*AZAAD JUNAID* The young Billionaire Na Jeeddah Aliyu *Haske Writers Association* *mg's skincare* Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩 Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️ Shin kinafama da Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata? Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫 Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind Available product👇 Herbal whitening black soap:3k Beauty kit:11k Blacksoap/molato whitening soap: 3500 Bridal kit:20k Muna maraba da masu siyan daya ko sari Chat 08062991549 Call 08064532391 Facebook: mg's skincare Instagram:glow_with_mgs Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩 Then @mgs skincare gat you covered 💯 Now is time to glow😍 Pamper ur skin🦵 Shine like bride👰🏻‍♀ Glow🧖‍♀? 💯 tested nd trusted🤝 Guarantee Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166 08062991549 Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549 Mungode🤝 Free Page 1.... "Wai ke Salima wacce irin mace ce sau nawa zan faɗa miki ban amince da wannan tafiyar taki ba?" Ta cikin mirror da take zaune a gabanshi tana gyara daurin d'an kwalin dank'areren lace da ke jikinta ta aika mishi Kallon uku saura kwa6o tare da ta6e bakinta. Kana ta mik'e ta nufi wata k'atuwar show glass mai d'auke da tarin designers shoes & handbags tsaye tai ta k'urawa show glass ɗin idanu tana nazari wanda ya dace tasa Ta d'auki half cover golden in colour na company lamis elwan tare da handbag ɗinsu. Ta ra6a gefenshi ta wuce abinta sosai hakan ya k'ara linka masa 6acin rai da yake ciki, ya dunkule hannunshi na dama ya nushi bango d'akin ba tun yau ba yake nukurkusa bakin cikin matarshi Salima wacce shi kanshi a yanzu ya fara yarda da tafi k'arfin shi. Bai isa ya faɗa ta ji ba tabbas a wannan karon zai tabbatar mata da shi ke iko da ita ba ita ke iko dashi ba. Cikin zafin nama ya bi bayanta da k'arfi yake taka steps hakan ne yasa yai nasarar cin mata a downstairs parlor. "Salima! Yadda ya kira sunanta da k'arfi yasa housemaid ɗin da ke cikin parlor suka fice da sauri ba tare da sun bari ya had'a idanu dasu ba. Nanny Lacey da ke zaune a dinning room tana ba wa k'aramar 'yar su Ahlam abinci tai sauri daukarta ta nufi d'akin yara da ita. "Wannan wane irin wulak'anci ne ina magana za ki fita ki bar ni wato ga mahaukaci ko?" Ya k'arasa magana yana huci. "Look Azaad Kar ka nemi tashin hankali dani domin karshenta za ka dawo kana regretting. Ta faɗa ba tare da ta juyo ta dube shi ba ta ci gaba da tafiya. "Da gaske nake yi ban amince ba asalima inaso ki rubuta resigning letter, lokaci ya yi da za ki zama full housewife ki kula da tarbiyyar 'ya'yanki domin gaba d'aya tarbiyyar su a gur6ace take. Kina kallon abin da ya faru yau a school ɗinsu yaushe aka haifi Anisa da har za tai dambe da schoolteacher ɗinsu..... "Enough is enough Azaad! Ta katse shi cikin tsawa da tada murya tuni sautin muryar ta ya kere nashi kana ta ci gaba da faɗin "Na fahimce dukan da aka yiwa Anisa kai ko a jikinka asalima so kake yi ka d'auki laifi kachokan! Ka dora min. Idan har kana jin ba za ka iya sauya mata school ba, to ni zan iya domin sani kanka ne ban dogara da abin hannunka ba.... "Ya ishe ki Salima! Nace ya isa! Har sau nawa kike so a sauyawa Anisa makaranta sa'o'inta suna aji huɗu a secondary amma ita tana jss three shin hakan Kaɗai bai isa ya haska miki lalaci 'yar ki ya yi yawa ba?" "Yar ta Azaad kace 'yar ta wato ni Kaɗai Allah ya ɗorawa tarbiyya yara kai ubansu ba da kai ba ko?" "Kwarai kuwa domin kece uwa ke ya dace ki zauna gida cikin 'ya'yanki ki kula dasu ba ni ba. Abin da ya rataya akaina shine hakkin ci da sha kuma dai-dai gwargwado na tsare muku su. sannan ki tuna ina da hakki akanki sai mu share watani uku Salima ban had'a shinfid'a dake ba. Angaya miki ni dutse ne ko waliyi da bana buk'atar mace?" "Yanzu kan na fahimce inda ka dosa Azaad kawai ka fito fili ka faɗa min ba ka so ci gabana. Allah ya rufa min asiri na dogara da kaina bana tsayawa jiran sai kayi min, shine kake so ka tauye ni to bari ka ji inaso aikina domin bana ko tantama da banida kud'i ko na fito gidan babu da ba yadda za a yi kai ɗin ka aure ni. Cike da takaici yake K'are mata kallo ko wane furunci dake fitowa daga bakinta k'ara mishi 6acin rai yake yi, shi mutum ne da bayaso hayaniya yana da matuk'ar sanyi hali shiyasa a koda yaushe Salima take zantar da hukunci kuma dole ya bi koda hakan bai masa dad'i ba. Amma tsabar sanyi halinsa ba zai ta6a bari ta fahimci hakan ba, ita kuma anata 6acewar basira take gani kamar tsoronta yake yi. "Ki sani Salima furuncin nan kin sha faɗa min shi ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Kin faɗa min shi bila'adadin, kuma yana cikin kalamin ki da ke matuk'ar sosan rai "ka ga Azaad ka bar ni haka nagaji da saurare tsofaffin maganganun ka, domin duk ciki abin da ka faɗa babu sabon abu a wurina kana bata lokaci ne kawai. Ta gyara mayafin jikinta wanda shi babu duk d'aya ta buɗe k'ofa ta fice abinta, ya bi k'ofar da ta fita da kallo zuciyarsa tamkar za ta fasa k'irjinshi ta fito ya d'auki dogon lokaci tsaya a falon kafin sake haura upstairs saidai a wannan karo tangamemen bangare shi ya nufa katon parlor na farko ya fara wucewa kafin ya iso na biyu wanda yafi na farko tsaruwa saidai na farkon yafi girma, ya buɗe k'ofar gilashi wacce za ta sada shi da Master bedroom ɗinshi, kaitsaye resting chair ya nufa ya zauna, ya shiga shafar kwantattace saje shi da hannunshi na dama. Ya rasa a duniya me Salima take nema ne duk wani jin dad'i duniya Allah ya bashi ya tara dukiyar da har jikokin 'ya'yanta za su mora to me ya rage da za ta nema face lahirarta. Kuma gaba d'aya a tsarinta babu lahira a ciki a shekaru 16 da aure har kawo yau ɗinan ba wani abu da zai bugi k'irji yace ya samu na farin ciki, kullum rayuwarshi a k'unci take gashi Allah ya bashi duniya amma ya ga-gara samun farin ciki ya tashi maraya ba uwa ba uba a wurin haihuwar shi mahaifiyarshi Hindu ta rasu, a hannun kakar shi Jadda ya taso wacce ta haifi mahaifiyarshi yana degree shi na farko ya rasa mahaifin shi wanda ya rasu yabar tarin dukiya ta fitar hankali, da kuma tarin 'ya'ya domin yabar matan aure uku mahaifiyar Azaad ce ta uku bayan rasuwar ta ne ya sake wani aure, Kuma duk a cikinsu ita ce mai d'a d'aya Azaad. Azaad Junaid matashi ne ne d'an shekara 47 cikakke business tycoon ne wanda tauraronsa ke haskawa a faɗin duniya. Ya mallaki dukiya wacce shi kanshi a yanzu bai san adadinta ba. Azaad Junaid mutum ne mai matuk'ar sauk'in kai ba za ka fahimci hakan ba har sai ka zauna dashi. Azaad yana da matuk'ar kyauta da alkhairi ga tallakawa yana kyautatawa na k'asa dashi yana da gaskiya da rik'on amana, mutum ne mai rik'o da addini sai dai san baya daukar reni yana son a girmama shi matuk'a. Babbar matsala shi a duniya ita ce matarshi Salima sun yi aure a bisa so da k'auna, Salima mace mai zurfin ilmin boko na addini ne ya yi k'aranci a gareta, ba yadda ban yi ba akan ta zurfafa ilmin nata na addini amma abin yaci turo dole yana ji yana gani ya zuba mata idanu. Ga wasu Dabi'u da halayenta da take dasu, sun sha ban-ban da na matan hausa/fulani mace ce mai bala'in girman kai da dogon buri babban burinta sunanta ya zagaya duniya, tayi fice fiyye da mijinta. Mahaifinta mai kud'in gaske ne kuma ita ce babban 'yar shi sai k'anneta maza uku sai Wanda suke 'yan uba su biyar maza biyu mata uku. Salima tayi karatu mai zurfi akan kasuwanci saboda kwarewar da iya kasuwanci yasa mahaifinta Alhaji Kabir Dala tun kafin ya rasu ya mik'a mata ragamar kula da babban kamfaninsa na building and contracting company wanda a halin yanzu ita ce mafi rinjayi hannu jari a company. Burinta ta mallake company ita Kaɗai, sai da 'yan uwanta sun amincewa su sayar mata da hannun jarinsu tasha alwashi sai ta mallaki company kamar yadda ta mallaki wasu k'anana companies ɗin nasu. Azaad Junaid ya haɗu da Salima ne a wani meeting a birnin tarayya Abuja, dukansu su na neman contract d'aya na gina wasu gidaje a nan birnin tarayya Abuja tun kafin su fara gabatar da meeting ɗin ya ji firar da Salima take yi da wata colleague ɗinta yadda samun contract ɗin yake da matuk'ar muhimmanci a gareta da irin hasara da za ta tanka idan ta rasa shi, saboda har makudan kud'ad'e ta yi bribery ɗin wasu daga mukarabai gwanati. Duk abin da take faɗa batasan cewa akan kunne Azaad Junaid sai kawai ya yi sanyyaye murmushi domin yasan muddin ya ri gata gabatar da presentation shine zai sami contract ɗin, tausayi ta bashi matuk'a ba tare da sanin ta ba yasa aka bata contract ɗin duk da akwai 'yan kwangila da suka fi ta amma kasancewar the young Billionaire ne ya yi magana sai aka bata, a lokaci ba k'aramin dad'i da farin ciki ta ji ba. Suna fitowa daga conference room ta mik'a mishi tattasan hannunta da nufi su yi shaking hands sai ya ɗaga mata yatsun shi biyu, ya wuce wurin motar shi tun daga lokaci ta dinga bibbiyar shi har ta sami nasarar suka k'ula alak'a ta friendship daga bisani abuta ta rikide ta koma soyayya. Azaad Junaid yana matuk'ar son Salima ita ma haka abin yake a wurinta, ko wane su commitment ya yi mishi yawa kullum cikin neman duniya suke. Sai su share dogon lokaci ba su haɗu ko a waya su na d'ibar kwanaki ba su yi waya wa junan su ba. Suna kawai sun yi aure a haka ta haifi Anisa tun tana jinjira ta mik'a ragamar kula da ita a hannu Nanny Lacey Anisa tana da shakaru 6 ta sake haifar Airah wacce ita ma ta bi ayarin tawali'u hannun Nanny Lacey, tun daga haifar Airah tace ta gama haihuwa Allah da ikonsa babu zato ba tsanmani sai ga ciki Ahlam ba yadda bataso tayi abortion amma ciki yak'i ya fita, a lokaci ba k'aramin tashin hankali suka yi ita da Azaad ba sai da ya kai fagge furta mata muddin ta zubar mishi da ciki a bakin aure ta shine dole ta hak'ura. Duk a cikin yaranta Ahlam ta fiso rashin samun kulawarta duk watani tara ne da ita amma duka bai fi sau biyu ko uku da tasha nono Salima ba. Shiyasa babu wata shakuwa a tsakanin su daga Nanny Lacey sai siblings ɗinta sai Kuma Daddynta Kaɗai tasani. Saboda duk yawan commitment ɗinshi ya kan ware lokaci na musanmman ya zauna tare da yaranshi wani lokaci har daukar su yake yi tare da Nanny Lacey wacece ta maye musu gurbin uwa su fita kasashe waje yawon buɗa ido. Anisa ta taso da masiffafen girman kai da faɗin rai ga d'an banza rashin kunya da fitsara, kowa kallon bai isa ba take mishi kullum Madam Salima cikin sauya mata school take ko Kaɗan bataso a faɗi laifin yaranta, dama bahaushe yace inda saniyar gaba tasha ruwa anan ta baya za ta sha, duk wani iskanci na Anisa K'anwar ta Airah ta kwashe tass duk da haka Airah tafi ta dama domin ita idan Nanny Lacey ta tsawa ta mata tana ji. Ba yadda Jadda ba tayi da Azaad ya k'ara aure amma yak'i saboda duk duniya ba abin da Madam Salima ta tsana irin kishiya, sai kuma ta taki sa'a da Azaad Junaid ba shi da ra'ayi mace fiyye da d'aya. Shiyasa take tsula tsiyarta iya son ranta yanzu haka Jadda bata da daraja da za ta shiga bangare ta alhali su na rayuwa a gida d'aya asalima ba wacce ta tsana irinta saboda kawai tana faɗa mata gaskiya sai ta d'auki k'iyayyar duniya ta ɗorawa mata. K'arfaffiyar ajiyar zuciya Azaad Junaid ya sauke kafin ya mik'e ya sauya kaya jikinsa zuwa tsadaddiyar shadda getzner ash colour, ya ɗora hula zanna bukar wanda ta dace da kayan jikinsa. Ya saka penny loafers a k'afarshi yayin da yake fitar da sihirtattace k'amshi designer perfume na poundland black dust, ya tattara wasu documents da ke kan center table tare da wayoyin shi har guda uku. A hankali yake taka steps duk da ranshi babu dad'i ba kowa bane zai fahimci hakan ba, saboda koda yaushe fuskarshi a murtuk'e take bashida yawan fara'a ko abu ya yi mishi dad'i sai dai kawai ya yi murmushi, ba kowa a downstairs parlor muddin yana gida housemaids ba su kai da kawo ko wane su zai ya kame kanshi, musanmman yau da gida yake a hartsune dole su yi taka-tsan-tsan. Tun daga main gate direbanshi mr Richard ya hango shi da ya tashi ya jawo mota ya iso daff dashi kafin mr Richard ya fito ya buɗe mishi k'ofa ya budewa kanshi. ******************* Kuka take yi sosai tana d'auke da marar lafiyar K'anwata Amal wacce bata motsi, wuyanta ya langwa6e ya yi baya bata da ban-banci da matatciya tunaninta ma ta mutu ne. Cikin hak'i ta shiga d'akin kakarsu wacce ta haifi mahaifinta tsabar tashin hankali da take ciki yasa ta manta da dokar da Dadda ta shinfid'a musu na hanasu shiga mata d'aki daga ita har k'anneta guda biyu twins Amal da Amrah. Ta ban kad'a curtain da k'ani mahaifinta ta fara yada ganinta akan shi, da sauri ta nufe wurinshi cikin muryar kuka take magana. "Baffa Don Allah ka taimaka ka duba min Amal bata numfashi na shiga uku Baffa ba dai Amal ta mutu ba?" "Ke! Ya daka mata tsawa yana muzurai kamar zai kife ta da mari, cikin hargowa ya ci gaba da faɗin. "Kar ki sake ki kawo ta kusa dani. Na duba ta ni likita ne ko ke ba ki san hanyar asibiti bane?" saboda tsabar iskaci da rashin mutunci za ki kawo min ita" "Allah yasa ta mutu mu rage mugun iri jinin arna" Hajja Dadda ce ta faɗa tana baro wajen zamanta sai lokaci Aslamiyya tasan da zamanta a falo, a fusace cikin rashin tausayi ta dank'e dantse hannun Aslamiyya ta hankad'a ta waje da k'arfi daga ita har Amal ɗin take d'auke da ita suka faɗi yayin da Aslamiyya ta faɗa kan hannunta na hagu, ta kwalla k'ara Amal kuma kanta ya buge sumunti hakan ne ya haddasa mata jan dogon numfashi ta farfado daga suman da tayi, duk da tsananin zogi da hannun Aslamiyya ke mata hakan bai hana mata rerafawa akan gwiwoyinta biyu ta jawo Amal cikin jikinta a matuk'ar tsorace ta ɗago ta tace. "Amal! Amal! Kina ji na kuwa?" Don Allah idan kina ji na ki buɗe idanuwanki nagani, Amal karki mutu ki bar mu. Muna matuk'ar buk'atarki ni da Amrah ki tuna ba mu da kowa sai junan mu. Don girman Allah ki tashi kin ji K'anwata?" Cikin tsananin zafin ciwo Amal ta shiga k'ok'arin buɗe idanuwan nata dake rufe ruff! Da kyar da sudin goshi tai nasarar buɗe su sai dai dishi-dishi take gani Aslamiyya. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske Writers Association. Top Ten Takun Haske Batch: A Free page 2.... Tafiya mai nisa gaske suka yi kamar za su bar gari, kafin suka nufe wani katafare kamfaninsa na sarafa danye gold mai suna AJ Gold Company ba wai iya sarafawa company ya tsaya ba. Yana siye tsofaffin gold ya mayar dashi new model, su na kuma siyarwa. Gate ɗin company Kaɗai abin kallo ne za ka yi zaton shima da gold ɗin aka k'era shi, sakamakon yadda yake shek'i da daukar ido. Da sauri securities dake tsa-tsaye birjik su na ba wa company tsaro, biyu daga cikinsu suka wangale musu gate. Sai daff da k'ofar reception mr Richard ya yi parking d'aya daga cikin security dake tsaro k'ofar ya hanzarta buɗewa Azaad Junaid k'ofar mota ya fito cikin tsananin miskilancinsa da k'assaita ya ɗagawa ma'aikatan da ke mik'a masa gaisuwa hannu, k'ofar reception ɗin ta tsuge kanta kasancewar ta gilashi ce. Kaitsaye ya nufi elevator ya hau wanda zai sada shi da office ɗinshi dake hawa na 6 mutane biyu ne suka take masa baya har izuwa cikin tangamemen office ɗin nasa. ***************** Gani Amal ta buɗe idanuwanta yasa Aslamiyya ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta shiga k'ok'arin ɗaga ta sai dai kashh! Ta kasa sakamakon yadda ta ji hannunta ya rik'e kamar an daure mata shi da igiya. Sai kawai ta fashe da kuka mai ta6a zuciya ta kifa kanta akan cikin Amal ta ci gaba da rera kukanta, Amrah ce ta shigo gidan bakinta d'auke da sallama hannunta rik'e da bak'ar leda mai d'auke da koko da ta siyo musu, su karya kumallo. Kafin ta k'arasa sallamar idanuwanta suka yi tozali da siblings ɗinta zube a tsakar gida ga Aslamiyya tana ta faman kuka batasan lokaci da ta jefar ledar koko ba, ya buge bango ledar ta fashe kokon ya malale akan sumunti, ta kwasa da gudu ta nufi wajensu. Aslamiyya na ganinta ta ɗago idanuwanta da suka fara renewa zuwa jajayye. "Subhanalillah! Miyya me ya faru ne me kuke yi anan kuka me kike yi?" Kusan a tare Amrah ta jero mata wad'annan tari tambayoyi ba ko shed'awa. "Amal ce ta suma na zaci ko ta mutu ne na kawo ta wurin Dadda ta duba ta, shine ta hankad'o ni waje" Ajiyar zuciya Amrah ta sauke cike da tausayi 'yan uwanta. Har sai yaushe Allah zai yanke musu wannan bak'ar wahala da suke ciki?" Kullum addu'ata da fatanta Allah ya kawo wanda zai za me musu bango majingina, ya yi musu gatan da suka rasa. wanda zai fitar dasu daga bala'in k'unci da tsangwama da suke ciki. Ranta a 6ace ta ɗago Aslamiyya ta mik'ar da ita tsaye "Daina kuka Miyya in da sabo yaci ace kin saba da tozarci da ake mana, a gidanan. Da wahala tana kisa da tuni an shafe babin mu a doron duniya, sai Kuma gashi ubangiji ya yi mana tsawon rai duk da yadda akeso kawo k'arshen numfashin mu. Ta k'arasa magana tare da sunkuyawa ta ci-ci6i Amal da ke kwance tana numfashi guda-guda, tsabar yadda ciwo ,ya cinyeta yasa ta dawo tamkar 'yar shekara huɗu ba 13 uku ba. Ta nufi d'akin da ya kasance mallakin su a gidan. Za ka sha matuk'ar mamaki ace d'akin da suke ciki mai rai ke kwana a cikinsa amma su ko a jikinsu saboda sun ri ga da sun saba da rayuwa a ciki. Akan wasu tulin tsomakarai wanda su ne suka kasance wurin kwanciyarsu Amrah ta shinfid'e Amal idanuwanta taff da hawaye sai k'ok'ari danne su take bataso Miyya ta gani, duk da kasancewar ita ce k'arama amma tafi Miyya k'arfin zuciya Aslamiyya irin jinsi mutane nan ne masu raguwar zuciya da rauni batada hayaniya ko Kaɗan ga sanyi hali kamar ruwan fridge, ga ta da matuk'ar hak'uri duk abin da za ai mata bata ta6a tankawa sai dai taci kukanta in tagaji tai shiru. Rayuwarta gaba d'aya ba abin da tasani ta kuma saba da shi irin kuka. Duk cikin su uku Amrah ce kawai halinsu ya ban-banta da nasu ita ma Amal halinta sak! Irin na Miyya ne. Amrah ta dubi Aslamiyya da ke tsaye a jikin k'ofa tana ci gaba da aikin nata na kuka tace. "Wai Miyya ba za ki hak'ura ki daina kuka nan haka ba?" Wallahi ki yiwa kanki k'iyamulaili ki adana raguwar hawayenki kada su k'are akan wad'anan mugaye mutane azzalumai da babu burbushin imani a zuk'atansu" Sai da Miyya ta ja majina da ke k'ok'arin fito mata ta k'ofufin hanci ta maida ta inda ta fito, ta kuma ja dogon karan hancinta da yatsunta biyu kana ta k'arasa shiga d'akin ta zauna kusa da Amal, ta shiga shafa kanta a hankali Amal ta ɗago farare idanuwanta ta dubi yayar tasu wacce ta maye musu gurbin uwa da uba tasaki mata murmushin k'arfin hali ita ma Miyya murmushi tayi hawaye na zuba akan kumatunta. "Sannu Amal Allah ya ba ki lafiya Allah ya kawo miki k'arshen wannan ciwo, Allah ya canza mana k'addarar mu ya kawo mana sauyi wata rana mu d'and'ani rayuwar farin ciki. Da sauri Amrah ta durkusa ta rungume Miyya suka fashe da kuka, ba ka ji komai sai sautin kukansu gwanin ban tausayi, sai da suka ci kuka iya son ransu kafin su rarrashi kansu. Sai lokaci Amrah ta tuna da kokon su na naira hamsi da ta zubar zuciyarta tai mugun bugawa saboda tasan sanadin tashin ciwon Amal hadda yunwa a ciki, zubur ta tashi ta nufi k'ofar fita Miyya na kwalla mata kira ko juyowa ba tai yi ba ta fice daga gidan. ******************** Tun shigowar shi office ɗinsa ya kasa aiwatar da aikin komai ga tarin files zube akan desk da zai yi signing up. Amma ya ga-gara tabuk'a komai cire hular kanshi ya yi, ya aje akan desk ɗin ya shiga shafar suma kanshi. Damuwa tana neman tai mishi yawa tsoronshi daya kada ciwon hawan jini ko ciwon zuciya, ya kama shi. Ga dukiya mai tarin yawa Allah ya albarkace shi da ita amma ya ga-gara samun farin ciki da natsuwar zuciya kullum cikin k'unci da 6acin rai yake. K'arar k'ararawa da ya karad'e office ɗin nashi ya dawo dashi daga duniyar tunani da ya nutse, ya kai duban shi akan allon cctv da ya ke iya gani wanda keso shigowar office ɗin, amininsa kuma MD na company sa Abdul-hakeem Daura ya gani tsaye yana jira ya buɗe masa k'ofa ya shigo, kasancewar k'ofar tana using da code dole sai in shi ya buɗewa mutum zai iya shigowa da remote control ya yi amfani k'ofar ta zuge kanta Abdul-hakeem ya baiyana. Duk faɗin duniya ba shi da wani amini d'an uwa sai Abdul-hakeem saboda 'yan uwanshi da suka had'a uba ba k'aunarshi suke yi ba. Su na bak'in ciki da hasada da daukakkar da Allah ya yi mishi. Burinsu a kullum bai wuce su sami hanyar da za su kawo k'arshen sa. Da shigowar Abdul-hakeem ya yi tsaye ya saka Azaad gaba yana kallo, nan take ya fahimci halin damuwa da yake ciki. ko bai tambaye shi ba yana da tabbaci Madam Salima ce damuwar shi, saboda duk faɗin duniya ita ce matsalarshi ita ce mai jefa shi halin damuwa. Ya girgiza kai haɗi da jan kujera dake kallon Azaad ya zauna. "Aj ya kamata ka dinga sassautawa kanka yawan tunani kada ya zo ya shafi lafiyarka. Tunani ba shi bane solution ɗin matsalolin ka ba. Azaad ya ja gwaron numfashi kana ya lashe lips ɗinsa, cikin zazzak'ar muryarsa mai dad'i da tafiyar da ruhin mai sauraren shi yace. "Ni kaina ba so tunani nake yi ba Abdul zuwa min kawai yake yi. matsaloli su min yawa ga na 'yan uwana ga na iyalina da wane zan ji?" Yanzu duk wanda ya gani zai dauki cewa na fi kowa farin ciki a duniya saboda ina da tarin dukiya ba asan cewa wani tallaka wanda bai da ci yau balle na gobe ya fi ni domin shi, yana samun natsuwar da kwanciyar hankali daga iyalinsa. "Zance na gaskiya Aj kaine ka za6awa kanka wannan matsala, Salima ba za ta ta6a sauyawa ba. To saboda me kai ba za ka nemowa kanka mafita ba?" Tun yaushe ni da Jadda muke ba ka shawara ka k'ara aure amma ka k'i sai ka zauna bak'in ciki mace d'aya ya kashe ka. "Please Abdul-hakeem ka fahimce matsalata ba ta k'arin aure bace. sai fa ka ji dad'i abu kake neman k'arinsa. "Matsalarka kenan Aj idan aka yi gabas sai kayi yamma, dole fa sai ka cire tsoron Salima ko don farfado da tarbiyyar 'ya'yanka ka tuna yaranka mata ne dole su na buk'ata ingantattaciyar tarbiyya. Idan mahaifiyarsu ta kasa sai ka nemo wacce za ta maye gurbinta mana. Mik'ewa Azaad Junaid ya yi hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi, ya taka a natse zuwa gaban widow da ke kallon titi. Yaye labule idanuwanshi suka sauka akan motoci da ke kai da komuwa. Shima Abdul-hakeem mik'ewa ya yi ya isa daff dashi kana ya dafa kafad'arsa. "Ka yarda dani Aj aure shine yafi dacewa da kai ka tuna kullum shekarunmu k'ara tafiya suke yi dole sai muna samun natsuwar da kwanciyar hankali, so ka ga kenan don ka k'aro aure ba wani abu bane. Allah yasani kayi hak'uri iya hak'uri da Salima lokaci ya yi da za ka d'and'ani zak'i da gard'i dake cikin aure" D'an gajere murmushi Azaad Junaid ya yi wanda ya tsaya iya fatar bakinshi, kana ya juya yana facing Abdul-hakeem. "To naji idan ma na amince zan k'aro aure wa zan aura?" Sani kanka ne Abdul tun daga lokaci da na auri Salima ko mafalki ban ta6a kallo wata 'ya mace naji ina sonta ba. Ta ya ya ka ke tunani zan yi aure?" "Mtsss...! Abdul-hakeem ya ja siririn tsaki da ke baiyanar da takaicinsa a fili. "Ba dole bane sai ka ji son mace za ka aure ta ba, kai da za ka yi auren huci haushi ina ruwanka da soyayya. Alhaji ka amince kawai ka ga aiki da cikawa ni da kaina zan nemo ma matashiyar budurwa wacce Nonuwanta suke tsaye cakk! Ka sha shagali abinka. Zaro idanuwa Azaad Junaid ya yi tamkar ya ga abin tsoro kana yasa dariya wanda rabon da ya yi irinta har ya manta. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske Writers Association. Top Ten Takun Haske Batch: A Free page 2.... Tafiya mai nisa gaske suka yi kamar za su bar gari, kafin suka nufe wani katafare kamfaninsa na sarafa danye gold mai suna AJ Gold Company ba wai iya sarafawa company ya tsaya ba. Yana siye tsofaffin gold ya mayar dashi new model, su na kuma siyarwa. Gate ɗin company Kaɗai abin kallo ne za ka yi zaton shima da gold ɗin aka k'era shi, sakamakon yadda yake shek'i da daukar ido. Da sauri securities dake tsa-tsaye birjik su na ba wa company tsaro, biyu daga cikinsu suka wangale musu gate. Sai daff da k'ofar reception mr Richard ya yi parking d'aya daga cikin security dake tsaro k'ofar ya hanzarta buɗewa Azaad Junaid k'ofar mota ya fito cikin tsananin miskilancinsa da k'assaita ya ɗagawa ma'aikatan da ke mik'a masa gaisuwa hannu, k'ofar reception ɗin ta tsuge kanta kasancewar ta gilashi ce. Kaitsaye ya nufi elevator ya hau wanda zai sada shi da office ɗinshi dake hawa na 6 mutane biyu ne suka take masa baya har izuwa cikin tangamemen office ɗin nasa. ***************** Gani Amal ta buɗe idanuwanta yasa Aslamiyya ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta shiga k'ok'arin ɗaga ta sai dai kashh! Ta kasa sakamakon yadda ta ji hannunta ya rik'e kamar an daure mata shi da igiya. Sai kawai ta fashe da kuka mai ta6a zuciya ta kifa kanta akan cikin Amal ta ci gaba da rera kukanta, Amrah ce ta shigo gidan bakinta d'auke da sallama hannunta rik'e da bak'ar leda mai d'auke da koko da ta siyo musu, su karya kumallo. Kafin ta k'arasa sallamar idanuwanta suka yi tozali da siblings ɗinta zube a tsakar gida ga Aslamiyya tana ta faman kuka batasan lokaci da ta jefar ledar koko ba, ya buge bango ledar ta fashe kokon ya malale akan sumunti, ta kwasa da gudu ta nufi wajensu. Aslamiyya na ganinta ta ɗago idanuwanta da suka fara renewa zuwa jajayye. "Subhanalillah! Miyya me ya faru ne me kuke yi anan kuka me kike yi?" Kusan a tare Amrah ta jero mata wad'annan tari tambayoyi ba ko shed'awa. "Amal ce ta suma na zaci ko ta mutu ne na kawo ta wurin Dadda ta duba ta, shine ta hankad'o ni waje" Ajiyar zuciya Amrah ta sauke cike da tausayi 'yan uwanta. Har sai yaushe Allah zai yanke musu wannan bak'ar wahala da suke ciki?" Kullum addu'ata da fatanta Allah ya kawo wanda zai za me musu bango majingina, ya yi musu gatan da suka rasa. wanda zai fitar dasu daga bala'in k'unci da tsangwama da suke ciki. Ranta a 6ace ta ɗago Aslamiyya ta mik'ar da ita tsaye "Daina kuka Miyya in da sabo yaci ace kin saba da tozarci da ake mana, a gidanan. Da wahala tana kisa da tuni an shafe babin mu a doron duniya, sai Kuma gashi ubangiji ya yi mana tsawon rai duk da yadda akeso kawo k'arshen numfashin mu. Ta k'arasa magana tare da sunkuyawa ta ci-ci6i Amal da ke kwance tana numfashi guda-guda, tsabar yadda ciwo ,ya cinyeta yasa ta dawo tamkar 'yar shekara huɗu ba 13 uku ba. Ta nufi d'akin da ya kasance mallakin su a gidan. Za ka sha matuk'ar mamaki ace d'akin da suke ciki mai rai ke kwana a cikinsa amma su ko a jikinsu saboda sun ri ga da sun saba da rayuwa a ciki. Akan wasu tulin tsomakarai wanda su ne suka kasance wurin kwanciyarsu Amrah ta shinfid'e Amal idanuwanta taff da hawaye sai k'ok'ari danne su take bataso Miyya ta gani, duk da kasancewar ita ce k'arama amma tafi Miyya k'arfin zuciya Aslamiyya irin jinsi mutane nan ne masu raguwar zuciya da rauni batada hayaniya ko Kaɗan ga sanyi hali kamar ruwan fridge, ga ta da matuk'ar hak'uri duk abin da za ai mata bata ta6a tankawa sai dai taci kukanta in tagaji tai shiru. Rayuwarta gaba d'aya ba abin da tasani ta kuma saba da shi irin kuka. Duk cikin su uku Amrah ce kawai halinsu ya ban-banta da nasu ita ma Amal halinta sak! Irin na Miyya ne. Amrah ta dubi Aslamiyya da ke tsaye a jikin k'ofa tana ci gaba da aikin nata na kuka tace. "Wai Miyya ba za ki hak'ura ki daina kuka nan haka ba?" Wallahi ki yiwa kanki k'iyamulaili ki adana raguwar hawayenki kada su k'are akan wad'anan mugaye mutane azzalumai da babu burbushin imani a zuk'atansu" Sai da Miyya ta ja majina da ke k'ok'arin fito mata ta k'ofufin hanci ta maida ta inda ta fito, ta kuma ja dogon karan hancinta da yatsunta biyu kana ta k'arasa shiga d'akin ta zauna kusa da Amal, ta shiga shafa kanta a hankali Amal ta ɗago farare idanuwanta ta dubi yayar tasu wacce ta maye musu gurbin uwa da uba tasaki mata murmushin k'arfin hali ita ma Miyya murmushi tayi hawaye na zuba akan kumatunta. "Sannu Amal Allah ya ba ki lafiya Allah ya kawo miki k'arshen wannan ciwo, Allah ya canza mana k'addarar mu ya kawo mana sauyi wata rana mu d'and'ani rayuwar farin ciki. Da sauri Amrah ta durkusa ta rungume Miyya suka fashe da kuka, ba ka ji komai sai sautin kukansu gwanin ban tausayi, sai da suka ci kuka iya son ransu kafin su rarrashi kansu. Sai lokaci Amrah ta tuna da kokon su na naira hamsi da ta zubar zuciyarta tai mugun bugawa saboda tasan sanadin tashin ciwon Amal hadda yunwa a ciki, zubur ta tashi ta nufi k'ofar fita Miyya na kwalla mata kira ko juyowa ba tai yi ba ta fice daga gidan. ******************** Tun shigowar shi office ɗinsa ya kasa aiwatar da aikin komai ga tarin files zube akan desk da zai yi signing up. Amma ya ga-gara tabuk'a komai cire hular kanshi ya yi, ya aje akan desk ɗin ya shiga shafar suma kanshi. Damuwa tana neman tai mishi yawa tsoronshi daya kada ciwon hawan jini ko ciwon zuciya, ya kama shi. Ga dukiya mai tarin yawa Allah ya albarkace shi da ita amma ya ga-gara samun farin ciki da natsuwar zuciya kullum cikin k'unci da 6acin rai yake. K'arar k'ararawa da ya karad'e office ɗin nashi ya dawo dashi daga duniyar tunani da ya nutse, ya kai duban shi akan allon cctv da ya ke iya gani wanda keso shigowar office ɗin, amininsa kuma MD na company sa Abdul-hakeem Daura ya gani tsaye yana jira ya buɗe masa k'ofa ya shigo, kasancewar k'ofar tana using da code dole sai in shi ya buɗewa mutum zai iya shigowa da remote control ya yi amfani k'ofar ta zuge kanta Abdul-hakeem ya baiyana. Duk faɗin duniya ba shi da wani amini d'an uwa sai Abdul-hakeem saboda 'yan uwanshi da suka had'a uba ba k'aunarshi suke yi ba. Su na bak'in ciki da hasada da daukakkar da Allah ya yi mishi. Burinsu a kullum bai wuce su sami hanyar da za su kawo k'arshen sa. Da shigowar Abdul-hakeem ya yi tsaye ya saka Azaad gaba yana kallo, nan take ya fahimci halin damuwa da yake ciki. ko bai tambaye shi ba yana da tabbaci Madam Salima ce damuwar shi, saboda duk faɗin duniya ita ce matsalarshi ita ce mai jefa shi halin damuwa. Ya girgiza kai haɗi da jan kujera dake kallon Azaad ya zauna. "Aj ya kamata ka dinga sassautawa kanka yawan tunani kada ya zo ya shafi lafiyarka. Tunani ba shi bane solution ɗin matsalolin ka ba. Azaad ya ja gwaron numfashi kana ya lashe lips ɗinsa, cikin zazzak'ar muryarsa mai dad'i da tafiyar da ruhin mai sauraren shi yace. "Ni kaina ba so tunani nake yi ba Abdul zuwa min kawai yake yi. matsaloli su min yawa ga na 'yan uwana ga na iyalina da wane zan ji?" Yanzu duk wanda ya gani zai dauki cewa na fi kowa farin ciki a duniya saboda ina da tarin dukiya ba asan cewa wani tallaka wanda bai da ci yau balle na gobe ya fi ni domin shi, yana samun natsuwar da kwanciyar hankali daga iyalinsa. "Zance na gaskiya Aj kaine ka za6awa kanka wannan matsala, Salima ba za ta ta6a sauyawa ba. To saboda me kai ba za ka nemowa kanka mafita ba?" Tun yaushe ni da Jadda muke ba ka shawara ka k'ara aure amma ka k'i sai ka zauna bak'in ciki mace d'aya ya kashe ka. "Please Abdul-hakeem ka fahimce matsalata ba ta k'arin aure bace. sai fa ka ji dad'i abu kake neman k'arinsa. "Matsalarka kenan Aj idan aka yi gabas sai kayi yamma, dole fa sai ka cire tsoron Salima ko don farfado da tarbiyyar 'ya'yanka ka tuna yaranka mata ne dole su na buk'ata ingantattaciyar tarbiyya. Idan mahaifiyarsu ta kasa sai ka nemo wacce za ta maye gurbinta mana. Mik'ewa Azaad Junaid ya yi hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi, ya taka a natse zuwa gaban widow da ke kallon titi. Yaye labule idanuwanshi suka sauka akan motoci da ke kai da komuwa. Shima Abdul-hakeem mik'ewa ya yi ya isa daff dashi kana ya dafa kafad'arsa. "Ka yarda dani Aj aure shine yafi dacewa da kai ka tuna kullum shekarunmu k'ara tafiya suke yi dole sai muna samun natsuwar da kwanciyar hankali, so ka ga kenan don ka k'aro aure ba wani abu bane. Allah yasani kayi hak'uri iya hak'uri da Salima lokaci ya yi da za ka d'and'ani zak'i da gard'i dake cikin aure" D'an gajere murmushi Azaad Junaid ya yi wanda ya tsaya iya fatar bakinshi, kana ya juya yana facing Abdul-hakeem. "To naji idan ma na amince zan k'aro aure wa zan aura?" Sani kanka ne Abdul tun daga lokaci da na auri Salima ko mafalki ban ta6a kallo wata 'ya mace naji ina sonta ba. Ta ya ya ka ke tunani zan yi aure?" "Mtsss...! Abdul-hakeem ya ja siririn tsaki da ke baiyanar da takaicinsa a fili. "Ba dole bane sai ka ji son mace za ka aure ta ba, kai da za ka yi auren huci haushi ina ruwanka da soyayya. Alhaji ka amince kawai ka ga aiki da cikawa ni da kaina zan nemo ma matashiyar budurwa wacce Nonuwanta suke tsaye cakk! Ka sha shagali abinka. Zaro idanuwa Azaad Junaid ya yi tamkar ya ga abin tsoro kana yasa dariya wanda rabon da ya yi irinta har ya manta. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A Free press 3.... Amrah na fita bata zarce a ko ina ba sai wani k'aramin super market, kamar za tayi siyaya sai da taga hankali mutane baya kanta. Ta dinga tsintar biscuits da Madara na sachet tana cusawa cikin zaninta batare da ta bari an ganta ba ta fice da mugun sauri. Gudun kada a ganota da fitarta ta kwasa da gudun bala'in ta nufi gida, cikin sa'a babu kowa a tsakar gida tai wuff! Ta shige d'akinsu kamar wacce aka jefo. Daga Aslamiyya har Amal sai da suka firgita domin a zatonsu ko Dadda ce. Kallo daya za ka yi wa Amrah ka gano bata da gaskiya sai wuk'i-wuk'i take da idanu kanta a k'asa ta k'araso cikin d'akin. Ta cire hijab tare da kayan da ta sato ta ajiye ta d'auki wani tsohon kofi wanda tun na aure mahaifiyarsu ne bata ce dasu k'ala ba ta fita gindin famfo ta nufa ta taro ruwa rabin kofi. Koda ta dawo d'akin Aslamiyya tana jujjuya biscuits da madara ɗin. "Ga ruwa ki k'adawa Amal madara ta haɗa da biscuit ko da na koma wajen mai koko ya k'are shine na siyo mana madara da biscuits sai dai na manta ban siyo sugar ba. Sai da na iso k'ofar gida na tuna. Tana magana Aslamiyya ta k'ure ta da manyan idanuwanta, sai da ta saki 6oyayyen numfashi kafin tace. "Ina kika sami kud'i Amrah?" Iya sanina naira hamsi muke dashi kin Kuma ri ga da kin siyo koko ya zube" "Keɗai miyya kin cika bincike wallahi" "Bincike dole ne Amrah banaso wani mugun abu ya faru daku saboda 6ata gari sun yi yawa mutane basu da imani. "Uhm...miyya ki dinga kyautata zato Abba Saleem ne ya bani kud'in wankau da nayi mu su na kwanaki, da basu biya ni ba. To shine Ina dawowa daga siye koko na haɗu shi a k'ofar gidanshi ya bani" "Amrah!" "Miyya!" Amrah ta kira sunanta kaman yadda Aslamiyya ta kira ta, har tana had'awa da turo baki. "Amrah idanuwanki sun nuna min akawai rashin gaskiya da kika yi faɗa min me kika aikata?" "Da zan shigo na haɗu da Baffa Sani a k'ofar gida nai kaman ban ganshi ba shine yaso ya dake ni dalili da yasa na shigo da gudu kenan baya ga wannan ban yi komi ba. "Ya yi miki kyau Amrah duk abun da na hane ki ba za ki hanu ba ko?". "I'm sorry mommana! Cewar Amrah tana rik'e k'unneta da hannunta daya yayin da ɗayan ke rik'e da cup. Miyya ta yarda da k'arya da Amrah ta shara mata dalili kuwa tasan tana bin bashin kud'in wankau gidan Maman Saleem. Sai kawai ta mik'a hannunta ta kar6i cup ɗin ta haɗa mu su madara, Amal ta fara ba wa tasha ta k'oshi saboda iya ruwan madara take iya sha. ********************** Sosai Azaad Junaid yake kyakyata dariya Abdul-hakeem ya rik'e baki yana kallonshi. Saboda shi bai ga abin dariya ba, da kyar ya yi controlled dariyar tashi, kana ya nufi water dispenser ya tsiyaya a handle cup ya sha fiyye da rabin ruwan. "You're insane Abdul in ban da kana mahaukaci ko zan yi aure sai na rasa wacce zan aura sai k'aramar yarinya?" Murmushi Abdul-hakeem ya yi kafin ya nufi kujera da ya tashi akai ya sake zama, ya dubi Azaad da girar ido a ɗage... "Gata nake so nai ma Aj ka samu ka more garar da muka dad'e muna kwasa" "Na yafe idan kana so mai nonuwan a tsaye ka nemi abarka, ni kuma nai maka alk'awari ni ne zan biya kud'in sadaki" "Wai gatse kake min?" "Miye abin gatse anan Abdul naga kaman ka fi ni buk'ata" Ya k'arasa magana yana gintse baki. "Shikenan Aj tun da ba ka so a yanzu amma nasan komai dare dadewa sai ka nemi hakan. "Allah ya tsare ni da abin kunya" "K'ara sunnah shine abin kunya?" "Ba haka nake nufi ba auren k'aramar yarinya ne ba zan iya ba. "Are you sure?" Abdul-hakeem ya faɗa yana murmushi. Sai da Azaad ya nemi daya daga cikin cushion ɗin da ke cikin office ɗin ya zauna, kafin ya furta. "Hundred percent sure! Har Abdul-hakeem ya yi yunk'uri sake furta wata magana ya katse shi ta hanyar faɗin "Please Abdul mu ajiye zance mai nonuwa a tsaye mu yi aiki da ke gabanmu" Daga haka suka shiga tattaunawa aKan contract ɗin da suke, aiki akai. Sai yamma lis suka rabu Azaad ya nufo gidanshi a downstairs parlor ya tarar da Nanny Lacey tare da Ahlam ke wasa da toys ɗinta. Airah tana Assignment princess Aneesa kuma tana d'akinta, tana chat da friends ɗinta. Nanny Lacey ta gaida shi ya amsa ta hanya ɗaga mata hannu, Airah ta ɗago tare da furta. "Welcome Daddy! Ita ma hannu ya ɗaga mata kamar yadda ya yi wa Nanny Lacey, kaitsaye ya wuce bedroom ɗinshi dake upstairs. Wanka ya yi ya shirya cikin dark blue ɗin jallabiya ya wuce masallaci sai da ya sallaci sallar isha sannan ya dawo gida ya shiga 6angaren Jadda koda ya mai aikinta Mero ya tarar a falo, Jadda tana bedroom ɗinta. Direct d'akin ya nufa tana zaune akan sallaya da casbi a hannunta, ya nemi gefen gadonta ya zauna. Cikin natsatsiyar muryarshi ya gaidata ta amsa mishi cikin kulawa. Kana suka zarce da fira sai ga Mero ta shigo da k'aton tray mai d'auke da tsadaddin warmers ta sauke a gabanshi, tasake fita ta dauko mishi lemo da ruwa. Jadda da kanta tai mishi serving tuwon semovita da miyar agusi taji tantakwashi da tsokar busasshe kifi. Sosai ya ci tuwon saboda shi mutum ne mai matuk'ar son abincin mu na gargajiya sai dai kashh! Allah bai had'a shi da wacce ta iya ba. Madam Salima ko ruwan zafi na shan tea bata da lokaci dafawa. Duk wata kulawa da ya dace ta ba wa mijinta housemaids ke yi mishi ga Azaad da shegen kyamkyami. Kuma gaba d'aya 'yan aikinta Christan ne ba Musulma ko d'aya, shiyasa Azaad ya k'auracewa abincin 6angarenshi sai dai ya zo na Jadda ya cika cikinshi. Bayan ya kammala cin tuwonshi hadda su taune k'ashi Jadda ta tsare shi da kallon tausayi, har sai yaushe Azaad zai zama cikakken mutum?" Domin a ganinta bai cika mutum ba rabin mutum ne, tayi iya k'ok'arinta akan ya k'ara aure abin yaci turo dole tana ji tana gani ta zuba mishi ido, duk da al'amarin iyalinsa yana ci mata tuwo a kwarya kullum cikin masa addu'a take Allah ya kawo mishi sauya. "Anya kuwa Datti wannan rayuwa da ka za6awa kanka za ta fishe ka kuwa?" "Jadda in-sha-Allah nesa ta zo kusa domin na sanar da Salima ta ajiye aikinta.... "Dallah..! Rufe min baki sakaran banza nusari kullum cikin faɗar haka kake yi har yau ka sa aiwatar da komi. Saboda haka na ba ka nan da wata uku ko ta ajiye aikinta ta cikakkiyar matar aure ta amshi ragamar kula da gidanta hannun arna. Ko kuma ni na nemo maka wacce za ta kula min kai da yaranka" "Ki yi hak'uri Jadda in-sha-Allahu ba ma zai kai mu da haka ba . "Sai ta Kai mu domin ba ajiye aikinta za ta yi ba ni kuma idan har ba mutuwa tai min sauri ba sai na auro ma 'yar mutunci mai nagartattaciya tarbiyya. "Ni dai ina k'ara ba ki hak'uri Jadda" "Hak'urin ka na banza da wofi, ka dai ji na faɗa ma wata uku na ba ka, idan ba haka ba k'arin aure ya zame maka dole. Ba kuma shawartarka nake ba ko jin ra'ayinka. "Jadda rigima Keɗai sam bakyaso a zauna lafiya mu ajiye wannan zance ki sha maganinki" Ya k'arasa magana tare da dauko mata ledar maganinta da ke aje akan bedside drawer, bayan tasha magani ya shafa mata na ciwon k'afa sannan ya koma 6angareshi. Har zuwa lokaci madam Salima bata dawo gida ba, Kuma tun fitar ta da safe. Dama haka take yi in tafita sai baba ta gani take dawowa dabi'unta sam ba su yi kama dana musu aure ba, tafi Kama da masu zaman kansu. D'akin yara ya wuce ya tarar da Airah tana game a laptop princess Aneesa, tana aikin nata na chat ganinshi yasa ko wace ta dakatar da abin da take yi. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A Free page 4.... Zaune suke a katafare falon farmhouse da ya kasance mallakin Alhaji Yusuf Junaid su taru ne kamar yadda suka saba taruwa a can baya. Domin gudanar da secret meeting ɗinsu. su 8 ne maza 6 mata biyu kowa ne fuskarshi a turbune da ka dube su za ka hango tsananin 6aci rai da suke ciki. Hakan ya samo asali ne da har yanzu sun kasa cimma dad'en burinsu akan d'an uwansu Azaad Junaid. D'aya daga cikinsu ne ya fara magana wanda da ganinshi yafi sauran mugunta da zafin rai, zuciyarsa na tafarfasa yace. "Tsakani da Allah nagaji da jiran gawon shanu, zuwa yanzu yaci ace mun shafe babin Azaad a ɗora k'asa kuna kallo dai yadda kullum k'ara daukaka yake yi dukiyarshi sai habbaka take yi kamar shuka ana zuba mata fertilizer mun kasa yi komai. Idan har dukanku kwakwalenku sun daina aiki ni zan sa ayi masa mai gaba d'aya haihuwa da hanji... "Dakata Ahmadu! Hajiya kubra ta katse shi a tsawace dama can kawarsu bata gamo ba, duk lokaci da suka haɗu sai sun yi uwar watsi. Ta ci gaba da faɗin "Kai miyasa ka cika fushi da daukar zafi?" Garin bak'ar zuciyar taka za ka iya kai mu ka baro kai mana shiru mu ji dalilin kiran gaggawa da muka samu daga babban yaya. "Ke Kubra ki shiga taitayinki dani nafi ki rashin mutunci wallahi... "Dallah ya isa haka ku kenan da zarar kun haɗu ba za ku ta6a rabuwa lafiya ba. Sai kun sai da hali. Alhaji Yusuf Junaid ne ya kawo k'arshen musayar yawun nasu. Ya ci gaba da faɗin. "Dalilin da yasa na me ganinku da gaggawa jiya ne Alhaji Buba ya zo min da labari wani shararren boka sha yanzu magani take. Aikinsa yana ci domin ya yi masa aiki cikin kwana uku buk'atarsa ta biya. Shine naga dacewar mu kai masa ziyara watakil adace ya kawar mana da Azaad. "Haba Yaya har yaushe za ku gano aikin bokaye nan duk k'arya da yaudara ne?" Kawai ku bar min wuka da nama ku ka aiki da cikawa 'yan ta'adda za nemo su yi mishi yanka rago. Hasheem ne ya yi magana yana hura hanci duk cikinsu shine mai k'anana shekaru. Alhaji Abdallah ne ya kar6e zance ta hanyar faɗin. "Kai dallah rufe mana baki idan har kai ba ka da hankali mu ba sakakkaru bane irinka, muddin muka sa aka kashe Azaad ta wannan hanya jami'an tsaro ba za su yi shiru ba, za su tsananta bincike kasancewar Azaad babban mai kud'i. Nan take za a gano mu. Saboda haka mu gwada zuwa wajen bokan ya kashe mana shi." "Shikenan Babban Yaya gaba ɗayan mu, mun amince gobe da sassafe sai mu shirya mu tafe k'auye da boka yake. Da wannan shawara suka kawo k'arshen secret meeting ɗin nasu. ********************** "Aneesa ina so ki bani aron kunnenki, ki saurare abin da zan faɗa. Azaad ya yi magana fuskarshi a daure tamau.. "Tam Daddy! Aneesa ta faɗa tare sadda kai k'asa tana wasa da wayar hannunta. "Daga yau mai kama da rana ta yau Kar ki sake bari na kama ki da laifi rashin ɗa'a a school ke ba iya school ba ko a gidanan naji labari kin ma wani daga cikin housemaids rashin kunya, za ki sha mamaki irin hukunci da zan zantar akanki. A dalili abin da kike yi aikatawa ga Airah nan ta fara koyi da halinki. Haka ku ke so rayuwarku ta dinga tafiya a baud'e?" Idan har ita mahaifiyarku bata damu tarbiyyarku ba, ni hakke ne da ya rayata a wuyana, da izzini ubangiji sai inda k'arfina ya k'are." Tun daga lokaci da ya fara magana har ya dasa aya bata ɗago ba jikinta sai rawa yake yi, saboda duk iya shegenta tana bala'in tsoran mahaifinta. Ta ɗago kanta da kyar bakinta na rawa tace. "Kayi hak'uri Dadda in-sha-Allahu na daina ba zan k'ara ba. "Da yafi miki. Ya faɗa a takaice kana ya juyo kan Airah wacce tuni tsoro ya gama bai-bayeta, dama tasan za a yi haka daga zarar ya gama da Aneesa kanta zai dawo. "Ke kuma da kike koyi da Aneesa miye abin burgewa a cikin halayenta da har za ki koya?" To bari ki ji duk irin hukunci da zan zantarwa da Aneesa kema irinshi zan maki. A matuk'ar tsorace Airah take kallon shi, har idanuwanta sun fara kawo ruwan hawaye. "Daddy Don Allah ka yi hak'uri ka yafe min sharrin shaidan ne. Ta k'arasa magana kamar za ta fashe da kuka, ya nemi kusa da ita ya zauna, a natse ya shiga yi musu nasiha ya kuma saka Aneesa ta rubuta apologies letter gobe ta kai school ɗinsu, sai around 9:40pm ya fito daga d'akinsu. Ya sauya kayan jikinsa zuwa na barci, ya dauko laptop ɗinshi ya yi switch on yana da online meeting sai misali k'arfe 11:30pm ya kammala yana cikin rufe laptop ɗin ya ji horn tara da k'arar buɗe gate, da sauri ya baro daga wajen zaman shi ya ye labulle widow ya lek'a ya hango madam Salima ta nufo cikin gida tana tafiya kamar bata kashi. Sosai ran Azaad ya 6aci yanzu fissibillahi matar arziki ce za ta fita tun safe sai dare za ta dawo. Zance na gaskiya ya kamata ya yi wa kanshi karatu ta natsu, idan har Salima ta kafe ba za ta bar aikinta ba. To tabbas kuwa zai bi shawarar Abdul-Hakeem da Jadda ko don saboda rayuwar 'ya'yanshi. Ya murzawa k'ofar d'akinshi key ya kwanta yasan ba nemanshi za ta yi ba. Da safe ma ta ri ga shi fita sosai hakan ya k'ara harzuk'a shi duk da hakan ba bakon abu bane a wurinshi. Cike da haushinta ya isa company. ***************** Koda safiya ta waye hannun Aslamiyya ya kumbura sumtum sai azabar ciwo yake mata, daren jiya ko runtsawa bata yi ba. A haka Dadda ta saka ta aikin gida Amrah kuma tai sammako bari gida ta tafi nemo musu abin karin kumallo. Koda Aslamiyya ta fito daga band'aki ta sace jiki ta fita. Tsintsiya ta dauko da ɗayan hannunta mai lafiya ta shiga sharar tsakar gida Dadda kuma ta kasa ta tsare sai antaya mata zagi take. "Yi maza ki kammala shara ki zo don uwarki arniya ki min wanke-wanke don ni babu ruwana da ciwon hannunki shegiya yarinya tsatso kafurai. Sosai zagi ya k'ona mata rai duk ta saba jin iri-irinsa daga bakin Dadda amma zuciyarta ta kasa sabawa, duk lokaci da tai musu irin zagin sai zuciyarta ta buga. Kuka take yi har hawayenta su na diga a floor. Da Amrah ta fito daga gida yau bata je super market ɗin jiya ba, sai ta nufi wani provision store kasancewar safiya ce babu mutane sosai a shagon sai kawai ta nemi gefe ta tsaya, kamar tana jiran wani sai kawai taga mai shagon ya fito da sauri da waya a kunnenshi tana gani ya fita ta afka shago ta dauko k'aton bread ta cusa cikin hijabinta, dai-dai mai shagon ya shigo ashe lokaci da ta shi ga shagonshi ya ganta shiyasa ya dawo. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A Free Page 5.... Koda Aslamiyya ta kammala shara zuwa lokaci ta jigata matuk'a, ga yunwa ga azabar zogi da hannunta ke yi kamar zai tsinke. Duk da halin da take ciki bata fasa tattaro tulin wanke-wanke wanda ba na Dadda Kaɗai bane hadda na surukanta. Tun daga lokaci da ta fara wanke kwanuka har ta kammala kuka take yi idanuwanta sun yi luhu-luhu. Amrah tai ido biyu da mai shago da ya tare k'ofar fita, gabanta yai mummuna faɗuwa gani yadda mutume ya murtuk'e fuska ya haddasawa cikinta murd'awa. "Ke! uban me ya shigo dake shagona?" Yadda ya daka mata tsawa yana zare ido ta daburce ta rasa abin faɗa jikinta ya fara mahaukacin rawa. Gani haka ya fahimtar dashi bata da gaskiya musanmman da ya shiga K'are mata kallo ya ga hannuwanta cikin hijabinta tana kiciniya 6oye wani abu. "Menene a cikin hijabinki me kika sata fito dashi don ubanki?" Kusan tare ya watsa mata wad'annan jarin tambayoyi, tsora ne ya k'ara lullu6eta,ta tabbata yau dubunta ya cika, mai kwatar ta hannun wannan mutume mai zubin samudawa sai Allah. Ta shiga yawo da idanuwanta lugu da sako na shagon ko Allah zai sa taga hanyar fita kafin ta gama dube-dubenta ta ji an finko ta da k'arfi bai tsaya wata-wata ba ya cire mata hijab sai ga bread sakade a hamanta ta. Ta saki bread ɗin ya fado k'asa. "Don Allah malam kayi hak'uri wallahi ba halina bane yunwa da rashin gata yasa ni na sata maka bread... Tun kafin ta k'arasa magana ya kifa mata mari, wasu jajayyen taurari suka ma-maye ganinta cike da rashin imani ya shiga jibgarta kamar ya sami sa'anshi. Ya sukunce ta ya fito da ita waje yana mata ihun 6arauniya kafin kace kwa6o wurin ya cika da mutane yara 'yan makaranta sa'o'inta sai kallonta suke yi. Baki da hancinta na zubda jini Amrah bata k'ara shiga tashin hankali ba sai da taga mutume yana faɗawa mutane wai ko jiya ya gannta ta shigo mishi shago tana fita, ya nemi kud'insa dubu d'ari ya rasa saboda haka ta fito mishi da kud'insa ko ya mik'a ta hannun 'yan sanda. Sosai take kuka tana mishi magiya mutane da ke kallo abin da ke faruwa sai la'anta ta suke yi, gata k'aramar yarinya ace tana sata. Tana ji tana gani ya kwashe ta zuwa police station, tana kallonshi ya ba wa 'yan sanda statement ɗin k'arya wai ta sace mishi dubu d'ari. Ba tare da duba da k'aranci shekarunta ba suka jefa ta bayan kanta, cikin muryarta da ta disasshe saboda kuka tace. "Ku dubi girman Allah ku yi min rai wallahi azim ban d'auki kud'insa ba. Biredi na sata kuma tun a shago na ajiye mishi abinsa... "Ke! Rufe mana baki 6arauniyar banza da wofi daga ni idanuwanki za ki aikata, iri-irinku ne idan kun girma ku ke zama shararrun 'yan ta'adda. Wani dogon d'an sanda ne ya ke magana har yana nuna ta da kulkin hannunshi. Tun Amrah tana kuka da hawaye har ta dawo kukan zuci ga yunwa na nukurkusar hanjinta ga d'an banza duka da tasha hannun mutumen. Ga kuma tsoro shigowar ta hannun police domin abu ne da bai ta6a faruwa da ita ba. Duk k'anana sace-sace da take yi cikin gidaje da shaguna ba a ta6a kamata ba. ******************** Madam Salima tare da k'awarta Hafsat Shinkafi a office ɗinta dake cikin kamfaninta, asalin Hafsat 'yar jahar zamfara ce aure ne ya kawo ta Kano mijinta ya rasu ya barta da yara 4 bata sake yi aure ba, a ganinta aure zai ta kura ta ya hanata neman kud'i, duk wani gantali neman duniya tare suke yi abinsu. Dabi'unta da na Madam Salima sak iri daya babu ban-banci shiyasa k'awance su ya yi armashi. "Salima duk laifinki ne sau nawa ina faɗa miki ki fitar da yaranki k'asar waje su yi karatu za su fi samun cikakken kulawa, dukiyar nan Allah ya ba ki ita kullum cikin nema kike kina tarawa, to miye amfaninta idan 'ya'yanki ba su sakata sun wala ba?" Sai da Madam Salima ta shak'i iska kana ta fesar ta k'ofufin hancinta kafin tace. "Ba wai nak'i shawara ki bane Hafsat kema kinsan kafiya da taurin kai irin na Azaad, ba zai ta6a bari yaranshi su yi nesa da gida ba. Yanzu ɗin ma kullum a cikin tuhumata yake akan tarbiyyarsu. Ina gaya miki jiya da haukar shi ya motsa cewa ya yi sai na ajiye aikina ko uban me zan sama idan na zauna gida?" "Whats! Ki ajiye aikinki?" "Wallahi kuwa haka ya faɗa. Sai dai ko kusa bushak'insa bai yi tasiri akaina ba. "Zance na gaskiya Salima ki tashi tsaye domin sare-sarin hauka zubda miyau. Na fahimci manufar Azaad guda biyu ne dole ɗaya daga ciki ya kasance gaskiya na d'aya kodai so yake ya rusa ki yana bak'in ciki da yadda duniya ta fara haska tauraronki. Saboda ya ga kin fara kamo k'afarshi a arziki shine yake so yai miki k'afar ungulu. Na biyu Ko so yake ya k'aro aure.... "Dallah ya isa Hafsat haka! hasashen ki ne ya ba ki hakan. Azaad ba haka yake ba, kawai dai yana so na kar6i ragamar kula da gidana saboda yaranmu sun fara girma.... "Matsalarki kenan Salima har yau kin kasa buɗe idanuwanki ki fahimci gaskiya, kin yarda da Azaad ɗinan shi kuma Sam bai yarda dake ba, kin d'auki soyayyar duniya kin ɗora mishi shi Kuma ya gaji da zama dake duk wannan salo ya fito miki da shi ne saboda kin kasa haifa mishi d'a namiji wanda zai gaje shi, shiyasa ya fito miki ta wannan sigar "No....no... please Hafsat don't say that me ya kawo zance haifar namiji da rashin haihuwarshi?" Kar ki saka min shakku akan mijina mana. Ina miki korafi ne akan rashin jituwa da muke fuskanta a koda yaushe ke kuma kina neman shigowa da wani sabon al'amari. "Ba sabon al'amari bane Salima kece kika kasa gano hakan da kanki, ki yarda dani Salima akwai k'amshin gaskiya a cikin abubuwan da na lissafa miki. Shi zama yake yi ne gida naga kullum yana yawo a sama kamar tsuntsu yau yana wannan k'asar gobe yana waccan. Ko kuma ke Kaɗai Allah ya dorawa nauyin tarbiyyar yara?" Ki yi amfani da kwa-kwalwarki mana. Har Hafsat ta dasa aya a zance ta idanuwan Madam Salima na lumshe tana girgiza kanta, ta d'auki lokaci a haka kafin da sauri ta buɗe idanuwanta gabanta na mugun faɗuwa mik'ewa tayi da sauri tare da harde hannuwanta a k'irji sai ta kai bangon farko na office ɗinta ta dawo na k'arshe. Hafsat sai bin ta da kallo take gani safa da marwanta ba mai k'arewa bane yasa ta mik'e ta kamo hannunta "calm down k'awata.... Ta fincike hannun nata da k'arfi ta ja da baya tana wani girgiza kai, cikin kaushin murya tace. "Kina faɗar min mijina zai k'ara aure kuma kina gaya min I should calm down as how Hafsat tell me as how??" "Ni ban ce dake zai k'ara aure ba kawai I'm trying to get your brain clean up" Ajiyar zuciya tayi ta dako cike da izzarta da tak'ama ta iso gaban Hafsat ta dafa kafad'arta, tace. "Hafsat a rayuwata abu biyu nakeso neman kud'i da Azaad. Haka zalika abu biyu na tsana talauci da kishiya. Ki sani Azaad ba shida ra'ayi mace fiyye da d'aya haka zalika yana matuk'ar so 'ya'yanshi fiyye da son da ni nake musu, bai ta6a nuna min yana son haifar ɗa namiji ba. Da mace da namiji there are all equal to him ko yanzu ya bijiro da zance ajiye aikina a dalilin dambe da Aneesa tai da schoolteacher ɗinsu. Saboda haka tun wuri mu ajiye wannan zance, kafin maganganunki su yi tasiri a zuciyata" "Kenan kin amince za ki bi abin da yake so za ki mika ragamar kamfaninku ga 'yan uwanki, burinki na mallakar kamfanin ke Kaɗai ya bi iska?" Yatsine fuska tayi kana cikin zallan izgilanci tace. "Bari ki ji Hafsat ko ubana Kabir Dala da shine silar arziki na ace zai baro lahira ya zo duniya ya nemi na ajiye aikina billahil-azim ba zan masa biyayya ba, balle wani Azaad Junaid da yake tamkar steering mota sai yadda na juya shi. Lokaci ɗaya suka kwashe da dariyar shek'inyaci tare da tafawa, Hafsat ta shiga kod'ata tana zuba mata kirari. ****************** Fitowar Azaad Junaid da Abdul-hakeem Daura daga meeting wayar Abdul-hakeem tai ringing, ya ɗaga tare da k'arawa a kunnenshi. Muryar k'anwarshi Zainab ya ji tana rera kuka. "Will you shut up and tell me what exactly happened?" Shiru ya yi yana sauraren bayani da zainab take mishi, ya shiga furta "Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Zainab sau nawa zan faɗa miki ki daina tafiya mai nisa ba tare direba har sai kin kwarewa da driving, da yake kunnen k'ashi ne dake ki ka k'i ji. Shi Kenan ganina zuwa" Ya kashe waya ya mayar da dubanshi kan Azaad wanda ya tsare shi da idanuwa. "Zainab ce ta kirani wai ta buge wani d'an acha6a tana police station. "Subhanalillah....Allah yasa da sauk'i ka je kawai za mu yi waya" Cikin sauri Abdul-hakeem ya fice kaitsaye police station ɗin ya nufa, cikin yarda Allah d'an acha6a bai ji ciwo sosai ba machine ɗinsa ne ya yi damage cikin k'ank'ani lokaci Abdul-hakeem ya biya kud'in machine ɗin ya kuma yi bail ɗin K'anwar sa. Tun yana cikin office ɗin inspector ya ke ji kukan Amrah da magiyar da take wa 'yan sanda.... *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A 6.... Aslamiyya ta mik'e zubur ta nufi k'ofar gida, wannan fitar da tayi shine karo na shidda. Da taje k'ofar gida tayi tsaye tana kallon hanya ta ina Amrah za ta 6illo. Tun fitarta take jin matsananci tsoro haɗi da faɗuwar gaba. Ta je makota inda take sa ran gani Amrah yafi a kirga gashi Kuma tana tsoro ta fita daga unguwa zuwa nemanta, ta bar Amal ita Kaɗai saboda yanayi jikinta. Abin ka da ruwa-ruwa babu juriya sai afki kuka, lokaci zuwa lokaci take sharar hawaye gashi tun safe babu abinda suka ci, inda Allah ya taimake ta akwai raguwar sachet daya na madarar da jiya Amrah ta sato, ta k'adawa Amal. Da batasan inda za ta nemowa Amal abinda za ta ci ba. Sake komawa tai cikin gida tana shiga d'aki ta tarar da Amal zaune, da alama yau jikin nata da sauk'i jiki a sanyyaye ta zauna kusa da Amal k'ok'ari take ta 6oye mata hali da ake ciki. Saidai kashh! Tuni Amal ta gano damuwar da take ciki ga kuma idanuwanta da suka nuna tayi kuka. "Meke faruwa Miyya naga kamar kina cikin damuwa?" "Ba komai. Ta faɗa a takaice tare da kauda kanta tana kallon bangon d'aki. Amal ta matsa daff da ita ta kwantar da kanta aKan kafad'arta cikin sanyi muryarta mai kama da Aslamiyya sak tace. "Miyasa za ki 6oye min Miyya bayan ga idanuwanki nan sun nuna kin yi kuka?" "Amal tun safe da Amrah ta fita bata dawo ba. Wani irin fargaba haɗi da tsoro ke damuna. Ina tsoro kada wani mummuna abu ya sameta. Ta k'arashe magana tana hawaye. A hankali Amal ta sauke ajiyar zuciya kana tace. "Ki kwantar da hankalinki da yarda ubangiji ba abin da zai same ta. in-sha-Allah za ta dawo cikin k'oshin lafiya. "Allah yasa! Aslamiyya ta faɗa tana goge hawayen fuskarta. *************** Cakk.... Abdul-hakeem ya tsaya Yana kallon Amrah wacce ke ta faman rusa kuka, duk da yadda wani tsamurarre constable ke mata tsawa da hargagin ta rufe mu su baki ko ya maketa da kulkin hannunshi. Bata fasa kuka da magiya ba. Ya dawo da ganinshi akan inspector Sa'eed wanda rashin gaskiya ya baiyana 6aro-6aro akan fuskarshi. Gaba d'aya ya rud'e sai wani kame-kame yake yi. "Ranka ya dad'e sata tayi shine aka kawo ta nan. "Waye ya kawo ta, me kuma ta sata?" "Wani mutum ne yace kud'insa ta sace har kimani naira dubu d'ari, yarinyar tana da kafiya da taurin kai, tak'i ta faɗi inda ta 6oye kud'in" D'an murmushi gefen baki Abdul-hakeem ya yi. "Gaskiya inspector ba kasan aikinka ba wannan k'aramar yarinya ce za ta iya satar dubu d'ari?" "Ranka ya dad'e haka mai shago ya faɗa. "Kai kuma da yake kidahumi ne sai ka yarda. Kafin inspector Sa'eed yai magana Amrah ta riga shi ta hanyar cewa. "Wallahi-tallahi Abba ban d'auki kud'insa ba. Biredi na dauka kuma ya kar6e abinsa, Don Allah Abba ka taimake ni yadda Allah ya taimake ka, fitarda ni wurinan. Sosai Abdul-hakeem ya k'ure mata idanuwanshi babu ko kyaftawa, kyakkyawar yarinya fara tass...a shekrunta na haihuwa ba za ta zarce goma sha biyu zuwa sha uku sa'ar Sadiq ce second born ɗinsa. Tausayin ta ya yi mishi dirar mikiya, sai kawai ya rufe police ɗin da faɗa kaman zai dake su musanmman inspector Sa'eed, kasancewar D.P.O baya nan shine babba a wurin. Kamata ya yi ya tsananta bincike haka kawai daga kawo mishi 'yar mutane ya k'argame ta. Sai Kiran mai shago aka yi da ya zo shima ya rudewa ya yi gani attajirin mai kud'in da ya tsawa Amrah, daga k'arshe sai faɗan gaskiyar al'amarin ya yi. Ya dawo yana ba wa Amrah hak'uri. "Ka ga irinta ko inspector yanzu ina za ku da hakki yarinya nan kun zalince ta ba Kaɗan ba?" "A yi hak'uri Ranka ya dad'e sharrin shaidan ne. "Rufemin baki ba wani sharrin shaidan so zuciya ne da kar6a cin hanci da har abada ba za ku bar shi ba. Ke zo mu tafi Allah ya saka miki, yadda suka yi miki Allah yai musu haka nan. Jikin Amrah yana rawa ta fito daya daga cikin constable ya mik'a mata hijabinta da slippers, ta saka da sauri Abdul-hakeem ya rik'o hannunta har sun kai bak'in k'ofar fita, ya juyo ya dube su yana faɗin. "Maganar nan ba wai ta k'are iya nan ba, ku jira abin da zai biyo daga baya. Daga mai shago har inspector cikinsu ya hau k'ugi da mugun sauri suka bi bayan Abdul-hakeem, wanda ya har ya kai wajen da ya yi parking motarsa. "Ranka ya dad'e Don girman Allah kayi hak'uri ka rufa mana asiri" Cewar inspector har yana durkusawa k'asa. Amrah ta dubi Abdul-hakeem da kumburarrin idanuwanta tace. "Abba ka yafe musu dukkansu na fiso laifi domin da na bi nasihar da Miyya take min a kullum da hakan bata faru dani ba. Ta k'arashe magana wasu zafafan hawaye masu zafin gaske, suka gangaro saman kuncinta. Jikin Abdul-hakeem yai sanyi ya kalle inspector da har lokaci ya ke a durkushe. "Shikenan ku tashi ku tafi Allah ya so ku tana da kyakkyawar zuciya ta yafe muku da sai na koya maku hankali. Godiya suka shiga yi masa bai bi ta kansu ba ya buɗewa Amrah backseat ta shiga, saboda har lokaci takaicinsu bai k'arashe sakinsa ba. Zainab dake front seat wacce tun a police station bata furta uffan ba sai lokaci ta Sami damar waigawa gefen da Amrah take tace. "Ya sunanki wacce unguwa kike?" "Sunana Amrah a kawo nake. "Ke kuwa me ya kai ki satar biredi?" Shiru Amrah tai ta rasa amsar bata sai