[14/07 à 11:59] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...* 🪆 🪆 🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 1_2* *AOKIGAHARA* shahararren daji ne a ƙasar Japon,wanda mutanen duniya sun yi itifaƙin cewa shi ya na ɗaya daga cikin hatsabiben dajika huɗu da suka yi shuran hatsari a duniya.Dajin zubar da jini,dajin fatalwa,shi ne laƙabinsa. Mutane ne sama da ɗari jere rasa sun yi layi biyu,masu sanye da baƙaƙen kaya su ne a hannun hagun,yayin da uwanda suka saka jajaye suke hannun dama.Dukkansu da manya hulluna a kawunansu ta yadda ba a iya ganin fuskokinsu.Rugugin da tekun ta ɗauka ne ya saka su fara yin wani yare su na karanto wasu ɗalasamai “Kanzakhani yelolini,barhan yakulu,isbaryeyejanye” tamkar su na zuga shi haka yake yin sama ya na zafir kamar zai kamo sama bisanin can ya lafa ya yi tsit. A hankali wani dattijo ya fito daga cikin ruwan ,a ƙalla zai kai shekaru sattin a duniya.Fari ne sol,ka na ganinsa ka Bayahude saboda gashin bakinsa da ya yi wani tsini da tozo.Fuskarsa a murtuƙe,ya zo ya tsaya a gabansu daga shi sai wani jan ƙyalle a ƙugu. Shiru suka yi suka bar karanta ɗalasaman tsafin,daidai nan wata baƙar guguwa ta taso ta shiga saka wa mutumen nan da ya fito wasu fararen kaya tare da doguwar sarƙa har ta na shirin taɓo cibinsa. Yaf! Yaf!Yaf aka fara yin wasu yayyafi,kamar haɗin baki a tare suka ɗago kawunansu da sauri har hullansu na fita su na mai furta “Shugaba Marlin! Shugaba Marlin! Shugaba Marlin!” A hankali ya fara soma takawa,ya na bin ɗaya bayan ɗaya ya na tsaka tafukan hannunsu da wata aska.Tuni jininsu ya fara ɗigar da jini ya na ɗiga a ƙasa,a ƙarshe ya yankan nasa sannan suka je suka wanke hannayensu cikin Kogin. *Bobby* cike da jarumta ya fito hannunsa riƙe da mashi,har ya nufi hanyar fita ya ji muryar Daddynsa “Bobby ina za ka je haka? Ko ka manta yau ranar murna ce shagali za mu yi?” Bobby ya ce "Daddy training kawai zan yi ,ba zan jima ba” Daddy ya gyara maɓalan suit ɗin jikinsa ya na mai cewa “babu inda za ka je,wuce ka canza kaya mu wuce ” Bobby ya ɓata rai ya ce “wai Daddy murna mice ce? ” “ta na samu ƙarin girma yanzu ni ne shugaba” Mamy wacce ta fito cikin wata fitinaniyar doguwar riga wacce ko hannu babu ta ce “ chéri ka san Bobby bai son taron mutane kawai ka barsa,sai mu je mu biyu” “waooo! Kin kyau muaaah” cewar Daddyn ya na mai zuwa ya rungume matarsa tare da sakar mata kiss,“na gode ta furta ta na godiya” Ba don ransa ya so ba haka ya je ya shirya tsaf cikin baƙaƙen suit ya fito suka wuce.Babban shagali ne ake,duk wanda suka hallarci taron hamshaƙan masu kuɗi ne.Banda barasa babu abin da suke bankama,su na cashewa.Bobby na daga gefe ya na kallo kawai,shi sam bai son hayaniya.Aka riƙo hannunsa,ya ɗago kai sai ya ga Daddy ne.“Taso mu je na haɗa ka da abokaina ” ya miƙe ya bisa. Wani waje na musamman suka shiga,Friends ɗin Daddy ne su biyu ko wane da Ɗansa.Bayan sun gabatar da kawunansu sai su ƴaƴan suka keɓe kansu. “sunana Kameel Mohan” “ni kuma Fadeel Martan” “Bobby Marlin ne nawa sunan” ya faɗa ya na ɗan sakin murmushi. Cikin ƙanƙanen lokaci suka yi mugun sabo kai kace wasu abokai ,wanda hakan kuma shi ne burin iyayen nasu wanda daga can gefe su na ankare da ƴaƴan nasu. Baban Fadeel ne ya yi magana wato Martan ya ce “Na taya ka murna sosai da ka shigo tsagen mu ka zama shugaba kamar dai mu” “Hhh! A kullum tunani ya na kan result ɗin ku,ina tambayar kaina ko cikin masu *Blue tsafi* wane ne zai zama zakara? Ashe kai ne” cewar Mohan wanda shi na sa tsafin kuma ya kasance *Jan tsafi* Marlin ya murmushi ya ce “ duk na gode,Martan mi ya sa ka zaɓi *Baƙin tsafi* ?” “saboda ni mugu ne na ƙarshen lamba,sannan ina samun kuɗi sosai a harakar don duk tsiyar mutum in na yi masa asiri ba zai warware shi ba”Martan ya faɗa wanda ya kasance Nasara ne. Mohan kuwa shi baƙar fata ne asalin ɗan Senegal ne,ya ce "Ni kuwa abin da yasa na ɗauki *Jan tsafi* saboda a ƙasashenmu soyayya na wahalar da mutane,shi yasa musamman masu ɗawainiya da sha'awar wasu” “Ni kuwa harakar Aljannun ruwa ita ta fi burge ne,saboda su na da cikon alƙawari ”cewar Marlin wato mahaifin Bobby. “Ya kamata ƙungiyarmu ta samu ci gaba,a kawo sabbin abubuwa musamman saboda yaranmu da za su taso” “eh kam! Wannan shawara ce mai kyau,a fara yin sacrifice ta yadda zamu samu kuɗi irin sosai ɗin nan” “to ai dama ana sacrifice,kawai dai sani ne ba ku yi ba.Amma Ni na san da hakan saboda ina hulɗa da Aljannun ruwa" . Ire-iren wannan hirarakin kawai suka yi ta yi bisanin taron ya watse kowa ya koma gida. Bobby na kwance kan makeken gadonsa ya samu saƙon su Kameel akan yau za su fita da dare.Shi ɗin ba ma'abocin ƙiriniya ba ne kamar yadda duk ma'akasarin samari kan yi amma bai son baiwa abokan nasa kunya shi yasa ya ƙudiri aniyar zuwa.Ƙarfe tara cicif suka faka mota ƙofar gidansu,a nutse Bobby ya fito cikin shigar riga da wando na jeans blue da riga fara. Fadeel ne ke driving,Kameel na gefensa yayin da Bobby ke can gidan baya.Sautin waƙar Céline Dion ke tashi,a haka har suka iso babban club ɗin. “wooo! Dubi wata Baby kyakkyawa ta sha kyau” cewar Fadeel ya na daidaita tsayuwar motar,Kameel ya yi tsuki ya ce “ to kar ka bayar da mu mana,ka ja aji sosai” “no yawuna sun tsinke doli na je gun ta” ya na gama faɗa ya buɗe murfin mota ya fita. Bobby ya fito shi da Kameel suka samu haɗaɗen wuri suka zauna kan kujeru. Serveur (irin masu aiki gidan abinci,wanda suke hidima da baƙi) ya zo ya ce “mi za a kawo maku?” Kameel na faɗin kalolin ababen kurɓewa shi kuma ya na rubutawa a jikin takarda,“shikenan abin da za a kawo banda abinci?” “Bobby ko za ka ci wani abu ne? ” Kameel ya tambaya,ya girgiza kai ya ce “no! Ban buƙata in akwai sigari dai a kawo min” Serveur ɗin ya ce “ok ku bani minti biyar” ya na faɗa ya yi gaba,bai jima ba ya zo ya didire masu abubuwan da suka buƙata. Bobby ya kunna sigari ya na sha hayaƙi sai tashi yake,can ya ce “na tambaye ka mana Kameel,a can Senegal duk haka fatar ku take ko ya ya?” Kameel wanda ke kwankwaɗar giya ya ƙyalƙyale da dariya bisanin ya ce “ana samun masu haske,amma mi yasa ka yi min wannan tambayar?” “kawai dai ina tunanin yaya ƴan matan garin ku za su kasance ne,irin wannan baƙi kamar tukunya” Kameel ya ɓata rai ya ce “ƴan ubanci ne za ka yi min? Hum! Ka san can farko na tsani Turawa saboda baƙar azabar da suka gana wa baƙaƙen fata” “lokacin jahiliyya ne,amma ai baƙaƙen fata sun fi ƙarfi da juriya shi yasa ma nake son baƙar mace”Bobby ya faɗa ya na wani lumshe ido.Kameel ya ƙware da barasar da yake sha ya na ta yin tari bisanin ya ce,“ka na nufin ɓakar mace ta fi burge ka kan ƴan uwanka Nasaru?” “Ni Bayahude ne fa,ina son mace baƙa sosai” “halan ka taɓa tarayya da ita ne?” “no ba haka ba ne,ni wannan harakar ba ta gabana?” “pardon! Tu peux dire quoi exactement ? Ka na nufin ba ka taɓa sanin ƴa mace ba?” Kameel ya tambaye shi ya na wani tsure shi da ido. Bobby ya girgiza kai ya ce “no! Ba haka ba ne,ka ga kawai abar maganar bani barasar na sha” “Hum! Sha sai ka min bayani” ya cika masa kofi tare da miƙa masa, Bobby ya karɓa ya kwankwaɗe ya ce “ Kameel ka na son tuna min rayuwar baya ne?” “A'a ina dai son sani ne” “To je suis pas un puceau ! Na san mace amma ita ɗaya ce tal a duniya”Bobby ya faɗa ya na jin wani irin ƙunci na taso masa har ƙasan zuciya. Kameel ya shiga yin dariya har da riƙe ciki ya ce,“ka na son raina min hankali ne ko mi? ” Bobby ya ɗan ware idonsa kaɗan,ya waiga inda su ka bar Fadeel ganinsa ya yi rungume da Babyn nan su na kissing da sauri ya kawar da kansa . “aboki ya haka kuma? Ina za ka je?” Bobby ya ɗan dafe kansa ya ce “ina ɗan jin jiri ne,bani keey na koma can cikin mota” “a'a jira mu tafi kawai”Kameel ya faɗa ya na miƙe wa shi ma. Bobby ya shiga gidan gaba ya zauna,yayin da Fadeel da budurwarsa suka zauna baya Kameel ya ja su. A cikin mota sautin numfashinsu sosai ya takura Bobby,sam bai son ji ko ganin abin da ya shafi mu'amalar mace da namiji.Da sauri ya kai hannu ya buɗe volume duka ,sai kuma ya yi lamo cikin kujera a haka har suka iso gidansu. Ko sallama bai yi masu ba ya fice ,ya na shigo wa babban falo Daddy ya kira sunansa “Bobby!” bai ko juyo ba balle ya tsaya,direct ɗakinsa ya wuce ya zube kan bed. Daddy ya bi bayansa,gefen gado ya zauna ya fara shafar sumar kan Bobbyn bisanin ya ce “ya ne? Ya soirée ta kasance?” shiru Bobby bai ce komi ba sai goshinsa da ke tsatsafar da zufa. Daddy ya ja wata doguwar ajiyar zuciya,ya na mai juyo da fuskar Bobby sai ya ga tuni ashe bacci ya ɗauke shi. Fita ya yi ya nufi ɗakin sirrinsa,zigidir ya yi haihuwar uwarsa ya tsaya jikin madubi ya na karanta ɗalasiman tsafi. Wani farin tsoho wanda gashin kansa yake kamar na giginya tsabar fari ya bayyana.Daddy ya lumshe ido sannan ya buɗe su ya na mai cewa “Father ina son sanin damuwar Bobby ne, wannan banzar tabi'ar ta shi na baƙanta min rai! Shi ne magajina wanda zai maye gurbina nan da wasu ƴan shekaru a haka mi zai tsinana wa ƁOYAYYAR DUNIYA ? ” “Ba komai ba ne ke ɗawainiya da Bobby illa gubar soyayya da kuma sha'awa.Shekarun baya ya haɗu da wata ƴar Pakistan sun yi soyayya sosai wacce ta kai su da yin mu'amala tarayya,sai dai yadda Bobby ke da ƙarfi sosai ya rinjaye Anita ita kuma sam ba za ta iya juriyar hakan ba shi ne ta datse alaƙarsu.Bobby na son wacce za ta maye gurbin Anita sai dai ya na tsoron kar ita ma ta guje shi kamar waccan.Ɓangaren magie wato tsafi zuciyar Bobby na da girma sosai,RUHIN ALJAN zai yi wuyar ratsa ɓargon jikinsa!” Father ya faɗa cikin wata shaƙaƙar murya. Wani tuƙuƙin baƙin ciki da tashin hankali ne suka rufe Marlin ,ya ce “mine ne mafita kenan?” “Mafita ɗaya ce ka fara shirin rantsar da Bobby ayi masa wankan shiga ƙungiya tun yanzu.Sai an tsafa shi sosai ta yadda a nan gaba ba za mu sha wahala ba” “Gobe zan shirya komi ba sai an ɗauki lokaci ba,yau babu meeting ana hutu ai da tun yau zan aiwatar da komi” “A'a ba a tsafe Magaji da dare doli sai in zazzaɓin rana ya keto,za ku je can AOKIGAHARA ayi masa wanka da ruwan kogi daga nan sai ku je kusurwar dajin domin neman tabaraki” Father na gama faɗar haka ya ɓace.Daddy ya fita,ya koma cikin iyalansa. A ɓangaren su Kameel kuwa can club suka sake komawa suka cashe ayarsu da ƴan mata.Sosai suka yi ta ɓarin kuɗi su na raye-raye,ƴan mata sun samu abin da suke so sai zubar da aji ake. BOBBY Wani mafarki ne ya yi mai kama da saƙo,ya na zaune kan kujera sai ƙoƙarin ɗora masa kambun sarauta ake amma abu ya cuttura.Tamkar ya hau kan garwashin wuta haka yake ji,so yake ya tashi amma kallon da Daddynsa ke yi masa ya ƙi basa wannan damar. Kamar daga sama ya ga wata kyakkyawar sura ta bayyana gare shi,abin da ya lura shi kaɗai ke ganinta.Hannu ta saka ta kamo nasa tare da jansa ta fitar da shi daga cikin taron jama'ar,farin mayafin da ta rufe fuskarta ta fara ƙoƙarin cire wa daidai nan Bobby ya farka da wani matsanancin ciwon kai. Washegari Tun da suka yi breakfast Daddy ya shaida masa da akwai inda za su je. Hatsabibin dajin suka je,tafiyar a jirgi suka yi ta.Kamar yadda Daddy ya yi tsammani tuni ƴan ƙungiyarsu sun hallara. Bobby ya san da mahaifinsa na tsafi,ba baƙon abu ne gare shi ba amma bai yi tunanin layi zai kawo kansa ba. “Bobby yau bikin ka ne,kar ka ji tsoron komi ina tare da kai.Duk wata matsalar ka za ta kau har Anita za ka manta da ita sannan ka samu wata wacce ta fi ta” cike da mamaki Bobby ke kallon Daddynsa,har zai yi masa tambaya sai kuma ya katse masa hanzari “ka cire kayan jikinka ka shiga ruwa ” “Daddy...” da sauri ya ɗaga masa hannu,ba don ya so ba haka Bobby ya bi umarnin mahaifinsa ya cire kayan jikinsa ya bar ɗan ƙaramin wando. Tuni members suka fara rera wakokinsu na ɗalasiman tsafi, Bobby ya shigar da ƙafafunsa girrr ! Haka ya ji kamar lantarki ya ja shi bisanin ya fara nutsewa a hankali cikin ruwan har suka kawo ga wuyansa,kansa na nutse wa suka ido huɗu.... [14/07 à 15:29] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 3_4* Suka yi ido huɗu da kifi-mutum (irin kifayen nan masu rabin jiki na ƴan Adam ) fuskar Bobby ya riƙe gam nan take ya fara ganin wasu taurari na gifta masa.Ya ja shi can ƙasan ruwa,tuni numfashin Bobby ya fara barazanar ɗauke wa . Kifi-mutum wanda ya kasance Sarkin ruwan gaba ɗaya ya shaƙe wuyan Bobby na second uku nan take ya dawo hayyacinsa ya yi tsaye kan ƙafafuwan shi kai kace bisa doron ƙasa ne yake tsaye. Ruguuuu! Kifaye suka fara ɓullo wa ta ko wace kusurwar kogin su na zuwa inda su Bobby suke,wannan ya saka ruwan motsawa su na zillo kamar za su taɓo sama. Bobby na cikin ruwa amma ya na jin muryoyin mutanen da ya baro can gaɓar ruwa su na karanta ɗalasiman tsafi,wanda yake jin tamkar su na azalzala masa huta ne a gangar jiki. Ga shi dai cikin ruwa yake tsumbul amma azababen zafi yake ji,ya na ratsa fatar jikinsa ya na shiga ɓargonsa.Idonsa ne abu na farko da ya fara ɗaukar caji,wani zuuuu! Nan take su ka canza launi su ka koma kore kamar na mage. Sarki ya kwantar da Bobby bisa dutsen Barclay wanda a nan ne ake tsafar da bil'adama da ke son pouvoir/can/ƙarfin iko.Rawa dutsen ya fara yayin da fatar Bobby ta fara fitar da jini,wanda kafin ƙyaftawar ido ruwan kogin sun ɗauki launin ja.Tsit duk members ɗin suka yi da karanta ɗalasiman.Jikin Daddy ya ɗauki wani irin rawa kamar mazari hankalinsa ya tashi. Ƴar kallon-kallon aka fara tare da yin zugum saboda wannan alama ce ta rashin sa'a.Kamar fitar tusa haka gangar jikin Bobby ya ɓullo daga cikin ruwa sam babu alamar numfashi a tattare da shi. Father ne ya bayyana daga can tsakiyar ruwa dogon farin gemunsa na ɗigar da wani haske.“Kar ku jinkirta ku ɗauke shi ku shigar da shi NOIRA(wuri ne na musamman da ke cikin dajin wanda a nan ne duk hatsabiban hadarurruka ke ci) zai farfaɗo ku yi masa abubuwan da suka dace” ya na gama faɗa ya ɓace. Mutum shidda ne suka ɗauki Bobby su na tafe su na yin wata waƙa kamar ta jinnu har suka isa kusurwar dajin.Tun daga bakin ƙofarsa gaban ka zai faɗi yadda wata ƙatuwar halitta ta yi bake-bake ta kace hanyar shiga. Fukafukinta ta kaɗa hakan ya bata damar tashi sama ta shiga gaba su kuma su Daddy na take mata baya.Gidin wasu bishiyoyi uku masu kaloli ja,bulu da kuma baƙi aka kwantar da Bobby. “Tun da ake kawo bil'adama ban taɓa ganin wanda ruhinsa ke da mugun ƙarfi ba kamar wannan.Shin ɗan wane addini ne? don bai yi kama da wanda bai da abun bauta ba” NATA wacce ta kasance ita ce mai gadin wannan kusurwar ta tambaya ta na mai kai hannunta ta shafi kumatun Bobby. Wulk! Ya buɗe idonsa tarau kanta,da mugun sauri ta ja baya ta na mai ci gaba da kallonsa. Cike da murna Daddy ya bada umarnin a fara karatu,duk suka lumshe ido su na jero ɗalasiman tsafi cikin salo. Sayun bishiyoyin ne suka rinƙa ɓaɓakowa daga cikin ƙasa su na ɗaga Bobby sama yayin da kuma suke laulaye gangar jikinsa. Ihu ya fara saboda tatsar shi suke kamar wata awara,an ɗauki kamar minti biyar kafin su yi ƙasa da shi nan kuma furanni suka fara zuba bisanin guguwa haɗi da cida. Ruwa suka fara zuba kamar an karkata bakin ƙwayar,a na cikin haka dajin ya ɗauki wani irin duhu.Bobby ya yi saurin rufe idonsa saboda gane-ganen da ya fara yi,sai dai hakan ma da ya yi ba ta canza zane ba.Matattu kawai yake gani su na gifta masa sanye da fararen kaya,wasu kuma ƙwarangwal yayin da kuma wasu ke zo masa a siffar aljan-mutum. “Daddy!” Bobby ya furta cike da tsoro jin hannu ya dafa kafaɗarsa,sai dai shiru Daddy bai amsa masa ba.Kukan Mujiya🦉 ne ya fara tashi busanin jemagu,da sauri ya sa hannu ya toshe kunnuwansa. “shuuuwuu! Huuukmm! Rhooo!” sautin da ya fara ji kenan a kunne tamkar za a zaro amadun kunnensa. Ya zabura ya miƙe tsaye ya na shirin guduwa,dajin ya washe ya dawo rana fayau. Ido tulu-tulu Bobby ke kallon sawun namun daji da tsuntsaye,su Daddy kuwa sam ba su nan.Waige-waige ya fara,kamar daga sama ya ji muryar na magana “Sunana itaciyar BLUANT wacce ke sarrafa duk wani blue tsafi da ya shafi aljannun ruwa” kallon bishiyar ya yi sai ya ga launinta irin na sararin samaniya ne,daga gefensa kuma aka ce “ni kuma itaciyar ROUGEAU ,aikina shi ne haddasa hutar sha'awa ta hanyar tsafi” dubansa ya maida da jar bishiyar,daga bayansa ya waiga sai ya ga baƙar bishiya ce “ni kuwa sunana NOIRANT ,ni ce ke aman duk wani baƙin tsafi ” Muƙut! Bobby ya haɗiye wasu yawu,burinsa ɗaya ya fita daga cikin wannan baƙin dajin.NATA ta yo fifike ta sauko ƙasa,Bobby ya ja baya kaɗan ganin ƙatuwar Mace a siffar bil'adama amma da fukafuki. “Kar ka ji tsoro kyakkyawa,mu je na kai can gun sauran members” ta na gama faɗa ta ɗauke shi ta ɗora kan kafaɗarta bisanin ta tashi sama.Sun yi tafiya mai nisa,Bobby dai ya na ta baza ido ya na kallon duwatsun da ke kwance a ƙasa kamar da shi aka yaɓen wurin. Ta na sauke Bobby aka saka masa kaya bisanin su shiga jirgi su dawo gida.Cikin zafin rai yake taka matakalen benen,Mamy na kiran sunansa sam bai tsaya ba.