HALIN RAYUWA 1 NA 07035586299 HAJ. HAFSAT C. SODANGI (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) 1 Hakkin Mallaka [m] Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat C. Sodangi ne GODIYA Godiyata har kullum ga Allah take Subhanahu ta'ala mai kowa mai komai, Makadaici, Mahalicci wanda a ke nufa da dukkan bukatu gwani mai hikima wanda yayi halittarsa bisa tsari na aure wato mace da namiji. Tsira da aminci su kara tabbata ga cikamakin Annabawa, shugaban Manzanni Annabin karshe Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe, wato ranar rarrabewa tsakanin karya da gaskiya (AIkiyama), Ubangiji yasa mu dace. Har wayau ina mika godiyata ta musamman ga daukacin makaranta littattafaee cikin kasa da waje, Ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karfafa zumuncin da ke tsakaninmu. Na gode, Haj. Hafsat C. Sodangi 6/7/1434 GODIYA Godiya mai dumbin yawa gare ki. Rabi'atu Faruk Jauro (Ministry of Commerce and Industry Yola, Adamawa State) Da Zainab Sunusi Kofar Gabas Danbatta, Zainab Abarshi Yawuri 2 HALIN RAYUWA A duk sanda naci karo da wata kalma da ta danganci rayuwa gabana kan fadi in tsinci kaina cikin wani matsayi na tsoro da razana, wani lokaci ma in ji na samu kaina cikin halin da zuciyata kan samu kanta cikin yanayi na kaikawo saboda tunawa da al'amuran da suka shafi jiyana da yau dina, in suke jin wani mummunan faduwar gaban idan na tunan ba ni da tabbatas ko masu niya bisa gobena. A mafi yawancin lokaci kuma in har nayi irin wannan tunanin to nakan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sanya mana wani tabbataccen al'amari ba in dai cikin wannann rayuwar tamu ne ta wannan dunyar, duk abinda ka gani zai wuce. Farin ciki ko bakin ciki yana da lokaci, komai yayi farko wata rana zai yi karshe. Wani karin maganar ma sai ya ce abin da ya baka tsoro a yau babu mamaki gobe ya baka tausayi, wasu ma da suka yi wa rayuwa irin fahimtar da suka yi wwa rayuwa irin fahimtar da suka yi mata sai suka ce wai ita din tamfar hawainiya ta ke, ta kan iya canza launinta a kowane lokaci. Al'amuran da na gani a shekaruna na kuruciya sun sanya ni son bayar da labarina ga na kasa dani ba don wani labarin dadin bayarwa 3 ke gare shi ba, a'a sai dai don ya zamo hannunka mai sanda a gare su. Ya zamo musu wani darasi da za su rika don su kauce daga aikata kurarai irin na kuruciya kurarai da kan zamo tanfar na tsalle daya mai jefa mai shi rijiya. Wannan labari da nake nufin bayarwa a yau labari ne da ya danganci halin da rayuwata ta kasance shekaru talatin baya da suka wuce a lokacin da na ke da shekaru tara kacal a duniya. Ni Maryam Abubakar, na taso ne a gidanmu gaban iyayena uwa da uba cikin gata kulawa da kuma tarbiya, a wantcan lokacin da nake magana a kai iyayena uwa da uha suna matukar sona musamman ma Babana wanda Sunan Mahaifiyarshi ke gare ni bisa hakanne ma bai fadin sunan nawa sai yake kirana da kalma ta Yacuwuna' kalmar da ke nufin ohaifiva ko uwa cikin harshen barbarci. Wani dalilin da ya kara tsananin soyayyarshi gare ni ko in ce muni da Yayata Khadija wacce take ta girme ni da yawa, don a lokacin da nake da shekaru. taranne a ka yi bukinta da wani saurayinta da suka so juna tun suna 'yan yara, Ibrahim shi ne din bai da kowa sai mu, nai da dangi ko kuma in ce ya dade rabonshi da yayi mu'amalla da su ba ya ma maganarsu. 4 Nasha jin Innata a wancan lokacin tana ce mishi Mallam ko ba don mu ba kai ni wurin 'yan uwannan namu in gano su saboda yaran nan su gansu su ban iyayensu da danginsu saboda in mu ne yau ba mu ne gobe ba, su kuwa dangi musamman na uba ko don maganin gori a neme su. A mafi yawancin lokaci ta kan yi irin wadannan maganganunne har ta gama ba tare da ya tanka mata ko ya ce mata uffan ba. Sai dai wannan bayani da nayi a kan Babana bai hana shi zamowa daga cikin mutanen kirki ba, mutumn ne mai tsananin hakuri mai gudun bacin ran wani, mai girmama makwabci wanda ba ya shiga harkar da ba tashi ba, ba mai yawan magana ba ne mafi yawancin lokaci hirarshi takan yi nisa ne kawai da makwabcinshi Mallam Hodijo wanda suka zama tanfar yan uwa shi da shi ga shi kuma sai aka yi dace Babana Babarbare ne wanda ko zanen da ke fuskarshi ya isa ya bayyanar da asalinshi. Haka shima Mallam Hodijo Bafulatani ne da bai bukatar sain an tsaya bayani a kan shi, don haka sai abin nasu ya kara zamowa gwanin sha'awa kullum a cikin zolayar junansu suke suna raha tare da barkwancin wasan fulani da 5 Barebari, haka kuma alaka take tsakanin Innata da matar Mallam Hodijo mai suna sumaye. Wani dalilin da ya karawa Babana sonmu ni da 'yar uwar tawa shine, kasancewar matarshi mata mai wabin 'ya'ya cikin haihuwa bakwai da aka yi ne aka samu mu biyun muka rayu. Rashin sanin dangin Babana ko rashin mu'amallar da su bai hana gidanmu zamo wa gidana Jama'a ba Innata mai 'yan uwa ce ban da haka kuma mata ce da ta iya mu'amalla da mutane da ke kuma iyakacin kokarinta wajen kiyaye hakkin makwabtanta. Ita din kuma mata ce da yawan mu'amallarta da 'ya'yan da ba nata ba, ya zamo dalilin da ta zamo uwar yara da yawa maza kuma da mata kanana da kuma 'yan samari. Gwanar kitson ce da kuma lalle bata laima da kwiya kan hakan sannan bata taba damuwa dayi don a biya ta ba, don haka kullum ta zaunar da ni da nufin yi min kitso ko lalle to zata hada ne da duk yaran da muke wasa da su a wannan lokacin tayi mana kitso da lallen tare da wannan dalili sai tayi sabo da iyaye da yawa na yaran da take yi mana kitson nan ko lallen tare wasu daga uwa godiya bayan sun aiko mata da abin hasafi ta mayar su biyo baya. 6 Wasu yaran da ta zamo uwa gare su kuma musamman yan mazan daga yawan ciyarwarta ne tana ganin yaro cikin wani zata zaunar da shi ta zuba mishi abinci in har ya yarda yaci zata gaya mishi gobe ma kazo daga haka har sai zuwaa wurin nata ya zame mishi jiki ko kuma dabi'a, don haka a ko ina yara suka ga Inna za ka ji suna Mama' Mama ina za ki? Mama kin dawo? Mama kin ga wane ko? Hatta wasu iyayen yaran da suka san Inna uwa ce a wurin 'ya'yansu, za ka ji suna gaya mata laifin yaran nasu don nufin ta taya su yi musu fada kan laifuffukan nasu kko kuma kin da suke yi wa makaranta. Cikin yaran da Inna ke yin mu'amallah mai karfi da su akwai Mubarak da Mansur wadanda su ba suna zuwa wurinta don cin tuwonta bane a'a sukam ma yan gata ne a gidajensu musamman Mubarak wanda shi shi kadai ne da namiji a gidansu a wurin kuma ubanshi Alhaji Mühammadu wanda a unguwar tamu duka babu maigidan da ya kai nashi girma da kuma kyau. To haka shima Mansur ko da suke da yawa a gidansu gidan nasu na rufin asiri ne, su suna zuwa wurin Inna ne kawai saboda gidannata ya zamo wurin zuwan yaran unguwar har kuma sai ka ji suna tambayarta Mama da wani abu ne mai dan dumi in akwai ta ce akwai in babu ta ce sai 7 garin rogo, wani lokacin ma har sai ka ji tana yi musu fada kan abin da tasan suna yi musamman Mubarak, kusan kullum ya shigo za ka ji tana tambayarshi kaje Makarantar ko yau ma ba ka je ba? In yaje ya ce yaje in bai je ba ya dan tsuke fuska yana yi mata bayani Mama ke ba za ki gane ba ne? ta ce Eh, ba zan gane ba in ba ka gaya min damuwarka ba amma in har za ka bude baki ka gaya min ai zanfahimci daidai gwargwado, tayi mishi nasiha lyayena ba masu hali ba ne, amma a cikin rufin asiri muke rayuwarmu, sana'ar Babana sana'a ce ta rufin asii, kayañ miya yake sayarwa a saman layinmu ba sni da tsawwalawa.kan kayanshi, don haka wurin nashi matattara ce ta cinikin yara. Mallam ban tumatir, Mallatu han attarugu, Mallam ban alayyaho, aikin ke nan. Don naka inhar ban je Makaranta ko gidan Yaya Dijah ba to yawanci na kan je wurinshi ne in rinka taya shi in yana bada kaya in rinka karbar mishi kudi saboda wasu yaran da tarbiya bata ishe su ba sukan karbi kayan miyan su tafi ba tare da sun ba shi kudin ba saboda ganin hankalinsi ya tafi wajen masu kokarin ya ba su nasu. Babana ba mutum ba ne mai dogon buri ko mako game da kudi, don hakan kullum ya dawo 8 daga kasuwarshi ya kan tattara duk cinikin nashi ne ya mika mata ko kuma ni ya miko min in shirya su in je in ajiye su a inda nasan tana adana kudi. Shi kuma ba mai yawan sa ido kan abubuwa ba ne, balle ka ji shi yana kididdiga ko tuhuma, don haka kusan komai Inna ce take tafiyarwa tana ganin wani rami a çikin gidanmu za ka ji ta kira wani daga cikin samarin da suke shigowa wurinta ta basu kudi ta ce maza suyo siminti ka toshe mnin wannan wurin. In kwata ce take nema ia cika zata sa su nemo mai kwasheta ya gyara suyi ciniki ya kwashe ta basu kudin suje su biya haka nan rufin kwano in ta hango alamar zuwan damina zata basu kudin foti su sayo su nemo mata mai hawa kwanon ya kara bin kusoshi da fotin din maganin yoyo. Haka nan kuma ko wata hidima ce ta taso bata jiran Babana sai dai ta ce mishi an yi kaza an yi kaza ko da kuwa ta sallah ce ko azumi ya ce mata to, ko da kuwa a kan shi ne zata yi tayi mishi tuni musamman da sallah, Mallam in fa baka sayi yadi ka bada dinkinka yanzu ba zaka rasa dinki, ya ce mata to don na rasa dinki menene tunda dai ke da yaran kun samu ai shi ke nan. 9 Tayi murmushi ta ce, Haba Mallam ana hidimar sallah ai zan so nima in ga mijina fes in Rara jin dadi da yiwa Ubangiji godiya, yayi kamar bai ji ta ba. Inna da makwabciyarta Babah Sumaye wani irin zama suke yi da yafi na 'yan uwan da babu fahimta da kauna ta zumunci a tsakaninsu dadi. Kusan kullum sai wata fa shigo wurin wata duk abin da suka girka sai sun aikewa juna, wata rana ma ka ji daya tana cewa dayar in za ki yi girki kiyi tare da nan gidan, don kasala nake ji ko kuma aiki zai yi min yawa-za a yi abu kaza da kaza su ce to. To haka Babana yake da mallam Hodijo ko'ina za su suna tare ko da kuwa Masallaci ne kullum kuma naje karbo cefanen gidanmu, to nakan hado ne da na gidan su Babah Sumaye. Innata ba wata jaruma ba ce in dai a kan neman kudi ne bata da wata sana'a da take yi ta maida taro ya zama sisi anima tana cikin wadata saboda halin mijinta na komai nashi a wurinta yake ajiye shi bai da kuma matsala don ta ce mishi ta kashe kaza kan abu kaza na hidima da ya taso haka nan ita din gwana ce kwarai ta shirya abinci mai dadi aci shima Baban nawa mai son cin dadin ne. 10 Sannan ta iya zama da shi ta iya tarairayarshi da tattalinshi duk da shi ba mai yawan magana ba ne, ko yawan dariya amma in suna tare shi da ita fuskarshi bata rabo da murnmushi, bini-bini kuma za ka ji shi yana yawan ambaton sunanta Ramatu. Gidanmu karamin gida ne dan madaidaici, dakuna hudu ne a ciki, ciki da falo guda daya wanda ni da Inna muke ciki, sai dai-dai guda biyu, daya Babana daya kuma tarkace na kwandunan tumatir din Babana da sauran kayayyakin Inna na aiki, kullum ka shigo gidanmu daga zauren gidan ka ke soma shakar kamshin turaren Innata. Ana cikin hakanne aka wayi gari a gidan namu Inna tana wani irin rashin lafiya da Babana yayi ta zarya yayi ta zirga-zirga da dawainiya mai yawa a kai, cikin wani irin farin ciki da zumudi mai yawa. Haka nan itama Babah Sumaye tayi ta hidima aikin gidanmu gaba daya ya zama nata, ta rinka kai kawo tana ta faman murna ashe, ashe wai Innar tawa wani cikin ne da ita, ni kam nayi farin ciki saboda ganin zan samu kani wata kila mace watakila namiji, wanda dama nasan Babana yana Son samunshi. 11 Sai dai kuma gabana ya fadi da na tuna da irin haihuwar da Innan tayi shekara guda da ya wuce inda ta kubuta da kyar. Kankana, abarba, lemo da ayaba basa yankewa a gidanmu, saboda kullum sai Mallam Hodijo ya kawo ya ce a kawo mata saboda abin sana'arshi ke nan a bakin asibitin garinmu. Haka a ka yi ta fama da ita har dai ta samu sauki ta wartsake ta koma kan al'amuranta. Muna nan a haka har cikin Inna ya bayyana ya fito sosai, dama kuma ita din mai katon ciki ne ina jin ta rannan a hirar da suke yi tana gaya mishi ni dai ban taba jin ciki irin wannan ba Mallam, ko kuma don mutum ya fara girma ne yake jin hakan oho. Yayi murmushi ya ce, "Ramatu ke nan, kina yar shekaru talatin da biyar kina gayawa kanki girma da kuma ni ne nayi kuskuren ba ki nace miki kin girma da kin ce.na hango wata yarinyar ne a waje yáa sani kiranki tsohuwa." Tayi murmushi ta ce, "Uhun! Mallam ke nan, to tunda a ka yi auren yarinyar nan kuwa har gata yanzu da juna biyu ai dole in kirawa kaina girma ni da kaina." Ya tayata murmushin kafin ya sake kallonta Cikin natsuwa ya ce mata, ai ba Dija ce mizanin da za ki rinka dubawa wajen gane girmanki ba, 12 ni za ki rinka dubawa ai ni ne ma'aurinki ya ya ki ke a wurina? Shi ne maganarki, ya ya nake kallonki? Shi ya kamata ya zama abin lurarki,to in kuwa ni ne ban taba kallonki na gane canzawarki ko bambancin da ke tsakaninki a yau da na ranar da mahaifinki ya kira ni ya ce min in dawo da yamma inga 'yar da yake da ita in tayi min in kawo sadaki a daura min aure da ita babu wata rana da nake wayar gari ko zan wayi gari ban yi wa wannan mutumin kirki addu'a ba Ramatu." Ta kalle shi ta dan yi murmushi ta ce, Uhun kai Mallam babu halin in kawo maka wata magana sai ka kawo wannan zancen ya ce, Eh ai bana gajiya da bada labarin ne saboda ya bani abin da ban taba tsammanin samu ba na kar6i aurenki cikin tsananin tsoro saboda nayi zaton za ki bijire sai kuma ki ka zamo yarinya mai albarka mai ladabi da biyayya, mai sanin darajar iyaye da aurenki. Tunda ki ka zo wurina ban taba ganin wani al'amari daga gare ki ba sai na alheri." Shiru Inna tayi tana sauraronshi sai da ya gaji ya canza zancen don kanshi ni nafi zaton canjin da kike ji din wata kila da namiji ne ai kin san gaba daya haihuwar nan da a ka yi in ban da na farin sauran 13 shidan duk mata ne amma tunda kin ce kina da damuwa to tashi kawai muje asibiti." Tayi maza ta ce ka ji Mallam kuma shekaran jiya ne fa naje awo suka kuma ce min babu matsala, iyaka dai in dan rage cin gishiri da barkono." Haka rayuwar Inna da Babana take kullum a cikin ganin alherinta yake, bai daga ido ya kalli wani al'amarinta ba balle ya gano kuskurenta baida wani labari wanda ya wuce na fadin alherin mahaifinta saboda ba shi ita da yayi ba tare da shi din ya neme ta ba ya kuma ba shi ita tana da shekaru goma sha biyar a duniya, bayan kuma gata da manema masu yawa da suke fatan ganin an ba su aurenta. Kullum Babana a cikin sayayyar haihuwar Inna yake komai ya gani ya bashi sha'awa zai sayo yazo da shi gida, rannan ina jin ta tana ce mishi wannan kayan fa Mallam yawansu ya isa haka. Kuma ma ni sai nafi son a hakura da sayayyar haka sai an ga an yi haihuwar tukuna saboda ni dai Mallam zuciyata a tsinke take game da haihuwar nan. Yayi maza ya dago ido ya kalleta za ki fara ko Ramatu? Kin san irin fadar min da gaban da kike yi kuwa idan kina furta irin wadannan 14 kalaman? Kin sani sarai ai kin uma san abinda kike yi in yi kike yi don in ji dadi kin sani, in ma don me kike yi kin sani. Kin sani sarai bani da kowa bani kuma da yan 'ya'yannan naki amma sai ki rinka gaya min maganganun da zan rinka hawa gadona da daddare ina kasa yin bacci saboda lissafe- lissafen al'amura. Tayi murmushi ta ce, "To kayi hakuri Mallam bari in je in kawo maka abincinka." Bai saki fuska ba ya ce, To wane abinci kumna zan ci ni yanzu bayan kin gaya min wannan maganar." Ta sake yin wani murmushin ta ce, "Kayi hakuri Mallam ba zan sake yin ba amma da wannan katon cikin nawa da wannan kwalliyar da nayi don ka ji dadi in girka abinci don kai ka ce ba za ka ci ba ai kai ma kasan in na soma fushi zan dade ban huce ba, burabusko fa nayi maka da miyar yakuwa, ta kuma sha kashi da tantakwashin ga kuma nama ka gani?" Ta zauna kusa da shi tana nuna mishi in zuba maka? Ya ce To ko don tsoron kar kiyi fushi ai zan ci Ramatu amma in don yunwar da na dawo da ita ne ai ta tafi tunda taji irin kalaman ki tayi maza ta ce ai ba zan sake ba kayi hakuri ya ce ya wuce Ramatu. 15 Anyi hakan bai dauki wasu kwanaki da suka zamo masu yawa ba na farka cikin dare naga kofar dakin Innata a bude alhalin sanda zamu kwanta ni da hannuna ne na rufe kofar har na sanya mata salanta nayi kamar in gyara ruhuwata da na fahimci zamewanta ne yayi dalilin farkawar tawa saboda tsananin sanyin da a ke yi har na juya da nufin komawa baccina sai kuma na tuna ai ban ga Innata a wurin kwanciyarta ba da sauri naji baccin ya sake ni nayi mika na bude idanuwa sosai a kasa na ganta a durkushe da gwiwoyinta a kasa ta dafa wata kujera 'yar tsugune wacce dama ta zamanta ne a kicin nantake na karan wartsakewa ina kara bude ido don in ganta da kyau har nayi nufin saukowa in da take sai ga Babana ya shigo dakin cikin sauri rike da kwanon sha karami a hannunshi alamar rubutu yaje ya yiwo mata daga wannan rubutun dai Ramatu in bai yi ba sai kawai mu tafi asibiti kin ga nakudar tayi tsawo kar muzo muyi irin na wancan karon shima asibitin yana da amfaninshi ai duk rama ce ta Ubangiji ta kawomasu bata dai tanka ba. Ya isa gare ta ya durkusa a gabanta shi ma kan gwiwoyinshi karbi ki sha rubutun nan Ramatu, bata motsa ba daga yanayin ta na 16 sunkuyar da kan da tayi tana kallon 'yan yatsunta. A hankali cikin matsananciyar taushi da laushin murya ta ce mishi ka yafe min abubuwan da nayi maka Mallama. Ya kara zuba mata ido watakila ba wannan ne karo na farko da tayi mishi irin wannan rokon ba saboda jin da nayi ya ce mata, To ni wai me kika yi min ne Ramatu da ki ke ta nanata min wannan maganar? Ai ni ban san komai ba game da ke in ban da alherinki shekaru ashirin din aurena da ke sune shekaruna na jin dadi da samun farin cikin rayuwa in ban da ke da wata kila ban taba sanin jin dadi ba, na zauna da ke kina yi mini biyayya kina tattalin farin cikina, kina kyautata min, ban taba yi miki umarni kin ki bi ba, ban taba cewa ga yanda za ki yi kin ce a'a ba. A kullum ckin kiyaye bacin raina ki ke, to me zan ce miki? In har akwai abin da ki ke yi min da ki ke kuntatawa rayuwata ai bai wuce irin wadannan kalmomin naki ba, tunda kin san me suke nufi a gare ni, kina yi min nuni ne da zan iya komawa in da na baro har gara ma wancan lokacin ban taba danddanar wani madandani da ya kwadaitar da ni son rayuwar duniya ba kamar yanzu, to suma na yafe miki tunda nasan kina 17 cikin wani hali ne yasa ki ke yi mini hakan. Ubangiji ya raba ki da wannan ciki lafiya. Ni da nake kwance shiru a kan gado nake ta faman kukan sharbe na kasa saukowa daga kan gadon saboda tsoron kar a ce min in fita waje ba wai don tsoron daren ba sai don tsoron kar a hana ni ganin halin da Innata ke ciki saboda nasan a duk lokacin da Babana ya shigo dakin Innata ba a barina in shiga in ma ina ciki zan yi sauri in tashi in fita tunda nasan ko ban yi hakan ba ita Innan zata sani ni ce cikin zuciyata na amsa addu' ar tashi na ce amin. Mallam yayi maza ya ce na' am Ramatu me ki ke son 6aya min? me ki ke so in yi miki? A hankali ta ce mishi Mama ce. Gabana ya yanke ya fadi jin ta ambaci sunana. Cikin natsuwa ya ce mata "Eh, me Maman nawa tayi? Ta sake rage murya kafin ta ce mishi, ka baiwa Innata rikonta zata rike maka ita kamar ina raye. Cikin nutsuwa ya ce mata, In har ina raye to a'a duk inda zan shiga zan shiga ne tare da ita, zata rage min kewarki yayi maza ya share wasu zafafan hawaye da suka zubo daga idonshi. Ita din ai kama da ke take yi, kina raye ma nakan kalle ta in yi mamakin kamanninta da ke balle kuma in kin tafi kin bar ni. 18 Wasu hawayen suka ci gaba da zubowa daga idanunshi har suna jika rigarshi, ban taba yi miki karya ba, ba zan yi miki a wannan lokacin ba, zan dai yi miki alkawari a duk lokacin da na hango wata alama ta katsewar rayuwata, to cikin taimakon Ubangiji zan mika mata ita. Yana gama fadin hakan yayi maza yà miko wata Jaka ya dauko wacce yasan nan Inna take tara kayan haihuwarta yana cikin haka sai ga Babah Sumaye da Baba Hodijo sun shigo alamar kofar gidanmu ma a bude take sun kuma san da abinda Inna ke ciki. Mallam Bukar ga motar nan fa a waje mun samota, da sauri Babana ya ce, To mu tafi." Yasa hannu ya daga Inna ya tsaida ita, Babah Sumaye ta daura mata zani tana fadin "Iko sai mai shi." Gaba daya cikin ya tattara ya dawo kirjinta. Tuni na sauko daga kan gadon ina ta faman kuka ina rike da hannun Innata wacce itama ta kama nawa hannun ta kankame a cikin nata. "Sake ta mu tafi, muje ki shiga gida ki samu Jumare ku kwanta tare tazo tana nan a ciki, ki kuma daina wannan kukan da ki ke yi, kiyi mata addu'a kawai in Ubangiji ya kawo saukin lamarin da sassafe sai ki ga mun dawo tare da 19 sabon yaronmu ko yarinya. Ki samu wata 'yar uwar. Wadannan duka kalaman Mama Sumaye ne don haka na dan samu natsuwa har na wuce na shiga cikin gidan nasu naje na samu Jumare muka kwanta mu kuma namu gidan aka sa kwado a ka kulle shi. Jumare 'yar kanwar Babah Sumaye ce da ke yawan zuwa wurinta, ta girme ni da shekarun da suka kai hudu, don haka ta fini wayo tana ganina ta ce min ke share hawayenki kizo muyi kwanciyarmu haka ake yi in za a haihu gobe za ki ga sun dawo da sabon yaro ko mace ko namiji, wanne ki ka fi so? Na dan yi shiru wai zan yi zabi, nan da nan kuma naji bani da wani zabi bana ma dokin abinda za a haifan tunda naga wahalar da take ciki, bukatata kawai in ganta ne ta dawo gida lafiya. Duk da kalaman da aka yi min na Inna haihuwa zata yi ba daga kwanciyata nayi bacci ba saboda na riga na tsorata da abinda na gani, daga baya ne kawai da yake shi bacci 6arawo ne ya sadado yazo ya dauke ni. Farkawa nayi daga baccin nawa a dalilin nayi ya ishe ni ga kuma hasken rana da ya cika dakin da sauri na diro daga kan gadon na fito dakin da 20 gudu, gidanmu nake nufin zuwa inga o zanga Inna da sabon yaron da aka ce kan safiya zata haife shi Jumare na gani a zauren gidan ta rabe tana leke. Nima na tayata yin leken don in ga abin da take gani, cincirindon jama'a ne gaba dayansu kuma maza babu mace ko daya gashi kuma yawan nasu yakai inda ya kai. Can gefe ga yara 'yan saffa suma maza mafi yawancinsu kuka suke yi. Da sauri na kalli Jumare meye a ke yi? Ta kara lekawa tana kokarin tantancewa kamar fa rasuwa a ka yi amma ban sani ba. Muna cikin haka sai ga makara an fito da itaa daga cikin gidanmu da mutum shimfide a ciki, ina kallo a ka yi sahuana sallar amma wai ban gane Innata ce a ciki ba, ina ji Jumare tana gaya min wanda ya rasunne a ciki, na kuma ga zanin Innata lullube kan likafanin amma kwata-kwata ban kawowa kaina cewar ni ce na rasa Innata ba saboda ban taba zaton zan rasata a wannan lokacin ba, ban taba zaton zata daukan min mahaifiyata ta raba ni da ita kamar yanda tayi wa daruruwan yaran da ba za su kidayu ba. "Waye ne ya rasu Jumare? nayi tambayar cikin tsananin tsoro da firgita ba wai don ina zaton abin ya kasance ne a kan Innata ba, sai dai 21 kawai don naga abin da ban taba gani ba, wanda kuma yayi matukar tsorata ni. Na sake yi mata tambayar mai yawa na sake yi mata tambayar da sauri ta ce min, "Ke ban sani ba. Saboda itama ta shiga wani yanayi na kuma yarda har a yau dinnan na yarda Jumare bata san Innata ake sallata ba. Ban san yanda aka yi ba ina ganin an dauki makarar nan an tafi da ita din, bin Jama'a sun bi bayanta cincirindon yara suka yi ta dalewa kan manyan motoči za su bi don yi mata rakiya na kama kuka sosai da sosai Jumare tana bani hakuri. Daga baya ne kawai na soma jin matan da ke wucewa ta bayangidan za su shiga gidanmu, suna fadin "Ikon sai Ubangiji! Ashe Ramatu ce ta rasu? Ban san yadda a ka yi ba, ganina kawai nayi a cikin gidanmu Yaya Dijah tana kankame dani a jikinta tana ta faman kuka, bai yiwuwa in tsaya kwatance ko bada labarin abinda ya faru. illa iyaka dai kawai an yi zaman makokin Ina na kwana uku cikin matsananciyar kewa da jimam da addu'o'i ba daga wurin mu ya'yanta ko mijinta ko danginta ba kawai. Har daga wurin Jama'a masu yawa da suka santa ko suka Ji 22 labarinta wurin kira da mutanen da suka san rayuwarta. An watse daga zaman makokin Inna, 'yan uwa da abokan arziki duk suka watse aka bar mu daga mu sai mu a gidanmu, ina nufin daga Babana sai ni sai ko Yaya Dijah da take nan bata koma dakinta ba. Muna zaune gaban Babanmu ni da Yaya Dijah da take tashe da tsohon cikinta in ban da kuka babu abinda take yi, ni kam nayi kukan na gaji na bari watakila don ban gama fahimta ba ko gama gane girman abinda ya same ni shi yasa na hakyra da kuka na koma zare ido. To yaya za ayi ai sai hakuri kawai, ita kam ai ta huta wajen haihuwa.ta rasu banda haka kowa alherinta yake fada, dubi kuma irin mutanen da ta samu, kiyi hakuri kawai ki bar kukan muyi ta addu'a Ubangiji ya gafarta mata, muka ce Amin. Duk da hakurin da Babana ke ta bayarwa na muyi hakuri sau biyu ina ganinshi ya buya a dakinshi yana nashi kukan. Rannan da safe Yaya Ibahim yazo gaishe mu dama kuma tunda a ka watse zaman makokin bai taba fashin zuwa gaisuwar ba, suna gama gaisawa da Babana yayi tasa mishi albarka. Da zai tafi kuwa sai ya ce mishi in ka taso daga 23 kasuwar ka biyo ta nan ka tafi da matarka taie gida ta huta a dakinta, sai kayi ta hakuri da ita. Ya ce, To Baba yayi mishi godiya ya tashi ya tafi, rannan da yamma Yaya Dijah ta koma dakinta ba a wani dade ba kuwa ta haihu, ya mace ta haifa, Yaya Ibrahim ya sanya mata sunan Innarmu daga mu har Babanmu muka yi murnar alherin da yayi mana. Babah Sumaye ce taje ta zauna mata tayi mata biki har tayi arba'in saboda Yaya Ibrahim da iyayenshi sun ki yarda da dawowanta gida suka ce tunda babu, Inna to me za ta dawo gida kuma tayi? Sannu a hankali sai mutuwar Inna ta rinka shigarmu tana ratsa tsoka da kashi da bargo da zukatanmu, gaba daya ta makurkusa mu ta canza mu daga yanayin da duk muke tun ma dai ba Babana ba. A farkon al'amarin ni kam ma gani na rinka yi tamfar karya ne tana can asibitin. ne kawai watarana zata dawo wani lokaci kuma in rinka jin tanfar wani mummunan mafarki ne da zan farka in ga al'amarin ya sauya in da duk abin ba haka ba ne amma ina? Sannu a hankali sai kwanakin suka fara tafiya daga daya har a ka je uku a ka yi bakwai har aka kwana arba'in ban ga Inna ta dawo ba, babu ita 24 babu dalilintà sai dai yan uwanta da abokan arzikinta su dan zagayo su duba mu a duk sanda za su tafi kuma hakuri ne dai suke ba mu tare da fadin Ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa, ya kuma sa alherinta ya bita, amma ita kam shiru kake ji. Wannan shi ne abinda yafi komai ba ni tsoro, a wannan lokacin sai na zama babu abinda nafi so irin in zauna in yi ta kuka saboda na riga na fidda ran sake ganinta tunda ban taba ganin randa tayi tafiyar da ta wuni ta kwana ba tare da ta tasa ni a gaba ta tafi dani ba. In ban da kewarta da kadaicin babu abin da yafi komai damuna, ko ina yayi min fadi gani nake tanfar ni.kadai ce a raye babu wani abinda nake ji in ji na gani su balle in ji dadinshi in tsaya bayani, na kewar da Inna ta bar mu a ciki ma to na 6ata bakina ne na kuma san duk yanda nakai da jin wani abu' kan rasata da aka yi to Babana yafi ni, illa iyaka dai kawai shi baya cewa komai. In bani nayi mishi maganarta ba, ba ya yi mini. In na cika kawo mishi zancenta ma sai ya ce min yawaita yi mata addu'a zai fi yawaita hirarta amfani in ce mishi to. Tunda Inna ta rasu ba mu taba dora tukunya a gidanmu da sunan yin girki ba, Babah Sumaye 25 ke sanya mana abinci rana da dare kamar yanda ta rinka yi sanda Innarmu ke rashin lafiya. Abin karyawa kuwa sayo mana nake yi wata rana koko da kosai, wata rana waina da miya wata rana shayi da burodi. Kullum dai ni Babana yake tambaya me nake so? In gaya mishi ya ce in je in da kudin suke in dauko inje in saya, in na tati kan in dawo sai in samu yayi sharar tsakar gida da kicin har da wankin bayan gida muna gama karyawar sai in tattara kwanukan da muka yi amfani da su in wanke su in kife in uye ruwan wanka in je in yi. Innata ma mata ce mai matukar tsabta, don haka har bayan bata nan din ma ba ma iya barin gidanmu da datti, kullum ka shigo tšab zaka ganshi, kamshin turarenta ne dai a yanzu babu shi a gidan. Gidanmu gida ne na Jama, 8, kafin rasuwar Inna amma a yanzu da bata nan wuni muke yi a ciki babu wanda ya leko mu har yaran ma sun daina zuwa dan gara gara ma Mansur jifa-jifa ya kan shigo ya gaida Babana, ni kuma ya kawo min dan wani abin lasawa. Don haka nima ban cika zaman cikin gidan ba in Jumare tana nan in shiga gidan Babah Sumaye in bata nan in je wajen Babana in taya shi sai da kayanshi sai ya taso in debo mishi 26 kwanduna mu dawo gida in shiga wurin Babah Sumaye in karbo mana abincinmu mu zauna muci tare a kwano daya ni da shi. A duk ranar Juma'a kuma yakan sani in shirya in je in gaida dangin Innata mafi yawanci nafi zuwa gidan Yakunbo Halima wacce ita ce yar Inna da take bi in naje wurinta wannan Juma'ar sai wata Juma'ar, kuma in je wajen Yaya Dijah. Babana yana mutunta Yakunbo saboda sona da take yi, sai dai duk da haka bai yarda ya bata rikona ba duk da har turowa tayi a rokar mata shi ya bata ni. Sai ya ce a bata hakuri gani nan dai a tsakani ai duk na ishe su. Tunda Yaya Dijah tayi arba'in kusan duk sati sai tazo gidanmu sau biyu in zata zo kuma takan zo mana da lafiyayyar miya wacce take yi mana da naman kaji ko kayan cikin saniya wata ran har ta kirbo mana sakwara wai mijinta ne yake yin cefanen ya ce tayi ta kawo mana mu rinka ajiyewa ko biredi ma rinka ci da ita shima zuwanshi biyu wurin Babana kan maganar ya basu ni. Ya kalle shi yayi murmushi ya ce to in baku ita Ibrahim kai da matarka ga kuma 'yarku sai in kara muku da ita ni fa? In zauna ni kadai? Ai ba zan iya ba. 27 Surukuta mai dadi Babana yake yi da Ibrahim da kawai ya maida shi saboda yayi sa'a shima Ibrahim din mutumin kirki ne ga sanin darajar surukuta. Don haka Baba yana sonshi yana kuma son diyarshi da ya yi wa Innarmu takwara da ita ba kadan ba har ma sai yayi mata lakani yake kiranta da suna. Rannan ina jin Babana yana cewa Ibrahim din ka gayawa Dijah ta daina zirga-zirga da yarinyar nan a kan hanya tana diban mata sanyi, ya dan yi murmushi cikin girmamawa ya ce, Ai ba komai Baba, Babana ya ce a'a ta zauna aa dakinta kawai zuwan nata ba wani dadi ne da shi ba tunda maimakon tazo ayi wata magana da ita sai tazo ta wuni tana kuka gara ta hakura kawai ta zauna a dakinta ya ce to Baba, ya tashi ya tafi tun daga nan sai ya zama kannenshi ne suka kawo mana duk wani abin da za su aiko mana da shi ita kuwa ta koma zuwa jifa-jifa. Inna ta rasu ne cikin watan Jimadah Thani, sannu a hankali sai gamu mun iso cikin watan Sha'aban har shima ya kusa zuwa karshe mutane sai shirye-shirye da dokin isowar Ramadan suke yi mukam a gidanmu ba a shirin komai. Da Inna tana nan da mu ma muna nan muna ta shirye-shirye abinda zuciyata take ta gaya min 28 kenan sai dai ban gayawa Babana ba saboda yawan ce min da yake yi mata addu'a yafi yawan hirarta amfani. Ana gobe za a fara Azumi Babana ya bani sugar mudu bibbiyu da madarar (Peak) dozin dai-dai ya sani na bi yayun Inna mata da ke gidan aurensu na kaiwa kowacce nata na gidan Babanta kuwa shi da kanshi yaje ya kai musu haka nan gidan Baba Hodijo. Yaya Dijah kuma mu ma ta aiko mana da abubuwa masu yawa kala-kala kuma masu dadi na kamun Azumi. Washegari kuwa mai alfarma Sarkin Musulmni ya bada sanarwar ganin watan Ramadana mai albarka don daukacin Musulmi maza da mata suka yi niyyar daukan Azumi. Sanda Inna ke raye na kan yi Azumin amma ba mai yawa ba, ban san dalili ba a wannan lokacin sai Babana ya ki yarda sai da nayi tayi mishi kuka ya bar ni na dauka har watan ya kai ashirin kuwa ban yi abin da yafi guda bakwai ba. Shiga goman karshe da aka yi ne ya nuna gabatowar sallah karama daga ko'ina sai aiken kayan sallah ake yi min dangin Inna maza da mata zai wuya a ce ga wanda bai yi min ba, sai dai kawai na wani yafi na wani haka kawayen Inna da Iyayen 'ya'yan da ta saba yi wa kitson 29 sallah da lalle kyauta, Babah Sumaye ma Yaya Dijah da mijinta kam ba a maganarsu ga kuma Yakunbo. Babana ya tara kayan a gabanshi yana dubawa, idanuwanshi suka cicciko da hawaye ya ce, Wannan duk arzikin Ramatu ne Ubangiji ya gafarta mata na ce mishi amin Baba. Mun wayi gari a gidanmu ranar sallah kamar yanda ta kasance a gidajen sauran Musulmi baki daya, sai dai mu kam maimakon walwala da farin ciki irin na sallah samun kanmu muka yi cikin matsananciyar kewa. Mutuwar Inna ta zamo mana sabuwa saboda ganin babu kowa cikin kicin din gidanmu, da yanzu tana nan tana fama da cincirindon yaran dake karbar abincin sallah a kofar kicin dinta wanda yawanci burabuskon gero take yi da miyar yakuwa saboda shi ne mafi soyuwar abinci a wurin Babana, sai kuma tayi masar shinkafa da miya don rabo na sosai da sosai wanda ni zata yi ta aika ina mikawa sai wadanda suka san da burabuskon nata ne zaka ji suna aiko ni ki gayawa Ramatu ta fa sanmun burabuskon nan ina so, in ce musu to. Yau kicin dinmu shiru babu kowa a cikinshi, na shiga cikinshi har na gaji ina ganin kamar zan 30 ganta a mazauninta ban ganta ba, babu ita babu dalilinta. Ga fa kwanukan abinci nan an tara mana zo ki zabar mana wanda zamu ci ki fitar da saura ki samu masu ci ki basu don kar ya lalace nayi maza na ce to Baba. Nazo na dudduba na dauko kwanon Yakunbo, tuwon shinkafa ne miyar kuka da man shanu da yaji, ga kuma naman da nayi zaton na Talo-Talo ne a ciki na ce mu ci wannan Baba ga kuma masa da miya. Mansur ya kawo na Yaya Dijah, kwan doya ne da cincin mai nama da gasasshiyar kaza, sai miya a wani kwano su na adana mana sauran zan fitar in baiwa yaran da suke so ya ce, To. Duk da lodin kayan sallar da ke gare ni ban wani yi kwalliya ba,bayan wankan da nayi sai da Babana ya ce min to gyara jikinki mana Yahcuwuna kiyi kwalliya kamar sauran yara, sannan naje nayi. Nayi kyau ba kadan ba, ga kitsona da Babah Sumaye tasa a ka yi min sun sauka har kafadata na shiga gidan taga kwalliyata ta kuma aike ni gidan su Jumare na kai musu abincin da tayi har da gidan Yakunbo saboda mu'amallah sosai suke yi a tsakaninsu. 31 Kwalliyar sallah sosai na rinka yi muka kuma yi yawon sallah ni da Jumare wacce take ganin ita din budurwa ce tunda 'yanmata a wancan lokacin sha hudu ne sha biyar in an yi tsanani sha shida wacce ta makara sosai sha bakwai. Har gidan zoo Jumare ta kai mu muka kuma samu goron sallah, osai wurin dangi da kuma masu son Jumare. Tun sanda Innata ta rasu ban sake zuwa Makarantar boko ba, ko kuma ta Alkur'ani, ina zaune ne kawai a gida bana komai tanfar dai a ce da gani har Babana nawa mancewa muka yi da ana zuwa Makarantar sallah da sati guda. Ina tare da Babana, labarin yawon sallarmu da Jumare nake ba shi yana jinjina kai cikin yanayi na nuna alamar murna da gamsuwa don dai ya kara min jin dadi da na gama sai ya kalle ni ya ce min, gobe kuma ina za ku ke nan? Nayi dariya na ce babu, ai hidimar sallah ta Kare tunda yau sallah na da kwana bakwai. Ya sake kallona ai kuwa dai haka ne hidimar sallah ta kare kenan, na ce eh Baba. Ya ce, To ai ina ganin sai kiyi shiri ki soma zuwa Makarantarki, kin ga kin dade ba ki je ba, in ma kin ga ba za ki ta bokon ba shi ke nan amma ta allo kam da ta Asuba sai ki rinka zuwa na sake ce mishi to Baba. 32 Jimawa can ya sake kallona cikin natsuwa ni a ta bokon aji nawa ki ke ne? a wancan lokacin da ba a cika sanya yara a Makaranta kafin cikarsu shekaru bakwai ba, saboda bin ka'idar hannun dama ya taba kunnen hagu kafin a dauki yaro a Makaranta sai na ce mishi aji uku. Yayi maza'ya ce, A'a to ashe ma kin fara nisa ina ganin har ita sai ki koma don ki samu ki gama aji shidan ki koyi karatu da rubutu da dan turancin kai yara asibiti. Ban amsa ba saboda jin nauyi a dalilin gane in da maganar tashi ta dosa, iyaka dai nayi shiru don komawa kan karatuna da na bari nima yafi min don zai rage min zaman kadaicin da nake ciki. Kwana biyu bayan nan na soma zuwa Makarantar boko wanda sai da naje ta allo kafin nayi hakan gab ake da fara jarrabawar canjin aji, a lokacin da na koman sai, dai da yake dama can ina cikin yaran ajin masų fahimta gashi kuma ina da kawata da muke benci daya Hasiya Jibrin, sai na samu hayewa zuwa aji hudu. Rannan na dawo daga Makaranta na shiga wajen Babah Sumaye karbar abincina na zauna a nan wurinta ina ci muna hira tana bani labarin al'amuran da take ganin ya kamata in sani, na gama na mike na kai kwanon gun wanke-wanke 33 na hada da kwanukan da na samu a wurin na wanke su tas, na kife na wuce bandaki nayi wanka na fito na wanke uniform dna na shanya. Na shiga dakinta na shafa mai na dauki kayana da ke wurinta na fito ina rungume da allona, na ce mata za ni Makaranta Babah, ta ce a'a sai kin karbo min cefane, ajiye allon anan kiyi gudu ki karbo min cefane ki kawo min sai ki tafi, na ce mata to. Nayi yanda ta ce din kafin na tafi makarantar. Mu'amallah ta uwa da 'yartga Babah Sumaye take yi dani, yanda take tafiyar da ni sanda Innata take raye haka a!'amarin yake, har yanzu sai dai ma kari. Don yanzu tana sa ido sosai a kaina hada kayanki kiyi wanki, in ce to. Dauki kibiya ki tsefe kanki, tunda ba wani son kits ake yi ba in ce mata ban iya ba ta ce in gama abinda nake yi in kawo kibiyata tayi min tsifan kowane lokaci a cikin yi min fada take, sai dai in bata ga nayi laifi ba ko da kuwa a gaban waye. Ina ganin har dan hakanne yasa Yakunbo bata dadewa bata zo wurinta ba, in tazo kuwa ta rinka yi mata godiya ke nan, ita kuwa Yay. Dijah kusan kullum in zata zo zata riko mata wani abun hasafi ko dai sabulun wanka dana wanki ko kayan tea. 34 A wannan lokacin a gida na daina barin Babana yana sharar tsakar gida da kicin, ina idar da sallah nake fita in yi komai in gama abin da ke bukatar wanki in wanke na gyarawa in gyara tunda ba wani kwanannen datti ba ne a gidan. Sai kaga nan da nan nayi na gama na shiga wankana, yawan abubuwan da Yaya Dijah kke kawo mana kwana da yawan maganar da take yi min kan fita kullum aje sayen abin karyawa kowa yana gani yasa na rage sai in ce Baba muci abu kazan da muke da shi kawai ya ce min to. Kullum na gama shiri zan tafi Makaranta sai Babana ya ce min matso nan in gyara miki hodar nan taki, in ce to. In matsa yasa gefen rigarshi ya goge min fuskata kafin ya umarce ni dasa hannu in dauki Naira daya a cikin kudin da suke dakin, lokacin nan kuwa Naiara daya ba karamin kudi ba ne a wurin yara, don kuwa tana iya sayen waina ta sayi biskit har ta hada da kwalbar lemo wani lokaci ma har da alawa don haka kudi sosai nake zuwa da su Makaranta. Ina tare da Babana a gida duk da Innata ta rasu yana matukar kula da ni, wai abin da yake yi min din ma sanda Inna take nan bana samu, don kuwa ita mai kwaba ce mai kulawa kuma da tarbiya, iyaka dai kawai zama kusa da Inna da 35 yunwa yafi zama a inda bata nan cikin daula da da na sha. , Babana ya dawo daga Masallaci sallar asuba ya zauna ya gama laziminshi da addu'ar da zai yi ya gama ya shafa nima na shafa tunda a kusa da Sinl nake zaune na soma gaishe shi kasancewar ranar ta Lahadi ce ya sani gyara zama kusa dashi tunda ba Makarantar boko zani ba. Zan gama abin da zan yi ne in tafi makarantar allo wannan kuwa sai wajen tara. Daga ido nayi na kalli Babana cikin natsuwa na ce mishi Baba, ya ce Na' am Mamana, na tambaye shi yanzu duk addu'o'in da muke yiwa Inna suna zuwa inda take? Yayi maza ya gyada kai tare da fadin da yardar Ubangiji kuwa, kin san ai akwai wasa ayyuka na sadakatul jariya masu gudana da dan Adam kan bari a duniya ladar ta rinka kaiwa a gare shi a bayan rayuwarshi daga cikin irin wadannan ayyuka da ladansu bata yankewa akwai 'ya'ya na gari. Ba kina sallolinki a kan kari ba? Nayi maza na ce mishi eh babu, ba kya kuma sabon Ubangiji da gangan, na girgiza kai nuna lamar a'a, ya ce To in sha Allahu in kin yi addu'a ladan zai kai gareta ga kuma Yayarki da take zaune a dakin aurenta, tunda a ka yi aurenta ba'a taba jin 36 wani abu na rashin jin dadin game da ita ba, kin gani? Cikin yardar Ubangiji addu'o'inku za su1 rinka kawai gare ta. Na sake kallon shi a hankali na ce mishi menene sabo Baba? Ya zuba min ido kafin ya gano ta inda zai Bullowa lamarin, irin su karya, gulma da shiga harkar da ba taka ba, da bijirewa iyaye ko zina da makamantansu kin gane? Nayi maza na ce na gane, kusan kullum sai na lissafawa kaina laifuffukan da Babana ya lissafa min a matsayin zunubi ko sabo, don kar in aikata su saboda kar in aikata su su zama sanadin da addu'o'ina za su daina kaiwa ga Innata. Kusan kullum na zauna tare da Babana muna hira zai yi min nasiha da cewar in kasance mai gaskiyaa kan al'amurana in kuma tsare mutuncina kar in yarda wani yayi min wayo duk abin da na gani naji ina so in gaya mishi ban da karbar abin hannun wani ita mace bata da wata daraja komai kyanta in har bata zama mai kamun kal da tsare mutuncin rayüwarta ba, in ce mishi to din ba tare da na san mé maganar tashi take nufi ba har na gane komai. Rannan na idar da sallar Asuba ina ta doki da zumudin Babana ya shigo in ba shi labarin da ke 37 Cina a raina, yana shigowa na soma gaishe shi ba tare da na jira ya kai mazauninshi. Cikin natsuwa na kalle shi na ce mishi Baba zan yi sadaka yau, ya kalle ni cikin natsuwa ya ce sadakan me kike son yi uwata? Na ce ko na meye ma Baba jiya da daddare nayi mafarkin Inna wai tazo gidannan na ganta lullube da fararen kaya tana kallona tana ta faman murmushi ni kuma sai tambayarta nake yi Inna dama ashe za ki iya zuwa wurinmu shi ne tunda kika tafi baki taba zuwa kin duba mu ba, ni da Babana? Ina maganar tana kallona murimushinta kawai take yi ni kuma ina kurarin matsawa kusa da ita don in taba ta ina cewa Inna kiyi mini magana mana har zan taba tan sai kawai naga ta 6ace sai kuma kawai naga ra farka daga baccina. Cikin natsuwa ya zuba min ido a allona lokaci mai tsawo bai kawar da idamuwanshi daga gare ni ba har na fara jin tsoro ko yayi fushi ne saboda maganarta da nayi mishi tunda ya sha ce min in an tunata ayi mata addu'a kawai basai an yi zancenta wani ba har zan buda baki in bashi hakuri tare da alkawarin ba zan sake yi mishi hirarta ba sai naji ya ce min jiyan da kika yi mafarkinta ai jiyan ta shekara. 38 Nayi maza na daga ido na kalle shi a firgice saboda razanar da nayi sai ya ce min kin gani in ha ki manta ba ta rasu ne ranar sha tara ga waran Jimada Thani, to yau ma ai shataran ne ko ashirin ga watan. Na ce Haka ne Baba, lokaci mai tsawo ya dauka yana yi mata addu'a tare da sauran Jama'ar Musulmi da suka rigaye mu baki daya in kuma tamu cikawar tazo to Ubangiji ya azurtamu cikawa da kyau da Imani. Nayi maza na ce amin Baba tsawon lokaci muna zaune shiru babu wanda ya sake furta wata magana sai na bude baki da nufin fadin abinda ke kai kawo cikin raina a hankali na soma yin maganar cikin yanayin girmamawa da tsoro don kar ya hana ni abin da nake nufin fadin tunda yasha gaya min cewar maimakon yawan ambaton Inna da yawan maganarta mu rinka yawan yi mata addu'a kawai. Zuba min idon da yayi yana kallona shi ne ya kara tabbatar min da cewar ni yake sauraro, don haka cikin natsuwa da ladabi sai na buda baki nace mishi Baba tafiyar ta Inna ta fara nisa duk da a lissafi ne kawai Inna ke da shekara guda a yanzu in a kewa da kadaicinta ne mun kai wani matsayi da ba zai yiwu mu kwatanta ba. 39 Duk da haka shekara gudan lisafin ma lokaci ne mai tsawo da yawa in ban da tafiyar tata bata dawowa ba ce da yanzu ta dawo ko kuma damun soma sa rai da dawowan nata. Cikin natsuwa ya ce min eh, Maryam ai tafiya taia wata irin tafiya ce da dadewa bai sawa a dawo da dadewa kansa a dawo ai da mu ma iyayenmu sun dade da dawowa. Nayi maza na ce haka ne Baba, kamar in yi mishi wata maganar sai kuma naga to bari kawai in ja bakina in yi shiru. Kamar in sake yin wata maganar sa kawai naga bari kawai in ja bakına in yi shiru. A wannan lokacinne na shiga aji shida na Makarantar Primary na fara girmia har Babana ya fara barina ina tafiya gidan Yayc Dijah ni kadai don yi mata wuni. Ina matukar son awa gidanta saboda yanda na lura na gane bata da wani wanda take so da kyautatawa irina. Kullum naje gidanta to bata gajiya da tattalina da tarairayata komai na ce mai kyau ne cewa take yi in dauka tana ganin na kwana biyu ban je ba zata shiga aiko kanen mijinta suzo su ga lafiyata, in kuwa naje bayan aiken nata zan gamu da fushinta kan dadewan da nayi ban je ba kullum a cikin yi min nasiha take tana ganin zani aikata kuskure zata yi maza ta gyara min. 40 Yanda Yaya Dijah ke sona da ji da ni haka shima mijinta yana ganina zai fara murmushi ina Inna take? Zo maza ga Mamanki tazo. Sanin da yayi kullum naje gidan Yaya Dijah zata tasa ni a gaba da aikace-aikace har da su hidimar girki wai kar in girma ban iya aikin mace a gidanta ba, yasa yana ganina zai je yayi sabon cefane ya kawo ko da kuwa ba a ranar suke bukatar cefanen ba sai ya ce in na girka in tafi mana dashi gida muyi amfani da shi ni da Baba. Ina son Yaya Dijah da mijinta ina kuma matukar son 'ya'yanta Inna da Abbati, ina son su irin son da ba zai kwatantu ba, saboda gani nake tamfar su din su kadai sune dangin da nake da su sai kuma nake kallonta kallo irin na uwa, ganinta nake tamfar ita ce madadin Innata da na rasa. Dangin mijinta kuma 'yan uwa saboda suna sonta kowane lokaci kaje'gian sunanan aurenta aure ne na soyayya, fahimta da kuma kyautatawwa juna, don haka gidanta gida ne na farin ciki da kwanciyar hankali, kudi masu yawa ne kawai ba su da su amma suna cikin rufin asiri. Ni da Yaya Dijah kamannin da ke tsakaninmu ba wasu masu yawa ba ne, ba su wuce wadanda zaman ciki na kasancewa shakikai ke haddasawa 41 ba, yayin da nake matukar kama da Innarmu ita kuma kama da Babanmu take yi. Haka nan ko a halayenmu mun bambanta mace ce mai matukar hakuri bata kuma da kwaramniya. A wannan lokacin saboda na riga na fara yin wayo na fara fahimtar me nake ciki sai na zama babu abin da nake so nake fata da buri irin in ganni nayi haddar Alkur'ani mai girma a dalilin kullum sai Malaminmu na Alkur'ani yayi mana bayani kan falala, girma da kuma darajar mahaddata Alkur'ani a ranar alkiyama su da yayensu. Sai na zamo ina matukar kwadayin nima iyayena musamman ma Innata da nake rayuwa cikin tsananin kewarta da begenta su samu irin wannan matsayin a gobe kiyama. Kowane lokaci a cikin taka tsan-tsan nake na kauce wa aikata laifi musamman yin karya da duk wani abin da Mallaminmu ya ambata cewwar laifi ne don in samu in zama ya ta kwarai saboda ya ce mana ya'ya na kwarai suna daga cikin sadakatul jariya da mutum ke bari a duniya wanda ladansu ba su yankewa a gare shi. Rannan ina tare da Babana a cikin gidanmu da daddare a kishingide yake a kan tabarma yayin da yake jan carbinshi a hankali cikin 42 natsuwa idanuwanshi a kaina suke tare da natsuwar shi saboda sauraron haddar da nake kawowa na suratul 'ANKABUT". Sai da na kai karshe na sake kallonshi cikin natsuwa kan in gaya mishi abinda nake nufin gaya mishin sai ya ce min kina da murya ta karatun Alkur'ani Maryamu, kar ki yarda ki daina, kar ki yarda kiyi wasa ta basirarki na ce mishi to Baba, kan in yi wata magana sai ya sake bani umarmi na in maimaita surar, ya ji ta dá kyau. Sau biyu na maimaita sannan yayi murmushi ya ce a'a lalle hadda ta zauna sai kiyi ta tilawa kar ki yarda kina yin sake don shi Alkur'ani kana barinshi sai shima yayi nesa da kai, don haka ki dage da tilawarshi. nayi maza na ce to Baba. Yi mana addu'a, na sake cewa to nayi muka shafa sannan muka je muka kwanta. Rannan da safe muna aikace-aikacenmu a gida ni da Babana kafin ya fita kasuwarshi nima in tafi Islamiyyata tunda ranar ta Asabar sai naji ya ce min ni Mero ba ki iya komai ba ne cikin girke-girken da ki ke cewa 'yar uwarki tana nuna miki? Nayi maza na bar abinda nake yi na kalle shi Cikin natsuwa da zumudi na ce mişhi Baba duk abincin da nake zuwa da shi gidan nan fa ni nake 43 yi Yaya Dijah zama kawai take yi tana kallo in taga zan yi wani abu ba daidai ba ta gyara min. Shiru yayi yana kallon wuri guda nuna alamar a cikin tunani yake, na bar abinda nake yi na sake kallonshi tare da tambayarshi mene ya faru Baba? Kaji miyar bata yi dadi ba ne? Yayi maza ya gyada kai uh'uh ba haka ba ne Mero tunani dai nake yi na in har ke ce da gaske ki ke yiwo mana wannan girkin to ai gara in hutar da wadannan yan uwa namu da suke ta faman dawainiya damu shekara guda har da wasu watanni tunda mahaifiyarku ta rasu ba su taba hutawa da hidimarmu ba. Don haka in har za ki iya to sai in sauke musu nauyin girkinmu su rinka.yin nasa kawai in rinka kawo cefanenmu kina yi mana. Nayi maza na ce eh Baba gara kawai muyi hakan can cikin zuciyata murna nake yi da zumudi saboda babu abin da nake so nake kuma sha'awa irin in ganni ina girki ni kadai ba tare da ana nuna min ba wai ni a dole na iya. Wannan maganar da muka yi da Babana bata wani dade ba don ko kwana bakwai bata yi ba, naje karbo cefane kamar kullum yanda na saba ni ke zuwa wurin shi in karbo cefanen kayan miya gami da su manja ko man gyada da maggi 44 in kai ma Babah Sumaye shikuma Baba Hodijo yayi abin da ya saura tare da hatsi. Ina tsaye ina jiran ta gama hada min in dauka in kawo mata sai kawai naga ya miko min ledoji guda biyu, ungo ki kai mata daya ke kuma ki girka mana daya. Gabana ya yanke ya fadi tamfar dai' ba ni ce na ce mishi na iya girkin ba. Zaro idanuwa nayi ina kallonshi yayin da shi kuma ya ci gaba da yi min bayani, na riga na yi wa Mallam Hodijo bayanin komai, don haka kaiwa ita uwar taki kunshi daya ki rike daya. Kije ki girka mana abinda ki ka san shi ki ka fi iyawa kin gane ko? Na ce mishi to Baba, na kamo hanya ina dawowa gabana sai faduwa yake yi ban taba yin girki ni kadai babu wani babba a wuri ba hasalima kafin rasuwar Innata bana shiga kicin da sunan ya yi girki ko da kuwa na wasa ne. Babah Sumaye ta zubawa cefanen ido tana kallo yanzu nan bawan Allahn nan da gaske yake yi sai ya raba girkin nan? Ta dan gyada kai tare da fadin to ai shi kenan tunda haka ya gani daya, amma menene'? Ai mun riga mun zama dan abincin da a ke sa mishi guda nawa yake? Ban da haka ma kullumn fa cefanen nan a wurinshi ake karbo shi amma ya ce wai 45 dawainiyar da ake yin tayi yawa, ni dai nafi zaton ko subutan bakin da nayi na ce a gaya mishi ga wata bazawara na saman mishi ne duk ya kawo hakan. Ni kuma ba nayi hakan ne don na gaji a sa mishi tuwo ba a'a ko kadan ba haka ba ne nayi mishi tallan bazawarar ne don ganin hankalinta da natsuwarta shi kuma yana ta zaune a haka yau kusan shekara daya da rabi da rasuwar Ramatu, wanda wasu da kyar suke jira ayi arba'in sai kawai ka ji sun daura aurensu. Yanda dama ban san anyi wannan magana da Babah Sumaye ta rattaba min ba haka a yanzun ma da ta rattaba min ban nuna naji ko na gane inda Zancen nata ya nufa ba, balle in furta wata kalma. Sa hannu kawai nayi na dauki leda guda daya na juyå da nufin fita daga gidan saboda nima ban san dalili ba sai naji maganar ta dan sosa min zuciya ina fita daga gidan dai ina jinta tana cewa bai fahimce ni ba ne, ban gaya mishi hakan don ban damu da rashin da aka yi ba sai dai don sanin da nayi cewar yanda duk muka kai da son Ramatu to babu yanda za muyi tunda ta riga tayi tafiyar da babu dawowa a cikinta sai dai kawai muyi ta binta da addu'a. 46 Ina shiga gida na juye kayan cefane na kama wankewa sai da na gama tsaf naja na tsaya ina kallon kicin din wanda rabon da a girka wani abinci mai muhimmanci a ciki har an, manta sai a lokacin ne kuma naji na dibibice na rude na rasa ta ina ne ma zan faro? Na zubawa murhun ido ina tuñanin yanda ma za a yi in hada itacen su kama su zama wutar da zata kama ta girka abincin da zai nuna zama tuwon da za a ci. Tsawon lokaci ina tsaye a wurin nan ina tunanin ta inda zan faro sai ga Jumare ta shigó da saurinta. Babah Sumaye ce ta ce in zo in ga abinda kike ciki da cefanen da ku ka zo da shi in taya ki girkin da za ki yi. Nayi maza na ce mata gashi nan saboda taimakon nata yazo min ne a daidai lokacin da nake bukatarshi. Duk da taimakon da Jumare ta kawo min da aiken da Babah Sumaye tayi-tayi na ayi kaza kar ayi kaza abincin da muka girkan yawanshi ba kadan ba ne, dandanonshi kuma ba wani mai gamsarwa ba ne ko in da aiken nata da zuwan Jumaren wane irin kwaba zan yi? Oho. Duk da min karbi girkin abincinmu Babana bai daina bada kayan miya a gidan Baba Hodijo ba babu kuma wani abinda ya canza a tsakani ni 47 kam ma dai ban daina zuwa karban abincina ba ina shiga gidan Babah Sumaye zata ce min ga abinci can in za ki ci jeki ki diba in ce mata to dama kuma hakan take yi min. Haka nan duk wani abu na kulawa da take yi min bai sauya ba, ina dawowa daga Makaranta wurinta nake fara zuwa in tube kayana in canza da wanda ke nan a wanke a goge in ci abinci in yi wanka in yi sallah in yi shirin tafiya Makarantar allo bayan na karbo cefane na kawo. Zan iya cewa kwanon Babana ne kawai aka cire shi ne kuma mai cin abincin da nake kwabawa da sunan girki sai ko yaran da nake turawa a cikin gidan wadanda rasa uwata da nayi ya koya min lura da sa ido wajen sanin 'ya'yan da ba Su da uwa a dalilin suma mutuwa ta daukan musu ita kamar yanda ta daukan min tawa kokuma a'a sakin uwar tasu aka yi aka bar su watse a tsakar gida. Duk.munin abin da na girka Babana bai cewa komai, bayan sannu da kokari sai yayi bisimillah yayi komai uku yayi hamdala ya ce in kawar ko in nemi wadanda zan ba, in ce mishi to in je in kawo mishi ruwa. Zuwan da nayi gidan Yaya Dijah ne na bata labarin dukkan abubuwan da suka faru har da bayanin da Babah Sumaye tayi ina ji, shiru yayi 48 Dijan tayi cikin wani yanayi na nuna tsananin tausayi ta ce uh'uhummn, Baba ina jin tausayinshi in na tuna Inna na tuna halin da na samu kaina a ciki a dalilin rasata da muka yi. Sai in tambayi kaina to shi kuma fa yaya yake ji? Ta dan yi shiru cikin wani irin nazari da tunani mai zurfi, jimawa kadan sai ta dago ta kalle ni idanuwanta sun kada sunyi jazur alamar suna shirin fara zubar da hawayc, sai ta ce min dama yayi auren kawai zata debe mishi kewa zai samu abokiyar mu'amallah zai kuma huta da cin wannan danyen abincin naki da ki ke kwabawa bakya ci nayi maza na ce ina ci mana ai ba danyen ba ne kuma kullum ya ci zai yi min addu'a. A wannan lokacin zan iya cewa bani da wata matsala ko kuma damuwa da ta wuce ta bani da uwa mahaifiya in ban da wannan ban rasa komai ba, ban nemi wani abu na rasa ba, Babana yana matukar sona yana kula da ni yana tattalina, komai nake so yi min yake yi duk wani abinda ya ba shi sha'awa saya min yake yi. Fura da nono, kankana, gasasshen nama, wannan kadan ne kusan kulllum zai saya min sai in ni ce na ce ba zan ci ba. 49 Babah Sumaye ma a tsaye take a kan al'amarina, kitso, wanki, kula da kai, tsaftace jiki lura da tarbiya bata gaji ya min kan komai ba. Ga dangin Innata da kusan kowane lokaci hankalinsu a kaina yake, don haka ina yawan tuna Innata ne a dalilin tsananin kauna da shakuwar da ke gare mu amma ba don na samu kaina cikin wani hali na wahala ba. Rannan ina tare da Babana a gida yana kishingide yana jan carbin shi a hankali cikin natsuwa tare da sauraron kira'ar karatuna da nake yi a gobe, sai da na kammala komai na maida Alkur' anin nawa mazauninshi. Bayan na gama addu'o'ina na shafa sai muka shiga hira da Babana irin wadanda suka shafe mu har na shirya zan tafi in kwanta sai naji ya ce min ni fa da wata yar shawara na ce zan yi da ke. Da sauri na dawo na zauna cikin natsuwa ina kallonshi cikin yanayin girmamawa da kuma sauraro can cikin zuciyata kuma tunani nake yi wacce shawara ce wannan da Baba bai da mai bashi ita sai ni? Ban sani ba ko ganin irin yanda na tattara komai na mayar gare shi ne yasa shi mikewa ya zauna ko kuma a'a shi ma hakanne yaga ya fiye mishi daidai, kina jina ko Maryamu? 50 Nayi mazana ce mishi eh Baba can cikin zuciyata kuma na kara girmama al'amarin da Babana ke bukatar shawarar tawa a kai tunda yayi dalilin da yasa shi ambaton sunana na Maryamu' tunda nasan ba kasafai ya kan yi hakan ba, saboda kasancewar sunan nawa suna mai girma a wurinshi. Mutane ne suka dame ni da maganar in yi aure, nan da nan na tuna kalaman Yaya Dijah na cewar duk randa ya sake yi min wata magana da ta danganci aure in yi mishi in karfafa mishi gwiwa kan yayi auren don shi ma ya samu saukin al'amuranshi. Bisa wannan dalili yasa nayi maza na ce mishi to kayi auren mana Baba Inna fa wajen shekararta uku ne yanzu da rasuwa kana ta zaune kai kadai yin auren kuma zai rage maka wasu damuwowin. Ya bar abinda yake yi ya zuba min ido yana kallona, kalamanki ne wadannan ko kalaman yar uwarki? Don dai nasan ba ki da wannan nisan tunanin, ban boye. mishi ba na kwashe hirarrakin da muke yi ni da Yaya Dijah kan rashin auren nashi. Yana ji na bai ce min komai ba sai zuwa can naji ya ce min to bari dai kawai in yi tunda kuma kuna ganin ya dace in yi amma 51 in ba haka ba ni bani da wata damuwa kan hakan. Tunda muka yi wannan maganar Babana bai sake ce min komai a kan maganar ba, sai kwana goma bayan nan na kammala wanke-wanke na kife kwanukan nazo inda yakena zauna saboda kiran da yayi, ga ni Baba. Nayi mishi maganar cikin girmamawa, ya kalle ni cikin wani yanayi da na kasa tantanc wanne ne yafi rinjaye a ciki? Maganar nan tamu ce nake ganin kamar zata tabbatą. Nayi maza na tambaye shi wacce magana Baba? Yayi maza ya rage fara'ar wace magana kuma ki ke tambayata? Nayi sa'a cikin hanzari maganar ta fado min, don haka nayi maza nace mishi eh Baba na tuna ta na tuna kayi hakuri. Ya dan yi shiru kadan kafin jimawa kadan ya ce min, akwai wata yarinya nan da a ka nuna min tana da dan fasali kadan an kuma ce wai tana da ya'ya biyu da mijinta ya rasu ya barta da su, to kin ga maganar ya'ya tunda marayu' he ai nima ga ki sai tazo mu hadu mu rike ku musamman da yake shi maraya rike shi ba karamin al'amari ba ne akwai falala mai yawa a cikin al'amarinshi. Na ce "Haka ne Baba." Tun daga wannan lokaçin bai sake min wata maganar ba sai a wata ranar Juma'a da safe 52 bayan na dawo daga Makarantar Asuba. Na zauna kusa dashi na gaishe shi sai yarkalle ni ya ce min to yi maza kije gidan "yar uwarki ki gaya mata zancen nan ya tabbata an yi daurin auren yau da asuban nan. Nayi maza na ce "Lah, har an daura Baba?" ya ce, Eh uwata an daura to me za a jira tunda dai za ayi? Ai ita din na gaya miki yanda al'amarinta yake, don haka da ta koka min maganar aikin kafinta saina gaya mata tabi a hankali da tayi shawara dani ma da bata sanya kanta cikin dawainiya ba balle har taje tana 6acin rai, don haka ta tare kawai tazo ta fara amfani da wadannan kayan har kafin kafintan ya bata nata sai a kwashe wadannan din. In har da wani lokacin da naji dar ko wani faduwan gaba kan maganar auren na Babana to a wannan lokacin ne ban san dalili ba sai naji ban ji dadi ba, a ce amarya tazo ta shiga dakin Innata tanana amfani da kayan Innar tawa da dai ace yau ne yake neman shawarata to da na ce mishi a gaya mata kawai ta jira kawai kafintan ya gama mata aikin nata to amma babu halin in ce komai. Yi sauri kije ki gayawa Dijah ki dawo sai mu dan yi kwalimar da zamu yi wa gidan kar baki su zo su ga kazantarmu ko kuwa? Na ce mishi haka ne Baba. 53 Gidan Babah Sumaye na fara shiga tana hidimarta cikin kwanciyar hankali iko sai Ubangiji yau sai a ka wayi gari da maganar daurin auren Mallam Bukar na ce haka al'amari yake in kaga ba a yi abu ba to lokacinshine bai yi ba Ubangji ya bada zaman lafiya na ce amin Baba. A maganar da muke yi ne nayi mata hirar bayanin da Babana yayi min. Cikin sauri ta dago ta kalle ni anya ayi haka kuwa? To ko da yake dai duk yanda a ka yin daidai ne fata dai a zauna lafiya amma kuma ai ita Halima a sanina akwai akwatinanta da nasan akwai muhimman al'amarinta a ciki a dakin an fita da su ne? nayi maza na ce mata a'a suna ciki ta ce, to maza je ki ki tito da su ki kawo nan in Dijah tazo sai ta tafi muku da su gidanta. Na ce, Mata to, da sauri na koma gida cikin sa'a Babana ya zaga nayi maza na fitar da su na kai mata, haduwa muka yi da shi zai shiga ni kuma zan fita ina rungume da hotunan Innata guda biyu a jikina, ina za ki kai wadannan? Cikin natsuwa na ce mishi zan fitar ne a dakin, tsawa ya daka min nayi maza naje na maida su nazo na wuce shina tafi aiken da yayi min. Dawowa gida nayi na samu tuni har Babana ya gama kwalimar da ya ce zamu yi tare, dan 54 karamin gadon bonon Innata shi ya kawo min daya dakin wanda da na baki ne dan akwatina kuma yana karkashinshi. Duk abubuwan da suke faruwa ina bi ne kawai da kallo ba sosai suke yi min dadi ba, to amma kuma har cikin zuciyata murna nake yi Babana zai yi aure da za a tambaye ni abinda ke SOsa min ran kuma ba zan iya vin wani cikakken bayani ba. Anyi hidima su girke-girke da dafe-dafe saboda isowar amarya da 'yan rakiyarta Babah Sumaye ce kuma ta jagoranci duk wani abinda a ka yi tunda shi mijinta ne ma ya zamo wakilin1 Babana da ya karbar mishi auren itama Yaya Dijah ba a barta a baya ba, don har da sayayya tayi ta kawowa Babana wai a kara a cikin kayan aure. Yayi murmushi ya ce, wane kayan aure ne ma? Ke dai tunda kin kawo wadannan din a bata a ce mata 'yarta ce tayi kwalliya, to Baba ta fadi tana murmushi, ya tayata murmushin tare da yi mata addu'ar Ubangiji yayi mata albarka, ya kuma jikan Mahaifiyarmu da rahamarsa muka yi maza muka ce amin. Ban fara gane irin fasalin auren da Babana yayi ba sai bayan da 'yan buki suka watse mukai saura daga ni sai Babana sai ko Amaryarshi a 55 gidan, lokacin ne na soma gane wani canji ya same ni. Dakin Innata dakin da nan ne a ka haife ni, a cikinshi muka yi rayuwarnmu ni da uwata bayan rasuwarta kuma nan ne wurin zamana komai zan yi a cikinshi nake yi sai na zamo ba ni da halin shiga cikinshi in zauna in sake ina shiga na dan zauna sai a ce min to je ki waje ko. Gashi kuma daga in da duk a fito nan nake dosa saboda kwata-kwata ban ma saba da in da aka maida ni din ba, ga shi kuma sai nake ganin tanfar dakin da abinda ke cikinshi duka nawa ne ko kuma na Innata amma a ka fitar da ni a ka sanya wata a ciki. An wayi gari da safe ina durkushe daga bakin kofar dakin gaishe su nake yi a cikin barin jiki saboda al 'amarin da idanuwana suka gani wanda ba sabawa da ganin hakan suka yi ba. Babana na gani kwance shame-shame kan gadon Innata me rumfa da aka canzawa shimfida a ka sanya sababbi, ita kuma zaune a gefen gadon da daurin kirji a jikinta kanta babu dan kwali jikinta babu riga sauri nayi na sunkuyar da kaina kasa, ban lura naga halin da Babana yake ciki ba balle in gane da rigar a jikinshi ko babu?. Yana fita waje ya bar gidan naji ta kwalo min kira, da sauri na amsa naje ina işa tayi maza ta 56 cafke kunnena ta rike bayan ta dirma min wani nannauyan dundu da sai da yayi sanadin gantsarewata. Kina hauka ne ki ke shigo min da a fadi sunan uwar miji gara na uwa mahaifiya. Da sauri. Babana ya ce mata ko? Ta langabar da kai nuna alamar girman maganar da zata yin, to wacce ta haifan maka miji Mallam? Da wani abin da yafi aure daraja ne? Da sauri Babana ya ce mata babu shi babu shi fa kam. Sai dai fa sanin hakan wurin mutane kadanne a wannan lokacin, ta ce Uhun ai kuwa dai wanda ya raina aure bai yi wa kanshi adalci ba. Bakuwar ta ce tayi sallama abinda yayi dalilin katsewar hirar tasu, a ka shiga barka da sannu da zuwa a'a ke Lantana 'yar taki ki ka tasa a gaba nan za ki koya mata son miji? Amaryar Babana da a yanzu naji an kirata da Lantana nasan sunanta shi kam Babana Malama naji yana kiranta. Ta kyalkyale da dariya ta ce, to me zan jira ita mace ai tun daga haihuwarta ake koya mata tattalin miji da tarairayar aurenta, to ai shi ke nan. Ta juyo gare ni da dariyarta ke 'yar amarya bakinki da maiko. 57 Nayi maza na soma gaisheta tunda a jiya an gaya min in rinka gaida mutane in na gansu kafin nan ban damu da gaida kowa ba in ba 'yan uwan Innata ba ne sai ko na Babah Sumaye. Ke Yaacuwuna kawo musu dan abin nan mana yayi maganar daidai ya mike ya kama hanyar waje bayan sun gama yiwa juna gaisuwar gajiya da fatan Ubangiji ya sanya alheri, a zuciyata nace sai kirana da sunan Yaacuwuna yake yi sunan da ya dade bai kira ni dashi ba alamar dai yana cikin farin ciki mai yawa. Miyar kajin dai saura aje na kawo musu wacce Yaya Dijah ce tayi mana tare da timemen biredin da yake kai na ajiye musu, suka bude kwanon kawar tata ta fara uh'uh'uh ke da arziki cikin lamarin nan naki fa wannan karon. Suka soma cin naman miyar suna hirarsu ni kuma ina can gefe daya a rakube saboda yanayin da na gani a fuskarta, baki dan tsakura kika sanma 'yar taki ba? Tayi maza takai tsokar da ke hannunta baki ta lankwame kafin ta sake gutsuro katon biredi ta dannan a kai ta kora da ruwan shayi sannan ta soma yi wa kawar tata bayani wannan 'yar tawa a rike take nan inda ki ke kallonta bata cin komai a jikin kazasai cinya, ai kuwa kin ga bana bata cinya ni in zauna haka ba ko kuwa?. 58 Ke Lantana ke fa sharrinki yawa ne da shi yaushe ki ka bata ta ce miki cinya kawai take ci? Yanzu wannan fuka-fukin in kin bata sai ta ce bata ci? Tayi dariya ta ce a'a to in ma sharrine ubanta yayi mata ni kam yaushe nazo balle in fara nawa? Shi ne ya kawo kaza dankwaleliya gasasshiya. Yasa hannu ya balle cinyoyin duka biyu ya mika mata ya bar ni da sauran jikin wai abin da take iya ci kenan a jikin kaza. Kawar tata ta kyalkyale da dariya ta ce, Ai da ga ni kasan Kura za ta ci Akuya 'yar tashi aî ta kiwatu komai nata luwai-luwai da shi, ga ta kuma dama tubarkallah, ke dai irin wadannan mutanen sai anyi hakuri a ke iya zama da su. Uhun ai kuwa ni nasan sai anyi hakuri kin ga Ramatu! Ramatu!! Ramatu!!! Tana ambaton sunan Innata tana kwatanta yanda sunan yake fitowa daga bakin Babana, yayin da kawar tata ta zuba mata ido tana kallonta Abinda a ka kwana' ana gaya min ke nan, labarinta ake ta bani ana yi ana karawa ni kuwa ina ta uh, wannan anyi mutuniyar kirki, garin ba ni labarinta hawaye suka soma zubo mishi, yana kici-kicin share su ni kuwa nayi maza na rushe mishi da kuka. 59 Kawar tata ta kwashe da dariya kafin ta ce "Kuka gaba daya? Ta ce to me ki ke so in ce mishi yana bani labarin matarshi yana share hawaye ba sai in taya shi kukan mutuwar tata ba? Taja wani mummunan tsaki ta juyar da kanta can gefe. To ashe ba ku' samu kun yi wancan abin ba kenan? Ni kuma da nazo ne in ji yanda a ka kwashe. Ta dago ido ta kalle ni. "Ke tashi ki bani wui, kin wani tsare mutane da ido suna magana kina kallonsu, na mike na nufi hanyar fita daga gidan, tayi maza ta ce "Ina za ki? Yau ga abinda ya ishe ni, yazo ya same ki a waje? To ba wajen na ce kije ba dakinki za ki shiga." Na shiga dakin nawa na zauna sai dai cikin rashin sa'a nan din sai ya zamo nafi jin zancen nasu. Ni na rantse miki kar ki ce maganar wasa dingishin nan da kika ga ina yi ba na iyashege, ba ne, don ma nayi aiki da ruwan zafi sosai, gaba daya suka kwashe da dariya, ke kice min kawai mutumi garau din shi yake. A*a kalau yake Lami, sannan kin san ya kwana biyu rabonshi da abin, kuma gaskiya hadin nata mai kyaune, komawa zaki yi ki sake karbo min. 60 Wari-wari ya soma shigo min daki, nayi maza na waiwaya wurinsu don ganin abinda ke faruwa, karan Siga ri na gani a hannunsu suna zuka cikin mummunan faduwar gaba nayi magana cikin zuciyata don kar su ji ni na ce Sigari kuma? Ke dai kar kiyi asa da wannanauren naki, zawarcin shekaru bakwai fa ki ka yi wannan karon kafin shi kuma kin yi na shekaru hudu har da watanni ki ka yi aure muna murna auren yazo ya kare a watanni uku kacal, kin ga in an hada zawarcin shekara goma sha daya ke nan. To don me za a hada bayan ga auren wata uku a tsakani, wata uku wasa ne? Suna hirarsu ni kam tuni zuciyata ta shagala tunanin ashe mata ma suna shan taba sigari, na dauka maza ne kawai... Ban ankara ba sai naji hirar tasú ta koma bayanin ai yarinyar bata da tarbiya, goyon gwauro yayimata sannu a hankali na gane wai maganata da Babana suke yi. Tunda aka yi auren Babah Lantana kullum da irin kawayen da ke zuwa wurinta wadanda Babana zai yi ta hidima da su in ya fita kuma ka ji suna hira mai ban mamaki gashi kuma wani abin da ya fi komai bani mamakin shi ne daga ita 61 har kawayen nata ba ka raba su da wani mele a gefen fuskarsu tamfar dai sun taba konewa. Rannan na nemi izini wurin Babana da itama Babah Lantanan don ya ce duk abinda zan yi ko nake so ita zan rinka tambaya wurin Yaya Dijah naje, muna zaune ni da ita yayin da "ya'yanta ke cikin gida wurin Kakanninsu. Ni 'yasu wannan mata da Baba ya aura rufa ido a ka yi mishi ne ko? Ba fa yarinya ba ce ga shi da ganinsu ita da kawayen nata kaga 'yan duniya, an yi bilicin har an gaji an kode an yi mele. Lokacin ne na gane melen da nake gani a jikin nasu na tabon mai ne. Kamar in ce mata ai ma na gansu suna shan sigari sai nayi maza na kama bakina nayi shiru saboda wa'azin Malamin Makarantar Asubaru da na tuna, da ya yi magàna kan tona asirin mutum bayan halin nashi bai bayyana kowa ya gane ba. Ni dai fatan da nake yi Ubangiji yasa maganar da wata makwabciyarmu nan baya tazo tayi min ya zama ba gaskiya ba ne, cikin natsuwa na tambayeta wacce irin magana ce? Yaya Dijah ta kalle ni ta ce min cewa tayi wai sun santa sani mai kyau, aurentaa shidana Babanmu ne na bakwai,kuma wai "ya'yanta guda biyun da take cewa na Alhaji Tukur ne mijinta 62 da ya rasu karya ne, asalin ubansu ne wai ba a sani ba. Kamar ya ya ke nan? Nayi mata tambayar da ta zamo tamfar tuni a gare ta, cewar wannan maganar ta wuce sanina, don haka tayi maza tai gyara ta hanyar fadin mu dai mu bar wannaan maganar kawai muyi abinda yake gabanmu. Shi kuma Baba muyi mishi addu'a, na ce to. Muka ci gaba da harkokinmu da muka saba yi in naje. Rannan ina tare da Babah Sumaye da Jumare da tazo mata kwana biyu hirarmu muke yi muna wasanmu ni da ita sai naji Babah Sumaye ta ce min, Ke Mero kina da wata matsala ne naga kin yi wannan zubewar haka? Da sauri na dago ido na kalleta. Nan take kuma na maida kallon nawa ga jikina da take fadin ya zube, me ki ka gani Babah? Ta ce, Uh'uh gani nayi dai kamar kin ragu kan in ce komai sai Jumare ta ce mata, zama da wannan matar ta Baba ba wani dadi. zai yi ba, da na shiga gidan fa ba ki ga irin kallon da take yi min ba, kuma na rantse miki sigari na sameta tana sha. Babah Sumaye tayi murnmushi ta ce, shan sigari wurinmu ne muke ganin shi kamar da aibu, amma wurin mutanen Bauchi da Katsina ba komai ba ne yin hakan face kwalliya, ko gaye 63 tunda za ki samu har 'yanmata a wurin kawance suna sha, da haka ta kashe hirar tamu a kan Babah Lantana. Wani abinda na kasa hakura dashi in daina yin shi shi ne shiga dakin Babah Lantana, ban san dalili ba daga in da duk na fito sai na shiga, sai dai in na shiga naga ledar dakinne nake tunawa musamman ma da yake sau biyu tana rankwashina a kan taka mata ledar da nayi da kafata bayan kuma ni take sawa in goğe mata ita. Yau ma nazo zan shiga kaci6is muka yi muka hadu a Rofar dakin ni zan shiga ita zata fito, don haka nayi maza naja na tsaya nan take kuma na juya zan koma nawa dakin ita ma har ta nufi kicin sai kuma naji ta ce min ke ni zo nan mana in tambaye ki, nayi maza na dawo kusa da inda take din kafin naja na tsaya cikin natsuwa ina sauraronta. Wai zaryar me ki ke yi min a daki ne? ba ki ji kashedin da nayi miki ba ko? Ba fa za ki iya hana ni komai ba, ni kuma da ki ke ganina fa ko da Ramatu na samu a cikin gidan ba za ta takura min da komai ba, don bata isa ba sai dai ma in bata yi sa'a ba in korata waje, don kuwa da shirina na shigo. Jikina ya dauki rawa yayin da ita kuma ta daga murya wajen yi min magana, haba wacce 64 irin jarababbiyar yarinya ce wannan babu hali ki ganni da mijina a daki sai ki kama yi min zarya ki ce biro, ki ce pencil, ki ce kudin jarrabawa. Da ya ce ki rinka tambayata raina ni ki ka yi kina ganin ban isa ba ko? To ai kwa za ki gane ke ce ba ki isa ba sakarya kawai, shashasha da ta gaji iyayi da munafurci wurin uwarta, kai ke kam ta tafi ta barki da mummunan abu za kuma ki sha wahala. Taja tsaki kafin. ta wuce ta bar ni ina ta faman bari ban saba jin irin wadannan kalaman ba balle kuma a ce a kan Innata a ke yin su. 'Yan kwanaki kadan da zuwan Babah Lantana gidanmu sai nayi matukar tsorata da ita, ko maganarta naji sai gabana ya fadi, gashi bana sanin lokacin da nake aikata laifin da take cewa nayin, balle in rinka kiyaye mata ban saba da mu'amalla ta tsawa da yawan duka ba, sai kawa1 aka wayi gari na tsunduma a cikinshi. Yar tsarabar' da Babana ya saba kawo min ina ci na kwalama bayan abincin gida na daina samu saboda yanzu komai yazo dashi ita yake mikawa wai ita ce mai bani, ita kuma sai ta cinye ina kallo. Hakan bai dame ta ba a farkon zuwanta gidanmu, ban cin komai jikn kaza in ba cinya ba ne amma bata cika kwanaki arba' in da zuwa ba 65 sai da na zama har kai da kafa ci nake yi, wanda mu da sanda Innarmu take raye ba a sa sua cikin miya. A kowane lokaci a cikin yi min kashedi take in kika ce abinda zamu yi da ke kenan to kuwa laiie zamu sa kafar wando daya ni da ke a gidan nan, ba kuma zata fito ta ce min ga abinda nake yin ba wanda zai yi dalilin da za a sa kafar wando dayan da ni ba. Rannan ta cika sati shida da zuwa gidanmu, wato kwanaki arba'in da biyu kenan, daga Makarantar allo na taso don haka na biya ta wurin Babana don in dan zauna mu dan yi hira inji dadi, tunda shima mu'amullar tamu ta dan sauya. Bai bar ni na zauna ba ya ce min maza je ki gida uwarki tana can tana jiran dawo erki tunda in ba kin koma gidan ba ba dora girki take yi ba, sai tayi ta jiran zuwanki. Kamar in ce wa Babana a'a Baba bata jirana ni bata sani ma wani aikin da ya danganci girki tuna ta ma hana ni shiga kicina dalilin wan naman miyarta yana bata, amma sai na kasa cewa Babana komai, na kamo hanya ka na dawo gida. Naje na gaishe ta sannu da gida Babah, bata amsa ba sai da nayi sau biyu sannan ta daga ido 66 ta kalle ni sai yanzu ki ka dawo? Ai ni da ke nea gidan nan na wuce sumsum na shiga dakina na zauna don yanzu na riga na saba da zaman cikinshi. Ban dade da zaman cikin nashi ba naji wata murya tayi sallama, ban ji amsa ba iyaka dai naji an kurma ihun da ya sanya ni nayi maza na yiwo waje saboda firgitan da nayi, sai dai sabanin yanda nayi zato abin tsoro ta gani ashe wai murna ne haka don ganinsu nayi sun rungume juna ita da bakuwar tata. Nayi maza na koma dakin nawa na zauna a zuciyata ina mamakin yanda babba zai iya kwallara ihu irin wannan da sunan oyoyo ko murna. "Na rantse ko jiya sai da nayi maganarki cikin zuciyata, ashe kina hanya Delu. Delu ta ce "Ke Lantana juna biyu ki ka samu ne naga kin habake kin zama wata danya? "Juna biyu wane iri? Kalau dina nake shimna dai maigidan na ji shi yana maganar waiko juna biyun ne, ni kuwa bai sani ba yaushe rabona da al'ada, na fashekara sai dai zan koma wurin mutumin nan ko zai bani maganin da al'adan tawa zata dawo. 67 Ta kyalkyale da dariya "Tana tafiya ne dama ta dawo? Ai in ta tafi ta tafi ke nan in dai ba ciwo ne yayi dalilin daukewar nata ba." To ai nima ciwon ne. Delu ta sake wata 'yar dariyar kafin ta ce "Ke dai kin samu gida na kuma yi miki murna don da gani ba sai an tambaya ba kin yi shar da ke har kuruciya ta dawo miki, kai ni'ima da dadi take, sai dai kawai in bawa bai samu ba ya hakura Ubangiji ya samu a danshinku." "Kai Delu kenan, abin dariyarki yawa ne da shi. Tayi maza ta mike ta shiga cikin daki ta fito mata da abubuwanci da na sha da Babana yake kawowa tana hana ni tana ci tana 6oye saura don masu zuwa mata. Haba, gaskiya ni'ima ir bayyana a jikinki ke ki ce gara kawai yake shirya uiki ke in ban da ita haihuwa lokaci ne da ita da sai in ce gianta ki ka zo ki neme ta." Babah Lantana tayi dariya, ai iya shegenki yawa ne da shi kina nufin lokacin nata ya wuce ne a wurina? To bari mu gani. "Ke ki ce aure sosai ki ka yi, ai tunda ki ke aure ma ina ganin in banda aurenki na biyun nan ba ki taba dacen aure irin wannan ba, sai aka yi rashin dacewa aka tare mishi da dan zani, ai daga rikicin cikin nan nc abin duk ya shiririce 68 zama ya ki dadi sai da aka rabu daga baya ma yazo ya rasu. "Delu ke nan to wa ya tambaye ki wannan dogon bayani ko kuma duk a san jin naman a na kawo miki ne ki ke kokarin yi min wannan tonon asirin?" Delu tayi dariya ta ce, "To gida mu biyu tonon asirin me zan yi miki Lantana? Auren naki ne ya bani sha'awa, ga shi kin yi fes da ke da alamar shi mutumin bai da wata damuwa. Ta ce, Eh to kamar dai hakan nake zato tunda zuwa yanzu ban ga wata damuwa a wurinshi ba, shi ba a musu da shi in kuma takamanki son kudi ne ma to shi ke zai baiwa ajiyar ribar cinikin nashi ya dauki jarin da gobe zai koma dashi kasuwa, duk abin da ki ka ce kin yi da kudin kuma ba magana zai yi ba. In har ina da wani abinda ya tsaya min a rai game dashi to yar shi ne sai ko matarshi da ta rasu, kinga ita 'yar duk inda tayi yana bin ta da kallo sau goma kuma in zai yi miki wata magana to shida a kanta ne hudin akan uwarta da bata duniya. Yanzu haka akwai wani hoto na uwarta da ya kakaba min a cikin dakin maganar hoton kawai nayi kan ko za a cire shi ne a dana tunda dai mai shi ta riga ta mutu kar kiga irin fushin da yayi, to 69 ga maganar wadannan yaran da nake so in dawo da su gidan nan a matsayin 'ya'yan Yata da ta rasu ta bar min su. Kin san ba zai yiwu in ce mishi nawa ne ba don ya ma taba tambayata su na ce mashi ai tunda ubansu ya rasu danginshi suka kwashe su suka tafi dasu ni ko zuwa bana yi ke ce mai zuwa don na gaya mishi ke Yayata ce. "Au, haba? Yanzu nan ni surukarshi ce? ta ce, Eh abinda na gaya mishi kenan, ta ce to ai shi kenan su kuma yara kin hadawa Alhaji Tanimu ko? Tunda shi kam ya mutu ai magana ta kare, sai mu tafi a hakan unda kuma abin ya zama haka to bari ni kuma kiga abinda zan yi miki. Zan je miki wurin Mallam na kan tudu a kan damowowin naki duka sai mu ji abin da zai ce, da sauri Babah Lantana ta ce ma to Delu na gode." "A'a ba kin gode ne maganar ba, saura kuma in yi miki rana ke kiyi min dare, in taimake ki ke ki samu mijinki a hannunki ni kuma kiyi min iyashege menéne naku ban sani ba?" "A'a to ni kam ai ba sanin yau ki ka yi min ba, in ma ya ya nake kin fi kowa." "To ni kawvo min abinda za ki kawo min in tafi." Ta tashi ta shiga daki ta fito ban san nawa ta kawo mata ba, 70 amma naji ta tana godiya tare da fadin wannan duka? Ai babu komai kuma tunda ba wani nisane damu ba zan sa miki kwano ki rinka turowa ana daukar miki abincin dare, bakuwar Babah Lantana Dela tayi ta godiya tamfar dai wacce aka ce an baiwa kyautar kujerar Makkah. Rannan na shirya zan tafi makaranta da safe a bakin kofa na tsaya nayi sallama aka amsa min na bude baki nace Babah zan tafi ne? tunda abinda Babana ya ce in rinka yi kenan. Da saurinta ta fito tana fara'arta har kin gama shirin ne? Na ce mata eh, ina kallon irin kallon da tayi wa gidan amma ba ta ce min komai ba sai ta ciro sule ta miko min, *"To ga sule nan sai ki sayi abinda ki ke so ko? na ce, To. Na juya na tafi. Ina dawowa gida ko amsa salamar da nayi mata bata yi ba ta rufe ni da duka titim-titim ""Ni ki ka mayar 'yar iska saboda kin ganni a gaban ubanki ko? Ba kiyi min sharar tsakar gida ba ki Rarasa min wanke-wanke ba ki ka kama hanya ki ka tafi, ni baiwarki ce? Nayi maza na ce, a'a. mara kunya kawai mara tarbiya dama kin nemi zama lafiya dani da ya fiye miki, ina canjina? Nayi maza na kara zaro 71 ido cikin tsananin tsoro a dalilin ban san tana bukatar in kawo mata canji ba. Ko duka ki ka kashe kudin da sauri na ce mata eh, don kar ta ce na bata mata lokaci wajen amsawa, ai duka kika kashe? Uh lalle ina da aiki, ni Lanti ni Lanti in ban yi da gaske ba lalacewa za ki yi a zo ana cewa ni ce sanadi wato a yanda ki ke din nan kina iya kashe sule guda a wuni. To in ba ki bi maza ba kuwa kiyi me? Tayi wuf ta sake kamo ni ta tittime ni kafin ta sake ni ta wuce ta tafi tana to kuma a bakin abincin ranarki kin ji na gaya miki. A wannan lokacin kusan kullum sai Delu tazo gidanmu ta kawowa Babah Lantaa wani abu ta kuma kar6i kudin wani ab1 da za a sake karbowa kusan duk lokacin da taro kuma za kaji ta tana tambayarta kina ganin wani ranii a tare da shi? Ta ce to abinka da wanda baya magana wancan na sakawan dai a karo min shi, ta ce to kin gane kyanshi ke nan ta ce eh. Rannan Babana ya dawo daga wurin tumatir din shi ta kawo mishi abincin shi ban san dalili ba naji ya kwalo min kira da sauri na amsa na fito ungo cokali Yaacuwuna zauna kici abincin nan kin ji." 72 Cikin hanzari na gyara na zauna na kanma cin abincin nan sa da na cinye shi tas na debi kwanukan naje na wanke su na kife na sake daukan tsintsiya na share wurin tas na dawo zan wuce in shiga dakina sai naji Babana yana cewa ni Malama in tambaye ki mana. Da sauri ta ce mishi "Menene fa? ya ce, ba ki lura da irin ramar da yarinyar nan tayi ba, gaba dayanta fa ta zube kasusuwa sun bayyana a jikinta, ita kuma fa ba mai kashi ba ce, ramar tata tayi min yawa tun ina daurewa ina hadiyewa har abin ya gagaren na gaji na furta. Ita mai cikakkiyar fuska ta zama wata yar siririya, in dai ba bata da lafiya ba ne yasa ta zama haka ai akwai matsala babba ke nan a tare da ita wanda ya kamata abincika. Da sauri Babah Lantana ta ce, cikin hanzari kuwa, gara ma a fara binciken tun yanzu, ke Yacuna zo nan, ta sake zabura cikin hanzari ta shigo dakin nawa ta taso ni a gaba ta tsugunar da ni a gabanshi. To gata nan tayi bayani da bakinta, yauwa bawa da bakinshi ai wuyan sai dawa gare shi. Ina dalilin wannan kiran da kika yi mata? Babu halin' muyi magana ni da ke sai ki kira yarinya ki tsomataa a ciki? Yarinya? Tayi tambayar cikin wani yanayi na tsananin fusata 73 wannan ce yarinyar? Tafdijam, ba yarinya ba ce mace ce. To menene bata sani ba Mallam? Ai da kadan na fi ta sanin duniya wane sharri daa makirce-makirce ne bata kulla min? Tun farkon zuwana gidan nan fa kana ganin irin karbar da tayi min amma me na mata? Gata nan ai tayi magana da bakinta, ke ta zuba min ido tana kallona ina ba ki abinci ko ba na ba ki? Na ce kina ba ni. Ta gyada kai to, ina zaginki ne ko dukanki? Na girgiza kai tare da fadin a'a, ta ce to amma a hakan ne ki kaje ki ka hada ni da ubanki a dole ke ga mai uba ko? To mu ma da bamu da uban ba kinmu a ke yi ba yasa a ka daukan mana su masharranciya kawai. Watakila shirun da Babah Lantana taga Babana ya yi ne yasa ta tayi ta maganganu da tashin hankali mai yawa, bai ce mata komai ba yayin da ni kuma nayi matukar tsorata don gani nake tanfar zata mike ta rufe ni da duka ne. Har tayi ta gaji bai ce mata komai ba nima kuma ban matsa daga inda ta durkusar da ni ba, sai da a ka kira sallar Magriba ya mike zai fita sai ya ce min je ki kiyi sallah nå ce mishi to. Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar Isha'i naji shigowanshi a tsakar gida ya samu Babah Lantana tana goge kafarta da dutse bayan 74 ta fito daga wanka naji shi ya ce mata "In kin gama abinda ki ke yi kije gidanku sai nazo." Ko da bana nan a kusa nasan ba karamar firgita Babah Lantana tayi ba da jin maganar tashi saboda irin na'am din da naji tace kafin daga baya ta soma maganganu irin na borin kunya "Ai gara haka, ni dama tuni na dade ina jiran irin wannan maganar ta fito daga bakinka ba ka furta ba ne sai a yau. To kuma sai me? Ai ta fi nono fari in dai a kan wannan munafukar yar taka ne ai yanzu kasa hannu da aure. Bai ce mata komai ba har ta gani da maganganun ta figi gyalenta ta fita. Tana fita ya tashi ya fita shima bai wani dadee ba sai ga shi ya dawo min da gasasshen nama, nayi maza na karba na lamushe sabanin da da in ya kawo min na rinka yanga kenan yana rarrashina ina cewa an labta yaji yayi ta karkadewa yana cewa to ungo wannan na cire miki yajin. Washegari ma haka tare muka karya gidan ya zama gwanin dadi kusan kwana biyar babu Babah Lantana alama na Babana bai bi bayan nata ba tunda cewa yayi taje sai yazo, cikin zuciyata babu abinda nake fata irin a ce ta tafi kenan ba za ta sake dawo mana gidanmu ba. 75 Tun kwanaki ukun farko na barinta gidanmu yanayin jikina ya soma sauyawa na soma dawowa cikin hayyacina. Rannan muna zaune ni da Babana tsiren Salim mai nama ya kawo min ina ci ina korawa da ruwan tea mai kauri sai kawwai muka ji sallama, Babana ya amsa yayin da ni kuma na dauki abinda nake cina shige dakina na zauna cikin fargaba da faduwar gaba saboda sanin Delu ce tare da Babah Lantana. Cikin ladabi naji Babna yana yi mata gaisuwa irin ta surukuta saboda gaya mishin da Babah Lantana tayi cewar ita din yarta ce. Kayi hakuri Mallam maigidan ne baya nan sai dazun nan ya dawo ya samu Lantana a gida na kuma yi mishi bayanin kwanakin da tayi a gida shine ya hau ni da fada ina dalilin da zan barta tayi ta zama haka ban dawo da ita ba? Na ce, To naga baya nan ita kunma ta ce min kace kana zuwa ya dai yi ta fada kan rashin hankalin da ya ce nayi ita kuwa in ban da da mutane a gidan nan yau da ta gane kurenta ba kadan ba, don niyya yayi ya bata ka shi sosai, to sai a ka rirrike shi, ya ce in. baka hakuri kafin Va zo da kanshi. Da sauri Babana ya ce mata, aa ba sai yazo ba nima zan zo gidan, kuma ayi min godiya 76 amma gaskiya in ban da wannan bayani da ki ka zo min dashi da kuma ganin girman surukuta ba zan iya tozartata ba, wannan da cewa nayi ku koma tare. To ina jin kunya. Da sauri Delu ta yi ta magana tana ba shi hakuri, "Ai shi ma maigidan ya ce ba karamin abu tayi maka ba." Kalamanta suka sanya har Babana ya shiga yi mata bayanin abinda ya faru duka, a gabana tana aibanta min yarinya har tana cewa wai da kadan ta fi ta sanin duniya, me take nufi? Ni fa saboda irin wadannan al'amuranne yasa nayi ta zama a haka dagani sai 'yata, saboda bana son kananan maganganu da fitina, ban saba da su ba. Ni matata bata saba min da irin wannan kace- nacen ba, ba kuma zan yarda in saba da su ba, a yanzu da girmana da komai. Gaskiya ne Mallam, wannan maganar taka ita ce gaskiya in ban da rashin hankalinta ita wannan yarinya ai 'yarta ce yanzu ita marayunne da ita ba hawa-hawa? Ga nata na kanta ga kuma na yarta da su kuma babu uwa babu uba, to don me ba za ta rike wannan da kyau ba, shi al'amarin duka ai yiwa kai ne, kayi hakuri in naje gida kuma zan yi mishi bayanin da kayi min duka. To na gode Yaya, in ji Babana, ina ita uwan take? Babana ya kwala min kira saboda jin Delu 77 tana kirana, don haka na fito nazo na durkusa na gaishe su, uh'uh uh lalle yarinyar ta zube amma ba ka ga kamar har da macijin ciki a ciki ba Mallam? Ina ganin a nema mata maganın macijin cikin, ka san shi shegen abu ne sai yayi ta ci a ciki ba a sani ba šai dai ayi ta tsotsewa ana motsewa a tsaye ba a kwanta ba, tana maganar tana tafiya bayan tasa hannu biyu ta karbi abinda ya bata na alheri tayi godiya. Bho Kwana biyu bayan dawowan Babah Lantana, Babana bai sake mata ba, itama kuma ta shiga Cikin natsuwarta sosai. Rannan sai ga Delu tayi sammakon dawowa tun Babana bai fita kasuwarsh1 ba, suna gaisawa naji tana ce mishi maigidanne ya ce in zo in kara duba ku in kuma kara baka hakuri don babu abinda ban gaya mishi ba da na koma ranshi ya baci sosai hankalinshi yayi mummunan tashi ya ce wannan ai nema take ta zubar mishi da mutunci. Ya dan yi murmushi kadan are da fadin a'a haba, ai ba a haka ka hukunta wani kan laifin da wani ya aikata maka ba adalci ba ne, ita kam mace ai dama kowacce da irin halinta ba a kuma yin shaida a kanta iyaka dai kawai akwai wacce tafi wata dama-dama. 78 Haka ne Mallam, suka ci gaba da yan hirarrakinsu irin na surukai kafin yayi mata sallama da cewar zai tafi kasuwa ta sake sa hannu biyu ta karbi alherin da ya bata tare da godiya. Sai dai yana barin gidan ta juya wurin Babah Lantana, uh'uh'uh kai wannan miji naki da taurin kai yake, bai rusunawa kan ra'ayinshi, ga shi da kafiyar tsiya bai kuma damu ya fadi abinda ke ranshi ba, ko da kuwa yasan hakan zai iya batawa wani rai. Babah Lantana ta ce, Uhun, ai ba ki ma sani ba, tunda muka dawo din nan fa bai saki jikinshi da ni ba, ba ya ma yarda ya hau gado ya kwanta sai kawai yayi shimfidarshi a kasa. To me ki ka ce mishi? Zuba mishi ido kawai nake yi in na nuna mishi na damu ai sai ya rinka yi min irin wannan wulakancin. Ai ke ce ma Lantana da wautarki ba ki tàbbatar kin kama shi a hannunki ya kamu ba za ki fara kawo mishi iya shege. Wannann aiiya shege ne, don me za ki tasa mishi 'yarshi a gaba? Tasata nayi a gaba Dela? Babah Lantana ta taso, Delu ta ce, ai ke dama haka ki ke, in mutum ya ce zai gaya miki gaskiya sai ki zabura ki ce za ki yi fushi don ba kya Sonta. 79 Wannan kuma a kan wannan yar tash1 in ba ki yi hankali ba komai ma zai iya faruwa, kar ki ce ba komai ma zai iya faruwa kar ki ce ban gaya miki ba, yanzu dai ga wannan shi wancan mutumin ne ya ce a kawo miki ki samu gero kwaya bakwai ki hada da wannan garin maganin ki make shi a gefen bakinki sanda ki ka tabbatar kin shawo kanshi zai kula ki sai ki kwana da shi gari in ya waye sai ki juye har da yawun baccina faranti ki shanya shi a dakinki kar rana ya taba, sai ya bushe sai ki dake shi lukui-lukui shi za ki rinka zuba mishi a abinci da komai ma ko da kuwa ruwan da zai sha ne. Ta ce mata to, Delu na gode babu kuma addu'ar da za a yi ko? Da sauri ta ce, a'a za ki yi addu'a mana kar ya ji kar ya gani, abinda za ki rinka fada ke nan tayi maza ta sake yin godiya. Delu da kanta tazo ta samu Babana ta roke shi wai ya yi wa wata yarta da ke gidan miji taimakon ta samnu zaman lafiya da mijinta, saboda kullum a cikin barazanar korarta yake, ga ta kuma da kananan 'ya'ya har guda biyar. Ina jin Babana yana gaya mata cewa in ban da kananan 'ya' yannan da a ka ambata ba zai yi ba, don mata ba wani kirki ne da su ba, suna samun kan namiji to su kuma sai rashin imaninsu ya tashi. 80 Delu ta ce ina za a yi haka Mallam ita da take neman yanda za a yi ta zauna a kan 'ya'yanta? To a dai gaya mata in ta samu yanda take so ban yarda ta zalunce shi ba, in kuwa tayi haka ita da Ubangiji da sauri ta ce zan gaya mata Mallam, ai don ma ba ka santa ba ne. A kan idona Babana ya rinka yin rubutu a jikin allon karfen shi yana wankewa sai a bayan idonshi in ga Babah Lantana ta kafa kai ta kwankwade shi tas. Ni ina kallo ko Yaya Dijah ban taba gayawa ba, balle wani can daban saboda kullum naje gidanta ta ganni sai tayi kuka 'yar magana ba mai tsanani ba in na gaya mata itama tayi ta kuka don haka na koyi kame bakina. Ban kuma tabbatar jagwalgwalo da aikin da yake yi wa kanshi ya kama shi ba sai a ranar da nake sharar tsakar gida da safe yayin da shi kuma yake cikin dakin a kwance a kan gado. Naga an yiwo fito da wani hoto babba waje, gilas dinshi ya tarwatse. Da sauri na nufi inda hoton ya fadi cikin tsananin tsoro da fargabar kar abinda nake zaton ya tabbata, ina daga hoton gabana ya fadi, jikina ya dauki rawa 'shi ne hoton Innata da zamanshi a dakin ya dade yana tukurawa rayuwar Babah 81 Lantana bata samu yancin yin yanda take so da shi ba, sai yau. Ina cikin tunanin Baba bai san ta cire mishi hoton shi ba sai na jiwo ta tana ce mishi ni fa na Cire wannan jarababben hotonn da a ka kakaba min a daki. Shekara da shekaru tana can a kwance har kashinta yayi fari amma ka ajiyewa mutane ita a wuri tana nema ta rinka yi musu fatalwa, wannan in banda ni din ni ce ai da bata bar ni na zauna a dakin ba, to kullum na hafa ido da ita sai na zare mata nawa nima in kuma ce mata kurwata kur taci kanta tasha bakinruwa. Ban ji ya ce mata komai ba, to balle uma ni na dai sunkuya kawai na dauke hoton na kuma tsince gilasan da suka fashen har suma ban zubar ba, kulle su nayi a wani tsumma naje na adana su a cikin kayana na zauna nayi kuka sai da na gaji na share hawaye. Tunda Babah Lantana ta samo kan Babana ta Kara bayyanar da kiyayyar da ke tsakaninta da Babah Sumaye da mijinta, tun farkon zuwanta dai dama bata yarda tayi wata mu'amallah da su ba, sannan duk wani lokacin da wata magana ta taso da ta shafe su za ki ji tana yawan aibanta su ko ta kira kirkinsu da Babana ke fadi da kirkin munafukai. 82 Nan take kuma ta shiga rattabo mishi aibobinsu, a yanzZu ta kaima ta raba Babana da Baba Baidu cin abincin da suke yi da daddare ban dai san yanda a ka yi ba gani kawai nayi sun daina. A bakin Babah Sumaye kuma naji tana ta fadin, ai mace shu'uma ce in ka gamu da ja' ira tosai dai addu'a kawai, amma in ba haka ba yaushe? Yaushe za a zaci za a yi haka? A wannan lokacin ta kai ma ko makarantata ta boko bana samun zuwa a kan lokaci, karatuna na Alkur'ani kuwa tuni tasa kafa ta shure shi ko a gida ta ganni ina karatun Alkur'ani zata shiga zage-zage tana fadin ai Ubangiji ya riga yayı magana a kan irinku masu yi don ace su ya tashi ni ki bani wuri, munafuka kawai. Ni da na rayu da Innata ina wanka safe da yamma har bayan ta ma a haka nake ina tashi nayi ayyukana na safe zan yi wanka kafin in tafi Makaranta in na gama komai zan kwanta ma zan sake yi kafin zuwan Babah Lantana gidanmu na dauka ka'idar rayuwa ne yin hakan. A yanzu duk na daina saboda babu halin ta ganni nayi wanka ko zan yi sai ta ce wai kishi da ita nake yi ranan har tana zaunar da ni tana vi min bayanin da ki ke ganina ina wanka safe da yamma ba ra'ayina ba ne yin hakan fitinar ubani ce ta kan sa ni, in ban da haka babu abin da zai 83 sa in yi ta jika jikina da da ki ke kwaikwayona ke a wane dalili ki ke yin naki? Irin wadannan kalaman nata suka sanya ni na zamo sai in yi kwana uku hudu ban yi wanka ba balle ayi maganar wanki ga shi a yanzu tsanin da ke tsakanin gidanmu da na su Babah Sumaye ya rikida ya zama wari tunda takai ma har Babana ya kafa min dokar shiga gidan. A wannan lokacin kuncin da nake ciki ya kai in da yakai kusan kowane lokaci a cikin yunwa nake yawo ga kazantar jiki da na kaya gaba daya na hade na zama babu kyan gani. Tuni Asabe ta dawo gidanmu a zama, sai dai ta dawo ne a matsayin 'yar da Yayarta ta rasu ta bari ba a matsayin ita ta haifeta ba ni da Asabe kai daya muke a tsawo sai dai ta dan fi ni kauri kadan saboda ta girme ni idonta a bude yake kwarai saboda za ka ji manya-manyan maganganu a.bakinta. A wancan lokacin da ban san komai ba game da al'ada saboda kuruciyata ita bata jin kunyarta a wurinta na fara ganin ta saboda bata damu da kintsa kanta tayi ta gama wani na kusa da ita bai sani ba. Tunda Asabe ta dawo gidanmu da zama al'amura suka kara tsananta a gare ni dakina da dah nake yawan zama a cikinshi saboda kuntatar 84 da nake yi a tsakar gidan yanzu ba ni da halin yin hakan in ji dadi saboda ni da ita ne a ciki gadonmu ma daya dan kankanin motsi zan yi ta rufe ni da duka babu mai cewa ya isa balle aje ga tambayar dalilin dukan. Ni kuwa a kwance muke a gado da daddare to matse ni take yi a jikin bango da kuma zan ji tsananin yakai tsanani in dan yi motsi sai kawai tayi min gula da gwiwar hannunta. In nayi kuka Babah Lantana ta fito ta kare min tanadi tana fadin ai duk bakin cikinki ba ki isa ki kori Asabe daga gidannan ba ina zamnan ubanki ne ita kuma tana zamana yauwa in takamar ki maraici itamna marainiyar ce ta uwa da uba, bata da kowa sai ni din nan da ki ke ganis Don haka babu in da zata yauwa yarinya 'yar kankanuwa da ke sai bakin cikin tsiya tunda Asabe ta dawo gidannan ki ka dauki karan tsana ki ka dora mata me ta tsare miki ne haka? Duk abinda ke faruwa kuma Babana yana ji amma sai ayi a gama bai ce komai ba, kamar ba ya nan a gidan. Tunda Asabe ta dawo gidanmu Delu ta rage zirga-zirgan karbowa Baba Salamatu abubuwanta sai Asaben ce mai karbowa kusan kullum sai ka ji ta karbo nata wani lakanin 85 asirin saboda duk samun Babana da tayi bai ishe ta ba tana neman kari. Rannan ina daga dakina a zaune ina hangen su Babah Lantana ce ta kama wani kii mai rai ta shake shi yayin da Asabe ke rike da wata 'yar kankanuwar làya da taje ta karbo mata a hannu. Yana bude baki sai kiyi maza ki jefa layar a ciki in ji Babah Lantana Asabe ta amsa da to. Hakan kuwa a ka yi wahala tana isan kifin nan ya hangame bakinshi Asabe tayi maza ta jefa laya a ciki nan take kuma suka yi maza suka kama balkin nashi suka matse suka sa zaren lilo suka daure tamau. To dauki maza tun bai mutu ba kije da sauri ki jefa shi a cikin rafin nan na kasan layi yan uwanshi su cinye shi a haka. Da sauri Asabe ta ce mata to, ta kuma suri ledan da suka jefa kifin tayi waje da shi don kai wa rafin da ta gaya mata. A yanzu ta kai a ko a waje naga Babana ko na same shi a wajen tumatirinshi ba ya iya sake jiki yayi magana da ni balle yayi min wani taimako, don haka nima sai ban cika zuwa in da yake din ba. Don haka a yanzu sai na zama kan dakalin gidanmu ne wurin zamana ko kua in yi zamana a cikin zauren gidanmu kan tsohuwar tabarmar Innata da nake shimfidawa. 86 Rannan na samu naje Makaranta daga can na saci jik na wuce gidan Yaya Dijah a dalilin itama a yanzu bana tambayar zuwa gidanta a kyale ni saboda wai ita ce take kara koya min iya shegen da nake yi. Ina zaune a dakin nata ina cin abincin da naje na debo a kicin dinta yayin da ita kuma take share hawayen da ke zuba a idonta a dalilin zancen da take yi min ashe abin da matar nan tayi wa Yakunbo Halima ke nan da taje gidanmu kan maganarkı? Shiru nayi ban amsa ba, sai taci gaba da magana cikin tsananin kaduwa da mamaki tamfar a lokacin ta fara jin zancen, wai ta kawowa Yakunbo Halima diga da cebur ta ce mata taje kawai ta tono Innarmu a inda a ka binneta tazo ta rike ki tunda nata rikon bai yi ba an raina? Na ce Eh nayi shiru ta gyada kai to babu darnuwa ba zamu je nu tono ta ba amma kowa zai tafi inda taje din lokaci ne kawai wata rana kuma sai labari Baba ya bada ke ya ki? Ya hana ni ke ya hana su Yakunbo amma ya kasa hana wulakancin da a ke yi mana a kanki na kullum mutum ya ganki sai yayi kukan bakin ciki. Ta dan yi shiru kafin zuwa can ta sake cewa ko da yake dai shima ba jin dadin zaman nan 87 nasu yake yi ba, yana dai yin shiru ne kawai tunda gaba daya ya zube Baba mai tsabta amma duk ya zama wani iri ta soma kuka sosai. Na mike na ce mata zan tafi, tayi maza ta bar kukan da take yi ta koma tambayata tun yanzu? Ki tsaya mana in taya ki tsifan kanki ayi miki kitso. Na.ce a'a in nayi kitso zata gane na biyo ta gidannan ta gayawa Baba. Da sauri Yaya Dijah ta zaro ido tana kallona Baban ya hana ki zuwa wurina ne? nayi maza na ce mata a'a amma ai ban ce mishi zan zo ba daga Makaranta ne kawai na biyo, da wannan bayanin ne ta dan samu natsuwar zuciyarta ta tashi taje ta kawo kudi ta bani nasa hannu na karba na juya zan tafi tana bina tana yi min magana ki adana su kina kashewa a hankali kar kuma ki rinka zama da datti, gobe gari yana wayewa ki tsefe kanki kije kiyi kitso na ce mata to na wuče na tafi. A farkon zuwan Asabe gidanmu na sha ganin Babah Lantana tana feshe mata kanta da sheltox din da Babana ke kawowa gida saboa kashe sauraye da sauran kwari saboda kwarkwatar da take fama da su amma daga baya da suka yi sa'a tata kwarkwatar ta mutu saura kuma suka dawo kaina sai Asabe ta ce wai ba za ta rinka kwanciya da ni a gado daya ba don kar in sanya mata kwarkwatata a kanta. 88 Babah Lantana ta ce kwarai kuwa ina ma ake haka me kwarkwata da mara ita su hau gado daya su kwanta? Don haka ta bani zabi tsakanin abu biyu ko dai in tsaya ta aske min gashin kaina tayi min malu saboda kwarkwatar da ke kam nawa tayi yawa ba zai yiwu a tsaya yin wahalar taba ko kuma in dawo Rasa in rinka yin shimfida ina kwanciya. Ita Asabe tana kwana a gado duk da ban bude bakina nayi zabin ba hukuncin da Babah Lantana ta zartar min ke nan dawo da ni kwanciyar kasa kan wata tsohuwar tabarma saboda na ki yarda in tsaya ta mayar min da kaina tal kwabo. A wannan lokacin ko da gaske Babana ya daina Sona ne kamar yanda masu yaran suke gaya min? ko kuma a'a masifar da take balbale shi ta ita ne baya so yasa duk abinda zata yi yake zuba mata ido ban sani ba, duk abinda take yi bai cewa komai hakan kuma bai sa ya tsira daga masifar tata ta bar shi ya zauna lafiya ba. Ko cinikinshi ya kawo mata kamar yanda ya saba in har bai kawo da yawa ba sai tayi mishi fada gashi babu halin ya ce mata a cikin kudin nan ayi abu kaza, sai ta ce a wane kudin? A irin hidimar gidan nan ne wani abu zai rinka raguwa a wadannan 'yan kudin da ka ke kawowan. 89 Kullum sai ta tasa shi a gaba ya bata kudin cefane daga kudin aljihunshi amma kuma bata yin girkin kullum in tayi miya guda daya to bata sakewa ko da kuwa bata yi dadi ba sannan ko zata kwana uku to sai ta kare kafin a sake wata. A wannan lokacin ne na samu kaina cikih wani irin hali da ya tabbatar min da maraicin uwata da nake ciki na rasa Inna na rasata kuma irin rashin da na kara ganewa cewa rashi ne nahar abada bani kuma da mai yi min maganin halin da na samu kaina a ciki a dalilin rasatan da nayi. Kullum dai Yaya Dijah da su Yakunbo Halima suna yawan gaya min cewar wata rana zai wuce sai dai in bada labari to amma yaushe ne wataranan zai zo? Wannan ita ce tambayar da kullum ta ke tsayawa a raina don gani nake amar ba zai kare ba tunda kullum abin nata karuwa yake yi. Ina makale a zauren gidanmu kuka nake yi saboda bakin cikin kalamin satan da Babah Lantana tayi wai ni na shiga dakinta na diban mata kudinta saboda kawai tayi min bincike cikin kayana taga kudina da nake 6oyewa ina tsakura a hankali ta kwashe wai nata ne alhalin Yaya Dijah da 'yan uwan Innata ke ba ni. 90 Don haka wai in fito mata da duk sauran kudin nata ma da bata gani ba, bayan kuma ni ko shiga dakinta bana yi ta kuma san hakan. Asabe tazo zata wuce ni da kwano a hannunta a rufe nayi zaton ai kanta a ka yi tana isowa inda nake sai kawai naga ta saki kwanon a kasa tayi maza ta kama ni tana fadin gata Babah ga ta nan na kama miki ita. Sai kawai naga Babah Lantana ta shigo zauren ashe damà tana makale a kusa, hannu ta saka ta kama ni ta rike wani irin riko mai tsanani, ta shiga jana zuwa cikin gida ni kuma ina ta ihu saboda sanin da nayi cewar zan sha wahala ko daga jin irin kamun da tayi min. Muna shiga gida ta takarkare ta sakar min wani irin azababben dundu da yayi sanadin da na durkusa a kasa nan take kuma tarufe ni da duka tana kuma yi min tambayoyi ni na kashe miki uwarki ne da za ki tasa ni a gaba da masifa? Kiyi min sata kar in yi magana? Ni nan da ki ke kallona ubanki ma ba tsoro yake bani ba balle wasu can banza a banza in na gama dukan naki kije yau ma ki nuna musu ina nan ina jiransu su zo Su same ni don ni nan da ki ke ganina warki ce daidai nake da mazaunan kowa. Ki min sata ki ce kar in yi magana? Inaki ka min sauran kudin? Sau nawa kina yi min sata ina 91 kyale ki? Eye? Haka kawai ni da gidan mijina kin takuramin kin hana ni sakat kin ishe ni da fitina wai a kanki ke kadai a ka fara maraici ne? iye ta sake rufe ni da wani irin duka har ina fitsari a jikina amma bata fasa ba. Sai ga Babah Sumaye ta shigo kai haba wace irin musiba ce wannan? Wannan wane irin duka ne da bai karewa haka? Haba yarinyar nan kin san tana nan fa ki ka aurar mata ubanta kin kuma zo mata gidansu kin tasata a gaba da masifa bayan ke ga taki kin kawo kina rike da ita a ina a ke haka ne dan gida ya wulakanta agola ya zauna lafiya in ban da wurin azzalumai irin ki? To ki. rama mata mana tunda kin shigo da kanki shugabar munafukai. "Ba zan rama mata ba zamani ne zai tantance komai shi ne zai yi dalilin da sakamako zai hau kanki don ba za ki dauwama a haka ba." Bakin cikina ne zai kashe ku munafukai mijina kuma ba ku da yanda za ku yi dani a kan shi yana sona. Babah Sumaye ta ce, wane bakin ciki za a yi da ke Lantana? Matar da ta gama rayuwarta a gwagwarmayar rashin gaskiya, yau ana nan gobe ana can duk in da a ka je din kuma sai an yi cinta? Menene naki ba a sani ba? Har dakin da ki ka zauna ki ka haifi shegun 'ya'yanki an nuna min, babu wani abinki da ban sani ba, 92 wai ma Mallam Habun muna nan muna yi mishi addu'a Ubangiji ya fitar da shi daga halin da yake ciki, ya bayyanar mishi da ke ya gane asalinki, ki kawo shegiyar yarki gida ta sake amma ki hana yarinya sakat, to ana me ina dalili? Ta juya ta fita ta bar Babah Lantana tana fadin ai tunda ki ka kulla min irin wannan sharrin to hukuma ce kawai za ta raba ni da ke, za kí san kin iya sharri. Tana kuka tana kurma ashar ganin da nayi Babah Sumaye ta fita ta bar ni da ita cikin wannan hali yasa nima nayi maza na fita na bar gidan saboda ban san abinda zata yi min ba in ta dawo hankalinta ta gane ni ce a zaune kusa da ita. GidanYaya Dijah naje tana ganina ta soma kuka me ki ka yi mata tayi miki wannan azabar kai yau kan abin ya ishe ni haka da sauri ta aika a kira mata Yaya Ibrahim, yana shigowa ya ganni tun kafin tace mishi komai ya zuba min ido yana kallonä wai me kike yi wa matar nan ne? Saboda Allah me zata yi mata? Tayi tambayar cikin yanayin kuka, a'a zata yi mata mana haka kawai zata yi tayi mata irin wadannan abubuwan ne wane irin mugun hali ne haka? Shi halin dan wani da uwar wani kuma ai sai a hankali sannan 93 ba ka marawa naka baya ko da kuwa zaluntarshi ake yi musamman idan ka san shi ne karami shi yasa nake yawan gaya miki ita uwa ki ninka yi mata fada kina nuna mata muhimmancin ta rinka girmamata. Kalaman Yaya Ibrahim ne suka yi matukar rage karfin fushin Yaya Dijah amma duk da haka sai ta nemi izininshi don muje gidan tare. To babu laifi amma ban yarda in kin je kiyi fada da ita ba, kiyi magana da ita cikin natsuwa don kiji abinda ke faruwa cikin natsuwa da nuna girmamawa gare shi ta ce to. Duk da mummunan karbar da Babah Lantana tayi wa Yaya Dijah tabi umarnin mijinta nata tabi al'amarin a hankali. Ina wuni? Ta kalleta a lalace au gaisuwa za ki tsaya yi ai na dauka za ki rufe ni da duka ne kawai, ban zo dukanki ba amma nazo ne in ji laifin da take yi miki kike yi mata irin wannan azabar, a'a aha aji kawai abin zai tsaya ai na dauka za ku yi fushin zuciya ne dawo da uwar taku kawai, haba yara kun tasa ni a gaba sai ka ce ni na kashe muku ita a yi min sata a hana ni yin magana. Yaya Dijah ta kalleta a lalace ta ce me ki ke dashi da uwa zata satan miki? Ke da kika tare a gidanmu ko gadon kwanciya ba ki da shi a kan 94 gadon uwarmu fa ki ke kwanciya duk wani abin da yake gidan kuma nata ne har yanzu ban ga naki ba. Gorin da ki ke yi mana kuma na mu tono ta to ba zamu tonota ba don bamu taba ganin in da aka yi hakan ba sai dai kema za ki je in da taje din da ana tonowa kuma to da mijinta ya riga kowa tono ta don da bai kwaso ki kin zo kin addabe shi kin addabi iyalinshi da makwabtanshi ba. Ta tashi zata fita daga gidan yayin da Babah Lantana ke ta faman zagnta tana hadawa har da Innarmu da Babah Sumaye tare kuma da jaddada ita ubanmu ma ba tsoro yake bata ba balle wani can banza a banza. Yaya Dijah ta ce tunda mijinki ma ba komai ba ne a wurinki ai kowama lada ne sai dai kanki ki ka yi wa tunda miji ai aure ne aurenki ki ka wulakanta mai auren kuma ya tanadi maganin irin ku, mara mutunci wacce bata san a girmamata ko mu din kuma ba tsoronki muke yi ba kina cin darajar ubanmu ne kawai." Nabi bayanta ta shiga gidan Babah Sumaye ni kumana zauna a kan dakali ina jiran fitowar tata tun da yanzu bana shiga gidan. Babana yana dawowa ta kwashe bayani na karya da gaskiya duka ta gaya mishi gaba daya maganganun da Babah Sumaye ta gaya mata da 95 na Yaya Dijah ta hada duka ta ce Yaya Dijan ce tayi mata su. Babana yayi fushi mai tsanani wai ta raina shi ne yasa ta iya buda baki ta 7agar mishi matarshi, in ba haka ba ai matarshi uwarta ce da sai ta kai mishi karar abinda ya farun taga abinda zai yi, kan wannan maganar sau biyu Yaya Ibrahim ya rako Yaya Dijah suka baiwa Babana hakutri, sai ya ce wai shi ya wuce a wurinshi amma sai an ba Babah Lantana hakuri tukuna ita kuwa Babah Lantana da aka bata nata hakurin sai ta ce to ya wuce amma daga yanzu babu sauran mu'amallah a tsakani. A wannan lokacin saboda tsabar samun wuri ba Asabe kadai ba 'ce a gidanmu har da wanta Sallau wanda gansamemen saurayi ne sosai, sai kawai a ka bude mishi daya dakin aka sanya mishi sabuwar katifa, shi kuma Babana ya zama bai da wani wurin da zai dan shiga ya rauna sai dakin Babah Lantana kawai da wannan gırma nashi kuma bai hana shi ma ya dora hannu a jikina ba da sunan dukan wai shi ma ina yi mishi laifi. Rannan na fito waje ina zaune kan dakalin kofar gidanmu, kuka nake yi saboda al'amuran sun ishe shi wahala tayi min yawa duk wani taimako da da a ke yi min an daina gaba daya 96 makwabta sun fita harkata saboda kowa haushin Babana da dabi'arshi ta fada a kan mata a ke ji a kan kuma rashin gaskiya. Na shagala babu abinda nake yin sai kukan ta hanyar sharbe yayinda na sunkuyar da kaina kasa ina kallon 'yan yatsun hannuna ban ji wani motsi ba balle in san wani yazo in da nake sai da naji ya buda baki yana tambayarta ke Maryam me ya same ki ki zama haka? Nayi maza na dago kai na kalle shi duk da na dade bana ganinshi, kallo daya nayi mishi na shaida shi, Mubarak ne ya girma yayi kyau gayenshi yayi matukar karuwa sai kamshi yake yi. Nayi maza nayi shinu saboda ganin irin kallon da yake yi min me ya hana ki tafiya Makaranta yau Talata? Baniya ce mishi komai ba saboda ban san me zan e mishi ba, tashi ki shiga gida kije kiyi wanka ki wanke kayan jikinki kar kuma in sake ganinki a gida a ranar karatu kin ji ko?" ban ce mishi komai ba ya wuce ya tafi bayan ya ga tshina zuwa cikin gida. Tun daga ranar ban sake fitowa waje na zauna ina kuka ba sai dai in yi zamana a zauren gidanmu ranan ma ina wani kukanne a cikin zauren a dalilin Babah Lantana ta ce wai tana 97 shirin duba ni saboda ta gane na fara bin maza shi yasa babu halin ta aike ni sai naje na dade. Ban san yanda aka yi yasan ina cikin zauren ba sai ganinshi kawai nayi yana tsaye a kaina, yau ma kuka ki ke yi? Yayi tambayar cikin natsuwa yayinda fuskarshi take daure sosai wai me ke faruwa ne a gidan nan naku? Ban ce mishi komai ba ban kuma daina kukan da nake yi ba. Yau ma ranar Makaranta ce ba ki je ba jiya, na ce makarantar taku ban same ki ba Malamarku ta gaya min ba kasafai ki ke zuwa ba, nayi magana aa Ummana ta bani wasu labarai marasa dadi a kan matar Babanku kar ki yarda ta hana kikaratu ungo wannan ki share hawayenki ki fyace majinar da ki ke mayarwa ciki kina shanyewa. Nabi umarnin da ya bani nasa halu karba na kai hancina, kamshi mai dadi irin kamshin da ke tare da shi ne, ina gama fyace majinar yasa hannu ya karbi hankicin ba tare da ya ji kyamar majinar tawa ba ya miko min ledar da ke hannunshi karbi wannan kici yanzu ina kallo nasa hannu na karba ba tare da nayi musu ba, saboda sanin alakarshi da Innata shi da Mansur. Iyaka dai na dade sosai ban ganshi ba na kuma san yana canne wajen hidimar karatunshi. 98 A sanina sanda Mama take raye kina cikin wadanda ake yi wa kyautar tsabta a makaranta to don me kika yarda ta maida ke haka? Ga ki da kokarin karatu duk kin daina, ai ba ayin haka ita rayuwa ai bata tabbata a wuri daya komai canzawa yake yi, wani mutumin da ya yi wa rayuwa irin fahimtar da yayi mata ma sai ya ce Tt is the law of nature and condition of all thing for all things are craselessly changing. Komai da ki ke gani zai wuce wata rana kuma sai labari. Kalamai masu dadi har ban san sanda na Cinye mneat pie din da ya kawo min tare da lemon gwangwanin, ba gashi kuma dama ya same ni cikin bukatar abin saboda ko karyawa dama ban yi ba. Natsuwa tazo cikin zuciyata har ña fara baiwa Mubarak amsar tambayoyin da yake yi min, ni kina aji nawa ne? na ce biyu, to ki shirya gobe zan tsaya a kofar gidanmu don in ga wucewarki da safe kin ji ko? Na ce mishi to, yanzu shiga gida kiyi wanka ki wanke wannan kayan jikin naki ki daina zama cikin kazanta ba ki ga yanda ki ka zama ba ne? ban ce mishi komai ba na mike na shige cikin gidan, sai dai wanka da wankin da ya ce in yin 99 ba su samu ba, a dalilin wai ba za ta bani sabulu ba. Rannan tun dare nayi wanke-wankena saboda in samu damar tafiya makarantar da wuri, amma da garin ya waye a kaga ina shiri sai a ka sake taro min wasu kwanukan da ban ma san ta inda suka fito ba, na gama shara da wanke bayan gida nazo na same ta cikin ladabi na ce a bani abin karyawa in na dawo daga Makaranta zan yi sauran aikin. Da sauri ta juyo tana kallona da wani bawanki ne a gidan zan da zai yi miki aikin? Na tsaya ina kuka saboda ganin Babana a wurin ko zai tausaya yasa baki cikin maganar, sai kawai naga ya tashi ya shiru takalmanshi ya suri kwandonshi ya fita aimar wai wajen tumatirinshi zai tafi. Ganin haka yasa na bar kukan da na fara na sunkuya nasa hannu da nufin daukar fatattakakkiyar jakata in tafi saboda in bi umarnin da Mubarak ya bani sai naji ta ce ai kin bar kukan ne munafuka? To ai babu inda za ki sai kin je kin yi min wanke-wanke nan. Na ajiye jakar a tsakar gidana kama yanke- wanke, sai kawai naji muryar Mubarak daga cikin zauren gidanmu yana kwala min kira. 100 Da sauri Babah Lantana ta.fito tana tambayar waye a nan? Waye ne mai keta min haddin cikin gida? Suna hada ido da shi taja ta tsaya tana kallonshi tare da sharbebiyar bulalar da ke rike a hannunshi yana gaisheta yana kallona. Tayi maka laifi ko? Ya ce eh, Makaranta nace taje bata je ba, a to ai ga ta nan, ta wuce ta tafi dakinta. Daga inda yake din ya kira ni, na taso na tafi bayan na wanke hannuwana da kafafuwa, bata kula ba saboda watakila tayi zaton dukan zai yi min tunda ta ganshi da sharbebiyar dorina a hannunshi. A zauren gidanmu ya tsare ni babu alamnar wasa a tare da shi na duba naga bulalar Baah Lantana bata gama karasa girman tashi ba, amma irin jin jikin da nake yi in tayi min duka da ita to balle kuma wannan. "Me yasa nace kije Makaranta ba ki je ba?" ban 6oye mishi komai ba, nayi mishi bayanin komai don tsoron kar ya ce na raina shi yayi min duka. "To wuce muje na." na wuce muka je din, shagon unguwarmu ya kai ni ya saya min sandal da littattafai da biro ya kuma kawo sule biyu ya bani "Ki ci abinci a Makarantar, ki kuma yi sauri kar ki tsaya a hanya." Na ce mishi "To." 101 Sanda na dawo daga Makarantar hana ni abincin da Babah Lantana tayi bai wani daga min hankali ba, saboda a koshe sosai na dawo gida. Tun daga wannan lokacin karfe bakwai da rabi nayi in Mubarak bai ga wucewata ba zai tako yaZo zauren gidanmu ya tasa ni a gaba ya ce in wuce in tafi Makaranta, komai kumaa na Makarantar yi min yake yi, kan ka ce meye wannan? Sai ya zama shi ne babban abokin gabar Babah Lantana. Kusan kullum sai ta kai maganarshi wurin Babana, wai yayi misi kashedi a kaina don lalata ya' yan