*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM* *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 01 *_Assalamu alaikum warahmatullah,barkanmu da sake kasancewa da juna,da fatan anyi ibadu dukka lafiya,anyi kuma sallah lafiya,Allah ya karbi ibadunmu ya sanyamu cikin 'yantattun bayinsa_* ______________________________ *_COEUR BRISE_*(BROKEN HEART) "hasbunallahu wani'imal wakil" ama ta sake furtawa a karo na barkatai cikin adadin da batasan yawansa ba na faduwar da gabanta yakeyi. Tun lokacin da motarta ta saitu saman hanya zuciyarta ta fara wani irin tsinkewa da batasan meye dalili ba. Ta laluba tunaninta kaf bata hangi wani abu daya faru ko zai iya faruwa da ita ba,hakan ya sanya ta alaqanta faduwar gaban da sauyin yanayi ko kuma tabuwar sashe na jiki da yakan iya faruwa haka siddan ba tare da wani dalili ba. Turaren data gama feshe amarya da shi ta sakarwa gwaggon amaryar da suke kira da inna batula duk da ce matan da takeyi ta riqe,amma yawan hayaniya dake wajen da kuma yadda hankalinta taji sam bai kwanta da zama a wajen ba,taji tanason tayi nesa da hayaniyar ya sanya hanakalinta baikai kan abinda inna batula ke fada ba. Tana sake nesa da wajen tana dan jin relief cikin ranta. Sai ta taka can nesa kadan da wajen da ake gudanar da kamun amarya,inda wasu fararen kujeru ke ajjiye a wajen zaman jiran wanda keda buqatuwar zama a kansu. Kujera daya taja ta zauna akai tana zare mayafinta dake saqale a kafadarta guda. Light purple veil ne wanda a iya idanu kadai kana iya qiyasin adadin tsadarsa ba tare da ka kai ga tabawa ba. Hannunta tasa ta shafi dogon farin wuyanta da ta yima ado da wata siririyar sarqar gold me matuqar tsari da daukar idanu,duk kuwa da cewa adadin yawan jelar sumar kanta tadan rufe wani sashe na wayar amma hakan bai hana bayyanuwar kyawunta ba. Iska ta furzar daga bakinta,ta zaro wayarta qirar iPhone 15 tana duba lokaci. Dududu basu haura awa hudu da baro gidan ba,amma kuma batasan meye ne yaketa fusgar hanakalinta zuwa gida ba. Sake duba lokaci tayi,ta shirya daga nan ta wuce gurin dinner din 'yar qawarta ne,kuma qananun mintuna suka rage lokacin ya cika,amma cikin ruhinta sai taji kaman ba zata iya qarasawa can gurin daya bikin ba. Dafa qasa bibi tayi tana miqewa bayan ta shafa addu'arta "Kiramin modu maza,gida nakeson komawa,sultana ita kadai kamar mayya,wancan ja'irin ba ya hanata fitowa saboda kawai neman fitina" bibin ta fadi tana gyara yafen lallausar mayafin doguwar riga cotton dake jikinta "Yarinyar da har kuka zargawa igiyan aure kuke taraddadin kun baro a gida bibi?" Inna hassu ta fadi tana kama haba hadi da sakin siririyar dariya "Naga alama ko haihuwa sultana tayi ba zaki daina lelenta ba bibi" jakarta kawai ta miqa hannu ta dauka tana riqeta a farin hannunta da yasha jan lalle sannan ta dubi hassun ta gefe "Kwadaiji dashi,ni na wuce,idan sun dawo ciki kya gaya musu" "Muje nayi miki kiran modu din" inna hassu ta fada tana ajjiye sevenniours din hannunta a gefan gado. Kaman yadda bibi ta buqata din hassu bata gayawa kowa zata tafi din ba,saboda karanta da tayi kaman hankalinta ya karkata ga gida don haka ta qofar baya ta bude mata suka fice. Suna tafe suna dan taba hira jefi jefi. Danne danne kawai takeyi cikin wayarta ba tare da tasan ainihin me take dubawa ba,tayi nisa a tunani ta jiyo muryar bibi din da hassu. A hankali ta cira kanta tana duban sashen da take jiyosu din,sai ta maida wayarta jaka tana ci gaba da dubansu har zuwa sanda suka iskota "A'ah,kema kina ta nan?" Bibi ta tambayi ama tana dubanta. Kai ama tadan gyada tana sakin fuskarta "Na gaji ne haka kawai kaman wadda tayi wani aiki,abokin tafiya gida ma nake nema" "Shikenan an huta neman modu,ga bibi ita dinma gidan takeso komawa ta baro wai shalelenta ita kadai" harara bibi tadan watsawa hassu "Kekam idan baki rage magana ba wataran sai an kumbura wadanan lebunan,muje ko hamdiyya,idan sun gama raye rayen kya gaya musu mun wuce mu" bibi ta fadi tana bin bayan ama da tayi gaba tana qoqarin fiddo key din motarta. Shuru ne ya wanzu cikin motar,daga ita har bibi babu me cewa komai. Haka kawai jikkunansu da bakunansu ke a mace. Duk da akwai surukuta tsakani,kuma duk da dadewar zaman hamdiyya dasu bata cika sakewa qwarai da bibi ba. Har yau tana surukuta da ita,kamar yadda take bata girma yadda ya kamata. Tamkar masu rakiyar gawa haka sukayi cikin motar. A nutse ama ke tuqi wani abu da batasan meye ba yana mata kai kawo qasan zuciya har zuwa sanda suka isa gidan. Horn biyu batayi na uku ba daya daga cikin security na gidan suka dage mata gate ta cusa hancin motar nata. Sai data tsaida motar sannan ta zagayo ta budewa bibi. Bibi din tayi bismillah ta sanyo qafafunta a waje sannan ta miqe ta fito,ama ta maida.murfin motar ta kulle tana jin bibi tana cewa "Yau gidan kamar anyi shara haka,ba kowa?" Itama ama ta kula da hakan "Wataqil suna ciki suna hutawa" ama ta bata amsa tana riqe mata 'yar purse dinta. Tunda dai daga ita sai ita din tasan dole ta rakata zuwa ciki. Bibi na gaba tana biye da ita. Daf da zasu sanya kai zuwa ga sassan bibi din sautin muryar tanja ta mamayi kunnuwansu "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,na shiga uku jama'a kuzo ku ganemin sultana" "Sultana?" Bibi tabi qarshen muryar tanja da tambaya da sunan sultana din. Yayin da ama taji kamar an finciki wani abu daga cikin tsakiyar zuciyarta haka kawai ba tare da tasan dalili ba. Kamar wadanda aka kafe a wajen haka sukayi carko carko harsai da tanja ta iskesu hannunta saman ka hawaye na sharafinsa saman fuskarta. Tamkar an tunkudata haka ama taji,ta rabe ta gefan bibi cikin sassarfa ta durfafi tanja. Hannunta ta riqe gam tana cewa "Ke mene haka tanja?,meye zaki dagawa mutane hankali haka?" "SULTANA ce,ta mutu wallahi,ama kizo ki gani" "Waye ya kasheta?!" Bibi da ama suka hada baki gurin fada kowanne sautin muryarsa na nuna zallar tashin hankali "Maina ne!,Aliyyu ne wallahi,shine naga shigarsa dakin" wani irin mahaukacin bugu dukkaninsu zukatansu sukayi "Maina?,aliyyu?" Ama ta maimaita a fili,yayin da kunnuwanta suka dode na wasu 'yan sakanni kafin tabi ta gefan tanja tana wuceta zuwa ciki da wani mugun sassarfa har tana gogar kafadar tanja din ba tare data lura da abinda take aikatawa ba. Duk a saurin da takeyi qafafunta rawa sukeyi kaman zasu lanqwashe "Maina ne?,me ya yiwa sultanar?,da gaske kasheta yayi?,kada dai ace baqar muguwar zuciyarsa ce ta kitsa masa haka?,amma aliyyun duk zuciyarsa zai iya iya kisa kuwa anya?" Tambayoyin da suka dinga yi mata gizo kenan kafin ta samu Isa ga dakin. Tambayoyin da suka dinga sanyata taji kamar tayi tsuntsuwa ta isa ga dakin ta tabbatarwa idanunta abinda tanja ke fada din. A kwance kuma lullube ta sameta saman gadon,tamkar kwatankwacin yadda ake lullube gawa. Tashin hankali me tsanani ya sanya tanja ta kasa wani motsin arziqi bare ta suturtata da riga. Don tunda ta janye bargon sau daya ta fahimci meye ne maina ya aikatawa sultanar. Da sassarfarta ta qarasa gadon zuciyarta na yankewa tana kuma raya mata da gaske sultana ta rasu. Ta miqa hannu tana janye blanket din,amma kuma cikin wani irin mahaukacin shock ta sakeshi tana kauda kai zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi kamar zata tsinke daga qirjinta "La haula wala quwwata illa billa" ta fada da mugun qarfi bayan lokaci guda kwanyarta ta gama gaya mata meye ne ya fara faruwa da sultana din kafin ta mutun. "Ya kasheta din ko?,ni dama na sani,jikina dama yanata bani,da biyu kenan ya turani biki yace bazan tafi da ita ba" bibi dake qarasowa cikin dakin ta fada jiki da muryarta dukka suna rawa,tanja dake bayanta tana qoqarin riqeta gudun kada ta fadi. Hannu takai itama zata yaye bargon,saidai tuni ama tasa hannu ta ruge blanket din da kyau wani abu yana tsaga zuciyarta. Koda mutuwa sultana tayi ba zataso bibi taga abinda idanunta suka gani ba,koda mutuwa sultana tayi ba zataso bankadar asirinta ba,koda mutuwa kuma sultana tayi ba zataso bibi taga abinda xai xamewa zuciya da ruhinta miki ba,miki kuma na har abada "Ki barni naga fuskarta,ki barni nayi mata kallon qarshe" bibin ta furta da wani irin mugun rauni da ya sanya hawayen idanun ama zubowa "Bata mutu ba bibi,kada kije fa ki fadi" ama din ta furta da confidence tana riqe hannun bibi din da kyau. Ganin hakan bazaiyi ba sai kawai ama ta miqe daga wajen ta kama hannun bibin tana jayeta daga dakin "Na miki alqawarin sultana ba zata mutu ba bibi,na daukar miki wannan alqawarin" "Hamdiyya sultana ce fa?" Bibi ta fada furucin na fita daga qasan zuciyarta "Na sani bibi" "To meye Aliyyu yayi mata?,me ya sameta?" Ta jefa tambayar ga ama din,don ta karanci wani abu saman fuskarta. Qasa ama tayi da kanta tana qoqarin hana idanunta fidda hawaye karo na biyu "Ba lokacin wannan bayanin bane bibi kiyi haquri,sultana nada buqatar ganin likita" ama ta fadi tana zame hannunta daga na bibi bayan ta tabbatar ta nesantata daga dakin,sannan ta juya da hanzari ta koma dakin sultana din. Da kanta ta daga sultana din bayan ta sanya tanja ta dauko wasu kayan ta sauya mata. Jinin daga gani saman gadon ita kanta ya firgitata ainun. "Zan fita da sultana ki kulle dakin,kowa ma a gidannan banason ya shigo dakinnan har sai na dawo,koda bibi" "To" tanja ta fada har yanzu jikinta da zuciyarta suna rawa,saboda gani takeyi tamkar sakacinta ne ya jawo komai, tunda bibi a hannunta tabar amanar sultana. Har sun shiga mota ita da tanja dake rungume da sultana wadda har zuwa yanzu bata motsa ba bibi ta qaraso. Kallo daya ta yiwa fuskar sultana din ta janye idanunta zuciyarta na sake bugawa tare da yin rawa. Bude daya side din tayi ta shiga "Muje hamdiyya,bazan iya zama ba" ita kanta ama dukka hannunta rawa sukeyi,wannan ya sanya dole modu driver ya karbi tuqin motar. Sauran ma'aikatan gidan da su sukayi saura na tsaye carko carko cikin alhini ba tare da sanin ainihin abinda ke faruwa cikin gidan ba har motar ta fice *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* *BOOK 02 PAGE 02* Wani irin zuciyar ama keyi cikin qirjinta "Maina?,maina?,me yakai maina aikata irin wannan mummunar ta'asar duk da cewa sultana halalinsa ce?" Tambayar data dinga yawo kenan a qirjinta tana sanyawa zuciyarta wani irin zafi. Zallar rashin imani da tausayi kawai ta hango tattare da maina din wannan karon,abinda bata taba gani ba tattare dashi,yana da zafin zuciya,yana da tsananin fushi,amma sam bashi ta gefen bushewar da rashin tausayi,hasalima cikin halittarsa tausayi yake,yana kuma daya daga cikin abinda yasa tayi bore a shekarun baya tayi GUDUN K'ADDARA,amma kuma sai gashi yanzun alamu na gwada mata dukka wani dagewa da taqarqarewarta wajen gujewa qaddarar kamar ma biye take da nata sawayen qafa da qafa. Sam bibi ta rasa ma wanne irin tunani zatayi,gaba daya kwanyarta ta toshe,da waye zata tarbi wannan babban tashin hankalin?,waye zaya tayata dauka?,waye zai iya?,kawai sai ta fidda waya tayi kiran aba ta gaya masa kai tsaye asibitin da zai sameta ba tare data qara komai akai ba. Rufe ido ama tayi tana jin bugun zuciyarta har bibi ta gama waya da aba,ta sani dole zaya sani,kuma a yau din itama bata goyon bayan aliyyu,hakanan ba zata iya tare masa komai ba daga zazzafan hukuncin duk da zaya fuskata daga familyn MAYAK'I. Wayarta ta fidda har yanzu jikinta yana rawa,ta lalubi number wayar Dr chafa'atou. Amintacciyar likitarta qwaya daya tal cikin asibitin da ya kasance wajen karakainar familyn MAYAK'I,duk da a yawancin lokuta home service ne ake musu,sai idan ta baci irin haka "Ki shirya keda wasu likitocin gamu tafe da mata lafiya,amma don Allah J'ai besoin d'intimité(ina buqatar sirri)" "Ne vous inquiétez pas(kada ki damu),zaki samu sirri har fiye da yadda kikeso in sha Allah" Dr chafa'atou ta amsa mata cikin bata tabbacin da yayi gaining mata wani dan qaramin qwarin gwiwa. Suna isa aka fidda gado,bisa rakiyar dr chafa'atou da kanta suka dauki sultana zuwa ciki. Bibi da ama din duka suka taka zuwa cikin suma tanja dake share qwalla tana biye dasu. Daga ama har bibi ba wanda ya samu qwallar ta fita daga idanunsa bare ya samu sassaucin radadi da tashin hankalin da yake ciki,hakanan duka su biyun duka gagara zama zaman tsararrun kujerun dake lubby din wanda aka tanada musamman saboda zaman jiran tsammani irin haka. Kimanin mintuna ashirin suna a haka kafin ama taja wani zuzzurfan numfashi "Indai baki zama jaruma ba hamdiyya sai yaushe?,ke zaki bawa kowa qwarin gwiwa kuma ke zaki zama jagorar kowanne tashin hankali da zai ruftowa a halinki" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata cikin qarfafa gwiwa,maganar data taso tun daga can wani saqo na zuciyarta,ya kuma bata qarfin gwiwar dosar bibi. Hannuwan bibi dukka biyun ta kama tana karantar tsananin tashin hankalin dake kwance saman fuskarta. Ko kadan bataga laifi ga hakan ba,don kuwa koda itace fiye da haka ma zai iya fuskantarta. Duk da cewa a yanzun tana kyautata zaton tana jin fiye da abinda bibi keji cikin qirjinta. Ko ba komai duk tsiya sultana tatace,ga kuma wanda kuma yayi barnar ya kasance wani sashe me girma na jiki da zuciyarta "Kiyi haquri bibi ki zauna,tsaiwar tayi yawa haka" ama ta furta cikin laushi. Tsakiyar idanun ama bibi ta kalla,kaman zatayi magana sai ta fasa,tabi ama din har zuwa sanda ta zaunar da ita,sannan ta koma bakin qofar dakin da suka shiga da sultana tamkar me jiran qofa. Dakin dai ta zubawa dukka idanunta,duk wucewar daqiqa daya sai bugun zuciyarta ya qaru,tayi imanin inda ace ayau tana dan qaramin hawan jini babu abinda zai hanashi hauhawa,wataqila yakai jallin da zaya sanyata zubewa. Ko a yanzun ita daya tasan me takeji,musamman da take duba agogon hannunta take ganin yadda daqiqoqi ke shudewa ba wani motsi daga cikin dakin. Su biyu ne cikin dakin suke checking na sultana,amma daga ita har Dr nadra ba wadda yanayin da suka riski sultana be ratsasu ba. "Wanne mahaukacinne yayi mata irin wannan mummunar fyaden?" Dr nadra ta fadi tana zare glasses din idanunta bayan sun tabbatar da cewa dole sultana na buqatar stitches ta ciki da waje,stitches din me me yawan da ko haihuwa tayi iyaka kenan "Ban sani ba Dr......amma kuma....J'ai entendu des nouvelles(naji wasu labarai)kwanaki kaman sun mata auren gida da cousin din mamanta fa.....Je pense(ina tsammanin)daren farkonsu ne yaje mata da gagggawa irin ta matasan yanzu,kinsan kusan dukkaninsu a kame suke" "Wanne irin daren farko ne haka DR.....baki lura da ciwon dake gefen idanunta fa?,ina tsoron da wuya idan bai taba lafiyar idanunta ba..... kalli fuskarta fa da kyau Dr" hannu dr chafa'atou ta miqa tana juya kyakkyawar fuskar sultana data sauya saboda kumburi da kuma jazur din da tayi "peut être(maybe)ko tayi masa taurin kai ne..." Ta fadi a mugun sanyaye,saboda ita kanta yadda idon dake bangaren hannun hagunta yadda ya daga din sosai ya sanya mata shakka da kokwanto. Basu buqaci kowa ba cikin qananun ma'aikata,dr chafa'atou da dr nadra su suka gyara jikinta tsaf bayan sun tabbatar da dawowar numfashinta dake fita a hankali a hankali kamar ana sammata shi,sai da suka tabbatar da daidaituwarsa sannan suka fara mata aikin dinkin,wanda sai da suka fara dinne suka sake fahimtar adadin yawan barnar da maina yayi mata. "Sai idan ta farka sai ayi checking idanunta dinna,sabida kumburin da kwanciyar da fatan wurin tayi yayi yawa" Dr chafa'atou ta qarashe bayaninta idanunta saman fuskar aba oncle bashar oncle umar da oncle issoufou,bibi ama da aunty ta'ibah matar oncle umar data biyo bayansu daga baya. Iska me zafi aba ya furzar daga bakinsa. Komai yana jinsa ne tamkar almara cikin kunnuwansa,maina?, aliyyun shi ya aikata wannan ta'addancin akan marainiyar Allah?,koda akace an aura masa ita ai ba lasisin ci mata zarafi irin haka aka bashi ba. "Ba za'a shiga dakinta ba, za'a barta taci gaba da baccinta har sai ta huta sosai ta tashi da kanta,kuma koda ta tashi din bata buqatar hayaniya,saboda abinda ya faru da ita din zai zaman kaman dai dai yake da RÃPÉ ne a wajenta". Dukka idanunta ama ta sanya ta kalli dr chafa'atou kafin tayi qasa da kanta. Kalma mafi girma da muni da tunda take bata taba ganin kalmar da aliyyu ya tsana a duniya irinta ba,tayi fama dashi kan ya shiga harkar kasuwancinta,tafiye tafiyenta da dukkan wani sabgogi da suka shafeta,amma game da harkar qungiyarta ta yaqi da fyadewa qananun yara da mata.... Ko sau daya batayi wahalar gayyatarshi ba,shi da kansa ya shiga saboda mummunar tsana da gabar dake tsakaninsa da abun,sai gashi yau kalmar na shirin lanqwashewa cikin jikinshi. Akwai kyakkyawar kula cikin asibitin da koda babu me jinyarka za'a kula da kai. Hakan ya sanya sukayi zaune kawai cikin farfajiyar da zata sadaka da dakin. Wani irin zama maras dadi da bakuna duka gaza furta abinda ke cikin zukata,sai saukar ajiyar zuciya lokaci lokaci daga zukatan al'ummar wajen. A yanzun basu da wani sauran zanceme amfani da suke ganin zasu tattaunashi,farfadowar sultana da dawowarta cikin hayyacinta shine abu guda daya filo mafi muhimmanci da kowa ke sanya idanu da ran ganinsa. Har zuwa lokacin da lokaci ya cika na zaman ganin maras lafiya ya cika sultana bata motsa ba,wani irin baccin takeyi wanda ko juyawa batayi,abinda ya sake tasar hankalin bibi kenan,har ta fara fidda qwallar da a baya batayi ba "Hamidou.....idan har yarinyar nan ta rasu gwara su gayamin kawai,ni din musulma ce,zan kuma iya daukar qaddarar rashinta,kamar yadda na dauki qaddarar rashin mahaifinta da ma mahaifiyarta gaba daya" kamar ana tsira mashi a qirjinta haka ama keji,duk sanda ta tuna cewa aliyyu shine sila na faruwar komai.....shine musabbabi na wanzuwar ahalin cikin wannan mummunar halin sai taji wani irin nauyi ya sake saukar mata,sai taji tamkar ta nutse a wajen. Kuka daga idanun mutum me shekaru ba abune da kowacce zuciya zata iya dauka ba,bibi bata danya dangana ba sanda suka buqaci tafiyarsu gida da alqawarin bata kulawa har sai da aka dangana da ita dakin sultana,ta kuma gani da idanunta yadda qirjinta ke dagawa da komawa tabbacin akwai numfashi a gangar jikinta "Bazan barta ta kwana ita daya ba" "Zan zauna da ita bibi,zan koma gida na shirya na dawo" ama ta fada tana jin cewa duk duniya itace ahaqqu da daukar wannan nauyin. Bibi bata musanta ba,saboda ita din shaida ne na yadda hamdiyyan ke iya hidima ga kowanne yaro na gidan tamkar daga cikinta ya fito,sai ta juya tana fita a dakin, zuciyarta da bakinta fal da addu'ar samun sassauci wa sultana. Daga ita sai tanja cikin mota,saboda aba ya dauke tsohuwarsa a tasa motar. Barinsu tayi,saboda ta tabbatar a barnar da yaronta ya tafka dole suna buqatar kebewa da tattauna abubuwa masu yawan da ta tabbatar ba lallai taso jin wasu abubuwa ba. Ta musu uzuri,kuma dukka wanda zai zargi aliyyu ko yaga laifinsa tana tunanin itace mutum na farko game da hakan. Tun saman hanya ta gaza jure isarta gida ta taras dashi,zuwa lokacin ta tabbatar koda bai dawo gida ba to yana a kusa da gida din. Tasan cewa zaiyi wuya ya dawo a lokacin da ya saba saboda ya sani shi din me laifi ne,don haka ta soma lalubar number dinsa ta wayarta. Tun bugun farko éteindre(a kashe take)haka computer ta gaya mata,amma tayi burus kaman bata fahimci yaren da computer din ke magana dashi ba ta shiga maimaita kiran nasa babu ji babu gani,saidai kuma amsa daya ce dai ake bata,dole ta maida wayar gefanta ta aje tana jan doguwar qwafa hadi da ajiyar zuciya. Wato yasan ta'adin da yayi shi ya sanyashi kashe dukka wayoyinsa?,batajin wannan lokaci zata daga masa qafa ko qanqani,kafin aba ya hukuntashi itace mutum ta farko da zata fara masa nata hukuncin. Batasan inda bibi da aba suka tsaya ba amma dai ta rigasu isa gida,maimakon ta zarce sassanta sai kawai ta wuce sashen bibi din tana karbar key din dakin sultana data damqa ajiyarsa a hannun tanja. A nutse ta bude dakin cikin sanyin jiki,ta sanya hannu ta kunna makunnin fitilar dakin. Tarwai haske ya gauraye dakin,yamutsatsen gadon da ta tabbatar akai sultana tasha dukkanw ata azaba daga hannun maina ya bayyana cikin idanunta. Takawa tayi a nutse din tana nufar gadon,har tsakiyar ranta tana jin abinda maina din ya yiwa sultana. Koba komai ita din diya macace,kuma tasan irin zafi da radadin da kowacce mace ke fuskanta a duk lokacin da zata rasa wannan abun me muhimmanci cikin rayuwarta koda kuwa an karbeshi ne cikin lallashi riritawa da kuma soyayya,ballantana uwa uba kuma karba ta fun qarfi,karba ta qarfa qarfa da nuna izza isa da iko. Hannu ta sanya ta tattare dukkan abinda ke saman gadon,kama daga zanin gadon da ya gama baci da jini zuwa pillow din da tuni ya zame daga cikin gidansa, blanket dinta da shima jini ya taba,sai kayan sawarta da suka gama zama tsumma. Sanda take rungume da zannuwan gadon zuwa toilet din sai taji zuciyarta tayi nauyi,data waresu cikin toilet din ta fara wankesu kuwa dukka qwalla da zafin da zuciyarta keyi wanda taketa riqewa sai ya gaza riquwa. Wata siriryar qwalla tabi ta gefan idanunta tana bin jinin da kallo,tausayin sultana ya tsargama zuciyarta irin wanda bata taba ji ba. Wannan zallar rashin imani aliyyu ya gwada mata,wanne laifi tayi masa da zafi haka daya zabi yiwa rayuwarta wannan ta'addancin?,ba zata qyale maina ba koda kowa kuwa zaice a daga masa qafa. Zaiyi wuya a yawan jinin data gani jikin zanin gadon yarinyar bata buqaci qarin jini ba. Cikin raurawar zuciya ta dinga wanke zanin gadon zuwa blanket din,abinda tsahon rayuwarta bata taba yi ba da hannuwanta. Cikin mintuna arba'in ta kammala wankesu tas duk kuwa da nauyinsu,ta koma ta kintsa dakin shima tamkar ba hamdiyya abdu me kano ba. Tana kammalawa bibi na turo qofar dakin,sai ta saki siriryar boyayyar ajiyar zuciya da bibin bata isketa tana tsaka da wanke kayan da haidar din yayi aika aikarsa akai ba. *_wanda bai samu guri a HUGUMA CLOSET ba yayimin magana na sama masa 08187255862_**_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* *BOOK 02 PAGE 03* _______________________________ *_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_* *_SUTURA ABAR TUNQAHO_* *_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_* _Magana akeyi ta_ *UMMU MAHNOOR LUXURIES* *UMMU MAHNOOR LUXURIES* _GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_ *_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_* *_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_* *_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_* *KYAU* *QUALITY DA DAUKAN HANKALI* *LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA* *GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA* *_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_* 08135142610 *INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES *FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA *_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_* *_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_* *_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_* *TASTED AND TRUSTED*👌👌👌 _______________________________ Ido suka hada da bibi,dukkansu sai aka rasa me cewa dan uwansa wani abu,duk kuwa da cewa alamu sun nuna kowanne bakinsa cike yake fal da maganganu. Qarasowa bibi tayi ta zauna tana duban ama,ba tare data buqata ba ama ta sulale ta zauna aqasa tana duban bibi "Har yanzu kunqi yimin cikakken bayanin meye maina ya yiwa sultana?" "Ya karbi budurcinta ne bibi ta qarfin tsiya" ama ta amsa mata kai tsaye kanta a qasa tana me matuqar jin nauyin bibi din,don babu magana kwatankwacin hakan data taba ratsawa a tsakaninsu,uwa uba babu wani buqatar ci gaba da boyewa bibi din,don kuwa me afkuwa ta riga data afku. Dif bibi tayi tana juya abun cikin ranta,duk da ta riga ta gama hasashen komai cikin ranta da zuciyarta "Bansan da wanne baki zan fara neman gafararki ba bibi...." Katseta bibi din tayi ta hanyar daga mata hannu "Daga haidar har sultana waye bare?,waye zan ware nace ba nawa bane hamdiyya?" Ta fada da wani irin tune na sarewa da sanyin gwiwa "Ni babu abinda zancewa da ubangiji na saidai ALHAMDULILLAH har da ya haskamin,ya kuma hanani nutsuwa sai dana tabbatar na maida sultana halalinsa. Yau inda ace ita din ba halalinsa bace ya aikata mata hakan nayi imanin zuwa yanzu wala'alla ina kushewata......saidai duk da hakan......." Ta fadi daga qarshe muryarta na karyewa da wani irin yanayi "Duk da hakan abinda yayin banbancinsu kadan da fyaden bibi......sultana nawa take bibi?,duka duka shekarunta nawa?,a musulunce ya kamata a nufeta a haka?,bibi....... kinsan dinki nawa aka......" kasa qarasa tayi saboda yadda zuciyarta ta karye hawaye ya sake tsargo mata a karo na biyu. "Akul......kul kika sake bari hawayenki ya fita akan wannan batun,idan ba haka ba zamuyi mugun samun sabani ni dake,kin manta masifar hawayen uwa akan d'anta?" Bibi ta gada a hargitse kuma cikin gigicewa. Ba aliyyu takewa kuka ba sam sam sam, a'ah tana tuna girma da masifar zafin stitches ne koda jikin babbar mace bare sultana da duka duka bata wuce raino ba. Sau uku tana zirya sashen maina don ganewa idanunta ko ya shigo gidan kafin ta fita amma bataga alama ba,haka ta shirya duk wani abun buqata ta dauki daya cikin masu aikinta da driver dinta suka koma asibitin. A hanyar komawar dai duk sammakal,tunda ta zauna cikin motar zuciyarta ta lula a tunani. Fuskar aba take hangowa kawai,har ta fito daga gidan babu wata magana data hadata da shi,ta tabbatar kuma abunne yake dukansa kamar yadda yake dukanta. Cikin qanqanin lokaci moudu driver ya sauketa cikin asibitin. Shi ya fiddo komai da tazo dashi. Abinci ne tasa zunnira ta shirya cikin qananun warmer's masu kyau,saboda batasan sanda sultana zata farka ba,kada ta farka cikin dare ta kuma buqaci abinci,sai kuma kayan sanyawar sultana din da wasu qananun kayan buqatu nata. "Idan ba damuwa kaje ka shirya ka dawo,ina da buqatar ka kwana cikin asibitin tare damu,don bansan meye zai iya tasowa ba na gaggawa" tace da moudu sanda ya gama kwashe kayan tsaf ya shigar mata dasu ciki,ta furta maganar tana fiddo kyawawan qafafunta dake sanye cikin wani rufaffen takalmi maras tudu "To ba damuwa ma'am in sha Allahu" ya amsa mata a ladabce. Akwai taqaitar zirga zirgar jama'a sosai cikin asibitin,abinda ke alamta maka cewa lallai dare ya soma tafiya. Cikin wani irin kasala mutuwar jiki da rashin jin dadi jiki da kuma na zuci take takawa har ta isa dakin. Ta iske qwararrun nurses biyu zaune a dakin,suna hirarsu qasa qasa ta yadda ba zata damu mara lafiya ba bare ta tadashi. Sunfi kowa sanin ita din wacece cikin qasar nijer,don haka girmamawa ta musamman suke bata. Sannu tayi musu cikin halin sauqin kanta idan taso,suka amsa mata,sannan suka sake duba komai,kama daga file din sultana,ruwan dake shiga jikinta da sauransu suka tabbatar komai yana kan order "Zamu wuce ma'am,duk abinda kk da buqata akwai waya da zaki kira(ta fada tana nuna mata inda wayar take a girke)" "merci(na gode)" ama ta furta idanunta akan sultana "c'est bon" suma suka maida mata amsa sannan suka nufi qofa suna mata sallama. A hankali ta matsa gaban gadon tana sake dora idanunta akan fuskar sultana. Kyakkyawar baby face dinnan,wadda bata rabo da tsiwa da rashin kunya gaba daya ta canza,qaramin bakinnan da baya rabo da murgude murgude yau din gaba daya a kumbure yake. Kyawawan idanunta masu wani irin maiqo kaman an diga ruwa a yau din ba sosai kake hangosu ba saboda kumburin da gefansu yayi. Wani abu taji ya motsa zuciyarta,karo na babu adadi taji abun ya sake taba zuciyarta sosai. Inda ace saddi mace ne kwance haka cikin wannan halin wani d'a namiji yayi masa haka ya zataji?. Tambayar data sanyata jawo kujera ta zauna sosai gaban gadon tana ci gaba da kallon fuskartq zuciyarta kuma na hakaito mata yadda abun ya gudana tsakaninsu,wani nauyi na sake sauka mata a qirji. Fuskar nafessa take hangowa "Ya rabbbb.....kada ka kamani da laifin gudun qaddarar da nayi,ya ilaheee ASTAGFIRUKA" ta furta a fili saidai can qasa hawaye suna cika idanuwanta. A hankali sai zuciyarta da kuma tunaninta suka fara komawa baya suna mata tunin wasu abubuwa da suka faru shekarun baya da suka shude. *_WANNE QULLI NE ZARGE QARQASHIN WANNAN IYALI DAKE DADADADDEN TARIHI?,SANIN KOMAI DANGANE DA TARIHIN WANNAN AHALI SHINE TAMKAR MADUBI HASKE KUMA FITILA TA LABARIN GABA DAYA_* *_WHO DIED? WHO LIVES?