Ɗakinsa ya shiga ya fara watsi da kaya,sosai yake jin baƙin cikin duk abubuwan da suka faru da shi a yau. Wata uwar tsawa Daddy ya yi masa,tare da ɗaga murya ya ce “Bobby ! Ka yi hauka ne ? ” “Eh hauka nake! Daddy kawai don ina yin duk abin da ka ce shi kenan sai ka tsafa ni ? Na ji na yarda kai ɗan ƙungiyar asiri ne,ban damu ba wannan ra'ayin ka ne.Amma akan wane dalili za ayi min duk wannan shirmen?” bai rufe bakinsa ba Daddy ya ɗauke shi da wani mari wanda ya saka shi faɗuwa ƙasa bai shirya ba. Da yatsa ya nuna shi ya ce “kar na kuma ji ka kira wannan da shirmen,in kuwa ka yi kuskuren yin haka zan guntsire ma halshe.So ka ke Father ya yi fushi da mu ko mi? Wannan abun da ka ke kira shirme to shi ne madogararmu,tun kakanni da iyaye.Ni ma gada na yi gun mahaifina,shi yasa kai ma doli ka karɓa in kuma ka ƙi to duk za mu hallaka sannan Mamynka ita ce ta farko da za ta su kashe” Hankali tashe Bobby ya ɗago kansa wanda tunda Daddy ya maresa ya sunne,ya ce “su wa za su kashe ta? Daddy kar ka bari wani abu ya samu Mamyna in hakan ta faru mutuwa zan yi” “kisan gilla za su yi mata kuwa,namanta za su rinƙa yanka wa su na ci har sai ta zama ƙwarangwal ta mutu” cewar Daddy ya na mai jan wata doguwar ajiyar zuciya bisanin ya ci gaba da cewa “ka na ji Bobby ? Duk wannan abun da nake wa kai ne fa! Ina son ganin ka cikin kyakkyawar rayuwa,kuma ta wannan hanyar ce za ka samu cikon burin ka wato Anita budurwar ka” “ Daddy ka san Anita ne?” “Eh na santa,Father duk ya bani labarinta” “Wane ne Father ?” “Shuganmu baki ɗaya na *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI*” “Ka na nufin ya na da ƙarfi ne har haka? Har ya san mun yi soyayya da Anita?” Sai da Daddy ya ƙyalƙyace da dariya sannan ya basa amsa da “duk yadda ka ke tunaninsa to ya wuce nan,shi ɗin fa ba mutum ba ne,komi ya na gani yanzu haka hirar da muke a yanzu duk zai samu labarinta” “Daddy da gaske zan samu Anita ?” “Eh za ka same ta Bobby muddin ka bi ƙa'idodin duk abin da za shimfiɗa ma” Bobby ya yi wani murmushin farin ciki ya ce “zan yi komai akan Anita sai dai fa Daddy ban san gidansu ba?” “Kar ka damu,mu da muke da Father duk zai faɗa ma.Mu je ka ci abinci”Cewar Daddy ya na mai jan hannun Bobby suka sauko ƙasa. Umarni ya bada aje a gyara ɗakin Bobby ɗin,Mamy kuwa da mamaki ta ce “ya haka? Ka shiga da fushi ka sauko da murna?” Bobby ya shagwaɓe fuska ya ce “ a bani abinci yunwa nake ji” “Jansh? Janash ?” Mamy ta ƙwala kiran ƴar aikin nasu,da saurinta ta fito ta na mai amsawa “ki zo ki yi saving ɗin mu kafin ki ci gaba da aikin ki” duk suka samu wuri suka zauna,Janash ta zuba masu frite da niƙaƙen nama suka fara ci su na hira. Daddy ne ke shaiwa da Mamy yadda lamarin tsafar da Bobby ya kasance a ƙarshe ya ƙara da “Ruhinsa na da ƙarfi sosai wannan ya sa Father cewa a fara tun yanzu don akwai jan aiki a gabanmu,sam ban yi tunanin Bobby zai fito da rai ba yadda na dutsen Barclay ya ƙi karɓarsa ” “Kar ka ji komai,ai tun ranar da na haife shi na faɗa ma Ɗana waliyi ne ya na da wata baiwa ta musamman ”Mamy ta faɗa ta na murmushi. Bobby ya ce “oh! Na manta bari na je na ɗauko wayata ina son jin su Kameel” ya faɗa tare da tashi ya nufi ɗakinsa. Wayar ya ɗauko sannan ya fito zuwa filin training inda yake wasar mashi da ta doki.Cikin rumfa ya shiga sannan ya buɗe data, group ɗinsu na su uku ya shiga ya yi masu hi! Ai kuwa dama duk su na online su ka maido.Hira suka fara taɓa wa,hannun Bobby har rawa yake wajen rubuta masu abubuwan da suka faru.Tuni suka ruɗe wanda har ta kai su da bada wurin haɗuwa domin su tattauna. Da sauri Bobby ya koma ɗaki ya shirya tsaf,cikin motarsa ya tafi can gidan shakatawar.Har sun zo,hannu ya basu suka gaisa sannan ya samu kujera ya zauna “Mu fara cin abinci kafin ka bamu labarin al'mara ” cewar Kameel ya na dariya don shi sam bai yarda da maganar ba. “Ni kam na ci abinci kafin na fito zan sha da lemu” Bobby ya faɗa. Fadeel kuwa sam ya kasa cewa komai sai tunani yake in kuwa hakan gaske ne ya zama dolai shi ma ya je. Bayan an kawo masu abubuwan da suke buƙata Bobby ya ƙara jadadda masu komai kamar dai can farko. “Aboki ka ce ita mai gadin wurin mace ce,kuma wurin na da haɗari ? Kaiii ban yarda ba” cewar Kameel. “Amma mi yasa Daddyn ka ya kai irin wannan wurin mai haɗari? AOKIGAHARA fa duniyar fatale ce,duk wanda ya shiga dajin ba zai dawo da rai ba,in ma ka fita da ran to fa a mahaukaci ne kawai” Fadeel ya faɗa cike da nutsuwa. “To ni dai kam mun je,in kuma ba ku yarda ba sai ku shirya na kai ku ” “abin da ke raina kenan,amma yadda Kameel ke da tsoro ina ga ba zai iya zuwa ba” Fadeel ya faɗa ya na dariya. Kameel ya kai shawarma bakinsa ya ce,“in za ku je mi zai hana ni zuwa?” “Bobby tunda haka ne yaushe za ka kai mu?” Fadeel ya tambaya. “Duk lokacin da kuka shirya” Bobby ya basa amsa. “Awa ɗaya ce daga nan zuwa AOKIGAHARA ina ga mu na iya tafiya yanzu” cewar Fadeel cike da zaƙuwa. “Dare na iya yi mamu a hanyarmu ta dawo wa,ku dai bari har gobe” Bobby ya faɗa. “Hum! Dama nace ƙarya ce,ga gaskiya nan ta bayyana sai kwana-kwana ka ke” Kameel ya faɗa don shi sam bai yarda ba. “Ku tashi mu tafi” Bobby ya faɗa ya na miƙewa tsaye,“da motocin za mu je ko mu tafi da ɗaya kawai?” Fadeel ya tambaya. “Mu je da ta Bobby kawai ,in mun dawo sai mu biyo ta nan ka ɗauki taka” Kameel ya faɗa. Haka kuwa aka yi suka shiga mota ɗaya,Fadeel shi ne ke driving Bobby na gefensa yayin da Kameel ke zaune can gidan baya. Hanyar da za ta kai ka dajin sam dama babu wasu gidaje sai irin uwannan mutanen maras galiho da suke ɗan buga gidan roba.Tafiyar awa ɗaya da rabi suka bisanin su kawo ƴar siririyar hanyar da za sada su da can cikin ainahin dajin. “Mota ba ta shiga” cewar Fadeel ya na samun wuri ya yi parking duk suka fito. Bobby ke gaba su na binsa baya,ko tako goma ba su yi ba suka ji wata irin ƙara ƙiiiiii! Suka waiga a tare mi za su gani? Hanyar shigowa ta rufe ruf.... ★SENEGAL Wasu ƴan mata biyu ne zaune kan capet,su na cin kayan marmari.Kallo guda za ka yi masu ka san ƴan gata ne,duba da yadda baƙar fatar su take wuwulniya ta na sheƙi kamar ka lashe. A tare suka ɗago suka kalli ƙofar shigowar,“mtsss!” ɗaya daga cikin Twins ɗin ta yi tsaki,yayin da ɗayar kuma ta amsa sallama cikin sanyin murya ta na mai cewa “wa'aleykum salam! Kawun ina wuni? Ya hanya ya kuma iyali?” Wanda ta kira da Kawun,ya ƙarasa shigowa ya na amasa wa ya ce “lafiya lau Zahra ,ya wajen ku fatan na tarar da ku lafiya?” “Ba a sani ba! In ba tsabar iya yi ba ai ka gan mu ƙalau mine ne na tambaya? To Abba bai nan sai a tattare tsamokaran tsumman da aka kwaso ƙafa aka zo da su mtsw!” Kawu ya ce “Bintu ina matsayin Yayan ubanki ki ke ja min tsuki? Eh lalle! Amma ba laifin ki ba ne,laifin wannan munafukar uwar taki ce da take koya miki fitsara” Bai ida rufe bakinsa ba wata kyakkyawar mata ta fito ta na cewa “hayaniyar mi nake ji haka ne kamar ana yaƙin duniya?” su na haɗa ido da Kawu ta wani yamutsa fuska ta na haɗe rai ta ce “Yaya Mansur ne?” “A'a ba ni ne ba! Wato Hajara bayan kin mallake ƙanena shi ne kuma ki ke koyar da ƴaƴansa mugun hali ko? ” “Eh ta je ta...” uwar tsawar da aka daka mata ce ta sa ta yin shiru ta na turo baki haɗi da kallon Abban nata. “Ya Mansur ina wuni? Ya su Inna fatan duk su na lafiya?” Abba ya faɗa cike da kulawa. Mansur wanda suke yi wa laƙabi da Kawu ya haɗiye wasu yawun baƙin ciki ya na kallon gizner Ƙanen nasa wanda su biyu tal uwarsu ta haifa. “Alhamdullah! Dama zuwa ne na yi tunda kai an shanye ka ba ka da ta cewa ka auro alaƙaƙai.Yanzu Ayub shikenan ka tsinke igiyar zumuncinmu? Yaushe rabon ka da ƙauye ? ” “Don Allah Yaya ka zauna ,ko fa ruwa ba ka sha ba amma ka fara yin ƙorafi.Maman Twins haɗa wa Yaya abubuwan motsa baki” Abba ya faɗa ya na mai jawo hannun ɗan uwansa ya zaunar da shi kan salon. Bintu ta yi wani saurin tashi ta na toshe hanci,sarai Kawu ya ganta.Momy kuwa ba don ranta ya so ba ta shiga kitchen,ba a jima ba sai ga ƴar aikinsu ta shigo da tray ta ajiye a gabansa. Saboda mugun kari irin na Kawu ƙiri-ƙiri ya ƙi cin komai.Ji yake kamar ya shaƙe Abba ya mutu don ya gaji dukiyarsa. “Don Allah Yaya ka yi haƙuri in sha Allah sati mai zuwa zan je ” “Hum! Kullum haka ka ke faɗa,daga ƙarshe kuma ka ƙi zuwa” “Wannan karon in sha Allah zan je kar ka damu” “Zan koma,dama don na yi maka tuni ne akan haƙin da rataya kan wuyanka tunda an juye ma kwanya” cewar Kawu ya na miƙewa. Abba ya yi murmushi,ya san halin Yayansa sosai.“Haba Ya Mansu kar sheɗan ya hana ka yin aikin lada,duba fa da niyyar kwana ka zo tunda ga kayan ka nan ma ka zo da su.Yi haƙuri ,Zahra tashi ki gyara masa ɗakin baƙi” Da “to Abba ” ta amsa kafin ta miƙe,ta je ta ƙara gyara ɗakin sannan ta kwashi duk abincin da aka kawo wa Kawu ta kai masa can masaukinsa. Abba ya fita dama wajen aiki zai je, Kawu kuwa ya na shiga ɗaki ya fiddo tarkacen layun da bokansa ya basa kafin ya maida su ya na dariyar mugunta..... Share please [16/07 à 08:07] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 5_6* Bayan Kawu ya ci ya ƙoshi ya yi kwance sai faman murmushi yake.Dare na yi ya fara aiwatar da aikinsa duk ya bi gidan ya turbuɗe da layu. Washe gari Abba ya basa kuɗi masu yawa ya ce "ga wannan kafin na dawo" Kawu ya karɓa ba godi balle na gode ya saka aljihu . Falo ya fito ya zauna kan kujera ya na kallon TV,Bintu ta Zahra ne suka fito cikin shigar kaya kala ɗaya don komai nasu iri ɗaya ne wannan ya saka ba kowa ke iya banbance su ba,sai da halinsu don Bintu fitsararra ce ta ƙarshen aji,ita kuwa Zahra babu ruwanta asali ma tsoro ne da ita. "Ina kwana Kawu an tashi lafiya ?" "Lafiya lau tauraruwa alhamdullah ya fama da mai mugun hali?" Sai da Zahra ta ɗan yi murmushi ta kalli ƴar uwarta Bintu ta ce,"sai haƙuri Kawu" "Kin fi ƙarfin ko gaishe da magajin ubanki to ina kwana?" Kawu ya faɗa ya na hararen Bintu .Ita kuwa baki ta zumɓuro ta na gunguni,"kin yi wa ubanki Ayuba da uwar ki Hajara shigiya fitsararra wacce sheɗan ya yi ma fitsari akai" "Ni dai ba shegiya ba tunda da ubana kuma har aka kwaso jiki aka zo wajensa don cin banza..." Bintu ke faɗa cike da rashin kunya,Mama ta katse ta "Bintu mi na faɗa miki? Ban ce kar na kuma ganin kin yi wa babba rashin kunya ba?" "Mama shi ya fara ja na fa" ta faɗa a shagwaɓe. Jiki na ɗan rawa Mama ta ida sauko wa daga step ɗin ta na taɓa hannuwa "Yayan mahaifin naki ki ke faɗar shi ya fara jan ki?" Wani irin dundu ta kai mata a baya kafin ta balbaleta da masifa. Kawu Mansur ya yi wani murmushin mugunta,ƙasan zuciyarsa fal farin ciki. "Ya Mansur don Allah ka yi haƙuri ka san har yanzu ƙurciya ne da ita,duka 15years babu yawa" "Ko ma dai mine ne ai ke ki ka koya mata,kin ga ma tafiyata" ya na gama faɗa ya shiga ɗaki ya a haɗe kayansa ya koma can ƙauyensu *Djifer*.Ɗansa babba Halilu ya tarbe shi,"Baba ya ya komai ya tafi daidai ?" "Fiye da yadda ka ke tunani,kawai ka fara shirin zuwa kamun kifi gobe wanda za a yi masa girki" Halilu ya washe baki ya ce "Baba har na matsu garin Allah ya waye wayyo daɗi " "Ai wannan karon ba zai kubce mana ba,yadda na bi ƙa'idodin da boka ya ce tabbas zai zo.Wai ka ga yadda shegiyar matarsa ke min ladabi? Da zan tawo har da haƙuri ta yi ta bani hhhhh" Halilu ya ce "Haba dai? Kenan ita tuni asirin ya fara aiki a kanta? " "Eh sosai! Shi ma uban gayyar har wani rawar hannu yake da zai bani kuɗi inda can farko ne bai wuci ya bani dubu goma ba" "Baba ka san kuwa ina son Bintu?"cewar Halilu ya na wani karkace baki. "Mu bar wannan maganar ka ji! Bari na shiga daga ciki" Halilu ya bi bayansa da kallo kawai ya na jin ko sama da ƙasa za su game Babansa bai isa ya hana shi auren Bintu ba. A can kuwa ɓangaren Mama sosai take mugun shakkar Kawu Mansur ɗin.Sam zuciyarta ta ƙi sukuni,haka ta kira Daddy murya na ɗan rawa ta ce "Baban Twins Kawu fa ya yi fushi ya koma Djifer(ƙauyen su) ina ta basa haƙuri amma ya ƙi saurarena" yadda Abba ya ji hankalin matar shi a tashe ya ɗaga nasa hankalin babu shiri ya dawo gida. "Kawai ka je Djifer ka basa haƙuri" cewar Mama. Abba ya ce "ina da aiki sosai a office sai dai zuwa gobe,mine ne ya faru har ya yi fushin?" "Bintu ce ta masa fitsara,ka san ba mutumci ne da ita ba" "Ina take?" "Sun tafi makaranta" "To ki kwantar da hankali don Allah,zan je na basa haƙuri har gida" "To Allah sa ya haƙura ɗin,sam zuciyata babu daɗi baban Twins" Kumatunta ya ɗan bubuga tare da rarrashinta,dakyar ta barsa ya koma can wajen aikinsa. Makarantar islamiyya ce suka tafi,ba wani sosai suke maida hankali ba ga karatun amma babu laifi sun iya karatun sallah.Zahra duk hankalinta ta tattare wuri ɗaya ta miƙa wa malam wanda yake karatu kan Tauhidi. Bayan sun taso daga makaranta ,su na shigowa falo suka tarar da Mama ta rabka uban tagumi. "Mama ina ta yin sallama ba ki amsa ba" Zahra ta faɗa ta na mai durƙusawa ta cire mata tagumin. "Har kun taso?" "Eh Mama" su yi gamon baki suka amsa mata. "To ku je ku yi wanka ku ci abinci" "Mine ne ke damun ki Mama?" Zahra ta tambaya. "Babu komai kawai zuciyata ce nake jin ta yi min nauyi babu daɗi sai ƙunci" Mama ta faɗa kamar wata sakarya. "Zai wuce Mama ki yi ta addu'a " Ɗakinsu suka wuce ko wace ta yi wanka ta saka kayan shan iska.Su na cin abinci su na hira,Bintu ce ke bata labarin barkwanci da kuma na ban tsoro ita kuwa baiwar Allah Zahra har tsoratar take. Da Abba ya dawo sosai ya yi wa Bintu faɗa ,kafin ya haɗe su da Zahra ya yi masu nasiha.Mama na daga gefe ta bi ayari ta yi shiru kai kace sabuwar musulunta. Washegari Ƙauyen Djifer Abba ya yi sammako.Daidai ƙofar gida ya parker motarsa sannan ya fito ya shiga bakinsa na shirin yin sallama ya ji ƙafarsa ta yi wani girrr. Halilu da ke tsaye ya na wankin kifi ya ga komai sarai ya ce "ka shigo mana Baban Twins " Abba ya haɗiye wasu yawu dakyar sannan ya shigo,"babu kowa gidan?" "Baba da Inna sun tafi gona,Habiba kuma ta na ɗaki ta na yi wa Tsohuwa tausa" Halilu ya basa amsa. Abba ya sake matsawa ya yi sallamar da ya so yi tun a bakin ƙofa,aka amsa sannan ya shiga. Mahaifiyar tasa wacce suke kira da tsohuwa ya gaida bisanin ya yi zaune,Habiba ta gaishe shi ita ma ta na fitowa waje. "Ga ruwa nan a langa ki kai masa ya sha" "Halilu daga zuwansa ?" "Na ci uwarki ki ɗauka na ce" Habiba na zumɓurar baki ta ɗauki ruwan wanda ainahi boka ne ya bado su ta kaiwa Abba .Cike da ladabi ta ce "an kwaso hanya ga ruwa nan Abba " ta ajiye a gabansa ta fita. Abba ya ɗauki ruwan ya sha kaɗan ya ajiye.Ya na nan zaune sai ga Inna matar Kawu ta shigo,gaisawa suka yi ya na mai tambayarta "ina Yaya Mansur ɗin?" "Ya shiga banɗaki yanzu ya fito" Kawu Mansur kuwa ya na gun Halilu da ke faman gasa kifi sai barbaɗa magani suke su na hira ƙasa-ƙasa. Abba da ya gaji da jiran shigowarsa ya fito ya na mai kiran sunansa.Kawu Mansur ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba,sannan ya zo suka gaisa da ƙanen shi. "Ina dawowa gida aka ce min har ka tafi,shi ne na zo na ji in lafiya?" Abba ya faɗa . "Hum! Ta ga dama ta baka dama ka zo?" "Don Allah Yaya ka bar wannan maganar ai dai gani na zo ta ƙorafi ta ƙare" Kawu Mansur ya ɗan washe baki tare da rungume Abba ya ce "har na ji daɗi ƙanena,Habiba shimfiɗa min tabarma can gidin bishiya mu yi hira ni da ƙanena " Ganin murmushi kan fuskar Kawu Mansur sai Abba ya ji wata irin nutsuwa. Kan tabarma suka zauna su na hira ,kafin Halilu munafiki ya kawo hasashen kifi babba da ƙarami "Baban Twins wannan ne naka ,Baba kai kuma ka yi haƙuri ka ci wannan tunda kullum ka na ci" cike da munafurci yake faɗa tare da ƴar dariya . "Babu komai ka basa har da nawa ɗin,ka je ka ƙara kamo wasu sai ya tafi da shi can gida" cewar Kawu Mansur ya na kishingiɗa. Abba kuwa a duniya babu abin da ya fi so kamar kifi wannan ya saka babu jira ya fara ci,ya ce "a'a Yaya wannan ma ya ishe ni" jin haka ya saka Mansur ɗaukar nasa shi ma ya bi bayan Halilu suka koma can bayan gida su na ƙyalƙyata dariya. Tsohuwa ta fito waje,"tsabar mugunta a gasa kifi shi ne ba za a ban ba?" Ta faɗa ta na tako a hankali. Abba ya yi saurin raba wa biyu ya bata rabi, tsohuwa ta fara ci ta na saka masa albarka. Kawu Mansur ya na dawowa ya ga kifi a hannun tsohuwa da mugun sauri ya ƙaraso ya na cewa "Tsohuwa ba dai kifin ne ki ke ci ba?" Abba ya ce "Ni na bata ya na ga hankalin ka duk ya tashi?" Kawu ya haɗiye wasu yawu ya ce "a'a babu komai" Sai marice lis Abba ya koma can gida. ★JAPON “Kar ku ji tsoro ai dama haka ne ƙa'idar dajin da zarar ka shiga yake rufewa ” Bobby ya faɗa ya na saka masu murmushi bisanin su ci gaba da tafiya. Kameel ya yi ihu ya na mai dawowa tsakiyar su Fadeel. “Lafiyar ka?” “Wlh ji na yi kamar an taɓa kafaɗata” Kameel ya faɗa . “Ku Afirka wa Allah ya yi ku da shegen tsoro,mu uku ne kawai to wane ne ya taɓa ka ɗin?” cewar Fadeel cike da masifa. “Oho! Dai ina na nan tsakiyar ku ba zan gusa ba,dama ku da Aljannu banbacinku kaɗan ne”Kameel ya faɗa ya na wani riƙe rigar Bobby shi da ke gabansa. Duwarwatsu ne ta ko ina yayin da gayen ya yi kore tsanwa shar,dajin tsit ba ka jin komai sai kukan tsuntsaye da kuma sawun sawayensu. A haka har suka shigo tsakiyar dajin inda yake mai faɗin gaske."