HALINTRAYTWA3 Hafsat G. Sc LTTATTAFAN SODANGI Uwar Miji Naga ta kaina Waiyo duniya Rabon kwado Cikar alkawari Mata da kicin dinsu Duk daya Shamaki Hattara Yiwa wani Abu naka Tabbataccen ál'amari Kyautata Wacece ai? Ayi dai nu gani Wata fuskar Mata masu duriya Biyan bukatar rai Nufin Allah Mijin ta ce In kunne ya ji Halin rayuwa Gani gareka Kiff na ganinka Daga kin gaskiya Da kamar wuya Garin banza Me zanu ce da maza Masu ftowa nan gaba Me Daki Bugun zuciyarmu daya Mata da kicin dinsu na biyu (2) Mai uwa 3 HALIN RAYUWA 3 Kartawa nayi da gudu cikin duhun daren nan na rinka bi cikin kwararo da lunguna ba tare da ina jin tsoro ko duhun daren ya dameni ba, ji nake tamkar gudun da nake yi din gudu ne na ceton rai, ban tsaya a ko ina ba har sai da na isa kofar gidan su yaya Khadija duk da nisan dake tsakanin unguwannin namu. Sau daya kawai na taba kofar gidan nasu na jiwo muryar yaya Ibrahim yana tambayar wanene? Alama dai na su ma ba su yi bacci ba. Ni ce na amsa cikin wata irin murya mai tsananin rawa saboda barin da jiki na ke yi. Nan da nan na ji yana kokarin bude kofar, bai tsaya yi min wata magana ba ya kauce daga hanya ya bani wuri alamar wai in shiga, sai dai ban iya motsawa ba sai da ya yi min magana da bakinshi, to shiga mana maganar ta shi ta zamo tamkar nuni ko tunatarwa a gareni. Falon yaya Dija na shiga saboda ganin da nayi mishi a bude ban ganta an an ba don haka na wuce can cikin dakinta akan sallayarta na ganta tana salla yayin da hawaye ke gudu a kan kumatunta, na nemi wuri na zauna har ta idar ban mtosa ba shima yaya Ibrahim bai shigo ba wurinshi ya shiga sai da ta shafa fatiha bayan ta kammala addu'o'inta sannan ta juyo gareni. 4 Wannan musiba ta kai inda duk ta lkai sai dai duk da haka ban fidda tsammani ba zata wuce wata rana har ki ga kina bayar da labarinta, babu abin da ya kuma jawo mana wannan fitinar irin rasa uwar mu da mukayi karo na farko da yaya Dija ta fito fili ta fadi hakan da bakinta tana gama fada kuma ta kama kuka nima na shiga tayata kukan da take yi. Yaya Ibrahim ya turo kofa ya shigo, ke Dija wane irni rashin hankali ne wannan? Yaya zaku hadu kuna yiwa mutane kuka a cikin wannan tsohon daren, wai a kanku aka soma ganin irin wadaanan abubuwan ne balle ku ce naku yayi daban da na kowa? Ina ce ga ta nan a gabanki in kuma kaddarar ta ce aurenshi kina da wata hikima ne na hana hakan farIwa ni bana son rashin hakuri. Fada sosai yaya Ibrahim ya yi kafin ya juya ya tafi wurinshi, nima na mike na shiga bandaki nayi wanka na fito nazo na sanmeta kwance a kan gadonta, na hau muka kwanta tare kowa ya yi shiru lokaci mai tsawo har ta kai ma na soma tunanin ita kam ta samu tayi bacci sai na jiyota tana tambayata, kin yi bacci ne Maryam? Na ce mata, uh uh. Yaya aka yi kika fito? Ban 6oye mata komai ba na kwashe bayani na duk abinda ya faru a daren na gaya mata. Zumbur ta mike ta zauna a tsakiyar gadon kika bashi kyautar budurcinki fa kika ce? Kan in san amsar 5 da zan bata kan subutar bakin da nayi nayi mata wannan bayani tuni har ta rufeni da duka duka ukma ba mai sauki ba, kina nufin saboda Mubarak sai ki yiwa kanki sanadin tsiya, tana dukan tana kuka, ke wace irin yarinya ce wane irin so kike yiwa Mubarak? Tsananin tsoratar da nayi da abinda yaya Dija ta aikatamin shi ne ya yi dalilin dana shanye duk wata azaba da ta gana min abinda bai taba faruwa ba a tsakaninna da ita. Shi waye da zaki kai mishi budurcinki? Haba wacce irin fitina ce wannan? Ke wacce irin shashashar yarinya ce da bata san darajar rayuwarta ba? Bayan ta hakura ta bar duka da kukan ne take furta irin wadannan kalmomin abin da tayi min din nc ya yi dalilin da bai karasa gaya mata sauran abubuwan da suka faru ba na nemi wuri na makure vwuri daya yayin da ita kuma ta ci gaba da tsaki tana fadin, mahaukaciya kawai da kin cuci rayuwarki da kinja mana bakin ciki da tozarta a cikin jama'a. Har gari ya waye bata sake kwanciya ba bata kuma daina yi min fada ba, namiji aka ce miki ana yi mishi irin wannan kyautar ne? Ai ni ban san haka kike ba. Washegari da sassafe yaya Tbrahim ya yi shiri cikin kwalliya ta burgewa gidanmu ya nufa don halattar daurin aurena da Alhaji Nalami kamar yanda dama aka shirya ya shigo ya yi mata sallama ya fita. 6 Gabana ya yi mummunan faduwa kamar yanda na san itama yaya Dija ba ta ji dadin tafiyar tashi ba sai dai ta shanye 3aboda har yanzu fuskarte a daure take alamar wai bata daina fushi da ni ba kan maganar da nayi mata, a zuciyata na ce to da Mubarak ya karbi wannan kyauta da nayi mishi ko de yaya muka kare da yaya Dija oho? Ina tayata aiki ina Rokarin ganin tą wartsake don mu koma kamar yand amuke, yaya Ibrahim ya gani da baije wajen daurin auren nan ba cikin matsuwa ta ce min, ai ba zai yiwu ba sai a yi zaton da wani abu a Kasa a gane ya san inda kike sannan ko ba don haka ba ma zai yiwu ace babanmu ya kira shi hidimar gidanmu bai je ba, ai kuma sai ya zama karnar da raini a cikin lamarin, nace to kuma baka ne. Ina zaune a gefen gado cikia natsuwa duk da hucewar da na ga kamar yaya Dija tayi bai sa ni jin wani dadi a tare da ni ba, a takure kwarai nake zuciyata sai harbawa takeyi da sauri sauri saboda tsananin tsoron da nake ciki. Tashi ki yi wanka ki gyara jikinki jki karya kafin ya dawo mu ji abinda suke ciki sai mu ma mu san menene abin da za yi. Nace mata to. Muna zaune a falnota bayan mun karya, jikina sai faman bari yake yi tamkar wacce sanyin hunturu ke kadawa babu abinda yafi komai kadani irin kallon agogo da nayi naga karfeara saura minti gonan safe, 7 ahalin daurin auren kuma an ce ne za a yis hi da karfe bakwai da rabi na safe, to kome yaya Ibrahim din ya tsaya yi a can oho? Da ya dawo ai da mun san abin da ake ciki. Muna nan zaune a wurin muna jiran dawowar nashi lokaci sai tafiya yake yi, yaya Dija ta gaji tace ko me ya tsare babansu har yanzu bai dawo ba oho? Daurin auren da aka ce tun safe za a yi shi har yanzu ba a dawo ba. Tana yi tana kallon agogo don kara tabatarwa kanta da lokaci. Muna cikin hakan sai yaya ibrahim din ya shigo gaba daya muka tsareshi da idanuwanmu sai dai babu wanda ya iya buda baki ya ce mishi kala saboda tsananin tsoratar da muka yi. Yanayin shi yana nan a tsakani wato baina-baina ko kuma kadahan-kadahan arn yi daurin auren kenan? Zuciyata ce ta raya ain hakan Lafiya dai babansu na ji ka shiru gashi kuuma duk jiinka yayi dabbare- dabbare bayan sanda ka fita bar daukan ido kayanka suke yi saboda farin su. a gyara zama akan kujera bayan ya kwabe babbar rigar tashi da ya tube ya jefa can gefe. Lafiya dai babansu? Ta sake yin tarabayar a yanayi na zuba mishi ido. Wannan al'amari ai yana da ban mamaki gaba daya muka sake zaro idanuwa muka Zuba mishi, yayi shiru, me yaf aru baban su? Rashin hakuri ya sa ta sake yi mishi tambayar. 8 Tun barina gidan nan fa ba wani abu.da na sawa bakima. Ina jin haka na mnike na nufi kici don kawo mishi abin karyawa na shigo dauke da tiren abinci a hannwma na sameshi yana yi amta bayani, Samarin unguwar ne suka watsa taron mutane da duwatsu da goruna, sanduna ba a samu damar yin daurn auren ba. Da sauri yaya Dija ta sake tambayarshi ba a samu yin daurin aure ba kace babansu? Cilán natsuwa ya ce mata, eh ai rikici babba abin ya zama. Tana jin haka ta fadi a kasa tana sujada alamar godiya ga ubangiji. Ya bita da kallot ana tasowa ta shiga furta kalmomi na godiya da shukure baiyane ta matso gabanshi tana shirya mishi abin karyawa tana sauraron bayanin da yake yi mata, nima ina gefe ina ji jiya ashe wai da suka ankara suka gane Maryamu bata cikin gidan sai sukayi zaton ta sake fita ne ta sake komawa wajen Mubarak tunda dama a can suka kamota don haks suka sake yin gaiya guda suka koma musu bar cikin gidansu har wajen iyayenshi da aka duba ba a sameta ba maimakon a hakra a yi neman a wani wuri tun da baban si da kanshi ya fito yayi mishi magana ya ce bata wurinshi, sai ita babar taku ta nufi ofishi 'yan sanda ta debo su mota guda tana fadin wai iyayen nashi ne suka daure mishi gindi yana lalata 'ya' yan muytane a gidan don haka ba zata yarda da maganar baban nashi ba, a cikin daren suka kama 9 Mubarak suka tafi da sh1 suka tsare bayan dattawan unguwa sunyi kokarin shiga tsakani ta ce wai bata yarda ba aje gaban hukuma kawai don su din dukansu munafukai ne don haka su kuma samari suka fusata suka ce ta wulakanta musu iyaye banda haka kuma dama shi Mubarak mai mmu'amala da su ne don haka suka ja suka tsaya cewa zasu ga yanda za a yi a yi daurin auren, sai da suka bari jama'a sun taru har an sanar da isowar wakilan ango sai kawai suka firfito da sanduna da gorori suka fadawa jama'a musamman tawagar angon da jama' arshi wasu kuma daga can nesa suka yi ta auna mutane suna yi musu ruwan duwatsu, gava daya suka tarwatsa jama' a, shi dai angon nan in dai ba karyashi suka yi ba to sun turgudashi a wani wuri don da kyar muka kwaceshia hannunsu, sai faman nisa uka yake yi yana neman taimako. Assha assha namiji da neman taimako kuma babansu 1lallai fa da gaske ne abinda ake fadi akanshi cewar shi din ba namiji bane daudu yake yi. Yaya Ibrahim ya daure fuska, wane irin zancen wofi ne wannam daga nace yana ihun kiran maza su yit aimako kuma sai ki dangantashi da daudu kin san ma'anar daudu kuwa? Wuya tana da dadi ne? In ka ji fa kayi ihun kuma taimamko ai ba laifi bane. Tace haka ne, daidai lokacin da ya mike ya nufi waje don tafiya wajen harkokinshi. 10 Daga ni har yaya Dija babu wanda ya iya cewa wani komai bayan fitar tashi kallon juna kawai muka yi cikin wani irin yanayi da ba zan iya kwatantawa ba, da kyar na iya bude bakina na ce mata wato dai duk wani al'amari yaya Dija na ubangiji ne. Tayi maza ta ce ai shi ne madogara ta dindindin in har ka dögara da shi din kuma to baka tabewa. Duk da wannan labari mai dadi da yaya Ibrahim ya zo.da shi saukin damuwa kawai muka samu amma ba wai mun fita daga cikinta bane muna te addu'a tare da sauraron abinda zai biyo bayan abinda aka yi. Ina nan zaune a gidan yaya Dija har adadin kwanaki hudu jinin jikina har ya fara dawowa na soma farfadowa daga mummunar gigitar danayi sai ga YakumboHalima ta zo gidan don dama ta san ina nan saboda aiken da yaya Dija tayi na a gaya mata saboda ta samu kwanciyar hankali. Muna zaune g abanta muna hira bayan ta gama ian abincin da na kawo mata tana kara bamù albarin abubuwan da suka faru ko ince suke faruwa sai naji ta ce, shi kam malam Habu ai ya shiga mas'ala koma ince ya shiga uku ina amfanin ace namiji baida katabus komai sai yanda akayi da shi. Da sauri yaya Dija ta ce Yakumbo bafa haka kawai bane da abinda tayi mishi. Ke matsa can ni ki bani wuri a kanshi aka fara yiwa maza asiri? Ai shi asiri da kike gani bance miki babu shi ba amma mafi 11 yawancin lokaci hali yake tararwa, yauwa shima kuma gashi nan ya gamu da hashi gamon don dazu da safen nan nake jin albarin wai ya yanke jiki ya fadi cikin kwandunan tunatiri a kasuwarsu sai da aka ciccibo shi rangatanga aka kawo shi gida. Ni da yaya Dija salati mai kafi muka kama yi yayin da it akuma ta ci gaba da fadni, uhun menene wannan in ba bakin ciki da damuwa ba da yake nema ya haddasa mishi ciwon nan na zamani da ake fama da shi na hawan jini. Ni da yaya Dija bamu iya daukar abinda ya.samu babanmu a yanda Yakumbo Halima ta dauke shi ba wato a'inda babanmu ya shuka ne yake girba tausayin shi ne ya kamamu nan take muka soma yin kuka muna fadin, ba laifinshi ba ne Yakumbo ba laifinshi bane kune kawai baku san abinda muguwar matar nan take yiva baba ba na asirce-asirce da sihiri iri-iri. Yaicumbo ta mike tsaye nuna alamar tafiya tana fadin, to ai shi kenan ku kuka san abin yi tunda ubanku ne ni kam ni nazo na gaya muku sai kusan abinda kuke ciki. Yaya Dija ta kawo kudin mota ta bata. Tana barin gidan ta kalleni, daga irin wannan faduwar ne fa ake rasa wani bangaren na jiki, ni yasu baba Lantana ta ciccire mu a rayuwa in kuma.muka barta ta zama sanadin nakasar ubanmu muna kallo to ta gama damu don wa muke da shi kuma bayan shi din? A hankali 12 nace mata babu musamman ma da yake kullum a cikin alkawarin neman, mana dangin ubanmu kike sai dai har yanzu shiru. A fusace ta juyo gareni kefa ba wani hankali ne da ke ba bakya ganin kullum a cikin mas'aloli muke bamu fita wannan ba mu sake fadawa wancan? Bain sake yin wata magana ba bayan fadin haka ne da nayi. Nan da nan muka shirya tafiya gida bayan ta tura an gayawa mijinta halin da babanmu ke ciki, a hanya sai kallonmu ake yi ana zunde ana nunamu tamkar dai ba a sanmu ba, wai dan rikicin da akayi a gidan nan ne ta ya sa mutane suke yi mana irin wannan kallon, nace mata eh tace to ai sai su yi tayi su ne abin fada baya yi musu kadan nace haka ne. Muna shiga gida baba Lantana ta soma sakin magangaiiu'ai dama da kika gudu can wajenta kika tafi ta 6oye lki to ai zancen bai kare ba in ma kuma yi kukayid on ku kunyatani in tozarta gaban mutane to ba ni kuka yiwa ba ubanku kuka yiwa shi kuka kunyata kuka tozarta kuka nunawa jama'a cewa shi din ba komai bane a wurinku bai kuma isa da ku ba ko ba komai kuma ni kam ai gani nan a zaune daram lafiyata kalau shi ne bakni cikinku yake sashi yanaa tintsirewa a cikin jama'a yana faduwa, in kuka yi sanadinshi bukatarku zata biya tunda dama fatanku kenan gashi can a kwance magashiyan ai cikin yardar ubangiji bakin cikin ku ne zai yi sanadinshi. 13 Wani irin mummunan faduwar gaba na samu abinda na tabbatar kuma shi ne itama yaya Dija abinda ta ji kenan saboda zaburar da naga tayi ta nuf dakin da yake kwance. Ku daiyi a hankali kar ku takamin leda da kafafuwanku masu datti don yanzu na gama gogeta babu kuma komai na uwarku a ciki balle ace za a shiga min da gadata. Halin da babanmu yake ciki yafi gaban bayani numfashi yake yi sama sama ga kuma karin ruwa ana yi mishi. abinda muka tabbatar shi ne wadanda suka dawo da shi ne sukazo da wanda ya dan dubashi da gani har yaya-Dija kuka muke yi saboda bamu taba ganinshi cikin halin rashin lafiya irin wannan ba. Ai ba ku yi kuka ba tukunna sai randa kukayi mishi farat daya ko kukayi mishi sanadin hannu da kafa ranar ne zaku gane kunyi kuskure, ai kun san ni dai ba-zan yi zaman jinya ba ko balle inje ina hidima da dawaniyar najasa. Yaya Dija ta mike tsaye ta kalleta rike da labulen dakin nata-da tayi tace mata, matan arziki ai su ne masu hidima da jinyar mazajensu don neman albarka da rahamar ubangiji ai ke ubangiji ba zai yi miki wannan alherin ba ba zai jarrabi wani da jinyar da za ki yi hidimarshi ba balle ki samu wannan alherin. Yaya Ibráhim ya shigo ya samesu nan take ya soma yiwa yaya Dija fada, ke da kika zo kika samu 14 wannan al'amarin kumą mre ya kaiki tanka wata magana. Ya juya ya fita bayan ya bamu umarnin kintsa baban namu don tafiya asibiti. Muna kokarin kintsa shin baba Lantana bata fasa magana ba ba, ba dai ke ce mai daure mata gindi ba? Yarinyar da ta san taje kwanan gida gidan saurayi an kamata tana yin hakan yafi a kirga anyi nufin aurar da ita don neman mata rufin asiri kin sata ta gudu taje wajenki kin 6oye ta? To da albarkar masu albarka sai ta durkusa a tsakiyar dakinku ta haifar muku dan shege kuma kun goyashi a bayanku ke da ubanku da yake biye muku, babu wanda ya sake tanka mata. Gwajin farko a asibiti likita ya bayar da tabbacin hawan jini ne ya yi mishi yawa yake nema ya taba mai zuciya kan haka ya bashi gado aka kwantar da shi a dakin masu cutar hawan jini. Yaya Dija da mijinta suka koma gida ni kuma na zauna tare da shi, ban san yanda akayi ba cikin dare sai ga Sallau ya zo, sannu Mero. Na ce mishi yauwa ba tare da na daga kai na kalleshi ba, yaya mai jikin? Nace da sauki. Ya ja ya tsaya yana kallon baba nima na ci gaba da al'amurana, na ce ko zan karbe ki ne kije gida ki huta in kwana tare da shi in yaso da sate sai ki zo ki karbeshi? Lokacin ne na san na dago na kalli Sallau da nufin tanbayarshi shi kuma a waye dinshi da za mu yi irin wannan canjin ji da shi? Yanayin da na gani a tare da shi ne ya hanani yin 15 hakan cikin natsuwa sai na ce msihi a'a Sallau jeka gida kawai abinka na gode. Bai tafin ba sai ya tsaya muka kwana tare a asibitin, yanda kuma banyi abcci ba haka shima bai yi ba. Da sassafe yaya Ibrahim ya zo duba mu ya kuma kawo mana abin karyawa da zai tafi ya kawo kudi ya ba ni ya ce in rike a hannuna ko za a nemi wani abu, nace mishi to tare da godiya. Yaya Dija bata zo ba sai da ta kammala abincin ranar gidanta ta zo mana da shi hakan Yakubo Halima ta kawo mana tuwon dare. Mutanen unguwarmu makwabta, abokan zaman baba na kasuwa suka yi ta zirga-zirgar zuwa don dubashi duk wanda yazo kuma zai kawo wani dan alheri ya bayar sai dai kalamand a suke fürtawa ne basa yi min dadin ji kai rashin van uwa kow ani tsayayye bai da dadi in banda haka yaushe za a ce yarinyar da ta ja maka irin wannan tozartar tayi maka sanadin wannan mumnunan ciwon ita ce kuma mai yin jinyarka to yaushe ma kuma zaka warke? Hankalina tashi yake yi a duk lokacin da na ji suna fadin hakan in kasa fahimtar abinda na yi na tozarta babana, kamo ni da aka yi a gidan su Mubarak ne tozartawar da suke magana a kai ko kuwa watsa taron masu daurin auren da yara suka yi? To ko ma dai menene sai nake ganin tamkar in har da adalci cikin almarin ba laifi ne da ya dace a daukeshi a doramin ni kadai a kaina ba. 16 Tunda baba Lantana ta gane irin zirga-zirgar da mutane suke yi wajen zuwa asibiin sai itama ta soma zuwa kulum ta kan zo ne da tabarmarta ta shimfida a hanyar da ta san itace tas higowar mutane tana ganin an zo sai ta tari masu zuwan tayi musu jagora zuwa inda babana ke kwance in suka gaisheshi suka ba da abin da zasu bayar tayi amza ia karbe ta saka a cikin yar fos dinta ta koma kan tabarmarta ta zauna ba kuma zata sake tasowa ba sai wasu bakin sun zo daga ni har yaya Dija babu wanda ya daga ido ya kalleta balle ya ce mata kanzil. Kwana tara baba ya yi kafin aka sallameshi a hakan ma matsawar shi ce ta sa aka yi ta saboda yawan maganar da yake yi bai son zaman asibiti bai taba zuwa asibiti don kanshi ba sai dai don ya zo duba mara lafiya, yaya Ibrahim ne ya yi duk wata dawainiya har da biyan kudin sallamar muka dawo gida. Likita ya sallame mu ne bisa dokoki na a kiyaye. bacin ranshi a kula da abincinshi banda gishiri banda barkono banda farin magaji banda kanwa banda yawan cin man gyada. Tun likita yana bayanin baba Lantana ta somna fadin, hu un wannan banda bandan ai ya yi yawa. Yaya Dija ta kalleni cikin natsuwa bayan munje gidamnu da baba tace min debi kayan da zaki diba mu tafi nace mata a'a je ki kawai ni zan zauna a gida, da 17 sauri ta sake källona za ki zauna fa kika ce? Nace e, amma ai kuma kin san gidan ba zai zaunu miki ba a yanzu a yanda take fusacen nan ina nan ma kina jin irin maganganun da take furtawa balle kuma ace na tafi na barki ke kadai. A hankali na daga ido na kalleta kafin na tambayeta, to in muka tafi dukanmu muka bar baba a yanda yake din nan wa zai yi mana jinyarshi? Wa zai bashi magani? Wa zai kula da abincinshi balle ya tsaya yaga an tsare dokokin da aka sa mishi? Tace to kuma haka ne ta bude jakarta ta fito da kudi ta bani tare da fadin, to rike wannan a hannunki kafin inje gida in ga abinda zan iya hadawa nace mata to. Na koma zaman gida tare da baba Lantana da ya'yanta biyu ga kuma babana a kwance yana jinya tunda ko fita runfarshi baya iyawa balea yi maganar kasuwarsu, dan garama dai Sallau don shi kam yayi mana mutunci kwanakin asibitin baba duka tare da shi muke kwana. Duk lokacin da na zo shiga dakin baba Lantana don yiwa babana wani abu ko bashi magani sai tace wai bata yarda ba ina shiga ne ina ganar mata sirrinta shi ba zai sha da kanshi ba sai an bashi kamar wani dan yaro? An wani tasashi a gaba ana shagwabashi ita bata son gulma da iya yi. 18 Babana kuwa shan maganin yake yi a kan dole sai na yi ta rarrashi ina bashi hakuri kafin ya yarda ya sha. Ganin da nayi takurar ta kai inda ta kai ya sa na shiga dakin da Sallau ke ciki yana kwance kan katifarshi na ce mishi, Sallau kawar da katifarka ka .koma can gefe zan yiwa baba shinfida anan don a samu saukin mu'anala, cikin sauri ya ce min to, nan da nan kuma ya mike ya soma yin abinda nace mishin har ya tayani na shiga dakina na dauko katifar da nake kwanciya a kai nad awo mishi da ita nan na shinfida mishi ita naje na samu babana na ce mishi tashi baba mu koma dakin Sallau don zai fi mana saukin zama ya ce min to. Na dawo da baya ina jiran fitowar tashi Sallau ya leko daga cikin dakin yana tambaya ta Mero wannan ai katifar gadoski ce nace mishi eh, ya ce to ki maida ita mana kawai sai ya yi amfani da wannan ni zan rinka yin shimfidar tabarma ina kwanciya, har zance mishi a'a ya barta kawai sai baba Lantana ta taso da saurinta to ai ba tasu bace wannan din da kake neman gwaninta a kanta tawa ce da kudina na sayeta don haka ban yarda ba, ta sake kallonshi cikin wani irin yanayi da takaici yafi komai baiyana a idonta kana tsoronta ne saboda wancan dan iskan ko? Dama ka wartsake kayi hidimarka shima yanzu ta kanshi yake 19 yi sakaraí matsoraci bani katifata ka rinkak wanciyar tabarmar da ka zabarwa kanka. Na kalleta cikin natsuwa na ce mata, to ki fito min da wacce take kan gadonki ai wannan tamu ce tunda ta gadon innarmu ce. Ta zabura kamar zata ki famin mari saboda hakan dana gaya mata ban san yanda akayi ba ta fasa ta kuma bar katifar ta tayi nima naja tawa na mayar kan gadona. Dawowar da babana yayi dakin sallau sai ya bani damar dana rinka kula da shi dama duk wani ala' marinshi ko wane lokaci ina tare da shi komai naga ya dace in yi mishi bana jiran sai ya ce a yi mishi, wanka, wanki, komai a kan lokaci. Duk wannan abinda yake faruwa baba Lantana bata cas bata as kan abinda ya shafi rashin lafiyar mijinta taja ta tsaya kan wai raina mata mukayi ya sa na zo na kasa na tsare a kanshi don haka itama ta cire hannunta kan lamarin shi tunda shi dama abinda ya'yanshi suke so yake bi baya kuma gudun abin kunya na aikata babban laifi bai ce min komai ba ya tasani a gaba yana kallona masu ya'ya mza ma sun hukunta 'ya'yansu amma ni ya yi kamar bai san abinda na yi ba. Yanda dama can babu mai ce ma ta komai in tana maganganunta haka yanzu ma a wannan lokacin ko wani wadataccen girki batayi sai ta ce wai ba a fita an 20 kawo mata ba me zata girka? Don haka kullum gidan a bushe yake babu abinci ni dai ina tsare da cikin babana ba na yarda ya ji yunwa ba na ma zaton ya san baba Lantana bata girki in dai ba ya lura ya gane abinda kalamanta 11a tsakar gida suke nufi ban e. Wurin Isiyaku da ya zo gaida babana da jiki na samu labarin wai ashe Alhaji Muhammadu baban Mubarak korarshi yayi daga gidan saboda samuna da akayi a dakinshi da kuma cin mutuncin da baba Lantana ta je musu da shi cikin gidan tun yana tsare a wurin 'yan sandan wai ya aike mishi cewar in ya fito ya nufi inda ya nufa amma ba gidanshi ba, ya kuma turo har abokan baban sun zo sun b ashi hakuri yaki ya hakura ya tsaya kan bai son sake ganin shi a yanzu. Gabana ya yi mummunan faduwa saboda jin irin hukuncin da baban Mubarak ya zartar a kanshi bayan kuma na san matsayin da yake da shi a wurin iyayena nashi na yi matukar kaduwa, tausayinshi kuma ya kamani har na rinka ganin tamkar ni naja mshi tunda ai ni naje wurinshi ba shi ya kirani ba, cikin zuciyata na ce to abinda baba Lantana ta je kenan tana fadin masu ya'ya maza ma sun hukuntasu amma nawa yana kallona saboda abin kunyar da na aikata bai dameshi ba sai wani lallangabewa yakeyi ina tarairayarshi wai shi nan ga mai 'ya. A wannan lokacin ba zan iya zama in kwatanta halin da nake ciki ba na kunci, takura da kuma bakin 21 ciki a halin dan a samu kaina a ciki, na gane ashe ba auren Alhaji Nalami kadai bane karshen bakin cikin rayuwa ko da yake dai ni a wurina ina ganin tamkar shi ne ya yi min sanadi na shiga duk wani hali da nake ciki, ban kara sanin irin cikin wani hali na shiga wata gagarumar fitina ba sai da na ji Asabe tana rera wata irin waka da na sha jinta a bakin yara ban atba kulawa na gane abinda suke fadi ba sai ko yau da na ji ta a wurin Asaben shị ne na gane ashe wai ni aka yiwa wakar. A wancan lokacin da ko yawan kula, samari budurwa take yi yan mata yan uwanta suke rera mata wakar, mace mai wasa da maza karya nayi mamakin kaina matuka na kuma ga sakarcina da tun asali ban gane da ni ake yi ba wai sai da na ji wakar a bakin Asabe, masu gatama masu ya'ya samari basu tsallake wannan wulakancin ba balleni da bani da kowa in banda babana sannan tun can asali damab a wani farin jini ne da ni ba a tsakanin yan mata da samarin unguwar iyaka dai tsoron Mubarak ya tserar da ni daga duk wani wulakanci ko iya shege da za a yi nufin yi min to yanzu kuwa babu shi kowa kuma ya san ta kanshi yake yi don kuwa wannan hukunci da babanshi zai yi ba sannan a yanzu bama maganar wasa da maza bace mas ala ta an kamo ni ne a dakin saurayi na kai mishi kaina baba Lantana kuma ta sake rattaba bayani a gaban kowa a cikin daren da babu 22 siri a cikinshi cewar ba ranar na fara 'zuwajne kwana a wurinshi ba. Na yi kuka rannan irin wanda na tababtar ban atba yi ba a rayuwata nayi bakin ciki.na rasa inda zan tsoma raina in ji dadi na rinka jin tamkar ina ma dai imsda jlkon bude kasa in 6uya a cikinta saboda tsaranin kunya. Duk inda tozarta ta kai duk inda wulakanci ya kai duk inda muzantawa ta kai kalmomin da suke cikin wakar sun kai harma sun wuce gashi saboda wulakanci da raini sai aka yi anfani da sunana ta yanda kowa zai gane da ni ake yi amma shi