kawai ta shiga wasa da yatsu hannunta. "Amrah ki yi magana mana? A wannan karon Abdul-hakeem ne ya yi magana. Cikin zazzak'ar muryarta tace. "Saboda ba mu da abin da za mu ci nida 'yan uwana. "Ina iyayyenki?" "Abbana ya rasu tun Ina da 2yrs mamanmu kuma naji Dadda tace bayan mutuwar Abbanmu ta gudu tabar mu nida twins sisterna da Yayata Miyya, wacce ita ce take kula damu tun baya da muka rasa iyayyen mu. K'arfaffiyar ajiyar zuciya Hakeem ya yi sosai tausayinta ya k'ara lullu6e shi. Cikin sanyi murya yace. "Ina dangin mahaifinku dana mahaifiyarku da za su bar ku da yunwa Amrah za su iya kula da ci da shan ku, ba sai kin yi sata ba?" ""Hannun kakarmu wacce ta haifi Abbanmu muke ita kuma bata sonmu. Kullum cikin gana mana azaba take, dangin mahaifyarmu kuma ba musan su ba. Asalima ba musan gari da suke ba. Tsabar rud'ani da Hakeem ya shiga yasa ya kasa magana Zainab ce tai k'arfin halin cewa. "Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Ki ka ce mahaifiyar Abbanku, ke kuwa Amrah me ku ka aikata mata har haka da ta tsane ku. "Saboda Abbanmu ya aure mahaifiyar mu ba da saninta ba sannan kuma mahaifiyarmu ba Musulma bace. "Amrah wannan ba hujja bace da za ta dogaro da ita har ta tsane ku, ai ba laifinku bane na mahaifinku ne saboda shine ya yi mata ba dai-dai ba. Kuma babu inda addinin musulunci ya yi hani da aure wacce ba Musulma ba. Kawai dai kakarku muguwa ce azzaluma sai Allah ya yi muku sakay.... "Ya isa haka Zainab! Hakeem ya katse mata numfashi daga haka ba wanda ya sake magana a cikinsu, wani super market ya tsaya ya yi wa Amrah shopping na kayan tea da bread haɗi da indomie har dasu chocolate cake da biscuits. Tun a farkon layin unguwarsu tace ya sauke ta bai ce komai ba, ya yi parking ta fito shima fitowa Amrah tai mishi godiya har ta juya ya kira sunanta ya fito da shopping bags da kwalin indomie ya ajiye a gabanta bai ce komai ba ya shiga mota har ya yi reverse sai kuma ya tsaya ya kira ta, da ta zo ya mik'a mata card mai d'auke da phone numbers tare da company address ɗinsa. Ta koma wajen tulin kayan da ya ajiye mata ta ɗora kwalin indomie aka ta d'auki shopping bags, ta nufi gida sai da ta fara lekawa tsakar gida kamar yadda ta saba ta ga babu kowa tai wuff ta shige d'akinsu kasancewar su ne a farkon shigowa... ***************** Yau ma da wuri Azaad Junaid ya shigo gida, sai da ya lek'a 6angare Jadda saboda ya zame mishi al'ada duk dare sai ya je yaci abinci a wajenta sannan yake dawowa apartment ɗinsa. Sai da ya duba lafiyar yaranshi kafin ya nufi nashi d'aki, yana cikin online meeting ya ji an turo k'ofar d'akinsa. Ko bai ɗago ba yasan ko wacece ke da zarar shigo mishi d'aki a dai-dai wannan lokaci, shiyasa bai damu da sai ya kalli wanda ke shigowa ba. Cikin dakon k'assaita da nuna ita ɗin wata ce ta shigo ba ko sallama sai wani yatsina da take yi, sai uban k'amshi na fitar hankali dake fita daga jikinta sanye take da sleeping gown wacce ta sauka izuwa gwiwarta, cike da izza haɗi da tak'ama ta nemi gefen gado ta zauna. Ta ɗora k'afa daya kan daya, har ta zauna bai da niyar ɗagowa ya kalle ta balle tasa ran za tanka mata. Ta aika mishi da malalacin kallo, mai nuni da batasan darajarsa ko Kaɗan ba. Wani sai kad'awa k'afafuwanta take yi. Cikin gadara tace. "Azaad inaso nai magana da kai please can I have your attention?" Ya ci gaba da magana da yake da colleague ɗinsa da suke online meeting yai banza da ita, hakan ba k'aramin sosa mata rai ya yi ba. Abin ka da mai hurt temper har ta harzuk'e. "Da kai nake magana Azaad ka yi wani kunnen uwar shagu dani. kuma san na tsani ina magana ayi banza dani, kai kuma abin da ka fi kwarewa dashi kenan. Ta k'arashe magana cikin ɗaga murya, da sauri ya yi disconnected video call ɗin tare da rufe laptop ɗin. Gudun kada hankali colleague ɗinsa ya dawo kanshi har su fahimci abun da ke faruwa, A tsanake ya ɗora manyan idanuwanshi masu masifar daukar hankali akan kyakkyawar fuskarta da batada make up amma sai glowing take abinta. Yayin da hasken blue colour bulbs dake d'akin yana k'ara haskaka fuskarta ta, ya jefa mata kallon nan nashi mai sanyi da kashe jiki tare da faɗin. "Me kike nema a bedroom ɗina a dai-dai wannan lokaci?" "Na zo ne muyi magana akan sauyawa Aneesa school d'azu na aika P.A ɗina ya je school ɗinsu su ya kar6o min transferring letter ɗinta, sai ya dawo min da zance wai kayi magana da principal Aneesa za ta ci gaba da karatu a school ɗinta har da saka Aneesa ta rubuta apologies letter for what reason za ta ba da hak'uri?" "Tunda ta fara magana idanuwanshi ke kafe akanta babu ko kyaftawa yayin da wani tuk'uk'in bak'in ciki haɗi da takaicinta suka mishi dirar mikiya a karo na ba adadi, saboda ba yau ne ranar farko da ya fara jin hakan akanta ba... *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A Free page 7.... Ido biyu Amrah tai da Aslamiyya kallon tuhuma ta bin ta dashi har tasauke kwalin indomie da ke kanta, bata dauke idanuwanta daga kanta ba. Tana jin lokaci da Miyya ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta buɗe baki a rud'e ta ce. "Subhanalillah....Amrah me same ki ne naga fuskarki da idanuwanki a kumbure?" Amrah ta sadda kai k'asa idanuwanta suka ci-ciko da hawaye tasan asirinta ya ri ga da tonu babu saura 6oye-6oye, cikin muryar kuka ta zube gaban Aslamiyya. "Don Allah kiyi hak'uri ki yafemin miyya nasan abin da na aikata ban kyauta miki ba, wallahi na tuba ba zan k'ara satar kayan kowa ba.... A matuk'ar tsorace Aslamiyya ta finciko kafand'unta ta mik'ar da ita tsaye. "Na shiga uku Amrah sata fa kika ce?" Amrah ta gyada kanta saboda kukan da yaci k'arfinta ba zai bata damar buɗe bakinta ba. "Kin cuceni Amrah kin yaudare ni wato ba gidan Maman Saleem kike zuwa tayata aiki ba, sata kike fita wayyo ni Miyya wacce irin rayuwa Amrah ta jefa kanta?" "Ban cuce ki ba Miyya asalima ina yi sata ne domin kare mutuncina sau uku Baban Saleem, yana yunk'uri lalata min rayuwa da taimakon ubangiji nake samun na kwace kaina. Haka ma gidan Maman Bobo sau babu adadi Bobo yana ta6a min k'irji. Na 6oye ban faɗa miki ba gudun kada ki shiga tashin hankali. Tun daga lokaci na daina shiga gidajen jama'a sai dai na bi shaguna na sato mana abin da za mu ci" Da sauri Aslamiyya ta rungume Amrah tana wani irin gunji kuka, kamar ranta zai fita. Amal da ke kwance sai kallonsu take tana shar6a hawaye. Bayan Amrah ta tsagaita da kukanta, ta shiga ba Miyya labarin taimakon da Abdul-hakeem ya yi mata. "Allah yasaka mishi da masauki a gidan aljanna firdausu! Ina gargadinki Amrah daga yau kar ki sake ta6a kayan kowa ba tare da sanin mai abu ba. Sata babban kask'anci ce tana zubar da mutunci da k'ima tana rusa darajar mutum a idanu jama'ar duniya, duk hali da muke ciki mu dogara da Allah sai ki ga ya kawo mana mafita ba tare da dabarar mu ba. "Na daina wallahi ba zan sake ba. Ai naga aya in-sha-Allah babu ni ba sata har abada" Aslamiyya ta sauke ajiyar zuciya tare da zaunawa kusa da Amal. **************** "Azaad da kai nake magana fa" Sai da ya sauke zazzafan numfashi kafin ya ce. "Saboda ni ne mahaifin Aneesa ni ke da cikakken iko akanta ba ke ba. "Wow! Thats good to hear that from you Azaad ashe kasan da haka ka keso rusa min career, ka ke so ka hana min business ɗina, Wato abin naka mugunta ne ko?" Ta k'arashe magana tana ɗage girar idanuwanta, da ka kalle shi za kasan cewa he's deeply in hurt babu komai a cikin zuciyarshi sai takaici da bak'in ciki how long zai ta kasancewar cikin wannan takaici da 6acin rai?" "Salima! Ya kira sunanta cikin zazzak'ar muryarshi ma'abociya sanyi, duk yadda ranshi ya kai da 6acin ba kasafai yake nunawa ba. Sai dai ya 6oye shiyasa duk ranar da aka kaishi mak'ura hukunci da zai dauka sai ya girgiza mutum, shiyasa bai cika yanke hukunci nan take ba saboda kaifi d'aya ne. "Ina da hak'uri Salima kema kinsan da wannan, kada ki yi amfani da hak'uri na ki yi min yadda kike so hakan ba dai-dai bane Salima ki tuna ni fa mijinki ne uban 'ya'yanki..... "Dallah ya isa! Ni ba wannan ne ya kawo ni dakinka ba, ka nace aKan lallai sai Aneesa ta yi karatu a school ɗin da banaso okay fine naji amma inaso kasani idan har zan zantarwa da hukunci akan yara ka nuna min ban isa ba, har kana faɗin kafini k'arfin iko akansu to hakan na nuni da babu amfani ka cilastani mik'a ragamar dukiya ta a hunnun wani. Don haka na faɗa da babbar murya ba zan ajiye aikina ba. "Shikenan naji abin da kika faɗa amma inaso ki sani ba cilasta ki nake ba umarni ne a matsayina na mijinki, idan har ke ba ki min biyayya ba. Nima babu amfani na bi son ranki. Saboda haka ki bi yanda ranki yake so nima na bi nawa anan za a tantatace waye gaba tsani ni da ke. Cikin izgilanci ta kece da dariyar reni, kana ta mik'e tsaye tana tafa hannuwanta, ta dube shi a wulak'anci ta ce. "Babu abin da za ka iya Azaad tun yaushe kake wannan 6a-6atun da cika baki, sai fa ka gama wannan cika bakin naka ka dawo kana rarrashi da bani hak'uri. "Shikenan naji Salima duk abin da za ki faɗa go ahead ba zan hanaki ba. Domin ban isa ba amma inaso ki rubuta ki ajiye ni Azaad Junaid sai na shayar dake zallan ruwan mamaki.....oya fita min daga d'aki I don't want any arguing with you just go and do what you want. "Zan fita dama ban shigo ba don in zauna d'akinka amma kafin in fita inaso ka dawo min da passport ɗina da ka d'auke na nema kaura wambai ban ganshi ba. Na kuma tabbatar kaine ka d'auka ka dawo min da kayana domin tafiyata babu fashi. "I say get out of my room before I loose my control.... "I'm not going anywhere until you return my passport. A fusace ya mik'e ya buɗe closet ɗinshi ya zura hannun cikin aljihun coat ɗinshi, ya ciro passport ɗinta ya jefa mata. "Ga tsiyar ki nan dauka ki fita min daga d'aki" "Hakan ya fi ma alkhairi da kunnu wutar da ba ka da ruwan kasheta. Ta faɗa tana wani shegen blushing na reni ta sunkuya ta d'auki passport ɗin, ta fice abinta cikin yanayi ko a jikina. Kasa ci gaba da meeting ɗin ya yi zuciyarsa sai tafarfasa take yi tabbas lokaci ya yi da zai nunawa Salima shi ba su-su bane kamar yadda ta dauka, sai yasaka ta nadama a bisa kowa ne furuncinta. Da wannan bak'in cikin nata ya kwanta. **************** *AFTER TWO DAYS*{BAYAN KWANA BIYU} Yau ne ya kasance ranar tafiyar Salima kasancewar morning flight za ta bi, batada niyar faɗawa Azaad tafiyarta saboda dama haka ta sabar mishi za ta bar k'asa batare da saninshi ba, sai ta isa k'asar da za ta sannan ta kira shi. Wani lokaci ma sai ta share wasu kwanaki kafin ta kira shi. Nanny Lacey janye da luggage ɗinta ita kuma tana biye da ita jikinta sanye da wide legs trouser tare belted top ta ɗora long black frock jacket ta yane kanta da multiple colour scarf, k'afarta sanye da kitten heel na company Hermes hannunta na dama rik'e da bolide handbag ita ma ta company hermes ɗin ne ga k'amshin designer perfumes dake fita daga jikinta. Cikin tafiyarta ta izza da tak'ama take saukowa daga stairs, dai-dai lokaci da Azaad ya fito daga 6angare shi zai shiga gem room suka haɗu ta dauke kanta tana mai ci gaba da kashewa Nanny Lacey gargadin ta kula da gida. Sosai jikinshi ya yi sanyi wato da gaske sai Salima tayi wannan tafiya da bayaso a natse ya kira sunanta gani batada niyar kula shi. "Salima! Kamar ba za ta tsaya ba sai kuma ta tsaya ta waigo fuskarta, a murtuk'e gudun kada yaga damarta ya kawo mata wargi. "Ina za ki je da sanyi safiya?" "Duk inda zan je is none your business please stop wasted my previous time to your silly questions. Ta juya kawai ta ci gaba da tafiya, ajiyar zuciya ya yi tare da fesar da zazzafar iska daga bakinshi ya biyo ta a baya a parking lot ya tarar da ita har ta shiga mota ya dafa k'ofa, da sauri ta kalle shi saboda bata ta6a tunani zai biyo ta ba. "Ina rok'onki a karo na ba adadi ki fasa wannan tafiya duk abin da kike so zan miki Salima. Ina da tarin dukiya mai yawan gaske miyasa za ki dinga wahalar da kanki?" "Saboda inaso nai building ɗin nawa future ba na dogara da kai ba. "Ke mace ce Salima wannan yawo bai Dace dake ba. "Kaine kake gani rashin dacewar shi" "Ina k'ara rok'onki da ki janye wannan tafiya" "Ba zai yu ba saboda na jima ina neman wannan opportunity ba kuma Zan yi wasa dashi ba. "Shin zan iya biyanki makudan kud'i domin ki yi handling business dinki ga siblings dinki, ki zauna gida ki kula min da kanki da yarana?" "Ba kud'inka nakeso ba ko wata k'addara taka ba nawa nake nama gumin jikina nakeso Kai ma kasan da wannan Azaad?" "Me kike nema Salima wallahi-azim zan miki, ni dai burina ki jinginar da wanna yawace-yawace da kike yi da sunan business ki zama full housewife" "You're dreaming Azaad. "I'm not Salima please accept my offer. "Wallahi-tallahi ba zai yu ba Ina business ne ba don komai ba sai don na tara tawa dukiya, babban burina nayi suna a duniya inaso a lissafa sunana a cikin mata masu kud'in duniya, saboda haka kabarni na tafi kana 6ata min lokaci a banza. "Shikenan Salima Allah ya tsare ya kai ki lafiya ya ba ki abin da kike je nema. Ni kuma Allah ya musanya min abin da na rasa Allah yasa wannan tafiyar taki ta zame mana buɗewar k'ofufin alkhairi ina miki fatan samun nasara a rayuwarki. Daga haka ya juya yayin da yake ji kamar zai kife k'asa sakamakon wani duhu da ya lullu6e wa ganinsa, tafiya kawai yake batare da yasan inda yake jefa k'afarshi ba. Yana wucewa Salima ta ja tsaki. "Mtsss.....aikin banza naga uban da ya isa ya hanani tafiya. Adaddafe Azaad Junaid ya isa master bedroom ɗinshi, ya kwanta akan tangamemen gadonshi. Zuciyarsa na wani irin bugawa a duk lokaci da ya tuna da irin hukunci da ya tanadarwa Salima indan har tai wannan tafiya. Gaba d'aya yini ranar a d'aki ya yi shi zazza6i mai zafin gaske ya lullu6e shi, bayan ga coffee ba abin da yasawa cikinsa. Gashi yana da very importance meeting sai Hakeem ya kira ya wakilce shi. Kusan kwana sa biyu a gida tare da yaranshi ko compound bai fita ba. Sai a kwana na uku ya fita office yana zaune a office ɗin nashi damuwa ta taro ta mishi yawa. Abdul-hakeem ya shigo d'auke da wasu files a hannunshi a natse ya shiga k'are mishi kallo ya rame sosai har ramar tashi ta baiyana k'arara akan kyakkyawar fuskarshi. "Aj wai meke damunka ne, ni fa ban yarda da wannan rashin lafiyar nan taka ba gaba d'aya ka sauya bakada wal-wala da kuzari sai d'an banza tunani ka faɗa min menene ke haddasa maka shiga wannan hali?" Sai da Azaad ya ja gwaron numfashi kana ya shafa kwantattace sajenshi, ya dauko d'aya daga cikin wayoyin shi ya danno wani ke66en folder batare da ya yi magana ba ya mikawa Hakeem. Jikinshi a sanyyaye ya kar6i wayan ya shiga karanta abin da ke rubuce, tun kafin ya k'arasa karatu ya ɗago a firgice yana kallon Azaad Wanda ya kauda kanshi yana kallon wani gun dabam. "Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Cewar Hakeem yana faɗa yana k'ara nanatawa gaba d'aya ya dimauce ya gigice har yana k'ok'arin fita daga hayyacinsa...... *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A Free page 8... Tsabar d'imaucewa da Hakeem ya yi yasa kasa tsayuwa akan kafafuwanshi, da sauri ya ja kujera dake fuskantar Azaad ya zauna. Sai ya yi yunk'uri furta magana bakinshi ya dinga kakkarwa, da kyar ya yi control ɗin kanshi ya sami damar furta. "Why Aj?" Shiru Azaad ya yi har zuwa lokaci bai d'auke hannunshi daga kan sajenshi ba, sai faman sha-shafa shi yake yi tamkar shafar ce za ta rage mishi radadi da k'unci da yake ciki a karo na biyu Hakeem yasake watsa mishi tulin tambayoyi. "Miyasa Aj, miyasa ka yanke irin wannan danye hukunci, miyasa ka bari shaitan ya rinjaye ka, ka yanke hukunci cikin fushi nasan Kuna matuk'ar son junanku Kai da Salima miyasa za ka sake ta alhali sakin zai iya cutar daku?" "Ba a ciki fushi na yanke wannan hukunci rabuwa da Salima ba Hakeem. Nayi iya k'ok'arina nagani hakan bata faru a tsakaninmu ba, amma tak'i bani haɗin Kai. "Amma sai nake gani kamar hakan bai dace ba Aj akwai hanyoyi da za a magance wannan matsala, ba wai sai lallai wannan da ka bi ba. "Hakeem na bita na rarrashe ta duk da ni nake da cikakken iko akanta amma kamar k'ara ingizata ake yi. Idan har nace zan cigaba da hak'uri da Salima menene makoma ta da yarana?" Salima ta za6i neman duniya fiyye da igiyoyin aurena. Shin Salima ita Kaɗai ce mace da ba zan rayu ba sai da ita?" "Ba Kaɗai bace Aj shiyasa tun farko na zo maka da shawarar Karin aure... "Ya isa Hakeem aikin gama ya riga ya gama babu saura komai a tsakaninmu domin text ɗin ka karanta tun ranar da ta bar k'asar nan, na turo mata a hali yanzu inaso na nemowa kaina farin ciki da narasa tun ganiyar kurciyata. Nima inaso na zama sarki a cikin fadar gidana, idan nace ayi sai ayi idan nace abari abi umarnina ba wai ni na bi ba. "Aj ni aganina ko don albarkaci yara bai kamata ka saketa ba. "Me take tsinanawa yara dukansu babu Wanda yasan dad'inta ita da babu duk daya yake a wurinsu, rabuwarmu ba abin da zai shafe su dashi. "Shikenan Allah yasa shi yafi zama alkhairi Allah ya musanya maka da wacce tafi ta wacce za ta kawo farin ciki a rayuwarka. "Amin thumma amin! Nagode Sosai da wannan addu'a taka Hakeem. in-sha-Allah rabuwarmu za kawo wani haske a rayuwata Ina jin hakan a jikina. Shiyasa na yanke shawara zan yi aure kafin ta dawo kuma na mik'a maka ragamar nemo min mata wacce ta fito gidan tarbiyya 'yar mutunci wacce za ta mutunta ni da yarana. Murmushi Abdul-hakeem ya yi farin cikinshi ya kasa 6oyuwa, ya taso da sauri ya rungume Azaad tare da furta. "Al-hamdu-lillah! Al-hamdu-lillah! Allah kaine abin godiya. Azaad ya janye shi daga jikinsa ya mik'e tsaye tara da saka hannuwanshi cikin aljihu, ya yi tattaki izuwa gaban fridge sai kuma ya tsaya tare da juyowa ya dube Hakeem kana ya ce. "Banso budurwa bazawara za ka nemo saboda za ta fi kulawa da yarana" Take annurin kan fuskar Hakeem ya gushe, ya dube shi da baki sake. "Amma wallahi Aj kai wawa ne, banda wawanci uban me za ka tsinta a jikin bazawara sauran wani. "Uban da ake tsinta a jikin kowa ce mace. "Look abokina kar ka 6ata goma biyar bata gyaru ba, kabar komai a hannuna wallahi-tallahi zan nemo maka wacce tafi dacewa da kai, in ma bazawarar ce ko budurwa muradinka dai 'yar mutunci mai ingantattaciyar tarbiyya. Azaad ya ja iska ya fesar daga bakinsa ba tare da yasake tankawa Hakeem ba, ya nufi k'ofar fita da sauri Hakeem ya bi bayansa. ****************** Zaune suke a gaban wani k'aton mushirinki boka wanda bashida kyau gani, ko Kaɗan. Wata katuwar kwarya a gabanshi mai d'auke da ruwa farare tass...sai tafarfasa suke alhali ba a kan wuta suke ba. Wani yare yake yi mai kama da buzanci can kuma ya tsaya da tsoki burutsunsa, kafin ya tattaro hankali da natsuwarsa akan Alhaji Yusuf Junaid tare da k'annesa uku da ya zo tare dasu don ayi komai akan idanuwansu. Sai kuma Alhaji Buba wanda shine ya yi musu jagoranci zuwa wajen bokan. Cikin muryasa mai amon sauti ya fara magana. "Tuni aka sanar dani zuwanku miyasa ku kayi gareje tun lokaci ba ku zo ba sai yau?" Alhaji Yusuf Junaid ya gyara zaman babban rigar shi, ya ce. "Tafiya ba zata ce ta zo min zuwa Abuja sai jiya na dawo. Shiru boka ya yi yana ta bin su da jajayyen idanuwanshi, kafin ya ɗaga gefen buzun fatar daminsa da yake zaune akai, ya dauko wata katuwar layya, ya jefata cikin kwayar a hankali layya take nutsewa cikin ruwan har nutse duka kana ya dawo da ganinshi akansu ya ce. "Kun zo nan ne domin kashe d'an uwanku Azaad Junaid, kun je wajen bokaye da malaman tsinbo bila'adadin amma ba ku yi nasara ba?" "Haka ne.... Ahmadu ya faɗa a hanzar ce. "A yau dad'add'e burinku zai cika ni nan zan cika muku shi amma a bisa sharadin, za ku biya naira miliyan uku za ku kawowa aljanu jini jariri sabuwar haihuwa, sai kuma shanu manya guda bakwai. Kafin Alhaji Yusuf Junaid ya yi magana Ahmadu ya riga shi ta hanyar cewa "Idan har za ka kawar mana dashi fiyye da abin da ka lissafa za mu yi maka mu dai burinmu, mutuwar Azaad Junaid domin ita Kaɗai ce hanyar da za ta sada mu da mafalkinmu. Boka ya kece da dariya mai kama da kukan aurakin jaki, sai da ya yi mai isarshi kafin ya ce. "Tabbas yau burinku zai cika ku zuba idanu ku sha kallo. Jefa hannunshi cikin ruwan yana jujjaya shi tare da kiran sunan Azaad Junaid, ba a d'auki dogon lokaci ba hotonshi ya baiyana a cikin ruwan yana tsaye ya kare waya a kunnenshi yana magana, boka ya dauko wata karamar wuka da ganinta za tai mugun kaifi ya dubi saitin zuciyar Azaad ya caka sai kawai Aslamiyya ta baiyana a gabanshi kafin wuka ta ta6i jikinta wuta ta kama kwaryar hatta da wukar dake hannun boka ci take da wuta, duk iya k'ok'arinsa naso ya jefar da ita ya kasa hannunshi sai ci yake da wuta da ya ji uwar bari ya zabura da gudu bala'in ya fita daga bukkarshi. kamar jira ake bokan ya fita kwaryar tai wani irin tsalle ta dire kasa ta tarwatse, wuta ta kama bukkar, su Alhaji Yusuf Junaid suka kwasa da gudu suka nufi k'ofar fita gashi k'ofar karama ce, sai tu-ture juna suke, da kyar Ahmadu ya samu ya ture Alhaji Buba da ya yi ba-bakere a jikin k'ofar shi bai fita bai kuma janye ba. Ahmadu yana samu ya ture shi gefe ya fice Alhaji Abdallah ya biyo bayan Ahmadu, har Alhaji Yusuf Junaid ya yunk'ura ya tashi daga faɗuwar da ya yi saboda lokaci da Ahmadu ya ture Alhaji Buba shi kuma ya faɗa masa, suka faɗi kasa a tare sai dai wani abin mamaki ya kasa tashi kamar wanda aka danne, shi ma Alhaji Buba ya gwada tashi ya kasa, su Ahmadu dake wajen bukkar sai ihu da neman agaji suke abin ka da dokar daji babu wanda zai ji su balle ya kawo musu d'auki. Alhaji Yusuf da Alhaji Buba su na ji su na gani wuta ta fara cin jikinsu, sai ihu suke tun su na ihu har suka sulele k'asa, bukkar kuma ta Kama gaba d'aya...... *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A Second to the last Free page 9... Los Angeles international airport {LAX} A tsakiyar dare jirgin da ya dauko su Salima ya yi landing a los Angeles international airport. Tsakiyar dare ne amma sai kamar lokaci safiya ta waye, Salima tana gaba Hafsat Shinkafi tana biye da ita a baya. Cab suka hau zuwa Roosevelt hotel wanda tun kafin zuwansu k'asar suka yi booking. Hotel ne mai mugun tsadar gaske Kuma a cikinsa ne za a gudanar da seminar da suka zo. Seminar ce ta manyan mata 'yan kasuwa na duniya duk wata gwaska Wanda ta amsa sunanta international business women tana wajen hatta da ticket ɗin shiga wurin idan ka ji makudan kud'i da ake siye ta sai ka girgiza, tun saukar Salima k'asar wayarta ke rufe. Tana zaune a room ɗinta jikinta sanye da bathrobe towel fitowar ta daga wanka kenan. Ta d'auki system ɗinta, ta shiga duba sak'oni email, anan taci karo da sakon Azaad Junaid a maimakon ta girgiza ko ta rud'e sai ma wani shegen blushing take, wanda ke nuni da ko Kaɗan sakinta da Azaad ya yi bai dame ta kawai dai tayi mamaki inda ya sami kwarin gwiwar rubuta mata message na saki har biyu. Ta kudurta a ranta bata saku ba domin a ganinta Azaad bai isa ya yanke hukunci shi Kaɗai ba ita ma tana da ikon ya ji nata ra'ayinta idan ta amince su rabu idan ta amince, shikenan sai ya saketa amma ba wai ya yi gaban kanshi ba. Sam bata amince wannan rabuwar ba. Saboda haka ta ci gaba da sabgoginta a dalili ta d'auki saki a matsayi shirme yasa ko sanar da aminiyarta Hafsat ba tayi ba. *************** Aslamiyya tare da Amrah su na duk'e a gindin famfo sai darza uban wanki suke yi, yau tun da asuban fari suka k'arya kumallo da wankin kayan Baffa Sani. Tuni Baffa ya daina kai wanki sai dai su yi masa, abin takaici gashi da gardawan 'ya'ya maza sai dai su Miyya su masa ba zai saka 'ya'yanshi ba. tsabar mugunta sai ya tara kaya da yawan gaske yake saka su wanki gashi yawanci tufafinshi duk babbar riga ne. Tun da asuba yana dawowa daga masallaci ya tisa su a gaba, duk sanyi da ake tsulawa bai dame shi ba ga ruwan tanki sun yi mugun sanyi kamar na fridge Amrah tana tsoma hannunta a ruwan taji mugun sanyi ya ratsa k'asusuwanta, ta fara you wa Baffa Allah ya isa miyya tana ji ta amma bata ce uffan ba. A haka suka ci gaba da wanke kayan sai wuraren karfe biyu suka kammala, zuwa lokaci sun gaji likisss..... Aslamiyya ta jik'a musu indomie da Hakeem ya siya musu su na cikin ci indomie ɗin suka ji muryar Dadda tana kwada musu kira. "Aslamiyya, Amrah uban me ku ke yi kunshe a d'aki ku fito maza ga nawa wanki na fito dashi, shegu yara marasa son aiki" Da sauri Aslamiyya ta fito jikinta sai rawa yake yi, Allah ya saka mata tsoro tsiya a rayuwarta Amrah kan zamanta tai tak'i fitowa, daga k'arshe sai Miyya ce tai wanki. Da taga akwai raguwar kumfa ta dauko nasu kaya ta zuba a ciki tana cikin wankewa Dadda ta fito, tana kyala ido taga Miyya tufafinsu ne take wankewa, ta fara surfa mata zagi. "Eh! Lallai Aslamiyya kin nuna min ke isasshiya ce nasaki wanki ki haɗo har naku, saboda ga sabulun banza ko?" Jikinta ya d'auki kyarma sai kakkarwa take yi, cikin muryarta mai cike da tsoro tace "Dadda wallahi ban saka sabulunki ba ruwan kumfa ne kawai ga ma raguwar sabulunki can na kai miki, k'ofar d'aki..... Sai da Dadda ta sakar mata bak'ar harara kafin ta shiga zazzaga mata ruwan masifa. "Rufemin baki shegiya yarinya tsinaniya wacce ta tsotsi nonon kafurci, shegu gur6attaci. Zo nan don uwarki arniya. Ta k'arashe magana tare da ya fito ta da hannu, tuni Aslamiyya tafara kuka, Amrah ce ta fito daga d'akinsu tana faɗar "Haba Dadda,! Wai me muka tare miki a duniya ne kullum sai kin k'ikk'iro da hanyar da za ki musguna mana, dad'in abin ba ki da wuka kankare zamowar mu jikokinki, saboda haka kema kina da had'i da jinin arna. Amrah ta k'arashe magana tana murguda baki. "Iyeee.....Amratu ni ki ke yiwa rashin kunya?" "Ba wani rashin kunya Dadda gaskiya ce na faɗa, kema ai kin zama arniya saboda abin da kike yi wani arne ba zai yi irinshi ba. Amrah bata gama rufe baki ba Dadda ta wawuro tsintsiya da nufi dukanta, Amrah tana ganin ta nufo wajenta ta 6alla da gudu tayi k'ofar gida, sai kawai ta dawo kan Miyya. "Ke kuma daga yau duk abin da kika san nawa ne a gidanan karki kuskura ki ta6a shi, yadda na tsani mutuwata haka na tsaneku. Ta k'arasa magana tare da fyadawa Miyya tsintsiyar aka, Aslamiyya ta durkusa k'asa tare da ɗora hannuwanta bisan kai, tana gunji kuka. ******************** Alhaji Yusuf Junaid tare da Alhaji Buba suka kone kurmusss.....a cikin bukkar boka, Alhaji Abdallah da Ahmadu sai ihu suke har bukkar ta cinye duka sai toka kawai da gawawakin su Alhaji da suka yi bak'i k'irin.... kamar an babbaka awakai. Boka kuma da ya zura da gudu ya shiga jaji, wuta da keci a hannunshi sai dad'a k'aruwa take yi a maimakon hannunshi yanzu kuma duka jikinsa ke ci da wuta, tun yana iya gudu har k'arfinshi ya K'are ya faɗi. Kamar fashewar bomb haka boka ya fashe naman jikinsa ya tarwatse gunduwa-gunduwa abin zallan tashin hankali. Alhaji Abdallah da Ahmadu basu k'ara shiga tashin hankali ba, sai da wuta ta mutu suka ga gawawakin su Alhaji kuka suke yi babu mai rarrashin wani daga k'arshe Ahmadu ya jawo motar da suka zo da ita suka tattaro gawawakin suka zuba sai k'auri ke tashi, tsawon rayuwarsu ba su ta6a ci karo da mutuwar mai tashin hankali iri wannan ba. Duk lokaci da suka tuna da musanbabin mutuwar tasu sai tashin hankalinsu ya k'ara linkawa. Gashi kuma ba su san me za su faɗawa iyalai su ba. Gara ma Alhaji Yusuf jininsu ne watakila abin ya zo musu da sauk'i sa6ani Alhaji Buba da yake 6are kuma fitattce d'an siyasa 'yan adawa za su iya cewa an had'a baki dasu sun kashe shi. Kaitsaye farmhouse ɗin Alhaji Yusuf suka nufo inda suka saba yi secret meeting ɗinsu har suka iso basu sami kwakwarar dabarar da za su yi ba. Sai kawai suka kira abokan kullin tugunsu, dukansu sun tsorata da jin afkuwar al'amari ko wane su fuskarshi ta bayyanar da firgici da yake ciki ga dai babbakakin gawawaki zube cikin mota sun rasa yadda za su yi dasu. Can Hasheem ya ja dogon fasali kana yace. "Ku bani aron hankalanku inaso ku sani muddin sanadin mutuwarsu ya bayyana, mu ma kashinmu ya bushe, Kuma ba lallai bane iyalinsu su yarda da labari yadda suka mutu ba. Saboda haka ku bar min komai a hannuna. "Sai ka faɗa mana dabarar taka mu ji?" Cewar Hajiya Kubra wacce ita da Alhaji Yusuf da Alhaji Abdallah uwarsu d'aya. A natse Hasheem ya shiga koro musu bayani plans ɗin nashi, take suka yi hamdallah tare da amincewa. *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{ The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten Takun Haske Batch:A Last Free page. 10... A cikin dare mummunan labari ya riske iyalan Alhaji Yusuf Junaid tare da na Alhaji Buba sun yi mummunan accident, sun kone kurmusss.....ga baki daya iyalan sun shiga tashin hankali musanmman da suka ci karo da gawarwakinsu. Wannan duk shirin Hasheem ne su kansu 'yan uwanshi sun yabawa basirarsa matuk'a, tun a cikin daren mummuna labarin ya riske Azaad bawa Allah duk yabi ya rikice duk k'iyayyar da 'yan uwanshi ke nuna mishi hakan bai hana shi k'aunarsu ba. In ka ganshi sai ya ba ka tausayi kuka yake yi sha6e-sha6e da hawaye. A washe gari aka yi jana'izzarsu jama'a sun taro sosai, abinka da manyan mutane. A duk lokaci da Ahmadu da Alhaji Abdallah suka yi arba da Azaad sai gabansu ya yanke ya faɗi, wani irin mashahurin tsoronshi ya shige su, shiyasa duk inda suka ganshi zaune ba su zama a gun, gani suke kamar yana sane da abin da ya faru. Tun daga ranar da aka fara zaman makoki Azaad Junaid ya d'auki nauyi kawo abinci da za a ci haɗi da lemo har ma da ruwan sha, daga wani tsadadden restaurant ake kawowa. Bayan an yi sadakar bakwai kowa ya kama gabanshi sai raguwar 'yan uwa na jiki. ******************* A tsakiyar dare ciwon Amal ya tashi yau kuma da sabon safuri ya zo, don kuwa sai aman jini take, kakarin amanta ne ya tashi Miyya da Amrah a gigice Amrah ta kunna bulb haske ya gauraye d'akin kan shinfid'arsu duk ya 6aci da jini hakan ba k'aramin ɗaga musu hankali ya yi ba. Miyya sarkin kuka tuni hawaye suka wanke mata kuncinta. Yayin da numfashi Amal sai ya yi sama ya dawo kasa, Amrah ta buɗe k'ofa haɗi da fallawa da gudu ta nufi d'akin Dadda ta shiga knocking tana kuma kiran sunan Dadda. Dadda tana cikin mutane da basuda nauyin barci duk k'ank'anta motsi akan k'unneta, tun fara buga kofar ta ji ta sarai kawai biriss...tai da ita. Duk dauriya irin na Amrah sai da ta fashe da kuka, tasake ficewa da gudu ta nufi 6angaren Baffa Sani tashiga dukan k'ofa kamar za ta karyata a bisa dole Baffa Sani ya taso ya buɗe mata, tun kafin ta sanar dashi dalilin knocking ɗinta ya d'auke ta da bahagon mari, ya kuma shiga surfa mata zagi. "Ka ga 'yar iska yarinya bashin uwarki naci da za ki dinga gana min azaba ta hanyar duka min k'ofa a sulusili dare?" Duk da taji zafin marinta da ya yi hakan bai san ta fasa faɗar. "Baffa ciwon Amal ne ya tashi yau har da aman jini take yi..... "Amal ɗin taci uwarta ba aman jini take yi ba Allah yasa ta amayar da 'yan hanjinta ba abin da ya shafe ni maza 6ace min da gani tun kafin na murd'e miki wuya. Amrah ta fashe da matsananci kuka ta durkusa, tana rokon Baffa magiyarta ya taso da mai d'akinsa Habiba, cikin murya wanda aka katsewa barci ta ce. "Wai meke faruwa ne Alhaji?" "Nida 'yar banzar yarinya nan ce Amrah wai Amal ce batada lafiya shine don tagadi iskanci gaba da baya take min wannan mahaukacin knocking. "Mtss..... lallai Alhaji Amrah ta rena ka banda reni Ina ruwanka da rashin lafiyar Amal da za ta katse mana barci. Baffa Sani ya yi kwanfa tare da maida k'ofarshi ya rufe ruff.....dole Amrah ta tashi ta dawo d'akinsu. Aslamiyya na d'auke da kan Amal a cinyarta har zuwa lokaci numfashinta bai dai-daita ba. Sai kawai suka saka Amal gaba su na rera kuka, sai zuwa asuba Amal ta daina gurnani da take yi kamar wacce tai barci, sai kawai Aslamiyya ta shinfid'eta ta fita waje ta dauro alwala, ita ma Amrah alwalar tayo suka yi sallah su na kammala sallah Amrah ta dubi Aslamiyya ta ce. "Miyya bai dace mu bar Amal haka ba kamata ya yi mu kai ta asibiti, saboda tun da take ciwo nan bata ta6a aman jini ba. "Nima nayi wannan tunani Amrah saidai zuwan namu bai da amfani saboda komai sai da kud'i, mu kuma ba mu dasu. "Duk da haka Miyya mu gwada kaita zai fi da mu barta gida tana sha wuya . "Shikenan je ki nemo adaidaita bari na canza mata kayan jikinta duk sun 6aci da jini. Daga haka Amrah ta fice jefi-jefi take haɗuwa da mutane unguwa saidai ba wanda ya ce da ita kazal.....tana tsaye a bakin titi har gari ya fara haske bata samu adaidaita ba, kamar daga sama taji an anbace sunanta. "Amrah me kike neman da sassafe nan akan titi?" Da sauri ta waiga sai kawai taci karo da fuskar mutume nan mai shago da ta yi wa satar bread, cikin sanyi murya ta gaida shi ya amsa kana ta faɗa mishi dalilin fitowarta da taimakonshi ta sami adaidaita, ya kuma biyota zuwa gidan nasu tashiga gida suka fito da Amal lokaci da za su fito da ita Dadda tana tsaye a k'ofar d'akinta ta kalle su ta watsar. Lokaci da suka fito da Amal kamar matatciya, sosai Bello mai shago ya tausaya musu saboda tun ranar da al'amari nan ya faru tsakaninsa da Amrah ya yi nadama. Ya kuma kudurta a ranshi duk ranar da ya haɗu da ita zai taimaka mata kuma ya rok'e ta gafara, shiyasa yana ganinta ya biyo ta. Kaitsaye Nassarawa hospital suka wuce da ita a emergency, kasancewar dama ko acan baya anan ake kawota. Har zuwa lokaci Bello mai shago yana tare dasu, hatta da katin gani likita shi ya biya musu k'udi, bayan likita ya duba ta ya basu zungureriyar takarda, mai d'auke da list ɗin magunguna da drip haɗe da allurai da za su siyo. Amrah ta kalle miyya a hankali ta ce. "Bari naje Bello yana jira na a waje mu siyo magani ki kula da ita yanzu nan zan dawo" "Amrah waye wannan mutume da mu ka zo tare dashi?" Miyya ta aika mata da tambaya tare da tsare ta da idanuwanta. Ajiyar zuciya Amrah tayi kafin ta faɗa mata waye shi. "Amrah bakinsan mutume nan ba bai kamata ki yi sauri yarda dashi ba. "Nasani Miyya amma dole ce tasani yin hakan amma nai miki alk'awari kula da kaina in-sha-Allah ba zan yi abinda zai ta6a martaba ba. "Shikenan ki je amma ki faɗa masa duk abinda ya kashe mana dangin kud'i, rance ne za mu nemo mu biya shi daga baya. Amrah ta fito waje rik'e da prescription, da tunani ina za ta nemo kud'i saboda k'arya ta yi wa Aslamiyya na cewa za su je siyan magani ita da Bello domin tun a wajen siyen kati suka rabu dashi. Kafin ya tafi ya bata dubu biyu. Tana fitowa daga asibiti pharmacy ta wuce aka buga lissafi kud'in magani kusan dubu ashiri da biyu da d'ari bakwai, gashi dubu biyu ce da ita duk yadda taso su kar6i dubu biyu ɗin su bata Koda drip da allurai ne in ta kawo ciko kud'in su bata raguwar magani, amma suka k'i daga k'arshe korar kare suka yi mata, kusan saida ta yawace duka pharmacy dake wajen har ta sadakat....sai ta tuna da complementry card ɗin da Hakeem ya bata da sauri ta nufi bakin titi ta tari adaidaita sai gida, a gigice ta shiga gida, ta tararda Dadda zaune a tsakar gida, ko kallo bata isheta ba. Ta shiga d'akinsu a gaugauce tafara neman card ɗin, tasha bak'ar wahala kafin ta gano inda ta ajiye. Ajiyar zuciya ta sauke yafi a kirga da ta gano card ɗin. Da gudu ta fito Dadda sai kwalla mata kira take, a tunanina ko Amal ta mutu ne shine dalili shigowar Amrah a rikice ta kuma sake ficewa a firgice, Amrah tana jin duk kira da take mata tai banza da ita. Wayar d'an adaidaita ta ara ta shigar da number Abdul-hakeem, lokaci da kiranta ya shigo wayar shi yana tare da Azaad Junaid su na tattaunawa aKan zance neman matar aure da yasa Hakeem ɗin ya nemo masa, tai ringing har ta tsinke Hakeem bai ɗaga ba. Amrah ba ta hak'ura ba sai mai-maita kira take, can taji an yi picking tasa kuka cikin muryar kuka ta ce. "Don Allah ina magana da uncle Hakeem ne?" "Shine wacece? "Amrah ce yarinyar da a kwanakin baya ka yi bailing ɗinta a police station" "Subhanalillah..... Amrah lafiya me kike yi wa kuka Allah yasa ba satar ce kika k'ara yi ba?" Cikin shasshekar kuka ta faɗa mishi dalilin kira nashi da tayi, sosai tausayinta ya lullu6e shi tsabar tausayawa ko sallama bai yi wa Azaad ba ya fita, da mugun speed ya iso Nassarawa hospital ya ma ri ga Amrah isowa yana tsaye ya hangota da sauri ya nufi wajenta. Ya kar6i prescription ɗin ya je ya siyo magunguna ɗin sannan suka dunguma zuwa emergency, sosai mamaki ya lullu6e Aslamiyya na gani Amrah tare da wani babban mutum, nan take aka wuce da Amrah d'aki na musanmman likitoci suka dukufa akanta. Cikin hukunci ubangiji numfashinta ya dawo normal. Tun zuwan Hakeem asibiti yake kallon Aslamiyya, dai-dai da second d'aya bai d'auke ganinshi daga kanta ba. Har sai da Miyya tagano da kanta yana kallonta duk sai ta bi ta tsalgu. Sai kawai ta shige bathroom tai zamanta a ciki, gani haka yasa fita ya siyo musu abinci sai da ya tabbatar da ya yi musu duk wani abu ya dace kafin ya wuce gida. ***************** A washe gari ya sauya musu asibiti zuwa ta kud'i, Al'awwab spine care shine private hospital ɗin da Hakeem ya kai Amal. Asibiti ne mai tsadar gaske suna da kwararu likitoci har da turawa dama ciwon zuciya ne ke damunta an haife ta da hole a zuciya{rami} wanda tun haihuwar ta ya kamata ayi mata surgery amma rashin gata ya hana. Tana girma ne ramin yana k'ara girma shine dalili da yasa ta fara aman jini. Ba tare da 6ata lokaci ba Hakeem ya biya milliyan goma da aka buk'ata ranar Miyya tasha kuka domin abinda suka yi shekaru suna nema sai gashi Allah ya kawo Hakeem rayuwarsu, babu haɗin iya balle na Baba yai musu. Cikin yarda ubangiji aka yiwa Amal surgery kuma ana sa ran nasara. Satin su biyu a hospital ko kare bai zo ba daga dangin mahaifinsu babu kuma wanda ya damu da sani hali da suke ciki. Kullum addu'ar Dadda Allah yasa sun shiga duniya kenan bata fatan su dawo mata gida. Sosai Amal ta sami sauk'i ta murmure kamar ba ita ba hatta da jikinta ya fara dawowa, har zuwa lokaci Hakeem da matarsa Zaliha ke dawainiya dasu, Zainab K'anwar Hakeem ke taya Miyya kwana Amrah Kuma ta koma gidan Hakeem da zama Lokaci da Zaliha ta ji labarinsu sai da ta zubda hawaye, shiyasa ta d'auke su tamkar 'yan uwanta na jini. Kusan kullum indan Hakeem ya zo asibiti sai Miyya tai mishi godiya, baya cewa uffan saidai yasaki mata k'ayatattace murmushi. A sati na uku aka yi discharge ɗin su kai tsaye Hakeem ya nufo gidanshi dasu Sosai hakan ya daurewa miyya kai, tana da kawaici shiyasa bata tambaye shi dalili kawo su gidanshi da ya yi ba. Zaliha ta ware musu d'akinsu dabam.....an k'awata shi da komai na more rayuwa, sai suka tsince kansu a cikin wata sabuwar rayuwa wacce ba su ta6a mafalkinta ba. Yau satinsu biyu a gidan tuni su Amal da Amrah sun zama 'yan gida musanmman da ya kasance Rayham second born ɗin Hakeem sa'arsu ce. Miyya ce Kaɗai ta kasa sakin jikinta, a kullum burinta su bar gidan duk da bak'ar wahala da suke sha a hannun Dadda ta gwamaci su koma can domin nan ne asali da tunshe su. A wani yammaci ne Miyya da Zainab su na zaune a d'aki, Rayham ta shigo ta sanarda Miyya Daddy yana kiranta. Nan take ta ji wani matsananci faɗuwar gaba, ta saka hijabinta. Lokaci da ta shigo falon faɗuwar gabata ya tsananta har wani duhu-duhu take gani. Da fuskar Baffa Sani ta fara cin karo yana zaune yasha babbar riga brown colour, sai kuma Dadda wacce tun da tashigo ta kalleta ta watsar. Cikin sanyi murya tai sallama Hakeem tare da Zaliha suka amsa mata, ta nemi sama center carpet ta zauna murya can k'asa ta gaida Baffa da Dadda ba wanda ya amsa mata a cikinsu. Kaitsaye Baffa Sani ya fara faɗar abin da ya kawo su. "Aslamiyya dama mun zo ne domin mu yarda kwallon mangwaro mu huta da kuda, tun daga ranar da Usman ya bijerewa mahaifinmu ya auro uwarki muke d'and'anar bakin cikinsa, sanadin bakin cikinsa mahaifinmu ya rasa ranshi, a duk lokaci da na kyala ido na ganku ji nake kamar na kashe ku. Kwatsam....sai ga wannan bawar Allah ya zo mana da zance aurenki dama muna neman kai dake shiyasa babu 6ata lokaci na amince yau ɗinan aka daura miki aure, Kuma ina mai tabbatar miki daga ke har shegun k'anneki banaso ko kusa da katangar gidana na ganku. Ku sa aranku wannan shine danginku dama can shegiyar yarinya nan Amratu ta sha faɗar ke ce uwarsu ke ce ubansu, yanzu kuma ga dangin kun samu. Da sauri Miyya ta ɗago idanuwanta da babu komai a cikinsu sai tsoro, ta kafe Baffa dasu ji take kamar wani yare ne yake mata ba hausa ba........ *TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪 *ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION* *TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.* *INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR* *IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D* *WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN* *WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎* *NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄* *ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈* *KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY* *AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU* *TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU* KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER* SHIRIN YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA* SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA* *ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.* *DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S* GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal. *GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A* *SAI YA TURA KUDINSA TA* 2083371244 Zenith Bank Aisha M.Salis *Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar* +447894142004 *Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼* 07043079282 *Shaidar biya ta wannan* 07065283730 *DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!* *ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya naira 200 kacal ba idan kina\kana buk'ata sai ku tura kudinku ta 2083371244 Asha M.Salis Zenith Bank sai ku tura shaidar biyan kud'in zuwa ga wannan lambar +447894142004 ko katin waya na MTN ta wannan number 07043079282 shaidar biya ta 07065283730* *AJ* 11... "Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Miyya ta faɗa a firgice, sai k'ara zare idanuwa take yi tare da bin su Baffa Sani da kallon tsoro. Dadda ta rafka mata katuwar harara cikin masifa ta ce. "Ka ji min marar kunya yarinya mugun abu muka aikata da za ki bi mu da innalillahi wa'aina illahim raji'un! To bari ki ji aure dai ne an riga an daura kuma ko kinaso ko bakyaso k'arshen zaman mu dake ya zo. Saboda haka tun wuri ki rufawa kanki asiri ki kar6i k'addararki a hannu don ni nan da kika gani ba zan jure cigaba da zama daku ina tuna bak'in cikin da sanadin auren uwarku ya haifar min" "Daina 6ata yawun bakinki Dadda domin ko za ta mutu zaman aure nan ya zame mata dole Shi din ban da kyau d'an maciji da ya rud'e shi me zai tsinta a wurinki, sau nawa ina ba dake sadaka ana barina dake. Ina tabbatar miki ba ma buk'atarki daga ke har k'anneki ku k'addara cewa ba ku ta6a saninmu ba. Ku saka aranku bamu da wata alak'a daku. Tun da Baffa Sani ya fara magana Miyya ta fashe da kuka wani irin k'unci da bak'in cikin take ji marar misaltuwa, bata ta6a tsanmani k'iyayyar da suke musu har ta kai mizani haka ba. Hakeem ya yi sanyayyar ajiyar zuciya yana mamaki wannan wacce irin k'iyayya ce me yara k'anana kamar su Miyya su ka yi da suka can-canci tsana irin wannan, abin takaicin shine daga kakarsu wacce ta haifi mahaifinsu da k'anishi uwa daya uba daya shi Kaɗai ne k'anishi a duniya wai su ne ke nuna musu wannan zazzafar k'iyayya. Shi tun da yake a duniya bai ta6a jin inda aka hukunta wani akan laifi wani ba, sai akan su Miyya saboda kawai mahaifinsu ya aure Christan ta kuma haifesu an Kuma waye gari mahaifin nasu baya duniya, shine suke fuskantar wannan tasku. Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu cikin sanyi murya ya ce. "Baffa ni dama burina Miyya ta ji zance aure nan daga bakinku, to Al-hamdu-lillah! Ta Kuma ji iya wannan nake buk'ata daga gareku. Kamar yadda na faɗa muku tun ranar da naje da buk'atar neman aureta, zan rik'eta ita da k'anneta bisa amana, zan kula dasu na basu tarbiyya tamkar 'ya'ya da na haifa. Kuma in-sha-Allah zan kasance mai rik'e wannan alk'awari. Fuska Dadda ta tanke ta dubi Hakeem ta ce. "Da ka rik'e su amana da kada ka rik'e su ni wannan bai shafe mu ba, idan ma ka ga dama ba iya ci amanarsu ba, ka yanka su kaci wannan ba damuwar mu bace. Ni dai inaso ka k'ara jaddada musu basu ba gidana dama dole ce tasani zama da 'ya'ya kafira 'ya'ya da aka daura auren uwarsu a coci, saboda haka yanzu sun dawo mallakinka..... Cikin matsananci kuka Miyya take kallon Dadda tana girgiza kai tana faɗin. "Haba Dadda! Haba Dadda duk da kasancewar mu 'ya'ya kafira ki tuna cewa kafira nan ita Kaɗai ba za ta samar da 'ya'ya ba dole sai tare da namiji. Wannan namiji kuma shine d'anki jinin jikinki ashe kuwa ko duk duniya za su taru su juya mana baya ke bai kamata ki wofitar damu ba. Dadda duk musgunawa da kike mana wallahi-tallahi ban ta6a jin tsanarki a zuciyata ba. Na saka araina wata rana za ki hak'ura ki so mu ashe tunanina ne ya bani hakan..... "Ke! Baffa Sani ya daka mata tsawa. "To tunaninki ya gayamiki k'arya har gaba da abada ba za mu ta6a sonku ba, na Kuma faɗa banaso ko katangar gidana ku ra6a. Dadda tashi mu tafi. Ya k'arashe magana yana kama hannun Dadda ta mik'e da kyar saboda tana fama da ciwon k'afafuwa. Miyya tana gani haka takara sautin kukanta, tana faɗar "Baffa Don Allah kada ku tafi ku bar mu hannun Wanda bamu gama saninshi ba, gara zama daku koda za ku yanka naman jikinmu ku yi gunduwa-gunduwa dashi. Ku dubi girman Allah Kar ku bar mu a gidanan. "Mtsss..... shegiyar yarinya bak'ar ja'ira can ku k'arasa mu kam Allah rabamu da jafa'i, Allah yasa k'addarar mutuwarku tana hannunshi dare yau ya fara shan farfesunki, dama duk a cikin ɗiyan Usmanu kinfi debo kamani kafirar uwarki. Cewar Baffa Sani har yana had'awa da galla mata harara da idanuwanshi, masu kama da na mujiya. Jin furuncinshi na k'arshe yasa Miyya ta k'ara fashewa da kuka, ta rarrafa ta kama k'afar Dadda. "Haba Dadda wannan wace irin rayuwa ce ku ke k'ok'arin jefa mu ciki, idan aure ku keso ku yi min ku aurardani gun wanda ku ke da cikkake sani akansa. Ba wannan ba da ku kanku ku ke zarginsa da yankar kai.... Da sauri Hakeem ya mik'e ya nufi Miyya, ya durkusa a gabanta cikin sanyayya murya ya ce. "Aslamiyya ki kalle ni da kyau ban yi kama da wanda zai iya cutar da ko dabba balle mutum d'an adam mai darajar, haɗuwata daku wani babban al'amari ne wanda haɗi ne na Allah, ki d'auki haɗuwarmu a matsayin k'addararre al'amari. Har Miyya ta buɗe baki za tai magana ta ji saukar abu akan fuskarta, Baffa Sani ya jefa mata buddle ɗin 'yan one-one thousand. "Ga sadakinki nan indan kin ga dama ki kyasta musu ashana ki k'ona. Yana k'arashe magana ya ja Dadda suka fice kamar makaho da dan jagora, har Miyya ta yunk'ura ta bi su Zaliha ta baro wajen zamanta da sauri ta rik'eta. Ita kuma sai turjewa take yi, kururuwar kukanta ne yasa Amrah da Amal suka fito daga d'akinsu, hankalinsu a tashe har su na had'a baki wajen tambayar dalilin kukanta. Zaliha ce tai k'arfin halin faɗa musu a maimakon Miyya taga tashin hankalinsu sai kawai taga bayyanar farin cikinsu a fili, duk sai taji tausayin kanta saboda ta fahimci jin dad'i da hutun da ya fara ratsa 'yan uwata, yasa idanuwansu rufewa basa hango mata babban k'alubali da yake tunk'aro rayuwarta. Sai kawai ta zare hannun Zaliha daga rik'on da tai mata, ta kwasa da gudu ta shige d'akin da ya kasance mallakinsu. Ta murza key. Ita babban abin da ya daure mata kai bai wuce yadda Zaliha bata nuna ta ji zafin aureta da Hakeem ya yi ba. Al'amarin nasu ko shakka babu akwai lauje cikin nad'i. Idan ba wata manufa a ciki wacce sakaryar mace ce za aiwa kishiya ta nuna halin ko in kula musanmman a wannan zamani da mata suke da mugun zafin kishi. Tun Miyya tana kuka da hawaye har hawayenta suka kafe ta dawo kukan zuci, duk knocking da magiyar da ake mata bai sa ta buɗe musu k'ofa ba. ******************* Azaad ya fito daga bathroom daure da brown towel, hakan ya bayyanar da muscles ɗinshi haɗi da six packs ɗinshi a jere jikinshi a murd'e yake ba sai an gayamaka mai k'arfi bane kai da kanka za ka gane. Cikinshi a shafe yake kamar baya cin abinci, alhali idan ya sami tuwo abin ba kyau. Irin jikin Azaad Junaid bature yai wa lak'abi da invested triangle body shape. Azaad yana da matsakaici tsayi yana dauke da round face fatar jikinshi chocolate colour ce tsananin hutun da ya ratsa shi, yasa fatar shi take shek'i, babban abin da yake burge mata a jikinsa la66anshi da suke pink idanuwanshi masu girman gaske, suna dauke da eyes ball brown colour, kamar dai na magge gashin kanshi bak'in wulik dashi. A natse yake tsane raguwar ruwan wanka da ke jikinsa, tsakanin jiya da yau ya rasa gane kanshi, musanmman idan ya tuna da jiya aka daura mishi aure da yarinyar da baisan ta ba. Babban tashin hankalinshi bai wuce yadda zai rayu da wata mace ba Salimarshi ba. Duk da yana da yak'ini akan Hakeem ba zai mishi za6en tumun dare ba. Lokaci da ya zo mishi da zance yarinyar ya faɗa mishi cewar har da yara biyu take da, shiyasa nan take ya amince da aurenta domin yana gani tun da har tana da yara za ta fi ba wa yaranshi kulawar da yakeso. Shima ya yi alk'awari zamewa nata yara uba kasancewar Hakeem ya faɗa mishi mahaifinsu ya rasu. Ya shirya cikin dark grey suit bai saka coat ɗin ba ya rik'e ta a hannu, jikinsa na fitar da k'amshi turaren avon ever truth, walking majestically ya sauko downstairs parlor yaranshi na zaune a dining room su na taking break fast food. "Good morning Daddy! Suka faɗa a tare cikin sakin fuska har yana had'awa da murmushi, ya amsa musu. "Morning my beautiful babies. Daddy zai yi tafiya amma ba zai wuce two to three weeks ba, uncle Hakeem zai kawo muku new Aunt za ta dinga kulawa daku kafin na dawo, ina so ku girmama ta kada wanda ya sake ya yi mata rashin kunya. Aneesah tai dropping fork ɗin hannunta, kana kafe Daddynta da idanuwanta, can kuma ta ta6e baki tana yatsinar fuska ta ce. "Daddy me za mu yi da new Aunt baya ga Nanny Lacey, tana kula damu dai-dai gwargwado iyawarta in fact mommy bataso kwashe-kwashe you have to ask her first.... "Aneesah! Ya kira sunanta a fusace saboda ya tsani ko sunan Salima a anbata mishi nan take ya ji wani irin 6acin rai..... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya naira 200 kacal ba idan kina\kana buk'ata sai ku tura kudinku ta 2083371244 Aisha M.Salis Zenith Bank sai ku tura shaidar biyan kud'in zuwa ga wannan lambar +447894142004 ko katin waya na MTN ta wannan number 07043079282 shaidar biya ta 07065283730* *AJ* _{The young billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Wattpad:-jeedddahaliyu Haske writers Association. Top Ten takun Haske Batch:A 12... Ya nunata da yatsa cikin kakkausar murya ya ce "Bana cike da iskaci Aneesah ki natsu ki san waye a gabanki, nan gidana ne ba na Salima ba. Ni nake da ikon nasa ayi ni kuma nake da ikon hanawa, don haka wannan ya zama kashedi na k'arshe idan ina magana ki sako min zance mommynku" Sosai Aneesah ta tsorata da yadda Azaad yake mata magana cikin kaushin murya, a tunaninta kafin ma ya kammala magana zai wanka mata mari, saboda tsawon rayuwarta ba ta6a gani yana magana irin haka ba. Cike da tsoro ta baro wajen zamanta ta durkusa gabanshi, saboda duk iskacinta tana matuk'ar tsoron Daddynta. "I'm sorry Daddy wallahi ban faɗi wannan magana don na 6ata ma rai ba. Nayi ne saboda sani halin mommy da nayi za ta iya dawowa ku sami matsala akan hakan. Daddy ina matuk'ar sonku kai da mommy ko Kaɗan banso abin da zai kawo sa6ani a tsakaninku, amma in-sha-Allah ba zan sake maka maganarta ba" Ta k'arashe magana tana hawaye, mik'ar da ita tsaye ya yi tare da goge mata hawaye kuncinta yana alhini ranar da za ta sami labarin rabuwarshi da Salima. "It's okay princess ke ɗin ce wani lokaci kin cika faɗar shirme" "Ka yi hak'uri Daddy ba zan sake ba. "Shikenan amma inaso ki sa aranki duk abin da nake yi Ina yi ne domin farin cikinu da inganta tarbiyyarku, inaso ku zama yara nagari abin alfaharin iyayye. Saboda haka duk wani abu marar kyau princess ki daina kin ga ke ce babba k'anneki dake suke koyi" "in-sha-Allah Daddy na daina duk abin da ka keso shi zan yi. Ya sauke sanyayyar ajiyar zuciya tare da sumbatar for head ɗinta, ya mik'awa Airah hannu wacce tai tsuru-tsuru da idanuwa ya ce "zo nan Mamana naga duk kin yi wani iri" Kamar jira take yi ta taso da sauri ta rungumeshi, ya game su duka biyu ya rungume tsawon lokaci yana jin ɗumin jikin yaranshi, yayin da k'aunarsu mai tsanani gaske ke ratsa ko wane sasshe na jikinsa. Ya buɗe baki a hankali ya ce da Airah. "Mamana je ki kira min Nanny Lacey ta zo min da Ahlam inaso naganta kafin na tafi. Da sauri ta nufi d'akin Nanny Lacey sai gashi sun dawo tare tana d'auke da Ahlam, sai da ta fara gaidashi kana ta mik'a mishi Ahlam ya kar6e ya mannata a k'irjinshi a hankali yake shafa gadon bayanta, ita kuma lafe ya ke6e gefe da Nanny Lacey a natse ya sanar da ita zance aure da ya yi da zuwan amaryar tashi nan da 'yan wasu kwanaki. Ya faɗa mata ne domin akwai yarda mai k'arfi a tsakaninsu. Tun farkon aurenshi da Salima take tare dasu basu ta6a samunta da cin amanarsu ba. Sai dai ya 6oye mata zance rabuwarsu da Salima a ganinshi wannan sirri ne a tsakaninsu bai kamata kowa ya sani ba. Sosai Nanny Lacey ta kad'u da jin zance aurenshi saboda, tafi kowa sani bak'in kishin Madam Salima, akan Azaad komai za ta iya aikatawa. Jikinta yai matuk'ar sanyi cikin tausasa murya ta taya shi murna, ya ji dad'i sosai yadda ta nuna farin cikinta akan auren nashi. Mak'udan kud'in ya bata kamar yadda ya saba bari a duk Lokaci zai yi tafiya duk da akwai wadatatce komai na buk'ata a gidan. 6angare Jadda ya shiga yai mata sallama har ya juya zai fita ta dakatar dashi ta hanyar faɗin "Zo ka zauna Datti zan yi magana da kai" A natse ya dawo ya zauna daff...da ita. "Datti indan lissafina ya tafi dai-dai yau kwana goma da daura maka aure, saidai abin da ban fahimta ba har sai zuwa yaushe amaryar taka za ta tare?" Murmushi ya yi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa, ya yi shiru kamar mai nazari kafin ya ce. "Jadda nayi magana da Hakeem ya ce cikin sati nan za ta tare amma za ki iya bincikarshi da kanki. "Shikenan tashi ka tafi Allah ya tsare yasa ayi kyakkyawar tafiya" "Amin thumma amin! Ya faɗa tare da sa kai ya fita bakinshi d'auke da addu'ar fita daga gida. *************** Tun daga ranar da Miyya ta ji zance aurenta ta tashi hankalinta, yayin da Aunty Zaliha take bin ta da rarrashi haɗi da nasiha sannu a hankali nasiharta tafara tasiri akanta. Hakan yasaka Aunty Zaliha ta dukufa wajen gyarata idan ka ga yanda Miyya ta dawo da matuk'ar wahala ka iya gane nan take. Tayi bul-bul k'irjinta ya k'ara cika, fatar jikinta tayi smooth gwanin sha'awa ita kanta sau dama idan ta shiga wanka sai ta 6ata dogon lokaci gaban mirror tana kallon yadda jikinta ya dawo ita kanta tana jin sha'awar kanta balle ga lafiyayye namiji ya yi arba da ita.. Zaune take gaban dressing mirror fitowarta daga wanka kenan, jikinta na fitarda sihirtattace k'amshi saboda ko wanka za tayi sai Aunty Zaliha ta zuba mata kalolin turaruka wanka daban-dabam shiyasa duk idan ta zauna sai tabar k'amshinta. Aunty Zaliha ta shigo rik'e da ma-dai-daci cup tana shigowa Miyya ta 6ata fuska saboda ta riga da tasan kwanan zance. "Kar6i ki shanye ki bani cup" Bata yi gardama ba ta amsa ta shanye tass ta mik'a mata cup, aunty Zaliha tana murmushi ta juya ta fita. Miyya ta bi ta da kallo har yau ta kasa daina mamakinta. ***************** "Hasheem Kaɗai bi lamari nan a natse cikin hikima da dabara, wallahi-tallahi Azaad ya fi ka shu'umanci. Kana dai kallon irin mutuwar k'as-k'anci da Babban Yaya da Alhaji Buba suka yi ko kare gidana bana fatar ya yi irinta. Ahmadu ya faɗa yana share d'an uban gumin da ya tsatsafo mishi a goshi, ya rasa dalili ko sunan Azaad ya anbata sai ya tsinci kanshi cikin mugun yanayi. "Mtsss.... Kaɗai Yaya Ahmadu an yi matsoraci ni nan da ka ganni ba Azaad ba ko uwarshi dake lahira da za ta dawo duniya sai na wulak'anta rayuwarta, balle wani k'aramin gwaro irinsa. Jin furuncinshi yasa Alhaji Abdallah ya girgiza kai sai da ya k'are mishi kallo kafin ya ce. "Kaɗai bi a hankali kamar yadda Ahmadu ya faɗa Hasheem. Gudun kada allura ta tono galma, da za ku d'auki shawarata da nace mu hak'ura da son ganin baya Azaad, saboda ba tun yau ake ruwa k'asa tana shanyewa ba. Ku duba tsawon lokaci da muka d'auka muna binsa da bi ta da k'uli sai asarar dukiyoyinmu muke yi wurin malaman tsinbo da bokaye a banza. Har ta kai da mun fara rasa rayukanmu, tsakani da Allah banaso nayi mutuwa irinta su Babban Yaya mu je gidan shahararru bokaye har ma da matsafa ko yau ɗinan mu je wurin wani matsafi, da idanuwanku kun ga abin da ya faru ya kira sunan Azaad a madubin tsafinsa a maimakon ya fito shi Kaɗai sai ya fito tare da aljanarsa dake bashi kariya. Dakyar mu kasha saboda haka magani bari kar a fara ni mu dai ri ga da mun fara amma Kuma lokaci bai k'ure mana ba mu rufawa kanmu asiri mu watsar da makaman yak'inmu, ko don gudun mutuwar wulak'anci.. "Dakata Alhaji Abdallah! Hasheem ya faɗa cikin tsawa tamkar yana yi da sa'anshi. "Tun farko ba kidahumancin ku ne ya jawo ba. Na sha faɗa muku bokayenku duk makaryata ne, basu iya komai ba sai gilla k'arya. Ku bani dama za ku ga aiki da cikawa zan nemo professional killers su cika masa aiki kyaftawa gira su turo shi garin da ba a dawowa. "Shikenan ku je Allah ya bada sa'a saidai inason ku sani a wannan karo kuma a wannan tafiya ba dani ba, saboda gani ga wane ya isa wane tsoron Allah. Cewar Alhaji Abdallah yana k'arashe magana ya Kade babbar rigarshi ya k'ara gaba, gaba ɗayansu suka bi shi da kallo kafin su sake dawowa da natsuwarsu kan Hasheem, wanda ya fito da karan sigari ya jefa baki yana shirin cinna mata wuta Hajiya Kubra ta dakatar dashi. "Kar ka sake ka kuna mana sigari anan domin ba so warinta nake yi ba yanzu nan sai ta ɗaga min hankali, ka bari sai ka fita can waje ka kunna abarka. Ya galla mata harara kana ya yi kwafa tare da cizo la66anshi na k'asa, yana jinjina ranarda duk tashigo hannunshi irin wulak'anci da zai shuka mata dole ya cire sigarin ba don ranshi naso ba. Ahmadu kan ya kasa yak'i da zuciyarsa sai ya ji kamar ya bi bayan Alhaji Abdallah sai kuma wata zuciya ta kwa6e shi gara ya zauna ayi dashi gudun kada giwa ta faɗi aci nama ba dashi ba. Kuma ai ba wurin boka za a je ba balle Aljanar Azaad ta kashe su. *************** A yau Hakeem ya yanke shawarar ya faɗawa Miyya gaskiyar al'amarin, saboda yana so ta tare kafin Azaad ya dawo daga business trip ɗin da ya tafi. Shiyasa ya aika kiranta lokaci da sak'on ya risketa sai da taji matsananci faɗuwar gaba. Tsawon lokaci da ya aika kiranta ta kasa tashi ta je sai tufka da warwara take yi saboda tun daga ranar da taji zancen aurenta dashi take wasan 6oya koda kuskure bata bari suka haɗu ba. Shi kanshi Hakeem yana shakkar yadda zai faɗa mata wannan bak'on al'amarin saboda sun yi wasa da hankalinta ba Kaɗan ba. Amma dole ce tasa su yin hakan. "Wai Miyya ba za ki fito daga d'akin bane ko sai Abban Rayhan ya zo da kanshi?" Muryar Aunty Zaliha ce ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula, cikin sanyi jiki ta fito sanye da dogon hijab har k'asa tana shigowa falon ta sadda kanta k'asa can nesa dasu ta nema ta zauna, ta shiga wasa da babban yatsar k'afarta ta dama. Hakeem ya rasa ta inda zai fara kama bakin zare sai musu- musu yake da baki kamar mai jan casbi, can dai ya yi ta ɗiya maza ya yi gyaran murya kana ya ce. "Da farkon dai zan fara cewa dake Aslamiyya ki yi hak'uri domin akwai abubuwa da yawa da ya kamata ki sani kafin yau sai dai na 6oye miki ne na bi ki da yadda kika fahimci al'amari ba don komai ba sai don ki sami natsuwa da kwanciyar hankali to Al-hamdu-lillah burina ya cika. Miyya dangane da zancen aurenmu dake ba gaskiya bane amma zancen an d'aura miki aure gaskiya ne. A zahirin gaskiya ba dani aka d'aura miki aure ba da aminina ne kuma d'an uwana Azaad Junaid. A firgice Miyya ta ciro kanta daga k'asa ta jefawa Hakeem wani irin rikittace kallo mai cike da tarin tambayoyi hakan yasa ya gintse bakinshi ya kasa ci gaba da magana... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 13... Kallo d'aya za ka yiwa Miyya ka gano ba k'aramin firgici da tashi hankali take ciki ba. Ta kasa gasgata abin da kunneta ya ji daga bakin Hakeem gani take yi kamar wasa ne yake yi, kawai so yake ya gwadata shiyasa ya bijiro mata da wannan zance mai kama da almara. Gani ta kasa furta kalma ko d'aya daga bakinta yasa Hakeem ya ci gaba da faɗar "Azaad mutumin kirki ne abokina ne tun na yarinta nasan shi ciki da waje da yana da wata matsala ko gacci da ba zan nema mishi aurenki ba. "Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Hasbunallahu wal'imal wakil.....Ni kan na shiga uku ni Miyya wai meke shirin faruwa da rayuwata ne?" "Alkhairi Miyya Alkhairi ne yake bibbiyarki, wallahi-tallahi da Azaad yana da wata matsala ina da tabbacin Abban Rayhan ba zai shige mishi gaba wajen naman aurenki ba... "Ya isa nace ya isheku haka! an gayamuku rayuwata kwallo ce da za ku dinga jefata raga a duk lokaci da ku kaso?" Ko an gayamuku don banida gata yana nufi ku yi wasa da zuciyata yadda ku ga dama?" Kasa ci gaba da magana tayi sakamakon wani irin nauyi da k'irjinta ya yi kamar an ɗora mata dutsi, tasa hannu ta dafe saitin zuciyarta da ke bugawa da k'arfin gaske. Aunty Zaliha ta taso da sauri ta ɗagota kana ta mik'ar da ita tsaye. Miyya ta kalli Aunty Zaliha da idanuwanta suka fara komawa jajjaye muryarta na rawa ta ce. "Sake ni Aunty Zaliha duk abin da ku ka yi min ba zan ga laifinku ba. Domin da Baffana da kakata ba su ba ku k'ofa ba da ba za ku yi wasa da hankalina har haka ba. Ban ta6a jin haushi kasancewata marar gata ba sai yau. Da ina da gata ko Kaɗan ba za ku kwatata rikita min hankali da tunani ba. "Miyya please Kar ki yi mana mummuna fahimta da fari ki natsu na fahimtar da ke ta yadda za ki fahimci lamarin cikin sauk'i. "Haba uncle Hakeem ya ka ke magana tamkar kana nufi babu zuciya a k'irjina. Miyasa tun farko ba ka fito min a mutum ba. Sai ka yi amfani da rud'add'iyar hanya ka rud'a zuciya da tunanina?" "Nasani Miyya ta yanda mu ka fito miki ba mu kyauta ba. Amma inaso ki sani mu yi hakan ne a dalili ta yanda ki ka fahimci al'amari, mun za6i mu 6oye miki ne saboda ki sami natsuwa da kwanciyar hankali. Ba mu yi haka don cutarwa a gareki ba mu yi ne domin samuwar farin cikinki. Miyya Ina da yak'ini akan Azaad Junaid zai inganta rayuwarki, zai ba ki duk wani farin ciki da kika rasa haɗi da gatan da kike kirara kin rasa. Allah shine shedata na d'auki ke da 'yan uwanki tamkar 'ya'ya da na haifa idan har zan iya cutar dasu to tabbas zan cutar daku. "Na ji uncle Hakeem ba za ka iya cutar dani a zahiri ba amma kasani ka cutar dani a badili, da tun farko ka umarce ni da na aure abokinka nan take zan amince ba tare da dogon tunani ba. Domin hallaci da ka yi min ni da 'yan uwana ka can-canci ka bani umarni na bi. Ka tuna Uncle kaine ka ceto rayuwar 'yar uwanta Amal a lokaci dangin mahaifinmu suke so labarin mutuwarta ya riske su. Ka sanya su makarantar islamiyya da boko ka yi musu gatan da Baffa da Dadda suka kasa yi mana shin wannan Kaɗai bai isa ya haska maka girman da k'ima da kake dashi a idanuwana ba. Fargaba ta d'aya uncle shima Azaad ɗin da saninshi ka auro masa ni ko shima wasa da hankali ka yi mishi kamar dai yanda ka yi min?" Wani irin faɗuwar gaba Hakeem ya ji ya kasa koda kwakkwaran motsi sai kawai ya tsare Miyya da idanuwanshi ya rasa abin faɗa gani haka yasa Miyya ta ce. "Kar ka damu uncle Hakeem tawa k'addara ce ta zo da haka. Kafin ya lalla6o abin faɗa ta cire hannun Aunty Zaliha daga rik'e ta da tayi, ta nufi d'akinsu. Hakeem ya kalli Aunty Zaliha yai mata nuni da ta bi ta har ta buɗe baki za tayi magana ya tari numfashinta. "Je ki kawai Zaliha ki k'arasa faɗa mata anjima za mu rakata gidan mijinta. "Amma Kuma Abban Rayhan..... "Kar ki ce komai Zaliha kawai ki yi abin da nace. "Shikenan. Ta faɗa ba don ranta yaso ba. *********** LOS ANGELES. Su Madam Salima an kammala taro successfully, burinta ya cika ta haɗu da manya-manya jiga-jigai 'yan kasuwa na duniya babu wani kwakkwaran bincike ta dinga zuba hannu jari a duk wani company da ya yi mata. Anan ta haɗu da wata fitattaciyar 'yar kasuwa mai suna Roseline Yaqub Gambella 'yar asalin kasar ethiopian. kasancewar Miss Gambella ta yi suna sosai a duniya kusan ita ce ita the most popular business woman ta biyu a duniya ta shahara a kasuwanci ba Kaɗan ba. Ita ce special guest a taro tun daga lokaci da madam Salima ta kyala ido ta ganta taji tanaso kula alak'ar kasuwanci da ita. Saboda haka ta shiga bibbiyar ta sai a rana ta k'arshe da za a kammala taron ta sami damar haɗuwa da ita, cikin kwantar da kai madam Salima ta nemi da su k'ula k'awance har ta nemi miss Gambella da tasaka hannun jari a company ta da farko miss Gambella bata so ba, saboda ko sunan k'asar Nigeria bata so ta ji an anbata mata, sakamakon wani babban al'amari da ya faru da rayuwarta a can. Wanda har yau ta kasa mantawa balle ta goge shi daga zuciyarta. Yanda madam Salima dinga rarrashinta yasa ta amince, ba don ranta yana so ba sai don wani tunani da ya faɗo mata,ta ware manyan kud'ad'e tai investing hakan a wurin madam Salima ba k'aramar nasara bace domin da yawa su na so tai investing a kamfanoninsu amma basu sami wannan damar ba. Shiyasa alfarinta da izzarta suka k'ara linkawa, tana gani wani tudu ne ta fara takawa na nassarar cika burinta. Washe gari da suka kammala taro ta sake lulawa kasar Turkey, ko tunani yaranta da ta baro bata yi tun lokaci da ta baro gida Nigeria kusan three weeks kenan bata kira waya ta ji lafiyar su ba. Ko Kaɗan yara basu dameta ba ko tana gida ba wani kulawa suke samu daga gareta ba. Sai ta share kwanaki bata saka su a ido ba alhali suna gida d'aya, babu abinda ya dameta tana d'akinta suna nasu kuma bata basu damar zuwa mata bedroom ba. ko shekara d'ari za su yi basu gannta ba, ba su isa su je nemanta a bedroom ɗinta ba. Shiyasa babu shakuwa irin ta uwa da 'ya'yanta a tsakaninsu. A takaice ma mugun tsoronta suke yi. ***************** Misali k'arfe biyar da rabi na yamma aunty Zaliha ta shiga d'akin da Miyya, ta tararda ita ta zabga tagumi ta dukufa tunani makomarta a gidan mutumin da ta ji an kiranshi da suna Azaad. Tashin hankalinta bai wuce Uncle Hakeem ya ce a wurinshi za ta bar Amrah da Amal a cewer shi sai ya ga ta kwantar da hankalinta a gidan mijinta, sannan zai dawo dasu hannunta. Taso tai mishi turjiya saidai kwarjinishi ya hanata. Dafa kafad'arta da Aunty Zaliha ta yi yasa natsuwarta ta dawo jikinta. "Tashi mu tafi Abban Rayhan yana jiran mu a parking lot" Miyya ta 6ata fuska tamkar za tasa kuka, sai kawai tayi k'ok'arin danne hawayenta bata so ta yi kuka gudun jefa k'annaita a damuwa. Batare da ta ce komai ta mik'e already ta shirya cikin Abaya maroon colour, tayi rolling da veil ɗin rigar. Aunty Zaliha ta rik'o hannunta a falo suka iske su Amrah su na jiran fitowarsu. kaitsaye parking lot suka nufa inda Hakeem ke zaman jiran fitowarsu, Amal ta buɗe k'ofar mota aunty Zaliha ta zaunar da ita sai lokaci tai k'arfin hali ɗago idanuwanta ta dubi 'yan uwanta wanda ko Kaɗan bata ga damuwa rabuwarsu da ita akan fuskokinsu ba. Sai ma farin ciki da ta ga su na yi ta girgiza kanta tana mamakin kurciyarsu. Su har sun ga abin farin ciki anan gudun kada ta rusa musu farin cikin nasu yasa ta dangana ta mik'awa ubangiji al'amuranta, abu d'aya tasa aranta muddin 'yan uwanta za suyi farin ciki to kuwa za ta sadaukar da nata. Har Hakeem ya ja mota suna ɗaga mata hannu. Bata mayar musu ba domin gani take da ta mayar musu sun rabu kenan har abada. Suna tafiya Hakeem da Zaliha na mata nasiha da haka suka iso katafare tangamemen Azaad Junaid mansion, tun daga bakin gate ɗin gidan ta gano wata daula duniya ce ta shigo wacce ko a mafalkinta bata zaci za ta tsinci kanta a ciki ba. Kasancewar securities ɗin gidan su san Hakeem da kuma matsayinsa a wurin Azaad Junaid yasa nan take suka buɗe masa gate ya wuce gate na d'aya kana ya zarce na biyu anan ma buɗe masa aka yi sai daff da shiga k'ofar main falo ya yi parking Aunty Zaliha ce ta fara fitowa kana ta buɗewa Miyya k'ofa wacce ta dawo tamkar jini baya gudana a sassa jikinta, idanuwa da gangar jikinta kawai ke aiki yayin da tunani da natsuwarta suka kaura a gareta. Hakeem ya wuce gaba suka mara mishi baya door bell ya danna cikin abin da bai fi 60 seconds ba Nanny Lacey ta buɗe k'ofa...... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 14... A babban falon gidan suka zauna. Nanny Lacey ta kawo musu ruwan sha da juice. Murya can k'asa Hakeem ya gabatar mata da Miyya. Ya kuma k'ara gargadinta kada ta faɗawa kowa matsayinta a gidan duk da k'asa-kasa ya yi magana kuma cikin harshen turanci ba wani turanci kirki take ji ba amma ta fahimci abin da yake faɗi. Sosai ta k'ara shiga damuwa har ta fara zanci zuci "oh! Ni Miyya naga takaina wannan wane irin aure ne ya Rabbi ka taimake ni ka bani ikon cinye wannan jarabawa" "Miyya wannan ita ce Nanny Lacey ita ke kula da cikin gidanan tasan komai akanki, sannu a hankali za ta sanarda ke abin da Azaad yake so da wanda baya so za ta kuma warware miki duk wani abu da ya shige miki duhu. Miyya ta ɗago da idanuwanta ta kalli Hakeem kana tasake sadda kanta k'asa, batare da tace komai ba. Hakeem ya umarci Nanny Lacey da ta kira mishi Aneesah da Airah. Ko wace tana d'akinta a k'unshe sun ri ga da sun saba da zaman d'aki idan basu d'aki suna study room. In ko ka ga sun fito downstairs parlor abinci za su ci ko kuma malami da ke faɗa musu karatu al'qur'ani ne ya zo. Rayuwarsu a tak'ure take basu san komai ba sai karatu gara Princess Aneesah tana chat da school mates ɗinta. Shima a 6oye take yi saboda dokar Daddy ce bai amince da social media platform ba, shiyasa take taka tsan-tsa kada ya gani. Airah ce ta fara fitowa tana sanye da pink belted top ta sauka iya guiwarta, ta yane kanta da white scarf kafafuwanta sanye cikin black thongs slippers irin masu taushin gaske. Da gudu ta k'arasa saukowa daga kan staircase tana zuwa ta faɗa jikin Hakeem, ta rungumeshi tana dariya kana ta ce. "Welcome uncle I miss you so much! "I miss you too baby girl how are you doing?" "I'm fine uncle. Ta dawo da ganinta akan fuskar aunty Zaliha ta gaidata zaliha ta amsa mata cikin sakin fuska, Aneesah ta sauko tana murmushi jikinta sanye da sky blue three quarter haɗe da white armless top gaban rigar na d'auke da zane teddy bear, kanta ba d'an kwali gashi kanta ya sha gyara tayi matuk'ar kyau duk da fuskarta ba makeup. Da fara'a ta k'araso ta ce. "Good evening uncle. Good evening aunty" Kusan a tare suka amsa mata kana Hakeem ya nuna mata kusa dashi. "Princess zo ki zauna we have to talk" Da sauri ta zauna tana mai ci gaba da murmushi su na matuk'ar k'aunar Hakeem saboda yana sake musu sosai fiyye da yadda iyayyensu ke musu gashi da wasa da dariya akwai shak'uwa mai k'arfi a tsakaninsu a duk lokaci da ya zo gidan ya kan 6ata lokaci mai yawa a tare dasu. "Daddy kafin ya tafi ya faɗi maku zan zo muku da new Aunt ko?" Hakeem ya faɗa yana kallon fuskokinsu, domin ya ga yana yi da suka Kar6i zance nashi. Airah tai sauri faɗi. "Yes uncle amma har yanzu ba ka kawo ta ba. "Gata can na zo muku da ita tana da kirki sosai hope ba za ku yi mata rashin kunya ba?" Ya k'arashe magana tare da pointing Miyya da finger shi, kusan a tare suka kalle side ɗin da ya nuna. Airah ta tashi sauri ta nufi wajen Miyya tare da sa hannunta ta ɗago fuskarta. "Wow! She's very beautiful I like her uncle Hakeem. Airah ta faɗa very excited. Yayin da Aneesah ta yatsine fuska tare da mak'e kafad'arta irin I don't care attitude ɗinan. Kusa da ita Airah ta zauna ta shige jikinta Miyya dai sai murmushin yak'e take yi. "Uncle wannan ita ce kuwa new aunt Daddy ya ce ka kawo mana because na ganta k'arama wannan she's just my age mate fa?" Da sauri Hakeem ya tarin numfashinta ta hanyar faɗin. "Da kyau miss complainer dama nasan za a yi haka to friend na kawo miki kawai ki kwantar da hankalinki tana da kirki za ki ji dad'in k'awance da ita. Ta mik'e tare da kallon uncle a ɗage ta ce. "Uncle bari na tafi zan yi karatu I have a test tomorrow. Daga haka ta nufi staircase ta haura da gudu kusan su duka suka bi ta da kallo, kafin ya dawo da ganinshi akan Nanny Lacey ya mik'a mata makulli mota ta daukowa Miyya luggage ɗinta a mota ya gyara zaman shi tare da kiran sunanta. "Aslamiyya!" "Na'am! Ta amsa can k'asan mak'oshi. "Ki yi hak'uri da duk abin da za ki gani a gidanan na dad'i ko kuma sa6aninsa. Ko wane mataki na nasara a rayuwa ba zai zo cikin sauk'i ba dole akwai wasu challenges ki sa aranki Aneesah tana d'aya daga cikin challenges da za ki fuskanta anan gidan. dangane da ci gaba da karatunki kuma in-sha-Allah idan Azaad, ya dawo daga tafiya mu yi magana akai. Ta kasa amsa mishi sakamakon kuka da yake shiri kwace mata, alhali bata shiryawa zuwansa ba. Nanny Lacey ta shigo janye da luggage ɗinta. Hakeem ya kalleta duk tausayinta ya kama shi da kyar ya iya buɗe baki ya ce. "Kada ki sa damuwa aranki Miyya I know you're a strong girl you can do it tashi ki bi Nanny Lacey za ta nuna miki d'akinki. Da kyar ta mik'e tsaye sakamakon yadda kafafuwanta suka yi mata nauyi, Airah ta rik'e mata hannu Nanny Lacey ta wuce gaba suka biyo ta a baya. Ɗaya daga cikin rooms ɗin da ke downstairs Nanny Lacey ta kaita bata yi ganganci kaita upstairs ba, saboda gudun abin da zai iya faruwa idan madam Salima ta dawo. ***** **** ***** Hasheem tare da professional killers ɗin da ya gayyato tun daga cross river, yana tsare musu yadda yake so kisan Azaad Junaid ya kasance, cikin muryarshi m cike da zallan mugunta yake magana. "Azaad zai dawo Nigeria nan da two weeks da zarar ya fito daga airport akan hanyarsa ta zuwa gidanshi nakeso ku kundume shi banaso a sami kuskure komai k'ank'antarshi ku hal6e shi a kai kamar yadda muka tsara" "Don't worry sir Hasheem king Kevin bai ta6a missing target ba kawai ka tanadi remaining balance ɗinshi yana kammala maka aiki zai koma inda ya fito. "Kar ka damu Tajo kud'i ba matsalata bane tun da na bashi rabi raguwar ma za a cika masa. **** ***** **** A cikin kwanaki huɗu da Miyya tai a gidan tayi sabo da Airah da Nanny Lacey sai Kuma Ahlam wacce da farko bata yarda da ita, amma yanzu koda yaushe tana wajenta hakan ba k'aramin dad'i Nanny Lacey ta ji ba. Ko ba komai Miyya ta fara rage mata wani nauyi. A wajen Aneesah ne har yanzu ba wani canji inda za su yi haɗu sau dubu a downstairs parlor ba za yi wa Miyya magana ba. Saidai ita Miyya tai mata kuma ba lallai bane ta amsa. Kasancewar yau Saturday babu school Airah ta shigo d'akin Miyya rik'e da story book a hannunta. "Pretty zo mu je garden na karanta miki story book ɗinan yana da dad'i sosai" Miyya ta ɗago daga gyarawa Ahlam gashinta da take yi tana murmushi ta ce. "Keɗai Airah bakya gajiya da karatu kamar wata alhudada ba kuma na faɗi miki ki daina kirana da pretty ba. "Ni fa nafi jin dad'i kiranki da Pretty fiyye da ko wane suna, kema da sannu za ki zo ki saba saboda gidanan ba mu da wani aiki da ya wuce karatu. Dariya mai d'an sauti Miyya tayi, kafin ta ce. "Inaso karatu Airah amma ba iri wanda ku ke yi ba ace Dan adam bashida hutu a rayuwarshi sai na karatu ai sai kwakwalwar mutum ta cushe. "Mu ai ya zame mana jiki ba abin da kwakwalwar mu zai yi. Tun da ba ki so story ki zo mu je mu yi wasa 'yar 6oya irin na jiya naji dad'inshi sosai. "Bari na kammala gyarawa Ahlam gashinta sai mu je amma fa yau za a rufewa idanu, don na fahimci Airah ba k'aramin wayau ne dake ba. Miyya ta k'arashe magana tana hararata. Dariya Airah tayi har tana had'awa da rungume Miyya, a duk lokaci da suke tare Airah na tsintar kanta cikin farin ciki da nishadi zuwan Miyya ba k'aramin sauyi ya kawowa rayuwarta ba. Tana k'arasa gyarawa Ahlam kai suka fita a compound, Miyya ta cire d'an kwali kanta ta rufewa Airah idanuwa ta gudu bayan flowers ta 6oye yayin da Airah take ta faman lalla6e nemanta. Aneesah ta gaji da kwanciyar a d'aki ta fito a balcony tayi tsaye hannuwanta rungume a k'irjinta cike da sha'awa take kallon Miyya da Airah da ke wasan su cikin nishadi da kwanciyar hankali har batasan lokaci da ta fara murmushi ba. Sosai irin wasani nan ke burgeta saboda tun a yarinta ba a basu damar yi sa ba. Tana so ta sauka k'asa ta je su yi da ita amma tana ji tafi k'arfin yin wasa da Miyya kasancewata housemaid. Ana ta tunani Miyya 'yar aiki ce shiyasa har yau ta kasa sakin jiki da ita duk da a wasu lukata tana matuk'ar burgeta. Sai daff da magarib suka dawo cikin gida bayan sun kammala sallah, Airah tai matashi kai da cinyoyin Miyya sai surutu take zuba mata ita ko sai murmushi take yi zafi-zafi take tankawa. Nanny Lacey ta shigo rik'e da waya a hannunta ta mik'awa Airah. "Daddy is on the line" Ta faɗa lokaci da ta bata wayar cike da zumudi Airah ta kar6i wayar ta kara a kunneta. A hankali take magana Daddynta tamkar ba Airah ba sarkin surutu, kamar daga sama miyya ta ji tana faɗin. "Daddy in bai wa pretty waya ita ma ta faɗa maka abin da take so, ka siyo mata nata tsaraba?" Rass....rass....gaban Miyya ya shiga dukan tara-tara ba bu shiri ta dafe k'irjinta da hannunta na hagu. 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 15.... "D'an dakata mana Mamana" ya faɗa kamar mai koyon magana. Ta fasa cire wayar daga kunneta. "Ba sai kin bata waya ba duk abin da na siyo miki ita ma zan siyo mata irinshi. "To Daddy amma yaushe za ka dawo?" "Maybe next week. "Okay Daddy take care I love you. "Love you too my baby bye. Ya datse kira Airah ta ciro wayar ta mik'awa Nanny Lacey da ke tsaye tana jiranta, Miyya ta kalli Airah na wani lokaci kafin a hankali ta saki ajiyar zuciya saboda ko Kaɗan bata shiryawa magana da Azaad Junaid ba. Tun sanda Airah ta nuna mata hotonshi ta ganshi babban mutum, kuma kyakyawan gaske mai cike da haiba da kwarjini, take jin tsoro da fargaba haɗuwa dashi. Sosai taga wauta Uncle Hakeem na had'a shi aure da ita ba sai an faɗa mata ba ita da kanta ta gano ba level ɗinta bane. "Yadai pretty tunani Amrah da Amal ki ke yi ko?" Airah ta faɗa tare da lek'a fuskar Miyya. Shiru tayi ta kasa bata amsa sai kawai Airah ta ci gaba da faɗin. "Ba nace ki bari na faɗawa Nanny Lacey ta kira uncle Hakeem ya kawo miki su ba, kin ce a'a amma kuma sai tunaninsu ki ke yi. Miyya ta sake jan numfashi kana ta sauke cikin muryarta mai cike da natsuwa ta ce. "Tashi mu yi sallar isha yau da wuri nakeso na kwanta" Daga haka Airah bata sake magana ba sai kawai ta bi umarninta. A kwana a tashi lokaci yana ta tafiya Miyya har tayi cika two weeks a gidan, sosai shak'uwa da k'auna mai k'arfi ta shiga tsakaninta da Airah da Ahlam har ta kai a yanzu a d'akinta suke kwana. A koda yaushe idan taga Nanny Lacey a kitchen ta kan je ta tayata girki, sosai ta sami kar6uwa a wajen housemaids ɗin gida kowa k'aunarta yake yi saboda Miyya mutum ce mai saurin shiga rai. A two weeks da tayi da yana yi mu'amalarta da mutane gidan za ka zaci ta shekara da saninsu. Miyya tana da hak'uri uwa-uba sanyi hali gata shiru-shiru magana ma wahala take mata ga yawan murmushi saidai akwai saurin yin kuka. Rashin kulata da Aneesah ke yi ba k'aramin damunta yake yi ba. Har cikin ranta take ji k'aunarta shiyasa a duk lokaci da ta ga Aneesah ta sauk'o k'asa sai ta gaidata, burinta su sami kyakkyawar mu'amala. Tun Aneesah bata amsawa har ta zo yanzu tana amsawa saidai a gajarce. Yau ma dukansu suna zaune a downstairs parlor, suna cin pancake da Miyya tai musu Aneesah ta sauk'o cike da yanga wacce ta zame mata jiki ta kalle su ta d'auke kai, ta nemi kujera da ke nesa dasu ta zauna tare da crossing legs ɗinta. Miyya ta dubeta tana murmushi ta ce. "Barka da fitowa Aneey" Sai da ta yatsine fuska tukun kafin ta amsa da "Sannu! Miyya ta d'auki plate ta zuba mata pancake ta sauke Ahlam daga jikinta, ta nufi wajenta ta mik'a mata. "Aneey ga pancake nai mana ci ki ji ko ya yi dad'i?" Ta faɗa da yalwatattace murmushi akan innocent face ɗinta, shiru Aneesah tayi tana tattance irin kalar wulak'anci da za ta yi mata. Sai kawai ta buge plate ya faɗi pancake ɗin ya zube akan tiles, cikin tsawa ta ce. "How dare you to bring me this trash ban faɗa miki ba ki daina shiga harkana ba?" Ko dole ne sai na kula ki what kind heartless you're?" Tuni idanuwan Miyya suka kawo ruwa sai k'ok'ari hana su zubowa take yi, Airah ta taso cikin fushi ba k'aramin haushi take ji ba a duk lokaci da Aneesah ta yiwa Miyya wulak'anci. "Wai miye haka ne Aneey ke ko Kaɗan ba a miki abin kirki ne sai kin ma mutum wulak'anci, wallahi da nice pretty da tuni na tattara ki na zubar a bola. A fusace Aneesah ta mik'e ta nuna Airah da yatsa tana faɗi "Hey...watch your tongue "An k'i ɗin sai ki zo ki dakeni. Airah ta faɗa tana galla mata harara. Sosai hakan ya k'ara harzuk'ata ta soma zazzaga masifa. "Tuni nagano Airah kin fiso stranger akan ni 'yar uwarki ta jini, kwatata kin daina kulani saboda ita amma ba komai ki jira mommy ta dawo wallahi sai tabar gidanan. Ta k'arasa magana muryarta yana rawa kamar za ta fashe da kuka. "Tun kafin mommy ta dawo ki zo ki fitar da ita ai kema kin isa ko?" Airah ta faɗa a fusace kuma cikin shouting. Da sauri Miyya ta jawo hannunta. "Miye haka Airah yayarki ce fa?" Bai dai-dai bane ki faɗa mata irin wannan magana. Kafin Airah tai magana Aneesah ta rigata ta hanyar furta. "Ba wani nan duk ke ce kika janyo kafin zuwanki gidanan Airah bata isa na faɗa ta faɗa ba, saboda haka dole ki bar gidanan. "Ba isa ki ba wallahi Aneey you're not a Daddy saboda shi keda iko zantarda hukunci Kuma shine silar zuwanta gidanan. Ita ma Airah ta faɗa a fusace. "Airah please ya isa haka tun farko laifina ne da na kasa daina shiga sabgarta. Miyya ta faɗa cikin sanyi murya kana ta kalli Aneesah ta haɗe hannuwanta alamar rok'o. "Ki yi hak'uri Aneey tun da bakyaso ba zan k'ara ba kinji?" "Haba pretty miye na bata hak'uri ita ya dace ta ba ki hak'uri ba ke ki ba. Airah tayi magana cike da jin haushi hak'uri da Miyya take bata. "A'a Airah laifina ne dole na bata hak'uri. Ina k'ara ba ki hak'uri Aneey. "Go to hell!!! Aneesah ta faɗa cikin ihu wanda ya janyo hankali Nanny Lacey ta fito da gudu daga d'akinta, tana tambayar meke faruwa. Aneesah bata bi ta kanta ba ranta a mugun 6ace ta juya da gudu ta haura staircase ta shige d'akinta. Airah ce tai mata bayani Miyya kuma ta duk'a ta shiga tsince pancake ɗin da Aneesah ta zubar. Hak'uri Nanny Lacey ta bata. "Its ok Nanny. Ta faɗa a gajarce tare da nufar kitchen ta kai plate, za ta fito dai-dai Airah ta shigo tana zuwa ta rungumeta cikin taushin murya ta ce. "I'm sorry pretty karki damu da abin da Aneesah take miki, bata da halin kirki she's very bad girl... Da sauri Miyya tasaki wa Airah duddu a gadon bayanta tare da faɗin. "Za mu 6ata Airah idan kina faɗawa yayarki kalaman rashin ɗa'a. "Ouchh.... pretty da zafi fa. Ta faɗa cikin shagwa6a tana shafa gun da Miyya da buga. "Sorry.... Cewar Miyya tana dariya kana suka fito daga kitchen ɗin, Airah ta kalli Miyya with serious face ta ce. "Ni fa pretty na ganoki kin fi so wannan arrogant Aneey akaina" Murmushi kawai Miyya tayi ta d'an ture Airah, ta wuce d'akinta. Miyya bata daddara ba da yamma ta ga Aneesah bata fito ba sai kawai ta sulelewa Airah ta nufi d'akinta, sai tayi niyyar knocking sai kuma ta fasa tayi haka kusan sau uku sai a na huɗu tayi knocking on. "Yes come in the door is open" Ta tsikayo muryar Aneesah daga ciki, ta danne zuciyarta ta tura k'ofa wannan shine karo na farko da ta fara shiga d'akinta. Tana bibiyar Aneesah ne saboda ta fahimci saboda su Azaad Junaid ya aure ta. Don haka ta k'udurta aranta za ta yi hak'uri ta bi ko wace hanya da za su sami jituwa a tsakaninsu. "Assalamu Alaikum! Da sauri Aneesah ta ɗago idanuwanta taga game ɗin da take yi a wayarta, fuskarta ta kasa 6oye mamaki gani Miyya a d'akinta nan take ta daure fuska. "Aneey cewa nayi amincin Allah ya tabbata agareki amma kuma kin kauda fuska addini musulunci babu kyau ai ma mutum sallama ya kasa amsawa" Miyya ta faɗa cikin tattausan lafazi jikin Aneesah ya yi sanyi ta juyo amma bata bari ta had'a ido da miyya ba ta ce "Wa'alaikum salaam! Shikenan ko?" Ta faɗa tana yatsine fuska. "Dama na zo ne na duba ki naga tun safe ba ki k'ara saukowa falon k'asa ba?" Shiru Aneesah tayi tana k'ara mamakin Miyya wacce irin zuciya ce a k'irjinta da take jure wulak'anci. "Aneey kin yi shiru ba ki ce komai ba, Ko dai har yanzu fushi kike yi dani?" "Bana fushi da mutane da basu da muhimmanci a gareni. Yadda tai magana bai ma Miyya dad'i ba don har hakan ya nuna akan fuskarta, amma sai ta daure ta sake cewa. "Na sani Aneey banida muhimmanci agareki amma ni kina da a wurina saboda muhimmancinki yasa har na dako k'afata a dakinki. Furuncinta ba k'aramin rikita tunani Aneesah ya yi ba, duk ta ji wani iri sai ta hana hakan tasiri akanta cikin muryar reni hankali da gatsali ta ce. "To naji za ki iya tafiya Ina buk'ata huta banaso damuwa. Ta k'arashe magana haɗi da pointing k'ofar fita da yatsanta, jikin a sanyyaye Miyya ta buɗe k'ofa ta fito karaf idanuwanta suka faɗa cikin na Airah da ke tsaye tayi folding hannuwanta a k'irji tana facing k'ofa. Ta ɗage girar ido tana kallonta kafin ta girgiza, ta ra6a ta gefenta ta shiga d'akin na Aneesah, jin k'arar buɗe k'ofa yasa Aneesah ta taso a fusace a tunanina ko Miyya ce ta sake dawowa sai idanuwanta suka sark'e da na Airah, ta galla mata harara kana ta koma ta kwanta ta bata baya. Airah tayi murmushi tare da zaunawa kusa da kafafuwanta cikin tattausa murya ta ce. "Aneey please wake up we have to talks. "About what??" Ta tambaye ta batare da tashi ba, balle ta kalleta. "Pretty! Airah ta faɗa a gajarce. Sai da Aneesah ta 6ata lokaci kafin ta tashi zaune tana mai k'ara tanke fuskarta. "Aneey zuwan pretty gidanan ta miki wani laifi ne da yasa kika tsane ta har haka?" "Banaso silly questions Airah. "Babu zance silly questions Aneey abin da kike yi kwatata bai dace ba, nasani haka kawai kika tsaneta alhali bata miki laifin komai ba. "Ni nace dake na tsaneta?" "Ba sai kin faɗa min ba Aneey ga alamomi nan a bayane, ko magana tai miki a lalace kike amsawa Ina laifin wanda ya damu da kai. "Wai ke Airah meke damunki ne huh?" zuwan wannan Miyya gaba daya kin canza, ba ki da zance sai nata wato ta zo ban bata fuska ba shine ta turo ki, da yake bakida kunya shine za ki zo ki cika min kunne Dan Allah tashi ki fita min daga d'aki banaso tak'ura. Haushinta ne ya turnuk'e Airah ta juya a fusace ta buɗe k'ofa da k'arfi, ta fita. A falon k'asa ta tararda da Miyya tana zaune Ahlam tana kwance akan cinyoyinta taso tai mata korafi akan zuwanta d'akin Aneesah sai kuma ta fasa, ta kalleta a natse ta ce. " Pretty ko za ki tashi mu tafi flat ɗin Jadda kwana biyu ba mu lek'a ta ba.?" Da sauri ta tashi dama tana sanye da gown na atamfa ta yane kanta da k'aramin veil. A falo suka iske Jadda tare da mai aikinta Mero, da yake wannan zuwan shine karo na uku da Miyya ta je 6angare Jadda. Da yake Jadda tasan komai akan Miyya, ta yaba matuk'a da hankali da natsuwarta Sosai taji ta kwanta mata a rai. Saidai fargabarta d'aya idan uban gayya Azaad ya dawo zai kar6e ta kuwa ya kuma zamanta da Madam Salima zai kasance?" Da yake Azaad bai faɗa mata ya saki Madam Salima ba. Shiyasa duk lokaci da suke je 6angarenta sai ta ke6e gefe d'aya da Miyya tayi mata nasiha. Sosai Miyya ke jin k'aunar Jadda a zuciyarta. **** ***** ****** Misali k'arfe biyu na dare ciwon mara mai tsanani ya tashi Aneesah, sai juyi take yi ita Kaɗai akan gado dama ga goganyar taku da raki tsiya ta 6are baki ta shiga rera kuka duk lokaci da za tayi menstruation sai tayi ta fama da ciwon mara. Tun tana kuka da k'aramin sauti har ta dawo tana yi da k'arfi, gani kuka ba zai mata magani komai ba ta d'auki wayarta, ta kira Nanny Lacey. Can cikin barci Miyya ta ji ringing ɗin wayar Nanny Lacey da Airah ta aro mata tayi waya da Amrah da Amal, ashe Airah ta manta bata mayar mata ba. Cikin magagin barci ta mik'a hannu ta d'auki wayar da ke aje akan bedside, da nufi tai switch off ɗinta sai kawai taci karo da sunan Aneesah gabanta ne ya fara faɗuwa, saboda tasan da wuya in kira na lafiya ne kasancewar da ta dauko wayar sai da dubi lokaci. Tai picking tare da karawa a kunneta cikin muryarta mai cike da barci ta ce. "Hello.....Aneey Miyya ce wayar Nanny Lacey tana hannuna kina bukatar wani abu ne ko na Kai mata wayar ne?" "Wayyo Allah pretty ki taimake ni zan mutu... Muryar Aneesah tai mata dirar mikiya a dodon kunneta, babu shiri ta wartsake daga raguwar barci da bai k'arasa sakinta ba. Cikin azama ta mik'e zaune. "Subhanalillah.....Aneey ba ki da lafiya ne?" "Mara ta ke ciwo dan girman Allah ki taimaka min ki kira Nanny Lacey. "Okay..gani nan zuwa. Ta faɗa cikin rawar murya a rikice ta saka thongs slippers ta buɗe k'ofa, a rud'e take haura staircase tana murd'a handle ta ji k'ofa ta buɗe, ta kutsa kai ta hango Aneesah kwance sai mul-mula take yi in ta kai k'arshen gado ta dawo farko da gudu ta nufe ta gaba ɗaya ra rungumo ta zuwa jikinta. "Sannu....sannu....Aneey kin sha magani kuwa?" Cikin tsananin zafin ciwo Aneesah ta girgiza kanta. "Akwai magani ne ko na tashi driver mu kai ki asibiti?" "Ki duba cikin bedside drawer yana ciki. Aiko kamar jira Miyya take yi ta ɗora kanta a pillow ta k'arasa da sauri ta binciko magani, ta buɗe fridge ta dauko water bottle hannunta na rawa ta 6alle murfi tare da 6allo magani ta ɗago Aneesah tasa mata a baki tasha. Sai faman sannu take mata. Aneesah sarkin raki ta bi ta k'am-k'ame Miyya, hakan da tayi sai ya k'arawa Miyya tausayinta, batasan lokaci da ta fara tayata kuka ba. Sai daff da asuba barci ya d'auke ta, kanta na bisa cinyoyin Miyya ita kuma ta jinginar da bayanta ga gado a haka tayi barci k'arar alarm da ya karad'e d'akin ya falkar da Miyya ta dauke kan Aneesah a hankali daga cinyoyinta ta ɗora a pillow kana ta wuce bathroom tayi koda ta kammala sallah Aneesah ta buɗe idanuwanta a hankali ta bi d'akin nata da kallo karaf idanuwanta ya sauka akan Miyya. Kwakwalwarta ta soma yi mata backwards ɗin abin da ya faru, da hanzari Miyya ta cire hijabi ta nufo wajenta. "Sannu Aneey ya jikin naki?" Da sauri ta rufe idanuwanta cike da tsan-tsan kunyar tunawa da irin wulak'anci da ta dinga yi wa Miyya, amma bata kunlace ta ba. Ta kuma taimake ta a lokaci da take tsananin buk'atar taimako. Kasa amsawa tayi sai kawai ta yunk'ura ta sauk'o daga gado batasan cewa lokaci da take barci period ɗinta ya zo gaba ɗaya sleeping dress ɗin jikinta da bedsheet ya lalace da jini. Da sauri ta runtse idanuwanta Miyya ta dafa kafad'arta cikin sanyi murya ta ce. "Sannu Aneey tun da ya zo ai lafiya ta samu bari na had'a miki ruwan wanka. Bata jira jin ta bakinta ba ta shiga bathroom da saurinta ta had'a mata ruwa kana ta fito da towel t mik'a mata, jikin Aneesah ya yi sanyi lak'ass...ta kar6i towel ɗin cike da kunya ta cire kayan jikinta tana rik'e da kayan ta shiga bathroom Koda ta fito Miyya ta canza mata bedsheet. Tana cikin saka kaya Miyya ta shiga bathroom babu kyama balle kyakyami ta wanke bedsheet da kayan da ta cire ta fito dasu cikin rubber bucket. Sosai Aneesah ta girgiza da gani hakan nan take ta tuna da ranar da ta fara menstruation hakan ne ya faru da ita a lokaci, madam Salima tana gida bata yi duba da shine ranar ta na farko ba ta 6al-6aleta da masifa, wai bata so k'azanta da sakarci haka ta fita abinta tabar ta sai Nanny Lacey ce ta taimaka mata ta kuma nuna mata yadda ake yi. Tsabar haushi abin da mommynta tayi mata yini tai tana kuka a d'aki sai gashi yau, wacce ta rena ta kuma tsana tayi mata abin da uwar da ta haife ta ta kasa yi mata. Har Miyya ta fita ta Sanya kayan a backyard ta dawo Aneesah tana tsaye gaban mirror tana zuba tunani. "Aneey ki kwanta ki huta yau ba sai kin je school ba tun da ba ki da lafiya bara na haɗu miki breakfast" Muryar Miyya ta dawo da ita natsuwarta, har Miyya ta juya ta ji Aneesah ta rungumeta ta baya tana shasshekar kuka cikin muryar kuka take faɗin. "I'm very sorry pretty please forgive me I know I hurt you several times, Dan Allah ki ce kin yafewa marar kirki Aneey... Da sauri Miyya ta juyo da ita ta rik'e hannayenta duka biyu ta kalli cikin idanuwanta tana murmushi, kana ta ce. "Na yafe miki Aneey dama ban ta6a rik'e ki a zuciya ta ba. Kawai nasaka araina rashin fahimta ne a tsakaninmu, Kuma wata rana za ki fahimce ni. "Thank you so much Pretty you're the simplest, sweetest and best person I ever come across in my entire thank you for having you in my life. Zuwanki alkhairi ne a gidanmu da ma rayuwarmu duka. Ta k'arasa magana tare da sake hugging Miyya tightly, tuni tasa Miyya 'yan mata hawaye Aneesah ce ta fara janye jikinta, tasa hannu ta goge hawayen kumatunta tana jin wani irin farin ciki da annashuwa wanda ta dad'e rabon da ta ji kanta a ciki. Miyya ta fice kaitsaye d'akinsu ta wuce koda ta shiga Airah ta fito daga wanka, a gurguje ta ba wa Airah labari abin da ya faru sosai Airah tai farin ciki jin Aneesah ta sauko har ta ba wa Miyya hak'uri. Daga ranar Miyya da Aneesah shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakaninsu suka dawo k'awaye, dukansu sun matsu daddy ya dawo akai miyya school ɗinsu. A cikin dare jirgin da Azaad Junaid ya shigo ya sauka a Malam Aminu Kano international airport..... *Not Edited!!* 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 17.... Yana yi yadda yake kallonta yasa ta k'ara rikicewa, yayin da Yana yinta ke sauyawa a hankali ta sauke idanuwanta k'asa, a dalili wani bak'on al'amari da take ji yana shigarta. Ci gaba da k'ureta da kallon kurilla ya yi, babu ko alama dake nuna shi ɗin zai d'auke rikitattun idanuwanshi daga kanta. Ya ja dogon numfashi kana ya sauke, a hankali ya girgiza kai so yake ya k'aryata zarginshi ko ta hali yaya, sai kawai ya ciro wayarshi, daga aljihu ya kira Dr Jannat ita ce likitar da ke kula da yaranshi. Ya dubi Miyya da raguwar mamaki da har yanzu ya kasa sakinsa cikin dakakkiyar muryarshi mai cike da k'asaita ya ce. "Je ki tsaftace mata jikinta kafin Doc ta k'araso. Da sauri Miyya ta nufi d'akinta da ita cikin k'ank'ani lokaci ta gyarawa Ahlam jikinta ita ma ta sauya kayan jikinta, kasancewar Ahlam bata da Kaya a d'akinta yasa ta lullu6e ta cikin towel ta fito sa6e da ita a kafad'a. Ta haura upstairs inda d'akin Ahlam yake babu ce kawai babu a d'akin. Duk wani abu na more rayuwa an zuba mata a ciki kama daga toys da teddy bear gasu nan birjik. Duk lokaci da Miyya ta shigo d'akin nata sai ta tsaye ta k'arasa masa kallo kusurwa-kusurwa, tana mamaki yarinyar da bata ko cika shekara d'aya ba ke da wannan tangamemen d'aki. Closet ɗinta ta buɗe mai d'auke da suturanta kala daban-dabam. Ta ciro pink gown tana cikin saka mata ta sake shak'a wani amai, gaba ɗaya rigar tasake lalacewa. Tsananin tausayinta ya sake kanainaye zuciyar Miyya, musanmman yadda take ta kakarin amai, dole ta sake komawa bathroom da ita ta wanke mata jikinta, ta kuma wanke gun da amai ya sami rigarta. Tana fitowa sa6e da ita a kafad'a Azaad tare da Doc Jannat su na shigowa. Miyya tai tsaye turuss...a bakin kofar bathroom ta kasa k'arasowa, suna had'a idanu ta ji wani iri yarrrr....tsigar jikinta ya tashi. "K'awo ta mana na duba ta" Sautin muryar Doc Jannat ya hankaltar da ita hali da take ciki. Ta tako a hankali kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ta mik'awa Doc Jannat ita da sauri Ahlam ta mak'alewa Miyya alamar bata zuwa, gani haka yasa Miyya ta dosana duwawunta a gefen gado yayin da Doc Jannat ta dukufa duba ta. A hankali Miyya ta ɗago idanuwanta ta saci kallon Azaad Junaid da ke tsaye a dai-dai k'ofar shigowa ya tattara hankalinshi akan wayar hannunshi. Jikinshi ya bashi cewa ana kallonshi yana ɗagowa Miyya na sauri sadda kanta k'asa, tuni ya gano ita ce mai kallon nashi. Doc Jannat ta kammala duba Ahlam ta fiddo da drip ta saka mata ihunta yasa Miyya ta ɗago babu shiri, Doc Jannat ta gani rik'e da hannun Ahlam tana, neman jijjiya, duk inda ta soka allura sai ta cire saboda, bata do gun da jijjiyar take ba. Ta saki ɗayan hannunta ta sake kama ɗayan. Duk lokaci da Doc ta soki hannun Ahlam sai Miyya ta runtse idanuwanta tamkar jikinta ne ake hudawa. Duk abin da ta ke yi Azaad yana kallonta ta gefen ido yadda take runtsar idanu yai masifar bashi dariya sai kawai ya yi murmushin gefen baki. Sau biyu doc Jannat tana sukar hannun Ahlam bata Sami jijjiya ɗin ba. Tana shirin yi na uku Miyya ta rik'e mata hannu tamkar za ta fashe da kuka ta ce. "Please Doc ki kyaleta haka mana, kalli dukan hannuwanta duk ki bi ki huda su kamar kin sami kwarya" Dakatawa Doc Jannat tayi ta ɗago da yawaltatce murmushi akan fuskarta ta ce. "Nima ba a so raina nake huda ta ba, ki yi hak'uri na k'arasa aikina. K'in sake ta tayi sai ma k'ara dank'e hannun nata tayi, yayin da idanuwanta suka ci-ciko da hawaye. "Ki barta tayi aiki kada ki 6ata mata lokaci" Muryar Azaad ta daki dodon kunneta, ta ɗago manyan idanuwanta ta galla mishi harara, don ba k'aramin haushinsa take ji ba. Tun shigowarsa yake tsaye yana dannar waya, kamar bai damu da taratsi kukan Ahlam ba. Ba don ranta ya so ba ta saki hannun Doc Jannat, tare da kauda fuskarta sai da Doc ta kammala mata fixing drip ɗin sannan ta dawo da ganinta akan Ahlam wacce ta lumshe idanuwanta alamar tanaso tayi barci. Gani haka yasa Azaad ya fita daga d'akin Doc Jannat tattara kayanta ta bi shi a baya. A downstairs parlor ya tsaya still idanuwanshi na kan wayarshi ya shiga tambayar Doc Jannat ciwon da ke damun Ahlam. "Zazza6in hak'ora ne ke damunta Yalla6ai zan dawo da yamma idan bata daina amai ba, gaskiya sai an sake k'ara mata wani drip" Ya jinjina kanshi. Doc Jannat ta mik'a mishi prescription ta tare da furta. "Kafin na dawo ayi k'ok'ari a siyo wad'annan magunguna. Nan ma sake jinjina kanshi ya yi bayan doc Jannat ta tafi, ya nufi 6angaren Jadda ya nufa zuciyarshi a cakude bayan ya gaisa da Jadda mero ta kawo mishi Karin kumallo ya d'an tsakura Kaɗan saboda damuwar da yake ciki, zance na gaskiya idan har hasashen shi ya hasaso masa gaskiya wannan tatsutsuwar yarinya da ya gani sa'ar Aneesah matashi to kuwa akwai matsala babba. Wannan ai abin kunya ne gotai-gotai dashi ya aure sa'ar 'yar cikinsa. Ai sai girma da k'imarshi su zube a idanu mutane duniya. Wayarshi ya dauko ya kira Hakeem ya zo yana so ganinshi gara ya zo su yi ta manya-manya daga tushe, kafin Hakeem ya iso ya kalli Jadda da ke mishi zance Aslamiyya kamar tasan abin da ke nukurkusar zuciyarsa. Rai 6ace ya fara magana. "Wai Jadda kina nufi wannan 'yar k'ank'anuwa yarinya da nagani ita ce matar tawa?" "Kwarai kuwa ita ce ai nice nace da Hakeem ya 6oye kada ya yi saurin baiyana maka da ita gudun kada kace tayi maka k'ank'anta, ka fasa auren ni kuma a duniya nan ta maliki yaumidini bana da buri da ya wuce ka k'ara aure kai da yaranka za ku sami kyakkyawar kulawa da gantalalliyar matarka ta kasa ba ku. Ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke tare da shafa kwantattace sajenshi wanda hakan ya zame masa dabi'a. Kafin ya tattaro natsuwashi wuri guda ya ce. "Jadda idan kina min hasashen kulawa to kin tafka kuskure domin wannan kwaila ba abinda za ta iya, azahirin gaskiya ni an cuceni tare da linkeni bai-bai saboda Hakeem ce min ya yi bazawara ce har da yara biyu. Ashe duk k'arya ce da yaudara saboda haka yadda yadda kawota haka zai dawo ya d'auki abarshi don ni ba mutumin banza bane balle araina min hankali" Hakeem da ya turo k'ofa zai shigo karaf furuncin Azaad na k'arshe ya sauka a kunnenshi, cikin mutuwar jiki yai sallama Jadda ce Kaɗai ta amsa Azaad kuma ya amsa a cikin zuciyarsa. Muryar Hakeem Kaɗai da ya ji saida ya k'ara linka masa 6acin rai da takaicinsa. Hakeem ya mik'a masa hannu da nufi su yi musabaha, ya kwada masa katuwar harara, ya kauda fuska. Hakeem ya mak'e kafad'a tare ta6e baki ya nemi cushion dake facing ɗinshi ya zauna, ya gaida Jadda ta amsa kana ya zarce da faɗin. "Jadda ki shiga cikin lamari nan saboda Aj ya dau zafi dani, ni kuma shawara da kika ɗorani akai na bi. Don haka kar ya sake ya ga laifina. "Wannan haka yake Hakeem tun kafin ka zo na faɗa na Kuma k'ara jadaddawa Aslamiyya tayi min d'ari bisa d'ari.... "Haba Jadda ya za ki faɗi haka gaskiya ni dai ba ai min adalci ba?" Kuma inaso kasani Hakeem saboda yarda da nayi maka yasa na ba ka ragamar rayuwata da ta iyalina sai gashi ka rusa wannan yarda. "Karka faɗi haka Aj domin wallahi-tallahi ban zantar da hukunci ba saida amincewar Jadda, aganina ko mayya Jadda ta nuna tanaso ka aura za ka amince da gaggawa ba tare da tambayar ba'asi ba. Balle yarinya mai cike da nagarta iri Aslamiyya wacce samun irinta a wannan zamani sai an sha matuk'ar wuya. Duk wani qualities da kakeso a jikin mace Aslamiyya tana dashi, ita ce mace da za ka faɗa ta ji, ka kafa doka ta bi ba tare da tayi fatali da ita ba. Ita ce za ta girmamaka ta mutunta igiyar aurenka ta kuma zame maka ma'adanar sirrinka, ta so ka ta k'aunace 'ya'yanka Aj kada ka bi rudin zuciya ka daure Dan Allah da manzonsa ka kar6i, Aslamiyya a matsayin matarka. Yarinya nan rayuwarta cike take da k'alubali a tunanina kaine za ka kawo mata sauyi a rayuwarta kamar yadda nake da yak'ini za ta kawo babban sauyi a rayuwar gidanka" Azaad ya dafe kokon kanshi saboda Hakeem da Jadda sun ri ga da sun gama daure shi da kalamansu. Yana matuk'ar k'aunar Jadda domin ita Kaɗai ta rage mishi ita ce yake kallo a matsayin mahaifiyarshi yayin da Hakeem yake da babban matsayi agareshi, abokinshi ne tun na yarinta duk wata gwagwarmayar rayuwa a tare suka yi shima maraye ne kamar shi saidai Hakeem yana da K'anwa daya kachal Zainab sa6ani shi da Jadda ce Kaɗai yake da sai shirgin 'yan uba da kullum burinsu su ga bayanshi. Kasa magana ya yi hakan ya bai wa Hakeem damar zayyane masa tarihin Miyya bai 6oye masa komai ba. Sosai ya ji ya tausaya musu ya kuma kudurta aranshi zai kula da ita a matsayi 'ya ba mata ba, har sai zuwa lokaci da za ta mallaki hankalin kanta ta yadda za ta iya 6ance-6ance tsakani abin da takeso da wanda bataso. Ya yi shiru bai sake magana ba sai ma jinginar da gadon bayanshi ya yi a jikinta ya lumshe idanuwanshi gani haka yasa Hakeem ya yi hamdallah domin shiru da ya yi shine amincewarsa da bai amince ba tashi kawai zai yi ya bar musu falon. **** ****** ***** Miyya tana rik'e da hannu Ahlam ko nan da can bata gusa ba, yanzu haka fitsari take ji amma ba za ta iya shiga bathroom ta barta Kaɗai ba. Sai da drip ya k'ara ta fita kiran Nanny Lacey ta zo ta cire mata sai lokaci ta faɗa bathroom ta rage nauyi tare da d'aura alwala saboda lokaci sallar Azhar ya yi har kuma zuwa lokaci Ahlam tana sharar barci abinta. Hatta da abinci Nanny Lacey ce ta kawowa Miyya a d'aki sai misali k'arfe uku Aneesah da Airah suka dawo daga school, sai lokaci su ka san Daddynsu ya dawo sosai suka shiga murna ganinshi. Yini daya kacal har Ahlam tayi rama tun tana mamaki rashin dawowar Azaad ya duba Ahlam har ta dawo tana zance zuci. "Wannan wane irin uba ne?" Fissibillahi 'yarka bata da lafiya ka kasa nuna kulawarka akai. Wani 6angare na zuciyarta ya ce. "Daina ganin laifinsa Miyya mahaifiyarta ta fi shi laifi kasancewar mace Kuma uwa amma ta iya tsallakewa uwar duniya ta bar 'yarta mai watani goma. Abin da ke d'aure mata Kai ya Kuma k'ara dumulmula mata tunani tare da hargitsa mata kwakwalwa, bai wuce tun zuwanta gida dai-dai da rana d'aya bata ta6a gani Madam Salima ta kira waya domin ta ji lafiyar yaranta. Dama Azaad kafin ya dawo kusan kullum sai yai waya dasu which means Azaad ya fi damu dasu fiyye da Madam Salima. Idan kuwa hasashenta ya kasance gaskiya tabbas Madam Salima batasan ciwon kanta ba, ta kuma san darajar 'ya'ya ba. Ta 6angaren Azaad Junaid yana damu sosai da son sani hali da Ahlam take ciki, ya tambayi Nanny Lacey ya kai sau uku ya jikinta sai ta ce dashi tana barci duk da haka hankalinshi bai kwanta ba, yana so ya je d'akinta ya gannta sai kuma ya tuna da Miyya tana d'akin baya so duk wani abu da zai danganta shi da ita. Gudun kada ta rena shi. misali k'arfe biyar na yamma ya Kira Doc Jannat ta zo ta k'ara duba Ahlam ta ji sauk'i sai da zafin jikinta da har yanzu bai rage ba. Amma ta daina amai duk da haka sai ta sake sa mata wani drip. Gani yadda Ahlam ta jigata ya k'ara linka masa haushi da tsanar Madam Salima, ya kuma jefa shi cikin nadama haɗi da danasani aurenta. Misali karfe 8:30pm ya 6aro flat ɗin Jadda ya kira Nanny Lacey ta kawo mishi Ahlam ya gannta yana part ɗinshi. Koda Nanny Lacey ta shigo d'akin Miyya har tayi shirin kwanciya barci saboda throughout bata huta ba tana ta fama da Ahlam. "Pretty har kin kwanta ne?" Cewar Nanny Lacey lokaci da takai dubata wurin da Miyya take kwance sanye da sleeping gown yayin da Ahlam take kwance akan cikinta, sai da tayi k'ok'ari tashi zaune kana ta amsa da cewa. "Eh! Nanny nagaji ne sosai ga Kuma barci da nake ji. "Ayya sannu pretty ai kina k'ok'ari sosai ba Kaɗan ba, dama Yalla6ai ne ya ce akawo mishi Ahlam ya gannta" Jin abin da ta faɗa yasa Miyya ta6e baki wato sai yanzu ya yi lokaci Ahlam ɗin, fuskarta babu wal-wala ta shiga k'ok'arin mik'awa Nanny Lacey Ahlam, yayin da Ahlam ta fasa ihu da sauri Miyya ta dawo da ita jikinta ta rungumeta tana shafar gadon bayanta. "Nanny ki faɗa mishi wallahi yau gaba ɗaya yarinya nan k'iyya take ji bata yarda da kowa ai dai kin ga yadda nake fama da ita ko bathroom ban isa na shiga na barta ba. "Nasani pretty daurewa za ki yi ki kai mishi ita tun da ni bata yarda dani. Da sauri Miyya ta kalli Nanny Lacey fuskarta cike da zallan mamakin furuncinta......... *Not Edited!!* 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 16.... Azaad ya fito daga jirgi as usual fuskarshi a murtuk'e babu annuri ko Kaɗan. Ya shak'i sanyayye iskar mai dad'i gaske, kana ya saki ajiyar zuciya. Direbanshi mr Richard ya je daukarshi. Duk da yana cikin yana yi na rashin jin dad'i hakan, bai hanashi furta addu'ar neman tsari daga sharrin abin hawa ba. "Bismillahi majraha wa mursaha Inna Rabbi laa ya gafurum Rahim" Mr Richard ya buɗe mishi k'ofa ya kame a owners corner, tun shigar shi jirgi yake jin canji a jikinshi wanda ya rasa gane na menene. Ta 6angaren Hasheem Kuma ya sami labarin dawowar Azaad. Ya tura 'yan ta'adda da ya yo hiring su ka la6e a wajen Airport su na jiran fitowar Azaad. Akan idanuwansu Mr Richard ya fito daga cikin airport King Kevin ya duba agogon hannunshi k'arfe biyu da rabi yasaki kafirin murmushi, kana ya fito da silent pistol ya gyarata da kyau. Kana abokin aikinshi Tajo ya kai hannunshi da suna ya tashe mota, ya ji babu key da sauri ya kunna haske dake cikin motar ya ga babu key cike da zallan mamaki ya ke duba k'asan kafafuwanshi Koda ya subuce ya faɗi. Wasa-wasa key ɗin ya ci tudu ya ci rafi, da sauri dukan su suka fito daga mota Tajo sai faman lallu6e ajihunshi yake yi cike da takaici ya shure tayar mota tun su na iya hango hasken motar Azaad har ta 6ace musu fatt....su na ji su na gani mission ɗinsu ya yi failed. Babban abin da ya daure musu kai bai wuce lokaci da suka koma cikin mota ba sai ga key sakale a jikin mota, alamar yana nan a mazauninsa su ne Allah ya d'aukewa gani, shiyasa basu ganshi ba. Cikin kariyar ubangiji da tsarewarshi Azaad Junaid ya iso gidanshi, cikin k'oshin lafiya. Ya yi amfani da k'ofar baya ya shiga part ɗinshi dama haka yake yi duk lokaci da ya yi tafiya ya dawo cikin dare ta k'ofar yake bi. **** ***** ***** *A WASHE GARI* Tun Asuba da Miyya ta falka bata koma barci ba, ta zauna tana morning azkar, sai misali k'arfe 7:00am ta kammala. Ta sauya kayan jikinta zuwa wata half gown wacce ta sauka iya gwiwoyinta, d'an zamanta da Aneesah ta koyi amfani da english dress. Kitchen ta nufa ta tararda da Nanny Lacey tana fera Irish ta shiga taya ta cikin k'ank'ani lokaci suka kammala arranging table, kana ta wuce d'aki tayi wanka tana cikin sanya earrings. Aneesah ta shigo cikin school uniform, murmushi suka sakewa junansu. "Ina Airah?" Miyya ta faɗa tare da daukar perfume bottle tana fesawa jikin kayanta. "Tana Dining room ke muke jira za mu wuce school kada mu yi latti. "Okay mu tafi kawai dama na kammala shiryawa sai na tuna ban saka earrings ba shine na tsaya sakawa sai gashi kin shigo. Ta k'arashe magana tare nufar k'ofar fita Aneesah tana biyo ta baya a haka suka isa dining room, agurguje Aneesah tasha ruwan tea, Miyya tai musu rakiya zuwa parking lot idan direbansu ke zaman jiransu. Har motarsu ta fice daga gate ɗin gidan tana tsaye rungume da hannayenta a k'irji, sosai take sha'awar karatun boko saidai a duk lokaci da tuna Amrah da Amal suna zuwa school, sai taji wani irin dad'i marar misaltuwa ya lullu6e ta. Ko bata samu damar ci gaba da karatu ba tun da siblings ɗinta sun samu shikenan burinta ya cika. ta d'auki dogon lokaci a tsaye kafin ta dawo cikin gida. Sai misali k'arfe 11:45am Azaad Junaid ya falka daga barcin gajiya ya yi wanka ya shirya cikin brown jallabiya, ya saka flip flops a k'afarshi jikinsa na fitarda sihirtattace k'amshin turaren casual oud gold edition. Cikin takonshi na k'asaita yake saukowa daga staircase. K'amshin turarenshi da Nanny Lacey ta shak'a daga kitchen ya isar mata da sak'on dawowarshi. Da sauri ta wanke hannuwanta ta fito, ta iske shi tsakiyar falo tsaye. "Barka da dawowa Yalla6ai. Ta faɗa cikin hausarta da ta zauna daram a halshenta. Ya amsa mata ba tare da ya kalle ta ba. "Yalla6ai akwai abinci a dining room na zuba maka ne?" Ta faɗa kanta yana kallon k'asa. Sai da ya d'auki lokaci kafin ya jinjina kanshi, da mugun sauri ta nufi dining room. Miyya na zaune a d'aki rungume da Ahlam wacce ta lafe a jikinta tun jiya ta ji jikinta da zafi da safe da ta zo yi mata wanka ta ji jikin nata yafi jiya zafi a haka ta lalla6ata tai mata wanka ta shiryata cikin riga da wando ta ɗora mata cardigan akai. Lokaci da ta je had'a mata madara a kitchen, ta sanarda Nanny Lacey ta bata maganin zazza6i madarar ma Kaɗan tasha ta kauda fuska, sai kawai Miyya ta bata magani shine fa ta sake yin barci a cikin barci ta zabura kamar wacce ta tsorata, ta fara tsala kuka a rikice Miyya ta fito daga bathroom. Ta d'auke ta taji jikinta ya yi wani irin mugun zafi, kafin tayi wani yunk'uri Ahlam ta fara kwara mata amai ta baki da hancinta duk idan hankali Miyya yake ya tashi, da gudu ta fito da dukan k'arfinta take kwallawa Nanny Lacey kira. "Nanny Lacey! Nanny Lacey! zo ki gani jikin Ahlam ya yi tsanani sai amai ke fitowa ta baki da hancinta, na shiga uku Nanny Lacey kada wani abu ya sami ta... Idanuwan Miyya sun rufe sam bata lura da Azaad Junaid dake tsaye nesa da ita Kaɗan yana waya da Hakeem, hatta da Hakeem sai da ya ji ihunta, ta cikin waya nan take ya ji matsanancin faɗuwar gaba a nufinshi yanzu da suke waya yana yunk'urin baiyanawa Azaad wacce ya auro mishi sai gashi Miyya ta rage mishi aiki ta baiyana kanta. Tun kafin shi ɗin ya baiyyanata. A gigice Nanny Lacey ta fito daga dinning room hannunta rik'e da serving spoon tsabar rudewar da tayi manta da yana hannunta. Azaad ya waiga a zafafe inda Miyya ke tsaye ya ga wacece ke mishi wannan ihun na fitar hankali, dai-dai lokaci da Ahlam ta sake kwara wani amai gaba ɗaya ya wankewa Miyya jiki. Gudu-gudu ya iso wajen Nanny Lacey ta mik'a hannu za ta kar6e ta, sai kawai tsala ihu tare da k'am-k'ame Miyya. "Kawo ta nan" Cike da k'asaita ya yi magana tare da mik'a mata farare hannuwanshi tass.....da k'arfi Miyya ta kalle shi yadda take kallonshi ba ko kyaftawa zai tabbatar maka da ta tsorata matuk'a da ganinshi. Tsananin rudewar da tayi yasa bata lura da lokaci da ya iso kusa dasu ba. Yadda take kallonshi yai masifar bashi haushi. "Ke nace ki mik'o min ita! Ya faɗa cikin tsawa hakan ya tsorata Ahlam ta k'ara k'am-k'ameta, tana mai k'ara sautin kukanta. Jikin Miyya ya d'auki rawa ta shiga k'ok'ari ciro Ahlam daga jikinta yayin da ita kuma sai k'ara rirrik'eta take yi. Gani ba za ta iya rabata da jikinta cikin sauk'i ba yasa Azaad ya zagaya bayan Miyya don Ahlam taga fuskarshi. "Zo nan Ahlam zo wajen Daddy kinji?" Ya yi magana tare da rik'o hannunta, ta ɗago idanuwanta ta kalle shi kamar tana so tunawa da fuskarshi, sai kuma ta sake fashewa da kuka ta fincike daga rik'e mata hannu da ya yi. Wani irin mashahurin mamaki ya rufe shi saboda Ahlam bata ta6a mishi haka ba. Sosai shiga rud'ani wacece wannan yarinya menene alak'arta da gidanshi da har 'yarshi ta shak'u da ita har haka?" Take furuncin Hakeem ya faɗo mishi lokaci da yake waya dashi, ya ji lokaci da ya ce dashi "Aj Ina so mu yi magana ta fahimta akan amaryarka... Sai kawai ji sautin ihun Miyya dole ya katse kiran. Cikin tsananin tsoro mai cike da zallan tashin hankali Azaad Junaid ya dawo gaban Miyya ya ɗaga dara-dara manyan idanuwanshi, ya bi tun daga tsakiyar Kan Miyya har zuwa ga kafafuwanta da kallo..... *Not Edited!!* 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 18.... Cikin tsananin fusata Hasheem ya cakume collar rigar king Kevin yana k'ok'ari kai masa nushi gani haka yasa Tajo ya taso da sauri ya rik'e masa hannu domin ya tabbata idan har ya kuskura hannunshi ya sauka a jikin KK tabbas da wuya ya kai gobe. Yayin da KK yake kallonshi hankali kwance jira yake yi ya aikata abin da yake nufin aikatawa ya tashi kokon kanshi da alburushi. Tajo ya ja shi gefe yana bashi baki da kyar ya shawo kanshi ya k'ara musu two days idan har kwana biyu ya cika basu kashe masa Azaad Junaid ba, dole su dawo masa da kud'insa. Wanda daga Tajo har KK suke gani ba abu mai yuwa bane dawo da kud'i koda kuwa ba su sami nasarar cimma manufarsu ba. 6ata musu lokaci da baro garinsu da suka yi ba za su yi shi a banza ba. Idan har Hasheem ya kafe lallai sai sun dawo mishi kud'insa to kuwa haka yana nufin numfashinsa za bar gangar jikinsa. ***** **** ***** "Ya naga kin 6ata rai?" Nanny Lacey ta faɗa tana kallon Miyya wacce fuskarta ta baiyyanar da rashin walwalarta a fili ta ce. "Ki yi hak'uri Nanny bai kamata na shiga flat ɗinshi ba, gara na tsaya matsayina na mai kula da yaranshi" Cikin kwantar da murya Nanny Lacey haɗi da rarrashi ta ce. "Haba pretty miyasa za ki faɗi haka ne? Shi fa mijinki ne mallakinki idan har kika ce za ki dinga nisanta kanki dashi babu amfani auren naku kenan. "Ba laifina bane Nanny Lacey sai nake gani kamar shi ma ya fiso hakan" "Ba haka bane Pretty yalla6ai yana da sauk'i kai ta wani 6angare zan iya cewa yana da wuyar sha'ani. Amma ba za ki fahimce hakan ba har kin bai wa aurenku muhimmanci. "Nanny ba za ki gane bane shi ma fa yana da manufar da yasa ya aureni" "Ke yarinya ce k'arama pretty ba za ki yi saurin fahimtar wasu abubuwa cikin sauk'i ba. Ki sani na dauke ki tamkar jikata shiyasa nakeso ki sami rayuwa mai inganci. Rayuwar Yalla6ai Azaad tana tsanani buk'atar mai tallafa mata, Kuma kece za ki kawo wannan tallafi ki d'aure ki yi min biyayya bisa ko wane umarni da zan dinga ba ki, wallahi ba zan ta6a yi abin da zai cutarda ke ba. Shiru Miyya tayi tana nazari maganganu Nanny Lacey d'aya bayan d'aya hakan ne ya bai wa Nanny damar ci gaba da fayyace mata, yana yi rayuwar Azaad Junaid da ta iyalinsa. Kana ta zarce da rarrashinta da kalaman kwantarda hankali da haifar da natsuwa. Sosai jikin Miyya ya yi sanyi ta tsinci kanta da tausayawa su Amrah ko Kaɗan ba ta ji tausayi Azaad ba ganinta shi ya siyawa kanshi saboda shine miji madam Salima mata duk dokar da ya kafa mata dole ta bi koda ace ranta bayaso. Nanny Lacey ta d'an buge kafad'arta ta dawo natsuwarta ta sauke ajiyar zuciya. "Naga Ahlam ta sami barci ki kwanta kawai zan faɗa mishi kun yi barci amma dan Allah pretty da safe ki yi k'ok'ari ki kai mishi ita kinga shi ba girmanshi bane ya dinga zuwa d'aki nan ba kinji yarinyar kirki?" Miyya ta jinjina kanta amma a k'asan zuciyarta tana ji kamar ba za ta iya ba ta amsawa Nanny Lacey ne kawai don ta shafa mata lafiya. Nanny tai mata sai da safe ta fice kana Miyya ta maida kanta bisa pillow tare da rungume Ahlam cikin jikinta daga haka barci mai dad'i ya yi awon gaba da ita. Da fitar Nanny Lacey ta kira Azaad a waya ta faɗa mishi Ahlam tayi barci, duk sai ya ji ba dad'i saboda yana so yaga yanayi jikinta tun safe rabonshi da ita ya fi tsawon minti goma yana safa da marwa daga wannan kusrwa zuwa wannan, daga k'arshe yasaka flip flops a k'afarshi ya fito cikin takonshi na k'asaita d'akin Ahlam ya nufa duk da ba shi da tabbacin ko zai tararda ita, ko Kuma k'ofar d'akin tana a buɗe. A natse ya turo k'ofar luckily ta buɗe ya yi amfani da wayarshi ya haska d'akin idanuwanshi suka hasko masa kan gado Miyya rungume tsam....da Ahlam tamkar ita ce ta haifeta bai san adadin mintocin da ya d'auka yana kallonsu cike da sha'awa wani irin girma da matsayi ya ji zuciyarshi ta bai wa Miyya ya k'arasa daff dasu ya harde hannuwanshi yana mai ci gaba da kallonsu ji yake ko zai shekara a tsaye ba zai gaji da kallonsu ba. Irin kulawar da yake so ya ga Madam Salima tana bai wa yaranshi kenan saidai kashh...Salima bata da lokacinsu business ɗinta yafi mata muhimmanci fiyye da kula da yaranta sai gashi Allah ya kawo k'aramar yarinya mai k'anana shekaru ta magance masa wannan matsalar wacce bai ta6a tsanmani magance ta cikin sauk'i ba. Ya girgiza kanshi tare da hamdallah, kana ya fice daga d'akin yana shiga d'akinshi ya zarce bathroom ya yi alwala ya shiga zuba nafilfili tare da rokon ubangiji ya k'ara wanzar da farin ciki a rayuwarshi da ta iyalinsa. **** ****** ****** Washe gari da wuri Miyya ta tashi kamar yadda ta sabawa kanta, ta taimakawa Nanny Lacey suka had'a breakfast bayan Aneesah da Airah sun wuce school ta dawo d'aki tayi wanka ta shirya cikin tsadaddiyar material gown irin dinki ready made wanda ake zuwa dashi daga Dubai. Yana d'aya daga cikin kayan da Hakeem ya siya mata a yanzu kan hutu ya zauna a jikinta fatar jikinta ta k'ara haske sai shek'i take. Miyya 'yar duma-duma ce bata da tsayi sosai za a iya sakata a jerin gajeru, tana da doguwar fuska tana da hanci dai-dai gwargwado tana da yalwatatce gashin kai da na gira k'irjinta cike yake fam...ga Kuma manyan hips tubarakallah Ma-sha-Allah! Bata cika so d'an kwali ba shiyasa ta yane kanta da k'aramin veil da ya dace da kayan jikinta tana cikin fesa turare, Ahlam ta falka daga barci ta d'auke ta nufi bathroom da ita tai mata wanka, ta shiryata cikin red gown ta d'aure mata gashinta da red band, tayi matuk'ar kyau duk da ta d'an yi rama cikin hukunci na ubangiji yau da tashi babu zazza6i a jikinta. Ta d'auke ta suka fito downstairs parlor kaitsaye kitchen ta nufa ta tararda Nanny Lacey tana goge gas cooker yayin da Linda ke wanke plates ɗin da su Aneesah suka yi amfani dasu. zaunar da Ahlam tayi akan kitchen cabinets saboda tasan halinta ba yarda za ta yi wani ya d'auke ta ba. Ta kammala had'a madara a fida sake daukarta tayi suka fito zuwa parlor tana cikin bata ta shak'i k'amshinsa take ta ji faɗuwar gaba haɗi da tsoro ya ratsata, batasan lokaci da tayi wata 'yar shassheka kamar mai jin sanyi. Ta ɗago idanuwanta a hankali kamar wacce aka yi wa dole karaff... idanuwanta suka sark'e da nashi yana sanye da ash colour suit ya ɗora green colour necktie ya yi mishi balthus Knott style sosai kayan suka k'ara fitowa da shahararren kyawonshi. Da sauri ta janye idanuwanta daga gareshi, saboda Sam bata iya jure kallon cikin fitinannu idanuwanshi sosai suke rud'ata tare da cika mata nata idanuwa. Ya yi kamar bai gannta ba ya nufi dining room, da sauri Nanny Lacey ta fito daga kitchen ta kalli Miyya tai k'asa da murya kamar mai rada ta ce. "Pretty tashi ki je ki yi wa Yalla6ai Azaad serving tun da kina nan babu amfani na ci gaba da yi mishi. Wani iri kallo Miyya take mata baki buɗe kafin ita ma cikin rad'a ta ce. "Ni kuma Nanny haba Dan Allah miyasa kike so ki dinga jefani hurumin da ba nawa ba?" "Saboda ke matarsa ce pretty saboda irin wannan sakaci ya jawo wa Madam Salima zuwanki gidanan, har kika kafa fada mai girma ban kuma san me zai faru anan gaba ba. Miyya tai shiru tana wasa da fida da ke rik'e a hannunta, yayin da gabanta ke ci gaba da dukan tara-tara. "Tashi mana kada ki 6ata masa lokaci yana da kyau ki kiyaye wannan Yalla6ai bayaso wasa da lokaci. Batare da ta ce uffan ba ta tashi d'auke da Ahlam Nanny Lacey bata yi yunk'uri kar6a Ahlam ba, saboda tasan yana da buk'atar ganinta. Ta bi bayan Miyya da kallo tana tuna girman wannan aikin da Hakeem ya sakata tun tafiya ta yi nisa ta fara gani haske. Cikin tafiyarta ta natsuwa mai kama da yanga ta ratso cikin dining room ɗin, hankalinshi yana kan wayarshi yana duba sak'oni{messages} sallama ta fara yi cikin sanyi murya, kafin ta gaida shi. Can k'asan mak'oshi ya amsa mata lips ɗinshi haɗi da adams apples ɗinshi taga sun motsa ya shine ya bata tabbaci ya amsa mata. Ya ajiye wayarshi akan dining table ya mik'o mata santala-santala hannuwanshi tuni ta gano abin da yake nufi ta matsa kusa dashi tare da mik'a masa Ahlam, wacce taso tak'i zuwa ya fizgota da k'arfi ya shiga yi mata wasa. A fakace Miyya ta galla masa harara saboda ya bata haushi ta yadda ya fizge Ahlam ɗin. Batasan cewa duk abin da take yana ganinta ba. Haka zalika duk abin da ya faru tsakaninta da Nanny Lacey ya ji su sarai. Ta zari plate ta zuba masa soyayar doya da haɗin source na kidney & liver ta zuba masa kunu gyada a mug. Sannan ta kar6i Ahlam har ta juya kamar daga sama taji sautin muryarshi. "Nagode Sosai da irin kulawar da kike bai wa Ahlam idan buk'atar wani abu ta taso ki zo kaitsaye ki faɗa min. Miyya ta ja dogon numfashi tare da saukewa abin ya zo mata wani iri tarasa amsar da za ta bashi sai kawai tayi murmushi tare da juyawa ta fice daga dining room ɗin. Cike da natsuwa ya shiga cin abincinsa har ya kammala yana jin kansa kamar ba shi ba. Ya bi ta flat ɗin Jadda ya duba lafiyarta kana ya wuce office, yana shiga office ɗinshi Hakeem na danno kai dama tun d'azu yake dakon zuwanshi, shaking hands suka yi kafin ko wane su ya nemi matsugunni. "Ya ake ciki Aj mijin kwaila ya ka baro kwailar taka?" Hakeem ya faɗa yana k'unshe dariyar shek'inyaci. Azaad ya bata rai cike da miskilancinsa ya ce "Ban kira ka office ɗinan ba don ka karanta min iskaci ba. Na kira ne domin nasan menene matakin karatunta tana da buk'atar komawa makaranta, kasancewarta mai karancin shekaru bai kamata a tauye mata wannan damar ba. Hakeem ya saki murmushi yana kallon Azaad Junaid da girar ido a ɗage, shi Kaɗai yasan abin da yake karanta akan fuskarshi kafin ya ce. "Karatunta ya tsaya ne a matakin k'aramar sakandire {junior secondary School} Azaad ya ta6e baki cikin izza ya ce. "Sai abu na gaba gargadi ne ina fatar za ka natsu ka bani aron hankalinka saboda banaso ace sai na sake mai-maita gargadin nawa....... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 19..... Hakeem ya k'ure shi da kallon mamaki kafin ya ta6e baki ya ce. "Karata gargadin naka kunne ke ji saboda haka ina saurarenka. Saida Azaad ya share 60 seconds kafin ya ce. "Sabon suna da naji ka kirani dashi Ida ka sake kirana dashi za mu kwashe za mu hau sama mu faɗo saboda haka ka kiyaye.... Kafin ya k'arasa magana Hakeem ya kwashe da dariyar mugunta har da su dafe ciki, Azaad ya tsare shi da idanuwa yana mamaki abin da yakewa dariya. Sai da Hakeem yaci dariya iya son ranshi sannan ya kalli Azaad da raguwar murmushi akan fuskarshi ya ce. "Ai yanzu Aj bakada suna da wuce mijin kwaila ko mijin mai nonuwa tsaye Kaɗai ka yi k'ok'ari ka kafa ka tsare ka bada himma nan da wata tara mu sami second Aj... Yadda Azaad ya zazzare idanuwa za ka yi tsanmani wani mugun abu Hakeem ya faɗa, gaba daya ya kasa koda kwakkwaran motsi wani irin tsoron Allah ya lullu6eshi. "Kai miye haka ka wani tsareni da jarababbun idanuwanka Miyya ce ba ta isa daukar ciki ba ko kaine kwanka ya daina fidda tsiro?" "Mtsss.....!! Azaad ya ja dogon tsaki kana ya ɗage girar ido yana yiwa Hakeem kallon kama rena ni. "Gaskiya Hakeem bata ta6a sani da k'asurgumin mahaukaci nake zaune ba sai yau. Har ni Azaad Junaid kake kwatatawa da haɗa shinfid'a da yarinya k'arama sa'ar 'yar cikina? Tsakani da Allah Hakeem ka cuceni and I'll never forgive you.... "D'an dakata mana abokina haramun ne don ka kwanta da sa'ar 'yar cikinka naga dai matarka ce ta sunnah mun shaida ka biya sadakinta, wallahi tun wuri kada ka sa girman kai ka cuce kanka ka ba kasan cewa masu k'anana shekaru nan sun fi juriya da jajircewa ba. D'aure fuska Azaad ya yi saboda ya fahimci damarshi da Hakeem yake gani ne yasa yake kawo mishi wannan zance banzan. "Hakeem please mu rufe wannan zance mu yi abin da yake gabanmu domin kana daff da k'ure min maleji" "To shikenan amma ina tabbatar maka muna nan dakai wata rana za ka canza shek'a ka yi wadak'arka ba tare da ka tuna da k'aranci shekarunta ba. "Aikin banza da wofi an gayamaka ni tsuntsu ne da zan canza shek'a dallah malam ka bani files ɗin na duba ko na bar ka da kayanka. Da sauri Hakeem ya mik'a masa documents ɗin hannunshi ya fizge da kar6i yana dubawa yana zabga tsaki, saboda ba k'aramin haushi Hakeem ya bashi ba. Yayin da Hakeem sai dariya yake yi k'asa-kasa. ***** **** **** A cikin kwanaki biyu Azaad ya nemawa Miyya gur6i karatu a school ɗin su Aneesah, saboda tsabar murna da Aneesah da Airah saida suka haɗa kwarya-kwayan party a d'akin Aneesah har da su saka music suka sha rawa abin da ba su ta6a yi ba tsawon rayuwarsu. Ranar da Miyya ta za ta fara zuwa school tsabar zumudi tun kiran asuba na farko ta falka duk da zumudi da take yi sai da ta shiga kitchen taya Nanny Lacey suka haɗa breakfast. Karfe 7:20am direba ya ajiye su lokaci da Miyya ta shiga aji ta kasa sakin jikinta irin dai bakunta nan da new students ke yi. Sai misali karfe uku suka dawo gida a gajiye ko wane su ya wuce d'akinshi, kawai Miyya tayi ta fito neman Ahlam wacce taci kukan nemanta tana ganinta tafara zillo hannuwanta da sauri Miyya ta sunkuceta ta ɗagata sama tana mata Wasa ita kuma sai wangale baki take yi. Da dare da Azaad ya fito ya yi dinner Nanny Lacey ta shiga har d'akin Miyya ta taso ta ta zo tai mishi serving wanda zuwa yanzu har ya bi jikin Miyya a natse za ta zuba mishi abinci tai tafiyarta abinta sau dama Nanny Lacey tana mata faɗa akan tafiyar da take yi ta barshi, ta kasa sabawar kanta da zaunawa idan yana ci abinci gani take yi kamar zai iya embarrassed ɗinta. Lokaci da Nanny Lacey ta faɗa mata tana kwance sanye da silky material gown mai armless, tasaki gashin kanta ita kanta Nanny da ta kalleta sai da taji ta burgeta matuk'a balle ga d'an namiji mai cikakkiyar lafiya. Turo baki tayi saboda sam bataso abin da zai kusanta ta dashi, ita Kaɗai tasan yanayi da take tsintar kanta a duk lokaci da ta ke6e daga ita sai shi. Mita tashi ga yi wa Nanny. "Nanny please ki barni na huta mana yau fa ne first day ɗina a school dole akwai gajiya a jikina, ga kuma assignment ɗin da aka bani yanzu nakeso nayi kika shigo. "Pretty yaushe kika zama stubborn girl huh?" "Ba haka bane Nanny naga da can kafin zuwana ke ce mai kula da abincinshi, yanzu ma tun da ina da uziri ba sai ki fanshe ni ba?" "Ba zan fashe ki ba kuma dole ki tashi ki ba mijinki abinci wannan ai sakarci ne da rashin sani ciwon kai tashi mana ina magana ki na zaune. Nanny ta k'arashe magana cikin tsawa babu shiri Miyya ta mik'e tsaye tare da daukar k'aramin mayafinta da ke aje a gefen gado{Lol..dama kusan mutuniyar taku da d'an banza tsoro kamar farar kura} jikinta har rawa yake yi saboda ta zaci bayan tsawa za ta ji saukar yatsun Nanny Lacey akan kumatunta. Cikin rashin kuzari ta isa dining room gaba ɗaya k'amshinsa ya cika dining ɗin, tayi sallama cikin siririyar murya kana ta d'an runsuna ta gaida shi ya amsa mata kamar yadda ya saba amsawa, ta zuba abinci a plate ta kai gabanshi, duk abin da take yi yana satar kallonta yayin da har yanzu jikinta bai daina rawa ba ta nufi fridge ta dauko ruwa da drinks, ta je ajiyewa ta take masa k'afa batare da ta lura da k'afar tashi ba. Sosai ta firgita cikin tsananin tsoro ta zabura, sai kawai k'afarta ta bugi kujerar da ke kusa da ita, tayi baya za ta faɗi cikin zafin nama ya rik'o hannunta. Daga zaune da yake bai tashi ba gashi yanayi da ya cafko hannunta taji zafi, ta runtse idanuwanta ga jikinta sai rawa yake yi kamar mai jin sanyi. "Ki dinga duba idan kike tafiya garin wannan rawar kan naki za ki illata kanki a wofi. Cike da k'asaita ya yi magana bai kuma kalleta ba. Miyya ta buɗe tsoratattacin idanuwanta ta sauke su akanshi mamaki ne ya kamata haɗi da kwankwato anyya kuwa shine ya yi magana?" Shine mana Miyya ba gashi nan rik'e da hannunki ba Kuma ai kin waye muryarshi ko a cikin magagin barci za ki iya sheidata. Ta ja gwaron numfashi tare da saukewa a sanyayye ta ja hannunta dake cikin nashi gani haka yasa ya sake ta. Sai lokaci ya ɗago mayatattun idanuwanshi ya kalleta dasu.... _Not Edited!!!_ 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 20... Dukkan jikin Miyya ya d'auki rawa komai yana neman kwance mata, ta rasa wane irin sirri ne a cikin idanuwanshi da duk lokaci da ta kalleshi noti kanta ke kwancewa. A hankali ta juya cikin sanyi jiki bata wuce tako biyu zuwa uku ba ta ji sautin muryarshi. "Ki faɗawa Nanny ta kai min hot coffee falona. Da k'arfi ta waiga ta kalleshi yana ci abincinshi hankali kwance, tasaki ajiyar zuciya kana ta k'arasa ficewa kaitsaye d'akin Nanny Lacey ta shiga ta sanarda ita sak'onshi. Har ta juya Nanny ta tsayar da ita. "Ai kin iya haɗa coffee ki je ki haɗa ki kai mishi a falonshi dake sama" "Ni Kuma Nanny ke fa yace ki kai mishi ba ni ba?" Murmushi Nanny Lacey tayi ta mik'e tsaye ta dafa kafad'ar Miyya, ta ce. "Daga yau ke ce za ki dinga kai mishi kuma banaso gardama ki je kawai ki yi abin da nasaki. "Nanny please ki daina sakani hurumin da ba nawa ba kina gani ko yanzu sai da ya yi min gori ya kirani da mai rawar kai" Ta k'arashe magana kamar za ta fashe da kuka. Nanny ta d'aure fuska tamau alamar babu wasa a tare da ita. "Pretty wai miyasa kike da taurin kai ne?" "Ba haka bane Nanny wallahi mutumin nan ko gaida shi nayi da kyar yake amsawa" "Koma menene wannan ba zai zama hujjar da za ki dogara da ita ki kasa kyautata mishi, a matsayinsa na mijinki. Pretty na fi ki shekaru dole na fi ki sani abin da ya dace da wanda bai dace ba dan haka ki shafawa kanki lafiya ki bi umarni da na ba ki. Kasa furtawa Nanny uffan tayi cikin yana yi na takaici ta juya ta buɗe k'ofa ta fita, zuciyarta tana wani iri tuk'uk'i duk k'ok'arinta na ta hanawa kanta zubda hawaye hakan bai samu ba sai da zafafan hawaye suka wanke kuncinta. Kitchen ta wuce tana haɗa mishi coffee tana shar6a hawaye ko Kaɗan bata k'aunar abin da zai haɗata da Azaad domin ita Kaɗai tasan hali da take shiga a duk lokaci tayi arba dashi. Ta kammala haɗa coffee ta daura mug ɗin aKan k'aramin tray, cikin tsoro take taka matattak'alar benen da zai sada ta da 6angarenshi da ta iso k'ofar falonshi na farko zuciya ta k'ara sautin bugawa fiyye da farko tahowarta, sai ta kai hannunta za ta turo k'ofa sai ta janye, da kyar ta rinjaye zuciyarta ta turo k'ofar ta wangale bugun zuciyarta ya k'ara tsananta cikin tako d'addaya ta fara takawa zuwa cikin ainihin falon. Bata tararda shi cikin falon ba hakan yasa ta sauke k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta dire tray ɗin kan center table ɗin da tagani a tsikyar falon. Ta juya abinta har ta rik'e handle ta tuna da Nanny ta ce da ita ba a falon farko za ta kai ba a falonshi na biyu ji tayi kamar ta ɗora hannu akai ta kurma ihu. Dawowa tayi dole ta sunkuce tray, ta nufi k'ofar glass ta tura batare da ta tsaya shawara ba kamar yadda tayi a farkon shigowarta, Yadda ya ɗago da sauri kalleta yasa ta daskare a tsaye ita bata k'arasa ba bata kuma koma inda tafito ba. Mamaki ganinta yake a dai-dai wannan lokaci a kuma falonshi da ko yaranshi basu ta6a shigar shi ba. Iyakacinsu su tsaya a falonshi na farko. Siririyar sallamarta ce ta katse mishi mamakin da yake. Ya amsa mata cikin taushin murya, sadda kai k'asa tayi ta kasa k'arasawa duk da ya amsa mata sallama. Ya maida ganinshi akan screen ɗin laptop da ke gabanshi, shiru-shiru bai ji ta k'araso ba ya ɗago kanshi ya ganta tsaye kamar an dasa ta ya kira ta ta hanyar ɗaga mata yatsanshi. Tafiya take ta doshi wajenshi yayin da kafafuwanta ke neman hard'ewa waje guda. Da taimakon Allah ta iso gabanshi. k'aramin center table ɗin da ke girke a gabanshi, ta ture tulin files ɗin da ta gani a gefe kana ta aje tray ɗin. Cikin sanyi murya ta ce. "Barka da hutawa Daddy" A natse ya ɗago idanuwanshi ya sauke su akan kyakkyawar fuskarta, sunan da ta kira shi dashi ne ya ji shi wani iri duk da ba yau ne karo na farko da aka kira shi sunan ba. Ya d'an waro idanu waje tare da shafo sajenshi. "Yauwa Sannu" Ya faɗa cikin izza da k'asaita. "Nanny ce ta ce na kawo maka coffee" "Uhmm... thanks! Ya faɗa a takaice yadda yake furta magana cikin izza da k'asaita yai masifar burgeta, har batasan lokaci da murmushi ya subuce mata ba. Har ta kai k'ofar fita ta waiwaya ta kalleshi sai kawai ta tsinci kanta da faɗar. "Daddy iya coffee kake buk'ata Koda akwai wani abu da za ai maka?" Jin muryarta ya sanya shi sake ɗagowa ya cire medical eyes glass, dake lullu6e da kwayar idanunshi hakan ya bashi damar k'are mata kallo from head to toe, ya lefe jikin resting chair da yake zaune tare da lumsashe idanuwanshi. Sai kawai Miyya ta harde hannuwanta a k'irjinta itama ta shiga kare mishi kallo, tana yaba kyawon halittarshi ganinshi take tamkar saurayi d'an shekara 25 idan ba farin sani kai mishi ba. Ba za ka ce shine ya haifi su Aneesah ba. Duk yadda taso ta dauke idanuwanta daga kanshi kafin ya buɗe nashi idanu hakan ya ga-gareta yana ɗago idanuwanshi shima samun kanshi ya yi da kallon cikin idanuwanta, take wani maganadisu ya tsarga musu a jiki tamkar an jona musu wutar lantarki, da sauri ta runtse idanuwanta da baya-baya ta isa ga bango falon ta jinginar da bayanta gudu kada ta faɗi. Wannan shine karo na farko da ta ta6a samun kanta cikin yanayi irin wannan. "Daddy in tafi?" Ta tambaye shi cikin lafazinta mai kama da na mai koyon magana. Samun kanshi ya yi da girgiza mata kai, a hankali ta baro jikin bango ta tunk'aro shi duk takonta d'aya sai ya ji faɗuwar gaba wanda ya rasa na menene. Ta kalleshi tana murmushi wanda ya k'ara jefashi cikin rud'ani. "Daddy me kake so ai maka ne?" Shiru kawai ya yi yana aikin kallonta turo d'an k'aramin bakinta, tayi wanda bata masan tayi ba muryarta cike da shagwa6a ta ce. "Daddy kayi magana mana" Sauri Kiriss numfashi Azaad ya fita daga gangar jikinsa da kyar ya iya dai-daita natsuwarsa, ya zuba mata idanuwanshi wanda suka soma sauya launi. "Za ki iya gyara min gado?" Ya faɗa cikin taushin murya. "Zan iya mana" Tayi magana tana k'ara k'awata fuskarta da yalwatatce murmushi, da hannunshi ya nuna mata Master bedroom ɗinshi wanda tsawon rayuwarshi madam Salima ce Kaɗai ke shigarshi sai kuma yau da shi da kanshi ya lamuncewa yarinyar da ya yi kirari da ba abin da zai yi da ita. D'akin ta nufa tana wani iri cat walks wanda za ka zaci da gangan take yi shi, alhali kuwa halitta ta ce a haka. Bai d'auke idanuwanshi daga kanta ba har saida ta shige d'akin ya daina ganinta kana ya yi ajiyar zuciya. Tana shigar bedroom ɗin ta ja tayi tsaye tana kallon haɗuwa da tsarin d'akin nashi ba k'aramin burgeta d'akin ya yi ba. Komai na d'akin very neat gado ba wani ya lalacewa da ya yi, sai kawai ta canza mishi bedsheet ta wanke bathroom. Koda ta dawo falo ya mik'ar da bayanshi ga jikin resting chair, ya ɗora kafafuwanshi akan center table idanuwanshi suna rufe, saida ta kalle mishi fuska iya son ranta kafin ta dai-daita muryarta ta furta. "Daddy na gama har bathroom na wanke maka" "Thank you! Ya faɗa cikin muryarshi da bata fita sosai saboda k'arfin izza da k'asaita, da kuma bakon al'amari dake yawo cikin jini da bargonsa. "Goodnight Daddy" "Goodnight! Ya furta can k'asan mak'oshi still idanuwanshi a rufe, ta taka a hankali ta nufi k'ofar fita tana daff da ficewa ta waiwaya ta kalleshi idanuwanshi fess...akanta tasaki mishi murmushi mai tsayawa a rai tare da rufu k'ofar. Tana ya fita ya ja k'arfaffiyar ajiyar zuciya gaba ɗaya jikinshi ya saki kasala ta lullu6eshi. Ya kasa ci gaba da aiki da yake yi sai tsallake tulin files ya yi ko ta kanta coffee da ta kawo mishi bai bi ba, ya shige bedroom, ya tsaya tsakk.....yana kallon yadda ta gyara mishi gado karo na farko a tsawon rayuwarshi da mace ta gyara mishi gado kasancewar bai yarda housemaids su shiga mishi d'akin kwana ba. Madam Salima kuma ko lokaci kanta bata da balle na gyara wani abu wai shi gado. Numfashi ya sake saukewa kana ya bi lafiyar gado. Da fitar Miyya ta zarce kitchen ta dauko rubar ruwa a dalili wani irin bushewa da mak'oshinta ya yi d'akin Ahlam da yanzu ya kasance nata ta nufa gefen gado ta zauna ta sha fiyye da rabin ruwan, ta ajiye raguwar bisa bedside kana ta nemi kusa da Ahlam ta kwanta tana runtse idanuwanta kyakkyawar fuskarshi ma'abociya kyau da kwarjini ta bayyana gareta da sauri ta buɗe idanun nata duk yadda taso barci ya d'auke ta hakan ya kasa samuwa. Ta 6angare Azaad shima hakan ce ta faru dashi sai misali karfe uku na dare barci ya d'auke shi, saidai wani abin mamaki gaba ɗaya barcin nashi ya raya shi ne cike da mafalkan Miyya, cikin tsananin firgita ya falka ya tashi zaune kana jinginar da jikinsa ga kan gado, yasa hannunshi yana shafar kwatattce sajenshi cikin yanayi na mamaki da Kuma al'ajabi yake backwards ɗin mafalkin nashi a hankali yabi jikin wando pajamas ɗin jikinsa da kallo, ba ko shakka wanka janabba ya Kama shi. Tun a farkon balagarshi rabon shi da ya yi mafalkin yana saduwa da mace sai yau ko yau ɗin da Miyya da yake yi wa kallon 'yar cikinsa. A gareshi wannan babban abin kunya ne wannan wacce irin masifa ce takeso kunnuwa rayuwarsa?" Ya sauk'o daga gado ya shiga bathroom zuciyarsa fal.....damuwa a haka ya tsaftace jikinsa wani abin mamaki wata irin natsuwa da gansuwa yake ji tamkar a fili ne ya rage mararshi ba a mafalki ba. Yadda ya sami wannan gansuwar a mafalki a wurinta, ya tabbata a bayyane zai sami fiyye da yadda ya samu a mafalki. Praymat ya shinfid'a ya shiga zuba nafilfili yana kai wa ubangiji mai kowa mai komai buk'atunsa. Misali karfe 7:15am Miyya ta fito downstairs parlor sanye da school uniform, tea kawai tasha saboda daren jiya bata samu wadatatce barci ba. A dalili tunanin Azaad Junaid da ya hanata sakatt..... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 21..... Sai kai da komo Hasheem ya ke yi ya kasa zaune ya kasa tsaye, idanuwanshi sun kad'a sun yi jajir lokaci zuwa lokaci yake fesar da zazzafar iska daga bakinsa. Can kuma ya dunk'ule hannunshi na dama ya nushi tafin hannunshi na hagu ya yi hakan yafi a kirga. Tajo ya buɗe k'ofa saida KK ya fara wucewa sannan shi kuma ya biyo shi a baya, tun kafin su k'araso tsakiyar falon Hasheem ya nufe su da gaggawa 6acin ranshi ya kai koluluwa shiyasa yana zuwa ya chafko wuyan Tajo. "Ni za ku yaudara ni za ku cinyewa kud'i batare da kun min aiki da nasaku ba sannan har kai Tajo kake min barazana a waya?" Kafin Tajo ya yi yunk'uri kwatar kanshi Kk ya fito da pistol daga aljihun black leather jacket ɗin jikinsa, ya nuna Hasheem da ita cikin kakkausar muryar ya ce. "Sake shi ko na tashi kokon kanka da wannan. Da mugun sauri Hasheem ya saki Tajo jikinsa ya shiga kakkarwa. "Karka yi haka kk ka dawo min da kudina tun da kun kasa aiwatar da contract ɗin, na k'ara muku two days nan ma kun kasa komai kuma a gabanku Azaad Junaid zai wuce ba ku yi masa komai ba. Ko jiya ina la6e ina kallonku naga lokaci da ya fito daga gidanshi ya wuce ku amma ba ku yi masa komai ba. Hakan ke nuni da cewa ba za ku iya ba..... "Rufemin baki kafin na sauke dukkan fushina akanka Hasheem. Kana tsanmani kisan Azaad Junaid sauk'i ne dashi?" Kaine kake yi wa Azaad kallon sakarai amma shi yasan abin da ya taka. Shu'umancinsa ya zarce naka, zai fi maka alkhairi da ka hak'ura da son ganin bayansa. A cikin kwanaki biyu da ka k'ara mana kasan irin bala'o'in da muka dinga cin karo dasu a duk lokaci da muka yi yunk'uri sheke shi?" Jiya har dare muna la6e a jikin katangar kamfaninsa, a maimakon na kashe shi ni ne na kusa mutuwa saboda haka ka nemo wani yai maka wannan aiki, Amma inaso kasani duk yadda kake tunani Azaad Junaid ya zarcewa tunaninka. Kud'inka kuma k'arfi yaci idan ka matsa sai na dawo dasu to kasani komai zai iya faruwa daga ciki har da rasa rayuwarka. Saboda haka ka za6a ranka ko kud'inka?" "Ba zai yu ba kk kud'inan su na da yawa fa..... Kafin ya k'arasa magana kk ya buge tsakiyar kanshi da bindigar hannunshi, zafi da radadin azaba suka ratsa kwakwalwar Hasheem ya kurma ihun neman taimako tare da sulelewa k'asa yana dafe da fasashe kanshi da ke zubda jini, duk da haka kk bai kyaleshi ba saida ya har6eshi a k'afarshi ta dama yana k'ok'ari sake saki mashi wani harsashe a k'irji Tajo ya dakatar dashi ta hanyar jan shi da k'arfi suka fice daga falon. Kasancewar a gidan gona suke, gate yana da nisa da inda suke shiyasa duk ihu da kururuwar da Hasheem ke yi maigadi bai ji ba. Har jini ya buge shi ya some. ***** **** ****** A hankali take saukowa daga matattak'alar jirgi yayin da k'awarta Hafsat Shinkafi ke biye da ita kamar jela. Tun kafin su k'araso direbanta mr Michael ya buɗe musu k'ofufin mota duk lokaci da tai tafiya Mr Michael ne Kaɗai ke sani dawowarta. Duk gaisuwa da yake mata ko kallo bai isheta ba, sai Hajiya Hafsat ce ta amsa mishi. Sai da suka fara sauke Hafsat Shinkafi gidanta koda ta iso gidanta ana kiran sallar magarib. Cike da izza ta fito daga mota da azama mr Michael ya nufi k'ofar main parlor ya buɗe mata, jin k'arar takon takalminta ya sanya Nanny Lacey ɗagowa daga tattara toys ɗin da Ahlam da ta gama wasa dasu, gabanta ya yi mummunan faɗuwa sakamakon gani madam Salima. Jikinta na rawa ta gaidata tsabar girman kanta da izzarta basu bari ta amsa ba sai yatsunta guda biyu ta ɗagawa Nanny Lacey, ta haura staircase ta nufi 6angarenta. Nanny ta bi ta da kallo inda sabo ta saba da ɗagawa da izzar madam Salima. Yanzu duk tsawon shekaru da ta d'auka tana mata hidima da yaranta ace bata kallonta da gashin arziki, kusan watani biyu har da sati uku kenan da tayi tafiya ko a waya bata ta6a kiranta ta ji lafiyar yaranta ba. Hakazalika ta dawo ko ba za ta tayi lafiyarta ai ta tambaye na yaranta. Shigowar mr Michael janye da luggage ɗinta ya katsewa Nanny zance zuci da take. Ta kar6i trolley ɗin daga hannunshi ta kai mata d'akinta koda ta shigo tana cire kayan jikinta a hankali ta ajiye mata luggage ɗin har Nanny ta buɗe k'ofa za ta fita ta ji ta kira sunanta. "Nanny! "Yes madam! "Ki sanarda Azaad na dawo amma karki faɗawa yara ki bari sai zuwa gobe, saboda ina da buk'atar cikakken hutu. Tsabar takaicinta da ya lullu6e Nanny Lacey kasa magana tayi sai jinjina kanta tayi, har ta koma d'akinta tana yaba rashin k'awa zuci irin na madam Salima. Miyya ta fito daga wanka a gaugauce ta tsane raguwar ruwan jikinta ta zura doguwar riga da hijab tayi sallar magarib bata tashi ba har saida tayi sallar isha. Samun kanta tayi da yi simple makeup ta sanya wide legs trouser haɗi da pink bias top ta yane kanta da scarf jikinta na fitarda sanyayye kamshi. D'akin Aneesah ta shiga domin ta k'ara mata haske akan assignment ɗin da aka basu bayan su kammala assignment ɗin. Su kayi dinner sannan ta dawo d'akinta. Nanny Lacey na cikin goge dining table Azaad ya shigo cikin girmamawa suka gaisa, kana ta sanarda shi madam ta dawo nan take annurin kan fuskarshi ya d'auke cakk... kamar an yi ruwan sama an dauke, ita kanta Nanny ta lura da sauyawa tashi faratt d'aya. Bai ce da ita uffan ba ya nufi 6angarenshi. Har Miyya ta kwanta ta tuna da bata bai wa Daddy abinci ba ta tashi zubur, ta d'auki scarf ɗinta da ta cire ta fito downstairs parlor. Ta nemi cushion ta zauna tana jiran fitowarshi har 11:00pm ta buga bai fito ba. Batasan cewa yau a 6angaren Jadda ya yi dinner ba. Da taga ji da zama sai kawai ta yanke shawara ta kai mishi coffee. Tana sanda kamar 6arauniya haka take tattaka matattak'alar bene da zai sadata da 6angarenshi, tana zuwa k'ofar falo bata tsaya neman izzini ba ta buɗe ta shiga kanta tsaye ta wuce falonshi na biyu. Yana zaune da system a gabanshi yana gudanar da online meeting, sallamarta ce tasa shi ɗagowa, har ta k'araso inda yake zaune bai d'auke idanuwanshi daga kanta ba. A k'asan zuciyarshi yake yaba tsin-tsan kyau da tayi a cikin kwanaki nan completely ta sauya wa sanin da ya yi mata, gashi ta hanawa zuciya da gangar jikinsa natsuwa bashida aiki sai na tunaninta, idan har bai yi da gaske ba yarinya k'arama za ta zauta shi saboda haka zai taka mata birki, kada ta kai shi da aikata abin kunya. Ta sauke tray hannunta akan center table cikin sanyayya murya ta ce. "Daddy yau lafiya ba ka fito dinner ba?" Ya kalleta cikin d'aure fuska gudun kada taga damarshi, ya ce. "Naci a 6angaren Jadda. "Iyeee....ashe yau Daddy dad'i kaci. Ta faɗa tana dariya mai ban sha'awa...... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 22.... Baisan lokaci ya da ya saki mata murmushi ba, a k'asan zuciyarshi so yake ya taka mata birki ta daina shigowa mishi part amma ya kasa furta mata sai kawai ya tsincin kanshi da faɗin. "Kema za ki iya zuwa ki ci dad'in. Ya k'arasa magana yana zuba mata idanuwanshi, masu rikita ta a duk lokaci da ya kalleta dasu. Ta rausayar da kai tana ci gaba da murmusawa cikin sigar shagwa6ar da murya ta ce. "Ba wani nan Daddy da kaso naci dad'in da ka zo min da nawa ko kuma lokaci da za ka je 6angarenta da ka aiko min da katin gayyata" Yadda take magana tai masifar tafiya da ruhi da gangar jikinsa, ya gama fahimta muddin bai da gaske ba tsaf k'aramar yarinya nan za ta zuzuta shi a hankali ya ɗago idanuwashi ya sauke su akan fuskarta wacce ke ta glowing cikin haske bulb ya saki murmushi tare da furta. "Wai ke bakya ji barci ne?" "Uhm..bana ji" Ta faɗa tana turo d'an k'aramin bakinta, hakan ya k'ara kunna wutar abin da yake ji akanta da sauri ya kauda fuskarshi yayin da gabanshi ke wani iri bugawa da k'arfi. Ya sauke numfashi kana ya nuna cushion ɗin da ke facing ɗinshi da hannunshi batare da ya yi magana ba. Da kanta ta fahimci abin da yake nufi cikin salon tafiyarta mai jan hankali ta nufi kujerar ta zauna, ta ɗago idanuwanta suka sark'e da nashi bugun zuciyarsu ya tsananta. Tai sauri runtse idanuwanta tana jan wahalallen numfashi. Ta sadda kanta k'asa. Shiru ya biyo baya shi bai tanka ta ita kuma bata sake yi magana ba ko wane su yana faman da bugun zuciya, Azaad ya kasa samun wadatatciyar natsuwa da zai ci gaba da gudanar da meeting ɗinshi lokaci zuwa lokaci take ɗagowa ta saci kallonshi kuma duk sanda ta ɗago idanuwashi na kafe akanta tamkar yana karanta wani abu, akanta ne. Rashin natsuwa da yake ji yasa sai faman shafar sajenshi yake yi can kuma cikin rikitatciyar murya ya ce. "Pretty ki je ki kwanta please kinsan gobe kina da school ko kinaso ki yi latti tashi ne?" Kamar jira take yi ya bata umarnin tashi ta mik'e zubur ta nufi k'ofar fita saida ta rik'e handle ta juya tare da faɗin. "Goodnight Daddy! "Goodnight" Ya faɗa kamar mai ciwo hak'ora. Ta k'arasa ficewa kamar yadda ta shiga part ɗin nashi cikin sand'a haka ta fito tana sand'a tana isa k'ofar d'akinta tai wuff....ta shige tare da rufu k'ofa. A tsorace take gudun kada tsautsayi ya gitta Aneesah ko Airah wani daga cikinsu ya gannta ta fito part ɗin Daddynsu, dole su tambaye me ta je yi a halin yanzu batasan amsar da za ta basu wacce za ta zama kariya agareta. Da wuri Miyya ta tashi kamar yadda ta saba ta shirya cikin school uniform ɗinta sosai uniform ɗin suka k'ara fidda kyawonta. Side by side suke tafiya ita da Aneesah zuwa parking lot kasancewar Airah tariga su fita tuni take zaune a mota tana zaman jiransu sai faman zabga tsaki da duba agogo take yi, saboda tana da presentation gashi suna so 6ata mata lokaci. Azaad Junaid da ke tsaye a balcony da mug ɗin coffee a hannunshi lokaci zuwa lokaci yake sipping idanuwanshi suka sauka akan fuskar Miyya dai-dai tana kai ma Aneesah duka a kafad'a da alama Aneesah ɗin tana tsokanar ta ne. Har suka isa gun mota suna wasa a tsakaninsu. Yayin da dai-dai da second d'aya bai d'auke idanuwanshi akanta ba. Gani yadda skirt ɗin uniform ɗinta ya tsaya iya gwiwoyinta, gashi d'an k'aramin hijabi half sunna suke sakawa ga hijabi yabi k'irjinta shiyasa ake iya gani satin cikakkun boobs ɗinta. Take ji wani iri mashahurin kishi wanda tsawon zamanshi da Salima bai ta6a ji kwatan-kwacinsa ba. Ga Salima ba iri banzar shigar da bata yi da sauri yasa ɗayan hannunshi ya dafe saitin zuciyarsa da ke mishi barazanar tsalle ta faɗo k'asa. "Na shiga uku ni Azaad meke shiri faruwa dani?" Ya faɗa a baiyane, yayin da fuskarshi ta bayyana tsoron da ke shigar shi ya sauke wata k'arfaffiyar ajiyar zuciya, jikinshi a mace ya nufi gym room{d'akin motsa jiki} gym mat machine ya fara hawa tsawon lokaci ya share akanshi kafin ya yi switch off ɗinsa. Jikinshi ya jik'e sharkaf da gumi. Direct bathroom ya wuce ya yi wanka cikin minti goma ya shirya cikin black suit yana cikin ɗora wrist watch, ya ji an turo k'ofa ta jikin mirror da yake tsaye ya hango madam Salima tana sanye da bathrobe ta ɗora small white towel akanta da alama fitowarta daga wanka kenan ta shigo part ɗin nashi. Yana arba da ita ya ji wani irin 6acin rai shiyasa yai sauri d'auke idanuwanshi akanta ya mayar bisa wrist watch ɗin. Ta k'araso cikin izza da jiji da kai ta zauna gefen gadonshi tai crossing legs ɗinta babu sallama balle ya ci daraja gaisuwa ta kalleshi cikin izzarta da tafi komai bashi haushi a tattara da ita ta fara magana kamar wacce aka yi wa dole. "Ina da tabbacin kana da masaniya da tun jiya na dawo, am very sure Nanny ta faɗa maka sak'on dawowata. Ta d'an dakata da magana tana wani yatsine fuska tana jiran ta ji ya fara apologies ɗinta sai taga kawai yana k'ok'arin saka derbies black cover shoe ɗinsa Kuma ta lura da tun lokaci da ta shigo ko kallonta bai yi ba. Hakan ba k'aramin sosa mata rai ya yi ba. Cikin fushi ta kira sunanshi. "Azaad! A hankali ya ɗago idanuwashi ya k'are mata kallo tass....kana ya cije lower lips ɗinshi tare da ɗage girar ido idan Azaad Junaid yana so yai mata mutum wulak'anci irin kallonan yake yi gani yake ba k'aramin koma baya bane a gareshi ya tsaya, musanya yawu da ita musanmman da yake da important meeting, saboda haka ya d'auki briefcase ɗinshi da ke aje akan bedside drawer ya nufi k'ofar fita cikin yanayi tafiyarshi ta k'asaita. "What hell think you're Azaad ina magana da kai you're ignored me?" Lets me tell I can take this anymore. Girgiza kanshi tare da buɗe k'ofa ya fice abinsa, ta taso cike da masifa ta biyo shi a baya tana ci gaba da zazzaga mishi masifa. "Azaad come back here I want to talk to you karka fita ka tsaya nace zan yi magana da kai banso wulak'anci you already know that. Har suka sauko downstairs parlor bai tsaya ba ita kuma bata fasa bin shi ba tana zubda ruwan rashin mutunci. Da gudu 'yan aikinsu suka watse Nanny Lacey ma d'akinta ta shige har da su murza key tana tsanmani, Azaad ya faɗawa madam zance aure da ya yi ne shine ta buɗe kwadon masifa da sanyi safiya. "Dole ka dawo ka ji da matsalata first kafin ka fita, ko kana da abin da yafini muhimmanci ne? Jin abin da ta faɗa yasa shi sakin handle ɗin k'ofa ya juyo a mugun fusace, cikin kakkausar murya ya ce. "Me kika ce Salima?" Yadda yai mata tambayar tasan ta reni ce da so gani k'arshenta, shiyasa ta kalleshi da murtuk'akk'iyar fuskarta. "Duk abin da na faɗa ka ji ni sarai....so no need to repeat.. Ta faɗa tana irin mak'e kafad'a da watsi da hannuwanta da ke nuni da zallan reni. "A tunanina Salima its over between us ko kin manta we're already divorce? Saboda haka ki fita harkana a hali yanzu kwata-kwata bana buk'atarki a rayuwata. Tun daga ranar da kika sa k'afa kika fita daga gidanan tare da yi fatali da umarni da rantsuwata ni kuma tun daga ranar I erased all the moment I'll have spend together.... "Ya isheka haka Azaad! Ta faɗa sounding very angry idanuwanta suka firfito, ta kuma finciko towel ɗin kanta tai jifa dashi tasoma tattaki ta nufo shi tare da nuna k'irjinta da yatsa gaba ɗaya mamakin maganganunshi take yi ta kasa yarda daga bakinsa suke fitowa. "Ni...ni Salima...Azaad kake gayyawa you erased all the moment I'll have spend together are you insane?" "Lokaci ne za ban-bance mana tsakani ni da ke waye mahaukaci. "To wallahi-tallahi bari ka ji Azaad ban amince da wannan saki ba saboda haka you have to cancel it, an gayamaka na shirya rabuwa da kaine?" You have to ask me first kafin ka yanke wannan banzar hukunci naka, saboda haka ni ban shiryawa rabuwa da kai ba because I want to spend the rest of my life with you so you better cancel that stupid divorce.... Cikin kad'uwa Azaad yake kallonta tare da waro idanuwanshi. "Ashe duk tsawon shekaru nan da kidahumar jahila nake zaune ban ta6a sani Salima ke k'asurgumar mahaukaciya bace sai yau da kika fito min da 6oyayyen asalinki. Inaso ki buɗe kunnuwanki ki saurareni da kyau wallahi-azim idan duk duniya nan za taru akaina na gama aurenki. Yana k'arasa magana ya juya cike da 6acin rai ya buɗe k'ofa da k'arfi ya fita yana bi sa hanyarshi ta zuwa kamfaninsa, na Gold Hakeem ya kirashi ya fesa mishi mummunan labari an har6en Hasheem a gidan gonar babban Yaya fasa zuwa company ya yi nufi prime hospital inda Hasheem yake likitoci sun duk'ufa ceto rayuwarshi, ana sa ran sai an cire mishi k'afa a dalili kwayoyin cuta sun shiga cikin raunin har sun ta6a naman k'afar tashi kasancewar har saida ya kwana ya yini kafin maigadi ya farga da hali da yake ciki. Madam Salima ta fi minti goma a tsaye ko kwakkwaran motsi ta kasa da kyar ta iya jan kafafuwanta da suka yi mata mugun nauyi har kamar ba nata ba. Har wani bishi-bishi take gani, ga zuciyarta dake mata mugun tuk'uk'i a haka ta soma tattaka matattak'alar bene duk lokaci da ta taka one stairs sai ta tsaya ta sauke wahalallen numfashi, kamar mai cutar asthma koda ta isa d'akinta ta jigata matuk'a, sai kawai ta kife akan tangamemen gadonta. Sai tayi yunk'uri yi kuka ko za ta ji sauk'i abin da take ji yana mata yawo a kahon zuciya, sai ta danne shi da k'arfin tsiya a ganinta zubda hawaye na rakwaye mata ne ba na iri-irinta jajirtattu bane. Idan har ta bar hawayenta suka zuba akan kumatunta hakan na nufi ta faɗi, kwata-kwata a tsarinta babu faɗuwa sai zallan nasara. Tabbas Azaad ya taro match kamar yadda ya faɗa ne idan duk duniya za su taru akanshi ya gama aurenta. Ita ma abin haka yake a wurinta idan duk duniya za su taru akanta yanzu ta fara zaman aure dashi. Yayin da shed'aniyar zuciyarta ta ce da ita "Haba Salima yaushe kika fara sakin jiki da har wani mahaluki zai haifar miki da damuwa?" Azaad ya k'ikk'iro wannan hanya ne domin ya sami lagonki ya rusa miki business career dinki idan kika bari yai nasara akanki shikenan babban company zai koma hannun 'yan uwanki, karki manta burinki ya ta'alak'a ne da son mallakarsa ke Kaɗai. Babu shiri ta mik'e zubur a lokaci d'aya k'arfi da kuzarinta da rasa na wancan gadin suka dawo jikinta tamkar ba abin da ya faru da ita a cikin k'ankani lokaci ta shirya cikin Indonesia gown mai adon sequence sai kyali da daukar ido take. Ta fice abinta daga gidan kaitsaye gidan aminiyarta Hafsat Shinkafi direba ya sauke ta.... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 23.... Tun lokaci da ta fara labartawa Hafsat Shinkafi labari abin da ya faru, tai k'uru da idanuwa tana kallonta duk tsawon shekaru da tai da madam Salima batasan cewa bata da ilimin addini kwata-kwata ba. Ta zaci kawai dai bata yi zurfi a ciki ba ashe tunani da hasashenta ne ya bata hakan. Cabdijam.... lallai Salima jahila ce lamba d'aya wato ita tsabar ruwan boko da ta kwankwad'a da kuma cudanya da masu jajjaye kunnuwa ta kwashe dabi'unsu tsaf in banda hauka da jahilci a ina aka ta6a sakin mace har ta kusa gama iddah ta ce bata aminta da saki ba. Watakila bata ma san menene iddah ba. Ajiyar zuciya Hafsat ta sauke kana ta cire tagumin da tayi cikin natsuwa ta fara magana. "Gaskiya Salima kin tafka babban kuskure na 6oye min message ɗin da Azaad ya turo miki, da tun farko kin faɗa min da na wayar miki da kai. "Mtsss....dallah ya isa Hafsa ni fa kwata-kwata ban d'auke message ɗin da muhimmanci ba. Azaad bai isa ya yanke alak'ar aurenmu ba... "D'an dakata mana Salima! Hafsat ta faɗa da sauri tare da tasowa ta zauna daff da Salima kana ta zarce da faɗin. "Salima idan ke ba ki da ilmin addini ko tantama bana yi Azaad yana dashi. Kuma shi ɗin ba mahaukaci bane, a lissafi na saura kwanaki Kaɗan ki kammala iddarki idan har kika kammala ta batare da Azaad ya furta ya dawo dake ba. To ki sa aranki aure ke dashi hayatan-hayatan har sai ya sake biya sadaki an ɗora muku wani aure. Da Kuma saki uku ne ba za ki sake halatta agareshi ba har sai kin sake wani aure idan Allah ya kawo k'addarar rabuwarku da wancan mijin da kika aure sannan ne kike da damar sake aure Azaad Junaid. Salima babban abun da ya cuce ki rashin ilimin addini da kina dashi ko kusa ba za ki furta rashin amincewa da sakin da Azaad yai miki ba. Allah {S.W.T}ya halatta saki a hannun maza saboda mace tana da saurin fushi da saurin yanke hukunci. Mafi yawanci mata suna tafiyar da al'amuransu akan abinda zuciya ta raya musu. Amma shi namiji yana da zurfin tunani da hangen nesa, Kuma zai yi hasashe tare da yin aiki da hankali. "Dallah....ya isa haka Hafsat kin wani tsareni da dogon sarhi in fact kwakwalwarta ba za ta d'auke shi ba. Gara kawai ki faɗa min hanyar da zan bi na dai-daita al'murrana. Doguwar ajiyar zuciya Hafsat ta sauke tana girgiza kanta tabbas sai yau ta k'ara yarda da magana nan ta masu iya magana da ke cewa jahilci yafi hauka. "Salima ni fa ina k'ok'ari na haska miki haske ko za ki fita daga mummunan duhu da kike ciki, ke kuma kina danganta ni da dogon sarhi. Wallahi-tallahi idan har kika ci gaba da tafiya a haka gaba ɗaya al-amurranki ba za su dai-daita ba. Saidai su ta6ar6are gwara tun wuri ki natsu na ɗora ki akan hanya. "Na ji Hafsat amma ni wannan karatun naki zai shigeni ne bayan ki faɗi hanya da zai bi Azaad ya dawo da aurenmu. "Mtsss....wai Salima meke damunki ne huh?" Sai nayi gabas kiyi yamma yanzu nan ma ba hanyar ce nake faɗa miki ba. "Shikenan Hafsat ina sauraren ki. Ta faɗa cike da izza tare da nuna k'osawarta. Yayin da Hafsat ta gyara zamanta ta cigaba da faɗin. "Salima a halin yanzu dole sai kin sauke wannan girman kan naki da izza, ki bi hanyar maslaha ki karkato da hankali Azaad kafin iddarki ta cika ya dawo da aurenku karki sake iddarki ta cika bai dawo da ke ba. Idan har da gaske kina da burin ci gaba da zama matar Azaad Junaid dole ki sauke girman. Ki bashi hak'uri idan ta kama ki durkusa on your knees.... "Whats?" Hafsat kinsan abin da kike faɗa kuwa? No....no... Its can not be possible haba ki sake shawara ban da wannan na durkusa fa kika ce? "To ai shikenan tun da ba za ki iya ba amma inaso ki fara lissafa kanki a jerin zauwarawa, ki kuma fara hango Azaad Junaid da tsaleliyar amaryarshi. Zuciyar Madam Salima ta buga da k'arfi duk duniya ba abin da ta tsana irin ta ji an danganta Azaad ɗinta da wata mace ba ita ba. Cike da 6acin rai ta kalli Hafsat ta ce. "Hafsat zan dawo da Azaad gareni batare da na k'ask'antar da kaina ba, ki tuna ni mace ce mai k'arfin iko da izza ban ta6a yarda da faɗuwa ba sai nasara saboda haka Azaad zai dawo gareni ko yana so ko bayaso. "Salima karki yi ganganci domin iddarki tana daff da cika, ki tuna aiki da hankali yafi aiki da agogo. "Kai... Hafsat...kai! Gaba ɗaya kin isheni da zance iddah wai wacece wannan iddar da keso shiga tsakanina da mijina?" "Innalillahi wa'aina illahim raji'un! Hafsat ta faɗa tana tafa hannuwanta cike da kad'uwa take kallon madam Salima, kafin ta girgiza kai tana ta6e baki. "Ni dama nasan za ayi haka hasashena kuwa ya tabbata gaskiya, Salima iddar ce ba ki sani ba anyya kuwa Salima kina gudanarda addininki yadda shari'a ta sharad'a?" 6ata fuska tayi cike da izgilanci ta ce. "Banso maganar banza Hafsat za ki faɗa min wacece iddah ko na d'auki jakkata na bar miki gidanki?" "Uhmm....jahili ya fi mahaukaci hauka. Hafsat ta faɗa cikin zuciyarta a bayyane kuma sai ta ce. "Yanzu kuwa zan faɗa miki wacece iddah? Iddah ba mutum bace kamar yadda kika zata. "Idan har ba mutum bace to wacece ita ko aljana ce?" Madam Salima ta watsa mata tambaya tare da yatsine fuska. Hafsat bata bi ta kanta ba ta gyara zamanta ta tattaro natsuwa da dukkan hankalinta ta mayar dasu akan Salima. "Iddah ita ce zaman jira da mata ke yi bayan sun rabu da mazajensu kafin su sake yi wani aure. Ita kanta iddar kala biyu ce akwai iddar rasuwa akwai iddar rabuwa. "D'an dakata mana Hafsat ita iddar hadda ta mutuwa akwai? Cab.... gaskiya wannan iddar akwai rikitarwa. "A wurin marar ilimin kan tana da matuk'ar wahala fahimta amma a gun mai wadattace sani ba abin da ya fi ta sauk'i. "Ban fahimci ki ba Hafsat ki yi min magana da yare da hankali da tunanina zai d'auka?" "Idan har kinaso hankali da tunanina su dauka sai kin daina katse ni kawai ki buɗe kunnuwanki ki saurare abin da nake faɗa domin ke zai amfana ba ni ba, saboda ni nasan da wannan babin tun ina da shekaru goma sha uku a duniya. Sosai ran madam Salima ya fara 6aci tsakani da Allah ba don tanaso sani wacece iddar nan ba, da tuni ta wufce jakkarta tabar ma Hafsat Shinkafi gidanta. Gani yadda take cika tana batsewa yasa Hafsat bata jira jin ta bakinta ba ta ci gaba da cewa. "Iddar rasuwa ita ce bahaushe yake kira da takaba. Ita ɗin ma kala biyu ce akwai takabar mai ciki ita iddarta tana kammala ne daga lokaci da ta haihu. Wacce ba mai ciki ba Kuma zata zauna ne tsawon watani huɗu da kwanaki goma. Nau'in iddar rabuwa ta kasu kashi uku iddar mai ciki, da iddar mai jini haila sai Kuma mace da bata fara jini haila ba. Ko Kuma wacce ta fidda rai daga zuwan jini haila bima'ana tsohuwa. Iddar mace mai ciki za ta zauna ne har zuwa lokaci da ta haife ciki. Idan ta haihu to iddarta ta k'are Koda kuwa ranar da aka sake ta ɗin ne ta haihu. Iddar mace mai jini haila, sai tayi jini uku. Da zarar tayi jini uku shikenan iddarta ta kammala kamar ke kenan tafiyar da muka yi kin yi menstruation sau biyu yanzu da zarar kin sake yin wani kin gama iddarki sai fatan samun wani miji idan kina da sha'awar sake aure. Sai Kuma iddar tsohuwa ko k'aramar yarinya...... "Ya isa Hafsat ai kin riga kin faɗi iya abin da nakeso ji ki bar saura kawai idan natsuwata ta dawo jikina Kya faɗa min. Jikinta na rawa ta mik'e ta d'auki handbag ɗinta da ke aje akan center table, ta dubi Hafsat da idanuwanta da suka fara canza launi ta ce. "Hafsat zan tafi gida tabbas a yau ɗinan zan kira ki da albishir ɗin Azaad ya dawo da aurenmu. "Ina miki fatan haka Salima amma idan burinki ya cika ki nemi malamin addini, ya k'ara miki haske akan sha'ani addini kada ya zamana kina amsa suna musulunci ne kawai. Gaba ɗaya rayuwarki Salima neman duniya kawai kika sa gaba, kin manta da neman lahira al'hali lahira a duniya ake nemanta wallahi da zarar ka mutu shikenan.... "Nagode da shawara Hafsat. Ta katseta cikin k'osawa da zancenta, ta juya cikin tafiyar sauri koda ta fito direbanta yana zaune a mota yana jiran fitowar yana d'aya ɗaga k'a'idojinta duk idan ya kaita bai isa ya tafi ba dole ya zauna har ta gama abin da ta je yi. ***** ***** ******* Duk wani shige da fice na asibiti Azaad ne ya yi hatta da jini da za a yi wa Hasheem surgery nashi aka d'iba, ko Kaɗan bai so a cirewa Hasheem k'afa ba so ya yi ya fitar da shi waje, saida doctors ɗin suka yi connecting ɗinshi da wani asibiti dake Germany suka turo musu bayyanai Hasheem su ma sun bada shawarar a cire k'afar kawai saboda ta riga ta fara lalacewa. Daga k'arshe sai yanke k'afar aka yi, lokaci da aka fito da Hasheem daga theatre room Azaad har dasu kuka saboda ba k'aramin tausaya mishi ya yi ba. Saida ya ga an kammala komai sannan ya wuce kamfaninshi koda ya iso tuni Hakeem ya wakilce shi meeting ɗin da za su yi. Bayan sun Miyya sun dawo daga school suna zaune a downstairs parlor, Nanny Lacey ta fito daga kitchen sai lokaci take sanarda Aneesah da Airah dawowar Mommy. Nan take gaban Miyya ya faɗi duk wani annuri da ke kan fuskarta ya gushe, har wani zazza6i ta ji yana neman rufe ta. Daga Aneesah har Airah ba wanda ya nuna farin cikinshi da dawowar mommy ɗin, sai ma aikin gabansu da suka ci gaba da yi. bayan kamar minti goma da Nanny ta faɗa musu dawowar madam, suka ji karar buɗe k'ofa a zatonsu daddy ne ko wasu bak'i sai kawai suka yi tozali da madam Salima fuskarta a murtuk'e ko daga yanayi tafiyarta Kaɗai za ka gano irin zallan 6acin ran da take ciki. Miyya tana ɗago idanuwanta sai akan fuskarta kasa ci gaba da kallonta tayi shiyasa tai maza ta mayarda ganinta akan Ahlam da ke kwance a cinyoyinta tana barci. "Welcome mommy! Aneesah da Airah suka faɗa a tare yadda suka gaidata bai yi kama da gaisuwa irin ta uwa da 'ya'yanta ba. Daga haka ba wacce ta k'ara koda kallonta ne. Ita ma hannu kawai ta ɗaga musu ba wani kulawa balle ta nuna tayi kewarsu tana daff da fara taka matattak'alar bene idanuwanta suka hasko mata Miyya...... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 24... Har ta buɗe baki da nufi yi magana sai kuma ta tuna da k'alubali da ke gabanta. Yanzu ba lokaci tambaya da neman sani wacece wannan bak'uwar fuska da ke hakince a falonta wacce ko arziki gaisuwa bata samu daga gareta ba. Ba komai ko ma wacce idan ta dawo natsuwarta za ta ji da ita. Tayi kwafa har da su cije le66e ta haura sama da shigarta d'aki tai wulgi da handbag tare da mayafinta kana ta cire kayan jikinta wani iri nauyinsu take ji. Miyya tana gani madam Salima ta haura sama, ta tashi da sauri ta shige d'akinta. Aneesah ta bi ta da kallo saboda ta lura da sauyawarta tun daga lokaci da tai arba da mommynsu. Miyya ta kasa samun sukuni shigarta d'aki bai amfana mata komai ba. Sai ma k'ara mata fargaban zuci da ya yi zazza6i da take ji ya k'ara tasiri a jikinta ta haye gado tare da shigewa cikin duvet ita kanta tasan musanbabin zazza6inta ya samo asali ne daga tsorata da gani madam Salima da tayi a gefe d'aya tana ji radadin da za ta shiga idan ta daina tozali da kyakkyawar fuskar Daddy. Batasan dalili da yasa yanzu idan bata ganshi ba take rasa natsuwa da kwanciyar hankalinta ba. Tun lokaci da Madam Salima ta baro gidan Hafsat Shinkafi bata sake samun natsuwa ba. Ta rasa wacce mafita za ta kama so take haɗa dabarorin da take ganin za su zama sanadiyar da Azaad zai dawo da aurensu ba tare da ta k'ask'antar da kanta agareshi ba.Tana ji a jikinta Azaad ba zai ta6a iya k'arasa rayuwarshi babu ita ba a dalilin mahaukaci so da yake mata. Har dare ya yi tana k'unshe a d'aki har zuwa lokaci bata ware d'aya daga cikin dabarar da take gani za tai amfani da ita da za ta karkato da hankalinshi. Kiran sallar magarib ne ya falkar da Miyya daga wahalallen barcin da ya kwashe ta. Jikinta gaba ɗaya ya mutu bata ji kuzari ko Kaɗan, ga wani irin masiffafen ciwon kai da ya sakota a gaba. Da kyar ta sauko daga kan gado tana dafe da for head ɗinta ta shiga bathroom ruwa ta watsawa jikinta koda jikin nata zai saki. Tana kammala sallah ta taso daga kan praymat ta nufi window da ke saiti da harabar gida ta buɗe shi sanyayyar iska mai dad'in gaske tana shigowa, ta rungume hannuwanta a k'irji. Sai bayan sallar Isha Azaad ya shigo gidan Nanny Lacey Kaɗai ya tarar a falo tana ba Ahlam abincinta, ya faɗa mata ta gayawa yaranshi yau a tare za su yi dinner. Lokaci da Azaad zai shigo gida Miyya tana tsaye tun daga fitowarshi mota bata d'auke idanuwanta daga kanshi ba, adadin kallon da take mishi adadin bugawar da zuciyarta ke yi. Lokaci da tai tozali dashi wani irin abu take ji mai kama da tafiyar tsutsa yana bi jini da 6argonta. Kamar ta ruga ta rungumeshi take ji aganinta hakan ne Kaɗai zai samar mata da natsuwa. Yana 6acewa ganinta ta ja k'arfaffiyar ajiyar zuciya, ta baro jikin window ɗin. A sanyayye ta zauna a gefen gado bata jima da zama ba Airah ta shigo da sallama tana fara'a. "Yadai pretty?" Saida Miyya ta yatsine fuska kafin ta amsa da cewa. "Headache ke damuna" "Ayya sannu. "Yauwa. "Kin sha magani kuwa?" Ta girgiza kanta mai ciwo. "Ki tashi mu je mu yi dinner sai ki sha magani dinner yau special ne Daddy ya yi inviting ɗin mu, shine na shigo na faɗa miki. Anbato sunanshi Kaɗai da Airah tayi saida bugun zuciyarta ya k'aru, ta lumshe idanuwanta. "Ki je kawai Airah ba zan iya zuwa ba. "Shikenan bari na kira Nanny ta kawo miki abinci da magani anan" Jinjina kanta tayi saboda wani irin sarawa da ta ji kanta ya yi mata, Airah ta juya ta fita koda ta fito Daddy da Aneesah har sun hallara a dining room, yayin da Daddy ke yi wa Aneesah 'yan tambayoyi da suka shafi karatunta. Bayan Airah ta gaidashi ta ja kujera ta zauna Nanny Lacey ta shiga zuba musu abinci. "Nanny ki d'ibawa pretty abinci ki haɗa da Panadol extra ki kai mata d'akinta, headache ke damunta ba za ta iya fitowa ba. Airah ta faɗa cikin k'aramin sauti, gaban Azaad yai mummunan faɗuwa gaba ɗaya ya ji hankalinshi ya tashi, duk da haka bai nuna wata alama da yaranshi za su gano sabon yanayi da shige shi. Aneesah ta ɗago cike da damuwa ta ce. "Gaske dai tun d'azu ban k'ara ganinta downstairs parlor ba. Nanny ki yi mata sannu kafin na shigo. "Okay! Ta faɗa a takaice kana ta d'auki plate ɗin da ta zubawa Miyya abinci, ta nufi d'akinta bayan fitar Airah ta kwanta tare da tattakewa cikin hijabinta tana tukure a gefen gado. Da sauri Nanny ta aje plate ɗin hannunta akan bedside drawer ta ɗago kanta tare da tatta6a goshinta. "Sorry pretty jikinki ya yi zafi tashi ki ci abinci koda Kaɗan ne, sai ki sha magani. Bata yi musu ba ta tashi zaune tana yatsine fuska iri na wanda ciwo ya matsawa, Nanny ta mik'a mata plate ta kar6a ba don tana ji so ci abinci ba asalima bata ji appetite a bakinta d'aci-d'aci take ji a bakin nata kamar wacce tai zazza6in malaria. Nanny ta fita ta dauko mata ruwa da juice ta mik'a mata Panadol tare da yi mata fatan samun lafiya sannan ta fice. Tana fita Miyya ta aje plate ɗin abinci ta sake komawa ta kwanta. Madam Salima ta fito daga 6angarenta sanye da bubu na silky material kanta ba d'an kwali gashinta ya sha gyara na musanmman ta sake shi ya sauko zuwa gefe-gefen wuyanta. Cikin takonta na k'asaita mai cike da k'arfin izzarta take tattaka staircase, tun kafin ta k'araso dining room k'amshinta ya isar da sak'on zuwanta. K'amshin turarenta Kaɗai da Azaad Junaid ya shak'a sai da ya ji tsanarta ta k'ara daduwa a zuciyarshi. Haushi da takaicinta suka lullu6e shi. "Hey kids! Ta faɗa sa'ilin da ta shigo dining ɗin. "Hey.... Mom" Suka faɗa a lokaci d'aya daga haka ba wacce ta dad'a ko ta k'ara sai ci abincinsu suke hankali kwance. Nanny Lacey ta shigo dining ɗin da sauri saboda taga shigowar Madam ta ja mata kujerar da ke kusa da Azaad saida ta kalli reaction ɗinshi kafin ta zauna a yangace. Cikin girmamawa Nanny Lacey ta tambaye me za a zuba mata cikin kallon nan nata na izza ta furta. "Anything yummy! Nanny tai mata serving ta aje plate ɗin a gabanta hatta da ruwa sai da ta zuba mata kafin ta koma nesa Kaɗan dasu ta tsaya. "Aj dinner ka shiryawa muku shine you're not invited me ko?" Tayi magana k'asa-k'asa tana wani shegen blushing wanda ya k'arawa Azaad haushinta, ba don yana gudun yaranshi su gano rashin jituwarsu ba da ko kusa ba zai kulata ba balle har ya bata amsar maganarta. A wulak'ance ya ce. "I think you're not interested shiyasa ban faɗa miki ba. "Uhm! Ta faɗa tare da ta6e baki ta maida ganinta akan Aneesah ta ce. "Princess ya school hope ba wani matsala?" "Babu mommy. Aneesah ta bata amsa a gajarce. "What about you my little princess?" Ta faɗa tana kallon Airah. Ba tare da Airah ta kalleta ba ta furta. "The same with her. Tana cikin cin abinci ta sake watsa musu tambaya wacce duk cikin maganganunta tafi ba Azaad haushi. "Where's my little girl Ahlam ko tayi barci ne tun da na dawo ban zauna ba balle na sami cikkaken lokaci da ita. Airah ce tayi k'ok'arin bata amsa ta hanyar faɗin. "Tana d'aki tare da pretty" "Pretty...uhum.... pretty! Ta faɗin sunan ta sake mai-maitawa yanayi yadda take furta sunan zai tabbatar maka da mamaki take yi, can kuma ta sake cewa. "Ko ita ce d'azu na gani a downstairs parlor d'auke da Ahlam?" "Yes mommy ita ce. "Wa ya kawo ta gidanan?" Airah ta kalli Aneesah ta sauke idanuwanta cikin plate ɗin abincinta, Aneesah ta ce. "Uncle Hakeem ne! "Uncle Hakeem! Ta mai-maitawa sunanshi da Aneesah ta faɗa, sai kawai tayi kwafa ta kalli Azaad wanda tun lokaci da ta fara tambayoyinta ya ke ji tamkar ya shak'o wuyanta ya danna fuskarta cikin plate ɗin gabanta. A lokaci d'aya Aneesah da Airah suka mik'e tsaye, tare da furta "Goodnight Daddy, Goodnight mommy! "Goodnight kids! Azaad ya amsa musu yayin da Salima hankalinta ya bar jikinta ya lula da ita wata duniya ta daban. Saida suka fara shiga d'akin Miyya su duba ta tana ji motsinsu tai sauri runtse idanuwanta, kamar tayi barci. Gani haka yasa suka fice kowace su d'akinta ta nufa. Azaad yana Aneesah da Airah sun fita ya dire spoon ɗin hannunshi da k'arfi cikin plate, dama saboda su ne yake zaune, yanzu kuma da ba su nan bai ga amfani zamanshi ba. Ya mik'e da saurinshi ya fice daga dining room ɗin ya haura sama, Salima ta bishi da kallon mamaki kafin tayi kwafa tare da saki katuwar ajiyar zuciya ta tabbatar akwai jan aiki a gabanta, abinci ma sai ya fice mata arai ta ture plate tare da jifar da spoon ta tashi a fusace ta nufi d'akinshi. Yana cikin saka rigar barci ta tura k'ofa ta shigo da sauri ya kauda fuskarshi, tayi tsaye tana kallonshi kamar yau ne ta fara ganinshi sosai kwarjinishi da kyakkyawar surar jikinsa suka k'ara linka mata sabuwar soyayyarshi tayi gyaran murya tare da faɗin. "Da izzininka Hakeem ya kawo min bak'uwar fuska a gida?" Ya juyo ya zuba mata fusatattun idanuwanshi, a ranshi yana raya ya wanke mata fuska da kyakkyawan mari ko za ta dawo hayyacinta. "Point of correction Salima gidana ne asalima ba ki da wata danganta da gidanan, ko kin manta da na tsikar igiya biyu daga cikin igiyar aurenki uku da suke hannuna?" "Azaad please ka daina zance saki nan ni fa gaskiya na faɗa maka ban yarda ba, kawai ka sauke duk wani zafin kanka ka dawo da aurenmu" Cike da takaici yake kallonta up and down kafin ya ja dogon tsaki, idanuwanshi suka bayyanar da tsananin tsanarta k'arara. "A tunanina a zaman da muka yi yaci ace kin san waye Azaad Junaid, ni fa kaifi d'aya ne idan nace a'a no matter how ba zan canza ba. Da kinsan yadda nake ji tsanarki da ba ki zo kusa dani ba. Karki ga na barki a gidana ki nemi wuce makadi da rawa nayi haka ne don na sauke hakkin musulunci da zarar kin gama iddarki ki tattara komatsanki ki barmin gidana. Ya k'arasa magana cikin fushi da zallar 6acin rai. Wani irin gumi ya tsa-tsafuwa Madam Salima karo na farko a rayuwarta da ta shiga yanayi irin wannan ta saki baki da hancinta tana kallonshi ta kasa koda kwakkwaran motsi. Miyya ta tashi zaune tare da jingina bayanta ga pillow, zuciyarta sai azal-zalarta da so gani Azaad take yi yayin da a 6angaren d'aya take ji tsoro kada ta je ta haɗu da madam Salima, abin ka da mai raguwar zuciya sai ta fara zubda hawaye suna zuba a kumatunta ta gogewa da bayan hannunta cike da kwarin gwiwa ta diro kafafuwanta k'asa. Sannu a hankali ta buɗe k'ofar d'akinta sai da ta fara lek'awa lungu da sak'o na downstairs parlor bata ga kowa ba. Kafin ta fito kitchen ta shiga ta haɗa coffee, cikin sand'a tamkar tsohuwar 6arauniya ta dinga taka matattak'alar bene..... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 25.... Madam Salima tayi k'ok'arin danne duk wani tashin hankalin da ta shiga, ta kalli Azaad da idanuwanta masu cike da zallar alhini ta kwantar da muryarta ta ce. "Azaad... Ko ɗagowa bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata sai ma k'ok'arin bar mata d'akin da ya yi yana buɗe k'ofa, ta rik'o hannunshi na dama hakan yasa ya juyo a fusace. A hankali Miyya ta buɗe k'ofar falonshi na farko dama tana da yak'ini ba za ta tararda shi a ciki ba. Sai kawai ta ci gaba da tafiya tana tunk'arar falo na biyu. Cikin tsawa da ɗaga murya ya ce. "Sake min hannu Salima tun kafin ki kaini bango nai miki abin da tsawon rayuwarki ba za ki ta6a iya mantawa dashi ba. "Kayi hak'uri Azaad ka manta da abin da ya faru ka d'auke shi a matsayin kuskure, in-sha-Allah hakan ba za ta sake faruwa ba. Ta faɗa tamkar wacce aka cillastawa, ta kuma kauda fuskarta ba tare da tasaki hannunshi ba, kamar yadda ya buk'ata. Tun kafin Miyya ta k'araso ta hango su tsaye hannuwansu sark'e da juna kasancewar ya ri ga da ya buɗe k'ofar bai kai ga fita ba Salima ta rik'o shi. Wani mummunan faɗuwar gaba yai mata dirar mikiya hatta da kanta saida ya sara, da sauri ta juya yadda ta juya ya haddasawa tray ɗin hannunta subucewa ya faɗi mug ɗin coffee ya tararratse, gani haka yasa ta kwasa da gudun bala'i take tattaka staircase. K'arar da suka ji yasa Salima ta sake shi babu shiri kusan a tare suka fito falon, dukkan su coffee da ke malale akan tiles tare da fasashe mug suka bi da kallo. Ya ja numfashi da k'arfi kana ya sauke tuni ya gano pretty ce ta shigo kawo mishi coffee kamar yadda ta saba, to amma bai san dalilinta na zubar dashi kuma ta gudu ba. Ya duk'a yana tattare fasashe mug ɗin yana zubawa cikin tray. Miyya tana saukowa da gudu dai-dai Aneesah na fitowa daga d'akinta za ta kitchen ta d'auko ruwa saboda na cikin fridge ɗin d'akinta sun yi mata sanyi sosai. Cike da tsoro ta bi bayan Miyya da kallo wacce sam bata lura da ita ba. Ta shige d'akinta idan Aneesah ta dubi d'akin miyya ta dawo da idanuwanta akan 6angaren Daddy ta kasa fahimtar me Miyya ta je yi 6angaren Daddynsu. Wanda ko su da suke 'ya'yanshi ba kasafai suke zuwa ba, gashi ta fito da gudu da alamar akwai abin da ya tsorata ta, ta sauke ajiyar zuciya ta nufi d'akin, so take ta ji abin da ya tsorata ta har haka. Har taka kama handle ɗin k'ofa sai kuma ta saki ta juya zuwa kitchen, zuciyarta cike da tarin tambayoyi. Cikin masifa Salima ta ce. "Wai waye ya yi wannan 6arnar kuma ya tafi ba tare da ya gyara ba?" Uffan Azaad bai ce da ita ba sai aikin gabanshi yake yi, gani yadda bai kula ta ba yasa ta ci gaba da faɗar "Ka barshi kawai na kira Nanny Lacey ta zo ta gyara waya sani ko ita ce ta zubda shi, nasanta da kaudin tsiya ko uban wa yace ta kawo maka coffee a cikin dare nan... "Mtsss.....ya katse ta da tsaki kafin ya ɗago ya watsa mata mugun kallo duk lokaci da ta yi magana haushi da tsanarta k'ara hauhawa suke yi da shi mabugi mata ne da tuni ya ba je ta. "Dalla.....malama fita ki bani waje surutunki ya isheni. "Ba zan fita ba Azaad har sai ka hak'ura ka janye saki da ka yi min. "Ashe kuwa za ki k'are rayuwarki kina jiran gawon shanu. "Kana nufi ba za ka hak'ura ba kenan?" "Zance na hak'ura ko ban hak'ura ba ya kau saboda ni taimakonki ne nayi na ba ki full freedom da za ki ci gaba da han6aka business career ɗinki. Ki shiga duk inda kike so ba wanda zai tak'ura ki. "Azaad ban zo dakinka ba don ka dinga faɗa min duk maganar da ta fito daga bakinka ba. Na zo ne don neman sulhu wane hali kake so yaranmu su shiga idan suka sami labarin abin da ka aikata?" Bai tanka mata ba sai da ya k'arasa tattare gurin ya mike a natse ya aje tray ɗin akan center table, kana ya dubeta a ɗage. "Dad'ina da gobe saurin zuwa ashe akwai ranar da za ta zo da za ki tuna da kina da 'ya'ya. To albishirinki daga ni har yaran naki ba ma buk'atarki. Saboda haka ba sai kin yi amfani dasu ba cikin yaudararrun kalamanki ba. Langwa6e kai tayi tana kallonshi tamkar ba Azaad ɗinta ba, mutumin da ada ko magana zai mata sai ya tausasa harshensa yau shine ke zaro mata maganganu masu zafi da d'aci. Tabbas tasan ba yin kansa bane. Akwai manafukai da ke zuga shi ba kuma kowa bane sai Jadda da Hakeem, saboda haka gaba ɗayansu sai ta wanke musu allonsu tass... Idan har ta ci gaba da bashi hak'uri zai ci gaba da gasa mata maganganu marasa dad'i. Ita kuma ba hak'uri za ta yi ba ta zuba ido ba. Saboda haka ta juya jiki a sanyayye ta fice. Azaad ya bita da kallon tsana tare da faɗin "Lallai Salima ke ɗin shahararriyar 'yar wasa ce na yaba miki tare da jinjina miki akan wannan fasahar taki. Da sannu za ki yi nadama a lokaci da ba ta da amfani. Salima tana fitowa ta hango Aneesah ta fito daga kitchen, gabanta yai mummunan faɗuwa zuciyarta ta shiga kintsa mata Aneesah ce ta shiga kai ma Azaad coffee watakila ta ji faɗansu shine ta tsorata ta zubar da coffee ɗin. Yadda Salima take mata kallon tuhuma ita ma hakan ne. Aneesah tana kallon mommy ne zatonta ita ce silar zuwan Miyya 6angare Daddy saboda tasan halin mommy bata so gani kowa ya ra6e su. "Ke princess zo nan. Madam faɗa tare da nufar d'akinta tana zama akan cushion ɗin da ke d'akin Aneesah na shigowa. "Gani mommy! "Dama tambayarki nakeso yi. "Tam....mommy Allah yasa ina da amsar tambayar taki. Saida Salima ta tsareta da idanuwa kafin ta ce. "Miyasa da kika je kai ma Daddynku coffee kika zubar a maimakon ki tsaya ki gyara 6arnar da kika yi sai kika gudu?" Gaban Aneesah ya faɗi rass....wato shine dalilin gudun Miyya, idan har ta faɗawa Mommy gaskiya Allah ne Kaɗai zai ceto Miyya daga wurinta saboda haka ta ce. "Nima ba a son raina hakan ta faru ba amma ki yi hak'uri mommy in-sha-Allahu zan kiyaye gaba. "Shikenan je ki kwanta. Salima ta faɗa tare da shigewa bathroom Aneesah tai hamdallah. Ta fice. Miyya tana shiga d'akinta ta faɗa kan gado, duk lokaci tai yunk'uri rufe idanuwanta hoton Azaad da Madam Salima take gani rik'e da hannuwan juna, duk yadda taso ta goge hoton abin a zuciyarta ya ga-gara gogewa. Ga zafin ciwon kai ga zafin gani Azaad da Salima wanda ta rasa dalilinta na jin zafin ganinsu tare. Tana so tai barci amma yak'i zuwa ya dauketa ga wani mugun zafi da take ji a k'irjinta da rasa yadda za tayi sai ta shiga rera kuka. Bayan fitar Salima Azaad da kanshi ya goge coffee ɗin duk sai ya ji shi wani iri, kamar wanda bai da lakka a jikinshi akwai abin da zuciyarsa ke so gani amma ya rasa gane menene wannan abun. Ya tusa tulin files a gabanshi ko d'aya ya kasa buɗewa, da ya ji motsi Kaɗan sai ya yi saurin kallon k'ofa yana zaton ko Miyya ce. Dare ranar dukkan su uku Azaad, Salima da Miyya ba wanda ya yi barcin kirki. Misali karfe 7:00am Miyya ta fito cikin Shirin tafiya school, tsabar kukan da tasha idanuwanta sun yi luhu-luhu da ka kalleta ba sai ka tambaya ba, za ka fahimci kuka tayi ba Kaɗan ba. Ta zauna a kujerar da ke kallon upstairs, addu'a take a k'asan zuciyarta Allah yasa Daddy ya fito kafin su wuce school. Airah ce ta fara fitowa tana arba da ita ta zaro ido. "Subhanalillah.... pretty me ya sami idanuwanki ko har yanzu ciwon kai ne?" Ta gyada mata kai saboda ko Kaɗan ba ta k'aunar tayi magana muddin tayi magana to kuka ne zai biyo baya. "Sannu Allah ya ba ki lafiya amma kan da kin hak'ura da zuwa school ɗinan, kin ga yau Friday short time ne. Kauda fuskarta tayi gudun kada Airah taga hawaye da suka silalo mata a kuncinta. "Zan iya zuwa ba sosai Kan yake min ciwo ba, kuma kinsan yau muna da test ɗin chemistry banso nayi missing. Tayi magana cikin dasasshiyar muryarta da bata fita sosai. Kafin Airah ta sake yi magana suka ji muryar Aneesah tana faɗin. "Good morning girls! I'm sorry yau na tashi a makare...... Ta kasa k'arasa magana sakamakon gani idanuwa Miyya wacce ta juyo lokaci da ta ji muryarta. "Na shiga uku pretty ba dai Apollo ne ya kama ki ba?" "A'a! Ta faɗa a gajarce. "To me ya sami idanuwanki haka kin ga kuwa yadda suka kumbure?" Kasa bata amsa Miyya tayi sai kawai ta ce. "Aneey ki je kuyi breakfast ni na sha tea banso mu yi latti kinsan yau Ina da test, wannan kumburin da idanuwana suka yi na rashin wadatatce barci ne jiya na kwana ina karatu. "Saidai Airah don nima nasha tea a d'akina. Aneesah ta faɗa tana kallon Airah girgiza kai Airah tayi tare da faɗin. "Nima am okay mu tafi kawai. Tuni Miyya ta mik'e ta wuce gaba suka biyo ta a baya yayin da Aneesah ke tsokanarta. "Pretty yau duk tunani test ne yasa ba za a goya school bag a baya ba aka rik'e ta a hannu?" Wata harara ta yi wa Aneesah da kumburarrin idanuwanta, Aneesah ta fashe da dariya Airah tana taya ta. Tun kafin su k'arasa parking lot idanuwanta suka yi tozali da mutumin da daren jiya ta raya shi da tunaninshi. Yana tsaye ya yi folding hannuwanshi a k'irji jikinshi sanye da dark blue ɗin jallabiya mai gajeren hannu yana magana da d'aya daga cikin securities ɗin gidan. Gaban Miyya ya yi mummunan faɗuwa, ta sadda kanta k'asa tana kusantar parking lot gabanta yana k'ara bugawa. Hatta da yana yi tafiyarta saida ya sauya jikinta ya shiga kakkarwa kamar mai jin sanyi ko wacce zazza6i ya kama, hak'oranta har wani hard'ewa suke yi. Azaad yana tozali da ita ya kasa d'auke idanuwanshi daga kanta, ya shiga yawo dasu bisa jikinta tana sanye ne da white sports wears dogon farin wando haɗe da farar t-shirt ta ɗora farar cardigan akai, k'afarta sanye da white sneakers kanta kuma dauke da p-cap ita ma white a sama p-cap ɗin an rubuta white house. Aneesah da Airah ma irin kayan ne a jikinsu saidai kowace da irin colour house ɗinta Aneesah pink house Airah kuma red house. Shi kanshi security ɗin sai da ya fahimci hankali Azaad ya karkata wani gun dabam, sakamakon yana magana bai ji ya amsa mishi ba. Sai kawai ya bi da idanuwanshi gun da ya ga yana kallo. "Good morning Daddy! Aneesah da Airah suka faɗa lokaci da suka iso kusa dashi. "Morning my beautiful babies! Ya faɗa cikin sexy tone ɗinshi, saukar muryarshi a kunne Miyya yasa ta ɗago da sauri, idanuwanta suka sark'e da nashi bugun zuciyoyinsu ya karu aka rasa wanda zai janye ganinshi, tuni wani irin shauk'i ya d'ibe su ya lula dasu wata duniya mai wuyar fahimta. Aneesah da Airah har sun kai wajen mota kamar an ce Aneesah ta juya ta ga Miyya tsaye ta kafe Daddynta da maye kallo kamar tsohuwar mayya, yayin da shima Daddy ya tattaro dukkan natsuwarshi akanta tamkar ya ga wata sabuwar halitta da bai ta6a gani ba a tsawon shekaru da ya yi a cikin duniya, zaro idanu tayi cikin kidimewa ta dafe k'irjinta tare da furta "Na shiga uku ni Aneesah...... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 26..? Daga ranar da Hasheem ya falka ya ga an cire masa k'afa, kullum sai ya yage baki yana kuka tamkar k'aramin yaro. Yau ma hakan ce ta kasance, kuka yake yi har dasu shassheka matarsa Haneefa ta kalleshi taja dogon tsaki "mtsss... dallah malam ka rufewa mutane k'aton bakinka ka bi ka ishe mutane da kukanka na banza da wofi. Hasheem ya ɗago jajjaye idanuwanshi da ke tsiyaya hawaye ya dubi Haneefa, cikin muryar kuka ya ce. "Haneefa ba ki da imani ko Kaɗan wallahi Ina cikin wannan hali shine ba za ki tausaya min ba ni fa mijinki ne Haneefa?" Wani k'ullutun bak'in ciki ya tokare ta, ta zabga mishi katuwa harara. "Ba zan ta6a tausaya ma ba Hasheem domin mugun so zuciyarka na tsiya wanda ka tsotsa a nono shi ne ya janyo ma hali da kake ciki, wato kana zato bansan kaik'ayi ne ya komawa mashek'iya ba, jiya duk abin da kuke faɗa Kai dasu Ahmadu akan kunnena, jira nake da zarar an sallame ka daga asibiti ka bani takarda ta na k'ara gaba don ni ban iya zama da musaki, ka je can ka nemo musaka irinka ka aure. Da lafiyata ba zan lalace a wofi akan ba" Sosai kalaman Haneefa suka 6atawa Hasheem rai, musanmman da ya tuna duk wani faɗi tashi da yake yana k'arewa ne akanta da 'ya'yanta shine yanzu don ya haɗu da tawaiya tun kafin tafiya tai nisa za ta guje shi. "Karki yi min haka Haneefa kinsan inasonki ba zan iya rayuwa babu ke ba.... Jifa da tayi da gwangwani madarar peak yasa ya haɗiye raguwar kalamanshi, sauri Kiriss gwangwani ya kai gareshi gaba ɗaya madarar ta zube dama tana shirin haɗe mishi tea. Cikin masifa da ruwan bala'i ta rufe shi da faɗa kamar za ta cinye shi. Ahmadu ya buɗe k'ofa ya shigo duk da ta ganshi bata fasa faɗar duk abin da ya zo bakinta ba. Tsoron Allah ne ya kama Ahmadu ya yi tsaye k'ik'an kamar bishiyar kwa-kwa yana kallonta inda take shiga ba nan take fita ba. Yayin da Hasheem ke ta babbaka kuka. "Kai daina yi mata kuka! Ahmadu ya daka masa tsawa. "Amma Keɗai Haneefa an yi lalatatciya marar imani da tausayi kalli hali da bawan Allah nan yake ciki..... "Dakata Ahmadu!" Ta daka masa tsawa kamar ba yayan mijinta ba, cike da rashin kunya ta ce. "Duk hali da yake ciki shi ya siya da kud'insa, Kuma muddin bai cire hassada da mummunan buri akan Azaad ba, ya dinga gani masifa da bala'i kenan. Wata rana sai an tsinto gawarsa tsakiyar bola karnuka na yaga. "Innalillahi.....Haneefa anya kinaso ki ga manzo Allah mijinki ne fa uban 'ya'yanki shine kike masa bak'in k'azafi da mummunan fata, tsakani da Allah da matuk'ar wahala ki shiga aljanna. "Mtsss.....ku ne dai ba za ku shiga ajanna ba masu zuciyar kafiran farko, wanda babu Allah a zuciyarsu Kaɗan ku ka fara gani. Wallahi Muddin ba ku tuba ba mutuwarku sai tafi ta su Babban Yaya da Alhaji Buba muni da k'azanta. "Kai....Kai....Kai... Ahmadu ya faɗa cikin kad'uwa yana k'ank'ance idanu, wannan shi ake kira kana barci wani yana maka minshari. "Hasheem ashe kai sakarai ne ban sani ba shine don tsabar lalacewa ka yashe sirrinkan mu tass...ka faɗawa figaggiyar matarka mai kama da an tsoma tantabara cikin ruwan zafi?" "Wallahi-tallahi Yaya Ahmadu ban faɗa mata komai ba jiya muna magana tai mana la6e. Hasheem k'arasa magana yana goge hawaye, da gefen hospital gown dake sanye a jikinsa. Haneefa tai musu kallon sama da k'asa ta watsar ta buɗe k'ofa ta fice Ahmadu ya bi ta da zagi. **** *** ******* A hankali idanuwa Miyya suka fara lumsashewa numfashinta ya fara yi sama, sannu-sannu hankalinta ya fara barin jikinta. Ta saki k'ara mai firgitarwa ta faɗi k'asa a some kamar gitawar walkiya Azaad ya iso wurinta. Aneesah da Airah da gudunsu suka nufo wurin har security ya kai hannunshi ya ta6a ta da sauri Azaad ya rik'e hannu, tare da watsa mishi mugun kallo. Ya durkusa gefen fuskata ya rik'o hannunta ya ji wani irin mugun zafi. "Subhanalillah......Daddy me ya sami pretty ne? Airah ta faɗa muryarta tana rawa kamar za ta sa kuka, Aneesah ma duk ta bi ta rud'e. Ya ɗago ya kallesu ya ga kowace su hankalinta ya yi matuk'ar tashi ya ce. "Ku kwantar da hankalinku zazza6i ne kawai ke damunta na ji jikinta da zafi, ku tafi direba yana jiranku kada ku yi latti" Ba don ransu yaso ba suka tafi har motarsu ta fice su na waiwaye ta. Azaad ya sunkuce ta, ya nufi wurin mota da gudu direbanshi ya dauko key ya buɗe mishi backseat ya shiga tare da rungumeta jikinsa zafin jikinta yana sauka a nashi jiki, lokaci zuwa lokaci yake kiranta sunanta yana d'an bubbuga kumatunta. Duk bubbugata da yake yi ko ko d'an yatsanta ba ta motsa ba, sai can ya ji taja wani dogon snoring bai san sanda tayi barci barci, ba sai snoring ɗinta ya ji ga Kuma idanuwanta a birkice la66anta suka fara kakkarwa ta shiga wani irin yare wanda duk yawon duniyarsa bai ta6a ji irinsa ba. Nan take ya ji tsigar jikinsa ya tashi wani irin tsoro yana shigarsa tun tana magana a hankali Wanda shi Kaɗai ke ji har ta dawo yi da k'arfi hakan ya janyo hankali mr Richard har ya juyo yana tambayar Azaad wane irin yare ne take yi, Azaad ya daka mishi tsawa babu shiri ya maida ganinshi akan steering. Addu'ar ya shiga karantawa yana tofa mata, kafin su iso asibiti ta daina surutun da take Azaad ya umarci Mr Richard da ya kai su prime hospital, saboda tafi kusa abinka da asibitin kud'i nan take aka shiga dubata musanmman ma da ya kasance the young billionaire ne ya kawo patient ɗin da kanshi, special room aka kaita tare da yi mata fixing ɗin drip. Duk wani abu da take yi ta daina kasancewar allurai da aka yi mata akwai na barci nan take tayi barci. Sai lokaci hankali da natsuwar Azaad suka fara dawowa jikinsa, Saidai sam bai ji dad'i da doc Jamal ya faɗa mishi ciwonta har da damuwa a ciki kuma idan bata rage tunani ba za ta iya kamuwa da hawan jini. Ko nan da can bai ɗaga ba yana nan zaune har drip ya k'are aka cire mata, da zimmar anjima za a sake saka mata wani. Sai lokaci ya kira Hakeem ya faɗa mishi, Miyya bata da lafiya su na asibiti ya yi handled clients ɗinsu. Duk tsawon zaman da Azaad ya yi dai-dai da second d'aya idanuwanshi ba su gushe daga kallonta ba. Tausayinta ya ke ji har can k'asan zuciyarshi gani yake yi aurenshi ne silar shigarta damuwa ya k'udurta aranshi zai sauk'ewa mata ba zai so ya ci gaba da ganinta cikin wannan hali ba. Balle har hawan jini ya kama ta. Haka ya ci gaba da tunani iri-iri kala daban-dabam duk akan Miyya. Ya d'an jinginar da bayan shi akan kujerar da yake zaune akai, bai san lokaci da barci ya d'auke shi ba. Dama daren jiya bai yi barcin kirki ba. Sha biyu da rabi Miyya ta falka ta buɗe idanuwanta ta shiga yawo dasu kafin ta sauke su akan fuskarshi, ta ja ajiyar zuciya kana ta shiga murmushi yadda yake barci hankali kwance ba k'aramin burgeta ya yi ba. Ta matsa jikinta Kaɗan ta ɗora hannunta a shoulder shi ta kira shi cikin siriyar muryarta. "Daddy! Ya buɗe idanuwanshi da suka yi ja Kaɗan. Ta langwa6e kanta tana kallonshi da idanuwanta masu rikirkita mishi lissafi, ya d'auke kanshi da sauri cikin faɗuwar gaba wacce ya rasa ta me ce ce ya ce. "Sannu pretty ashe kin falka" K'asa tayi da kanta tana murmushi ta ce. "Daddy barci kayi a zaune ko na sauko na ba ka gado ka kwanta?" Murmushi ya yi tare da girgiza kai, a tunaninshi bata gane inda take ba. Daga haka ba wanda ya sake tankawa sai satar kallon juna suke yi kowa ne da abin da yake ji Miyya tanaso ta tashi ta shiga bathroom fitsari take ji sosai, amma tana jin kunyarshi Allah ya taimake ta aka kira wayarshi tana gani ya yi pick up tare da mikewa tsaye, ya yi nesa da ita Kaɗan ta sauko a hankali, ba ta wuce yi tako biyu zuwa uku ba jiri ya d'ibe ta, tayi baya za ta faɗi kamar an ce ya juyo ya ga tayi baya bai san lokaci da ya jefar da waya ba, ya rugu da gudu kafin ta kai k'asa cikin zafin nama ya dank'o dantse hannunta. Ita kanta sai da ta ji zafin rik'on da ya yi mata kamar daga sama ta ji ta akan k'irjinshi, yasa hannunwanshi ya zagaye bayanta ya rungumeta irin runguma da ake yi wa laqabi da duk runtsi muna tare. Lumshe idanuwanshi ya yi yana ji bugawar zuciyarta yayin da numfashinta mai d'an zafi-zafi yake sauka a gefen kafad'arshi kasancewar akwai raguwar zazza6in da bai k'arasa sakinta ba. Wani shock mai k'arfin gaske ya ja shi gaba ɗaya magudanar jini jikinsa ta tsaya cakk...cikin wani bakon yanayi ya shiga shinshina gefe-gefen wuyanta yana had'awa da murza gadon bayanta da dukkan hannuwanshi, yana fitar da numfashi da sauri-sauri k'arar buɗe k'ofa yasa shi dawowa hayyacinsa idanuwanshi suka yi tozali da fuskar da ta rikita shi ta kuma firgita shi.... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 27.... Hakeem ya yi tsaye ya saki bak'in da hanci tare da zaro idanuwanshi yana kallon ikon Allah. Sam ya kasa gasganta abin da idanunshi ya gane mishi arrogant Azaad Junaid ne rungume da yarinyar da ya yi kirari cewa ba abin da zai yi da ita tai mishi k'ank'anta. Wata irin mashahuriyar kunya ce ta lullu6e Azaad ya tabbata ganye shi ya Kad'e Hakeem ya ganshi yana romancing ɗin Miyya yau kam sai da ya toshe kunnuwanshi da auduga, don sai ya sha tsiya kala daban-dabam. Azaad ya shiga yakice ta daga jikinshi ɗagowa da za tayi tai tozali da Hakeem da yai mutuwar tsaye, saurin sadda kanta k'asa tayi ta ra6a gefen Azaad ta shige bathroom da sauri ta maida k'ofa ta rufe. "Sai ka rufe k'ofar ka k'araso wannan dai halin banza ne ka shigowa mutane d'akin bakatatan...ba knocking on. Azaad ya faɗa a fusace yana wani muzurai shi a dole so yake ya fuske. Hakeem ya kwashe da mahaukaciyar dariya shak'inyaci har dasu dafe ciki ya maida k'ofar ya rufe yana ci gaba da ban-banka dariya. Dama Azaad yasan hakan zai faru yau kan ya shiga uku. Wai me ma ya kai shi romancing ɗinta miyasa ya kasa haɗiye kwadayinsa gashinan rashin hak'urinsa ya jawo masa shak'inyaci Hakeem. K'arasowa Hakeem ya yi kusa da shi ya tsagaita da dariya amma still da murmushi akan fuskarshi. "Kai mutumina tabarma kunya da hauka ake nade ta, to bari ka ji duk ta yanda ka nadeta ba zan fasa faɗar abin da idanuwana suka gane min ba. Yanzu fissibillahi....Aj nufinka a d'akin asibiti za ka haik'ewa 'yar mutane?" Azaad ya yi shiru tare da lumshe idanuwanshi yana shafar sajenshi, hakan ne ya ba Hakeem damar ci gaba da yi masa tsiya. "Ai wannan d'an gadon ba zai d'auke ku ba in fact bata da lafiya kodai har kayi abin ne shine silar rashin lafiyarta ta?" "OMG.....! Azaad ya faɗa sounding very angry ya buɗe jajjaye idanuwanshi ya kalle Hakeem dasu. "Kai fa ba k'aramin tantiri bane Hakeem abin da ka gani ba wani abu bane jiri ne ya d'ibeta za ta faɗi na taro ta.... Kafin ya dasa aya Hakeem ya sake kwashewa da dariya har yana had'awa da bugun gado, Azaad ya kauda fuskarshi zafin dariya nan ta Hakeem yake ji ba Kaɗan ba. Sai da bashi da yadda zai yi illa ya zuba masa idanu. "Gaskiya Aj mugun jarababbe ne kai bayan wanda kayi a gida a asibiti ma ba za ka bar 'yar mutane ta huta ba?" "Banso iskaci Hakeem ka daina yi min wannan wasan banzan ka ji ko?" Azaad ya faɗa cikin fushi. Hakeem ya sake tintsirewa da wata sabuwar dariya da ta fi ta farko da Azaad ya fahimce mahaukaci k'arfi da yaji Hakeem zai maida shi sai kawai ya kalle shi da girar ido ɗage ya ce. "To wai kai miye naka a ciki don na raya sunnah a asibiti haramun ne?" "Ba haramun bane saboda matarka ce halak-malak amma kuma ka tuna ana bari halak don kunya" "Ashe dai kasan cewa matata ce saboda haka ka yi shiru da bakinka ka daina wannan dariyar iskancin naka, ko na kora ka waje. Hakeem ya dafe bakinshi da hannunshi yana dariya mamaki yake yi yaushe Aj ya yi baki har haka, ba shakka Aslamiyya ta fara canza shi. Da shigarta bathroom ta faɗi zaune dabasss....ta jingina bayanta ga bango tana sauke numfashi bi da bi, sosai take ji kunya haɗuwa da uncle Hakeem shikenan ya ganta ita da Daddynta su na rungume da juna yanzu Allah Kaɗai yasan irin fassara da zai musu. Mararta ta murd'a a dalilin fitsari da ya cika ta taff...da rarafe ta isa wurin toilet seat tai fitsari tare da kama ruwa ta koma wajen da ta taso ta zauna. Saida Hakeem ya gaji don kanshi, da yi wa Azaad tsiya kala daban-dabam wani ya mayar masa wani kuma sai ya yi shiru. Kafin suka d'auko wata fira can dabam har suka gangaro akan ciwon Miyya. "Ikon Allah! Gaskiya Aj bana gani damuwarta ta ta'alak'a ne ga aurenka, kawai dai akwai abin da ke damunta da dabam amma ba wannan ba. Hakeem ya faɗa yana kallon Azaad numfashi Azaad ya sauke tare da kallon k'ofar shiga bathroom kafin ya ce. "Bana tunani a k'anana shekarunta ace akwai abin da zai jefa ta damuwa face wannan Kar ka manta Hakeem ba a son ranta aka yi mata aure ba. Kaga kuwa dole ta sa damuwa a ranta, ni gaskiya nayi decided na saukewa mata kuma in-sha-Allah zan ci gaba da kula da ita. Ba zan bari duk wani abun cutarwa ya ra6e ta ba. Zan yi gagarumin yak'i da duk wanda ya yi yunk'uri 6ata mata. Tun tsawon lokaci da ya fara magana Hakeem ya tsare shi da idanu yana karanta reaction ɗinshi, ko wace kalma da take fitowa daga bakinshi yana fassarata da tashi fahimta. "Aj are you in love with her?" Hakeem ya watsa mishi tambayar ba zata damm..... gabanshi ya faɗi bai zaci wannan tambaya za ta fito daga bakin Hakeem ba. Shiru ya yi tare da haɗe tafin hannuwanshi wuri d'aya yana murzawa. Murmushi Hakeem ya saki haɗi da yin hamdallah, ya karance halayar Azaad sosai duk lokaci da ka yi mishi tambaya bai yi maka kallon girar ido ɗage ba which means ya amince da tambayar da ka yi mishi. Hakeem ya yi k'asa da murya ta yanda Azaad Kaɗai ne ke ji abin da yake faɗa tamkar dai mai rad'a ya ce. "Aj kai ba k'aramin yaro bane balle ka ce ba kasan hanyoyin da za ka bi ka nemi soyayyar mace ba. Ko mace irin Miyya da batasan menene so ba, cikin ruwan sanyi za ka mallake zuciyarta. Aj Kana da matuk'ar buk'atar kulawar mace, shiyasa nakeso ka d'auki Miyya a matsayin babban kyauta daga Allah. Ubangiji ne ya dubi halin da kake ciki ya kawo Aslamiyya a rayuwarka domin ta zame maka waraka. ka zauna ka yi tunani da kyau za ka gano kai da Aslamiyya haɗin Allah ne bana mutum ba. Azaad ya yi shiru yana sauraren bayani Hakeem shi da kanshi yasani ya kamu da son Miyya so ba na wasa ba. Amma muddin ya yi bincike ya gano shine silar jefata damuwa tabbas zai danne soyayyar da yake mata, ya saukewa mata aurenshi saboda yana so ta dauwama cikin farin ciki musanmman da yasan bak'ar wahala da tasha hannu kakarta da Baffanta. Cikin karaya zuciya ya kalle Hakeem ya ce. "Hakeem inasonta wallahi-azim Ina matuk'ar k'aunarta ina mata irin muguwar soyayya da fatar baki ba za ta iya faɗa ba. Ita ɗin ta kasance wani 6angare na jikina. Sai dai ba zan iya jure ganinta cikin damuwa ba balle har nayi sakaci da hawan jini zai kamata ba. Hakeem muddin na gano aurena shine matsalarta tabbas zan saukewa mata. "Dan Allah Aj ka daina zance rabuwa tsakaninku babu rabuwa, ka d'aure ka sauke duk wani ji-ji da kai ka nemi soyayyarta wallahi za ta so ka watakila fiyye ma da yadda kake sonta. "Da wuya ta soni koda rabin son da nake mata ne Hakeem. Ina gayamaka abokina sosai nayi zurfi a son kwailata. Ya k'arasa magana da wani shegen blushing, Hakeem kan dariya ya yi tare da bugun shoulder ɗin Azaad yana faɗin. "Keep fighting abokina in-sha-Allah nan da d'an lokaci zan d'auki second Azaad Junaid da hannuwa nan nawa" "Allah ya kawo wannan ranar na rantse da Allah sai nai maka kyautar da za ta girgiza ka. Azaad ya faɗa yana kallon Hakeem yana murmushi. Ihu Hakeem ya saki har da mik'ewa yana taka rawa, Azaad ya zabura da sauri ya rik'o shi yasa hannunshi ya rufe mishi baki. "Kai fa ba kada hankali tana bathroom za ta iya jiyo ihunka dan Allah tafi kawai saboda kutse da kayi mana yasa ta ji kunya shiyasa ta mak'ale a bathroom, da zarar ka tafi zan fito da kayana. Zaro idanu Hakeem ya yi sosai ya kadu da jin furuncin Azaad, kafin ya gama mamaki Azaad ya tura shi waje ya rufu kofa har da su murza key. Yana murmushi ya nufi k'ofar bathroom wani nishadi yake ji tamkar Miyya ce ya faɗawa sirri dake zuciyarshi. A hankali ya tura k'ofar ta buɗe ya shiga tare da sake rufe ta, Miyya da ke zaune akan tiles ta sunne kanta tsakanin gwiwoyinta biyu, ta ɗago a razane gani shine tasaki ajiyar zuciya kallo d'aya tai mishi ta kauda fuska cike da k'asaita ya iso gabanta yana kallon gefen fuskarta ya tsuguna tare da sa hannunshi ya rik'o ha6arta ya juyo da fuskarta ta su na haɗa ido ya saki mata k'ayatattace murmushi irin mai kashe sassan jiki. Ai kuwa ya yi nasarar tayar mata da tsigar jiki ta ji yarrrr....ta lumshe idanuwanta da sauri-sauri take sauke numfashi. Gani yadda take fusgar numfashinta yasa shi rudewa cikin kidimewa ya ce. "Ya aka yi ne pretty ina ke miki ciwo?" Kusan a tare ya haɗa mata tambayoyi biyu a lokaci d'aya, ta sadda kanta k'asa cikin k'aramin sauti ta furta. "Daddy kaina kawai ke ciwo shima ba sosai ba za mu ma iya tafiya gida" Ajiyar zuciya ya yi tare da hamdallah wato ta ma gano asibiti suke tsabar yarinta ce yasa ta ce za ta bashi gado ya kwanta. "Uhm...kuruci dangin hauka" Ya faɗa cikin zuciyarshi a bayyane kuma sai ya mik'a mata hannuwanshi ta ɗago a hankali ta kalli santa-santala hannuwan nashi masu d'auke da dogaye yatsu farare tass...a kunyace ta saka tafin hannuwanta cikin nashi wani irin taushi ta ji ya ratsata tamkar ta damk'i auduga, ya mik'e tare da ɗagota ta tashi tsaye ya sakala hannunshi na hagu a waist ɗinta, ya rungumeta a tsagin jikinsa tsintar kanta tayi da kwantar da kanta a dantse hannunshi saboda yafi ta tsayi shiyasa kanta ba zai kai ga shoulder ɗin shi ba. Da suka iso wajen gado ya d'auke ta cakk...kamar ya d'auki Ahlam ya zaunar da ita ya nemi daff da waist ɗinta ya zauna cike da zallar kulawa ya rik'o hannunta ya dank'e cikin nashi. "Pretty faɗa min gaskiya karki 6oye min meke damunki?" "Babu komai Daddy na faɗa maka ciwon kaine kuma yanzu ba sosai yake min ciwo ba" "Ba wannan nakeso ji ba pretty asalin abin da ke haifar miki da matsananci tunani, doc yace idan har ba ki rage damuwa ba za ki iya kamuwa da ciwon hawan jini. Ni kuma ba zan so hakan ta faru ba. Shiyasa nakeso ki faɗa min gaskiya idan har bakyaso aure nan zan saukewa miki. Cikin tsananin firgita Miyya ta ɗago ta k'ura mishi idanuwanta, wanda har sun fara cikowa da hawaye sosai kalmar rabuwa ta dagi zuciyarta tamkar an halba mata kibiya ko mashi. Tana kifta idanuwanta sai ga hawaye sharrr...akan tattausan kumatunta biyu. Wani irin zafi Azaad ya ji a kahon zuciyarsa tamkar an watsa mishi tafasashe ruwan zafi. Yanzu ya tabbatar ashe ba hasashen banza ya yi ba. Da gaske ne shine silar damuwarta shikenan alk'awali da ya yi ba zai k'arya shi ba zai saukewa mata, dama can ba kalar aurenshi bace k'addara ce ta haɗa su haka zalika k'addara ce za ta zama silar rabuwarsu. Ya mik'e zubur jikinshi yana wani irin kerma da za ka tambaye shi da zai ce wannan ita ce rana da tafi kowace rana kunce a gareshi. Batare da kalleta ba ya ce. "Zan tafi gida ki kwanta ki huta akwai nurses za ku kula da ke. Daga haka ya juya cikin tafiyar sauri ya fice ta bi shi da kallo yayin da k'irjinta yake bugawa da k'arfi, ta kife kanta a pillow ta shiga rera kuka duk duniya idan akwai abin da zai rabata da farin ciki bai wuce kalmar rabuwa da Daddynta ba. Ita kanta a yanzu ta amince da shine cikon farin cikinta bugun zuciyarta rashinsa tamkar rusa duniyarta ne. Madam Salima zaune a dining room ta ca6a ado na ban mamaki wanda ada bata yi kwata-kwacinsa ta zauna gida sai in za ta fita officer ko kuma in an gayyace ta dinner party. Yanzu ɗin ma tayi ne a bisa ga shawarar Hafsat Shinkafi ta yadda za ta karkato da hankali Azaad. Lokaci zuwa lokaci take kallon wall clock da ke manne ga bangon dining room ɗin, can kuma ta ja tsaki ta rasa wacce duniya Azaad ya lula da sassafe muryar Nanny Lacey ta ji tana mishi sannu da zuwa da mugun sauri ta mik'e gari sauri taci d'an uban tuntu6e da ta faɗi, jikinta har rawa yake yi ta fito daga dining. Koda ta k'arasa fitowa har ya fara haura matattak'alar bene, ta bishi da sauri tana kiran sunanshi wanda sai in tana cikin nishadi take kiranshi dashi. "Dattinaa! Sometimes Jadda ke kiranshi da suna tun shine yaro Jadda ke kiranshi da Dattijo a dalilin sunan mahifinta ne dashi, sai ta gajarta suna take cewa Datti ko Dattinaa. Dai-dai yana haura last stairs ya ji ta kira shi ya tsaya cakk....tare da juyawa Azaad yana masifar son suna dalili Jaddarshi ce ta rad'a mishi yana kuma girmama hakan. Shiyasa a duk lokaci da Salima ta kira shi da suna ya kan tsinci kanshi cikin nishadi da walwala. Yana nan tsaye har ta k'araso cikin izza ta ce. "Dattinaa Ina ka je da sassafe Nanny ta faɗa min ko breakfast ba ka yi ba ka fita hope everything is alright?" Kallon uku saura kwa6o ya yi mata da ada ne kwalliyarta ba k'aramin tafiyar da ruhinshi za ta yi ba, amma a yanzu da ya dube ta sai ya ga ta dawo mishi kamar fatalwa ko Kaɗan bata burge shi ba. Sai yake gani kamar a shekarunta ta wuce wannan kwalliyarta. California gown ce a jikinta brown colour tasaki gashin kanta, tasha red ɗin jan baki a takaice dai tayi simple makeup a zahiri tayi matuk'ar kyau a wurin Azaad ne abin yasha ban-ban. "Mtss....ya ja siriri tsaki ya juya tare da buɗe k'ofar falonshi duk da haka ta danne zuciyarta ta bi shi a baya kusan a tare suka shiga master bedroom ɗinshi. Yana sane da tana bin shi amma ko ya nuna hakan. "Dattinaa ba ka ce nayi kyau ba saboda kai nayi wannan Make up ɗin?" Ya waiga ya kalleta up and down kafin ya ta6e baki a lalace ya ce. "Tsakani da Allah Salima kin tsofa ya kamata ki daina abin k'anana yara irin wannan kwalliya bata dace da ke ba. Ki bar wa yara sabon jini su ne za su yi su burgeni amma kan kamar kurar wasa musanmman wannan eyes shadow da kika sa zallar k'yak'yami zuciyarta har tafara tashi fita Dan Allah kada nayi amai. Ya k'arashe magana yana ya mutsar fuska kamar da gaske aman zai yi. Madam Salima tai mutuwar tsaye wannan shine karo na farko a tarihin rayuwarta da aka ta6a ci mata zarafi Kuma mutumin da take kira da shine jigon rayuwarta. Wani irin k'atoto k'ololo bak'in ciki ya taso ya tokare mata gadon zuciya, bata San lokaci da ta zube bisa tiles ta ratsa kuka mai k'arfin gaske..... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 28.... Sosai Miyya tasha kuka kamar ba gobe da ta gaji da rera kuka ta rarrsshe kanta. Daga bisani tayi barci. Hasheem ya dubi Ahmadu da fusatattun idanunshi, yana huci kamar bak'in kumurci. "Na ratse da wanda rayuwata take hannunshi ba zan bar Azaad ba har sai naga bayanshi duk shu'umancinsa kuwa. mu zuba ni dashi shege kafasa. "Hasheem ka hak'ura da wannan burin naka ka ji da hali da ka tsinci kanka mana. Ubangiji yana sonka da rahama shiyasa yabarka da numfashinka kayi amfani da raguwar lokaci da yai saura gareka wajen rokar gafarar ubangiji da Azaad wallahi kada ka bari shaidan ya ci gaba da buga maka gangarsa zai kai ka ne ya baro. Duk da muna da mugun son zuciya amma ba za mu so mu yi mutuwar kask'anci ba. Hajiya Kubra ta faɗa tare da daukar jakkarta dama ta zo duba Hasheem ne ta tararda shi da Ahmadu suna sake shirya sabon shirinsu na gani bayan Azaad Junaid. "Ni dai na hak'ura kamar yadda Alhaji Abdallah ya cire kanshi a cikin wannan tafiya ni ma ba dani ba na fita, kuma Ina mai ba ku shawara da ku dangana...... "Ya isa kubra ga k'ofa fita ki ba mu wuri muddin Ina raye da ikon Allah sai na cimma mummunan manufata akan Azaad koda ni Kaɗai nai saura a wannan tafiyar" Hasheem ya k'arasa magana yana nuna mata k'ofar fita da yatsanshi, Hajiya Kubra ta kad'a kai batare da ta sake magana ba ta fice abinta. Ahmadu yana so ya hak'ura saidai mugun kwadayinsa ba zai bari ba domin yana tsoron kada Hasheem ya yi nasarar kashe Azaad shi Kaɗai. Da zarar sun kauda shi mallakar dukiyarshi ba zai musu wahala ba, idan ya hak'ura Hasheem ya yi nasara shi Kaɗai zai mallake dukiyar shiyasa tunaninsa ya rabu gida biyu. Sabon shiri suka shirya sosai wanda suke gani koda bala'i sai sun cimma manufarsu. **** *** ****** Cike da takaici Azaad yake kallon Salima sosai takaicinta ya kamashi musanmman yadda ta yage baki tana 6arka kuka kamar wata k'aramar yarinya. "Mtsss....! Ya buga mugun tsaki ya shige bathroom abinsa har ya fito daga wanka tana rera kuka fiyye da yadda ya barta, ko Kaɗan bata bashi tausayi ba saima ji haushinta kamar ya rufe ta da duka in yaso tayi kuka da dalili. Ta ɗago idanuwanta da suka yi jajir mascara da kwali haɗi da eyes shadow da tasa suka ca6e wuri d'aya, sai ta dawo tamkar wacce tai kwalliyar wasan tashe. Tayi tozali da Azaad d'aure da blue towel iya waist ɗinshi cikinshi a shafe ga six packs a jere kwanin sha'awa. Ta bi gaba ɗaya jikinshi da kallo ta ja dogon numfashi sakamakon wata masiffafiyar sha'awarshi ta taso mata ya biyo ta gefenta yasa k'afarshi ta dama ya shure kafafuwanta cike da wulak'anci ya ce. "Ke dallah.....jaye min kafafuwanki na wuce kin saki kafafu tula-tula kamar doya, ni ban masan haka kafafuwanki suke ba abu ba ko kyau gani" Ya k'arashe magana yana tafiyar tak'ama yana hura hanci, ya nufi gaban mirror ya shiga shafe lallausar fatar jikinsa da lotion mai sanyi k'amshi. Madam Salima ta yunk'ura ta tashi da kyar saboda kasala da tsananin sha'awa da suka taso ta gaba. Azaad ya ajiye robar lotion yasake ra6awa gefenta ya wuce ko kallonta bai yi ba. Ya nufi dressing room yana cikin buɗe closet hankalinsa ya raja'a da kallon kayan da zai saka, sam bai ji shigowarta ba sai kawai ya ji ta rungumeshi ta baya, da dukkan k'arfinta ta zagaye cikinshi da hannuwanta tana gunji kuka cikin muryar kuka take faɗin. "I'm sorry Azaad please forgive me It’s never been easy for me to say “I’m sorry,? but I’m saying that now. Please give me another chance... Tana magana tana kuka tare da goga fuskarta a gadon bayanshi, yadda take mishi saura Kaɗan towel ɗin jikinsa ya zame saida ya gyara zaman towel ɗin kana ya daddage iya k'arfinshi da Allah ya albarkace shi dashi ya tureta ta goshinta ya buge bango kana ta faɗi k'asa, cikin gaggawa ya shirya cikin shadda getzner sky blue d'inki babbar riga yasa hula zanna bukar da ta dace da shaddar, faɗuwar da tayi ba k'aramin ciwo ta ji a goshinta ba. Amma ko ya bi ta kanta ya fice abinsa duk da haka ta sake tashi ta biyo shi a baya tana mai ci gaba da bashi hak'uri. "Azaad!... Azaad Dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min Azaad Please give me a chance to prove that I can change. I’m sorry, and I’ll take my punishment. Amma ka tsaya mu fahimce juna.. Ko waigawa bai yi ba. Balle tasa ran zai amsa kafin ta k'arasa saukowa har ya fice sani tayi idan ta bishi zai ci gaba da disga ta ne a gaban housemaids ita Kuma ba za ta yi sake da daraja da k'imarta su ragu ba. Sai kawai ta wuce 6angarenta ta ɗora Abaya akan tufafin jikinta, ta zari handbag ta fice kaitsaye gidan Hafsat Shinkafi direbanta Mr Michael ya sauke ta. Azaad yana fitowa ya shiga 6angaren Jadda ya yi breakfast ya kuma umarce Mero mai aikinta ta zubawa Miyya. Sai lokaci ya faɗawa Jadda tana asibiti sosai Jadda ta tausaya mata har ta nuna za ta bishi asibiti ta dubata, ya k'i amincewa ya kuma kafa mata hujja yau ko gabo za a sallameta ba don ranta yaso ba, ta zauna tayi mata fatan samun sauk'i, Mero ta kai ma Mr Richard basket ɗin abinci yasa cikin mota. Dai-dai Mero tana kawowa k'ofar shiga, shi kuma yana fitowa ta janye ta bashi hanya ya wuce. Koda suka isa asibiti sha biyu ta gota yana gaba Mr Richard yana biye dashi rik'e da food basket suna zuwa k'ofa Azaad ya tsayar dashi ya kar6i basket ɗin. Mr Richard ya koma gun mota, sannu a hankali ya tura k'ofa ta buɗe cikin k'aramin sauti duk da haka saida Miyya da ke kwance ta waigo da k'arfi karaff idanuwanta suka sark'e cikin nashi ya saki mata k'ayatatcen murmushi irin mai shiga jiki ya yi wa jini da bargo babbar illa, saboda tuni ya yi awon gaba da ruhi haɗi da gangar jikinta. Ta rausayar da kanta yayin da zuciyarta ke ta faman bugawa da k'arfin gaske. Cikin mutuwar jiki ta tashi zaune. Ya k'araso tare da ajiye basket ɗin cike da kulawa mai d'auke da zallar wutar so da k'auna ya ce. "Prettyn Daddy ya jikin naki hope ba inda yake miki ciwo?" Sabon suna da ya kira ta dashi ba k'aramin farin ciki ya haifar mata ba. Tsabar dad'in da ta ji yasa tasaki murmushi mai sauti, ta tsare shi da idanuwanta da ke masifar burgeshi. "Ni fa Daddy sumul nake. Yadda nake ji ma tamkar ban ta6a wani ciwo ba ko kaina dake ciwo yanzu ya daina gida kawai nakeso zuwa banaso Aneesah da Airah su dawo daga school ba su ganni ba za su tashin hankalinsu. Ga kuma baby Ahlam idan bata gani ba za ta iya kuka" Yadda takevmagana cikin shagwa6a6iyar murya ya k'ara rura mishi wutar sonta, wani maganadisu ke yawo a jinin jikinshi tamkar electric shock, lumshe idanuwanshi ya yi kafin ya ware su tass...akan kyakkyawar fuskarta kana ya tattara babbar rigarshi yanda ba za tayi squeezing ba, ya zauna daff da waist ɗinta ya Kamo hannunta ya haɗe da nashi yasa ɗayan yana tatta6a gefen-gefen wuyanta ya ji ko da raguwar zafi, yadda yake shafa wuyanta yasa tsigar jikinta tashi yarrrr.....ya ji ko Kaɗan babu zafi kana janye hannun nashi daga wuyanta. "Gaskiya kin ji sauk'i sosai babu zafi a jikinki amma sai in doc ne da kanshi ya yi discharge ɗinki sannan ne zan amince da tafiya gida. Yayi magana yana massage ɗin tafin hannunta, hakan ba k'aramin k'ara mata mutuwar jiki ya yi ba, ta langwa6e Kai ta ce. "Allah Daddy ni gida nakeso zuwa kaga ko d'azu da uncle Hakeem ya zo duba ni na tabbata sai ya faɗawa Amrah da Amal muddin suka zo suka sami ni anan hankalinsu zai tashi ba Kuma zan so haka ba. A wannan rayuwar su Kaɗai nake da su ɗin ma ni Kaɗai suka sani nice uwa nice uba a garesu haɗuwarmu da uncle Hakeem ya kar6e wannan matsayin duk da haka ina tattalin farin cikinsu. Dai-dai da kwarar zara banaso su shiga damuwa. Cikin kalamanta Kaɗai ya fahimce muhimmancin da 'yan uwanta suke da a wurinta, nan take ya k'udurta aranshi ba zai sake bari su yi maraci ba daga na uwa har na uba. Da kanshi ya yi feeding ɗinta sai ya tabbata ta k'oshi sannan ya kyaleta. "Nagode Daddy Allah ya saka maka da gidan ajanna firdausi" Ta faɗa cikin k'aramar muryarta mai dad'in saurare, cheeks ɗin ya kama da hannuwanshi biyu yana dariya. "Amin thumma amin Prettyn Daddy amma karki sake yi min godiya duk abin da nayi miki kin can-canci fiyye da hakan a wurina" Dariya tasa mai ban sha'awa kana ta ce. "Kamar yadda na can-cance fiyye da hakan a wurinka nima kana da babbar daraja da k'ima a idanuwana ba kuma zan gaji da gode maka ba har izuwa k'arshen numfashina. Furuncinta ba k'aramin jifa shi farin ciki ya yi ba shiyasa ya saki kumatunta ya rik'o hannunta, ya matse cikin nashi ya ce. "Ki yi min alk'awali ba za ki sake shiga damuwa ba balle ta shafi lafiyarki. Ki d'aukar min alk'awali Pretty za ki faɗa min asalin abin da ke damunki, ni kuma zan yi iya bakin k'ok'arina na magance miki damuwarki. Idan matsalarki ta kud'i ce Pretty ina da kudin da ni kaina bansan adadinsu ba. Idan kuma ta wannan aurena ne da yake kanki shima zan iya hak'ura na saukewa miki duk da hakan zai iya rabani da farin ciki da na fara samu, ni dai burina ki kasance cikin farin ciki. Ta sadda kanta k'asa tana wasa da zip ɗin cardigan ɗin jikinta, duk lokaci da Daddy ya yi anbaci kalma rabuwa sai ta tsinci kanta cikin mugun yanayi sai ta ji tamkar ta ɗora hannu aka ta kwatsama ihu ta tsani jin wannan kalma tana fitowa daga bakinshi. "Pretty yi magana mana so nake naji musanbabin damuwarki?" Ta ɗago cikin rauni da karaya zuciya sai ta buɗe bakinta tayi magana sai kuma ta datse bakin nata, ta rasa abin faɗa. Sai musu-musu take da baki ga wani irin gumi da ya karyo mata. Hakan da Azaad ya gani sai zargi batason aure shiyasa tak'i magana k'ara matse hannunta ya yi zuciyarsa na bugawa da k'arfi kamar za ta fasa k'irjinshi ta faɗo k'asa sakamakon nauyi da girman maganar da zai furta. "Pretty ba ki so aure nan ko?" Shiru tayi ta kasa furta uffan sai ci gaba da wasa takebda zip ɗin yayin da ɗayan hannunta ke cikin nashi, shiru-shiru ba ta yi magana ba. Batasan cewa shirun nata yana barazana ga lafiyar Azaad ba. "Please talk to me mana banaso shiru nan naki saboda yana jefa ni cikin tunani kala daban-dabam. Tai ajiyar zuciya tare da ɗagowa ta kalleshi kafin ta kauda fuskarta cikin tattausan lafazi ta ce. "Daddy ni Musulma ce na yarda da k'addara mai kyau da marar kyau. Tun daga ranar da uncle Hakeem ya kawo ni gidanka nasa araina zan zauna da kai da zuciya d'aya duk da a lokaci basan waye kai ba. Amma nasa araina mutuwa ce Kaɗai za ta rabani da kai. A lokaci da na gama sani waye kai sai na fahimci kafi k'arfina nesa ba kusa ba. Ni ba ajin aurenka bace amma duk da hakan ban fidda rai wata rana nima zan sami gur6i a gidanka koda ban sami gur6i a matsayin matarka ba. To Al-hamdu-lillah ko yanzu burina ya cika saboda irin kulawar da ka bani a yau ɗinan Kaɗai ta haska min irin muhimmanci da nake dashi a wurinka. Tun daga lokaci da ta fara magana idanuwanshi suke bisa lips ɗinta, yana mamakin yadda take jeru kalamai cikin tsaftace halshe tamkar wata mai manya shekaru, alhali bata wuce 16-17 years ba. Kalamanta sun haifar mishi da farin ciki da ya jima bai ji kanshi a cikin irinsa ba. Batare da wani dogon tunani ba ya jawo ta cikin jikinshi ya rungumeta tsaf....yana shafa gadon bayanta yayin da fuskarshi ke bayyana irin farin ciki da yake ciki. Ya kai bakinshi daff da kunneta ya rad'a mata. "Thank you so much my pretty you're truly a blessing in my life. Ke ta dabance pretty kin fi lu'u lu'u tsada da daraja a wurina girmanki da k'imarki sun dad'a hauhawa a zuciyarta, in-sha-Allah ba za ki yi danasani aurena ba" A hankali ya janye jikinshi daga nata ya mik'e tsaye, yana kallonta tare da murmushi akan fuskarshi kafin ya kalli agogon hannunshi kana ya dawo da ganinshi akanta idanuwanta na kafe akanshi. "Lokaci zuwa masallaci ya karato banaso na rasa huɗuba ki kwanta ki huta kafin na dawo kin ji?" Ta gyada kanta, ya rik'o kanta da hannuwanshi ya sumbace ta a for head runtse idanuwanta tayi, tana ji lokaci da ya gangaro bisa lips ɗinta tun kafin bakinsa ya sauka akan nata tayi wata ajiyar zuciya, iskar da ta fito daga k'ofufin hancinta biyu ta sauka akan fuskarshi hakan ya k'ara rura wutar abun da yake ji akanta. Cike da kwarewa ya yi connecting lips ɗinshi da nata. Cikin salo na burgewa tare da tafiyar da ruhi da gangar jiki yake tsotsar bakinta, ba don ya gaji ba ya cire bakinshi daga nata. Sai don yana gudun kada ya rasa sallar juma'a. Gaba ɗaya jikin Miyya ya mutu mutusss.... kasala da kunya suka lullu6e ta tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya yi dariya tare da faɗin. "Ashe haka Prettyn Daddy take da kunya, Ki ce Daddy yana da aiki?" Da sauri ta kwanta tasa pillow ta k'ududdune fuskarta sosai ta bashi dariya yasa dariya mai ban sha'awa tare da rik'o k'afarta da hagu yana mata tafiyar tsutsa can cikin pillow take kwasar dariya tana d'an shura k'afarta. Da kyar ta fizge k'afarta ta yana dariya ya ce. "Shikenan na tafi tun da kin kore ni Nanny Lacey za ta zo tare da su princess su taya ki fira kafin na dawo. Bai tsaya jin amsar da za ta bashi ba ya buɗe k'ofa ya fita yana zagba fara'a da kalle shi sau ɗaya za ka fahimce duniya ta masa dad'i. Tun bayan tafiyarsa lokaci zuwa lokaci Miyya take murmushi, wani irin farin ciki da take ji wanda ta rasa na menene. A haka su Aneesah suka tararda ita da gudu suka rungumeta. Aneesah ta shak'i k'amshin turaren Daddynta a jikin Miyya gaba ɗaya jikinta k'amshin turarenshi yake yi, a firgice ta janye jikinta daga jikin Miyya zuciyarta na bugawa da k'arfi yayin da tsoro ya lullu6e ta. Cikin rawar murya ta ce. "Pretty ya na ji gaba ɗaya jikinki yana k'amshin turaren Daddy?" *Afuwan please jiya ban samu nayi update ba throughout jiya ba mu da wuta transformer ɗin mu ya lalace.* 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 29..... Kamar wacce aka jefo daga sama haka Hafsat Shinkafi taga Salima ta faɗo mata cikin falo, tana zuwa ta durk'usa bisa center carpet tamkar mai rokon gafara ta rushe da matsanancin kuka. Hankali tashe Hafsat ta taso ta dafa kafad'arta tana tambayarta. "Subhanalillah.....Salima lafiya ba dai mutuwa aka yi miki ba Kodai matsalarki ce da Azaad?" Tsananin kuka da take yi yasa ta kasa magana gaba ɗaya ta birkitawa Hafsat tunani ta rasa yadda za ta yi da ita sai faman rarrashinta take yi kamar wata k'aramar yarinya. "Haba Salima wannan fa ba girmanki bane koda mutuwa aka yi miki a wannan shekaru naki bai dace ki dinga rusa kuka haka ba. Balle ma nasan ba mutuwa bace matsalarki ce da Azaad ne ko?" Hak'uri za ki yi duk abin da ya faru da bawa muk'addari ne daga Allah tun ran gini tun ran zane. Ba wanda ya isa ya sauya k'addararsa, asalima imanin mutum ba zai cika ba har sai ya yi imani da k'addara mai kyau da marar kyau. Salima ki yi hak'uri ki mik'awa ubangiji al-amurranki kuka ba zai miki magani komai ba. Ba kuma zai warware miki matsalolinki ba, sai ma ya k'ara jefa ki cikin mayuwaci hali. Cikin shasshekar kuka da muryarta da bata fita sosai ta ce. "Hafsat na shiga uku na lalace Ina zan tsoma raina, na ji sanyi ji nake tamkar hankalina zai gushe wayyo......ni Hafsat ki taimake ni banaso na rasa Azaad. Wallahi Ina matuk'ar son mijina. Ta k'arashe magana tana sake rushewa da wani sabon kuka wanda yafi na farko. Hafsat tayi ajiyar zuciya jikinta ya yi sanyi lak'ass....dama tasan irin wannan ranar za ta zo da Salima za ta gir6i abin da ta shuka duk yadda take da ita da zarar ta fara bata shawara ta gyara zamantakewar aurenta, rufe idanu take yi ta ci mata mutunci sau dama sun sha faɗa akan ta bata shawara ta daina yi wa aurenta rik'on sakainiyar kashi. "Salima kina da girman kai wallahi duk yadda na ba ki shawara ba ki amfani da ita..... "Wallahi-tallahi Hafsat duk abin da kika faɗa min ba wanda na yar asalima shawararki da na d'auka ita ce silar kukan na nawa. Tana kuka tana zayyanewa Hafsat irin wulak'anci da Azaad ya shuka mata, tun da ta fara magana Hafsat ta yi shiru hak'ik'a Azaad ya shammace su yadda yake shiru-shiru nan ga d'an banza hak'uri bata ta6a zaton zai iya zuba rashin mutunci irin wannan ba. Duk da tasan iskanci da Salima take mishi ba kowane namiji zai iya jure shi ba. Duk tsawon shekaru da suka yi da aure zaman hak'uri Azaad yake da ita bai isa ya faɗa ta ji ba, bashi da ra'ayi sai nata duk abin da ta faɗa ya zauna koda kuwa ranshi bayaso. Batasan darajarshi ba balle ta aurenshi da ke rataye a wuyanta kwata-kwata a rayuwarta ba abin da tasani ko ta iya daga neman kud'i sai izza da tak'ama. "Kukan ya isa haka ki share hawayenki, ki natsu ki bani aron hankalinki dole ta inda aka hau tana ake sauka a yanzu kina da two options dole ki yi amfani da d'aya daga cikinsu" Madam Salima ta ciro mayafin abayar jikinta ta goge fuskarta tare da fyace majina, tattaro dukkan natsuwarta ta kafe Hafsat da jajjaye idanuwanta. "Salima tun farko kin ri ga da kin 6ata rawarki da tsalle ko ba a faɗa ba daga jin yadda Azaad yake ci miki fuska yana kushe halittarki, kin fice mishi a zuciya ko kaɗan a yanzu ba bu ke gabanshi. Kuma duk kece silar faruwar hakan saboda haka girman kai ba naki bane ki sauke duk wani jiji da kai naki, ki nemi Jadda ko Hakeem sune Kaɗai mutane da Azaad baya iya fatali da umarninsu. Su Kaɗai ne za su iya yi mishi magana ya dawo da aurenku. Ina ga wad'annan mutane guda biyu su kaɗa ne damar da suka rage miki. Madam Salima ta rafka tagumi har ga Allah bataso maganar rabuwarsu ta yad'u a duniya shiyasa, za ta d'auki wannan shawarar ta Hafsat da ba don haka ba daga Hakeem har Jadda basu isa ta rok'i alfarma a wurinsu ba saidai su rok'a a wurinta. *** **** ***** Gumi ne ya karyowa Miyya gaba ɗaya ta rud'e ta rasa amsar da za ta ba Aneesah, gashi ta kafe ta da idanuwanta ba ko kiftawa ba shakka Aneesah tana zargin wanzuwar wani abu tsakaninta da Daddy. "Ke dai Aneey kina da shegiya mantuwa yanzu har kin manta d'azu da safe da Pretty ta suma Daddy ne ya d'auko ta zuwa hospital Kin ga kuwa dole tayi k'amshin turarenshi. Airah ta faɗa tana kallon Aneesah da murmushi akan fuskarta. Kusan a tare Miyya da Aneesah suka sauke ajiyar zuciya, duk abin da suke faɗa Nanny Lacey tana zaune a gefe rungume da Ahlam tana kallonsu. "Al-hamdu-lillah.....Allah nagode ma da Airah ta yi sauri kar6e zance nan da batasan me zan ce da Aneesah ba. Miyya ta faɗa cikin zuciyarta, daga haka su ci gaba da firar abu da ya wakana yau a school jefi-jefi take tsoma bakinta. Da ta gaji da sauraren surutunsu ta mik'e ta shiga bathroom tayi alwala ta kabarta sallar azhar tana raka'ar k'arshe sai ga Aunty Zaliha tare da Amrah, Amal da Rayhan tana sallamewa bata tsaya doguwar addu'a ba ta mik'e, Amrah da Amal suka rungumeta ta yi matuk'ar farin ciki da gani su. Ta saki jiki suka shiga fira tamkar ba ita bace marar lafiya ba. Misali karfe biyar da minti goma Azaad ya tura k'ofar d'akin da Miyya take, tana zaune tsakiyar gado ta mi-mik'e kafafuwanta yayin da Ahlam take kwance akan cinyarta tana wasa da doll ɗinta, Miyya tana ɗagowa taga shine tai sauri sadda kanta k'asa gudu kada tayi abin da Aneesah za ta sake dasa mata alamar tambaya. Yana shigowa gaba ɗayansu suka daina magana ka ji tsittt....kamar ruwa ya cinye su d'aya bayan d'aya suka dinga gaida shi can k'asan mak'oshi yake amsawa, sai kayi da gaske za ka iya jin abin da yake faɗa. Aunty Zaliha Kaɗai ya d'an sakewa fuska suka gaisa. "Daddy manya ba dai miskilaci ba. Miyya ta faɗa cikin zuciyarta. "Nanny zo ki d'auki Ahlam direba yana jiranku a waje" Ya yi magana batare da kalli gefen da Nanny Lacey take ba, ta taso da sauri ta d'auki Ahlam kuka Ahlam tasa alamar bata zuwa. Cikin sanyi murya Miyya ta ce. "Nanny ki barta kawai tun da bataso in Daddy ya tashi tafiya ya wuce da ita. Kallon da ya yi wa Nanny Lacey yasa bata bi ta kan Miyya ba ta wuce da sauri sa6e da Ahlam a kafad'a sai taratsin kuka take yi, yayin da sosai kukan nata ya ta6a Miyya shiyasa ta runtse idanuwanta. Aneesah ta ce. "Get well soon our Pretty" Murmushi kawai Miyya ta saki mata, kamar jira su Aunty Zaliha ke yi su Aneesah su fita suma suka mik'e. Miyya ta kallesu tamkar za ta rushe da kuka ta ce. "Aunty Zaliha ba dai tafiya za ku yi ba?" "Eh....tafiya za mu yi Aslamiyya mun baro gida ba kowa. "Aunty ki barmin twins da Rayhan su tayani fira, bana ji dad'i zama ni Kaɗai, wallahi na gaji da zaman asibiti nan" Murmushi Aunty Zaliha tayi saboda yadda taga Azaad Junaid ya kasa ya tsare so yake su bar mishi d'aki, ta dubi su Amrah ta ce. "Ku tashi mu tafi mana" "Aunty ba ki ji Miyya ta ce ki barmu anan ba?" Cewar Rayhan tana turo baki, harara aunty Zaliha ta galla mata babu shiri suka mik'e, Miyya tana kallonsu suka fice. Suna ficewa shima ya fice kaitsaye office ɗin doc Saheeb ya nufa, tare suka dawo d'akin doc ya sake dubata, ya ga tadawo normal kana ya yi 'yan rubuce-rubuce a cikin folder ɗinta kana ya mik'awa Azaad discharge papers yana murmushi. "Al-hamdu-lillah....jikinta ya yi kyau za ku iya tafiya Yalla6ai saidai ta dinga kula da shan magani cikin lokaci, ta kuma daina sa kanta damuwa Allah ya k'ara bata lafiya. "Amin Doc Saheeb thank you very much. Azaad ya yi magana tare da mik'a masa hannu suka yi musabaha. Doc Saheeb ya buɗe k'ofa ya fita sai lokaci ya kalleta, ta sunyarda kai tana wasa da yantsun hannunta a natse yake yawo da idanuwanshi akanta, ta cire cardigan ɗin jikinta ta bar white t-shirt kasancewar rigar fara ce yasa ake iya gani shatin black colour bra ɗinta. Gashin kanta a buɗe tayi parking ɗinshi wurin d'aya a yadda take ɗinan ba zai iya barinta ta fita ba text ya turowa Mr Richard ya nemo mata wasu kaya. Sannan ya nufi kusa da kafafuwanta ya zauna ta ɗago idanuwanta ta kalle shi, shima ɗin ita yake kallo duk bayan kowace dak'ik'a k'ara mishi sonta ake yi. Ya mik'a mata hannunshi na dama ta dubi tafin hannunshi sumul-sumul dashi alamar ba a aikin wahala dashi cikin mutuwar jiki ta ɗora hannunta cikin nashi. "Daddy Dan Allah mu tafi gida haka nan wallahi na ji sauk'i. Tayi magana cikin siriyar muryarta mai taushi, ya kalleta tare da maka mata harara da sauri ta kauda fuskarta. Ya d'an gyara murya tare da matsawa kusa da ita ya ce. "Prettyn Daddy ba ki so kasancewa tare da ni ko?" Da sauri ta ce "ba haka bane Daddy kawai dai naji sauk'i babu amfani ci gaba da zamana anan. Ya ja gwaron numfashi ya sumbace hannunta dake cikin nashi. "Ki k'ara hak'uri kaɗan na aiki Mr Richard ya siyo miki kayan da za ki saka mu tafi gida. "Kaya kuma Daddy bayan wannan da ke jikina ai Ina da wasu kaya a gida da zarar mu isa gida zan canza, ni dai ka tashi mu tafi. Ta k'arasa magana tana cire hannunta daga nashi ta shiga k'ok'arin saukowa, Azaad ya kalleta da girar ido ɗage lallai yarinyar nan akwai zallan kurciya a cikinta, ai ko karen hauka ya cije shi ba zai barta ta fita da wannan kayan a jikinta ba. Hannu yasa ya dawo da ita bisa gado ya d'aure fuska ta kalleshi sosai yai mata kwarjini da sauri ta sadda kanta k'asa. Mr Richard ya yi knocking on Azaad ya mik'e ya kar6o shopping bag ya buɗe ya ciro long hijab ya saka mata batare da ya tanka mata ba ya nufi k'ofar fita da sauri ta diro daga kan gado ta d'auki sneakers ɗinta a hannu ta bishi a baya kamar an ce ya waiga ya ganta tafe babu takalmi a k'afafuwanta. Ya ja tsaya har ta k'araso cikin d'aure fuska ya ce. "Ke banaso shirme ki tsaya ki sa takalminki nan asibiti ne kina tafiya ba takalmi salon kuma wata cuta ta kama ki. Cike da jin kunya tasa takalmin yana gaba tana bin shi suna daff da isa parking lot suka haɗu da Ahmadu sai lokaci Azaad ya tuna da Hasheem a asibitin yake cikin sakin fuska ya mik'awa Ahmadu hannu su gaisa a maimakon Ahmadu ya bashi hannu sai kawai ya ɗaga masa hannu cike da wulak'anci yake kallon Azaad. Miyya ta k'araso wajensu cikin sanyi murya ta gaida Ahmadu yana ganinta cikin dogon hijab har k'asa gabanshi ya yi mummunan faɗuwa nan take ya tuna da inda yasan fuskarta tabbas ita ce aljana da ta fito cikin kwaryar zafi boka ta kasheshi tare da babban Yaya da Alhaji Buba. Shima ta biyo shi ne domin ta kashe shi cikinshi yai masifar murd'awa, a tsorace ya dinga ja da baya yana furta. "Innalillahi wa'aina illahim raji'un.....Ita ce wallahi ita ce aljana da ta kashe babban Yaya da Alhaji Buba ki duba girman Allah ki yi min rai karki kashe ni wallahi-tallahi babu hannuna a cikin wannan tafiya, gaba ɗaya shirrin Hasheem ne. Ahmadu yana magana yana ja da baya da sauri Azaad ya rik'o shi ya buge mishi hannu ya kwasa da gudun bala'i ya nufi gate ɗin fita ko ta kan motarsa bai bi ba. Azaad ya dawo wurin da Miyya take tsaye tayi folding hannuwanta a k'irji hankalinta kwace ba abin da ya razana ta. "Daddy amma wannan mutumin motsatsi ne ko?" Tsabar mamakin abinda ya ji Ahmadu ya faɗa ya hanawa Azaad bata amsa sai kawai ya kama hannunta suka nufi wajen mota, da sauri Mr Richard ya fito ya buɗe musu k'ofa suka shiga kana ya ja motar cike da kwarewa da driving. A maimakon su nufi gida sai ta ga Mr Richard ya d'auki hanyar Nassarawa GRA a sultan road wani tangamemen gida ya tsaya horn guda ya yi security ya buɗe mishi gate. Azaad ya fara fitowa kana ya taimaka mata ta fito, a fakace take kallon compound ɗin gida sosai ya burgeta yana rik'e da hannunta suka jera side by side bata k'ara tabbatar da gidan ya haɗu ba sai da suka shiga parlour anan taga matuk'ar haɗuwa za ka ci ba a Nigeria kake ba. Da shigarsu parlour ya saki mata hannu ya nufi upstairs muryarta na rawa ta ce. "Daddy me za mu yi anan ni fa gida nakeso zuwa?" "Hutawa za mu yi gida Kuma ba yanzu ba. Ya faɗa yana ci gaba da tatttaka matattak'alar bene, jin abin da ya faɗa yasa gabanta yai mugun faɗuwa cikin sauri ta bishi tana faɗin. "Wane irin hutawa Kuma Daddy?" Ni dai Dan Allah ka maida ni gun su Aneesah ko Kuma gidan uncle Hakeem, wallahi kwata-kwata gidanan bai kwanta min arai ba. Ya tsaya cakk.... batare da ya juyo ba ya ce. "Wannan kuma matsalarki ce ki zo mu je na nuna miki bedroom ɗinki ki yi wanka tun safe kike sanye da kaya d'aya ke ko k'azantar su bakya ji. Turo baki tayi tana gun-guni k'asa-kasa "ka ji min mutum haka kawai ka d'auko ni ka kawo inda bansani ba ka ce ba zan yi magana ba. "Me kika ce?" "Ban ce komai ba Daddy" Ta faɗa cikin marairaice murya. Ya ci gaba da haura staircase dole ta bi shi a baya, ya buɗe k'ofar d'aya daga cikin d'akuna uku da ta gani a jere, dai-dai k'ofa ta ja birki tana tunani ta shiga ko ta koma inda tafito. Bata gama tunani ba ta ji ya jawo tana jin saukar numfashinsa daff da fuskarta, ya cire mata hijabin jikinta idanuwanshi suka sauka akan boobs ɗinta da suke cike tabbb....a k'irjinta har sun so su rinjaye ta sauk'inta d'aya a tsaye suke cakkk kana ya jefa hijab ɗin nata bisa gado, ya ɗora hannuwanshi masu masifar taushi aKan kafad'arta ya mutsa da ita cikin jikinshi, kafin ta yi yunk'uri kwatar kanta ta ji ya sumbace ta a gefen wuya ya cigaba da shinshina gefe-gefen wuyanta yana zuba mata dafi kisses k'ok'arin tura hancinshi yake tsakiyar rigarta wacce rabin boobs ɗinta ke waje jikinta ya d'auki rawa kamar mazari batasan lokaci da ta ture shi ba ta falla da gudu ta nufi wata k'ofa da take tsanmani bathroom ne. Tana shiga ta datse k'ofar da key. Sai da Azaad ya d'auki dogon lokaci yana dambe da numfashinsa kafin ya samu ya dai-daita, a kasalance ya buɗe k'ofa ya wuce d'akin da ya kasance mallakinshi a gida wanka ya yi ya shirya cikin milk colour ɗin jallabiya, yana cikin fesa turare Hakeem ya kira wayarsa, ya yi picking up ya kara a kunnenshi. Kafin ya yi magana Hakeem ya ri ga shi ta hanyar faɗin. "Aj duk abin da ka ke yi ka aje shi ka zo yanzu-yanzu nan Jadda tana son ganinka" "Lafiya Hakeem Jadda keso ganina da gaggawa?" "To zan iya cewa lafiya Salima ce ta kawo kararka wajenta. "Uhm... Salima! Ya furta sunanta cike da takaici ko kaɗan bai so Jadda tasan ya saki Salima ba har sai ta gama iddarta gudun kada ta cilasta shi ya dawo da ita sai gashi an gudu ba a tsira ba. "Shikenan Hakeem ka faɗa mata ganina zuwa. Daga haka ya kashe wayar tsabar haushi da takaici yasa ya fita batare da ya lek'a Miyya ba. Koda ya iso ana kirar sallar magariba ya tsaya anan masallaci dake k'ofar gidanshi ya yi sallah k'a'idarshi ne in ya shiga sallar magarib sai ya yi isha yake fitowa daga masallaci. Bayan an kammala sallar Isha yana fitowa ya yi arba da Hakeem ya mik'a masa hannu suka yi musabaha suka jera zuwa cikin gida suna tafe suna tattaunawa dangane da kiran da Jadda take mishi. "Aj miyasa ba ka faɗawa Jadda ka saki Salima ba?" "Saboda banaso ta cilastani na dawo da ita har ga Allah naso ace iddarta ta cika kafin Jadda tasani, a zahirin gaskiya Hakeem banaso dangatakar aure ta sake haɗani da Salima. Musanmman a yanzu da na fara son kwailata. Ya k'arashe magana da annuri akan fuskarshi, murmushi Hakeem ya yi kafin ya ce. "Ai abokina ba k'aramar sa'a ka taka ba yarinya danya latsar sai yadda ka bi da abarka ba za ka faɗi ta faɗa ba. Saidai zance na gaskiya dole ka hak'ura ka dawo da Salima ko don albarkaci yaran dake tsakaninku. Kuma ga dukkan alama duniya ta fara yi mata atishawar tsaki, koda na fito sallah na baro su ita da k'awarta Hafsat Shinkafi Jadda tana wanke mata allonta tass....sai kuka take yi tana rokon Jadda Allah da Annabi ta sa baki ka dawo da ita...... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 *SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣?* *SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️* *SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️🗣?