Ƙwaƙwaƙwa! Tsutsutsu! Tsitsitsi!" Kawai ke tashi kamar ana ruwa. Kameel ya ɗaga kansa sama,ido huɗu suka yi da wani tsuntsun mai manyan ido ya tattakura ya fasa ƙara ya na cewa “wayyo! Aljani! Aljani! Ku duba ” Su ka kece da dariya Bobby ya ce “mujiya ce fa! ” Fadeel kuwa ƴar bangar Kameel ya yi sannan ya ce,“haka ake aljani? Mtsw! ” “Ku biyo ni wannan ita ce hanyar shiga kusurwar dajin inda bishiyoyi ke magana” cewar Bobby ya na mai yin gaba suka take masa baya,Kameel sai waige-waige yake a haka har suka iso ƙofar shiga NOIRA wanda yake tamkar kogo. Yau babu mai gadi,Bobby ya fara shiga sannan Kameel a ƙarshe Fadeel . “Hiiyihiyi! Zhumm!” haka kogon ya fara ɗaukar wannan sauti bisanin ya fara juyawa kamar majaujawa. Mutane masu fararen shiga suka fara ketowa ta ko ina su na dariya,wacce sautinta kawai ake ji amma ba a ganin fuskokinsu sai ƙwarangwal. Abin da bai kashe Kameel ba, lokacinsa ne kawai da bai yi ba.Wani uban tsalle ya yi ya ɗale jikin Fadeel wanda shi ma a tsorace yake. Bobby ne ya fara magana “kar wanda ya cutar da su abokaina ne,kar ku matso kowa ya tsaya inda yake” ya na maganar ne idonsa na ɗaukar wani irin haske . Da sauri duk suka fara ja baya,domin hasken ba ƙaramin cutar da su yake ba. “Kar ku ji tsoro ina tare da ku” Bobby ya faɗa wa abokansa,“Bobby ka fitar da mu don Allah zuciyata za ta tsinke” Kameel ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba. Fadeel ya wani cire shi daga jikinsa ya ce “ƙaton banza matsoraci! Buɗe ido ka ga yadda fatalwa ke tsoron Bobby saboda miracle ɗin da ke fitowa a idonsa” Kameel ya buɗe ido ya sauke su kan Bobby wanda har zuwa yanzu idonsa ke fitar da haske kamar wanda aka saka masa ƙwan fitila a ciki. “Matsafi! Bobby kai matsafi ne?” Kameel ya faɗa cikin ɗaga murya ya na waro ido. Dirar mikiya NATA ta yi masu ta ɗauke Kameel da Fadeel ta yi sama da su, bisanin ta fara magana cikin fushi “ka aikata babban kuskure na zuwa da bare a cikin kogon NOIRA wanda babu mai shigarsa sai wanda aka yi wa wankan TSAFI.Wannan kusurwa ce ta musamman domin members kawai,don haka zan saka abokan ka gidan Yari in ka na son su to ka kawo sacrifice ka fanshe su” ta na gama faɗar haka ta jefa su Kameel cikin wata raga da ke can rataye ga icce. Bobby ya ɗaga kai ya kalli abokansa sai ihu suke su na neman agaji. Hasken idonsa sam basa iya yi wa NATA komai. Murya na ɗan rawa ya ce “Ki yi haƙuri daga yau ba zan sake ba” Nata ta sauko ƙasa ta na mai komawa ƴar matashiyar budurwa ta ce “a wannan duniyar ba a san kalmar haƙuri ba,jini ake bayarwa a maimakonta.In ka na so na sauko ma da su to ka kawo jinin ƴan yara biyu da ba su balaga ba kafin nan da faɗuwar rana” ta na gama faɗar haka ta wani hura masa iska a fuska,Bobby bai tsinci kansa a ko ina ba sai a waje kusa da inda suka ajiye mota...... [17/07 à 11:26] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 7_8* Bobby ya dafe kansa ,ya na mai sake duba yanayin garin da tuni duhun magrib ya fara ketowa.Tunaninsa ɗaya ina zai samu yara biyun da za ayi sacrifice ɗin? Ya na mugun son abokansa sai dai sam ya rasa tudun dafa wa. Keey ɗin motar ma ya na can ga Fadeel ,a hankali ya fara yin tafiya bisanin gundu. Ya gaji sosai,sai dai yin gudun shi ne mafita gare shi.Sama da minti ashirin kafin ya zo bakin hanya wacce take tsit tamkar an shareta. Bobby ya riƙe ƙugu ya na haƙi tare da waige-waige,bai da nisa da dajin AOKIGAHARA ɗin wannan ya saka yake iya ganin abin da ke faruwa. Wasu irin gizai-gizai ne baƙi ƙirin suka haɗu daidai dajin kawai sai walƙiya yake.Gaban Bobby ya faɗi,in ba zai manta ba ya na ɗaya daga cikin abin da Sarkin ruwa ya shaida masa.Da mugun sauri ya koma,ya fara gudu kamar ransa zai fita har zo hanyar da za ta sada ka da dajin. A buɗe take,kawai shiga ya yi har ya isa ciki. Kogon NOIRA ya shiga,ko tako biyu bai yi ba ya ji muryar Nata a bayansa “ina yaran biyu da aka ce ka kawo?” Bobby ya juyo suka haɗa ido da ita,muƙut! Ya haɗiye wasu yawu bisanin ya ce “ban san inda zan same su ba” Nata ta shiga ƙyalƙyata dariya har sai da ƙasa ta amsa bisanin ta ce “Sacrifice ya zama dolai,ko kum....” ba ta ida kai ƙarshen maganar ba ta ji murya Marlin bayanta. “Nata ki kawo mana su can gaɓar Teku ” Da mugun sauri Bobby ya juya ya na ganin mahaifinsa ne ya ji wani sanyi a ransa.Sai dai yadda fuskar Daddy take kicin-kicin ya saka Bobbyn shan jinin jikinsa. NATA ta ɗauko Kameel da Fadeel uwanda tuni sun fara fita hayyacinsu ta kai su gaɓar Teku .Daddy na fita Bobby ya take masa baya har suka isa can gaɓar ruwan. Tuni an cire ma su Kameel kaya an saka su cikin ruwa,Bobby ya yi tsaye kawai ya na kallon Mohan da Martan. “Ka matso kusa” Daddy ya umarci Bobby ,a sanyaye ya matsa tare da jerawa layi ɗaya da su ya rufe ido kamar yadda suka yi. Kogin na fara yin ruguuuu suka fara karanto ɗalasiman TSAFI.Bobby bai san ta yaya ba amma samun bakinsa ya yi da rera harafofin. An ɗauki sama da minti goma sannan kogin ya kwanta.Duk wata ajiyar zuciya suka sauke,Bobby ya kalle su a zuci ya ce ‘ko mi hakan ke nufi?’ Kameel da Fadeel suka fito cikin ruwa fatarsu na wani irin sheƙi ba kamar lokacin da suka shiga ba. Cike da murna Daddy ya rungume su ya na mai cewa “Barka da shigowa cikinmu yarana” ko wanensu murmushi kan fuskar shi ya amsa ma Daddy bisanin su je ga iyayensu. Kogon NOIRA suka dugunzuma,aka ci gaba da yi masu sauran tsibace-tsibace.Fadeel ya ɗauki baƙin tsafi,yayin da Kameel kuma jan tsafi.Bayan sun gama zaɓa aka basu wasu ruwa cikin wata tsohuwar ƙwarya.Ruwan baƙi ƙirin suke,su na shan ruwa duk illahirin gangar jikinsu ta ɗauki caji suka fara jin banbanci su na jinsu a duniyar sama saboda pouvoir/can/ƙarfin ikon da aka basu. Bayan an gama komai iyayen suka fito.Bobby ya ce “na ji tsoro sosai abokanai na yi zaton zan rasa ku ne” Kameel ya ce “to ga shi a yanzu mu ma an yi mana wankan shiga mun zama ɗaya” Fadeel ya karɓe da “a'a fa,abin da na lura kamar mun fi Bobby ƙarfin iko” “Eh haka ne saboda ni ba a bani ruwa na sha ba sai nan gaba” “Nan za ku kwana ko kuwa?” NATA ta tambaye su. “Yanzu za mu tafi” “Yauwa saboda akwai meeting da za ayi ” Ko da su Bobby suka fito ba su ga mahaifan su ba.Cikin motar da suka zo suka koma,sai da suka biya inda suka ci abinci Bobby ya ɗauki motar shi sannan duk kowa ya kama gabansa . “Bobby?” ya ji muryar mahaifinsa, ya dawo baya ya na amsawa “na'am Daddy ” “Dube ni cikin ido” “Daddy ban iyawa,ka yi haƙuri ” “Mi yasa to ka yi haka?” “Tsautsayi ne” “Ka san irin haɗarin da ka saka rayuwar ƴaƴan mutane? Ba don Allah yasa na shiga ɗakin sirri ba na ga alamar matsala da sai ya ya kenan? ” “Daddy nace ka yi haƙuri ba zan sake ba” Bobby ya faɗa a shagwaɓe ya na mai ɗagowa ya kalli mahaifinsa. Daddy ya ja wani huci ya ce “zan baka wasu ɗalasamai da za ka yi bita kafin lokacin da za a ida naka rantsawar,ban so a samu matsala Bobby .Abokan ka ga shi nan sun shiga gaban ka,sai sun fi ka saurin samun matsayi” “Daddy ni fa ba wani son wannan abun nake ba” “To ka manta da Anita kawai!” Daddy na faɗa ya miƙe tsaye,Bobby ya ce “No Daddy ina sonta sosai” murmushin gefen baki kawai Daddy ya yi . Bobby ya shiga ɗakinsa ya yi wanka,ya canza kaya.Kwnonking aka yi ya bada izini,Janash ce ta shigo riƙe da tray .Kan ƙaramin table ta ajiye masa ta ce “ga abincin ka nan,Madam ta ce na tabbatar ka ci sosai” “Fita!” shi ne kawai abin da ya furta,Janash ta fice da sauri. Wayarsa ya ɗauko ya yi danne-danne sannan ya kara a kunne“Mamyyyy!” ya faɗa kamar zai yi kuka,can ɓangaren ta ce “ya ne Bobby? Ka ci abinci?” “Ina ki ka tafi ba tare da na sani ba?” “Wajen meeting ,ba zan dawo ba sai dare ya yi sosai” Ya furzar da iska ya ce “okay! Na ji!” ƙittt ya kashe wayar . Abincin ya ci bisanin ya fara aiki a system ɗinsa,a haka har dare ya tsala sosai a gajiye kwana ya ɗauke shi. Ƙarfe biyun dare agogon Japon ta buga,a lokacin da kowa ke kwance ya na bacci su Daddy kuwa farke suke su na shagalin murnar samun wasu members. Fadeel da Kameel tamkar wasu sarakai haka aka yi ta gaishe su.Kalolin jus kuwa babu kalar da babu wanda ainahi ana sarrafa su da jinin bil'adama. Zoben tsafi aka baiwa kowanensu ya saka a yatsan tsakiya na hagun bisanin taron ya watse. Washegari Daddy ne tsaye kan Bobby da ke ta sharar bacci.A hankali ya fara bubuga kumatunsa ya na kiran sunan shi,Bobby ya yatsina fuska ya na mai buɗe ido. Daddy ya sakar masa da murmushi,“tashi ka yi wanka ina son kai ka wani wuri” Bobby ya yi wani tashi da sauri ya shiga toilet,a nutse ya yo wanka ya fito.Cikin suit farare ya shirya kafin ya je can falo inda Daddy ke jiransa. “Bonjour la famille !” Bobby ya furta,Mamy ta ce “Morning Babyna” ya yi mata kiss a goshi ya ja kujera ya zauna,Janash ta yi saving nasu. Bayan sun gama Daddy da Bobby suka fito,direba ya ja su a mota.Tafiya mai nisa suka yi kamar za su barin gari bisanin su isa wani ƙaton waje wanda aka yi masa doguwar ƙatanga kamar ta gidan fir'auna. Ƙaton gate ɗin aka buɗe,“wooo! ” Bobby ya furta saboda aljannar duniyar da ya gani.Kusan unguwa guda ce Daddy yasa aka tsara masa haɗaɗen gida mai game da masana'antar shi. Ma'aikata ne birjit ta ko ina,baƙaƙen fata sun fi yawa sai aiki suke tuƙuru.Duk tsayawa suka yi su na gaishe da su Daddy,cike da tausayi Bobby ke kallonsu har da mata da ƴan mata. “Kar ka wani tausaya masu kuɗi suke so,duk yarinyar da ka gani nan to iyayenta ne suka kawota don yi aiki a biya su ” Daddy ya faɗa ya na mai jan hannun Bobby ya fara zagaye da shi. “Amma Daddy su matan bai kamata ace su na aikin ƙarfi ba,wai su na ma cin abinci kuwa?” “Akwai ma'aikatan da kawai aikinsu girki ne,wasu kuma wankin kwanoni.Maleek?” Daddy ya ƙwala kiran wani saurayi,da gudu ya ƙaraso “ka kai Bobby ko ina na wajen nan ,zan shiga daga ciki ai ka shirya komai ko?” Maleek ya ce “Eh yalaɓai tun jiya da ka shaida min za ka zo na shirya komai” Bobby ya bi bayan Maleek,ya na sake nuna masa wasu wuraren. Daddy kuwa katafaren sashen ya nufa ,ya na buɗe ƙofa ya hangeta zaune kan gado cikin shigar kaya shara-shara.Ya lumshe ido ya na jin wani sanyi a ransa, Babyn ta haɗu sosai.Ta na ganinsa ta fara fari da ido kamar yadda Maleek ya shaida mata don saye zuciyar shugaban nasu. Daddy bai wani ɗauki lokaci ba suka fara masha'ar shi da yarinyar da a haife ya haifeta.Wannan shi ne halin Daddy holewa da ma'aikatan shi wanda musamman ya ɗauki Maleek aiki don duba masa wacce zai rinƙa holewa da ita a duk ƙarshen mako. Bayan ya gama biyan buƙatarsa ya shiga toilet ya yi wanka,ita kuwa tuni ta saka wasu kayan wanda suka ɗan suturta jikinta. A gajiye Bobby ya ce “Mu je ka kai ni wurin Daddy ” Maleek ya ce “Yalaɓai akwai wurin da ban kai ka ba,mu je lambu can za ka huta sosai sannan ga ƴaƴan marmari wanda za su sa yawun ka su tsinke” Haka Bobby ya bi bayansa suka shiga lambun,Maleek da kansa ya rinƙa wanke su apple da sauran su ya kawo gaban Bobby .Ya na tsaka da ci wayarsa ta ɗau ƙara,ya na dubawa sunan Fadeel ne da sauri ya ɗaga “aboki ya ne? Mun zo gidan ku ba ka nan” “Eh mun fita ni da Daddy ne,ya ne ko ta samu ne?” Bobby ya tambaya. “Eh mun shirya shagali ne akwai ƴammata iri-iri har da Black Baby musamman na yi oder domin ka”Kameel ya faɗa ya na dariya alamu wayar a main libre/ hand free take. “yaushe ne za ayi shagalin?” Bobby ya tambaya. “Tuni an fara don wuni ɗaya za mu yi muna holewa, please ka bar Daddyn ka kawai ka tawo” “Ok gani nan zuwa” Bobby ya faɗa ya na mai tashi tsaye,ya dubi Maleek ya ce “mu je akwai inda zan je” Direban da ya kawo su shi ya tuƙa Bobby ,tuni ya shaida ma su Kameel inda za su haɗe ko da suka kawo mararrabar hanya ya tsinkayi motar Fadeel . Da ɗan sauri ya fita ya je ya same su,ihu suka yi kafin Fadeel ya ja mota a guje sai waƙa ke tashi. Gidan da suka ɗauka don yin shagalin suka yi tsinke,komai ya tsaru kan tsari.Black Baby kusan goma aka tanada saboda Bobby ,Fadeel ya zo dab da kunnensa Bobbyn ya ce “ka zaɓo biyu zafafa wanda za ka shiga da su,na ɗauki nauyin biyansu” Bobby ya ɗan yamutsa fuska ya ce “babu wacce ta burge ni,tsantsaninsu ma nake” Kameel da ya ji furucin Bobby ya ce “mine? Mi ka ke tsantsani?” “Wai Black Baby” Fadeel ya basa amsa. “Ina ƙawar ka wadda ka ce duk nacin namiji za ta iya da shi?” Kameel ya tambayi Fadeel shi kuma ya basa amsa da “ta na bisa hanya za ta zo” “To ai shikenan,ita baturiya ce ƴar uwar ka hakan ya yi?” Bobby ya ce “yes!” cikin wani ɗaki suka shiga Fadeel ya saka system ɗin da ke kula da duk wata Camera a gaba. “Kameel ka lura da kyau ka zaɓa mana ƴammatan da suka fi ƙurciya domin sacrifice” “Sacrifice? Ku tsaya,mine ne ku ke shirin yi?” Bobby ya tambaya. Shiru duk suka yi,sai yanzu Fadeel ya farga ashe Bobby bai fara zuwa meeting ƙungiya ba. “Bobby Babynka ta iso ga shi ta na kirana” cewar Fadeel ya na duba screen ɗin wayarsa.Bobby kuwa tuni ya manta da wani zancen sacrifice ya ƙura ma system ido ya na kallon haɗaddiyar babyn da ke tsaye bakin ƙofa. “Jira na je na tarbota” cewar Bobby..... ★SENEGAL Tamkar mai ciwon haihuwa haka tsohuwa ke saffa da marwa goshinta kuwa sai fitar da gumi yake.Kawu Mansur kuwa kukan jini ne kawai bai yi ba da ya je gun boka ya tabbatar masa da tabbas tsohuwa mutuwa za ta yi kuma aiki ya rushe ba zai kama Abba ba. Tsakar dare sosai, tsohuwa ta fara shaƙuwa kafin wani lokaci ta ce ga garinku nan.A gaban idon Kawu Mansur ta mutu,ransa ya yi baƙi ƙirin.A duniya babu wace yake so sama da mahaifiyar shi,ita ɗin BANGO ce. A cikin wannan daren ya kira Ayub sai dai bai ɗauka ba. Washegari Abba bayan ya dawo daga sallar asuba ya duba wayarsa.Jikinsa har rawa yake wajen maida kira ,da kalmar “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” ya sauke wayar daga kunne. Mama da ke shafa addu'ar sallah ta ce “baban Twins lafiya?” “Tsohuwa ce ta rasu?” “Wace tsohuwar ? Innalillahi!” “Ki je ki sanar da Twins