_* *_MUHAMMAT MAYAK'I_* Dattijon arziqi shine sunan da jama'a da yawa ke kiransa dashi cikin ainihin mahaifarsa dake qasar nijer garin AGADEZ. Garin da ya zama tushe kuma makafar buzayen dake qasar nijer din. Babban family garesu wanda yayi tambari sannan yayi suna ta fannin ilimi siyasa da kuma arziqin kansa. NADEEYA na daya daga cikin mutanen da suka sake sanya sunan family din MAYAK'I yayi shuhura. Qasaitacciyar 'yar boko 'yar kasuwa,wadda Allah ya huwacewa baiwar kwanya basira da iya sarrafa rayuwa. Gefe guda kuma tana daya daga cikin matan da koda cikin buzaye kyawunsu na dabanne. Wani irin kyau da akayi ittifaqin har xuwa yanzu shike bibiyar jininta,'ya'ya da kuma jikokinta. NADEEYA din ta fita daban,saidai a yanzun za'a iya cewa HAMDIYYA ABDU ME KANO wato AMA ita ke biye da sawayen NADEEYA da dukka tarin wadannan abubuwan da nadeeya din ta mallaka tamkar dama can ama ta fito daga tsatson nadeeya dinne. Saidai Sam,ita kanta ama batasan nadeeya da idanu ba wadda su aba ke kira da granny saboda ita din kaka ce a wajensu. Ko cikin mata nadeeya ta dabance,wanann ya sanya ake tunanin ya zame mata kambun data riqa wanda ta zauna gaban Bobbi wato kakansu aba ita daya tal!,har zuwa lokacin da bobbi din ya rasu ya barta. Ita daya taci gaba da kula da 'ya'yanta cinsu shansu karatunsu har zuwa tarbiyyarsu. Allah ya albarkaceta da yara maza ne gaba daya su biyu,tayi mata sau biyu suna rasuwa,duk yadda takeson ta ganta da 'yar budurwa haka ta haqura. Allah ya raya mata yaranta rayuwa me kyau. ABDALLAH shine babban d'anta da ya zame mata gishiqi kuma madogara,wanda ta dora bisa dukkan wasu hanyoyi nata saboda halin rayuwa. Ya kama kuwa fiye da yadda ma takeso,wannan ya kwantar mata da hankali,saidai duk da haka bata nutsu ba har sai data tabbatar ta aurar dashi shi da me binsa wato ABDURRA'UF. ABDALLAH ya auri bibi nana halimatou asalin bafulatana kuma buzuwa 'yar asalin garin AGADEZ. Kafin ya samu daukar halimatou bibi yasha fama a lokacin saboda wani irin farinjini Allah yayi mata,hakan kuma itama baya rasa nasaba da zallar kyau da Allah ya huwace mata,uwa uba tana da wata irin nutsuwa kamun kai da cikakkiyar tarbiyyar da takai duk yammatan unguwarsu idan an tashi kwatance da ita akeyi musu. Gida guda nadeeya ta gina musu ita da yaranta,saboda tana da sha'awar su rayu tare. Wani irin gini tayi musu mahadi ka ture,ginin da saidai gidan sarakuna da manya manyan attajirai irinta. Rayuwarsu na tafiya kaman yadda nadeeya ke buri,tsufa yana dada kamata,amma kulawar da take samu ya sanya take da cikakkiyar lafiyar da ciwo dai saidai irin wanda me dattijan da shekaru suka soma musu rubdugu basa rabuwa dasu. A hankali bibi ta soma hayyafa,saidai faccalarta aseeya har zuwa lokacin shuru. Ba wanda ya daga mata hankali ko ya daga nasa hankalin,saboda dukkansu masu aiki da ilimi ne. Dukkan me rai mamaci ne,sanda bibi keda yaranta maza har guda shida a lokacin ajali ya saukarwa granny nadeeya,lafiya lau akayi sallama da ita da dare ta tafi ta kwanta aka wayi gari babu ita. Sunyi kuka,sun kuma shiga tashin hankali sosai,saboda tsanani sabo da shaquwa da kulawar da suke samu daga yaran nata har jikokinta. Tayi masifar dasa musu wata irin qaunar juna a tsakaninsu,bawa juna kulawa da damuwa da damuwar juna, dabi'ar data bi jininsu qwarai da gaske,ta kuma zarce cikin jikin jikokinta har zuwa sanda suka zama cikakkun samari. MOHMOUD da HAMIDOU sune yaran da bibi ta haifa da tazarar shekara hudu a tsakaninsu,batayi haihuwa ta uku ba kuma sai data shekara biyar ra haihuwar HAMIDOU(ABA) sannan ta haifi MUHAMMAT,sai oumar bashar sannan issoufou autah. Babban tashin hankalin da suka fuskanta bayan rasa nadeeya shine na rasuwar mahaifinsu alhaji ABDALLAH wanda gaba daya sunansa yafi fice da sunan kakansu na ainihi wato MAYAK'I. Rasuwar da tayi mugun girgiza su,ta kuma daga musu hankali,don shi dinma kamar dai nadeeyan,babu wani ciwo,face dai tunanin da suke rasuwar mahaifiyar tasa ya maqale a rai har ta zame masa ajali. Hakanan cikin wani irin ciwo da rashin rabo sukaci gaba da rayuwa,cikin rashin jin dadi da kuma walagigi saboda basu saba rayuwa haka ba su kadai,don kuwa a sannan baaba ABDURRA'UF yayi nisa da agadez,bama agadez ba gaba daya nijer,tun bayan rasuwa granny da aka bashi gadonsa ya lula duniya fatauci. Tun bayan tafiyarsa sai matsalolin rayuwa suka dinga taso musu,wadansu mutane sabbin fuska da basusansu ba,kowa yazo zaice yana bin nadeeya ko abdallah abu kaza,sai sunyi duba da wani abu me qwari cikin dukiyarsa suce yayi jinginarsa a garesu. Babu wanda bibi ta tsaya ja'inja dashi,ta barsu kawai,a sannan mohmoud yaso ya taka birki duk da kwata kwata shekarunsa a sannan basu goma sha biyar ba amma bibi ta hanashi "Zukatan mutane a yanzu sun qeqashe da son abun duniya,komai na duniya a nan aka sameshi kuma a nan za'a barshi,yau ina wanda ya tara dukiyarma?,ka barsu nafi buqatar taka rayuwar akan abinda aka tara muku,watan watarana sai kaga Allah ya albarkaceku da abinda yafi abinda kuka rasa" qananun shekaru da kuma zantukan bibi ya sanya hakanan suka zuba ido,basu qyalesu ba saida suka tabbatar sun rabasu da manyan kadarorin da mayak'i ya mallaka. Shekarar da mohmoud ke aji na biyu na university,hamidou (aba) yake ajin qarshe na secondry school rayuwa ta tsananta a garesu,gidan da suke ciki ma ya soma niyyar gagararsu zama a ciki. MOHMOUD wani irin halitta ta daban Allah yayi masa,bibi tasha daga hannu ta godewa Allah da ya bata kyautar mohmoud a matsayin d'a. Yana da kyakkyawar zuciyar da zai iya yin kuka saboda kawai wani yayi dariya. Yana da kyakkyawar zuciyar da zai iya hanawa kansa saboda wani ya samu,yana da kyakkyawar zuciyar da zai iya wanzuwa cikin radadi rudani da firgici muddin wani zai wanzu cikin walwala nutsuwa da kuma sukuni. Wanna dabi'a tasa bawai iya cikin gida ba har zuwa ga mutanen waje. Ranar da abun yaci tura ranar da ya kammala jarabawarsa ne daga aji biyu zai shiga aji uku,sakamakon jarabawar hamidou kuma ya fito,an gama komai na cuku cukun tafiyarsa jamia,amma kudin da ake da buqata don yiwuwar hakan basu babu dalilinsu. Idanunsu jajur yayi zaune gaban bibi yana gaya mata ya ajjiye karatunsa,ya yanke shawarar bidar kudi kota halin qaqa kota kuma wacce hanya muddin wannan hanyar halastacciya ce don ya kula da ita ya kuma kula da rayuwar qannensa "Amma mohmoud ta yaya?,karatun naka dake sake nisa ta yaya zaka ajeshi?" Kai ya girgiza "Sam sam karatuna a yanzu bashi da amfani,koda na yishi bazanyi farinciki ba mahaifiyata da qannena da basu da kamata suna cikin matsi da buqatar rayuwa" daga bibi har hamidou tsit sukayi suna duban mohmoud,ya fadi maganar ne har tsakiyar rai da zuciyarsa. Daga kuma randa ya furta wannan batu ya fara aiwatar da abinda ya tsara din kamar yadda yace. Tinja tinja aka dinga yi tsakaninsa da hamidou,yace shi kuma sam bai yarda ba,bazai zama silar rujewar farinciki da kuma burikansa da shi yafi kowa saninsu ba. MOHMOUD bashi da wani babban buri a duniya da ya wuce ya zama cikakken likita,ya shaidawa bibi shine zai tallafi karatun yayan nasa,idan yayan nasa ya gama shi yayi nasa. Wani kallo sheqeqe ya watsawa hamidou,har yanxu wannan kyakkyawar soyayyar da qaunar da granny nadeeya ta dasa musu yana biye da jinin jikinsu "Saboda gani babban banza ko?, bakaji mr bahausa suka ce ba?, babban wa magajin uba ko?,to gwara ka soma shirin tafiyarka makaranta,don ko bakaje din ba dama karatuna tangal tangal yakeyi ai, karatun lafiya sai dan wane da wane kai kafi kowa sanin haka,ni ba babbabn kwabo bane ra zan zauna qanina ne zai tallafi buqatun qannena dana mahaifiyata ba,indai nayi hakan meye amfani na?,meye amfanin girman da Allah ya bani?". Tun daga lokacin da ya ajjiye karatunsa ya shiga neman kudi idanu rufe saidai bisa tsaftatacciyar hanya,baya raina abinda zaya kawo masa kudi komai qanqantarsa koda kuwa kwasar kashi ce. MOHMOUD dan gayu dan gata sai gashi tashi daya rayuwa na tamaula dashi tana sauya masa kamanni da tsarin rayuwa. Yasha dawowa gida ya kasa bacci saboda ciwon jiki ciwon kai ko ciwon qafafu,amma baya bari kowa ya sani. Saidai kuma wannan dashashiyar qaunar tana nan tana kewayawa,duk wani motsin MAHMOUD din bisa idanu da kiyayewar HAMIDOU ne, hamidou din yasha boyewa yayi kuka saboda ganin yadda yayan nasu ke bautar da kansa saboda su,iya yadda yake tunanin yaa mohmoud yana sonsu sai a yanzu ya tabbatar abun ya zarce haka,ya kuma shallake hankali da tunaninsa. MOHMOUD ne faskare, MAHMOUD ne tura ruwa, MAHMOUD ne dako, MAHMOUD ne share share goge goge da wanke wanke a gidajen saida abinci duk don kada karatun hamidou ya samu tangarda,kada karatun su oumar ya tsaya,kada bibi ta buqaci wani abun ta rasa,ya gwammace shi yayi kuka muddin su zasuyi dariya. Ranar da ya gaza jurewa ganin dan uwan nasa ahaka cikin wani darene da MAHMOUD din ya kasa bacci saboda radadi da hannunsa ke masa saboda yawan itacen daya faskara duk don ya qarasa hada kudin registration din hamidou. Yana ganin hamidou din ya motsa yayi saurin boye hannuwansa,saidai kuma tuni shima ya kama hannuwan yana kalla. Wasu hawaye suka zarto daga idanunsa yana dubansa "Hamma....wannan abun da kakeyi a kanmu yayi yawa,ka sassauta gangar jiki da zuciyarka don Allah hamma" hamidou ya fada yana hawaye. Jawoshi kawai mohmoud yayi yana bubbuga bayansa "Inajinku ne tamkar 'ya'yan da suka fita a ciki na,zuciyata da ruhina ba zasu taba samun nutsuwa ba muddin dayanku na cikin buqata" sun jima a daren hamidou yana gasa masa hannunsa,tun kuma daga ranar yasa ya masa alqawarin daina boye masa wasu abubuwan,sannan wasu lokutan tare suke fita ayyukan,amma yanayin karatu ba kasafai yake barin hamidou din binsa ba. Shima kuma MAHMOUD din yafison hakan,yace yafison yayi zamansa ya maida hankalinsa akan karatunsa shi shine farincikinsa.......*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* *BOOK 02 PAGE 04* _________________________________ *_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_* *_SUTURA ABAR TUNQAHO_* *_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_* _Magana akeyi ta_ *UMMU MAHNOOR LUXURIES* *UMMU MAHNOOR LUXURIES* _GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_ *_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_* *_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_* *_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_* *KYAU* *QUALITY DA DAUKAN HANKALI* *LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA* *GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA* *_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_* 08135142610 *INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES *FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA *_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_* *_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_* *_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_* *TASTED AND TRUSTED*👌👌👌 _________________________________________ *HAMDIYYA ABDU ME KANO* Yarinyar da tafi kowa kyau cikin school din,ajjiye kyau a gefe,idan ana batun gata za'a iya cewa kaf makarantar babu diyan da ya kaita gata wala mace ko namiji. Ita din diya ce ga attajiri alhaji abdullahi me kano,mashahurin dan kasuwa wanda inda arziqi yana yawa za'a iya cewa nashin har yayi yawa. Arziqi da aka nemeshi da zuciya da kuma qwanji,aka tara shi cikin albarka iyaye data al'umma. Yaranshi uku kacal a duniya,tajuddeen da ake kira da taj,sai mebi masa abdulhakeem sai kuma 'yar daya daya 'yar gatansu kuma 'yar gaban goshin kowa wato hamdiyya(ama). An haifi hamdiyya ne a lokacin da kowa ya fidda rai daga sake samun haihuwar mahaifiyarta hajiya aisha a duniya,bayan wasu shekaru harsu abdulhakeem sun fara yin hankali,don a qalla a cikinsu babu wanda ya bata qasa da shekara goma. Tazo a dai dai sanda suke da kwadayin qananun yara a gidan,kuma tazo a jinsin diya macen da basu da ita,wannan ya sanya gata yayi mata rubdugu tako ina,kowa kawo nashi gudunmawar gatan yakeyi. Idan akace gata ana nufin gata me sunan gata,gatan da ya sanya take cike da haushin yadda rayuwar sultana take,domin kuwa idan za'a dora mizanin gatan da sultana ke samu da wanda ita ta samu a zamanin quruciya zata iya cewa sultana din bata samu kaso daya cikin goman nata gatan ba,saidai natan bai hanata samun cikakkiyar tarbiyya da kulawa ba. Sam sam alhaj abdullahi da aishatu matarsa basa cikin jerin sahun mutanen da suka aza dukiya a gaban tarbiyya yaransu. Sau da dama yanayin tarbiyya yaran alhaji abdullahi na bawa daruruwan mutane mamaki. A yadda mahaifinsu keda kudi ruwa ruwa kamar su kasheshi,ko kadan ba zaka taba tsammatar samun tarbiyya haka daga yaransa ba,sakamakon yadda ya zama kamar wani tambari ko al'ada na yaran da iyayensu ke da hali,sukan tashi a sangarce,babu ganin girman babba bare akai ga sanin haqqin qarami,gaisuwa ma kam ba kowanne ke tashi da iyata ba,wanda wannan babban kuskure ne ga rayuwa,domin da 'ya'ya da dukiya dukka amana ce kuma jarrabawa ce,idan ka jagorancesu ta hanya me kyau kaci moriyarsu cikin kwanciyar hankali da farinciki,idan ka jasu kuma ta akasin hakan lallai bone da nadama yana nan tafe. Hajiya aishatu mahaifiyar ama itace haifaffiyar qasar NIJER, CIKAKKIYAR buzuwa gaba da baya wadda har rayuwa tayi mata zurfi cikin nijeria bakinta baya fidda hausa tar kamar yadda ya kamata. Sun rayu kuma tashi da tsananin zumunci,daga dangin mahaifi har na mahaifiya babu wanda suka bari a baya wajen sada zumuncinsu,wannan ya sanya alaqa me qarfi tsakaninsu da dangin mahaifiyarsu dake nijer. A duk sanda suka samu hutu suna ware lokaci sosai da zasuje ga dangin mahaifiyarsun suyi masu kwanaki su juyo,wannan ya sanya nijer taso janye hamdiyya banda tsananin son da suke mata da tuni zamanta a Nigeria ya zama labari,saidai duk da hakan bayan ta kammala secondry school kakarta ta dauketa da zummar hutu kawai zatayi ta dawo,sai gashi zama ya miqa,duk da yadda abbanta dama su abdulhakeem ke jelen ta dawo gida "Yo ku meye naku ne bayan kowannenku yana nashi gidan da iyalinsa?,ku jiyemin yara da sanabe?" Hajja kakarsu ta fadi tana kama haba "Gidan ne ba kowa fa,daga maama sai masu aiki" tajuddeen ya fada "Sai kuma kayita yi,amma tabbas jikina ya bani nijer saita janye hamdiyya" ta fadi saboda yadda taga tana sha'awar qasar sosai da son zuwa tare da son zama a cikinta. Kai tsaye qanin mahaifiyarta ya soma mata cuku cuku sanda aka fara diban dalibai a matakin karatu na gaba da secondry. A tsarin jami'ar hamdiyya bata da wani aibu ko nakasu da zaya hanata samun gurbi. Results dinta sunyi kyau har abun ya dinga basu mamaki,saidai kuma ba abun mamaki bane,saboda baiwar wata budaddiyar kwanya Allah ya bawa ita hamdiyya din,abun kuma sai ya hadu da nacin son karatu da take dashi. Sanda ta shiga makarantar hamidou(aba) yana aji uku,kuma shine president na makarantar gaba daya. Ranar data fara zuwa ranar ta fara ganin aba din, saboda a ranar sun gudanar da zanga zangar lumana cikin makarantar. Tana zaune daga qasan bishiya tana jiran driver ya iso ya dauketa,tanata zumbura baki irin na yaran da gata ya yiwa yawa,tana jin yadda zafin rana ya bude a sararin makarantar ya hadu da rairayin yashi yake bada wani hucin zafi har saman fatarta,daidai sanda dandazon matasan makarantar suke yowa ta area din da take. Tsaki taja me qarfi tana qorafi cikin ranta na yadda ko zafin ranar sukam basuji?. Tana zaune har suka qaraso inda take suna wucewa da ifce ifcensu wanda yake cikin tsari ne ba hauka bare sauka daga tsari. Da idanu take binsu kawai bakinta a tabe daya bayan daya,tanason gano waye shugaban wannan wahalar?,sukam me suka rasa da zasu damu kansu da surutai haka da rally cikin makaranta?. Caraf idanunta ya sauka saman fuskar kyakkyawan matashin buzun. Sanye yake da wasu jajayen kaya da baqar p cap wadda duk da ta dan rufe fuskarsa kadan amma hakan bai hanata hango gumi da yadan jiqa goshinsa ba,ya kuma bada damshi saman kyakkyawar fuskarsa dake da wani irin sassanyan kyau me matuqar jan hankali. Kaf yawun bakinta ya katse,ta qifta idanunta ta sake budesu duka lokaci guda tana hadiye busashen miyau din da yayi saura a bakinta. Tunda take zata iya cewa idanuwanta basu taba tozali da namiji me kyan aba ba. Bata cika buri cikin rayuwa ba,bata da wulaqanci sai son jama'a da take dashi,bata da daukan rayuwa da zafi saboda ta fito daga gidan wadata,amma kuma tana da wani buri qwaya daya da kaf gidansu hatta da abbanta da wasu makusantanta na kurkusa sunsan dashi,wato tana son KYAKKYAWAN NAMIJI. Ba wai abu bane data tsireshi bayan ta girma ba,ko kuma bayan ta fahimci ita dinma me kyau ce ajin farko, a'ah tun tana qanqanuwarta take da wannan dabi'ar. Mama mahaifiyarta bata zafafa mata ba tun daga quruciyar,saidai ta zafafa wajen addu'ar idan ta isa munzali qaddarar aure ta zowa diyartata ubangiji ya hadata da nagartaccen miji salihi kuma managarci. Tun su abdulhakeem suna tsokanarta har suka fahimci da gasken gaske a jininta ne kuma raayinta ne hakan,sai suka daina tsokanar suma sai lokaci bayan lokaci. Akwai tarin maza da suka amsa sunansu,masu kyau irin kyan nan abun kwatance da suke maqurar qaunarta da neman soyayyarta,to amma sai Allah ya sanya mata wani irin hali na shariya da miskilanci. Duk son jama'arta da haba haba dinta miskilar kanta ce idan taso. Bada umarnin da aba yayi wajen dakatawa aje a bada faralin sallah ya sake fusgar hankalinta,tana nan a zaune taron ya watse,ya nufi hanyar masallacin makarantar bangaren maza yana zare pcap din kansa shi da 'yan tawagarsa suna tattaunawa,cire hular kuma da ya sake bayyanar mata da asalin kyansa. Tun daga ranar bata sake ganinsa ba,hakanan zuciyarta bata huta da tunanin waccan ranar ba. Bata kuma sake ganin nasa ba sai bayan watanni shida,karatunta ya soma yin nisa,ana shirye shiryen fara exams da tafiya hutu. A sannan ne dalibai suka qirqiri wasu programs da sukan gabatar a lokuta irin wadannan,ciki harda zaben sarauniyar kyau ta makarantar. A lokacin sai kawai gani tayi sunanta ya fita cikin list din wadanda zasu tsaya a matsayin. Ranta ya baci hankalinta kuma ya tashi. Tana da qawaye tunda ita din macace me kirki,bata raba dayan biyun a cikinsunne wata ta bada sunanta,kuma tunaninta ya tafi kan mutum daya data tabbatar bazata wuce ita bace wato ummuhani mammadou. Koda ta tuhumeta din kuwa ita dince. Fada ta balbaleta dashi akan ba zata shiga ba,tace kuma tun wuri su zame sunanta don ba abinda tazo yi ba kenan. Lokacin aba na zaune cikin 'yan kwamitin tsare tsare ummahani ta shaidawa hafeez wanda shi ya qirqiri abun cewa hamdiyya na buqatar a zame sunanta,ta kuma baiwa hafeez haquri,wanda koda bayan ummahani ta wuce bai fasa qorafi ba "Ita daya ce zata sanya makarantarmu taci wannan competition din,yanzun wace zata maye mana gurbinta?" "A soke wannan cikin tsare tsarenmu hafeez, banason irin wadannan abubuwan" shine kawai abinda aba yace. Bai taba ganinta ko lura da wanzuwarta ba sai ranar da aka fara programs din. Sai kuma a ranar program din da aba yace a soke yaji basu soke din ba,don a wajen aka fara neman 'yammatan da suka shiga suzo su fara rehearsal. Ko motsi hamdiyya batayiba sanda aka kira sunanta saboda tasan tuni ta bada sanarwar fita daga lamarin. Aka dinga maimaita kiran sunanta amma ko motsi,abinda ya sanya MC pointing dinta don shi ya hangota,take kuwa idanu sukayi caaa a kanta. Adadin idanuwan ya sanya kanta sarawa,sai kawai ta miqe tsam ta dinga ratsawa ta cikin jama'a har ta fice daga hall din. Haka kawai aba yaji ranshi yayi matuqar baci,bai wata wata ba ya karbi mic daga hannun mc din ya fara bada sanarwa dakatar da shirin. Sanarwar data hargitsa hall din qananun maganganu suka dinga tashi,shidai a matsayinsa na shugaba ya riga ya zartar da hukunci,ya tabbatar kuma dukka mataimakansa ba wanda zaija da hakan saboda zuwan halayensu kusan iri daya,sai kawai ya saka kai shima yana barin hall din. Baisan tana ta wajejen ba sai daya isa ya tsaya yana furzar da iska sai yaji sautin sheshsheqar kuka kuma ana waya "Kice musu su qaraso su daukeni gida zan koma" idanu ya zuba mata cikin mamakin yadda qatuwar budurwa irin haka ke kuka shabe shabe da hawaye,jajayen labbanta sun sakeyin ja haka bakinta. Taku biyu tayi Don gyara tsaiwarta santsin wajen ya kwasheta zata fadi. Da hanzari yakai mata taimako Allah ya taqaita kafin ya isa gareta ta samu ta dafa wata qaramar bishiya ta tsaya "Ki ding kula mana" ya fada cikin nuna damuwa. Kai ta daga da sauri,idanunsu suka gauraya waje guda,wani irin abu me qarfi ya sauka zuciya da gangar jikin kowannensu,sai kowa cikinsu yayi hanzarin janyewa da baya,yayin da ciwon kan hamdiyya ya qaru har sai data saka hannu tadan riqe kan "Baki da lafiya?" Ya tambayeta yana qoqarin kallon qwayar idanunta. Idonta ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu da bata taba yi ba ta gyada masa kai "Saiki tafi gida ko ki wuce hostel ki nema magani Kisha" ya fadi yana janyewa baya saboda shi din ba gwanin kula mata bane. Ta qasa qasa take kallonsa,qafafunsa sake cikin wasu Black sneakers na motsawa da alama wajen zaya bari "Ka taimakeni ka miqani gida,bazan iya tuqi ba,bani da nisa daga nan" dukka ta bashi maganar lokaci daya. Dan jim yayi yana kallonta duk da baya iya ganin zahirin fuskarta. Kamar zai musanta sai kuma ya tuna da maganar da Bibi ke yawan gaya masu "Su mata ababen tausayi ne,a duk sanda suke cikin taimako ku taimaka musu gwargwadon iyawarku" wannan maganar ta sanya ya koma ya amshi key din a hannunta yana satar kallonta,haka kawai zuciyarsa ke bugawa a kanta tun ganin farko da yayi mata dazun. Ya zagaya ya bude mata ta shiga sannan ya rufe ya dawo ya shiga shima ya tayar da motar yana godewa Allah da ya sanya ya koyi mota da yau baisan yadda zaiyi ba. Yadda yake tafiya a hankali da motar,da alama kuma yana yin hakanne dukka don ciwon kan nata sai ya sake narkar mata da zuciya a kansa,sai take ganin yaa tajuddeen da yaa abdulhakeem tattare dashi,haka suke mata irin wannan riritawar. Zuciyarta nata mata saqe saqe akansa,yayin da shi kuma yayi nisa wajen satar kallonta ta cikin madubin gaban motar yana tsarkake ubangiji da irin kyawun halittar da ya bata. Ita ta dinga kwatanta masa hanya har suka iso gidan,a LOKACIN sai da jininsa yadan daskare na wucin gadi,tsoro kuma ya kamashi na ganin yarinyar da ya rako "Yanzun idan tayi maka wani qazafin fa?" Abinda ya bashi fargaba kenan,amma da yake namijin duniya ne sai ya daure ya cusa hancin motar har zuwa farfajiyar gidan. Sanda dukkansu suka fito a motar sai kowa ya rasa bakin magana,ita tana tauna abinda zatace ne kada ta zubda ajinta da kimarta na mace,shi kuma yana dari d'arin ya kawo kansa gidan dafa kansa. Muryar hajja ta katsesu ta qaraso tare da uncle din hamdiyya. Cikin nuna matuqar kulawa take dubanta kamar tana neman gurin da aka gutsireta tana tambayarta "Ya akayi kika iya dawowa da kanki?,ke da nace ki jira su soja sun tafi dauko mato daga airport suna kusa daku saisu daukoki?" Hamidou ta nunawa hajja tana mata bayanin shine ya taimaketa. Abinda ya daure masa kai harda qarawa abun gishiri da armashi. Kaman hajja ta goyashi haka ta dinga zuba masa godiya tamkar wanda ya qwato mata jika daga wajen kidnappers. Hanashi tafiya hajja tayi,cikin lokaci kadan sai gashi ta sanyashi ta dole ya sake cikin gidan. Cikin mintuna kadan yaga kamanceceniyar halaye tsakaninta da granny nadeeya dinsu da har yau basu manta da ita ba. Ya kusa awa daya tana jansa da hira,sannan ta cika masa gaba da kayan ciye ciye. Koda ya tashi tafiya amana me nauyi ta aza masa,wato amanar kula da jikarta "Ka taimaka.ka karbi wannan aikin,duk da nasan na aza maka nauyi,don Allah,saboda kowacce makaranta akwai bata gari na sani,to amma zasu kiyaye idan sunsan akwai wani namiji a tare da ita,nayi nayi a sama mata masu tsaron lafiya koda mutum biyu ne amma ta qiya,ita wai sam batason irin wannan rayuwar" dan satar kallonta aba yayi,daga yanayinta kawai da yadda yazo ya samu family dinta yasan lallai tana da sauqin kai da rashin daukar rayuwa da zafi,a arziqin da Allah yayi musu yayi imanin inda watace ma sam tabar rayuwa a Nigeria. Tsohuwar ta masa kwarjini da yawa dole ya karbi amanar hamdiyya ba don ya shirya ba. Wanda hakan ya fara kawo alaqa tsakaninsu me qarfi,ta dauke tamkar yayanta,shima kuma kaman qanwarsa,wani lokaci ma tare suke tafiya makaranta cikin motarta,donma yana goggocewa kasancewarsa mutum da ya iya kamun kansa yasan kuma kimar martaba da darajarsa. Duk da haka komai nata saita tsomashi a ciki,idan yaqi ma takan hadashi da tsohuwar dole saboda girmamawa yayi din. Shi da ita dukkansu soyayya tayi musu mugun kamun da basu zata ba,ga hamdiyya dai tasan tabbas ta fada dumu dumu cikin soyyayar hamidou,amma kuma ba zata taba yin abinda zai watsa mutunci da darajarta ta diya mace ba. Abinda bata sani ha hamidou ya fita shiga garari,domin kuwa kusan har walwalarsa abun yaso.tabawa,daga bibi har hamma mohmoud ba wanda bai Kula ba,tambayar duniya ya kasa basu amsa,saboda shi kansa yasan bai daukowa kansa da su turba me bullewa ba,su da suke ririta rayuwarsu ta yaya zai dauko wannan babban aiki?. A yanzun yana tsaka da karatunsa kuma nauyinsa yana wuyan wani mutum ne wato mohmoud,mohmoud din da ya kashe tasa rayuwar saboda ya raya tasa rayuwar?,ta yaya zai iya duban qwayar idanunsu yace ya fada soyayya?. **_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 05 _______________________________ *_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_* *_SUTURA ABAR TUNQAHO_* *_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_* _Magana akeyi ta_ *UMMU MAHNOOR LUXURIES* *UMMU MAHNOOR LUXURIES* _GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_ *_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_* *_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_* *_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_* *KYAU* *QUALITY DA DAUKAN