Mubarak babu nashi sunan a cikinta, na samu kaina cikin wani yanayi da na rinka ganin tamkar babu wanda ya taba shiga cikin wannan yanayin sai ni kadai. Da kyar na ke iya fita waje sai in dolen ta kama dole ina nufin in zan saiwa babana wani abin in ta kama hakanma sai na yi ta leke naga mutane sun dan dauke sannan ne zan ruga da gudu inje shagon kusa da gidanmu in sayo in dawo saboda yara suna ganina suke fara rera wakar wasu suna anshi cikin tafi sannu a hankalima dana lura sai na gane ba waka daya aka yi min ba kaloli ne daban-daban kara fito da sabbima suke yi, baki ciki in ya dameni sai inji kamar in gudu in yi tafiyata in tafi can inda babu wanda ya sanni in yi zamana sai kuma ince to babana fa, wa zai yi min jinyarshi? Yaya Dija fa ita me tayi min da zan tafi in 23 barta? Sai in tsinci kaina dayin wani tunanin ince to ai ina ji ana cewa babu wam dauwamammen abinda ya ke zuwa ya tabbata, in dai ba ikón ubangiji bane don haka duka binda ake yi zai wuce in rudi kaina da cewar da nake yi nayi na wai watarana sai labari ina fadin hakan kuma zanji zuciyata tana tambayata to yaushe ne naki wataran zai zo? Wanda ni kaina ban sani ba ina raye ne zanga wataran ko sai na mutu ban sani ba tunda ni kam ai kullum al'amurana kara cabal6alewa suke yi bakin cikina kuma yana kara karuwa. Yaya Dija ta zo duba jikin babanmu samuna da tayi cikin wani irin hali ya yi matukar bat amata rai saukin abin ma shine da muka san ba ku yi komai ba amma da ya karbi wanna mahaukaciyar kyautar da kikayi mishi ai da bamu san iyakacin bala' in da muke ciki ba a yanzu amma yanzu kina yin aure shi kenan mijin da ya aurehi da duk wani wanda ya danganceshi zai ce karya ne sharri kawai aka yi mana mai yin sakamakon kuma zai yi mana wato da Mubarak ya taba ni da musibar ta wuce haka kenan bata tsaya ba ni amsar maganar ba sai ta ce min Umman Mubarak ta aiko da kayaiyakinki da suke wajenta ciki kuwa har da wani bakin karfe ta tsareni sosai da idonta kafin ta buda baki ta tambayeni kin gane abinda hakan ke nufi? Nace mata eh, bata bar ni ba sai ta ce min me yake nufi? Cikin natsuwa na ce mata kar in sake shiga 24 gidansu tayi maza ta ce to madalla gara da kika gane hakan, da ya karbi kyautar da kikayi mishin ma da irin korar da sukayi mishi kenan koma su yi wadda ta fita. Ko yake ko dan Umma bata yiwo min irin wannan aiken ba nima ba zan sake dosan gidansu da nufin wata mu'amala ba saboda abin kunyar da ya faru ga kuma irin abinda hakan ya zamewa Mubarak amma kuma sai naji tamkar ba ta yi min adalci ba ko kadan ban ji dadin abinda tayin ba don kuwa ita din uwa na dauketa duk da da itama na sani don Mubarak din take yi min duk wani abinda take yi min. A wannan lokacin sai na rinka iin tamkar tubeni aka yi sirara aka jefar da ni cikin taron jama'a da bani da kowa a cikinsu balle wani mai taimako amma kuma ban yarda na munawa yaya Dija tsananin damuwata ba don kar in kara mata tata damuwar tunda har itama marasa atuncin yaran unguwarmu in suka hangota rera mata wakokin suke yi kasa-kasa amma ba da karfi ba kamar yanda suke yi min. Sannu a hankali sai babana ya saau sauki har ya Soma fita kasuwarshi saboda tababcin da likita ya bayar na jinin nashi ya sauka amma ba ana nuiin ya warke ba ne shi jini in ya riga ya soma hawa to ba a daina sha mishi magani don ko wane loakci zai 1ya tashi, wannan shi ne bayanin da likitan ya yi mana a ranar da mukaje ganinshi ni da baban nawa. 25 To Dr. Meke kawo ciwon hawan jini? Na yi mishi tambayar don in kara sani, sai ya ce min akwai jinsin mutanen da ke da jini wanda yake da irin wannan matsalar su ne masu yin ciwon a dalilin sun gajeshi sannan Wasu yakan sansa a dalilin tsananin damuwa ko kuma yanayin abincin da ake ci shi yasa yake de kyau mu rinka kula da abincinmu mu kiyayi abubuwa marasa amfani irinsu gishiri, barkono, kanwa da makamantansu, sannan mu rinka yawan motsa jiki, motsa jiki yana da amfani kwarai ga lafiyar jikiumu kin gane? Nace mishi eh Dr. Na gode. Rike wannan bayanin da likita ya yi min da nayi sai na ejiyewa kaina ya zama ka'ida kullum in baiwa babana magani kwaya daya da kuma yayi min korafi kan maganin yana sashi yawan taba ruwa sai na mayar mishi da shan amganin nashi a lokacin dare haka nan jin saukin babana baisa na fita hanyar kula da abin karyawarshi ba ko da kuwa iyakar abinda nake da shi kenan saboda na iga na gane har da yunwa cikin rashin alfiyar tashi, ina kuma yawan gaya mishi cwar baba ka rinka shan timatir in ka gansu masu kyau kana kuma cin danyar kubewa kar kuma ka rinka yarda mai kankana ko ayaba yana wuceka baka saya kaci ba komai kankantarshi ya ce min to. Baba Lantana dake yawan kasa kunne wajen sauraron maganarmu ta ce eh 'yan kudin da yake kawowa wadanda dama ba isar mutane suke yi ba su 26 ne.kike koya mishi yanda zařtinka cinyesu a waje ba saboda. sharrinki kankana da ayaba kuma maganin me suke in ba iya shege ba. Babana ya fara fita kasuwa sai dai abin mamaki shi ne ashe wai har shima bai tsira daga wakar da ake reramin din ba in an ganshi sai a yi tayi wasu 'yan iskan su rinka nunashi suna fadin shi ne mutumin da aka kama' yarshi a dakin saurayi har a dalilin hakan mijin da zai aureta ya ce ya fasa auren shi sauranyin ubanshi ya koreshi a gidan shi amma shi yana tashe da tashi 'yar a gabanshi sai ma kara sonta da ya yi. Wasu su ce to ance duk abin da take samowa shi take ba wa, ai mafi yawancin iyaye yanzu in dai ya'ya zasu basu kudi to magana ta Kare sai su yi abinda suka ga dama suna kallo kai amma kuwa to tir, wato shi yana can yana kici-kici da tashi matar itama ana can ana kici-kici da ita kenan? Sai a kwashe da dariya. Su m a yaran dake cincirindon sayen timatirin babana har ana layi ba a barsu a baya ba sun daina yayen su ng suka hanasu ko su suka hana kansu saye sai su saka sauri hatta rijiyar gidanmu da bata kafewa wacce kullum baba Lantana ke fada da masu zuwa diban ruwan cikinta su ma yanzu ba a zuwa diba. A wannan lokacin kusan kullum sai anyi kwashen timatir babana ya zama bage tuni sai jarinshi ya soma rushewa sai mai kawo kwandunan timatir 27 attarugu tattasai albasa alaiyahu kubewa masu yawa sai ya zamo da kyar ake hada kudin daidai don haka in tsaya fadin an shiga wani halima a gidanmu na tsaya bata baki ne kawai. A wannan lokaci saboda samun wuri Asabe abinda ta ga dama talke yi min ina kallonta bana cewa komai sabdoa yanzu yanzun nan ne zata fara rera min waka in taga fuskata ta canza ta ce ba ni na kar zomon ba raiayc kawai aka bani, bana tanka mata don nasan bani da yanda zanyi da ita in karfin dambe ne ta jini gatan da nake da shi din da yasa ake tsorona babu shi banma san inda yake ba ga kuma aiken da Ummanshi ta yi min daga gidansu wanda nasan na nuna karshen mu'amalata da su ne. Asabe tana cikin tatamin irin tsiyar da taga dama ne rannan na farka cikin dare na ganta tana kwarara amai a cikin wani kwano duk da tsananin tsoratar da tayi da ganin da nayi mata ban gane abinda hakan ke nufi ba, na hadaki da girman Ubangiji kar ki gayawa baba kin ganni ina amai ba zan sake yi miki wakar da nake yi miki ba. Naceki yi mana ni ance miki wakar ta dameni ne? Amai kam ai sai na gaya ma ta na ganki kina y1 a kwano. Tayi ta bani hakuri mamakinta yayi ta kamani ko ina ruwana da ita da uwarta da zanje ina cewa na ganta tana amai oho? 28 Tun daga rannan Asabe ta daina nemana da tsokana a fita hanyata da abubuwa iri-ii abin sai mamaki yake ta bariï sai a ranar da yaya Dija ta zo gida ne ina rakata take tanmbayata nalin da muke ciki da Aabe na bata labarin abinda ya faru sai naga ta ja ta tsaya tana kallona cikin natsuwa kafin ta ce min, akr dai ciki ne da yarinyar nan? Kai haba gashi yau na ganta ta canza to ita uwar ta ta ba zata ganc ba sai an gaya mata wacce irin shashashar uwa ceh aka? Shiru nayi cikin tsananin faduwar gaba, ciki? Na yiwa kaina tambayar a cikin raina. Ai baka cima masharranci sai ka yiwa kanka mafi yawancin lokaci ai abin da ake yiwa dan wani shi yake samun naka ki ja bakinki ki yi shiru karki yardaki yi abinda uwar ta ta zata gane tunda ita mahaukaciya ce nace mata to... Rannan ina zaune a tsakar gida ina hidimar wankin kayan babane bayan na gama nawa a yanzu bana fada da kowa saboda Sallau dai mun dan shirya da shi tun daga kwanciyar asibitin baba da kuma lura da nayi naga yana mutuntamin baban nawa, Asabe kuwa tsoro take ji karmu yi fada in fadi abinda ta roke ni kar in fada bata san ma ni ko munyi fadan ba fada zanyi ba tunda yaya Dija ta ce min kar in fada. Cikina ne ya yi wani irin kuka na tunanin da irin dadewar da nayi ban bashi wani abu na hatsi ba, na waiwaya a hankali na kalli Asabe da baba Lantana da 29 suke zaune cikin rana wai suna shan hantsi su ma zazzare idanu suke yi nuna alamar yunwar su ke ii kamar ni tunda a yanzu duk mun zama daya ni babu su ma babu, yanda nake kaiwa Azahar ban karya ba haka su ma suke kaiwa har gara nima yunwa bata cika gigitani ta fitar da ni cikin haiyacina ba don kuwa da ana sabo ko wani kawance da ita to da na ce munyi ba a yi ne kawai yasa ba zan fadi hakan ba amma duk da haka zan iya cewa na saba jinta haka nan a duk halinda nake ciki bana rasa wani dan canji kulle a bakin zanina wanda nake dan tsakura ina baiwa babana abin karyawa in ayso ni in hakura don bana yarda ya fita su kuwa nasan da kyar ne in suna da wani abu. A wannan lokacin a gidanmu rashin yin girki bai zamo komai ba tunda baba Lantana tana kin yin girki da gangan yanzu mai dalili ya sameta, kasuwar babana ta yi kasa jarinshi ya yi matukar karyewa tun yana kawo mata dan cinikin da yake yi tana rainawa tayi watsi da su ko tayi ta zage-zage tana tambayarshi wadanann me za su yi mata har ta hakura ta zuba ido don ta gane abin bana kare bane tunda kullum raguwa yake yi sai da ta kai ma tana tambayama ace mata ta yi hakuri tayi ta maganganu to yanzu babu kawai yake cewa ya ja bakinshi ya yi shiru ya barta ta fadi duk abinda take son fada. 30 A wannan lokacin sai ta zama bata da aiki sai na fushi ko mita ko ka ji ta tana baiwa Asabe labari irin zaurawan da suka nemeta wai ta kisu ta auri babana sai ta yi kwafa ta ja tsaki tace, to rabon wahala ni kuwa sai in kyalkyale da dariya tayi ta zagina, Asabe tana kallonta bata tsoma baki nima bana cewa komai baya ga dariyar can cikin zcuiyata ina kiranta da sunan da na saba jin Alhaji Nalami yana kiranta wato Butulu. Muna cikin wannan zaman ne muka ji an kwada wata irin sallama a kusa da kofar shigowa gida gabana yayi mmmunan faduwa arnma kuma nasan na baba Lantana yafí nawa faduwa saboda yanayin da na gani a tare da ita tun kafin ta kai ga amsa salalmar tashi sai gashi ya fado tsakar gidan. In ce ko da ba za a amsa sallamar tawa ba ne? Ta soma kame-kame tana rantse-rantsen wai bata ji salalmar tashi ba nan da nan ta shiga yi mishi oyoyo tana sannu da zuwa cikin sauri ta shiga ta dauko mishi shimfida tana yi tana, habawa yaya za a yi inji sallamarka in ki amsawa to a wanne dalili? Ta gyara zama, yana fadin a dalilin cuta mana aike tsunma ce. Na mike na soma tsince kayana da suka soma bushewa na wuce na nufi dakina cikin zuciyata ina kokarin danne dariyar rawanin da naga yayi wanda yafi kama da na waziri aku. 31 Rawani kuma Alhaji ya koma yi? Tayi tambayar cikin yanayin sakin füska da fara'a, ko an baka wata yar sarauta ne ban šani ba Alhaji Muhammadu? Ta sake janshi da watą rahar. Ya kara tsuke fuska saboda watakila fara'ar tata ta yi mishi yawa, kinga bana son irin sunayen da kike kakabg min ni, naje Makka*ne da kike ce min sunana Muhammądu? Nalami kawai sunana kenans hi na fi so shi nafi sani. Ta yi murmushi Alhaji ai sunan mai niyya ne bana wanda ya je bane, Muhammadu kuwa ai sunan maza ne menene aibi don an kiraka da shi tunda Nalami ai ba sunan gaskiya ba ne. To ni shi nafi so da shi aka yanka min ragon suna ko sai ace bai yanku ba? Ta ce ya yanku, ya ce to ni ba ma wannan ne ya kawoni ba. To ka cire rawanin naka mana ka sha iska. Ya yi maza ya ce na ki din in cire yaran unguwarku da basu da tarbiya su hangoni su zo su kara sani ko? Ko da yake an gaya min cewar ke kika biyasu kika ce musu su kasheni in nazo wurin daurin auren to ta Allah ba taki ba gani nan daramin gabanki da raina da lafiyata. Da sauri ta tambayeshi ni? Insa a kasheka ake wane dalili? A dalilin dukiyata da kika karba man tunda ai an gaya min komai ba kudina ni kadan kika ci ba, tayi murmushi, wanda ya gaya makan bai gaya 32 ma kag gaskiya ba, niikam ai ina nan a kan bakana tunda dai kaima ka.ganta da idoka tana nan ba... .Ba ta karasa ba ya ji maza ya ce ma ce a'a bana so ina? Ai wautar tawa ba ta kai haka ba ai ni kuma kin, sanni ba a cutata: sau biyu ko da yake dai ke zatiddawahice ko gamsheka bata kaiki sharri ba wato in sake dawowa da sunan karbar aure don ki samu su karasani ko tunda burinki bai gama cika ba a kaina to naki bana son auren shiga kawai ki fito mirn da abinda kika sani nawa sauri nake yi. Ban san yarıda akayi ba naji baba Lantana ta rage murya, tayi wata magana sai dai kuma shi bai rage muryar ba wajen bata amsa don haka na gane abinda ta ce mishi. Asabe kuma? In zo in auri Asabe to a kan me? Ai dai kasan ba finta komai tayi ba tunda ita Asabe ma ga kirji a cike ga mazaunai ga diri ita wannan ai haka singul take tsawo ne kawai kamar sanda. Ya yi tsaki ya ce ai duk a banza gara ma singul din ita Asabe in ita nake so ai 1asan inda zan sanieta bani kudina akwai. Ranta ya 6aci da jin maganar tashi cikin yanayin fusata sai ta ce mishi karfa ka ce zaka yi min wulakanci ina binka cikin sauki kana sake baki kana caba min ma gana da wasu labbanka masu kama da saukan markade nawa ne kudin naka? 33 Ya gyada kai una alamar gamsuwa da jin maganar ta ta cikin natsuwa ya ce basu da yawa kawo min su in tafi in bar miki gidanli jaka bakwai ne. In banda baba Lantana a zaune take sanda ya ambaci jaka bakwai din nan watakila da ta fadi kasa warwas saboda tsananin kadirwar da tayi, a'a jaka dari zaka ce ba jaka bakwai ba in ka tsaya a jaka balkwai ma ai sharrinka bai kai sharri ba la'anannen tsoho kawai matsiyaci da ma abidna ya sa ka zo kace in baka ita kenan don ka samu damar kullamin sharrin daka dade kana son kullamin? To bani da su ban ma san su ba. Nan take kuma ta soma rusa wani irin kuka. Ban yi mamakin ganin gigicewar baba Lantana kan ambaton kudin da Alhaji Nalami ya yi ba saboda a wancan loakcin jaka bakwai din ba karamin kudi bane kudi ne da ake iya siyen gida da su kudi ne da akc iya biyan aikin haji da su har aje a karbi guzuri na zunzurutun kudi dalar Amcrica dubu daya a can kasa mai tsarki, haka nan ko da ban san abinda yake tsakanin baba Lantana da Albaji Nalami a kan maganar kudi ba to nasan shi Nalami zaiyi wuya warai in yana da kudin da suka kai jaka bakwai balle ya iya bada su saboda bai da kamannin wanda ya mallaki irin wadannan kudaden. Yanzu nan banda fam hamsin dinika guda uku da ka bani ka taba kawo wani abu bayan nan ka bani? Sai da ya kara juya mata keya kafin ya ce, fam 34 hamsin hamsin sau uku wasa ne? Tunda kika ambanci wadannan da bakinki ai sauranma zaki fito da su ai kin yi kokari ni kam ma ai duka nayi za ki ce ban taba baki komai ba küma in ma iyakar abinda na baki kenan to zaman nawa sukayi a wurinki? Da a wurina suke ina ta juya abina da yanza nawa suka zanma? Sannan dukan tsiya da kiką sa aka yi min fa? A nawa dukan yake? Nawa kuma na kashe wajen yin jinyar kaina? Dankwala dankwalan kajin da na rinka sayowa ina kawo muku kuna ci ke da mijinii da su lemon gongoni da na kwalaye fa? Su a nawa suke? Ko kina nufin za ku ci bulus ne? Sannan kwana nawa nayi ban fita kasuwa ba a dalilin jinayr? Zan dau asara ne? Ai kema kin san riba nafi ganewa ba na fahimtar asara. A fusace ta ce mishi to asara kam sau nawa kayi ta a rayuwarka? Babbar sana'arka fa daudu ne? Yayi maza ya ce yaurwa ga kudin kulla sharri da bata suna ai hada lissafni koami nayi n8 rattaba wuri daya don haka ki bani kudina tun muna sheda juna dake cikin mutunci tun bamu kai ga wulakanta juna a bainar jama'a ba don ba zai zamomin komai ba in kai maganar gaban alkali in kira masu sheadr zur mu yi lada da su su je su yi rantsuwa su yi min sheda gaban alkali ya karfar min kudina in biyasu ke ni na yarda ma in bar musu kudin duka su cinye zaifi min dadi akan ace na bar miki su. 35 Fita min daga gida fita tun ban kira yara sun zo Sun nada maka dukan tsiya ba, tayi maganar cikin wani yanayi dake kara baiyanar da tsananin bacin ranta. Ya yi murmushi to ai gara ki hanzarta yin hakan kinga inda sai na tafi neman shedar zur kafin in samu biyan bukata a kotu sai ya zamo ba sai na yi hacan ba zan samu don hakan zan sake gaya mikiki bani kudina da na gaya miki jaka bakwai ko kin san tunda na ambacesu zan karbesu ai kin sanni sarai nima na sanki ni dake kar ta san kar ne kin san abinda zan iya da, Wanda ba zan 1ya ba, ya rantse da kwarankwatsa da aradud a matsattsaku in baki bani kudin nan ba, Ya gyada kai nuna alamar wani babban abu zai auku ko yanzu din nan in gaya niki babu fa inda zani sai kin bani don ba zai zame min komai ba in kwana a kan gadon da mijinki ke kwanciya irin kuma tsakaninku bari ma ki gani. Yayi maza yu mike ya nufi hanyar shiga dakinta itama tayi maza ta sunkuci tabarya taje gabanshi ta tsaya. Kasheni kenan za i yi da kika sunkuto wannan shirgegiyar tabaryar kamar za ki kashe maciji. Ai gara maciji da kai Nalami ai kai tsohon banza ne tsohon najadu wanda ya tsuta bai san ya tsufa ba kullum kai kenan kana riga fuska da jiki da shuri don na kashcka ai babu abin da zai faru shigowa kayi cikin gidana wadanda suka sanka kuma sun san 36 mugun iri aka rage shiga dakin ka grni yanzu in ba nuna maka kai din lalataccen tsoho bane matsiyaci. Cikin duk zagin da baba Lantaria tayi msihi Da lura babu abinda yafi tsaya mishi a rai irin cwar da tayi mishi lalataccen tsoho don abinda yafi nanatawa kenan, ni ne lalataccen tsohon? Wato ni ne tsohon kuma ma lalatacce? Yanzu nan ni tsoho ne? Tayi amza ta ce na banza ma kuwa. Ganin da yayi ta fara yi mishi cin mutunci irin wanda bai zata ba ya sa shi hamzarin fara kudundumarta yana rantse ranste saukin abin ma shi ne yana jin tsoron daga murya don gani yake tamkar in yaran unguwa suka gane shi ne zasu shigo su sameshi anan din sa karasa aikin da suka fara, amma duk da haka sai da suka kacame suka haura sama suka sauko sai kuma na ji su suna daidaitawa a kan yanda zasu y1 su warware lamarin a tsakaninsu ba tare da wasu sun ji maganar ba da kanshi ya ce ya yi mata ragin jaka biyu ta nemi biyar ta ajiye mishi amma babu sauki a haka don kar ta ga ya yi mata sassauci ta dauka ko tsoro ne yana dai so ne kawai su rabu lafiya saboda darajar tsohuwar sanaiya ba a san inda za a sake haduwa ba. Kai kam bana fita in sake haduwa da kai a ko ina har abada kuma. Ya ce to ai shi kenan ni kam ai duk mutumin da na sani bana yardamu yi rabuwar banza ni dea shi don 37 ban san abin da gobe azta haifar ba a tsakaninmu na tafi zan dawo bayan wkana. bakwai ina fata in zo in samu kudina a ajiye. Bai jira amsar ta ba ya sa hannu ya gyara rawaninshi ya sa kai ya fita ya bar gidan. Yana fita daga gidan yanayin baba Lantana ya sake canzawa kana ganinta zaka gane ta tsunduma cikin wani irin al'amari da ita kadai ta san abinda take ji maimakon ta ja bikinta ta yi shiru ko don ta huta gajiyar cacar bakin da sukayi tayi dana Nalmi sai kuma ta shiga kurme kurmcn asahar da isine tsine wanda yawanci ni take yiwa. Wannan tsinannen aure da me ya yi kama? Haka kawai ni banci nanin ba nanin zata ci ni, jalka biyar? To jaka biyar ina na ganta/ ta sake rushewa da wani sabon kukan. Watakila Sallau ya gaji ne da ji ko ganin abinda ke taf aruwa ya sa shi buda bakinshi ya ce mata to wannan abin duka baba ai ke ika jawa kanki in ba haka ba yaushe ake haka ba fa ke kika haifi yarinyar nan ba da ya ce ki bashi ita ai sai ki gaya mishi ba taki bace, amma ba ki yi haka ba sai kika je kina ci mishi kudinshi kina shirya yanda za a yi a bashi ita ba tare da kin nemi hadin kan ta ba, ita gaskiya ai guda daya ce daga kinta kuma ance sai 6ata, mai kwadayi kuma kowa ya san yana tare da wulakanci yanzu wannan jaka biyar din.... 38 Ban ji karshen zancen ba sai ca ji saukas mari mai karfi kau, bai sake cewa koami ba haka nan itama. Washegari da safe babana ya yi shiri zai fita kasuwar timatirinshi nima na yi maza ne zo na tareshi da abin karyawar shi dana shirya misali wanda kunu ne kawai sai yan kosan da basu da wani yawa a dalilin ina tattalin kudin da ke wurin nawa saboda sun kusa karewa ban kuma hango wata hanya ta zuwan wasu ba sai dai addu'a kawai da nake tayi na neman rufin asiri wurin Ubangiji. Yaya nake ganinka wani iri hak baba? Nayi mishi tambayar saboda yanayin dana gani a tare da shi. Jikin nawa ne bana jin dadinshi bani da keri ina kuma ganin wasu abubuwa kamar 'ya'yan sama suka yi min yawo a idona. Ya'y,an rana suna yawo baba be jinin ne yah au ba? Shi ne ba zaka gaya min ba zaika kama ita a haka? Na soma yi mishi kuka sosai, a'a to menene in na fi tan'? Na kalleshi kafin na ce mishi to baba amma in kaje kasuwa kaje ka fadi fa? Ai ka bar fitar kawai ka shiga daki ka yi kwanciyarka in kaji sauki gobe si ka je. Bai yi magana ba na dauke kwandon tumatirin nashi naje na adana, ya yi min magana a hankali, to in na kwanta me za a ci a gidan ne'? 39 Tana daga daki tayi maza, yauwa gara dai kai da kanka ka yi mata wannan tambayar ta baka amsar. Nayi kaar ban jita ba-na ce, to in babu abinci a gida baba sai kaje kana jiri a cikin m utnae kana faduwva suna kwasokasuna kawoka gida? Lafiyar ka bata fiye mana komai ba? Na soma uke, saboda yawan ciwon nashi yana daga min hankali, loakcin da kake da shiai Ciyar da wanda ya kamaka dama wanda bai kamaka ba yanzu kuwa da baka da shi sai kowa ya yi hakuri wanda ba zai yi ba kuma ya san abinda yake ciki. Ke na ce ke za ki zage ni ne? Na ce ba zan zage ki ba amma kuma ba zan barki ki tura min uba cikin halaka ba ina kallo shekara da shekaru ya yi yana kawowa don yanzu bai kawo ba kuma babu mai takura mishi, jeka ka kwanta kaji baba? Tayi maza ta ce, to ba dai dakina ba don ban ga yanda za a yi namiji ya kwanta mia a gado zankwankwan ba don takamar zuciyarshi ta mutu. Na sá hannu na bude dakin Sallau ya shiga, kwanta kan shimfidar shi, cikin raina na tabbatar da ma can dole ce kawai zata fitar da shi amma ba dadi yake ji ba. Yana kwanciya na sake daukan kwano naje na sayo waina da miya na kawo mishi yaci ya koshi har ya rage sannan na kawo magani na bashi kamar yanda likita ya gaya min in tafiyarshi kalau ya sha sau daya in da alamar motsawar jiki ya sha sau biyu kafin mnu zo ganinshi, ya kurkure baki ya gyara ya kwanta nima 40 na dawo dakina a cinye masar da ya ragen na wanke kwanon na kife kafin naci gaba da harkokina. Ina dakina a kwance ina sauraron farkawar babana sai na jiwo baba Lantana tana kiran Sallau da sabe wai suje su karfbi abincisu ta gama girki na tashi naje na dauki kwano na kai mata a zubawa babana a nan in kai mishi nashi. Wani irin lalataccen kallo tayi min kafin ta ce min yana daga kwancen ne zan rinka yin girki ina bashi yana kalmasa baki yana lamushewa? Ba ya ce bashi da lafiya ba mai ciwo yana cin abinci ne? Na zuba mata ido cikin tsananin mamakin kalaman nata kafin ince mata komai sai ta ci gaba ai ba nice zan ciyar miki da shi ba ban yi miki wannan alkawarin ba duk ran da kika sashi ya kwanta a gida yaki zuwa kasuwa toni kuma babu shi a abinci na kin ganima don ki kara sanin banyi dashi ba kin ga barkono ga farin magi ga gishiri duk a ciki na zuba in kuma ke ce za ki fake da shi ki ci to banyi niya ba ni ba baiwarki ba ce in kin kallem kuma za ki gane ni ba matar da za a mayar baiwa ba ce. Ban san yanda akayi ba naji bakina ya kama ce mata, to me kike da shi da za a ce ki ciyar da baba? Nace mai ciyar da miji in ya rasa ai babbar mata ce wacce ta san rama alheri da alheri ba mai ci ta goge baki ba saboda butulci. 