su shirya za mu tafi Djifer” Abba ya faɗa ya na mai zama bakin bed hawaye na zubo masa. Da kuka Mama ta zo ta sanar da su Kakarsu ta rasu su shirya za su tafi ƙauye.Zahra ce kawai ta yi kuka ta na yi wa kakarta addu'a yayin da Bintu ke masifar za su tafi ƙauye ita fa ba son zuwa take ba. Cikin kayan atamfa suka shirya sannan kuma suka haɗa wasu kayan cikin akwati.Direba ya ja su zuwa ƙauyen Djifer,Abba ne zaune gidan gaba yayin da Mama da Twins ɗinta suke baya. Ko da suka isa tuni ƙofar gidan ta cika da mutane .Halilu ne ya karɓi kayan su shi da abokansa suka shigar da su ciki,sai wani baza ido yake ya na kallon Twins ya na son banbance wace ce sanyin idaniyarsa don mugun kama suke. “Wai lafiya kamar wani tsohon maye ka ke wani rarraba ido ka na kallona? Mtsw baƙauye kawai” “Laaa! Bintuna,kin ga fa dama so nake na tantance ki sai gashi kin yi halin naki ” Halilu ya faɗa cike da fara'a don ba ƙaramin so yake yi mata ba. Mama ta ce “mai hali ai bai fasawa,kin ga kowa ba shaida ƙwarai yake yi miki ba.Wajen masifa kawai ake gane ki” Bintu ta turo baki ta na gunguni haɗi da hararen Halilu wanda sam ya kasa kawar da kallonsa gare ta har suka isa can cikin ɗaki. Gaisuwa suka fara yi wa junansu,Inna da Mama ita kuwa Habiba kusan su Twins ta koma ta na yi masu sannu da zuwa.Zahra ce kawai ke amsa wa cikin sanyin halinta. Kawu Mansur na ganin Abba ya je ya rungume shi ya na kuka,ya ce “ɗan uwana shikenan tsohuwa ta rasu, Allah sarki rabon ku ga juna” yadda yake kuka kamar wani ƙaramin yaro sai ya baiwa kowa tausayi. Abba na kuka ya fara rarrashin Yayansa tare da jajanta ma juna. Gawar tsohuwa aka fiddo wacce tuni an yi mata wanka an suturceta.Sallah aka yi mata bisanin a ɗauke ta zuwa maƙabarta ,a gaban kabarin Kawu Mansur ya zube ya na kuka dakyar aka rarrashe shi suka dawo. Bintu duk a takure take,sam ta tsani mutane ita rayuwarta ba ta son takura.Tsukin da ta yi ya cika buhu, can ta miƙe ta fito waje.Zahra da Habiba suka biyo ta,ta ɗan taɓe baki ta ce “Su kuma kalar al'adar tasu kenan an yi rasuwa amma shinkafa da miya aka dafa” “Eh kin san jiya da Abba ya zo duk ya kawo su,to babu wake a ciki” Habiba ta bata amsa,Bintu ta ce “shi ne kuma ba ku iya sayen waken?” “Bintu don Allah ki yi shiru,kar fa ki manta mutuwa ce ba wani buki ba” cewar Zahra. “Ke ni zaman gidan nan ya ishe ni,dubi tsabar munafurci ba su tashin yin kuka sai sun zo nan mtws! ” “Ku zo mu ci abinci”Habiba ta faɗa ta na ɗauko tray guda na shinkafa da miya. Ba su yi breakfast dama,Zahra ta tsugunna ta fara ci ita kuwa Bintu kallon hadarin kaji ta fara yi ma abinci kafin ta ce “Ni kifi nake so” Zahra ta ɗago kai ta na kallonta,Habiba ta ce “bari na faɗa ma Halilu sai ya kamo miki ” “Da gaske?”Bintu ta tambaya cikin jin daɗi “Eh jira ni” cewar Habibar ta na mai fita ƙofar gida,ta kuwa ci nasarar ganin Halilu da hannu ta yi masa alama ya zo. “Bintu ce ta ƙi cin abinci wai kifi take so” Halilu ya washe baki “ok ce ta jira na kamo sai ki gasa mata” Habiba ta dawo ta shaida ma Bintu yadda suka yi da Halilu ,ba a ɗau lokaci ba kuwa ya dawo hannunsa riƙe da manyan kifi har uku. Habiba ce ta gasa duk suka ci,sai a lokacin Bintu ta ɗan saki ranta ta na mai cewa a zuci ‘ashe su na da kirki’.... [19/07 à 10:00] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 9_10* Kawu Mansur ne zaune a gaban boka ana yi masa bugun ƙasa. “Aikin ka na da girman gaske! Haɗarinsa kuma shi ya fi komai cakwalkwali.Ba zan ɓoye maka aikin nan ya fi ƙarfina,amma in ka ji za ka iya zan haɗa ka da babban malami Mohan sai dai fa shi aikinsa ba maganar kuɗi ce ba” bokan ya faɗa ya na kallon Kawu Mansur wanda zuciyarsa ta ƙeƙashe babu ɗigon imani. “Ko ma mi yake buƙata zan basa muddin buƙatata za ta cika.Yadda ya yi sanadiyar mutuwar maifiyata to tabbas shi ma doli ya bi bayanta.A ina zan samu shi Mohan ɗin?” “Nan cikin Senegal yake a wani ƙauye da ake kira Joal sai ban tsammanin ya na nan saboda duk ƙarshen shekara su na haɗuwa can ƙasar Japon domin a ƙara masu ƙarfin iko” Maganar boka ta sanyaya zuciyar Kawu Mansur,sai yake ganin tamkar ma har burinsa ya cika. “Zan je na tambaya” ya furta ya na sakin wani murmushi. “A'a ba sai ka je ba,jira na kira maka shi ta madubin tsafi” bokan ya faɗa tare da tashi ya ɗauko wani madubi da yake rufe da jan ƙyalle. Ya shafi madubin ya na ambaton surkulle,babu jima wa muryar Moha ta bayyana “Ya aka yi bokan bokaye? ?” “Aiki ne aka samu ranka shi daɗe,talaka ne shi bai da kuɗin da zai iya biyanka da su wannan ya saka na ga gwara ayi masa aikin daga nesa kamar yadda ka saba” “In ya amince da sharaɗin to ya rubuta ya ajiye ɗan uwansa zai mutu a yau ba sai gobe ba” Mohan ya faɗa,ko kafin ya rufe baki ya ce “na yarda” kalmar yarda da ya furta ya saka boka kifar da madubin tsafin. Kawu Mansur ya koma gida,nan ya tarar da Abba su na ta shirin kowa ya gida kasancewar tuni an yi sadakar bakwai. Har mota suka yi masu rakiya,Halilu wanda ke ta ƙoƙarin ya saye zuciyar Bintu wani awarwaro ya bata ta ƙi karɓa duk da a ido ya yi mata kyau. Ta na shirin shiga mota ya kamo hannunta tare da saka mata shi,ta wani harare shi kamar idonta za su faɗo ƙasa. Direba ya yi wa mota key suka fara sharara gudu sai da Abba ya yi masa magana sannan ya rage. Das! Das! Das! Haka sautin bugun zuciyar Abba ke ɗan canza yanayin bugawa.Hannu ya kai da niyyar kunna ƙira'a amma wani abun mamaki tamkar wanda sanƙarau ya kama haka hannun ya sandare. Wata ƙatuwar Mujiya ce ta dira a gaban motar tare da fara bugun glass ɗin ta na son fasa shi.Bakin Abba ya kasa furta komai ,sai kai da yake faman girgizawa. Babu mai ganin Mujiyar sai shi ɗaya,kamar ƙyaftawar ido motar ta kife. Kasancewar har sun fara shigowa gari ya sa suka samu agajin gaggawa.Abba da direba an mutu nan take,Mama ta samu kariya a ƙafa yayin da Twins kuma suka sume don firgici. Kawu Mansur na samun kira,ya kwashi duk ahalinsa suka tafi can asibitin da aka shaida masa. Kuka yake wiwi kamar ransa zai fita,a ƙasan zuciyarsa kuwa tamkar ta saurayin ango. “Ga gawarwakin can a mutuware ,ka sa hannu sai a baka su” wani likita ya faɗa ya mai miƙa ma Kawu Mansur wasu takardu. Mai gadin gidan gawar ne ya yi masa iso har ciki.Gawar direban aka fara buɗe wa bisanin ta Abba,da sauri Kawu Mansur ya ja baya ya na kallon ɗan uwansa babu ido sai gurbinsu. Muƙut! Ya haɗiye wasu yawu bisanin ya fita. Da kuka Mama ta farka,su Twins ta gani ko wacce kwance sanye da ƙarin ruwa. Abba ta fara kira ta na gwanjin kuka,Inna ce ta fara bata haƙuri sai dai ta ƙi yin shirun. A can waje kuwa Kawu Mansur ya kira dangi da abokan azirki domin sallatar gawa.Har aka kai su makwancinsu ya na tunanin ta ya aka yi Abba ya rasa idonsa sai dai babu damar tambaya don ya na tsoron abin da zai je ya komo. Su Twins ko da suka farka suka samu lafiya.Tare da mahaifiyarsu suka shiga kukan rashin Abba don ƙiri-ƙiri Kawu ya shaida masu rasuwar. Sati guda currr ta yi a asibiti sannan aka sallamo su. Kawu Mansur da iyalansa tuni sun babakere da komai na Abba,sai abin da ya ce ake zartarwa.Ya cire su Twins daga makaranta a cewar shi tunda Habiba ba ta yi boko ba su ma ba za su yi ba. Mama na zaune Zahra na bata abinci a baki,hawaye suka zubi mata shaaa. “Mama don Allah ki bar kukan nan tunda Abba ya riga ya mutu,a yanzu addu'ar mu yake buƙata”Zahra ta faɗa ta na goge mata hawayen. “Shikenan kuma sai a gurgantar maku da karatu? Babban baƙin cikina da ba zan iya tafiya ba da wlh tuni mun bar gidan nan” “Dukiyar ubanmu fa? Shikenan sai mu tafi mu bar masa? ”Bintu ta tambaya. Mama na shirin magana Kawu Mansur ya fito cikin wata gizner fara .Fuska ya turniƙe ya na mai cewa “uwar mice ce kuke faɗa?” duk shiru suka yi sai Bintu ce ta murguɗa baki ta na cewa “abin da kunnuwan ka suka ji” yatsunsa biyar ya sauke mata a fuska. Ta fasa ƙara ta shiga rera kuka kamar amaryar lalle, da sauri Inna ta fito wacce ke kitchen ta na yi masu girki. “Kawun yara za a fita?” ta tambaya ta na wasar baki,kallonta ya yi sai ya ga ta ƙara yi masa kyau sam bai taɓa sanin haka Inna ke da kyau ba ashe talauci ne ya nakasata. “Eh zan tafi can office ,kin san na ɗora wani yaro akai shi zai rinƙa yi min aiki kafin Halilu ya kammala karatun sai na ɗora shi matsayin tunda dai ni ban yi boko ba” “To Allah tsare ya maido ka lafiya,irin wannan ɗawainiya da kake Allah biya ka .Da wani ne ai banzatar da Iyalin ɗan uwan zai yi” Inna ke faɗa cikin kalar tausayi ta na kallon su Mama. Kawu ya fice bayan ya amsa addu'ar da ta yi,ita kuma ta koma kitchen. “Mama sam abin da Baba ke yi bai kyauta ba,duba fa ki ga ya hana Twins zuwa makaranta.Ina ma laifin ya ce su dinga koyar da ni har na cimma masu?” Habiba ta faɗa wacce ke taya mahaifiyarta aikin. Shiru Inna ta yi kafin ta ce “kuma fa kin kawo shawara,ina ga haka za ayi bari har ya dawo” Cike da murna Habiba ta ce “yauwa Innata!” Girkin suka ci gaba da yi har suka kammala,Habiba ta zo falo gun Zahra su na ƴar hira yayin da Bintu ke can gefe sai cika take ta na batsewa a zuci kuma ta na zagin Kawu Mansur. Wanka Inna ta yi,ta zaɓi kalar kayan atamfa cikin na Mama ta saka sannan ta fito falon.“Sannu Hajara ya ƙarfin jikin?” Mama ta dube ta sannan ta ce “alhamdullah!” “ko a zuba miki abincin?” “A'a ban jin yunwa” “To babu damuwa,Zahra ki kuna mana kallo mu kalli dandali” cewar Inna ta na kallon Zahrar. Cike da ladabi ta ce “toh!” ta tashi ta fara harhaɗa wayoyin ta kunna masu Arewa24. Ana suka shiririce har lokacin cin abinci ya yi,Inna ce ta zuba ma kowa kafin su je su yi sallah. Bintu kuwa kan bed ta kwanta,tunani take yadda duniya ta yi masu juyin waina.Ta ja wani ƙyaci,Zahra da ke karatun Alkur'ani ta ɗago ta dubeta “ke lafiyar ki?” “twin yanzu saboda Allah mafarkina na zama cikakkiyar lauya ba zai cika ba?” kawai sai ta fashe da kuka. “Haba Bintu ya kike yin abu kamar wata ƙaramar yarinya wacce aka cire daga mama? Ina ce dai a gaban ki ranar nan malam ya ce ilimin boko iyakar mu da shi nan duniya ne.Ki gode Allah da bai hana mu zuwa islamiyya ba,kuma Kawu ai tamkar Uba yake a wurin mu?” Cike da takaici Bintu ta jefe ta da pilow ta ce “je can wawuya,ni bai haife ni kuma har abada ba zan ɗauke shi matsayin Uba ba” ta na gama faɗa ta tashi ta shige toilet.Shower ta sakar wa kanta ta na ta faman kuka. Kai kawai Zahra ta girgiza bisanin ta ci gaba da yin karatun. Kawu Mansur sam bai da yarda wannan ya sa ya ƙara Camerorin tsaro fiye da can farko.Bai iya komai ba,sai dai yaronsa ne ke yi masa aikin shi kuma ya na daga gefe. Sai zuwa marice ya shigo gidan,bayan ya yi wanka ya ci abinci Inna ta same shi da maganar da suka yi da Habiba na zancen su Twins su koma makaranta. “Zan yi tunani akai” shi ne abin da ya faɗa. “Wane tunani kuma? Don Allah kawai ka amince” “Ina baƙin cikin zuba kuɗin da za su yi karatun ne” “Haba Kawun yara,su fa kuɗin nan ainahi na ubansu to miye da ka zuba masu?” Cike da ɓacin rai Kawu ya fita.Ana daf da yin kiran sallar magrib ya saka direba jansa a mota,ba su zarce ko ina ba sai ƙauyen Djifer. “Ka tsaya nan ka jira ni ina dawo wa” Kawu ya faɗa ya na mai bin wata hanyar da za ta kaisa gun bokansa wanda a yanzu ya na cikin aminansa. “Mansur ne? Ai kuwa kamar ka shiga zuciyata ina son ganin ka.Da akwai wata matsala da na ga ta na tunkaro ka” boka ya faɗa. Kawu Mansur ya samu wuri ya zauna ya na mai cewa “ai kuwa dai ita ɗin ce ta kawo ni,ina son ayi min asirin da zai saka kaf ma'aikatana da su kansu ahalin gidan su dinga shakkata da mugun tsorona” “In dai wannan ne babu matsala an gama” “Yauwa sannan ina son ka haɗa ni da wannan malamin Mohan” “Sai wani sati mai zuwa yake dawowa ” boka ya basa amsa. Kuɗi ya basa kafin ya koma gida,shi kuwa boka tun a daren ya fara aiki... ★JAPON Da sassarfa Bobby ya iso gare ta,“Salut!” ya furta ita ma ta mayar masa da “Hi!” ya ɗan murmusa bisanin ya tara mata hannu.Sai da ta kalle shi da ƴan ƙananan idonta bisanin ta saka nata hannunta.A hankali suka fara tafiya hannunsu sarkaye da na juna,Bobby ne ya ce “kin zo kin tsaya kamar wata baƙuwa” “Eh to mice ce ? Ban san kowa ba a nan sai wanda ya gayyace ni kuma shi ne nake kira” “Kenan ni ba ki sanni ba?” Bobby ya yi mata tambayar ya na mai tsayawa da tafiyar,ta kalle shi cikin ido kafin ta ɗan girgiza kai.Ya kama haɓarta ya ce “yauwa ko ke fa! Sunana Bobby ke kuma fa?” “Sabitry” “Jolie nom! Nice name” ya furta daidai nan suka shigo ɗakin show ɗin. “thank you” Wurin zama suka samu suka zauna,sai ƙoƙarin kiran lambar Fadeel take yayin da shi kuma Bobby ke ɗan baza ido ya na kallon masu rawa. Muryarta ya ji “Tu veux danser?/Ka na son yin rawa ne?” Ya ɗan yi murmushi ya ce “pourquoi pas? Surtout avec une charmante comme toi/mi zai hana, musamman da kyakkyawa irin ki” “ok allons-y” ta faɗa tare da tashi tsaye,Bobby ya miƙe shi ma tare da jan hannunta suka fara yin rawa irin a hankalin nan su na kallon juna cikin ido. “An taɓa faɗa miki ke ɗin kyakkyawa ce?” “Hum! In ma ba a taɓa ba ai ga shi kai ka faɗa” “Gaskiya ki na da kyau, musamman idon ki am...da kuma laɓan ki” Bobby ya faɗa ya na mai ƙura ma lips ɗinta ido,Sabitry ta ce “Allah sa dai wannan zancen naka har zuci yake” “Don mi?” “Saboda dayawan maza mayaudara ne, musamman in su na son kwantawa da mace” Bobby ya ɗan saki murmushi ya ce “ba cewa na yi ina son ki ba fa! Kawai na ce ki na da kyau” “Daga ƙarshe kalmar so ɗin ce za ta biyo baya” “Shikenan mu yi dai rawar,ko kin gaji ne?” “In na gaji mi za ayi?” ta tambaye shi idonta ƙur cikin nasa. “Eh to! Na kai ki ɗaki ki kwanta” Wata dariya ta yi ta na mai kai hannunta kan fuskar shi ta ce “wai gaske? Hutun zan yi ko kuwa dai?” sai maƙe masa ido ɗaya. Bai ce mata komai ba ya ja ta zuwa wani ɗaki,kai kace wata matarsa haka suka holewarsu. Bobby ya dubi Sabitry ko ƙyaftawa bai yi,“ya dai irin wannan kallon?” ta tambaye shi. “Ina mamaki ne kawai yadda ki ka jure min” dariya ta shiga yi kamar mahaukaciya kafin ta ce “Wai da gaske,halan budurwar ka raguwa ce” “No matata dai” Da sauri Sabitry ta dubi hannunsa sai ta ce “ya aka yi ban ga zoben aure ba?” “Sai nan gaba za mu yi aure ” ya bata amsa. Sabitry ta ɗauki jakarta dama tuni ta kimtsa ta tashi ta fita,Bobby ya yunƙura zai tashi wayarsa ta ɗau ruri. Daddy ne,ya na ɗagawa ko magana bai yi ba Daddyn ya ce “Bobby duk rintsi ka nemo yarinyar nan da ka kwanta da ita,in kuma ku na tare kar ka bari ta gusa gani nan tafe” ƙittt ya kashe wayar,zuciyar Bobby ce ta fara dakan tara-tara. *Uwanda suka shirya za su iya fara yin payement don free page na dab da ƙarewa 400 ne kacal za ki biya kuɗin karatu book na ɗaya da na biyu ,ki tura ta wannan account ɗin* 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank Sai ki turo min da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin mtn,ƴan Nijar kuma carte Moov ko airtel ta 400f. MRS SADAUKI 💫 [20/07 à 17:10] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 11_12* Da mugun sauri Bobby ya fita,duk da bai san taƙamaimai mine ne ba amma ya san Daddy ba zai kiransa kan banza ba. Cak ya tsaya ganin Sabitry na fizge-fizgen ƙwatar kanta gun Kameel da ya yi mata wani mugun riƙo. “Mais lâche moi! Ka sake min hannu!” shi ne abin da take ta faman faɗa,kowa na ɗakin taron ya tsaya cak ya na kallonsu. Muƙut! Bobby ya haɗiye wasu yawu bai ma iya furta komai ba.Fadeel da ke can gaban Camera ya ga abin da ke faruwa ya fito da sauri,can ɗakin suka koma su duka. “Sabitry dama duk abin da ki ke da tsafi ki ke amfani ban sani ba?” Fadeel ya yi mata tambayar ya na mai dafe goshi. Kameel ya ce “Allah ya yi sa'a ta na fitowa na ci karo da ita,ba don haka ba da shikenan ta saka rayuwar abokinmu cikin cakwakwali” “Wai don Allah mine ne ke faruwa,kaina ya ɗaure! Daddy ya kira ni ya ce kar na bari ta gusa ku kuma ku na wani zance”Bobby ya tambaya ya na son samun haske. “Bobby wannan yarinyar da ka ke gani muguwa ce,za ka iya kiranta da BOKANYA kai tsaye.Duk ƙarfi da juriyar da aka ce ma ta na da to tsafi