[11/10/2019, 1‪+234 803 588 3279‬: *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy This Novel Is Free. But After This Free Book, Comes Payed one. 1⃣ “Bana son na yi aure a gidan da za'a saka min gadon dubu ɗari biyu da hansin su riƙa girmamani suna ganin girman da ganin mahaifina yana da rufin asiri, na fi son na yi aure gidan da za'a saka min gadon miliyan uku su dinga ganin mahaifina talaka ne suna raina min wayo. Ma'ana dai har yanzu ina kan bakana na auren mai kuɗi fiye da talaka!” Na yi dariya ina sauraren zance ko burin Jidda da ta saba nanata min a duk lokacin da muke zancen aure da ita. “Ƙawata ba za ki taɓa ganewa ba, kin fiye maida zancena shirme Wallahi Nawwara rayuwar nan ɗa muke sam bata dace da mu ba” Dariya na sake yi a karo na biyu kana na dube ta irin duban na nake mata a duk lokacin da nake son ta ɗauki zance na muhimmancin. “Kina da yawan buri Jidda kamar yadda nima nake da shi, sai dai duk da haka na ki be kai nawa ba, gwargwadon rufin asiri Jidda kuna da shi, amman kina tsawwalawa rayuwarki akan son aure mai kuɗi, ba ko wane kuɗi ba ne na halak, ba ko wane mai kuɗi ba ne bane mutumen arziki, da da yawanzu basa darajanta talaka basa ganin girman iyayen matansu, basa kunyar taka kowa saboda suna ganin suna da kuɗi. Wasu masu kuɗin maneman mata ne Jidda, ke da kike matarsu sai su wulaƙantaki musamman idan suka sa ke ɗin ba kowa bace, nafi sha'awar auren takala ɗan'uwana mai ilmi da ganin ƙimata, mutumen da zai taimake ni na gyara lahira ta, kuma na inganta rayuwar yaro na, ya mutunta iyayena ko da bayan raina, ni iya wannan ya wadatar da ni matuƙar yaƙar yana da halin da zai iya ciyar da ni” Jidda ta dafani a lokacin da ta lura da hawayen da ya sauko daga idona ba tare da sani ba har sai da ta yi min magana. “Share hawayenki Nawwara, nasan abunda kike ji, amman rayuwar nan da muke ciki ne bata da daɗi, ka tashi cikin talauci ka girma a haka kai ma kana son sauyin rayuwa, kana son ka taimaki iyayenka, karatu nan ma fa Nawwara ba zai yiyu ba idan babu kuɗi, idan baka da kuɗi kai ba kowa ba ne, yadda aka ga dama haka ake takaka, babu mai son takala sai Allah” Na yi murmushi ita kuma ta amsa kiran da Mahaifiyarta take mata ta tashi. Na san yadda ƙawata take ji haƙiƙa rayuwar talauci babu daɗi, sai dai ni har yanzu rayuwar masu kuɗi bata burgeni saboda nasan yadda take, ba ko wace ƴar takala ce ke auren mai kuɗi ta jidaɗin rayuwaba, ko da kuwa ya aje mata banki ne a cikin ɗakinta. “Kin gani ko kullum baƙin tuwon dawa sai na masara babu wani sauyi, ni Wallahi rayuwar nan ta isheni, ni ina tausayin rayuwar yarana idan nayi aure zasu tashi suna cin tuwon dawa duk suyi baƙi, ke Wallahi Nawwara da kwana ɗari da talaka ƙara kwana ɗaya da mai kuɗi” Jidda ce take wannan maganar, yayinda take dire kwanon samira mai ɗauke da ƙatowar mulmular tuwon dawa da miyar kuka, agabana. ‘Allah sarki rayuwa ku har kun samu tuwon dawa’ Na faɗa a raina, a fili kuma sai na ce. “Aifa sai ki yi mitarki kuma ki ci tuwonki dan ni dai a ƙoshe na ke” Jidda ta wara ido tana min kallonta na iskanci wanda ta saba min a duk lokacin da aljannun rashin mutunci suka hau kanta. “Maman Nura, Maman Nura yi sauri ki zo” Nayi saurin kai hannu ina rufe mata baki jin tana kiran mahaifiyarta, nasan wata ƙulalliya zata ƙulla min. “Jid” Ban yi furucin ba sai ga Maman Nura a cikin ɗakin wato mahaifiyar Jidda. “Maman Nura tace gida zata je da shi” Jidda ta faɗa sai Maman Nura ta ce “To bari a ƙara mata” Da sauri na ce. “Wallahi ƙarya take min Mama, ban ce ba” Juyowa ta yi ta watsa min wata uwar harara kamar zata zo ta fanɗareni da mari, kana ta nuna ni da yatsanta. “Kin gani Nawwara wannan halin naki yana ɓata min rai, kina rage ƙima idona, ko abu kika tarar a gidan nan ba zaki ɗauka ki kai gida ba, ni da Mamanki ba ɗaya ba ne ko? Allah wata rana sai na ƙwaɗa miki mari idan kina min irin wannan iskanci, fitsarriya” Ta juya a fusace ta fice. Ni ko na kaiwa Jidda duka. “Kin haɗa ni da ita kin jidaɗi” “Ai nasan idan ba haka na yi miki ba, ba za ki co shi ba, marar mutunci, ni idan naga abu a gidanku tambaya nake ba ɗauka nakr na tsire ba” Na girgiza kai ganin yadda take magana da tsire baki. “Allah ya shiryaki Jidda” “Amin Wallahi, idan Allah be shirya ni ba ai na shiga tara bama uku ba, Jidda ai sai Nawwara” Bayan Maman Nura ta ƙaro min tuwon na taso Jidda ta rakoni ƙofar gida, a lokacin ana kiran sallah magariba. A bakin ƙofar gidansu ta karɓe tuwon. “Kawo zan bawa Nura ya kai miki, kinga su idi can ƴan sa ido, ko Sallah ba zasu tashi su yi ba” Ta taimaka min matuƙa, domin nima kaina ina jin kunyar fitowa da kwano a wani gida saboda ƴan sa'idon unguwa masu zaman kashe wando, zaman ƙirga atamfarki da kuma inda zaki je ki dawo. Sallama nayi mata tare da sai da safe sannan na kama hanya, bayan nayi nisa sai na hango Nura tare ɗauke da kwanon tuwon, sauri na ƙara dan bana son ya cin ma, nasan halin Nura zai iya cin min a hanya ya ce karɓi tuwonki. Lokacin da na shiga gida har sai da na ɗan tsaya a bakin ƙofa jiransa, tuƙuna ya ƙaraso na karɓi tuwon yana mita ya juya ya koma, ni kuma na shiga gida ina doka sallama. “Amin wa'alaikissalam Nawwara” Ya faɗa yana aje butar da yayi alwala, sannan ya ɗauki tsohon rediyonsa da ke aje ya miƙa min. “Shiga da wannan ɗaki” “Tau Baba, Allah ya tsare” “Amin, Amin” Ya faɗa yana kallon kwanon tuwon da ke hannuna, kamin yasa kai ya fice. A ɗaki na samu Inna ita da Habiba da Sakina, da mai sunan mama, wato Jamila da muke kira da Ummi. “Wai Allah na” Na faɗa ina ƙoƙarin zama kusa da Inna. “Nawwara kin dawo?” “Eh ga tuwon dawa Maman Nura ta haɗo ni da shi” “Tau Allah ya saka mata da alheri, zuba ki ci tun safe rabonki da abinci Nawwara” Na tada kai na kalli Inna. “Ai ni matuƙar zaku ci, ko ban cin ba bana jin komai, amman idan na ci ku kuna jin yunwa hankalina ba zai kwanta ba, Habiba zuba ma Baba da Inna sai ku cinye sauran” Inna ta ce “Sai fa kin ci, ai ƙara su ma ɗazu Babanku ya samo naira hansi na basu suka siyo garin kwaki suka saka gishiri suka ci” “Habiba zuba min kaɗan, ina Noor wai?” Na tambaya ganin baya cikin ɗakin. “Na aike shi ya samomin batir gurin Hajara wai mu samu na haskawa a fitila anjima” Cewar Inna, ni kuma na amsa da “Okay” Tare da unƙurin tashi na cire hijab domin alwala. Ko kamin na yi alwala na gama, har sun cinye tuwon abun ka da masu jin yunwa. Bayan na gama Sallah Magariba Habiba ta miƙo min ɗan tuwo can laƙe ga kwano. “Gashi nan ke da Noor” Karɓa nayi na aje a gabana. Sai ga Baba ya shigo yana faɗin. “Bari naje gidan ciyaman na jirashi, ko Allah zai na samu wani abu, sai mu karya da safe” Wani abu naji ya zo ya tsaya min a zuciya, wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da Babanmu zai je yawon maula. Ina jin lokacin da Inna ta ce “Allah ya tsare” Habiba kuma ta ce “Baba ga tuwon dawa” “Ina aka samo tuwo?” “Nawwara ce ta samo gidansu Maman Nura” “Ku cinye, sai na dawo” “Allah ya bada sa'a” Da Amin ya amsa, sannan ya fice. Ni ko na aje carɓin da ke hannuna, na miƙe tsaye ina amsa sallamar Noor. “Momy a ci abinci gidan Maman Hajara, tace na faɗawa Mama Habiba ta zo ta ɗauki tuwo, Momy har da kifi a miyarsu” Duk dariya muka sa masa, daman Noor be iya cin daɗi ba, komai ya ci sai ya bada labari. Yasa hannunsa aljihu ya ciro batir ɗin ya miƙawa Inna, sai ya sake saka ɗayan hannunsa a aljihu ya fiddo kifi ɗan tsito ya miƙa min. “Momy ungo na rage miki, ci ki ji” Kai na girgiza masa. “Cinye abun ka nima zan je can na ci” “Yarinya ya ƙare ai” “Ni ce yarinya?” Na tambaya ina nuna kai na, sai ya sa dariya yana tsalle. Haka rayuwarsa take ba duk abu ne yake damunsa ba, ko da bai fahimcin inda duniyar ta dosa ba ne oho. ______________________________________ As i said bayan ZAGON K'ASA zan yi RAI BIYU kuma free. 😍 How do you like my surprise 🤔 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣ Bayan mun yi sallah isha'i Inna take labarta min irin dukan da ka yi ma Noor a makarantar islamiya yau saboda rashin biyan kuɗin sati biyar. “Momy duba nan bulala ya kwanta min” Ya faɗa yana nuna min hannunsa fafaren idanuwansa na cika da hawaye. Abun ka da farin mutun bulalar ta masa ja sosai kwanci jini ya kwanta a hannunsa. Hannunsa na kama ina murmushi. “Ai lada kuke samu idan aka dake ku” “Ni ba zan sake zuwa ba, Malam Usman azzalumi ne” Ya faɗa yana taɓe pink lips ɗinsa. Sai na yi saurin rufe masa baki. “Ba a zagin malami Noor kar na sake ji” Habiba ta bige min hannu. “Wallahi bar shi ya faɗa in ba zalumci ba miye na dukan ƙaramin yaro kamar Noor, ai dai yasan babu kuɗin ne da yanzu an bada, ji yadda ya bugar masa fatar hannu har ta yi ja, yaro ba a saba dukansa gida ba haka kawai wani ƙato zai dake shi” Taja hannunsa suka fita waje ta shimfiɗa tsohuwar tabarma suka zauna, ni kan murmushi ne nawa, masifa ai Habiba ta iya ta har ta gaji musamman akan Noor duk wanda ya taɓa zai ga babu kyau. Baba be shigo gida ba sai goma har da kwata a lokacin har Inna ta soma bachi, balle kuma Jamila da Sakina ba mota, daman su da anyi sallah isha'i suke bachi. Ni da Habiba ne kawai ba mu yi bachi ba, sai Noor da ke faman ƙirga taurariya, ina daga cikin ɗaki Baba yayi sallama, Habiba da Noor da ke waje suka amsa masa. Motsin rufe ƙofar gida da Baba ke ƙoƙarin ne ya tashi Inna daga ɗan guntun bachi da ta fara. “Malam ka dawo?” Ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗankwalinta, shi kuma ya amsa mata fuskarsa da damuwa sosai. “Na dawo amman ban samo komai ba” “Ciyaman ɗin be dawo ba ne?” Inna ta sake tambaya. “Ya dawo amman be fito ba kuma be ce mu shigo ba, sai kawai aka rufe gate” Kai na girgira kana ka ce “Ai ba zaku samu ba, zai ce kullum kuna zuwa kuma masa maula a ƙofar gida, wata rana wulaƙancin ma sai ya fi haka, ni Wallahi Baba da ma zaka ji shawarata da ka daina zuwa gidan kowa roƙo yana zubar da mutunci da ƙimar mutum take” “Zuwan ne ai ya zame mana dole tun ba babu wata sana'ar yi mai ƙarfi, tsaran icce ne ba kullum ake samu ba, jarin kuma mun cinye rayuwa ta yi tsada yanzu, dole sai mun haɗa da haka indai kana gida babu wanda zai ɗauko ya aiko maka. Ga ɗari na ranto gurin Malam Sahabi, da safe a karya” Ya ciro naira ɗari a aljihunsa ya miƙawa Inna. Baba yana da gaskiya ba ko wane mai kuɗi bane mai zuciyar tausayi da taimako mafi yawansu kansu suka sani. Unƙurawa na yi na tashi, na nufi ɗakinmu da muke kwana a ciki. Ganin haka yasa Habiba ta shigo da Noor sai ta koma ɗakinsu Inna ta taso da su Jamila da Sakina. WASHE GARI... Bayan na yi sallah asuba na zauna ina askar na safe da na saba yi a duk lokacin da na gama Sallah. Misalin ƙarfe bakwai da rabi Jamila taje ta siyo mana koko na naira ɗari, aka rarraba haka nan aka sha gayarsa ba tare da suga ba muka sha. A lokacin ne Sakina ta yi ma Noor shirin makaranta, ta kama hannunsa shi da Jamila tana cewa sai sun dawo. Har ya tafi sai ya sance hannunsa daga na Sakina yazo a guje yayi min kiss a goshi, sannan yayi min bye-bye yana dariya suka fice. Ban san inda ya samo wannan dabi'ar ba, ni dai nasan ban taɓa masa sumba idan zai je makaranta ba, ban kuma saba masa idan zai fita ba, amman shi yana yawan min a duk lokacin da zaije Makaranta. Sallama muka ji ni da Habiba dake saka wandon makaranta. “Daga ji Malam Hamisu ne, yabi ya takura mana akan kuɗin haya da be taka kara ya karya ba, baƙin Azzalumin banza mugu mtsss” Ta ƙarasa tana jan tsaki. Na tada kai na kalleta. “Kowa a gurin ki Azzalumi Habiba, ina laifin mutumen yana ɗaga mana ƙafa dai-dai gwargwado ke kin san da wani gurin ne da yanzu an koremu, amman kowa ki riƙa kiransa da Azzalumin hakan be dace ba sam” Kamar jira take sai tayi cikina da faɗa. “Kowa Azzalumine Nawwara na faɗa, waya kula da halin da muke ciki har ya damu kowa dai kansa ya sani, na faɗa kowa na duniyar nan Azzalumi ne” Tana kaiwa nan ta saka farin hijabinta ta ɗauki jakarta ta fice ina mata Allah ya shirya. Bayan ta fita na tashi ya leƙa ɗakin Inna dan yi mata ina kwana. “Lafiya ƙalau Nawwara Allah yasa dai kin sha kokon dan nasan halin fa” “Na sha Inna, har sai da na raga” Na faɗa ina dariya, sai ga Baba ya shigo. “Baba ina kwana?” “Lafiya ƙalau Nawwara an tashi lafiya” “Lafiya ƙalau, ya lafiyar jikin” “Alhamdullilah, Hamisu ne ya zo na ce yayi haƙuri har zuwa satin sama, sai dai ya ce daga wannan ba zai ƙara ɗaga mana ƙafa ba” Ya faɗa yana zama kusa da tsohon rediyonsa. “Allah gamu gareka, ka iya mana” Cewar Inna tana sauke ajiyar zuciya. Ni kuma na miƙe tsaye ina faɗin “Bari naje na shirya na koma can na gani dan jiya sun ce min na dawo da safe” Baba ya ce. “Sun ce zaki samu aikin ne?” “Inshallah zan samu, saboda gurin Babansu naje kuma yana da mutuncin sosai” “Wai aikin me ne?” Inna ta tambaya tana daga kwance. “Sharar ti'ti ne kuma kullum ake biya” Ta yi saurin tashi zaune. “Wane irin sharar ti-ti kuma Nawwara? Wannan sam ba mutuncin ki ba ne, Wallahi zaginki za a fara daman sun saba” “Dukan masu zaginmu Inna babu wanda ya taɓa ɗauko Naira ɗari ya bamu ya ce mu siye wani abu, kuma na muku alƙawarin kare mutuncinna, Hijab zan saka idan har na samu aikin nan” “Ba irin wannan aikin ya dace da ke ba Nawwara, ni nafi kowa dacewa da na yi shi” “Baba ka san kana da Asma ba zai yiyu ka yi irin wannan aikin ba, kuma na maka alƙawari da zarar ka samu wani aikin zan daina wannan” Ya girgiza min. “Ba zaki yi ba Nawwara, sai dai ba zan hana ki bincikar wani aikin na daban ba, shi ma kuma kamin na samu wani abun yi” Na ɗaga masa kai cike da ladabi. “Tau Baba zan koma Candy Restaurant ko Allah zai sa a dace, amman Baba dan Allah ban da turin baron nan da ka taɓa yi kasan yadda zuciyarka yake idan ka ɗauki abu mai nauyi, ni Wallahi bana son kana dakon nan” Na faɗa kamar na yi kuka, dan har ga Allah nafi tsanar dako fiye da komai a duniyar nan. Baba yayi murmushi irin nasu na manya sannan ya ce “Nawwara kenan, ni dai ina jan hankalinki kan tsare mutuncinki da kuma na mu gaba ɗaya, Nawwara ke rai biyu ce mai maka da rai dubu a gurin mu, dukan abunda zai zubar da mutuncin ɗan ki da ni Mahaifinki karki kuskura aikata shi, ki riƙa tuna ke uwace, kuma ɗiyar wani wacce idan kika yi abun assha za a zagi Ubanki, ɗan ki kuma ayi masa jawabi, ni dai na san irin tarbiyar da na baku Wallahi ko cikin maza dubu zaki shiga matuƙar baki watsar da tarbiyar gidan nan ba, nasan zaki fito lafiya. Ni da kan ɗan ki rai biyu ne a gareki Nawwara, abu kaɗan kika aikata zai iya saka zuciyata ta buga, ɗan kuma zai tsanake ni ya riƙa nadamar da kika kasance uwarsa, saboda haka ki riƙe mutuncin ki, Allah ya muku albarka” Ni da Inna muka amsa da Amin. Haka yake min a duk lokacin da zan fita neman aiki ko wani abu makamancin wannan, waɗannan nasihohin suna tasiri a gareni matuƙa, sukan katangeni daga duk wani tayi da wasu suke min na siyar da mutuncina, ko kuma musanya mutuncina da takarɗun aiki. Comment on every single line. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣      Bayan na baro ɗakin Inna na ɗibi ruwa a shiga ban ɗaki na yi wanka. Atamfata ta sallar bara na ɗauko na saka, akwai da son saka gyale duk da kasancewar Baba baya son haka, daman ba ko waɗanne uwane suke son ƴarsu ta saka gyale ba, sai dai nawa gyalen ba irin na barbarɗaɗɗin ƴan mata nan ne ba, me zai kai ni saka ƙaramin gyale bayan ina da ɗa kuma ba budurwa ba ce ni, duk da yake wani lokacin Jidda da Habiba har da mutanen waje kan faɗa min babu wanda zai kalleni ya ce ni bazawara ce har sai idan ni na faɗa, wani lokacin ko da na faɗa ba a yarda har sai idan waɗanda suka san ni ne.  Ina da kyau jiki dai-dai gwargwado wannan yasa mutane basa yarda idan har na faɗa cewar ni Bazawara ce har da ɗa, wannan baya rasa nasaba da auren wuri da aka min, a lokacin da nake ganin kamar ban isa auren ba, auren da ya gurɓata min rayuwa ya canja ƙaddarata daga mai kyau zuwa mummuna. Atamfata miyan goro ce mai ratsin ja, hakan yasa na saka jan gyale saboda atamfar ta ƙara fita, talkamin Habiba na ɗauka na saka masu launin ja. Fes na fito sam baza kalleni kace ina da wata damuwa a wannan lokacin ba, idan ba ka birkice atamfata gaka ta roba bace sai ka ɗauka ni ƴar wani shegen mai kuɗi ce, ba laifi ni kaina ina sarawa kaina indai babin kwaliyana ne na iƴa fito kamar matar minister. “Inna zan tafi” Na faɗa ina tsaye daga jikin ƙofa, kai na jingine da ƙofar ina kallon Baba da ke unƙurin tashi. “Tau Allah ya kiyaye” Inna ta faɗa, Baba kuma sai ya ce “Ni ma bari na shiga kasuwa na ga abunda Allah zai yi” Salamar Maniru muka ji wato almajirin Hajiya Murja, maƙociyarmu masu babban gida, matar babban soja wacce bata taimako sai idan da dalili. Ni da Inna muka haɗa baki gurin amsa masa, Baban kan ya amsa masa da. “Bata nan taje makaranta” Domin yasan Jamila take nema, takan aiko kiranta a duk lokacin da wani aiki ya sha gabanta, domin kawai ta taya ta aikin sai ta sammata wani abu daga abincin rana ko dare da aka yi a gidan.   Bayan Maniru ya fita Baba ya haɗe fuskarsa saboda mu ɗauki zancensa da muhimmanci, ya saba mana a duk lokacin da yake hanin mu kan aikata wani abu ko kuma ba mu umarni. “Bana son zuwan da Jamila take a gidan Manjo Faruku, kowa ya tsaya inda Allah ya aje shi” “Ni kaima bana son zuwanta a gidan domin yaron gidan nan ba shi da tarbiya, sannan yunwa babu abunda bata sawa musamman ga waɗannan da suke yara” Na faɗa cike da jin zafin tuna irin satar da ta taɓa ɗorawa Sakina a kwanakin baya. Inna dai bata ce komai ba bayan ajiyar zuciya da ta sauke. “Na tafi nidai ayi min addu'ah” “Tau Allah ya bada sa'a karki daɗe dai, kuma ki kula.da irin mutanen da zaki yi hulɗa da su” Cewar Inna ni kuma na amsa da tau na kama hanya ina addu'ar fita daga gida wato.  _Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah._ _بِسْمِ اللَّهِ تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللَّهِ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ_ Babu ko ƙwandala a hannuna ƙasa na kama hanya duk kuwa da kasancewar unguwar akwai ɗan nisa da ta mu. A bakin ti-ti na haɗu da Bilal wato abokina ko kuma na ce mutumen da muke mutunci da shi sosai har mutane suke raɗin-raɗin wai akwai soyayya a tsakanin mu. “Nawancy” “Bilal ya gida?” “Lafiya ƙalau Wallahi Ina zaki je haka?” Bana son faɗa masa ainahin inda zanje, ba kasafai nake son mutane su san ina zuwa aiki ba nafi son aji na samu aikin kawai, musamman Bilal da yake yawan nuna min baya son neman aikin da na ke. “Nan zan je gawon nama gidansu wata ƙawata Zinatu” Ya matso da mashin ɗinsa Honda “Hau na sauke ki” “A'a na gode” Na faɗa ba dan bana son hawan ba sai dai bana son yasan gurin da zanje. “Dan Allah ki hau mana, t-t ne balle ki ce kina jin kunya an mun fito cikin unguwar” Bana da wata dabara ta da wuce na hau ɗin, babu tantanma idan har na zaɓi zuwa a ƙafa zan wahala sosai.    Abun ka da mai nema sai kawai na gyara zane na na haye mashin kamar na yayana ko kuma na ce na Ubana. Bilal ba baƙona ba ne hakan yasa na sake da shi sosai muna fira har muka isa bakin ƙofar gidansu Zinatu. Na sauka ina masa godiya. “Am Nawancy na manta ban labarta miki wani abu ba, mun samu sabon shugaba a kamfaninmu kuma ya buƙaci sauye-sauye saboda yana da zafi sosai, kuma duk ya zubar da ma'aikatan gurin ya ce sabbi za a ɗauka, sai dai be faɗi rana ba, so ina fatar idan za a ɗauki wasu zaki yi applying” “Kai ka ce kai ma kun tsallake rijiya da baya” “Wallahi mun tsallake kan, domin mutumen akwai zafi sosai, gashi baya ganin kowa da mutuncin, ko dan yana kamfanin Mahaifinsa ban sani ba” “Ai fa ka ji to mu da ba wani zurfin ilmi mukayi an ya zai ɗauke mu kuwa, Bilal kafa san SSCE ne kawai da ni” “Abun sa'a ne Nawancy zaki iya shiga kuma ki yi sa'ar samu, ai kisan mataki mataki ne” “Naga Babban kamfani ne Bilal” Yayi wani abu da fuska yana matse hancin, irin yadda yake min a duk lokacin da zai zolayeni. “Trust me girl zaki samu babu tantama” Na yi murmushin da ya fitar da dimple ɗina, ina ƙara jan gyalena dan rufe jikina. “Ni zan wuce aiki kar na yi latti ya kore, dan ya faɗa mana idan ka ƙara minti ɗaya zai koreka daga kamfanin” “Tau Allah ya kiyaye na gode” Hannunsa ya ɗaga min. “Ina gaida abokina Noor” Kai na ɗaga masa as respond na juya kamar zan shiga gidansu Zinatu, ina hango ya kama hanya, na juyo dan har ga Allah ba gidansu Zinatu zanje ba na san ma by this time bata gida, ko ma tana nan mi zanje na yi a gidansu yarinyar da bata ƙaunar zuwa gidanmu.    Miƙe ti-tin gawon nama na yi har na ɓullo ta gurin gidan Alu, wato tsohon gonnan, na  miƙe na tsallaka babban titi na doshi Candy Restaurant.    Restaurant ne mai kyau da tsari ga tsafta, ba laifi ma'aikatan gurin suna na'am-na'am da mutane tun a farkon zuwana na lura da hakan. Kai tsaye na nufi gurin wanda na ke zaton babbansu mai sanye da riga orange an rubuta mata Candy Restaurant da fafaren harufa. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikissalam” “Sannu ko ka gane ni?” “Gaskiya ban gane ki ba, abun da yawa” “Ni ce wacce na zo kwanakin baya ka ce min Khadeeja Candy bata nan” “Ayya Allah sarki, sai kuma kika ƙara rashin sa'a yau ma bata nan” “Dan Allah ko kasan yadda za'ayi ma sameta?” “Gaskiya bata garin nan tana Gusau kusan yanzu a can take zama, ko tana garin ma da wahala ta shigo nan” “Dan Allah ko zaka taimaka min da numberta?” “Gaskiya ba zan iya baki numberta ta saboda matsala ta tsaro, amman ke zaki iya barin Number idan ta shigo gari sai na sanar da ke” A take na rubuta masa Number Jidda domin bana da waya, kuma Baba ko Inna babu mai waya a cikinsu. “Idan ka kira ka ce Nawwara kake nema” “Tau Inshallah” “Na gode” “Yauwa a sauka lafiya” Jiki ba ƙwari na juya na fito. Har ga Allah ban jidaɗin rashin ta tararda mai restaurant ɗin ba, ga kuma uwar hanyar da zan miƙe duk da yaƙe rana be yi sosai ba, sai dai ina jin kamar zan wahalar da kaina tafiya a ƙafa har zuwa unguwarmu. “Allah ƙa zame min gata” Na furta a fili ina busar da iskar bakina. Dabarar na je gidansu Zinatu ne ya faɗo min a rai duk da ban yi niyar hakan ba.    Haka na kama hanya na miƙe na koma ta inda na fito har na isa ƙofar gidansu Zinatu. Har na kai hannu zan buga ƙofar gate ɗin sai mai gaɗinsu ya wangale gate ɗin gaba ɗaya daga can ciki. Zinatu hakince a motarta ta kunno kai da alama fita zata yi, har ta yi kamar zata wuce sai kuma ta tsaya ta sauke gilashin motarta tana kallona ta cikin baƙin gilashin da yake idonta. “Khadija Musa Kafinta” Ta kirani da sunan da nake amfani da shi a makaranta, nima kuma sai na kirata da nata. “Zinatu Alhasan Hamshaƙi” Ta yi wani shu'umin murmushi tana cire gilashin idonta. “Nawwara ashe ana ganinki ko dai hanya ce ta biyo da ke?” “A'a haka kawai yau na ce zan kawo miki ziyara” Ta yi ƙis a ƙasan maƙoshinta wato ƙwafa na ƙasan maƙoshi. “Aiko kin kyauta gashi kuma zan fita, ki shigo na saukeki gida kawai” Na ji wani sanyi a raina daman abunda nake nema kenan. “Okay” Na faɗa sannan na buɗe motar na shiga. Jefi-jefi muke firar makarantarmu wato Nana Girl's Secondary School, kamin na ɗauko mata zancen masters da naji ance ta fara yi. “Wallahi ina nan ina yi yanzu haka kuma na samu aiki a wani babban kamfani this monday zan fara” “Mashallah, Allah ya taimaka” “Amin ai ke kin ƙi karatu ko?” “Uhmm” Na yi murmushi kawai ina danne abunda ke raina, yawancin mutane sukan faɗa min haka musamman abokaina wai na ƙi karatu bayan kuma karatun ne ya ƙi ni tun da komau sai da kuɗi, hawan napep zuwa da dawowa ma ai sai da kuɗi. Har ta sauke ni ƙofar gidanmu bata kalma bata sake fita daga bakinta, nima kuma ban sake ce mata wani abun ba. “Na gaida Inna” Ta faɗa lokacin da ta ga na buɗe mota zan fita. “Inna zata ji na gode” “Okay” A bakin ƙofar gidanmu na tsaya ina kallonta cike da sha'awar rayuwarta, duk mutune da yayi karatu burgeni yake, balle ita da ta fara cin amfanin karatun a yanzu. Sai da na daina hangota kan kwanar gunguwarmu mai kwatannin sannan na shiga gida. Inna na samu a tsakar gida tana shara, gyale na kawai na yaye ya karɓi tsintsinyar dake hannunta na cigaba da shara. “Allah yasa dai an yi sa'a” “Wallahi ba'ayi ba Inna wacce na je nema bata nan, amman na bada number wayata aje mata” “Allah yasa mu da ce,  amman dai daga yau karki saki zuwa wani gurin ki haƙura idan ” “Amin, inshallah nima zan haƙura indai da rabon na samu zan samu” “Allah ya miƙi albarka” “Amin” Ta shinfiɗa tabarma ta zauna ni kuma na cigaba da sharar ina labarta mata cewar Zinatu ce ta kawo ni gida. Bayan na gam sharar na tattara na kwashe, muka ji ana sallama a ƙofar gida. Inna ce ta amsa ni kuma na nufi ƙofar dan duba ko wanene. Ganin mutun sanye da kakin ƴan sanda yasa gabana faɗuwa sosai. “Nan ne gidan Musa Kafinta?” “Eh Nan ne” Na amsa murya na rawa. “Musa Kafinta yana police station na guiwa locos, ana son a sanar da iyalansa ne kuma baya da waya shiyasa na zo” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miya faru?” “Idan kika je can zaki ji” Ya juya yayi tafiyarsa, ni kuma na juyo cikin gida idona na zubar da ƙwalla. MAI KUKE TSAMANI A PAGE NA GABA? *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 4⃣ Inna ta doso inda na ke a yayinda da juyo cikin gida hawaye na bin fuskata. “Nawwara lafiya?” Ban san ta ya zan faɗa mata ba, sai dai babu wata damar ɓoye mata dole na faɗa mata gaskiya. “Wai Baba aka kama, yana station ɗin ƴan sanda” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Ta faɗa tana dafe kanta fuskarta na bayyana tashin hankalin da ke zuciyarta. “Mi yayi musu?” “Nima ban sani ba, na tambaya ya ce idan na je can zan sani” “Mun shiga uku muna cikin wannan halin kuma wani za mu shiga” “Ina ganin sharar fage ne ga wata sabuwar rayuwa” Na faɗa ina hawaye. Bata kula zance ba ta shiga ɗaki ta ɗauko tsohon Hijabinta ta saka tana ce min. “Zan je na faɗawa Dahiru muje tare, ke kije ki faɗa a babban gida” Bata ko tsaya jiran abunda zan faɗa ba ta fita hankalinta a tashe. A take nima na saɓi mayafina, na ja ƙofar gidan na nufi babban gida wato gidan kakaninmu. Babban gida ne mai ginin ƙasa da laka irin gidan nan da ake a zamanin baya wanda a yanzu ake kira da family house, ba kasafai na ke son zuwa gidan ba saboda mutanen da ke ganin mutunci na da na ubana basa a raye a yanzu, wato kakanin na kenan waɗanda suka haifi ubana, sai dai ƙanen da ƴaƴansu da suke ganin kamar Baba yayi mana gata dan ya ware mu daban, duk laifin duniya da ganin kamar mu munfi kowa sai suka ɗauka suka ɗora mana har wasu na cewa wai dan Tsoho ba shi da rai ne tasa Baba yin haka. Alhalin ba haka ne kawai Baba baya son rigima ne da ƙaƙanan maganganu da yawan anyi an'ce kamar ya kashesu. Sashensu Yakumbo na fara shiga wato gwaggo Babana, tana ganin hawaye a fuskata tasan ba lafiya. “Tsohuwa Lafiya?” “Baba aka kama” “Kama kamar ya? Kamu na ƴan sanda ko mi?” A take ya zayyana mata komai ina hawaye. Miƙewa ta yi tsaye ta fita tsakar gida duk da jikin nata babu wani dogon ƙwari saboda tsufa. Kan ka ce kwabo har ƙofarta ta cika da ƴan cikin gida kowa na tambayar ba'asi, abunda na faɗa mata shi na faɗa musu, sai tasa aka kira ƙannen Babana wanɗanda basa nan a waya ta sanar musu. Ban baro gidan ba sai da aka kira sallah azahar kuma har lokacin Inna bata dawo ba. Sakina da Jamila kan suna tsakar gida zaune, Noor ne kawai yake sha'aninsa, ina shiga suka yo kaina da tambaya. “Anty ina kika je?” “Baban gida na je” “Me kika je yi, ina Inna?” Yara ne ƙanana a tunani be kamata na sanar su wannan maganar yanzu ba. “Na riga Inna fita ban san inda taje ba, ni na je gaishe su ne kawai” Noor ya zo ya riƙe min hannu. “Momy yunwa na ke ji, kunon da na sha ya ƙare” Hannu da ke cikin nasa na sunce na nufi ɗaki dan bana son yaga ƙwalla da suka cika min ido. Ɗan kuka na yi kaɗan a ɗakin domin idan na yi da yawa zai tona asirin abunda na ke ɓoyewa Sakina da Jamila ne, fito na yi waje na yi alwala na koma ɗakin na shinfiɗa ɗankwalina na yi sallah azahar, babu irin addu'ar da ban yi am Baba ba duk ya ke ban san halin da yake ciki ba ko kuma dalilin kama ɗin shi ɗin ba, na roƙar masa mafita da sauƙi ga Allah, tun a cikin sujudar ƙarshe har a cikin zaman tahiya zuwa addu'ar da ake bayan sallamewa. Ƙarfe biyu da kwata Habiba ta dawo gida cikin uniform ɗinta na makaranta. Tun da ta yi sallama na kasa amsa mata ta fahimci akwai matsala. Hijabi ne kawai ya zame mata dole ta cire ta nufo inda na ke zaune ta dafa ni. “Nawwara mi ya faru” Idan na ce zan ɓoye mata hawayena to zan yaudareta ne kawai, domin ta riga ta ga yadda hawayen ya ke sauƙowa daga idona, bakina kuma a gumɗe ina gintse kuka da ke son fito. “Ki faɗa min mana ina Inna?” Ta sake tambaya idonta na cika da ƙwalla. “Habiba ƴan sanda sun kama Baba, tun safe Inna ta je har yanzu bata dawo ba” Ta ɗora hannu saman kai. “Mun shiga uku? Mi yayi musu?” “Wallahi ni ma ban sani ba” A gurin ta zauna ta fara kuka kamar an yi mana mutuwa, daman Habiba bata da taurin zuciya irina, zan iya ɓoye kukana ko kuma bayyanawa a duk lokacin da nake buƙatar hakan amman Habiba bata iya wannan, a duk lokacin da abun kukan ya sameta a take zaka gane. Sakina da Jamila har da Noor suka shigo ɗakin a guje suna kallonta, nima kallonsu na ke hawaye na bin fuskata. Sallamar Inna da muka ji ne yasa muka ɗunguma gaba ɗaya muka fita waje, tana kallonmu sai ta fashe da kuka ta faɗi zaune. Daga ni har Habiba kasa tambaya mukayi kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarsa, musamman ni da nake zargin ko sun kashe she ni. Jamila da Sakina ne suka ƙarasa inda take suna tambayarta. “Sata ake zargin mahaifinku yayi ta kimanin dubu ɗari biyu da saba'in” Tana faɗar haka ta ƙara fashewa da kuka, Habiba ta faɗi zaune irin jikinta ya mutu sosai, ni kuma na lumshe ido wasu zafafan hawaye suka zubo min. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 5⃣ Haƙiƙa mahaifina talaka ne, amman bana tunanin wannan talaucin zai saka Baba sata, sai idan wani tsautsayin ne ko ma zai sata ba zai saci kuɗi har naira dubu dari biyu da saba'in ba, tau ina zai kaisu? “Miya ɗauka har na dubu ɗari biyu saba'in?” Habiba ta yi tambayar da na ke da niyar yi ma Inna. “Dako ya je yi kasuwa, wacce yaje yi ma dakon wayoyinta da ɗankunenta na zinari ya ɓata, ta ce wayoyinta na dubu ɗari da ashirin ne, ɗankunen zinarinta kuma dubu ɗari da hansi” Sulalewa na yi ƙasa hawaye na min zuba, babu zancen da nake tunawa kamar maganar mu ta ɗazu da safe, yadda na ke nanata masa kar yaje dakon nan kamar na san abunda zai faru. “Babu irin roƙon da ba'ayi mata ba ta ce ita ba zata haƙura sai an biyata” Inna ta faɗa cikin kuka. Sai duk muka saka kuka har su Sakina da Jamila, daman Habiba bakinta a buɗe yake tana aikin kukan. “Ku daina mana kuka tun da ba mutuwa aka yi ba” Cewar Inna tana share hawayenta. Bayan Inna ta bar gurin na miƙe tsaye na koma cikin ɗakin na zauna ina aikin kuka. Haka muna yi sallah isha'i cikin zullumi da tunanin makomar Baba har ma da tamu gaba ɗaya, bayan an yi sallah isha'i ne maƙota suƙa riƙa shigowa suna mana jaje. Ban taɓa yarda tashin hankali na hana bachi ba sai a wannan karon ina ji ina gani bachi ya ƙaurace daga idona. Alwala na fara gabatarwa kamin sallar nafila, har aka kira sallah asuba ina zaune saman ɗankwalina ina tasbihi, bayan na gama na yi ma Baba addu'a sannan na gabatar da sallah asuba. Tun da dungu-dungun safiya muka ji an buga mana ƙofa, Habiba ce ya je ta buɗe yayinda ni nake zaune ina karatun ƙur'ane. Ina jin lokacin da ta zauna kusa da ni sai dai ban kalleta ba har sai da na kai ƙarshen ayar da na ke karantawa, sannan na rufe ƙur'anen ina ambatar sunanta “Jidda” “Na'am Nawwara, jiya cikin dare na ke jin abunda ya faru kuma kin san Abba baya bari mu fita da dare, da gaske ne?” Na ɗaga mata kai hawaye na bin fuskata. “Baba ba zai yi sata ba, sai dai idan wani sheri ne aka masa” Cikin kuka na zayyana mata abunda Inna ta faɗa mana. A take ta fashe da kuka. “Nawwara ki yi haƙuri jaka ƙaddara take zuwa wani lokacin, yanzu bari na je na shirya sai muje mu ganshi” “Babu ko naira hannuna Jidda” “Ina da ɗari uku zasu ishemu” “Tau Jidda na gode” Miƙewa ta yi tsaye ta fice, ni kuma na tashi na nufi ɗakin Inna, gaisheta na fara yi sannan na faɗa mata yadda muka yi da Jidda. “Tau bari na jira har ku dawo sannan muje” Tashi na yi na koma ɗakinmu na cire tufafin jikina na ɗaura zane na ɗibi ruwa a robar da muke wanka na shiga banɗaki na yi wanka da ruwan sanyi. Tufafin jiya na ɗauka na saka ban damu da shafa mai ba, domin ba kwaliyarce a gabana ba, sai takwas har da ƴan mintuna sannan Jidda ta dawo, baƙar abaya ce jikinta sai jan mayafi, hannunta ɗauke da kular abincin. “Nawwara zo muje” Abunda ta faɗa kenan tana shigowa. Inna ce ta rigani fitowa tana gaisawa da Jidda. Sannan na fito sanye da hijabi. “Jidda sai yanzu?” “Yi haƙuri dan Allah taliya na tsaya dafa masa” Ta faɗa cike da damuwa. Jidda ƙawar arzikice dukan abunda ya dame ni kamar ya sameta ne, tana damuwa sosai da duk abunda ya shafi rayuwarta, shiyasa bana da ƙawa a duniyar nan da ta wuce Jidda. Tare muka fita tana min bita kan haƙuri da yarda da ƙaddara, ni ko bana iya cewa komai sai hawaye da ke min zuba, ganin haka yasa ta daina maganar domin tana ƙara min ƙarsashin abun ne kawai. Tun da muka shiga Napep har muka fita ni da ita babu wanda ya ce Uffan, gabana ya faɗi sosai lokacin da muka doshi station ɗin wata ƙila saboda ban saba ba ne ko kuma ina fargabar ganin halin da Baba yake ciki ne. Jidda ta lura da hakan shiyasa ta wuce gaba ta bar ni a baya saboda kawai ta ƙarfafamin guiwa. Ƴan sanda da yawa muka tarar a gurin, ta kuma ɗai-ɗaikun jama'a waɗanda nake sa ran suma sun zo kan nasu matsalar ne, muna shirin tambayar sai na hango Baba Sulaiman wato ƙanen mahaifina da kuma yayyunsa. Cikin rashin kuzari da raunin zuciya na ƙarasa kusa da su idona na zubar da ƙwalla. Baba na zaune saman tebur fuskarsa a buge jini har ya dasƙare masa saman kai da alama tun jiya suka dake shi ko kuma da dare. Ƙasa na zauna kusa da shi na riƙe masa ƙafafu kasancewar shi yana zaune saman banci ne tare da ƴan'uwansa. Kasa kallona yayi wannan baya rasa nasaba da kukan da na ke wata ƙila baya son kuka a gaban jama'a ne. Kwanon ɗumame na gefen da na zauna nasan su Baba Sulaiman ne suka zo da shi. Tsawar da Baba Ayuba ya katsa min ne yasa ni tsagaita kukan da nake har na dawo hayyacina. “Ai yanzu sun yarda za su bada belinsa amman wai sai an bada dubu ashiri” Cewar Baba Salisu yayan Baba. Ni ko na dafe kai ina sauke ajiyar zuciya, ko yanzu tsugune bata ƙare ba, ina zamu samu wannan dubu ashirin ɗin. ‘Oh Allah mun gode maka’ Na faɗa a raina ina ta ƙoƙarin tare kukana. A nan Baba Sulaiman yake faɗa mana yadda matar take son a je kotu, wai ashe dpo ɗin station ɗin ne ƙanen wacce aka yi ma satar. Bamu ƙara minti goma a gurin ba, wani ɗan sanda ya zo yana faɗa mana lokaci yayi. Duk miƙewa muka yi tsaye a nan na samu kallon bayan mahaifina kasancewar ba shi da riga ne, babu komai sai kwancin sanduna, yanayin yadda baya son motsa jikinsa kaɗai ya isa ya karantar da kai jikin na masa zafi da ciwo ne. Ban san lokacin da kuka ya zo min ba, na rumgume bayansa ina mai jin kamar na yi tsuntsuwa ni da shi mu ɓace daga gurin gaba ɗaya. “Mahaifinku be yi sata ba Nawwara, kuma be taɓa yi, ki gamsar da ƴan'uwanki da wannan” Abunda Baba ya faɗa min kenan, ni kuma na ƙara ƙanƙanme shi. Hankalin duk wanda ke gurin sai da ya dawo kaina saboda kukan da nake, babu tausayi haka ɗan sanda nan ya tisa ƙetar Baba gaba suka wuce da shi ciki. Ni kuma Jidda ta rumgume muka riƙa kuka tare. “Haba Nawwara akan ki farau? Miyr haka wuce kuje gida, mu zamu koma can zamu san yadda za mu” Cewar Baba Sulaiman. Ƙarfin hali na yi na riƙa hannun Jidda muka fito tare, a nan Baba ya Ayuba yake faɗa min wai a tura Sakina ko Jamila ta karɓo mana ɗumame. Har muka iso gida kuka na ke, Jidda ce ta iya tsayawa ta zayyana ma Inna abunda ya faru. Ba laifi na ga farincikin Inna wata ƙiƙa saboda sun yarda zasu bada belinsa ne. Bayan Jidda ta wuce Sakina ta je karɓo abincin, ni kuma na tashi na nufi ɗaki kaina na mugun ciwo, abincin da aka karɓo ma ban iya ci ba, kamar yadda Inna da Habiba suka kasa ci duk da kasancewar muna jin yunwa. Ni dai ina cikin ɗakin har aka kira sallah azahar, bayan na yi sallah na nufi ɗakin Inna, a nan take tambayata Habiba. “Bata ɗaki na ɗauka tana nan ma” “Bata nan ƙila ta je baban gida” Haka kawai gabana ya faɗi zuciya ta riƙa nasalta min kamar ba can ta je ba. Babu wani hirar kirki tsakani na da Inna saboda bana son labarta mata halin da na samu Baba duk da kasancewar idanuwana sun saka goge hoton abunda suka gani. Misalin huɗu da rabi Baba Sulaiman ya shigo gida yana faɗar an haɗa dubu shida da ɗari takwas abun da ƴan'uwa masara son zumunci, taya za a ce duk yawan familyn Babban gida ace dubu shida kawai aka haɗa. Takaici da baƙinciki ya hanini cewa komai haka na koma cikin ƙarƙashin iccen dalbejiya na zauna. Ɗari da hansi ya cire a cikin kuɗi ya miƙawa Sakina wai su saye wani abu su ci. Inna kuma ta saka Hijabinta suka fita tare wai zasu je station ɗin su kai musu ko zasu karɓa. Ni dai nasan wahala ce kawai zasu yi, ƴan sanda da basa da imani, kuma sun ce dubu ashiri ya za'ayi su karɓi dubu shida. Noor ne ya zo ya zauna kusa da ni yasa hannunsa yana share min hawayen da ban san sun zubo ba. “Momy ki daina kuka” Murmushin ƙarfin hali na yi na shafa kansa. Kan Habiba na fara hangowa ta leƙo sai ta koma ta laɓe, hakan yasa ni miƙewa tsaye ni nufi ƙofar, ƙaton hijabinta ne na islamiya a jikinta, sam babu natsuwa a tare da ita idonta ya kumburo kamar ba nata ba. “Ina kika je Habiba?” A maimakon ta amsa ni sai kawai ta jefomin wata tambayar. “Inna na nan tsakar gida?” Kai na girgiza mata alamar a'a ina kallon yanyinta. Baya na yi hakan ya bata damar shigowa cikin gidan, hankalinta be kwanta ba sai kalle-kallen tsakar gidan take kamin da wuce ɗaki da sauri. Cikin rashin kuzari na rufa mata baya, ina shiga cikin ɗakin sai ta kama hannyena ta danƙa min sababin kuɗi ƴan dubu-dubu. “Nawwara ga dubu ashirin ɗin nan kije ki kai su saki Baba, daga baya sai a biyata kuɗinta” Wani jiri na ji ya kamani na kasa riƙe kuɗin, suka suɓuce daga hannuna suka watse ƙasa. Ita kanta ta tsorata da yanayi da sauri ta soma yin baya-baya tana fashewa da kuka. COMMENT AND SHARE *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 6⃣ Faɗuwa na yi saman guiwoyina na kai hannu na taɓa kuɗi, kamin na tada kai na kalleta. “Habiba ina kika samu wannan kuɗin?” “Tsinta na yi” Ta faɗa cikin kuka mai ƙarfi. Miƙewa na yi tsaye na matsa kusa da ita ina nunata da yatsa. “Karki raina min hankali Habiba, ta ya zaki tsince dubu ashiri a wannan halin?” Na faɗa ciki wata murya da ban san ina da ita ba. Sai ta rufe bakinta ta matsa baya. “Kyauta aka ba ni” Na watsa mata wani irin mahaukacin mari. “Ba ƙaramar yarinya ba ce ni, karki yi wasa da hankalina” “Mustapha ne ya ba ni” Ta sake faɗa tana dafe fuskarta saboda zafin marin da na yi mata. “Mustapha” Na maimaita sunan, tabbas Mustapha zai bata fiye da dubu ashiri, zai iya bata miliyan ma, amman idan ta ba shi mutuncinta. “Ya taya mutuncinki ne ya baki kuɗin ko kuma kin riga kin siyar masa ne?” Na tambaya gabana da dukan shida-shida, zuciyata kuma na ala-ala idan bata siyar ba. “Na siyar... Nawwara idan ba haka na yi babu inda wannan kuɗin zai fito, ki duba halin da Baba yake ciki, babu ruwan kowa da mu” Baya-baya na yi har sai da na jingina da ƙofar ɗakin. “Habiba kin kashe mu, ya kike tunanin Inna zata yi idan ta ji wannan abun? Kina tunanin wannan abun da kika aikata zai burge Baba? Da wane ido zaki kallesu” Da sauri ta ƙaraso kusa da ni ta riƙe hannuna tana kuka har muryarta na karkarwa. “Dan Allah karki faɗa musu, saboda su na yi wannan abun idan suka yi fushi da ni Wallahi mutuwa zan yi” “Kin san da wannan kika je kika siyar da mutuncinki? Allah da ya samu cikin wannan hali shi zai mana mafita, kina kunyar iyayenki amman baki kunyar Allah ki? yanzu ina kika son na ce mun samo wannan kuɗin?” Risinawa ta yi a gurin da cigaba da kuka mai taɓa zuciya. Sallamar Jidda ce ta razanar da mu daga ni har Habiba ɗin. Da sauri na fita waje domin na tareta karta shigo, na manta da hawayen da ke fuskata har sai da Jidda ta min magana. “Nawwara kuka kike yi?” Nasa hannu na share hawayen yayinda wasu suke ƙara zubo min, kuka ya zama biyu a yanzu. Hannu ta kama ta danka min dubu uku. “Ga dubu uku ku ƙara” “Ke kuma ina kika samu wannan kuɗin?” Na tambaya muryata na rawa. “Wayata na siyar vivo” A maimakon na yi mata godiya sai kawai na fashe da kuka, hakan ya karantar da ita ba wannan ne kawai damuwata ba, lallai da akwai wani abun a ƙasa. “Nawwara ko dai wani abun ya faru ne?” Ɗurƙushewa na yi a gurin na fashe da wani sabon kuka, har su Sakina suka yo kaina. Hakan yasa na katse kukan na miƙe tsaye na kama hannun Jidda muka shiga ɗaki. “Jidda Habiba ta siyar da mutuncinta ta kawo dubu ashirin” Na faɗa ina nuna mata kuɗin. Ita kuma ta ɗora hannu saman kai tana faɗin “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Inna ta ji? ” “Bata sani ba, amman yanzu dole zata sani idan ta ga wannan kuɗin” “Habiba miyasa kika yi haka?” Jidda ta tambaya hawaye na bin fuskarta. Habiba kan aikin kuka kawai take, ta ma kasa ɗaga ido ta kalli Jidda. “Ina zaku ce kun samo wannan kuɗin Nawwara?” “Nima ban sani ba” “Karki faɗawa Inna, bari na je da kuɗin ni nasan yadda zan yi” Duƙawa ta yi ƙasa ta tsince kuɗin ta fita. Har na cira ƙafa zan bita sai Habiba ta kirani cikin muryar kuka. “Nawwara” Juyowa na yi na dawo. Sai ta tashi zaune “Dan Allah karki faɗawa Inna” “Ba zan faɗa ba” “Idan na yi tafiya ba zata ga ne ba?” “Ba zaki ita tafiya ba ne ba?” “Gurin zafi ya ke min sosai, bana iya haɗe ƙafafuna da kyau” Wani ƙololon bakin ciƙi na ji ya ratsa zuciyata. Cikin rashin ƙwarin jiki na fita waje na kunna wuta na ɗora mata ruwan zafi, Sakina kuma na ce su je su siye wani abu su ci da kuɗin da Baba Sulaiman ya basu. Sai da na cika mata roba da ruwan zafi sannan na zuba mata wasu a bota, da kaina na kai mata banɗaki, naje na riƙo ta kaita banɗakin. Tana gurin wankan Inna na ta dawo, fuskarta da alamun damuwa tun daga yanayin sallamarta na lura da hakan balle ma lokacin da ta zauna kusa da ni. “Kin dawo” Na tambaya ina ƙoƙarin ɓoye hawayena. “Eh mun kai musu kuɗin amman sun ce sai an cika sauran, ba su bar mu mun ganshi ba” “Allah yayi mana mafita” Na faɗa ina sauƙe ajiyar zuciya. Yayinda idona ke kallon Habiba ta tsaya tana leƙon. Na san tsoronta ɗaya kar Inna ta gane halin da take ciki, ina baƙin cikin halin da Habiba ta faɗa da ƙananan shekarunta ni kaina mai shekara ashirin da huɗu mutane kan kirani da ƙaramar yarinya balle ita mai sheƙaru goma sha bakwai. Tunanin dabarar da zan yi ma Inna ya ɗaukr hankalinta har Habiba ta samu ta wuce na ke, sai ga Jidda ta shigo kamar ta san ina nemanta. Saman tabarma ta zauna tana gaishe da Inna, ko da wasa Jidda bata kalli inda na ke ba, sai kawai ta fara jerawa Inna irin ƙaryar da data tsara. “Inna ga dubu ashirin na kawo, na siyar da kayan Kitchen ɗina ne, Maman Nura ma bata sani ba kuma idan ta ji zata min faɗa, dan Allah karku faɗa mata, inyaso idan Allah ya kawo sai ku biyani” Ya ƙarasa tana danƙawa Inna dubu ashirin ɗin, Inna ta saki baki. “Haba Jidda ayi haka?” “Zan iya muku komai Inna ni dai ki rufa min asiri karki faɗawa Maman Nura” “Ba zan faɗa ba, Allah ya saka miki da alheri ya biyaki da aljanna, ya baki miji na ƙwarai” Da ido na yi ma Habiba magana akan ta zo ta wuce saboda hankalin Inna ya ɗauko kan kuɗin, sannan na amsa da “Amin Jidda mun gode Allah ya bar zaman tare” “Ba komai ai yi ma kaine” Inna ta kalleni. “Ai ban ga ta zama ba ni kan, bari na je na samu Sulaiman mu kai musu cikon kuɗin ko?” “Inna ana kiran magariba kuma? Da dai kin haƙura har a jima ko gobe” Cewar Jidda. “A'a Jidda tun da har Allah yayi mana mafita ƙara muje mu kai musu kuɗin, baki san halin da bawan Allah ya ke ciki ba” Na kalli Inna zuciyarta cike da tausayinta da kuma tausayin kaina da na Jidda, na san tun safe bata ci komai ba ga rashin kwanciyar hankali da ke damunta. Hijabinta da ke gabanta ta ɗauka ta saka ta miƙe jikinta har rawa yake ta saka talkaminta ta kama hanya. Na kalli ƙawata Jidda tare da yi mata godiya. “Na gode sosai Jidda” “Ba komai, ki yi magana da ƴar'uwarki Nawwara ki kwantar mata da hankali karta sake shiga wani hali, ni zanje gida kar Abbah ya dawo” “Na gode sosai Jidda” Tashi ta yi ta fita, ni kuma na tashi nayi alwala na yi sallah, shiru-shiru Inna bata dawo ba har bayan Isha'i, sai dai hakan be sani tsoro ba a tunani ko zasu ɓullo da wani abun ne na daban. Takwas da rabi Inna ta dawo ita kadai cikin yanayin damuwa. Sai dai ban tambayeta komai ba har sai da ta yi alwalah ta rama sallah magariba ta yi isha'i bayan ta sallame na matso kusa da ita na ce “Inna ya kuka yi da su” “Lamarin ƴan sanda nan yana ba ni tsoro Nawwara, basu bar mun ganshi ba, amman sun karɓi kuɗin wai zasu zo anjima su kawo shi da kansu, ni ban taɓa jin inda aka yi haka” “Ko dai ba zasu bada belin nasa ba ne?” “Ni ya zan sani, an ce dpo gurin ƙanen wacce aka yi satar ne, kin san kuwa sai yadda Allah yayi” “Baba Sulaiman be ce komai ba?” “Babu irin roƙon da ba mu musu ba Nawwara, Har Salisu da Dahiru duk sunje, amman sun ce ba zasu ba da shi ba sai dai su kawo shi da dare, shine su suka wuce gida ni kuma na dawo” “To ko wasu kuɗin zasu ce a ƙara musu kuma?” “Ban sani ba” Ta faɗa tana fashewa da kuka. Iya ƙoƙarin da nayi na danne kukana sai na kasa saboda ganin hawayen mahaifiyata yana zuba. Shiru-shiru har goma na dare babu wani labari, daga ni har Habiba da Inna muna cikin tashin hankali da zullumi, dukanmu hankalin sai ya tattara ya koma gurin ƙofa ko iska ya kaɗa sai muga kamar Baba ne za a shigo da shi. Sha ɗaya da rabi na dare na tashi zan rufe gida, izuwa yanzu kan mun sadaƙar ba zasu kawo shi. Ina kaiwa bakin ƙofa sai na hango motar ƴan sanda ta faka a ƙofar gidanmu ahankali, ta yadda ba za a ji ƙarar motar ba, fitar motar ma a kashe take. Ban ƙara tabbatar da ƴan sanda bane har sai da naga sun fara fito daga cikin motar. Da gudu na juya na koma cikin gida dan faɗawa Inna. “Inna Inna ga su can sun zo” Ba Inna kawai ba, har Sakina da Jamila da ke bachi sai da suka farka duk muka ɗunguma muka fito waje da gudu. Sai dai abunda muka yi karo da shi ya faɗar da gabanmu dukanmu. Baba ne suka aje gefen icce sai wasu ƴan sanda uku kusa da shi ɗayansu ya ƙaraso kusa da mu yana mana bayanin da ban gane kansa ba. “Zuciyarsa ce ta buga, ku kai shi asibiti da safe” Yana faɗar hakan ya juya da sauri suka fice daga gidan. Mu kuma muka ƙarasa gurin da Baba yake kwance, hannu na kai na girgiza shi be motsa ba, na kira sunansa be amsa ba, na jijjiga amman be yi wata alama ta mai rai ba. Firgice na nasa hannu na yaga rigar yadin da ke jikinsa, sai ga ƙirjinsa da dukan jikinsa da jini, tashin hankali ya mantar da ni cewar dare ban san lokacin da na kwala ihu ba, na yi tsalle na dire na faɗi ƙasa na mulmula na mulmulo ina kuka, Habiba kuma ta faɗo kaina sumammiya. YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING. 🙌 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 7⃣ Cikin tashin hankali na kwantar da Habiba da ta faɗo kaina, na nufi Inna da ke baya-baya tana nuna Baba da yatsa. Ina riƙata sai ta cafki hannayena jikinta na karkarwa. “Gawa suka kawo mana Nawwara, sun kasheshi, miya musu? Basu yarda zamu biya kuɗin ba? Ko dan sun maida mu talakawa? Saboda ba mu da galihu? Akan ƴan kunnen zinari da wayoyi suka ɗauki rai? Miyasa za su kawo mana shi? Saboda muma mu taru mu mutu ko? Sun maida mu mahaukata...” Daga kalaman da take na fahimcin ƙoƙarin fita hayyacinta take. Riƙata na yi na zaunar, Sakina da Jamila da ke kuka na tura su ɗaki. Sai kuma na dawo tsakar gidan na yi tsaye ina kallon Baba, kana na kalli Habiba da ke sume, sai kuma Inna da ke zaune tana kallona, neman kukana na yi na rasa ashe akwai ranar da zaka buƙaci kukan ya ƙi zuwa maka, idona gaba ɗaya na ƙafe kamar hawaye be taɓa taruwa a ciki ba, yawun bakina na bushe kaina kuma yayi mugun nauyi kamar an ɗora min dala. Ban damu da rashin mayafi da babu a jikina ba da kuma takalmi na fita da gudu zuwa babban gida. Gudu na ke amman gani nake kamar ƙara maida ni baya ake, tsakaninmu da su babu nisa amman yau sai ya koma min kamar gari da gari. “Keeeeeeee” Na ji an kirani sai dai hakan be sani tsayawa ba, har sai da na ji an harba bindigar mahalba. A firgice na juyo ina ɗaga hannuna sama yayinda su kuma suka tunkaroni suna nuna ni da bindigar, ɗaya daga cikinta da dalla min fitila mai tsananin haske da kashe ido. “Nawwara miya fito da ke cikin daren nan?” Jin muryar Baban su ƙawata Ruƙaiya yasa na gane cewar ƴan sitirine masu yawo da zarar dare yayi domin kama ɓarayi. “Babanmu ne aka kawo shi ne zan je na faɗawa Baban Sulaiman, Babban gida zani” Na faɗa cikin wani irin mugun haƙƙi da sarƙewar murya. “Tah koma gida zanje na faɗa musu, Ibrahim rakata” Ya ƙarasa yana kallon ɗaya daga cikin yaransa. Wanda aka kira da Ibrahim ɗin ya saka ni gaba shi ya rakani har ƙofar gida sannan ya koma. Ko da na shiga na samu Inna zaune gaban Baba ta zuba masa bokiti biyu na ruwa sai fifita take masa da ɗankwalinta, atunaninta ko ya yi doguwar suma ne wata ƙila idan ta yi masa haka zai farko. Ƙarasa na yi ƙusa da ita na ɗauki ragowar ruwan da ke bokitin na juyewa Habiba sai gata ta farka a firgice tana haƙi kamar na fitar rai. A nan Inna ta juyo ta kalleni fuskarta a taɓe tana shirin fasa kuka. “Shi wannan ya mutu kenan?” Wani irin uhu Habiba ta saka iya ƙarfinta tana shurin ƙafafunta, tana danƙar ƙasar tana watsarwa. Ni kuma na yi zaune a gurin bana kuka kuma bana iya bawa ɗayansu haƙuri daga ita har Inna da ke kuka, ƙaɗan-ƙaɗan juri yake ɗibata ina jin sautin kukansu kamar a cikin bachi. Kan kace kwabo maƙota sun cika gidanmu kamar ba dare ba, masu taya Inna kuka na yi wasu kuma na girgiza kai, shigowar su Baban Sulaiman ne yasa kowa yaja baya, Baba Dahiru ya shiga duba Baba, Baba Sulaiman kuma ya fasa kuka yana faɗin “Sun kashe min ɗan'uwa ba bisa haƙƙi ba, Wallahi ɗan'uwana be yi sata ba, ya rantse min da Allah be ɗauka ba, sun ɗauki alhakin ɗan'uwana Allah ya isa Allah ya isa” Yasa taɓar rigarsa ya share hawayensa sai kuma ya faɗin a gurin yana kuka. Har sai dai sauran ƴan'uwansa suka riƙashi, sai ya fisge kansa ya nufi ƙofa yana faɗin. “Bayan sun karɓi dubu ashirin na beli sai kuma su kawo mana gawa, ba zata saɓuba” Baba Dahiru yayi saurin riƙeshi. “Sulaiman ina zaka je cikin dare nan?” Komawa yayi ya zauna yana rawar ƙafa alamun masifa na tare da shi. Inna A'i ce ta zo ta riƙa Inna ta tasheta daga gaban Gawar Baba ta maidata can gurin ƙofar ɗaki ta zaunar da ita. A nan suka shiga tambayar Sakina yaushe suka kawo shi, kasancewar itace mai wayo saman da Jamila, cikin in'innar kuka ta zayyana musu abunda ta sani. Ni kan ina zaune gurin kamar kayan wanki komai ina ganinsa kamar mafarki, har kuma lokacin babu hawaye a idona balle alamun kukan. Habiba na gefena tana rusar kuka. Can ƙasa-ƙasa na riƙa jiyo muryar Baba Sulaiman yana faɗin. “Sai da ya faɗa min suna ta dukansa akan sai ya karɓa laifinsa cewar yayi satar, shi kuma ya rantse min da Allah ba zai amsa ba sai dai su kashe shi, amman da naje na samu ƴan sanda nan na ce mu mun yarda yayi satar kuma za mu biya, daker suka yarda zasu ba da belinsa dubu ashiri, da yamman mu ka cika musu kuɗinsu sai kuma su kawo mana gawa? Shiyasa suka ƙi bamu shi, suka ce sai dai su kawo shi da kansu ashe sun san sun kashe shi, kuma suka karɓe kuɗin, Wallahi ba zamu bar wannan maganar ba, ba zamu barta ba” Faɗa yake cikin kuka kamar ba mace ba, sai yana buga ƙafarsa yake da ƙasa. Magana da shi ta ƙarshe a police station ne ya dawo min a rai. _“Mahaifinku be yi sata ba Nawwara, kuma be taɓa yi ba, ki gamsar da ƴan'uwanki da wannan”- A take na ji idona ya cika da ƙwalla, kan kace kwabo sai ga hawaye suna saukowa daga idona kamar ba gobe, ban san lokacin da na kwara wani uban ihu ina kiran sunansa ba. “Baba! Baba!! Baba!!!” Mama ladi ta zo da gudu ta rufe min baki, sai na faɗa hannunta ina kallon fuskarta da ke min gizo kamar ta mahaifina... *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 8⃣ Riƙani ta yi ta tayar ta maida can kusa da Inna ta zaunar tana bani haƙuri da kalaman da za su sanyayamin zuciya. Kuka muke ta yi ni da Habiba, yayinda Inna ta rafka uban tagumi tana kallon gawar Baba. Baba Dahiru ne yaja janena dake kan igiya ya rufa masa. Haka muka zauna har garin Allah ya waye babu wanda ya runtsa. Su Baba Dahiru ne suka yi alwala suka tafi masallaci yayinda mu muka yi namu sallah a gida, bayan na gama na ɗauko alƙur'ane ina karantawa, izuwa yanzu bana da buƙatar wani kuka bayan wanda na yi jiya ya haddasa min ciwon kai da kumburewar idanu, ina jin yadda maƙota na nesa da na kusa ke ta shigowa suna jajantama Inna, wasu na san gulma ce ta kawo su tun da gari ma be gama wayewa ba amman har labarin ya zaga unguwarmu da ma unguwanin da ke kusa da mu. Bayan fitowa Masallci sauran ƴan'uwan Babana suka shigo maza da mata cikin har da Yakumbo. masu kuka na yi masu faɗa na yi, Baba Ayuba ne ya bada shawarar a ɗauki gawar Baba aje da ita police station a mayar musu, Baba Sulaiman kuma ya hana wai ba za a tagayar masa da gawar ɗan'uwa ba, idan aka yi haka ɗan'uwansa aka wulaƙanta. Daga ƙarshe suka yanke shawarar zuwa station ɗin ba tare da gawar Baba ba, a ɗakin mu aka saka shi sai aka rufe ɗakin duk muka kwaso muka dawo ɗakin Inna. Noor ya zo kusa da ni ya zauna, Jamila da Sakina kuma suka zauna gurin ƙofa suna ta aikin kuka kamar yadda Habiba ke yi. Ni kuma ɓa noce kaina ƙasa bana kuka kuma bana tunani kaina kamar fanko na ke jinsa, shigowar Jidda da Mahaifiyarta ce ta ɗaga hankalin kowa, saboda kuka da take kamar ita akayi ma mutuwar, sai gida ya ɗauki kuka muryarta muryar Habiba da Inna sai kuma Jamila da Sakina. Yakumbo ce ta katsa musu tsawa tana faɗa kan kuka da suke, musamman Inna da take ganin ita ya kamata ace ta rarrashe mu amman ita take kukan ma. “Mamaci addu'a yake so ba kuka ba, bawan Allah nan fa yana cikin gidan nan amman kuna ta masa kuka, kuka ai ba zai dawo da shi ba, ba zai muku maganin komai ba, amman addu'a zata iya sanyaya muku zuciya kuma ta canja lamarinku, sannan shi kuma Allah ya karɓa yayi masa rahama. Yanzu ke Hajara ke da ya kamata ace kin bawa yaran nan haƙuri, sai ki zauna kina kukan tare da su, Allah be yi wani dan wani ba, be yi Musa dan ku ba kuma be yi ku dan Musa ba, shi ya hallita abunda yasa masa rai yanzu kuma ya karɓi abunsa, gode masa ma ya kamata ku yi kuma ku yi haƙuri sai kuga Allah ya yi muku wata mafitar” Ba laifi kalamanta sun yi tasiri gurin Inna da har tasa hannu ta share hawayenta tana ta kokuwar tsayar da kukanta, Habiba kan kunne uwar shegu ta yi sai abunda ya cigaba, kusa da ni Jidda ta dawo ta zauna ta kama hannuna ta riƙe sai hawaye take, ni kan kallonta kawai na ke ina jin kaina kamar babu komai a ciki. Tun da suka ta fi basu dawo ba sai ƙarfe goma na safe har da ƴan mintuna, mutane da suka je tun hasken alfijir ba gama yayewa ba. Tare da tawagar ƴan sanda suka zo wanda hakan ya haddasa mana dandazo jama'a a ƙofar gida. Dpo ne ya shiga da kansa ya duba gawar baba tare da wani ƙaramin ɗan sanda mai ɗaukar hoton jikin Baba, bayan ya gama dubawa ne ya dawo gurinmu, a bakin ƙofa ya tsaya yana ba mu haƙuri tare da faɗar za a ɗauki mataki da ya dace. “Wacan ƴarsa ce?” Ya tambaya ganin ni kaɗaice na kasa ɗago kai na kalleshi tun da ya soma maganar har ya gama. Inna A'i ta nuna Habiba da Jamila da kuma Sakina “Eh da wannan da wacan da wacan, su kaɗai Allah ya bashi” “Allah sarki ku yi haƙuri zamu ɗauki mataki, yanzu haka mun sa an kama ƴan sandan da suka yi wannan aika-aikar kuma za a gabatar da su a gaban kotu In'sha Allahu” Ya ƙarasa yana ciro duba goma da uku ya miƙawa Jamila da ke kusa da shi, kana ya miƙe tsaye yana mana sallama. “Mu za mu tafi Allah ya sanyaya zuciyarku” Na yi zaton ya tafi hakan yasa na ɗago idona da ke cike da hawaye na kalli ƙofa, karaf idona sai cikin nasa, sauke na sa idon yayi ya wuce ƴan sanda na take masa baya. Na yi baƙin cikin haɗa ido da shi domin a yanzu ko mutuwa ban tsana kamar yadda na tsanesa ba, da saninsa aka yi ma mahaifina komai saboda ƴar'uwarsa har suka kashe shi. Bayan fitarsa Baba Sulaiman ya shigo yana mana bayanin yadda abun ya wakana lokacin da suka isa station ɗin. “Ko da muka je dpo baya nan, muka faɗawa ƴan sanda da ke nan, sai suka ce wai matarsa ce ta danka ta zo ta tafi da shi da ɗansa, Ayuba ya ce ai ba shi da ɗa namiji ma, kuma jiya mun zo nan kuka hana mana shi, sai suka ce bayan tafiyar mu matar da ɗansa suka zo suka tafi da shi, a gurin aka riƙa rigima wai su zayi ma ƙazafi, ɗayan su har da barazanar a barshi ya harbe mu, da suka ga abun na mu bana wasa ba ne yasa suka kira dpo, yana zuwa ya rufe su da faɗa, yasa aka tuɓe kayan ƴan sanda da suka yi aikin dare aka shigar da su cell, ya bamu dubu ashirin ɗin sai kuma ya biyo mu nan yana ƙara ba mu haƙuri” Baba Dahiru yaja tsaki. “Allah ya waddaran ƙasar nan, ai daga gani da saninsa aka yi komai, kuma babu matakin da zasu ɗauka, Allah dai ya isar ma ɗan'uwanmu kawai” Ni kaina jikina be bani za a ɗauki wani matakin ba, saboda na san mahaifina ba kowa ba ne a cikin unguwarmu balle kuma a gari. Maƙocin mu ne yayi ma Baba wanka saboda Inna ta kasa duk da kasancewar ta iya raunin zuciya be barta ta iya masa wanka ba, ban tabbatar da mai rai ba a bakin komai ya ke ba sai da aka ɗauko karaga aka saka gawar Baba aka fita da shi waje dan yi masa Sallah. Allahu akbar shine abunda na iya faɗa a zuciyata, na kwantar da kaina jikin Jidda hawaye na bin fuskata. Baba ya samu mutane sosai daman mutumen mutane ne, kuma wannan abun da ya faru ya ƙarawa mutane ƙaunarsa, har wasu na baranar idan ba a ɗauki mataki ba zasu ƙona station ɗin. Bayan an kai shi makocinsa suka dawo, mazan unguwa na ta shigowa suna mana gaisuwa, ciki har da Bilal da Babansa. Mutanen da suke zuwa mana gaisuwa kamar turo su ake, maza da mata ta ko'ina gaisuwa suke zuwa mana suna yi ma Baba addu'ah, maƙota kuma na ta kawo mana abinci, sai kuma gidan Baban gida da suka haɗa kuɗi duka siyo mana buhun shimkafa. Can da yamma Baba Sulaiman ya shigo yana tambayar mu ko ana binsa bashi. “Sai dai a tambaya guraren da yake zama amman Malam be cika cin bashi ba, shi dai bar shi da zuwa gidan ciyaman neman kuɗi” “Toh zamu bincika, Alhaji Sani ma ya zo nan yace yana muku gaisuwa” “Toh muna amsawa, Allah ya bada lada” Baba Sulaiman ne yayi ta ɗawainiya da mu tun da Baba ya rasu har ranar da aka yi addu'ah ukunsa. A daren ranar sai gidan ya zame nama wayan kamar Baba be taɓa wanzuwa a cikin gidan ba. Ina daga cikin ɗaki na hango Habiba ta ɗauki tabarma ta je ta shimfiɗa gurin da Baba yake zama ta kwanta. Tausayinta ne ya kama ni na unƙura na tashi naje kusa da ita na zauna, sai ta ɗago kai ta kalleni. “Nawwara” “Na'am” Na amsa mata ina danne tausayinta da ke raina. “Yanzu ya zan yi Baba ya yafe min? Na yi tunanin Baba zai rayu na roƙi gafararsa wata rana” Hannu na kai na ɗaga kanta na ɗora saman cinyata yayinda fuskarta ke fuskantar ƙofar ɗakin Inna, cikin ƙarfin hali da dauriya na soma mata magana. “Idan har Allah ya yafe miki, to Baba ma ya yafe miki, amman Habiba kin ga abunda kika aikata be amfana miki komai ba, tun da kuɗin ma be amfana komai ba, da kin yi haƙuri da baki siyar da mutuncinki ba” “Wallahi Nawwara ban ɗauka Baba zai mutu ba, a tunani zai rayu ne, kuma ni ina ganin kamar bamu da wata mafita sai wannan” “Da sata kika je kika yi Habiba ko kika yi bara, zai fi wannan abun da kika aikata” Shiru ta yi tana shesshekar kuka, yayinda ni nake hawaye. Can ƙasa-ƙasa ta soma magana. “Masu kuɗi suna da kuɗi Nawwara amman basa taimako, babu ruwansu da matsalar mu, idan mun ci babu ruwansu idan ba mu ci ba sai dai mu mutu” Ajiyar zuciya na sauke cike da gasgata zancen Habiba, haƙiƙa masu abu na da shi amman babu ruwansu da mu, ko ɗan abincin nan a zuba a abawa maƙota basa yi. Tashi ta yi zaune tana kallona, cikin kuka ta soma magana. “Nawwara sai da na je gidan Hajiya Murja na faɗa mata halin da muke ciki, har ƙarya na yi mata Inna na ce tace a ara mata kuɗi, ta ce min bata da kuɗi amman dai za ta yi ma mijinta magana. Da na fito sai na haɗu da ɗanta Mustapha a harabar gidan, shi ya kirani ya tambayeni miya kawo ni gidan, na faɗa masa sai ya ce zai bani kuɗin amman na masa alƙawarin duk abunda ya ce zan masa, na ce na yi, muka fita daga gidan gaba ɗaya, ya fiddo kuɗi da yawa a aljihunsa ya ƙirga dubu ashirin, har zai ba ni sai kuma ya fasa, ya ce sai idan na aminta na na bashi abunda ya ke so yanzu, na ce mi yake so, ya ce kawai taɓa jikina zai yi sai ya bani kuɗi shi ba iskanci zai yi da ni ba, har da min ratsuwa” Ta yi shiru. Can kuma sai ta cigaba. “Na ƙi yarda na nufo haɓyar gida, har na kawo sai kuma na ga ba mu da wata mafita sai wannan, dole tasa na koma, ko da na koma ya fita, sai nasa mai gadinsa ya kirashi a waya yace ina nemansa, sai yace na same shi gidansu killers, haka na je gidan na same shi shi kaɗai a gidan, sai... Sai... Sai. Ya ya.. Riƙani Wallahi Nawwara cewa kawai yayi zai taɓa jikina ya ba ni kuɗi, amman shi ne ya kira har da abokinsa suka.. Suka.. Suka yi.. Yi iskaci da ni...” Ba shiri na buɗe baki ina kallonta hawaye na bin fuskata. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 9⃣ “Miyasa ba ki masa ihu ba?” “Mi zai sa na yi masa bayan ni na kaina? Idan na masa ihu ba zai ba ni kuɗin ba kuma zai iya dukana ma” Kwantar da ita na yi jikina, ina kuka kamar yadda ita na take. Har dare ya bara muna zaune ni da ita a gurin muna aikin kuka. Wannan abu shi ya zame min jiki, a duka lokacin da na keɓe ni kaɗai na kan yi kukana sosai, saboda tausayin rayuwar Inna da Sakina da Jamila, sai kuma Habiba da kullum na ke zullumin idan ciki be shige ta ba. Yau ce ranar da Baba ya cika sati ɗayda rasuwa, har kuma tsawon lokacin ba mu sake jin wani abu daga gurin ƴan sandan ba, da yamma Baba Sulaiman ya samu Inna a gida yana faɗa mata gobe zasu je su ji halin da ake ciki, ita kan uffan bata iya ce musu ba, Bilal ya sallama a ƙofar gidan mu yana nemana. Cikin rashin kuzari na miƙe tsaye kasancewar Hijabin da na yi sallah da shi yana jikina ne. Jikine da ƙofa na same shi yana rumgume da hannayensa, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Sallama na fara masa kamin na miƙa masa gaisuwa. “Lafiya Ƙalau Nawancy ya haƙuri?” Ya tambaya ba tare da ya kalleni ba, har lokacin idonsa na kallon wasu gidajen da ke fuskarta na mu. “Mun gode Allah” “Nawancy kawai ina son na ɗan miki wasu tunatarwa ne akan abunda ya faru-” Na tsaleshi tun kamin ma ya fara. “Dan Allah Bilal ka karka so ma idan ba kuka na kake son ya dawo sabo ba” Ya juyo ya kalleni ido cikin ido. “Na daina Nawancy” Yaja wani dogon numfashi ya sauke yayinda ni kuma na ke tare ƙwalla da suka cika min ido. “Am sorry ban zo nan dan saka ki kuka ba, daman na zo ne na faɗa miki aiki da nace miki za a ɗauka a gurin aikinmu an fara” “Yaushe?” “Tun lokacin da abubuwan nan suka soma faruwa, kawai ban miki magana ba ne saboda ina ganin kamar be dace ba, gobe ma za a rufe, daman kwana goma ya bada” “Da gaske? Amman suna ɗauka masu ssce?” “Yeah sai dai aikinsu goge-goge da kuma mopping sai aikin kai documents ko ɗaukowa, maza kuma shara da buɗe ƙofa” “Indai zasu ɗauke ni zan iya Bilal, ina ake applying?” “A can gurin mu zakije ki bada takardun idan sun duba sun ga ka cancanta zasu nemaka ta waya” “Ƙarfe nawa ake zuwa?” “Goma” “Allah ya kaimu zan zo” Ya ɗaga min, sai ya miƙa min nokia hannunsa. “Wannan ki saka layinki saboda kira suke ba zuwa ba, ara miki na yi ba kyauta ba” Na san ya ce haka ne dan kawai na karɓa, duk da nima bana da wata mafitar da da wuce na karɓa ɗin, kasancewar babu waya a hannuna ga shi kuma number Jidda da nake badawa wani lokacin yanzu ta siyar. “Aro” Na faɗa yayinda na ke miƙa hannuna na karɓa. Murmushi ya yi “Yes aro, da kin fara aiki ki siya min sabuwa,ko da yake albashinku mai yawa ba ne” “Nawa ne?” “12k” “Ba laifi Bilal indai zasu biya ƙarshen wata” “On 25 suke biya, baki da matsala da wannan” “Allah dai yasa na samu” “Zaki samu inshallah” “Na gode” Na faɗa cike da ƙosawa da kuma son ya tafi, ba kasafai nake son ana ganin ina tsayuwa da shi ba, saboda ƴan sa idon unguwa. Shi kansa ya lura da hakan sai yayi min sallama ya tafi ni kuma na dawo cikin gida. Bayan Sallah isha'i nake labarwatawa Inna maganar aikin har ma na nuna mata wayar da Bilal ya bani. “Allah ya bada sa'a” Kawai tace min ta jingina da gini tana jan carbi, wanda hakan san be min daɗi ba, Habiba ce kawai ta zo ta zauna kusa da ni tana tambayar yadda aikin yake. A cikin dare na ɗauko tsohon layina na saka a wayar da Bilal ya ba ni. Washe gari ta kama ranar alhamis, ranar na tashi da azumi, daman duk litanin da alhasmis na kan yi azumi wani lokaci, musamman yanzu da ya zama ba komai na ke ci ba idana ban yi azuminba zan wuni da yunwa ne kawai. Misalin bakwai na safe na ɗumama su Jamila tuwon shinkafar da na yi musu jiya miyar kuka, Inna kuma na dama mata kunu ita da Habiba saboda shi kaɗai suke iya sha ko da rana da dare kuma ruwan tea. Bayaɓ na gama na je yani wanka na shirya ciki wata farar atamfa na saka baƙin Hijabi sai kuma tsofi takalmi waɗanda suka kasance baƙaƙe sannan na sake dawowa ɗakin Inna na same ta har lokacin tana shan kunu. Jaƙar da muke ajiye kayan karatu na buɗe na ɗauki takarduna na makaranta na buɗe ina duba tare da tunatar da Habiba maganar zuwa makaranta. “Ya kamata ace kin je makaranta gobe ko kuma monday nan mai zuwa, yau kusan kwana nawa baki je ba, kuma jarabawa kuke fa, gashi rashin zuwanki ya haddasa har su Sakina sun daina zuwa” Ta turo baki. “Ni ba zan sake zuwa ba, karanta mo zai tsinana min, ko na yi karatu ba zan wuce babbar makaranta ba, kema da kike da ssce min kika amfana da shi” Murmushi na yi, nasan tana tunanin babu wanda zai iya ɗaukar ɗawainiyarta ne da har zata yi babbar makarantar gaba da secondry, tun da karatun ya zama sai da kuɗi. “Na miki alƙawari zan ɗauki nauyin karatun ki, ke dai ki dage ki cigaba da wannan ki kammala sai kije babbar makaranta” “Ta yaya?” Ta tambaya tana hararata irin bata yarda ɗin nan ba. “Wannan aikin idan na samu zan riƙa aje wani abu daga albashina saboda ke Habiba” “To Hajiya bari har ki samu” Ta faɗa tana ɗaukar Noor ta ɗora saman ƙafafunta. Ni kuma na yi murmushi na kalli Inna na ce “Ni zan ta fi Inna” Fillo ta ɗaga ta ɗauko ɗari biyu ta miƙa min. “Ki hau Napep, karki manta da nasihar da mahaifinki yake miki akan mutuncinki Nawwara” “In'sha Allahu” Na tashi cikin jiki ba ƙwari na fita. Yau kan sai da na yi nisa sosai sannan na samu Napep, kai tsaye na kwatanta masa inda zai kaini wato koko road. Nesa da Company ya sauke ni na bashi kuɗinsa, sannan na aikawa Bilal please call me kasancewar babu ko na flashing a wayar, sai ga shi ya kirani cikin ƴan mituna, na sanar masa ina kusa da gurin. “Ki ƙaraso mana gani nan fitowa” Bayan na amsa masa da okay na doshi company gaba sai dukan uku-uku yake, wata ƙila ko dan ban taɓa zuwa babban kamfani kamar wannan ba oho.. *ONE-ON-ONE LIMITLESS* _One of the Largest Metal Companies in the world_ A hankali na karanta, ina ƙara faɗaɗa ido ga kallon ƙofar gate ɗin company ma da ta kasancewa ƙatuwa. ‘Anya za su ɗauke ni aiki kuwa’ Na tambayi kaina ina kallon securities da ke bakin gate ɗin sanye da uniform kamar na ƴan police sai dai na su farar rigace sai baƙin wando. A ƴar ƙaramar ƙofar da ke gefen gate ɗin na hango Bilal ya fito sai sauri yake ya doso inda na ke. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣0⃣ Na ɗan faɗaɗa fuskata da murmushi kaɗan na kuma gyara tsuwata. Shi ko haƙoransa a watse har ya ƙaraso kusa da ni. “Miyasa baki shiga ciki?” “Waɗannan jibgin securities ai ba za su bar ni na wuce ba” “Haka zuciyarki ta nuna miki, ai su aikinsu tsaro ba hana mutane shiga ba, kin tsorata ne?” “Sosai ma” Sai kawai yasa min dariya har da tintsirawa. “Haba sai ka ce wacce bata zauna ƙasashen turawa ba, ai zaki saba da su ne, amman fa zan yi fama da kishi dan suna sakewa da mata sosai” “Kishi?” Na tambaya cike da mamakin kalaminsa, haka wani lokacin ya ke sakar min magana kamar mai suɓul da baka. Sai kawai ya shafa fuskarsa be bani amsa ba ya zuma hannayensa aljihu ya kama hanya. “Mu je” Kai kawai na kaɗa, na bi bayansa yana gaba. Faɗuwar gabana ne ya ƙaru yayinda da muka doshi ƙaton gate ɗin nan, yana isa suka buɗe masa ƙofar da biyo ɗazu ya wuce suna zolayarsa ni kuma ina bayansa. Tafiya mika mai nisa sosai sannan muka isa katafaren kamfanin, hakan ya bani damar kallon gurare da dama a harabar gurin, daga dama wani ɗan madaidaicin guri ne mai kamar ma'aikata an rubuta masa RESTAURANT, sai kuma wani ƙaranin gate dake can hagu an rubuta masa PARKING SPACE, a can gefen gurin kuma an wani gate ne mai zagaye da falawoyi an rubuta masa GARDEN GROVE. Duka cikin manyan harufa masu ƙyali da burgewa. “Gurin nan na da girma sosai Bilal” Na faɗa ina kallon gaban kamfanin da duk madubi har takalminka kana gani a ciki da duk wanda zai zo bayanka, gida sama ne mai hawa biyar, na gane haka ne ta windows ɗin dana ƙira, hawa-hawa har biyar. “Yeah kin ga can gurin cin abinci ne, can kuma duk wani mai abun hawa can zai aje shi, garden kuma gurin hutawa ne ko kuma fira ko meeting haka, kamar idan wanda ba ɗan kamfaninba ya zo ganinka zaku iya tsayawa a can ku yi firarku” Ya ƙarasa yana nunnuna min guraren, ni kan sai bawa idona abincin na ke, gaba ɗaya na zama baƙauya sam ba zaka taɓa cewa Nawwara ce wacce ta taɓa zama a London ba, ko da yake shekaru da yawa yanzu na zama baƙauya. Ƙofa biyu ce a gurin ko wacce ƙatowa, ɗaya a dama ɗaya a hagu mutane na ga suna ta shiga da damar masu fitowa kuma na fita ta hagun, muna ƙarasawa sai ƙofar ta buɗe mana da kanta a ƙasan gurin inda mutun zai ɗora ƙafarsa an rubuta WELCOME ɗa manyan haruffa masu ƙyali. Tsaye na yi ina kallon yadda mutane ke zirga-zirga ba dan ina tare da Bilal ba dan zan iya rantsewa wata ƙaramar duniya ce na shigo, kamin ka shigo fuskar kamfanin duk madubi ce cikinsa kuma komai kamar zinari yake, ga wasu manya-manyan plasma da ke tallata abubuwan da kamfanin ke yi. Reception ne ke facing ɗin duk wanda ya shigo, ma'aikatan gurin na sanye da suit maza da mata. a dama da Reception ɗin manya lifted ne guda huɗu, a hagu kuma Excavator ne babban guda biyu na hawa da kuma na sauka, a can gefe kuma wani ƙaton guri ne mai kamar falo an jera ƙasaitatun kujeru ga plasma a gurin, ko ina security camera ne a gurin, ac ta ko'ina ratsa jikin mutum ya ke. “Nawancy...” Kiran da Bilal ya yi min ne ya dawo da ni hankalina, har na kalli inda ya dosa, na rufa masa baya da sauri. lifted da ke farko ya danna, sai da muka yi tsayin minti biyu zuwa uku sannan ta buɗe mutun uku daga cikin lifted suka fito sannan muka shiga, bayan mun shiga muka juyo muna fuskantar ƙofar sai ya kai hannunsa a maɓallan da ke gurin ya danna number four, sai lifted ta rufe. “Wow...” Na furta ina lumshe ido. Sai kawai Bilal yasa min dariya, har da ciro wayarsa yana ƙoƙarin min video. Lokacin da lifted ta buɗe mun tarar wasu na jiran mu fito ta su shiga. A nan na ma ashe wata duniyar ce, da komai na ta na glass ne, mutane sun kasu kashi-kashi, wasu na ta aikin akan documents wasu na gaban computer. “Haka aikin na ku ya ke?” “Yeah nan na masu diploma ne, kin san mu NCE ne da mu muna hawa na biyu” Yana min maganar muna cigaba da tafiya har muka isa wani ƙofar wacce kana tsinkayar wanda ke ciki shi ma kuma yana tsinkayarka. Buɗe min yayi na shiga sannan shi ma ya shiga ya nuna min gurin zama, yana mikawa wanda ke gaban conputer hannu su gaisa. “Manir” “Ya Bil ya aikin?” “Ba daɗi, ga baƙuwar da na ce maka zata kawo takardunta” Wanda aka kira da Manir ɗin ya juyo yana min wani kallo baki a sake. “Wow Welcome Ma'am, gaskiya tana da kyau sosai gata fara mashallah” Bilal ya shafa yancinsa yana satar kallona fuskarsa ɗauke da murmushi, yanayin yadda Manir ɗin ya yi min ya karantar da ni kamar akwai abunda Bilal ɗin ya ce masa a kaina. “Sannu ya aiki?” “Hooooo i beg see golden eyes” Ya furta yana ba Bilal hannu su taɓe. Na yi ma Bilal wani kallo da shi kansa ya san ba na lafiya ba ne, sai kawai ya miƙa hannu ya karɓi takardun hannuna ya miƙa masa. “Gashi ka shigar da bayanan mu zamu wuce” Ya miƙa hannu ya karɓa yana dariya. “Okay ba matsala, Allah ya sanya alheri ya tsare, perfect match” Har na buɗe baki na ce wani abu sai Bilal ya yi saurin buɗe ƙofar. “Muje Nawancy” A dole tasa na miƙe tsaye na nufi ƙofa, ƙamin na ƙarasa sai yayi saurin tare ni. “Sorry Nawancy bari Oga ya wuce” “Wane Oga?” “Mai kamfanin” Jin hakan yasa ni miƙa wuya dan na hango mai tarin wannan dukiyar, sai dai ban yi sa'ar ba dan har ya shige Lifted. A nan Bilal ya ba ni hanya na fito muka jera muka nufi lifted da muka shigo ɗazu, ƙashim turaren da na ji ya sani faɗuwar gaban da har ya haddasa min ciwon kai a take, saboda na tsani wannan ƙamshin kamar yadda na tsani mutuwa, jin sunan turaren kaɗai zai iya haddasa min hawan jini saboda tunawa da mai shi. “Wannan da ya wuce ogan mu ne, mahaifinsa ne ke da wannan kamfanin, shi baya son idan na zo a lifted kai ma ka zo, sai dai kowa ya ja baya har sai ya zaɓi wacce zai shiga idan ya shiga sannan kowa ya shiga, kuma baya son yaga mutun ba a gurin aikinsa ba, abu kaɗan kan iya sakawa ya ƙoreka aiki, ba shi baya ɗaukar ƙaddara idan kika fasa masa kofi sai an cire cikin albashinki, ba a latti zuwa gurin aiki, minti ɗaya kika ƙara daga lokacin da kike zuwa aiki sai an rubuta, da kin yi haka sau goma sha biyu zai koreki, idan wata matsalar ta same ki sai kin faɗi dan wuri ki rubuta takardarki ki aika idan ba haka ba zai koreki” “Kai amman ya cika tsauri, sai kace turai” “Gashi ba shi da dariya, kuma baya son kallo” Na haɗe yawu ina jijina lamarinsa, domin nima kaina bana son kallo. Ya cigaba da ba ni labarin kamfanin da kuma yadda suke abubuwansu har muka iso bakin ti-ti. “Kamfani da ke saffara duk wani abu da shafi ƙarfe, kuma kamfani da ke siye da sai da hannu jari, ga kwangiloli kala-kala kamfanin yana yi, kuma akwai wasu ƙananan kamfaninni da suke ƙarƙashin kulawarsa” “Ayyah za su ɗauke ni aiki kuwa?” “Za su ɗauke ki kan, amman sai kin yi haƙuri da kuma kin jure ba a makara ba a ɗauke ƙafa, kuma ba a kuskure” “I will try” Sama-sama yake ta labarta min abubuwan akan kamfanin, kamin ya tarar min Napep, ya faɗa masa inda zai kai ni, ya miƙa masa dari biyar ya ce ya bani ragowar canji. Ni kan jikina har rawa yake na isa gida na labartawa Habiba abunda idanuwana suka gani da kuma ji. My page is depend on your comments, ku da kuke cewa ina short page don't blame me, blame your comments 😂 Idan an gama karatu sai ku zo ki siya garin ɗan wake, da kuma ƙwaryar kwaliyar ɗaki ko falo da faifai duk domin ƙawata ɗakinki. Ga mai sha'awa sai a ku nemi number nan 08036126660 muna aikawa ko'ina a arewa cin ƙasar nan. Tau Lemme come and be going 🚶.... *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣1⃣ Tun da na baro kamfanin sai komai na titi ya riƙa burgeni, idanuwana har yanzu kallon komai suke kamar kamfanin wata ƙila saboda labarin da ke ƙumshe a bakina ina son na labarta musu Habiba da Inna yadda gurin ya ke da kuma aikin shi kansa. Tunawa da zancen Bilal ya sani dariya tare da furta sunansa a fili. “Bilal kenan wai zan sha fama da kishi” Ajiya zuciya na sauke ina tuna irin kallon da Mutune yake min ɗazu, lallai da akwai abunda Bilal ya faɗa masa akaina. “Sauke ni a nan” Na faɗa ganin Mai Napep ɗin yana ƙoƙari wucewa ta har cikin unguwarmu, ba kasafai na ke son napep ko achaɓa ya sauke ni ƙofar gida ba. “Ba ni canjin” Ya buɗe akwatinsa na kuɗi dake cikin napep ɗin ya ɗauko ɗari uku ya miƙa min, ni ko na ƙi karɓa. “Haba Malam ya zaka ɗauko ni daga Koko road ka kawo nan kawo nan arƙila kuma ka ce zaka cire har ɗari biyu” “Haba Hajiya kuɗin nan fa Mai gidane ya bada su ba ke ba, miyasa ku mata kuke son tauye mu ne wai” Hannu ya kai ya ɗauko naira hansin ya miƙa min, ina ƙoƙarin karɓa na ji takun mutun a bayana yana katsawa mai napep ɗin tsawa. “Kai wane irin mahaukaci ne zaka kawo mashin ɗinka a nan ka tarewa mutane hanya nonsense mtssssss” Juyowar da zan yi sai idanuwana suka yi arba da Mustapha, mutun na biyu da na tsana a duniya, ba da ni yake maganar ba amman sai na ji kamar da ni yake saboda tsanar da na yi masa da kuma sanin yadda baya ɗaukar kowa da mutuncin a unguwarmu. Tassss na wanke masa fuska da mari sannan na katsa mashi tsawa kamar wata uwarshi. “Haka kuke ba ku ganin kowa da mutuncin, kowa a gurinku wulaƙantaccene, uban kowa baka ganin mutuncinsa a unguwarnan, sha-sha-sha marar tarbiya” Mamaki da al'ajab ya kafe shi a gurin ya kasa ko da motsa idonsa balle ya yi wani motsi. Ni ko a zuciyata tsoro fal marata har ta cika da fitsari, amman a zahiri kallonshi na ke kamar yadda shi ma yake kallona sam ba zaka kalli fuskata ka gano akwai alamar tsoro a tare da ni ba. Matsowa ya yi kusa da ni ya ɗaga yatsansa ya nuna kamar zai yi magana sai kuma ya cige bakinsa ya yi ƙwafa ya juya koma cikin motarsa, ribas ya yi ya koma inda ya fito da alama ya fasa shiga unguwar ma. Sai a lokacin na samu sa'idar sauke ajiyar zuciya na juyo gurin mai Napep ɗin na karɓi hansin ɗin da yake miƙa min. “Kai amman ke wannan ƴar bala'i ce, Allah ya raba mu lafiya” Ba shi kaɗai ba ko mutanen da ke kusa da mu sun yi mamakin yadda na wanke mutun kamar Mustapha da mari, ni ba mafaɗaciya ba, kuma kowa yasan halin Mustapha a unguwarmu, ni kaina sai a yanzu na ke jin kamar ba ni ce na mareshi ba, wata ƙila kuma saboda na tsane shi ne shiyasa har idona ya rufe haka. Sai dai mamakina yadda ya ƙyale ni be rama ba, yaron da harararsa ma baka isa ka yi ba saboda yana taƙama ubansa wani ne a cikin garin sokoto. Da wannan tunanin da kuma mamakin dalilin ƙyaleni da ya yi na iso gida, duk wani ɗuki da na ke na labartawa su Inna gurin aikin sai ya kau saboda wannan abun da ya faru tsakanina da Mustapha ya tsaya min a rai. Ko da na shiga na samu Habiba tana da fa shimkafa da wake, Sakina na daka barkono (Yaji) Inna kuma na ɗaki kamar kullum. “Har kin dawo ashe ba a daɗewa” Cewar Habiba tana ƙara tura itacen murhu. “Eh kin san da yake ba aikin ba ne, takardun ne kawai za a kai” “Allah ya baki sa'a ya sa su ɗauke ki” “Amman Babban Kamfanine Habiba, ba lallai ne su ɗauke ni aiki ba” “Zan riƙa tufa musu fatiha a tsakar dare” Na yi murmushi, kana na doshi ɗakinmu dan cire mayafina. Bayan na fito na doshi ɗakin Inna, ita na fara labartawa yadda kamfanin yake kamin Habiba ta shigo mana da abinci mu soma ci gaba ɗayanmu, ko lokacin da Baba na dai baya ƙwanar ya ga mun raba abinci daga manyan mu har ƙanana, sai dai kowa ya wanke hannunsa a ci a guri ɗaya, yana yawan faɗa mana cin abinci tare yana saka zumuncin da nishaɗi da kuma son juna, kuma ta nan zaka iya karantar halin mutun da lurar shi irin cin abincin da ya dace ya yi. Hakan yasa suka muka saba bama iya raba abinci inda wanda za a ci ne, ko da ɗayan mu baya nan sai mun jira ya zo ko da kuwa Jamila ce ita da ta kasance ƙaramarmu, balle kuma Noor da ko ina muka je baya cin abinci sai da ni matuƙar ina gurin. Na bijiro musu da zancen marin da na yi ma Mustapha, a take hankali Inna da Habiba ya tashi har ma da Sakina “Ina ruwanki Nawwara ai ba da ke yake ba, kuma ko da ke yake ai kya shafa kanki lafiya ki bashi haƙuri, yanzu wannan abun da ya faru da mahaifinku be isheki ishara ba? So kike ki ƙara jawo min wani?” Cewar Inna. Habiba kuma ta ɗora da cewar “Da ma ba ki mareshi ba Nawwara, kar ya ce kuma zai miki wani abun, kin san halinsa idan ma ya ƙyale iyayensa ba za su ƙyale ba” Ganin yadda hankalin Inna ya tashi ƴasa ni yin ƙarya. “Ke wasa na ke daman kawai ina son naga yadda zaku yi ne, ban mare shi ba kuma da ya zo yana faɗa da mai Napep ɗin ma na bashi haƙuri” “Da Gaske?” Na gyaɗawa Inna kai ina dariya saboda ta yarda. Sai dai na lura da Habiba kamar bata yarda da ni ba, har muka gama cin abincin ban ga yanayin Inna ya dawo dai-dai ba. Bayan sallah la'asar Jidda ta shigo gidanmu, a lokacin ina zaune waje ni da Habiba Inna kuma tana ɗaki, Sakina da Noor da Jamila suna islamiya. Kusa da ni ta zauna ina kallin bakinta na san da akwai magana, sai dai tana tsoron furtawa ganin Habiba na kusa da ni. Murmushi na yi na ce “Saki jikinki Jidda faɗa min ko minene ai Habiba kamar ni ce, dukan abunda kika sani nawa to Habiba ta rigaki saninsa, abunda duk na ke iya faɗa miki to Habiba ce ta fi cancanta na fara faɗawa, ni da ita abu ɗaya ne bama ɓoyewa juna abu” Sai ta yi ƴar dariya. “To ai ban sani ba ko gidan ba su ji ba ne” “Minene?” “Cewa aka yi wai kin mari Mustapha” Habiba ta yi min wani kallo tana jiran ta ji abunda zai fito bakina. “Ba wai ba ne na mare shi ɗin ɗazu” Habiba ta riƙe baki “Ashe da gaske ne” “Na ɓoye ne saboda na ga kamar ran Inna ya ɓace” Jidda ta kama hannuna. “Ke ko miya kaiki? Miya haɗa ku?” Shiru na yi ina tunanin irin amsar da zan bawa Jidda, domin bata san shine mutumen da ya yaga rigar mutuncin Habiba ba, a lokacin da abun ya faru ban labarta mata ko wanene ba kawai dai na faɗa mata cewar Habiba ta siyar da mutuncinta ta kawo dubu ashirin. “Ba komai kawai wai dan Mai Napep ya tsaya a bakin hanya shine ya zo yana mana rashin mutunci, ni kuma na mare shi” “Aka ce mari har uku wai, ai ƙara da kuka mareshi basa ganin mutuncin kowa a unguwar nan” Na zaro ido “Ɗaya ne kaji mutane da canja magana kuma, wai yanzu zancen nan har ya kai miki” “Wallahi ina zaune gida aka kawo min shi, wai ƙawata ta mari Mustapha, ai ko ni kika mara sai zancen ya zagaye unguwa balle kuma Mustapha guda” Dariya na yi, domin a yanzu duk wani tsoro da ke raina na ɗazu ya gushe. Labarin kamfanin na ɗaukowa Jidda ina ta faɗa mata yadda abubuwan suka, ita kanta da bata je gurin ba sai da abubuwan suka burgeta saboda yadda na tsaya na tsara mata komai kamar anyi a gabanta. Har muka ci firarmu da Jidda muka suɗe Habiba bata saka bakiba, Jidda kuma bata bar gidanmu ba sai da ta yi sallah magariba sannan na rakata sannan na dawo. Shikafar ɗazun na ɗauko na ɗumana na zuba mana muka zauna gaba ɗayan mu muka ci, ban da Inna da daman nata daban ake zuba mata balle kuma yau da ta ce ba zata ci ba. Muna cikin cin abincin nokiyar da ke gefena ta yi ringing, abun ka da wanda ya daɗe ba shi da waya tun da na saka layin ba a taɓa kirana da shi ba. Number Waje ma'ana ba nunber nigeriya ba ce, cikin rawar jikina na ɗauka dan nasan mace ɗaya zata iya kira na da wannan layin wato Salima “Hello Ƙawata” Sai ta amsa min daga ɗayan ɓangaren. “Ƴar'uwata, kin jefar da ni kullum ina kiranki bata shiga” “Wallahi bana da waya ne a yanzu, wannan ma ara min aka yi na saka layina” “Allah sarki ya gida? Ina Baba da Inna?” “Sai dai Inna tana nan lafiya ƙalau, Baba kan Allah ya yi ikonshi” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yaushe? Miya same shi” “Rashin lafiya kwana biyu” Na yi ƙarya saboda ba kowa zaka iya faɗawa dalilin mutuwar Baba ya gasgata cewar Baba be yi satar ba, duba da yadda muke fama da rashi. Bayan ta yi min gaisuwa ta yi ma Inna sannan ta yi ma Habiba, Sakina da Jamila sannan suka maido min da wayar. “Kin rasa RAI BIYU masu muhimmanci Nawwara mutuwa mai ɗaci , kin rasa Abban Noor yanzu kuma Babanki Allah ya baki ikon ɗaukar wannan lamarin” “Amin Salima na gode” “Inshallah idan na dawo Nigeria zan zo har nan na yi miki gaisuwa” “To Allah ya yarda” Daga haka muka yi sallama, na amsa mata da to ne kawai ba dan na gamsu zata zo ɗin ba, duk tsawon zaman da muka yi da ita bata taɓa tako ƙafarta sokoto ba ai ba zata taɓa zuwa ba. Da gudu Noor ya zo gurin yana ƙoƙarin karɓar wayar. “Momy waya baki waya? Momy kira min Gwaggota Murja kin ji” Haka yake idonsa idon ganin waya, baya da magana sai ta a kira masa Murja wato Ƙanwar mijina wacce ya shaƙu da ita sosai. “An ya ma sun ji maganar rasuwar baban ku kuwa?” Maganar Inna tasa na ɗago kai na kalleta. “Ina zasu ji tun da ba a nan suke ba kuma babu waya a lokacin” “Ya kamata dai kan ki faɗa mata” “Bari na mata please Call me dan ba ni da kati gaskiya” A take na aikama mata please Call, ko minti biyu ba a ƙara ba sai gata ta kirani, mun gaisa sosai sannan na bata Inna, ita ta labarta mata cewar Baban mu ya rasu, ta shiga ɗimuwa da kiɗima sosai, har da kukanta kamar Babanta ne ya rasu. Bayan ta yi min gaisuwa ta faɗa min zata shaedawa sauran ƴan'uwan margayi Sadiq zasu zo har sokoto su yi min gaisuwa, duk ƙoƙarin dakatar da ita da na yi akan zuwan sai ta nuna min sam ba zai yiyu sai ta zo, ai daga sokoto zuwa Kebbi ba wani nisa ba ne. Sun daɗe suna waya da Noor sannan bashi yaranta suka yi magana sai ta kashe. Takwas da rabi wayar Bilal ta shigo, ina ɗauka ya shaida min yana waje. Sai da na faɗawa Inna sannan na tashi na saka Hijab ɗina na fita. Jikingine da ƙofar gida na same shi, ina masa sallama ya amsa fuskarsa da murmushi har wani ƙyali take. “Nawancy” “Bilal” Sai yasa dariya. “Ina jin daɗin ki kira sunana yana mugun daɗi a bakinki” Na yi murmushi ina rausayar da kai. Bayan mun gaisa ya bijiro min da fira cikin har da zancen marin da na yi Mustapha, sai na nuna masa ya yi min ba dai-dai ba ne shiyasa. Sai tara da rabi muka yi sallama. WASHE GARI.... Yau kan ba laifi dukanmu mun tashi cikin walwala, Sakina da Jamila tuni suka wuce makaranta, Habiba ma shirin makarantar ta ke, ni kuma ina gyaran gida, Inna kuma na ɗaki tana bachin safe. “Nawwara canjin kuɗin Koko yana nan ƙarƙashin fillo, Inna ta ce a siye ruwa” Cewar Habiba tana tsaye riƙe da littafan makarantarta. “Yau Fanfan ba zai zo ba ne hala?” “Yau kwana biyu be zo ba, ruwan da muke amfani da su sun ƙare, ƙara a siya da wuri idan ma ya zo kin ga kaɗan kawai za mu ɗebo” “Allah ya bada sa'ah” “Amin na tafi” Fitarta da kamar minti biyar, wata matashiyar yarinya ta shigo sanye da dogowar rigar atamfa da wani minafukin gyale a kafaɗa, sallama ta fara yi na amsa mata. “Assalamu alaikum” “Wa'alaikissalam” “Sannu ina kwana?” “Lafiya ƙalau” “Dan Allah nan ne gidan Musa Kafinta?” “Nan ne, lafiya?” “Lafiya ƙalau, Sunana Shafa Ibrahim ni ƴar jarida ce ina aiki da jaridar Arewa a yau, tare da abokin aikina na ke ina son mu tattauna da iyalansa ne akan abunda ya faru” Ta ƙarasa tana miƙa min katin shedarta. CANDY ✍️ *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy RIJF Mama A'i, ke da kika tafi ba ki yi sauri ba, mu da mika rage ba mu yi nawa ba. Allah kasa mutuwa ta zama hutu gareki Allah ya miki rahama ya gafarta miki kurakuranki. I will never forget you. Allah kayi mana kyakkyawan ƙarshe. 1⃣2⃣ Na kai hannu na karɓi cati na duba, sunanta ne da kuma hotonta a jikin catin hakan ya tabbatar min da cewar lallai ƴar jaridar ƙwarai ce. Na mayar mata da katinta. “Ba mu san komai a kai ba, waya faɗa miki nan gurin kuma?” “Jama'a ne suka kwatanta min, kuma na tabbatar min da cewar ƴan sanda suka duki margayin har ya mutu” Na nuna mata ƙofar fita raina a ɓace. “Fita ki bar mana gida, mutanen da suka labarta miki abunda ya faru ki je can su ƙarasa miki, mu bamu san komai ba” “Haba Baiwar Allah...” “Ki fita Wallahi ko na sa taɓarya na fasa miki kai yanzu” Da gudu ta juya ta fice daga gidan. Ni kuma na cigaba da aikina zuciya na zafi har na gama gyara komai, ciki na shiga na samu Inna har lokacin tana bachi Hijabina na saka na ɗauki kuɗin da suke ƙarƙashin filo na fita neman mai ruwa. Karo na ci da Dpo dake tsaye jikin motarsa yana kallon ƙofar gidanmu, ban gama tabbatar da shi ɗin ne ko a'a ba saboda yau a cikin kayan gida yake. “Assalamu Alaikum Malama” A maimakon na amsa masa sai kawai na watsa masa wata muguwar harara. “Ni ba gurinki na zo ba, matar gidan na ke son magana da ita” “Bachi ta ke” “Ki taimaka ki tashe ta kuma ki nema minlH izinin shiga cikin gidan” “Saboda?” Ya gyara tsayuwarsa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Na ga dai ke ba ƴar jarida ba ce, be kamata ki tsare ni kina min irin waɗannan tambayoyin ba, beside ni ba gurinki na zo ba gurin Inna na zo” “Gida mallakinmu, mahaifiya bachi take baƙincikin kashe mahaifinmu da ka yi take ragewa saboda hawan jini” Ban tsaya jiran abunda zai ce ba, na cigaba ta tafiyata. Sai ya zagayo ta gaban motarsa ya sha gabana, cikin ɗaga murya ya fara magana. “Miyasa kuke rayawa zuciyarku cewa ni na kashe mahaifinki? Mi mahaifinki ya yi min da zan kasheshi? Idan na kashe shi wace riba zan ci?” Nima cikin zafin rai na zaburo masa. “Saboda zalincin ƴan sanda, yayarka ta laƙaba masa sata bayan kuma be sata ba, kuka yi ta dukansa har sai da kuka kasheshi akan kawai sai ya amsa laifinsa, wannan ba halinku ba ne? Saboda yayarka tana taƙamar kai dpo ne yasa kuka wulaƙanta mana mahaifi cika tozarta shi sannan kuka ɗauki gawa kuka kawo mana, yanzu kuma kana raina mana hankali har kana wasa da hankalinmu” Ya matso kusa da ni ya nuna ni da yatsa yana magana cikin jin zafin kalaman da na yi masa, har haƙoransa na ƙasa na haɗuwa da na sama yana cizonsu tare da zaro min ido. “Karki sake saka bakinki a akan aikina, karki sake yin furucin akan abunda kika jahilta, i hate nonsense, na zo nan ne dan na faɗa muku karku kuskura bada bayanin mutuwar mahaifinku ga ƴan jarida” Na yi baya-baya ina hawaye, tare da murmushin da ya fi kuka ciwo. “Kamin ta zo nan ashe sai da ta bi ta gurinka, ka yi nasara ban faɗa mata komai ba, amman yanzu kan ni zan tara ƴan jarida da kaina na labarta musu irin zaluncin da kuka mana, wato so kuka a rufa muku asiri kar kowa ya ji ko? Ta yadda muma zaku samu damar ɓatar da mu, Wallahi Allah ba zai barku ba azzalumai macuta-” Ya ƙara matsowa kusa da ni har sai da na matsa baya. “Ki tara ƴan jarida, ki faɗa muku ƴan sanda sun kama mahaifinki sun masa duka har ya mutu, za su tambaye ki dalilin hakan, kuma ki faɗa muku komai karki ɓoye, ni da ke za a ga waye zai ji kunya, idan ba ki yi haka ba to baki haifu ba!” Yana kaiwa nan ya haɗa hannunsa na dama da na hagu ta taɓa saitin fuskata, har sai da na rufe ido. Sannan ya buɗe motarsa ƙirar 406 ya shiga ya fisgeta kamar zai tashi sama, ko da na ɓuɗe idona ƙurar motar kawai na gani hawaye ya sauko daga idona, lallai wannan shi ne a dakika a hana kuka, kuma a mareka a ƙwace maka jaka! Kasa zuwa kiran mai ruwan na yi saboda kuka da ya ci ƙarfina, na koma cikin gida da sauri. Bana son na tashi Inna balle har ta ga hawayena hakan yasa na shige ɗakinmu na kwanta saman tabarma, na ci kuka na sai da na ƙoshi sannan bachi ya yi gaba da ni. Motsin shigowar su Habiba ne ya tasheni daga dogon banchin da ya ɗaukeni, babu komai a mafarkina sai wacan tashin hankalin da ya faru, Baba ne kawai na ke ta gani sai kuma irin zamantewar da muka yi a gidan kamin rasuwarsa. Ko da na fito na samu Inna ta farka har suna fira da Habiba ma da ke cire safa. “Nawwara kin tashi?” Inna ta tambaya tana kallona, sai na zauna bakin ƙofar ina amsa mata. “Eh ashe rana ta yi” “Tun ɗazu su Noor suka dawo na ce kar ya tasheki kin gaji da yawa, ƙara ki samu bachi ki ɗan huta” Kallo ɗaya Habiba ta yi min ta ɗauke kai, kamar ba ta ganni ba, hakan ya karatar da ni da akwai wani abu a ƙasa, sai dai ban ce da ita komai ba na tashi na ɗauki bula na shiga banɗaki, bayan na fito na yi alwala na shiga ɗakinmu dan Sallah. A ciki na sameta tana ɗaura zane, naje kusa da ita na tsaya. “Habiba kamar akwai abunda ya ke damunki?” Ta ɗaga kai ta kalleni a maimakon ta yi magana sai ta kawar da kai ta soma magana. “Nawwara ɗazu da zanje makaranta na haɗu da Mustapha, na tsayarda shi na bashi haƙuri akan abunda kika masa, sai yake tambayata ke yayata na ce eh, shine ya ce wai tun da yake a rayuwarshi wata mace bata taɓa ɗaga hannu taareshi ba ko da uwarsa ce sai ke, akan me zaki mareshi, bayan da ke yake magana ba, kawai ya buga motarsa ya yi tafiyarsa. Nawwara miyasa kika mareshi? Zaki ƙara ja mana matsala” “Shiyasa kike jin haushi na? Babu abunda zai faru Habiba, kuma bari kiji na faɗa miki ko da Mustapha zai yanka ni ya dafa namana ya soma ya ci, ba zan bashi haƙuri ba, ke ma kuma kinyi kuskure da kika tunkare shi kika ba shi haƙuri wannan ba halinki ba ne Habiba” “To ya kike son na yi? Bamu da wani gata sai na Allah mutane kamar jiranmu suke su yi mana abu, yanzu idan wani abu ya sake samun family mu ban san ya zan yi ba, Allah kasa ni ce zan fara bin Baba na gaji da wannan rayuwar” Ta fashe da kuka. Ni kuma na riƙeta muka zauna tare ina rarrashinta. “Babu abunda zai sake faruwa inshallahu, na miki alƙawari, share hawayenki kar Inna ta ji” Ta ɗaga min kai tana share hawayen. Haka muka zauna cikin jiran tsamanin abunda zai same ni daga Mustapha domin na san ba zai bar ni ba, Habiba ma kullum cikin tunanin wannan abun take, bata ƙaunar ko waje na leƙa saboda gani take kamar zan iya haɗuwa da shi ya yi min wani abu. Wasa-wasa muka kwashe sati uku babu abunda ya faru sai dai tunanin abun zai faru ya hanani sukuni ni da Habiba, a cikin satin ne su Murja da Hajiya Umaima da Hasana suka zo min gaisuwa tun ɗaga Kebbi. Wato Yayar tsohon mijina da kuma ƙannensa, mahaifiyarsa kuma ta yi min aike ni da Noor. Ba su kwana ba ranar da suka zo ranar suka koma bayan mun yi ma Noor tsaraɓar kayan maƙulashe da kuma tufafi, Inna kuma suka kawo mata atamfa da buhun kishinka ƙarami. Ranar da suka kwana biyu da tafiya ina zaune tsakar gida misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe wayata ta yi ƙara alamar saƙo, ban kulata ba dan na daina ɗaukin aikin a yanzu tunani ba zan samu ba, tun da kullum ina sa ran ganin saƙon kamfanin amman sai na samu saƙon mtn. Sai da na gaji da kwancin da nake na tashi zaune ya miƙa hannu na ɗauki wayar da ke kusa da ni ina dubawa. Ina ganin sunan Kamfanin One-On-One jikina ya fara rawa, cikin zumuɗi na buɗe saƙon Congratulations na ga an rubuta a sama.ban iya tsayawa karanta sauran ba na buga tsalle ina ihun daɗi. WHO IS READY FOR THE NEXT CHAPTER? I can't wait to see Nawwara in One-On-One limitless company. 😍 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣3⃣ Ihun da na yi ne yasa Inna fitowa daga ɗaki da sauri tana kallona. “Na samu aikin Inna sun ɗauke ni” Murmushin haukan da na ke ta yi, tana girgiza kai for first time bayan rasuwar mahaifinmu yau na ga murmushin Inna. Zuwa na yi da gudu na rumgumeta ina ta murna kamar babu abunda ke damuna. Haka na wuni cikin farinciki da jindaɗi kamar wacce aka yi ma kyautar kujerar makka. Ban san farincikina kaɗan ne har sai da Habiba ta dawo na sanar mata da labarin sai ta yi kamar zata haɗe kanta dan murna kai kace ma ita ta samu aikin ba ni ba, a ranar Habiba bata iya cin abincin rana ba dan tsananin murna, da maraici ta siye alawa da kuɗin Inna ta yi sadaka. Haka ta ke nunawa kulawarta da damuwa a duk lokacin da wani abun ya sameni, ta kan zauna ta labarta min abunda Inna bata sani ba, zata iya ɓoyewa Inna abu amman ni bata ɓoye min ba, mutune har mamakin yadda muke son junanmu suke, ganin ita take bina amman bama taɓa samun saɓani, ko ma mun samu tun anjima kaɗan zanje na rarrasheta ko kuma ita ta zo ta bani haƙuri ko da kuwa ni ce bana da gaskiya, irin tsabanin da ake samu tsakanin mabiyi da mabiyi ni ban cika samunsa da Habiba ba, muna son junanmu sosai, ko ciwo ɗayan mu yake sai ɗayan ya ji kamar ya cirewa ɗan'uwansa ya sakawa kansa. Lokacin da Baba na da rai idan ya tashi zolayarmu har cewa yake yadda muke son junanmu bama sonsa haka, wani gurin ma idan mukaje ba dan kamanni ba da mutane za su ce Habiba ƙawata ce ba ƙanwata ba. Ba zan iya misalta irin son da take yi ma Noor ba, tun da na haifeshi ita ce da ɗawainiyarsa har ya kawo yanzu, babu kuma wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa a unguwarmu ko ma a cikin gidanmu ni kaina ban isa na hukunta Noor ba indai a kan idon Habiba ne. Ni kaina shaƙuwar ta kan ba ni mamaki, wata ƙila dan akwai tazarar shekara bakwai a tsakaninmu. Duk farinciki da ɗaukin aikin da nake idan na tuna Baba ba ya raye sai na ji babu daɗi, na so ace na samu aikin yana da rai na san zai yi farinciki sosai, sai dai kuma ƙaddara ta riga fata abunda Allah ya rubuta dole shi zai samu bawa. A daren ranar da na samu aiki sai ga Bilal ya kirana ni a waya na yi zaton zai ce na fito ne sai ya ce na aiko masa Noor yana bakin ƙofar gida, ba musu na miƙawa Noor wayar, ban san mi suke tattaunawa ba kawai dai na ga Noor yana dariya yana ɗaga kai sai kuma ya wulgumin wayar ya tashi ya fita da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa. “Falfala da gudu ɗan gidan Bilal sai in be kiraka ba” Cewar Habiba tana dariya. Nishaɗin dake fuskarta shine a fuskar Inna da Jamila har ma Sakina da kuma ni kaina. “Bilal ɗin nan yana son Noor kuma na tabbatar son da yake miki ne ya shafe shi” Na ɗago na kalli Inna da furucin da ta yi. “Ba fa so na yake ba, mutunci ne kawai a tsakaninmu, be taɓa cewa yana so na ba” Habiba ta watsa min harara. “Ji matar nan muna-muna munafuka, Wallahi son junansu suke amman shi ba zai iya faɗa ba ita ba zata ba shi dama ba, ai da yanzu an wuce gurin, duk alamun da yake nunawa ai na son ki ne, ke kuma kina kauce masa” Na yi dariya ina girgiza kai. “To ya kike son na yi?” “Ya dai kamata ki bashi dama, zama haka ba zai yiyu ba, Allah kaɗai yasan iya gulmar da ake muku a unguwarnan, kin kore kowa kin zauna a gida gashi har mahaifinki ya rasu be ga wani auren na ki ba” Wannan karon Inna ce ta yi maganar, kuma maganar da ta yi ta ɗan taɓani, tabbas mutuncin ƴa mace da kuma darajarta a gidan aurenta ne, sai dai ba kowa ne zai maka son tsakani da Allah ba, wasu kan zo so na saboda sha'awata da sun gwasa sun gano ni ba ƴar iskar barawarar nan ba ce sai su gudu, wasu kuma su nuna maka ba zasu yarda da je da yaron ka ba, wasu kuma basa da wani sana'ar kirkin da za su iya riƙe sauran iyalansu ma balle kuma a haɗa da ni, kowa da irin matsalarsa. Bilal ɗin ma laƙe min ya yi da sunan abota, sai dai ko da wasa ban bashi alamun da zai iya nuna min so ba, saboda na san iyayensa ba zasu yarda ya auri mace da taɓa aure har biyu ba kuma har da ɗa ma. Uffan ban ce ba, Inna da Habiba kawai ke ta nanata maganar. Muna nan zaune Noor ya shigo da ƙatuwar leda a hannunsa har biyu a hannunsa baki har kunne. “Momy kalli abubuwan da siyo min, kuma ya ce Mama Habiba kawai zan bawa kar na sammi ki, kuma ya ce yana kiranki yana ƙofar gida” Shi da Habiba suka riƙa kokuwar buɗe ledar, ni kuma na zari Hijabina na nufi ƙofar gida. Tsaye na sameshi yana kallon ƙofar gidanmu da alama dai yana jiran fitowata ne. “Ina ta zuba ido na ganki yau a kamfaninmu ban ganki ba” Ban bashi amsa ba sai da na yi masa sallama ina murmushi. “Assalamu alaikum” Sai ya amsa min da murmushi. “Wa'alaikissalam Nawancy, na zo na taya ki murnar samun aiki, ai na faɗa miki zasu ɗauke ki” “Ɗazu na samu saƙon, na jidaɗi sosai” “Mutane na ta zuwa karɓar uniform amman ke ban ganki ba” “Uniform kuma?” “Yes ai Uniform zaku saka, tun safe ake zuwa ƙarɓa kin ga ɗaga yau zuwa gobe ne kawai ake bada uniform ɗin, on monday zaku fara zuwa aiki, kuma idan kunje karɓar uniform ɗin za a nuna muku irin aikin da zaku yi” “Gobe zanje Inshallah, ai ban san ana zuwa yau ba” “Sai dai matsala ɗaya, Nawancy bana son ki saka wando, ina ganin kamar ba be dace ba” ‘Musamman ga irina masu manyan mazaunai’ Na faɗa a raina. A fili kuma sai na ce. “Ai zan iya saka Hijabi ko abaya a sama” “Amman baya son haka, sai idan kin tashi aikin ko kuma idan zaki shigo, shi be yarda ma ko hula a saka a gurin aikin ba balle kuma Hijabi” Cike da mamaki na ce “Ba musulmi ba ne hala?” “Wallahi musulmi, amman mutumen sai a hankali, haka zaki ga tattoo a jikinsa, ina jin ya zauna waje ne” Na taɓe baki cike da ƙyamar halin mutunen duk da ban san shi ba “Allah ya kyauta amman abun baƙinciki ne ace musulmi ya rinjaya wani addini sama da nasa, ga shi ka ce ya cika tsanani” “Yana da tsanani sosai, amman tsananinsa yana burge ni wani lokacin, kin ga dole kowa ya riƙe aikinsa da muhimmanci, kuma kin ga wacan da aka canja baya damuwa da duk waɗannan abubuwan shiyasa duk ƙarshen wata sai an siyo kayan abincin da cups da aikatan gurin suke aiki da su, amman zuwan wannan ya saka dokar duk wanda ya fasa masa cups za a cire cikin albashinsa, dole kowa ya riƙa taka tsantsan da abubuwan gurin” “Amman daman ba a biyan kuɗin abincin ne?” “No ana biya restaurant ɗin da ke cikin kamfanin ai nasa ne, amman idan ba restaurant ba kin ga ma'aikici zai buƙaci shan ruwa ko wani abun ko kuma tea musamman ga masu zuwa tun safe, ko kuma idan aka yi baƙi, to duk da wannan cups ɗin ake amfani. Bayan ma wannan kamfani suna da Sabuwar Asibiti da aka buɗe nan by pass, One-On-One Special Hospital, amman ance ta masu kuɗi ce dan katin ganin likita ma ɗari takwas da hasin ne” Na jinjina kai ina faɗin. “Kamfanin ma akwai girma, ni Allah yasa ma har na yi aikin na gama ba zan ganshi ba” Sai kawai yasa min dariya. “Kina tsoro ne Nawancy?” “A'a ba tsoro ba ne, kawai ba zan iya jurar wulaƙanci ba ne, kaga ƙara ma ace bamu haɗu ba” Mun daɗe muna fira yana ta labarta min kamfanin da kuma wasu abubuwa na cikinsa da kuma yadda aikinsa yake, kamin hirar siyasar ƙasar nan ta shigo ciki, sai tara da rabi muka yi sallama ya tafi ni koma na cikin gida. Ko da na shiga su Habiba sun ci sun ciye an gutsura min ɗan tsiton cake da nama ƙwara ɗaya an aje min sai kuma ice cream a cibi. “Yanzu wannan abun kawai zaku bar min?” “Eh mana dan kin samu ma mun rage miki” Cewar Habiba, tana bani amsar tambayar da nayi, sai Noor yasa dariya yana cin namansa ya ce “Momy ƙyale Mama Habiba sai ta yi bachi zan ƙara miki karki kuka kinji?” Sakin baki Habiba ta yi. “Au ni zaka watsawa ƙasa a ido?” Ta kai masa dudu. Inna tasa dariya, yau kan ba laifi muna cikin farinciki farincikin da muka daɗe ba mu yi ba tun bayan rasuwar Baba, sam ba zaka gan mu a yanzu ka ɗauka akwai wata damuwa a ranmu ba. Daman can talauci baya hana mu walwala ko kuma farinciki, idan ka ganmu a damuwa to muna jin yunwa ne, da kuma mun samu mun ci sai mu gode Allah da wannan ni'imar, mu kuma roƙi na anjima. *** *** *** Kamar yadda muka kwana cikin farinciki haka muka tashi da shi, abun ka da sabon shiga su Noor na wucewa makaranta nima na shirya muka fita tare da Habiba ita ta wuce tata makarantar ni kuma na ɗauki hanyar gurin mu a Napep. Yau ma da na isa ban shiga ba sai da na ƙira Bilal na sanar masa ina bakin gate, shi ya fito ya shiga da ni, sai mita yake wai ya kamata ace na shigo ciki da kaina tun da Monday zan fara aiki, ni kuma ina taka tsantsan ne gudun ƙar na yi wani abun da ba daidai ba, shugaban ya ce zai hukunta tun ban fara aikin ba. Ciki ya shiga da ni har muka isa cikin wani ƙaton haɗi inda na faɗa musu sunana suka duba sannan suka ɗauko uniform ɗin dake cikin leda suka ba ni, sai kuma wasu takalmi masu kama ta da malaman lafiya na asibiti, suka miƙa min wasu takardun na saka hannu sai suka buƙaci idan zan dawo na zo da ƙaramin hoto na guda biyu, wai zasu saka a file ɗayan kuma a kuma na saka a catin zan rayata a wuya na shedar aikina. Ɗaya daga cikinsu ne ya yi min ja gaba har gurin da zan yi aikin nawa, kitchen zan riƙa gogewa da kuma da ake aje files kusan ɗaki biyar, sai dai ba ni zan yi sharar ba aikina Mopping ne kawai, kuma idan zamu yi mopping ɗin sai mun saka safar hannu idan mun gama mu jefar, sai kuma goge kofuna da jerasu a muhallinsu, shi ma sai mun saka safa, tsarin kamfanin kamar na turawa, lallai sai a yanzu na tabbatar da zancen Bilal na cewa Kamfanin yana takara da kamfanonin duniya. Mai nuna min aikina ya jaddada min kamin na jera kofunan sai na ƙirga ko guda nawane na rubuta a file ɗin gurin da kuma time da na fara da time ɗin da na gama, da kuma ko kofi nawa na tarar, daga ƙarshe Bilal ya kai ni reception ya nuna min gurin da zan saka sunana da kuma lokacin da na shigo, idan kuma na gama sai na saka sunana da kuma lokacin da na fita, ƙarfe bakwai zan fara aikin na ƙare tara, hakan na nufin bakwai ta yi min a can kenan. Irin yadda tsari da dokokin kamfanin suke sai duk na ji aikin ya fara fita raina kamar ba zan iya ba, sai dai babu yadda na iya tun da nema na ke yi kuma ba anan zan dauwamaba. Har bakin titi Bilal ya rakoni, muna tsaye da shi na hango motar Zinatu ta shiga kamfanin, na tabbatar da ita ɗin ce saboda hangota da na yi ta gilashin motar da ke sauke. Bilal ya tara min Napep na hau sannan ya koma ni kuma na kama hanyar gida ciki da mamakin tsare-tsaren wannan kamfani, gaskiya ba dan ina son aikin ba da na haƙura da yinsa, a gurin da na saba sauka na ce mai Napep ɗin ya aje, sai na karɓi ragowar canjin kuɗin da Bilal ya bashi na nufi cikin unguwarmu. A hanya na haɗu da mai gidan da muke haya, wata irin kunyace ta mamaye mu nasan yayi mana karamcin tun da be mana magana tun baya rasuwar Baba ga shi har Inna zata gama wanka takaɓan ta cikin wannan satin. Sun-sun-sun na gaisheshi ya amsa min yana murmushi tare da tambayar ya haƙuri. “Mun gode Allah dan Allah ka yi haƙuri akan maganar kuɗin nan, inshallah za a kawo” “Kuɗin me? Ai Bilal ya biya be faɗa muku ba ne? Tun Margayi be yi sati da rasuwa ba ya kawo kuɗin dubu arba'in cif” Na saki baki ina mamakin ikon Allah. “Wallahi ba mu sani ba” “Wallahi ya biya sai dai ayi masa godiya” Sallama na masa na wuce zuciyata cike da hauƙin Bilal, bakina kuma har rawa yake naje gida na labartawa Inna wannan labarin. A hankali wata mota da ta fito ɗaga gidansu Manjo ta doso inda na ke, mai maotar na kawowa daidai ni sai ya sauke baƙin gilashin motarsa. Ashe Mustapha ne, cikin shigar manyan kaya wato farar shadda da kuma barar hula sajensa na kwanta sai sheƙi yake, da alama jumma'a zai je tun da yau friday, fuskarsa cike da annuri, sai dai bana mutanen kirki ba, na kuɗi da kuma kyawun hallita da suka nuna isa a fuskarsa. Kallona yake ba ko ƙyafta ido, ni kuma na bawa banza ajiyarsa sam babu tsoro a tare da ni saboda na shirya tarbar ko minene daga gareshi. Haka nasa kai na wuce na barshi a gurin zuciyata har wani zafi take min saboda da tsanarsa. Da sallama na shiga gida, Inna da dpo suka haɗa baki gurin amsa min, hakan yasa naji kamar na janyo sallamar na mayar da ita a bakina, yau ma ya taki sa'a na sauke idona cikin nasa hakan yasa ni jin kamar na ƙarasa a inda yake zaune gaban Inna na shaƙe wuyansa. THE GAME IS ABOUT TO START .*RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣4⃣ Na ɗauke kaina kamar ban san da zaman mutun a gurin da Inna take ba. “Har kin dawo?” Inna ta tambaya, ni kuma na nufi ƙofar ɗakin mu ina amsa mata domin bana son na juyo idona ya haɗu da na azzalumin mutunen nan. “Eh Inna” Na ɗaga labulen ɗakin mu na shige zuciya cike da abubuwa guda biyu farincikin abunda Bilal ya yi mana da kuma baƙincikin ganin dpo a gidanmu. Kayan da ke hannuna ma saman katifa na jefasu, na zauna ƙasa raina a jagule. Jidda ce ta faɗo min a rai, ya kamata ace na tabarta masa samun aikin nan da na yi, har na unƙura zan tashi na fita sai na tuna dpo yana tsakar gida, hakan yasa na koma na zauna, sai tunanin Bilal ya dawo min rai. Lokaci zuwa lokaci na kan samu kaina da murmushi tuna irin abubuwan alherin da Bilal yake mana, wanda na san har ƙasa ta naɗe ba zan taɓa saka masa da abunda ya yi min, ya sadaukarda abubuwa da dama saboda farincikina. Kiran da Noor yake min a tsakar gida ne ya katse min tunani, ina unƙurin tashi na fita sai ya shigo ɗakin da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa. “Momy duba aka raɓa mana sabon littafi a makaranta” Na faɗaɗa fuskata da murmushi ina karɓar littafi tare da buɗewa ina dubawa, littafi rubutu ne mai hoton ciyaman, da alama ya kai musu ziyara ne, daman naji a rediyo ana cewar zai ziyarci makarantu. “Momy da idona na ga Ciyaman yana jawabi har da godiya ya yi mana, sai aka raba mana littafai” Na kai hannu na shafa fuskarsa ina dariya “Amman Ciyaman ya kyauta da ya bari Noor ya ganshi” Sai ya ƙyalƙyale da dariya ya rumgume ni. Haka ɗa na yake, masu kuɗi da ƴan siyasa suna burgeshi ko a mota ya ga mutun sai ya tsaya kallonsa har sai ya daina hangoshi sannan hankalinsa ya kwanta, a ranar kan labari sai abunda ya manta. Zaunar da shi na yi saman jikina, na soma cire masa talkamin makaranta tare da safa, shi kuma yana duba littafin tare da karantawa. Habiba ce ta shigo ɗakin babu ko sallama, kana ganinta kasan a gajiye take jikar littafanta ma a bakin ƙofa ta sakesu ta kwanta kusa da ni tana ƙoƙarin cire hijabinta. “Lafiya kike kuwa?” Na tambaya ina kallonta, Noor kuma ya tashi da sauri ya fita waje. Ɗan guntun tsaki taja irin na wanda baya son magana kana ta ce “Wallahi bana jindaɗi, amai na biyu makaranta kuma kaina ciwo yake sosai” Dukan shida-shida gabana ya yi tsaɓanin uku-uku da na kowa keyi, a take nima na ji ciwon kan ya kamani, dafe kaina na yi na lumshe ido yana sauraren yadda zuciyata take bugawa. Ƙoƙarin kawarda abunda ke zuciyata nake, yes cikin zai iya nunawa a sati biyu amman ba ko wanne ba, cikin Noor ma a sati biyu aka gano ina da ciki balle kuma Habiba da ke da wata ɗaya har da sati ɗaya, tunda ranar litanin Inna zata cika wata ɗaya da sati biyu cikin taƙaba. ‘No ba ciki ba ne, maleriya ce inshallah ba ciki ba ne’ Zancen da nake a zuci shi Habiba take a zahiri. “Nawwara na ce ƙila maleriya ce, saboda idona har nauyi yake” Na buɗe ido na kalleta tare da ɗaga mata kai alamar ‘Eh’ “Ita ce, bari na aika Sakina ta siyo miki Anti-Malaria shago” “Tau” Ta juyo min baya tana dafe da kai, hakan ya bawa hawayen da ke maƙƙale a idona saukowa zuwa kumatuna, ban taɓa tabbatar da hawaye na da zafi ba sai a wannan lokacin, gumi ne ya soma keto min ta ko ina kamar wacce ta yi rashin gaskiya. Cikin hanzari na kai hannu na share hawayena saboda motsin Sakina da na ji zata shigo ɗakin, sai na miƙe tsaye na nufi ƙofar fita. Ashe magana take min ban ji ba har sai da ta riƙoni. “Anty Nawwara, wai ɗan sanda nan yana kiranki a waje” Da kai na iya amsa mata, daman Hijabin da na shigo da shi yana jikina sai kawai na zarce ƙofar gida, har ga Allah ba dan ina cikin ruɗu ba babu abunda zai sa dpo nan ya kirani kuma har na tafi. Tsaye na yi masa idona a ƙasa ina ta tunanin makomarmu, idan har ta tabbata Habiba na da ciki mun shiga uku, lallai mutane zasu gasgata cewar Mahaifinmu ya yi sata, tun da ga ƴar'uwata da cikin shege, duk wani yabo da ganin mutuncinmu da ake a unguwarnan zai zube, ya Inna zata yi idan ta ji Habiba na da ciki? Ita kanta kanta Habiba ya zata kasance? Ni kaina da suka san na yi aure lokacin da na haifi Noor sai da suka kira shi shege balle kuma Habiba. “Nawwara” Kiran sunana da dpo ya yi na yasa na dawo hayyacina har na kalleshi, ashe tun da na zo gurin magana yake min amman ban fahimtaba saboda tashin hankalin da ke zuciyata. “Ki yi haƙuri dan Allah, ki share hawayenki, duk abunda na faɗa miki zanyi ki yarda da ni” Sai a lokacin na kula da hawayen da ke ta zuba a idona, cikin sauri na sa Hijabina na gogesu ina jan magina. Sai ya ɗora da zancen da ban gane masa ba, ba dan kuma yana min wani yaren ba sai dan hankalina baya gurin, babu komai a zuciyata sai fargaba tunani da kuma zullumin abunda zai je ya dawo, na tabbatar da za'a auna jinina a lokacin za a tarar ya haura ɗari uku da wani abu bama ɗari biyu ba. A gurin na barshi tsaye na shige gida ba tare da hawayen sun tsaya min ba, haɗa ido da muka yi da Inna yasa idona ƙara cika da ƙwalla, tausayinsa ne ya kamani tabbas Mahaifiyata ba zata iya ɗaukar wannan ba, duka-duka yaushe ta rasa mahaifina kuma yanzu ta ji Habiba na da ciki. “Lafiya?” Tambayar da ta yi min ne yasa na share hawayena ina ƙoƙarin ƙirƙiro ƙaryar da zan mata. “Ba komai kawai mun yi magana kan Baba ne” “Nawwara ki yi haƙuri idan ma a duniya ba a yi komai ba, lahira za'ayi domin Allah baya zalumci kuma zai ƙwatar mana haƙƙinmu” “Haka ne, Inna kina da kuɗi a siyowa Habiba maganin Malaria?” “Duba a cikin jakata ba za'a rasa ba, tace kanta ke ciwo” Ban iya tsayawa amsa mata ba, na nufi ɗakin na ɗauko kuɗin na aiki Sakina ta je siyo mata, bata daɗe ba ta dawo da kuɗin wai sunje masallaci. Kayan jikana na tuɓe na koma gaban murhu ina hura wuta domin ɗora girkin rana, har na yi girkin na gama kuka nake a boye saboda bana son Inna ta gano ina kuka hakan zai raunana mata zuciya kuma dole zata tambayeni dalilin kukan wanda ba zan iya faɗa mata ba. Bayan na gama na shiga banɗaki na yi wanka tare da kuka a can, domin a nan babu wanda zai san da damuwata, bayan na fito na raba abincin na sake aikin Sakina ta je ta siyo mata maganin. Da kaina na ɓalla na bata ta sha na zuba mana abinci sai ita ta kasa ci saboda zazzaɓin ya rufeta sosai, jikinta ya yi zafi sosai. Ni kaina kasa cin abincin na yi, sai mutuwar Baba ta dawo min sabuwa, da ace ƴan sanda nan ba su masa duka ba, da be mutu ba da Habiba da ni da Inna duk ba mu shiga wannan halin ba. Bana son kowa yasan kukana hakan yasa na ɗauki buta na shiga banɗakina na ci kukana sao da na ƙoshi sannan wanke fuskata na fito, a lokacin ana kiran sallah la'asar. Ba laifi Habiba ta samu sauƙi bayan shan maganin da ta yi, da muƙa gama sallah magariba ba har waje ta fito muna ɗan taɓa fira da ita, har ma ta ci ciwon masarar da na yi, hakan ba ƙaramin faranta min rai ya yi ba, gar na samu sakewa na labartawa Inna zancen Bilal, babu irin ruwan albakar da Inna bata sa mishi ba, Habiba ma sai yabonsa take. Inna ce ta cilasta ni kiransa a waya na sanar masa tana son ganinsa. Bayan Sallah isha'i ya zo Inna tasa na shigo da shi har cikin gida ta yi masa godiya, bayan mun fito ni nake masa godiya duk da nasan cewar ba da sanin mahaifiyarsa ya yi mana wannan abun ba, da ba zata bari ba domin ta ƙi jinin ta ganmu tare ma balle kuma har kyauta ta shiga tsakaninmu, mun daɗe muna fira shi sannan muka yi sallama. Bayan na dawo nake labartawa Inna yadda gurin aikin yake da kuma irin ƙa'idojinsa sai kuma zancen yadda kace min Shugaban ya ke, ta yi murna sosai ita da Habiba sun ƙarfafa min gwuiwa kuma suka min addu'ar samun nasara. Washe gari naje na sanar da Jidda zancen samun aikina, ita ta yi murna sosai kusan sai na ce ta fini farinciki, haƙiƙa Jidda ta wuce ƙawa a gurina mun zama ƴan'uwan juna ni da ita, mun sha fira sosai yadda na ke labarta mata gurin aikinmu ita abun ma burgeta ya yi, wai ban sanar mata da wuri ba da ta kai takardunta na diploma sun ɗauke ta aiki a guri. Sai yamma na baro gidansu bayan na haɗu ni da kwanon shinkafa da miya, abincin da na ke marmari. *** *** *** MONDAY MORNING... Hankalina ya kwanta sosai a kwanan biyu da Habiba ta yi bata sake ko da ciwon kai ba, hakan ya gamsar da ni lallai malaria ce take damunta. Dukan mu shiri muke bayan mun gama karyawa, ni ina shirin zuwa gurin aiki su kuma suna shirin zuwa makaranta, ban shafa hoda ba bayan na shafa mai, domin kawaliya bata dame ni ba, balle ni da zan fita tun 6:30am. Uniform ɗin na ɗauko na cire daga cikin leda, dogon wando ne ash color da farar riga, sai kuma wata ƴar ƙaramar riga marar hannu da za a ɗora saman wacan farar rigar ita ma ash, sai da na gama kallo ni da Habiba sannan na saka. Cas na fito kamar wata ma'aikaciyar banki musamman da na saka baƙaƙen takalmin nan masu kama da cover shoes. “Wow Nawwara kin wanku” Cewar Habiba tana kallona, ni kuma na yi dariya ina mai jindaɗi a raina. Ba Habiba kaɗai ba har Noor da Inna sai da suka yaba ni, ni kaona na san shigar ta yi min kamar wata ma'aikaciya, idan ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce aikin Mopping zan yi. Wata ƴar ƙaramar baƙar hula na ɗauka na saka a kitson da ke kaina, sannan na ɗora ƙaton Hijabi yaɗi huɗu da rabi na saka, a gaggauci na fito daga gida gudun kar na yi lattti gashi yau ne farkon zuwana, duk yadda Habiba ta so na tsaya mu fito tare ƙiyawa na yi gudun kar na ɓata lokaci. Sai da na kawo bakin titi sannan na tuna da hoton da aka ce na kawo, da gudu na koma gida na ɗauko na sake fitowa ina ɗan jin kunya saboda mutane da ke kai da kawo a unguwat sun ɗan fara fitowa, duk da yake ba za'aga uniform a jikina ba amman sai na samu kaina da jin kunya saboda ban saba saka wando na fita da shi ba. Ko da na isa kamfanin bakwai sauran minti biyar, yau kan sun tare a bakin ganin suna ɗan bincikata, sai na faɗa musu komai har ma na nuna musu uniform ɗin da ke jikina da kuma katin sheidata, sannan suka bar ni na wuce. Kamar yadda Bilal ya nuna min sai da na fara isa na saka sunana da lokacin da na shigo da kuma rana sannan suka nuna min gurin da zan aje Hijabi da wasu kaya idan na zo da su, na nufi gurin na na cire Hijabina na aje a lokar da suka ba makullinta, na samu kaina da jin kunya sosai ganin babu komai a jikina sai uniform ɗin da kuma ƴar ƙaramar hular da ke kaina, sai da na ɗan jima tsaye a gurin sannan na juyo na fara takowa, sai ɗaya ɗaga mutanen da ke reception ya ɗaga hannushi yana nuna min hular da ke kaina, a dole na juya na je na cire na aje, na juyo ina wani taku kamar wacce bata son saka ƙasa babu komai a tattare da ni sai kunya, shi kanshi ya lura da yanayina, hakan yasa ya sakar min murmushi, nima na sakar masa kaɗan idona a ware, ina kalle-kalle ala-ala na ke kar naga wanda na yasan ni har na nufi Lifted na danna ta buɗe na shiga sai na danna number 3 ta rufe ta soma tafiya da ni, zuciyata sai bugawa take da ƙarfi irin bugarwa nan na ɗoki da kuma tsoro a lokaci ɗaya. Muna isa number 3 ta buɗe na fito sai na samu masu irin uniform ɗina suna ta aikin gyara gurin, ganin duk mata ne yasa ni na ɗan saki jikina na nufi gurin da aka nuna min da zan ɗauki kayan aikina. A ciki na tarar da wata yarinya mai far'a da son mutane domin ita kaɗai ce ta amsa min sallamar da na yi har ta yi min kyautar murmushi. “Da alama ke baƙuwace a nan” “Haka ne, yau zan fara” “Haba shiyasa” “Mi kika gani hala?” “Naga kin yi sallama ne, ai a nan ba a sallama ba a gaisuwa saboda mai Kamfanin baya buƙata, idan kika ga ana fira da juna tau angama aikine ko kuma an fita can waje” “Tau shi kuma haka yake” Ta yi dariya tana nuna min camera. “Ki yi a hankali, Camera tana ɗaukar komai” Security camera ce daga gabanmu tana ɗaukar komai, sai na yi saurin gumɗe bakina na ɗauki kayan aikina na yi gaba. Na ji wuyar aikin sosai wata ƙila saboda ina farkom farawa ne, ko kuma saboda ɗakunan da aka haɗani da su suna da girma sosai, ga kuma gyara kofuna da jerawa bayan na gama ƙirgasu, sai da na gama sannan naje gurin da ake rubutawa na rubuta ko nawa na tarar sannan na nufi gurin aje kayan aikin na aje, na aje na kaiwa mutumen jiya wanda yace na kawo mashi ƙananan hotona, ɗaya ka karɓa ya saka a file sannan ya karɓi ɗayan na saka min a katin sheidata na rataya a wuya sannan ya ce min. “Idan kina da account ki rubuta a nan, idan kuma baki da shi zan cika miki wata takarda sai ki riƙa karbar albashinki hannun kashiya” “Gaskiya na daɗe ban yi amfani da shi ba, ina tunanin yanzu ma baya aiki” Wata takardar ya ɗauko ya yi rubuce-rubuce sannan ya bani na saka hannu sai ya maida takardun ya aje, ya ce “On 25 zaki riƙa zuwa gurin kashiya kina amsar kuɗin albashinki 12k” “Tau na gode” Na juyo duk da ban tambaye shi iya kashinyan yake ba, na fito daga gurin gaba ɗaya. A ƙaton agogon da ke reception na ga 12:14pm, lallai na daɗe ina aikin nan, sai da na saka hannu kuma na rubuta lokacin da na gama aikin sannan na nufi gurin da Hijabi yake na ɗauka, ina sakawa na ji mutun a bayana. “Nawancy” Da sauri na juyo na kalleshi. “Ka ganni ne kamin na saka Hijab?” Sai kawai ya ƙyalƙyale da dariya ya ɗora min ɗari biyar a lokar dana ɗauki Hijabina. “Allah dai ya bar min ke, ga wannan ki hau Napep, a sauka lafiya” Sai ya kama gabanshi ya yi tafiyarsa. Cike da kunya na fito na daga cikin kamfanin ita tunanin anya zan iya aikin nan zuwa? “Sannu ƴar'uwar yau nima na ti latti gama aiki” Na kalli mai min maganar da ke gefena na dama fuskarta ɗauke da murmushi, yarinyar ɗazun ce, sai dai wannan karon ita ma tana sanye da Hijabi, hakan yasa nima na yi mata murmushi. “Da wuri kike gamawa kenan?” “Eh gaskiya ten na ke gama aikina. Sunana Amina ke fa?” “Nawwara” “Suna mai daɗi” Sai duk muka yi dariya, muna ta ɗan taɓa fira da ita kamin motar da ta wuce mu ta dawo dai-dai mu ta tsaya. “Nawwara” Jin muryar Zinatu yasa na yi saurin kallon motar, ita ce hakimce a motar idonta sanye da baƙin gilashi. “Zinatu Ya kike?” A maimakon ta amsa min sai kawai ta jefo min tambaya. “Me kike a nan?” “Aiki” “Aiki aiki aiki wane irin aiki?” “Mopping” “Nice amman yau kika fara ko?” “Eh” “Good kowa zai ji muna aiki a guri ɗaya Sai dai ba level ɗaya ba, and people may not know the different, congratulations” Ta tashi gilashin motarta ta kunna kai zuwa harabar da aje motoci. Maganar ta sosa min rai har Amina ta lura da hakan. “Kin santa ne hala?” “Eh tare muka yi primary school” “Allah sarki” Kamar ta ce wani abu sai kuma ta yi shiru, muka cigaba da tafiya. A gurin hawan Napep muka rabu ni na ɗauki hanyar gidanmu ita ma ta kama hanyar na su gidan. Kamar kullum a inda aka sake sauke ni na sauka na ƙarɓi canjina na nufi gida, zuciyata cike da tunanin kalamin da Zinatu ta yi min, bana son fassarata da wata fuskar da kuwa da kasancewar na san halin na tsanar mutane irina da ta yi wato talakawa, haka kawai na samu kaina da faɗuwar gaba wata ƙila na tunanin da nake ne, sai da na shiga gidanmu na fahimcin faɗuwar gaban bana tunani ba ne na abunda zan tarar ne. ______________ SHARE, COMMENT AND VOTE. Sauran na ji wani ya ce short page ne na buge masa baki 😎 BEST REGARDS 🌹 Khadeeja Candy💜.. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣5⃣ Habiba ce kwance tsakar gida amai na gefenta da alama yanzu ta gama shi, domin Inna ta ɗauki makwashi da tsintsiya ta je ɗebo ƙasa. Da sauri na ƙarasa kusa da ita jikina a mace na dafata. “Sannu Habiba mi ke damunki” “Wallahi kaina ne ke ta ciwo ban ma iya dawowa daga makaranta ba sai da malaminmu ya kawo ni, sai faman aman na ke, kuma bakina babu daɗi” Samun kaina na yi da kuka marar sauti, hawaye na bin fuskata kamar babu gobe. Na samu kaina cikin wani irin tashin hankali wanda ban taɓa samun kaina a ciki ba. “Ai zata samu sauƙi ina jin malaria ce bata sake ta ba” Inna ta faɗa ganin ina kuka, sai faman rufe aman take. “Allah yasa malaria ce, Allah yasa ta tabbata malaria ce ba ciki ba” Maganar ta fito daga bakina kamar antseni. Hakan yasa Inna ta kalleni “Nawwara, akwai abunda ya kamata na sani ne?” Na yi saurin girgiza mata kaina hankalina a tashe. “Babu babu komai” Ta saki tsintsiyar hannunta, ta kalli Habiba da ta soma kuka daga inda take kwance. “Akwai abunda kuke ɓoyewa ne?” Na girgiza mata kai alamar a'a. Amman bata yarda ba. Ta soma ƙirga da hannunta. “Tsaya dakata, Habiba tana da ciki kenan?” Habiba ta yi saurin tashi zaune ta matsa gefena kamar zata shige jikina tana girgiwa Inna kai. “A'a Inna” Ta faɗa cikin kuka, kamar yadda nima na ke kuka. Sai ina ta kalleta idonta cike da hawaye ta nunata da yatsa. “Kina da ciki Habiba, na lura da haka domin yanayinki ya canja gaba ɗaya, amman saboda karna munana zato a gareki yasa ban bari zuciyata ta ƙawata min wannan ba, ashe yaudara kuke ke da ƴar'uwarki, na shiga uku na lalace ina kika samo shi?” Ta ɗora hannu saman kai ta nufi ɗaki tana kuka. Hakan yasa na cire Hijabin da ke jikina na aje a gurin tare da wayata na rufe mata baya. Safa da marwa na tarar tana yi a cikin ɗakin tana kuka, kamar jira take na shigo sai ta rufeni da maganganu marar daɗi. “Kun cuce ni Nawwara, wannan ba tarbiyar gidan nan ba ce, ina kuka ɗaukota? Kun ƙara shafa mana baƙin fenti acewa mahaifinku ɓarawo ku kuma a kiraku ƴan iska, wayyo Allah na” Ta faɗi tsakar ɗaki tana kusar kuka. Kusa da ita na ƙarasa na ɗafa ina kuka na ce “Wallahi ba mu watsar ba Inna, ita ma yaudararta aka yi” “Waya yaudareta? Faɗa min waya rusa mana ɗan farincikin da ya rage mana?” A nan na feɗe mata daga biri har wutsiya akan abunda ya faru, sai dai ban labarta mata cewar Mustapha ne ya aikata mata haka ba, saboda bana tabbacin cikin nasa ne ko ba nasa ba ni dai abunda na sani ba shi kaɗai na ya yi lalata da ita ba, nasan kuma duk na faɗa mata cewar shi ne zata iya zuwa ta samu iyayensa wanda hakan na san ba zai mana daɗi ba, domin zasu iya ɗauka ko wane irin mataki a kan ɗan su ƙwalli ɗaya da suke ji da shi. Can ƙasa-ƙasa na hango muryar Inna tana cewa. “Habiba ta ci amanata kuma ta ci amanar kanta, ta zubarda ƙima da duk wani mutuncin da yake gidan nan, a yau na yi nadamar haihuwarta, baƙincikinta zai kasheni, ni ma nice na tafi ba mahaifinku ba, Allah be ƙaddara ya ga wannan abun kaico da wayyo a rayuwarsa ba sai ni, Habiba kin cuce mu...” Duk wannan furucin da Inna take akan kunnuwan Habiba saboda tana jikin ƙofa tsaye ne, sai da Inna bata iya ganinta saboda ta bata baya ne. Muna haɗa ido da ita sai ta bar jikin ƙofar ta nufi ɗakinmu. Da sauri na tashi na bita saboda irin hawayen da na hango suna zuba a idonta. Ko da na shiga na tarar tana ta saurin cire uniform ɗin jikinta ta saka wasu tufafin. Jin motsina yasa ta juyo da sauri ta kalleni. “Nawwara guduwa zan yi, ba zan zama dalilin mutuwar Inna ba, ba zan rasa Baba kuma na rasa Inna ba-” Ta juyo ta cigaba da haɗa kayanta. Ƙarasa na yi kusa da ita ya miƙar da ita tsaye na kama hannyenta da ke zafi sosai saboda zazzaɓi na riƙe gam, ina kuka kamar yadda itama take yi har ɗayanmu baya iya yiwa ɗan'uwansa magana. GOOD NIGHT.... 🤧 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣6⃣ Haƙiƙa akwai ƙurciya a rayuwar Habiba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta aikata abunda ta aikata, wanda take tunanin kamar mafitane, sai gashi ya zame mana matsala, yanzu kuma tana ganin kamar guduwa ta bar gida shi ma mafita ne, ni ko nasan duk yarinyar da ta gudu ta bar iyayenta lallai tana tare da na sani da kaico a rayuwarta. Ba zan bari ƴar'uwata ta aiwatar da wannan ƙudirin nata ba, ko da kuwa haka yana nufi salwantar rayuwar mahaifiyata ne, ba zan bari ta sake aikata wani kuskuren ba. Ƙoƙari nake na tsayarda kuka ta yadda zan ƙarfafa mata guiwa da rarrashi amman hawayen da ke min zuba sun ƙi bani haɗin kai. Idan har ban yi ƙarfin halin shiga tsakaninta da wannan kuɗirin nata ba, lallai zamu iya rasata wanda na san hakan zai iya sama sadiyar rasa Inna. Hannayenta na saki na share hawayena ina kallonta, cike da ƙarfin hali na ce “Babu inda zaki je Habiba, irin wannan tunanin na ki ne yaja miki kika jefa mu cikin wannan halin, yanzu kuma zaki sake aikata irinsa? Kina tunanin aikata wannan abun shine mafita? Ba zai canja komai ba, sai dai ma ya ƙara ɓata ran Inna har ta kasa yafe miki, mu kuma ki ja mana ɓacin suna, haka kike so?” Ta girgiza kai alamar a'a, muryarta a shake ta ce. “Ta ce ta yi nadamar haihuwata ni ce ajalinta, ba zata yafe min ba” Hannu na kai na sake riƙe hannayenta. “Zata yafe miki Habiba, ni ma uwace na san halin da Inna take ciki, akwai zafi idan wani abu ya samu ɗanka musamman mace, idan wani abu ya sami Noor bana iya yafewa kaina, bana iya controlling kaina bana iya juriya, kin san saboda me? Saboda Ina ƙaunar Noor, a duk faɗin duniya babu wacce zata gwadawa ɗa so kamar uwarsa, duk abunda Inna ta yi miki saboda tana ƙaunarki ne ke kanki kin san Inna tana son ki, karki yarda ki gudu idan har kika gudu babu ni babu ke har abada!” “Ba zan gudu ba, ba zan je ko'ina ba na miki alƙawari, ko da kuwa Inna zata yanka ni ne” Ya faɗa cikin kuka. Sai na zaunar da ita ina share mata hawayenta, tare da yi mata wasu kalaman da zasu ƙarfafa mata guiwa. Ban bar ɗakinba sai da na tabbatar kuka da take ya tsagaita, sannan na fito na shiga ɗakin Inna. Gurin da barta a nan na sameta sai wannan karon tana daga kwance ne, gurin da fuskarta take ya jiƙe da ruwan hawaye kamar an zuba ruwa a gurin. Daga inda na ke tsaye na soma mata magana ciki da ƙarfin hali. “Habiba ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin kamar hakan shine mafita, ta aikata abunda ta aikata saboda Baba da ke da kuma mu duka, kin yarda da ƙaddarar da ta samu Baba har kika riƙa bani haƙuri, shin miyasa ba zaki yarda da wannan ƙaddararba...?” Tashi tayi zaune ta kalleni a tsawace ta amsa min “Saboda ita ta kai kanta” Na matsa kusa da ita “Akwai ƙurciya da tare da ni balle kuma Habiba, hankalinta da tunaninta be kai inda kike tunaniba, babu banbanci tsakanin wannan ƙaddarar da kuma wacan dukansu ƙadarori ne, babu wanda ya dace ya nunawa Habiba soyayya a yanzu fiye ke, babu wanda zai mata magana hankalinta ya kwanta fiye da ke” “Habiba ta ɗauko wata rayuwa wacce bata gidan nan ba, sam wannan ba tarbiyarmu ba ce” “Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar ƙaddarace, ashe ko haka ya isa yasa ki rumgumeta ki nuna mata kina tare da ita” Ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalleni “Kina da ƙarfin zuciya Nawwara, haƙiƙa Muhammad Noor ya yi sa'ar uwa” “Ƙarfi guiwata taki ce Inna, kin rigani zama uwa kin fini sanin komai a rayuwa” Wani dogon numfashi taja ta sauke tana cige baki ta ce. “Wani lokacin kaina ya kan kulle har na yi tunani ba dai-dai, Allah ya kan jarrabi bawa da abubuwa da dama har bawa ya ga kamar Allah baya sonshi” “Zamu jarrabeku da yunwa da tauyewar ƴaƴan ittatuwa da rayukan da dokiyoyi, ka yi bushara ga masu haƙuri (Masu jure waɗannan jarabce-jarabce) Waɗanda idan masifa ta samesu sai su ce (Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un) Mu ɗaga gurin Allah muka fito kuma a gare za a maida mu, kyakkawar yabo ya tabbata agaresu daga Ubangijinsu, haka Allah ya faɗa a ciki alƙur'ane mai girma, akwai kuma inda Allah yake cewa ‘Ko wane tsanani yana tare da sauƙi har ya sake maimaitawa Haƙika ko wane tsanani yana tare da sauƙi, sai kuma ya ce Fasbir sabaran jaamila wato ya kai Annabi ka yi haƙuri haƙuri mai kyau, Allah yana tare da masu a haƙuri. Inna duka waɗannan Allah ne ya faɗa. Kin tuna lokacin da na yi aure? Na fuskanci wulaƙanci da ƙalubale kala-kala a gidan aurena, har na fito na haifi Noor cikin baƙinciki da damuwa, na sake wani auren har na fara jindaɗi sai Allah ya karɓe abunsa, na sake dawowa cikin wannan wahalar, sa'anina da wanɗanda muka yi makaranta tare da su, duk sun zama manyan mutane har basa son abota da ni, ni kuma ina nan, amman hakan be taɓa saka ni na yi tunanin ko Allah baya so na ne ba ko da sau ɗaya, da ace Allah ya yi ni kafira da zan yarda Allah baya so na saboda komai na tara a duniyarnan zan mutu na bar shi naje ƙiyama na shiga wuta, amman kin ga yanzu zan iya sha wahala a nan idan har na aikata aiki na ƙwarai ina zuwa ƙiyama kai tsaye aljannah zan wuce, kuma kin ga can ba a mutuwa ba a baƙinciki balle tsufa. Ki rumgume ƙaddarar nan Inna, karki yi Habiba abunda zai ƙara mata baƙinciki, ta ce min zata gudu ta bar gidan nan saboda kar ta zama silar ajalinki” Da sauri Inna ta miƙe tsaye da sauri hankalinta a tashe. “Ina take?” “Tana ɗakinmu” Da gudu ta nufi ɗakin, ni kuma na rufa mata baya. Ko da muka shiga ɗakin sai muka samu babu kowa a cikinsa, daga ni har Inna sai da gabanmu ya faɗi, Inna ta juyo ta kalleni nima na kalleta. “Habiba” Na kira sunanta da ƙarfi, sai ta amsa min daga bayan gambu da take ɓoye, a zatonta Inna zata faɗa mata wata maganar marar daɗi ne ko kuma ta daketa hakan yasa ta ɓuya a nan. Da sauri Inna ta duba gurin domin ta fini kusa da shi sai ga Habiba a tsaye tana hawaye jikinta na rawa tana jiran sakamakon Inna. “Zo nan ƴata na yafe miki duniya da lahira, Allah ya yi miki albarka, ya isar miki” Inna ta faɗa tana miƙa hannu taja Habiba jikinta ta rumgume, sai suka fashe da kuka, sai nima na fara nawa kukan da daga inda na ke tsaye, a raina kuma ina ta godiyar Allah. *** *** *** Haka muka wuni a cikin gidan kamar waɗanda akayi wa mutuwa, Sakina da Jamila ma sun lura da haka su kansu basa wani sakewa saboda ganin kamar muna cikin damuwa, Noor ne kawai yake ta sha'aninsa shi kan be ma damuba. Washe gari kasa zuwa aiki na yi saboda na tashi jikina da kuma zuciyata babu daɗi, duk yadda Inna ta so naje sai na ƙi, su Sakina kawai suka je makaranta, mu kuma muna gida shiru-shiru babu wani motsin kirki da ɗayanmu ke yi, misalin ƙarfe ɗaya da rabi Bilal ya kirani ina ɗauka sai ya fara tambaya miyasa ban je aiki ba, ni kuma na amsa masa da cewar babu komai, sai dai ban yarda ba yana ganin kamar ɗan ya ganni babu hijabi jiya ne yasa na yi fushi. Jikin Habiba ya ƙara tsanani da yamma, har na ke bada shawarar mu kaita asibiti sai Inna ta ƙi saboda aganin asiri mu zai tonu. “Idan mukaje asibiti zasu faɗa mana ciki ne, wanda nasan nan da nan za a ji a unguwar nan, ya kike so acewa Yakumbo da kuma mutane babban gida? Da wane ido zamu kallesu, yanzu zasu ce dan margayi ba shi da rai ne na ƙyale Habiba ta aikata wannan abun ni zasu ɗorawa laifi” “Da ido da muke kallonsu Inna, tun bayan da aka gama amsar gaisuwa kin saki ganin ƙafar wani a gidan nan? Ba mu da nisa da su amman basu taɓa ɗauko ƙafa suce bari su leƙo mu suga ya muke ba, kowa harkar gabansa yake” Ta yi shiru kamar ba komai kamar mai tunani can kuma ta kalleni “Ni da wai na ce ko zubar da cikin zamu yi?” Gabana ya faɗi, naji maganar kamar saukar aradu. “A'a Inna idan muka je zubar da cikin ai dole za'aji” “Ba asibiti ba wai gida” “Taya zamu zubar da ciki gida?” “Ƴan kayan ɗacin nan da ake badawa mana, tun da kin ga yanzu be yi ƙwari ba kuma a iya busa masa rai ba, idan har be zube ba sai mu ƙyaleta” Na kasa cewa komai saboda na lura ranta ya kwaɗaitu da a zubar da cikin, duk da ina ganin zubar da cikin yana daga cikin alamomin rashin yarda da ƙaddara. Tausayin Habiba ne ya kamani sai na ji ina ma nice ba ita ba, hawaye suka zubo min sai na yi saurin tashi tsaye ina faɗin. “Bari naje na siyo mata maganin zazzaɓi” Inna ta amsa min da tau cikin yanayin damuwa, ɗaki na nufa na ɗauko Hijabina ina kallon Habiba take kwance malala kamar lakka. Kamar na fasa kuka haka na fito ɗaga ɗakinmu bayan na ɗauko ƴan canjina na fita zuwa siyo mata magani, har na isa tunanin maganar Inna nake, ta yadda zan yi na hanata kawai na ke nema. Bayan mum gaisa da mai shagon maganin sai na miƙa masa ɗari biyu na ce ya haɗa min maganin zazzafi kala-kala. Ya haɗa min kusa kala takwas cikin har da na malaria da na ciwon kai da na zafin jiki, ya ɗora min a saman gilashin da suke ɗora magani ni kuma na karbi leda na saka ina jiran canji. Sai kawai na ga Mustapha cikin shagon kamar an jefoshi, matsawa yayi kusa da ni sosai yana min magana ta yadda babu wanda zai ji “Ki yi haƙuri da abunda ya faru ranar nan, Wallahi ba da ke nake ba da mai Napep ɗin daya ɗauko ki na ke” Ji na yi kamar ace akwai wuƙa kusa da ni na daɓa masa a ƙirji, wani ɗogon tsaki naja wanda ya jawo hankalin duk wanda ke shagon zuwa garemu, na ɗauki canjina na fice zuciyata na bugawa kamar zata fito saboda ɓacin rai. NOT EDITED ⚠️ SHARE, COMMENT, VOTE. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣6⃣ Haƙiƙa akwai ƙurciya a rayuwar Habiba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta aikata abunda ta aikata, wanda take tunanin kamar mafitane, sai gashi ya zame mana matsala, yanzu kuma tana ganin kamar guduwa ta bar gida shi ma mafita ne, ni ko nasan duk yarinyar da ta gudu ta bar iyayenta lallai tana tare da na sani da kaico a rayuwarta. Ba zan bari ƴar'uwata ta aiwatar da wannan ƙudirin nata ba, ko da kuwa haka yana nufi salwantar rayuwar mahaifiyata ne, ba zan bari ta sake aikata wani kuskuren ba. Ƙoƙari nake na tsayarda kuka ta yadda zan ƙarfafa mata guiwa da rarrashi amman hawayen da ke min zuba sun ƙi bani haɗin kai. Idan har ban yi ƙarfin halin shiga tsakaninta da wannan kuɗirin nata ba, lallai zamu iya rasata wanda na san hakan zai iya sama sadiyar rasa Inna. Hannayenta na saki na share hawayena ina kallonta, cike da ƙarfin hali na ce “Babu inda zaki je Habiba, irin wannan tunanin na ki ne yaja miki kika jefa mu cikin wannan halin, yanzu kuma zaki sake aikata irinsa? Kina tunanin aikata wannan abun shine mafita? Ba zai canja komai ba, sai dai ma ya ƙara ɓata ran Inna har ta kasa yafe miki, mu kuma ki ja mana ɓacin suna, haka kike so?” Ta girgiza kai alamar a'a, muryarta a shake ta ce. “Ta ce ta yi nadamar haihuwata ni ce ajalinta, ba zata yafe min ba” Hannu na kai na sake riƙe hannayenta. “Zata yafe miki Habiba, ni ma uwace na san halin da Inna take ciki, akwai zafi idan wani abu ya samu ɗanka musamman mace, idan wani abu ya sami Noor bana iya yafewa kaina, bana iya controlling kaina bana iya juriya, kin san saboda me? Saboda Ina ƙaunar Noor, a duk faɗin duniya babu wacce zata gwadawa ɗa so kamar uwarsa, duk abunda Inna ta yi miki saboda tana ƙaunarki ne ke kanki kin san Inna tana son ki, karki yarda ki gudu idan har kika gudu babu ni babu ke har abada!” “Ba zan gudu ba, ba zan je ko'ina ba na miki alƙawari, ko da kuwa Inna zata yanka ni ne” Ya faɗa cikin kuka. Sai na zaunar da ita ina share mata hawayenta, tare da yi mata wasu kalaman da zasu ƙarfafa mata guiwa. Ban bar ɗakinba sai da na tabbatar kuka da take ya tsagaita, sannan na fito na shiga ɗakin Inna. Gurin da barta a nan na sameta sai wannan karon tana daga kwance ne, gurin da fuskarta take ya jiƙe da ruwan hawaye kamar an zuba ruwa a gurin. Daga inda na ke tsaye na soma mata magana ciki da ƙarfin hali. “Habiba ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin kamar hakan shine mafita, ta aikata abunda ta aikata saboda Baba da ke da kuma mu duka, kin yarda da ƙaddarar da ta samu Baba har kika riƙa bani haƙuri, shin miyasa ba zaki yarda da wannan ƙaddararba...?” Tashi tayi zaune ta kalleni a tsawace ta amsa min “Saboda ita ta kai kanta” Na matsa kusa da ita “Akwai ƙurciya da tare da ni balle kuma Habiba, hankalinta da tunaninta be kai inda kike tunaniba, babu banbanci tsakanin wannan ƙaddarar da kuma wacan dukansu ƙadarori ne, babu wanda ya dace ya nunawa Habiba soyayya a yanzu fiye ke, babu wanda zai mata magana hankalinta ya kwanta fiye da ke” “Habiba ta ɗauko wata rayuwa wacce bata gidan nan ba, sam wannan ba tarbiyarmu ba ce” “Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar miki da cewar ƙaddarace, ashe ko haka ya isa yasa ki rumgumeta ki nuna mata kina tare da ita” Ajiyar zuciya ta sauke kana ta kalleni “Kina da ƙarfin zuciya Nawwara, haƙiƙa Muhammad Noor ya yi sa'ar uwa” “Ƙarfi guiwata taki ce Inna, kin rigani zama uwa kin fini sanin komai a rayuwa” Wani dogon numfashi taja ta sauke tana cige baki ta ce. “Wani lokacin kaina ya kan kulle har na yi tunani ba dai-dai, Allah ya kan jarrabi bawa da abubuwa da dama har bawa ya ga kamar Allah baya sonshi” “Zamu jarrabeku da yunwa da tauyewar ƴaƴan ittatuwa da rayukan da dokiyoyi, ka yi bushara ga masu haƙuri (Masu jure waɗannan jarabce-jarabce) Waɗanda idan masifa ta samesu sai su ce (Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un) Mu ɗaga gurin Allah muka fito kuma a gare za a maida mu, kyakkawar yabo ya tabbata agaresu daga Ubangijinsu, haka Allah ya faɗa a ciki alƙur'ane mai girma, akwai kuma inda Allah yake cewa ‘Ko wane tsanani yana tare da sauƙi har ya sake maimaitawa Haƙika ko wane tsanani yana tare da sauƙi, sai kuma ya ce Fasbir sabaran jaamila wato ya kai Annabi ka yi haƙuri haƙuri mai kyau, Allah yana tare da masu a haƙuri. Inna duka waɗannan Allah ne ya faɗa. Kin tuna lokacin da na yi aure? Na fuskanci wulaƙanci da ƙalubale kala-kala a gidan aurena, har na fito na haifi Noor cikin baƙinciki da damuwa, na sake wani auren har na fara jindaɗi sai Allah ya karɓe abunsa, na sake dawowa cikin wannan wahalar, sa'anina da wanɗanda muka yi makaranta tare da su, duk sun zama manyan mutane har basa son abota da ni, ni kuma ina nan, amman hakan be taɓa saka ni na yi tunanin ko Allah baya so na ne ba ko da sau ɗaya, da ace Allah ya yi ni kafira da zan yarda Allah baya so na saboda komai na tara a duniyarnan zan mutu na bar shi naje ƙiyama na shiga wuta, amman kin ga yanzu zan iya sha wahala a nan idan har na aikata aiki na ƙwarai ina zuwa ƙiyama kai tsaye aljannah zan wuce, kuma kin ga can ba a mutuwa ba a baƙinciki balle tsufa. Ki rumgume ƙaddarar nan Inna, karki yi Habiba abunda zai ƙara mata baƙinciki, ta ce min zata gudu ta bar gidan nan saboda kar ta zama silar ajalinki” Da sauri Inna ta miƙe tsaye da sauri hankalinta a tashe. “Ina take?” “Tana ɗakinmu” Da gudu ta nufi ɗakin, ni kuma na rufa mata baya. Ko da muka shiga ɗakin sai muka samu babu kowa a cikinsa, daga ni har Inna sai da gabanmu ya faɗi, Inna ta juyo ta kalleni nima na kalleta. “Habiba” Na kira sunanta da ƙarfi, sai ta amsa min daga bayan gambu da take ɓoye, a zatonta Inna zata faɗa mata wata maganar marar daɗi ne ko kuma ta daketa hakan yasa ta ɓuya a nan. Da sauri Inna ta duba gurin domin ta fini kusa da shi sai ga Habiba a tsaye tana hawaye jikinta na rawa tana jiran sakamakon Inna. “Zo nan ƴata na yafe miki duniya da lahira, Allah ya yi miki albarka, ya isar miki” Inna ta faɗa tana miƙa hannu taja Habiba jikinta ta rumgume, sai suka fashe da kuka, sai nima na fara nawa kukan da daga inda na ke tsaye, a raina kuma ina ta godiyar Allah. *** *** *** Haka muka wuni a cikin gidan kamar waɗanda akayi wa mutuwa, Sakina da Jamila ma sun lura da haka su kansu basa wani sakewa saboda ganin kamar muna cikin damuwa, Noor ne kawai yake ta sha'aninsa shi kan be ma damuba. Washe gari kasa zuwa aiki na yi saboda na tashi jikina da kuma zuciyata babu daɗi, duk yadda Inna ta so naje sai na ƙi, su Sakina kawai suka je makaranta, mu kuma muna gida shiru-shiru babu wani motsin kirki da ɗayanmu ke yi, misalin ƙarfe ɗaya da rabi Bilal ya kirani ina ɗauka sai ya fara tambaya miyasa ban je aiki ba, ni kuma na amsa masa da cewar babu komai, sai dai ban yarda ba yana ganin kamar ɗan ya ganni babu hijabi jiya ne yasa na yi fushi. Jikin Habiba ya ƙara tsanani da yamma, har na ke bada shawarar mu kaita asibiti sai Inna ta ƙi saboda aganin asiri mu zai tonu. “Idan mukaje asibiti zasu faɗa mana ciki ne, wanda nasan nan da nan za a ji a unguwar nan, ya kike so acewa Yakumbo da kuma mutane babban gida? Da wane ido zamu kallesu, yanzu zasu ce dan margayi ba shi da rai ne na ƙyale Habiba ta aikata wannan abun ni zasu ɗorawa laifi” “Da ido da muke kallonsu Inna, tun bayan da aka gama amsar gaisuwa kin saki ganin ƙafar wani a gidan nan? Ba mu da nisa da su amman basu taɓa ɗauko ƙafa suce bari su leƙo mu suga ya muke ba, kowa harkar gabansa yake” Ta yi shiru kamar ba komai kamar mai tunani can kuma ta kalleni “Ni da wai na ce ko zubar da cikin zamu yi?” Gabana ya faɗi, naji maganar kamar saukar aradu. “A'a Inna idan muka je zubar da cikin ai dole za'aji” “Ba asibiti ba wai gida” “Taya zamu zubar da ciki gida?” “Ƴan kayan ɗacin nan da ake badawa mana, tun da kin ga yanzu be yi ƙwari ba kuma a iya busa masa rai ba, idan har be zube ba sai mu ƙyaleta” Na kasa cewa komai saboda na lura ranta ya kwaɗaitu da a zubar da cikin, duk da ina ganin zubar da cikin yana daga cikin alamomin rashin yarda da ƙaddara. Tausayin Habiba ne ya kamani sai na ji ina ma nice ba ita ba, hawaye suka zubo min sai na yi saurin tashi tsaye ina faɗin. “Bari naje na siyo mata maganin zazzaɓi” Inna ta amsa min da tau cikin yanayin damuwa, ɗaki na nufa na ɗauko Hijabina ina kallon Habiba take kwance malala kamar lakka. Kamar na fasa kuka haka na fito ɗaga ɗakinmu bayan na ɗauko ƴan canjina na fita zuwa siyo mata magani, har na isa tunanin maganar Inna nake, ta yadda zan yi na hanata kawai na ke nema. Bayan mum gaisa da mai shagon maganin sai na miƙa masa ɗari biyu na ce ya haɗa min maganin zazzafi kala-kala. Ya haɗa min kusa kala takwas cikin har da na malaria da na ciwon kai da na zafin jiki, ya ɗora min a saman gilashin da suke ɗora magani ni kuma na karbi leda na saka ina jiran canji. Sai kawai na ga Mustapha cikin shagon kamar an jefoshi, matsawa yayi kusa da ni sosai yana min magana ta yadda babu wanda zai ji “Ki yi haƙuri da abunda ya faru ranar nan, Wallahi ba da ke nake ba da mai Napep ɗin daya ɗauko ki na ke” Ji na yi kamar ace akwai wuƙa kusa da ni na daɓa masa a ƙirji, wani ɗogon tsaki naja wanda ya jawo hankalin duk wanda ke shagon zuwa garemu, na ɗauki canjina na fice zuciyata na bugawa kamar zata fito saboda ɓacin rai. NOT EDITED ⚠️ SHARE, COMMENT, VOTE. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣7⃣ ‘Ba a banza ya baki haƙuri ba, taya zai baki haƙuri mutumen da ba ya ganin kowa da mutuncin, ba dake yake ba kika mareshi sai kuma yanzu ya zo ya baki haƙuri, lallai akwai abunda yake nufi da ke’ Shine abunda na ke ta saƙawa a zuciyata, a zahiri kuma sai nan nemin tsarin Allah akansa. “Allah ka min tsari da sherinsa” Har na iso gida ina ta saƙe-saƙen abubuwa biyu a raina, maganar zubar da cikin Habiba da kuma haƙurin da Mustapha ya ba ni. Na samu kaina da faɗuwar gaba sakamakon hango Bilal da na yi a tsaye ƙofar gidanmu, cikin rashin kuzari na ƙarasa daman can babu kuzarin a tare da ni. Lokacin da na ƙarasa kusa da ƙofar gidanmu sai na tsaya dai-dai inda yake tsaye ina masa sallama. “Assalamu alaikum” A maimakon ya amsa min sai kawai ya ɗaga idonsa dake ƙasa ya kalleni. “Miya hana ki zuwa aiki yau?” Ajiyar zuciya na fara saukewa sannan na haɗe yawun da ke bakina na fara magana a daƙishe. “Bana jindaɗi ne” “Miyasa baki kira kin sanar min ba?” Yanzu kan bansan mi zan ƙara ce masa ba, shirun da na yi ne ya bashi damar fassara ni da abunda yake hasashe. “Saboda kin yi zaton na ganki ko? Wallahi Nawancy ban ganki babu Hijab ba, lokacin sa kike aikinki ina can ina nawa aikin, ba zan miki alƙawari ba amman zan yi ƙoƙari na kawar da idona daga kallonki idan kina aiki” “Wallahi ba saboda haka ba ne Bilal, kawai akwai abunda ya ke damuna” “Ko zan iya sanin minene?” “Sanin ba shi da amfani, barin wannan sirrin a cikina zai fi min amfani” Magana nake kamar zan fara kuka saboda damuwar da ke raina. Shi kansa ya fahimci haka saboda be saba ganina cikin irin wannan yanayin ba. “Allah ya yaye miki damuwarki Nawancy, Allah ya zama gatanki, ƴa shiga dukan lamarinki ya tsareki daga dukan sheri, ya jiɓɓanci lamarinki, kada Allah ya barki da kanki” “Amin” Na amsa hawaye na bin fuskata. Ya lumshe ido ya buɗe. “Ki shiga ciki, ni zan wuce, daman na rubuta wasiƙa a gurin aiki amadadakin cewar baki da lafiya” “Zan shigo gobe” Na faɗa ina share hawayen idona. “Karki dakurawa kan ki, and if you need someone to talk to i'm here” “Thank you Bilal you have encouraged me every time, Without you I don't think I could ever be fine” Na faɗa kuka na cin ƙarfina sosai. Har ga Allah ina jindaɗin zama da Bilal yana ƙarfafan min guiwa, yana damuwa da damuwata ko kaɗan baya son ganin ɓacin raina. “Get some rest” Na gyaɗa masa kai sannan na shiga cikin gida ina jin kamar na rafke na faɗi. Ɗakinmu na nufa jiki babu ƙwari, sai na samu Habiba a zaune tare da Inna kwanon ruwa na gaban Habiba jiƙe da magani. Na zauna nima ina buɗe ledar maganin. “Gashi ya ce wannan uku zaki sha, wannan kuma biyu biyu sai wannan shi ma uku” Na faɗa mata yadda ya rubuta a jikin kwalin maganin, sauran kuma duka na ɗiba ne, wasu biyu wasu huɗu. “Tau ki bari har a jima ki sha, yanzu na jiƙa mata tagargade da gishiri ta sha” Cewar Inna ni kuma na kalleta cike da mamaki. “Tagargade da gishiri kuma Inna?” “Ee yana yanke mara, wai ko za a samu cikin ya zube” Wani dogon numfashi naja na sauke, na san ko na yi magana ba lallai ne Inna ta fahimta ba, idan har kuma nasa ta bar cikin a can gaba wani abun ƴa faru zata ɗora laifin a kaina. “Bani maganin na sha ko zan samu sauƙin zazzaɓin nan” Habiba ta faɗa tana miƙo min hannu. Tashi na yi na ɗebo mata ruwa na miƙa mata maganin ta sha, sannan na je na yi alwala har na yi sallah tunani ne a raina.   A tare da ita muka kwana a ɗakin, duk bayan minti biyu zuwa uku Inna sai ya miƙa mata tagargaden ta sha, haka ta kwana wulle-wulle sai abun ya zame mata biyu ga zazzaɓi ga ciwon ciki. Ita ke ciwon amman ni na kwana kuka ina jin zafin ciwon kamar a jikina ya ke, can kusan asuba Allah ya bata sauƙi har ta samu bachi. Ni kuma na tashi da ciwon kai na yi alwala na yi sallah, ina zaune saman carpet ɗin ina karatun ƙur'ane har rana ta soma huduwa.  Tashi na yi cikin ƙanƙanen lokaci na shirya na aika Sakina ta siyo kunu suka sha domin ni ko ruwa bana iya kaiwa a bakina. Haka na kama hanya zuwa gurin aiki ba tare da na saka komai a cikina ba, duk kuwa da kasancewar ana cewa fita ba a karya ba bashi da kyau. Har na isa gurin aikin jina nake kamar ba ni ba, sai nake jin kamar ba ni nake motsa jikina ba, wata ƙila saboda nauyin da na tashi yana min yau ne. As usual sai da nayi duk abunda ya dace tun daga kan rubuta suna da time na yi komai sannan na shiga cikin kamfanin na soma aikina. Ina daf da ƙarewa a ɗaki na ƙarshe, Amina ta shigo tana min magana kaɗan-kaɗan. “Ƙawata ana kiranki, wai kin yi mopping da ruwa da yawa, matar nan sai masifa take” “Wacece?” “Wata mai'aiki a nan ce amman ita babba ce dan har office tana da shi” Ba musu na bita muka tafi inda ta ce ana kirana ɗin wato a ɗakin dana fara mopping, abun mamaki sai na samu Zinatu tsaye a ɗakin tana sanye da suit da baƙin gilashi hannunta riƙe da wani ƙaramin akwati. “Nawwara ke kika yi mopping ɗin gurin nan?” Na ɗaga mata kai alamar Ee. “Amman fisabilillahi haka ake mopping? Wai miyasa idan zaku yi abu baku yinsa tsakani da Allah, yanzu idan gidanku ne haka zaki yi, aikin nan fa biyanku za'ayi amman kuka abu da kissa kamar kyauta kuke yinsa haka sam be dace ba, yau da safen nan meeting zamu yi da manyan mutane yanzu idan suka shigo suka duba yadda kamfanin nan yake ai sai kuja mana ɓacin suna” Yadda ta runtse ido take min masifa kamar bata san wacece ni ba, tabbas na bar ruwa saboda ga gurin nan har yanzu be bushe ba, sai dai ba da gangan na yi haka ba, na yi mopping ɗin ne a lokacin da hankalina baya gurin, sai dai ban jidaɗin yadda take ɗaga min murya ba kamar wata uwata. “Ki yi haƙuri zan kiyaye a gaba” Na faɗa abunda yake har a zuciyata shine, ƙawata sai dai a nan kuma ita ce babba a gurin aikina, kuma dole ne na bita idan har ina son cigaba da aikin. “Better” Ta furta tana ƙoƙorin juyawa sai ga wani mutun ya shigo shima cikin shigar suit sai dai na shi blue ne tsaɓanin nata da suke baƙaƙe. Har ya buɗe baki ya yi magana sai kuma ya fasa sakamakon idonsa da suka sauka a kaina. Bakinsa a sake yake kallona fuskaraa na nuna alamun mamaki, hakan yasa kunya ta rufe ni domin tun da na shigo kamfanin a yau ban samu kaina da jin kunyar tufafin da ke jikina saboda damuwata ta mantar da ni komai. Sai dai kallon da yake min ya ya karantar da ni da akwai wani abu, wata ƙila ya daba ganina da Hijabi yau kuma ya gan ni babu Hijabi ko kuma dai yana mamakin yadda na ke aikin ne, tau tsaya ma wai ni ina na san shi balle na yi tunanin haka ni dai fuskarsa bata min kama da wanda na sani ba, wata ƙila dai shi ya sanni ne kai sai ka ce wata ƴar film ko mawaƙiya. Ni kaɗai na ke ta tsaƙe-tsaƙe na domin kuwa Zinatu ta daɗe da ficewa ɗakin, yanzu daga ni sai shi ne sai kuma Amina. “Newcomer?” Ya tambaya ni kuma sai na gyaɗa masa kai. “Your Name?” Ya sake tambaya. “Nawwara” Ya rausayar da kansa sannan ya sake kallon na from head to toe sai ya juya ya fice. “Shine mai kamfanin?” Ma tambayi Amina bayan ya fice, sai ta zaro ido. “Tab mai kamfanin zai tsaya tambayar sunanki, ai yana zuwa gurin nan zai ɗaukeki mari sai kin manta hanyar garinku” “Saboda me?” “Saboda wannan kuskuren da kika yi” Na taɓe baki. “Ni kan ba zan yarda ya wulaƙanta ni ba, saboda kawai ina aiki ƙarƙashinsa” “Aiko idan baki ɗauki wulaƙanci ba, baki shirya aiki a kamfanin nan ba, amman na ga mutumen kamar ya san ki” “Ni ban ma taɓa ganinsa sai yau, da alama shima a nan yake aiki ko?” “Shi ma babba ne a kamfanin nan, kuma ance suna shiri da mai kamfanin sosai wai amininsa ne, ko meeting ne idan be samu damar zuwa ba shi yake turawa” Haka muka fito tana ta labarta abubuwa da dama akan kamfanin da kuma ma'aikatan gurin cikin har da Zinatu da take ita sabuwar zuwa, sai dai ita ta rigani zuwa da wata huɗu, yadda take ta yabon kirki da kuma halin Zinatu har sai da abun ya ban tsoro wata ƙila duk wannan mugun halin nata mu take yi ma shi mu da muke tsofin ƙawayenta. Komawa na yi ɗakin na gyara sannan na dawo na cigaba da aikina, bayan na gama na fito na nufi gurin da ake rubuta suna na rubuta duk abunda ya kamata ina kamawa sai ɗaya daga cikin mutanen da suke reception ɗin ya miƙa min wata farar takarda, ya bani wani file wai na saka hannu, bayan na yi karɓa na nufo gurin da na aje Hijabi na ɗauka na saka sannan na kama hanyar fita daga kamfanin ina warware takardar. Naira ɗari biyar ce a ciki sai kuma sunan Bilal a jikin wata ƙaramar takarda, na san ya yi haka ne saboda na nuna masa bana son na ganni babu Hijabi. Ƙasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskata murmushin da na manta rabon da na yi irinsa. Ƙamarar takardar mai sunansa na ɗauka na jeta a bakina na taune zuciyata cike da shauƙi Bilal. Wannan shauƙin shi ya kawar min da komai na damuwata har na isa gida. Da sallama na shiga Jamila da Noor suka amsa min domin sune a tsakar gida, Inna tana ɗaki tare da Habiba. “Miya hana ku zuwa makaranta?” “Noor ne ya ce ba zai je ba” Cewar Jamila kamin Noor ya karɓe mata. “A'a Wallahi ita ta fara cewa ba zata je ba, Anti Sakina ce kawai ta tafi” “Daman haka kuke so, idan bana a cikin gidan nan babu mai matsa muku kuje makaranta” Da faɗan na shiga ɗakinmu, sai na samu Habiba ita kaɗai kwance ƙasa ƙafafunta lulluɓe da ƙaton kuma tsohon Bedsheet ɗin Inna. “Habiba” Na kira sunanta a hankali, sai ta ɗago ta kalleni amman da dukan alamu kamar bata cikin hayyacinta, domin alamu sun nuna hakan. Hannu na kai na buɗe bedsheet ɗin dake rufe da ƙafafunta sai ga jini a gurin kamar an juye jalkar manja, ba shiri na saki bedsheet ɗin na yi baya-baya dafe da baki ido a waje, zuciya mugun bugawa kamar an ce min ga mutuwata nan kusa da ni.! NOT EDITED *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣8⃣ Na yi saurin rufe bakina idona cike da hawaye na nufi waje da gudu, ɗakin Inna na shiga ban sameta a ciki ba, ina fitowa waje Inna na fitowa daga banɗaki tana riƙe da buta. Kallo ɗaya ta yi min ta ɗauke kai ta nufi ɗakinmu, ni kuma na rufa mata baya hankalina a tashe. “Inna kin ga halin da take ciki kuwa?” Ya gyaɗa min kai. “Ko minti talati ba ki yi da fita ba, ta fara zubar jini ina jin cikin ne yake zubewa” Tsugunawa na yi a gurin na dafe kai ina hawaye. “Inna bata cikin hayyacinta” “Dole ne zata yi haka saboda wannan ne na farko kuma kinga yarinya ce, amman zata warke zata dawo lafiya ƙalau” “Inna dan Allah mu kaita asibiti” Na faɗa ina fashewa da kuka, sai ta ce “Babu inda zamu je Nawwara, zata warke” Ta janye bargon ta soma gyara mata jiki ni ko ina duƙe a gurin ina aikin kuka. Haka muka wuni muka kwana babu wani canji sai ma ƙari, tun ina ganin tausayinsa har zuciyata ta fara raya min wasu abubuwa marasa kyau. Ita kanta Inna ta soma tsorata ganin mun kwana da ita a haka babu wani canji, ni ko na kasa zuwa aiki saboda ina ganin kamar idan na je na barta zan dawo na tarar ta mutu, ina jin kamar idan ina kusa da ita babu abunda zai sameta. Can da yamma abun ya fara zuwa da sauƙi da har ina maganar ko Inna bata so sai na ɗauke ta na kaita asibiti saboda gudun kunya ba zan bar ƴar'uwata ta mutu ba. Jikin nata babu ƙarfi amman hankalinta ya dawo, har ma ta ɗan jiro hannunta kaɗan ta ɗora saman nawa, kasancewar ina zaune ne kusa da ita saman tabarma. Numfashi take wahalce gaba ɗaya idanuwanta sun canja kamar wata tsohuwa. “Sannu Habiba” Na faɗa cikin muryar kuka ina mai tausayin ƴar'uwata, sai ta yi min murmushi hawaye ya fito daga gefen idonta. “Ina Inna?” Ta tambaya daker cikin muryarta na marar lafiya. “Taje maƙota zata samo miki lafiya dubu” Ta yi shiru tana lumshe ido, hakan yasa na tashi na ɗebo mata ruwa, na ɗan ɗaga kanta na kai mata kofin a baki, ba laifi ta sha da yawa kamar zata haɗe kofin har mamaki na yi na ce. “Na ƙaro miki?” Sai ta girgiza kai alamar a'a, sai ta rufe idonta tana numfashi a hankali. Ganin haka yasa na miƙe tsaye domin naje na kira Inna sai na ji ta kira sunana. “Nawwara...” Sai na koma na zauna ina kallonta. “Na'am” Na amsa ina kallon idonta dake rufe. “Ance mace data mutu gurin haihuwa ana kyautata mata zaton samun aljanna saboda ta yi shahada, tau idan kuma mace ta muru gurin zubar da cikin banza fa?” Ji nayi kamar jiri ya ɗibeni, hawaye uku-uku ya soma sauko min, ta farkon ido da kuma tsakiya, sai kuma ta gefen ido. Me Habiba take nufi ne? Wannan wace irin tambaya ce take min haka? Bakina a sake nake kallon yadda take numfashi. Ina haka Inna ta shigo, da fari gabanta ya faɗi ganin hadda hawaye suke min zuba sai dai ganin Habiba ta buɗe ido yasa ta ɗanji sanyi har ma da yin murmushi ta zauna kusa da ita tana nuna mata kulawa irin ta ƴa da uwa. Ta tsorata lokacin da takai hannu ta gwale idon Habiba, ya yi ɗorawa kamar marar jini, sai ta kalleni. “Kamar bata da jini” Kai kawai na iya gyaɗawa mata, sai ta miƙe tsaye da sauri tana kiran Sakina. “Sakina zo ki siyo mata maltina da madara ta sha kamin muje asibiti” Da gudu ta shiga ɗaki ta ɗauko kuɗi ta bada a siyo mata maltina uku da madara ta bata, sai kuma ta dawo ta zauna kusa da ita tana kuka. “Na yi wauta Habiba yanzu zan kai ki asibiti, ban ɗauka abun har ya kai haka ba, kin zubar da jini da yawa” A wahalce Habiba ta soma magana. “Karki kai ni asibiti Inna, ko kin kaini mutuwa zan yi, kuma mutane zasu ji, na barku da damuwa, ƙara baki je ɗin ba domin Wallahi mutiwa zan yi-” Na yi saurin kai hannu na rufe mata baki, sai ta lumshe ido, Inna ta tashi a firgice ta fita daga gidan tana kuka, kamar jira take na janye hannuna daga bakinta sai ta ce. “Nawwara zan tafi na barki ke kaɗai...” Na sake rufe mata baki ina kuka. Sai ga Inna ta shigo. “Riƙata ga Napep can na na tsayar zamu kaita asibiti” Kamar waɗanda suka ɗauki takarda haka muka ɗaga Habiba, jikinta ya yi sanyi sosai ƙwayar idonta baƙar ta ɓata ɓat sai farin kawai kake gani. Cikin hanzari muka saka mata wasu tufafin muka saka mata Hijabi muka ɗauketa sai gurin mai Napep. Muna shirin shiga Napep ɗin Sakina ta dawo daga siyen madara da maltuna, tsabar hankalin Inna ya ɗauku bata ko iya karɓa ba muka kama hanyar asibitin uduth dake gawon nama, duk da da kasancewar mun san asibitin ta kuɗi ce. Gudu sosai mai napep ɗin ke yi amman kasancewar tsakanin unguwarmu da asibitin uduth akwai ƴar tazara sai da tafiyar ta yi mana nisa. Muna isa bakin gate ɗin asibitin, Habiba ta sauke wani irin ajiyar zuciya ta kwanto da kanta dake jikina zuwa jikin Inna, rai ya yi halinsa ƴar'uwata ta amsa kiran mahaliccinta...! I will updated 19 tomorrow morning. RIJF Habiba😭 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 1⃣9⃣ Inna ta kai hannu ta kwanto da fuskarta zuwa saman hannayenta tana murmushi. Haske sosai fuskar Habiba take goshinta ya soma taruwa da gumi. “Allah ga yata nan, ta aikata kurkure kuma na yafe mata, ina roƙon ka Allah ka yafe mata, ka karɓi baƙuncinta, Allah ka zama gatanta bata da gata sai naka, yau ƴata ta koma gareka Allah kuma nasan ba ka yi dan ƴata ba, kuma ba kayi ƴata dan ni ba, Allah ga ƴata nan ta dawo gareka, ƴata mutuminyar kirki ce dukan abunda ta aikata ta aikata ne saboda mu, Allah ka yafe mata, haƙiƙa kai mai yawan gafara ne” Inna ce take maganar tana shafa fuskar Habiba, hawayen idonta na zuba a fuskar Habiba. Sai kuma ta ɗago ta kalleni. “Kin ga abunda na aikata ko Nawwara? Saboda gudun kunya na kashe ƴata, ba a tambayar Allah miyasa ya aikata abu, abunda ya ga dama shi yake aikata a sanda ya so ga kuma wanda ya so, amman da ace ni ce na mutu a wannan lokacin zai fi, ko ba komai ni naga duniya Habiba ko yanzu take tasowa, Habiba ƴarinyar kirki kin samu rana, mutane da yawa suna fatar mutuwa a cikin wannan ranar ta jumma'ah-” Tsakanin Habiba da Inna sai na rasa wanda zan tausayawa, Habiba da ta bar duniya da ƙirciyarta ko kuwa Inna da zata shiga wani tashin hankalin a dalilin rashinta? “Na rasa *RAI BIYU* Ran mahaufinku da kuma na ƴar'uwarku, na mahaifinku saboda zalinci na ƴar'uwarku kuma saboda talauci, Allah na gode maka” Mai napep ɗin ya juyo ya kalletaa dai-dai lokacin da ya faka napep ɗinsa bakin ƙofar emergency,idonsa cike da ƙwalla ya ce “Ta mutu ne?” Sai ta ɗaga masa kai. “Juya mu koma gida daman ta ce karna kawo ta asibiti” “Da kin bari an dubata ko dogon suma ta yi” “Jikina ya bani ƴata ta tafi har a bada, sai idan na iskota” Shi ne ya matsa har aka fita da ita aka shiga da gawarta emergency, likitoci biyu suka dubata suka tabbatar mana da cewar ta mutu, sannan suka saka mana ita a motar ɗaukar gawa na asibiti saboda tausayin halin da suka ga muna ciki, mai Napep ɗin kuma ya ƙi karɓar kuɗinsa sai kuka yake kamar ƴar'uwarshi ce ta mutu. Ni dai bana iya aikin komai sai na kuka har muka iso gida. Jiniyar motar asibitin ce ta ɗago hankali kowa izuwa gidanmu, kan kace kwabo maza da yawa sun taru ƙofar gidanmu cikin har family Babanmu na babban gida, sai kuma family Inna maza da mata wanɗanda suke unguwar da kuma waɗanda bama da wata tazara mai nisa tsakanin unguwarmu da ta su. “Miyasa ta? Tun yaushe ne bata da lafiya?” Shine abunda kowa yake ta tambaya, masu kuka na yi, ciki har da kawayenta na makarantar islamiya da boko, tsakanin Sakina da Jamila bana iya banbance waye ya fi kuka a tsakaninsu, babu abunda ya fi bani tsoro kamar Noor da ya koma gefe ɗaya ya zauna ya natsu sosai ya kasa ko da guntun hawaye. Jidda ce ta shigo gidan da gudu tana ihu kamar zata tashi gidan, kuka take sosai tana kiran sunan Habiba kamar zata dawo da ita. Inna kan hawaye kawai take iya yi kamar yadda nima nake. Can kuma sai muka ji muryar Noor ya saka kuka ya yi waje da gudu yana kiran sunanta. “Wayyo Mama Habiba-” Ɗana ƙarami ne amman yasan mutuwa, yasan duk wanda ya tafi baya taɓa dawowa yasan ya yi rashin uwa har abada...! Ƙanwar Bilal ta biyu ce Zulaihatu ta shigo tana kuka sai ta kama hannuna. “Taso muje gida Bilal ya ce na zo da ke” Bana iya uh bale uh uh tana jan hannuna na bita kamar babba da yaro ina ƙwalla ita kuma tana kuka, har muka isa gidansu. Gidansu Bilal irin babban gidan nan ne mai yalwa amman ba sosai ba, ba kuma irin na masu kuɗi ba na masu rufi asiri dai-dai gwagwado, gidane da ke cike da ƴan mata daga ƙanensa da kuma cousins ɗinsa da ake riƙo gida wasu saboda suna makaranta a sokoto wasu kuma zaman ne kawai, sai kuma Mahaifiyarsa da kishiyar mahaifiyarsa, da ƙanwar babansu wato Gwaggo Rabi. Sun tausaya min sosai sun nuna kulawarsu a kaina, daga iyayen har ƴan matan da suke gida, a falon kishiyar mamansu aka fara shiga da ni na zauna sai kuma wata cousin ɗinsa ta shigo ta fita da ni zuwa ɗakin Bilal dake can gefen ɗakunan mazan gidan kuma a farkon shigowa gidan. Kamshin turarene ya fara yi mana murhbun sai kuma lallausan carpet, ya gyara ɗakin kamar na mata komai akan tsari kamar na wani babban mai kuɗi. Wutar daƙin da kunna duk da kasancewar ɗaya da rabi na rana ya yi. A saman gadonsa ta zaunar da ni har ta juya sai kuma ta juyo ta dawo ta kwantar da ni saman gadon kaina akan matashin kai, sannan ta ce “Ya Bilal ya ce a kawo ki nan saboda gudun hayaniya” Ta juya ta fice. Ƙaton hoton Bilal da ya yi da Noor nake kallo, a zahiri hoton na ke kallo amman hankalina yana can gurin Habiba da Inna. Zuwa can na lumshe ido bachin wahala ya yi gaba da ni. Ko da na farka dishi-dishi na fara gani kamin na ga dai-dai, Bilal ne zaune gurin kaina idonsa na kaina Noor kuma na bayana yana bachi sai faman sauke ajiyar zuciya yake yana wani ɗaukar numfashi, da alama ya yi kukan ne har ya gaji. Kallo kallo muka riƙa yi ni da Bilal ni na kasa tashi daga kwance da nake, shi kuma ya gagara motsawa har sai da yaga idona ya fara zubar da ƙwalla. Sai ya yi saurin kai hannunsa for the first time ya riƙa ya tayar da ni zaune, babu wani kuzari a jikina ko ƙire ji na ke kamar ba ni ce ba, fashewa na yi da kuka sai ya yi min masauki a ƙirjinsa ya rungume tsantsan. “Shiiiiiiiii” Rarrashina ya ke amman ji nake kamar yana ƙara min ƙarfin kuka, ban lura da shafa baya da yake alamar rarrashi ba sai da kukan ya tsagaita min, sai na yi saurin barin jikinsa na miƙe tsaye, shi ma ya miƙe tsaye yana kallona. “Ina zaki je?” Ban iya amsa masa ba na juya ina kuka, sai ya y hanzarin kai hannu ya juyo da ni ya rumgume a karo na biyu, a nan na rushe da kuka muka durƙushe da a ƙasa tare ni ina kuka shi kuma yana hawaye suna sauka saman kaina. Wata irin natsuwa da kwanciyar hankaline suka ziyarce ni, na ji daɗin rumgumar da ya yi daman i need some shoulder to cry, har ga Allah na san ba dan wani abun Bilal ya rungume ni ba sai dan rarrashi da kuma tausayi, hakan yasa na sake jiki na yi kuka iya yadda zan iya sannan yasa handkerchief ɗinsa ya goge min fuska yana shafa saman kaina kamar wata yarinya. “Shiiiiiii karki tashi Noor, daker na samu ya yi bachi” Gunɗe bakina na yi na lumshe ido ina sauraren bugun zuciyata, yanayin Bilal yana min kamar na tsohon mijina wato Margayi Faruk, yau a bayar tafiyarsa wani namiji mai natsuwa da kamala ya rumgume da har na samu natsuwar da na kasa samu a farkon aurena, sai dai wannan ba da ijiya uku ya rumgume ni ba. Tuna wannan yasa na yi hanzarin barin jikinsa, duk yadda ya so ya tsayar da ni sai na ƙi a dole ya biyo bayana yana min magana amman ban kula shi ba har na bar gidan. JUMMA'AT MUBARAK...😘 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣0⃣ I dedicated this chapter to each and every RAI BIYU fan's, especially RAI BIYU CONVERSATION and RAI BIYU FAN'S GROUP together with KHADEEJA CANDY NOVELS. Thank you so much for your lovely and meaningful Comments. Son So Fisabilillah 😘 •••~••• Ko da na isa gida na tarar ƴan'uwa da masu karɓar gaisuwa suna Sallah la'asar, ashe huɗu ta yi ni ban ma sani ba kasancewar na kwanta ne a lokacin da ba a fara zuwa masallaci ba. Ba zan iya kwatantan yawan mutane da na tarar a gidanmu ba, daga ɗakinmu har ɗakin Inna da tsakar gida cike ya ke da ɗan adam, hakan ya tabbatar min da an kaita gidanta na gaskiya kenan. Duk yadda na so na danne kukana sai na kasa saboda raunin zuciyata, kuka na ke haƙuri ake ba ni amman kamar wuta da fetur na zama, haƙuri na ƙara min kuka, daker mutaneɓ suka rarrasheni har wasu suka samu damar yi min gaisuwa, da yawa na ji suna faɗar dole zan yi kuka saboda shaƙuwar da ke tsakaninmu da Habiba. Bana iya kwatanta yawan mutane da ke ta zuwa gaisuwa ba, tsakanin ita da Baba bana iya banbance waya fi yawan jama'a, tun daga maza har mata, ta samu addu'ah da yabo sosai, kowa ya ji mutuwar Habiba har ma da waɗanda basu danta ba gani ko kuna jin ta rasu haka kawai babu wani ciwo. Ban tabbatar da na yi rashin ƴar'uwa ba sai da dare ya yi naga inda take kwantawa babu kowa sai matashin kanta, da kuma komatsan kayanta a gefe, ban san lokacin da na fashe da kuka ba sai kuma dariya ta biyo baya, wata ƙanwar Inna ce ta shigo ɗakin ta fita da ni zuwa ɗakin Inna, amman har lokacin ban bar kuka da dariya ba, ni kaina zan iya cewa na kusa na haukace ne a wannan lokacin. Addu'ah suka riƙa min suna tofa min har sai na dawo ina kukan kawai babu dariya, kuka ne ya saka Inna kuka, ni da ita aka rasa mai rarrashin wani. Ni da Inna ba mu runtsa ba sai dai ƙannenta ne suka samu suka yi bachi, ni kuma na tashi na raya dare ina tayi ma Habiba da Baba addu'ah da kuma Faruk, sai mutuwar ta dawo min ta yi min tsaye, duk mutanen da suka da muhimmanci a rayuwata ina ta rasa su. Ka rasa mahaifina sai kuma na ƴar'uwata, na rasa RAI BIYU masu muhimmanci a rayuwata, kuma duk a cikin shekara ɗaya. Har aka yi kwana ukun Habiba aka gama bana aikin komai sai kuka, bana iya cin komai sai ruwa, a wannan babin kan na yarda Inna ta fini tawwakkali domin da kanta tana kan zauna na bani haƙuri tana min maganganu masu tausasa zuciya, amman na kasa jurewa wannan ƙaddarar kan na saka ɗaukarta, a kowa ne dare gani nake kamar Habiba zata dawo, bana da mafarki sai nata, da naja numfashi na sauke addu'ah nake mata, ƙiriƙiri bachi ya gagareni duk dare bana iya bachi har garin Allah ya waye, wani lokacin Bilal ya kan shigo har cikin gidan saboda bana fita ya riƙa min nasiha yana jana da hira wai ko zan sake amman ina na kasa kai zuciya nesa, Jidda ma ta yi iya yinta har ta gaji ta sa min ido. Haka na kwashe sati biyu babu wani canji tsakanin ni da Noor domin shi ma idan yana bachi kiran sunanta yake, idan zai ci abinci sai ya ambaci sunanta saboda mun saba cin abinci tare, da an taɓa shi ya buɗe baki yana kiran Mama Habiba. Ranar da ta cika kwana goma shabiyar a ƙabarinta ina zaune waje ina karatun ƙur'ane Noor ya kwanto jikina yana kuka. “Momy miyasa idan aka mutu ba a dawowa?” Kallonsa na yi, da farko rasa na yi mi zaɓ ce masa sai kuma na yi ƙarfin halin ba shi amsa. “Haka Allah yaso, kuma duk wanda ya samu lahira baya ƙaunar dawowa duniyar nan, sai dai mu iskeshi” “Momy nima ina son na mutu naje inda Mama Habiba, kullum ina mafarkinta bana jindaɗi idan bata nan” Ya faɗa yana kuka, sai na rufe ƙur'ane na aje gefe na kwantar da kansa saman cinyata ina shafa kansa, shi kuka ni kuka. Na yi kuka sosai har sai dai na jawa kaina ciwon kan da ban taɓa irinsa ba, domin har cikin ƙashin bayana yaƙe sauko min, a ranar bana iya ko da motsin kirki har sai da aka kira wani nurse ya duba ni ya bani magani. Wasa wasa ciwo ya fara min yawa yau ciwo gobe lafiya tun abun be kama Inna ba har ya soma bata tsoro, sau biyar ana min ƙarin ruwa amman kamar zubarwa ake, duk nabi na rame na lalace farar fatata ta soma ɗuhu, gashi bana iya cin komai. Haka Inna zata saka ni a gaba tana kuka tana cewa ni ma rasa ni zata yi, damuwar da nake ganin tana ciki ne yasa na ragewa kaina tunani ta yadda zan samu na riƙa cin abinci ko da kaɗan ne, domin nurse ɗin ya faɗa min matuƙar ban daina tunani ba ba zan taɓa jin sauƙi ba, kuma ba zan taɓa iya cin komai ba, idan zan kwanta sai na shimfiɗa zanen da Habiba take shinfiɗawa na yi matashin kai da fillonta hakan yasa sai ma ji kamar tana kusa da ni. Da addu'o'i da ƙarfin hali na fara samun sauƙi, cikin sati ɗaya na koma normal sai dai ban iya maida jikina ba, lafiyata ma bata dawo gaba ɗaya ba, amman Alhamdulillah na dawo cikin hayyacina ma miƙa lamarina ga Ubangijina, har na kan fita naje gidansu Jidda saboda rage kewa, Bilal kuma ya yi min sallama na fita mu gaisa na tattara komai na adana a zuciyata, na tabbatar da ace ana buɗe zuciya da tawa zuciyar idan aka buɗe ba za a tarar da komai ba sai damuwa, baƙincikin, tunani, da kuma hudu na rashin RAI BIYU da na yi. Walwalar da nake tasa Noor ma ya sake har yana sawarsa da yara, sai dai duk da haka idana ka masa wani abu sai ya shigo yana kuka ko ya ce da Mama Habiba na nan da yanzu ta rama masa, Sakina ce ta ɗauke halin Habiba a gidanmu duk wani aiki da Habiba take Sakina ce take yinsa a yanzu, Noor ma idan aka masa wani abun itace kan gaba wajen magana, sosai take ɗauke min kewar Habiba daman suna kama sosai da Habiba ta fuska da kuma ta magana, inda suke da banbanci Habiba tana da tsawo ya yinda Sakina take gajeruwa sai dai ba can sosai ba. A kwana a tashi hasarar mai rai! Wasa-wasa kwanaki suka soma ja, har Habiba ta haura wata ɗaya da rasuwa, a zuwa yanzu kan mun fara sabawa da rashinta, sai dai duk da hakan kewarta bata bari na bachi har sai na kwantar akan shinfiɗarta. Ranar da Inna ta fita wanka, wato ta gama taƙaba sai mutuwar Habiba da ta Baba ta dawo mana sabuwa. Mutane da dama kama daga ƴan'uwa, maƙota abokan arziki suyi ta shigowa suna mana barka da fita wanka da Inna ta yi lafiya. Sai dai babu Family Bilal ko ɗaya da ya zo mana barka da fita wanka, hakan be bani mamaki ba daman can na san ƴan gidansu ba son alaƙar dake tsakanin mu suke ba. Bilal kan sai dare ya zo, ya kawo ma Inna atamfa vilisco ta dubu biyar da kuma wax ita ta dubu biyar da Hijab mai kyau yadi huɗu, sai turaruka da man shafawa da kuma kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, abunda yan uwan Babanmu suka kasa yi, ko atamfar roba ka rasa wanda zai siyo ya kawo ma Inna da suna ta saka na fitar wanka saboda rashin haɗin kai da kuma halin ko'in kula nasu. Duk yadda Inna ta so ta rage kaya sai Bilal yaƙi yarda wai idan har ta mayar masa hakan na nufin bata ɗauke shi ɗa ba. A bakin ƙofar gida muka tsaya muna fira da shi, a nan yake min zancen aikina wanda ni har na watsar da lamarin. “Ya kamata ki koma kin ga idan kina fita zaki fi sakewa, kuma ita kanta Inna zata ji daɗi” “Amman Bilal ni aikin ya fita daga raina ma” “Aiko yanzu ne ya kamata aiki ya shiga kanki domin Sakina da Jamila da Noor suna da buƙatar taimakonki, ga kuma Inna” Gaskiya ya faɗa tun da bamu da wasu ƴan'uwa masu son taimako dole ne mu tashi mu nemi namu, daman hausawa na cewa ‘indan ma ɗan'uwa nemi naka’ Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi duk da kasancewar ba zan iya ganinsa ba saboda babu hasken farin wata, ita kan wutar nepa na manta rabon dana ganta a gidanmu domin an daɗe da yanketa, sai dai idan maƙota sun kunna wuta hasken gulob ɗinsu na haska gidanmu musamman masu gidan samman nan dake kusa da mu, sai dai yau basu kunna ba sakamakon babu wutar gaba ɗaya a unguwa. “Amman basu kore ni ba? Na daɗe ban zo ba” “Na basu rahoton cewar baki da lafiya, dan haka idan kin shirya zuwa kije kawai” “I will try” Na faɗa ina tsotsa lips ɗina. Bayan zancen aiki sai kuma muka ɗora da wani zancen na daban, ba laifi na saki jiki mun yi fira har da dariyata kamar ba ni ba, da wannan na yarda cewar zuciyata ta fara zaurancin son Bilal domin ina jin nishaɗi a duk lokacin da muke tare da juna, ko sunansa na tuna sai na samu kaina cikin hauƙi da murmushi. Bayan kwana biyu da faruwar hakan na shawarci Inna akan maganar aikina, na yi zaton zata hanani ne ko tace wani abu sai naga ta nuna farinciki sosai har tana ce min wai na fara dawowa a mutun ɗinta, farincikin dana gani a tattare da ita ne ya ƙarfafa min guiwa na yi jimmar wanke uniform ɗina na zuwa aiki. Washe gari na shirya tsaf na ɗauki Hijabina na saka, sai kuma na buɗe jakar da nake aje tarkace na na ɗauko ƙaramin hoton Habiba na saka a aljihu, hakan zai kwantar min da hankali kuma zai ƙarfafamin guiwa domin a duk lokacin da nake kusa da wani abu da ya danganceta ina jin kamar ƴar'uwata tana kusa da ni. Sai da na yi ma Inna sallama sannan na fita bayan na yi addu'ar fita daga gida. Bana baƙinciki ba farinciki na isa gurin aikin, kamar yadda nake a baya, sai da na fara zuwa na rubuta sunana da lokaci na aje hijabina da wayata a inda aka tanada domin aje irin waɗandanan abubuwan sannan na domin sai sannan na nufi gurin aikina, ina cikin aiki na ji muryar wani namijin yana faɗin “Khadija Musa Kafinta you're fired” Da sauri na juyo na kalli mai maganar yana sanye da black suit hannunsa riƙe da file. “Saboda me?” Na tambaya cike da mamaki. “Saboda rashin zuwa da kika yi, shugaba baya son haka, kuma ya ce be yarda da rahoton da aka bada cewar baki da lafiya ba” A take raina ya ɓace sosai, taya zai ce be yarda ba shi beda uzurine hala! Sai da na fara aiki za a ce an koreni, ni ko ba zan yafe haƙƙina na kwana biyu da na yi ina aiki ba. “Na ji an koreni amman a bani kuɗina na aikin da na yi na kwana biyu da rabi” “Kwana biyu da rabi?” Ya maimaita fuskarsa a haɗe. “Ee ai na yi aiki sau biyu a wannan kamfanin kuma yanzu na yi rabin aikin, dan haka a biyani haƙƙina” Ta yadda na yi masa maganar ya fahimci ina cikin zafin raine, domin a hasale nake ina katsa masa tsawa, yasan duk ya yi wasan sake ce min wani abu zan haukace masa ne. “Kije hawa na biyar bi faɗawa mai kamfanin, ba ni zaki faɗawa ba” Ya faɗa yana juya ya fice, ni kuma na bishi da bala'i ina cewa. “Ai kai ya aiko dan haka kai zan aika” Can kuma na soma tambayar kaina, wai shi wannan mai kamfanin wane irin mutun ne, miya ɗauki mutane ne? Aiko Wallahi ba zan iya yafe masa haƙkina ba ko da be bani kuɗin ba sai na faɗa masa marar daɗi sannan na bar kamfanin. Haka na kuɗiri aniyar sai na nuna masa ahi ba kowa ba ne, kai ina ma son ganin shi wane irin hallita ne da yake wulaƙanta ɗan adam, wato shi wannan yana tunanin kamar ba zan iya ba shiyasa na ce naje ko? “Aiko zan baka mamaki” Na faɗa a fili, sai na saka ƙafa na yi shuri da bokitin da nake mopping ɗin ruwan suka watse a ƙasa na fice a fusace. Kai tsaye na nufi gurin da lifted take na danna ta buɗe sai na shiga na danna 5. Gadan-gadan na fita daga lifted babu tsoro ko kaɗan a tare da ni, wannan gurin ma kamar wacan yake sai dai wannan ko wane office a kulle yake, an yi rubutu an laƙa a saman ƙofar. Ɗaya bayan ɗaya na riƙa bin ɗakunan ina duba wai ko zan ga wanda aka yi wata alama ta mai kamfani amman ban samu ba. Har na juyo sai ga wani mutume ya fito daga wani ɗaki riƙe da files, tsaidashi na yi ina tambayar office ɗin mai Kamfanin. “Lafiya kike nemansa?” “Shi ya aika ya ce yana nemana” Wani kallo ya yi min daga sama zuwa ƙasa sannan na kalli sunana dake rataye a wuyana. “Sai kin hau Excavator can, zaki ga Office guda uku jera, a na tsakiyar zaki tsaya akwai wani maɓalli a gurin sai ki danna” Sai da ya gama min kwatancen sannan na lura Excavator ɗin dake can gefen dama da offices ɗin. “Na gode” Na faɗa inanufar gurin, shi kuma ta bi bayana da kallo. Ni ban kula shi ba na hau Excavator ɗin. Ina kawowa sai na hauye saman tile ɗin na ƙarasa gaban offices dake jera, a na tsakiyar na tsaya, dama na ni na hango maɓallin da yake magana a kai na kai hannu na danna. Wata ƴar tsuwa na ji sai wata fitila ta hasko saman kaina. “What do you want?” Muryar namiji ce mai tambayar, kaina na ɗaga saman ina kallon camera dake ɗaukata. “Ina son ganin oganku ne” “Ur Name?” “Nawwara” Bayan na bashi amsa da kamar minti biyu sai ya ce. “You don't have an appointment with him” “Amman shi ya ce yana son gani na” Na faɗa a tsawa ce ina kallon camera kamar ance mutumem ne a gabana. “Sorry Ma'am you're not in the list” “But he's the one who tell me to come and meet him here” Na faɗa cikin turancina na yan ƙaramar makaranta. Sai kawai ƙofar ta rabu biyu ta buɗe min, da ɗan tsoro na kutsa kai ciki sai na gano ashe cikin wani ɗan kumbo ne na ke ciki, sai da kumbon ya gama scanning ɗina sai muryar ta sake min magana. “Keep your passport inside the box” Muryar ɗazu dai ce ta yi min magana, sai na saka hannu na ciro hoton Habiba na saka cikin wani ɗan ƙaramin akwati dake gefena, sannan ƙofar ta buɗe min tana min WELCOME. Wani ɗan madaidaicin Office ne na samu kaina ciki shi ba babba ba kuma ba ƙarami ba, an ƙawatashi da kayan alatu, da gangan na hana idona kallon wasu abubuwa na office ɗin saboda karna manta abunda ya kawo ni. Matashin Saurayi ne zaune saman kujerar dake office ɗin, laptop biyu a gabansa a daga gefensa kuma desktop computer ce a aje, can nesa da shi kuma an jera wasu desktop computer har biyu da kujerarsu daban. Can a farko shigowa office ɗin an jera kujeru masu kyau na san ba zasu wuce na zaman baƙi ba. Matsawa na yi kusa da shi da jimma na fara masa masifa domin a haukana na ɗauka shi ne mai kamfanin, sai ya rigani magana. “Stay where are you, i have to call him first” Telephone ɗin dake kusa da shi ya ɗauka ya fara danna wasu numbobi, hakan yasa na yi janzarin ƙarasawa kusa sa shi sosai. “Sir a young lady... ” Yana fara magana na fisge telphone ɗin na fara tawa maganar domin nasan idan har ya faɗa masa zai ce shi be san da zuwana ba, ba zasu bani damar magana da shi ba. “Azzalumi macuci, ka koreni ai sai ka bani kuɗin aikin da na yi na kwana biyu da rabi kuma kaima baka wuce Allah ya ɗora maka ciwon ba-” “Nawwara...-” Ɗaga can cikin wayar ya ambaci sunana. Tun da muryarsa take daki kunnena yawun bakina suka tsinke, kaina ya fara jiri wani abu na ji na tsikareni tun daga saman kaina har cikin ɗan yatsan ƙafata, gaba ɗaya jikina sai ya mutu. Mutunen nata ƙoƙarin fisge telphone ɗin daga hannuna sai na saka masar na juya da gudu na nufi inda na ke hango wata ƙofa dake can dama da teburin mutumen amman nesa da shi. Da gudu na banki ƙofar na shiga, sai na samu kaina cikin wani irin ƙaton office mai cike da sanyin ac. Yana hakimce saman kujerar alfarma wani irin ƙaton tebur mai takardu da kayan kawata teburin office haɗi da system na gabansa. Ji na yi kamar ana zooming ɗina a take hawaye suka fara bin fuskata, na san idona ba gizo suke min ba, ba mafarki na ke ba. Daga saman kujerar da yake zaune ya ɗagawa secretary sa dake ta kokuwar fitar da ni hannu, ya yi masa alama da ya fita sai ya juya ya fice yana ja ƙofar office ɗin. Shi kuma ya taso da sauri ya doso inda na ke yana kira sunana muryarsa har rawa take. “Naaa...Naww...Nawwarraa....” Tafin hannuna na kama taɓa sai ya yi saurin kai shi gefen fuskarsa ya lumshe ido, sai hawaye suka zubo masa. Fisge hannuna na yi ina yin baya-baya, Tabbas shine, shine mutumen da ya yi nasarar canja ni daga mutum zuwa mutum mutume, shine mutumen da ya ce yafi ƙaunar ganin mutuwarsa sama da ni, shine mutumen da ya kirani ƴar talakawa marar daraja, shine mutumen da daya wulakanta ni ya sani a rana kuma yasa duniya ta zargeni, shine muteme da ya yanke min duk wani jindaɗi ma rayuwar duniya, shine mutumem da ya fara saka ni a ɗakin kuka da baƙinciki. Kai na nake girgizawa ina cigaba da yin baya-baya shi kuma yana matsowa kusa da ni, duk ya rikice kamar zai cinye ni, idonsa har sun soma canja kala, jikinsa na ta rawa hawaye kuma na ta aikinsu a fuskarsa. Muna haka Mutumen da ya taɓa tambayar sunana a wacan lokacin da na ke aiki ya shigo, shi ya kai hannu ya dafe masa ƙirji saboda kar ya ƙaraso kusa da ni, ni kuma na juya da gudu na fice ina kuka, ina jiyo sautin muryarsa yana kiran. Da kuka na sauko ƙasa na ban tsaya saka sunana ba na nufi gurin da Hijabi ya ke tare da wayata na ɗauka na saka na fice ɗaya ɗaga cikin mutanen da suke reception na ta kirana wai na zo ga saƙo amman nayi banza da shi ina ta aikin gudu da kuka. Sai da na yi nisa da kamfanin sannan na fara tafiya ina hawaye, tare da tambayar kaina wasu tambayoyin da ba ni da amsar su. ‘Shi da yake likita miya kawo shi nan? Daman ƙamfanin na su ne? Daman shi ne mutumem da Bilal yake faɗa min, miyasa ban gane shi ba a lokacin da Bilal ya faɗa min suna da Asibiti? Na taɓa jin ƙamshin turarensa miyasa ban ga ne shi ba? Ya faɗa min yana da tattoo miyasa ban ga ne shi ba?’ “Lallai ke wawuyace Nawwara” Na furta a fili hawaye na min zuba, yau kan ƙasa na kama hanyar gida duk kasancewar akwai tazara mai tsawo tsakanin unguwarmu da kuma inda kamfanin ya ke, amman baƙincikin da ke raina ba zai bari na iya tsayawa na tari abun hawa ba. Ƙarar tsayawar motarsa ce ta riƙa ta dawo min kamar a yanzu ne abun ya ke faruwa, irin yadda ya fisgoni ya jefar gefen titi ne ya riƙa min yawo a ƙwaƙwalwa. Wani irin jiri ne na ji na ɗibeni sai na ji ƙafafuna kamar an cankesu an ja ni, duhu na soma gani, ko kamin na kai ƙasa numfashina ya daɗe da barin jikina. ___________________________________ Dogon shafi kamar yadda kuke bukata 😂 Dan haka nima dogon comment na ke son ji idan ba haka ba next chapter sai nan da one week kuma short chapter 🤷 Ko wanenen wannan mutumen ne? Bari nima na bi Nawwara na sha labari 😉 #COMMENT #VOTE #SHARE *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣1⃣ JIBRIL POV (Point of view). Sanyi da yaji a tafin hannunta ya tabbatar masa da ita ɗin ce, hawaye ke zuba a idosa ba tare da ya san suna zuba ba, baya-baya take tana hawayen da yake jin ɗigarsu har cikin ransa, a hankali ya ke maye duk wani footsteps nata da take backwards, ga wani irin abu da ke jansa na ɗimaucewa da al'ajab ɗin ganinta kamar zai fita hayyacinsa he just can't believe Nawwara ce yau a gabansa. Shigowar Siraj ya bata damar fita da gudu, shi kuma ya yi hanzarin binta sai Siraj dakatar da shi, ta hanyar ɗora hannunsa saman ƙirjin Jibril. “Calm down Jibril” Be saurari abunda ya ke faɗa ba ya ƙwala ma Nawwara kira da dukannin muryarsa yana mai jin kamar ya yi tsalle ɗaya na fisgota. Ya sauke idonsa da suka yi ja suka rine akan Siraj yana ambatar sunan Nawwara cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai. “Nawwara ce fa” “I know” Siraj ya amsa masa yana ta matsar da shi baya har ya zaunar da shi saman tebur burinsa. “Nasan zaka haɗu da ita tun ranar da na yi arba da ita tana aiki a kamfanin nan, ni ma dan bata san ni bane yasa ta zauna da ace ta san kamfaninka ne ba zata yi aiki a nan ba” Cewar Siraj Hannayensa akan kafaɗar Jibril, sai ya ture masa hannaye yana masa kallon mamakin furucin da ya taɓa masa a can baya. “Miyasa ka ce min ta mutu? Kasan iya shekarun da na ɗauka ina nemanta? Saboda ita na aminta na yi aiki nan saboda kawai ta taɓa rayuwa a nan garin, Siraj kasan yadda take da muhimmanci a gurina kuwa?” “Na sani wannan dalili ne yasa na ce maka ta mutu, saboda ka yi focusing akan abubuwan da ke gabanka, na yi nemanta har na gaji ban samu ba, amman tun daga lokacin da na ganta a kamfanin tana aiki nasan wata rana zaku haɗu” “So kasan tana aiki a nan kuma ka ƙyale baka faɗa min ba? Ban taɓa sanin kai maƙiyina ba ne Siraj sai yau” “Na ganta sau ɗaya lokacin da muke duba ɗakunanan ni da Zinatu” Miƙewa Jibril ya yi cike da ɓacin rai, ya nufi ƙofar zimmar fita, sai Siraj ya bishi da kallo yana faɗin “Ina keka tunanin tafiya? Gurinta? Ai ba zata taɓa saurarenka ba ko ka manta irin wulaƙacin da ka yi mata?” Tsayawa ya yi cak hawaye na ta cigaba da masa zuba kamar ba shi ba, abun ka da farin mutun har fatar idonsa ta yi ja. Tabbas ba zata saurareshi ba ba ma cancanci Nawwara ta kalleshi ba balle har ta saurare abunda zai fito daga bakinsa. ‘What can i do now? Oh God...’ Ya juyo cikin rashin kuzari ya zauna saman kujerasa ya dafe kansa yana lilo da kujerar. “Take this” Siraj ne ya yi maganar yana aje masa farar takarda mai ɗauke da Cocaine saman tebur. Jin ƙamshinta yasa ya buɗe ido ya kuma sauke idanuwansa akan cocaine ɗin, hannu ya kai ya yagi gefen takardar ya fara mata aiki kamar ba gobe, sosai ya shaƙeta ko da ya ɗago ƙasa da kuma gurin tsinin hancinsa ya yi ja sosai. Yana san cocaine ne kawai saboda ta zame masa jiki ba wai dan tana masa aiki ba, tun lokacin da tunani Nawwara ya sashi gaba ya addabe shi yasa ya fara shanta, saboda ta ɓatar masa da hankali, da wasa-wasa ta kamashi har ta zame masa jiki ta yadda idan ransa ya ɓace sai ya shata yake jin sawaba, izuwa yanzu kan ta daina masa aiki ajiki saboda sabon da ya yi da ita, ko ya sha baya jin komai sai dai kawai ya sha dan ta zame masa kamar a abincin. Miƙewa ya yi tsaye yana tsotsar pink lips ɗinsa sai wani numfashi yake kamar zakin da ya yi faɗa ya gaji, hannu ya ɗaga ya daki teburin da ke gabansa iya ƙarfinsa. “Ya za'ayi na sake ganinta Siraj?” Siraj ya ɗauke ragowar cocaine ɗin ya mayar a wani ɗan ƙaramin box yana faɗin. “Malam ka fa koreta daga aikin ko ka manta?” Wani dogon tsaki yaja ya fice daga office ɗin yana ciro wayarsa dake cikin aljihu, wata number ya nemo bugu ɗaya aka ɗaga. “A fito min da mota waje” Yana fitowa sekaterinsa ya miƙe tsaye yana faɗin. “Sir akwai meeting tsakaninka da Managen Daherr Global Prints yanzu” Juyowa Jibril ya yi a fusace zai jefa masa baƙar magana sai Siraj da ya fito daga office ɗin Jibril yanzu ya yi aurin karɓa masa. “I will attend the meeting” A fusace Jibril ya juya ya fuskanci ƙofar sai ta buɗe masa da kanta. Da ya fito be iya tsayawa Excavator ya sauko da shi ƙasa ba ya riƙa tattakowa ya sauko da sauri, kai tsaye ya fita daga harabar gurin, kamar zai tashi sama haka ya nufi lifted, Already sun saba indai zai shiga babu mai matsowa kusa da gurin har sai ya shiga ya sauka. Kamin lifted ta dawo dashi hawa na ɗaya har ya matso sosai, sai gumi yake kamar wanda yake kusa da wuta, lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya, babu komai a cikin zuciyarsa da ƙwaƙwalsa sai Nawwara. Ina zan ganta ta ina zai fara nemanta shine abunda yake ta tunani har ya isa gurin motarsa da aka fito masa da ita aka kawo masa har gaban kamfanin, duk gaisuwar da ma'aikatan gurin suke masa be ji ko ɗaya ba saboda hankalinsa kwatakwata baya jikinsa, su kan basu kula ba tun da sunsan halinsa ayi masa magana ya ƙi amsa tun da ya maida kowa maƙasƙanci saboda kawai suna aiki a ƙarƙashinsa, idan har ka gaisheshi ya amsa maka lallai kuwa ka isa irin sosai ɗin nan a gurinsa. Direban na tsinkayarsa ya yi saurin fitowa ya buɗe masa mazaunin baya, a tunaninsa zasu fita tare ne sai yaga ya ɗaga masa hannu ya nufi driver seat. Da sauri ya rufe masa motar ya matsa can baya yana kallon yadda ya fisgi motar kamar zai tashi sama, abun har tsoro ya bashi. Tun kamin ya ƙaraso security guard suka buɗe masa gate, domin sun san halinsa ba tun yau ba, shi baya jira a buɗe masa gate sai dai gate ya jirasa. @360 yake gudu kamar ba a cikin gari yake ba. Minti ɗaya zuwa biyu yake furta sunanta zuciyarsa na wani irin bugawa kamar zata filo. “Nawwara Where are you?” Titi yake bi zuciyarsa nata raya masa zai ganta, bayan kuma be san inda ta bi ba, haka ya yi yawonsa na neman Nawwara amman har aka kira sallah azahar be haɗu da ko da sawonta ba balle ita. “I'm very stupid human being, taya za ayi ta bi titi? Tana gidansu by this time” Ba bawa kansa da kansa amsa, sannan ya bugi sitarin motar iya ƙarfinsa, sannan ya juya akalar motarsa zuwa sama road. Tuna hannunta da ya riƙa yasa jin relief har miskilin murmushi ya bayyana a fuskarsa murmushi da ya kasa gushewa har ya isa ƙerarren gidansa end of discussion da ke sama road. Yau kan be yi parking a inda ya saba ba sai ya fito cikin wani irin yanayi shi ba farinciki ba kuma ba akasinsa ba ya nufi ƙofar Babban falonsa, yana shiga idonsa suka sauƙa kan ƙaton hoton Nawwara dake tsaye a falon yana fuskartar ƙofa, matsawa ya yi kusa da hoton ya kai hannu yana shafa fuskarta kamar ance masa ita a gabansa tsaye. “I love you Nawwara i love you so much” Hawaye ne suka zubo masa, sai ya nufi bedroom ɗinsa yana buɗe maɓallan rigarsa, saman bed ɗinsa ya zauna ya buɗe bedside drawer ya ɗauko wani madaidaicin diary mai zaganen zuciya ya yi masa kiss sannan ya bude shi. Pages da yawa ya wuce a cikin diary sannan ya bude new page da ba ayi ma rubutun komai ba ya ɗauki biro ya zana zuciya a saman zuciyar ya rubutu. _Finally i meet her today she's still alive _ a kasan zuciyar kuma sai ya rubuta _Naj_ ya zagaye shi da biron ya yi ma yatsunsa biyu kiss ya liƙa hawayensa sannan na manna a jikin sunan da ke ƙasan heart ɗin, a take gurin ya jiƙe. Rumgume diary ya yi ya kwanata rai-rai yana bin ɗakin nasa da kallo kamar wani baƙon. Daga bangon gaban na ɗakin zuwa yamma babu komai sai hotunan Nawwara, dagana kudu zuwa arewa babu komai sai horunan Nawwara. “After the game, the king and the pawn go into the same box, every step I took since the moment I could walk was a step towards finding you, and i find you Naj ba zan iya rasa ki ba i can't lose you again” Ya tashi zaune ya fiddo wayarsa daga aljihu ya kira waya number. “A cikin waɗanda aka kora akwai wata Nawwara wacce ta zo yau, ka aika mata da saƙon neman ta dawo aiki yau, kuma ka duba addreshinta ka aiko min da shi right now” Yana faɗar haka ya kashe wayar, yana wani irin nishi shi ba na wahala ba, ba kuma na fushi ba, ba na jindaɗi ba, kansa ya shafa yana faɗin. “Ina son ki Nawwara, ina son ki har cikin zuciyata, idan na rufe idona ke nake gani, idan kuma na buɗe ke nake da buƙatar gani kece ruhina Nawwara ina son ki matuƙa” Magana yake da kansa yana kallon hoton, zuwa can idanuwansa suka sauka kan gmt ɗin dake ɗakin sai ya yi hanzarin tashi ganin uku saura kwata be yi sallah azahar ba. NAWWARA POV. Ƙoƙarin buɗe ido nake sai na ji sun min nayi sosai, bana iya tuna abunda ya faru da ni balle har na gane inda nake har sai da nayi ƙarfin halin buɗe idona dake ciki da danshi domin bana iya gani da su sosai. “Sannu” Bana iya tantance mai muryar amman tabbas na taɓa jin wannan muryar ko a ina ne, da sannu idanuwana suka buɗe wasai har na iya tantance a asibiti na ke, yanzu kan na tuna abunda ya faru amman waya kawo ni asibiti? Kamar ance na kalli gefena sai idanuwana suka sauka kan Mustapha idonsa narai-narai kan nawa. Unƙurin tashi na yi amman babu wani kuzarin kirki a jikina. “San..nu..” Ya faɗa murya na rawa, kansa ƙasa-ƙasa kamar mai saunata. lallai ma wannan mutumem ya raina min da hankali miya kawo shi a inda na ke ma? Tambayar da na kasa amsawa kaina kenan, cikin ƙarfin hali na ɓalle drip ɗin da aka saka min a hannu, na sauke ƙafafuna ƙasa, hannun da na ɓalle cannula yana ta jini na ɗauki Hijabina da ke saman durowa na saka. “Nawwara....” Ya faɗa yana miƙewa tsaye idonsa a razane kan hannuna dake ta zubar da jini. Da hannun na nunasa ina masa wani mugun kallo. “Kar sunana ya sake ziyartar laɓɓanka, kar kuma ka sake ƙoƙarin furta wata kalmar a gareni, ban taɓa tunanin kai hasararren ɗa bane sai yau, zakka marar tarbiya, Zahili dan gantali haihuwar hasara” Tun da na fara wannan maganar kansa na ƙasa ya rumtse ido yana ta saurarena, mi kuma tuni na fara takawa zuwa gurin ƙofa to my surprise sai ga Jidda ta shigo rike da kaya niƙi-niƙi a hannunta. “Har kin farka?” Da ni take magana amman idonta yana kan Mustapha da kamar akwai wani abu a ƙasa. Ƙarasa ta yi ta aje kayan da ke hannunta ta zo ta dafani, sai na kaɓe mata hannu idanuwa cike da ƙwalla zuciyata kuma har wani fisga take kamar zata fito. “Me kuke yi a nan” “Suma kika yi a hanya, sai Mustapha ya ganki ana neman inda za a kaiki shine ya kwaso ki ya kawo asibiti” Kai tsaye ta bani amsar, Mustapha kan tuni ya yi mutuwar tsaye saboda kalaman da na masa. “Ya akayi kika sani?” Na tambaya yayinda da hawaye suka sauko daga idona suka wanke min fuska. Sai da ta kalli Mustapha sannan ta kalleni ta ce “Mustapha ne ya faɗa min” Dauƙe kai na yi na cigaba da tafiyata na ƙi kula kiran da take min har na fice daga ɗakin. ‘Taya Mustapha yasan alaƙar da ake tsakanina da Jidda? Miyasa be kira wani daga cikin gidanmu ba kira Jidda?’ Shine abunda na ke ta saƙawa a raina ina tafiya, Jidda na bina da kira. ‘Amman kuma ai bata san illar da Mustapha ya yi mana ba, bata san aibunsa a garemu ba’ Tuna wannan yasa na tsaya har na saka Hijabina na danne Hannuna ina jiran ta ƙaraso. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣2⃣ “Haba Nawwara abunda kike ba shi da kyau Wallahi na san kin tsani masu kuɗi amman wannan mutumen fa taimakonki ya yi ban san abunda bawan Allah nan ya yi miki ba duk kin bi kin tsaneshi, haka sam be dace ba, ni kaina na tuhumesa lokacin da ya zo har gida ya faɗa min na ce miyasa be faɗa ba gidanku ya ce yana gudun zargin ne kuma da na zo nan asibitin na tarar mutun biyu da suka kawo ki tare, Wallahi babu wani abu Nawwara dan Allah ki kwantar da hankalinki” Shine abunda Jidda ta faɗa lokacin data ƙaraso kusa da ni. Mustapha kuma na daga can nesa da mu ya sako min ido kamar zai cinye ni. Kallo ɗaya na yi masa na ɗauke kai ba tare da na ce da ita komai ba na cigaba da tafiyata, zuciyarta na mugun bugawa kamar zata faɗo. Tare muka fito da Habiba a har bakin gate ɗin Specialist hospital dake sokoto, motar Mustapha ce ta sha gabanmu be ce komai ba ya miƙa hannu daga inda yake zaune ya buɗe mazaunin baya. Jidda ce ta iya riƙa ganbun motar ni kan ko kallo bata isa ban na kauce mata na cigaba da tafiyata har na tsada mai adaidaita na shige ina faɗa masa inda zai kaini, yana ƙoƙarin tashi sai ga Jidda ta dakatar da shi ta shigo tana min masifa wai abunda na ke bana kyauwa, ni dai ban kulata ba saboda na san bata san zafi da irin ƙiyayyar da raina ta Mustapha ba, tun da ban taɓa faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi sanadiyar muturwar ƴar'uwata ba. A gurin da aka saba saukeni na ce ya ajeni na saka hannu aljihu na ciro kuɗi a bashi sai a lokacin na tuna da hoton Habiba da na baro a wacan baƙin kamfanin da bana fatar ko a mafarki na sake zuwa, gaskiya na ji babu daɗi sosai domin shine kaɗai hoton Habiba da nake da shi a yanzu wanda take da girmanta, ta ɗaukeshi ne lokacin da zata yi canjin makaranta daga Hafsatu zuwa Nana girl's, abunka da takala ba hotone a gabanmu ba sai idan wani abun ya tashi na dole sannan muke zuwa yin hoto. “Ina wayata?” Na tambayi Jidda bayan mai adaidaita ɗin ya bamu canji, hannu tasa cikin jakarta ta ɗauko wayar ta miƙa min. “Gashi” Ina karɓa na sa kai gabana muka cigaba da tafiya tare. “Gaskiya halinki bashi da kyau Nawwara, idan har baki yabawa Mustapha ba to ba zaki zageshi ba” “Ce miki ya yi na zageshi?” “Ko baki zageshi ba kin faɗa masa magana marar daɗi domin alamu sun nuna haka, ban san abunda bawan Allah ya yi miki ba, ko dai akwai wani abun ne?” Na tsaya ina kallonta “Wai miyasa kika damu ne Jidda?” “Saboda ya taimakeki, da be kawo ki asibiti ba da Allah kaɗai yasan halin da zaki kasance akan hanya” “Da barina ya yi akan hanyar mota ta takani ko kuma mutane suka ɗaukeni suka jefar a bola, da ya fi min farinciki sama da ɗauko da ya yi ya kawo asibiti, dan Allah ki tattara duk wani abu da ya danganci maganar nan ki ajeta a gefe” Na tada kai na cigaba da tafiyata har na isa gida ban waiga na kalli Jidda dake gefena ba. Ita ce ta faɗawa Inna abunda ya faru da kuma irin abunda na yi ma Mustapha har Inna da kanta ta dinga ganin rashin kyautawa da kuma faɗar abunda na yi ba halina ba ne. Ni dai ban iya cewa Inna komai ba tun da nasan ita ma ban faɗa mata cewar shine mutumen da ya yi ma Habiba aika-aika ba. Tufafin jikina na cire na saka a murhu na ƙone tare da Hijab ɗin duka na haɗa na ƙone saboda mutun biyu Mustapha da kuma Jibril tsakanin su ba zan iya banbance wanda zuciyata ta fi tsana ba. Ina gaban Murhu Inna ta fito daga ɗaki jin ƙauri ta saka salati. “Lafiya kike ƙone kayan aikin kuma Nawwara mi yake damunki?” “Inna sun koreni dan haka bana da buƙatar wannan kayan” “Garin ya wani abun kika yi?” “Ban yi komai ba, saboda kawai na daɗe ban je ba” “Ba kince Bilal ya faɗa musu baki da lafiya ba?” “Wai basu yarda ba shugaban Kamfanin ne bashi da mutunci” “Allah ya kyauta ya baki wani” Ta faɗa cikin muryar da ke nuna bata jidaɗin haka ba. Ƙarasowa ta yi kusa da ni ta riƙani ta tayar tsaye. “Tashi gaban hayaƙi, bari na saka miki ruwa ki yi wanka” “A'a zan iya Inna” “Babu ƙarfi jikinki Nawwara baki ga yanxu kika dawo daga asibiti ba” Da kanta ta haɗa min ruwan na shiga banɗaki na yi wanka, bayan na fito na ɗauki buta na yi alwala na shiga ɗakinmu sai na samu Inna zaune tana yanka min albasa a wake da shinkafa, saboda ta san ina son na saka albasa da tumatur idan zan ci wake. “Gashi nan idan kin gama sallah sai ki ci, bari na kawo miki ruwa” Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita ni kuma sai na yi saurin dakatar da ita. “Haba Inna kina ta min abu sai kace ƙaramar yarinya ni ya kamata ace ina hidima dake ba wai ke ki yi da ni ba” Tsayawa tayi jikin ƙofa tana murmushi tare da wasa da wuƙa da kuma ragowar albasar dake hannunta ta ce. “Nawwara ji nake kamar da nayi wani sakaci kaɗan rasaki zanyi, ɗazun da baki dawo a lokacin da kika saba dawowa ba hankalina ya tashi sosai, ba san yadda zanyi ba idan har na rasaki bayan na rasa Habiba, kuma kina a matsayin RAI BIYU a yanzu ni da kuma ɗanki, shi ma ya damu da be ganki ba lokacin da ya dawo daga makaranta, yana ta tambayar ina Momy nace mishi kina gurin aiki amman daker ya yarda ya tafi islamiya, ɗanki yasan zafin rabuwa da mutun yasan idan aka tafi ba a dawowa shiyasa saboda ya rabu da Habiba dan haka ba zamu iya jure rashinki ba” Tana faɗar hakan tasa kai ta fice idonta cike da ƙwalla, ni kuma na jingina na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya, wani irin tausayinta ne ya rufe ni. Jin wayata tayi ƙara yasa na buɗe ido na nufi inda wayar take, tun kamin na ɗauka gabana na faɗi saboda saƙone daga One-On-One Limitless Company, ji nayi bana da buƙatar sanin abunda saƙon ya ƙumsa, dan haka na danna delete na goge shi ba tare da na karanta ba. Sai da na gama rama sallah azahar sannan na gabatar da sallah la'asar, sai na zauna na ci abincin sai ba sosai ba saboda bana jindaɗin abinci a yanzu, sai dai shigowar Inna yasa na zage dantse na yi ta auna abinci domin nasan zata damu idan ta ga banci da yawa ba. Na yi ƙoƙarin ganin na danne damuwata amman mahaifiya ta fi gaban wasa ita da kanta ta tsinkayi hakan a cikin idona. “Nawwara kamar akwai abunda yake damunki, idan dai dan maganar aikin nan ne ki kwantar da hankalinki Allah zai sake baki wani kamar yadda ya baki wannan” Kai kawai na iya ɗaga mata domin na gansu maganar aikince kamar yadda take hasashe, domin idan har ta tiƙe ni ban san mi zan faɗa mata ba. Tashi tayi ta fita jin wata maƙociyarmu ta shigo, ni kuma na rafka uban tagumi ina kallon ƙasa amman hankalina yana can gurin rayuwata ta baya. FLASH BACK. _“Yau za'ayi ina fatar zaka samu zuwa kai da madam, tau ya yi sai kun ƙaraso”_ _Haka na ji ya faɗa a waya, sannan na miƙe tsaye yana min wani gumun kallo ya ce._ _“Wallahi duk kika sake abokaina suka zo gidan nan kuma kika fito sai na halakaki, kinji ni ko?”_ _Da sauri na ɗaga masa kai hawaye na zuba a idona, sai ya kaɗa kai fuska babu annuri ya nufi ɗakinsa yana wani irin jinkansa, ni kuma na zube a gurin ina kuka saboda zafin ruwan zafin da ya watsa min a hannu kuma ya hanani kuka saboda tsabar zalumci. Ina a gurin ina aikin kuka har ya shirya ya fito sai ƙamshin turare yake ya tsaya a kaina ya nuna ni da yatsa_ _“Ki shiga cikin ɗaki ki kulli kanki karki yarda ki fito”_ _Na amsa masa da tau jikina na rawa ina ta ƙoƙarin haɗe kukana nasan idan har na yi kuka a gabansa zai iya dukana, kamar yadda ya umarce ni haka na shiga cikin ɗakin na rufe kaina wanda hakan ya bani damar tausayawa kaina da kaina. Can zuwa dare na soma jin hayaniyar abokansa ta hirar da suke na iya gane ashe muƙamine ya samu amman ya gagara faɗa min saboda ƙiyayyar da yake min, haka yake duk lokacin da wani abun ya sameshi sai dai na ji a waje ba dai ya faɗa min ba. Har suka yi abunda zasu yi suka gama ban fito ba, bayan fitarsu da minti ashiri na ji an buga ƙofar ɗakina, yanayin yadda aka banki ƙofar ne ya fahimtar da ni cewar Jibril ne yake buga ƙofar, cikin hanzari naje na buɗe saboda na san baya son jira, sai nayi arba da yatsunsa biyar a kuncina, ma'ana wanke min fuska da mari yana faɗin_ _“Ke kiƙa faɗawa Abbah zanje meeting ba dake ba ko?”_ _Baya-baya na yi ina girgiza masa kai_ _“Na rantse da Allah ban faɗa ba, Wallahu ba ni bace”_ _Na faɗa cikin kuka, sai ya watsa min harara, yace na canja tufafi muje amman duk na masa kuka cikin mutane sai ya ɓanlani, jin wannan yasa hawayena ya yanke tun kamin ma mu fita domin na san haƙinsa ne sarai zai iya ci min mutunci a gaban kowa, sai dai ban daina jin zafin marinba har muka isa gurin da ake tare, gurine dake cike da manyan mutane an ƙawata gurin anyi masa kwalliya gwanin sha'awa. kowa da mazauninsa, an kasa mutane daban-daban wasu na tare da matansu wasu kuma na tare da familysu. Tare muka shigo da shi amman muna shiga harabar gurin sai yayi kamar be sannin ba tare da gargaɗina akan karna yarda na nuna cewar ni matarsa ce. Guri na samu kusa da wasu baƙin na zauna, bayan an gama jawabin da akeyi aka kirashi aka karramashi, sai yaje ya karɓi Award ya yi jawabi godiya, a lokacin Abbah da Hajiya basa nan dan haka babu wacce zai kira bayan su sai ni da nake matarsa, amman abun mamaki sai ya kira sunan budurwarsa Asiya ko kuma ma nace karuwarsa, haka ta miƙe tsaye tana ta karairaya ta haura gurin tana taya shi murna. Ni kuma ina daga nan zaune ina hawaye_ _Wani mutun ne ya miƙo min tissue yana min kalaman da mijina abokin rayuwata be taɓa min ba_ _“Kuka be cancanci kyakkyawar fuskarnan taki ba dan Allah karɓi ki share hawayenki”_ _Kallonsa na yi amman na kasa karɓa saboda idon Jibril na kaina, haka mutumen ya matsa min amman naƙi kula shi har aka tashi taron, a gurin da zamu shiga mota ya tare mutumen ya riƙa bugar masa baki wai ya yi magana da matarsa, babu kalar baƙar maganar da saurayin be faɗa masa ba, sannan aka rabasu ni kuma ya sakoni gaba muka dawo gida, kamar jira yake mu iso ya sakani gaba da duka wai na kula wani namijin har wani huci yake kamar zaki..._ BACK TO STORY Shigowar Noor ne ya katse min tunani, sai ya yi saurin aje allon dake hannunsa ya nufo yana share min hawayen da ban san sun zubo ba. “Momy miyasa kike kuka? Shiru shiru shiru kinji Allah ya miki albakar, yi shiru shiru faɗa min waya taɓa ki?” Shine abunda yake faɗa tare da saka haɓar rigarsa ya goge min fuska, ina kallonsa gabana ya faɗi fuskar Jibril ce shimfiɗe a fuskarsa babu inda ya ragoshi tun daga kan hancinsa har ido da baki da fari komai na ubansa ne, rumgumeshi nayi muka kwanta saman kafitar da nake zaune. _“Ba cikina ba ne...!”_ Shine abunda ya faɗo min a rai, sai na ƙara ƙanƙame Noor kamar ance za a rabani da shi. Bachine ya kwashemu ni da shi bamu farka ba sai da Sakina ta shigo tana tashina wai anyi magariba. Bayan Sallah isha'i Bilal ya kirani a waya yace min yana ƙofar gida, nasan daman zaizo tun da yau ban karɓi kuɗin da ya saba bani ba. Sai dai na sha mamaki lokacin da fita muna fira da shi. “Miyasa kika fita Kamfani ɗazu kina kuka?” Shine abunda ya fara tambayata, nasan wata ƙila wani ne ya faɗa masa, ni kuma sai na masa ƙarya da cewar saboda sun ƙoreni yasa ni kuka, ya nuna min damuwarsa sosai har ma ya yi alƙawarin zai yi wani abu wajen ganin an maidani aikin, amman na nuna masa bana so. Sai tara da rabi muka rabu ban faɗa masa cewar na suma a titi ba duk na san nan gaba kaɗan zan ji a gurin Jidda domin bata ɓoye masa komai da ya dangance ni. Ko da na shiga gida wayata na ta ringing ko da na duba sai naga baƙuwar number, kamar kar na dauka sai kuma na ɗauka tare da sallama, sai na ji ba a amsa min ba kuma ba a ce komai ba har na tsawon lokaci, hakan yasa na sake sallamar nan ma shiru har sai da na duba wayar naga mai kiran be kashe ba, na sake karawa nayi sallama a karo na uku ba amsa min ba kuma ba a ce komai ba, hakan yasa na kashe wayar dan da alama mai kiran yana son sauraren muryarta ne kawai duk da ban san ko wanene ba. WASHE GARI... Misalin bakwai da rabi saƙon kamfanin ya sake shigowa, nan ma ban karanta ba na goge, na shigaba da haɗa abun karinmu da nakeyi. Sallamar baƙuwar murya yasa na ɗago daga gaban murhun da nake na amsa mata ina mata kallon rashin sanin, sai da ta gaisheni sannan ta matso kusa da ni ta aje min leda biyu dake hannunta ta ce “Wai gashi inji Ya Mustapha ya ce abawa Nawwara, kuma wai yana mata sannu da jiki” Har na buɗe baki zance mata ta ɗauki kayan ta koma da su sai ga Inna ta fito daga ɗaki tana amsawa kamar tasan ni ba zan amsa ɗin ba. “Mashallah ki ce an gode Allah ya saka da alheri, jiki kuma ya yi sauƙi sosai” Da wannan budurwar ta juya ta koma wacce nake san ran riƙonta ake a gidansu Mustapha domin iyayensa shi kaɗai suka haifa. Tana fita na ɗauki kayan na fice na bar Inna tsaye tana kallon ikon Allah domin nasan idan har na ce yarinyar ta ɗauki kayan ta koma dasu a gabanta ba zata bari ba, amman yanzu bata san mi zanyi ba dole ta saka min ido. Ina fita na yi karo da shi a ƙofar gidanmu sai ya ɗanyi nisa da gidanmu kaɗan yana sanye da jallabiya, daga inda nake tsaye na jefa masa ledodin na juyo abuna. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣3⃣ “Me kika yi kenan?” Ina shigowa gida ta jefo min wannan tambayar, da fari na tsaya tunanin abunda zan ce mata sai kuma daga baya na yanke shawarar faɗa mata gaskiya. “Mayar masa da abunsa na yi, bamu da buƙatar taimakoshi” “Amman Nawwara ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, mutumen da ya tsinceki gefen titi ya taimaka miki ya kaiki asibiti garin Allah ya waye kuma ya aiko ganinki shine zaki mayar masa da kayansa? Wannan wace irin rayuwace Nawwara? Mi yake damunki? Wulaƙanta ɗan'adam? Kuma mutun kamar Mustapha yaron da babu wanda ya isa ya nuna masa ɗan yatsa amman har kike ƙoƙarin ci masa zarafi?” Yanayin fuskarta da kuma lamanta na fahimci ranta ya ɓace sosai akan abunda na yi, ni kuma na marairaice mata kamar zanyi kuka. “Inna kin san waye Mustapha ana yaba masa da neman matan banza, dan me zai kawo min abu na karɓa, bayan ban san manufarsa a kaina ba” Ta ƙaraso kusa da ni “Shiyasa na ke son ki lallaɓa da shi ku rabu lafiya, da baki watsa masa kayansa ba sai ki amsa ki masa godiya in yaso daga baya sai ki nemi ya rabu da ke” “Zan kiyaye nan gaba” Da wannan muka raba na nufi murhu na cigaba da hura wuta, ita kuma ta koma ɗaki tana cewa Sakina ta zo ta siyo mana ƙosai. Har na dama kumun tunani ɗaya ne a raina, na faɗawa Inna gaskiya game da Mustapha ko kuma na barwa cikina, idan ma na faɗawa Inna amfanin me zai mata? Idan kuma na bari ban faɗa ba ni amfanin me haka zai min? Ina cikin wannan tunanin naji muryar Namiji yana sallama a ƙofar gidanmu, bayan naji tsayawar mota da kamar minti huɗu, dakan uku-uku gabana ya yi duk da ban san ko wanene ma. Ko da na bar gaban murhun Jamila har ta kai waje, sai gata ta dawo da sauri tana kirana. “Anty wai ki zo ana kira a waje” “Waye?” “Wanine” Mustapha na fara kawowa a raina, amman da shi ne ai Jamila ta sanshi da shine ai ba zata ce wani ba. Miƙewa na yi tsaye na tare da bokitin da na dama kunun na nufi ɗakin Inna na aje mata sannan na ɗauki Hijabinta na saka na nufi ƙofar gida gabana sai faɗuwa yake musamman da na yi arba da mutumen dake sanye da rigar kamfanin da kuma hularsu, tun kamin na masa sallama shi ya fara min tare da faɗin sunana. “Khadija Musa Kafinta” “Sunana ne” “Zaki saka hannu a nan sai na baki saƙon da aka aiko miki” “Bana da buƙata ka mayarda saƙon, kuma ka faɗawa shugabanku ya dakatar duk wani saƙo da suke aiko min bana da buƙata” Sakin baki mutumen ya yi yana kallona, kamin ya barshi tsaye a gurin nayi shigewata, zuciyata cike da tunanin abunda ke cikin saƙon a lokacin na riƙa da na sanin ƙin karɓa da na yi domin sosai na so naga abunda aka rubuta, sai dai kuma ta wani babin bana da buƙatar duk wani abu daya dangancin Jibril idan har na saka masa fuska tabbas zai sake nuna wasa da ni kamar yadda ya yi a baya. Wani mugun murmushi na samu kaina da yi lokacin da na tuna hawayen da na gani a fuskar Jibril, ashe zai iya zubar da ƙwalla saboda ganina har ya riƙa hannuna ya shafa a fuskarsa, mace da ya ce kashe yafi ta daraja a gunsa, lallai akwai babban labari a cikin hawayensa, domin ba kasafai Jibril ya ke nadama akan abunda ya aikata ba. “Kee... Lafiya kike murmushi ke kaɗai kuma?” Tambayar da tayi min ta dawo dani daga duniyar tunanin da na tafi har na yi dariya na matsa kusa da ita na rumgumeta. “Ina sonki sosai Mamana” “Waye ya zo yanzun kuma?” “Daga kamfanin da nake aiki ne, suka aiko saƙo amman ban karɓa ba” “Saboda me?” “Nasan babu komai a ciki sai wulaƙanci” “Ai da kin karɓa kin duba wata ƙila zai miki amfani” “Ya riga ya tafi” “Allah ya kyauta” Sai duk muka amsa da Amin. Bayan mun gama karyawa, su Sakina suka shirya suka tafi makaranta tare da Noor, sai dai gabana nata faɗuwa saboda ina ganin kamar wani abu zai faru da ɗana. Sai da suka je makarantar suka dawo sannan hankalina ya kwanta. Can da yamma sai ga Jidda ta shigo gidanmu da manyan ledoji, daman ta saba a duk lokacin da nake rashin lafiya sai ta riƙo min wani abu take zuwa gidanmu dubani, sai dai abunda ya ban mamaki siyayar da ta yi min ta fi ƙarfin Jidda duk da nasan sun fimu rufin asiri. Bayan sun gama gaisawa da Inna ta ƙasaro inda nake zaune ta dire min ledojin tana zolayata kamar yadda ta saba. “Gawa ta ƙi rame, kin ƙi ki mutu mu ci gado” “Mutuwata ba yanzu ba yarinya sai ke da danjinku kaf kun ƙare” Sai duk muka saka dariya har Inna dake ninkar kayan da na wanke ɗazu na su Jamila. Mun sha fira sosai da Jidda daga bisani na tambayeta inda ta samo wannan kayan domin ita kanta tasan na san wannan kayan yafi ƙarfinta, bata ɓoye min komai ba ta faɗa min daman can Jidda bata ɓoye min komai. “Wallahi Mustapha ne ya kawo ya ce idan zanje na riƙa miki wannan, wai kar nake hannu sake, daman ina ta tunanin abunda zan riƙo miki dan bani da kuɗi kuma bana son zuwa haka nan” “Daman kuna waya da shi?” “A'a ɗazu dai ne ya zo yake tambayata jikinki kuma ya bani number wayarsa wai idan zanje dubiyarki na faɗa masa, shine fa ya kwaso min wannan kayan” Bana son Jidda ta zargi wani abu, hakan yasa ban ƙara masa wata tambayar ba, sai kawai muka ɗauko wata firar. Sai da aka kira sallah magariba sannan na rakata ƙofar gida ta wuce tana mintar rashin adalci na mai kamfanin da nake aiki, domin na labarta masa cewar ya koreni. Tun daga wannan ranar kullum sai Mustapha ya aiko da saƙon a gidanmu da sunan ganin lafiyar jikina, wasiƙar gurin aiki kam kullum sai tazo gidanmu bayan ta waya da ake aiko min, tun Inna na lallaɓa na koma aikin har ta gaji ta zuba min ido domin ta fahimci ba zan koma ɗin ba, na kan faɗa mata ni bana son aiki a kamfanin ne saboda dokokin kamfanin. Bilal ma ya yi mamaki matuƙa ji da ganin yadda kamfanin yake neman na koma aikin bayan ance an koreni, shi da kansa yake faɗa min ko da harkar kasuwanci kanfanin zai ƙulla da kai da zai ci riba matuƙar suka koreka ba zasu nemeka ba balle kuma ma'aikaci, babu irin tambayar da bai min ba akan ko nasan wanine a kanfanin amman na nuna masa ni bansan kowa ba har ma na yi masa iƙirarin cewar ai na fada cewar ban yafe Haƙƙina ba wata ƙila shiyasa suke son na dawo aikin. Sam ban taɓa ɗaukar lamarin Mustapha azimun ba ne sai yau da mahaifiyarsa ta zo dubani, ita kanta Inna mamaki ya cikata kuma ta ɗan tsorata da lamarin kamar yadda nima nake ta almarar abun tare da tunanin abunda yake ƙoƙarin aikatawa. Kana ganinta kasan zuwan cilas ne domin ƙyamar gidanmu take sosai, zama na sai ya gagareta sai wani kallon gidan take a hankaɗe a tsaye ta yi min ya jiki ni kuma na bawa banza ajiyarta har sai da Inna ta amsa ta tana ta ƙoƙarin kareni, saboda ta tsarku da yadda na share Hajiyar a tsaye ko gefenta ban kalla ba balle har na iya gaisheta. “Iska ne da ita abubuwan ne sai a hankali” Ta taɓe baki tana gyara tsayuwar gilashin idonta. “Daman Son ne ya faɗa min akwai yarinyar da kai asibiti yana son na zo na dubata, ni zan wuce” Ko sakon biyar bata ƙara a gidanmu ba ta fice tana wani irin taku na ƙasaita Inna ta bita tana masa godiya, ni kuma na bita da harara, daman ba zan lissafata a cikin mutane mn da suka mana gaisuwar Habiba ko Baba ba duk da bana iya tantance kowa da kowa amman da tazo da dole wasu zasu ganta ko da ba ni ba, gashi tsanar ɗanta ya dasa nin tsanarta musamman yanzu dana fahimcin bana sha'awar mutane irinmu. Inna na dawowa daga rakiyarta ta cire takalmin ta buga min a kai, kana ta nuna ni da shi tana faɗin “Allah ya canja miki wannan baƙin halin da ya taso miki, ai ba ita kika kunyata ba ni kika kunyata” Tana faɗar haka ta nufi ɗaki ranta a ɓace, rabon da Inna ta ɗauki wani abu ta dakeni tun ina junior high school lokacin da na zo wani hutu, amman yau gashi ranta ya ɓace har ta buga min takalme a kai saboda ɓacin rai. Tashi na yi na bita ɗaki na bata haƙuri tare da shaida mata ba zan sake sannan muka shirya da ita har ma tayi min bitar zaman da mutane da kuma taka tsantsan na ka samu ka rabu da kowa lafiya. Haka muka zauna muna ta fira har su Noor suka dawo daga makarantar allo na tura masa karantunsa ya wanke allon yana ta murna wai malaminsu ya ce ya iya idan yaje gida ya wanke allo gobe yi masa wani rubutun. Bayan sallah magariba Bilal ya sallamomin kamar yadda ya saba sai dai yau sallamar tasa ta musammance domin firar kansa yake min wai mutane nata maganar ya kamata ya yi aure har da ƴan gidansu, ni dai murmushi kawai nake inda kuma ya kamata na yi dariya sai nayi dariya, har muka rabu beji wata kalma da yake zato daga bakina ba, hasalima ban barshi ya daɗe kamar yadda ya saba ba ganin inda akalar labarinsa ya dosa a yau. Misalin tara da rabi muka kulle gidanmu bayan mun gama fira da Bilal, na bawa Sakina ta kai min wayata maƙota saboda na samu caji, sai na alwalar na shigo ɗakin Inna na yi sallah isha'i, sannan na shiga na gyarawa su Sakina gurin kwanansu, ni kuma na dawo ɗakin Inna domin a yanzu na daina barinta tana kwana ita kaɗai. Saman gado muka haye ni da Inna Noor na bayana daman duk inda nake kwana a nan yake kwanan, na yi matashin kai da fillon Habiba kamar yadda na saba sannan na yi Noor addu'ah bayan wacce ya karanta ta shiga bachi, ni ma na yi muka kwanta cike da aminci da salama. Can cikin bachi naji Inna na tashina a hankali, ina buɗe ido hankalina ya tashi sosai, sakamakon jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gidanmu da muka ji ana yi, ashe nice bachi ya lula da ni sosai ban ji ba har sai da aka tasheni su Sakina da Jamila kan tuni suka ji har sunyo ɗakinku sun ta ɓoya bayan Inna suna kuka, Noor ma yana ƙanƙame da Inna jikinsa sai rawa yake. “Ku shige ƙarƙashin gado” Inna ta faɗa kaɗan-kaɗan, ni kan araina na ce wane irin ƙarƙashin gado kuma ƙarƙashin gadon da itace ne muka saka a ƙasa ni da Habiba, saboda a samu yabuɗaɗɗiyar katifar ta tsaya. Kamin mu yi wani unƙuri sai dirowar mutane muka ji cikin ɗakinmu, daman ƙofar ɗakin ta cire ta can farkon shigowa gidace kawai ta rage muke rufe gidan da ita. Fitila mai haske sosai ɗayansu ya dallo min ba shiri na rumtse ido jikina na rawa na rumgume Inna ina saki fitsari abunka da mai mugun tsoro... TO SU WAYE KUMA WAƊANNAN😨😱 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣4⃣ Sakina da Jamila ne suka saka da Noor ne suka ihu ganin bindiga nikan dabam idanuwana a rufe suke addu'a kawai nake karantowa. “Ku yi mana shiru..” Ɗaya daga cikinsu ya faɗa a tsawace cikin wata murya mai kamar doro, sai duk suka yi tsif kamar babu su a gurin. “Dan Allah dan Annabi karku cutar min da yara ku yi haƙuri” Shine abunda Inna take ta roƙo muryarta na rawa alamar tsoro yana tare da ita. “Ki kwantar da hankalinki ba zamu miki komai ba ba zamu taɓa kowa na ki ba, kuɗi muke so ko abun kuɗi” Jin wannan yasa na sassauta riƙon da nayi wa Inna na buɗe ido tare da ɗagowa na kalli fuskokin waɗannan mutane da suka zo neman kuɗi a gidanmu, ina ɗagowa ɗayan ya dalla min fitila a ido gashi ba shiri na sake rumtse ido. Ɗan abunda Inna ta san tana da shi na canji taje ta ɗauko ta kawo musu jikinta sai rawa yake tana faɗin “Shikenan na ke dashi a gidan nan Wallahi ba muda komai mu talakawa ne” “Kina da ɗan kunnen zinari ko azurfa?” “Wallahi bamu da shi” Ta bashi amsa ciki kuka mai cike da tsoro. Ban sake jin sun ce komai ba sai kawai na jin nayi suna da bincikar kayan da ke ɗakin wasu kuma suka nufi ɗakinmu wacan dake waje suna bincika, hakan ya bani damar buɗe idona a karo na biyu na kalli mutun huɗu da suke ɗakin suna mana bincike, daga ganinsu manyan ɓarayi ne domin ɗauke suƙe da manyan bindigogi fuskarsu sanye da fuska irin ta manyan ƴan fashin nan dukansu danye suke da baƙar riga da jean banƙi. Mun ga ikon Allah a wannan ranar domin komai sai da suka bincike, sam basu yarda bamu da komai ba, har tufafinmu sai da suka bincika suka tsince masu kyau, ragowar shinkafar da ta rage mana mana dafawa har da ita suka haɗa, wani abun ɗaure kai har da tukunyar da muke dafa abincin sannan suka ce duk mu rufe idonmu kuma mu kwanta, sannan suka fice suna cewa duk wanda ya ɗago sai sun halbeshi. Ni dai ba buɗe ido ba ko motsi ban sake yi ba har na kusan minti talati saboda kawai tsoro. A daren babu wanda ya sake runtsawa daga ni har Inna da Sakina, Jamila da Noor ne kawai suka yi bachi, Noor ma sai da na rumgumeshi. Abu ɗaya ne ya tsaya min a rai har garin Allah ya waye, miyasa basu shiga gidan manyan masu kuɗi ba sai gidanmu? Beside waɗanne irin ɓarayi ne ma da zasu ɗauki tsofin sutura da ragowar shinkafa da ƴan canjin da basu kai dubu biyu ba da sunan sata da alama mu fa manyan ɓarayi ne ba ƙananan ba. ‘Turosu aka yi’ Shine abunda zuciyata take ta yawan nanata min, sai dai kuma waya turo su? Washe gari mutane suka yi ta shigowa suna mana jaje tare da fatar allah ya tsare gaba ciki har da ƴan babban gida, sai dai wannan besa ɗayansu ya yi tunanin cewa mu koma can ba, duk kuwa da kasancewar rayuwarmu tana cikin hatsari saboda suna ganin idan muka koma zama tare da su lalurar mu ce zata hau kansu, kai tirrr da wasu ƴan'uwa! Da yamma Jidda ta zo ita da mamanta suna jajanta mana take labarta min abunda ake faɗi a unguwa, wai gurin dai suka zo har wasu na cewa ba zasu rasa min fyaɗe ba sai dai ba zan faɗa ba, maganar ta ɓata min rai daman nasan dole mutane su zargi haka ganin bamu da Komai kuma ace sun zo gidanmu. Baba Sulaiman ne ya kira mai gyara ya gyara mana tsohon ganbun na ƙofar gida da mutane suƙa ɓalle suka shigo. Tun da yamma muka bar gidan saboda ƴan'uwan Inna da suka sha kai akan sai dai mu dawo can da zama, ranar a tudun wada muka kwana gangaren tallatu sayin salamatu mai tuwo. Sun nuna mana mana kulawa sosai aka wuni ana firar ta nan na fahimcin Inna ma ta gano turosu aka yi, sai dai ita ta allaƙa abun ne ga Mustapha har take min faɗan wai na lallaɓa mu rabu lafiya da shi. Bayan sallah isha'i Bilal ya kirani na kwatanta masa inda nake, ko minti arba'in ba a ƙara ba sai gashi ya iso tudun wada, na fito titi na shigo da shi cikin lungun na mu. Gaisawace first abunda muka fara yi sai yasa na kira masa Inna ya gaisheta tare da yi mata jaje sannan ya ce an gidansu suna gaisheta. Bayan Inna ta shige ya dawo kaina sai bugun cikina yake yana ta son ya ji idan sun min wani na san wannan ba zai rasa nasaba da maganganun mutane da yake ji ba. “Kaima ka yarda da abunda mutane duke faɗa kenan” Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara tsayuwarsa ya ce. “Yarda ta da rashin yardata duka suna gurinki, Wallahi komai kika faɗa min zan yarda da shi Nawancy” “Idan har ka yarda da ni toh ka yarda da duk abunda zan faɗa maka, Wallahi basu min komai ba ko hannuna basu riƙa ba, babu wanda suka taɓa a gidanmu” Sanyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da jinginawa jikin iccen tarbejiya dake ƙofar gidan yana hamdala. “Allah na gode maka, Wallahi Nawancy da sun taɓa ki ban san yadda zan yi ba ban san iya halin da zan shigaba” “Da ba zaka iya aurena ba ko?” Hakan yasa shi ɗagowa daga jinginen da yake da sauri yana kallona fuskarsa da ɗauke da murmushi. “Nawancyta da gaske kike maganar nan da kika yi?” Ya tambaya yana matsowa kusa da ni kamar zai haɗa numfashinsa da nawa, hanzarin matsawa baya nake sai ya yi caraf ya cafke min hannun yana cigaba da matsosa kusa da ni. “Kin san waye ni babu abunda zan miki, kawai ina son na tabbatar ne, Wallahi Nawancy i'm ever ready to marry you dan Allah ki taimaka min” “Mutane fa zasu gani” Na faɗa a tsawalle ina kawar da fuskata, sai na yi sa'a ya sake ni, ina ganin hakan na juya da gudu na shige gida. Babu irin kiran da be min ba ta waya amman na ƙi ɗagawa har ya gaji ya tafiyarsa. Kwanan mu biyu a can muka dawo gida saboda tsallawa da muka yi saboda gidan gidan taro ne babu sakewa sosai, ga yaran gidan basa da ragowa a gaban idona suke buge Noor ba damar nayi magana ace na yi rashin ta ido su kuma ba zasu iya yi ma yaransu magana ba. Ranar da muka dawo ma mutane sun ta zuwa yi mana jaje mutanen da basu samu zuwa mana washe garin da abun ya faru ba, saƙon kamfani kan kamar ƙa'ida ko da muka dawo mun tarar da wasiƙa biyu wacce aka kawo yau ita ce ta uku ban da ta waya da nake ta karɓa ko wace safiya da kuma yammaci. Bayan na gama gyare-gyaren gida na shinfida tabarma na zauna tsakar gida ina ta nazarin abubuwan rayuwa ciki har da wannan abun da ya same mu, da kuma maganar ƴan sanda da suka yi mana izgilanci amman shiru har yau babu dpo babu labarinsa, ga kuma Jibril da ya sakoni a gaba yanzu. Wai shi Jibril me yake nufi ne ya yi nadama ko kuma so yake na koma aiki ƙarƙashinsa ta yadda zai sake gallazamin ya ɗauka kamar da ne? “Kut” A fili na yi ƙwafa, kana na ɗaga kaina dake ƙasa na kalli Inna wacce ta fito daga ɗaki tana maganar aikina. “Ni fa wannan lamarin har tsoro yake bani Nawwara, ban taɓa ganin wanda aka matsawa ya koma aiki kamar ki ba, anya babu wani abu?” Na yi dariyar da ni ƙaɗai nasan abunda yake nan. “Babu komai Wallahi kawai dai kin san abu idan aka ce maka da turawa ne, shiyasa” “Amman ke miyasa kika tsaya kai da fata akan ba zaki koma ba, nifa ina jin da kamar akwai wani abu” “Babu komai kawai ina musu jan ajine saboda susan ba ko wanne mai neman aiki ba ne wulaƙantacce, zan koma aiki Inna ai dole ma ne na koma aikin ko dan na bawa marar ɗa kunya! Kuma ni kaina ina da buƙatar aikin saboda zai taimaka mana mi tallafawa kan mu da kan mu” Na faɗa ina sauke ajiyar zuciya Inna kuma tana amsa sallamar Malam Haruna mai gidan da muke haya...! *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣5⃣ Bayan Inna ta amsa sallamar ta je ta ɗauko hijbinta ta saka sannan ta ƙarasa ƙofar gida suka gaisa da shi. Sama-sama na ke jiyo firar da suke har Inna na faɗin Innalillahi, kamar na unƙura na tashi sai kuma wata zuciyar ta ce na zauna tunda maganar manya ce ake ko ma minene idan ta zo ai zanji, sai dai jikina na ta raya min ba abun daɗi ba ne.   Sun ɗan ɗauki lokaci suna maganar daga bisani na ji muryar Inna tana roƙon a tausaya mana shi kuma yana faɗin babu yadda zaiyi. Bayan sun gama maganar Inna ta dawo cikin gida jikinta a sanyaye fuskarta kuma na nuna alamun damuwa. “Lafiya Inna miya faru?” Zama ta yi kusa da ni tana nuna min kuɗin dake hannunta. “Wai an sai da gidan ya kawo mana ragowar kuɗin hayarmu na wata takwas kuma wai sati ɗaya wanda ya siye gidan ya bamu” Kamar daga sama aka jefo maganar haka na jita cikin kunena, zuciyata ta hau bugawa da hauri na zaro ido hannuna a ƙirji na ce “Sati ɗaya kuma? Waya siye gidan ne?” “Oho” Ta faɗa idonta cike da ƙwalla, furucin da na yi na ɗazun ne ya fito da Sakina, Jamila da kuma Noor da gudu suka nufo inda muke zauna suna ta rabon idon da son jin abunda muke tattaunawa. “Inna miya faru?” “Tashi zamu yi Sakina an saida gidan” Inna ta amsata cikin wani irin kalar murya marar daɗi. “Tau ina zamu koma, waya siye gidan hala?” Jamila ta tambayi Inna. “Allah masani” Dukansu ɓata fuska suka yi da alama suma maganar tashin be musu daɗi ba domin sun saba da unguwar anan haifesu ga ƙawaye da ƴan'uwa kusa da su taya zasu jidaɗin tashin? Idan muka tashi ina zamu koma ? Babban gida ko ina? “Haya yanzu tsada take ina ma zamuje a bamu ɗaki ban sani ba, babban gida ma idan muka ce zamu zauna babu guri tun da duk sun kame ɗakunan waya ma zai bamu haya da dubu ashirin datara da suka rage mana na ragowar kwanakinmu kai Innalillahi wannan rayuwa daga wannan sai wannan” Cewar Inna hawaye na zuba a idonta, ni kuma na kalleta na ce “Ko dai karin kuɗin hayar yake so?” “Na tambayeshi yace aa shi ai ya riga ya siyar da gidan” Na yi shiru inata nazari wannan wane irin saida gidana ne ba a shigo ciki anga yadda gudan yake ba kawai sai muji labarin an siye shi kuma wai sati ɗaya mu tashi? Lallai wannan daga gani shiri ne, kuma ba zai wuce Mustapha ba shine kawai na ke zargi. “Inna ki kwantar da hankalinki zan koma aiki idan aka biyani kuɗin aikin sai mu haɗa da wannan mu kama wani gidan haya, zan roƙeshi ya yi mana haƙuri har ƙarshen wata zamu tashi mu bar masa gidansa” Na faɗa ina kallon Inna sai Sakina ta ce “Ko kuma a faɗawa Ya Bilal” Na katsa mata tsawa. “Ke wane irin Bilal kuma Wallahi duk wacce taje cikinku ta faɗa masa sai na ɓata mata rai, haka kawai sai mu ɗauki lalurar duniya mu aza masa, shi ma ai yana da tashi lalurar” Haka muka wuni gidan shiru-shiru kamar wanɗanda aka yi ma mutuwa duk jikinmu ya yi sanyi, tsoron kwana da muke ji a gidan sai ma ya cire mana saboda hankalinmu ya karkata kan wannan matsalar. Bayan sallah magariba Inna tace naje Babba gida na faɗa musu halin da ake ciki, ba musu na tashi na ɗauki Hijabin da na cire wanda na yi sallah da shi na saka na kama hannun Jamila muka nufi ƙofar fita. Abun mamaki muna fitowa muka dami Mustapha a tsaye kamar daman can mu yake jira, kallon kallo muka riƙayi da shi, idonsa narau-narau fuskarsa abun tausayi kamar mai shirin yin kuka, ni ko babu komai a idona sai wuta mai tsananin ci a lokacin da ta ga maƙiyinta. “Guri....guri...gurin.. inna na..zo Daddy ne ya aiko...ni-” Haka maganar ta riƙa taƙe mishi kamar marar gaskiya, ni kuma abun sai ya bani mamaki kuma ya sakani murmushin takaici. “Like seriously? Wai Mustapha ko baka san gidansu Habiba ba ne? Baka san ni yayarta ba ce?” Sai ya amsa min da sauri. “Na sani! Zan iya rantsewa da Allah ni ban taɓa kula kina cikin unguwar nan ba sai da kika mareni, daga lokacin da kika mareni sai na sa aka min bincike kanki a maimakon na tsargu sai na samu kaina da tausayin halin rayuwar da kuke ciki kuma na yi nadamar abunda na yi ma Habiba kasancewarta ƙanwarki, a lokacin da ta sameni ta bani haƙuri akan karna cutar da ke ina ta shirya abunda zan miki na rama abunda kika min amman sai zuciyata ta hanani saboda tausayinki da take, kin fini kwarjini da ƙima Nawwara kuma ke jaruma ce na gano haka ne daga lokacin da kika ɗaga hannunki kika mareni bayan kuma ba dake nake faɗan ba siya kika yi, wannan ya karantar da ni wani abu a rayuwata lalle ni a idon wasu ba kowa bane tun har mace kamarki zata iya ɗaga hannu ta mareni a bainar jama'a, bayan ko ƴaƴan masu kuɗi basu taɓa unƙurin nuna min ko da yatsa ba balle kuma harara. Na rasa natsuwata daga lokacin da labarin mutuwar ƴar'uwarki ya same ni, mutuwar Habiba ta canja ni Nawwara, ta tunatar da ni abubuwa da dama da na manta i understand the distance between right and wrong, ta kuma ta sanar da ni abubuwan da ban sani ba a rayuwar duniya, if i begin to tell you how terrible i feel for what I did to your family Nawwara you will find a place in your heart to forgive me, da ace kun sanar da ni tana da ciki da na karɓi cikin kuma na ɗauki nauyin komai na ta, but it too late labarin mutuwarta kawai ya sameni ba a faɗa min dalilin mutuwarta ba amman ni na san cikine saboda ance ta yi zubar jini, Nawwara i'm looking forward to corrected all my mistakes, i made a mistake because I am only human dan Allah Nawwara ki yafe min” Ta yanayin muryarsa nake fahimtar hawayene suke zuba a idonsa, domin duhu ya sauko bana iya ganin fuskarsa da kyau, sai dai na fahimci hawaye yake kamar yadda nima nake tunawa da ƴar'uwata. “It's too early to ask my forgiveness Mustapha, i know you are here to play a game with me too” “No don't get me wrong, i know it too early i'm sorry i shouldn't talk about this, ga wannan ko zaku buƙaci yin wani abu da shi” Jamila na ganin damin kuɗin da ya miƙo min ta juya da gudu ta koma cikin gida. Ni kuma na yi murmushi ina share hawayena. “Baka ba kanka dariya ba? Tsayawa kana magana da ni be isa yasa ka ji kunyar kanka ba? What kind of stupid are you Mustapha? What make you think zamu karɓi wani taimako daga gareka? Wannan ne yasa ka turo aka kwashe mana komai kuma ka siye gidan da muke ciki just to humiliate us? Or to force us accept your apology? What kind of person are you?” Na faɗa cikin kuka, har ya buɗe baki ya yi magana sai kuma ya yi shiru kamar mai nazari, isowar Inna ce tasa ni saurin share hawayena. “Lafiya Nawwara?” “Lafiya ƙalau daman Zakkace aka fitar shine Daddy ya ce a kawo muku” Shine ya amsata yana miƙa mata kuɗin, ni kuma na yi karaf na ce. “Karki karɓi kuɗin nan Inna, kuɗin maƙiyinki ne, shine mutumen da ya yi ma Habiba fyaɗe ya yi sanadiyar rabaki da farincikinki kuma shi ya turo mana ƴan fashin nan ya siye gidan da muke ciki saboda kawai mu karɓi taimakonsa...” Mutuwar tsaye Inna tayi na ɗan wasu mintuna sannan taja hannun Jamila da Sakina ta mayar da su cikin gida ni kuma ta ce da ni. “Nawwara shiga gida” Ba musu na juya na shige cikin gida sai ta maida ƙofar ta rufe, duk muka yi ɗaki har ita, na yi tsammanin zan ga hawaye ko makamancin haka a idon Inna amman ban ga komai ba muryarta ce kawai take iya karantar da ni damuwarta. “Daman na yi zaton shine ya aiko da ƴan fashin nan, kuma na san babu wanda zai saye wannan gidan sai shi, amman ban taɓa tsamanin shine ya lalata min rayuwara ƴa ba...” Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciyata, daga ni har ita bamu kwana cikin daɗi ba a wannan daren gashi zuciyata na ta saƙa min zuwa gurin aikin ko kuma na haƙura. *** *** *** JIBRIL POV. Jingine yake jikin kujerar dinning hannunsa saman kofin tea yana ta zagaye bakin kofin ya gagara sha, babu abunda yake tunani sai rayuwarsu ta baya da Nawwara. Yana jin lokacin da take waya da Inna Inna na faɗa mata zata so har Abuja ganinta ita kuma tana ta ɗauki da murna, amman sai ya haya ya nuna mata sam baya son sanin family ta. “Kina jindaɗi kin auri mai kuɗi ko? So that ki kawo min su a gida ko? Ni ke na aura ba iyayenki ba dan haka bana buƙatar ganin kowa a gidana” Matsowa ta yi kusa da shi kamar zatayi kuka. “Jibril ya kamata ka san iyayena suma kuma su sanka, ko lokacin da za ayi aurenmu ƙin zuwa ka yi ka gaishesu, bayan kuma an yi auren sau ɗaya suka taɓa ganinka ba zasu tantance ka ba...” Tsawa ya katsa mata ya shaƙe wuyanta. “Na faɗa miki bana buƙatar ganin kowa anan, ba iyayenki ba har abokanki bana da buƙatar ganinn kowa karki kuskura kawo min kowa a nan, annoba kawai...” Tuna wannan yasa shi sauke wani dogon numfashi har yana buɗe baki. “Taya zan tunkaresu yanzu? Ya Allah help me” Ya faɗa yana kallon Siraj da ya shigo yanzu riƙe da file a hannunsa. “An gama komai mum nika masa kuɗin gidansa ya sayar mana ya bamu takardu mun bashi kuɗi kuma mun faɗa masa sati ɗaya muka ba ƴan hayan” “What...?” Ya ture kofin tea ɗin ya miƙe tsaye. “Sati ɗaya ya yi nisa Siraj a basu kwana biyu ko uku, miyasa baka da tausayi ne baka san halin da nake ciki ba i can't live without her” Siraj ya matso kusa da shi ya dafa kafaɗarsa. “Cool down my friend, Nawwararka ta dawo aiki yau da safen nan” Jibril ya juya baya yana lumshe ido tare da jan sauran cocaine ɗin dake hancinsa. “Joke apart Siraj” “i'm not joking, yanzu aka kirani wacce ake aikawa saƙon ta dawo aiki ta dawo amman bata da uniform na ce a bata sabo” “Oh my God” Ya furta ya nufi bedroom ɗinsa da sauri yana cire vest ɗin dake jikinsa. Siraj kuma ya bishi da kallo yana taɓe baki. *** *** *** MUSTAPHA POV. Yafi ƙarfin waya ɗaya a tsaye ƙofar gidan bayan Inna ta rufe gidan, sannan ya kama hanyar gidansu yana tafiya da ƙafa kamar yadda ya zo zuciyarsa cike da mamaki, daman sai yanzu Nawwara take faɗawa Inna kenan Habiba Nawwara kawai ta faɗawa bata faɗawa Inna ba. Ko da ya isa gida jikinsa a mace ko part ɗin mahaifiyarsa be leƙa ba ya yi shigarwasa part ɗinsa, sallah isha'i a cikin ɗakin ya yi ta. Tunani Nawwara ne ya tsaya masa a rai har garin Allah ya waye be bachi be ko zo kusa da idonsa ba balle ya ɗauke shi, be taɓa samun kansa cikin irin wannan halin ba sai a yanzu. Kamar sallah isha'i itama sallah asuba a cikin ɗakinsa ya yi ta, yana ta roƙon Allah ya yi masa sauƙin abunda yake ji a zuciyarsa. Misalin sha ɗaya da rabi mahaifiyarsa ta shigo ɗakin sai ya yi saurin juyawa kamar mai bachi. A aladar shi tara na safe yake fitowa su yi breakfast goma ya shirya ya wuce gurin aiki amman yau ga shi har shaɗaya na safe bata ji ɗuriyar ɗanta ba dole ne ta duba tun da taga motarsa ta tabbatar da yana gida. “Son...” Ta kira sunansa a hankali tana zama saman gadon kusa da shi. Juyowa ya yi ya kalleta ba tare da ya amsa ba. Jan da idonsa suka yi suka kumbura ya tashi hankalinta sosai, da sauri ta kai hannu ta taɓa kansa. “Baka da lafiya ne your temperature is so high, miyasa same ka, bari na kira likita” Tana miƙewa tsaye sai ya riƙa hannunta. “Please tell me Mom ya zakiji idan kika rasa ni?” “What...?” Ta dawo ta zauna tana masa wani razanannen kallo, shi kuma ya tashi zaune yana kiran amsarta. “Zan haukace Son, ƙara dai ni na mutu kai ka rayu, kai kaɗai gareni fa bani da kowa sai kai i can't afford to lose you, don't talk about this please, you have no idea how mother could feel if she lose her own child, her happiness, kai kaɗai gareni Son ka daina kawo zancen mutuwa a yanzu” Razani, tsoro da fargabar da ya ganin a fuskar mahaifiyarsa ta karantar da shi halin da mahaifiyar Habiba take ciki. “Ba zasu taɓa yafe min ba losing a father, mother, child is unforgettable pain ba zasu taba yafe min ba” Ya furta idonsa na kallon window ɗakinsa. Sai mahaifiyarsa ta kama hannayensa. “Su wa?” “Ƴan'uwan Habiba” “Wace Habiba?” “The woman i raped” “When... How” “Yarinyar da tazo gurinki neman kuɗi kika hanata, ni na yi mata fyaɗe na bata kuɗi and now she's dead” Hankalinta ya ƙara tashi. “Fyaɗen da kayi mata ne silar mutuwarta? Taya?” “Ciki tayi iyayenta suka je zubar da cikin garin zubar da cikin ta rasu” Ta yi saurin riƙa fuskarsa dan bata son tashin hankalin ɗanta ko kaɗan. “That's the point Son ba kaine silar mutuwarta ba karka matsawa kanka, su sukaje zubar da cikin ƴarsu suka kasheta” “Amman ni ne silar cikin” Shiru ta yi tana ta tunani babu yadda ba tayi ba akan ya daina neman mata amman yaƙi ita kanta abun yana damunta amman gudun ɓachin ransa yasa take ɗaga masa ƙafa ga kuma ubansa da ya tsaya masa kai da fata akan yadda duk yadda yake so a gari ga taka wanda duk ya yi masa ba dai-dai ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta ɗora hannayenta saman kafaɗarsa ta ce “Son kai ne Sila amman idan ka roƙi Allah zai yafe maka, kuma hukunci za a masa sai dai ayi maka mukuncin wanda ya yi zina su kuma iyayenta ayi musu na kisan kai, zan toƙa maka Allah ya yafe maka kuma kaima ka roƙa Allah ya yafe maka” “Amman Mom su iyayenta ba zasu yafe ba, musamman yayarta Nawwara” “Idan Allah ya yafe maka ko da su basu yafe maka ba babu komai, kawai ka natsu na daina wannan halayyar” “Na daina Wallahi Mom, amman idan Nawwara bata yafe min ba i will never ever being in peace and happiness, because i love her...” Kamar wacce akayi ma shocking haka ta ɗauke hannayenta daga kafaɗar Mustapha tana kallonsa baki sake. #RAI BIYU #RB #TEAM MUSTAPHA #TEAM BILAL #TEAM JIBRIL Bari mu ga TEAM ɗin wa suka fi yawa....? 😁 CANDY ce 👌 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣6⃣ Bayan su Sakina da Jamila sun wuce makaranta ni kuma na shiga gyaran gida, ina tsaka da wanke-wanke wayata ta ringing kamar ba zan ɗaga ba saboda bana son tashin idan ina aiki har sai na kammala, sai kuma na cire kuiya na miƙe tsaye na nufi saman window inda wayar take na ɗauka, Bilal ne ke kira da gangan na tsaya masa yanga har sai da ta kusa tsinkewa sannan na ɗaga cikin muryata mai nuna tsatsan babu ruwana. “Assalamu Alaikum” “Nawancy i'm glad muryarki na fara ji yau da safen nan” “Baka je aiki ba?” “Yanzu zan wuce ɗan leƙo waje na ganki” “Bilal duk na yi datti aiki nake yi” “Ai nafi son ganinki da dattin kin fi kyau, leƙo mana ke kaɗai nake jira” Babu yadda na iya dole na amsa masa da tau na ɗauki Hijabi na saka na leƙa waje da fuskata a she yana nan daf da ƙofar gidan jikingine yana jiran fitowata. Murmushi na sakar masa ina kallon yadda suit ɗin jikinsa ya karɓesa ya fito da kyausa chocolate skin ɗinsa sai shining take kamar wani sabon ango. Shi ma murmushin yake min yana nuna min wani bafulatani dake tsaye da jarkokin ruwa a wheelbarrow. “Ragowar ruwan da aka zuba mana a cikin gidane Mama ta ce a kawo muku” “Na gode sosai Allah ya saka da alheri” “Amin” Ya faɗa ni kuma na juya da nufin komawa cikin gidan domin nunawa mai amalanken inda zai zuba ruwan, sai kawai na ji Bilal ya kirani. “Nawancy” Ina juyowa sai kawai ya kanne min ido ɗaya sannan ya kama gabansa yana tafiya kamar ba shi ba. Nikan dariya ma abun ya bani wani lokacin Bilal yana min abu kamar wani ƙaramin yaro, hakan kuma ba ƙaramin ƙara min son kasancewa da shi nake ba. Komai na cikin gidanmu sai da aka ciki har muka bada sauran jarka biyu maƙota kasancewar ruwan ya yi mana yawa, hakan ne ya tabbatar min da cewar ba Mahaifiyarsa ce ta siye ruwan ba shine dai ya siya ya yi mata kamfen, taya ma zata siya mana ruwa haka kawai. Bayan mai ruwan ya gama juyewa na koma na cigaba da wanke-wankena zuciyata na ta shauƙin begen Bilal, alƙairinsa nake ta tunawa da kuma irin son da yake yi ma Noor da kulawar da yake bamu, lallai idan har rayuwarsa zata kasance a haka har abada to kuwa matarsa ta yi dacen mijin da zai taimaka mata ta tashiga aljanna, domin ni kan nasan ba ajina bane domin babu yadda za'ayi mahaifiyarsa ta barshi ya auri bayan ta yi iƙirarin wayo kawai nake masa wai na yi aure har biyu kuma da yaro kuma na ce zan auri ɗanta shi da yake saurayi ƴan uwansa ma basa so mahaifinsa ne kawai be ce komai ba shi ma kuma ina tunanin baya ra'ayin haka. ‘Amman tun da shi yana son ki ina ruwanki? Ai da shi zaki zauna ba da iyayenshi ba’ Wata zuciyar ta tambayeni, har ga Allah idan har na ƙi auren Bilal saboda iyayensa zai iya ɗaukar na yi masa butulci ne kawai domin shi baya la'akari da wannan shi di kullum maganar ɗaya ai shi dai yana so na, na san ko da na aureshi ba zai taɓa bari kowa ya wulaƙantani ba kuma zai maida Noor kamar ɗansa. Haka nake ta saƙe-saƙe na ina aikin har na gama na shiga wanka na fito ina ta tunanin alfanun auren Bilal domin ni dai har yau ban hango wata illa auren Bilal ba idan har iyayensa zasu amince ya aureni ɗin, sai dai kawai na shirya fuskarta familynsa masu uban yawa da cecekuce. Abaya na saka na ɗauki ɗankwalin abayar na yafa akai na, na saka baƙaƙen talkami sai dai fuskata bata da wata kwalliya domin ko hoda ban shafa ba bayan man da shafa, na ɗauki jar jakata na saka wayata a ciki na nufi ɗakin Inna, ina shiga sai na sameta har yanzu tana bachi, daman na san za a rina tunda jiya ta raya dare da tunanin Habiba a duk lokacin da na farko zaune na ke ganinta saman carpet ta rafka tagumi nasan wannan ba zai rasa nasaba da maganar da na faɗa mata ba jiya lokacin da Mustapha ya zo. Tashin na ta ya zame min dole ne domin bana son na je aiki ba tare da ta sani ba, dan haka na taɓata a hankali na tasheta har ta buɗe ido sannan na faɗa mata zan tafi, addu'a tayi min da fatan nasara ni kuma na fice ina amsawa da Amin. Kamar ni ake jiran an fito sai na samu motar kamfaninsu Jibril a tsaye direban yana neman yaron da zai aika, yana ganina ya yi saurin fitowa cikin ladabi ya miƙa min wasiƙar ni kuma na karɓa ina wani shu'umin murmushi na yi sighing sannan ya wuce ni kuma na jefa takardar a jakata na kama hanyar zuwa gurin aikin. Ko da na isa bakin gate ɗin kamfanin, ƙarfe tara ta yi har da rabi, da fari guards ɗin dake bakin gate ɗin sun tareni a da na nuna musu id cart ɗina da ya rage ban ƙone ba a cikin kayan aikim kamfanin sai suka bani dama na shiga bayan sun tambayeni dalilin saka Uniform ɗin sai nan faɗa musu uniform ɗin ya ƙone ne, da na shiga kamfanin sai na nufi gurin da aka tanada domin aje wasu abubuwan da mutun yake shigowa da su wato wani ɗan katon cabinets ne da aka tana domin ma'aikatan gurin su riƙa aje komai na su idan sun rufe sai su tafi ta makullin. Wayata da jakata na aje bayan na kulle na nufi reception na rubuta sunana da kuma lokacin da na shigo sannan na yi musu complain ɗin bana da uniform sai suka ce na wuce kawai. Da kunnena na ji lokacin da ɗayan yake sanar da zuwana a telephone da halshen nasara wato turanci. Yadda na tarar da gurin ya tabbatar min da wata ta fanshe a aikin, domin alamu sun nuna wata ta yi mopping ɗin kamin zuwana. Amman hakan be dame ni ba na ɓa ɗaure mayafin abayata a kaina na ɗauki bokiti da mop na fara aikina mutane dake ta kai kawo a gurin na ta kallona domin sun san an yi mopping ɗin gurin ni kima na zo ina ƙara yi. Irin ƙamshin turaren da naji lokacin da muka zo tare Bilal irinsa na ƙara ji a wannan karon, ƙamshin turaren dana tsana a duniya wanda ke haddasa min ciwon kai a duk lokacin da na jishi. Ko da wasa ban yarda na juya ta baya da nufin ganin mai ƙamshin ba, duk da jikina ya bani akwai mutun tsaye a bayana. Mutane dake gurin da waɗanda zirga-zirga na ga duk sun fice ɗaga gurin kamar ƙyabtawar ido wata ƙila da kai ya yi musu magana da su fita domin ni ban ji kalma ko ɗaya ba, kawai dai na hango yadda duk suke shiga natsuwarsu daga bisani kuma naga sun tashi sun fice da sauri kamar wanɗanda aka kora. Hakan yasa na juyo sai idanuwana suka sauka cikin nasa, hakan yasa ni haɗe fuska kamar baƙin hadari, na wulgarda abunda ke hannuna na nufi ƙofar fita, sai ya biyoni da sauri yana kiran sunana. Juyowa na yi a fusace ina jiran jin dalilin kiran sunan, shi kuma ya gagara cewa komai bakinsa sai rawa yake idonsa na yawo saman fuskata. Ganin ba shi da abun cewa yasa na juya na cigaba da tafiya lifted na nufa shi kuma yana biye da ni sai kiran sunana yake mutane dake gurin kowa yaja baya ganin ya nufo lifted waɗanda suke cikin office's kuma na kallonmu kasancewar duk office's ɗin glass door ne na ciki yana hango na waje kamar yadda na waje zai iya hango na ciki, kallon mamaki suke ganin yadda ya biyoni yana kirana ni kuma naƙi na tsaya. Daf da zan shiga Lifted ya miƙa hannunsa ya riƙoni. “Nawwara ki saurare ni mana....!” Tassss na yi ƙarfin halin wanke masa fuska da mari mai kyau, har sai da ya lumshe ido, komai da ke hawa na uku sai da ya tsaya kasancewar ma'aikatan dake aikin gurin suka ɗauke hannayensa masu tafiya kuma suka tsaya cak suna kallon ikon Allah. “Karka sake kuskuren kai Hannunka ka taɓa min jiki, ka ɗauka nima kamar sauran ƴan matanka nake ko? Karuwai masu binka? To ni ba ƴar iska ba ce kar hannunka ya sake taɓa jikina shashasha kawai” Har lokacin da nake masa wannan furucin be buɗe ido ba, ni kuma ban fasa faɗa masa abunda nake so ba, a gurin baka jin ƙarar komai sai na muryata da kuma sautin takun talkamin Zinatu wacce ta doso inda muke rai a ɓace, tana ƙarasowa kusa da mu ta ware hannu zata rama marin da na yi ma Jibril sai ya yi saurin buɗe ido ya yi karaf ya riƙe mata hannu. “Don't...” Ya faɗa cikin muryarsa dake amsa amo biyu. Cike da tsananin mamaki Zinatu ta kalleni da kalleshi ta ce. “Baka ga abunda ta yi maka ba?” “She's My wife....” Ya faɗa rinannun idanuwansa da suka kaɗe suka yi ja suna kaina, ni kuma na yi murmushin takaici na tattara yawun bakina na tofa masa a fuska. “Tuuff Allah ya tsare Nawwara da zama matar Jibril, matar da ka kira da annoba yau ita kake kira da matarka? Matar da kace ganin baƙin maciji ya fi maka ganinta, matar da ka ce baka ƙauna bata dace da kai ba yau ita kake kira da matarka? Matar da ka wulaƙanta ka fifita karuwa akanta? Matar da ka kira mashiririciya ƴar talakawa ita kake kira da matarka? Matar daka zalumta ka dannewa haƙƙi ita kake kira da matar da baka son abokanka su ganta yau ita kake kira..” “Enough....!” Ban ƙarasa ba ya katsa min tsawa idonsa cike da ƙwalla wasu kuma sun ganganro zuwa kumatunsa. A maimakon na yi shiru sai hakan ya bani damar cigaba har ma da nuna shi da yatsa. “Ba irin da bane Jibril, Nawwara da ka sani a baya ba ita ba ce a yanzu, tirr da kai Jibril, tirr da haihuwar ɗa irinka, na yi nadamar da na taɓa saninka a rayuwata, azzalumi macuci maha'inci, wanda be san komai ba sai zalinci da cin amana” Hawaye nake ina faɗin wannan maganar kamar yadda shi ma yake hawaye kamar ba gobe, a ada ne na faɗa masa wannan maganar dukana zai yi har sai na faɗi uban da ya aikoni, amman abun mamaki sai ya faɗi saman gwuiyoyinsa ya fashe da kuka yana ƙoƙarin riƙa ƙafafuna abunda ya bawa kowa na gurin mamaki. “Ki yi haƙƙuri Nawwara dan Allah ki yafe min...” Da gaske hawaye yake kamar yadda nima nake hawaye na tsanarsa da kuma tuna irin zalumcin da ya yi min. Mutume nan ne ya shigo wanda ya taɓa shigowa a wacan lokaci da nake cikin office ɗinsa, shi ne ya yi ma duka ma'aikatan dake gurin magana suka fice da sauri ciki har da Zinatu da jikinta ya gama yin sanyi da mamaki. Sai kuma rage daga ni sai Jibril sai kuma wannan mutumen, baya baya nayi sai Jibril ya matso da sauri ya rumgume min ƙafafu yana kuka kamar ba shi ba. “I'm sorry Nawwara i'm so sorry” “Haƙuri kake bani da gaske ko Jibril?” Ya yi saurin ɗago kansa yana gyaɗa min kai a tunaninsa zan haƙura ne. “Waya faɗa maka zan yafe maka? Miyasa zaka yaudari zuciyarka da abunda ba zai taɓa zuwa maka ba? Nawwara will never ever ever forgive Jibril for what he did to her, indai har wannan ne yasa ka riƙa aikamin wasiƙar aiki to ka daina wahalar da kanka” Ya yi saurin miƙewa tsaye ya riƙa fuska yana girgiza min kai. “No no no ba haka ba ne Nawwara i just want be close to you i need..” “Close to epidemic? Close to black snake...” Ya yi saurin rufe min baki yana kuka kamar ƙaramin yaro. “Nawwara please...” Hannu nasa na janye hannunsa ɗaga baki na ce “Na tsaneka Jibril na tsani duk wani masoyinka, na tsani farincikinka kukanka shine farincikina na tsaneka Allah ya wandaranka” Na juya cikin kuka na danna lifted ta buɗe na shiga, ina jin yadda yake ƙoƙarin riƙoni abokinsa ya hanashi. Ko da na fito reception kowa kallona yake nasan baya rasa nasaba da hawayen dake zuba a idona. Gurin dana aje jakata na nufa na ɗauka ina hawaye na fice. #RB #TEAM MUSTAPHA #TEAM JIBRIL #TEAM BILAL. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣7⃣ *MUSTAPHA POV.* A hankali ya yi parking ya fito daga motar kamar marar lakka ya nufi part ɗin mahaifiyarshi. Tana hakimce saman kujeara ya shigo jiki ba ƙarfi kamar marar lafiya, gaba ɗaya sai ta tattara hankalinta ta maida gunsa tana kallonsa har ya zauna a kujerar dake gefenta na dama. “Son na yi ta kiran wayarka kashe, tun da ka fita baka dawo gida ba sai yanzu hankalina duk ya tashi, kuma ka kashe duka wayoyinka” “Ina Office” Ya amsa mata cikin muryar dake nuna tsantsar damuwarsa. Tashi tayi takoma kusa da shi ta zauna tana ɗaga bayansa. “Duk tsawon lokacin nan kana office? Haba son miyasa zaka riƙa wahalar da kanka kana damuwa ga abunda har ga Allah baka da laifi? Bafa kai ka kashe yarinyar nan ba dan mai zaka damu kanka su suka kashe ƴarsu da kan su” Juyowa ya yi ya kalleta. “Momi ke kika siye gidansu Nawwara?” “What why would i?” “Lokacin da naje gidansu Nawwara ta yi wani furuci da ke nuna an siye gidansu kuma an basu kwanaki kaɗan su tashi ke ce ko Momi?” “Wato Mustapha har gidansu yarinyar nan kake zuwa fira? Yarinyar da basu da tarbiya ga shegen hassada ya yi musu yawa, dan Allah ka cire yarinyar nan a ranka Wallahi ba ajinka ba ce” “Da ace ni na sakawa kaina son ta da na cire shi cikin sauƙi ba tare da kanki kin sani ba, na yi iya ƙoƙarina na ganin cewar na gujewa soyayyarta amman sai na kasa, babu yadda za'ayi na sakawa kaina ƙaunarta Momi Allah ne ya saka min” Ya miƙe tsaye ya zuba hannayensa a ajihu. “Please Mom ki maida musu da gidansu, kuma karki sake yin wani abu da zai takurawa rayuwarsu, idan har baki tayani neman yafiyarsu ba to be kamata ki ƙara ɓata min suna a gurinsu ba” Yana kaiwa nan ya nufi ƙofar fita cikin yanayi marar daɗi, Hajiya ma miƙewa ta yi tsaye ta bishi da kallo har ya fice sannan ta ce “Wato revenge ɗin da zata ɗauka ta haɗa ni da ɗana ko? Uhmm Wallahi Nawwara kin deɓo ruwan dafa kanki, duk kika ce zaki shiga tsakanina da ɗana bake ba kaf ɗanginku sai na hana musu zama lafiya, kuma Wallahi ɗana ba zai taɓa aurenki ba ƴar matsiyata kawai” faɗa take tana huci tsabar jin zafin ɗanta ya kamu da son Nawwara. Ɗakin ta nufi tana da bala'i har su Zarah da Ikram suka fito ɗaga ɗakinsu jinyo muryarta tana matsifa. *** *** *** Around eight am kowa ya hallara a dinning ɗin cin abincin safe ban da Mustapha, hakan be damu Hajiya ba domin ta san halin da ɗanta yake ciki, sai kawai ta cigaba da jera kayan abincin tare da su Ikram da kuma Ma'u mai aikinta. Fitowar Alhaji ne yasa Zara dake ɗaki fitowa domin yin breakfast ɗin, ganin babu kowa a kujerar Mustapha yasa Alhaji ya kalli uwargidansa ya ce “Yau ma ba zai yi breakfast ɗin ba?” Ikram ta yi karaf ta ce “Ai daman sai tara yake karyawa” Hajiya kuma ta taɓe baki tana cigaba da haɗawa Mijinta tea ta ce “Ai ina ganin tsakanin jiya da yau in ban da ruwa babu abunda Mustapha ya ci, ko jiya be fita aiki ba sai sha biyu na rana be dawo gida ba sai da isha'i” Kallon rashin fahimta Alhaji ya yi mata yana ɗaukar tea da ta aje masa ya kurɓa “Saboda mai?” “Uhmm saboda yarinyar nan mana” Wani dogon tsaki Alhaji yaja ya kalli Ikram a fusace ya ce “Jeki kira min shi wannan ai iskancin banza ne” Da sauri Ikram ta tashi ta nufi ƙofar fita, bata ɗauki dogon lokaci ba sai gata ta dawo falon tare da Mustapha dake cikin shigar kayan bachi. “Good morning Dad” Ya faɗa murya can ƙasa-ƙasa kamar wanda baya son magana. “Seat” Alhaji ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar da ya yi masa ba, ba musu Musyapha yaja kujera ya zauna yana fuskarta Daddynsa, mahaifiyarsa taja kujerarta ta zauna tana kallon ɗanta a natse Alhaji ya fara magana ta yadda ɗan nasa zai fahimta. “Mustapha ka daina damunka kanka nayi imani har ga Allah baka da laifi akan wannan lamarin, saboda ba kai ka kasheta ba iyayenta ne silar mutuwarta. And a part from her sister ka aje shi a gafe domin ba tsararka ba ce, idan ma aure kake so ka nemo ko ƴar wani gidace ni zan aura maka ita amman ba dai wannan yarinyar ba” Sauke idonsa ya yi ya kalli tea ɗin da Ikram ta aje masa a gabansa sannan ya sake data kai ya kalli mahaifinsa ya ce “Dady ita kaɗai ce macce da nake so” “No Look Son yarinyar nan ba ƴar gidan mutunci ba ce sannan aurenta biyu fa kai kana sauranyinka ka ce zaka aureta, after that yaron dake hannunta yanzu ana zargin shege ne fa bashi da uba, wasu ma na cewa babu wani aure da tayi zaman banza ta yi abuja ta dawo da ciki sai wannan auren da ta yi na biyu, ba ƴar gidan tarbiya ba ce Mustapha ƙara ka auro ƴar mutunci kuma ƴar gidan mutunci” Mahaifiyarsa ya kalla domin yasan ita kaɗai ce zata iya faɗawa Daddynsa wannan maganar, kallon mahaifinsa ya sake yi “Amman ina fatar Momi ta faɗa maka ni na lalata ƙanwarta ko?” Alhaji ya yi saurin girgiza kai. “No no son ba kai ka ɓata ta ba, daman can yarinyar lalatacciya ce, mahaifinta ma ance sata ya yi da aka mashi aka masa shegen duka har ya mutu....” Zarah dake aikin tsire baki tayi karaf ta ce. “Wallahi sam yaran gidan nan basa da mutunci ko kaɗan” Tsawa Mustapha ya katsa mata. “Idan ana maganar tsakanin Uba da ɗa ki daina saka bakinki a ciki” Momi ma ta katsa masa tsawa. “Ta daina saka bakinta iya ba ƴar'uwarka ba ce? Wai mi yake damunka ne Mustapha?” “Nima ban sani ba, kawai ni dai abunda na sani zuciyata na son Nawwara” Ya amsa mata da cikakiyar gaskiyarsa, shi kansa a yanzu ba zai iya ayyana abunda yake damunsa ba, kawai dai yana samun kansa cikin wani kalar yanayi da be taɓa samun kansa a cikinsa ba. Alhaji ya buga tebur ɗin da ƙarfi “Ba zaka aureta ba Mustapha, ana nuna maka hanya kana ba haka ba, ka bar ganin kai kaɗai na haifa zan iya shafe labarinka a doron ƙasa matuƙar ka zaɓi yarinyar can ƴar nasara mutunci” Miƙewa ya yi tsaye ya nufi ƙofar fita ba tare da wata kalmar ta ƙara fitowa daga bakinsa ba. “Could you see this?” “Na gani, ni gani nake kamar ba banza suka barshi ba, dan ni ban taɓa ganin yarimyar da Mustapha ya zo ya ce min yana so ba duk wanda na gansu tare zai ce abokiyar aikinsa ce ko abokiyarsa, amman be taɓa buɗe baki ya ce min ga wacce yake so ba sai wannan zagalar, duk yabi ya canja saboda wata ƴar iskar yarinya, jiya ma haka ta zugoshi yazo ya rufeni da masifa wai na siye gidansu, ni kuma ban san na siye wani gida ba wata ƙila so take ya ɗauki maƙudan kuɗi ya ɗanka mata” “Bari ai zamu saka ƙafar wando ɗaya da shi” “Da shi kuma? Sai dai da su ai su suka susuta naka yaro, shi kaɗai fa Allah ya bamu idan ka saka ƙafar wando ɗaya da shi ai abun akan mu zai koma” Ƙwafa ya yi ya cigaba da shan tea ɗinsa yana ta huci. *** *** *** JIBRIL POV. Be bar kamfanin ba sai tara na dare, ko da ya isa gida jikinsa da mugun nauyi kamar wanda ya yi wani aiki, bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower ya lumshe ido yana sauraren yadda tsanyin ruwa ke ratsa jikinsa. ‘Nawwara will never ever ever forgive Jibril for what he did to her’ Shine abunda ke ta masa yawo a cikin kai, zuciyarsa na wani irin zafin, sai goma har da kwata sannan na bar bathroom ɗin cikin yanayi marar daɗi. Vest ya saka da ɗan guntun wando, be shafa mai ba amman ya shafa turare, sannan ya fito parlour ya haɗa ma kansa tea ya zauna saman cushion yana kallon hoton nawwara Tea ma sai ya gagara sha. Yana zaune gurin har shaɗayan dare ta buga be ko motsa daga inda yake ba. Siraj ne ya turo ƙofar falon ya shigo hannunsa riƙe da takardu masu yawa, ɗakin karatun Jibril ya nufa ya aje takardun sannan ya dawo ya zauna kusa da shi yana faɗin. “Gaskiya yau Jibril ka bani mamaki, wai su waye iyayen yarinyar nan ne da har zata wulaƙanta a gaban jama'a ka ƙyaleta?” Sai a yanxu ya gincira saman kujerar yana cigaba da kallon hoton Nawwara. “Maruƙar haka zai sa ta yafe min, zan jure har sai ta yarda da na yi nadama kuma na tuba” “Wannan ba revenge ba ne, it's an embarrassment, ko ma mi kayi mata baka cancanci ta yi maka wannan tuzarcin ba, su fa mata ba a ƙyalesu hakan ya bata damar cigaba ne, gaba ɗaya yau ak kamfanin nan kai aka wuni ana magana wannan ai tozarci ne” Murmushi Jibril ya yi ya kalli Siraj ya ce. “Data mareni a gaban mutane na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta airport, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a gaban iyayena, na ji yadda ta ji a lokacin da na mareta a bakin titi na jefar da ita na yi tafiyata, at least now na san yadda mutun yake ji idan aka disgashi gaban jama'a” Siraj ya juyo yana fuskarta shi da kyau ya ce. “Kana da banbanci da kowa Jibril be kamata ka auna kanka da sauran jama'a ba, weather you like or not abunda yarinyar nan ta yi maka bata kyauta ba” Miƙewa Jibril ya yi tsaye ya nufi window falon yana faɗin. “You're my new tight friend Siraj, bana son kana faɗar wata kalma marar daɗi a kan nawwara, saboda hakan zai sa na tsane ka ita kuma na ƙara ƙaunarta, zan iya jure ko wani kalar wulaƙanci daga Nawwara matuƙar hakan zai sa ta yafe min, soyayyata da ta rasa a can baya ita nake son nuna mata a yanzu, kulawar da na gagara bata a da, ita na ke son bata a yanzu. Na wulaƙanta yarinyar sosai Siraj irin wulaƙanci da ban taɓa tsamanin Allah zai jarrabeni da son kamar haka ba, a gaban idonta na ke shigowa da budurwa a gidanta kuma ta dafa mana abinci ta haɗa mana ruwan wanka, ta san fasadi muke aikatawa amman haka be taɓa damunta ba, ko da yana damunta bata taɓa nuna min ba. Idan ta dafa abinci sai ta kawo min tana jiran na yaba mata amman sai na kushe wani ko ci ba zan ba, idan ta yi kwalliya tana jiran na yaba mata ba zan kalleta ba, ban taɓa riƙa hannunta da nunan sha'awaba sai idan zan hukunta ko kuma na doketa, idan mahaifina ya tambayeta ko akwai wata matsalar sai ta ce masa babu komai muna zaune lafiya...” Hawaye ya zubo masa sai yasa gefen hannunsa ya shafe yana cigaba da kallon titi kasancewar window yana fuskantar titi ne. “Lokacin da na gano tana da ciki, sai na saka mata maganin bachi a lemu ta sha, da tayi bachi sai na cire mata tufafi na ɗauki hotonta na kai ayi editing aka haɗa da na wani, da gangan na sa aka ɗauko min mahaifinta aka zo da shi garin abuja na tarasu da mahaifina na ce cikin da ke jikinta ba nawa ba ne ga wanda ya yi mata shi nan, i'm very fool Siraj can you imagine na ɗauki hoton mamata na haɗa da hoton wani saboda kawai bana son ta kuma ban shirya haihu da ita ba a wannan lokacin...” Ya zuba hannayensa aljihu hawaye na ta masa zuba, sannan ya sauke ajiyar zuciya. “A gaban mahaifinta da mahaifina na nuna waɗancan hotunan kuma na ce na saketa saki uku, sai mahaifina ya ce min saki uku idan aka yi su a take a matsayin saki ɗaya suke dan haka na yi haƙuri na maida matana, jin wannan yasa nace na sake tsaki ɗaya tsaki biyu tsaki uku, a ranar Nawwara ta riƙe min hannaye tana roƙon na rufa nata asiri na karɓi cikin nan, wannan roƙon da ta yi min sai yasa mahaifina ya yarda cewar ba cikina ba ne. A ranar mahaifina ya tabbatar min da sai na yi nadamar abunda na yi mata, saboda yana ganin ta bi maza ne domin kawai na kasa bata kulawa, ashe da gaske zan yi nadama. Bayan na rabu da ita mace huɗu na aura suka kasa zama aure da ni, wasu basa mutunta ni kamar yadda take, wasu kuma su nuna min suma ƴaƴan manya ne ba zasu iya abu kaza da kaza ba, daga lokacin na fara kewar Nawwara, kuma duk wannan auren da nayi babu wacce ta taɓa samun ciki da ni, kuma ba dan bana haihuwaba ba dan ina da wata matsala ba sai dai isgilancin da na yi Allah ya jarrabe ni, sai bayan na yi aure na biyar ashe ita ba ɗana ba ne ban ganr haka ba sai da na auna jininsa, gudun afkawa cikin wata matsalar sai step mom ɗita ta aura min ƙanwarta, sai da tafiya ta tafi sai na gano kasheni take son yi ta ci gado tun da bana haihu ita kuma tana son haihu amman bata son fita ta bar ɗaular gidana, sai ta saka min guba a abinci shine ciwon da har yanzu yaƙi warkewa a jikina, bayan na rabu da ita na dawo na cewa mahaifina ina son naje gidansu Nawwara, sai ya ce min shi ba babu ruwansa kuma ba da yawun bakinsa ba, saboda na kunyatashi na tozarta shi kuma na ci amanarta bayan shi ne silar aurena da ita, daga ƙarshe ya ce be yafe min na taka ƙafata ƙofar gidansu Nawwara ba, tun daga lokacin sai tunaninta da halin damuwar da na saka ta ya riƙa damuna, wani lokacin na kan rufe kaina ni kaɗai a ɗaki ina kukana amman babu mai bani haƙuri saboda mahaifita bata raye. Komai nawa sai ya tsaya cak, idan naje asibiti bana iya komai sai tunani da damuwa, wannan ne ƴasa Abbah ya dawo da ni kamfaninsa na nan sokoto saboda na rage damuwa, na jidaɗi da Abbah ya yi min haka ko ba komai ni ma zan yi rayuwa garin da Nawwara ta taɓa rayuwa, lokacin da na zo na haɗu da kai, na saka nemanta sai ka ce min ta mutu kuma iyayenta ma sun mutu, daga lokacin na yafe farinciki da walwala a tare da ni.” Ya juyo ya kalli Siraj sannan ya ce “Nawwara ce kawai macce da ta samu ciki da ni ta hanyar halak, Nawwara ce kawai take kula da ni kamar mahaifiyar da ta haifeni, Nawwara ce kawai zuciyata ke ƙauna, ko a can baya ba ƙaunarta ne bana yi ba kawai dai ina ganin ta shigo rayuwata ne a lokacin da be kamata ta shigo ba. Dan haka karka sake faɗin wata mummunar kalma akan Nawwara, na zan iya tukararta kai tsaye ta yafe min ba, amman idan muna zama a guri ɗaya ita da kanta zata fahimci halin da nake ciki ta yafe min, i need to work with her, i need to be close to her” Yana kaiwa nan ya share hawayensa ya nufi Bedroom ɗinsa, ya bar Siraj a tsaye yana jinjina lamarin. *** *** *** Kukana ya yanke tun kan na iso gida, sai dai hakan be hana mahaifiyata fahimtar ina cikin damuwa ba, ga shi na dawo da wuri ban daɗe ba. “Lafiya kika dawo yanzu?” “Lafiya ƙalau kawai faɗa muka yi da wani na mareshi sai suka ce na dawo gida” “Faɗa kuma? Da namiji miya haɗa ku” “Na goge gurin ne sai yazo yana min masifa har da riƙa hannuna na ni kuma na mareshi” “Tau kin kyauta kin yi abun a yaba miki kowa ya yi miki ba dai dai ki riƙa hannu kina marensa kinji Allah ya miki albarka” Na san baƙar magana ta yi min wacce ke nuna bata jidaɗin abunda na yi ba. “Amman Inna ni ce nai gaskiyafa” “Idan kina da gaskiya sai ki ɗaga hannu ki mareshi wata ƙila ma ya girmeki, duk wani hali da ba naki ba Nawwara yanzu kin ɗauka kin ratawa kanki, wannan zabin zuciyar na Habiba ke aka saukewa shi? Ita tafi sai masifar ta dawo kanki, wannan ba halinki ba ne Nawwara, kuma ba tarbiyar gidan nan ba ce” “Yi haƙuri Inna na miki alƙwari ba zan sake ba” Na faɗa idona cike da ƙwalla, domin ni kaɗai na san halin da nake ciki, ita kanta da tasan wanda na mara da bata min wannan masifar ba. Ɗakinmu na wuce na ci kuka sai da na gode Allah sannan na fito. Bayan sallah magariba, Bilal ya kirani a waya ya sanar min yana waje, na ɓata lokaci kamin na fita saboda na san maganar da zai min ba zata wuce ta abunda ya faru yau ba, sallama na yi masa amman be amsa min ba sai ya jefo min tambaya. “Ance min kin kirashi da azzalumi, shi kuma ya baki haƙuri har ya yi iƙirarin kiranki da matarsa, shine Baban Noor ko Nawancy” Na gyaɗa masa kai “Shine” “Daman kin san nan kamfaninsa ne kike aiki?” “Ban sani ba sai yau” Wani dogon numfashi yaja ya sauke. “Na yi farinciki da ya gane kirkurensa, ko ba komai Noor zai san mahaifinsa na gaskiya” Na yi saurin girgiza masa kai idanuwa cike da ƙwalla. “Ba zai sani ba Bilal ba zan iya bashi Noor ba, be san zafin ɗana ba, be san yadda na yi na haifi ɗana ba, be san wahalar da na sha kamin da bayan na haifi ɗana ba, ko sau ɗaya ƴan'uwansa ba su taɓa biyo sawunna su duba lafiyar ɗana ba, Noor be cancanci Uba irin Jibril ba, Dan Allah dan girman Allah karka faɗa masa ina da ɗa zai iya raba ni da ɗana Bilal” “Ba zan faɗa masa ba, amman dole wata rana zai gano, lokaci yana zuwa Nawancy zaki koma ke da shi kamar ba ayi ba” Ya faɗa muryarsa na nuna tsantsar damuwar dake cikin ransa. “Ba zamu koma ba Bilal, babu wanda zuciyata take so take ganin ƙimarsa kamar kai, kai kaɗai ne mutun da zan tuna na yi murmushi, Wallahi kai kaɗai zuciyata take ƙaunara Bilal” “Ina jin tsoron faruwar wani abu Nawancy” “Babu wani abun da zai faru, sai idan ba son aurena kake ba, ba son ƙwarai kake min ba, daman can zaka biye abunda mutane suke cewa ka gujeni” “Ba zan taɓa gudunki ba Nawancy, ina ƙaunarki sosai” Ya faɗa yana ƙoƙarin kai hannu ya share min hawayena sai na yi saurin saka nawa hannun na share, sai kawai ya saka min dariya. “Na jidaɗin wannan abun ko ba komai kin nuna min yadda kika so na” Ni kuma sai na cire talakmena na gwaɗa masa a hannu har sai da ya yi ƙara. “Ka daina taɓa ni da wannan hannun” “Nima ba son raina yake taɓa ki ba, kawai dai shi ɗin ne ya damu sai ya taɓa ki, amman ranar da zai taɓa halalinsa zan ga bakin da ya isa ya hana shi” Na zaro ido ina mamakin kalaminsa, sai ya kannemin ido ɗaya yana murmushi. Mum yi firar da ta ɗebe min kewa fira irin ta masoya firar da ta gusar min da duk wani tunani da damuwa har sai da na dawo cikin gida. Bayan na yi sallah isha'i na ci abincin dare kaɗan saboda kar Inna ta gano abunda yake damuna. Dakimmu na dawo da zimmar bachi amman sai na kasa rayuwar da na yi a abaya ta dawo min... FLASH BACK....... _______________________________________ I can't wait na ji tarihin Nawwara zamanta da Jibril.. 💃 #RB #TEAM MUSTAPHA #TEAM JIBRIL #TEAM BILAL *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣8⃣ Khadija shine sunan da mahaifina ya saka min, sai ya yi min alkunya da Nawwara, duk da kasancewar ba ni ce ta farko ba, ƴaƴƴuna hudu maza duk basu tsayaba sai ni da nazo a ta biyar kuma mace.   Bayan ni sai da mahaifiyata ta shekara biyar sannan ta haifi Habiba, a lokacin Mahaifina yana ta faɗi tashin rayuwa na nema mana abunda zamu ci. Ba zan kira kaina da kyakkaywa ba, sai nasan ni ba mummuna ba ce, abunda kawai zan iya shaidar kaina da shi shine na ɗauko fari da kuma dogon hancin mahaifiyata kasancewarta fulani, gashin kan ba a magana na girata ma askewa nake balle kuma na gadon bayana dake ƙayatarda mai kallo. Siye da siyarwar na fatoci, Sana'ar iyaye da kakkanina ce sana'ar wacce mahaifina ya buɗe ido ya samu kansa a cikinta har muma muka zo muka tarar anayi, kowa ya tashi a gidan ana buɗa masa shago ko kuma a haɗashi da wanda zai riƙa masa ja gaba kan sana'ar har ya kafa tashi. Kusan zan iya cewa sana'ar bata karɓi mahaifinmu ba, tun lokacin da ya fara ba riba ba kuɗi, wani lokacin har kuɗin wani sai sun shiga ciki su ƙi fita, duk lokacin da mahaifinmu ya siyo fata da zimmar saidawa sai karaya ta sameshi wacce zata zama silar da ba zai iya maida kuɗin ba, yayyunsa da Yakumbo da kuma Hajiya Lamtana Allah ya jiƙanta sai suka ɗauki karan tsana suka ɗora ma Ramatu wato mahaifita, a ganinsu ita ce bata da ƙashin arziki, sukan ce wai can kamin ya aureta a lokacin da yake saurayinsa yana sa'arsa lafiya sai da ya aureta sannan komai yaso ya lalace. A lokacin ina ƙarama amman abun yana min zafi sosai saboda yana damun mahaifiya sosai, har na riƙa kallonsu a matsayin maƙiyanmu wanda har yau shine a zuciyata, domin a lokacin a gaban idonmu suna faɗa wai uwarmu mai farar ƙafa ce wanda hakan suke tunanin ba komai bane ko kuma mu bamu kula ba alhalin yana mana zafi sai dai bamu isa mu nuna ba kasancewar gidan taro ne, ko tari kayi sai anji, Babban gida irin gidan nan ne da kakanni suke siye sai iyaye da jikoki su taru a gidan kowa ya keɓe wani ɓangare nasa ya kafa nasa iyalin. Lokatuta da dama takan keɓe ita kaɗai ko kuma da mu tayi ta kuka tana roƙon Allah ya bawa mahaifina wani aikin duk da bashi da wani karantun zamani a wacan lokacin, muna haka wani maƙocinmu Malam Buba kuma abokin Baba da yake yawan zuwa Abuja ya faɗa ma Mahaifimu cewar wani attajirin mai kuɗi a garin Abuja yana neman mai masa gadi kuma ya ce baya buƙatar kowa sai bahaushe ɗan'uwansa, Malam Buba ya kasance yana masa gadin wani babban kamfanin siyer da kayan alatu ne dake can garin Abuja. Muna zaune gida ranar wata talata, bayan mun gama cin kwaɗon ƙanzo, sai Baba ya shigo da far'arsa yana labarta mana abunda Malam Buba ya faɗa masa, Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta, a nan suka yanke shawarar ba zasu sanar da Yakumbo da Hajiya ba saboda sunsan ba zasu bari yaje ba, sai suka haɗa kai da Malam Buba ya faɗa musu Babanmu zaije Abuja ya kai fatune saboda ana bukatarsu a can, sun yi na'am suka masa addu'ah da fatan nasara, sai Baba ya karɓi fatun bashi da sunan idan yaje can zai aiko da kuɗin. Ranar da zai tafi munyi kuka sosai ni da Inna har ma da wasu mutanen gidan saboda muna ganin kamar ba zai dawo ba, tafiya nisa kuma har garin Abuja garin da a wacan lokacin muke ɗaukarsa kamar wata ƙasar dabam. Bayan wata ɗaya da tafiyar mahaifinmu sai gashi ya dawo cikin shigar mutunci da kamala, sai dai ya ɗanyi rama kaɗan ya kuma yi haske, ya labarta mana komai yake muna nan cikin ranshi wannan tunanin ne ya hanashi ƙiba, har ma yake faɗa mana cewar mai gidansa ya ware masa wani ɓangare na gidansa ya bashi ya ce ya ɗauko iyalansa su dawo nan kuma ya zo mana da kuɗi mai yawa. Ba ƙaramin yaƙi akayi ba kamin Hajiya ta yarda ta barmu aka tafi da mu, a nan ma sai da ya yi mata wata ƙaryar cewa ya canja sana'a yanzu yana siye da saida takalma ne na fatu har ma ya ce mata hayan gida ya kama a ƙauyen Abuja acan zai zauna da mu ya cigaba da sana'arsa. Amaina huɗu a mota kamin mu sauka zaria, aka siya min abinci da ruwa na cika cikina ni da Habiba sannan muka cigaba da tafiyar, ko da muka shiga garin Abuja ina bachi, sai da motar ta tsaya sannan Inna ta tasheni muka koma can wani ɓangare na tashar, Baban mu ya ari wayar wani ya kira Alhaji ya sanar masa mun iso domin ba a shiga da wani abun haya a unguwar. Dare ya yi sosai har Baba ya yanke shawarar zuwa gurin abokinsa Malam Buba mu kwana a can sai ga ƴan komisho sun zo suna neman Malam Musa Kafinta, a nan suka haɗa mu da mutumen yanayin yadda Baba ya gaisa da shi sai ya tabbatar da cewar ya sanshi, ashe direban Alhajin ne. Ni da Inna duk da tsoro muka shiga motar saboda ganin Babbar motar kamar wannan wacce ni dai zan iya rantsuwa hannuna ma be taɓa kaiwa akanta, amman yau zan shigeta. Ina ta rabon ido har muka iso wata kyakkyawar unguwa. Idona be ƙara buɗewa har sai da muka iso cikin ƙaton gidan dake cike da ababen more rayuwa. Iyalan mutumen ne da Alhajin shi kansa suka fito suna tarbonmu, har yake bawa Baba haƙuri akan rashin ɗaukoshi da wuri wai yaje meeting ne kuma sai ya manta sai da ya dawo gida sannan ya tuna. Cikin Falonsu muka shigo sai suka saka mai aikinsu ta kwashi kayanmu ta kai BQ, mu kuma suka kawo mana abinci da abin sha. Cikin sati ɗaya muka sake da ƴan gidan kasancewarsu mutane da suka san darajar ɗan'adam tun daga Hajiyar gidan har yaranta, Ƴaƴanta maza biyu manya sannan mata uku ɗayar tana aure sauran biyu kuma a lokacin suna karatune, sai ƴar ƙaramar ƴarta Salima, wacce ta kasance ta shida a cikin yaranta takwas. Shaƙuwa sosai da sosai ta shiga tsakanina da Salima, har ta kai zuwa makaranta ne boko ne kawai yake rabamu, kasancewar ni bana zuwa bokon sai dai islamiya Alhaji Dahiru wato mahaifinta ya sakani Islamiyarsu. Duk ƙarshen wata Baba yake zuwa gida duba Hajiya, wani lokacin kuma sai dai ya yi mata aike a haka muka kwashe shakara ɗaya a gidan Tsohon ambasadan nigeria a ƙasar London, muka zama kamar ƴan gida, shaƙuwa sosai ke ƙara shiga tsakanina da Salima, da kuma Babban yayanta Jamal, shi yake koya min karatu duk da ba a sani makaranta ba a lokacin, Jamal mutum ne mai son jama'a da far'a, har ta kai idan be ganni ba sai ya aika an kirani, bayan ya gama koya min karatu sai ya ce na yi masa gatana, ba laifi a lokacin na iya zuba gatana har da wacce ba'a taɓa yi ba, haka zai zauna ya yi ta saureren shirme na wani lokacin har da Hajiyarsu. Shi ya fara yaba ƙwazo na sai ya yi ma mahaifinsu magana aka sakani a makarantarsu Salima, na kashe kuɗi sosai gurin samo transfer dake nuna daga wata makarantar na ke, sannan aka samu sa'a aka sakani aji ɗaya da Salima, Habiba kuma aka sakata wata maƙarantar wacce ƙannen Salima suke yi. Tare muke zuwa mu dawo, mu tafi islamiya tare, wasa-wasa sai na tattara kayana suka na koma ɗakinta da zama, a lokacin Inna na da cikin Sakina, komai a iri ɗaya muke da Salima bana da ƙawa sai ita itama bata da ƙawa sai ni, idan ba a ganta ba sai an tambayeni haka itama. Ta ɓangaren Jamal kuma soyayyace mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu duk a lokacin ban san miye so ba, na kan samu kaina da tunaninsa da kuma rashin jindaɗi a duk lokacin da baya gida. Muna daf da ƙare makarantar secondary school ni da Salima Hajiya ta samu labarin cewa Baba gadi yake a wani gida, babu irin bala'in da bata mushi ba cikin har da zance zata tsine masa gidan be dawo ba, wai Inna zata kaishi ta baro yana biye zancen mace. A dole tasa Baba ya tattara ya koma gida sai dai be zauna gidan ba sai ya kama haya kusa da su inda muke zaune har yanzu. Ni kuma a aka barni nan da sunan idan na gama zana jarabarwar za a maidani gida, bayan mun gama jarabarwa ta fito ta yi kyau, a lokacin ne ɗan wani mai kuɗi ya fito neman auren Salima, Alhaji Dahiru ya yi na'am ya sallama masa bisa sharaɗin zai jirata ta yi karatu na gaba, a lokacin shi kansa yaron be kammala karatunsa da yake ba. Bayan sati ɗaya da faruwar haka sai Ya Jamal ya fara min zancen aure, ni kuma ina ta tsoro saboda ina ganin kamar iyayensa ba zasu yarda ba, sai na nuna masa bana son shi, duk abunda muke a tsakaninmu ne iyayensa basu sani ba, har Salima ma tada zame min jinin jiki ban taɓa labarta mata ba, shi ma kuma be taɓa nunawa kowa ba. Bayan takadun mu sun fito sai Alhaji Dahiru wanda muke kira da Daddy ya turo mu gida ni da Salima, bayan ya cika mana bayan mota da abinci, a lokacin an haifi Sakina har ta soma wayo. Watan mu ɗaya muka garin Abuja saboda sabo sai zaman sokoto ya yi ma Salima wuya, ni kan ban so haka ba, sai dai babu yadda zan yi tun da mun zo tare dole mu koma tare, bayan mun koma sa sati ɗaya na sake dowa, Alhaji Dahiru ne yasa ka Ya Jamal ya rakoni har gida, sai dai wannan karon tafiyar Jirgi muka yi saboda Ya Jamal ya ce ba zai iya bin mota ba zuwa sokoto. Kwanansa ɗaya ya koma, ni kuma na zauna a nan har na tsawon wata uku a lokacin Mahaifina yana sana'ar siyar da itace a ƙofar gida, wata rana mu cinye ribar wata rana kuma Allah ya buɗo mana, haka muke ta faɗi tashin rayuwa ga masu neman aurena sai fitowa suke. Kwatsan Alhaji Dahiru ya kira ya ce a sanar min ya samo mana gurbin karatun lafiya a ƙasar burtaniya wato London, cikin sati ɗaya na shirya na koma Abuja, duk wani shirye-shirye ina can aka yi shi, bayan kamar wata ɗaya da ƴan ƙwanaki aka kammala komai, sai da na koma gida na yi bankwana da su Inna a lokacin ne Yakunbo ta so tanani zuwa saboda a ganinta kamar za a siyar da ni ne ko wani abu makamancin haka. Kamar na mafarki na fara karatu a City, University of London, a ƙasar da ban taɓa mafarkin zuwa ba, ƙasar da nake ji a labarai da kuma jaridu, burtaniya ƙasar turawa ce wacce bata da matsatsi akan addinin kowa a wacan lokacin, ba ko yaushe nake irin shigarsu ba wato shigar ƙananan kaya, nafi saka doguwar rigar atamfa ko abaya sai na samu ƙaramin ɗankwali ko hula na yi rolling kaina da shi. Ɗakin mu ɗaya da Salima da kuma wata tsohuwar ɗaliba makarantar wato Farida, wacce ƴar asalin hijar bauchi ce, cikin ƙanƙanen lokaci muka saba da Farida duk da kasancewar ba gurin karatun mu ɗaya ba. Ranar da muka fara zuwa lab wani babban likita muka tarar ɗan Nijeria dan asalin garin Kaduna, wato Doctor Jibril Bashir Makama, sai da ya fara gabatar mana da kansa sannan na soma bamu darasi tare da nuna mana wasu abubuwan a zahiri. Tun da idona suka sauka akansa sai ya tafi da imani da duk wani tunani da natsuwata, Jibril na da kyau da ba zaka iya tantanshi aa cikin ƴaƴan turawa ko larabawa, fatarsa fara ce fes ga shi da tsaye hancinsa ya sauko a ƙasan hancin an yanka masa madaidaicin baki, fuskarsa na ɗan faɗi, yana da manyan ido sai dai ba fararene ba, suna da surkin ja ƙaɗan, a gefen wuyansa tattoo ɗin taurara ne aka jera masa har cikin bayansa. Hankalina baya kan abunda yake ƙoyar da mu yana kansa, duk wani ƙyabtawar idonsa ƙirgawa nake, ina haɗɗace yadda bakinsa yake motsi da turansa da yake watsowa kamar baturen burtaniya, duk bayan daƙiƙu sai na lumshe ido saboda ƙamshin turarensa da ya cika lab ɗin. Murmushi nake masa ba tare da na san ina yi ba, har sai da ya katsa min tsawa. “You deaf...” A firgice na dawo hayyacina cike da kunya, ƙasa-ƙasa na ke kallon wata abokiyar karatuna Katherine Williams wace ke sonim dariya ita da wasu da dake kusa da ni. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 2⃣9⃣ Tun daga lokacin bana da tunani sai na shi, mafarkina ma nasa ne, duk wani abu da zai kusantar da ni gareshi na kanyi ƙoƙarin aikatashi, duk hanyar da zan ganshi ita na ke bi, duk da na lura da babu ruwansa da sha'anin kula wasu matan na daban hakan yasa na fara tunanin ko yana da mata ne. Salima kanta ta lura da yadda nake ta rawar jiki da son ayi zancesa, idan kuma wata macen ta kalleshi sai naji kamar naje na shaƙeta, a gurin Salima na ke samun labarinsa, kasancewar ta sanshi farin sani wai ɗan abokin Daddy ne, na yi mamakin da ban san shi ba duk tsawon zaman da na yi a gidan, duk da kasancewar na san Mahaifinsa amman ban taɓa kawowa zuciyata cewar shine ɗansa ba, sai dai duk wani mummunan hali nashi na wulaƙanci da rashin son mutane ta hanyar Farida na ke jinsa saboda ta rigamu zuwa makarantar duk wani abu da ya danganceshi ta san shi sosai. Salima ce take labarta min cewar Jibril shine ɗa na uku a gurin Mahaifinsa, kuma ɗa na farko a gurin mahaifiyarsa kasancewarta Amarya, yana da Step mother wacce ita ce ke da ƴaƴa da yawa kuma ita ta riƙashi a hannunta ya tashi, a gurin haihuwarsa Allah ya karɓi ran mahaifiyarsa wannan yasa mahaifinsa yake sonsa kuma yake tausayinsa domin ko da Jibril ya buɗe ido be san mahaifiyarsa ba sai step mother. Wata ranar da muka yi practicing akan thigh surgery, ya yaba min sosai kuma ya nuna jindaɗinsa akan yadda na maida hankali sosai, a ranar kasa bachi nayi saboda farinciki duk bayan minti ɗaya zuwa biyu uku fuskarsa na ke gani. Hakan yasa na ƙara maida hankali akan karatuna, da muka samu hutu sai muka soma shirin ziyarar gida kasancewar dkanmu munyi marmarin gida saboda haka muna samun hutun muka shirya muka dawo gida. Bayan mun dawo Abuja da kwana biyu na fara shirye-shiryen zuwa gida sokoto domin ganin iyayena, ranar da anje gurin kitso na dawo sai Daddy ya aiko yana kirana. A ɓangaransa na sameshi tare da Momi Aisha wato Hajiyarmu, da sallama na shiga bayan na gaishesu sai na maida kaina ƙasa ina wasa da carpet zuciyata cike da son jin dalilin kiran nawa, da farko na yi tunanin akan tafiyata ne sokoto ko kuma karatu. ‘Wata ƙila zai ce na haƙura har sai mun sake samun wani hutun ne ko kuma wani abun’ Haka na yi ta saƙe-saƙe na kamin na ji abunda Daddy yake faɗa. “Nawwara ko akwai wani wanda kike so? Ko kuma iyayenki suke son haɗa ki da shi?” Na yi mamakin da ya yi min wannan tambayar, a take Jamal ya faɗo min a raina na fara tunanin ko ya faɗawa Daddy wani abun ne, ko shiyasa tun da na zo ban ganshi ba. Cikin natsuwa da ladabi na ɗaga kai na kalleshi na ce “A'a babu Daddy” “Mashallah” Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciyar da ke nuna ya jidaɗin hakan, ya gyara zamansa yana fuskanta ta sannan ya ce “Alhaji Bashir Makama aminane a tare muka taso tare muke duk wani abu da ya shafi siyasa ko kasuwanci, sai dai shi be cika zama a garin Abuja ba shiyasa ba ki wayeshi sosai ba, yafi zama Kaduna wato mahaifarsa sai kuma garuruwan da yake gabatar da kasuwancinsa. Few days ago mun tattaunada shi akan ɗansa, yana son haɗa zuri'a da ni, ni kuma na duba a cikin ƴaƴana na ga babu wacce ta dace da shi sai ke, na yi hakan ne ba dan komai ba sai dan sama miki rayuwa mai kyau da nagarta, na san idan har kika auri ɗansa zaki ji daɗi sosai, saboda yaron yana da aiki ba irin ƴaƴan masu kuɗin nan ba ne shashashu kuma yana son yaronsa sosai, matsalar sa ɗaya baya son zaman da yake a waje kuma baya son yarinyar da yake tare da ita” Sosai na ji babu daɗi duk da bani da wanda zan iya fitar a lokacin na ce gashi shi nake so, amman hakan yasa ni jin babu daɗi, sai dai ban yarda na nuna masa ba domin na san ba zai min abunda zai cutar da ni ba. “Ai kin san Alhaji Bashir ko? Ɗan sa da yake waje yana aiki, ta hanyarsa ma Daddy mu ya samo muku gurbin karatun, ba zaki rasa sanin Jibril ba dan ance makarantar ku yake koyarwa, kuma a can zamu zauna sai kin gama karatun sannan ku dawo gida gaba ɗaya” Wannan karon Momy ce take maganar da ta kwantar min da hankali kuma ta saka ni farinciki, cikin nuna tsantsar ladabi na ɗago na kalli Daddy na ce “Ba zaka taɓa yi min abunda zai cutar da ni ba, ni kuma ba zan taɓa butulce maka ba, ko wuta ka kunna kace naje na shiga zan iya shiga na ƙone kaina balle aure, fatana Allaj yasa haka shine alheri” Ya ji daɗin farucina har ma yasa min albarka shi da Momy sannan na taso zuciyata cike da farinciki fal na dawo sashenmu, jikin har rawa yake na labartawa Salima abunda ake ciki, ita ma tayi farinciki sosai sai da nayi mata alƙawari karta faɗawa kowa kuma karta nunawa Daddy ina sonsa, ita kuma ta yi min alƙwarin haka. Bayan kwana ɗaya muka yi shirin zuwa sokoto ni da Salima wannan karon ma jirgi muka bi, Inna ta yi farinciki ganin sosai ni kaina ban san na canja ba sai a wannan lokacin na yi mamaki da Inna ta ƙara haihuwa ba tare da ƙara wasu shekaru biyar ba, kuma ace har anyi sunan Jamila ba a faɗa min ba. Dare muke rayawa ni da Salima muna labarta Inna da Baba rayuwar waje, Habiba kan ta shige cikina tare muke kwana a shinfiɗa ɗaya, a wannan lokacin ne na samu damar ziyarar abokaina da muka taso tare ciki wasu kuma da muka yi makarantar islamiya da boko a tare kamin tafiyata Abuja, cikin har da Zinatu da Baraka da kuma Jidda a lokacin duka muna unguwa ɗaya kamin su Zinatu su koma kware road gawon nama. Wasu basa yarda ina karatu a waje saboda suna ganin mahaifina ba kowa bane, kuma ba kowa ne mai arziki ba ne zai iya yi mana yadda Daddy ya yi mana. Inna ta labarta min yadda ake ta tsigumi a unguwarmu wai saboda kwaɗayin abun duniya zai siyar da mutuncin ƴarsa ya yarda naje na yi karatu bayan na secondry da aka ce na yi, a cewarsu wai yaƙi ya yi min aure jira yaƙe sai na gama karatun sai mai kuɗi ya zo ya aureni. Ni kaina maganar bata min daɗi ba kuma daman nasan za a samu haka, mutane ba zasu taimakeka idan kuma wani ya tallafawa rayuwarka sai koma gefe suna zagi da ganin hakan be dace ba. Sai da muka yi sati biyu a sokoto ana sauran kwana uku mu koma Abuja, Baba ya shigo ya same ni a ɗaki a lokacin ina ni kaɗai ya soma labarta min maganar da Daddy ya yi masa, ganin na ƙi cewa komai yasa ya kira Inna suka sakani a gaba akan ina son haka ko bana so domin shi ba zai yarda ayi min auren dole ba. Ni kuma na yi shiru ban amsa ba, hakan ne ya tabbatar masa da ina so ɗin kamar yadda Annabi ya faɗa shirun budurwa shine amsarta. “Amman yasan ke ba ƴar Alhaji ba ce ko? Saboda bana son ayi abu daga baya ya dawo na rashin daɗi” “Wallahi Baba ban sani ba, amman na san ba zai rasa faɗa masa ba” “Idan ma be faɗa masa ba ni zan buƙaci.ya faɗa masa, ƙara yasan ko wacece gudun kar sai anyi abu wani abu ya biyo daga baya, kuma ina son yasan mu talakawa ne iyayenki ba masu kuɗi ba, idan ya ji zai iya aurenki a haka walillahil hamdu idan kuma ya ce ƴar mai kuɗi yaƙe so sai mu jira Allah ya kawo miki na gari” “Hakan shi yafi Allah ya zaɓa miki alheri” Cewar Inna, ni dai ban ce komai ba, Allah kawai na ke roƙo ya zaɓa min abunda ya fi alheri. Bayan mun koma Abuja Momy take faɗa min wai cikin satin nan Jibril ɗin zai dawo dan haka na shirya tarbonsa a kowane lokaci, a lokacin hutunmu sauran sati uku ya ƙare. Shiru-shiru Jibril be zo ba, da sunan ganin matar da zai aura, hakan ya tabbatar min da cewar shi ma baya son auren wata ƙila shi ma an masa yadda aka min ne, wato haɗi. A week later Momi ta ce na shirya ni da Salima zamu je area 1 gurin abokin Daddy mu ƙarɓo saƙo, duk kalar tufafin da na saka sai Momy tace ba su yi ba naje na canja, kuma ni kawai take cewa ba da Salima ba, daga ƙarshe sai ta shigo ɗakinmu da kanta ta zaɓa min tufafin da zan saka kuma tasa na canja kwaliyar fuskata na feshe jikina da turare sannan ta kira direba ta ce ya kaimu. Na samu kaina da faɗuwar gaba sanin gidansu Jibril ne zamu je, sai dai ko da wasa ban kawowa raina cewar zan je mu gaisa ba ne, iya abunda na zata zamuje karɓo saƙo ne wata ƙila yana nan shiyasa take son na yi kwalliya ta yadda ko da ya ganni ba zai raina ni ba, amman abun mamaki bayan mun isa gidan mun gaisa da Hajiya Zainab Step mother ɗinsa sai aka nuna min wani falo wai na shiga zamu gaisa da Jibril. Na ji babu daɗi duk da kasancewar ina sonshi amman sai nake ganin kamar hakan be dace ba, shi da yake namiji ya kasa zuwa ya ganni sai ni da nake mace za a ce naje mu gaisaz, ba zan iya mata musu ba tunda ita a tunaninta Momy ta faɗa min haka tun gida. Da sallama na shiga muryata can ƙasa-ƙasa, amman be amsa min ba kuma be ɗago ya kalleni yana ta aikin dannar wayarsa fuskarsa a haɗe kamar baƙin hadari, his perfume make me feel comfortable har na zauna duk da be min izinin zaman ba. From head to toe ya kalleni sannan ya jinginar da kansa yana taɓe baki ya ce “Ke kuma haka tarbiyar gidanku take? Mata su suke zuwa fira da kansu? What kind of woman are you, kin cika arha da yawa gaskiya abun har cikin gida” “Ni ma ba a faɗa min da kai zan gana ba, saƙo aka ce min zan karɓa shiyasa yazo da ko mayafina baka isa ka gani a gidan nan ba” Ba bashi amsa kai tsaye, sai ya tashi zaune yana taɓe baki tare da cigaba da kallona. “Really? Kuma kika ci kwalliya haka? Kina tunanin zan ga kyauki ne ko? Mutumen da yake son ki zai yaba kyauki, amman ba ni ba dan ni kamar baƙin maciji nake ganin ki, ki taimaki rayuwata baiwar Allah ki ce baki so na, Wallahi zan biyaki ko nawa kike so” “Kai miyasa ba zaka taimaki rayuwata ka faɗawa mahaifinka cewar baka so na ba” Still bakinsa a mere ya miƙe tsaye yana zuba hannayensa a aljihu ya nufi window. “Ban san ko sau nawa zan faɗa masa ya yarda ba, Wallahi na faɗa na ƙara duk wata mace da ba Aisha ba bana son ta, amman mahaifina ya tsaya kai da fata akan sai na auro wata, ya neman min auren ƴar Alhaji Dahiru ne saboda yana yaba tarbiyar gidan kuma yana son zumuncinsu ya ƙara ƙulluwa, after that you're not his biological daughter, jin wannan yasa Mahaifina ya ɗaga min ƙafa, amman Alhaji Dahiru ya dage akan shi yana son ayi, har da cewar wai baya son auren ya ɗauki lokaci. Aurena da ke baiwar Allah ba alheri ba ne, domin ni dai har ga Allah bana son ki, lemme ask you some questions, shin zaki iya auren namijin da ya taɓa kusantar wata mace kamin ke? Zaki auren Namijin da ya taɓa sanin wata mace kamin ke? Zaki iya zama da namijin da zuciyarsa da gangar jikinsa duk na wata macen ne? Could you?” Na girgiza masa kai. “No i couldn't, ba zan iya auren namijin da ba be san ƙimar zaɓin iyayenshi ba” Ya matso kusa da ni cikin ɓacin rai, ya riƙa fuskata ya soma magana cikin murya mai amsa amo biyu. “how dare you, ke iyayenki sun san ƙimarki ne zasu barki hannun wani saboda ƙwadayin abun duniya, bayan baku haɗa komai da shi ba daga gadi! Wallahi duk kika aure kin saka rayuwarki cikin matsala sai kin ƙwammace kiɗa da karatu, duk wanda ya ce zai raba ni da Aisha ba zai sha da daɗi ba” Ya ciro wayarsa da ɗayan hannunsa ya nuna min hotonta da ke gaban wayarsa, yana matsar min fuska iya ƙarfinsa, a nan na fara kokuwar kuɓucewa amman na kasa. “Wannan matar ta fiye min ke sau dubu ɗari, dan haka karki yaudari zuciyarki kar kwaɗayin abun duniya yasa ki salwantar da rayuwarki ni da ke kamar RAI BIYU ne wuta da ruwa ba zamu taɓa haɗuwa ba, you bitch...!” Yana kaiwa nan ya wulgar da ni saman manyan cushion, ya yi ficewarsa cikin zafin rai. Ni kuma na tashi zaune da sauri ina taɓa bakina da nake tunanin yama fara jini saboda zogin da yake min. Na kusan minti goma a falon sannan na fito ina ta ƙoƙarin ɓoye abunda ke fuskata. Ban tararda Salima a falon ba, sai Hajiya Zainab da yaranta ƴan mata da ke ta min kallon uku saura kwata. “Direba zai maida ke gida, Salima ta koma tuni saboda an kira Daddy ku ba lafiya” Gabana ya faɗi sosai, miya samu Daddy ina ta tambayar kaina har na fito harabar gidan na nufi inda direba yake, na shiga bayan motar sai ga wata budurwa ta zo da jakunkuna ta saka min a motar sannan direba ya kama hanyar gida da ni, tun kamin mu isa gida na fara hawaye saboda tunanin abunda ya sami Daddy da kuma baƙin cikin abunda Jibril ya yi min. **RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣0⃣ Ganin Motar Anty Mairo da Zubaida wato manyan ƴaƴansa guda biyu a harabar gidan ya ƙara tayar min hankali, cike da fargabar abunda ya samu Daddy na fita motar na nufi cikin gidan. A falon Momy babu kowa sai ƴar aikinta Suwaiba, ban tsaya komai ba na nufi part ɗin Daddy. Mamaki ne ya maye gurbin tashin hankalina, sai ya zo akasin tunanina da kuma furuncin step mother ɗin Jibril cewar Daddy ba shi da lafiya. A sanyaye na shigo falon idona kan Daddy dake making call yana murmushi, ban ankaro da ban yi sallama ba sai da Anty Zubaida ta hankarar da ni ta hanyar amsa min da. “Wa'alaikissalam” Saurin share hawayen fuskata na yi na yi sallamar duk da kasancewar na kai tsakiyar falon. Sai duk suka haɗa baki gurin amsa min ciki har da Momy. Cike da mamaki na zauna kusa da Anty Zubaida ina cigaba da kallon Daddy. “Nawwara har kin dawo?” Cewar Momy. “Eh ko da na fito Salima ta dawo gida ko da na fito Hajiya tace min Salima ta wuce wai Daddy ba lafiya” “Ee na kirata na ce ta dawo gida jikin Daddynta ya tashi amman da sauƙi daman jinin ne ya hau amman ya sauka” Ajiyar zuciya na sauke na kalli Daddy da ya aje waya a kunnensa ina masa ya jikin. “Alhamdulillah, ya kika baro can ina fatar kina son shi?” Har na buɗe baki na yi magana sai Momy ta yi karaf ta karɓe. “Kana maganar tana son shi Alhaji wace mace ce zata kalli Jibril ta ce bata son shi, ai Hajiya ta kirani ta faɗa min sun fahimcin junansu sosai kuma shima ya yaba da ita sosai” Ƙasa na yi da kaina saboda bana son ƙaryatata ko kuma na kunyata ta a gaban ƴaƴanta akan wannan zancen da ba haka yake ba. “Maa Sha Allah, haka muke so Allah ya tabbatar da alheri a ciki, mahaufinsa ma ya faɗa min yana son a ɗaura masu aure kamin ta koma makaranta albashi idan ta kammala sai ayi bikinsu” Jin wannan maganar ta Daddy yasa idanuwa cika da ƙwalla. Anty Zubaida da Anty Mairo suka shiga tsokanata har ma da Salima, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na tashi da gudu na bar falon. Ɗakinmu ma dawo na zauna bakin gado ina ta kuka, wata zuciyar na raya min na kira Baba na faɗa masa wata na cewa a'a, tabbas a lokacin ina son Jibril amman rashin aurensa shi zai fi min alheri tun da har ya nuna min akwai wacce yake so.   Ina ta tunanin mafita sai ga Momy ta shigo ɗakin tare da Salima tana faɗin. “Kun saka min ƴa kuka bari na rarrashi abata” Tana zaunawa kusa da ni sai ta kore Salima daga ɗakin da sunan zata rarrasheni, Salima na fita sai ta canja fuska ta kalleni “Iyakar halacci Nawwara mun miki ke da iyayenki, ashe ko ba mu cancanci komai ba sai kyakkawan sakamako, kin dai san Alhaji ba zai miki zaɓin da zai cutar da ke ba, kuma wannan auren da kike gani idan har kika aureshi ke da danginku duk kun warke, ƙin yi wannan auren zai ɓata abotar Daddynku da shi na tsawon  shekaru ashirin, idan kuma kika yarda kika aureshi tam kamar kin zuba babban jari ne a dukiyar gidan nan da kuma ta gidanku, domin mahaiɗinsa na cikin masu kuɗin da ake ƙirgawa da su a africa ba ma Nigeria kaɗai ba” Na ɗaga kai na kalleta cikin muryar kuka na ce “Amman Momy baya so na yana da wacce yake so, kuma ya faɗa min matuƙar na yarda na aureshi sai na yi nadama” “Ai nasan baya son ki, daman taya za'ayi Namiji kamar Jibril ya so mace irin ki? Yaron da yake ganin ƴaƴan turawa da larabawa, kuma ɗan da magana kawai zai yi ma kuɗi su faɗo ƙasa sai kalli ƴar talaka irinki ya ce yana sonta? Ke ni fa Salima na so a bashi amman Alhaji yaƙi wai wani ya riga ya bada ita ba zai ce ya fasa ba saboda wannan, amman idan kika yi haƙuri da sannu zai fara sonki har ya kyautata miki, ke ko be so ki dole zai kyautata miki domin su masu kuɗi matuƙar suna auren mace dole ne su kyautata mata domin dukiya bata musu zafi. Nawwara karki yarda ki faɗa ko ki nunawa Alhaji cewar baki son zaɓin da ya yi miki domin hakan zai iyasa zuciyarsa ta buga ya mutu gaba ɗaya, dan Allah ki yi min alƙawari zaki auri Jibril albashi idan daga baya kika ga zaki fito sai ki ce ya sakeki, kuma kin ga waje ma zaku zauna kina karatunki shi yana sha'aninsa” Ta ƙarasa tana riƙe hannuna cike da magiya. Kai kawai na iya ɗaga mata alamar na amince ba dan raina ya so ba, har ga Allah ni kaɗaina ina ganin kamar idan ban auri zaɓin Daddy ba ban masa halacci ba. Bayan fitarta Salima ta shigo tana zolayana, yadda ta ga ina kuka ya tsorata ta har ta soma tambayar ko wani abun ne ni kuma na amsa mata da ba komai. A haka na jure na kauda kaina daga duk wani abu da zai nuna bana son auren saboda kar ran Daddy ya ɓace, su kuma sai hidimar ɗaurin auren suke har ana daf da ɗaura aure Baba be daina min magana akan idan bana sonsa na faɗa ba, amman na ƙi na faɗa, ni dai kawai na ɗaukarwa kaina alƙawarin zan jure ko ma minene saboda na zama ƴar halak a gurin Daddy da Momy. Ana cikin haka ne Ya Jamil ya samu transfer gurin aiki zuwa Jos, ni kaina na jidaɗin haka nasan idan ya yi nisa da ni zan fi samun sakewa. Sai da ana sauran kwana biyu ɗauren auren Jibril be taɓa kirana ko a waya ba, kuma be je ya gaishe da Baba ba, sai dai Mahaifinsa ya tafi tare da muƙƙarabbansa suka gaishe da Baba, komai a ɗaurin auren a nan Abuja aka yi saboda haka sai ranar da aka ɗaura min aure sannan mahaifina ya ga fuskar mijin ƴarsa kasancewar ya samu halarta tare da wasu ƴan'uwansa. Na ji ni daban a cikin wani yanayi marar misaltuwa a wannan ranar, bana farinciki kuma bana baƙinciki ni dai kuka kawai na ke kukan da ban san dalilinsa ba, ganin haka yasa Momy ta kaini ɗaki ta ja min kunne akan na daina kukan kar mutane su zargi wani abu, haka na wanke fuskata na keɓe kaina a ɗaki har sai da ka ce na fito ga Baba can zamu gaisa. Babu wata gaisuwa da na yi da dashi sai ta kuka kuka na yi sosai har sai da shi ma na saka shi kuka, ya yi min nasiha sosai akan rayuwa da kuma zamantakewar aure, ya faɗa min yanzu na tashi daga ikonsa na koma ikon wani, hakan yasa na ji ni cikin wani babban ɗaki mai nauyi. Washe gari ma da zai koma sai da ya kirani shi da ƴan uwansa suka zagaye ni suna min huɗuba mai ratsa jiki. Kwana biyu da ɗaura min aure aka kwantar da ni a babbar asibitin Abuja saboda rashin lafiyar da ya taso min, a wannan ranar ce Jibril ya hau jirgi ya bar ƙasar nan, har na yi jinyar na gama be taɓa kirana ba sai dai mahaifinsa da wasu Sisters na sa sun zo duba ni da kuma step mother ɗinsa, Mahaifinsa ne ya fi nuna min kulawa da damuwa, su kan kamar daman sun zo ne by force. Bayan an sallameni da kwana biyu Salima ta fara shirin zuwa makaranta, ni kuma Daddy ya hana ni da sunan wai ba zan koma ba sai na ƙara jin sauƙi, ni kuma ban musa musu ba na amince, ina ji ina gani Salima ta koma makaranta ni ina nan. Yana lura da yanayi na sosai, har ta kai wata rana ya kirani a ɗakinsa ya tambayeni ko dai bana son auren ne, sai an kasa amsa masa, ya yi min nasiha akan haƙuri da halin Jibril wai daman yasan za a samu haka saboda baya son auren kwata-kwata babu zancen aure a gabansa, wannan yarinyar ce kawai yake kulawa ita kuma ba ƴar mutunci ba ce zaman kanta take wannan dalilin ya saka mahaifinsa ya ƙi yarda ya aureta, a ranar yake labarta min cewar Jibril ne ya hana na koma makaranta wai ya ce be bada izinin na koma makaranta ba. Ranar na yi kuka sosai har sai dai na raina kaina, mutumen da ba zai iya kirana ya tambayi tafiyata ba shi ne zai ce bada umarnin kar a barni na koma karanta kuma a ƙyaleshi saboda kawai yana taƙama da kuɗi. A haka na kwashe wata shida a ban koma makaranta ba, idan kuma nunawa Momy ina son anje gida gurinsu Inna sai ta ce min ba haka ba, wai ba zata bari na tafi bada izinin mijina ba. Tun daga ranar da aka ɗaura min aure da Jibril duk wata sai Alhaji Bashir Makama ya aikowa da Momy kuɗi ya ce a bani amman bata taɓa bani ko naira ba, bata ma taɓa faɗa min ko nawa ba ne tana dai faɗan min ya aiko saboda kawai na yi masa godiya. Tun da Jibril yasa ƙafarsa ya bar ƙasar nan be sake waigo Nigeria ba, kuma be taɓa ɗaukar waya ya kirani ba, wani daga familynsa be taɓa zuwa da sunan ganina ko duba lafiyata ba. Da wannan baƙinciki na ke kwana na ke tashi ban taɓa nunawa kowa ba, sai dai hakan be hana Daddy damuwa ba, wata rana bayan na gama haɗa abun karyawa mun sai ya aiko yana kirana, ko da na shiga sai na samu Momy tare da shi, guri na samu na zauna na natsu ina ta sauraren abunda yake faɗa min. “Na gaji da wannan halin na Jibril, ba zai yiyu ya ce ba zaki koma makaranta ba, kuma baki tare ɗakinki ba, tun da ya tafi be ma kira ya tambayi lafiyarki ba, dan haka na faɗawa mahaifinsa idan ba zasu iya tanƙwara ɗan su akan abunda suke so ba, ni ba zan cutar da ƴata ba, na faɗawa mahaifinsa idan har yana ganin rabuwa da ke shine maslaha tam mu muna maraba, kuma ina fatar wannan hukuncin ya yi miki” Kamin na ce wani abu sai Momy ta yi karaf ta ce. “Haba Alhaji yaran zamani ai sai an yi haƙuri, karka yi maganar raba auren su ko shekaran jiya na tambayeta ta faɗa min ita tana son mijinta, kawai ka yi ta musu addu'ah” Kallo ɗaya na yi mata na ɗauke, wata ƙila tana min haka ne saboda ni ba ƴar ta ba ce, Daddy kan tuni ya gama gamsuwa da bayaninta, jiki a sanyaye na taso na fito daga part ɗin Daddy. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣1⃣ A nawa tunani Momy tayi min haka ne tun farko saboda kar na auri ɗanta, yanzu kuma bata son a kashe auren ne saboda dukiyar gidansu Jibril tasan duk wulaƙancin da zai min ni ba ƴarta ba ce saboda haka wannan ba zai taɓa damunta ba, babu wanda zai fi jin zafi jin zafin ɗa kamar uwar da ta haifeshi, ni kaina da Mahaifana ne ce zan iya fahimtar da su kuma su fahimta, amman wannan duk abunda zan yi sai dai su kalleshi a a matsayin butulci. Duk da maganar da Daddy ya ce yi ya sai da aka kwashe wata ɗaya har da kwanaki rana ɗaya Momy ta kirani wai na je na shirya yau Jibril zai zo ganina, gabana ya faɗi sosai har na ji ina ma ba zai zo ba har abada domin na san zuwan nasa ba alheri ba ne. Wanka na sake na saka wasu tufafin kwaliya kan ban yi ba, mai ma dan ya zamin ne jikine yasa na shafa, daman ta saka mai aikinmu ta shirya masa abinci da lemu haɗin gida. Haka na zauna tun sha biyu na rana har magariba be zo ba kuma be kira ba, misalin goma sha na dare Momy ta shigo ɗakina wai na taso gashi can ya zo, Ba musu na tashi na cire kayan bachi dake jikina na ɗauki atamfa na saka da mayafi na saka takalmi na fito jikina a sanyaye na nufi part ɗin baƙi. Tun a bakin ƙofar falon ƙamshin turarensa ya daki hancina hakan yasa gabana faɗuwa, da sallama na shiga falon amman be amsa min ba sai dai idonsa na kaina har na zauna a kujera na soma miƙo masa gaisuwa a kufile, nan ma be amsa ba, sai wani shan ƙamshin yake ya tsare fuskata da kallo kamar mai neman munina. “Saboda ke Daddyna yasa na dawo garin nan, saboda ke ya cilasta min dawo wa da aiki a nigeria gaba daya, ke dan Allah ba ki jin kunyar yadda ake ta turaki gurin namiji kamar ni?” Ɗagowa na yi na kalleshi kallon mamaki da takaici ina ma zai san abunda ke zuciyata da ya taimakamin ya rabu da ni, akwai tsantsan tsoro da fargaba a tare da ni a wacan lokacin shine abunda yake ta cutar da ni sai kuma zurfin ciki da ya zame min hali. “Zuwanka da rashin zuwanka duka ɗaya ne a gurina, ni dai ina neman izininka zan koma makaranta” Be ci komai daga abunda Momy tasa aka kawo masa ba, sai ya tashi tsaye ya nufo inda nake ya zauna kusa da ni har jikinsa na shafar nawa ya matso da fuskarsa kusa da tawa ta yadda ni kaɗai zan iya jin abunda zai fito bakinsa sannan ya kalleni ya na ƙara haɗe fuska ya ce. “Ba aure kika zaɓa ba? Tam zaman aure zaki yi babu ke babu karatu har a bada, ai baki san waye Jibril ba kina da butaƙar sanin wanene tuƙunan” Yana kaiwa nan ya tashi tsaye na saka hannunsa aljihu ya ciro kuɗi ya watsa min. “Ga tsiyarki nan” Ni kuma na miƙe tsaye ina kallonsa na ce “Tsiyarka dai, tsiyar da ta saka baka ganin kowa da mutunci, na ji ni ƴar talaka ce kuma ni talaka ce amman haka ba zai baka damar ka yi min duk kalar wulaƙancin da ka ga dama ba, kuɗi kawai kake da shi Jibril ni kuma na ɗara ka da tarbiya da biyayya” Murmushin gefen fuska ya yi ya taɓe baki. “Fine, zamu gani” Daga haka ya fice, ni kuma na koma cikin gida ko inda kuɗin suke ban kalla ba, zuciyata cike da ƙuna. Tun daga wannan lokacin be kuma sake zuwaba sai da aka sake yin wata ɗaya sannan ya kira Momy a waya yana tambayar lafiyata shi ma kuma na san cilasta masa aka yi, bayan ya tambayi Momy aka kawo min wayar sai ya kashe ba tare da ya ce da ni komai ba, a ranar n samu Momy na yi mata bayani akan bana son Jibril kuma bana son zaman aure da shi sai ta muna min na yi haƙuri komai zai wuce da zarar na tare a gidansa, ganin bata goya min bayan rabuwa da shi ba yasa na samu Daddyda kaina na kuka masa halin Jibril da abunda na ke hangowa a zamantakewar auren da zamu yi, amman sai ya bani haƙuri saboda a tunaninsa saboda na daɗe a gidana ne yasa nake wannan tunanin shi ma sai ya kasa fahimta ta, wannan ƙorafin da na kaima yasa ya kira mahaifin Jibril ya yi masa magana akan tarewar mu. A cikin watan nan aka yi kawo lefena kayan masu kyau da tsada, bayan sati ɗaya aka yi walimarta Daddy ya aika da ƙaramar mota aka ɗauko Mama da wasu daga ƴan'uwanta da kuma ƴan'uwan Baba. Ranar da akayi walimar aka kaini gidansa bayan anyi min huɗuba sosai ciki har da Mama da take ta kukan rabuwa da ni, ni kaina ba zan iya misalta irin kuka da na yi a wannan ranar ba. Tun tara na dare aka kaini gidansa amman abokansa basu shigo da shi ba sai ƙarfe goma sha biyu, su kansu kamar sun sam baya son auren suka mana addu'a suka fice tare da wasu ƙawayena. Misalin ƙarfe ɗaya na dare ya bar gidan, ban saka shi a ido ba har garin Allah ya waye, haka na kwana na wuni be shigo gidan ba har sai da aka kwana huɗu tsoro duk ya kamani saboda ƙaton gida ne gashi ni kaɗai ke ciki sai ƴan aiki da safe ne kawai ake aiko mana da abinci daga gidan Momy, yau ma da yake rana da huɗu ne ba a kawo ba ni na girka da kaina. Sai a ranar na biyar ya shigo shi ma kuma tare da budurwa Aisha, a gidan suka wuni suka kwana idan yana buƙatar wani abun ko kuma tana buƙata sai ya aiko min da saƙo a waya na tashi na yi musu, ni dai na yi ma kaina alƙwarin ba zan taɓa nuna masa ina jin zafin abunda yake ba, ba kuma zan taɓa saɓa umarnin iyayena na cewar na yi duk abunda ya saka ni. Ranar da na gaji da zama gida na fita maƙota, gidan wata matar na shiga wacce gidanta ke kusa da nawa sosai, ba laifi matar tana da son mutane da far'a Cikin ƙanƙanen lokaci muka sabu har ta kai gidan naje gidanta sai dare zan dawo shi ma kuma idan mijinta ya dawo, ita da kanta ta fara fahimtar irin zaman da nake da miji har ta tambaye ni na labarta mata kaɗan sai ta bani shawarwari akan na daina biye masa kuma na nuna wayeta sosai saboda shi yana shiga ƙasashen turawa ne dole idonsa zai buɗe da yawa. Gaskiya Ummi Faisak na da kirki na koyi abubuwa da dama a gunta ciki har da girki da kuma iya kwalliya, sai dai ban taɓa gwada ko ɗaya ba saboda na san irin mijin da na ke aure. Wata rana ina gidanta har dare sai gashi ya kira ni na ce masa ina maƙota yanzu zan so, ko da na fito sai na same shi bakin titi yana jiran ƙarasowata shi da wani abokinsa, ina isowa ya wanke min fuska da mari da har sai da na ga wasu ƙananan taurari, har abokinsa ya yi ƙoƙarin riƙeni saboda tangal-tangal da na yi zan faɗi, abun mamaki sai ya fara faɗa da abokinsa kamar zai cinye sa wai taya zai yi ƙoƙarin riƙa masa mata ai ko baya so na yasan zafina na matarsa kar an ya sake masa haka. A ranar na wuni da zugin marin shi kuma ya wuni yana ta mitar fitar da na yi, hakan yasa ya kulle kitchen kuma ya karɓe wayar da ke hannuna, wai naje gurin matar da nake zuwa ta bani abinci. Daga lokacin kullum da yunwa na ke wuni na kwana sai ya ga dama zai dauko wani abun ya bani jiki na rawa na karɓa na cinye, sai na koma abar tausayi, da na masa laifi kaɗan sai ya dakeni kamar wata ƴarsa, yana yawan shigowa da Aisha ta kwana a gidan ko ta wuni yasa na dafa musu abinci na kai musu ruwan wanka idan sun gama sai naje na ɗauke kwanukan, sai dai duk da haka ko da wasa be taɓa sakewa Aisha fuskar da zata rainani ba baya bari ta sakani aiki ko ta faɗa min wata maganar marar kyau idan ma an wulaƙanta a gidan to shi ne kawai yake da wannan damar. Wata rana ina zaune falo cikina na kukan yunwa, shi kuma yana ɗaki sai gashi ya fito ya jefo min wayata wai zan yi waya da Mama, sannan ya juya ya fice daga falon. “Babanki ba lafiya Nawwara, kuma bamu da komai, shine na ce idan da wani abu a hannunki ki aiko mana dan Allah, ko abinci sai mu siya” Shine abunda Mama ta roƙa ni kuma na ce mata zan aiko mata, bayan na kashe wayar na soma raira kukan da ban san ta inda yake fito min ba, ina haka abokinsa ya shigo hakan ba ƙaramin ɓata ran Jibril ya yi ba saboda ƙananan kayana ne jikina kuma abokin nasa ya ganni, ya yi min masifa sosai har da dukana ya yi akan haka. Muna cikin wannan halin Daddy ya yi rashin lafiya ya rasu, sai komai ya koma min sabo domin ganin Babu Daddy ya bawa Jibril damar azantar da ni da kalar azabar da yake so, sai dai bayan rasuwar Daddy sai Mahaifinsa ya kira ta wayarsa ya riƙa tambayata ko da wani abun ni dai ban taɓa faɗa masa ba. lokacin da Ya Jamal zai koma Jos sai ya biyo inda na ke dan mu gaisa, kamar ƙaddara sai ga Jibril ya dawo a ranar na sha duka wai akan me zan shigo masa gida, ya yi faɗa da Ya Jamal sosai har Ya Jamal yake masa faɗa akan yadda ya maidani kamar wata tsohuwa saboda wahala. Na sha fama a gidan Jibril ga shi baya son Sallah akan lokaci idan kuma na tasheshi sai ya yi ta masifa da ni, wata rana sai kamo tashar musulunci dake cikin receiver wa'azi wani babban malami yake akan irin azabar da ake ma masu wasa da sallah da kuma halin da suke shiga tun nan duniya, da gangan na cika murya dan yaji ashe kuwa saƙon ya isa dan tun daga wannan lokacin be sake wasa da sallah ba, wani lokacin da asuba har tashi na ke na tarar da ya riga ni tashi. Abun da na lura da shi Jibril yana da rayuwar turawa saboda zama da ya yi a can tun yana da ƙurciya har girma, gaba ɗaya rayuwarsa ta turawace, sai dai a wannan lokacin Jibril ba ya cin goro ma balle taba, rashin ilmin addinin islamiya ne yake ta cutar da shi, idan ina karatun ƙur'ane ya kan natsu yana saurarena musamman da asuba, akwai ranar da ya taɓa tambayata wai waya koya min karatu manyan surori haka na ce makarantar islamiya, daga ranar kuma be ƙara tambaya ba, ni kuma na maida tashar wa'azi ta zamo abar saurarena kullum, sai dai hakan be hana shi zalunta ta ba, be kuma hana shi yin fasiƙanci da Aisha ba, be kuma sanya shi ciyar da ni ba, ni dai iya abunda zan iya shidunsa da shi shine kishi, Jibril yana kishina sosai dan ko abokansa baya bari su gan ni, idan kuma wani ya yi magana da ni ko ya nuna kulawarsa akaina ranar zai wuni yana masifa kamar ya cinye kansa. Haka na bi na lalace ba ƙarfin yau bare na gobe, wata rana mahaifinsa ya aiko da mota aka ɗauko ni aka kaini gidansa, muka gaisa ya ɗauki wayarsa ya kira Jibril yana zuwa ya fara masa akan yadda ya ga na lalace sai Jibril ya yi tunanin ko na faɗa masa wani abun ne, bayan ya sallame ni da kuɗi mai yawa muka fito ni da Jibril na shiga motarsa muka kama hanyar gida. Sai da ya tabbatar na yi nisa da gida sannan ya faka motarsa ya fisgoni da ƙarfi ya jefar a gefen titi ya koma cikin motar ya yi tafiyarsa ya bar ni a gurin. Haka na zauna a gurin har aka kira magariba sai da wani mutun ya zo zai wuce ya tsaya ya tambayeni na nemi ya taimaka min ya taimaka ya ɗauko ni a motarsa ya kawoni gida, a ranar sai da Jibril ya mareni kuma ya yi min duka mai kyau. Washe gari sai ga Momy ta zo gidan ta karɓu kuɗin da Daddynsa ya bani, ni dai na roƙeta akan ta raba biyu ta aikawa Baba rabi duk da nasan ba zata yi ba. Jibril ya kan kirani da ko wane irin suna, idan na yi masa wani abu ba dai'dai ba sai ya ce min annoba ko baƙin maciji, yana yawan faɗar cewar ya fi son mutuwarsa da ni. Tun da ya aureni be taɓa bari naje gida ganin Baba ba, gidan momy kawai na yake kaini shi na kuma da dare yake kaini bayan ƴan mintuna ya ce na taso mu dawo gida. Ranar da zamuje raka daddynsa zuwa airport ya mareni a bainar jama'a saboda kawai na zubar da ice cream ba da gangan ba, aiko ranar ya sha faɗa a gurin mahaifinsa har sai da ya raina kansa. Bayan mun dawo gida ya wuce ɗakina na yi kuka har na gode Allah, daga nan bachi ya yi gaba da ni ina cikin bachin na soma jin ana shafani, hakan yasa na farka a firgice ina ihu, sai ya ji haushin ihun da na yi ya mare ni ya riƙa ya jefar ƙasa har sai da kaina ya bugu da madubin gadon, sai kuma ya taso ya doso inda na ke gadan-gadan ya dake fiskgata ya jefa saman gadon. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣2⃣ A ranar Jibril ya maidani cikankiyar mace, da safe ni na taimakawa kaina na shiga banɗaki da kaina na haɗa ruwa na yi wanka sannan na ɗora da alwala na fito a wahalce na yi sallah. Da safe be shigo ya tambayi ya na tashi ba duk da yasan halin da ya barni, ban fito daga ɗakin ba sai tara da rabi na safe kai tsaye na nufi kitchen sai na samu ya aje min makaroni da mai da tumatir da sauran kayan da zan sanrafa na dafa makaroni ɗin, cike da tausayin kaina na dafa makaronin ɗin ne na dawo ɗaki ina ta aikin kuka. Haka nake wuni na kwana babu ruwan Jibril da ni a gidan, tun daga ranar kuma be saki kuni da sunan zamantakewar aure ba, idan baya nan gidan Ummu Faisak na ke zuwa na zauna musha fira ta haka nake samu na cika cikina da abincin gidanta, ban taɓa labarta mata irin yadda Jibril yake azabtar da ni ba, sai dai tasan irin zaman da nake a gidan ko da yaushe tana ƙoƙarin koya min abubuwan da zan yi na burge Jibril ko kuma na janyo hankalinsa akaina. Ranar wata lahadi yana zaune gida na same shi a garden inda yake zaune yana hutuwa na risina har ƙasa na roƙoshi akan ya taimaka ya sake ni, amman ya ƙi har ma ya soma iƙirarin shi yanzu ya fara zama da ni, sai dai ya taimaka min ya ba ni makullin kitchen, daga ranar kullum abinci kala uku na ke girkawa wani lokacin ya ci wani lokacin kuma ko kallonsa ba ya yi. Yana zaune falo shi da abokinsa ni kuma na nufi kitchen saboda miyar da na ɗora karta ƙone, ina nufar kitchen ina jin yadda yake faɗawa abokinsa wai Aisha tana da ciki and he's so happy and excited akan cikin da aka samu babu aure, ina kitchen ɗin na tarar da ni ya shaƙe ni yana tambayar ina Hijabina taya zan fito haka babu mayafi a gaban abokinsa, da kansa yaje ɗakina ya ɗauko min Hijab na saka sannan na wuce ta gaban abokinsa, har abokin yana zolayarsa wai shi yana ganin matan wasu amman shi ba a ganin nasa. Ma samu sasauci sosai daga lokacin da ya bani makullin kitchen ɗin saboda kullum zan girka na ci, sai dai wata rana sai na gama girkin na ji bana so ko kuma na ji wannan na ke so bana son wannan abu a kaɗan sai amai, nan da nan zazzaɓi ya rufeni haka na kwashe kwana uku ina fama da rashin lafiya kamar zan mutu amman ko da rana ɗaya Jibril be taɓa shigowa ya duba lafiya na ke ba. Ranar da na samu sa'ida na ɗaure na fito falo saboda na gaji da zaman ɗaki, ranar sai ya shigo ya sameni falo yadda ya ga na rame shi kansa ya bashi tsoro, da kanshi yana zo yana tambayar me ke damuna cikin nuna halin ko in kula saboda kawai na ce be damu ba. Bayan na faɗa masa ya ɗauko min roba ya ce na yi fitsari sai kuma ya ɗibi jinina, ya bani wasu magunguna. Washe gari sai gashi ya dawo cikin gidan a rikice kai tsaye ɗaki na ya nufa. “Ina kika samu ciki?” Shine abunda ya fara tambayata fuskarsa na nuna tsantsar ɓacin rai da ke tare da shi, ni kuma na ɗago kai a hankali na kalleshi na maida kaina domin bana iya amsa masa. “Ni ban shirya haihuwa yanzu ba, saboda haka ki san yadda zaki yi da cikin nan, daga yin abu sau ɗaya sai ace ciki ya shiga, zubar da shi zan yi ko kuma ya zama ƙarshen auren mu” Ni dai uffan ban ce da shi ba ina ta aikin kuka, ban san miya aikata ba bayan kwana biyu ya shigo ɗakina ya bani lemu ina sha hankalina ya ɓace ban farko ba sai da aka kira assalati. A week later ya ɗauki ni zuwa gidan Daddynsa ashe ya kira Baba ni ban ma sani ba sai da muka isa, a falon ya yi min tozarci da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ya tozarta ya yi min ƙazafi a gaban Mahaifina da mahaifinsa ya fiddo wasu hotuna na tsiraici tare da wani ya nuna musu kuma ya yi min ƙazafin cewar na aikata zina da wani a waje kuma da aurensa. Ban iya cewa komai ba sai aikin kuka, har ga Allah ban san inda ya samo wannan hoton ba amman ni dai nasan babu wani namiji da wata mu'amala ta taɓa shiga tsakaninmu sai shi amman ya juya baya ya murje ido ya ce ba nashi ba ne, a ranar na riƙa hannunsa na riƙe shi akan ya karɓi cikin nan sai ya tureni yana faɗin taya zai karɓi cikin da ba nasa ba. “Ni kan ban haifi ƴar iskaba kuma na san irin tarbiyar da na bawa ƴata” Shine abunda Baba ya faɗa, Shi kuma ya sakeni saki uku mahaifinsa ya ce idan an saki mace a lokaci ɗaya kamar saki ɗaya ne dan haka ya maida aurensa ya yi haƙuri, sai kawai ya ce ya sani saki ɗaya ya sake ni saki biyu ya sake ni saki uku saboda kawai kar na koma gidansa sai Baba ya kama ni muka fito daga gidan, gidan aurana na koma na ɗauke duk abu na wa mai muhimmanci daga nan kai tsaye muka nufi tashar mota, sai dai ba mu kawo sokoto ba sai washe gari saboda ko da muka taso yamma ta yi sosai a zaria muna kwana, dawowata ta bawa kowa mamaki musamman da aka fahimcin ina da ciki sai aka fara zancen cewar ba aure na je yi ba iskaci naje yi wasu kuma su ce daman haka sai ya faru tun da Baba ya nuna kwaɗayinsa a kan abun duniya, har ma da masu cewa babu makarantar da na tafi. Baba ne yake ta dawainiya da ni shine ci na shana har na haihu da ƙarma ƙarama ya samo aka yanka rago ranar suna, yaro ya ci suna Muhammad Noor. Bayan na haihu Inna ta ce ya faɗa masa sai azo a auna jininsa da na yaron amman Baba ya ce ba zai yi ba, ai namiji idan ya girma shi zai nemi ubansa, kuma yasan komai daren daɗewa sai Jibril ya dawo gurin ɗansa. Da wannan na zauna a gida ina rainon ɗana har ya cika shekara biyu da wasu watanni, a lokacin ne muka fara sabo da Bilal saboda gaisuwar arziki da take haɗa ni da shi, abotarmu da Jidda kuma ta ƙullu sosai, a gunta na ke jin labarin ai mahaifin Zinatu yana ɗaukar aikin local government har da masu ssce, haka na ɗauki takarduna naje gidansu Zinatu neman ta yi ma Babanta magana akan aikin amman sai ta tsaya tana kallona har ma da zolayata wai ina karatun da aka ce ina yi a waje har tana dariya, daga baya take faɗa min cewar mahaifinta ya ce sai masu degree yake ɗauka. A hanyata ta dawowa daga gidansu na haɗu da da Faruk, tun daga unguwar yake bina har sai da na iso gida sannan ya yi min magana, ya kuma gabatar min da kansa ni kuma na faɗa masa ko wacece ni ban ɓoye masa komai. Daga nan sai alaƙa mai ƙarfi ta ƙullu tsakaninmu har ta kai ga neman aure duk da ban so haka ba Baba da Inna suka buƙaci na aureshi tun da har ya nuna yana son aurena. Faruk mutum ne mai hallaci da kawaici yana so na tsakani da Allah, da kansa ya ce na daina cewa Noor babansa ya mutu saboda na yi masa ƙarya tun farƙo na faɗa masa cewar Baban Noor ya rasu ne, wasu mazan basa yarda mace ta yi aure da ƴaƴan wasu a gidansu amman shi kan ba zaka taɓa gane cewar ba shine ya haifi Noor ba, duk abunda ya kamata uba ya yi ma ɗansa shi yake ma Noor ba dan kuma baya da ƴaƴanba, domin yana da aure har da yara biyar, sai dai yana aiki ne a sokoto amman mutumen kebbi ne, acan yake zaune da duk familynsa, sai ya bar ni nan, ita kuma yana zuwa can inda take a kebbi. Iyayensa basa jindaɗin zama da matarsa irin matan nan da basa ragawa uwar miji da ƴan'uwanta ko kaɗan duk da ba guri ɗaya suke ba, wannan dalilin yasa mahaifiyarsa ta buƙaci ya maidani kebbi kusa da ita saboda ta yaba da tarbiyata a ɗan zuwan da muke ina gaisheta. Sai ya tattara ya maida ni a kebbi tare da Noor, su kansu family ɗinsa suna son Noor kamar ɗansa yan'uwansa haka, ga mahaifiyarsa tana mugun so na ni da ɗana saboda ina kyautata mata sosai, ɓari na biyu a gidan Faruk amman Allah be bani haihuwa ba, aiko ranar na ga gata a gurin danginsa da shi kansa kamar su haɗeni saboda tausayi. Muna haka kwatsam labarin mutuwarsa ta same mu sanadiyar haɗarin motar da ya yi a hanyarsa ta zuwa sokoto gurin aikinsa. A ranar nima sai da na yi kamar zan mutu saboda kuka, a nan gidan na yi taƙaba na gama familynsa suka riƙe Noor kamar yaron da muka haifa saboda sun ga babu yaro a tsakaninmu kuma basa son alaƙarmu ta yanke gashi Noor ya ɗaukesu a matsayin yan'uwan mahaifinsa. Bayan na gama wankan taƙaba na dawo gida. A duk lokacin da suka samu lokaci sukan kirani ko kuma su zo duba Noor, bayan na dawo sai Bilal ya maida Noor kamar abokinsa kullum zai zo gidanmu kiran Noor da wannan alaƙa mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu muna girmama junanmu sosai ni da shi, sai dai iyayenaa basa son alaƙar da ke tsakaninmu ko ƙaɗan saboda sunan ganin ni bazarawa ce kuma da ɗan da ake zargin shege ne shi kuma saurayi mai mutunci, wannan dalilin yasa na ƙi bashi wata dama da zai nuna min soyayya. Har kuma tsawon lokacin Momy bata taɓa kirana ba, ni ma kuma ban kira ta ba, Ya Jamal ma sau ɗaya ya taɓa kirana be ƙara ba, Salima ce kawai muke yawan gaisawa akai akai ita kaɗai ta san na haifi Noor kuma na nemi ta min alƙwarin ba zata faɗawa kowa ba, duk da nasan sai ta faɗawa Momy amman Jibril be san yana da ɗa ba da ni ba. BACK TO STORY.... Tuna irin rayuwar da na yi aba ya hanani bachi har garin Allah ya waye. ‘Baka cancanci yafiya ba Jibril kuma hanyar da zan rama abunda ka yi min ita ce ta hanyar yin aiki tare da kai kamar yadda ka buƙata’ Shine abunda zuciyata take ta raya min ni kuma ina nanatawa kaina cewar ba zan taɓa yafe masa ba... YANZU LABARIN ZAI FARA...😄 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣3⃣ MUSTAPHA POV. Bayan ya baro part ɗin Hajiya sai ya dawo ɗakinsa ya zauna saman kujera ransa a jagule ya dafe kansa yana sauke ajiyar zuciya. Shi kansa yasan Nawwara ba zata taɓa kula shi ba, yasan ba zata taɓa ƙaunarsa ba, gani yake ya cancanci ko wace irin jarrabawa amman ban da ta son Nawwara, yarinyar da ya wulaƙanta ƙanwarta sai kuma yanzu ya zo ya ce yana son ta. Miƙewa ya yi tsaye ya nufi gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa, tunani yake abunda zai aikata wanda zai cire masa son Nawwara amman ko sunanta ya tuna sai gabansa ya faɗi. “Allah na san na aikata laifi mai girma Allah kaine mai yawan gafara mai tausayi Allah ya yafe min, Allah ka musanya min wannan jarabar ta son Nawwara zuwa wata Allah indai wannan ba ita ce ajalina ba” Shine abunda ya ke faɗa idonsa cike da ƙwalla. “Son...” Ya juyo da sauri jin motsin mahaifiyarsa, sai ya zauna gefen gado, ita ta ƙaraso kusa da shi ta zauna ta dafa shi “Son ka yi haƙuri da abunda Daddynka ya yi maka ka kwantar da hankalinka ka ji?” “Bana da kwamciyar hankali Mom tun daga lokacin da Allah ya jarrabe ni na zama silar mutuwar wata kuma Allah ya jarrabe ni da son macen da ba zata taɓa so na ba, kullum kuma ina tunanin abunda zai faru da ni gaba, ina jin kamar ajalina yake kusa da ni saboda wannan tunanin da rayuwar da na shiga ba zata taɓa bari na rayuwa mai tsowo ba” Ta yi saurin rumgume shi tana ƙoƙarin kuka. “No Son no ka daina zancen mutuwar nan, ka daina saka kanka damuwa akan abunda ba kai ka aikata ba, yarinyar nan ba kai ka akasheta ba su suka kashe ƴarsu so stop blaming yourself, Nawwara kuma ka cireta a ranka ba ta dace da kai ba, so kawai take ta yi amfani da wannan damar ta wulaƙanta ka” Be damu da hawayen da ke zuba a idonsa ba ya ce. “Mom Wallahi ba ni na sakawa kaina son yarinyar nan ba, ban san yadda aka yi son ta ya shiga raina ba duk wata hanya da zata cire min son ta nemanta na ke amman na kasa samu” “Zamu samu Son ka kwantar da hankalinka” Ya ɗago yana share hawayensa tare da ɗaga mata kai. “Bari Ikram ta kawo maka abinci ka karya anjima za mu yi magana” Nan ma kai ya gyaɗa mata, sai ta shafa masa kai cike da so da kuma ƙaunar ɗan ta. “Allah ya maka albarka” Ta tashi tayi ta fice, bayan kamar mintuna goma sai ga Ikram ɗauke da kwanonin abinci ta shigo ɗakin da sallama ta aje masa a gabansa. “Ba zan iya cin abincin nan ba Ikram” Ya faɗa yana kwantar da kansa saman gadon saboda zazzaɓin da yake jin ya fara taso masa. “Idan baka ci Mama zata damu” Cewar Ikram tana buɗe wasu plates, sauƙowa ya yi ƙasa ya zauna ya tsurawa Ikram ido kamar mai karantar abu a fuskarta. “Ikram zaki iya aurena...?” Ɗago kai ta yi da sauri ta kalleshi har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta yi shiru ta ɗaga masa kai alamar Ee. “Amman miyasa Nawwara ba zata iya so na ba” “Ni da ita akwai banbanci, ni na rayuwa a cikin gidan nan ita kuma ta rayu a gidansu, kana da kyau da isar da kowace mace zata ce tana son ka, sai dai ita a halin yanzu ba soyayyace a gabanta ba, duk macen da aka yaudareta ko aka yaudari wani nata ita ma zata ga kamar wani zai yaudareta ne, babu yadda za ayi Nawwara ta kula balle ma har ya kai ga ta so ka, saboda abunda ka aikata ma ƙanwarta, kullum da wannan abun zata riƙa kallonka ko da kuwa wata mace ka yi ma balle kanwarta. Sannan akwai banbancin tarbiya a tsakanin kai da ita da kuma gata, kaga duk wannan abun da aka aikata iyayenka goyon bayanka suke suna ƙoƙarin nuna maka baka da laifi, i'm sorry to say idan har ka biyesu zasu iya rabaka da Ubangijinka duk da kuwa suna iyayenka, saboda suna kallo kana aikata zina kuma suka ƙyale saboda gudun ɓacin ranka, ƙara ma Momy wata rana tana maka magana amman baka ji, Allah ya ce kar mu kusanci zina balle har mu aikata ta, kai ko ya aikata adadin da baka san iyaka ba, kasancewar nan da muke ɗaki ɗaya ba shi da kyau Ya Mustapha domin idan mace da Namiji suka kasance su kaɗai suka kaɗaice to sheɗan ne na ukunsu, amman wannan be taɓa zuwa a ran Momy ba balle kuma kai da ace hankali ko kuma sha'awarka ta kwaɗaita maka ni da yanzu ka gama da ni kuma ba za ayi komai ba saboda kai ɗan gata ne. Ka misalta kanka Ya Mustapha da ace kana aikata zina da wannan yarinyar ne Allah ya karɓi ranka mai zaka faɗawa Ubangijinka? Kamar kaina da bawa ka ce karya aikata abu kaza wata rana sai ka sameshi da tsabama Umarninka har ma ya yi maka sata kuma ka kamashi dumu-dumi wane irin hukunci zaka yanke masa?” Tun da ta fara maganar jikinsa ya yi sanyi hankalinsa ya tashi tun da yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa tsayawa ya faɗa masa gaskiya kamar Ikram, yana sauraren wa'azi amman be taɓa natsuwa ya yi aiki da shi ba. Hawaye yake hawayen da ke nuna nadama da tashin hankalin da ke fuskarsa. “Miyasa baki faɗa min wannan ba tuntuni? Da kin tunatar da ni da yanzu ban faɗa wannan halin ba” “Ko da na faɗa maka zaka faɗa saboda ƙaddaraka ce a haka, kuma a lokacin na san ba zaka saurareni ba saboda ba zaka taɓa ganin munin abunda kake aikatawa ba, ban ga sha'awa ga abincin da zan wanke hannu na ci ba wani yazo hannunsa da datti ya ci wani ma yazo hannunsa da datti yasa ya ci ni kuma na zo na sake saka hannu na ci, sam babu kishi kuma babu imani ga duk mutumen da yake aikata Zina, ban san miye daɗinta ba balle kuma ribarta, saboda yawan mata da kuma yawan wasu ɗabi'u na ɗan adam Allah ya halattawa maza auri mace sama da ɗaya amman kai kaba ma yi auren ba ka faɗa a zina kana neman hallaka kanka, a wannan halin da ka shiga a yanzu ina tunanin shiriyarka ne yazo, dan haka ka yi ta istigifari kana neman Allah ya yafe maka abunda ka aikaka kuma ka yi ma Allah alƙwarin ba zaka taɓa komawa a cikin wacan ƙazamin halin ba, ka yi ta aikata dik wani abin da ka san zai kusantar da kai ga Ubangijinka” Ya gyaɗa mata kai alamar gamsuwa. “Amman Nawwara ba zata yafe min ba ko?” “Zata yafe maka matuƙar kana kyautata mata, kuma kan tuba tuban gaske sai Allah ya dafa maka ta yafe maka har ma ta so ka idan ƙaddarar sonka yana cikin ƙaddararta” “Idan kuma so na baya cikin ƙaddararta fa?” A hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce. “Zai iya zama son ka yana cikin tawa ƙaddarar...!” Da sauri ya miƙe tsaye ya share hawayensa daman tun ba yau ya lura da take-taken Ikram da ke nuna alamar tana son shi. “Ki ɗauki abincin idan na fita waje zan ci, na gode sosai Sis” Yana faɗar hakan ya nufi banɗakinsa dake cikin ɗakin, murmushi ta yi murmushin da ke nuna rashin jindaɗinta sannan ta kwashe kayan ta fice. bayan ya fito wankan ya ɗauki wayarsa ya nemo number Jidda bugu uku ta ɗaga muryar a sake har wani zaƙi take ƙara mata. “Hello Mustapha” “Ya kike?” “Lafiya ƙalau” “Kina gida?” “Ee ina gida lafiya?” “Lafiya ƙalau, kawai ina son ganinki ne akwai wata magana mai muhimmanci da na ke son mu yi da ke idan babu takurawa kuma idan kina free” “Aiko bana free dole zan samu time dominka, faɗa min yaushe zaka zo i mean time?” “Yanzu nan gani nan har na yi wanka” “Okay sai ka shigo” Yana aje wayar ya nufi gurin da tufafinsa suke ya buɗe, cikin ƙanƙanen lokaci ya shirya cikin manyan tufafi riga da wando na shadda, sannan ya fito ya nufi gurin motarsa ya shiga sai ƙofar gidansu Jidda. Waya ya buga mata sai gata ta fito ba ɓata lokaci fuskarta ɗauke da kwalliya sai ƙamshin turare take kamar sabuwar amarya, motar ta buɗe ta shiga kasancewar be fito ba ne yana daga ciki zaune. Front seat ta zauna tana ƙara miƙa masa gaisuwa ciki kashe murya fuskarta ɗauke da murmushi, bayan sun gaisa ya koro mata da bayanin da ke tafe da shi. “Jidda ko kin san wanda yake da gidansu Nawwara da suke haya?” “Ee Malam Haruna ne yana nan gaba da su kaɗan, ya aka yi?” “Na je gurinta ne sai take zargin ko nine na siye gida na saboda ance an siye gidan” “Haka nima na ji amman ban san waya siye ba” “Ai nasan Malam Haruna zan masa magana na ji wanda ya siya sai ya fansar min. Am Jidda ina son ki faɗa min duk wani abu da Nawwara take so da wanda bata so da kuma taimaka min akan duk wani abu da zai ƙara kusancina da ita na san ke zaki iya daboda kinfi kowa saninta” Ta kalleshi Jiki a sanyaye. “Saboda me?” “Saboda ina ƙaunarta son ta na ke Jidda wannan dalilin yasa na ƙulla abota da ke” Tafiyar daƙiƙu biyar zuwa shida numfashinta ya yi sannan ya dawo jikinta har ta iya jiyo bayanin da Mustapha yake koro mata. Be ɓoye mata komai ba daga irin son da yake yi ma Nawwara da kuma abunda ya aikatawa Habiba, ko da ya ƙarasa bata labarin kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro. Lumshe ido ta yi ta haɗeye yawu sai hawaye suka sauko mata, hawayen da ita kanta ba san na minene ba na tausayin Habiba ko Nawwara ko kuma kanta ko Mustapha, wani baƙon al'amari ya ziyarceta labarin ya zo mata banbaragwai domin Nawwara bata taɓa labarta mata wannan ba, sai dai yanzu ne ta gano dalilin tsanar da Nawwara take yi ma Mustapha. “Please help me...” Ya faɗa cikin muryar kuka. Sai ta kalleshi tana kukan kamar yadda shi ma yake yi. “Zan yi tunani akwai, ina da buƙatar natsuwa bana iya banbance komai a yanzu” Tana faɗar hakan ta buɗe motar ta fita ta shiga gida da sauri tana kuka. Ya kusan minti talatin sannan ya bar ƙofar gidan zuciyarsa na mugun ƙona ya nufi gidan Malam Haruna. *** *** *** Anya zan iya aiki tare da Jibril kuwa? Mutumen da ya wulaƙanta ni zan iya bashi wannan damar ta kusanci da ni? Yes zaki iya, ga dukan alamu ya gane kuskurensa yanzu kan ya san ƙimarki tun da har zaki maresa a gaban jama'a ya ƙyaleki, yanzu ne ya fi dacewa ki nuna ko wacece ke, yana da kyau yasan ba wacan Nawwarar ba ce this is the time da zaki rana abunda ya yi miki kuma the same time da zaki nunawa Bilal son gaskiya kike masa, kuma idan har ban yi aiki da shi ba na gallaza masa hakan zai bashi damar da zai riƙa bibiya ni da familyna. Da wannan tunanin na tashi yau ina ta son tsayarda matsaya ɗaya akan na yi ko kar na yi. Su Sakina sun kama hanyar makaranta Inna kuma na bachinta kamar yadda ta fara dabuwa kanta a yanzu da bachin rana, ni kuma na fito na gyara tsakar gidan na yi wanka sai na shirya cikin koriyar atamfata ta roba, jin na yi bana ƙaunar zama gidan dan haka na saka Hijabina na ɗauki wayata na nufi Babban gida daman na kwana biyu ban leƙa ba. Ina cikin tafiya wayata ta yi ƙara alamar saƙo, da fari na yi zaton mtn ne ashe Bilal ne ya aiko min da saƙon barka da safiya. _Morning text does not only mean good morning. It also means, I think about you when I wake up, I love you._ Wani kalar farinciki ne da annashuwa suka nemi inda zuciyata take suka mamayeta, at that time phone ɗin ta nokia @360 ta yi ringing da number nan da aka saba kirana da idan wacce sai na ɗauka sai ayi shiru aƙi magana. Kamar ba zan ɗauka ba sai kuma na daure na ɗauka a tunani na Mustapha ne ashe Jibril. “Kai wai wane irin shashasha ne? Akan ne zaka riƙa kirana ne wahalalle” “Dan Allah ki yi haƙuri Wallahi na kira ne kawai na tambaya idan zaki zo aikin saboda na ga baki shigo ba yau” “So kai ne ko? Daman kai ne kake kirana ka ƙi magana ko?” “I just want to hear your voice” Ya faɗa muryarsa a ɗaƙile, ni kuma na ja tsaki na kashe wayar ma gaba ɗaya, saboda ya ɓata min rai. Ban wani daɗe Babban gida ba kasancewar ban tarar da Yakunbo ba domin a ɗakinta na ke shiga na kwanta saboda rashin hayani, mun ɗan yi fira da wasu cousins ɗina mata, sannan na taso na nufo hanyar gida. Ina shigowa gida na tarar da Inna ta rafka uban tagumi tana kallon ƙofar shigowa, da sauri ma ƙarasa kusa da ita. “Inna lafiya” “Mahaifiyar Mustapha ta zo gidan nan ta min cin mutunci, kuma ta gargaɗe ni matuƙar baki ƙyale ɗanta ba sai tasa an ci mana mutunci, har tana iƙirarin wai mun yi ma ɗanta magani mun zugashi yaje ya ci mata mutunci” Faɗuwa na yi zaune shi ƙenan mu dan muna talaka ba mu da gata kowa ya ɗauko shararsa sai ya juye akan mu wai mai muka yi mutanen nan ne...? JIBRIL POV. Lilo yake ta yi da kujerarsa hannunsa dafe a kai ya lumshe ido, sai shaƙar ragowar cocaine ɗin dake hancinsa ya ke. Siraj ne ya turo ƙofar office ɗin ya shigo riƙe da wasu takardu a hannunsa. “Kana ta takurawa kanka Jibril yarinyar ba zata zo ba, ɗazu fa nan ka kirata amman ta kashe maka waya, akwai mata da yawa fa a garin nan da ma wajen gari be kamata ace kana damun kanka akan ƴar talakawa ba...!” Da mugun ƙarfi Jibril ya daki teburin dake gabansa har wasu abubuwan suka zube ƙasa, ya kalli Siraj cikin wani irin ɓacin rai ya ce. “Oh s*** how many times do i have to tell you ka daina faɗin wani abu marar daɗi akan yarinyar nan ne, baka san wacece ita ba ka daina saka bakina a kan maganarta, you're just my friend so stay where are you” Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya nufi window yana huci tare da busar da iskar bakinsa. Siraj ya tsorata sosai da yanayin Jibril duk zamansu tare be taɓa masa haka ba sai yau, cikin sanyin jiki ya ce. “Akwai wanda yake son ganinka” Ba tare daya juyo ba ya ce. “Yana da appointment da ni ne? Idan yana da ayi cancelling bana buƙatar ganin kowa a yanzu sai NJ, na faɗa maka idan ma wani abun ne akan aikin nan zaka iya wakiltata” “This one is important too, ya zo ne akan maganar gidan nan da ka siya na su Nawwara, ni ya kira na faɗa masa inda kake ya zo PA ya hana shi ganinka, so shiyasa ya ƙara kirana ya matsa yana son ganinka” Da sauri Jibril ya juyo yana kallonshi da idonsa da suka kaɗe sukayi ja. “Waye shi?” “Ban sani ba ya ce dai sunanshi Mustapha” “Bar shi ya shigo” “Ka faɗawa PA ɗinka ya barshi ya shigo domin yana reception yana jira” Daga haka Siraj ya juya ya fice, Jibril kuma ƴa nufi telephone ɗinsa. WHAT DO YOU EXPECT NEXT ....? *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee ❤* 3⃣4⃣ Tare da Siraj suka shigo a lokacin Jibril na zaune saman kujerarsa yana kallon ƙofar shigowa office ɗin. Tun da suka haɗa ido da Mustapha zuciyarsa take ta raya masa wani akansa, Siraj ne ya nuna masa gurin zama a cikin kujeru dake gaban teburin Jibril suna facing ɗinsa, domin Jibril in banda kallonsa babu abunda ya ke. Mustapha ya miƙa masa hannu. “Sunana Mustapha Faruk Turaki” Jibril ya daɗe yana kallon hannunsa sannan ya miƙa masa. “And...?” Mustapha ya yi mamakin ganin yadda yake amsa masa kamar baya maraba da mutane, sai dai be nuna masa komai ba ya ɗora akan abunda ya kawo shi. “Na zo ne akan wani gida da yake guiwa, wanda ka siya ta hannun Malam Haruna” “Me gidan ya yi maka?” “Be min komai ba, ance min ka siye gidan ne milion ɗaya ni kuma zan baka 1.5 million ka mallaka min gidan” Jibril ya yi murmushi tare da kwantawa saman kujerarsa yana lilo tare da wani shegen murmushi. “Waya faɗa maka ni na siya gidan?” “Malam Haruna ne ya faɗa min, naje gunsa ina son na siye gidan sai yace min wani ne ya siya sunansa Jibril, amman ya ce be san waye Jibril ɗin ba, yaro ne ko babban na buƙaci gani ka, yace bashi da number ka sai da ta wanda suka yi cinikin domin ya bar number akan idan mutunen gidan su tashi a faɗa masa, na buƙaci ya bani number wanda suka yi cinikin ne sai ya bani number wannan Siraj ɗin, ni kuma na kirashi sai ya yi min bayanin ba shi ya siye gidan ba kai ka siya kuma shi baya da wani abu da zai yi sai dai na yi magana da kai” Hannu Jibril ya kai yana wasa da wata ƙwallo da ake saman teburinsa mai ruwan zinari wance aka ɗora saman wani abu mai kama da turmi. “Amman miyasa zaka siya gidan har 1.5 million?” “Saboda kai da ka siye gidan ka bawa waɗanda suke cikin gidan kwanaki su tashi, that's why na ke son siye musu gidan” Siraj ya haɗa ido da Jibril sannan ya kalli Mustapha ya ce “Kana da alaƙa da ƴan gidan ne da har zaka siye gidan da kuɗi da yawa haka, gidan da be wuce dubu ɗari shida ba?” Mustapha ya watsa masa wani shegen kallo tare saboda yadda yaga sun maida shi ƙaramin yaro. “Mr gida na zo siye ba bincikar alaƙata da ƴan gidan na zo ku min ba” Jibril ya yi murmushi yana ciagaba da juyawa saman kujerar. “Come on tell me boy maybe i can help” Mustapha ya maida dubansa gurin Jibril jin irin isgilancin da yake masa, yanzu kan zuciyarsa ta fara raya masa akwai dalilin da ya sa Jibril ya siye gidan. “Ban girmi ka karani boy ba? Name what ever you want zan baka am not here to play a game” Jibril ya miƙe tsaye yana dariyar ƙeta ya nufi gurin window sa yana faɗin. “In banda kai daƙiƙi ne baka taɓa tsayawa ka yi tunani ba, baka taɓa tambayar kanka dalilin da yasa ka na siye wannan gidan ba? Taya zan zuba har milion ɗaya na siye gidan  dubu ɗari biyar sannan ka zo ka ce na fansar maka ni ba a min wasa da kuɗi sai dai ni na yi ma wasu wasa! Mu kamfaninmu baya siye da siyar da gidaje ni ma kuma ba sana'a ta ba ce, so wannan gidan akwai dalilin da yasa na siye shi, so walk out of my office ba zan siyar ba” Mustapha ya tashi tsaye yana murmushi. “Zuciya na raya min ka siye gidan nan ne saboda wata manufa is that the reason yasa ka basu lokacin tashi? Kuɗin ka be amfane ka ba Mr Billionaire, tun da har zuciyarka zata raya maka siye gidan talakawa kuma ka takura musu bayan kasan babu su da inda zasu koma me suka maka ne?” Jibril ya ƙyalƙyale da dariya daga inda yake tsaye ba tare da ya juyo ba ya ce. “Na siye gidan ne saboda na isa na siya, ni mijin Nawwara ne idan ma akan ta kake wahalar da kanka so ka daina yaudarar kanka” Mustapha ya yi murmushi tare da zuba hannayensa aljihu. “Her ex-husband dai Nawwara bata da wani miji a yanzu” Jibril ya juyo yana kallon Mustapha murmushin da ke fuskarsa yana dusashewa, can kuma sai ya fara dariya. “Yeah yeah it Funny am laughing, amman bari na faɗa maka wani abu ka bar irin wannan wasan i don't play when it comes to Nawwara” Mustapha ya nufo kamar yadda Jibril yake doso inda yake. “Kana son zaka saketa? Ƙarya so kake mata tun da har ka iya siye gidan da suke ciki dan kawai ka takura mata, a haka ake so? Ko dai jikinta kake so ne huh? Da nine na samu damar auren Nawwara ko ƙuda ba zan bari ya taɓa ba balle har ya kai ga na saketa ko da kuwa kullum ruwan zafi take zuba min a jiki, but look at yourself ka yi arzikin aureta amman ka saketa ooph so sad maybe rabona ce shiyasa ka saketa” Cewar Mustapha yana wani abu da fuska kamar mai magana da ƙaramin yaro yana murmushi, cikin zafin rai Jibril ya kai masa bugu a fuska ya sake kai masa wani a gefen baki, cikin zafin nama Mustapha ya ɗago zai rama sai Siraj ya yi saurin riƙeshi ya jashi baya, hakan ya bawa Jibril ƙara kai amsa wani dukan a baki sai jini ya fara zuba. “Abraham” Siraj ya ƙwalawa PA ɗin Jibril kira sai gashi cikin ɗakin da sauri. “Riƙe min wannan” Da sauri ya Siraj ya saku Mustapha ya nufi Jibril ya riƙe shi yana faɗin. “Take him out” Ganin Abraham ɗin ba zai iya fitar da shi shi kaɗai ba, yasa Siraj ya saki Jibril ya nufi Mustapha suka fitar da shi tare. Juyowa Jibril ya yi ya nufi teburinsa ya buge System ɗin da ke saman ta faɗi ƙasa. “I need to see her, we need to talk zan bata haƙuri zan yi komai akan ta, ba zan bari wani ya ɗauki muhallin na a zuciyarta ba” Komawa ya yi gaban teburin ya ɗauki wayarsa ya danna number Abbah, yawo ya riƙa yi cikin office ɗin zuciyarsa na mugun bugawa, a ƙarshe ya samu tsayawa jikin window saboda Abbah ya yi picking. “Afternoon Abbah” “Afternoon Jibril ya aiki?” “Alhamdulillah, Abbah we need talk” “About?” “Nawwara Abbah na gano inda take” “Ai nasan zaka gano inda take, shiyasa na ce ban yafe maka kaje ƙofar gidansu da sunan neman gafararta ba, kai yanzu dan baka da kunya sai kaje ƙofar gidansu har ka iya haɗa ido da ita? Mu muka zaɓa maka ita lokacin da zaka aureta ka butulce ma umarninmu ka ce kai ba haka ba yanzu kun rabu miye na bibiyar yarinyar mutane?” “Na tuba Abbah Wallahi na tuba” Ya duƙa har ƙasa kamar yana gaban Abbah. “No ban yarda ba” “Abbah ko dan na nemi gafararta ba, ina da buƙatar na tambayi abunda yake cikin maybe ta haihu, you know how i love to see my carbon copy Abbah kasan yadda na ke son haihuwa” “Sai ka ƙara aure ka yi haƙuri har Allah ya baka” “Abbah kasan na yi aure ba ɗaya ba amman Allah be bani haihuwa ba, taya Allah zai bani haihuwa bayan na yi masa butulci” “Sai ka yi haƙuri" Abbah na faɗar haka ya aje wayar. Sai Jibril ya miƙe tsaye yana cizon lips ya wulgarda wayar ƙasa iya kar ƙarfinsa, kamar mahaukaci ya fara bugun ginar gurin da duka hannayensa har sai da jini ya fitowa ko wannensu sannan yaja baya yana haƙi. Zinatu ce ta shigo office ɗin da sauri hankalinta tashe ta doso inda Jibril ya ke. “Miya same ka haka?” Zata taɓashi sai ya yi baya yana ɗaga mata ɗayan hannunsa. “Don't touch me, na yi ma kaina alƙawarin ba zan sake taɓa wata mace ba sai Nawwara, wata mace kuma ba zata sake taɓa ni sai ita” Mutuwar tsaye ta yi a gurin ta, kamin ta juyo ta kalli Siraj da ya shigo yanzu. “Miya faru kuma? Zinatu go and call doctor please” Kainta kaɗa sannan ta juya ta fice jikinta a sanyaye. Siraj ya nufo Jibril yana faɗin “Be kamata ka tada hankalinka akan wannan gayen ba” “You don't know what Love is you have no idea how i feel so karka faɗa min wannan maganar” “Ina ƙoƙarin faɗa maka wannan gayen be isa ya ƙwace Nawwara daga hannunka ba har sai idan kai ka so” “Kasheshi zan yi Siraj babu wanda ya isa ya so Nawwara sai ni kaɗai ne wanda Nawwara zata so sai ni” Siraj ya kai hannu ya dafa ƙirjinsa. “Baka buƙatar kashe shi, sai idan kasheshi zaka yi da ranshi babu wanda ya isa ya yi gasa da kai Jibril sai idan ka so” Wata kujerar da ke gefe Jirbil ya nufa ya zauna yana ta sauke ajiyar zuciya, wani haushi yake ji da baƙincikin da be shaƙe Mustapha ba. *** *** *** Misalin huɗu da rabi ina zaune tsakar gida ni da Inna muna tattauna abunda ya faru a ɗazu. Kamar daga sama sai muka ji sallamar Zinatu daman na ji tsayar mota a waje sai dai ban ɗauka mai motar nan zata shigo ba. Na yi mamakin yadda na ganta fuska a sake kamar ba ita, cike da walwala ta gai da Inna sannan ta kai min duka irin na wasa. “Ke ƴar gari gurinki na zo” Cike da mamaki na tashi ina dariya na nufi ɗakinmu sai ta biyoni, bayan ta zauna saman katifar mu sai na fita na ɗebo mata ruwa na dire mata gabanta. Sai ta ɗauke ruwan ta maiyar gefe ta fuskance ni ta ce. “Nawwara ranar da kika mari Ogan mu, abun ya ban mamaki, abu na biyu kuma ya matsa akan yana son ki dawo aiki wai sai ya mugun wulaƙantaki, shine na ke son na san wace irin gaba ce a tsakaninku har haka duk da yake na ji ya kiraki da matarsa amman abun ya ɗaure min kai” Murmushi na yi a zuciyata ina cewa ki ce gulma ce ta kawo ki kenan. A fili kuma sai na ce “Babu wata alaƙa fa, kawai ya taɓa hannuna ne ni kuma bana son yadda maza suke taɓa ni shiyasa na mare shi” “Amman miyasa ya kira ki matarsa?” Ido na ƙura mata ina ta tunanin abunda zan ce mata, ban sani ba ko shine ya aikota ko kuma ta zo ta san wani abun ne. “Shi ya kamata ki yi ma wannan tambayar, ai na yi zaton ke ɗin budurwarce ko ƙanwar da har kika yi unƙurin rama marin da na masa” Ɗan murmushi ta yi. “Nawwara kenan, ai ban za ci akwai wata alaƙa tsakaninki da shi ba shiyasa na yi hakan domin be kamata ki mari babban mutun kamar shi ba” “Gaskiya ne, ke ma be kamata ace kin biyo ƴar talaka har gida kina bugun cikinta ba” Miƙewa ta yi tsaye tana cigaba da murmushi ta dafa ni. “Anyway daman na zo ne akan na baki shawara akan karki yarda ki koma aikin nan domin kuwa Jibril na shirya wulaƙantaki ba kaɗan ba” Har ta juya sai kuma ta juyo ta kalleni “Da ni ce ke ba zan taɓa yarda na haɗa ido da mutumen da ya wulaƙanta ni ba balle har ya kirani kariwa kuma na yarda na kula shi, Wallahi ba ayi irin wannan mijin ba” “Sai kuma aka yi rashin sa'ah zuciyar Nawwara da ta Zinatu ba iri ɗaya ba ce” “Ai ba zasu taɓa zama ɗaya ba har a bada ni dai shawara ce kawai na baki domin bana son ya cutar da ke” “Tau na gode Ummu ta gaida Aisha” Daga haka ta juya ta fice, ni ɗauki ruwan da bata sha ba na fice da su daman na san ba zata sha ba tun da ƙyamarmu take. MUSTAPHA POV. Gudu ya ke kamar zai tashi saman ko da ya iso gida kamar baya cikin hayyacinsa saboda ɓacin rai. Shi kansa be san iya adadin horn ɗin da ya yi ba kamin a buɗe masa gate, abunda ya tashi hankalin Hajiya ta fito a firgice tana kallon yadda ya faka mota kamar wani mahaukaci. “Son what happen to you?” Ta faɗa tare da nufar inda yake tana kallon fuskarsa hankalinta a tashe. “Wani ne ya yi min haka saboda Nawwara Mom” Hannayenta biyu ta kai ta riƙe fuskarsa tana kallon yadda gefen bakinsa ya soma kunbura ga fuskarsa ma tayi ja sosai abunka da mai farar fata. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee ❤* JIBRIL POV. Bayan an gama wanke masa hannun aka bashi wani magani da zai sha, sannan likitan ya ɗauki box ɗinsa ya fice daga office ɗin zuwa chemist ɗin dake kamfanin kasancewar yana aiki a ciki ne. “Siraj ka sake aikawa yarinyar da saƙo ko kuma ka kirata” “Ya kamata mu bata time Jibril, idan har kana son Nawwarar nan ta yi aiki tare da kai kuma ta yarda ta yi aikin dole ne sai ka nuna mata cewar kai ma Namiji ne, rayuwarka ta baya dole sai ta fara aikin a kanta ya yadda zata gamsu aikinne dai kuka yi ba wani abu ba, matuƙar ka ce zaka kwanta ta hau ta takaka zata yi maka abunda baka tsammani kuma daga ƙarshe mu zo bamu samu abunda muke so ba” Shiru ya yi tana nazarin kalaman Siraj yasan yana da gaskiya wani ɓangaren, a halin yanzu ya san Nawwara ba zata taɓa yarda ta yafe masa kai tsaye ba, kuma taya zata gane ya canja da gaske yana sonta idan har kusance ba idan kuma har be bi shawarar Siraj ba yasan babu kusanci a tsakaninsu domin zata yi ta nesantarsa ne. Ganin Yadda Jibril ya natsu ya bawa Siraj damar cigaba da bayaninsa. “I zuwa yanzu ya kamata mu dakata daga tura mata da saƙon neman ta dawo aiki ko kuma kiran da kake mata mu ɗaga mata ƙafa na ɗan wani lokaci” “Baka san yadda na ke ji ba Siraj idan naji sunan yarinyar nan ji na ke kamar na runtse ido na buɗe na ganta a gabana, Siraj ina neman duk wata hanya da zan nuna mata da gaske na gyaru kuma ina sonta, abu na ƙarshe ba zan bari wannan wawan ya shiga zuciyarta ba” “Ka yi haƙuri da sannu komai zai wuce, ka bata ɗan lokaci kaɗan, amman fa dole sai ka zama namiji domin ba zai yiyu ta riƙa maka wannan cin kashin ba” “Idan kuma bata dawo ba fa?” “Zata dawo na tabbatar zata dawo saboda tana tunanin ɗaukar fansar abunda ka yi mata ta hanyar wulaƙanta a gaban ma'aikanta, ai ta yi na ɗaya ka ƙyaleta dole zata yi ƙoƙarin yin na biyu har zuwa adadin da take ganin zata gallaza maka, idan kuma ba ta dawo ba sai mu bi wata hanyar ta dabam” Ya saka hannunshi aljihi ya ciro ƙaramin hoto ya miƙawa Jibril. “Ga wannan Abraham ya bani wai Nawwara ta manta shi lokacin da ta shigo office ɗin nan, ina tunanin yana da muhimmanci sosai a gareta” Hannu Jibril ya miƙa ya karɓa yana duba, yasan ba Nawwarsa ba ce amman wacce ke cikin hoton tana kamada ita sosai, ajiyar zuciya ya sauke ƙana ya ce. “Idan har Nawwara ta furta kalmar so gurin wannan yaron ko? Ba makawa kisa ya tabbata akansa” Miƙewa ya yi tsaye ya fice daga office ɗin maganganun Mustapha na ɗazu suna ta masa yawo akai, yanzu kan bashi da babban maƙiyi kamar Mustapha domin duk mai son Nawwara a gurinsa maƙiyinsa ne indai namiji ne. MUSTAPHA POV. “Sai yaushe zaka ga ne Nawwara nan ba ajin ka ba ce Son? Dan me zaka bar wani ya yi maka haka akan macen da ko a mafarki be kamata ta zama budurwarka ba balle matarka ba, na je ɗazu na ma mahaifiyarta jan kunne akan karta sake bari ƴarta ta kula ka idan ma wani maganin ne tau ta yi gaggawar karyashi” Ya janye hannayenta dake fuskarsa ya riƙe yana nuna mata tsantsar damuwa a fuskarsa. “Haba Mom a maimakon ki taimaka min gurin neman soyayyarta sai kuma ki ɓata abun? Kin ce kina so na miyasa ba zaki so abunda na ke so ba? Wallahi yarinyar nan bata min komai ba, kawai Allah ya ɗauki sonta ne ya ɗora min dan ya jarrabe, dubi ki ga fuskata kin san dalilin da yasa na dawo gida yanzu? Saboda na nuna miki wannan abun ki san ba ni kaɗai na ke son Nawwara ba, kuma ki taimaka min wajen neman yafiyarta da soyayyarta, na je gurin wanda ya siye gidan da suke ciki ne akan ya fansar min amman sai yake nuna min kamar ya fini son Nawwara saboda shi mahaukaci, ni kuma na yi alƙawari ba zan taɓa bari ya auri Nawwara ba, ba zan hanata Nawwara son wanda zuciyarta take ƙauna ba, amman ba zata taɓa zaman aure da wani ba sai ni, saboda ta haka ne kawai zan iya gane cewar ta yafe min” Hawaye ya fito a idanuwan Mahaifiyarsa ta yi mutuwar tsaye a gurin tana kallonshi. “Shikenan sun gama juye min kan yaro, s8n gama da kai Mustapha ba zaka taɓa jin abunda zan faɗa maka ba” “Ke kuma ba zaki taɓa gane abunda na ke nufi ba...!” Yana kaiwa nan ya sake mata hannu ya nufi part ɗinsa. *** *** *** Bayan na aje ruwan da bata sha, sai tambayarta da kuma abunda ta faɗa min ya dawo min a rai, ya aka yi ta san Jibril ya wulaƙanta har haka? Ko dai shi ya faɗa mata ne? Idan har shi ya faɗa mata wannan yana nufin shi ya turota kenan? Amman taya zai turo ta bani shawara akn karna koma aikin kuma. “Lafiya kuwa Zinatu ta zo?” Ya ɗago daga tunanin da na ke na kalli Inna ina ƙirƙiro murmushi tare da nufar inda take zaune na zauna. “Ba komai ta zo ne akan aikin nan wai yau ban je ba na faɗa mata se gobe shine wai bata son ina wasa da aikin ne” “Nawwara be kamata ace kina ɓoye min wani abu ba, ni fa mahaifiyarki ce, bana son noƙe-noƙen nan da kike haka kuka yi ke da Habiba har ta Allah ta kasance” Rumgumata na yi ina murmushi. “Wallahi Inna maganar aikice ta zo ta bani shawara, babu wani abu kin ji na rantse miki” Hakan yasa hankalinta ya kwanta, ni kuma na zari Hijabi na nufi gidansu Jidda. A tsakar gidansu na sameta kwance saman tabarma ta yi rufa da zane da alama bata jindaɗi duk ta rame kamar ba ita ba. Da mahaifiyarta muka fara gaisawa sannan na nufi inda take hankali a tashe, hannu na kai na taɓa jikinta sai na jishi da ɗan ɗumi. “Tun yaushe ne baki da lafiya?” “Shekaranjiya, maleria ce ke damuna” “Allah ya baki lafiya, Wallahi ban sani ba sannu” Kai ta gyaɗa min sai ta miƙo hannunta ta kama nawa hannu ta jimƙe a sosai ta lumshe ido sai hawaye, a take hankalina ya tashi ji nayi kamar itama tafiya zata yi ta barni ban san lokacin da na fara nawa kukan ba, sai Maman Nura tasa mana dariya wai daman mu ƴan raki ne idan muna ciwo. Ban bar gidan ba sai da na yi sallah magariba a nan, ko da na dawo gida kaina na ta ciwo saboda kuka da na yi a gidansu Jidda. Da kaina na labartawa Inna rashin lafiyar Jidda, ita ma kanta bata jidaɗi ɓa domin ta san yadda na ke da Jidda kuma ta san irin halin da Jidda take shiga idan bani da lafiya. “Zata ji sauƙi ai kin san maleria yanzu yadda take ma mutane balle Jidda da rakin tsiya, Allah ya sauwaƙe sai gobe zanje na dubata” “Amin amman gaaskiya tana jin jiki domin ta rame sosai jikinta kuma da zafi kamar ba a mata allura ba” “Allah ya bata lafiya, ai malaria yanzu sai an sha allura sosai ake tashi” Na tashi cikin rashin kuzari na nufi ɗakinmu. Washe gari da wuri na tashi kamar kullum bayan su Sakina sun tafi makaranta ni kuma na shirya cikin wata doguwar rigar yadi na yi ma Inna sallama tare da faɗa mata zanje gurin aikin sannan na saka Hijabi na fice. Gidansu Jidda na nufa dan duba lafiyar jikinta, una tafe ina ta mamakin tun jiya ba mi yi waya da Bilal ba be kirani ba ni kuma ina tsoron kiransa saboda ban saba ba kuma ban san hali da yake ciki ba, sai dai gaskiya a kwana biyu nan da ya saba min da kiran yasa ni jin babu daɗi. Na yi mamakin ganinta ƙofar gidan tare da Mustapha suna magana duk da ban san mai suke magana akaiba na samu kaina da tsoro sosai saboda sanin wanene Mustapha. Daga ita har shi ido suka ƙura min ganin irin kallon tuhumar da na ke musu, ba ma kamar shi da natsu guri ɗaya kamar na rikice da ganina. “Kin san waye Mustapha a unguwar nan Jidda karki yarda ya yaudareki” Na faɗa ina kallon Jidda da idonta ke cike da ƙwalla, shi kuma sai ya yi saurin girgiza kai yana faɗin “Wallahi ba abunda kike tunani ba ne Nawwara” Ni kuma na watsa masa wani shegen kallo. “Mi na ke tunani miye bana tunani? Kasan na san waye kai ka gwadani baka samu ba shine zaka dawo gurin ƙawata? Ko kuma bayan ka gama da ita ne ka dawo kaina?” “Babu komai a tsakanina da shu Nawwara nan ma ya zo ne saboda ke...” Cewar Jidda hawaye na mata zuba. “Saboda ni ko? Ki cigaba da biye masa har ya kaiki ya baro, waya sani ma ko ya lalata miki rayuwa kema” Ina faɗar haka sai na juyo na kamo hanyar dowowa, zuciyata cike da zargi kala-kala. Sai da na yi nisa sosai na kai bakin titi ina ƙoƙarin tare Napep sai ga Mustapha ya sha gabana da Mota ya fito da sauri ya fuskance ni. “Wallahi ba abunda zargi ba ne, na canja na Nawwara Wallahi na miki alƙwari ba zan sake yin wani abu marar kyau ba” “Ka dawwama a cikin abunda kake aikatawa ko kuma ka tuba babu ruwan Nawwara a ciki wannan farincikin iyayenka ne da kuma masoyanka, Kuma dan Allah ka fita daga hanyata mahaifiyarka ma ta yi mana cin mutunci saboda kai tace muna zugaka kana ci mata mutunci akan gida, dan Allah ka ƙyale karka sake jamin wani bala'in gida dai zamu tashi mu bar maka abunda very soon In Shaa Allah” “Ba ni na siye gidan ba Nawwara, wani ne ya siya sunansa Jibril ya ce shi mijinki ne” Mamaki ne ya cikani. “Ina ka ganshi?” “Malam Haruna ne ya faɗa min na je na sameshi yace shi mijinki ne” “Daga kai har shi baku da hankali, Kuma na faɗa maka ka fita hanyata” ina kaucewa ya sake shan gabana. “Nawwara mi zan yi ki yafe min mi zan yi ki yarda da ni? Faɗa min ko minene zan yi Nawwara ki yafe min?” “Zaka iya dawo min da Habiba?” “Wanda ya mutu baya dawowa kuma...” Sai na tari Numfashinsa. “Tau ba zan taɓa yafe maka ba” Ina faɗar hakan na kauce na cigaba da tafiyata na bar shi nan tsaye yana kallona fuskarsa kamar wanda zai fasa kuka. Na yi sa'ar samun Napep da wuri, ko da na isa gurin aikin takwas da ƴan mintuna, tun a bakin gate na haɗu da Amina abokiyar aikina, a tare muka ƙarasa ciki muka rubuta suna tare har tana cemin yau kan munyi latti ita tama daina ganina kwana biyu ina wasa da aikina, nikan dariya kawai na yi na ɗauke kai na nufi gurin aje Hijabina sannan na muka shiga ciki tare. “Khadija Musa Kafinta” Daf da za mu shiga lifted na ji an kirani sai muka waigo tare, wata ƙabila ce ta kira sunan nawa tana sanye da suit. “Please Follow me” Sai da muka haɗa ido da Amina sannan na bita ita kuma ta shiga Lifted, wata lifted muka nufa muka shiga tare sannan ta danna 5 lifted ta rufe muka fara tafiya. Ni dai ban kalli inda take ba itama bata ce da ni Uffan har muka isa sannan ta fita nima na fita muka doshi wani gurin daban. Ina hango inda na bi shekaranjiya na shiga office ɗin Jibril na yi tunanin kalwaɗowa zata yi mu shiga office ɗin sai naga mun iso wani ƙaton ɗaki mai cike da computers da kuma files. Muna shigowa sai matar ta juya ta fita wannan abokin nasa ya miƙe tsaye yana ɗaukar documents ɗin dake gabansa ya yi min magana ba tare da ya kalleni ba. “Congratulations Miss Nawwara, kin samu baban promotion zuwa office ɗin Oga Jibril you're now his new PA, Rabi zata zo ta miki bayanin komai” Mamaki ne na cikani new pa haka kawai bayan bana da dogon karatu? “Amman ban yi wani zurfin karatun da za a bani wannan matsayin ba” Kamar daga sama na ji muryar da nafi tsana a duniyar nan wato muryar Jibril ashe yana bayana ta gurin kujerar da ke farkon shigowa, ni ban ma san da shi ba kasancewar ban kalli gurinba tun da na shigo idona yana kan abokin nasa. “Shi kuma ga damar baki idan kuma ba zaki yi ba you can leave” Ba yabo ba fallasa ya faɗi haka ya kana ya miƙe tsaye suka fice tare da abokin nasa suka barni nan tsaye ina mamaki. __________________________________________ Kalamaina sun yi ƙaranci su gode muku fans akan irin soyayyar da kuke nunawa littafin nan. #Team RB #Team Nawwara #Team Jibril #Team Mustapha #Team bilal Na gode na gode sosai Nawwara ta ce a gaishe da masoyanta.😜 Soyayyar da kuke nunawa littafin nan a yanzu Allah yasa ku nuna min irinta a littafi na gaba mai suna HAFSATU MANGA labarin ƙauye. Ina muku son so Fisabilillah a duk inda masoyin littafin nan yajke. 😍 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy 3⃣6⃣ Wata kyakkyawar mace ce ta shigo mai far'ar fuska da kuma ta ruhi domin kuwa muna haɗa ido da ita sai naji kamar na santa, hannu ta miƙa min. “Sannu sunana Rabi Ismail” “Nawwara” Na faɗa ina miƙa mata nawa hannun. “Zo muje zan nuna yadda aikin naki yake” Tana gaba ina biye har muka isa office ɗin Jibril, a gaban computer ta fara isa ta nuna min yadda zan danna na buɗe ƙofar farko ta shigowa, sannan muka ƙarasa ciki ta nuna abubuwan da zan yi da zarar na iso da safe, sai kuma abubuwan da Jibril yake buƙata da kuma tsarin yadda zan jera masa komai. “Aikinki ne ki sanar da shi idan zai yi meeting kamin lokacin ya cika, da zarar ya shigo da wuri saki sanar shi duka abubuwan da zai yi, wayarsa da ke nan office ke zaki riƙa amsa ta, idan wani na buƙatar ganawa da shi ke zaki tabbatar da tsaro kuma ke saki saka time, yanzu kan ba zaki tashi aiki ba sai 4:00pm, kuma dole ne ki shigo 8:00am, masu kowa ƙorafi ko wani bayani na cikin kamfanin nan ke zaki kula da su shi kuma sai kije ki masa bayani a tsanake, aikinki ne gogewa da kuma gyara ɗakin nan, idan na shigo dole ne zaki tashi ki gaishe kuma ki tambayeshi abunda yake buƙata” Ya juya ta ɗauko wata leda dake saman teburinsa ta miƙa min. “Wannan kuɗi ne naira dubu ɗari biyar zaki siye tufafin da zaki saka masu kyau saboda Oga baya son ana saka tufafi marar rsada musamman yanzu da kike new PA ɗinsa, wannan kuma makullin gida ne dake Abdullahi Fodio Road a gidan zaki zauna komai akwai a ciki” Na sauke ajiyar zuciya ina kallon makullin data fiddo daga aljihunta tana miƙa min. “Daman idan mutun ya fara aiki haka kuke masa a wannan kamfanin?” “A'a Karamci ne kawai irin ya Oga Jibril ina tunanin kina da muhimmanci a gareshi sosai shiyasa” “Ki bar kuɗin ki aje makullin kuma ki faɗa masa ba zan yi aikin ba” “Amman miyasa?” Ban bata amsa ba na juyo na yi tafowata zuciyata na ta raya min abubuwa da dama, idan har na yarda na yi aikin nan tau Jibril ya ƙwareni kuma duk wulaƙancin da ya yi ya tashi a banza kenan, taya mutun zai wulaƙanta ni sai kuma na dawo na fara aiki a tare da shi? Ya samu danar wulaƙanta ni saboda kuɗin da yake da su, yanzu kuma sai na yarda ya yi amfani da kuɗin ya maye gurbin abunda ya aikata? Lallai ni wawuya ce. Haka na ke ta tunanina har na iso reception na ɗauki wata a inda na aje tare da Hijabi na saka na nufi ƙofar fita ba tare da na saka lokacin da na tashi ba. “Nawancy” Da sauri na juyo jin muryar Bilal, sai na sakar masa murmushi kamar yadda shi ma yake min. “Ashe kin shigo?” “Ee amman yanzu zan koma” “Har kin gama aikin ne?” “Ee yau baka kirani ba, duk na damu” Ɗan murmushi ya yi muna fara takawa tare yana faɗa min akwai abunda ya ɗauke masa hankali. “Amman ko minene ai ya kamata ka min ko da massage ne” “Haka ne am sorry my dear ba zan sake ba” Hango Jibril da na yi a tsaye a gate ɗin garden yasa na washe haƙura ina kallon Bilal. “Ma yafe maka ammam karka yarda ka ƙara” “Allah ya Huci ran sarauniya ba zan ma sake ba” Haka mike tafiya tare muna firarmu sai dai yadda na ke dariya sai ka ɗauka wani labarin ban dariya ne yake ba ni. Muna dosar gate Jibril kuma ya doso cikin kamfanin tare da mutumen da suke magana tare. “Good Morning Sir” Bilal ya faɗa cikin girmamawa a lokacin da Jibrilya kawo kusa da mu, ni kan ko kallonsa ban yi ba har sai da na ji maganar da ke fitowa daga bakinsa. “Miye tsakaninka da wannan yarinyar?” Ƙasa Bilal ya yi da kansa ya kasa amsawa kamar mai tsoro sannan ya buɗe baki xai yi magana sai na yi karaf na karɓe duk da ba ni ya tambaya ba. “Wanda zan aura ne” Sai ya juyo kaina ya kalli fuska a ɗaure ya ce “Bamu gina wannan kamfanin domin masoyaba, idan zaku yi soyayyarku sai ku yi ta a can waje nan kam domin aiki muka ɗaukeku dan haka bama buƙatar ganin wani abu daya alaƙancin soyayya a nan. Ku wuce gurin aikinku” Kallona Bilal ya yi ya sakar min murmushi. “Sorry Nawancy zan kira ki” “Okay Dear I love you” “I love you too” ya mayarmin da martani sannan ya juya ya koma ciki. Ina kallon yadda Jibril ya ɗauke kai ya haɗe yawu da ƙarfi, ya saka hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan kuma ya jimƙeshi sosai. “Wuce kije office” “Ba zanyi aikin ba” Na bashi amsa kai tsaye, sai ya ɗaga kafaɗunaa alamar ko a ajikinsa. Ni kuma na kama hanyar fita daga harabar kamfanin. Ina cikin Napep kira ya shigo wayata da fari na ɗaukar Jibril duk kasancewar baƙuwar number ce, hakan yasa na ƙi ɗauka, sai dai har na isa gida ba a daina kiran ba da zarar ta tsinke sai a sake kira ni kuma na ƙi na ɗaga. Ko da na shigo Inna na wankin tufafinta na sakawa, da sauri na cire Hijabina na aje na tsuma hannayena cikin wanki ina faɗin ta cire nata. “Amman dai yau ma kin yi saurin dawowa” “Na gama aikin ne da wuri” “Bayan fitarki Ɗansandan nan ya zo be tararda ke ba ya ce zai sake dawowa” “Ya yi wata magana ne?” “Cewa Ya yi suna nan suna cigaba da bincike amman yana son ganawa da ke, ya kuma tambayeni akan yadda muka tararda Babanku lokacin da muka je duba shi” “Uhmm su dai suka sani” “Wayarki tana ƙara” “Barta a can kiran bashi da muhimmanci” Na faɗa ina ɗauraye kayan da ta fara wankewa, a hankali na ji ta kira sunana. “Nawwara? Kwana biyu nan kin chanja kamar akwai abunda ya ke damunki, ki daina barin damuwa a ranki ki riƙa sanar da ni abunda ya kamata na sani tun wuri” Na tsayar da abunda na ke na kalleta. “Babu komai Inna, kawai ina tunanin Noor ne da makomarsa” “Makomar Noor tana hannun Allah da kuma shi kansa, ki daina damuwa da matsalarsa idan ya girma zai nemi mahaifinsa da kansa ko kuma shi mahaifin nasa ya nemeshi, amman ki daina damuwa arzikinki Noor na mijine ba mace ba” “Amman ni Inna ina ganin kamar ba zan iya ƙyale Noor yaje gurin mahaifinsa ba, bayan wulaƙancin da ya masa ya yi min sai kuma ace na yarda na bada ɗan gaskiya ba zan iya bari Noor ya kusanci wannan mugun mutumen ba” “Ko da ya gane kuskurensa ya nemi yafiyarsa? Ba a shiga tsakanin ɗa da uba Nawwara yanzu kin ga duk wannan abun Noor be san da shi ba aiko abun farincikin ki idan har yau Allah ya kawo babansa ya nemi ɗansa da kansa” Idona ya cika da ƙwalla. “Amman Inna kamar akwai ƙwaruwa a ciki, ku kuka raini yaron nan sai kuma a ɗauka a miƙawa uban bayan uban be san darajarsa? Gaskiya ni ba zan iya yafe masa ba” “Ban ce ki yafe masa ba kuma ban ce karki yafe masa ba, amman bashi ɗansa kan dole ne indai har ya buƙaci haka, yara su tashi a gidan iyayensu maza yafi daraja da ƙima fiye da iyaye mata, ke kanki zaki fi jindaɗi na san ba zaki so Noor ya yi agolanci ba, saboda ba ko wane uba ne yake son a kawo masa ɗan wani a gida ba, ba duk miji ba ne zai so ki ya so ƴaƴanki, ni kuma ba burina ki yi ta zama a gida ba bana da natsuwa Nawwara har sai kinyi aure kin zauna ɗakin mijinki” “Amman ai be zo karɓan ɗansa ba kwata-kwata be taɓa sakashi a ido ba, kuma irin wannan mutumen kike goyon bayan na bashi ɗansa?” Na faɗa ina kuka, ji nake kamar da gaske rabani za'ayi da ɗana. “Misali ne kawai na ke baki, ba wai na tabbatar zai zo ba ne, amman zuwansa yana da muhimmanci Nawwara domin zai wanke zargin da mutane suke miki, kuma Noor zai san waye ainahin ubansa na gaskiya” “Ni gaskiya zan maida Noor gurin Gwaggonsa” “Wace Gwaggonsa kuma? Zumuntar uwa suka haɗa ko ta uba da zaki ɗauki yaro ki kai mata saboda kawai kin auri yayanta? Faɗa min abunda kike ɓoyewa Nawwara ko shine yake kiranki?” “Ni ma ban sani ba, amman Inna Noor zai iya rayuwa ko babu babansa a kusa da shi ko da ma ace Ubansa ya mutu” “Allah ya kyau” “Amin” Na amsa ina kuka sosai har da mazina. Ban gama wankin ba sai da aka yi azahar, a lokacin su Sakina suka dawo makaranta, Noor da ciwo a ƙafarsa wai yaje buga Boll ya buge da dutse har jini ya fita. A ranar ba tare da shi suka je Islamiya ba saboda ciwon ƙafan, da suka dawo ne suke labarta mana wai yau sun yi babban baƙo a makarantar su har ya saka gasar karatun sirratul nabiy wacce ta yi ta ɗaya za a bata gida ta biyu kuɗi dubu ɗari biyar ta uku kuma dubu ɗari biyu da hansin, kuma su uku kawai aka zaɓa Sakina sai wasu ƙawayenta biyu. Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindaɗinta har tana addu'ar Allah yasa Sakina ta ci, ya yinda ni kuma na ke ta tunanin kamar ba gasar Allah da Annabi ba ce. JIBRIL POV. Shi kansa ya san ya cancanci a yaba masa akan namijin ƙoƙarin da ya yi na ɗauriyar sauraren kalma mai tsada da Nawwara ta furtawa Bilal. Sai dai tun daga lokacin baya jin sukuni har yanzu, kalmar kawai yake ta ji a kunnensa tana masa yawo kamar wanda zai haddace sautinta. “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Shine abunda ya fi furtawa a duk lokacin da yaji abun ya haye masa zuciya. Safa da marwa yake ta yi a ɗakin ya kasa natuwa guri ɗaya. “Am so so sorry Naj am so so sorry please forgive me” Ya furta yana janye hannun rigarsa sai ga sunanta shimfiɗe a ɗamtsensa da tattoo, shafa gurin ya shigayi ya lumshe ido sai ga hawaye. “I love you so much bana son na zama wani kalar mutum Ya Allah help me” Zaunawa ya yi bakin gado yana ta tunanin abunda zai fissheshi, can ya miƙe tsaye ya saka hannunsa ɗaya ya saka aljihu ya fiddo wayarsa ya danna number Nawwara, haka ya jera mata kira biyar bata ɗaga ba sai ya sake kira na shida ya bar wayar saman madubi ya fita zuwa kitchen ɗan haka wa ƙansa tea. “Hello Momina tana banɗaki idan ta fito zan faɗa mata” Noor ne yake maganar sannan ya katse kiran jin ba a amsa masa ba, a daidai lokacin Jibril ya dawo ɗakin ɗauke da kofin tea, wayar ya sake ɗauka ya duba sai ya ga anyi picking, da sauri ya sake kira sai aka kashe ya sake kira aka sake kashewa sai kawai ya yanke shawarar aika mata da saƙon karta kwana wato sms. Da kansa ya tsara rabutun ya tura mata sannan ya jefar da wayar ya miƙe tsaye ya nufi window yana ta kurɓa tea ɗin zuciyarsa na mugun zafi, ji ya yi ba zai iya jurewa ya aje kofin ya nufi wani ɗakin, da shigarsa ya ɗauko wani akwati ya buɗe ya ɗauki ƙwanƙwaƙo ƙarami ya buɗe sai ga cocaine cikin wata farar leda da sauri ya ɓasge ledar ya zuba garin a hannu yana shaƙa kamar ba gobe. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy *Dedicated to My Asmee* 3⃣7⃣ Ina fitowa daga banɗaki na zauna saman tabarma da na tashi sai Noor ya miƙon wayata da ke hannunsa. “Momy gashi an kira na ɗauka amman ba ayi magana ba” Ina karɓar wayar na duba sai na ga number Jibril number nan ce da ya saba kirana da ita. “Ka yi magana?” “Ee amman ban ce ance komai ba, sai na ce idan kin zo zan faɗa miki sai na kashe” “Na shiga uku Noor miyasa ka yi magana?” Hankalina ya tashi sosai zuciyata na ta raya min Jibril zai gane cewar Noor ɗansa ne. “Momy ban ce komai ba” Ya faɗa ganin yadda duk na bi na rikice, kai na gyaɗa masa naja shi zuwa saman ƙafafuna na zaunar da shi na rumgumeshi, muna haka wayar ta ƙara ringing ina dubawa na ga Number Jibril sai na kashe wayar gaba ɗaya, gabana sai faɗuwa yake, zuciyata na nuna min Jibril zai uya zuwa gidan nan a yanzu ko anjima saboda ɗansa. Unƙurawa na yi na tashi sai ga Jidda ta shigo bakinta ƙumshe da sallama, sai jikina ya ƙara yin sanyi har na ke ganin kamar ita ma tare take da Jibril. “Noor tashi kaje ɗaki yi sauri” Sai da ya gaisheta sannan ya tashi ya nufi ɗakin, ita kuma ta zauna kusa da ni tare da dafani. “Ki kwantar da hankalinki ba zan cuceki ba, ba kuma za a haɗa baki da ni a cuceki ba” “Idan har ni be cuceni ke zai cuce ki” “Mustaphan da kika sani a baya ba shi ne a yanzu ba, Wallahi ya canja Nawwara kuma saboda ke ina ganin wannan kaɗai abun farincikine ace ta dalilinka wani ya shiryu” Na gyara zamana ina kallonta da kyau. “Bakin san waye Mustapha ba shiyasa kika wannan maganar, baki san iya ta'asar da ya yi ba shiyasa kike ganin kamar ya canja” “Ya canja Nawwara ko ki yarda ko karki yarda Mustapha ya canja, ganin da kika mana tare yazo gurina ne saboda yana neman yafiyarki, yana son na taimaka masa na nema masa yafiyarki” “Kin san abunda ya aikata min kuwa?” “Shine mutumen da ya yi fyaɗe ya bata dubu ashirin ko? Ko ba wannan ba ne?” Kallon mamaki na yi mata. “Ya faɗa miki kenan?” “Ya faɗa min komai saboda kawai yana neman yafiyarki, ki dubi girman Allah Nawwara ki yafe masa ko ya samu sassaucin rayuwa” “Taya kika san tuban gaskiya ya yi? Maza suna yaudararmu Jidda saboda sun san mu mata muna raunin zuciya, sukan yi amfani da wannan damar su sake cutar da mu” “Ba zai taɓa cutar da kr ba Nawwara, tun daga lokacin da kika taɓa marinsa ya ƙyaleki zuciyata ta raya min Mustapha son kin yake ko kuma son wani na ki, ya isa shaidar kirki cewar Mustapha tuban kirki ya yi tun da ya biyo ki har ƙofar gidanku ya nemi yafiyarki, idan har yana son cutar da ke ba zai taɓa neman yafiyarki ba, zai iya sakawa a ɗauko masa ke ya yi miki yadda ya ke so, zan iya dafa miki ƙur'ane cewar Mustapha tuban ƙwarai ya yi kuma ya yi nadama” “Ba zan yafe masa ba da gangan mutun zai aikata abu sai kuma ya dawo neman yafiya, da ace be mata fyaɗe ba da bata samu ciki ba da duk be kaita ga halaka ba, da yanzu ƴar'uwata tana nan raye” Na faɗa zuciyata na mugun ƙuna. Sai dai abunda ya fito daga bakin Jidda ya kusa ya ruɗar da ni ko kuma ma na ce haukatarda ni gaba ɗaya. “Ashe jahila ce ke Nawwara, karatun addininki be amfaneki da komai ba, baki da imani ko kaɗan saboda baki yarda da ƙaddara ba, kuma bari na gyara miki kalamanki da ace yar'uwarki bata je ta kai kanta gunsa ba da be samu damar yi mata fyaɗen ba, kuma ko da Mustapha ko babu Mustapha dole Habiba zata mutu kuma dole sai wani ya yi mata fyaɗe kuma dole sai ta yi ciki saboda yana rubuce cikin kundin ƙaddararta, tirr da halinki Nawwara tirr zuciyar da bata yarda da ƙaddara marar kyau ba sai mai kyau, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle ke da Allah zai cewa faɗi ki mutun kuma ki faɗin ki mutu dan dolenki, zuciyarki bata da kyau Nawwara saboda babu imani babu tausayi a cikinta, bawan Allah nan ko shi da hannunsa ya kashe Habiba ya kamata ki yafe masa tun da har yace miki ya tuba, balle fyaɗen da idan aka bincika daga shi har ita suna da laifi-!” Tun da ya fara maganar na ke kallon yadda take dantsar baki tana faɗa min duk maganar da tazo daga bakinta idonta na hawaye kamar yadda nima nawa idanuwan suke hawaye, cikin muryar kuka na ce. “Faɗa min nawa Mustapha ya biyaki Jidda? Dala dubu nawa ya biyaki da har tasa kika goya masa baya tsaɓanin aminiyarki? Da me ya siye zuciyarki har kika ƙoƙarin ɓata abotarmu?” “Da imani da tausayi ya siye zuciyata, ni na yarda da ƙaddara a yayinda ke baki yarda da ita ba” “Saboda baki dan yadda na ke ji ba Jidda, a gaban idona yar'uwata ra rasa ranta saboda wannan azzalumin” “Na san yadda kike ji, amman na fi jin yadda Mustapha ya ke ji saboda ƙaddara ta faɗa kansa wacce bata wuce faɗawa kowa ba” Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye ta fice ta barni a gurin ina ta hawaye da mamakin kalamanta. Jin ana kiran sallah isha'i yasa na tashi na wanke fuskata na yi alwala a waje na yi sallah isha'i kamar yadda na yi ta magariba. Bayan na gama addu'o'ina na tashi na nufi ɗakin Inna, ko da na shiga na tarar tana sha'u da wutiri Noor da Jamila kuma na saman gado suna mugun wasa, ƙasa na zauna kusa da ita ina jiran ta ƙare idona suna kan ɗana da ke ta sukuwa saman gadon. “Noor bari mana gadon Inna zaka yi sukuwa” Da sauri ya sauko sai ya nufo inda na ke yana faɗin. “Momy zaki ara min wayarki na yi game ko?” Sai a lokacin na tuna da na bar wayar a wajen da na zauna har na yi a zamar tashi na fita na ɗauko wayar cike da fargaba na kunnata ina shigowa ɗaki, zan miƙawa Noor naji ƙarar shigowar saƙo, hakan yasa na tsaya dubawa. _Matiƙar baki dawo aiki gobe ba, wannan shegen saurayin na ki zamu sallameshi kuma try me_ Ba shiri na zaro ido gabana ya shiga faɗuwa na furta shiga uku da kirama kaina hallaka. “Na shiga uku na lalace” Da sauri duk suka kalleni har Inna dake jan carbi. “Miya faru?” Kallonta na yi sai kuma na rasa ta yadda zan mata bayanin ga Noor da Jamila har Sakina duka idonsu a kaina, saurin goge saƙon na yi na miƙa masa wayar. “Ungo je kayi game ɗin” “Momy miya faru?” “Ba komai kuje waje da Mama Jamila sai ku yi” Yana karɓa sai suka yi waje ni kuma na zauna kusa da Inna idona cike da ƙwalla na kama hannunta na riƙe sai na kasa yin magana hawaye suka fara yin aikinsu. “Nawwara mi yake damunki?” Hannuna ɗaya na kai na share hawayena yayinda wasu ke ƙara zubo min. “Inna ko na faɗa miki ba zaki fahimce ni ba, kuma fushi zaki yi da ni” Nan take hankalinta ya tashi ta damƙe hannayena biyu tana kallon cikin idona. “Me kika aikata har haka ne Nawwara? Abunda ƴar'uwarki ta aikata shi kika aikata kema?” “A'a Inna Jibril ne” Na faɗa ina sosa kaina hawaye na sauka a fuskata. “Wane Jibril?” “Baban Noor” Da sauri Sakina ta tashi zaune daga kwancen da take tana kallona, Inna kuma ta saki baki. Ni kuma na rasa ta inda zan fara mata bayani. “Kamfanin da na samu aiki ashe na Jibril ne, ni ma ban sani ba sai daga baya....” Haka na bi na zana mata komai tun daga farko har ƙarshe ban ɓoye mata komai ba, har maganar siye gidan da kuma wannan saƙon da ya aiko min yanzu. Lunshe ido ta yi ta jingina da gado tana sauke ajiyar zuciya. “Miyasa kika ɓoye min wannan tun farko? Da ace kin shawarce ni da duk abun be kai haka ba, har yanzu baki san ƙima da matarba uwa ba ko? Wani na waje ya ji sirrinki mahaifiyarki bata sani ba? Akwai wanda ya cancanci ki yi sirrin da shi fiye da ni?” “Ba haka ba ne Inna, kawai ina tunanin irin halin da zaki shiga ne idan na faɗa miki, wata ƙila ma ba zaki fahimce ni ba, kuma abun zai tsaya miki a rai ki riƙa tunanin wanda ni kuma ba zan so haka, Wallahi ban ɓoye miki da wata manufa ba bayan wannan” “Ƴaƴan mazani kenan masu yarda da ƙawaye fiye da uwaye, masu yin gaban kansu waɗanda suke ganin kamar tasu zata fisshesu” “Dan Allah Inna ki yi haƙuri” Na faɗa ina kuka. “Amman da gaske Jibril ya baki haƙuri kuma kika mare shi ya ƙyale ki” Sakina ta tambaya, ni kuma na ɗaga mata kai. “Idan har yafiyarki yake nema ba zai tsaya jiran ki kawo kanki ya nemi yafiyarki ba, sai dai na nemi inda kike ya zo ya baki haƙuri kuma ya nuna miki ya yi nadama” Cewar Inna, ni kuma na ce. “Bana ma son ya zo dan ba zan yafe masa ba” “Allah ma aka masa laifi aka roƙi ya yafe balle ɗan'adam? Idan baki yafe masa ba ai kya bashi ɗansa idan ya zo karɓar abunsa” “Haba Inna duk wulaƙancin da ya yi min ya ce ɗan nan ba nasa ba ne sai kuma na bashu Noor gaskiya ba zan iya ba” “Akwai hujjar da ta zata hana ni ganin ɗansa ne?, idan har ya dawo ya buƙaci ɗansa ki bashi kawai shine masliha a gareki da kuma mu, ku bar shi da Allah Nawwara idan har kika yi haƙuri sai ki ga kyakkyawan sakamako daga gurin Allah amman matuƙar kika ce zaki rama abunda ya yi miki Allah zai iya barinki da dabararki a ƙarshe sai ki cuci kanki, amman idan har kika barshi da Allah sai ya saka miki. Ma a son mace da irin zuciya da halinki Nawwara, duk da zata iya ɗaga hannunta ta mari namiji ta kuma tsaya ta ci masa mutunci akan abunda zata iya kawar da ido ana mata kallon marar tarbiya kuma marar mutunci da kamun kai, raunin zuciya tausayi kawaici kunya haƙuri abubuwa da aka fi samu sun gurin ƴa mace, Na san Jibril ya zalinceki Nawwara, amman ki barshi da Allah karki yarda ki ce zaki ɗauki fansa wannan ba halin musulmin kirki ba ne” Daker na iya tsayar da kuka da na ke har na furta. “Ni ba zan iya yafe masa ba Inna” “Ban ce ki yafe masa ba, amman ki bishi a hankali kuma ki yi taka tsantsan” “Kuma ba zan bashi Noor ba be cancanci zama ubansa ba, ni ba zan iya yafe masa ba” “Har gobe ina faɗa miki rufin asirinki ne idan har ya dawo ya nemi ɗansa, ni kuma ban ce ki yafe masa ba” Sakina ta dawo kusa da mu tana faɗin “Amman gaskiya idan har aka bashi Noor ya ci riba biyu” “Ba riba ya ci ba, Wallahi ina da tabbacin Allah ba zai barshi hakan nan ba, wata ƙila ya jarrabeshi ko zai jarrabeshi nan gaba, duk ɗa ai ƴaƴan maza ne ba na mata ba, itama wani auren zatayi ta haifi wasu ƴaƴan, ni dai abunda na ke so da ke ki yi min alkawari zaki riƙe mutuncinki kar kuɗi da ƙyaliƙyalin duniya ya yaudari zuciyarki ya kaiki ga faɗawa halaka” “Na miki alƙawari Inna ba zan sake sakaki hawaye ba” “Allah ya miki albarka, ki je gurin aikinki ki koma kamar yadda ya buƙata, amman karki taɓa nuna masa saboda Bilal kika dawo, kar ki nunawa Bilal saboda shi kike aikin, ko wannensu ki nuna masa saboda kanki kike yi kuma zaki iya dainawa a ko wane lokaci, idan har kika bar aikin yanzu zai kori Bilal kamar yadda ya faɗa, wanda hakan zai jefaku ciki wani halin, kuma baki san ta wace hanyar zai ƙara ɓullo miki ba” “Amman Inna ina ganin kamar yana son ya yi amfani da damarsa ne ya sake cutar da ni” “Ba zai sake cutar da ke ba, waya sani ko saboda ke ya dawo garin nan da aiki? Wanda ma yake likita miya kawo shi aikin kamfanin? Baki taɓa tambayar kanki ba?” Na yi shiru ina nazari, sai Sakina ta yi karaf ta ce “Wata ƙila yasan ta samu aiki a kamfanin shiyasa ya zo” Inna ta amsa mata. “Nima haka na ke tunani, ƴaƴan manyan masu kuɗi basa ganin irinmu talakawa da mutunci, yana ganin kamar ƙasƙanci ne a gareshi yazo neman yafiyarkin kai tsaye, bana tantama shi ne ya aiko mana da ɓarayin nan kuma ya siye gidan nan saboda ki matsu ki koma aikin a kamfanin kamar yadda yake buƙuta ta yadda zai iya kyautata miki har ya nemi yafiyarki cikin sauƙi, da ace cutar da ke yake son yi da wata hanyar zai ɗauko ba wannan ba, kuma kin ga idan har yana da wata niyar ta daban akanki babu yadda za'ayi ya ki mareshi a bayanar jama'a ya ƙyaleki har ma ya risina ƙasa yana baki haƙuri, wannan saboda yana ganin bashi wata mafita sai ita ne shiyasa ya ɓullo miki ta hanyar Bilal” “Amman ina tunanin be san da Noor ba ko?” Sakina ta tambaya. Sai Inna ta amsa ta “Ya san ya barki da ciki, sai dai be sani ba ɗan yana raye ko baya raye, wata ƙila ma yasa an masa bincike akan haka, amman ki yi tunani Nawwara dukan mutumen da ya yi miki wannan wulaƙanci yana kunyar ya tunkareki kai tsaye ya nemi yafiyarki, kuma ta hanyar aikin nan da zaki yi a ƙarƙashinsa zaki iya fahimtar irin rayuwar da ɗan ki zai yi idan har ya zauna gunsa, ke da shi duka ƙurciya da wauta tana cinku” Shiru na yi ina ta nazarin maganganun Inna akwai hiƙima da kuma ƙamshin gaskiya a duk abunda ya faɗa, ni kaina na san da Jibril be yi nadama ban iya na masa irin wannan cin kashin a gaban ma'aikatansa ba, kuma babu dalilin da zai ya riƙa bibiyata har yana neman na dawo aiki. Ajiyar zuciya na sauke nasa hannu ina share hawayena, Inna kuma tana amsa sallamar da almajiri yake yi. “Assalamu alaikum wai ance ana sallama da Nawwara a waje” Da fari gabana ya faɗi na fara tunanin mai min sallamar. “Waye ne?” Na tambaya a cikin muryata mai amon kuka a cikinta. “Haka ya ce wai bawon Allah ne” Zan ƙara tambayarsa sai ga Noor ya shigo da gudu ya miƙa min wayar. “Momy ga Uncle Bilal ya ce na baki” Ina karɓa na kara a kunne already Noor ya yi picking. “Nawancy gani nan akan hanya” “Ka ce ma ka iso” Sai kawai ya yi dariya ya kashe wayar, jin haka yasa na ce da almajirin ya ce ina zuwa, wayar na miƙawa Noor ni kuma na tashi na je waje na wanke fuskata na shigo na shafa mai sannan na saka Hijabi na fita. Mustapha na tarar ƙofar gida sanye da jallabiya yana kallon ƙofar gidan, waigawa na yi gabas na duba yamma ban ga mai kirana ba hakan ya tabbatar min da cewar shi ne yaƙe kirana. “Miya kawo ka nan kuma? Kamin nan dai bari na fara taya ka murna ka yi nasarar haɗa ni da ƙawata ta faɗa min har abunda ban zaci zata iya faɗa min ba, burinka ya cika” “Ba burina kenan ba, burina ki yarda na tuba kuma ki yafe min” “Akwai aiki a gabanka babba Mustapha, yafiyar Ubangiji ta fi cancanta ka nema ba tawa ba” Sai ya kirana sunana a hankali. “Nawwara idan na kai kaina kotu aka min hukunci zaki tafe min?” “Allah ya rufa maka asiri karka tonawa kanka” “Ina ma ace zan iya raba zuciyata biyu ki karanta ki ga abunda yake raina” “Kasan zaka nemi yafiya ka aikata?” “Ƙaddarata ce ta zo a haka, an rubutoni a cikin ƙaddarar Habiba kamar yadda aka rubutoki a cikin ƙaddararta, Wallahi da nasan Allah zai jarrabe ni da sonki da ban yarda ba kalli Habiba balle har wani abu ya shiga tsakanina da ita” Ya faɗa yana ƙwalla, har na buɗe baki na sake masa wata maganar sai na hango Bilal tafe, sai na tattarahankalina na maida gurinsa gudun kar ya zargi wani abu, hakan yasa Mustapha waigaya ya kalleshi. Tsayawa Bilal ya yi cak sai kawai ya ɗago min hannu daga can inda yake ya juya ya koma. “Ka gani ko? Ka hana masoyi ya ƙaraso kusa da ni” Na faɗa a tsawace. “Yi haƙuri” Sai ya yi saurin juyawa ya bar gurin cikin sauri, na daɗe tsaye bakin ƙofar wai ko zan hango Bilal ya dawo amman har na gaji ban dawo ba hakan yasa na juya na koma cikin gida raina a jagule. Assalamu alaikum habibaties. Ina nan lfy kalau sai dai phone dina ce ta ci screen amman yanzu an gyara, Alhamdulillah. A cigaba da gashi... *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣8⃣ MUSTAPHA POV. Be taɓa tattabar da cewa yana son Nawwara ba sai yanzu, wani irin abun yake jin yana dibarsa masar misaltuwa, kalamar da ta furta ga waninsa na masoyin da ta kira Bilal yake jin kamar ace shi ne. Kai tsaye ya wuce part ɗinsa sai ya kwanta rairai ƙasan carpet ya lumshe idonsa, babu abunda yake tunani sai halin rayuwar da ya jefa kansa, da ace be kasance mazina ci ba da babu abunda zai hana Nawwara ta so shi, tunani yake abunda zai faɗawa Allah idan har ya mutu a yau ba tare da ya tuba, son nawwara yasan jarabawace Allah ya ɗoro masa gashi tana da ɗawainiya da shi ta hanashi sukuniina ga ya mutu? Tabbas zai yi ƙoƙarin juye rashin Nawwara amman azabar Allah fa zai iya jureta? Wacan azabar da za'ayi ma mazinata ba da irin wannan jarabawar ba ce da wuta mai kamar kunu za a ƙona fatarsa bayan azabar da za a gada masa cikin ƙabari. Buɗe ido ya yi sai ya ɗaga hannunsa sama yana kallon farar fatar hannunsa, sai ga hawaye sun gangaro daga idanuwa zuwa gefen kuncinsa, unƙurawa ya yi da zimmar tashi zuwa alwala ya yi sallah ya ƙara nemi yafiyar Ubangijinsa, sai dai hango Mahaifiyarsa da yayi jikin ƙofa tana kallonsa tana hawaye yasa shi yin zaune tana share nasa hawayen. Ƙarasowa ta yi kusa da shi ta zauna kana ta riƙa hannunsa tana kallon fuskar ɗanta cike da tausayinsa. “Son kuka kake yi?” Ya yi shiru be ce komai ba. “Zan je na nema maka yafiyarta, in har hakan zai faranta maka rai, damuwarka damuwata ce a duniyar nan bana da wani farinciki sai naka, amman ina son ka sani ba kai ne ka kashe yarinyar nan ba” “Ba ni na kasheta ba Mom na sani, amman ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sannan Allah ya jarabeni da abunda ban taɓa tsamani ba, son yayarta, kuma kun kasa fahimtar hakan balle ku goya min baya” “Na yi magana da mahaifinka zamu nema maka yafiyar Nawwara, da kuma aurenta matuƙar hakan zai kwantar maka da hankali” Ya yi saurin kallonta kamar be yarda ba. “Mom da gaske?” “Kai kaɗai na ke da a duniyar idan ban faranta maka ba wa zan farantawa? Bana son na rasa ka” Ya kwantar da kansa jikinta yana murmushi tare da sauke ajiyar zuciya. “Thank you so much Mom i love you” “Love you more” Ta faɗa tana hawaye, har ga Allah ba dan tana son nawwara zata nema masa ita ba sai dan kawai ɗanta ya samu salama hankalinsa ya kwanta, amman ita har gobe gani take ɗanta be dace da nata kamar Nawwara ba. Sun daɗe a haka sannan ta sake shi ta fita shi kuma ya shiga banɗaku dake falon ya wanke fuskarsa ya canja Jalabiyar da ke jikinsa ya zuwa wata jalabiyar black sannan ya fito a compound ya nufi gurin da motarsa take ya shiga horn ɗaya mai gadin ya buɗe masa gate ya ɗauki hanyar gidansu Jidda. Tun kamin ya ƙarasa ya kirata ya faɗa mata ta fito gashi ƙofar gida, sam ba zaka ganshi a yanzu ka ce mutumen ɗazu ne ba, farinciki ya mamaye masa zuciya ji yake kamar da Momy taje ta bawa Nawwara haƙuri haƙura zata yi ta kulashi. Yana zaune cikin motar har Jidda ta fito sanye da Hijab tana tafiya kamar marar laƙƙa, jinginawa ta yi jikin motar yana miƙa masa gaisuwa shi kuma sai ya kashe motar ya fito yana murmushi. Gabanta ya faɗi zuciyarta ta fara bata wani tunani na daban kar dai ya cutar da ƙawarta, mutumen da tasan yana cikin damuwa yanzu kuma har da murmushi a fuskarsa. “Naje na yi magana da Nawwara amman har yanzu bata fahinta ba, har na faɗa mata maganar da be kamata ba, amman na san nan gaba zata gane kuma zata yafe maka ni dai abunda na ke fata karka cutar da ita dan Allah” Ya sake yin murmushi yana kallonta fuskarsa da annuri. “Zan iya cutar da kaina ban cutar da Nawwara ba, da kin san yadda na ke sonta da baki min wannan zargin ba, amman na san duk mutumen da yasan wanene dole zai zargeni, faruncikin da kika gani a fuskata na zo ne na faɗa min cewar Mom ta yarda har ma ta ce zata taimaka min wajen neman yafiyar Nawwara” “Wow amman na yi farinciki, Allah ya shiga cikin lamarin kuma ya sa ta kula ka” “Amin nima fatana nan” Ya faɗa yana kallon hawayen da suka zubo mata, wanda hakan yasa shi wani tunanin na daban. “Hawaye kike?” “Ni?” Ta yi saurin kai hannu ta share hawayen, da alama bata san sun zubo mata ba. “Kawai ina farinciki ne” Ya mata murmushi as respond ba dan ya gamsu hawayen nata na farinciki bane, ita kanta bata san hawayen mi take ba, iya abunda ta sani zuciyarta na yaudararta ne da son cuta mata abunda ta san ba zai taɓa yayuwa ba. ‘i'm very stupid taya zan so mutunen da ke son ƙawata?’ A fili kuma sai ta kalli Mustapha ta ce “Zan shiga ciki” Nan ma kai ya ɗaga mata yana murmushi da iya fatar baki kawai ya tsaya masa. Har ta juya sai ya kirata. “Jidda...” Ta juyo tana kallonsa “Thank you” “Anything for Nawwara” Sai da ta shiga gida sannan ya juya ya shiga motarsa zuciyarsa na raya masa wani abu da baya son kawowa akansa, he's happy at first amman yanzu sai ya nemi farincikin ya rasa tunanin hawayen da Jidda take ya tsaya masa a rai. Ko da ya isa gida part ɗin Mom ya fara shiga sai dai be sameta ba saboda bata gidan, Ikram ce kawai a falon tana game, yana shigowa hankalinta ya dawo kansa. “Mom taje zata yi magana da Nawwara abunda ka daɗe kana jira amman kuma sai naga kamar baka farinciki” Ya kalleta irin kallon nan na sai yanzu ya lura da maganar da take. “Ofcourse am happy i was just thinking of something else” “Like?” Sai yayi murmushin da ya bayyana haƙoransa ya miƙe ya shiga kitchen yana faɗin “Manta kawai ba wani abu bane mai muhimmaci” Freezer ya buɗe ya ɗauko gorar ruwa ya kai a bakinsa ya sha sai kuma ya nufi gurin window yana ta tunani. “Impossible” Ya sake cika bakinsa da ruwa, sai kuma ya yi murmushi yana sauke ajiyar zuciya. “I love you so much” Ya daɗe a kitchen ɗin sai da yaji motsin shigowar Mom sannan ya juyo ya fito riƙe da gorar ruwan ya nufo falo. “Mom ya kuka yi?” Ya tambaya tun kamin ta cire mayafin da ke kanta, sai dai bata bashi amsa ba sai da ta zauna saman kujera fuskarta da murmushi. “Sun ce ba zasu yafe ba” “You must be joking Mom” “Ka ci gidanku, ni zan maka wasa” Ya zauna kusa da ita yana kallon murmushin da ke fuskarta. “Na yi magana da su kuma sun ce sun yafe maka, baka ga yadda mahaifiyarta ta tarbeni ba kamar daman can babu komai” “Da gaske? Amman Nawwara fa?” Ta ɗanyi shiru sannan ta ce “Ita ma ta yafe maka har ma tace a gaisheka” “Mom da gaske” “Sai kaje ka tambaya idan baka yarda ba” Wani irin tsalle ya yi ya dare kamar mahaukaci. “Mom i love you so much” Mom ma tana farinciki ganin farincikin ɗanta, cikin zumuɗi ya fice daga falon ya nufi part ɗinsa. A ranar kasa bachi ya yi saboda farinciki, sai ya kwana yana istigifari da hamdala ga Ubangijinsa, a zatonsa da gaske Nawwara ta yafe masa har ma ta miƙo gaisuwar gunsa.   Around eight o'clock in the morning Mustapha ya fito part ɗinsa zuwa part ɗin Mom, sai dai hango motar abokinsa da ya yi yasa shi tsayawa baƙin ƙofar yana jiran ya ƙaraso. NAWWARA POV. Cikin rashin daɗin rai na shiga gida, Inna ma ta lura da haka sai dai bata cemin komai a zatonta tsakanina da Bilal ne wani abu ya faru. Misalin takwas da rabi na dare muka ji sallama a ƙofar gida, Inna ce ta amsa ni kuna idona na kan Noor take ta faman game baya gajiya. Sarai muryar Hajiya mahaifiyar Mustapha a ɗaki kunnena a sallamarsa ta biyu, gabana ya faɗi ba dan tsoro ba sai dan tunanin abunda yake tafe da ita. Inna ce ta unƙura ta fita sai kuma ta dawo ta ɗauki tabarma ta sake fita, sama sama nake jiyo firar da suke da dukan alamu yafiya take nemawa ɗanta abun mamaki har da su wa'azi da nuna ƙaddara, zuwa can kuma dai na ji Inna ta kirani daga inda na ke na amsa mata sannan ya miƙe na fita. Hajiyar ce zaune saman tabarma yayinda Inna take zaune saman kujerar mata ta tsakar gida. “Nawwara ce” Hajiyar ta faɗa tare da kunna fitilar wayarta ta haska fuskata. “Ina wuni?” “Lafiya ƙalau, ayi ta haƙuri kinji haka abubuwan duniya suke zuwa” “Allah ya bamu haƙuri” Daga haka ban ƙara cewa komai ba na miƙe tsaye na dawo ɗaki. Bata ɗauki tsawon lokaci ba tayi ma Inna sallama ta fice. Inna kamar jira take tana shigowa cikin ɗaki ta hau ni da masifa. “Wannan halin ba na ki ba ne Nawwara ba irin wannan tarbiyar muka baki ba, yafiya da afuwa ga wanda ya yi maka ba daidai shu aka fi ga musulmi, duk yadda zaki so Habiba ko ki nuna baƙincikinki akan mutuwarta be kai ni uwarta, tun da har na yafe kema ya cancancanta ki yafe, Ƙaddarace ni da ke duk ba mu wuce faɗawa a cikinta ba, yanzu da ace ɗan uwanki ne ya faɗa a wannan halin ko kuma ɗan ki Noor yaje yana neman yafiyar wata ba ta yafe masa ba zaki jidaɗi? Komai zaka yi ka riƙa kwatantawa da kanka” Tun da take maganar na ke hawaye, Inna ta min fahimta baibai, ta kasa gane irin zafin da ɓakincikin rashin yar'uwata da nake, ko da Habiba tana raye dole na ƙyamaci Mustapha saboda ya yaga mata rigar mutunci, tana ɗora min laifi akan Jibril saboda tana ganin kamar na zufafa da yawa, ni kou na san irin zafin da na ke ji idan na tuna wulaƙancin da ya yi min ya yi min ƙazafin zina a gaban iyayensa da iyayana yasa mutane unguwa suka kira ɗa na da shege ni kuma aka kira da karuwa, irin waɗannan mutanen ne take ganin na zufafa ƙiyayyata a garesu? “Ki yi haƙuri Inna, zan yi iya abunda zan iya na danne zuciya daga abunda take ji, dan Allah ki yi haƙuri kuma ki roƙa min Allah ya sassauta min abunda nake ji” Na faɗa ina ta kuka kamar zan haɗiye zuciya na mutu, sai Inna ta zauna kusa da ni ta dafani tana lallashina. Sama sama na samu bachi a daren ranar saboda kuka da na kwana ina yi ga kuma tunani ƴar uwata da ya dawo min sabo. Washe gari da wuri na farko bayan na gama raka'atayal fajir sai na jira aka tayar da sallah na masallaccin da ke kusa da mu bayan na gama na karanta azkar na safe, da ayatul kursiyu na fara A 'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem. Allaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwal-Hayyul-Qayyoom, laa ta'khuthuhu sinatun wa laa nawm, lahu maa fis-samaawaati wa maa fil-'ardh, man thai-lathee yashfa'u 'indahu 'illaa bi'ithnih, ya'lamu maa bayna 'aydeehim wa maa khalfahum, wa laa yuheetoona bishay'im-min 'ilmihi 'illaa bimaa shaa'a, wasi'a kursiyyuhus samaawaati wal'ardh, wa laa ya'ooduhu hifdhuhumaa, wa Huwal- 'Aliyyul- 'Adheem. sannan ɗora da ƙula'uzai Allahu ahad, Allahu assamad, Lam yalid walam yoolad, Walam yakun lahu kufuwan ahad. Qul a'aoothu birabbi alfalaq, Min sharri ma khalaq, Wamin sharri ghasiqin ithawaqab, Wamin sharri annaffathatifee al'uqad, Wamin sharri hasidin itha hasad. Qul a'aoothu birabbi annas, Maliki annas, Min sharri alwaswasi alkhannas, Allathee yuwaswisu fee sudoori annas, Mina aljinnati wannas. Sai kuma na karanta hasbiya ƙara bakwai Hasbiyallaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-'Arshil-'Adheem Sai kuma na karanta Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem.    Ƙafa uku. A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min sharri maa khalaqa   Sau uku Waɗannan addu'o'i ne na neman tsari matuƙar ka karantasu babu abunda zai same ka daga iska har tsafi har ma da wasu ƙwari masu cutarwa, bayan na gama na ɗora da azkar ɗin godiya ga Allah waɗanda ake son musulmi ya karanta safe da yamma. Sannan na rufe da shugabar istigifari wato Allaahumma 'Anta Rabbee laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, khalaqtanee wa 'anaa 'abduka, wa 'anaa 'alaa 'ahdika wa wa'dika mas-tata'tu, 'a'oothu bika min sharri maa sana'tu, 'aboo'u laka bini'matika 'alayya, wa 'aboo'u bithanbee faghfir lee fa'innahu laa yaghfiruth-thunooba 'illaa 'Anta. Yana na gama na yi salatin annabi ɗari istigari ba ɗari, sannan na yi hasbiyalahu sau ɗari huɗu da hansi, wacce ake karantawa a duk lokacin da mutane yake cikin matsala na halin rayuwa ko neman mafita, kamar neman aure warwarewa al'amura duk ka lamuncin karantawa zaka samu mafita cikin gaggawa. Ko da na fito har Sakina ta dama kamu, Inna kuma ta aiki Jamila da Noor su siyo ƙosai da suga, bayan sun dawo muka sha kunun har Inna sannan na kama kan Noor na yi mas addu'a irin wacce Annabi yake yi ma jikokinsa Hasan da Husaini U'eethukumaa bikalimaatil-laahit-taammati min kulli shaytaanin wa haammatin, wa min kulli 'aynin laammatin. Bayan na gama da Noor na karantawa Jamila sannan na suka kama hanyar makaranta tare da Sakina. Ni kuma na tashi na shirya cikin wata atamfar roba na saka Hijab ɗina mai kama da atamfata, sannan na zo yi ma Inna sallama da karɓar kuɗin Napep. “Inna zan tafi aikin” “Allah ya tsare Nawwara Allah ya miki albarka, ban miki faɗa jiya dan wani abun ba sai dan ki gyara” Ta faɗa tana miƙo min ɗari biyu. “Ko babu komai kika min faɗa ba zanga laifinki ke uwace kina da damar ki yi duk yadda kike so da ni, kuma abunda kika min faɗa akai kina da gaskiya, ni kaina na san ina da buƙatar ganin na canja ta yadda zan cigaba da rayuwa na manta komai, ni dai fatana ki kasance mai min addua da kuma haƙuri da hali na miki alƙwarin zan canja” “Addu'a ai wajibi ce ga dukan uwa ta yi ma ƴaƴanta, Allah ya miki albarka ya baki miji na gari wanda zaki ji daɗin zama mai son ki tsakani da Allah” “Amin Inna” Na faɗa ƙasan zuciyata na ta kira min Bilal, tun jiya be kirani ba kuma be dawo ba ni kuma ban kira ba. Sai da na fito daga gidan sannan na soma kiran Bilal amman wayarsa a kashe, hakan yasa ni jin babu daɗi zuciyata na raya min kamar fushi yake da ni, daman na san dole sai ya zargi wani abu ganina tare da Mustapha. Na yi sa'ar samun napep da wuri amman sai da ya sauke mutun biyu sannan ya ƙarasa da ni inda zai kai ni, koda na isa tara saura kwata tunda na doshi kamfanin zuciyata ta soma rayamin wasu abubuwan sai sai tunawa da maganganun Inna yasa na kawar da komai na nutsa kai cikin kamfanin, na yi mamakin yadda kowa yake kallona kamar wace suka ga baƙuwar fuska, wataƙila an faɗa musu wani abun ne akai na ko kuma dan na yi latti suke kallona oho, ban damu da cire Hijabina ba a ganina yanzu ai an canja min aiki dan haka bana buƙatar cire Hijabi duk kuwa da kasancewar ban taɓa ganin kowa da Hijabi ba a kamfanin. Har na doshi lifter tunani na ke irin kallon da Jibril zai min da kuma irin wanda zan yi masa idan har na yi aiki a gurin. Ina dosar office ɗinsa gabana ya shiga faɗuwa, ba faɗuwar tsoro ba ko fargaba ba faɗuwa irin ta maƙiyi zai yi arba da maƙiyinsa. Kamar wacan zuwan nawa na farko haka na yi saka buɗe min, yau ma sai da aka tantance ni a cikin ɗan ƙaramin gilashin nan mai bayyana komai na jikin mutun sannan aka bani damar shiga Office ɗin, ban ji ya ce na aje wayata da ƴar ƙaramar jikar da ke hannuna ba, ni kuma ban aje ba na shiga da abu ta, shi ɗin ne dai mutumen da na taɓa tararwa wacan karon. Tun kamin na yi magana ya rigani. “Please go in” Ya doshi ƙofar da ya nuna min gabana na ƙara faɗuwa, ajiyar zuciya na sauke sannan na kai hannu ya tura ƙofar, ba tare da na waigo ba na maida ƙofar na rufe ina kallon bayansa, kasancewar ya bani bayana ne domin shi yana tsaye ne jikin window ya maido hannayensa baya yana kallon waje. Har yanzu akwai tattoo ɗin taurari a bayansa, mamaki ya kamani sosai ganin sunana rubuce cikin style ɗin wasu harufa tattoo a hannunsa, nasan be san da shigowata ba ko da yake yaji an buɗe ƙofa, ni kuma na gagara kiran sunansa sai kawai na ce “Excuse me” Da sauri ya juyo ya kalleni, irin kallon nan na mamaki sannan ya yi hanzarin warware hannun rigarsa ya nufi ƙasaitacciyar kujerarsa ya zauna. “Kin zo latti, ba a faɗa miki 8am zaki riƙa zuwa ba?” Na yi shiru ban amsa masa ba. Sai ya soma kallona daga sama zuwa ƙasa. “Ba a saka mana Hijabi a nan next time ki san irin tufafin da zaki saka” “Ba za'a saka muku Hijab ba saboda ku ba musulmai ba ne?” Ya yi murmushin gefen fuska sai ya taso daga inda yake ya doso ni yana faɗin. “Aiki muke a nan ba addini ba” “Da wannan aƙidar ka cuci kanka, kai kana ganin kamar babu ruwan addini ko Allah a cikin abunda ya shafi aikinka ko rayuwarka ko? Kana da mummunar aƙida Jibril” “Ko?” Ya tambaya yana ta matsowa kusa da ni ni kuma ina matsawa baya, har sai da na kai jikin ginin ɗaki, sosai ya matse ni yana kallon fuskata idanuwa cikin nasa idon, har na buɗe baki na yi magana sai ya duƙa ya kama zanen atamfata ya murja. “Me kake ƙoƙarin yi ne?” Ya miƙe tsaye bakinsa kusa da nawa kamar zai haɗe bakinmu. “Dirty mind, ni ba ɗan iska ba ne” Ya faɗa kaɗan kaɗan kamar mai raɗa, sannan juya ya doshi kujerarsa. Hakan ya bani damar lumshe ido na sauke ajiyar zuciya, jin abunda yake faɗa yasa ni buɗe idon ina kallon yadda ya haƙimce saman kujerarsa mai juyawa yana min magana cikin isa. “Dan me za ki saka min tamfar roba?” “Ba kai na sakawa ba, kaina na sakawa” “Miyasa kika yi rejecting kuɗin da aka baki ki siye wasu tufafi?” “Bana da buƙata, tufafin jikina sun isheni” “Saka ƙananan tufafi marar daraja na zubarwa kamfanin da ƙima, ya kamata ki san wannan” Ya faɗa fuskarsa babu alamun dariya, sannan ya danna telephone ɗin da ke kusa da shi ya yi magana da halshen nasara. “You can go now” Sannan ya kalleni. “Tea please” Tsaye na yi a gurin kamar an dasani, shi kuma ya bawa banza ajiyata yana ta aiki da system ɗin da ke gabansa. Waige-waige ɓa farayi har na hango teburin dake ɗauke da kayan tea na doshi gurin zuciyata na ta raya min maganar ɗazu, wai shi ba ɗan iska ba ne, wato ni ce ƴar iskar ko? Har na haɗa tea ya kawo masa maganar bata daina min yawo a kunne ba. “Ƙarfe uku zaki tashi aiki, idan kuma har muna da meeting ko aiki da yawa zaki iya kaiwa har dare, kuma a shigo min office haka nan kawai, saboda karki tararda ni cikin wani yanayi, har sai idan ni na kiraki, idan wata magana ce akwai telephone a gurin dannawa kawai zaki yi ki kirani” Ban ce masa komai ba na juya na fita, zuciyata na mugun ƙuna, anya zan iya jurewa na yi aiki a ƙarƙashin Jibril? Sai da na ƙarewa office ɗin kallon sannan na zauna a saman kujerar mai juyawa, komai daki daki na bishi ina kallon da dubawa sannan na kula da ƴar danjar da ke ƙara a gefen teburina, sai kuma computer ta soma nuna min mutumen da ke waje, wato Bilal yana riƙe da wasu takardu. Gabana ya faɗi sosai sai na soma tunani da wace fuskar zan kalli Bilal shi kuma wane irin tunani zai min.? JIBRIL POV. He's just can't believe Nawwara tana ƙarƙashinsa a yanzu, wani irin daɗi yake ji yana ta yi ma Allah hamdalla, cike da so da ƙauna yake kurɓa tea da ta haɗa masa yana wani lumshe ido. Jin ya yi ba zai iya jure jin wannan farincikin shi kaɗai ba, ya ɗauki wayarsa ya danna number Siraj dan labarta masa. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 3⃣9⃣ Ba ni da wani zaɓi face na bashi damar shiga, domin nasan komai dare daɗewa dole zai sani. Kamar yadda Rabi ta nuna a wacan karo haka na danna sai ƙofar ta buɗe masa, a ta biyu mai gilashi muka riƙa kallon kallo ni da shi. Ƴar ƙaramar danjar sai tsuwa take tana nuna min agogon hannunsa da pose ɗin kuɗinsa sai kuma takardun da ke hannunsa. Ban damu da ce masa ya aje ba na sake dannawa ta buɗe ya shigo yana ta kallona kamar wanda be sanni ba. Hanzarin miƙewa na yi tsaye Cikin yanayin damuwa na zan masa magana sai ya rigani “Takardun nan zaki kai wa oga ya saka hannu” “Na yi ta kiran wayarka ban samu ba, miyasa ka kashe wayar” “Zamu yi maganar anjima let's do this now” Yawun bakina na haɗe kana na ɗaga masa kai sannan na karɓi takardun kai tsaye na nufi office ɗin Jibril duk kuwa da kasancewar ya yi min gargaɗi ɗazu akan na daina shigowa ba noticing, waya na tarar yana yi fuskarsa shimfiɗe da farinciki tea da na haɗa masa yana hannunsa sai kurɓa yake, yana ganina sai ya yayi hanzarin yanke wayar ya kalleni, sai dai be ce min komai ba jira yake ni na fara masa magana. “Hannu zaka saka a waɗannan takardun Bilal ne ya kawo” Na faɗa kamar mai shirin yin kuka, domin har ga Allah ban jidaɗin yadda na ga fuskar Bilal kamar baya cikin farinciki. Saman tebur na aje masa takardu sai ya duba ya saka hannu sannan ya miƙa min. Ni kuma na karɓa na juyo jiki ba gwari na miƙawa Bilal takardun sai ya karɓa yana faɗin “Congratulations” Ni dai ban ce masa komai ba har ya juya ya isa gurin ƙofar sai ta buɗe masa da kanta ya fice. Faɗuwa na yi saman kujera da ke kusa da ƙofar ta zaman baƙi ina sauke ajiyar zuciya, har ga Allah na san dole ne sai Bilal ya zargeni amman ta yarda zan fahimtar da shi ne aiki tasowa na yi na dawo saman saman kujera ko kuma na ce kujerar office ɗin na zauna zuciyata a jagule, ina ta tunani mafita sai bachi ɓarawo ya yi gaba da ni. Babu komai a mafarkina sai Jidda da Mustapha, wai ya mata fyaɗe kuma ya kasheta ga ƴan sanda da mutane cike a gidansu, ni kuma sai aikin kuka na ke ina kiran Mustapha, abunda ban sani ba ashe har a fili na ke kiran sunansa. “Mustapha...” Abunda na furta kenan daga farkowatawa, sai na ga Jibril tsaye a kaina yana kallona, hakan yasa ni saurin zabura na tashi. “Me zaka min?” “Me kike tunanin zan miki? Mayaudariya kina spn Mustapha kina yaudarar Bilal ko?” “Ina ruwanka babu ruwanka da rayuwata” Sai ya mire baki tare da ɗaga kafaɗunsa sama alamar abun be dame shi ba. “Tashi muje meeting, baki da aiki sai bachi abunda ya kamata ace ke zaki faɗa min lokacin meeting ɗin ya yi amman wani ne daga can waje yake sanar da ni” Na tashi tsaye idona kan agogon office ɗin da ke nuna ƙarfe goma sha ɗaya na safe, shi ya fara fita ni kuma ina binsa a baya har muka shiga Lifter, a nan ya miƙa min ƙaramar jakar da ke hannunsa. “Kin duba akan me zamu yi meeting ɗin?” Na girgiza kai alamar ban sani ba, sai kawai ta cigaba da kallona ko kunya baya ji, ni kuma na yi kamar ban ganshi ina ta kallon numbobin lifter, sai dai haka be sa ya ɗauke idonsa daga kallon da yake min ba har lifter ta tsaya a hawa na uku ta buɗe da kanta, sai na yi saurin fita duk da ban san inda zamu shiga ba, sannan shi ma ya fito sai ga Rabi ta tare mu ta karɓi layin wayata wai zaa saka min numbobin ƴan ƙamfanin ta yadda zan gane duk wanda ya kirani. Ko da muka shiga ɗakin taron mun tarar da mutum biyar wannna abokin nasa Siraj sai kuma Zinatu da wasu ɓakin fuska uku, yana shigowa duk suka miƙe tsaye ya miƙa ma baƙin fuskar hannunsa suka gaisa sannan ya gabatar musu da ni. Ɗaya daga cikinsu ne wanda na ke zaton ba musulmi ba ne ya miƙo min hannu dan mu gaisa yana faɗin sunansa. “Divid Sam” Sai Jibril ya yi saurin miƙa masa na sa hannun a ƙaro na biyu, ya kuma amsa masa kamar ni ɗin. “Nawwara” Ni kuma na zauna a kujerar da ya nuna min, ban maida hankalina kan abunda suke tattaunawa ba, sai dai hakan be hanani fahimtar cewa wani kamfanine yake son siye, har aka yi meeting ɗin aka gama Siraj da Zinatu idonsu na kaina duk wani motsi da nake suna kallona har na soma jin babu daɗi. Tare muka fito daga ɗakin taron sai ya koma daga bayana yana kallon tafiyata, hakan yasa ni ƙara sauri na shiga tifter, sai da tana daf da rufewa sannan ya ƙaraso ya shigo, still yanzu ma idonsa na kai, da alama dai kallona daɗi yake masa, ko kuma yana min ne dan kawai na tsargu, sau ɗaya na ɗago na kalleshi sai yayi min kwarjini sosai na yi saurin sadda kaina ƙasa ban sake kallonsa ba har Lifter ta sauke mu a hawa na biyar, har na miƙa jiki na fita sai ya riga fita. “Baki iya competition da ni” Ya furta daidai lokacin da zai fice, a nan na kalli bayan kansa sannan na fito muka doshi office ɗin, da fari na tsaya tunanin wa zai buɗe mana tun da ba mu bar kowa a ciki ba, muna isa sai kawai naga wata ƙaramar na'ura tana ɗaukar fuskarsa, sai ƙofar ta buɗe masa ya shiga, ina zuwa na shiga sai wani jan layi ya shata yana ta ƙara. “Ki tsaya a nan karki raunata kanki, ba zaki iya shiga yanzu ba saboda bata tantance fuskarki ba” Bayan ya shiga ciki da kamar minti biyu sai ƙofar ta buɗe min. Ina shiga ya jawo ni gaban computer ta ɗauki hotona ya saka sunana sannan ya juya ya shige Office ɗinsa. Ina zaunawa idanuwa suka kai kan agogon Office ɗin na ga ɗaya da kwata, lokacin Sallah azahar ya yi, wata ƙofar da ke cikin Office ɗin na nufa ina taɓawa sai ta soma ƙara tana nuna min na saka password, ta biyu kuma ina turawa na ga toilet, daman shi na ke nema, alwala na yi na fito na d8ba ko'ina na gurin babu carpet ɗin Sallah sai na shimfiɗa ɗankwalina na yi dashi bayan na gama, na nufi Office ɗinsa dan tunatar da shi lokacin Sallah ya yi. Zaune na sameshi yana ta aiki a system ɗinsa, kamar jira yake na shigo mayun idanuwansa suka dawo kaina har na ƙaraso kusa da teburinsa. “Lokacin Sallah ya yi” Iskarka bakinsa ya busar sannan ya kalli tsadadden agogon hannunsa. “Idan na gama aikin nan zan yi” “Har sai ka gama aikin? Jibril mi ka ɗauki sallah ne? Sallah ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunan addinin musulunci, kuma ita ce gimshiken addinin musulunci. Barinta kafirci ne da yake fitar da mutun daga cikin addini, babu addini babu musulunci ga wanda ya bar sallah namiji ko mace!” “Ba fa kafiri ba ne ni, ina sallah” “Na san ai kana sallah, amman ba akan lokacinta ba, ina mamakin avunda zai ɗaukewa mutun hankali har ya watsar da bautar Ubangijinsa, kasan irin azabar da Allah ya tanadarwa masu wulaƙanta sallah kuwa? Jinkira sallah lokacin ya fita ba tare da wani uzuri na shari'a ba, wannan tozarta sallah ne kamar yadda Allah ya faɗa a suratul Maryam aya ta hansi da tara zuwa sitti : Sai mutanen banza suka maye bayansu, suka tozarta sallah, suka bi sha'awace-sha'awace na saɓo; to ba da daɗewa ba zasu haɗu da gayyu wato wani gwalolon azaba a cikin wutar jahannama, sai fa wanda ya tuba. Farkon abunda za a maka hisabi da shi a cikin ƙabarinka sallah ce, kuma ita ce zata tayaka zaman ƙabari (Allah ka bamu ikon tsaida Allah akan lokaci 🙏😭)” Tun da na soma maganar yake kallona fuska a sake, da alama na burgeshi ne ko kuma mamakina yake oho, but to my surprise sai na ji ya ce “Thank you, da kika tunatar da ni, babu wanda ya taɓa faɗa min wannan, inshallah zan gyara ko dan na samu damar rayuwa da ke a aljanna” “Aljanna kowa gidansa daban, na Jibril daban haka ma na Nawwara daban” Dariya ya yi kamar ba shiba ya miƙe tsaye ya nufi wata ƙofar da nake zaton banɗakine a ciki. Ni kuma na juyo na fito, sai na samu computer tana nuna min Rabi da ke waje, sai da na zauna sannan na buɗe mata sai ta shigo fuskarta a sake kamar ko yaushe. “Ga sim ɗinki anyi miki dukan abunda ya dace” “Thank you, amman yanzu idan ina son na kira general meeting a madadin Jibril ya zanyi?” “Sir Jibril zaki ce ko kuma mai gida” Ta faɗa sannan ya buɗe wani ɗan ƙaramin littafi dake gefen teburin ta soma nuna min “Wannan number zaki kira, idan an ɗaga ba sai kin tsaya gaisuwa ba, kawai ki ce Sir Jibril ya ce haɗa masa general meeting, idan emergency ne sai ki faɗa, idan kuma meeting ɗin yana da date da time sai ki faɗa, zasu haɗu a hawa na biyu room 24 domin shi ne kawai ɗakin da yake iya ɗaukar yawan ma'aikatan da ke kamfanin nan, idan har ya yarda ki yi magana a madadinsa zaki iya zuwa kiyi idan kuma shi zaiyi da kansa sai ki raka shi” “Thank you so much” “Your welcome” Sannan ta juya ta fita, ni kuma na saka number da ta nuna min a telephone zuciyata na ta raya min kar na yi, idan har na yi haka na yi karanbani, wata zuciyar kuma na nuna min idan har na yi haka na taimaiki Jibril da rayuwarsa har da da sauran ma'aikatan. Sai kawai na dannan kiran na ce ina buƙatar a haɗa min meeting ɗin gagawa, ni kuma na tashi na fita riƙe da wayata na nufi lifter, ina sauka hawa na biyu na soma ƙirga ɗaki, har na hango ɗakin da mutane suke shiga. Tsayawa na yi sai na kasa ƙarasawa ina ta tunanin ma yadda zan ce musu abunka da wanda be saba ba, sai kawai na juya na koma lifter, na yi mamakin yadda ina isowa bakin ƙofar office ɗin sai kawai ta buɗe min. Ina shigowa na samu Jibril tsaye yana jiran shigowata. “Akan mi kika kira general meeting kuma emergency?” “Am sorry” “Ba hakuri na ce ki ba ni ba, dalili zaki faɗa min” “Da na yi ƙoƙarin na faɗa musu idan lokacin sallah ya yi kowa yaje ya yi sallah, sai kuma na ga kamar na maka karanbani” “Karabanni ne mana, ba yau yau kika kama aikin ba?” “Am sorry” Na faɗa cike da nadama sai ya matso kusa da ni. “Is okay, zan faɗa musu da kaina indai har haka kike so, follow me” Yana faɗar hakan ya nufi ƙofar fita na bishi, tare muka isa da kansa ya faɗa musu cewar a yanzu da lokacin sallah ya yi kowa ya aje aikin da yake yaje ya yi sallah, daman akwai masallaci a cikin kamfanin. A yanayin yadda fuskokin musulmin ma'aikatan suka nuna sun yi farinciki sosai kuma sun nuna jindaɗinsu har ma da yin godiya. Ina tsaye gefen Jibril Bilal na kallona kamar zai cinye ni, irin kallon nan da mutum zai kasa gane manufarsa sai hakan yasa duk na bi na tsargu, mu muka fara fita sannan sauran suka fito. A bayan na tsaya ina amsa waya shi kan gogan na ku tuni ya yi nisa tare da Siraj. Dpo ne ya kirani wai an bashi number ta daga gida, saboda ya zo be sameni ba kuma yana son magana da ni, a ina nake ya zo ya tafi da ni. “Na kusa dawowa aiki, idan na dawo zan kira ka” “Okay” Daga haka na kashe wayar, na cigaba da tafiyata. Ko da na shiga office ɗin ƙpfar Office ɗin Jibril tana buɗe ina hango abokinsa sai dai ban san mi suke tattaunawa a akai ba har sai da na zauna sannan na soma jiyo muryar abokin nasa. “Be kamata ka sake mata har haka ba, so ai ba hauka ba ne....” Sai kawai na ji an ba ƙofar gam an rufe, bayan wani ɗan lokaci sai abokin nasa wato Siraj ya fito kamar cikin ɓacin rai ya fice ba tare da ya kalli inda na ke ba. Takardar da ke gabana na ɗauka na duba sai na ga lokacin meeting ɗinsa da wani Hon Usman Dahiru ya yi, a maimakon na kira sai kawai na tura ƙofar na shiga. Saurin saka bayan hannunsa ya yi ya kare hancinsa, sai dai abunda be sani ba abunda ke gabansa a farar takarda mai kamar hoda ya taɓa masa hannu, juyawa na yi zan fita sai ya kira ni. “Naj” Ina juyowa ya ce “Madarace na ke sha ina fama da ulcer” Ni dai ban ce masa komai ba na juya na fita, ina shirin zama sai gashi na fito daga office ɗinsa ya biyoni. “Madara ce Naj” Nan ma kallonsa kawai na tsaya yi, sai ya ɗaga hannayenasa sama domin shi ma yasan ban yarda da shi ba. “Fine cocaine ce shikenan?” “Allah ya wadaranka Jibril, kullum abunka gaba yake ba baya ba, har yanzu akwai tattoo a jikinka, yanzu kuma cocaine kake sha bayan neman matan da kake? A haka iyeyenka za su nuna ka a matsayin ɗansu ɗan ka kuma ya nuna ka a matsayin uba? Iya yau kawai na zauna da kai, amman na ga halaye masu marar kyau a tare da kai, wasu baka canja ba wasu kuma sabbi ne, na yi nadamar da na taɓa saninka a rayuwata Jibril...” Na faɗa cikin hawaye da kuka na ɓakinciki da jin zafi, yanzu irin wannan mutunen ne na haihu da shi? Ina baƙincikin da ya kasance uban Noor sam, ɗa na be yi dacen uba ba, dan haka ban zan nuna masa ko kuma faɗa masa cewar Jibril ne ubansa na gaskiya ba. “Bana neman mata Naj, Aisha ce kawai na ke taraiya da ita ma kuma na daina na tuba, cocaine ɗin ma akwai dalili shanta da na ke, amman na ji kamar kin yi wata magana, na ji kin ce ɗa me kike nufi akwai abunda ya kamata na sani ne?” Ganin yadda yake matsowa yasa na yi hanzarin miƙewa tsaye har ina ɗauke numfashi, shi kuma yana ta kallona kamar mai karantar abu a fuskata, sai takowa yake har sai da ya kowa daf da ni...! “Ina da ɗa ko Nawwara...?” ____________________________________ Zaku ga wasu kalmomin kamar ba a ƙarasa ba wasu kuma ana mistakes da yawa ana dai akwai errors or omissions a ciki, hakan yana faruwa ne saboda rashin editing, idan har na ce zan tsaya editing zai ɗauke ni tsawon lokaci ban yi updated ba domin editing ya fi bani wahala fiye da typing. Fatar zaku fahimta kuma zaku min uzuri 🙏 FOLLOW ME VOTE COMMENT SHARE *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @Khadeeja_Candy *Dedicated to My Asmee* 4⃣0⃣ JIBRIL POV. “Ee kana da ɗa” Shine kawai abunda Jibril yake son jin ya fito daga bakin Nawwara, wani irin bugawa zuciyarsa take da sauri, ido cikin ido yake kallon Nawwara tsantsar gaskiyarta yake son ganewa, yadda ta saki baki tana kallonsa shi kansa yasan subul da baka ta yi, yadda take numfashi yake karantar da shi irin faɗuwar gaban da ke ranta. “Kana da ɗa mana ƴaƴama zan ce, ba ka auri Aisha ba ta haifa maka ƴaƴa, na tuna ai tun kamin ka aureta ma ta samu ciki, wanda kake labarwa abokinka farinciki fal a ranka, kuma bayan ita maybe ka ƙara auren wasu matan sun mahaifa maka ƴaƴa ko kuma ka musu cikin shege” Lumshe ido ya yi ya haɗe yawun dake bakinsa ya dunƙula hannunsa ya matse sosai kamar zai dake, har ga Allah baya jindaɗin kalamanta, duk lokacin da ya tuna rayuwarsa ta baya yana jin babu daɗi ballr kuma ace ita ce da kanta take tuna masa da wannan, hakan na karantar da shi cewar ba zata taɓa yafe masa ba kuma ba zata manta ba. “Ina cikin da na barki da shi?” Ya faɗa yayinda da buɗe idonsa da suka rine suka yi ja sosai. “Cikin da ka kace ba naka ba ne? Ai na zubar domin ba zan iya ɗaukar shege a cikina ba” “Ba zaki iya zubarwa ba, ba zaki iya kashe rai ba ko da kuwa ɗan shegen ne da gaske” Kallonsa ta yi sai ta yi murmushi. “Ashe kai da kanka ka san ba ɗan shege na ɗauka a cikina ba, amman ka ce ba naka ba ne ka haɗa hotona da hoton wani namiji wanda ban taɓa sanin inda ya fito ba, saboda kawai kana neman rabuwa da ni? Da na dawo da ciki sai suka kira da karuwa wannan dalili yasa na zubar da cikin” Ta faɗa hawaye na fitowa daga idonta fuskarta kuma ɗauke da murmushi. Wani irin ƙuna yake ji a cikin ransa, zuciyarsa zafi take kamar an kunna masa wuta, yana jin rashin kyautawa a duk lokacin da ya tuna abunda ya aikata mata, tabbas yanzu ya yarda akwai wawanci, shashanci a tare da shi, duƙursawa ya yi ƙasan guiwoyinsa ya kama Hijabinta sa gashi yana hawaye. “Dan Allah Nawwara ki yi haƙuri dan Allah ki yafe min” “Daman na faɗa, saboda ka riƙa neman yafiyata yasa ka cilasta min aiki a tare da kai” “Ba dan haka ba ne Nawwara, saboda na samu kusanci da ke, ina sonki sosai Nawwara” “Ni kuma bana son ka, bana kaunarka Jibril” “Na sani” Ya fada yana hade maganarta ciki da dacin rai. Zaunawa ta yi shi kuma ya mike tsaye na koma office dinsa, sam be gamsu ba shi da tsakaninsa da Nawwara ba, tabbas ya bar ta da ciki kuma ya san ba zata iya zubar da cikin ba. ‘Ta haife shi, idan har babu haihuwa tsakamina da ita mi zai sa ta yi wannan maganar?’ Shine abunda zuciyarsa take ta raya masa, wayarsa ya dauka ya kira Siraj bugu biyu Siraj ya yi picking. “Siraj ina son kasa a bincika min duk wani abu da ya shafi Nawwara, akwai da a tsakanina da ita Siraj kasa a abincika min” “Okay” Daga haka ya kashe wayar ya kira Abbah, sai da ta dade tana ringing sannan ya dauka yana kiran sunansa. “Hello” “Jibril” “Abbah ina wuni” “Lafiya kalau ya aiki?” “Al-hamdilillah, Abbah akwai da tsakanina da Nawwara” “Waya fada maka?” “Ita ta yi subul da baka” “Kaje gidansu ko? Bana fada maka karka je ba” “Ban je ba, Abbah a nan kamfanin take aiki” “How when?” Ya kwashe komai ya fada ma Abbah amman be fada masa zance ya cilas mata aiki a tare da shi ba. Abbah ya yi shiru kamar mai tunanin abunda zai ce. “Abbah we're meant to be” “Kana son ta ka saketa? Bana son ka zama cikin irin mazan nan da ake fada Jibril ni yanzu ko wani aure ban yarda ka kara yi ba sai ka gane kuskurenka” “Wallahi Allah Abbah na canja zan zauna da Nawwara zama na tsakani da Allah ba zan taba sakinta ba, Abbah ita kadai ce take so na tsakani da Allah” “No ba yanzu, kuma na fada maka karka kuskura taka kafarka gidan nan” “Tau Abbah ba zan yi ba, amman da Mahaifiyata tana da rai da ta roka min kai ka amince, rashinta ne yasa na rasa komai, ba ni da mata ba ni da ɗa sai kai kadai kai kuma ka kasa fahimta ta” Yana fadar haka ya kashe wayar ya aje saman table, sai ya dora hannayensa saman table din ya dafe kansa ya dinga rusar kuka kamar karamin yaro. Kuka yake sosai kuka ina zai saka kanshi, kuka neman mafita, be san mahaifiyarsa ba domin be tashi tare da ita ba, amman yana jin zafin rashinta kamar yanzu ta mutu ta barshi, ji yake ina ma tana raye da yanzu ta roka masa Nawwara ta yafe masa, ta shiga cikin lamarinsa ta gyara masa komai, be taba jin zafin rashin mahaifiya ba kamar yau. Hannunsa yasa ya janyo aljihun table din da take zaune ya dauko hoton wata matashiyar mata mai kama da shi yana ta kallonta yana kuka kamar mace. Kuka ya yi sosai har sai da ya soma jin kamar jiri yana dibarsa sannan ya tashi ya shiga bathroom ya wanke fuska ya dawo ya dauki ruwan freezer ya sha, sai ya dora gorar saman freezer ya nufi kofar fita. Ko da ya fito Nawwara na zaune tana duba abubuwan da suke cikin computer, ya samu thirty seconds yana kallonta mugun burgeshi take gani yake a duk duniya babu wata mace da ta kaita daraja da kima da kuma kyau, ji ya yi kamar yaje ya rumgume kamkam a kirji, sai dai yasan ba shi da wannan damar. Karasa ya yi inda take yana kallonta da manyan idanuwansa masu kamar madara kamar zai cinyeta. “Lokacin cin abinci ya yi, a nan zaki ci ko restaurant zamu je?” “Ka ce min idan uku ta yi zan iya zuwa gida idan har babu aiki da yawa, kuma na ga yanzu uku sauran kwata” Ta fada ba tare da ta kalleshi ba dan gaba daya ta tattara hankalinta ya maida kan computer. “Ee amman a ka'ida karfe biyu da rabi zuwa uku ma'aikata suke zuwa cin abincin rana, taso muje restaurant” Mike ta yi tsaye yana gaba tana biye har suka sauko kasa gaba daya, tare suke daga kafa kuma su aje tare har suka isa restaurant din dake cikin kamfanin, wani abun da ya bawa Nawwara mamaki suna shiga sai duk wanda ke gurin ya tashi ya fita, aka barsu su kadai daga ita sai shi. Karasa ya yi can guri wani teble wanda shi kadai yake zama akansa ya zauna ita ma ta zauna a kujerar dake fuskantar tasa. Waiter ne ya zo da sauri yana tambayar abunda za a kawo musu. “Fried rice and chicken soup” “And drink?” “Fanta” Ya juyo gurin Jibril. “And you Sir” A hankali ya juyo ya kalleshi ba dan yasan a abunda yake tambaya ba sai a lokacin ya kula da shi domin gaba daya hankalinsa yana gurin Nawwara. “And you Sir” Ya sake maimatawa ganin kamar be ji abunda ya ce ba. “Just water” Nawwara ta masa wani kallo “Ni ladai zan ci abincin kenan?” “No” Ya yi saurin amsa mata sannan ya sake kallon mutumen ya ce “White rice and pepper soup” “Drink?” “Lemun juice” “Okay” Ya juya da sauri ya koma inda ya fito. Cikin yan seconds sai ga abincin an kawo musu, Nawwara ce ta fara dan ta nuna masa ita fa cin abincin kawai ya kawota ba komai ba, shi kan kasa taba abincin ya yi ya tsura mata ido kamar mai kirga lomomin da take, zuwa can ta dago ta kalleshi, sai ya yi saurin daukar spoon ya soma wasa da abinci dan har ga Allah baya jin cin abincin, kawai saboda ita ta samu ta ci ne yasa shi zuwa ko ba komai hakan zai kara masa kusanci da ita, yadda take cin abinci mugun burgeshi take ya tattara hankalinsa gaba daya ya mika mata, har ta gama cin abinci be yi ko da loma daya ba. Wani abun da ya ba waiters din mamaki biya bill din abunda be taba yi ba, idan ba ya ci abinci a guri sai dai pa dinsa ya biya ko da kuwa shi da wani suka ci, amman yau shi ya biya da kansa sannan suka fita. A lifter ma kallota yake ta yi zuciyarsa na mugun fisgarshi kamar zata fasa kirjinsa ta fito. “Can i hug you?” Ta juyo da sauri ta kalleshi kamar yadda yake kallonta, idanuwansa sun yi fari kal har wani ruwa ya kwanta a ciki. “Baka da hankali Jibril, ka rumgume ni muharramarka ce? Ko dai ka dauka kamar Aisha na ke ne? Gaskiya kana bukatar komawa makaranta ka fahimci addini sosai” “Am sorry” Ya furta yana dauke idonsa daga kallonta so zai samu sauki zuciya, tare da danke hannunsa ya matse sosai. Suna shiga Office ya wuce Office dinsa ya zauna saman kujera ya dora hannunsa saman goshinsa ya rufe ido yana sauraren bugun zuciyarsa. Bayan an mintuna Nawwara ta shigo Office din rike da jakarta. “Ni zan wuce” Bude ido ya yi ya kalleta sai ya dauki wayarsa ya kira direbansa, yana yin picking. “Get ready” Yana fadar haka ya kashe wayar, da kansa ya dauki akwatinsa ya saka laptop dinsa da tardunsa sannan ya mika mata jikar. “Aje saman teble” Sai da ya aje sannan ta dauka suka. “Ni fa gida zanje fa naga garin hadari ma ya hadu” “Na sani a ka'idar kamfanin nan as you are my pa dole ni zan saukeki gida ko kuma direban kamfanin nan” Ya yi tunanin zata musa masa ne, sai dai shi ba ya yi ba ne dan kawai ya kara kusanci da ita, haka dokar kamfanin take. Tare suka fito duk mai son kallonsu sai idan sun bada baya sannan ake daga ido a kallesu domin sun san abunda Jibril ya fi tsana shine kallo. Ko da suka fito daga cikin kamfanin har an fara yayyafi motar da Jibril zai shiga kuma tana fake daidai bakin kamfanin, direban na ganinsa ya bude masa gidan baya da sauri yana kara masa umbrella, shi kuma sai ya zagaya ta wacan bangaren ya budewa Nawwara dan baya son ta shiga gaba, abunda ya bawa direban mamaki, ba tare da tunani komai ba ta shiga ta zauna, sai ya maida kofar ya rufe sannan ya zagayo ya shiga direban ya rufe masa, sai ta dora akwatin a tsakiyarsu ta maida hankalinta gurin gilashin motar tana kallon yadda ruwan sama ya soma sauka da karfi. “Guiwa locos” Ya fada yana kallonta, sai direban ya fisgi motar kamar ba ruwa sama ake ba, har aka shiga cikin unguwarsu bata juyo ta kalli inda Jibril yake ba, shi kuma idonsa na kanta, a hankali ya kai hannu zai taba hamnunta sai a ya yi dai dai da juyowarta tana fadawa direban inda zai aje ta. Hakan yasa shi saurin janye hannunsa ya danke ya maida kallonsa gurin gidajen da suke unguwar da yadda mutanen suka fake saboda ruwa. “Ya isa” Direban na tsayawa ta bude motar zata fita sai ya yi karaf ya ce “Akwai ruwa sosai ki dan jira a rage” “A'a” “Tahir kara mata lema” “A'a” Haka ta bude motar ta saka kafafunta cikin cabon da ke gurin tana tafiya ruwa na dukanta, sai da ya daina hangota sannan ya bude motar ya fita ya zagayo gefen da ta fito yasa hannunsa ya kwashi kasar da ta taka wacce ta fitar da sawon kafarta ya danke a hannunsa sannan ya koma cikin motar. “Gida” Kai tsaye direban ya nufi Sama road da shi, a hanyar ta tafiya ce ya fiddo wayarsa ya jira Rabi. “Zan aiko miki da kudi duk abunda ya kamata ki siye, sai ki ka a addiren da zan turo miki yanzu amman sai kin tambaya saboda ban ga ainahin gidan ba” Daga haka ya kashe wayar, har suka isa kasar na jinke a hannunsa ji yake kamar Nawwara ce ya rike, suna isa ya fita motar direban na tara masa lemar ya daga masa hannu alamar ya bari. Falonsa ya shiga da hannu daya ya cire kayan jikinsa faffadan kirjinsa ya bayyana muscle din jikinsa duk suka fito real namiji, sai ga karensa ya zo da gudu yana kada masa bindi, shi kuma be kula shi ba ya nufi wata kofar ya bude ya shiga harabar gidan dake can ciki, kwantawa ya yi saman tile din ya shafa kasar a kirjinsa ya ware hannayensa ya lumshe ido ruwan saman na dukansa. NAWWARA POV. Sai da na tabbatar ba zasu hango ni sannan na hada da gudu ina ta tunanin subul da bakan da na yi, da yanzu ya gane ya zanyi kenan? Gaskiya ina da yauta sosai ni mi ya kaini wannan maganar ma. Kamin na isa gida komai nawa ya jike saboda ruwan da ake sosai. Inna ma ta yi mamaki ganina cikin ruwa, a bakin kofa na tsaya na cire tufafina sannan na saka wasu su kuma na rabasu gefen kofa har ruwan ya dauke. Wayana ma ruwa ya shiga ciki ya taba shi sai dai na yi sa'a be yi komai ba. Saman kujera na zauna sai Noor yanzo kusa da ni ya zauna ya jingina kansa da jikina. “Momy ki ara min wayarki na yi game” “A'a kai baka da aiki sai game” “Momy dan Allah” Ya fada kamar zai yi kuka, ni kuma na hana shi domin wayar babu carji sosai a ciki, sosai na maida hankalina kan Sakina da ke ta rihazar din sira da zasu yi gasa a kai, Inna kuma ta dauko kur'ane tana karatu. “Inna ki min addu'ah Allah ya sa na yi ta daya” Cewar Sakina ganin Inna tana addu'a bayan ta gama karatun kur'anen. “Yaushe ne ma?” “Gobe kuma?” “Eh daman kwana biyu aka bamu ai” “Allah ya bada sa'a” Na fada tare da tashi na fita waje dan yi alwalar la'asar. Bayan na gama sallah ne Inna take tambaya ya aikin na amsa mata da Al-hamdilillah, sannan na dauki wayata na kira Bilal sai ta saka min user busy, haka na yi ta har biyar na yamma ta yi amman bata shiga ba, hakan yasa na fahimce cewar na saka numberta a blacklist ne, amman mi na masa har haka ne? Ko dai yana fushi da ni ne? Sallama muka ji da bakuwar murya, duk kokarin da na yi na rike Noor sai ya ci tura domin tuni ya kai bakin kofa shi da Jamila daman rigangan suke gurin amsa sallama ko leke aga wanene. “Nawwara na nan?” Na ji kamar muryar da na sani, hakan yasa na yi wuf na fita waje, Rabi ce tsanye da gown ta dora rigar sanyi sama fuskantar dauke da murmushi kamar kullum, sai dai ba ni take kallo ba Noor take kallo cike da burgewa, hakan yasa na maida shi bayana sai ta kalleni tana cigaba da fadada murmushinta, kamin ya matsa jikin kofar gidanmu ta ce “Bismillah” Sai ga wasu maza su biyu suna ta shigowa da kayan abinci da kuma manyan akwatuna guda uku suka dora saman barandar dakin Inna. Ni dai kallo na bisu da su har suka gama ganin ta juya zata fita yasa na ce “Waya ce a akawo?” “Ke ma ai kin sani” “Dan Allah ki koma da kayan nan” “Ni ba zan iya ba, amman zaki maidawa da kanki” Inna da ke tsaye bayana ta ce “Malama jeki abinki mun gode kinji” “Nima na gode Mama, Handsome boy sai anjima ko” Noor ya daga mata hannu yana murmushi da ya fitar da dimples dinsa. “Okay Anti mun gode” Ji na yi kamar na buge masa baki. Bayan ta fice Inna ta kalleni ta ce. “Ba a maka alheri ka maida ko ya yake Nawwara, idan ma har kina jin ba zaki iya amfani da abunda ya baki ba, zaki iya kyautarwa, kuma idan har kika cigaba da nuna baki son abun hannunsa ba zaki karba hakan yana nufi har yanzu kina sonsa, amman idan har kika karba kika manta da komai kika nuna masa ba komai hakan zai kidimar da shi, domin zai gane cewa yanzu kina mu'ala ne da shi kawai ba ta so ba” “Amman ai kamar ina son sa ne idan na karba” “Ba daga nan take ba” Sakina taje ta bude akwatin tana duba babu komai a ciki sai tufafi da abaya da kuma gowns, sai atamfa da lace wadanda ba a dinka ba, “Amman gaskiya ba za a maida wannan kayan ba, ai ba mu muka ce ya kawo ba, mun ci banza” Cewar Sakina tana gwada wasu tufafin a jikinta. “Wallahi Anty ko ba zaki aureshi ba ki tatsi banza ko zafi ki rage” Ni dai ban kulata ba balle banzan zancenta, haka na zauna cikin rashin dadin rai har dare saboda Bilal be kira ni kuma na tura masa sako be maido min da amsa ba. Bayan sallah isha'i dpo ya zo gidanmu, ya yi wasu tambayoyi ni da Inna sannan na fada mana ya shigar da kara kotu kuma karshen watan nan ne za a fara zaman kotu, hakan ya faranta min rai sai na dan sake zuciyata ta washe. Washe gari ba mu karya da abunda muka saba karyawa ba, saboda Indomie da aka kawo mana ita Sakina ta dafa suka ci ita da Jamila da Noor shi kan har tsalle yake yana direwa kasa yana jindadi sun ci indomie. Inna kan kunu ta sha as usual nima shi na sha dan bana son ko warin indomie na ji balle kuma na kalleta har ya kai ni ga ci. Bayan sun wuce makaranta, ni kuma na soma gyara gidan, sai da na gama sannan naje na samo mai ruwa ya zuba mana jalka shida Inna ta bashi dari da hansi, sai na zuba na shiga wanka. Ina cikin bandaki na ji sallamar Baba Sulaiman da Baba Dahiru, wato kanen mahaifina da kuma yayansa, sai dai ga dukam alamu ba su kadai suke ba, domin Hayaniya ta yi yawa, ko da na fito Inna ta shimfida musu tabarma suna zaune ciki har da abokin Baba wanda ya sama masa aiki a Abuja da kuma Alhaji Bashir Makama wato mahaifin Jibril da wani dattijo tare da su. Na ji dadin da Allah yasa na shiga wankan da Hijabi da fitowa ta yi min wuya, karasa na yi na durkusa har kasa na gaishesu, sannan na wuce dakinmu zuciyata cike da maganganu kala kala. Ina cikin saka tufafi Inna ta kira hakan yasa na yi hanzarin saka kayan na saka wani Hijabin na fito na zauna kusa da ita. “Nawwara kin gane ni” Na dago na kalli Alhaji Bashir da ya yi maganar sannan na daga masa kai. “Zuwa na yi na baki hakuri akan abunda muka miki, hakika bamu kyauta ba, na sani amman dan Allah dan darajar iyayenki ki yafe mana, Wallahi har ga Allah Jibril ya canja kuma ya yi nadama, be san na zo nan ba ba shi ya turo ni ba, kuma bana son ya san na zo, na yi niyar yin haka tuntuni amman kunya da nauyinki yasa na kasa yi, yanzu ma sai da na biyo ta bangare Babanninki suka karfafa min guiwa sannan na samu na karaso ki dubi girman Allah ke da mahaifiyarki ku yi hakuri da abunda muka muku” “Ba fa kai ka yi ba” Cewar Baba Dahiru, sai ya amsa da “Ai da na ya yi kamar ni na yi kenan” Ni dai bance komai ba banda hawaye babu abunda na ke, Inna ce kawai take amsa masa, shi ma sai da su Baba Sulaiman suka saka baki, daga karshe ya yi magana agaisuwar rashin Baba, sai kuma ya tambaya yi Noor. “Sun tafi makaranta” “Amman Jibril be san yana da ba ko?” Kai na daga masa, sai ya soma labarta mana yadda Jibril yake son da da kuma irin halin rayuwar da ya shiga bayan rabuwarmu. Ya dauki kudi mai yawa ya bawa Baba Sulaiman da Baba Dahiru, sannan ya miko mana bandir din yan dubu daya. Sannan ya yi mana sallama yana cewa yau ya zo kuma yanzu zai koma daman saboda ni ya zo. Bayan sun tafi Inna ta zaunar da ni tana ta fada min maganganu akan rayuwa da kuma hakuri, ganin irin kuka da na ke. “Na hakura Inna amman ni fa ba zan taba komawa ba” “Babu wanda zai cilas miki komawa, amman ko dan ɗan dake tsakaminku ya kamata ace kun yafi juna” Tashi na yi na fita na koma dakinmu na zauna na yi kuka sai da na koshi sannan na shirya na fito na yi ma Inna sallama. Gidansu Jidda na nufa da Mamanta muka fara gaisawa sannan na shiga dakinta sai ta juya min baya tana dannar wayar da ke hannunta. Ban damu ba na zauna gefen katifarta na soma mata magana. “Jiya na yi mafarkinki Jidda, na yi mafarkin Mustapha zai cutar da ke” Tayi banza da ni kamar bata ji ni ba, ganin hakan yasa na tashi zan fita sai ta kira sunana. “Nawwara” Hawaye na gani a idonta. “Yi hakuri” Dawowa na yi na zauna sai na dafata na fashe da kuka sosai, kwantar da ni tayi kafadarta sai da na yi kuka na gaji sannan na labarta mata abunda ya faru tsakani da Jibril da kuma iyayesa da suka zo gidanmu. “Ki kara hakuri Nawwara ba gashi kin fara ganin sakamako ba, ni dai abunda na ke so ki yafewa Mustapha” “Zan yafe masa” “Amman..... Zaki iya” Sai kuma ta yi shiru. “Tashi kije karki makara” Ta fada, ni kuma na tashi sai ta rakoni har kofar gida sannan na fice ita kuma ta koma. A hanya na hadu da Mustapha ina tunanin ita ta fada masa gani nan na fito, sai ya sha gabana da motarsa sannan ya bude ya fito, sai kuma ya kasa ce min komai sai kallona yake. “Na yafe maka Mustapha ka dauka kamar komai be faru ba, amman zan gargadeka karka sake shiga hanyata, dan Allah dan Annabi ka fita hanyata” Ina fadar hakan na kama gabana na cigaba da tafiyata na barshi nan tsaye yana ta kallona. Har na yi kamar na bi ta gurin gidansu Bilal duk da na san by this time yana gurin aiki, sai kuma na bi hanyar da na saba bi. Na isa gurin aikin da misalin sha biyu saura kwata, yau ma atamfar roba ce a jikina da gyale. Kai tsaye na wuce gurin aikina zuciyata cike da son ganin Bilal, sai dai ban san takamaiman inda yake aiki ba. Ina isa kofar ta bude min, office dina na fara gyarawa sannan na shiga na shi Office din baya cikin hakan na nufin be shigo ba kenan, sai na na gyara komai sannan na fito, ko da na dawo nawa Office din wato office din farko wayata na ringing alamar kira ko da na duba sai na ga Number Zinatu da fari na yi mamakin da sunanta ya yi appearing a wayata sai dai tuna Rabi data karbi wayata tace za a saka min numbers mutane kuma nima a basu tawa yasa danna picking na kara a kunne. “Nawwara dan Allah ki sauko hawa na biyu yanzu” “Me zanyi?” “Dan Allah dai ki sauko Bilal yake nemanki” “Okay” Cikin hanzari na fita na shiga lifter, a hawa na biyu na sauka komai na gurin glass ne ma'ana wani ma'aikacin yana iya hango dan uwansa, haka na rika duba sunayen da ke gurin har na kai ga wanda aka rubuta Bilal Usman na tura na shiga, sai na samu dakin cike da mutane duka tsaye wani katon cake na gaban Bilal da wuka a jiki, Ina shigowa sai hankalinsa ya dawo kaina kamar marar gaskiya, sam baya farinciki kamar ba shi suke yi ma wakar happy birthday ba, kasa jurewa na yi sai idanuwa suka cika da kwalla, shi kuma ya gagara karbar cake din da Zinatu take kokarin kai masa a baki. “Happy birthday my dear” Shi kuma hankalinsa gaba daya a tashe yake ni kawai yake kallo. __________________________________________ Masu son ganin Jibril da Mustapha da Bilal da Nawwara ku kwatantasu a idonku, ni dai iya abunda na sani Bilal ya fi su kyau 😜 #COMMENT #VOTE #SHARE #FOLLOW. kalmomi dubu hudu na yi🙄 dan haka har na jibi ne wannan 👻 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy *Shafin yau na ku ne Maman Hannep Novels Group, Rai Biyu Fan's Group Khadeeja Candy Novels Group*❤🖤 4⃣1⃣ Tana daf da kai masa cake din a baki sai ya yi saurin rike hannunta. “No thanks” “Haba Bilal sai ka ce wani abu yau ne birthday ka fa” Sake kai masa a baki da karfi har tana shafa masa ragowar da yake hannunta a fuska tana dariya ita da mutane da suke cikin office din. Sannan ta juyo ta kalleni “Karo mana Nawwara let's have fun” “No ina da aiki a ciki, Happy birthday Bilal” Na fada idanuwa cike da kwalla, sannan na juya na fito hawaye na bin fuskata. Ban yi nisa a tafiyarba na ji muryarsa yana kirana ni kuma na kara sauri kamin ya karo inda nake har na shige lifted, ina sauka hawa na biyar na shige Office ina kuka, ko mintuna ban yi da zama ba sai gashi yazo gurin kofar, ina kallonsa ta computer na ki budewa sai kuka na ke har ga Allah na ji zafin wannan abun, da ya gaji da tsayuwa ya kirani, ban daga ba har ta yi ringing ta gaji ta katse, haka ya jera min kira har guda goma sha uku ban dauka ba, be bar gurinba sai da Jibril ya karaso sannan ya yi hanzarin barin gurin, ni kuma na yi saurin tashi na share hawayena, sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka na yi ba. “Good morning” Na fada ina a tsaye idanuwa a kasa muryata na bayyana kukana, a maimakon ya amsa min sai kawai ya karaso gaban table dina yana kallon fuskata. “Me kike yi ma kuka?” “Ba komai” Na fada idanuwa na kara cika da kwalla. “Fada min mana waya taba ki?” “Babu” “Aikin ne baki so?” Na kasa amsawa sai hawaye nake. “Mi Bilal ya zo yi nan? Miyasa kika ki bude masa?” “Ba komai” Ya daki table dina. “Dole ne ki fada min abunda yasa Gimbiyata zubar wannan hawayen mai daraja da tsada” Ya fada kamar ba shi ya yi maganar fuskarsa babu alamun wasa sai ma kara hade rai da ya yi “He's just come to apologise” “Apologise for what?” “Yau ya yi birthday, shine ya yi celebration tare da Zinatu” Kallona ya tsaya yi sosai kamar mai karantar abu a fuskata, sai kuma ya kyalkyale da dariya har sai da office din ya dauka gaba yana amsa amonsa. “Wow wow so that's means Zinatu ya ke so ba ke ba? Daman can ba saurayinki ba ne ko? Ko kuma...” Ganin yadda na ke hawaye yasa shi saurin rufe baki yana gintse dariyar da ke cinsa. “Okay calm down Naj-Babe i will talk to both of them” Yana fadar hakan ya nufi office dinsa sai cigaba ya ke da dariyar, kamar cikinsa zai fashe. Ni kuma na zauna a gurin hawaye na ta min zuba zuciyata kuma na mugun zafi. JIBRIL POV. Be shigo office din da dadin rai ba, amman wannan labarin na ya faranta masa rai. “Excellent” Ya furta yana kokarin zama, abun ya fi tsaya masa a rai Zinatu da gaske tana son shi ko kuma ta yi ne kawai as a friend ita kuma Nawwara kishi ya rufeta. “Wow” Ya furta yana dora kafarsa daya saman daya yana lilo da kujerar. “Allah ya kara raba kanku” Bayan kamar thirty minutes Nawwara ta shigo Office din idonta a kasa. “Kana bukatar wani abun ne?” Kallonta yake, ya ji dadin abunda ya faru amman wannan halin da take ciki baya son shi ga hawayen da ta kasa dainawa har yanzu, yasan tana jin kwatankwacin irin zafin da yake ji a duk lokacin da ta kula wani ba shi ba. Mika hannu ya yi zai riko hannunta sai ta yanje ta yi cikinsa da masifa. “Miyasa kake son taba hannuna ne? Miyasa kuka dauki rumgumar mace da taba hannunta a matsayin wayewa? Baka san zunubin da ke akwai a taba hannun mace da ba muharramarka ba? Baka da rayuwa mai kyau Jibril” Uffan be ce mata ba har ta juya ta fita, sai dai maganganunta suna masa zafi, baya jindadin yadda duk maganar da ta zo mata a baki take fada masa, ciwon da ke damunsa ne ya taso masa har yana neman numfashinsa sai da ya dinga sauke ajiyar zuciya yana dafe zuciyar sannan ya samu sassauci har ya nufi freezer ya sha ruwa, sai kuma ya bude durowarsa ya dauko cocaine ya zo ya zauna gaban teburinsa ya soma shaka. Sai ga Nawwara ta shigo da wasu takardu a hannunta tsayawa ya yi kallonta kamar yadda ita ma take kallonsa. “Kana da meeting da pearls global company misalin sha biyu da rabi, wannan kuma daga Dr Ishak Hacker ne zaka saka hannune a maida masa” Ta fada tana dora masa takardun saman table dinsa, kamar be damu da ganin da tayi masa yana shan cocaine ba ya dauki pen ya saka hannu, ita kuma ta juya ta fice ba tare da ce masa komai ba. Wayarsa ya dauka ya kira Siraj. “Ka bincika?” “Eh amman ance bata da wani da kuma binciken ya nuna bata ma taba yin ciki ba” Ya busar da iskar bakinsa dan ba abunda yake son ji kenan ba. “Ka tabbata?” “Yes, walimar da kasa a shirya yau za'ayi” “Thank you Siraj ayi abunda ya dace” Ya katse kiran yana ta tunani, sam zuciyarsa bata yarda babu da tsakaninsa da Nawwara ba, ji yake kamar dai Siraj be yi binciken daidai ba, ko kuma Nawwara tasa a boye masa ne. Rabi ya kira dan jin yadda aka yi daman tun da ta kai kayan ta kirashi be dauka ba sai ta aiko masa da sako amman be bude ba. “Good morning Sir” “Ina jinki!” “Na kira wayarka baka daga ba kuma na aiko maka da sako, anyi komai yadda ya dace Sir sai dai ita kadai na yi ma siyayyar” Ta fada da zimmar ta ji abunda zai ce tace ba tayi ma yaronta ba dan ita a zatonta Jibril ya san da shi. “Eh daman ita kadai zaki yi ma” Yana fadar hakan ya kashe wayar yana jin kansa kamar marar lafiya. Sha biyu saura kwata Nawwara ta sake dawowa office din. “Akwai wani abun da ya kamata muje da shi gurin meeting din ne?” “Ee takardun kamfanin nan, suna cikin can” Ya nuna mata wani katon box dake lake da ginin gurin, karasawa ta yi tana kokarin budewa amman ta kasa. “Sai kin sa password” “Miye password din?” “N¹¹A²³W²¹W³¹A³³R¹³A” Sunanta ne zere sai mixing da aka yi da numbers, tana saka. Password din sai ya bude, farkon box din cocaine ce mai yawa, na biyu kuma zinari ne irin wanda aka ciro cikin kasa ba a sarrafashi ba, sai dollars dake binsu daga karshe ne takardun suke. “Duka zan dauko?” “Ki duba files din wanda aka rubutawa 001 zaki dauko” Daki-daki ta bisu har ta wanda yake magana akai ta dauko, sannan ya maida marfin box din ta rufe ta taso ta nufo table dinsa. “Miyasa kake son shan cocaine ne?” Yaja ragowar dake hancinsa sannan ya dauke idonsa daga barin kallonta. “Saboda na rage damuwa da bacin rai” “Waya fada maka tana cire damuwa?” Ya mike tsaye ya nufi gurin window ya tsaya tare da sanya hannayensa aljihu. “A lokacin da na haukace akan tunaninki na rabu da kowa, na watsar da dukan abokaina sai Allah ya hadani da Siraj, shi ne kadai mutumen da ya taimaki rayuwata na fara dawowa mutum da wannan cocaine din, a duk lokacin na shakata ina samun sassauci akan tunaninki, musamman a lokacin da take buguna ba kamar yanzu da bata min aiki ba” “Amman miyasa kake sha?” “Saboda ta zame min jiki” “Idan har kana son ka kore damuwa ka rika daukar kur'ane kana karatu, ina tunanin ka san illar wannan cocaine din” Ya juyo ya kalleta. “Ba ni da wani zabi ne saboda tunaninki na fara shanta” NAWWARA POV. Ban sake ce masa komai ba na juyo ya baro office din, zuciya cike da rashin jindadin halin rayuwar da jibril yake yi. Yanzu akaf a familynsa a rasa wanda zai tsaya ya fada masa gaskiya akan rayuwa? Babu mai iya bata lokacinsa ya zauna da Jibril ko dana dan lokaci ne? Abun bakiciki ne namiji kamarsa ace be san abunda ya dace ba, shikenan saboda be da mahaifiya a raye mahaifinsa ba zai iya zauna da shi ya fahimci rayuwar dansa ba? Ni kadai ce zan iya canja rayuwar Jibril a yanzu, saboda ni kawai yake saurare ni ce kadai zan matsa tsawa be maida min ba, dole na taimaki rayuwarsa ko dan dana ba ni da wani zabi a yanzu da ya wuce wannan ko na ki ko na so uban Noor ne kuma dole wata rana Noor zai yi rayuwa da Ubansa, idan bashi a tafarki mai kyau taya Noor zai kalleshi? Tunani kenan sai kuma wata zuciyar ta jefo min tambaya. ‘Yanzu mutumen da ya wulakanta ya nuna baki da muhimmanci a rayuwarsa mutumen da ya kiraki da annoba? Yasa aka kiraki karuwa? Ya ce dan da kike takama da shi ba nasa ba ne? Ya wulakanta mahaifanki ya tozarta ki a idon duniya ya ce ganin bakin maciji ya fi masa ganinki, shi zaki taimaka? Irin wannan mutumen zaki tausayawa? Wanda ya kasa baki taimako daga lokacin da kike bukatarsa ya fifita karuwa akanki?’ “No no ba zan iya ba” Na furta a fili idanuwana cike da tsanarsa. “Yaje ya yi ta yin rayuwar da yake ganin zata fidda shi ni babu ruwana a ciki” Ina rufe bakina yana fitowa daga office, ni kuma na mike tsaye na dauki takardun. “Naj ina ɗa na?” Wani wawan kallo na watsa masa. “Da kuma? Ko cocaine din ta fara bugunka?” “Ina cikin hayyacina na san abunda na ke ina dana ko yata?” “Mtssss kana hauka Jibril baka ma san abunda kake fada ba” Ina yin gaba na ji an fisgoni na fado kirjinsa sai ya rumgume kamkam ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa numfashinsa kuma na fita da sauri. Iya karfin da Allah ya bani da kuma dabara ya saka wajen ganin na kwace kaina amman na kasa ko kwakkwaran motsi, saboda karfinsa ya ninka nawa sau saba'in. “Ka sake ni ko na maka ihu” “Ko kin yi ihu babu wanda zai zo” Ya fada idonsa a lumshe yana kara kwamtar da kaina a kirjinsa. “Kina jin yadda zuciyata take bugawa ko Naj saboda ke” “Idan baka sake ni ba zan sake zuwa aikin nan ba, daman saboda ka rika min haka ka tirsasani yin aiki a tare da kai ko?” Ya dora kansa saman kaina. “Ina ma zamu dawwama a haka” “Ba zan sake zuwa aikin nan ba” Ya yi saurin saki na. “Ina son ki sosai Naj ina miki irin son da wani da namiji be taba miki ba” “Ni kuma bana son..” Na kasa karasa saboda hannunsa da yasa ya rufe min baki, sai kuma ya duka kasan guiwoyinsa ya hade hannayensa. “Dan Allah dan Annabi Naj ki yafe min abunda na yi miki, dan Allah ki manta da komai” “Na manta da komai saboda ka san ka zalince ni ko? Mugu bakin azzalumi” “Ki kirani da ko wane irin suna zan karba miki, ki ayyanani a duk kalar mutumen da kike gani zan dauka, ki ci mutunci a gaban kowa zan jure matukar hakan zaisa ki yafe min” “Ba zai taba sa na yafe maka ba” “Fada min abunda zan yi ki yafe min Naj, ni kadai na san irin abunda na ke ji a zuciyana, na kan tsani kaina idan a duk lokacin da na tuna abunda na aikata miki, tunaninki ya haddasa min ciwo da damuwa, rashin kulawar nan taki ina jin kamar yana kokarin rabani da rayuwata ne, i will die soon Naj mai yuyuwa a wannan lokacin zaki tausaya min ki zo gaban gawata ki yafe min” Hawaye yake irin hawayen nan dake nuna tsantsar abunda ke zuciyarsa, ga nadama da damuwa nan ƙarara a fuskarsa. “Lokaci meeting yana wuce” Na fada tare da daukar takardun na nufi kofar fita. A ranar meeting hudu muka yi uku a cikin kamfanin daya kuma a wani kamfanin da muka je tare, sai dai sam babu walwala da sakewa a fuskar Jibril da ma yadda yake maganarsa da mu'alama da mutane, dukan abunda zan yi hankalinsa yana kaina, da muka dawo na yi sallah shi kuma ya dora alwala ya fita zuwa sallah a masallacin da ke kamfanin ni kaina ban taba sanin akwai masallaci a kamfanin ba sai yau, bayan na dawo ya cilasta min zuwa cin abincin rana kamar jiya, da muka shigo office ya dauko wasu takardu ya aje min wai na yi typing dinsu a computer shi kuma ya nemi wata kujera ya aje gaban teburina yana kallona har na yi aikin na gama. Tare da shi muka shiga mota, ya kawoni a inda ya aje jiya sannan ya mika min wata sabuwar laptop, wai da ita zan dinga zuwa office kuma na je gida ta aiki ce sai kuma na bukaci na kwashe duk abunda ke cikin wacan computer ta office na saka a laptop din, ni dai ban ce masa na gode ba balle sai anjima na fito na yi tafiyata. Ko da na isa gida yamma ta yi lis saboda yau na dade sosai a gurin aikin, na darar da gidanmu cike da mutane suna ta mana murna wai Sakina ta ci gasa an bata gida kuma wanda yasa gasar ya dauki nauyin karatunta sannan ya yi mata kyautar dubu dari biyu da hansin, ita kanta kamar zata hade kanta dan murya. Jibril kawai zuciyata ke raya min ya saka gasar nan, sai kuma daga baya na soma tunanin Mustapha domin shine a unguwar ya fi kowa sanin inda Sakina take karatu, har dare mutane nata shigo mana, Inna ta siye minti ta yi sadaka, bayan sallah isha'i Bilal ya kirani a waya na ki na daga sai ya aiko min da sako wai yana kofar gida, nan ma ban mayar masa da amsa ba jim kadan sai ga yaro ya shigo wai ana sallama da Nawwara, sai na yi karaf na ce “Je ka ce ba zata zo ba” Inna ta saki baki. “Ba zaki zo ba? Ba kyau wulakanta dan adam fa, Wallahi ki kama kanki, ni bana son yawan zuwan da ake ama miki sallama, wallahi ko aikin nan da kike zuwa hankalina be kwance yake ba, bani da kwanciyar hankali idan ba aure kika yi ba” “Inna Bilal ne fa” “To dan me ba zaki je ba?” “Wai birthday yayi yau shi da Zinatu suka yanka cake din kuma a gurin aikinmu wai har da kirana dan na gani” “Kishi kike kenan, ashe ana kishin abunda ba a so?” “Ni ina son shi” “Kina son shi kike nuna baki son shi? Kina son shi miya hana ki aure shi? Yanzu ke kina ganin zaki samu namijin da zai so ki kamar yadda Bilal yake son ki? Babu abunda ba a fada masa ba a kanki amman ya toshe kunne ya ce yaji ya gani shi dai son ki yake, kuma kina da ɗa shi yana saurayi kuma a haka yake son ki, babu irin kulawar ta cusa kai da be nuna miki ba amman kiki bashi dama, sai yanzu dan ya kula wata zaki ji haushi har ki zo kina kishi? Wane iriin zama kike son ku yi da shi? Shi dai aure yake son ki idan baki bashi dama ba ai dole yaje inda wacce zata bashi dama, Idan har son Bilal kike da gaske tau ki bashi dama ya ga magabatanki, sai ki yi kishi mai dalili, amman yanzu ai cin amanarsa zaki yi ki hana shi aurenki kuma ki ce ba zai kula wata ba?” “Amman Inna ai kin san yan gidansu basa so na, ni bana son na yi aure inda zan wahala ni da Noor” Na fada ina kuka, sai ta ce “Zaki wahala dai ke, Noor kan ai ba zai zauna tare da ku ba, duk son da Bilal yake nunuwa Noor ana daura miki aure dole a gida zaki barsa sai dai ya rika zuwa yana ganinki, saboda Bilal Saurayi ba mai mata ba, da ma ace yana da mata da zakiniya zuwa da danki ya rika shi, amman wannan kan ai sai ya kara kiyayyar ki ga yan uwansa kuma jama'a ma sai su zageni ace na bari aka je da yaro ya takura masa, ina tunanin ba a gidansu zai aje ki ba ko da ya aureki, dan haka yan uwansa su daina damunki ba akansu zaki zauna ba, indai mijinki na son ki babu wanda ya isa ya taka ki, sai dai ki shiryar fuskantar kalubale daga garesu” Na kara fashewa da kuka, ni dai har ga Allah ina son Bilal dina, kuma bana jin zan iya auren wani namiji bayan shi. *** *** *** Washe kamar marar lafiya haka na tashi jiki babu dadi zuciya ma babu dadi, bayan mun gama karyawa suka tafi makaranta ni kuma na gyara gida sannan na shiga na yi wanka ina fitowa na shirya cikin wata bakar abaya, da mayafinta, sannan na dauki laptop din da jakata na nufi dakin Inna ina mata sallama. “Amman dai ina tsoron ki rika wannan abun a hannu, kin san garin ne ko maza ya suka kare balle mata” “Ai kin ga a ciki jaka take ba wanda zai san abunda ke ciki, kuma ina addu'a inshallah babu abunda zai sameni” “Tau Allah ya tsare ya kai lafiya, ni jiya ma duk a tsoro na kwana saboda gidan nan da yan kudi da aka bamu, yau zanje na kai gidan Ya Umma na fada mata komai duk shawarar da aka yanke idan kin dawo sai kiji” Ta karasa tana miko min dari biyar na hau Napep. “Tau Na gode sai na dawo” “A dawo lafiya Allah ya tsare, ga wayarki da kika bari jiya” Nasa hannu na karba, miss call talatin da bakwai Siraj ya yi min, sai kuma kiran Jibril guda daya, da kuma wata bakuwar number ni dai ban wani maida hankali kan wayar ba nasa kai na fice ina ta tuno abunda ya faru jiya sai na ji raina ya sosu. Yau na ji da wuri sai dai duk da hakan ya rigani zuwa, a gabansa na gyara office din na jera komai yadda ya dace sannan na hada masa tea, files din da aka kawo dake kofar office din farko na dauka ina duba wanda zai saka hannu na kai masa wanda kuma ni zan yi aikin na maida hankalina ina ta yi, misalin sha biyu na shiga na fada nasa meeting din da muke da su da kuma mutane da yake da appointment da su, be samu kansa ba sai biyu daidai saboda ganawa da yake da mutane, abun mamaki sai gashi ya fito da alwalarsa ya sauka saka ya yi sallah, ni dai already na yi sallah duk da kasancewar ina jin marata tana murda min tun Shekaran jiya alamar menstruation dina na daf da zuwa, sai dai na san kamin ta zo na kan yi kurajen fuska ko da kwara daya ne ko biyu, rashin ganin kurajen yasa ban maida hankali akan tararta ba. Bayan ya dawo ya shiga meeting, yana fitowa yasa na hada masa tea, na shiga office din ya fi a kirga ina kai masa files da documents, sannan na koma na cigaba da saka kwashe abubuwan da suke cikin computer ina sakawa a laptop, muma haka danjar nan tayi kara alamar da mutun a bakin kofar office din, a computer na ga Rabi sai na bude mata ta shigo fuskarta da murmurshi kamar kullum, wata bakar leda ta aje min saman table ta ce “Oga ya ce a baki wannan” Tana ajewa ya juya ya fita, ni kuma naja ledar na soma budewa, abaya ce mai dankwali green color sai dozing din pant da pad da kuma turare. Gabana ya fadi mi yake nufi ne, sauri mikewa na yi tsaye na duba baya ashe rigata ta bace, gashi abaya ce ba Hijab balle ya kare min, arzikina ma bakar abaya ce, amman ya aka yi ya zubo min ban ji ba? Wata irin kunya ce ta rufe ni tunanin daya fado min a rai shine. A haka naje meeting din ko dai bayan mun dawo cikin office haka ya faru? Kaddara dai ta riga fata, bathroom na shiga na tsabtace kaina sannan na wanke rigar da karamin saket dina da ya bace da pant dina, na saka abunda ya bani, sannan na kulle wadancan kayan a ledar na fito na saka a jakata. Ina zaune da kunyata sai gashi ya fito daga office dinsa yana fadin “Ba zamu samu damar cin abinci a kamfanin nan ba, saboda akwai wanda zan mu magana da shi a waje, saboda haka tare zamu fita sai na shiga meeting din ke kuma ki ci abinci” Ni dai ban ce komai ba kuma na ki na kalleshi, sai dai kijina na bani so yake na kalleshi din, na dauki jakata na rayata sannan na rika jakar dake hannunsa a dayan hannuna kuma laptop ce. Tare muka shiga motar ina jin kamar na natse saboda kunya, har muka isa ban kalli inda yake ba, shi kuma yana ta motsi yana son na kalleshi din. Kamfanin da muka je kamfanin Chinese ne yan nigerian da suke aiki ciki basa da yawa, komai a tsare gwanin sha'awa. Wani bahaushe ne mai far'a da son mutane ya tare mu kuma ya yi mana iso har inda za'ayi meeting din. Da zai shiga ya juyo yan karbi jakarsa da laptop din dake hannuna ya kalleni ya ce “Duk kika sake kika yi fira da wani sai na yanka miki baki” Be tsaya jiran amsar da zan bashi ba ya shigewarsa tare da mutumen, ni kuma na zauna a gurin ina kallon mutunen dake ta kai da kawo, bayan kamar minti biyar sai ga mutumen ya kawo min abinci na karba ina masa godiya ba dan ina iya ci ba, saboda mutane kowa kallona yake ba zan iya bude baki a irin wannan gurin na ci abinci ba wannan ba mutunci ba ne. Fira ya soma yi da ni sama sama yana danna laptop dinsa, ana nan yake labarta min cewar shi dan Zaria ne, muna haka wayata ta soma ringing, bakuwar number ce har na yi kamar karna dauka sai kuma na daga, muryar Sakina na ji tana kuka. “Anty ki yi sauri ki zo Noor ya samu accident gashi nan za a kai shi asibiti” “Wace asibiti?” Na tambaya hankalina a tashe. “Specialist Hospital” “Gani nan zuwa” Na kashe wayar a lokacin har na fara kuka, “Lafiya?” “Ɗa na ya yi haɗari” “Bari a fada masa mana” “A a” Ina fadin haka na fita da gudu hankalina a tashe har bana iya gani da kyau. *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣2⃣ Sun samu kusan mintuna arba'in suna meeting din sannan daga karshe suka cimma matsaya daya akan kwangilar da kamfanin zai bawa kamfaninsu Jibril. Hannu ya mikawa Jibril suka gaisa sannan ya fito, daman hankalinta yana can gurin Nawwara zuciyarsa na raya masa tana can tana fira da wannan mutumen na dazu. Da ya fito sai ya samu Mutumen shi kadai yana ta aikinsa sai wasu mutun biyu da suka zauna a kujerar da ya bar Nawwara dazu, kamar ba zai tambaya a zatonsa tana can wani gurin ne ko kuma ta koma cikin mota. “Mai gida matar da kuke tare ta fita wai dan ta ya yi hatsari” Sai Jibril ya tsaya cak kana ya juyo ya kalleshi. “Dan ta?” Ya fada. “Ee tun dazu ta tafi na ce bari a fada maka sai ta ce a a” “Kasan matar da muke tare kuwa?” “Ee wacce kuka shigo tare, ai ni na tarboku na santa wata fara doguwa ba sosai ba mai dan fadin fuska tana sanye da abaya green” “Amman dan ta ka ji ta ce ko kanenta?” “Dan ta dai ta ce indai ba rudewa ta yi ba, saboda waya aka kira aka fada mata” “Kaji wani abu bayan wannan?” “A a gaskiya hankalinta a tashe yake bata ce komai ba” Da sauri Jibril ya fita daga harabar gurin direbansa na hangosa ya san a uzurce yake kuma ya san babu abunda ya tsana irin jira, tun kamin ya karaso ya janyo mota kuma ya bude masa. Har Jibril zai shiga sai kuma ya mika masa jakarsa da laptop dake hannunsa. “Nawwara ta tafi” “Ee naga ta fice da gudu tana kuka har wani na tambayarta a abunda ya faru bata dai kula shi ba” Ya amsa masa yana saka Laptop din a mota, juyawa Jibril ya yi ya koma ciki gurin mutumen dazu. “Please ko kaji inda zata je? Ko kuma inda hadarin ya faru?” Mutumen da dan yi shiru sannan ya daga masa kai. “Ee na ji ta ambaci Specialist Hospital gaskiya ina jin ko can aka kai yaron ko kuma can hadarin ya faru” “Thank you” Ya juyo da sauri ya nufi gurin motarsa, driver seat ya nufa ya ce direban ya fita ya hau achaba shi akwai inda zai je, @360 ya fisgi motar kamar zai tashi sama, wani irin vibration jininsa yake yana jin kamar ya runtse ido ya gansa a cikin asibitin. “Dan ta...” Yana ta maimaita hakan ya iso Abuja road sai ya dauke hanyar da zata sada shi da Specialist, gudu yake sosai kamar dan shi aka yi titi ko kuma ance masa babu ababen hawa sai nasa kadai. Lokacin da zai kunna kai a gate din Specialist din sai da ya yi kamar zai buge wani magidanci da ke kokarin fitowa. Ko fakin din kirki be yi ba ya fito yana ta waiwagen inda zai shiga, tsabar rude daman can sau daya ya taba shigo asibitin loacin da yake farkofarkon zuwa sokoto sika yi wata mata tiyata. Da sauri ya nufi emergency wajen yan hatsari, har ciki ya karasa ya karasa inda Nurses suke ya muna masu id cart dinsa sannan ya soma tambayarsu ko an kawo wani. “Eh an kawo mutun daya yanzu” “Zai kai minti nawa?” “Ten haka yanzu yanzu” “Babba ne ko yaro?” “Gaskiya dattijo ne” “No wanda na ke nema karamin yaro ne yana tare da mamansa ina jin za ayi awa daya yanzu da kawo shi” “Eh an kawo wani yaro dazu, yana ciki bayan shi ma an kawo wani” Dayar Matar ta fada. “Bari na duba” Ya nufi ciki da sauri ya soma bin dakuna, sai gashi ya hadu da wani likita abokinsa. Shi ya rike Jibril dan hankalinsa gaba daya sama yake baya ganin kowa. “Jibril” “Dan Allah wani yaro na kr nema wanda aka kawo ya yi hatsari dazu” “Yaro ne sosai?” Ya dan yi shuru yana tunanin ta yadda zai amsa tunda ba sanin yaron ya yi ba. “Yeah yeah yaro ne” “Akwai wanda aka shiga tiyata da shi yanzu akwai kuma wanda ya rasu dazu, amman ba a fita da gawarsa ba saboda basu biya hospital bill ba” “Wait...” Ya fada sai ya fiddo wayarsa ya kira Nawwara duk da yasan ba zata bari ya karaso ba, ringing biyu aka daga da muryar Sakina tana masa sallama. “Ina Nawwara?” “Bata da lafiya” “Wacece ke?” “Ni kanwarta ce” “Kuna ina ne Nawwara tana ina” “Muna nan asibiti?” “Wani waje?” “Dakin Balaraba” Ya katse wayar yana kallon likitan. “Ina ne sashen balaraba?” “Ta can ne, ko shine yaron da ake neman jininsa aka zo diban na uwar ta suma?” Jibril ya rike. “Please zan iya ganin yaron” “Yes this way, amman an shiga tiyata da shi gaskiya ba zaka iya ganinsa yanzu ba sai dai a jira ya fito” Tare suka karasa sashen da ake yan tiyata, jikin Jibril sai rawa yake sosai ya so ya shiga amman likitan ya hanashi saboda tiyata ake masa kuma yasan irin matsalar da zai janyo matukar ya ce zai shiga yanzu. “Ka yi hakuri da sun fito zaka ganshi” Safa da marwa kawai jibril ya ke yana matsar hannunsa. “Jini ma ake nema garin bada jinin ne Mahaifiyar yaron ta yi ta amai daman da kuka ta zo, sai gashi ta sume mana dole muka kaita sashem Balaraba, kakarsa taje ta siyo” “Please Doc Ismail muje ka gwada nawa idan zai yi” “Okay yaron ya ji ciwo sosai gaskiya ya zubar da jini, amman yaron ka ne ko naga kuna da kaman sosai kuma yadda ka tashi hankalinka haka...” Be gama maganar ba Jibril ya rike shi “Da gaske muna da kama? Da gaske?” Ya gyada masa kai cike da mamaki, ko da suka karasa lab Jibril be sani ba saboda hankalinsa yana can gurin tunani. Sai da aka dibi jininsa kadan aka gwada ya bada result iri daya da na Noor sannan Doc Ismail ya kawo masa, Jibril na ganin takardar hawaye suka fara masa zuba jikinsa ya yi mugun sanye, sai da ya karantar result din ya fi a kirga sannan ya yarda da duniya yake, fashewa ya yi da kuka sai kuma ya yi saurin guntse bakinsa tunawa da inda yake, saman table ya aje takardar ya nufi wani bangare na lab din hannayensa a baya yana jin wani irin abu marar misaltuwa. “Doc Jibril ko ka fasa bada jinin ne?” Sai ya juyo da sauri ya dawo yana share hawaye abunda ya bawa kowa mamaki, sai dai su abunda suke dauka saboda yaron ya ji rauni sosai ne yake hawayen, har wasu na cewa wai kamar ba namiji ba namijin ma kuma likita wanda be kamata aga yana kuka saboda sun saba ganin tashin hankali. Dakin da ake dibar jiki ya shiga ya kwanta a saman kujerar nan mai kamar gado, aka saka masa abun diban jinin aka tasti leda biyu sannan ya tashi yana fadin. “Doc Ismail muje yanzu ko sun fito” “No Doc kai kansa kasan dole ka dan zauna yanzu na ga kamar a hankalinka a tashe yake” Tashi tsaye Jibril ya yi da zimmar tafiya, ganin hakan yasa Doc Ismail ya bishi suka koma gurin tare sai suka tarar ba a fito da shi ba har yanzu. Sai kawai suka zarce inda Nawwara take domin itama yana da bukatar ganinta, basu sha wahala wajen nemanta ba saboda farko farko take. Irin dakinnan ne da ake jera masara lafiya dama da hadu, tana kwance saman gadon asibiti idanuwanta a rufe kamar tana bachi ga drip an daura mata a hannu, Sakina na zaune a kujerar da ke kusa da ita tana ta hawaye. Kallonta yake sosai cike da tausayinta a nan Sakina ita ta samu damar kallonsa a take ta raya a zuciyarta cewar tabbas wannan baban Noor ne domin kamar har ta ba ce. Zaunawa ya yi gefen gado yana ta kallon fuskar Nawwara kamar yau ya fara ganinta, can kuma ya dago ya kalli Doc Ismail dake ta faman kallonsa da mamaki ya ce “A sama mata daki inda zata zauna ita kadai ta samu kulawa, if babu zan so ka mata transfer zuwa asibitina” “No nan din ma akwai” Gurin Nurses din ya nufa ya yi magana da su sai suka zo suka canja mata daki zuwa wanda take ita kadai sai dai shi kudinsa da daban ne. A nan ma ya dade yana kallonta sannan ya cire rigarsa yar sama kasancewar suit ne a jikinsa ya lulluba mata saman jiki. “Ki kula da ita please” Ya ce da Sakina sai kace ita Nawwara wata karamar yarinya ce. Tare suka fito da Doc Ismail har suka hadu da wani likitan Jibril dai be bi ta kansa ba dan hankalinsa yana can gurin dan da aka ce na Nawwara ne. Sun yi sa'a suna isa ana fitowa da shi dakin tiyata, Sai Doc Ismail ya tsayar da su saboda abokinsa ya samu ganin yaron, mutuwar tsaye Jibril ya yi a gurin idanuwansa suka cika da kwalla kamar ba namiji ba, be ankaro da nauyin da kafafunsa suka yi ba har sai da ya daga kafarsa daya ya taka zuwa gurin gadon da Noor yake kwance. Sama yake kasa yake duniya yake lahira yake? Sai ya kasa ganewa iyakar abunda idanuwansa suke kallo kamaninsa dake zuba a fuskar Noor, yasan ba mafarki yake ba kuma idanuwan ba gizo kuke masa ba, abunda yake gani zahiri dake shiga har cikin kwakwalwarsa, faduwa ya yi a gurin yana kuka muryarsa na karkarwa. “This is my Son, ba ko tantama wannan da na ne, he's my Son jinina da na na cikina” Hannu ya kai zai shafa fuskarsa da ke manne da bandeji sai yaji ya rike masa hannun cak.... ____________________________ GOOD NIGHT HABIBATIES 😘😍 Duk Inda Masoyan RAI BIYU Suke Ina Gaishesu Ina Muku SON SO FISABILILLAH ❤ Na yi Wannan guntun Page din ne saboda ku 😍😘 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣3⃣ Dago kai ya yi da sauri domin ganin wanda ya hana hamnunsa zuwa ga gudan jininsa, ganin Nawwara cikin bachin rai da daure fuska yasa shi mikewa tsaye sai ya kama duka hannayensa biyu yana kuka kamar zai narke a gurin. “Naw.....” Fisge hannayenta ta yi ta ture da dukan karfinta. “Karka kuskura ka taba min ɗa, hauka ta daina dibanka kana taba jikina ni ba halalinka ba ce” Ta fada cikin wani irin zafin rai. Doc Ismail ya karasa ya rika Jibril yana kallon Nawwara tare da fadin “Amman ke baki da mutunci ta ya zaki wulakanta babban mutum kamar Jibril a gaban mutane” “Babu ruwanka karka saka min baki a nan” Jibril ya share hawayen da suka ki tsaya masa ya nufi gurin Noor sai ta tsaya masa tsawa hawaye na zuba a idanuwanta. “Karka taba min yaro” Rike shi Doc Ismail ya yi ya ce da Nurses din su wuce da Noor, a gurin Nawwara ta zube kasa saboda jirin da ya dibeta, Doc Ismail ne ya kira wasu Nurse suka kamata suka mayar da kin da ta baro. Hakan ya bawa Jibril damar shiga dakin da aka kai Noor. Ko da ya shiga ya samu Nurses din suna daurashi saman gadon sannan suka saka masa robar jini daya. Fita suka yi daga dakin baya sun gama komai sai Jibril ya karasa inda yake ya durkusa kasan guiwowinsa gurin gadon wasu sabbin hawaye suna zubo masa. Ko da bachi yake ya farka ya kalli Noor yasan dan sa ne, fuskarsa ce shinfide a fuskar Noor babu inda Noor ya rage shi da komai, hannu ya kai ya rika hannun Noor sai yaji wani irinsa ya shiga hannunsa jini ya hadu da jini Noor din ma da be san inda hankalinsa yake ba sai da ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Kuka Sosai jibril ke yi irin kukan da aka san mata da yinsa, sai kuma yaja hannun Noor ya kai a fuskarsa ya lumshe ido, yana ta goga hannun a fuskarsa, sannan ya yi masa kiss sai kuma ya soma shinshinar hannun kamar zai cinyeshi. “Am sorry Son, ka yafe min na wulakanta akan haukana, mahaifinka ya tuba ya gane kuskurensa na yi nadama, ban san miya shiga kaina ba ban san miyasa na aikata ba, am really sorry for what i did, please forgive me” Ya kara fashewa da kuka har numfashinsa na son tsayawa, shigowar Doc Ismail ne yasa shi tsagaita kukan ya dago ya kalleshi. “Wai miyake faruwa ne? Miye alakar ka da wacan matar ne? Na san dai wannan ba dan ka ba ne ko?” Tambayar da Doc Ismail ya yi masa kenan. “Dana ne, ita kuma mata ce” Daga haka Doc Ismail be kara cewa komai ba, yasan Jibril baya cikin yanayin da zai iya yi masa bayanin komai a yanzu, after that be kama ya saka kanshi akan matsalar iyali ba. Juyawa ya yi ya fice zuciyarsa cike da mamaki bakinsa kuma gumde da tambayoyi. NAWWARA POV. Ban san iya awanin da na dauka a sume ma ba, ina farkowa na ji goshina ya cika da nauyi har bana iya gani sosai. “Sannu” Muryar Inna ce take gaisheni sai na gyada mata kai dan bana iya magana a wannan lokacin, na dade ina kallon silin sannan idanuwana suka dawo daidai har ya kalleta. “Ina Noor?” “Yana can an kaishi wani dakin” Sai a yanzu na tuno da abunda ya faru, ashe fa wannan suma ta biyu ce na yi. “Inna miyasa kike bari Jibril ya zo har ya ga Noor” “Ba zan iya ce miki ga dalilin zuwansa ba, ban kuma san ta ina ya ji ba, nima na tafi neman jini ko da na dawo na tarar ya bada jininsa kuma ya sa an canja miki daki an dawo da ke a nan, shi kuma yasa aka kai shi dakunen nan masu tsada” Na yi sauri sauka saman gado duk da ina jin jikina kamar babu gwari sosai. na fita daga dakin na mike hanya har na isa manyan dakunan, na bude na farko ba shi bane na biyu ma haka na uku hudu biyar haka na bi dakunan sai da na kai daki na bakwai ina turawa sai na hango Noor kwance Jibril kuma zaune saman kujera ya dora kansa gurin jikin Noor hannun Noor kuma a saman kansa dayan hannunsa kuma na sanye cikin na Jibril. Ban damu da na rufe kofar ba na karasa kusa da gadon cike da tausayin halin da Noor yake ciki, ina tsayawa dai dai kan Jibril sai ya bude idanuwansa da suka kumbura suka ja a hankali ya kalleni, sai kuma ya lumshe. “Jibril tashi ka fita” Na fada a tsawace, sai ya bude ido ya yi ma hannun Noor kiss sai ya sake shi, na yi zaton tsaye zai tashi sai kawai na ga ya zube kasan gwuiwowinsa ya fashe da kuka yana hade hannayensa. “Ki dubi girman Allah Nawwara, ki sassautawa zuciyarki dan Allah ki yafe min, Wallahi na canja dabi'u da halayya duka na canja ki ceci raina kuma ki ceci ran yarona ki taimakeni ki yafe min ba ni da wani buri da ya wuce na ki da na wannan dan nawa, please Nawwara for the sake of our Son ki hakura mu sake sabuwar rayuwa, zuciyata na cike da kuna ina bakincikin abunda na yi muku, kaina a kasa yake ki taimaka min ki bani damar da zan gyara laifina, ba ni buri sai na ki, ki min masauki a gefen zuciyarki dan Allah Nawwara” Hawaye na zuba a idanuwansa yake min wannan rokon da ya soma karyar da zuciyata, nima na fara hawaye. “Bata lokacinka kawai kake Jibril, ka fitar da ni a ranka ka manta da ni a duniyarka, kai ba tsarata ba ne, na rumtse ido daga kallo duk wani abu da ya shafi rayuwata” “Ji ceci rai Nawwara, idan yanzu na fadi na mutu ke ce sila, ki taimaka ko dan dan mu” “Dan mu? Ko da na? Dan da ka ce ba naka ba ne? Ka wulakanta ni saboda cikinsa? Dan da tun da ka turo ni gidanmu ba ka taba saka kafarka ka zo duba shi ba? Dan da baka san cin sa ba baka san shansa ba? Dan da baka san ya rayuwarsa ta ke ciki ba? Dan da ka kasa yankawa ragon suna kasa a ka kirashi da shege? Mahaifina shi ya yanka masa rago ya saka masa suna, yanzu har kana da bakin da zaka kira shi da danka? Kana da idon da zaka zo rana tsaka ka kalleshi kuma ka fada masa kai ne mahaifinsa? Ta wace fuskar zai kalleka? Taya zai kiraka Uba?” Tun da na soma magana ya rumtse ido ya matse hannayensa da ke hade guri daya yana cizo baki, da alama maganar tawa bata masa dadi, sai kuma ya dago fuskarsa da ta yi ja ya kalleni. “Fada min abunda zan yi wanda zai sa ki yafe min, fada min tafarkin da zan bi Noor ya karbe ni a matsayin ubansa? Taimakeni Nawwara, ki tausayawa rayuwata zan yi komai kike so am ready to die for you” “Ka wuce sanina Jibril, kaje ka nemi matar da zata so ka ta aureka ta haifa maka yaya, shawara daya zan baka kaje ka yi abunda zai taimaki rayuwarka ina maka fatar samun irin matar da kake so Allah baka sa'a” Mikewa ya yi tsaye ya fice cike da nauyin kafafu, ba tare da ya share hawayen da ke fuskarsa ba. Ni kuma na zauna kusa da dana ina kukan da ban san na minene ba, tausayin da na ko kuma rayuwar da na cinci kaina a ciki.? Bayan sallah isha'i Jidda da mahaifiyarta suka zo duba Noor, daman tun da magariba wasu daga cikin mutanen babban gida suka zo duba shi. Bayan fitarsu sai ga Bilal ya shigo hannayensa da ledoji har gudu hudu har kuma lokacin Noor be farka ba gaba daya hankakina ya tashi duk da likitan ya fada min zai dauki tsawon lokaci yana bachin. Kallo daya na yi ma Bilal na kawar da fuskata, bana ganin komai sai wacan abun da ya faru shekaranjiya wani irin kishi da bakinciki sai suka taro min har na ji kamar na dauki wukar da aka aje ta yanka lemu na daba masa a kirji. Da Inna ya fara gaisawa sannan ya gaishe da wata abokiyar Inna suka gaisa da Sakina, sai duk suka tashi suka ba mu guri, daya ya zama daga ni sai shi sai kuma Noor da baya cikin hayyacinsa. “Nawancy... Wallahi ba abunda kike tunani ba... ” Hannu na daga masa “Kai ko Zinatu ko wani abu da ya shafi rayuwarku a yanzu be dame ni ba” “I know i shouldn't, ya jikin Noor?” “Da sauki” “Allah ya kara sauki” “Amin” Bayan wannan bata maganar bata sake shiga tsakanin mu, da ya gaji da zama ne ya mike tsaye ya karasa kusa a Noor cike da nuna kulawa ya duba shi sannan ya kalleni ya ce “An kama wadanda ya kade sa?” “Ya gudu, amman mutane sun ce da gangan mutumen ya yi cikinsa da mota ya kadesa, kuma likitan ya ce min Noor ya karye a hannu” Na fada ina fashewa da kuka. “Sorry a wani waje ne?” “Sun taso makaranta ne, mutunen ya gudu” “Amman Mahaifinaa ya sani?” Wani kallo na watsa masa na sakar masa idanuwana ina ta kallon fuskarsa cike da tsanar furucinsa. “I mean Jibril” “Kaima kana cikin mutanen da je ganin laifina akan Jibril ko?” Yayi saurin komawa ya zauna. “No ba hakan na ke nufi ba, Jibril ya wulakanta ki Nawancy kuma ya cancanci ko wane irin sakamako daga gareki, Wallahi ko ke ce baki da gaskiya i will support you ballantama kina da gaskiya, kawai bana son abubuwa su miki yawa ne, tunani a yanzu ba na ki ba ne, ki sassautawa zuciyarki, kuma ki rika neman shawara akan abunda ya shige miki duhu” Na share hawayena na maida idanuwana gurin da na, sai na cinkayo muryarsa yana fadin. “Ni kaina ban san ranar birthday dina yayi ba, sai a Facebook, su suka turo Zinatu kuma friend dita ce a fb few weeks ago ta turo min friend request na yi accepting ba tare da tunanin komai ba, ta yi min happy birthday tun ana saura kwana daya na yi birthday na, ina tunanin ta nan ta gane xan yi birthday a ranar har ta siyo wannan cake din, ina zaune ta shigo da shi ta kira abokan aikina ban ma san ta kira ki ba sai da na ganki office din” “Mi zai sa ta yi haka? Daman can tana son ka?” “Gaisuwa bata taba shiga tsakanin da Zinatu ba, idan har kiga na mun hadu sai idan aiki zamu yi, ina tunanin ta yi hakan ne saboda ta shiga tsakaninmu ko kuma...” Sai ya yi shiru be karasa ba. “Ko kuma me? Jibril ne ya sata ko? Zai iya saboda mugu ne” “Ni dai iya abunda na ke son ki sani, ba zan taba cin amanarki ba” “Amman miyasa ka yi blocking din number ta? Kuma ina ta tura maka sako baka min reply” “Saboda na baki damar yin tunani da zuciyarki, ina ganin kamar ina kan hanyar da ba zata bulle ba ne, zuwan Jibril a karo na biyu cikin rayuwarki ya karyamin kuzari, bana son na shiga tsakanin farincikinki da kuma tunaninki, bana son na yi abunda zai raba hankalinki gida biyu, na yi hakan ne saboda na daga miki kafa kuma na samawa rayuwata mafita saboda bana so na rasa a take, zuciyata na raya min kamar ba zan aureki ba Nawancy, kin ki bani damar da zan ga magabatanki kuma gashi Jibril zai yi duk abunda zai yi wajen ganin ya mallakeki” Tausayinsa ya kamani, duk da kasancewar ni ma ina tausayin kaina. “Kokarin mallakata yake Bilal kai kuma tuni ka malleke zuciyata, idan har Nawwara bata auri Bilal ba to ban cancanci auren ko wane irin namiji ba a duniyar nan, na fara rayuwa sau daya sai kuma na mutu, kai ne ka dawo da ni duniyar da mutane suke rayuwa, ka yi nasarar canjani daga mutum mutume zuwa mutum wacce ta san mi ake nufi da rayuwa, na rayu a lokacin da rayuwa take da muhimmanci a gareni, sai Jibril ya kashe min ruhi kuma ya kona shi ya maidashi toka ya shekarda da shi ya bi iska, kai ne mutumen da ka hada tokar ruhina ka tattarata ta sake zama cikakken ruhi na maida shi a cikina, har zuciya ta bude ta kamu da son ka. Kai ne kadai mutumen da nake so Bilal kai ne mafarkina, burina idan har ka ga ban aureka ba ka tabbatar gawata ce ta ke magana ba ni ba” Lumshe ido ya yi ya hade yawu sannan ya bude kamar dai be yarda da ni ba, sai ya mike tsaye yana fadin. “Idan kina bukatar wani abun ki fada min, ko ki kirani, ina son ki san da wannan Nawancy ina sonki sosai ina kaunarki kauna ta hakika” Da kallo na bishi har ya fice, sannan na juyo ina share hawayena na kalli Noor da ke motsi. _______________________________ I dedicate this chapter to my wattpad people 😘😘😘 *RAI BIYU...♥️🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣4⃣ Bayan fitar Bilal su Inna suka shigo tare da Mama Turai wato Yayar Inna wacce suke uwa daya uba daya. Inna ta zauna saman tabarma ita kuma ta zauna saman kujerar da ke gefen gadon ta Kalli Noor sannan ta kalleni ta ce. “Innarki ta labarta min komai, kuma abunda kike ba ki kyautawa, tun da har ya tuba ya dawo ya nemi ganin dansa ai sai ki bashi dama, ke yanzu in ban da Allah ya nufa ko hanya kin isa ki hada da babban mutun kamar wannan balle har ya zo yana rokonki? In wani ne karbe dansa zai yi da karfi ya barki nan, kin samu ya dawo yana neman yafiyarki kina ta masa wasa da kwakwalwa kamar karamin yaro” Na tada kai na kalleta. “Ke ma laifina kike gani ko Mama Turai?” “Ai dole na ga laifinki, mutumen arziki irin wannan mai kudi haka, ai sai ki bashi dama ko arzikin nasa ku tatsa ni Wallahi da yana son yata da na aura masa mu ga karshen iskanci” “Amman yanzu har kun manta irin cin mutuncin da cin zarafi da ya yi min?” “Yanzu ba ya dawo ya tuba ba? Ai Allah ma mukan masa laifi ya yafe mana balle ke da wani be san da zamanki a duniya ba, ke kikan irin laifin da kike yi ma Allah ne?” Idanuwa sun cika da kwalla saboda na san babu wanda zai fahimce balle ya goya min baya, ni kadai na ke jin abunda na ke ji wata kila saboda ni Jibril ya yi ma abun ba kowa ba. Wannan karon Inna ce ta dora da “Idan har sakamakon Ubangiji kike so tau ko ya kamata ki mika lamurranki gurinsa, ba yin kanki ba ne Allah ne ya jarrabeshi da sonki kuma ya saka masa nadamar abunda ya yi saboda ya jarrabeshi, ki yanzu ba jindadinki ba ne mutumen da ya ce Noor ba dan sa ba ne yanzu har yake risina miki kasa yana neman ki hada shi da dansa? Allah yana son masu yafiya, kuma ba a rama cuta da cuta sai dai a maye cuta da alheri, ina ji miki tsoron kar wannan abun ya dawo kanki, kuma da Noor ya girma ya nemi ubansa ai kara ya girma da Ubansa” Ganin yadda na ke sharar kwalla yasa Inna ta taso ta dafa. “Na san ya cutar da ke yata amman karki mata shi ma Allah ba zai barshi ba, kuma ba kisan halin da ya shiga ba kamin ya gane cewar ke alheri ce a gareshi, ba dan Jibril yana da arkizi na ke son ki yafe masa ba, sai dan hakan zai wanke ki daga zargin da duniya take miki, kuma Noor zai samu rayuwa mai kyau, ke kuma zaki samu damar gina taki rayuwar a gidan aurenki idan kika auri wanda kike so” Bani da wani zabin na yafiya ga Jibril saboda yadda Inna take son na yafe masa din, na kan yi kokarin yin abunda duk mahaifiyata take so ko kuwa abun nan baya min dadi, ba dan komai ba sai dan na san ba zata cutar da ni ba, kuma yarda Allah tana tare da yarda iyaye, na yi ma uwar wasu biyayya ma balle tawa uwar wacce ta dauki ciki ta yi nakuda ta haifeni ta raineni na girma, hakika bana da wani farinciki sai na mahaifiyata. “Zan yafe masa Inna matukar yafe masa din zai faranta ranki, zan yafe masa” “Na jidadi Allah ya miki albarka kema ya baki yayan da zasu yi miki biyayya” Ajiyar zuciya na sauke na share hawayen da ke min zuba ina kallon Mama Turai da ke wasar baki. “Haba ko ke fa, amman ace zuciya kamar ta kafiran farko, Allah ya shiga ya tsakaninku ai mun fi son a shirya” “Dan na yafe masa ba yana nufin zan aureshi ba ne, dan Allah karku tirsasamin yin wani abun daban kuma” “Babu wanda zai tirsasa miki, wata rana ke da kanki zaki karanta mana sirrin zuciyarki” Cewar Inna, ni kuma na kalleta na ce “Zuciyata bata da wani sirrin bayan wanda ke zahiri ke kanki kin san babu wanda na ke so bayan Bilal, be kamata ki zargeni da son wani bayan shi ba” Sai  Mama Turai ta taso ta karaso kusa da ni tasa hannunta ta tallafo fuskata yadda zan fuskanceta. “Tausayin Bilal kike Nawwara amman asalin son yana gurin Baban Noor, ke kanki ba ki san abunda ke damunki ba a yanzu, kina tausayin Bilal amman ba za ki iya aurensa ba, kaddarar da ta hada ku ba zata iya bari ku yi aure ba, saboda ke makwafin RAI BIYU ce a gurin Baban Noor idan babu ke koda ya samu Noor rayuwarsa bata kammaluba, haka ma Noor kina matsayin RAI BIYU a gunsa matsayin uwa kuma uba, babu rabon Bilal a jikinki shiyasa kika kasa bashi dama, Baban Noor kuma be da rabo a jikin kowa ce mace sai ke shiyasa kaddara ta sake hada ku kuma zuciyarsa ta kasa barinsa zama lafiya har sai ya nemo mata yar'uwata, ke ma kuma baren zuciyarki yana gurin Noor da Babansa wannan yasa har gobe ba zaki iya amsa kanki a matsayin cikakiyar mace mai jin kanta a mace ba, kika kasa bawa kowa damar sake aurenki gashi Baban Noor ya dawo. Wani baya auren matar wani Nawwara, da kika auri Faruk baki haihu da shi ba ya mutu ya barki saboda Baban Noor ya samu damar sake aurenki, ko da kin haihu da Faruk sai kin fito saboda kaddara ta yi niyar hadaki da tsohon mijinki Nawwara, kurciya ce take cin ki ke kanki yanzu baki san abunda kike so ba, da yanzu za a daura miki aure da Bilal da ba zaki iya zaman aure da shi ba saboda ba shi zuciyarki ke so ba, kuma kaddara ba zata barku ku yi zaman aure ba, ya kamata ki yi tunani karki aikata abunda zai cutar da ke” Tana gama fada min haka ta kalli Inna ta ce. “Ni na tafi Allah ya ba Noor lafiya” Binta Inna ta yi suka fita tare suka barni a dakin ina faman hawaye, ba zan iya bari kalaman Mama Turai su yaudari zuciyata ba, tabbas ni dai na san Bilal na ke so kuma shi zan aura, ba zan zargi Inna ma domin nasan bata cikin irin mutanen nan da ke son yayanta su auri mai kudi, amman wani lokacin ina ganin kamar saboda Jibril yana da kudi ne yasa take son shi, duk da kasancewar Bilal ba talaka ne talak ba, yana da aikinsa kuma ya yi karatu familynsa ma suna da rufin asiri, amman zuciyar Inna ta fi karkarta gurin Jibril. Motsi Noor ya sake yi a karo na biyu har yana kokarin bude idonsa yana motsi da hannu. “Momy... ” Na yi saurin share hawayena na kama hannunsa. “Na'am Noor sannu ka ji” “Momy da zafi sun jimun ciwo sosai” “Kyalesu Allah ya isar maka ya baka lafiya” Ya kalleni da idanuwansa da suka yi fari sosai, sai kuma ya kalli gefena. “Momy na yi mafarkin Babana ya zo nan” Gabana ya fadi. “Wane Baba kuma?” “Wanda ya rasu” Ajiyar zuciya na sauke. “Wanda ya rasu ai baya dawowa Noor, mafarki kawai ka yi” Na shafa kansa sannan na mike na fita dan kiran likita. JIBRIL POV. Da taimakon Allah ya isa gida, zuciyarsa ta yi masa mugun nauyi, ko parking din kirki be yi ba ya fito ya nufi main house jiri na dibansa, yana shiga falo na fadi a bakin kofa yana tari a wahalce gubar da ya taba ci ta taso masa ta hadu da dattin cocaine dake cikin huhunsa (lung) sai aman jini, har idanuwansa suka canja kala kamar ba zai rayu ba, gashi falon babu kowa sai shi kadai. Tun yana iya gani har ya koma yana gani dishi-dishi sai kuma numfashinsa ya soma nisa hankalinsa ya ba ce 6at. Ko da ya farka an dora masa kyalle mai sanyi saman kai, yana kwance saman doguwar kujera, Siraj na zaune kusa da shi Zinatu kuma na fuskantarsa fuskarta dauke da tausayinsa. Unkurawa ya yi ya tashi zaune sai ta yi hanzarin miko masa ruwan gora mai sanyi ya karba ya sha. “Yaushe kuka shigo?” “Tun dazu, gashi har an yi magariba kana sume, Zinatu ce ta gyara gurin kuma da taimakonta muka doraka saman kujerar nan” Cewar Siraj, sai Jibril ya tada kai ya kalleta ya ce “Thank you” “Never Mention Allah ya sauwake ni zanje gida” “Ba zaki bari na sauke ki ba?” Ta kalli Siraj da ya yi maganar ta ce “No zan je da kaina ya kamata ace ina gida by this time, ka kula da abokinka please” Daga haka ta dauki jakarta ta rayata ta fice, sai Jibril ya unkura zai tashi kirjinsa ya yi masa wani mugun tsuka hakan yasa shi saurin komawa ya zauna yana yar kara.    Siraj ya dafa shi. “Ka bari ka kara hutawa mana, Jibril kana matsawa kanka da yawa akan yarinyar nan, direban ka ya fada min ka bi bayanta sai kuma na zo nan na sameka cikin jini, ka rika sassautawa kanka dan girman Allah ina tausayin halin da kake ciki” Jibril ya kalleshi irin kallon nan da shi kadai ya san fassarasa. “Miyasa ka ce min ba ni da Nawwara? Bayan kuma ina da shi” Siraj ya hade yawu da karfi. “Wane irin kana da shi? Ban fahimce ka ba” “Na ga dana da idanuwa Siraj dan da na haifa da Nawwara dan me zaka boye min?” “Wace riba zan ci idan na boye maka? Mi zaisa na boye maka? Amman ka tabbatar dan ka ne?” “Da na ne, jinina da nasa iri daya ne, kamata da tasa iri daya ce, da ace ba a kade shi ba da ba zan samu ganinsa da wuri ba” “Amman abun nan ya bani mamaki, sai gaskiya akwai wani a abu a kasa, domin wanda nasa na bincika mana ba zai yi karya ba, shi ya fada mana Nawwara bata da da ko daya, sai idan mutumen dan uwanta ita kuma ta nemi ya boye mana din” “Taya xaka yi bincike kuma ka nemi dan uwanta? Dan ina ne mutumen?” “Dan unguwarsu ne, amman abun nan ya bani mamaki amman ka bincike Nawwara ta tabbatar maka da danta ne? Shin yana ma raye?” “Yana raye wani ya kade shi da mota, and nayi duk wanda ya taba min yaro ko da Nawwara ce ba zan kyale ba” Siraj ya karkato ya kalleshi “Amman idan kaddara ce fa?” “Ban san kaddara akan da na ba, da ce ni ta mai motar ya kade zan dauka ko amman da na? No never da yanzu na rasashi fa? Kasan halin da Nawwara zata shiga ko kasan halin da ni zan shiga? Who's ever that person is i will never forgive him” Wani gumi ne ya soma saukowa Siraj, Jibril kuma ya mike tsaye yana jin zafin da kirjinsa ke yi ya nufi bedroom dinsa, saurin mikewa tsaye Siraj ya yi ya rufa masa bayan. “Yanzu ya zaka karbi danka hannun Nawwara?” “Shine abunda na ke tunani, zan yi duk yadda take so wajen ganin ta bani da na” “Ni abunda na ke tunani mai zai hana ka fara fake love da Zinatu, so that ka samu kan Nawwara kuma ka gane idan har yanzu akwai soyayyarta cikin ranka” Jibril ya kalleshi “Wani lokacin kana yin abu kamar baka san waye ni ba Siraj, am straight forward, if yes yes if no that's means no for sure” “Baka fahimta ba ne Jibril ai fake love na ce, kuma da sani Zinatu zaka yi” “Ba zan yi ba, ka tafi kawai zan samawa kaina mafita” Cikin sanyin jiki Siraj ya juya har zai fita sai kuma ya juyo ya kalli Jibril ya ce. “Cocaine...” “No please bar ni na ji da abunda ke damuna” Ya fada yana daga masa hannu, sai Siraj ya juya kunya kunya da shi ya fice. Bathroom Jibril ya shiga ya sakarwa kansa ruwa sosai sannan ya yi wanka gaba daya tare da alwala ya fito, ya saka jallabiya ya rama sallah la'asar ya yi magariba, yana saman carpet din har aka kira isha'i, bayan ya yi ya taso ya dawo parlor ya shiga kitchen ya hadawa kansa ruwan tea. Sai kuma ya dawo falo ya zauna hoton Noor kawai idanuwansa ke nuna masa, sai ga wayarsa na ringing sai a lokacin ya kula da inda wayar take gefen kofa inda ya fadi dazu. Zuwa ya yi ya dauka sai yaga number Abbah. Gaiswa suka fara yi da Abbah kamin ya rufe shi da fada. “An fada min baka da aiki sai shan cocaine, ka maida kanka wani kalar mutun, idan ba zaka iya ba zan karbe ragamar kamfanin nan na mika a hannun Siraj tun da ya fika kula” “Waya fada maka ina shan cocaine Abbah” “Kai ka fada min, kai kullum abun ka gaba yake ba baya ba” “Ka yi hakuri Abbah zan canja” “Da ya fi maka” Daga haka Abbah ya kashe wayar. A ranar Jibril be gi bachi ba sai ya tashi ciki dare yana ta sallah nafila abunda be taba yi ba a tsawon rayuwarsa, kuka ya yi sosai ya kaima Allah bukatarsa, shiriyace a cikin abubuwan da ya fi roko sai kuma Nawwara, da asuba ma bayan ya yi sallah asuba ya dora da istigifari yana kankantar da kansa yana neman Allah ya yafe masa. Washe gari ya kira wani abokinsa ya hada shi da mai tattoo ya zo har gida ya wanke masa tattoos dake wuyansa da kuma na sunan Nawwara da ke hannunsa. Bayan mutanen ya fita ya shiga kitchen ya soma kansa kwai duk da yana da kuku be nemi ya yi masa ba sai ya hada tea da kansa, a dinning room din kitchen ya zauna yana ci sai ga Siraj ya shigo, bayan sun gaisa ya zauna shima ya zuba ma kansa yana ci, bayan sun gama ya budewa Jibril cocaine. Sai da Jibril ya yi kamar ba zai sha ba sai kuma shaeidan ya zugashi ya dauka ya shaka sosai, sannan ya mike tsaye yana fadin. “Ba zanje office ba, ka yi duk abunda ya dace, Nawwara ma ba zata je ba, saboda dan mu ba lafiya” Be jira abunda Siraj zai ce ya fito daga kitchen din na nufi bedroom dinsa. Saman gado ya kwanta ya rika bachi kamar wanda ya mutu, be farka ba sai da aka yi sallah azahar. A daren ranar ma sai da Jibril ya raya shi da nafila yana ta rokon Allah ya karkarto masa da hankalin Nawwara kuma ya shiga tsakaninta da duk wani mai son ta bayan shi, abu daya yake ce masa tuwo a kwarya a yanzu ba komai bane face rashin iya karatun kur'anen, haka zai dauko kur'anen ya rike but he can't read it ko baki be iya hadawa balle har ya tada ya karanta aya, and now he need to know his religion more than everything, yana son yasan abunda Allah ya ce da kuma wanda ya hana, zuciyarsa na raya masa idan har ya shiryu ya zama na kwarai Nawwara zata so shi, a duk lokacin da ya tuna da dansa yana asibiti sai ya ji kamar zai mutu saboda yana son naje ganinsa sai dai yasan Nawwara ba zata bari ba. Haka ya jera kwana uku be sake saka Noor a ido ba a duk lokacin da tunaninsa ya taso masa sai ya dauki cocaine din ya sha sannan ya samu sassauci. Misalin karfe biyu dare yana zaune saman carpet yana istigifari sai ga Abbah ya kirashi, da fari ya ji tsoro dan yasan Abbah be saba kiranshi a irin wannan lokacin ba, sai kuma daga baya wani tunanin ya zo masa na cewar wata kila Abbah zai masa fada ne akan rashin zuwa aiki da ya yi kwana biyu. “Hello” “Jibril kana lafiya?” “Lafiya kalau Abbah” “Ka tabbata?” “Lafiya ta kalau” “Allah ya tsare ka, kawai na yi wani mafarki ne marar kyau ina fatar babu komai ko? ” “Babu komai Abbah sai damuwa, Nawwara ta ki fahimta ta Abbah kuma akwai da a tsakaninmu” “Ni ma na samu wannan labarin lokacin da na je zan bawa iyalanta da kuma ita kanta hakuri akan abunda ka yi musu, sai dai ba samu ganin yaron ba” “Abbah da gaske? Yaushe ka zo?” “An kwana biyu, kawai dan ban fada maka ba ne” Abbah ya labarta masa komai daga zuwansa da kuma abubuwan da suka faru, Jibril ya ji dadi hakan ya tabbatar masa da mahaifinsa yana sonsa kuma yana tare da shi. “Abbah ka taimaka ka min izinin zuwa gidansu Nawwara Dan Allah” “Ka yi alkawarin ba zaka yi wani abu marar kyau ba?” “Taya mai neman hanyar gyara zai yi wani abu marar kyau? Wallahi Abbah ina son Nawwara sosai kamar zan hauka ce” “Amman da muka zaba maka ita ai cewa ka yi baka son ta” Ya yi shiru be ce komai ba, sai Abbah ya kara da “Kuma kasan sai dai ka yi hauka dan babu aure a tsakaninku ko? Kasan saki uku ka yi mata fa” Idanuwansa sun cika da kwalla. “Yanzu Abbah babu wani gyara da za a iya yi? Ba wata mafita?” “Babu zan kwanta sai da safe” Abbah ya kashe wayarsa, sai Jibril ya fara surutai “Dole akwai mafita Wallahi, dole a samu mafita No no no” Wannan tunanin ne ya hana shi bachi har garin Allah ya waye, tun da asuba ya shirya ya fita, kai tsaye asibitin ya nufa. Ya taki sa'a yau Nawwara ce kwana asibitin, ko da ya tura kofar dakin ya shiga zuciyarsa na bugawa dan ya yi tunanin zai samu Inna a ciki ne ko kuma ya tararda Nawwara a farke, sai ya tarar tana kwance bayan Noor saman gadon asibitin suna ta bachinsu a tare, karasawa ya yi kusa da su fuskarsa dauke da murmushi yana kallon iyalinsa. Wayarsa yasa ya dauke su hoto sannan ya cire jacket dinsa ya lulluba musu ya zauna saman kujerar da ke facing dinsu yana ta kallonsu cike da shauki. “Na bata komai, da yanzu muna nan a iyali daya” Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana Noor farkawa daga guntun bachinsa ba, sosai da sosai yake kallon Jibril ganin wani babban mutum mai kama da shi, sai kuma ya unkura ya tashi zaune zai yi magana Jibril ya dora hannunsa saman bakinsa ya yi masa alama da ya yi shiru. “Shiiiiiiiiiiii” Sai ya mika masa hannu alamar ya zo, ba musu Noor ya mika masa nashi hannayen sai ya dauke shi ya zaunar saman jikinsa ya rumgume ya lumshe ido. Hawayen farinciki da bakinciki suka cika masa ido lokaci daya. “Waye kai kai likita ne?” Noor ya tambaya da muryarsa yar karama. Sai Jibril ya girgiza masa kai alamar a a ba tare da ya bude idon ba. Shi kuma sai ya sake tambaya cike da mamaki yana ta kallon fuskarsa. “Kai ne wanda Inna ta ce min zaka zo ka ganki? Kai ne Uncle din?” Ya gyada masa kai still be bude idon ba dan baya son Noor ya ga hawayensa, Nawwara kam bachi kawai take abinta bama san ana yi ba. NAWWARA POV. karar bude kofar da aka yi ne ya tasheni daga dogon bachin da na ke, sai turaren da na fi tsana a duniya ya yi marhaban sannan na kula da jacket din da aka lulluba min saman jiki. Inna na gani zaune tana jan karbi ba Noor a kusa da ni kamar yadda muka kwanta, saurin zabura na yi. “Ina Noor?” “Yana gurin Babansa” “Dauke sa ya yi? Miyasa kika bari ya shigo?” “Ke ya kamata na tambaya dan nan na shigo na sameshi” Na sauka saman gadon hankalina a tashe sai Inna ta rike hannuna. “Ba gudu zai yi da shi ba, sun fita waje ne su sha iska, ina tunanin ya canja Nawwara a nan ya durkusa yana ta ba ni hakuri, wannan abincin karyawar da kika gani daga kamfani yasa aka kawo” “Wallahi zai iya gudun min da da mugu ne” Na fita daga dakin hankalina a tashe, ina fitowa harabar asibitin sai na hango Noor saman motarsa zaune shi kuma na jikina jikin motar ya rumgume Noor. Karasa na yi ina masa fada. “Waya baka izinin fitar min da da?” Sai ya dago ya kalleni sai ya sauko da Noor da ko riga babu a jikinsa. “Ki yi hakuri na fita da shi ne ya sha iska” Daukar Noor na yi na koma da shi ciki, shi ko sai zuba min tambaya yake akan wannan Uncle din nasa da Inna take fada masa zai zo ya duba shi. A ranar duk wanda ya kawo mana ziyarar dubiya ya tararda Jibril a asibitin saboda nan ya wuni, duk wani tafiyar numfashin Noor yana kula shi hannun kuma maikaraya yana kula da shi sosai, na yi mamakin da Zinatu ta zo ganin Noor ko da yake ba abun mamaki ba ne duba da Jibril yana cikin asibitin, yau kan Bilal dake zuwa kullum duba Noor ya tarar da Jibril wanda hakan yasa shi kin sakewa sosai daman kwana biyu nan na rasa gane kansa, hakan be min dadi ba dan ban jidadin ganin da Bilal ya yi ma Jibril a asibitin ba, ni kuma na raka shi har gurin gate din asibitin sannan na dawo. A lokacin Jibril ne kawai cikin dakin Jibril ne kawai sai Noor suna rike da hannun juna, daman Inna waje ta koma da zama bata iya zama a cikin dakin matukar Jibril na ciki. Kamar jira yake na shigo sai ya mike tsaye ya nuna ni da yatsa fuskarasa a kumbure saboda bacin rai ya ce. “Kar Bilal ya sake zuwa duba min yaro wannan ya zama na farko kuma na karshe...” Kallonsa na ke sai ma na rasa abunda zan ce masa, daman na san za a rina saboda ya tsargu da yadda na nunawa Bilal kulawa kuma ina ta masa kalamai masu dadi a gaban idonsa, sai dai mai? Ai be isa ya hana Bilal zuwa ganin Noor ba ko dan na bashi dama ya wuni da shi ya bashi damar samun guri har ya fada min wannan maganar? Bana son na yi wata magana a gaban Noor saboda kar ya fahimci wani abu, wannan yasa na kumde maganar da ke bakina har sai ya fita na bishi na fada masa. Turo kofar da aka yi aka shigo ne yasa dukanmu muka kalli kofar Mustapha ne ya shigo cikin manyan tufafi tare da manyan ledoji Jidda na gafensa. [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣5⃣ MUSTAPHA POV. Mustapha ya yi farincikin tararda Jibril da ya yi a dakin ko ba komai yasan Jibril ba zai jidadi ba, a farkon shigowarsa ya shigo da fargaba da kuma tunanin irin kallo da wulakancin da Nawwara zata masa, amman ganin Jibril ya sashi sakewa kamar daman can sun saba da Nawwara. Murmushin fuskarsa ya fadada ya kunno kai cikin dakin tare da Jidda yana kallon Nawwara. “Pretty ashe Babynmu babu lafiya, Wallahi ban sani ba sai jiya ya jikinsa” Sai da Nawwara ta hadiye yawu sannan ta amsa masa fuskarta ba yabo ba fallasa. “Da sauki” Kana ta watsa ma Jidda harara. Kamar be san an hallici mutum a gurin ba haka ya bi ta kusa da Jibril ya karasa kusa da Noor ya dire ledodin da ke hannunsa. “Cute Boy waya kade min kai” Noor ya dade yana kallonsa kamin ya amsa masa bakinsa da nauyi. “Nima ban san shi ba” “Am sorry dear” Ya fada yana zama kusa da shi tare da duba hannun sai kuma ya juyo ya kalli Nawwara. “Pretty amman da sauki sosai ko?” Nawwara kamar ba zata amsa shi sai dai ganin Jibril yasa ta karaso gurin tana fadin. “Eh a hannu kawai ya kare” “Wallahi ban sani ba sai dazun nan Jidda ke fada min” Nawwara ta kalli Jidda sai Jidda ta dan zaro idon tana daga kafadarta. “Ya matsa ne sai ya ganki kin san yadda yake damuwa” “Sorry na zo ban fada miki ba” “Ba komai” Cewar Nawwara. Jibril ya rumtse ido ya sauke ajiyar zuciyar da ta mamaye masa kirji, sai ya juyo cikin facin rai ya ce. “Ya kamata ku tafi yanzu, amman kai yaron nan i warning you karka sake shiga sabgar Nawwara ko ban fada maka ba” Daga Nawwara har Mustapha da Jidda kallonsa suke. “Waye wannan daman ka san shi ne?” Jidda ta tambaya tana kallon Mustapha, sai Jibril ya yi cikinta kamar zai dake ta. “Babu ruwanki a ciki” Matsawa baya Jidda ta yi ganin yadda temper dinsa take, sai Mustapha ya taso daga inda yake zaune kusa da Noor yana murmushi ya karaso daf da Jibril ya soma gyara masa kwalar rigarsa. “Ka kwantar da hankalinka Man, macece fa ba namiji ba kasan namijin da ya amsa sunansa namiji baya taba dukan mace, ko da yake kai ragon namiji ne, shiyasa kake duka kuma kake cin zarafin yarinyar nan marainiyar Allah, anya babu kai a cikin kashe mata mahaifi kuwa? Saboda na ga ka tsawwalla rayuwarsu ne da yawa ka siye gidansu... oops sorry na manta she's your ex...- ” Ya karashe maganar yana murmushi. Jibril ya daga hannu cike da hasala zai naushi bakinsa sai Mustapha ya rike hannunsa cikin zafin nama ya kai masa na shi naushin a baki har sai da Jibril ya yi baya baya ya rike bakin. “1-1” Mustapha ya fada yana murmushin keta. Sai Nawwara ta katsa musu tsawa. “Miye haka? Ya zaku rika yin abu kamar kananan yara?” Murmushi Jibril ya yi ya kallon Noor da duk tsoro ya gama mamayeshi ya ce “Wasa ne fa kawai karki daga hankalinki, amman ki fada masa karya sake zuwa kusa da yaro na” “Ba dan ka na zo nan ba dan Nawwara ne, duk kuma abunda ya shafi Nawwara dole ne ya shafe ni” Jibril be kara ce masa komai ba, domin yasan wani furuci na fitowa a bakinsa ba mai dadi ba ne, kuma baya son ya yi abunda be kamata ba a gaban dansa, sai kawai ya karasa kusa da Noor ya zauna yana shafashi tare da fiddo wayarsa ya kunna masa game. “Mu zamu koma, daman na zo ne kawai ganin Noor Allah ya tsare gaba” “Amin” Cewar Nawwara, sai Jidda ta daga mata hannu. “Zamu yi waya” “Ok thanks” Suna fita Mustapha ya fara tambayar Jidda labarin Jibril, sai dai bata fada masa komai ba saboda tana tunanin sirrinsu ne ita da Nawwara, but itama tana mamakin yadda aka yi Nawwara ta hakuru har haka ta bari ya zo ganin Noor. “Amman shi Nawwara take so ko?” Mustapha ya tambaya yana driving, sai Jidda ta kalleshi. “Bata son shi, ni dai iya sanina Nawwara Bilal take so” Kamar zai sake cewa wani abu sai kuma ya yi shiru, sai dai ransa yau yana cike da farinciki saboda abunda ya yi ma Jibril. A bakin kofar gidansu Jidda ya sauketa sannan ya juyo ya dawo gida. Tun a yanayin shigowarsa ya tabbatarwa da Momynsa yana cikin farinciki, Daddy sa ma ya lura da hakan kasancewar dukansu suna zaune falo ne har su Ikram da Zarah suna kallo harin da aka kai Iraq a channel din Al Jazeera. “Dad Mom barka da dare” Sai da suka amsa masa sannan ya zauna saman cushion yana kallon tv kamar yadda suma suke kallo, sai dai ko kadan hakalinsa baya gurin yana can gurin Jibril tunanin halin da Jibril zai kasance kawai yake yana murmushin da be san ya fito masa ba. “Son lafiya kake wannan far'ar?” Ya kalleta kamar be san ya yi ba. “Ba komai, but Mom Dad ya kamata ce kunje ganin yaron Nawwara ya samu accident” “What...?” Dadynsa ya fada. “Mu zaka fadawa muje mu duba yaron Nawwara? Hajiya baki fada masa ya fita harkar yarinyar nan ba? Daman yana nan akan bakansa?” Momy ta yi saurin dagawa Dadyn hannu. “Komai da sannu ake binsa kasan halin Mustapha” “Babu ruwana da wani halinsa, ka var ganin kai kadai na haifa zan iya shafe labarinka a doron kasa matukar ka ce zaka auri yarinyar, ka dauki kanka a matsayin matacce matukar ka tsaya kai da fata akan yarinyar nan” Mustapha da zuciyarsa ke boiling gumi ya zubo masa ya bude bakinsa da ke rawa ya ce “Daddy ina son yarinyar nan...” “Baka san so ba Mustapha, taya zaka so mace da ta auri namiji biyu kuma ta haihu? Kuma in banda haukarka macen da kayi ma kanwarta fyade zaka ce kana sonta kuma da aure? Kana tunanin zata aureka ne? Kana batawa kanka lokacin ne kawai, kuma na fada maka karna sake jin maganar yarinyar nan a cikin gidan nan, ka nemo yar kowa zan aura maka amman ban da ita” Yana gama fadar hakan ya mike tsaye ya kabe babbar rigarsa cikin bachin rai ya fice, sai Momy ta matso kusa da Mustapha tana kokarin yi masa bayani “Look son.. ” “No Mom ke kika ce min Dady ya yarda da maganar yarinyar nan, ashe ba da gaske ba ne? Miyasa ba zaku so abunda na ke so ba? Miyasa kuka gagara ganewa?” Magana yake kamar ba shiba har numfashinshi na hawa wani kan wani, kamin ta kara cewa wani abu ya tashi rai a bace ya bar mata falon. NAWWARA POV. Ba jidadin zuwan Mustapha ba domin ban fiye son yana shige min ba, bana son wata alaka tana shiga tsakanin ni da shi, dan ban yarda mutum ya cuceni kuma ya dawo ya ce zai rabe ni ba Jibrrma dan babu yadda zan yi ne. Bayan fitar Mustapha da mintuna talatin na kalli Jibril fuska a daure na ce. “Ina son na kwanta dare na yi fa? Kuma ka san Inna tana waje kai take jiran ka fita” “Ba zan je ko ina ba, a nan zan kwana tare da da na” Ban yi mamakin furucinsa saboda cocaine yake sha mahaukacin mutum komai zai iya ai, musamman idan ya samu guri in ban da rainin hankali daga kawai na bashi damar ganin Noor sai kuma ya soma yi min katsalandan a lamurrana. Tashi ya yi ya fita hakan yasa na bishi baya saboda na samu damar fada masa maganganun da ke bakina, ina fita na samshi bakin kofa a ashe ni yake jira. “Daga Bilal har wannan dan iskan yaron bana son su sake zuwa gurin da na” “Baka da damar da zaka shardanta min wanda zai so gurin da na da wanda ba zai zo ba, kai yanzu ko kunya baka ji ka kira Noor da danka? Har kana ikirarin kar wani ya zo dubashi?” “Yes da na ne, alakar da ke tsakaninku daban babu ruwana a ciki” “Ni na haifi yarona a hannuna ya girma baka da wannan hujjar Jibril, kuma ko zaka wulakanta kowa ban da Bilal saboda ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta ni da dana, shi Noor ya sani a matsayin Uncle dinsa ba kai ba, da kuma ba naka ba ne nawa ne” “Ko tau zamu gani” Na watsa masa harara, ina kokarin juyawa na koma cikin dakin sai ya fisgoni da karfi ya dawo da ni “Ban yarda ki kwana da shi ba, Inna zata kwana da shi i don't trust you” Dariya na farayi saboda abun ya bani dariya sosai. “I'm laughing it's funny very funny” “Ba wasa nake miki ba Inna zata kwana da shi ba ke ba, idan ba haka ba, ni zan kwana da shi” “Ban ga dalilin kwana tare da dan da ka kira da shege ba? Kai baka ma jin kunyar yanzu ka kira shi da danka?” Hannu ya daga kamar zai dakeni sai kuma ya juya baya ya dafe kansa da hannu daya. “Na dake ni mana, ai ka saba cin zarafina ko? Ka saba yi min wulakanci a gaban kowa, na yi min cin mutumcin da ya fi ko wanne ai ba ka hada hoto da na wani ba? Ka fadawa iyayena cewar ni karuwa ce..” “Enough...!” Ya fada a tsawa ce har sai da hankalin wanda duk wajen dakin ya dawo kanmu, wadanda suke cikin daki kuma suka fito waje, sai dai hakan be sashi fasa fadan abunda zai fada ba. “Ya isa haka Nawwara ya isa haka, wace irin zuciya ce dake haka? Ke kan wace irin mace ce me ke damunki miya ke cikin kanka? Miyasa kika zabi nanata maganganun nan a ko yaushe ne? Kin san abunda yake raina? Kinsan bakinciki da yake raina? Ban isa na wuce wannan kaddarar ba shiyasa na aikata but abunda kike yi babu tausayi a ciki Nawwara, am lemme tell you abunda kike ba burgewa kike ba kokarin kashe rai kike, kokarin rusa wata rayuwar kike kuma babu abunda zai sa na canja daga manufata” Yana gama fadar hakan yaja hannun Noor ta da fito waje suka koma cikin dakin, Inna hango Inna take na rufa masa baya rai na a bace. Noor na ganina ya yi saurin sakin Jibril ya dawo guna cike da tsoro, dan Noor ya tsani ganin ana fada. “Da na ni ya sani ba kai ba, karka sake shiga rayuwarsa” “Dole na shiga rayuwaraa saboda ni ne asalin ubansa” “Yes ubansa ne kai na gaji da boyewa” Na juyar da Noor ina nuna masa Jibril. “Ka ga wacan? Ba Uncle din ka ba ne shine asalin ubanka Baba Faruk ba babanka ba ne rika ka kawai ya yi, wacan azzalumin ne mahaifinka, shine wanda ya ce kai ba dansa ba ne, da aka haifeka be yanka maka rago ba, kuma be san zafinka ba...” Ban karasa na naji an dago ni an sauke min kyakyawan mari har biyu a fuska, wanda ya haddasa min daukewar wutar cikin kaina tare da ganin wadansu kanana taurari.. ___________________________________ Ku yi hakuri da wannan guntun page din 🙏 Mutane da suke cewa kar Nawwara ta yafewa Jibril sai ta musguna masa kuma su ke cewa Nawwara ta cika tsauri da yawa wai zuciya kamar ta kafiran farko 😂 Ni dai nawa ido 👁👁 [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣6⃣ Zafin marin ya haddasa min ganin duhu a idanuwana, sai na kyabta idon sau biyar sannan na ga Inna dake tsaye tana hararata, Noor kuma ya fashe da kuka ya rike min kafafu da dayan hannunsa. Hawayene suka soma zuba a idanuwana ina dafe da kuncina, sai na juyo na kalli Jibril da shi ma idanuwansa ke cike da kwalla, juyawa ya yi ya bar dakin ba tare da ya ce komai ba, sai da yaja kofar dakin sannan Inna ta soma fadamin maganganu marar dadi. “Ina miki kallon mai hankali ashe baki da hankali, abunda kika aikata a yanzu ya fi abunda Jibril ya yi ma Noor shekarun da suka wuce, miye abun burgewa a cikin fadar irin wannan maganar a gaban idon dansa? Wane irin kallo kike son dan sa ya masa? Kina tunanin burgeshi zaki yi? Ki haddasawa danki tsanar ubansa da kanki? Idan ke baki son shi karki shiga tsakanin uba da da, Wallahi da Noor zai girma a cikin talaucin da ya fi wannan kuma daga baya ya hadu da mahaifinsa dole ne sai ya masa biyayya saboda haka Allah ya ce. Wace irin zuciya ce da ke Nawwara, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne? Wa kika fi? Idan ma ba zaki yafe masa ba ai ba sai kin shiga tsakaninsa da dansa, Wannan ba halinki ba ne Nawwara kuma ba halina ba ne ba kuma halin Babanki ba ne, ban san inda kika dauko wannan bakar zuciyar ba” Tun da ta soma maganar na lumshe ido hawaye na cigaba da min zuba, sai na ji ta fisge Noor daga rikon da ya yi min ina bude ido ta nuna min hanyar fita. “Fita ki bar dakin nan” Na bude baki zan yi magana ta daga min hannu. “Bana son jin wata magana daga bakinki ki fice kawai kije gida” Juyawa na yi kafafuna da nauyi zuciyata kuma da rauni na fito daga dakin ina share hawayena. Kowa kallona yake ni kuma na ki na kalli kowa na fito ina wata tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na nufi bakin gate din asibitin. Miyasa kowa ya kasa fahimtata? Miyasa ni kadai na ke jin abunda na ke ji babu mai ji min zafi? Ni kadai na san irin wulakancin da na fuskanta a gidan Jibril amman yau Inna har ta tana marina saboda shi? Zama da mutane da kalubale shi yake canjawa mutum rayuwa Inna ta kasa fahimtar hakan. Har na isa gida kuka nake, mai Napep din har tambaya ya yi wai ko an yi min mutuwa ne nidai ban amsa shi ba, da hawayen fuskata na shiga gida Sakina da Jamila suna zaune waje suna shan iskar hadari da ke kadawa, yanayin shogowata yasa Sakina ta taso ta sauri ta tari ne sai ta haska fuskata. “Lafiya Anti Nawwara? Ko Noor ya mutu ne?” Na girgiza mata kai alamar a'a, ina kallon yanayinta da ya yi min kama da na Habiba, banbancinsu da Habiba ce rumgumeni zata yi ta fashe da kuka ko da kuwa bata san abunda na ke wa kuka ba. “Anti Nawwara miya faru?” Ta tambaya tana jijjigani zuciyarta cike da fargabar abunda ya saka ni kuka. “Na rasa komai Sakina, na rasa karatuna wanda shine gimshiken rayuwata saboda Jibril, na rasa mahaifina mai fahimtar kukana, na rasa yar'uwar da ke goyon bayana, yanzu kuma zan rasa Noor Inna kuma tana goyon bayan Jibril, ni kan miya ragemin a duniyar nan? Kowa baya fahimtata, babu mai jin yarena, ni kadai na ke kukana, damuwata ni kadai ta dama, ni kadai na ke jin zafina, duniya ta juya min baya ta kona min komai na farinciki, duk abunda na taba zafi yake min, mai amfanin kuma ta mayarda shi toka da na taba sai dai ya bi iska, na kasa gane bayana balle na fuskancin gaba, babu ranar tsayuwar hawayena” Ta rika hannuna tana kuka kamar yadda Habiba take min. “Allah yana tare da ke Anti Nawwara shi zai miki maganin komai” Na gyada kaina alamar gamsu har na saukarda nauyayyen ajiyar zuciya. Sannan na share hawayena na nufi dakinmu. “Habiba” Ina shiga na ambaci sunanta kamar tana jina, sai kuma na kwanta saman katifa ina hawaye, wayar da ke hannuna ta yi kara alamar sako, ina dubawa na ga number Jibril. _I'm so Sorry Nawwara i'm sorry_ Haka ya rubuta a sakon, wai na yi wurgi da wayar na kara fashewa da kuka. A ranar kwana na yi ina kaiwa Allah kukana saboda bachi ya yi kaura daga idona. Na mikawa Allah lamurana, sannan na bar masa zabi akan dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata, a ranar na roka idan ma mutuwa ce ta fi alheri a gareni Allah ya matso min da ita, idan kuma ba iyakar wahalata kenan ba, Allah ya bani zuciyar da zan iya dauka, saboda shi ya tsara min komai. Washe gari Inna bata dawo ba sai tara da rabi, ban ga annuri a fuskarta ba wanda hakan ke nuna har yanxu bata huce ba kenan, ban kuma ji ta ce na shirya na je ba, daman ni na ke kwana da shi sannan ita kuma da rana taje ni sai na dawo na yi wanka na shirya sannan na koma. A daki na sameta na durkusa kasa na rike kafafunta ina kukan da ni kadai nasan zafin fitar hawayena “Inna ki dubi girma Allah ki yafe min, Wallahi duk kika yi fushi da ni Allah ma fushi zai yi da ni, ke kadai kika rage min a duniyar nan, ba ni da wani gata sai na Ubangiji da yayi min ta hanyarki, zan iya jure komai amman ban da fushinki da rashinki babu dan da zaiyi albarka matukar uwarshi tana fushi da shi, mai yawan neman yafiyar mahaifiyarsa da mahaliccinsa kuma dan gata ne har a gurin Allah, kuma ba zai taba tabewa ba, yarda Allah tana tare da yardar iyaye, idan suka yarda da kai to Allah ma ya yarda da kai, ki taimaki rayuwa kada na zama daya daga cikin masu tabewa, kar soyyayyar wami yasa ki yi fushi da yarki” Zaunawa ta yi bakin gadon tana kallona fuskarta dauke da damuwa. “Ba zan taba fushi da ke ba, domin na san illar fushin uwa ga yayanta, na mareki ne kuma na daure miki fuska ne saboda ki gane abunda kika aikata babba ne, na san zuciyarki zata zargeni da cewar ina son Jibril fiye da ke, ba saboda kudin Jibril yasa na yi miki haka ba, da kudinsa na ke kwadayi da na cilasta miki komawa gidansa ko kuma kulla wata alaka da shi, ba wannan na ke dubi ba Nawwara, rayuwar dan ki ta nan gaba nake hangowa da kuma taki rayuwar, wata rana zaki gane gaskiya nake fada miki wata kila a lokacin bana raye, amman za ki gasgatani, ba zan taba cilasta miki gurin auren Jibril daman tun farko bamu cilasta miki ba, amman na san ko da mahaifinki yana raye kwatankwacin abunda na aikata shi zai aikata a gareki, ba zan taba fushi da ke ba” Na kwantar da kaina saman cinyoyinta wata kalar rahama ta uwa tana shiga cikina. “Na gode Inna, na miki alkawari ba zan sake yin abunda zai sa ki fushi ba, ko da kuwa abun nan baya min dadi” “Allah ya sauwake miki wannan rayuwa ya baki wanda zuciyarki take muradi wanda zai share miki kukanki kuma wanda za ki more hakurin da kika yi ta hanyarsa” “Amin” Sakina ta shigo tana tambayar jikin Noor, sai Inna ta amsa mata da “Ya ji sauki, yanzu wanka zan yi na koma” “Bari na shirya na je” Na fada ina kokarin tashi tsaye, sai Inna ta rike min hannu. “Aa ba sai kin je ba, ki hutar da kanki daga yau zuwa gobe” “Saboda mai?” “Saboda ki samu sukuni a zuciyarki, kuma ki shirya amsa tambayoyin da Noor zai miki, domin yana ta min na ce masa ban sani ba ke kadai kika sani, dan haka yana nan yana jiranki, kuma Jibril yasa an canja mana wata asibitin tun jiya da dare an kaimu wata” “Tau Inna” Na amsa ba dan raina ya so ba, tabbas Jibril na daf da rabani da dan na ni kadai na sha zafin daukar cikinsa na raineshi kuma na haifi abuna saboda kawai shi yana da dukiya. JIBRIL POV. Shiru ya yi ya rasa abunda zai cewa Abbah, zuwa can ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Abbah sam na manta da ranar ma sai yanzu” “This is rubbish kasan hasarar kwangila irin wannan tana janyo a fara raina mana kamfani? Kowa ya sa rai mu za a bawa kwangilar nan amman saboda sakacinka komai ya lalace” “Abbah kasan ba guri daya hankalina yake a yanzu ba” “Fine ka mikawa Siraj ragamar kamfanin nan, a duk lokacin da ka dawo cikin hayyacinka sai ka kamfanin ya dawo hannunka, amman ba zai yiyu muyi ta hasara hakan nan kawai ba” “Okay Abbah nima hakan zai fi min an gaskiya bana cikin kwanciyar hankali a yanzu” “Ai kai ka jawa kanka komai saboda baka jin magana, da gaskiyar Hajiya (step mother dinsa) da take cewa na rika kyaleka duk da gangan kake komai” Ajiyar zuciya Jibril ya sauke be sake cewa komai ba, yana ta sauraren fadan da Abbah ke masa, kamin daga bisani ya kashe wayar. “Oh Allahna kai kadaine gatana” Ya furta yana shafa fuskarsa. Siraj dake gefensa ya dashi “Ka kwamtar da hankalinka Jibril komai zai wuce, matsalar ka kawai kana sakewa Nawwara ne da yawa, be kamata ace tana maka irin wannan cin mutuncin ba” “Idan bata min wannan cin mutuncin Siraj ba zan taba gane cewar tana so na ba, kuma a duk lokacin da ta yi fushi ta kan fadi kalmar da zata amfaneni, jiya ma ta fadi kalmar wani Faruk wanda na fada maka maybe tsohon mijinta ne” “Ba lallai ya zama tsohon mijinta ba Jibril ina ta nanata maka, maybe wani dan uwanta ne ko makocinsu, ni abunda na ke ganin ya fi kawai ka ka fitar da kudi sai a nemo wani wanda zai aureta ana daura auren sai ya saketa kaga shikenan sai kai kuma ka aureta hankali kwance zuciya zaune, sai a nemo wani talaka mai neman na kansa ko da tsoho ne Nawwara ta aura” “Amman dai kai wawa ne Siraj, taya zan bari Nawwara ta auri wani? Ai itama ba zata taba yarda ta auri wani dan ta fito ta aureni ba, and ba zan iya barin kowa ya kwanta kusa da ita ba saboda har yanzu ita iyalina ce, duk wanda ya kwanta gado daya da matata sai na hora shi, ballantana kaddara ta kaishi ya kusanceta ko waye mutuwa kawai ta dace da shi” “No Man no ba ina nufin ya aureta ba ya kwana da ita ba, ana daura auren zai saketa shikenan fa, idan kuma kana jinnrashin natsuwar hakan sai ka nemi wanda yake kusa da kai wadda ba zai musa maka ba sai ya aureta” “Zan yi tunani akai, amman ina son ka bincika min gaskiya magana akan auren nan, and Abbah ya ce na mika maka ragamar kamfanin nan yanzu” “What...?” Ya amsa da karfi zuciyarsa kuma cike da farinciki. “Saboda mai?” “Ba komai kawai ina ganin kamar akwai wanda yake tsegunta ma Abbah wani abun ne akan kamfanin da kuma rayuwata, saboda kwanaki ma yayi ta min fada akan wai ina shan cocaine yanzu kuma yana fada akan kwangilar gobnatin taraiya da muka rasa ta gina gidaje, wai an fada masa ko takardar kamfaninmu bamu tura ba” “Gaskiya akwai wanda yake labarta masa wani abu akai, amman gaskiya ni ba zan iya daukar ragamar kamfanin nan ba, taya kai za ace ka aje abu ni kuma sai ace na dauka? Gaskiya ba zai yiyu ba” “No no he trust you ne, ai kasan Abbah idan be yarda da mutum ba ba zai saka shi a arkar kasuwancinsa ba, ni ma da be yarda da ni ba ai da ba zai kawo nan a wannan kamfanin ba, so karka bashi kunya kawai ka yi aikin nan nima zaka taimakamin domin zan samu na kula da Nawwara” “Zan yi tunani a kai” “Ba wani tunani sai ka karba” Siraj ya tashi tsaye yana nuna kamar be jidadin abun ba, alhalin kasan zuciyarsa farinciki ne kawai da murna. “Zan tafi xan sa ayi bincike akan Nawwara din” “Thank you so Friend Allah ya bar mu tare” “Amin akwai hoda idan...” “Hodar nan tana daya daga cikin abunda Nawwara ta tsana, ina ta kokarin daina shanta ina son na zama mutumen kirki Siraj, ina da yaro a yanzu kuma ina son Nawwara ta dawo rayuwata dole ne wani halin za a zubar da shi” Tabe baki Siraj ya yi. “Nawwara dai Nawwara, ga Zinatu tana son ka amman hankalinka yana gurin wacce bata ganin tausayinka” “Ka tafi kawai zai fi maka, bana son kana min maganar kowa ban da Nawwara” Ya fice yana wani sunsun da kai. Yana fita Jibril ya kira Rabi ta waya yana fada mata abunda yake son ta yi. “Bincike na ke son ki min akan Nawwara saboda na san Siraj ba zai samu dama ba a yanzu saboda shi ne new ceo din ku yanzu” “New ceo Sir? Why ka bar garin ne?” “No Abbah ya bukaci a bashi ni akwai abunda na ke, ki bincika sosai please” “Okay Sir amman miye alakarka da ita saboda na san irin binciken da zan yi” “She's my wife, my ex-wife mother of my only Son” “Okay Sir zan yi komai inshallah” Sai ya kashe wayar ya mike tsaye ya shiga bathroom, in 40 minutes ya shirya ya fito ya nufi asibitin zuciyarsa cike da zumudin ganin dansa. Tunda ya shigo cikin aaibitin ake ta gaishe shi har ya isa sashen da Noor yake be riko masa komai ba, saboda yasa a rika kawo masa abincin da abun tabawa daga wani kasaitaccen restaurant sau uku a rana. Yana tura kofar dakin ya shiga, sai ya nemi farincikin da ke zuciyarsa da fuskarsa ya rasa, saboda ganin Bilal da ya yi zaune saman hospital bed din rumgume da Noor da ya shige jikinsa sosai ya labe kamar mai bachi. “What are you doing here?” Ya tambaya kamar be san inda Bilal ya fito ba. Uffan Bilal be ce masa ba ya yi kokarin sauke Noor daga jikinsa sai Noor ya kara lake masa wanda hakan ya bata ran Jibril. “Uncle Bilal zan bi ka” “Aa baka ganin baka da lafiya? Kana bukatar kulawa idan ka ji sauki da kaina xan zo na daukeka na kaina gida sai muje yawo ka ji” Ya gyada masa kai yana kuka. “Uncle Bilal zaka dawo anjima ko?” “Eh zan dawo” “Tau ka zo min da Momy” “Zata zo, aiki take yi shiyasa bata zo ba” Sai da Bilal ya shafa kansa sannan ya fita sai Jibril ya bishi a bakin kofar dakin ya jefa masa wata magana. “Nawwara bata fada maka karka sake zuwa ganin Noor ba” “Bata fada min ba” “To ni na fada maka” Bilal ya kalleshi ta kyau sannan ya ce. “Look Jibril duk abunda na ke maka a kamfani ina yi maka ne sabida you're my boss a gurin kuma ina aikine dole duk abunda ka ce na bi, a waje ma ina respecting dinka so karka zubar da girmanka” “Karka soma fada min wata maganar banza a nan, daga Nawwara har Noor mallakina ne” “Noor ne kawai Mallakinka, amman Nawwara ba mallakinka ba ce, ka bar ganin kana da duka ba komai kudi yake siya ba, rashin arziki kuma ba shi zaisa takala ya wofintar da kanta a raina shi ba, ka taka a hankali” Sai kawai Jibril ya yi dariya ya juya ya koma ciki. A ranar ya sha fama da Noor kamin Inna ta zo saboda Noor na ganin kamar Nawwara ba zata sake zuwa gurin ba, a ranar ya saka cewar kar securities din su sake bawa kowa damar ganin dansa in ban da Inna sai kuma wanda Inna ta fito da kanta ta zo da shigo da shi. Da dare ya koma gida jikinsa agajewa ba dan kuma ya yi wani aikin ba sai dan tunanin da ke zuciyarsa ne ya saukar masa da gajiya. A lokacin ne Rabi ta kira shi take labarta masa abunda ta samo kamin fa kara bincike. “Sir Nawwara ta auri miji biyu bayan baban Noor da auri wani Faruk amman ya rasu, sai dai mutane suna zargin cewa aurenta na fari ba aure ta yi ba saboda an boye abun kuma sai ta dawo gida da ciki” Ya dan yi Jimm kamar ba zai ce komai ba. “Ina kika ji wannan” “A wani gidan makotansu ne na ji, saboda na nuna musu yayana yana son ya aureta ita kuma ta boye masa tace budurwa ce” “Thank you, akwai wani abun da ya kamata na sani ne bayan wannan” “Babu amman nace suna fama da talauci sosai, Babanta ya rasu saboda sukan da police suka masa akan sun kamashi ya yi sata wacce matar da yayanta suke cewa wai ba gaskiya bane, wasu kuma ce gaskiya ne, yar uwarta kuma ta rasu wacce ta fi so a cikin kananeta, zan fadada bincike nan har sai idan na kammala sannan zan labarta maka komai” “Na gode, na san ba aikinki bane amman na gode, ki turo min account number dinki” “Okay Sir thank you” Yana sauke wayar sai duk jikinsa ya yi sanyi, wani irin tausayin Nawwara ya rufe shi. Ranar kwana ya yi da tunaninta da kuma tunanin irin wahalar da ta fuskanta gidansa. Washe gari sun da safe ya shirya ya nufi asibitin dan yana son ya yi breakfast tare da Noor, sai ya samu Nawwara bakin kofar harabar da zata sadata da dakin an hanata shiga, tana ganinshi ta sauke kanta kasa har sai da ya karaso kusa da ita. “Nawwara da yanzu ban dawo rayuwar Noor ba, haka za ki yi ta masa bitar maratun na ko?” “Akwai sama ko kasa da abunda ya kamata na karanta masa ne bayan abunda ya faru? Kana da sa'a Jibril komai kake so kana samu, na raini da na rana daya ya zo ya zama naka” Ya cije lebensa na kasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce “Kina ganin kamar darin duniya ne abunda kawai nake so? Ba shi ne kadai gata ba Nawwara, matukar babu ke babu Noor ina jin kamar rayuwata bata da amfani a duniyar nan, ni taimake ni Nawwara ki bani damar da zan zama silar farincikinki” Ta tada kai ta kalleshi da idanuwata dake cike da kwalla. “Idan na yafe maka zaka daina shiga sabgata?” “Zan daina matukar za ki daina shiga rayuwar da na....!” [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣7⃣ Na yi murmushin mamaki ganin irin karfin halin Jibril, lallai maza basa da kunya yanxu har yana da bakin da zai ce min wai sai idan zan rabo da dansa? Ni zai kalli tsabar idanuwana ya ce min haka? “Ba zaki iya rabuwa da Noor ba, ni kuma ba zan iya rabuwa da ke ba, ba kuma zan daina neman ki yafe min ba” “Zan iya shiga?” Na tambaya ina kallon security da ya tare kofar, sai ya kalli security ya ce “Bata hanya ta wuce matata ce” Da sauri ya janye min ya bude min kofa, ni kuma na shiga ina murmushin jin ya kira ni da matarsa lallai iska na wahalar da mai kayan kara. Ina gaba yana bina ba dan na san inda dakunan suke ba daman can Inna ce ta kwatantamin, har na wuce dakin sai ya kira da sunan da be taba kirana ba har na dauka cewar ba da ni yake ba “Mrs Makama” Ganin ban waigo ba yasa ya kara da cewar “A nan dakin yake” Juyowa na yi na dawo na shiga kofar da ya bude min, a yanayin yadda dakin Noor yake sai ka rantse da Allah ba cikin asibiti ba ne, ya kawata masa dakin da teddys ga wani madaidaicin plasma dake lake gurin freezer din dakin. Noor na ganina ya yi saurin saukowa saman gado ya doso inda na ke sai muka rumgume juna. “Momy miyasa baki zo ba jiya da wata jiya kamin jiya?” Dariya na yi na shafa kansa. “Tan ba ga Daddynka yana kula da kai ba?” Ta da kai ya yi ya kalli Jibril. “Momy da gaske shine Babana?” “Ee mana ba ga kamaninka nan kana ganin a fuskarsa ba?” “Amman Babana Faruk fa?” Daukarsa na yi na dora saman hospital bed din sai nima na zauna, Jibril kuma ya zauna a kujerar da ke fuskantarmu, sai na kama hannayen Noor na ce “Baba Faruk ya rike ka kamar dansa, saboda a lokacin Babanka baya nan ya yi tafiya zuwa gurin karatu wata kasar, kuma baya son ace maka baya nan shiyasa ya fadawa Baba Faruk cewar ya ce shine mahaifinka kamin ya dawo” “Miyasa Inna ta mareki saboda shi?” “Saboda na boye maka gaskiya tun farko ban fada maka ba sai yanzu, tana ganin kamar ba zaka fahimta ba” “Miyasa kika ce Uncle dina ne sai kuma yanzu kika ce shine Babana kuma?” Yanzu kan ban san mi zan kara ce masa ba kuma, jin na yi shiru ban amsa masa ba yasa ya kara aiko min da wata tambayar. “Ko dai da Baba Faruk ya rasu sai wannan ya dawo?” “Aa kamin na auri Faruk na fara auren Babanka sai kaddarar aure ta raba mu, ya tafi karatu wata kasar sai Faruk ya aureni kai kuma ya rika ka kamar dansa saboda yana so na kuma ya san kimata, amman ba shine asalin mahaifinka ba, wannan shine mahaifinka na gaskiya shiyasa ake kiranka da Muhammad Jibril ba Muhammad Faruk ba” Ya yi shiru kamar mai tunani sai kuma ya yi murmushin da ya bayyana hakoransa. “Momy na gane, yanzu Babana be rasu ba kenan?” “Gashi a gabanka kana gani, kuma yana son ka sosai kai har ma ya fi ni son ka” Na fada ina nuna masa Jibril Murmushi Noor ya yi sosai ga dukan alamun yaji dadin haka, sai na rika shi ya sauka saman gadon ya nufi inda Jibril yake yana ta kallonsa. “Kuma fuskarmu guda ko Momy?” “To ai shine mahaifinka shiyasa kuka yi kama, kaga ai baku yi kama da Baba Faruk ba ko kun yi kama?” “A'a” Sai Jibril ya daukeshi ya dora saman cinyoyinsa ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya. “Thank you so much Dear” Ya fada yana kallona fuskarsa na nuna jindadin da ke cikin ransa. Tun daga ranar na ke ta kokari wajen kawarda duk wani abu da zuciyata take nuna min, hakan ba karamin faranta ran Jibril da Inna ya yi, ni ko farincikina farincikin mahaifita da kuma da na, sati daya da muka a asibiti ya isa ya samarda wani kudi na littafin soyayyar uba da da tsakanin Jibril da Noor, saosai da sosai Noor yake son babansa yana shiga jikinsa wani lokacin haka zai kyaleni ya yi ta sha'aninsa shi da mahaifinsa, Jibril kuma kamar ya cinye shi yake ji cikin kwana biyu ya yayatawa duniya cewar yana da, abun mamaki har Abbah sai da ya zo ganinsa yan uwansa ma wadanda suke uba daya sai da suka zo, abokaninsa na nesa da na kusa suna ta zuwa ganin Noor saboda ya fada musu dansa ya kare a gabana wasu ke cewa daman wai kana da? Mun samu alheri sosai domin duk abunda ka bawa Noor Jibril baya dauka ni yake barwa, sai dai wani abun da yake bani mamaki duk cikin masu nan ban taba ganin Siraj ba duk kuwa da kasancewar ba ko yaushe na ke tare da Noor ba, amman a yadda nake ganin abotarsu ya kamata ace Siraj gana zuwa ko da be zo kullum ba ya zo ko da sau hudu ne a sati. Ranar da Noor ya kwana takwas a asibitin na bukaci a sallamemu amman sai ya ki, ni kuma ba dan komai na ke son komawa gida ba sai dan Bilal saboda kwana biyu nan na rasa gane kansa ya kasa fahimtata yawan zuwa da nake asibiti jinyar Noor yana ganin kamar wata sabuwar soyayyace ke kulluwa tsakanin da Jibril. A ranar da muka fara zuwa kotu zama na farko na sha kuka a ranar saboda ya tuna min da mahaifina da kuma Habiba, na yabawa Dpo sosai domin ya nuna kulawa akan case din ga kuma police din da alkali ya bada ikon tsarewa har zama na gaba, wani abun da ya bani mamakin matar da ta ce Mahaifinmu ya yi mata sata tana da yanayi da Siraj sosai kuma ita ba ce a tsareta ba saboda tana da kudi ko kuma tana da daurin gindi ko kuma dan tana da kokarin kare kanta cewar ba ita ta saka su ba oho. Ni dai har muka fito daga cikin kotun ban daina harararta ba ita kuma bata daina kallona ba. Tare muka fito da Inna da Sakina, sai Jidda da Bilal da kuma yan uwan Baba da na Inna, kowa da abunda yake fada ni dai ban ce komai ba, har muka shiga Napep muka dawo gida. Muna shigowa gida Jidda take labarta min cewar Mustapha ba shi da lafiya jiya aka kai shi asibitinsu Jibril. “Miya ke damunsa?” “Ke kika damunsa Nawwara” “Kamar ya? Ai na ce na yafe masa” Ta yi shiru bata sake cewa komai ba. “Kinje kin duba shi?” “Ina tsoron mahaifansa” “Mai tsoro baya zama gwanin Jidda matukar kika saka tsoro a zuciyarki Mustapha ba zai taba fahimtar cewar kina son shi ba” Ta kalleni da sauri. “Waya ce ina son sa? Mustapha da yake son ki sai kuma ace ni ina son sa?” “Ba fada min aka yi ba, a idanuwanki na karanta” “Baki min adalci ba Nawwara baki san komai a kaina ba” Ya mike tsaye a fusace ta fice, ni kuma na bita da kallon mamaki domin ban ga abun daga hankali a cikin wannan maganar ba. Tashi na yi soma dora girki muna ta firar yadda zaman kotun ya wakana ni da Inna, da dare sai ga Bilal ya kirani a waya wai na fito yana kofar gida. Na yi mamakin jin hakan saboda kwana biyu ya dauke min kafa daga zuwa fira ko da kuwa ni na bukaci hakan sai dai mu gaisa a waya, na dauri aniyar sakashi farinciki a yau ko da kuwa ba da niyar hakan ya taho ba, dan haka na dauki kayan kwaliyata na dandasa kwaliya mai kyau na feshe jikina da turaren da Jibril ya aiko min cikin kayan da ya siyo min kwanaki, na dauki gown din atamfa da take cikin kayan da Jibril ya aiko min na saka, ni kaina na san na yi kyau a wannan dare, Inna ma kallona kawai ta yi tayi murmushi, nima na fice ina murmushi. A yanayin yadda na tararda shi yasa ni jin babu dadi, domin kuwa fuskarsa babu annuri jikinsa kamar a sanyaye, bayan na masa sallama sai ya amsa min idonsa akaina kamar zai cinyeni. “Nawancy kin yi kyau” “Dan kai kadai na yi ta na gode da ka yaba” Sai dan yi murmushi. “Aiko ya kamata na bada tukuici ko?” “Ka adana tukuicinka da daddadan kalamanka har sai na fada maka dalilin wannan kwaliyar tawa” “Akwai wani daliline bayan wanda na gani?” “Sosai ma, a wancan gani ka yi, wannan kuma ji zaka yi” Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi. “Nawancy kina yaudarar zuciyata da yawa, da fushi na zo nan gurin, amman kin shiga kin yi nikaya kin tarwatsa duk wani damuwa da fada da na zo da su” “Ai daman haka ya kamata ko wace amarya ta kasance gurin angonta, mai wanke danuwarsa ta shimfida farinciki a zuciyarsa” “Ina ma da gaske Nawancy amaryar Bilal ce da yafi kowa farinciki a duniyar nan” “Akwai wanda ya isa ya hana abunda Allah ya zo kasanewarsa tun farkon hallitar Nawwara?” “Babu” “Ashe ko Nawwara sai ta fi Bilal kasancewa a cikin farinciki daga ranar da aka daura aurenta da angon da ya fi ko wane ango tsada a duniyar nan” Ya yi murmushi yana kallona tare da lumshe ido. “Ina son ki sosai Nawancy” “Kai so na kawai ka ke ni ko kaunar ka na ke” Ya sauke ajiyar zuciya. “Kamin ki kaini duniyar da ba zan iya dawowa ba, fadan min dalilinki na yi wannan kwaliyar” “Kamin na maka albishir mai tsada ya kamata ace ka fada min abunda ya kawo ka nan” “Yo tun yaushe kika duniyar kwakwalwa kika mantar da ni wanene ni ma, balle abunda ya kawo ni nan kuma” “Yanzu dai rumtse idonka sai na fada maka albishir din” “Ai kunnene yake ji ba idanuwa ba” “Ina gudun kyawawan idanuwan nan naka su ba ni kunya ne” Sai ya yi dariya ya lumshe idanuwasa. “Inna ta ce na fada maka, idan ka shirya ka turo magabatanka suje can Baban gida su gana da nawa magabatan” Da sauri ya bude idanuwansa ya kallini “Da gaske Nawancy?” “Na saba maka irin wannan wasan ne?” Wani ihu ya yi ya daka tsalle ya dire, ni kuma na yo cikin gida da gudu ina dariya. Da na shigo sai na ce da Inna Bilal ya ce zai turo magabatansa amman be saka rana ba. “Mashallah Allah ina fatar kina sonshi dan karki yi wa kanki zabi irin na baya, kuma ina son ki bawa Allah zabi a cikin lamurranki nima zan taya ki da addua idan aurenki da Bilal alheri Allah yasa ayi, idan kuma ba alheri ba ne Allah ya kawo maslaha” “Amin Inna, inshallah Alheri ne” Daga wannan sai fira ta biyo baya Inna na ta nanata min burinta na ganin na yi aure domin shine kwanciyar hankalinta, a daren Bilal ya yi min kira ya fi a kirga ni kuma na ki dagawa, misalin uku da rabi na dare na tashi na yi nafila na Mikawa Allah zabina akan ya zaba min dukan abunda zai fi zama alheri a rayuwata. Washe gari bayan na gama komai na shirya na nufi asibiti zuciyata cike da tunanin yanayin Jidda gabana kuma nata faduwar da ban san daliliba. Jirbil kawai na tarar a dakin Noor baya nan, na gaisheshi cikin ladabi kamar yadda na saba masa a yanzu. Be amsa min ba sai ya matso kusa da ni yana ta kallona kamin ya risina kasa wanda hakan yasa ni ja da baya. “Nawwara dan Allah ki yafe min abunda na yi miki na san na yi kuskure amman ki dubi girman Allah ki yafe min” “A kwanakin nan da muka dauka be isa yasa ka fahimci cewar na yafe maka ba?” Ya mike tsaye yana kallona. “Ki kalli cikin kwayar idanuwana ki ce kin yafe min” Ya fadi hakan ne saboda ya tabbatar da yafiyar tawa, domin yasan babu abunda zan gani a cikin idanuwansa sai tsanarsa da kiyayyarsa, ras na sauke idanuwa cikina nasa zuciya a natse bakina ya furta cewar. “Na yafe maka Jibril Allah ma ya shaida na yafe maka” Lumshe ido ya yi sai ga hawaye sun sauko masa, yaja wani dogon numfashi ya sauke, sannan ya bude idanuwansa ya kalleni “Yanzu za ki iya aure na kenan?” “Dan na yafe maka ba shi yake nufin zan iya sake zaman aure da kai ba, ni ina da wanda zuciyata take so” “Wa kike so Nawwara? Wanene wannan wanda ya fini sa'a da dacewa a rayuwa? Wanene wanda be shirya zaman duniya a yanzu ba?” Na shiru ina kallonsa. “Mustapha ne ko?” Kamin na ce wani abu sai wata nurse ta turo kofar dakin ta shigo hannunta rike da na Noor. “Sir an gama” “Thank you” Ya fada yana share hawayensa, sai da ta fice sannan ya nufi Noor ya dauke shi ya rumgume. “Come here my happiness” “Momy yanzu kika zo?” Na daga masa kai sai na karasa gurin gadon na zauna, Jibril kuma ya zauna a kujerar da ke fuskantata yana rumgume da Noor, idanuwansa na ta xika da hawaye tana kallona. Muna haka aka turo kofar dakin a aka shigo Zinatu ce tare da Rabi sai kuma wani bakon mutun da ban waye fuskarsa ba. Da dan farka ta karaso kusa da mu ta aje ledodin da ke hannunta sannan ya zauna kusa da ni tana kallon Jibril. “Ashe kana nan” “Akwai wani gurin da ya kamata na kasancene bayan nan?” Ya fada yana mikawa mutumen hannunsa su gaisa. Rabi kuma ya zo tana mikawa Noor hannu “Zo nan dan Daddynsa” Dariya kawai ya yi mata amman be yarda ya bar jikin Jibril ba, ya labe sosai kamar wani karamin yaro mai shan mama. “Sir Akwai maganar da ya kamata mu yi” “Tana da muhimmanci ne sosai?” “Eh akan abunda kasa ayi ne, kuma Siraj yana waje yana jiranka ya ce a gaishe da Noor” Zinatu ta mike tsaye ta karbi Noor shi kuma ya tashi ya fice dare da mutumen da kuma Rabi. “My Son ya jikinka?” “Na ji sauki Daddy ya ce nan da kwana biyu za a warware hannu” “Mashallah Allah ya tsare gaba ya kara lafiya” “Amin” Ya amsa bakin nan chakoi, sai ta kalleni. “Kin kusa komawa aiki kenan ko?” “Inshallah” Daga haka ban sake cewa wani abu ba, itama bata sake cewa ba, sai ma dauko ledar da ta zo da ita da tayi ta bude ta fiddo chocolate mai shegen tsada ta mikawa Noor. Bayan kamar mintuna talatin sai Rabi ta sake shigowa tana fadin. “Zinatu Siraj na kiranki wai ki zo zai wuce” Zinatu ta sauke Noor saman jikinta ta aje shi kasa tare da yi masa kiss. “Allah ya kara sauki da na” “Amin na gode” “Nawwara na wuce” “Mun gode Zinatu Allah ya bar zumunci” “Amin” Bayan ta fice, Rabi ta maida kofar dakin ta rufe ta nufo ni tana fadin. “Nawwara ina son muyi magana da ke mai muhimmanci” “Akan me?” “Akan ke da Noor da Jibril da kuma Siraj abunda ya shafi rayuwarku ne ku duka” Gabana ya fadi “Ban gane ba” “Asirrance na ke son mu yi maganar, amman kamin nan ko kin san cewar Jibril ya kori Bilal a kamfani tun last week? And there's something behind Noor accident...” Na mike tsaye da sauri. “When how i don't understand?” Kamin ta kara cewa wani abu sai ta ga Jibril ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta yi saurin juyawa tana dariya. “Kin jiki Nawwara da wata magana, masu kudi ai suna can inda suke, ni dai na tafi Allah kara lafiya” Kamar na ce wani abu sai kuma na amsa da. “Amin na gode” Tana ficewa, Jibril ya kalleni ya ce. “Kin san an kawo Mustapha a asibitinmu kuma ba shi da lafiya sosai, yana icu room 14” “Na sani” “Mi kike son a masa?” Na masa wani kallo kamar ban fahimci abunda yake cewa ba. Sai yasa hannunsa aljihu ya ciro karamin hoton Habiba ya mika min. Na karba hannuna na rawa sam na manta da inda na jefarda hoton ma. Ina karba sai ya juya ya fice ya bar nan tsaye da mamaki, ya aka yi yasan abunda Mustapha ya aikata? Ina ya samu hoton Habiba? Me yake nufi da abunda nake son a yi masa, ga kuma maganganun Rabi da suka tsaya min a rai. Saurin juyawa na yi na fita harabar asibitin ina tambayar inda icu yake, aka fada min sai na doshi gurin da sauri ina duba number din room din har na kai ga mai 14, ina dosar dakin sai Jibril ya fito tare da wasu Nurses, kallona kawai ya yi ya dauke kai ya fice, ni kuma na saki baki jikina a sanyaye ina kallon dakin, Mustapha nake hangowa da ke kwance kamar gawa, Mutanen da ke cikin dakin suna ta rusar kuka, ban san lokacin da nawa hawayen suka fara zuba ba, na juyo da sauri na biyo bayan Jibril hangosa na yi tsaye yana magana da wani likita na doshi inda yake ina hawayena bakina na rawa kafafuwana kuma kamar zan fadi. Yana hangoni ya yi saurin sallamar mutumen ya shige dakin, ni kuma ina isa na baki kofar office din na fada. “Me ka masa Jibril? Me ka masa?” Ya zauna saman kujera yana kallona “Duk mutumen da ya kashe rai shima kisa ne ya cancanta da shi, daukar fansar yar uwarki na yi miki” “Be kashe rai ba, fyade kawai ya yi mata miyasa zaka kasheshi mi ya kama?” “Ba shi kadai zan kashe ba?” “Mutum nawa zaka kashe?” “Adadin mutanen da zasu furta ko kuma su nuna soyayyarsu a gareki, kamar Bilal” Ya fada yana tabe baki, ni kuma na zaro ido naja baya baya har ina kokarin faduwa, sai kuma na juya a firgice na fice daga office din kamar mahaukaciya. ____________________________ Da gaske Jibril ya kashe Mustapha? Ko dai mafarki ne Nawwara take? Mai Rabi zata fadawa Nawwara mai muhimmaci har haka ne? Mi ta sani akan Siraj da Noor da kuma Nawwara? I can't wait for the next chapter 😍 KhadeejaCandy ce ✍️ [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣8⃣ Har na kawo bakin gate din asibitin kuka na ke ina ta tunanin abun yi, wane irin mutum ne da zai kashe rai saboda cin ma wata bukata tasa ta kanshin kansa? Ko ni da na tsani Mustapha ba zan iya kasheshi ba ko na saka a kasheshi ba, bayan shi kuma ya ce Bilal ne next, dole ne na sanar da police wannan maganar ba zan iya kyalewa ba, wayata na dauko na kira Bilal bugu daya ya dauka muryarsa da walwala da alama yana cikin farinciki. “Nawancy” “Kana ina” “Ina kofar gidanmu” “Dan Allah ka sameni guiwa station yanzu” “Lafiya? Kuka kike yi” “Ka zo yanzu ka ji” “Okay tau” Daga haka na kashe wayar na tari achaba na hau domin shi ya fi kusa da station, ko da na isa har ya isa bakin station din yana ta yi min waya, yana ganina ya doso inda na ke yana tambaya dalilin kiransa da na yi. “Bilal Jibril ya kashe Mustapha kuma ya ce kai ne na biyu” “What? Nawancy kin san abunda kike fada kuwa” “Na sani na gani da idona ya kasheshi” Na fada ina kuka, sai ya matso kusa da ni yana kwantar da hannayensa. “No listen Jibril is very smart ba zai kashe Mustapha, maybe dai yana miki wasa ne, ko kuma yana son ya yi amfani da wannan damar ne ya cinma wani buri nasa” “Wallahi da gaske ne, na ga gawar Jibril da kaina” Na fada ina cigaba da kuka, sai ga wani dan sanda ya zo kusa da mu yana tambayar dalilin zuwanmu gurin. “Dpo na ke son gani shi yace na same shi nan akan case din mahaifinmu” “Amman baki da number shi?” “Ba ni da amman shi yana da tawa number, dan Allah ka fada masa da gaggauwa” “Okay” Ya juya ya koma ciki, na yi wannan karyar ne saboda na samu gamin dpo cikin sauki, domin nasan duka wadannan kananan yan sandan ba zasu iya handling case din Jibril ba. Bayan kamar minti biyar sai ga police din ya dawo ya ce mu shiga ciki, sai dai basu bamu damar hakan ba sai da suka binka komai na mu. Cikin office dinsa muka sameshi yana sanye uniform dinsa na yansanda yana ta rubuce rubuce a takardun da ke gabansa, da hannu ya nuna mana kujerar zama. “Bismillah” Na zauna hawaye na ta bin fuskata, sai ya aje rubutun da yake ya fuskance mu. “Lafiya dai Nawwara?” “Ba.. Ba.. Ba akan case din Baba na zo ba, na ce haka ne saboda na samu ganinka” Na fada ina kuka, sai mika hannunsa ya dauko tissue ya bani na share hawayena da majinar da ta zubo min, sai kuma ya mike tsaye ya nufi freezer sa ya bude ya dauko gorar ruwa da kofi ya bulbula min. Ba musu na dauka na shanye, ya sake zuba min na shanye sai ya karbe kofin ya maida gefe ya zauna yana kallona. “Relax ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ki a nan” Na gyada masa kai sannan na sauke ajiyar zuciya wanda hakan ya bani damar soma masa bayani. “Wani ne yake barazana ga rayuwar Bilal ya ce sai ya kasheshi” Ya kalli Bilal a kaikaice. “Miye tsakaninki da Bilal din?” “Shine wanda zan aura” “Wacan wanda yake barazana ga rayuwarki fa?” “Tsohon mijina ne” Jinginawa ya yi da kujerar yana kallonmu. “Fada suka yi da har maganar kisa ta shiga ciki” “Aa kawai dai baya son shi ne, yanzu ya kashe wani kuma ya ce Bilal ne na biyu” “Dan taadda ne mijin na ki?” “Aa likita ne, amman yanzu yayi ma wani allura ya mutu” Ya kalli Bilal “Kai namiji ne maybe zaka fi yin bayani mai gamsarwa, ko fada ya taba hada ka da mutumen? Ko kuma wani abu ya shiga tsakaminku” “Gaskiya babu abunda ya taba shigo tsakaninmu” “Haka kawai yayi maka barazanar kisa?” “Aa shi besan an yi ba, ni ya fadawa kawai ina son a shiga tsakaninmu da shine domin duk abunda ya samu Bilal shine” “Okay amman dole ne zamu yi magana da shi, yanzu zan sa a dauki statement dinku, kin san inda zamu samu wacan din?” “Ee ina da number wayarsa” “Tau ki bamu sai mu kira” Daga haka ya dauki telephone dinsa ya kira wani police yana shigowa ya sare masa shi kuma ya nuna mu. “Kaje ku dauki statement dinsu, kuma ka karbi number a hannunta ka kira mutumen ka ce ana nemansa” “Yes Sir” Tare muka fito da police din suka kawo mu reception suka dauko takardar aka saka sunana da na Bilal sannan na soma yi musus bayanin komai, bayan mun gama na basu number Jibril suka kira shi, ko thirty minutes ba a kara ba sai gashi ya iso gurin fuskara babu annuri. Sai aka sake maida mu gurin dpo tare da statement din da aka dauka. Muna shiga Jibril ya mika masa hannu suka gaisa ya zauna saman kujera ba tare da ya jira an masa izinin zaman ba, Bilal ya zauna a kujerar da ke fuskantar ta Jibril, ni kuma na zauna a kujerar da ke bayan Bilal. “Dpo kun ce kuna bukatar ganina” “Yes Nawwara ta kawo kararka akan cewar kana barazana ga rayuwar mijin da zata aura Bilal” Sai ya juyo ya kalli Bilal kamar daman can be san da shi a gurin ba sai yanzu, sai kuma ya maida dubansa gurin dpo. “Mi nayi?” “Ta ce ka ce sai ka kashe Bilal, kuma ka kashe wani kamin shi ka ce shine next” “Yanzu dpo tsakanin da Allah na maka kama da mai kisa?” “Ai abun ba daga kama ba ne” “Idan ina son kashe Bilal ba sai na fadawa Nawwara ba, kuma taya namiji mai iyali kamar ni xai bata lokacinsa gurin wannan wasan kamar wani karamin yaro? Ni ban kawo kararshi ba shi zai kawo karata? Mutumen da kake gani yana barazana ga rayuwata da ta iyalina, my friend has told me Bilal din nan yana da hannu a kokari kashe min yaro, amman ban masa komai ba saboda ban tabbatar da gaskiyar ba na fi son na kama shi red handle, wannan yasa na koreshi daga kamfanina, a kamfanina yake aiki amman babu irin cin fuskar da baya min da matar nan saboda ya san ina sonta” Ya juyo ya kalli Bilal. “Saboda na koreka daga aiki shiyasa kake kokarin bata min sunan asibiti ko? Kake kokarin saka Nawwara against me ko? Idan mun gama da wannan case din zan shigar da nawa case din akanka, dan zaka iyayi min komai wajen ganin ka bata min suna ko aikina” “Kana ganin xaka iya taka kowa saboda kana da kudi ko Jibril? Zuciyarka tana yaudararka akan ka aikata dukan abunda kake so saboda kana da kudi ko? Har yanzu zuciyarka karya take fada maka, ka kasa fahimtar cewar ba komai kudi suke siya ba, kana yaudarar kanka da yawa Jibril” Cewar Bilal cikin fushi. Sai Jibril yasa dariya ya kalli dpo ya ce “Kaga abunda na ke fada maka ko? Babu komai a zuciyarsa sai tsanata da neman hanyar da zai lalata min suna” Ni kuma na mike tsaye ina fadin. “Ba bata maka suna zai yi ba, gaskiya ya fada, kuma ni ka fadawa cewar sai ka kashe Bilal kuma yanzu haka ka kashe Mustapha” Dpo ya daga mana hannu. “Ba fada muka kiraku ku mana a nan ba” “Kamin nan dan Allah dpo ina son ka bani yaranka suje su duba wanda ta ke cewa na kashe” Mun dade a office din Bilal da Jibril suna ta musayar yawu, sannan saka rubuta yarjejeniyar cewar duk abunda ya samu Bilal Jibril ya saka hannu akan cewar ya yarda aka kira Siraj ya yi sheida Bilal kuma aka kira mahaifinsa. Daga bisani muka dunguma gaba daya muka nufi asibitin. Abun mamaki muna shiga dakin da Mustapha yake sai muka same shi zaune yana cin abinci kamar ba shi na ga a mace ba dazu. Yana ganina ya rika kokarin saukowa saman gadon sai mahaifiyarsa ta katsa min tsara. “Ke kan kin shiga uku Nawwara, ba zaki bar dan mu ya huta ba, wannan wace irin rayuwa ce saboda ke dan mu yake kwance nan yanzu kuma sai ki biyoshi har nan asibiti akan wane dalili” Juyawa kawai yan sanda suka yi suka koma ni kuma na sulale kasa a gurin ba dan na suma ba sai dan kafafuwana da suka min sanyi, ga hawayen da suka soma nin zuba babu kakkautawa. “Haba Mom miyasa kike min haka ne? Wallahi da ki yi ma Nawwara fada kara ki yi min” Tasowa ta yi ta karaso inda na ke. “Ban san kaddara ba Nawwara, duk na rasa dana saboda ke ki fara kirga irin asarar da zata sameki kema” “Tir da mace dattijowa irin ki ta tsaya tana fadin bata yarda da kaddaraba, ke an fada miki Nawwara son Mustapha take ne?” Cewar Bilal yana kokarin defending dina, wata muguwar harara Hajiyar Mustapha ta watsa masa. Sai mahaifin Bilal ya katsa masa tsawa. “Bilal wuce muje” Sai da ya kalleni kamar ba zai iya bari a gurin ba, sai kuma ya juya ya fice tare da mahaifinsa, ni kuma na unkura na tashi ina nuna na fito daga gurin na nufi sashen da Noor yake. Ko da na tura kofar na shiga Noor yana bachi hankalinsa kwance, kusa da shi na zauna hawaye na zuba a idanuwana, na kai hannu na shafa shi. Ina haka sai Jibril ya turo kofar dakin ya shigo yana sanye da labcoat, bayan ya maida kofar ya rufe ya zuba hannayensa cikin aljihu ya doso inda nake. “Na sallami yan sandan” Ban dago na kalleshi ba balle kuma har na amsa masa. “I'm sorry Nawwara” “Na tsane ka Jibril” “Na sani” Ya amsa min a takaice. “Ka sake dawowa saboda ka ruguza sauran farincikin da ya rage min ko?” “Wallahi ba dan haka na dawo rayuwarki ba, Nawwara ba ki cancanci auren kowa ba sai ni ko dan Noor, yanzu kin fi son ki barwa wata uwar ta yi miki rainon da? Dan kin san ba zan taba bari kije min da shi gidan duk wanda kika aura ba ko?” “Kowa kallon mahaukaciya yake min, ka kunyata ni a gaban mahaifin Bilal” “Bani da wani zabin ne Nawwara, Wallahi ina son ki sosai, saboda ke nake ta canja rayuwata Nawwara, dis week wani Malami zai fara zuwa yana karantar da ni saboda kawai na samu xama cikakkane namiji da kike so, amman hankalin ya koma kan Bilal, kin kasa fahimtata Nawwara” Na daga kai na kalleshi. “Bana son ka Jibril miyasa ka kasa fahimta? Hakika Noor be yi dacen uba” “Babu wanda zuciyarki take so sai ni Nawwara, Nawwara idan kika aure wani ba ni ba, rayuwata da ta Noor tana cikin hadari” “Bari idan na auri Bilal din, ku fadi ku mutu” Ina fadar hakan na mike tsaye na share hawayena na fice daga dakin zuciyata na mugun kuna. Ko da na iso gida numfashina har sama yake kamar zan hadiye zuciya na mutu saboda bacin rai, tun daga yanayin sallama ta ya kwantarda Inna irin damuwar da na taho da ita ga wani uban ja da idanuwa suka yi sun kumbura sosai saboda kukan da nayi. Muryata a dakishe na zauna saman tabarmar da Inna take zaune na fara rusa kuka, sai hankalin Inna ya tashi. “Lafiya miya same ki?” “Jibril ne” “Yi hakuri tsagaita kukan sai ki min bayani, amman kamin nan kina da bakuwa” “Wacece?” Na tambaya cikin kuka. “Muma ba mu santa ba, amman tun dazu take jiranki” Na share hawayena na mike tsaye na nufi dakin Inna domin ganin wacece, abun mamaki sai na samu Aisha zaune tana kallon kofa da alama ta ji shigowata kuma ta ji lokacin da na doso dakin. _____________________________ Assalamu alaikum fans i will be offline for awhile saboda fever na damuna sosai, jiya ma daker na yi typing yau ma karfin hali kawai na yi Wallahi dan kar na barku kuna ta jira, zan je ganin doctor gobe so yanzu kan sai na samu sauki sosai sannan zan sake yin typing. Thanks All Best regards ♥️🖤 [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 4⃣9⃣ JIBRIL POV. Bayan fitar Nawwara ya zauna kusa da gudan jininsa yana ta kallonsa, shi kansa yana jin rashin kyauta a abunda ya yi ma Nawwara sai dai ya yi hakan dan ya bata ta a gurin iyayen Bilal, kuma ya banbance wanda ta fi so tsakamin Bilal da Mustapha.   Hannunsa yasa aljihu ya dauko wayarsa ya kira wata nurse ta kawo masa wani file tare da sai ya cire wata kadarda ya rubuta ma Noor takardar sallama, sannan ya dauki dansa ya saba a kafada hakan yasa Noor farkawa sai ya soma jijjigashi kamar jariri. “Shiiiiii cigaba da bachinka Daddynka ne” Hakan yasa Noor tafewa a kafadar Jibril ya fito tare da shi harabar asibitin ya sakashi gaban mota sannan na zagayo ya shiga driver seat ya tashi motar sai kuma ya daga wayarsa ya kira wata number “Ki shiga dakin da aka sallami Noor ki kwashe komai zan aiko da dareba ya dauka” Yana fadar haka ya kashe wayar, ya tashi motar ya hau titi dake cikin asibitin kamin ya sadu da babban titi marafa dan baba da ke cikin birnin sokoto. Duk bayan seconds ya kan kalli gefen da dansa yake sai idanuwansa su cika da kwalla, hamdalla yake yi ma Allah akan yau yana da gudan jinin wannan dalilin kadai ya isa yasa ya cigaba da tirsasa kansa gurin Nawwara, domin ita ce kadai macen da ta kawo masa wannan farinciki a rayuwa, bayan ya yanke tsammanin zuwansa. ‘I promise you Noor i will to my very own best na ga na zama uba na gari a gareka, i will make you and Nawwara proud of me’ A kasan zuciyaraa yake wannan tunanin yana sauke ajiyar zuciya. “Ba zan iya hakura da kw ba Nawwara, kema kina bukatar farinciki a rayuwarki, ni na bata komai dan haka ni ya kamata ace na gyara komai” Wannan karon a fili ya yi furucin yana danna horn a bakin gate din gidansa, a hankali ya yi parking sannan ya dauko wayarsa ya yi ma Nawwara text akan cewar an sallami Noor saboda kar taje asibitin bata tarar da kowa ba, sannan ya fita motar ya zagaya ya bude ya dauko Noor da ke kokarin bude idanuwansa. “Zan iya tafiya” Ya fada saboda ya samu a sauke shi ya samu kallon gidan da kyau, kamar Jibril ya sani sai ya sauke shi ya rika hannunsa suna tafiya a hankali, rabon ido kawai Noor yake kamar zasu fado sabo kallon yadda kukasan wani tsohon bakauye, yana saka kafarsa cikin falon sai sayin tile din ya ratsashi ga sanyin ac da ya mamaye ko ina a cikin falon, suna shigowa Jibril ya sake shi ya nufi bedroom yana amsa waya, sai Noor ya daga kansa sama yana kallon pop falon da fankar kamin da dawo gurin kujerun falon da suka katsance farare sol kamar fentin falon da kuma center carpet din da ke falon, karasawa ya yi gurin kujeru sai ya zauna kasa ya kai hannu yana shafa manyan cushion din idanuwansa kuma suna kan katuwar plasma TV mai daukar ido gashi an kawata gurin da wallpaper fari mai daukar hankali, ga wasu manyan flowers da aka aje a gurin suma farar kamar labulayen falon. “Noor Son tashi tashi zauna saman kujera ya zaka dauka kasa” Jibril ya fada ganin dansa a kasa kamar wani almajiri. “Momy ta ce idan mun shiga gidan mutane mu daina hawa musu kan kujera, kuma wasu mutane fada suke idan aka hau musu kujera” Noor ya fada yana kallon Jibril da ya risino da kansa ya dauke ya dora saman kujerar ya rumgume ya lumshe ido, jikinsa ya yi sanyi sosai taya za a ce yana da irin wannan kudin amman ya kasa bawa dansa kulawa ta musamman da har wani abun na duniya zai burgeni ya kasa hawa? Shi ai iyayensa sun bashi kulawa taya ya kasa bawa dansa? ‘Lokaci be kure ba yanzu ma zaka iya he's still a boy’ Wata zuciyar ta amsa masa wanda hakan yasa shi jin sauki, har ya bude ido ya kalli hoton Nawwara da Noor ke nuna masa. “Laaaa ji Momy can” “Kai ma za a maka naka ina son ka sosai Noor” Noor ya dago ya kalleshi ganin ya yi masa abunda ba a saba masa ba, wato kiss shi dai yana ma Momysa amman ita bata masa jara ma Mama Habiba wani lokacin tana masa kiss idan ya yi abun kirki. “Me kake so ka ci?” “Bana jin yunwa a yanzu sai anjima, amman akan wacan abun zan ci” Ya fada yana nuna dinning area da aka kawata da farin dinning table da aka kawata da farin cabinets mai kyau da kuma freezer da ke hade da cabinets din har baka iya banbancewa. Jibril ya shafa kansa yana murmushi. “Idan ma a saman dakin nan kake son cin abinci Noor zan dora ka ka ci, ka saki jikinka nan gidanku ne” “Da gaske?” Ya gyada masa kai. “Har da Momy nan zata zo mu zauna? Kuma da Inna?” Ya sake gyada masa kai yana murmushi, sai Noor ya sauka saman kujerar yana kallon falon bakinsa har kunne hakuran nan a watse bakauye ya shigo gari. “Can ina ne?” Ya nuna Kitchen. “Jeka ka gani” Sai ya mika hannunaa ya riko hannun Daddynsa “Aa zo muje tare dai” “Idan na rigaka isa ba zan bari na shiga ciki ba idan kuma kai ka rigani isa ba zaka bari na shiga ciki ba, ka yarda?” Ya daga kai yana dariya, sai suka fara yar tseren gudu shi da Jibril da yana lakkame da hannunsa mai ciwo, da gangan Jibril ya bari Noor ya riga shi isa sai duk suka rika dariya Noor har da tsalle, abunda ya dauki hankalin babansa sosai yana kallonsa kamar ya hadeyeshi saboda Kauna. Suna fitowa daga kitchen din suka sake rigangan shiga bedroom haka suka bi suka zagaje gidan Jibril ya nuna masa ko ina har Swimming pool, a Garden sai da Jibril ya hau icen guava ya katso masa sannan aka sauna lafiya. “Acan za a saka maka lilo” Jibril ya fada yana nuna wani bangare na Garden din, sai Noor ya zaro ido. “Da gaske” “Eh har dakinka za a maka daban, a saka maka komai da komai har da tv ka da games” Dadi ne yasa Noor ya rumgumeshi yana dariya, sai kuma ya dago kai ya kalleshi “Sai gobe zamu je mu lallabata sai ta dawo nan mu zauna, mu a nan zamu kauna har gobe ko?” Ya daga masa kai, sai Jibril yasa hannunsa ya daukosa suka nufo falo, saman kujera ya zaunar da shi ya yi masa hotuna kala kala har da video sannan ya kunna masa tv ya saka masa kids channel sai yazo ya dauke ya rumgume suna kallon tv tare. NAWWARA POV. Tsayawa na yi kallonta saboda na tantancewa idanuwa ita din ce ko kuwa wata ce mai kama da ita, idan har ita dince to gaskiya ta canja sosai fuskarta ta yi kala biyu fari da kuma wani farin na daban, ga wata uwar rama da ta yi fuskarta ta matse sosai. “Na san zaki yi mamakin ganina Nawwara, kin yi kokari da baki manta fuskata ba duk tsawon wannan lokacin” “Taya zan manta fuskar da ta kwace min yan ce a gidan aurena? Fuskar da mijina ya fifita sama da tawa” “Ashe har yanzu a akwai soyayyar Jibril a cikin zuciyarki tun da har za ki iya kiransa da sunan mijinki” “Miya kawo ki gidanmu? Taya kika zo me kike nema a gareni?” “Wacce daga cikin ukun tambayar ki nan zan fara amsawa?” “Duka zaki amsa min kuma ki tashi ki bar mana gida” “Zan tafi Nawwara gidanku ya yi min yawa da zama, amman ina son ki bani lokacin ki ki saurari abunda zan fada miki ko kuma na ce zan rokeki” Kamar ba zan zauna ba, sai kuma na zauna saman gadon Inna ina kallonta da jiran abunda zai fito bakinta. “Na san za ki yi mamaki ganina a wannan lokacin kuma a cikin gidanku, abun da ya fi ko wanne mamaki ma taya aka yi yarinyar da ke Abuja ta zo har sokoto kuma ta gane gidanku ko” “Ba abun mamaki ba ne Jibril zai iya fada miki” Na fada mata kai tsaye, sai ta yi murmushin da ke nuna cewar maganar ta soketa. “Mai zai sa Jibril ya fada min inda kike bayan ya gargade da cewar na fita daga rayuwarsa? Rabon da na saka Jibril a ido shekara biyu da rabi kuma saboda ke Nawwara” “Ni kuma?” Na tambaya da mamaki sai ta gyada min kai. “Ke fa, sai bayan ya rabu da ke ya gane yaudarar kansa yake da cewar baya son ki, ni kaina a wacan lokacin na san yana sonki ko da kuwa baya son ki tau ya san kimarki domin baya taba bari wani ya fadi wata magana marar dadi gareki a gaban idanunki ko bayan idonkin ciki kuwa har da ni” “Ban tambayeki labarin abunda ya wuce ko abunda zai zo gaba ba, dalilin zuwanki kawai nake son ji” Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleni idanuwanta raurau ta ce. “Yafiyarki na zo nema Nawwara” “Ai ni baki min komai ba” “Na yi komai Nawwara, na tozarta aure na yi amfani da dama ta na ci mutunci auren wata taya Allah ya zai bar ni na gina tawa rayuwar auren a cikin kwanciyar hankali? Bayan ban so yar'uwata abunda na so wa kaina ba? Kaddarorin rayuwa sun yi ta faruwa da ni Nawwara wanda na ke sa ran saboda na ci mutuncin aurenki ne, a iya sanin da kika min ina budurwa har yau ina nan haka ban yi aure ba, a lokacin da muke soyayya da Jibril muna tsaka da maganar aure sai kawai babansa ya cilasta masa aurenki, a wacan lokacin Jibril sai yake ganin kamar idan ya rabu da ni be aureni ya ci amanata, da wannan damar na yi amfani na dauke masa hankali, ni da kaina na rika jan ra'ayinsa har muka fada kogin aikata alfasha wato zina, a tunani wayewa ce na yaudari kaina sosai da sakewa namiji jiki tun kamin ya aureni, ba ni da tufafin sakawa sai na tsiraici gyale ma irin wanda zai bayyana siffar jikina na ke sakawa saboda na dauki hankalinsa, haka duniya ta yi ta yaudarata har muka tsufa a kogin alfasha ban ankaro ba, bayan Jibril ya rabu da ke sai na bijirowa da Jibril maganar aurenmu abun mamaki sai ya ki amincewa, kin san dalili? Saboda ya riga ya san ni a ya mace tun kamin ya aureni, sai ya zamo baya ganin kimata kuma rashin yarda ta shiga tsakaninmu har ta kai shi da kansa yake cewa ko ya aureni ba zai samu natsuwa ba domin zuciyarsa tana raya masa bayan shi zan iya taraiya da wasu mazan, ina ji ina gani Jibril ya auri wasu matan ya bar a lokacin na ko sunana baya son a kira, ni kuma na gagara samun wani mijin aure na kirki saboda kowa kallon yar iska yake min, saboda na riga na gama zubar da mutunci na tun a yanayin suturata, duk wanda yanzo ba da aure zai neme ni ba sai dai da lalata ko kuma soyayya, wadanda suka zo neman aurena da gaske kuma sai a bi a zuge, a haka zama garin Abuja ya gagareni na koma gurin Yayata Kaduna, na natsu sosai a lokacin na zama ta kwarai fiye da yadda kike tsammani, amman mutuncin da na gagara tsarewa tun a wacan lokacin sai ya kasa bani damar na yi rayuwa yadda na ke so, a haka na fara shafa man nan na mai saka haske wai ko farina zai karu na kara burge maza amman a banza sai ma lalata fatata da na yi, ke ce kadai kika tsaya min a rai ina gani kamar hakkin ki ne yake bibiyata dan Allah dan girman Allah dan darajar Annabinsa ki dubi girman Allah ki yafe min Nawwara” Kuka take sosai tana kokarin kama kafafuna, wanda hakan ke tabbatar min da cewar lallai Aysha ta yi nadama, sai dai me abunda bata sani ba, ba hakkina ne kawai yake binta ba, tabbas hakkin aure ba zai barta ba saboda ta tozarta da aure a lokacin da ta samu dama, amman an baro kyau tun ranar haihuwa, domin kuwa ta yi abun da yan mata yanzu suka dauka wayewa wato bayarda kai ga Namiji tun kamin ka aureshi da kuma shigar banza wacce Annabi Allah da kansa yake cewa masu wannan shigar tufafin ba zasu shiga aljannaba kuma ba za su ji kamshinta ba, taya namijin da ya sakin tun a gidanku zai yarda ya aureki? Ko da kuwa ya aureki ba zai taba ganin darajar ki ba kuma babu aminci na zaman aure a tsakaninku har a bada ga kuma azabar Allah tana jiranki matukar baki tuba ba, daman shi namiji duk abunda ya aikata ado ne, ko ina a qur'ane idan Allah zai ambata da da namiji yake farawa sannan mace amman da aka kai babin Zina sai Allah ya fara da macen kamin namiji saboda mace tafi shiga tarko kuma idan bata bada dama ba babu yadda za ayi ta namiji ya aikata. Ajiyar zuciya na sauke zan yi magana sai ga text ya shigo a wayata na Jibril, wai an sallami Noor kuma ya tafi gida da shi sai gobe za su zo nan. Aje wayar na yi na kalleta zan yi magana sai ga Inna ta shigo cikin dakin tana tambayar lafiya jin shisshikar kukan Aysha. ____________________________________ Al-hamdulillah godiya ta tabbata ga Ubangijin da ke ba mu lafiya da rashinta, na samu sauki sosai na gode sosai da kukawarku da addu'o'inku Jazakallahu Khairan 😘 Let my advice be here, For those ladies da suke daukar mallaka kai ga saurayi ko da an muku engaged a matsayin wayewa ko soyayya Wallahi babu soyayya babu wayewa a cikin zina, kuma ko da mutun ya aureki baki da wata kima da mutunci a idanuwanshi, wani ma ba zai aureki ba kin ga kin ga kin zubar da mutunci a banza, kar kalaman banxa su yaudari zuciyarki kar karatun wasu littafan yasa ki rika daukar saka suturar banza a matsayin wayewa Wallahi ba duka writers ba ne include me suke rubuta dai dai ko rashinsa ba me some of our readers suna daukar dukan abunda aka rubuta ko abunda duniya take yayi a matsayin wayewa wanda sam ba haka ne kama mutunci da kimarki shi zai nunawa duniya ko wacece ke kuma mijinki da yayanki zasu yi alfahari da wannan, kar ki ga wata ta yi haka at the end ta auri a mijin kwarai a novels ne ko movies irin wannan abun yake faruwa, in reality 75% basa auren mutanen kirki matukar kika maida kanki karuwa babu namijin kwarai da zai so ki a matsayin matarsa, su ma mazajen na banza ai matan kwarai suke nema su aura, be wise, women with attitude na kwarai a lady with class class din kuma na kare mutunci ba na zubarwa, ko da ke ta kwarai a irin shigar da kike wani zai dauka ke yar iskace ko kuma marar tarbiya. Some will say ya zata kawo mana wannan dogon sharhin nan ko? 😂 Wallahi abun yana ci damuna ne sosai kuma wannan ce kadai damar da na ke da ita wanjen yin wannan bayanin. Wanda na batawa rai ya yafe min Allah ya shirya mu gaba daya. See you next page i can't wait na ji labarin da Rabi zata bawa Nawwara 💃idan Nawwata ta ji za tayi wani abu kuwan? Anya Iayayen Bilal zasu bari ya auri Nawwara kuwa? Duka zai zo a next page Inshallah. 😘 [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy _This Chapter is yours Auntie Sis♥_ 5⃣0⃣ “Lafiya?” Inna ta tambaya. “Lafiya kalau magana ce kawai muke” “Kin tabbata?” “Ba komai Inna” Ba dan ta yarda ta juya ta koma waje, ni kuma na gyara zamana na kalli Aysha na ce “Ba ni kika cuta ba Aysha kan ki kika yi ma, daman duk mai cutar wani yana jin dadi kansa yake cuta domin alhaki zai dawo akansa wata rana, idan ma hakkina ne yake bibiyarki Wallahi na yafe miki daga yau ba zai sake binki ba” Dagowa ta tu ta kalleni da idanuwanta da take faman kuka da su bakinta na rawa ta ce “Wallahi Nawwara ke ta daban ce ban tsammaci zaki yafe min da wuri haka ba, na gode sosai Allah ya saka miki da Alheri” “Amin, amman dan Allah ina son ki fada min taya aka yi kika gane gidanmu?” Sai da ta share hawayenta ta koma saman kujerar ta zauna daidai sannan ta kalleni “Siraj ne ya kwatanta min” “Siraj kuma? Waye haka” Na mata kamar ban san waye shi ba. “Wani abokin Jibril ne, shi kadai ne wanda Jibril ya aminta da shi a yanzu, shine kadai mutumen da yake karfafa min guiwar cewar zai yi duk yadda zai yi wajen ganin Jibril ya aure ni” “Yanzu kina nan akan bakarki cewar Jibril rai aureki duk bayan yaudarar da ya yi miki?” “Bana jiransa shi kadai, idan wanda zai aureni da gaske ya zo zan aureshi, na dade da yafe masa abunda ya yi min saboda na san tun farko laifina ne ba nasa ba, kuma har gobe ina son Jibril” Na sauke numfashi a hankali ina mamakin karfin hali irin nata son wanda baya son ka, ko da yake ya so ta da farko,amman ai ya cuce dan me zata wahalar da kanta gurin son sa. Kamar ta san abunda ke raina sai kawai ta ce “Na san za ki yi mamakin jin har yanzu ina son Jibril, ke ma da ace kina son shi tun farko ko kuma rabo ya shiga tsakaninku da za ki kula shi, ko da yake Siraj ya fada min yanzu matsalar rashin haihuwa take damunsa shiyasa babu ruwansa da ko wace mace” “Haka ya ce miki? Yaushe rabon da ki yi magana da shi?” “Ko jiya mun yi waya da shi” “Amman har yanzu be fada miki Jibril na da da ba?” “Haka ya ce min Jibril ba shi da da kuma ya lalata rayuwarsa da shayeshaye hakan yasa mahaifinsa ya koreshi daga kamfanin da yake ya dora Siraj” “Amman gaskiya Jibril be kyautawa rayuwarsa” “Ni ma da na ji ban jidadi ba, amman Siraj ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya dawo da shi hanya” “Allah ya bashi iko” “Amin” Sai da ta shafe fuskarta ta gyara Hijabinta sannan ta dauki jakarta ta rayata ta mike tsaye. “Na gode sosai Nawwara zan wuce” Har bakin kofa na rakata sai zuciyata na ta tunani akan abokinsa Siraj, miyasa be fada mata cewar yana da da ba? Haka ma yasan lokacin da na fara aiki a kamfanin amman be sanar da Jibril bayan yasan Jibril yana neman ganina, amman kuma miye damuwata da shi ai abokinsa ne babu ruwana a ciki, maganganun Rabi ne suka fado min a rai kan na ankaro Inna ta jefo min wata tambayar. “Wacece wannan yarinyar? Kamin nan miye shigo da ke kina kuka?” Sai a lokacin na tuna da cewar na shigo ina kuka, sai wacan bacin rai ya dawo min na soma jin tsanar Jibril sosai a raina. Kusa da ita na zauna. “Inna wannan Aysha wacce ta yi soyayya da Jibril ce lokacin da ya aureni, ita ce wacce ya ce yana so, shine yanzu take neman gafarata” Haka na kwashe firarmu gaba daya na fada mata irin halin rayuwar da ta ce ta shiga bayan rabuwarsu da Jibril, sai kuma na dora mata da bayanin abunda Jibril ya yi min kamin ya fada mata cewar ya ansallami Noor daga asibiti. “Jibril be kyauta ba, be da ce ya yi miki haka ba, ina tunanin ya yi haka ne saboda ya bata ki a gurin iyayen Bilal kuma suma ya saka musu fargabar wani abu zai iya faruwa da dansu matukar ya aureki” “Ni Inna na tsane Jibril bakin mugu ne Wallahi ni ya dawo min da yarona ba zan barshi ya kwana a can ba” Na fada ina shirin fashewa da kuka. “Ai kara ki kyale Noor ya shaku da Ubansa tun wuri domin kin san dai Jibril ba zai ta ba bari ki je masa agolanci da dansa ba, ke ma kuma ba za ki ji dadin zaman auren ba matukar kika je da Noor domin Mahaifinsa zai rika amfani da wannan damar yana cin zarafinki da mijin da zaki aura, idan kuma mijin da kika aura ya nuna baya son zaman Noor ki ce baya son ki” “Allah ka min mafita” Na fada a fili a zuci kuma na ce Jibril din nan yabi ya tare min ko ina bana da wani sakewa. Muna nan zaune su Sakina suka dawo daga islamiya sai muka dauko wata firar har take fada mana wai malaminsu ya ce satin saman za a kawo kudin da zasu ba iyayensu domin su cigaba da daukar nauyin karatunsu. “Wai Inna ba zamu koma sabon gidan nan ba?” Ta tambaya, ni har na manta da maganar gida domin ban taba zuwa ma ganinsa ba. “Ba zamu koma ba, ko kudin nan ba zamu karba ba duk Jibril ne yake shirya wannan abun, saboda ya siye mu da dukiyarsa” “Ya fada miki shine?” Inna ta tambaya. “A a amman na san shi kadai zai iya wannan abun, idan ba shi ba ne waye ne” “Nima na yi wannan tunani” “Dan Allah Inna karku sake karba komai na sa idan ya baku, Wallahi mutumen ya raina mana hankali sosai ma saboda ya maida mu talakawa, ai da masu kudi ne mu be isa ya taka mu ba” “Kin dai ce kin yafe masa, bana son wata rigima kuma bamu je muka rokeshi ya bamu ba bana son wata fitanar kuma” “Ba zan yi komai ba ai, amman kawai abun yana ci na sosai Wallahi ya ci amanata sosai, kuma ya raina min da wayo da har zai ce ya wai yana neman ya sake aureni, Wallahi aurena da be so da Bilal sai an yi sai dai ya mutu azzalumi kawai” Na fada cikin daga murya hawaye na zuba a ido, ji nake kamar ace Jibril yana kusa da ni yanzu na shakeshi ya mutu. Bayan mun yi sallah magariba na kira Bilal a waya sai ya dauka, na yi tsammanin zan ji shi a cikin wani yanayi marar dadi ko makamancin haka amman sai ya zo a kasin tunanina na jishi cikin farinciki da walwala “Yar halak kin kirani daidai lokacin da zan kiraki na ce ki fito waje gani nan” “Bilal kai ne” “Ni ne mana, wani kika je kira ne kika kirani?” “Aa kawai na ji na cikin farinciki” Ya yi dariya “Cikin bakinciki kike son jina” “Aa kawai na dauka zaka ji haushi na ne kai da Abbah” “Akan me zan ji haushinki Nawwara, abunda kika aikata be kara min komai ba sai kaunarki, yanzu dai fito gani nan kofar gida” Daga haka ya kashe wayar ni kuma na lumshe ido cike da jindadi na sauke ajiyar zuciya, sannan na fadawa Inna na dauki Hijabi na saka na fito kofar gida, jingine da ginin gidan na sameshi kamar kullum yana jiran fitowa. “Pearl” Na kalleshi fuskarta da murmushi. “Wallahi ban tsamaci haka ba ko kadan, na yi tsamanin Abbah zai maka fada ne” “Nawancy kenan, ya yi min fada sosai amman akan rashin kunyar da na yi ma Hajiyar Mustapha ba wai akan abunda ya faru ba, kuma ko da yayi min fada akan ai ba zan dora laifin akanki ba, shine ma ya bani shawarar karna fadawa Mama cewar kin je station domin ya fahimci muna son junan kuma idan Mama ta ji zata yi fada” “Na gode Allah da Abbah ya fahimta” “Kuma ya ce na fada miki cewar Assabar din nan mai zuwa zai zo ya ga su Baba Sulaiman” Na rufe idona da sauri saboda dadi da kunya da suka rufe ni lokaci daya. “Da gaske?” “Aa da karya” Ya fada da fuskar zolaya, sai na sa dariya. “Mama fa mi ta ce?” “Me kike tsammanin zata ce?Addu'a kawai ta yi mana da fatar Allah ya sa alheri a ciki” Na san yace haka ne kawai dan ya kareta amman ba zata so aurena da danta saboda tana ganin kamar kwaruwace xan yi ma danta bayan na yi aure biyu har da kuma yanzu na ce zan auri danta. Mun sha fira sosai a wannan daren sai da aka fara kiran sallah isha'i sannan muka yi sallama ba dan ran mu ya so ba ya tafi ni kuma na dawo cikin gida. Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindadinta akan maganar har ma ta yi mana addu'a, daga baya kuma ta tambaya abunda iyayensa suka ce kan abunda ya faru yau, ni kuma na labarta mata kamar yadda ya labarta min. Bayan mun gama sallah isha'i wayata ta yi ringing ko da na duba sai na ga number Rabi na yi mamakin kiranta a wannan lokacin sai dai hakan be hanani dauka ba. “Assalamu alaikum” “Wa'alaikissalam Nawwara kina gida?” “Ina gida lafiya dai?” “Lafiya kalau akan maganar nan ne, bana son na yi shigowar rana wani ya gan ne, alhalin kuma ba Oga Jibril ba ne ya aiko ni” “Yanzu zaki zo kenan” “Idan zan samu dama ba” “Allah ya kawo ki lafiya” Daga haka na kashe wayar sai ga kiran Jibril ya shigo wayata, da gangan na ki dauka saboda ina tunanin wata maganar zai min ta daban, har sai da ya yi min kira fiye da uku sai kuma ya aiko min da sako karta kwana wato sms cewar Noor ne yake son magana da ni, da ya sake kira sai na dauka cikin rashin walwalah saboda tsanarsa da na ke ji cikin raina. “Hello” “Babe-Naj ga Noor zai yi magana ina fatar kina lafiya” “Zan bashi but ki amsa min mana ko sanyi na ji” “Zan kashe wayar idan baka ba shi ba” “Allah ya huci zuciyarki, ya dorani akan ki Naj” Yana fadar haka ya mikawa Noor wayar. “Hello Momy ina wuni? Momy i miss you” “I miss you too miyasa ka bi Daddynka ba ka zo nan ba?” “Daddy ne ya zo da ni, kuma ya ce ke ma za ki zo gobe, Momy ki zo yanzu mu kwana nan dan Allah” “Ba zan zo ba Noor, gobe ma ba zan zo ba har abada ba zan zo ba, idan kana son zama da ni ka ce ya dawo da kai gidanmu” “Saboda me ba za ki zo ba?” “Saboda nan ne gidanmu ni ba zan zauna ko ina ba sai gidanmu” “Momy gidan yana da kyau fa, har ya fi na su Sadiq kyau dan Allah ki zo” “Ba zan zo ba Noor, idan kana son zama tare da mu ka ce ya dawo da kai gida gurin mu” “Momy zan yi kuka” Ya fada cikin muryarsa mai nuna yana shirin yin kuka da gaske. Sai na ji muryar Jibril yana fadin “No no don't cry Noor tana maka wasa ne kawai zata zo” Ni kuma na katse wayar na kalli Inna. “Inna rabi zata zo yanzu, akwai maganar da zamuyi da ita” “Wace magana ce?” “Wallahi nima ban sani ba, amman dai ta ce tana da muhimmanci sosai” “Da wa kike waya yanzu” “Noor ne” “Amman shine kike fada masa wannan maganar kamar wani babba? Kina son ki saka danki a damuwa ko? Ki raba masa hankali gida biyu” “Amman Inna ai kara na fada masa gaskiya saboda yasan ba zan taba zama da mahaifinsa ba tun yanzu” “Amman be kamata ki masa magana ta wannan hanyar ba, ki daina sauke masa haushin mahaifinsa akansa” “Inshallah Inna ba zan kara ba” “Allah ya kyauta gaba” Sai da na amsa da Amin sannan na tashi na soma duba dakin inda be kintsu ba kimtsa saboda kar Rabi ta zo ta tarar da dakin ba a natse ba. Tara saura kwata ta Rabi ta shigo gidanmu da lullubinta na katon gyale kai baka ma ce ita ba ce, duka muka hada baki gurin amsa mata sai na fita na shigo da ita cikin dakin ta gaisa da Inna sannan Inna da su Sakina da Jamila suka fita waje suka bar mu mu kadai. “Ina tunanin babu wani gurin da ya kamata mu yi maganar nan sama da gidanku shiyasa na zabi na tarar da ke a gida, kuma idan da dare ba kowa zai gan ni ba balle har a tsammaci wani abu” “Me kike so mu tattauna mai muhimmanci har haka?” “Na fada miki akan ki da kuma dan ki da kuma Noor” “Me muka yi?” “Ba ku yi komai ba sai dai wanda ake shirin yi muku” “Ban fahimta ba” Ta sauke ajiyar zuciya. “Nawwara ke kadai ce mace da zata iya tsamo Jibril daga tarkon Siraj a yanzu, ke kadaice zaki iya raba alakar da ke tsakaninsa da Siraj a yanzu” “Miye nawa a ciki da har zan shiga na raba alakarsu? Babu komai fa tsanina da Jibril” “Na san babu komai a tsakaninku a yanzu, amman ai akwai yaro tsakaninku, iya abunda na fahimta Oga Jibril yana son ki sosai, ke ce kadai zaki iya anrar da shi daga ramen da yake kokarin fadawa” “Ni fa ban gane wannan bayanin na ke ba” “Nawwara Siraj ba abokin kwarai ba ne, kokarin zamewa Oga jibril kafafu yake ya dilmiyar da shi, kokarin kwace duk wani abu da Jibril ya mallaka yake kokarin ganin ya zama na sa. Sunana Rabi'at Abdulrazak, ni ba bahaushiya ba ce ni ibira ce asalina ni yar jihar kogi ce, ina zaman gurin Antyna ne a Abuja bayan na gama karatu na, daga baya na samu aiki a kamfanin One on One limitless company da ke Abuja, da sannu na fara aikina kwarewata da kuma jajircewa ta a akan aiki yasa mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir yake yaba min sosai kuma ya dauki yarda ya bani, lokacin da zai turo Jibril aiki a nan sokoto sai ya sa muka zo tare akan na rika kula da duk wani abu da Jibril yake yi saboda yana ganin kamar Jibril ba zai iya kula da kamfanin yadda ya kamata ba, da muka dawo nan sai Jibril yasa aka yi ma Siraj transfer daga Abuja zuwa nan, ban san cewa Siraj abokin Jibril ba ne sai a wannan lokacin, ba zan iya fada miki dalilin alakarsu ba domin ni ma ban sani ba, amman da aka dawo da shi nan sai Jibril ya dauki yarda da amana ya mika masa, idan be samu zuwa meeting ba Siraj yake turawa, komai za ayi sai ya ce a a nemi Siraj” Ta gyara zamanta kana ta yi dariya. “Ba ina kishin Siraj ba ne Nawwara, sai dai akwai abubuwan da na lura da su akan Siraj, ina tunanin kamar shi ya koya masa shan cocaine saboda ua haukarta shi ko kuma ya juyar da hankalinsa zuwa wani gurin ba dan damuwar Jibril kawai ba, idan har dan damuwa ce shi Siraj baya da ita? Miyasa baya sha sai Jibril yake bawa? Abu na biyu ni yake sa na kira mahaifinsa na fada masa dukan abunda yake gudana a kamfanin marar kyau, Siraj ne yayi kokarin kashe Noor saboda yana tunanin idan har Jibril ya san yana da da zai sashi ya daina abunda yake kuma ya natsu, wanda ba haka Siraj ke so ba kuma yana ganin kamar idan Noor yana raye dole wata alakar zata sake kulluwa tsakaninki da Jibril wanda baya son haka shi be ki ma Jibril ya mutu ya mamaye dukiyarsa ba, da hadarin ya faru sai ya dorawa Bilal laifin ta hanyar sanar da Jibril cewar wani ya fada masa cewar Bilal ne ya yi kokarin kashe Noor saboda yana bakinciki Jibril, wannan yasa Jibril ya koreshi daga aiki har ma yayi kokarin kai kararsa kotu amman sai Siraj ya hana a cewar su wai basu da hujja su jira har sai an samu wani abun na daban wanda zasu rike su yi hujja da shi, ke kanki rayuwarki tana cikin hadari domin Siraj zai iya sawa a kasheki kuma a kashe Noor saboda Noor ya ga fuskarsa lokacin da ya yi kokarin kadeshi da mota, ya yi nadanar hakan kuma ya ji bakinciki sosai da Noor be mutuba, daga baya kuma sai ya wani tunanin ya zo masa cewar miyasa be sa wani ya aikata ba sai shi ya aikata? Wannan ya tabbatar da cewar nan gaba ba da kansa zai je kashe ki ko Noor ba wani ko wasu zai sa su yi, yana tunanin idan ya yi haka shikenan ya gama da rayuwar Jibril sai kuma ya yi amfani da cocaine ya karasa halaka shi. Na san zaki yi mamakin jin haka ko kuma ki yi mamakin a ina na san duk wannan ko? Na sani ne saboda Siraj ya fada min, yana amfani da ni ne a matsayin wacce mahaifin Jibril ya yarda da ni, ya ce min zai aureni kuma duk abunda ya samu zai raba rabi ya bani rabi abunda yake kokarin yi yanzu ya mallaki nasa kamfanin ta karshin wannan kamfanin, a yanzu haka mahaifin Jibril ya sauke Jibril ya dorashi akan kamfanin kin ga ya fara samun dama kenan, ni kaina rayuwata tana cikin hadari domin mugun mutum baya yarda da kowa, ni kaina xai iya cutar da ni idan ya samu abunda yake so, saboda yana ganina kamar ba bahaushiya ba yasa yake son ya yi amfani da wannan damar ya cilla burinsa saboda yana ganin kamar muna da son kudi kuma idanuwana a bude suke, na masa na amince ne saboda na san idan har na ki amincewa zai iya kashe ko ya kulla min wani sheri saboda ya san na san sirrinsa, kuma a matsayin na wacce ke aiki karkashin Jibril ba zan iya fada masa wannan ba, bana da wata hanyar sai ta ki, ke kadai ce zaki iya hankaltar da shi domin ceton rayuwarki da ta danki da kuma ta Jibril har ma da tawa gaba daya, ki kuma tsirarta da Bilal daga sherin da yake kokarin laka masa, kin san idan wani abu ya samu Noor dole Jibril ya zargi Bilal kuma ba zai taba kyaleshi ba” Hannu nasa na rufe bakina sai kuma na sauke ajiyar zuciya, kaina ya yi nauyi sosai kalamanta sun min hawa har na rasa wanne zan fara tunani balle na samu abunda zan ce mata, ji na yi ta dafani. “Nasan yana da nauyi Nawwara, ki yi tunani akai, ban san abunda ya raba ki da Jibril ba, amman yana da kyau ki shiga rayuwarsa ko dan gaba ko kuma na ce ko dan danki, abu na karshe da zan fada miki shine Jibril yana son ki sosai da sosai, domin lokacin da Siraj ya sanar masa cewar kin mutu ya yi kamar na haukace, ba sai na gargadeki akan karki fadawa kowa wannan sirrin ba saboda ina ganin a mace mai tunani da hangen nesa na barki lafiya” Da ido kawai na bita har ta fice, sannan na dawo duniyar mamaki da aljabi anya zan iya wannan aikin kuwa? Mi ma zai kai ni taimakon mutumen da ya nemi salwantar da tawa rayuwar? Abu na farko da ya zo min a rai shine Inna dole ne na fada mata komai ko dan neman shawararta, cikin hanzari na tashi na fita waje gurin Inna. [11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣1⃣ Inna ta tsorata sosai da abunda na fada mata hankalinta duk sai ya tashi. “Taya zaki iya shiga cikin wannan lamarin Nawwara?ke fa mace ce ba namiji ba, kuma irin wadannan mutanen hatsarine rabarsu” “Nima abunda na ke ta tunani kenan! Ona ganin aiki zan sa Jibril ya koma sai mu koma tare kin ga duk wani taimako zan iya bashi ta nan kuma ina lurar da shi akan wasu abubuwan” “Gaskiya Nawwara ina jin tsoro, karki je ki janyo mana wani abun na daban kuma” “Babu komai Inna ba zan fito kiri da muzu na fada masa abunda yake faruwa ba, ta dabara zan yi” “Kina tunanin hakan ba zai haifar da wata matsala ba?” “Inshallah ba zai haifar ba” Ta kawar da kai ba dan ta yarda din ba, ni kuma ina ganin bana da wata mafita sai wannan. JIBRIL POV. Lokacin da Noor ya ji cewar Momynsa ba zata zo ba sai duk yanayinsa ya canja ya koma cikin jin bakinciki da damuwa, duk yadda Jibril ya so kar ya bata rai sai da Noor ya bata kuka ma sai da ya yi. A gado daya suka kwanta under one bedsheet, misalin biyu da rabi na dare Jibril ya farka ya shiga bedroom ya dauro alwala ya fito ya shinfida carpet ya soma sallah nafila da a yanzu ta soma zame masa jiki. Kuka ya yi sosai yana neman yafiyar Allah akan abubuwan da ya gabatar marasa kyau sannan ya roko Allah bukatunsa tare da neman shiriyar Allah. Be san yadda zai karanta qur'ane ba but yasan yadda zai yi iistigifari da hailala da kuma tasbishi da kuma salatin Annabi. Yana zaune saman carpet din har aka yi asalati sannan ya tashi ya fita zuwa masallaci. Misalin takwas da rabi Noor ya farka a lokacin Jibril na kitchen yana hada musu breakfast, ko da Jibril ya fito ya samu Noor tsaye bakin kofar bedroom yana ta kallon falon. “Good morning Noor” Sai kawai ya saka dariya kamar ba shine ya kwanta da fushi jiya ba, kuma ya rufe ido wai yaji kunya an gaishe shi. Jibril ya aje kayan da ke hannunshi saman dinning sannan ya nufo Noor ya duka daidai shi ya kama hannayensa ya rike. “Ka tashi lafiya?” “Lafiya kalau, Dady na manta ban tashi ba sai yanzu” “Yeah ai kara ka yi bachi mai kyau ka samu ka huta ko?” “Momy da wuri take tada ni na yi sallah” “Yanzu ma ai lokaci be kure ba muje bedroom ka yi sallah” Tare suka shiga bedroom din Jibril ya taimaka masa ya wanke bashinsa sannan yaa yi masa wanka ya yi alwalah sannan ya daura masa tawul suka fito yana dauke da shi. Ko da ya fito wayarsa na ringing da sauri ya dauka ya kara a kunne. “Assalamu Alaikum Malam, okay gani nan fito” Sai ya zaunar da Noor saman gado. “Jira ni a nan ina zuwa” Number Rabi ya nemo ya tura mata sakon daga bisani ya yi mata transfer na kudi i zuwa account dinta dan ta siyoma Noor tufafi, ko da ya fito Malamin na tsaye waje kusa achabansa yana jiran fitowarsa, cikin girmamawa Jibril ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya dora masa da. “Na san yau ya kamata ace mun fara but yau ina tare da yarona kuma yanzu idan mun gama karyawa zan kaishi gida, so ina baka hakuri zuwa gobe sai mu fara, kuma in fa hali ina son bayan mun yi da safe mu yi da yamma” “Ba matsala, zamu iya farawa gobe din Allah ya kaimu amman kamar wane lokaci?” “Irin takwas na safe haka, da dare kuma tara na dare nasan bayan wannan lokacin ina gida, sai salarinka nawa ake biyanka per month?” “Aa ranka ya dade bana son sisinka, zan koya maka komai saboda da Allah” “Kai amman ina godiya sosai Allah ya saka da alheri” “Amin amin sai dai littafan da za a siyo” “tau kamar nawa za a kashe?” “Zamu siyo ahalari sai kuma husnul muslim da kuma dan goma mai hade da bakaken harufan arabi ta yadda zai maka sauki ganewa” “Kana da account ne?” “Eh akwai” “Okay ina zuwa” Wayarsa ya bude ya yi masa transfer 10k na siyen littafan, har Malamin na cewa kudin ya yi yawa sai ya ce ya dauki sauran abunda ya rage. Cikin dadin rai ya dawo parlour saboda yana jin ya fara taka wani mataki na gyara rayuwarsa, abunda yake ta kokarin yi shine ya zama uba na gari gurin Noor wanda zai yi alfahari da shi ko bayan ransa. Da kansa ya yi feeding Noor sannan ya shiga wanka ko da ya fito Rabi tana parlour zaune ta kawo masa kayan Noor da ya bukaci taje ta siyo, ita yasa ta shirya Noor, shi kuma ya shiga ciki ya shirya kansa sannan suka fito tare harabar gidan ita ta wuce shi kuma ya kama hanyar gidansu Nawwara tare da Noor dake gaban Mota. Jibril ne ya fara fitowa cikin motar sannan ya zagaya ya budewa Noor ya dauko ya dorashi kofar gidan. “Shiga ciki ka ce da Mamanka ina waje” Da gudu Noor ya shiga cikin gidan, bayan few seconds ya dawo ya ce “Wai ta ce ka shigo” Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya dora kafarsa a kofar gidan ya shiga bakinsa kumshe da sallama. “Wa'alaikaissalam” Inna da amsa masa, sai ya zube a gurin yana kwasar gaisuwa kai baka ce ma shi ba ne, kansa a kasa yana mai jin kunyar Inna sosai kamar yau ya fara haduwa da ita. “Tashi Jibril shigo ciki, ashe an sallami Noor” “Eh an sallame shi jiya shine naje da shi gida” “Allah ya kara lafiya” “Amin ya rabb” Daga haka ya mike tsaye. “Bari na wuce daman wani gurin zanje na ce bari na fara kawoshi” “To an gode” Tashi ya yi ya juyo ba dan kuma yana da gurin zuwan ba, yace hakan ne kawai saboda ya kare kansa, yana son ya tambaya ina Nawwara kuma yana jin kunyar haka ga alheri yana son ya yi ma Inna kuma be san yadda zata kalleshi ba. Bayan na fito ya nufi motarsa sai yaji Muryar Nawwara ta kirashi. “Jibril” Ya juyo da sauri ya dawo zuwa inda take. “Nawwara kina lafiya” “Lafiya kalau” “Am sorry about yesterday” Ya fada yana kallon yanayinta sai kawai ya ga murmushi a fuskarta abunda ya bashi tsoro da kuma mamaki a lokaci daya, dan ya yi zaton wata bakar maganar zata fada sai kawai ya ji ta ce “Never mind, ni har na manta da wannan ma, amman Jibril ka ce min zaka canja ko?” Ya kara matsowa kusa da ita. “Na canja Nawwara ba wai zan canja ba, Wallahi na canja” “Idan har ka canja zaka zama uba na gari Jibril, kuma da na gari gurin Mahaifinka” “Abunda na ke kokarin yi kenan ganin na zama uba na gari wa Noor” “Miyasa zaka mikawa Siraj ragamar kamfanin mahaifinka?” “Saboda na yarda da shi kuma mahaifina ya yarda da shi, kuma ba zan iya jan raganar kamfanin ba a yanzu” “Saboda mai?” “Saboda ke Nawwara tunanina da damuwata duka akanki suke” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “Ya kamata ka yarda da kaddara Jibril, ka yarda abunda ya sameka da wanda zai sameka nan gaba duka daga Allah ne, ka daina saka tunani a cikin ranka saboda ni matar wani ce, idan har ka yarda da kaddara ina son ka cireni a cikin rayuwarka, Jibril ina son ka nuna min irin son gaskiyar da kake min ta hanyar maida hankalinka akan rayuwarka da kuma ta danka, ina son ka min alkawari Jibril cewar ba zaka sake shan cocaine ba, kuma zaka maida ragamar kamfanin mahaifinka a hannunka, ina son ka zama jarumi Jibril” Kallonta yake yi ido cikin ido yake karantar gaskiyar kalaman dake zuciyarta, duka abunda ta rokeshi yayi zai iya yi matukar hakan zai faranta ranta. “Na miki alkawari Nawwara zan yi duka abunda kika fada” “And lastly ina son ka cireni cikin ranka Jibril, ka yi focusing akan rayuwarka ta nan gaba da kuma ta danka, ka sa a ranka ko babu Nawwara zaka iya rayuwa, domin can baya babu ni a duniyarka, a yanzu ma idan babu ni zaka iya, na tabbatar min da canjin da kake cewa ka yi Jibril ka zama namijin gaske” Ya gyada mata kai yana murmushin da yafi kuka ciwo. “I promise you Nawwara zan yi dukan abunda kike bukata” “Zan maka addu'ah, kuma ina son na koma aikina tare da kai” “Zamu koma yaushe kike so?” “Allah ya kaimu, but Nawwara ina fatar ba za ki hanani kusanci da dana ba, kuma ba za ki hanani kyautatawa family ki ba” “Na fi kowa son ka yi kusanci da Noor Jibril saboda na san ko nayi aure ba zaka bar ni naje da shi, so tun yanzu ina son Noor ya saba da kai sosai da sosai, matukar wannan canjin da na gani a yanzu a tare da kai ya tabbata zan fi kowa farinciki Jibril I'm ever ready to help you ko dan saboda Noor” Matsowa ya yi kusa da ita kamar zai taba ta sai dai yasan babu wannan damar domin bata son ya tabata kuma shi ma kansa yana son sabawa kansa da wannan. “Thank you so much Nawwara, Wallahi Ina son ki sosai ina son ki yarda da wannan” “Na yarda Jibril” “Ina jin kamar mafarki na ke Nawwara, you actually changed” Ta yi murmushi tare da sanda kanta kasa abunda ya kara burge Jibril ya ji wani sonta na kara shigarsa, sai dai kalamanta na cewar ya fitar da ita daga ranshi be masa dadi ba, but shi kansa yasan yana bukarta cireta a ranshi ko dan ya samu sukuni a rayuwarsa. MUSTAPHA POV. Yau kwanansa biyu da dawowa daga asibiti, tun lokacin da Hajiyarsa ta yi ma Nawwara wannan furucin ransa ya sosu matuka yake jin rashin dacewa da kyautawa abunda Momynsa ta yi. Dan haka ya yanke shawarar yau sai ya kaiwa Nawwara ziyara saboda ya bata hakuri kan abunda ya faru, dan haka yana fita sallah magariba be dawo ba ya wuce gidansu Nawwara, ya taki sa'a yana aikawa kiranta sai gata ta fito cikin Hijabi sai kamshin turare take, sallama ta fara masa sannan gaisuwa ta biyo baya, daga nan kuma sai dukaninsu suka yi shiru ita tana jiran abunda zai fada mata shi kuma yana tunanin ta ina zai fara, da ta fara gajiya da shirun ne yasa ta ce “Ya jikinka? Sorry ban je na dubaka a asibiti ba” Yayi mamakin jin furuncinta domin sam be tsammaci ma zata fito ba balle har ta kula shi haka har da tambayar jikinsa. “Naji sauki sosai Nawwara, ina son na baki hakuri akan abunda Momy ta yi miki last time...” Ta daga masa hannu. “Mahaifiyarka tana da gaskiya Mustapha, na kaina uwa ce kuma uwa kadai tasan abunda wata uwar take ji game da danta, ni kaina ba zan yarda dana ya rasa rayuwarsa akan wacce bata san zafinsa ba, wacce na san ba zata taba aurensa ba. Mustapha ya kamata ka yi tunani, ni da kai ba daya ba ne, ballanta wani abun ya shiga tsakanin ni da kai, yar uwata ka yi ma fyade taya kuma ni zan aureka? Zuciyarka ta daina yaudararka abunda ba zai taba tabbatuwa a gareka ba, ka daina hangen abunda ba naka ba, Ina tunanin mutuwar Habiba ta canja mana rayuwa dukanmu, ta zamo silar shiriyarka, shin miyasa ba zaka tsayardar tunaninka guri daya ba ka yi abunda zai fiddaka? Duk yadda zaka so ni aikin banza ne, saboda komai ya riga ya lalace, a zan boye maka Mustapha soyayyarka ba zata taba samun gurbi a zuciyata ba ko da kadan ne, ka daina wahalar da rayuwarka akaina, ka yarda kaddara ce a haka sai kaga Allah ya kawo maka mafi alherinta” “Thank you Nawwara na gode da kika fada min gaskiya, har gobe ina alfari kuma zan kasance a cikin alfari da son ki har abada, domin son ki ya canja min rayuwa, ya sa na zama kalar da ban taba tsammanin zama ba” Ya fada idanuwansa na cika da kwalla. “Ina maka fata ta gari Mustapha, domin ni Bilal zan aura kai ma ina maka fatar samun matar da zata so ka sosai kuma iyayenka su so ta tadda zaka ji dadin zama da ita” “Thank you but ina son ki taya ni da addu'a domin abun ba sauki” Ya fada yana murmushin karfin hali tare da share hawayen da suka zubo masa. “Zan taya ka, ina maka fatar alheri” Ya dade a tsaye yana kallonta yadda zai yi rayuwa babu ita yake hange, ya san gaskiya ta fada masa shi kanshi yana jin kamar ba zata aureshi ba, sai dai a ganinsa idan har bata aureshi ba ba zai taba gamsuwa cewar ta yafe masa ba, but kalaman da tayi masa a yanzu yasa shi canja tunaninsa kuma ya samu gansuwa a ransa cewar Nawwara ta yafe masa har zuciyarta, ya riga yasan matukar yana son ya shirya da iyayensa dole ya rabu da ita, duk da yana jin a yanzu ta zama wani bangare na jikinsa. Kamar marar lafiya haka ya dawo gida nan da nan sai zazzabi ya rufe sai dai be bari mahaifiyarsa ta sani ba. [11/8, 9:40 PM] CANDY_♥️🖤: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣2⃣ SIX MONTHS LATER... Rayuwar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba ita na ke a yanzu, ni kaina ina canjin da na yi a jikina da kuma ruhina, na zama RAI BIYU a gurin mutum biyu Noor da Jibril, na yi fadi tashin rayuwa kamin na kawo yanzu, na yaki zuciyata kuma na yi nasara akan kudirina. Komai ya canja a yanzu wa zai yarda da ni idan na ce ina rayuwa da Jibril a matsayin kanwa kuma abokiya, ni kaina na kan yi dariyar kaina kamin mamaki ya biyo baya, na zauna a matakin da ban taba tsammanin zan zauna ba, na shiga na fita na gyara rayuwar da na fi tsana a duniya abunda ko a mafarki ban taba tsammanin afkuwarsa ba, a yanzu Jibril ba shi wani madubi ko kuma tsarin rayuwa sai nawa, dukan wani abu daya shafi kamfaninsa da rayuwarsa ko kuma ta Noor da ni yake shawara kamin ya aiwatar da shi, hakan yasa kara tsanar da Siraj ya ke min har bayan son ganin sai dole, gashi case din da muke a kotu ashe yayarsa ce da ke aure nan domin a asalinsu su yan kaduna ne, shi kansa be taba sani ba sai da muka yi zaman kotu na hudu aka je da shi muka hadu, akwai nasara sosai a shariyar ta mu kasancewar Dpo ya tsaya kai da fata wajen ganin an yi mana adalci kuma an bi maka hakkin mahaifinmu, gaskiya na yaba da irin kokarin da dpo yake mana hakan ya kara tabbatar min mana cewar ba duka yan sanda marasa na na gari ba, domin a cikin bata garin ana samun na gari a cikin na garin kuma ake samun bata gari, Inna ma ta yaba da kokarin shi duk da ita tafi maida hankalin akan cewar wai so na ke, ni kan ina ganin kamar dai yana yi dan Allah kawai domin ni ai yasan an samin rana, duk da wani lokacin haka kawai xai kirani a waya ya ce fira yake son muyi ko ya ce yana son jin muryata, sai dai duk wannan firar da muke a waya Bilal be sani ba da sai ya kusa hadiye zuciya saboda mugun kishina da yake ko da yake na lura kamar ya fi kishina akan abunda ya shafi bangaren Jibril, kamar yadda shi ma Jibril yake nuna min kinshinsa na banza a duk lokacin da na ambaci Bilal a gabansa ko kuma na yi waya da shi, ni kuma na kanyi hakan ne saboda ya daina wahalar da kansa yana kusa kansa gareni domin na dade da zama matar wani. Na yi nasarar shiga na kanannade duk wata hanya da zata sa Siraj ya samu wani abun a karkashin Jibril, idan zuwa wani aikin ne ko taro ni kaina na ke cilasta Jibril zuwa, kuma na sa ya karbe komai nasa da yake hannun Siraj duk da be so haka ba, har ta kai ta kawo idan ban ga dama ba Siraj ba zai iya ganin Jibril ba indai a office ne,  da fari Jibril da shi kansa Siraj din sun zarge ni da shiga tsakaninsu na neman rabasu, sai dai nasarorin da Jibril ya yi a cikin watan nan shida ba tare da Siraj ba yasa na fahimci shi kadai ma zai iya ba sai tare da wani, ko da wasa ban taba fadawa Jibril cewar Siraj yana masa Zagon kasa ba, sai dai na kan yi kokarin nuna masa haka ta hanyar wasu abubuwan da Siraj yake yi, tare da Rabi muke komai ita take sanar da ni duk wani kudiri na Siraj ni kuma sai na yi kokarin Jibril aikatawa, Jibril bw taba yarda da ni sosai ba kamar lokacin da na daukeshi muka je bypass da kansa ya ga kamfanin da Siraj yake ginawa wanda be taba fada masa ba, hakan yasa shi ma na ya fara ja baya da shi har suka soma samun sabani saboda rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu Jibril yana ganin be kamata ace Siraj ya boye masa abu mai muhimmanci kamar haka ba, shi kuma Siraj yana ganin Jibril ya dauki amana ya bani har ina shiga tsakaninsu. Jibril ya sake shiga rayuwata a karo na biyu, na sake jiki da shi irin sakewar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba, ya canjawa Noor da Jamila makaranta daga makarantar gwanati zuwa Imam international school, da school bus ake kawo su kuma a dauke su da safe, shakuwar data shiga tsakanin Noor da Jibril a yanzu har mamaki take bani lallai na yarda da aka ce yara sun fi sabawa da iyayensu maza. Sakina kuma ya maida Khalifa International School wace ke can kusa da Polytechnic bypass, dukan wani abu da za'a ci a gidan daga aljihun Jibril yake zuwa, idan na yi magana yace dansa yake yi ma, ni kuma na kan bashi damar hakan ne saboda nima na samu damar shiga cikin tasa rayuwar, ni ce na yi ruwa na yi tsaki a rayuwar mutumen da na fi tsana a duniya, bana da matsala a yanzu sai ta mutum biyu Bilal da kuma Siraj, na rasa yadda zan yi na fito kai tsaye na nunawa Jibril irin kudirin da Siraj yake da shi akansa, ina son nayi masa yadda zai fahimta ne kuma ya kamashi dumudumu amman na rasa yadda zan fahimtar da shi. Sai Bilal da ya kasa fahimta ya kasai daina zargina duk kuwa da kasancesar an saka ranar aurenmu a yanzu, zuciyarsa ba raya masa kamar ina son Jibril ne, ga kuma ta bangaren Familynsa har yanzu mahaifiyarsa fushi take dashi ta kasa sakewa da ni saboda bata son auren, gashi tana ganin kamar saboda ni aka kore shi aiki daman mahaifinsa ne ya tsaya kai da fata akan maganar har aka saka ranar auren.   Ko ranar da aka kawo tufafin sakawata sai sa yan'uwansa mata suka yi ta Maganganun kamar na habaici, ni dai ko kadan hakan be dame ni domin iya abunda na sani Bilal yana so na ni ma kuma ina son shi so kiyayyar yan'uwansa ba zata dame ni ba, domin ina jin a jikina zan iya canja musu rayuwa su soni ta hanyar kyautata musu da kuma yi musu biyayya.   Ban tsammaci Bilal zai zuba min lefe kamar haka ba, domin kala talatin da biyu ya yi min kamar wata budurwa babu abunda be saka ba a cikin lefen, da na masa magana sai ya ce wai daman ya dade da siye ya aje ba a yanzu ya siya ba, baya aikin komai a yanzu sai tsaron wani shagon computers suna biyanshi kullum, amman ya yi applying a cbn da kuma aikin kaki har guda biyu, sai dai aikin naija sai a hankali za ka yi applying dauka sai na manta ma, baya son komawa kamfanin Jibril aiki kamar yadda nima bana so saboda kar Jibril ya dauka cewar Bilal da kamfaninsa kawai ya dogara. Ban taba sanin cewar Bilal yana da zafin kishi ba sai a yanzu, domin ko kallona ya yi sunan Jibril yake kira wai ai daman yasan ina son shi ni kuma wani lokacin har dariya yake bani domin idan ya bata rai abun baya masa kyau. Yau ta kama Friday ina dawowa aiki na zauna na shiryawa Bilal Snack saboda yana ciki favorite dinsa musamman ma idan ni nasa yana ci sosai, sai da magariba na gama sai na yi wanka na shirya cikin wata jar kamfala, ta karbeni sosai saboda jan abu yana fitar da farin mutum, sai na bi jikina na fashe da turare sai na dauki blue mayafi na saka, na dauki wayata na kirashi bugu biyu ya daga. “Hubby ina nemanka yanzu” “Me za ki ban?” “Sai zan baka wani abu kawai na ke da ikon ganinka?” Na fada kamar zan fasa masa kuka. “Gani nan zuwa” Yana fada ya kashe wayar, haka yake mina yanzu zuwa fira ma sai yaga dama saboda kawai yana fushi da ni wai ala dole ni soyayya na ke da Jibril, ko kadan bana ganin laifinsa domin na san ko a littafi ba za a samu namijin da zai yarda ya kyale matar da zai aura tayi aiki karkashin wani ba a Wai dan kawai da taimaki rayuwar danta. Ta bangaren yan uwansa ma nasan ba a rasa masu masa magana domin abokansa da yake zuwa da su wani lokacin sukan zolayeni da Maganganun marar dadi ko kuma na bugun ciki domin kawai su ji abunda zan ce, amman ya toshe kunnuwansa domin kawai ya bani damar cin ma kudirina har shi yake kokarin kare ni wani lokacin. Bayan kamar mintuna talatin sai gashi ya aiko min sako wai na fito yana kofar gida, ni kuma na yi murmushi na dauki snack din na kira Noor ya rika min lemun kwakwa hadin gida da na yi masa muka fito tare fito Noor na aje jug din yaje da gudu suka rumgume juna. “Uncle Bilal i miss you” “I miss you too Noor” “Wannan Saturday data wuce ka ce zaka zo kaje da ni yawo kuma baka zo ba” “Mantawa na yi but dis weekend zamu je” “Gobe ko? Gobe weekend fa” Bilal ya dafe kansa. “Oh na manta tau gobe za muje” “Thank you” Ya fada har da tsalle, sai kuma ya tsaya yana kallon bakina da shi yadda muke gaisawa, ganin hakan yasa na umarce shi da ya wuce cikin gida. “Ga snack din da na maka” Sai ya kawarda kai baya ma son kallon snack din. “Bana jin cin komai a yau” Hakan yasa ni jin babu dadi amman sai na daure na dauki daya na mika masa a hannu. “Dan Allah ka ci da kaina na hada maka” “No na koshi yanzu na gama cin indomie” “To ga lemun kwakwa nan da kaina shi ma na hada” “Ai ko baki fahimtar hausa ne?” “Na fahimta dan Allah Bilal ka daina fushi da ni, na san ka yi hakuri ni kaina ba dan raina yana so nake aikin nan ba, kuma na yanke shawarar aje aikin a wannan week” Ya kalleni “Saboda mai?” “Saboda ya kamata na aje, na yi iya kokarin da zan yi na taimakon Jibril, sai dai na bishi da addu'a kawai, kuma kaga aurenmu sauran wata uku a wannan lokacin ne ya kamata na aje aikin ai” Murmushi ya yi ya soma wasa da yatsun hannunsa. “Har yanzu kina son Jibril ko Nawwara?” Kallonshi na yi jin tambayar banbaragwai da kuma yanayin yadda ya kira sunana kai tsaye ba kamar yadda ya saba kira ba. “Wannan kuma wace irin tambaya ce Bilal?” “Tambaya ce dai kamar ko wace tambaya amsarki kawai na ke so” “Idan har baka so ba aikin nan Bilal ba zan yi ba” “Na isa na hanaki? Ban riga na aureki ba Nawwara balle na gindaya miki wasu sharadodi, so ban isa na hanani aiki tare da Jibril ba, idan ma na yi kokarin hanaki sai Inna da ke sun ga laifina” “Babu wanda zai ga kaifinka saboda kana da cikakken iko a kaina, be kamata ka zargeni ba Bilal” “Mi zan yi bayan zarginki Nawwara? Jibril first love dinki kuma karya kike yanzu ki ce min babu son shi a cikin zuciyarki, na san yana son ki sosai kuma zai yi komai dan ya ga ya same ki, ya fini kudi na sani kuma ya kyautata musu da abunda ni ba zan iya ba” Idanuwa sun cika da kwalla kalamansa sun ratsa zuciyata cikin rashin jindadi na hadeye yawun da ke bakina na ce “Jibril ya fika kudi amman be fika karbuwa a zuciyata ba, Jibril ya wukanta ne Bilal irin wulakancin da wani da namiji be taba ma mace ba, kuma a yanzu kake zargin zan iya aurensa? Bayan an saka mana rana da kai mika dauki iyayena ne zasu canja magana ta da kai saboda kawai Jibril ya fika kudi?” “Idan har baki son shi dan me za ki taimaki rayuwarsa? Har ku kuma kuna zama kamar wasu masoya, dan Allah Nawwara baki ji kunyar kanki ba?” “Da ka nuna min baka so tun farko da ban yi ba, dukan abunda na ke ma Jibril ko kuma na yi masa na yi ne saboda Noor idan ya gyaru Noor zai amfana idan kuma ya lalace Noor ne zai tagaiyara miyasa ka kasa fahimtata ne?” “Saboda Noor ko? Komai ma ai saboda Noor ne Nawwara i understand” Yana fadar hakan ya saka hannayensa aljihu ya wucewarsa ya barni nan tsaye ina faman hawaye. JIBRIL POV. Daker yake numfashi saboda nauyin da zuciyarsa ta yi masa, daman yanzu abun ya zame masa kamar jiki idan yau be yi ba gobe sai ya yi, sai dai duk wannan abun be taba yarda ya yi gaban Nawwara ba, idan har suna tare abun ya taso masa sai ya kulle office dinsa ko kuma ya bar kamfanin ya dawo gida.   Daker ya unkura ya tashi ya nufi bathroom yana shiga sai aman jini yau kan be yi shi da yawa ba kamar yadda ya saba, sai da ya wanke bakinsa sannan ya bude cabinet ya dauko wasu kwayoyi ya hade tare da ruwa sai ya juyo ya fito daga bathroom ya zauna saman kujera ya lumshe ido yana sauke numfashi a hankali. Nawwara ce kadai macen da yake gani idan ya rumtse idonsa, duk da a yanzu ya sadakar ba zata taba zama tashi ba, yana ji a jikinsa kamar ba zata sake rabarsa, but he's happy da ta yi aiki da shi ta maida da shi cikakken namiji, dukan wani canji daya samu a rayuwarsa yasan ta dalilin Nawwara ne, domin be yi zaton zai iya daina shan cocaine ba amman gashi yanzu komai ya zama tarihi, and now he can read Quran duj da be yi nisa sosai a ciki ba amman ya san bakin domin kullum Malaminsa yana zuwa yana koya masa har ma da wasu littafan na daban da kuma bayani akan sallah da wasu abubuwan na addini, shi kansa a yanzu yana jin dadin rayuwarsa Saboda yana jin ya kara kusanci da Ubangijinsa hakan yasa ba janye dokan hana saka hijabi a kamfaninsa domin a yanzu ya fahimce babu komai a cikin addininsa sai rahama da jinka ga gata da addinin musuluncin yake ma ko wane musulmi, bashi da wata matsala ta rayuwa a yanzu sai tunanin Nawwara da ya zame masa kamar abinci, idan suna office har baya son su rabu saboda kewarta da yake komai ya zo masa kamar a mafarki ace Nawwara ce ta sake jiki da shi suna aiki haka, but a duk lokacin da ya tuna zancen aurenta da Bilal sai yaji kamar ya hade zuciya ya mutu, wannan tunanin ya yi tasiri a zuciyarsa da har ya zurfafa masa ciwon dake damunsa, a iya yanzu ya sadakar kuma ya yarda rayuwarsa ba mai tsawo ba ce a duniya, saboda matsala da cocaine ya haifar masa da kuma yawan tunanin da yake a baya ga kuma wanda yake a yanzu, wannan yasa shi yin saku saku da rayuwa. Wani lokacin yana kan kamar ya samu Nawwara ya fada mata hakan sai dai yasan ba zata fahimta ba kuma zata zargeshi da cewar saboda yana son bata alakarsu da Bilal ne, wannan yasa ya danne komai ya barwa zuciyarsa sai kuma mahaifinsa da Siraj da suka san da matsalar. Kalaman da ta yi masa yau a office na cewar zata aje aikinta a wannan satin mai zuwa ne suka haddasa masa ciwon kai har ya abun ya sauko a zuciyarsa, kullum sai ya kirga kwanakin da suka rage na aurenta da Bilal kamar da shi za a daura auren. Ji yayi yana da bukatar ganin dansa domin a yanzu shine kawai farincikisa, a duk lokacin da Noor yake kusa da shi yana jin dadi sai ya dinga jin kamar Nawwara ce a kusa da shi. Unkurawa ya yi ya tashi cikin karfin hali ya koma bathroom ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki wayarsa da car keys ya fice daga dakin. Har ya fito harabar gidan be daina jin zafin da zuciyarsa take masa ba. Haka ya shiga motar ya dauki hanyar da zata kaishi gidansu Nawwara. A kofar gidan ya yi parking sannan ya dauki wayarsa ya kira Nawwara, bata dauka ba har ta katse sai ya sake kira haka ya jera mata kira hudu ba tayi picking sai ya fita daga motar ya je kofar gidan ya buga, sai gata ta fito hawaye shabe shabe a fuskarta. “Dan Allah dan girman Allah karka sake zuwa kofar gidan nan Jibril da sunan ganina, yanzu yanzu Bilal ya bar gurin nan da ya tararda kai ai ba zai ji dadi ba, saboda kai yau na fada min magana marar dadi, kuma na fada maka cewar komai ya kare a yanzu, tun da zaka iya komai da kanka shiyasa nima zan aje aikin saboda na samu damar kula da Bilal da kuma kaina” “Ina son ganin Noor ne shiyasa na zo” “Idan kana son ganinsa ka sanar da ni zan sa a kawo maka shi har gidanka, amman a i zuwa yanzu ka daina zuwa nan sai na yi aure” “Okay Nawwara ba zan sake ba, and ki bawa Bilal hakuri akan abubuwan da suka faru, na san mun shiga hakkinsa but yanzu komai ya wuce” Ba tare da ta sake cewa komai ba ta juya ta koma ciki, shi kuma ya cikama bakinsa iska ya busar sai ga Noor ya zo da gudu, sai Jibril ya risina kasa ya shafa fuskar dansa sai kuma ya rumgume shi ya lumshe ido. ‘Ni na jawa kaina komai saboda haka dole na yarda da rashinki’ Ya fada a ransa, a fili kuma sai ya dago fuskar dansa ya kalleshi ya ce. “Dukan abunda Nawwara ta yi da wanda na yi mun yi ne saboda kai Noor, ina son ko da bana raye ka kasance mai alfahari da ni a matsayin ubanka” “Ni ban gane abunda kake cewa ba” “Zaka gane wata rana, ina son ka zama mai biyayya ga Mahaifiyarka ita ce zata rayu da kai har ka girma, na yi farincikin da na rayu da kai Noor ina son ka sosai” Ya rumgume shi idanuwansa cike da kwalla, sosai da sosai yake shakar kamshin jikin Noor, domin haka na masa dadi yana jin kusan da dansa sosai. “Noor zamu je yau ka yi weekend gidana ko?” “Ee amman Uncle Bilal ya ce zai je da ni yawo gobe Saturday” “Yaushe ya zo?” “Dazu” “Okay, idan kun dawo sai na aiko a dauko min kai ka ji” “Okay Daddy Momy har da cake ta yi ma Uncle Bilal” Wani irin daga kai ya yi ya sauke numfashi saboda yadda maganar ta sokeshi. “Okay je cikin gida ni zanje gida kar dare ya yi” Ya sumbanci goshinsa. “Goodnight” “Goodnight” Noor ya fada yana daga masa hannu sannan ya shige cikin gida, shi kuma ga mike tsaye ya jingina da motarsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. Ya samu thirty minutes a gurin sannan ya bude motaraa ya shiga cikin rashin dadin rai. *** *** *** NAWWARA POV. Na farka yau cikin rashin dadi rai saboda abunda ya faru jiya, sam ban jidadin yadda Bilal ya kasa fahimta ta ba, duk da nasan kowa waye dole ya zargi wani abu a tsakaninmu, amman komai ya kare a yanzu ba zan sake bari wata alaka ta shiga tsakanina da Jibril ba da har zata sa Bilal ya zargeni. Na dade a kwance kasancewar yau weekend har su Noor da Jamila suka dawo daga islamiyar safe ban tashi ba ba dan kuma ina bachi ba sai dan ina jin jikina da rayuwata babu dadi, ina son na labartawa Inna sai wata zuciyar ta hanani saboda na san ba komai ya kamata ace iyaye sun sani ba musamman a abunda ya shafi fada a tsakanin ma'aurata ko kuma masoya, har sai idan ya kai ya akwo mun kasa shawo kan abun. Wayata na dauka na aika masa da sakon barka da safiya amman be maido min da amsa ba, hakan yasa na kirashi sai be yi picking ba. Tashi na yi na fita tsakar gida na gyara ko ina sannan na shiga na yi wanka na shirya cikin bakar abaya, Inna ma ta kula da yanayin da na ke cikin na rashin dadin rai, sai dai bata min magana ba, wata kila ta fahimci akwai abunda ya shiga tsakaninmu da Bilal jiya da dare saboda na dawo ina kuka duk da kasancewar ta tambaye dalilin kuka na ki fada mata. Misalin sha daya da rabi Bilal ya kira ni ina picking ya ce “Ki shirya ma Noor gani nan zuwa” “Tau, har yanzu fushi kake da ni ko?” Sai kawai ya kashe wayar, ni kuma na ja dogon numfashi na sauke na tashi na fita. Ko da sha biyu ta yi da kwata Bilal na kofar gidanmu yana jiran Noor, ban san miyasa ba na samu kaina da rashin jindadin fitar shi tare da Noor duk da sun saba fita amman yau ina jin daban gashi gabana sai faduwa yake, wata kila saboda bana cikin dadin rai ne ko kuma wani abun ne daban oho. Da kaina na riko hannunsa na kaiwo shi kofar gida, saiga wayar da ke hannuna ta yi ringing Jibril ya kira, daman yakan kira da safe ya yi waya da dansa haka ma da dare idan zai kwanta sai dai yau yayi ranar kira domin har sha biyu ta gota ko da yake yasan yau weekend ne Noor baya suwa school. A nan na mika masa wayar ya gaisa da Jibril sannan Bilal ya rika hannunsa ba tare da yace da ni komai ba suka tafi Noor nata dariya yana dago min hannu. Cikin gida na dawo na dora girkin rana, sannan na dauko tufafin Inna da suka yi datti muka soma wankewa ni da Sakina muna fira sama sama, sai dai faduwar gabana na ta karuwa, ina jin kamar na yi kuka kuma ba dan a min wani abun ba. Da la'asar Jibril ya aiko da dare bansa a daukar masa Noor sai na fadawa direban cewar basu dawo ba, daman idan suka fita wani lokacin har isha'i suna kai wa basu dawo ba, direban na wuce da kamar minti biyar sai ga Bilal ya kirani a waya hankalinsa a tashe. “Nawwara Noor ya dawo?” “Aa kun dawo ne?” “Bayan fitar mu be dawo ba?” “Aa be dawo ba, lafi... ” Kamin na tambaya ya kashe wayar, ni kuma jikina ya yi sanyi na soma ambaton Allah a hankali “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” [11/10, 6:59 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣3⃣ Jina yi kamar bana da karfi a jikina na kasa shanyar da na ke, sai na zauna a gurin gabana nata faduwa. “Nawwara” Inna ta kirani saboda ta lura da yanayina, sai na kasa amsa mata saboda kukan da ya cika min zuciya nasan ina bude bakina zai fito. “Lafiya miya faru? Dawa kike waya?” “Bilal ne, tambayata yake wai Noor ya dawo” Na fada ina ta kokarin danne kukana. “Kamar ya? Ba tare suka fita ba” “Tare suka fita” “Amman shine zai kira ya tambaya ya dawo bayan kuma ya san tare suka je? Wane irin rainin wayo ne wannan?” Cewar Sakina tana matse zanen Inna. “Wata kila wani abun ne ya faru, ina ji jikina ba dadi” “Tun jiya na lura da ke sai dai nasan matsalar bata wuce tsakaninki da Bilal ba shiyasa ban yi magana ba, sabodana bana son ina yawan shiga fadanku, amman babu abunda zai faru da Noor Inshallah” Ajiyar zuciya na sauke ya share guntun hawayen da ya zubo min na tashi na koma bakin kofar dakinmu na zauna, Sakina ta cigaba da wanke kayan. Haka muka zauna shiru har aka kira magariba Bilal be sake kirana ba gabana kuma be daina faduwa ba. Bayan na sallah isha'i na dauki waya na zimmar na kira Bilal sai kuma nake ganin rashin dacewar hakan, saboda ya saba fita da Noor su kai har dare basu dawo ba, dan me yanzu zan soma kiransa ai sai ya zargeni yace ko dan munyi fada ne, haka na maida wayar muhallinta na aje, kamar Inna ta san abunda ke raina sai kawai na ji ta ce “Karki ji kunyar kiranshi Nawwara, ki kirashi mana ko muma hankalinmu zai kwanta” Ba musu na daga wayar na kira number Bilal amman har ta gama ringing be dauka ba, haka na jera masa kira hudu be daga ba, daga baya kuma sai naji wayar a kashe, hakan ya kara fadar min da gaba, ina kokarin fadawa Inna cewar wayarsa a kashe take sai ga sakon Jibril ya shigo. _Nawwara Noor ya dawo? Ina son gani dana zan aiko da mota yanzu_ Ni kuma na yi saurin mayar masa da sakon cewa basu dawo ba, sai ya sake aiko min da wani _Dan Allah karki shiga tsakanina da dana Nawwara na roke ki, kiyi min duk abunda zaki min amman karki hana min Noor_ _Idan sun dawo zan fada maka_ _Gani nan zuwa na dauki dana_ _Aa karka zo_ Bw sake cemin komai ba, nasan be yarda da ni bane yana ganin kamar ina kokarin hana masa Noor ne. “Inna na ta kira na kira be daga ba daga baya kuma sai aka kashe wayar” “Allah dai yasa lafiya” Cewar Inna ni kuma na amsa da Amin, kamin mu hada baki gurin amsawa Jidda da ta shigo a yanzu kamar marar lafiya, ina kallonta na san ba lafiya ba, sai dai ban kawo cewar maganar Noor bane saboda a tunani bata san sun fita ba. Kasa gaisawa ta yi da Inna sai kawai ta sakar min ido hawaye ya soma mata zuba “Ke lafiyar ki?” Na tambaya ina dafata. “Nawwara” Sai kuma ta yi shiru kamin ta cigaba. “Dazu da Bilal ya fita da Noor wai ya tsaya da shi a AGG MALL ya siya masa chocolate shine sai yaga wani abokinsa suka tsaya gaisawa, wai Noor ya fito daga ciki ko da suka gama gaisawan ya nemeshi ya rasa” Nina mike tsaye da sauri Inna kuma ta dinga furta “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Sakina kuma ta dora hannu saman kai tana kiran “Mun shiga uku” “Yanzu ina shi Bilal din yake?” Inna ta tambaya hankalinta a tashe. “Yana can gidansu, wai besan yadda zai fada muku ba shiyasa be zo ba tun dazu, nima yanzu yake fada min kuma ya ce ya bada report gurin yan sanda da gidan radio” Ni dai ban iya cewa komai ba ban da hawayen da nake, muna haka naji tsayawar mota a kofar gidanmu wanda hakan ya tabbatar min da cewar Jibril ne kuma daman yana kusa da unguwar a lokacin da ya kira. “Ga Jibr.. Il nan... Yace tafiya zai yi da Noor” Na fada muryata na rawa. “Ki fita ki fada masa gaskiya dole ne ya sani” Inna ta umarceni, tashi na yi na fita ina hawaye, nasan Jibril ba zai yarda ba amman ya zama dole na fada masa, ko da na fito yana jingine jikin motarsa yana danna wayarsa da alama ni zai kira. Fitowata tasa ya dago kai ya kalleni yanayin yadda na ke tafiya na doso shi yasa ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata. “Karki fara min complain ba gurinki na zo ba Wallahi, kawai zan dauki dana ne kuma nasan idan ban zo da kaina ba ba zaki bari taje ba, and i need to be with my son” “Jibril.... Noor ...... Noor” Na kasa magana saboda kukan da ya ci karfina. Ya sakar min ido sosai yana son jin abunda zai fito daga bakina. “Noor ya bata....” “What? How?” Na kasa magana sai kuka na ke. “Look Nawwara, idan ma kin shirya hakan ne dan ki samu nisanci da ni to wannan ba hanya ba ce, dan zan iya jure komai ban da rashin Noor, dan Allah ki canja tsari” “Wallahi ba wasa na ke ba Noor ya bata” Ya tsaya kallona dan tabbatar da zancen da nake gaskiya ne ko akasin haka. “Kamar ya Noor ya bata bata ya bata ya bata as how?” Ya tambaya yana mai daga murya tare da hannyensa sama, ni kuma sai kuka na ke ina ta kokarin rufe baki. “Ki daina wannan banzan kukan naki ki fada min yadda aka yi dana ya bata” Na razarana sosai saboda yadda ya katsa min tsawa da kuma irin bacin ran dake cikin muryarsa. “Da suka fita da Bilal shine suka tsaya Agg mall siyen chocolate sai ya nemi Noor ya rasa” Ya yi dariya marar sauti “Ki ce Bilal ya sace min yaro ya siyar ko kuma ya boyeshi ya nemi kudin fansa” “No Bilal ba zai yi haka ba, Wallahi Bilal ba zai taba cutar da Noor ba” “To wa zai cutar da shi waya batar da shi a yanzu?” Ya fada a tsawace. “Wallahi Bilal ba zai cutar da Noor...” Hannunsa ya daga zai mareni sai kuma ya kaiwa gilashin motarsa bugun yana wani irin huci. “Akan dana zan iya taba kowa Nawwara kuma kowa da kowan nan har da ke, idan kin san wani abu ne kula da Bilal tau ki gaggauta kanwace shi tun wuri” Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya bar ni nan tsaye ina aikin kuka, sai ga Sakina ta fito da gudu ta nufi hanyar Babban gida, ni kuma na juya na koma, ko da na shiga Inna na ta buge bugen waya tana kuka kamar yadda Jidda take. Ko da tara na dare ya yi gidanmu ya cika da jama'a makota da kuma yan uwa, maza suna suka shiga gari inda ake sa ran za a ganshi har Agg mall din anje amman ba a ganshi ba, ko da Baba Sulaiman ya aika Sakina ta kira masa Bilal sai ta dawo ta fada mana cewar wai yana police station an tafi da shi tun dazu, kowa yayi mamakin wanda zai kulle Bilal a wannan lokacin sai da Baba Sulaiman da Inna suka fada cewar Jibril ne, a ranar duk wanda yake cikin gidan nan ya tabbatar da cewar Noor yana da Uba. Ni da Inna da Mama turai da Baba Sulaiman da Sakina da kuma Jidda muka kwasa muka je station din, daidaikun mutanen unguwa suka bimu saboda gulma. Mun tararda Jibril a can sai mahaifin Bilal da mahaifiyarsa tana ta kuka, sai wani kanensa daya. “Ina Bilal din yake?” Inna ta tambayi Mahaifinsa sai ya amsa mata cikin rashin dadin rai. “Yana can ciki sun ce ba zasu fito da shi ba, tun dazu muke a nan tsaye babu irin rokon da ba mu musu ba” “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Cewar Inna, ni kuma na doshi gurin Jibril sai yayi saurin tashi ya fice daga station din, da gudu na bishi ina kiran sunansa daker ya juyo ya kalleni fuskarsa babu annuri. “Minene” “Wallahi ba Bilal ba ne ya sace shi” “Ke kika sace shi” “Wallahi ba Bilal ba ne, dan Allah ka kyale kasan yan sandan nan basa da mutunci zasu iya ji masa fa” “Ke ta Bilal kike ni kuma ta da na nake, babu ruwana da alakarku ya fito min da da na ya zauna lafiya” Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga ya barni nan tsaye. Wasa wasa aka kwashe kwana uku ana abu daya, Jibril ya ki bari a saki Bilal saboda yana zargin shi ya batar masa da da, ita kuma mahaifiyar Bilal da yan uwansa suna dora laifin akaina, a ganinsu ko da da gaske Bilal ya batar da Noor ai be cancanci a ayi masa irin wannan wulakancin ba, har fade take wai danta be taba zuwa cell ba sai dalilina, babu irin magiyar da bana ma Jibril amman kullum maganarsa daya Bilal ya fito masa da da, ni da shi baka iya tantance waye ya fi shiga damuwa, sai dai Jibril ya fini shiga tashin hankalin sosai saboda haukacewa yake kokarin yia kan neman dansa, har mahaifinsa sai da ya zo har sokoto saboda wannan maganar Noor, kullum mafarki na Noor sai dai har yanzu zuciyata bata zargin Bilal. Ranar talata ranar da mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir ya yasa a kashe maganar gurin yan sanda muna station mu dukanmu Jibril ya saka Bilal gaba yana masa magiya har da kukansa. “Dan Allah dan Annabi Bilal ka fada min inda da na yake? Idan kudi kake so ka fada min zan baka ko nawa ne, kuma Wallahi na maka alkawari ba zan bari a ama ka komai ba, amman Noor shi kadai ya rage min ka tausaya min Bilal dan girman Allah” Bilal ya kasa magana sai hawaye yake, gaba daya kamaninsa sun canja. “Wallahi Bilal be dauki Noor ba” Na fada cikin kuka, sai mahaifiyar Bilal ta kwatse ni. “Ke dan Allah can rufewa mutane baki, baki fada tuntuni ba sai yanzu tsohuwar munafuka, ko da yake Allah ya kara ai kai ka ce ka ji ka gani” Ban kara mata magana ba, har muka fito station din, muna dawowa gida sai ga Jibril ya iskoni har gida be tsaya a waje ba ya shigo cikin gidanmu da sallama ba tare da ya nemi uzinin shiga ba, ban tabbatar da irin ramar da yayi ba sai a wannan lokacin idanuwansa sun fada sosai. Gaban Inna ya je ya risina yana hawaye kamar karamin yaro “Inna na rokeki ki saka Nawwara ta fada min wani abu akan batan da na, shi kadai ya rage min a duniyar nan, yau kwana hudu kenan ba a ga Noor ba, duk wanda ya dauke ke Noor rayuwarsa yake so ba kudi na ba, da kudi nane da yanzu an kira an ce na bayar, babu inda ban duba ba, babu irin binciken da ban sa anyi ba amman an kasa ganin Noor” Inna ta kasa ce masa komai, ni da nake zaune nesa da ita na kalleshi cikin hawaye na ce “Ban san komai a akan batan Noor ba, idan kuma baka yarda da ni ba, zaka iya sakawa a kulleni kamar yadda ka yi ma Bilal” “Na rasa mahaifiyata Nawwara a lokacin da ban san miye duniya ba, ban sani ba ko zan iya jure rashin Noor” Haka kawai ya fada ya mike tsaye ya shafa kansa ya fice. Sai da ya fice sannan Inna ta ce “Miyasa baki fada masa gaskiya akan abokinsa ba? Mai yiyuwa shi ya sace Noor” “Idan kuma ba shi bane fa Inna? Sai mu dauki laifin mu dora masa? Mai yuyuwa yan satar mutane ne suka sace shi ko kuma yan garkuwa da mutane sai mu dauki laifin mu dora masa?” “Amman idan ba a bullowa wannan matsalar da wuri ba zata iya zama babba, kina da dalili da hujja mai karfi ta zargin wannan mutumen kuma shi kadai ya rage a yanzu wanda zamu iya zargi” Tabbas ni kaina zuciyata a yanzu Siraj take zargi, amman ina cikin kwankwanto saboda kar na yi zargi na jefa rayuwarsa cikin matsala daga karshe kuma ya zama ba shi din ne ba. Ina jin kewar da na sosai kullum mafarkinsa na ke yadda muke rayuwa da shi a cikin gidan yana ta min gizo a ido wani lokacin har ji na ke kamar yana kirana. JIBRIL POV. Daga gidansu Nawwara kai tsaye ya nufo gida har ya iso be daina hawaye ba, zuciyarsa kuna bata daina kuna ba, nan da nan ya fara tarin jini sai da ya saka tissue ya goge, babu wanda idanuwansa suke son gani kunnuwansa suke son jin muryarsa a yanzu irin Noor, daman tun kamin faruwar hakan jikinsa yake masa ba dadi ashe na rabuwa da dansa ba, rabuwansu na karshe ya tuno lokacin da yaje daukarsa yace Bilal zai fita da shi, rumgumar da ya yi masa ya dingajin kamar yanzu yake masa ita. “Ina kake Noor ina kake?” Ya tambaya yana buga sitarin motarsa yana kuka sosai kamar makaramin yaro. “Miyasa nake ta rasa abubuwan da suke da muhimmanci a rayuwata ne? Miyasa ne? Allah karka karbi rayuwar da na a yanzu da na fi bukatarsa Allah kada ba basu damar cutar da shi Allah ka kubutar min da dana” Kamar zai fadi haka ya fito daga motar yana kuka be damu da ma'aikatan gidan su ga kukansa ba shi dai matsalarsa da isheshi. A falo ya zauna yana ta misalta irin yadda Noor yake idan ya zo gidan, sai kuma ya dauko wayarsa ya bude gallery yana kallon hotunan Noor da kuma wanda suka yi tare. “Wa zai min haka a duniyar nan? Mina tarewa wani? Bilal mi na maka? Oh Allah” Ya mike tsaye yana share hawayensa, a dare kasa bachi yayi kamar dai ko wane dare yana ta aikin sallah da rokon Allah ya fito masa da dansa, kudi mai yawa ya diba ya bawa Malamin nan mai koya masa karatu akan yasa a yi masa addu'a Allah ya bayyana masa dansa. Yana zaune yana shan ruwan tea kamar kullum domin tun da abun ya faru baya cin komai sai ruwan tea maganinsa ma ya daina sha. Sai ga Kiran Abbah ya shigo wayarsa cikin yanayin damuwa ya daga. “Assalamu Alaikum” “Wa'alaikassalam Jibril ka zo gida yanzu nan ina jiranka” “Okay” Yana kashe wayar ya mike tsaye ya shiga bedroom ya canja kayan jikinsa daga jallabiya zuwa kananan kaya, a gaggauce ya fito saboda yasan yau Abbah zai bar sokoto yasan dalilin kiransa ba zai wuce ya fada masa Maganganun hakuri ba. Ko da ya isa Abdullah fodio road ya tararda Abbah tare da wani bako, bayan sun gaisa sai Abbah ya gabatar masa da shi. “Ga Dsp Sani Muazu nan na fada masa komai akan case din Noor, abunda yasa na ce kasa a saki Bilal saboda a bullo masa ta wata hanyar, tun da har ya kwashe kwana uku a station da duk irin wahalar da ake bashi be fadi gaskiya ba zai taba fada ta hanyar tsiya ba, so wannan dsp ya san yadda xai bibiyi Bilal har a gano gaskiyar lamarin” “Thank you Abbah” Abbah ya dafashi. “Ka kwantar da hankalinka Jibril Noor dinka yana nan lafiya kalau, kuma za a gano shi da yarda Allah duk wani bayani sai kanyi masa ni yanzu zan wuce” Sai da Abbah ya koma ciki yayi yan mintuna sannan ya fito Jibril ya raka shi har gurin mota suka yi sallama dan baya jin xai iya binsa har airport, bayan Abbah ya wuce ne Jibril ya dawo ya cigaba da yi ma Dsp bayani akan abunda ya sani a game da Bilal sai Dsp ya nemi hoton Bilal da addirensa da komai nasa. Suna haka wayar Jibril ta yi ringing yana dubawa ya ga Number Siraj cikin sauri ya dauko a tunaninsa ko zai sanar da shi wani abun ne, domin shi ma ya damu sosai akan batan Noor duk wani shiga da fita da ake tare da shi ake yinsa. “Hello Siraj” “Jibril kana ina ne?” “Ina nan Abdullah Fodio Road lafiya?” “Nawwara ce ta kirani a waya tana kuka tana min magiya wai na fada mata inda danta yake” “What? Ita da kanta?” “Yes ita ce ni abun ya bani mamaki ne” “Kana ina ne? ” “Ina gida” “Bari naje na sameta” Yana kashe wayar ya mike tsaye yana kallon Dsp “Taso muje can inda zamu samu hotonshi” Tare suka fito sai Dsp ya shiga motar Jibril suka nufo gidansu Nawwara. Sai da ya tsaya nesa da gidansu Bilal ya nunawa dsp gidan sannan ya karaso kofar gidansu Nawwara, kiranta ya yi ya sanar mata yana kofar gida yana son magana da ita sai ta ce ya shigo ciki. Ko da ya shigo ya sameta tsakar gida tana aikin kuka duk ta rame ta yi baki sosai kamar ba ita ba, sai da ya gaisa da Inna sannan ya zauna saman tabarmar da Inna ta shinfida masa yana kallon Nawwara har cikin ransa yake jin kukanta. “Ki yi hakuri Nawwara dan Allah ki daina kukan nan kina tada min da hankali” “Jibril Siraj ne ya sace Noor” Ta fada cikin kuka. “What?” Ya kalli Inna sai kuma ya maida dubansa gurin Nawwara a tunaninsa bakinciki ne yake son taba ta. “Listen Nawwara...” “Wallahi ba karya na ke ba, shi ya kade Noor kuma yana cikin plan dinsa kashe Noor da ni da kuma kai” “Okay na ji shikenan zan masa magana” “Ba hauka na ke ba Jibril ka tambayi Rabi ka ji ita ta fada min komai, shiyasa na koma aiki tare da kai nasa ka karbe kamfanin daga hannunsa ya dawo hannunsa shine yake kiran Abbah ya fada masa komai saboda ya lalata maka rayuwa yasa ka fara shan cocaine, kuma shi ya kade Noor da mota lokacin da suka taso makaranta, Noor ya ganshi shiyasa ya ki yarda su yi ido hudu da Noor saboda karya nuna shi” “No Nawwara Bilal ne ya kade Noor” “Ba shi ya kade ba, lokacin da Noor ya yi hadari Bilal yana kamfaninka yana aiki, shine duk ya tsara wannan Jibril ka karda da ni, Rabi ce ta fada min komai idan bata fada min ba babu yadda za ayi na sani” Wayarsa ya dauko ya kira Rabi tana dauka ya ce. “Duk inda kike ki zo ki same ni yanzu nan gidansu Nawwara” Be tsaya jiran abunda zata ce ba ya kashe wayar ya kira Siraj. “Siraj ka zo nan gidansu Nawwara gani nan na iso” Nan ma kashe wayar yayi sannan ya kalli Nawwara. “Siraj ba zai min haka ba, babu dalilin da zai sa Siraj ya sace Noor” “Wallahi da gaske nake Siraj ne ya sace shi” Siraj ya riga Rabi isowa duk da kasancewar ta fishi kusa da unguwarsu Nawwara, bayan ya shigo cikin gidan ne sannan Rabi ta iso, Nawwara na ganinsu ta mike tsaye tana hawaye “Rabi fada masa gaskiya fada masa abunda kika fada min akan Siraj” Rabi ta nuna kanta. “Ni Kuma? Mina fada miki ne?” Nawwara ta girgiza kai. “Karki min haka dan Allah ki fadi gaskiya” “Gaskiyar me zan fada? Ni ban san komai akai ba” Inna ta matso kusa tana kallon Rabi da mamaki ta ce “Yar nan ki ji tsoron Allah ki fada gaskiya, ke fa kika sami Nawwara a cikin gidan a nan kika fada mata cewar Siraj so yake ya kashe Jibril da ita kuma shi ya kade Noor” “Haba Inna da girmanki be kamata ki yi wannan maganar ba, bata dace da ke ba, ni gaskiya ban san komai a kai ba” Jibril ya kalleta “Look Rabi ki fada mana gaskiya” “Sir Jibril ban san komai a kai ba, idan ma wani abun ne ai kai zan sama na fadawa gaskiya ba Nawwara ba” Faduwa Nawwara ta yi kasa tana kuka da tureturen kasa kamar mai aljanu, hakan yasa Jibril zargin tana kokarin fita hayyacinta ne. Sai ya kalli Siraj “Siraj yi hakuri dan Allah ka je gida yanzu zamu kaita asibiti Rabi ku wuce kawai” Siraj da tuni gumi ya gama keto masa ya juyo a firgice ya fice, sannan Rabi ita ta fice hankalinta sam baya jikinta. Sai Dsp nan ya kira Jibril gefe yana tambayarshi alakar da shi tsakaninsa da Siraj, Jibril be boye masa komai ba ya fada nasa sannan Dsp ya bi bayan Rabi. NAWWARA POV. Ba zan iya cewa ga halin da na ke ciki ba, ni dai nasan bayan abunda ya faru a gidanmu Inna da Jibril sun kawo ni asibiti shi ma sama sama nake gani kamin Jibril din ya shigo ya yi min allura, sai yanzu da na farko sai na ke ganin komai kamar a mafarki hudun da na hango a window ne ya tabbatar min da cewar dare ya yi domin ko da abun ya faru da safe ne misalin tara zuwa goma. Tashi na yi zaune sai naga drip a hannuna, tunawa da Noor yasa idanuwa cika da kwalla, dakin babu kowa sai kayan tea da dan karamin freezer, ina haka Jibril ya turo kofar dakin ya shigo. “Sannu” Ya fada yana cire min drip din a hannu. “Ka yarda da ni Jibril Wallahi Siraj ne” “Na yarda Nawwara” Ya fada sannan ya cire safar hannunsa ya shi ya shiga hada min tea. Wayarsa ce ta yi ringing sai ya aje hada tea da yake ya yi picking. “Eh miya faru? Da gaske? Okay gani nan zuwa” Haka kawai na ji ya fada sai ya juyo ya kalleni. “Anga Noor police sun tafi da shi asibitin Uduth za a duba shi” Da sauri na sauka saman hospital bed din hankalina a tashe. “Jibril zan je” Tare muka fita, a waje muka hadu da Inna sai duk muka dugunduma gaba daya muka nufi Uduth din dake gawon nama. Kamin a isa har jin na yi kamar na runtse idona na ganni gaban asibitin. Muna isa parking space din na asibitin na bude na fito da sauri ni da Inna sai dai duk da haka jibril ya rigamu isa Emergency din kasancewarsa Namiji kuma ya hada da gudu, muna isa muka tararda Dsp din nan na dazu tare da wasu yan sanda sanye da uniform. Muna isa sai ya tare mu wai Jibril kawai zai shiga ya ga Noor ba tare da ni ba. “Kamar ya ni ce mahaifiyarsa fa” “Na sani amman shi zai shiga” Zan kara magana Inna ta rike ni ta ce ta Jibril din ya shiga, sannan ta shiga kiran yan'uwa tana sanar musu a waya. Jibril ne ya fara shiga ni da Inna muka tsaya ina ta jin kamar na yi tsalle na shiga na gani. Muna haka Jibril ya fito a daya daga dakunan dake Emergency din fuskarsa da hawaye, kamin ya karaso kusa da mu ya zame kasa ya fadi yana kokarin rike wata kofa dayan hannunsa na danne da zuciyarsa. [11/11, 10:56 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣4⃣ JIBRIL POV. Wani irin nauyi zuciyarsa ta yi masa har ta kai kafafunsa ba sa iya daukarshi, yadda ya ga Noor yana ta masa yawo a idanuwa, but Nawwara da ya hango ta fadi zaune tana hawaye, sai tausayinta ya lullube masa zuciya, a kokorin mikewa ya yi tsaye ya tunkareta yana kokarin buye damuwarsa. “Ya mutu ko?” Ta tambaya cikin rawar muryar da kuka ya dakishe mata ita. “No lafiyarsa kalau” Ya fada yana kokarin tare hawayen da suke son zubo masa. Daukar Numfashi Nawwara ta fara yi idanuwansa na kokarin rufewa kamar wacce za a cirewa zuciya. Inna kuma ta dora hannu saman kai ta fashe da kuka tana rika Nawwara. “Help us please” Jibril ya fada yana karasawa kusa da ita, hankalinsa a tashe dan shi a yanzu ba nata yake ji ba na Nawwara yake ji, sai wasu Nurses suka zo da gudu suka rikata suka dauketa suka dorata saman gado suka nufi wani bangare da ita, shi kuma ya juyo ya dawo dakin da Noor yake kwance kamar gawa likita biyu ya tarar a gurin sai Nurse daya da ta mika masa wasu takardu Jibril ya saka hannu sannan suka dauki Noor din suka fita da shi zuwa dakin tiyata. Jinginawa Jibril ya yi da kofar gurin ya lumshe ido hawaye suka zubo masa, zuciyarsa na ta raya masa kamar Noor ba zai rayu ba, an yanka masa ciki da wuka har hanjinsa sun bayyana ga gefen fuskarsa ma ya kumbura. Sai da ya share hawayensa sannan fito daga dakin ya nufo gurin da Dsp din yake wani irin bakinciki da bacin rai na fisgarsa. “Dsp taya haka ya faru? Na fada maka idan har kun gano inda yaron nan yake ku fada kamin ku yi komai” Dsp be ce masa komai ba sai da suka fito daga Emergency din sannan ya kalleshi ya ce “Aikinmu muke yi Jibril da ace na tsaya kiranka da wata kila yaron nan be rayu ba, domin a can cikin daji muka dauko shi, can cikin arkilla tanki can cikin dajin nan dake saman dutse” “Ina Siraj din yake?” Ya tambaya yana sauke ajiyar zuciya. “Yana can station nasa a tsare shi, karka damu da wannan” “Rabi fa?” “Am sorry jami'an mu gawarta kawai suka samu” “How” Ya tambaya a rude. “We don't know yet but idan komai ya laba zamu bincika” Kansa ya daga sama ya kalli taurari zuciyarsa na mugun quna. “Siraj...” Sai yasa yatsansa ya share hawayen da ke gefen idonsa. Juyowa ya yi ya dawo ciki, tafiya yake amman ji yake kamar ba taka kasa yake ba, numfashinsa ba ji yake kamar ba a jikinsa yake ba, yana karasowa kofar Emergency Inna na isowa cikin tashin hankali. “Noor ya mutu ko?” Dsp ne ya shiga mata bayani Jibril kuma ya doshi dakin tiyata yana safa da marwa, gabansa sai faduwa yake. Awarsu biyu a dakin tiyatar sannan suka fito da Noor unconscious, da sauri Jibril rika gadon da Noor yake ya kai hannunsa ya taba gefen wuyansa sannan ya sauke ajiyar zuciya. Daya daga cikin likitan biyu da suka masa tiyata ya san Jibril farin sani saboda sun yi aiki a tare asibitin Abuja, shi ya dafa Jibril ya ce “Ka kwantar da hankalinka, tiyata ta yi kyau sai dai ka masa fatar samun sauki” Kai kawai Jibril ya iya dagawa ya saki gado ya rike ginin gurinsa saboda mugun ciwo da zuciyarsa take, daker ya mike tsaye daidai ya bi bayan Nurses din har suka isa icu suka canjawa Noor gado saka dora masa oxygen sensor sannan suka masa wata allura a hannu mai hade da drip, sannan likitan ya dauko wani abu mai guda biyu mai kamar iron ya hada shi ya goga sannan ya kurga 1 2 3 ya danna gaban Noor dai dai zuciyarsa. Sai ga Noor ya numfasa da mugun karfi sai kuma ya lumshe, numfashinsa ya shiga nunawa a sensors. “Al-hamdulillah” Shine abunda Likitan ya fada da duka Nurses din kasancewarsu musulmai. Wani irin lumshe ido Jibril ya yi ya bude bakinsa kunshe da godiyar Allah. NAWWARA POV. ban san iya awa nawa na yi a sume ba ni dai na farka na ganni saman gado oxygen na sanye a fuskarta, abunda ya faru ne ya soma dawo min zuciyata na ta nuna min cewar da na ya mutu. Ban san akwai mutum a kusa da ni ba har sai da na fara hawaye. “Am sorry Nawwara Noor yana nan raye an masa tiyata kuma an yi nasara” Kallo daya na yi masa na kawarda fuskata, sai na rika kokarin sauka saman gadon. “Babu inda zaki iya zuwa a yanzu karfe uku na dare ne, kuma babu wani karfi a jikinki a yanzu, Inna tana tare da Noor ni ma bata san ina nan ba, Sakina aka sa ta kwana da ke tana waje” “Ya mutu ko?” Na tambaya ina kuka duk da nasan amsar ba zata min dadi ba amman ina da bukatar jinta, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce. “Be mutu ba” “Dan Allah karka boye min Jibril ka fada min gaskiya” “Zan raka ki yanzu ki ganshi” Saukowa na yi daga kan gadon duk da babu kwarar kuzari a jikina, sai dai na samu gwarin guiwar tafiya ne saboda jin cewar zan ga Noor ne hakan ya tabbatar min da cewar basu kashe shi ba kenan. Hankalina ya tashi sosai lokacin da na ga halin da Noor yake cikin, duk kokarin da Inna da Mama Turai suka yi na hana ni kuka hakan be yi tasiri ba sai da kuka sosai kamar Noor din ya mutu ne. “Ina aka ganshi? Waya masa haka?” Na tambaya ina kallon Jibril a zuciyata kuma ina jin cewar zan iya daukar ma dana fansa a kan duk wanda ya yi masa wannan abun. Be bani amsa ba sai ya juya ya fita ni kuma na bishi duk da babu wani kuzari a jikina Inna ta biyoni tana kirana sai ya juyo ya daga mata hannu alamar ta bari hakan yasa ta juya ta koma. Haka na cigaba da binsa har muka koma dakin da aka kwantar da ni wanda ya kasance babu kowa a dakin sai ni da shi. “Siraj ne” Ya fada ba tare da ya kalleni ba. “Amman da na fada maka karyata ni ka yi, da ace ka dauki mataki tun a lokacin da haka be faru da Noor ba, amman sai ka maida ni mahaukaciya” Kallona ya yi da idanuwansa da suka rine suka yi ja sosai saboda kuka da kuma bacin rai ya ce “Kin riga kin kira Siraj kin tuhume sa, ni kuma na kirashi tare da Rabi ne saboda na tabbatar da abunda kike fada, da ace na sa ana rike Siraj a lokacin nan da har yanzu Noor be bayyana ba, da ganga na kai shi asibiti saboda ya yarda cewar haukace take son kama ki, amman ban boyewa Dsp komai ba a game da Siraj, hakan yasa ya bi bayan Rabi saboda ni da shi duka mun lura da yanayinta, da ace ban turki Rabi a wannan lokacin ba da ba zata taba fadin gaskiya kamar yadda ta yi a yanzu ba, ashe all this while Rabi ta san inda Noor yake amman ta kasa fada saboda tana tsoron abunda zai biyo baya, Siraj ya bata yarda shiyasa ya fada mata inda ya aje Noor, and Nawwara na san idan har Rabi bata fada miki ba babu yadda za ayi ki san wani abu daya shafi kanfanina ko kuma rayuwata kuma na san idan har bata fada ba babu yadda za ayi Inna ta goya miki baya, i do believe you sai dai babu yadda za ayi na nuna hakan a gaban mutumen da na daukeshi kamar dan'uwa, Rabi da kanta ta fadawa Dsp inda Noor yake a lokacin da komai ya kure saboda isha'i ta yi a lokacin kuma ta fadawa police cewar rayuwarta tana cikin hatsari, but ko da suka je sun yi latti an riga an kasheta, Noor kuma suka same shi a cikin gidan da ta fada musu an yanka masa ciki” Hannu nasa na rufe bakina saboda kukan da ke son ya ci karfina, sai na rika gadon na zauna ina kuka a hankali. “Komai ya faru saboda ni Nawwara” Ya fada yana hawaye tare da danne kukan da ke son kubuce masa. “Rabi ta rasa ranta saboda ni, an yanka cikin Noor saboda ni, kin sake shiga tashin hankali saboda ni, da ace ban dawo rayuwarki a karo na biyu ba da duk haka be faru da ke ba, kina da gaskiya Nawwara, kina da dalilai na ki na, a duk lokacin da na kusance ki sai wani abu marar kyau ya faru da ke, ni ne silar lalacewar rayuwarki a karon farko, na dawo a yanzu da tunanin zan iya gyarata na saka miki farinciki saina sake bakanta miki wanda ba hakan raina ke so ba, but komai ya kare yanzu. Na miki alkwari daga ranar da Noor ya ji sauki ya tashi, ba zaki sake sani a idanuwanki ba, balle na dame ki ba zaki sake kuka da ni ba, kowa ma ba zai sake kuka da Jibril ba, zan tafi wata duniyar wacce babu wanda na sani kuma babu wanda ya san sai na yi rayuwa a can har ta Allah ta kasance, saboda ciwon da ke jikina yana tabbatar min da cewar mutuwata tana kusa da ni a yadda na ke ji a zuciyata na san ko da wane irin lokaci zata iya bugawa na mutu, ina tsoron sake kusantarku ke da Noor wai Nawwara saboda kar wani abun ya same ku... Ki yi hakuri da duk abunda ya faru, but no matter what Nawwara har gobe ina son ki, ko da na mutu a yau na mutu da ciwon son ki ina son ki san wannan, ina son zuciyarki ta gansu cewar ni masoyinki ne ba makiyinki ba” Yana fadar hakan ya juya ya fice be damu da ya share hawayen da suka bata masa fuska ba, ni kuma na bishi da kallo zuciyata cike da tausayinsa da na kaina da kuma na Rabi da Noor... [11/13, 6:25 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣5⃣ JIBRIL POV. Haka ya fito harabar asibitin hawaye na bin fuskarsa, babu komai a zuciyarsa na sai tausayin dan sa, kansa kuma empty har ya rasa da ina zai fara tunani akan Siraj. Be damu da tsakar dare ba ne ya shiga motar ya kamo hanyar sama road. A bakin gate dinsa ya tsaya cikin mota ya kira mai gadinsa a waya ya zo ya bude masa gate sannan ya shiga ciki ya faka motarsa ya fito jikinsa babu gwari ya shiga falonsa, saman sofa ya jefar da makulin motarsa ya shiga bedroom ya cire kayan jikinsa sannan ya daura tawul ya shiga bathroom.   Gaban madubin da ke bandakin yaje ya tsaya ya kallon still hawaye ba su daina masa zuba ba. “Why Siraj mi na maka?” Ya tambaya kana ya fashe da kuka sosai ya fadi kasa zaune ya dafe kansa. Kuka ya yi sosai mai sauti kamar mace sannan ya tashi ya nufi shower ya sakarwa kansa ruwa, ya lumshe ido yana ra sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai kusan hudu da rabi na asuba ya fito daga bathroom din shi ma dan wayarsa dake ta ringing ne. Gaban madubi ya karasa inda wayarsa take ya dauka ya duba, number Abbah ce yana ta kiransa cikin hanzari ya yi picking. “Assalamu Alaikum Abbah” “Jibril kana lafiya?” “Lafiya kalau” “Am sorry na kiraka da dare, na damu ne kawai and Jibril ka yi hakuri da yadda rayuwa ta zo maka dan Allah, dsp ya yi min bayanin komai nasan kana cikin tashin hankali dazu shiyasa ban kiraka ba, gobe muna nan zuwa tare da yan'uwan Rabi ka kwantarda hankalinka ka ji” Sai kawai ya fashewa Abbah da kuka. “Ba ni da wani sauran kwanciyar hankali Abbah, na rasa komai kuma saboda ni komai ya faru Abbah ni ne silar komai” “Aa Jibril ba kaine ba, haka Allah ya tsara babu yadda za'a yi ka tsalleke karka sa komai a rana ka” “Toh Abbah thank you” Ya fada yana share hawayen idonsa, sannan ya aje wayar ya kalli kansa a madubi. “Al-hamdulillah Allah na gode maka, komai ka yi daidai ne, Allah kai ka tsara min haka a rayuwata ban isa na tsalleke ba, Allah ka bani hakuri dauka abunda duk ka rubuto zai faru da ni, ka yafe min abunda na maka Allah, ka karbi rayuwata ina mai shauki da murnar haduwa da kai, Allah karka karbi raina ina mai bakinciki da damuwa kusantar ka” Yana gama fadar hakan yaji wani irin rahama da natsuwa sun sauko masa a zuciya. Komawa ya yi bathroom din ya yi alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya yi nafila sannan ya tsaya jiran assalati ya dora da asuba, bayan ya gama ya zauna ya yi azkar na safiya tare da istigifari da salatin Annabi, sannan ya karanta abunda ya sauwaka a qur'ane sannan ya tashi ya nufi freezer ya dauki ruwa mai sanyi ya sha. Sannan ya dawo ya shiga bathroom ya yi wanka yana fitowa ya shirya cikin farar shadda ya dauki hanyar station. Ya yi rashin sa a ko da ya isa ya tarar ya an wuce da shi gidan yari kai tsaye ba a station aka aje ba, a nan ya kira Dsp ya bashi hakuri akan ya yi hakuri har zuwa anjima idan Abbah ya zo. A dole ya hakuri ya koma cikin motarsa ya dauki hanyar asibitin Uduth.    Hasbiyallahu yake ta karantawa cikin mota saboda ya samu salama a zuciyarsa, a izuwa yanzu ya fawwalawa Allah komai. Yana faka motarsa ya fito ya nufi cikin asibitin, dakin da Noor yake ya nufa mai tsaron gurin ya bashi damar shiga ne saboda ya nuna masa shaidarsa ta likita mai zaman kansa. Nawwara kawai ya samu a ciki tana zaune saman carpet tana tilawar a qur'ane da kai, ta yi matukar burgeshi hakan sai ya kara masa sonta da sha'awar zama da ita amman ya san babu wannan damar domin a yanzu ya riga ya tabbatar da cewar Nawwara ta masa nisa. “Assalamu Alaikum” Ya yi sallamar yana duka kofar sai ya tsaya a bakin kofar yana jiran izinin shiga. Juyowa ta yi ta kalleshi idanuwanta sun yi fari sosai fuskarta ta kode kamar ba ita ba, wani irin tausayinta ne ya kamashi har sai da ya yi daukerwa wutar seconds biyar sannan ya numfasa. “Wa'alaikassalam shigo mana” Sai ya maida kofar ya rufe sannan ya karaso ciki yana duba dansa. “Ya jikinsa?” “Likita ya ce da sauki ta duba shi, amman dai har yanzu be farka ba” “Zai farka ki kwantar da hankalinki kinji?” Ta gyada masa kai. “Ya naki jikin” “Na ji sauki” “Ina Inna?” “Taje gida” “Ke kadai aka bari” “Kasan asibitin ba a bari mutune su shiga sai 4pm” Ya dan yi shiru yana kallon ta ita kuma tana kallon Noor. “Abbah zai zo anjima tare da yan uwan Rabi” Can kasa kasa ya sinkayo muryar Nawwara ta na cewa. “Laifina ne, ni sakarya ce wani lokacin, na kan dora wani abu da ba muhallinsa a wani muhallin, da a ce ban yi wannan maganar ba da Rabi tana nan raye” “No no no karki zargi kanki Nawwara, daman can haka Allah ya tsara, ba laifinki ba ne laifina ne, kuma shi Siraj din yana gidan yari yanzu haka yan sanda sun cika masa file sun turashi, kuma za a yanke masa hukuncin abunda ya aikata” Kokarin kwantar mata da hankali yake, domin a yanzu tausayinta yake baya son abunda zai daga mata hankali ko kadan baya son damuwar Nawwara a yanzu, gani yake ta sha wahalar rayuwa a yanzu be kamata ace ta sake shiga wani halin ba. Sun dauki lokaci a haka yana ta lallabata yana ta kokarin kwantar mata da hankali, daga baya ya dauki wayarsa ya kira Candy Restaurant ya yi order abinci da za a kawo su Nawwara. Sai sha daya da kwata ya bar asibitin a lokacin Inna ta dawo sai suka gaisa da ita sannan ya fito tare da Nawwara suka shiga mota saboda zuwa gurin Siraj, tun da suka shiga motar Nawwara bata kalli inda Jibril yake ba, shi kuma ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta har suka isa.   Abbah kawai suka tarar sai step mother din Jibril da kuma babban yayansa da wani abokin Abbah, da dsp. Abbah ya damu sosai da ganin yadda Jibril ya koma ya rame sosai ya yi wani fari kamar marar jini.   