* *NUCEEYLUV😘 NA MUKU ALBISHIR DA DATA DINTA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA, MAZA KU GARZAYO SAUKI DATA A CANCARE KU DA DATA A BAGAS🤸🏻‍♀?, TURAWA BABU BATA LOKACI 📤👌🏻* *MTN* 50mb-50 150mb-100 500mb-200 1GB-300 2GB-600 3GB-900 5GB-1500 10GB-3k 20GB-5k *Codes for check balance, *131*4#* *1MONTH VALIDITY* *AIRTEL* 100mb-150 300mb-250 500mb-300 1GB-600 2GB-1200 5GB-3k 11GB-4500 *Codes for check balance, *140#* *1MONTH VALIDITY* *GLO* 1.35GB-550 2.9GB-1200 4.1GB-1600 5.8GB-2200 7.7GB-2600 10GB-3200 14GB-4k *Codes for check balance, *127*0#* *1MONTH VALIDITY* *9MOBILE* 1.5GB-1200 2GB-1500 3GB-2k 11GB-4k *Codes for check balance, *228#* *1MONTH VALIDITY* CALL 09039118754 OR CHAT ME PRIVATE 09039118754? *YADDA ZAKI BIYA, ZAKI TURO KUDI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 1445626295. NUSAIBA MUSTAPHA ACCESS BANK* *IYA KUDIN SIYEN DATA IYA SHAGALIN KU🤸🏻‍♀? BANA AMSAR KATI PLS😁👌🏻, KADA KU BARI AYI BA KU WANNAN GARABASAR😍, ZAKU IYA SAVING NUMBER NAN 09039118754 DOMIN SIYEN DATA KAI TSAYE BABU BATA LOKACI KO BANA ONLINE KU KIRA KAWAI MASOYA💃🏻* 30.... Miyya tayi tsaye gaban mirror tana kallon tsakiyar rigarta da Daddy ya gama tura kanshi a cikin, wata kunya ta sake lullu6e ta har tana rufe fuska tamkar tana a gabanshi. Daga bisani ta cire kayan jikinta tayi wanka ta zari d'aya daga cikin jerin white towels da ta gani a bathroom ta d'aura, ta buɗe k'ofa a hankali saida ta fara lek'awa taga Azaad ya fita kana ta fito, agaggauce ta tsane jikinta ta shafa lotion da ta gani akan mirror. Shopping bag ɗin da ya aje mata bisa gado ta d'auka ta zazzage kayan da ke ciki. Ɗaga su sama ta dinga yi tana kallo tana yatsine fuska sakamakon babu ta kirki a ciki kusan seat biyar ne biyu sleeping dress ne, suma duk wasu fingilallu dasu. Ta ɗaga wata belted shift ga ta tayi kyau har ta gaji musanmman da ta kasance her favorite color saidai ba za ta wuce iya cinyoyinta ba. Tsaki ta ja ta aje ta, ta d'auki Indonesia gown ita kuma spaghetti hands ne da ita Kuma za ta iya wuce gwiwoyinta. "Kai amma wallahi Daddy d'an duniya ne yanzu shi ko kunya ba ya ji ya siyo irin wad'annan kayan" Miyya ta faɗa tana ta6e baki haka nan ta d'aure ta saka Indonesia gown ɗin ba don ranta yana so ba. D'aya daga cikin perfumes da take akan mirror ta fesa, kana tasa hijab ɗin da ya bata wanda ya sauka mata har k'asa tayi sallah. Jahilin tsaki Azaad ya ja kamar zai gutsire harshensa "mtssss.! Cikin 6acin rai ya kalli Hakeem don har idanuwanshi sun fara canza launi ya ce. "Tuban mazuru ne kawai tayi ni nasan wacece Salima hawainiya ce a ko wane lokaci sauya launi take da zarar tayi nasara na dawo da ita za ta ci gaba da halinta ne, ba abin da za ta fasa. Ba zan 6oye maka ba Hakeem wallahi-azim Salima ta fita daga raina, kamar an yi ruwa an d'auke ji nake tamkar ban ta6a rayuwar aure da ita ba. "Hak'uri za ka yi Aj tsakani da Allah kaima kana da naka laifi tun farko kaine ka bata damar da tayi yawa har ta zo tafi k'arfinka. Kuma tun farko ba ka duba nagarta da tarbiyya ba ka biyewa soyayya ka kwasowa kanka jangwa, ko a wancan lokaci ni da Jadda mun nuna maka illolin da ke tattare da auren Salima amma ka rufe idanunka. Kafin Azaad ya bashi amsa suka iso k'ofar shiga falon Jadda, dole ya ja bakinshi ya yi shiru tun kafin ya k'arasa shiga falon ya d'aure fuska tamau alamar babu wargi a tare dashi, Salima tana ganinshi ta k'arawa kukanta armashi har wani shan majina take yi, kallo d'aya Azaad ya yi mata ya wulga mata harara ya kauda fuska. Hafsat shinkafi sai faman gaidashi take yi yak'i amsawa ya kalleta a ɗage ya watsar kana ya nufi cushion ɗin da Jadda take zaune ya zauna kusa da ita. Jadda kan sai kallonshi take yi ta kasa gasgata ya saki Salima gaba ɗaya gani abin take kamar al'mara. "Gani Jadda" Ya faɗa cikin dakakkiyar murya tare da sunkuyar da kai. "Idonka kenan Datti wato da raina da lafiyata ka saki matarka shine ba ka faɗa min ba. tsabar baka d'auke ni a ba ki komai ba ko?" Sosai ya ji ranshi ya k'ara 6aci musanmman da ya fahimce ran Jadda ya 6aci a dalilin rashin faɗa mata ɗin da ya yi sai duk ya ji wata sabuwar tsanar Salima ta kamashi. Ya fara magana rai 6ace. "Da farko ina mai ba ki hak'uri Jadda, Allah ya huci zuciyarki. Inaso ki sani Jadda idan kika cire soyayyar Allah da manzonsa ke ce abu mafi soyuwa a zuciyata matsayinki a guna ya zarce na kowa a faɗin duniya, basan dad'in uwa ba balle na uba kece uwata kece ubana duk wani abu da na zama a rayuwa albarka ki ce take bina. Banso ko kaɗan ki saka bakinki a lamarin nan ba ke kanki sheda ce akan tsawon shekaru da na d'auka ina kunsar bak'in ciki Salima. Suna kawai Ina da aure ne amma a zahirin gaskiya banida ban-banci da gwaro. Ni da gidana ban isa na faɗa aji ba hakazalika yarana sai ta nuna tafi ni iko dasu, a takaice dai Jadda tafiya ta shirya nace ba da yawuna ba, saboda ba ta d'auke ni da daraja ba tasa k'afa takalmi tayi tafiyarta sai sanda ta ga gama gantalinta sannan ta dawo. Ba irin rok'on da ban mata ba akan ta fasa tafiyar nan amma ta murje idonta tak'i, daga k'arshe tayi abin da ranta yake so nima shine na nemawa kaina mafitar da ta dace da ni. Iya hak'uri nayi hak'uri yanzu kuma tura ta kai bango nagaji Jadda wallahi-azim na gaji da zama da Salima kwata-kwata ta fice min a rai, babu ko burbushin sonta a zuciyar nan tawa. Ya k'arasa magana ya nuna saitin da zuciyarsa take, tun kafin ya dasa aya Salima ta d'aura hannu aka ta kwatsama ihu, tana kururuwa sam bata zaci jin wad'annan zafafan maganganu daga bakinshi ba. "Dallah....kama mana bakinki ai duk kece silar faruwar komai, wallahi Salima kin yi girman wofi, kin yi faɗuwar bak'ar tasa ba nauyi. Jadda ta daka mata tsawa tana zuzuba mata harara mai cike da takaici, ji take tamkar ta rufe ta da duka. Rufe idanuwa Jadda tayi tasake wanke mata allonta tass ta inda take shiga ba ta nan take fita, ta zage ta iya son ranta takaicinta na tsawon shekaru da take k'unshe dashi yau saida ta sauke mata shi. Kafin ta juya kan Azaad ta fara mishi nasiha haɗe da rarrashi. "Datti hak'uri nan da ka saba yi ko yanzu shine zan ba ka, mai hak'uri yana tare da Allah kuma ba zai ta6ewa ba. Ubangiji da kanshi ya hallata saki amma kuma bayaso idan har kace ka gama zama da Salima, to yaranka fa duk da su ɗin ma ba dad'inta suka sani ba?" "Uhm...har ga Allah Jadda banso maganar nan ta zo gunki ba, saboda ba zan iya Musa miki ba amma duk da haka ina neman alfarma a wurinki da ki cire bakinki tun da kema ba girmanki take gani ba, Kuna zaune a gida d'aya sai ta share shekara bata lek'o 6angarenki ba da suna ta zo duba lafiyarki duk da tasan matsayin da kike takawa a guna. Me Salima take nema a duniya indai ta fanni arziki ne Dai-dai gwargwado Allah ya azurtani da dukiya mai dinbin yawa amma tsabar rashin godiyar Allah irin nata a kullum burinta tayi building nata career na rasa gidan uban da za ta je da daud'ar duniya. Ni yanzu jira kawai nake ta gama iddarta ta tattara komaitsa ta ta barmin gidana. Cikin muryar kuka Salima take faɗin. "Azaad kayi hak'uri ka dawo dani wallahi-tallahi na daina duk wani abu da baka so daga yau ba zan sake fita ko nan da k'ofar gida sai da izzininka. A dalilin soyayyar da nake maka tun lokaci da Hafsat ta faɗamin da zarar naga menstruation ɗina iddata ta kammala wallahi pills nake sha na hana mishi zuwa da bana son zama da kai da ba zan hanawa period ɗina zuwa ba. Gaba ɗayan falon in kacire Azaad salati da sallalame suke yi, ba tun yau ba Jadda tasan Salima kunsurgumar jahila ce amma bata zaci jahilcin nata ya kai haka ba. Tsabar takaici Azaad sai jan iska yake ta k'ofufin hancinsa yana fesarwa. Tsawon lokaci suka d'auka a falon aka rasa wanda zai yi magana gaba ɗayansu mamaki ya gama kashe su. Azaad ya yi k'arfin hali furta. "Ban yi mamaki jin wannan magana daga bakinki ba saboda ke jahila ce Salima wacce ba abin da tasani akan addininta ni Kuma a yanzu mace mai wadattace ilmin addini nakeso, natsatsiya ba ballagaza irinki ba. Saboda haka idan har kinaso ci gaba da zama dani sai kin koma islamiyya kin zama kalar mace da nakeso to a lokaci zan d'an yi tunani ko zan iya sake aurenki. Kuka sosai Salima take yi tsawon rayuwarta bata ta6a kuka irin wannan ba, muryata ta dusashe da rerafe ta isa wajen Jadda ta kama kafafuwanta ta ce. "Dan girman Allah Jadda ki sa bakinki wallahi na tuba, zan nemo malamin addini ya dinga koyar da a gida. "Shikenan tashi ki tafi zan yi magana dashi zan neme ki daga baya. "To amma Jadda ban ji Azaad yace ya dawo dani cewa fa ya yi.... "Salima a halin yanzu Datti a fusace yake duk wata magana da za ta fito daga bakinsa ba mai dad'i bace, gara ki tafi har ya huce. "Tam....Jadda nagode.... nagode Allah yasaka miki da alkhairi, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana. Jadda kam...kasa amsawa da Amin tayi saboda tun zamanta da Salima ko gaisuwa kirki bata ta6a haɗasu ba, sai gashi yau da wuya tayi wuya har fatan nisan kwana take mata. Duniya rawar 'yan mata na gaba ya koma baya. Hafsat shinkafi ta taso daga gun zamanta ta kama kafand'un Salima, ta mik'ar da ita sakamakon gani yadda ta kasa tashi daga durk'uso da tayi. Kamar makaho da d'an jagora haka suka fice daga falon Azaad ya bi su da harara. Jadda ta kalleshi a natse kafin ta ce. "Datti inaso ka dubi girman Allah ka dawo da Salima gudun kada ta jefa kanta babbar masifa, ni ban ta6a jin inda aka sha magani dakatar da zuwan jini haila ba don kawai kada iddah ta kammala sai a wurinta. Ajiyar zuciya Azaad ya yi tare da shafar sajenshi Wanda yin hakan ya zama mishi d'abi'a, ranshi a matuk'ar 6ace ya ce. "Gaskiya Jadda ban da ra'ayi sake zama da Salima ni fa yanzu Prettyn Daddy ta ishe ni rayuwa ba ma buk'atar third party a zaman mu. Zaro idanu Jadda tayi yayin da Hakeem ya tintsire da mahaukaciyar dariya. "Abdul-hakeem me Datti yake faɗa ne kwata-kwata ban fahimci turancinsa kai kuma ka yage baki kana babbaka dariya?" Hakeem ya tsagaita da dariya da yake yi ya mik'e tsaye ya ce. "Ba za ki gane ba Jadda saboda Aj ya zurma a soyayyar kwailarshi, bai ji bai gani ita kaɗai yake gani a gabanshi a takaice dai ita ce tauraruwar da ta dusashe hasken madam Salima a zuciyarsa. "Hoo.... ja'iri lallai Datti baka da kunya gotai-gotai da kai ace kana soyayya. Jadda ta faɗa tana dariya sai lokaci Azaad ya saki fuskarshi hadda su murmushi yana sosa keya kana ya mik'e tare da nufar k'ofar fita. "Datti ka dawo ba mu gama magana ba. "Jadda na baro matata ita kaɗai a bakon wuri bai kamata na shantak'e a wurinki ba tun da kina da ra'ayi da Salima ga ki nan ga ta. Ya k'arasa magana dai-dai yana kama handle Hakeem ya biyo shi da sauri yana faɗin. "D'an tsaya mana Aj ina ka kai 'yar mutane da ko isasshiyar lafiya batada, kada kace min angwacewa za ka yi. "To ko haramun ne?" "A'a...amma ka yi duba da kasancewarta kwaila anya kuwa za ta iya d'aukarka ka tuna weight ɗin ka fa abokina?" Ya k'arashe magana yana sake fashewa da dariya, tsaki kawai Azaad ya yi yana isa gun mota Mr Richard ya buɗe mishi k'ofa ya shiga duk iya shegen da Hakeem yake mishi bai sake tankawa ba. Kafin su isa gida ya umarci Mr Richard ya tsaya a wani tsadadden restaurant ya yi musu takeaway ɗin abinci ya kuma siyo musu lafiyayyun gasassun kaji. Koda suka iso gida goma da rabi ta gotta, dai-dai k'ofar main parlor ya kar6i kayan dake hannun Mr Richard. Kafin ya Isa d'akinta sai da ya wuce kitchen ya d'auko plate haɗi da drinks masu sanyi, a kwana nan ya k'ara gyara gidan hatta da foodstuffs akwai, a hankali ya buɗe k'ofa ya tsaya cakk dalili hango ta da ya yi ta jingina bayanta ga bangon d'akin tana sharar barcin abita. K'ayatatcen murmushi ya saki ya ajiye kayan hannunshi akan mirror kana nufi wajenta ya tsuguna yana kallon innocent face ɗinta yayin da zazzafar soyayyarta ke k'ara huda sassan jikinshi, ko zai kwana anan yana kallonta ba zai gaji ba. Yatsanshi yasa yana zagaye tattausan lips ɗinta suna d'aya daga cikin halittar jikinta da yake masifar so. Can cikin barcinta mai dad'i ta ji ana mata tafiyar tsutsa a le66e tai sauri buɗe idanuwanta tass...akan kyakkyawar fuskarshi, tasake lumshe idanunta masu cike da barci k'ok'arin rabata da hijabin jikinta da yake yi yasa ta sake buɗe idanuwanta. Cikin mayen barci ta ce. "Daddy ka dawo?" "Eh....my pretty ki yi hak'uri na bar ki da yunwa tashi ki ci abinci. "Daddy barci nake ji ka ajiye abinci nan da safe zan ci. "Haba.... Prettyn Daddy kina so yi min sakaci da lafiyarki ki d'aure ko d'an kaɗan ne ki ci. Ya k'arasa magana dai-dai ya cire mata hijab, ya ajiye shi a gefe ya kamata ta mik'e tsaye sai lokaci ya lura da rigar jikinta saura Kiriss numfashinsa ya fita daga gangar jikinsa, ba k'aramin namijin k'ok'ari ya yi ba da ya samu ya dai-daita shi. Akan resting chair ya zaunar da ita ya d'auko abinci ya juye a plate, yatsine fuska tayi kafin ta ce. "Banaso ci abinci Daddy ka bani tea ya isa ko fresh milk" Fresh milk ɗin ya d'auko ya zuba mata a cup ya dinga bata a baki yana haɗa mata da kazar amaryaci sosai taci har dasu gyatsa, ya kalleta ya yi gyaran murya ya ce. "Tashi ki je ki yi brush da alwala ki zo ki kwata. "Haba Daddy wane irin brush da dare nan?" Ta tambaye shi tana tura baki. "In ba za ki iya zuwa bathroom ɗin ba, bari na zo na kai da kaina" Yana dasa aya ta zabura da sauri ta tashi, koda ta fito ba shi cikin d'akin ya fita cikin sauri ta haye gado, ta lullu6e jikinta da duvet fuskarta kawai ta bari a buɗe ta lumshe idanuwanta, k'amshin turarenshi da ta shak'a ya ba tabbaci dawowar shi ta ware idanunta tana kallonshi, ya sauya kayan jikinsa zuwa royal blue pyjamas yana zuwa ya ye duvet ɗin da ta rufawa jikinta ya rik'o kafand'unta dole ta tashi zaune. "Tashi mu yi sallah" Ya faɗa cikin dakakkiyar murya gudun kada ta kawo mishi wargi ta 6ata mishi dare, gani yadda ya haɗe fuska yasa ta kasa yi mishi gardama bayan su kammala nafila raka'a biyu ya shiga yi mata tambayoyi game da addini cikin natsatsiyar muryarta take bashi amsa. "Ma-sha-Allah ashe Prettyn Daddy hafiza ce qur'ani ce?" Ya faɗa yana murmushi wani irin farin ciki yake ji musanmman da tace dashi ta haddace al'qur'ani mai girma. "Ban zaci kina da ilmin addini mai tarin yawa ba pretty musanmman, idan aka yi duba da yadda ku ka taso a hannu Dadda?" Murmushi tayi tare da sadda kanta k'asa ta ce. "Uhm.....shima Dadda tayi ne dalilin kada mu yi sha'awar addini mahaifyarmu, ta datse mana karatun boko a cewar ta garin bokon ne Abbanmu ya auro umminmu sam ba za ta bari tarihi ya sake mai-maita kanshi ba a ganinta idan ta wadata mu da ilimin addini musulunci ba za mu ta6a sha'awa kasancewar tare da mahaifyarmu ba. Murmushi ya yi tare da danke hannunta cikin nashi a hankali ya shiga massaging tafin hannun nata. "Allah ya sakawa Dadda da gidan ajanna bisa ga jajircewa da tayi kika sami dinbin ilmin irin wannan. Turo baki tayi tana gun-guni k'asa-kasa don ita kan bata ga dalilin wannan addu'a da ya yi wa Dadda ba. Matar kullum burinta su mutu. Mik'ar da ita tsaye ya yi ya cire mata hijab, ya matso ta cikin jikinshi ta yadda babu rata a tsakaninsu ya zagaye waist ɗinta da hannuwanshi wani irin abu yake ji yana ratsa jinin jikinshi yana so ya hak'ura da kusantarta saboda tayi k'ank'anta da yawa ba za ta iya dashi ba a wani 6angare na zuciyarsa yana k'ara azalzalar shi, ya kasa kama makama guda daya kwakwara ya yi ko ya hak'ura ya danne masiffafiyar sha'awarta da ke barazana raba shi da numfashinsa.... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 31... Da taimakon Hafsat shinkafi Salima ta iya kawo kanta flat ɗinta. Nanny Lacey kawai suka tararda a main parlor inda Allah ya taimake ta su Aneesah suna rooms ɗinsu. Koda ta shiga bedroom ji take yi kamar numfashinta zai fita ne daga gangar jikinta. Hafsat ta d'auko rubar ruwa faro mai sanyi ta 6alle murfi ta kafa mata a bakin cikin fitar hayyaci ta dinga tsuk'a sai da tasha fiye da rabi kafin Hafsat ta ciro rubar daga bakinta ta maida murfi ta rufe. Tayi ajiyar zuciya kafin ta ce. "Salima idan kina so aurenki dole ki bi duk wata doka da order da Azaad ya kafa miki, ni dai ina k'ara shawarta ki da d'aura ki nemi sani akan addini kin ga ko sallarki ba za a rasa kurakurai ba a cikinta, ki sani ba wayewa bace zama cikin duhun jahilci, ki godewa Allah yana sonki da rahama shiyasa ya kawo sabanin saki tsakaninki da Azaad domin ki yi amfani da wannan damar ki gyara gobenki da kin mutu a wannan hali da kin shiga uku. Ajiyar zuciya Salima tayi kafin ta ciro kanta ta kalli Hafsat cikin muryarta wacce daga ji ta kasan taci kuka har na fitar hankali ta ce. "Banida bakin gode miki Hafsat ke k'awa ce tagari wacce za a sha matuk'ar wahala kafin a sami ta biyunki. Da ace tun farkon Ina d'aukar shawara da nasiharki da ban tsinci kaina a wannan yana yi ba. "Ba komai Salima aminci da ke tsakaninmu ya zarce yadda kike tunani, inaso ki sa aranki no matter how ina tare da ke. *** **** ***** A kowace dak'ik'a k'ara rura mishi wutar sha'awarta ake yi, kyakkyawar runguma yai mata cikin jikinshi yayin da bugun zuciyarsu ya tsananta sai faman sauke numfashi suke yi, cikin fitar hayyaci ya lalla6o zip ɗin rigarta ya yi zipping ɗinta ta faɗi k'asa. Hannuwanshi suka dinga kai, da komo a sassan jikinta musanmman k'irjinta da suka fi zauta shi sosai tsoro ya lullu6e ta 'yar k'aramar kwakwalwarta ta kasa dauka sabon darasi da Daddynta yake koya mata. Yadda jikinta ke rawa yasa ya ɗagata cakk ya shinfid'eta akan gado ya yi mata rumfa da faɗaɗɗen k'irjinshi ya haɗe bakinsu wurin d'aya, sosai ya yi romancing ɗinta kafin da kyar da sudin goshi ya samu ya dan kutsa ta kasancewar k'ofar k'arama ce sai dai sannun a hankali yake bi da ita saboda shi kanshi yana tausayawa k'ananu shekarunta, a hankali kake ji fitar sautin kukanta, Azaad bai barta ba saida ya kauda matsalarshi ta wata da watani. Wata irin natsuwa yake ji tana shigarshi rungumeta yai cikin jikinshi sai sauke numfashi yake akai-akai Miyya kuma sai rera kuka take, a hankali yake shafar gadon bayanta yana hura mata iskar bakinshi cikin kunneta na dama tayi lamo tana sauke ajiyar zuciya alamar taci kuka. Bayan Hafsat shinkafi ta wuce Salima ta lalla6a ta shiga bathroom tayi wanka, simple makeup tayi tasaka sleeping gown mai jan hankali ta nufi part ɗin Azaad a tunaninta yana bathroom, kasancewar bata ganshi a parlor ba kuma baya cikin bedroom sai tai zaton ya shiga bathroom ta nemi gefen gado ta zauna. Wasa-wasa ba Azaad babu labarinsa har ta fara gyagyadi, jikinta a sanyayye ta tashi ta nufi k'ofar bathroom ta buɗe nan take taji mashahurin faɗuwar gaba kafafuwanta suka k'asa daukarta, jiri ya kwasheta tai sauri dafa bango wani irin abu take ji mai nauyi ya tokare mata zuciya, kasa maida kanta d'akinta tayi a wahale ta hau gadonshi ta kwanta ta lumshe idanuwanta tare da dafe k'irjinta. Bata k'ara shiga tashin hankali ba saida taga karfe uku dare ta buga Azaad bai dawo ba. Wasa-wasa har asuba Salima bata ga Azaad ya dawo ba. Hankalinta ya k'ara tashi fiye da farko. Saboda tasan ba halinsa bane kwana waje muddin yana gari. Barci sosai suka yi Azaad na farin ciki Miyya Kuma na wahala da rashin sabo koda Azaad ya falka har karfe bakwai ta gota, ya manta rabon da ya yi missing sallar asuba. Idanuwanshi ya sauke akan kyakkyawar fuskarta tausayi da sabuwar k'aunarta suka dinga huda sassan jikinshi, a hankali ya sauke kanta bisa pillow da sauri ya shiga wanka ya fito d'aure da towel ya buɗe k'ofa ya nufi d'akinshi yasa white jallabiya ya yi sallah. Duk abin da yake akan idon Miyya basan cewa tun lokaci da ya janye jikinshi daga nata ba ta falka, tsananin kunyar da take ji ne ya hanata nunawa. Tana gani ya fice ta tattaro bedsheet ta suturta jikinta dashi ta shiga k'ok'arin saukowa daga gado, jin tayi tamkar an d'aure mata kugunta da kafafuwanta da igiya, duk lokaci da tai yunk'uri tashi ta ji ta kasa, kuma ko kaɗan bata so ya dawo ya tararda ita a haka ta dafa bango cikin tsananin azaba ta tashi tana bin bango saura kaɗan ta isa ga k'ofar bathroom, taga an turo k'ofa cikin sauri ta waiga bayanta ta haɗa idanu dashi. "Subhanalillah......! Ya faɗa cikin sarkewar harshe cikin sauri ya iso wurinta kafin ya k'araso ta sulele k'asa ta sunne kanta cikin bedsheet ɗin jikinta. Yana zuwa d'auketa yasa k'afarshi ya tura k'ofar bathroom. "Dan Allah Daddy ka sauke ni zan iya tafiya da kafafuwana" Murmushi kawai ya yi, ya zaunar da ita akan toilet seat ya haɗa ruwa masu zafi cikin bathtub, sai magiya take mishi ya fita za ta iya da kanta banza ya yi mata sosai ya gaggasa mata jikinta, ita kanta ta ji dad'in hakan ya fita ya barta ta tsalkakke jikinta, kanta a k'asa ta fito Azaad ya ɗago daga dambe da yake da bedsheet, da sauri ya aje pillowcase ya nufo ta, ya kamata gefen gado ya zaunar da ita ya mik'a mata ash colour abaya cike da kunya ta kar6a daga zaune da take ta zura rigar tasa hijab ya shinfid'a mata praymat, tana sujadda ya fita. Koda ya dawo dauke da mug ɗin tea ta gama sallah har ta koma bisa gado ta kunduddune kanta, kunyarshi take ji matuk'a shi kuma yak'i ya fahimta. Bata ta6a tsanmani irin wannan abun zai shiga tsakaninsu ba. Kusa da kanta ya zauna cikin taushin murya ya ce. "Prettyn Daddy tashi kisha tea yanzu nan zan kira doctor ta duba min ke Allah yasa ban ji miki ciwo ba?" Sunan doctor da ya anbata yasa tai sauri janye hijabin da ta rufe fuskarta dashi, cikin kad'uwa take kallonshi, kafin ta fara hawaye cikin k'aramin sauti ta ce. "Daddy please karka kira doctor za ka tona mana asiri ne. Murmushi mai sauti ya yi ya matso ta jikinshi kana ya ɗago ha6arta, tai sauri runtse idanuwanta ya sumbace cheeks ɗinta. "Lallai Prettyn Daddy kurciya ta miki yawa in bada haka miye abin tono asiri sai kace wanda suka aikata zina, ko kin manta ke ɗin mallakina ce halak-malak sai da na biya sadaki kafin Baffanki ya daura mana aure. "Duk da haka Daddy banaso ka kira doctor in-sha-Allah zan warke in ka kafe lallai sai ka kirata wallahi zan yi ta yi maka kuka" Ta k'arasa magana cikin shagwa6a6iyar murya, dariya ya yi tare da jan karan hancinta. "To shikenan ba zan kiranta ɗin ba amma tashi ki sha tea, na ba ki pain killer ki sha sai ki yi barcinki kin ji my pretty?" Kar6a mug ɗin tayi daga hannunshi ta shanye tass dama yunwa take ji kamar an yashe mata hanjin cikinta, pain killer ya bata tasha kana ya kwanta tare da ɗora ta a k'irjinshi ya rungumeta tamkar zai mayarda ita ciki a haka barci mai dad'in gaske ya d'auke su. Har gari waye Salima ba ta ga Azaad ya dawo ba ta kira wayoyinshi duka a rufe nan take hankalinta ya k'ara tashi, ba dai saboda ita Azaad ya bar gida ba. Hankalinta ya kasa kwaciya ta kira direbanta ya bata number direbanshi Mr Richard ta kira shi da ya d'auka ya sharara mata k'arya da cewa Azaad yana meeting jiya kuma a gida ya kwana saidai ya kai dare sosai kafin dawo da zarar ya fito daga meeting zai faɗa mishi ta kira. Tun jiya da Ahmadu ya ga Miyya a hospital ya kasa samun natsuwa da kwaciyar hankali da ya rufe idanuwanshi ita yake gani tsaye sanye da dogon hijabi tana kallonshi da idanuwanta masu kama dana magge, yau kuma mafalkin ya yi ta rutsa shi da shar6e6iyar wuk'a da tana zuwa ta yanke shi a datse hannunshi na dama, ta kuma kashe mishi gargadi da muryarta mai matuk'ar ban tsoro muddin bai daina bin Azaad ɗinta da sharri ba sai ta kashe shi. Cikin ihu da kururuwa ya falka daga mugun mafalki da yake yi abin mamaki sai ya ga jini yana zuba daga hannunshi shatata...kamar an buɗe famfo, da gudu ya banke k'ofar d'akinshi ya fito yana ta kurma ihu matanshi da yaranshi suka yi dafifi su na kallon ikon sai ya kai harabar gida ya sake dawowa cikin gida da gudu, haka ya dinga yi kamar zautatce da taimakon maigadi da makwacinsa suka kama shi a ka saka shi mota zuwa asibiti. Azaad da Miyya barcinsu suka sha sosai sai misali sha biyu da rabi Miyya ce ta fara falkawa saida ta k'arewa kamilalliyar fuskarshi kallo, sannu hankali ta cire jikinta daga nashi, sannan ta sauko daga gado tayi mik'a tare da salati cikin zuciyarta. Cikin dingishi ta shiga bathroom, ta haɗa ruwan zafi kamar yadda ta ga Daddy d'azu da safe ya haɗa mata saida ta gaggasa jikinta sosai kafin tayi wanka da liquid soap mai k'amshin strawberry. Koda ta fito bata ga Azaad ba dama akan idonshi ta falka. A natse ta shirya kanta cikin d'aya daga cikin gowns ɗin jiya ta sauka mata iya cinyoyi. Ta tattare gashinta da ke da sauran dashin ruwa ta d'aure da hairband. Tana fesa turare ya shigo d'akin da sallamarshi, ta juyo cike da kunya ta zuba masa idanu a ranta take raya yanzu shikenan ita dashi sun zama abu d'aya?" Tai saurin kawar da tunaninta ta hanyar cewa. "Ina kwana Daddy?" Ta faɗa tare da d'an runsuna, ya matsa jikinta ya rungumeta ya ɗora kanshi a kafad'arta, fuskarshi cike da annuri ya ce. "Lafiya qalau my pretty ya jikinki hope babu inda yake miki ciwo?" Cikin sanyi murya ta bashi amsa ta hanyar faɗin. "Al-hamdu-lillah! Akwai zafi saidai ba kamar d'azu da safe ba. Shima zuwa anjima in nasake shiga ruwan zafi zai daina gaba ɗaya. Murmushi ya yi yana shafar kumatunta ya yabawa jarumtar ta matuk'a, bai ta6a tsanmani za ta iya d'auke shi ba, ya zaci duk ranar da ya kusanceta sai ya danganta ta da asibiti sai gashi ta tashi garau, har tana tafiya da kafafuwanta. Sai yanzu ya fahimci abin ba daga shekaru bane. "Daddynki bai kyauta ba my pretty duk ya bi ya wahalar min da ke, yanzu faɗa min me kike so ki ci na kira waya akawo miki?" "Duk abin da Daddyna yake so" Tayi magana tana sanda kanta k'asa d'an siriri hannun rigarta ya ja yana murmushi jin kanshi yake tamkar bashi bane kamar an sauya shi daga Azaad Junaid ɗin da yasani a baya. Yana rungumeta da ita suka fito zuwa parlornshi, ya zauna tare da zaunar da ita a gefenshi hannuwanta ya dank'e cikin nashi with serious face ya ce. "Ba zan 6oye miki ba Aslamiyya ina jin soyayyarki wata kyauta ce ta musanmman agareni, da ban ta6a samun kwata-kwacin ta ba a rayuwarta. Da farko na zaci aurena da ke ba mai ɗorewa bane, bansan ya aka yi ba na waye gari dumu-dumu a soyayyarki, har ji nake tamkar akanki na fara sani kalmar so. Farin ciki baya ɗorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, saboda haka ki sa aranki a kowane hali na tsincin kaina ba zan ta6a mantawa dake ba. Aslamiyya kin zama jini jikina, bugun zuciyata na kan raba dare ina rok'on Allah ya haɗa ni da mace tagari wacce za ta goge min bakin ciki da na share shekaru a ciki sai gashi Allah ya kar6i addu'ata ya bani ke. A yanzu babban burina a duniya shine kasancewa tare da ke har abada wannan kaɗai ya isheni rayuwa. Har ya dasa aya a zancesa bata d'auke idanuwanta daga kanshi ba, maganganunshi sun ratsa jinin jikinta su bi bargo da jijiyoyin magudanar jininta, ta kuma yi musu muhalli na musanmman ta adana su cikin zuciyarta. Bata ta6a tsanmani za ta sami dadd'ad'an kalaman soyayya irin wannan daga bakinsa ba. Musanmman da tayi duba da yana yin shekarunsa a tunaninta ya riga da ya gama mallakawa Madam Salima su ashe da akwai raguwar su ba duka ya bata ba ya rage mata saura. Kunyarshi take ji sosai ba za ta iya mayar mishi da martani kalamanshi ba amma tayi alk'awali duk lokaci da kunyar ta rage za ta bashi mamaki, sai kawai ta matsa tasake haɗe tazarar dake tsakaninsu ta ɗora kanta a kafad'arshi ta lumshe idanuwanta, hannu yasa dinga shafa sumar kanta, yana da tabbaci kunyarshi da take ji ne ya hanata magana shiyasa ko kaɗan shirunta bai dame shi ba. Throughout bai fita ko nan da k'ofar gida ba yana manne da ita wayoyinshi duka rufe su ya yi sai in yana buk'atar wani abu ya buɗe ya kira Mr Richard. Aneesah ta fito daga studies room, kallo d'aya za ka yi mata ka gano damuwar da take ciki. Kaitsaye kitchen ta wuce Nanny Lacey ta tarar tana zuzuba abincin dinner cikin warmers, wannan shine karo na uku kenan da ta tambaye ta Miyya. "Sannu da aiki Nanny?" Aneesah ta faɗa lokaci da ta shiga kitchen ɗin ta jingina bayanta a kitchen cabinet. "Yauwa princess barka da fitowa. "Nanny har yanzu babu wani labari akan Pretty wallahi hankalina yak'i kwanciya, ina fargaba idan ba rashin lafiyarta ne ya yi tsanani ba?" Gashi yau mommy tana gida bata fita ba balle na saci jiki direba ya kaini hospital na duba ta. Kuma duk lokaci da na kira wayar Daddy a kashe take balle naji ko yana da labarinta. "Ki kwantar da hankalinki princess ki ci gaba da yi mata addu'a mu jira zuwa gobe idan muka ga bata dawo ba, nai miki alk'awali zan je da kaina na dubata. "Tam.... shikenan Nanny bari naje nayi sallah. Ta faɗa tare da ficewa daga kitchen ɗin. Nanny Lacey ta bi ta da kallon tausayi, tana fargaba zuwan ranar da Aneesah za ta san cewa Miyya matar Daddynta ce. Cikin kwanaki biyu kacal Azaad da Miyya sun yi shak'uwa ta daban mamaki, tun tana d'ari-d'ari dashi har ta dawo ta saki jikinta kunyarshi ma da take ji yanzu ta ragu hatta da wanka tare suke yi Azaad ya yi mata sabo da abubuwa masu yawa a cikin sauk'i ba za ta iya rayuwa babu su ba. Ta fito cikin shirin tafiya gida don tun safe take mishi magiyar ya maida ta gida, gashi gobe monday akwai school, ga Kuma Aneesah da Airah da ta ke da yak'ini suna cikin damuwar rashin ganinta. Daddy sai ja mata rai yake yi shiyasa yanzu ta fito cikin shirinta ko ya kaita ko ta kai kanta..... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 32.... Kallo daya za ka yi ma madam Salima ka fahimci irin damuwar da take ciki ta zabge tayi muguwar rama, ko office ta daina zuwa kullum tana k'unshe a d'aki. kusan two days kenan rabon da tasa Azaad a idanuwanta in ta kira wayarshi a kashe ko kuma yak'i ɗaga kiranta. Ga baki ɗaya al'amuranta sai k'ara dagulewa suke yi, ta rasa tudun dafawa. Tana tsoro ta fita cikin mutane kada su fahimci tana cikin damuwa Bata Kuma tanadi irin amsar da za ta bayar ba idan aka tambaye dalilin ramarta shiyasa ko mahaifiyarta bata gayawa aurenta ya mutu ba. Duk duniya Hafsat shinkafi kaɗai ta faɗawa. *** ***** ***** Karar buɗe k'ofa yasa Azaad ya ɗago ya ga Miyya ce ta shigo sanye da dogon hijabinta har yana ja a k'asa, yai sauri ciro wayar da ke manne da kunnenshi, ya saki mata k'ayatatcen murmushi irin mai shiga jiki ita ma ta mayar mishi da martani murmushin nashi hannunshi ya mik'a mata ta mak'e kafad'a alamar ba za ta zo ba. Ya nuna kanshi ta gyad'a kai ya waro idanuwanshi alamar mamaki. "Wa ya ta6a min prettyna? "Kaine! Ta faɗa cikin shagwa6a6iyar murya tana cuno baki. "Lallai Daddy bai kyau ta ba zo naji laifin da nayi" Cikin shagwa6a6iyar murya tamkar za ta rushe da kuka take faɗin "Daddy please ka tashi ka maida ni gida haka nan in Kuma ba ka gaji da zaman gidanan bane ka faɗawa Mr Richard ya maida ni. Ajiyar zuciya ya sauke saboda yasan yana da aiki ba kaɗan ba. Ya sake mik'a mata hannunshi a karo na biyu bata yi gardama ba ta kama hannun nashi, fizgota da k'arfi ya yi ta faɗa jikinshi ya shiga k'ok'arin rabata da hijabin jikinta da sauri ta rik'e hijab ɗin. "Please Daddy ka barmin hijabina mana. Da sauri ya ɗago ha6arta yana kallon cikin idanuwanta yai wani had'e rai, ta kauda fuskarta tana gun-guni k'asa-kasa. Yadda take magana sam ba ya ji abin da take faɗa bakinta kawai ke musu-musu, lips ɗinta ya kama da yatsunshi biyu. "Ouchh....Daddy da zafi karka cire min le66e mana. Ta yi magana tana k'ok'arin ciro yatsunshi daga le66enta. Murmushi ya yi tare da fincike hijab ɗin ya jefar ya kwantarda kanshi a shoulder ɗinta, hancinshi ya tura ta gefen wuyanta yana shak'ar fitinanen k'amshinta sai faman tu-ture take yi tana kukan shagwa6a kuka da babu hawaye. Hak'oranshi yasa akan spaghetti hand ɗin gown jikinta ya saukar dashi zuwa hannunta, sai ruwan kisses yake mata a jiki. Da k'arfi ta fincike kanta ta mik'e tsaye jikinta sai rawa yake yi bata manta bak'ar azabar da tasha two days ago ba. Muryarta yana rawa ta ce. "Ni fa Daddy nagaji da wannan masifar ka tashi ka maida ni gida. Ya ɗago idanuwashi da suka fara canza launi ya tsare ta dasu gabanta yai mummunan faɗuwa, wani irin tsoronshi ta ji yana shigarta, kalamanta sun yi matuk'ar ta6a shi wato shine masifa shi za ta danganta da masifa kalmar tai mishi tsauri ta kuma 6ata mishi rai, sai kuma yai sauri danne zuciyarshi tunawa da yai da karancin shekarunta dole akwai wauta a tattare da ita watakila bata faɗa don ta 6ata mishi rai ba. Mik'a hannunshi ya yi cikin zafin nama ya jawota ta faɗa jikinshi yai mugun matseta, sai da tasa k'ara ya hade bakinshi da nata wani irin hot romance yake bata tamkar yau ne ranar farkonshi, Miyya ido ya rena fata sai migiya take mishi ya kyaleta, Azaad kan bidirinsa kawai yake yi bai masan tana yi ba, tana jin lokaci da kwatarda ita ya yi mata rumfa ta kasa daurewa sai ta fara kuka cikin sautin mai k'arfi bai saurara mata ko kaɗan ba sai da ya sami natsuwa, ya rungumeta a jikinshi sai faman sauke ajiyar zuciya take, a k'asan zuciyarta kuma sai Allah ya isa take mishi. Haka kawai zai dinga nanikarta ko gajiya ba ya yi ita kan ta gaji gara tun wuri tayi ta kanta kada ya k'arar mata da ruwan jiki. Kamar yasan abin da take faɗa akanshi ya juyo da ita yana kallon fuskarta da idanuwanta da sun ka kumbura murmushi ya yi yana shafar lips ɗinta. "Wa ya ta6a min prettyna naga idanuwanta da fuskarta sun kumbure?" Buge mishi hannu tayi tasake fashewa da kuka, cikin muryar kuka take faɗin. "Wallahi Daddy kai mugu ne daga yau ba zan k'ara kula ka ba. "Haba prettyna yi hak'uri ba zan k'ara ba har sai kin nema da kanki" Ture shi tai ta d'auki rigarta za ta saka ya fizge rigar ya yar ya jawota ya sake rungumeta, cikin kunneta ya rad'a mata I am terribly sorry for all the things I’ve done, please forgive me my pretty. "Ko a wacan karo haka ka dinga faɗa ba za ka sake ba sai gashi ka sake yi, ba zan sake amincewa da kalaman bakinka ba. Sosai furuncinta ya haifar mishi da nishadi, yasa dariya mai ban sha'awa ita kuma ta fashe da kuka ya cire ta daga jikinshi ya sauka daga gado yana k'ok'arin d'aukarta. "Lemme take my pretty to the bathroom. Ya faɗa yana dariya, buge mishi hannu tayi cikin kukanta mai cike da zallar sangarta ta ce. "Leave me alone I don't want your help. Ya sunkuceta ya nufi bathroom da ita sai faman wuntsila kafafuwa take yi, sai cikin bathtub ya sauke ta har ya gama wankanshi ya fita idanuwanta suna a rufe wai ita a dole kunyarshi take ji. A natse tayi wankanta muddin yana bathroom ɗin ba za barta tasami irin wannan natsuwar ba ya dinga jagwalgwalata kenan. Ta fito d'aure da towel a k'irji hannunta rik'e da wani k'aramin towel tana goge jik'ak'k'iyar sumarta, ta bi ta gabanshi za ta wuce cikin sauri ya rik'o waist ɗinta ya dawo da ita gaban mirror da k'afarshi ya jawo stool ya zaunar da ita, ya kar6i towel ɗin hannunta ya shiga goge mata sumarta, sai faman kumbura fuska take yi tana turo baki gaba, shi Kuma sai zabga murmushi yake yi komai nata burgeshi yake, wannan tura baki da take yi ba k'aramin k'ara mishi kyau take yi ba. Ji yake kamar ya hadiye ta. Hannunshi ta rik'e cikin marairaice murya take magana. "Daddy Dan Allah maida ni wurin su Aneesah ni dai wallahi na fi so can. "Uhm... Pretty da ke mayya ce in kika dank'e kuruwar mutum da wuya ki saki, kin cika naci wallahi. "Koma me za ka faɗa Daddy ba zai dameni ba idan har za ka barni na tafi ka kirani da abin da yafi mayya. "Gara tun wuri ki soma shirya mana irin rayuwar da za mu yi anan gidan don kin zo kenan, ke da wancan gidan sai dai ziyara. A mugun tsorace ta juyo ta kalleshi don gani take yi ta cikin mirror ba zai gansar da ita ba, ta zazaro idanuwanta cikin kad'uwa ta ce. "Me kake nufi Daddy kayi min bayani gwari-gwari ta yadda zan fahimta?" "Ina nufi nan shine gidan da na za6a mana da za mu yi rayuwa ni da ke a ciki, Ina da tarin gidaje da yawa a Nigeria har ma da wajenta idan wannan bai miki ba ki faɗa min na sauya miki wani. Saboda ba zan so wani abun cutarwa ya ra6e ki ba farin cikinki da kwanciyar hankalinki nakeso shiyasa na ware miki naki gida daban. Ranta yai mugun 6aci har wani dishi-dishi take gani me Daddy yake nufi shikenan ya raba tsakaninta da yaranshi duk shak'uwar da suka yi ta tafi kenan ta ya za ta fara tunani rayuwa ita kaɗai a wannan k'aton gida?" Ba wani farin cikinta da yake so ya yi ne kawai don biyan buk'atar kanshi. A fusace ta ce "Haba....Daddy....Haba...Dan Allah wannan ai son kai ne da tun farko nasan wannan ne kudurinka da ban amince na biyo ka ba. Tun farkon zuwana gidanka ya kamata ka gabatar da ni a matsayin matarka ba 'yar aiki ba sai yanzu da rana tsaka za ka bijiro da wannan zance da hankali ba zai dauka ba. Tsananin mamakinta ya hanawa Azaad furta uffan sai kallonta yake, ba ko kiftawa gani ya yi shiru yana kallonta yasa ta bangaje shi ta wuce tana faɗin. "Bani hanya na wuce yanzu-yanzu nan zan bar gidanan ba sai anjima ba, da tun farko ina da masaniya akan manufarka da ban tsaya 6atawa kaina lokaci ba da tuni ka nemi ni ka rasa ko an gayamaka bansan hanya bane. Bari ka ji Daddy dole tarayyarmu ta ci gaba da kasancewa a 6oye banaso yarda da aminci da ke tsakanina da Aneesah su sami rauni. Da sauri ya rik'o hannunta ya jawota da k'arfi saura Kiriss towel ɗin jikinta ya cire tai sauri dafewa, kallon cikin idanuwanta yake yi so yake ya gasganta wai ita ɗin ce ko musanya aka yi mishi, gani yadda yake kallonta yasa ta sadda kanta k'asa, ya ɗago ha6arta tai saurin kauda fuska. "Aslamiyya ni za ki nunawa 'yar da na haifa ta fini muhimmanci a wurinki, ashe kin fi k'aunar Aneesah akaina?" Ya faɗa cikin taushin murya. A razane ta dawo da ganinta akan fuskarshi ba komai bane yasata razana face sunanta da ya kira tsawon zamansu bai ta6a kiranta da sunanta ba, har ayyanawa take yi baisan sunanta na yanka ba. "Kin kyauta Aslamiyya ba laifinki bane laifina ne da na nuna k'arara na mutu akanki, kuskuren nawa ne da na k'asa danne masiffafiyar soyayya da nake miki. je ki shirya Mr Richard zai kai ki duk inda kike so ba wurin Aneesah ba in kin iya ki tafi bango duniya da izzini ubangiji saboda da ke ba zan daina numfashi ba. Yana k'arasa magana ya sake ta ya nufi dressing room, sosai maganganun shi suka ratsa ta ita fa ba nufinta Aneey ta fishi bane asalima k'aunar da take mishi ne ta shafi yaranshi, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi abin ka da mai raguwar zuciya sai kawai tasa kuka tana tsaye ya fito sanye da shadda blue colour kanshi sanye da hular tangaran, bi ta gefenta ya yi ya wuce saida ya buɗe k'ofa sannan ya tsaya ya ce. "Lallai yarinyar nan dad'i yai miki yawa ni ne ya dace nai kuka ba ke ba. Amma bari na wakilce ki tun da kin fasa zuwa gun Aneesah ɗin ni bari naje na faɗa mata a yanzu matsayinki ya haura daga k'awarta kin koma second mom ɗinta. Kafin tai magana ya maida k'ofa ya rufe, komawa tayi gefen gado ta zauna ta ci gaba da rera kukanta. Azaad yana jin kukanta har cikin zuciyarshi ya yi mata haka ne, dalilin yadda ta nuna tafi gudun zuciya yaranshi akanshi, duk da yasan ta faɗi gaskiya maganarta dutse ce ba abar yarwa bace. Shi kanshi yana fargaba ta yadda zai gabatarwa da yaranshi ita. Da wannan tunani ya fito compound Mr Richard ya jawo mota ya buɗe mishi ya shiga, ɗayan gidanshi suka nufa gara ya je ayi ta ta k'are so yake ya zauna da yaranshi ya faɗa musu matsayin Aslamiyya, gara su ji a bakinshi da su ji a bakin wani. Ya fahimce Aslamiyya tana so ta haddasa mishi bugawar zuciya yadda yake ji soyayyarta ba zai iya 6oyeta ba a gaban ko ma waye, saboda haka gara a d'auko ta daga tushe Har suka iso gidan bai sani ba saboda ya yi nisa a tunani k'arar buɗe mishi k'ofa da Mr Richard ya yi ne ya ankarar dashi. Cikin tafiyarshi ta k'asaita ya nufi cikin gida, ya murda handle ɗin k'ofar main parlor ya ji ta a rufe knocking ya shiga yi Nanny Lacey da ke kitchen ta amsa da "Yes I'm coming" Tana buɗe k'ofa tayi arba dashi ta runsuna tare da gaidashi ya amsa, cikin sanyi murya saida ya fara haura matattak'alar bene sannan ya juyo ya ce ta sanarda da Aneesah da Airah yana nemansu. Akan idanuwa madam Salima Mr Richard ya shigo tana tsaye a balcony, har Azaad ya shigo main parlor tana kallonshi cikin sauri ta koma bedroom ɗinta ta sauya kayan jikinta, zuwa gown na atamfar super exclusive ta shafawa fuskarta powder ta zizirawa idanuwanta kwali bata shafa jan baki ba gudun wulak'anci Azaad sai kawai ta d'an shafawa lips ɗinta man le66e, turare kusan k'ala biyar ta fesa jikinta na fitar da mahaukaci k'amshi cikin takonta na tak'ama wanda ya zame mata jinin jiki ta tura k'ofar falonshi, idanuwanta suka sauka akan kyakkyawar fuskarshi yana zaune ya ɗora kafafuwanshi akan center table ya ture hular kanshi baya hannunshi rik'e da remote ɗin decoder yana canza channels cikin. Wani irin faruwar gaba taji ta rasa dalilin da yasa yanzu har tsoron haɗuwa da shi take yi ta kai morethan 3 minutes a tsaye ita bata shiga ba bata kuma koma inda ta fito ba. Dogon numfashi ta ja kafin tattaro dukkan courage ɗinta, ta soma tattaki izuwa cikin falon tun farko shigowarta ya ganta sai faman shak'ar k'amshinta yake sallama tayi cikin taushin murya ya amsa mata a dakile. "Sannu da zuwa" Ta faɗa tare da sadda kanta k'asa bai amsa ba sai ma k'ara d'aure fuska da ya yi, shiru ya biyo baya ita bata sake yi magana ba shi kuma sai faman canza channels yake yi, can ta danne tsoro da fargabarta ta ce....... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 34... *Assalamu Alaikum* Sako na musanmman zuwa ga makaranta wannan littafi Ina mai ba ku hak'uri a dalilin yankewar labarin ya faru ne bisa ga dauke min waya da aka yi in-sh-allah za ku dinga gani update saidai ba kullum ba. A dalili har yanzu ban mallake waya tawa ta kaina ba. Ku k'ara hak'uri in-sh-allah saura kad'an na kammala, da fatan za ku kar6i uzirina da hannuwa bibbiyu. Garin farfasa gilasai da madam Salima ke ta faman yi babu kakkautawa ya yanke ta a hannu jini ya soma zuba duk da ta ji zafin yankar hakan bai sa ta dakata da tu'anati da take yi ba. Sai ma k'ara mata kaimi da ya yi yanda Aneesah ta ga jininta yana zuba yasa ta tsorata da gudu ta iso wurinta ta rungumeta ta baya tasa kuka mai ta6a zuciya cikin muryar kuka take fad'in. "Haba mommy miyasa kike so ki illata kanki akan abin da kika ri ga da kinsan kin rashi shi?" Bata jira jin ta bakinta ba ta ci gaba da fad'ar. "Wannan abin da kike aikatawa ba shi zai sa Daddy ya dawo gareki ba, ba kuma zai gyara abin da kika 6ata ba sai ma ya ta6a lafiyarki. Da karfi Salima ta finciko Aneesah ta dawo da ita gabanta ta dire ta, tsabar masifar da ke cinta idanuwanta sun kad'a sun yi jajir, cikin hargowa ta ce. "Princess idan har Daddynku ba zai dawo gareni ba, to kuwa ba zai ta6a zama mallaki ko wace 'ya mace ba a duniya. idan har hakan yana nufin na rasa shi kenan, nima ba zan barshi shi da wannan k'aramar yarinya sun yi numfashi mai dad'i ba. "Mommy please ki dawo hayyacinki ki dai-daita harshenki, ba girmanki bane fad'ar iri-iri wad'annan maganganu ba. Aneesah ta k'arasa magana tare da sake rushewa da kuka, don gani take yi tamkar mommy ta zare ne. Sakamakon yanda take ta fad'ar maganganu marasa dad'i da ma'ana, duk abin da ya zo bakinta fad'a take yi kamar dai wata zararriya. Suna cikin wannan badak'ala sai ga Hafsat shinkafi ta shigo hankalinta a tashe direban madam Salima ne ya kira ta ya fesa mata wannan labari shine bata yi k'asa da gwiwa ba ta garzayo, da shigowarta idanuwanta suka sauka gane mata yadda Salima ta hargitsa falonta, ta fidda shi cikin hayyacinsa, ba k'aramar 6arna ta yi ba ta farfasa abubuwa masu matuk'ar daraja da tsada. Ran Hafsat ya 6aci sosai saboda a ganinta ko Aneesah da take 'yar Salima ba za ta yi wannan haukar ba balle madam Salima da ta gama mallakar hankalin kanta. Wannan ai abin kunya ne da zubar da daraja da k'ima. Da kyar ta iya kamata suka shiga da ita d'akinta, ta zaunar da ita a gefen gado sai faman sauke wahallale numfashi take yi, Hafsat ta kai dubanta wurin Aneesah da ke tsaye a jikinta k'ofa tana faman goge hawaye da bayan hannunta, sosai tausayin yarinyar ya kamata cikin taushi murya ta ce. "Aneesah ba mu wuri zan yi magana da Mommynki. Ta juya batare da tayi magana ba. *** ** ***** Shiru ya yi tare da lumsashe idanuwanshi, yana sauke mata numfashinsa mai d'an zafi-zafi a gefen wuyanta, jin shiru nashi yana neman ya yi yawa yasa ta shafo kwatatcen sajenshi cikin siriryar murya mai taushin gaske ta kira sunanshi. "Daddy!" "Uhm! Ya amsa mata batare da ya bud'e idanuwanshi ba. "Dan Allah ka yi hak'uri ka yafewa mommy nasani ita d'in mai girman laifi ce agareka, amma duk da haka ba zan kasa furta maka kayi hak'uri ka dawo da aurenku..... "Ya isa pretty! Ya katse ta cikin kakkausar murya alamar da ke nuna maganarta ta fara 6ata mishi rai, duk magana da za a yi da ta shafi Salima komai k'ank'antar harzuk'a shi take yi, ranshi a 6ace ya cireta daga jikinshi kana ya mik'e tsaye fuskarshi a had'e babu annuri ko kad'an ya sauke mata fusatattun idanuwanshi, ai kuwa ba k'aramin kad'awa hanjin cikinta ya yi ba. "Pretty ba ki san wacece Salima bane shiyasa kike k'ok'arin dawo da ita cikin rayuwarmu. Salima mace ce mai mugun zafin kishi duk da batasan ta yadda ake kulawa da tattalin miji ba amma tana tsananin kishina ko kad'an bataso ta ga mace koda 'yar uwa ta jini ce ta ra6eni matuk'ar kika kafe sai na dawo da ita to ki sani ke ce za ki wahala domin ba za ta, ta6a barinki ki zauna gidanan lafiya ba. Aslamiyya ki rufe babin Salima kamar yadda na rufe hakan ne kadai rayuwarmu za ta inganta ni da ke. Yana k'arashe magana ya shige bathroom ya barta tsaye, rungume da hannuwa a k'irji tana so Daddy bata tunani nan kusa da akwai abin da zai iya raba tsakaninsu, kana tana jin tausayin yaranshi har k'asan zuciyarta saboda tasan illa da ke tattare da rashin iyayye duk da tana da tabbaci, da wuya yaran Azaad su fuskanci irin rayuwar da tayi ita da siblings d'inta. Za ta ci gaba da lurarda Daddy hadi da rarrashinshi har sai ya amince ya dawo da mommy ko don albarcin su Aneesah da take ji k'aunarsu sosai a cikin zuciyarta. Saukar ruwa taji a fuskarta ta zabura a firgice Daddy ta gani tsaye a gabanta har ya yi wanka ya fito yana daure da brown towel, raguwar ruwan wanka da ke hannunshi ne ya yarfa mata a fuska. Shagwa6e fuska tayi tana turo baki hannunshi yasa kama hannunta ya ja ta zuwa ga dressing mirror ya mik'a mata k'aramin towel din da ke hannunshi. "Da wannan tunani da kike da ma taimakawa mijinki kika yi ya shirya, kin tsaya kina tunani abin da bai shafe ki ba. "Haka ma za ka ce Daddy yanzu abin da ya shafe ka bai shafe ni ba ko?" Ta k'arasa magana tare da kar6a towel din ya ja stool ya zauna ta cikin mirror yake kallon kyakkyawar fuskarta, saida ya saki mata murmushi kafin ya ce. "Ina sonki prettyn Daddy ke ce cikon farin cikina idan babu ke bansan ya rayuwata za ta kasance ba. Ta k'ara matsawa ta tsaya bayanshi tare da dora towel din hannunta a shoulder shi, tana murmushi har farare hak'oranta suka baiyana. "Daddy sarkin wayau wato so kake yi ka shashantar da tambayar da nai maka, ta hanyar bani wannan amsar ko?" "A'a kawai dai inaso ki kore duk wani abu da zai yi yunk'uri kawo mana cikass a yayin zamanmu, musanmman akan abin da ya shafi Salima. Shiru tayi tana kallonshi ta cikin mirror kafin ta girgiza kai ta shiga goge mishi jikinshi, ta ajiye towel din ta dauki robar lotion ta matsa a tafin hannunta, sannu a hankalin ta ke bin sassan jikinshi tana shafawa yayin da gogan naku ya lumshe idanuwa yana sauke numfashi akai-akai. Tuni ta fahimci yana yinsa yana sauyawa a duk lokaci da tafin hannunta ya sauka a fatar jikinshi, k'afadarshi ta d'an buga tana dariya ta ce. "Kai Daddy daga shafa mai ka fara gyagyadi a zaune idan barci ka ke ji ka tashi ka je ka kwanta mana, ni kan kar ka yi min barci anan. Murmushi ya yi tare da kar6a robar lotion ya ajiye ya jawo ta ta zauna akan cinyoyinshi, ya rungumeta gam har saida tayi 'yar k'ara. Cikin shagwa66iyar murya ta ce. "Daddy wannan rungumar fa kada ka fasa min ciki mana?" Kuncinta ya sumbata tare da kashe mata idonshi d'aya. "Ba zan fasa ba my pretty ni da nakeso nan da nine months ki haifa min kyakkyawar baby girl mai kama da ke. "Cab....gaskiya haihuwa ba yanzu ba Daddy sai na k'ara girma. Tayi magana tana murguda baki, hakan da tayi tai masifar bashi dariya sosai ya ci dariya kafin ya mik'e dauke da ita ya nufi dressing room. "Mu je ki saka min tufafina ta hakan ne girmanki zai k'aru, ki haifawa baby Ahlam k'anwa da wuri. "Daddy please ka sauke ni sai faman koya min rashin kunya kala-kala kake yi, na fahimci idan ban yi da gaske ba zan nemi kunyata na rasa. Kowane furuci da ke fitowa daga bakinta nishadi yake haifar mishi, shiyasa yake ta faman kwasar dariya duk yadda take mishi magiya ya sauke ta yak'i sai da ya shigar da ita dressing room d'inshi ya direta ya yi kamar zai cire towel din jikinshi, da sauri ta runtse idanuwanta. Yana dariya ya matsa daff da ita ya kai bakinshi akan karan hancinta yasa hak'oranshi ya cije ta kad'an, babu shiri ta bude idanuwanta tana ihu tare da yarfe hannuwa ita a dole ta ji zafin cizon. Shi kuma sai faman yi mata dariya yake yi ya nufi katuwar closet ta gilashi wacce ta cinye daga farkon bango d'akin zuwa karshensa cike tafff da tarin suturunsa kala daban-dabam gasu nan birjik ya zuge gefen da jallabiya's d'inshi suke ya ciro coffee colour ya saka, har ya kammala shiryawa Miyya tana tsalle-tsallenta dafe da hanci hannunta ya cire daga kan hancinta nata, ya kalli dai-dai gun da ya ciza ya ga shatin hak'oranshi a hankalin ya matsota jikinshi ya dora harshensa gun da shatin hak'oran nashi yake sannu a hankalin ya shiga yawo da harshensa a wurin kafin ya gangaro zuwa ga bakinta, bata yi gardama ta bude mishi bakinta ya zura harshensa idanuwanta suna rufe ruff ta shiga taya shi wannan shine karo na farko da ta mayar mishi da martani sosai hakan ya k'ayatar dashi, wata irin natsuwa suka ji tana saukar musu a cikin sassan jikinsu gaba d'aya ji suke yi kamar suna wata duniya ta daban ne ba wacce tun farko suke ciki ba. Sun d'auki tsayin mintuna ahaka suna tsotsar bakin juna kafin Miyya ta d'an ture shi, kasancewar jikinshi ya mutu bashida wani k'arfi kirki ya yi baya kamar zai fad'i Allah ya taimake shi ya dafa bango, cikin zallar shauk'in so take kallonshi tana dariya, kafin ta shiga tafiya da baya-baya sai da takai ga k'ofar fita ta tsaya ta ce. "Daddy ka ji tsoron Allah ka dinga sassautawa 'yar marainiya Allah kada soyayyarka ta lalatani gaba d'aya. Tana k'arasa magana ta kwasa da gudu ta fice daga d'akin, a hankali ya k'arasa sulalewa k'asa ya zauna bai ta6a tsanmani zai ji irin manya-manyan maganganu iri wad'annan daga bakinta ba. Shi fa gaba d'aya kallon kwaila wacce bata da wayau yake mata ashe ta girmewa tunaninshi ya shiga shafa sumar kanshi yana fad'in. "Alhamdullilah....ya Allah da ka albarkace ni da wannan babbar ni'ima, Allah nagode maka da wannan sauyi da ka yi min ya ubangiji ka bani ikon rike wannan yarinya bisa ga gaskiya da amana Allah ka kare min ita bisa ga kariyarka. Koda Miyya ta dawo parlor bata tarar da Airah ba, kaitsaye d'akin da taga Nanny Lacey ta shigar musu da kayansu ta nufa. *** **** *** "Innalillahi wa'inna illaihim raji'um!....shikenan Salima kin 6ata komai garin haukar kishinki na wofi kin k'arasa lalata alak'arki da Azaad. Hafsat tai magana cike da haushi da zallar takaici ji take tamkar ta rufe madam Salima da d'an banzan duka, ga mace har mace amma kwakwalwarta kamar ta dusa. Ta rasa wacce irin kwwaya ce a cikin kokon kanta, bata iya dai-daita komai ya koma a gun muhallinsa ba kawai dai ta kware ne wurin 6atawa ba gyarwa ba. "Wallahi-azim Hafsat ba zan ta6a bari Azaad ya rayu da wata mace ba, ko ta halin yaya sai na raba tsakaninsu.... "Dallah ya isa Salima! Nace ya isa haka ke yanzu fissibilillah....ba ki ji kunyar fitar wannan maganar daga bakinki ba?" "Kunya fa kika ce Hafsat wacce kunya zan ji?" "Kunyar abin da kika aikata kunyar nunawa da kike yi a yanzu kin damu da Azaad har kina nuna kishinsa a fili alhali kece kika jawo ya tsinka igiyoyin aurenku ya kuma maye gurbinki da wata. "Ki sa aranki Hafsat idan har akan Azaad ne banida kunya ko kad'an ba ma za kisan hakan ba sai kin ga irin abubuwan da zan aikata nan ba da dad'ewa ba sannan ne za ki tabbatar da rashin kunyata. "Salima.... Salima please calm down nuna fushi a fili ko k'udurta mugun nufi ba naki bane,ki kore duk wani mugun zafin kishinki ki jinginar dashi gefe mu bi hanyar maslaha ko Allah zai sa Azaad ya ba ki dama ta biyu. Shi fa namiji da kike gani kulawa da soyayya hadi da tattali yake bukata a wurin mace matuk'ar ya sami wannan sauna yake komawa a gunta, da alama abin da kika kasa bashi na tsawon shekaru ya samu a wajen k'aramar yarinyar da kika gama renawa. Kuma da kike zance za ki raba tsakaninsu ta ina za ki fara?" Ai Salima kin riga da kin 6ata rawarki da tsalle, tun da har kika ga Azaad ya tattara yaranshi kafff ya bar miki gida hakan yana nufi ya gama dake babu saura wani abu da yai saura a tsakaninku. "Wayyo Allahna! Madam Salima ta fad'a da k'arfi tare da fashewa da wani irin kuka, Hafsat bata hana ta kuka ba ko tayi yunk'uri rarrashinta kyaleta tayi taci kuka mai yawan gaske kafin ta dawo ta rarrashinta kanta, ashe ko kuka rahama ne saboda Salima ta ji bakin cikinta ya raguwa da kashe uku cikin d'ari ta tashi ta shiga bathroom ta watsa ruwa masu sanyi ko za ta ji sanyi a zuciyarta, ta dai ji sanyi a fatar jikinta amma zuciyarta ko kad'an bata sanyayya ba. Ta nemi riga mai karanci nauyi tasa, ta dawo kusa da Hafsat shinkafi ta zauna tare da zabga dank'areren tagumi ta zurawa Hafsat kumburarrin idanuwanta. Saida Hafsat ta gyara zamanta kafin tayi k'asa da muryarta ta fara magana. "Salima a yanzu dama d'aya ta rage miki wacce nake tunani da ita kadai za ki yi amfani, watakila Azaad ya saurare ki idan Allah yasa aka dace sai ki ga ta cikin ruwan sanyi ya gyara aurenku. "Please Hafsat in za ki yi magana go straight to the point, zuciyata bata daukar noke-noke duk abin da za a yi na fiso ayi shi kaitsaye. "Aneesah ita ce damarki ta k'arshe da ta rage miki saboda haka ta cikin hikima da dabara za mu yi amfani da ita Azaad ya dawo da aurenku. *** ** **** Ahamdu ya dawo tamkar mahaukaci ba shi da aiki sai surutu yana tonawa kansu asiri, iri mugaye abubuwa da suka dinga yi wa Azaad, Hasheem kuma k'afarshi tak'i warkewa kullum ba a gani sauki sai ca6ewa take yi tana fidda ruwa masu mugun doyi, dama in za ka gina ramin mugunta ki gina shi gajere ba ka sani ba watakila kaine za ka rufta a ciki. Allah ya kare mu da son zuciya yasa mu fi k'arfin zukatan mu.{Amin} 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 35... Hafsat shinkafi bata tafi ba sai da taga ta dora Madam Salima a hanyar da take gani za ta dai-daita mata al-amurrata, duk da tasan da matuk'ar wahala Salima ta bi shawarwari da ta bata tai aiki dasu d'aya bayan d'aya. Tun daga lokaci da Aneesah ta shige d'akinta take kuka, zuciyarta ta kasa kar6a sabbabin k'addarori da suka kunnuwa rayuwar gidansu. Duk sanda ta tuna da yanzu fa iyayyenta sun rabu, sai ta ji wani irin kunci da 6acin rai babban takaicinta bai wuce auren Pretty da Daddy ya yi ba, da ta kasa jurewa fitowa tayi fuskarta tayi mata jajir saboda d'an uban kukan da taci. Kaitsaye 6angare Jadda ta nufa tana zuwa ta zube a jikinta tasa kuka, gaba d'aya ta tashin hankalin Jadda sai faman tambayarta take me yafaru, cikin shasshekar kuka take fad'i dalilin kukan nata shiru Jadda tayi tamkar batasan da labarin ba, daga bisani ta shiga yi mata nasiha cikin hikima irin ta tsofaffi ta dinga kawo mata misalai da ke haddasa mutuwar aure ta kuma kawo mata dalili kwarara da ke nuni da babu illa don Daddynsu ya auri sa'arta. Kasancewar Aneesah yarinya ce mai kaifin tunani tayi na'am da duk abin da Jadda ta fad'a mata, duk wani haushin Daddy da pretty da take ji sai ta ji ya ragu. Azaad ya fito cikin shirin shi na fita a downstairs parlour ya tararda miyya da yaranshi, wani irin farin ciki ya ji ya kama shi, zuciyarsa tayi wasai a yanzu bai da saura damuwa fuskarshi ta cika da k'ayatattcen murmushi k'amshin turarenshi da Miyya ta shak'a yasa tai saurin kallon bene ta ganshi tsaye ya yi folding hannuwanshi a k'irji yana ta faman zabga murmushi, batasan lokaci da ta mayar mishi da martani murmushin nashi ba, ta bi shaddar jikinshi da kallo ya yi matuk'ar yi mata kyau, a kullum k'ara gani take yi yana zama yaro. Mik'ewa tayi dauke da Ahlam ya k'araso kusa da ita ya kar6i Ahlam yana mata wasa kafin ya dawo da ganinshi akan fuskarta. "Zan fita! Ya furta cikin k'aramin sauti. "Allah ya tsare ya dawo mana da kai lafiya" "Amin! Mu je ki raka ni koda a bakin k'ofa ne. Murmushi tayi tare da bin bayanshi. Airah ta d'ago daga game din da take yi a wayar Nanny Lacey, ta kalle shi tana murmushi tare da furta. "Daddy Allah ya Tsare ya kai ka lafiya" "Amin Mamana. Suna zuwa k'ofar fita, ya tsaya ya tsareta da rikitattun idanuwanshi masu rikita mata kwakwalwa, yadda yake kallonta ya haddasawa tsigar jikinta tashi ta lumshe idanuwanta kana ta ware su tana kallonshi k'asa-k'asa tana murmushi. "My pretty ba za a bani good-bye kiss bane?" "Uhm....ni dai babu ruwana Daddy idan Airah ta ganka gara tun wuri ka kama gabanka, ka tafi gudun kada kayi abin kunya a gaban yara. Tana rufe bakinta taji saukar bakinshi cikin nata, yana zare bakinshi ya mik'a mata Ahlam ya k'arasa bud'e k'ofa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi. Aneesah tana baro 6angare Jadda ta nufi d'akin mommy tana so ta duba ta, sannan ta k'ara kwantar mata da hankali tana shiri bud'e k'ofa ta ji sautin muryar Madam Salima tana waya, gudun kada ta katse ta sai kawai ta juya ta koma d'akinta ta nemi gefen gado ta zauna talla6e da kumatu sai tunanin mommy take yi, ta rasa wacce irin zuciya ce a k'irjinta ko sai yaushe za ta natsu ta soma gyara kurakuranta?" Kiran sallar magarib ya tashi Aneesah daga tunani da ke yi, ta shiga bathroom tayo alwala da ta gama sallah tsawon lokaci ta dauka tana yi ma iyayyenta addu'a idan da akwai alkhairi a zamansu Allah ya dai-daita tsakaninsu. Azaad yana fita kaitsaye farmhouse d'inshi ya nufa, tun kafin Mr Richard ya yi parking ya hango Hakeem tsaye ya jingina jikinshi a motarshi, tun kafin ya k'arasa wajenshi ya ga yana mishi dariya nan tashi ta shak'iyanci. Hannu Azaad ya mik'a masa suka yi musabaha kafin ya ce. "Naga tun kafin na k'araso kana min dariya, me hakan ke nufi?" "Ina dariya ne saboda naga kusan three days kenan ba ka zo office ba, ko d'azu da ka kirani ka ce mu hadu a gidan gonarka nayi mamaki saboda na dauka sai ka gama cin amarci kai da kwalarka kafin na iya ganinka. Ta k'asan ido Azaad yake kallonshi yana tsotsar lower lips d'inshi, kafin yai murmushi tare da fad'in. "Allah ya shirye ka Hakeem kadai ba ka rabu da iskaci, Aslamiyya fa 'yarka ce ni kuma sirikanka amma ka zauna kana sa mana ido. Sosai Hakeem yasa dariya yana nuna k'irjinshi da yatsa. "Lallai yau za a yi ruwan sama har da k'ank'ara Aj da bakinka ka amsa cewa ni sirikanka ne?" "Kwarai kuwa saboda dadin da naji na aura min 'yarka da kayi yasa na nemi da mu hadu anan firstly nai maka godiya secondly inaso ka rakani gidan Baffanta inaso zan yi magana dashi akan mahaifiyarta. Tsagaitawa da dariya Hakeem ya yi kafin ya ce. "Babu godiya a tsakaninmu Aj ka manta ne we're brothers, duk abin da nai maka tamkar kaina nayi wa, saboda haka babu kalmar godiya a tsakaninmu. Sai kuma batun zuwa gidan Baffa sani ko yanzu idan a shirye ka ke za mu iya tafiya. Murmushi Azaad ya yi cike da farin ciki ya rungume Hakeem, kafin ya sake shi suka jera zuwa wajen mota inda Mr Richard ya fito da sauri ya bud'e musu k'ofa anan farmhouse Hakeem ya bar motarshi, koda suka isa unguwarsu Baffa Sani ana kiran sallar magarib saboda haka suka nemi masallaci mafi kusa da gidan suka yi sallah. Bayan fitar Azaad daga gida Miyya ta goye Ahlam ta nufi kitchen da kanta ta girkawa Daddy abincinsa, ko kad'an bata wasa da darussa da aunty Zaliha ta dorata akai musanmman da ta fad'a mata Azaad yana masifar so abinci gargajiya shiyasa ta duk'a masa tuwo semolina da miyar agusi, hadi da farfesu kayan ciki. Gani an fara Kiran sallar magarib yasa ta barma Nanny Lacey ta zuba a warmers ita kuma ta koma d'akinta ta shinfid'e Ahlam da tai barci sannan ta shiga wanka, ta shirya cikin Australian gown mai dauke da spaghetti hands ta zura dogon hijab tayi sallar magarib da isha'i, da ta kammala sallah ta zauna ta tsantsara kwalliya ta dauk'ar hankali bakinta ya sha pink colour din lipstick ta tattara gashinta ta daure da katon hairband tayi mishi style din doughnut. Jikinta na fitar da k'amshin Arabian perfumes, ta k'ara gyarawa Ahlam kwanciyarta kafin ta bud'e k'ofa ta fito zuwa downstairs parlour. Madam Salima ta fito daga d'akinta ta nufi na Aneesah tana turo k'ofa Aneesah da ke zaune akan praymat din da tayi sallah, ta zabga tagumi ta juya a razane tana kallonta da idanuwanta da suka cika da zallar tsoro da fargaban zuwan nata d'akinta, gefen gadonta Madam Salima ta nema ta zauna. "Taso ki zauna anan Princess inaso nai magana dake" Madam tayi magana tare da pointing kusa da ita, 6oyayyiyar ajiyar zuciya Aneesah tayi, ta mik'e jiki ba lakka ta zauna inda madam ta nuna mata. Saida ta riko hannu Aneesah cikin nata kafin ta marairace murya ta hanyar cewa. "Princess kin ga irin butulci da Daddynku ya yi min ko?" "Uhm! Aneesah ta fad'a tamkar za ta fashe da kuka, har ga Allah bataso mommy ta ji haushinta bata kuma tunani za ta iya supporting d'inta ko ta furta wata mummunar kalma akan Daddynta ba. Saboda yanzu ta fahimci mommy ce mai laifi duk ita ce ta janyo sanadin rabuwarsu. "Princess! Ta kira sunanta gani kamar hankali da tunaninta sun karkata wani gun daban, ba a wurinta ba. "Na'am mommy! Aneesah ta amsa cikin taushin murya yayin da hawaye da take 6oyewa suka silalo a kumatunta, kallon hawaye da ke bin fuskarta Madam Salima tayi tasa hannunta ta d'ago ha6arta. "Princess ba kuka nakeso ki tayani dashi ba so nake ki kira Daddynku ki fad'a mishi za ki zauna a wurinshi sauran bayani kuma sai kin je can gida zan sanar miki. Cikin tsananin razana Aneesah ta d'ago da idanuwanta tana kallon mommy, zuciyarta har tana wani irin bugawa. Wato wata manufa take so ta cimma shiyasa za ta tura ta can gidan. "Ni kuma mommy miyasa zan je can d'in ni bana da ra'ayi zama dasu?" Ta fad'a cikin rawar murya tare da sark'ewar lafazi, zare mata idanuwa Madam Salima tayi kafin ta bata amsa ta hanyar cewa. "Saboda ki dai-daita tsakanina da Daddynku ko bakyaso ya dawo gareni ne?" "Inaso mommy amma Dan Allah kada ki cilastani zuwa can gidan banaso na fiso na zauna kusa dake. "Ke! Madam Salima ta katse ta hanyar daka mata tsawa tare da fizgo k'afadarta tamkar za ta 6alla mata ita. "Banaso shanshanci banza da na wofi princess idan kika zauna anan uban me za ki tsanana min?" "Mommy ki yi hak'uri wallahi ba zan iya abin da kike so sakani ba, duk da bansan menene shi ba, kisani Mommy Ina sonki, burina a kullum ki kasance cikin farin ciki sakoni a sha'ani zamantakewarku da Daddy ba dai-dai bane, idan har Daddy yana da ra'ayi sake zama dake ba sai kin yi amfani dani ba ta wata siga da bata dace ba..... "Ya isa princess nace miki ya isa haka wad'annan maganganu da suke fitowa daga bakinki, uban waye ya koyar da ke su fad'a min uban waye ya dora ki akansu domin ba su yi kama da tunaninki ba?" Kuka Aneesah ta fashe dashi sai faman girgiza kai take yi, yadda kuka ya ci k'arfinta yasa ta kasa magana. Cike da zallar 6acin rai Madam Salima ta tureta ta fad'i kwance akan gado ta mik'e tsaye ta nuna ta da yatsa. "Muddin ba ki yi abin da nasaka ki ba ki manta da kina da uwa daga yau sai ki fara tunani wannan k'aramar yarinyar sa'arki da ubanki yake kirarin matarsa ce ta maye miki gurbina" "Mommy please karki fad'i haka ke mahaifiyata ce ba wacce za ta iya cike min gurbinki a wurina, mommy Dan Allah ki saurareni saboda na faranta miki rai na k'i bin Daddy kin kuma san halinsa sarai baya daukar reni, idan har naje mishi da zancenki Allah ne kadai yasan irin hukunci da zai dauka akaina. Dan Allah mommy ki cire ni cikin wannan lamarin. Cewar Aneesah cikin muryar kuka ta taso da nufin ta riko Madam Salima, kafin ta iso wurinta ta bud'e k'ofa ta fita abinta. Komawa Aneesah tayi ta kwanta ta ci gaba da shasshekar kuka, a k'asan zuciyarta tana mamakin wacce irin mahaifiya ce garesu mai masifar so kanta da yawa ita kwata-kwata damuwarta ita ce damuwa duk wanda zai shiga damuwa bai shafe ta ba. Bayan su Azaad sun kammala sallah suka fito daga masallaci kaitsaye k'ofar gidansu Miyya suka nufa, gidan nan yadda Azaad yasan shi duk da sau d'aya ya ta6a zuwa gida sai yaga ya lalace fiye da farkon ganinsa dashi. D'aya daya daga cikin yaran Baffa Sani ne ya fito daga cikin gida, suka aika shi yai musu sallama da Baffa bai dauki dogon lokaci ba sai ga shi ya fito tare da Baffa. Kallo guda Baffa Sani yai musu ya sheda su daure fuska ya yi don yana tunani ko wani abu ne yafaru da su Miyya yadda suka rabuda yaran ko kad'an baya fatar su sake dawo mishi gida. Bayan su mik'a mishi hannu suka yi musabaha, kana Hakeem ya zarce da cewa. "Baffa wata muhimmiyar magana ce ta kawo mu gunka idan da hali ka ba mu damar shiga daga ciki mu tattauna saboda bai dace mu yi ta tsayuwa a k'ofar gida ba. Ba don ran Baffa Sani yaso ba yai musu iso zuwa 6angare Dadda, ita kanta Dadda ta sheda su shiyasa tai sauri tashi daga kishingid'e da take batada wadatattaciya lafiya kwananan ciwo ya sako ta gaba, sai kuma ga Azaad da Hakeem fatanta Allah yasa ba dawo mata da 'ya'yan arniya nan za su yi ba. Duk sai tayi kici-kici da fuska ta kalli Baffa Sani ta ce. "Sani lafiya ka shigo min da k'artti a tsakar dare nan?" "Dadda ba ki sheda su bane mijin Aslamiyya ne tare da abokinshi?" "Mijin Aslamiyya k'ani ubana ne da za ka shigo min dashi falo kaitsaye batare da neman izzina ba?" Kafin Baffa ya bata amsa Hakeem ya riga shi ta hanyar furta. "Allah ya ba ki hak'uri Dadda ba wani abin tashin hankalin bane ya kawo mu, ki taimaka ki ba mu aron lokacinki kad'an magana mai matuk'ar muhimmanci ce ta kawo mu. Sai da Dadda ta galla-galla musu harara kafin ta ce. "Ku yi gaggawa fad'ar abin da ya kawo ku ni barci nake ji. Murmushi Hakeem ya yi yayin da Azaad sai faman bin ta da idanuwa yake yi, dattijuwa ce mai cikar kamala ya rasa dalilinta na dorawa su Miyya karan tsana. "Dadda Dan Allah ki taimaka ki ba mu cikkake tarihi iyayye Aslamiyya. Shiru Dadda tayi kafin idanuwanta su ciciko da hawaye, cikin sanyi murya ta ce. "Mijina margayi malam Abubakar ladan shahararen malamin addini ne, mun yi aure saurayi da budurwa na yi haihuwa kusan sau biyar suna mutuwa sai Usman mahaifin Aslamiyya ne ya rayu, sai da ya shekara goma kafin na sake haifar Sani daga kansu Allah bai sake bani haihuwa ba. Daga Usman har Sani sun taso cikin nagartattaciya, tarbiyya Allah ya yi wa Usman fasaha da baiwa ta zane tun shi na yaro yake zane-zane musanmman motaci da gidaje, usmanu yaro ne natsatsi gashi da hak'uri da matuk'ar wahala ka ga abokin fad'ar shi. Shiyasa malam ya dauke soyayyar duniya ya dora akanshi, Cikin hukunci na ubangiji yana kammala karatun sakandire d'aya daga cikin masu kud'i da ke zuwa neman addu'a wuri malam ya nema mishi scholarship ya sami gurbin karatu a London. Bayan ya kammala karatunshi yai nasarar samun aiki a wani kamfani k'era motoci a can London da farko malam bai so ya kar6i aikin ba, amma gani usman yana da sha'awa yasa ya amince mishi. Duk bayan shekara guda Usman yake kawo mana ziyara wani zuwa da ya yi sai gashi ya taho mana da babban tashin hankali, wanda ya rusa farin cikin ahalinmu ya jefa mu cikin k'unci. Arniya ya zo mana da ita har da 'ya a matsayin matarshi da 'yar da suka haifa mai shekaru uku da haihuwa, ashe tsawon shekaru hudu kenan da ya yi aure bai fad'a mana ba. Karka so ka ga yadda muka tashi hankula mu ta sanadiyar hakan ne malam ya yanke jiki ya fad'i ya had'u shanyewar 6arin jiki, wata malam uku yana jinya kafin Allah ya kar6i ranshi. A gaskiya tun lokaci naso Usman ya datse duk wata alak'a da ke tsakaninshi da wannan kafira yarinya amma yak'i duk da kuwa yadda nakai da nuna mishi 6acin raina. Haka na hak'ura na zuba mishi ido saidai daga matar tashi har 'yarshi Aslamiyya na tsane su kiyayya nake nuna musu ba ta wasa ba. Bayan wasu shekaru matar Usman ta sake haifar tagwaye duka mata saidai guda d'aya ta zo da matsala a zuciyarta, hakan bai sa na tausaya musu ba sai ma fatan mutuwa nake yi wa yarinya. Amrah da Amal suna da shekaru hudu a duniya Usman ya had'u da ajali ciwon Amal ne ya tashi cikin dare kuma maganinta ya k'are, gashi ana shek'a ruwan sama, don ba zan manta ranar talata ne uku ga watan hudu shekara ta dubu biyu da takwas yadda ya ga ciwon nata ya yi tsanani yasa ya fita ya siyo mata magani ana ya had'u da wani direba marar imani ya buge shi da mota kuma ya gudu, tun anan wuri Allah ya kar6i ranshi, bayan kwana uku da rasuwarsa matarsa ta zube mana yaranshi ta gudu har yau ba mu sake jin labarinta ba. Azaad yana jin date din da Dadda ta anbata hankalinshi yai mugun tashi, wani irin gumi ke feso mishi a sassan jiki, ya runtse idanuwanshi gam yana jin maganganu Dadda suna mishi kai komo a cikin kwakwalwarshi. Kusan a tare Hakeem da Baffa Sani suka sauke ajiyar zuciya, a wannan karon ma Hakeem ne ya yi k'arfin halin fad'ar. "Dadda a labarinki ba mu ji kin kira sunanta ba ko suna kasar da take, ko a can London din take?" Shiru Dadda tayi tana sharar hawaye da ke bin kumatunta, saboda mutuwar Usman ta dawo mata sabuwa fil, ji take tamkar yanzu ne al'amarin ya faru, gani ba za ta yi magana ba yasa Baffa Sani ya dubi Hakeem ya ce. "Sunanta Roseline 'yar asalin k'asar Ethiopia ce.... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 36... Duk dogon bayani da Baffa Sani yake yi Azaad bai fahimci ko d'aya ba, saboda hankali da tunaninshi sun karkata wani gun daban. Magana Hakeem yake mishi bai amsa ba saboda ya yi zurfi a tunani, saida Hakeem ya zugure shi a k'afa sannan ya yi firgigit kamar wanda ke barci aka watsa mishi ruwan sanyi a fuska, numfashi ya ja tare da rintse idanuwa yana dafe goshi. Koda ya bud'e idanuwanshi har Hakeem ya mik'e tsaye, yana kallonshi da alama yana karatar sauyawarshi a lokaci guda ne. Jiki ba lakka ya mik'e suka yi ma Dadda sallama, Baffa kuma ya rako su har zuwa k'ofar gida kana yai musu sallama ya juya cikin gida. Har suka shiga mota Mr Richard ya ja motar ya dauki hanyar farmhouse inda Hakeem ya baro motarshi, Azaad ya kasa dawowa cikin natsuwarshi. Sannu a hankali Hakeem yake yawo da idanuwanshi akan fuskar Azaad, kafin ya yi gyaran murya ya ce. "Ya aka yi ne Aj tun d'azu na fahimci sauyawarka a lokaci d'aya kalli yadda zufa yake karyo maka duk da ac da ke cikin motar nan a kunne yake, jikina ya bani akwai abin da ke damunka?" Azaad ya ja dogon fasali yayin da bugun zuciyarsa ya tsananta. Ya bud'e bakinshi da ya yi matuk'ar yi mishi nauyi ya ce. "Hakeem akwai matsala kuskure da na aikata a baya ne yake shirin dawo min a dai-dai lokaci da na fara sabuwar rayuwa. "Ban fahimci abin da kake k'ok'arin fad'a ba, Aj kayi min magana da yare mafi sauki fahimta. "Shin za ka tuna mutumi da na ta6a bugewa da mota shekaru goma sha hudu da suka gabata, wanda na bi shawararka na barshi kwace cikin jini, wanda har yanzu na kasa goge hoton al'amarin a cikin zuciyarta,?" "Innalillahi wa'inna illaihim raji'um.....Aj kada ka ce min wannan mutumi shine Usman mahaifin Aslamiyya?" "Shine Hakeem domin date din da Dadda ta fad'a da kuma lokaci da al'amarin ya faru, ya yi dai-dai da faruwar wancan al-amari ko shakka babu ni na kashe mahaifin Aslamiyya. "Daina fad'ar haka Aj ba da gangan kayi ba tsautsayi ne kuma ko a wancan lokaci mun koma wuri da hatsarin ya faru, aka ce mana bai mutu ba har an kai shi hospital ba irin neman da ba mu yi shi mishi ba kusan duk wata asibiti da ke kusa da wuri mun je nemanshi har wacce ke nesa da wuri mun je amma ba mu yi nasarar ganinsa ba. Daga k'arshe dole muka hak'ura. Idanuwan Azaad ya suka yi jajir gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka tashi, ya dafe goshi sai faman furgar numfashinsa yake yi, ya shiga tashin hankali marar misaltuwa, duk yadda Hakeem yake kwantar mishi da hankali ta hanyar dad'ad'd'an kalamai hakan bai rage radadin da yake ji a zuciyarshi ba. "Aj please ka manta da wannan a.... "Ya isa Hakeem! Ya dakawa Hakeem tsawa ya nuna shi da yatsa, tare da zazzare manyan idanuwanshi zuciyarshi na tuk'uk'i ya ci gaba da fad'in. "Na sani Hakeem tsautsayi ne amma akwai gangaci domin da a wancan ranar ban bi shawararka ba, na kai shi hospital da watakila ya rayu da rayuwar 'ya'yanshi bata tagyara ba. Duk abin da ya faru dasu Aslamiyya hakkinsu yana rataye a wuyana, me kake tunani zai faru idan Aslamiyya tasan cewa nine na kashe musu mahaifi nine sanadi shigarsu kunci da maraici?" "Aj nasani mun aikata babban kuskure a baya kuma har gobe kana nadama akan hakan, ni fa tun farko haduwa ta da Amrah na ji a jikina akwai wani 6oyayyen al'amari a tsakaninmu. Saboda haka yanzu ba lokaci dorawa juna laifi bane ka natsu mu nemo mafita. Murmushi takaici Azaad ya yi saboda gani yake yi muddin labari nan ya fita, Miyya za ta guje shi, abin da baya fatar faruwar shi. Duk yadda Hakeem yake kwantar mishi da hankali ji shi kawai yake yi ba don maganganu shi sun yi tasiri a wurinshi ba. Da suka iso farmhouse kasa fita daga mota Hakeem ya yi sai ci gaba da rarrashinshi Azaad yake yi. "Dare ya yi Hakeem ka tafi gida mu jira zuwa wayewar gari, kafin mu san abin yi. Azaad ya fad'a ba tare da ya kalli gefen da Hakeem yake ba, bud'e k'ofar mota Hakeem ya yi ya fita jikinshi ya yi matuk'ar sanyi shi kanshi yana kwantar wa da Azaad hankali ne kawai amma yasan akwai gagarumar matsala ba kad'an ba. Miyya ta kasa zaune ta kasa tsayi lokaci-lokaci take janye curtains din window bedroom din Azaad ta leka compound ko za ta hango motarshi ta shigo ta rasa dalili da yasa take jin matsananci fad'uwar gaba, a wannan karo da ta janye curtain din kasa sakewa tayi sai kawai tayi tsaye, tana kallon securities din gida dake kai komo domin tabbatar da tsaron gidan. Tana gani an bud'e gate tun kafin ta hango motarshi ta sauke ajiyar zuciya, domin jikinta ya bata shi din ne. Kasa dauke idanuwanta tayi da barin kallon gate din har sanda Mr Richard ya yi parking ya fito ya bud'e mishi k'ofa, kafeshi da idanuwanta tayi yana 6acewa ganinta tai maza ta saki curtain ta 6oya a ciki, cike da rashin kuzari ya turo k'ofar d'akin nashi. A can k'asan makoshi ya yi sallama duk da yana da tabbaci babu kowa a d'akin. Saida ta ga ya zauna a resting chair yana cire takalmin k'afarshi kasancewar su rufaffi cikin sand'a ta fito daga ma6oyarta, tana zuwa ta rufe mishi idanuwa da tafin hannunta tare da kwantar da k'irjinta a gadon bayanshi, wani irin gundari sanyi dad'i ya ji yana bin sassan jikinshi, ya ja dogon numfashi tare da saukewa cikin taushin murya ya furta. "Prettyn Daddy!" "Uhm...Daddy ya aka yi ka gano ni nan take?" Ta fad'a cikin shagwa66iyar muryarta tare da cire tafin hannun nata daga idanuwanshi, ta sakala su a wuyanshi ta turo fuskarta ta gefen wuyanshi kumatunta yana gogar nashi. Yatsanshi yasa yana zagaye tattausan lips d'inta, kafin ya bata amsa ta hanyar cewa. "A duk lokaci da prettyna ta zo kusa dani koda idanuwana ba su yi tozali da ita ba bugun zuciyata zai tsananta hakan zai tabbatar min da tana kusa dani balle kuma tattausan tafin hannunta ya sauka akan fatar idanuwana, pretty ke ta daban ce a cikin zuciyar Daddynki. 'Yar k'aramar dariya tayi mai ban sha'awa tare da fad'in. "Daddy wai Ina ka shiga ne Allah ba ga yadda na tashi hankalina ba da naga 10 o'clock ya yi ba ka dawo gida ba, ka ga yadda gabana ya dinga fad'uwa kuwa?" Saida ya yi murmushi mai sauti tare da jawo ta ta fad'o kanshi, ta saki ihu saboda ya yi mata bazata sam bata zaci zai iya jawota ba, rungumeta ya yi ya tura hancinshi cikin gashinta yana shakar k'amshin man gashi da tai amfani dashi, sai wani lum-lumshe idanuwa yake yi kamar mai jin barci. "Miyasa za ki tashi hankalinki prettyna bayan kinsa duk nisan da nayi kina cikin zuciyata?" "Ba za ka gane bane Daddy na damu da kai sosai da son samu ne ko nan da k'ofar gida banaso ka fita, na fiso ka zauna nai ta kallon wannan kyakkyawar fuskar taka da bana gajiya da kallonta. D'ago ta ya yi ya zuba mata rikitattun idanuwanshi, yana kallon cikin idanuwanta, tai saurin kawar da kanta tare da yunk'urawa ta tashi da sauri ya maidata jikinshi ji tayi yana sauke numfashi akai-akai tai sauri d'agowa ta kalli fuskarshi tasa hannunta akan kwatatcen sajenshi tana shafawa a hankali, cike da damuwa akan fuskarta ta ce. "Daddy ya naji kana sauke numfashi ko ba ka da lafiya ne?" "Lafiyana qalau na dai kwaso gajiya ne. Ya fad'a cikin sauri tare da basarwa, gudun kada ta yi saurin gano yana cikin damuwa, domin shi mutum ne ba iya 6oye damuwa ba. Sai kawai yai saurin cireta daga jikinshi yana fad'in. "Bari nai wanka ko jikina zai saki. Ya yi magana tare da nufar bathroom, kafin ta sake yi magana har ya bud'e k'ofa ya shige bathroom din. Har ya fito daga wanka idanuwanta suna kafe a k'ofar bathroom, ya fito daure da white towel a k'ugunshi yayin da yake goge sumar kanshi da k'aramin towel tai sauri tasowa ta nufe shi. "Daddy har ka fito?" "Nayi sauri ne?" "Ka dai dad'e saura kiriss na bi ka ciki Kawo towel din na taimaka maka. Ta fad'a tana kallonshi tana dariya, mik'a mata towel din ya yi ya nufi gaban dressing mirror ya ja stool ya zauna yana cewa. "Ai da kin bi ni da sai wanka yafi armashi. Harararshi kawai tayi ta ci gaba da goge mishi jiki, komai ita tayi mishi hatta da kayan da zai saka ita ta za6a mishi. Sai lokaci ya mayarda hankalinshi akan gown d'inta take sanye da ita. "Wow....gown d'inan tayi matuk'ar yi miki kyau, kamar na cinye ki prettyna. Sosai furuncinshi na k'arshe ya bata dariya, ta dawo gabanshi tana ci gaba da dariya ta shiga jujjuyawa ta yadda zai k'ara gani rigar da kyau. Riko ta ya yi yana tayata dariya da take yi. "Da gaske nake yi prettyna idan kina min irin wannan kwalliyar da wuya na iya fita. "Rufa min asiri Daddy kada ace maka mijin tace ni dai mu je na ba ka abinci kada gari wannan zuzutawa da kake min kaina ya fashe. Hannunshi ta riko suka nufi kofar fita, yana cewa. "Karki damu prettyna wannan suna an jima da kirana dashi, ba a kanki za a fara ba, zan yi farin ciki idan aka kirana dashi ta dalilinki. Wani irin farin ciki marar misaltuwa kalamansa suka haifar mata, sai murmushi take dokawa, da suka iso dining room tai sauri ja masa kujera ya zauna kafin ya kai zaune ya ce. "Ban ji motsi Airah da Ahlam ba?" "Ahlam tayi barci tana d'akin Nanny Lacey, Airah kuma tana d'akinta wayau nai mata nace zan je na gyara maka d'aki. Ta k'arasa magana tana dariya tare da bud'e warmer mai dauke da tuwo ta ciro guda d'aya ta cire ledar da ke jikinshi ta saka a plate ta zuba mishi miya a k'aramin bowl ta sake bud'e warmer da farfesu yake ciki shima ta zuba mishi. Tun kafin ya ci tuwon yawunshi ya tsinke ya kalleta yana murmushi. "Ashe my pretty tana da wayau har haka, ai ni na zaci yau ba zan ganki cikin sauki ba. Saida ta tura mishi plate din gabanshi ta ja kujera ta zauna, kafin ta ce. "Daddy kenan ai tuni ka gama awon gaba da zuciyata, shiyasa ba zan iya jure zama nesa da kai ba. Ko fitar nan da kayi Allah saida zazza6i ya kamani. Zaro manyan idanuwanshi ya yi yana kallonta baki bud'e, tai sauri daukar murfin warmer ta kare fuskarta dashi, dariya ya yi tare da girgiza kai ko kad'an bai zaci Aslamiyya za ta iya maganganu masu tafiyar da ruhi har haka ba. Har ya bud'e baki zai yi magana tai sauri tarar numfashinsa. Batare da ta cire murfin da tasa ta kare fuskarta ba. "Daddy please ka ci abincinka kada ya huce abinci yau special ne girki amarya ne fa in kaci sai ka bada tukuici na musanmman. Ta k'arasa magana tana k'ara sunne fuska cikin murfin warmer din, dariya ya yi yana k'ara jin sonta yana k'ara link'aya a cikin zuciyarshi. Yana ci tuwo yana gyada kai alamar ya yi mishi dad'i kusan rabin ya cinye kafin ya dauki bowl din farfesu shima yaci sosai sannan ya sha ruwa da drinks d'inta ta zuba mishi a handle cup. "Alhamdullilah....girkin amaryata ya yi dad'i ba kad'an ba saidai next time idan za tai min girki karta cika yaji sosai saboda angon nata bayaso yaji. Kuma in-sh-allah zan bada tukuici da abu mafi tsada da daraja. Tun da ya fara magana take kallonshi tare da langwa6e kai, tayi rau-rau da idanuwanta ta ce. "Afuwan rabin raina wallahi bansan na cikawa miyar yaji ba amma in-sh-allah a gaba zan kiyayye. "Karki damu prettyna a hakan ma nagode miki sosai na kuma yi farin ciki marar misaltuwa, da zan iya tsaga zuciyata da na tsagata ki shiga ki ga yadda kika haifar min da farin ciki, domin yau shine ranar ta farko da ni Azaad Junaid naci abinci da matata ta aure ta girka min da hannuwanta, idan nace dake pretty ban ta6a cin abinci da Salima ta girka da hannuwanta ba. Watakila ba za ki yarda ba ko?" "Zan yarda mana Daddy saboda na tabbata ba za ka fad'i abin da ba gaskiya ba. Shiru ya yi zuciyarshi tana mishi wani iri anbatar suna Salima kadai da ya yi, hannunshi ya mik'a mata ta kama tare da tasowa yai mata masauki a cinyoyinshi. "Bari nai feeding dinki prettyna saboda naji cikin nan naki ya k'are shafewa da yawa. "Na goshi Daddy mun ci pancake ni da Airah. Ta fad'a tana k'ara kwantar da kanta a k'irjinshi, a hankali ya sauke ajiyar zuciya sun jima a zaune suna ta6a fira yawanci firar ita ce ke yi iyakancinsa ya bata amsa a takaice ko kuma ya yi dariya mai k'aramin sauti, dogowur hamma tayi kafin tasa tafin hannunta ta rufe bakinta yai sauri kai nashi hannu ya rufe mata, da ta gama hammar ya cire hannunshi tare da sumbatar gefen wuyanta daga zaune da yake ya mik'e da ita ba tare da ya direta a k'asa ba. Ya nufi upstairs dauke da ita hannuwanta ta sakala a wuyanshi, har suka iso bedroom d'inshi tana aikin kallonshi, duk duniya idan da akwai abin da bata gajiya da kallonshi bai wuce fuskar Azaad ba. Da kanshi ya sauya mata kayan jikinta zuwa sleeping dress, ya kwantar da ita kamar wata 'yar baby kana ya wuce bathroom ya yo brush, yana fitowa wayarshi tana fara ringing Miyya tai sauri mik'a hannunta akan bedside ta dauko mishi wayar, kamar an ce ta kalli sensor din wayar sai kawai ta ga suna Salima yana yawo gabanta yai mummunan fad'uwa.... 5/12/22, 12:25 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 37... Hannu Azaad ya mik'a mata da ta mik'o mishi wayarshi, kasa mik'a mishi tayi sai kawai ta tsare shi da idanuwanta masu cike da zallar tsoro da fargaba. "Pretty bani wayar mana kada kiran ya tsinke" Ya fad'a cikin taushin murya. Sai lokaci ta ankara da abin da tayi cikin sauri ta mik'a mishi dai-dai kiran yana tsinkewa jikinta a sanyayye ta koma ta kwanta har da su jan duvet ta lullu6e rabin jikinta tare da lumsashe idanuwa. Gani sunan Salima a matsayin wacce ta kira shi yasa ya ja siririn tsaki yana shirin rufe wayar ga baki d'aya kiranta na sake shigowa ranshi ya sake 6aci a fusace yai received cikin kakkausar murya ya ce. "Ya aka yi ne Salima?" "Ba irin wannan tambayar ya kamata kai min ba Azaad. "Look Salima banaso shashanci ki fad'i maganarki kawai idan kuma ba ki da abin fad'a Kira kawai kika yi domin ki katse min jin dad'i da iyalina, ki sani ba za ki sake kira ba balle har na d'aga. Sosai furuncinshi ya daketa tamkar an da6a mata wuka a kahon zuciya, batasan lokaci da ta fashe da kuka ba. Cikin muryar kuka take magana "Ban ta6a tsanmani ni Salima zan zama abin wulak'antawarka ba, duk 6acin rai da ka shiga bai dace ka dinga fad'awa uwar 'ya'yanka uku bak'ak'en maganganu ba. Amma ba komai Azaad nan da d'an wani lokaci za ka fara nadama za ka dawo kana denied duk wasu munana kalamai da ka dinga furta min da bakinka. Wani mugun tsaki Azaad ya yi yana huci domin ba k'aramin bak'anta mishi rai kalamanta suka yi ba, in banda wawanci da dabbanci har shine zai yi nadama ba ita ba. Tsabar takaici kashe wayarshi kawai ya yi ya nemi kusa da k'afafuwan Miyya ya zauna ya dafe kokon kanshi yana fitar da iska me zafin gaske daga bakinshi, tun daga lokaci da ya fara magana da Salima Miyya take aikin rarraba idanuwanta akanshi duk da ba wata maganar arziki yake yi da ita ba amma wani irin zafin take ji a can cikin k'asan zuciyarta. Wanda ta rasa na menene sannu a hankali ya dora hannunshi a tafin kafarta ta hagu yana mata tafiyar tsutsa, har cikin kwayar kanta take ji tafiyar tsutsa da yake mata dariya ta shiga yi tana jan k'afarta saida ya gaji don kanshi sannan ya saki k'afar ta ta, ya nemi kusa da ita ya kwanta tare da shigarta da ita cikin k'irjinshi yana shafar gadon bayanta a hankali cikin sanyi muryarta ta ce. "Daddy kayi hak'uri Dan Allah ka dai-daita tsakaninka da mommy, in yaso ka kafa mata dokokin na tabbata a wannan karo ba za ta sa6a maka ba. Har ta dasa aya a zancenta bai katseta ba, bai kuma furta uffan ba yai shiru tamkar yana nazarin maganganunta daga bisani ya ja numfashi ya sauke tare da cewa. "Please prettyn Daddy karki k'ara 6ata min rai mana shin bana fad'a miki banaso kina min zancenta ba?" "Amma Daddy ba shi zai sa nai shiru na zuba maka idanu ka cutarda iyalinka. Infact yaranka da matarka suna bukatarka Daddy please kada ka zama mai son kai... "Ya isa pretty! Ya katseta cikin kakkausar murya wacce ke nuna ya fara hasala da zantukanta, ya cire ta daga k'irjinshi ya dora kanta a pillow ya mik'e ya shige bathroom, Miyya ta bishi da kallo kafin ta gyada kai ta lumshe idanuwanta kafin ya fito har tayi barci ba k'aramin dadin hakan ya ji ba. Domin ya tsani ayi mishi zance Salima ko wane iri ne. Madam Salima kasa barci tayi sai tufka da warwara take yi ta rasa mafita guda d'aya kwakwara har asuba bata rintse ba. Da wuri Miyya ta tashi ta shiga kitchen da taimakon Nanny Lacey ta kammala had'a breakfast, ta bar Nanny tayi arranging dining table ita kuma ta wuce d'akinta ta fesa wanka, ta shirya cikin atamfar super Holland style din skirt and blouse dinki yai masifar kar6a jikinta, bata daure d'an kwali ba sai ta yane kanta da k'aramin mayafi. Jikinta na fidda k'amshin Arabian perfumes, ita da kanta sai da ta yabawa kanta da irin kyau da tayi d'akinsu Airah ta nufa koda ta shiga Airah ta shirya cikin school uniform d'inta tana zaune gefen gado tana sanya takalminta, fuskarta dauke da murmushi ta ce. "Good morning my Airah! "Morning our pretty. Airah ta fad'a tare da d'agowa ita ma da murmushi akan fuskarta, kana ta cigaba da fad'in. "Wai pretty yaushe za ki koma school ne?" Ajiyar zuciya Miyya tayi kafin ta jingina bayanta a bango, jikinta a sanyaye ta ce. "Bansani ba Airah don har yanzu Daddy bai yi maganar komawa ta ba, gashi next month za a fara exams. "Kiyi mishi magana mana pretty kada karatunki ya koma baya. "Shikenan zan yi mishi taso mu je kiyi breakfast kada ki yi latti. Airah ta mik'e tare da daukar katuwar schoolbag d'inta ta bi bayan Miyya, saida ta raka Airah parking lot kana ta nufi d'akin Daddy tana tura k'ofa yana fitowa daga wanka, tsaye tayi a jikin k'ofa tana kallonshi tana murmushi cikin shagwa66iyar murya tayi magana. "Good morning my Daddy! "Morning prettyna kin yi matuk'ar kyau kamar na hadiye ki, amma miyasa kika gudu kinka bar Daddynki, bansan cewa kin tashi ba saida na lalla6oki naji wayam saura kiriss na fashe da kuka?" Ya k'arasa magana cikin shagwa6e murya, kamar dai yadda take mishi. Hakan ba k'aramin burgeta ya yi ba, bata ta6a gani babba yana shagwa6a ba sai akan Daddy shiyasa tasa dariya tare da rufo k'ofa ta nufi wurinshi tana mai cigaba da dariya ta mik'a hannunta, ta kar6i towel din da yake goge dashin ruwan jikinshi. "Wai Daddy ka manta ne ba mu kadai bane a gidanan ba?" "Uhm...dama nasan da wannan za ki dogara idan kika ce ki dinga nuna min wariya launin fata zan kwashe yaranki na maida su idan suka fito. Ya yi magana cikin zolaya tare da kallon cikin idanuwanta. "Tuba nake yi my Daddy kai ma kasan kaine bugun zuciyata dai-dai da second d'aya banaso kayi nesa da ni, soyayyar da nake maka ce ta shafi yaranka. Sosai kalamanta suka haifar mishi da farin ciki, hannunta ya riko ya sumbace tafin hannun nata. "Ina sonki pretty so da bansan adadinsa ba kiyi min alqawali a duk yadda rayuwa ta zo mana ba za ki gujeni ba. Murmushi tayi tare da dank'e hannunshi. "Nayi alqawali Daddy har izuwa k'arshen numfashina Ina tare da kai ba kuma abin da zai sauya hakan. "Nagode prettyna Allah ya ba ki ikon cika wannan alqawali. "Amin thumma Amin! Daga haka ta shiga taimaka mishi ya shirya cikin suit dark green colour, tana rike da briefcase d'inshi suka sauko k'asa gani ya nufi k'ofar fita tai sauri dakatar dashi. "Daddy ya naga ka nufi k'ofar fita breakfast din fa?" "I'm sorry my love na manta ban fad'a miki ba ina azumi. "Azumi kuma Daddy?" Ta fad'a da zallar mamaki akan kyakkyawar fuskarta, hannunta ya rike sannan ya sauke numfashi cikin sanyaya murya ya ce. "Kwarai kuwa azumi nake yi my love kiyi k'ok'ari ki had'a min abinci bud'a baki. "A iya sanina Daddy Monday and Thursday ake yi azumi yau kuma talata ko ka zaci yau Monday ne?" Girgiza kai ya yi yayin da jikinshi yai masifar sanyi damuwa ta baiyana k'arara akan fuskarshi, yai saurin kauda fuskarshi gudun kada ta fahimci halin da yake ciki ya rintse idanuwanshi yana jin wani irin zafi a k'asan zuciyarshi. "Daddy please ka answer me kana fad'ar azumi kake yi naji hankalina ya tashi... Cikin hanzari ya katseta ta hanyar fad'ar. "Karki damu prettyna azumin kaffara ne a shekaru baya na ta6a buge wani mutum har ya rasa ransa shine yau na fara azumi. Cikin kaduwa ta zaro manyan idanuwanta muryarta yana rawa ta furta. "Daddy mutum ka kashe azumi sittin fa za ka yi?" Tayi magana tana dafe k'irji tare da zaro idanuwa ta kakkafe shi dasu. Cike da rauni ya gyada kanshi, ya mik'a hannu ya kar6e briefcase d'inshi da ke hannunta ya juya cikin sauri ya bud'e k'ofa yana fadar. "Na tafi prettyna sauri nake yi ina da meeting banaso nayi latti, ki had'a min abinci mai dad'i amma kada ki cika yaji sosai irin na jiya. Ta bishi da kallo tsigar jikinta na tashi Sai kawai ta tsinci kanta cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, da kyar ta iya jan k'afafuwanta ta nufi d'akinshi ta gyara mishi har ta kintsa d'akin batada natsuwar zuciya. Azaad Junaid yana fita da direbanshi mr Richard basu yi tafiya mai nisa ba direban madam Salima ya fito daga ma6oyarshi ya bisu a baya, wanda madam ce tasaka shi duk wani shige da fice na Azaad Junaid ya binciko mata tun karfe 6 yake zaune a unguwar sai yanzu yaga fitarshi ya fito da wayarshi jikinshi har rawa yake yi ya kirata ya sanar mata fitarshi, nan ma umarni ta bashi ya ci gaba da binshi ita kuma ta wafci handbag d'inta ta fito direban yara ya dauke ta suka fice daga gidan. Mr Richard yana cikin tafiya yaji mota ta fara jacking ya gangara gefen titi ya yi parking Azaad ya yi nisa a tunani shiyasa bai fahimci abin da yake faruwa ba saida ya ji saukar muryar mr Richard a dodon kunnenshi. "Sir motar nan tana da matsala kuma ni kaina ban fahimci tana da matsala ba sai yanzu da ta fara mana jacking. Shiru Azaad ya yi yana shafar sajenshi damuwa da yake ciki ba zata bashi damar dogon surutu ba, kafin yai nasarar bud'e baki yai magana mr Michael ya yi parking kusa da motarsu ya fito tare da knocking glass din k'ofa mr Richard ya saukarda glass din yana murmushi farin ciki saboda yasan matsalarsu ta ragu. "Sir ga mr Michael ka fito ya k'arasa da kai company ni kuma zan jira zuwan engineer Bello ya wuce da motar garage. Nan ma Azaad bai tanka ba Mr Richard ya fito da sauri ya bud'e masa k'ofa ya fito, suka nufi waje motar Mr Michael ya shiga kana Mr Richard ya ajiye masa briefcase din shi kusa dashi sai lokaci mr Michael ya gaidashi hannu kawai ya d'aga mishi suna cikin tafiya wayarshi tayi ringing jikinshi a sanyaye yai picking. "Hakeem! Ya furta cikin wani irin murya da jin sautinta kasan mai ita yana cikin zallar damuwa. "Aj kana ina akwai kyakkyawan labari?" "Ina bisa hanyar zuwa Aj gold company. "Shikenan sai ka k'araso Amma ya naji muryarka wani iri?" "Hakeem damuwa ce ta taru ta yi min yawa a duk lokaci da na tuna nine silar mutuwar mahaifin Aslamiyya sai naji wani iri matsananci tsoro ya lullu6eni. Hakeem ta wacce hanya zan fito na fad'a mata ni na kashe mata mahaifi?" "Aj please ka natsuwa kasan abin da kake fad'a yadda kake magana tamkar da gangan ko da wata mummunan manufa ka kashe shi, idan ka kwatar da hankalinka sannu a hankali za mu nemo mafita in-sh-allah komai za tafi dai-dai. "Ba za ka gane bane Hakeem al'amarinan fa babba ne domin na ragewa kaina nauyi yau na tashi da azumi yanzu kuma Ina neman ta yadda zan fad'awa Aslamiyya da kakarta ni na kashe Usman.... "Aj ya isa haka sai faman nanatawa kake yi kai ka kashe mahaifin Miyya wai kana jin dad'i fad'ar hakan ne?" Dan Allah mu aje wannan maganar har ka k'araso company bai kamata muna tattauna irin wannan maganar ba akan hanya. Ajiyar zuciya ya sauke tare da kashe wayar sai lokaci ya tuna da mr Michael yake tare ba amintattacesa ba mr Richard ba, a karo na biyu ya sake sauke numfashi da ya fahimci hankali mr Michael yana kan driving. Koda suka iso company zuciyar Azaad kamar za ta tsaga k'irjinshi ta fad'o k'asa, duk yawan employees din da ke gaidashi bai amsa ba sai hannu yake d'agawa, yana shiga office d'inshi Hakeem yana shigowa. "Har ka iso kenan?" "Uhm! "Tsakanin jiya da yau Aj har kayi rama Dan Allah ka kwantar da hankalinka, komai fa muk'addari ne daga Allah ba mu isa mu canzawa kanmu k'addara ba, fatanmu Allah ya sauya mana ita zuwa alkhairi. A hankali Azaad yake yawo da yatsanshi akan lips d'inshi, kafin ya ja iska ya fesar ta kofofin hancinshi biyu. Cikin sanyi jiki ya d'ago ya kalli gefen da Hakeem yake tsaye ya ce. "Wai ni Hakeem sai yaushe zan kasance cikin farin ciki ne a rayuwata?" "Aj komai ka gani a duniya yana da farko hakazalika yana da k'arshe, idan kayi hak'uri ka mik'awa ubangiji lamaurranka sai kaga komai ya zo ya wuce kamar ba ayi ba. "Ina fatan hakan ta kasance dani Hakeem nima inaso nai farin ciki nai walwala kamar kowa. "Mu ci gaba da addu'a abokina in-sh-allah hakan za ta kasance. Sai dangane da mutuwar mahaifin Miyya bai kamata ka 6oye mata ita da danginta ba a shawarce gara tun wuri mu sanarda su tafiya da bata da fashi zama baya bai kamace mu ba. Wani irin gumi ya shiga tsatsafowa Azaad a sassan jikinshi, a duk lokaci da aka dauko wannan zance ko ya tuno dashi tashin hankalinshi k'ara linkawa yake yi. Kafin yai magana d'aya daga cikin wayoyinshi da ke zube akan desk tai ringing, kasancewar layi 'yan uwanshi kadai ke kira shi dashi yasa ya dauka Alhaji Abbas ne ke kiranshi bayan mutuwar babban yaya Alhaji Yusuf Junaid, Alhaji Abbas ne ya maye gurbinshi kasancewar shi ke binsa. "Assalamu Alaikum Yaya Abbas barka da safiya?" "Barka Alhaji Azaad na kira ka ne domin na sanarda kai wani babban al'amari ya kunno kai a family shiyasa muka had'a meeting din gaggawa, saboda haka komai muhimmanci abin da kake yi ka ajiye shi ka zo yanzu-yanzu nan a family house kowa ya hallara kai kadai muke jira. Tun daga lokaci da Alhaji Abbas ya fara magana Azaad Junaid yake ji fad'uwar gaba me kuma yake shirin faruwa, daga wannan sai wancan bai gama magance wata matsala ba wata ta kunno kai. "Azaad kana jina kuwa?" Alhaji Abbas ya katse masa zance zuci da yake yi, da kyar ya iya sarafa harshensa ya amsa da. "Shikenan Yaya Abbas in-sh-allah ganinan zuwa. Ya ciro wayar daga kunnenshi ya kashe kiran, kafin ya ja k'arfaffiyar ajiyar zuciya kana ya sauke cike da mutuwar jiki ya d'ago idanuwanshi da babu komai a ciki face tashin hankali da rashin natsuwar zuci ya kalle Hakeem cikin sanyi murya ya bashi labari kiran da Alhaji Abbas yake mishi. Hannu Hakeem ya zura a cikin aljihun rigar shaddar jikinshi ya ciro magazine ya jefa a gaban Azaad, kana ya ja kujera ya zauna. "Aj ka dauki magazine d'inan ka duba a shafi na biyar za kaga hoton da ya girgiza ni, da sanyi safiyar nan shine mak'asudin da yasa na kiraka kana kuma ka kalli wannan hoton da Baffa Sani ya ba ni na mahaifiyar Aslamiyya shin za ka fahimci abin da na fahimta a cikin magazine d'in?" 5/12/22, 14:22 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 38... Gaba d'aya jikin Azaad Junaid ya dauki rawa baisan lokaci da ya mik'e tsaye ba, sai faman yawo yake yi da idanuwanshi daga hoton jikin magazine zuwa da wanda Hakeem ya bashi ba ko tan-tama wannan matar ta jikin magazine da hoton da ke hannunshi na mahaifiyar Miyya ya yi kama sak da na jikin magazine miss Roseline Yaqub Gambella ce fitattaciyar 'yar kasuwa wacce tayi fice a duniya. Ba sai ya tsaya wahalarda kwakwalwarshi ba wurin tanttace kamanunta da Miyya ba saboda kamar tasu har ta 6ace da ka kalleta kasan ita ce mahaifiyarta saidai ita ta d'an tsofa sa6ani Miyya da ke da zallar kurciya amma duk da haka kamarsu d'aya sak. "Alhamdullilah.....Allah abin godiya ba ko shakka miss Gambella ce mahaifiyar prettyn Daddy na rasa ina zan jefa kaina saboda farin ciki Hakeem. "Lamarin ubangiji kenan Aj kawai mu ci gaba da godewa Allah da sannu al-amurranka za su dai-daita, yanzu ka bar komai a hannuna zan shirya mana tafiya zuwa Australian, saboda a bincike da nayi na gano tana zaune ne a Australian ba k'asarta, ta haihuwa ba Ethiopia. Gara mu je mu zo da ita a Nigeria aganina hakan zai fi saurin walwale mana matsalolinmu. "Shikenan Hakeem duk yadda ka tsara dai-dai ne zuciyata cike take da tsintsa farin ciki prettyna za ta had'u da mahaifiyarta, watakila a dalilin hakan za ta yafemin kashe mata mahaifi da nayi. "Koda ba ka had'ata da mahaifiyarta ba Aj in-sh-allah Aslamiyya ba za ta kulace ka ba, domin tasan k'addara yanzu ka tashi ka je ka ji neman da Alhaji Abbas yake maka Allah yasa alkhairi ne sa6ani abin da muke tunani. "Amin Hakeem amma tare za mu je saboda mr Richard yana wurin gyaran mota. "Okay ba damuwa tashi mu tafi. Shi kanshi direban yara ya shiga tashin hankali ba kad'an ba, lokaci da madam Salima ta sanarda shi buk'atarta na zuwa gidan da Azaad ya kai Miyya. Saidai bai isa ya bijirewa umarninta ba domin bijire mata yana nufi rasa aikinshi gaba d'aya. Da suka iso gate din gidan hannunshi har makyarkyata yake yi, da ya je danna horn security ya bud'e musu gate ya danno hancin motar a farfajiyar gidan da parking d'inshi da fitar Madam Salima duk lokaci d'aya tun da ya dauko ta yasan ba alkhairi bane ya kawo ta yanzu kuma da ta fice daga mota cikin sauri ya k'ara tabbatar da zarginshi. A tsorace ya fito daga cikin mota ya jingina jikinshi da motar ya bita da kallo ji yake kamar ya kira Azaad ya fad'a mishi zuwanta gidan amma tsoron hukunci da zai biyo ta kanshi ya hana shi. Ma'aikatan gidan sai faman gaidata suke yi kasantuwa sunsan matsayinta ga maigidan. Tana zuwa ta turo k'ofar shiga main parlour da karfin gaske cikin sa'a k'ofar ta bud'e yadda ta bude k'ofar ya janyo hankalin Nanny Lacey dake kitchen tana wanke-wanke da sauri ta fito tana goge hannunta da d'an k'aramin towel da kuzarinta ta fito amma tana arba da madam Salima ta kasa k'arasawa cikin parlour tai tsaye turusss tana mata kallon tsoro. "Zo nan munafukar banza har ni za ki ciwa amana Nanny Lacey na yarda dake amma kika munafuce ni. Kasa bin umarninta Nanny Lacey tayi sai ma tayi k'ok'arin komawa kitchen, a nufinta ta shiga kitchen ta kargame k'ofa kafin ta cimma manufarta madam Salima ta nufo wajenta da sauri ta cafko dantse hannunta tare da fizgota da mugun k'arfi kamar za ta raba hannunta da gangar jikinta ba k'aramin zafi Nanny Lacey ta ji ba. Har sai da ta rintse idanuwanta, sosai madam Salima ta zageta tasss ko kad'an bata raga mata ba hakan ba k'aramin konawa Nanny Lacey rai ya yi ba, abinka da zuciya batada k'ashi sai tai k'ok'arin maida mata martani ta hanyar fad'ar. "Madam ki daina gani laifi idan ma akwai mai laifi ce to ke ce, ni fa 'yar aikinku ce kawai. Daga ke har yalla6ai Azaad ina bin umarni duk abin da ku ka umarce ni saboda haka ki tuhume mijinki da laifi cin amanarki amma ba ni ba. Baki bud'e madam Salima ke kallon Nanny Lacey tana mamaki ina ta samu wannan kwarin gwiwar mayar mata da magana, duk tsawon shekaru da suka dauka tana aiki a gidanta bata ta6a musanya yawu da ita ba sai yau lallai idan bata yi da gaske ba hatta da 'yan aikinta za su rena ta saboda haka cikin tafarfasar zuciya ta wankewa Nanny fuska da tagwaye maruka a kuncinta na hagu da dama kana ta nunata da yatsa tana huci. "How dare you Lacey! Har ni za ki kalla ki fad'awa magana lallai kuwa k'arshen zamanki ya zo a gidanan, ai ba Azaad ya dauke aiki ba ni ce sanadin zuwanki kano saboda haka a yau d'inan za ki tattara komatsa ki, ki koma Jos. "Ban yi mamaki ba madam don kin mare fuskata, ban kuma yi mamaki jin irin wad'annan maganganu sun fito daga bakinki ba. Saboda nasan a irin halin da kika tsinci kanki fiyye da hakan ma za ki aikata saidai ina miki albishir da cewa idan kika ga na bar garin Kano yalla6ai Azaad ne ya sallame ni ba wai ke korarriyar gida ba. Daga haka Nanny Lacey ta juya dafe da kunceta, ta nufi kitchen yayin da Madam ta bita da ashariya. "To shikenan Nanny zan nuna miki ni nake da iko da gidanan da zaran na gama da tsinaniya yarinya nan akanki zan dawo sai nasa kin kwashe kashinki a hannu banza butulu. D'akunan da ke downstairs ta fara bi tana bubbudawa ko za ta ga Miyya, ta dai ci karo da Ahlam tana sharar barci abinta ko ta kanta bata bi ba. Ta haura upstairs tana bud'e d'aki na biyu wanda ya kasance na Azaad ta hango Miyya a kwance akan katafare gadon barcinsa, wani irin duhu ya mayewa ganinta jin k'arar bud'e k'ofa yasa ta kalli k'ofar shigowa tai tozali da wacce ko a mafalki bata ta6a zaton ganinta ba. Kafin tai wani yunk'uri Madam ta iso gunta daga kwance da ke ta saka hannuwanta biyu ta shak'e mata wuya saida taji tana kakarin mutuwa sannan ta saki mata wuya ta shiga zuba mata maruka a kumatunta tuni baki da hanci Miyya suka fashe jini sai zuba yake akan pillow da kanta yake kai. Da k'arfi madam Salima ta finciko ta ta yar6e ta akan tiles tasa k'afarta ta dinga ball da ita ihu da Miyya take yi ya isa kunne Nanny Lacey, da gudu ta shigo d'akin duk k'ok'arinta na gani ta kwaci Miyya abin yaci turu kasancewar Madam Salima tafi ta k'arfi nesa ba kusa ba. Daga k'arshe ma sai had'e su tai su biyu tana bugu kamar wata sabon kamun hauka. Gani haka ya sanya Nanny Lacey ta kwaci kanta tasake kwasa da gudu ta sauko k'asa, ta fita compound ta nemo agaji securities. Da madam Salima ta gaji da jingar Miyya ta cukume wuyan rigarta ta jawo ta a k'asa kamar dai kana jan dabba ba mutum d'an adam ba. A haka ta tattaka matattakala bene da ita a garin jan da take mata hannunta ya buge k'arfen da ke jikin bene ta kwalla k'ara mai tsananin gaske kana ta suma. Daga lokaci bata sake sani me ke faruwa ba. Koda Azaad ya iso family house babban falo ya cika taff da 'yan uwanshi, da shigowarshi ya bisu d'aya bayan d'aya yana basu hannu sun yi musabaha kafin ya nemi kujera ya zauna sai lokaci idanuwanshi suka yi mishi tozali da Ahmadu dake kwance a k'asa yana sauke numfashi d'addaya, sai kuma Hasheem da ke zaune a keken kuragu idanuwanshi sun yi jajir ga wani irin miyau mai yauk'i yana fita daga bakinshi. "Subhanalillah.....me yafaru da Hasheem shi da yake asibiti me ya kawo shi nan?" Shi kuma Ya Ahmadu me ya same shi ne, ko shima bashida lafiya ne?" Azaad ya fad'a fuskarshi dauke da tsagoron mamaki, yana kallon fuskar Alhaji Abdallah wanda shi yake facing da sauri Alhaji Abdallah ya kauda fuskarshi yayin da wasu hawaye bazata suka biyo kuncinsa. "Shine babban mak'asudin taruwar mu anan Azaad, daga Ahmadu har Hasheem sun tsinci kansu a wannan halin ta dalilinka. Ba wai iya su biyu kadai ba hatta da mutuwar babban yaya Alhaji Yusuf da amininsa Alhaji Babu... "Ni kuma Yaya? Azaad ya katse shi a razane har yana nuna k'irjinshi da yatsa, cikin matuk'ar mamaki ya sake fad'in. "Me ya alak'anta ni da mutuwar babban yaya da amininsa, balle halin da su Ya Ahmadu suke ciki?" Yaya Abbas kowa anan wurin yasan cewa babban yaya da Alhaji Buba accident suka yi Hasheem kuma wasu 'yan ta'adda da ba a san ko su waye ba suka har6eshi shi kanshi yace baisan su ba. Ya Ahmadu kuma bansan me ya faru dashi ba sai yanzu nan da na shigo na ganshi kwace a cikin wannan hali. "Kwantar da hankalinka Azaad duk Wanda ke cikin falonan yasan kai mutume kirki ne mai tsalkakkiyar zuciya, shiyasa ubangiji ya kare ka a duk lokaci da 'yan uwanka suka yi yunk'uri cutarda kai daga k'arshe ma sai kaik'ayi ne ya koma kan mashek'iya ga dai su nan a zaune su ba ka labarin abin da suka aikata da bakinsu waka a bakin mai ita yafi dad'in sauraro, ni kan ba zan arin bakinsu naci musu albasa ba gara ka ji daga bakinsu. Tirya-tirya Ahmadu ya shiga bankad'o sirrikansu daga nan kwance da yake wanda ba dasu cikin tafiyar ba suka dinga tafa hannuwa suna salati da sallalame tare da yi musu tofin Allah tsine, gaba d'aya falon ya kaure da hayaniyarsu. "Ya isa haka! Alhaji Abbas ya daka musu tsawa dole suka yi shiru ba don ransu yaso ba, yayin da Azaad Junaid ya sadda kanshi k'asa hawaye na bin kumatunshi biyu, yasan cewa 'yan uwanshi ba su k'aunarshi amma bai ta6a tsanmani kiyayyar tayi kamari har haka ba. Wani irin zafi yake ji can cikin k'asan zuciyarshi. "Azaad ka ji abin da 'yan uwanka na jini suka aikata maka domin babu bare a cikinsu, da Allah ya tashi tona asirnsu aljana ce ta shiga jikin Ahmadu tun jiya take bashi wahala ita ce ta tilassa shi fad'ar gaskiya, ga malam Abubakar nan zaune shine yai magana da ita ta fad'a mana tun kana yaro take ba ka kariya duk wanda ya yi k'ok'arin cutarda kai sai ta kawarda shi a dalilin kakarka Jadda ta ta6a taimakonta a tunaninta mutum ce tun daga lokaci take bibbiyar al'amurranka. Da sauri Azaad Junaid ya d'ago kanshi ya kalli Ya Abubakar wanda duk cikin 'yan uwanshi tasu tafi zuwa d'aya. "Kwarai kuwa Azaad aljana ce ta kuma tabbatar mana da zarar ka zo sun fad'in gaskiya za ta bar jikin Ahmadu. Malam Abubakar ya fad'a fuskarshi shinfid'e da tausayin Azaad. Tsawon lokaci Azaad ya dauka shiru yana dafe da bakinshi ya rasa wacce kalma zai furta gaba d'aya al'amari ya zo mishi wani iri gani yake kamar al'mara da kyar ya rinjaye raunaniyar zuciyarshi ya ce. "Me nai muku da ku ka tsaneni har haka shin a cikinku akwai wanda nai wa wani laifi ne da na cancanci irin wannan hukunci daga gare ku?" Shiru suka yi ba wanda yake da kwarin gwiwar amsa mishi sai malam Abubakar ne ya amsa da cewa. "Ba abin da kayi musu Azaad tsabar hasada ce kawai da son zuciya, kuma gashinan inda son zuciyar tasu ya kai su sai ka k'ara godewa Allah da ya kare ka daga kaidinsu, ko a haka Allah yabarsu sun ga aya ya kuma zama izzina da masu irin hali nasu. Sosai furuncin malam Abubakar ya k'ara karyawa Azaad zuciya hawaye suka ci gaba da silalowa akan tattausan kumatunshi, ya kalle su d'aya baya d'aya kana cikin rauni murya ya ce. "Nagode wa Allah da ya kare ni daga sharrinku, kamar yadda ya Abubakar ya fad'a ko a haka kun ga aya 'yan uwana ne ku banida tamkar ku duk da kun kasance ba ku k'aunata ni ina sonku har abada ba zan ta6a sauya k'aunar da nake muku ba, saboda haka ku je na yafe muku. Gaba d'aya falon dauki amon sautin muryoyi daban-dabam saboda basu zaci zai yafe ciki sauki ba, saida Alhaji Abbas ya tsawata masu kana suka yi shiru malam Abubakar ya kai duba gun da Ahmadu yake kwance yana nishi d'addaya ya ce. "Ya ke wannan baiwar Allah ki yi hak'uri ki fita daga jikinshi domin wanda aka cutar ya furta da bakinshi ya yafe kamar yadda kika buk'ata. Azaad ya kar6e zance ta hanyar fad'ar. "Dan Allah ki fita daga jikinshi kuma na rok'e ki daga yau kada ki sake cutarda wani akaina. "Tabbas Azaad ka banbanta da sauran bil'adama kana da kyakkyawar zuciya in-sh-allah za ka yi farin ciki rayuwarka za ta cika da haske kadai k'ara jurewa ka kuma ci gaba da addu'a. Aljana Bahijja da ke jikin Ahmadu ta fad'a ta hanyar sautin muryasa daga haka tai musu sallama ta fita daga jikin Ahmadu yayin da jama'ar dake falon suka shiga ba Azaad hak'uri musanmman Ahmadu da Hasheem kuka suke yi kamar ransu ya fita. "Ku daina bani hak'uri ya isa haka gaba d'ayanku na yafe muku suma su Babban yaya ina musu fatan rahama ubangiji. Azaad ya fad'a yana d'an murmushi da bai wuce iya fatar bakinshi ba, ya mik'e yana cewa. "Ni zan tafi na bar Hakeem a k'ofar gida yana jirana na barku lafiya. Ya k'arashe magana tare da ficewa gaba d'ayansu suka bishi da kallo, tun kafin ya k'arasa wajen da suka yi parking mota ya hango Hakeem yana safa da marwa Hakeem yana hangonshi ya rugu da azama muryarshi tana rawa ya ce. "Aj ya aka yi ka jima a ciki? "Abubuwan ne suka yi kamari Hakeem bansan ta ina zan fara ba ka labari ba. "Aj ka jinginar da labarinan har mu sami natsuwa bayan shigar ka ciki aka kira d'aya daga cikin wayoyinka, da na duba mai kira sai naga Nanny Lacey ce sai kawai nai receiving hankalinta a tashe take fad'amin Salima ta je can gidan ta yi wa Miyya d'an banza duka har ta suma yanzu haka sun dauki Miyya zuwa asibiti...... 5/13/22, 21:24 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 38... Gaba d'aya jikin Azaad Junaid ya dauki rawa baisan lokaci da ya mik'e tsaye ba, sai faman yawo yake yi da idanuwanshi daga hoton jikin magazine zuwa da wanda Hakeem ya bashi ba ko tan-tama wannan matar ta jikin magazine da hoton da ke hannunshi na mahaifiyar Miyya ya yi kama sak da na jikin magazine miss Roseline Yaqub Gambella ce fitattaciyar 'yar kasuwa wacce tayi fice a duniya. Ba sai ya tsaya wahalarda kwakwalwarshi ba wurin tanttace kamanunta da Miyya ba saboda kamar tasu har ta 6ace da ka kalleta kasan ita ce mahaifiyarta saidai ita ta d'an tsofa sa6ani Miyya da ke da zallar kurciya amma duk da haka kamarsu d'aya sak. "Alhamdullilah.....Allah abin godiya ba ko shakka miss Gambella ce mahaifiyar prettyn Daddy na rasa ina zan jefa kaina saboda farin ciki Hakeem. "Lamarin ubangiji kenan Aj kawai mu ci gaba da godewa Allah da sannu al-amurranka za su dai-daita, yanzu ka bar komai a hannuna zan shirya mana tafiya zuwa Australian, saboda a bincike da nayi na gano tana zaune ne a Australian ba k'asarta, ta haihuwa ba Ethiopia. Gara mu je mu zo da ita a Nigeria aganina hakan zai fi saurin walwale mana matsalolinmu. "Shikenan Hakeem duk yadda ka tsara dai-dai ne zuciyata cike take da tsintsa farin ciki prettyna za ta had'u da mahaifiyarta, watakila a dalilin hakan za ta yafemin kashe mata mahaifi da nayi. "Koda ba ka had'ata da mahaifiyarta ba Aj in-sh-allah Aslamiyya ba za ta kulace ka ba, domin tasan k'addara yanzu ka tashi ka je ka ji neman da Alhaji Abbas yake maka Allah yasa alkhairi ne sa6ani abin da muke tunani. "Amin Hakeem amma tare za mu je saboda mr Richard yana wurin gyaran mota. "Okay ba damuwa tashi mu tafi. Shi kanshi direban yara ya shiga tashin hankali ba kad'an ba, lokaci da madam Salima ta sanarda shi buk'atarta na zuwa gidan da Azaad ya kai Miyya. Saidai bai isa ya bijirewa umarninta ba domin bijire mata yana nufi rasa aikinshi gaba d'aya. Da suka iso gate din gidan hannunshi har makyarkyata yake yi, da ya je danna horn security ya bud'e musu gate ya danno hancin motar a farfajiyar gidan da parking d'inshi da fitar Madam Salima duk lokaci d'aya tun da ya dauko ta yasan ba alkhairi bane ya kawo ta yanzu kuma da ta fice daga mota cikin sauri ya k'ara tabbatar da zarginshi. A tsorace ya fito daga cikin mota ya jingina jikinshi da motar ya bita da kallo ji yake kamar ya kira Azaad ya fad'a mishi zuwanta gidan amma tsoron hukunci da zai biyo ta kanshi ya hana shi. Ma'aikatan gidan sai faman gaidata suke yi kasantuwa sunsan matsayinta ga maigidan. Tana zuwa ta turo k'ofar shiga main parlour da karfin gaske cikin sa'a k'ofar ta bud'e yadda ta bude k'ofar ya janyo hankalin Nanny Lacey dake kitchen tana wanke-wanke da sauri ta fito tana goge hannunta da d'an k'aramin towel da kuzarinta ta fito amma tana arba da madam Salima ta kasa k'arasawa cikin parlour tai tsaye turusss tana mata kallon tsoro. "Zo nan munafukar banza har ni za ki ciwa amana Nanny Lacey na yarda dake amma kika munafuce ni. Kasa bin umarninta Nanny Lacey tayi sai ma tayi k'ok'arin komawa kitchen, a nufinta ta shiga kitchen ta kargame k'ofa kafin ta cimma manufarta madam Salima ta nufo wajenta da sauri ta cafko dantse hannunta tare da fizgota da mugun k'arfi kamar za ta raba hannunta da gangar jikinta ba k'aramin zafi Nanny Lacey ta ji ba. Har sai da ta rintse idanuwanta, sosai madam Salima ta zageta tasss ko kad'an bata raga mata ba hakan ba k'aramin konawa Nanny Lacey rai ya yi ba, abinka da zuciya batada k'ashi sai tai k'ok'arin maida mata martani ta hanyar fad'ar. "Madam ki daina gani laifi idan ma akwai mai laifi ce to ke ce, ni fa 'yar aikinku ce kawai. Daga ke har yalla6ai Azaad ina bin umarni duk abin da ku ka umarce ni saboda haka ki tuhume mijinki da laifi cin amanarki amma ba ni ba. Baki bud'e madam Salima ke kallon Nanny Lacey tana mamaki ina ta samu wannan kwarin gwiwar mayar mata da magana, duk tsawon shekaru da suka dauka tana aiki a gidanta bata ta6a musanya yawu da ita ba sai yau lallai idan bata yi da gaske ba hatta da 'yan aikinta za su rena ta saboda haka cikin tafarfasar zuciya ta wankewa Nanny fuska da tagwaye maruka a kuncinta na hagu da dama kana ta nunata da yatsa tana huci. "How dare you Lacey! Har ni za ki kalla ki fad'awa magana lallai kuwa k'arshen zamanki ya zo a gidanan, ai ba Azaad ya dauke aiki ba ni ce sanadin zuwanki kano saboda haka a yau d'inan za ki tattara komatsa ki, ki koma Jos. "Ban yi mamaki ba madam don kin mare fuskata, ban kuma yi mamaki jin irin wad'annan maganganu sun fito daga bakinki ba. Saboda nasan a irin halin da kika tsinci kanki fiyye da hakan ma za ki aikata saidai ina miki albishir da cewa idan kika ga na bar garin Kano yalla6ai Azaad ne ya sallame ni ba wai ke korarriyar gida ba. Daga haka Nanny Lacey ta juya dafe da kunceta, ta nufi kitchen yayin da Madam ta bita da ashariya. "To shikenan Nanny zan nuna miki ni nake da iko da gidanan da zaran na gama da tsinaniya yarinya nan akanki zan dawo sai nasa kin kwashe kashinki a hannu banza butulu. D'akunan da ke downstairs ta fara bi tana bubbudawa ko za ta ga Miyya, ta dai ci karo da Ahlam tana sharar barci abinta ko ta kanta bata bi ba. Ta haura upstairs tana bud'e d'aki na biyu wanda ya kasance na Azaad ta hango Miyya a kwance akan katafare gadon barcinsa, wani irin duhu ya mayewa ganinta jin k'arar bud'e k'ofa yasa ta kalli k'ofar shigowa tai tozali da wacce ko a mafalki bata ta6a zaton ganinta ba. Kafin tai wani yunk'uri Madam ta iso gunta daga kwance da ke ta saka hannuwanta biyu ta shak'e mata wuya saida taji tana kakarin mutuwa sannan ta saki mata wuya ta shiga zuba mata maruka a kumatunta tuni baki da hanci Miyya suka fashe jini sai zuba yake akan pillow da kanta yake kai. Da k'arfi madam Salima ta finciko ta ta yar6e ta akan tiles tasa k'afarta ta dinga ball da ita ihu da Miyya take yi ya isa kunne Nanny Lacey, da gudu ta shigo d'akin duk k'ok'arinta na gani ta kwaci Miyya abin yaci turu kasancewar Madam Salima tafi ta k'arfi nesa ba kusa ba. Daga k'arshe ma sai had'e su tai su biyu tana bugu kamar wata sabon kamun hauka. Gani haka ya sanya Nanny Lacey ta kwaci kanta tasake kwasa da gudu ta sauko k'asa, ta fita compound ta nemo agaji securities. Da madam Salima ta gaji da jingar Miyya ta cukume wuyan rigarta ta jawo ta a k'asa kamar dai kana jan dabba ba mutum d'an adam ba. A haka ta tattaka matattakala bene da ita a garin jan da take mata hannunta ya buge k'arfen da ke jikin bene ta kwalla k'ara mai tsananin gaske kana ta suma. Daga lokaci bata sake sani me ke faruwa ba. Koda Azaad ya iso family house babban falo ya cika taff da 'yan uwanshi, da shigowarshi ya bisu d'aya bayan d'aya yana basu hannu sun yi musabaha kafin ya nemi kujera ya zauna sai lokaci idanuwanshi suka yi mishi tozali da Ahmadu dake kwance a k'asa yana sauke numfashi d'addaya, sai kuma Hasheem da ke zaune a keken kuragu idanuwanshi sun yi jajir ga wani irin miyau mai yauk'i yana fita daga bakinshi. "Subhanalillah.....me yafaru da Hasheem shi da yake asibiti me ya kawo shi nan?" Shi kuma Ya Ahmadu me ya same shi ne, ko shima bashida lafiya ne?" Azaad ya fad'a fuskarshi dauke da tsagoron mamaki, yana kallon fuskar Alhaji Abdallah wanda shi yake facing da sauri Alhaji Abdallah ya kauda fuskarshi yayin da wasu hawaye bazata suka biyo kuncinsa. "Shine babban mak'asudin taruwar mu anan Azaad, daga Ahmadu har Hasheem sun tsinci kansu a wannan halin ta dalilinka. Ba wai iya su biyu kadai ba hatta da mutuwar babban yaya Alhaji Yusuf da amininsa Alhaji Babu... "Ni kuma Yaya? Azaad ya katse shi a razane har yana nuna k'irjinshi da yatsa, cikin matuk'ar mamaki ya sake fad'in. "Me ya alak'anta ni da mutuwar babban yaya da amininsa, balle halin da su Ya Ahmadu suke ciki?" Yaya Abbas kowa anan wurin yasan cewa babban yaya da Alhaji Buba accident suka yi Hasheem kuma wasu 'yan ta'adda da ba a san ko su waye ba suka har6eshi shi kanshi yace baisan su ba. Ya Ahmadu kuma bansan me ya faru dashi ba sai yanzu nan da na shigo na ganshi kwace a cikin wannan hali. "Kwantar da hankalinka Azaad duk Wanda ke cikin falonan yasan kai mutume kirki ne mai tsalkakkiyar zuciya, shiyasa ubangiji ya kare ka a duk lokaci da 'yan uwanka suka yi yunk'uri cutarda kai daga k'arshe ma sai kaik'ayi ne ya koma kan mashek'iya ga dai su nan a zaune su ba ka labarin abin da suka aikata da bakinsu waka a bakin mai ita yafi dad'in sauraro, ni kan ba zan arin bakinsu naci musu albasa ba gara ka ji daga bakinsu. Tirya-tirya Ahmadu ya shiga bankad'o sirrikansu daga nan kwance da yake wanda ba dasu cikin tafiyar ba suka dinga tafa hannuwa suna salati da sallalame tare da yi musu tofin Allah tsine, gaba d'aya falon ya kaure da hayaniyarsu. "Ya isa haka! Alhaji Abbas ya daka musu tsawa dole suka yi shiru ba don ransu yaso ba, yayin da Azaad Junaid ya sadda kanshi k'asa hawaye na bin kumatunshi biyu, yasan cewa 'yan uwanshi ba su k'aunarshi amma bai ta6a tsanmani kiyayyar tayi kamari har haka ba. Wani irin zafi yake ji can cikin k'asan zuciyarshi. "Azaad ka ji abin da 'yan uwanka na jini suka aikata maka domin babu bare a cikinsu, da Allah ya tashi tona asirnsu aljana ce ta shiga jikin Ahmadu tun jiya take bashi wahala ita ce ta tilassa shi fad'ar gaskiya, ga malam Abubakar nan zaune shine yai magana da ita ta fad'a mana tun kana yaro take ba ka kariya duk wanda ya yi k'ok'arin cutarda kai sai ta kawarda shi a dalilin kakarka Jadda ta ta6a taimakonta a tunaninta mutum ce tun daga lokaci take bibbiyar al'amurranka. Da sauri Azaad Junaid ya d'ago kanshi ya kalli Ya Abubakar wanda duk cikin 'yan uwanshi tasu tafi zuwa d'aya. "Kwarai kuwa Azaad aljana ce ta kuma tabbatar mana da zarar ka zo sun fad'in gaskiya za ta bar jikin Ahmadu. Malam Abubakar ya fad'a fuskarshi shinfid'e da tausayin Azaad. Tsawon lokaci Azaad ya dauka shiru yana dafe da bakinshi ya rasa wacce kalma zai furta gaba d'aya al'amari ya zo mishi wani iri gani yake kamar al'mara da kyar ya rinjaye raunaniyar zuciyarshi ya ce. "Me nai muku da ku ka tsaneni har haka shin a cikinku akwai wanda nai wa wani laifi ne da na cancanci irin wannan hukunci daga gare ku?" Shiru suka yi ba wanda yake da kwarin gwiwar amsa mishi sai malam Abubakar ne ya amsa da cewa. "Ba abin da kayi musu Azaad tsabar hasada ce kawai da son zuciya, kuma gashinan inda son zuciyar tasu ya kai su sai ka k'ara godewa Allah da ya kare ka daga kaidinsu, ko a haka Allah yabarsu sun ga aya ya kuma zama izzina da masu irin hali nasu. Sosai furuncin malam Abubakar ya k'ara karyawa Azaad zuciya hawaye suka ci gaba da silalowa akan tattausan kumatunshi, ya kalle su d'aya baya d'aya kana cikin rauni murya ya ce. "Nagode wa Allah da ya kare ni daga sharrinku, kamar yadda ya Abubakar ya fad'a ko a haka kun ga aya 'yan uwana ne ku banida tamkar ku duk da kun kasance ba ku k'aunata ni ina sonku har abada ba zan ta6a sauya k'aunar da nake muku ba, saboda haka ku je na yafe muku. Gaba d'aya falon dauki amon sautin muryoyi daban-dabam saboda basu zaci zai yafe ciki sauki ba, saida Alhaji Abbas ya tsawata masu kana suka yi shiru malam Abubakar ya kai duba gun da Ahmadu yake kwance yana nishi d'addaya ya ce. "Ya ke wannan baiwar Allah ki yi hak'uri ki fita daga jikinshi domin wanda aka cutar ya furta da bakinshi ya yafe kamar yadda kika buk'ata. Azaad ya kar6e zance ta hanyar fad'ar. "Dan Allah ki fita daga jikinshi kuma na rok'e ki daga yau kada ki sake cutarda wani akaina. "Tabbas Azaad ka banbanta da sauran bil'adama kana da kyakkyawar zuciya in-sh-allah za ka yi farin ciki rayuwarka za ta cika da haske kadai k'ara jurewa ka kuma ci gaba da addu'a. Aljana Bahijja da ke jikin Ahmadu ta fad'a ta hanyar sautin muryasa daga haka tai musu sallama ta fita daga jikin Ahmadu yayin da jama'ar dake falon suka shiga ba Azaad hak'uri musanmman Ahmadu da Hasheem kuka suke yi kamar ransu ya fita. "Ku daina bani hak'uri ya isa haka gaba d'ayanku na yafe muku suma su Babban yaya ina musu fatan rahama ubangiji. Azaad ya fad'a yana d'an murmushi da bai wuce iya fatar bakinshi ba, ya mik'e yana cewa. "Ni zan tafi na bar Hakeem a k'ofar gida yana jirana na barku lafiya. Ya k'arashe magana tare da ficewa gaba d'ayansu suka bishi da kallo, tun kafin ya k'arasa wajen da suka yi parking mota ya hango Hakeem yana safa da marwa Hakeem yana hangonshi ya rugu da azama muryarshi tana rawa ya ce. "Aj ya aka yi ka jima a ciki? "Abubuwan ne suka yi kamari Hakeem bansan ta ina zan fara ba ka labari ba. "Aj ka jinginar da labarinan har mu sami natsuwa bayan shigar ka ciki aka kira d'aya daga cikin wayoyinka, da na duba mai kira sai naga Nanny Lacey ce sai kawai nai receiving hankalinta a tashe take fad'amin Salima ta je can gidan ta yi wa Miyya d'an banza duka har ta suma yanzu haka sun dauki Miyya zuwa asibiti...... 