ne,da zarar ta kwanta da namiji babu shi ba zaman lafiya sannan ƙarfin jikinsa za ta dinga tatsa su na saffara abubuwan tsafinsu” Kameel ne ya basa amsa. Bobby ya yi masa wani kallo irin kamar ban gane ba, wannan ya saka Kameel ci gaba da cewa “ni ma na fahimci haka ne saboda ƙarfin iko da nake da a duniyarmu” kafin wani ya sake yunƙurin yin wata magana aka turo ƙofa. Daddy ne,fuskarsa ta yi jawur.Wani gigitacen mari ya ɗauke Sabitry da shi wanda ya saka ta faɗuwa ƙasa wanwars ba ta shirya ba.Gashin kanta ya cakumo ya ɗagota sama,kuka ta fara ta na basa haƙuri.Bakinta ya taɓe ya saka yatsansa manuni wanda yake ɗauke da zoben tsafi a ciki.Kamar yadda gashi in ya shiga cikin ruwa ko mai yake yin sama haka wani baƙin hayaƙi ya fara fita daga bakin Sabitry ya na shiga zoben Daddy.Can ya yi yarɓi da ita ya na mai cewa “Ƴar iskar yarinya! Ke kin yi kaɗan ki taɓa rayuwar yarona wanda tun kafin ya zo duniya nake kula da duk wani motsinsa saboda mugayen mutane irin ki” ya gama faɗa ya fita. Jiki babu ƙwari Sabitry ta fice,yayin da su Kameel kuma suka samu kujeru suka zauna. Fadeel ne ya ce “ban taɓa sanin da tsafi take aiki ba,sai yau.Shi ma ɗin don yanzu ina cikin ƙungiya ne” “Kenan in mutum na cikin ƙungiya ya na iya gane duk wani mai amfani da asiri ko tsafi?” Bobby ya tambaya. “Eh sosai! Da ace Kameel bai ganta ba da shikenan ” cewar Fadeel. “To ai ni ma ina cikin ƙungiyar ko?” Bobby ya faɗa,a tare suka kece da wata irin dariya bisanin Kameel ya ce “kai fa dutsen Barclay bai karɓe ka,wanda kuma shi ne yake babban jigon ƙungiya ” “Sai nan gaba sannan ka shigo sawun mu ka ƙara haƙuri ” Bobby ya ɗan taɓe baki ya ce “ni fa ban wani damu da harakar tsafi ba,kawai don ban son baiwa Daddy kunya ne” “Ko ma dai mine ne mu je mu yi shagali” cewar Fadeel tare da miƙewa,su ma suka mara masa baya. Bobby wuri ya samu ya zauna kawai,sosai ya yi mamakin ta yadda aka yi har Sabitry ta ɗauki hankalinsa alhalin shi duk matan duniya su da maza duk ɗaya suke a wurinsa in ka fidda Anita. Ya lumshe ido tare sakin murmushi,a hankali ya furta “ina son ki Anita ” bugun zuciyarsa ne ya ji ya amsa. Sosai aka yi shagali aka cashe bisanin duk kowa ya kama gabansa. Bobby na zuwa gida Daddy ya tarbe shi da pasport ɗinsa wanda tuni an yi masa VISA . “Ga shi gobe in Allah ya kai mu jirgin ka zai tashi zuwa Pakistan,na yi magana da mutumena ya yi bincike kan Anita ya gano inda take.Lambar wayarta da address ɗinta duk a wajen shi za ka samu” Daddy ya faɗa ya na miƙa masa pasport ɗin. Wani tsallen murna Bobby ya yi,ya rungume mahaifinsa sannan ya shiga sumbatarsa ya ce “na gode sosai Daddy bari na shiga ciki na haɗa kayana” Mamy wacce ke zaune kan salon ta ce ,“My Prince tuni na haɗa maka komai ya na cikin trollyn ka,fatana kawai ka more rayuwar ka.Ina son ace ko da ka ke dawo wa ƙasar Japon ace kai da Anita kun yi saka zoben alƙawari in son samu ne ma ace da Baby a cikinta” Dariya duk suka shiga yi, Daddy ya mirza sumar kan Bobby ya ce “to ka ji dai don haka ka sa himma! Je ka yi wanka ka zo ka ci abinci” “Ban jin yunwa,zan dai huta ne don na gaji sosai” Bobby ya faɗa ya na mai haurawa sama passeport ɗinsa a hannu. Bayan ya yi wanka ya shiga group ɗin su na WhatsApp ya shaida wa abokansa.A nan ne shi ma Kameel ya sanar da su za su koma Senegal shi da mahaifinsa.Fadeel duk sai ya ji babu daɗi sam sai babu yadda za su yi.... ★SENEGAL Sai da Kawu Mansur ya danne zuciyarsa sannan ya bar su Twins domin su ci gaba da karatunsu.Habiba wacce ta fita daga boko tun primary malami ya ɗaukar mata ya na koya mata a gida,sannan kuma ɗaya ɓangaren Zahra na koyar da ita. Sosai ta maida niyya wannan ya saka,Kawu biya mata kuɗin makarantar ita ma sai dai irin ta ƴan gayu ce mai masifar tsada. Ranar farko da Habiba ta shiga aji,sai ta zama banban da sauran.Duk da dai kowa uniforme ce a jikinsa amma duk ƴan matan sun sha kwalliya sun zubo gashi,wasu gashin doki ne ma amma banda ita. Yadda ta ga ana kallonta ya saka ta gane bai rasa nasaba da burkiɗeɗen hijabin da ke jikinta. Bayan ta dawo gida ta baiwa Zahra labari,“Habiba kar ki biye masu ki ci gaba da shigar da ki ka saba mana.Kin ga ni da Bintu After dress muke ɗora wa a saman uniforme ko ke ma ita ake nemo miki?” “A'a ina son ni ma gashin kaina ya koma dogo har ga baya ” “Wai kin ɗauka gashin kansu ne? To na doki kuma babu kyawu saka shi” “Ni dai kam ya burge ne zan shaidawa Baba ya bani kuɗi sai ki yi min rakiya na sayo”cewar Habiba ta na jin son ganin canjin rayuwarta. “Ok babu damuwa,yanzu dai mu yi karatun Alkur'ani zuwa dare sai na koya miki lesson” “Kai na gaji sosai ki bari zuwa dare ni ma sai na koyar da ke” Zahra ta maraice fuska ta ce “don Allah Habiba ki tausaya ki faɗa min ko da aya biyar ce” ba don ta so ba ta yi wa Zahra ƙarin karatu kasancewar ita Habibar ta na da ilimin addini. “Ku zo ku ci abinci,ina Bintu ?” ina ta tambaya ta na mai ajeye trayn abinci a tsakiyar falo. “Ta na ɗaki,wai kanta ke ciwo” cewar Zahra . “To ku zo ku fara ci,bari na tasheta ta zo ta ci abinci sai ta sha magani” Inna ta faɗa ta na mai nufar ɗakin su Bintu. Tsakiyar gado ta tare da ita ta yi rub da ciki,“Bintu? Bintu?” ba tare da ta amsa ba ta ce “taso ki ci abinci sai na baki magani” kai ta girgiza ta ce “ban jin yunwa” Inna ta ce “kin sha magani ne?” ta girgiza kai alamun a'a,da sauri Inna ta fita babu jimawa ta dawo hannunta riƙe da kofin ruwa da kuma magani amma ƙememe Bintu ta ƙi sha sai da Inna ta je ta kira Halilu wanda a yanzu ta fara jin tsoronsa. Fuska ya haɗe cikin bayar da umarni ya ce “ki tashi ki sha” kuka ta fashe ta na mai cewa “ni ba zan sha ba, chocolat nake so” Halilu ya dubeta sake da baki ya ce “kenan lafiyar ki lau?” kai ta ɗaga masa ta na shagwaɓe fuska. “To tashi ki shirya mu je mu sayo” da murna ta sauka daga bed ɗin ta shiga toilet ta wanke fuskarta. Gaban madubi ta tsaya ta shafa mai da hoda sannan ta juyo ta dubi Halilu wanda duk inda ta yi idonsa na kanta,Inna kuwa dama tuni ta yi tafiyarta . “Ka fita ina son canza kaya” ta faɗa a sanyaye.Halilu ya maƙe kafaɗa ya ce “a'a ba zan fita ba,kawai ki canza na yi miki alƙawari ba zan kalle ki ba” Bintu ta turo baki,zumbulele hijabi ta saka ta yadda ba za a ganin ƴar ƙaramar rigar jikinta ba. A jere suka fito,su na daf da shiga mota suka ji muryar Kawu Mansur kamar aradu “gidan uban waye za ki kai min Ɗa? ” a tare suka juyo su na kallonsa. Bintu ta taɓe baki bisanin ta kawar da kai gefe,“Baba za mu tafi mall ne ba za mu jima ba”cewar Halilu cike da nutsuwa don yanzu ya ƙara wayewa. “Ita ta dawo kai ka tafi” “Lilu wuce mu tafi don Allah rana sai gasa ni take” Bintu ta faɗa a mugun shagwaɓe,wanda ya saka Halilu tattaro hankalinsa kanta. Murmushi ne ya suɓuce masa jin da sunan da ta kira shi,uwa uba kuma yanayin maganarta.Bai san lokacin da ya buɗe mata ƙofar mota ba ta shiga,shi ma ya zagaya ya zauna ya yi wa motar key suka bar Kawu Mansur tsaye sake da baki. A cikin mota Halilu sai surutu yake zuba mata kamar Akun kuturu,har suka isa mall ɗin.Kai kace wata Baby haka ya ɓata kuɗinsa wajen saya mata kayan maƙulashe da kuma wani ƙaton Teddy pink. Lokacin da suka dawo sun tarar Kawu Mansur na ta balbalin masifa kamar zai tadi gidan.Ko kaɗan babu tsoronsa a fuskar Bintu ,ido cikin ido suke kallon juna da ita. A zuciye ya kifa mata mari ya na mai cewa “shegiya mai ido tsakar kai,ke ga ƴar iska wacce ba ta samu tarbiyya ba.Dama ta ya ya barewa za ta yi gudu ɗanta ya yi rairafe.Amma zan yi maganin ku ke da munafukar uwar ki” ya na gama faɗa ya sa hannu zai karɓe ledar hannunta,da sauri Halilu ya tare shi ya na cewa “Bintu shiga ɗaki gani nan zuwa” Idonta sun yi ja amma ba ta yi kuka ba,wata uwar harara ta banka wa Kawu bisanin ta wuce ciki. Zahra ta bi bayanta,falon sai ya rage Kawu da iyalansa. “Baba wannan abun da ka ke sam ba ka gyara min,ka yi kowa sanin irin mugun son da nake yi wa Bintu .Da ya ya na yi na samo soyayyarta? Aiki na yi tuƙuru babu dare babu rana sannan na samu ta fara saurarena,amma shi ne kake rushe min ginin da na tsara” “Halilu rufe min bakin ka,mahaifin ka ne fa.Kuma ai ba ka fi shi sanin daidai ba,abin da ba ka sani ba rabin dukiyar Marigayin Ayub Bintu ce kawai ta san inda take sannan akwai takardun da doli sai ta saka hannu sannan su zama mallakinmu.Ko ka yi tunanin banza yasa har yanzu ni ban fito da mugun halina ba? ” Inna ke faɗa ta na matsowa kusa da Ɗanta. Halilu ya ce “ni dukiya ba ta gabana Inna ,wlh na fi son Bintu fiye da duk komai na ƙyalƙyalin duniyar nan.In kuka kwantar da hankalin ku ni nan da kaina zan karɓo komai,ya kuke gani in na aureta?” Kawu Mansur wanda takaici ya rufe da sauri ya yi gaba,ɗakinsa ya shiga .In akwai abin da ya tsana to ya na bayan zur'ar Ayub ,ba don gudun zargi ba da guba yake zuba masu duk su mutu. Safa da marwa ya fara ya na tunanin malam Mohan da aka ce masa gobe zai shigo Senegal.Kamar wani zararre ya fara magana shi ɗaya “zan yi maganin ki,gobe in Allah ya kai mu ƙarfe bakwai na safe a Joal zai yi min! Hum! Haba! Duk za ku ci ubanku ” Halilu kuwa ɗaki ya bi Bintu nan ya tarar su na rigima ita da Zahra akan teddyn da ya sayo. “Lilu wai ita ma sai an saya mata ko kuma ta toye shi” Bintu ta faɗa ta na dariya har dimple ɗinta ya lotsa. Halilu ya dafe goshinsa ya ce “oh! Shaf na manta da komai iri ɗaya ku ke yi,Bintu laifin ki ne amma in sha Allah da dare zan sayo mata” Sai a lokacin Zahra ta saki ranta, toilet ta shiga don lokacin makaranta ya kusa. Halilu ya zauna kusa da Bintu ya ce “ina sonki sosai” ta dube shi da sauri yanayin fuskarta na canzawa.Ya ja dogon numfashi ya na shirin kamo hannunta ta yi saurin tashi,“zo ki zauna babu abin da zan yi miki ” ya faɗa ya na mai kafeta da ido. Ta maƙe kafaɗata haɗi da turo baki gaba ta ce ,“ni dai don Allah ka fita” “Don mi?” “In dai ka na sona ka fita” “Hakan shi zai sa ki yarda ina son ki?” kai ta gyaɗa masa da sauri shi kuma ya miƙe,ta gabanta ya wuce ya yi ƙoƙarin yi mata kiss a goshi ta ture shi ya yi dariya fita. Zahra na fitowa ita ma Bintu ta shiga ta yi wankan,sannan suka shirya suka tafi islamiyya. Ko da suka sauko tuni har Halilu ya sayo wani teddyn da murna Zahra ta ɗauke shi ta na cillawa sama. “Wai sai yaushe Mama za ta dawo?” Bintu ta tambaya. Zahra ta ɗan tsaya da abin da take sannan ta ce “Sati ɗaya ta ce” “Ciwon ƙafa ya ƙi ci ya ƙi cinye wa kamar wacce aka asirce” Bintu ta faɗa cike da damuwa. “Zato zunubi ne” Zahra ta faɗa. “To Malama na ji,yanzu dai zan kwanta” “Ana shirin yin magrib ɗin?” Zahra ta tambayeta,ko dubanta ba ta yi ba balle ta bata amsa haka ta yi kwanciyarta ba ta jima ba bacci ya ɗauke ta. Sai bayan sallar isha'i Bintu ta tashi agajiye.Wanka ta fara sannan ta yi sallolinta ta fito ta ci abinci sannan ta wuce wurin su Zahra da suke karatu ita da Habiba. Washegari Kamar yadda Kawu Mansur ya yi alkawari hakan ce ta kasance.Tun da safe ya tashi direba suka je Joal,sai dai ga mamakinsa duk uban sammakon da ya yi akwai uwanda suka riga shi.Ko wane cikin gizner sai ƙamshi ke tashi,da Kawu ya ga alhazzai sai da ya raina kansa. Haka suka yi ta jira da ɗaiɗaya ake shiga har layi ya zo kan Kawu Mansur. Kansa ya fara shigarwa ya buɗe baki da niyyar yin sallama sai kuma ya yi shiru sakamakon aljannar duniya da ya gani.Ɗakin tarben client ɗin kai kace fadar Sarkin Makka tsabar haɗuwa da kyau. Can bisa wata kujera ya hangi wani baƙin mutum a zaune ya hakimce hannunsa riƙe da wata ƙatuwar lula mai haske . Muƙut! Ya haɗiye wasu yawu kafin ya ƙarasa,da hannu Mohan ya yi masa nuni ya na mai cewa “ba a kallon cikin idona muddin ka na son tsira da ganin ka”.Kawu Mansur ya zauna kan capet ɗin a gabansa,ya wani sunne kai. Mohan ya ci gaba da cewa “mi ke tafe da kai?” Kawu ya yi gyaran murya ya ce “dama aiki nake son ayi min kan wata yarinya....” kafin ya ida Mohan ya ce “ta na da taurin kai ne,sannan duk da ƙarancin iliminsu na addini mahaifinsu ya koyar da su yadda ake riƙe Tauhidi shi yasa bokan ka ya gagara aiki a kanta.Amma tunda ka zo nan komai ya wuce ” “Ina son a aika mata baƙin aljani wanda zai hanata shaƙat har sai duk dukiyar da ke hannunta ta dawo gare ni” Kawu Mansur ya faɗa. Mohan ya ce “ba ma tura aljani haka kawai sai da sharaɗin aure” Kawu Mansur ya ɗago,da sauri ya mayar da kansa zuciyarsa na bugawa saboda ganin kamannin Mohan ya canza daga nan bil'adama sak. Cikin rawar murya ya ce “kamar ya aure?” “Na ɗaura masu aure da aljanin,zai rinƙa amfani da ita kamar yadda ma'aurata ke yi har su haifi yara” Mohan ya basa amsa ya na mai kallonsa. Kawu Mansur ya washe baki ya ce “ai hakan ya yi don ina so a ƙarshe ya haukatar da shegiya” Mohan ya ce “ƴar ɗan uwan ka ce ko?” Kawu Mansur ya gyaɗa kai,Mohan ya ce “ok ka na iya tafiya” “Ba ka faɗa min nawa zan bayar ba” “Sai in na gama aiki ake biya” Kawu Mansur ya fito zuciyarsa fara tasss..... 400 ne kacal za ki biya domin karanta littafi na ɗaya da na biyu na wannan littafin wacce ta shirya za ta iya tura kuɗinta ta wannan account ɗin 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank Sai ki turo min da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN na 400,ƴan Nijar kuma carte Moov ko airtel ta 400f [22/07 à 07:37] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 13_14* Tamkar daren sallah haka Bobby yake ji.Tun da ya sauka a filin jirgi Léo ya zo ya tarbe shi ya kaisa can inda zai zauna.Cikin shiga irin ta ƴan Pakistan ya shirya har da wani ɗora farin rawani akai,sai kuwa ya yi kyau sosai. Léo ya miƙa masa duk wasu takardu masu ɗauke da bayanai kan Anita ,sannan ya ce “ka kula da kyau kamar yadda na shaida ma mahaifiyar Anita musulma ce,mahaifinta kuma Kirista ne don zan iya ce maka ma kusan kowa ya san shi a garin nan saboda yawan wa'azinsa da kuma taimakon da yake raba wa al'umma” Bobby ya saki ɗan murmushi ya ce “kar ka damu Léo duk zan kula,salamu aleykum! Shi ne gaisuwar musulmi ko? ” Léo ya jinjina kai alamar eh,Bobby ya ci gaba da cewa “Mohamad shi ne wanda suka fi so duk duniya,saboda shi ne shugaban annabawan su” Léo ya ce “annabawan mu dai! Ya na gaban Annabi Musa ” Bobby ya ɗage kafaɗu ya ce “sunan fa ina Bayahude ne ,amma da za ka yi min tambayoyi kan annabinmu ban sani ba” Léo ya ce “don mi?” “saboda ni ban yarda da ko wane irin addini ba” Bobby ya basa amsa ya na mai ɗora baƙin gilashi a fuska ,da sauri Léo ya cire shi ya na mai cewa “no! Kar ka saka shi” “ok mu je ka ajiye ni” Harabar hotel ɗin suka fito,Léo ne ya tuƙa su har zuwa wani haɗaɗen gida mai zagaye da furanni. “Ka sauka ka ƙwanƙwasa,zan jira ka a nan”cewar Léo . Bobby ya fita daga mota ya je ya yi knowking ,an kai minti biyu kafin wani ya buɗe alamu sun nuna dai mai gadi ne. Bobby ya yi masa sallama bisanin ya tambaya “wajen Anita na zo” Cike da wata irin murna ya buɗe masa gidan. Bobby ya sa kai,mai gadin ne ya yi masa iso har cikin falon wanda ba ka jin komai sai sautin TV ta na waƙoƙin Mohamed zain na larabci. “Assalamu aley...” saurar sallamar ce ta laƙe a maƙoshinsa ganin Anita ta fito daga wani ɗaki ƙugunta ɗaure da towel, ta na girgiza kai jiƙaƙen gashinta sai yawo yake. Cak ta tsaya ta na kallon Bobby ,tun daga fararen fartun ƙafarsa har zuwa fuskarsa wacce ya fidda ma gashin baki ya bar saje kawai. Fuuu ! Ta koma ɗakin da fito,Bobby ya fara kiran sunanta “Anita? Anita?” amma ba ta saurare shi ba. Bai yi wani tunani ba ya bi bayanta,ya na shiga ya ganta tsaye ta baiwa ƙofa baya. Ya ja wani dogon numfashi bisanin ya ida takawa dab da ita,kamar mai rawar sanyi haka hannunsa ke kyarma wajen ɗora shi kan ƙunta ya juyo da ita . Hawaye ne ya gani cikin idonta su na shirin zubowa.