HANKALI* *LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA* *GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA* *_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_* 08135142610 *INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES *FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA *_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_* *_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_* *_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_* *TASTED AND TRUSTED*👌👌👌 __________________________________ ".............ya fada soyayya?,yana nufin kenan aure yake da buqatar yi?,bama fadawa soyayyar ba,wadda ya fada soyayyar da ita, yarinyar dake da gatan da ya kerewa nasa,suke da dukiya da tarin gatan da ya yiwa hankali nisan tazara,kai koda ma ace ya kammala karatunsa ya kama aiki ina yaga kudin auren hamdiyya abdu me kano?,ko yana da kudin aurenta dinmma sakayyar da zai yiwa bibi da mohmoud dake tsaye a kansa ba dare ba rana?,ya tattara 'yan kudinsa yayi aure ba tare da sun mori komai daga gareshi na wahalar da suka sha dashi ba?. Kansa ya girgiza yana bawa kansa amsa da A'AH,ya zama dole ya sake nisanta kansa da zuciyarsa daga soyayyar hamdiyya,hatta da mohmoud sai yanzun yaga an fara tada zancan aurenshi,idan bai manta ba wancan satin yaga ya fara shigo da akwati guda uku bibi na mata wajen ajiya,ta yaya shi da yaie sanya ran zai zamesu musu sanyin idaniya ya buge da wannan zancan?. Dama bai bari ko kadan zancan hamdiyya ya fasu cikin gidansu ba saboda gudun tashin hankalin bibi da kullum tsaronta akansu ne,sai kawai ya yanke shawarar fara janye jiki daga gareta da kuma dukkan al'amuranta. Hakan bai haifar da komai ba saima sake dagula al'amarin da yayi,ta zube dukkan wautar dan fari da shagwabarta,kwatsam sai kawai gashi ta dauko mahaifinta tun daga Nigeria yayo tattaki ya iskeshi har cikin makaranta wai yazo sasantashi da hamdiyya,tace batasan laifin data yiwa yayanta hamidou ba yake gudunta. A ranar hankalinsa yayi matuqar tashi,ganin babban mutum me girman daraja wai yazo gareshi ban haquri?. Kame kame ya dinga yiwa abban don baisan ma me zaice masa ba. Daga qarshe kawao abban ya saki murmushi yana dubansu "Inaga gwara kawai na yanke muku wannan wahalar da kukeyi akan juna,kai yayan hamdiyya,indai ka aminta kanason hamdiyya ka shaidamin zan baka aurenta,ku sasanta kanku bari na baku waje" abinda abba ya fada kenan ya fita daga wajen cin abincin daya kama musu table daya. Kamar zata hadiye zuciyarta haka ama taji sanda taji furucin bakin mahaifinta,tabbas inda ace ita daya ce a wajen ihu zatayi tayi tsalle tayi shewa,amma.yanzun duk yadda albishiri din yakai ga faranta mata dole ta kame kanta ta kuma zuba masa idanu tana jiran jin ta bakinsa. Kau dakai tayi sanda yayi nufin kallonta,a yanzun yana jin bazai iya boye mata komai ba "Ina tsananin qaunarki hamdiyya bazan iya boye miki ba,amma kuma bani da halin aurenki saboda a yanxu nidin ba kowa bane,kuma bani da komai ban kuma bawa kowa ajiya ba,idan nace zan aureki hamdiyya na cutar dake,bani da arziqin riqeki,ki bari kiyi aurenki na gata,ki auri dan gata irinki da zai iya baki irin rayuwar data dace dake..." "Ba wanda yayimin cikin maza babu kuma wanda nakeso saikai, hamidou xan aura ba alatun duniya ba,dukka maganganunka a yanxun ba hujja bane,saidai idan kanaso ka fake ne,ni hamdiyya ban maka ba" ta fadi tasirin sonsa na yawo cikin idanunta da wani irin kaifi. Duk da ba'a mode da zaiyi dariya suke ba amma sai daya murmusa,bayajin tana masa rabin son da Allah ya jarabceshi dashi nata "Baya ga bibi da 'yan uwana ban taba jin soyayyar wata halitta a zuciyata ba haka....." "Indai hakane ka sanya a ranka ni hamdiyya matarka ce,ban kuma fi qarfinka ba" ta tari numfashinsa kai tsaye. A nan gurin ta lalata masa dukkan wani tunani nasa da zazzafar soyayyarta ta hanyar kalaman bakinta,suka rabu suna kewar juna ainun saboda a yau din dukka wani qulli ya kwance soyayya kuma tayi ambaliya ta bayyana kanta. Wajen tara na dare yana rungume da littafi yanason yayi karatu amma ya kasa saboda tunaninta,wayar hannu sai me wadata,su dinma ada akwaita cikin gidan,amma yanzun da rayuwar ke neman fin qarfinsu dole suka sakata a kasuwa suka saida. Yana kwance daga daki yana jiyo hirar bibi da mohmoud,ya dawo daga aiki futu futu da tarin gajiya bibi ta zaunar dashi tace sai ya fara cin abinci kafin yayi wanka. A hankali yaji suna sako batun aurensa da bintou,da yadda za'a yi asiri ya rufu ayi komai a gama,don ma itama bintou din ba yar gidan wani bace,asalima bafulatanar katsina ce,yanayin aiki ya kawosu nan din,saidai kuma suna da tarin rufin asiri daidai gwargwadon yadda dan adam zai iya rayuwa cikin walwala. Yadda yaji suna maganar ya sake sanyayar masa da jiki,sai yaji batun hamdiyya tamkar ya ajeshi a gefe don baiga ta inda zai yiwu ba. Washegari jinkirin isowarta makaranta kadai akan lokaci ya hautsinashi,ya gaza shiga aji ya zauna har sai da driver dinta ya ajeta. Ta fito tana masa hararar wasa da fararen idanunta "Kada kacemin komai,ina shakka akan son da kace kana yimin,tunda har na qara awa daya kusan da rabi amma ka gaza zuwa ka taho dani har sai da driver ya taho dani" murmushi kawai yayi yana jin sassauci cikin qirjinsa tunda ta iso lafiya. A ranar kafin su rabu ta damqa masa waya me kyau a hannunsa "Mu dinga communicating,dare yanamin tsaho kafin wayewar gari nazo na ganka" amsa din kawai yayi yana juyata a hannunsa,bayason zaqewa ko zura jiki da yawa,bayason kuma su sake nisa shi da ita abun yazo baiyiwu ba ya zame musu ciwo shi da ita. Baice bazai karba ba bai kuma ce ya karba din ba,yabar wayar a hannunsa dai ya kuma shiga gidansu da ita. Sam ya manta tana jikinsa har suka gama hira da bibi yaci abincinsa,yana shirin shiga daki ya watsa ruwa kira ya shigo,shi da bibi din duk sukayi sak sai ya ciro wayar yana dubawa. Alarm ne, kasheshi yayi ya matsa gaba ya ajjiye wayar gaban bibi yau yana yankewa a ransa ya shaidawa bibi komai,tunda cikin maganganun da sukayi a yau da hamdiyya ta shaida masa abbanta ya bawa aba din damar fitowa neman aurenta saboda duniya ta shaida shima ya huta da zirya da neman irinta da ake faman zuwan masa. Yana fara gayama bibi komai sai ga mohmoud shima ya shigo,duk da lokacin shigowarsa baiyi ba,hannunsa biyu dauke da.ledoji niqi niqi yana fadin "Bibi yau nayi babban samu,nace bazan iya jira lokacin tashi yayi ba banzo na shaida miki addu'arki ta daren jiya ta karbu ba,bibi yau kaji kawai zamuci a gidannan" yanayin da ya gansu ya sassauta karsashinsa,sai bibi ta nuna masa gefanta "Zauna nan" ba musu ya aje ledojin ya kuma zauna din,aba kuma ya dora da bayaninsa. Bai boye musu komai ba,komai ya bayyana musu,falon yayi shuru kowa yana juya abun cikin ransa. Tsahon wasu mintuna sannan bibi tace "Kai yanzun kana ganin hamdiyya kininka ce?" Ta jefa masa tambayar kai tsaye wadda ya kasa amsa mata "Banason na sake jin wannan zancan,hamdiyya ba tsararka bace,koda ka dage kan zaka aureta ba lallai ka samu abinda kakeso daga matarka ba,cikin abinda akeson miji yafi matarsa akwai dukiya wadda kusan ita ke riqe da auren,kai kuma baka da ita,uwa uba ma yanzun haka dan uwanka ake maganar ya samu ya fara auren,kada na sake jin wannan batun" "In sha Allah" ya amsa mata cikin matuqar girmamawa,har ransa kuma yakejin ya gamsu da hakan zai kuma yi qoqarin bi iyakacin qarfinsa. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 06 Shi da hamdiyya dukka sun dauki abun da wasa,bayan ya shaida mata zai haqura din saboda rashin goyon bayan mahaifiyarsa da bai samu ba,ita dinma zuciyarta tadan tabu,kuka ta amince zata dafa masa baya akan hakan,amma sai su duka zukatansu suja gaza jurewar. Qarewa suka dinga yi suna rama shi da ita harda qananun lalure lalure,at last dai abban hamdiyya ya sake shiha maganar,yayi tattaki da kansa ya iske bibi har gida,ya kuma bata tabbacin amincewarsa shi da hamdiyya din,sannan kuma ya qara mata da albishir din cewa baya buqatar komai daga hannun hamidou illa sadaki. Abban hamdiyya ya barsu da tarin kyautatawa da alkhairinsa wanda baya boyuwa daga cikin kyawawan halayen da yake dasu. Yabar bibi cikin tarin tunanin yadda wannan al'amarin zaiyiwu,sam ba batun auren hamidou bane a gabansu,batun auren mohmoud sukeyi,ta yaya za'a dauko mata abinda ba zata iya ba?. Cikin dare MAHMOUD ya tayar da hamidou dake kukan zuci yana dubansa, murmushi ya saki "Haba,ba'asan namiji da karaya bafa.....kada ka damu,muddin ina raye kuma hamdiyya kakeso zaka aureta" "Ta yaya hamma?,bayan bibi har yanzun bayan wucewar abban hamdiyya batayi na'am ba?" "Zan dosheta kuma zata fahimta" ya fadi yana duban idanun hamidou cikin bashi tabbaci. Washegari bayan mohmoud ya gama shirin fita wajen aiki ya zauna da bibi akan maganar, hamidou yana labe ya kasa zaune ya kasa tsaye yana jiran yaji me bibi ta yanke?. Mohmoud yasha fama da ita ba kadan ba kafin tayi amanna,tsananin murna ta sanya hamidou fitowa daga inda yake laben ba tare daya shirya ba. Da kallo galala bibi ta bishi "Ja'iri dan nema,dama kana a wajen kenan" kunya ta kamashi,ya samu waje ya zauna yana sinne kai. "In sha Allah bibi na miki alqawarin ba zakuyi nadamar shigowar hamdiyya cikinmu ba,hamdiyya bata da wani aibu ko makusa ta fannin tarbiyya,ni kaina inda nasan da matsala bibi wallahi bazan saki jiki da lamarin ba" "Allah yayi zabin abinda yafi alkhairi" "Yanzun abinda na yanke hamma ya samamin wani aikin da zan dinga yi,duk sanda bamu da lecture sai na fito nayi na koma makaranta" kai mohmoud ya girgiza yana murmushi,a duniya bashi da burin da ya wuce yaga farincikin 'yan uwansa "Aiba wani lokaci za'a diba ba mallam,zaka tsaya tarin kudin aure kenan?,wannan yammatan yadda kuka mato akan juna banajin zata iya jiranka" kunya tadan kama hamidou amma kuma yana mamakin yadda za'a hada komai a qaramin lokaci,duk da abban yace baya buqatar komai daga wajensu face sadaki,amma ko bazai yadda ya auri hamdiyya baiyi komai cikin hidimar aurenta ba,ko yaya ne zaiyi daidai iya abinda Allah ya hore masa,a qalla dai da babu gwara ba dadi. "Zakayi lefe kaman yadda kowanne namiji yakeyi in sha Allah,za kuma ka biya sadaki" abinda mohmoud ya fada kenan yana miqewa zai wuce wajen aiki. Tunda yaji mohmoud ya fadi hakan yasan zai matsawa kansa ne,kuma sai yayi dukka abinda ya fada din,wannan ya sanya a sace shima ya soma 'yan buga bugarsa,abun kamar wani yayewar lullubi sai yayita samun ayyuka,abun ya dinga bashi mamaki,saidai yayi shuru bai gayawa bibi ko hamma mohmoud ba,saboda yasan yanzun zai hanashi yace karatu kawai zaiyi,shi dinne zaiyi komai. Cikin wata guda kacal ya samu 'yan kudadensa a hannu masu dan kauri,yanata mamakin yadda daga fara buga bugarsa qofofi suka dinga bude masa,aka dinga kiransa ayyuka daban daban da kuma kudi masu gwabi. Da yake su din damuwar danuwansu shine tasu,akwai asusu da yake yiwa oumar na jarabawar da zasuyi,wanda ya kallafawa kansa shine zai biya wannan karon hamma mohmoud ya huta shima,asusun ya bude,ga mamakinsa ya tara kudi ashe ba laifi ba kamar yadda yake tunanin bai wani tara abun arziqi ba,ya ware kudin jarrabawar oumar y dauki sauran ya hada da kudin hannunsa ya aje yana jiran dawowar hamma oumar. A falo suke hira yana cin abinci,a kaikaicw hamidou ke kallon hamma mohmoud din saboda yadda gaba daya shekarunsa suka ninka akan nasa saboda da wahala da neman na abinci,har ya kammala mohmoud din ya kalleshi "Ya kaketa kallo na ne kaman kaga hamdiyya?" Dariya dukka sukayi sai ya soma sude miyar hannunsa yana cewa "Ka kwantar da hankalinka,lefenka ya gama haduwa,amma saidai su karba da haquri,akwati biyu ne" baki hamidou ya bude yana kallonsa,yayi imani ba wani lefe,lefensa ne da ya kusa shekara yana hadawa zai sadaukar masa,sai ya girgiza kai "Aah hamma,ni bazan karba lefenka ba saboda na tabbatar shine,ni ina da kudadena da na tara" "Kajimin yaro,yo kudadenka daka tara ai bance ba za'a karba ba,a ciki za'a fidda sadaki ka samu na dinkunan biki da dan abinda zaka bawa amarya ko bibi?" Ya fada yana maida dubansa ga bibi wadda ta kasa magana,wani irin abu me nauyi dake sauka zuciyar uwa akan danta ya tsaya mata iya wuyanta,zata iya cewa bata taba ganin mutum me tausayi da rahama ba irin mohmoud dinta,wanda ke maida matsalar wani tasa "Haka ne,amma mohmoud kaine kafi cancanta da kakai lefen nan,ko ba komai kaine babba" murmushi yayi kawai yana nade hannun rigarshi "Karki damu bibi,muddin kina mini addu'a tabbas zan hada wasu a kurkusa in sha Allah" daga bibi har hamidou ba wanda baiyi qwalla ba "Yanzu gidan da zaka zauna nake qoqarin sama maka a biya haya kota shekara daya ce" mohmoud ya sake fada "Wa?,ni?,ba inda zanje, gidanmu akwai wadatar sassa da babu kowa a ciki,a ciki zata zauna hamma ba inda zani na barku" hamidou ya fada da sauri. Abinda suka kai sam hamdiyya ko mahaifanta basu raina ba,hakazalika ita da kanta ta qarfafi ta zauna dasu bibi din. Sashe daya cikin biyun dake cikin gidan aka bude aka yiwa dan kwaskwarima. Da yake gini ne dama asalam na masu kudin,rayuwace dai kawai data samesu sai wajen yayi kyau ya kuma dace da zaman rayuwarsu da tsarin kayan alatun da ake burin zubawa hamdiyya. Sanda labarin aurensu ya fantsama dukka makaranta sai ta dauki dumi,saboda ba kowa keda masaniyar soyayyar dake tsakaninsu,don daga hamidou har hamdiyya kamammu ne,sun kame kansu sosai,basa wani abun da zai nuna ma akwai soyyaya tsakanin. Mazan da hamidou ya kasa suna da tarin yawa, cikin makaranta cikin nijer dama nigeria,sun kuma cizi yatsa ainun da ganin wanda hamdiyyan ta zaba ya kuma kasasu. Biki akayi na hanakali, ba'a barnatar da dukiya ba,saidai duk abinda mohmoud ya tara saboda nashi auren ya narkar dashi gurin auren qaninsa hamidou,ya sadaukar da komai nasa ga hamidou din,ba abinda ya ragewa kansa,ya kuma tsaya ya zame masa makwafin uba mahaifi,duk abinda uba zaiyi shi yayi masa,hasalima shine alwalinsa,shi ya karba masa auren hamdiyya. Anyi biki lafiya an watse lafiya amarya kuma ta tare a dakinta. To zamansun zama ne me dadi matuqa,duk yadda bibi da farko ta dinga dari dari da tsoron halin yaran masu wadata hamdiyya ta goge mata wannan,babu raini ko ganin ta fisu,ta sake sosai tamkar itama bibi dince mahaifiyarta. Biyayya takewa.bibi kaman yadda takewa hamidou, bashar oumar da auta dukkansu ta maidasu kaman jininta ne,ta zama dai 'yar gida sosai,ba zaka taba cewa surukar bibi bace. Karatunta taci gaba dayi hankali kwance,don tare suke fita da hamidou a motarta da tuni ta mallaka masa ita,saidai yaqi sakin jiki ya karba din,har zuwa sanda ya gama nasa karatun ya zama ita ta rage amma shike kaita ya kuma koma ya dauko matarsa. Duk wasu shares da dukiya ta hamdiyya mahaifinta ya tattaro ya damqa amanarwa hamidou saboda yadda da yayi da tarbiyyarsa. Bai boye komai ba yace ga amana nan. Qememe hamidou yaqi amsa,yace zaidai aje mata takardu da kayayyakinta. Wannan qin amsar shine karon farko da suka fara samun sabani shida hamdiyya,ta dinga fushi tana cewa ya qullaci wani abune akwai a ransa game da ita ko kuma bai aminta da ita da kuma soyyayar da take masa ba dari bisa dari, Sharia har gaban hamma mohmoud da bibi,suka rasa me zasu yanke saboda su kansu ba zasuso ya cusa kansa cikin dukiyar ta ba,ko a yanzun jigila da kuma hidima take masa da kudinta da jikinta,itace cefane itace siye siyen kayan more rayuwa cikin gidan,hakanan komai ta gani ya burgeta saita siya masa. Ba shiri ya dakatar da abun "Munyi alqawarin zaki aureni ki zauna dani daidai qarfina,bamuyi dake zakina mun hidima ba" nan ma dai haushi taji,tilas amma ta rage wasu abubuwan saboda cika umarninsa. Wannan dalili ne ya sanyashi fara neman aiki ka'in da na'in. Allah kuma cikin hikimarsa sai gashi ya jefo masa da aiki da matsakaicin albashin da yasan zai iya riqeshi da yardar Allah. Wani lokaci abba ya kawo musu ziyara,ya kuma samu hamidou ya soma aikin nasa. Sam aikin shi bai masa ba,saboda salary din da suke basun baifi albashin qaramin ma'aikaci a kamfanin hamdiyya ba. Wannan karon da kansa ya sake neman arziqin hamidou ya dawo aiki kamfanin hamdiyya kaman hakan zaifi dacewa,ya jima yana juya abin,ya kuma gayawa bibi tace ya nema zabin Allah,sannan uwa uba mutumin surukin arziqi ne,bai kamaci ace yanata neman alfarma kala kala daga garesu suna sullubewa ba,wannan shine silar da ya fara jagorantar dukiyar hamdiyya,saidai komai yana yine cikin takatsantsan da kiyayewa,albashinsa kuma ya yankewa kansa kamar na kowa,daga gefe guda kuma ya fara saving duk wani halalinsa da yake samu silar aikin da tunanin fara shima gina kansa,saboda bazaiyiwu ace zai dawwama yana qarqashin dukiyar matarsa ba. Duk da cewa wannan abun ba abinda ya qara face soyayya me qarfi da qarin girmamawa daga wajen hamdiyyan,iya tarbiyya ta sameta,sam batasan wulaqanta dan adam ba. Rayuwa ta fara daidaita gidan marigayi mayak'i silar wanzuwar hamdiyya a cikinsu. Abu daya ne a yanzun ya fara musu cikas shine rashin samun haihuwa shekara ta biyu da aurensu. Tun bata damu ba duk da maitar son yara da Allah ya zuba mata,to amma saboda lokacin tana cikin kai kawon karatunta har hankalinta ya fara dawowa jikinta saboda a sannan karatu ya kammala sai business dinta da takeson kamawa. Sannu a hankali ta fara tadawa hamidou hankali,har takai anje an gwadasu,an kuma tabbatar musu mahaifar hamdiyya ce take da dan rauni. Hankalinta yayi mugun tashi duk da yadda hamidou ya nuna shi hakan ba matsala bacea wajensa,ya dinga qoqarin kwatanta mata da kwantar mata da hankali amma ta birkice masa,sun dauki watanni a haka kafin ta dan sanyawa zuciyarta salama,sai kuma zancan auren mohmoud ya taso Gadan gadan. Haka kawai shaidan ya sanyata ta dinga jin babu dadi cikin ranta,saita dinga tsarguwa kaman za'a qaro wata surukuwar ne cikin gidan don itadin bata haihu ba. Wannan dalilin ya sanya har akayi bikin aka qare aka kawo amaryar hamma mohmoud daya sashen a tsarge take,wannan ya sanya tayi bala'in kamewa daga shiga shirgin matar hamma mohmoud. Bintou baiwar Allah,gwanar haquri da kawaici,kyakkyawar bafulatanar katsina,wadda tasha gwagwarmayar mayar rayuwa da wahalar riqo hannun kishiyar uwar da aka fita aka bar mata. Girmama hamdiyya takeyi duk da itace matar yaya,amma tana kallon cewa ta rigata shigowa gidan,bata da hayaniya bata da magana,shuru shuru da ita kullum. Yanayin rayuwar da bibi tasan tayi ya sanyata take yawan jan bintou jikinta don ta samu ta ware ta kuma dinga jinta mutum kamar kowa. Akwai banbancin rayuwa sosai tsakaninta da hamdiyya data taso cikin gata da soyayyar dangi gaba daya. Wannan abun sai ya dinga yiwa hamdiyya ciwo kadan kadan,duk da bata taba nunawa ba amma tana jin babu dadi a ranta,tanajin kamar Bibi nason wareta ne da nuna mata banbanci don bata haihu ba,wannan yayi mata tasirin data soma janye jiki daga al'amura da yawa na gidan,ta zama 'yar ba ruwana,dabi'ar miskilancintanan ya motsa,sai ayi abu cikin gidan ma bata sani ba,inda zakaji motsinta kawai ayi baqi yara ko ayi baqi da yara a cikinsu yanzunnan zakaga yadda zata sake jiki tayita hidimawa yaran,musamman idan akwai baby girls a ciki. Tanason 'yar yarinya mace sosai,takancewa hamidou tafison ta haifi mace akan namiji. Tun bibi na qoqarin fahimtarta da son fahimtar meye ya sanyata sauyawa ta nuna babu komai,har bibi ta haqura ta barta da sabon halinta,tundai ba fada takeyi da kowa ba cikin gidan,tana kuma ci gana da girmama kowa kamar yadda takeyi a baya. Ba jimawa kwatsam ciki ya bayyana jikin bintou,yadda gidan ya rude da murna kuma kowa hankalinsa ya koma kan cikin sai ya soki zuciyar hamdiyya sosai(kusan duk macen dake neman haihuwa bata samu ba tana da shigen wannan ciwon a ranta,ko hirar haihuwa akeyi saita tsargu taga kaman da ita ake bare ace wance ai ciki ne da ita,ba wanda zai fahimci hakan sai wanda ya taba tsintar kansa a irin situation din),wannan ya sanya ta sake kame kanta da zama a sassanta ita kadai. Sai taji bata sha'awar ta rabi kowa ko wani ya rabeta,to Allah baisa cikin yana da dogon zango bama bintou tayi barinsa. Sai kuma a sannan hamdiyya ta dinga jin ba dadi,ta kuma dinga tausayin bintou, hankalinta kuma yayi mummunan tashi sanda bintou ta dinga ciwe ciwe, daga bisani gwaji ya bada cikakken bayanin bintou sicklier ce. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 07 Ta tsorata ainun hamdiyya a sannan,don mutum uku cikin familyn ummanta da taga yadda sukaci wuya da ciwon sicklier daga bisani kuma dukkansu suka rasu,wannan yayi sanadiyyar da tayi matuqar tsanar ciwon sicklier. Hatta da hamidou duk son da take masan sai da sukayi gwaji kafin aure. Cikin hikima ta ubangiji a sannan din ashe tana maqale da cikin ALIYYU MAINA,wanda kwata kwata sam ko da alama bata sani ba bare kuma hamidou(aba). Bata tashi sanin da ciki a jikinta ba sai da yayi watanni hudu ya fara harbawa a mararta,ta tsorata dajin hakan ba shiri suka wuce asibiti. Bibi bata hanasu ba illa dariya da take musu qasan ranta, tasan yadda sukaje haka zasu dawo da borin kunyarsu. Ilai kuwa sai gasu din,sun dawo mata shabe shabe da kukan murna da kuma kunya. Fadin yadda hamdiyya ke lele da qaunar cikin aliyyu ma kai tsaye za'a iya cewa bata baki ne, ba'a taba jarabtarta da wani abu da takeso sama da cikin ba baya ga mahaifin yaron. Motsi kadan kuma bini bini suna hanyar asibitin wai check-up a duba lafiyar yaronta,tun bibi na zuba musu idanu har ta gaji da gani ta tsawatar musu,sai suka koma fakar idanunta suna zuwa,sai kawai ta tarkatasu ta watsar. Shirin haihuwa sukayi na garari,da ba'a qasar taso haihuwa bama amma ganin yadda bibi da bintou ke da kwadayin ganin yaron ya sanya ta haqura. Cikin aminci ta haifi aliyyu maina,sambalelen yaro da ya gaji kyau ta fannin uwa da uba da 'yan uwan uba dinma duka. Tun asali da farinjininsa maina yazo,uwa naso uba naso qannen uba naso,hamma mohmoud kuwa ba'a ma maganarsa,don yadda yakejin haidar din har cikin jininsa,yadda yake qaunarsa da qulafucinsa har yaso ma yafi mahaifinsa. Sannu sannu tun haidar na jaririnsa sai zamansa yaso yafi qarfin hannun hamdiyya,duk da mahaukacin son da take masa. Yadda sukeson janye haidar din sai yadan fara tabata,ganin kamar ganin yaron yanaso yafi qarfinta,shayarwa ce kawai ke dawo dashi wajenta. Cikin ikon Allah watan haidar shida uku kacal Allah ya albarkaci bintou da wani cikin,tayi murna qwarai ita da hamma mohmoud sosai. Haidar maina nada shekara guda kacal bintou ta sambalo tata yarinyar da taci sunan NAFESSA. Da nafessa da haidar kusan duka rainon bintou suka koma,saboda tun haidar nada watanni hudun yasan idan yana kuka aka ajjiye baby nafessa a gabansa watsal watsal dinta ya dauke masa hankali ya tsaida kukan da yakeyi. Sanda ya cika shekara ta biyu kuwa yasan ya kama hanya tiryan tiryan zuwa sassansu nafessa,duk kuwa da dan banzan qyuya da yake da ita. Ya kama sunan hamma mohmoud da suke kira da pappa da kuma sunan NAFESSA daram a bakinsa fiye da sunan kowa. Wasa wasa wata irin mahaukaciyar shaquwa ce ta shiga tsakaninsu ta yadda bacci ne kadai ke rabasu,saidai idan sunyi baccin a dauke nafessa shima a daukeshi a maida sassansu. Alaqar dake tsakaninsa da nafessa din ta nesanta shi da ama din,tun bai isa yaye ba,tun kuma bata saba ba har ta saba. Kusan duk yininsa yana wajen bintou ne,idan kima nafessa na sashen bibi shima yana can acan zasu wuni sur saidai ya leqota. Kishin hakanne ya fara kamata ganin sannu sannu yana barin sassanta da kuma raguwar shaquwar dake tsakaninsu duk da irin qulafucinta da yakeyi. Gashi daga itan har bintou daga kan yaran ba wadda ta sake samun wani cikin,gwara bintou dama an shawarcesu da daukan dogon hutu kafin ta sake samun wani cikin saboda yanayin lalurarta, hakanan ta sha wuya sosai wajen haihuwar nafessa,nisan kwana kadai ya kawota yau. Duk yadda zata ja maina a jiki abun ya faskara,ta kuma lura ita bibi hakan yana mata dadi qwarai,tana yawaita fadin Allah ya qara hada mata kansu shi da nafessa din. Nafessa na da shekara hudu maina nada shekara biyar alamun ciwukan sicklier suka fara bayyana a jikinta,yau ciwo gobe lafiya,qwarai bintou taso aje ayi mata gwaji amma tsoron kada ya tabbata nafessa nada sicklier hamma mohmoud ya qiya,amma dole da gumu tayi gumu ya bari akaje aka gwadata din. Ta tabbata sicklier dince kuwa, sicklier dinma irin chronic sicklier dinnan,don kuwa kwata kwata rayuwar nafessa kusan rabinta a ciwo take. Allah ya mata halitta me sanyi,nafessa din yarinya ce me tsananin sanyin hali,shuru shuru,matuqar girmama duk wanda ya girme mata,ga tsananin son karatu kamar me?,saidai kuma karatun nata kusan rabi ne,rabin tana yinsa ne ga gadon asibiti. Duk da ana cewa sickle suna girma ciwonsu yana qara ja baya,ga nafessa abun ba haka yake ba,tana girma ciwon yana sake nuqurqusarta. Duk sanda ciwon nafessa ya tashi ba zaka iya banbance waye me ciwon ba tsakanin ita da maina. Ita kuka maina kuka,idan kaga walwalarsa to nafessa ta samu kanta. Koda bacci yakeyi muddin yaji murya ko nishin nafessa bacci ya qare masa. Abun ya sake dagawa ama hankali,tana ganin shaquwar kamar ta wuce hankali. Buqatun nafessa da hidimarta itace gaba data kowa cikin gidan,walwalarta itace tashi. A haka shekaru suka dinga tafiya,shine komai na nafessa,shine gatan nafessa shine kuma mai tsaya mata,muddin yana wajen ba wanda ya isa ya tabata. Ya wuceta da aji daya,amma yasa aka maidashi baya ya koma ajinsu nafessa din,daga boko har islamiyya haka yayi ba tare da ama ta sani ba. Ranar data samu labari kuwa tashin hankali tayi sosai,har ta dinga ji a ranta anya wannan abun nashi na lafiya ne?. Tun nafessa nada shekara goma daga mohmoud har bintou raayinsu yazo daya na aurar da ita da wuri,saboda yanayin lalurarta suna ganin taci gaba da karatu ma kamar sun wahalar da lafiyar gangar jikinta ne. FURUCIN da bibi tayi a wani lokaci kusan shi ya sake sanyata tsaiwa da qafafunta akan aliyyun nata. Ranar suna tasowa daga makaranta,sai ta rigashi tahowa,ashe wani ya biyota ya kuma tsaidata,maina din ya shigo gida yana cika yana batsewa, bibi tayi dariya tace "To ko 'yar gida za'a yi?, irin wannan kishi haka maina?" A kunnuwan ama tayi zancan,saidai bata daga kai ta kallesu ba,saidai maganar ta sauka sosai cikin zuciyar ama din,ta kuma tsaye mata a rai,daga lokacin ta fara takatsantsan da fara janye maina din daga nafessa dama harkokin gidan gaba daya,makaranta ta sake samar masa wadda zai zamana sai kusan bayan isha'i zai samu sakewa cikin gidan. A lokaci shi da nafessa din duka suna ss.2, shekara daya kawai ya rage musu su zana jarrabawar kammala secondry school. Rashin ganin maina din kwanakin da suka biyo baya ya sanya nafessa din zuwa har sassan wajen ama nemansa,abinda ba kasafai ta fiya yinsa ba idan ba mamanta ko bibi ta aiketa ba,duk da cewa ba wani abu ama ke nuna mata ba,hasalima tana mata komai na kyautatawa kaman kayan qyale qyalen rayuwa da sauransu saboda ita daya ce mace a gidan,don ko da su oncle bashar da ocle oumar sukayi aure yara mazan suma matansu dukka suka haifa,sannan ita dinma data sake samun ciki namijin dai ta sake haufa,duk da addu'ar data dinga yi da kuma qulafucin samu diya mace data dinga yi. Haka kawai dai ba sakewa tsakaninsu,ita ama zurfin alaqar dake tsakaninsu dinne bataso,da yadda dukka haidar ya tattare tsakaninsu da kuma bibi,ita din ta zama kamar ta haifa musu shine kawai. "Yana makaranta" kawai ama tace da ita,sai ta miqe a sanyaye ta fice. A wannan tsakanin hamani ya dawo gidan sanadiyyar karatu da ya maidoshi nan garin,hamani d'a ne ga qanin mahaifinsu aba,hamani din kamar cousin yake a wajensu. Yana da matuqar kirki da son jama'a,uwa uba matashine me addini kamewa da sanin ya kamata. Cikin lokaci qanqani ya fara sabawa da kowa na gidan,dukka yaran idan sukaji shuru na wasu awanni basujishi ba sun shiga cigiyarsa ina oncle hamani,harda nafessa kuwa,don kusan shike mata lesson din da yanzu maina baida cikakken lokacin yi mata shi yadda suka saba a baya. A lokacin manema suka fara zuwanma nafessa din,duk wanda zayazo gurinta ko yace yana sonta sai maina ya sani,tare suke shawarar komai. Kusan a kowacce qasa,kuma kowacce al'umma da yawanmu suna da qyamatar auren masu lalurar sicklier,to irin wannan qalubalen ne nafessa ta fara fuskanta. Tana da kyau ainun dake jan hankalin kowanne namiji,tana da nutsuwa da kamun kai dake bawa maza sha'awa,to amma kuma da zarar sunji irin lalurarta sai ka nema mutum ka rasa. Da yake auren bai kanta da farko bata wani damu ba har sai da tafiya ta fara nisa ta fahimci qalubalen dake a gabanta,ta kuma ga zallar damuwa tattare da mommanta. A hankali ta soma fahimtar komai,ya kuma soma damunta,maina dinne dai abokin shawara da fadawa damuwarta,sai kuma oncle hamani. Duk sanda wani yazo ya tafi da maina take tattauna damuwarta "To sai meye?,yayita tafiya,Allah zai kawo miki wanda ya fishi" duk sanda ya fadi hakan hankalinta yana kwanciya sosai. Ranar da zuciyarta ta karye sosai ranar da wani hafizzou ya shaida mata soyayyarsu ba zata iya ci gaba ba. Shigowar maina gidan kenan daga makarantar manya ta dare,yaga fitar hafizzou ya kuma ga shigewar nafessa ciki da sassarfa sassan bibi,sai kawai ya take mata baya yana addu'ar Allah yasa bame afkuwa bace ta auku. Yana shiga ya sameta saman cinyar bibi din tana sharba kuka. Aba na falon haka haka ama,suna list na abubuwan da bibin keso ama zata taho mata dasu daga Nigeria,don saura kwana uku ta wuce can din,kasancewar bata rabo da zuwa don suna da tamfatsetsen gida a can da idan sunso suna iya share wata uku ciki kafin su dawo niger,ita da aba ko ita daya dinma. "To sai meye?,a kansu kike zubda hawayenki nafessa?,suyita tafiya din,ni zan aureki,na yarda ni aliyyu zan aureki" ya fada cikin tsanani fushi da zafin zuciya. Ba ama kadai maganar ta yiwa luguden duka ba,har bibi da ita kanta nafessa din. Dif falon yayi abinda maina bai tsaya wani la'akari dashi ba yaci gaba da zazzaga masifa. Sakale ama kawai tayi tana kallon ikon Allah kuma zatonta yana sake qarfafa lallai aliyyun wasu ta haifawa. Zuciyarta ta gaza daurewa ta daka masa tsawa me qarfi "Yima mutane shuru dalla,shashasha!,fita ka bawa mutane guri" ta fadi a harzuqe. Har ya fitan suka gama abinda sukeyi ta fice itama babu wanda yace komai akan maganar. Cikin kwanakin ukun tanata shirin tafiya Nigeria amma ranta a matse yake,gaba daya ta rasa walwalarta,hatta aba da maina sunga canzawarta,tanata juya furucin maina a ranta,tana kuma hankalce da yadda suketa dan shige da fice a sassan bibin lokaci zuwa lokaci. Bataji koda d'ar ba,saboda ta riga ta sama ranta ko sama da qasa zasu hade ba zata yarda maina ya auri nafessa ba,abumma sam bai kama hankali ba,ko ita da mahaifinsa da sukayi aure duniya nada ragowar kwanciya ai dukkansu sai da suka mallaki hankalin kansu sannan sukayi,uwa uba ma kuma bataga dalilin da zai sanya ta bari maina din data dora buri a kansa ya auri sicklier ba,duk da nafessa bata da matsala ko makusa tako ta ina,amma abun ita sam bai kama zuciyarta bama bare hankalinta. Haka ta tattara harda maina din suka wuce Nigeria,abinda yasa ta gane da wani abun a qasa,tun sanda zasu taho basuyi sallama da aba ba yadda suka saba,sannan a qa'ida tare suka tsara zasu tafin amma shi ya janye tashi tafiyar,bataji dadi ba amma ko a jikinta suka wuce din. Sanda ta kammala kwanakin data diba zatayin sai taji kwata kwata bata sha'awar komawa nijer,tayi zamanta a nan din duk da lura da tayi maina ya takura su koma din. Suna hutu ne a sannan,kuma hutunsu yakan dauki dogon zango wani lokaci wata uku har hudu ma,ba guntun hutu irin namu ba,wannan ya sanya ta sake miqe qafa,tayi biris kamar bata karanci damuwarsa ba. Sati guda ta qara akan ainihin kwanakinta aba yayi mata dirar mikiya. Hakanan kadaran kadaham babu wannan karsashin kamar yadda suka saba. Kwana daya kwana biyu shuru,a kwana na ukun suna breakfast da safe ya dubeta yana gaya mata labarin da ta jishi kamar saukar aradu "Mun yanke shawarar daura auren maina da nafessa" a wani hargitse ta dago tana dubansa "Wanne maina din?,kana nufin aliyyu haidar?,wanda ko qaramar secondry bai gama ba?dududu shekarar haidar din nawa?,,baya ga haka ka manta nafessa sa'arsa ce?,watanni sha biyu kacal ya bata?,ka manta matakin lafiyarta?"*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 08 "Dukka wadannan lissafinki ne,ba ruwana dasu" ya furta cikin halin ko in kula. Wannan magana ita tayi silar kawo rikicewar familyn MAYAK'I a karon farko,ta nesanta zazzafar soyayyar dake tsakanin aba da ama me matuqar danqo,soyayyar da bibi bata taba sasanci ba a tsakaninsu,saboda ba qarya hamdiyya ta iya riqon miji qwarai da gaske. Batayi qasa a gwiwa ba ta yanki tikitin komawa nijer saboda ta tabbatar ba shi daya yayi wannan shawarar ba. Ta dire gaban bibi takuma lissafa mata dukka hujjojinta na rashin amincewa da batun auren maina da nafessa. Bibi din jinjina kai kawai tayi, bata fidda matsayarta ba,don a duniya ba wanda zai kaita son ganin maina da nafessa qarqashin inuwa guda. Ganin yadda abubuwa keta rikicewa cikin gidan ya sanya oncle mohmoud wanda tunda aka fara lamarin har sanda su bibi suka yanke hada auren bai taba magana ba sai yanzu ya gurfana gaban bibi yace yana roqon alfarmar abar wannan batun,ko don hamidou ya samu zaman lafiya da iyalansa,maina kuma ya samu albarkar mahaifiyarsa. Kai da fata aba yace shifa baisan zance ba,ya riga ya bawa maina nafessa,babu kuma fashi, saidai hamdiyya tabar aurensa. Sosai maganar ta taba bibi,salin alin ta kwabeshi itama,tace kuma an janye maganar. Kamar jira hamani yakeyi yace shi zaya auri nafessa. Ba wanda ya qyamaci abun a cikinsu,saboda hamani din managarcin mutum ne,kuma dama can shi bame kule kule bane,hasalima babu wata yarinya da yake nema. Dai dai sanda ya kammala Phd dinsa daidai sanda nafessa ta kammala secondry school,babu jinkiri aka gabatar da komai,aba ya daure qarqashi akayi gagarumin biki, Wanda kamar ama tasan za'a yi hakan ta saka maina a gaba suka wuce Nigeria. Tunda suka tafi din bai dawo nijer ba,hasalima sai ya fara neman gurbin karatu a can,don baijin zai dawo nijer kuma rayuwa taci gaba da gudanar masa kamar yadda yakeso. duk da yayi murna qwarai da nafessa ta samu mutum kamar hamani,yayi imani ba ita babu kuka saboda nagarta da kyan zuciyarsa. Duka duka auren nafessa watanni shida,tana da ciki wata hudu bintou mahaifiyarta ta rasu. Mutuwar ta girgiza ta ta kuma jijjiga mohmoud,saboda shi kadai yasan irin macen da Allah ya bashi. Albarkacin samun nagartaccen miji dukan mutuwar yazo mata da sassauci,ya tsaya kai da fata ganin matarsa bata fuskanci raurawa ba. Watanni uku da kwana goma nafessa ta haifi SULTANA, yarinyar da ta samu soyayyar da har ta dara wadda mahaifinta da kuma maina din ya samu,yarinyar data debo kamannin NADEEYA abinda ya qara adadin soyayyarta a zuciyar kowa da kowa. A sannan tuni dukiya ta fara yiwa aba ambaliya,ya fara shiga jerin sahun attajiran 'yan kasuwa masu cin gashin kansu,don bai jima da dukiyar ama a hannunsa ba ya damqa mata komai ya dorata akan turba ya kuma bata cikakken damar kula da dukiyarta kamar yadda kowanne namiji zaiyi shi kuma ya waiwayi tasa. Iya bikin suna kawai kudade aba ya zuba masu ciwo yace ayi,duk da hamanin ma ba baya bane gurin samu,don tun yana lavel one a jami'a ya fara kasuwanci,kawo yanzu kuwa shima ya zama babban qwaro. Gata iya gata ta kowanne fanni. Ga hamma MAHMOUD jin sultana yake kamar wani yanki na jikinsa, soyayyarta bata taba boyuwa muddin zaka zauna dashi koda na minti talatinne. Ya zubawa sultana so wani irin so me tsayawa a zuciya tun tana zanin goyonta. A haka aka fara rainonta kafin me afkuwa ta afku,mutuwa ta rabata da mahaifiyarta nafessa. Mutuwar ta daki maina matuqa ta kuma galabaitar dashi,sai kuma a lokacin mutuwar ne ya fara dora idanunsa akan sultana da a sannan take koyon zama watanni uku da kwanaki a duniya. Wani irin masifaffen so ya azawa sultana,bama shi kadai ba kusan kowa na cikin gidan,yana ji a ransa kamar yanzun sultana responsibility nasa ce,kamar shike da alhakin komai nata. Rasuwar nafessa da samuwar sultana ya sanyashi ajjiye karatunsa ya dawo gida nijer. A hannunsa sultana ta taso,ya zama shine uwa kuma shine uba a gareta,tsarkin kashi wanka raino rashin lafiyarta dama walwalarta dukka na hannun maina. Maina ta budi idanu ta gani a matsayin uwarta kuma ubanta tun gabanin ma hamani da hamma mohmoud din suma subi bayan nafessa sanadiyyar hatsarin motar da suka samu shi da shi a hanyarsu ta dawowa daga ziyarar kabarin nafessa din. Wannan maraicin da sultana ta sake tsunduma ya sake ninka soyayyarta,ya kuma sanyashi sake ninka kulawarsa ninkim baninkin a kan sultana,ya ajjiye karatunsa gaba daya saboda ita,wasu abubuwan tun bai iya ba har ya qware sosai,hatta jakar goyon sultana yana da ita,yadda yarinyar ta taso tana qulafucinsa sai ya masa kamanceceniya da mahaifiyarta. Ta dabance sultana cikin gidan kamar yadda komai nata ya zama na daban,tana da farinjinin da kowa ya shigo sai ya dauketa ko ya tankata,tana da yawan surutu tun shekarunta suna qananu ainun,tana da kazar kazar irin ta masu cikakken lafiya. Halasci da sadaukarwar mohmoud ba abune qanqani ba da zaiyi saurin bacewa zukatansu ba,ba qaramin abu bane da zaiyi saurin shafewa a rayuwarsu ba,a wajen aba hamma mohmoud din uba ne wanda yayi masa komai a rayuwa,bashi da abinda zai saka masa dashi face ya bawa jininsa qwaya daya tal da ya bari a duniya dukkan soyayya qauna da kulawa,wannan ta sanya ya fifita sultana akan kowa cikin gidan,buqatarta ta zama gaba akan buqatar kowa. Ya koma makaranta a nan maradi amma saboda hankalinsa nakan rainon sultana sai karatun nasa ya zamana asha ruwan tsuntsaye ne,yaqi ya maida hankalinsa duk da karatunsa karatu ne me tsada da wahalar samu,yake kuma da buqatar maida hankali akai. Aba da kansa da ya fahimci muddin yana tare dasu ba karatun zaiyi ba,sai ya maidashi niamy,ya tafi kuma da sharadin sai yayi shekara cur aba yaga kamun ludayin karatunsa sannan zai barshi ya fara zuwa gida weekend. Itadai ama bata tanka ba,don zuwa sannan ta zama 'yar don't care game da komai na cikin gidan,ba komai take sanya baki ba duk da dama ba halinta bane shishshigi,sa'annan har kawo yau aba zafinta yakeji akan hana auren maina da nafessa. Dukka tulin soyayya da suke nunawa sultana bataga aibu ba,don sultana din jinin mohmoud ce, MAHMOUD kuma abun asoshi ne,ko ita yana daya daga cikin mutane masu muhimmanci cikin rayuwarta,abu daya ne ta dinga jiye musu wanda a yanzun ya riskesu,sangarcewa da lalacewar tarbiyyar da maina keta fadi tashin ganin tafi kowanne yaro cikin gidan,abinda ta dinga gane musu kenan,amma taja bakinta tayi shuru don tasan ba muhallin da zatayi magana bane,don ba lallai su fahimceta ba. Kaf yaran gidan ita kanta sultana din tafi shiga ranta,tana tausayinta saboda maraicin da take ciki ta kowacce fuska,amma hakanan ta barma ranta hakan saboda a qalla dai a samu wanda koda da kallo zaya nuna mata kuskure idan ta aiwatar cikin gidan,sannan ba lallai su gamsu da ita ba wai don ta nuna tana qaunarta,duk da cewa tasan kusan komai ya riga ya wuce,family ne da basa da riqo sam sam sam,daya daga cikin halayensu dake burgeta. Sanda ya cika shekara ya fara zuwa gidan bai fahimta wani sauyi sosai daga gareta ba. Saidai bahaushe yace sannu sannu hata hana zuwa saidai a dade ba'a je ba, shekara guda da fara zuwan nasa ya karanci komai,hankalinsa ya dagu sosai,yayi iya bakin dukka qoqarinsa wajen saita komai amma inaaaa......wannan shine ya zama SILA kuma SANADIN KADDARAR data samesu a yanzu.........KADDARAR da zata budewa SULTANA da MAINA qofofi masu tarin yawa..... _Barkanmu da sauka😄,muje zuwa guwa ga tsakiyar labarin_🤩 *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 09 Numfashi me nauyi ama ta aje tana sake murza tafin hannun sulatana dake tsakiyar hannunta wanda ya sake yayi laushi sosai "Ya hayyu ya qayyumu birahmtika astageesu" ta furta qasa qasa tana lumshe idanuwanta. Batasan me qaddara ta tanadarwa gobensu ba gaba daya,saidai ko meye tana fatan yazo ya wuce sa gaggawa,ko meye kuma tana fatan yazo ya wuce musu cikin sauqi. Hannunta ta saje miqawa ta jawo wayarta tana sake lalubar number wayar maina,har yanzu akwai dacinsa da ciwonsa qasan zuciyarta,tana sake jaddadawa kanta da gayawa kanta ba zata masa ta sauqi ba,ba zata kuma sassauta masa ba dole tayi masa mafi munin hukunci,saboda ba haka takeso ya rayu da nashi iyalin ba,ba haka takeso ya soma gina rayuwarsa data zuri'arsa ba,tana da buqatar tsatso me kyau wankakke daga wajensa tamkar yadda ahali da salsalar mahaifinsa suka kasance. Babu wani abu da ya canza,har yanzu dai gaya mata akeyi wayar na a kashe ne. Furzar da iska tayi daga bakinta tana sake gayawa kanta duk nisan kiwon da yayi zaije ya dawo ya sameta. Sai data duba lokaci taga yadda dare yaketa sake nisa sannan ta fidda hannunta daga na sultana,ta miqe ta zare yalwataccen mayafinta da kowanne motsi yake fidda qasaitaccen qamshi. Toilet ta shiga ta dauro alwala don batajin zata iya samun bacci,ta shimfida darduma ta tada salla. Raka'a shida tayi ta sallame,ta bude ipad dinta tana buda app na qur'ani cikin nutsuwa ta soma karantawa ko zuciyarta zatayi sanyi daga abinda takeji. Duk bayan kowannw minti sai ta aza idanunta akan sultana da har yanzu jiya iyau. Tayi nisa takai gwargwadon izifi biyu ta sake dora idanunta akan sultana,sai taga hannunta da qafafunta suna wani irin motsi kamar ana jijjigasu. Da hanzari ta aje qur'anin ta kuma miqe tana nufarta da sassarfa,dab da zata isa inda take sultana din ta soma fusge fusge kamar wadda aljanu suka yiwa mummunan kamu,kafin daga bisani ihu ya biyo baya da dakusashiyar muryarta data fara budewa. Gaba daya gigicewa ama tayi da irin abinda taga sultana din tanayi,sosai take jijjiga tana kuma ihu tare da kiran sunan maina kaika dauka wasu gaggan mayu ne suka kamata. Rungumeta tayi sosai a jikinta gudun kada ta farke dinkin jikinta ko ta jiwa kanta rauni,tana rungume da ita din tana kiran sunanta,saidai bisa dukkan alamu bata fahimtar ma abinda takeyi bare wanda ke kusa da ita,abinda ya sanya hawayen tsananin tausayinta ya sauka a idanun ama. Tanason ta matsa gaban abun kira ta kirayi nurses amma tana tsoron sakin sultana din,cikin taimakon Allah kamar Dr chafa'atou tasan halin da ake ciki sai gata ta turo qofar dakin ita da Dr cha'aibou. Hannuwanta dake cikin aljihun labcoat dinta ta zare tana nufosu da gaggawa "Ta farka ne?" Ta tambayi ama tana tayata riqe sultana "Ta farka Dr amma a mafi munin yanayi" ta bata amsa tana qoqarin dauke qwallar data sauka saman idanunta. Dr cha'aibou ta yiwa magana ya qaraso ta sanyashi ya duba allura cikin drawer din da suka ajjiye dukka tarkacen allura ruwa da magungunan da sukasan ciwonta yana da buqata. Shi ya hada allurar ya kuma yi mata. A hankali sai yanayinta ya fara daidaita,saidai kuma dukka jikinta ya fara sakewa,kafin daga bisani ta sake komawa wani baccin. Shuru dakin ya dauka idanunsu dukka a kanta,kafin daga bisani Dr chafa'atou ta furzar da iska tana maida dubanta ga ama "Dole zata hadu da attack dama irin wanda aka yiwa rape suke haduwa dashi,saboda wannan abun da akayi matan kusan daidai yake da rape a tunani da kuma qwaqwalwarta,tunda anyi shine bisa qarfi da tilastawa,kwanyarta sam batasan meye sahihin ma'anar aure ba bare ta banbance,amma in sha Allah ina saka ran idan ta sake farkawa zata farka babu dukka wadannan abubuwan,ki kula da kyau don ba dogon bacci zatayi kamar irin wannan data fark daga shi ba,ko na turo miki nurse hajja ta tayaki zama?" Kai ama ta girgiza a sanyaye,bata buqatar kowa ya tayata tunkarar wannan,bata da buqatar wani ya aboceta cikin wannan lamarin,tanason ta tunkari komai ita daya da zuciya da gangar jiki irin ta UWA. Tunda Dr chafa'atou ta fadi haka ta tattara ta dawo gaban gadon ta tare,qarfe biyu qarfe uku qarfe hudu dukka saman idanunta suka wuce,bacci ko gezau baibi ta kusa da ita ba bare ya gwada daukarta,har zuwa sanda sanyin dake bayyana gabatowar asuba ya soma busawa,a sannan sultana din ta fara bude idanunta a karo na biyu,wannan lokacin cikin nutsuwa,saidai kuma tana jin dukka jikinta wani iri babu dadi,sannan daya idon nata kuma yaqi bude mata da kyau yadda takeso. Jin hakan ya sanyata daga hannu da niyyar shafa fuskar taji me ya hanawa idon nata budewa da ganin abu da kyau. Riqe hannun nata ama tayi da sauri tana fadin "Bari karki goce qarin ruwan" a nutse ta waiwayo gefanta,idanunta suka sauka kan fuskar ama din,a hankali kwanyarta ta fara tuna mata abinda ya faru da ita na qarshe. Tunanin da ya sake hargitsata karon farko cikin hayyacinta,sai wani irin nannauyan kuka me sauti ya kufce mata. Tana iya tuna sanda maina ya tsiraitata ya yage kowanne tufafi dake jikinta,tana iya tuna sanda hannuwansa ke kaiwa guraren da ita kanta tana kyautata zaton ma qilan bata taba tabawa ba,tana iya tuna sanda lokacin da ya sadar da kansa da wajen da ko kallonsa bata yi duk da a jikinta yake......wani kukan ya sake qwace mata me matuqar sauti fiye dana baya,sai dukka wani qarfin hali da qwarin gwiwar ama ya kwaranye,ta rungume sultana din sosai a jikinta tana lallashinta. Sun jima a haka kafin kukan nata ya ragu,sai ta koma sauke ajiyar zuciya kafin ta bude bakinta cikin hardewar harshe tace "Ruwa" sakinta ama tayi ta bude carton din ruwan dake aje gefe ta ciro guda daya ta hado da glass cup din da aka shirya a wata qaramar cabinet a dakin. Ajjiuesu tayi a gefe sannan ta fara qoqarin tadata zaune don taji dadin shan ruwa. Siririyar qara sultana ta saki tana runtse ido saboda azabar da taji na ratsata,kowacce gaba ta jikinta ciwo takeyi mata "Sannu,daure kisha ruwan sai na saka ruwan dumi na gasa miki jikinki ko?" Ama ta fadi a tausashe tana kallon qwayar idanun sultana cikin matuqar tausayin ta shigo stage din da bai kamata ce ta shigo shi ba. Tana qananun qwalla tana komai ama ta tada ta,ta zuba mata ruwan ta shanye ta kuma sake buqatar wani,haka ta dinga zuba mata tana shanyewa har sai da tasha rabin gorar sannan tace ta qoshi. Da kanta ama ta tara ruwa me dumi qwarai ta dawo cikin dakin "Muje ki wanke jikinki ko zakiji dadi" a hankali sultana ta kauda kanta gefe kadan tana jin zuciyarta kamar zata fashe,ganin ama kawai tuna mata yake da maina da abinda ya aikata mata,wai shin ta yaya zata iya ci gaba da kallon ama?,ta yaya zata iya tubewa ama jikinta tayi mata wanka?. Mutum biyu rak a rayuwarta suke mata hakan,daga bibi sai tanja,batajin akwai sakewa tsakaninta da ama da har hakan zata kasance "Ina bibi ta?" Ta tambaya cikin rauni ba tare data Kali ama ba "Suna gida,dare yayi yanzunma asuba ce,amma goben nasan da sassafe zaki ganta" "Zata yimin idan tazo" tace da ama tana jin kamar harshenta take yanka a duk sanda ta buda baki tayi magana,saboda sam sam a yanzun furta kowacce kalma ta daina bata sha'awa,tafi sha'awar kurumtaka da bebantaka akan komai,batason jin duk wani sauti ko kuma kalma bare ta tuna mata da ALIYYU MAINA. Tsaiwa ama tayi kawai tana nazarinta,har yanzu taqi waiwayowa bare ta dubeta,sai ta taka a hankali ta isa sashen data maida kanta ta zauna,ta jawo hannunta ta saka cikin nata "Sultana?" Ta kirata kiran da ya ratsa mata jiki,ta kuma daga kumburarrun idanunta da dayan bai iya gani da kyau ta kalli ama sannan ta maida dubanta qasa "Inason ki daukeni daga yau a matsayin bintou mahaifiyarki da baki santa ba,inaso daga yau ki sanya a ranki ni ba babar maina bace,ban haifi d'a aliyyu ba,ke kadai na haifa,zaki iya daukata a matsayin mamarki da zaki iya gayawa dukka damuwarki?" Kiran sunan maina din ya saukar mata da wani zafi daga zuciyarta,amma kuma data dubi ama saita tuna cewar.......matar bata taba takura mata ba,bata taba shiga huruminta ba bare ta dameta ko ta hantareta cikin gidan yadda sauran matan kawunnanta suke mata,bata taba mata wata mummunar magana ba,hasalima ko meye zatayi ba ita cikin masu yi mata caaa. Abinda kuma ta gani idanun ama din a sannan yayi kama da abinda d'a yake gani cikin idanun mahaifiya,haka kawai taji wata nutsuwa ta saukar mata tattare da ama din,bata daice mata komai ba,amma kuma bata sake musawa ba,ta kamata ta kaita bandakin ta kuma fara yi mata dukkan wani abu da tasan zai sanya taji dadi cikin jikinta,cikin hikima kuma tana shaida mata ciwukan dake jikinta don kada tayi wani abu me qarfi da zai kawo matsala a wajen. Abun yayi mugun yi mata banbarakwai tare da daure mata kai,dinki a wajen hanyar fitsarinta?, tabbas kasheta kawai maina yaso yi,bata taba gani ko jin an dinke wajen ba,sai qwalla ta cika mata idanu ta kuma ga gangaro tabi ta saman kuncinta ta hade da ruwan wankan dake a jikinta,dama koda ama bata gaya mata ba tasan wajen ba lafiya yake ba,don ita kadai tasan yadda taji gurin yayi mata,tanajin kamar ba'a jikinta yake ba,zallar radadi da zugin da yake mata ne kadai yake tabbatar mata a jikinta har yanzu yake. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 10 Kuka sosai ta sakarwa ama saboda kalar azabar da takeji sanda ama din ke gasa mata jikinta. Tausayinta ya cika zuciyar ama din fal,kamar ta zauna itama tayita mata kuka ko ta barta kawai taji da ciwukan jikinta,saidai kuma hakan ba zaya yiwu ba,gatan da zata mata kenan hakan kuma shine zai sanyata ta warware da wuri. Itama ama din bata hanata kukan ba,tana ganin idan tace tayi shuru ko kada tayi kuka bata yi mata adalci ba,aika aikar da maina din yayi mata ko uwar mata ce ita sai taji jiki,bare yarinyar da har yanzu rainonta akeyi. Tsaf ta wanketa ta lullubeta da towel,ta kuma riqeta cikin takatsantsan suka dawo cikin dakin ta tayata ta shirya,ta fidda simple gown cikin kayanta ta bata tace ta saka,sannan ama din ta matsa gaban kayan tea dake jere ta fara hadawa sultanar wadda tunda ta gama shiryawa ta maida idanunta ta kulle. Gaba daya ji takeyi ko duniyar batason kalla,yanzun waye da waye yasan abinda maina yayi mata?,me zata cewa mutane?,da wanne ido zata kalli 'yan gidansu?,qawayenta dama 'yan unguwarsu?,me ta yiwa maina haka daya gwammaci ya kasheta ya huta?,bata taba zato ko tsammanin zata farka ta ganta cikin gidan duniya ba. "Tashi kisha sultana" ama data gama hadawa ta dawo ta zauna gefanta ta fadi cikin salon lallashi. Bata iya bude qullallun danunta da hawaye ke ratsasu yana fitowa ba ta girgizawa ama din kai. Batajin akwai wani abu me sunan abinci da zaya isha shiga cikinta,sam ita bata sha'awar komai ma koda kuwa ruwa don ya zame mata dole ne ta karba a dazun ta sha. Duk yadda ama ke tunanin zata lallabeta ta karba tea din amma ta qiya,daga bisani ma daina amsawa ama din tayi,sai ta koma kamar wadda bacci ya dauka,dole ama ta mayar ta aje,saita koma kujerar dake fuskantar sultana din tana nazarinta lokaci lokaci,yayin da wani kaso na hankalinta ya tafi ga ci gaba da karatun qur'aninta ko zata samu sassauci cikin zuciyarta,ta wani bangaren kuma bata gaji ba hakanan bata sare ba da gwada kiran wayar maina,amma dai duka sammakal,ba abinda ya sauya,wayarsa a kashe take. Kafin a kirayi sallar asuba baccin gaske ya sake daukar sultana,wani irin wahalallen bacci da babu armashi ko karsashi ko kadan a cikinsa. Gyara mata kwanciya kawai tayi ba tare data tasheta ba,ta wuce bandaki tayi wanka ta hado da alwala sannan ta dawo ta tada salla. Sallamarta daga sallah yayi dai dai da shigowar aba,ta bishi da kallon mamaki,tamkar wanda baiyi sallar asuba ba?,ko kuma a nan cikin asibitin yayi?,tafi zaton hakan,don fuskarsa batayi kama da fuskar wanda ya tashi daga bacci yanzu ba,tafi kama da fuskar mutumin da bai samu cikakken bacci ba. Da sallamarsa ya shigo,fuskarnan sam babu walwala ko ta gamun gafara sai tarin damuwa da firgici. Kujera yaja gefan gadon sultanan dake bacci,ama tayi qoqarin shafa addu'arta cikin rashin qwarin gwiwa ta soma gaidashi. Gaisuwa daya rak ya amsa mata yabiyo bayanta da tambayar "Yaya ta kwana?" "Gata nan alhamdulillah" "Da sauqi jikin nata?" Ya sake jefawa ama tambayar kai tsaye "Eh,da sauqi,don har nayi mata wanka" "Yaushe likita zai shigo?" Ya kuma tambaya yatsunsa harda cikin na juna "Basa wuce shida na safe" sai ya jinjina kai kawai,bai sake cewa komai ba ya zaro wayarsa ya soma gwada kiran wata number. Bugu biyu ta shiga ya soma magana da wanda ya daga kiran "Inason ayi cancel tafiyar nan,a maidata sati na sama.....eh yau din gobe dama jibi duka ina da wani uzuri..... okay yayi Allah ya kaimu" ya fadi qasa qasa. Maganar da taji aba din yanayi shi ya tuna mata da shirin tafiyarta Nigeria wanda da a yau zata yishi,sam wannan abun ya sanya ta manta da komai,sai ta ciro wayarta tana dubawa. Tarin miscal ta gani na masu aikin gidanta na nigeria,musamman bilki miscals dinta yafi na kowa yawa,sai kuma miscal din yayanta. Dukkansu tasan kowa yanason yaji qarfe nawa ne zata sauka,ta duba lokaci har yanzu a biyar da rabi suke,idan ta kira yaaya din a daidai lokacin yayi safiya da yawa,tunda ko banza me iyali ne shi,don haka saita soma kiran bilki. Dab da zata katse ta daga tana fadi cikin girmamawa "Afuwa hajiya,bacci ne ya daukeni bayan na idar da sallah,ina kwana?" "Lafiya lau bilki"ta amsa mata cikin rashin karsashi "Yauwa dama inata son naji qarfe nawa zaki sauka don nasan me za'a tanadar miki,don tun jiya an gama kintsa gidan,me gyaran batiran inverter dinnan ne kawai bai iso ba,amma shima yace qarfe bakwai na safiya zai shigo" Boyayyen numfashi ta saki "Ya taho a nutse,kada kuma ku dora komai saboda ni,tafiyar nan ba yau ba" "Toh hajiya,sai gobe kenan?" "Ba gobe ba kuma jibi ba,kawai duk sanda na shirya sake zuwan zai sanar muku" "To hajiya,Allah yasa lafiya,Allah ya bamu aron rai" "Ameen" kawai ama ta amsa mata tana gimtse kiran. Yadda dakin yayi shuru da yawa saita kasa sakewa,haka kawai takejin wani iri,daga ita har aba kalma daya game da ciwon nata hadasu ba wai da zummar tattauna,batasan inda ya dosa ba ko kuma me yake saqawa a ransa ba,sai kawai ta buge da danna wayarta,wanda ita kanta batasan me takeyi ba,kafin daga qarshe ta shiga sms ta soma rubutawa maina gajeran saqo ta number wayarsa _"Duk inda kake kada ka kuskura kakai dare baka dawo gida ba,wannan din umarnina ne"_ . Abinda ta rubuta masa kenan a gajarce ta tura masa. Qofar aka taba sannan kuma aka murdata aka bude. Dr chafa'atou ce sanye da kayan gida,kai bazaka taba cewa likita bace ita din. Da alamu sammako itama tayi,kuma duk yadda akayi ta kwana da abunne itama cikin ranta. Cikin girmama juna suka gaisa,ta gaida aba cikin matuqar girmamawa shima,sannan ta fara duba sultana din tana yiwa ama tambayoyin yadda suka kwana. Tun sanda Dr chafa'atou ta shigo sultana ta farka,amma data fahimci ba su kadai bane cikin dakin harda aba sai ta kasa bude idanunta,saidai kukanta data dora ta hanyar fidda qwalla,wanda sam basu lura ba sai da Dr chafa'atou tasa hannu ta juyo da fuskarta tanason ganin yanayin idanunta. Ta fahimci ta farka kuma kuka takeyi,sai kawai ta yagi tissue tana goge mata hawayen cikin takatsantsan din kada ta fama mata fuskarta,tasan tana tsananin yanayin da take ciki,so ba buqatar ayi maganar da zata ji ta takura ko a tilasta mata boye damuwarta ko don gudun kamuwa da depression da tayi imanin indai ba'a yi da gaske ba tana iya tsintar kanta a ciki muddin ba'a kula da kyau ba "Dr ina fata komai lafiya" aba ya tambayi Dr chafa'atou kai tsaye. Sai data dan juyo kadan ta kalleshi sannan ta maida dubanta ga fuskar sultana "Eh lafiya alhamdulillah,saidai idanun nan nata inajin anjima kadan sai an dubashi sosai,don yaqi sauka daga kumburin da yayi,sannan da alama ma kamar bata iya budashi da kyau ma ko?" Tayi tambayar tana me neman amsa daga wajen ama. Kai aman ta gyada mata tana bata tabbaci. "Oh.....bayan abinda ya aikata kuma har sai daya hada da illatamin idanun yarinya?" Aba ya fadi da wani irin tune,wanda sai a yanzu ta gama fahimtar inda aba ya sanya gaba akan case din. "Ba matsala in sha Allah" Dr chafa'atou ta fadi don ta kwantar masa da hankali. Kai ya jinjina da qarfin gaske hannayensa zube a aljihun wandonsa "Kuyi mata cikakken bincike,idan da wani matsala inaga zaifi kyau ku bani ita na fita da ita waje ayi mata dukkan abinda ya kamata" Ya fadi yana hadiye wani abu me daci dake taso masa,tsantsar tausayin yarinyar da kuma rashin imanin maina qarara yana bayyana a idanuwansa. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 11 _______________________________ *_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_* *_SUTURA ABAR TUNQAHO_* *_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_* _Magana akeyi ta_ *UMMU MAHNOOR LUXURIES* *UMMU MAHNOOR LUXURIES* _GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_ *_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_* *_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_* *_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_* *KYAU* *QUALITY DA DAUKAN HANKALI* *LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA* *GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA* *_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_* 08135142610 *INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES *FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA *_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_* *_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_* *_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_* *TASTED AND TRUSTED*👌👌👌 _____________________________ "karka damu alhaji,in sha Allah zamuyi duka bakin qoqarinmu" kai kawai ya jinjina sannan ya waiwaya yana duban ama "Na kirashi yafi sau shurin masaki ban sameshi ba,ban sani bama ko blocking dina yayi?,me yiwuwa tunda ke uwarsa ce bazai iya miki haka ba,idan kin sameshi ki shaida masa saqon da yabar mana ya riskemu,munga result kuma a qasa mun gode" daga wannan ya sanya kai ya fice,sai ama ta bishi da kallo baki sake. Me aba yake nufi ne?,baisan yadda suke nemansa itama hakan bane,ta kirayeshi bata sameshi ba?,sannan tayi zaton zaiyi maganar ya dawo gida ne ya karbi hukuncin da ya dace dashi,a maimakon hakan sai taji wata magana ma yakeyi daban wadda a nata ganin a yanzun ba nanata maganar bane ya kamata a dinga yi,abinda yafi kyau shine asan meye abu na gaba da ya kamata ace an aiwatar. K'arfe bakwai da rabi sai ga bibi an kawota,ita da matar oncle umar. Jikinta sanye da lallausar bubu cotton 'yar saudiyya,hannunta riqe da casbahar da kana gani kasan itama ita ta kwana ja. Dukkansu suna a gaban gadon sultanar suna mata sannu,saidai ba wanda ta tankawa,hasalima ko qwayar idanuntan taqi ta bude ta kalli koda bibi dinne,sai hawaye da suke bulbulowa ta qasan idanun. Juyin duniya bibi tayi ta bude ido amma ta qiya,duk da dama daya idon ba wani buduwa yakeyi sosai ba,koda ta bude dinma bawai ganin komai tarwai takeyi ba. Da bibin ta gaji ta koma lallabata ta tashi taci abinci,abincin da tafiso ta sanya tanja ta dafa mata tun sassafe,shima har bibi din tayi ta gama bata ko motsa ba bare ta nuna tasan me sukeyi,daga qarshe ma sai ta gyara kwanciyarta ta basu baya ta fuskanci bango sanda 'yan dubiya suka fara isowa dakin. Ita daya tasan me takeji cikin zuciyarta,wani baqinciki da wani abu me tauri ne tokare tsakiyar maqoshinta. Kunyar kallon kowa takeji,hakanan kuma haushin kowa takeji. Ta tabbatar inda bibi bata biyewa umarninsa ba ta sakata a gaba sun tafi yadda suka saba da yanzun babu abinda ya sameta. Kusan ta tarkata dukka laifin ne ta azawa bibin,tana ganin sassaucin da ta yiwa maina dinne har ya samu qofar aiwatar da mummunar nufinsa a kanta. Wasa wasa sai gashi takai har qarfe biyu na rana bataci komai ba,maganinta ma babu wanda tasha a ciki sai uban kuka data saka gaba. Duk wani motsin sultana din yana kan idanun ama,a yanzun tana sake jinta ne kamar saddi,tana ji kuma har cikin rai da zuciyarta nauyinta ce sultana,dolenta ce sultanar. Biyun da 'yan mintuna su yasmine da aminata suka shigo da abincin rana. Muryoyinsu kadai suka sake haifarwa da zuciyarta wani sabon rudanin. Yanzun fa kenan itan ba daidai take dasu ba?,dukkansu sun fita walwala nutsuwar zuciya da kuma 'yanci?,a cikinsun yanzun itace daban kenan?. Har suka gama leqata suka mata sannu bata motsa ba kaman yadda takewa kowa. Hankalin ama yana kai,don haka bibi na fita sallah ta sanya kowa yabar dakin,ta maida qofa ta rufe sannan ta tako a nutse inda sultanan ke kwance. Kiran sunanta tayi amma bata amsa ba,bata tsaya batawa kanta lokaci ba ta durquso saman kanta ta kuma sanya hannayenta dukka biyun tana dagota daga kwanciyar tana fadin "Haba sultanan bibi.....subhanallah" ama ta fadi kuma daga baya bayan taji yadda jikinta ya dumame da wani mugun zazzabi. Zagayowa tayi ta zauna sosai kusa da ita tana riqe tafin hannunta idanunta akan rufaffun idanuwanta "Yanzun da wannan zazzabin a jikinki kike kwance?,sultana kinason kashe kanki ne?,kinaso yayi miki dariya yace yayi winning a kanki?,kinaso yaji cewa burinsa ya cika na cusguna miki?,kinason sanyawa bibi hawan jini ne?,ko kinaso aba ya shiga matsananciyar damuwar da zai dinga kasa komai?" Shuru bata amsa ba,saidai kukanta yanzun ya qaru ya zama me sauti ba kaman daxu da take yinsa silently ba. Tana jin inama ace ama zata iya farka qirjinta ta cire mata zuciyar daga qirjinta ko zata samu sassaucin abinda takeji,inama ace mutum yana iya shafe rayuwarsa gaba daya ya sake rubuta sabuwa,inama ace ta rufe ido ta bude taga ba itace sultanar familyn MAYAK'I ba "Sultana.....babu ci babu sha babu shan magani,me kikeson yi idan ba kisan kai ba?,kina azabtar da kanki bayan shi wanda yayi miki laifin har yanzu bai waiwayi gida ba bare yasan kinayi,me yasa kike azabtar d kanki da kanki?,duba......yanzu lokacin sallah ne amma tunaninki ko kiyi sallar baya baki?" Sake barkewa tayi da kukan tana cusa fuskarta tsakanin cinyar ama tare da qanqame ama da kyau. Kuka takeyi sosai me sauti,sautin kukan dake fita da wani irin mugun radadi da ciwo da zukata suka tara. Sosai ta sake karya zuciyar ama,sai ta dora hannunta saman kanta tana shafa sassalkan gashinta da ya zama kamar na tsohuwar mahaukaciya tsakanin jiya da yau saboda tsananin firgici da tashin hankalin da take ciki. Sumar da ake bata lokaci wajen gyarata da qalqaleta amma a yau bata da maraba da radaddagaggen zare cikin tarin tarkacen bola. Ta yarda da maganar Dr chafa'atou sai anyi da gaske akan sultana din,idan ba haka ba depression din tsaf zaya kamata. Bata dakatar da ita daga kukan ba,saidai itama tata zuciyar tayi nisa wajen tunanin yadda zata tafi da yarinyar. Sai da tayi shuru don kanta sannan ta dagata tana cewa "Banaso daga yanzu ki sake irin haka sultana,idan maina ya tsaneki ya zalunceki ya kuma cusguna miki mu dukka nan ke mukeso,mu dukkaninmu walwala da farincikinki mukeso,kuma zaya dawo ya fuskanci mafi girman hukunci,hukuncin da kuma kece zaki zabeshi da kanki". A duk sanda ta furta sunan Aliyyu ko maina sai taji wani abu tsakiyar kanta yana mata yawo kamar ana sakatar qwaqwalwarta,ambatar sunansa kadai yana sake sanya mata wata mahaukaciyar tsanarsa da takejin tamkar zuciyarta zata tsage ta fado,to amma batun hukuntashi dake hannunta kamar yadda ama ta furta sai ta samu kanta da laluben amsa,cikin manya manyan hukunce hukuncen da akema dan adam cikin rayuwa batasan wanne iri zata zaba masa ba,take kuma taji kanta ya sara kamar zai rabe biyu,tunaninsa ko daya bata qauna cikin kwanyarta,karon farko ta bude bakinta a hankali muryarta na fita da wani irin sarqaqqen amo "Ama don Allah.....kibar kiramin sunanshi.....kaina kamar zai rabe biyu" ta qarasa maganar dukka jikinta yana kakkarwa saboda wani sabon zazzabi me cakude da ciwon kai daya sake saukar mata. Yadda taga jikin nata yana rawa tilas ta kiranyi likita,a sannan dr chafa'atou ta fita sai dr nadra. Dr nadra tafi Dr chafa'atou fusata da lamarin,ta sake checking sultana da kyau tace a dakatar da shigowar masu dubiya,idaninta kuma da magariba likitan idanu Dr nouhou zai shigo zai dubata. A barta ta huta kawai,a qyaleta duk abinda take so tayin,shine zai sanya zuciyarta samun sassauci daga abinda takeji. To ba'a sake matsa matan ba,saidai duka ranar ama din tana tsaye akan sultana din,sai yamma liqis ruwan da suka sanya mata ya qare,ama ta lallaba ta sanyata tayi alwala tayi sallah daga zaune saboda dinkin da yake jikinta,ta hilaceta da qyar ta samu tasha tea cokali uku,na hudun kuwa dawowa yayi bai iya shiga cikinta ba. Ganin hakan sai ta qyaleta,tana fatan gobe tasha abinda yafi hakan. Suna tsaye daga bakin window inda zasu dinga hangota sosai ita da bibi din data gagara tafiya guda tun safen. Wayarta na hannunta dai still ya zuwa yanzu batasan adadin sau nawa tayi kiran layin maina ba. Duk sanda zata kira akace mata wayarsa na akashe sai taji ranta ya ninninka baci akan na baya. Me yaron yake nufi?,ya maishesu mutanen banza kenan?,yayi aika aikarsa ya wuce gararin gabansa babu abinda ya shalleshi?,baya tunanin a yanayin da ya barta ma ya dawo ya tabbatar da ingancin rayuwarta ko kuma akasin haka?. Isowar likita gab da dakin ya sanyasu motsawa,yace a dauko wheelchair a kawota ya duba idanun nata. Numfashi ama ta sauke tana duban bibi,dukkansu a firgice suke,sannan kowannensu kana kallon fuskarsa zakaga yayi wata rama tsakanin jiya da yau kawai "Bibi dare yana yi, inaga ya kamata ki wuce gida hakanan kodon yanayin jikinki,na miki alqawarin zan bawa sultana dukkan kulawa tamkar yadda mahaifiya zata bawa d'anta na cikinta kulawa" *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 12 __________________________________ *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba_* https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr ________________________________ Ko daya bibi bata da haufi da ama,kaf yaran gidan a gabanta aka haifesu,kuma babu wani wanda ya taba kuka da ita. Abu daya ne da ita,bata daukan raini ko qanqani,bata kuma son sakarci,duk wanda ya santa ya santa da wannan halin,don haka babu haufi bibi din tabar mata sultana,saidai kafin ta tafin tabar musu tanja saboda ama din kanta ta samu sauqin zirga zirga,sannan kuma tace da ama din "Kome ake ciki banason ki boyemin,daga maina har sultana dukkansu jini na ne,kuma jikokina ne" "In sha Allah bazan boye miki komai ba" ama ta furta tana lanqwasa yatsunta tana jin wani nauyi bibin ta sake aza mata. Sun kusa a qalla awa biyu harda wani abu kafin Dr cha'aibou ya kammala gwaje gwajensa. Ya daga result na gwajin da aka yima idanun nan cikin asibitin yana kalla sai ya maida takardar saman teburinsa yana duban ama "Ta samu matsalar rainin gani a idonta guda daya,jijiyoyin dake dauko haske sun tabu saboda duka da ya samesu ko buguwa....." A firgice ta juya tana duban sultana saboda yadda sakamakon ya daketa da kyau. Idanunta fes ta zubewa sultanar,tana zaune saman lallausan kujerar da Dr din yace ta zauna akai,ko motsi kyakkyawa batayi ba bare wani reaction,itakam meye wai ya rage mata?,ita a yanzu ko cewa akayi maina ya kasheta dawowa tayi sam ba zatayi mamaki ba "Amma ba damuwa in sha Allah,zamu dorata saman magani zuwa wani lokaci mu gani?,idan kuma akwai buqatar ayi mata glass zuwa lokacin zamu gani" ya fadi yana zaro takarda yayi rubuce rubuce akai. Hawaye kawai idanun ama keson xubarwa amma tana dannewa,don ta tabbatar muddin ta zubda hawaye akan maina alhali yana raye ko a macen ma tamnar ruwan masifa ta fidda masa. Tsananin tausayin sultanar kamar ya fasa zuciyarta. Cikin qasa da awa ashirin da hudu duka yarinyar kamanninta sun jirkice,tayi wata irin wawuyar ramar da hatta rigunanta basa zaunar mata sosai a jikinta. Da qyar da daren ta lallabata tasha madararta,madararta ta amana wadda muddin bata shata ba kaf gidan babu me rintsawa,amma sai gashi wai yau lallabata akeyi tasha din. Kamar jiya bacci ya riga daukar sultana kafin ita,kaman jiyan dai haka ta zauna,gefe qur'ani gefe wayarta tana tusa kiran maina amma dai komai bai canza ba. Batafi awa biyu da zama ba sultanan ta farka firgice tana kiran sunan maina din da qarfin. Da ita da tanja da itama ta fara bacci batasan waye ya riga wani isa gareta ba. Kuka take sosai dafe da kanta,ta ture hannuwan ama dake riqe da ita da qarfi,sai ama din ta fahimci kaman batason ganinta. Bataji komai ba don tasan situation din da take ciki,kuma Dr chafa'atou ta mata bayanin komai,zata iya tsintar kanta cikin razana da firgita da kuma miyagun mafarkai na abubuwan da suka faru da ita. Don haka ta yiwa tanja alama taja da baya ta basu waje. Sun kusa kwashe wata awar tanja na lallabata da hikimomi da dabarun data saba mata kafin ta samu kukan yaja baya,ta bata ruwa tasha saita maida bayanta kawai ta kwanta hawayen na ratsa gashin idanunta yana jiqasu da hawayen dake diga har cikin kunnenta. A wannan daren ma sam ama bata iya bacci ba,tunani ba kalar wanda batayi ba,a haka asuba ta rusketa. ********Kwanaki bakwai kenan da faruwar abun amma babu abinda ya canza. Al'amarin da ya haifar da rashin walwala rashin kuzari da karsashi cikin family din MAYAK'I. Kusan dukka sa'aninta dake gidan tamkar suma sun shiga alhini na abinda ya farun. Cikin dangi kuwa masu zuwa dubiya ne keta zarya,dadinta daya Dr chafa'atou ta hana shiga wajenta saboda tana buqatar hutu da qarancin hayaniya. Abinda ya daurewa ama kai shine fitar zancan, saidai bata da tabbacin sunsan ainihin abinda yayi silar kwanciyartata. Daga ama har bibi babu wanda bai rame ba,kada ma ama taji labari wadda kullum dare tausayin sultana yake sanyata a gaba. Kowanne dare yarinyar cikin firgici da kuka take yinsa,idan an dace bacci ya dauketa kuma tun batayi nisa ba take farkawa a razane,muddin tayi wannan razanar kuma nata baccin ya qare itama. Fargaba zullumi da rashin isashen bacci ga jinya suka taru suka yiwa ama din yawa. Gefe guda ga aba wanda bata sake ganin walwalarsa ba tun daga wancan ranar. Kullum rana zai shigo da safe ya duba sultana din,ya jima da ita yana tambayarta me takeso?,saidai babu um ba um um,hakan da dare zai sake dawowa ya kashe lokaci wajenta. Rashin maganarta ya fara tabashi,tsahon zamanin da aka haifi sultana bata taba zaman minti.biyar bakinta shuru ba,koda bata da lafiya bata lamunci zaman kurum ba,abun ya soma ganin ya wuce tunaninsa,yadda takebin kowa da komau da idanu,tana iya yin kwanaki koda nawa ne a hakan ba tare da buqatar canjin yanayi ba, kodon haka a kwana na takwas ya sanya Dr chafa'atou a gaba yace lallai ayi mata gwaje gwaje ko bayan idanunta da ya kusa nakasa mata qila ya shaqe mata mafitar maganarta ma,don wanda yayi hakan babu abinda bazai aikata ba. Dan dariya maganar ta bawa Dr chafa'atou,itadai tasan lafiya gurin yake,zallar daya daga cikin illolin da irin wadannan abubuwan suke haifarwa ne kawai data tsinci kanta a ciki. Don dai hankalinsa ya kwanta ta sanya akayi mata gwaje gwaje,kuma komai ya fito normal,ta bashi gwajin tana cewa "Kulawa ta musamman kawai take buqata aci gaba da bata,don kamar depression ne take ciki har yanzu,komai zai wuce in sha Allah,a yawaita faranta mata ranta da dukkan abinda akasan tafiso,tare da qauracewa furtawa ko tuna duk abinda zai sakata a damuwa". Lafiyar tata da aka tabbatar masa tayi masa dadi,sai ya qara adadin lokutan zuwansa,ya zauna yayita janta da irin hirarrakin da a baya yasan tafiso. Kafin wani lokaci dakin asibitin nata ya cika da kayayyaki,kama daga teddies chocolates,madararta,games kala kala da tarkacen kayan computer. Komai saidai ta bishi da ido,yadda zai gwada mata ya aje shi a wajen bata sake tabashi. Tana jin bata qaunar komai,bata buqatar komai,hakanan komai bai bata sha'awa,inda zasu gane su qyaleta ita daya cikin daki,kowa kada ya kulata,kowa kada ya tanka mata da hakan zaifi faranta mata. Don kusan kowa ta gani da ya danganci gidansu bata ganin komai tattare dashi sai ALIYYU MAINA,suna Mafi girman da ta yiwa mafifiyar tsana,sunan da inda tana da hali da daga rana irin ta yau ta shafeshi a doron duniya,halittar da takejin a rayuwa babu halittar data cancanci azaba irinta. Sannu sannu komai bai canza ba illa ciwukan jikinta da suka warke din,kumburin fuskarta ya sabe dai dan tabbai masu launin pink,hakanan dinkin qasanta ma ya hade kasancewar akwai quruciya tattare da ita,sannan kuma ama ta tsaya tsayin daka tayi bata kyakkyawar kulawar da banda ciwon dake cikin zuciyarta da babu abinda zai hanata mulka qiba. To a maimakon qibar sai wata mummunar rama da tayi mara kyan gani. Kwanansu ashirin cif Dr chafa'atou ta tabbatar da samun lafiyarta ta kuma rubuta mata sallama tare da bawa ama qarin shawarwarin yadda zata ci gaba da kulawa da ita don a samu rayuwarta ta koma daidai kamar ta kowa. Motoci biyu ne cikin motocin gidan iyalin mayak'i sukazo daukarsu. Karon farko da ta fita daga asibitin tun ranar da ta kawo sultana. Tun dava randa ta koma ta wanke zanin gadonsu bata sake barin asibitin ba,don duk inda zata motsa sai taga kamar sultana zata rasa wata kulawar,kamar sultana zata buqaceta,kamar wani abun zai samu sultana din kafin ta dawo. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku* *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 13 ______________________________ *_Shin kin isa mace?,don magana akeyi ta ISASSUN MATA_* *_SUTURA ABAR TUNQAHO_* *_Ado da kwalliya shine cikar 'YA MACE_* _Magana akeyi ta_ *UMMU MAHNOOR LUXURIES* *UMMU MAHNOOR LUXURIES* _GIDAN QAWA ADO NA KECE RAINI_ *_INA AL'UMMAR KADUNA ABUJA SULEJA DAMA NIGER......HAR MA FADIN NIJERIA GABA DAYA_* *_KIN SHIRYA FITA KUNYA?_* *_MAZA HANZARTA KI LALUBI KALOLIN SUTURAR DA TA DACE DAKE,KAYAN ADO MASU_* *KYAU* *QUALITY DA DAUKAN HANKALI* *LACES NE,SHADDA CE,ATAMFOFI NA 'YAN QWALISA* *GA KUMA DESIGNERS TAKALMA DA JAKANKUNA NA ALFARMA DA FITA KUNYA* *_ZAKU IYA SAMUN MAMALLAKIYAR KAMFANIN KAI TSAYE TA WANNAN NUMBER WAYAR_* 08135142610 *INSTAGRAM* UMMU_MAHNOOR_LUXURIES *FACEBOOK* MUSA GARBA SHIFA *_Ga wadanda ke cikin garin abuja kuma zasu sameta kai tsaye a_* *_system property Nefelix estate,near amasco,galadimawa roundabout_* *_KARKI BARI A BAKI LABARI,KARKI KUSKURA KI ZAMA 'YAR KALLO_* *TASTED AND TRUSTED*👌👌👌 ______________________________ Cikin jikin ama din take kwance luf,ga duk wanda yasan sultanan zai iya rantsuwa a yanzun ba ainihin sultana da ya sani bane,ta koma wata maras kuzari ko kadan,so silent,tana daukan lokaci me tsaho kafin ka tsinci kalma guda daga bakinta. Bibi batasan da dawowarsu ba sai da suka isa farfajiyar gidan. Dukkan ma'aikata dake da duty da safen suka marmatso suna musu barka da zuwa tare da sakeyi mata sannu da jiki. Sannu da jikin da takejin kamar da gayya akeyi mata ita,duk wanda yace mata ya jiki maimakon taji dadin hakan sai wani bacin rai ya lullube. Ama na fiddota bibi ta qaraso,ta sanya hannu ta taya ama fiddo ta "Ki kwashe duka kayan ki shiga dasu ciki,wadanda keda buqatar gyara kuma a gyarasu don Allah" ama ta waiwaya tana riqe da sultana ta yima tanja umarni "An gama ranki ya dade" ta fadi a ladabce sannan ta zagaya bayan motar tana yiwa modu driver maganar ya buda boot din. "Sannu" bibi ta fada wadda ke riqe da hannun sultana daya. Kai kawai ta gyada mata bata iya kallon qwayar idanunta ba. Sun taka har veranda din bibi da zata sadaka da ainihin qawataccen falon dattijuwar. Taku daya tak sultanan zatayi ta sanya qafafunta cikin falon,har ta daga qafar sai kuma ta maida ta sauke tana ja baya kadan tamkar wadda ta hangi wani shamaki a gabanta. Daga bibin har ama duban fuskarta sukeyi,fuskar data sauya lokaci daya tana fidda wasu irin emotions dake nuna zurfin abinda ke danqare a zuciya "Mu qarasa ciki sultana" bibi ta fadi tana dubanta. Sake girgiza kai tayi a karo na biyu,sai kuma ta juya da hanzari da qaramar sassarfa,tafiyar da tana yinta ne kawai amma iska ke barazanar bugar da ita daga hagu zuwa dama,sai ama ta take mata baya,sannan cikin hanzari ta sha gabanta gudun kada ta isa farfajiyar gidan kuma wani abun ya faru ta tara musu 'yan kallo. Koda tasha gabanta kuka take haiqan qirjinta na dagawa,zaka tsammaci gasar tseren gudu ta shiga. Kamo hannunta ama tayi da kyau ta damqe cikin nata hannun,bata manta da bitar da Dr chafa'atou tayi mata kafin barowarsu asibitin,don haka cikin tausasawa ta tambayeta "Ki kwantar da hankalinki ki nutsu,u r safe,maina bai isa ya miki komai ba,yanzu ke 'yar gatan bibi da ama ce,ga aba oncle omar oncle bashar ma" kai take jijjigawa,sannan cikin muryar kuka tace "Bazan shiga ba ama" ".....akwai abubuwan da zasu iya kada hankalinta su kuma firgitata,kamar wajen da abun ya faru,abubuwan dake zagaye da ita sanda komai ya faru da sauransu,so ayi qoqarin goge da kauda komai don kwanyarta ta samu cikakken waraka....." Ama ta tuna maganganun Dr chafa'atou. Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai "Is okay ya isa,muje sashena,zaki zauna a dakina?" Idonta ta runtse hawayen dake maqale ya qarasa gangarowa,saita daga kanta a hankali tana ayyana ashe akwai ranar da zata guji rayuwar kusa da bibinta?,bibinta abar qaunarta?,ashe akwai sanda zataji gwara rayuwa nesa bibi?. Batayi yunqurin maidata sassan bibi ba ta wuce da ita kai tsaye nata sashen,saidai bibin na biye dasu,don tana kai sultana dakinnata ta barta da daya daga cikin masu aikinta,ta kuma dawo falon don ta sanya a kwaso sauran kayanta dake dakinta can sassan bibi saiga bibi din da kanta. "Wani abunne kuma hamdiyya?" Yadda bibi tayi tambayar a sanyaye sai tausayinsu su dukka ya kamata,a yau maina ya zama silar nesantarsu da juna duk da irin son da sukewa juna "Ba komai bibi,zauna na miki bayani" a nutse ta fahimtar da bibin,ta kuma fahimta duk da fuskarta ya nuna lamarin bataso ya kasance haka ba,amma a yanzun samun cikakkiyar lafiyar sultanan da dawowarta hayyacinta shine gaba da komai. Kafin yammaci komai na sultana ya koma sassan ama,ta fidda komai nata daga dakin ta sanya an sauya mata daki,ta barwa sultana wannan. Zuwa magariba komai ya kammala. Da kanta bayan ta kintsa ta dawo ta saka sultana a gaba tayi wanka,ta bata kaya ta sauya sannan ta sake tusata sai data ci abinci. Abinci ne lafiyayye da tasan zai sanyata ta ciko ta kuma tada komada. Tana da buri da fatan nan da sati daya kacal ma sultana din ta sauya ta fara komawa sultananta ta asali. Ko na minti daya ama bata barinta ita daya bare tayi wani tunani da zai hatsinata. Bayan sallar isha'i ta sanya bilki ta fiddota ta zauna falo kaman kowa. Dai dai lokacin aman tana zaune saman daya daga cikin kujerun falon. Tab ce a hannunta tana duba hotunan kayayyakin dake cikin container dinta data sauka wadda bata samu nutsuwar dubawar ba sai yanzu,saidai rabin hankalinta na ga wayoyinta wai ko zataga gilmawar wani abu da ya shafi maina. Ita kanta ama din ta fada tayi fayau,amma wannan kyan dai da gayun nata yana nan. Ko a yanzun wani cotton material ne a jikinta da aka yiwa budadden dinki,dogon hannu ne saidai an tsagashi ta sama har kusa da damtsenta. Qafafunta na harde guri guda,saddi yana zaune daga qasa kusa da qafafun na yana tattare mata wasu takardu. Tunda taji alamun tahowar bilki ta shinfidadden marbles din dake malale a dukka ilahirin sassan ta dauke hankalinta daga tab din ta maida inda suke nufowar don taga sultanan tayi wankan kwanciya ta kuma sauya kayan kamar yadda tace mata tayi. Batakai ga lura da wannan ba idanunta suka sauka kan fuskar sultanan,wadda gaba daya manyan fararen idanunta ke kafe waje daya a falon,sai kuma a hankali a hankali ta soma tsaiwa kafin taja da baya da gudu kuma ta koma ciki da sassarfa kuka yana qwace mata. Kwata kwata ama batasan da shigowar aba ba sai data waiwaya tana duban abinda ya sanya sultanar razana da kuma komawa cikin. Babban hoton maina ne. Sanye da wasu kaya na asalin buzaye, kayansu na gargajiya,kanshi yasha nadin rawani irin nasu fari qal,kamar yadda ainihin kayan suke baqaqe ne da adon farin zare. Hoto ne da ama din ke masifar so,saboda ya fita aininun,ya kuma fidda kamannin maina da baiwar zallar kyau da Allah yayi masa,kyawun dake cakude da quruciya da tashen shekaru. "Kai saddi!,zo ka cire hotonnan" aba ya furta cikin kakkausar murya wani abu me zafi yana gilmawa ta cikin idanunsa. Ba musu saddi din ya miqe cikin sanyin jiki bayan ya ajema ama takardunta,ya nufi hoton yana jawo wani stool me kyau dake gefe wanda aka azama decoration flower,ya sauke flower din ya taka saboda tsahonsa bazai kai ba,maina dinne da kansa ya kafa hoton bayan an wankoshi,naira dubu talatin da biyar ama din ta bayar akayi mata shi. Qasa ya saukeshi kamar yadda aba ya buqata,yana tsaye daga bayan saddi din ya sake cewa "Juyashi ya kalli bango" juyashin yayi kamar yadda ya buqata,sai ya sake kallonsa "Duk wani hoton aliyyu dake sassannan komai qanqatarsa a fiddashi,banaso na sake gani" ya fadi yana nuna saddi da yatsa kamar shine me laifin "To aba" ya amsa masa cikin ladabi. Bai sake cewa komai ba ya juya yana wucewa qofar da zata sadashi da gefansa,sai sannan ama tayi qarfin halin cewa "Sannu da zuwa" "Yauwa" ya bata amsa yana dan dubanta kadan kafin yaci gaba da tafiya. Rasa waye zatabi tayi cikin aba da kuma sultana?,daga qarshe ta yanke shawarar bin sultana din,don a yanzun ita keda cikakken buqatar a rarrasheta,aba kam batasan meke yawo a kansa ba,alamu sun nuna kamar ma dai ita yakewa kallon maina. Kallon saddi tayi daketa aikin bi yana kauda hotunan maina din, fuskarsa shima ta nuna yadda zuciyarsa ke masa rashin dadi,sai kawai ta fasa maganar ta juya tana fita a falon. A takure ta sameta,fuskarta tsakiyar qafafunta tana rusgar kuka,wannan karon harda marayan sauti dake fita daga muryartata. Duk sanda taga kuka ya barke mata irin hakan tana narka zuciyar ama,tasan cewa yau koda da wayonta maina yayi mata haka dole taji abun har zuciyarta,koda tana sonshi,balle ita din da ta tabbatar babu komai tsakaninta da maina din sai ADAWA DA GABA DA KUMA TAKUN SAQA. Qarfe goma harda rabi tabar dakin bayan bacci ya dauketa bayan ta gama koke kokenta. Ta fahimci bawai hotunan maina ba kawai,hatta da sunansa bata qaunar jin wani ya furta koda bawai ana nufin shi aliyyun ba. Tanason shiga ta iske aba,amma sai zuciyarta tafi karkata da ta tafi dakin maina din. Iya qurar dake jikin handle din qofar dakinsa kadai ta isheka amsar cewa yayi nisa da wajen,nisan da ko qofar dakin da alama babu wanda ya sake tabawa bare a samu sassaucin qurar dake sauka. Ga mamakinta key din dakin yana maqale a jiki. Hannu tasa ta murza ta tura qofar ta shiga. Da idanu tabi falon nasa da kallo,falon da baya rabo da tsafta,falon da baya rabo da qamshi,falon da ko yaushe cikin qyale qyale yake,amma a yanzun qura ta soma samun wajen zama. Takawa tayi cikin falon ta danyi shawagi,idanunta manne da hotunansa qwaya hudu rak dake maqale a bangon falon. Dauke kanta tayi ta tura qofar dakin gadon nasa wadda itama dai a bude take,barin qofar kuma a bude na sake haifar mata da tunani da kuma kokwanto me yawa. Dan razana tayi kadan da ganin mutum cikin dakin,amma yana dago fuskarta data fahimci waye saita daidaita nutsuwarta "Qaraso ciki mana" aba ya fada ganin taja ta tsaya daga qofa yana maida hankalinsa ga gurin da maina ke ajjiye duk wani abu nasa me muhimmanci "Kema sahunshi kika biyo?" Ya sake jefawa ama tambayar. Ganin yanayin aba din kawai sai ya haifar mata da rauni "Aba,kwana........" "Kwana goma sha hudu kenan ba.....babu shi ba dalilinsa,bai nememu ba bai kuma dawo gida ba,ai dama bazai dawo din ba,saboda mu din ba wasu mutane bane dake da muhimmanci a tattare dashi ba,inda muna da muhimmanci muna da kima da martaba tun asali da bai aikata abinda ya aikata din ba,yarinya qarama tsakiyar iyayenta da kakanninta, bashi da asara kota sisin kwabo shi yasa ya tsallaketa ya kuma biyo ya dakinsa ya iya tsaiwa tattara komai nasa me muhimmanci,kinga yabar mana saqo tare da tabbacin cewa kada muce zamu nemeshi,don a yanzun ya zama d'an kanshi bashi kuma da buqatar wasu iyaye". Kalaman aba daya bayan daya suka dinga dukanta har sai da suka sanyata sulalewa ta zauna gefen gadon maina dake a mulmule sai 'yar qura data sauka akai. Hannunta har dan rawa yakeyi sanda ta kalli wajen taga kaf komai nashi da suka sani me daraja yana adanawa a wajen fes babu komai wajen. Duk da taga zahiri amma zuciyarta taqi aminta da nata zargin da kuma sharhin aba,sai ta fara girgiza kai idanunta suna nuna zallar tashin hankalin dake yawo a jiki da zuciyarta. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 14 _________________________________ _Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr __________________________________ "kar kayi haka aba,kaifa uba ne.... kada ka yanke hukunci cikin bacin rai da kuma zato....." "Wanne zato kike magana akai hamdiyya?,bayan ga zahiri?,ga zahirin da duk me hankali yasan inda ya dosa?,ya kuma san abinda yake nufi?" "Aba.....don Allah ka tsaya mu tattauna.....bai kamat......" "Meye bai kamata ba?,shin kinsan mummunar illar dake tattare da barin hawaye yana zuba a idanun maraya?,kinsan illar kukan maraya?" Kai ta girgiza da sauri "To ya isheni hakanan,aliyyu yayi abinda rai da shaidan ya raya masa ko?,to nima banga abinda zai hanani daukan mataki a kansa ba". Ta sanshi farin sani,ta sanshi magana daya yake,ta kuma sanshi cewa kaifi daya ne,tunda yahau dokin naqi bazai saurareta ba,to amma ita din cikin jikimta da zuciyarta taqi gamsuwa da hasashen aba akan maina,bawai don tana daure masa qarqashi bane,a'ah......ita kanta taci alwashin hukuntashi a duk sanda ya bayyana cikin gidan,to amma kuma wannan shirun fa?,ba kwana daya ba biyu ba?,ba sati daya ba ba biyu ba?,shi din ba gwanin yin nesa da gida bane,hakanan ba gwanin son yawace yawace ba. Baya shan komai bashi kuma da abokan banza,ina yayi da nesa haka?. Ita daya cikin dakin nasa bayan aba ya fice ya bata guri takewa kanta wadannan tambayoyin. Sai kawai ta fidda wayarta ta soma laluben numbers din mutum biyu cikin abokansa kuma roommate dinsa,wato faisal mus'ab. Suna gama gaisawa suka cillo qorafin daukewar maina daga makaranta,bayan ya sani lokacine da suke dab da fara jarrabawa,ana da buqatarsa,jarabawa ce me matuqar muhimmanci wadda zata bashi damar shiga gaba ta biyu ta karatunsa,gabar kuma da zata baka tabbacin sake samun gurbi da kuma gindin zama cikin karatun. Jikinta a sanyaye sukayi sallama dasu suma suna jimanta batun,wai ba'a san ina maina ya shiga ba?,kamar qaramin yaro?,hankalinsu yadan dagu saboda basusan ainihin abinda yake faruwa ba,sundai yima ana alqawarin bincikoshi muddin yana niamy cikin makaranta ko wajen makaranta. Ji tayi kaman ta sanya hannunta saman kanta tayi kuka. Jarabawar da zasuyin yanzun ya jima yana bata labarinta tare da buqatar addu'arta. Ta tabbatar bawai qanqanin abu bane zai sanyashi tafiya ya barta ba,amma kuma tana saka ran ko ina ya shiga jarabawar dake tsaye a ranshi zata koro musu shi. Da daya da daya take kiran duk wanda tasan zata iya samun wani abu game da maina,saidai har ta gama kiran aqalla mutum ashirin cif ba wanda yaga koda gittawarsa. Dole ta sare ta kuma tabbatar zaiyi wuya idan ba wata GAGARUMAR K'ADDARAR bace ke shirin sake tunkarota. "où est-il allé?(ina ya tafi?)" Ta yiwa kanta da kanta tambayar da itama amsarta take nema. ********K'arfe sha daya ne na safiyar ranar asabar wadda ke dauke da yanayi maras zafi duk da cikin yanayin zafin ake. Saidai a ranar sosai zafin ya sassauta saboda alamu dake bayyana yiwuwar samun ruwan sama kowanne lokaci. Cikin gidanma babu wata hayaniya,don kusan duka yaran gidan sun fita da safen saboda yin siyayyar komawa makaranta a ranar litinin dinnan me zuwa. Cikin qawataccen falon ama din wanda ke dada qara nuna alfarmarta da alfarmar dawwamar arziqin masu gidan,tamkar ma basu taba wani zamani da kalmar babu ta ratsa ta tsakaninsu ba. Sultana ce zaune saman daya daga cikin royal chairs na dinning din. Cikin wata irin nutsuwa take zaunen,tana sanye da wasu cotton kaya hot pink. Gown ce me gajeran hannu data saukar mata har gwiwa,sai wandonta da ya lafe a jikinta. Kanta off_white silk scarf ne da ya lullube asirin sassalkan gashinta wanda ke daure a siririn band, yafi qarfin boyuwa ta cikin scarf din don haka ya fiddo ta qasansa ya bazu zuwa sassan kafadunta. Warwaraye ne sirara guda hudu da ama ta siya mata a nigeria masu kyau masu kalan gold jere a kyakkyawan hannunta,ta sanya yatsanta guda daya tana wasa dasu ta hanyar warasu da kuma hadesu waje daya. Tun daga qofan kitchen da ama ke takowa dauke da kofin madara take qare mata kallo. Cikin wata biyu da faruwar abun qaramin fadi tashi tayi ba wajen ganin sultana din ta farfado. Ciki kuwa harda dauketa da tayi sukabar nijer gaba daya suka tafi nigeria. A nigeria dukka tayi wasu yaqin,ta kuma samu nasarar don sultana din ta soma komawa hayyacinta. Burbushin damuwa da suka ragewa zuciyarta kusan dukka ta ciresu,ta karbi zaman Nigeria da kyau,ta canza sosai,abinda ya yiwa kusan kowa dadi. Duka duka basufi sati guda da dawowa ba. Yanayin zaman da sultanan tayi saman kujera ya tabbatarwa ama wani tunanin takeyi. Abinda kuma sam bataso kenan,amma dan adam ne,duk yadda takai ga qurewa wajen ganin ta bata kulawa dole akwai abubuwan da bata isa ta hanata ba,dadin da takeji cikin ranta kawai shine sauyi da take sake samu,ta soma yin wani irin fresh,haskenta tamkar ana qara mata shi,qiba ce har yanzun babu ita sam. "Tunanin me akeyi?,a bawa ama labari" ama ta fadi sanda ta isa gabanta tana jan kujera guda daya dake kusa da sultana din tana zama. Dago fuskarta tayi suka hada idanu,sai sultana din ta dan saki murmushi,alamun kunya dukka suna nunawa cikin qwayar idanunta. Zata iya cewa ba zata iya tuna zaqi ko dandanon soyayyar uwa ba,amma adan tsukin da tsautsayin ya saukar mata ta samu dukkan wata kulawa da d'a ke samu wajen uwa. Wani irin sabo me tarin yawa ya shiga tsakaninta da ama irin wanda bai taba hadasu ba,har wasu lokutan idan ta kebe take mamakin ashe dama haka take da kirki?,ashe da gaske ne abinda su aminata ke fadi a kanta a baya?. "Ba komai" ta fada da wani irin sanyi wanda ya soma zame mata dabi'a,sanyin da abaya sam sam sultana bata sanshi ba cikin rayuwarta. "To Allah yasa,maza ungo" aman ta fada tana miqa mata mug din hannunta me dauke da madarar shanu data tafasa mata ita da duminta. Bata musa ba ta miqa hannu ta dauka,a nutse takai bakinta sai kuma ta sauke tana duban cup din "Yaya dai?" Ama data dauki wayarta tana son duba calendar don ganin yau din adadin kwanaki nawa maina ya qara rabonshi dasu ta furta tana kallon fuskar sultana "Na qoshi" ta fadi a sanyaye tana dan dora hannunta saman wuyanta. Da mamaki ta dubeta "Amma kaman ke kika cewa bilki a kawo zaki sha ko?" Kai kawai ta dagawa ama,sai ama din ta sake maida hankalinta kanta,cikin sassauta murya tace "Sultana banaso ki dawo da dabi'ar qin cin abinci fa,don Allah karki maido mu baya kinji?,na lura tunda muka dawo nijer kike gujewa abinci,idan nijer dinne bakiso mu koma nigeria ne gaba daya to" kai ta girgiza mata alamun a'ah,sai kuna wasu siraran qwalla suka biyo fatar idanunta. Ita batasan yadda zata yiwa ama din bayani ba,kwata kwata kamar an cire mata sha'awar abinci,tanason ci amma da ta kaishi bakinta sai taji gaba daya ta qoshi,idan kuma ta tilastawa kanta din dai amai ya fara taso mata. Ama ta lura da hawayen,hankalinta yadan dagu ta ajiye wayar tata saman table "Idan kina da damuwa ni mamarki ce ki gayamin sultana" ta fadi mata tana ritsata da idanu. "Ba komai,kawai qoshi nayi" ta bata amsa tana saka yatsunta tana dauke hawayen "Ko madararki za'a kawo miki?,yanzun sai nayi waya niamy su sakota a jirgi don tafi saurin zuwa?" Kai ta sake girgiza mata alamun dai a'ah. Duk yadda ta rayu da qaunar madarar da shauqinta da kuma jin gardinta gaba daya yanzun bata burgeta "Zansha wannan din anjima" "Kinyi alqawari?" "Eh" ta amsa mata,sai ama ta gyada kai sannan ta maida dubanta ga calendar din. Lissafinta dai dai yake,kwanakin shurawa suke tamkar cikin mafarki,duk yadda take tunanin zuwa lokacin zai nemesu zai waiwayi gida zai dawo zai kirata koda a waya ne abun ya sabawa tunaninta,babu ko daya a ciki. Tayi cigiya iyakar yinta,har a kafafen tv da radio amma shuru kakeji. Aba kuma ya nade hannunsa yana kallonta,baice komai ba bai kuma sanya baki ba. Koda yaje Nigeria ma acan din su yaaya abdulhakeem fada suka dinga zabgawa kaman su ari baki "Kuna wasa ne,dan mutum guda kamar batan nama a miya?" Sun kira aba amma har suka gama fadansu baice komai ba,daga qarshe yace dasu "Aiba yaro bane qarami,ya fimu sanin ciwon kansa ma yanzun,duk inda yaje zai dawo tunda dai ba qanqanin jariri bane" ran uncle abdulhakeem ya baci qwarai,saboda ya fahimci kamar m abun bai dameshi ba. Hayatudden ne ya karba da yake ya fishi sanyi da sauqin kai yayi masa magana shima "Kuma iyayensa ne,na baku wuqa da nama yaaya,kada ku damu" jin ya fadi hakan sai ya rabu dashi kawai. Cigiyar suma suka baza sosai,amma har suka gama zamansu suka dawo da nijer din da Nigerian ba wani bayani. Tana shiga fargaba wasu lokutan,tana shiga tunani me zurfi kan yana ina,wanne hannu zai fada?,da waye zai hadu?,sai ta furzar da iska me zafi daga bakinta daidai sanda suka hada ido da sultana. Maida wayar tayi ta ajjiye cikin zuciyarta tana maimaita addu'ar data zama sirri tsakaninta da ubangijinta na ya bawa aliyyun tarbiyyarsa dama lafiyarsa kariya,kada ubangiji ya kamashi ko ya jarabcesu silar zubar hawaye a idanunsu. "Meye ra'ayinki kan komawa makaranta?" Tayi maganar tana monitoring mode dinta. Ambatar makarantar kadai kuwa ya canza yanayinta din,tayi qas da kanta,saidai kafin tace komai sai ga yasmine ta shigo,rungume da ledar data tabbatar siyayyyar da suka fita yine "Sultana ga mariam inoussa ita da aicha ousmane,muna dawowa muka gansu wai basusan a nan guraren kike ba,'yan uwan gidansu alhaji saddam ne ashe". Kaf walwala da fara'ar fuskarta ta dauke,ta saki baki kawai tana duban yasmine kafin tayi magana a hankali "Ki dakatar dasu ki gaya musu bacci nakeyi" ta fadi maganar da iyakacin gaskiyarta ne,saboda a yanzun bata qaunar hulda da duk wadanda ta sani a baya,musamman qawayenta na makaranta dama na cikin unguwa gaba daya. Gani takeyi kowa ma yasan meye ya faru da ita?,kuma kowa kallonta yakeyi da abun. Turus yasime tayi tana duban sultana,kwata kwata ta canza,ko su dinma ba komai take shiga nasu ko ta sanya baki ba "Yasmine,jeki ki gaya musun" ama ta yiwa yasmine magana,sai ta amsa tana juyawa tare da barin falon. Tun a nan ta fahimci tana da buqatar canjin makaranta ne,don haka a washegari lahadi tayi mata register da wata makarantar daban. Makaranta ce me mugun tsada wadda har tafi waccan tata ta bayan tsada kuma tsari. Tasan muddin idan ba hakan tayi ba ba zata sake ba,gwara ta kaita cikin wadanda bata taba sani ba,yadda ba zatayi dari dari ko ta kasa sakewa tayi karatu cikinsu ba. Duka a ranar lahadin ta sauya mata komai da komai,hatta da ruwa da drinks na zuwa makaranta da zata iya buqata kamar wata 'yar free nursery. Duk dai a ranar ta fidda mota guda cikin motocinta duk da dama already sultanan akwai motar kaita makarantar,amma tace a ajjiyeta,saboda tana da burin ta sake sabuwar rayuwa,batason komai nata data taba amfani dashi a baya yanzun a dawo dashi,don hatta da sutturu duk uban tulin kayan sawarta ta sanya tanja ta fiddasu,batasan rabawa sukayi tsakanin ma'aikatan ba ko menene oho,itadai duka tayi mata juyen closet nata. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 15 *_les jumeaux_*(the twins)??? K'arfe biyu da rabi motocin yaran gidan dake jigilar kaisu makaranta suka fara saukesu,a lokacin ama tana zaune a samanta,tana jin motsi da kai kawonsu,saidai aikin da takeyi ya dauke mata hankali,batajin zata iya saukowa a sannan,saddi ne yana yima kansa komai don ba qaramin yaro bane bare tace zai nemi wani abu daga gareta,sai sultananta da tasan ita dinma indai ba wani abu ta buqata ba ba lallai ta nemi ganinta. Waya ta dauka ta kirayi bilki me aiki tace ta duba mata sultana ta dawo?. Ba jimawa ta sake kiranta "Ta dawo hajiya" "Yauwa to,ki bincika ko akwai wani abu da take buqata,idan babu shikenan,sai la'asar ni zan sauko" "To hajiya" ta amsa mata a ladabce tana aje wayar. Mintuna biyu rak bilkin ta sake kiranta "Hajiya qofarta rufe take" dan shuru ama tayi "Lafiya?" "Eh kaman lafiya gaskiya don na danji motsinta" "To yayi,ki rabu da ita wala'alla hutawa takeyi,sai na sauko din" "To a sauko lafiya" bilki ta amsa mata. Wayar ta aje tana dan nazari kadan tare daci gaba da aikinta da take gab da kammalawa. Lissafin shekara shekara ne,wanda bayan ta kammala din take fidda zakka haqqin Allah. Tana gamawa din yadda taso ta zauna ta huta sai tayi sallar la'asar kuma amma sai taji hankalinta yayi kan sultana. Kashe mini laptop din tayi,ta zura tausasan slippers dinta ta miqe tana nufo stairs din. A nutse ta sauka ta kuma nufi sashen dakunan dake qasa. Tana ratsa falon suna gaisawa da masu aikinta da yau duka basu samu ganinta ba,tana amsa musu tana dosar dakin,har ta isa qofa. Murdata tayi har yanzu tana kulle,ta kira sunan sultana din sau biyu bata amsa ba,sai ta juya yana yiwa fainusa magana kan ta duba store ta ciro mata spare key. Cikin qasa da minti daya fainusa me aiki ta dawo da key din ta miqa mata,ta karba ta soma gwadawa har ta samu na dakin. Dundum yake kamar ba rana ba,cikin mamaki ta kunna fitilar dakin haske ya gauraye,idonta ya sauka kanta sanda take nade tsakiyar gado lullube da qaton duvet. Mamaki ya kama ama ta kira sunanta tana takawa ciki hadi da cewa "Bakijin zafi zaki rufa haka?,wanne irin bacci ne wannan sai an rufe kai?" Ta furta tana janye duvet din. Razana tayi ganin yadda sultana din ke qudundune guri guda tana rawar sanyi sosai. Farar fuskarta ta sauya launi zuwa pink color kaman yadda tasan tanayi a duk sanda take zazzabi irin wannan ko wani ciwo. Tun bata kai hannunta ba take iya jin hucin dake fita daga jikinta gaba daya,duk da hakan sai ta miqa hannunta da sauri tana taba sassan wuyanta. Saukar hannun ama a jikinta sai taji kaman an qara mata ciwon,ta maqale wuyan wasu siraran hawayen suna fita daga idanunta "Ya salam ya Allah" ama ta furta,zafin dake jikinta yayi yawa qwarai,sai ta dauki remote na ac din dake gefan gadon ta soma da kasheta,sannan ta juyo ga sultana din tana zama sosai a gabanta "Dama dashi kika dawo daga makaranta?,tun yaushe ne?" Ta tambayeta cikin tsananin damuwa "Tunda na shiga classe(class)" kai amma ta girgiza tana jin hankalinta yana daguwa "Bari na kira Dr chafa'atou,zafin zazzabin yayi yawa" ta fadi tana sauka daga saman gadon sannan ta koma zuwa sassanta da gagggawa. Qasa tayi da kanta tana lumshe idanuwanta bayan fitar ama. Wasu hawayen masu zafi kwatankwacin zafin zazzabin jikinta suka biyo kuncinta. Ita daya tasan me takeji cikin jikinta,tanajin kamar ana kama qasusuwanta ana ballasu daya bayan daya,kowacce gaba ta jikinta ciwo take mata sosai. Wasu sabbin hawayen suka kuma biyo idanunta,tun daga wancan ranar...... tun daga randa yayi mata fyade......tun ranar da ya zalunceta ya cuceta bata sake samun lafiya ba......bata sake jin qarfi cikin jikinta ba,ya tafi da dukka kuzarinta,ya tafi da walwalarta da kuma farincikinta,tana jinta a cikin jikinta ita karan kanta kamar ba sultanan bibi ba,kamar ba itace ke rayuwa a wannan gangar jikin ba. Dukka wayoyinta ta debo ta dawo dakin tana gwada layukan wayar Dr chafa'atou. Bude qofar dakin ya sanya sultana bude fararen idanunta da suka sauya kala saboda tsabar zafin zazzafin dake fita a jikinta "Sannu sultana.....sannu" ama ta fadi cikin kulawa ainun tana zama saman bedside drawer tana kuma sauraren wayar Dr chafa'atou dake ringing. Dab da zata katse ta daga,cikin girmama juna suka gaisa "Jikin patient dinki ne ba lafiya médecin(Dr)" "Tofa,me ya sameta kuma?" Dr chafa'atou dake shirin zama saman kujerarta daga can cikin office dinta ta tambaya "fièvre ne me zafi,dashi ta dawo daga école(school)" "Subhanallahi,idan yayi zafi da yawa ki samu mouchoir(handkerchief) me kyau da ruwa a goge mata jikinta,gani nan na tashi gida zan wuce dama,zan qaraso na dubata" "d'accord(okay),amma ina neman alfarma,zan saka motocin mayak'i yanzu suzo su taho dake,je ne veux pas de retard(banason jinkiri)" "Hakan yayi ba damuwa" wayar dukka suka ajjiye. Idanunta a lumshe,yadda jikinta ke zafi da quna haka zuciyarta,tana jin sanda ama ta iso da ruwan da qaramin towel ba tare data nema kowa ba "Tashi a goge miki jikin sultana la fièvre est si élevée(zazzabin yayi yawa)" kai ta girgiza a hankali sannan tace "A kiramin bibi,bibi nakeson gani" "Za'a kirata,amma a ragewa jikin naki wannan zafin kada tazo ta gani hankalinta kuma ya tashi,ko kinaso hankalinta ya tashi kuma?" Kai ta girgiza a sanyaye,sannan ta yunqura ama na riqe da ita ta zaunar da ita sosai ta rage mata uniform din,ya zamana daga half vest din da ta soma kare martabar qirjinta da su,sai gajeran wando mahadin vest din. Sam ba wani kunya tsakaninta da ama,don ta zama tamkar uwar da babu shamaki a tsakaninsu. Tana goge mata din ta kirayi layin tanja donta kira bibi din bata sameta ba,tace ta shaida mata sultana ke rigimar son ganinta yau kuma,ta tashi da wani dan zazzabi. Tanja din ta amsa mata sannan ta kashe wayar ta maida saman drawer. Tana gama goge matan akayi knocking qofar sannan aka turo. Bibi ce sanye da lallausan abaya cotton 'yar marocco ta mata me hade da mayafi. Ama ce ta amsa mata tana miqewa hadi da tattare towel da roban ruwan,ta kuma jawa bibi kujera zuwa gaban gadon da sultana ke zaune. Idanun bibi qur cikin na sultana bayan ta daidaita zamanta saman kujerar,sannan a hankali ta maida dubanta ga qirjin sultanan wanda ba baqonta bane. Wata mummunar faduwar gaba ta samu kanta da ita "La haula wala quwwata illa billa" ta fadi qasan zuciyarta,sannan ta janye idanunta ta juya zuwa ga ama dake qoqarin saqale towel din jikin qofar toilet "Me ya sameta?" "Zazzabi ama,daga tafiya makaranta" "Zazzabi kawai?,kuma iya yau?" Ta tambayi ama cikin mamaki a sautin muryarta "Wallahi bibi,kuma koda safen lafiya lau ta shiga ta miki sallama nima tayimin sallama,sun dawo nasa azo dubata su bilki suka samu qofanta a rufe,sai da na sauko dubata na sameta kwance" aman ta yiwa bibi bayani dalla dalla. Kai kawai bibi ta jinjina jikinta yana wani irin sanyi,dukka gwiwoyinta kamar an bubbugesu,wani irin fargaba ya cika mata zuciya,ta samu kanta tana furta addu'a can qasan zuciyarta......dai dai lokacin aka shaidawa ama isowar Dr chafa'atou wadda drivern mayak'i mansion ya daukota. "Kiyi mata iso ta shigo" tace dame aikin nata tana komawa opposite bibi tana zama itama,jikinta yana sanyi da ganin sauyawar reaction na bibi cikin tambayoyin da tayi mata. Har qasa Dr chafa'atou ta tsugunna ta gaida bibi. Sannan ta qarasa gaban sultana tana kallonta. Kallo na kusan minti guda,kallon da ya sanya sultana janye nata idanun daga kan Dr chafa'atou,haushi yana cikata duk da ciwon da takeji a dukka gabobinta,don meye zata sakata gaba da kallo kaman taga wata dodo?. "Bayan zazzabin kinajin wani abu dabanne?" Dr chafa'atou dake qoqarin bude dan akwatin aikinta ta fada. Da qyar ta motsa lallabanta ta bata amsa a gajarce "Babu" "Okay.....yaushe rabon da kiga period dinki na qarshe?" Tambayar da ta sake sanya razani me yawa a zuciyar bibi,ta kuma saka ama barin abinda takeyi tana duban Dr chafa'atou da batasan ma duka suna kallonta ba,don ita nata zargin yayi wani waje daban,don haka ta yankewa kanta yin abu guda daya da take da babban zato a kansa ba tare data batawa kanta lokaci ba. "Bana tunanin zata iya riqewa,don kwata kwata al'adarta ma ina jin batayi yakai sau shida ba,niketa qoqarin tsara mata calendar dinta da sanar da ita lokaci donta dinga kiyayewa" bibi ta yiwa Dr chafa'atou bayani tana dubanta "Okay ba matsala" ta amsawa bibi bayan ta gama fidda container dinta "Kina Jin fitsari?" Ta tambayi sultana tana kallonta "Kadanne" "Yimin shi a nan koda dan kadan dinne" sai ta miqawa sultana container din. Daga bibi har ama bin container din sukayi da.kallo,dukkansu sunsan gwaji akeyi da ita,kuma batun gwajin fitsari wani al'amari ne me zaman kanshi "Amma ba fièvre du paludisme(zazzabin malaria) bane Médecin?(Dr)" "Yanzun zamu gani in sha Allah hajiya" ba wanda ya iya sake cewa komai. Dr chafa'atou dince ta riqe hannun sultana har qofar toilet sannan ta dawo tana fidda kayan gwajinta. Duka duka bata wuce minti daya ba ta miqawa Dr din kwalbar ta koma saman gadon ta lafe tana rufe idanunta,don a yanzun babu abinda takeso da qauna irin ta ganta a kwance,cikin daki me qarancin hayaniya irin haka. Duk motsin Dr chafa'atou suna biye da ita,har zuwa sanda ta kammala tsatsube tsatsubensu na likitoci,ta daga pt strip din da ya bayyana komai dara dara yana sake bata haske. Saukeshi tayi tadan saci kallon ama da bibi,akaci sa'a dukkansu idanunsu yana kanta. Ajiyar zuciya ta sauke ta koma ta zauna,ita kanta tana jin fargabar bayyana sakamakon gwajin,amma kuma har kusan hada baki ama da bibi sukayi wajen tambayarta "Ya dai?,an kammala?" Kai ta gyada musu,ta aro dukka jarumta da dauriya irin ta likitoci sannan tace "JUNA BIYU GARETA!" Dif wutarsu ta dauke na dan wani wucin gadi,haka kunnuwansu suka tsaya da aiki na wucin gadin,kamar yadda kwanyarsu ta daina banbance saqon da aka aika mata dashi na wasu daqiqu. SULTANA dake a kwance kuwa taji dukka kalmomin Dr chafa'atou,amma abu daya zuciyarta da kwanyarta ta gaya mata "Bafa dake take ba,magana take akan wata" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata zuciyar na wani irin mugun bugu kamar ta balle daga qirjinta "Kin duba da kyau kuwa Dr?" Ama data tattaro dukka sauran maqalallen busashen yawun dake saman halshenta ta fadi "Na tabbata,a yadda kuma ya nuna shi sosai bana tunanin ma yana qasa da wata daya ne" "Mun gode kawai Dr,tattara kayanki kije,banda rainin wayo ta yaya zaki kalli kaman sultana kice tana da ciki?, shekara sha ukun?,lallai na yarda da akace wani lokaci qwqwalwarku tana tabuwa" bibi ta fada da wani irin yanayi da zai gaya maka lallai ba cikin hayyacinta sosai take magana ba.