Tare suka shiga da Nawwara da Jibril sannan dan gandireba ya fito musu da Siraj anyi handcuffed dinsa. Da dingishi ya fito wani gurin a kansa har jini ya bushe masa, har ya zauna be daga kai ya kalli Jibril ba, Dukaninsu babu wanda ya zauna, Jibril ya matsowa kusa da shi sai Dsp din ya shiga tsakani. “Ba sai ka taba shi, ai hukunci za a yanke masa dai dai da abunda ya aikata, abun jindadi ma ya amsa laifinsa da kansa, kuma mutane da muka kama a gidan da aka aje Noor sun fadi cewar shi ya saka su kuma be karyata ba” “Ba komai zan masa ba tambayarsa kawai zan yi” Jibril ya fada yana jin kamar ya kama wuyan Siraj ya shake. “Mina hana maka Siraj? Mina maka ka aikata min haka? Me ka nema na hanaka? Mi Rabi ta maka? Me Noor ya maka?” Ya dago kansa da idanuwansa da suka kumbure saboda duka, har baya iya gani da idon sosai gaba daya an canja masa kamani kamar ba shi ba. “Baka min komai ba Jibril sai alheri, ni kaina ina jin rashin kyautawa a abunda na aikata, sai dai babu yadda zan yi saboda zuciya ta dibeni tun farko, abun da na ke ta kokarinyi da gani na fika Jibril, saboda ina bakincikin ace ni ne a karkashinka ba kai ne a karkashina ba, irin rufin asirin da Allah ya baka na so na samu da karfi sai ya gagara, na sa an kashe Rabi ne saboda ta tona min asiri ta ci amanata kuma na san nima kasheni za ayi, a a yayinda ita kuma za a yafe mata kuma za a yaba mata, Noor ya ganni lokacin da na yi kokarin kasheshi shiyasa na sace shi nasa a kashe shi saboda kar wata rana ya fadi sai gashi Rabi ta lalata komai” “Hassadace ta cuce ka Siraj ka ci amanar kanka kuma daman hassada ga mai rabo taki ce, mun dauki amana mun baka sai ka cuce mu Allah ya waddaranka Siraj” Cewar Abbah cike da bacin rai. Jibril ya matso kusa da shi ya chakumi wuyansa ya matse game yana kokarin aikashi lahira, daker aka kwaci Siraj a hannun Jibril har aka wuce da shi Nawwara kawai yake harara idonshi na kanta. “Ka kwantar da hankalinka Jibril kotu za ta yi komai, litanin din nan muke son fara zaman kotu alkali zai yanke masa hukuncin ai” Cewar Dsp yana rike da Jibril ta dake ta faman huci. Daga gidan maza station suka wuce saboda wasu statement din Nawwara da za a dauka. Sun yi awa daya a gurin sannan suka baro gurin tare da tawagar yan sanda zuwa rinjin sambo gidan wani dan'uwan Rabi da take zaune a gidansa. Ko da suka je sun tararda jama'a anyi dandazo a gurin duk kuwa da kasancewar an rufe gidan gaba daya kuma sun bar police uku da zasu yi gadin gurin. Suna isa police din suka bude musu gidan, Nawwara ce a baya tare da Jibril, ya yinda Dsp yake can gaba tare da su Abbah da kuma wasu police din. “Are you sure zaki iya kallon gawar Rabi? Ance fa dadsatsata suka yi” Tsayawa ta yi cak sai ya kalleshi. “Idan kin san zai daga miki karki kalla” Sai kawai ta fashe da kuka. “Duk laifina ne” “Ba laifinki ba ne, haka Allah ya tsara” Kamin ta kara cewa wani abu sai ga wayarta tana ringing, Baba Sulaiman ya kira ya ji inda suke ya zo, da kanta ta tsaya tana masa kwatanci sai Jibril ya shiga ciki ya bar nan waje tsaye. Shi kansa da yaga gawar Rabi sai da hankalinsa ya tashi domin datsata aka yi aka mata guntu-guntu ko ina ya bace da jini, suna cikin gurin su Baba Sulaiman da wasu kanenn mahaifin Nawwara suka iso, isowarsu ta yi daidai da isowar yan uwan Rabi kana kallonsu zaka gane ba hausawa ba ne dukansu yanayin shigarsu da kuma tsagen da ke fuskarsu, da kuka suka shiga cikin gidan maza uku mata biyu a nan suka yi ta ihu har da mai faduwa tana tashi tana buga kasa. Daker suka tsagaita kuka har aka dauko gawarta aka fito da ita zuwa motar police. NAWWARA POV. Ana fitowa da gawarta hankalina ya tashi sosai lallai mai rai ba komai ba ne, duk kyau rabi da far'arta sun tafi kenan, a gurin na raina kaina saboda ina ganin kamar sakacina ne yasa hakan ta faru, amman Jibril ya yi kokarin dorawa kansa laifin ko kuma ya ce min haka Allah ya tsara zai faru, mahaifin Jibril ne yaso a tsaya a yi mata jina'iza a nan amman yan uwanta suka ki, a dole tasa ya hakura ya bawa police kudin mai dan su rakasu har can kogi inda iyayenta suke, a ranar yan uwanta suka juya suka koma a mota tare da gawarta da kuma rakiyar yan sanda. Mahaifin Jibril kuma muka dawo asibiti tare da shi ya duba Noor ya yi masa addu'a tare da step mother dinsa, sannan ya yi mana bankwana akan cewar zai koma abuja a yau gobe tun da safe zai hau wani jirgin yaje kogi saboda ayi jana'iza a tare da shi, sosai ya so Jibril ya bishi amman Jibril ya ki wai sai yaga idon dansa, Abbah ya sashi gaba yana ta masa nasiha sosai akan rayuwa da kuma abubuwan da suka faru. Da yamma lis Abbah ya yi mana sallama ya bar asibitin kasancewar an kira an fada masa jirginsa ya kusa tashi. Mutane na ta zuwa ganin Noor makota da kuma yan'uwa da abokan arziki ciki har da wasu familyn Jibril da suke garin nan da kuma abokansa. Gurare takwas da rabi na dare Jibril ya bar asibitin saboda kiranshi da aka yi, ko minti goma ba ayi ba sai ga Jidda ta shigo tare da Mustapha i was very surprised dana gansu tare saboda ni na ma dauka Mustapha baya kasar nan dan tun lokacin da nayi magana da shi ban sake hada hanya da shi ba, hankalin Jidda ya tashi sosai har da kukanta Mustapha kan yana tsaye kan Noor yana masa kallon da ban san na minene ba. “Ya aka yi aka barku kuka shigo?” Na tambaya bayan Jidda ta zauna har yana kokarin bude abincin da ta zo da shi. Sai Mustapha ya kanne min ido daya yana murmushi “Cin hanci na bayar” Na sauke kaina kasa, sai ya yi yar dariya kadan ya ce. “Allah ya kara sauki ya tsare gaba, kai gaskiya an yi arziki da mun rasa yaro mai kyau, ni da nake son na hada surukuta da ke, dan gaskiya idan na haifi ya mace sai ta auri Noor ko kuma da na ya auri yarki” Ya fada yana dariya kamar babu abunda ya dame shi, ni dai bance masa komai ba, Jidda kuma ta kasa daga kai ta kalleni duk tabi ta tsargu. “Ba ganin danki kawai na zo ba Nawwara, na zo na fada miki cewar na samu matar da na ke so” Sai Jidda ta yi saurin kallonshi. “Haba Mustapha wannan wane irin magana ne, baka ga halin da take ciki ba? Ko ma minene ai ni ya kamata na fada mata” “Na ga kamar ba zaka iya fada mata ba ne, shiyasa ni na zabi fada mata da kaina” “Amman dai ba a yanzu ya dace ka yi wannan maganar ba” “Fine ba zan kara ba” Ya fada yana daga hannunsa sama tare da yin murmushi. Ina tunanin Mustapha ya yi min haka ne saboda bakinciki ya yi min yawa a tunaninsa zan ji zafi idan ya ce ya samu wacce yake so duk da nasan ba zata wuce Jidda ba domin alamu sun nuna hakan, ko rantsuwa na yi bana kaffara Mustapha ya so Jidda ne kuma zai aureta ne saboda na ji bakinciki tun da aminiyata ce, kuma yana son bakinciki da nake ciki na rashin lafiyar Noor ya karu akan kishi ne saboda na ki shi, ni kuma na kasa damuwa saboda daman can bana son shi kuma ina ganin sonshi a idanuwan Jidda dan haka sun fi dacewa da juna duk kuwa da kasancesar ta kasa fada min ne saboda karna zargeta ko kuma na yi tunanin wani abu. Basu wani dade sosai ba Mustapha yasa hannunsa aljihu ya dauko kudi mai dan dama ya aje mana saman gado tare da yi mana addu'ar Allah kara lafiya, sannan ya yi gaba sai na kamo hannun Jidda ya riketa har sai da ya wuce sannan na kalleta na ce “Amintakarmu ta fi karfi mu boyewa juna abu” “Nawwara ban yi nufin boye miki ba, kawai ban san yadda zaki kalli abun ba ne” “Ta fuska mai kyau zan kalleshi Jidda, na san ke aminiyata ce kuma ba zaki taba cin amanata ba, Wallahi ko da Mustapha be furta da kansa yana sonki ba zan hada soyayyarku saboda dacewar da kuka yi da juna, kuma ina ta tabbacin idan har ya aureki ba zai sake wata rayuwa marar kyau ba” “Ba a yanxurya kamata mu yi maganar nan ba Nawwara, ki kula da Noor please” Ta fada tana dafa kafadata sannan ta wuce. Ni kuma na dawo na zauna na saka Noor a gaba ina ta kallonsa zuciyata cike da tausayinsa. Misalin goma na dare Jibril ya dawo, yana shigowa dakin Noor na farkawa da kuka yana kiran sunana. “Momy Momy” “Gani nan” Na yi saurin kama hannunsa. “Momy sun yanka ni wasu sun ce zasu kashe ni” Sai Jibril ya yi saurin karasowa ya kama dayan hannunsa kuma ya shafa kansa. “Shiiiiiiiiiii you're safe kana kusa da Momy da Daddy babu wanda zai taba ka” “Daddy sun ce sai sun yanka ni sun yanka min ciki ma, kuma sun buga min kai” Sai kawai yasa dariya. “Ashe Noor dina ba jarumi ba ne, kadan fa suka yanka ka, kuma na sa police sun kama su” Matsawa ya yi sosai ya kwanta gefen Noor ya rumgumeshi ya matse hannunsa cikin nasa. “Allah ya baka lafiya ya raya min kai Noor kai kadai ka rage min sai Abbah na” Tashi na yi na fita wajen kiran likita saboda ya ce idan Noor ya farka a kirashi. _________________________________ Ku yi hakuri da wannan 🙏🙏🙏. [11/14, 4:00 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣6⃣ A GURGUJE.... Bana tunanin Bilal yana da wata hujja ko dalili na yin fushi da ni, duk kuwa da kasancesar Jibril ya sa an daureshi kuma an masa kai wulakanci da kasa guguwa a fuskar yan uwansu, amman idan har zai min adalci babu hannu a ciki balle kafata, sai dai shi ya kasa fahimtar hakan domin tun lokacin da abun ya faru zuwa yau be taba daga waya ya kirani ba, idan kuma na kirashi sai ya dinga min magana cikiciki kamar baya son magana da ni, sau uku Baba Sulaiman yana daukar mutane suna dubashi bayan sallamoshi daga asibiti, ni kan ban jeba domin Inna taje ba bata dawo da farin rai ba duk da bata fada min abunda suka mata ko suka ce mata ba, na fahimcin hakan ne a fuskarta da kuma yanayinta. Al-hamdulillah sauki yana ta zuwa ma Noor ta ko ina domin a farko ya firgita sosai har na dauka ko kwakwalwarsa ta tabu ne, sai dai kulawar da likitocin Uduth da kuma addu'o'in da muke sai komai ya daidaita, tiyatar da aka masa ma cikin sati biyu ya samu sauki su kansu sun yaba da irin kyau fatar Noor, yana samun kula sosai da sosai wani abun da Jibril yake masa har mamaki yake bani kamar zai dauke sa ya cinye, a dan zaman da muka yi na asibitin Noor har ya sagarce abu kadan zai fara kuka yana kiran Daddynsa. A zaman da mukayi asibiti sau biyu Jibril na aman jini a gabana abun har sai da ya bani tsoro domin na dauka zuciyarsa ko kuma hanjin cikinsa zai amayar gaba daya, sai dai shi sai ya nuna kamar be damu ba, da alama abun ya zame masa jiki. Ana gobe za a sallamemu daga asibiti muka yi zaman kotu na karshe akan case din Baba a ranar na sha mamaki ashe matar da ta lakawa babanmu sata yayar Siraj ce daamn ina ganin alamaun haka sai dai ban tabbatar da sai yau da aka yanke hukunci na karshe, saboda yan uwan Siraj da suka zo sune wadanda aka tsaya masa a lokacin da aka yi shigar kotu ta farko case dinsa. Hukunci kazafi alkalin ya yanke mata su kuma aka yanke musu hukuncin kisa bisa ga shaidu da hujjoji kwarara da aka gabatar gaban kotu. Na yi farincikin sosai da sosai a wannan ranar daga ni har Inna da duk wani mai son ganin na kwatowa Baba hakkinsa, na yaba ma dpo daya tsaya kai da fata wajen ganin ya bi mana kadin mu. Abunda ya faru abun mamaki ne kuma abun a yabawa masa ne domin ba ko wane dan sanda bane zai kashe mutum kuma an hukunta shi kamar yadda doka ta ce, a ranar na ji kamar na zuba ruwa kasa na sha saboda farinciki mutane na ta zuwa har gida suna mana murna. Washe garin ranar aka sallamo Noor daga asibiti, a abun mamaki sai ga Zinatu ta zo ganinsa wani sukuku da ita kamar ba ita ba, na yi mamakin ganin ta zo gida dubashi bayan bata taba zuwa asibiti ganinsa ba. Da fari jajanta mana ta farayi akan abunda ya faru sannan ta dora da bayaninta. “Na san zaki yi mamakin rashin zuwa ganin Noor asibiti ko? Wallahi Jibril ne ya hanani, saboda na kirashi ina jajanta masa abunda ya faru sai ya gargade akan karna yarda na kusanci dansa, saboda yana ganin akwai aminci da shakuwa sosai a tsakanina da Siraj wata kila yana zargin zan masa wani abun ne” “Ayyah kin san dole ne ya tsorata kuma ya yi taka tsantsan saboda abubuwan da suka faru” “Amman ai ba halina daya da Siraj ba, miyasa zai yi tunanin haka” “Ban da abinki Zinatu ai shi hali ba a fuska akae ganeshi ba, shi ma Siraj din ai bamu dauka cewar zai yi haka ba, ni kaina a yanxu ba kowa zan yarda da shi ba balle kuma shi” “Haka ne, ni kaina da be koremu daga kamfanin ba, na kudiri aniyar aje aikin domin ba zan iya aiki inda ake ɗari ɗari da ni ba” “Ya sa kun aje aikin ne?” “Eh kwana biyu da faruwar hakan duka ya canja ma'aikatan kamfanin, yanxu kuma yana nan yana daukar wasu” “Ayya abun be yi dadi ba sorry” “Ba komai Allah kara lafiya, amman gaskiya Siraj ya bata mana suna Allah ya isar mana” “Amin Amin shiyasa ake son ka yi taka tsantsan da mutanen duniya ai” Tayi min wani kallo sai kuma ta mike tsaye tare da daukar jakarta ta yi min sallama ta fice. Inna ta zo ta zauna kusa da ni tana fadin “Ki yi hankali da wannan ma domin kin san ba yarinyar arziki ba ce” “Na sani Inna amman Allah ya fita kuma shi zai tsare mu” “Haka ne” Firar Siraj muka bijiro da ita, a nan nake labarta Inna wasu abubuwa da bata sani a lokacin da ina aiki tare da shi, mun dade muna fira mutane kuma nata shigowa suna mana barka da dawowa ga Noor a tsakar gida yana da game da dayar wayar Jibril daya bar masa ya buga game kamin ya karba. Bayan sallah magariba Bilal ya kira ni i was very surprised da na ga kiransa domin rabon daya kirani har na manta, gabana ne ya shiga faduwa sosai sai kuma tsoro ya kamani kamar ba zan daga ba sai kuma na daure na dauka, na yi tunanin wata maganar zai fada min sai ya ce min gashi nan kofar gida na fito. Sai da na canja Hijab din da ke jikina sannan na sanar da Inna itama kanta ta yi mamaki, ni dai jikina a sanyaye na fito. Sai na same shi a daidai inda ya saba tsayuwa yana jingine da ginin gidanmu sanye da kananan kaya. “Assalamu Alaikum ” Sai ya dago ya kalleni, sai kuma ya yi murmushi. “Kin tsorata ko sarkin tsoro?” Na yi shiru ban ce masa komai ba, sai ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Ki yi hakuri da duka abubuwan da suka faru, na so naje ganin Noor asibiti sai dai ban samu dama ba, saboda Mama ta furta cewar bata yafe min ba idan na taka asibiti ganin Noor ke ko waya na kira na tambaya jikinsa bata yafe min ba, wannan dalilin ne ya hanani zuwa ganinsa” “Ba komai, Mama tana hujja ai nima kuma ban kyauta ba” “Babu abunda kika na rashin kyautawa, face fifita son Jibril akan nawa da kika yi” “Haba Bilal karka dauki zigar mutane mana duk wanda ya fada maka haka ya yi maka karya” “Ba fada min aka yi ba, gani na yi da idona” “Babu abunda ka gani Bilal kawai kana son ka yi amfani da wata damar ne ka ci min fuska” Sai ya gyara tsayuwarsa ya kalleni “Ki rantse min da Allah a yanzu nan babu son Jibril a zuciyarki!” Sakin baki na yi ina kallonsa sai idanuwa suka cika da hawaye, na kasa karyata kaina balle kuma na karyata shi, Allah yake son na rantse da shi taya zan yi rantsuwa akan abunda ba ni da tabbaci ni kaina a yanzu ba zan iya cewa akwai son Jibril a zuciya ko babu abu. “Kin gani? Kina son shi har gobe Nawwara, dan haka karki yaudari kanki, wannan dalili yasa na ke jin kamar ba zan iya aurenki ba saboda zuciyarki tana gurin Jibril ko da na aureki gangar jikinki kawai na aura” “Wannan ne kawai dalilin?” Na tambaya hawaye na bin fuskata. “Ba wannan ne kawai ba, mahaifiya bata son ki Nawwara kowa ma a gidanmu baya son ki sai ni, wani lokacin abunda iyaye basa so babu alheri a cikinsa, and ko na aureki ba zamu taba jindadin zaman aure ba abubuwa za su yi ta faruwa wadanda ba zasu mana dadi ba. Ban yarda Jibril ya fini son ki ba, amman na yarda son ki yafi yima Jibril illa sama da ni, Nawwara Jibril yana da ciwon zuciya wanda zata iya bugawa a kowa lokaci ta rasa ransa kuma ke kadaice maganin wannan ciwon nasa, na san zakiyi mamakin inda na ji ko? Na samu labarin ne ta hanyar abokan aikinmu da muka yi aiki a kamfaninsa tare, idan na aureki a yanzu na shiga tsakaninki da muradin zuciyarki kuma na shiga tsakanin Noor da Jibril na raba masa hankali gida biyu, Last two weeks da suka wuce Jibril ya kirani muka hadu a Shukura Hotel da shi, kin san abunda ya yi min? Gafarata ya nema akan abubuwan da suka faru kuma ya rokeni da na rike masa dansa amana kuma na tarbiyantar da shi, da za ayi gasar son ki Nawwara da ni zan zama gwani kuma zakara, amman a wannan lokacin sai da na raina kaina saboda tausayin Jibril da ya kamani, saboda ya canja Nawwara saboda ke mutumen da baya kallon kowa da kima amman har ya nemi ya yafe masa kuma na masa alkawarin ba zan bari komai ya samu dansa ba, har ma ya yi ikirarin mayarda ni aikina, but yanzu idan baki aureshi ba kin san irin halin da zai shiga? Wata kila rayuwarsa marar kyau zai koma yi, kuma Noor ma ba zai ji dadi ba domin a yanzu ya saba da mahaifinsa, ya kamata ace shi ma yasan dadin mahaifa kamar ko wane da, Dukan abunda Jibril ya yi miki abaya ya yi ne a cikin jahilci yanxu kuma ya dawo yana neman yafiyarki ya kamata ki yafe masa he deserved a second chance so that ya gyara duka laifin da kuskuren da ya yi, kuma shi ya fi cancanta da ya zauna da ke a yanzu saboda ya goge miki zargin da duniya take miki, kuma zaki samu ingattaciyar rayuwa ke da iyayenki wacce ni ba zan iya baki ita a yanzu ba, ko da zan iya baki sai nan gaba amman shi yana da abun duniya wanda ya kamata ace kema kin jidadi kuma kin more hakurin da kika yi, Abu na karshe da zan fada miki shine, dukan mu ran mu a hannu Allah yake, amman masu ciwo irin na Jibril basa dadewa a duniya, kuma Jibril be da wanda zai iya tsawata masa a yanzu sai mahaifin da bashi da lokacinsa, ga jarabasar cin amanar da Siraj yayi masa wannan kadai ya isa yasa ki tausaya masa, ina son ki Nawwara amman son da nake miki na ki samu farinciki ne bana na aureki ba yan uwana da iyayena su saki a gaba, kuma ina son ki auri Jibril ko dan saboda Siraj da Zinatu, domin idan baki aureshi ba mamaki ya auri Zinatu wanda baki san iya abunda hakan zai haifar ba” Hawaye nake babu kakkautawa kamar yadda shi ma yake. “Kar tausayin wani yasa ka cutar da kanka kuma ka cutar da ni Wallahi ina son ka Bilal ina sonka sosai” “Na san kina so na, amman ko mun yi aure zamu yi ta samun matsala ne kawai Nawwara, kuma ina da kishi sosai ba lallai ne muji dadin zaman aure ba, na san yanzu ba zaki fahimta ba, amman a nan gaba kadan zaki gane gata ne na yi miki kuma na yi ma kaina, ni dai zan bi zabin iyayena wanda ina tunanin Allah zai bani wacce zan so siye da ke saboda na yi ma iyayena biyayya, kuma in da rabon na aureki sai kiga na aure ki din gaba” Durkusa na yi a gurin na hade hannayena ina rokonsa “Ka yi ma Allah da annabi ka aureni Bilal zan iya jure duk wani cin fuska da wulakanci da zaka min ko na yan'uwanka Wallahi ina son ka, Bilal sauran fa sati biyu da kwana uku ayi auren nan dan Allah karka janye, kuma ko da ka fasa aurena ba zan taba auren Jibril ba, igiyar aure ba zata sake shiga tsakani na da Jibril ba” “Idan har baki auri Jibril ba Nawwara to son da kike min na karya ne...!” Ya fada a tsawace sannan ya share hawayensa ya yi tafiyarsa abunsa ya bar nan ina aikin kuka. Da kuka na shigo gida ina labartawa Inna abunda Bilal ya yi min sai tasa salati tana mamaki karfi hali irin nasa. Misalin tara da rabi Jibril ya kirani a waya wai gashi nan kofar gida ya siyowa Noor abu, a lokacin idanuwa sun kumbura kaina kuma yana mugun ciwo saboda kukan da nayi, nasan ba dan ni ya zo ba, amman ina da bukatar magana da shi saboda abunda ya faru tsakanina da Bilal hakan yasa na fito a lokacin yana tsaye shi da Noor yana bare masa ayaba. “Noor shiga gida” Na fada cikin muryata dake nuna na yi kuka har na gaji, ba musu Noor ya taka a hankali ya shigo cikin gida, ni kuma na kalli Jibril na ce “Rokon Bilal ka yi ka ce karya aureni ko?” “Miya kawo wannan maganar kuma?” “Ban sani ba, duk abunda ka yi be isheka ba sai ka saka Bilal a gaba ka rokeshi” “Wallahi ban rokeshi ba Nawwara, ni dai na masa magana ne akan ya rike min Noor da amana a matsayinsa na wanda zai aureki kuma na nemi yafiyarsa akan abunda ya faru daga karshe kuma na ce zan maidashi aikinsa ya ce min baya so yayi applying wani gurin sai dai idan wani abun ya fada miki daban wanda ba wannan ba” Na dafe kaina ina kuka. “Ki yi Hakuri Nawwara ban san haka zai bata miki rai ba da ban yi ba, nasan komai nayi a gurinki bana gwaninta” Ya fada da muryarsa mai nuna tsantsan nadamarsa. Kasa ce masa komai na yi sai ya juyo na dawo cikin gida cike da zazzafan zazzabi. MUSTAPHA POV. Har yau har gobe son Nawwara na nan cikin zuciyarsa, sai dai ba kamar da ba, yana son ya auri Jidda ne kawai saboda Iayayen sun ki yarda da Nawwara kuma yana jin Jidda zata maye masa gurbin Nawwara ko ba komai hakan zai kara wanke shi a idon Nawwara ta yarda zata yarda ya canja har abada, kuma yasan hakan zai kara kusancinsa gareta, a tunaninsa idan ya auri Jidda hakan zai yi ma Nawwara zafi kasancewar aminiyarta ce, kuma yana yawan ayyanawa a ransa cewar ko Nawwara tana kasa giɗa sai ya aureta amana dai ko da ta tsufa ne dan shi har gobe be cire rai daga aurenta ba. Momynsa ta yaba da Jidda ganin ita budurwa ce kuma ba a mata irin shaidar da ake yi ma Nawwara cewar ta haifi shege, mahaifinsa ma ya yaba da ita duk kuwa da kasancesar ba ita ya so ya aura ba, amman ganin ita ce zabinsa a dole ya amince da ita. Ba zai ce baya son Jidda ba iya abunda ya sani yafi son Nawwara da Jidda sau dubu ma ba dari ba, irin soyayyar da Jidda ke nuna masa ne ma yasa yanzu ya maida hankali sosai a gurinta har manyan suka shigo cikin, duk da kasancewar ba a saka ranar auren ba iyayensa sunje sunga iyayen Jidda kuma an tsaida magana akan cewar satin sama za a yi musu engaged. Duk irin shakuwa da so da kauna da ya shiga tsakaminsu har yau Jidda bata taba labarta Nawwara komai ba, ba dan kuma tana son boye mata din ba, sai dan tana nuna kamar ba zata kalli abun ta fuskar daya dace ba, tana ganin kamar Nawwara zata zargeta cin amanarta duk kuwa da kasancesar ta san cewar Nawwara bata son Mustapha amman bata san ta wace fuskar zata kalli alakarsu ba. [11/17, 12:17 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣7⃣ JIBRIL POV. Cike da bacin rai ya isa gida, abunda ya kasa ganewa miyasa Nawwara ta kasa sakewa da shi ne miyasa abu kadan zata rika ganin laifinsa, sai yaushe zata fahimci irin son da yake mata? Yaushe zata gane duk wani kalami marar dadi daga gareta yana taba masa zuciya, har sai yaushe Nawwara zata fara sanin ciwonsa? “O.... Ya Allah” Ya jefar da keys dinsa ya fadi zaune saman kujera yana sauke ajiyar zuciya. Can Bilal ya fado masa a rai sai ya maida laifin a kansa daman baya son ganin laifin Nawwara, yana da bukatar jin ta bakinsa da haka dole ne ya kirashi, wayarsa dake aljihu ya ciro ya nemo number Bilal ya aika masa da kira, ta dade tana ringing kamin ya dauka. “Hello” “Bilal a Maganganun da muka yi a akwai wata magana dana fada maka wacce bata kamata ba ne?” “Babu” “Dan me zaka je ka samu Nawwara ka fada mata mun yi magana? Ba dan kowa ya sani yasa na kiraka ba sai dan ganin da na yi hakan ya dace” “Nima dacewar na gani shiyasa na aikata abunda na aikata, na fada na fasa aurenta ne kuma gobe zan tura a karbo min kayan aurena da na kai gidansu shine kawai abunda ya tada mata hankali take ganin laifin” Jibril yay saurin mikewa tsaye, maganar ta zo masa a baibai ya fasa aurenta as how shi ba ko dazun da Nawwara take ta kuka tana masa bala'i be tsaya ya tantance takamaimain dalilin da yasa ta haka ba, kawai abunda ya fi ji maganar sa da Bilal da yayi kuma ta ji. “Ban fahimce ka ba?” “Na fasa aurenta na ce, hakan yasa tayi tunanin ko kaine ka yi min wani abu sai na fada mata haduwarmu” “Am amman miyasa ka fassa aurenta?” “Saboda mahaifiyata bata son auren” Yana fadar hakan ya kashe wayar be jira ya kara jin abunda Jibril zai ce ba. Farinciki ne da bakinciki suka zo masa a lokaci daya. Ya fasa aurenta yasa shi farinciki but what if shine dalilin fasa auren? Hakan zai sa Nawwara ta kara tsanarshi, bayan haka yasan Bilal yana son Nawwara idan shine yake kokarin aurenta kuma sai wani ya kwace masa ita ya zai ji? “Amman kuma ai mahaifiyarsa yace da Bilal yana da niyar fasa auren Nawwara saboda da da tuni yayi, ina tunanin abunda ya faru ne yasa mahaifiyarsa ta hana ya aureta” Ya furta a fili sai ya fadi zaune saman sofa ya lumshe ido. “Wow da ace zan ganki matar nan da na miki kyauta mai tsoka” Can kuma ya bude ido. “I hope you're not fooling me, no he's not ai da Nawwara ba zata yi kuka ba har tana zargina” Shi kadai yake ta maganarsa ransa fari fal ba zaka ce shine ya dawo gidan da bacin rai ba. Mikewa ya yi tsaye yana ji a ransa cewar addu'arsu ce Allah ya amsa kuma gana ganin he deserved happiness again tun da rayuwarsa ba mai tsawo ba ce. Wayarsa ce dake kan sofa ta yi ringing sai ya juyo da sauri. “Nawwara” Ya furta gabansa har bugawa yake da karfi, yana daukar wayar ya ga number Abbah lumshe ido ya yi. “Oucccc am such a fool taya Nawwara zata kirani yanzu ba bayan fushi take da ni” Bude idonsa ya yi ya danna picking ya kara a kunne. “Hello Abbah” “Jibril kana lafiya?” “Lafiya kalau Abbah ya Abuja” “Al-hamdulillah ya Noor yaushe zaka shigo” “Da dai cikin satin nan ne amman yanzu ban sani ba gaskiya” “Ya dai kamata kasa lokaci ka zo” “Wani abun ne?” “Akwai maganar da ya kamata mu yi” “Ba zamu iya yi ta waya ba?” “Magana ce mai muhimmanci zai fi kyau idan kana nan zaka fi fahimtar abun” “Idan magana mai muhimmanci ce ka fada min a waya dan bana tunanin zuwa yanzu” “Magana ce akan aurenka Jibril be kamata kana zaune haka nan ba, yarinyar nan da keke so aure zata yi,  zama haka ba ba zai maka ba, na sha baka dama ka fitar da wacce kake so sai ka ce sai Nawwara kuma yanzu gashi yarinyar nan aure zata yi, dole ne idan ta yi aure zaka karbo dan ka dan ba zamu barshi can ba, babu yadda zaka yi ta gujeka kuma ta zauna da danka, na san ka yi kuskure kuma ka zalinceta amman ai an bata hakuri so dole ne ka nemi matar aure wacce zata rike maka yaronka” “Haka ne Abbah amman har yanzu ba a daura mata aure ba ba lallai ne ta auri yaron da yake son ta ba” “Wai kai ba zaka cire ranka a gareta? Yanzu dai mun yi magana da Hajiya (Step Mother din shi) akwai wata yarsa margayi Alhaji Dahiru wato Salima wacce ta fito sai kaje ka gani idan kana sonta ba zamu cilasta maka ba, amman fa bazawara ce yaranta hudu sai dai duka yaran suna hannun Babansu” “No Abbah wanda zai auri Nawwara ya fasa aurenta saboda mahaifiyarsa ta hana just saboda abubuwan da suka faru tsakanin mu, shine sai Nawwara ta bada damar na tura nawa magabatan” Abbah ya dan yi shiru kamin ya ce “Jibril ka tabbata?” “Yes Abba, jiya take fada min haka kuma kasan yadda na ke son ta Abbah, ni yanzu abunda na ke so da kai kasa rana cikin satin nan ka zo ku ga iyayenta” “Jibril ka tabbata” “Yes Abbah” “Shikenan zan samu iyayenka na nan mu yi magana” “Thank You” Daga haka Abbah ya kashe wayar, sai Jibril ya yi murmushi. “Idan ma karya ne Bilal yake ai idan Abbah ya zo dole familynta zasu fada masa gaskiya” Ya fada kana na nufi kitchen dan hada kansa tea. NAWWARA POV. Na ci kuka sosai a daren nan, na kasa yarda da abunda Bilal ya fada min na san yana so na dan me mahaifiyarsa zata shiga tsakaninmu? Miyasa idanuwan wasu suke rufewa su kasa fahimtar komai sai kansu. Washe gari da asuba bayan na gama sallah na dauki qur'ane na karanta Yasin wato zuciyar qur'ane, Suratul Yasin tana da fa'idodi da yawa ga musamman ga mutumen da yake cikin matsala da damuwa ta matsalar mijin matukar ka karanta sau goma sha biyar zama daya idan ya gama ya roke Allah bukatarsa idan da hali sai mutum ya yi sadaka, ba ni da halin karanta Yasin sha biyar hakan yasa na karanta ta sau daya na karanta Ayatul Kursiyo dari domin ita ma tana da nata fa'idan sosai kuma idan Allah ya amsa maka kamar yankan wuka yake, bayan na gama na roki Allah ya zaba min abunda duk yafi zama alheri a rayuwata, sannan na aika Jamila ta siyo min kosai na yi sadaka, a lokacin Sakina har ta shirya mana abun kari sun yi breakfast ni ce kawai ban ci komai ba tun tashina. Dakin Inna na shiga na gaishe ta a lokacin Sakina ta gama shiryawa ita da Jamila suka kama hanyar makaranta, bayan sun fice Inna ta kalleni ta ce. “Nawwara ki yi hakuri da yadda rayuwa ta zo miki, kuma ki yarda duk abunda Allah ya zaba miki shi yafi zama alheri a gareki, ni dai ina nan ina ta yi miki addu'a, dan haka ki daina sa kanki a damuwa, tashi kije ki zuba abinci ki ci” Na tada kai na kalleta idanuwa cike da hawaye. “Amman Inna kina ganin wannan dalilin kawai ya isa yasa Mahaifiyarsa ta hana shi aurena?” “Ya isa mana, idan kika duba daman can ai ba sonki take ba, kuma tana ganin an wulakanta mata da, ni kaina babu irin maganar da bata fada a gabana ba lokacin da na ke zuwa duba shi, amman idan har Allah ya rubuto ke matarsa ce Wallahi bata isa ta hana ba, ki sawa kanki wannan” Na gyada mata kai na share hawayena sannan na mike tsaye ina amsa sallamar da naji wani namiji na yi a waje, bakin kofar na nufa babu mayafi a jikina hakan yasa na leka da kai na yayinda jikina yake cikin gidan, wani saurayi saman babur hannunsa rike da ledoji sai ya miko min. “Ga sako daga Candy Restaurant Jibril ya ce a kawo ma Noor” Kamar ba zan karba ba, sai kuma na mika hannu na karba ba tare da na ce masa komai ba, dakin Inna na dawo na aje ledodin tare da fadin. “Wai Jibril ya aiko a kawo ma Noor, ni ban gane masa ba ya raina abincin gidan nan ko mai?” “Ba raini ba ne, yana ganin dacewar hakan ne kawai” “Ina Noor din?” “Yana bandaki tun dazu ya shiga” Cewar Inna sai gashi ya shigo dakin yana tafiya a hankali. “Momy gurin kaikayi yake min” “Karka sosa dai ciwon zai iya tashi” Na fada masa, sannan na juya na koma dakinmu jin wayata na ringing. Jibril ne yake kirana katse kiran sai ya sake bugowa cikin fushi na dauka “Wai ba zaka daina kirana ba ne?” “Amman kin san ba ke na kira ba Noor na kira dan me zaki dauka? Na ce ina son magana da ke ne? Da na na kira kuma kin sani na ce zan siya masa waya saboda na rika kira ta nan kin hana ya kike so na yi” “Akan me zaka aiko masa da abinci bayan kuma kasan muna da shi” “Ta nan kika bullo kuma? Na aiko masa ne saboda na san ya saba da abincin ba zai iya cin wani abinci bayan wannan ba a yanzu, kuma ina da hakki na ciyar da dana bana son wata dogowar magana da ke dan Allah ki bashi waya na tambayi lafiyarsa ko kuma na zo gida yanzu na duba shi” Kashe wayar na yi na koma dakin Inna sai gashi ya kira na mikawa Noor suka gaisa, sun dade suna waya daga karshe Noor ya fita daga dakin ya koma can gurin bandaki yana magana kadan-kadan da alama wani abun yake fada masa, sannan ya dawo ya kawo min wayar. “Momy wai ya ce yana gaida Inna da kowa da kowa amman ba da ke ba” Ya fada yana dariya, tabe baki na yi na tashi naje ya dauko kofi na zuba koko nasa suga na dawo dakin na zauna ina sha, domin shi kadai na ke jin zan iya sha kasancewar bana cikin dadin rai. Guraren goma da kwata ina yi ma Noor wanka tsakar gida sai ga Baba Sulaiman ya shigo bakinsa kumshe da sallama. Ina kallonsa nasan ba lafiya ba “Baba ina kwana?” “Lafiya kalau ina mahaifiyarki?” “Tana daki. Inna fito ga Baba” Na kwara mata kira bayan na bashi amsa. Sai ga Inna ta fito sanye da Hijabinta ta zauna bakin baranda tana gaisawa da shi. “Na ce masa ko akwai abunda ya shiga tsakanin Bilal da Nawwara ne?” Na tsayar da wankan da nake ma Noor na kalleshi gabana na faduwa. Sai Inna ta ce “Miya faru” “Ya aiko yanzu nan wai a bashi kayan aurensa ya fasa kuma wai ya yi magana da ita ya fada mata yace ta fada mana zai aiko ya karba” “Sulaiman ai gaka ga yarka waka a bakin mai ita ta fi dadi” Inna ta fada tana nuna masa ni. “Ke Nawwara ya aka yi?” “Jiya ne da yazo ya ce wai mahaifiyarsa ta ce bata yafe masa ya aureni ba, shine ya ce ya fasa aurena...” Na fada ina kokarin fashewa da kuka. “Daman Wallahi sai da muka raya a haka dukan mu sai da muka yi maganar nan, daman nasan irin rigingimun da suka faru ba zata bari ya aureki ba, Yakunbo ma sai da ta ce haka, amman matar nan ba ta yi tunani ba sam” “Ni kaina na zargi hakan ganin irin maganganun da suke ta fada gabana” “Ni kaina ina jin wasu abubuwan sai dai ka toshe kunnenka tun da ba a taruwa a zama daya, kuma a unguwar nan ma har a abunda ya kai unguwarmu babu abunda mutane basu fada ba, kuma kin san mutane da zuga Allah yasa haka shi ya fi alheri” “Amin, nima haka na ce kuma in mijinta ne babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu” “Tau Allah ya kyauta daman dai na ce sai na ji ta bakinta ne kamin mu bada kayan, Allah ya baki wani” Ya fada ganin irin hawayen da nake, sannan ya mike tsaye ya fice cike da damuwa, daman kayan ba a nan suke ba, tun da aka kawo lefen aka maida shi can gurin Yakunbo kasancewar nan gidan ba Namijj kuma ina tsoron kar a biyo dare a tararda mu. A gaskiya na ji babu dadi na ji ni a cikin wani kalar yanayi mai kamar an yi min mutuwa, ban tabbatar da cewar Ina son Bilal sai a wannan lokacin, yanzu shikenan an raba mu kenan? A wunin ranar kasa sukuni na yi a cikin gidan mu, ana kiran la'asar na dauki Hijabi na nufi gidansu Jidda. Ina shiga na fashe musu da kuka daga ita har Maman Nura wato mahaifiyarta sai da hakalinsu ya tashi, sun tausaya min kuma sun nuna min rashin jidadinsu a fili lokacin da na labarta musu abunda ya faru. “Yanzu duk soyayyar nan da kuka yi da Bilal ace be aureki ba gaskiya abun be yi dadi ba” Cewar Jidda, sai Mahaifiyarta ta ce. “Ni daman Wallahi ban dai fada ba ne, amman na san ba duka iyayene zasu iya bari dansu ya auri bazarawa ba, ko mai aure daya balle mai biyu kuma har da da, yanxu kuma ga abunda ya faru” “Amman ni Wallahi da zaki min wani abu da kin auri Jibril ko dan mahaifiyarsa ta ji haushi, kuma ga Noor sannan mutumen yana son ki sosai, kin ga sai ma ya maiye gurbin kwanakin da suka rage a daura miki aure da shi” Jidda ta fada, sai mahaifiyarta ta karba nata. “Ni dai haka na gani, wani lokacin abunda kake so ba lallai ne ya zama alheri a gareka ba, kuma so da yawa kana kin abu ya zama shine alheri a gareka, ki baiwa Allah zabi kawai” Wani irin abu na ji ya daki zuciyata, sam bana jin zan iya kara zaman aure da Jibril, indai har ban aure Bilal ba to be cancan na auri Jibril ba, taya ma zan yi zaman aure da mutumen da ya wulakanta ni ya nuna min ba ni muhimmanci a rayuwarsa. “Na baiwa Allah zabi kuma na san zai zaba min abunda duk yafi zama alheri a gareni, amman ina jin kamar ba zan iya zaman aure da Jibril ba” Jidda ta dafani. “Zaki iya Nawwara, tunda kina son Noor kuma kina son farincikin danki, karki damu da rashin son da kike masa, abu mai muhimmanci shi yana sonki kuma so mai tsanani, kuma kinsan hausawa na cewa mai son ka be ganin ramarka, kuma kara ka auri wanda sonshi ya fi na ka yawa zaka fi jindadin zaman aure fiye da wanda ke kika fi sonshi, zan cigaba da miki addu'a kamar yadda na ke yi ma kaina Insha-Allah” Hawayena na share na gyara zamana, ita kuma ta tashi ta fita saboda kiranta da aka yi a waya. Sai kusan magariba na baron gidan na dawo gida. Bayan na yi sallama magariba na zauna ina ta karanta lahaula wala'kuwwati da carbi adadin da zan iya, saboda tana yaye damuwa kuma matukar kana cikin damuwa ka lizinci karanta ta Allah zai maka mafita. Can kusan sallah isha'i na kira wayar Bilal sai suka nuna userbusy haka na yi ta trying suna amman na kasa samu daga karshe na gane ya saka number ta a blacklist ne. Wasa wasa aka kwana uku a haka na kasa cin abincin kirki saboda tunani, ba damuwa ce ta dame ni ba damuwar Bilal ce ta dame ni domin na san yana so na, kuma mutane da yawa zasu masa dariya idan har be aureni ba, duk na bi na rame kamar marar lafiya, jikina babu wani kuzarin kirki kasancewar bana iya cin abinci mai nauyi sai fura ko koko ko tea. Ranar da aka kwana hudu da faruwar hakan ina zaune, da misalin biyar da rabi na yamma sai ga Asiya yar wajen Baba Sulaiman ta zo kiran wai na zo Baba Sulaiman da Baba Dahiru suna kirana, gabana ya fadi da farko kuma naji tsoro sai dai ance karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifi da ka yi, kuma ina tunanin addu'a ta ce Allah ya amsa wata kila iyayen Bilal ne suka dawo a gyara maganar. Sai da na fadawa Inna sannan na dauki Hijabi na saka muka fita tare. Muna shiga zauren gidan gabana ya fadi ganin Baba Sulaman da Baba Dahiru da kuma Baba Audi wato kanen mahaifina da yayyensa a zaune saman tabarma tare da Mahaifin Jibril da abokinsa wanda suka zo tare lokacin da wadancan abubuwan suka faru da kuma Yayan Jibril da wasu mutane maza da ban wayancin fuskarsu ba a zazzaune. Sallama na fara yi bayan sun amsa gaishesu sai Baba Sulaiman ya nuna inda zan zauna, ba musu na zauna kaina a kasa gabana sai faduwa yake ina jiran jin dalilin kiran. “Jibril ne ya aiko da iyayensa su nema mishi aurenki kuma ya ce kun yi magana da shi akan cewar zai aiko kin amince, amman mu baki fada mana ba, hakan yasa na ce ba za a yanke hukunci ba sai an kiraki an ji ta bakinki” Na yi shiru ban ce komai ba, still kaina a kasa zuciyarta cike da tsanar Jibril. Sai Baba Audi ya katsa min tsawa. “Ki bude baki ki yi magana mana, dukan mu ba yara balle ki tsaya yi mana wasa, da baki muke son jin amsarki ba da shiru domin ke bazawara ce ba budurwa ba, cewar kin amince shi zai tabbatar mana da cewar kin amince haka Annabi ya ce” Dago kaina na yi na kallesu dukansu ni suke kallo amsata kawai suke son jin... [11/18, 10:07 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣8⃣ Kaina ya yi nauyi sosai ta ya zan iya watsa kasa a gaban manyan mutane kamar wadannan? Mi zai biyo baya idan na ce ban amince ba? Wane irin fahinta Baba Sulaiman da Baba Dahiru zasu min? “Ban zata zai aiko da wuri haka ba, shiyasa ban fada muku ba” Na fada yayinda nake maida kaina kasa. “Yanzu dai ba wannan ba, kin amince ko baki amince ba?” Baba Dahiru ya tambaya. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na amsa. “Na amince” “Al-hamdulillah, Allah ya miki albarka Nawwara kin ceci rai” Abunda ya fito daga bakin Mahaifin Jibril kenan fuskarsa shinfide da farinciki. “Tashi ki koma gida” Cewar Baba Sulaiman, haka na taso kamar marar lakka a jiki na fito daga gidan na nufo gida, tun a hanya kuka ya fara kamani amman ban yarda na yi ba sai da na iso gida, ina shiga na fashe da kuka kamar an min mutuwa. “Lafiya miya same ki?” Inna ta tambaya tana rike da tsintsiya. Faduwa na yi zaune. “Inna wai iyayen Jibril ne suka zo neman aurena?” “Ban gane suka zo neman aurenki ba” “Mahaifinsa ya turo da wasu mutane ya ce ni nace su zo, wai su nema masa aurena, shine Baba Sulaiman da Baba Dahiru da Baba Audi suka kirani suka tsareni suna tambayar wai na amince ko aa” “To mi ya faru?” “Na ce na amince” “Shine kuma kika zo nan kina kuka” “Ni bana son shi Inna ba zan aureshi ba” Sai Inna ta nuna ni da tsintsiyar da ke hannunta. “Wallahi kin yi kadan karyar karya take Wallahi, wato ni gani ice mai dadin zama shine zaki zo nan kina min kukan ba zaki aureshi ba ko? Ni da kika raina ai miyasa baki fada musu tun can ba” “Baba Audi zai iya yanka ni” Na fada cikin kuka. “Oo to sai ni da nake rarrashin ki zaki xauna kina min kuka kamar yadda karamar yarinya ko?” “Wallahi ko an daura auren nan ba zan tare ba” “Tashi kije gasu can ki fada musu tun basu tafi ba, ko kuma ni na yafa mayafina na je na fada musu kina nan kina kukan ba zaki yi auren ba” Jin haka yasa na yi saurin tashi na shige dakin Inna dan nasan duk Baban Audi ko Baba Dahiru suka ji wannan maganar na shiga uku yanxu bayan na ce na amince kuma na ce ban amince ba ai zasu ce ina musu wasa da hankali. Kuka na yi sosai dakin Inna rayuwar da zan yi gidan Jibril nake hangowa, taya zan rayu da mutumen da ya wulakanta ni? A yanzu ma zai iya kara wulakanta ni saboda yana ganin a bagas ya same ni kamar wacan lokacin, kuma zai yi ta tunanin ina son sa wanda hakan zai bashi damar sake wulakantani kuma na san har duniya ta nade Jibril ba zai taba sanin mutuncina ba. Sai da yamma Baba Sulaiman da Baba Dahiru suka zo gidan tare da kwalaye minti da cingan da sauran abubuwan da ake kawo wa na baiko, suka labartawa Inna abunda ya faru, ta nan nake jin sun yanka sadakina dubu talatin abokin Abbah ya biya dubu dari kasa, kuma sun saka kwana shida da suka rage na aurena da Bilal sun maye gurbinsu da Jibril. Baba Sulamain har dadi yake ji wai yafi son haka ta yadda Bilal kawai da familynsa zasu ji an daura min aure. A daren ranar kasa bachi na yi sai na kwana ina raya daren da sallah nafila da karatun qur'ane Allah na mikawa lamurrana har yanzu ban cire rai daga auren Bilal ba. JIBRIL POV. Tunda su Abbah suka kama hanyar gidansu Nawwara gabansa ke ta faduwa yana sauraren irin amsar da zasu dawo da ita, Abbah na kiranshi ya tsaya karanta addu'a sannan ya daga zuciyarsa cike da fargaba. “Kana ina?” “Ina gida Abbah” “Ka zo gida ka same ni yanzu” “Abbah bata amince ba ko?” “Ta amince har mun biya sadaki kuma kwanakin da suka rage na wacan da bata aura ba aka maida da naka” Rudewa ya yi yana tsaye ya zauna sai kuma ya sake tashi tsaye. “Abbah are you serious?” “Ah wasa na ke da kai? Ko wasa ake da lamarin aure?” “No no i mean thank you gani nan zuwa” Abbah ya kashe wayar yana murmushi. Sai Jibril ya fadi ya yi ma Allah sujudar godiyar, sannan ya mike tsaye yana wani irin dariya kamar mahaukaci har da jjjiga jiki, zuwa can kuma ya fara rawa takawa ya farayi a hankali a hankali kamin ya fara yi da karfi har da su kada kwankwaso, sai kuma ya yi tsalle ya fada saman kujera. “Oh my God i just can't believe this Al-hamdulillah Allah” A take ya fara hango irin rayuwar da zasu yi da Nawwara idan aka daura musu aure, ya dade yana ta ayyana irin jindadi da gatan da zai nuna mata sannan ya tuna cewar Abbah yana can yana jiranshi kuma yau zai bar garin. Cikin hanzari ya fita gida, zuciyarsa fari kal saboda farinciki, har ya yi kamar ya kira Nawwara sai ya tuna da riske yayi mata sai ya fasa dan yasan tana nan tana fushi da shi. Ko da ya isa ya samu su Abbah na cin abinci shi kan ko ruwa kasa sha ya yi saboda farinciki, rabon da ya yi farinciki irin wannan har ya manta, kallo daya zaka masa ka gane yana cikin farinciki. Wasu batutuwan Abbah ya tattauna da shi akan auren bayan ya fada masa yadda komai ya gudana. Sannan suka tsaya tsara yadda za ayi. “Zan ba Hajiya ta hada mata kayan sawa na tufafi da komai da komai da ake, kai kuma sai ka bata kudin da zata yi hidima da wuri saboda kar lokaci ya kure, na fadawa iyayemta bama son komai, saboda haka idan an daura aure sai ka fara gyaran gidan kamin nan da wata daya ka gama sai ta tare” “No Abbah a cikin week din nan ma za a iya komai a kudi ne matsalar kuma da an bada kudi za ayi komai a cikin lokaci, kuma ba dole sai furniture ba dole sai anyi order a abroad ba a nan ma Kano Kaduna ma za a iya samu na wajen, Abbah na fi son ana daura auren ta tare ranar gudun kar wani abu ya shiga” Abbah ya dan tsaya kallonsa ya so ya fahimce cewar cilastawa Nawwara yayi sai kuma ya tuna da irin son da yake mata ko da ita din bata son shi ba matsala ba ne. Su yi maganganu sosai akan auren da kuma yadda za a tsara komai, ciki har da zancen da Jibril ya bijiro da shi cewar baya son a yi masa taso sosai gurin daurin auren domin ba kowa yake son a sanarwa ba. Bayan sun gama Jibril ya raka Abbah da babban yayansu da kuma abokin Babansu da Kannen mahaifinsa airport suka hau Jirgin Abuja, shi kuma ya dawo gida. Tun daga ranar Jibril ya fara shirye shirye, a bokansa na baya da baya ja a jikin saboda abotarsa da Siraj yanzu kan ya zubar da wannan halin yaja kowa a jikinsa, sai dai be yarda ya yi amini a cikinsu ba domin a yanzu ya wayance da duniya. NAWWARA POV. Tun da aka saka lokacin Inna ta cigaba da shirye shiryenta kamar yadda ta fara, babu yadda Jidda ba tayi ba akan na je gurin gyaran jiki amman na ki, duk wani shirye shiryen da amarya take idan an kusa aurenta ni ban yi ba, ban da rama da baki ma babu abunda na yi, ranar da step mother dinsa da yayanta da wasu familyn Jibril suka kawo lefe ma na sha kuka sosai, basu karbi komai ba, ni ban ma san za a kawo lefen ba dan tun lokacin da aka saka mana rana ban taba daga waya na kira Jibril ba, shi ma kuma be kirani ba ko gaisawar da yake da Noor sai ya daina. Idan har zai yi wata magana da ta shafi auren sai dai ya kira Baba Sulaiman, idan kuma ya bukaci ganin Noor sai ya aiko da direbansa ya daukeshi a akai masa shi. Bilal kuma ban sake saka shi a idona ba, duk da ba fita na ke ba tun lokacin da aka saka min rana, Mama Turai ce take zuwa tana bani shike-shike na itatuwa da wasu abubuwa wasu na kan sha saboda fadan da take min, wasu kuma da na kafaici idonta sai na zubar. Ni dai bana shirin komai duk wani shiri daya danganci auren Inna ce take yi tare da Sakina da Jidda sai kuma yan uwnata da kuma yan Babban gida. Ina jin yadda suke shirya za su yi walima ni dai Uffan ban ce musu ba, a nan naji cewar Jibril ya ce ranar da aka daura auren zan tare, ji na yi kamar na rabe biyu saboda bakinciki. Kallo daya zaka min ka fahimci cewar bana son auren. Ana sauran kwana uku a daura auren familyn Jibril suka kawo danyin abinci kama daga shinkafa da duk wani abu da za a sarrafa a ranar bikin, sannan suka bada kudi mai yawa na hidima. Cikin kudin ne Inna ta diba ta gyara gidan aka cike inda duk da fashe aka shafe gidan sam kai bama ka ce gidan mu ba ne. Yau ta kama Assabar ranar da aka saka dauren aurena da Bilal, yau na tashi cikin damuwa da tunani, tun bakwai da rabi na safe Bilal ya turo min sakon da ya hanani sukuni. _I love you so much Nawwara, na yi abunda na yi ne saboda ki samu farinciki, ni san Mama ba zata taba bari ki samu farinciki a gidana ba ina miki fatar alheri_ Ina gama karanta sakon hawaye suka wanke min fuska, wani abu marar dadi ya zo ya tsaya min a zuciya. Karfe Goma dai dai na safe aka daura aurena da Jibril, a lokacin ne na fara kuka kamar an min mutuwa a ranar sai da na fita ran kowa daga Inna har yan uwan babana da yan'uwanta duk suka kasa fahimtata, Mama turai ce ta yi min fada sosai hakan yasa na daina kukan na koma yin na zuci. Da hudu na yamma aka yi walima a a Women development center, walimar da ta bawa kowa da mamaki saboda kayan da aka rana, ko da yake wasu sun riga sun ji cewar mai kudi zan aura, daman na san wasu gulma ce ta kaisu domin ni bana shiga mutane balle kuma biki amman aka taro sosai ga yan uwan Su Jibril suka yi nasu takeaway daban suka rabawa mutane. Malama Aisha ta yi nasiha sosai akan zamankewar aure da kuma hakuri da tsabta nidai duk abunda take fadi jinta kawai na ke dan ban shirya yi ma Jibril ko daya ba. Misali takwas na dare ya aiko da motoci daukar amarya motocin har sun yi yawa, Jidda ce ta cilasta ni ta yi min kwalliya ba dan na so ba, ta dauko min wata farar farar atamfa na saka, bayan na saka Inners farare sannan na saka fararen takalmi da farin gyale, Inna na min nasiha tana kuka kamar yadda nima na ke yi, sai aka wuce da ni babban gida su Baba Sulaiman da Yakunbo suka min tasu nasihar sai aka saka ni a mota ina ji ina gani aka dauki hanyar Sama road da ni. Na yi zaton gidan kai tsaye za a wuce da ni ganin ni bazarawa ce amman sai da aka biya wani babban gida inda yan uwan Jibril suka sauka aka kaini gurin Step mother dinsa da wasu kanen mahaifiyarsa da gwaggonsa suka min nasiha sannan aka sake sani a mota. Ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa wani katon gida mai farin fentin da gate golden color, ko ina na gidan haskene kamar da rana. Ana fitowa da ni daga mota na done kaina kasa ban sake dagawa ba har aka shiga da ni bedroom din gidan, da kafar dama na shiga kuma tare da bismillah. A tsayar gadon na zauna fuskata a bude hawaye kawai na ke ganin hakan yasa Jidda ta ja min mayafina ta rufe min fuska, yan uwansa suna ta daukata hoto wasu kuma na ta kokarin ganin fuskata sai Jidda ta hana. Bayan kamar minti arba'in Jibril ya shigo tare da abokansa sai zolayarsa suke, a gafe gado ya zauna, sannan wasu daga cikin abokansa suka shiga yi mana nasiha daga karshe suka rufe da addu'a. Ina jin lokacin da suka fita tare da nawa yan uwan da kuma Jidda, suka bar mu mu kadai a cikin dakin. Mun kusa minti talatin daga ni har shi babu wanda ya ce da wani uffan, baka jin komai sai shesshekar kukana. A hankali na ji ya kai hannunsa ya yaye mayafina ya dago fuskata, hawaye yake kamar yadda nima na ke yi. “Ki yi hakuri Nawwara na san ba ni kike so ba, na san na yi miki kutsu a rayuwarki, amman ina da tabbaci zaki auri Bilal nan da wani dan lokaci kadan, da shi zaki yi rayuwa dawwamamma irin wacce kike so” Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba. “Ada na yi tunanin idan an aureki zan kasance a cikin farinciki, amman wannan hawayen da na gani a idonki ya sani jin babu dadi kuma ya sani jin nadamar cilasta miki aurena” “Ba zan taba son ka ba Jibril, ka rabani da komai nawa, idan har kana da kunya a idonka ba zaka taba kai hannunka ka taba jikina ba, jikin macen da ka hada hotonta da wani ka ce karuwa ce mai neman maza da aurenta, ka rabani da mutumen da yake so tsakani da Allah saboda kawai ka samu farinciki, to bari na fada maka, ka kara matsowa da mutuwarka da bakinciki da damuwa da nadama a kusa da kai” Na fada ciki kuka. Sai ya yi saurin dauke kansa ya sauke wani numfashi da alama maganata bata masa dadi ba. Tashi ya yi tsaye ya cire Babbar rigarsa ya aje. “Taso mu yi sallah” Ya fada cikin muryar da ke nuna rashin jindadin da ke cikin ransa. Ban masa musu ba a nan na sauko saman gadon sai ya wuce gaba ya nuna min inda bandaki yake ya bude min, na shiga ciki na yi alwala ko da na fito ya shinfida carpet da alama shi da alwalar ya shigo. Wardrobe ya bude ya dauko Hijabi ya miko min na saka sannan ya yi gaba ni kuma ina baya ya kabbatar sallah nafila. Bayan mun gama ya yi addu'a nima na yi tawa addu'ar sai juyo ya rika goshina ya soma karanta addu'ar da annabi ya koyar da mu wacce miji yake rika goshin matarsa ya karanta saboda niman tsarin da zaman lafiya. اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ Allaahumma 'innee 'as'aluka khayrahaa wa khayra majabaltahaa 'alayhi wa 'a'oothu bika min sharrihaa wa sharri maajabaltahaa 'alayhi. Na yi mamakin jin wannan addu'ar daga bakin Jibril lallai ba da wasa ya riki karatun qur'ane ba tun da har ya iya maida hankali ga yin addu'o'i ma. Bayan ya gama ya tashi ya dauko manyan ledoji ya aje a gabana tare da plate da cups. Ni kuma na mike tsaye na nufi hanyar da aka shigo da ni wato falo. “Zo ki ci abinci mana” “Bana jin yunwa” Ita ce kawai amsar da na bashi na nufo falo na zauna, sai kuma na kasa yin kukan da na fito yi, haka na zauna a saman manyan kujerun alfamar ina ta kallon yadda aka tsara falon, ba dan ina ganin sha'awa ba sai dan na rasa abun yi zuciyata cike da tunanin Bilal. Har sha biyu ina zaune falon ni kadai kuma Jibril be fito ba. Jin na yi na tsallawa da kayan dake jikina kasancewar atamfar ta matseni sosai hakan yasa na tashi na koma dakin dan dauka wasu tufafin domin Jidda ta fada min inda ta aje min kayan da zan canja idan zan kwanta. Aabunda na tarar ya tashi hankalina sosai, Jibril ne kwance kamar matacce ga jini nan gefensa da alama amai ya yi. A firgice na kai hannu na taba shi amman be motsa ba. “Na shiga uku Jibril Jibril Jibril” Shiru be amsa ba balle ya motsa, tun ina girgizashi kadan har na fara yi da karfi ina kuka, hannu na kai daidai hancinsa sai na ji baya numfashi hakan yasa ni fasa ihu na fito a firgice falo ban san lokacin da na fito harabar gidan ina ihu ba. Ban san da akwai mai gadi ba har sai da ya taso ya nufoni yana tambayar lafiya. “Jibril ne ya suma ya ya ya mutu” Na fada cikin Matsainancin kuka da tashin hankali. Tare muka dawo dakin da shi babu abunda ke fita bakinsa sai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana girgiza Jibril tare da fadin “Mai gida Mai gida” Amman Jibril be motsa ba. “Mi ya same shi” Ya tambaya yana cigaba da girgiza shi cikin tashin hankali na ce “Wallahi ban sani ba, ni ma ina falo ko da na shigo na ganshi haka” Wayarsa ya ciro ya kira wani wanda ban san ko wanene ba, cikin kankanen lokaci mutumen ya iso a nan na gane direban da Jibril yake aikawa a gidanmu ne. Tare da taimakonsa suka saka Jibril a mota nima na shiga muka dauki hanyar asibitin One On One Special Hospital. Muna isa aka karbeshi aka shiga dashi wani dakin suka shiga bashi taimakon gaggawa, sai direban ya dawo yana cewa na kira iyayensa na fada musu. “Babu waya hannuna tana hannun Mamana” “To ki kira line sai ki sanar musu idan kina da number a kai” Ya fada yana mika min wayarsa. Cikin hanzari na karba na saka numberta na kira, sai da tayi ta ringing har ta katse na sake kira sai a na uku Inna ta dauka cikin muryar bachi. “Assalamu Alaikum” “Inna Nawwara ce ni ce, muna asibiti Jibril ba lafiya ya suma ko ya mutu” “Wani abun kika masa ko?” Na yi shiru na kasa amsawa sai kuka nake. “To kin kyauta, kuma bari kiji na fada miki ko mutuwa ya yi karki kuskura ki dawo inda na ke, ki nemi wata uwar can ba ni ba fitsararriyar yarinya” Tana fadar hakan ta kashe wayar. Sai na mika masa ina kuka kamar zan hadiye zuciya na mutu. “Ki kira mahaifinsa ki fada masa” Kuka da nake ya hanani fadin bani da numbersa numfashina har gargada yake. Shi da kasan ya kira Abbah ya fada masa, kusan a tare suka iso da Inna da wasu yan uwan Inna. “Miya sameshi” Shine abunda mahaifin Nawwara yake ta tambaya, ni kuma na kasa magana saboda kuka, Inna kan ban da hararata babu abunda take. Bayan likitoci sun gama bincikensu daya daga cikinsu ya zo yana ma Abbah bayanin cewar Jibril yana da heart attack kuma da alama an bata masa rai ne shiyasa wannan dogon suma. “Zuciyarsa ta buga a yanzu, kuma an barshi ya dade ba a kawo shi asibiti ba, ban da Allah ya masa tsawon rai da yanzu ya mutu, da alama an bata masa rai ne ko kuma be samu wani abu da yake so ba ko ya rasa wani abu, so shawarar da zan baku ku yi kokarin kawarda duk wani abu da zai bata masa rai saboda in ta sake bugawa gaskiya zaku rasa shi yanzu ma sa'a ce kawai da kuma rabon shan ruwa a gaba” “Mun gode likita zamu kiyaye” Shine abunda Abbah ya fada, kallo daya ya yi min ya dauke kansa, ya nufi dakin da Jibril ya ke ya shiga, har su Inna suka shiga aka barni nan ni kadai tsaye kamar marar gata. Su Inna ne suka fara fitowa ban san ko karfe nawa a wannan lokacin amman tabbas dare ya yi sosai amman hakan be hana Inna da yan'uwanta bin daren au koma gida ba. Bayan Abbah da yayan Jibril sun fito tare da wasu yan uwansa mata na shiga, sai na tararda wasu yan uwansa a cikin dakin, sai dai ina shiga duk suka fita waje aka bar ni ni kadai. Zaunawa na yi saman kujerar dake kusa da gadon ina hawaye, sai na dora kaina saman gadon da yake kwance ina kallon fuskarsa. Oxygen ne a bakinsa sensor na nuna yadda numfashinsa ke tafiya, tausayinsa ne ya fara kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya... [11/19, 1:12 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 5⃣9⃣ Ina biyu aka yi sallah asuba, sai na shiga bandakin da ke dakin na yi alwala da na fito sai na shimfida dankwalina already ina da Hijabi a jikina wanda na yi sallah da shi a daren jiya, sai kawai na kabbatar sallah. Dukanin addu'a ta ta nemawa Jibril lafiya, na tsorata sosai da yanayinsa ina tsoron na zama ajalinsa gashi mahaifiyata ta soma fushi da ni mahaifinsa kuma ba zai taba yafe min ba, duniyarta zata sake rikice har ma ta fi ta baya. Idan har ban yi hakuri zama da Jibril ba duk abunda ya same shi a yanxu ni za a zarga, kuma nasan Bilal ba zai aureni a yanxu ba, ko da kuwa na kashe auren ne na fito. Saboda bakin jinina kowa ni zai dorawa laifi, addu'ah nake hawaye suna min xuba, mafita kawai na ke nema a gurin Ubangijina, ina rokon ya sassauta min zuciyata ya bani ikon mantawa da komai. Bayan na gama na dawo saman kujera na zauna ina ta kallon fuskarsa tashin hankali da zullumi cike a zuciyata. Misalin bakwai da rabi Mahaifinsa ya shigo ina ganinsa na sauka daga kan kujerar na duka har kasa na gaisheshi amman abun mamaki sai ya ki kallon inda na ke balle ma ya amsawa. Ban tashi daga duken da nake ba likita ya shigo ya kara duba jikinsa ya yi musu bayanin cewar jikinsa da sauki kuma zai farka nan da wasu yan awoyi. Likitan na fita sai Step mother din Jibril ta shigo tare da wasu yan uwansa, su kan da na gaishesu sun amsa min har ma suka tambayeni mai jiki na ce da sauki. “Hajiya kuje waje likita ya ce a barshi ya samu isasshen bachi, kuma akwai maganar da nake son mu yi da matarsa” Shine Abbah ya fada abunda ya fadarmin da gaba, ba musu suka fice suna Allah ya sauwake, bayan fitarsu Abbah ya kalleni irin kallon nan na tsana ya ce. “Bari kiji na fada miki duk da na ya mutu sanadiyarki kema sai kin mutu, ko wane ango aka kai masa amarya farinciki yake yana zumudi balle ma Jibril da yake jin kamar ya hadiyeki, amman daren da aka kai shi daren aka kwasoshi zuwa asibiti yan biki ko watsewa ba su yi ba, Wace irin macece ke wani irin kallo kike so duniya ta miki? Jaruma ko hajirtacciya? Duniya zata miki kallo wawuya ne marar hankali wacce ilmimta be amfaneta da komai ba. Da kin san irin son da da na yake miki da ko ko da baki bari ya taba shi ba balle har ki bata masa rai, ban taba sanin cewar dana yana da heart attack ba sai yau, kuma na san saboda ke ne, idan kika kashe Jibril da wane ido zaki kalli Noor? Anya Nawwara akwai imani a zuciyarki kuwa?” Zubewa na yi kasan guiwoyina ina kukan da ban san ta ina yake fito min, kukan da ya hanani cewa komai har su Inna suka shigo sai Abbah ya juya ya fita bayan ya gaisa da su. Inna kamar jira take ya fita sai ta hau ni da masifa ranta a bace “Karkar kuka kike Nawwara, da kukan jini zaki yi, ba sakike kike so ba? Bari Allah ya bashi lafiya zan sa ya sakeki kije ki auri Bilal din mahaifiyarsa ta yi ta gasa miki garwashi a hannu ba ma gida ba, mutumiyar banza marar hankali wannan hakin naki ba haline na mutanen kirki ba, kuma duk mai irin rayuwarki ba zai taba jindadin zama duniya ba, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne ko ke kin fi uban kowa ne, Jahila kawai ilminki ba shi da amfani Nawwara kin yi hasara jindadin zama da mutane indai haka zaki cigaba da rayuwa” Babu bakar maganar da Inna bata fada min ba, ita da Mama Turai mutuwa ce kawai ban yi a gurin saboda kuka, amman har numfashina kokarin fita ya rikayi. Hakan be sa Inna ta tausaya min ba sai ma haushina da take ina kokarin rike mata zane ta buge min hannu ta fice a fusace, babu wanda ya tsaya ya saurari ni. Kuka na yi a gurin har sai da na gode Allah sannan na tashi na koma saman kujerar na zauna ba dan hawaye sun daina min zuba ba. Wata yar uwar Jibril ce ta shigo da kayan abinci ta aje sai ta dafani “Adda Nawwara ki yi hakuri Yaya zai tashi Insha-Allah” Uffan ban ce mata ba har ta fice, sai na maida kaina na kwantar jikin gadon na lumshe ido kaina na mugun ciwo kamar zai tsage. JIBRIL POV. Misalin goma da rabi na safe ya bude idonsa, ya dade yana gani dishi² sannan ya soma gani dai dai har ya gane asibiti aka kawo shi. A hankali ya maida dubansa gurin Nawwara da kanta ke kwance saman gadon idanuwanta a lumshe da alama bachi take amman sai shesshekar kuka take. Hannu ya kai ya shafa saman kanta, ya lumshe ido. Sai kuma ya kai dayan hannunsa ya cire oxygen din da ke bakinsa ya unkura cike da karfi hali ya tashi zaune, yana jin zuciyarsa kamar zata rabe biyu. Hakan ne ya farkarda Nawwara daga bachin da take suna hada ido sai taga abun kamar mafarki saurin mikewa tsaye ta yi sai ta rumgume shi tsabar jindadin ya farka be mutu ba, sai ta fashe da kuka. “Ka yi hakuri Jibril ba zan sake ba, ban zata abun ya kai har haka ba” Rumgumeta ya yi tsantsan a kirjinta ya lumshe ido, rabon da yaji irin wannan sukunin da sakewa har ya manta, a take ya ji sanyi a zuciyarsa har wani kuzari yana rabarsa. Saurin sakinsa ta yi tana share hawayenta. “Bari na kira likita” Sai ya rike mata hannu ya bude ido a hankali yana kallonta da bakinsa da ya yi fari ya bushe. “Doctor be da abunda zai min Nawwara, ki ce likita na komai za a min a duniyar nan ba zan warkeba matukar babu kulawarki da sonki a kusa da ni, babu ciwon da zai rabeni matukar kina kusa da ni, na san ba nine wanda kika so but please stay with me ko da na dan lokaci ne, i feel like rayuwata ba zata tsawaita da har zan hanaki jindadin rayuwarki ta nan gaba i need you” Dawowa ta yi ta zauna bakin gadon da yake zaune, hannunta na cikin na shi fuskarta kuma na zubar da hawayen, dayan hannunta tasa ta jimke hannunsa a tsakiyar hannayenta. “Har yanzu akwai son Jibril a zuciyarki, ki rantse min da Allah baki son Jibril, ba zan iya aurenki ba saboda zuciyarki Jibril take so ko da na aureki gangar jikin kawai na aura. Haka Bilal ya fada ranar ganina na karshe da shi saboda ya ga son ka a idanuwana, karya na ke na ce bana son ka Jibril kawai na kasa manta abunda ka yi min ne, amman yanzu komai ya wuce i promise you ba zan sake yin wani abun da zai tashi hankalinka ba” Hawayene suka zubo masa hawayen da shi ma kansa be san na minene ba. Hannunsa ya dauka ya dora saman nata. “Fada min wani abu Nawwara, ina jin kamar ba ke bace, wata kila saboda na kusa mutane ne kike so na yanzu” “Daman can ina son ka nothing changed no one can take your place, da ace yau na rasa ba da na wayi gari cikin wata duniya mai rudani da rikitarwa, ban tabbatar da ina son ka ba sai da na ganka kwance a saman gadon nan, Jibril i love more than I did before” Ido ya tsura mata yana ta kallonta, gaskiyar zancenta yake karanta a idanuwanta, kawai ya kasa yarda cewar Nawwara din ce, abunda ya dade yana jiran jin daga bakinta yau ya jishi. Hannunshi ta daga ta kai gefen kunci ta lumshe ido. “Am sorry” Ta furta cikin kuka. Sai ya matsa kusa da ita ya sumbaci goshinta ya sumbanci saman hancinta ya sumbanci lips dinta, sannan ya rumgumeta shima ya lumshe ido kamar yadda na ta idon suke a lumshe.... [11/22, 9:43 AM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 6⃣0⃣ Jihadin da na yi ba duk mace ba ce zata iya yinsa, zama da mutumen da ya nuna maka ba kaunarka, yanzu kuma ya dawo yana son ka kamar ya mutu. Annabi ya yi gaskiya da ya ce mu yi so kadan kuma mu yi ki kadan domin wata rana masoyinka ya kan iya zama makiyinka ko kuma makiyinka ya zama masoyinka, har ga Allah ya yarda Jibril yana so na kuma i believe without me there is no Jibril. But for what Jibril did to me is unforgivable pain, hada hotona da hoton wani namiji shine abunda na ke gani a duk lokacin da na kalli fuskar mijina. Ina cikin hada masa tea na ji hannayensa zagaye da kunkuruna ya dora fuskarsa saman wuyana yana goga min hancinsa a gefen fuskata. “Karki wahalar da kanki gurin hada tea nan ba zan iya shan sa a yanxu ba” Ya fada saitin kunnena kadan-kadan kamar mai rada. “Saboda me?” “Saboda ban wanke bakina ba kuma ban rama sallah da ake bina ba, kara ki bari kawai har muje gida” “Fine zan je gida da kaina sai na dauko maka brush din da toothpaste” Kokarin juyowa na ke amman sai ya ki bani dama saboda ya ji dadin yadda muke tsaye a haka. “Kar wani ya tarar da mu a haka fa” Ya sakeni sai na juyo na kalli fuskarsa yana murmushi sai ya dora hannayensa saman kafadata ya hade goshinsa da nawa. “To miye a ciki haramun muka aikata?” Har na bude baki na yi magana sai a turo kofar dakin aka shigo hakan yasa dukanmu muka tsargu ganin Abbah ne, bama kamar ni da nafi jin kunya, domin shi nuna yayi kamar be yi komai ba ya zauna saman gado yana gaisheshi.   Nima gaisuwar na mika masa ga mamakina sai ya amsa min sai dai fuskarsa babu yabo ba fallasa. Kofa na nufa da zimmar fice sai ya kirani hakan yasa na juyo ma dawo still kaina na kasa. “Ki yi hakuri da abunda na fada miki, raina ne kawai ya bace amman dukan wani furuki da na yi agareki bana da nufin aikata ko daya kawai dai na ce ne dan an tsorota ki” “Ba komai Abbah” Na fada sai Jibril ya kalleni ya kalleshi “Wani abun ne ya faru?” “Lokacin da kake unconscious na fada mata masu Maganganun da basu da ce ba, saboda na yi tunanin ko da hannunta a abunda ya faru da kai ne” “Aa ita ma bata san abunda ya same ni, domin na turata kitchen ta dauko plate kawai sai na ji jiri ya dibeni ban sake sani inda nake ba” Abbah ya juyo ya kalleni. “Amman Nawwara shine baki fada ba, kika kyale ina ta miki fada?” “Ba lallai ne ka saurareni a lokacin ba, amman yanzu komai ya wuce, bari na je na dauko maka brush din” Na karasa ina kallom Jibril sai ya kada min kai. “Amman kisa direba ya kai ki karki hau Napep” Da kai na amsa masa sannan na fice zuciyata cike da jindadi da kuma rashin jindadin da ban san na minene ba. Harabar asibitin na nufa inda aka faka motoci a nan na samu direansa da ban san sunansa ,bayan mun gaisa ya tambayani mai jiki sai na ce masa ya kai ni gida. Gida bayan na shiga shi kuma yana mazaunin direba kamar kullum.   Ko da a muka isa gida wato sama road ina hawayen da bansan na minene ba. Bayan ya faka motar na bude na fito ina share hawayena na nan na samu damar kallon wani bangare na gida, irin tsarin nan na manyan masu kudi gurin faka motoci an kawata ko kna da furanni masu kyau da daukar hankali.  Babbar kofar shiga falon kuma tana da stairs biyar an kawata gefen karfen stairs din da furani kamar gidanjen turawa ko kuma na ce na indiya.   Ina shiga na samu falo kamar yadda na barshi, sai dai komai na falo fari kamar fentin gidan, ya kawata falon da hotuna na da na Noor sai kuma na Abbah da na Mahaifiyarsa, amman babu nasa ko daya. Lokacin da na shiga bedroom sai na manta da abunda ya kawo ni gidan kawai na hau gyara dakin saboda ya bace da jinin da Jibril ya amayar jiya da dare. “Allah ka bani ikon jure komai” Ya roka yayinda na ke dauke kazar jiya da har ta soma yauki, bayan na gyara ko ina na shiga bandaki na hada ruwa na yi wanka, sannan na fito na shafa mai na dauki atamfa maroon color na saka, gaban madubi ya zo na tsaya ina kallon kaina kitson da aka min ya kwanta a kaina sosai gashina ya yi baki kuma ya sauko har gadon bayana. Kamar a mafarki na hango mutum ta cikin madubi ya doso inda yake fuskarsa dauke da murmushi, saurin juyowa na yi na kalleshi. “Ya aka yi ka zo” “Baki ji mota ba?” Ya fada yana muna min window. “Sam ban ji ba” “Hankalinki yana iya?” “Yana can asibiti gurin mijina” Goshinsa ya hade da nawa ya kama hannuna na dama ya shinsshina ya lumshe ido. “Ya akayi aka barka ka fito? Na san dai babu likitan da zai sallami mai jiyanci irin a yau din na asibitin bayan kuma jiya da dare aka kai ka” Be amsa min ba sai na ji kafarsa saman tawa yana goga min ita a hankali. “Su Momi suna waje suna jiranki” Ya furta sai ya sakeni ya yi baya baya yana murmushi har ya isa bandaki, sannan ya bude ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke a hankali sannan na dauki mayafi na ya rufe kaina na nufi falo. JIBRIL POV. Zaune yake ruwan shower na dukan kansa, sai dai hakan be hana hawaye zubo masa ba, kuka yake kukan da be san na minene ba farincikin dawowar Nawwara a duniyarsa ko kuma bakincikin kwanakin da yake ji a jikinsa su suka rage masa, wanda hakam ba zai ba shi damar rayuwa irin wacce yake so a tare da ita mai tsowo ba? Bayan na gama wanka yaje gaban madubi ya wanke bakinsa sai ya bude cabinet ya dauko maganinsa ya sha, sannan ya juya ya fito daga bathroom din. A gaggauce ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan na fashe jikinsa da turare ya fito falo. Hajiya ya samu wato Step Mother dinsa tare da sisters dinsa a zaune suna ta fira da Nawwara sama sama.   A ranar wuni suka yi baki daga masu zuwa ganin amarya wandanda  ba su san an kwantar da Jibril asibiti ba, sai masu zuwa diba shi idan sun je asibiti ace musu ya dawo gida. Abbah dai tun asibiti suka yi sallama da shi Hajiya ce kawai ta jira taga jikinnasa kamin ita ta kama hanyar abuja gobe. NAWWARA POV. Sai kusan isha'i sannan kowa ya watse, muka shiga gyara gidan ni da Jidda da Sakina, sai da muka gyara ko ina muka masa tas sannan muka kunna turaren wuta gidan ya dauki kamshi. “Gaskiya Nawwara kin da ce, ga mijinki yana son ki duk abunda kike so shi zai miki, yan uwansa ma ba baya ba suma na ga suna son ki” Ta fada tana karewa falon kallo. Ni kuma na yi murmushi na ce “Ni ko kin ga duk wannan dukiyar bata gabana, na rasa dalilin da zai sani na ji dadin zama a gidan nan” “Aiko kara ki fara ji tun yanzu, domin wanda kike takama da shi ya yi aure rana daya da ke” “What? me kike nufi” “An daurawa Bilal aure da wata yar'uwarsa, Mamansa ta ce ba za a daga ranar ba tun da kowa ya san an saka rana kara kawai ya auri yar'uwarsa wata yarinya ce da ake riko a gidan” Na ji babu dadi, dan nasan ba dan yana son ta ne ya aureta ba sai dan kawai mahaifiyarsa ta cilas masa. “Hakika ta yi dacen miji mai kawaici da sanin ya kamata, miji mai gudun kukan matarsa mai son duk wani abu da zai faranta rai” “Kuma ba ki ganta ba, ta ninka ki kyau sau ashiri” “Ina ruwana” Na fada ina harararta, ita kuma ta sa min dariya, sai da Jibril ya dawo sannan suka fice suka barmi cikin rashin dadin rai. Ina ta kokarin kawai da abunda yake zuciyata gudun kar Jibril ya zarge ni ko kuma damuwata ta saka masa damuwa, iya inda far'ata take na yi kokarin nemota na yabama fuskata. Bayan na fito wanka na hada masa nasa ruwan na fito daure da tawul da kuma Hijab a jikina. Tun da na fito daga bathroom din ya sakarmin ido yana ta kallona har na zauna bakin gado kamar yau ya fara ganina. Hakan yasa na soma tsarguwa. “Ga ruwan wanka can na hada maka” Murmushi ya yi sai ya bar jikin kofar dakin da yake tsaye ya nufoni ya zauna daf da ni ya kawo fuskarsa kusa da tawa har muna iya juyo mumfashin juna. Jin bakinsa daf da nawa yasa na runtse idona na dauki numfashi ina sauraren yadda yake watsa da yatsansa a gefen fuskata. “I love you” Ya furta muryarsa can ciki kamar marar kuzari, ji nayi yana huramin iska kamshin sweet candy a hankali daga saman goshina zuwa bakina. Lokaci daya na daina jin iska hakan yasa na bude ido sai na gashi tsaye yana kallona fuskarsa da murmushi. Hannayensa yasa ya tasheni tsaye ya rumgumeni tsantsan a kirjinsa. “Ina son ki sosai Nawwara” Ya furta yana kokarin ciremin Hijab din da ke jikina, ni ko gabana sai faduwa yake, hannuna ya rika ya dora saitin zuciyarsa, wani irin bugawa na ji zuciyarsa na yi da karfi har sai dai na tsorata, Dagowa na yi na kalleshi sai ya sauke idonshin cikin nawa yana min wani kallo mai wuyar fassara, hannunsa ya kai ya kama fuskata ya soma sumbantar bakina. Kasa kasa na ke saboda na kwaci kaina shi kuma sai biyoni yake hakan yasa muka fada saman gadon a tare. Dariya ya soma yi kamar yadda nima na ke dariyar, kunya tasa na yi saurin juyowa na kife fuskata cikin Bedsheet, sai ya dora kansa a bayana yasa yatsansa yana wasa da wuya. Sai da ya sumbanci kunnena sannan ya tashi daga bayana da dora kansa. “Babe-Naj gaskiya wankan nan tare ya kamata mu yi shi” Ya fada yana kokarin jan tawul din da nake daure da shi, hakan yasa na yi saurin sauka saman gado ina zare ido. “Na fa yi nawa wanka kuma ka gani” “Gaskiya ban gani ba” Ya dosoni gadan-gadan hakan yasa na haye gado na koma can karshe ina ta kokarin rike tawul din dake son subucewa daga jikina. “Ki sauko nan kawai Hajiyata” “Aa gaskiya haka kawai na yi abuna kuma ka ce sai na sake wani” Na fada ina turo baki, sai ya yi dariya. “Fine” Kokarin hawan gadon yake ni kuma na sa masa ihu. “Tsaya tsaya zan sauko, amman Wallahi na yi wankan kwarai” Tsayawa ya yi na sauko da kaina fuskata kamar na fasa kuka ina daga masa na ce. “Dan Allah karka cilasta min wanka tare da kai Wallahi na yi wanka na kwarai” Kyaleni ya yi har ya juya sai kuma ya juyo da sauri ya janye tawul din dake jikina, rudewa na yi na rumgume shi ina kokarin fashewa da kuka. Shi kuma sai ya fashe da dariya ya duka ya dauko tawul din ya daura min. “Yi hakuri” Kuka na ke da gaske har da hawaye domin na ji haushi kuma na ji kunya sosai musamman rumgumar da na masa. Sai ya nufi bathroom yana ta kyalkyatar dariyar mugunta kamar ba shi ba, ni ma har na soma dariyar kaina. Sai da ya shiga bandakin ni kuma na je na kulleshi daga waje. “Sai ka fadi wanda ya aikeka ka yi min haka nan ko kuma ka kwana a bandakin nan” “Yi hakuri idan na fito sai ki rama” “Ni ba zan rama ta yadda ka yi min ba, sai dai ta wannan hanyar” “Ashe ke matsoraciya ce ma, karki yarda na fito sai na miki abunda ya fi wannan yarinya” “Waye yarinya?” “Ke mana, kin san da auren kauye aka min da yanzu na haifeki” “Sannu Baba” Na fada ina dariya, da gangan na ki bude shi har na shirya cikin kayan bachi na nufi falo inda ya aje ledodin da ya shigo da su dazu. Zaunawa na yi a dinning din na ci abincina sai da na koshi sannan na bude freezer na dauko ruwa na sha. “Al-hamdulillah” Na furta ina mamakin yadda na soma sakewa a gidan kamar ba ni ba, ina kokarin maida ruwan na ji hannayensa kan kwankwasona, ba shiri na saki goran ruwan ya juyo da sauri ina ihu. “Ya aka yi ka fito” “Aljanine ni, waya ce ki ci amin abinci” Shi ma kayan bachi ne a jikinsa irin kalar nawa sai dai na shi na maza ne nawa na mata. Hannayensa yasa ya daukeni kamar wata yar baby, ni kuma na dora hannayena saman wuyansa. “Mrs baki da kunya, jiya fa aka kawo ki gidan nan amman har sakin tawul kike gabana” Na yi saurin boye fuskarta a kirjinsa ina dariya. *RAI BIYU...♥🖤* Wattpad @KhadeejaCandy 6⃣1⃣ JIBRIL POV. Yana zaune saman kujerarsa yana juyawa wayarsa ta yi ringing, yana duba mai kiran yayi dariya, da gangan ya ki dauka domin a yanzu ba zai iya da rigimarta ba, idan ya dauka ba zai tsira ba idan kuma ya dauka still dai masifar ce zata masa. Haka ta jera masa kira har uku sannan ya dauka. “Kina ta damuna da kira kuma kin san ina tare da budurwata” “Au haka ma zaka ce min?” “To kin fi son na yi miki karya?” “Kana ina?” “Ina gurin budurwata, ba ke kika ce karna dawo ba?” Ya katse wayar, shi kuma ya mike tsaye yana dariya ya fice daga office din, cike da so da kaunar matarsa ya fito daga lifter kallo daya zaka masa ka fahimce yana cikin farinciki, rayuwa yake da matarsa irin rayuwar da be tsammani zai samu daga gurin Nawwara ba, irin son da take nuna masa be tsammaci samunsa a gunta ba, rayuwa suke irin rayuwar da ko a littafi aabu ce mai wahalar samu. A yanzu ya zama mutum kawar kowa ciwon da yake jin kamar ba zai barshi ba, gashi yanzu ya samu sauki tun bayan jinyar da yayi a india, he can now read Quran daga fatiha har bakaqa and Nawwarar tana tare da shi da Noor what else zai roka bayan godiya ga Ubangijinsa? A masallacin da ke unguwarsu Sama road ya yi sallah la'asar sannan ya shigo cikin gida, a hankali ya yi parking dan baya son ta ji tsayawar motarsa. Yasan by this time Noor yana makarantar islamiya dan haka Gimbiyarsa ce kawai a gidan, yana fitowa daga motar ya leka window kitchen hangota da yayi tsaye gaban fanfan yasa shi jindadi sai ya dawo kofar shiga falon ya tura kofar a hankali ya shiga, amman hakan be sa ya tsira ba, sai saukar ruwa ya ji a jikinsa. “Haba Madam miyasa baki min adalci babu ne?” “Adalcin kenan kai waya ce ka jikani” “Amman dai dazu da kayan bachi a jikinki na jikaki, ni kuma shadda ce kuma gurin zan ce zan je fa” “Fade kawai kake amman babu wata mace da zata kulaka” “Inji wa? Kin ga yadda ake rushing din na kuwa kai ni fa handsome guy ne irin na bugawa a jarida ma” Ta ji haushi har da zuba masa ragowar ruwan gorar a jiki. “A haka din duk ka wani tsufa ai ni kadai zan iya da kai” “Ko yanxu ina driving wata har kashe min ido daya take” “Karuwa ce” “Wane irin karuwa kuma? Kin ganta kuwa kyakkyawa ga dogon hanci ga karamin baki gata fara kuma ga katon ciki haihuwa yau ko gobe sai shegen matsifa ta fitini kowa ta hana kowa sakewa” Ta jefa masa gorar ruwan tana ƙaƙarin kuka ita ala dole ta yi fushi da gaske, yayi saurin kai hannu ya rika ya juyo da da ita sai ya risina ya kara kunnensa dai dai cinin cikinta. “Yi hakuri Babe na fada min ya Baby yake?” “Ban sani ba” Ta fada tana kokarin ture kansa daga cikinta. “Ni dai Allah yasa karki haifo min fitininayar yarinya, Wallahi Nawwara kin cika masifa” “Au haka ma zaka ce” Ya yi saurin rufe bakinsa ya mike tsaye. “Mantawa na yi” Ya jata ya zauna saman kujera sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa. “Fada min miye na wannan fushi? ” Ta kara turo baki. “Baka siyo min komai ba” “Daga gurin budurwata na ke kin san kuma...” Be gama ba ta ja masa kunne har sai da yayi yar kara. “Wace budurwa kuma ba zaka daina jana ba?” “Wallahi ba wasa na ke miki ba, akwai wace ta dauki min hankali sosai, bana son jin muryar kowa sai nata bana son ganin kowa sai ita sunan kawai idan na ji raina fari yake” “Nawwara ce” Ya fada da fuskar zolaya sai ya maida ita kirjinsa ya rumgume suna dariya. Hannunsa ya kai ya shafa cikin ya lumshe ido. “Ban tsammaci zan kara samu wani dan ba bayan Noor but look at us right now” Murya kasa kasa yake mata maganar kamar mai rada, har kasan ruhinsa yake jin son Nawwara da duk wani abu da ya dangance ta, more especially ma cikinsa da take dauke da  shi a yanzu bayan ya cire rai daga haihuwa tun bayan a abunda ya faru da shi amman gashi yau Nawwararsa tana dauke da cikinsa. A yanzu ba shi da wani buri da tunani sai na Nawwara, ko da wasa baya son abunda zai bata mata rai, idana yana zaune tare da ita a gida har baya son fita ita kuma ya yi nisa da ita suna makkale a waya, tunaninta ta dinga addabarsa kenan kamar yadda ita tuaninsa yake hanata sukuni, lokatu da dama idan zai anbaci sunan wata sai ya kira Nawwara shi da kansa wani lokacin yana mamakin kansa, a lokacin da ya fahimce cewar tana da ciki sai ya kasa sukuni kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda murna da jindadi. Yau ma kamar kullum Jibril be sake fita ba tun da ya dawo, tare suka karasa girkinsu na dare,  around six direba ya dauka Noor daga islamiya, da gudu ya shigo yana sallama tare da fadin. “Daddyna ya dawo” Yana shigowa Jibril ya safkeshi ya yi sama da shi. “Oyoyo dan daddynsa” Dauke da shi ya shiga bedroom dinsa wato dakin Noor dakin da aka kawata da kayan wasan yara da duk wani abu na jindadi. “Ka cire uniform ka zo muje masallaci an kusa sallah” Ya fada yana direshi saman gado. “Okay Daddy” A nan jibril ya juya ya shiga bedroom din Nawwara, a gaban madubi ya sameta tana gyara kayan da ke gurin, a jikin kofa ya ya jingina yana kallonta har sai da ta kammala sannan yaje ya rumgume ta baya ya dora kansa saman wuyanta. “Ke baki gajiya da aiki ne? Ba na ce ki bari sai gobe mu gyara ba” “Haka kake ce min tun shekaran jiya ai, Noor ya dawo” “Eh ya dawo yana dakinsa uniform din islamiya zai cire” “Ya cire ya zo nan sai na masa duka ai” “Mi kuma yayi miki?” “Da ya gama cin abincin rana haka ya bar min plate a falo ya wuce islamiya kuma na sha fada masa ya daina min haka amman ya ki” “Saboda wannan zaki dakeshi” Ta yi shiru, sai kawai ya yi dariya ya kara rumgumeta, domin a yanzu ya saba da halin abu kadan zata ce sai ta hukunta shi ko Noor ko da kuwa abun be kai ya kawo ba, tun da ta dauki cikin nan ba wani zaman lafiya, kullum da kalar fitinar da take masa shi da Noor. A bakin kofar bedroom din Noor ya tsaya ya leko kansa dan yasan laifin da ya yi ya ce “Daddy muje an fara kira” Suna hada ido da Nawwara ya yi saurin komawa yaja kofar. “Ni gaskiya sai na dakeshi ko kuma kai na hukunta ka” “Hukunci ai ba zai wuce na cewar ba zamu ci miki abinci ba, ni kuma sai na dauki da na muje restaurant mu ci abinci mai dadi” “Ba dai irin nawa na” “Har ya fi naki dadi ga waiters din da iya tarbon baki” Ya fada yana kanne mata ido daya. Ita kuma ta dauki filo ta jefa masa ya gwace yana mata dariyar keta. Washe gari ma haka ta tashe da masifar ta kamar kullum, sassauci daya ta samu bayan Noor ya wuce school ya dora kanta saman cinyarsa ya bude suratul kaffi yana karanta, ita kuma tana saurare har bachi ya dauketa, bayan ya gama ya dauke kanta ya maida saman matashin kai ya shiga kitchen ya shirya musu abun karyawa, bata farka ba sai kusan goma na safe. Da taimakonsa tayi wanka ta saka abaya black, sannan suka dawo falo suna karyawa. Shi yake feeding dinta ita tana feeding dinsa kamar yadda suka saba har a gaba ko da kuwa Noor yana nan. Basu gama karyarwa ba aka danna door bell amalar akwai wani a bakin kofar, har ta kai je zata tashi sai ya zaunar da ita. “Bari na duba” Yana bude kofar ya karbi sakon da ke hannun mutumen sai ya maida kofar ya rufe, ya dawo yana fadin. “Rufe idonki” “Mi zaka bani?” “Just close your eyes please” Mikewa tayi tsaye ta soma zagayensa ita ala dole sai ta ga abunda ya shigo da shi shi kuma ya rika juya hannayesa ta kasa ganin a dole ta hakura ta rufe idanuwanta. “To na rufe” “Ban yarda da wannan rufewan ba, juya bayanki” Ba musu ta juya baya, zuciyarta cike da zumudin son ganin abunda yake boye mata. Da sauri ya juya ya koma gurin kofar ya bude musu suka shigo da kayan da suke dauke da su suka dora saman center table sannan suka fice da sauri, har lokacin Nawwara bata juyo ba duk ta tana jin kamar motin abu a bayanta. “Juyo ki bude idonki” Juyowa tayi sai dai bata bude idon ba, har sai da ya sake fadin ta bude idonta. A hankali ta soma bude idon sai idanuwanta suka sauka kansa. Still har yanzu hannayensa suna bayansa da alama akwai abunda yake cigaba da boyewa. “Minene tau?” Ya nuna mata tsakiyar falon inda center table yake, what a surprise katon cake ne a saman teburi an rubuta masa HAPPY BIRTHDAY MY PRINCESS, da mayan haruffa da sauri ta doshi gurin tana kallon cake din cike da excitement. Katuwar farar paper da ke gefen cake din da aka kawata da flowers da masu harufa an rubuta FOR MY LOVELY WIFE, ta kai hannu ta dauka ta bude jikinta ya rawa ta soma karantawa. _Happy birthday to someone close to me, today my queen was born, the queen of queens, how can I forget your birthday Queen? The woman whos make feel better person, she's stay by my side i learned many things about life and love, she's the only woman i love and i know lucky is the man who is the first love of a woman, but luckier is the woman who is the last love of a man, you got it all Baby, I loves you yesterday. I love you still. I always have .. I always will. Happy birthday to you my heart_ Dagowa ta yi ta kalleshi idanuwanta cike da kwalla. “My soul i love you so much” Hannunta ya kama ya saka mata zoben da ke hannunsa mai alphabet din NJ. “Happy birthday Princess” “Thank you, ni na manta da yau ne birthday na ma” Ta kwantar da kanta jikinsa tana hawaye. “Ni kan ba zan manta ba, taya zan manta birthday din babbar mace kamar wannan? Matar da ita farincikina mace da ta zame min RAI BIYU, kuma muka zama RAI BIYU ni da ita” Ta yi farincikin da abunda ya yi mata har bata iya misalta jindadinta, haka yake mata a ko da yaushe yana surprising dinta da abunda zai sata farincikin ko ya kara mata son sa a zuciyarta. A ranar farinciki ya hana Nawwara bachi kamar yadda yake hanata a duk lokaci da wani abun farinciki ya same ta, baya da bukatar godiyarta domin yana tunanin duk wata hanya da zata gode masa ta yi masa yawa, shine ya kamata ace yana gode mata ko dan canjin rayuwar da ya samu. *** *** *** BAYAN WASU SHEKARU..... Rayuwa ta canja mana, lallai dukan abunda Allah ya rubuta zai samu bawa babu makawa sai ya sameshi, lokuta da dama muna son abu sai ya zamo ba alheri ba ne a garemu wani lokacin kuma mukan ki abu kuma ya zama shine alheri a garemu, shiyasa ka bawa Allah zabi shine abunda ya fi domin shi zai zaba maka dukan abunda zai zama alheri a gareka ko kuwa kai kana ganin kamar ba alherin ba ne. Kaddara data rubuta cewar ni matar Jibril ce a karo na biyu ita ce ta sake rubuta min farincikina da jindadi a gidansa, abunda ko da a mafarki aka cemin zan yi rayuwar jindadi da farinciki a gidan Jibril ba zan yarda ba amman yau gashi ina ganin kamar ma nafi kowa ce mace dace da mijin aure, you deserved happiness shine a abunda yake yawan fada min kuma yake ta kokari wajen ganin ya faranta min a rayuwata. Lallai Jibril bango ne shafi kuma jigo a rayuwata majinginata mai share hawayena a duk lokacin da kuka ya tunkaroni. Bayan yankewa Siraj da abokan ta-addacinsa hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso bamu da sauran fargaba ni da Jibril, ba ma kamar yanzu da hankalina ya kwanta sosai ganin cewar Zinatu ta yi aure, macen da take barazana ga rayuwata da kuma ta miji, irin rayuwar da nake a gidan mijina rayuwace da ko wace mace mai aure zata so kasancewa a cikinta, domin kuwa Jibril yana sani na manta da damuwata a duk wani fargaba da yake tare da ni, a da na yi tunanin rasa Yar'uwata Habiba da na yi da kuma Mahaifina farinciki ba zai sake ziyarta ta, ashe shirme na ke ta yi Allah ya tsara min wani jindadi da farinciki a gidan Jibril. Wani lokacin na yi dariya idan na tuna irin kiyayyar da na nuna masa ko kuma na ce irin soyayyar da na yi da Bilal wacce na ke ganin kamar idan babu shi babu farinciki a rayuwata, lallai yan karon magana sun yi gaskiya da suka ce karshen kiyayya soyayya domin kuwa ni da Jibril a yanzu kamar mu hade junanmu muke wa ma zai ganmu a yanzu ya zaci mun taba wata rayuwar ta bakinciki da kiyayyar juna. Lokuta da dama na kanyi ma Allah godiya akan zabin da yayi min na auren Jibril sama da Bilal domin kuwa a yanzu na gane irin tazarar dake tsakaminsu da kuma irin rayuwar farinciki da jindadi da Bilal yake ciki, domin shi ma na samu labarin irin rayuwar jindadin da yake da matarsa tun bayan da kama aiki a kamfanin hakar man fetur na dangote dake Lagos, wata kila da ni ya aura da mahaifiyarsa ba ta barmu munyi zaman aure kamar yadda ta barshi yana zaune da matarsa a yanxu ba. Na kanyi kokarin taimakawa a duk gurin da na ana bukatar taimako domin kuwa a yanxu na fahinci yadda rashi yake da kuma shiga halin rayuwa, duk a yanxu muna cikin ni'imar Allah Al-hamdulillah. Inna ma a yanxu ba zaka ganta ka ce ita ba ce, domin sun tare da sabon gidan da Jibril ya siya musu, duk wani wulakanci da halin ko inkula da familyn suke nuna mana a yanzu ya wuce mu ne kan gaba a komai, ashe daman rashin yake sa ake wulakanta mu kamar marar galihu. Bayan Haihuwar Nana Asma'u wato yata ta biyu da take bin Noor na sake haibuwar Bashir wanda na kira da Babana, sai kuma na sake haihuwar Fatima da Aisha, a duk lokacin da muka samu hutu mu kan kwashesu muje hutu Abuja. Idan kuma muna sokoto ranakun Assabar da Lahadi sai na sa direba ya kaisu gurin Inna a can suke hutun sati, har bana son su dawo saboda hayaniyarsu. A ranar da muka samu hutun karshen shekara nasa ya kaimu Katsina gurin Hajiya Aisha wato matar margayi Alhaji Dahiru, ta yi mamakin ganinmu kamar yadda na yi mamakin halin da na sameta a cikin, da bakinta take fada min, zaman abuja ya gagareta saboda gadon da Alhaji ya bar masu ta soma business da shi tana zuwa har Dubai da china amman abun be karbu ba sai ya kare a yanzu ma babban danta ne yake dauke da ita sai taimakon da sauran yayanta nata suke kawo mata, na yi mamakin ganin har yanzu Salima bata sake wani auren ba wato autarta wacce ta kasance kawata a lokacin da nake gidan, na ji mutuwar aurenta tun lokacin da Hajiya Aisha ta so a hada Jibril da ita a lokacin da aurenta ya mutu. Kwanan mu biyu a garin muka koma garin Abuja gurin da yara suka fi jindadin zama. MUSTAPHA POV. A ko yaushe yana yi ma Allah godiya da ya bashi Jidda a matsayin mata, domin kula da soyayyar da take nuna masa, a yanzu yana ganin ko Nawwara ya aura ba zai sameta ba, shi kansa a yanzu ya zage dantse yana nuna mata kula sosai domin ko da wasa baya son bacin rai Jidda kamar yadda ita ma bata son bacin ransa. Gudun wannan yasa ya nemi transfer aka maida shi Kaduna domin a ganinsa idan ya yi nisa da mutumen da yake ganin kamar barazana ne a rayuwarsa zai fi samun kwamciyar hankali, musamman ma Nawwara da ya kasa cirewa a zuciyarsa. A Kano ta haifa masa Amina da Amal wato twins duka mata, a lokacin har baya iya misalta irin farincikinsa, a dole tasa suka tattara suka dawo garin sokoto da zama har yaran suka yi kwari duk da kasancewar can yake aiki sai dai yaje ya dawo. Bayan yara sun yi wayo ya dauki matarsa suka koma Kaduna tare da mai ronon yara saboda rage mata aiki, ita kanta Jidda a yanzu take jin ta yi dacen abokin rayuwa, domin kuwa be rage ta da komai ba, irin soyayyar da yake nuna mata har sai ka zata ita ya fara so ba Nawwara ba. A haihuwarta ta biyu Nawwara ta so ta je amman Jibril ya hanata saboda yana ganin Mustapha a matsayin masoyinta, be duba aminta dake tsakaninsu da Jidda kirkiri ya hanata zuwa a tunaninsa idan taje can Mustapha zai ganta kuma a gidansa zata sauka, shi be ga dalilin da zai sa ya barta taje ba. Babu irin fushi da fadan da Jidda batayi da Nawwara ba akan hakan domin ita a nata tunanin Nawwara ce ta ki zuwan ba wai Jibril din ne ya hanata ba, domin a yanzu tana ganin kamar Nawwara da Mustapha an zama yan'uwa ba dai masoya ba, domin tun aurensu da Mustapha be taba mata maganar Nawwara ba ko da wasa, idan ma ta dauko masa maganar abunda ya shafeta sai ya nuna mata baya so hakan yasa bata taba zancen Nawwara ko wani abunda ya shafeta a gaban Mustapha. A lokacin da Nawwara ta haifi Aisha Mustapha be hana Jidda zuwa ba duk da yana bakin aiki a lokacin sai ya sa direban abokinsa ya kawota har sokoto domin ahi kansa a lokacin ta matsa masa da zancen gida, tayi marmarin gida. Bayan suna da sati daya ta dawo domin ya bukaci hakan, ita kuma bata son tsabawa matsa, kawayenta har zolayarta suke wai ta cika son mijinta da yawa, ita kuma ya nana musu cewar shi ma yana ji da ita ne, kuma ya san darajarta kamar yadda ta san tashi darajar. A zamantakewar rayuwarsu abun burgewa ga ko wadanne ma'aurata abu ne mai wahala ka ji kansu ne, tana kokarin kare mutuncin mijinta Jidda bata daga cikin matan nan da zasu zauna suna fadin sirrin mijinsu ko kuma familysu wanda ya zama ruwan dare a yanzu, hakuri shine abunda ya gina gidanta kuma ya ingantashi, da kuma bawa juna shawarwari, tana saurin bawa mijinta hakuri idan ta bata masa rai ko da kuwa ita ce mai gaskiyar, idan ta ga abunda be mata ba ta kan fito ta yi nuna masa ko kuma ta masa magana sai ya gyara saboda gaba, shi ma haka yake mata idan ta bata masa rai ko da masa wani abun ba daidai ba ya kan fito ya fada mata. Basa kunlatar junansu da komai wannan ne yasa a kullum suke cikin farinciki da kaunar juna marar misaltuwa. NAWWARA POV. Rayuwa ta koya min abubuwa guda uku zuwa hudu, na farko shine hakuri wanda shine jigon komai da komai na rayuwa da kuma zaman duniya, na koyi juriya da kuma jajjircewa akan komai na rayuwa, akan yasa na kara tabbatar ayar nan da Allah yake fadin lallai ne bayan ko wane tsanana akwai sauki a tare da shi, sam ba zaka ganni a yanzu ka ce mi ce a wacan duniyar mai hayaki da gobara ba, har sai idan na bude maka shafin rayuwata. Rauwa ta da koya min zama da mutane da iya rike sirrin, ba kowa mutum ba ne na kwarai kamar yadda Siraj ya ha'incin Jibril akwai kawayena na kwarai irin su Jidda da Salima, kawaye da a yanzu sun ce na ce muau aminar muna kiran junanmu da yan'uwan juna. Yar'uwata haka na rubuta a Number Jidda kamar yadda ita ta rubuta My Blood Sisi a numberta. Wani lokacin idan na zauna ina tunanin yadda rayuwa ta zo mana ni da Jibril sai abun ya rika bani dariya da kuma mamaki, lallai abunda duk Allah ya so ga bawa babu wanda ya isa ya hana shi ko da kuwa duniya zata taru akansa ne, abunda kuma Allah ya rubuta zai sameshi sai ya sameshi no matter what. Hakika soyayya bata tsufa sai dai masoya su tsufa, ban taba yarda da wannan ba shiyasa kullum cikin kwaliyata na ke da yin duk wani abun da zai daukewa Jibril hankali, ban yarda akwai wata mace da zata iya daukewa hankalin mijina ba, sai dai ni na dauke masa hankali daga wasu matan, idan yana gida ina makkale da shi, domin yarana sun bude ido sun ganni tare da Abbasu so na abun mamaki bane idan na kwanta a jikinsa kamar yadda dukansu wani lokacin suke zuwa mu kwanta tare mu tausheshi muna dariya. Idan kuma baya gida to waya tana kunnena ina jin labarin duk wani abu da ya gani a waje, kamar yadda nima nake labarta masa dukan abunda na aikata a gidan matukar ba aiki yake ba. Sakwannin barka da safiya kan sun zame min kamar jiki dole ne kullum sai na tura masa a waya, ko kuma na rubuta masa a paper ma aje masa. Goodnight massage kuma kullum sai na tura masa kamar yadda shi ma yake turo min, wa zai ga rayuwarmu a yanzu ya ce mune a wacan lokacin? Lallai na yarda Kaddara ta riga fata! Kamar yadda aka rubuta a iv yau ce ta kama 23 ga watan November, yau ake daura auren Sakina da angonta wato Mahmoud, hakan yasa na tashi da wuri na yi duka aikina amman hakan be hanani yin latti zuwa gida ba domin Jibril ya yi rantsuwa ba zan bar gidan ba sai na gyara masa ko ina kuma sai na tafi da yara kamar yadda yake min a duk lokacin daya fuskanci bana son zuwa da yara gida. Ko da tara tayi na gama komai na yi ma yara wanka ni ma na yi. Aai dai ba mu shirya ba domin bana son au bata atamfar ankonsu tun yanzu kara su kara wasu tufafin da aka dinka musu na cin biki kamin mu isa can. Muma tsaye harabar gidan gurin mota muna jiran fitowarsa ya aje mu gida domin direbansa baya nan yana can ana hidima da shi ni kuma ya ki yarje min na toka motata wai a ganinsa ban gwari yadda ya kamata ba, hakan yasa indai da yaransa zan je yawo baya bari na yi driving sai idan ni kadaice ko kuma ni da shi. Farar shadda ce a jikinsa ta karbeshi sosai kai ka ce ma shine angon, fuskarsa sai annuri take, yana ta kamshin turare. Kallo daya na yi masa na ji kaunarsa ta kara shiga zuciyata, hakan yasa na kasa dauke idona akansa har ya shiga motar ya yi mata keys. “Wannan irin kallo haka barakkala Masha-Allah karki cinye ni” Sai duk muka sa dariya har yara da suke bayan mota. Ni dai ban ce masa komai ba har muka isa gida yana aje mu ya wuce gurin daure aure da aka ce goma na safe za ayi. Mun yi biki lafiya mun kare aka kai Sakina Birnin Kebbi gurin da Mijinta yake aiki, kasancewar mai mata ne ta aura sai dai asalinsa shi ma dan sokoto. Ranar data zagoyo Assabar babu kowa gidan sai ni da Jibril, a ranar muka sha soyayyar kamar wasu sabbin ma'aurata, washe gari shi ya girka mana abun karyawa domin ni ban tashi ba sai da rana ta fito. Haka muke a duk lokacin da yara basa nan sai abunda muka manta ne kawai bama yi amman ko wace irin kulawa da soyayyar na yi kokarin nunawa mijina kamar yadda shi ma yake muna min, muna jindadin zama da junanmu sama da yadda duk wani mai tsammani yake tsammani, ba mu da wata fargaba ko tunani a zama da muke da juna,muna karan junanmu da sunan da yayi mana dadi, idan kuma yana fushi da ni nasan irin sunan da yake min ka kaka da kakkani, ko ya kira da wani suna a cikin kayan girki, nima kuma na akan masa wannan lakanin kamar yadda yake min. Al-hamdulillah a ko yaushe na kan yi ma Allah godiya da ya bani miji kamar Jibril domin ni da shi RAI BIYU ne bayan RAI BIYU da na rasa wato Habiba da kuma mahaifina. A yauzu a kullum ni nawa godiya ne a garin Allah. ___________________________ Al-hamdulillah nima na gode Allah daya nani ikon gama RAI BIYU Lafiya, duk da kasan ba kuso ya kare a haka ba ko kuma na ce a yanzu ba, ku gafarci idan akwai idan na bata musu rai tun farkom fara rubutun nan zuwa yau, ma gode da irin goyan bayan da kuka bani da kuma juriyar karanta lattafin da ba ayi editing ba. Mu tara a littafi na gaba mai suna HAFSATU MANGA yarinyar kauye kuma labarin kauye kuma labarin sarauta mai sarkakiya da ban dariya da kuma tausayi, sai dai shi ba Free ba ne kamar wannan, HAFSATU MANGA na kudi ne, kuma ina fatar zaku bani hadin kai kamar yadda kuka ba ni a wannan, da ma sauran da zasu zo a gaba. Godiya ta musamman gareku Whatsapp people baki ba zai iya gode musu akan irin soyayyar da kuka nuna min a littafin nan, sunanyenku ba zai lisafu ba amman ina son ku san cewa Khadeeja Candy tana son ku so na hakika. Gaisuwa da yabo gareku Wattpad readers I really appreciate your votes your comments your support, thank you so much, I love you All fisabilillah. Littafin nan Sadaukarwa ne gareki Asma'u My Asmee Allah ya bar kauna da zumunci mai dorewa har Aljanna. Ga Mai son siyen Littafin Hasfatu manga wanda zaizo nan da one month Insha-Allah ba wato 2020 zai iya nemana ta wannan line 08036126660, ta layin zaku iya turo min gyara ko kuma shawara akan littafin RAI BIYU da ma wasu littafan da suka gabata ko kuma masu zuwa nan gaba, I thank you so much my fans without you guys there's no Khadeeja Candy 😍 LTTAFAINA MASU ZUWA HAFSATU MANGA (Labarin kauye) KILAKI (Karuwa) HASKEN ANNURI (the light and darkness) And many more.... Best regards 😍 Khadeeja Candy One heart One love. #Don't forget to follow me and also add Hafsatu manga to your library, thank you all stay bless 😪🙌