“Ki yi haƙuri in zuwana ya ɓata miki rai,laifin ruhina ne da ya kasa sukuni saboda rashin ki a kusa da ni” cikin sanyin murya ya faɗi haka . Anita ta kai hannu ta goge hawayen da suka yi nasarar zubowa kan kumatunta sannan ta ce “Bobby mi ya sa? Na yi kewar ka sosai! Na yi ta jira da tsumayen zuwan ka shiru sannan ba ka taɓa bani address ɗin ka ba .Har makaranta na je amma abu ɗaya suka faɗa min kai ɗan asalin Israel ne....” kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sa ta yin shiru. Bobby ya jawota ya manna a ƙirjinsa ya na bubuga bayanta,haɓarsa ya ɗora bisa kanta ya ce “Je t'aime pour toujours ! Ina sonki na har abada!” Anita ta ɗan ɗago kanta suka tsura ma juna ido,a sannu a hankali suka dinga matsa fuskokinsu har Bobby ya yi nasarar sunkuyowa ya fara kissing nata. Sumbata ce irin ta an yi kewar juna,zuciyoyin su har wani bugawa suke da sauri. Anita ta yi saurin janye wa ta na mai cewa “Bobby koma falo ina zuwa” ya girgiza kai haɗi da jawota ya ci gaba da kissing nata. Anita ta ƙara yin nasarar janyewa ta ce “Bobby Maman ta kusa dawowa daga aiki please ka koma falo” ba don ya so ba ya dawo nan falon ya zauna. Kamar minti biyar Anita ta fito sanye cikin doguwar riga blue.Ta yi kyau sosai,ta sakar masa murmushi ta na mai buɗe frigine ta ɗauko masa ruwa ta tsiyaya a kofi ta basa. Bobby ya karɓa ya sha,face da shi ta zauna suka fara taɓa hira. Maman ce ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama ,Bobby ya yi saurin amsawa da “wa'aleykum Salam ya Ummi!” Maman ta saki murmushi ta zo ta zauna,suka fara gaisawa yanayin shigar Bobby ta zata musulmi ne.Sosai ta ji daɗi,“Anita ki kawo ma baƙon abinci mana” cewar Maman. Bobby ya ce “Alhamdullah ! Ban jin yunwa” “Masha Allah! Bari na bar ku to” Maman ta faɗa ta na mai wuce ɗakinta. “Maman na son musulmi,burinta kullum na auri ɗan addininta.Alamu sun nuna ta yi zaton kai ma ka na sallah ” “Shi yasa na yi bincike kafin na tawo” “Hum! Haɗuwar ku ta gaba doli ta gane kai ba ka da ma addini,don sai ta yi ta ma tambayoyi” Bobby ya waro ido ya ce “ki ce tsugunne ba ta ƙare ba an saida Kare an sayi Biri” Anita ta yi dariya ta ce “sosai kuwa don haka faɗi gaskiya tun yanzu” “A'a zan yi tunani a kai” hira su ka dinga yi bisanin Bobby ya fito. A waje ya tarar da Léo ashe bai tafi ba ya na nan dai zaune cikin mota.Har sai da suka hau titi sannan ya tambaya “Ya ne? Babu dai wata matsala ko?” Bobby ya furzar da huci ya ce “eh to! Babu sai dai fa doli na koyi wasu abubuwan na musulmai muddin ina son in mallaki Anita ” “Ai babu wani wuya zan nemo malami” da haka suka isa hotel ɗin,Bobby ya fita daga motar yayin da shi kuma Léo ya yi tafiyarsa. Wanka ya yi sannan ya yi commande ɗin abincin da zai ci,ma'akaciyar hotel ɗin ce ta kawo.Bobby ya gyara zama ya na ci ya na taƙila waya har ya gama.Kiran Léo ya shigo,“ka shirya ƙarfe tara na dare zan zo na ɗauke ka zuwa inda za a koyar da kai” shi ne abin da ya faɗa ,Bobby kuma cike da murna ya amsa da “okay!” ★SENEGAL Lokacin da Kawu Mansur ya dawo gida ya tarar duk su na cin abinci.Duk gaishe shi suka yi banda Bintu da ta kawar da kai gefe ta na mai ci gaba da harakar gabanta. Ya dubeta ya ce “ke ba za ki gaishe ni ba ko? ” duk da ta san da ita yake amma ba ta juyo ba. Zahra ta ƙyafito ta da hannu “Bintu Baba na yi miki magana ” “ke wai mene ne? Ban son takura” cewar Bintun ta na mai tashi ta nufi bedroom. Kawu ya yi murmushin mugunta ya na jin burinsa na daf da ya cika.Wayancewa ya yi ya ce “ Allah ka shiryi Bintu duk yadda nake son yarinyar nan ta zama kamar ƴar uwarta ta ƙi,iskancin nata sai ƙara gaba yake kamar wacce sheɗan ya yi wa fitsari akai” ya na gama faɗa ya wuce ɗakinsa. Ɓangaren Bintu zuciyarta har tafasa take tsabar takaici.Ƙululun baƙin ciki ya turniƙe mata wuya,kan bed ta yi tsalle ta faɗa ba tare da kakaɓe shimfiɗar ba ko ambaton Allah. Lummmm! Wani sanyi ke ratsa gangar jikinta,sam ba ta damu da yanayin ba har sai da ya nune mata jiki ta koma liƙis.Kasa ta yi wa duk wata gaɓar jikinta sarƙa,kanta kuwa kamar mai mura haka ta ji ya kume wuri ɗaya ya zama ɗingimeme. Haka kawai idonta ya fara fitar da hawaye,a haka wani bacci marar daɗi ya yi awon gaba da ita.Mafarkai ta fara na namun daji bisanin Kare ya dinga biyar ta da gudu har ya samu nasarar cizonta a ƙafa.Firgigit! Ta tashi ta na mai dafe kai wanda zuwa yanzu mugun sara mata yake ga kuma idonta har rufewa suke tsabar wani baccin da take ji. Zahra ta shigo ta na mai cewa “ƙarfe tara fa har ta gota ko ba za ki je makaranta ba?” “Bacci nake ji” cewar Bintu kamar za ta yi kuka. “Ki tashi ki yi wanka zai sake ki” “To jira ni kar fa ki tafi ki bar ni ” Bintu na gama faɗar haka ta tashi ta shiga toilet. Bayan ta fito ta saka uniforme suka wuce islamiyya.Sam ba ta jin daɗin karatun kawai dai haƙuri ne take har aka taso.Ko da suka zo gida ba ta yi wa kowa magana ba ta shige ɗaki,wani baccin ta yi.Ba ta farka ba sai da Zahra ta tashe ta don yi sallah zhur. Da kwandon masifa ta nufi ƴar uwarta,“tsabar baƙin ciki mutum na bacci ki zo ki tashe shi? Ina ruwan ki don ban yi sallah ba ke dai ba kin yi ba?” Jikin Zahra ya yi sanyi,sam ta kasa gane kan ƴar uwarta a yau.Haka ta fita ta barta, Bintu kuwa rasa abin da za ta yi kawai sai ta fashe da kuka.Sai da ta yi mai isarta sannan ta je ta yi wanka,dakyar ta gabatar da sallar ta fito falo. Abinci ta zubo ta rakuɓe can gefe ta fara ci kamar mayunwaciya.Duk kowa sai da ya yi mamakin yadda Bintu ta ci plate biyu na abinci har da hauda madarar bido. Da lokacin makarantar marice ya yi,ƙememe ta ƙi zuwa nan ta shiririce wajen kallon tv. Da dare,sun yi shirin bacci Zahra ta dubeta ta ce “Bintu don Allah ko za ki faɗa min abin da ke damun ki? Gobe Kawu ya ce zai kai mu gun Mama ban so ta ga wannan canjin da ki ka samu” “Babu abin da ke damuna,kawai na yi kewar iyayena ne.Kin ga ni bacci nake ji sai da safe” Bintu ta faɗa ta na mai juya ma Zahra baya. Ita ma a doli ta kwanta ta na saƙe-saƙen zuci. Kusan ƙarfe biyun dare amma baccin ya ƙi ɗaukar ta,duk yadda ta so ya yi awon gaba da ita.Ta juyo ta na mai facing Zahra wacce ita tuni baccinta take.Shiru Bintu ta yi bisanin ta lumshe idonta,a nan take wata damina ta fara luluɓeta ta na sanyayya fatarta.A sannu a hankali ta fara shiga duniyar mafarki mai kama da gaskiya. Tsikar jikinta ne ya yi wani mugun tashi, lokaci ɗaya ta fara jin amai yayin da kuma tsoro ke daɗa aurenta.Ta yi baya za ta gudu kawai ta ji an cirata sama ƙafafuwan ta na yi reto a iska.Ihu ta fara sai dai alamu sun nuna babu mai jinta don muryata sam ba ta fita.Timmm! Aka saketa ta faɗi ƙasa,bakinta ya fashe jini ya fara zuba.Mumunar hallitar nan ta ga ta dumfarota,Bintu ta rumtse ido ta na addu'ar Allah zare ranta ta huta da wannan masifa. Hannunsa ta ji ya na shafar fuskarta,tamkar garwashin wuta haka tafinsa ke da mugun zafi.A karo na biyu ta buɗe ido ta kalle shi,idonsa ɗaya da ke can kusa da kumatu ya kafa mata,yayin da kuma yake wani juya ƙawon da ke gefe da gefen kansa. Jikinsa duk gashi ne babu kyawun gani,murya na ɗan rawa ta ce “wane ne kai?” “mijin ki ne?” ya bata amsa cikin wata ruɓaɓiyar murya ya na mai cire kayan jikinta.Tamkar wacce aka yi wa allurar kashe jiki haka ta gagara hana shi har sai da ya biya buƙatarsa.Ihun da ta fasa ne ya dawo da ita daga duniyar mafarkinta.Kalle-kalle ta fara bisanin da sauri ta sauka ta nufi falo don ɗauko ruwa ,tsit kake ji babu motsin komai.Kitchen ta shiga ta ɗauko ruwan ,hannunta har rawa yake wajen buɗe murfin sai dai kash ta na ɗaga butalin sama kamar magie ruwa ko ɗigo ɗaya babu. Daga bayanta ta ji motsi,a tsorace ta waiga ta na fitar da wani sauti “haaann” sai dai wayam babu kowa ta na shirin ajiye butalin ta ɗauki wani sai kuma ta ga ya cika da ruwa da sauri ta kai bakinta ta shanye su tasss. Innuwar mutum ta gani,a hankali ta fara ɗago kanta zuciyarta na halbawa sai dai kafin ta yi tozali da fuskar mamallakin innuwar wutar gidan ta ɗauke ɗifff.Ta buɗe baki da niyyar yin ihu ta ji wani kakauran hannu ya toshe mata baki tare da cewa “shiiit!” Masu son ci gaba sai mun haɗe a PAID GROUP,400 ne kacal Hajiya .Ki tura ta wannan account 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 Talla Assalamu alaikum,ina masu fama da shafar aljannu ko sihiri to ku matso kusa ga wani book na musamman da na ware domin wannan matsalolin a cikinsa akwai bayanai daki-daki akan ko wace matsala sannan da addu'o'in ta.Akwai su a rubuce sannan kuma da wanda za a saurare a samu waraka bi'izinillahi ta'ala. *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI* ƙirƙirarren labari ne mai ɗauke da darussuka,masu cutar hauka,ko damuwa ko jinnu duk za ku samu addu'o'in ko wace matsala na karatun malumai da suka tsaya suka zaƙulo ayoyin Allah daga cikin Alkur'ani na dangane da ko wace irin cuta. Uwanda ba su iya karatu ba za su iya saurare ko kuma su bayar wani ya karanta masu cikin ruwa. A cikin wannan littafi na fitar da kalolin asiri uku wanda su ne aka fi samu. Akwai masu fama da djinn ashiq bayyananne ko ɓoyayye irin wanda bai nuna alama ko kuma ya tashi.Da yardar Ubangiji shi ma zan yi magana akai tare kuma da karatunsa domin samun lafiya in Allah ya so. Domin samun wannan littafi 400 kawai za ki biya na saka ki group +22795045822 [23/07 à 14:41] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 15_16* ```Assalamu alaikum jama'a,ina yi ma kowa fatan alkhairi saboda yawan ƙorafin cewa babu kuɗi a yanzu a rage mana.To zan bayar da book one a free na *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI* book 2 kuma za ku biya 200 kacal😓 ga masu buƙata su yi min magana pc. Katin MTN ko transfer,ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 200f🙄``` Jikin Bintu ya fara yin wata irin kyarma, kamar ranta zai fita haka zuciyarta ke wani bala'in bugawa.Ƙiiii! Ya rinƙa janta har suka isa wani ɗaki,daidai nan hasken ya dawo ya kuma sakar mata baki.A wahalce ta juyo ta dube shi,Kawu Mansur ne tsaye ƙiƙam ya na aika mata wata muguwar harara bisanin ya yi gaba ya ɗauko wata system. “Ki buɗe matakan tsaron da ke ciki,PA ya tabbatar min ke ɗaya ce ki ka san sirrin ubanki” Kawu ya faɗa cikin bayar da umarni. Bintu ta haɗiye wasu yawu,tsoro take ya yi mata wani abu hakan ya sa jiki na kyarma ta fara buɗe duk wasu abubuwan da ke da code.Ta ɗago hawaye sai zuba suke yi mata,cikin rawar murya ta ce “na buɗe” Kawu Mansur ya wangale baki ya na mai ɗauke system don shi bai san komai ba da ya shafi boko. “Fice ki ban wuri ki ka wani tsaya ki na kallona da shegun idonki” ya daka mata tsawa.Bintu har tuntuɓe take wajen fita,direct ɗakinsu ta wuce ta na mai fashewa da wani marayan kuka. Hankali tashe Zahra ta farka daga bacci,“lafiya mike damun ki?” “Kawu Mansur ne shikenan duka dukiyar mahaifinmu zai kwashe” ta faɗi haka cikin kuka. “To mine ne na kukan? Kin ga don Allah ki bar zancen dukiya,ina ce dai wanda ya tara ta ma ya mutu ya barta balle mu da gado ne za a bamu” Zahra ta faɗa ta na jawo Bintu a jiki,ita kuwa sai kuka take kai kace yanzu aka shaida mata mutuwar Abba. Washegari da kumburar fuska Bintu ta tashi tare da matsanancin ciwon kai.Halilu ya shigo har ɗaki domin dubata,ta wani yi banza da shi . “Mene ne ya saka ki kuka? Zahra ta ce min ba ki da lafiya” ya furta ya na mai zama bakin bed tare da ɗan jan zanen da ta rufa da shi. “Ka je ka tambayi maci amanar ubanka” ta faɗa sautin muryarta bai fita sosai.Halilu ya rumtse ido jin furucinta,“mi shi Baba ɗin ya yi miki? Na san dai ba zai dake ki ba” “Don Allah ka fita ka bar ni ban son surutu” “To ki tashi ki sha magani” “Ban sha” “Don mi?” “Saboda jikina ne ba na uban wani ba” “Bintu ni ki ke zagi?” “In akwai fiye ma da haka zan yi” “To na ji! Amma ki daure ki sha maganin,ko kuwa na kai ki asibiti ” Bintu wacce tun shigowarsa ta rufe ido,ta yi saurin buɗe su ta na kallonsa kafin ta ce “kai a su wa?” “Mijin ki” Halilu ya bata amsa,ita kuma ta ja dogon tsuki bisanin ta juya masa baya. Fita ya yi ya sawo maganin ,cikin kofi ya jiƙa shi sai da ya narke duka sannan ya yi wa Bintu ɗuren shi.Duk yadda ta so ta ƙwaci kanta hakan ya cuttura saboda ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba.Babu jimawa gumi ya fara keto mata,a sannu ciwon kan ya fara sauka.Ta ja ajiyar zuciya ta na mai sake yin lamo a ƙirjinsa don har yanzu bai saketa ba. Tafin hannunsa ya kai kan goshinta ya goge zufar,ta buɗe idonta masu kama da mai jin bacci ta saka su cikin nasa.Ya ɗan hura mata iska ya ce “ya jikin?” ta turo baki ta na hararen shi.Halilu ya ɗan ja ajiyar zuciya ya ce “Bintu ban so ki na tayar da hankalin ki akan dukiya,na yi miki alƙawarin ba zan taɓa bari ta salwanta ba.Ni ke nake so,ban damu da wasu kuɗi ba don haka da zarar na kammala karatuna duk wasu abubuwa za su dawo ƙarƙashin kulawata kin ga shikenan sai na mayar miki da komai” Da sauri ta yunƙura tare da janye wa daga jikinsa,“bakin ku haɗe kai da mahaifin ka.Kamar ku na jiran mutuwar Abba duk ku ka dawo gidanmu alhalin babu wanda ya ce ku zo.Mama ba ta lafiya amma tsabar mugunta ta Kawu a gabanta yake cutar da mu, wannan ya saka ta gwammaci ta koma zaman asibiti.Na tsane ku dukan ku ban son ku,ban san ma ya aka yi mu ka haɗa alaƙar jini da ku ba” “Kenan ba ki yarda da ni ba? Ko kuwa soyayyata ce har yanzu ba ki gamsu da ita ba? Bintu dube ni cikin ido” Ta ɗago suka haɗa ido,sai kuma ta yi saurin sunne kai saboda ba za ta iya jurar kallon cikin su ba har wata zaiba-zaiba take gani da kuma wani abu mai kashe jiki. “Ina son ki,kuma in sha Allah babu wanda ya isa ya cutar da ke ciki kuwa har da shi Kawun” jin furucinsa ya saka ta sake dubansa ya jinjina mata kai. Wani ɗan sanyi ta ji ya ratsa sashen zuciyarta,duk da ba ta yarda ɗari bisa ɗari ba amma ta yarda da soyayyar da yake yi mata. “Lilu....” sai kuma ta yi shiru,shi kuwa wani murmushi ne ya ƙwace masa ba ƙaramin daɗin sunan Lilun nan yake ji ba.Cikin zaƙuwa ya ce “mine ne Bintuna?” Sai da ta yi ɗan jimmm sannan ta ce “da gaske ka na sona? Sannan za ka iya zama da ni a ko wane irin ƙuncin rayuwa?” Sai da ya riƙo tafukan hannunta sannan ya dube ta cike da kulawa ya ce,“Babu wani hali da Bintu za ta shiga wanda Halilu ba zai zauna da ita ba,da ace za ki zama kuturwa,makauniya kuma kurma to ki saka a ranki ɗigo ɗaya na soyayyar da Halilu ke yi miki ba zai ragu ba” Bintu ta zumɓuro baki ta na wani hararen shi,ya tambaye ta “mi na yi kuma?” “Sai wani kiran kan ka kake da sunan ubanni,kawai ka ce Lilu ya fi kyau da daɗi” cike da yarinta ta yi maganar,wanda hakan ya saka shi yin dariya har sai da haƙoransa suka bayyana. Bintu ta yi kasaƙe ta na kallonsa,ba ta taɓa sanin ya na da kyau ba sai yanzu,sai kuma ta kawar da kai. Halilu na shirin yin magana Kawu Mansur ya shigo ɗakin. “Uwar mi kake yi nan? Ke kuma ki tashi ki yi shirin makaranta don ubanki tunda ba kuɗin banza na zuba ba”Kawu ya faɗa ya na hararenta. “Kawu ba ta da lafiya ne,yanzu nan ta sha magani”cewar Halilu . “Ka je can falo ina son ganin ka,ke kuma na baki minti goma ki shirya ” Kawu na gama faɗa ya fice. Cike da tausayi ya dubeta ya ce “ki tashi ki shirya kin ji? Ni zan kai ki da kaina ” Bintu ta jinjina masa kai.Ya miƙe ya fita,ta bi bayansa da kallo bisanin ta je ta yi wani wankan. Bayan ta fito ta je kitchen ta samu ruwan zafi ta gasa idonta,duk kumburin ya baje.Cikin uniforme ta shirya,ta zo falo ta yi zaune ta na jiran fitowar Halilu don tuni su Zahra sun tafi. Daga inda take zaune ta na jiyo sautin muryar Kawu,alamu sun nuna masifar ce da ya saba yake yi wa Halilu.Ta nan zaune ya fito ransa a ɗan ɓace,su na haɗa ido ya sakar mata murmushi ya ce “tashi mu tafi” ta take masa baya har zuwa mota. Shi ya tuƙa ta ya kaita makaranta,a hanya sai hirar soyayya yake yi mata ita dai sai dai ta mayar masa da martanin murmushi. HABIBA Tun da a ka sa ta makaranta ta fara wayewa,don yanzu tsakanin ta da hijabi sai in za ta yi sallah.Hullar gashin doki kuwa ita kanta ba ta san rabon da ta cireta a kanta ba,kamar ibada kullum ta na ga kanta. Ƙawarta guda duk faɗin makarantar,sunanta Mardeeya ƴa ce ga shugaban ministan kuɗi.Abotar tasu ta samo asali ne tun ranar da ita Mardeeyar ta fara zuwa aji babu wuri sai ita Habibar ta yi mata nuni da kusa da ita shikenan suka