HALIN RAYUWA 2 NA 07035586299 HAJ. HAFSAT C. SODANGI (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) 2 Hakkin Mallaka [m] Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat C. Sodangi ne GODIYA Godiyata har kullum ga Allah take Subhanahu ta'ala mai kowa mai komai, Makadaici, Mahalicci wanda a ke nufa da dukkan bukatu gwani mai hikima wanda yayi halittarsa bisa tsari na aure wato mace da namiji. Tsira da aminci su kara tabbata ga cikamakin Annabawa, shugaban Manzanni Annabin karshe Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe, wato ranar rarrabewa tsakanin karya da gaskiya (AIkiyama), Ubangiji yasa mu dace. Har wayau ina mika godiyata ta musamman ga daukacin makaranta littattafaee cikin kasa da waje, Ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karfafa zumuncin da ke tsakaninmu. Na gode, Haj. Hafsat C. Sodangi 6/7/1434 2 GODIYA Godiya mai dumbin yawa gare ki. Rabi'atu Faruk Jauro (Ministry of Commerce and Industry Yola, Adamawa State) Da Zainab Sunusi Kofar Gabas Danbatta Zainab Abarshi Yawuri GAISUWA Gaisuwar littafin naka ne Muh'd. Kabir Sodangi (A.T.B.U BAUCH) 3 LITTATTAFAN SODANGI: Uwar Miji Naga Ta Kaina Rabon Kwado... Cikar AIkawari Wayyo Duniya Yi wa Wani... Abu Naka... Mata Ma su Duniya Nufin Allah Kifi Na Ganinka.. Daga Kin Gaskiya.. Da Kamar Wuya.. Mai Uwa. Duk Daya.. Mata Da Kicin Dinsu Wacece Ni? Wata Fuskar.. Mijin Ta ce Garin Banza... Ga ni Gare ka Biyan Bukatar Rai Shamaki Hattara Mata Masu Duniya Kyautata Ayi Dai Mu Gani. Tabbataccen Al'amari 4 HALIN RAYUWA 2 Washegari da safe gaba daya mutanen gidan kowa a cikin natsuwarsbi yake, in ban da Babah Lantana da ke ta faman zirga-zirga tana fadin maganganu kamar yanda dama al' adarta take in har wani abu ya 6ata mata rai. Haka kawai a cizan mun yarinya sannan wani Rato ya shigo har cikin gida ya dakar min yaro, to wane irin rashin yanci ne wannan? Ai kayi hukuncin da za ka yikawai in gani. Lalle ne kuma kayi hukunci me tsanani don in ba haka ba kam... Sai tayi kwafa tare da fadin "Hanya ratatata nuna alamar abinda zai farun ba karamin al'amari ba ne. Koda Babah Lantana bata furta irin wadannan kalaman ba zan kasance ne a cikin natsuwata sosai don na saba jinta tana bada umarnin a rama cizo ko da kuwa bayan shekara guda ne, to balle ni da nayi cizo jiya, cizon kuma ya haifar da sakamako mai tsanani don daga Asabe har SaHau babu wanda bai samu kanshi cikin wani hali ba matsananci. Asabe dai tana kwance tana fama da matsanancin zazzabi, Sallau kuwa bai iya rufa bakinshi ya daina kurma ihun da yake kurmawa ba, sai da aka kira Mallam Bahago yazo ya gyara mishi targaden da aka yi mishia kafada. Don haka sanin a nayi Babana yana cikin gidan nan dai shi ne abinda ya zaunar dani a cikinsh da 5 kuma ganin Asabe a kwance tana fama da kanta nasan a haka ba za ta ce zata rarume ni don ta rama cizon da nayi matan ba, amma duk da haka ina ganin Babana ya dauki kwandon tumatirinshi da nufin fita. Nima zan yunkura in bar musu gidan don ba zai viFu in 2auna tare da su ba tunda nasan zama da su din ba zai haifar min da da mai ido ba. Ina cikin wannai tunanin ne na bango Babana tsaye a tsakar gida rike da kwandon tumatirinshi a hannu alamar zai fita kenan nayi maza na jawo gyalena kusa da ni, don yana fita in bi bayanshi sai kawai naji ya ce ing Yaacuwuna take? Nayi maza na ce Gani nan Baba, na fadi daidai lokacin da na tsuguna a gebanshi, karki sake li fita daga gidan nan. Gabana yayi mummunan faduwa, "Kin ji na gaya miki ko ba kiji ba?" cikin sanyin jiki na ce mishi naji Baba. Na mike tsaye jikina a sanyaye na koma dakin na Zuna na jawo littafina ns karatu ina dubawa sai dai gaba daya hankalina ba a kan shi ya ke ba. "Kai Sallau!" Sallau ya yunkura ya fito gani Baba, shirya ka bar min gida ka koma inda dama ka ke, tunda ka zo kana yi min fada a gida shima wancan din na aika a gayawa Babanshi ya gaya mishi kar ya sake shigo min cikin gidana." gama fadin hakan yasa kai ya wuce zai tafi. 6 Babah Lantana ta bishi da kallo irin na takaici tare da fadin "A hau, ahau wannan shi ne hukuncin naka? Taja wani mummunan tsaki ta juya taga Sallau da ke tafiya da kyar yana rike da ledar kayanshi a hannu zai bar gidan don cika umarnin da maigidan ya ba shi. Sai kawai naji ta daka mishi tsawa "Ina za ka da wannan jikin naka? Maza maida ledar nan kayi kwanciyarka ka huta, ai ko za ka bar gidan nan sai bayan kun rama abinda a ka yi muku tukuna. Cikina ya badasautin kulululuu! Don nasan me maganar tata ta ke nufi Sallau ya koma daki yayi kwanciyarshi yayinda lia ma ta koma kan hidimominta da maganganun da take ta yi. Ana cikin haka ne naji wata irin murya tayi sallama a bakin kofar shigowa tsakar gidanmu. Muryar ta mata amma abin mamakın shi ne da sunan maza naji Babah Lantana ta kira bakuwar. "Nalami ne kuma har cikin gida ba za ka tsaya daga waje ka ce ayi maka iso ba? yayi 'yar shewa tare da 'yar dariya kafin ya ce "In ba kiyi min haka ba ai ba ai ba ki cika 'yar halak ba, ai ba zan ce kin amsa sunanki na Butulu' ba ko ba sunan da dama yan gidanku suke kiranki ke nan ba? Butulu ai dama kazo ne har gidan mijina ka ci mutuncina? 7 Yayi maza ya ce "A'a ko kadan ai darajar aure ya shige haka komai iya shegenka in har ka samu ka shiga karkashin inuwarshi to ka zama mai mutunci sai a mutuntaka saboda darajar shi, don haka ba zan ci mutuncinki a gidan mijinki ba. To tunda ka fadi haka da bakinka muje daga waje, ya ce a'a nan kuma daya a nan din nan zaan zauna bau ce zan shiga dakinki ba balle kiyi tunanin zan hau kan gadonki in kina tsoron kar mijinki ya shigo ya ganin ne babu komai yana shigowa sai in gyara zama in maida kaina kanin Babanki in kuma ki ka ce za kiyi min iya shege to kema kin san ni babanki ne a nan ma. Ina iya zuwa har wurin 7aman nasu in yi koma1, ai ta can na biyo an nuna min shi,don haka dauko tabarma kawai ki shimfida min." Ta kawo tabarmar tana shimiidawa yayinda ni kuma zuciyata ke ta faman kai-kawo a tambayata wane irin mutum ne wannan? Na yunkura na matsa na kebe ta matsin kyauren dakin namu mutum har mutum yasha babbar riga har da hula zanna sai dai kalamanshi. "Ashe har mazaunai ne da ke haka? yayi tambayar daidai ya kaiwa mazaunan nata duka gabana ya sake faduwa, tayi maza ta kars daure fuska kafin Nalami ba ka da mutunci ya gyad zama 8 kan tabarmar ya ce, Eh komai ma kina iya gaya min ni na zo. Ta ce to ka tafi mana ko ni na kira ka? Ya kalleta a'a ba ke ba ce ai kin samu wurin zama sai cin mutuncin Jama'a ki ke yi ja' ira kawai mara tuna baya, kai bebi baki da tuna alheri. "Dakata ka ji Nalami, na daina amsa wannan sunan duk wani abu makaman cin wannan da ka sani na daina shi, mijina mai mutunci ne. " Yayi maza ya ce "Gaskiya kam gaskiya kam ai na ganshi ruan Malamai ne da shi inda tambayar take dai na yanda aka yi ya iya zama da ke ne." Ta zuba mishi ido cikin takaici ai ba za ka bari muyi magana ta gaskiya ba ke nan? Ya tsura mata nashi idanuwan da suka fi kama da gauta saboda kaduwarsu kafin ya ce ai ba ki da ita ne, gaskiyar balle ayi maganarta da ke. Ta gyada kai tare da fadin to shi ke nan naji me ya kawo ka? A haka zan fara magana ina zuba tun ban ci komai ba? Ai sai ki kawo min da na shar kajin da a ka bani labarin kullum a ka zo' gidanki sai an ci. Yana cin naman da ta kawo mishi yana magana zuwa nayi in dangwali arzikinki tunda kin shigo cikin inuwarshi don kuwa nima babu irin taimakon da ban yi miki ba, sanda su sarka suke wulakantaki, ko sanda ki ka haifiyaran nan..." Tayi maza ta katse shi "Ba fa tarihi ka zo karanta min ba, arziki ka ce ka zo ci." Yayi maza ya ce, "Eh 9 haka na ce, to kai duk abinda ka ke da shi bai ishe ka ba sai ka zo wurina ni da nake zaune a dakina ko sana' a bana yi? To ai ku ne masu rufin asirin amma na wajen nan menene ne a cikin abin? Kin san fa shari'ar nan da a ke ta kafawa ta karya darajar al'amuran namu kana gaba daya ke dai ayi shiru kawai tunda kana Musulmi ba zai yiwu ka buda baki ka ce ba ka ji dadin abin ba. Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta mika mishi to ungo rike wannan ko sigari ka sha, lokacin ne na tuna farkon zuwan Babah Lantana na gidanmu har sigari sha take ji amma yanzu kam ta daina don na ma manta in ban da yanzu da naji ta ambata da bakinta. Maimakon ya karba yayi godiya kamar yanda al'adar wanda a ka yi wa kyauta take sai kawai naga ya harari abinda ta ba shin ya ce kyautar matsiyata za ki yi min? ko da na ce miki ba ni da harka ai kin san nafi Rarfin irin wannan kyautar don kin san kont waye? To in tsaya daga waje mana in yi bara ki bai wa yara su kawo min sadaka, ai a sauwake abinda za ki bani in bar gidannan bakina alaikum jaka guda ne. Da sauri ta ce mishi a'a buhu guda ba jaka guda ba gaka guda lafiya ce da za ka ce in baka ita ina na ganta? Kai barawo ne? A'a to sai in gyara zama ai 10 sai kin samu, to sai in gyara zama ai sai kin samu to ma me za ki kira ni kuma oho ni dai kin san ba Delu ba ce da ta taimake ki ta rinka yi mii zirga-zirgar gidajen Malamai da 'yantsubbu bayan irin wahalar da tai tayi miki da 'ya'yanki Sai da ki ka samu kan miji ki ka mallake shi taf ya zama bai da katabus sai naki sannan ki ka yi mata irin tukuicin da ki ka saba yi wa wadanda suka saba taimakonki wanda yayi dalilin da suka rada miki sunanki na ainihi 'Butulu' ki ka koreta ki ka ce kar ta sake zuwa miki gidą don ba ki yarda da, ita ba." "Ita taje ta turo ka ke nan? " kan ya bata amsa sai naji yaro yana magana a tsakar gida wai Maryan ana kiranta a waje." Da sauri Nalami ya kalli Babah Lantana cikin yanayin rage murya dama ba mu biyu ba ne a gidan shi ne ba ki gaya min mun yi maganar a hankali ba? Ba ki kyaufa ba Lantäna, ai wata kusar tafi wata. Ai in da ná sani ba zan yi îrin wadannan kalaman wani ya ji ba, na fito zan wuce in je'kiran da a ke yi min ban sani ba ko zaman Nalamin ne ya hanata tuna min da dokar da Babana ya. kafa mini ko kuma don taga ita ma bata bi dokar ba ne oho, tunda nasan tafi kowa jin an ce ana kirana a waje. Ina fitowa muka hada ido da Nalami barin komai yayi ya shiga bina da kallo, wani irin kallo da yafi 11 kama da na kidima, uh' uh uhhh, wacece wannan Lantana? Tambayar da naji shi yana yi mata kenan yayin da ni kuma na shige cikin zaure na bar su a nan ban jiwo amsar da ta ba shi ba' lna daga cikin zaure na hango Mubarak a tsaye daga waje yayi kwalliya sosai. Karo na farko da ya taka yazo kofar gidanmu tunda ya dawo daga Ibadan, sai ko jiya wannan kuwa naji an ce wai Babah Sumaye ce da taji ihun da nake yi ta aiki Almajirinta da gudu yaje ya gaya mishi abinda ke faruwa. Daga cikin zauren naja na tsaya ban ce mishi komai ba, shi ya matso bakin kofar zauren ya tsaya kina da wata matsala ne? yayi tambayar yana kallona, na girgiza kai a hankali nuna alamar babu. Ya miko min ledar da ke hannunshi cikin zauren na mika nawa bhannun na karba ya juya ya tafi ba tare da na ce mishi komai ba. Na koma baya ta cikin lungun zauren saboda jin ledar da nauyi ga kuma sai da na nemi wuri mai dan kyau sannan na zauna na fito da abinda ke ciki, gasasshiyar kaza ce katuwa tayi matukar gasuwa gashin injin ga yaji a wata takardar ga kuma ruwan lemo na kwali mai sanyi. Lokacin ne na kara tuna har a wannan lokacin da agogo ya kai kan sha biyu da rabi ban sa komai a 12 bakina ba, da bai zo ya kawo min wannan kazar ba kuma to da ban san lokacin da zan samu abinda zan ci ba, ko a haka kuma Babana yake ganin zan iya tsare dokar da ya kafa min ta kar in tafi ko'ina? Oho! Ci nayi sai da naga na koshi sannan na dora ruwan lemon nan a kai sannan na mike na dauki saura na nade na adana shi a cikin gyalena, na shiga cikin gida har lokacin Babah Lantana magana take yi da bakon nata, sai dai a yanzu maganar tasu ta dan sauya da alamar sun dan samu daidaituwa. Yana ganina ya saki wani lallausan murmushi har hakoran Makkanshi suka fito guda biyu, kuma jajaye yana ganin mun hada ido da shi yayi maża ya sakar min signal da idanuwanshi. Nima nayi maza na galla mishi wata irin matsiyaciyar harara na wuce na shiga dakina. Wasu sabbin kwanukan abincin na gani wurin Asabe da alamun fitan da nayi ya kara bada damar da aka sake kawo mata wani abin. "Yanzu dai kin gani Hajiýa bani kawai abinda ki ka ga za ki ba ni tunda ga bayanin da ki ka yi min na halin da kike ciki in an kwana biyu ai zan dawo." Da sauri ta ce, "A'a-a'a ni kar ka dawo min gida in ba so ka ke ka kara min wata matsalar ba." "A aha, ai ke halinki ke nan ki ka sani ko zuwan nawa na alheri ne? To ta ina zuwanka zai zame min alheri ni kuwa?" ya yi murmushi "Uhum, Babah 13 Lantana kenan, ai na daina kiran sunan naki gatsau sai na sakaya miki shi da Baba ko kuma Hajiya. Ai kin san shi sunan Hajiya ma mai niyya yake nufi." "Kai dai karbi amma ni kar ka dawo min gida." Ya karba yana kirgawa, ai tunda na ce zan dawo zan dawo din ne kiyi fatan kawai dawowan nawa ya zame miki alheri." Ya tashi ya tafi. Ina zaune a gida Babana dokarshi a kaina ni kadai take aiki, Babah Lantana da 'ya'yanta babu abinda ya shafe su da ya dawo yazo ya samu Sallau a gidan ma bai ce mishi kala ba, sannan da zai kafa min dokar daina fita daga gidan sai ya manta bai sanya ta bani abinda zan ci dole ba. Duk da haka na bi umarnin da ya banin na in daina fita saboda magnar da Yaya Dijah take yawan gaya min in bi duk wani abinda zai sanya ni komai wuyarshi, kar in ki yi mishi yayya a kai kar kuma in lura da cewar wasa ba su yi mishi ba ni ce ya zama wajibi a kaina in bishi ba su ba. Ina zaune a haka cikin wani irin matsanancin hali in ba Mubarak ne ya kawo min abinda zan ci ba babu mai bani a hakan kuma ga barazana gami da wulakanci da neman tsokana Kowane lokaci a cikin maganar ake haka kawai sai ka ci Babah Lantana ta ce ah cizo? Ai sai kin rama a natse za ki rama kara warkewa dai kawai karfinki ya kara dawowa jikinki." 14 Ina kallo Asabe take fitowa daga wanka ta shafa maina tayi kwalliya da kayan kwalliyata in ta gama ta jawo akwatin kayana ta zabi wanda yayi mata ta daura, bana cewa komai saboda ina tsoron kar maganar da zan yin ya zama sanadin da zamu yi fadan da zata rama cizon. Sannan in ta gama abinda take yin sai ta mike ta bar komai a hakanshi sai na gyara wanda ni shi ne ma yafi bata min rai. Rannan da hantsi Mubarak yazo muna tsaye muna magana sai ga Sallau yazo ya wuce mu yana taku dai-dai, ya bishi da kallo kafin ya dawo da kallon nashi gare ni wannan ya bai tafi ba ne? na ce mishi ch, ya dan yi shiru jimawa kadan ya ce uhun, wato shi Baba ke kadai yake iya hukuntawa? Ban ce mishi komai ba sai ya sake kallona "Ba suyi miki wani abu ba ko? Har na ce mishi Eh, sai kuma naga to in ban gaya mishi ba wa zan gayawa? Don haka na kwashe bayanin komai nayi mishi, ya ce To babu laifi." Hirarmu muke yi sosai ina daga cikin zaure yana waje sai ga Asabe tazo zata shiga cikin gida, cikin dace zanina ne a jikinta kuma shi ya saya min shi, wani lalataccen kallo tayi mishi ta wuce da nufin shiga gida, ba karamar kiyayya Asabe ke yi wa Mubarak ba. 15 Duk sanda ta bude baki zata yi magana akanshi munanan kalamai take yi. Ina wuni Asabe? A lalace ta ce mishi lafiya, dan saurare ni mana minti bivu Ta waiwayo tana yi mishi kallo na sama da kasa. lafiya? Ta ce, bani da lokaci. Ya ce To je ki zan aiko agogo yazo ya gaya miki ama kafin ki ji sakon daga wurinshi kina shiga gida ki cire wannan zanin da ke jikinki ki wanke shi ki goge shi ki maida shi inda ki ka same shi ki ajiye. Ta ce ai ka san don ku kadai Bature yayi iinshi, bai tanka mata ba sai kawai ya kira wani yaro mai kimanin shekaru sha biyar da ke can gefe. Zo nan Isiyaku, maza haura can saman layi ko bayan layi kaje ka kira min agogo ka ce mishi ina nan na jiranshi yazo yanzu. Hankalina yayi matukat daurewa saboda ganin yanda jikin Asabe yayi matukar yin sanyi da jin an tura a kira agogo. Me ke tsakaninta da agogo? Kuma wancne ma agogo? Wadannan sune tambayoyin da suka tsaya a raina. Ga ni! Ta fadi tana mai kallonshi cikin natsuwa ya buda baki ya ce mata, in kin shiga ki gayawa Mamanku saboda nasan uwa ta gar tana karbar shawara wurin danta in dai tasan shi din mai hankali ne. Ki bata shawarar kar ta sake saki ke ko wani ku bugi Maryamu, kai ko da ita kanta ne kar ta sake? 16 Ku barta ta zauna lafiya a gidan ubanta don ta samu tayi ta bin dokokin da yake saka mata." A lalace ta kalle shi ta ce, in ba haka ba fa? Bai kau da ido daga gare ta ba ya ce in ba haka ba ranku ne zai fi na kowa baci, don ke da ni zan shiga cikin lamurranki ba kadan ba, kin san babu abinda ban sani ba a kanki zan sa a gayawa Agogo labarin Dangana kin kuma san abinda hakan ke nufi. Zan sa shi Agogon-ya kula min da lamarin gaba daya, ina yi muku wannan kashedin ne saboda kiyaye hakkin makwabtaka tunda akwai iyayenmu a tsakani, in kuma ba ki ji ba to kuje kuyi. Ke Maryam kar ki tsokani kowa a cikin su, amma mugun kallo idan suka yi miki ki gaya min, na ce to. Ya kau da kai daga garcta alamar maganar ta kare ta gane hakan don kanta ta wuce ta shiga gida ba a dauki lokaci mai tsawo bayan nan ba nima na shiga cikin gidan. Daga shigan da nayi na gane akwai wani canji a tare da Asabe don ban samu kayana a jikinta ba, Babah Lantana ce dai na same ta tana huci tana fadin, Aikin banza aikin wofi, ni kam ai rashin jini rashin tsagawa. Abinda zai hana ni dukan mutum bai tabo ni ba ne kawai, amma duka ai har da na tsiya zan yi mata 17 ko ma don in ga abinda za ayi min, sai nayi na wuce daki na barta tana maganganunta. Asabe dai na gane ta dan ji abinda Mubarak ya gaya mata, ana cikin haka sai ga Sallau ya shigo gidan "Mama ina so muyi magana da ke." Ta bar abinda take yi ta tsaya tana kallonshi, yayinda shima yaja ya tsaya Kerere a gabanta suna kallon juna, "Menene ya faru? tayi mishi tambayar tare da sauraron abinda zai gaya mata. "Wannan yarinyar ce nake so in ce miki ki fita hanyarta, ki bar kowa ya zauna lafiya, abinda kawai zan gaya miki ke nan." Da sauri ta tambaye shi, "Wacce yarinyar?" "Mero." Ya fadi sunan cikin wani yanayi. Kan ya gama karasa sunan ya ji saukar mari a gefen fuskarshi tau! Da iyakacin karfinta tayi mishi marin, a kan wannan shegiyar yarinyar ka ke yi min wannan maganar, in ce ko dan tumurmusan da yayi maka ne yasa ka tsorata da shi haka har yake aiko ka da irin wadannan maganganun ka gaya min? To na rantse sai nayi mata duka har cizon da ta yi wa Asabe sai na sata ta rama ko in rama mata da kaina, aikin banza aikin wofi, barazanar banza da wofi. Ni za a kawowa iya shege? 