41 Ina fadin hakan na ga Asabe ta fito daga dakinmu da gudu tana tambayata zaki zage ta ne? Tun kan in amsa baba Lantana ta soma kuka tana fadin to zagi kam na nawa ai ta riga ta zageni. Kan in san menene abin yi tuni har Asabe ta rufeni da duka tana tambayata wannan wane irin raini ne a gabana za ki zage ta. Sanin da baba Lantana tayi na kullum mukayi fadan dambe tsakanina da Asabe ita ke kwarata ya sa wucewa tas higa dakinta ta barmu muna danben. Danbe mai tsanani muka fara yi sai dai ba a je ko ina ba sai ga shi na sunkuceta na fyadata da kasa a gigice ta kurma ihu mai tsanani wanda ya yi dalilin fitowar baba Lantana cikin sauri da kyar ta iya banbareni a kan Asaben tana rabamu ta nufi kan Sallau ta wankeshi da mari, gigitaccen mari tambayarshi kana kallo aka yi hakan ina amfanin zamanka a wurin? Ya ce uhun baba kenan kema ba kina kallo aka fara ba kika wucekika tafi? Ni na daina irin wannan abin na daina shigarwa kowa fada ni dukan su daya ne a wurina dukansu yan uwana ne in banda rashin kunyar tsiya meke hadani da Asabe da zanje ina tayata fadan rashin gaskiya. Tayi ta zage-zage da addu'o'in da ta ga zata iya yi mishi. Ina daki ina jinta tana cewa Asabe ke dama baki shirya fadan ba kika zo kika rarumeta? To dame 42 wannan abinda kikayi yayi kama ai in ba sake danben nan aka yi ki ka yi mata dukan tsiya ba to raini kawai kika kara jawa -kanki a tsakaninku da can da kike dukanta ma yaya kika kare da wulakancinta balle yanzu da ta jibgeki ta yi miki irin wannan kayarwar? Lalle ne na gaya miki daga nan zuwa gobe ki san abinda kike ciki da ita. Duk da na ji maganganun baba Lantana banyi nufin sake yin wani fadan da Asabe ba don nima na fi ganin tsananin sa'a ce ta sani kada ita, amma da gari ya waye da safe naje na sayowa babana abin karyawa zan wuce ta ta sa hannu ta kabe min shi ya kife a kasa na daga ido na kalleta cikin salati mai karfi naji ta ce min, wai rama abinda nayi mata jiya tayi inji in da dadi ai gurin danben da na jata da shi ne na yi dalilin kifewar abincin ta sai kawai na ji tsoron ya gushemin ban tsaya tambayarta yaushe aka yi hakan ba sai na sunkuya na kwashe abinda zan iya kwashewa naje na ajiyewa kaina na sake daukan wani kwanon naje na sayo wa babana wani na kawo mishi sai da naji ya gaya ci na bashi maganinshi ya sha sannan na fito na shigo dakinmu na kama diro da kayan Asabe ina yin watsi da su a waje ina fadin in baki rama abinda nayi miki ta hanyar wulakanta abincin da ubana zai ci ba ai ba zan kara gane ke baki da uban ba Asabe wanda ya san darajar ubanshi ai zai san na uban wani don haka 43 yau za ki bar min gidan nawa uban tunda ya rufa mi1k asiri baki gane haan ab. Da gudu ta baro wurin baba Lantana da suke tare ta 20 zata rarume ni nayi maza na juya kanta muka rincabe da danbe ba a je ko ina ba yauma na raruma Asabe na dagata sama na fyadata da kasa. Baba Lantana tana ganin haka ta zabura da gudu ta dauko itace wai zata bugamin tana fadin na gaji da danben rashin da kike yi min a gida don haka yau za ku gamu da ni za ku ji a jikinku kumą ta fara nufowa da itacen nata nayi maza na kamashi na rike na kalleta cikin natsuwa na ce mata babu sauran duka a tsakanina da ke wanda kikayi min a baya ya isa, na sakar mata itacen ya fadi kasa. Ta zabura ta nufi dakin da babana yake kwance tana fadin, ina malam din yake kana jin abinda yake faruwa amma kayi gum. da bakinka kamar. na yi maza na katseta ta hanayr gaya mata cewar ya isa haka kar ki sake zaginshi a gabana kar kumaki nemi ki daga mishi hankali. In nayi hakan me zaki yi? Za ki buge ni ne? Ban ce mata komai ba na wuce na nufi dakinmu. Sallau ya ce uhun baba kenan ai ba ki yarda ba ne da kin yarda....kan ya karasa ta sunkuci itacen da tazo da shi din ta shiga rafka mishi tare da fadin zo ka bar gidan nan zo ka tafi. 44 Ai babu inda zanje baba in dai ba baba da kanshi ne ya koren ba ban taba samun inda na zauna lokaci mai tsawo a rayuwata ba sai da na zo hannunshi in har kuwa ki na so in atfi to ki kwatantamin inda zan samu dangin ubana tunda kin ce wai ya mutu su kam in kika nunamin su to ba zan sake zuwa inda kike ba sai don gaisuwa amma haka kawai ba za ki kora ni in shiga duniya ba. Na fito daga wanka na kalli A sabe na tabbatar jikinta yayi matukar sanyi kan abinda ya faru tsakanina da ita jiya da yau nace mata haka a yanda kike na fama da abinda kike fama da shi kice zaki buge ni ina budurwa gal a leda? Ai ke ma kin san Karya kike yi ubana ai ya rufa muku asiri dukan ku. Daga ita har baba Lantanan babu wacec ta tanka min iyaka dai na ganta tayi wanka ta shirya ta fita ta bar gidan ta tafi, nima nas hirya na nufi gidan yaya Dija na gaya mata halin da jikin babanmu ke ciki sai dai ban zauna ba na dawo gida. Ina shigowa na samu baba Lantana tana rabon abinci nayi maza na kwaso kwanuka guda biyu ance mata ga nawa ga na babana, tayi kamar ba zata zuba ba ban san tunanin da tayi ba sai kuma naga ta dan minmindira mana a zuciyata nace oho na dauka na tafi na kaiwa babana ya ci ya rage sannan naci, ban wani dade da dawowa ba sai ga yaya Dija ta iso babana ya yi ta fada kan zuwan da nayi na gaya mata. 45 Ta ce to baba za ka yi ta ciwo ne ban sani ba? Ya ce to wannan ciwo da ya riga ya zama jiki ai ba kullum ya tashi ne za a je a fada ba tunda dai ikitama ya riga ya yi bayanin shi cewar ba a warkewa shi abokin tafiya ne, nayi maza na ce a'a baba ba fa haka ake nufi ba ai kca da hanyar tafiyar shi bai kuma zama dole don kana da shi a ce shi ne abokin tafiya ba ai ana jin saukin shi. Ya ce uhun fata dai ai bai wuce na rokon ubangiji ya bamu sa'a ba rmuka ce amin. Ta gima abinda zata yi ta fita zata tafi na bita ina yi mata rakiya ina bata labarin abin da ya faru tsakanina da su Asabe da uwarta sai dai babu alamar natsuwartı tana tare da ita saboda yanda na ga tana ta faman har dewa har tana buga tuntube. Yanzu nan har yanzu wadannan mayun yaran basu dain aw adannan wakusn naSu na sharri ba? Na ce mata ch, tyo amma shi ne kike fita? Na yi murmush na ce to vaya zanyi? Ai ya zama min dole in fi ta ta ce haka ze hausawa suka ce wai watan kwaram daya ne in ya mutu sai na wnai ya kama amma mu namu watan kwaran din bai zamo guda daya tunda yau waien kwane sittin ne har da bakwai har yanzu bai mutu ba, bance mata komai ba shiru kawai nayi har ta gama maganganunta muka yi sallama na juyo gida. Da daddare ina zaune a dakina ni kadai saboda tunda Asabe ta fita ta bar gida bata sake dawowa ba 46 shirin tafiyarmu asibiti nake yi gobe saboda umarnin da yaya Dija ta bani kenan ta kuma kawo mana kudin zuwa asibiti. Ina cikin kammala abubuwan tunda nasan sai munyi sammako sosai ne zamu iya ganin likitan a kan lokaci sai ga Sallau ya daga labulen kofar dakin tare da ya min magana a hankali, sannu Mero. Na daga kai na kalleshi, yauwa sannu Sallau, ya ya mai jikin? Na ce mishi da sauki. Ya sake rage muryar tashi ta kara yin kasa kafin ya ce min da wata shawara nazo da ita ban sani ba ko zata samu karbuwa a wurinki. Na ce to shigo màna in ji shawarar, cikin natsuwa ya shigo ya nemi wuri ya tsuguna kamar wani mai shirin biyan bukata. Da ka zauna ai kamar zai fi yi maka dadi, a'a babu damuwa, na ce to shi kenan me ya faru? Ya danyi kame-kame kadan kafin ya iya fitowwa sosai ya yi min bayanin rumfarn an ce ta baba da kullum in bashi da lafiya ake rufeta babu kowa tumatirin ciki dama duk wani abinda ake da shi su yi ta lalacewa tunda ba masu jirar zaman bane shi ne nace ko zan rinka bude ta ne ina zama a ciki? Sanin da nayi da gaskiyar magana Sallau din ya fada na kuma san in ma ban barshi ya bude rufmar ya zauna ya dan taba abinda ya taba na cikina ba to duk ranar da aka budeta za a kwashe komai ne a zubar tunda za su gama lalacewa to da a yi irin wannan asarar kuwa 47 gara ko ba zai baiwa baban koami ba ya bude ya sayar, nasan shi zai dan samu wani abu don haka sai na kalleshi na ce mishi, to ai hakan yana da kyau Sallau gobe da safe sai kaje ka bude tunda shi baba goben zaije ganin likita, ya ce to Ubangiji ya sa mu gani lafiya, na ce mishi amin. Washegari da yamma mun dawo daga asibiti bayan sallar La'asar a dlailin dogon layin da muka tarar daga nesa na hango Sallau a cikin rumfar baba yana tashe da yan timatirin da suka saura muka wuto shi muka shiga gida sai kusan magariba ya dawo ina kallonshi bance mishi komai ba baya ga gaisuwar da muka yiwa juna sai da ya tabbatar baba Lantana ta shiga dakinta ta kwanta sannan ya turo kofata ya shigo a hankali gaba daya cinikin da ya yi ya zube min a gabi.na na zuba ido ina kallo nace a'a ciniki mai kyau aka yi ne haka Sallau? Ya ce eh an dan taba kadan, to madalla na fada ina mai sauraron abyaninshi sai da ya gama na ce mishi, to su wadannan kudin sai ka rikesu kawai a wurinka ba ka ce kayan bai karasa karewa ba? Ya ce e, na ce to daga nan zuwa biiba ya gama jin sauki sai mu ga abinda za a yi, ya ce min to sai da safc ya fita. Kwana uku bayan nan baba ya fara bude rumfarshi bayan ya saro wani sabon timatirin a dalilin saukin da ya samu ban san yanda akayi ba sai na ganshi tare da Sallau suna zaune a rumfar tare shi 48 yana can ciki a zaune Sallau yana salalmar masu zuwa saye, ni ma kasuwar zai tafi sai ya tasashi a gaba su tafi tare. Rannan ina kwance a kan dan gadona na bono da hantsi bayan na yi wanka na shafa man basilin din babana saboda gaba daya kayan shafana sun kare bani da komai in banda man wanke baki. Ina cikin tunanin halin da nake ciki ne sai kawai na ji an kwala sallama, ina jin sallamar na gane wanda ya yi ta nan take na shiga lissafin rabonshi da gidan yau zuciyata ta tunamin kwanaki tara ne cif. Sallama dai sallama dai, na fa iso na kuma san ana jina yauwa ita rana ai bata karya sai dai ko uwar diya ta ji kunya, to ni don kar a ji kunyar ma sai na mutunta na kara kwanaki har biyu kan alkawarin da aka yi min din, ga zatona za a biyoni da su har rumfata a mutunce to da ban gani ba kuwa gani na taho karbar halali na. Baba Lantana ta fito daga dakinta dankwalinta a hannu fuskarta kuma a daure abinda na tabbatar shi ne bata yi azton zuwan nashi ba a yau don kuwa jiya da shekaranjiya da ta yi tsammanin zuwan nashi tun sassafe take barin gidan bata dawowa sai cikin dare. Ah naso karbar halalina ya yi maganar cikin wani irin yanayi yana mai kawar da ido daga gareta, watakila saboda mummunan kallon da ya lura tana yi mishi. 49 Ai kai baka taba cin halal ba a rayuwarka tund aga kuruciyarka har kawo ga halin da kake ciki na tsufa a yanzu. Duk abin da za ki gayamin dai ba zan tanka miki don kudi ne dai sai kin bani su ko girma da arziki ko tsiya tsiya duk wanda kika zaba tunda dai na ma yi sa'a kawarki bata taimakeki kika samu miji a hannu ki ka yi mata alkawari kika saba saboda ganin bukatarki ta biya kika wulakantata kika barta tana bara bara karuwa karuwa ta yard ain munje kotun zata bada sheda a kanki kyauta ba sai na biya ba ai da sauki. Wacce kawa ke gareni da mukayi haka da ita in banda sharrinka? Da sauri ya ce mata Delu. Ni da kaina da babu ruwana a cikin maganar na san baba Lantana tayi amfani da kawayenta wajen neman babana a malamansu da kuma taga kamar ta samu yanda take so ta koresu ta hanyar yi musu wulakanci ba tare da ta cika musu alkawarin da ta yi musu ba cikin irin wadannan kawayen nata nata har da Delu. Jikin baba Lantana ya yi sanyi kwarai da jin cewar Delu zata bayar da sheda a kanta ta kuma san sauran ma zasu iya yin hakan koma fiye da haka, to su je su yi ta bayarwa mana, ya yi murmushi ai fa za su je. Takardar fuili nake da ita zan baka kaje ka sa filin a kasuwa ka sayar ka karbi kudinka, takardar fili 50 kuma? Ya yamutsa fuska ni da na bayar da kudi na tsaba a hannu sai kuma a ce za a hadani da wata takardar fili? In filin na arziki ne me yasa ke bak saida shi kin karbi kudin kin b ani ba? Da kyar Alhaji Nalami ya yarda baba Lantana ta fito dat akarda ya karba yanad ubawa tana yi mishi bayani, filin ya kai shekarauku da saye tun a wancan lokacin kuma jaka uku na sayeshi zuwa ina ganin zai iya kaiwa jaka goma in an saida shi a kawomin sauran kudin. A hankali ya matsa kusa da ita ya ajiye mata takardar tare da fadin, saidashi da kanki ki bani kudina kawai abinda nake so kenan shi ne kuma zai fiye miki rufin asiri a kan wannan neme nemen maganar da kikeyi da ni ai ke ma kin sani sarai tunda aka saida gonar mage aka saiwa bera daddaawa to kuwa tsugu ne ta kare msihi ni za a kawowa iyas hege filin da aka saya shekara uku bayan ne za a yiwa wannan bayanin ba ku yi magana a kan irinr agin da za ki yi a kai ba saboda sanin kullum darajar kasa raguwa take yi ba karuwa ba sai a ce ana neman kari? Darajar kasar ce take raguwa a garinku ake yin hakan ko? Ai sau dubu in kika zage ni nace miki ba zan rama ba, itama Delu shawarar da ta bani kenan, ambatar sunan delun yake yi kamar da gangan tamkar dai ace ya san hakan yana bakanta ran baba Lantana. Tun yaushe aka daina cin ribar fili saboda yanda darajarshi take ta faduwa ai kudi a hannu ana juyawa 51 su ne wani abu. Da kyar Nalami ya kar6i filin baba Lantana a jaka ukaun da ta sayeshi tun shekara uku da suka wuce ya kuma tasa Sallau a gaba don ya kaishi inda filin yake yana yi kuma yana yi m ata bayani, yo to ke in banda tsohuwar sanaiya da mutuncin dake tsakani zan karbi wannan filin ne a haka? Ai da sai ince sai masu saye sunje sun gani sunyi mishi kudii tukuna to babu irin wannan a tsakaninmu. Ya tasa Sallau a gaba suka fita. Cikin zuciyata na ce uhm uhn kudin babana ne da aka yi ta titsiyeshi ana tarawa yau Nalami ya zo ya karbe su a karin banza. Hausawa suka ce wai, Garin banza a farau farau din wofi yake karewa. Ban taba sanin duk wata fitina da nake ciki ko damuwa ko 6acin rai nafila ne ba sai a ranar da Isiyaku ya zo min da labarin cewar wai Mubarak zai yi aure. Samun kaina na yi rannan cikin wani irin yanayi da ba zai yiwu in tsaya ma kwatantawa ba, kwana nayi rannan idona biyu a zaune daram a tsakiyar gadona, ban kwanta ba balle in samu halin yin gyangyadin da zai zama dalilin runtsawa. Mubarak zai yi aure? Maganar dake ta faman kai kawo kenan a cikin zuciyata wacce kuma ita ce ta hanani sakat ta hanani jin dadi ta hanani natsuwa ta hanani zaman lafiya balle in yi maganar kwanciyar hankali, don saukin abin ma shi ne ni kadai ce a ciki 52 dakin tunda Asabe ta tafi har yau din nan bata dawo ba, don haka zagewa nayi nayi kuka sosai kuka irin na bakin ciki da tausayin kai sai da nayi na gaji don kaina nayi shiru, ina cikin share hawayen nawa ne naji zuciyata tana gayamin cewar ai kukan dadi kikeyi a yau da dai ace da kikayi mishi kyautar budurcinki kyautar wauta da shashanci ya sa ki kikayi ya karba hakan ta auku a tsakaninku to ya karbi budurcin naki to da yau kin yi kuka na gaskiya kuka iin na nadama da bakin cikin rayuwa, nayi kasake ina sauraron abinda zuciyar tawa take gaya min, lokaci mai tsaho ina sauraronta kafind aga bisani na yunkura cikin natsuwa na sauko daga kan agdon nawa na zo na soma binciken cikin kayana, hotunan da Mubarak nayi ta cirowa ina yagawa tare da konawa saboda tabbacin da zuciyata ke bani na shi kenan na rabu da Mubarak rabuwa kuwa ta har abada. Na kosa kwarai gari ya waye don in je in shedawa yaya Dija labarin aurcn Mubarak da naji, garin ya ki wayewa nisand aren ya kai matukar nisa duhun daren ma ya kai iyakacin duhu, gani nake tamkar in naje na gayawa yaya Dija tana da wani taimako da za ta yi min ko wani amfani da zata yi min, ko wani amfani da gaya mata zai amfanar da ni, waiyo waiyo waiyo abinda kawai nake iya ji yana fitowa daga cikin bakina kenan, saboda tsananin zafin da zuciyata ke yi, da kyar na samu garin ya waye. 53 Muna hada ido da baba Lantana a tsakark gida ta saki wani irin lallausan murmushi wanda rabon da in ganta tana fara'a tun ranar da Nalami ya karbi takardar filinta ya tafi, muna hada idon sai ta yi dariya ta ce, anya ashe kema kin ji labarin, ta sake sakin wani lafiyayyan murmushin kafin ta ce, uhun in dai da namiji ne ai kuka ba ki ma fara shi ba tukun balle ke da kika wulakanta jama'a a kanki ai kadan kika soma gani. Ban tanka mata ba na sa kai na fita gidan yaya Dija nake nufin zuwa. Ina fitowa daga gida na kara rudewa na kidime jikina ya dauki rawa karkar kar, cikin hanzari na juya da baya don in koma gida, amma saboda tsananin firgitar da nayi maimakon in shga gidanmu sai na smau kaina a zauren gidan su baba Sumaye, tsugunawa nayi a zauren cikin wani irin rudani, cincirindon mutanen da na hango a kofar gidan nasu Mubarak ne ya yi matukar razanani tafiya daurin auren nashi za a yi ko kuwa har sunje sund awo ne? Ban kara sanin irin rudewar da nayi ba sai da na ganni durkushe gaban baba Sumaye ina kuka alhalin ba abinda nayi nufin yi kenan ba. Za ki yi kuka mana Mero za ki yi kuka kai me sonki ma ai zai tayaki zubar da hawaye, wadannan abubuwan da suka faru dole ai ba kananan abubuwa bane ko ni din nan nayi kuka nayi addu'ar ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa sanda akayi bikin Dija da 54 yake tana raye ai ba a yi haka ba shiru akayi komai aka gama cikin rufin asiri da mutunci su na murn amuna murna, kema maraicinta ne ya ja miki shi ya sa bana jin zafinki sosai bacin raina daya ne da kikaje kika bashi kanki to ga abinda gari ya waya, yanzu waye a kasa? Waye kuma a wulakance? Babu amfani in tsaya ina yiwa baba Sumaye bayani kan cewar banyi abinda ake zargina da aikatawa ba, tunda nasan ba yarda zata yi ba don haka sai kawai naja bakina nayi shiru ina sauraron abinda ake gaya min. Ahmad Mubarak zai yi aure don yana son daidaitawada m ahaifinshi, yin aure da kuma alkawari na zai fita daga lamarinki gaba daya su ne ka' idojin da ya yarda da su kafin shi Alhaji Muhammadu ya yarda ya yafe mishi laifuffulkan da ya yi mishi, kema kuma don baki da mai taimakon kuruciyarki ya doraki a kan hanyar da tad ace ne ya sa aka barki kina wannan kai kawon ana yi miki wadannan wakokin na shakiyanci da iya shege, ni dai banga laifinsu kan abinda sukayi ba sun mutunta dansu ne shi da ai daraja ne gareshi sannans hi Alhaji Muhammadu shi kadai ke gareshi in dai a kan da namiji ne sannan ya' yanshi duk mata ne abinda ya 6atamin rai kawai shine da basu tausayawa maraicinki ba in ba haka ba komai kikayi ai kuruciya in ya hadu da maraici lamarin ba karami bane sai gyaran Ubangiji, to saukia Sunce bai zama dole a ce da dansu kadai kika lalace 55 ba don haka a matsayinsu na iyaye ya zama musu dole su tsaya su ga yayi aure mai tsabta don neman Zuriya mai albarka. A zuciyata na ce wato ni in an aureni ba zaa samu zuriya mai albarka ba saboda tunanin da sukeyi na na riga na lalace? To in ni a lalacen nake ba da dansu aka ce na lalacen ba? Wato in ma da dana baiwa Mubarak kyautar budurcin nawa ya karba irin hukuncin da za su zartar a kaina kenan? Tambayoyin da suka rinka kai kawo a cikin zuciyata kenan kafin lokacin da na katse maganar zuci na koma sauraron abinda baba Sumaye ke gaya min. Ai ita uwar goyon nashi, nayi maza na daga ido na kalleta saboda ban gane maganar da take son yi ba, uwar goyon wa? Cikin natsuwa ta ce min shi Mubarak mana, na sake kallonta sai ta shiga yi min bayanin saboda ta gane abn san komai ba kan maganar da take nufin yi min din. Ita Hajiya Ummulkairi ai ba ita ce mahaifiyarshi ba, na azro ido ina kallon baba Sumaye cikin tsananin mamaki, ban taba kawo irin wannan tunanin ba cikin raina, saboda ban taba tunanin akwai wata kyakkyawar mu'amala tsakanin matar uba da dan miji ba balle har aje ana samun dama ko shagwaba irin wacce na saba gain Mubarak yana yiwa Ummanshi ita kuma ta bar komai da takeyi tayi ta tarairayarshi. 56 Mahaifiyar Mubarak ai Hindatu ce budurwa ya aureta tazo ta haifeshi shi kadai zaman yaki dadita tsallakeshi ta yi tafiyasta tunda ta tafi kuwa ban sake jin ko da labarin ance ta zo ganinshi ba, ina ganin kuma sanda ta barehi baifi.shekara guda ba a duniya don sansdin mutuwar, aren ne. ya zama sanadin yayeshi saboda shi uhen ya ce ba zaa tafi mishi da shi ba, sai ya baiwa ita Ummulkairin shi da yake mata ce mai hikima sai ta sa hannu biyu ta rike irin rikon da ko ya'yanta bata yiwa haka ba, bata bari mummunan zaman da sukayi da uwarshi ya shafeshi ba. Na sake kallon baba Sumaye saboda tsananta mamakina yayin da ita ukma ta ci gaba da bani labarin da ban sani ba. Shi Alhaji Muhammadu ai ya auri mata da yawa a sanina nama akan idona ina ganin sun kai biyar, iyaka dai mafi yawancinsu basu haihu da shi ba daga ita Ummulkhairin ce sai A'indatu su ne masu 'ya'yan, ita Ummulkhairi ya'ya mata uku su ne su Kaltume ita kuwa dama ba budurwa ya aureta ba bazawara ce ta ma haifi 'ya'ya biyu a can wani gidan, a cikin jikokin ta na can gidan nema yanzu aka baiwa Mubarak din guda daya, ai Rumasa'u ce yarinyar da zai auran. Ban san yanda akayi ba sai kawai na tsinci kaina da tsanar Mubarak da Ummanshi da babanshi da ma i ta Rumasa' un tunda na santa na saba ganin tana zuwa gidan sai dai ban taba sanin alakar dake tsakaninsu 57 ba da ya wuce na 'yar babbar yarsu ce na fassarasu a matsayin wadansu irin mutane mayaudara marasa adalci wadanda basu san kowa ko komai ba in banda kansu. Shi da ai darajanta shi ake yi a adanashi a yi tattalin darajar shi da mutuncinshi baka barin shi ya wulakanta a gaban jama'a balel ya je yana lalacewa masoya da makiya suna kallo wasu na bakin cik wasu na madalla, shi Alhaji Muhammadu ya yi nufin adana danshi ne don ba zai yiwu ya zuba mishi ido yana nema ya shiga wani al'amari ba, ita kuwa Ummullkoiri sai tayi amfani da damar da tas am wajen oshi jikarta ya aura, kunga ai ya kara zama nata a. hakan kuma sai ta kara samunshi a hannunta kamar yanda hikimarta tasa ta samu mijinta, to shima malam Habu da. samun wani yayi ya daura miki aure da shi ya kaki dakin mijinki da ya fi ye mishi barinki da da ya yi ana yi miki wannan wulakancin da tozartarwar, to bai yi ba bai kuma da mafadi abokiyar shawararshi daya ce matarshi ita kuma bata taba shawarta mishi wani abin ariziki ba sai na sharni za kuma ta ga yanda abin zai juya mata. Sallama nayi da baba Suimaye na fita na koma cikin gidanmu na fasa zuwa gidan yaya Dija. Ina shiga gidan naga baba Lantana tare da Asabe a zuciyata na tabbatar labarin auren Mubarak da ta ji ne ya dawo da ita. 58 Baba Lantana sai farin ciki take yi tana kyalkyalewa da dariya irin wacce ta dade bata yi ba, ita mace kowacce ai tana da kufu'in aurenta in kana da hankali kaima ba sai an gaya maka ba ni dama can nasan wannan yaron mubarak ba zai aureta ba yaro dan gata irin wannan ya rasa matar da zai aura sai ita, ai kema kin san ba zai yiwu ba, a yanda yake da irin arzikin ubanshi da îrin gatan da yake da shi habawa? Timatiri ne fa sana'ar ubanta kowa ya sani to ko basu lalace tare ba yaushe zai aureta? Ita ba kyau ba ita ba gata ba, ita ba dangi ba, ita ba asali ba haka kawai? Ai idonsu ya rufe ne kawai.a kan sun duniya ba don haka ba da tuntuni suka gane gaskiya da akayi abin nan da sai malam ya bi bayan Alhaji Muhammadu Nalami ya bashi hakuri a daura' aure to baiyi ba saboda shi agwagwane bin ya'yan shi yakeyi yanda suke so haka ake yi don haka nunawa ido ne. dama kuma ina addu'a na kuma san alhakina ne ya fara kamasu, nayi nufin yi musu abin arziki in rufa mata asiri duk da cikin da na san tana da shi na hadata da wanda nasan zai aurcta duk da cikinta don asiri ya rufü itæ da 'yar uwarta da taimakon ubansu suka watsa min kasa a ido, to ai mu na nan da su. Ta yi kwafa ta mike ta nufi dakinta. Asabe dai ba ta ce mata ba to balle kuma ni can cikin zuciyata dai mamaki ne ya kamani na yanda ita da bakinta ta zauna tana bayanin gata irin na Mubarak 59 a yau alhalin kullum abinda ta saba fadi shi ne karyar banza karyar wofi mu za a kawowa barazana, daga karyar ziki kawai haka masu kudin suke. A wannan lokacin sai baba Lantana ta zama bata da wata hira sai na Mubarak da iyayenshi tayi ta bada labarin arziki da irin alherin Alhaji Muhammadu a wurinta a kuma bakinta naji wai ashe sabon gini aka yiwa Mubarak din a can cikin gidansu banda haka kuma aka saya mishi sabuwar mota, don ya yi angwanci a ciki, ai kwarya tabi kwarya in tabi akushi sai ta fashe, karin maganar da baba Lantana ke wuni tan ayi kenan a yanzu. Asabe dai bata shiga harkata ba nima ban shiga tata ba ta dai dawo gidanmu gaba daya har da kayanta da na watsar sai dai kuma a yanzu ba abinda yake gabana kenan ba ina ji da kaina, ina cikin wani irin tashin hankali da rudanin da ban san yanda zanyi in fita daga cikinshi ba. Gaskiya ne duk wani abinda baba Lantana ta fada akan Mubarak da irin gatan da iyayenshi suka shirya mishi tunda aka fara bikin ummanshi ke bin gidajen makwabta da abinci dana sha ko kaje gidan bikin ko kar kaje za a kawo maka nau'o'in abincin da aka girka kala kala, ina ganin tamkar a unguwar nan gaba daya gidanmu ne kawai bata yiwa irin wannan aiken ba. A ranar da aka kammala bikin kuwa ina kwance a kan gadona ina jin dirin motocin abokan Mubarak 60 da suka rakoshi wurin babanshr ya şa mishi albarka kafin su rakashi dakina maryarshi don ance wai tunda aka yi abin yau ne ranar farko da baban nashi ya yarda zai ganshi. A wannan daren bana iya kwatanta komai game da halin da zuciyata ke ciki, iyaka dai kawai na san kasancewar Asabe a dakin nan ba ya hanani yin kuka ba tare ikuma da na damu da ta ni ko bata ji yi kawai nake yi don in samu in samu saukin ciwon da kirjina ke yi. Ban san abinda take ciki ba sai jinta nayi ta ce, uhun dama kin hakura kim yi shiru tunda taki mas'alar ma ai mnai sauki ce. Ban kulata ba itama bata sake ce min komai ba. A wannan lokacin sai na zama babu abinda nake sha'awa irin in ga mutane masu yan uwa da dangi a wasu garuruwan na nesa sai in rinka jn tamkar inama dai nice da tuni na tattara kayana na koma can inda suke dan in samu in samu seukin 6acin ran da nake ciki, wani lokacin kuma nice inama dai dai babana yayi min irin abidna baba Sumaye ayi sha'awar ace ya yi min na aurar da ni ga duk wanda ya ga damada yanzu nima ina can gidan mijina ko ina son shi ko bana sonshi kuma ai zan zauna darajar shi baban nawa ne ya bani shi sannan ko bana son nashi kuma ina ganin ba zan gamu da bacin ran da ya kai wanda nake fama da shi ba a yanzu. 61 Ana gama bikin Mubarak kuma sai na sake zama abin nunawa wurin 'yan mata da samarin da dama na rike musu wuya sai da ya gama da ita sannan yaje ya auro gal a leda, abinda suke ta fadi kenan ko naji suna fada suna dariya bana kulasu ko kuma su yista rera wakokin da makada da mawaka sukayi ta rerawa Muberak din da iyayenshia wurin bikin, sai da ta kai ma na sake daina fita waje saboda tsananin dana shiga cikin zuciyata na rika tambayar kaina sai mace? Kullun in za a yi maganar ta nashi bangaren da ya gama da ni din akan furta a yansyin da bai yi kama da aikata wani iaifi ba sai dai ma kaga tamkar ya yi wani alin gwaninta ne ko bajinta, a nawa bangaren ne za a yi ta a yanayi na wulakanta ko tozarta ko kurna muna ailkata wani abin kunya da wuiakantar, kai da na lura da kyau da yanayin da ake bayar da labarurrukan sai na gane shi Mubarak ma sha'awa yake baiwa mutane ga kuna gatan da iyayenshi suka yi nishi wanda mutanen unguw8r basu gsiiya da bayar da iabarin, bisa wanan lurar da nayi da abinda ya sameni sai nima da kaina na yardanwar kang da cewar ita mace ita ce mai yin abin kunya in har abin kunyar ta zo, ita ce kuma mai tozarta in abin tozartar ya zo, ita ce mai shiga ta wulakanta saboda ita ce mai rauni komai ya faru a kanta yake karewa, ita ce a kasa, ita ce take bukatar mutunci da kunya don su 62 zamo sutora a gareta, shi namiji karfi kawai yake nema. Dana kara tsunduma cikin tunani sai na tuna da wasu kalmomi da na taba gani a cikin wani littafi a hannun Mubarak, ga abin da suka ce: MAN IS BORN FACE AND EVERY WHERE HE IS IN SHAKKLE" Da na natsu na dawo cikin haiyacina sai na samu kaina a yanayi na godiyar Ubangiji da ya taimakeni ya rufamin asiri ya bana Mubarak karbar kyautar da na yi mishi, in tuna kaina in tabbatarwa kaina ni din budurwa ce gal a leda, shi ne abin da yafi komai sanyaya min zcuiyata a wannan lokacin. Bikin Mubarak da kwana goma na hangoshi tsaye a Rfoar gidansu a dalilin fitowar da nayi za ni shago don sayawa babana ruwan swan din da nake amfani da shi wajen bashi magani, ban san yanda akayi ba ina tsaye as hagon nan cikin 6ari saboda kaduwar da nayi a dalilin hangoshi da na yi wanda shi ne ganina da shi na farko tun bayan faruwar abubuwan da suka faru a tsakaninmu. Motsi na ji a bayana tare da shakar wani irin sanyayyan kanshin da ya yi sanadin da na yi matukar tsarguwa da zuciyata ta yi, da sauri na juya don fidda rai daga zato saboda in samu natsuwa a tare da ni, sai kawai idanuwanmu suka hadu an yi maza najuya don karbar abinda nace a bani, jikina sai rawa yake yi har 63 kárkarwa tamkar sanyin hunturu ne yake kadani, cikin wata irin kwalliya yake ga kamshi gashi in ba kuskure nayi ba sai naga kamar kiba ya yi, nan tkae na ji Zuciyata tana gayamin shi bai da damuwa shi dadi yake ji, shi hankalinshi a kwance baida wata matsala a tare da shi, da sauri na mika hannu na kar6i ledar siyayyar tawa da ya yi nufin karba, ban 6ata lokaci wajeu tsayawa karbar canjin ba nayi maza na bar wurin. To tsaya mana Mero jirani mana ai wurinki na zo. Bai ji kunyar fadin hakan ba a gaban mutanen da suka cika a shagon, ina jin maganganun na shi na yi amza na kara maimakon sauri na yanka da gudu nayi amza na shige cikin gidanmu ba tare da na saurareshi ba. Kwana biyu bayan nan na fita gida da sassafe don sayawa babana kunu da kosan da na saba siya mishi, ina zaune wurin mai kosan ina jiran ta zubamin saboda na samu wasu a gabana da yawa sai kawai na ganshi ya iso wurin, kallo daya nayi mishi nayi maza na sunkuyar da kaina na.dora hannu akan guiwata yayin da na zagaye guiwar tawa da hannayena duka biyu, doguwar farar jallabiya ce a jikinshi duk da ban tsaya kare mishi kallo ba nasan ta karbeshi. Ina kwana baba? Ya soma gaida baba mai kosan tana amsawa, lafiya lau Amadu ya ya su Hajiya da iyalin naka? Lafiya lau. Ya amsa mata, sakun kosan 64 bai so kan Mero baba nc? Da sauri ta ce mishi ko baizo ba ai sai a zuba mata Amadu. Nan da nan ta zuba da yawa fiye kudin da na bata ta kunsa ta mikomin nasa hannu biyu na karba na dora a kan murfin kwanon kunun na dauka na kama hanyar zuwa gida, Mubarak yana biye da ni babu halin in ruga da gudu in tafi in barshi saboda tsoron kar kunun nawa ya zube. Ki tsaya mu yi magana mana Mero. Ban kula shi ba tafiyata kawai nake yi, ban fa yi miki laifin komai ba ballekice na za ki yi fushi da ni, ni da ke mun shiga wani irin al'amari ne a dalilins harrin da matar babanki ta kulla mana na kuma san ba zai yiwu ta shanye ta gama lafiya taga yanda take so a rayuwarta ba tunda ita sharri tasa a gaba, in ma kina da wani tunani ko kulli game da ni a zuciyakri to ki yi hakuriki sake kawai duk abinda kika gani kuma ya zama dole ne kawai ya sa kika ganshi a yanda kika ganshin, a shirye nake kuma in yi miki bayanin da zai gamsar da ke. Ban kalleshi ba balle in tanka mishi har muka zo kofar gidanmu muna isowa kuwa nayi maza na wuce cikin zauren gidanmu na barshi a can waje. Tun daga nan na zama bana fita daga gida kai tsaye sai na dan tsaya na yi waiwaye waiwaye in tabbatar ban hangoshi a kusa ba. 65 Rannan ina zaune a dakina ni kadai sai ga Isiyaku ya shigo yana sallama, na amsa sallamar tare da bashi izinin shigowa, ya nemi wuri ya zauna muka shiga gaisawa har da yin hira tun da dama can abokin hirana ne, na yi ta tunanin abin da zan dan kawo mishi ya dan taba saboda nuna girmamawa ga bakonka ban tuna ba don bani da komai a dakin don haka na hakura muka ci gaba da hirar a haka jimawa can sai ya ce min, Mero ni zan tafi. Nayi maza na ce mishi ai na gode maka Isiyaku sai dai ka shigo yau dakin nawa babu komai a cikisnhi. Ya yi murmushi tare da fadin, babu komai. Ya dan karkace kadan sai naga ya zaro wata takarda daga cikin aljihunshi ya miko min tare da takardun kudin naira ashirin ashirin cunkus a hannunshi wai gashi in kawo miki. Nayi maza na zuba musu ido tare da tambayarshi menene wannan? Cikin natsuwa ya yi min bayani, wasika ce tare da kudi ya ce in kawo miki. A hankali na sake tambayarshi, in ji wa? Ya dan yi murmushi kadan kafin ya ce min, inji yaya Mubarak mana wa zai yi mikıi irin wannan aiken in ba shi ba? Ya baka kudi ba kawo min? Ina yi mishi tambayar na soma kuka tun katin ya kai ga amsa min nan da nan ya hidime ya shiga bani hakuri yana yi min magana, to menene in ya baki kudi an shi Mero? Yanda duk kika dauki abin fa ba haka yake ba shi 66 yaya Mubarak. Na yi maza na katseshi, dakata na fadi hakan taré da share hawaycna da bannayena duka biyu, maida mishi kudinshi tare da wasikar na rokeka ka gaya mishi yayi hakuri ya fita harkata bana son kulanin da yake yi bana so bana so, ka gaya mishi na ce bana so. Zai yi min magana na yi maZa na salke ce mishi, acte bana so ko kuwa dole ne? Ya mike ya fita, ya tafi ni kuma na kwanta a nan wurin naci gaba da kuka cikin tsananin bacin rai da takaici, wautar kudin ce ta fi komai kona min rai wato ni kudi ne bukatata, duk abinda akayi min na wulakarici da tozartawa aiken kudi ya kanmata a yi min? Na tuna kalmomin da na ji baba Lantana tana furtawa na rainin arziki ne yasa iyayenshi suka hanshi aurena saboda sun ga babana ba kowa bane face mai saida timatiri, zuciyata ta sake rayamin wasu abubuwan, ya yi aurcnshi ban kulashi ba ban shiga harkarshi ba yana nema ya rinka shiga nawa bayan an tabbatar min da cewär har da fita hanyita cikin sharadin da babanshi ya'sanyå*mishi, ya amsa sanna ne ya cce ya yafe msihi ya dawo gida; to menene kuma ya saurä tsakanina da shi? Ban san dalilk bå sai na samu kaina da bacin rai mai yawa da na-kasa daurewa zaman gidan ma ya gagareni na nemi izini wurin babana na shirya na tafi gidan yaya Dija. Tana ganina da yar jakarta dana zbe yan zannuwana na canji a ciki ta saki mirhushi, 'haba to 67 ko ke fa? Ai tun ba yau ba nake fama dake ki baro unguwar nan ki zo nan mu dan kwana biyu tare ki dan huta, ni hun ban cika son barin baba bane a gidan nan shi kadai yanzun ma na dan fito ne kawai. Na kwashe bayanin komai nayi mata ban 6oye mata komiba. Cikin natsuwa ta kallehi, kin san abin da yafi bani tausayi a cikin al'amarinki? Na yi maza na ce mata a'a, sai kawai na ji ta ce min, wai son Mubarak da kikeyi. Nayi maza na cem ata ni? Ta ce eh ke. Nace la yaya Dija ni ai ba son shi nake yi ba. Tayi maza ta ce, ke. matsa can ki bani wuri karki nemi maidani yarınya karama mana in bakya sonshi meke sawa ki na yin bacni rai a kanshi, meke saki kuka? Ai so ne Mero, ya yi miki aike ba yau ko jiýa ya fare ba ya dade yanayi ba wulakanci bane in yanzu kin daina karba shi kenan babu 6acin rai a ciki da har za a je ana ta kuka shawarar da zan baki ita ce ki fidda shi a cikin ranki fito da miji kawai ki yi aurennki ga Mansur. Na yi maza na katseta ta hanyar fadin kai Mansur? A'a ni yanzu bana son kowa. Ta sake zuba min ido saboda Mubarak da iyayenshi sun ki mu shi ne shima Mansur laifin zai shafeni, ai in ban manta ba a nan ne mukayi maganar nan da ke cewar da Mansur din da kuma Mbarak rdukansu daya ne wanda duk maganar aurent a kama za a yi da shi, to ba za ki samu mas'ala ba za ki zauna lafiya da shi za kuma ki yi 68 mishi biyaiya domin su dukansu biyun masu alheri ne babu kuma wanda zai iyakacin lokacinki a kanshi. Nan take nas oma yi mata kuka saboda jin irin kalaman da ta tsareni da su na baro gide na zo wajenta don in huta ita kuma ta zo tana yi min wasu maganganu da suke karawa zuciyata nauyi. Assalarmu alaikum, wai ana sallama da Mero a waje. Sau biyu yayi maganar kafin na takarkare na daka mishi tsawa wanda watakila tsayar da nayi misHi'ne ya yi dalilin fusatar yaya Dija tayi maza ta zabura ta mike tsaye ta ce min, maza tashi ki je kiga waye mai kiran naki ai don Mubarak ya yi aure ba zai zamo danin karewar maza a duoiya ba, da ke wata mai zuciya ce ma da tsayawa kikayi kika fidda mijinki nan da kwata talatin a yi bikinki ki tafi gidan mijinki kije ki yi zaman aurcnki kowa ya huta. Na tashi na fito don ba zan iya yin jayaiya da ita ba. Mubarak na gani tsaye a kofar gidan tsaye jikin motar tashi da ga shi har ita sai wani sheki suke yi suna daukar ido, ga dukkan alamu dai shi Mugbarak dadinshi kawai yake ji bai da wata mas'ala a tarc da shi, wanna shi ne abin da yafi komai bata miu rai wato ni ce mai damuwa, ni ce a cikin bakin ciki, ni ce rashin zuciya ya hanani samawa kaina zaman lafiya da kwanciyar hankali, ina ma dai ace nima halina irin na yaya Dija ne?... saurayi na yi na katse tunanin 69 nawa saboda ganin ya nufoni zai zo in da nake tsaye, nayi maza najuya zan shiga gida, caraf naji ya kama gyalen da nake rataye da shi ya rike, abinda ya yi dalilin tsayawata. Kina ganin kamar kin tsayawar da za ki yi ki saurareni yana da wani abin da zai amfanar da ke ne? Ni da ke ai muna bukatar fuskantar juna ne don musan abinda muke ciki. Kaina a sunkuye saboda nauyin shi da nake ji, muryata tana rawa alamar idanuwana suna shirin zubar da hawaye na ce mishi, sake min gyalena bana so kar kuma ka sake yi min haka bana so. Da sauri ya sake min gyalen nawa, ban tsaya sake sauraron komai ba na yi maza nas hige cikin gida na barshi nan wurin a tsaye, maimakon in tsaya wurin yaya Dija tunda har lokacin tana zaune a inda na barta wucewa nayi naje can cikin dakinta na hau gadonta na kwanta ina kuka, na kaska gane dalili, na kasa gane al'amarina, na kasa fahimtar yanda za a yi in zama jarumar kaina in fita hanyar Mubarak in daina ganinshi ina jin wani abu ganie da shi, na zafi ko ciwo ko faduwar gaba a cikin raina. Ina kwance ina yin kukan yaya Dija ta shigo ta sameni, nayi zaton wani fadan zata sake yi min sai na ji ta ce min, ki yi hakuri Maryamu wani loakci zaozi da ke da kanki za ki gane ba Mubarak ne mijin da ya dace da aurenki ba, mijin da baya rarrashima me za a 70 yi da shi ne? Ke kanii kika ce min bai iya ramashiba, bai iya bada lakuri ba, bai iya fadin naganganun soyaiya ba, to ai Mansur ya iya wadannan duka yana kuma sonki domin ko bayan aukuwar wadannan al'amuran ya zo gidan nan sau biyu yanzu ma don baya nan ne yasa kika ga shiru, to don me za ki damu kanki, akan mutanen da suka ki mu? Kin mu fa suka yi sun kimu ne saboda sun rainarmu in ba haka ba wane irin wulakanci ne haka su zargi lalacewa tsakaninki da dansu sannan su barki su aura mishi wata? Wannan wane irin son kai ne wannan? Wannan wane irin rashina dalci suka yi mana? Bana sonsu, bana son dansu, bana son duk wani abin da ya shafesu. Tana fadin maganar tana kuka, nima kuma ina kara jin tsanar Mubarak da iyayerishi da duk wani abinda ya shafeshi cikin raina. Assalamu alaikum, wai a gayawa yaya Dija tanna da bako a waje. Sau biyu yaron yana shigowa yana fadin irin wann an maganar a tsakar gida, tana jinshi bata tanka mishi ba. Yaya Ibrahim ne ya fito daga úakin su yana yi mata magana, anene bakon na ki da yake wajen? Mubarak ne kuma bana son ganinshi, Eai yi magana ba ya fita wajen sai kawai gasu sun shigo tare, falon yaya Dija ya shigo da shi. 71 Sannu da zuwa Mubarak, ya nuna mishi wuri ta zauna shima ya zauna suka gaisa sosai har yana tambayar shi anyi hidima lafiya? Ya amsa lafiya lau to Ubangiji ya sa alheri a ka hada ya amsa main. Jin shigowar tashi ya sa yaya Dija ta matsa kusa da bakin kofar dakin nata ta labe bayan labule suka gaisa ba tare da sungajuna ba, itarna tayi mishi murnar auren nashi sai dai ita kam bai amsa addu'ar da tayi mishi ba, a hankli cikin natsuwa ya soma yn amgana wanda yake kamar dama ya samu na gaya musu abinda ke ranshi watakila don ya wanke kanshi. Mafi yawancin lokaci mutum yana shiga cikin wani irin al'amari da bai taba zatarwa kanshi ba, al amuran da suka faru a cikin watannin nan uku zuwa hudu da suka wuce wadansu irin abubuwa ne da babu wani abin da zamu ce sai dai mu kara hakuri mu kara yarda da cewar komai yana tafiya ne bisa tsari da rubutun kaddarar da take keddara mana komai. Yaya Ibrahim ya ce, haka ne, sai ya ci gaba da magana, ni dai gaskiya a Bangarena na shiga wani irin al 'amarin a kunci da damuwa, gami da bakin ciki da tsanani irin wanda bana fatan wani wanda ban sanshi ba ma ya samu kanshi a irin wanonan yanayin, duk wata fitina ina ganin kanar tana da sauki kwarai in har ta zamo babu fushin iyaye a ciki. Da sauri yaya Ibrahim ya ce mishi, kwarai kuwa fushin iyaye ai musiba ce mai hankali kuma baya 72 yarda ya zauna a irin wannan yanayin domin kullum fata muke mu rabu da su lafiya suna sanya mana albarka. Maganar da yaya Ibrahim ya yi ta zama tamkar susa ya yi mishi inda yake yi mishi kaikayi, da sauir ya ce, yauwa na gode da ka fahimce ni ina fata kuma itama yaya Dija tayi min irin wannan fahimtar halinda na samu kaina a ciki na fushin da'mahaifina ya yi da ni shi ne dalilin da ya sanyani karbar auren da suka ba ni don in samu in fita daga cikin wannan al'amarin amma ba yana nufin wani abu zai canza " bane tsakanina da Maryamu. Cikin natsuwa naji shima yaya Ibrahim ya soma yin tashi maganar bayan ya yi gyaran murya, to arna Ahmadin kayi haka ai ina ganin baka kiyayi bacin ran iyayen irin kiyayewar da ya kamata ka yi mishi ba, ci gaba da mu'amala da Maryam kaima kasan ba zai zamo karbabben abu ba a wurinsu domin rabuwa da ita yana cikin sharadin da suka sanya maka, ina ganin maimakon ka dage kan ci gaba da mu'amala da ita har hakan ya sake jawo maka wata mas'alar tsakaninka da su da rabuwa da ita kawai kayi tunda ai ka riga kayi aurenka itama ta fidda miji tayi nata, ina ganin wannan shi ne abidna zai fiye mana sauki domina I'amura sun riga sun faru marasa dadi masu bata rai da tayar da hankali, ya kamata ace mu dukan mu mu kiyaye sake aukuwarsu, don haka ina so in yi amfani 73 da wannan zaman namu in rokeka ka fita hanyar Mero ka daina bibiyarta ka barta ta samu natsuwa da kwanciyar hankalin da zata fuskanci al'amarin ta, kaima ka samu natsuwa tare da iyalinka don ka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da iyayenka. To amma yaya Ibrahim kana nufin don na kar6i auren da iyayena suka yi min sai hakan ya zama dlailind a ni kuma ba zan yiwa kaina nawa auren ba? Eh haka zaka iya yiwa kanka, bance ba zaka iya ba to amma kuma gaskiya ba Mero bace wannanm atar domin mun riga mun samu labarin komai don haka ina so in gaya maka cewar na rokeka ka fita hanyarta kawai. Ya ce to babu laifi na gode. Ya yi musu sallama ya mike ya fita. Yana fita daga gidan yaya Ibrahim yakirani din na zauna cikin ladabi ina sauraronshi, kin ji yanda muka yi da Ahmad, na ce mishi ch, ya ce to ki fitar da miji ki yi aure kinji ko baki ji ba? Na ce mishi naji, zai fitar ko ba zaki fitar ba? Na sake cewa zan fitar. Ya ji dadin yanayin da na bashi amsa r a ciki, to Ubangiji ya yi miki albarka, na ce amin. Ya tashi da nufin fita yana magana, dagan an zuwa rana itayau ina so in ji bayani wurin Dija, na ce mishi to. Da daddare rannan ina kwance kan gadon yaya Dija yayin da ita kuma take wurin mijinta bacci ne yaki daukata na rasa abinda ke yi min dadi, cikin 74 raina na sani ni da kaina na gayawa yaya Dija cewar da Mubarak din da kuma Mansur duk daya ne wanda duk aka bani zan zauna da shi, amma a yau sai na kasa jin irin kuzarinda nake tare da shi a wannan lokacin da nayi wancan maganar, gaba daya dai halin da nake ciki nayi jarumtakar daina hana kaina yarda da cewar son Mubarak ne yake haddasa min abubuwa da nake fama da su na faduwar gaba da kauracewar bacci a idona, na yarda da cewar bacin rai ne na wulakanci da tozartawar da aka taru aka yi min. Washegari da safe ina kicn ina kokarin sallamar ya'yan yaya Dija su tafi makaranta saboda bata fito ba a dalilin ta san ina gidan, ina cikin aikina sai kawai na jiwo muryar matar wan yaya lbrahim tana cewa wata da ban sheda ta ta muryar ba, lalle ne su hadu su je wajen uwar mijinsu su kai karar yaya Dija kan neman da take yi ta jawo ni ta dawo da ni nan gidan da zama bayan duk abin kunyar da na akata na jawowa iyayena da yan uwana abin magana, tana nema sai tayi dalilin da na shafa m usu na bata musu sunan gidansu, in mu bamu damu da abin kunya abin magana ba saboda bamu da yawa ba wasu dangi ne da mu ba ai su nan gidan dole su ji tsoron abin kunya ko don yawansu. Ko kadan ban ji dadin maganganun da na ji ba to amma kuma sai na kudurawa raina kame bakina in yi shiru ba tare da na gayawa yaya Dija abinda naji ba, 75 iyaka dai kawai in hanzarta barin gidan in koma namu tun ban haddasam ata wata fitina ba, don nasan in taji ba zata yarda ba aurenta kuma aure ne da bashi da wani tarihi na wata fitina mai karfi sai danabin da ba za a rasa ba, kawai wanda zo mu zauna zo mu saba ke haddasawa musamman ma kuma da yake kusan a hade suke da iyaye da 'yan uwa a wuri daya, ginin da yayi baisa ya yi nesa da su ba don haka ina gama aiyukan da zanyi mata sai kawai na yi shirina na jira ta fito nace mata za ni gida, tayi ta tambayata menene ban ce mata zan kwana biyu ba? Nace mata eh amma ai na fasa saboda zan bar baba shi kadai a gida. Ta gallamin harara, baba shi kadai m atarshi fa? An ce miki zaki yi ta zaman gida ne saboda baba? Kema zaki yi aurenki. Nayi dariya kawai na kama hanya na tafi. A gida ina zaune ne kawai bana komai bana kuma zuwa ko ina, ba makarantarboko babu ta allo, bana kuma fita ko ina ko daidai al'amura sun dan lafa na wakoki da rashe-rashen mutuncin da akayi tayi min a baya, na dan samu sauki na dan samu saukin ciwon da zuciyata take yi min a kan Mubarak saboda na daina yarda ina zama in bata lokaci wajan tunanin al'amufanshi, ina kuma kiyaye duk wani abin da zai hadani da shi ko da kuwa hango ni daga nesa tunda asan har yanzu ban samo maganin faduwar gaban da 76 nake fama da shi ba a duk lokacin da' na hangoshi ko na ji maganarshi. A cikin gida dai ni da su baba Lantana muna cikin wani hali ga babu ga kuma rashin dadin zama komai a tsaye yake cak, bani da komai nå abin amfani ba ni kuma da ko kwandala, rabon da in yi rashin irin wannan har na manta. Watakila tun ban isa komai ba tunda in ma ban samu an yi min a gida ba to dai bana rasawa zan samu wurin Mubarak ko Umamnshi, to yanzu babu su baban nawa kuma ba shi da shi, ta lafiyar shi ma ake yi bata maganar runfa ba don ma anyi sa'a Sallau yana matukar taimakawa a kan bude rumfar babana yana cikin wani hali na rasa karfi mai yawa a tare da shi, a hakan kumna wai baba Lantana bata tausaya mishi a bata dai a bata kawai ta sani ko da kuwa babu abinda take so a baka din kusan kullum zaka sameshi ne cikin jiri ko ciwon kai, amma hakan baya hanata zama tayi ta gaya mishi bakaken maganganu ni kam ma sai nake ganin tamkar karbem ata fili da Alhaji Nalami yayi ba kairamin kara mata son kudi da neman tashin hankali yayi ba. Rannan ina jinta ita da Sallau da ya dawo daga runfa in da ya danyi aiki, bani kudin nan duka nace maka ka bani su, a'a baba in na baki su dukan gobe fa? A ci yau a ci gobe ai shine cin rana daya, kumburin ciki ne. Nace maka ka bani su, ina ce dai rumfar bata gidanku ba ce? Cikin natsuwa ya ce mata, 77 eh baba bata gidanmu bace amma shi mai rumfar ai bai nuna min hakan ba don haka zan tattala mishi abinda yake ciki ko na samu nima in koyi sana'ar tunda dai ke baki kaini makaranta ba baki kai ni wajen koyon sana'a ba. Ina daga kwance ina jinsu ko motsawa banyi ba, cikin zuciyata na co kunfi kusa in kuka ga dama kuc inye su duka a yanzu. Ganewar da nayi Sallau da iyakacin gaskiyarshi yake mu' amala da baba na yasa nima ko kadan bana sa mishi ido kan cinikin da yake yi komai yace min kuma sai ince mishi to, bana dai sake mishi sosai don haka sai muka koma m u'amala ta matunci kawai da ganin girmanjuna, a wannan lokacin babu abinda yafi tsayamin a ai irin in kwanta da daddare in tuna gobe da safe bani da kudin da zan sayawa babana abin karyawa gashi a yanzu baba Lantana sai tayi kwana da kwanaki bata yi girki ba, wai abinda ake batan baya isa a yi girki, na kuma san har da daina yarda da ayi girki aci ni a hanani da na yi ya kara sata daina yin girkin. Kan hakı yasa naje na samu Sallau a rumfar baba na ce' mishi Sallau. Yayi m aza ya taso, anti Mero ai da kin jirani a gida ma zan zo. Nace e babu damuwa so nake mu yi magana. Ya ce to, nayi mishi bayanin da ya kawo kullum in kayi ciniki ka rinka cire kudin da zaka rinka saro kayan gobe abinda ya saura ka 78 kasashi biyar kai daya baba daya baba Lantana daya ni daya, dayan kuwa a rinka sakashi cikin bankin karfe dake cikin rumfar nan, saboda bacin rana, ya ce min to. Yana dawowa kuwa da daddare ya zo ya yi min bayanin abin da aka yi da yanda ya yi kasafinsu. Yaya Dija tana iyakacin kokarinta a kan mu sai dai kuma ita din mata ce da bata iya sana'ar komai ba duk wani abinda kaga tana yi in dai na kudi ne to daga aljihun mijinta ya fito ko kuma daga abinda ta iya tattalawa na canjin cefanenta don haka sai na kudurawa kaina ba zan taba zama bani da abin yi ba, ba zan zauna bana sana'a ba, ba zan iya zama sai an bani ba, zan nemi kudi ko don in yi hidimata da ta babana ba tare dan a tsaya jiran an bani ba sai dai a sana'ar ban san wacce zan yi ba. An wayi gari yau tun asuba zuciyata take ta kai kawo kan al'amarin Asabe wacce na lura tayi matukar canzawa duk wani abin da za ta yi ta kan yi shi ne ba a yanayin da ta saba ba, hatta zamanta da tashinta amma wai har yanzu baba Lantana tana kallonta bata gane abinda take ciki ba ko kuma ta ganę tayi shiru ne kawai oho. Tsawon lokaci ina wannan tunanin kafin na yi maza na kawar da wannan tunanin na koma kan nawa al'amarins aboda ganewar da nayi cewar in na tsaya kan nawa mas'alolin ma kawai sun isheni ba sai naje 79 ina shiga harkar da ba tawa ba ce, don haka na koma lissafin tawa damuwar gaba daya kayan sakawar baba sun kare sunyi datti bani da ko sabulun da zanyi mishi wanki, nmaganin da yake sha yana gab da karewa babu kudin sayen wani ga zuwa asibitin shima ya zo da dai ace so shine samu to da na samu wani abinda na rinkayi ina samuz ko da kwaho kwabo ne don in rinka aiwatar.mana da abubuwanmu ba komai ya taso sai naje na gayawa yaya Dija ba. Gari ya waye da safe nayi abubuwan da na saba yi mana ni da babana na yau da gobe na kai mishi ruwan wanka na dawo kenan sai ga yaro dan makwabta ya shigo, anti Mero wai inji Mansur wai ki zo. Na daga ido na kalli yaron yanda ya ambaci sunan Mansur din gatsu bai yi min dadi ba kamar in yi mishi magana sai na fasa na kame bakina nayi shiru cikin zuciyata dai na tabbatarwa kaina da cewar gimamai na gaba yana da dadi. Gyalena na dauka na yafe jikina na kama hanyar fita zuciya'a sai faman harbawa take yi don rabon a kirani inje har na mance da lissafin. Yana tsaye ne cikin zauren gidanmu kanshin shi ya gauraye ko ina. Kunyarshi ta yi matukar kamani na kasa sakewa a gabanshi saboda sanin da nayi ya ji komai yana da labarin duk kan abubuwan da aka yi tayi har wakokin da nayi ta fama da su duk nsan ya jisu, amma hakan 80 bai hanashi zuwa wurin yaya Dija ba gashi kuma yau a gabana, me yake nufi? Yana nufin har yanzu yana kan bakanshi bai fasa aurena ba kamar yanda yaya Dija ta gaya min kome? Kan in kai karshen tunanin nawa sai naj1 ya ce min, ran yan mata ya dade ina kwana? A kidime kwarai na nemi wuri na tsuguna, yan mata yake k irana bayan tun ba yanzu ba na saba jin mutnae masu zargi suna fadin ai ni din tun ba yau ba na salwantar da budurcin nawa, yana ganin an tsuguna shima ya nemi wuri ya tayani tsugunawa. A tsarge kwarai na soma amsa mishi gaisuwar tashi tun bayan faruwar al'amuran da suka farun yau ne ranar farko da ni da Mansur uka hadu a wuri daya. Ya ya Dai Maryam? Yaya jikin baba? Na amsa mishi da sauki, 'yan maanganu kadan mukayi hirar tamu ba ta yi wani nisa ba watakila don bamu saki jiki ba tamkar dai ace muna jin kunyar juna. Takardar naira ashrin guda biyu ya. miko min wato naira arba' in ko ince fam ashirin, hannu biyu na saka na karba tare da yi mishi godiya, bai tsaya jin wata magana ba ya ce min, zan tafi sai na dan huta na fito za ki ganni, na ce mishi to. Yana tafiya na dauki takardar naira ashirin guda daya na nufi shago don yi mana sayaiya, babu wani abin da ban saya ba na kayaiyakin amfani har man shafawa da na dade bani da shi na saya, sai dai 81 maimakon 10-0-6 da Mubarak ya koya min shafawa sai na koma man shafawa na kamfanin shield don dai in samu in kara fitar da duk wani tunanin shi daga cikin zuciyata. Na shigo gida na kama wankin babana cikin kuzari na gama nayi nawa nayi mana guga na adana mana kayanmu na gama ba tare da gajiyar aikin ta dameni ba can cikin zuciyata nace kai babu tana cikin mas'alolin da ke addabar rayuwar dan adam matukar dai shi din mai lafiya ne. Kudin da na samu wurin Mansir sai suka wattsakar da ni na samu kuzari mai yawa a tare da ni, nayi duk wani abinda ya dace, ranar asibitin babana ya zo mukaje muka daow na saya mishi magungunan da aka rubuta ba tare da na jira ko gayawa yaya Dija ba, sai da na gama komai ne sannan naje na gaya mata yanda aka yi. Tun daga wannan lokacin da Mansur ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Ghana sai gidanmu ya zamo nan ne wurinshi sai dai in baya nan, tun ina jin kunya ina nonnokewa saboda al'amuran da na san ya sani ya ji game da ni har na wattsake muka shiga harkar soyaiyar na samu natsuwa da kwanciyar hankalin da na dadeb an samu ba, na murje na yi kyau saboda nayi sa'a shima man shafawar shield din ya karbi fata ta. 82 Yaran unguwa sun yi matukar fita harkar yi min wake-wake sun yi sun gaji sun hakura, dama hausawa Sunce wai watan wataran din guda daya ne in naka ya mutu sai kuma na wani ya kama. Mu'amala ta da Mansur ta yi amntukar sama min natsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, har na samu karfin da na ji zuciyata ta daina faduwa don na hango Mubarak ko na ji wata magana game da shi, a wannan lokacin sai naji a shirye nake in har Mansur ya yi maganar aurena in amince don kuwa na yarda na sakankance da cewar shi din miji ne da zai kula da 1yalinshi ya samar musu farin ciki da natsuwa da suke bukatar samu. Ina zaune a dakina hutawa nakeyi saboda dawowa ta kenan daga asibiti don yau ma na raka babana ganin likita saboda gaya min da ya yi cewar ya yi kwanaki uku cur bai samu yin bacci ba da daddare, hutawar da nake yi tare da kara tuna kalmomin da likita ya yi game da jikin nashi sai naji yaro yana magana a tsakar gida wai anak iran Mero a waje. A zuciyata na ce Mansur kenan shi da yace in shiga gida in huta sai an jima zai zo me kunma ya tuna ya sashi fasa hakan? Na mike na fito na wuce baba Lantana tana fadni, o'o shi wacan ya ja jiki wannan Kuma ya maye gurbi ya samu an bashi wuri ya zama shi kadai. 83 Ban kalleta ba na yi wucewata na fita, ban ganshi a zaure ba kamar yanda ya saba shigowa ciki don haka na leka kofar gidayasan na zo ina lekawa sai kawai mukayi ido hudu da Mubarak, ya sha kwalliya cikin kananan kaya ya yi kyau sai dai ban ji faduwar gaba a tare da ni ba, dadi ya kamani na kara gamsuwa da kaina. Yana ganin naja baya ya biyoni cikin zauren, sunkuyar da kaina nayi don in kaucewa idanuwan da ya tsareni da su, zuwa nayi in rokeki ki yi min wata alfarma Maryam. Na dan yi kokari na daga ido kadan na kalleshi saboda maganar tashi da yanayin da yayi maganara ciki, alfarmar me ni kuma zanyi maka? Na rokeki na kuma sake rokonki ki yi min wannan alfarmar ki fita hanyar Mansur bana so ina ganinki tare da shi. Cikin natsuwa hankalina kuma a kwance na buda bakina na ce mishi, gaskiya ba zan iya ba. Maganar tawa tayi matukar bashi mamaki saboda abinda na gani a tare da shi, cikin wani irin yanayi ya tambayeni, ba za ki iya ba? Shiu nayi ban bashi amnsa ba, ban kuma sake daga idona na kalleshi ba, saboda har yanzu ina jin nauyinshi a zuciyata. Me na yi miki Mero? Me nayi miki haka da kike nemaki sani bakin ciki? Ai ban cuceki ba, ban zalunceki ba, ban yi miki wani laifi ba, in kumakina gani nayi to gaya min shi in abki hakuri Mero, ai in 84 rai ya baci hankali baya bata a kowane hali muke ciki ko muka samu kanmu, bai kamata ki rufe ido ki kasa ganin gaskiya tsakanina da ke ba. Juyawa nayi da nufin shiga gida in barshi a zauren, ban san yanda akayi ba sai kawai na yi kicibis da baba Lantana a kusa da bakin zauren watakit da shigowa zatayi taga abinda muke yi, tana ganin Mubarak ta shiga salati tana tafa hannu tare da fadin, yau ga abin da mamaki yau ga abin al'ajabi, yau ga wata musiba da ta addabeta ta addabi sauran jama'a, ashe ba iyayenka sun yi maka aure na rufin asiri don ka fita hanyar wannan yarinyar ku daina lalacewar da kuke yi ba, haba wannan wane irin al'amari ne shi? Aure baifi wata shida ba masifar ka ta sa kullum yarinya tana kan hanyar yin yaji ta tafi a dawo da ita, ta tafi a dawo da ita, to kar ka ji da wai zan wanke kafata inje har gidan iyayenka in kara yin kashedi tunda na san su ma ba son mu'amalarka da ita suke yi ba tunda ina da labarin komai sai da ka yarda da sharadir da šuka sanya maka na fita hanyarta sannan ne suka bar ka ka dawo suka kuma yi maka aure na rufin asiri wanda a yanzu kake wulakantawa ko da yake ba haka kawai suka barka ba 'yarta ai babu abinda ba zata iya ba. Wuceta nayi na shiga dakina na yi kwanciyata a kan gadona sai na ganta itama ta dawo na tabbatar tafiya yayi ya barta. 85 Wunin ranar nan bakin baba Lantana bai huta ba fadi suke haka kawai basu shirya yarinya ba sun kunsota sun kawo sun ajiye mishi ba dole su da ita su yi ta ganin abinda basa so ba, tunda ya riga ya saba da tsome-tsome ai zama da shi kuma sai an shirya, Maganar tayi matukar watsuwa ta yanda har Mansur ma yazo ya sameni hankalinshi a tashe, ranshi a bace, me ya saura ne tsakaninki da shi kuma? Na rasa yanda zan yi na rasa abinda zan gaya mishi saboda bacin ran da na gani a tare da shi, don haka na kama yi mishi kuka, kuka kuwa mai yawa irin wanda na kwana biyu ban yi ba. To menene kuma na kukan hakan? Ya soma yin maganar a yanayi na sanyin jiki alamar bacin ran da ya zo da shi din ya kau, to ni me nace miki da kike wannan kukan? Kinga share hawayen nan ki ji abinda zan gaya miki, to ai kuma na gane so kawai kikeyi raina ya baci shi yas akike ta kukan, in ba haka ko ma menene nace ki yi hakuri ki yi hakuri ina ce shi kenan zance ya kare. Kinga tunda abin nan ya zama haka ana nema a rinka kai kawon maganganu a tsakani to ina ganin gara kawai a kawo karshen al'amarin gaba daya in kina dakina da wani wanda ya isa ya zo yana Rananan maganganu ne a tsakani? Don hakan ni in kin yarda kawai a shirye nakwe in je in samu babana ya dawo 86 ya sake yin amgana da baban nan gidan a daidaita a sanya lokacin auren mu kome kika gani. Lokaci mai tsawo na dauka ban ce mishi komai ba har ta kaima ya sake tambayata, ba ki ce komai ba Mero ko kuna da wani tunani ne? Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi, kai ne dai nake ganin kamar ya kamata ka kara tunani akan maganar tunda ka sani sarai an fadi maganganu da yawa a kaina har yanzu ma ba a daina ba tunda ga ma wanda aka je har gidanku aka fada kwanan nan in... Ban karasa zancen nawa ba ya yi maza ya katseni, yanzu ina amfanin wannan maganar da kikeyi in dai ba so kike sai döle kin sa raina ya baci ba? Shiru nayi bance mishi komai ba, kar ki sake kawo min irin wannan maganar bana so. A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to kayi hakuri. Dadi ya kamashi saboda hakurin da na bashi, ya dan gyara tsayuwa kafin ya ci gaba da magana, shi baba yana dawowa zanje in same shi da maganar. Na ce Ubangiji ya dawo da shi lafīya, yayi maza ya ce amin Maryam. Kafin babansu Mansur ya dawo wata irin lafiyaiyar soyaiya mu ka shiga, ka'ida ne kullum sai ya zo ko da rana ko da daddare, wataran ya zo ya sake dawowa, in na ce mishi baka riga ka zo ka dazu ya ce ai wata magana ya tuna da ya manta dazu da ya zo din bai gaya mini ta ba. 87 Rannan muna hira ni da shi tattaunawa muke yi irin ta fahimtarjuna, ra'ayinshi yake fada kan irin tsarin da yake ganin zan gudanar a gidanshi wanda hakan yake matukar taimakawa ma'aurata bayan an yi aure. Kin fa san 'yan uwane da ni masu yawa ina fata zaki yi hakurin zamada su. Na yi murmushi na ce, insha Allahu. Can cikin zuciyata kuwa tunani nake yi ni da nake rayuwa cikin kewar 'yan uwan miji zasu isheni har in kasa yin hakuri da su? To kuma ba zan barki yin aiki ba don kar ki ji ina cewa za ki koma makaranta don ki samu takardarki ki yi tunanin ko har da aiki cikin lissafin nawa. Na yi murmusih na ce nima ban damu da yin aiki ba amma cikin zuciyata ina sha'awar yin sana'a, da sauri ya ce wonderful tamkar ace kin shiga zuciyatakin gani ai ni mai sha'awar taimakon mace yin sana'a ne, Maryamu ina son ganin matata ta tsaya da kafafunta tana dogaro da kanta saboda karki samu damuwa akan wannan wacce irins ana'a kike son yi? Na ce a'a ban sani ba tukunna ni dai kawai cikin zuciyata ina son yi amma ban zabi wacce zanyi bal to ai kin gani ma shi kenan sai in duba in ga abinda zaifi dacewa da ke ina ganin ma kawai dinki za ki yi domin shi ya fi bani sha'awa ko kuwa? Na ce mishi to. Tun ranar da Mubarak ya zo gidanmu ya rokeni alfarmar fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba 88 ya dauki mataki in ya ganni bei kulani ko yana fara'a ya hangoni sai ya yi maza ya tsuke fuska, a zuciyata na ce nima gara irin haka, abu guda daya dai da na kasa fahimta ko dalilin yin shi shi ne wunin da Isiyaku yake yi kan dakalin kusa da gidanmu a zaune bana dai ko amsa gaisuwarshi balle-wani abu ya hadamu tunda kowa ya san dan gidan Mubarak don haka na kara kiyaye mu'amala da shi don Mansur ya kara samun kwanciyar hankali. Ni da Mansur muka zama bamu da wani fata ko buri sai na jiran dawowar babanshi daga tafiyar da ya yi. Mansur dak ullum yake ce min ai kawai kwana daya zan yi mishi in ya dawo da rana in barshi ya kwana ya wayi gari kafin inje mishi da maganar. Sai gashi baban Mansur ya dawo har ya kwana bakwai babu wani motsi ko yunkuri daga gidan nasu shi da kanshi ma sai nake ganin shi tamkar a sanyaye yake ban dai ce mishi komai ba tunda dama can ba ni ce mai zumudin maganar ba ni yar tawa ce. Wurin baba Lantana mai yade maganganu a tsakar gida na samu labarin wai ashe da baban nashi ya dawo ya kai mishi maganar sai ya ce mishi ba zai sake takowa ya zo wurin babana kan maganar aurena ba ya dai zuwanf arko ya kuma isheshi haka don haka in har auren yake so da gaske to ga 'yan mata nan bila adadin tun daga na dangi har bare yaje ya duba gida na mutunci ya zabi yarinya zai tsaya ya aura mishi ita 89 ko da kuwa nawa zai kashe, amma bani ba in ba rashin hankali irin nashi ba ko iyayen Mubarak da suka san da dansu na rinka lalacewa ai ba su bar shi ya aureni ba balle shi. Wannan bayanin da naji a bakin baba Lantana ba Raramin dukan zuciyata yayi ba, don kuwan a riga na Sakankance na saki jiki zuciyata ta riga ta amince da maganar aurena da Mansur sai dai duk da haka ban bari yanayin da na sanu kaina a ciki ya baiyana ba sabdoa na riga na koyi shanye bacin rai ba komai ya taba zuciyarka sai na kusa da kai ya gane ba, haka nan 6acin ran da na samu bai sa naji haushin iyayen Mansur ba to balle kuma shi Mansur din da na tabbatar shima bai ji dadin hukuncin da aka zartar mishi ba, sai dai ya yi biyaiya kamar yanda kowane da na kirki yake yiwa iyayenshi biyaiya kan umarni ko hani da sukayi mishi, bai dai ce min komai ba nima kuma bance mishi na ji ba sai dai kuma biri yayi kama da mutum gaba daya ya canza fara'arshi, kuzarinshi duk sun sauya mainakon zuwa kullum ya koma yin fashi in yau ya zo gobe ba zai zo ba watarana ya yi kwanaki na yi kamar in ya zo in rinka kin fita sai kuma na ga to a na me? Rannan dai ya gaji shi da kanshi ya zaunar da ni ya yi min bayanin komai, hakuri mai yawa ya bani ya kuma rokeni kan kar gaya min gaskiyar da ya yi ya kawo karshen mutuncni dake tsakaninma, na ce 90 mishi a'a ko kadan ba za a yi haka ba sai dai ma a kara nima nayi mishi godiya kan alherinshi a gareni. Ko ban tsaya yin bayani nayi bacin rai ko ban yi ba an san nayi saboda na riga na so aure na kuma soo Mansur don haka fadama batawa ne kawai. Tunda Mubarak ya taso ya zo gidanmu ya rokeni in fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba na Tura al'amura sun sauya a tsakanina da shi amma ban kara sanin irin tsananta da lamarin yayi ba sai a ranar da nayi shiri da niyyar zuwa gidan Yakumbo Halima saboda dadewar da nayi banje ba har na samu labarin korafinta wajen yaya Dija. 'Yar madaidaiciyar kwalliya nayi a dalilin tsala kwalliyar ta daina burgeni ta daina sanyani nishadin da ta saba sanyani a baya sai dai kuma bai hana kwalliyar tawa zamowa mai ban sha' awa ba. Ina tafiya cikin natsuwa ba tare da na damu da kallo ko sanin su wa nake wucewa bisa hanya ba har na kai ga shiga lungund a fi ta daga cikinshi zan bulla kan layin da gidan su Yakumbo Halima yake. Kasancewar lungun a matse yake gashi kuma da .yawan kwata 'yar hanyar da ake bi din ba wata mai fadi bane ya sani hi hanyar waiwayawa in ga wanda ke biye da ni yana taku cikin sauri dan in kauce mishi in bashi hanya ya wuce in har naga alamar akwai bukatar hakan, abin mamaki Mubarak na gani gabana ya yi mummunan faduwa bisa dalilin guda biyu dalili 91 na farko shi ne faduwargaban da na saba samu a duk lokacin da na ganshi ko na ji nmuryarshi wanda kwanakin baya nakem urnar na rabu da shi to ya sake dawowa, daliil na biyu kuma shi ne mummunan kallon da ya tsiri yi min a tsakanin nan ko yana walwala ya hangoni sai ya yi maza ya daure fuskaw ani irin daurewa kuma mai tsanani. Na maida kaina kan hanyada nufin ci gaba da tafiyata, yayin da wani 6angare na zuciyata yake bani shawarar in karta kawai da gudu don in samu in yi nesa da shi tunda ga dukkan alamu zai kamoni saboda dogon taku: da yake amfani a tafiyar ta shi. Tsaya mana mu yi magana, na yi kamar ban ji abinda ya ce ba na ci gaba da tafiyata sai kawai na ji caraf ya kamo gyalena ya rike, ina yi miki magana kina ji nakina tafiya. Raina a bace saboda fusatar da nayi na rike min gyalena na juya da nufin yi mishi tuni kan hana shi yi min hakan da na taba yi in da hali ma in yi mishi tuni cikin tsiwa den kar gobe ya yi tunanin sakewa. Muna hada ido da shi gabana ya sake faduwa na yi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda wani irin kallo da yake yi min wanda ban saba da shi ba. Kina nufin ko saurarona ba ki da lokacin yi da pake kiranki kina ji na? So nake in tambayeki yaya naji maganar aurenki da.masoyin naki tayi sanyi kamar ma babu ita? Sakarya kawai sokuwa mara 92 wayo wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya kamace ta in taso in zo in rokeki ki fita hanyar shi ki ce min wai ba za ki yi ba? Ai nayi hakan ne don ina zaton ina da matsayi a wurinki saboda kin yaudareni kin yi min abinda na yi zaton ni din daban ne a wurinki sabdoa kin yaudareni kin yi min alheri wanda na yi zaton bani da abokin gami a wurinki, ashe ba haka bane to amma kuma na gode shi da akayi mishi hani a kanki ya hanu. Gabana sai harbawa cikin sauri yake yi, bakaken maganganunshi sun yi tsanani da nauyi cikin zuciyata kokari mai yawa nayi kafin na danne hawayen da ke shirin zubowa a idanuna na hanasu zuba don kar in yi kuka a gabanshi don haka najuya da nufin ci gaba da tafiya, sai naji ya ce, ni babu inda za ki sai kin bani amsar tambayar da na yi miki. Cikin natsuwa na bude baki wanda bai ma san zan bashi amsa ba dan ya san ban cika yin hakan da shi ba na ce mishi, kayi hakuri ba yaudara ya sani yi maka hakan ba kuskure ne. Ya yi maza ya gyara tsayuwa tare da kara tsareni da idanuwanshi cikin saurarona binda zai kara fitowaa daga bakin nawa, ni kuwa ban fasa ba na ci gaba da yi mishi bayani, kuskure na yi nayi maka abinda na yi makan wanda ya sanyaka yin tunanin kana da matsayi na daban a wurina da har zaka ganni a masoyina ka roki alfarmar in fita hanyarshi, ko Mansur ya rabu da 93 ni ba zan zamo wani sabon al'amari a wurina ba don sunnar magabata ya bi zan kumaci gaba da girmamashi tare da soyaiyar da muka yi wa juna saboda mun yi ta mun gama ta ba tare da ta yi min wani sanadi na wulakanci ko tozarta ba a wurin jama'a, na kuma gode maka da baka yi amfani da kuskurena da wautata da sakarcina da sokoncin da na rayu a ciki a dalilin bani da mafadi ya sani nayi a kanka ba da ka yi amfani da damar da wadancan abubuwan suka sanyani na baka a kaina da ka yi dalilin da na kara zama shashasha sokowa sakarya waçce ta aikata kuskure a rayuwarta, kuskure kuma har abada, don haka duk abinda ya faru tsakanina da kai tun daga farkonsa har zuwa karshensa kus... Ban kai karsen maganar da zanyi ba sai kawai na ii kafafuwana sun zurma cikin kwatar dake bayana, nayi maza na kalleshi cikin tsananin bacin rai nan take kuma na sake dago idanuwan nawa suka hadu da na Mubarak dake yi min wani irin kallo, yanayin da na gani a tare da shi ya tabatar min da cewar ba ji nayi kama ba shine ya hankadani cikin kwatar da na zurma. Kar ki sake yin kuskuren kallon idona ki ce za ki yi min rashin kunya irin wanda kika yi min yau in kuwa ba ki ji kashedinda na yi miki to za ki gane baki da wayo, sakarya kawai sokuwa shashasha mara wayo 94 wacce rashinmafadi ya hanata sanin abinda ya dace da ita. Yana gama fadin hakan ya ja wani mummunan tsaki ya wuce yayi tafiyarshi ya barni cikin kwatar ko a jikinshi. Da kyar na iya zare kafafuwana daga cikin kwatar takalmana kuwa asararsu nayi don kafafuwan nawa kadai na iya zarewa, a hakana rinka diddingisawa na doshi gidan Yakumbo Halima cikin zuciyata dai ni kadai nasan abinda nake ji game da Mubarak, na tsaneshi na kishi na rinka jin wani irin ciwo a zuciyata game da shi, babu abinda ke kai kawo a zuciyata in banda na tunanin yanda zanyi in dau fansa a kanshi kan irin wulakancin da ya yi min, da dai ace so shi ne samu to da na tashi daga wannan unguwar na koma wata don in yi nesa da shi in dains ganinshi dan ya daena shiga harkokina. A haka na shiga gidan Yakumbo Halima, tana ganina ta kama yin salati, wane irin rashin dabara ne wannan Mero? In zaki fada kwata sai kuma ki fada da kafa duka biyu kamar wata yarinya 'yar karama? Ban iya ce mata komai ba kuka kawai na kama yi don daman daurewa kawai nayi na hana kaina soma kukan tun daga waje. Cikin hanzari ta tsame hanunta daga cikin kullin danwaken da take jefawa da sauri ta iso inda nake tsaye ina ta faman kuka. 95 Haba Mero haba Maryamu da so don kin shiga kwata kuma sai ki tsayakina kuka? Ai tsautsayi ne shi kuwa kin ji ance bai wuce ranar shi ba, bari in kwara miki ruwa a kafar in wanke miki dagwalon sai ki shige bandaki ki yi wanka ki canza kayan jinki da wasu. Har nayi wanka na fito na gama abinda zanyi duka na zo wurin Yakumbo Halima na zauna ina tayata jifan danwakenta idanuwana basu daina zubar da hawaye ba, na kasa gane dalilin bakaken maganganunshi musamnman gorin da yayi min kan fasa aurena da Mansur ya yi sunyi min ciwo da yawa. Rarrashi, banbaki da wayon da Yakumbo Halima tayi tayi min ya sani kwashe bayani duka na yi mata. Dama ashe zancen da nake ji a gari na bar yanzu baku rabu da juna ba gaskiya ne? Tsuru na yi ina kallon Yakumbo ashe kuskure nayi da na yi mata wannan bayanin, ashe da ma kadan take jira da ni, to kuwa ba zai barki ki yi aure ba kin ji na gaya miki ke ya hanaki aure ya tsareki a waje a cikin gida kuma yana tare da matarshi duk tsiyar da yake yi mata wanda ke sanyata zirga-zirgar yaji tun da dai yana kusantarta ya biya bukatarshi a tare da ita ai aikin banza ne karyar iya shege kuma yake yi wanda bai Son mata ai baya kusantarta indai har da gaske yakeyi yanzu da ta tafi kwanan nan iyayenta suka aiko a gayawaAlhaji Muhammadu cewar tana da ciki wata 96 biyu yayi musun cikin? Ba cewa sukayi sun janye sakin da yayi mata ba sukaje suka dawo da ita dakinshi kuma suna nan tare su na zamansu ana tarairayarta ana murna zata haifar m usu da ko ya, shi ne ke ba za ki yi zuciya ki kama mutuyncin kanki ki fita harkarshi ba sai ki je kina biye mishi kuna lalacewa tare... ta kama kuka irin wanda bai kwatantuwa. Jikina ya kama 6ari hankalina ya yi mummunan tashi ganin irin kukan daYakumbon keyi, na rantse aiki Yakumbo... kan in fadi abinda nake nufin gaya matan tuni ta rufeni da duka da hannaycnta duka biyu, rantsuwar karya zaki yi min saboda kin maidani shashashar uwa to ai ni da yaya Ramatu duk daya muke uwa daya uba daya muka tasha nono ta bani da kike nema ki maidani mara mutunci. Tana kuka take wannan bayanin. Tuni nima na shiga nawa kukan, ba don dukan da tayi min din ba sai don bakin cikin al'amarina da bakni cikin yanda na zamo gaba daya iyayena da jama'ar gari suka yarda da cewar lalacewa mukeyi ni da Mubarak, yaya Dija ce kawai na tabbatar ta yarda da maganar da nayi m ata na babu komai a tsakanina da shi don ta babans kuwa ba zan iya cewa koami ba tundaban taba jin ya bude bakinshi ya fadi wata magana ba balle in san a wane hali ya dauki lamarin. 97 Ban san abinda ta gani ba ko abinda ya faru ba naga maimakon dukan da take ta kai min da hannayenta duka biyu ta jawoni jikinta ta kankame da karfinta kuka mai yawa ta yi kafin daga bisani ta sakeni, ki yi aure Maryamu ki yi aure abinda kawai zan gaya miki kenan. Magaiar da ta fara yi kenan bayan ta gama kukan nata. Cikin sauri na ce mata to Yakumbo ba tare da na san wanda zan auran ba sai dai kawai don in kwantar mata da hankali. Alkawarin da nayi wa Yakumbo Halima na cewar zanyr aure ya sans himmatuwa wajen ganin na fidda mijin aure ko da kuwa wane iri ne babu maganar tsayawaduba cancanta balle a yi maganar zabe, aure kawai nake so in yi ko zan samu in fita daga zargin da ake yi min na akwai wani abinda ke faruwa tsakanina da Mubarak na lalacewa sannan yin auren nawa zai zamo dailin da zan bar unguwarmu in yi nesada ita in daina ganin Mubarak wanda a yanzu na tabbatarwa kaina da cewar in har akwai wani mutumin da na tsana a rayuwata a halin da nake ciki to shi ne na tsani Mubarak, na tsani duk wani abinda ya shafeshi, na tsani duk wani labari da ya danganceshi, musamman ma labarin matarshi da cikin dake gareta wanda kuma ya zamo shi ne labarin baba Lantana da take wuni tana bayarwa ta rinka fadin karyar banza karyar wofa, yana kinta yake kwabewa 98 a gabanta? Sai kuma ta ja wani mummunan tsaki ta ce, ku dai da ya mayar sakarkaru ke da ubanli sai ku yi tayi ya rinka samunki yana rage gajiyarshi ta rana a kanki tunda haka kuka zaba. Rabon da in tankawa baba Lantana ko wani nata wata magana har na manta saboda abinda nake ji yafi karfin duk wasu maganganun na ta ciwo a raina. Rannan ina tsaye tare da wani sabon saurayi da nayi wanda inda ya biye min da ko kwana goma bai yi da fara zuwa wurina ba ya turo iyayenshi aka daura mana auren saboda irin karbar da na yi mishi da kuma za a tsareni a tambayeni dalili na na yin irin wannan bare-baren a kanshi abu guda da zan iya fadi kawai shine ba dan unguwarmu ba ne ina son aurenshi ne kawai don in samu in yi nesa da unguwar in banda haka babu wani dalili. Ina tarę da shi muna hira a kofar gidanmu sai kawai ga Mubarak tamkar daga sama aka jehoshi, gabana ya yanke ya fadi saboda ganin inda muek zaune ya tunkaro gauan-gadan nayi maza na kawar da kaina daga gareshi saboda irin kallon da na lura yana yiwa wanda muke tare da shi din wanda shima na gane ya tsargu da Mubarak din. Yana isowa sai na ji ya ce mishi, malaml afiya na ganka anan wurin? Da sauri mutumin ya daga ido ya kalleshi latiya? Ban gane tambayar taka ba, ya zuba mishi ido cikin natsuwa yana kallonshi, wannanai 99 iyalina ce baka ji abidna ke tsakanina da ita ba ne? Ya shiga waige-waige hankalinshi a tashe jin da ya yi Mubarak ya ce mishi ti din iyalinshi ce. Ai ban san matar aure ce ba ni asanina... Kan ya karasa bayanin ya yi maza ya ce mishi, bar nan kawai tun kafin abin ya kai ga ranka ya baci. Yanzu kuwa in ji mutumin, ko raina b a zai baci ba ma ai da sanina b za ni wurin iyalin wani ba, ita ta ha'ince ni ta boye min gaskiya, ya kama hanya ya yi tafiyarshi, nima na mike na shiga gida na barshi a wurin ban tsaya jin wata magana tashi ba. Ina gida akan gadona a kwance ina tunanin al'amarin cikin zuciyata dai nasan babu mutumin da yake shiga harkokina yake takuramin yake bata min rai yake sanyani bakin ciki a rayuwata irin Mubarak sai daiban san yanda zanyi da shi ba tunari mai tsanani na shiga ciki har daga karshe na yankewa kaina hukuncin komawa gaban Yakumbo Halima in gaya mata abinda ke faruwa don kar ta dauka ban ji maganar da tayi min na inf ito da miji ba. Na gyara na yi kwanciyata da tunanin na kaiwa Yakumbo Halima bayanin abinda Mubarak kc yi min. Ina kokarin tilasta kaina yin bacci kenan sai na ji Asabe tana kwalawa sunana kira, cikin irin muryar tsoro ne ya kanani saboda sanin da nayi cewar ni da Asabe bama ko ga maciji. 100 Waiyo-waiyo dama dai kawai in mutum in huta da wannan wahalar. Zumbur nayi na tashi na zauna saboda jin maganar ta ta, me ya satieki haka Asabe? A tsorace na yi mata tambayar. Bata tanka min ba, waiyo-waiyo, abinda kawai take te faman fadi kenan. Na sauko gareta ina kokarin riketa don in tsaida murkususun da take yi a kasa cikin yanayi na tausayawa ina isowa garéta na gane lamarin ba karami bane, ya kuma wuce duk yanda ake zato don haka nace mata bari in kira miki baba Lantana don tazo ta ga halin da kike ciki in yaaso a kaiki asibiti. Tayi maza ta ce min u'u barta kawai kar ki kira min ita ke dai kawai ki taikameni ki kaini cikin kankon bola ki barni a wurin in ma mutuwar zanyi in mutu a can. Tausayin Asabe ya yi matukar kamani, haba Asabe daina fadin irin wadannan kalaman kankon bola a cikin tsohon daren nan ko mahaukaci ai ba zai dunfari wurin ba, na shiga share mata gumi da majina da hawayen dake ta dalala. Ki yafemin abubuwan da na yi tayi miki Mero satar kayanki da ua rinka yi ina sayarwa da kudinki da sharrin da na... Kai haba Asabe bar irin wadannan maganganu ai zanman tare ne. Ana cikin haka naga Asabe tayi rigingine ta bankade komai babu sauran kunya a tare da ita, tsoro ya sake kamani jikina ya dauki rawa cikin muryar kuka nace mata Asabe, don naga alamar bata cikin 101 haiyacinta, kan in kai kkarshen bayani na hango wani abu yana shirinf itowa da gudu na nufi kofa na 6alleta cikin rawar jiki da karkarwa na buga kofar da take ta baba Lantana da babana, tana jin bugun kofar da nayi sai na ji ta soma cewa, yauwa ai ga ranar da nake jiran zuwan nata nan ta zo ranar da asiri zai tonu, ranar da zaka gane shirunda kake kame bakinka kana yi a kan komai ba dabara bace, ai tun dazu nake gaya makaa wannan zirga-zirgar da akeyi ana ziryar bayan gida da kyar ne in ba nakuda ake yi ba, ni na dade ina fatan ganin an haifar maka shege a gidan nan, ba dai kwadayin abin duniya ya sa ka zuba mata ido tana yin abinda taga dama ba? Yaro ya ki aurenta ya kai gida amma a waje ya maida ita matarshi? To muje ka karbi haihuwar da hannunka don kar ka ce sharri aka yi mata ba a jikinta ya fito ba don haka nuje a yi kornai a kan idonka, kaga ta inda yalke fita muje mu je. Ina jin hakan nasan fitowar zasu yi tare don haka na tsaya a inda ana bude kofar babana zai ganni. Abin kunya ina jin gadonshi kukeyi malam tunda ba haka ai nayi ta gudun makashi baka yarda da shawarat bane yasa baka koreshi ba sai da ya sameka saboda bai damcka ba, muje nace muje kana ji ana ta gurnanin nakuda ka ki kayi kuzari sai wani jan kafa kake yi kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. A na bude kofar mukayi ido hudu da babana, muje m ana kayi wani kerere ka tsaya min a hanya 102 kaki ka bani wuri in fita, abinda haba Lantana ke fadi kenan daga bayanshi saboda kasa motsin da ya yi a dalilin ganin da ya yi min a bisa da na tabbatar kuma shi ne da ni ya gani a cikin wani hali na abidna take gaya mishi watakila da ya yi faduwar da bai sake tashi ba don a haka ma tsinkewar da yayi ta kai duk inda ta kai. Kurdawa tayi ta bayanshi ta fito saboda ta kasa hakurin ya matsa ya bata wuri, tana ganina a tsaye tayi maza ta ja ta tsaya ta yi turus cikin tsananin kaduwa nan take tsoro ya baiyana a idonta, a'a to wake zirga-zirgar da gurnanin nakudar da ke fitowa. Ban ce mata kala ba balle kuma babana da ya zama tamkar mutum mutumi, to wane irin abu ne kuma haka mai nakuda tana tsaye kememe, da gani dai nasan kece kike wannan zirga-zirgar da gurnanin nakudar inma... Kan ta karasa maganganun nata masu kama da sanbatu sai kawai mika jiyo kukan jariri daga cikin dakin namu. Ina kallon yanda jiri ya debi baba Lantana ya yi wuji-wuji da ita kafin ya fyadata da kasa, tayi faduwar yan bori vato da mazaunanta, tsoro ya kamani saboda ganin irin faduwar da tayin, sai kawai na ga ta zabura da iyakacin karfinta ta yanka da gudu ta nufi cikin dakin namu. 103 Wato da ma shari ne abin? Watp ni za a kawowa iya shege? Dama da hadin baki ne tsakáninki da m atsiyacin likitan da yace min kaba ce da ke? Ni za ki kawowa tsiya? Ni za ki jawa magana? To ai kuwa yanzu za ki gane wautar ki don kuwa kasheki zanyi murus har lahira. Tana fadin hakan mulka jiwo-ibun Asabe da sauri Sallau ya fito ya fada cikin dakin; ba zaiki kasheta anan ba baba ba zaki yi mana kisan kai a gida ki jawo mana wata fitina ba, tunda dai har kin kaita gun likita ya ce miki kaba ce ai kin san da komai, lokacin baya ta kawo miki gasassun kaji kina ci kowa ai yana girban sakamakon abinda yake aikatawa ne. Da karfi Sallau ya jawo baba Lantana ya fito da ita waje, tana-kicin kwancewa daga gareshi tana kurma ihu da iyakacin karfinta, ka sakeni kawai in hadata ita da shegen dan natain murkushesu kowa ya huta. Wannan dai duk kina kokarin jawowa kanki wani abin magana ne kawai in har kika bari makwabta suka jiyoki suka gane abinda kike ciki da ma ki yi maza kin san abinda kike ciki da ita da dan nata kafin gari ya waye magana ta watsu. Daga cikin gidan baba Baidu muka jiwo muryar baba Sumaye tana cewa, kar makwabta su ji na nawa tunda ni naji? Ai ko ladan cikins hegen da tayi ta rokarwa ya'yan jama'a sai na baza wannan labarin, 104 barde a gonar wani sunkuru ya rufe naka, ddonki kam ya' yan jama'a ammakin kasa sawa naki balle ki gano abinda suke ciki, wai likita ya ce miki kaba ke gareta? Ta kwashe da dariya kafin ta ce, saboda ya gane ke din mahaukaciyar uwa ce shi ya sa ya yi miki hakan, kar kumaki ji da wai ba nan unguwar ba ko a wani wuri na ji 1abarin an tsinci mataccen jinjiri zan kai rahotonki don nasan halinki kin kuma furta zaki kashe uwa da da kat su jawo miki abin kunya, sai kace in da ana kashewa da ke kin kawo yanzu, ai yanda kika sa su Jkuka da bakin oiki lokacin da kikayi naki haka kema za á sa ki ki yi abinda,kukayi ne ai za a yi muku, shi kuma malam Habu Ubangiji ya yaye mishi abinda ya sameshi, yauwa duk inda naji an tsinci mataccen jinjiri nasan kece zan fada na kangon bola ma da aka gani kwanaki wa ya sani ko ke kika kaishi? Fitinannun mutane masu jawa mutane annoba iri-iri. Baba Sumaye tana rufe baki baba Lantana ta yi zumbur ta maike da sauri ta sake shigewa cikin dakin namu inda Asabe da dan jaririnta suke tamkar dai ace dama kasake tayi tana sauraron bayanin nata ban san yanda akayi ba sai ganinta muka yi ta fito tana rungume da dan jariri Asabe tana biye da ita cikin katon lullubi sun sa kai sun fita sun bar gidan, ganin sun bar gidan ya sa ni nufin shiga dakin namu wai in kwanta. Abinda na gani a tsakar dakin ya sani 105 kwallara ihun da na dawo da baya cikin sauri Sallau ya fito ya leka cikin dakin ya tayani ganina binda na gani, ya koma ya dauko leda ya sanya shi a ciki ya kuma. sa omo da izal da tsintsiyar zabori ya wanke dakin tas zuwa tsakar gida dama bayan gidan baki daya maimakon karni da kazantar jini ya koma tsabta da kanshin kayaiyakin da ya yi amfani da su. Na shiga dakin nayi salla na hau gado na kwanta cikin jimamin abinda ya faru, akan idona Asabe ta haihu ta haifi da babu aure ba shiri nake yi da ita da uwarta ba amma na tausaya mata tare da dan nata, ina cikin hakan na jiyo muryar baba Lantana tana cewa ba dai dani kuke yi ba ai za mu sa kafar wando daya ni da ku, munafukan banza munafukan wofi matsiyatan mutanen da basu san mutunci ba duk zaluncin ubanku. Na yi kasake ina sauraron zage-zagen nata cikin zuciyata na ce, oh oh wannan mata da jarumtaka take ko ita da su wa take yi oho. Ina jinta ta shigadakin da Sallau yake bamuji komai ba illa iyaka dai na jiumuryarshi yana ce mata to nan take kuma ya yi waje, nima na fito don in nemawa babana abin karyawa da kuma maganinshi, lokacin ne na gane daga tafiyarshi masallaci don sallar asuba bai sake dawowa gidan ba. Ina daki a kwance ina sauraron shigowar babana don ba dabi'arshi bacewucewa kasuwa daga 106 masallaci na ji muryar Salau alamar ya dawo daga aiken da ta yi mishi na ji shi a fusace yana ce mata, kin ganta ko mnama kin ganta ko baba kinga halin Asaben ko? A gabanki bakinta ta ce min Agogo ne ba? Gabana ya yi mummunan faduwa cikir raina na ce Agogo kuma? Ban kai karshen maganar zucin nawa ba naji Sallau shima yana karasa nashi bayanin to an je anzo da Agogo ya zo ya zare m ata ido yana tambayarta' shi kadai ne su sauran me yasa bata amabci sunansu ha sai shi? Mainakon taja ta tsaya a kan shi kadai ne sai kawai ta tsorata ta ce wai Alhaji Nalami ne. Kiis ya rage in rikito kasa daga kan dan gadon nawa saboda firgitar da nayi, nayi maza nasa hannu biyu na dafe kirjina saboda harbawar da ya kama yi, nayi maza na sake tambayar kaina, Ahlaji Nalami kuma? Wannan abin mamaki da ban tsorod a yawa suke, Nalami da Agogo su Asabe take tuihuma da yi mata ciki, ita kuwa wane batan basira ne ya kaita yin hakan? Tsawon lokaci ina tunanin tsakanin biyun wanne ne dama dama? Agogo dai shi ne mutumin da ya jagoranci abinda Mubarak ya sa aka yiwa Sallau wanta da suke uwa daya shi kuwa Nalami ba sai na tsaya ina wani dogon bayani a kanshi ba ko da yake dai baba Lantana tayi nufin badani gareshi ta kuma yi 107 mishi tayin Asaben don ta samu warware mas alar kudin da suka shiga tsakaninsu to amma tunda hakan bai yiwu ba wane birgewa ko sha'awa wannan mutumin ya baiwa Asabe da har ta yarda da shi har take tuhumarshi da zamowa uban danta? Na yi maza na bar wannan tunanin na shirme tunda gani nake tamkar bai shafeni ba na amsa sallamar da naji ana kwalawa a kofar gidanmu da sauri na fita don ganin masu salalmar, tunda na jiwo muryoyi da yawa alamar ba mutum daya bane. Ina fita naga an ciccibo babana rabe-rabe wai faduwa yayi a kasuwar timatirin su nan take na kama salati, ina yin kuka, wani daga cikin mutanen dake rike da baban nawa ya dakamin tsawa, kaice ki ba mutanc wuri munafuka kawai duk ba ku kuka jawo mishi ba, ita ce fa wacce kwanaki aka yi tsiyar nan a kanta ran daren da zan daura mata aure da wani aka kamota a dakin wani kato wanda shi babu yanda ba a yi da shi ba ya auretan ya ki amma don hauka da rashin zuciya taje ta kai mishi kanta shi kuwa warda zai auretan da ya ji labari ya cco ti ya fasa. Wani daga bayan yace, a'a to zai fasa mana da ka auri bduurwa fanko ai gara ma ka auri bazawara da ma kasan abinda ka aura, ni da aka bada labarni haihuwar yar tashi ai na dauka ita wannan din ce ta haih:, ashe wata ce kuma daban? Wato shi 'ya' yan nashi duk haka suke? Su matan lalacewa ta bin maza 108 shi kuma namiin kana ganinshi ba sai an yi maka bayani ba, baki a rube ko ina kuma a fuska tabon adda, to amma dai dan gara shi tunda ba zai dauko mishi irin wannan maganar ba, lalacewar 'ya mace ai babbar musiba ce ko ba komai kuma gashi ya fara dawowa kan hanya tunda yana binshi kasuwa yana kuma taimakonshi ba kadan ba. Kukan da nake yi bai hana zuoiyata tunamin maganganun nasu ba wannan wane irin rashin adalci ake yiwa babana wato su Asabe su Sallau din ma duk ya' yanshi ne? Ban kai karshe ba na ji wani ma ya kama bayanin 'ya mace, nifa shi yasa ma ban cika son haihuwarta ba na kuma yi sa'a 'ya'yana bakwai gaba dayansu maza ne babu mace ko daya. Wani kuma daga can gefe ya ce kai ba fa duka matan ne haka ba in akayi sa'ar su aka dace da na kirkin dadin al'atmari ne da su saboda su din masu tausayi ne, shi malam Habu har da laifinshi cikin lamarin iyalinshi don kana da hakuri ba dalili bane da zaka zuba ido ka barwa matarka da' ya'yanka sai yanda tayi da su ai cewa akayi ku kare kawunanku da iyalanku daga shiga wuta to shi ya zuba ido a kan komai ya bar mata tafi karfinshi, yaushe ake yin haka? Haka ne haka ne suka amsa. Suna barin gidanmu nima na fita don nemana motar da zata daukar min babana zuwa asibit, a kan idona ina ji ina gani nake jin mutnac suna bayani an 109 haifi shege yau a gidan malam Habu wanda ake yiwa bayanin sai ya tambaya wane malam Habun? Sai a tsaya bayani malam Habu mai tmnatiri, nan na wajen kan kwana baban wannan Maryam din da kwanakin can watannin da suka wuce aka kamota a dakin saurayin da take kwanan gida har kan haka mutumin da zai auretan ya fasa? Sai ace haka haka na tuna, dattawan unguwa kuwa fadi suke yi kai malam Habu bai yi sa'ar iyali ba. Raina ya baci zuciyata tayi zafi hankalina ya tashi, na rasa inda zan tsoma rayuwata in ji dadi, da dai ace nasan abin da zafi àru kenan to da na ja Asabe na fitar da itn daga gidanmu in ya so ko a kan titi ne ta haihu, gaba daya sai masu magana suka mance dabana ba shi ne uban Asabe da Sallau na asali ba suka kuna mance da cewar bayanin da nice 'yarshi ta asali yana da ya' ya Dina in ni ban zamo mutuniyar kirki ba ita ta kirki ce don kuwa in dai biyaiyar aure shi ne kirkin mace to yaya Dija ta kirki ce. Ina kuka nas higo gida lare da direban motar da na samo don ya tayani daukan babana, yaya Dija na gani a gidan ta zo saboda labarin da ya je mata sai dai kuma wai cacar baki na samu suna yi da baba Lantana, Asabe ai mai imani ce shi yasa ta haifi nata dan mai rai ke sau nawa kanwarki tana cikin shege kina cire mata? Ko ance miki ban sani ba ne. 110 Wuceta nayi ko kallonta banyi ba na shiga dakin da babana ke kwance na cewa direban shigo daga nan kan ya shigo ta biyoni ina kuka nace mata babanmu yana kwance kina fada da ita? Kan tayi min magana baba Lantana ta cafe tana zaton zan kyale ta ne take wani zuwa wai kar 'ya' yana su sake shigowa nan gidan to wannan gidan har wani gida ne da za a yiwa mutane doka a kanshi? Ban amsa ba itama yaya Dija ta yi shiru, ai a shirye nake don ni din warki ce dai dai da kugun kowa wanda duk ya shiga lamarina zan shiga nashi in ka gayamin cuta kuma zan gaya makam utuwa, munafukan banza munafukan wofi duk sai kun ci gidanku a hannuna. Muna jinta tana tayi muka fitar da babanam uka tafi asibiti gado aka bamu ni ce kuma na zauna tare da shi a wannan karon ko tayani kwanan da Sallau ke yi ban yarda ya yi ba. Ina zaune kan kujera gaban gadon babana yake kwance ina kallon babana da halin da yake ciki, tunani kawai nake yi na al'amuran dake ta faruwa da mu daga wannan mu koma wannan, sai ina ganin kamar al'amura sun soma wucewa an fara samun sauki sai kawai wani abin ya sake tasowa a sake fadawa cikin wata mas'alar da zan rinka ganin tamkar tafi wacce aka baro baya tsanani. 111 Ana cikin haka naji motsi a kusa da ni, nayi maza na daga kai don ganin ko waye? Mubarak na gani a tsaye daga gefe kadan kuma babanshi ne Muhammadu, cikin tsananin kaduwa da firgita nayi maza na sauka daga kan kujerar da nake zaunen na tsuguna a kasa karo na farko da na ga baban Mubarak bayan faruwaral'amuran da na daina shiga gidanshi. Tashi maryam tashi ki hau kan kujerar ki ki zauna. Ban iya motsawa ba ban iya tashi na hau kan kujerar ba ban kuma iya buda bakinan a gaisheshi ba, kuka kawai nake yi. Ubangiji ya bashi lafiya, Ubangiji ya sa kaffara ce, Mubarak ne ya amsa addu'ar da baban nashi ya yi da amin. Maganar da na ji Mubarak din ya fara yi min ta tabbatar min da cewar bayan yayi addu'ar bai tsaya ba tafiya yayi don haka na mike na zauna a kan kujerar da na bari. Kina ganin kamar akwai wani dauwamammen abu ne a rayuwa? Duk wadannan abubuwan da kike gani wata rana za su wuce don hakaki rinka yin hakuri. Ya ciro kudi masu yawa ya ajiye a gefen gadon, ki rike wannan a wurinki ni zan tafi baba yana jirana: Na yi maza na ce mishi bana so dauki kudinka ka tafi da su, bana bukatar komai daga gareka. Ya yi 112 kamar bai ji ba ya juya da nufin tafiya, nayi maza na ce mishi, da ka yardar kca daukárdon kar su zamo maka sanadin bacin rai saboda zan iyabadasu a kaiwa ma... Ban san yanda aka yi ba naji ba zan iya karasa abinda na yi niyyar gaya mishin ba, wucewa yayi ya yi tafiyarshi baftare da amsa min ba, nima na zubwa kudin ido ina kallonsu: lokaci mai tsawo kafin nasa hannu a kansu na daukesu na adanasu. Kwananmu uku kafin a ka sallamomu muka dawo gida. Mutane suka sake tasa babana da gidan mu da ni ma a gaba kai kace nice na haifi dan shegen. Ina dakina ina zaune cikin damuwa da tunani iri- iri na ji Sallau yana cewa, baba Lantana ai Asabe ta kamanta ruwa ido 6atan 6akatantan zata yi tayi dalilin da dan nata zai rasa madogara kamar.... Da sauri baba Lantana ta wulwulo ashar ta antaka mishi, ya ce to shi kenan baba nayi shiru na kuma ji ni mahaukaci ne to na rokeki ki taimakeni ki daina tunani wajen maganar Asabe da samarinta da dantaki samu masu hankali su rinka zuwa miki. A wannan lokacin wata irinr ayuwa na tsunduma yi da ba ma zai yiwu ince zan tsaya ina bada labarinta ba, abinda dai na sani kawai shi ne ina wuni ban kai wani abu bakina ba saboda kwata-kwata yunwa ta rabu da cikina mafi yawancin lokaci ruwan kawai 113 nake sha saboda bushewar makogaro dake yawan damuna. Rannan an wayi gari da safe wankin kayan babana nake yi saboda ya dan fara samun sauki ya yi amfani da tsabtataccen kayaya dan ji dadi, ina cikin yin wankin ne naji anyi sallama a kofar gidanmu, Sallau baya nan don haka na yi maza na leka tun da nasan babana bai mallaki karfin yin hakan ab. A hankali nayi leken don ganin mai sallamar a dalilin ban cika son hada ido da yaran unguwar ba, malamina na makarantar islamiyya na hanga malamn Yahuza da sauri na karasa fita wajen naje na tsuguna kasa cikin wani irin yanayi na kunya da kuma girmamawa, sannu da zuwa malam. Haba Maryamu shirun naki ai yayi yawa shiru- shiru shiru da ba zai yi auren ba ai sai ki dawo karatunki, ai ba haka rayuwa talke ba komai kika gani yana da lokacinshi shi aure lokaci ne in har lokacin shi bai zo ba babu yanda za a yi a yi shi, watakila mijin naki bai zo ba, ita kuma mace bata aure sai mijinta don hakaki dawo karatu kin gane ko? Nace mishi to malam. Kar fa kice min to'ki zo baki dawo makarantar ba don sau biyu ina turo yara abokan karatunki su zo su kiramin ke ba ki zo ba. Kamar ince mishi babu wanda ya zo ya kirani sai naga bari in yi mishi shiru kawai. Ai ba a girman da 114 ake wuce yin karatuna addini, shi dan adam yana rayuwa ne a kan neman ilimin sanin nahalicci don haka ki dawo makaranta kin gane? Na sake ce mishi e malam. Muka yi sallama ya tafi nima na shiga gida, a zuciyata na'rinka tunanin ko su waye malam ya turo su kirai oho, ina cikia tunanin hakan sai kuma na watsar na bari saboda na gane sanin ko.su waye din ba zai amfanar da ni da komaib a. Zuwan da malam Yahuza ya yi ya sanya ni na ji wani canji cikin zuciyata saboda irin nasihun da ya yi min, kwadayin karatu ya sake dawowa cikin raina, sai dai kuma yaya zanyi in sake fuskantar yan makarantar bayan duk irin kwaramniyar da na yi ta fama da ita? Da wane idon zan sake kallonsu? Wannan shi ne abinda ya fi komai tsaya min a rai. Kwana biyu bayan zuwan malam har lokacin ban fara zuwa makarnatar ba sai dai kumna bana jin dadin hakan da nayi, in na yi tunanin menene ya dame ni wanda ya sa zuciyata take yi min nauyi? Sai int una malarn Yahuza ya tako har gidanmu ya nemi in koma makaranta in yi ka ratu abin yi hakan ba, abinda ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba yin hakan rashin girmamnawa ne ga na gaba musamman malaminka. Rannan dai na daure na tafi gabana kuwa sai faman bugawa yake yi, kirjina yana ta faman harbawa da sauri-sauri, a tsarge kawai nake zaune a ajn motsi 115 mai dan karfi in akayi sai inji na kara takura in yi kamar ni ake nunawa ko ake bada labari na. Malam Wahuza ya yi matukar farin ciki da ganina ya yi mana karatu ma1 gamsarwa ya yi mana kuma nasiha kan yan uwantaka irin na musulunci tare da bayani kan wanene musulmi? Lokaci mai tsawo ya dauka yana bayani akan siffofin musulmi na kwarai da Manzon rahama (S.A.W) a kai daga cikinsu akwai kubutar musulmi dan uwanka daga sharrin harshenka ya gama, ya y mana addu'a muka shafa nad awo gida. Na soma zuwa makaranta a kunya ce a darare sai dai ba a dauki lokaci mai tsawo. ba sai na wartsake har ma karatun nawa ya zamo daga cikin abubuwan da suke ragemin damuwata su nutsar min da zuciyata musamman ma da yake yayi dalilin da na koma yin karatun Alkur'ani mai girma sosai da sosai wanda da na daina yi saboda damuwa da rudewa in ba haka ba ai na dade ina jin malamai suna fadin cewar shi Alkur'ani waraka ne ga duk wata cuta ciki kuwa har da na zuciya. Daga komawata makarantar Islamiyya sai mu'amala mai karfi ta kullu tsakanina da malam Yahuza, saboda kullum idonshi yana kaina na zo makaranta ko ban zo ba. Ki koma makarantar oko don ki samu damar mallakar takardarki ta karatun college, na ce a'a 116 malam ai ni bokon nan ba wani damuna yayi ba. Ya vi murushi to at ko bai dameki ba kin rigakin yi shi takardar da za ki mallaka ta zame miki shedar wahalar kiken emaki yi wasa da ita, alhalin ilimin yanzu ya ta'allaka ne a kan abidna aka gani a rubuce don hakaki koma ki yi karatunki karki yi wasa da lokacinki, shi lokaci da kike gani ba a wasa da shi tsada ke gareshi, baki ji abin da wani bature mai hikima ya fada ba? Ya ce "A man who dares to waste an hour of time was not discovered the value of life. Mamaki ne ya kamani jin da nayi malam Yahuza yana rangada lafiyaiyen turanci da bakinshi bayan na dauka arabiya ko larabci kawai ya iya. Shirund a nayi ya sashi tambayata ko kinfi gane dai ki jira mijin aurenki ya zo ki yi.aurenki kawai? Shiru nayi ban amsa ba iyaka dai kaina a sunkuye ban kalleshi ba, amma nasna murmushi yayi kafin ya ce min, iaina zamna jiran miji Maryam saka al'amura masu yawa a gabanki sai ki ga ma yafi saurin zuwa gareki tunda shima ya san bashi kadai kike jira ba kin gane? Na ce mishi to. Kalamai da nasihohin da malam Yahuza ya yi ta yi min su ne suka karfafa min zuciyata da ta riga ta karaya da al'amuran rayuwa har na rinka ji da ganin tamkar bani da wata mas'ala ko damuwa a tare dan i in dai ba ta rashin lafiyar babana ba ne. 117 Makarantar koyar da sana'o'in mata ta Markas wacce Mansur ya taba bani labari na shiga da taimakon malamina malam Yahuza shi ya karbomin form din na cike ya mayar ya kuma biya kudin form din gashi kuma anyi sa'a kyau ta ce form din kadai ake saya, ajin dinki na shiga shi en.a raina tun sanda Mansur ya ce min ya fi sha'awata da yin dinkin. Na fara zuwa Markas mas'alolin da na fuskanta ba su wuce na wahalar tafiyar kafar da nake yi da kuma dawowa gida da nake yi ban samu abincin da zanci ba sai na nemawa kaina hakan kuma na jira. Na wayi gari rannan ina gida banje wurin koyon sana' ata wato Markas a dalilin renar da Jumaa ce ranar Juma'a kuma ranar hutu ce a garemu, ina kwance kan gado na na hutawa bayan na kammala wanke mana kayanmu ni da babana sai kawai naji Sallau yana cewa uwarshi, kai an auná arziki yau dai an daura auren Asabe magana ta kare. Sauri nayi na kara maida hankalina wajen jin maganar tasu tare da tunanin Asabe tayi sa'a itama ta samu tayi aure dukd a cikins hegen da tayi ta haihu ni ce dai... kan in karasa tunanin zuciyar tawa sai naji baba Lantana ta ja wani mummunan tsaki tare da fadin, to wani kokari kayi a hakan? Ina ce takardar filina da ya karba kawai nace ka karbo min a matsayin sadakin auren nata ka kasa ka karbomin nera goma. 118 Ya ce, uhun baba kenan ba ki ma san yanda akayi ya bada nera goman bane abinda ja yayi ya tsaya a kan nera bakwai zai bayar sai da malamin da zai daura auren ya ce mishi bai kai rubu'u dinar din da shari'a ta yarda a karba a matsayin sadaki ba shi ne ya bada goamn, ni dai tunda Asabe ta samu mijin aure zata isa gidan mijinta yau danta kuma ya samu uba ba zai yi ta watangaririya a hanya bai san ubanshi ko danginsu ba ai shi kenan magana ta kare a wurina. Duk da ganewar da nayi Alhaji Nalami Asabe ta aure kalaman da Sallau ya yi sun sani girmamashi tare da auren da Asaben tayis aboda na gane aure daraja ke gareshi Sallau kuma na gane natsattsen yaro mai kuma hankali tsayaiyar tarbiya ce kawai bai samu ba. Na fara zuwa wajen koyon sana'a ta a Markas babu dadewa'sai kuma malam Yahuza ya sake yi min magana kan wata babbar makaranta ta ilimin addini mai zurfi da aka bude duk da irin kudaden da ya yi min bayanin za a kashe kafi in so ma karatun na shige ta saboda yaya Dija ta amince da shigar tawa ta kuma bayar da duk wani abinda aka nema shi kuma malam Yahuza sai ya taimaka min da manyan litattafai masu tsada a matsayin aro kafin ta samu ta saya min nawa in mayar mishi da nashi tunda shima ba daina karatun ayyi ba tunda shi littafi abin ajiyewar dalibi ne. A wannan lokacin sai na zama kusan kullum ina da abin yi mafi yawancin lokacin ma nakan fita da 119 safe ne in dawo da yamma saboda zan tashi daga nan in nufi can don ma dai kawai babana yana raina kowane lokaci. A wannan lokacin baba Lantanaa wuni take yi tana yiwa babana gorin auren da Asabe tayi da na hada 'yarka da shi kuka ki ai gashi ni na bashi tawa tana kuma zaunen abin ta tsaf cikin rufin asiri da kwanciyar hankali ga mutunci shi aure ai darajarshi yawa ne da ita ba kowane yake samun darajar yin shi ba. Na jinsu bana cewa koami, iyaka dai na sani na kuma yarda da kalaman nata duka iyaka dai can cikin zuciyata a yanzu bani da damuwa mai yawa kan maganar yin auren nawa na yarda na kuma gamsu da cewar dak ullum malam Yahuza yake yi na komai lokaci ne kowa kuma yana da nashi lokacin, Nalami kuwa in dai shi zan aura to ina ganin kamar gara in yi rayuwata kawai a haka ya fiyemin don haka ko kadan bana jin zafin kalaman nata. Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar magariba takardun da zan tafi da su wajen malam Yahuza nake hadawa saboda muraja'ar da yake yi min kan wasu darussan masu dan nauyi da nake bukatar fahimta mai kyau a kansu, har zan yafa hijabina in fita sai kawai naji yaro ya shigo yana cewa wai ana sallama da Maryam a waje. 120 Na daga ido na kalli agogo cikin zuciyata na ce kar dai Halliru ne ya z0 a wannan lokacin. Halliru shi ne sabon saurayina da Yakumbo ialima ta turo min a dalilin ya ce mata ta duba mishi budurwa mai hankali da iya kwalliya kasancgwar shi dan mijinta da ta rike ya sa ta ce bai dace da kowaccc budurvwa ba sai ni, ni kuwa a wannan lokacin bani da wani zabi na daina Pzaba ince ga irin saurayin da nake so ko ga irin mijin da zan aura, aurcn kawai nake so wanda duk yazo kuma a shirye nake zan aure shi, in dai huta babana ma ya huta mu duka mu huta damunmu da ake yi ana bada bayanin mu a kan idona sai ka ji dattawan unguwar suna cewa ai nan kusa kusa duk ai babu sauran sa'arta kai kannenta na kusa ma babu duk sun garna yin aure sai ita kadai. Na debi littafin nawa na rungume na jawo kofata na rufe na yiwa babana sallama na fito da nufin in mun gama maganar da za mu yi sai kawai in wuce na kuma san ganina tare da litattafan a hannuna zai kara sashi tafiya da wuri tunda yasan ina da abin yi. Ina fita waje maimakon in ga Halliru, Mubarak na gani a tsaye, wani irin lalataccen kallo ya yi min da ya sanya gabana faduwa cikin zuciyata na yi maza na ce, ban yafe maka ba zuwa kofar gidanmu da kayi ka fadar min da gaba. Shima malamin naki yana nema ya rikide ne ya Zama saurayinki? Da sauri na daga ido na kalleshi 121 cikin tsananin mamaki abinda ban taba zaton wani zai yi tunanin hakan ba don babu wata alama da take nuni da hakan. Idan kika kuskura na gane da wani abu a tsakaninki zaki bar karatun naki gaba daya ki koma Zaman gida in kumakina ganin kamar wasa nake yi to bari in gane halkan ki gani kina nufin don yana koyar da ke karatu a da sai kuma a yanzuki rinka kwasar litattafaikina zuwa wurinshi kuna zama ku biyu? A kidune nace mishi, ba fa mu biyu bane? Ya yi maza ya katseni ko ku dubu ne ban yarda ba kar in sake gani ko jin kin fita daga gida bayan sallar magariba, na gaya miki. Kuka na soma yi mishi saboda bakin cikin abinda yake yi min, takuraw ar ta kai duk inda ta kai, komai nake yi ya sani ko baya nan nayi in ya dawo zai ji labari. Cikin karfin hali na daure zuciya ta na ce mishi, to wai ni ina ruwanka da ni ne? Ina abinda ya shafeka da abinda nake yi, kullum sai ka shiga harkata, kullum sai ka takurawa rayuwa ta. Ban san dalili ba rannan sai na kasa zuwa wurin mraja'ar da Malam Yahuza ke yi min, maimakon washegartnma inje ban i cb a sai kawai na hakura da muraja' ar na koma maida hankalina sosai a aji wajen fahimtar dukkan darussan da ake yi mana. 122 Kullum dai burina bai wuce in samu lokaci in tatawa Mubarak rashin mutuncin da zai sa ya fita harkata kwata-kwata ba amma in na ganshi sai in kasa saboda kwarjininshi da yake yi min nauyi a idona. Gabatowar watan azutin ra:nadan mai girma ya sa aka shirya mana jarrabawar da a bayanshi muka samu hutun makaranta har sai bayan salla mu koma, farin ciki sosai nayi a wannan. Jlokacin a dalilin jarrabawa ta tayi kyau banda haka zan dan samu hutun wahalar da nake yi ta zuwa makaranta da kafa in dawo da kafa, Sannan zan dan fuskanci wani abinda nake kuma dokin yi shi ne dinki don na dan fara iyawa har yaya Dija ta gamsu da labarina bayan dinkin 'ya'yanta dana dade ina yi musu ta hada min har da nata nayi a dalilin hakan kuma ta ma karbar min na kawayenta da abokan zamanta. Ki natsu sosai ki yi musu mai kyau don sai ya zamo tamkar tallan iyawarki kikayi, nace mata to. A wannan lokacin hutun makaranta da dokin dinkin azumi da nake yi ne ya ragemin damuwa ko bacin ran da na samu kaina a ciki ra turowar da Halliru ya yi a ka karbe mishi kayanshi, shi ko kayan na gani ina so kamar yanda wasu suke fada da da ya kawo gidan mu haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba wadanda suka kawo kayan suka zo suka ce a yi hakuri a basu bisa wasu dalilai da suka ce wai su ne sukayi dalilin in sa auren nashi a wannan lokacin. 123 Yakumbo Halima dai ta ce min wai yayi mata bayani da cewar ya fasa auren ne a dalilin akwai wani dodo dake biye da ni mai tsoratar da mutane matukar kuma ba a tsaya an rabani da wannan dodon ba to aure na zai yi wuya. Bayanin 1ashi ya yi tasiri mai karfi a zuciyar Yakumbo don salati ta rinka yi tana fadin, wai dama tuni ta dade tana tunanin watakila aljani ne da ni wanda ya hanan11 yin aure. Ni kam tattara maganar nayi na ajiye a gefe ban yarda ba ban kuma karyata ba don ban san komai a kan irin wedannan al'arauran ba, abu guda daya dana sani na kuma yarda na tsaya a kan shine gaba daya mu mutane da kuma aljanu dukkanmu bayi ne na Ubangiji babu mai ikon cutar da wani a tsakani sai da abin da Ubangiji ya yarda ya kuma kaddara fil azal wannan din zai cutu da shi, wannan shi ne bayanin da kullum malamin mu na tauhidi yake yi mana da sai kuma na yarda sai na samu natsuwa da kwanciyar hankalin dana fuskanci al'amurana na dai san kawai na koyi yin addu'a. Sai dai kuma tawakkalin da sanin da nayi cewar babu mai yi ko hanawa sai Ubangiji bai hana zuciyata kuntata ba a dalilin aure nake so auren kawai nake so, SO nake in ganni nima a zaune a nawa dakin ina zaune ina aurena ga Asabe tunda ta yi aurenta tana dakinta ban sake ganinta ba, kullum kuma sai uwarta ta yada 124 magana a tsakar gida ta ce, yin aure ai rufin asiri ne Asabe asirinta ya rufu tana can dakinta cikin ntin asiri, ubangiji ya sanwaka ace yar mutum tayi ta galantoyi a gaban shi, yana kallonta kowa ya zo ya yi kamar zai aureta in ya taya ta sallama yaga araha sai kawai ya yi dani ya tafi. Tin, ta ja tsaki fa ci gaba da harkokinta. Cikin zuciyata dai na kan yi mamakin al'amarinta saboda a farkon abinda ya faru da Asabe na dauka zata fita banyar irin wadannan abubuwan sai ya zamo ko a jikinta ba ta ma tuna nata sai dai na wani dama bai karasa natan lalacewa ba. Ana cikin haka watan azumin ramadan ya iso sayaiya sosai Mansur ya yi min, ina zaune a dakina ina. buda baki mun kai azumi na biyu ina jin baba Lantana tana cewa babana wai ita din ai rabon wahala ne ya se ta aurenshi in banda haka ai shima ya san irin zaurawan da tayi, cikin zuciyata na ce ob oh kowa da irin yanda babu take zuwa mishi, watni ta kara mishi natsuwa wani kuma ta yis anadin wargajcwarshi, wata mai daraja irin' na azumi bai sa ta dan rusunawa al' amiaranta ba. Isiyaku ya yi sallama a kofar dakima ya shigo, anti ina wuni? An sha ruwa lafiya? Na amsa gaisuwar tashi ina mai kallonshi. Ya yi fes da shi ya yi kyau kamar in tambayeshi ka samu wani abin yi ne Isiyaku, sai na yi maza na fasa a dalilin ba wani shiri muke yi 125 ba a yanzu saboda gaba daya al'amuranshi na Mubarak ne. Ya karkata ya zaro envelop daga aljihun shi ya ajiye a gefena, wai gashi in kawo miki. Da sauri na ce mishi, Isiyaku ashe ban ce maka kar ka sake karbo wani abu daga wurin mutumin nan ka kawo min ba? To dauki maza-naza ka tafi mishi da shi ka kuma gaya nishi inji ni na ce ya fita hanyata ya daina shiga harkokina in bai sani ba ko bai gane ba to bari ni da kaina in gaya mishi na tsaneshi, na tsani al'amuranshi, na kuma tsani duk wani abinda ya shafe shi, in ya kuskura ya sake aikoka da wani abu wurina to zan karbi abin in aikawa matarshi don tasan yanda zatayi da shi, ya daina kula al'amarin. Wani irin lalataccen kallo Isiyaku ya yi min da ya yi dalilin da nan take na warware hannu na sheka mishi mari mai kyau a kumatunshi har sau biyu, ina wasa da kai ne da zaka yi min irin wannan kallon? Bai cc min komai ba sa hannu ya yi ya dauki envelop in ya sa kai ya fita ya bar gidan, ya barni ina huci da tunanin haka zan rinka yi mishi duk lokacin da ya kawo min wani sako tunda nace msihi ya daina yaki. Washegari mun taso daga wurin tafsir nufina in taff gidan yaya Dija don in yi mata barka da shiga tamadan mai albarka sai kawai naga Mubarak ya yi fakin din motarshi kusa da hanyar da muke wucewa 126 bai ii tsoron cincirindon matan da suke wucewa su na hangenshi ba ko don kar su gayawa matarshi. Yana ganina zan wuce ya yi maza ya fito daga cikin motar tashi ya tsareni, nmagana yake yi cikin natsuwa ta yanda na nesa ba za1 gane bakar magana yake yi ba. Malamin naki ne ya koya miki rashin kunya da rashin mutuncin da kike yiwa mutane ko? Na daggo ido na kalleshi saboda ambaton malamina da ya yi. Eh ai kafin kullewarku ke da shi rashin kunyarhi ba ta kai haka ba, ki mari Isiyaku, gansamemen saurayi kamar Isiyaku ki mareshi dame kika girmeshi? Kina nuiin in banda shf din yaro ne mai mutunci za a yi hakan'? Kina mace ki mari namiji kina nufin in ina da iko da ke ba zan yi miki hukunci mai tsanani na ladabtarwa ba? Sakarya kawai sokuwa, shasha:ha wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya dace da ita. Wani lalataccen kallo ya yi min gami da jan mummunan tsaki kafin ya wuce ya tafi ya barni, ance miki matata irinki ce. Haushi da takaicin kaina suka hadu suka kamani kan yanda akayi ya gama gaya nun bakaken magangnaunshi ya wuce ya tafi ba, tare da na iya ce mishi koami ba, babu kuma abinda yafi komai kona min rai irin cewar da ya yi wai matarshi ba irina ba ce, to wacce iri ce? Me yake nufi da wannan maganar ta 127 shi? Babu irin alkawarin da ban yiwa kaina ba a kan ba zan sake barinshi ya gayamin magana in kyaleshi ba amma gashi na kasa gaya mishi komai. Baba Lantana a wanann lokacin tsula tsiyarta take yi irin yanda ta ga dama, da yake Asabe mai imani ce da tayi cikinta sai ta reni abinta ta haif abinta ba ta je ta zubar da shi ba balle ta je tana dauka wani zunubin na kisan kai, gashi kuma a saradin hakas ai ta yi aurenta tanan an goye da danta tukarballa ta bar wasu a titi suna ta tanbele basu ga tsuntsu basu ga tarko. Da bain nata ya tsaya a kaina ni kadai da sauki yanzu yanzun nan ne zata sa shi a gaba ta sulleshi sai dai in ba zan leka kofar gida ba ko ka ji tana cewa, to ni in banda na lissafa naga duk tsiyarka kai da ya'yanka zan iya cinye wannan daki da nake ciki tunda dai su din mata ne ai da tuni na dade da rabuwa da kai in yi tafiyata yaushe zan iya zaman jinya, to ba zan tafi ba ne in bar kasona a ce rashin bhakuri doon haka nake zaune daram ina jira sai naga kwal uwar daka. Wadannan kalaman da na ji baba Lantanan tana furtawa wadanda na tabatar ba ta san na ji ta ba su ne suka yi dalilin da na yi sammaon zuwa gidan yaya Dija na bata labari. Shiru tayi tana kallona cikin wani irin yanayi, Jimawa can sai naji ta ce, i tsorona ma kar ta karasa 128 mana shi ba mu sani ba tunda take mapganar gadon dan wannan gidan wato ita idonta yana kanshi ta sake nisawa kafm ta ce, nifa da baba zai yarda ma de wani auren kawai ya kara. Da sauri na zaro ido ina kallonte cikin razana, aure kuma? Shi baba ya ce miki zai fya yin mata biyu ne? Hankalinta a kwance ta ce min to ba shi kenan ba in ba zai iya biyun mai zama ta zauna mai tafiya taa tafi, amma wannan fitina har ina? Daka akwai wata yarinyar bazawara nan kusa da ma takaba ta gama tana kuma da' ya'yanta biyu k inga in Akayi sa'a ma sai ya kara haihuwa ya ma huta da sharrin da take kulla mishi na baya iya tsinans mata komai, baba ai ba tsoho bane in ma bakan ne bakin cikin ta ne ya maidashi hakan, na dai ja bakina nayi shiru ina jinta tana maganganunta bance mata komai ba. Rannan ranar wata juma'a da yamna bayan saukowa daga sallar Juma'a naji babena ya karbi wasu baki a zaurenshi wadanda na tabbatar iyayen Mubarak ne wato Alhaji Muhammadu da amininshi ban san takamaiman abinda ya kawo sun ba na dai gane su din ne kawai ta dalilin ambaton sunansu da na ji baban nawa ya yi. Nayi maza na mike na shigs gida na basu wuri, can cikin zcuiyata dai ina taunsnin wanene kume Alhaji Muhammadu? A sanina a unguwarmu baban Mubarak ake kira haka to amma shi me zai kawoshi 129 gidanau? Yana dai zuwa duba babana daga baya bayan nan tare da Mubarak to amma wannan ai zai iya Z8ma makwabtaka ne ko kuma kwadayin alherin da ake samu wurin gaida mara lafiya. Ina ganin sanda babana ya shigo gida rike da tabarmarshi a hannu bai ma tarota inje in hade ba bai ce min komai ba nima kuma ban tambayeshi ba don dama can babu irin wannan mu' annaiar a tsakaninmu don haka sai kawai na ci gaba da harkokina. Da daddare ina zaune dakina takarduna na makaranta nake dubawa lokacin da na ji sallama a cikin zauren gidanmu gabana ya yanke ya fadi saboda jin da nayi tamkar muryar Mubarak ce da sauri na mike na fito da ita. Uhh lalle al'amarin babba ne har cicin zare kuma yanzu kake shigo mana? Ta yi kwafa ta ce ko baka yi haka ba ai an kuma hade. Tsayuwar da baba Lantana ta yi a wurin wai sai ta ji abinda ya kawoslhi ko zai fadi ya hanani tafiya in barshi don ba zan 6ata mishi rai a gabanta ba, wucewa na yi nace mishi muje daga waje mana, don haka muka fito. Tun kafin in tambayeshi abinda ya kawo shi gidanmu ta tsareni dai danuwanshi wai ni me baba yake nufi da ni ne? Tambayar tashi ta sanyani yi mishi tambayar wane baba? Da saurinshi cikin wani irin yanayi ya ce min, babanki mana. 130 Gabana ya yi mummunan faduwa jin yanda ya ambaci baban nawa, cikin zuciyata na ce, lalle mutumin nan yau yana jin rashin mutunci amma babu laifi, na kawar da tunanin nawa na naida hankalina Wajen sauraron abinda Zai gaya min a kAn baban nawa wanda na tabbatar ba mai dadi bane. Na rasa me nayi nish na rasa wane irin laifi na yi mishi wanda ya wuce gabai yafewa, tun aurena bai wuce wata uku ba na turo aminin babans ya zo wurinshi.kan maganar ni da ke bai saurari maganar ba na koma na sake rokon babane ya zo da kanshi ya yi mishi magana don ya fi ganin abin da muhimmanci ya zo ya sameshi bai ji kunyar idonshi ba ya ce mishi ba zai bani ke ba yau ya sake dawowa saboda na sake komawa gabanshi na rokeshi ya dawo ya sake rokonshi to ya sake dawowa shi kuma ya sake cewa matukar shi ne zai daura miki aure da kanshi to ba zai daura auren da ni ba, saboda na ci mutuncunshi na keta mishi haddin yarshi nayi sanadin da sai dake kuna wulakanta shi ne na ce bari in zo in ji me na yi? Me nayi miki na haka ni na taba ki ne? Ke baki gaya mishi babu komai tsakanina da ke ba sharri kawai matar shi ta kulla mana. Cikin natsuwa na tambayycshi, to in baka yi komai ba sai me? Dole ne sai ya baka aurena da za a je ana ta yi mishi zirga-zirga a gida? Sauran iyaye da sukayi hukunci a kan ya'yansu haka aka yi musu 131 Naga shima shi ya haifeni ko kuwa don an ganshi yana saida turmatir sai a ce bai isa ya zartar da hukunci a kan tashi 'yar ya zaunu ba sai an canza mishi? Bai nuna bacin rai da jin maganar tawa ba sai ya ce min, 1yaye suna zartar da hukunci mai tsanani a kan ya'yansu, Maryam yin hakan ba laifi bane amna kuma da yawansu sukan ciza ne sai kuma su hura a mati yawancin lokaci ma suikan taya ya'ya son abinda sukc so matukar sun gane babu cutuwa a cikin lamarin, me yasa shi ba zai yi hakan ab? Me ya sa ba zai tayaki son abinda kike so ba ya baki mijind a kika rayu kina so? Na ce, ai abinda nake son yake taya ni shi din ya san ban taba sonka ba ya kuma san duk wani abinda ya gudana tsakanina da ka ya faru e a dalilin kuruciya da kurna kuskure. To babu laifi, ya fadi hakan cikin wani yanayi don baka nayi maza na juya da nufin shiga gida sai naji yayi maza ya ce min to, uan dakata mana ki ji abinda Zan gaya miki. Na dan ja na tsaya ba tare dan a waiwaya na kalleshi ba, sai naji ya ce min, to amma ai shi baba yana da labarin rabo yana kashe mutane ko? Gabana ya sake yankewa ya fadi jin da na yi ya ambaci mutuwà a tsorace kwarai na tarabaye shi, me kake nufi da wannan maganar? 132 A natse ya ce min, abinda naken ufi kenan ki buda baki ki yi mishi m agana ki gaya mishi gaskiya babu komai tsakanina da ke ban taba mishi ke ba, na ce to in baá haka ba fa? Ya ce shi kenan sai ki yi ta zama sau goma in z2 a kawo miki kaya sau goman kuma za a zo a karbe. Gabana ya sake faduwa, kar dar ace Mubarak ne ya yi dalilin fasa aurena da Halliru? Kar dai a ce Mubarak ne dodon da Halliru ke gayawa Yakumbo Halima wanda ita ta dauka dodon dodanni ne ko wani aljani. Rasa abinda zan cewa Mubarak nayi in dan ji saukin abinda ke cin zuciyata don haka sai na ce mishi, a sanina dai baba na shi ne mahaifina yana da iko a kaina kamar yanda kowane uba yake iko da danshi saboda randa ya yis anadin zuwana duniyar nan babu wanda ya taya shi don haka in bar rabon wani ya zama sanadinshi to na rantse har abada ba zan auri wannan din ba sai dai ni ma rabon nashi ya sa yanda zai yi da ni kuma karka sake kulani. Ina fadin haka na yi maza na shige cikin gidanmu na barshi a nan wurin yana tsaye. Ko badan ban i haushin hana Mubarak aurena da babana yayi ba saboda tuni ya riga ya fita min a rai bana kallonshi inji zuciyata ta rayamin abubuwan da ta saba raya mina game da shi a baya sai dai in ganshi in ji faduwar 133 gaba ko in ganshi in ji haushi da takaicin shi sun kamani. A wannan lokacin ne kuma baba Lantana ta fito da wani irin salo a gidanmu duk wani wanda ya zo wurinta in suna hira bata kai karshen hirar sai ka ita tana gaya mishic ewar ita wannan zama da take yi ma ai ya kusa ya zama haramtaccen zarna, abokin hirar ta ta ya ce, haramtaccen zama kuma, Lantana sai ta ce eh to haramtacce mana tunda abinda ake yiwa zaman yayi karanci ace niji kana kallonshi yana kallonka shimfidarku daya amma sai ya sahfe kwana da kwanaki babu komai, babu wani motsi a can babu a tukubya ma babu ana yin zaman haka ne ai ni yanzu kiris nake jira don ma dai kawai kar ka tafi ne ya zama ka tafi ka bar ladanka. Haba Lantana haba Lantana yanzu ke a yanda kike din nan sai kin yi korafi kan irin wadannan al'amuran, m utumin da ko lafiya bata isheshi ba, tace a'a ni ban wuce ba sannan tun a can baya ma da yake da lafiyar me aka yi ne da za a ce yanzu in hakan ta faru kar in yi magana? Yaya Dija na baiwa labarin kalaman nata ita ce ta faiyacemin abinda take nufi, kasar kullum sai ta tasa babana a gaba tana yi mishi hirar gidan mijinta na baya, haushi da takaici ya yi ta kama ni na yanda sau daya babana ya kasa cewa ya sauwake mata nashi auren taje ta koma gidan mijin nata na bayan, yawan 134 fadan da take sashi a gaba da yi kIsaa kulium da yi ya sani bashi shawarar dawo da kwana dakin Sallau don ya rinka samun wadataccen bacci saboda mas' alar hawan jininshi, kamar bai ji shawarar tawa ba daga baya kuma sai naga ya koma dakin. Wata gomas ha daya cif nayi ina zuwa makarantar koyon sana'a ta Markas kafin aka yayemu saboda yarda da aka yi cewar mun iya mu gomas ba biyar aka yiwa yayen aka kuma yi mana kyautar dinki saboda gamsuwar da akayi da kwarewarmu, ko kafin nan kuwa nikam na dan dau loakci ina taba dinkina a gida a kekcn da yaya Dija ta saya min don haka dana samu wannan kyautar sai kekunana suka'zama guda biyu. Naso kwarai in koma Karkas in sake shiga wani ajin daga cikin azuzuwan sana'o'in dake wurin in kara koyon wata sana'ar haikan bai yiwu ba saboda karatun da nake yi a makarantar asidini mai zurfi, karatu ne dake bukatar sadaukarwa mai yawa banda haka kuma ga lalurar babana ta yawan rashin lafiya don haka sai na hakura. Tunda aka yayena a wuTin koyon dinki na soma yin dinkin sosa a gida sai mas'alolin da suka danganci babu sia yi matukar yi min sauki bana asa na sabulun wanka ko wanki bana rasa ta yin break a makaranta wani lokaci ma nakan raka babana asibiti ne ba tare da na shedawa yaya D1ja ba balle inje ina 135 jiran abinda zata bamu wannan-shi ne abidna yafi komai faranta min rai na. Shekaru uku ne yau tun bayan faruwar abinda ya faru tsakanina da Mubarak cikin shekarun nan kuwa nayi abubuwa masu yawa wanda kasancewata a yau ni din kwararriyar tela tace gani a fada a kuma kwaikwaya, ni din kuma gwanar girki ce saboda na koma makarantar Markas na sake shiga ajin koyon girki nau'o'inshi kuma malamaina na Markas irinsu malama Hindu da Basma wadanda mukayi matukar shakuwa a dalilin kulawar da suka nuna a kaina sunyi min taimako mai karfi wanda a daliiinshi na samu shiga exam center dake kusa da Markas din na samu rubuta jarrabawar dana samu mallakar takardar shedar gama karatun secondary indana samu credit guda hudu da pass biyu saura f9. A 6angaren da nake ganin kamar na yi nasara kenan, a daya bangaren kuwa Ina nan kamar yanda dama nake aure ya gagara babu kurna yanda banyi ba in yi shi hakan bai yiwi ba, zan iya cewa garama da da yanzu a lokacin da kuka sanni samarin sukan dan zo auren ne basa tsayawa a yi saboda wasu dalilai to a yanzu babu bani da wani wanda zan ce wannan saurayina ne. Mutanen unguwarmu tun suna nunani suna yin bayant a kaina zuciyata tana lissafi ta karyata maganar 136 ta su har na hakura na fita harkarsu ta barsu su fadi duk abinda suka ga dama. Tun ban a kama maganar mutane irin su Yakumbo Halima da suke fadin cikin biyu dai alkwai abu daya ko dai anyi min sihiri ne ko kuma ma aljani ne ya aureni ya hanani yin aure har na soma shiga rudani ina tambayar kaina to menene mas'alata, tuni dai na daina yin kawaye don na gaji da aurar da su da akeyi ana barina a wannan lokacin in har ina da wata kawa to kekena ne da kuma dinkina sai ko kwalliyar da nakeyi don kuwa ba sai an gaya min ni da kaina na san mu'amalar da nayi da malamaina na Markas irinsu Malama Hindu da Basma ya koya mina bubuwa iri-iri da suka danganci mace kwalliya, kamewa, mutunta kai, iyaka dai har yanzu hakan baisa na samu mijin da ya tsaya ya aureni ba su ma kamar yaya Dija sukan ce min wai lokacin auren nawa ne bai zo ba sai in yi murmushi kawai in yi shiru cikin zuciyata kuwa tambayar kaina nake yi ko yaushe ne lokacin oho? Saboda a wannan lokacin har na gaji na soma tambayar kain to koma dai ni din ina cikin matan nan ne da ba a halitt musu mazan auren ba? Tun ina kin yarda in yi amfani da abubuwan da Yakumbo Halima take bani in yi amfani da su na farin jini da wai maganin sihiri da kullum take zargin wai Mubarak ne ya yi min in yi murmushi in ce mata Mubarka bai ma yarda da irin wadannan abubuwan ba 137 Yakumbo shi fa dan boko ne ma digiri biyu ne da shi ya ma sake komawa karatunshi don neman na u yaushe zai zauna yana irin wadanann abubuwan? Sai ta ja tsaki bayan ta gallamin uban harara ta ce, ai sai ki yi dama in kana son mutum ai baka iya ganin laifnishi, ince mata ba haka bane Yakumbo ai ni yanzu bana son Mubarak abin da na sani ne kawai nake gaya miki, ta ce to baki san komai ba incem ata to na yarda. A wannan lokacin ta kaima ina zama in yi kuka ins hare bawayena tun ina yi ni kadai har ta kaima ina yi a gaban yaya Dija, menene mas'alar da ta hanani yin aure? Bani da fasali ne? Ta girgiza kai uh uh kina da shi daidai gwargwado, bani da tsabta ne? Ta sake cewa uh h kina da ita kin kuma iya kwalliya kina kuma yi iina da kamun kai da natsuwa gashi kin yi karatunki kina ma kai tunda har yanzu kina yi to amma lokacin auren bai zo ba, Maryam mijin naki ne baizo ba d on haka bani da yanda zai yi sai dai in yi ta baki hakuri in kuma kara rokon ki ki kara tsare mutuncinki komai zai wuce har kiga kina bayar da labarin al'amarin, ni dai nasan duk waenda ya yi dace da samun babbar mata mai aikairori iri-iri, in yi murmusbi ince yaya Dija kenan kenan kina dai gaya min hakan ne kawai don in ji sanyi a raina. Ita dakanta yaya Dija duk da irin wadannan kalaman sanyaya zuciyar da take yi min ta sha gaya 138 min cewar rashin aurena ya katse mata baccinta ya gusar mata da nishadinta ya sanyata ta ji zuciyarta ta kutata don haka mu yi ta istigfari muna rokon gafarar Ubangiji, in ce mata to wataran kuma in dan zolayeta ince mata ba kince zai wuce ba? Ta yi maza ta ce, kamar yanzu kuwa in har muna raye to zamu sheda wucewarshi. Yaya Dija ya ce a wurina da ta zame min uwa ita nake kallo a matsyain uwa saboda duk abinda take yi min yi take yi da iyakacin iyawarta tana da ya'ya maza da mata amma bata hada su da ni ba, na sha jin matan gidansu suna cewa ai ita wai kanwarta ta fiye mata kowa tunda ita ita kadai ke gareta ba kuma zata sake 'yar uwa irinta ba tunda uwar da zata haifar mata wata bata nan ba wadannan kalaman ne suka sa zuciyata yarda da yaya Dija bata hadani da kowa ba a aiyukanta ne a kaina shi yas anima bana wasa da ita duk abinda tace min to káwai nake cewa bana yi mata musu. Ina zaune a dakin ina yankan kayan da nake nufin dinkawa a wannan satin wanda na ankon wani biki da za a yi ne a unguwarsu aya Dija aka kawomin ina yankan cikin natsuwa da kwanciyar hankali saboda daga ni har dakin nawa tsab muke sai kanshi muke yi, bana tunanin komai cikin raina aiki na kawai nake yi sanda Asabe tayi sallama ta shigo cikin dakin, ashe kina ciki? Nace eh Asabe ki zo ne? Ta ce min, 139 ina kwana? Ina amsawa ina matukar jin tausayinta gaba daya t a canza ko rigar nono a wannan lokacin na ganiyar kuruciya bata iya sakawa, tsabtar ta duk ta kare kullum ka ganta gara jiya da yau ba ita ba ba 'ya'yanta kullum yanzu sai tazo gida kullum kuma da mas'alar da zaka ji tana fadi baba Lantana tayi tayi ta daina shiga dakina tana gaisheni ta ki dainawa, ban sani ba ta canza hali ne ko kuma sule biyun da nake baiwa ya'yanta in zasu tafi ne ya hanata daina wa oho? A wannan lokacin wanda. bai yiwa Asabe sani na hakika ba ba zai ganta ya ganerta ba ga karni da take yawo a ciki. Kin fito daga dakin kanwar uwar taki ne? Ban ji abinda tace ba naci gaba da aikina ina istigfari kan yawan damuwar da nake yi a kan rashin aurena, na yi imani da in yi aure irin wanda sabe tayi gara ma ina zaune a gida gaban iyayena ckin haiyacina da rufin asirina, tunda ba cewa akayi in ba a yi auren ba ba za a samu rahama ba sai dai in ba a yi aikin neman rahamar ba, ba kuma raina auren Asaben nayi ba yasa na fadi haka tunda na san darajar aure yawa ne da shi ko banyi shi ba kuma na karantashi a ganewa kawai a yanda ka'idar auren yake da bayanin shi da akayi a tsari irinw anda auren Asabe ka tafiya zai yi wuya kwarai in har ana samun ladan da ake nema din kullum a cikin korafi ake a zagi miji a zagi kishiya a 140 gaya mata irnin tsiyar da zataje ta yiwa mijin, ni kuwa ina zaune gaban iyayena cikin rufin asiri ina addinina daidai gwargwado ina neman ilimi, ina sana'ata ina kyautatawa mahaifina gwargwadon iyawa ta, a wannan loakcin banda sutura da hidimominshi har runfa nayi: nsihi sabuwa ciki da falo, kayanshi suna can ciki shi da Sallau suna wuri daya, Salau kuma yana iyakacin kokarinshi kullum babsn ayaną yi min addu'a yana samin albarka. Na karaa kallon al'amarin Asabe da aurenta wanda da ni aka so a tura cikin wannan wahalar Ubangiji ya tsarcni, kullum a cikin tashin hankali da miji ake kishiya kuma ta kamata tayi amta dukan tsiya ta kaima baba Lantana da kanta tayi damara taje har gidan Nalami wai zata ramawa Asabe dukan da matarshi ke yi mata ban san yanda akay ba sai naga tadawo kaca-kaca da kamar akwal rayuIwar addini a gidan nasu to da komai ma da sauki to babu. Daga tsakar gida na soma jiwo wata magana da ta katsemin maganar zucin da nake yi saboda an fara daga murya ana yinta sama-sama alamar rayuka sun fara hassala. To bakya cewa ya sakeki, ke wacce irin sakarya ce yaya za a ce miji ne zai auna maka hatsi abincin da ba zai isheka ba babu kudin cefane babu koami sai abinda kishiya ta baka, sannan in abincin bai isa ba sai ace. kai ne ka rasa, wannan wane inn zalinci ne, 141 Sannan in dare yayi ya zo ya fada miki da yunwar da komai ba dama ki ki yarda da shi, ke ko irin 'yar tirjiya da yangar nan da mata ke yi a rarashesu a yi musu abinda suke so baki iya ba. Ai rufeni da duka yake yi yana ganin alamar zan yi mishi tawaye sai kawai ya tashi ya zauna ya yi ta jigbata da duka wai ladan hatsinshi da na wuni ina ci, baba Lantana tayi shiru kamar yanda Asaben' ma ta tayata yin shiru, imawa cna na ji ta ja wani mummunan tsaki da bai da dadin ji kafin daga baya ta bishi da fadin, kai Nalanni dai tsnanne ne. Shi ne nace to ko zance ya sake nin ne kawai? Da saun ta ce ys sakeki mana tun yaushe nake gaya miki hakan? Ta dan rage nurya kadan ta ce, to amma fa ba Zai yarda in abr mishi wannan yaron a can ba ya ce wai zaunana ya ke yi na barin gidan shima zai bari wannan dai ya yarda nashi ne tunda yana kama da ya'yanshi amma si wannan ai bai ga ta inda ya daukoshi ba shi ne nace ko zan kawo miki shi ne kawai in bar mishi wannan din: wahalar da nake sha tayi min yawa kajin mafa day ake bani figarsu yana bani sisi-sisi ina samun na sabulu yanzu ta hanashi bani ko kwabo wai... Ni da nake kashc da kunne in ji abinda baba Lantana zata fadi kan kawo mata dan da Asabe ta ce Za ta yi sai naji ta hassala ta daka mata tsawa, ke barni haka da wannan mugun albari naki sakarya kawa 142 shashasha sauna mara zuciya ace mutum bai da wani aici sai na bayar da mugun labari? Ki dauko yaro ki kawo min ya zama duk tattakar da ya yi miki a banza kenan ko me? Wannan yaro ai dole ne ya girmaa gidanshi ladan sukurkutaki da ya yi ya maida ke wata yamutsattsiyar tsohuwa, tsinannan mutum kawai. Na ce oh oh ta kacame tsakanin siriki da sirika, ina zaune kan kekena ina dinkin kayan dana gama yankawa zuciyata tana tunaina al'amarina irin kokarin da baba Lantana tayi na ganin ta sa babana ya baiwa Alhaji Nalami aurena duk da tafi kowa saninshi da duk wani al'amarinshi tunda tun a loakcin ta sha gaya min cewar in dai matar Nalami tana nan a yanda ta santa ai zata yi mata magani na to gashi abin baiyo kaina ba sai ya fada a kan yarta nan take na tuna da karin amganar hausawa da ke cewa wai, mugunta fitsarin fako, in kayi sai ya dawo maka kanka. Kwalliya mai kyau nayi a ranar da na yi nufin kaiwa masu kayan kayansu, doguwar riga na sanya har Rasa ta farar atamfa da aka yiwa ratsi da kananan filawowi koraye da bulu, saman rigar na yi shi a matse yayin da na yiwa tsakiyar yankan umbrella ya sauka har Kasa, dankwalin yadin' atamfar ne a kaina na yi dauri mai kyau sosai na sanya yan kunne kanana na yafa farin gyale madaidaici a-kafadata yayin da na kawata hannayena da adon awarwarai, agogo da zobuna biyu na zinari daya kuwa na azurta 143 da aka yava kira mai kyau na shuri takalmana silifas 1masu igiya a baya yan Italy da suka kara kawatamin kwaliyar tawa, nasa garkamemen kwado na kulle kofar dakina a dalilin gajiyar da na yi da biyan mutane atamfofinsu da suke bata don haka nama canza kofar dakin gaba dayanta. Na baro gida rike da ledar kayan dinki da kuma pos a hannuna bayan na gayawa babana inda zani, yar tafiyar da nayi ba wata mai yawa bace na ja na tsaya don tarar mashin din da zan hau. Wat ke me yasa bakya įin magana ne? Sau nawa nake gaya miki in zaki fita ki daina amfani da turare ki kuma daina hawa mashin bana so. Ban kalteshi ba balle in bashi amsa iyaka dai nasan nayi mamakin ji ko ganinshi a wannan lokacin tunda nasan ya taf Legos bar kima san da dawowar tashi ba. Amma shi baba tsareki da ya yi a gida kike ta wannan zaman a gabanshi yana ganin kamar ya yi mishi daidai? Shi bai san kin kai kowane irin munzali bane, bai san kinas ha'awa ba? Ke ba za ki gaya mishi kina da mas'ala ba? A muku mukuns anyin nan kin fito za ki je ki kai akyan da kika dinkawa wasu in kina gidan aurenki mijinki zai yarda da haka? Gaskiya na gaji da ganinki a haka yanzu fa Rumasa'u ya' yanta biyu ne. 144 Maganar ta dak zuciyata a hankali na tunawa kaina da kullum muka gamu da shi bama rabúwa sai ya san yanda yayi ya sokamin abkar maganar da ta tsaya mina raina. To wai ni ina abinda ya dameka da ni ne? Kaga ni na damu da kai e? Kaga ina. daga ido ina kallcka ne balel in san abinda kake ciki? Ina dalilin da kake nema ka maida mahaifina abokin wasanka, kullum ka ganni sai ka san abinda ka fada a kanshi. Ban maidashi abokin wasa ba Mero amma gaskiya zan gaya miki yana 6ata min rai don me zai hanani ke? Don... Na yi maza na katseshi, in ya hanaka ni sai ka rinka gaya mishi magana a kan ido na wane hurumi ke gareka na yin hakan? Nace bana sonka nace ka fi ta harkata nace ina kwai wani mutumin da zance na tsana a yau to kai ne don me ba za ka yi zuciya ka fi ta hanyata ba? Ranshi ya yi amtukar 6aci da kalarman da nayi mishin, wani irin kallo ya yi min irin wanda shi kadai ya san abinda yake nufi da kallon, kina ganin kamar ba za a iya fita harkar taki bane? Kina ganin kamar in an fita harkar taki wani abu zai faru ne da kike wannan cika bakin? To ni don na fita harkar ki ma menene Maryamu? Ai ni ina da mace a gida har da ya'ya kece kike zaune ke kadai kece kike rayuwa cikin kewa da kadaici, duk sanyin da ya taso ya kare a 145 kanki kina zaune kan kujerar dinki, ni ai da aurena sannan karya kikeyi kice bakya sona in bakya sona me ya hanaki yin aure? Fitar da wani ki aura mana ki zauna kema a dakinki ki dandani dadi da zumar dake cikin auren sakarya kawai sokuwa shashsha wacce babu halin a batawa mutum rai ya gaya mata ta tausaya mishi, sai ta ce zata bishi da bakar magana sau dubu nawa yake so in turo mishi mutane kafin ya yarda ya bani ke? Me nayi mishi a rayuwa i banda adalci. Sauri nayi na tari mashin babur na dale kai muka tafi don kar bakin ciki da dacin da nake ji a zuciyata ya sa in fara yin kuka a gabanshi. Zagin da ba a taba yi min ba yi min, yayi min gorin aure da 'ya'ya da... na kasa karasa bayanin nawa na shiga yin kuka sosai da sosai, tana ta bani hakuri, jimawa can kuma sai ta nisa ta ce, nima dai abin yana damuna ina mamakin yanda baba ya ja ya tsaya ya ki baiwa Mubarak aurenki bayan nima nayi iyakacin tunanina ban gano laifin da ya yi mishi ba to inma ya yi a yafe mishi mana, Umma ma fa kwanaki tazo gidan nan maganar kuma ce ta kawo ta na kuma san ba dadi ne ya sa ta yin hakan ba, to ya bashi ke din mana kawai a huta, zan sake zuwa wajen baba in sake rokonshi inji.. Kan ta karasa na yi mata wata irin rantsuwa mai karfi kafin na ce mata, ba zan taba aurenshi ba har 146 abada ba zan taba aurenshi ba bana sonshi bana son shi ko da sunanshi ne a kusa da ni da in aureshi gara ma in yi ta za... Ta dakamin tsawa na kame bakina na bar maganar na koma yin kuka, tun ina yi ni kadai har itama ta shiga tayani muka yi tayi sai da muka gaji muka yi shiru. Mubarak ya saba zagina ko tsareni ya gaya min bakaken maganganu iya son ranshi a duk lokacin da ya turo maganar aurena wajen babana ya ce ba zai bashi ni din ba, to ni yake tsarewa ya gaya min duk wani abinda yake son fada, in yi bacin ran in hakura amma bai taba gayamin maganar da ta daki zuciyata ta sani bakin cki na yi kuka mai tsanani irin wannan karon ba. Na gaji, na gaji, na gaji da iin wulakanci da cin zarafin da yake yi min a kan aurena don kawai ya ga bani da auren da ina karkashin inuwar aure ai shima da bai isa ya yi min irin wadannan abubuwan da yake yi min ba don haka ya zame min dole in tsaya in yi duk wani abin da zanyi don ganin na yi auren saboda in huta da wannan wulakancin da kuma cin mutuncin kan haka yasa washegari da sassafe na yi shiri na tafi gidan Yakumbo Halima wacce ta dade tana kirana inzo muje wurin malaminta da take ta faman bani albari. 147 Ina shiga gidan ta fara murmushi, 'yar halal kin ko ambato yanzun nan nake maganarki a zuciyata. Na tayata murmushin kafin na tsuguna na sOma gashcta tana amsawa tana kallona cikin wani irin yanayi dake baiyanar da jin dadinta. Kai wannan yarinya da iya kwalliya kike wannan kuma wane irin dinki ne? Mu ganshi. Na numa mata ta gansi sosai, to me sunanshi? Na gyara na koma na zauna cikin natsuwa, kwalliya ta fa ke kadai take burgewa. Ta yi maza ta ce wane mutum ai duk wanda ya kalleki ya san ke din gwanar kwalliya ce Mero ai rashi aurenki ba yana nufin ke din kina da wani aibu a tare da ke ba ne a'a lalura ce dake wani aljani ke gareki wanda yake biye da ke bana baki albarin abinda wannan maiamin ya gaya min a kanki ba, ai nace miki ki zo muje wurinshi don ya ce min akwai abinda zai yi ya rabaki da shi kika fi zuwa. Na ce to ai gani na zo yau Yakumbo zuwa nayi don ki kaini inda duk za ki kaini na gaji, na gaji da wulakancin da Mubarak yake yi min, na kwashe bayani duka na yi mata. Maimakon yauma ta nanata maganarta da kullum take fadi cewar shi ne ya yi min sihirin da na kasa yin aure sai naga ta yi murmushi kafin ta ee, ja'ira shagwaba da gata ne suka sashi yin abubuwan da yake yi su ma iyayen na shi ai sun yi nadamar hanashi 148 aurenki da sukayi yanzu tunda kwanaki ai ance korar matar tashi ya yi ya ce a barshi kawai ya yi zamashi shi kadai tunda dai suna kallo an hanashi ke sun kumna yi ko oho da hakand a akayi saboda su basu damu ba ai shi ne dalilin da ya sa ita Hajiya Ummulkhairin ta kama hanya taje gidan Dijan to shi kuma babanki shima ya kafe akan ba zai basu ke ba. Na ce wannan ruwansu ne Yakumbo. Ta yi maza ta ce ruwan su ma mai ma ya kare musu bari in yi maza in shirya mu tafi tun rana bata yi zafi ba don akwai 'yar tafiyar kafa da za a taba. Nace mata to Yakumbo ai ma ni tafiyar kafa ba mas' alata ba ce na riga na saba da ita, tayi amza ta ce, aifa na tuna kin yi ta ba kadan sanda kike zuwa wajen koyon sana' ar nan gashi ya zama tarihi sai amfanin shi ake ci ko ince muke ci tunda yaushe rabon da raina ya 6aci a kan dinkuna? Ace jaruntaka babu dadi? Bari ki gani ins hirya yanzu mu tafi ba ma sai na tsaya wanka ba tsaka tsami kawai zanyi in mun dawo in ban ji kuiya ba na yi wankan. Nan da nan Yakumbo ta shirya muka kama hanyr fita, gani bata tambaya ba ya sani tambayarta, dama kin gayawa kawu ne? Ta dan yi murmushi, mu yan tsofaffini nan da auren mu ya riga ya tsufa yaushe za ace komai za mu yi sai mun tsaya wani tambaya ai shima yasan sabgogin iyali yawa ne da su. 149 Shiru nayi na ja bakina na tsuke tunda nasan babu halin in tsaya ina tambayarta Yakunbo shi aurenn yana tsufa pe a dalilin masu yinshi sun tsufa? Bayan mun sauka a mota tafiyar kafa fosai mukayi a ciki jeji muka wuce wasu rugage muka mika cikin wani irin surkukin daji Yakumbu damun san wurin nan haka yake ai da hayar babura muka dauko a dan kauyen nan da muka wuto. Hararata tayi, kufa yaran yanzu bakuda wata jaruntaka wai ke kina so ne ki nuna min kin gaji da tafiyar kafar da ake yi ko? Na yi murmushi kawai na yi shiru muka ci gabada tafiya da kyar muka iso wata mararraba da ta ce min wannan da muke kai yanzu ita ce mai kaimu gidan nashi nace mata to. Mun samu yan daidaikun mutane da ke jiran a sallamesu amma ana sanar da shi isowar Yakunbo yace a shiga da mu. Na yi mamakin ganin mutumin da ta ce min shi ne malamin na zaci ganinshi dattijo amma sai na ganshi matashi ma'abocin tsabta da natsuwa ga sutura tamkar dai ba a cikin dajin nan yake zaune ba. Hajiya barka da zuwa, ya yi maganar cikin murya mai cike da kamala suka gaisa nima na gaisheshi. Maryamu ko? Ta yi murmushi ta ce haka aka yi kuwa malam, idonshi a kaina ya ce, ai mun gani shi mutum ai kowa da sunanshi yake yawo, gabana ya fadi jin da nayi ya ce ya gani kar dai irinsu ne kullum 150 malamanmu suke yi mana wa'azi a kansu? Cikin Zuciyata na ke wannan tunanin. Ya jawo wani littafi ya bude yana karantawa na dan samu saukin damuwa a tare da ni ganin littafi yake karantawa su kuma malamanmu kulum suna yi mana wa'azin ne akan masu buda kasa suna masu duba ko bokaye to tunda wannan ba kasa bace littafi ne kenan ba duba bane yinshi kuma bai zamo laifi ba. Mas'alar aure ko? Ya yi tambayar ba tare da ya kalli kowa ba idonshi a kan littafin shi, ta yi maza ta ce mishi eh malam aure ne damuwar kullum sai manema sun fito mata gasu gasu kamar za a yi auren sai kuma a nemesu a rasa sun gudu, tun ina ganin laifinta ina ganin kamar ita ke korarsu har na daina jin zafinta na koma tausayi saboda na gane babu hannunta cikin lamarin. Ya girgiza kai cikin natsuwa tare da fadin, ai ba zai bari a aureta ba, wa kenan malam? Ta yi tambayar tana mai kallonshi. Ya ce mai ita mana ai wani maketacin aljani ne yake tare da ita shi ya sa babu halin tayi aure don ba zai bari ba shi yake korar mata samarin da siddabaru iri-iri suna tare da ita su rinka ganin ta caccanza musu tanayin launi lauru su ganta fara su ganta baka su ganta ja su ganta bulu ko kumna su rinka ganin fuskarta tana rabuwa biyu sai ta koma ta hade ta sake rabewa ta sake hadewa, to kinga kuwa ai babu lafiya. 151 Yakumbo tayi maza ta ce, ko kadan cikin sanyin murya ni da kaina da ba sosai nake yarda da irin wadannan abubuwan ba jikina bari yake yi jin bayanin malamin. To yanzu yaya za a yi kenan malam? Ya ce eh to da yanda za a yis ai dai kumaaiki ne babba sai an rabata da shi gaba daya in ba a tsaya an yi hakan ba ko anyi auren kashe mijin zai yi don haka sai an yi juriya da jarumtaka. In dai za a rabata da shi ai duk wani abin da za a yi ba zai gagara ba malam a gaya mana kawai abin da za a yi. Ya ce to babu laifi akwai aiki da za a yi wanda za a bukaci sadaka mai karfi ko dai shekararrun zakaru guda bakwai ko kuma rago sannan zata rinka zuwa nan muna yi mata wani aiki har kwana bakwai in har komai ya tafi daidai to kafin cikar kwanaki bakwan din nan mijin da zata aura zai baiyana ana gamawa sai a daura auren mu kuma in ayzo to shi ne zai biya ladan aikinmu baku ba. Nan da nan Yakumbo ta shiga yi mishi godiya tare da tambayar to wanne ya yi tsakanin rago da kajin? Ya ce a'a ao na za a hada ba rago yafi sai dai in babu hali sai a yi da kajin duk daya ne. Ta ce to bari mu bada kudin ragon nawa ne zai yi? Ya ce daga fan goma zuwa sha biyar ko ashirinn duk wanda kika bayar zai yi. 152 Na yi kasake ina tunanin ta inda kudin da ya ambata zasu fito sai kawai naga Yakumbo ta jawo lalitarta ta ciro kudi ta kirga fam goma sha biyar cif ta mika mshi, ya ce zuba nan cikin wannan kwaryar, ta bi umarnin nashi ta zuba muka yi mishi sallama muka fito. Babu abinda yafi komai yi min dadi irin cewar da ya yi kafin a kammala aikin mijina zai baiyana ana gamawa kuma sai a daura auren shi nne ma wai zai biyashi kenan nima zan yi aure babu sauran a tareni a zageni babu sauran a yi min gori, babu sauran a rinka nunani a unguwa ana fadin babu sauran sa'ata a' yan matan da ke yavwo a unguwar. Washegari da safe naje na samu babana a rumfarshi bayan na kammala shirina na dan zauna kamar zanyi mishi hira sai da na bari Sallau ya dauki kwanduna ya nufi kasuwa sai na kalli babana na ce mishi baba yaya Dija ta aiko ni wurinka wai ince maka akwa wata yarinyar bazawara mai hankali kusa da su ko za a yi magana da ita. Gabana yana faduwa na yi mshi bayanin, sai na ji ya ce to ina da kudi ne da za a yi min amgana da bazawara? Sannan da girmana da komai ita mace ace miki tana son tsoho ne a shekarun. kuruciyarta. A hankali na ce mishi, baba ai ita yaya Dija ina ganin kamar sun fahimci juna ita da matar tace min ne in yi maka magana in ka yarda ta turo maka ita don ka ganta, a hankali ya ce a'a ni kam ai ba sai na ganta ba in 153 dai ku tayi muku ai shi kenan fitina ce dai kawai ni bana so. Nace mishi too nayi mishi sallama na tashi na tafi, can cikin zcuiyata kuwa mamajki nake yi ban taba zaton haka amsar babana zata zamo ba, na kama hanyar tafiya wurin malam don karbo alkawarin da akayi duk da wata zuciyar tana nunamin in fara ganin yaya Dija tukunna sai kuma naga to bari dai kawai inje can din in yaso in na dawo sai in biyo ta wurinta in yi mata bayanin yanda muka yi da babana daga nan kuma taga abin da na karbo wurin malam. Wajen karfe goma sha dayan safe na isa kauyen nan inda daga shine muka soma yin tafiyar kara, nayi tafiyar kafar har na raina kaina sai da na soma kaiwa matuka wajen gajiya ne ma na tuna ko sunan malamin da zani wurin nashi ban ji ba balle kuma na kauyen da zanin, abin ace na bata hanya ban san yanda za a yi inyi tambayar da zata zamo mai amfani a gareni ba, sa'a kawai nayi da na ci gaba da tafiya sai kawai na ganni a mararrabar nan wacce daga ita ne muka dauki hanyar da ta nufi gidan malam. Tsayawa nayi cak. na zubawa hanyoin nan ido ina kallonsu tare da tunanin wacce muka hau ne a ranar? Na gaji da dubawa na yankewa kaina bari kawai in hau kan guda daya tunda bajuyawa baya zanyi ba don haka na kama ta tsakiyar nayi ta tafiya a kanta banga komai ba banga wata alama da na gani wacce ta karfafaa min guiwa ba don haka na juyo da baya zuwa inda 154 nararrabar nan take na sake zabar wata hanyar na hau an nma nayi iyakacin iyawata nayi tafiya sai da na fara debe tsammani ina cikin tunanin komawa da baya kawai in koma gida inje in gayawa Yakurmbo Halima cewar ban gane hanyar ba tazo kawai ta karbar min maganin da kanta ko ta tasoni a gata mu zo tare kamar yanda tayi min rannan tunda ni na kasa gane wurin da kaina sai kawai naga mutum tsaye cif a gabana tamkar daga sama aka jehoshi, tsoro ya.yi matukar kamani ba tare da ya ce min komai ba sai naji ya ce min, wuce mu tafi malam ne ya turoni in kai mishi ke saboda an gaya mishi cewar kin kauce hanya don haka ya kwatantamin inda zan sameki shi yasa na yanko ta cikin bishiyoyin can, nabi hannun nashi da kallo don inga can din da yake magana akai, wani irin surkukui ne da sunkurun duhun bishiyoyi da ban taba tunanin dan adam zai iya shigarsu ba ban iya buda baki na ce mishi komai ba haka nan duk da tsananin tsoron da nake cikin ba zai yiwu in yi musu binshi ba tunda ban san inda zan dosa ba. Tasani kawai yayi a gaba muka kama hanya 'yar tafiya "yar kankanuwa sai kawai gamu mun isa gidan. Shiga nan, yana bani umarni nayi maza na shiga sai ga malam zaune daram a kan buzunshi cikin manyan kaya ga hularshi a kanshi yayi kwalliya irin wacce ta dace da shi. Maryamn da so ya kira sunan nawa yana ma kallona, ina babar taki? Na isar da gaisuwarta gareshi bayan na gama gaisheshi ya ce, alheri ya gaieta, ai ga 155 kwaryar da na hangki a ciki can, nayi maza na waiwaya na kalli kwaryar da ya ce min daga cikin nata ya hangeni babu komai a ciki in banda ruwa, na sake juyawa gareshi na kalleshi don jin bayanin da yake yi, yayin da zuciyata ke ta faman harbawa 6al 6al 6al, daga nan din ne na kira wanda ya daukokin don kar ki je ki yi wa mutanen hanayr da kike ta kakkaucewar wani ta'adi unda su di mafi yawancinsu ba hakuri ne da su ba. Wani mutum ya ashigo rike da zangarniyar dawa a hannunshi ya tsuguna ya mikawa malam, bai kalleshi ba ya ce mishi, kwaya bakwai nake bukata, ya mika mishi kwaya bakwai din ya fita da zaugarmiyar a hannunshi. Malam ya jawo wani tsohon kasko fasasshe ya debo kasa tafin hannunshi uku ya zuba a ciki ya dauki tulun dake gefenshi ya jika kasar da ruwa ta jiku sannan ya shuka kwayoyin dawan nan guda bakwai a ciki kan kace meye wannan sai kawai naga dawar nan da ya shuka a kan idona ta kamna tsirowa a cikin kaskon, nan na zuba ido ina kallon abin mamaki wanda ben atôa ganin kwatankwacin makamancinshi ba, na yi matukar kokarina wajen 6oye halin da nake ciki na tsoro saboda ganewar da nayi ina cikin wani babban al'amari,don haka nayi maza na soma karanto addu'o'i na neman tsari. Kina da wani wanda ya dameki ne a yi miki maganinshi? Na'am na amsa ina kallonshi don ban fahimci abinda maganar tashi take nufi ba, eh abinda nake nufi kenan in kina da wani wanda ya dameki 156 kawo sunanshi mu gwada miki aikinmu a kanshi ta hanayar kashe miki shi nan take. Kalululu, sautin da cikina ya bayar kenan a lokacin da na ji maganar tashi, da kyar na iya girgiza kaina don nuna mishi alamar babu, cikin zuiyata kuma tarnbayar kaina nake yi me yasa malam yake yi min irin wadannan abubuwan tunda ni ai ba abin da ya kawoni wurinshi kenan ba, sannan me yasa bai yi ba ranna na gaban Yakunbo sai yau da ya ganni na zo ni kadai Kina saurarona? Na yi maza nace mishi eh, ita babar taki ta yi miki bayani a kan ka'idojin aikinmu ko? Na girgiza kai nuna alamar a'a, to muna da ka'idojn da karyasu yake da hatsari kwarai shi yasa muke bayani a kansu don kar mutum ya jawa kanshi wata fitina da zata zo ta dameshi ta damu duk wani wanda yake tare da shi, ba a yin musu da umarnin da ake bayarwa anan ko mai tsananinshi, sannan ba a yin gardama ko jayaiya domin nan din Wuri ne da ake mu'amala da nau'o in halittu guda uku wato jinsi mutane da na aljanu sai kuma rauhanai don haka ba wurin wargi kika zo ba, yin daya daga cikin ukun can dana ambata miki ina nufin musu gardma ko jayaiya sakamckonshi yin hauka ne hauka kuma irin wacce bata warkewa. Cikina ya sake bada wani sautin na kulutuiu har ma ya fi na farkon karfi saboda tsananin tsoro da na samu kaina a ciki din. Kin taba ganin aljani ko rauhani? Na yi maza na ce mishi a'a, to ai za ki ganshi yau din nan. Na ji kamar in 157 zabura in mike in karta da gudu in shige cikin dajin nan in huta. Ya gyara zama ya soma yi min bayani, kin san akwai jinsih mutum da na aljan da raunahni kafin mala'iku ko? Angi maza na ce eh ba tare da na fahimci koami ba da yake nufi ba. To mu nan fadar rauhani kika zo ki gane? Na sake yin karfin halin cewa eb. Ya zuba min ido yana kallona ban sani ba ko shima ya gane halin da nake ciki na tsoro ne. Yanzu kafin rauhanin da zai yi miki aikin ya iso tunda mum riga mun kirashi yana can yana dawafi ne in ya gama zai taho, kin taba yin sata? Tambayar tashi ta zo min a bazata, na yi maza na kalieshi don inji ko abinda aa jin daidai ne, ya ce eh abinda na tambayeyi kenan, kin taba yin sata? Na ce mishi a'a, sata ko wacce iri baki taba ba? Kin san fa ba a karya a nan, in ka riga ka shigo nan to gaskiya da gaskiya ne kawai, in kayi karyar ma za su gane ka don baka yi tunani sosai don kar su kamaki da laifin yin karya. Na gama tunanin da zanyi sai na ce mishi, sai dai ko na abinci ko naman miya a wurin matar babana. Ya yi maza ya ce, a'a ai wanna ba sata bace bari kawai a gaya musu baki taba sata ba ko da yake ma suna nan tare da mu suna jinki, ko kina yin karya? Na dan yi shiru cikin nazari kafin .shima na ce mishi wani loakci na kan yi amma ba ko da yaushe ba. Ya gyada kai tare da fadin, to babu laifi ya yi kya, kina da kiyayewa kenan? Na ce mishi ch, to ai shi kenan 158 sun jiki, tambaya ta karshe ki fa yi hakuri ba daga ni bane kaidarsu nake bi don haka suke bincike kan kamewar mutun kafin sù shigar mishi, kin gamsu? Na ce eh. Kin taba yin ziua? Na girgza kai na nuna alamar a'a, to ai ma shi kenan aikin naki mai sauki ne tunda baki da kazanta mai yawa a tare da ke sai ta kananan zunubai wannan kuwa dukkanmu ne don haka ki kwantar da hankalinki shi wannan nikin naki mai sauki ne kwarai an yi irinshi yafi sau nawa anan in dai kin bada hadin kai ai shi ke nan tsanani wana uku ne zuwa bakwai magana ta kare don haka bari ya iso ya sallameki, na riga na ji tasowarshi don haka bari in yi miki tuni ka'idojinshi banda musu banda gardama banda jayaiya ba abokin wasanki bane sakamakon yin hakan hauka ce da babu nagani kin gane ko? Na ce eh, can cikin zuciyata kuwa addu'o'i nake ta yi na neman rabuwa da rauhani lafiya. Ana cikin haka naji wani abu ya fara bayar da wani sauti na shuuuuuw sai dai ban san daga ina yake fitowa ba, wata irin iska'mai sanyi ta fara shigowa dakin. Yauwa gashi nan ya doso mu gashi nan ya dunfaro gashi nan zuwa kar ki mance da abinda na gaya miki don ni kaucewa zanyi in baku wuri banda musu banda jayaiya banda gardama, dif sai kawai naga wutar fitila ta mutu duhu mai tsanani ya baiyana, na yi matukar tsorata irin tsoratar da ba zai yiwu in kwatanta ta ba. A firgice kwarai na shiga furta kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shiiiii sautin da ke ta karuwa a 159 cikin dakin kenan sai kuma tsananin sanyin da ya fara lcadani, na shiga cikin wani irin yanayi mai tsamanin firgitarwa baranma dai da na ji wani abu ya sauka a jikina wanda ya yi min kama da hannun mutam, rauhanin ma yana da hannu ne irin na mutane? Tambayar da ta zo cikin zuciyata kenan, ban daina furta kalmomin da nake firtawan ba sai ma karawa nayi zuwa can naji abin nan da ya tabani mai kamar hannu ya cafko kullin da na yiwa zanina a ta bayana yana kokarin kwanceshi, kici-kici da kokawa mai tsanani ya kaure tsakanina da rauhani saboda ganin da nayi rauhani yana Rokarin gradamin karfi, ya yi min illar da bazan laminta ba, ganin da nayi kamar rauhanin zai yi galaba kaina yasa na sa hannu da kafa na kuma bude baki na kurma ihu da iyakacin karfina ina bana so bana so aikin a kyaleni, ban sani ba ko maganar da yaji nayin ne ya sashi bude bakinshi shima ya yi min magana da irin nashi zancen. Gyaaraaahhhh ki budeec kafahfuh mu sah miki albarrkah. Mu sake bin Maryamu cikin littafi na hudu don mu ji karshen labarin na ta tare suka fito. Fatan alheri gareku dukkanku na gode Ubangiji ya saka muku da alheri ya kuma kara zumunci a tsakaninmu. 160