mutane yake yi, Asabe ma wai ta ki yarda dashi ne yasa ya rabu da ita ya dawo kaina. Sai dai ban san dalili ba, bai ce mata komai ba, nima bai taba yi min Wa magana ta kashedi a kan shi ba, ban kuma zaci ya taõa tunkarar Mubarak din da maganar ba. Rannan ina zaune a dakina ina jin Babah Lantana tana cewa Babana waidama ya bayar da rikona ga dangin uwata da suke raina mishi kokarinshi a kaina, ko ma don ya ga uwar da za su yi min tunda shi basa ganin kokarinshi. Ya ce, mata a'a inda duk zai zauna zai zauna tare dani, ta tabe baki ta ce, ai sai kayi ta zama da itan tunda baka jin shawara, yar 102 kankanuwarta da ita maza sun fara yaudararta da abubuwa tana binsu kana kallo an baka shawara ka ki dauka, in ta zama budurwa kuwa tafi karfinka taje ta dauko maka abin magana babu ruwana, tunda ko a yanzun wannan yarinyar ai ba na zaton in nayi rantsuwa a kanta nace ba budurwa ba ce zan yi kaffara. Bai dai ce mata komai ba har tayi ta gama tayi shiru. Ina zaune a zauren gidanmu kwarkwatar kaina ce ta dame ni ga wasu kurarraji ma su ruwa da wari da kaluluwowi a bayan kunnena da keyata, ni kaina nasan ina cikin wani hali da kwarkwatar nan saboda ko a makaranta ni kadainake zama a benci saboda yara guduna suke yi kar in sa nusu kwarkwata. Don ba ta buya ba yanzunnan ne za ka ganta tana bin jikina ko rigata ko hijabi ban da haka ga bashin da nake yi, kan haka sai ya zamo min jiki, duk inda na zauna in yi ta tsigota ina kashewa. In kuma a cikin mutane ne nasa hannu cikin sa'a na kamo ta to sai kawai in saketa a kasa cikin hikima ba tare da na tsaya kasheta ba kar wani ya ganni. Ina zaune a zaure susa nake yi da hannayena duka saboda dadi har yawu yana diga daga 103 bakina, jifa-jifa kuma in na kamota sai in sata a kasa in kashe tayi kwas, na shagala ban san lokacin da ya shigo ba sai kawai idona ya kai kan kyakkyawar kafarshi da ke cikin wani kyak.kyawan takalmi budadde, wato open shoe A hankali nabi tsain kafar tashi da kallo zuwa jikinshi har kawó kan fuskarshi, da sauri na sunkuyar da kainà kasa daga dukkan alamu kuma na abinda na gani a fuskarshi ya dade a wurin yana kallon abinda nake yi. Shi ke nan shima zan rasa shi shima zai fara guduna yana jin kyamata a dalilin tsananin kazantata ga kwarkwata kamar yanda sauran yara da nutanen gidannu suke kyamata, na mika haninu a hankali na jawo kazamin dankwalin nawa na sake kulle cukurkudadden kan nawa ban yarda na sake dsoa ido na kalli fus karshi ba, fatana kuma da burina bai *e na inga kafarshi da ke kusa dani ta motsa ta bar Wun n ba. Ba zan yarda in sake hada ido da shi ba, abin da zuciyata ke raya min ke nan. Wanke hannunki kici abincin da nazo miki da shi. Cikin wata irin murya mai sanyi yayi min wannan maganar, ban motsa daga yanayin da nake ciki ba saboda wani 1irin yanayi da na smau kaina a ciki na tsananin jin kunya. 104 Tashi mana kije ki wanke hannun." Na ce, "To. Na mike da nufin in na shiga gidan ba zan sake fitowa ba, sai naji ya ce, Ko kuma muje gida kawai." Naja na tsaya kaina a sunkuye na ce, a'a sai dai iyakar abinda zan iya yi ke nan tunda shi ne a ta kusa da kofar shiga gidanmu. Uh'uh ki ka ce min? za ki yi musu daru ne'? cikin natsuwa ya jero min tambayoyin ban san yanda aka yi ba sai kawai naga na juya na kama hanyar zuwa gidan su Mubarak. Ba wani nisa ne sosai a tsakaninmu ba, sai dai duk da haka ba zan iya tuna rabon da in shiga gidan ba, watakila ma tun Innata tana raye. Sashin gaban gidan shi ne bangaren da Mubarak yake, amma bai tsaida ni a nan ba can cikin gidan ya wuce da ni wurin Ummanshi, tana ganinmu ta saki murmushinta mai ban sha' awa, Ahmad Mubarak bai fita ba ne? Cikin natsuwa ya ce mata, Na fita Umma dawowa nayi, to sannu da dawowa, Ubangiji ya Rara shiryar mih da kai ya kuma yi wa kokarinka albarka. Yayi murmushi amin Umma, Umma ba ki ga Maryam ba ne? Umma ta sake kallona, Maryam? Cikin nuna alamar tunani kan ya ce mata komai kuma sai ta kama salati, uwa ce wannan? Yayi maza ya ce mata eh Umma, ta zuba min ido tana kallona tare 105 da jinjina al'amarin yanzu Meron Ramatu ce ta zama haka? Cikin sauri ya sake cewa, eh Ummna. To Ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa ya ce amin Umma. To zauna mana, ta nuna min wuri nabi umarnin da ta bani. Umma! tayi maza ta ce na'am Ahmad Mubarak menene? Sha'awar mu'ammalarsu tayi matukar kama ni cikin zuciyata, na ce nima da Innata tana nan da haka zamu rinkayi da ita. Umma kan yarinyar nan nake so ki duba ki ga wani abin mamaki, naji kamar in ruga da gudu don tsananin kunya, da énsan abinda yasa ya ce in zo gidansu ke nan da ban yarda na biyo shi ba. "Muga kan naki Maryamu. Na dora hannu a kan nawa cikin yanayin sanyin jiki sai dai ban iya kin bin umarnin da ta bani ba, zuba ido tayi tana kallon kan nawa babu alamar damuwa a tare da ita, ki duba ki gani Umma wai kan mutum mai rai ne wannan. Umma tayi murmushi ta ce, eh ai babu komai anyi yafi haka maraici babu abinda bai sanyawa, wata rana kuma sai labari. Ya ce, Haka ne. suka dan yi shiru yayi: da ni kuma kaina ke sunkuye, 'yan mintoci kadan sai naji Mubarak ya ce to amma Umma ya ya za ayi da kannan ta samu saukinshi? 106 Kin ga wani ruwa-ruwa ma inda yake gangarowa ta bayan kunnenta ko sai dai kawai ayi aski? Da sauri na daga kai na kalle shi cikin wani irin yanayi na mummunar faduwar gaba. Kamar Umma ta gane halin da na shiga, don ni kam duk da wahalar da kannawa ke ba ni ina Son gashina. Aski kuma Ahmad.Mubarak don ka ganta a haka ko? ai maraici ne da uwar ta tana nan da yanzu wata santaleliyar budurwa ce. Yayi murmushi ya ce, budurwa kuma Umma? Ta ce, eh to ai bana shekara ina ganin tsakanin sha uku da sha hudu ta ke, ai kuwa kaga da ba haka ta ke ba tunda duk da wahalar da take ciki na kazanta da yunwa ai ta dan mike. Don haka ba za a aske, mata kanta ba, bari in gama abinda naké yi kawai na aikin abincin nan sai in duba mata shi. Ta mike ta shiga kicin tana aikin girkinta suna hirarsu da Mubarak ni kuma ina gefe a zaune a cikin hirar tasu ne na fahimci Mubarak ya kammala karatunshi na Jami'a ne a bana. Ta gama aikin abincinta ta rarraba ta baiwa kowa nashi ta kalli Mubarak ta ce mishi, To ba ni wuri mana ba ga naka can an kai ba, ko za ka tasa ni a gaba ne sai na wanke mata kan kana kallo? 107 Yayi maza ya ce, a'a Umma na zauna kina Son zaman nawa ne? ta ce a'a bana so, ya ce to ya mike yayi tafiyarshi. Ta kalle ni cikin yanayin kamewa sosai shiga kicin kici abincinki ga shi can na ajiye miki sai ki fito in gyara miki kan naki. Na daga kai na kalleta da niyyar cewa na koshi, yanayin da na gani a tare da itan ya wuce na a kawo mata wani wargi, don haka na mike na shiga cikin kicin din na samu abincin da take ci shi ne nawa. Shinkafa ce da dankalin turawa da miya, ga kuma nama zuku-zuku har guda uku ta zuba min a kai. na kama ci sai da na cinyeta tas na fito da kwanon nazo gun wanke-wanke da nufin wanke kwanon da naci a ciki na hada har da kwanuka da tukwanen da na smau a wurin na wanke shi fes na kife. Ina gamawa ta kira ni to zo daga nan mu gani, naje in da ta ce din wanda gaba kadan da inda nayi wanke-wanken. Ni da Umma ta fara wanke min kai ina tsugune sai da ta kai ma nayi zaman dirshan sosai a kasa, ta wanke kurarrajin tun suna fari har sai da suka zama ja tun ina jin dadin wankin da ake yi musu har suka koma yi min zafi. 108 Tana yi kuma tana yi min fada in ba ka da mai yi maka abu ai yi wa kanka ka ke yi, ina dalili za ki zauna da wannan kazanta haka, ji wuyanki fa, ji bayanki ta gogo inda take nufin da hannunta ta nuna yanda datti yayi .mujimurji a tafin hannun nata. In uwarki tana da laifi ai ke ma kina da naki na sakarci, Umma ta gama wanke min kai sannan ta kama cuda ni da soso da sabulu, wuya, baya, kirji, ke tafi can ni tsaya in cuda ki da kyau ina ruwana da nonuwanki? Kunyarta ta kara kama ni ta gama abinda take ganin ya dace tayi min ta mike da nufin barin wurin. Kiyi wanka mai kyau kowane lungu a jikinki ki wanke shi, ki goge kafarki sai ki cikin gida ki same ni na ce mata to. Nayi wanka da wadataccen ruwa naji dadi irin wanda na dade ban ji ba, na fito na shiga har cikin dakin Umma na tsuguna, ta kalle ni ta ce, Ga daki can nasu Rukayya shiga ki shafa ki dauki zanen da ke kan gadon ki daura sai ki zo in sanya miki magani, na ce mata to. Ni da na shiga gidan su Mubarak tun wajen sha dayan rana:ban fito ba sai bayan Azahar, kusan ma za a yi La'asar ina rungume da 'yan 109 kayana da na wanke suka bushe ta hana ni canza na jikina da na sanya a gidan ta ce in je da su. Rannan kwana nayi ina wani irin bacci mai dadi, ashe-ashe dama can ba kwanciyar kasa ko rashin abin ruhuwa ke hana ni yin bacci ba, masi far kwarkwata da kurarrajin nan ne yafi komai takurawa rayuwata. Sa idon da Mubarak yayi kan karatuna da ma duk wani abin da ya shafi al'amarina sai na dan samu saukin wasu al'amura, kullum za ni Makarantar boko da ta allo sai dai na daina zuwa ta Asuba da ta dare saboda ayyukan da na kan yi da safe kafin in je ta bokon. Da daddare kuwa Babah Lantarna ta ce ba Makaranta nake zuwa ba, gun samari nake zuwa, don haka na bari. Sanin da Babah Lantana tayi na ina yin lattin Makaranta Mubarak zai zo har zauren gidanmu da bulalarshi ya fita dani yasa ta fita harkar hana ni karatun, tunda tayi tayi Babana yasa baki ya hana shi yin hakan ya ki. Don haka ko baya nan "zuwa Makarantata nake yi saboda ba ta ganewa. Rannan ya dawo daga tafiyar da yayi da Babanshi kasancewarshi wanda ya karanta zane zane yayinda shi kuma Babanshi Alaji Muhammadu yake dan kwangila yasa tun bai 110 gama karatun nashi ba yake matukar taimaka mishi kan ayyukan nashi. Ina zaune a zauren gidanmu ni kadai littafaina na Makaranta nake dubawa, yayinda naji motsin shigowa da sauri na daga ido don ganin wanda ya shigo din. Ban san lokacin da nayi murmushi ba, ashe ka dawo? Ya dan saki fuska kadan ashe kina zuwa Makaranta? Ai daga can nake amma me yasa yau ba ki je ba? Cilkina ne yake tayi min ciwo yanzu ma ya dan lafa min ne na fito. Ciwon ciki kuma? yayi tambayar yana mai kallon cikin idona yayinda ni kuma nayi maza na kaucewa kallon nashi. Kin sha magani ne? nay1 mishi karya na ce eh, to zo muje gida. Nayi kamar zan yi musu, sai naji ya ce ai ba ki da kirki, Umma ta ce min ba ki taba zuwa kin gaisheta ba. Kunya ta kama ni gaskiya ban kyauta ba, irin hidima da dawainiyar da tayi da kazantata ga shi kuma hakan ya zama sanadin warkewan kan nawa. Kurarrajin ma duk sun warke, kwarkwata kuma ta mutu nima kuma tun daga ranar ban sake fashin wanka ba, balle wanki ko zan yi ana zagina sai nayi. 111 Sabulu kuwa bana tambaya a irin kudin break din da suke bani nake saye har da man shafawa na (Vaseline) ina adana abina. Tashi muje, ban musa ba na ce to. Yayi gaba yayin da ni kuma na bishi daga baya, kai tsaye nayi nufin wucewa cikin gidan kamar yanda naga rannan mun yi sai na same shi a tsaye a zauren gidan, shigo nan. Na shiga kofar da ya ce in shigan maimakon in ga dakin zaure kamar yanda nasan dakunan zaure wani lafiyayyen falo na gani mai dauke da wasu kofofi guda biyu wadanda suke rufe komai na wurin kamshi yake yi. Yau ke ba bakuwar Umma ba ce wurina ki ka zo, yana fadin hakan ya wuce ya shiga daya daga cikin kofofin ian da ke rufe bai wani dade ba sai ga shi ya fito rike da wata leda mai kyau a hannunshi. Zauna mana kin ja kin tsaya a tsaye ko kina tsoro ne? ban yi magana ba, na nemi wuri na zauna a gefen kujerar da ya nuna min, gwada wannan in gani. Sandal ne mai kyau na asalin fata, don zuwa makaranta na karba cikin farin ciki na gwada a kafata kamar donni a ka yi shi. Ya kalli kafar bayan ya mike tsaye ya juya zai shiga daya kofar yana tafiyar yana fadin nayi zaton haka shi yasa na saya miki shi. 112 Bai wani dade a ciki ba nan ma sai gashi ya fito da tire a hannunshi, gasasshen nama ne mai zafi har yana tururi tare da wuka a gefen tire din yazo ya zauna a kasa kusa da kujerar da na ke yana yanka naman da wukar. Sauko kici, na ce a'a na koshi. Ya dago ido ya kalle ni ya dan yi wani irin dan kankanin murmushi da bai kai a kira shi murmushin ba, shi kuma ba yake ba ne. Ya maida hankali kan abinda yake yi kin taba ganin na shiga gidanku sanda Mama take nan ta bani abu na ce na koshi? Shiru nayi ban ce mishi komai ba, raini ne babba na gaba da kai ya baka abu ka ce ka koshi, ko da ka koshin sai kaci kadan don yasan girmamawa ne ya sa ka yin hakan. Don haka sauko ki ci ban sake yi mishi musu ba, ya ci kadan ya mike yą bar sauran in kin cinye ga kankana nan ki shnaye, ya shiga dakin da ya fara shiga ya dan dade bai fito ba har na gama abinda nake yi. Naji tsoron kawar da tiren tunda ba zan shigar da shi in da naga ya fito da shi ba, don haka na mike na bar komai a wurin na fito waje cikin sa'a babu kowa a wurin, don haka maimakon in shiga wurin Ummanshi gidanmu kawai na dawo nayi zamana. 113 Ni da kaina nasan na samu sassauci ba wai wani canji na samu a gidanmu ba, amma yar tsabtar da nake yi wa kaina tana yi min dadi tana kuma yi wa Yaya Dijah. Har Yakumbo Halima ma da ta ganni sai da tayi min maganar gashi kuma a yanzu ba sosai1 nake jin yunwa mai tsanani ba. Saboda in dai Mubarak yana gida to ka'ida ne a wuni zai bani wani abinda zan ci mai dadi ko da kuwa sau daya ne. Kwanaki hudu bayan wannan ranar sai ya kasance ranar ta Asabar ce ina gida da safe bayan na kammala ayyukana na dauko allona za ni Makaranta, sai kawai muka gamu da Mubarak yanzu ne lokacin zuwa Makaranta? Yayi min tambayar yana kallon agogon hannunshi. Sai yanzu na gama ayyukana, na ba shi amsar a natse. Ki ka gama ki ka fito ba ki yi wanka ba? Sau nawa zan gaya miki wanka biyu ya kamata ki rinka yi? Ban amsa mishi ba, to in dai Makarantar Baba Mallam za ki je bai fi saura minti talatin ba a tashi, don haka wuce muje ki gaida Ummata da nake ta fama da ke kina kakkaucewa. A gidan su Mubarak kin yarda nayi in fara shiga dakinshi, kafin in shiga wurin Umman tashi, don haka muka rabu shi ya shiga wurinshi 114 ni kuwa na wuce cikin gidansu wajen Umman tashi. Tana ganina ta somna murmushi alamar taji dadin ganin nawa, Maryamun Mubarak. Nayi maza nasa hannayena duka biyu na rufe idanuna saboda kunyar yanda ta hada sunan nawa da nashi a wuri daya. Kurarrajin sun warke ko? nayi maza na ce mata eh, bata tambayi kwarkwatar ba sai ta ce ai gashi nan da gani an san kin samu saukinsu, don har jinin jikinki ya fara dawo miki, muga kan naki. Na matsa kusa da ita na bude mata shi don ban jin kunyar bude shi a yanzu, babu shakka yayi kyau yayi tsaf, gashi ne da ke mai kyau sai rashin kulawa, ki kula da kanki kar ki jira sai an ce kiyi. Kitso a kai a kai kin ji ko? na ce to Umma. Na maida dankwalina ina daure kan nawa, sai naji ta ce min, Yaya cikin naki dai? Mubarak ya ce min kwanannan kina yawan ciwon ciki? Na ce yayi sauki, na dauka karshen maganar kenan sai naji ta sake tambayata, kina ganin wani abu ne bayan kin yi ciwon cikin? Da sauri na dago kai na kalleta cikin mummunar faduwar gaba nan take kuma na sake sunkuyar da kaina. 115 Na ce kina ganin wani abu ne bayan ciwon cikin yana fito miki ta jikinki? Kuka na kama yi mata kamar yanda dama kukan nayi tayi lokacin da na fara ganin nashi. Ai ba abin kuka ba ne Maryamu, hali ne da dabi'a ta kowacce mace a kan haka a ka halicce mu, hakan kuma alama ne na girma. Sai ki kara natsuwa ki kuma kara kama kanki kar ki yarda wani namiji ya kusanci jikinki daga yanzu kuma kar kina yarda lokacin sallah yana wuce ki ba ki yi ba. Don ta hau kanki, haka nan Azumi in dai na ganin shi kuma za ki yi wanka tai tayi min bayanin yanda zan yi wankan, sai dai ban ji komai ba saboda kukan da nake yin ya tsananta. Mubarak ya shigo ya same mu da Umma, bai tsaya ba ya juya ya fita saboda shigowar nashi bai sata ta daina maganar da take yi min ba. Tashi ki share hawayenki ki wanke min wadancan kwanukan, sanya umarni na aiki a cikin maganar ya sanya ni hanzarin mikewa naje na kama aikin da ta sani, na gyara wurin fes na debo su na kawo mata, to ungo wannan gyara min shi, na ce To. Nasa hannu na karba na gyara shi na mika mata. In ce ko uwar taki tana koya miki girki ne? na ce a'a a gidan Yaya Dijah nake yi, Umma tayi 116 maza ta ce iko sai Ubangiji, har na mance Dijah tana garin nan tana nan a nan inda muka kaita? Na ce, eh Umma sai dai mijinta yayi nashi ne a can ciki suka koma, tayi addu'a kafin ta tambaye ni, ni yanzu 'ya'yanta nawa ne? na ce uku mata biyu namiji daya. Hira sosai muka yi da Umma har ta gama abincinta ta zuba min nawa naci na koshi wanda tuwon shinkafa ne miyar shuwaka sannan na fita na koma gida. Da yamma ina cikin gida Mubarak yazo yayi sallama da ni na fito na same shi a zaure, leda ya miko min nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya na juya cikin gida. Dakinmu na fara shiga na zauna a kasa ina cicciro abubuwan da ke cikin ledar, kayan mai ne guda biyu da a ka rubuta 10.0.6 lotion a jiki da sabulanshi suma guda biyu, sai hoda da tur are duka na 10.0.6 din ne. Sai sabulan wanki da kwalin omo shima guda biyu, sai wata leda da ta bani sha'awa sai dai ban san meye a ciki ba, na shiga kokarin budewa don in gani. Sai kawai Asabe da ke kwance a kan gado tayi maza ta fige tana fadin "Lahhh! Kan uba, lalle yau an kama ki wannan ai iskanci ne, ya sayo wannan ya kawo miki, da gudu ta fita ta 117 kaiwa Babah Lantana ta barni nan a zaune jikina yana ta faman rawa saboda an ga abin iskanci a wurina. A to, ai ni kam dama na fada ai na gayawwa ubanta abinda suke yi bai kula zancen ba ne in ta dauko mishi cikin shege ai yasan abinda yake ciki. In banda isklanci ace har abin jinin al'ada saya mata yake yi? Na sake tsorata, tsoro kuma mai tsanani. Maimakon in tuna na dade ina ganin Asabe tana yi in saki zuciyata sai na zauna nayi ta kuka. Babana yana dawowa kuma Babah Lantana taje ta kai mishi audugar al'adar nan da Asabe ta dauke cikin sayayyata ta nuna mishi a matsayin huijar da zai gasgata maganar da take fadi, na' cewar ni din lalacewa muke yi da Mubarak tunda har ga shi yasan ina al'ada yana saya min abin amfaninta. Bakin ciki mai tsanani ne ya same ni, irin wanda ba zan iya kwatantawa ba, gayawa Babana da a ka yi na rinka ganin tanfar wani gagarumin laifi na aikata irin wanda ba a taba aikatawa ba a duniya. Rannan Babana ya buge ni duka irin wanda ba a taba yi min ba a rayuwata, karo na farko kuma da ya taba taba jikina da sunan duka. 118 Sai dai ni kam ba azabar da na sha ne babban matsalata ba, irin kukan da na ganshi yana yi da hawayenshi. Na samu kaina cikin kunci mai tsanani da bakin ciki, nayi dalilin da Babana ya zubar da hawayenshi a kaina, to ni kuwa ina zan shiga in tsoma rayuwata in ji dadi? Da yake akwai al' amarin kuruciya mai yawa a tare da ni, a lokacin sai na rinka jin tanfar eh da gaske ne iskancin da ake cewa nayin nayi shi tunda a ka ga wannan abin a wurina, donni a lokacin ban ma san asali menene a ke nufi da iskancin ba. Tsawon lokaci ban sake yarda wani abu ya sake hada ni da Mubarak ba, ko da kuwa wane iri ne komai kuma kankantarshi, ko a waje ya hango ni ya soma kirana ko kokarin zuwa in da nake zan ruga da gudu in tafi in ba shi wuri. Zauren gidanmu da kofar gidanmu kuma Babana ya hana shi zuwa, sai dai shima bai san dalilin faruwan hakan ba. Ana cikin haka ne kuma muka rubuta jarrabawar mu ta gama aji biyu zamu tafi uku a tsawon wannan hutun babu abinda ya hada ni da Mubarak, bana ma ganinshi ko da kuwa a kofar gidansu ne in da wani lokaci yakan zauna tare da samari abokanshi. 