18 Ni fa nan da ka ke ganina ni ba matsoraciya ba ce, bana tsoron kowa duk iya shegen mutumn kallonshi kawai nake yi, yauwa! Ya'yan Babah Lantana sun dan shiga natsuwarsu kadan saboda ta ki yarda suyi aiki sosai da kashedin da aka yi musu wanda ya tsorata su, amma duk da haka Asabe ta fita hanyar kayana ta kuma kiyaye yi mun wulakanci. na kai tsaye. Illa iyaka dai ba ma magana da juna. Ina zaune a cikin gidan babu mai magana da ni in ba Mubarak ne yazo ya kira ni ba, shi kanshi Baban nawa gaisuwa ce kawai take hada ni da shi, amnma bayan nan babu wani abu. Tsananin kewa da kunci suka tarar min cikin zuciyata, na gane babu abinda yafi mu'amalla tsakanin mutum da mutum dadi, wanda ya rasa abokin mu'amallah kuma to ba karamar wahala ce ta same shi ba. Ana cikin wannan haki na kamu da wani irin matsanancin rashin lafiya, zazzabi mai zafi gami da mura ga matsanancin ciwon ciki saboda lokacin al'adata ya gabato, babu wani taimako da nake samu daga gidan, sai dai in Babah Lantana taga ina rarumen abinda za ayi ko zan ci, saboda yunwar da ke yawan damuna, sai ta rinka fadin ba dai kin ce da ni za ki yi ba? Ai mun sa kafar wando daya ke nan ni da ke, naga wanda zai fara zare kafarshi. 19 Mubarak yazo duba ni da yamma yana daga waje ina cikin zaure, yanzu ke kin rinka zama da ciwo ke nan? An ce ki fito a kai ki asibiti kin ki, shi Baban ba ya ganin irin ramar da ki ka yi ne ya bar ki a haka? Ban ce mishi komai ba na juya na shiga gida ina rike da ledar sayayyar da yazo min da ita. Ina shiga daki na zauna na bude ledar na jawo robar nono zan sha don kuwa nasan barin da jikina ke yi bana ciwo ba ne har da na yunwar da nake ji. na gama shan nonon na dawo-dashi gaba daya ta hanyar yin amai mai wani irin yawa da wari, ga shi yayi wani irin kala. Amai a -daki? Asabe tayi tambayar cikin wani yanayi na nuna tsananin kyama, to na rantse sai dai ki kwashe ke da kanki, don ni bana taba amai. Ina kwance ina jin ta ko daga ido in kalleta ban yi ba, cikin zuciyata dai fadi nake yi dadin abin ma a kan kayana nayi. Babah Lantana tana jin Asabe tana ambaton sunan amai ta rugo a guje, amai? A nan gidan yau'? Uhum, abinda na gudanwa Mallam ke nan abinda na gudanwa Mallam ke nan, abin da na gudanwa Mallam ke nan, bai gudunwa kan shi ba to tunda bai gudanwa kan shi ba kuwa ga shi nan ya same shi. Ni kuwa babu wanda zai zauna ya renan min cikin shege a gidan nan yauwa, don mu abin kunya 20 gudun shi muke yi saboda ba mu gaje shi ba, su dai ina jin suna da gadonshi shi yasa nake tayi mishi kashedi bai ji ba. Sannan al' amarin Mallam ma ai in ka duba akwai matsala, mutumin da bai da dangi Mallam fa ko sunan garinsu bai kira balle ya ambaci wani dan uwa nashi, wa ya san abin da yayi ya bar gidan? Duk da tsananin ciwon da ke damuna sai da na zubawa Babah Lantana ido ina kallonta. Ta ce, Eh kalle ni da kyau ko. karya nayi muku? Ana barin gida haka kawai ne?. ai yawanci abin kunya a ke yi a tafi in kin ga dama ki gaya mishi kema kin san a tafin hannuna yake. Ta muno min cikin tafin hannun nata, ta juya tana tafiya tana gayawa Asabe tafi can wajen tumatirinshi ki kira min shi yazo ya gani da idonshi kar ya ce karya nayi mishi, daganan kuma sai ya kwashe donni da hannuna ba zan kwashe aman cikin shege ba. Ina kwance ina jin shigowar Babana da irin maganar da Babah Lantana ta tare shi da ita, ai babu abinda ban gaya maka ba kan ciwon da yarinyar nan ke yi ba haka kawai ba ne, ciwo kwana da kwanaki kuma mai zafi haka ai kowa ma yasan menene sai dai a yi shiru. Da sauri Babana ya fadi cikin dakin jikinshi sai rawa yake yi, me ya same ki Yacuuwuna? Me ya 21 same ta ko me ya same ta kai nan sai an gaya maka abinda ya same ta? Yasa hannu ya daga ni a'a har da amai ki ka yi? Yasa hannu ya nade ya fitar ya dawo, Babah Lantana tana fadin ai gara kaga aman da idonka, kar ka ce ko sharri a ka yi mata. Tashi muje in kai ki asibiti, yasa hannu ya daga ni yana rungume da ni a jikinshi muka fito daga dakin za ka kaita a cire ne? ai binka zan yi don ba za ku ce ku dawo kayi min karya ba tunda dai wannan ciwon nata ai kowa ya ganta yasan ciki ne da ita. Ina jin irin lkaduwar da jikin Babana yayi sanda Babah Lantana ta ambata.mishi cikin nan ya dan ja ya tsaya na yan dakiku bai motsa ba, kafin ya ci gaba da tafiya. A asibiti a gaban Babah Lantana da Babang Likita ya gama duba ni ya gaya musu cewar maleriya da yunwa ne suka kama ni. A ka sanya min ruwa saboda ramar da nayi tayi yawa, a ka hada min da magunguna a ka sallame mu, Likita yana dada jaddadawa Babana lalle ne a kula da abincina don na rasa nauyi mai yawa a tare da ni. A gida ina jin Asabe tana tambayar Babah Lantana me Likitan ya ce? Ta tabe baki ta cc bai kai ta wurin wani asibiti na gaske ba, can wurin wani 22 dan iska ya kaita da bai ma iya aikin nashi ba, wai ciwon sauro ne da yunwa. Har yana wahi daura mata ledan ruwa in ma hada baki suka yi ya boye ai shi ciki dan duma ne muna nan sai ki ga ya fito mun gan shi da idonmu. Washegari Babana ya kawo min 'yan abubuwan ciye-ciye da yake ganin za su taimake ni. a gabanshi Babah Lantana ta rabe komai ta bani.abinda take ganin shine daidai a wurinta, tana yi kuma tana fadin "In dai cizon sauro ne lalurarta to wanene mai lafiya ne a cikin gidan nan ba gara ita ba ma tana fita ta sha sharholiyarta a waje, mu kam ai kullum muna ciki muna tare da saurayen. Inda na samu kulawa ta sosai-sosai daga wurin Umma ne da danta sai ko Yaya Dijah da mijinta, kusan kullum sai tayi min aike, kusan kullum din kuma zata ce wa dan aiken ya gaya min in naji sauki in zo tana son ganina in ce mashi to. Na soma jin sauki ke nan Mubarak ya zo yayi min sallama kan za su tafi Umra shi da Babanshi, nayi addu'ar Ubangiji ya dawo da su lafiya,; ya kuma sa suyi aiki karbab6e. Ya ce, To amin. Ban yi miki sayayya ba saboda sanin yanda gidan naku yake da nayi don haka ungo wannan ki rike a wurinki ki adana kar ki bari su gani, balle su kwashe miki duk abinda ki ke so ki saya kar ki yarda ki zauna Cikin damuwa. 23 Na gayawa Isiyaku kullum da safe yazo yaje miki aika ko wankinki ne ya taru ki ba shi zai yi miki, na ce mishi to. Lokaci mai tsawo ya dauka yana yi min kalamai na bada hakuri kan tafiyar da zai yi a cikin dani din ko wadatacciyar lafiya ba ni da itana ce mishi a'a babu komai. Na dawo daki na kirga kudin da ya banin Naira dari ne cif wato fan hamsin ke nan, a wancan lokacin kuwa mafi yawancin sadakin yanmatan unguwarmu da a ke aurarwa ma bai wuce tan goma wato Naira ashirin, in yayi yawa a karbi arba'in ko hamsin da kyar kwarai za ka ji an bada sadaki fan hamsin Naira dari ke nan. Mamaki ya kama ni, na in da Mubarak ya samu irin wadannan kudin ya kuma iya bani su, ganin kimar kudin da yawansu ya sanya ni tunanin in kaiwa Babana su sai naga to ai in na kai mishi ma wurin Babah Lantana zai dawo da su. To ko in kaiwa Umma ta ajiye min? nayi maza na canza saboda tunanin anya ya gaya mata zai ba ni irin wadannan kudin? In bai gaya mata ba ke nan na hada su, don haka na mike da sauri na fita na bar gidan ba tare da na gayawa kowa ba. Na tafi na kaiwa Yaya Dijah kudin da sauri na dawo nazo na boye Naira goman da ta bani ta ce in rike a wurina, saboda bukatuna. 24 Kamar yanda Mubarak ya gaya min cewar Isiyaku zai rinka zuwa min aika hakan a ka yi, da sassafe ya shigo ya gaida Babah Lantana kafin ya zo in da nake na dauko kudi na bashi, na gaya mishi abubuwan da zai kawo min yaje ya kawo ya karbi wankina ya fita da su. Ba a wani dade sosai ba sai gashi ya kawo min su a goge, dadin hakan yasa na mike'da nufin in je in yi wanka don in kara jin dadin jikina. Naje kicin da nufin in sanya ruwan da zan yi wankan da shi a risho don ya dan kore sanyinshi tunda ba gama wartsakewa nayi ba. Babah Lantana tayi maza ta ce min kar ki shigar min wurin nan ba ki da komai a ciki in dai ba tsamar min naman miya za ki yiba. Na dawo da baya nasa hannu na dauki bokitin robar da ake wanka da shi, nufina in tari ruwa a bakin famfo in je in yi wankan a haka, nan ma ta ce a jiye min bokitin nan tunda ba uwarki ce ta saya min shi ba. Na maida shi na ajiye na wuce naje na dauko wani bokitin karfe da ke can gefe na tara shi ina duban ruwan ta bar abinda take yi ta mike ta tsaya tana kallona wai ba nace kar ki taba min wani abina ba ne ko kina nemana ne da magana'? A hankali cikin natsuwa nace mata wannan ai ba naki ba ne kin ga ni? Bokitin Innarmu ne, abinda 25 kawai na fada kenan ta takarkare ta wanke ni da marin da nayi matukar kaduwa. Ba na ce ki daina ambaon min sunan shegiyar matar nan a cikin gidan nan a? ban san lokacin da na buda baki na ce wa Babah Lantana "Gaskiya Innarmu ba shegiya ba ce. Sai kawai ta rufe ni da duka. "Ai dama na gane talke-takenki nema ki ke ki fara zahina kiri-kiri, bayan na bayan idon da kike yi ana gaya min ba ki kuma isa ba don ni nan ko uwar taku ma da tana nan din ba za ta buda baki ta zage ni in kyale ta ba, to balle ke banza a banza. Duka iin wanda Babah Lantana tayi min bai kwatantuwa don kuwa yi tayi sai da ta gaji ta bari don kanta, babu wanda ya shigo gidan don kawo min agaji, duk da irin ihun da nayi ta kurmawa. Asabe ma tana daki a zaune ba ta ce mata komai ba. Ina zaunc a tsakar gida bayan matsanancin dukan da Babah Lantana tayi min ban sake komawa dakin ba saboda abinda nake tsoro wana ke kara sa ni zaman nakin ya faru, don haka ina zaune ne kawai a tsakar gidan amma ban iya daina kuka ba. Ita kuwa Babah Lantana tana ta kai-kawonta tare da fadin "Haba an ce miki ni ina tsoron wani ne? Ni fa da ki ke ganina bana tsoron kowa ina kyaleki ne kawai kina iskancin ina kallonki, amma ba don tsoro ba. 26 Yi ta zama a nan har uban naki ya dawo yazo ya same ki in ji abinda zai ce, ina ce zaman da ki ke yi a wurin ke nan, in kuma shi wancan dan iskan ne ina nan ina zaman jüran dawowarshi in ga abin da zai yi ko ni ma zai zo ya kirba min naushin ne?" Sallau yana shigowa gida ya ganni a zaune yayi turus ya zuba min ido yana kallona, cikin tsananin kaduwa ya juya inda Babah Lantana ke zaune tana sakucen naman da taci da tsinken zaburin shara. "Dukanta ki ka yi Babah, me tayí miki? Ba ta ma fa gama warkewa ba sannan in za ki buge ta ma Babah wannan wane irin duka ne? Da sauri Babah Lantana ta mike ta kifa mishi mari mai tsananin karfi ta sake kifa mishi wani. marin har sau uku da ya tsaya wata kila da abin yafi haka. Juyawa yayi ya fita, ya barta tana fadin, sakarai matsoraci, shashasha kai kam in ba sa'a nayi rakiya kayi wa maza zuwa duniya don duk wata harkarka ta tsoro ce, na bugeta wanda duk ke da abin yi yazo yayi ina nan ina zaman jiranshi, aikin banza aikin wofi, ni za a kawowa iya shege? Ina zaune a daki cikin matsanacin hali don wani zazzabin ne ya sake rufe ni, ga 6acin rai don na fara gajiya da irin wadannan al'amuran naji dawowan Babana da bayanin da Babah Lantana ke yi na nayi 27 mata rashin kunya itama kuma tayi min hukuncin da ya dace da ni. Sau dubu kuma in zan mata to sau dubu itama zata yi min in ina son zama lafiya to in kiyayeta gara tun wuri ya jaddada min in ba haka ba kuwa to ita babu ruwanta bai ce matakomai ba. Washegari da safe tunda na tashi da kyar nayi sallah na koma na kwanta saboda tsamin da jikina yayi ina jin sanda Asabe ta sauko daga kan gado ta take min kafata ban ce mata komai ba. Ta dawo dakin tana sallah na ji Babah Lantana tana ta kwala mata kira, cikin wani yanayi kamar dai wani abu ya faru, da sauri ta:sallame ta fita sai naji tana ce mata yi sauri ki tafi gidansu Delu ki gani ko a can Sallau ya kwana bai dawo gida ba jiya. Gidan su Delu kuma Baba me zai kai shi can bayan duk wannan abinda aka yi? Yanzu haka yana can wajen abokanshi sun sha a bar su suna ta barci. Ke wuce kije ki duba min shi mara mutuncin yarinya mai gardamar tsiya kuma Delun kike kira haka gatsau babu sakayawa babu komai? Asabe ta wuce tana kunkuni haka kawai mutum yaje ya kwana a wurin iskancinshi za a hana ni baccina na safe ace sai na dubo shi sai ka ce wani dan karamin yaro. To ko ni da aka ce Sallau bai kwana a gida ba nayi mamaki don ba mai irin wannan halin ba ne 28 amma sai na maida lamarin kan yayi fushi ne da abinda uwarshi tayi mishi saboda maganar da yayi mata a kaina tunda na saba ganin yana fushin da ita ta bashi hakuri. Abu wasa-wasa sai ya soma neman ya zama gaskiya kusan duk inda ake zaton ganin Sallau sai da aka je nemanshi babu shi babu dalilin shi. A ka wuni ranar babu Sallau, tun ana kokarin danne hankula kar su tashi har dai abin ya gagara a ka shiga tashin hankalin mai tsanani, nena har da Babana a ciki don ko wurin tumatirinshi bai je ba, har wajen yan sanda aka kai riport da kuma asibitoci shiru babu wani motsi. Har wajen taran dare suna zaune jungum- jumgun a tsakar gida, yayinda ni kuma nake kwance a daki sai naji Babah Lantana tayi magana cikin sauri duba Asabe naji kamar an shigo zauren gidan nan. Asabe ta mike tana fadin ke Babah ba za ki bar mutum ya huta ba, dazu ma fa haka ina zaman- zamana ki ka tashe ni wai kin ji kamar an shigo zauren gidan nan to in an shigo menene? Wani irin mummunan ihu Asaben ta kurma a daidai shiganta cikin zauren, abinda yayi dalilin da Babana da Babah Lantana suka karta a guje don ganin dalilin ihun nata. 29 Thun Babah Lantana ya biyo bayan ihun Asabe Babana kuwa sai faman salati yake yi yana karawa alamar abinda ya ganin yayi matukar razana shi. Makwabta ku kawo min agaji da iyakacin karfinta take fadin hakan sai dai babu wanda va shigo duk da ana jin ihun nata da kuma kiran agajin da take yi amma shiru, bata kuma daina ba tanfar dai a ce ta mance da irin zaman da take yi da su nasa mu jinta yayiwa kowa kashedi kan shiga gidanta da ake yi bata so. Bai san yanda aka yi ba naji maganar Baba Baidu cikin zauren yana fadin, a'a bai mutu ba ai ga wannan jijiyar tashi tana harbawa da sauran ran, da alama dai shi Baba Baidu ya amsa kiran neman agajin da take yi ya kawo mata. Ihu Babah Lantana take yi tana karawa bata yi shiru ba har Likitan da Babana yaje ya kira ya iso. Shigo da Sallau tsakar gida da aka yi yasa na koma ta inda nake hangensu, tabbas in dai ba hatsarin mota yayi ba ko wata Rakkarfar dabba ta tattaka shi to wanda duk yayi mishi wannan abin da aka yi mishin ya tabbata mara tausayi. Likita ya fara taba shi shima ya fara fadin na tuba na tuba ku bar ni kar ku kashe ni, kusan awa biyu Likita yana kanshi ana yi ana danne shi saboda zaburar da yake yi. 30 Gaba daya jikin nashi ciwo ne wajen targade shida ne da kuma tsagewan kashi guda biyu, bayanin Likita ke nan. Yayi abinda zai yi ya gama ya mike yana fadin, in hali yayi a kai shi asibiti a kara bincike na sosai amma a yanzu dai wadannan da muka gani mun kula da su. Baba Baidu yayi mishi godiya' yayinda Babana ya bi bayanshi alamar zai je ya sallame shi, ita kuwa Babah Lantaná sai faman kuka take yi tana fyace majina da bakin zaninta itama Asaben da ba wani shiri sosai suke yi ba kuka take tayi. Sannu Sallau, sannu ka ji? Sanu, Ubangiji ya baka lafiya maganar Babana ke nan. A hankali Sallau ya bude baki ya ce "Yauwa Baba, na gode." Da sauri Babah Lantana ta kara matsawa kusa da shi tana tayi mishi magana saboda ganin da tayi ya dawo cikin hayyacinshi. Da kyar ya yarda ya buda baki ya bata amsar tambayar da ta dame shi da ita "Su Agogo ne. gabana yayi mummunan faduwa jin ya ambaci sunan da Mubarak ya ambata a matsayin wanda zai sa yayi mishi maganin abin. Su waye su Agogo? Ta sake bukatar sani, bai ce komai ba sai da ta gaji da tambayar cikin natsuwa ta soma yi cikin karaji da tashin hankali sannan ya bata amsa ki tambayi Asabe tasan shi. 31 Da sauri Asabe ta daka mishi tsawa kai kul kasa sunana a Cikin abin ku da waui ruba66en bakinka. Gaba daya kowa yayi shiru daga inda nake dai ina jiwo mishin Sallau ba kuma san ba dadi ba ne ya kawo hakan can cikin zuciyata kuma ina tunanin Asabe da dan uwanta Sallau babu halin su hadu wuri daya sai sun yi fada na tuna ni da Yaya Dijah na ce to ko don mu ba mu da uwa ne yasa muke son juna oho? Zuwa can Sallau ya sake gajiya da tambayoyin uwar ta shi ya ce, to in na gaya miki abinda yasa Agogo suka yi min haka me za ki yi? Ba kin ce ko sama da kasa zata hadu ba za ki daina dukan Mairo ba, to wannan abinda a ka yi min ai ba komai ba ne kan abin da ki ka ce, don haka gobe ma ki sake dukanta. Shawarar da na baki ba ki dauka ba ne yaja min wannan wahalar gobe ma in kin sake za su sake da har sun je sun kama mijin Babah Delu da ki ke cewa wanki ne suka sake shi saboda ya gaya musu babu abinda ya hada ku in ban da zaman gidan baya, yanzu ma kuma bakwa tare don in sun baki shawara ba kya dauka. In ban da halin da Sallau ke ciki wata Rila da Babah Lantana ta gwabe mishi bakinshi a dalilin 32 wannan bayanin nashi, nmaimakon haka kurma ihu mai tsanani tayi, ta yi kuka irin na fitar hankali bayan ta tambayi Sallau yanzu saboda wannan shegiyar yarinyar a ka yi maka wannan azabar? Bai musa ba bai ce mata uffan ba, to ai kuwa ba zan daina dukantä ba, sai dai... kan ta karasa taji ya ce mata to nuna min kawai inda dangin ubana suke tunda shi kin ce min wai ya mutu in dai da gaske ina da shi ai ba zai rasa dangi ba don ni Babah Delu ta ce min duk abinda ki ke gaya min kar.. Kan ya karasa tayi maza ta tarke shi da mari a kan ciwon nashi, ni dama kashe ni kawai ki ka yi da yafi min tunda dai duk wahalar da nake sha a rayuwata ke ki ke ja min. Wannan din ma ke ce na kuma san za ki sake ja min wani tunda sun ce sau goma ki ka buge ta sau goma za su rama mata a kaina, to ba gara kawai ki nuna min in da ubana yake ba. Ganewan da Babah Lantana tayi cewar Mubarak ne yasa a ka yi wa danta irin wannan matsanancin dukan duka kuma irin na rashin tausayi, a matsayin kashe di mai karfi gareta kan abin da take yi min na azabtarwa yayi matukar tayar mata da hankali. 33 Ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, don bakin ciki ta rasa me zata yi ta dauki fansa kan wannan abinda yayi mata? Tayi kuka tayi kuka har sai da ta kwanta ciwo wanda ban taba ganin ta kwanta da sunan ciwo ba sai a wannan lokacin. Kwana biyu ita ma tana fama da kanta, rannan ta samu sauki ta fito tana zaune a tsakar gida kan turminta ashar take durawa Mubarak tana fadin tana nan tana jiran dawowarshi yayin da ni kuma take ta faman tsine min albarka. Asabe ta gaji ta ce mata, to ya dai tsaya a kan zagin kar kije ki sake jawowa mutane wata fitinar don ke ba kya jin shawara. Wani abin mamaki shi ne, Asabe sai ta kwaso kowacce irin magana ta yabawa Babah Lantana tana kallonta ba za ta ce mata omai ba, amma Sallau duk da kasancewarshi da namiji kuma shi ne babba bata yi mishi lamnunin hakan. Jinya sosai Tanimu ya kwanta yayi kwana da kwanaki yana yi Babana yayi ta dawainiya da shi, amma tun bai gama warkewa ba sai naji Babah Lantana tana cewa Babana wai yana gani ana nema a kashe mata da a kan matsiyaciyar 'yarshi amma ya kame baki yayi gum kamar na mai cin najasa, gum din din dai ya sake yi mata bai ce mata komai ba har tayi ta gaji tayi shiru. 