5/14/22, 09:49 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 39... Lokaci da Salima ta zo k'arshen stairs bai wuce tako uku zuwa hudu sai kawai ta wulgo Miyya, ta dinga mulmula yayin da kanta ya buge last stairs jini ya yi tsirtuwa ya wanke gaba d'aya fuskarta. Koda securities d'in da Nanny Lacey ta je neman taimakonsu suka shigo madam Salima na ci gaba da ball da ita, da gudunsu suka yo kanta biyu daga cikinsu suka rirrik'e ta yayin da guda d'ayan ya tsuguna gaban Miyya ya kai hannunshi a hancita ya ji tana numfashi saboda a zatonshi ta mutu cikin sa'a ya ji da raguwar numfashi a jikinta. A rikice ya kinkimeta da gudu ya nufi k'ofar fita Nanny Lacey ta bishi a baya a gafe d'aya Madam Salima sai zabure-zabure take yi su saketa, ta k'arasa kashe Miyya had'i antaya masu zagi tare da alk'awali sai ta kore su aiki saida da suka ga an fita da Miyya sai kawai suka sake ta, da sauri direban yara ya jawo mota suka saka Miyya wacce bata da maraba da matattaciya koda madam Salima ta fito har motar ta fice gateman yana rufe gate ko kad'an ba haka taso ba. Cikin tsananin tashin hankali Azaad Junaid yake yawo da idanuwanshi da ke cike da zallar tsoro yana kallon Hakeem kamar bai fahimci abin da yake fad'a ba. Fizgo hannunshi Hakeem ya yi yasa shi a mota ya rufe k'ofa kana ya zagaya ya shiga ya tashi motar da k'arfi, koda suka iso hospital din zuciyar Azaad kamar za ta yaga k'irjinshi ta fito da Nanny Lacey ya fara ci karo gaba d'aya White long sleeve shirt da ke jikinta ta rine da jini sai zarya take yi daga bango gabans zuwa na yamma, tana gani Azaad ta fashe da kuka tare da durk'ushewa k'asa da hanzari Azaad ya kana kafand'uta biyu ya tashe ta tsaye cikin rikitatciyar murya ya ce. "Nanny Lacey wane hali pretty take ciki tana raye ko ta mutu ne Dan Allah ki fad'a min halin da take ciki?" "Bansani ba yalla6ai Azaad tun zuwanmu aka shiga da ita wannan d'akin sun tabbatar mana ba za su ta6a ta ba har sai mun zo da police saboda murder Case ne direban yara ya je ya zo da police din... Kafin ta rufe baki Azaad ya yi wuff ya fad'a d'akin da ta nuna mishi likitoci biyu had'i da nurses uku ya gani tsaye akan Aslamiyya sun dukufa akanta, ya tsaya cakkk tare da long breath ya sauke gaba d'aya hankalin likitoci da nurses din ya dawo kanshi, basu sha wahala gane shi kasancewar fitatce kuma sananne, tun kawota da su Nanny Lacey suka yi suka fad'in cewa matarshi ce shiyasa ma suka fara duba ta kafin zuwan Police din. "Yalla6ai dan Allah ka fita waje mu k'arasa aikinmu. D'aya daga cikin doctors din ya fad'a cikin low voice. Jiki a sanyaye Azaad ya juya ya fito dai-dai direban yara na isowa da zuga police domin su na ji Case d'in daga gidan young billionaire Azaad Junaid ne jikinsu na rawa suka ciko mota guda, cike da girmamawa suka gaida Azaad tare da tambayar shi suna so su dauki statement, k'ala Azaad bai ce dasu ba sai Nanny Lacey ce ta fad'a masu yadda abin ya faru da suka ji cewa uwargidan Azaad ce tai wannan aika-aika sai kawai suka dinga kallon Azaad su na jiran su ji ta bakinshi, Hakeem ne ya matso kusa da su ya umarce su da su tafi kawai tun da sun dauki statement d'in. Kana ya kama hannu Azaad suka koma gafe. "Aj please ka kwatar da hankali in-sh-allah ba abin da zai sami Aslamiyya... "Innalillahi wa'inna illaihim raji'um..... Azaad Junaid ya fad'a tare da dafe kokon kanshi, da yake jinsa tamkar ba a jikinshi yake ba. Kana cikin rauni murya ya ci gaba da fad'in. "Hakeem na ga jarabawa a rayuwata daga wannan sai wannan, miyasa Salima za ta nemi salwantarda rayuwar innocent girl ni ya dace ta kashe domin ni nayi mata laifi ba pretty ba. "Ana ta hauka ba za ta fahimci haka ba Aj, ni wallahi narasa jinsi da zan jefa Salima ciki, ga dak'ik'anci ga zallar dabbanci da zubda k'ima banta6a sani mahaukaciyar ka auro ba Aj sai yau, to da ta kashe 'yar mutane tana gani za ta sha ne?" "Ko yanzu Hakeem ba za ta sha ba jini prettyn Daddy ba zai zuba a banza ba, na rantse da Allah a wannan karo sai na nunawa Salima nima tantiri ne na k'arshen littafi, sai na wulak'antata wulakanci da ko sunana ta ji sai zuciyarta ta buga" "Gaskiya this time ina bayanka abokina gara ka nuna mata kuskureta na dakar maka mata. Azaad ya yi kwafa tare da cizo lower lips d'inshi, kusan one hour likitoci suka dauka akan Miyya, an mata dinki a gefen goshinta ga gocewa a hannunta na dama sai small injuries da ke sassan jikinta, bayan su kammala treatment d'inta aka kaita special room Azaad ya yi tsaye akanta yana kallon yadda fuskarta ta kumbure suntum gwanin ban tausayi, hawaye ya ji sun zo masa da sauri ya goge su bai barsu suka sauko ba. Ya kalli Nanny Lacey ya ce. "Nanny Lacey ki zauna tare da ita zan fita amma ba zan dad'e ba zan dawo "Okay Yalla6ai! Nanny Lacey ta fad'a jiki a mace ta nemi d'aya d'aga cikin kujeru d'akin ta zauna, Azaad ya kalli Hakeem ya ce. "Zo mu tafi Hakeem. Cikin sauri Hakeem ya bishi a baya. Lokaci da Salima ta fito compound ta kira direbanta mr michael ya zo ya dauke ta, kaitsaye babban masana'antarta ya kai ta hankalinta kwace ta gudanar da meeting da employees kamfaninta, tana fittowa direbanta ya sake daukarta suka fice daga company. Duk inda Azaad yake sa ran gani Salima ya je bai ganta ba lokaci da ya zo company aka ce dashi bata dad'e da fita ba, dole ya hak'ura ya umarce Hakeem su koma hospital har zuwa lokaci Miyya tana sharar barci. Hakeem ya umarce Nanny Lacey ta tashi ya maidata gida, saboda yara ranta baiso ba so tayi sai taga Miyya ta farfado suna ficewa Azaad ya nufi gadon da take kwace ya kura mata idanuwa kafin ya zauna ya riko hannunta cikin nashi sallah ce ke fidda shi daga d'akin bata falka ba sai around 4:40pm, lokaci Azaad ya shiga bathroom koda ya fito tana rarraba idanuwanta kusurwa-kusrwa d'akin cikin sanyi jiki Azaad ya iso wurinta. "Sannu pretty ashe kin falka na shiga bathroom ne?" Ajiyar zuciya tayi batare da ta ce uffan ba ta shiga k'ok'arin tashi zaune, ya taimaka mata tare da saka mata pillow a bayanta ta jingina kana ya had'a mata ruwan Lipton mai zafi da tea spoon ya dinga diba yana bata a baki, saida tasha sosai kana ya zuba mata abinci da Hakeem ya kawo masu. "Daddy kayi hak'uri Allah bai nufi zan girka maka abinci bud'a baki ba kamar yadda ka buk'ata amma idan naji sauki zan maka ka ji?" Kamar daga sama ya ji zazzakar muryarta a dodon kunnenshi, da sauri ya d'ago daga rufe warmer d'in da yake yi yaga gaba d'aya idanuwanta na kanshi, wani irin tsananin tausayinta da zazzafar soyayyarta suka lullu6enshi baisan lokaci da ya jawota jikinshi ya rungumeta gam. "Allah sarki prettyn Daddy kina cikin wannan hali amma kina tunanina, karki damu farin cikina fatana Allah ya ba ki lafiya kuma in-sh-allah sai na bi miki hakkinki sai na nunawa Salima kuskureta na ta6a min ke da tayi... Da sauri ta d'ago daga jikinshi ta rufe mishi baki da tafin hannunta. "Daddy Dan Allah ka yafe mata kada kayi mata komai, ko ba komai taci darajar 'ya'ya da ke tsakaninku.. "Ya isa pretty na fahimci ke bakisan ciwon kanki ba idan ba ki son kanki ni ina sonki fiyye da so da nake yi wa kaina, ba zan lamunci wata banza wacce ta gama wulak"antani ta nuna min ban isa ba ta ta6a min ke wallahi-azim a wannan karo sai naci zarafin Salima, koda kuwa mutane duniya ga baki d'aya za su taro akaina" Yadda taga yana fad'a ya bata tsoro ta shige jikinshi ta zagaye cikinshi da hannuwanta, ya k'ara shigarda ita k'irjinshi yana shafar gadon bayanta wata irin natsuwa suka ji tana saukar masu a cikin sassan jikinsu. Anan asibiti Azaad ya yi bud'a baki daga fitarshi masallaci kaitsaye gidanshi ya wuce a masallaci k'ofar gidanshi ya yi sallah magarib da isha'i, koda ya shiga gida 8:30pm tayi saboda ya tsaya waya da Hakeem direct d'akin Salima ya wuce yana tura k'ofa tana fitowa daga bathroom sanye da bathrope 5/16/22, 17:44 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 40... Duk da ganinshi da tai a dai-dai wannan lokacin. Ya haifar mata da matsananci fad'uwar gaba. Hakan baisa ta nuna a fuskarta ba, sai ma kallon uku saura kwabo da tai mishi kana ta nufi dressing mirror cikin tafiyarta mai cike da izza da zallar k'asaita tana mai ci gaba da goge sumar kanta da k'aramin towel d'in dake rik'e a hannunta. Ganinta da Azaad yai da kuma halin ko in kula da ta nuna masa ga wata izza da tak'ama da take yi, ya k'ara harzuk'a shi, a fusace ya maida k'ofa ya rufe tare da murza mata key ya kuma cire key d'in ya saka a aljihun rigarshi. Cikin kidima da tashin hankali Salima ta kalle shi da idanuwanta da a yanzu suka baiyanar da tsananin tsoratatta a fili, musanmman da taga yana tunk'arota fuskarshi a murtuk'e babu fara'a ko kad'an, duk tsawon shekaru da ta share tare dashi bata ta6a ganinshi a cikin irin yanayi nan ba. Shiyasa cikinta ya murd'a ya bada sauti mai k'arar gaske take taji gudanawa ya zo mata da son samu ne da ta ruga bathroom ta rage cikinta. Saidai tazarar dake tsakaninta da bathroom idan ta ce za ta ruga kafin ta kai k'ofar bathroom d'in yai mata kamun kazar kuku, ta tabbata wannan zuwan nashi bana alkhairi bane domin bahaushe ya ce labarin zuciya a tambaye fuska, yanayi fuskarshi kadai ya isa ya gamsar da ita manufarshi akanta ba mai kyau bace. Duk ta bi ta rud'e ta rasa abin yi can kuma ta shiga ja da baya tare da furta. "Me ya shigo da kai d'akina a dai-dai irin wannan lokaci ko ka manta ne da ka sake ni, a yanzu babu saura komai a tsaka.... Kafin ta k'arasa magana yai kukan kura ya dank'o wuyanta ya kaita jikin bango ya manna ta shiga ihu da neman dauki, saida ya tabbatar da ta jigata, sannan ya saki mata wuya kana ya had'e hannuwanta duka biyu da hannunshi guda, yasa d'ayan hannu ya shiga wanke mata fuska da maruka babu kakkautawa hanci da bakinta ya fashe sai zubda jini take, shi kuwa ko a jikinshi saida ya gaji da marinta kana ya saki hannunta ya bi ta da duka ta ko ina jingarta yake yi, ya murde mata hannu da dukkan karfinsa shi da kanshi ya ji lokaci da hannun nata ya ce kattt! Alamar da ke nuna ya goce ko ya karye tsananin ihu da kururuwar da take yi ya janyo hankali 'yan aiki da securities d'in gidan. Aneesah dake d'akinta a kwance damuwa ta fara yi mata yawa, kamar daga sama ta ji ihu mommy kamar da wasa ta ji ihu sai k'ara k'aruwa yake, babu shiri ta diro daga gado ta bud'e k'ofa da gudu ta fito koda ta iso main parlor ta tararda masu aiki da securities tsaye cirko-cirko kowane su yana tsoro ya shiga apartment din madam ya kira wa kansa ruwa. Da kallo Aneesah ta bisu dashi kafin ta sake kwasawa da gudun fanfalak'i ta haura matattakalar bene da zai sada da ta da apartment d'in mommy, da k'arfi ta tura k'ofar bedroom d'inta sai ta ji k'ofar a rufe ruff da dukkan k'arfinta ta shiga bugun k'ofar had'i da kiran sunanta. "Mommy... mommy meke faruwa me kike yi wa ihu ke da waye a d'akin Dan Allah mommy ki zo ki bud'e k'ofar nan?" Tun Aneesah tana magiya har ta dawo kuka da sauti mai k'arfi saboda sai k'ara jin ihu mommynta take yi, da alama tana cikin matuk'ar wahala. "Na shiga uku mommy idan ba ki bud'e k'ofar nan ba wallahi zuciyata za ta iya bugawa. Aneesah tai magana tare da gunji kuka, ta sulele k'asa dafe da kai, tun zuwanta Azaad ya ji muryarta 6acin ran da yake ciki ne ya hanashi daina dukan Salima yanzu kuma da ya ji sautin kukan Aneesah da farucin da tayi sai jikinshi yai sanyi ya saki Salima ta zube k'asa numfashinta yana fita guda-guda. Yasa k'afarshi yai mata mugun shuri a ciki sannan ya nufi k'ofar ya bud'e ido biyu yai da Aneesah wacce tana jin k'arar bud'ar k'ofa ta mik'e zubur, wani irin kallo take yi wa Daddy nata mai cike da tarin manufofi, batare da Azaad yai mata magana ba ya bi ta gefenta ya wuce cikin sauri. Cikin zallar tashin hankali ta bishi da kallo domin ko kusa ba ta kawo aranta shine a d'aki ba ta dawo da ganinta akan k'ofar d'aki da ya barta a bud'e, ta k'arasa shiga ta tararda da Mommy kwace magashiyan, tana fidda numfashi da kyar a rikice ta durk'usa tana girgiza ta tana kuka. "Mommy Dan Allah ki tashi mommy ki tashi mana Dan Allah karki mutu ki bar mu... Da ta fahimce hakan ba zai fishe ta ba sai kawai ta mik'e da gudu ta sauko downstairs parlour ta nemi taimakon housemaid da har yanzu suna nan tsaye duk da akan idanuwansu Yalla6ai Azaad ya sauko ya wuce su ko gaisuwa da suke masa bai amsa ba. Balle su tambaye shi dalilin ihun Madam Salima. Mr Michael da d'aya daga cikin securities d'in gidan ne suka taitayo Madam Salima wacce bata da ban-banci da gawa yadda take sanye da bathrope haka suka nufi asibiti da ita. Azaad yana fitowa direbanshi mr Richard ya bud'e mishi mota ya shiga, kaitsaye asibiti ya koma. Koda ya shiga d'akin da Miyya take tana zaune Nanny Lacey ta dora mata bowl din fruits salad akan pillow tana sha da d'ayan hannuta mai lafiya, ta d'ago idanuwanta a hankali ta sauke su akan fuskarshi batasan lokaci da tasaki masa tattausan murmushi ba. Ya mayar mata da martani amma fa shi nashi bai wuce iya fatar bakinshi ba. Nanny Lacey ta gaida shi ya amsa can k'asan mak'oshi kana ya zarce da fad'in. "Nanny ki je mr Richard yana waje ya maida ki gida, ki Kula da yara please" "Okay sir! Ta fad'a tare da tattara warmers d'in d'azu Hakeem ya kawo abinci ta tafi dasu. Kusa da ita ya zauna ya lek'a bowl d'in gabanta kafin ya kalle ta cike da kulawa ya ce. "Ya jikin naki prettyna?" "Na ji sauki Daddy saidai hannun ne kawai yake min ciwo sosai. Ya kai dubanshi ga hannun nata cikin sigar tausayawa ya ce. "In-sha-Allah shi ma very soon zai daina amma fa sai kinsa dauriya I know you my pretty you're very strong girl thats why I love you so much. Ya k'arashe magana tare da jan karan hancinta, murmushi tai mai sauti ta je sauke bowl d'in da sauri ya kar6a tare da tambayarta. "Kin k'oshi ne? Ta gyad'a kai still da murmushi akan fuskarta, ta matso a hankali ta kwantarda kanta a kafad'arshi, ya ajiye bowl d'in ya k'ara shigar da ita k'irjinshi lokaci zuwa lokaci suke ta6a fira. Likitoci suka dukafa akan madam Salima ba su sha wuya ba wajen farfado da ita, a bincike da suka yi sun gano ta karye a hannu. Kuma likitan k'ashi baya nan dole sai zuwa safe za su nemo shi haka aka turata a gadon marasa lafiya zuwa ke6attace d'aki, daga Aneesa sai Kuma mr Michael ne tare da ita anan suka kwana mr Michael yana waje a cikin mota Aneesah Kuma ta kwana akan cushion d'in da ke girke a d'akin sai a washe gari madam Salima ta dawo hayyacinta yayin da Aneesah ta tsare ta da tarin tambayoyi. "Mommy me ke faruwa ne tsakaninki da Daddy?" "Me kika yi wa Daddy da har ya harzuk'a shi ya lakkad'a miki irin wannan duka kamar bai san inda kika fito ba?" Madam Salima ta d'ago kumburarriyar fuskarta da ta dawo kamar ta doddaniya ta kalli Aneesah da idanuwanta da jini ya gama kwantawa a cikinsu ga Kuma bakinta da ya kumbura sutumm dama la66anta suna da d'an tudu yanzu kuma da suka sha masga sai abin ya k'ara armashi, cikin tsananin azaba da radadin da hannunta ke mata ta ce. "Banaso iskaci Princess ni sa'arki ce da za ki tsare ni da wasu stupid questions naki, nan da nace ki had'a kayanki ki koma gidan tsinane Daddy naki ai k'in bi umarni na kika yi to gashinan abin da nake gudu ne ya faru, shegiyar matarshi ta zugu shi ya zo har cikin d'akin barcina ya ci zarafina wallahi ba zan kyale shi ba sai na kai shi kotu ta bi min hakkina." Har ta dasa aya a zancenta Aneesah tana kallonta da baki bud'e, kafin ta rausayarda kanta gefe tana wasa da igiyoyin da ke gaban rigar barci da ke jikinta. "Anya kuwa mommy wannan labari naki akwai k'amshin gaskiya a cikinsa, shi fa Daddy ba mahaukaciya bane balle a zugu shi ya zo ya rufe ki da duka akwai dai mummuna abu da kika aikata masa mommy haka kawai Daddy ba zai zo ya dake ki ba. Aneesah tana rufe bakinta mommy na ridar pillow da hannunta mai lafiya ta jefa mata cikin tsananin fusata ta ce. "Banta6a sani Princess bakya k'aunata ba sai yau yanzu duk cin zarafina da Azaad ya yi akan idanuwanki amma Kuma shi kike supporting maza ki 6ace min da gani tun kafin na tattaro fushina na sauke shi akanki banza heartless wacce batasan zafin mahaifiyyarta ba. "Allah ya ba ki hak'uri mommy wallahi ban fad'in wannan maganar ba don na 6ata miki rai, kawai dai nasan dukan mace ba hali Daddy bane ko mu da ya haifa bai ta6a dukanmu ba, balle ke da kike tsohuwar matarshi, adai tsananta bincike akwai babban laifi da kika yi masa kowa ya kalli yadda ya sauya miki kamanu yasan ba k'aramin laifi kika masa ba. "Princess ni kike fad'awa wannan maganar?" "Mommy I'm sorry inasonki ne shiyasa nakeso ki gyara halinki ki dawo good mother to us wallahi mommy na fi ki jin zafi dukanki da Daddy yai amma hakan ba zai sa na dake gaskiya na goyi bayan k'arya?. "Fita ki bani wuri Aneesah kafin na ci uban naki da kike goyo bayansa, fita nace karki sake zuwa kusa dani gaba d'ayanku na yafe ku, kema ki bi sahun 'yan uwanki. "Mommy please stop saying that.... "Aneesah ki fita na daina ganinki before I loose my control nai miki abin da ubanki yai min, ki fita nace! Ta k'arashe magana cikin shouting da gudu Aneesah ta ridi takalmin ta a hannu ta bud'e k'ofa ta fita saboda ta tsoro da yadda mommy ta, haiyak'o mata kamar za ta cinye ta. Saida ta fita sannan tasa takalminta tare da gyara hular kanta cike da jin kunya ta ratso reception sai faman kallonta ake yi, duk wanda ya ganta da sleeping dress ai dole ya kalleta tana zuwa parking lot ta hango mr Michael zaune cikin mota da saurinta ta bud'e mota ta shiga. "Mr Michael mai dani gida" "Okay! Ya amsa tare da yi wa motar key baya ya sauke Aneesah ya dawo hospital d'in... 5/20/22, 08:35 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 41.... *BAYAN KWANA BIYAR* A cikin kwanaki biyar kacal Miyya ta fara samun sauki kasancewar tana sumun kyakkyawar kulawa daga 6angarori biyu doctors da Daddynta. Wanda tsabar kulawar da yake bata ko nan da can bayaso ya kusa kullum yana manne da ita. Hakan ba k'aramin k'ara ma su kusanci da shak'uwa ya yi ba. Azaad tare da Hakeem na hango a Aminu Kano international airport yayi da Azaad yake rik'e da hannun Hakeem cikin sanyi murya yake magana. "Nagode sosai Hakeem bakina ya kasa bari gode maka Kai amini ne nagari Wanda samun irinsa a wannan zamanin da yarda da aminci suka yi karanci yake da matukar wahala, Ina maka fatar alkhairi Allah ya tsare ka ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai cikin k'oshin lafiya. Murmushi Hakeem ya yi kana ya fizgo hannu Azaad ya rungume shi tare da d'an bubbuga bayanshi. "Amin thumma Amin abokina! Nima Ina maka fatar wanzuwar farin ciki mai dorewa sai na dawo ka ci gaba da kulawa da Aslamiyya Kuma karka manta da maganar da muka yi d'azu Dan Allah da zarar ka koma asibiti ka fad'a mata sirri da muke, 6oye mata domin banga amfani ci gaba da 6oye mata ba na fiso kafin na zo da miss Gambella ka sanarda ita kome. "Shi kenan abokina yanda kace haka za a yi. Daga haka suka yi Sallama a maimakon Azaad ya nufi hospital sai kawai ya wuce gida da nufi ya sake wanka sannan ya kar6i abincin Miyya. Mr Michael ya tura k'ofar d'akin da Madam Salima take kwance, hannunshi dauke da basket d'in abinci duk lokaci da Aneesah ta biyo Mr Michael sai Madam tai mata kashedi kada ta sake ganinta, jiya saura kiriss ta mareta shiyasa yau tak'i zuwa ta ba Mr Michael abincinta ya kawo mata, tsakani da Allah ta gaji da ji zagin da take yi ma Daddynta. Gaidata Mr Michael ya fara yi kafin ya ajiye basket d'in, ta amsa mishi as usual a wulak'ance har yanzu fuskarta tana nan a kumbure bakinta ne ya d'an rage shi ma ba sosai ba. "Mr Michael Ina ka baro Princess?" "Tana gida Madam. Shiru madam Salima tai tana nazari kafin tai kwafa. Mr Michael ya nemi wuri ya zauna yana wani musu-musu da baki had'i da sosa k'eya alamar akwai magana a bakinshi saidai baisan daga inda zai fara ba. Saida madam ta wulga masa harara saboda haushin kowa take ji, hatta da k'awarta Hafsat Shinkafi sun 6ata tun a washe gari da aka kawota hospital dalili kawai ta nuna Azaad ya fita gaskiya, kuma duka da yai mata bata ga laifinshi ba. Shi kenan ta rufe idanuwanta taci wa Hafsat mutunci had'i da yi mata k'orar kare tun daga ranar Hafsat Shinkafi bata sake dawowa dubata ba. "Ya aka yi ne Mr Michael akwai magana ne?" Da sauri ya gyad'a kanshi yai zubur ya mik'e tsaye kamar dama jira yake yi tai mishi magana, ya isa kusa da ita. "Madam ki yi hak'uri da abin da Yalla6ai Azaad yai miki, shiyasa na yanke shawarar zan ba ki wata dauka da nayi{video} zai miki matuk'ar amfani. Ya k'arashe magana tare da ciro wayarshi a gaban aljihun White shirt d'in jikinshi, ya kamo ya ui scrolling video da yake so nuna mata yasaka play ya mik'a mata. A yatsine ta kar6i wayar daga hannunshi tun kafin video ya zo k'arshe ta mik'e daga kwance da take, ta ma manta da ciwo da ke hannunta jikinta har wani rawa yake yi, yayin da ta firfitowa da idanuwanta cikin kad'uwa ta ce. "Tun tsawon wane lokaci Mr Michael kake dauke da wannan video?" "At last four to five days madam da farko naso nai blackmail d'in Yalla6ai Azaad dashi sai kuma ga wannan dukan da yai miki saboda haka inaso mu had'a hannu ki dauki fansarki cikin sauki. Kuma wannan video zai raba tsakani Yalla6ai da waccan yarinya. Murmushi Madam Salima tai sai taji gaba d'aya ciwo da take ji ya ragu wani irin k'arfi ta ji a jikinta, cike da izza ta shiga tsarawa Mr Michael yadda take so sabon plans d'inta ya tafi. Mr Michael yai murmushi mugunta ya kalleta da idanuwanshi masu cike da zallar mugunta ya ce. "Don't worry madam your work is done. "Thats what I like to hear from you make sure ba a sami matsala ba. Murmushi kawai yai ya fice daga d'aki. Azaad na shiga d'akinshi ya d'an kishigid'e akan resting chair tun waye war gari yake ji kasala da ciwon kai na damunshi nan take barci yai awon gaba dashi. Miyya tana zaune ita kadai akan gado a d'akin da aka yi admitted d'inta, duk ta bi ta damu da rashi gani Daddynta ko me ya hana shi dawowa wurinta tun asuba da ya fita ya ce da ita zai raka Hakeem Airport zai wakilce shi wani business trip a Australia gashi har Ten of o'clock ta buga bai dawo ba. Bai Kuma ta6a yi mata haka ba matsalar abin bata da waya balle ta kira shi ta ji ko lafiya. Tana cikin wannan tunani ta ji an bud'e k'ofa da sauri ta waiga tana murmushi azatota ko shine sai kawai tai tozali da Mr Michael. Sai ta ji duk ba dad'i har fuskarta ta sauya ga kuma gabanta da ta ji ya fad'i, ya k'araso tare da gaidata da jiki ta amsa mishi ya nemi kujera ya zauna yana wani rausayarda kai kamar kadangare tare da yi k'asa-k'asa murya ya ce. "Kina da labarin Madam Salima ita ma bata da lafiya?" "Subhanalillah! Ai kuwa Daddy ya manta bai gayamin ba meke damu ta ne?" Murmushi yai kafin ya kalli k'ofar shigowa saboda yana jin tsoro kada tsautsayi ya gitta Azaad ya shigo ya ji abin da yake shirin fad'a. "Ai Yalla6ai ba zai fad'a miki ba saboda dukanki da tayi ne ya janyo mata ya je har can gida ya yi mata mugun duka, sai ma kin ganta za ki zaci had'arin mota ne tayi gaba d'aya fuskarta tai damage abin ba ko kyau gani in takaice miki labari har da karya mata hannu ya yi. Cikin kad'uwa Miyya ta zaro idanuwa, bakinta har rawa yake yi wajen furta. "Ban fahimce ka ba Mr Michael Dan Allah ka yi min bayani ta yadda zan gane inda labarin naka ya dosa. "Ai ba za ki fahimta ba cikin sauki saboda ke Yalla6ai Azaad yana tsananin sonki, akanki zai iya aikata kissan kai domin saura kiriss ya kai madam lahira. Duk da nima ban ga laifin shi ba duk Madam ce ta jayowa kanta. Ya yi shiru tare da tsare Miyya da idanuwanshi yana karantar reaction d'inta, ya ga gaba d'aya fuskarta ta nuna alamar razana dama haka yake so tun farko yana da yak'ini ba zai sha wahala wurin dumilmiyar da tunaninta ba, musanmman da yai duba da k'anana shekarunta. Da ya fahimci ta fara afkawa tarkonshi sai kawai ya zage dantse ta hanyar ci gaba da fad'ar. "Ba ma wannan ba pretty azahirin gaskiya Ina tausaya miki domin akwai wani 6oyayye sirri da Yalla6ai Azaad ya 6oye miki Wanda ni aganina bai dace ya 6oye miki shi ba. Idan kuma aka yi duba a wani 6angare dole ne ya 6oye miki watakila bai shiryawa tunka'arar guguwar da ke shirin tunk'aroshi ba. Cikin mutuwar jiki had'i da fad'uwar gaba Miyya take kallon fuskar Mr Michael saboda ya fara tsorata ta, kafin tai k'arfi hali furta. "Watakila 6oyayye sirri bai shafe ni bane Shiyasa ya 6oye min. "Ba ko d'aya kawai dak yana 6oye miki ne. "To wai wannan wane irin sirri ne Mr Michael ni fa banaso katsalandan akan abin da bai shafe ni ba?" "Pretty ni fa ina magana ne akan kashe miki mahaifi da Yalla6ai Azaad ya yi, zan kuma tabbatar miki da zancena babu karya a cikinsa. Saidai ina rok'o ki da wannan ya zama sirri a tsakaninmu idan har maganar nan ta fita kashina ya bushe domin nima Yalla6ai Azaad zai iya kashe ni kamar yadda ya kashe mahaifinki. Tsananin tashin hankali yasa Miyya ta diro daga kan gado. Batasan lokaci da ta isa gaban Mr Michael ba. Zuciyata na wani irin bugawa, cikin sark'ewar lafazi ta shiga magana. "K'arya kake yi Mr Michael Daddy ba mugu bane kyakkyawan halinsa ba zai bar shi ya kashe koda kiyashi balle d'an adam ba. "Ni kaina pretty da farko kallon hakan nake masa amma tun daga ranar da naji yana fad'awa abokinsa Hakeem a waya shi ya kashe miki mahaifi nayi matukar girgiza, amma bari na tabbatar miki da zancena babu k'arya a ciki. Ya k'arashe magana tare da nuna mata video da ya dauka a lokaci da motar Azaad ta lalace ya dauko shi zuwa company akan hanyarsu yake waya da Hakeem anan yai nasarar d'aukar video da nufi yai blackmail d'in Azaad sai Kuma yanzu ya canza shawara saboda yana hange samu mak'udan k'udi daga hannun madam Salima fiyye da in ya yi blackmailing d'in Azaad. Wani irin wahalallen numfashi Miyya ta sauke, a lokaci d'aya hankali da tunaninta suka goshe. Jiri ya d'ibe ta tai baya kamar zai ta fad'i da sauri Mr Michael ya rik'o kafand'unta ya nufi gado ya zaunar da ita, hawaye masu matuk'ar zafi suka wanke mata kumatu yayin da wani irin kululun bakin ciki ya tokare mata mak'oshi. Mr Michael ya durkusa da guiwowinshi biyu a k'asa ya hade hannuwanshi waje d'aya ya k'ask'antar da murya ya shiga rok'onta. "Na rok'e ki pretty ki rufa min asiri kada ki fad'awa Yalla6ai Azaad ni ne na fad'a miki wannan magana. Domin sanarda shi zai iya kawo k'arshen rayuwata. "Kada ka damu Mr Michael no matter how ba zan anbace sunanka ba, amma wallahi tallahi k'arshen zama na da Daddy ya zo. Wai me Abbana yai mishi ne da zai kashe shi?" "Pretty amsar wannan tambayar tana bakinshi idan ya zo ki tutse shi ya fad'a miki laifin da yai mishi, saboda ni dai bani da wannan amsar. Zan tafi amma ina k'ara rok'onki kada sunana ya fito a wannan zance. Kukan da ya zo mata ne ya hanata amsa mishi sai gyad'a kanta tayi, Mr Michael ya bud'e k'ofa ya fita yana murmushi duk da ya yi nasara amma a k'asan zuciyarshi tsoro ne fal domin ba k'aramin risky ne ya jefa kanshi ba. Saidai akan k'udi ba irin hatsari da ba zai iya tunk'ara ba. Koda Azaad Junaid ya farka daga naunauye barci da ya dauke shi 11:47am shi kanshi ya yi mamaki irin barci da ya nad'a shiyasa a gurguje ya yi wanka ya shirya cikin blue sky men material ya fesa favorite perfumes d'inshi yasa takalmin sannan ya bud'e k'ofa ya fito dai-dai yana saukowa daga matattakalar bene Aneesah na turo k'ofar main parlour janye da k'aramin trolley a bayanta kuma direban yara ne janye da manya-manya trolley d'inta har guda biyu bai mamakin ganinta ko kadan ba domin yasan hakan ce za ta faru, ba yanda za a yi zamanta da madam Salima ya dore. Yana k'arasa saukowa ta rugu da gudu ta rungume shi tana dariya, murmushi kawai ya yi ya ciro ta daga jikinshi kasancewar yana sauri yasa kira Nanny Lacey ta miko mishi basket d'in abincin Miyya, ya umarce Aneesah ta biyo shi saboda san akwai magana a bakinta. Akan hanya take bashi lafiya yanda ta wakana a tsakaninta da Mommy kana ta zarce da fad'in. "Daddy wai laifi me mommy tai maka ne ka daketa har da k'arya mata hannu?" Shiru ya yi ya kasa magana saboda ko yaya aka tuna mishi da Salima sai ya ji sabuwar tsanarta da 6acin rai sun lullu6e shi. Saida ya ji 6acin ran nashi ya lafa kana ya ba Aneesah labari abin da ya faru. Bata yi mamaki ba domin tasan hali mommynta za ta aikata fiyye da hakan, a 6angare d'aya ta tausayawa Pretty. Koda suka iso hospital 12:21pm Azaad yana gaba Aneesah da Mr Richard na binsa a baya yana tura k'ofa...... *Dan girman Allah ku k'ara hak'uri saura kiriss mu zo k'arshen labarin* 6/2/22, 20:27 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 42.... Ba k'aramin farin ciki madam Salima ta yi ba lokaci da Mr Michael ya je mata da labari ya cika aikinta saura kawai su jira sakamako. Azaad yana tura k'ofa da sautin kukan Miyya ya fara cin karo a kid'ime ya isa wajenta ya juyo da ita sakamakon ta basu baya, gaba d'aya idanuwanta da fuskarta sun kumbura a dalili kukan da ta ci. "Subhanalillah....kuka me kike yi pretty kodai hannu ne ya mutsa?" Ya fad'a a rud'e tana juyowa ta buge mishi hannu da k'arfi, cikin muryar kuka take fad'ar. "Karka kuskura ka sake zuwa inda nake ko kayi yunkuri ta6ani, saboda na tsaneka banaso ganinka mugu mai kashe mutane. Rass...rass.....fass..fass! Sauti da ya dinga fitowa daga k'irjin Azaad kenan, wani irin tashin hankali ya kawo masa ziyara, kafin yai magana Aneesah ta ri ga shi ta hanyar dallawa Miyya harara saboda har ta ji haushi yadda ta gayawa Daddynta magana. "Ke pretty kin haukace ne da za ki dinga fad'awa Daddy irin wannan maganar sa'anki ne shi?" "Ke ce mahaukaciya Aneey ni nan rass nake Kuma wallahi tallahi ba zan ta6a yafewa Daddynki ba tun da ya kashe min Abbana ya maida mu k'ask'antattun marayu sai Allah ya bi mana hakkinmu. Azaad yai matuk'ar rud'ewa da jin kalaman da ke fita daga bakin Miyya mamaki yake yi ko waye ya fad'a mata wannan magana, domin daga shi sai ubangijinsa sai Kuma Hakeem ne suka san da wannan maganar. Hakeem Kuma bayanan balle yai tunani ko shine ya fad'a mata, ya kuma tabbata Hakeem ba zai furta wannan maganar ga kowa ba. "Dan Allah pretty ki dawo natsuwarki, kidaina yi wa Daddyna k'azafi domin ina da cikakke yak'ini akanshi ba zai iya kashe kowa ba. A fusace Miyya ta dawo gaban Azaad ta kalle shi da idanuwanta da ke tsiyaya hawaye ta ce. "Idan har abin da na fad'a ba gaskiya bane Daddy ka kalli cikin idanuwana ka k'arya ta hakan. Kasa had'a idanuwa da ita yai sai kawai ya kauda fuskarshi. Cikin sauri Aneesah ta kar6e zance. "Daddy ka kalleta mana ka fad'a mata ba kai bane tai gaggawa kawarda wannan mummuna k'azafi akanka ko wallahi tallahi na manta da cewa ita d'in matarka ce Kuma k'awa agare ni. Cikin raunin murya Azaad ya kalli Aneesah domin ba zai iya kallon Miyya ba ya fad'i maganar da yake shirin furtawa. "Ba k'azafi bane Princess ni na kashe mahaifinta amma walla.... "Ya isa Daddy dama abin da nake jira kenan ka amsa da bakinka tun da ka amsa shi kenan komai ya zo karshe a tsakaninmu. Miyya ta k'arasa magana cikin muryar kuka har tana shed'ewa, Azaad ya juya ya kalli Mr Richard wanda tun lokaci yake tsaye a bakin k'ofa rike da basket d'in abinci. "Mr Richard please ka maida Aneesah gida. Har Aneesah ta bud'e baki za ta yi magana Azaad ya dakatar da ita. "Princess ki tafi gida kawai kin ji?" Ta gyad'a kai tare da toshe bakinta sakamakon kukan da ya zo mata, suna ficewa Azaad ya nufi Miyya yai k'ok'arin rik'ota tai sauri ja da baya da ya ci gaba a da bin ta yana rok'onta ta saurare shi kawai ta rugu bathroom tai locking up d'in k'ofa. Cikin tsananin tashin hankali had'i da kid'imewa, yake dukan k'ofar yana fad'ar. "Pretty please open the damm door we have to talk, ya kamata ki tsaya ki saurare abin da zan fad'a kafin ki yanke min hukunci. "Ba abin da za ka fad'a min da zan sake yarda da kai Daddy ka tafi kawai banaso ganinka mugu kawai. Miyya ta mayar mishi da amsa ta cikin bathroom. "Dan Allah pretty ki taimaka ki bani koda three minutes ne na fad'a miki yadda al'amarin ya faru wallahi-azim ba da gan-gan na kade shi ba tsautsayi ne. "Dallah malam rufe min baki! Wannan kuma wata sabuwar k'arya ce za ka kirkikkira ni kuma bani da lokaci saurarenka gara tun wuri ka kama gabanka. Yanda tai mishi magana cikin tsawa ya ji zafin hakan ba k'adan ba shiyasa ya rufawa kanshi asiri ya koma bisa cushion ya zauna dafe da kai tun yanzu ta fara daka mishi tsawa baisan zuwa gaba abin da zai biyo ba. Miyya ta zauna dabass a k'asa tiles ta ci gaba da rare kukanta tanaso ta ji ta tsaneshi amma zuciya da gangar jikinta sun k'i amincewa da k'udurinta. Kiran sallar azhar da aka fara yasa Azaad mik'ewa ya bud'e k'ofa ya fita duk halin da ya tsince kanshi sam baya wasa da lukuta sallah. Miyya ta ji lokaci da ya bud'e k'ofa ya fita shiyasa tai zubur ta tashi cikin kuzarinta, ta bud'e k'ofa ta leko da kanta k'adan ta tabbatar da ya fita tai wufff ta fito, ta dauki hijabinta da take sallah tasaka ta bud'e k'ofar fita cikin sauri ta ratsa reception yanda ta fito cikin sauri kamar wata walkiya ta fice daga gate d'in asibiti. Tana shiga adaidaita Mr Richard ya hangota da sauri ya yi reverse ya bisu a baya. Duk fad'in garin kano bata da inda ya fi gidan Baffanta da Kakarta Dadda shiyasa kaitsaye can ta nufa koda za su kore ta ba inda za ta je gara ta zauna dasu da ta zauna da makashin Abbanta. Dai-dai k'ofar gida mai adaidaita yai parking ta ce ya jira ta ta kar6o mishi kud'insa, ta nufi cikin gidan tashin hankali da ta ciki ya dusashe wanda za ta, tarar a ciki tana shiga cikin gida, Mr Richard yana yin parking ya fito daga mota ya biya mai adaidaita, kana yai sauri komawa mota ya ja ya tafi. Tana shiga gida da Baffa Sani ta fara cin karo fuskarshi da dashin ruwa yana gyaran hannuwan rigar jikinshi da alamar arwala ya yi zai tafi masallaci tana ganinshi tun kafin yai mata magana ta durkusa tare da fashewa da wani irin kuka mai ta6a zuciya. "Subhanalillah! Aslamiyya daga ina kike me ya same ki naga jikinki duk bandaging?" "Baffa Dan Allah karka koreni ka rufa min asiri ka barni na zauna tare daku, bani da inda ya fi nan. "Kwatar da hankalinki Aslamiyya ki shiga gida ki jirani in nadawo daga masallaci ki yi min bayani a natse. "Tam! Baffa amma tare nake da mai adaidaita wallahi banida ko kwandala da zan biya shi yana nan k'ofar gida. "Shi kenan tashi ki shiga ciki in na tafi zan bashi. "Nagode! Baffa. Ta fad'a a sanyaye tare da mik'ewa duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hana mata mamakin sauyawa Baffa Sani ba. Kasa shiga d'akin Dadda tayi sai ta nemi jikin bango ta raku6e. Baffa Sani yana fita bai ga d'an adaidaita ba ya duba kudu da arewa bai ganshi ba, gudun kada ya rasa jam6i sallah ya wuce abinsa masallaci. Azaad yana gama sallah bai ko tsaya doguwar addu'a ba ya koma d'aki da Miyya take, yana tura k'ofa yai tozali da k'ofar bathroom a bud'e cikin kid'imewa ya k'arasa bathroom d'in yaga bata ciki da sauri ya fice daga d'akin cikin tafiyarshi ta k'asaita duk da yana cikin tsananin tashin hankali rashin ganinta a lokaci d'aya ba za ka iya fahimtar hakan ba. A natse ya tambaye nurses d'in da ke reception ko sun ga fitarta su ka ce ba su gani ba. Yana fitowa harabar asibitin Mr Richard yana parking mota. Baffa Sani yana shigowa gida ya hango Miyya raku6e a jikin bango d'akin Dadda, wani irin tausayinta had'i da nadamar abin da yai musu ita da 'yan uwanki uwanta ya lullu6e shi. Har idanuwanshi suka kawo kwalla cikin mutuwar jiki ya k'araso kusa da ita da sauri ta ciro kanta, ta dube shi da idanuwanta masu cike da zallar tsoro kafin tai magana ya rigata ta hanyar cewa. "Wuce mu shiga daga ciki. Ya shige gaba ta bishi a baya, suna shigowa Dadda na shafa addu'a ta juyo da baki bud'e tana kallonsu. "Sani ina ka fito da Aslamiyya hatsari tayi ko me naga jikinta duk ciwuka ne?" "Zuwanta kenan Dadda nima tambayar da nai mata kenan amma bata bani amsa ba. "Taho nan Aslamiyya bud'e baki ki fad'a mana meke faruwa da ke Ina kuma kika baro 'yan uwan naki?" Dadda tai magana tare da mik'a mata hannunta, a maimakon ta kama hannu kamar yadda Dadda ta buk'ata sai kawai ta durk'usa k'asa tana kuka tana basu labari abin da ya faru. "La'illaha illallahu muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasalaam! Dadda ta fad'a tana tafa hannuwa tare da zaro idanuwanta, nan take ta fara kuka yayin da fuskar Baffa Sani bata nuna ya razana da jin zance ba. Sai ma sadda kanshi k'asa da ya yi yana saurare kuka Miyya da Dadda. Tun washe gari ranar da Azaad ya fahimci mutume da ya ta6a kad'ewa mahaifin Aslamiyya ne shi da Hakeem suka zo wurin Baffa Sani basu 6oye masa komai ba. Da farko hauka ya dinga yi musu da sai daga bisani Hakeem ya shawo kanshi ya fahimce su, da suka nemi gani Dadda saboda ita ma bai kamata a 6oye mata ba. Yanayi rashin lafiyarta yasa Baffa Sani ya hanasu sai ya nuna masu zai fad'a mata da kanshi, tun daga ranar har izuwa yau nema yake hanyar da zai bi ya fad'a mata sai gashi Allah ya kawo Aslamiyya. Ya sauke numfashi kana ya d'ago idanuwanshi ya kalli yanda Dadda ke ta faman zabga kuka kamar wata k'aramar yarinya cikin taushin murya ya shiga rarrashinta tare da fad'a mata, yadda suka yi da Azaad da Hakeem ya zarce da fad'in. "Dadda ki yi hak'uri ki daina kuka komai muk'addari ne daga Allah... Tun kafin ya k'arashe magana Dadda ta tsula mishi casbin hannunta. "Rufe min baki dallah! Ban ta6a tsanmani sakarcinka Sani ya kai har haka ba, a kashe d'an uwanka kissan gilla ace da kai tsautsayi ne kuma ka hau ka zauna akai... "Wallahi Dadda yadda kike tsanmani ba haka bane, Usman ya ri ga da ya mutu addu'armu kadai yake buk'ata idan ma nace zan kai k'arar Alhaji Azaad ga hukuma nine zan kwana a ciki, sannan kafin na furta na yafe masa saida nai kwakwaran bincike akansa. Aka tabbatar min da shi din mutume kirki ne. Dadda mu kanmu masu laifi ne a wani gefe ma Alhaji Azaad ya fi mu saboda ya rik'e yaranan amana sa6ani mu da muka dinga gallaza masu. Kasa cewa komai Dadda tayi hakan ne ya ba wa Baffa Sani damar ci gaba da yi mata nasiha mai shiga ciki. Aike da aka yi masa ana sallama dashi a k'ofar gida yasa ya fita yabar Dadda da Miyya suna shar6ar hawaye Dadda ta mik'awa Miyya hannunta a wannan karo bata yi gardamar kamawa ba, Dadda ta jawo ta jikinta tana shafar sumar kanta wacce garin kuka d'an kwali kanta ya zame. Baffa Sani yana fita ya ci karo da Azaad Junaid tare da direbanshi mr Richard suna tsaye cirko-cirko, kallo d'aya yai ma Azaad ya gano irin zallar tashin hankali da yake ciki. Ya mik'a mishi hannu suka yi musabaha kafin Azaad ya shiga zayyane masa abin da yake tafe dashi. "Karka damu Yalla6ai in-sh-allah komai ya zo k'arshe zo mu shiga daga ciki mu yi magana a gaban Dadda. Baffa ya juya ciki yayin da Azaad Junaid yake binsa a baya daga Miyya har Dadda ba wanda ya amsa masa sallama, ya zauna akan kujera cikin taushin murya ya shiga ba Dadda hak'uri har ya gaji da magana Dadda bata tanka masa ba. Saida ta gama shan k'amshinta kafin ta furta ta yafe masa. Miyya ta mik'e zubur daga jikin Dadda ta ce. "Kin yafa masa kika ce Dadda?" "Kwarai kuwa Aslamiyya ubangiji muna masa laifi mu rok'e shi gafara mu sa ran zai yafe mana balle mu 'yan adam masu rauni, kema inaso ki yafewa mijinki kowa da irin tasa k'addara tashi k'addara ce ta zo da hakan. "Cab! Ni dai gaskiya ba zan yafe masa ba idan har ba da wata manufa ya kad'esa ba miyasa ya 6oye bai sanar mini ba?" Ta k'arasa magana tana harara Azaad da sauri ya mik'e da nufi ya rik'ota, ta rugu ta shige uwar d'akan Dadda har da su rufe k'ofa. Duk yadda Azaad yaso ta saurare shi abin yaci turu, sai bore take masa Dadda ta rarrashinshi da kalamai masu dad'i. "Kyaleta kawai wannan bore nata zallar kurciya ce ke damunta ba wani abu ba, ka barta zuwa gobe idan ta sauko sai ka dawo ka tafi da matarka. Azaad ya gyada kai azahirin gaskiya ba haka yaso ba saidai ba shi da za6i, ya yi wa Dadda sallama suka fito tare da Baffa har zuwa k'ofar gida ya dauko magungunata ya ba Baffa tare da d'aya daga cikin wayoyinsa akai mata tashi dabara watakila idan ta waya ne za ta saurare shi. Bayan tafiyar Azaad Dadda ta isko ta har cikin d'akin ta dinga bata magana, ba ta so ta tukura ta shiyasa da ta fara kuka ta kyaleta. Baffa Sani yana bata wayar tai switch off d'inta, ta jefa ta k'asan pillow da take kwance akai magani ma bata sha ba sai zubarwa tayi. Washe gari tun 8:00am dai-dai Azaad ya yi wa k'ofar gidansu Miyya tsinke, koda yaje tana barci haka yai ta zama a falon Dadda yana jiran ta falka sosai tausayinshi ya kama Dadda ta kawo mishi koko da k'osai saboda ko bai fad'a ba yadda yai wannan uban sammako bai karya kumallo ba. "Nagode Dadda amma ina azumi. Ya fad'a cikin taushin murya tare da sadda kanshi k'asa, addu'a sosai Dadda tai mishi a dai-dai lokaci Miyya ta falka jin Dadda tana zabga mishi addu'a haushi ya turnuk'e ta, ta sauko daga kan gado tasawa k'ofar sakata ta koma ta kwanta abinta. Ba yanda Dadda bata yi da ita ba ta bud'e k'ofar amma tai biriss, jikin Azaad a sanyaye ya baro gidan kaitsaye gidan Hakeem ya nufa, ya kwashe abin da ya faru ya sanarda da zaliha matar Hakeem. Tai mishi alk'awali da zarar Amrah da Amal sun dawo daga school za ta d'ibesu su je gidan Dadda ta ba Miyya magana ko za a dace ta sauko daga dokin nak'i da ta hau.. 6/2/22, 20:27 - Ummi Tandama😇: *AZAAD JUNAID* _{The young Billionaire}_ Na Jeeddah Aliyu Top Ten Takun Haske Batch:A *Wannan littafi na kud'i ne yana daya daga cikin top ten takun haske don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ba domin mallakar littafan mu guda bakwai sai a tuntu6e wannan number* +447894142004 43... *K'ARSHEN LABARI...* *Australian* Cikin hukunci ubangiji Hakeem ya isa lafiya ya hau taxi ta kaishi hotel d'in da ya yi booking, sai a washe gari da ya sauka a garin ya fara processed d'in gani Miss Gambella kasancewar bai da appointment da ita shiyasa ya sha matuk'ar wahala don sai da ya kwana uku a garin kafin ya had'u da ita a katafare gidanta a guest room aka saukarda shi, bayan housemaid ta kawo mishi ruwa da lemo sannan Miss Gambella ta shigo suka gaisa a mutunce. Kafin Hakeem ya fito da envelope mai dauke da hotunan Miyya da twins ya mik'a mata, tana tozali da yaranta hankalinta ya tashi ta shiga rera kuka. *Nigeria* A washe gari ranar suka nufo Nigeria a cikin private jet d'inta, kwatsam Azaad ya gansu ba k'aramin farin ciki ya yi ba. Saboda tun tafiyar Hakeem sau d'aya suka yi waya. A gidan Hakeem suka yi mata masauki Bayan miss Roseline Yaqub Gambella ta huta Hakeem ya kira twins suna shigowa falon da take suka yi turuss suna kallonta, tun kafin a gabatar masu da ita suka ji a jikinsu suna da kyakkyawar alaqa da ita. Miss Gambella tana gani yaranta da ta gudu ta barsu suna da watani a duniya a yanzu sun girma har sun zama 'yan mata cikin sauri ta iso gare su ta had'e su dukkansu biyu ta rungume tare da rushewa da kuka bayan sun gama koke-kokensu suka duguma duka zuwa gidan Dadda anan ma wani sabon shafi suka bud'e na kuka musanmman Miyya da ta tsinci kanta kwance yau a jikin mahaifiyarta tana jin d'uminta Bayan komai ya lafa Dadda da Baffa Sani suka sake neman gafarar Miyya da twins. Suka Kuma kar6i Miss Gambella da hannu bibbiyu babu kyama balle tozarci ba kamar yadda suka yi mata a shekaru baya ba. Duk abin da ake yi Miyya bata ga Daddy ba tana so ta tambaye uncle Hakeem amma tana kunya abin da tai masa sai kawai ta hadiye abin da take ji. Har a washe gari bata ganshi ba daga nan ta fara shiga damuwa, Miss Gambella da kanta ta nemi Hakeem da ya kira mata manema labarai{press} ta gabatar da yaranta so take duniya tasan da zaman su. Hafsat Shinkafi tana zaune a office d'inta newspaper d'in yau ce a hannunta shafi farko tai tozali da abin da ya hartsuna mata tunani, jikinta har rawa yake yi nan take ta fito, direbanta ya kawo ta hospital wurin Madam Salima tana zuwa ta jefa mata newspaper d'in tare da murmushin mugunta. "Salima tayani gani yarinyar da kika rena kika ci wa zarafi a yanzu tai miki fintikau idan kuma kika yi wasa ba wai iya lafiyar jikinki da kika rasa saboda ita b. Hatta da dukiyar da kike tink'aho da za ki iya rasata, in takaici miki labari Aslamiyya 'ya ce ga Miss Gambella mace mafi rinjaye hannun jari a babban kamfaninki idan har ta sami labari irin wulak'anci da kika yi wa 'yarta to fa! K'aryarki ta k'are. Jikin Madam Salima ya dauki rawa a tsorace take kallon hoton fuskokin miss Gambella da su Miyya, ji take kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu tabbas zance Hafsat shinkafi gaskiya ne tak'are mata. Hafsat Shinkafi tana fita Mr Michael yana shigowa hankalinshi a tashe, yayin da hannunshi na hagu yake rik'e da bak'ar Jarida kamar yadda Madam Salima tai mata lakabi dashi. "Mun shiga uku Madam asirinmu yana dabb da tonuwa idan har Yalla6ai Azaad yasan cewa nine na nunawa Pretty wannan video, kashina ya bushe a yanzu mafita guda d'aya ta rage mana ki bani kud'ad'e da kika yi min alk'awali idan da hali amaimakon 20 millions sai bani 30 millions na bar garinan shine kawai final decision. Wani mugun kallo Madam Salima ta watsa masa kafin ta hayyako masa kamar za ta wanke masa fuska da mari. "Lallai mr Michael ba kada hankali aiki me uban me kayi min da zan dauki wadannan makudan kud'i na ba ka?" To bari ka ji wallahi tallahi ko kwadalla ta ba zan ba ka ba d'an 419 kawai dallah fita ka bani wuri nace ka fita! Ta k'arasa magana cikin shouting da sauri ya nufi k'ofar fita har ya bud'e sai kuma ya juyo ya kalleta da idanuwanshi da suka rikide zuwa jajayye yai mata kallon tausayi ya ce. "I'm sorry madam k'arshen ki ya zo sai na nuna miki ba a ci amanata sannan Kuma a zauna lafiya, sai na rushe duk wani abu da kike tink'aho da shi. Sai nasaki kuka da babu hawaye. Wani irin mashahurin tsoro ne ya kama madam Salima, tsawon rayuwarta bata ta6a jin irinsa ba cikin sauri ta bi bayanshi tana d'igishi da k'afa tare da kwada mishi kira yana juyowa ya cilla mata key d'in motarta a fuska, ya sake juyawa cikin sauri ya fice daga asibitin. Yau kusan sati d'aya da zuwan Miss Gambella ta siye tangamemen gida a nassarawa GRA ta tare ita da yaranta har ma da Dadda wacce yanzu ta dawo mai matuk'ar sanyi hali da kirki kamar ba Dadda da mu ka sani a baya ba. Yau tun safe da Miyya ta tashi take ji wani irin kewar Daddy ji take idan bata ganshi ba za ta iya zarewa, ta sha kiran layukanshi da wayar da ya bata amma baya picking kasancewar yau weekend ne Miss Gambella tana d'akinta haka ma Dadda 'yan biyu kuma tun jiya suka tafi gidan Uncle Hakeem. Cikim sauri Miyya ta sauko daga gado, ta dauki hijab da 1k had'i da wayar da Daddy ya bata, ta fice daga gidan cikin sauri. Masu gadi ne kawai suka ga fitarta. Ta hau adaidaita a bakin gate d'in gidan Azaad Junaid aka sauke ta duka ta mik'awa d'an adaidaita 1k d'in, yai mata godiya kana ya kama gabanshi. Bata wuce knocking d'in gate biyu zuwa uku ba, d'aya daga cikin securities d'in gidan ya bud'e k'aramar kofa ya lek'o da kanshi yana gani ita ce yai maza ya k'arasa bud'e k'ofar, ta shigo suka gaisa ta wuce cikin gida dai-dai main door ta hadu da Mr Richard yana ganinta ya fara zabga murmushi, ita kuma ta galla masa harara saboda shi ma fushin da take da Daddy ya shafe shi tun da ya ga hakan ya fahimce manufarta ya gaidata ta amsa tana kumbura baki. Tana shiga babban parlour tai tozali da Airah tana zaune rik'e da mug d'in tea. "Pretty oyoyoyo! Ga prettyn Daddy ta dawo Nanny Lacey fito ki gani wallahi prettynmu ce ta dawo. Airah ta fad'a cikin ihun farin ciki ta dire mug d'in tea akan center table ta rugu suka rungume juna, Nanny Lacey ta fito daga kitchen fuskarta lullu6e da farin ciki, Aneesah da ke d'akinta ta ji lokaci da Airah take ihu had'i da kiran sunan pretty, da sauri ta yaye duvet d'in jikinta ta fito da gudunta, ita ma tana zuwa ta had'e Miyya da Airah ta rungumesu. Gaba d'aya ihunsu ya cika parlour. "Prettynmu kin dawo kenan ko?" Airah ta tambaye Miyya a lokaci da suka zauna. Murmushi kawai Miyya tayi saboda batasan amsar da za ta bata ba. Sai kawai ta ce. "Ina Baby Ahlam?" "Tana barci. Aneesah ta bata amsa. Da Nanny Lacey ta kammala arranging table suka yi breakfast a tare, sai lokaci tai k'asa da murya tare da kallon gefen da Aneesah take ta ce. "Aneey tun zuwana gidannan ban ji motsi Daddy ba ko baya gida ne?" "Yana bedroom d'inshi kinsan azumi yake yi bai cika saukowa k'asa ba, sai lokaci bud'a baki yake saukowa. Ajiyar zuciya Miyya tayi ko kusa ba za ta iya jure har zuwa lokaci bud'a baki ba sannan ta ganshi, da suka kammala breakfast Airah ta wuce d'akinta tayi wanka Aneesah da Miyya kuma suka shiga study room, Aneesah tana duba wani littafi tayi zurfi sosai yayin da Miyya kan tayi nisa a cikin tunanin Daddynta sai wasa take da bango littafin hannunta, sake kallon gefen da Aneesah take tayi sai taga hankalinta yana ga karatun da take yi, sai kawai ta mik'e ta fice daga room d'in koda ta fito babu kowa a falon k'asa, cikin sauri ta haura upstairs kaitaye apartment d'inshi ta nufa ta wuce falo na d'aya da na biyu ta kutse kai a Master bedroom d'inshi, tana tura k'ofa dai-dai yana fitowa daga wanka yana daure da towel. Kamar wacce aka jefo daga sama haka ya ganta don shi har ta tsorata shi ko kusa bai yi zaton ganinta a dai-dai wannan lokaci ba. Shawarar Dadda ce ya dauka shine hana shi zuwa gunta dama Dadda ta gayamishi yana zaune zai ga Miyya ta kawo kanta da farko ya dauko zanceta ne kawai na tsofa ashe maganarta za ta zama gaskiya. Kallo-kallo suka shiga yi wa junansu sosai ta ga ya yi rama sai d'an uban kyau da kwar jini da ya k'ara yi mata, da gudu ta rugu ta fad'a k'irjinshi kyakkyawar runguma tai mishi ya rasa tsakani ita da towel d'inshi wa zai kama, da kyar ya yi jaruntar rik'e su dukka biyun. K'ok'arin cire ta yake yi daga jikinshi yana murmushi, ita kuma sai k'ara mak'alk'ale mishi take yi tana kukan shagwa6a cikin kunnenta ya rad'a mata. "Pretty azumi nake yi kada ki 6ata min azumi mana, ni kaina rungumar nan bata isheni ba amma a duba yanayin da azumina zai shiga" Da sauri ta janye jikinta tasa gefen hijabinta ta rufe fuskarta tana dariya sai da ya gyara d'aurin towel d'inshi kana ya rik'o hannunta suka zauna a gefen gado, kallonta yake yi fuskarshi ta cika da yalwatatce murmushi. "Nayi mamaki ganinki a gidannan pretty ban yi zato za ki dawo gareni cikin sauki ba?" "Nima ban yi zaton zan dawo cikin sauki ba sai gashi zazzafar soyayyarka ta hanani sukuni, basan lokaci da na saci jiki na zo gidanan ba. Ta fad'a tana kallonshi tana dariya mai ban sha'awa, yai sauri kai mata kiss a kumatunta na dama kafin ya mik'e ya shiga dressing room ya shirya cikin White colour d'in jallabiya koda ya fito ta cire hijabin jikinta, tana tattara masa takardu da ya zubar ko ina a cikin d'akin. Ganinta kawai da Azaad ya yi ya ji wani irin sauyi a jikinshi ya k'ara tabbatarwa da Miyya ita ce cikon farin cikinsa. Tun shigarta d'akin bata sauko k'asa ba tana manne da Daddynta, shi Kuma lokaci zuwa lokaci yake tunatarda ita azuminshi ita kan abin dariya yake bata. A can gidan kuma hankalin Miss Gambella ya tashi matuk'ar da ta nemi Miyya ta rasa, gudun kada tashi hankalin Dadda yasa bata yi saurin fad'a mata ba. Sai kawai ta kira Hakeem shi kuma Hakeem ya kira Azaad a lokaci ya yi matashin kai da ciyoyin Miyya ita kuma tana damuk'ar sumar kanshi wai kitso take yi mishi shi Kuma sai biye mata yake yi kamar wani k'aramin yaro. Yana gani Hakeem ya kira shi yasan kwanan zance yana yin picking up yasa dariya. "Aslamiyya ta dawo kuma kuna tare kenan?" Hakeem ya fad'a shi ma yana dariya. "Ya aka yi kayi saurin ganowa, Hakeem kodai kana duba ne bansaniba?" "Ba ko d'aya kawai dai wannan dariya nasan kana yi ta ne kadai idan kana tare da Aslamiyya. "Lallai ka fahimce ni abokina fiyye da yadda na fahimci kaina, banida kalamar da zan furta wajen gode ma. Ina maka fatar alkhairi abokina ka yi addu'a Miyya ta sami ciki mu ka yi ma takwara. Sosai Hakeem yake tintsirar dariya kafin ya ce. "Ba shakka Aj abin naka ya girmama to kadai tuna da kana azumi gudun kada kayi abin ashar! "Mtss! Ka dauka nima jarabbabe ne irinka?" "Ai abokin barawo, barawo ne ni da kai kwayar sama ce ke dukan ta k'asa, ka kuma tabbatar ka kira Miss Gambella ka fad'a mata inda ka sakad'e mata 'ya ni dai ba ruwana. Kafin Azaad ya sake yin magana Hakeem ya datse kiran, ya kalli Miyya ya ga ta turo baki cikin shagwa6a ta ce. "Ni ma ba ruwana ka kirata ka fad'a mata na dawo gidan mijina kenan ba kuma abin da zai fitarda ni a cikinsa sai mutuwa. Farin cikin sosai kalamanta suka haifar masa baisan sanda yasa hannunwanshi duka biyu ya zagaye waist d'inta ba. Suka sa dariya. Farin ciki suke ji sosai kamar ba su ta6a shiga 6acin rai da bak'in ciki ba. Mr Michael yana baro asibiti ya nemi wani hotel nesa da gari ya kama d'aki, saida dare ya raba tsaka irin around 3 o'clock ya fice daga hotel d'in kaitaye babban kamfanin Madam Salima ya yi wa tsinke, ya koma can bayan company ta yadda masu gadi ba za su ganshi ba. Ya zagaye lungu da sak'o na wuri da fetur ya cilla lighter akan idanunshi company ya kama da wuta, ya dinga cilla gallon d'in fetur a ciki yadda wutar za ta k'azanta. Ai kuwa ta k'azanta fire alarm sai kararawa yake yi kafin fire service su zo company ya k'one kurmus! Toka kawai yai saura. A takaice saida Mr Michael ya bi duk wani kamfaninta da manya-manya malls ya k'ona ya kuma tsire abinsa. Lokaci da labari ya riske madam Salima take furucin Mr Michael ya dawo mata, shi kenan duk dukiyar da take tink'aho da ita wacce tai shekaru tana fafutukar nema, tana tarawa ta kuna wofitar da igiyoyin aurenta da yaranta akanta cikin rana d'aya ta rasa ta. Nan take ta yanke jiki ta fad'i inda Allah ya taimake ta tana cikin asibiti da sai abin yafi muni rabin jikinta ya daina aiki kuma a tsagin da hannunta ya karye. Madam Salima ta dawo abin tausayi ita da matatciya basu da ban-banci suna tana raye ne kawai sai lokaci mahaifiyyarta da 'yan uwanta suka gano aurenta ya mutu har Azaad Junaid ya yi aure, ba k'aramin bakin ciki haka suka yi mata ba domin sun sa shi kenan ta rasa komai nata. Watani biyu Miss Gambella tayi a Nigeria kafin ta koma Australia da ta tashi tafiya da twins da Dadda ta taho da su anan twins za su ci gaba da karatunsu yara sun dawo 'yan gata gaba da baya. Azaad da Miyya rayuwa ta masu dad'i basu da sauran wata damuwa, ko a gaban waye bata jin kunya nuna mishi kulawarta da soyayyarta. Cikin hukunci ubangiji suna kammala final exams ta fara laulayin ciki. Azaad ya yi musu visa daga ita har yaranshi da Kakarshi Jadda suka nufi k'asar Australian kafin su wuce sai da suka biya ta gidan iyayyen Madam Salima inda take jinya har yau ba wani sauki saboda bata magana bata kuma gane kowa. Aneesah tasa kuka a duk lokaci da ta kawowa Madam ziyara da kuka take komawa gida, ita kanta Miyya bata zaci jikin nata ya yi tsananin har haka ba tun daga lokaci da kwanta jinya bata ganta ba sai yau daga Miyya har Jadda tsohuwar mai ran karfe kuka suke taya Aneesah gani sun taro suna kuka yasa Airah ta shiga tayasu baby Ahlam kan batasan wainar da ake toyawa ba. Gani haka yasa Azaad ya umarce su da su tashi su tafi kada su yi missing flight. A cikin dare jirginsu ya yi landing Miss Gambella ta tura tsadaddun motoci na alfama aka dauko su daga airport, tarba ta musanmman aka yi musu a gidanta lokaci da Miyya ta ga Dadda zaro idanuwa tayi cikin kad'uwa ta ce. "Dadda ina tsufanki gaba d'aya naga kin canza min kin dawo yarinya d'ayya sharaf! Gaba d'aya aka sa dariya Dadda ta shiga matsar hawaye tare da fad'in. "Bari kawai Aslamiyya ni kadai nasan irin kulawar da nake samu daga wurin Roseline, koda Usman yana duniya iya abin da zai yi min kenan. Da sauri Miyya ta rungume Dadda tana dariya. Wata irin rayuwa mai cike da zallar farin ciki suke gudanarwa a Australian kasancewar Azaad Junaid yana da gida anan shiyasa suka saki jiki gani yadda suke jin dad'in garin yasa Azaad ya yanke shawarar su zauna, zama na din-din. Hakan ba k'aramin farin ciki Miyya da su Aneesah suka yi ba. Rayuwa ta dawo musu sabuwa duk wani bak'in ciki da kunci da Azaad Junaid yake ciki a yanzu ya kau, a Koda yaushe ka ganshi yana ciki walwala da farin ciki. Cikin Miyya na da wata uku aka yi mata scanning likitoci suka tabbatar mata da 'yan uku ne{triplets} ita kan abin tsoro ya bata yayin da family d'inta ke murna da farin ciki musanmman uban gayya tun a asibiti ya kira Hakeem ya sanar mishi tun daga lokaci kulawar da yake bata ta linka ta baya linki-ba-linki. Hakan yasa ya dauko Nanny Lacey ita ma ta dawo Australia da zama. Idan ka ga yadda ciki Miyya ya yi girma ya rinjaye ta ga ta dama tana da manya nonuwa sai abin ya k'ara armashi {lol} cikinta yana da wata bakwai a duniya cikin dare nakuda ta taso mata suna zuwa asibiti nan take aka yi mata cs aka ciro Babys dukkansu maza, ranar kamar Azaad zai zare saboda murna da farin ciki a ranar ya yi wa Hakeem kyauta ta musanmman wacce tai matuk'ar girgiza kwakwalwar da tunaninsa ya mallaka mishi kamfanoninsa har guda biyu d'aya a China do d'aya kuma a gida Nigeria sai tangamemen gida aljannar duniya a babban birnin tarayya Abuja Hakeem har da kuka sai da ya yi. Baffa Sani ma ba a barshi a baya ba shima Azaad yasa an rusa gidanshi a sake gina mishi na zamani ya bashi mota ya kuma ba yaranshi biyu maza aiki a d'aya daga cikin manyan companies d'inshi. Ranar suna yara suka ci sunan Junaid shine babba suna kira shi da Ansar sai Usman me sunan mahaifin Miyya shi Kuma suna kira shi da Affan sai Abdul-Hakeem suna kira shi da Abdul. Yaran sun tashi cikin gata da kulawa ta kowa ne 6angare washe gari sunansu ne miss Gambella ta kar6i musulunci karki so kike ga farin ciki wurin wad'annan iyalin, Dadda ta fi kowa murna don har da kukanta musanmman da tuna da furucin da mahaifin Miyya yake mata a koda yaushe. "Ki yi hak'uri Dadda ki kar6i Roseline a haka ba Wanda ya isa ya shiryarda wanda Allah bai shiryarsuwa ba, idan Allah yaso ta da shiriya wata rana za ki ga ta kar6i musulunci. Sai gashi Usman baya duniya amma furuncinsa ya zama gaske. Inda Roseline ta tashi daga sunanta ta koma Aminatu. A gida Kuma Nigeria madam Salima ba abin da ya sauya kullum ciwonta gaba-gaba yake yi lamarin nata har ya shafi kwakwalwar ta. Duk d'an abin da ya rage na daga cikin dukiyarta ya k'ari wajen nema mata magani. Triplets na da shekaru hudu yayin da Miyya tana shekarar k'arshe a karatunta. Ta sake haihuwar d'a namiji yaci sunan Muhammad Azaad suka yi masa laqabi da little Daddy. Dama burin Azaad Junaid kenan ya tara iyali masu yawa sakamakon shi kadai mahaifiyarshi ta haifa, yayin da ita ma ita kadai Jadda ta haifa shiyasa bashida buri da ya wuce a haifa masa 'ya'ya, duk wani abu da Azaad Junaid ya rasa Saida ubangiji ya dawo masa da madadinsa. Shiyasa a koda yaushe cikin godiyar ubangiji yake. Aneesah ta kammala karatunta ta zama cikakkiyar likitan yara, Airah Kuma tana shekarar k'arshe a secondary school. Lokaci da Aneesah tayi graduation ta nemi alfarma a wuri Daddy za ta je Nigeria ta duba mommy bai hanata ba, washe gari ta d'aga sai Nigeria a cikin kwanaki da tayi a Nigeria cikin hukunci ubangiji Madam Salima tafara samun sauki tafara gane, mutane musanmman Aneesah don har tambayar ta Airah da Ahlam tayi. Hakan ba k'aramin haifar masu da farin ciki ya yi ba ashe saukin tafiya ne a cikin dare ciwonta ya tashi tun kafin su isa asibiti Madam Salima ta kar6i kiran mahalincinta. Aneesah ta sha kuka kamar za ta yi hauka sai aka rasa tsakaninta da Hafsat Shinkafi wacce tafi shiga tashin hankali, saboda tun lokaci da madam Salima ta kwanta jinya Hafsat Shinkafi take tare da ita har izuwa yau da ALLAH ya kar6i ranta. Sai a ranar sadakar uku Azaad Junaid ya iso Nigeria tare da iyalinsa. Saida aka yi sadakar bakwai sannan suka koma Australia. Haka suka ci gaba da gudanar rayuwarsu cikin tattalin juna had'i da zallar farin ciki, little Daddy yana da shekara biyar a duniya sannan Miyya ta sake haifar d'iya mace koda ta haihu Azaad bayanan ya tafi wani business trip a Ukraine. Koda ya dawo har Miyya da Aneesah sun rad'awa yarinya suna Salima little mommy, bai yi mamaki ba don Miyya ta yi wa Madam Salima takwara saboda yasan tsananin kirkinta da kawaicinta za ta aikata fiyye da hakan. A lokaci Miyya da Aneesah suka kirkikkira kungiya ta tallafawa marayu da gajiyyayu mai sunan Madam Salima foundation, sosai kungiyar tasu ke ba da tallafi ga mabuk'ata su yi hakan ne da nufi Allah ya kai haske kabarin Madam Salima. Miyya sanye cikin had'add'u riga da wando na barci masu masifar jan hankali tasha kwalliya ta ban mamaki kamar ba mai jego ba, sai uban k'amshin take zubawa. Kaitaye d'akin Azaad ta nufa tana tura k'ofa ta hango shi kwance akan gado yana ganinta ya mik'e zaune ya mik'a mata hannunshi ta kama, ya fizgota ta fad'a jikinshi yai mata kyakkyawar runguma, kana ya d'ago fuskarta ma'a6ociya kyau ya had'e bakinshi da nata yayin da ita ma cikin kwarewa ta shiga taya shi, gani yana k'ok'arin tsallaka border yasa ta shiga yi masa ihu. "Wayyo Allah na shiga uku please Daddy ka daina jego nake yi, banaso Dan Allah ka bari har nayi arba'in. "Ba arba'in ba sittuna za ki yi ni fa yau sabon ango ne ki yi ihu iya k'arfinki ba Wanda ya isa ya canza hakan... Kafin ta an kara har ya yi nasarar rabata da kayan jikinta duka ta dawo naked ya kashe bulb nan take d'akin ya guraye da duhu daga nan nace...... *TAMMAT BI-HAMDILLAH* MA-SHA-ALLAH DAMA DUK ABIN DA YA YI FARKO CIKIN HUKUNCI UBANGIJI YANA DA K'ARSHE NI MA ANAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN LABARI MAI TAKEN AZAAD JUNAID the young Billionaire KURAKURAI DA KE CIKINSA INA ROK'ON ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA YA YAFE MIN ABIN DA NA FAD'A DAI-DAI ALLAH YASA YA AMFANE NI DA MUSULMI BAKI D'AYA.