119 Sai dai maimakon rabuwa da Mubarak din da nayi ya zama sanadi da zan samu wani sauki ko sassauci wurin Babana, tunda yayi min hukunci na yarda ya bani umarnin fita hanyarshi nab umarnin da ya bani ban samu sassaucin ba. A gidan ma wani kuncin na sake shiga na koma zama cikin yunwa ga rashin abubuwan da da na daina nasa su Asabe tayi matukar tasa ni a gaba babu halin in yi magana kan komai sai Babah Lantana ta ce, To ba taga tana jini ba. Bakin ciki ya kama ni in mance da wanda nake ganin Asabe tana yi, kusan kullum sai tayi min duka, duka kuma irin na zalunci irin wanda babu mai ceto ko mai tambayar dalilin yinshi sai ta gaji kawai ta bar ni don kanta. Rannan na dawo daga makarantar allo a lokacin nan an kai kusan watanni shida da faruwar abinda ya farun, sai kawai gani ga Umman Mubarak a hanya ta fito gaida mara lafiya a makwabta. Rike baki tayi tana kallona, haba ke kuwa Maryamu, me yayi zafi haka da ba za ki shigo ki gaishe ni ba? Na sunkuyar da kaina cikin wani yanayi da ni kadai nasan abinda na shiga, in don Ahmad Mubarak ki ka daina zuwa wurina shi kamma ai ba ya nan... 120 Da sauri na kalle ta sai dai ban san lokacin da na dago na kalletan ba, ta ce eh ya tafi hidimar kasarshi yana can Ibadan inda aka tura shi, dama yana son kin tafiya Ibadan dinne yayi a nan kusa saboda ke da kuwa ki ka biyewa sharrin da mutanen gidanku suka yi mishi nasa shi ya kama hanya yayi tafiyarshi. Wuce muje gidan ai dama na dade ina neman in gan ki ko da kuwa a hanya ne ba mu gamu ba sai yau. Kunya da nauyin Umma yasa na bita, to wai me yayi miki ne a ka ce yana yi miki iskanci? Shiru nayi na sunkuyar da kaina kasa na soma yin kuka. Yana taba ki ne? nayi maza na girgiza kaina alamar a a, sun gan shi ya rungume ki ne? sake girgiza kai nuna a'a, ya gaya miki wata magana ne suka ji? Na sake nuna a'a, to menene? Ta tsare ni da tambayoyi, na kasa cewa komai har dai ta gaji tace duk mai yiwa dan wani sharri dai zai gani a kwaryarshi, tunda ni kam ai an ce ba a shaidar mutum amma ni zan yi wa Ahmad Mubarak shi ba mai irin wannan iya shegen ba ne, to yaushe ma ya kula wata da har a ka zo a ka samu ubanshi ana yi mishi togaciya a kanki? 121 Ga dambun zogale can nayi da za ni gaida mara lafiya, debo kici, na ce na koshi. Ta galla min harara tare da daka min tsawa, ke tafi ki debo bana son iya shege. Na debo nazo na zauna ina ci ita kuma tana kara jaddada 6acin ranta kan abinda a ka yi wa Mubarak, kewar Mubarak din nima ta kara kama ni, musamman da na gane ashe ma baya nan ne yasa na daina ganinshi. Da hikima da jan hankali Umma ta shawo kaina har nayi mata bayanin sabon halin da nake ciki, ta ce uhun dama abinda take so ke nan ta raba ki da duk wani wanda zai taimake ki, in ba haka ba ita kuma Dija me tayi miki da aka ce kafa miki dokar zuwa gidanta ita ma? Kai wannan uba naki? Ta dan yi shiru zuwa wani lokaci kafin ta sake cewa, to sai a hankali. Kin ga in gari ya waye daina jiran abin karyawarta, rinka zuwa nan kawai ki karya ki tafi Makarantarki na te mata to. Kashedin da tai tayi min ne yayi dalilin da na gama abinda zan iya na dauki Jakata nace wa Babah Lantana Baba a bani abin karyawana in na dawo sai in gama. Ta ce, a'a ai sharadin karyawa gama aiki, ko nima da ki ke ganin kamar ina daga zaune ne kawai nake ci ba haka ba ne, da amfanin da nake 122 yi wa uban naki ita kuma Asabe ita take girkawa shi kuma sallau yana karbo cefanen. Don haka kema sai kin gama naki nace to a bani kudin makarantar ta dago ta kalle ni da su zan biya wadanda za su karasa aikin in kin tafi kin bar shi. Na juya na kama hanyar fita daga gidan ina tunanin lokacin da Babana kan goya ni a kekenshi ya kai ni Makaranta, muna tafiya muna hirarmu komai na gani a hanya na ambaci sunanshi ya tsaya ya saya min. Tun ma ba a ce lokaci ne nasu tsada su lemon tsuntsu su malmo ba amma wai a yanzu sai a hana ni abin karyawa da kudin Makaranta a kan idonshi yana kallo ba zai ce komai ba. A gidan Umma nasha kunun gyada lafiyayyen alalan ganye sai da na koshi na dauki jakata zan tafi, ta ce min in an taso ki biyo ta nan kafin ki je gidan naki na ce to. Muna tasowa gidan nata na fara zuwa, na samu dafadukan shinkafa da wake mai manja ya kuma ji busasshen kifi a ciki da dan yaji-yaji. Na ci na koshi na nufi gidanmu, Babah Lantana bata bani ba nima ban tambaya ba, tunda dama ko nayi mata aikin duka ba kasafai nake samun abincin da zan cin ba. 123 Kusan wannan satin abinda ya rinka faruwa kenan, don haka har ranar Asabar ban saurari aikin Baba balle in je ina jiran abin karyawanta Umman ce kuwa ta koya min yin hakan da yamma na shigo gida na samu Babana zuane kan tabarmarshi an kawo mishi abincinshi. Ina kike tafiya ne Yaacuuwuna? Na kalle shi cikin ladabi na ce mishi, "Gidan Umma. i Ban san yanda a karyi ba bai yi min fada ba, sai naji ya ce min to dauki wannan abincin kici, na ce to. Ina daukan kwanukan Asabe ma ta zaburo da saurinta nima zan ci nima ban koshi ba Baba. To ku ci mana, yayi maganar a hankali. Tayi maza ta biyo ni, To ki ajiye mana. A ha ina za ki kai? kan in ce zan ajiye sai ga, Babah Lantana tazo ta fige kwanukan da ga hannuna ta tafi da su tana fadin. Aikin banza aikin wofi, ba ka iya komai ba sai lalatawa mutum tarbiya, a ina ake yin haka? stya'ya gansun-gansun kowacce a ka kaita gidan miji zata zauna sai kuma a ce kullum sai an basu sudin uba, to ban yarda ba". Ta juya ta tafi, duk. da nasan ita ta koyawa Asabe irin wannan iya shegen saboda kyashin dan abincin da wani lokaci Babana rage min amma ban damu saboda na riga na koshi. 124 An kai maka maganar yawonta ba ka ce komai ba kazo kana rage mata abinci, don daurin gindi duk abin da ta kwaso dai ai a kanku zai kare kai da ita, yaja bakinshi yayi shiru, to balle kuma ni. Washegari da safe na sake tambayarshi zuwa gidan Yaya Dijah cikin sa'a sai ya bar ni na tashi cikin zumudi da murna naje na gayawa Babah Lantana ta tabe baki ta ce sai kiyi ta tafiya. A gidan Yaya Dijah ranar kamar zata lashe ni don dadi saboda na dade sosai ban je ba itama kuma yanzu bata cika zuwa gidan sosai ba tunda Babah Lantana ta ce ta yafe amma wai babu sauran mu'amallah a tsakani. Muka yi hira na bata duk labaran da ke cina a cikina, tunda yanzu na kara sanin darajarta, kullum kuma kara sonta nake yi. Da yamma da zan tafi gida sai ta debo zannuwanta kala hudu da ta ce za su yi min da wasu sabbi da ta dinka man kala biyu ta hada min har da takalma guda biyu suma sababbi. Nayi ta murna na dawo gida zuciyata cike da farin ciki, na shiga daki na adana kayana a cikin dan akwatina a zuciyata ina tunanin tun da jibi ne Juma'a to sai jibin zan fara saka su. Ranar Juma'ar ina tasowa daga Makaranta ko gidan Umma ban biya na ci abinci ba na dawo 125 gida da nufin in yi wanka in yi kwalliya tukuna don ta ganni fes. Na gama wanka na shafa maina wanda shima Yaya Dijan ce ta bani shi, na shafa hodata na jawo akwati da nufin zaban wanda zan saka sai kawai kaya suka ce dauke ni a inda ki ka ajiye ni. Kuka sosai na kama yi kafin naje na kai maganar gun Babana, Babah Lantana tana ji ta ce wannan shi ne sharri da ki ka kawo wa ki ka nunawa? Kin nuna min? na girgiza kai kin nunawa Babanki? Na sake girgiza kai, to ai ma ba haka a ke sharrin ba, in ma ita ta koya miki in kin zo ki kala mana sata to bata koya miki daidai ba. Ta wuce ta taf ta bar ni ina kuka, Babana kuma yana yi min fadan yanda a ka yi aka bani kaya nazo na ajiye su ba tare da su sun taya ni murna ba, bakin ciki ne ya ishe ni na fita na tafi gidan Umma naje na gaya mata. Ita kam bata musa ba, hakuri tayi ta bani ta kuma bani abincin da ta ajiye min na ci na koshi sannan ta kawo wata atamfa ta ba ni ta ce in yi kwalliyar Juma'ar da ita. Sannu a hankali sai gidan Umma ya zame min gida na saki jiki sosai da ita ta zame min 126 tamfar uwa babu abinda bata nuna min na hidimar rayuwa. Hatta wankan al'ada ita ta koya min shi sosai na iya, ita ce kuma ta fahimtar da ni na gane ita al'ada ba laifi ba ne ba kuma abin kunya ba ce. Sai dai mutunta kai ne ka tsare ta in. kana yinta kayi ka gama ba tare da wanda ka ke tare da shi ya gane ba, ita Umman ce ta fahintar da ni cewar dabi'a ce ta cikar halittar mace. Tun daga nan ne na gane na ma daina yin kuka, in na ganta tazo min. ina zaune da Umma masa nake ci cikin sauri saboda tsoron da nake ji na kar in yi lattin makaranta. Sai ga Alhaji Mahammadu ya shigo har wajen kicin din yazo ya tsaya, yana kallonta ni ina ki ka samu yarinya ne? Yayi mata tambayar bayan ya anmsa gaisuwar da nayi mishi. Yarinyar nan ne yar gidan Mallam Habu mai Tumatir, nan da nan fuskarshi ta kara daurewa, dama kuma ba mai yawan fara'ar ba ne. Ba ku rabu da ita ba ke nan kamar yanda ubanta ya ce ayi? Cikin natsuwa ta ce, ubanta ai ba a ta tashi Alhaji, da sauri ya tambayeta, sai tawa? Tayi shiru bata bashi amsa ba. Mutum da 'yarshi ki ce ba a ta tashi, sai ta wa? Wane zancen banza ne wannan? Marainiya 127 ce Alhaji, Umma tayi mishi magana cikin murya mai taushi da nuna girmamawa, yayinda nake bake can gefe cikin rawar jiki saboda yanayin fuskarshi da kwarjininshi. Duk abinda aka yin sharrin matar gidanne, ba ka ga yanda yarinyar nan ta koma ba, bayan rabata da Ahmad Mubarak da aka yi shi yasa na dawo da ita. Macce ce rauni ne da ita ga shi kuma ta fara girma, in wahala tayi mata yawa abin ba zai yi kyau ba, yunwa ai musiba ce kuma bayan mu muke dubawa tare da rokon Ubangiji ya tsare mana su. A bankali ya ce, To amin. Alamar dai ya sauko har ma ya gamsu da kalaman matar tashi. Wuce ki tafi makaranta Maryamu in kin dawo ki biyo ta nan kar fa ki ki zuwa na ce mata to, har na wuce zan tati 'sai naji ya ce mata in da canji nan wurinki bata sule biyu ta ce mishi eh akwai, ta miko sule biyu nasa hannu biyu na karba tare da yin godiya, na kama hanyar fita ina jinta tana yi mishị karin bayani a kaina, har da Innata. Da yamma ban ki biyowa ta gidan ba ina dawowa ta bani abinci na zauna ina ci, ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min kin ga ma Babanku dazu sai yace min kullum in ki ka zo tafiya makaranta 128 in kin karya in ba ki sule biyu ki rinka cin abinci a makaranta, na ce mata to na gode. A wancan lokacin da nake magana akai sule biyu kudi ne masu daraja saboda sule goma ne a Naira guda daya, yayinda ita Nairar take daidai da dalar Amurka. Don haka sule biyu kudi ne tunda kuma ina cin abinci in koshi a wurinta in zan tafi in na dawo ma kuma za a samu in ci in koshin sai ya zamo ko ta bani sule biyun ba na karba sai in ce bar su kawai Umma, wata ran kuma in karbi sisi wato rabin sule daya ko kuma in ce kwabo biyar, ban sani ba ko ganin hakan da nake yi ne ya sanya ita Umma fara yi min banki a wurinta. To Hausawa suka ce wai yau da gobe bata bar komai ba, ana tafe a haka sai ga shi har mun gama aji uku mun kammala jarrabawa muna cikin hutun da zamu shiga (SS1), ko kuma aji hudu na Secondary a takaice dai na shiga Senior Section. Haka nan da ki da so da wahalar da komai da lokacin girmana yazo sai na girma saboda Hausawa sun ce wai in rana ta fito to tafin hannu kuma bai kare ta. A wannan lokacin na zama ba Asabe ba, hatta Babah Lantanar na kere ta a tsayi, haka nan duk da a hakan ma ban wuce a dake ni ba, amma dai 129 nayi matukar rage jin tsoronsu da nake yi tun ma ba na Asabe ba wacce kuma dama ita ce tafi kowa takura min ko dan maina Umma ta saya min a cikin kudina sai ta dauke min ko ta kawo wata kwalbar ta juye shi. Ana cikin haka Mubarak ya dawo daga hidimar kasar da ya tafi Ibadan, ni da shi ba ma kula juna, ganin da nayi ya ganni bai nuna wata alama ta zai kula ni ba, yasa nima nayi kamar ban ganshi ba. Sai dai hakan bai sa na daína shiga gidansu in yi hidimomina da Umma ba, saboda na riga na kudurawa raina babu abinda zai sa in sake dauke kafa daga zuwa wurin Umma, matukar ina raye a cikin hayyacina. Don haka shiga gidan nake yi yana kallona ina kallon babu mai cewa wani ci kanka ita kuma Umman bata taba nuna ta gane abin da ke faruwan ba, balle ta tàmbayi dalilin hakan zuba mana ido kawai tayi. A wannan lokacin zama tsakanina da Asabe matukar baci, saboda muna iya wuni mu kwana tare a daki daya babu wanda ya ce wa wani ci kanka. Muna cikin hakan ne kawai na dawo daga wurin Yakumbo Halima na samu Asabe ta tsala 130 kwalliya cikin sabuwar atamfata da Umma ta dinka min su kala hudu. Cikin natsuwa na kalleta na ce Asabe wannan ai tana cikin sababbin atamfofina da na karbo daga wurin dinki." Wacce? Na ce wannan ta jikinki tunda gama botin rigar nan da na sayo da hannuna. Eh ai na san taki ce aro na dauka ta zancen nata, na ce To gaskiya ban yarda ba cire min ita kawai tazuba min ido tana yi min wani irin kallo baki yarda ba fa ki ka ce? Na ce eh ban yarda ba ina ce tawa ce? Ba sai ki cire min ba kawai ni daa kayana? Ai, ke nan babu damar a ari kayanki ke ba kya aron na mutane? Babah Lantana tasa ba ki cikin maganar ban ji nauyinta ba na ce in na ari na wani ya kwace kar ya bar min shi ni dai a cire min nawa kawai. To ba zan cire ba tunda abin naki iskanci ne ana miki magana kina ba mutane amsa. Na ce gaskiya sai kin cire ban yarda da aron ba tunda ai ma ba ki tambayen ba in ban da na ganta a jikinki kuma da ba za ki dawo min da ita ba. Me ki ke nufi da wadannan maganganun naki? Abin da nake nufi ke nan ana diban kayana 131 ba da sanina ba ana salwantar min da nayi in na yi tambaya a ce na kalawa wani sata. Ko rannan ai nayi miki cigiyar doguwar rigata ta shadda ki ka ce' rainin hankali ne ya na tambaye ki ita shekaran jiya kuma sai muka yi kacibis ni da kawarki Nuriya da rigar a jikinta da na tambayeta in da ta same ta ta ce min canji ku ka yi ke da ita ki ka bata wannan. A fusace kwarai Asabe ta tambayen ke me ki ke so ki ce min na yi miki sata ko kuwa me? Na ce Oho ko ma a me ki ka fassara shi daidai ne, tunda kin daukar min kayana na tambaye ki kin ce ba ke ce ba ce nazo na gani a jikin kawarki da ta ce ke ki ka bata yanzu kuma ga wata na gani a jikinki kin dauka bada izinina ba kuma da kina so kiyi musun ba tawan ba ce. To ba ki da abin da zan .satar miki bari in gaya miki, to sau nawa? Ta tambaye ta cikin yanayin da ya kara fusatata. Taja wani mummunan tsaki ta wuce wai zata fita tayi tafiyarta, nayi maza na kama gefen zanin da ke daure a jikin nata na rike ai babu in da za ki da kayana a jikinki. Riketan da nayi ne ya zama dalilin da ta juyo cikin hanzari ta rufe ni da duka, nima nayi maza na maida martani don haka dambe ya kaure a tsakaninmu. 132 Kamar kullum yau ma Asabe ce mai galaba a kaina a damben. Sanin da nayi babu mai raba mu daga Sallau da ke zaune a gefe yana kallon abinda ke faruwa har Babah Lantana da taci gaba da harkokin aikinta tare da fadin, a to ai dama ke ki ka barta ta raina ki, yasa da na ji zata azabtar dani azabar da ta wuce ka'ida na same ta na gantsara mata cizo da iyakacin karfina. A gigice kwarai ta kurma ihu mai tsananin firgitarwa nan take kuma ta sake ni. Da gudu nayi nufin fita in bar gidan, caraf Sallau yasa hannu ya rike ni, saboda umamin da Babah Lantana ta ba shi na kar ya bar ni in fita. Ina ganin yayi nasarar kama ni na soma kurma ihu mai tsanani tare da kiran sunan Babah Sumaye, ina rokon ta kawo min agaji, duk da nasan ba zai yiwu ta shigo ba saboda wani rikici da ya faru tsakaninta da Babah Lantana a kan dukan da Asabe tayi min. Maganar har takai Babana ya shaiga ciki ya kuma nuna 6acin ranshi kan keta haddin gidanshi da a ka yi a ka shigo har cikin gida a ka yi fada da iyalinshi. Yana fadin haka Baba Baidu ya ba shi hakuri ya kuma yi mishi alkawarin Sumaye ba za ta sake shiga gidanshi tayi wata magana ba. 133 Sumaye! A'a Tasallah, Babah Lantana ce mai wannan maganar kafin ta koma fadin "Tafdijan! A nonuwa ki ka cijeta? Ki rasa inda za ki cijeta sai a nono don sharri da mugunta? 1o ai kuwa sai ta rama. Rike min ita tamau Asabe ta rama wannan sharri da tayi mata, ta sake yi wa Sallau bayanin. Tashi ke kuma shashasha ji yanda ki ke bari sai ka ce wacce a ka gutsurewa nonon gaba daya, zo ki daidaici inda tayi miki ke ma kiyi mata. Asabe ta iso gaskiya ne har lokacin jikinta yana rawa, alamar ba karamar wahala tasha ba. Tun kafin ta dora bakinta a kan nonon nawa don rama cizon da nayi matan na saki. fitsari a tsaye, saboda tsananin tsoratar da nayi da abin da ke shirin samun nawa. Wayyo! Wayyo!! Abinda kawai nake iya fadi kenan, yayin da zuciyata ke ta neman taimako wurin Ubangiji. Rike ta da kya inin rikon da ba za ta kubuce mata ba, shi kuma yayi maza ya sake damke ni a hannunshi irin rikon da a ke yi wa kazar kuku. Sai kuma ta juyo tana kallona ai daga yau ba za ki sake cizon wani ba a rayuwar...ba ta kai Rarshen maganar tata ba sai ga Mubarak ya shigo gidan a guje. 134 Kan ka ce meye wannan har ya kirbe Sallau da wani irin gigitaccen naushin da ya kifar da shi a kasa, nima na fada can gefe saboda hantsalawar da nayi. Shigowar da Mubarak yayi cikin gidanmu da gudu yayi dalilin da mutane da yawa suma suka shigo saboda sun dade suna jiwo ihun da a ke yi daga cikin gidan. Tankam gidan namu ya cika da Jama'a, sai dai kuma cikar da aka yin bai hana Sallau shan dukan tsiya a hannun Mubarak ba, saboda babu wanda ya koma takan yin rabo. Da gudu Babah Lantana ta suri tabarya tayi kan Mubarak zata rafka mishi ita, samari suka yi wuf suka café ta suna fadin. "Haba Babah, haba Babah, da girmanki ki bugawa mutum wannan a ka? Wannan ai ya zama kisan kai ko kuma ta'addanci, ai rabo ne yafi dacewa da ke. Babah Lantana sai ihu take yi tana fadin an shigo mata har gida ana so za a kashe mata da, ana cikin haka sai ga Babana ya shigo ban san wanda yaje ya gaya mishi ba. Bakin ciki mai yawa ya bayyana a fuskarshi saboda tsananin baccin da ke tare da shi duk ku fita ku ba ni wuri. Yayi maganar cikin natsuwa nan da nan kuma a ka yi ta fita. 135 Babah Lantana tana ganin haka ta soma rusa kuka mai tsanani tana fadin "An keta mata haddin cikin gidanta an keta mata haddin aurenta, an shigo har cikin gida an ci mutuncin iyalanta sakacin Babana yasa duk unguwar nan babu mai jin shakkar shigowa cikin gidan shi yaci mutuncin matarshi. Duk wadannan kalaman da Babah Lantana ke furtawa Babana yana jin ta bai ce mata kala ba, bai kuma cewa kowa ci kanka ba, illa iyaka dai da gari ya waye sai ya zartar da hukuncin da ya ke ganin shi ne daidai a wurinshi. Mu bi Maryam Abubakar cikin littati na biyu mu sake shan wani labarin, kafin nan ina yi muku fatan alheri. Taku; Hafsat C. Sodangi Na gode Tare suka fito da na (2) 136