ƙulla ƙawance. Zaune suke su biyu,Habiba ta dubeta ta ce “yanzu da gaske ba ki iya girki ba? To in ki ka yi aure wa zai dafa wa mijin ki abinci?” Mardeeya ta tuntsire da dariya ta ce “na yi miki kalar shiga kitchen? Hum! Ai ni yanzu haka ko wanka zan yi sai mai aiki ta cika min bawon wanka ta zuba kalolin sabulu da turare.Mijin da zan aura kuma ba ɗan nan ƙasar ba ne,Balarabe ne a facebook mu ka haɗu da shi” Habiba ta waro ido ta ce “yanzu yadda ki ke baƙar nan sai Balarabe ya aure ki?” “Ai sun fi son baƙar fata,ƙarshen week ɗin nan zai zo gidanmu ina gayyatar ki fatan ba za ki ƙin zuwa ba?” Mardeeya ta faɗa ta na kamo hannuwan Habiba alamar roƙo. “Zan zo mana,dama ina son zuwa gidan ku ke ce ba ki bani ƙofa ba” “Ko yanzu ki ke son zuwa sai mu tafi ai ba wani abu ba ne” cewar Mardeeya ta na mai tashi tsaye,Habiba ta washe baki ita ma ta miƙe. Inda ake ajiye motoci suka nufa, Mardeeya ta buɗe wata latsetsiyar farar mota ta shiga ,Habiba ta zauna a gaba. Cikin slow take driving ta na shan chocolat yayin da kuma bakinta ke bin waƙar Dadjou,a haka har suka isa katafaren gidan wanda a ƙofaf gidan har da jami'an tsaro. Aka wangale gate ta cinna hancin motar ciki,ta samu wuri ta yi parking sannan suka fito. Duk kurin da Habiba take da murnar su ma yanzu masu kuɗi ne sai ta ashe Kawu Mansur talaka ne in aka auna shi da mahaifin Mardeeya. Cikin falon kalolin kugerun zama sama da guda biyar,ƙaton falo ne irin sosai ɗin nan.Tsabar ƙauyanci ya saka Habiba yin tuntuɓe ji ka ke tassss! Ta ture faux du fleure . “Fatan ba ki ji ciwo ba?” Mardeeya ta tambayeta,Habiba ta girgiza kai a zuci ta ke cewa ‘oh! Ita ba ta damu da abun da na fashe ba ma’ “Ga ɗakina na nan” Mardeeya ta katse mata tunanin zucin,ta buɗe ɗakin ta shiga Habiba ta mara mata baya ta na mai cewa “mi ya sa ba a baki ɗaki can sama ba sai a nan ƙasa?” “Ɗakin Dad da kuma Ya Kameel ne kawai a sama hatta Momy a ƙasa take zaune” Mardeeya ta bata amsa ta na mai cire takalmin ƙafarta masu tsini. Habiba na shirin yin magana idonta ya yi tozali da ƙaton hoton wani Guy baƙi suluk,sai dai sajen da ya ajiye shi ya ƙayatar da fuskar tasa. “Ya Kameel ne wannan,shi ne babba gidanmu,bayansa an haifi wasu duk sun mutu.Ni ce aka haifa ta ƙarshe kuma ni ce auta” Habiba ta waigo ta dubeta,ita kuma ta ɗaga mata gira tare da cewa “Yes! Ko ya yi miki ne ki na son shi?” Habiba ta ce “mi zai yi da baƙauya, wannan da ganinsa ƴan matansa ba su ƙirguwa” Mardeeya ta ce “ai kuwa kamar kin sani ,don yanzu haka maganar da nake yi miki kusan kullum sai sun zo nemansa.Wasu ma har gyaran ɗaki suke yi masa,akwai kuma masu kwana a gidan nan duk domin samun soyayyarsa ” Wani baƙin ciki ne ya rufe zuciyar Habiba wanda ba ta san dalili ba,kawai sai ta taɓe baki ta na mai ɗan ƙarewa ɗakin kallo.Komai na cikinsa pink ne tun daga bed ɗin har labulaye da kuma kujeru biyun da ke ajiye. Takalmi ne kaloli a jere ras a cikin ƴar kwabarsu,haka ma hullunan mèche na gashin doki.Kan dressing mirror kuwa ba a magana,kai kace wani kantin kayan kwalliya da turarruka. “In kin ga abin da ya burge ki kawai ki ɗauka” Mardeeya ta faɗa ganin yadda Habiba ta baza na mujiya ta na kallo. “Ina son kayan kwalliya ,sai dai ban iya ba” “Hhh! Ai babu wuya bari na yi wanka sai na nuna miki yadda ake yi” ta na gama faɗa ta shiga toilet ta fara wanka,babu jimawa ta fito ƙugunta ɗaure da towel fari sol. “Ki shiga ki yi wanka,sai na yi miki kwalliyar” “Mardee kar fa aje ayi min ta ƙi yi min kyau” “Dalla Malama ki shiga kawai ki yi wanka in ba ta yi kyau ba ki ce ni ba Mardee Mohan ba ce” ta faɗa har da wani buga cinya irin yanda indiyawa kan yi, Habiba ta tuntsire da dariya bisanin ta shiga ta yin wankan. Bayan ta fito ne Mardeeya ta tsantsara mata kwalliya,kai kace wata amarya.Cikin kayanta ta zaɓo wa Habiba wata shuɗiyar doguwar riga.Kamar wata ƴar tsanar roba haka ta fito ta yi tsaf da ita,hotuna ta yi mata bisanin ita ma ta shirya kanta. “Yadda ki ka yi kyawun nan ina mai tabbatar miki in mu ka je gidan shaƙatawa sai an samu kyakkyawan saurayi ya wud da ke!” “Mardee kar ki sa kaina ya fara hayaƙi mana” “Allah gaskiya nake faɗa miki ” “To ina za mu je?” “Mu je mu sha crème glacée” Direba ya kai su wajen shan crème glacée ɗin.Su Na zaune su na taɓa hira,Mardeeya sai bata labarin yadda suka haɗu da Balarabenta take a haka har suka ida suka fito. Su na shirin shiga mota wani saurayi ya yi saurin ƙaraso wa gun su.Sallama ya yi masu suka amsa,ya dubi Habiba ya ce “don Allah in babu damuwa ina son lambar wayar ki” “Banda lamba” ta basa amsa. “Ba dai za a bani ba,to a sayar min ko nawa ne zan saya” Ta ɗan saki murmushi ta ce “tukunna dai ban fara riƙe waya ba,karatu nake” Saurayin ya dubeta,don Habiba ta kai shekara sha takwas. Ɗan waigawa ya yi,ya ce “in babu damuwa to ku jira na je na sayo miki wayar na kawo miki,don muddin ki ka suɓuce min na shiga uku” Ba Habiba ba hatta Mardeeya sai da ta dube shi,haɗaɗen gaye ne irin sosai ɗin nan. “Ok bari mu shiga mota mu jira ka” Mardee ta faɗa,ya yi murmushi ya ce ya “na gode” wata jar mota da ke parker a gun ya shiga,su ma suka shiga suka zauna. “Kin gansa kyakkyawa da shi” Habiba ta taɓe baki a zuci ta ce ‘ai bai kai Kameel kyau ba’ a zahiri kuwa cewa ta yi “mun dace da shi ne?” “sosai ma kuwa” “Ni kuwa bai kwanta min a rai ba” “Ki ƙara masa lokaci dai,duka fa yanzu ne kuka haɗu” Su na nan zaune ya dawo,ya ƙwanƙwasa glass dakyar Habiba ta fita ta karɓi wayar bisanin su yi tafiyarsu. ★JAPON Malami na musamman ne ke koyar da Bobby abubuwan da suka shafi Musulunci.Ba wai don ya yi aiki da su a karan kansa ba ne a'a,kawai dai ya na koyo ne saboda ya ci nasarar samun Anita. Sosai ya maida hankali wajen koyon babbaƙu,bai ɗauki dogon lokaci ba ya fara iya tada baƙi tare da koyon karatun Alkur'ani mai girma. Shi da Anita kuwa kullum su na maƙale a waya,tun ranar da ya je gidansu bai sake zuwa ba. Garin yau ya tashi da hazo,luf-luf ko ta ina hadari ne ya gangamu ya yi baƙi ƙirin.Bobby kuwa a tsanake ya ke ƙara gyara ɗakin nasa saboda ziyara da Anita za ta kawo masa.Flowers ya zuba kan gado ya rubuta kalmar I LOVE YOU da babban harufa. Komai ya shirya shi tsaf zuwanta kawai yake jira.Ya na nan zaune ya ji knowking,da mugun sauri ya je ya buɗe.Anita ce sanye cikin riga da wando ,ta harɗe gashin kanta a tsakiya. Blue idonta masu kama da na mage ta ƙura masa,Bobby ya ja ya bata hanya ta shigo sannan ya rufe ɗakin da key. “Waooo!” ta furta ta na kallon kwalliyar da ya yi wa ɗakin kamar ba hotel ba.Ya rungumeta ta baya ya ce “Oui je t'aime ! Ina sonki my Ani! ” dariya ta yi ta ce “ni ma ina sonka” Ya sake ta,ya nuna mata wurin zama ta maƙe kafaɗa ta ce “a samar ƙafar ka zan zauna” “oh! Hakan ya yi min daɗi” ya furta ya na mai zaunawa ,Anita ta hau kan cinyarsa. Jus ya zuba a kofi biyu,ya miƙa mata ɗaya ya ɗauki ɗaya. “Shikenan ka manta da ni,shiru ka ƙi zuwa wajen sati biyu kenan.Maman har sai da ta tambaye ni ko lafiya ?” “Lafiya lau,ina nan ina ta fafutukar iya addinin Maman don ta bar min ke” Bobby ya faɗa. Anita ta ce “Ka na nufin larabci ka ke koyo ko kuwa karatun?” “Duka biyun” Ta ƙura masa ido,bakin na ɗan rawa ta ce “dama har haka ka ke sona?” Ya bata amsa da “Fiye da haka” Anita ba ta san lokacin da ta yi saurin kwanto shi ba,ta na mai kai bakinta kan lips ɗinsa.Mai son kuka an jefe shi da kashin awaki! Bobby kamar mai jira ya yi mata kyakkyawan masauki akan ƙirjinsa.... Wacce ta shirya payement za ta turo 200 kacal ta wannan account ɗin 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte Moov ta 200f [24/07 à 15:40] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 17_18* Yadda yake sarrafa ta a haukace ya saka tsoro yi wa Anita dirar mikiya a ƙawon zuciya.Ƙoƙarin cire gangar jikinta take,amma sam ta kasa saboda kamun sandar makauniya da Bobby ya yi mata.Mugun sonta sai ƙara bijiro da tsohuwar sha'awarsa yake,duk yadda yake ƙoƙarin controling kansa ya kasa .“Bo..b...byyy please ka bari har bayan aure” Anita ta faɗa cikin fizgar numfashi bayan ta ci nasarar zare bakinta daga na shi. Ido tab hawaye Bobby yake dubenta,sam ya kasa yin magana .Rabon da ya tsinci kansa cikin irin wannan yanayin tun ranar da ya kawar da budurcin Anita. Hannunta ya yi saurin kamawa ya ɗora saitin zuciyarsa da take faman bugawa,ta sani sarai a wannan lokacin babu abin da Bobby ke da buƙata illa ta basa haɗin kai bori ya hau.Waiwayen baya da kwanyarta ke yi mata na uwar azabar da ya gana mata shi ke daɗa tsoronsa a zuciyarta. Ta ya haɗiye yawu haɗi da jan ajiyar zuciya ta ce,“zan taimaka ma ka samu nutsuwa amma please kar ka kusance ni” “Don mi?” ya tambaye ta hawaye na zubowa zirrr kan kumatunsa . “Doli Maman za ta gane in na koma gida.Bobby tun bayan rabuwata da kai babu namijin da ya taɓa kusantata,hasali ma ban yi wani saurayi ba ka ga kuwa muddin mu ka yi sex zan sha wuya ne” Da sauri Bobby ya girgiza mata kai ya ce “ba zan yi miki da ƙarfi ba, please Anita ki fahimce ni zan iya mutuwa fa” ya na faɗar haka ne tare da kuma kai hannu jikinta ya na sarrafata. Ta rumtse ido gam,Bobby ya cirata cak ya ɗora kan bed.Sai da ya sha daga sosai kafin ya raba Anita da kayan jikinta.A halin da ta gansa kawai ya sa ta fashe da kuka,bai saurareta ba ya toshe bakinta ta hanyar saka nasa ciki bisanin ya fara kusantar ta. Kamar wata amarya haka take kuka da faman fizge-fizge,an ɗauki ɗan lokaci kafin ya koma gefe.Cike da jin haushi Anita ta miƙe ta shiga toilet, Bobby ya take mata baya . Cikin bawon wanka suka shiga,suka yi wankansu bisanin su fito su ci abinci da ke kan table. Kayan jikinta ta maida sannan ta yi masa sallama ta fita. Bobby kuwa wani tsadadden murmushi kawai yake saki,wata irin nutsuwa yake ji da salamar ruhi.Group ya shiga suka fara yin message shi da Fadeel don Kameel tun komawarsa Senegal ba kullum yake hawa online ba. ANITA ta na cikin mota ta na tunanin scène ɗin su da Bobby .Ta ci wuya ba laifi amma a wannan karon ta ƙudiri aniyar ba za ta barsa ba za ta dinga jure wa buƙatarsa. Ta na isa gida ta tarar da Maman a falo ta na karatun Alkur'ani. “Oh! Allah ” ta furta cike da gajiya bisanin ta zauna ta na cire takalmin ta . “Ina shopping ɗin da ki ka ce za ki yi?” Maman ta tambayeta ta na mai ƙare mata kallo. Gaban Anita ya faɗi,sam ta manta da ƙarya da ta yi wa Maman kan za ta be shopping ne alhalin don ta je gun Bobby ne. “Am .. Eh...Su na can cikin mota Maman,amma mi yasa ki ka tambaye ni?” da i'ina ta yi maganar. “Ina matsayin mahaifiyar ki bai dace na san inda ki ka je ba?” “A'a ban ce ba! Kawai dai na yi mamaki ne yadda aka yi ki ka tambaye alhalin lokacin baya ba ki yin haka” Anita ta faɗi haka ta na mai kwashe takalminta ta nufi hanyar bedroom don gudun wata tambayar. “Ya shi Mohamed Bobby ɗin ya na lafiya ko?” Da mugun sauri Anita ta juyo ta kalli mahaifiyarta sai kuma ta shige ɗakinta ba tare da ta amsa mata ba. Ta na nan zaune bakin bed Maman ta shigo. “Anita ke yarinya ce! Ki na tunanin za ki iya yi min wayo? Dubi yanayin ki haka ki ka fita? Ina kwalliyar da ki ka yi ? Haka nan kawai ta goge?” Maman ta jero mata tambayoyin. Anita ta ɗan rikice duk alamomin rashin gaskiya sun bayyana a fuskarta. Murya na ɗan rawa ta ce “Maman na sani ! Na je gun Bobby amman babu abin da ya shiga tsakanina da shi.Ko kin manta na faɗa miki shi ma musulmi ne? ” “Ki yi hankali shi ne kawai abin da zan faɗa miki.Samun ciki a shekarun ki ba tare da aure ba shi nake guje miki.” Mama na gama faɗar haka ta fice.Anita ta ja wani dogon numfashi ta na mai faɗa wa kan bed ɗin ta yi kwance ta na kallon sama. ★SENEGAL Kamar jaririn da aka haifa yau haka suka zagaye wayar su na dubawa.Habiba zuciyarta fal farin ciki yau dai ta fara riƙe abun da su Twins ba su taɓa samu ba a rayuwarsu. “Na yi mamaki sosai da ki ka ce yau ne ku ka haɗu kuma har ya iya saya miki waya” Zahra ta faɗa. “Ya na sona ne shi yasa ke ma da zarar kin samu mai son ki zai saya miki ” Habiba ta bata amsa. Bintu ta ce “tun Abba na da rai kullum sai ya yi mana faɗa akan kar mu kula samari haka ma kar mu amshi abun hannun su to mi zai sa ta karɓa?” “Hhhh! Hassada ta dai ku ke yi in na gane,to na gaba ya yi gaba iyeee! Ƴan baƙin ciki” ta na gama faɗa ta miƙe ta fita daga ɗakinsu dama ta shigo ne ta nuna masu wayar. Twins suka kalli juna cike da mamaki, Bintu ta taɓe baki ta ce “Kin ga Zahra ki tashi ki ɗauki duk abin da ki ke so , Lilu ya ce zai kai mu asibiti gun Mama” “Can za mu kwana?” “Eh mana! Ko kin manta gobe weekend ?” “Amman ai za mu je islamiyya ” “Mtsw! Kullum ba mu na zuwa ba? Gobe ne kawai za mu yi fashi fa” “Ok to” Zahra ta faɗa ta na mai tashi ta saka kayansu kala biyu cikin wata jaka. Halilu da kansa ya zo ya yi masu magana suka fito ya sa su a mota ya kai su haɗaddiyar asibitin. Ko ina tsaf yake babu ƙazanta,a asibitin ba su buƙatar ƴan jinya likitocin ne ke kula da duk patients.In kuma ka na son ganin wani sai weekend. Da murna suka je suka rungume mahaifiyarsu wacce tsabar yadda ake kula da ita ya saka ta yi kyau. “Mama don Allah ki koma gida ” cewar Bintu. “Zan koma ƙarshen watan nan lokacin na iya tafiya da ƙafata ” “Mun yi kewar ki sosai” Zahra ta faɗa kamar za ta yi kuka. “Ni ma haka.Ya ya ƴan gidan? Fatan ba a takura maku?” Bintu ta ce “Hum! Kawu zai barin mu haka nan ba tare da tsangwama ba? ” “A'a bai da matsala ke ce ki ke takura kan ki” cewar Zahra. Bintu ta ce “Mama wannan da ki ke gani ba ta san ciwon kanta ba.Ko kin san da Kawu ya tursasa ni sai da na cire masa code ɗin system ɗin Abba ?” Mama ta yi murmushi ta ce “ki barsa shi da Allah ne! Haƙin zumunci kawai ya isa ya tambaye shi.Wai ban ma tambaya ba wa ya kawo ku?” “Lilu ne!” Bintu ta bata amsa. “Wane ne kuma haka?” “Wai Halilu kin san yanzu soyayya suke” Zahra ta faɗa ta na tuntsira dariya. “Kun ci abinci ne? ” “A'a sauri muke kar Kawu ya dawo ya hana a kawo mu” “Ok ku buɗe frigine akwai kaza da madara da kuma ayaba sai ku ci” Da murna suka je suka ɗauko,su na ci su na yin hira har suka gama suka shiga toilet suka wanke hannu. Hira sosai suke,bayan sun yi sallah isha'i ne wata nurse ta shigo ta kawo masu wasu ƙananan matala lakai-lakai guda biyu. Bisanta suka kwanta da dare ya yi. Bintu na cikin bacci ta fara jin sanyi na ratsa ta bisanin kuma wata zazzafar shafa mai shiga ɓargo.Ba ta san mine ne feeling ba sai a mafarki,tuni jikinta ya fara ɗaukar caji ta na jin daɗin yadda ake taɓa sassan jikinta.Lokacin da ya fara kusantarta tamkar ta yi ihu haka take ji don daɗi,a haka har ya gama ya sauka kanta.Daidai nan ta farka,da wani mugun sauri ta tashi zaune ta na mai dafe zuciyarta. Toilet ta shiga ,sai ta lura duk ta ɓata jikinta.Duk da ba ta da wani dogon ilimi amma a makarantar islamiyya an yi masu bayani kan babin wanka janaba da na jinin haila da kuma abubuwan da ke sharhanɗa wanka. A hankali ta kunna pampon ta yadda ƙarar ruwan ba zai tayar da su Zahra ba ta gabatar da wankan.Bayan ta gama ta yi alwala ta fito,a zaune ta tarar da Mama da sauri ta sunne kanta da ke ɗigar da ruwa. “Je ki kwanta Bintu kin wani zo kin yi tsaye” shi ne abin da Mama ta faɗa.A hankali ta ja wata ɓoyayyar zuciya,ta yi tunanin Mama za ta tambaye ta wankan mine ne ta yi. Kan katifa ta je ta kwanta,sai dai ta kasa yin bacci tunanin mafarkin nan kawai take yi wanda ba ta san dalilin yinsa ba . Sai wuraren asubahi ta samu bacci,wanda a ƙarshe Zahra ta tashe ta don yin sallah.Ta na gama wa ta ɓingire bacci. A zaune ta ganta cikin wani jeji mai furanni tsanwa sharrr.A gabanta kuwa wani kyakkyawan saurayi ne ya na sakar mata murmushi. Kyawunsa ne ya ja ta izuwa gun shi,kalaman soyayya ya fara faɗa mata ya na yi ya na shafar jikinta. Kan cinyarsa ta hau,ta ɗora bakinta kan lips ɗinta daga nan suka fara sarrafa juna,ya na gaf da ya kusanceta ta ji muryar Zahra ta daki dodon kunnenta. Kanta ya yi wani bala'in sarawa,cikin fushi ta tashi ta ce “mi aka yi ne?” “Ki tashi ki yi wanka sai mu ci abinci ” cewar Zahra,a harzuƙe ta ce “ban ci ” sai kuma ta yi luuuu ta koma ta kwanta. Idonta har wani dishi-dishi suke,cikin son ta koma baccin ya fara hura mata iska a fuska.Cikin sauri ya fara kusantar ta kamar abun yaƙi,ya na gamawa Bintu ta farka. Wannan karon haka kawai ta ji hawaye na yi mata zuba ba tare da ta san dalili ba.Can ta tsinkayi Zahra a zaune kusa da Mama su na cin abinci,dakyar ta miƙe ta shiga toilet.Baƙin cikin ganin yanzu ma jikinta ya ɓace ya saka ta fashewa da kuka,bisanin ta sakarwa kanta shower. Rigar da ta cire ta ɗaure kanta tamau don kar Mama ta ga gashinta a jiƙe.Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki ta fito,can gefe ta zauna ta shafa mai da turare sannan ta saka kaya. Duk abin da take Mama na ankare da ita kawai dai ba ta ce mata komai ba ne. Dakyar Bintu ta ci abinci, sam ta kasa sakewa saboda ƙuncin da take ji. A can gida kuwa Kawu Mansur sai da ya yi kamar zai daki Halilu da ya samu labarin ya kai su Twins can asibiti.Inna ce ta yi ta faman basa haƙuri,ita kuwa Habiba ta na can maƙale da waya ita da sabon saurayinta wanda tuni ya saye mata zuciya. Tsaf ta shirya cikin wasu riga da zane na atamfa,kamar yadda suka yi da saurayinta Haidar shi ya zo daidai inda ta kwatanta masa. Su na tafe a mota sai yaba kyawunta yake,ita kuma banda juya ido da murmushin jin daɗi babu abin da take a haka har suka isa gidansu Mardeeya. “Sai yaushe za ki koma gida?” Haidar ya tambaye ta . “Ina ga sai bayan sallar magrib,don yanzu aiki ne za mu yi sai kusan ƙarfe biyar baƙon nata zai zo” Habiba ta basa amsa. “Ok in kin gama sai ki kira ni,ki kula min da kan ki” Ta washe baki ta ce “to in sha Allah!” sannan ta fito. Mardeeya ta kira bisanin masu gadi su barta ta shiga,da ihu suka tarbi juna kafin Habiba ta aje jaka ta canza kaya sannan suka shiga kitchen. Yau kam mai aiki gefe ta koma ta na kallonsu, lokaci zuwa lokaci ta na ɗan taimakawa da abun da ba a rasa ba. Mardeeya kuwa sai murna take don tuni ta faɗa ma baƙonta da kanta za ta yi masa girki. Sai bayan sallah azahar suka gama,Habiba na fitowa daga kitchen ta yi kiciɓis da Kameel ya shigo shi da wata farar Baby sun nufi can saman bene. Wani takaici ne ya rufe ta ,a nan ta yi tsaye ta na kallon su har suka ɓace ma ganinta. “Oh! Nan ki ka tsaya? Bari na je na yi sauri na yi wanka” cewar Mardeeya ta na mai rugawa ta nufi ɗakinta. Sama da minti biyar Habiba na nan tsaye bisanin ,wata zuciya ta raya mata bin bayan su Kameel . Can sama ta hau,sai dai ta rasa wane ne ɗakinsa don ɗaki uku ne a gun.Har ta juyo za ta tafi wani sauti ya ja hankalinta.Da saurinta ta kai kunnenta jikin ƙofar,ta wani waro ido saboda kalaman da suke fitowa daga bakunan masoyan.Bugun zuciyarta ne ya tsananta bugawa da ƙarfi,yayin da kuma ta fara jin tamkar da ita ne Kameel ke tarayya.Hannunta har rawa yake wajen tura ƙofar ciki,ba tare da wani tunani ba ta kutsa kai ciki..... Masu buƙata shiga group 200 ne kacal kuɗin karatu,ki tura ta wannan account ɗin 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte airtel ko Moov ta 200f MRS SADAUKI 💫✍️ [25/07 à 11:46] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆 🪆 🪆🪆🪆🪆 ```MRS SADAUKI```💫✍🏻 FCWA ☀️ *Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822. *Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂 *Page 19_20* Habiba ta kutsa kai cikin ɗakin,cak ta tsaya ta na faman zaro ido ta na kallon Kameel da budurwarsa da ke ta sha'aninsu kan kujera.Sam ba su ma san ta shigo ba,suratai da kuma kalaman soyayya kawai suke amayarwa. Ido na zubar da hawaye Habiba ta fito daga ɗakin.A sanyaye take saukowa daga step ɗin,direct ɗakin Mardeeya ta shiga ta samu bakin bed ta zauna.Tun da take ba ta taɓa ganin wannan lamari ba,ko a TV iya kiss ne kawai ta saba gani yau kam da idonta ba a mafarki ba sai ga shi ta yi kallon yadda ake tarayya. Ta wani zabura ta na mai rumtse ido da sauri,bisanin ta buɗe ta kalli Mardeeya wace ba ta tsaya da yarfa mata ruwan yatsunta ba. “Tunanin mene ne ki ke haka? ” “Babu komai” ta bata amsa ta na mai tashi ta shiga wankan ita ma . Bayan ta fito Mardeeya ta yi mata simple make-up ta zaɓo mata abaya irin na Makka . “Waooo! Amma dai ba aro ki ka ban ba ko?” “Kin ji ki da wani zance,to kyauta na baki” cewar Mardeeya. Cike da murna Habiba ta saka rigar,ta kuwa karɓeta tsaf ta yi mata kyau.Mardeeya kuwa cikin wani mahaukacin Sahari ta shirya kai kace ba'indiya don ma dai fatarta na baƙa. Falo suka fita,tuni mai aiki ta gyara ɓangaren da za a sauke baƙon.Selfie kawai suke da wayar Mardeeya,su na nan zaune har sai da ya zo. A tare suka fita suka tarbo shi,suka yi masa iso ciki.Tamkar ƙaramar yarinya haka Mardeeya ke zuba masa shagwaɓa shi kuma ya na biye mata. Bayan ta gabatar masa da Habiba ne sannan suka fara taɓa kalolin abincin da suka yi. Nader sai santi yake ya na yaba abinci, Mardeeya duk da ba wata uwar ta tsinana wajen girkin ba amma ta ji daɗi sosai. “Bari na tashi na baku wuri don ku zanta da kyau” cewar Habiba ta na mai miƙewa. Mardeeya ta ce “fara yi ma hoto ni da Habiby kafin ki tafi” Ta karɓi wayar ta fara yi masu hotuna bisanin ta je can ɗakin Mardeeya.Wayarta ta ɗauka ta kira Haidar ,kamar yadda ta ɗauki darasin shagwaɓa haka ita ma ta fara yi masa ai kuwa ta samu karɓuwa duk ta rikita Haidar. “In ki na yin shagwaɓa sai ki sa na zauce” Haidar ya faɗa. Habiba ta ɗan yi wani far da ido ta maƙale murya ta ce “ai na fi son haka Babyna,ko kai ba ka so ne?” “Ina so mana sosai ,ji nake kamar ace ki na kusa da ni” “Ko zuwa za ka yi ne?” “Kin gama komai ne?” “A'a sai zuwa an jima” “To ki bari har ki gama my dear ” Hira soyayya suka ci gaba da yi,ba su yanke kiran ba sai da Mardeeya ta zo nemanta. Har bakin motarsa suka yi masa rakiya,mai gadi ya shigar da tsarabar da ya kawo mata bayan kuɗi da ya basu dukan su biyun. Habiba har tuntuɓe take wajen shiga falon don duba kayan.Cike da mamaki take buɗe duk ledodin ta na mai tambayar Mardeeya “na ce halan kuɗi gare shi irin sosai ɗin nan? Dubi kayan nan fa sun fi 500k/mill kamar dai za a haɗa lefe” Mardeeya ta saki wani murmushi ta ce “Yanzu dai ki duba wanda suka yi miki sai ki zaɓi ko kala goma.Kaina na yi min ciwo zan shiga daga ciki” “Ki turo min hotunan da mu ka yi kafin ki kwanta” “Na gaji sosai ki duba a status duk na saka su” “Har da na Balaraben?” ba ta bata amsa ba ta shige cike. Habiba ta shiga zaɓar wanda za ta ɗauka,kamar daga sama ta ji tsuki.Ta na ɗago kai ta yi arba da Kameel da budurwarsa da dukkan alamu kuma ita macen ce ta ja tsukin. Kamar gumki haka ta tsaya ta na kallonsu,har suka fice.Hawayen takaici ta goge,ƙunci da ke naƙarƙasasar ruhinta bai hanata zaɓar kayan ba.Sauran kuma masu aiki suka shigar da su can ɗakin Mardeeya wacce tuni bacci ya ɗauke ta. Habiba ta kira Haidar ya zo ya ɗauke ta ,su na tafe su na hira har suka kawo ƙofar gidansu.Haidar ya kama hannunta ya ce “yanzu Baby sai yaushe?” “Gobe mana,ko ba za ka zo makarantar ba?” “Zan zo mana,amma kafin nan ai za mu yi waya ” “Ba ka gajiya da waya” “Son ki ne silar haka” “Hum!” “Allah kuwa Baby ji nake kamar kar mu rabu” Yadda ya yi furucin ya saka Habiba saurin kallon shi. Haidar ya nitsa idonsa da kyau cikin nasa ya fara aika mata da wani mugun kallo mai kashe jiki.Hannunta da ke cikin nasa ya fara ɗan matsawa,Habiba ta wani jan ajiyar zuciya ta na haɗiye yawu muƙut! Sai kuma ta kawar da kanta. “Ko na ture iyayena su nema min auren ki?” Haidar ya furta kamar mai shirin kuka.Da mugun sauri ta juyo ta ce “Aure kuma? Duka yaushe ne mu ka haɗu da kai shi ne ka ke min maganar aure?” “Habiba shi muradin zuci babu ruwansa da jimawar masoya,kin san irin yadda son ki da sha'awar ki suke azabtar da ruhina?” Ta maimaitata kalmar ‘sha'awa’ a zuciya. Ba ta san lokacin da bakinta ya furta “mi ka ke nufi da sha'awa?” “Buƙatuwa mana,ina son kasancewa da ke na ji ki rungume cikin ƙirjina ina kissing ɗin ki” Zuciyar Habiba ce ta fara bugawa da mugun gudu,yayin da madubin idonta kuma yake hasko mata video Kameel da budurwarsa.Nan take jikinta ya ɗau rawa,da sauri ta fizge hannunta da ke cikin nasa ta tura ƙofa da niyyar fita Haidar ya tsayar da ita ta hanyar ƙara riƙota. “Gida zan shiga ban cikin nutsuwata,in an jima za mu yi waya” ta furta cikin rawar murya,ba tare da ya sake cewa komai ba ya barta ta fita.Sam ta manta da ledarta wacce ta zubo kaya,shi ma haka. Ta na shiga gida ta tarar da su Twins su ma sun dawo.Zahra na karatu yayin da Bintu ke yin hira ita da Halilu .Kamar zararra haka ta nufi ɗakinta wanda ita kaɗai ce mallakinsa,direct toilet ta shiga ta tsabtace jikinta. Kan bed ta kwanta ta na tunanin abubuwan da suka shuɗe a yau, murmushi kawai take saki a haka har bacci ya ɗauke ta . Bayan sallar magrib Haidar ya yi mata text akan ya na ƙofar gida ta fito ta karɓi ledarta.Kallabi kawai ta ɗora kan kanta ta fita,can nesa da gidan su ta tsinkayi motarsa inda ke da ƙarancin haske. Tun fitowar ta ya ƙureta da ido ya na kallon shap ɗin ta mai tafiya da hankali duk wani lafiyayen namiji,har ta ƙaraso.Daidai ɓangaren da yake zaune ta tsaya haɗi da bubuga glass ɗin.Haidar ya buɗe tare da ziro ƙafa ɗaya.“Ƴan mata adon gari” ya furta ya na mai kallonta,Habiba ta ce “ina ledar take ban so Baba ya zo bai gan ni ba” hannu yasa ya jawo ledar ya miƙa mata ta ce “sai da safe ko?” “ɗan duƙo ki ji” cewar Haidar Habiba sokuwa ta ɗan rage tsawo kawai sai jin bakinsa ta yi kan lips ɗinta. Kai ta girgiza ta bar gun da sauri shi kuma ya yi ta dariya. Ta na ƙoƙarin shiga ɗaki muryar Kawu ta daki kunnenta “uban waye wancan mai motar?” Gabanta ya bada ras! Ko kafin ta kai ga furta wata kalma Kawu ya zo gabanta ya sharara mata mari sannan ya nuna ta da yatsa ya ce “daga yau sai yau kar na sake ganin kin kawo min ƙato a gida.Ban shirya yi miki aure ba karatu za ki yi ki je can na baki aikin offishi,in kuma na sake ganinsa a ƙofar gidana za ki sha mamaki” Da gudu Habiba ta ƙarasa cikin ɗakinta ta na kuka,ba ta yi jinkirin sanar da Haidar furucin mahaifinta ba.Shawarar farko da ya bata shi ne ita sai ta rinƙa zuwa wajensa su na yin hira,abun ka da zuciyar da ta kamu da so sam ita ba ta ga illar yin haka ba. ƘAUYEN JOAL Mohan ne hakimce kan kujerarsa ta alfarma,bayan ya gama ganin mutanen da ke zuwa wurinsa da sunan ya yi masu aiki shi ne ya zauna ya na hutawa.Ƙatuwar wayarsa ce riƙe a hannunsa,saƙon mataimakin shi mai kula da duk wani fice dashigar kuɗi ya fara dubawa bisanin na sauran mutane.Har zai ajiye wayar sai kuma ya nufi ɓangaren status,na Mardeeya ya shiga.Murmushi ɗauke da fuskar shi yake kallon ƴar tasa wacce ke zaune ita da mijinta na gobe ,hotunan ya ci gaba da dubawa har ya faɗa kan na Habiba.Zoom ɗin hoton ya yi ya na ƙare wa duk wani lungu da saƙo na jikinta kallo,a ƙasan hoton an rubuta my Bestie. Mohan ya fiddo halshe ya wani lashi leɓensa na ƙasa kamar tsohon maye.Kusan shekaru biyar kenan da mutuwar matarsa,tun daga nan bai sake yin aure ba amma ganin Habiba ya saka jin kamar ya samu matar aure. Screenshot ya yi na hoton,bisanin ya fita daga WhatsApp ya kira Mardeeya. A shagwaɓe ta ɗauki kiran ta na mai cewa “Dad ka manta da ni ” “A'a ku na raina,in sha Allah zan shigo gobe.Na ga ashe Nader ya zo yau” “Wa ya faɗa ma? Cewa ya yi ko kai bai sanar ba ” “A status ɗin ki na gani.Har da hoton Bestie” Murmushi mai sauti ta yi sannan ta ce “Bestie Habiba ,ajinmu ɗaya a makaranta.Dad ka ga ƴar ƙauye ce ko ba ta dace na yi ƙawance da ita ba?” “A'a ko ɗaya,ai kun yi daidai kamar Twins.Wane ne mahaifinta?” “Dad na faɗa ma ƴar ƙauye ce ba su wani jima da dawowa birni ba.” “Ok ! Ina Kameel ?” “Ban ji ɗuriyarsa ba duk yau ƙila ya na can wajen dadiron shi” “Mardeeyyya!” ya kirata da wata irin murya . Kamar za ta yi kuka ta ce “saboda Allah Dad abin da Ya Kameel yake yi daidai ne? Gidanmu kamar wata club haka ƴan mata ke shige da fice,da zarar na yi magana kuma ka ga laifina.” “Ko ma dai mine ne ɗan uwan ki ,in ba ki rufa masa asiri ba wane ne zai rufa masa?” Ta turo baki kamar ya na ganinta ta ce “in ni aka yi ma abin da yake yi wa ƴaƴan mutane har kashe mutum zai iya! ” Dad ya murmusa ya ce “shi ɗin garkuwar ki ce! Ya ne kin ci abinci?” “Eh na ci sosai yau Habiba ce ta yi mana girki mai shegen daɗi ka san ƴan ƙauye sun fi kowa iya abinci gargajiya” “Ah haba? To gaskiya ni ma gobe a kira Bestie ta yi min girkin na ci na ji in ya yi daɗi sai na bayar da tukuici” Mardeeya ta shiga ƙyalƙyata dariya bisanin ta ce “Dad ai kuwa zan faɗa mata kawai ka shirya gift ɗin da za ka bayar,don Bestie maƙura ce wurin girki” Ido ya lumshe ya na jin sotayyar Habiba na daɗa hauhawa a birnin zuciyarsa. Washegari Kamar kullum direba ne ya kai su makaranta,su Twins ya fara ajiye wa sannan ya wuce da Habiba . A bakin ƙofar shiga makaranta ta ci karo da Haidar.Ta waro ido ta na kallonsa,“tun ɗazu ke nake jira,so nake na ga kyakkyawar fuskar ki kafin na je aiki” ya furta cikin taushin lafazi. Wani mayen daɗi ne ya rufe zuciyar Habiba,ta ce “na gode sosai masoyi” Ya ce “ki shiga kawai ni zan tafi ki kula da kan ki,ina son ki” bai bata damar da za ta mayar masa da martani ba ya yi saurin tafiyarsa ya shige motarsa. Habiba ta bi motar da kallo har sai da ta ɓace ma ganinta.Ta ja ajiyar zuciya bisanin ta shiga daga ciki.Saman bayan mota ta tsinkayi Mardeeya,da ƴar sassarfa ta ƙarasa. “Bestie albishirin ki? Jiya na baiwa Dad labarin girkin ki ya yaba sosai ya ce na gayyato ki yau ki yi masa shi ma ya na son ci” Mardeeya ta faɗa cike da zumuɗi . “Ki ce yau zan ga Dad?” “Eh! Mu na sauka daga makaranta sai mu wuce gidanmu ” “Da wane lokaci zai zo?” “Bai sanar da ni ba,amma dai ya ce girkin kawai yake son ci” Habiba ta saki murmushin jin daɗi,bisanin su shiga aji. Bayan sun sauka kamar yadda suka tsara haka suka wuce gidan su Mardeeya. Haɗaɗen girki Habiba ta shirya kala biyu,tuwon shinkafa da ɗanyar kuɓewa sai kuma tuwon macaroni da miyar ganye.Ɓangaren lemu kuwa mai aiki ce ta yi ,Habibar na kallonta don har yanzu ba ta ƙware ta wannan fannin ba. Mohan kuwa tun da wuri ya shigo cikin gari, office ya fara zuwa ya rage ayyuka sannan ya zo gida . Mardeeya ya tarar a daidai wurin da yake cin abinci kullum ta na gyara table ɗin.Da murna ta tarbe shi ta na mai cewa “yawwa Dad gwara da ka zo yanzu,Habiba na can na saka uniforme wai gida za ta kar ayi mata faɗa” “Ok zan shiga wanka,in ta fito ki ce ta tsaya sai mu gaisa ” ya na gama faɗa ya yi sama. Mardeeya ta shiga ɗaki,ta kalli Habiba wacce ta mayar da uniforme ta tuntsire da dariya ta ce “wai duk tsoron kar a dake ki ne ya saka duk ki ka yi wani iri?” “Mu je ki kai ni don Allah ban son surutu?” “Dad fa ya zo” Gaban Habiba ya faɗi ɗaram! Haka kawai ta ji zuciyarta ta shiga wani yanayi. Mardeeya ta ci gaba da cewa “mu je in ku ka gaisa sai na kai ki gida” Jiki a sanyaye ta fito,kan kujera suka zauna su na jiran saukowarsa. Kamar minti goma haka,Dad ya fara saukowa har ƙarar sautin takunsa ake ji. Habiba ta ɗaga kai ta sauke su kan dattijon da tuni farin gashi ya fara yi masa sallama.Su na haɗa ido gudun zuciyarta ya kusan tsayawa,a haka ta daure. “Barka da fitowa Bestie ” Dad ya furta ya na yi mata wani kallon ƙasa-ƙasa mai cike da kwaɗayi,Habiba ta buɗe baki za ta yi magana kenan Kameel ya shigo...... *Masu karatu yanzu ne ƙaddarar Habiba za ta soma,na san kun fahimci labarin na tafiya ne daki-daki a sannu a hankali ko wacce Star ta littafin zan zayyano irin ƙalubalen da ta fuskanta.Mun fara da Bintu mai namijin dare,sannan Habiba wacce a halin yanzu ta faɗa son Kameel yayin da kuma shi Mohan ke sonta shin ya za ta kaya?* Sai ku biyo NI cikin book 2 wanda a cikinsa ne duk lamurran za su faru,ita ZAHRA babbar Star ɗin ko ɓangaren ta ban ɗauko ba🤩 Masu buƙatar shiga PAID GROUP za su biya 200 kacal ta wannan account ɗin 3184721842 Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte airtel ko Moov ta 200f *NB:* daga lokacin da na kammala book ya zama complete 500 ne farashinsa.