki spoon kenan zata kai loma tace “Ammi baki bi kin yi wa Mamah magana ba ne?” “eh tana kan hanya” haka kawai ta faɗa saboda kada ta tayar mata hankali. Bayan Badi'a ta ci abinci ta ƙara barin reception ta nufi wurin A&E ta tsaya. Tana cikin tsayuwar Dr. Ya fito. Ganin ɗazu ya ganta tare da Ammi yasa ya nufe ta. “Baby ina mamar taku?” “tana can reception” kallon ta yayi yace ta ƙura Maman su. Da sauri ammi ta biyo bayan Badi'a suka taho. Ganin irin tashin hankalin da Maman nasu ta shiga yasa Dr. Yin murmushi. “Yauwah Hajiya ke ce kika kawo wannan yarinyar ko?” “e...eeeh nice ta farka ne?” “eh ta farka ammah bata cikin hayyacin ta, so yanzu za'a sauya mata ɗaki sai a bata abinci taci” “tooh shikenan” Bayan an sauya wa Zahrah ɗaki zuwa medical ward Ammi da Badi'a suka wuce. So da yake amenity suka kai ta ya sa duk su biyun suka shiga. Lumshe idanuwan ta suke yayin da fuskar ta tayi pale, sai kamannin ta da Mamah ya ƙara bayyana. Ƙarasawa wajen ta suka yi suna ambaton sunan ta. MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA