HALIN RAYUWA 4 HAFSAT G. SODANGI Mr. Yunus Abdullahi Dabai 1 Hakkin Mallaka (m) Sodangi Copyright O Sodangi GODIYA Godiyata har kullum ga Allah take, Masanin yau da gobe, mai kowa mai komai, Gwani mai hikima wanda yayi halitta tasa duka bibiyu, ya kuma halicci mutum da Aljan don su bautata mishi, Tsira da Aminci su tabbata ga cikamakin Anabawa shugaban Manzanni, Annabin Karshe Muhammad (SAW) da Alayensa da Sahabbansa da wadinda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zauwa ranar Altiyama, amin. Godiya mai yawa gare ku makaramta litattafaina, m kusa da na nesa, Ubangiji ya saka da alheri ys kuma Rara karfafa zumuncin da ke tsakani, na gode. SADAUKARWA Sadaukarwar littafin ta lyayena ce, Ahaji Chindo Muhammad Sodangi da Hajiya Fevime Musa Sodangi, Ubangiji ya saka muku da alheri ya kums fara muku lafiya amin. TUKUICI Tukuicin littafin naki ne: KHADIJA CHINDO SODANGI (Mrs Nasiru ldris) 2 JINJINA Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya laifi (Manc Umar) Zuhuriyya lbrahim (Mrs LAwal Chindo Sodangi), Ubangiji ya raya Umar da imani. FATAN ALHERI GARE KU Fatima Abdulkadir Kazaure Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi Khadija Usman Nasarawa Nafisatu Ibrahim Muhammad Fatima Ahmad Shehu Kaduna Maryam Muhammad Gusau, Zamfara Umaima Abubakar Umar Maijidda Uba Magaji Na gode, Ubangiji ya saka da alheri, amin. KUNA RAINA Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassarn Hajiya Jamila Ibrahim Na Bature Hajiya A 'isha Balarabe (Jazan) Ubangiji ya bar zumunci amin. 3 LITTATTAFAN SODANGI: 1. Uwar miji 2. Naga ta kaina 3. Rabon kwado.. 16. Wacece ni? 17.Wata fuskar.. 18. Mijin ta ce 19. Garin banza... 20. Ga ni gare ka 21.Biyan Bukatar rai 22. Shamaki 23. Hattara 4. Cikar alkawari 5. Wayyo duniya 6. Yi wa wani.. 7. Abu naka... 8. Mata ma su duniya 9, Nufin Allah 10. Kifin na ganinka... 11. Daga kin gaskiya... 12. Da kamar wuya... 13. Mai uwa... 14. Duk daya... 15. Mata da kicin dinsu 24. Kyautata 25. Ayi dai mu gani... 26. Tabbataccen al'amari 27. In kunne ya ji.. 28. Halin Rayuwa 29. Mai Daki... Littattafan ba sa nufin yi da wani ko habaici ga kowa, sai dai an rubuta su ne don fadakarwa da nishadantarwa, ana neman afirwa ga duk wanda yaga wani abu yayi kamar abinda ya shafe shi, ba da shi ake ba dace ne kawai. 4 HALIN RAYUWA4 A wannan lokacin ba zai yiwu in iya kwatanta halin da nake ciki, ba na tsoro, abu guda daya dai da zuciyata ta kasa yarda da shi, shi ne a in bar Rauhani ya yi min abin da yake son yi min, da in har shi ya yi min hakan sai na gwammace ma kawai gara duk abin da zai faru da ni ya faru koda kuwa wani abu ne da ya fi hauka muni. Tsayarwa kaina wannan hukunci da zuciyata ta yi, sai ya zama dalilin da na samu kuzarin takarkarcwa na kurmawa Rauhani ihu da iyakacin karfina. A bar ni bana son aikin, a bar ni kawai na ce a bar ni. Abinda nake ta fadi kenan. Iskar da ke kadawa a dakin ta tsaya nan take kuma haske ya bayyana a dakin, sai ga Mallan a zaune a wurin zamanshi, hularshi zaune daram a ken shi, nimaa nayi maza na mike na zauna muka fuslkanci juna ni da shi. Maryam kin 6ata aikinki,kin yi duk abinda aka ce miki kar kiyi, kin yi musu, kin yi gardama, kin yi jayayya har da kokawa. Ya tafí yana fushi yanzu ya ya kenan? Ban iya buda bakina nayi magana ba, balle in iya amsa mishi tambayar tashi, saboda har lokacin ina cikin tsananin tsoro, jikina ma bai daina 6arin da yake yi ba. Ban sani ba ko ya gane hakanne yasa shi kawo shawarar cewa ya sake kiran Rauhanin ya ba shi 5 hakuri, ya yi aikin da ya zo yin don kar haukan da ya yi alkawari ya same ni. Nayi maza na ce mishi "Aa, a bar ni kawai." "A bar ki hauka ta same ki? nayi shiru ban amsa ba, "Kin gwammace kiyi hauka ko?" Na sake yin shiru, "To shi kenan tunda abinda ki ka zaba kenan, dulk abinda ya faru da ke dai ba za a sake kawo mana ke nan mu karbe ki ba, tunda kina cikin bijirarrun mutane masu taurin kai. Sakamakon taurin kai kuma nadama ne. Ina kuma yi miki albishir da hauka kafin fitarki cikin wannan dajin." Yana fadin hakan naji an daka min wata irin tsawa, wanda saboda tsananin tsoro na kasa fahimtar daga in da tsawar ta fito Tashi ki ba mu wuri." Abinda naji an fadi kenan da karfi. Ina jin hakan nayi maza nayi waje, yankawa kawai nayi da gudu ba tare da na tsaya neman takalmina ko tunanin ta ina na fito ina kuma ya kamata in dosa? Gudu kawai nake yi a cikin jejin nan, bana ko waiwaye ban kuma san inda na dosa ba. Gaba daya fatana da addu'ata bai wuce in isa gaban mahaifina kafin haukar ta same ni ba. Ina gudun ina kokarin jaddadawa kaina har yanzu dai da hankalina, hauka bata fara samuna ba tukuna, tunda duk abinda nake gani ina ganewa, ina kuma iya tuna komai nawa sai in yi maza in ci gaba da karanta addu'ar da damna nake ta karantawa Hasbunallahu wani' imal wakil." 6 Ina cikin haka na hango wani mutum a gabanta, tsoro ya kara kama ni, ina tunanin ko Mallam ne ya turo shi ya zo ya mayar mishi da ni, Nayi kamar in juya da baya saboda tsananin tsoratar da nayi, sai kuma naga to ai in shi dinne ma zan iya juyawar ya sake tare ni a inda na koma din, don haka na dake zuciyata na ci gaba da taiyata har naje kusa da shi zan wuce naga ashe manomi ne yake aii a gonarshi, sai dai ban iya buda baki na tambaye shi hanya ba, saboda kar ya gane ni din bakuwar jejin ce. Nayi tafiya rannan har na raina kaina, amma zuciyata bata gaji ba, ko tsayawa in huta bana yi, kokarina kawai in fita bakin hanya ne in ga gari in ga ta inda na bulla don na riga nasan na kauce banya. Ina cikin haka na sake hango wani mutum da sauri na nufi wurinsli daga nesa kadan na tsaya na gaishe shi nayi mishi tambaya kan hanyar da zan bi in shiga gari Barin abinda yake yi ya yi ya taya yana lallona, ke kuwa ya ya aka yi ki ka kawo yanzu cikin dajin nan? Ban iya ce mishi komai ba, don haka ya gaji ya ce min Kina kusa da gari sai dai akwai tabkeken rafi a tsakaninki da shi, in kin iya ruwa ze ki iya bin nan ki fada raf ki tsallaka, in kuwa kin san ba ki iya ruwan sosai ba, sai ki bi nari don rafin yana da zurfi, in an yi ruwa ya kawo ba karamin ta'adi yake yi ba. 7 Na ce, Na gode. Har na fara tafiya ta nan din da ya ce, sai naji ya daga murya ya ce min kiyi ta tafiya har sai kin ga yar gada sai ki hauta ki tsallaka za ki ga kauye a nan za ki samü abin hawa zuwa cikin gari." Na sake cewa "To na gode. Wannan hanyar da ya nuna min din ita nabi nayi.ta tafiya har na kai inda ya ce zan ga gada, gadar ta langa-langa ne, wanda mutancn wurin suka hadu suka yi don su rinka samu suna tsallakawa zuwa inda gonakinsu suke in ban da gudun ceton rai nake yi babu abinda zai sa in iya hawanta. Na isa kauyen, a lokacin da duhun dare ya riga ya sauka ya mamaye ko ina, ga shi babu haske ko kadan, don kuwa babu. wutar lantarki a kauyen, babu kuma hasken farin wata saboda watan ya kusa karewa. A haka na wuce kauyen nan nayi tafiya har inda na samu wani mai mashin da ya yarda ya fidda i bakin hanya a dalilin tsananin gajiyar da ya gani a tare da ni. A kofar gida na samu Babana a tsugune yana tashe da fitilar kwai, daga ganin ikuma nasan ya yi wahala ya neme ni har ya gaji. Ina isa gabanshi na fadi a kasa ina kuka tare da fadin "Ka yafe min Baba." Ban wani tsaya bata lokaci ba nayi maza na attaba mishi bayanin komai, tunda nayi saa nazo gabanshi da hankalina, shi yasa nayi maza na gaya mishi don ya sani saboda kar haukar ta Same ni yayi tunanin zai yi ta wahalar neman min magani tunda ba hauka ce da zata warke ba, ka 8 taimake ni Baba ka tsare ni wuri daya kar ka bar ni in yi ta yawo a tube irin yanda nake ganin yan uwan mahaukata suna barinsu suna yi." "Ke Yahcuwuna. Ya kira sunan nawa cikin wani irin yanayi na damuwa, "Ki daina yin haka bari fadin irin wannan maganar, ya ya ki ke yi wa kanki mummunan fata irin wannan? Nayi maza na ce, "Baba mai Rauhani ne ya gaya min ai har kokawa da Rauhanin ma nayi. Ya mika hannu ya kama nawa "Zo mu shiga gidan, na godewa Ubangiji da ya dawo min da ke lafiya." Baba Lantana ta galla mishi harara ta ce, "Uhun, ai kai kam ka shiga uku, yarinya ta tafi taje ta gama barikinta ta dawo tana dingishin ta samu wadanda suka fi karfinta, amma kana bari kana fadin wai ka gode Ubangiji saboda ta maida kai sakarai." Isyaku ya yi sallama daga tsakar gida ya tsaya yayi tambaya, "Baba wai Anti Meron ta dawo?" Da sauri Babana ya ce, "Eh, ta dawo." Ba tare da ya tsaya tambayar in ji waye ba, ta sake fadin "Ka ji wani irin rainin hankali ma Malam, sai ka ce ba tare suke ba, sai ka ce ba shi ya kawota ya ajiye ya wuce gidanshi.." tayi maza tayi kasake ta bar maganganun da take yi ta koma sauraron bayanin da Baba yake yi min. Ai ba za ki yi hauka ba, ai karya yayi miki ba Rauhani ba ne, shi mutumin ne da kanshi yayi miki wannan abin don ya samu ya tsoratar da ke, ki yarda yayi lalata da ke. Ba mutumin kirki ba ne, Boka ne. Ko 9 Malamin tsubbu. Ba da Rauhani ki ka yi kokawa ba, bai yi nasara ba ne a kanki saboda ke din mutuniyár kirki ce, uwarki ma haka, Ramatu mutuniyar kirki ce sannan bata da tsoro. Baba Lantana taja mummunan tsaki "Wannan Ramatu ai bata kyauia ba da bata jaka ku ka tafi tare ba.". Tuni sai ta bar maganar da take yi ta ni da Mubarak muka fita yawo, ta koma ta Rauhani da hauka don tafi yi mata dadi. "Hauka kam ai sai kin yi tunda Rauhani ya ce sai kin yi, to shi yana karya ne ma da za'ka ce mata ba za ta yi ba? Ba dai har nan dama Dijan take kai ba? Ai kuwa dai kun tsokano tsuliyar Dodo." Sallau yayi sallama ya shigo tare da fadin "Baba ashe ta davo?" Ai ta dawo Sallau ya sake fita ya sayo min shayi da biredi in banda yayi wannan dabarar watakila da haka na kwana ni da Babana ba muyi wannan tunanin ba, balle Baba Lantana. Kwana muka yi Babana yana rike da allon Karfenshi yana rubutu yana wankewa yana bani ina sha, saboda na kasa ko da runtsawa ne in yi saboda tsananin tsoron da nake ciki. Washegari da sassafe sai ga Yakumbo Halima da Yaya Dijah sun iso, ita kam Yakumbo taje wajen Yaya Dijah ne wai ta ji taje na karbo sakon ko ban je ba naki Zuwa? Yaya Dijah ta ce, "AI ma wunin jiya ba a ganni ba ana ta nemana kan haka suka rankayo gida don Su 10 gani na dawo ko ban dawo ba? In ban dawo ba a nufi gidan Malami." Sai suka zo sulka same ni, Babana ya kwashe bayani yayi musu, suka yi wa juna barka saboda ban yarda na ambaci sunan Yakumbo Halima cikin bayanin da nayi mishi ba, da ban san yanda suka kwashe ba. Bayan fitanshi ne Yakumbo ta rinka rantsuwa wai tana so in yarda bata san haka yake.ba, don bai taba nuna mata ba. Yaya Dijah ta ce mata "Haba Yakumbo, bari wannan rantsuwa da ki ke yi, za ki kai ta in da za a cuce ta ne da saninki." Wai a wannan dan zuwan da suka yi sai da Baba Lantana ta sossoka musu maganganun da Yakümbo ta tanka mata suka yi fada kaca-kaca. Ba karamin rashin lafiya nayi ba saboda wahala da kuma ciwon da kafafuwana suke yi, tayi a dalilin raunukan da suka samu ta hanyar taka kayoyin da ke watse kan hanyoyin jeji da kananan itatuwa. Duk da halin da nake ciki na kusan kullum sai Babana yasa allura ya cire min wata kaya a kafa, ba wannan ne abinda yafi damuna da tsaya min rai ba, irin tabbatar min da Babana yayi cewar shi wannan mutumin da muka je wurinshi ba kowa ba ne illa Boka' saboda ni da kaina na ta6a kamanta wani hadisi da ya ce, "Wanda duk yaje gun Boka ya kuma yarda da abinda Boka ya gaya mishi, to ya kafurta da abinda Manzon Rahama (S.A.W) yazo da shi, in kuwa yaje 11 wurin Boka bai yarda da abinda Boka ya gaya mishi ba, to zai yi kwana arba'in yana Ibadar da ba za a karba ba." To wannene mai sauki a ciki? Sai na samu kaina cikin wani irin yanayi ma tsananin rashin lafiya a dalilin tsananin tsoro da tasin hankali, babu abinda nake tsoro iris mutuwa a tsakanin wadannan ban samu yar nutsuwar zuciyaia ba sai da Babana yayi min bayani dalla-dalla, lokacin ne na dan samu natsuwar zuciya ta na koma yin Istigifari da kyautata zato wurin Ubangiji tare da kudurawa raina ba zan sake ba. Ba zan sake zuwa wurin wani ba da sunan neman taimako akan aurena ko a kan wani dalili na daban, dama can ban taba ba, in ban da warinan lokacin to ba zan sake ba gaba daya lamurrana dama ga Ubangiji suke, ga. t shin kuma zan kara maida su, in kara dogara in har da rabon zan yi aure an ubuta cikin kaddarar rayuwata, to zan yi. Dor nayi Imani da kaddatsare mai kyau da mara kyau. Sanna rashin auren in har an kame kai ba zai zamo munnaunan kaddara ba in har ba a rinka watsewa ba, nan take nä shiga tunano manyan mata da suka gama rayuwarsu ba tare da sun yi auren ba, ko suka bar shi a shekarunsu naa kuruciya suka maida hankulansu kawai wajen yin Ibadarsu, da auren da baa san ka'idarshi ba, ba a tsare mutunci da sharuddodinshi ba, ai gara barin shi yafi. 12 Nan take sai naji zuciyata tana kara raya min tsare budurcina da yin komai wajen ganin budurcin nawa yaci gaba da kasancewa a tare da ni, matukar ina cikin hayyacina saboda in zamo daga cikin 'yanmata masu mutunci da ke kaiwa mazajensu 'yanmatancinsu, ko kuma suke gama rayuwarsu su koma ga Mahaliccinsu da abinsu a tare da su. Kan haka sai na kara kudurawa raina cewar zan Kara kyautata sana'ata in kara riketa hannu bibbiyu don ta zamo min abinda zan rike wajen ganin nayi ta karatuna, ban zamo mai dora nauyina ga kowa ba. Kusan satina biyu a gida ban fita ko'ina ba, ina jinyar kafafuna a kwanakin nan duka babu wata rana da gari ya waye har yamma tazo ba tare da Baba Lantana ta jaddada min haukan da Rauhani ya ambata min zai same ni ba, don kuwa in ita muna yi mata rashin mutunci muna kwana lafiya, don kawai Faddarar wahala ta kawo ta gidanmu, ta auri tsohon ubanmu, to ai shi Rauhani ba zamu yi mishi iya shege ya kyale mu ba, tunda ba tsoron ubanmu ya ke yi ba. Ko kallonta bana yi, maganar tata kuma ba ta damuna saboda a yanzu, na ragë damuwa da al'amarinta, ban da haka kuma nafi yarda dá maganar Babana a kan tata, don haka ina cikin kwanciyar hankalina, ga kuma neman auren da nasan Yaya Dijah tana yi wa Babana, wanda nasan ba da dadewa zai tabbata, tunda na shaida abubuwa da dama da ta gabatar. 13 eNa soma zuwa Makaranta, wai ashe dan wannan neman nawa da Babana yayi a gidajen makwabta da ke kusa ma wai abin magana ne, ya madidi ake tayi da ni da shi ana fadin wai ai gashi nan ya ki aurar da ni yana jira sai ya samu' dan mai kudi irin Mubarak. To ga shi nan na gaji da zaman gidan na fara gudu ina tafiya abinda kake yi a boye zan fara fito da shi fili. Ko kula zancen ban yi ba, balle in samu wata matsala, tunda an yi wadanda suka fi ta, na kuma ga wucewarsu lafiya. Abu guda daya da yafi bani mamaki shi ne, kowa ko kuma in ce ko wadanne mutane a gidansu sukan yi al'amarinsu shiru. Babu mai cewa konai, amma ni da Babana kemai muka yi sai an ce mun yi. Da ana tsayawa á iyakacin abinda muka yin ma to da sai in ce da sauki, amma ina sai an kara. Ta gidin Yaya Dijah na bi da muka tashi don tasan naji sauki har na fara zuwa Makaranta. Na same ta cikin farin ciki an kawo mata adashenta da tayi wanda dama tàci alwashin kashe kudin gaba daya a hidimar auren da za'a yi wa Babana. Dadi ya kama ni, amma ko kusa ban kai Yaya Dijah murna da dokin auren ba, duk da kudinta take kashewa. Ina dawowa naje na samu Babana a runfarshi, na zauna ina shan timatir din da na dauka saboda sha'awar da ya ba ni, muna 'yar hira ina ba shi labarin irin kąratun da aka yi a kwanakin da ban je ba. 14 Ya ce min "Eh, ai shi karatu haka yake, in dai har kullum kana zuwa ana yi da kai, to ba ka gane yawan abinda ake yin ya dame ka ba, sai in ka yi fashin zuwa. Na ce, Eh Baba." A hankali sai na shigar da bayanin abinda na tarar Yaya Dijan tana shirin yi, shi ne hada kayan aure don maganar tana kara karfi tana kuma kara matsowa. Wani irin shiru Babana yayi, ya kafawa kwandon alayyahun da ke gabanshi ido ba ya ko kiftawa. Har tsoro ya fara kama ni, kar dai ya ce ba ya so. Cikin natsuwa 8ai na tambaye shi "Me ya faru kayi shiru haka Baba? Ya ci gaba da aikin shirya alayyahun nashi yana daurewa saboda mna su zuwa saye yana yi min bayani, Wato ba wai bana son auren ba ne, fitina nake tsoro. Ta zo ta kashe kudinta da tayi ta tattalawa bata yi wa kanta ko ya'yanta wani abu sun ji dadi ba, in zo ni kuma ban ji dadin abin ba, wannan ta gidan må ya ya aka kare da ita kullum tana raina abinda ake kai mata, balle kuma a ce an je an dauko yarinya an kawo, alhalin ba wani abu nake da shi ba." "Kai ai ina ganin kama wannan ba za ta yi wata fitina ba Baba. Tare muka je gidansu dazu cikin maganganun da naji Yaya Dijan tayi mata, har da na daki ta ce mata guda daya ne kuma bai da wani girma. Sai naji ta ce, "Ai babu komai, shi aure in aka yi shi zaman lafiya ake bukata ba wani abu ba. 15 Babana ya ji dadin kalamin nata da na gaya mishi, nan take ya ce "To babu laifi, sai lkuyi." Ya mike yaje ya dauko wani tsohon bankinshi na karfe ya kwakulo makullin a inda yake boyewa ya bani ya ce min bude ki dibi abinda yake ciki na dai san babu yawa, amma je ki ki kai mata ko sabulu sai ta saya." Na ce mishi, "To Baba." Na louma yi mishi godiya cikin farin ciki, don kuwa bakan alama ne na shima yana son auren. A natse kwarai na yi wa Sallau bayani, ko ban gaya mishi abinda za ayi da dakin bá, amma nayi kokari na fahimtar da shi ya gane cewar bukatar dakinne ya taso, ba son korarshi nake yi ba. Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min "To, tunda haka ne Mero, in rinka kwana a zauren gidan nan mana kawai, ai shima wani babban dalki ne, in na rufe kofar waje na rufe ta ciki ba shi kenan ba?" Nayi maza na ce "Kwarai kuwa Sallau, to ai ma shi kenan tunda ka samarwa kenka wata dabara. " A haka al'amura suka ci gaba har na kai ga fita daga dakina na koma na Sallau na kira mai gyara ya y wa dakin gyaran da ya dace kafin mai fenti ya zo ya yi. Ita bata yi tunanin ba dom a ranar da ake aikin ma wuni tayi tana fadin, To tunda babu tsayayyen da zai tsaya ya kwasa ya kai gidanshi, can inda ake ta harin kuma uwar yarinya taja tayi damara ba dai a shiga ba, sai dai a kare a titi. 16 Ai sai kiyi ta gyara kina fenti don ki ji dadin zama tunda ba ki da ranar tashi." Ban kalleta ba ma balle tasan naji abinda take fadi. Da daddare ma da Babana ya dawo naji shi yana tambayarta ni ina butar nan ne? Sai naji ta ce mishi, Ni fa Mallam na wanke butocina na tura su a Rarkashin gado, don na fara gajiya da wannan auren na zuba ruwa a buta. Kai baka da wani aiki sai na a baka ruwa a buta, don haka rinka yi da na roba kawai ga su nan a bakin famfo suma a wanke suke nayi maza na tashi na fito na ba shi butar da nake amfani da ita, na koma dakina can ciki na zauna. Ina jin ta tana cewa, To, ni in ban da na san in ta kasance a kanka dolensu su bani ciki da falon da nake ciki zan yi wannan susutaccen zaman ne? To dadin abin duk tsiyarsu su din mata ne, mata kuma ba wani Rarfi ne da su ba da dai suna da namiji a cikinsu ne ai da anga tsiya to babu shi." Ranar Laraba da sassafe bayan an idar da sallar Asuba aka daura auren Babana da amaryarshi Safara a Masallacin unguwar su Baba Baidu ne yaje ya karbar mishi auren. Yana dawowa daga daurin auren Baba Sumaye ta rinka rangada guda tana fadin, "Kai, wannan ya da jaruntaka take, to ashe ma tana da irin wannan kokarin ta bar ubanta yayi ta rayuwa a cikin wannan fitinar? Ubangiji ka yi wa Hadiza albarka." 17 Da yake Baba Lantana bata tunanin koma1 game da Babana musamman kuma da yake tasan mu'amalah tayi matukar ja baya tsakaninshi da Baba Baidu balle iyalinshi, bata kawowa ranta komai ba sai kawai ta rinka jan tsaki tana fadin "Munafukan unguwa, ko ina ta samo wata Hadiza kuma oho." Sai tayi maza ta sake jan wani tsakin don ta tsani Baba Sumaye, ta tsani kuma ta jiwo muryarta tana wata magana sai tayi tsaki tayi ashar ko ta ce munafukan unguwa. Tsohuwar aminiyar aminiyarta Delu, ita ce tayi sallama ta shigo gidan, rabon da in ganta kuwa an dan kwana da yawa, ina jin tun lokacin da ta shirya aurena da surukinta Alhaji Muhammadu Nalami, ta gaiyaci tsofaffin abokai don su tayata sheda isowar ta da mallakarta shekaru hudu kenan da suka wuce. Delu ce yau a gidan? Tayi mata tambayar cikin wani irin yanayi na wulakanci da shirin tozartawa, "Kun gama zagaye-zagayen gulmarmakun naku ne kuma ki ka gaji ki ka zo wurina? To ai babu abinda bana ji, duk maganganun da ku ke fada suna dawo min, musamman ma ke. Tunda ke kam ai butuluci ne yake sa ki fadar magana a kaina, ko ma menene a tsakanina da Nalami ai aure ne tsakaninsu da Asabe ga shi nan kuma tana zaune tana ta haihuwa 'ya'yanta. Delu tayi murmushi ta ce, tana ta yawo dai wannan haihuwar tata ta ukun ina ce-a unguwa ta yi ta? Ko menene ba a sani ba? 18 Ita. kam Asabe ai abin tausayi ce ita don kuwa mugun abin ki ne ya shafeta, ni tausayinta nake ji tunda ko jiya tazo wurina." Bakin Baba Lantana ya dan rusuna a dalilin cewar da Delu tayi ko jiya Asabe taje wurin ta watakila taso 1ne yanda ta yanke ta share tsofaffin aminan nata, itama yar tata tayi haka. Delu tayi amfani da damar da ta samu na shirun da Baba Lantana tayi ta ce mata "Kinga ni fa ba fada ma ya kawo ni wurinki ba, zuwa nayi in ji dalilin da yasa hidima irin wannan ta taso miki, ba ki neme mu ba. Cikin natsuwa Baba Lantana ta tambaye ta hidimar me kuma nake yi yanzu in banda ta fama da tsohon mijin da bai iya hassala komai. Delu ta ce, Kai haba bai iya hassala komai aka daura mishi aure? Ko kuwa dai don ya yi aurenne yasa ki ke fadin haka akan shi don ki bata shi? "Aure?" Tayi tambayar a wani irin yanayi, "Wane aure kuma? Wace mata ce zata yarda ta auri Mallam a yanda yake din nan?" Baba Sumaye da ke cikin gidanta tana jiwo hirar tasu, kasancewar a tsakar gida suke, don ko dakinta bata kaita ba,s ai ta takarkare ta rangada wata irin matsiyaciyar guda mai ratsa kunne da jiki. Kafin ta ce "Ubangiji na gode maka, na kuma roke ka ka yi wa Hadiza albarka da ta raba ubanta da wannan musiba da ya dade yana rayuwa a ciki. 19 Kar dai dama da ni wannan matsiyaciyar matar take yi? Aure? Wane irin aure kuma. Mallam zai yi? Wace mata ce zata yarda ta aure shi? Ai kuwa da taci.." Baba Sumaye ta kwashe da dariya tare da fadin Yau fa za a ga hauka tunda an yi wa mahaukaciya kishiya, aiyururururii." Sai ta sake rangada guda.4 Gaba daya Baba Lantana ta birkice, Delu kuwa ta yi maza ta suri takalmanta ta kama hanyar fita, tana fadin Ke ni fa ban san ba ki ji ba da ban zo na gaya miki ba, alhalin maganar take yi fuskarta cike da murmushi alamar bukatarta ta biya. BoBaba Lantana ta kama fadin maganganu tamfar wata zararriya, "To Mallam ma har wani namiji ne da za a yi kishi a kanshi, sullutu a cikin maza, shi in ana kiran maza har zai buda baki ya amsa? Ai karyarsu ta kai karya, ace ya yi mata biyu bai isa ba, Baba Sumayc tayi maza ta ce to na náwa? Wai an tambayi tsuntsuwa sunanshi? Ya ce na nawa? Ta bar wannan ta koma durawa Baba Sumayen ashar, ita kuwa ba ta amsa ba. Tayi ta gaji ta koma kan Babana da ba ya nan zuwanta runfarshi biyu bata samun shi ta dawo tazo ta zauna ta zagi Innata ta hada da Yaya Dija da ni da makwabta ta gaji rushe da kuka ita kadai. Ana cikin haka sai ga Asabe ta shigo gidan, rabe- rabe da 'ya'yanta uku biyu suna biye da ita, daya tana 20 goye ganin uwar tata a yanayin da take ciki yasa ikinta yayi sanyi kiyi hakuri Mama. Tanfar tuna mata zaman nata tayi ta juya kanta da zagi da tsinuwa ba dai kin ce ke wurin makiyana za ki rinka zuwa ba? To ki daina zuwa wurina na yafe musu ke kije can ku karata na bar musu ke. Ta ufe mata ya'ya da duka gaba daya gida ya kaure da koke-koke. A A zuciyata na ce, "Kun gamu da mahaukaciyar Kaka, säi ga Yaya Dijah ta shigo ita da Aminanta, Anti Kubra da Anti Asiya. Nayi zaton zata rufe Yaya Dijah da duka, sai naga ba haka ba, sai da Yaya Dijan ma ta mika mata 'yan kayan da tazo mata da su a matsayin kayan fadin kishiya, shi ne naji ta ce mata je ki ki k2iwa Ramatu kin ji ko ba ki ji ba? Munafukai ke da yar uwarki." Ta ci gaba da zage-zagenta tana watsi da kayan. Ba su ce mata komai ba, sai lekowan da Anti Asiya tayi dakina ta ce min "Ke je ki ki karbo mana kayan cefane a wurin Baba, aiki muka zo yi don yanzu 'yan jere za su iso, na ce mata to. Ban dawo na samu Baba Lantana ba, kofarta a kulle itama Asabe ta tasa 'ya'yanta sun yi gaba sai kawai muka sake a gida muka yi ta hidimarmu, 'yan jere suka iso suka yi ta jerensu, makwabta ma suka yi ta shigowa suna yiwa Yaya Dijah murnar auren da ta yi wa Babanmu, sai hira ake yi ana aikin ana bada labarin haukar Baba Lantana ana kwashewa da dariya. 21 Da yamma yan biki suka tafi, bayan sun gama kintsa komai a kan sai da daddare masu kawo. Amarya za su kawo ta. Suna barin gidan sai kawai naga Baba Lantana ta balle kofar dakinta, ta fito, ashe wai duk abin nan da ake yi tana ciki ta kulle kanta, tana jin duk abinda ake fada. Muna hada ido da ita, ita ce ta ce min "Dukkanku kuma za ku ci ubanku, har da shi uban naku zan ga yanda za a yi ya yi mata biyu a cikin gidannan da ni ku ke yi." Tun kafin Baba Lantana tayi min wannan bayanin a tsorace nake da ita, balle kuma da ta gaya min hakan, ko dama can kuwa mafi girman tsoron nawa ya ii tafiya ne ga tunanin yanda za a yi Babana ya shigo dakin wata mata a gabanta, tana kallonshi, to halle kuma yanzu da tayi maganar da bakinta. Magriba kawai aka idar sai kawai jama'ar amarya suka dawo wai har sun kawo ta, nan da nan gida ya gauraya da kamshi, ba su wani dade ba kuma sai süka watse suka yi tafiyarsu. A ka bar amarya ita kadai a dakinta, nima ina nawaa dakin, ina fama da faduwar gaba saboda tsoron abinda zai faru tsakanin Babana da Baba Lantana in ya shigo gidan nan yau, tunda ta ji maganar ba u yi ido hudu ba. Kan turmi ta fito ta zo ta zauna da damara a kugunta, tana fadin "To duk wani iya shegen mutum ni kam ai kallonshi kawai nake yi, ni kam ai iyaka ce ai ni nafi tsumma lalacewa, yau zanga yanda za a yi 22 Mallam ya zo ya ce min yayi aure a gidannan zai shiga, wani daki, ai sai dai kowacce ta aura mishi ke din taz tayi gadinshi, in har ta matsu sai yayi abinda take so yayin da ke, munafukan banza munafukan wofi." Tana cikin wannan sambatun sai ga shi ya shigo da gyaran muryarshi da ya saba, da kuma sallama. Da sauri ta taso ta tare shi tana fadin Munafuki, na ce maka munafuki. Ina lekensu ta jikin kofa, na ganshi a tsaye yana kallonta, ai babu inda za ka je zan ga yanda za a yi ka ahiga wani wuri ba nawa ba, kai nan ma har wani namiji ne? nayi kamar in tashi in fita in taya Babana, sai kuma naga kai bari dai kawai in zuba ido in yi ta kallo, in har ta bana shi shiga dakin amaryar tashi shi kenan in gari ya waye in taga zata zauna ta zauna, in taga zata tafi ta tafi. Wane dadi ne ya kwaso Baba Lantana? Oho. Sai kawai na ganta tasa hannu biyu ta cukume wuyan rigar Bahana tana fadin "Kai din me? Me kuma aka yi..." Bata gama ba sai kawai naga tanfar an dagata sama ne kafin aka yi firo da ita ta tafi can nesa ta fadi. Mamaki yayi matukar kama ni, na ganin abinda yayin, nan take kuma sai na tuna ai duk iya shegen da Baba Lantanan ta rinka tsulawa a gidanmu bata taba gwada sa hannu ta shake wuyan Babana ba sai yau. Kafin ta taso tuni har ya gyara zaman rigarshi ta daidaita a jikinshi, yayi sallama kofar dakin Amarya ta amsa, ya shige ciki. 23 Ka fito Malam tun muna shaida juna da kai, tun tun muna girma da arziki da kai tun ban shigo nan din na same ka ba. Ta zabura wai zata shiga dakin Amarya, ban san yanda aka yi ba na dai ji Amaryar tana cewa. A'a haba wannan kuma ai neman wuce iyaka ne, koma dai daga can wurin zaman naki kawai in yana son ganin naki zai zo inda ki ke ya same ki." Ke har wata iyaka ce da ke? Ta soma zage-zage sai dai kuma ta kasa shiga dakin ta same shin, ana cikin haka naji an turo kofa an rufe girif an kuma sa sakata an kulle ta ciki. Buga kofar yayi matukar razana Baba Lantana, nan take ta kurma ihu mai karfi, ni kuwa nayi maza nima na sawa tawa kofar sakata, don kar ta fado min dakina, na hau gadona nayi kwanciyata aka barta a tsakar gida ita kadai tana ta faman sambatunta. Washegari kuwa farkawa nayi a dalilin an kwankwasa min kofa saboda makarar da nayi, saboda Baba Lantana bata bar ni na samu natsuwar da nayi bacci da wuri ba, shiga da fita ta rinka yi tana buga kofa kamar zata ballata, ban sani ba ko ni kadai ce kai kawon nata ya hana bacci. Ina bude kofar dakin nawa naga Amarya tsaye da murmushinta ga kamshinta na amarci a tare da ita, kai Yaya Dijah ba karamin ladan Babanmu ta samu ba, abinda zuciyata ta fada kenan sanda na karewa amaryar kallo. 24 Gajiye ce ta saki makara ko? Na tayata 1nurmushin da take yi nin, to in kin idar da sallar sai ki zo, na ce mate to. Ina shaia fatiha na shige dakin nata don kuwa dama na kosa inga Babana in ga yanayin da yake ciki. Yana zaune kan wata shimfidaddiyar darduma, kai da ka ganshi ka san yana cikin farin cikı, an tasa mishi abin karyawa a gabanshi. Na tsuguna na gaishe shi, farin cikinshi a bayyane yake, me ki ke so ki karya da shi? Tayi min tambayar bayan ta gana anmsa gaisuwar da nayi mata. Akwai tea skwai kunu, ge kuma farfesun kayan ciki. Na zuba musu ido ina kallo, can cikin zuciyata kuwa nasan da abinta tazo, ga kuma kayan tsarabar bikinki zan. Na ce, Na gode, a bar min & nan sai Za ni makaranta zan karba in kaiwa 'yar ajinmu. Babana ya ce, "A'a kar6i kici abinli in za ki je makeranta ki diba a nawe." Na ce, To. Hu'un, lalle namiji sai a bar shi, na kuma yarda lalle Mallam ba karamin algungumi ba ac, ashe duk halin naza shima ya iya, ina kallonshi sumu-sumu abin tausayi, ashe ba abin tausayin ba ne, ai inda nasan haka ne da ba karamin gasa shi nayi ba. Ashe dama lafiyarshi kalau? A zuciyata na ce da kin kashe shi dai ba gasawa ba in dai gasewa ne kawai ai dukanmu mun gasu. Ni da kain ba karemin mamakin Babana nayi ba, gaba daya kwanaki ukun nan na dakin Amarya ko rumfarshi ba ye budewa, yana nan a gida a kuma cikin dakinta, 25 yana kishingide akan darduma duk lekawan da zan yi kuma zan hango shi an tasa mishi wani dan abin motsa baki a gaba. In kuma ya fito don yin alwala zuwa Masallaci, sai kaga tana biye da shi tana rike mishi da butar tanfar dai ace gadinshi take yi. A wannan lokacin ba ka iya kwatanta yanayin da Baba Lantana take ciki, in ban da uhun maza? Babu abinda za ka ji ta tana fadi. Namiji? Kai lalle sei a bar su, ashe dai babu wani dan kankani a cikinsu. A haka aka koma dakin Baba Lantana ina daga dakina ina jiwota, "Oh, Mallam ashe lafiyarka kalau ka ke yi min irin wannan abin? Gaba daya ikwanan nan uku ba ka yi fahsi ba ko daya, ina kallonka yau din me ba za ka yi wani motsi ba ne ina yi maka magara kayi shiru ka lullube kai de bergo. Ko kana nufin a kaina ne ba ka da lafiy, amma in a can ne lafiyarka kalau? To i ba zai taba yiwuwa ba, nayi maza nasa yan yatsuna shabbaba na toshe kunnuwana da su don in samu in daina jin maganganun nasu, ko zan samu in yi bacci. Komai na Safara a tsare yake, kullum girkinta yazo zata ba mu lafiyayyan abinci da irin kudin da ake baiwa Baba Lantana tana rainawa, tana kin yin girkin. Ga ta gwanar iya abincin gargajiya ce iri-iri. Su burabusko, su gwate, su dan wake su danbu su gauda su gurasa, su sunasir su wasa-wasa, balle ayi 26 maganar tuwo, sai tayi sati biyu tana girki bata maimaita abinda ta girka ba. Haka nan abin karyawa tuni muka daina sanmakon fito nemanshi, ganin da tayi inä ita nemo mane ranar girkin Baba Lantana, yasa ta kirani ta ce min rinka zuwa nan kullum da safe muna karyawa kin ji, shi dai da ya ajiyeta ranar girkin nata su san wanda suke ciki, na ce mata to. Baba Lantana ta tsunduma. cikin wani irin abu.da bata taba zaton zata tsunduma cikinshi ba, a zamanta da Babara, ga kishiya te kwatsam wacce kuma ta haife ta ga shi tasa hannu ta kalallame shi, in ban da Beban nawa ba dan gayu ba ne, don su wanka da shafa man nan da duk sai tayi mishi, to ba zai yaria ba. Ga ehi tana ganin wadansı irin al'amura a wurinshi wadsnda bata taba tsammanin yana da su ba, sai ta zama kemar wata zareriya, babu abinda take so irin ta samu abokin hirar da zata yi zance da shi don ta rage damuvarta babu. Saboda babu mai zuwa wur inta duk ta kore su sanda ta samu daular gidan miji ita kuwa Amarya sai kai-kawo take yi da 'yan uwa da abokan zama, dan muguntan da take yi mana na kin yin girki muyi takai kawon neman abinda zamu ci yanzu duk ta kau. Ko kadan Safara bata kallon abincinta in ta gama ta ce su zo su ci ta ce to, tunda tare suke ci in bata gama ba ma oho. Za ta ci wani abu nima zata ba ni. 27 Bakin ciki ne ya ishi Baba Lantana, taga kamar in ta tayar da wuta zata iya korar Amaryar nan saboda taga komai take yi ba ta ce mata komai. Ta karbi kudin cefane ta ki yin. girki, ko taga shanyarta a igiya ta zube. Rannan an tashi da safe naji Anti Safaran na cewa Yaya ina kwana? Ko dama a lalace take amsa raata gaisuwar, amma bata daina ba. Yaya ina kwana? Ta sake maimaitawa, sai naji ta ce mata, ke raba ni da wani yaya, yayan mnunafurci, ki kira ni yaya a bayan idona kina yi min munafurci, rike yayarki bana so tunda ai ni ban ma ga wani abinda na girme ki da shi ba. Ta ce, To kiyi hakuri. Taja bakinta tayi sbiru bata. kiranta Yayan oa ta kuma kian sunanta, ana cikia haka ta sake cewa kicin nata ne a ranar girkitita bata yarda wani ya shiga ba. Nan ma ta ce, To sai ta fito de risho dinta in zata dan yi wani abu ta tura a baya kofarta tayi. Ba a gama da wannan ba sai kuma ta fito da wani salon in Safara ta gama abinci ta kawo ta kira ta ba za ta ce ba za ta ci ba, sai ta dauko kujerarta tazo ta zauna tasa hannu ta gutsuri lomar tuwon ta kai bakinta, sai ta fara tauna shi. Sai tayi wuf ta dawo da shi ta tofar tare da fadin, kai tir, wannan tuwon ai danye ne ke ba ki iya komai ba ne a tayuwarki sai jarabar bin miji? Ba ta ce mata. komai ba, rannan dai sai ta gaji ta ce mata da dai kin 28 daina irin wannan abin, tunda kema kin san baida amfani, shi hatsi ai be a yi mishi haka. Sai kuwa Baba Lantana ta zabura ta sake gutsurar weci lcmen te ka: bakinte, tayi mishi tauna daya te maido shi kan asalin tuwon da ke cikin kwanon wanda ite take ci, anyi din an yi wa hatsin rama mishi. Haka kawai sai ki rinka yiwa mutane danyen abinci kice sai an ci dole? To an yi an kuma karawa. Ta sake gutsura ta kai baki ta sake mayarwa cikin kwanon, ina daga dakina ina jin su ban san yanda aka yi ba sai kawai naji an kaure da dambe. Dambe kuwa ra gaske, tunda dukkansu karfafa ne, ko motsi ban yi ba balle in yi tunanin raba su, sai kawai raga an daga Baba Lantana an nanata da kasa, Safara ta haye kan ruwan cikinta tayi ta kirbar bakinta da duka, da ta ga hakan ma bai yi mata ba, sai ta shaketa her sai da wuya ta sa ia bude baki tayi maza ta kwaso gwajaljelon tuwon da ta tauna ta mayar te warba mata shi a baki ta matse bakin sai da ta hadiyo shi. Sannan ta saketa ta mike tayi tafiyarta tare da fadin "Haba, ina amfanin babban da bai san ciwon kansi ba? Ina kyale ki ba ki san kyale ki nake yi ba, to mu zuba shege ka fasa ni da ke." Da daddare Babana ya dawo, ta zaunar da shi ta rattaba mishi bayani, kala bai ce mata ba. Ta sake tunzura zata tasa shi a gaba da masifa, ya fito yazo yayi shimfida a tsakar gida yayi kwanciyarshi, duk da 29 sanyin da ake yi bai tashi ba sai da lokacin zuwa Masallacin shi yayi. Wannan zaman ai' ba dole ba ne, kai Mallam ai dama ba mijin mata biyu ba ne, muturmin da baya iya buda baki yayi magana yaya za ayi ya iya ajiye mata biyu? Kullum balki a rufe kamar na mai ciwon bubu. Gara kawai ka sauwake min ka sake ni ka ji ui ko ba ka ji ni ba? Bai kulata ba, ta gaji da fadan ita kadai ta shiga dakinta ta kama fitar da kaya, ai na ce na daina wannan matsiyacin auren, yau na daina shi ko ka bani takarda ko kar ka ba ni tafiyata zan yi. ina ganin ta gama kwashe kayanta ta tafi na shiga dakin na share yana, na share dattin dakiu tas na ce wa Anti Safara bari in taya ki ki kwashe kayanki ki koma can, da sauri ta ce min au haba? Na ce mata eh. Nan da nan muka bar komai muka koma aikin jidan kayanta muka maida su dakin Innata, dakin da nake ganin kamar babu vani daki da zan so kamar shi, muka gyara komai yayi tsaf gwanin kyau. Gidanmu yayi matukar yin dadi, Anti Safara tayi ta tattalinmu ni da Babana, har ma da Sallau. Sai dai sh1 kam bai iya zama ba, yana ganin Baba Lantana ta kwana biyu bata dawo ba, sai yayi wa Babana sallama. ya tafi sai dai bai fadi inda za shin ba. 'Yan kwanaki kadan da auran Babana, kwanakin da ko talatin ba su cika ba, sai ga Babana har ya yi kyau, yayi fes da shi in muna zaune mu biyu kuwa zai 30 dar rage murya ya ce min, "Oh, ashe lafiyayyar yarinya ku ka samar min? Ubangiji dai ya jikan Ramatu da rahamarse. In ce mishi amin. Randa Baba Lantana ta cika sati biyu da tafiya, raear Yaya Dijah tazo mana wuni da ita da ya'yanta duka, dama dan da Anti Safaran ta yaye Nasiru, rabon Yaya Dijah da yin irin wannan zuwan ni dai na manta. Babana ya wuni cikin farin ciki yana ta ina yaka saka da jikokinshi, itama Anti Safaran haka. Sai wajen. yamma ta shirya zata tafi, ya yi tayi mata addu'a yana sa maia albarka, ita zuciyarta gaba daya ko daga ji kuma kasan har da jin dadin abinda tayi mishi. Da zata tafi sai naji ta ce min ga dan hira nan na kawo miki, ya taya ki zama nayi maza na ce mata to na kama hannunshi na riks nayi mata rakiya muka dawo tarc da shi. Mu'amalla ce sosai tsakanina da Safara, duk da ta same ni a shekaruna na budurci sosai wanda a lokacinmu ma ba a cika samun 'yanmata masu shekaru irin nawan ba in dai ba a gidajen da 'ya'yansu ke karatu sosai ba. Amma hakan bai sa tayi wasa da kulawa da al'emurana dan kankanin canji in ta gani a tare da ni zata tsaya taga ta warware min shi. Haka nan sai aiki ya mana keza gyara abu kaza kar kiyi kaza, kaza da ki ke yi ki daina babu kyau. Abinda na tabbatar shi ne da ita ce ta zauna da ni a shekaruna na kuruciya, to da tarbiya sosai tayi min, n kuma zan fita to bai zamo meta komai ba in ce mata za ni 31 wuri kaza ta ce min kai a'a kina yawan fita ba dab1' ar budurwa mai mutunci ba ne yin hakan. Sai dai in makaranta za ni, in kuwa za ni Makarantar to ko ina da kudina tunda ina sana'ata tana gani zata kawo kudi ta ce min ungo ki kara, in yi mata godiya. A haka sai gidan namu ya sake zama wani wuri mai cike da ni'ima zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali ga kuma girmama na gaba, tana girmama Babana nima ina girmamata, tan kyautata min nima ina kula mata da danta. Gaba daya sai muka zamo muna son junanmu sosai. Rannan aka wayi gari Safara tana yin mashasshara da mura, ban kai gane kan kornei ba saboda ban taba kawowa raina cewar wani abu zai iya faruwa ba, na dai ga Babana yana ta kaiwa da kawowa cikin wani iri yaneyi na tsananin farin ciki, bai isya zama a runfarshi ya wuni kamar yanda ya saba, sai ya dawo gida dubata. Wani lokaci sau daya wani ma ahr sau biyu in zai shigo kuma bai shigowa hannu haka sai yazo oa wasi abinda zai miko min ya ce "Karbi ki wanke muku." in ce mishi To. In wanke in kawo mata ita kuma sai ta ce mun to dibi naki mana, in ce mata to in diba ta ce min kara in naga zan kara in Kara in kuwa ya ishe ni in ce ya ishe ni. Anti Safara da kanta ne ta gaji ta ce min ciki ne da ita saboda Iuran da tayi ta gane ban gane ba, mamaki gami da farin ciki suka taran mun, har ta gane abinda nake ciki. Mamakin me ki ke yi haka? Kin yi zaton ba zai kara haihuwa ba ne? Na ce, "Eh, to ai na gane kamar ya girma." 32 la sake wani murmushin tare da fadin "Don ya haifi Hadiza sai ya tsufa ko kuwa dai dun kin ji matarshi tana yi mishi sharin bai tabuka komai? Shira nayi ban yi magana ba, don kuwa naga kamar ta wuce sanina. sNa dai san kawai ba karamin farin ciki nayi ba, saboda ganin da nayi nima zan samu kani ko kanwa, in musu nima irin abinda Yaya Dijah take yi min na kulawa da tausayawa. Muna cikin wannan halin sai ga Baba Lantana tana shigowa da kayanta kwararam-kwararam tana ajiye su a tsakar gida, tana komawa tana shigowa da wasu. Ta rame tayi baki tanfar wacce ta tashi daga jinya mai tsanani. Yaya haka kuma naga an shigar min claki? Wannan wane irin neman magana ne? ba sakina aka yi ba, ba komai ba sai kuma kawai daga na fita da kayana ayi maza a shige nin daki? Ke Yachuwuna kina ganin irin wannan neman maganan ko? Nayi maza na kalleta a firgice na soma gaisheta cikin wani irin yanayi saboda rashin sabo da yin magana da ita. Babana ya fito daga dakin Safara ya wuce zai fita bai kulata ba ta bishi da kallo, Mallam kana gani na dawo ba za ka kula i ba? shiru yayi yana tafiyarshi, tayi maza ta sake ce mishi to kayi mata magana ta fita daga dakina ta bani wuri in sa kayana don kar hakan ya zama wata fitina a tsakaninmu. Bai tanka ba yayi ticewarshi ya tafi, bain ciki ya kama ta ta ce "Wannan shirnu na Mallam, wannan shiru na Mallam ashe ba zai daina ba?" Ta jinjina kai ta rasa abinda zata ce. A zuciyata na ee, da dai kin san abinda 33 zai faru kenan da ba ki yi mishi abinda ki ka yi mishin ba. Baba Lantana taja ta tsaya cikin wani irin yanayi na rashin sanin abin yi, da dai ba su taba gwada yar kashi da Safara ba, da tayi wani yunkuri. To babu hali, tana shakka gashi kuma Safara sai kai kawo take yi ko kallon inda take kuma bata yi ba, balle ta tanka mata. Ta gaji da tsayuwa tayi kamar ta kwashe kayan nata ta koma inda ta fito, ban san kuma me ta tuna ba. Sai naga ta bude wancan dakin tasa kayan nata a ciki. Ta gyara tayi zamanta. Tsoro yayi matukar kama ni, ko me yasa Baba Lantana tayi irin wannan canzawar? Mace ce mai fadin rai, nuna isa da ganin kowa ma bai isa ba, wani abu taje ta gano ya sa ta tayi wannan canzawar ko lkuwa dai wani abin take shiryawa? Na gama abincin daren' da nayi don tun zuwan Anti Safara mafi yawancin girkinta ni take sawa in yi, to balle kuma yanzu da take fama da laulayin cikinta. Ina gamawa na zubawa kowa har ds Babs Lantanan na kai mata nata na yiwa Babana shimfidar tabarma a tsakar gida inda ya saba zama, na ajiye mishi nashi a nan. Yana dawowa daga Masallaci ya shiga wurin Anti Safara yayi mata sannu da jiki, ya dawo ya hau kan tabarmarshi ya zauna ya soma cin abincinshi. Baba Lantana ta fito tazo daga bakin kofarta tana yi mishi magana, bai ce mata komai ba. To ka shiga daga ciki mana Mallam, wannan hirar da ka ke yi a waje ai ya wuce ka'ida." 34 Bai ce mata kala bá, har bacci ya dauke ni suna nan a wurin shi yana kan tabirma a zaune, ya jingina da jikin bango, ita kuma tana daga bakin kofarta. Ban san yanda aka yi ba, cikin dare ne kawai na farka a dalilin buga minkofar dakina da take yi da iyakacin karfintai tana gaya min wai in fito in ga abinda Babana yakeyi, girkinta ne amma gashi nan ya sake ta ya shige dakin wannan tsinanniyar matar yana yin abinda babu kyau. Duk da katse min baccin da tayi ta kuma hana ni sake runtsawa saboda buga min kofar da taki dainawa ban motsa ba, balle in yi yunkurin saukówa daga gadon nawa in fito. Ban saniba ko ta gane ba zan fito ba ne yasa ta bar tawa kofar ta koma buga tasu, a zuciyata na ce dama tuntuni hakan kikayi da yafi miki. Girki nane fa Mallam, yau a wurina fa kake, nan take ta soma kuka tana fadin "Ban yafe maka ba Mallam. Bazan yafe maka satan kwanan da kayi min kaje wurinta ba. Ban taba ji ko ganin Baba Lantana tana kuka ba a zaman da nayi da ita ba sai rannan, kuka kuma bana wasa ba, ko da yake babu wata kyakkyawar alaka ko wata kauna sa ke tsakanina da Baba Lantana. Amma kuma hakan bai sa naji dadin yansa Baban nawa yayi ba duk da dai itama bata taba yiwa wani adalci ba, a lokacin da ta samu damarta. Gari na wayewa nayi maza na gama abinda zan yi na suri jakata na saba a kafada na fita gidan na bar Baba Lantana a tsakar gida a tsaye rike da shirgegiyar tabarya 35 a hannunta, tana rantsuwar sai dai in ba za su fito ba, amma sai ta rafke su da tabaryar hannun nata. Na wuce na tati makarantar da nake zuwa TP, wato (Teaching Practice) saboda gab nake da kammala karatuna a Makarantar addini mai zurfi. A hanyata ta dawowa gida zuciyata tunani take yi kan yanda ta kare tsakanin Baba Lantana da su Babana. Ina isa gida ban san yanda aka yi ba sai kuma naga Baba Lantana da na bari da tabarya a hannu da kulu a goshi, ban tambayi Safara yanda aka yi ba, to balle kuma Baba Lantana da ban ma iya yin wata magana da ita ba. "Kin dawo ne?" Na ce mata "Eh." "To ga fura nan da nama Babanki ya aike da shi, na diban mii, nace to sannu. A zuciyata nace ko ba komai dai yanzu ina da kaso a abinda Babana yake kawowa. Na gama cin naman ina shan furar sai ga Baba Lantana ta fado cikin dakin nawa, nayi maza na mike tsaye saboda tsoratar da nayi, tunda ban taba ganin ta shigo dakin nawa ba. Ban sani ba ko itama ta gane tsoratar da nayi da itan ne yasa ta fara yi min bayanin avinda ya kawo tan cikin sauri kinga kulun goshin nan nawa ko?" Na daga ido na kalli kulun goshin nata da take tabawa da hannunta, kan in ce mata na gani sai kawai naji ta ce min, To Mallam ne yayi min shi. Nayi maza na sake kallon kulun saboda razanar da nayi da jin bayanin nata, kulun ya amsa sunan kulun ban san yanda aka yi ba naji bakina ya ce mata sannu, tayi maza ta ce yauwa. 36 A tsakanin wannan lokacin ba sai an gaya min ba, ni da kaina nasan Baba Lantana tara cikin wani halinba tsananin bacin rai kowane lokaci a cikin kuka take. Ashe haka Mallam yake? Tafdijam! Ashe shiru- shirun nan na shi ba na kalau ba ne? dama fa nasha jin ana cewa ka ji tsoron mai shiru-shiru, ban taba yarda ba sai a wannan lokacin, yanzu ne na gane lale Mallam munafuki ne. Ko kadan bana jin tausayin Baba Lantana, saboda azabtarwar da tayi mana ni da Bbana, ta wulakantamu ta tozarta mu, gara ma ni komai tayi min da sauki tunda a kuruciyata tayi min, amma shi Babana ta same shi ae da girmanshi da mutuncin shi a tsakanin mutanen unguwa. Kowa ya 1a girmnamasbi saboda ya kame kanshi bai shiga harkar kowa, bai sa ido kan abinda wani yake yi, balle ya yi gaba ya bada labari. Bai sa ido kan abin wani ya gamsu da abinda yake da shi amma zuwan Baba Lantana gidanmu sai da ta maida shi abin kwatancen mutane. Komai aka yi sai ka ji sun co kai haba, kar ka maida mu Mallam Habu mai anatir Mana, to amma duk da haka ba na jir dadin ganin yanda yake yi na hanata kwananta da yake yi yana barinta tana kwana ihu tunda a karatun da ake yi mana Malamai suna yin bayani kan rabon kwana a tsakanin mata wajibi ne abinda kayi a can ne bai zamo lalle sai kayi shi a nan ba. Amma akaiwa mace kwanan wannen dole ne, to shi Babana baya kaiwa. Da dai ace ina cikin masu baiwa Babana shawara, to da nace mishi cikin biyu ya zabi daya. 37 Ya yi ko dai ya rinka shiga dalkin Baba Lantana yana kwana tunda dai zaman aurenshi take yi ko kuma ya ce mata ta tafi. Ya sake ta don ya sauwakewa kanshi al amura. Sanin da nayi hakan da ake yi bai yi ba, ya sa ni tafiya gidan Yaya Dijah nayi mata bayani, a yatsine ta kalle ni to ke ina ruwanki? Inta ji babu dadi ta tafi mana. Na ce, A'a Yaya Dijah, ai ba don ita nake maganar ba, nayi mata gwargwadon bayanin da zan yi mata, ta ce to naji in na zo gidan zan yi magana da ma ina so in zo wurin Baban na ce mata ko na kama hanya na dawo gida. Yaya Dijah ba ta zo gida ba sai a ranar Laraba da safe, muna zaune a falon Anti Safara inda nan ne wurin zaman Babana a kowane lokaci. Hira muke yi cikin yanayi na jin dadi ni da shi da Yaya Dijah, yayin da Anti Safara ke kicin tana shirya abincin rana, ita kuwa Baba Lantana da yanzu ko tsakar gida bata cika fitowa ba take dakinta. "Oh Baba, yanzu har a irin alherin nan da yake shirin samunmu na Mero ma zata samu kani a bayanta zamu sake samun dan uwa ke 'yar uwa, maimakon mu biyu ko mu koma mu uku ba za ka yi hakuri ka gaya.mana inda danginka suke ba? Ba don mu kadai ba Baba ba ma don mu ba tunda mu kam ni da Mairo ai mun riga mun mallaki hankulanmu, mun fuskanci rayuwa mun kuma fara gane yanda take ba, komai dan Adam yake so yake samu ba. Don wadannan da za su zo daga baya Baba gaya mana inda danginka da garinmu yake in wani laifi suka 38 yi maka i Hadiza yarica na roke ka ka yafe musu ta kai menene? Ai ya wuce Baba kayi hakuri ka... Tayi maza tayi dib taja balkinta tayi shiru ta bar Karasa maganar watakila sai lokacinne ta daga ido ta kalli yanayin da ke fuskarshi wanda ni tunda ta fara maganar nasa na gani shi yasa nayi ta taba ta bata gane abinda nake nufi ba. Ta tashi ta bar dakin saboda daurewar fiaskar tashi, ta kai matuka nima na tashi na biyo ta muka dawo dakina muka zauna tayi kuka har a gaji tnyi shir ta iar hawayenta. Kwana biyu bayan nan Anti Safara take bani abarin cewar Babana ba lafsya te da shi ba, kartin hali ne kawa yake yi yasa ake ganinshi yana yawo. Na ce, To. A zuciyata dai fatana da addu'ata bai wuce ya zamo ba maganar da Yaya Dijah tayi mishi ba ne yake nema ya tayar mishi da jikin. Na rasa yanda zaa yi in fuskance shi da maganar rashin lafiyar tashi, saboda tun daga. ranar da na raka Yaya Dijah tayi mishi wannan maganar fuskarshi daure take. A zuciyata na kudurawa Kaina ba zan sake yarda Yaya Dijah ta ce min za ta yi mishi irin wanan maganar in bar ta ba, tunda baya so, shi kenan a kyale shi, yan uwanshi shi yasan abinda ke tsakaninsu. Abunda ya fi komai muhimmanci wurin da uba ne, tunda shi ne asali to mun gode tunda muna da shi kowa yasan muna da shi mun kuma san shi, mun rayu tare da shi, babu wanda zai yi mana gorin rashin uba, sai na rashin 'yan uwan uba. 39 Wasu suna nan su ba su ma san ubannin nasu ba balle suyi maganar danginshi suna nan kila a dadin su ma kuma suna rayuwarsu don haka na hakura itama zan gaya mata ta hakura suma yan bayan in sun hakura kamar yanda suka same mu mu ma akan hakurin. Rannan da daddare Anti Safara ta buga min kofa gabana yayi mummunan yankewa don kuwa na tabbatar jikin Babana ne yayi tsanani yasa aka tashe ni tunda tun da rana ina kallon iin wahalar da yake yi akan lai kawon numfashinshi da bai karasawa ya sauka cikn ciki sai dai a Kirji. Babu yanda Yaya Dijah da naje na kirawo a dalilin jikin nashi bata yi da shi ba akan muje asibiti ya ki yarda. Da sauri na 6alle kofar na fito na ufi dakin Anti Safara da ke bude a kasa, na samu Babana na zaune a cikin yanayin rauni mai yawa. Ko zama da kyau bai iyawa saboda ya riga ya rasa karfi a tare da shi, numfashi sai kaiwa da kawowa yake yi a tsakanin kirjinshi da makogoronshi. "Sannu Mallam, Ubangiji ya baka lafiya." Tana sannun tana share mishi hawayen da ke diga daga goshinshi, tana kuma kuka. Jikina ya dauki bari saboda yanda al'amarin ya tuna min da yanda naga Innata a daren da zata bar duniya. Da gudu na juya na bude kofa na bar gida. Nufina wai in je gidan Yaya Dijah in kirata tazo ta taya ni ganin abinda Babana yake yi, sai kawai muka yi kicibis da Isiyaku. Ban san daga ina yake ba,a wannan tsohon d aren ina za ki haka Anti? Me ya same ki ki ke kuka haka? Ban 40 iya ba shi amsa ba jikin Baba ne ya tashi? Nayi maza nace mishi "Eh" To ina zaki yanzu sha biyu saura kwata ne fa na dare. In asibiti kike so a kai shi ga makwabta." Lolkacin nena tuna ashe ma Baba Baidu ya kamata in fara gayawa ba wani ba, balle Yaya Dijah da ba ma kusa muke ba, tunda ance makwabcinka na kusa shi ne mutum na farko da ya Kamata ya taimake ka, in har ka shiga halin bukatar taimako. Tare da shi muka je na fara buga kofar gidan Baba Baidu, sai da ya ji ya bude kofar dakinshi zai fito sannan ya ce min, Bari in nemo mana motar da za ta kai mu. Na ce mishi "To, Isyaku na gode." Tamfar dai ba shi ne Isiyaku da na share ba na ko amsa gaisuwarshi ba. Ina tsaye a tsakar gida bayan na shiga dakina nayi shiru na debo duk kudin da nake da su, kuka mai yawa nake yi saboda yanda nake jin Babana yana magana cikin jarumtaka da kyar da kyar. Amanata yake baiwa Baba Baidu da matarshi, ni Mero sa shiga uku zan rasa uba mahaifi kamar yanda na rasa mehaifiyata yau ya ya zan yi? Gare ka nake bauta Allah, gare ka nake neman taimako ya Ubangiji, abinda kawai nake ta nanatawa kenan. Ana cikin hakan naji zuciyata tana zargina da cewar ni da Yaya Dijah muka fara haddasa mishi ciwon nashi da muka tasa shi a gaba muka yi mishi maganar da baya so. Ina yin wannan tunanin na sake rushewa da wani sabon kukan na nadama da bakin ciki. Isyaku ya shigo da sauri. 41 Ga mota Anti na samo." Ya wuce cikin dakin ya gaya musu. Babana bai iya takowa da Rafafunshi ya fito ba saboda karfi ya tafi sai da aka rirriko shi aka fito da shi muna isa asibiti aka ba mu gado. Dama kuma shi kwastoman asibitin ne, fayil dinshi aka dauko aka dora bayani akan wanda yake ciki. Mun kwana muk wuni a asibiti babu alama na samun sauki a tare da Babana, hankalinmu ya kai matuka wajen tashi, bar gara nima akan Yaya Dija. In ban da kuka babu abinda take yi, ni na tayar mishi da ciwon. Na ce, A'a Yaya Dijah, dama bai da wata lafiya, ba ki ji bayanin da Anti Safara take fada ba, na cewar ya dade ba ya bacci da daddare. A'a amna ai bai tsananta ba sai bayan da nayi mishi maganar duk kalaman da nake gayawa Yaya Dijah bai sa ta samu na suwa a tare da ita ba. Likitoci ne suka yi ta zuwa duba jikin Babana, kusan duk wanda yazo duba shin kume ya kar tafi ne a yanayi na tausayawa da fadin kai lalle Mallara Habu yana jin jiki, Ubangiii yasa kaffara ne. Wai kuma a wannan lokacin ne da ake cikin wannan al'ama rin naji Baba Lantana tana yiwa wata mata da in banda a zuwanmu asibiti ban yi zaton ta taba ganinta ba tadin Baban da al'amarinsu. Ai ni don dai kar a ce ban zo ba ne kawai amma 1n ba haka ba ai ko mutuwa yayi bani da wata asara mutumin da yake daukan girkinka yana kaiwa kishiyarka kana ji kana gani ba ka da yanda za ka yi. Yaje yana yin abin nan da ita. Ni kam ai alhakina ne ya kama shi yanzu ba sai suje suyi ba in gani? Kin ga tun 42 kafin yayi auren nashi sai ya yi wata biyu wata ku ba kula ni ba, a hakan... Ganina da suka yi ya katse hirar tasu ganin da nayi in sallami Baba Lantana in ce ta koma gida ita kadai ba zai zamo mai sauki ba, zai kuma kara bayyanar da rashin adalcinmu mu da Babanmu da ke fama da kanshi. Wanda ita take kokarin baiyanawa koya ya zama sheda akai, bisa haka sai na hada ta ita da Anti Safara nayi musu magana akan su koma gida wanda da kyar suka yarda hakan. In na tsaya cewa mun shiga wani hali ni da Yaya Dijah dama duk wani, wanda yake tare da mu a tausayawa to na tsaya bata bakina kawai nake yi. Ina zaune kan kujerar roba ina tashe da Babana bayan tafiyar Yaya Dijah da mijinta, in banda kuka babu abinda nake yi na roke ka ka yafe min abinda nayi maka. Baba abinda kawai nake iya fadi kenan ban ji lokacin da ya shigo ba saboda shagalar da nayi da abinda ke gabana sai ganinshi kawai nayi a tsaya ta daya gefen kusa da Babana. A daga ido na kalle shi Mubarak ne yana cikin natsuwa mai yawa yanayin da ke fuskarshi ce ta kara bayyanar da hakan. "Ubangiji ya baka lafiya Baba, yasa kaffara ce. Shi ciwo ai rangwame ne, domin kaffara ce ga zunubai sannan jikin naka ma da sauki ba haka nayi zaton ganinka ba." Babana ya dan daga ido ya kalle shi saboda jin kalamin nashi, ya sake yi mishi sannu kafin ya sake 43 daidaita tsayuwarshi, ya karanto addu'ar da ake yi wa mara lafiya. Kafin yayi mishi sallama ya juya da nufin tafiya. To zo mana, ban iya yi mishi musu ba duk da mun dade kwarai ba mu ga juna ba ban da haka ma mun dade da fita hanyar juna. Tun bayan abind ya faru a tsakaninmu, sai muka shiga kiyayyar juna, ai ba nisa za ki yi ba, ya gaya min hakan don kara karfafa min in zo din. Ke haka ake yin jinya ne? Nayi maza na kalle shi don in ji ta inda kuskuren nawa yake in gyara, kin tasa shi a gaba sai kuka ki ke yi, kina rokonshi gafara? To a kan me ki ke yin hakan, ki, Rara kashe mishi jiki ko ki kara-tsoratar da shi, ki karya mishi zuciya? Shi majinyaci karafa shi ake yi da kalamai na karfafa zuciya, ba yi tayi mishi kuka ba, shi ciwo ma da ki ke ganinshi be shi ne mutuwa ba fa. An yi yafi a kirga mai laifiya ya mutu ya bar mara lafiya a kwance, kin gane? Nayi maza nace mishi eh. Yanzu ke menene damuwarki da ki ke wannan kukan? Ban iya boye mishi ba ko in ce zanja mishi aji saboda halin da nake ciki, sai kawai na gaya mishi Babana bai da lafiya. Gashi an kawo mu wurin da kowa ya zo ya ganmu sai ya ce uh' uh hh lalle Mallam Habu yana jin jikı, a dakin da yake din ma na gobe da nisa ne kusan kullum sai an yi mutuwa a dakin dazu ma an yi wata mutuwar. A hankali ya ce min, to kiyi hakuri ba ni in yi magana a canza muku dakin a kaiku inda za ki dan samu natsuwa shima Baban ya samu kulawa ta musanmman. 