34 Duk da kudin da nakeda su a hannuna rashin Mubarak yasa nayi matukar. takura komai zan eii sai na saya ban saba wannan rayuwar ba, abinda nafi sabawa dashi a kawo min ne don haka kudin da ke hannuna bai hana ni jin yunwa ba, musamman ma da yake wani lokaci ana sayo min in kasa ci, don bai gamsar da ni ba tunda in yana nan ba irin wannan din nake ci ba. Babah Lantana tayi girki ta raba ta baiwa kowa nashi 'ya'yanta guda biyu da Babana yayinda ita kuma take zaune a kicin tana cin nata, na mike naje e same ta na ce Babah a bani nawa abincin. Ta kalle ni a lalace ta ce in ba haka ba fa a kore ni ko a yi ya ya? Shiru nayi na tsaya.ina kallonta, yayinda ita kuma take bayani a nemi kashe min da a kan ki sannan in yi girki in ba ki.ai ba zai yiwu ba. Daga bayana Babana ya ce min to zo ki dauki wannan nawan kici, na juyo da sauri ta biyo ni tazo ta fige kwanukan a hannuna in gadaranka kai ka kawo ai ni na girka, ni baiwarta ce? Bata danye itama ta girkawa kanta ai mace ce babu kuma abinda bata sani ba wani abin ma ta fini sanin shi. Wannan magana da Babah ILantana tayi ta in girkawa kaina shi ne dalilin da yasa da gari ya waye nabi bayan Babana zuwa wurin saida 35 tumatirinshi nace ya bani kayan miya, ya zuba a leda ya miko min. Na kalle shi cikin natsuwa na ce, to abin da zan dafa fa? Akwai a gida, na ce ba za ta ba ni ba, bai ce komai ba ya ciro kudi ya bani na wuce na shiga shago na sayi taliya guda daya na juyo na kama hanyar zuwa gida. Ran 'yanmata ya dade, na jiyo muryar tashi daga bayana na kuma shaidata ta Mansur ce, bàn waiwaya ba na dai ja na tsaya ina jiran isowarshi. Ai rannan na hango ki kina dawowa daga Makaranta nayi ta daga miki hannu ina haba in babu busa babu daga hann ne? sai na lura ma ba ki ganni ba. Nayi murmushi tare da fadin eh, ka kyauta min kwarai da kai da kanka ka gane ganinka ne ban yi ba. A'a haba ai nasan ba ki da irin wannan wulakancin ke dai kawai ganinki ne yana wuya da yake kin riga kin zama budurwa. Na ce, kai Mansur ke nan, barkwancinka yana da yawa, can cikin zuciyata kuwa mamakin dabi'arshi kanbama 'yanmatancina nake yi. Kullum muka gamu sai ya jaddada min ni din budurwa ce ni din mai kyau ce, ni din daba ce da saura, abinda kuma bai taba damun Mubarak ba ke nan. Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin ko 36 Mubarak. sya taba gaya min ifin wadannan kalmomin? Kai bani tuna ba. Kar dai a ce rashin lafiya ki ka yi bai sani ba? Na ce eh amma ba mai tsanani ba ne, ya zuba min ido yana kallona, kina nufin abinda yayi sanadin wannan ramar ba ma tsanani ba ne? nayi murmushi na cé. eh, ya ce to kuwa sai muyi ta addu'a kar mai tsananin yazo, na ce to amin. To mu ba yaran nan ledar cefanen mana don kar mu 6ata muşu lokaci na ce a'a babu komai cefanena ne, kina nufin kece za:ki yi girkin da kanki? Na ce, eh, ya ce a'a to shiga ciki kawai ina zuwa, bari in je in kawo cefane nayi maza na ce a'a ka bari. Ya daure fuska ya ce, to ai ba ke ki ka roke ni ba, na wuce shi da nufin tafiya gida, ya sake biyo ni ran yanmata ya dade, na dan rage takun da nake yi don nasan wata magana yake son gaya min, kina da bukatar wani abu ne? nayi maza na ce mishi a'a na tafi. Ina cikin tafiya sai ga Isiyaku da saurinshi, Anti ai nazo ki ka ce babu aika, na ce eh Isiyaku wurin Babana naje na karbo yasa hannu ya karbi ledar da ke hannuna muna tafiya yana bani labarin wahalar ruwan da ake yin da yanda suma matar Babansu ta 37 sanya dokar sai mutum ya ajiye bokitin ruwa goma kafin ta ba shi abincinshi. Ba ki ga fa inda muke tafiya diban ruwan ba, na ce eb to wata rana ai zai wuce Isiyaku, ya ce haka a ke fada, nayi tunanin shima yana da irin manina kenan, da zuciyata ke yi min a duk lokacin da a ka gaya min haka shi ne na in tambayi kaina to yaushe ne wata ranar zata zo? Cikin gida na shiga shima ya biyo ni duk da yasan Babah Lantana ta tsani shigar da yake yi cikin gidan kullum ta ganshi a ciki sai ta tambaye shi kai baka san nan gidan, gidan matan aure ba ne ba? Sai ya ce ya sani ye uce ta yayi abinda zai yi ya fita. Na shiga cikin kicin, tayi 2za ta biyo ni karki shigar min kicin kar ki taba min komai a wurin nan, don ba zai yiwu ni da ke a ciki ba, in kuma ke ma matar gida ce sai ku zo ke da ubau i ku gaya min." Ban tanka ba nasa hannu na dauko risho tare da tukunya mai murfi, ba na ce kar ki taba min komai ba, na kalle ta na ce, kin gani? Wannan ai na Inna ne, kadan ya rage ta kifa min mari saboda ambaton Inna da nayi a gabanta, ban san yanda a ka yi ba sai kuma naga ta fasa. 38 To juye min kananzir din ciki ko shi ma nata ne? naje na juye mata, ina fitowa Isiyaku da ke biye dani yasa hannu biyu ya karba ya bar ni ina neman wani tsohon galan da na san yana nan a cikin kicin din. Na fito ina kwance bakin zanina da na daure kudina don na daina ajiye su a ko'ina sai a bakin zanin da ke jikina, na zaro abinda zan ba shi ya tafi yaje ya sayo mana. kananzir, na rasa inda zan sa risho din saboda iskar da ke kadawa. Na wuce naje na kai shi dakina da nufin yin girkin, à can nan ma ta biyo ni dakin ai ba naki ba ne ke kadai, don haka ba za ki yi girki a ciki ba, balle kije ki rine mata kayanta da hayakin risho. Don haka ha koma cikin zaure na sa-shi a lungu tunda ni dai nasan kawai zan yi girki ina bukatar cin abincin, ga Isiyaku ma yana bukata, don tunda Mubarak ya hada ni da shi wurina yake zuwa ya karya ya kuma ci na rana, abinda Mubarak din ya gaya mishi ke nan nima ko ban yi niyyar saye ba in yazo sai in ba shi. Shiga wurin Babah Sumaye ka ce wai ta bani wuka da ludayin miya da kuma kwanukan cin abinci, ya ce to. Kai yau ga wani abin dadi, girkin ma a zaure a ke yin shi? Alamar dai ke nan da girkin ba na 39 tsayawa yaci. Na waiwaya cikin murmushi na Darowata ba ae mai wucewa a hanya ma zai iya kalle shi, manya-manyan edoji ne guda biyu a hannunshi a cike da cefane. Na rike baki na ce kai Mansur wacce irin hidima cekwannan? Ya yi maza ya daure fuska alamar bai son maganar tawa, in wanke hannu dai kawai kenan in yi shirin yankan attarugu da albasa tunda nasan zafinsu ai kin ga ba zai yiwu in bar ki ki taba su ba. Nayi murmushi na ce ai an riga an yanka su, sayayya sosaiaMMansur yayi na kayan tea daya ledar kuma kayan ciki ne wanda hanta yafi komai yawa a ciki, ga kuma a gada nono guca mai kyau da ita. Isiyaku yana ganin ledar kayan cikin ya sure shi ya shiga gidan Babah Sumaye yaje ya wanke shi tas ya kawo ya nuna min. ina, dubawa yana yi min magana naga gaushin da Babah Sumaye ta sauke girkinta ko can zan kai wannan? Na ce to kai Isiyaku in babu abinda zata dora a kai. Ko akiwai, ma ai naga wani kurfon buhun gawayi ne kuma da ita zan hura wata wutar, na ce mishi to. A zaure na soya agada na hada mana tea muka sha ni da Isiyaku bayan tafiyar da Mansur yayi a kan zai je gida ya dawo. 40 Sai da muka koshi sannan muka zaune yin girkin dafa dukan taliya mai hade-haden kayan lambu a ciki nayi mana na zubawa Mansur a karamin food flask na zuba mana namu ni da Isiyaku saura na juyewa almajirai da suka zo wucewa su biyu. Farfesun kayan ciki yayi Isiyaku ya shiga ya fito da tukunyar na zuba mana namu ni da shi, na zubawa Mansur da Babah Sumaye na hada baiwa Isiyaku duk yakai musu ya dawo. Muka hadu muka gyara wurin ya kuma yayi mana wanke-wanke ya kife ya dawo. Wai dan girkin nan da nayi naci sai ya haifar min da wata irin natsuwa da na dade ban samu irinta ba, damuwa tayi min sauki naji dadi cikin raina, don haka da na shiga gida ina ajiye kayan tea na' da sauran abubuwan da na shigo da su, sai kawai na wuce na shiga wanka don in kara jin dadi. Na fito daga wanka ina shafa mai na lura naga kamar an taba kayan da na ajiye, na mika hannu don jin ko da gaske ne an taba sai kawai naji an juye babu komai a ciki sai gwangwanayen aka bari. Cikin zuciyata na ce iko sai Ubangiji, na ci gaba da harkokina. 41 Washegari da safe ina kwance kan shimfidata ban motsa na tashi ba saboda nasan ko na tashin bani da wani abinda zan ci na kuma daina aikin Babah Lantana tunda ko nayi bani da rabo cikin abincinta. Jiran shigowar Isiyaku nake yi don in ba shi ya sayo mana abinda zamu karya dashi. Jimawa can sai gashi ya shigo rike da kwano mai shake da waina da wani kwanon kuma, miya ce da kashi da man shanu, cikin fara'a ya ajiye kwanon yana murmushi. ""Yaya Mansur ne ya bani wai in kawo in na gama kuma in je in same shi na ce mishi to." Wajen karfe goma sha daya da rabi na safe sai ga Isiyaku ya dawo dauke da cefane niki-niki har da kaji da kuma busasshen manya-manya. A.zaure rannan ma muka yi komai muka ci na zuba na Babah Sumaye da na Mansur na aiki Isiyaku ya kai musu na zuba mishi na Almajirai yaje suma ya kai musu. Sauran kayan kuwa gaba daya na sa shi ya diba yaje ya kai wa Babah Sumaye ya ce ta ajiye cefane ya zamo mishi wata ka'ida da ya dora wa kanshi kullum sai yayi ko da kuwa na jiyan bai kare ba. Kullum muka yi kuma zan zuba a kai mishi sannu a hankali kuma sai Mansur ya maida zauren gidanmu wurin hirarshi. 42 Rannan iną tare da Mansur a zauren tare da Isiyaku, muna hirar ne ina yi mana girki sai ga Babah Lantana tana ganin Mansur ta soma zagi da fadin lalatattun maganganu irin wadanda ta saba yi wa Mubarak. Nan da nan Mansur ya maida wukar da ke hannunshi wacce yake yanka min albasa, da ita ya daga ido ya kalli Babah Lantana cikin natsuwa ya ce mata ai ki na ambaton sunan 1yayena a cikan maganganun naki za ki gane kin jawa kanki matsala don ba zan bari ki zagan mun su ki kwashe kalau ba, zan gwammace in biyo ki har cikin gidan in sa dorinata in yi miki dukan tsiya. In yaso duk abinda zai faru bayan hakan ya faru zai fiye min sauki a kan kiyi wa iyayena zagin wulakanci irin wanda ki ka saba yi wa mutane suna kyale ki, kin taba ganin na shiga lamarinki? Kin taba ganin na buda bakina na gaya miki wata kalma ko da kuwa ta gaisuwa ce tunda ki ka zo layin nan? Kin taba ganin,na shiga harkokin da ki ke yi? Kin taba ganin na shiga harkar 'ya'yanki? Amma shi ne ki ka zo kina zagina har kina ambaton sunan ubana? To sake fadin kalma guda daya ki ka ga ni? In ma nayi mata ciki sai me? Ina 43 ruwanki ai ba zan barta tayi ta yawo da shi kamar yanda a ka barki kina yawo da naki ba. Ban san yanda a ka yi ba sum-sum naga Babah Lantana ta juya ta shige gida ta bar shi yana fadin haka kawai mata kin zo unguwa kin samu mutane kin tasa su a gaba suna kallonshi sun kyale ki? Ai karyar iya shege ki ke yi. Na shiga gida don taba ruwa sai kawai naji Sallau yana cewa Babah Lantana na rantse miki Mama in ki ka sake jawo wata fitina ta same ni sai kin gaya min inda Babana yake. Tunda na ce zan shiga duniya kin ce namiji don ya shiga duniya ba komai ba ne, ga maigidan nan ma ai shiga duniyar yayi ya bar danginshi da bai samu yanda ya ke so ba. Kuma ya bakura ya yafe su to na fasa shige duniyar tunda don na shiga bai dame ki ba, zama zan yi a inda ki ke iyaka in tara miki Jama'a su rokar min ke ki nuna min in da ubana ya ke, a to. Ya fadi a to din tare da gyada kai nuna alamar da gaske yake yi zai iya aikata abinda ya ce din. Rannan dai jikin Babah Lantana a sanyaye ya wuni saboda rasbhin mutuncin da Mansur yayi mata ga kuma kalaman danta wanda ko gama warkewa bai yi ba, yanda ta wuni jiki a sanyaye haka Sallau ma ya wuni yana mita ba fa gama warkewa nayi 44 ba har yanzu din nan ji nake kamar kasusuwan jikina Agogo ce suke kuma wai kina sake shiga sabgar wani saboda ba ke suke yi wa ba. Ina jin su babu uwana takura ta dai tayi matukar raguwa, gashi abin da nake so shi nake ci na rabu da yunwar da ke yawan damuna a yanzu kuma ina da yann hira ga Isiyaku ga 'yan Almajiraina guda biyu wadanda in ba wani muhimman abu za su yi ba basa barin gidan, sannan ga Mansur abokin hira mai dadi mai fadin kalamai masu dadi mai barkwanci, mai sanya zuciya taji tanfar a kan gajimare take yawo, saboda dadadan kalamanshi, ga shi kuma da yawan alheri. Tun daga ranar da Babah Lantana tayi haka da Mansur nima bata sake shiga harkata da yawa ba balle Mansur din iyaka dai kullum zan ji ta tana cewa Babana wannan yarinyar fa ba a rabu da bukar ba wancan ya tafi ne wani kuma ya mayye gurbinshi. Ta kwashe bayani na karya da gaskiya tayi mishi, rannan har tana yi mishi rantsuwar wai ta ganshi ya matse ni a lungu in banda ta shiga zauren da bata san abinda zai wakana ba. Yana jin ta tayi shiru bai ce mata komai ba, takaici ya kamata ta ce koda yake dai kai dama irin wadannan ba su dame ka ba, ba ka tsoron shege ta 45 kalle shi ta tabe baki tare da mikewa ta nufi dakinta tana tafiyar tana magana a hankali sai dai hakan bai hana a ji ta ba, don rage muryar na iya shege ne. Wa yasan abinda kayi ne ma Mallam kafin ka baro gida nake damun kaina a kan 'yarka? A zuciyata na tabbatarwa kaina raini ya kai duk inda yakai tsakanin Babah Lantana da Babana, tunda har zata iya furta mishi irin wannan maganar a kan idonshi, bai iya ce mata komai ba, na gaji da irin wadannan kalaman na tozartawa da take yi mishi, koda a bayan idonshi ne balle kuma abin ya kawo kan idonshi. Raina ya kai matuka wajen 6aci jikina har yana rawa na gaji da irin wulakancin da a ke yi wa Mahaifina a kan idonshi, a kan idona saboda raini da tozartawa. Ban san yanda aka yi ba sai kawai ji na nayi na bude baki ina cewa Babah Lantana, Babana ko ya baro garinshi da danginshi ai kuma bai yi kama da wanda ya aikata abin kunya ba. Don kuwa bai da wata alama ta rashin mutunci a tare da shi. Tana jin haka ta zabura ta mike da ke nake ko kuwa rashin kunyar taki ta kai ma za ki zage ni nc? ko ba da ni ki ke ba ai cin mutuncin mahaisina kia ke yi a gabana da kuma 'ya'yan da ke da su ya rufa muku asiri. 46 Ta shiga zage-zage tana dura min ashar, ni kuma ina daki ina fadin a'a haka kawai kullum sai kin wulakanta shi yana kallonki don kawai kin ga baya yi miki magana? Ana cin arzikinshi ana kushe shi? Babana in mutumin banza ne zai rike miki 'ya'yanki ne? Asabe tasa kafa ta taka min shimfidata kamar yanda ta saba yi kullum, maimakon .in karkadeta kamar yanda na saba sai na kalleta na ce mata gaskiya wannan wulakancin ya ishe ni haka ke ki taka min shimfida sannan a zagar min ubana ina ji, ya isa haka. Da sauri ta mike ta zauna a tsakiyar gadon, ke yarinya ina ganin fa wani abu yana yi miki yawo a kai, ni sai in sauke miki shi bari kiji in gaya miki na harareta na ce kai haba yarinya ai tana bayan uwarta. Ta zuba min ido, to ba zan daina ba yi abinda za ki yi ta sake tattakawa, na fita naje na tsaya a kofar dakin Babah Lantana don rabon da in shiga dakin har na mance da lissafin tun dai ranar da ta mare ni a kan na taka mata sabuwar ledarta. Naja na tsaya daga waje na ce Baba ya amsa na gaishe shi kafin nayi mishi bayanin abinda ke faruwa na taka min shimfida da Asabe ke yi kullum. 47 Kan ya ce komai sai kawai naji Babah Lantana ta karbe maganar, ai nan karar Asabe ki ka vi wurin ubanki ke nan ga mai uba ko? Aiya sannu mai uba yiwa wacce bata da uba wulakanci. Dadin abin shi kadai gare ki na juya zan koma dakin saboda jin shi Baban nawa bai ce komai ba. Sai naji tana cewa kai ku kam da kuna da wani asali ba a san irin iya shegen da ki ka yi wa mutane ba. Na ce uba ai shi ne asali Babah, ai ni da asalina a ka ganni tunda a gidan ubana aka ganni wanda ya rasa uba ai shi ya rasa asalirishi. Gari na wayewa nayi duk abinda na saba yi na yau da kullum dina, ia jira Babana ya fita sai kawai na leka na kira Isiyaku tare da yan Almajiran nan dama na gaya musu kar suyi nisa. Gaba daya kayan dakina na fitar da nawa da wanda ba nawan ba na share dakin tas na cire cinyayyar ledar da ke ciki na wurgar da ita ina aikin Babah Lantana tana jaddada min in dai hankali da kayan Asabe don ita duk kayanta masu tsada ne. Ban tanka mata ba na dauke yar shimfidata daga kasa na baje ta karkashin katifar da ke kan gadona sannan na maida katifar akai na jawo wani tsohon zanina na shimfida na gyara komai na maida kayan na ajiye kofar dakin ma na sanya 48 mishi sabon labulen da Yaya Dijah ta bani sanda ta gaya.min abinda zan yi ban iya ba, sai yau na kunna turaren tsinke. Nayi wanka nayi kwalliya suma su Isiyaku na ce sujeisuyi wanka su dawo na ba su kudi na ce su sayi sosa da sabulu na mika masu kwalbar Vaseline din da, dama yake boye cikin kayana bana amfani da shi. Daidaddare ina idar da sallar Isha'i na dare kan gadon nayi kwanciyata gabana sai harbawa yake yi, Asabe ta shigo ta ganni kan uba' abinda ta fara fadi ke nan kafin taci gaba da cewa, ai kema kin san ba zai taba yiwuwa ba k ce za ki dawo da kwana a gado. Za ma ki fito da shimfidarki duk inda ki ka kaita ko kuma ki san nayi saboda ba za ki hau gadona ki matse ni ba. A lalace na kalleta na ce mata kuna da gado ne a gidan nan? Ai duk wani gado da yake cikin gidannan in ba ki sani.ba in gaya miki na Innata ne, na sake kallonta na ce ina ce wannan ne ki ke cewa naki? Kan ta bani amsa na ce mata ba ki da kyau ba, don kuwa wannan gadona ne da na gada a wurin mahaifiyata, kin kuma san kayanta ba zai zamo na baitilmal ba, tunda tana da magada. Kace-nacen da muka fara yasa Babah Lantana fitowa tana tambayar Asabe menene? Ta tsaya 49 tana yi mata bayani, nima ina daga kwance ina mita tare da kunkunin da ake iya jiwowa. Haka kawai ni da gidan ubana an zo an takura min, in gaskiya ne abinda ake fadan kowa yaje gidan ubanshi ya zauna mana, wannan gadona ne da uwata ta mutu ta bar min a ka zalunce ni aka kwace min shi a ka maida ni kwanciyar kasa ba kuma zan sake yarda da hakan ba, sai dai duk abinda za ayi ayi amma ba zan sauka a kai ba." To ai sai ki gyara ku kwanta tare ko? Na ce a'a ba mai sake hawa min kai ai bata da gadonta balle ta ce ana ta kason take hawa, Hankalin Babah Lantana yayi matukar tashi, bata saba ganin ina yi mata rashin mutunci irin wannan ba, wata kila kuma bata taba zaton irin wannan ranar zai zo ba. Ni ki ke gayawa wadannan maganganun? Na ce oho, ni dai na gode ina da uba kowa ya san shi dangin uban ne kawai bani da su, yana kuma sona tunda ko unguwa bai barina in je balle yaje ga bada rikona wurin wadan su in je ina zama agola, sai dai a kai mishi karata ya yi min duka amma ba ya tura ni gidan wasu da sunan riko ba. Da sauri Babah Lantana ta juya wurin Babana da ta bari a daki tana yi mishi magana irin wacce ta saba, wato kana jin rashin kunyar da 'yar iskar 50 yar nan taka take yi wa mutane: amma kaja bakinka kayi shiru, kayi wani shememe a kwance kamar gawar sababi ko? To tashi ka bani wuri don a kan ka abin'zai kare tunda kai ne ka rasa abinda zaka haifa a duniya sai tyar iska. Tashi ka gani in sauke katifar inibáiwa Asabe ita kai ka san nayi, don ba zai yiwu,ita tana gado Asabe tana kasa'ba. Ina jin haka nayi maza na yiwo waje don nasan abu ne mai sauki Babana ya sauka a gadou Babah Lantana ta dauki katifar ta baiwa Asabe ita. Dakin na shiga na kara kallon katifar da Baban nawa ke kwance a kai sai da na fito tsakar gida sai na ce mata, Babah in dai wannan katifar ce to ba taki ba ce ta Innata ce, don haka ko kin fito da ita zan karbeta. Shiru tayi bata tanka min ba, ina shiga dakina na gane hikimar da Babah Lantana tayi min saboda ganin Asabe da nayi kan gadon a kwance ta babbake ko'ina. Ki bani gadona na fadi hakan tare da kokarin janye katifar da ke kan gadon ban san yanda a ka yi ba sai ganina kawai nayi muna wani irin dambe ni da Asabe, danbe mai tsanani irin nà kwatar kai. 51 "Dake ta Asabe, bugi ja'ira kar kiyi mata da wasa. Abinda Babah Lantana ke gaya mata ke nan. Sallau ya dogara sandarshi da yake dindingisawa ya fito daga dakinshi kwanaki tara da yin abin har lokacin bai gama warkewa ba. Babah kenan, za ki kara ba Mama? Iyaye suna yiwa ya'ya tattalin abin arziki suna gudarwa ya'yansu fitina amma ke kullum cikinta ki ke jefa su. Babah Lantana tayi maza ta juya gare shi ta kafa mishi wani gigitaccen mari kau! Tanfar ba shi ta gaurawa irin wannan marin ba, bai motsa ba daga yanayin da yake, ni kam ko sau nawa za ki maren ai zan gaya miki gaskiya tunda dai an ce min uwa ta kwarai tana yarda da shawarar ya'yanta matukar su din sun kai munzali na mallakar hankali. Ke Asabe in kin yarda ki bar fadan nan, fada ne fa na rashin gaskiya yarinya tana zaune a gidan ubanta mun zo mun kankane komai ai da gaske ne kowa a nuna mishi gidan ubanshi mu tafi mana. Sallau ne yasa sandarshi ya raba tsakanina da Asabe muka rabu da yake daga ni har ita babu wanda yaji alama na dukanmu muna son rabon da a ka yin sai dai hakan bai sa na yarda da mu kwana 52 mu biyu a kan gadona ba, bałe aje ana fito da katifar Babana a bata shi a bar shi a kan wayar gado. Duk abinda ke.faruwa Babana yana daki yana jin komai amma bai ce uffan ba, har a' ka yi aka gama ina jin ko shi. ne abinda yafi 6atawa Babah Lantana rai ta shiga-daki ta figo gýalenta ta fito tana fadin zo Asabe. fito nan yau, kam in kai ki gidan uban nan naki da kullum:a ke yi min gorinshi. Ta tasa ta a gaba suka fita suka bar gidan, naje na kulle kofar gida nazo na ihau gadon.na/kwanta, tausayin Babana yayi matukar kama ni, babu abinda yafi komai tsayawa a raina irin kifin nan da Babah Lantana ta jefawa laya abaki ta daure: da zaren ilo tasa a ka je aka jefa a rafi, awai yan uwanshi su cinye shi a haka. Zuciyata ta raya min acewar wata kila yi tayi don ta daure bakin Babana komai tayi kar ya ce mata komai, tunda ga skir a yariza ko ne, za'ayi a gabanshi ba zai bude bakinshi ya ce don me ba? To amma yayi ta zama a haka ke nana? Wannan shi ne abinda yafi komai damuna. A haka har gari ya.waye na tashi nayi sallah naje na gaida Babana, na kama hidimomin gida na Byara gidan tsaf lungu-lungu duk inda ya dade ba 53 a gyara ba ma na gyara shi komai yayi tsaf Babana ya fito daga daki yasa hannu ya dauki kwandonshi, kasuwa yake nufin tafiya, nayi maza na' 'ce mishi "Lah, Baba har za ka tafi kasuwar ba ka karya ba?" Cikin' natsuwa ya kalle ni ya ce min da wani abu ne a gidan? Na ce mishi eh Baba, ya ce min to ya nemi wuri ya zauna a kan shimfidar tabarmar shi na kawo mishi lafiyayyan abin karyawa ya karya abinda ya dade bai samu hakan ba don tuni Babah Lantana ta daina ba shi abin karyawa yaron nan ba yana nana a ciki ba? Na ce eh Baba, ya ce to ba shi mana ko babu ne in rage mishi a nan? Na ce akwai na diba naje na kaiwa Sallau na dawo na zauna a gefenshi, gabana ya fadi, ganin yadda wuyan rigarshi tayi dikin- dikin. Baba wannan rigar taka ai tayi datti ka canza wata mana, ya sunkuyar da kanshi ga rigar alamar yana kara dubata, ai duk rigunan nawa masu datti ne, na ce to bani in wake maka su. Ya ce To kafin .ya sake cewa ko ki bari sai gobe saboda sabulu. Na ce bani kawai Baba akwai sabulu, ya ce to. Isiyaku ne ya wanke min kayan ya goge su inaa kallon yanda suka tsufa suka zama 'yan fake-fake saboda jin jiki yayinda zuciyata ke tuna min da 54 dadewan da nayi ban ga Babana da sabon dinki ba ko da kuwa da sallah ne. Komai nashi a hanmun Babah Lantana yake, ita kuma bata da adaloin cewa shima ya yi wa kanshi don a gha mijinta fes ta kanta da 'ya'yanta kawai take yi ko ni ma da zaninshi nake jira in daura to da yanzu ta kai ma ba ni da na daurawa don tun sallar farko da Babah Lastana tayia gidanmu bata sake sawa an yi min sabon dinki ba Rannan a kicin nayi girkina ban je zaure ba, muka zauna tsakar gida muka yi hidimominmu na zuba a kwano na baiwa Ísiyaku ya kai wa Mansur, ni kuma na dauka da sauri naje na kaiwa Babana, na zauna na tsare mishi tumatirinshi ina yi mishi cinikin, yayinda shi kama ya koma dan lungu yaci abincinshi saboda Babana mutum ne mai kunya. A hanya ina rike da kwanon abincin da na kai mishin ina tunanin daga yau in dai zan yi girki to kuwa zan zuba in kai mishi sannan ba zan sake barin Babah Lantana da wankin shi ba, balle yaje yana yawo dikin-dikin. Yana dawowa da yamma naje na wanke bayangida na kai mishi ruwan wanka yayi ya fito na kawo mishi wankakkun kayan shi ya saka yana tayi min addu'a, naji dadi cikin raina har ina 55 tunanin ashe dai in ban da Babah Lantana da Babana bai canza min ba. Kwana uku da tafiyar Babah Lantana sai ga ta ta dawo, tsofaffin kawayenta suka dawo da ita, su Delu da sauran su. Suna kallona ina kallonsu ban ce musu kala ba sai gyada kai suke yi nuna alamar mamaki, in gumu ta gumu kuma su juya suyi kus- kus din su. Wata kila don a kaina suke maganar yasa suke yin kus-kus din don daga baya naji su suna cewa ai dan halal bai manta mafari, to ita Lantana da ta samu fili ta mike kafa sai ta ce babu shegiya sai ni, Ummm in banda dai hannunka bai rubewa yanke shi ka yar kuma Hausawa suka coe wai naka sai naka yaushe zan sake shiga wannan maganar? Ko ni cikin zuciyata na yarda da maganar Delu cewar da sa hannunta Babah Lantana ta samu yin abubuwan da ta yi wa Babana, don haka na kudurawa raina wannan karon ba zan taba yarda in ga za a sake yi mishi wani abin in zuba musu ido ba, sai dai ko suyi a boye amma ba kiri-kiri ba irin na da. Suka fito suka wuce ni a tsakar gida ina jin Delu tana fadin lalle wannan yarinya ta rike, ita kuwa Babah Lantana fadi take yi, ai ta wuce duk yanda ku ke zato, ni kuwa na bisu da kallo a 56 zuciyata na ce duk sun kode sun yamutse babu wata mai kyan gani a cikinsu in banda Babah Lantana saboda ba su sake samun wani mai tsautsayin a ka ba da zai kwashe su a matsayin aure ba. Washegari da safe na shiga kicin na koma can lungu ina aikina na bar wa Babah Lantana nata wurin da na tabbatar zał isheta, tana isowa sai taja ta tsaya daga waje, to fito ki bani wuri ko? Don ba zai yiwu in zauna ni da ke a ciki ba ga kuguna ga naki. Mai wuri yazo sai mai tabarma ya nade, nayi kamar ban ji ta ba, ina ci gaba da aikin da nake yi Ko ba ki ji ni ba ne? na ce ki dauki kayanki ki koma zaure ina ce dama a can ki ke aikinki? Na ce gaskiya ba zan rinka girki a zaure ba, bayan ga kicin a gidanmu, iye? Nayi shiru ko kallon in da take ban sake ba, to ba ri yazo ya raba wannan fitinar don na gaji da rashin kunyar da kike yi min ta ju ya ta tafi ni kuwa nayi girkina na zuba na zuba yanda na saba, naje na kaiwa Babana wurinshi na dawo da kwanukan sannan na zauna naci nawa yara ma suka ci nasu suka watse. Kwana biyu a jere Babah Lantana bata girki . bata baiwa Babana komai sai in ya fita tasan abinda taci ta baiwa Sallau, wai ba za ta sake yin 57 girkin ba sai ya raba rigimar da ya hada ya hana ni shiga kicin don yin komai tunda ai kicin na matar gida ne. Ni kuwa komai nayi in zuba da yawa in kai mishi ko mai fura da nono mai kyau na gani sai na saya na kai mishi ko ta lura ta gane bai samu matsalar da take so ya samu ba ne, tunda in dai don yayi magana tayi hakan ai tasan ba zai yi ba saboda ita tayi mishi wannan sanadin. A karin banza ga koma shiga kicin din tana yin girkin ga kuturin nawa ga natan. Gaba daya al'amura suka cakudewa Babah Lantana saboda ta gane kwata-kwata na daina tsoronta, ya' yanta da take sawa su azabtar da ni kuma ta gane ba zai yiwu ba saboda su dukansu sun tsorata da abinda ya samu Sallau. Rannan ina zaune a dakina sai ga Asabe ta dawo har da Jakarta da dah ta tafi da ita a kan za a kaita gidan ubanta ita ma. Ina ganin ta na daga hannayena duka biyu sama na ce Ubangiji na gode maka da kasa uwata ta haife ni tare da ubana da ka jarrabe ni da maraici ma ba ka jarrabe ni da na uban ba sai ka rufa mion asiri ka zaunar da ni tare dashi. Ka kuma sa shi ya so ni bai ta6a yarda da shawarar mugaye na ya bada rikona ga wasu ba, 58 na shafa a fuskata. na gyara zamana a bakin gadona. Da wa ki ke wadannan maganganun? Tayi tambayar a fusace na ce da wanda ya tsargu tunda ni dai ban ambaci sunan kowa ba, ina zaune a gidan ubana kuma to ai babu wanda ya isa ya hana ni 'yancin yin magana, haka kawai in mutum yaga abinda nake yi ban yi mishi ba to kowa yaje gidan ubanshi mana. In da gaskiya cikin lamazin ai cewa aka yi kije a kai ki wurin naki. don ki huta gorin da ake yi miki to sai kuma ki dawo mana yau? An dawo din sai kiyi abinda za ki yi na ce babu abinda zan yi sai gori babu kuma mai hana ni. Muna cikin haka sai ga Isiyaku ya shigo da saurinshi, murmushi yake tayi alamar yana cikin farin ciki, na kalle shi na taya shi murmushin dona in zolaye shi, na ce mishi yaya na gan ka da jallabiya har da bagaruwa da dabino, ko makwabcinku Alhaji Madugu ya dawo ne? Yaja wani mummunan tsaki kafin ya ce na rantse Anti Mero da gangan kike yi, Alhaji Madugu da ko katangar gidanshi bai yarda taba ba shi ne zai dawo Umra ya bimu da tsaraba irin wannan? Yaya Mubarak ne wajen mu goma ya Daiwa ya shiga lissafa min yaran na gidaje daban- 59 daban, na ce Ubangiji ya karba musu badar da suka yiwo, addu'o'in da suka yi mana ya karba mana ya ce amin. Dadi mai yawa ne ya kama ni don kuwa ba karamin kewar Mubarak nayi ba, dan sauki-saukin abin ma shi ne Mansur ya rage min kewar tashi da ba karamar waiala nasha ba. Za ka share zauren nan ne? Isiyaku yayi murmushi cikin yanayin nokewa, gaskiya kiyi hakuri Anti Mero gida zani inyi wanka, in sa kayana zan je in raka Yaya Mubarak sallar Juma'a, na ce to babu laifi sai kun dawo. Na koma daki na zaro tsintsiyar zaburi na nufi zaure don in kara kalelece zauren saboda in yazo ya samu wurin cikin tsabta tunda nasan saukowa daga Masallaci nan zai zo. Ina sharar zauren ina lissafin rabon Mubarak da gida a zuciya, na ce kwana ashirin da uku daidai, kwanakin sun tafi da yawa al'amura masu dama sun faru a bayanshi ga shi dama mun dade babu wata mu'amallah a tsakaninmu tun kafin tafiyarshi hidimar kasa, ko da dai shi ba mai hira ba ne balle in ce zamu baiwa juna labarai masu yawa. Ni kam zan yi kokari in koyi ba shi labarin abubuwan da aka yi baya nan, ina cikin haka sai kawai naga wata gabjejiyar kafa ta tako cikin 60 zauren, in daga ido don ganin mai kafar bakon Babah Lantana na gani yau ma ya dawo, ko me ya kawo shi kuma oho? Wani lallaus an faffadan murmushin da ya sake bayyanar min da hakoran gwal dinshi yayi min, nan da nan kuma ya sake kifta min ido wai signal yake yi min, nai maza na sake banka mishi wata irin uban harara kamar dai yanda muka yi da shi wancan karon. Ya wuce cikin gidan ya bar ni ina tunanin maza suna tafiya Masallaci don yin sallar Juma'a shi kuma ya shigo gidan mata zai zo ya nade kafa yayi ta zuba zance. "Me ya kawo ka gidannan yau kuma? Tayi mishi tambayar bayan ta mike tsaye ta tsura mishi idanuwanta tana kallonsa, "Kai ke kam Hajiya Lantana ba ki iya karbar bako ba, to alheri nazo miki da shi." "Ai ba ka da shi ne ko ka ambace shi an ganshi a farko to sai ka biyo bayanshi da wani sharri." To babu laifi, duk abinda ki ka ga dama ki gaya min ni naga abin ki nasa rai a kai." Ya gyara zama kan tabarmar mishi, na shigo gidan da nufin wucewa in je in yi wanka, idona ya kai kan sunkin kudin da ya tura mata tare da fadin "Ungo wannan rike naki ne ki da ta shimfida 61 Soma taba su, in maganar da na zo miki da ita ta samu karbuwa a wurinki to wannan din ba komai ba ne illa somin-tabin alherin da za ki samu a wurina" Ta zuba mishi ido tana kallonshi ba tare da ta taba kudin ba, ai sai kayi min bayani naji in da zancen naka ya dosa, sannan in naga za su ciwo in taba, ai babu abinda ban sani ba a hali irin naka baka fidda kwabo matukar ba ka hango yanda za' ayi ya jawo maka sisi su zo tare ba." Na shiga wankananabar su suna maganganunsu ban jin abinda suke fadi saboda bayan gidan a lungu ne na kuma rufo kofa, wanka mai kyau sosai na tsaya nayi saboda a yau ina matukar dokin saduwata da Mubarak. A wannan lokacin na riga na zama budurwa na kai munzalin yan matancin sosai nayi sha shida da yawan mutane musamman Mansur sunan da suke kirana kenan yanmata, ban san dalili ba sai pake jin zuciyata ta soma so da begen kalmomi masu dadi tsakanina da wanda nake ganin ya dace yayi min hakan. Ko da dai shi Mubarak bai taba furta min wata magana ko nuna wata alama ta gane na kawo wannan lokacin ba, a wannan lokacin ina ganin zai 62 gane hakan ko daga irin tarbar da nake shirin yi mishi. Kullum a Makaranta kawayena ba su da wata hira wadda ta wuce ta samarinsu da irin kalamansu masu dadin ji da sanyaya zuciya, amma ni ba ni da mai furta min irin wadannan kalaman, dan dama- dama ma Mansur. Ga shi kuma kusan kowa ya ganni zai yaba kyakkyawar halittar da aka yi min gani da tsabta gani da gyara, ga ni da ado daidai gwargwado ga shi kuma a wannan lokacin auren yara kan faro ne daga sha biyu sha uku sha hudu in ta dan yi tsayi sha biyar ko mu abinda yasa muka kai sha shida ba a damu ba don muna Makaranta ne, amma shiru ba ni da kowa. Na fito daga wanka daidai Nalami ya fito da Wasu soyayyun kaji daga cikin wata leda da ya shigo gidan da ita, gashi nan komai dan kankantanshi. Yana ganina sai ya canza maganar yana fadin da hannuna na soya miki ita don dai kiji-kiji dadi ki tuna da girkin maza, ban sake kallonsu ba na wuce na bar Babah Lantana ta fara yagar wata cinya tana ci. Kwalliya sosai nayi na sanya kayana, maimakon ma in zauna a cikin gidan sai kawai na fito zaure na zauna ina sauraron isowarsu, ana 63 cikin haka sai ga Mansur ya shigo da dardumarshi a hannunshi alamar ya dawo ne daga Masallaci. "Barka da Juma'a. na daga ido na kalle shi nayi murmushi har an sauko? Ya taya ni murmushin an sauko ranki ya dade, na sunkuyaar da kaina kasa ban cika son kana kirana da irin wadannan sunayen ba, kana sa ni ina jin wani iri. Yayi maza ya tsuguna a gabana ya zuba min ido yana kallona, me za ki ji don nayi miki addu'ar ranki ya dade? Ai bar ni kawai in ce miki ranki ya daden, ko na dan ji sanyi a raina, kin san yanda ki ke a'wurina kuwa? Ai kallonki nake tamfar wata tauraruwa in ban da kin takura ni kin hana bakina furta miki kalmomin da yake son furta miki da kin sha magana. Tsuke fuskar da nayi yasa shi yin maza ya canza maganar da tambayata, amma dai kwalliyar nan da ki ka yi ba unguwa za ki ba na zo na tsare ki da magana? Nayi maza na ce mishi a'a, cikin zuciyata kuwa fadi nake yi ina son jin irin wadannan kalaman amma ba daga bakinka ba. kwalliyar taki ce na ganta ta zama ta To ai kwalliyar taki ce na ganta ta zama ta musamman ta bambanta da irin kwalliyar da ki ka saba yi kullum wannan din tana da wani abin da take nufi ta kara miki kyau tasa ki kin zama 64 budurwa ta sosai-sosai da ganinki kuma an san ke din babbar yarinya ce mai daraja taimake ni ki gaya min gaskiya kwalliyar nan saboda wa ki ka yi ta? Kalamanshi suka yi dalilin da na ce mishi saboda kai, yayi maza ya ce ke bari zance Maryamu, kar, ki zuga' abin nan da ba a fadan sunanta ta hau kaya donni ki ka yi? Na ce, uhh, don in ganki in ji dadi? Na sake cewa uhh. Sai naji ya ce, To in dai donni ki ka yi da gaske don in gan ki in ji dadi saboda kina tattalin farin cikina to bani izini kawai in je gida in shaidawa Babana don yazo wurin Mahaifinki ya gabatar da zancena a wurinshi. Maganar tashi ta firgita ni ba abinda nayi zaton zai fito-daga bakinshi kenan ba, don haka na dago ido da nufin kallonshi, kafin in san irin amsar da zan ba shi, abin mamaki Mubarak na gani tsaye a bayan nashi cikin wani irin yanayi, ga dai kwalliya ta burgewa' yayi amma kuma fuskarshi takai matuka wajen daurewa alamar bacin rai mai yawa a tare dashi. Gabana yayi matukar faduwa, na firgita da ganin nashi nayi maza na sunkuyar da kaina kasa, ban san yanda a ka yi ya shigo cikin zauren ban ji motsinshi ba. 65 Ban san me Mansur ya gani ba da yayi dalilin da ya waiwaya cikin sauri, ganin Mubarak a tsaye bayan nashi ya sa shi hanzarin mikewa tsaye tare da mika mishi hannu. "Assalamu alaikum, barka da dawowa." Suka vi musabaha bai sake tsayawa ba ya wuce ya tafi Kusan minti biyu zuwa uku Mubarak yana tsaye kallcza kawai yake yi, ba tare da ya ce uffan ba jikina sai rawa yake yi, ji na nake tanfar na aikata wani zunubi. Cikin zuciyata sai tunani nake yi in ya tambaye ni me zan ce mishi? Ina cikin wannan zullumin ne sai kawai naga ya juya ya tafi ba tare da ya ce min komai ba, tafiyar tashi a sani cikin wani irin yanayi da na kasa jin dadin raina, jimawa can dai na wartsake na ce oho. Na mike na nade tabarmata a nufi cikin gida, har lokacin Babah Lantana tana ta da bakonta, sai dai ga alama sallama suke yi saboda na ! shi yana cewa, to sai yanda ta yiwu, ko me a ke ciki zan turo in ji bayani, ko kuma in zo da kaina, ta ce to duk wanda a ka yi. Nayi mamaki a raina yanda a ka yi bhirar tasu ta kasance sabanin ta ranar da ya fara zuwa gidan. Ina kwance a kan gadona zuciyata ta ca takai kawo cikin sake-saken al'amura, naji wani mai 66 sayen kwalla yana tambayar akwai kwalla ko tangaran ko tasoshi? Da sauri naji Babah Lantana tana cewa babu sai gado mai rumfa in kuna saye, yayi maza ya ce muna saye mana, ai mu duk wani abinda zamu samu amfani a kanshi saye muke yi. Nayi maza na mike a tsakiyar gadon don ganin gado mai rumfar da Babah Lantana ke shirin gado mai runfar da Babah Lantana ke shirin sayarwa tunda naji ta ce ya shigo. Ina daga zaunen najiwo ta tana kakkarya gadon Innata, Asabe tana tayata, 'wannan gadon ma ai tuni ya kamata in rabu da shi in canza na bari har wannan shegiyar ta zo tana yiwa mutane goshinshi. Ba ma a yayinshi fa Babah, ta ce ch ai in suka saya kauye suke kaiwa ko kuma su yankę shi su maida shi na familin mai Rarfe. Sai da suka fitar da shi zaure suka soma cinikinshi sannan nabi baya na kalli mai sayen nace mishi, kai Mallam gadon ba na sayarwa ba ne, mai gado ya kalle ni ya kalli Babah Lantana ya dan yi turus alamar rudewa. To ko dai tayin da aka yin ne bai yi miki ba? Babah Lantana ta ce, yau naga fitina, kai Mallam ba ni kudina ka ji na sallama maka. Na ce in ka saya ma banza ka saya gadona ne da na gada a 67 wurin Mahaifiyata, ban saida shi ba kuma ai babu mai sayar da shi ko kuwa? Yayi maza ya gyada kai tare da fadin in dai haka ne kam babu shi na ce a to, na leka na kira wani yaro na ce mishi gudu kaje ka kira min Isiyaku, yaron ya tafi da gudu, ni kuma naja na tsaya a Rofar gida ina kunkuni, to an zo da gado gidanmu ne balle a jawo gado a ce za a sayar ayi canji? To ku sasanta dai sai mai gadon ta gaya mnin kudin gadon in biya, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi amma ai nace maka ba na sayarwa ba ne za ka bar wurin nan ko sai na kira yaran can sun rakaka? Sum-sum ya kama banva ya bar wurin. Babah Lantana tayi kwafa ta kama gado zata mayar ciki na ce a'a ai tunda ya uto ba zai koma ba a zo a sayar da shi bana nan, katifar ma don dai ba zan bar Babana ya kwanta a kasa ba ne da na shiga na fito da ita na hada su. Ai sai ki fito da itan kawai ta ju ya ta shiga gida Isiyaku ya iso na ba shi gadon na ce ya hadu da yara su kaui shi gidan Yaya Dijah. A wannan lokacin ne Babah Lantana ta rasa yanda za ta yi da ni a dake dai ba zai yiwt ba in zagi ne ba zai gamsar da ita ba, tunda nima nayi rikan da bana rama zagin amma ina komawa gefe 68 in yi kunkunan da bata jin abinda nake fada wanda nasan yafi komai bata mata rai. Ga shi ta fito da gado da niyyar sayarwa ta karbi kudin wai-ita zata yi canji na kwace gadon na tura wa Yaya Dijah: shi babu kuma yanda zata yi dani, ina jin ta tana rattabawa Babana bayani na karya da na gaskiya don dai ta samun ya sa baki cikin maganar bai ce mata komai ba. Takaicinshi ya kama ta, ta kalle shi cikin yanayin bacin rai tare.da jan tsaki kai kam ai gaya maka magana ma ba ta da wani. amfani sai ayi a gama kana ji ba za ka ce komai ba, kayi wani gum da baki kamar na mai cin najasa. Bai ce komai ba nima ban ce tha cikin zuciyata dai ccwa nayi in ma kin yi ne don ki:cuci wani to kanki zai koma. Ban sani ba ko takaicin labiane yake yawan damunta ko kuma ta mantá ne:cewar dasa hannunta: cikin shirun na Babaha yasa naji ta tana mita ita kadai' a dakinta, a ce maigida duk abinda aka yi a gidanshi ba zai ce komai ba, sai yayi gum da bakinshi kamar na mai bubu? To ina zance? A hankali na buda baki na ce babu, sai dai nasan bata ji ni ba. Tsaraba mai daraja sosai Mubarak ya aiko min da itya, sai dai hakan bai sa da muka gamu da shi a 69 hanya na daga ido na kalle shi ba, balle in je ina kula shi saboda na gaji da yanda yake tafiyar da ni ba kuma zan lamunci miskilanci da jan aji irin nashi ba. A wannan lokacin mu'amallata da Ahmad Mubarak sai ta kara ja baya sosai mafi yawancin lokaci ko yana dan murmushi ya ganni daure fuska yake yi, ko yayi kamar bai ganni ba, nima bana kallonshi in ba a kan kuskure ba. In na san yana gida ma bana zuwa sai in bari sai baya nan in yi maza in je in gaida Umma in dama abin da zan yi mata ma in yi mata ina ganin ya dawo zan yi maza iu îta in bar gidan. Umma da kanta ta ganc mun yi 'yar tsama ni dashi don sau biyu tana tambayata ni me ke faruwa ne tsakaninki da Ahmad Muuarak Maryamu? Ina jin ta soma irin wadannan tambaycin sai kawai in gudu in barta. Sai dai irin wannan zaman da muke yi da shi bai sa ya canza komai ba na daga abubuwan da ya saba yi min kowane lokaci a cikin yi min aike yake, kayayyakin bukatar rayuwa irin su mai, sabulai, na wanka da wanki, under wears, audugar al 'ada, kudi babu abinda ba ya baiwa Isiyaku ya kawo min. 70 Ana cikin haka watan Azumin Ramadan ya iso, don dama su Mubarak sun yi umrarsu ne a watan Rajab, Isiyaku ya turo yazo ya tambaye ni me da me nake so a kawo min? na ce yaje ya gaya mishi bana bukatar komai har cikin zuciyata ban jina kamar ina bukatar wani abu nashi a wannan lokacin tunda abinda nake so yayi min bai yi ba abinda nake nema a wurinshi ban samu ba. Babu wata alama kuma da take nuna zan samu yanda nake so din a wurinshi, to ana me zai yi ta hidima yana ta dawainiya dani bayan shi ba sona yake yi irin son da nake yi mishi ba, in taimakona wake yi don kyakkyawar mu'amallar da yayi da Innata a shekarunsbi na kuruciya to ya kyautata ya taimake ni a bayanta har na kawo munzalin da nake ciki & yanzu. Don haka na gode ya bari haka, in don tausayi ne ma dai to na gode yanzu nayi girman da shi bai lura ya gane ba, don haka ya bar ni kawai in ci gaba ni kadai in ma wahalar ce in shata kawai. A yanzu abinda nake so ya so ni ne kawai irin son da nake yi mishi, soyayyar da zata rikida ta zama ta 8ure, aroma ba kullum a ji tausayina ba. A duk lokacin da irin wadannan abubuwan suka dawo a cikin raina zama nake yi in yi ta kuka 71 wani irin kukan da sai nayi na gaji kawai nake yin shiru. Ban san dalili ba cikin zuciyata babu abinda nake so irin aure, ban sani ba kowace yarinya ta kevo munzalin da nake abinda take ji ke nan ko kuwa ni don ina tare da Babah Lantana ne? matar da kuliu:burinta ta cutar da ni ne in kaga bata yi min hakan ba to abin ya gagara ne kawai. Sannan kullum hirar kawayena ke nan samarinsu da ranar aurensu, sai na samu kaina nima a irin wannan yanayi da matsayin sai dai kuma na kasa sakin zucivata in so wani ban da jin dadin wata magana in dai a hakin wani ta fito ta in da nake so ta fito din kuma abin ya gagara, to ya fita mana ko zan samu in saba da wasu irin sabon da nayi da shi in so su irin son da uake yi mishi ko na rinka jin dadin kalamansu. Gaya mishin da aka yi bana bukatar komai shi ne yayi dalilin da ya gangaro da kanshi yazo har kofar gidanmu sai dai yau ma cikin rashin sa'a tare da Mansur din yazo ya same ni, sai dai maimakon ya juya ya tafi bayan tafiyar Mansur din kamar yanda yayi wancan karon tsayawa yayi ya tsare ni da ido yana kallona, yayinda ni kuma na sunkuyar da kaina kasa nayi kamar ban san da tsayuwar tashi ba 72 Ni me ke tsakaninki da wannan ne? a hankal1 na ce wa'? Yayi shiru ya ci gaba da kallona ba tare da ya sake cewa komai ba, saboda sanin da yayi nasan wa yake nufi, na mike tsaye a hankali cikin natsuwa tare da karkade jikina a sakamakon zaman dirshan din da nayi a kasa sanda nake hirar. Cikin natsuwa na kalle shi na ce Mubarak, ya ce uhh, ya amsa ba tare da ya buda bakinshi ba watakila bai ji dadin yanayin da na ambaci sunan nashi a ciki ba. Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi yau ne ka ga ya dace ka tambaye ni abinda ke tsakanina da Mansur? Ya sake cewa uhhm, ba tare da na dago ido na kalle shi ba, nace to ai ka makara, na juya na shiga gida na bar shi a wurin yana tsaye. Na hau gadona na zauna a dalilin na kasa kwanciya jikina sai faman bari yake yi, yayinda Zuciyata ke ta faman harbawa a dalilin sanin da nayi na batawa Mubarak rai. Hankalina yayi matukar tashi na kasa jin dadin al'amarina. Tsawon lokacin ina cikin wannan hali kafin naji zuciyata tana rarrashina tana bani hakuri kalamai masu karfi take gaya min, ya zama dole in zama jaruma a kan lamarinshi in har ni kadai ce na 73 ke sonshi shi tausayina yake ji to ya tafi ya bani wuri mana kawai ya gani ko ba zan rayu ba. Ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni tare da masu sona irin son da nake bukatar ayi min a yanzu, ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni in yi harkokin rayuwata menene na tsare ni da tambayoyi? Na mike cikin kuzari saboda jin da nayi zuciyata ta gamsu da abinda na aikatan naje na debi ruwan sanyi nayi wanka na dawo na zauna goge jikina ina shafe shi da man shafawa na 10.0-6 man da Mubarak ya saban min da shafawa. Wani abin takaicin shi ne duk wani abinda ke kewaye dani shi ne don haka na tsayar ma raina da cewar cikin matakan da zan dauka na kamewa daga gare shi har da daina yarda da hidimomin da yake yi min. Ina cikin wannan halin sai ga Isiyaku ya shigo dauke da wani katon kwali shake da kayayyakin amfani na hidimar Azumi, ba zan iya cewa a mayar mishi ba don kuwa yana da girma da kima a wurina. Na karba na ajiye, Mansur ma ya kawo min nashi na sake hadawa daga gidan Yaya Dijah ma ta aiko da sako guda biyu, na Babana da nawa. Ina jin Babah Lantana tana gayawa Baba wai in ban da kar ta ce ya mayar wa Yaya Dijah da kayan kamun 74 AZumin da ta kawo mishi ace bata kyauta ba da ta fada don kuwa ba a kan son ranta ta bada nashin ba, tunda abinda ta bashin bai kai wanda ta ba ni yawa ba. A watan Azumin kullum na kan shiga gidan su Mubarak ne da safe in je in gaida Umma in kuma rike mata Alkur'aninta muje wajen jin Wa'azin Tafsir din da ake yi a babban Masallacin Juma'armu in a ka tashi sai na rakata gida kafin in zo gidanmu in yi alwala in yi sallah, in hau gadona in kwanta in yi bacci. Ba na farkawa sai karfe uku da rabi, sai in yi wanka in yi alwala in yi sallar La'asar in kama shirye-shiryen abin buda bakina wanda nake yi da dan dama don bani kadai ba ce, 'yan Almajiraina guda biyu da muka yi matukar sabo sai Isiyaku da Mansur da kuma Babana da kullum nake daidaitan dawowanshi daga wurin Tafsir tunda na dare yake zuwa in ba shi abinda nayi ya zauna yana ci, ni kuma ina gefe ina jiranshi sai ya gama in karbi kwanon ya wuce ya shiga gida kafin in bi bayanshi. A haka har Azumin yazo karshe muka shiga kwanaki goma mafiya daraja kwanakin neman daren Lailatul Kadri daren da AIkur'ani mai 75 girma ya ba mu labarin cewa darajarshi tafi ta watanni dubu, haka alkairorin da ke cikinshi. Ubangiji yasa mu dace, kullum abinda Umma ke fadi ke nan in taji Mallam yana ta nanata fadin alherin daren 'Lailatul kadri ni kuwa sai in ce mata anmin Umma. A wannan lokacin zan iya cewa ban taba samun kaina cikin hali na kunci da farin ciki lokaci daya ba irin wannan karon, ina cikin farin ciki saboda alkhairori da suke ta zuwa min daga wurare daban-daban. Kusan kullum gari ya waye sai an zo min da sako na kayan sallah daga wani wuri. Yakumbo Halima da ba wani karfi ne da ita ba ma atamfa 'yar Holland ta dinka min a dalilin wai na zama budurwa, Yaya Dijah tsalelen leshi gami da takalmi da Jaka da gyale. Umma atamfa da leshe itama da takalmi da Jaka da gyale mahadin takalmin duk da dai tace wai da kudin bankina ta saya min amma dai nasan alherin Umma bai kwatantuwa a wurina. Mansur yayi min kala biyu masu kyau shima tare da takalmi da Jaka tare da gyale, sai kuma a ka kawo min na Mubarak, Isiyaku ya aiko ya kawo min. Na zauna ina kallonsu suma kala biyun ne sal dai shi komai nashi daban ne da na saura, bai taba 76 mancewa da wani abu ba in dai har aiken zai yi min yadika ne masu kyau masu laushi kala biyu mai ruwan madara da kuma baki na rike su a hannuna ina kallonsu ruwan da suke yi ya kara tabbatar min da darajarsu. An yi musu adon zare a wuyansu kalan zaren ya dace da kalan takalma guda biyu da ya saka a cikin kayan kenan kowanne da mahadinshi gyale biyu sai kayan shafa da under wears ga kuma wani dan karamin akwati mai dauke da wata 'yar sarka mai dan madaidaicin 'yan kunne da zobe a wata yar takarda kuma wasu siraran wararai ne da agogo babu yanda za ayi a kushe hidimar Mubarak in dai zai yi ta matsalarshi guda daya ce ita ce ta ban san in da yasa gaba ba. Kuncin da nake ciki da takura kuma shi ne na tasa ni a gaba da Mansur yayi in bar shi ya tura iyayenshi wajen Babana magana ta wuce tsakanina da shi har yaje ya hada ni da Yakumbo Halima, ita kuma ta kira Yaya Dijah ta gaya mata cewar lalle ne ta gaya min in bar Mansur ya tura iyayenshi wajen Babana ayi maganar aurena in kuma ba shi nake so ba to in turo wanda nake son daga nan zuwa watan Sallah in har ba so mu nuna mata ba ita ta haife mu ba, amma ina amfanin wannan zaman da nake yi a gidanmu? 77 Shi karatun boko ai ba dole ba ne wurin 'ya mace, na Addini kuwa na same shi daidai gwargwado a gidan mijina ma kuma zan iya yi tunda neman sanin addini ne shi aure ai suturar 'ya mace ne. Yanda naga Yaya Dijah ta dauki maganar da karfi na tabbatar zai yi wuya a ce watan Sallah yazo ya wuce ba tare da an titsiye ni na fitar da mijin ba, to ya ya zan yi? Ba da sunan Mansur din zan yi shi da yake son a bada sunan nashi ko kuwa wata hikima zan yi da Mubarak zai san abin da nake ciki? Cikin hanzari na kawar da wannan tunanin saboda sanin da nayi cewar ba zan taba nuna mishi wani abu ya dame ni game da shi ba, ba zan taba karya 'yancina na kasancewata halitta mai daraja da Ubangiji ya karramata da kunya ba, wato halittar da aka yi min na zamowata 'mace Haba, mace ta rasa kunya? Ai kuwa dai tayi rashi mai girma, kalaman Yaya Dijah ke nan kunya ai adon 'ya mace ne, a bakin Umma na saba jin hakan, don haka na kara kudurawa raina babu wani abin da zai sa in nuna mishi wani abu in dai yaga ci gaba da yin shirun nashi yafi mishi to yaje yayi tayin shiru. 78 Aka wayi gari a gidanmu da ma sauran gidajen Musulmi na garuruwa daban-daban, hidimar sallah a ke yi, Jama'a sai kaiwa da kawowa suke yi cikin walwala da farin ciki ga dukkan alamu kuma an yi sallar ne cikin walwala da wadata. Tasa kayan sallar tawa nayi a gabana gaba dayansu ina binsu da kallo daya bayan daya, kafin zuwan sallar niyyata in sanya kayan da Yakumbo Halima tayi min ne ranar sallah don girmamawa a gareta, amma a yau da aka wayi gari ana hidimar sallar ga kuma kayan sallar tawa a gabana sai naji bazan iya kaucewa sanya daya daga cikin kayan sallar da Mubarak yayi min ba duk kuwa da niyyar da nake da ita ta daina mu'amalla da kayanshi. Duk da hakan sai na ce to tunda yanzu hidimar sallah a ke yi bari in bari bayan sallah na dauki wannan matakin amma yanzu bari in yi adon sallah kawai. Bakin yadin na sanya wanda jikinshi yafi kama da voil ko silk tasha ado irin na barnina a gaban rigar dan madaidaicin ado da yayi matukar kawata rigar ta zamo gwanin sha'awa, na sanya takalmi da gyale tare da Jaka da suka dace da kayan. Sannan na dauko 'yar sarkar da 'yan kunnena tana sanya ga kuma warwarai da agogo, in tsaya cewa nayi kyau ma bata baki ne kawai, na tsaya 79 gaban dogon yaron Innata da Babah Lantana ta fitar a dalilin hanata saida gadon da nayi na dauko shi na kawo dakin. Kallon kaina nake yi a cikin shi cikin zuciyata na tabbatar ban taba yin kyau irin na yau din ba, ko ba a gaya min ba kuwa dama nasan ni din mai kyau ce, don kuwa kowa ya ce da Innata nake kama Innata kuwa mata ce da ta rayu mutanen da suka santa suna ba da labarinta. Yau kam duk mishikilancin shi da taurin kanshi in ya ganni ba zai iya kame bakinshi yayi shiru ba, sai ya yabi kyan kwalliyata sai ya furta wata kalma da zata zamo mai karfi a tsakanina da shi. Ina tsaye a wurin ina kara feshe jikina da turare tare da kara kallon kaina a madubin Asabe ta shigo dakin tana zage-zage nayi kamar in tanka mata tunda nasan da ni take yi sai nayi maza na baiwa kaina shawarar kame bakina tare da hanzarta barın gidan don ba zai zamo mata komai ba ta rufe ni da dukan da zai yi dalilin da zata tumurmusa ni ta lalata min kwallioyar sallar tawa ba. Don haka nayi maza na yafa gyalena na kuma shuri takalmana nayi waje, gidan Umma na nufa zanje in yi mata barka da sallah daga nan taga kwalliyata. 80 Nayi maza na yamutsa fuska na ce, a'a Umma ni fa ba don kowa nake yi ba, tayi murmushi, au haka ne Maryamu kai wannan kayan sallah naki da kyau suke kai ji wata sarka kai kai kai, wa ya saya miki wannan sarka Mero? Na shiga dibi-dibi cikin sa'a ta sake tambayata, Dijah ce ko? Nayi maza na ce mata ch, lokacin ne na kara sanin darajar sarkar. Nabi umarnin Umma na shiga nayi wa Baba barka da sallah a falonshi na fito daidai Mubarak yana shigowa gidan ban daga ido na kalle shi ba balle in gane irin kwalliyar da yayi na dai san kawai na shaki kamshin turarenshi. Baba ya bani goron sallah, nayi maganar ina nuna mata kudin da ya banin, tayi godiya. Kai wannan kwalliya taki tayi kyau, bani plate guda biyu Umma zan ba wasu, zuciyata ta soma yin nauyi da na soma tunanin har uwarshi ta gane don shi nake yin abubuwa masu yawa amma shi bai gane ba, ko kuma ya gane ya ki nunawa saboda bai da bukatata. Babu wanda ya ganni bai yabi kwalliyata ba sai shi sai kokarin karbar waina yake yi wai wasu bakin sun kara zuwa mishi. 82 Iko sai Ubangiji, girman 'ya mace babu wuya ai duk in da budurwa takai kin kai Maryamu, kin kuma yi kyau irin wanda ba a zaton miki ba. Nayi murmushi na ce Umma kenan, na juya tare da cewa na tafi, da sauri ya biyo ni wata kila yayi zaton zan tsaya mishi ganin ban nuna alamar hakan ba ya sa shi fara yin magana ina za ki ne haka? Ban tanka mishi ba, da ke fa nake magana, na sake yin kamar ban ji shi ba, tafiyata kawai nake yi to tsaya mana ki ji maganar da zan gaya miki, cak naja na tsaya saboda abinda zuciyata ke raya min, ya biyo ki ne ya gaya miki wata muhimmiyar magana, zai yabi kwalliyarki ne wata kila ma yayi abin da zai fi hakan dadi a gare ki. Naja na tsaya ya iso ya same ni, maimakon in ji ya kama hanyar gaya min wata magana mai dadi sai naji ya fara jero min tambayoyi ina za ki ne haka? A hankali na ce mishi gida, to me za ki je kiyi a gidan da ki ke irin wannan saurin? Nayi shiru saboda ban ga kamar zan iya amsa irin wadannan tambayoyin ba. Muje in kai ki kiyi hoto, ban kalle shi ba na ce na daina yin hoto a daidai lokacin kuma na kama tafiyata cikin zuciyata ina tunanin bai iya komai ba sai sayayyan kaya mai kyau amma bai san yaga 83 kayan jikin wanda ya sayawa ya yaba kwalliyar da aka yi da su din ba, to ko meye amfanin sanya kayan nashi? Ina dosar kofar gidanmu na hango Mansur shi kuma yana fitowa daga zauren gidan namu ga alama nemana yaje yi daga in da ya hango ni ya saita kyamararshi ya soma daukana a hoto, kan mu gamu yayi min hotuna da dama. Muna gamuwa da shi ya soma furta min dadadan kalamanshi masu sanyaya zuciya da sanyata cikin wani hali na natsuwa da farin ciki. Alfarmarki nazo nema, ta me fa? Ya sake kallona cikin wani yanayi tanfar dai tsoro yake kar ya nemi alfarmar bai samu ba. Cikin natsuwa ya ce min gaishe-gaishen yan uwa da abokan arziki nake so in roke ki muje tare. Ba wani tsaya yin wani tunani ba na ce mishi muje, dadi ya kama shi don in kara mishi jin dadin kumá na sake ce mishi, jira ni ina zuwa, na wuce na nufi gidanmu da nufin in canza kayan jikina in sanya wanda yayi min. Cak! Naja na tsaya a cikin zaure ina sauraron maganar da nake ji tana fitowa daga bakin mutumin da zuwanshi gidan namu ya zama ka'ida in bai zo ba wannan satin to sati mai zuwa za ka 84 ganshi ya zo, a yanzu kuma har da tsaraba ya ke zuwa mata da shi Ba dai kin ce kin ba shi wadannan kajin yaci ba, ta ce eh, to ki gaya mishi kawai ba zai yi jayaiya da ke ba, cikin zuciyata na ce oh'oh shi kam Babana ko me a ke nema a wurinshi kumna yanzu oho? Sanin da nayi Mansur yana jirana shi ne abinda ya hana ni tsayawa in ji zancen nasu sOsai, na shiga gida kawai na wuce su na shiga dakina na canza kwalliyata cikin kayan da Mansur yayi min wanda suma suka yi matukar karbata. Na fito na same shi yana tsaye ni yake jira yana ganina ya saki wani lallausan murmushi, kin san kuwa al'amarinki yana bani mamaki, da sauri na tambaye shi mamakin, sai ya kalle ni ya ce min, to komai ki ka yi kyau ki ke yi Maryamu, komai ki ka sa yayi miki kyau ko kin taba sanin ke din daban ce da duk wata budurwa da ki ke gani? Ai ni a wurina da za ki bar ni da na yi wa kaina alfarma na daina kiranki da suna Maryamu in koma kiranki da sunan (Ta fi su) saboda ke din daban ce a cikin 'yanmata duka. Murmushi kawai nayi naje na shiga bayan motar da Mansur ya tanada don zuwa gaishe- gaishen yayin da shi da Isiyaku suke gaba. 85 Babu inda ba mu je ba har gidan Yaya Dijah da Jumare da Yakumbo Halima, shima ta bangarenshi mun je mun gaida tsohuwar Kakarshi ba mu dawo ba sai bayan La'asar. Ina fitowa daga cikin motar na hangi Mubarak a kofar gidansu ta wajen gidanmu yake fuskantowa abinda na tabbatar shi ne dawowana yake son gani. Yana hango nin kuwa na ganshi ya dunfaro gidanmu yana tahowa nayi maza na shige cikin zaure don kar ya same ni a waje. Ina shiga sai gashi ya shigo, sannu da zuwa nayi mishi gaisuwar duk da ba dabi'ata ba ce yinta bai 6ata lokacinshi wajen amsata ba. Me ke tsakaninki da Mansur? Abinda kawai ya bukaci sani kenan, na dan yi shiru saboda nauyinshi da nake ji, sai naji ya ce min kiyi magana mana, gaya min kawai ai gara in sani, me ke tsakaninki da shi? Cikin karfin hali da jarumtaka na bude bakina a hankali cikin natsuwa na ce mishi, saurayina ne, to da kyau! Abinda kawai ya fadi kenan ya juya ya fita. Ya bar ni tsaye a cikin zauren sai dai maimakon in wuce in shiga gida nima kasa motsawa nayi a wurin ban san dalili ba har kusan minti uku da fitan shi ina tsaye a inda ya bar ni. 86 Sunkuyar da kaina kasa nayi ina kallon faratun yatsuna can cikin zuciyata dai ba zan iya cewa ga takamaiman abinda nake tunani ba. Motsin da naji ne ya sani dagowa cikin sauri, Mubarak ne ya sake dawowa gabana yayi mummunan faduwa saboda yanayin da na gani a tare da shi, tsoro ya kama ni nan take naji jikina ya dauki rawa, dukana zai yi ko me? Bacin rai da ke fuskarshi ba mai tsanani ba ne, sai dai da ganin yanayin da ke tare da shi ka san ya shanye wani abu saboda yanda idanuwanshi suka canza launi. Me ki ka ce min yana tsakaninki da Mansur? Shiru nayi ban iya ce mishi komai ba, kiyi magana magana ki sake gaya min irin maganar da ki ka gaya min dazu. Wani shirun na sake yi ban tanka mishi ba. Ai ban san kin iya rashin kunya ba sai yau, kina nufin don kin koyi rashin kunya sai ya zama za ki ya cin fuskata kici mutuncina ki bata min, to ai ban san saurayinki ba ne shi yasa na bar ki kina hidimominki, to anma tunda ke da bakinki ki ka gaya min to ina so in sake ganinki da shi ki ga abinda zai faru. Ina so in sake ganinki da Mansur ko in ji labarin an ganku tare ki ga yanda zamu kare ni da 87 ke, mara kunya kawai, wacce ko wayo bata da shi, yana fadin hakan yayi shiru sai dai bai juya ya fita ba. Sake tsare ni yayi yana kallona wani irin kallo da ba zan iya tantance irinshi ba, saboda kainaa a sunkuye yake hawaye suna ta zubo min, yana kuma kallonsu amma bai sa shi tafiya ya kyale ni ba. Tun kwanaki ki ke nema kiyi min wulakanci me nayi miki? Me nayi miki da ki ke so sai kin bata min rai? Ki gaya min in laifi ne in baki hakuri in kuskure ne in gyara, amma ba zan lamunci, rainin hankali ba daga wurinki. Ya juya ya fita nima na lallaba na shiga gida na hau gadona na kwanta, kuka sosai na kama yi. Asabe tana kallona tun tana shiru har ta soma magana ita kadai, in dai namiji ne matsalarki ai kuwa ba ki yi kukan ba tukuna musamman ma wannan dan iskan da ki ka likewa mai kwashe- kwashen tsiya, ban dai tanka mata bá. Ban sani ba ko kashedin da Mubarak ya yi min ne ya tsorata ni na kasa sake fita tare da Mansur, ban iya sake zuwa ko ina ba sai dai kawai in yi kwalliyata in zauna a gida. A 'yan kwanakin da na zauna a gidan nan ne na gane Babana da Babah Lantana ba karamin 88 dasawa suke yi ba, ji da shi Babah Lantana take yi ba kadan ba, ko abinci zai ci sai ta zauna ta tasa shi a gaba yana ci tana kara mishi tana yi mishi wata hira mai dadi da zata sa shi ya ji natsuwa cikin zuciyarshi. A zuciyata na ce wato itama dai matar nan ta iya komai na kyautatawa raini ne kawai da wulakanci yasa bata yi, ko wanene ta samu yayi mata wa'azin da ta gyara halinta? Oho, tunda ko nima dai wannan sallar sau biyu tana zuba abinci a kwano tana bani, ban karba ba ta sake kawo min soyayyun kaji nan ma naki saboda zuciyata bata kwanta min kan in ci ba, amma duk da haka hakan da tayi yasa al'amura sun dan yi sanyi fiye da da. Kwana bakwai a ka yi Babana ya fara fita, Babah Lantanan ce kuwa ta ce babu in da za shi sai an kwana bakwai, ya zauna shima ya huta a cikin iyalinshi. Rannan ya fita ya dawo naji shi yana ce mata yau dai kasuwar ta dan yi nauyi ga abinda a ka samu, na kasa kunne in ji abinda zata ce mishi tunda kullum ya dawo ya ce mata babu kasuwa fada take kamawa tayi ta sababi tana fadin ya dai 6oye kudinne kawai amma wane irin rashin kasuwa bayan dazu ta wuce ta wurin taga yara sun kewaye shi suna sayen abubuwa? 89 Abin mamaki sai naji yau ta ce inishi to ai yau da gobe kenan, Mallam a ka ce wai kayan Ubangiji in babu kasuwa ai sai ka dawo gidanka ka hau sabon gadonka kayi kwanciyarka ka wataya. Ta soma zuba mishi abinci yana ci yayinda ni kuma can cikin zuciyata nake fadin to da haka ki ke yi mishi wa zai damu da rashin kirkinki balle har aje ana yi miki rashin kunya. Suna cikin hirarsu nima ina sha'anina a daki sai na jiwota tana tambayarshi, to in kirata ne ka gaya mata? Yayi shiru bai amsa ba, in ban da uh'uh din da na ji ya fada, don haka na kara kasa kunne wajen sauraron magana tasa sosai don na gane da ni a cikin zancen nata. To amma ai yau ne kayi alkawarin gaya mata, da safe ka ce a'a yanzu da yamma ka sake cewa uh'uh to me ka ke nufi? Ko za ka saba alkawari ne? Dattijo da saba alkawari? Ya sake yin shiru. Ai fa aikinka ke nan in ana magana da kai kayi gum da baki kamar wani mai cin najasa, taja wani mummunan tsaki alamar dai ranta ya soma 6aci, ko ma ya riga ya bacin, ai dama nasan karya ka ke yi ba za ka iya gaya mata ba ka ce za ka iya, abin bakin ciki wai uba yana tsoron 'yarshi. 90 To in ba za ka iya gaya mata ba ni in gaya mata tunda ni kam ai ba tsoronta nake ji ba yayi maza ya ce mata uh'uh to in kira maka ita? Yayi shiru ba ga ta can a daki ba? Kai Mallam kai kam ba ka da dattaku, kai tir!. Kalaman nata suka sanya ni naji wani iri, ga bakaken maganganun da take ta gayawa Babana ina ji, ban da haka kuma na tabbata ko wace irin magana Babah Lantana take son ya gaya min to ba mai sauki ba ce, kan haka sai naji maganganun nata sun sanya tsigar jikina yana tashi. Ban iya ci gaba da zaman da nake yi ba, mikewa nayi na fito nazo na durkusa a gabanshi cikin natsuwa da girmamawa na ce mish1 gaya min maganar da ta matsu in ji Baba, ko menene gaya min kawai zan iya dauka. Ai kai Mahaifina ne, kai ka rene ni ka kuma yi min duk alherin da uba ke yiwa da, na kuma godewa Ubangiji kana sona ba ka yarda ka bayar da rikona ga kowa ba, don haka babu wani dalili da zai sa ka rinka sa ranar gaya min wata magana kana dagawa tunda dai kasan dole ne zan ji ta to gaya min kawai zan fi jin sauki in na ji ta a bakinka maimakon a ce wani ne zai gaya min. A hankali ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min aure zan yi miki Yaacuwuna, na daga 91 ido na kalle shi, damuwa ce karara a fuskarshi ko ni da ya ce zai aurar ba tare da nasan mijin da yake nufin banin ba babu irin wannan damuwar a tare dani, tunda dai nasan a tsakanin biyu ne za a yi daya, ko a baiwa Mubarak ni ko Mansur, wanda duk aka yi da shi zan zauna tunda su dukansu ina da dalilan da za su sa ni zama da su. Na kawar da wannan tunanin daga zuciyata na daga ido na kalli Babana cikin natsuwa na ce mishi Baba wa ka ke nufin baiwa ni? Na dan sunkuyar da kaina kasa don kunya da girmamawa. Auren ai na zumunci ne, cikin hanzari na dago na kalle shi a zuciyata kuwa dadi ne ya kama ni, wato dama Baba yana sa ne da zumuncinshi da kullum ake yi mishi gori a kai, wato dama yayi niyya a kaina ne zai gyara zumuncin nashi ta hanyar bada aurena gare su? Ai kuwa dai duk wanda ya baiwa ni zan zauna da shi da zuciya daya in kuma yi mishi ladabi da biyayya irin na aure. Amma don in kara samun natsuwa cikin zuciyar tawa sai na tambaye shi cikin 'ya' yan wanka ne ko na kannenka za ka baiwa ni Baba? Sai da yayi gyaran murya saboda yanda ta make take nema kuma tayi rawa kafin ya iya ce min a'a wannan dan uwan uwar taki Lantana ma 92 zuwa gidan nan Mahammadu Nalami shi zan baiwa ke, don kara karfafa musu zumnuncinsu ai kin san abokin wasanta ne? Kadan ya rage in suma a tsugune saboda tsananin kaduwar da nayi. Nalami fa kace Baba? Ya gyada kai tare da cewa eh shi nace, ban san yanda a ka yi ba sai tsintar kaina nayi ina yiwa Babana tambayoyi. Zumuncin Babah Lantana yasa ka baiwa wannan mutumin ni naka zumuncin fa Baba? Shiru yayi yana kallona bakina ya sake yin subuta ya ce mishi, ba zan auri Nalami ba Baba, domin babu abinda ya hada ni da Babah Lantana balle zumuncinsu da har zan je ina auren danginta. Tuni na soma kuka ina fadin me nayi maka Baba? Me nayi maka da ka ke taimakon masu son ganin nayi bakin ciki a kaina? A gabana kayiwa Innata alkawarin ba za ka bada rikona ba ne saboda ba za ka iya rabuwa da ni ba to me yasa za ka bada aurena a inda kasan zan yi bakin ciki. Nan da nan kawai sai naji zuciyata tana raya min babu abinda yasa a ke yi min irin wannan musgunawar illa don uwata ta rasu, Yaya Dijah da aka yi aurenta Innarmu tana raye ai bata irin wannan tozartawar ba nan take na soma kuka da iyakacin karfina. 93 Kan ka ce meye wannan sai ga makwabta suna shigowa tambayar me ya faru? Babah Lantana ta tsaya tana yi musu bayani ai ba komai a ka yi mata ba tunda ga uban nata nan a zaune wai daga yace zai bada aurenta ga wani dan uwana shi ne take wannan borin kar ku dada kar ku rage. Maimakon a gamsu da bayariin nata sai kuma a hau salati dan uwanki? In ta ce eh sai a gyada kai a'a tayi ihu, to wane dadinki taji balle aje ana baiwa wani dan uwanki ita? Wannan ya gayawa wannan mutane sai shigowa suke yi yayinda ni kuma nake kwance a kasa ina ta faman kurma ihu. Gaba daya a wannan lokacin fatana bai wuce dayan biyu ya faru da ni ba, in ma dai Babana ya tausayawa kukan da nake yi ya fasa bada ni ga Nalami ko kuma azabar kukan yayi dalilin da nima zan bi bayan Innata in huta da bakin cikin zama da Babah Lantana. Ban san yanda aka yi ba har Umma taji tazo ba sai jinta nayi ta katse Babah Lantana tana mnai cewa, In ban da 'ya'yan yau ba su san biyayyar yaye ba yaushe za a ce ka tarawa ubanka irin wannan Jama'ar mu da yaushe? Umma tayi maza ta ce mata ke dai kam Lantana ba ki san biyayyar yaye ba da kin santa kuwa da ba haka ba, da ba ki a1kata ma irin abubuwan da ki ka aikata ba. 94 Ke wannan sharrin ma da ba ki kulla shi ba, me yasa baki ba shi tsohuwar yarki da ki ke tashe da ita shekara da shekaru ta rasa mijin aure ba? Wannan ai ba huruminki ba ne ki ka shiga don kuwa ba ki yi mata rikon da za ki zartar mata da irin wannan hukuncin ba. Da sauri Babah Lantana ta shiga fadin ai ni ce ma ni ce na hada? In ke ce in ma ba ke ce ba ce dai duk daya, yi kokari kiyi hakan a kan "yarki da ki ka bari tana tanbada kina kallo in ba nema ki ke sai taja miki irin abinda kema ki ka jawa iyayenki ba. Mero kam ai tayi sa'a tana da uban da za a sa shi yayi mata aure da mijin da aka san ba nata ba ne don a cutar da rayuwarta, sai dai ba tanan take wai an danne buduri a ka yace ai ba nan take ba. In kin yi ne don kin ga duk abinda ki ka yi mata a zaman da ki ka yi da ita bai ishe ki ba ruwanki kema kina da 'ya'ya abinda ka shuka kuma shi ka ke girba, mai rabon ganin badi kumna ko ana dakawa a turmi sai ya gani, haka ana muzuru ana shaho zakaran da Ubangiji ya nufa da cara sai yayi. Don haka tashi mu tafi Mero, ta sunkuyá ta kama hannuna na mike na tashi tsaye tana fadin ke ai kin yi arziki da Ubangiji ya ce yayi miki miji 95 wasu ba gasu nan ba sun tsufa a titi da suna da iyayen na gaske ai da ba su zuba musu ido ba. Ki tafi da ita ina za ki kaita? Ko za kije ne ki kara bijirar da ita? Umma ta waiwayo ta kalleta cikin nutsuwa tace mata ai mu ba mu bijirewa iyayenmu ba balle mu haifi masu bajirewa, ba zan bar miki ita ba ne balle kiji dadin cusa mata wani bakin cikin tunda ke ba Imani ne da ke ba. Babu wata za dai ki kai mishi ita ne yayi abinda ya saba, ta ce eh zan kai mishi ita biyo ni ke kuma ki hana ni ko ki kwace ta. A kofar gida muka samu Mubarak yana tsaye, ganina tare da Umma ya sa shi wucewa gaba ya fara tafiya muna shiga gidan yaja ya tsaya, wacce irin musiba ce wannan Umma? Ta ce, Eh ai rayuwa ta gaji ganin al'amura da dama sai addu'a kawai don haka ba' yana nufin komai ya kare ba ne. To me ya saura Umma? Tayi murmushi tare da fadin da yawa. Ni kam in ban da kuka babu abinda nake yi, duk bayanan da Umma ke yi na zai wuce watarana kuma sai labari jinta kawai nake yi kullum abinda a ke gaya min ke nan wata rana sai labari, har yanzu kuma ban ga alamar abubuwan za su wuce ba tunda kullumn wasu muna nan abubuwan sai kara samuna suke yi, duk wata fitina 96 ko tashin hankali da na gani a rayuwata ban taba ganin abinda ya kai cewan da Babana yayi wai zai ba da aurena ga Nalami ba, in dai ba tashin hankalin rasa uwata da nayi ba ne. Ana cikin haka sai ga Baban Mubarak Albaji Muhammadu ya shigo, menene ne haka a ke ta kuka ke kuma kin tasa ta a gaba kina kallonta? Umma ta shiga rattaba mishi bayanin abinda ya faru. Hankalinshi a kwance ya ce to ba shi kenan ba ina ce yarshi ce? Kowa yayi shiru har da ni din saboda ba zan iya ci gaba da yin kukan a gabanshi ba, jimawa kadan sai kuma yayi tsaki kafin ya sake cewa amma bai kyautawa kanshi ba da ya bari a ka maida shi abinda a ke cewa an maida shi din, bari in je wurin Mallam Sule mu tafi wurin nashi tare muji yanda za a yi. Umma ta ce, To Ubangiji yasa muji alheri, ya ce amin. Nayi kukan bakin ciki a wannan lokacin har sai da na rasa hawayen a idona, na rinka jin tanfar ni din komai nawa ya kare ciki kuwa har da farin cikin rayuwata. A duk lokacin da Mubarak ya zaunar da ni da Dufin rarrashina ko ba ni hakuri kan balin da nake Ciki bana sauraronshi, saboda ni kam can cikin Zuciyata bana jin haushin Babana da mutane ke ta 97 fadin maganganu marasa dadi a kanshi, nafi iin Ciwon Mubarak gani nake tanfar inda yayi wani abu mai karfi da wuri tun lokacin da nayi ta fata da burin yayin watakila da wannan abinda ya farun bai faru ba. To wai sai a yanzu da Babana ya riga ya furta wannan maganar shi ne suke ta faman zirga-zirga aje wurin wannan aje wurin wancan ana kamun kafa wanda bana zaton zai yi wani tasiri don magana daya kawai Babah Lantana zata yi ta birkita komai shi ne kai din ba Dattijo ba ne tunda ga shi kayi alkawari za ka canza. Daga ranar da Alhaji iuhammadu yace bari ya kira Mallam Sule suje wurir Babana zuwa cikar kwana bakwai ya tura wa Bapaia mutane daban daban har sau biyar daga ciki akwai tawagar da Liman ya jagoranta ta Malamai wadanda suka yi mishi nasihohi a kan muhimmancin bayar da aire a inda ya dace wato bin kufu'i don a samu zimatu lafiya fahimtar juna da girmamawar da a ke bukata tsakanin miji da matarshi. Haka nan mai unguwa ya jagoranci mayan unguwa bayanshi Alhaji Muhammadu abokanshi Sun je har sau biyu. Yanda na samu kaina cikin kunci da bak ciki haka Mubarak ba zan ce ya fini ba ne, kawai don 98 ni kadai nasan abinda zuciyata ke ciki, amma ko daga jin irin aiken da Babanshi ke yi daya bayan daya an san lura da halin da dan shi ke ciki yasa shi yin hakan duk wanda yaje ya dawo kuma maganar guda daya ce ita ce ta ya riga yayi alkawari don haka ba zai saba ba. Daga gidansu Mansur ma an turo suma ba su yi nasara ba. Yaya Dijah da mijinta ma sun zo suma duk a banza, haka Yakumbo Halima wacce ita kam kaca-kaca suka sake yi da Babah Lantana, a wannan lokacin bana iya zaman gida ko da na mintuna ne, Babah Lantana da Asabe ba su da wata hira sai ta bukin nawa suna lissafin irin kwalliyar da za su yi. Don haka ina idar da sallar Asuba in na mike gidan Yaya Dijah nake tafiya a hanya nake gama lazimin da nake yi da addu'o'ina a gidan Yaya Dijah ba ma komai sai kuka ko kuma muyi shiru amma duk da halin da muke ciki na bacin rai taja ta tsaya kan bata yarda in tafi ko ina ba. To ki tafi ina Maryam? Kuma ki tafi ki bar ni da wa? Ki bar ni ni kadai? Tambayoyin da ta jero min kenan lokacin da na gaya mata niyyata ta barin gida in yi tafiyata in shiga duniya ya fiye min auren Nalami sauki. 99 Tana maganar tana kallona, yanzu nan za ki iya tafiya ki bar ni ni kadai? To ni kuma in zauna in yi me? Ba a karbarwa mutum ne Maryam da na karbar miki wadannan fitintinun da ki ke rayuwa a cikinsu, tana fadan hakan ta kama kuka, kuka Auwa mai tsanani. Hakan yasa shi kawar da wannan tunanin saboda sanin da nayi gaskiyar magana ta gaya min da ana karbarwa dan uwa wani al'amarin na kaddarar rayuwarshi na yarda da Yaya Dijah zata iya karbar min don ban taba shiga wata fitina ta bar ni na shigeta ni kadai ba. Gaba daya na bijirewa Mubarak na daina sauraronshi na daina shiga gidansu gani nake tanfar har da sakacinshi ya kara jawo min abinda Babah Lantana tayi min na hada ni da Nalami. Kina nufin ke kin fini shiga fitina ne yasa ki ke nema ki hada min da wulakancinki Kan halin da nake ciki? Tambayar da yayi min kenan a ranar da ya biyo ni gidan Yaya Dijah na ki fita ia ba shi umarnin shigowa har cikin falonta in da nake kwance tunda har falon mijinta da ya fara shiga na ce ba za ni ba. Niyyata yayi maganarshi ya gama ban ce mishi uffan ba amma ban san yanda aka yi ba hakan ya 100 gagare ni, na' samu kaina da tambayar menene fitinarka ba abinda kake so aka yi ba? Zuba min ido yayi yana kallona cikin matsananciyar kaduwa me yasa ki ka gaya min wannan maganar? Na kawar da kaina gefe don kar in ga kallon da yake yi min. A hankali na ce ai ba yau ka ke ganina ba. Yayi maza ya ce kuyo Maryam kwadayi ne da ni a kan karatunki ganin badi kamar yanzu kina shirin fita ne yasa yin hakuri na danne zuciyata. Dago ido nayi na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi 'Boko?; ya ce eh, na ce to na daina yin shi daga yau har abada kuma ba zan yi ba tunda dai saboda shi ne kayi sakacin da kaja min wannan musibar. Don haka kara kina kawai ka daina wahalar da kake yi a kaina tunda bokon da zai sa ka aure ni ban yi shi ba, ba kuma zaih yi shi ba. Cire ni kawai cikin matan da za ka aura, koda yake ma ni ban taba sanin kana son aurena ba in ban da wannan karon ban taba jin ka ce kana sona ba na soma kuka. Ka kyale ni kawai ka fita hanyata bana sonka bana kuma son komai naka, daga yau kuma kar ka sake yi min wani aike ba na so ka daina jin tausayina. 101 Mikewa yayi ya fita daga falon ya tafi ba tare da ya tsaya yiwa Yaya Dijah sallama ba. Yaya Dijah ta shigo bayan tafiyar tashi, da kin daina yiwa Mubarak irin wannan abinda ki ke yi mishi da wanne zai ji ne? ni dai ban taba jin Lausayinshi irin na yau ba kinga irin zubewan da yayi? Bakin ciki ai baida kyau, ni kuma ban tabbatar ma za ayi aurenki da Nalami ba don jikina da Zuciyata ba su yarda da hakan ba nafi zaton wata hanya zata bullo da zata zame mana wata mafita ta warwarewar al'amuran kałamanta suka sanya ni na samu natsuwa har na yarda nayi wanka na shafa min na sanya daya daga cikin kayanta. Muje kicin muyi girki ka utanen gida su ji yunwa ba mu ba su abinci ba, na kalli agogo na ce ga su Inna ma sun kusa dawowa daga Makaranta, muna cikin girkin Isiyaku ya sake shigowa ya gaida Yaya Dijah kafin ya gaishe ni ya kuma shaida min tare da Mubarak suke. Yaya Dijah tayi maza ta kalle ni ya dawo, to kar ki yarda ki sake 6ata mishi rai na ce to na tashi na fita na same shi gaba daya idanuwanshi sun kada sun yi jazur. Ki ka ce ba ki tab6a sanin ina sonki ba saboda ban taba gaya miki ba? Shiru nayi ban ce mishi 102 komai ba, ya sake yi min wata tambayar shi yasa ki ka nemi wulakanta ni saboda. wasu suna gaya miki su suna sonki? Wani shirun na sake yi ban tanka mishi ba, to tunda ban taba cewa ina sonki ba, yanzu a wane matsayi ki ka ajiye ni ke nan? Ban kalle shi ba na ce mishi kayi hakuri, ina gaya mishi hakan fushin da yazo da shi ya gushe. Rannan ina kwance a dakina cikin dare idona biyu bacci ne ya gagare ni, in ban da sakar zuci babu abinda nake yi, in saka wannan in kwance, in saka wancan. Aurena da Nalami da kullum Yaya Dijah ke cewa bata tabbatar za'ayi shi ba saboda jikinta da zuciyarta ba su ji kamar za'ayi shi ba. Kullum kara matsowa yake yi, Babah Lantana da kawayenta tare da 'yarta sai shirye-shirycnshi suke tayi ko a ina take samun kudin a take ta kashewa oho. Ni kam cikin zuciyata ban tabbatar da maganar ta Yaya Dijah ba tunda ban hango wani juyi da zai zo ya hana aukuwar auren ba, in dai ba wata kaddara ta Ubangiji ba ne tunda dai komai na auren Babah Lantana ta sayo irin wanda taga yayi mata daidai. To haka zan zauna in yi ta zuba ido ina kallo har ranar auren yazo a daura a kai mishi ni? In har 103 aka yi haka kuma to me zai faru? Me zai biyo bayan hakan? Wanne hali zan shiga? Wacce irin rayuwa zan yi a gidan Alhaji Nalami? Rayuwar aure da Alhaji Nalami to a ya ya zata kasance ke nan? Wadannan sune jerin tambayoyin da suka addabi zuciyata, da na zurfafa cikin tunani mai tsanani sai naga aurena da Nalami kamar baya cikin jerin biyayyar da ya kamata in yi wa Babana, domin shima sa shi aka yi ba ra'ayin kanshi ba ne yin shi. Ita kuma wacce ta hada din da ta hango wani alheri a ciki komai kankantarshi to da bani ta tura ba tunda ni kam ai bata nufina da wani alheri, to haka zan zauna in yi ta yarda kullum Babah Lantana sai ta cuce ni ta cuci Babana? Ina kawowa nan na mike na sauko daga kan gadon na tsallake shimfidar Asabe da ke kwance a kasa na bude kofa nayi waje ko ban tafi na bar gida ba a yau ina son ganin yanda duhun dare yake in da hali ma kuwa ina ganin tafiyata kawai zan yi in yaso bayan wucewar ranar auren na dawo. Sannu a hankali cikin sanda na nufi kofar gidanmu, zare sakatar na sake jawo kofar a hankali na rufe don kar in bar musu kofa a buda bayan kuma dare ne kasancewar dama kudina a kulle suke a bakin zanina yasa ban tsaya tunanin komai 104 ba na kama hanya, hanyar baya na yi nufin bi don kar wani tsautsayi yasa in gamu da wani don in yi nisa da gida kafin gari ya waye in san in da na nufa. Ban yi wata tafiya mai yawa ba naja na tsaya cak saboda muryar da na jiwo a bayana tana tambayata ina za ki cikin daren nan? Kadan ya rago in karta da gudu saboda tsananin kaduwar da nayi in ban da kawai a kowane hali na kasance ko na samu kaina muryar da na jin ba za ta taba bace min ba, in dai ba Mubarak ba ne wannan to Aljani ne abinda naji uciyata tana gaya min ke nan, to shi kuma me zai fito da shi waje a cikin duhun daren nan a kuma daidai wannan lokacin na karfe biyu da rabin dare, in ban manta ba abinda na gani ke nan a dakinmu kafin fitowàta. Ina kike nufin zuwa a wannan lokacin? Kina nufin tana da asara in ki ka aikata wani abu makamancin wannan da kike shirin aikatawa? Ai bata da asara, watakila ma abinda tafi son gani ke nan. Kalaman nashi suka sanya zuciyata ta sakankance cewa lalle shi ne ba wani aljani ba, don haka na juyo muka fuskanci juna, hasken farin 105 wata yayi dalilin haduwar idanuwanmu nan take na soma kuka. Kawo hannunki kiji, kawo hannunki kiji irin abinda kirjina ke gaya min, kawo hannunki ki taba nan din nan ban ba shi hannun nawa ba sai dai na dcga idona na kalli nan din da ya ke nuna min, mazaunin zuciyarshi ne. Kwana nake yi ina zaune Maryam ban samu mutsuwar da na iya dora kafadata a kan shimfidata ba shi yasa nake barin dakin in fito waje in yi ta zirga-zirga tsakanin gidanmu da naku, tsoro nake kar su fake ni su sace min ke suyi sanadin shigata cikin halin da yafi wanda nake ciki. Tunda na gane abin da suke son ganinn nayi kenan to amma yanzu da ki ka fito din nan za ki tafi ban sani ba yar uwarki bata sani ba, me ki ke nufi da yin hakan'? Kina nufin za ki iya bada kanki ga wani ne? Kin san abinda barin gida ke nufi kuwa musamman wurin 'ya mace? Kina nufin za ki iya tafiya inda za ki rayu ba tare da ni ba yar uwarki ba? Kina nufin in akwai alheri a cikin tafiyar taki ni ba zan baki wannan shawarar ba? Don me ki ka shirya tafiya ba tare da kin nemi mu tafi ni da ke ba? Ke ce ba kya sona ki k: cewa ni ne saboda kawai ban ta6a buda baki na gaya 106 miki ba, ban taba zaton sai na furta miki da fatar baki ba, baki ai yana furta karya Maryamu, zuciya kuwa takan tilasta gabobi suyi bayanin abinda ke cikinta. Ban iya cewa Mubarak komai ba saboda kukan da nake tayi. Yi min alkawari a yau a in da muke tsayen nan a cikin sararin nan na Ubangiji cewar ba za ki taba fita ki tafi wani wuri ba tare da kin gaya min ko kin gayawa 'yar uwarki ba. Ki kuma yi min alkawarin ba za ki ta6a auren wannan mutumin ba ke ba shi kadai ba Maryamu yi min alkawari na wani ba zai taba taba min ke ba. Nayi maza na gyada kaina tare da furta kalmar nayi da bakina, duk kuwa da ban san yanda zan yi in cika alkawarin da yake tasa ni ina yi mishin ba, to muje in maida ke gida ki kwanta. Nayi maza na girgiza kai nuna alamar a'a, cikin nutsuwa ya dago idonshi sama na tsawon lokaci kafin ya dawo da kallon nashi gare ni, kina ganin zai yiwu muyi ta tsayuwa a nan har gari ya waye? Da sauri na ce mishi eh, ya girgiza kai a hankali nuna alamar a'a mutane za su yi mana mummunan fahinmta marasa tunani daga cikinsu su zarge mu da abinda bai kamata zargin zai fi tsanani a kanki ba zan so ayi hakan ba, don zai iya 107 zamowa bata suna zai iya zamowa dalilin da Baba zai yi fushi da ke, ba zan ji dadin hakan ba, ina so ki rabu da shi ne lafiya kin gane? Na gyada kaina nuna alamar na yarda. Muje in kai ki gida, ban sake yin musu da shi ba ya tasa ni a gaba sai da yaga shigana cikin gidanmu har sai da na maida kofar na kulle sannan ya juya ya tafi. Na sake yin wata sandar a hankali zan shiga dakinmu, sai kawai naji kofar dakin a kulle, abinda ya tabbatar min da cewar Asabe tana kallon fitana daga dakin bata dai yi min magana ba ne, kawai sai da taji na fita na bar gidan ta mike ta rufe kofa ta koma tayi kwanciyarta. Yaya zan yi? Abinda na tambayi kaina lokacin da na taba naji kofar dakin a kulle, fita zan yi in koma inda na baro Mubarak ko kuwa zama zan yi a nan in jira gari ya waye ta tashi ta bude in shiga? Ko kuwa sa hannu zan yi in buga kofar don taji na dawo ta tashi ta bude min in shiga? In yaso kowa ma yasan na fita da daddaren. Har na matsa jikin kofar da nufin fara bugawa sai kuma naga kai to in Babana ya fito ya tambaye ni ina naje a cikin tsohon daren nan in ce mishi me? In yi sanadin da zai yi bakin ciki? Kai ba zan iya ba da in yi haka gara kawai in kwana a tsakar 108 gidan in jira gari ya waye a bude in shiga in yaso ko don in kaucewa 6ata mishi sai in ce fita fitsari nayi Asaben ta kulle kofar. Don haka na shiga kicin na hau kujera na zauna ina kallon irin berayen da ke zirga-zirga daga kicin din zuwa tsakar gida da wurin wanke-wanke wanda yawan ta'adin abinci ya kara haddasawa. Wajen Asuba naga fitowar Babana zai wuce ban dakin gidan, nayi maza na kauce daga inda nake zaune na koma lungu sosai ya gamå abinda zai yi ya fita ya tafi Masallaci, sai ga Babah Lantana ta fito daga ita sai zani a kirji tana ganin kicin dinta a bude ta leko cikinshi tana haskawa. Satar min naman miya za ki yi? Kamar in tambayeta ko ta taba ganin inda da ya zamaa 6arawo a gidan ubanshi? Sai kawai naga to a na me zan tsaya ina irin wannan cacar bakin da ita, bayan ta riga ta buge ni tayi nasara a kaina tasa Babana ya dauke ni ya baiwa mutumin da babu wanda yasan me ke tsakaninsu sai su biyun suka san abinsu. Ba fa satan miki naman miya taje yi ba, iskancinta ta tafi shi ne ni kuma na maida kofar na kulle ta dawo ta same ta a kulle shi ne ta shiga kicin din ta zauna don kar ta buga kofar a ji ta a 109 tambayeta daga ina take? Iskanci kamar ya ya? Ta bukaci sani. Asabe ta tsaya tana yi mata bayani, ai dama rana dai-dai ne bata bude kofa cikin dare ta tafi can wajenshi sai sunyi abinda za su yi sannan ta dawo ta shigo ta kwanta gajiya nayi jiyan na rufe mata kofar. Babah Lantana ta tabe baki ta ce, ki ka sani ma da ba ki rufe mata ba kin barta ta shiga tayi kwanciyarta ta huta ni kam yanzu ai bani da sauran matsala da ita balle har in je ina kai kararta wajenshi a kan tana zuwa kwanan gida, to a na me? Kwanaki tara ne fa kacal suka ragewa zaman nata a cikin gidan nan, gidan da kullum sai ta yi wa mutane gorinshi sai kuma ta koma gidan Nalami, Nalami kuwa wannan matar tashi in dai tana nan a yanda nasan ta tooo ta dan yi murmushin iya shege ta wuce ta shiga bayan gidan tana fadin, dama in mutum ya ce ba zai yi sharar Masallaci ba ai zai yi na kasuwa. Duk abinda suke fada ina jin su shiru kawai nayi saboda ba ni da wani abinda zance musu huce bakin cikin da suka sanya ni a ciki. A haka muka kasance a çikin gidan nan har a ka wayi gari ana cewa saura kwana biyu ne daurin 110 auren nawa abinda yayi dalilin da na zama tanfar mara hankali saboda tsananin kidima da gigicewa, babu abinda bai zo ya roki Babana ba amma yayi shiru bai ce komai ba. Babah Lantana sai hidimarta take yi, babu abinda yafi komai. daga min hankali irin tsananin farin cikin da take ciki, wuni take yi tana dariya bata gaji ba, kan abinda bai taka kara ya karya ba ma sai ta kyalkyale da dariya ta bugi cinya tare da shewa kafin ta ce sai ni Lantana 'yar Babanta, mata a gidan Mallam Habu mai timatir, kowa yaci tuwo tare da ni miya yasha. In rasa in da zan tsoma raina in dan ji dadi nayi kuka a wannan lokacin har na fige na fita cikin hayyacina, ga shi bana ci ba na sha nayi mummunar ramar da na zama tanfar majinyaciya, wai a irin wannan halin da nake cikin kuma sai manya su rinka zaunar da ni suna cewa wai in yi hakuri wata rana sai labari. Ba don dai kar in yi wata magana na ce na fadi ba daidai ba ga shi ni kuma a' yanzu nema nake in rabu da kowa lafiya don gani nake tanfar ba zan wuce wannan lokacin ba, bakin cikin da ke addabar zuciyuata zai kashe ni kowa ya huta, da na tambaye su ni yaushe ne wata ranar nan da kullum a ke gaya min amma ban taba ganin tazo kan 111 al'amarina ta mayar min da shi abin bada labarin ba? A wannan lokacin ko gidan Yaya Dijah bana iya zuwa saboda rashin kuzari na wuni nake yi a kwance kamar yanda nake kwana a kwance don haka ban san abinda take ciki ba amma dai itama na gaya mata na gaji da jin zancenta na bata tabbatar za'ayi aurena da Nalami ba saboda wai jikinta da zuciyarta ba su yardan mata za'ayi hakan ba. Na ce to sai yaushe za su yarda? Sai sun ganni a dakinshi? Daina gaya min haka Yaya Dijah, bar ni kawai in fuskanci abinda yake gabana, ina fadin hakan ta kama kuka nima ban tsaya bata hakuri ba nasa kai na fita na bar gidan, ban sake komawa ba. Mubarak kuwa sai yazo kofar gidanmu sau biyu sau uku ban iya tashi na fita ba saboda bani da jarumtakar yin irin wadannan abubuwan kuma a wannan lokacin sai nafi sha'awar a ce kowa ya fita harkata a bar ni kawai ni kadai in yi ta kwanciyata ina tunanin Innata da sauran abubuwan da sukai saura. Bikin nawa ba wani biki ne da Babah Lantana tayi wa wani sayayya na abin arziki ba, amma ta shirya kawatashi ta hanyar tara tsofaffin kawayenta da suka yi gwagwarmayar rayuwarsu 112 tare har ma da Dafau Mai kalangu naji tana cewa zata kira. A al'ada ranar sakun lalle rana ce da Amarya tare da kawaycnta kan tafi yawon ban kwana, sai cikin dare take dawowa in an je an kamo ta a kawo ta gida a sa mata lalle, a irin wannan ranar ni na wayi gari ne a kan gadona ina kwance babu wata kawa a tare da ni ba a kira min ita ba nima kuma ban nemarwa kaina ita ba. Ina daki a kwance ina kallo Asabe ta sha kwalliya ta fita itama Babah Lantanar hidima sosai take yi tare da 'yan bukin da suka fara zuwa mata. Ina daki ni kadai in saka wannan in warware in saka wancan wai Nalami Babana ya yarda zai bada aurena gare shi in zama mallakinshi? To zai yi hakan a dalilin ya daina sona ne ko kuwa dai da gaske abin yafi karfin nashi ne? wannan shi ne abinda yake ta kai kawo a cikin Zuciyata. Da daddare kawar Babah Lantana ta sani a lalle saboda babu wanda ya tako cikin gidan, cikin dangin Innata da Yaya Dijah don sun ce babu ruwansu da bikin. Ni da mai sakun lallen kallon juna muke yi da ido zuru-zuru ta juya tana fadin oh'oh amaren 113 yanzu suna da abin mamaki babu ruwansu da duka don an saka musu lalle. Babah Lantana ta taso daga inda take tana fadin ai bata yi kukan sakun lallen ba, ita wannan ai tata rashin kunyar ta daban ce, ni kuma ba a wannan abinda ni bari ka gani, in na zo na sharara mata mari ai zata yi mai dalili. Ta zabura ta taho cikin saurinta da nufin shararan min marin, wasu cikin kawayenta masu dan hankali suka tare ta tare da fadin a'a haba mai shararawa Amaryar tana cikin lalle ki sharara mata mari me yayi zafi haka? Ina ruwana ni da lalleta tunda dai bata da mutunci a sa mata lalle ta ki yin kuka saboda ta matsu a kaita gidan mijin ko me? A haka dai ana wasa ana dariya a ka cimma burinta na dukana a cikin taron kawayenta da ta tara a gidanmu. Wata daga cikin kawayen nata da naji suna kira da sunan Lari baby duk da kokkodewarta wai baby take amsawa, ta matso kusa da ni cikin natsuwa ta ce min kin gani ko Amarya " yanmata ke yarinya ce don haka zan gaya miki lamarin duniyar nan sai a hankali, kar ki yarda kiyi abinda za ki cuci kanki. Zauna wuri daya kawai ki nutsu kar kiyi abinda zai je yazo ya dame ki shi lallen nan da ki ke gani ba karamin al'amari ba ne, wasa da hakkokinshi 114 wurin amarya al'amari ne babba. Shi ke sawa ki ga wasu amaren sun zama wasu, kar ki yarda ki ce za ki fita daga dakin nan ki fita waje kin ji ko? Amarya mai fita da lalle haukacewa take yi kin ji ko? Na ce mata to, saboda tsoratar da nayi da irin bayanin da tayi min din. To ina ruwanki ne da ki ke rattabo mata wannan bayanin? Tayi tambayar tare da galla mata harara kai ke daima da dogon baki ki ke, taja tsaki ta juya ta fita. Uh'uh Anti Lantana gara in gaya mata ta sani shi da ai na kowa ne, ai sai kiyi ta fita ta fita. Duk da bayanin da matar nan tayi min zuciyata bata hakura ta bar ni na zauna lafiya ba, kai-kawon da take yi yayi tsanani ko mikewa a gadona gagarata yayi ina zaune ne kawai ina sauraron abubuwan da take gaya min. Daren nan na yau shi kadai ne yai saura min gari na wayewa za a daura min aure tunda daurin auren ma na safe a ka ce za'ayi kenan daga nan zuwa wayewar gari ne yai saura min, to haka zan zauna shi ke nan magana ta kare ko kuwa ya ya zan yi? Shi ke nan sai in zauna a daura min aure da mutumin da Babah Lantana ta kawo min? da Babana ne don ra'ayin kanshi yaga zai bada ni 115 gare shi da ba zan yi jayayya da auren ba tunda ni din mallakinshi ne, to amma Babah Lantana, in zauna in karasa waycwan gari a Cikin gidan nan yana nufin na yarda da auren da za'a daura min. In sa kai in fita kuma ina tsoro saboda bayanin dakawar Babah Lantana tayi min, ina cikin wannan kai-kaWon sai kawai na tsoro matsayar da ta sanya ni mikewa tsaye ita ce ta da in zauna a daura min aure a kaiwa Alhaji Nalami ni gara kawai in fita in bar gidan in yaso duk abinda zai faru da ni ya faru dani a can gaba. Da wannan tunanin cikin zuciyata nasa kai na fita daga gidanmu sai dai ban san yanda aka yi ba ganina kawai nayi na kama hanyar zuwa gidan su Mubarak. Ina dosar gidan na hango shi zaune a kan dakalin kofar gidansu yayi zaman dirshan a kasa kanshi a sunkuye, har na isa kanshi bai ji motsi ba saboda ya riga ya shagala kan abinda yake yi. Na kasa ce mishi komai don ban san me zan ce mishi ba, kusan mintoci biyu zuwa uku kafin ya dago kai daga sunkuyon nashi yana ganina ya dan kadu bai ji isowar tawa ba da sauri ya shiga goggoge fuskarshi da tafukan hannayenshi duka biyu. 116 Me ya fito da ke a cikin daren nan? Tambaya yayi min cikin wani irin yanayi na nuna karfin hali da jarumtaka ban tsaya ba shi amsa ba sai kawai nasa kai na nufi cikin gidansu, maimakon in wuce can ciki kamar yanda na saba kofar wurinshi na tura na shiga nasa kai na wuce falon na shiga har can cikin dakin nashi abinda bai taba faruwa ba a rayuwata hasalima yau ne shigana wurin Mubarak na biyu. Can cikin dakin nashi a kayace yake matuka ga Ramshinshi da na saba ji a tare da shi katuwar katifa a yashe a kasa tasha shimfida mai daraja ga tarkacen takardu tare da laptop a gefe sai wardrope wacce na tabbatar kayanshi a ciki. Gabana sai faduwa yake yi yana harbawa da sauri da sauri, me ke shirin faruwa ne? me ya shigo da ni nan wurin? Abinda ke ta kai-kawo cikin raina ke nan. Mubarak ya biyo ni har can cikin dakin yaja ya tsaya a bayana cikin wani irin yanayi na sanyin jiki da tsorata da abinda yaga nayin me ki ke so a kawo miki Maryam? Ban tanka ba ban kuma waiwaya na kalle shi ba, na kai guiwowina duka biyu kasa na durkusa a kansu, ya sake biyo ni kasan yayi yanda yaga nayi muka fuskanci Juna. A hankali cikin nutsuwa cikin wata irin murya mai laushi da taushi a dalilin karaya da tsoratar da 117 tayi na soma yi mishi magana, zuwa nayi a yau don in yi maka godiya bisa dawainiyoyinka da alhairorinka a garce ni. A sanina ban taba sanin wani mutumin da ya kai ka yawan alhairi ba ka taimaki maraicina ta hanyoyi daban-daban da ba zai yiwu in fade su ba. To me ya kawo wadannan maganganun Maryam? Yayi min tambayar a sanyaye idanuwanshi kuma suna kafe a kaina. Na kawar da kaina daga kallon da yake yi min kafin na soma ce mishi Babana yayi nufin aurar da ni ga wanda yayi niyyar bada ni gare shi bana zaton akwai wani dalili da zai hana shi yin abinda ya shiryan in dai ba wata kudura ba ce ta Ubangiji. Ban ki auren don raina maganarshi ko bijirewa umarninshi ba, naki auren ne a dalilin sanin dalilin kulla shi da aka yi a yanzu ina cikin wani hali da ba zai fadu ba, don haka nazo wurinka in roke ka kayi min wani alheri tunda kai mai alherin ne kullum a gare ni. Da sauri ya tambaye ni me ki ke so in yi miki Maryam? Gaya min shi ko menene shi zan yi miki. Na sake sunkuyar da kaina kasa sosai kafin na soma ce mishi, ni din budurwa ce nafi zaton daren yau shi ne dare na bankwana a tsakanina da kai, 118 don haka nazo wurinka ne in yi maka kyauta daa abinda nake ganin tanfar naka ne. Muryata ta soma rawa jikina ya soma kaduwa, hawaye suka soma gudu daga idona suna zuba shar! Shar!! Shar!!!! Gaba daya hankalin Mubarak ya sake tashi, ya tsunduma cikin wani hali da ya fi kama da kidima. To menene na wannan kukan? Me ki ke so in yi da ki ke wannan kukan yanzu a gabana? Na ce ki gaya min kawai ko menene zan yi miki shi, kiyi shiru. Nace kiyi shiru. Kwan! Kwan!! Kwan!!! Muka jiwo kwankwasa kofar falon nashi, lokacinne