44 Koma wajen shi ina zuwa, ban ce mishi komai ba na tashi na tafi na dawo na samu Babana a yanayi na canji. Nan take na tuna da addu'ar da Mubarak yayi mishi wacce na taba ganin bayanin da Manzon rahama yayi a kanta cewar duk sanda mai duba mara lafiya ya karantawa mara lafiya ita, Ubangiji zai saukar mishi da wani rangwame a halin da yake ciki, ko da kuwa cutar ta ajali ce. Nayi maza na matsa kusa da shi. "Sannu Baba." Ya amsa a hankali "Sannu Yachuwuna, kina ta wahala da ni, Ubangiji ya yi muku albarka." Na dauko kofi na tsiyayo kunun gyada na zauna kusa da shi ina gauraya kunun da cokali don ya yi sanyi. "Bari in kurkure maka baki ka dan sha kunu Baba, ka dade ba ka ci komai ba." Ya dan sha kunun kadan kafin ya daina kar6a nima na kyale shi ban matsa ba tunda dai ya dan sha Na gyara zama a kan kujerar da nake zama tare da jingina a jikin gadon nashi ban san yanda aka yi ba, sai ji kawai nayi ana ta shina. Nayi maza na bude idona da gaske ashe bacci nayi, ga dukkan alamu kuma yayi nauyi, don na dan ji canji a tare da ni. Na kalli Nos din da ta tashenin bisa zaton ko lokacin shan maganinshi ne yazo, sai naji ta ce min "Bari mu canza muku dakin ko?" Nayi maza na kalleta duk da bayanin da Mubarak yayi min akan canjin dakin ban dauka da sauri ne haka ba. 45 Yayanki ya ce a maida sBaba privater ward. " Na ce mata To. Aka dauke mu aka maida mu private ward. Mu kadai nea wurinbga tsafta ga kulawai ta musamman sai dai maimakon saukin das Babana ya dan samu ya dore sai kuma jikinya: kara táshi, kasancewar likitoci baba tsinkewa a wurin sai sukal yi ta: kai kawo suna bincike kan oalanarine nashi, ina daga gefe ina kallonsu cikin natsuwa yayin da zuciyata take ta faman karanto addu'o'i iri-iri, kafin gari yawaye har an canza mishi magungunan da yake sha gaba daya. Ganin haka ne ya sani matsawa kusa da shi sosai lokacin da wani lokaci ya sake shigowa don duba yanayin jikin nashi da safe, sanmu da aiki doctor. Ya juyo ya kalleni, yauwa sannu ko? Ya ya jikin nashi? Na yi màza nace da sauki, yanayin da na gani a tare da shi ya karamin kumarin yi mishi tambayar da nake son yi mishi, Dr. An ganw wani abu ne a tare da shi da yasa aka canza mishi magu agunan nan? Sai dai ya daga ido ya kalleni kafin ya maida kallonshi ga aune-aunen da yake yi, mara lafiyan mene ne dinki? Na yi maza na ce mishi, babana ne mahaifi, to me za ki yi in kin sani? A hankali na ce babu komai, nayi shiru ban sake ce mishi komai ba, ya ci gaba da abinda yake yi har sai da ya gama zai fita sai ya sake kallona ya ce min, me sunanki, na ce mishi Maryam, har ya yi kamar zai juya ya tafi sai naji ya ce min, menene aikin zuciya a jiki? Cikin nutsuwa na ce mishi harba jini zuwa sassan jiki, to daya ko biyu daga cikin jijiyoyin da sukeyi mishi wannan aikin ne ya samu matsala. Jikina ya yi sanyi sosai da jin bayanin nashi amma da yace min kin gane? Sai na yi karfin halin ce 46 mishi eh kamar in sake yi mishi wata tambayar sai naga to kar ya ce na dameshi don halka na hakura nace mishi, na gode, ban san tunanin da ya yi ba wanda ya sashi ci gaba da yi min bayani, bangaren hagu na zuciyarshi ne ta samu matsala har ya dan kumbura kadan saboda jjiyoyin wurin basa aiki sosai shi yasa numfashi yake yi mishi wahala. Bayanin da ya yi min ya sani tambayar shi, to yanzzu menene abin yi Dr? Za mu yi mishi ailki nę mu gyara Jjiyoyin.... bai gama yi min bayanin ba sai ga Mubarak ya shigo duk da sanin likita. ne ko kallonshi ban yi ba balle ya ce bari ya gaisheshi na juyo da kallona gareshi da nufi gaisheshi saboda mutuncin da nalke ganin yayi min na kulawar da nake -ganin ya nuna a kan rashin lafiyar babana, wani irin lalataccen kallo naga ya yi min, jkina ya kara yin sanyi cikin zuciyata ina tunanin laifin me nayi mishi, sai kawai na ji ya ce min, shi. ma wannan din saurayinki ne? Gabana ya yi mummunan faduwa nan take kuma na ji mummunan bacin rai a zuciyata, wacce irin mummunan magana ce wannan, ina fama da jikin babana ya kalleni ya ce, wai ina samartakan, me ya maidani? Nayimaza na kawar da maganar tashi daga cikin zuciyata na dai kudunawa raina kamewa in daure mishi fuska sosai watakila don yaga na dan sakar mishi ne yasa yake so ya yi min wulakanci irin wanda ya saba. Yaya Ibrahim ya iso tare da yaya Dija kamar yanda suka saba yi kullum ta zo ta tayani mu yi mishi abinda ya dace sai su tafi sai lkuma ta gama abinda zatayi sai ta zo mana da abincin rana daga gida kuma Anti Safana take zuwa mana da kunun gyada da baba yake sha sai da 47 daddare Yakumbo Halima ta kawo mana abincin dare ita kam baba Lantana ko tazo da wani abu bana yarda ta baiwa babana saboda na riga na jita tana fadin alhakinta ne ya kamashi banda wannan ma na ji ta tana fadin' ko ya mutu bata da asara, ashe Alhajit Mubarak ya zo? Nayi shiru ban amsa mata ba to me ya sa kika yarda yad awo da mu nan? Ban tsaya yi mata wani bayani ba na ce mata ki yi hakuri mu ne zamu biya, bata sake yin maganar ba sai ta tambayeni, to yaya kuka kwana da jikin nashi? Ban boye mata ba sai nayi mata gaba daya bayanin da likita ya yi min, dama ana yin irin wannan aikin ne? Ta yi min tambayar cikin wani irin yanayi, na ce nima ban sani ba tana jinnace ban sani ba ta soma kuka, ban iya bata hakuri ba kukan nima na shiga yí muka hadu muka yi sai da muka gaji muka yi shiru don kanmu. A sallameshi kawai, nayi maza na kalleta a sallameshi" yaya Dija mu yi yaya da shi da wannan numfashi nashi? Ai ba gida zamu maidashi ba wani asibitin zamu sake mishi in da za a bashi magani ya ji sauki ba tare da an yi mishi aiki ba, kin taba ganin wanda aka yiwa irii wannan aikin dą sukace za su yi mishi ná gyara jijiyoyin zuciya? Nayi miaza maca mata uh-uh ta ce to. Gaba daya muka sake tsundurma cikin wani hali na kunci da danuwa. Mubarak ya sake dawowa shi da abokinshi Amiru kulawarshi da tsayawarshi kan al'amarin babana abin sha'awa ne don kuwa gaba däya ma'aikatan wurin sun dauka shima dan babana ne komái yake yi baya sauraron kowa duk abinda aka ce za a yi sai ya ce a yi sau biyu ina zuwa wajen sayen maganin da aka 48 rubuta sai su ce kudinku da kuka ajiye bai kare ba na luma san shi ne ya ajiye kudin amma a kame kwarai nake da shi in ba shi ne ya tambayeni wani abu ba bana tanka mishi, shima kuma ba sosai yake shiga harkar tawa ba sai ta kama ina dai kaffa-kafia da sh saboda na riga na sanshi na kuma kara ganeshi shi mutum ne mai iya wulakanci a ko ina kuma a kuma ko da yaushe a shiryc yake ya yi min in ba haka ba banga dalilin da zaisa ya kalleni a halin da nake ciki na rashin lafiyar babana ya ce wai a asibitin ma samari nakeyi. Cikin natsuwa da girmamawa na gaida Amiru, yaya mai jikin? Na ce mishi da sauki, ashe aiki za a yi mishi ko? Na dean yi jim kadan cikin tunani kafin na ce mishi, anya? Anya wane iri? Ya yi min tambayar cikin wani irin yanayi na tsatsuwa mai yawa, na sunkuyar da kainaa saboda yanayin da yake kallcna a ciki sai naji ya ci gaba da yin magana, ba yanzu muka fito daga wurin likitocin da za su yi aikin ba ni da Alhaji Ahmad? Ai ya riga ya gama maganar da su har ya yi setting din bill din da suka bayar baki san komai bane a kai? Ban iya cewa komai in banda sa hannun da nayi na soma share hawayen da suka Soma zubo min. Ban sani ba ko ganin hawayen nawa ne ya sashi saurin juyawa wajen Mubarak din, kai baka yi mata bayanin komai ne? Ya ya za ka tsaya kan yiwa mahaifinta aiki irin wannan ba tare da ka yi shawara da ita ba? Kuma. mcke tsakaninka da ita tunda dai ka hadiycshi ka zo ai sai ka bar komai ka fuskanci maganar rashin lafiyar kawai in ya koma gida sai ku dora daga inda kuka tsaya. 49 Har a mu'amalar da takeyi da samari sai in yi hakan dai ta? Gabana ya fadi saboda jin mu'amala da samarin da ya ke ikirari, ba sha'anin gabanta take yi ba ba sai in kyaleta nima in yi nawa ba? Wani irin mummunan tsaki Amiru ya ja kafin ya ce mishi, kaif halinka kenan a ko ina a ko wane hali a kuma kowane irin yanayi wai kana iya yin kishi. Ran Mubarak ya soma baci da jin maganar tashi a fusaceya soma ce mishi, a'a kai Amru kar kaja ta raina ni fa wane irin magana ne wannan? Ni kishi nakeyi a kanta? Yanzu kai baka ga irim abinda suke yi ita da wannan likitan da muka samu a nan ba tana yi msihi magana una wani yauki tana wani kakkashe mishi murya shi kuma sai zirga-zirga yake yi yana kaiwa da kawowa don ya gane abinda take nufi. Amiru ya ja tsaki kafin ya saki wani lallausan murmushi ya ce, ban ga komai ba Alhaji kai ne kaga hakan ni dai na san a halin da Maryam take ciki a yanzu in ma kaga tayi wani abu makamancin hakan to sai dai tayi don ya zama dabi'arta amma ba don ta burge wani ba don haka kayi hakuri ka rage sa mata ido ku fuskanci juna kai dai ta don ku f jin dadin mu'amala a tsakaninku. Kai kam ai dama baka son laifinta ban taba kawo maka zancenta kan abinda take yi min ka goyi bayana ba sai ka ce wai sa ido nane ya yi yawa. Bai sake tanka mishi ba sai ya juyo gareni, ke rabu da shi kin ji Maryam daina kuka ki share hawayenki kin ji? Ni zan tafi. Nayi naza ma share hawayen nawa kamar 50 yanda ya bani umarni na kuma yi mishi godiya, Mubarak yabi bayanshi nayi maza na koma wurin babana. ai n sBa a wani dade da yin hakan ba sai na hango shi yana dawowa alamar rakyar ba mai yawa ya yi mishi ba don haka na yi maza na sake fitowa daga dakin na tare shi a dan dogon falon da kofofin dakunan ke ciki a hankali cikin natuswa ta yanda babu mai jin abinda nake fada na ce mishi, ko zaka daina zuwa ne don kar mu zo muna batawa juna rai? A yanayin da nayi mishi maganar a irin shi ya bani amsa, ranki ya zo yana baci dai amma ni me zai 6ata min rai? Aiina ganin so mi somin hakan na daga wurinki zan yi maza in yi maganin abin don gaba daya zan hanalki zuwa asibitin kamar yanda kika hana matan gidanku zuwa. Gabana ya yi mummunan faduwa na yi amza na daga ido don in kalleshi saboda mamakin maganar tashi in ga irin karfin halin da ke gareshi da zai yi min irin wannan hukuncin alhalin ni da mahaifina ne, wani irin lalataccen kallo naga yana yi min, kina nufin kinfi kowa kusa da shi ne ko kinfi kowa sonshi ne? Ki yarda in ga wani abinda bai yi min ba ki gani? In gani in zan hanaki zuwan ki zo ki ga wulakancin da zan yi miki baki iya rashin kunya ba? Kar ki dauka kuma wai kishinki nake yi kamar yanda Amiru yake fada ko daya. Rasa abinda zance mishi nayi na soma yi mishi kuka saboda sanin da nayi cewar zai iya aikata abinda ya ce din. Sakarya kawai sokuwa wacce ko ciwon kanta bata sani ba sai rashin kunyar tsiya. 51 Ya wuceni zai tafi nayi maza na ce mishi, to bana son aikin da kake son sawa a yi msihi. Maimakon ya ce min to kamar yanda nayi zaton ji daga gareshi sai naji ya ce min to ai bake ke da shi ba yana kuma da bakinshi dona cikin hankalinshi yake. Ya wuceni ya shiga ciki na share hawayena nabi bayanshi a kan kujerar da nake zama na sameshi yana tashe da babana da ke kwance yana fama da kanshi. Sannu baba ya soma yi mishi gaisuwar cikin natsuwa da yardar Ubangiji zaka samu saukin wahalar numfashin nan nan ba da dadewa ba tunda likitoci sun gano kan al'amarin sun kuma yi bayani da cewar dan karamin abu ne ya sameka don haka za su yi aiki su gyarashi in aka gano kan ciwo baba to ai shi kenan magana ta kare sai kawai a yi addu'a Ubangiji yasa a dace da abinda za a yi don haka nake so in rokeka ka yi hakuri ka kuma kwantar da hankalinka kar ka ce zaka sanyawa ranka wani damuwa don kar jininka ya zo ya hau aikin da za a yin ba wani mai wahala bane. Ya zubawa babana ido tare da saurarona binda zai ce, yayin da nima na yi hakan tare da fatan in ji ya ce baya son aikin tunda mu kam ni da yaya Dija ba ma so gashi kuma ba shawara da mu ya yi ba kafin ya zartar da hukuncin sai kawai na ji babana ya ce mishi na gode Ubangiji ya yi maka albarka. Ya ce amin, ya mike ya fita ba tare da ya nuna alamar ya san da tsayuwata a wurin ba. Wulakanci irin na Mubarak yawa ne da shi ga dukkan alamu kuma watakila shima ya san shi din gwani ne tunda shi da kanshi ma yana barazanar zai yi shi don haka sai nà kudurawa raina in ma za a yiwa babana aikin 52 to ba shi ne zai dauki nauyin abinda za a kashe ba kamar yanda na lura yake nufin yi yan kadarorina zan sayar da na samu na tara da kudin da nake samu a sana'ata ta dinki zan sayar in baiwa yaya Dija kudin ta hada da abinda ke hannunta ta mikawa mijinta ya hada tunda naga alamar aikin zai ci kudi masu yawa. Yaya Dija ta iso na bata labarin duka binda ake ciki da wanda ya faru tsakanina da Mubarak, fada ta rufeni da shi a kan wai ai ni nake jawoshi ta hanyar sakar mishi fuskar da nakeyi mishi amma in ba haka ina ruwanshi da mu da har zaizo yana yi mana irin wannan shisshigin? Aje ya ji da harkokinshi ya barmu mu ma mu yi namu sannan ta riga ta gaya min bata son aikin ba za a yi ba ban ce mata komai ba har ta yi ta gama har ma ta tafi iyaka dai kawai addu'a nake yi da kara gayawa Ubangiji halin da mahaifina yake ciki wanda kuma nasan ya fini sani. Ana idar da sallar magariba sai ga Amir ya sake zuwa dubamu na ji, dadin ganinshi saboda ganin shi kadai ne ya zo ya duba babana ya juya zai fita nayi amfani da baccin da ya tarar baban nawa yana yi na biyoshi waje muka tsaya a dan tsaye a wajen da muka tsaya da Mubarak. Cikin natsuwa na soma yi mishi magana wanda roko ne na ya taimakeni ya gayawa Mubarak cewar ya fita hanyar jinyar da babana yakeyi ya daina zuwa asibitin bana kuma son duk wani taimako nashi. Wani dan siririn murmushi ya yi mai hade da ajiyar ciya a hankali cikin natsuwa ya tambayeni, wai ni in sani mana me Alhaji Ahmad yake yi miki ne? Ni dai 53 basan tunkina yar kankanuwarki yake tare da ke tun baki isa komai ba tun baki ma san ke wacece ba, amma har zuwa yau din nan bai samu matsayin da ya dace dashi ba a wurinki. Nayi maza na kalli Amiru cikin ntusuwa saboda jin kalaman nashi kan in san abinda zan budi baki in gaya mishi sai naji ya ci gaba da cewa, saboda kawai kin san yana sonki saboda kin gane ba zai iya fita harkar ki baa duk motsin da za ki yi idonshi yana kanki iyayenshi sun bashi aure amma kin hanashi natsuwa da zai zauna lafiya da iyalinshi lafiya ya iya jaruntaka kan komai amman in akan ki ne sokancinshi yawa ne da shi, ni da kaina na sha bashi shawara kamar yanda nasha yi mishi gori a kan ki wai dan ya yi zuciya ya kawar da kai daga gareki amma ya kasa ya yi aike gidanku ace an hanashi yafi a kirga kullum kuma ya zo kusa da ke sai kin san abinda kika yi kika 6ata mishi rai amma yana biye ba zan ce mishi ya fita harkarku ya daina zuwa ba don ko na gaya mishi ba ji zaiyi ba don haka in ya zo ke da kanki ki kara gaya mishi in ya ji shi kenan in kuma bai ji ba sai ya yi tayi na dai san har da alhakin abubuwan da yake yiwa matarshi uwar 'ya'yanshid a take matukar sonshi cikin wadannana bubuwan da kike yi mishi. Ya wuceni ya yi tafiyarhi ba tare da ya tsaya ko da don yi min sallama ne ba. Na koma dakin da babana yake kwance na jawo kujerar robar da na saba zama a kanta cikin natsuwa na zauna zuciyata cike da tunanin kalaman da Amiru ya yi min nice mai yawan batawa Mubarak ko shi ne mai yawan bata min a sanina kullum a cikin kaffa-kaffa da shi nake matukar yana wuri bana sakewa in yi abinda na 54 ke so kai ko baya nan bana iya saba dokarshi saboda tsoro ko gudun bacin ranshi da nake yi amma a hakan bana tsira sai ya san abinda ya ce na yi wanda ya yi min wani abinda zan raina kaina ko in zubar da hawaye a dalilinshi amma ka ji irin kalaman da baokinshi yakeyi min to babu laifi. Har dare har washegari Mubarak bai dawo ba maimakon in sake in ji dadin rashin ganin nashi sai na zama ko iya amsa gaisuwar likitan nan bana yi saboda tsoron kar mu na cikin gaisawar ya shigo ya ganmu ya ce ba a yanayin da nake amsa gaisuwar sauran mutane nake amsa mishi ba. Wunin ranar nan har dare bai shigo ba sai wajen karfe goman dare a lokacin nan kuwa babana yana cikin wani hali da ya yi dalilin da sai da naje na kirawo likitoi saboda kei kawo mai tsananin da numfashin nashi kc y1, a-hankali ya turo kofar ya shigo bai nufi wajensu don gani ko jin abinda ke faruwa ba wurina ya zo ya tsaya bai yi wata magana ba har sukayi abinda za su yi suka gama suka tafi, da sauri muka isa inda baban yaku wance don ganin halin da yake ciki gaba daya ya jike da gumi cikin Zuciyata na ce ya wahala, hawaye suka sake zuba daga idanuwa na sharr, bance mishi komai ba haka nan shima Mubarak din ya juya ya fita ya barmu a dakin, na kai guiwowina kasa na durkusa yayin da na kwantar da kama a gefen gadon nashi hawaye suna ta zubo min, jimawa kadan na sake dagowa na kalleshi saboda yanayin numfashin nashi da naji ya sauya bacci ne ya daukeshi na dan ji dadi kadan saboda tunanin yanayin da zai sake farkawa a ciki. 55 A hankali naji an turo kofar an shigo na waiwaya don ganin wanda ya shigo Mubarak na gani cikin zuciyata na ce, ashe ba tafiya yayi ba, to dawo daga nan mana tunda ya samu ya runtsa. Ban yi musu ba na koma daga nan din da yace na zauna, a hankali ya mikomin ledar da ya shigo da ita, bude ki cinye abinda ke ciki ba hilkima bane don kana jinyar mara lafiya ka yi ta zama da yunwa in ka yanke jiki ka fadi sai jinyar ta zama ta mutum biyu maimakon da ana yin na mutum daya. Na sa hannu na karba ina ci shi kuma yana yi min nasiha shi mutum hakuri yakeyi ya koyi jaruntalka idan al'amari irin wannan ya sameshi ba ya yi ta kuka yena kin cin abinci ba kinga irinr amar da kikayi kuwa? Na maida ledar na ajiye saboda koshin da nayi na bude robar ruwa ina sha, sai da yaga itama na maida ita na ajiye sannan ya tambayeni, amma yanzu ai kin gane ya zama dole mu tsaya wajen ganin an yiwa baba aikin nan ko? Na yi maza na daga ido na kalleshi saboda jin dolen da ya ambata sai naji ya ce min, to zai yiwu ne mu barshi a cikin wannan halin? Kin ga haka zai yíwu? Sannan ba zai yiwu a cireshi daga nan a kaishi wani wuri ba domin nan teaching hospital ne. Kalamai da mabayani masu yawa yayi min a natse har dai na bude baki na ce mishi, to ai yaya Dija ma ba ta son aikin. A hankali ya ce min to ai baban naki ne Maryam kin fita iko da shi ke lika fi kowa shan wahalarshi in yana cikin rashin lafiya kamar kina ciki ne dubi yanda kika zama a dan tsakankanin nan, kece kuma baki da kowa sai shi in aka rasa shi kinfi kowa rashi ita tana aure tana da mijinta da iyalinta ga ya'yanta ke ce baki da kowa sai 56 shi, Ina jin ha tadi hakan na soma kuka'saboda yarda da zuciyata tayi cewarni ce bani da kowa sai babana in aka Pasashi ni nafi kowa rashi. Kukan da nake yi bai hanashi ci gabs da yi min magana ba, ke madadin da namiji ce a wurin shi duk kuma abinda da namiji ke yiwa uban a laulawa da taimakawa shi kikeyi mishi ke kinfi wani da namijin ma jaruntaka don haka tsaya kawai a matsayin da ya dace da ke ki taimaki mahaifinki ya samu lafiya in kuma ailkin ya zo da akasi to kar ki ji zafin kanki ki dauka kawai kaddarar kenan kin kuma rasashi ne a kokarin da kikeyi na nema mishi lafiya. Kalaman Mubarak sukayi matukar shigata ta yanda har naji na yarda da magamar yin aikin nan take kuma sai naji zuciyata ta daina tsodo addu'a kawai nake yi a yi aikin a sa'a. Da safe yaya Dija tana isowa ita da mijinta a gabanshi nayi mata maganar ina ganin mu bar neman sallama don komawa wani wuri mu tsaya a nan a yi msihi aikin kawai don ba zai yiwu ya yi ta zama a cikin wahala irin wannan ba. Tayi maza ta ce min, a'a ba zai yiwu don ba zai yiwu mu yi abinda zaum sanyashi cikin hatsari ba ban taba ganin inda akayi irin wannan aikin ba ba kuma zai yiwu a fara a kanshi ba. Ai hatsari bai wuce ciwo ba yaya Dija gardama mai tsanani ta shiga tsakaninmu, saboda taja ta tsaya a kan bata son aikin tunda itace babba kuma itace zata fadi yanda za a yi, nace mata a'a ni ya kamata in facla saboda nice tare da shi a wuri faya ni nafi ki tsoron rasashi saboda nasan zan fiki maraicinshi ni ce ni kadai bani da 57 Uwa bani da... ban iya karasawa ba kuka na soma yi mata. Yaya Ibrahim ya kalleni cikin natsuwa ya ce min, kece mai fadin abinda za a yi mishi Maryam tunda kina so a yi mishi aikin za a yi ké Dija ki yi akan wannan ra'ayinta za a yi. Karo na farko a rayuwarmu ai da yaye Dija da jayaiya irin wannan ta shiga tsakaninamu bata taba cewe gAma yanda zaa yi nace mata a'a ba, hankelina ya yi matukar tashi da abinda ya farun musamman da na ganta tana ta kuka saboda ta riga taki aikin da za a yin sai karfinta kawai akayi bata yarda ta zauna ba ma a asibitin kamar yanda kullum take yi kama hanya tayi ta tafi, To in ailkin nan bai yi nasara ba me cewa yaya Dija? Tambayar da na yiwa Mubarak kenan a lokacinda ya zo don jin yanda mukayi da ita, bata fuska ya yi sosai kafin ya ce min, to in kama ska yi nasarar fa? Ke ba a i yi addu'ar yin nasara b sai ki zausa kina abrin zaciyarki tana raya miki mnanan abubuwa? Da wani wanda yake rike da rayuwar wani ne ko kuwa da wata hikima ne da za ta sa mutum ya tsallake wa'adinshi? Da irin wadannan kalaman na yarda na sanya hatmm a kan takerder ailkin da Za a yiwa babana. Cikin tsananin tsoro da fargaba ina gama sanya hannun na koma gefe ina kuka yana rarrashina. Yanda babana ya wuni karfashin dokar lilkita na bar ya ci komai ko da kuwa ruwa ne baka nima na wuni ban iya sanya komai a bakin nawa ba gashi babu yaya Dija sai Inma yarta babban da dama take zuwa tayani zama in ita bata zo ba saboda aiki ko wani aikin sai dare suka 58 zo ita da yaya Ibrahim idanuwanta a kumbure alamar tayi kuka har ta gaji ban iya ce mata komai ba na daga hannu ko bayanin likita na cewar za a shigar da shi Dtiyata da misalin karfe goma da rabi na dare ba. HASBUNALLAHU WA NI'IMAR WAKL' abinda kawai nake karantowa kenan a bakina da kuma zuciyata suka gama abinda sukeyi suka tas. Wajen Rarfe taran dare Mubarak ya iso babu abinda bai zo min da shi ba wanda ya san ina so amma ban iya cin komai ba saboda tashin hankali sai kaduwa nakeyi tamkar awcce sanyin hunturu ke kadata. Ana cikin haka har lokacin ya iso gadon likita naga an fara kawowa cikina ya bada sautin kulululu ban iya daurewa ba sai da na ruga da gudu na shiga bandaki kafin in fito na samu har an canza mishi kayan jikinshi da rigar likiten na raca yaada zenyi da raina na rinka jin tamkar ince na fasa abar yi mishi aikin kawai, shi da kanshi babana za gane ya shiga wani hali saboda jinshi da nayi yana cewa, Mubarak na gode Ubangiji ya yi muku albarka in har ban fito ba kuma to ka rike min uwata amana. Maimakon Mubarak ya ce misbi to ko ya gaya mishi wata magana da zata yi mishi dadi sai kawai naji ya ce mishi, a'a baba ni kar kace ka bar min amanar Mero don ba zan karba ba in zaka bani aurenta kawai ka bani ga mutane can a wancan dakin inka yarda in yi hanazrin kiran mutum biyu kawai ko uku don su tayan shedawa. Haushin Mubarak da takaicinshi suka kamani har a halin da babana yake ciki yana iya yi msihi musu da sauri na ce mishi, a'a baba daina cewa ka baiwa wani 59 amanata ai lafiya zaka shiga ciki ka kuma fito lafiya babu abinda zai sameka sai alheri, kai në zaka fito ka ci gaba da kula da ni mu ci gaba da zamanmu babu abinda zai sameka sai alheri, babu abin da zai sameka sai alheri, nayi ta nanate fadin hakan tamkar dai shi ne abidna zai sa hakan ya zamo ya yiwu. Ni da shi muka bi bayan gadon da ake tura habana, babana yana ta salati ni kuma sai kuka nakeyi shi kanshi Mubarak ya shiga wani hali, watakila don ganin babu kowa a wurin daga ni sai shi saboda batta su anti safara da na tuntubesu kan aikin basu bani goyo baya ba balle inji daiin gaya inusu cewar vau da daddare za a a yi, don haka babu wani wanda yake: da cikakkiyar masaniya na abinda ake ciki. Suna tafiya muna biye da su har muka kai inda aka tsaidamu shi kurna aka wuce da shi ciki. Kwanciya nayi a kasa ina kuka, tashi-tashi ki gani? Tashi ki zauna, kin taba ganin inda kuka ya yiwa wani amfani ko ya zama sanadin samun biyan bukatarshi? Addu'a ai itace ta kamace mu tashi ki zauna. Da irin wadannan kalaman nashi ne na mike na zauna kan daya daga cikin kujerund a ke wurin shi, kuma ya fita ban san inda ya je ba jifa jif dai yakan shigo ya zo ya sameni ya gaya min kalmomi na karfafa zuciya da kara tuna min muhimmancin tsayawata kan addu'a maimakon kuka ko yawaita damuwa ba zan iya tuna irin addu'o'in da nayi a ranar ba, fatana da burina da a yi nasara ne a fito da shi yana raye don in aka samu akashi kan hakan to ban san abinda zan cewa yaya Dija da 60 sauran wadanda suke da hakka kan rayuwar tashi ba gaba daya Saboda tsananin kidima da damuwa bana iya tantance dadewar da sukayi a ciki gaba daya in banda duk abinda ake yi a cikin duhun dare ne guda daya da Dayi zaton anyi adadin kwanakin da basu kidayuwa saboda dadewarsu da na gani. Mubarak ya sake shigowa ya sameni a inda ya barni a zaune. Sannu Maryam, da kyar na iya buda bakina na ce mishi, yauwa saboda jin da nakeyi tamkar la66an bakin nawa a manne suke, cikin yardar Ubangiji za a yi nasarar aikin da ake yiwa baba Ubangiji kuma zai yi miki sakaiya kan al'amuran rayuwarki gaba daya bance mishi komai ba ya nemiw uri ya zauna yana kallon agogo in dai komai ya tafi daidai ai sun kusa fito da shi. Cikina ya sake bada wani sautin na kuluulu saboda jin da nayi ya ce in komai ya tafi daidai kenan in bai tafi daidai ba ma an kusa sanin abinda ake ciki kenan. A haka muka ci gaba da zama a wurin babu mai cewa wani komai, idona yana kan agogo in banda tafiyar lokaci babu abinda nake dubawa, zuciyata kuwa tana ta karanto addu'o'i haka, a haka a irin wannan yanayin da awowi suka zama tamkar kwanaki a hakan kuma dai har muka kai lokacin da suka ambata na kammala aikin da za 8u yiwa baban nawa sai kuma gashi an fito da shi kwance a kan gadon babu wata alama ta motsi a tare da shi, muka Sake biyo bayansu zuwa dakin da dama muka bari aka dorashi a kan gadonshi aka kwantar da shi, abu guda daya kawai da ya dan kwantar min da hankali shine 61 tabbacin da naji suna ta baiwa Mubarak ina anyi nasarar aikin da aka yi mishin. Amma ban samu natsuwa a tare da ni ba har sai kwanaki biyu bayan nan da naga babana ya soma wattsakewa daga mummunar wahalar da ya sha har kuma gashi numfashin nashi ya daidaita saura ya samu karfin jikine kawai. Mutane sukayi ta zuwa duba babana saboda jin labarin aikin da aka yi mishi kai kace ahi kadai ne mara lafiya a asibitin nan, ina jin wani daga cikin yan kasuwar tumatirin nasu yana gayawa abokin tafiyar tashi, kaga ja'irar yarinyar nan yar gidan Malam Habu mai tumatir, kai wannan yarinya da jarumtaka take bata gajiya da hidimar mahaifinta kullum a cikin kai kawo da dawainiyarshi take shi yasa duk iya shegenta sonta yake yi. A to ba dole ya sota ba Malam ko da na mijine ya ke irin hidimar da yarinyar nan take yi akan mahaifinta ai yaci a yaba mishi balle ita yara irin wadannan ai haka suke sunada halin tsiya da na arziki, kai ba duka ba inji wani da bansan ko waye ba ita dai wannan anyi dacentane Ubangiji kuma zai saka mata ya shiryar da ita ya bata mijin da zai sota ya riketa duk da iya shegen nata. Babana bai cika kwana biyar da yin aiki ba sai da kowa ya gamsu da aikin da ak yin ya kuma ce gwara da akayi hakan ciki kuwa harda yaya Dija. Tun kwana biyu da aikin babana sanda ya soma dawowa cikin hayyacinshi Mubarak ya dauke kafa ya daina zuwa asibitin baya zuwa da daddare balle kuma da rana, ko dama can kuwa mafi yawancin zuwan nashi kan 62 zamo cikin dare ne lokacin da zirga-zirgar dubiya tayi sauki in dai ba wani dalii mai karfi ne ya kame na yazo da ranar ba. Rannan da safe ni da yaya Dija ne kawai a tara da shi bayan mun goggoge mishi jiki mun gyarashi mun tsabtace komai na dakin sai kamshi yake yi yaya Dija ce a kusa da shi tana bashi ruwan tataccen kabeji da karas yana sha a hankali yayin da ni kuma na gama tattara kayan wanke-wanken mu na mikawa Inna nace taje ta wanke sai kawai mukaji an turo kofar dakin a hankali tare da yin sallama, gaba daya muke amsa sallamar tare da maida hankalinmu wajen kofar. Gabana yayi mummunar faduwa saboda ganin mai sallamar, Umma ce ko ince Umman Mubarak tare da Rumasa'u da Rukaiya, kadan ya rage in dibibice in rude saboda rabon da muyi gaba da gaba da su haka an dade ko ince tun daga ranar da abinda ya faru tsakanina da Mubarak na samuna da akayi a dakinshi da al'amuran da suka biyo baya wa ta mu'amala bata sake hadani da wani daga cikin mutanen gidan ba, wacce tayi dalilin haduwarmu a wuri daya kamar hakan ba dan gara-gara Rukaiya in ta kure mana a makaranta mukan gaisa saboda munyi karatu tare. Sannu da zuwa Umma yaya Dija ce ta fara yin gaisuwar daidai tana mikawa Umman kujerar zama, na mika hannu don karbar yarinyar da take hannun Rumasa'u duk da yanayin dake fuskarta tamkar dai ace mu din ba wasa tare muke yi ba, gaba daya aurenta da Mubarak ya canza al'amuran dake tsakaninmu ni da ita kowa ya fi jin zafin wani oho?. Ko da yake dai nikam can 63 cikin zuciyata na sani bana jin zafin Rumasa'u kamar yanda nake jin zafin Mubarak da wadanda suka sashi aurenta. Gaba dayansu na bisu na gaishesu kamar yanda naga yaya Dija tayi, yaya jikin na malam? Yaya Dija ta sake amsawa Umma zancensu ni kuma na dawo da hankalina wajen sauraron abinda Rukaiya ke gaya min naga Hasiya jibirin shekaran jiya ta tabaye ni ke na gaya mata tace in gaisheki itama zata zo, nayi murmushi na ce mata ai jiya tazo nan ta kusa wuni muna zancenmu ban sake Juyawa na kaili Rumasa'u ba saboda bata bani fuskar da zan iya fuskantarta in kakalo wata naganar da zanyi da ita don haka na ci gaba da wasa da 'yarta da kuma hira da Rukaiya, kc kadan dai banji dadin sammakon da sukayi mana ba an saukin abiıma sun zo sun samu babana da kuma dakin da muke ciki cikin tsabta. Bayan tafiyarsu yaya Dija ta kalleni tayi murmusbi ta ce, kai kishi babu kyau mata suna kokari, ban tanka mata ba balle zancen ya yi nisa na kalli knna na ce mata, jeki ki yi mana wanke-wanke kin ji? Ta ce to ta tashi ta fita ba fa zuwansu bane ina jin Alhaji Mubarak ne ya turosu. Na sake kin amsawa don kuwa ban san dalili ba sai naji bani da ra'ayi a kan zancen nasu. Sati biyu da aikin babana aka sallatmo mu muka dawo gida bisa dokoki da aka jaddada mana binsu. Ranar wuni nayi ina aiken Inna gidajen mutanen da sukayi ta zirga- zirga suna ta dawainiya da mu irinsu Jumare gidan baba Hodije Yakubo Halina, Hasiya Jibrin, malamaina ua Markas irin su Malama Basma da Hindu abokan karatuna na makarantar mu ta ilimi addini mai zurfi 64 musamman wadanda mukayi aji daya da su wadanda har karo-karon kui suka yi suka kawo min don taimakawa Zumunci irin wanda mutane suka nuna mana a wannan. lokacin babu abin da zamuce musu sai dai addu'ar Ubangiji ya sakawa kowwa da alherinsa amin summa amin. Mun dawo gida da babani a dalilin saukin da ya samu kowa murna yake yi muna farin ciki musamman da yake a yanzu yana da mata mai kula da tattali da kokari ganin asirin gidanta ya rufu sai dai kuma hakan bai hana hankalina da zuciyata tafiya wajen tunanin abitda ya hana Mubarek zuwa yiwa babana muriar dawowa gida ba rabonshi da zuwa asibiti tun kwana biyu ko uku da yin aikin bai sake takawa ba to yanzu kuma mun dawo gida ga mu ga shi ba zai shigo ya gaisheshi ya karasa ladanshi ba bayan duk irin hidima, dawainiya da ya yi da rashin lafiyar tashi, to ko dai matarshi ce ta hanashi zuwa? Tanbayar da ta zo cikin zuciyata kenan, nayi kokarin in kawar da hakan ta hanyar tambayar kaina anya Mubarak yana yiwa matarshi irin wannan tsoron kuwa? To amma me akayi mishi? Da dai naga damun kaina kawai zanyi sai nayi maza na cire wannan tunanin daga cikin zuciyata na maida hankalina kawai wajen lura da halin dà babana ke ciki ina kuma rama bacci da gajiyar zaman asibiti tinda muka dawo matarshi ke kula da shi ga anti Safina ga baba Lantana ba a je ko ina cikii kulawar ba na soma jin maganarshi daga dakin baba Lantanar yäna cewa uh'uh ba fa zan iya irin wadannan abubuwan ba a yanzu in kin ga da matsawa kawai jeki ni bani da wata damuwa a yanzu. 65 Mamakin babana ya kamani cikin zuciyata nace kar dai ace babana zai fara yin magana ne. Ba a dauki wani lokaci ba baba Lantana ta fito da halayenta da akafi saninta da su na kin yin girki da sauransu saukin abin kawai anti Safana tana nan tana kuma tsaye kan al'amuran mijint adama ni kaina da take matukar ji da ni batama ko kiran sunana a yanzu wai sai maman baba wani irin ji da ni takeyi ban sani ba ko gani take tamkar don ita da abinda ke cikinta na yi jinyar baban nawa. Rannan da sassafe na idar da sallar asuba na shafa fatiha na shiga dakin anti Safara inda nasan ya kwanaa don in gaisheshi in kuma bashi magungunanshi da naki yarda wani ya bashi, yana shan magungunan muna yar hira magana kadan kadan. Baba kana cin zaitun din an kuwa? Magani ne fa ba kadanka. Kafin ya bani amsa sai kawai naji muryar yaya Ibrahim yana sallama tare da shigowa cikin gidan, shigo mana Ibrahim, baba ya yi mishi umarni don haka ya shiga har cikin falon. Kan maganar zuwan mutumin nan ne ikita na ce a kira min kai inji kayi binciken a kan nashi ne? Na mike na fita saboda ganewar da nayi maganar a kaina ne tunda na ji ana ambaton likita wato Dr. Bello wanda ya biyo mu gida da kai kawo da hidimomi iri-iri. Ni fa baba binciken da'nayi kan mutumin nan ba wani mai yawa banc saboda ga Alhaji Ahmad a kusa da mu wanda aka dade ana tare yaushe za a je ana bincike kan wani sabo kuma? Gabana ya fadi jin da nayi ya ambaci sunan Mubarak, babana yayi maza ya ce, 66 Mubarak kuma? Cikin zuciya na ce, a to ai gara dai da ko tambayeshi. Cikin natsuwa va ce mishi, eh baba i ni a wurina banga wani wanda ya fishi ba, babu ma wanda ya kaishi cancanta in dai har za a bada auren ne bisa cancanta da dacewa babu wanda ye fishi dadewa a cikin nemankullurn kuna a tsaye yake a kan al'amarinta ga zaman tare da makwabtakar dake tsakani, don haka in har ba shi ne ya ce bai da bukatar auren ba to babu wani dalili da zaisa mu je muna binciken shi ikita, to yaushe ma muka sanshi? Cikin natsuwa da yanayi na rage murya naji babana ya ce mishi, to ai banga kamar har yanzu yana kan naganar nan ba tun yaushe rabon da ka ji sun turo kan maganar? Sannan tunda akayi aikin nan da kwana biyu har zuwa yanzu ban sake ganinshi ba. To in baya cikin neman saboda wa yake hidimar da yakeyin'? In ana tunanin ko makwabtaka ne shi yafi kowa sanin hakkin makwabtaka baba? Ai ya gaji da turowar ne yasa ya hakura ya zuba ido yaga iya kar al'amarin. To tunda ya nuna ya gaji yanzu sai a yi yaya da shi Tbrahim? Ba shi kenan ba sai a yi da wanda bai gaji ba yake ta kai kawo. Cikin zuciyata na sake cewa a to. A'a baba a basu hakkinsu tukunna sai in sunce basa so shi kenan sai a yi da wannan din, a ra'ayina ina ganin a yi musu aike a gaya musu in suna so su zo in suka ce basa so shi kenan. Hannu biyu na saka na dafe kirjina saboda tsananin harbawar da yake yi cikin tsananin karfi saboda tsoratar 67 da nayi da maganar tashi, ban taba jin muguwar shawara ba irin wacce ya baiwa babana a yau. A tambayi Mubarak da iyayenshi sai in sunce basa so na ne za a aurar da ni ga wani wannan wane irin zace ne? Tambayar da nake yiwa kaina kenan sai naji ya ci gaba da bayani yin hakan ba komai ba ne baba ba kuma wulakanta kai bane aure ne shi kuma auren darajarshi ta wuce duk yanda ake zato, in wasu sunyi mana mummunar fassara ma to mu kam ai babu ruwanmu tunda mun san alheri muke nufi ba kuma don wani abin hannunsu ba. Bayani sosai ya yiwa babana har dai ya gamsar da shi ya yarda da shawarar tashi. Cikin zuciyata na ce, na shiga uku yanzu bayan duk abinda na wuce a baya kuma bai isa bah er sai an sake jawo min wani wulakancin mai salo na dabna. Yaya Ibrahim yana barin gidan naje.na samu anti Safara wai in yi mata magana ko zanyi sa'a ta yarda ta yiwa babana magana kan rashin dacewar abinda suke shiryawa sai kawai naga ta kalleni cikin natsuwa ta ce min, to ai yana jin maganarki kema ki sameshi mana kawai ki gaya mishi. Yanayin da íayi mnaganar a ciki yasa na gane abinda take nufi don ahka na wuceta nayi tafiyata. Ina jin baba Lantana daga dakinta tana fadin ina ma dai in anje su koro wanda yaje din kwadayi mabudin wahala, in da kwadayi da wulakanci, kuda wajen kwadayi yake mutuwa, yaron nan da iyayenshi ba tun yau ba sunce basa so basa so ba sa so amma kun ki yarda ku hakura kun manne sai dole sun kar6i kai tir. 68 Duk da irin wadannan kalamai da baba Lantana ta wuni tana yi basu sa babana ya canza daga abinda suka shirya ba. Washegati da safe naji yana cewa anti Safara, yau fa za ni sallar juma'a da wuri kuma zan tati don sai naje gidan Alhaji Muhammadu nayi mishi maganar nan kafin in wuce masalllacin. Da kanka kenan zaka? Ya yi maza ya ce, ei ai gara inje kawai da kan nawa babu komai ai 1aganar aure ne ya yi magana da dan shi ne in suna so shi kenan su zo in kuma basa so shi kenan mun fita hakkinsu sai a yi da wannan da yake tsayen, ta ce haka ne Ubangiji ya zaba mana mafi alleri, ya ce to amin. Hankaline ya yi matukar tashi ben taba ganin yariyar da aka yiwa irin wannan tallan ba sai ni dama dai inyi sa'a suce basa so shima Dr. Bellon ya ji labari ya ce baya so na ya fasa in ga yanda babana da yaya Ibrahim za su yi da ni tun da dai na lura gajiyar da sukayi da ni ne ya sa suka yanke hukuncin yi min irin wannan wulakancin. Ban san abinda ya faru tsakanin babana da Alhaji Muhammadu mahaifin Mubarak ba illa iyaka dai da daddare Isiyaku yayi sallama a zanren gidanmu da anti Safara ta amsa mishi kuma ya slhigo har dakina ya sameni cikin fara'a ya soma gaisheni ina amsawa a natse sai da muka gama gaisuwar sai ya kalleni cikin murmushi yana susar eyarshi ni da yaliaba: ranki ya dai ya dade ne yana zaure yana son ganinki, nace to madalla. Ya dan saurara ko zaiji na sake yin wata magana bai ji ba ya gaji ya sake tambayata, me zance mishi? Ban 69 kalleshi ba na ce mishi abinda kaga ya N maka, ya gaji da tsugunno ya tashi ya tafi ban san yaya saka, kare ba. Kwana biyu a jere ko leken kofar gida bapyi ba saboda bakin ciki da takaicin yanda yaya lbrahim da babana suka hadu suka zubar min da 'yancina, ban salke jin wani motsi ko wata magana. daga wurin kwoab a sai kawai na gane Mubarak da iyayenshi sun karbi tallan aurena da su babana suka kai musu a daliin wasu yan al'amura da na lura da su shiryawa nayi da, safe cikin. kwalliya mai sauki mai kuma ban sha'awa riga da-siket din atanfa ce a jikina ni'na yiwa kaina dinkin don haka ba sai na tsaya cewa sun dace da jikin nawa ba pa sanya. takalmi silifas dan Italy tare da 'yar faramar jaka ta pos a hannuna, maimakon in yi tafiyaa-a haka- ko, in yi damara kamar yanda 'yan mata a loacin sukeyi sai ya jawo wani dan madaidaicin gyale na yane jilkin, pawa sai dai bai hana kwalliyar tawa baiyana ba'ta fto.tsalcar gida ina gayawa anti Safara zanje wajen yaya Dija yanza zan dawo. Ta tsaya tana kallona nuna alamar bata gamsu, da yanda nayi mata bayanin ba, sanarwa kenan ba neman izini ba, na yi maza na ce mata yi hakuri anti ba sanarwa ba ne neman izini ba zan dade ba. Ta yi murmushi ta ce, to ki gaisheta, nace mata to za ta ji, na kamo hanya na fitod aga gida ina jin baba Lantana tana fadin, anyi jiran anyi jirani abin ya gagara har an koma yin talla, ban kulata ba çikin zuciyata dai na shirya zuwa wurin yaya Dija ne don in san menene ake ciki, in kuma gaya mata ra'ayina kan hakan da aka shirya don ta sani. 70 Yar tafiya 'yar kankanuwa na fara nir tina in kara ba bakin hanya inda zan samu abin hawa sai kawai ga Isiyaku ya biyoni da sauri har yana haki, wai lki dawo in ji shi. Na ja na tsaya ina kallon Isiyaku cikin takaici, kai Isiyaku kafin in gaya mishi abinda nake nufin gaya mishi sai naga ya saki wani lallausan murmushi, ai ba dagani bane ya hacla da rantsuwa kafin ya ce shi yallabai ranka ya dade din ne ya ce in zo in gaya miki kar ki tafi ko ina gashi can suna tsaye shi de bakinshi. Ban san dlaili ba bana iya karya dokar Mubarak ko da dai a lolkacin zuciyata tana raya min ne wai zanbi umanin nashi in komá gidan ne in bar tafiyar saboda kar in kunyatasbi a gaban bakin nashi amma can cikin raina ni da kaina na sani ba haka bane ba don su ba ne maganar guca daya ce a duk hali ko yanayin da muka samu kanmu a ciki ni da shi bana iya sabawa ko bijirewa umarninshi. Na juyo da baya na korna na nui gida a makogarona ina fadin don dai kana da baki ne kawai a zuciyata nasan ya zama min tilas in koyi jaruntakar da zan koyi bijirewa irin wadannar dokokin nashi ba komai ya ce min shi kenan ba. Ina tsaye a kofar dakina ina kokarin bude kofar tare da yiwa anti Safara bayanin sai an jina za ni sai na jiyo sallamarshi a cikin zauren gidanmu da kanshi ya yi sallama alamar bai zo da dan aike ba nayi kamar kar inje sai kuma naga to ai baba Lantana tana kallona ni kuma bana so ta sheda wani al'amari a tsakanina da shi don haka na juya na koma zauren tuni har kanshinshi ya 71 mamaye ko ina a wurin kwalliyar kananan lkaya ya yi, sun kuma yi matukar karbarshi. Ina zaki da safen nan kikayi wanna kwalliyar haka? Ban san yanda akayi ba naji bakina ya bashi amsa, gidan yaya Dija, to yaya za ki fita baki gaya min ba? Ba ki ji maganar da babu yaje ya gayawa baba bane? Nace ban ji ba na fadi hakan a daidai lokacin da zuciyata ke nanata maganar tashi, ba ki ji maganar da baba ya je ya gayawa baba ba ne? Wato babana ne ya je ya gayawa babanshi cewar da nayi banjin ba da yanayin da nayi maganar a ciki ya sashi zuba min ido yana kallona, ba ki ji bane ko kina da wata magana ne, tsakanina da ke ai babu wani 6oye-6oye ko kin yi nufin 6uyan ma ba zai yiwu ba don babu wani al'amarinki da ban sani ba, don haka fadi gaskiyarki kawai in kina da wata magana ne kuma kiyi. Na daure fuska sosai kafin nace, ina da ita, da sauri cikin natsuwa ya ce, ai kinga hakan yafi fadeta inji. To ni gaskiya ba da yàrdata aka yi miin hakan ba a ma. shawaceni ba don haka bana so karma ka dauki hakan da wani muhimmanci da har zaisa ka rinka neman ka shiga harkokin rayuwata bana so. Ya dan gyara tsayuwarshi kadan kafin ya tambayeni bakya son me? Na yi shiru bakya so kamar yaya? Ai magana za k yi don in gane abinda lkike mufi. Na sunkuyar da kaina don kaucewa kallon da yake yi min in kuma ji dadin gaya mishi abinda nake son gaya mishi. Nace bana son auren da ake shiryawar saboda bakai nake son aura ba ina son auren saurayi ne dan uwana kamar yanda nake budurwa ba inje ina auren mijin wata ba. 72 Hankalinshi a kwance ya tambayeni, to yanzu yaya kike so a yi? Na ce rokonka zanyi ka fita hanyata ka daina kulani ka daina shiga harkokin da suka shafi gidanmu. Wani irin lalataccen kallo ya yi min kafin ya tmabayeni, kenan har kina da wata harka taki da ake shiga, yaushe rabon da kika ga daga ido na kalleki. Kirana aka yi kirjina ya bada wani irin sauti na dum, a dalilin jin kirana aka yi nan da ya ambata na shiga uku ni yasu tawa ta sameni, yaya Ibrahim ne ya yi min sanadin wanman wulakancin gashi tun ba a je ko ina ba an soma gorantamin ban iya daurewa na soma kuka ban iya tsayawa ba na juya da nufin in shiga gida sai ya yi maza ya tura kofar zauren dake wurin ya rufe ya hanani shiga ban daina kukan da nake yi ba. Kin shiga ulu ke 'yasu taki ta samehi yaya Ibrahim ne ya yi miki sanadin wulakanci gashi tun ba a je ko ina ba an soma goranta miki, to da akayi miki me? Kina so ki gaggantsaramin maganganu ina kallonki inja bakina in yi shiru? Ya soma yin magana kamar yana nufin yin rarrashi, nayi naza na bijire mishi gaba daya tunda gori ay shiga cikin maganar ai kuma shi kenan magana ta kare ban shiga ba ma kenan ina kuma ga na shiga gaskiya ba zan iya ba da wanne zan rinka ji da gorin da zaka rinka yi min ko da wnada matarka da 'yan... Kinga Maryam kinga, nayi maza na bar maganar saboda jin kinga-kingan da ya fara ambatawa don haka na koma yin kukan kawai ina fyace majinata da bakin gyalena. 73 Nace in kina da magana mai ma'ana ki yi ina jin ki na tsaida kukan da nakeyi cikin natsuwa na ce mishi a fita hanyata kawai, ban sake yin wata magana ba ya juya ya fita yayi tafiyarshi na dawo cikin gida na zauna ina tunanin al'amurana úa Mubarak babu wani alherinshi ko taimakonshi a kaina da ban tuna ba ko ince na manta a'a komai irin sa ne dashi sai dai yanda zuciyata take rike da wannan lissafin hakakuma take rike da abubuwan da suka faru tsakaninmu da gidansu, da baubuwan da mutanen unguwas uka yi ta fadi tuni dama mutane da yawa suke fadin wai babana yaki aurar da i ne yana jiran Mubara din saboda kwadayin dukiyar gidansu ba wannan ne abinda yafi komai damuna ba irin dauke kafar da ya yi fun muna asibiti har kawo dawowarmu gida bai zo ya gaida babana ba yana ganina ina ganinshi sai ya yi kamar bani yake kallo ba sannan a hakan wai an bisu har gida ance in suna so su zo bayan ga wani yana takai kawo a kaina an san za a bashi ni me yasa ba a bashi din ba tuntuni tun sanda suke zirga-zirgar aike shi da mahaifinshi sai a yanzu da suka tattara nmutane suka yi watsi da su? Ina alwalar sallar azahar a tsakar gida Rukaiya ta yi Sallama ta shigo, ran amaryarmu ya dade, ban wani kulata ba don ana jin kamar ina son wasan nata, anti Safara tayi ma'a sannu da zuwa ta kuma jagoranceta Zuwa dakinta hakan ya kara tabbatar min da cewar ba wurina tazo ba, a cikin zuciyata dai na kasa tunano yaushe rabonta da shigowa gidanmu? Dakina na wuce na soma gabatar da nafila kafin in yi farillar har ta bar gidan kuwa ban san yanda na tashi daga kan salalyar ba don 74 amin amin, dakina ta sbigo ta samen, ke kuma menene haka kika shige daki kika hau gado kika zauna ba za li bar gidan ba sai masu kawo kayan sun zo sun sameki? Na tashi na zauna ina kallont,a kayan me za a kawo? Harara da dakuwa ta hadamun gaba daya, ba fa na son rashin kunya, na ce to yaya dija ni ina sanin abinda ake ciki ne? Kin san irin bakaken maganganun da ya zo ya dankaramin kuwa? Ni gaskya, ta ce to ba yanzu ne lokacin fadin gaskiyar taki ba mai gaskiya tashi ki shiga gidan baba Sumaye don kar su zo su sameki a nan a ce kin yi rashin kunya tunda ina ganin kamar za su zo da yawa saboda ya ce min zai hada komai a azo da shi kayan na gani ina so kayan sa rana, kayan aure da kuma na sakun lalle don baya so a saka mishi lokaci mai nisa. Ban iya ce mata komai ba saboda hayaniyar da akeyi a cikin gidan alamar mutane suna kara shigowa, anti Safara kuma sai kai kawo take yi tana kokarin ganin kowa ya sarou abinda zai kai bakinshi. Duk da kokarin da yaya Dija tayi na ganin na fita gidan ba tare da an ganni ba sai da wasu suka gannin basu kuma ja bakunansu sun yi shiru ba sai da suka yi tambaya, ai dama amaryar tana gidan ne? Sai dai ba su yi sa'a sun sami mai basu amsa ba muka wuce kofar baba Lantana a kulle kamar bata nan nayi maza na kalli yaya Dija na ce mata, tana ciki fa ta kulle kofar ne kawai irin yanda tayi ranar da aka je jeran anti Safara, bata amsa min ba. A gidan baba Sumaye dakin da muka saba zama sanda muke yara na shiga na hau dan gadon bonon da ke wurin na kwanta, maimakon zuciyata ta tsaya wajen 76 tunanin alamarin dake faruwa a kaina a halin dan ake cii sai ta koma tunanin da rayuwar kuruciyata tun sanda nake yar karamata sosai mu'amalata da su Jumare har kawo ranar da na wayi gari a wannan dakin ina baccin da ake kira baccin hasara na rasa Innata ban sani ba, hasken rana ta tashi na fito waje idanuwana suka sheda dimbin jama'ar dake sallatar wata gawa dake shimfide cikin makara a ka kuma lullubeta da zanin Innar tawa amma ban gane itace a kwance a ciki ba, hawaye suka soma zuba min ganin babu kowa a gidan sai ni kadai ya sa ni na sake nayi kuka har sai da na gaji nayi shiru don kaina ban kuma wani dade ba bacci mai nauyi ya daukeni wanda ban tashi ba sai da naji ana taba ni na bude ido naga baba Sumaye a firgice na ce mata, magariba har tayi baba? Ta ce eh, nayi maza na ce ban fa yi la'asar ba, ta ce to ai sai ki tashi ki yi, na idar da sallar magariba ina addu'a ita kuwa baba Sumaye sai fadi take yi, kai uh-uh uhhh, ta gyada kai jimawa kadan ta sake nisawa ta ce, mu mata muna da aiki shi namiji a kan matar da yake so ai maganin shi hakuri ne kawai in kayi hakuri komai sai ya wuce amma in ba haka ba ai abin da wahala wannan irin kaya da Alhaji Mubarak ya yi miki dame sukayi kama ni Sumaye? Ta kama baki ta rike tana fadin, kinga ni ko Kayan auren ban gama gani ba na tashi balle kuma sauran komai fa a ciki sha biyu ne dozin sai bayani baba Sumaye take yi min tamkar dai ta mance ni ce amaryar a wancan lokacin namu kuma ba a hirar aure ko kayan aure da wacce za a yiwa aure. 77 Ban samu ganin kayan auren da baba Sumaye ta bani labari ba saboda gaba daya kayan babana ya ce yaya Dija ta tafi da su can gidanta ta adanasu. Kwana uku da kawo kayan auren Mubarak ya zo a zauren gidanmu na sameshi da ganinshi nasan zuciyarshi a soshe take saboda yanayin da na gani a tare da shi, daga wurin yaya D:ja nake naje wajenta ne don ina so in yi muku adalci dake har ita da na so da sai kawai in samu malam Ibrahim in nemi alfarimar lokacin da nake so a sanya main na biki to banyi hakan ba sai naje na sameta don in baku damar ku me kika gaya mata da yasa ta ce min wai zaia shiga wannan maganar ne kawai in mun warware mas'alar da ke tsakaninmu? Menene a tsakanina da ke? Me bayi miki? Me yasa ke baki da sassauci kan abinda ya sihafeni? Daga shekaru biyar zuwa yau za ki iya tunaw da wani abin da kika yi min guda daya da niyyar ki i in ji dadi? Kina tsammanin in banda wani al'amarin 1e na daban a tsakaninmu da ke zan lamunci irin wadar nan abubuwan ne? Ai bana son 6acin rai Mero abinda ya kenan ya tsare mutum ya yi ta gaya mishi maganganu in banda hzka bai iya komai ba gaba daya samarin da nayi ban taba ganin wanda baya zama ya gaya min irin son da yake yi min ba sai shi tsawon rayuwata da shi bai san ya vabi kwalliyata ba sai dai ya saya min kayan adon kawai dana kai munzali na 'yan matanci gaba daya burina ya yabi kwalliyata ne don inji dadi bai yi ba ko ince baya yi na kai wani matsayi na bukatar ace ana sona bai yi ba wasu suka yi ta furta min hakan na kasa jin dadin kalmar a bakunan su saboda ba a wurinsu nake son jinta ba, bai buda baki ya gaya min irin 78 son da yake yi min ba sai a loakcin da al'amura tsakanina da shi suka rikice ko ince suka lalace ya fadeta a sanda fadin nata bai amfanar mana da komai ba tunda wannan lokacin kuma bai sake gaya min wata magana makamanciyarta ba da zata sani in ji sanyi ko inji dan wani sassauci a zuciyata, ban san yanda aka yi ba naji nakina ya ce mishi, nifa nafi son auren mutumin da zai rinka furta min kalmomi masu dadi yana gaya min irin son da yake yi min. Maimakon da ya ji hakan ya gaya min wata magana mai dadi sai na ji ya ce min, to ya ya za ki yi da kaddarar rayuwarki Mero? Ko wace mace ai da irin kaddararta ke taki kaddarar ita ce ta ba za ki auri saurayi ba mijin wata za ki aura ba kuma za ki auri wanda zai zauna yana yi miki irin wadannan kalmomin ba don bai iya ba. Na 6ata rai na ce ko kuma a kaina ba? Eh to watakila a kankin ne kawai nake hakan da kuma za ki yarda da shawarar da zan baki da kin daina kawo zancen wata a tsakanina da ke. Na yi shirn shima ya tayani yin shirun na dan wami lokacin kafin ya kawar da shirun da tambayata, da ma damuwar kenan? Ban kula shi ba, sai na ji ya kara sassauta muryarshi a hankali, cikin nutsuwa a soma cewa, ban yarda na koyi irin wannan rayuwar ba ne Maryam saboda nafi so da sha'awar rayuwa irin wacce na samu iyaye da kakannina a kai ina irin rayuwa ta kunya da kawaici kan abindą kake so musamman mace kin gane? Shiru nayi ban ce mishi komai ba har ya yi min sallama ya tafi a kan gobe zai yi sammakon tafiya 79 Legos nace to Ubangiji ya kiyaye hanya, ya ce to amin na gode. Kwana hudu bayan tafiyar Mubarak aka yi bakon wani dattijo a gidanmu ganin shi da zanen barebari irin na babama da nayi da kuma sanin da nayi cewar babana yana mutunta duk wani mutumin da ya gani da irin wannan zanen a fuskarshi ya sa nima na mutunta wannan dattijon ta hanyar shinida mishi tabarma a cikin zaure na,kawo mishi ruwan sanyi tare da butar alwala da kuma abincin da aka girka wanda bai yarda ya taba komai a ciki ba in banda butar da ya dauka ya je ya taba ruwa ya sake daura alwalarshi da ta kárye a sanadin taba ruwan da ya yi sannan ya dawo kan tabariar ya sake zama ya zubamin ido yana kallona cikin natsuwa ya tambayeni a daidai lokacin da ya ci gaba da jan dogon carbinshi yana kos kos kos, to ina malam Bukar din da tace nan din gidanta ne tace babanta ne? Kai tsaye na fahimci inda yake nufi tunda shiua baban nawa shigen irin hausar da yake yi kenan na ce msihi e maiam shi ne babana, ya gyada kai ya ci gaba da abinda akeyi, ni kuma na mike na shiga gidi na dauko gyaiena bayan na shedawa anti Safara cewar zanje kiran babana saboda wani bako mai irin zanen shi ya zo wai yana son ganinshi ta ce to yi maza ki kira mishi shi nace mata to na fita. Bako da irin zanena ya zo nema? Ya yi min tambaya cikin yanayin murmushi na yi maza na ce mishi ci baba, ya ce to muje gani nan zuwa, na ce mishi to na dawo na cewa bakon gashi nan zuwa na Wuce ciki bayan ya amsa min ta yanayin gyada kai saboda ya riga ya shagala da mu'amalar da yakeyi da carbinshi. 80 Ina daga cikin dacina a zaune na ji isowar babana ssboda kaurewa da yayi da wani irin barbarci na sha jin shi yana furta lcalmomi har da hira cikin harshen nasu idan yaga abolkan harshen nashi amma ba irin na yau ba aa hankali na sake fiitowa daga dakin nawa cikin sanda na leka zauren don in ga melke faruwea mutumin na ganii a tsaye ya saba gorarshi ta ruwa da tun sanda na kai mishi buts ya sake cikata da ruwa alamar tafiya zai yi yayin da shi kuma babana ya bajea kasa yasa hannu biyu yana rike da kafafuwanshi cikin yanayi na bada hakuri. s A Ka yi hakuri Abba Gana ka yi hakuri kar kace zaka tafi nasan nayi maka laifi amma tunda har ka iya nemana to layi halkuri ka zauna. To tayi hakuri ta zauna tayi menene? Ba ta riga ta ganta ba ba shi kenan magana ta kare ba, ai ta ganta taji dadi ta gofe tasan tana raye itace kawai bata je wajenta ba. Gabana ya fadi kar dai dan uwanka ne wannan ga zatona a zuci nake yin maganar ashe ban sani ba ta fito sai kawai naji babana ya ce min, eh Yacuwuna babanki ne wana ne uwarmu daya ubanmu daya, ban san sanda na kama ihu ina buga tsalle tamkar wata zararriya da sauri anti Safara ta fito tana tambayata menene? Ban iya bata amsa ba kartawa kawai nayi da gudu na nufi gidan yaya Dija don in kai mata labarin, gaba daya muka dawo har da yaya Ibrahim da yaran ya kwaso mu a motarshi saboda na sameshi a gidan. Tuni har zaurenmu ya fara cika da jama'a makwabta baba Bairu da baba Hodijo da ma wasu makwabtan sun hadu sai taya babana bashi hakurin ya zauna suke yi, shi 81 kuwa yaja ya tsaya sai nanata kalmominshi yake yi ta riga ta ganta ai ta gode ta ganta da ranta da lafiyarta to inta zauna me zata mata? Ka yi hakuri malam ka yi hakuri ka zauna na rokeka ka yi hakuri, cikin yanayi na natsuwa da girmamawa yaya Ibrahim yake bashi hakurin baba Baidu ya kaelshi ya ce mishi, kayi mana malam wannan mai rokon naka ai surukinka ne shi ne mijin babbar yar taka? Abba Gana yana jin haka jikinshi ya yi sanyi alamar surukuta tana da karfi da muhimmanci a wurinshi, a hankali ya koma kan tabarmar ya zauna sai dai kuma yana zaman sai ya daso ido ya kali mutanen da ke wurin cikin wani irin yanayi ya tambayesu to da da saa ta zauna ta hanata tafiyan nan kam me zata yiwa Bukar ne bayan ta tafi ta barta shekara talatin da daya? Yana fadin hakan ya soma shisshikar kuka shima baban nawa haka, nayi maza na karasa cikin gida da gudu ban tsaya gurin ganin abinda ya ci gaba da faruwa ba. Kafin magariba dai har makwabtas unf ara zirga- zirga a gidanmu kowa ya ji dan uwan malam Habu mai timatir ya zo sai yazo wai ya zo gaisheshi, kowa ya zo ya fita kuma da abinda zakaji ya zo fadi, wanshi aka ce ne ko kaninshi? Abokin magana ya ce a'a wanshi dai sai ace a'a to ai ma yafi malam Habun karfi da kuruciya, a'a ba zai fishi ba barijn gida da dangi wasa ne? Sannan shi malam. Habu wannan ja'irar mata da ya gamu da ita ai sa'a ma akayi da aka sam eshi a haka kasan ba karamin amfani auren nan yayi mishi ba don ma yayi jinya kanan nan ai duk sanadin ta ne duk masifar ta ce ta jawa mutumin nan wannan Wahalar. 82 Wasu kuma suka ce oh ka ji wani abin mamaki wai yana da 'yan uwan shi har da shakikai amma shekara talatin da daya bai nemesu ba ko me suka yi mishi haka oho? Kai koma me suka yi mishi bai kyautawa kanshi ba ko da yake dai ance wai in ka ga bera ya rugo da gudu ya fada wuta to binda ya koro shin ya fi wutar zafi. Daya mutumin ya ce uhun ai gara da kai da kanka ka fadi hakan don ni yanzu babu abinda ke kadani ya razanani in tsorata irin inga yanda mutnae suke wasa ko suke cin mutuncin zumuncinsu sai ince oh oh anya a irin wannan hali da muke zumunci dake kan siratsi kuwa da akace zai rinka fisgo mutanen da suka tozartar da shi a rayuwarsu ta duniya ya rinka jefasu cikin wuta a ranar alkiyama? Rabbi sallim sallim gaba dayansu suka ce amin amin nima nayi maza ciki zamu tsallake makatan na tayasu fadin amin din. Ban taba ganin babana a yanayi na farin ciki kwatankwacin wanda na ganshi a ciki ba rannan cikin zuciyata na ce oh ashe dai yana son 'yan uwan nashi in da suke ne kawai bai son zuwa, ita kuwa baba Lantana wacce itace mai abincin gidan nan nan taki ta tsaya ta yi wani abin arziki sai tsaki takeyi tana fadin, uhun malam wai shi ma nan yana da wayo yaga ya samu zai cusa yarshi gidan masu kudi yaje ya nemo dattijon babarbare wai shi ne wanshi don ya wanketa daga gorin rashin dangi da asalin da kishiya zata rinka yi mata to dadin abin shi ne babu abinda ban sani ba. Dadin abin shi ne babu ta inda abinci bai yi ta shigowa ba daga gidansu Mubarak ma katuwar kula aka kawo cike da farfesun kayan ciki ga kuma tuwo miyar 83 kuka nima a cikin gidanmu nayi mishi burabuskon gero da miyar kuka da naman kaji a ciki na kuma zubawa kowa har da baba Lantana da ta k tsayawa ta yi girkin, Anyi sallari sha'i sanda naji zuwan Alhaji Muhammadu ya zo yiwa wan babana barka da zuwa va kuma dade a wurin suna hira kafin ya yi musu sallama ya tafi. Gaba daya 'yan hira suka watse aka bar babana da dan uwanshi saboda kafafuwa sun fara daukewa alamar dare ya fara nisa gashi kuma lokaci ne na sanyi amma duk da haka baba Abba Gana ya shiga gida ya ki shiga wai shi zauren ma ya isheshi don haka a nan sukaci gaba da zamansu nima nayi maza na hura wuta cikin kasko na kai musu. A haka suka kwana suna hira ba na zaton sun samu runtsawa don sau biyu ina farkawa cikin dare ina jin zancensu sai dai bana gane me suke fadi saboda barbarcinsu suke yi. Washegari da safe daga gidan yaya Dija aka kawo lafiyayyen abin karyawa wanda basu da cikin gidanmu ba kawai har gidan su baba Sumaye sai da aka kai musu. Ina zaune a gefe sai taya babana murmushin da yakeyi nakeyi saboda jin dadin ganin dan uwa da yayi a zuciyata kuma ina tunanin yanda muke ni da yaya Dija haka su ma suke uwa daya uba daya sai dai kawai su maza ne mu kuma mata, ina wannan tunanin ina kuma kwatanta girman al'amarin da ke tsakaninsu sai na ji yaya Ibrahim yana ce mishi, baba ai sai kawai ka tsaya a yi daurin aure kafin ka tafi tunda ita Yacuwunan ai kwanan nan ne za a daura auren nata. 84 Da sauri ya ce a'a a'a a'a ba za ta tsaya a nan ta daura aurenta ba zata kai ta can gida dangi ma ta ganta mijinta tana sonta ta bita can gida ma zata bata in bata Sonta ta zauna ta bata miji a cen shi kenan miji kam tana karewa ne? Duk da irin yanayin da yayi maganar a ciki kowa ya gane abinda yake nuff gaba daya sukayi tsuru tsuru ana kallonshi an rasa mai karfin halin da zai musu maganar tashi ni kuwa ko a jikina ban damu ba don ya ce zai tafi da ni tunda dai babana ya yarda wanshi ne uwa daya uba daya kowa ya gansu tare kuma sai ya yi magana a kan kamanninsu dan uwan babana ne ban damu ba duk yanda yaga dama ya yi dani musamman ma kuma da yace zai kaiwa dangi ni don su kara yarda da cewar shi din ya ga Abubakar yana nan a raye har ga sheda nan ya zo da ita na yarda mai kama da shi karo na farko da na ji wani ya ce wai ina kama da babana. Yaya Ibrahim ya shiga yi mishi kalamai da bayanai na nuna mishi wai ai tunda ya riga ya zo sun ganshi sunji bayanin komai to yana tafiya za su je don haka ba sai ya tafi da ni ba daga zarar an gama bikin zai gayawa angno ya kawo musu ni ko ma mu taho tare dukanmu ai kaga uban angon baba shi baya nan ne ya yi tafiya. Baba Abba Gana ya kalli yaya Ibrahim cikin natsuwa ya tambayeshi, a'a Ibrahimu zata hanata tafiya da abinta ne? Yayi maza ya ce a'a baba ba haka bane. Ya gyada kai tare da fadin, to insha Allahu zata je da 'yan uwana. Ya sake bude baki cikin natsuwa ya ce mishi, to ko zaka daga tafiyar daga gobe ka kai jibi don mu yi shiri mu maida kai gidan. 85 Haka nan ba yanda nayi zaton ganin Gaidan din na ganta ba gari ne babba da ya ci gaba a kan al'amura da yawa musamman ma masarautarsu haka nan zamantaaekwar garin akwai sha'awa a ciki mutane ne masu kula da lamuran addini. Babana yan uwa ne da shi sosai abin har abin mamaki yanda ya iya tsallake yan uwa da dangi masu yawa haka yayi tafiyarshi ba tare da ya taba waiwayarsu ba. Sai dai banfi kwana uku da zuwa garin ba na soma jin labarai iri iri na abinda ya yi dalilin da ya sa babana ya tsallakesu ya yi tafiyarsu, labaran dai iri-iri ne kowa kuma da irin abinda yake fada sai dai wanda nafi kamawa shine wanda matar baba Abba Gana ta bani da kanta wato Kabudi sunan da na ji suna kiranta kenan ita ce ta shedamin cewar su su babana su biyu ne wurin uwarsu daga shi sai Abba Gana saboda ita uwar tasu ta rasu da wuri hasalima bayan haihuwar baban nawa da kadna ne ta rasu, sun fara maraicin mahaifiyarsu baa wani dade ba sai na uba ma ya samesu don haka sai rikon nasu ya koma hannun kanin mahaifinsu wanda ko kadan bai kula ya tsare zumuncin dake tsakaninshi da dan uwanshi da ya rasa ba banda gadonsu da ya cinye tun basu isa komai ba sai kuma suka taso a hannun nashi cikin wahala mai yawa shekara da shekaru dai su ne masu noma mishi gonakinshi da suka taso kuma yaga sun isa munalin aure har wani tsohon aminin babansu da ya rike zumunci ya baiwa Baba Abba Gana auren 'yarshi shi sai ya nuna yarshi da ta soma tasowa yace in ta isa aure ta babana ne tana isa auren kuma sai dan mai kudin 87 garin ya zo ya ce yana sonta sai kawai ya dauketa ya bashi ya ce babana ya yi hakuri ga kanwarta nan in ta isa auren zai bashi itama da ta isa auren sai ya dauketa ya sake baiwa wani da ya zo daga waje ya bashi kudi bai lura da cewar shekara da shekaru babana ke nomoe mishi gonakinshi ba, ana cikin haka ne ya sake cewa an satar mishi kudinshi da yake binnewa a gonarshi a gindin bishiya babu kuma wanda zai yi mishi wannan satar in banda babana don yafi kowa sanin gonar a dalilin haka ne ya yi mishi wulakanci a bainar jama'a, tare da fadin wai tuni dama shi ya gane duk sace-sacen da ake yi a nan gidan dama makwabta ba kowa ba ne ila shi kam haka ya kwace mishi 'yan kadarorin shi da ya yi aikin kodago ya dan adana kwanaki biyu ne kawai da faruwar hakan da safe ya dauki garmarshi ya fi ta kamar yanda ya sabayi kullum sai aka ga shiru bai dawo ba aka bishi gonar ba a sameshi ba sai garmar tashi aka gani a ajiye a kan daukota aka dawo da ita gidan tund aga ranar babu wanda ya sake sa Bukar a idonshi sai ko wannan ganinn da dan uwanshi yaje ya yi mishi, sunyi nema sun yi nema har suka gaji 'yan kwanaki kadan da tafiyar tashi sai ya baiyana kowa ya gane ba shi ne mai yin dauke dauken nan ba dan kanin baban nasu ne da suke kai daya da shi don ko da ya bar gidan ba a daina ba banda haka ma sai kawai aka kama shi da akuyar mutane ya yanka ta ya durata a buhu, hankalin babban nasa bai yi mummunar tashi ba sai da ya ga damuna tazo ya rasa mai nome mishi gonarshi ga kuma dan nashi da surkayen nashi suna kallo lokacin ne ya yi nadama mai tsanani ya yi kuka har ya gaji ya nemi Bukar har ya zama abin 88 tausayi a kan neman nashi ko zuwa akayi aka bashi labarin cewar anga wani mai kama da shi a wuri kaza sai ya debo kudin mota ya ce a tafi a gani ko shi ne sai aje a dawo a ce mishi ba shi bane, sula yi nema har suka debe tsammani, suka hakura sai a 'yan shekarun nan da yan uwan Malam suka yi ta rasuwa sai hankalinshi ya sake tashi ya sake yin niyayr zai sake neman Bukar ko zaiyi dace in har yana raye su ga juna kafin rai ya yi halinsa shekaru biyar kenan yanzu tunda ya koma bai da wani aiki sai na rokon Ubangiji ya sadashi da dan uwanshi in har yana raye in kuwa baya raye to ya nuna mishi wata alama da zai gane hakan don ya samu natsuwar da zai hakura to a cikin hakan ne ya samu labarin anga wani mai kama da shi a can kasar kudu ya shirya ya tafi ya yi iyakar neman da zai yi har ya gaji ya dawo bai sameshi ba wannan fitar da ya yi dai na wannan karon shi ne fita ta uku ko hudu da ya yi sai kuma gashi ya dawo cikin nasara. Cikin natsuwa nace mata, shi kanin baban nasu ya dade da rasuwar ne ya kabidi? Bana shekararshi tara kenan, cikin shekaru taran nan kuwa ba karamin zuba akayi ba a gidan kin ga wancan dakin da wanene da wance a ciki wannan ma da su wanene in takaice miki dai a yanzu daga babanki ne sai dan uwanshi goni su ne manya a gidan shi kuwa goni shi ne dan karami baban nasu kanin wancan da suka taso tare da Bukar. Tausayin al'amarin ya kamani can cikin zuciyata na yi tunanin duk yanda abu ya kai da zai tsakaninka da dan uwanka to yafiya ituce maganin al'amarin tunda in ma baka yi hakan ba watarana sai a wayi agri ba wani a 89 cikinku, sannu a hankali kuma sai dukkan ku ma ku kai ga karewa. Babana dangi ne da shi masu yawa ku san kullum sai baba Abba Gana ya bada umarnin a kaini wajen wasu da ya dace su ganni duk da na gane abu mai zati aka yiwa babana wanda ya yi dalilin barinshi gida babu ma dai irin satar da aka dala mishi don kuws na sah jm manya su na fadin wai ita satar dan halal ma baya yinta to amma duk da baka sai na rinka ganin tamkar da bai yi fushi mai tsanani ba haka da yayi ya tafin ya samu kamar wasu shekaru da basu tsananta ba da sai ya waiwayi dangi musamman ma da yake a can in da ya tafin shima ya samu rubonshi na aure. Baba Goni shima mutumin kirk ne amma da ganin tsarin zarman nasa da baba Abba Gana kasan ba karanmin hakuri yakeyi da shi ba. Wata irin kulawa baba Abba yake yi min amman duk da haka bai hana sanda na kwana bakwai a gari naji hankalina ya kona gida ba kewar mutacn da us baro ta fara damuna babana, yaya Dija da iyalanta sannn a hankali sai naji shima Mubarak ina som ganinshi ban kuma ji hankalina ya tashi na gane har a vanzu da kulım nake kin auren Mubarak ba kararmin son shi nake yi ba don kuwa a ranar da na ji kishin kishin wurin Yatakabudi cewar baba Abba Gana ya ce ba zai sake barina in koma gida ba zai rike ni ne kawai ya aurar da ni a nan don da hakan ne kawai yake ganin zai karfafa zumunci tsakaninmu da yan uwanmu da mu da su ba wan shakuwa muka yi ba tunda in ya aurar da ni a nan to ko Su basu raye zumunci zai dore a tsakaninsu yaya Dija 90 zasu rinka zuwa ko ba don kowa ba don ni su ma nasu ya'yan tunda gani a cikinsu zasu kula da zumuncin dake tsakaninmu da su yaya Dija, kasa bacci nayi kwana nayi rannan ina tunanin duk da tunanin nashi unari ne mai kyau ama anya zan iya zama da wani mijin kuwa matukar ba Mubarak ba ne? Duk wani mutumin da ya taba zuwa wurina kan maganar aurena na amince wani dalili yana hana auren nake mancewa da shi inji garama da ba a yi auren ba ya fiye min in gamu da shima ban yi komai ba saboda bani da wata danuwa gamne da game al'amarin shi amma banda Mubarak, Mubarak ne mutum daya da zuciyata ta kasa daina kishinshi na kasa daina jin zafinshi na kasa fita cikin harkokinshi in daina son jin abinda yake ciki, na kan dai daure in kawar da kai game da shi har in bude baki ince mishi ya fita harkata amma a zahiri ne kawai hakan yake faruwa yana gwada zai fita harkar tawa sai inji nayi matukar takura, dan sa'an da nayi ma shi ne shi din ba wani jarumi bane kan lamarin fita harkar tawa da ban san yanda na rinka ji ba a raina. Kwana biyu bayan maganar da Yakabudi tayi min naje dakin baba Abba Gana da safe don gaisheshi kamar yanda da ma kullum nake yi tun zuwana gidan sai ya zaunar da ni yana yi min bayani game da muhimnmancin yin auren zumunci a wurina ga dan Uwanki nan da na yiwa Bukar takwara da shi don shi ne dan da Kabudi ta fara haifa bayan barin shi gidan sai in hadaki da shi dan uwanki ne amma ba zan yi hakan ba sai na baiwa mutumin da aka gaya min cewar yana sonki lokaci na kwanaki ashirin da dayu in har ya biyoki kafin cikar wadannan kwanakin to shi kenan ke din rabon shi ce in 91 kuwa bai zo ba sai bayan cikarsu ko da da karin kwana biyu ne to ba zai saurareshi ba. Hankalina a kwance na ce mishi to baba saboda ni da kaina na gamsu da adalcin da ya yi na bada wa'adin kwanaki ashirin da daya duk da dai a lokacin ina da waje kwanaki tare ne a gidan. Yan uwan babana sun nuna min gata na zumunci sun martaba zamaa a cikinsu sun kamama bakuntata irin karramawar da har na rinka yin mamaki sai dai duk da haka zuciyata tafi son in koma gida kusa da babana da yar uwata yaya Dija da iyalinta in so kuma shi ne samu to zanso ace na wayi gari a gidan Mubarak a matsayin ni din matrshi don haka sai nayi ta addu'a ya iso Gaidan kafin cilar kwanakin da baba Abba Gana ya dibar mishi na kwanaki ashirin da daya. Ranar da na cika kwana goma sha hudu wato sati biyu cif da zuwB garin Gaidan sai ga Mugaram ya iso babu wanda ya yi zaton ganinshi a lokacin har nima farin ciki irin wanda nayi bai raisaltuwa sai dai ban bari an gane ba. Sub iyu ne suka zo abinda naji ana gayawa Yakabudi kenan sai nayi zaton ko shi da Amiru ne, sai da na shigga dakin da aka saukesu na gansu eai naga ashe ba Amiru bane, rana marya ya dade, inji abokin nashi. Mubarak ya harareshi, kai nan har wani kulata zakayi? Ya yi dariya to ba zan kulata ba me ya kawoni? lta amaryar ma ance maka ta na yin laifi ne? To ai shi kenan tunda a wurinku bata.yin laifi. Na gaida abokin nashi cikin mutunci da girmamawa a hankali Mubarak ya tambayeni, kin ganeshi kuwa? Na 92 gyada kai muna alamar eh, ya sake kallona a ina kika sanshi da kikace kin ganeshi, na yi murmushi kawai nayi shiru, gayamin sunanshi in har kin gane shin da gaske, ban fadi sunan ba saboda in girmamashi sai na ce mishi na taba ganinku tare da salla ka ce min daga Kaduna yake. Ya yi murmshi ya ce, a to ai tace maka ta ganeni kai Icafi so sai ta ambeci sunana ga tsal ita kuma mai kunya ce, to ni shikenan yi ta zugata. Na matsa kusa da kwanukan abincin da na samu an kai musu na soma budewa yallabai ai baku ci abincin ba, bai kalleni ba ya ce, to abinci muka z0 ci sunje sun dauko min mata ba da sanina ba sun kawo min ita nan ni banyi musu muzurai kan abin da suka yi min ba sai su ne kuma wai za su yi min? Cikin natsuwa na ce mishi, too kayi hakuri si kasan iyaye ne. A hankaii ya dago ya kalleni har da shi ma wannan gorin a cilkin iyayen ya kare? Jin yanda yayi maganar a kanshi ya sani yin maza na ce msihi, shima fa kanin babana ne. Ya yi kamar bai sani ba, au haba? Ai na dauka shima yana cikin maneman naki ne? Abdulhamid ya yi murmushi tare sdaa fadin, kai kam Ahamad Ubangiji ya shiryeka surikin naka kake cewa yama cilkin manema. Mubarak ya murtuke fuska ya ce, to menene don ya nema ba 'ya'ya maza suke da babanta ba ta haramta ne a wajenshi? Ai ni wannan mutumin ban yarda da shi ba don bai yi min kama da wanda zan yi surkuta da shi ba baka ga ko kadan bai yi murnar zuwan namu ba? 93 Na kau da kai daga zancen nashi saboda ganewar da nayi bai san komai maganganunshi ne dai kawai na'zato da kishi da ya saba da su na soma zuba abincin da aka kawo musun na mika mishi ya karba ya ajiye a gaban Abdulhamid kafin ya sake karbar wanda na sake zubawa ya ajiye a gabanshi. Suna gama cina bincin Abdulhamid ya mike, kai nifa zan sha iska a waje daga nan inga yanayin wurin, bai jira amsar da Mubarak din zai bashi ba ya ficewarshi. cikin nutsuwa na kalli Mubarak na ce mishi, ashe ka dawo? Ya ji dadin irin karbar da nayi musu ha watakila bai zaci hakan don haka cikin murmushi ya ce min, na dawo na zo ban sameki ba na ce darma ana yin haka ne mace tayi tafiya mai tsawo irin wannan babu izinitn mijinta ba a gaya musu an riga an bani ke ba ne? Gashi anzo suna cewa wai ba za ki bini ba ni kuna na zo ne da niyyar tafiya da ke ban gane abinda suke ba fa ko kin san da wani abu ne? Na ce mishi a'a sai dai a'a da nace bai hanani gaya mishi bayanin da baba Abba Goni ya yi min na ce to amma ai kazo kafin cikar lokacin da ya diban. Ya kalleni cikin nutsuwa ya ce, ke dai kawai ki danyi gaban ki jiramu a kan hanayr can ta shigowa unguwar in muka fito sai kawai mu daukeki mu yi tatiyarmu don in ba haka ina ganin wadannan ba rabuwa da su lafiya zan yi ba. Na yi murmushi na ce, haba yallabai ranka ya dade ai kaima ba zaka so in yi irin wannan salamar da su ba in ka bisu a hankali sai ku daidaita shi baba Abba Gana ai al'amuranshi masu sauki ne gashi kuma mutumin kirki ne sosai. 94 Hira sosai mukayi da Mubarak irin wanda ko da bamu taba yin irinshi ba ko kuma mun dade har na mance rabon da mu yi irinshi, nayi mishi kalamai masu 8aua ya samu natsuwaa tare da shi. In dai sake komawa wuinshi kenan da maganar? Nace mishi eh, to babu laifi bari in kira Abdulhamid muje inda tuntuni haka kikeyi min Meor ai da babu dalilin da zaisa in yi ta sakin baki ina daddankara miki bakaken maganganu, to in nazo da damuwa sai kice sai kin karamin to in ban gaya miki bakin ki ji kema inda dadi ba yaya zanyi? Ban tanka mishi ba na wuce na tafi don su samu damar sake ganin baba Abba Gana. Sai bayan sallar la'asar ya sake aikowa a kirani a jikin motar da suka zo a ciki na sameshi, to mun daidaita da su Maryam duk da dai ba haka naso ba to amma tunda mun ajiye matsayar da muka yarda da ita shi kenan magana ta kare, ya ce a nan zan yi daurin aure a nan zai yi biki saboda ba zai yiwu a ce za a dibi jama'a a je can ba lokacin biki kuma da kyar ya yarda da kwanaki talatin da biyar nan gaba sati biyar kenan sannan wai a nan za a bariki. Na ce to ai kamar yanzu ne sai kaga lokacin yazo, ya ce to yi min wata magana komai kankantarta da zai sa in ji damuwar da ke zuciyata tayi min sauki don bana son tafiyar da zanyi in barki. Cikin natsuwa na sunkuyar da kaina kasa don in tabbatar bai taf ida wata damuwa ba sai na ce mishi, ai ko ka tafi ka barni a nan din ba wani abu bane babu wani abin da zai faru a bayan naka sai alheri, ya ce to babu laifi. 95 Sai bayan tafiyar su Mubarak din ne na gane banda dinbin tsarabar da ya kawo musu har da kyautar manyan kudi ya yi musu ga kuma lissafe-lissafen da Yakabudi tayi mishi nasu a wurinsu ans bada kudin yin lalle da kuma na turare ya tambayi yewan su ta fada suma ya bayar. Sallama mukayi da Mubarak ba tare da ya gaya min cewar zai dawo ba amma sati biya bayan tafiyar tasu sai gashi ya zo shi da Amiru wani sati biyun mns beym nan ya sake dawowa a lokacin nan kawa baifi kwanaki biyar sulkz saura a fara bikin ba. A Ciki wadannan kwanakin kuwa babu abin da Yalkubudi bata yi min ba wanda suke yi wa amarensu ko da yake ma kamar karasawa ne don tafi kwanaki talatin tana min jike-jike, hayake-hayake, tsime-tsimw, gogo goge, gyare gyare, kuilum kuma ta kan yi ne tare da yi min bayami wannan uban zirga-zirga da wamuiea yro yake yi ai gara a kara gyara mishi ke ya sameki.. kin san ance wai ko kana da kyau to ka kara da wanka kar ki yarda ki zauna bakya gyaran jikinki don shi namiji da kike kallonshi.... ta danyi shiru kada katin ta ce, uhuyy ke yanzu yarinya ce ba za ki gane yanda alamarin yake ba tukunna. Ana cikin haka kwanakin biki suka iso jama'a suka yi ta haduwa fiye da duk yanda ake ko daga gida mutanan da sulka zo bikin ko kadan banyi zaton ganinsu haka ba Umman Mubarak, Yakumbo Halima, baba Sumaye, baba Lami, manyan dattawa wannan yan matasa yaran mata kuwa akwai anti Asiya aminiyar yaya Dija da malamata malama Basma akwai yar anti Safara 96 ga wasu mata su uku da suka gabatar min da kansu a matsayinsu ne angwaye alamar ko dai kanne ko kuma abokan wasan Mubarak sai dai ban san ta ina ba maza kam babu adadi don kuwa naji ana ta maganar yawan nasu abokan Mubarak da yawa sun zo daurin auren ga samarin unguwa irin Isiyaku su ma ba a barsu a baya ba don kuwa shi mai mu'amala da na kasa da shi ne abokan babana irinsu baba Baidu da baba Hodijo kasuwar timatir su ma ance mota guda suka zo abin dai gwanin dadi gwanin sha'awa. Ina kwance a dakin da nake zaman lalle ina lullube da kaina na ji an shigo an zo an durkusa a jikina a hankali na bude ido don ganin waye hakan? Inna na gani da sauri na saki wani lallausan murmushi yaya Dija ta zo ne? Ta ce a'a babanmu ne ya zo da mu ni da Abba, sannunku da zuwa na mike na zauna ina nunam ata kwanukan da na san akwai abinci a ciki don taci ta girgiza kai nuna alamar ta koshi. Buki baba Abba Gana ya yi irin wanda yake yiwa ya'yan da ya haifa a cikin shi kona ince fiye da haka dno kuwa yayi hidima ya ciyar da jarna'a abin ba a magana, bayan san kowa daga jama'a ne aka yi daurin auren bai yarda an dauki amarya kamar yanda abokan Mubarak suka so su yi ba sai ya ce tafiyar tayi nisa baza a dibi mutane masu yawaa yi irin wanan tafiyar da su ba a cikin dare. Don haka aka bari sai washegari a waunan lokacin ango baya zuwa wurin daurin aurenshi don haka Mubarak bai zo Gaidan ba yana Kaduna wurin harkokinshi. 97 Washe gari ana gama karyawa akayi ta shiri ana fita don shiga motocinda zasu dibi jama'a ganin da Baba Abba yayi kaiyade masu zuwan zai iya kawo bacin rai yasa shi yin shiru yace su angwayen su debi adadin abinda suka ga zasu iya diba su kuwa su Amiru da Abdulhamid suka ce duk wacce take son tafiya kawai ta fito, mata kuwa sukace me za su yi ba tafiyar ba. An fito da ni aka kaini wurin Abba Gana a lokacin nan kuwa yana tare da dan uwanshi Baba Goni alamar da tafiya ta zo ke nan kuka nakeyi sosai daga kuma cikin zuciyata kukan ke fitowa saboda tausayin abubuwa a yanzu kuma sa naga zaa tafi sai naji bana son tafiyar cikin dangin ubana. Yakumbo Halima ta shigo dakin ga alama kuma kiranta akayi suka gaisa da baba Abba a cikin yanayi na mutunci da girmamawa, kece uwartasu? Tace eh Mallam suka dan yi hira kadan a cikin hirar tasu ta sake jaddada mishi ita da inna mu uwa da uba daya suke ita ta sha nono ta bar mata, to Ubangiji ya jikansu da Rahamarsa in tamu tazo kuma yasa mu cika da imani aka amsa amin amin, to mun gode fa mun gode mun gode yayi ta nanata godiyar tamkar dai wani abin akayi mishi sai da suka soma yi mishi sallama zasu tafi sai ya ce, to ungo ana Kabudi mika musu wannan sadakin da uban mijinta ya zo dashi ne wannan kuwa ni na bayar in kunje ku sai mata abinda kuka ga ya dace Yakumbo tasa hannu biyu ta karba tare sa yi mishi godiya me yawa. Motar amarya itace motar da ta tashi a karshe kenan duk sauran motocin sunyi gaba kafin ita daga ni sai 98 Yakabudi ne kuma a bayan motar yiuyin da Amini da wani wanda ban sani ba suke gaba. Kafceciyar wayar cellular da ke hannun Amiru tayi kara ya dauka tare da anmsewa, ran ango ya dade ban ji abinda Mubarak ke gaya mishi ba na dai ji shi Amirun ayna ce mishi, gabn daya jama'a dai sun taso suna ka hanya amma mu garu nan a kofar gida ba ma taso ba saboda shi warnan baban na ta da kake bani labari ya ki bada ita. s Mutumin dake tukin ya yi murmushi, kai Ahlaji Amiru kar ka se ango ya shide kai in banda Allaji Adbulhamid ya dage ai da cewa ya yi wai shi ma zai biyo mu in yaso ko a Goabe ya tsaya shi nc ya ce sai dai ya taho mu mu zauna. Kai dai muna hanya amma mn biyo bayansu ne, ban san abinda yace ba naji Amirun ya sake ce mishi to amin. Muna zaune a bayan motar ni da Yakabudi bacci takeyi saboda gajiyar hidima da kuma sanyin AC da ya ratsaya, ni kuwa tunanin al'amura da yawa nake yi Innata na fara tunswa 'yar rayuwar da mukayi tare dan sanin da nayi mata mu'analar da nakeyi tunawa a tsakanina da ita, rasuwarta da yanda hakan ya zama sanadi na la'amura masu yawa, zamana da babana, mu'amalar da ta gudana tsakanina da shi, na tausayawva da kulawa har kawo zuwan baba Lantana gidanmu al'amuran da aba Lantanat ayi mana sanadinsu a Zuwanta gidanmu tausayin babana ya kama ko ncc ya kara kamani musamnan da na tuna yanda ya bar gida ya bar danginshi ya fito ya soma rayuwa tare da lanaia rayuwar da da kunnena, na ji shi yana tabbatar mata da 99 cewar ita ce banagre mafi dadi da rayuwarshi ta dandana yazo ya rasata a lokacin da bai zata ba ya yi bakin ciki irin wanda bai misaltuwa bai gama wattsakewaa daga rashinta ba da kewarta ya zo ya fada hannun baba Lantana, alamuran da sukayi ta faruwa har kawo wannan lokacin da muke ciki, wata rana sai labari ai babu wani abinda yazo ya tabbata in dai ba kudurar Ubangiji ba ne, wannan jimlar jimlace da mutane daban-daban suka yi ta furtamin ita a lokuta daban-daban bisa faruwar al'amura edaban-daban sai dai ban taba kawo tsammanin wucewar tasu za ta zo min a haka ba saboda tsananin daci da ciwon abubuwan da sukayi ta faruwar sai na rinka ganin tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin tamkar nawa mas'aloli da damuwowin ba masu wucewa ba ne masu dawwama ne don haka şai na zamo a duk lokacin da wani babba ya tabbatar min da cewar zasu wuce wata zai wuce har ki ganki kina bayar da labari sai in samu kaina da tambayar kaina to yaushe ne? Yaushe ne wata ranar da zai wuce? To gani a yau sai na samu kaina da yarda da cewar tabbas mutum mai gaggawa ne mai sauri ne a kank al'amuranshi, saboda ganin da nayi tamkar daurin aurena da Mubarak da akayi kawai ya kawo karshen al'amuran duka zamana da baba Lantana da ma shi baban nawa a gida daya ya kare, lissafin da ake tayi min na dadewar da nayi babu aure a ce nan kusa babu sauran sa'a ta shima ya kare a yau ni din matar aure ce, matar ma kuma ta Ahmad Mubarak wanda duk kwaramniyar a kanshi aka yi ta yi haka na zurfafa cikin tunani mai tsawo nayi nazári mai zurti kan al'amuran rayuwa da kai 100 kawon al'amuranta abubuwan da na shiga da wadandA idona ya gane min sai na kara tabbatarwa kaina da cewar rayuwar gaba daya wata rana zata kai ga kaaewa, tausayi ya yi matukar kamani har na kasa hana idanuwana zubar da hawaye. Sannu a hankali sai gashi ahr mun iso garinmu har gamu muna shiga unguwarmu, bude ido ki gani Maryan nisan tafiyar da kika sanyamu ta kare gamu mun iso gida, Amiru ne ya ke yi min wannan magana,r ban tanka mishi ba. Babana na hanga a kofar gida cikin kwalliyar da ban taba ganin yai irin ta ba, habbar riga da 'yar ciki da wando ga kafceciyar hularshi ta zanna a kanshi, bakin da ke fita daga cikin motocin dake tsayawa yake yiwa sannud az uwa wadanda yan uwanshi ne da suka biyo motocin amarya sai dai nasan 'yan daidaiku ne kawai zai iya shaidawa a ciki sauran duk sai anyi mishi bayaninsu, tunanin babana ya sake dawomin ban taba yin kwana bakwai ban ganshi ba don ban taba zuwa wani wurin da na bar shi na abr unguwaru da aka haifeni da gidanmu naje na kwana bakwai ban dawo ba, to inama nake zuwa? Gidan yaya Dija ne sai ko Yakumbo Halima da sauran dangin Inna nan din kuwa bana iya zaman da zanyi kwana bakwai nake gudowa in dawo gida sai wannan karon de nayi tafiyar dana kwana sittin da daya. Ganin da nayi za a wuce kofar gidanmy bayan nayi zaton nima a nan za'a saukeni yasa nayi maza na cewa Amiru, a'a a'a ba a nan za a saukeni ba? Gaba daya shi da mai tukin suka hada baki wajen tambaya ta gidanku? Ai furta kalmar na bayar na karar mishi da baba sukayi 101 tare da baba Abba Gana ya rabaki da shiga gidanku ba tare da izinin angon ba yarinya shi kuwa tuntuni aikina jin wayoyin da yake tayi jaddadawa yake yi lalle ne a wuce da ke gida kar a ce za a tsaidake a ko ina, ban san dalili ba ina jin bayanin na Amiru na soma yin kulka hawaye suna ta gudu a kan fuskata, a hakan aka shigar da ni gidansu Mubarak sashin Umman shi aka fara kaini itace ma ta jagorance mu ta wuce gaba muna biye da ita a baya zuwa inda tace can din ne wurina muna tafiyar ina tunanin shekaru biyar ne cif har da wasu watanni ban shiga gidan ba da nake shiga irin shi tafiyar da mukeyi kafin mu isa inda zata kaimin ya sani fahimtari rin canjin da gidan ya samu a shekarun da nayi ban shiga ba. To ga nata wurin nan bismilla ina jin ta fadi hakan na soma karanto addu'o'i iri-iri ko dama can kuwa tun isowata kofar gidan nake addu'ar ban fasa ba man tarar da su anti Kubra, anti Hindu, Hasiya Jibrin da mutane da yawa wadanda ba zai yiwu in yi ta lissafinsu ba, aikin jere suke ta yi daga ganin jama'ar dake wurin dai kai ka san ba karamar gaiyata yaya Dijat ayi ba. Mun kuma shigo. ne muka sama su Yakumbo Halima da su baba Sumaye da suka rigamu isowa suna fadni, kai masha Allahu tubarakallahu Ubangiji ya yiwa Hadiza albarka mafi yavwancin mutanen dake wurin sukayi a amin, amin, ita kam ai uwa ce ba ya ba. Wani daki da babu komai a ciki daga labule sai katifar da aka yiwa shinfida mai kyau aka kaimu ni da Yakubudi ina shiga anti Kubra ta biyomu ta yiwa Yakubudi sannu da zuwa ni kuwa kallona tayi ta tsuke fuska kafin ta ce min, maza share hawaye ki hadiye 102 kukan da kikeyi ya ishen haka na gani a wurin Hadiza jiya tun da akayi waya akace an daura auren ki da Alhaji Ahmad take kuka tun ina rarrashinta ina bata hakuri har sai da ta kureni nayi mata kaca kaca nace ina dalilin da za ki tara jama'a irin wannan ki yi t skuka a cikin su, to maza kema sharesu ni ma ina nan kika tuna in na naki kukan na dadin ganin burinki ya cika ne kin auri mijin da kike so duk daya kar in sake ganin hawaye a idonki Ban tankawa anti Kubra ba iyaka dai dama nasana halinta na kuma san tana cilkin mutanen da suke sen yaya Dija. Hasiyan Jibrin ta shigo na lama ji dadin shigowar tata, kin gani abokan tasowarki har sunyi salla suna cin abinci ke kina zaune wanan doguwar tafiya ai ko mura kike ya rage ga ruwan zafi na zube miki ki yi wanka si ki yi alwala ki yi salla ki dan ji dadi, nace mata to kafin in idar har ta tanadar min abubuwa masu saukin ci wadanda ba za su gunduren da sauri ba irinsu strawberry grabus citrus da apple masu ban sha'awa wadanda ko don kyansu zaka iya 6ata lokaci mai tsawo kana cinsu basu gundureka ba, itama Yakabudi ta kai mata tare da abincinta tana ci ita kuma ta dawo wurina muna hira, ai naso in zo her Gaidan din nayi maza nacem ata gara daa bakije ba Hasiya da Walid yasha wahela tafiyar tayi tsanani da yawa, ta yi murmushi ta Ce, to ba biki uwarshi akeyi ba, na yi murmushi a karo na farko tun bayan da bikin ya fara na ce, ai kuwa da uwar tashi bata kyauta mishi ba don da ta wahalar da shi. Hira kadan aukayi sai naji ta soma tambayata ina ata dai kin shigo ne da shirinki shiri kamar yaya Asiya? A 103 hankali cikin muryar rada ta soma yi min bayani, shirin rike mijinki a hannunki mana ko kin san yau kwana hudu kenan da dawowar uwargidanki daga yaji, gabana ya yi mummunan fadiuwa saboda a anzu zaman lafiya nafi so ba fitina ba, duk da ta gane faduwar gaban da na samu bata yi shiru ba sai ta ci gaba da bani labarin da take son bani alamar dai ta matsu sai ta gaya min, ai rikici mai yawa akayi bayan tafkiyari ta ja ta tsaya kan in dai Alhaji Ahmad zai aureki to ita ya sauwake mata saboda wai kina waje ma baki bar aurenta ya zauna latiya ba balle kuma a ce kin shigo gida gaba daya kuna daga ita har yan uwanta sun mara mata baya.suna fadin ai da aurenki gara a ce wasu kishiyoyin ya kawo mata su zama hudu, wajen kwana talatin ta yi bata nan shi da abokanshi suka yi ta zuwa biko ana yi musu wuiakanci wasu abokanshi har suka fusata suka ce ya saketa ya ce a'a ashi ba zai yi aure don ya rabu da ita ba ne dukanku yana sonku ya kuma yi alkawarin matukar ba ita ta tsoma kanta cikin abinda bai shafeta ba zai yi iyakacin kokarinshi wajen ganin yayi adalcin da zai tsarevwa kowa hakkinshi. Na yi ajiyar zuciya mai karfi ba tare da na ce mata komai ba baya ga Ubangiji ya bashi ikon yin hakan saboda iyakacin gaskiyata nake nufi nafi son zaman lafiya a kan gutsiri tsoma. Sau biyu anti Kubra ta kawo min kan wayar telephone din dake dakin wai in kar6a zai yi magana da ni ban kara ba saboda sai nafi son ya kyaleni kawai in zauna shiru ko zan samu natsuwar da nake bukata a tare da ni, tunda na soma gane cewar nan gidan nashi dana zo ma zai yi wuya in har zan samu zancan shirun da nake 104 Dukata don ina daga kwance na jiwo baba Sumaye tana cewa, kun ga dangin uwargidan nan babu abinda suke nema in banda a yi rikicin da za a yi kaca-kaca a bikin nan to na rokeku kar in ji wani cikinku ya kulasu. Tana fagfin hakan na ji mutanen dake wurin su na ta bayaninai mu ma kaza mu ma kaza tun jiya suke yi. mana wulakanci abu kaza da kaza har suna gori wai.. Yakumbo Halima ta katse masu kokarin yin bayanin kan irin gorin da suke yin tare da fadni, abin dai bai yi dadi ba da kwabar yarsu suka yi suka nuna mata muhimmancin zaman lafiya da yafi musamman ma da yake akwai sanaiya mai karfi a tsakanin mu da su, haduwarsu karkashin miji daya kuma wannan kaddara ce su dukansu biyun matan shi ne in banda haka ai da Mero ya fara aura da ya aureta a wancan lokacin kuma da ba ma zaton zai koma auren 'yoarsu to kaddara don haka mu ba ma fada da ita sai dai mu yi mata addu'a, yanzu ita wacce tayi sanadin abin ina take? Itama ba ance shekaranjiya ta tafi ba itama ta yiwa kanta sanadin nata auren saboda sharrinta, shi mutum duk yanda ka kai da kinshi ai baka iya hana shi samun abinda kaddararshi ta rubuta mishi in da hakan yana yiwuwa ai da auren Mero da Alhaji Mubarak bai yiwu ba. Na zaro ido ina kallon Hasiya Jibrin don son jin karin bayani kan maganar da na ji Yakumbo Halima ta fada na wacce tayi sanadin da aurena da Mubarak bai yiwa ba a wancan lokacin itama ta yiwa kanta sanadin nata auren na kuma san da baba Lantana take nufi, sai Hasiya Jibrin ta gyara zama ta ce min, ei ai ranar da ake shirin tafiya daurin aure baba yasa a yiwa 'yan kasuwar timatir dinsu 105 abinci na musamman ya ce su ci a kuma zuba nmusu a kula a sa musu a motar da suka yiwo shata saboda nisan tafiyar sai baba Lantana ta ce zata yi wannan tana kai kawo tana hidimar girki ana raha ana barkwanci da ita har muna cewa a'a kaga baba Lantana abin mamaki ta sake sai hidima ake ta yi da ita, ashe ashe baba Lantana da abinda ta shirya, kamar baba ya sani ya ki fita daga cikin gidan nan har muna ganin kamar ya daan takura mana ashe ashe in bali labari sai kawai idonshi ya kai kan baba Lantana tana zuba wani abu a cikin abincin nan bayan an gama shi ai kuwa dai nan da nan ya isa wurinta ya tambayeta me take zubawa a çikin abincin? Ta ce bata zuba komai ba ya yi yayi ta ki yarda da cewar ta zuba wani abu ya ce to ta diba tayi nan ma ta ki. Hannu biyu na saka na dafe kaina saboda sarawar da yakeyi a dlai in tsoratar da nayi ban iya barinta ta kai karshen baya iin ba na tambayeta me take zubawa a ciki Hasiya? Sai ca ta kuramin ido kaíin ta ce, guba su ci su mutu ko ince duk wanda ya ci ya mutu, salati na rinka yi ina karawa kr fin daga bisani na shiga yin hamdala ina godiya ga Ub.ngijin da ya yiwa babana wannan rufin as rin bai barta ta ja mana wannan abin akin cikin ba ko me muka yiwa baba Lantana ni da babana ta ki mu irin wannan kiyaiyar? Akmar in tsaya yin wannan tunanin sai kawai ma na kavwar da shi na kalli Hasiya na ce, to sai aka kare a ya ya? Ta ci gaba da takaicin abinci ta kama kuka da zage- zage wai zai kulla mata sharrin da ya saba kulal mata, ya ce a'a ai babu sauran sharri je ki na sauwake miki auren ya isa haka, za ta yi rashin mutunci su Anti Kubra suka 106 fitar da ita daga gidan aka dauki abincin aka je aka tona rami aka juyeshi aka rufe don kar wani abu mai rai ya ci, na ce hodijan na kame bakina nayi shiru. Rannan dai da daddare bacci ya gagara ta yayi gaba daya mutanen dake dakin sunyi bacci amma ni idona biyu. A baya a duk lokacin da na kan zauna in yi tunani a kan yin aure na kan ga kamar yin auren hutu ne amma tunda auren ya gabato ni na samu kaina cikin wani irin yanayi da yanzu da wadannan al'amuran suke ta faruwa sai na gane lalle akwai wani babban al'amari a cikin don haka maimakon in yi ta juyi idona biyu ni kadai saboda bacci ya gagareni sai na koma karanta kalmar Lahaula wala kuwwata illa billa kalmar da Manzon rahama ya tabbatar mana da cewar tana maganin musibu kala daban-daban har guda dari daya babu wato casa'in da tara mafi kankantar musibun nan kuwa shi ne bakni ciki har gari ya waye ban daina ba da na idar da sallar asuba ma komawa nayi na kwanta na ci gaba da karantawa. Ina cikin haka sai ga anti Safara ta shigo dakin da nake nayi maza na mike na zauna na tare ta da murmushi cikinta ya fito ta kuma kyau ba kadan ba. Amarya ta ango, anya da wata amaryar dá ta fiki morewa kuwa Yahcuwuna? Nayi maza na katse murmushin da nake yi kafin na tambayeta, wacce irin morewa kuma anti bayan duk wannan kwararmniyar? Ta ce kin auri mijin da yake sonki ban taba ganin so irin wanda Alhaji Amadu yake yi miki ba kwaramniya kuwa ina ruwanki da ita tunda dai kinyi sa'a Ubangijin mu ya 107 rufa muku asiri ke da babanki duk abinda akayi nufin ya same kun bai sameku ba. Nayi maza na ce haka ne anti, to zuwa nayi yanzu don in ganki in gaya miki kisa hannu biyu ku karbi al'amarin mijinki kar ki yarda ki tsaya sakarci ko tunanin wai ko ke amarya ce a'a yi hidimar aurenki kawai ke ko iya shegen nan amare a yi ta tsiya ana wani iface-iface ban yarda ki yi mishi ba kin ji na gaya miki, hannu biyu na saka na rufe idona tare da fadin ki yi min irin tuwon da kike yi min jiya anti. Zanyi miki ma yafi na jiya dadi ki ci tare da angonki don nasan ba wuya ace ya wuce yau din nan bai dawo ba, kisa hannu biyu ki karbe shi in yaso babu kuma ruwanki da kwaramniyar da take cikin gidanshi kar ki daga ido ki kallesu balle su ganekin san abinda suke ciki, ita mace da kike gani ko wace da halinta tak Zama, nace to na gode anti, tayi min sallama ta tafi har cikin zuciyata sai naji dadin iin kalaman da ta yi min. To haka akayi wunin bikin ranar cikin wani irin cikar da ba zai ki atantu ba ta wurin mu ma dai muna da yawa ga yan uwn babana da suka rakoni daga Gaidan ga dangin Inna ta wadanda su ma masu yawa ne babu laifi ga gaiyar yaya Dija na kawaye da dangin mijinta masu kara nan gidan su Mubarak ma ba a magana uwargida kuwa kai kace tamkar da gadara yan uwanta suka zo don su nuna su din masu yawa ne. A wancan lokacina marya 6oye kanta take yis aboda k unya da kawaici ba kamar yanzu ba da amarya ke kai kawo a tsakanin yan bikinta sai dai hakan abi hanani tsala ado, wuni nayi ina kwalliya ta burgewa kwalliya 108 kuma mai tsada da kowacce nayi sai kaga kamar kar in cireta saboda ina tare da gwanayen kwalliyar irinsu malama Hindu da malama Basma ga uma anti Asiya wacce ita dama babbar sana'arta kenan gyaran amare ciki da waje, in nace ciki da waje kema sai ki gane abinda nake nufi. A gaba daya sashinmu a wancan lokacin bakina ne bikin farko da mutanen mu suka sheda video coverage ana daukar su ana kuma yi musu tambayoyi, me zaku ce game da wannan aure na Alhaji Mubarak da amaryarshi Maryam? Wasu su yi magana wasu kuwa kunya da rashin sabo ya hanasu cewa komai in banda kyalkyalewa da dariya wasu kuwa da abin yayi matukar burgesu duk da sun kasa cewa komai fadi sukeyí yau ku zo ku gani bin mutnae akeyi ana yi musu tambayoyi da irin abin nan na masu rahoto. Malama Basma itace tayi magana ta ilimi har ta samu jan hankulan mutane gaba daya aka koma sauraron bayanin nata tayi magana ne a kan matsayin aure da kuma' menene kishi a musulunci, tayi magana sosai ta kuma karfafa magangnaun nata da ayoyi da hadisai tare da kawo misalai na manyan mata magabata yanda suka tafiyar da rayuwarsu tsakaninsu da mazajensu da kuma kishiyoyin nasu duk da ba wai basa kishin bane ya sa suka yi hakan a'a sai dai su fahimtarsu a kan kishin daban mu ma a yau tamu fahimtar daban. Da ta kawo karshen jawabin nata sai tace ya ku yan uwanam ata ina kira garemu da mu yi gyara a kan yandaa muke tafiyar da al'amuran da suka danganci kishinmu a yau mu daina kishi na jahilci kishi na rashin sanin ya 109 kamata mu koma yin kishi irin na shari'a wanda shi ne ibada. Wassalamu alaikum wa rahamatullah, gaba daya wuri ya kaure da kabbara malama Ubangiji ya saka miki da alheri abinda kowa ke fadi kenan. Ana gama wannan aka shiga yin hotuna wai duk ribibin da kaeyi nayin hotuna da amarya ita Rumasa'u da kyar ta yarda aka yi mana hoto guda daya ni da ita da aka kawoni dakinta kuwa kamar yanda aka saba bisa al'ada na kai amarya wurin iyayen miji da uwargidanta in har tana da ita yan uwanta basu ji kunyar fadin babu wata amana tsakanina da ita ba tundai ta din ba wan girmana tayi ba banda haka kuma ai banbancin dake tsakainta da ni kadan ne iyaka ita tana ciki ne ni ina waje ba manyan dattawan da suka kaini ba wadanda shekarunsu suka kai fassara musu al'ar ari ko da kuwa da kafa ka iadeshi ba da baki ba ko ni da nake lullube a gabansu na gane abinda suke uui, to balle kuma su a haka muka tashi muka fito aka dawo da ni dakina tunda dama sai d aka kaini wurin Umma kafin a kawo ni wurinsu mun dawo' daki nuka ci gaba da harkokinmu sai a wata yar uwarta ta shigo wai ga kudin sayen bakina marya an manta ba a bayar ba, anti Astya ta ce, aki haba a1 babu komai mayar masu kawai, ita wannan amaryar ai ba sai an sayi hakinta ba. Ana cikin haka aka soma rade-radin ango ya dawo ango ya dawo kan kace meye wannan har labarin ya bazu ko ina ango ya dawo, ai kuwa dai dama na san da kyar ace bai dawo ba yau, kai wannan ango da zumudi yake, maganganun mutnae daban-daban ne wannan. 110 Kan kace meye wannan sai na jiwo muryar tsiyaku a falo yana gaida jama'a, wani abu kake so ne suna tambayarshi ya ce a'a yalla6ai ne ya ce in shigo in gani in mutane sun danyi sauki ya shigo, ata mai iya shege ta ce mishi, jeka ka gaya mishi bamu yi sauki ba muna nan cike a wurin. Gaba daya suka kwashe da dariya suna fadin, ke dai baki da dama, ita kuwa tana dariyar tana fadin, a'a to haka kawai da rana tsaka ba zai jira abokai su kawoshi ba? Ba fa saurayi bane ta ce, eh ko ba saurayi bane ba zai shigo yanzu ba. Wajen karfe hudu da rabi aka soma walimar maza a masalacin unguwarmu wanda dama yafi kusa da gidan Alhaji Muhammadun don shi ya gina shi walima sosai aka shirya don saniya sukutum aka yanka dominta banda ciye-ciye da abubuwan sha iri-iri malamai kuma daga wurare daban-daban aka gaiyatosu. e Ana cikin haka Isiyaku ya sake shigowa falon, wai ina anti Asiya, tayi maza ta ce mishi gani nan, wai ince miki in babu matsala yana so ya shigo. Ta ce, to to kaje ka ce mishi ya danyi min hakuri kadan, Isiyaku yana fita ta mkie tace, kai jama'a surukuta fa ba wasa bane bikin nan ai munyi shi mu dan ragu mu koa gidan Hadiza, wasu suka ce ka nufi gidanka ma kai ai yamma ta riga tayi, a can gefe kuma wasu suna Rorafin wane irin rashin hakuri ne wannan ko bai yi hakan ba ai za a tafi a bashi wuri. Isiyaku ya sake shigowa, anti wai gashi duk wacce zata tafi a bata atamfofi ne wadanda akayi don bakin, hoton ango da anmarya ne a jiki da hakan ya kashe bakin mitar da suka soma yi mishi nan da nan aka shiga rabo, 111 bayar kowacce ta karba sai ta wuce ta tafi tana murna da godiya da fatan karin budi haka a dawo suna ana facin amin amin, kafin karfe shidan yamam sai ya zama babu kowa daga ni sai Hasiya Jibrin sai ko ita anti Asiyan saboda suna kokarin ganin komai yayi tsaf, a haka kuwa Mubarak ya shigo ina jin gaisuwar da ya tsaya yi da su nayi maza na jawo gyalena na lullube kaina, yana shigowa bai tsaya yin komai ba ya durkusa a gabana ya sa hannu biyu ya yaye lullubin gyalen nawa ya sake sa hannunshi na dama ya ture dankwalin dake kaina kafin ya sake sa hannun nashi ya damki gashin da ke gaban goshina ya iike amma ba damka mai karfi ba, addu'o'i yayi ta karartawa sai da ya gama ya tofa min a fuskata sannan ya mike ya fita, yana fita anti Asiya ta shigo tayi min sallam ta tafi sai muka zama dagı ni sai Hasiya Jibrin mai ji an mijinta ya zo daukarta ita ce ta kara gara min komai ko ina ya zama sai kamshi yake yi kasancewar ilama ta samu wata a gida su ma kuma suna fafatawa ya a iayi te hapi shawarwarin da take ganin tamkar za su yi min amtsni na ce kai ai dai Hasiya nafi son zaman lafiya a kan rikicin nan ni yanzu ba na son bacin rai na ri za na gaji da shi, ta ce to ai bashi da dadi ni su din ne gadara ne da su sai su rinka fadin mai mazansu aka aura, nayi daríya kawai bance mata komai ba. to Kafin a yi sallar magariba shigowar ango biyu shi ne ma ya bada mtoar da ta maida Hasiyan gida tare kuma da yi mata alheri. Yana idar da salar magariba ya sake shigowa, kin yi salla ne? Yana daga tsaye ya yi mint ambayar na ce 112 mishi eh, ya ce to bari in koma wajen wa'azin nan kar su Abdulhamid su sani a gaba don ba wani kirki ne da su ba ga sa ido, na yi murmushi na ce mishi to, amma ai kin san in anyi sallar ish'ai zamu shigo tare da su ko, zasu rakoni sayen bakin amarya, ban ce mishi komai ba ya sake juyawa ya fita, ni da kaina tunani nake yi cikin zuciyata ina tambayar kaina kot a ina yake biyowa yake wannan zirga-zirgar oho? Ko da yake Mubarak bai bar kawaen da na zo da su daga Gaidan sunz auna ba sai ya ce aje da su in gari ya waye zaije ya yi sallama da bakin gaba daya zai hada har da su ni kadai din sai nayi shiri na tunda ashekaru baya can na taba yin kawancen su Jumare su Hasiya Jibrin, na kara gyara kaina ko da dai dama akwai kwalliya mai kyau nake wacce kuma ban dade da yinta ba ga kuma kanshi mai dadi a tare da ni. Ina jin sanda suka shigo falon saboda sallamar da suka yi sai dai ban yi musu amsawar da zasu ji ba daga falon suka zauna a kan kujerun dake wurin, to ina amaryar take? Kai Alhaji Ahmad to ka kori 'yan matan amarya yaya za a yi a sayi bakin amaryar? Maimakon ka barsu in munzo mu maidasu? Ai sai ka fito mana da ita. Mubarak ya leko dakin da nake a takure cikin lullu6i zo ki basu ko ruwa ne Maryam in kuma da wani abu ki hado musu, ban yi musu ba na tashi na shiga kicin na shirya musu 'ya'yan itace a plate daya sai da na cikasu da nau'o'insu kala daban-daban sannan na cika wani plate din da kayan tsarabar amarya na zuba soyayyan naman rago da yaya Dija ta sa a kawomin a wani plate din na hadasu kan wani madaidaicin tirem ai kyau na 113 kawo musu, maimakon in yi shiru kawai in ajiye musu sai na manta na kara gaishesu, Mubarak ya ce, shi kenan ta hutar da ku sayen baki, Abdulhamid ya ce, a'a a'a kai kayi mata wayo ka korar mata kawaye ka kuma sanyata aikin da yayi dalilin da ta yi magana don haka ga kayan sayen balkinta nan turarurruka ne akwati guda muka kawo mata ta yi ta fesawa tana yin kanshi. Sunkuyar da kaina kasa nayi nayi shiru tare da kasa rufe fuskata da gyalen dake hannuna saboda kunya, Ubangiji ya zaunar da wannan aure naku lafiya Maryam ya kuma sanya albarka mai yawa a rayuwarku, gaba dayan maganar Amiru kenan yayin da Abdulhamid ke fadin, amin amin. Kawo ledoji in akwai ki juye musu kayan su je da shi can, ban yi magana ba na tashi naje na kawo ya juye musu suka yi min addu'a suka tafi, shima ya bi bayansu don rakiya da kuma zama wurin wa'azin da akeyi, ina jin duk karatunad akeyi har aka kai ga gamawa malamai suka yi addu'o'i ga kasa, jama'ar kasar, al'umarm usulmi da kuma ango da amarya, ina jin hakan na tabbatar ya kusa shigowa don haka nayi maza na jawo gyalena na kudundune a kasa na rufu da shi na daddanne ko ina ina jinshi ya shigo yanakiran sunana Maryam, Maryam, to wai-ke ya ce miki amarya tana yin bacci ne tun kafin angonta ya shigo, ban motsa ba shima bai tsananta ba sai ya juya ya fita, motsin ruwan da naji ya saa na gane wanka yake yi, ya sake shigowa dakin Maryam, sau daya kawai ya kira sunan nawa sai kawai ya sunkuya ya sa hannu biyu ya sureni ya nufi falo da ni, ke ance miki amarya irin ki tana da wani lokaci ne na yin bacci a 114 darenta na farko? Muje ki biyamin karatunki in ji, doguwar kujera ya nufa ya zauna ya mike kafarshi guda daya a kanta ya zunar da ni a kan cinyarshi ya sake dauko daya kafar tashi ya dora a jikina nayi matukar takura da hakan da ya yi min saboda kunya da rashin sabo bana zaton a tsawon dadewar da nayi da shi ya taba taba jikina da nufin shi in dai ba a kan wani dalili mai karfi ba shima a wancan lokacin ne nan baya ba a wannan karon ba, a yau din kuma da ya dorani a hakan rigar baccin da ke jikinshi mai igiyoyi ce ko tsayawa daureta bai yi ba sai dan gajeran wando kirjinshi gaba daya a bude yake har zuwa kan cibiyarshi hannu biyu na saka na rufe fuskata yayin da jikina ke ta faman bari. sWai ina kike kokarin zuwa ne? Da kike mutsu mutsun kwacewa, ya sa hannayenshi duka biyu ya cire nawa da na rufe fuskata da su ban yarda na bude ido ba balle in ga yanayin da yake ciki sai kawai naji ya dora bakinshi a kan nawa, gaba daya ya kidimani ya sanyani na shiga wani hali da ban ma san yanda zanyi in kwatantashi ba sai dai kuma nasan babu mamaki ya samu kanshi a yanayin da ya wuce wannan don sau biyu zuwa uku yana cewa me za ki ci Maryam, ga abubuwanci na kawo mkiki kin san bai kamataki kwanta baki ci komai ba, sai dai ya kasa sakina balle in iya ganin abin da yake cewa ya zo da shi din bale har in iya samun zarafin da na iya kai wani abin bakina, yanda ya fito da ni falon adauke haka ya mike ya sake maidani dakin a dauke ya dorani a kan shimfidar,a jiyar da na bari wurinki za ki bani, kyautarda kika dade da yi min nake so in karba a yau, a kankame nake a jikinshi yake wadannan kalaman 115 ina jinshi ban tanka ba ban kuma motsa daga yanayin da nake ciki ba sai na ji shi ya soma cewa. Yi min wani alheri guda daya mana Maryao so nake ki martaba min irin martabawar da kika yi min a wancan ranar da wancan lokacin tashi ki sa hannuki rage min wadannan kayan na jikinki da kanki karki barni ki ce sai dai ni inyi yi min wannan alfarmar don in kara jind adi in kara farinciki zuciyata ta kara gamsuwa kuzarina kuma ya karu saboda na san zan karbi ajiyar tawa ne in. karbi kyautar tawa cikin yarda da gamsuwa da amincewarki ba tilastaki zanyi ba. Yana gama fadin hakan na mike na zauna na sa hannu na soma cire kayan da ke jikina da kaina yana karbar su yana yin jifa da su ba tare da yana lura da inda suke tafiya ba, sannu a hankali har na cire duk wani abin da nake sanye da shi saura rigar nono na maida hannayena baya da nufin in balleta itama kowa ya huta, sai naji ya ce min uh'uh Maryam bar min wannan in karasata da kaina, ai ko a wancan ban barki kin cire ta ba, yana daga kwancen ya miko hannayenshi ya balleta itama ya yi wurgi da ita komai naki yana nan tsaf Maryam kamar yanda na fara ganinshi sai dai ma kyau da kwarjini da suka kara. Zai yi wuya rannan in har akwai wani wuri a jikina rannan da Mubarak bai yi mishi irin abinda yake ganin shi ne ya kamaceshi ba saboda wani irin yanayi da ya samu kanshi a ciki na kidima tamkar dai ace bai taba sanin wata mace a tube a gabanshi ba tsawon rayuwarshi sai a wannan ranar. 116 Gyara ki ji dan tsaya ki ji abinda zan gaya mia taimakeni ki karantamin wannan addu'ar don mu karantata tare da ke.... ya soma karantota ni kuma nayi maza na sake maida tafukan hannuna a kan fuskata na rufe saboda tsananin kunya da nauyin da ambatonta a bakina ya yi min, sai dai nayi dabara na karantata cikin zuciyata... Waiyo Maryam, waiyo Maryamu, Wayyo Mairona, bani da nake wahala da hakuri da juriya a dalilin shi ce nake furta kalmomin ba shi da yake yin yanda yake so ne kuma yake furta kalmomin da yake so ban iya ce mishi komai ba... Nace in sonki Maryam nace ina sonki kin ji abinda na fada ko ba ki ji ba? Ba dai ke burinki ince ina sonki ba? To sau nawa yau kike jina ina furta miki wannan kalmar? Maganar yake yi cikin yanayi na jaruntaka saboda gajiyar da ke tare da' shi da dai ace so shi ne samu da shiru ya yi ya yi baccinshi don jikinshi ya samu hutund a yake bukata, ni kuwa ina jinshi bance mishi yi shiru ka huta ba saboda gani nake nima tamkar bai yiwa nawa jikin irin adalcin da ya dace ya yi mishi ba. Washegari da safe ni kan farkawa nayi a makare saboda bude ido nayi na kalli agogo hannunshi dana gani kusa da ni na ga karfe shida ne har da mintoci guda biyar na mike na shiga bandaki nayi wanka sosai na yiwa jikina duk wani abinda nake ganin zai taimake shi nayi alwala na fito ina cikin yin salla ne na ganshi ya shigo dakin ya koma gefen gado ya zauna sai da na idar na shafa addu'ar da nayi sannan ya mika hannu ya sake kamoni ya dorani a kan cinyarshi kamar yanda yayi min 117 Jita, saukin abin kawai babu irin mas'alolin jiyaa tare da shi banda haka kuma a yanzu yana sanye da sabuwar jallabiya ne da ta saukar mishi har idon sawunshi. Kin yi min addu'a kuwa? Na gyada kai a hankali nuna alamar eh, don kuwa ban tashi a wurin ba sai da na yi mishi, ya ji dadin amsar da na bashin, cikin natsuwa ya ce min addu'o'i masu yawa nayi miki Maryam na kuma yiwa Inna. Muka dan yi shiru kafin ya kawar da shirunda tambayata me kike so ki ci yanzu nasan kina jin yunwa musamman ma da yake kin kwanta ba ki ci komai ba, ban yarda mun hada ido ba na ce mishi nafi so in yi bacci. Ya yi maza ya mike na kwanta ya tayani gyara kwanciyar sai da na ce mishi ya yi sannan ya fita ya ja kofar dakin wai don in kara samun nutsuwa. Na farka ne ina tunanin lalle nayi bacci saboda yanda naji yanayin jikina ya canza ban dade da farkawa ba na soma jiwo muryar Mubarak a falo yana magana da wata da nake zaton Umminshi ce. To ko Maryam ce kadai a gidan yau kam ai ab za ta yi girk ba, 8in ta ga dama tayi in bata gani ba ta bari duk abinda take ganin kamar in tayi ita ta yiwa ta bari ba ita na yiwa aurena ba. Ban ji maganar Umman ba saboda muryarta ba mai karfi ba ce kamar tashi sai na ji shi yana cewa, eh Umma dukansu nawa ne na kuma yi alkawarin yin adalci a tsakaninsu, to amma yana daga cikin adalcin ne ace don na kwana a dakina marya jiya ace yau ta fito ta yiwa mutanen gida girki? Banji abinda tace ba na sake jinshi ya ce, a'a Umma ku yi hakuri kar ku roketa na gaji da 118 rokon da ake yi mata in dai alfarmar yiwa Maryam girki ne kar ta yi bana so. Assalanmu alaikum, wata sassanyar murya ce na ji tayi sallama na kuma ji dadi saboda na gane mai ita, a'a Ramatu ce Umman ce ta fadi hakan ta amsa eh ta soma gaisheta kafin naji tana cewa Mubarak sannu kawu, ya amsa tare da amsa gaisuwar da take yi mishi, yaya su babanki da antin, tace sunce a gaisheku. Ban san me ya gani ba naji yana ce mata, ai tana bacci ne, cikin ladabi ta ce msihi ba dakin zan shiga ba zan shiga kicin ne in ajiye kayan da nazo da shi ya ce mata to. Tana shiga kicin din naji motsin ruwa ya fara zuba a fanfo na tabbatar zata gyara wurin ne tayi wanke wanke, Inna yarinya ce da yaya Dija ta yiwa tarbiya iyawar iyawarta aka kuma yi dace ita din mai daukar tarbiyya ce. Tashi nayi na shiga bandaki na sake watsa ruwa a jikina an fito na zauna nayi shafa nayi kwalliya da wani lallausan leshi na sanya 'yan kunne da sarka na zinarin da ake yayi loakcin me ludayi nayi matukar yin kyau ga kashi na fito na tsaya a bakin kicin din ta juyo ta kalleni saboda motsin da taji cikin natsuwa ta soma gaisheni mama ina kwana? Na ce mata lafiya Inna yaya su Abbati? Ai da wai zasu biyoni Mamanmu ce ta hanasu zuwa to a kan me? Na yi tambayar daidai na shiga kicin din na dauko kwalbar zaitun da cokali na dora kan dan karamin tire saboda hangen Mubarak da nayi a falo a mike kan doguwar kujera a hankali na ma tsa kusa da shi na durkusa cikin nutsuwa na tambayeshi, kana bacci ne? 119 Ya yi maza ya bude ido ya kallen, uh'uh ina jiran farkawarki ne, sai dai kuma idanuwan nashi sun canza launi watakila bacci gami da gajiyar hidimar da akayi watakila damuwa ko bacin rai. Ba ki karya ba, kai kaci wani abu ne? Uh'uh na fara mikam ishi robar ruwan swan, ya ce a'a na sha ruwa na ce to ungo zaitun magani ne bai yi musu ba ya karba ya ci kwaya uku, wai me za ki ci ne? Na danyi murmshi kafin nace mishi, me yasa ka damu da yawa, a daki na fa nake maganar tayi mishi dadi ko kina dakinki ai ke din bakuwa ce Maryam ban amsa ba na mike na shiga kicin don nasan ina da wasu abubuwan a ciki sai kawai na ci karo da kayan da Inna ke cewa zata ajiye sinasir ne da miyar taushe da ya ji kayan ciki a ciki da kashi na bude oven na sa kwanon farfesun kajin da tun jiya ta aikomin da shi ban samu naci ba ga kuma gasassun kajin da shi Mubarak din ya shigo da su bai barni na tabasu ba, nan da nan na kewayeshi da abubuwa iri-iri kasancewar kuma dama na riga na saba da cin abinci a gabanshi sai kawai na zauna muna ci tare, ga dukkan alamu kumna dadi ne ya kamashi watakila ya ga alamar in ma so ake a takurashi kan abinda zanci to zai iya samun sauki ta wurina tunda zan iya kula da kaina kina nufin duk da bakuntar dake tare da ke zaki iya hidimominki? Cikin natsuwa na ce mishi me zai hana? To yi min wani alkawari man Maryam, a hankali cikin natsuwa na tambayeshi kamar wanne fa? Tsareni yayi da idanuwanshi kafin ya ce min,n a zaki barni in zauna lafiya za ki barni in samu natsuwa a tare da ke, na zaki 120 barni in yi hukunci da duk wani abinda kika san nawa ne, Za ki taimakeni in fita daga mas'aloli in har ina cikin su. Ban kalleshi ba na ce mishi in har kayi min bayanin yanda zanyi in yi maka hakan ina ganin kamar zanyi amma yanda kayi min maganar a haka ai ba zan gane abinda zanyi ya zama D8 1ya yi maka wadannan abubuwan ba. Yana kallona ya ce min, ki taimakeni ki yarda in na saki iki yi in na hanslki ki cikin sauki na ce mishi zanyi saboda ba tare da na tsaya yin wani tunani ba saboda yaya Dija da sauran mutanen da suke ganin sun isa su gaya min inji sunyi ta gayamin cewar in ya hanaki ki bari in ya sa ki i yi shi aure da kike gani ba komai bane face ladabi da biyayya sai ko mututnawa na ce musu to don haka hankalina a kwance na ce mishi to kamar yanda Suma na gaya musu. Wanka yayi ya tsalo wata irin kwalliya da zan iya cewa ban taba ganin yayi kyau irin na rannan ba ya wuce can cikin daki, zo mana, na tashi na bishi ina tunanin ya yi kiran ne don ina tare da Inna. Wannan hular da wannan wacce ya fi kamata in saka? Na reba kallo tsakanin hulunan duka biyu kafin ance mishi, wannan bai sake dubava ba ya sanya wacce nace din. Me da me kike so a kawo miki? Na gane abinda yaken ufi na ce ni fa nafi so in yi girki da kaina, kina amarci kina girki? Ba a yin haka abubuwa sai su yi miki yawa, ki kwanta ki yi bacci ki huta, nace uh amma ai Inna tana nan za ta yi min aiki bai sake magana ba kudi ya cire ya ajiye a gefen madubi, zan turo Isiyaku ki yi 121 mishi lissafin abinda kike so a kawo miki, nace mishi to a dawi lafiya, ya ce Ubangiji yasa ya fita. Kudin da ya ajiye din masu yawa ne sosai har Zuciyata tana tunanin me zan saya da su haka? Ina zaune ina jiran zuwan Isiyaku cikin tunanin ko dai bai ganshi bane ko kuma ya manta ya yi tafiyarshi? Sai ga Isiyakun ya shigo da manya manyan ledoji a hannunshi kicin ya wuce ya ajiyesu na ce mishi, kai Isiyaku ba nice mai girkin gidan ba kai musu can, ya ce a'a nan ya ce in kawo wadannan ga nasu can a waje na ajiye musu, Inna nasa ta duba kaji ne da koda, sai kayan ciki da kuma sauran abubuwan da zan nema ba tare da na tambaya a gidan ba na dawo na zauna ina tunanin a yanda zanyi da aiki irin wannan na sani da bance mishi zanyi ba saboda dai karfin hali kawai na ke yi nake daure amma gaba daya jikina ciwo yakeyi sai ga anti Kubra ta yi saliama ta shigo bayan na ji ta tana gaisawa da Rumasa'u a tsskar gida ina ganinta naji dadi ya kamat sannu a zuws anti, sannu 'yar albarka ke dai ai daga gidan Hadiza nake ina can sai ga mijinki yaje kunyar ambatonshi a matsayin mijina ya kamani saboda yanayin da take magana a cilcin nashi yaje ya kai mata fan hamsin ya ce ta sailami duk wasu baki da suke nan daga wurinta har zuwa gidan baba ya kuma sake bada jakar guda ya ce a sai miki abinda aka san zai yi miki amfani don ya tambayeki kin ce ba kya son komai. Kunyar anti Kubra ta sake kamani na sunkuyar da kaina kasa har na kasa dagowa, ato ina masu cewa ita tana aiki ne kawai ke kina waje yanzu ai tun a wajen ana 122 tare ne kawai ba komai ake yi ba? Shiru nayi ban iya ce mata komai ba. Itace ta sarrafa duka bubuwan da ta samu an kawo din ta adana na adanawa ta girka na girmawa irin kayan shan farfesu ki sha romo sosai saboda kula da jikinki bayanin take yi min bayam ta titsiyeni na ci na sha adadin da yake nema yafi karfin cikina, ai garama da tayi miki haka mu kishiya wacce iin yunwa ce bata gana mana ba ga abin nan a wadace amna bata sarrafa shi ba balle ta baka sai ita da 'ya'yanta ta san hikimar da tayi ki kula da kanki na gaya miki ki ci gasasshe nama ki sha farfesu ki kuma hora kanki ba yanda za ki citu ba kama hanya a tafi ta bar Inna tana gyaran wajen. An idar da sallar azahar Mubarak ya shigo baba da yaya Dija suna gaisheki naje na yi musu bangajiyar baki, nace ina amsawa ya ka barosu? Lafiya ni zan kwanta ko za ki zo mu je tare? Na ce uh'uh na nuna mishi Inna da ke kici bai yi magana ba ya wuce ya shiga daki sai wajen hudu ya fito. Rannan da daddare mnuna kwance a gadon mu gwanin dadi yana manne da ni a jikinshi hira yake yi min yana bani labari baki sani ba Maryam a hankali na tambayeshi menene, cikin nutsuwa ya ce min, sai in rinka ganin tamkar a mafarki nake sai na ganki a zahiri ko na jiki a jikina sai in gane ba mafarki bane, sai in tuna lokacin da baba yake lallashina yana gaya min cewar in matarka ce zaka aureta wani ai baya auren matar wan ashe ashe ashe kuwa haka din ne, a hankali cikin natsuwa na ce mishi baban? Ya ce eh mana ance miki ni na iya irin wannan noke noken ne irin naki? Kana son 123 abu kana kaiwa kasuwa? In banda na nuna mishi zahirin al'amarina zai yi ta wannan zirga zirga ne da ya rinka yi ke fa kina jin yanda nake ji ko na rinka ji, gaya min gaskiya sau nawa kika taba yin mafarkina? Ni bana Rarya maryam bana kaiwa kwana ashirin ban ganni tare da ke ba a taccina har na rinka sanmun mas ala na wankan da nakeyi ban san dalilinshi ba na yi kamar ince ishi ai nima ganin nake tamkar mafarkin nake yi sai na fasa neyi maza na ja bakina na tsuke, a hankali kuma sai na ce mishi to mu yi bacci mana yallabai ko zaka samu ka kara wattsake gajiyarka. Kwanaki uku a jere ni nake hidimomina ni nake yin girkina babu fashi kuma kullum yaya Dija zata aiko min da abin karyawa mai dadi da gamsarwa Inna zata zo tayi min duk aiyukan da suka dace ta kuma tayani hira sai lokacin makaranta ta yi shiri ta tafi in ta taso ma nan wurina zata sake dawowa haka shima Isiyaku kullum zai kawo min cefane.. Rannan na cika kwana hudu cikin daki ban ito ba saboda ajiyar Mubarak bai yarda munyi irin kwanciyar da muka yi a kwanak biyun da suka biyo bayan daren angwancinmu ba ina jin sanda Inna ta shigo ta gama abinda zatayi tazo ta tsaya daga bakia kofa ta gaisheni ta ce min zata je makarantar allo ta dawo na ce mata to kin karya ne? Ta ce eh nace to sai kin dawo, ina cikin hakan ne Mubarak ya sake shigowa dakin ko za ki zo muje can wajen Rumasa'u mu karya, kamar in ce mishi tuntuni bata kirani karyawa ko cin abinci ba sai yanzu da na riga na zama 'yar gar? Ban iya yin hakan ba na ja, bakina kawai na yi shiru. 124 Ya nemi wuri a balkin gadon ya zauna, bana so wata mas'ala ta taso ace ta wurinki ne Umma ta kirani ta ce min wai anyi mata fada taji kuma zata gyara kuskurenta, don kar in yi musu da shi ya sa na tashi na dauki gyalena na yafa a kan doguwar rigar da ke jikina na bi bayanshi zuwa dakin nata na kalli zirga-zirgarta na gaisheta kafin na nemi wuri na zauna a kan shimfidar da na samu ya riga ni zama. To ki yi ki kawo mana. ruwan zatin mana, ya yi magana saboda ganin bata gama kammala abubuwan ba, ta ce to ta kawo ta ajiey taje zata zauna kadan ta rage ta hau kan cinyar shi in banda ya yi hanzarin kawar da jikinshi ina jinda nan din ta zama, nan da nan naji zuciyata ta yamuise wani bangaren na ta ya rinka rayamin cewar so take ta una miki cewar nan din wurin zamanta ne kokari mai yawa na yi kafin na dawo da kaina ga natsuwata nan taek kuma nayi ta tunawa kaina da cewar matarshi ce matar sai ce a hankali na zuba ruwan zafi a kofi na tsoma ifton a cikin a soma sha. Wane irin karyawa ne wannan Maryam? Kina mufin duk abubuwan da ke nan ba za ki ci komai ba sai ruwan lifton, daurewa na yi in banda haka da nayi mishi kuka na dago idanuwana do in yi mishi magana karab suka hadu da na Rumasa'u itama ni take kallo ba kuma kallon dadi ba ne watakila 'yar kulawar da ya nuna ne ba ta yi mata dadi ba, sai yau muka ga juna ido da ido daga ganin da nayi mata a asibiti da suka zo duba babana zuwa yau din ta zabge sosai sai dai in aka barni sai ince tafi kyau a hakan don da ta bar kanta ta ajiye teba mai yawa. 125 A hankali na ce.mishi, na manta ne na fito ban yi brush din bakina ba ko inje in yi in dawo? Har ya ce eh ban san abin da ya tuna ba sai naga ya miko min kwano guda daya na karba na dawo na ajiye na shige bandakina na kwanta cikin zuciyata ina tunanin ba zan sake yarda ya dorani a kan cinyar shi ba wato dama shi dabi'arshi kenan dora mace a kan cinya to na daina yarda in hau.nan take naji zuciyata tana raya min Wasu al'amuran da nan take na ji babu abinda nake so iri in yi kuka shi ne Tmutumin da nalke so a rayuwata na yi ta bunn auren shi sakacinshi da sharrin baba Lantana su ne suka taru suka yi sanadin da burin nawa bai cika ba a wancan lokacin har yaje ya auri wata matar ya Soma yi mata abubuwan da ya kameta a ce ni kadai zei yi wa, motsin shigowar da ya yi ya sani nayi amza na share hawayena amma duk da haka sai da ya gane kukan nakeyi, me ya saIneki? Na yi shiru zuwa dakin nata ne bakya so? Nayi maza na ce mishi a'a, to menene? Na ce mishi bana jind sdi ne, to in bakya jin dadi sai ki yi kuka ba za ki gaya min ba? Ko dai wani abu yana yi miki ciwo ne, nayi amza na ce mishi a'a, a kaiki asibiti nas ake cewa a'a Isiyaku ya siyo min maganin zazzabi. Ya ce in to ki yi wanka ki yi kwalliya in ganki in ji dadi na ce mishi to a haka na wattsake, ana gobe zai fita dakina ma sai da ya sake takurani ya yi yanda ya so da rannan kam kuka nayi ta yi msihi saboda na kasa hakuri in jure tun yana rarrashina har va soma mita wato kenan baki gamsu da adalcin da nake vi miki ba kenan ko So kike in tattara hannu in zuba miki ido ina kallonki, banyi magana ba iyaka dai ranar ya koma dakin Rumasa'u ni 126 kuma na kwana tare da Inna shi ne ya cew yaya Ibrahim kar a ga bata dawo ba zata tayani kwana yace mishi to. Tunda karyawar safe ta zama ka'ida za mu yi ta tare har da shi sai ya zama ka'ida kullum sai ta san abinda tayi ta bata min rai da na yi tunani naga abin bana karewa bane sai na yi maza na cire abubuwan da nake ganin tana yi mishin a raina tunda dai ni ba zan iya yi mishi hakan a gabanta ba bale ince zan rama. Satina uku da zuwa gidan aka soma azumin watan ramadan babu yanda banyi da shiba ya barni in je in yiwa babana barka da shiga watan mai albarka ya ki wai shi ya je ya yi mishi hakan itama yaya Dija ban jeba bata zo ba nayi aike har na gaji na hakura taki zuwa sai ana gobe zamu tafi umarar da aka yi ta rikici akan tafiyar da yace zai yi da ni har sai da babanshi ya sa baki cikin maganar shine wai tazo yi min sallama, na sunkuyar da kaina kasa na ki kallonta naki yarda kuma nayi shiru in daina kukan da nake yi mata, wata uku? Wata uku bamu ga juna ba amma baki yi marmarin ganina ba? Baki kuma ji tausayina ba? Tayi murmushi, to yi hakuri Maryamu yi hakuri Merona ai Meron Alhaji Ahmad kwanaki talatin din nan da kikayi a gidanshi kinga yanda kika zama? Ko da yake dai shima naji babansu yana cewa wai kwanciyar hankali dai shine wani abu banga yanda Alhaji Ahmadu ya zama ba amma zai yiwu ne inyi tayi muku zirga-zirga a gida? Yanzu ma ba ki ji ana cewa kullum sai na aiko Inna ta kawo miki magani ba da sassafe? Na daga ido na kalleta saboda jin maganar tata tayi maza ta kawar da zancen ta hanyar fadin in kin yi dawafin Umra kiyi addu'a Ubangiji ya baki 'yan 127 tagwaye, ban kulata ba na shiga daki naje na kawo mata abinda nake nufin kawo mata watakila sai gab da salla mu dawo watakila sai bayan sallar ki yi wa su Inna sayaiya ta ce min to. Sati uku cif mukayi sai ana gobe salla muka dawo, kudin sadakina da wanda baba Abba Gana ya bani kyauta ya ce a kawowa 'yar uwata ta sai min abinda ya dace su yaya Dija ta kawo min da zamu tati da su na sayo ra rai masu kyau don ma naki karbarj aka gudan da Mubarak ya bani na ce ya rike su. Hirar da Mubarak ya yi min a car wanda a ciki ya tabbatar min da labarin da baba Sumaye ta taba bani na cewar ba ummanshi ce mahaifiyarshi ba ya sani yiwa ban gaya mishi ba, nayi rabon tsaraba na dai dai mahaifiyar tashi sayaiya mai yawa don tsarabarta sai dai gwargwado na kuma yi rabon har da mutanen Gaidan na aika musu da shi. A wannan lokacin ni da Mubarak anarci sosai mukeyi saboda duk abubuwan da a farkons l'amarin suke masu tsanani da sanya faduwar gaba a tsakani sun zamo masu sauki a yau da sanya nishadi in tsaya fadin ji da ni yake yana tarairayata ya zama tamkar sakarci ne zanfi gwammacewa in ce muku duk abinda yake so shi nake yi mishi. Ashe duk wannan kwaramniyar da wannan kai kawon Maryam ashe dai ke din matatace, ince mishi eh yallabai ni taka ce da rabon dai kawai za a ji jiki ne, sai ya yi maza ya ce a1 babu komai ba gashi yanzu ya wuce ba darussan da muka koya tare da mu kuma suna nan 128 Zamu rkesu iya tsawon rayuwarmu? in ce mishi eh, sa ya ce to ai shi kenan. Kwananmu shida da dawowa randa mka dawo ya sauka a dakin Rumasa'u ne ni ma ranar ban wani damu sO nake in dan samu sararawa ya yi kwana biyu ya dawo wurina ranar ma ina hutun sallah ya yi biyu yau koma can ya sake yin wasu biyun ranar zan karbeshi ya shigo wurina da safe akwai wata mas'ala ne? Na ce mishi, a'a ni kin fara ealla ikuwa? Na sake ce masa a'a har ya juya zai tafi sai na ce mishi da ina so in rokeka wata alfarma, ya juyo yana kallona, kamar wace iri kenan, nace so nake ka sa a kaini jaji ina so inje wajen su Inna. Ya danyi shiru kadan kafin ya ce min, to ki saurareni na ce mishi to ya juya ya tafi. Banda vvannan girkin da nayi da ya koma wajen Rumasa'u zai sake dawowa wurina sai muka tafi. Wajen karfe hudu da rabi muka isa duk da ya ce sammako zamu yi mu isa wajen sha daya ko sha biyu in mukayi la'asarm u wuce Kaduna gidan Abdulhamid mu kwana a can ban san yanda akayi sarnmakon bai yiwu ba. Hirar baki ba za za ta iya fahimtar da mutum ya gane irin son da Mubarak yake yiwa mahaifiysarshi ba sai yaje inda take da zama yaga irin gatan da yayi mata shi ba mutum ne ma yawan magana a kan mahaiñyarshi baa ssannan bakina da nashi sai ya tabbatar min da cewar yana dadewa baije wurinta ba a dalilin babu wata shakuwa a tsakaninsu ya santa ne bayan ya girma har ya soma karatu a jami'a ya nemeta don kanshi ita bata taba waiwayowa ta kalleshi ba watakila an bata mata rai ne ya sa tayi mishi hakan watakila kuma don ta ga ta haifi 129 wasu mnasu yawa ne ya sa ta hakura da shi tunda shi kadai ne. Cikin natsuwa na ce mishi, ko kuma don kunyar kai din dan fari ne ba'? lyayenmu ai masu kunya ne, yayi shiru ya bar maganar. Muna isa Jaji na sha mamaki gidan da aka tsaida motar da muka yi tafiyar a ciki gida ne ginin kasa ko ince block din kasa ginin mutanen karkara sai dai babba ne so sai cikin zaure gidan muka shiga muka fada tsakar gidan mai matukar girma, Isiyaku ne yake jagoranta ta den daga hirar da nayi ma sai nags kamar yafi yallabai din yawan zuwa garin a'a ahah kar dai amarye ce yau a gidan namu? Na daga ido a yanayi na girmamawa ina sauraron kalamanta cikin zuciyata na tabbatarwa kaina da cewar itace dattijuwar da ban gane ba a Gaidan ashe daga nan taje can din. A'a wuce mansa wuce ki karasa ina uan shigowa, na bi umarmin da ta bani naci gaba da bin bayan Isiyaku ban karasa inda zanin ba naji tana cewa sannu da zuwa Alhaji kun zo ba? To hannurkn da zuwa hannunku da zuwa. Wata kofa na shiga wacce na dade ina hange saboda nisanta wani tabkeken gida na gani a cikin wata kanmalalliyar katanga ginin block, sannunku da zuwa ta yi min sannu da zuwa cikin matsananciyar fra'ar da ta baiyanarda jajayen hakoran makkanta guda biyu dan kamannin da ke tsakainta da shi kacna ne sai dai kuma hakan ba zai hanaka sheda cewar ita din mahaifiyarsa ce ba shi dogo ne ita. kuwa bata da tsayi shi ingarma ne ita mai dan jiki, ita fara shi wankan tarwada a bakcan kuma 130 su na da dan wani abinda ya hadasu da ya danyi shigenta kadan sai dai ban gane menene ba? Har kun fito? Cikin ladabi na ce mata, ah to sannu da Zuwa shiga mana na shiga falon na ta na samu daya daga cikin luntsuma-luntsumarn kujerun da ke wurin na zauna a cikin ina mamakin wurin nata yafi kama da na sabbin amare saboda irin kawatuwar da akayi mishi, sannu da Zuwa ta sake fadi daidai ta zauna a kan kofar shiga daya dakin nima ra sauko kasa na zauna muna gaisawa tana tambayata yaya gida? Yaya manyan duka? Ina amsa m ata da na ji ta danyi shiru sai na tambayeta Inna ina Izzatu, tayi dariyar jin dadin tambayar yar autar ta ta da na yi ta ce, ai kuwa dai yanzu na aiketa wurin yayarta dake nan bayanmu. Mubarak ya yi sallama ya shigo ya koma can gefe sannu Inna daga yanayin maganar tasu na kara gane gaskiyar abinda ya gaya min, baba baya nan ne? Ya yi tambayar bayan surn gaisa ta ce eh ya zaga baya can kasan sunf ara sharar gona saboda ana ganin kamar damuna tana gab da zata fara zube ya ce haka ne. Isiyaku ya yi ta shigo da tsaraba yana jibgewa a wani daki na daban wanda yawanci kayan amfani ne ya gama ya miko min jakunkunan guda biyu na dauki daya na mika mishi daya na ce a amyar min da ita ta ce a'a haba jaka tayi ta zama a cikin mota a sa miki su a dak mana. Mubarak ya ce ai ba dadewa ma zamu yi ba Inna Kaduna zamu uce gidan abokina, ta ce a'a ai dai ku ku wuce amma ita wannan ai nan ta zo za ta zauna ta ga yan uwanka su ganta ta sansu su santa in ya so in kuka juyo sai ku biyo ku dauketa. 131 Shiru yayi ni kuwa naji dadin hakan da ta fada tunda ni kam asalin niyyata dama ai ta zuwa wurina ne ya ce sai mu karasa Kaduna na ce to. Ashe kuma baki sun zo ta amsa a yanayi na kunya, saboda hada jam'in maganar da akayi sai naji ta ce ni fa amarya ta fito na ce wannan tafiya mai nisa da tayi gashi ba ta gama hutawa ba ta sake yin wata ko da yake dai wannan tai bada ce muka gaisa da matar da na wuto a tsakar gida tajuya ta tafi cikin natsuwa na ce mata, Inna ban san da mutane a gidan ba ni su Izzátu kadai na yiwa tsaraba na tura mata jakar da tsarabar ke ciki, wannan duka su Izzatu? Ai kuwa dai su suka kwashe kayan jakar taki, to Ubangiji ya yi mulu aibarka ya rufa m uku asiri ya zaunarmuku da wannar aure na lau lafiya ya kuma kareku daga sharrin mahassada. Mubarak dake can gefe ya ce anin ni kawa nayi shiru. Ta mike ta fi ta ta kallei, ni fa zan wuce na ce mishi a'a mu kwana tare, da sauri ya kalleni a ina? Na nuna mishi ga dakuna in ma ba zaka kwana anan ba ai ba za ka rasa dakin kwana a gidan ba duk yanda za su kai da jin dadin ganin ai bai kai su ganmu tare ba, ta daure fuska mai don kar in ga yana wasa nima nayi kamar ban ganshi ba na kau da kaina gefe ta sake shigowa zata wuce, cikin natsuwa ta ce min wai so nake in yi sauri don mijinki ya danci wani abu kafi ya tafi, ban kalleshi ba na ce mata ai kwana zai yi, da sauri ta ce au haba? Lalle yau da bak a gidan to a zo a gyara muku wancan daki mana, ta fita tana kiran Izzatu mai yawon nunawa kawaye tsarabar da aka kawo mata. 132 Amma ba kina shirin turani wancan dakn ne ke ki dawo nan ki kwana ba ko? Na yi maza nace mishi share dakin tasa aka yi ta canza labule ta fitar da katifar dake ciki ta sa aka kai wata akayi shimfida yana dawowa daga sallar magariba na ce mishi kO zamuje can ne in kai mana abinci? Bai yi musu ba daki ne har da bayan gida a ciki ya fita sallar isha'i ya dan tsaya wajen mai gadin suka gaisa wanda shima ya jid adin ganinshi don har nan ya biyoni wai mu gaisa Innan ce ta ce mishi ai nima zanzo in gaisheshi ya ce to ba yanzu ba a barni sai da safe saboda duhu. Nayi hira yar kadan wurin Inna saboda sanin da nayi mijina yana can shi daya a dakin, sai da safe Inna, ta ce min to sai da safe 'yar nan dauki wannan kwanon ki tafi muku da shi na ce mata to, a dakin kwanciyar namu Mubarak ya yi kwanciyarshi iritn ashi bako ne ni kuwa na mike na zauna kan shimfidar na soma zare kayan da ke jikina daidai da daidai ina yin wurgi da su ba tare da ina lura da inda suke faduwa. Da sauri ya dago kai ya kalleni a hankali cikin murya kasa-kasa da ke kare baiyanar da bakuntrshi a urin ya ce min, "Ke Maryam a gidan mutane kike irin wannan tubewar?" Ban kula shi ba, ya yi maza ya jawo gefen babbar rigarshi ya rufe fuska, wai ma ba zai bari ya ga abin da nake yi ba, ban daina ba bar na kai ga babu abinda ya saura min sai r brazier da ke jikina na mika hannu daya da nufin in karasata itama sai na ji caraf ya rike hannun nawa. 133 "Tun da dai abin da kike so kenan to barni kawai zan karasa wannan din." Ban sani ba ko bakuntar da yake ji a zuciyarshi ne ya hanashi makara duk da abubuwa masu dadi da suka kasance a daren wadanda suka hanashi samun baccinshi, kiran sallar farko naji ya tashi ya kammala abubuwan da zai ya yi nufin fita masallaci ina jinshi yana tashina ban ayrda na tashin ba. Mubarak da dole dole ce ta sanyashi kwana a gidan nan sai gashi shi da kanshi ya cewa Inna zai bar tafiyar sai gobe saboda ganin yanda yan uwa ke ta isowa suna fadin sun zo ganin babban yaya da amaryarshi, ita kuwa Inna duk wanda ya shigo mace ko namiji dan uwa ne ko abokan zama abokan mutunci sai ta dauko wani abu cikin tsarabar da mukazo mata da ita ta mika mishi a yi ta godiya ana sa albarka, shi ma Mubarak rannan ya yi kyauta har na rinka tsorn kar dai kudin nashi su kare sai dai kuma anyi sa'a basu karen ba, bai yiwuwa in tsaya cewa Ina tayi farin ciki sai dai kawai in ja bakina in yi shiru. Washegari da hantsi ina zauze a gabanta yayin da Mubarak yake waje wajen mai gidan don yin sallama da shi saboda tafiya za mu yi sai ta kalleni ta ce min "Ubangiji ya yi miki albarka ya rufa miki asiri ya baki zuriya mai albarka, ya jikan mahaifiyarki da rahamarsa, in kunje gida kuma ki sa hannu ki kar6i girkin gidan mijinki da yace min baki soma ba ki rinka girki kina baiwa uban mijinki yana cin abincinki, itama matar gidan uwar taku kar ki yarda ki samu mas'ala da ita don tana da tasiri mai karfi a kan al'amarin mijinki sannan 134 ya'yanshi ki sa hannu biyu ki rikeiSu babu ruwanki da uwarsu kin ji ko baki ji ba ko? Na ce "Naji Inna na gode Ubangiji ya kara girma. Izzatu ta shigo dakin kuka takeyi wai zata bini na ce "To Inna inje da ita mana ai itama 'yar yata da na goya haka take kamarta. Ta yi maza ta ce "A'a ba yanzu ba in kin haihu dai za ta zo ta tayaki jego." Shiru nayi ban amsa ba. Inna ta ban tsaraba kashi biyu tace daya namu daya kuwa na yaya Dija, muna barin Jaji Kaduna muka karasa gidan Abdulhamid muka sauka shima mata biyu ne da shi sai dai shi amaryarshi har ta haihu nan din ma fafatak ishi mai zafi akeyi a tsakaninsu. Mun dawo da kwana uku anti Safara ta haifi da namiji zuwa ginin yaron da nayi shi ne shigata gidanmu na farko tun taifiyata Gaidan shi ma barka kawai naje bai yarda naje sunan ba wai ban kai zuwa suna ba don haka Rumas'au ya tura taje a madadina duk da ba wani shiri muke yi ba. A wannan lokacin ne akayi gagarunin zama tsakanin Rumasau da Mubarak da kuma iyayensu gaba daye ashe duk wani iya shege da takeyi da nunannin ita da miji kut da kut suke a mane dajuna ita kishi ne kawai ya sa take yin hakan tsakanin nasu ba mai dadi bane. Wurin yan tsegumi masu kai kawo tsakanin jama'a na samu labari don a bakin Mubarak dai ba zan ji ba saboda baya yin maganar wata a wurin wata musamman ace ba ta nan. Ashe wai tun sanda babana ya zo ya yiwa Alhaji Muhammadu maganar nan cewar in har Mubarak yana 135 da muradin aurena bai fasa ba to su zo su karbi auren ya basu, ya ce eh basu fasa ba, da ta ji maganar ta rokeshi va yi mata alfarnmar neman wata ya aura in yaso ma kar ya auri guda daya ta yarda za kuma ta zauna da su lafiya in har ni zai hakura da ni ya ce mata a'a wannan bai shafe ta ba in tana da wani abin dai ta fada, ta ce ita kadai ce ya ce to a'a ba huruminta bane don ba itace zata zabar mishi matar da zai aura ba, tund aga nan in yazo gareta da bukatarshi bata sauraronshi ba ta yarda da shi, haka suka yi ta zama har akayi bikina watanni uku don haka da na zo gidan shi kuma sai bai salke komawa ta kanta ba shiga dakin yake yi ya yi baccnishi in gari ay waye ya tashi ya fita, ba ki ga yande ta kare ba, na cewaa mai bani albarin ai bana kallonta, ta ci gaba da bayani, ai yanzu ba ta fi rabin da ba don irin wannan wulakancin ciwo ne da shi to yanzu shi ne ta gayswa kakar ta ta irin zaman da sukeyi shi ne akayi zaman to yanzu wai an sasantaus shi aayi mishi fada an gaya mishi laifinshi ya ce a yi hakuri zai gyara itama anyi mata na ta fadan ta rokeshi gafara ya ce ya yafe. Hausawa suka ce wai kishi kumallon mata gashi dai dama can ban san irin zamand a sukeyi a tsakaninsu ba amma da akayi min wannan bayanin sai na dan ji nauyi a zuciyata nan take kuma sai ta fara tunano min to wato abinda ya faru kenan shi yasa jiya na ganshi ya makara a dakinta bai kuma iya fitowa mun karya da safe ba har na gaji na karya a wurina ni da Inna wai yana bacci kan kace meye wannan sai zuciyata ta soma nunawa idanuwana irin bare-bare. da zumudin da Mubarak din 136 yake yi a kan daidaitawar tasu nan da nan sai naji na kullace shi a cikin raina. Kusan sati biyu ay kasa gane al'amarina tun yana kallon abin a wani irin yanayi har dai ya gaji ya tambayem Kina da damuwa ne? Na ce babu, to meke faruwa ne? Na ce ba komai, a'a yaya za ki ce min babu komai, na mike na tafi na barshi wuri bai sake ce min komai ba muka ci gaba a haka. Rannan mun kai sati hudu a wannan lokacin ko yarda mu hau gado daya da shi bana yi cikin dare ya taso ya zo ya sameni a kan katifar da nake kwance na yi zumbur na tashi na zauna, wani irin lalataccen kallo ya yi min, ke kar ki maidani sakarai mana kina ganin kamar wai zan tilastaki ne? To a kan me? Ai ba haka nake ba ko sanda nake da mace daya bana wannan shirmen bale yanzu. Maganar tashi ta soki zuciyata naji zafin ta ba kadan a raina na ce ai kuwa dai sai dai mu yi ta zama a halka in don ka ga ana kai kararka ne, ya katsemin tunanin nawa a dalilin maganar da ya yi, so nake in tambaye ki wane laifi nayi miki? Na tabe baki tare da girgiza kai don in nuna mishi bai yi min komai ba, ya zubamin ido yana kallona haka kawai kike nishadin ki ka ga bari ki yi min wulakanci? A zuciyata nayi nufin ce mishi eh sai dai ina dagowa da nufin yin maganar idanuwanmu suka hadu sai naji ba zan iya ba nayi maza na sunkuyar da kaina kasa, ba kya ganin kamar in na gaji da hakurin da nakeyi zan iya ramawa don kema ki ji inda dadi? Cikin natsuwa na ce mishi ai gara ka raman, ya ce to shi kenan ya mike ya koma in dai ya fito ya yi kwanciyarshi. 137 Washegari da muka tashi ko gaisheshi ban yi ba na ci gaba da harkokina na kuma zuba ido cikin sauraronta ina ramakon nashi zai faro. Ina cikin dakina a kwance sai kawai naji sallamar yaya Dija da sauri na taso ina rike da dankwalina a hannuna kai yaya Dija bakya ko jin tausayina, sai ki ki zuwa in yi ta jin marmarinki har in gaji in hakura, bata amsa ba ta nemi wuri ta zauna na wuce naje na kawo mata abubuwanci citrus wrapes, perrz da arapers ciko farantin nayi nazo na ajiye mata na sake komawa naje na kawo mata soyaiyan naman rago na sake komawa na kawo niata kindirmo na sake juyawa na dauko wani kwanon tayi maza ta dago ido ta lkalleni, ke bana soon rashin bankali ina zan kai wadannan abubuwan da kike taramin? Zo ki kwashe su duka 'ya'yan itace kawai nake bukata yanzu nace mata to. Wani abu ya faru ne? Tayi min tabmayar bayan mun gama gaisawa a hankali na tambayeta me kika gani? Idonta yana kaina ta soma yi min magana cikin natsuwa, Alhaji Amadu ne ya aika a gayawa babansu wai in babu damuwa yana son ganina yanzu, na taba baki tare da girgiza kai, fuskarta tayi saurin canzawa alamar ba ta ji dadin yanayin amsar da na bata ba kan atce min komai sai gashi ya shigo adonshi yayi kyau gashi sai kanshi yake yi. Ki yi hakuri na tasoki, ta ce a'a babu mas'ala ina fata dai babu damuwa, ya ce eh babu a hankali ya soma magana, ba ina nufin kawo kararta ba ne don gaskiya ba dabi' ata ba ce ma yin hakan amma ina so in rokeki a yi mata magana saboda bana son fitina a tsakanina da 1ta, 138 na tambayeta in wani abu akayi mata ta fada ko ba ni ba in wani ya yi mata tana da yancin gaya min domin zamana take yi taki ta yi magana nace zAn rama abinda take yin don itama tai in da dadi ta ce wai gara inr ama, kinga kenan tana sane da abinda take yi tana yi ne kuma da wata manufa shi yasa na nemeki me akayi mata? To in an yi mata sai ta nemeka da fitina wane irin al'amari ne wannan? Me akayi miki? Nayi shiru kenan gobe ko ya ganki kina yina binda kika ga dama kar ya nemeni don ban isa ki gaya min damuwarki ba? Ya mike ya fita ya barmu ni da ita, tana ganin yaf itant a soma yi min fada mai tsanani ni kuma na soma yi mata kuka dont ayi shiru taki yarda ta yi shirun. Ke ba za ki gane abubuwan ba ne, a halin da ake ciki fa ni babu mai sona a gidan nan nice bare, su kansu a hade yake in banda kwarata babu abinda ake son gani. Me suke yi miki na kwarar? Nayi shiru na rasa ta inda zan bullo mata, to a soka a gidama ai halinka ke ja maka kuma yaushe kika zo gidan har kika soma wadannan maganganun? Kenan har kin fara samun mas'ala da mijinki Maryam in banda mummunan tarbiya da kika samu? To kin girma gaban mai cewa miji ya kunshe baki kamar masai ai ni dama gabana yana faduwa ina tunanin wane irin zaman aure za ki yi? Kuka sosai ta soma yi har tana fyace majina da zaninta, wace irin magana kike so kija mana? Yanzu a irin yanda akayi auren nan naku da irin dawainiyar da mutumin nan yayi babu abinda ba a fada ba babu wahalar da baiyi ba ga 6acin rai a kan aurenn ne fa mnatar tayi ta tsalle tana cewa gara mata kishiyoyi hudu da ke ke kadai bata sani ba ma ashe sakarya za a 139 kawo mata, kai ba a kyautar zuciya Maryam da na samo Wacce tafi dacewa dake na baki. Ganin 6acin ranta da ambaton matarshi da tayi ya sa ni ce mata, to ai yafi sonta da ni kinga bare-baren da yake yi ne... ban karasa ba ta katseni, ba dole yafi sonta dake ba ita sulhu take nema a tsakaninta da shi ke kuwa kina nemanshi da fitizaa, haba in banda namiji bai gajiya da abinda yake so wane dadi yaji ne a tare da ke kuma karya kike yi mishi wane bare-bare zai yi a kanta da ya wuce wanda ya rayu yanayi a kanki? Kurna sai me in ya yi ba matar shi ba ce, ba da ita kika sameshi ba, na kara tsaranta kukan da nakeyi saboda tsananin bacin ran da kalaman anta suka kara min gaba daya yaya Dija ba zata fahimceni ba ban san yanda akayi ba sai naji bakina yana ce mata kwacemin shi akayi aka bata, kwace min shi akayi saboda ita tana da gata ai ba nata bane ni ba mijinta na aura ba ia ta auran min. To yan ya ya za ki yi Maryau? Tambayar da ta yi ta fito a lafazi na baiyanar da canjin da zuciyarta ta samu, ki yi hakuri ai kaddarace ta yi miki hakan ba wani ba ne, itama matarshi ce rabon ta kuma yaî naki zafi baki ga ke har yanzu baki da komai ba? Ita wate tara babu kwana biyar tayi ta haihu a gidan nan ina lissafi ban yi magana bane kawai kina nufin da ya aureki a wancan ba zai aureta ba'? Zai aure ta domin 'ya'yan dake tare da itan nashi ne. Don haka ki yi hakuri, ina share hawayena da bakin gyalena na ce, to shi kenan ni na hakura ya daina taba ni bana so bana so na hakura da shi tunda rabon ta ma yafi 140 nawa karfi to na bar mata shi ni ya kyaleni kawai, na ci gaba da wani kukan. Mubarak ya sake shigowa bayan ta amsa sallamarshi bari muje in saukeki sai in wuce don za ni Bauci, to ko zakaje kawai in na gama sai in tafi? Ya ce a'a uje kawai ai babu damuwa. Ta tashi suka tafi amma dai ranta a bacei watakila saboda ganin kamar zuwan nata bai samar da wata mafita ba. Ina zaune a falon ni kadai ina tunanin haushina takeji saboda bata san kishi bà saboda tayi sa'a ita kadai ce a gun mijinta ba zata iya fahimta ta ba saboda bata taba jin irin zafi da ciwon da nake ji a cikin zuciyata ba. Da kyar na iya tashi nayi wanka nayi salla na hau gado na kwanta ko nemarwa abin da zanci ban yi ba ina jin Rumasa'u tana ta kyakyacewa da dariya na kuma san dadi ne ya kamata Mubarak ya yi tafiya a ranar da zan karbi girki. Nayi duk abinda na sabayi na al'adata na sa makulli na kulle kofata na hau gadona na kwanta nufina wai in yi bacci da wuri sai dai baccin bai daukeni ba wajen karfe tara da rabi na dare na ji ana kwankwasa kofar tawa, na tso nazo na bude shi na gani a tsaye fuskarshi a daure alamar ranshi ya baci da kulle kofar da nayi, ban ma tsaya a falon ba balle in yi tunanin yi mishi wani abu ina jin shi ya. yi kaikawon da zaiyi ya gama maimakon ya shiga dakin da yake kwanciya ya kwanta sai naji shi ya shigo wurina nayi maza na gyara rufata. Tashi muje wancan dakin, nayi maza na ce mishi a'a ni a nan zan kwana.... wani irin cafka ya yi nmin mara 141 dadi kan kace meye wannan sai gani a inda yake nufin ganin nawa, yi hakuri ki sa hannu ki rage kayan jikin naki, na sake cwa uh'uh ba zan yi ba bana so kar kuma.. nayi maza na canza maganar saboda ganin abinda ya soma yi to ai kai kace baka tilasta mace ko sanda kake da guda daya ma baka yi hakan ba balle yanzu ya ce eh ita kadai zan rinka yiwa wannan adalcin banda ke tundakin bari na ganc ki na riga na gane ita daba ke daban, ni kuma zan iya zama da ku dukanku bisa tsarin da ko wacce take so banda haka kuma daga yau ba zan sake kai kararki ba tunda na gane baki da mutunci mara kunya kawai sokuwa sakarya wacce gata yia hanata fahimtar abinda take ciki, zagin da ya yi min din zagi ne na wulakaci bai kuma hanashi yin duk abinda ya shirya yi ba. Ance miki tsoro ne ya sa ni, kai traganarki wurinia? Tana da girma ne a wurina da kika barta har ta fita baki bata hakuri kan bacin ran da ta gmu da shi ba a dalilinki, sannan duk maganar da kikayin naji wani abin da baku i. himta b ke da Rumasıi'u shi ne ni din babu wacce za 1a sa ni n yi abinda banyi niyya ba, sannan baa zan saki wata a cikinku wani kato yaje ya auran min mata ba, ba kuma zan yarda in karkata karkatar da zata cutar da ri ba, dukkanku ing ennku ina kuma son dorewar zamana da ku don haka zan zauna da kowacce ne a bisa tsarin da ta nemi mu yi zaman ni da ita wacce ta nemi zaman lafiya mu yi wacce ta nemi sabanin haka ma ina shirye in wani zai yi min laifi in kyaleshi kuma ina tabbatar miki in kikayi min ba zan kyaleki ba, ba zan yarda ki bata min rai ki ga kamar kin ci bulus ba za ki 142 rinka tuna wane da kikayi min kaza nima nayi miki kaza ba kalau kik kwashe ba, don haka admision din da na saman miki na karanta Is!amic law a jami'a na janye shi na fasa ba za ki yi karatun ba. Na soma kuka ina bashi hakuri ya ce ai sai ki yi ai ba hauka nake yi ba saboda kishi sai ki hanani taba jikinki tsawon wata guda? Kina so ne ki rinka tirsasani da hakan? Ai itama ban barta ta ci nasara a kaina da hakan ba balel ke, zuciyata ta kara kutata zafin da ke cikinta ya kara karuwa kwoacce magana zai yi sai ya hadani da ita kowacce magana zai yi sai ya nuna min ta fini, za ki rinka tuna sanda kika hanani kanki na hanaki, karatu saboda na gane wanda kakayi a baya bai yi miki amfani ba don bakya aiki da shi nan gabe in kika koyi sanya iliminki a cikin aya kanki sai mu san abin da muke ciki. Babana a shirya zuwa Gaidan wurin danginshi karo na farko cikin shekaru talatin dabiyu shi da anti Safara da jaririnta da su yaya Dija yaya Ibrahim nema zai kaisu a cikin sabewar motar da tace min Mubarak din ya bashi banje musu sallama ba banje musu sannu da zuwa ba saboda bai ga dama ba, na rame na zube haskena ya ragu saboda abubuwan da na samu kaina a ciki, a hakan kuma na soma girkin gidan gaba daya saboda yace in karba ko dama can kuwa tund awowar da' mukayi daga Jaji na soma yiwa baba abincinshi na safe da na dare saboda kasancewarshi mai lalurar suga. Banje ko ina da fara yin girkin ba naji hirar Rumas'au da kawarta tana gaya mata cewar a'a abubuwan sunyi sauki sun kuma lafa daman ashe doki ne kawai ya firgitata har ya nemi sata ta gudu ta bar ladanta 143 ai yanzu wayar gari take yi tana kwance tana hutawarta a dakinta nike tashi da sassafe in yiwa yara wanka in shiryasu in basu abinci su ci su tafi makaranta dole kuma in yi ko don in zauna da shi lafiya tunda shi a kan ya'yanshi babu abinda ba zai yi ba ko ita da ta haifesu lallabashi take yi in dai a kansu ne. Raina ya baci na samu kaina cikin wani al'amari nayi kamar in daure in ci gaba kawai da abinda nakeyi sai kuma naga ba zan iya in dai hidimar yuran zai iya zama sanadin zarnana to ina ganin gara kawai ya zama ko na samu in huta da 6acin ran da nake gamuwa da shi gashi ko bacci bana iyawa matukar yana dakinta to ni kuma bana iya bacci da daddare gashi tsakanina da shi abin ya ki dadi. Na kar6i girki ina cikin dakina a wkance da safe ban fito ba balle in yi abincin karyawa ball in yiwa yaran wanka, Ummulkairi ta shigo falon ina jinta ana gaya mishi baba wai inji mamauau wai zamuyi lattin makarant, to menene? Wai anti tazo tayi mana wanka ta shiryamu. Ina jira i ji kiraná zaiyi ko me zai yi Sai naji ya ce mata ke tafi bani wuri ba a dade ba naji isowar uwartata na ce Ummu tazo ta gaya maka za su yi lattin makaranta, ya ce to menene? Ta danvi shiru kafin ta ce, nace. wai wankan ba zata fito ba ne? Wacece mai wankan? Ke kuturwa ce da ba za ki yiwa 'ya'yanki wanka ki shiryasu ba, sai wata tayi musu? Ta ce ahh hakama zaka ce? To su bar zuwa makarnatar mana ya' ya na ne? Ai dama na sani tunda ka samu kwana biyu...: ya yi maza ya katseta, in kika 144 gayamin magana a gaban yara, bata tsaya ba ta juya ta fita, ban san yanda akayi ba sai naji an tafi kaisu makarantar bai kuma dai fita ba balle ince ko shi ya yi musu girki biyu a jere ban yi ba. Rannan ya zaunar da ni yana tambayata, kina da mas'ala da shirya yara da safe ne Maryam? Na ce mishi ch, menene mas'alar? Na ce a canzamin wani aikin kawai ba wannan ba, bai ja ba ya ce, to ki rinka yi m usu lesson, na ce to, za ki yi? Na ce eh zan yi, ay ce to shi kenan na tashi nayi tafiyata ba tare dan a tsaya gaya mishi wani dalili ba balle aje ana kace nace, da na samu zarafin gaya mata magana kuma sai na gaya mata cewar ni din zama kaina nake yi a wurin mijina ba zamanw ani ba duk wata kunatawa da zan yiwa wani to zan yi ne don in kara gyara auren nawa amma ba don ina tsoron kar ya zamo mishi wani sanadi ba. Rannan ya dawo daga tafiya ya shigo dakina ya sameni Inna da Izzatu suna gaisheki da sauri na tambayeshi kaje ne? Ya ce min eh, na ce amma baka gaya min zaka ba'? Ya ce e ban yi niyyar cewa najen ba sakon da ta bani in baki ne ya sa na gaya miki, tana ta tambayata wani har yanzu haka kike babu komai? Nace mata eh shi ne ta bani wani ita ce tace ni kawo miki wannan amma na gaya mata cewar ke din maganin hana haihuwa kike sha, ban yi mamakin jin maganar a akinshi ba don naji irinta ko makamanciyarta a bakin Umam bance mishi komai ba na sa hannu biyu kawai na karbi Itacen na ce mishi na gode na kai daki na adana. To a haka abin yake jifa-jifa zan danji wasu kalamai Suna fitowa daga bakinshi wanda nasan ba ganin abin yayi ba gaya mishi aka yi kamar in tambayeshi ta inda 145 maganganun suke zuwa msihi sai na fasa na ja bakina kawai na yi shiru. Ni da Rumasa'u kuma a wannan lokacin wani irin zama m ukeyi na kai da gindi iyaka dai naki yarda mu yi zaman gaba zaman da babu wata mu'amala a tsakaninmu ko bata kulani ba gaisheta nakeyi sai dai hakan ba yana ufin zata yi min in kyaleta ba ne ina kuma mu'amala da yara in musu lesson in yi musu alheri gawargwadon iyawata in kuma sukayi min ba daidai ba in hukuntasu tun ina yi m usu hukuncin a ce su jira babansu in ya zo Su gaya mishi har abin ya zama rikici tsakanina da ita ban daina ba shima ukam ban taba ji ya yi min magana ba. Rannan Mubarak yana dakin ban san yanda akayi ba dasawamukeyi tuns afe dai nasan yake tattalina yake tarairayata watakila saboda yana bukatar daren ya zamo mai cike da kwanciyar hankali, to dansa hannu ki rage kayan jikin nan naki mana Maryam yaushe rabon da ki yi min irin wannan mututnawar? Ba fa najin dadin irin wadannan abubuwan na tashi zaune na soma cire kayan jikin nawa saboda nima ba jin dadin karfin da yake gwada min nake yi ba, dadi ya kamashi, yanzu in duniya tana da gaskiya Maryam ni ace tsakanina da ke zaki iya hanani jikinki? Wannan jikin dai to na wane ne? Ban kalelshi ba nace naka ne, to me nayi miki ya sa kike gayawa mutane ba za ki yi a zama da ni ba? Wa ya gaya maka? Ya ce uh'uh kar ki tabmayen wanda ya gaya min kin fada ko baki fada ba? Cikin natsuwa na ce mishi, na taba gayawa yaya Dija banda ita ban taba gayawa wani ba itama kuma nasan ba zata fada ba, ya yi maza ya ce 146 haka ne me nayi miki? Bance mishi komai ba sai naji ya ce min, kishi ne ya yi miki yawa Maryam ni kuma bakya barina inji tausayinki sai kice zaki tirsasani, ba zan iya ba ba zan iya yarda da hakan ba saboda ina gani na cancanci abubuwa guda uku daga wurinki saboda dalili guda daya, na cancanci kulawa tausayawa da kuma rangwame, ki kula da ni ki kyautatamin saboda kasancewata a tsakaninku a tsakanin naku kuma ina cikin zargi, dole kuma in yi adalci saboda shari'a bata barni in yi abinda naga dama ba ta kewayeni da dokoki in nayi miki kuskure kuma ki yi min rangwame saboda kin san kuskure nayi kin sani sarai ba zan 6ata miki da gangan ba ai ina gudun 6acin ran naki bakya ganewa na wadannan abubuwan kuma don kin yi min su ba komai bane saboda ina sonki ba dabi'ata bace fadin hakan amman kin sani na koya karfi da yaji a hakan kuma ban tsira ba. A hankali na ce mishi, to ka yi hakuri, ya ji dadi sosai, a hankali ya sake ce min, to yi min wani alkawari bayan hakurin da kika bani don in kara samun natsuwa a raina, ba zan sake hanaka jikina ba, ya sa hannu juyar da ni ta yanda muka fuskanci juna, ba za ki sake ganin bacin raina ba kenan ai ko laifi kikayi nasiha kawai zan rinka yi miki ba fada ba, ai da wata ce tayi min yanda kika yin sai in bata wata shida to amma ke da yake kin san ba zan... na katseshi ta hanyar tambayarshi, ya cem aka ina hana kaina haihuwa? Ya ce uh'uh ai nace kar ki tambayen amma ba ga magani nan Inna ta ce ta kawo miki ba ki sha ba me yasa? Yaya Dija ce ta ce in ajiyeshi tukunna, ya danyi shiru kadan kafin jimawa ya 147 sake tambayata, da ma ita antint asan da wani abu ne? Nayi shiru to shi nę ni ba za ki gaya min in sani ba, Inna ma in gaya mata hankalinta ya kwanta, kinga yanda ta kosa taji kina da wani abu kuwa sai kace bata taba ganin jika ba. Tun daga ranar muka koma zama mai dadi tsakanina da shi sai dan abinda ba za a rasa ba ban sake yarda wani abu ya faru tsakanina da shi da ya zama dalilin da nayi mishi rowar kaina ba, hakan kuma sai ya zama sanadin raguwar bacin rai a tsakaninmu. Ana cikin hakanc ikina ya kai watanni bakwai yaya Dija ta soma yi min aiken magugunan zaki da saukin nakuda sai dai bana sha don basa yi min dadi rannan ta zo dubani muna hira sai ta ce min bakya shan magungunan saboda bakinki ya saba da zaki bari zan Rara tambayar baba Lami inji rake ne yake maganin zaki ko zuma ne? Wadannan kam ai za ki sha ko? Nayi maza na ce garama dai ace raken ne, to ki dai bari in kara bincike tukunna nace to. Tun daga washegarin ranar na soma shan rake a matsayin maganin zaki da kuma saukin nakuda, sai in wuni ina sha ina gyatsarshi ina karawa in naga ya kusa ya kare mi ince Isiyaku a kawo min rake ya ce to ya kawoshi cikin wheelbarrow, ke Maryam kin tabbatar raken nan da kike sha haka maganin zakin ne ko? Ince mishi eh baba Lamin gidan su yaya Dija ce fa ta fada ita kuwa ka san babba ce haihuwarta goma sha hudu sai Mubarak ya ce min to babu laifi. Rannan na wayi gari bani da lafiya nayi maza na yiwa baba abincinshi na safe da na dare na aike mishi da 148 shi saboda tun daga jin cabkar farko da nakudar nan ta fara yi min na gane uh lalle da magana ba karamin artabu za a yi da ita ba. Kafin hantsi har na fara gundura da ita na fara gurnani ina mita tafdijan yanzu duk uban raken nan da nayi ta sha dama haka zamuyi da nakudar nan? Mubarak ya kalleni ya kawar da kai, to rake da kika yi ta sha ba dadi kika sha ba? Na soma kuka, yayi maza ya dakatar da ni, ke Maryam tsaya in gaya milki mata fa basa kuka in zasu haihu har ki yarda ki yi abinda Rumasa'u za ta zo tana yi miki gori don ita ba ta kukan haihuwa. Hankalina a tashe na ce to kar tayi din mana ni ina ruwana? Ya mike ya kama hanyar fita tare da fadin, bari in kira su Umma su zo su kaiki asibiti da wuri tun baki jawa kanki wani abin magana ba a gidan. Sy Ynna syja sgugi daudau uba cewa uh uh uhh tafi can lalle yau za a yi ta, ba za a yi komai ba, lafiya yau za ki haihu ai duk wanda kika gani da danshi abinda ya ji kenan kafin dan ya kai ga zuwa hannu. Waiyo waiyo kwankwasona ai yau kam ina jin gaba daya zai ratattake ya zube a kasa da dai ace na san haka ne da ban bata lokaci ba ma wajen shan raken nan. Rumasa'u ta kyalkyale da dariya har tana neman wurin zama a dalilin dariyar ta tsananta lalel yau mata zasu haihu tafdijan. Takaici ya kama Mubarak ya rasa yanda zaiyi dani to wai ke babu dama ki rufe bakinki ki yi shiru ne? Umma ta ce a'a to wai kai ina ruwanka da ita ne? Nace uhun kyaleshi kawai bai san yanda abin yake ba ne waiyo waiyo kwankwasona. 149 Sannu Maryam, Umma ce mai yi min sannun sai in ce mata yauwa Umma na gode. A haka mukaje asibiti muka samu yaya Dija don an gaya mata za a kaini asibiti, ita kam saboda takaici ji ta rinka yi tamkar tayi amai don bakin ciki, to wai ke ba dama ki yi shiru ne? Sai ince uh uh yaya Dija ba ki fa san abinda nake ji ba kin san ke naki masu saukin kikeyi da rakin da magana, ganin da kukan da ihun kiran likitan gaba daya basu sa haihuwar tazo ba sai da lokacinta yayi wajen karfe goma da rabi na dare gabjejen yaro kato ga girma ga nauyi tubarkalla gashi mai kyau sai raba idanuwa yake yit amkar dai ace kallon mutane yake yi. Suna Mubarak ya yi irin wanda Rumasa'u da yan uwanta sukace wai bai taba yi ba ya kuma sanyawa yaron suna Muhammad ya kara yiwa babanshi takwara bayan da ya yi mishi da danshi na biyu wanda yake namiji 'yan uwan Mubarak na Jaji sunzo sunan ba kadan ba sun kuma zo min da alheri mai yawa, Inna ma ta cika alkawarin da ta yi na turo min Izzatu ita da Inna ne da kuma tsohuwar da aka daukar mun suke tayani hidimar jegon. Duk kokarin Mubarak na ya boye ya barwa zuciyarshi al'amuranshi don ya samu tsaida adalci tsakanin iyalinshi ya kasa kawar da kai a kan al'amarinshi yana ganinshi yake sakin lallausan murmshi na kuma san da wuya in har ya san sanda yake yin hakan. Wani irin lafiyayyan jego nayi ni da yaron muka zama tubarkalla in banda ina aka saka damu babu abinda Mubarak yake yi da mu. 150 Rannan ya shiga dakina ya fito a lokacin nan kuwa satina uku ne da haihuwa na tsala wata irin kwalliya da in ka ganni sai kayi zaton ranar ne zan karbi hidimar mai gidan, biyosyi nayi tsakar gida ina rungume da yaron a kafadata, karbeshi mana to ba ka ce wurin baba zaka ba? Kaje mishi da shi mana, maganata nakeyi ba tare da na damu da zaman Rumasa'u a tsakar gidan ba. Mubarak ya juyo ya karbeshi yana kara lillibeshi atre da fadin, ki fa rinkayin hankali da shi girman jiki ne kawai... bai karasa ba sai kawai muka jiwo Rumasa'u ta kwallara ihu da sauri muka juya don ganin abin da ya sameta kwankwaso naga ta rike da iyakacin karfinta gabana ya yi mummunan faduwa don tsoron abin da take shirin yi don kuwa damkar da naga ta yiwa kwankwason nata irin wanda na rinka yiwa nawa kwankwason ne a ranar da nayi gwagwarmaya da nakuda waiyo-waiyo kwankwasona, Umma ina jin dai yau din nan za a yi abinda ba a taba yi ba don gani nake tamkar kwankwason nan nawa zai tarwatse ne ya ratattake ya zube a kas,a me rake kai yara ku kira min mai rake. Mubarak dai tunda ya yi mata kallo guda daya bai sake ba balle ya nuna ya ji ko ya ga abinda take yi, hannu biyu kwai ya saka ya dauke danshi ya wuce ya yi tafiyarshi da shi ya barni nan wurin a tsaye ina kallon busasshen wulakancin da Rumasa'u take yi min, ni ba abin in sureta in fyadeta da kasa ba damben tsiya za mu yi kafin in kaita kasa don itama karfi ne da ita to balle a halin da nake ciki yanzu na jego danye. 151 Humhum hum waiyo waiyoo bayana in dai kuka raken yakema to ba zan sake shanshi ba, ta kwashe da dariya ai kuwa dai an bar dadi. Na shigeta nayi tafiyata na shiga daki na zauna ina jirani zuwan Mubarak don ya san da ni takeyi amma ya ja bakinshi yayi shiru. Yana shigowa na soma magana yanzu nan haka matar nan za ta yi tayi min irin wannan wulakancin a gidan nan ba za ka tsawatar mata ba? A fusace kwarai ya ce min an ki a tsawatar din sanda kikeyi ban yi miki kashedi ba? Bance miki za ki yi abin da za ta zo tana yi miki iya shege da shi ba don ita bata kukan haihuwa kikace tayi din, sai kuma yanzu da kika jawa kanki abin magana inje ina tare miki? Ba zanyi ba in taji kin yi shiru ba ki tanka mata ba za ta gaji ta bari ai babu abin da ya tabbata kar ki kulata kin ji? A kan dole na ce mishi to don na gane ba zai yi komai a kai ba. Ta tasoni a gaba abin har ba a magana, kyakkyawar dariya in taji nayi sai ta shiga kwalawa mai rake kira. Rannan kawai nayi sa'a tana cikin tsala tsiyarta a tsakar gida tana murde-murde da iface-ifacen a rike mata kwankwaso zai ratattake ya zube a kasa sai kawai na ji muryar baba yana kwalawa Ummana kira, ina Ummulkhairi ta ke? Da sauri Umman ta fito tana rike da dankwalinta a hannunta, gani Alhaji lafiya dai ko? Bai amsa mata ba ya soma jero mata tambayoyi, yanzun nan kina nan a gidan nan ake yin wannan iya shegen baki hana ba? Ko kina jira ne sai abin ya zama tashin hankali a tsakaninsu? A kidime Umma ta ce mishi, nayi magana Alhaji.. Da sauri ya sake tambayarta ba ta ji ba kenan 152 saboda kema ta raunaki? To ai kuma shi kenan na riga na gano kan al'amari na gane dalilin da ya sa fitina taki karewaa tsakaninsu shi ne na kina da bangaren da kike marawa da kinja kin tsaya a matsayiniki na uwar danki kawai wanda ya yi ba daidaiba ki tsawatar mishi da abin nasu bai yi tsanani haka ba don haka zanyi maganin abin in kuma na sake jin sunyi fada to na san mai laifin tunda na gane ita din fitinanniyar yerinya ce. Tu daga nan jikin Rumasa'u ya yi sanyi ta shiga tsoron kar wani abu ya hadani da ita baba ya ce itace mai laifin, ni kuwa sai nayi arnfani da wannan darmar nima muna hada ido da ita sai in mata gwalo, rannan ina falona a kan kujera shirya Muhammad nakeyi sai ga Mubarak ya shigo zuwa ya yi ya zauna kusa da ni ko ince manne de i tamkar dai a ce maida mu cikinshi zai yi dagan i har yaron, rike yake da kafarshi yayin da shi kuma yake ta faman modar nono. Ban taba ganin mai son da ba irinki gyara dai gyara dai kowane lokaci balkya gajiya da gyarashi ke duk kokarinki wai ki nunamin kin fini sonshi ne ko? Da sauri na ce mishi wace ni yallabai? Baba ne ya ce alkai mishi shi shi ne nake kara kintsashi. Ya kara baiyanar da jin dadinshi ya ce min, kin san abinda yasa baba yake son yaron nan, nayi maza nace mishi uh'uh, to tunawa yake yi da irin wahaloli da kai kawon bacin ran da nayi ta gamuwa da su a kanki Maryam domin shi din shi ne takuici na duk wani abinda kika sani a tsakanina da ke na bada yaron aka fita da shi ya knkameni a jikinshi na tsawon lokacin da yaga hakan ya isheshi sai da ya sake ni don kanshi sai kuma ya kalleni ya ce min, na ganki kina 153 yiwa Rumasa'u gwalo dazu kar ki sake don ba zai zamo min komai ba inje in sameshi in gaya mishi cewar ba ita kadai ce fitinanniyar ba ku dukanku biyun mutane ne daa baku da kirki don baku damu da son zaman lafiya ba, too kawai nace mishi na ja bakina nayi shiru ban dai sake ba. Rannan sai ga Asabe ta zo wurina a wan1 irin yanayi da ba zai kwatantu ba na rashin kyan gani ga kazanta na tuna tsabta da kwalliya irin ta Asabe wai ta zama kazamar da karnintama kawai ya isa ga 'ya ya uku su ne biye da ita daya kuma a bayanta hudu gaba dayansu callo duya zaka yi musu ka kawar da kai, aka ce min kin haihu shi ae nace bari inzo in ga yaron daga nan in yi miki barka, na ce ai na gode bari in kawo miki shi ki ganshi, ne shiga daki don dauko mata shi. Mubarak dake wurin ya kalleni, ke kada ki rinka yi min rashin hankali kin ji ko? Na ce mishi to na dawo na sameta muka dan soma hira har ta kaima na tambayeta ina baba Lantana'? Ta tabe baki ta ce tana can Enugu tana jin dadinta mu tayi banza da mu a nan ta barmu tamkar ba itace tayi mana sanadin wannan wahalar ba, ai ko rannan da naje wajen yaya Salau da sauri na ce a'a Sallau yana ina ne Asabe, ta ce yana can wani gari nan baya yana ta sana'arshi ta gwari, na c kai madalla kowa Ubangiji ya bashi yanda zai yi, maimakon tace amin sai ta ce uhun kai kam ai uwa ta riga ta lalata maka komai sai dai sakaiyar Ubangiji kawai don ta ciceka, zuba mata ido nayi ina kallonta cikin zuciyata na ce, me wannan haihuwar ta amfanar? Iyayen da akace mu yi musu addu'a ita sakaiya take nema a kanta uwar uba kuwa dama ba a maganarshi na sake yin wani tunanin na tuna 154 rayuwar dá baba Lantana ta so inyi kenan a gidan Nalami sai kuma reshe ya juye da mujiya da hannunta ta kai yarta. Kinga baya bamu sabulun wanka bare na wanki balle man shafawa balle zani abincima na dare kawai yake bayarwa in nayi magana ya ce wai shi yana ganin kokarin kanshi in nace zan yi sana'a matarshi ta hana in wasu sukayi tausayina suka bani abu tace satar mata nayi shi kuma yana kallo bai cewa komai don tsoronta yake ji tafi karfinshi. Mama ga kudin cizo a jikinki tayi maza ta kai wa yarinyar duka wannam ne kudin cizo? Kyankyaso ne, na mike na shiga daki na debo turare guda biyu na kawowa Asabe tare da kudi masu dan aiki don na Mubarak ne na gani a ajiye tayi ta godiya ta tafi ta bani ina tunanin rayuwa tare da tambayar kaina ko me baba Lantana taje yi a Enugu? A wannan shekarar ne dai babana ya tafi aikin haji Alhaji Muhammadu mahaifin Mubarak ne ya biya mishi amma sai ya ce wai Muhammad dan jariri ne ya biya mishi. Shekaru biyar bayan wannan lokacin na sake jin wani jegon jegona na uku sai dai a wannan lokacin ina yin jegon ne a wani sabon katafaren gida da Mubarak ya gina mana in da ni da Rumasa'u muka zama sai wacce taga dama ne take shiga wurin 'yar uwarta don bama ma jin motsin juna iyaka dai katanga ta hadamu a wannan lokacin kuma ina jegon nawa ne bayan na kammala karatuna na digiri a jami'ar garinmu banda wannan kuma wani karin jin dadin shi ne ina yin jegon ne a karkashin 155 kulawar uwar miji wacce bata taba zuwa gidan dan nata ba sai a dalilin haihuwar tawa ga kuma baba Sumaye da na riketa matsayin uwa saboda sanin da nayi taso uwartawa sanda take raye taso ta kuma bayan bata nan ta kuma ike amanar dake tsakaninsu yana kuma daga daga kuntatawar da da zai yiwa iyaye a bayansu ya mutunta wanda suke mutuntawa. Inna da Izzatu suka shigo su biyun a yanzu manyan ya mata ne in ka barni ma sai in ce shirin aurensu Mubarak yake yi ko da dai bai gaya min ba don su din a hannuna suke. Shirin mikewa nake yi inje wurinshi saboda dawowarshi da naji sai gashi ya shigo da murmushina na tareshi ina fadin, yallabai kaji wai ashe musakai da mabaratan nan da gwamnatin kudu ta tattara ta dawo arewa da su ashe wai har da baba Lantana a cikinsu ashe can Enugun da taje bara takeyi sannan wai bata barar hakan kawai sai ta lallankwaye ta maida kanta tamkar wacce aljanu suka taba yanzu kuma da aka daw0 ia su anyi juyin duniyá ta koma yanda take abu ya gagara komai ya makale tana can sai zuwa kalon ta akeyi tana ta kuka. Juyawa yayi zai fita ba tare da ya ce min kala ba, Inna tayi maza ta ce mishi haba kai kuwa wane irin miskilanci ne wannan? Yarinya tana ina taka saka da kai sai faman gwaleta kana shassharewa kakeyi me tayi maka ne? Ranshi a hade ya ce, haba Inna gajiya nayi da abin kunyar da yarinyar nan take jawa mutane, yanzu ace ita ba zata daure tayi hakuri da bainda sauran mata suke 156 hakuri da shi ba? Kullum in zata haihu ta rinka ihu kenan tana yi mana bankada a wuri ana kallona? Kuma wai har a gabanki ba zata fasa ba? Inna ta ce mishi kai tafi can da wannen maganar taka kai dai fitinannen mutum ne yanzu yanda wurin nan ya kacame da iface-ifacen mata har kana iya sheda ga muryar wata a ciki? Duk matan ma yanzu ba kukan haihuwar suke yi ba? Kai kasanta ne? Da sauri ya ce ba dukansu bane Inna ai Rumasa'u bata yi shiru take haihuwarta sai dai a ganta da danta kawai, haushi da takaici shi suka taru suka lullubeshi in har akwai wani abidna na tsana bai wuce misalin da yakeyi min da haihuwar Rumasa'u ba. Da sauri naji Innan tayi mishi tsawa, kai tafi can ka bani wuri wadannan 'yan mitsi mitsin 'yayau da take haifowa in tace za ta yi kukama ba sai a dake ta ba, dadi ya kamani shi kuma yayi murmushi, Inna ba ki son laifin Maryam to a dan bani yaron in kaiwa abokaina da suka zo min barka su ganshi. Yana barin dakin nayi kwafa na ce bari tunda abin nashi ya zama hakan nasan abinda Zanyi ba sai na yarda na kara baihuwar ba ne ma zai sake yi min irin wannan wulakancin? Ai yafi kowa son 'ya'ya tunda shi ne mai zirga-zirgar nunawa jama'a su to na daina ba zan kara ba. Ta harareni da gefen ido kafin tayi tsaki ta ce min kinji shirmenki kuma ni ina cewa wani abin za ki yi don ki kwato 'yancniki a wurinshi ya kame bakinshi ya daina wannan iya shegen? To in kin bar haihuwa wa kika yiwa? Danki ai arzikinki ne, yanzu ni baki ganni ba? 157 Haihuwarshi fa akayi aka kwace min shi na hakura na tafi da ya girma bai nemoni ba? Da sauri na ce mata ya nemeki Inna, to da wanda ya kai ni morarshi ne a yanzu? Da sauri nace babu. Ta gyada kai, to nemo wata mafitar amma ba wannan ba na ce to. Kwanakin jego sun kare har inna da baba Sumaye sun koma gidajensu daga ni sai iyalina ne a gida 'yayana uku Muhammad, Khadija sai mai sunan babana Abubakar Siddik sai kuma 'yan mata na Inna da Izzatu da masu aikin gidan a yanzu ban cika lura ko neman sanin me Rumasa'u ke ciki ba balle ta dameni musamman da na gane irin roaganganun da yake yi min suke yi min ciwo na ita dabn ce ba halinku daya ba ita ai tana jin maganata, ashe itama yanayi mata dace nayi naji shari'ar da akayi musu inda take ta kuka tana fadin kusan kullum sai ya kirata da sunan Maryam banda haka kauma sai ya gaya mata ni din daban ce ni ina girmamashi ina jin maganrshi ina gudun bacin ranshi tun daga nan na tattara maganganun nashi na ajiye a gefe saboda na gane dabi'ar shi ne in za a yi fada da shi ya fadi mai zafi in kuma ana zaman lafiya kaga tamkar bai iya komai ba sai alheri. A yanzu kokarina yafi tafiya re wajen ganin ban bashi damar da ya sake shigo min da wata ba amma, Rumasa'u wata a tsakaninmu ya fada ya kara nanatawa wacce bata shigo ba za a iya hana shi kawota ya hakura amma wacce take ciki to babu mai rabashi da ita don shi din wani irin kishi ne da shi da ba zai iya lamuntar ganin wani kato ya aurar mishi matarshi ba don haka sai ya 158 gwammace in tayi mishi yayi mata in anji jiki a gyara amma ba saki ba. Ita kuwa Rumasa'u a yanzu babi abinda take so irin ganin ya kara aure ya dai kawo wata wai nima in ji irin abinda taji sanda aka kawoni. Mubarak ya shigo dakina bina yakeyi da kallo ban fa gane irin yangar da kike yi min ba na lura wani yanga kike yi min kin a wani shan kanshi kina jammin rai ko sanda zan karbi ajiyata a wurinki ai ba irin wannan jan ajin kika yi min ba, wuce shi naje zanyi yayi maza ya cafko kuguna ya rike zo ki gaya min me ya faru? Wata uku da haihuwarki amma har yanz ba ki yi min ban gajiya ba. Na daure fuska sosai don kar yaga alamar wasa na ce ai ni na daina irin wadannan abubuwan, wadanne? Nayi shiru ban amsa ba ia magana dai kenan ya jani zuwa inda yake nufin kainin ya shimfideni shima ya kwanta a gefena nayi maza na tashi na zauna, me kike yi ne haka? Na ce mishi a'a ai ba zanyi bane ba kuma zan yarda in sake ba da inje ina yin abinda zai zama sanadin da zan rinka ja maka abin kunya a cikin mutane suna kallonka ai gara ba a fara ba. To a ina kika ga ana yin hakan Maryam kicekin daina samun ladan mijinki kin daina faranta mishi rai, kin daina menene menene? Wai zna me yakawo wannan ma ganar ne kinji wani ya ce miki wani abu ne? Na bata rai na ce, ina ruwana da wani? Me wani zai yi nin ya dameni? Wulakancin ka ne kawai ya isheni na gorin da kake yi min a kan kukan hai... 159 Ban karasa ba ya yi maza ya ce, ni Maryam ai babu sharri a tsakanina da ke to ni yaushe nake iya sheda wata murya a wurin nan abinda Inna ma ta ce gaba daya duk matan zamanin yanzu kukan haihuwar sukeyi, ai in dai don ta wannan ne sha kuruminki gasa wannan bakin nawa' zanyi ba za ki sake jin wata kalma ta fito daga cikinshi in dai a kan ihun nan ne sai san barka da godiya, don haka sa bannayenki biyu kawaiki rage min kayan nan dake jikiniki don ki sa ni in ji dadi in samu farin ciki da natsuwa a zuciyata saboda sanin duk abinda nake yin yinshi nake bisa yarda da amincewarki, kina so ne nima ina so ba tilastawa ko fin karfi na nuna miki ba. Sannu a hankali cikin yanayi na natsuwa da jan rai irin na mace don dai in kara sashi ya kara matsuwa da abinda ya riga ya matsu, nasa hanu na soma zare kayan dake jikin nawa ina jifa da su daidai da daidai ba tare da na danu ko na lura da inda kayan suke faduwa ba. Wassalam Taku HAFSAT C. SODANGI Fatan alheri gareku dukanku, na gode Ubangiji ya saka muku da alheri bisa kulawar da kuke yi ma rubutuna na gode. 18/2/2015 160