na san bai shigo ba sai da ya kulleta da sauri ya mike wajen kofar ya bude. Me ke faruwa ne Ahmad Mubarak? A hankali naji Umma tana yi mishi tambayar, me ki ka gani Umma? Ta dan yi shiru kafin ta ce mishi ji nake kamar ba kai kadai ba ne. Ya sake cewa me yasa ki ka fadi haka Umma? Ta canza tambayar da tambayarshi to me ka ke yi har yanzu idonka biyu? Bakin ciki ne ya dame m Umma, ina bakin cikin raba ni da Maryam da a ke son a yi. Rabuwa kam ai an raba ka tunda gari na wayewa za a daura aurenta, kai dai kayi hakuri 119 Kamar yau ne za ka ga ya wuce wata rana kuma ai sai labari, ko ma ka kwanta kar in sake Jin ka a waje, ya ce mata to. Ta juya wurinta shima ya maida kofar ya kulle ya dawo har lokacin ina durkushe a inda ya bar ni ya sake kai guiwowin nashi kasa ya sake durkusawa kamar yanda dama yayi muka fuskanci juna. Da gaske ne Babana zai raba mu don haka nake so in yi maka kyauta ta alfarma don ta zamo girmamawa ga al'amarinka da ke cikin zuciyata. Yayi ajiyar zuciya mai karfi kafin ya tambaye ni mecece kyautar taki Maryamu? Ban kalle shi ba na ce mishi 'BUDURCINA' yayi matukar kaduwa da jin kalmar da na furta, don kuwa sai da hakan ya bayyana a fuskarshi, ban yarda mun hada ido ba na ce mishi karbi budurcin kawai a wurina bani da sauran bukatarshi bada shi zan je gidan nashi ba shi yasa nazo' yanzu don in kawo maka shi. Mubarak ya zama tanfar wani mutum-mutumi sai faman bari yake yi tanfar wanda yayi wanka da ruwan sanyi a cikin sanyin hunturu, da kyar ya buda baki ya soma yin magana, a'a kar muyi haka, ba sai kin yi min haka ne zan san ina da matsayi mai girma a wurinki ba. 120 in kin bar shi a nan ma nawa ne, ai nawa i Maryam zan kuma karbe shi ai ke tawa ce naa kuma yi sa'a kin gane ke din tawa ce, kar kiyi gangancin bada shi ga kowa. Na dan dago kadan na kalle shi a rikice kwarai yake bakinshi ne kawai mai jarumtakar furta kalmomin da yake fadin. Ba ka sona? Da sauri ya soma fadin ina sonki mana Maryamn, ina sonki, ya ya ma za ki ce bana sonki? Ina sonki, ina son ki, ina sonkki. Ina jin ya fara furta irin wadannan kalmomin na soma cire kayan da ke jikina ina ajiyewa a gefe dai-dai da dai-dai, kan kace meye wannan sai gani na zama daga ni sai 'yar shimin da ke jikina wacce bata ma gama sauka kasa ta cinyoyina ba, itama na saki hannayenta kirjina ya bayyana na maida hannayena baya don balle rigar nonon shima in ajiye shi a gefe. Da sauri Mubarak ya taso yana fadin uh'uh Maryam uh'uh kar muyi haka wannan kam ba zan barki ki cire ba, ya miko hannu da nufin hana ni cireta, a wannan lokacin kaduwar da yake yi takai duk inda takai, kar muyi haka Maryan maida rigarki jikinki kiji abinda zan gaya miki. 121 Yayi maza ya mike ya shiga wata kofa da ke cikin dakin zuban da naji ruwa yana yi ya fahimtar da ni ban daki ne. Kusan minti biyar kafin ya fito yanayinshi ya sauya daga yanayin da ya shiga bayan gidan, a ciki can gefe ya koma ya nemi wuri ya zauna ya soma yi min magana a hankali, shiga kiyui alwala za ki dan ji sanyi a cikin ranki. Kaina a sunkuye na ce mishi uh'uh kar kiyi tunanin bana sonki ko kin fi ni shiga cikin wata damuwa duk wami abinda ki ke zato a kan wannan al'amarin na shigo abinda yafi haka, ina sonki fiye da duk yanda zuciyarki take iya kwatanta miki, son naki kuma zan iya cewa yana daga cikin dalilan da suka sa ba zan iya yin hakan da ke ba, don kina da girnma da kinma mai yawa a wurina. Mahaifiyarki tana dashi, iyayenmu mutanen kirki ne, yin hakan kuma ba zai rage min komai ba na daga ciwonki da nake ji cikin raina, hakika na sani an zalunce mu ko kuma in ce ana shirin zaluntarmu tunda har yanzu ban tabbatar da daurin auren ba, ina sonki ne ba don sha'awa ba, ina sonki ne ba don kaina ni kadai ba, ina sonki tare da girmamawa da mutunta duk wani al'amari naki. Don haka ba zan so mu aikata wani abin da zai taba mutuncinki ba, don haka mu kara hakuri da 122 Juriya da jaruntakar da zamu kai ma cimma nasara kar mu sanya sabon Ubangiji a cikin lamarinmu, ko kin ta6a jin inda darajar mutanen da suka gama rayuwarsu ta duniya suka koma ga Ubangijinsu ba su taba aikata zina ba a ranar Alkiyama? Ina yi mana fata da addu'ar shiga cikin irin wadannan manyan mutanen da muyi haka Maryam gara mu kama hanya mu bar garin ni da ke muyi tafiyarmu zuwa can wani wuri muyi zamanmu su neme mu su rasa, sai komai ya lafa mu dawo kin ga lokacin komai ya warware sai a sake gabatar mishi da maganarmu. Ban ce mishi komai ba ban sake daga ido na kalle shi ba, saboda kunyarshi da ta kama ni, girma da darajarshi da kimarshi suka yi matukar karuwa cikin raina, zuciyata ta kara tabbatarwa tare da sakankancewa cewa tabbas Mubarak mutum ne mai girma da daraja wanda bai nuna son kai kan abinda yake so. Bai saurari yardata ko rashin yardar ba ya mike yana fiddo kaya a cikin wardrope dinshi da yawansu kayan mata ne gaba dayansu kuma sabbi, sunkin kudi ya dauko yana kokarin adana kudin a jikinshi yana yi min bayani muje in kai ki in da za ki zauna in kuma zauna tare da ke in tsare 123 mutuncinki har kafin wannan maganar ta lafa sai in... Bai kai Rarshen maganar ba muka ji ana buga kofar dakin nashi da karfin tsiya, tare da hayaniya mai yawa, alamar dai mutanen da ke dukan kofar ba mutum daya ba ne ko biyu adadi ne na Jama'a masu yawa. Gabana yayi mummunan faduwa nan take kuma jikina ya dauki rawa nayi matukar tsorata, tsoro kuma matsananci irin wanda ban taba jin irin shi ba a rayuwata saboda gane muryar Babah Langana da nayi a cikin masu maganganun nan. Wayyo! Wayyo!! Jikina sai rawa yake yi. Mubarak ya zuba min ido yana kallona cikin tashin hankali saboda shima a tsorace yake amma duk da haka kokari yake ya rarrashe ni ya kwantar min da hankali kan irin tsoratar da yaga nayi. Kai ku bar dukan kofar nan haka ina ganin kamar babu kowa a ciki, wata daga cikin matan da ke wurin ne suka fadi haka. Babah Lantana tayi maza ta ce, a'a ai babu maganar bari a tunbuke min kofar gaba daya sai na shiga na gani da idona na gaji da iya shegen da ake yi min ina kallo duk wanda yayi a baya bai ishe shi ba sai yayi a yau dinnan na daren aurenta masu bugun kofa suka ci gaba saboda a umarnin 124 da Babah Lantana ta basu ga dukkan alama kuma so suke su tunbuke kofar dakin da gaske. Kai haba wane irin hauka ne wannan? Umma ce ta iso wurin take yin tambayar kai ku bar wannan abinda ku ke yi in ba so kuke ta jawo muku abinda zai dame ku ba. Me zai dame su? Ai in abinda danki ke yi bai dame shi ba wannan ba zai dame su ba tunda shi da yake kwana da matar wani bai ji tsoro ba sa masu tun6uke kofa? Mero ai matar wani ce tunda gari na wayewa za a daura aurenta in kuma takamarka iya shege to bari in gaya maka, shi mijinta ya fi ka sanin kan tsiya don shi wannan in yaga dama zai iya kasa tsiya a tire ya saida ita saboda saninta da yayi. To ta shafe ku ku kadai in ji Umma, kai ku kauce ku bani wuri in yi magana da shi, in kuma bata ciki to zan yi maganin rashin mutuncinki, za ki gane ba ki da wayo zan nuna miki ke din mahaukaciyar tsohuwa ce sau uku kenan kina kulla mishi irin wannan sharrin, to daga yau ba za ki sake ba. To in aka same ta a ciki fa? Uwar banza mai daurewa danta gindin yayi lalata da matar aure. Da kyar a ka shiga tsakanin Umma da Babah Lantana ba don yawan mutanen da ke wurin ba da 125 ba karamin gwabzuwa suka yi ba don kuwa su dukansu biyun majiya karfi ne. Umma ta matso kusa da kofar ta jijigata ta ji ta a kulle kana ciki ne Ahmad Mubarak? Da sauri ya amsa mata da eh Umma, ina ciki. To zo ka bude min kofar mana don wannan azzalumar taji kunya ta gane kai ba irin abinda take zato ba ne. Ya mike ya nufi bakin kofar duk da sanin ina cikin saboda ta ba shi umarnin budewa, ina ganin ya kama hanyar fitar jikina ya kama rawa kar-kar- kar saboda sanin da nayi bude kofar yana nufin Babah Lantana tana da mutanenta su ganni. Masharranciyar mata kawai wacce ta rasa wanda zata tasa a gaba da cuta sai marainiyar 'yar mijinta, ai kin ji kunya za kurma ki kara jin kunyar tunda baki da aiki sai na kullawa 'ya'yan Jama'a sharri ba kin haifa ba ke ma? Bude kofar Ahmad Mubarak ya sake cewa to Umma abinda na tabbatar kuwa shi ne shima ba son bude kofar yake yi ba, iyaka dai kawai ba zai iya bijire mata ba ne. Kar wanda ya shigo min daki, kar wanda ya matso min nan in baso yake ranshi ya abinda naji ya fara fadi kenan daga bude kofar tashi, ga dukkan alamu kuma kashedin nashi ya 126 shige su don ban sake jin wani yana yunkurin shiga ba. Uhun yasan ba shi da gaskiya yasan in an shiga za'a fito da ita ne shi yasa yake wannan zare idon, Babah Lantana ce mai fadin hakan. Ke matsa ni ki bani wuri ja' irar mata kawai da tun zuwanta unguwar nan take haddasawa Jama'a da 'ya'yansu fitintinu iri-iri da sharri daban-daban sai ya koma miki kanki. Babah Lantana ta ce eh fadi duk abinda za ki fada naji ba kuma zan bar nan wurin ba sai an fito min da ita sai an fito min da ita kin daurewa danki gindi yana lalata 'ya'yan Jama'a, wannan dai ya isa haka wanda a ka yi a baya ya isa na hana kumna tunda nayi mata miji zata je gidanshi ta zauna a can sai kuma ki sake neman mishi wata tunda da saninki yake yin komai. Ban sani ba ko Mubarak yayi yunkurin yiwa Babah Lantanan wani abu ne naji Umman tana ce mishi a'a-a'a kyaleta a kanta sharrinta zai kare ba dai kin iya hawa kan laifin 'ya'yanki ki hango na ya'yan wasu ba ai kina da shirin shan mamaki. Kai Mubarak gaya min gaskiya kawai kasan inda Mero take? A natse ya ce mata eh, da sauri ta sake tambayarshi tana ina nc? ban ji yayi wata 127 magana ba kafin na sake jin Ummanshi ta tambaye shi tana wurinka ne? Ya ce mata eh Umma, tana wurinka fa ka ce? Ya sake cewa eh Umma, da dukkan alamu Umma ta firgita kwarai da jin da tayi Mubarak ya amsa ina cikin dakinshi. Ahaha, da kin ce bata ciki gashi tana ciki kin ce ke danki na kirki ne gashi ya bayyana miki cewar yafi na kowa lalacewa kin ji kunya kin ji kunya abinda Babah Lantana ke gaya mata ke nan. Da kyar ta iya buda baki ta ce mishi to fito musu da ita, kan ya ce komai sai Babah Lantana ta sake café zancen da fadin to ba dole ba, ba dole ba ma ya fitowa mutane da matarsu ba, matar mutane ce fa ya samu yana tur...kai tir da wannan baki naki kin girma ba ki san kin girma ba? Ke kin san kin san, kin girma da ki ke daure mishi gindi yana lalata 'ya'yan Jama'a shiru Umma tayi bata tankawa Babah Lantana ba to fito musu da ita ta sake ba shi umurnin, in fito musu da ita Umma? Bata tsaya ba shi amsar tambayar tashi ba sai kawai naji shigowarta. Kan ka ce meye wannan sai gata tsaye a kaina hannu da sakata kama ni ta jawo ni muna isowwa falon muka gamu da Mubarak ga dukkan alamu 128 biyo ta yayi yaga abinda zata yi kar ki ba su ita Umma muna gamuwa abinda ya fara cewa ke nan. Na roke ki kar ki ba su ita yana nata rokon nashi saboda ganin alamar ba za ta saurare shi ba, tana jin haka ta saki hannuna ta juyo gare shi a fusace tau! Tau!! Tau!!! Wasu irin zafafan marika ta sakar mishi a jere cikin sauri har guda uku. Jikina ya sake daukan wani rawan kar-kar-kar na kara tsorata wani irin matsanancin tsoro ban taba ganin dan gata kuma shagwababben da irin Mubarak ba, amma ga abinda Umman tayi mishi a yau a kaina kuka sosai na kama yi yayinda Mubarak ya kai guiwowinshi duka biyu kasa kiyi hakuri Umma bata saurare shi ba ta sake kama ni muka yi waje ta dankawa Babah Lantana ni a bannunta, to yi waje ku bani wuri. Yanzu kuwa kin taba ganina a gidanki in ban da yau? Kin taba ganin kafata ta tako cikin gidanki? Gidanki ai ba gidan zuwa ba ne, gidan da uwa ke daurewwa danta gindin ya rinka lalata 'ya'yan Jama'a? ai kukan karya ki ke yi. Duk abinda Babah Lantana ke fada Umma ba ta ce mata komai ba kuka kawai take yi sai dai ban san asalin dalilin kukan nata ba na ganina a dakin Mubarak ne ko na tausayin al'amurana ne oho. 129 Babah Lantana ta damko ni tamfar zata karya kashin hannun nawa saboda tsananin rikon da tayi min bayan kuma ni ko nuna alamar jayayya ban yi ba. Muna tafiya sauran Jama'a suna biye damu a baya duuuw! Ita kuma tana bayani duk da daren ba mai boye sirrin magana ba ne, tun bata isa komai ba yarinyar nan take bin maza, nan in da ku ke kallonta babu irin lalacewar da bata sani ba in a kan namiji ne babu kokarin da ban yi ba a kanta abin ya faskara, a ce yarinya kamar wannan ta iya bin namiji har gidanshi taje kwanan gida? Ai kuwa randa ta rika akwai magana kenan, ni wannan tana da aiki ko in ce mijinta yana da aiki in ba a dace ya zamo irin ta ba. Ga dauke-dauke ko bera bai fi ta sata ba, ni fa yanzu da lalita nake yawo saboda duk inda zan ajiye zata dauka tanfar mai wankin ido take tayi na kudi tayi na naman miya, bani da halin in motsa a gidana sai tayi min ta'adi bani da sakat. Bayanin nata ban sani ba ko ya gunduri. wasu daga cikin Jama'ar tata ne naji wata mata daga bayanmu ta fara cewa ba a yi wa da irin wannan tonon asirin Lantana musamman ma da yake ke din uwarta ce ba a bakinki ya kamata a ji wadannan kalmomin ba ai tsakaninki da ita 130 addu' ar ce Ubangiji ya shirya mana musamman ma kuma da yake yau din nan shi ne darenta, na karshe a tare da ke zata gidan mijinta gobe kamar yanzu fa ita din matar aure ce tana can a gidan mijinta. Cikina ya bada wani irin mummunan sauti na kulululu! Saboda jin da nayi ta ce, gobe kamar yanzu ni din matar aure ce ina gidan mijina.' Addu'a ya kamata ki dage kiyi tayi mata na Ubangiji ya shiryeta ta bari fiye da haka ai anyi an kuma bari kawo ki ka gani yana rayuwa yana da kuskuren da ya aikata lokacin kuruciyar wanda in da za a sake dawo mishi da kuruciyar tashi a yanzu ba zai maimaita wancan abin ba don ya gane bai yi wa kanshi daidai ba. Wata can daga gefe ta sake cafe maganar itama maganar take yi shi sabulun wankan aure ma wani irin siddabaru ne da shi saboda sabulu ne mai albarka wanke dauda yake yi yayi tas, ya wanke duk wani mugun hali ya zama mai kyau mara hankali ta zama mai hankali kiga an kai yarinya daki ana tsoron al'amarin ta sai kuma kijita shiru ta zauna sai wanda yasanta yasan kuruciyarta shine kawai zai san ta taba yin wani abu. Babah Lantana taja wani mummunan tsaki wato nan duk bayanin nan da nake yi muku 131 haushina ku ke ji da sauri dayar ta ce ba haushinki ba ne muka ce kiyi mata addu'a ta sake jan wani tsakin to da addu'arta zan ji ko da ta nawa ya' yan? Gaba daya suka hada baki wajen cewa aiya kin yiwa wani addu'a kin yiwa kai ne don kuwa ita addu'ar yana daga cikin sharadin karbanta in ka yi wa kanka ka hada da sauran Musulmi baki daya da kuma za ka bar yiwa kanka ma ka koma ba ka da aiki sai na rokarwa al'ummar Musulmi ko wani dan uwanka to kai ma da kaga biyan bukatunka cikin sauri. Babah Lantana ta ce, ai sai kuyi tayi ina jinku wannan dai babu abinda zai sa in zauna ina bata lokacina kan wannan ba don ni kadai ni nasan irin abinda ta guma min iyaka dai tunda zaman namu tare yazo karshe shi kenan magana ta kare, zata je gidan mijinta nima ta bar ni in zauna da nawa mijin lafiya a gidana, aniyar kowa kuma ta bishi, kowa yayi shiru yana jinta babu wanda ya sake ce mata wani abu. Muna shiga gida naji ta kai min wani irin wawan dukan da ban zata ba sai da na kife a kasa saboda tsananin buguwan da nayi nan take kuma ta biyo ni ta sake dannewa tana duka tana fadin har a daren ranar auren naki ma sai kin je kwanan gida duk wanda ku ka yi a baya bai ishe ku ba sai 132 kin sake kai mishi kanki a yau saboda ki samu kaiwa dan uwana kazantarku ko? Tana yi tana duka tana mintsini tana bugun kai a Rasa, ga kuma bayanin da take yi fatanki da bai wuce ki sa mutanc su zage ni su ce ban iya tarbiya ba, toaniyarki zata biki dadin abin kuma shi ne ba ke kadai ba ce a gidan ga yar uwarki nan Asabe ita ce gaba da ke ko da yake ba sosai ba ne amma sai ki tsallaketa tana kwance kije wurin iya shegenki tana kallo babu ruwanta saboda bata gaji wannan tsiyar ba. Mafi yawancin mutanc suka fusata da dukan da Babah Lantana ta rufe ni da shi fadi suke yi haba a ina ake wannan abin amarya kuma ayi mata duka tun a wurin sakun lalle take burin dukan yarinyar nan a ka hanata shi ne yanzu ta fake da wannan abin tayi mata irin wannan nagazawar. Aka kwace ni da kyar daga hannun Babah Lantana a ka kai ni daki a ka zauna da ni na makure wuri daya cikin tsananin takaici da bakin ciki ga masifar 6acin ran auren dolen da tasa ayi min ga bakin cikin azabar da ta gana min ga wulakantani da tayi wurin mutanen da ba su sanni ba, babu ma kuma abinda ya hada ni dasu balle su san sharri ta kulla min na maganganun da ta fadi a kaina. 133 ina zaune ina kuka yayinda mutane a tsakar gida suka yi cincirindo suka zagaye Babah Lantana suna sauraron karin bayanin da take yi musu a kaina na game da mugayen halayena sai kawai naga wata mata da ban santa ba ta fado cikin dakin tana shigowva tasa hannu caraf ta damke hannuna. Nayi kamar in kurma ihu saboda tsananin tsoro don nayi zaton ko bayanin da Babah Lantanan ke yi musu ne ya kara fusatata har taga bari tazo ta ja ni kawai zata kai ni a sake yin rubdugu a lakada mini wani uban dukan. Sai naga tayi maza na dora dan yatsanta a baki tare da fadin shhhhi alamar kar in yi wani motsi mai karfi da zai jawo hankalin Jama'a gare mu don haka na mike cikin nutsuwa ina biye da ita sannu a hankali cikin hikima da kulawa ta fitar dani daga cikin tirmitsin Jama'ar nan ta nufi kofar gida da ni. Muna fita waje ta kalle ni cikin nutsuwa ta ce min kama hanya kiyi tafiyarki kin ji yarinya, wannan fitinar tayi yawa je ki abinki babu wani abinda zai same ki sai alheri shi da ai na kowa ne babu mai yi mishi sharri sai wawa. Zuba mata ido nayi ina kallonta a tsorace gani nake tanfar wani sharrin take so ta sake kulla min 134 don gani nake tanfar duk wani wanda yakc tare da Babah Lantana mugu ne sai naji ta ce min, ke fito da ke nayi fa don ki samu kiyi ta kanki, yi maza ki bar wurin nan tun bata ankara ta gane ba kya nan a cikin gidan nan ba. Kallon da nake yi mata cikin tsananin tsoro ne wata kila ya sa ta maimaita cewa yi ta kanki na ce don ki samu ki kubuta daga sharrin wannan muguwar ja'irar, ta sake maimaita kalmar shi da na kowane babu mai muguntarshi sai wawa, jeki duk inda ki ka ga yayi miki daidai kin ji wata rana in kina raye sai kiga kin bada labari. Ina jin haka na gane da gaske tayi nufin taimakona ban sake tsayawa wani 6ata lokaci ba yankawa kawai nayi a guje duk da kasancéwar lokacin, lokaci nc na nisan dare ga kuma duhu. TIRKASHI! Ku biyo ni mu sake bin 'yar gidan Mallamn Habu Mai Tumatir cikin littafinmu na uku don muji da ta yanka da gudu a cikin nisan dare da duhunshi ina ta dasa? Me kuma ya faru bayan haka? Meene karshen maganarta da Babah Lantana da kuma auren Alhaji Nalami? 135 Fatan alheri gare ki dukkankuu na gode da kulawarku kan harkar rubutuna na gode, Ubangiji ya sakawa kowannenmu da alherinsa ya kuma sada nu cikin Aljannarshi ta Firdausi domin rahamarSa, Amin summa Amin. Taku, HAFSAT CHINDO SODANGI 6/7/1434 5/5/2014 36