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 page 16 "iya abinda na gaya muku hajiya bana tunanin akwai son rai a ciki ko kuma ba dai dai ba.....dukkanmu munsan me ya faru,ina ganin ba abu bane na mamaki don ance ciki ne da sultana ba......" Ta qarashe fadi cikin tausasa harshe da kuma dukka yunqurinta nason ganar da bibi abinda ke wakana. Wani irin gumi ne yake yanko musu su dukka. Yayin da sultana dake kwance taketa qoqarin fasa maganar Dr chafa'atou cikin kanta. Wanne irin ciki take nufi tana dashi?,shin mene ne ma cikin wai?. Wani muguwar razana tayi sanda tunaninta yakai inda ya kamata yakai din,ita kanta batasan yadda akayi ta isa gaban Dr chafa'atou ba bare bibi da ama dake zaune kowanne jinin dake jikinsa nason daskarewa. Kyakkyawan riqo ta yiwa Dr chafa'atou, muryarta da wani irin galabaitaccen amo......fararen idanunta da suka sauya launi dukka sun fito waje tana duban Dr chafa'atou,hucin da jikinta ke fitarwa bai damunta ko kadan "Ba Bibi tace ki tafi ba?,me yasa kikeson sake jefani cikin halaka?" Ta jefawa Dr chafa'atou tambayar "Don Allah medicin kice ba haka bane.....kice kuskure kikayi......me nayi miki zaki jawomin wannan abun?,ta yaya zan iya haihuwa?,kinga cikina fa dan qarami ne amma kike cewa wai ciki ne dani?" Ta sake fada tana sakin Dr chafa'atou,sannan taja da baya da wani irin hanzari tana tattare rigar jikinta har saman qirjinta,plate tummy dinta wanda ke shafe hade da bayanta ya bayyana. Daga jajayen idanunta tayi tana maida dubanta ga Dr chafa'atou dake tsaye tana karantar yadda kwanyar sultana din ke shirim birkicewa "Kinga cikina?,ko plate din abinci daya bazan iya cinyewa.....amma kikayi qarya kikace ciki......." Bata barta ta qarasa ba ta sanya dukka hannunta a tausashe ta jawo sultana cikin jikinta ta rungumeta tsam "Kiyi haquri......wasa nake miki,kinyi qanqanta sultana,har yanzun ke yarinya ce" ta fada muryarta na rawa,tsananin tausayin sultana yana taba zuciyarta yana ratsa jikinta. Daga bibi har ama gaza riqe hawayensu sukayi. Hawayen tausayin sultana,ta yaya zata iya karbar wannan qaddarar da qananun shekaru irin haka?,ta yaya zata iya fuskantar wannan qaddarar cikin rayuwarta?,ya rayuwarta zata zama?,ciki a shekarun da duka duka basufi sha uku zuwa sha hudu ba. Sun jima a haka dakin tsit,bakajin komai sai sheshsheqar kukan sultana,wanda tun tanayi da ragowar qarfin da ya ragewa jikinta har ya zama bata iya koda motsi saboda wani mahaukacin zazzabi da yafi na baya daya sauko ya rafketa. Cikin hanzari Dr chafa'atou ta fara bata taimakon gaggawa don kada zafin zazzabin ya kaita ga convulsion musamman da yake ba ita kadai bace,zazzabin zai iya zama illa ga abinda ke mahaifarta,duk da cewa ta lura har yanzu bibi ko kadan bata yarda da abinda ta gaya musu ba. Kimanin awa daya kafin bacci ya dauketa,don Dr chafa'atou ta sanya ruwan allurar bacci cikin ruwan,saboda a yanayin da take ciki yanzu bacci ne kawai maslaha. "Zan wuce,Allah ya bata lafiya,saidai koda baki yarda da abinda na fada ba yana da kyau a kula da lafiyarta,a sake gujewa sanyata damuwa" tayi musu taqaitaccen bayani dukansu da ama da bibi din. Qwaqwwaran motsi aka rasa wanda zaiyi a cikinsu,ta tafi ta barsu da tarin tunane tunane qulle qulle da kuma kwancewa. Ita dai ama bata da abinda zata iya cewa bibi,maina ya tafi ya barta da dukkan wani nauyi da kuma kunya. Yayin da Bibi take juya maganar Dr chafa'atou wadda take jinta kamar a duniyar mafarki. Shigowar aba dakin shi da goumar shi ya katse shurun da yake wanzuwa a dakin tsahon wani lokaci. Dukka suka daga kai suna amsa sallamar tasa yayin da nashi idanun suke kan ledar ruwan dake shiga jikin sultana. "Dama bata da lafiya?" Yayi tambayar wa bibi. Da qyar ta iya buda fatar bakinta guda biyu tana gyara qafafunta da sukayi tsami "Dazune kawai bayan fitarta makaranta" "Subhanallah" aba ya furta bayan ya isa gaban gadon yana taba temperature na jikinta wadda ta fara sauka "Allah ya sawwaqe ya taqaita gaba......amma ba damuwa bace har yanzu a ranta bibi?" Ya sake yin tambayar yana waiwayowa hadi da duban bibi. Kai ta girgiza da qyar kamar me ciwon wuya alamun a'ah "Wannan abinda ke damun nata a yanzun yafi qarfin damuwa muddin abinda Dr chafa'atou ta fadi gaskiya ne......muddin abinda tace yana damun nata da gaske ne dukkanmu muna cikin tashin hankalin da bamusan inda zamu ajeshi ba,bakuma musan da wanne ido mutane wadanda basusan sultana matar maina bane zasu kallemu" tamkar an doke masa gwiwa haka yaji,sai ya qaraso gaban bibi din ya zauna sosai saman qafarsa yana kallonta. Tun daga zuciya zuwa ruhinsa addu'a yakeyi, ubangiji yasa ko meye kunnuwansa zasu jiye masa yanzu su jiye masa sassauqar qaddara "Ya salam.......wani mummunan ciwo ya shafa mata?" Tambayar da yayin sai data motsa ran ama. Tayi qasa da kanta tana jin babu dadi,yaronta kamammen mutum ne wanda tsahon zamanshi dasu ko sau daya basu taba gani ko jin labarin ya tsaida yarinyar kowa bama,amma me yasa tunanin aba koda yaushe ke zarga masa mummunan zato game da maina din?,dan cikinsa?,me matuqar masa biyayya?,don kawai Allah ya kawo tsausayin faruwar wannan abun?. "Ba ciwo bane,juna biyu gareta wai" qas aba yayi da kansa zuciyarsa na cika da wasi wasi. Ko kusa ko alama baiyi tunani ko tsammanin jin haka ba. Maganar shima sai tayi masa nauyi,bakinsa kuma ya sarqafe ya kasa furta komai. "Inaso gobe ni dakai da ita muje wani asibitin a sake gwadata,don inason sanin gaskiyar batun" ta fadi da alamun da gaske take maganar tun daga zuciyarta har harshenta "In sha Allah". Dukka sauran maganganun ama tana ji batace komai ba,nata tunanin yayi nisa ne kan yadda rayuwa zata kasance a garesu gaba daya. Batasan ME GOBE TA TANADAR MUSU BA.... BATASAN ME K'ADDARA TA AJIYE MA GOBENSU BA......yadai tabbata GUDUN K'ADDARA GUZURIN TADDATA CE....... **********Dogon lallashi wayo da dabaru tayi kafin ta samu nasarar da sultana tayi wanka. Ta tabbatar a yadda jiya aba ya kwana da zancan cikin ranshi zaiyi wuya basuyi fitar safiya da ita yawon gwadata ba. Breakfast me kyau kamar kullum ta shirya mata da kanta. Ta sameta zaune tsakiyar gadon. Gaba daya ta jeme ta lalace,tun daga wancan lokacin sultana bata sake kyawun gani ba,ta firje ta firgice,tsakanin jiya zuwa yau kuma gaba daya ta sake zama kamar wata susutacciya. Da kanta ta zauna ta fara bata breakfast din bayan ta sha kanta. Saidai loma daya kacal ta fara kelayowa ama amai kamar me shirin amayar da dukka kayan cikinta. Hankalin ama din ya tashi qwarai ganin yadda take maida numfashi kamar wanda ke shirin qwace mata. Ita ta gyara wajen tas ta kuma gyara mata jikinta,sannan ta sauya mata wasu kayan. Zaune tayi kawai gaban sultanar wadda keta rera kuka da galabaitacciyar muryarta. Abinda takeji din tunda aka haifeta bata taba jin makamancinsa ba,wani irin ciwo takeji da rashin dadi da sukuni,dukka duniyar takejin ta mata wani irin zafi kamar ma ta mutu ta huta,ba abinda takeso,babu kuma abinda yake burgeta. Sau uku tana bude bakinta da zummar baiwa sultana haquri sai kuma taga na meye?,me zata cema sultana din?,babu wata kalma a yanzu da zata gayawa sultana da zata cire mata radadin da takeji yanzu a qirjinta. Laulayin cikin ba qaramar masifa bace ga duk macen da Allah ya jarabceta dashi. Inda idanun bibi a bude suke bata makance da son jin akasin gaskiya ba tana tunanin yaci ace ta fahimci da gaske ciki ne da sultana. Jiya bayan duk sun fice sun barta daga ita sai ita ta qarewa sultanar kallo. Komai nata ya canza,hatta qirjinta da suke matasa zuwa yanzu sun fara cikowa,abinda dukkansu suka makance idanuwansu basukai ga ganinsu ba. Dukkansu ubangiji ya kauda hankalinsu daga ganin wannan,sai a yanzu da yaga dama ya bayyana abinsa. Saddi ne ya shigo a hankali idanunsa akan fuskar sultanan. Shi kansa mugun tausayinta yakeji,yakan kuma tambayi kansa kuma ME YA MAINA YAYI MATA NE WAI?,ME YASA YAYI MATA ABINDA YASAN BATASO?. "Aba yace sultana ta fito" kai ta daga ta kalleshi "Kace masa gata nan zuwa,zataci abinci ne" amsawa yayi ya juya ya fita. Shuru tayi tana tunanin me zata bata?,kaf tunaninta a yanzun bawai gudu yakeyi ba,batasan me zata bawa 'yar marainiyar Allahn da zai riqeta ba. Wani tunani ne ya fado mata,ta tuna abinda nafessa tafi yawanci sanda tana da cikinta,may be idan tayi gado itama ta iya ci din. Cikin mintuna ta kammala ta dawo ta sameta,har yanxu kukan takeyi da wani irin rashin kuzari. "Taso kiji sultana" ama ta fadi tana zama kusa da ita tare da dagota. Sanda takai spoon din kusa da bakinta kai ta girgiza tana kauda kai "Don Allah ba don ni ba ki karba" karon farko da ama tayi mata magiya tsahon tarayyarsu,sai taji nauyinta ya kamata. Hidima take mata tsahon dare da wuni,duk da tarin 'yan aikin dake sassanta amma ta maida hidimarta saman wuyanta kamar yadda hidimar aba ta zame mata dole,batajin koda su saddi da suka fito daga tsatsonta sun samu nau'in kulawar da take samu cikin wata ukun daga wajen ama,wannan ya sanyata bude bakinta zuciyarta na mata nauyi. Batayi tunanin ko Loma biyu zata karba ba,amma sai gashi har takai biyar,ata shida ta kauda kanta hawaye naci gaba da tsartuwa daga idanunta. Ko iya hakan da taci ya yiwa ama dadi,tasan dai aqalla dai ba za'a ce babu komai cikin cikinta ba. Hijabi me kyau a tsaftace ta fiddawa sultana,ta sanya mata sannan ta bata takalmi ta saka ta sakata a gaba zuwa parking lot na gidan. Acan ta samu oncle bashar oncle umar da matansu. Batace komai ba ta budawa sultana bayan motar inda bibi ke zaune ta sakata "Duk inda kikaji kin gaji ki samu waje ki zauna har sai jikinki da yanayinki ya daidaita" abinda ta cewa sultana kenan kawai ta juya tana barin wajen ba tare da tace da kowa komai ba,ba kuma tare da tayi tayin binsu din ba,saboda tasan yawo ne kawai zasuyi tare da batawa kansu lokaci. Abu daya data sani shine,ko kadan a zuciyarta bataji tana qyamatar cikin da sultana ta samu ba,bata kuma ji baqinciki ba,kawai dai ta razana da jin sakamakon......tana kuma tsananin tausayin sultana da ciki a qarancin shekarunta.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 17 Tunda ta koma ciki wayarta ke hannunta,sai tayi kaman zata kira bibi ko aba din sai ta fasa. Haka kawai takejin zafin yadda suka dauki abun da zafi suka girmameshi haka,a nata zaton yau ko fyaden da babu aure maina ya yiwa sultana,sannan har rabo ya shigo ciki,tayi zaton zasu karbi abun da sunan qaddara,su kuma rufa abun don yiwa juna halacci da kuma kyautata alaqar juna tare da girmama tsatso. Daga qarshe data gaji da kai kawon da bashi da amfani sai kawai ta shiga kitchen da kanta. Dukka masu aikinta suna ciki,kowacce na hidimar da take alhakinta ce. Cikin girmama suka matsa suna bata hanya. Bilki ce ta fara tambayarta "Ko akwai abinda kike buqata?" Kai ta girgiza "Ba komai,zan dan gwada wasu qananun abinci ne ko za'a dace sultana ta samu wanda zata iya ci a ciki kafin su dawo" . Bata bawa kowa aiki ba,tace dai kowa yaci gaba da aikin dake gabansa. Tana aikin amma sam ko qananun hirarrakin dasu bilki keyi a tsakaninsu bata iya tantancewa,saboda tsabar nisan da tunaninta yayi. INA MAINA YA TAFI?,wasa wasa kwanaki nisa suke suna kuma jirkicewa zuwa watanni,a ina yake?,ina yaje?. Ba qaramin damunta abun yakeyi ba cikin rai,a duk sanda ta sanya haqarqarinta a qasa zata kwanta maina dinne yake soma fado mata. Abinda ta lura ko sau daya aba bai taba tada maganarsa ba,sau biyu oncle umar da oncle bashar suna masa maganar sai yace dasu "Ai ba yaro bane shi,ya fita sahun yara ko samari,magidanci ne yanzu,duk inda yaje ma zai dawo da qafafunsa,bani da lokacin bata lokaci wajen nemansa" itadinma ko sau dayan batayi gangancin masa maganar ba,tana iya nata qoqarinne kawai a bangarenta wajen samun koda labarin inda yake. Shuru office din likita na uku da suka ziyarta a ranar yayi. Asibiti na qarshe da dukkansu sukayi yaqinin ba inda za'a gaya musu sama da abinda zasu gaya musun,saboda qwarewa da ingancin asibitin da har takai bayan ainihin asibitinsu Dr chafa'atou shine asibiti na biyu da ya samu lambar yabo daga qasar France,suke kuma da qwararrun likitoci da wasunsu 'yan asalin qasar France dinne. Kanta na kwance saman kafadar bibi tana wani irin kuka kamar numfashinta zai dauke. Aba dake zaune ya gaza cewa komai,saidai dukka hankalinsa yana kan mahaifiyarsa saboda dimbin tashin hankalin da ya gani saman fuskarta. Shekarunta sun fara jaa,yana tsoron kada wani ciwon ya sarqafeta. "Wannan kukan da takeyi yayi yawa,yanzu haka da na duba awon jininta,jininta ya hau daga qa'idar yadda ya kamata ya kasance,tana buqatar kulawa ta musamman,saboda shekarunta sunyi qanqanta qwarai da iya rainon juna biyu,muddin anason ta rayu lafiya ita da abinda yake cikinta dole a kula da damuwarta" kai bibi ta girgiza "Ba zamu taba iya hanata wannan kukan ba.....mu dinma inda da hali barin namu idaniyar zamuyi ta zubda qwalla....... abu daya kawai na sani......bazan bari rayuwarta ta galabaita ba muddin ina numfashi" bibi ta fada da qwarin gwiwa. "Yanzun zamu dan riqeta saboda tana da buqatar kulawar likita gaskiya qwarai da gaske,zamu sanya mata ruwa saboda jikinta babu isashen ruwa,sannan hawan da jininta yayi ma banajin yana da kyau a qyaleta ta tafi gida,akwai gwaje gwaje da dukka za'a yi mata a ajjiye koda buqatar gaggawa zata taso". Yana kaiwa nan nurse din ta shigo cikin harshen faransanci take gaya masa sun gama shirya komai "Ku rakata dakin" ya fadi yana hada tarkacensa dake saman table din. Tashin hankalin da takeji ya zarta duk yadda zata misalta. Sanda ta miqe nurse din ta kama hannunta sai taji ba zata iya sakin hannun bibi ba,a hankali taji idanunta sun soma rage kaifin ganinsu,wanda guda dayan da aka yi mata glasses saboda shi zuwa sannan ya sake samun raunin gani sosai sakamakon hawayen da take wuni ta kwana tana zubdawa. Babu wata ranar banza a gareta da zata fito har ta fadi hawaye basu fita daga idanunta ba. "Muje ko?" Nurse din ta fadi cikin kwantar da murya. Qoqari take taga ta taka amma sai taji qafafunta kamar an riqesu,qirjinta kamar an aza masa wasu kaya masu nauyi,kanta kamar an daketa da wani qaqqarfan abu,duhu kuma ya soma mamaye hasken tarwai da office din yake dashi,ba tare data shirya ba hannayenta suka zame daga cikin na bibi,babu abinda taji sai salatin bibi da wani irin qaqqarfan sauti. **********Tamkar wadda ake tasa daga bacci ta soma bude idanunta,wanda tun kafin takai ga gama bude idon gaba daya ta danji muryoyin qasa qasa. Sannu a hankali ta gama bude qwayoyin idanunta,fes suka sauka cikin dakin. Mutum biyu ne zaune gaban kujeru ukun dake gaban gadon nata,sai kuma oncle umar da oncle bashar dake tsaye daga saman kanta. Saitin qafafunta kuma mamma kausara ce(qanwa ga mahaifinta hamani uwa daya uba daya). Kusan kowa yunqurin mata sannu yakeyi,yayin da ama da mamma kausara suka matso suna qoqarin tadata zaune ganin tana mutsu mutsu "Dole ki gaji,kwanciya ace tun jiya?" Ta danji mamaki cikin ranta,to amma kuma a yanzun ita duka ba wannan bane gabanta ba. Duk sai da suka gama mata sannu da jiki sannan ama ta kawo ruwa ta bata. Tasha da yawa sosai,sannan ta kamata ta sauko da ita zuwa bandaki "Kiyi wanka kizo ki rama sallolin da ake binki ko da a zaune ne" ama din ta fada. Tayi wankan ta kuma rama kuma sallolin,saidai daga haka ba abinda ta iya qara yi,tana daga zaune saman abun sallar kawai. Ita ba tunani ba ita ba bacci ba, hakanan ita ba ido biyu ba,a haka 'yammatan gidan sa'anninta sukayi sallama suka shigo. Aminata,yasmine,najma almu sai atta biye dasu. Sai da suka gama gaida iyayensun sannan suka qaraso inda take zaunen. Zagayeta sukayi kowa yana mata sannu cikin nuna kulawa da qauna ta 'yan uwantaka. Banda kalmar DA SAUQI ba abinda ta iya sake furtawa. Da idanu kawai take binsu wani abu yana kai kawo cikin zuciyarta,sai kawai ta hade qaffaunta waje guda tana cusa kanta tsakanin cinyoyinta,don kuka take da buqatar ta sakeyi. Wannan kukan batasan yaushe zata daina yinsa ba tsayin rayuwarta,su aminata sha'awa suke bata,tana jin dama itace su,su dinma kamar haka rayuwarta take a baya ba?,tashi daya zallar zalunci irin na maina ya kutsa rayuwartata ya wargaza mata komai ds komai,ya rusa farincikinta da walwalarta,yayi rugu rugu da mafarkinta,a yanzun bata da wani sauran mafarki ko buri na rayuwa,tana jin rayuwarta dai dai take da fanko,tana kunyar kallon idanun su aminata su hanan da sauran qawayenta su ganta dauke da wani abu waishi CIKI!,cikin da suke gani jikin yayyensu?,cikin da suke ganin jikin iyayensu?. Batasan ya akayi sautin kukanta ya fita ba,saiji tayi su yasmine suna rungume da ita suna bata haquri,dukka muryoyinsu suma a karye,abinda ya sanya bibi miqewa kawai ta fice a dakin. **********Dukkan iya abinda likitoci zasu yi mata na taimakon da ya dace sun bata,saidai kuma jigon samun sauqinta yadda ake da buqata yana hannunta. Nutsuwa kwanciyar hankali da taqaita damuwa,abubuwa ne kuma da zasuyi wuyar gaske ace an samesu daga wajenta a yadda take ciki a wannan lokacin. Wani irin matsanancin laulayi mai matuqar azabtar da ruhi da gangar jiki. Ta fita hayyacinta ainun,tayi wata irin rama da bata taba kwatankwacinta ba,har takai jallin da dukka suturunta sunyi mata yawa basa sanyuwa a jikinta. Bata iya cin komai,hakanan bata iya shan komai,kusan qarin ruwa shine abinda akafi yi mata duk bayan kwana biyu saboda samarwa jikinta abinci. Wannan yanayin ya daga hankalin bibi matuqa,ta dinga jin kamar lokacin da zata rasa sultana ne yayi,kaman yadda ta rasa MOHMOUD ta rasa BINTOU ta kuma rasa NAFESSA. Wannan tunanin yayi matuqar razanata,ya kuma sanyata tattara dukka 'ya'yanta harma da ama da kuma mamma kausara ta shaida musu hukuncin da ta yanke ba kuma tare da neman shawararsu ba. Shawarar da take ganin ita daya ce MAFITA,ita kadai ce kuma hanya ta yankewa wannan AZABA da sultana ke sha, sa'annan qilan ta zama silar warwarewar bakin zaren komai. *******A ranar data nemesun ta shaida zamanne bayan sallar isha'i. Cikin daya daga cikin falukanta masu kyau da tsari,wanda sam basu cika girma ba,sannan bata fiya wani zama cikinsu ba saboda ba falo bane dake a farko farkon sassanta ba. Ama ce qarshen shigowa,sai data tsaya ta tabbatar abu me ruwa ruwa ya shiga cikin sultanan bayan wunin da tayi a wunin yau sur bata sanya komai a cikinta ba,sai uban amai da ya galabaitar da ita liqis. Duk sanda ta tashi da rikicewar yanayi irin hakan wuni ama din takeyi itama cikin tashin hankali. Tuntuni ta sauke dukka wasu harkokin business dinta ta damqawa wasu daga cikin mataimakanta,sai kuma saddi da yake yaayan atta da almu data dora masa wani nauyin shima,duk kuwa da cewa shekarunsa ba wasu masu yawa bane,duka duka sha bakwai yake amma lalura ta sanya dole ta fara dorashi bisa hanya. Ta samu tasha oat da madara dan qaramin cup da baifi cup din yaro dan yaye ba,saidai duk da haka ama murna takeyi da ya zauna acikinta har ma bacci ya dauketa. Tun jiya da bibi ta shigo wajen sultana,ta kuma buqaci ama ta basu waje zasuyi magana taji hankalinta bai kwanta ba. Duk wani kuka da damuwa da take ciki babu shi daga jiya zuwa yau din,sai laulayin kadai dake hanata sukuni. Maganar qarshe da taji bibi na fada bayan ta dawo canzawa sultana beadsheet ta tsaya mata a rai,ta kuma dinga juyata cikin ranta. Ta qure dukka maqurar tunaninta wajen son gano abinda maganar ke nufi,amma mahanga daya kwanyarta ke kaita,a ma'ana daya duk wani ma'aunin fassara yake zuwar mata,ma'anar da taqi gamsuwa da ita,zuciyarta taqi aminta da hakan. "Karki damu,kwana uku kawai zakiji sauqi ki koma rayuwa kamar 'yan uwanki,duk wani ciwo zai wuce" to meye qarshen maganin laulayi haka da gaggawa?,laulayin da ba abu bane me yankewa yau ko gobe ba?,har sai sanda rabbi ya dauke maka,ko kuma zuwa sanda ka haife abinda yake cikinka?. Da sallama ta shiga falon,sai taga kamar dukka idanu sunyo kanta. Bata wani bada muhimmanci ba ta qarasa daya daga cikin kujerun dake daura da aba,ta dauke filon kai ta zauna,ta kuma gyara zamanta sosai tana fuskantarsu *_Tofa!,taron na meye?,me karatu muje zuwa,akwai sauran tirka tirka_* *_wai ina Aliyyu haidar ya shiga ne?,ko team SULTANA NE SUKAYI MASA KURCIYA?_*🫣🫣🫣 *HUGUMA CE* *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 18 "Tom,nasan dukkanku kuna mamakin abinda yasa na taraku a nan wajen?......a taqaice ba wani doguwar magana bace me tsaho,sannan kuma ba shawara na taraku nayi daku ba,na kiraku ne don na shaida muku,babu buqatar cikin dake jikin sultana a yanzu,saboda dukkaninmu munsan abinda likitoci suka fadi gami da hatsarurrukan dake tattare da lafiyarta,kuma ita din munfi buqatarta akan abinda take dauke dashi,saboda haka na yanke shawarar aje A CIRE CIKIN JIKINTA ma'ana A ZUBAR DASHI! don ta tsira da rayuwa da lafiyarta" Dif dakin ya sake yi,kowa ya zubawa bibi idanu sona son gano wasa takeyi musu?,ko tana fadin maganar ne da gaske. Kaf dinsu babu wanda yaga digo ko alamun wasa tattare da bibi din, fuskarta ta sauya zuwa wani yanayi da yake sanya musu shakka a duk sanda wani ya yunqura zaiyi jayayya da umarninta. Ba wanda baiji saukar maganar har tsakiyar zuciyarsa ba. Kusan daqiqa uku kowa ya gaza tofa komai kafin daga bisani oncle oumar ya motsa yana matsowa gaba kadan daga kan kujerar da yake zaune "Amma bibi......" Hannu ta daga masa tana cewa "Dakata oumar,ya isa,bana buqatar qarin bayanin kowa,inajin dukkaninku ba wanda yasan ciwon sultana sama dani......." "Sai kuma maina.....wanda shine yaci kashinta yaci fitsarinta,shine wankanta shine wankinta,tare suke jinya kukanta nashi ne damuwarta tashi ce....... shine cikinsa yake a jikinta a yanzu.....cikinsa na halak ba shege ba.....cikin da baya biya sadaki da albashinsa na dan makaranta.....shine cikin da ake cewa yanzu a cireshi?" Ta qarashe maganar tana jefawa bibi tambaya "Hamdiyya...... meye haka?,kinsan a gaban wa kike a tsaye?,kisan me zaki fadi......" "Me zan fada?,me zan fada ma?,to ban qarasa ba.......indai nice mahaifiyar Aliyyu,kuma akwai haqqinsa a wuyana,akwai kuma nawa haqqin a wuyansa.....ina fada da harshensa da nawa......ban yarda a fidda abinda yake tare da sultana ba,ban yarda ba har abada........!" Saita qarashe da wani kukan da bata shiryawa ba ya kufce mata,sai ta juya da gudu gudu sauri sauri tana fita daga falon,tana jin qirjinta yana mata nauyi,wani abu ya tokare mata qirjinta. A gurguje a gurguje ta dinga ratsa farfajiyar gidan har ta isa sassanta. Can cikin dakinta ta yiwa kanta masauki,ta zube daga bakin gado a qasa kuka yana qwace mata. Shin ta yaya?,ta yaya ma zata bari a zubda cikin aliyyu?,da wanne dalili zata bari hakan ta faru?,koda cikin shege bare na halak?,idan su dukka tunaninsu ya toshe hankalinsu ya gushe da soyayyar sultana don kawai su sama mata mafita to ita din tana a dai dai cikin hayyacinta. Tayi kukan data jima batayi irinsa ba,ta kuma jima a nan zaune tana tunanin hanyar ra zata hana faruwar abinda bibi ta qudurta. Ta sani ta kuma yankewa ranta ko a mutu ko ayi rai,koda igiyar aurenta zata girgiza ba zata taba bari wannan abun ya faru ba. Sanda ta kalli agogo sai ya nuna mata qarfe biyu da rabi na dare. Ta share sauran qwallar da suka rage mata cikin idanunta tana miqewa. Mafita guda daya ce yanzu tak ta rage mata ta amintar da sultana takuma sauketa daga doron amincewar da bibi ta sanyata tayi kan a zubda cikin. Bandaki ta nufa ta daura alwala saboda ta samu sassaucin abinda takeji tsakiyar qirjinta,sannan ta fito ta dauki medium veil me santsi mahadin rigar jikinta ta yane kanta,ta jawo wayarta ta kunna data sannan ta nufi qofa ta buda a nutse ta fice a dakin. Sau daya tak ta murda qofar dakin ta bude,saita tura a hankali tana shigewa. Fitilar gefan gado ne kawai a kunne,saman gadon kuma babu kowa alamun sultana din ta tashi,sai ta zauna saman sofa bed din dake daura da ita tana jiyo motsin ruwa a bandaki,sai ta tattara hankalinta akan wayar tana ci gaba da research kan abinda take da buqatar A nutse ta kammala fitsarin tayi tsarki,saita matsa gaban wall mirror dake jikin bandakin,ta murda famfo ta wanke fuskarta da kyau,bayan ta gama taja qaramin towel ta soma goge fuskarta,a sannan ne idanunta suka fada kan fuskarta data fito tarwai ta cikin madubin kamar rana saboda wadatar haske da bandakin yake dashi. A hankali take qarewa fuskartata kallo,fuskar da aqalla ta dauki watanni sama da uku rabon data kalleta. Lumshe idanunta tayi tana jin ciwon yadda dukka kamanninta suka canza,ta sanya hannu a hankali ta shafa gefan idonta da har yanzu akwai sauran tabo na bahagon marin da ya kaiwa fuskarta har ya zame ma idanunta illa. Janye hannun tayi tana jin wata irin mahaukaciyar tsanarsa tana ambaliya cikin zuciyarta,nau'in tsanar da tunda tazo duniya bata taba jin digo ko kwatankwacinta cikin ranta game da wata halitta ba. A hankali sai kuma takai hannunta saman shafaffen cikinta. Itakam har yanzu bata yarda da zancan wai ciki gareta ba,bataji cikinta ya dago ba,bataga ya qara girman komai ba,hakanan batajin komai banda qinson cin abinci da dan banzan fitsari da take yawaita tashi cikin dare,sai kuma rashin lafiyar da ai ita dai tasan normal ne kowa yana iya cuta. Kamar kuwa jira akeyi takai qarshen tunanin nata taji wani abu ya harba sau biyu a marartata kwatankwacin bugun zuciya. Ta miqa hannu da sauri dai dai gurin ta danne tana zare ido tare da saka ran sake jin wani abu. Saidai kuma tsayin sakanni shuru bataji komai ba,wannan ya sanya ta saki hannun nata hawaye na cika mata idanuwa. Indai da gaske ne cikinne ita wallahi babu abinda zatayi dashi,d'an maina ne fa kenan ko?,ita zata haifawa baqin mugu azzalumi yaro?,sun hada jini kenan kamar yadda taji ana fada?,Allah ya kiyaye ya kuma sawwaqe ta hada jini da maina,la shakka shawarar bibi itace dai dai,bibi din masoyiya ce ta gaske,wadd bata qaunar kukanta ko damuwarta,batason dukkan wani abu da zai zamewa rayuwarta barazana,tsahon shekaru tana akan haka. Towel din ta maida cikin zafi tana jin cewa gari yana wayewa zata buqaci bibi ta kaita a cire d'an aliyyu daga jikinta,ta tako da kuzarinta daga bandakin tana fitowa. Tsaiwa tayi daga bakin qofar cikin mamaki tana kallon ama wadda ke zaune sosai cikin dakin,ta kuma qarawa dakin haske da qwayaye biyu dake manne a bango gudun kada sultana din ta tsorata. Idanu ta daga daga inda take zaunen tana duban sultanar,sai ta gyara zamanta tana cewa "Qaraso ciki,nazo dubaki ne na tarar bakya ciki" sakin qofar tayi tana takowa cikin dakin,har cikin ranta tana jinjina tsantsar kulawar da ama ke bata,ta yadda da wannan dari bisa dari, kowanne motsinta ama na dame dashi,ko yaya kuma ta sauya tana riga kowa fahimta ta kuma bi ba'asin matsalar ta maganta mata. Wayar hannun nata ta ajjiye bayan sultana din ta zauna tana dubanta "Sultana,magana nazo muyi dake,ki nutsu sosai ki fahimceni kinji?" Kai ta gyada a hankali tana kallon qwayoyin idanun ama "Me yasa kikeso ki MUTU?" Ama ta jefa mata tambayar kai tsaye,tambayar data saka sultana zaro fararen idanunta tana duban ama a rude "Ni kuma ama?,ni nakeso na mutu?,banaso na mutu ama......" "A'ah,qarya kikeyi,keda bibi duka so kukeyi ki mutu" sake rudewa tayi ainun,saboda kalmar mutuwar girma take mata "Allah a'ah ama,banaso" "Amma kikeso a zubda miki ciki?,bakisan duk wadda aka zubarwa da ciki mutuwa takeyi ba?" Tsam tayi tana duban ama hawayen nan nata da basu da wuyar fita tana zartowa daga idanunta. Tsaf ama ta karanceta,da alama abu ya fara tabata,saita dora da cewa "Ungo wannan ki gani,ki kuma karanta,adadin mata nawa ne suka mutu duk akan silar zubda ciki" hannu tasa ta karba din,ta shiga folder din da ama ta shirya komai ta soma kalla wani kuma ta karanta bayanan da suke da harshen France. Bata iya qarasawa ba cikin matuqar tsoro da razani ta miqawa ama wayar hannunta yana rawa,ama tasa hannu ta karba tana dorawa da cewa "Dukansu KARUWAI ne sultana, ba'a daura musu aure da ubannin masu cikin ba,me zai kaiki layin karuwai?,don kawai kin tsani MAINA......" ".......ama don Allah,daina kiran sunansa" ta fadi da sautin kuka sosai,tana jin mafitar da take hango qofarta a bude qofar ta ida rufewa ruf,gaba kura baya sayaki,ashe sauqin da take hasashen samu babu shi,ta tsorata da irin bayanan data gani,itakam ya za'a yi taso ta mutu haka?,da irin wadannan shekarun qanana?. "Na daina kiran sunansa sultana,kiyi haquri......amma.......ki share hawayenki,ki kuma bani aron hankalinki nan" shuru ya ratsa dakin na wasu mintuna sultana na qoqarin saisaita kanta sannan tadan samu 'yar qaramar nutsuwa "Kin yarda bakison ki mutu?" Ama ta tambayi sultana. Da sauri ta daga mata kai "Amma tunda bibi tayi zancan bansan ta yadda zance mata kada a zubar ba" "Ni nasan yadda zan hana haka faruwa don banason ki mutu,abinda nakeso kawai shine,kibar cikin ki haihu,zan karbi ko meye kika haifa ke kuma kiyi tafiyarki kiyi rayuwarki babu me takuraki,kinga shikenan babu ke ba mutuwa" "Amma wajen haihuwar ai ake mutuwa ama" ta fada da sautin quruciya fal muryarta "Inji wa?,inda haka ne suk da bamu haifeku ba ai ko?,waye a cikin gidannan kika taba gani ya mutu don zai haihu?" Shuru tayi tana son tunawa. Babu,babu wadda ta gani ko ta sani iya wayonta da akace ta mutu wajen haihuwa,amma wajen zubda ciki kuwa gasunan yanzun ta gansu da idonta bila adadin. "Kin yarda zakibi dukka tsarina ni kuma na tsallakar dake daga fadawa mutuwa?" Duk wanda zai kauda maka mutuwa aiba abun gudu bane,bare ama din da zuwa yanzu take jinta kamar mahaifiyar data haifeta,don haka ta gyada mata kai "Da kyau,amma abinda nakeso fa dake shine,kada ki gayawa kowa wannan maganar da mukayi dake kinji ko?,idan ba haka ba zasu daukeki sukaiki gun cirewa da wurwuri kafin na gama nawa tsarin" "To ama" "Yayi kyau,maza kwanta sai da safe,kada kuma kiqiyin bacci kinji ko?komai zai wuce in sha Allah" Kai ta jinjina mata. Ama bata bar dakin ba sai data tabbatar ta kwanta,ta kuma lullubeta ruf sannan ta kunna mata karatun qur'ani da madaidaiciyar qira'a ta kashe hasken dakin sannan ta fice. A daren bata kwanta ba sai data ci rabin plan dinta,don tana ganin tana kwanciya kamar lokaci zai qure mata,don bata da isashen lokacin gama komai da komai da takeso. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 19 A daya daren kuma ta kammala shirinta gaba daya,cikin daren da kowanne ya kwanta a cikin gidan,daren da suke sanya ran washegarin safiyar ranar za'a fita da sultana a zare tayin cikin......a daren ta shammaci kowa a cikinsu,harda 'ya'yan cikinta saddi da almu,a daren dai ta fice daga gidan,ITA TANJA DA SULTANA ba tare da sani ko ankarewar kowa ba. K'arfe sha biyu na daren ranar amma tamkar rana ce cikin zuciyar ama. Mace mai kamar maza wanda ko sau daya tun daga quruciya zuwa girma zuciyarta batasan karaya ko tsoro ba. Ita ke tuqa motar da hannuwanta ba tare data dorawa kowa nauyin tuqata ba bare a buqaci sanin ina ya kaisu?. Gudu kawai take shimfidawa cikin lafiyayyar motar tata,sultana na bacci abinta lakadan a baya,tanja na zaune daga gefan ama din tana rarraba idanu. Har yanzu cikin fargaba ita take,ga tsoron daren da suke ketawa saman shimfidaddiyar kwaltar da zata sadaka har cikin qasar nigeria. "Ki saki jikinki tanja,ba abinda zai biyo baya sai alkhairi,ba kuma abinda zaya faru" ama ta fadi idanunta nakan kwalta data cika da full light na fitilun motar masu tsananin haske. Ajiyar zuciya ta saki tana gyara zamanta "Amma hajiya,bakya tunanin dole zasu bibiyi inda muke?" "Ta yaya?,na cire duka layukan wayata,sannan koda yayyena da muke uwa daya uba daya basusan inda na nufa ba,tanja......zan iya sadaukar da komai nawa saboda na kubutar da cikin maina......zan iya sadaukar da numfashina dama rayuwarta,JINI NA NE......jinin maina ne" ta fada zuciyarta na tsinkewa,rauni yana son saukar mata don batasan a nahiyar da mainan yake ba,bata kuma san a wacce duniya yake ba a yanzun. Dai dai sanda saqonta ke sauka ga wayoyin dukkan mutanen dake da muhimmanci a gareta,suka kuma cancanci tayi musu bankwana dai dai lokacin tayoyin motocinta ke shiga qasar KANO. ta zabi kano dinne saboda tasan zaiyi wuya hankali yakai can,asalima ta zabi kano ta zama hanyar fitarta daga nijer da nigeria din gaba daya, saboda batasan kowa ba acan,basu da kowa ballantana a samu fargabar wani da suka sani ya gansu. Ba bata lokaci tabi cikakken kwatancen da dillalin data kama hayar gidan na sati biyu a hannunsa ya turo mata. Cikin kwanciyar hankali ba tare da kuskure ko batan kai ba sai gasu sun isa qofar gidan dake jerin rukunin gidajen SHARADA NNDC QUATERS. "Alhamdulillah,alhamdulillah,allahumma inni as'alukal birru wattaqwa" ama ta furta tana zare belt din jikinta sannan ta buda murfin motar tana fita. Seat din baya ta bude,sultana dake zaune kawai ba tare da sanin ainihin meke faruwa da ita ba ta daga kai suka hada ido da ama. Murmushi ama ta sakar mata "Sannu daughter,fito mu shiga ciki ki huta" tayi maganar da sakakken murmushi akan fuskarta hadi da miqa mata hannunta. Ba musu ta kama hannun aman ta fito da ita,sai ta miqawa tanja key tana cewa "Ki bude ku shiga ciki,zan daidaita parking motar sai na biyoku". A ladabce tanja ta karba,tana gaba sultana dake takawa da qyar tana biye da ita,don bata tana kusan doguwar tafiya irin haka a mota ba. Duk inda zasu muddin yanabda airport to tabbas jirgi zasubi suje su dawo,zata iya cewa wannan shine karon farko data taba shigowa nigeria ta mota. ⚜️⚜️Ya sani har ya kwanta bacci bata shigo dakin ba,to amma yayi tsammanin taras da ita bayan ya farka sallar asuba amma sai yaga lokacinma wayam. Yayi tsammani dukka fushi takeyi dashi akan maganar da Bibi tun ta shekaran jiya,to amma shi ya dauka zata yi masa uzuri,ta dauki bibi a mizanin mahaifiya wadda bazai iya musanta mata ba,saidai yayi mata gyaran kusakuranta cikin hikima idan buqatar hakan ta taso. To a lokaci irin wannan,matsalar sultana da maina matsala ce me matuqar sarqaqiya,dukkaninsu daga maina har sultana babu wani wanda zaiqi a cikinsu,babu kuma wanda bayaso,saidai dole yayi kaffa kaffa game da duk lamarin da ya shafi maina,saboda gudun son zuciya ya shigo ciki,ko kuma duniya tayi masa kallon maras adalci meson kansa da d'ansa,dole ya sanya buqatun sultana da maslaharta a gaba data maina,kodon maraicinta. Bayan ya gama addu'o'insa ya jawo wayarsa da zummar kiran ama din ya nuna mata kulawa ko yaya ne,ko ba komai ita din uwa ce,itama tana jin yadda kowa yakeji a ransa game da d'ansa,saidai kuma saukar saqon da sunanta saman screen din wayarsa ya katse masa dukka wani hanzari nasa. _amincin Allah ya tabbata a gareka,nayi imani a sanda saqonnan zai riskeka tuni na jima da yi muku nisa ni da d'iyata kuma surukata,inason shaida maka cewa munyi nisa ni da ita domin tseratar da abun farautarku,nisan da banajin nemanku zai iya cimmana,ina rubuta maka wannan saqonne don baka zabi guda biyu......ko ka jirani har na dawo daga balaguron tseratar da rai nayi.....ko ka sawwaqe igiyar aurenka dake kaina idan kaji ba zaka iya zaman jiran hamdiyya ba,ga yarana nan zasu iya kulawa da kansu na sani haqiqa.......ina muku fatan alkhairi......ina kuma fatan saduwarmu ta gaba ta zama da alkhairi,bissalam_. Hannunsa ya sanya ya sharce gumin dake goshinsa yana jin wani tashin hankali yana sauko masa. Babu MAINA babu HAMDIYYA sannan kuma babu SULTANA gaba daya,duka cikin wat uku kacal?,wannan wacce irin jarabawa ce haka ke tunkararsu?,wacce irin musiba ce haka?. Kaman an mintsini aba sai ya miqe cikin hanzari,ko slippers din qafarsa bai maida ba cikin sassarfa ya nufi sashen ama. Loko da saqo na cikin sassan ya fara bincikewa kamar wani zautacce,kaf ya karade sannan ya koma kewayen gidan ba ama ba dalilinta,sai ya sake komawa bedroom dinta a nan yaga shaida. Ta kwashe duk wani abu nata me muhimmanci kamar yadda maina yayi. Haka dakin sultana an kwashe kusan komai nata me muhimmanci,a farfajiyar gidan kuma da ya duba yaga babu motarta guda daya,a nan ya saddaqar da cewa lallai abinda ta fada din da gaske ne. Bai tsaya duba qarfe nawa ba a sannan ya soma dokawa abdulhakeem kira. Da alama yana kusa da wayar,don bugu daya ya dauka. Abirkice aba ke tambayarsa hamdiyya ta iso?. "Ta iso ina?" Ya tambayeshi cikin daurewar kai "Don Allah idan ta iso kada ku bata dama ta sake fita ko ina" "Akan me kake magana ne hamidou?,ina hamdiyya din tace zata je?,ina cewa ko jiya munyi waya tana nan nijer,bata kuma cemin zata zo Nigeria ba" komawa da baya aba yayi ya zauna,sannan ya warwarewa abdulhakeem komai. Shi dinma ya rude,don har yanzu ana ju da auta,wanann gatan da soyayyar ba inda suka je,musamman mutuwar iyayensu ya sanya sun sake dora mata gata "Kada ka damu aba,muddin tana cikin Nigeria dinnan ba zata fita ko ina ba,zamu dubata kuma zamu tabbatar ta dawo dakinta" abdulhakeem ya fadi cikin fargaba xa kaduwa,duk da yana boye hakan a zahiri gudun sake jefa aba cikin wata damuwar. Ya jima zaune a wajen,baisan ta yaya zai tunkari bibi yace mata ama ta dauke sultana ba, ba'a san kuma ina suke ba,ina suka dosa?,sanda kuma zasu dawo din kwanaki ne da suka tasamma watanni sha biyu qila harda doriya. Yana wannan tunanin sai ga Omar kamar an jefoshi,wayarsa a hannu,ya tsaya gaban aba yana miqa masa Wayar. Hannu ya sanya ya karba yana dubawa. Saqo ne dai daga hamdiyya tana dora ma Omar din alhakin yiwa bibi bayani _"Ka gaya mata Omar ta kwantar da hankalinta,nayi alqawarin dawo mata da sultana cikin aminci"_ wannan shine statement dinta na qarshe......... ⚜️Komai akwai cikin gidan,kusan ba abinda suka shiga dashi sai kayan sawarsu da ba wani masu yawa ba,sai kuma kayan abincin gida da tayi order ta wani app suka iso gidan babu dadewa suka dire mata komai. Sai bayan magariba ta nutsu,wunin ranar suna dan gyare gyare cikin gidan ita da tanja,sultana na baccin gajiya,zuwa magariba din har abincin dare tanja tayi,bayan sallar isha'i dukkansu suka hadu cikin madaidaicin falon da duka duka baifi girman toilet din ama ba nacan nijer da kuma gidanta na nan dake abuja ma. Zuwa magariba tanja da ama sun kintsa gidan tsaf,duk kuwa da cewa bawai zama zasuyi ba gaba zasu qara nan da wasu 'yan kwanaki amma ama ta tanadi komai da zasu buqata a kwanakin,ciki harda abincin ci ruwan sha da drinks. Zuwa magariba har girkin dare tanja ta gama. Ama na gama sallar magariba din ta fito falon tana cewa tanja "Shiga ki duba sultana,tun yamma data kwanta banji motsinta ba" ta fadi tana zama saman kujerar falon hadi da kunna tv plasma din dake zaune saman TV stand. Bata da wata sanayya da gidajen tv sosai,don ba ma'abociyar kallo bace,don haka tabar tv din saman channel din dake haska labarai a dai dai lokacin. Bata gama maida numfashinta ba tanja ta fito a dan rude "Hajiya zazzabi ne ya saukarwa sultana fa,kuma irin me zafinnan da likita yayi magana akai" ajjiye wayar hannunta da zuwa yanzu ta sauya layi zuwa na Nigeria,shima temporary ne,don dole tana da buqatarsa wajen neman visa dinsu da kammala komai na tafiyarsu,uwa uba kuma ita din ma'abociyar hawa social media ne duba labaran kasuwanci da sauran al'amuran da suka shafi rayuwa "Subhanallah,ya salam,muje na gani" ama din ta fada hankalinta yana dan daguwa. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku* *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 20 Riris ta sami jikin nata,dole ta soma laluben asibiti dake kusa da GRA din ta hanyar taimakon MAP. Allah ya taimaketa ta samu wani private hospital nan kusa dasu wanda ko a qafa ma kana iya takawa. Ta sani dama babu makawa,qarin ruwa ne dole shi za'a mata,saboda irin wannan zazzabin gaba daya sanyawa yake lokaci daya ruwan jikinta yayi qasa. Nan gabanta suka kwana, tausayin sultanan yana ratsa ama. Ta hadu da azababben laulayi me zafi,bata sani ba ko harda quruciya a ciki?. Cikin taimakon Allah washegari taji qwarin jikinta sukayo gida. Sai yamma sannan suka zauna cin abinci. Cakula abincin kawai takeyi,hankalin ama duka yana kanta. Ta yaya wannan dan tayin dake manne da ita zai zama yadda akeso?,bayan kwata kwata bata wani iya cin abinci?,duk irin lokacin da ama ke kashewa tayi mata nau'ikan abinci kala kala. Bata taba damuwa da bata lokacin da takeyi ba,duk da aba kadai take kashewa lokacinta a kitchen,aah.....damuwarta na rashin cin abincin sultana dinne. Afakaice bayan rashin cin abincin ta karanci kamar akwai damuwa boye qarqashin zuciyarta,don haka ta kirayi sunanta a hankali. Kai ta daga tana kallon ama da zugaggun idanunta da a yanzun kullum a kode suke tasss kamar danyen nama "Banason ganin wannan damuwar sultana,zan cika miki alqawarinki......zan maidaki wajen bibinki,zan kuma karbi ko meye kika haifa,idan kinso kice ma ba kece mamarsa ba dukka na yarda......amma muddin kina son hakan ta kasance sultana sai kina sakin jiki kina cin abinci" wasu hawaye ne masu sanyi suka gangaro daga idanunta "Basa ciyuwa abincin ama.......sai naji ko kallonsa bana sonyi,bazan iya ci ba amma yadda kikeso" sake sassauta murya ama tayi "Shikenan,calme-toi(kwantar da hankalinki),ba lallai bane sai kinci duk abinda aka dafa din ba.....duk sanda kikaji akwai abinda kike sha'awar kici to komai rana kome dare ki gayamin ko ki gayawa tanja,zamu tabbatar an dafashi kinji?" Kai ta gyada mata a sanyaye "Yauwa,madalla......yanzu wacce qasa kikeso mu wuce?,don banaso mukai sati uku a nan,inason na kaiki inda za'a kula dake,ba zaki sha wahala ba" har qasan ranta taji danji sanyi ya saukar mata,abinda zata iya cewa ta jima rabon da ta jishi. Ta dan lumshe idanunta tana jin yadda zuciyarta ta gamsu da tayi nesa da NIJER qwarai da gaske,tayi nesa da qawayenta dama idanun da suka santa,tayi nesa da dukkan cakwakiya,a yanzu idan ka debe bibi da aba bata qaunar ganin duk mutumin da ta sanshi a baya,tanaso ta nesanta kanta da kowa,da da halima zataso ta rayu ita kadai "Wacce qasa kikeso?" Ama ta datsi tunaninta tana sake tambayarta. Abaya dukkan burinta shine aba ya kaita France,kullum zancanta kenan,har yana tsokanarta "Tunda kikaje makka kikaje madeena aikin gama yawo sultanan bibi.....amma itama France din zan kaiki,amma fa sai ranar da kika gama école secondaire(secondary school),naga kuma résultat(sakamako)nki yayi kyau,zan hadaki da ama idan an dace zata shiga ta can ku tafi tare har sai kin gaji sannan ki dawo". A wannan karon sai taji kamar an zare qasar fit daga zuciyarta,maimakon ta cewa ama itace zabinta sai ta buda baki a hankali tace "Austria" "Austria?" Ama ta sake tambaya,don itama France ta tsammaci zata ce. Kai ta gyadawa ama din tana me tabbatar mata,sai ama din ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "Très bien(ba laifi)" sai ta jawo wayarta ta kunna data ta soma danne danne. *********Sati biyun da sukayi cikin garin kano sunyi shine cikin gida ba tare da zuwa ko ina ba,idan ka gansu sun fita din to tabbas zasu miqa sultana ne asibiti. Sultanan da ko yaushe jikinta ke qara zafi da rikicewa. Wani irin bahagon laulayi takeyi mai bala'in zafi da wahala. Duk yadda ama tayi shekaru a duniya,taga kuma masu ciki kala kala,itama kuma tayi kalar nata cikin har sau uku ta jima bataga masifaffen laulayi irin na sultana ba. Sosai take a galabaice,bata iya komai sai kwanciya,sai kuma kuka daya zame mata tamkar sallolin farilla guda biyar. Kullum gari ya waye rana ta fito bawa kanta mutuwa takeyi,azabar da takeji a kowacce gaba ta jikinta tana jin ba irin nau'in azabar da zakaji ka rayu bane. Ta sake zama 'yar firit da ita,sai wani mahaukacin haske da tayi,idanunta suka sake fitowa tare da yin wani irin haske me sheqi. Saidai kuma duk yawan gashin nan nata da sumar nan babu su,yanzun haka qaramin ribbon ya isa ya riqe 'yar sumar dake kanta. Bata um bata um um,kuka a yanzun ya fiye mata komai cikin rayuwarta. Yanayin sultana din ya sake cirewa ama nutsuwa,tausayinta takeji kamar kamar me,inda tana da iko da kuma me yiwuwa ne da tuni ta fidda cikin daga jikinta ta dawo dashi nata jikin ko zata samu hutu koda na kwana daya ne tak. *_AUSTRIA_* *VIENNA* *_VIENNA INTERNATIONAL AIRPORT_* _(flughafen whien_schwechat VIE)_ A nutse suke saukowa daga jirgin Ethiopian airlines wanda yayi jigilarsu daga kano ta dabo suka yada zango a Addis ababa,daga addis ababa din suka sauka London,daga london kai tsaye zuwa Austria babban birnin Austria din wato Vienna. Hannun sultanan wadda tayi wani dan qaramin kyau cikin wasu skirt and blouse da suka dace da jiki da kalar fatarta,sai headscarf data nannade kanta dashi,wanda hakan ya bayyana fuskarta data bayyanar da rama quru quru. Backpack bag ne a kafadarta guda daya, sauran duka luggage dinsu yana hannun tanja. Shima ita ta dage kan zata iya amma aman hanata tayi. Hannunta cikin na aman,wadda ke saye da wata doguwar riga me rubi biyu beig color saqar qasan oman,sai rufaffen takalmi data saye qafarta dashi. Qwayar idanunta lullube da wani sun glasses baqi da ya qara mata kwarjini ainun. Kana kallonta kaga classy maama,muddin baka santa ba ba zaka taba tsammanin ita ta haifi saurayi haka kaman aliyyu ba, zakayi tunanin almu shine yaronta na fari. Tana da kyan jiki,tana da son ado,idan akace ado ado me aji wanda bai fiya daga hankali ba,irin adon da duk wanda ya kalla zao burgeshi ya kuma ga cewan ya dace da age dinta. Duk da ba kasafai ta fiya zuwa Austria ba,to amma abune na aiki da ilimi,don haka tun kafin su tsoma qafarsu cikin qasar hatta da inda zasu zauna tsahon wadannan watannin ta gama dashi,don haka suna sauka taxi suka dauka kai tsaye suka wuce masaukinsu. *_SECOND DISTRICT Leopoldsdadt_* Unguwace dake da wani irin tsari me kyau tare da saukar da nutsuwa, nutsuwar da tunda suka shigo unguwar har qasan rai da zuciyar sultana taji yanayin unguwar yayi mata. Suna da wasu irin jerarru kuma tsararrun Street da aka cikasu da bishiyu dake bada wadatacciyar iska da inuwa me kwantar da hankali. A nutse suka isa second floor,inda anan apartment nasu yake. Babban falo ne yalwatacce dake dauke da dining area,budadden kitchen,balcony daga gaban gininsu da zai baka daman samun iska me kyau da ganin yanayin ginin unguwar,sai dakunan bacci guda uku madaidaita dake manne da toilet kowannensu. Yanayin ginin gini ne me matuqar tsari wanda ama tayi amanna zai dace da tsarinsu,komai an zuba,hatta da kayan abinci basu da abinda zasu buqata. Tun daga daren har zuwa wayewar gari ama bata zauna ba. Kwanaki biyu tayi a tsaye,sai data tabbatar duk wani da zai zamewa rayuwarsu tilas na su nemeshi ta gama da matsalarsa a tsahon shekara guda da take sanya rai zasu kwashe a qasar. Tun daga booking na asibitin da sultana zata dinga zuwa anti natal,tayi mata register da wani center na bawa mata masu juna biyu kulawa da kuma shawarwari,ta sake mata register da cikakken likitan dake lura da matsaloli da qwaqwalwa kamansu depression anxiety da sauransu. Center ce me kyau data jima tana bin qwaqwafi da bincike a kanta,tanason duk wani damuwa ya gushe daga zuciyar sultana din,tana sha'awar taga sultana ta fuskanci rayuwa da kyau,tanaso ta haihu successful ba wani matsala da zata shafeta ko ta shafi abinda ke cikinta. Ta canza layukan wayarta,ta kuma canza dukka accounts nata da take amfani dasu,kama daga Facebook page dinta,instagram dinta da watsapp dinta,daga ita har sultana suna buqatar nutsuwa,suna da buqatar su manta da kowa da komai na wani dan lokaci.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 21 Hutun sati guda kacal sukayi duk wani abu data biyawa sultana din tayi qoqari taga ta fara zuwa. Duk da zuwan nata sai ya zamana asha ruwan tsuntsaye saboda yanayin jikinta na yau lafiya gobe babu. Cikin nasara da taimakon Allah sannu sannu tana zuwa ganin likitanta sai aka fara samun sassauci,don an samu ci gaba tayi katari da irin abincin da takeso a wata fita da ama tayi dasu cikin unguwarsu. Street food ne da sukeyi a wani kebantaccen waje,ama din bata taba tsammanin sultana zata iya cin abincin ba,don har ta kira waitress tace a maida,sai ta buda baki da muryar nan tata data zama sasaanya tace "Ama ni zanci" a mamakance take kallonta,cikin harshen German tace su ajjiye. Kaman wasa ta koma da baya ta zubawa sultanan idanu,sannu sannu sai gashi ta tashi dashi. Abun ya yiwa ama dadi,sai suka maida wajen gurin zuwansu duk dare,don acan ne kadai sultanan ke iya ci ta qoshi,koda zataci tayi amai,amma tanaso,hakanan ana samun wani yana zama a cikinta. Kaman yadda taci burin sadaukar da komai nata ta sadaukar din,don lokutta da yawa tanja na girmama girman qaunar data karanci ama na yiwa cikin dake manne jikin sultana,ko kadan batajin kudin dake fita a jikinta,duk da cewa ita din ahalin abunne,ta tara da yawa an kuma tara mata,amma saidai daga qasar har zuwa unguwar da suke zaune din tana cikin nau'in gurare masu tsadar rayuwa a duniya,amma tanja bataga alamun hakan sam sam yana damun ama ba. Sannu sannu suka kwashe watanni uku a Austria......daidai watannin cikin sultana shida cif,ba labarin gida a kunnuwansu kamar yadda gida basusan wacce duniya AMA TANJA DA SULTANA suke ba.....bare maina da tun daga wancan ranar ko me kama dashi basu sake gani ba,basu sake jin komai da yayi kamanceceniya dashi ba..... tun uncle abdulhakeem suna cigiya har gwiwoyinsu ya sare.......tun suna cigiyar maina kadai har suka koma hadawa da cigiyar ama......tun hankalin aba bai tashi da yawa ba,yana ganin kamar adadin Tex naban haqurin da yake tura mata yana riskarta......girman soyayyar dake tsakaninsu zata hanata yin nisan zango.......zata kuma waiwayeshi.....har ya sare ya fara tunanin ta ina zai nemo hamdiyya?,ta yaya zai maidowa da bibi farincikinta?. Duk wani kuzari da walwala na family din MAYAK'I yayi nasa guri sai abinda ba'a rasa ba. BA MAINA BA AMA BA SULTANA wadannan abubuwa dasu suke kwana kuma dasu suke tashi cikin zuciyar duk wani ahalin mayak'i. ********K'arfe takwas na dare agogon qasar Austria,daidai lokacin da ama ke tsaye gaban cupboard din sultana tana zaqulo mata kaya. A qalla kayan dake zube saman madaidaicin gadon sultana din sun kusa kala ashirin,saidai kowanne a ciki sultanan ta gaya mata baya shigarta. Daga qarshe hannunta ya damqo wata free size gown,golden brown ce da ratsin baqi,ama ta dagata tana kallonta hadi da sauke ajiyar zuciya. K'ofar toilet din dakince ta bude,sultana ke takowa a hankali daure da babban towel. Idan a watanni biyun baya kaga sultana a yanzun zaka iya rantsewa ba ita bace,ko kuma kace "Wanne irin ci takewa abinci haka?" Zaka kuma iya qaryata duk mutumin da yace maka baqar wahala takesha,bata iya bacci da dare sosai,bayan dukka 'yan kwanaki sai ta ziyarci likita ya qarawa jijiyoyinta ruwa. Kamanninta tun daga jikinta zuwa fuskarta sun dauki hanyar bacewa. Tana takowa gaban ama ama din na kallon idanunta "Kuka kikayi cikin bandaki sultana?" Ta jefa mata tambayar data sanya sultana ala dole kauda kanta. Kukan tayi,kukan data kwan biyu batayi irinsa ba saboda rashin qwarin jikinta. Fuskarta ta kalla taga yadda ta koma,gaba daya kaman ba sultanan bibi ba?,me yasa ama ta tilastata akan tabar cikinnan?,me yasa bata yarda da shawarar bibi ba?,kullum rana ji takeyi kamar ruhinta zai fita daga gangar jikinta,wani lokaci ma sai taji numfashi kamar na mata wahalar shaqa,wani abu ya yiwa cikinta qabe qabe,yayita mata motsi kuma yana dukan bangon cikinta,wani lokaci ta tashi ta zauna a firgice cikin dare,wani lokaci ta dafe gurin ta saki kuka me tsuma zuciya. Tunda uwarta ta haifeta bata taba jin ana motsi cikin mutum ba,a ranar data fara ji din kusan haukacewa ama tayi da kuka da firgici. Ita sa tanja sai da suka kusa kwashe awa guda suna mata bayani suka kuma kwatanta mata kafin su samu ta sassauta,saidai har yau idan cikin zai motsa to yana motsawa ne da wani irin miki a zuciyarta. Ganin tayi namijin shanye damuwarta sai ama din bata kuma tuhumarta ba,ta zauna tana miqa mata kaya tana shiryawa. Gaba daya girman cikin ba zakace na haihuwar fari bane,bayan haihuwar fari ma ace cikin yarinya kaman sultana?. Duk da a yanzun wani girman dole yazo mata,ta cika ta zama mace,amma idan ka qare mata kallo tsaf idan kana da nazari zakazan yarinya ce danya shataf. Ko a jiya sai da sukayi zancan girman cikin da tanja "Next month zamu koma ganin likita,zan masa complain naji me zaice" ama ta cewa da tanja "Amma hajiya anya baki tunanin tagwaye ne a cikin nan na sultana?" Sai da gaban ama ya fadi "Tagwaye a cikin sultana kuma?,ina zata kaisu?" Ta tambaya da fargaba,sai kawai tanja tayi murmushi "Shikenan,Allah dai ya raba lafiya kawai zamuce cikin amincinsa" "Allahumma ameen" ama ta amsawa tanja,saidai cikin ranta tana nazarin maganganun tanja din A nutse ta gama shirinta tsaf sannan ama ta sanyata a gaba suka fito. Yau din tanja tace zata zauna cikin gida,ita ta soma gajiya da kallon masu jajayen fatar nan. Sosai maganar ta bawa ama dariya,sultana kuwa murmusawa tayi qasan zuciyarta ba tare da fuskarta ta nuna ba. Hakan kaman qa'ida ya zamewa ama tun sanda likitan ya basu shawarar fita strolling da sultana din saboda sake samun qarin lafiya da kuma gujewa qaruwar hauhawar jininta. Tare suka jero ta layin unguwar da yafi kama da titi sabooda shimfidaddiyar kwalta data maye gurbin qasa da mu muke fama dasu cikin layukanmu. Idan ka hangesu daga nesa zakayi tunanin yaya ce da qanwarta,idan suka kusance ka kuma sai kaga UWA da 'YA sak. Yau din shuru ne ya soma ratsa tafiyar tasu,har sai da ama tayi gyaran murya "Yau bakison kowanne labari ne?" Ta fadi tana dan satar kallon sultana,wadda tun sanda ta fara zuwa center din data mata register ake samun sauqin wasu abubuwan,koda ba zaka ganta tana dariya ba amma a qalla akwai raguwar dakuwa kaso sittin cikin saba'in data dawwamarwa fuskarta,to amma yau din da alama akwai wani abu da ya taba zuciyarta "Inaso" ta fadi a taqaice,sai ama ta dage dukka kafadunta "Shikenan,zan baki labarin qasar Germany,sanda mukaje da abbana duka duka shekaruna goma sha hudu......amma saikin gayamin meye yake damunki,karki manta......munyi alqawari dake kin daina boyemin komai" ama ta fada taba nuna fuskar sultanan da dan yatsa. Duk yadda taso jurewa saida hawaye suka taru a idonta,tasa bayan hannunta ta matsesu sannan bakinta yana dan rawa tace "Na gaji da cikin ama,don Allah yaushe zai baki na huta?" Tausayi da dariya dukka suka kama ama din,amma tausayin ya rinjayi dariyar. Tsabar sangarta da gata batasan ma wata nawa ne ciki yakeyi a jikin mace ba kafin ta haihu,tsabar qanqantar shekarunta ma batasan yadda zatace Mata yaushe zata haihu ba,sai ta kama hannunta suna dab da wani shop na Shan coffee da snacks don haka suka qarasa. Kujera taja mata ta kalleta,ko batayi magana ba tasan me take nufi,don haka sai tayi taku biyu,ta isa gaban kujerar ta zauna,fararen idanun nan a narke. Murmushi ama din ta sakar mata,ta daga mata yatsanta guda sannan ta shiga shop din. Da kallo sultana ta bita harta bace cikin shop din,sai ta zuqi numfashi wanda yakai mata har tsakiyar hunhunta. Da sauri tare kuma da wani irin gaggawa ta saki numfashin hadi da fesar dashi waje tana zare idanunta. Cikin kowacce kafa ta numfashita.....cikin kowanne sasanni na shiga da fitar numfashinta qamshin yakai. Qamshin da tafi tsana a duniya,qamshin da batajin ko da tana kwance ne a kushewarta muddin qamshin zai gitta ta gurin zata iya jiyoshi,qamshin da jikin mutum daya ta sanshi,ta kuma yi masa mummunar hadda me wuyar mantawa a baqar ranar da tayi silar jirkita dukka farinciki walwala da tarin mafarkan data tanadarwa rayuwarta. Tsam ta miqe tsaye dukka jikinta yana rawa,ta ware idanunta tana duban kowanne sashe na wajen. Ba kowa,bata ga kuma kowa ba,hasalima kaf wajen kamar ita daya ce baqar fata,sai kuma ama data shiga ciki. Dafa kafadarta taji anyi,abinda ya sanyata wani irin bahaguwar juyowa,sai idanunta ya fada cikin na ama. Kallon kallo suka tsaya yiwa juna,ama tana kallonta cikin mamakin abinda ya firgitata daga shiga ta fito bayan wajen safe yake,yayin da ita kuma razanar da tayi da kuma tuna mata da mummunar ranar da sanadiyyar wanzuwar qamshin ya haifar mata ya sanya zuciyarta raurawa,kawai saita aza fuskarta saman kafadar ama ta saki siririn kuka. Tasan dama akwai sauran qunci cikin zuciyarta,wanda babu wata hanya da zata samu sassaucinsa saita hanyar kukan,don haka batace komai da ita ba,ta jata jikinta sosai tana bubbuga bayanta,har sai data nutsu don kanta sannan ama din ta maidata saman kujerarta,ta kuma tura mata daya daga cikin nau'in abin shan da shima akan dace ya zaunawa cikinta. Bata tambayeta ba hakanan batace mata komai ba sai da taga tana diba da kadan da kadan kamar me ciwon baki tana sha sannan ama din tayi gyaran murya tana gyara zamanta "Next month zamu koma asibiti,zan tambayeshi wacce rana ne zaki haihu,zakiji in sha Allah,amma kinsan zai iya ce miki ba yanzu ba?" Da sauri ta daga kai tana wulqa idanu,idanun nata cikin na ama, fuskarta ta narke sosai cikin nuna zallar fargaba. Sai ama ta dage mata dukkan girarta "Eh mana,ya hana wannan koke koken,sannan yace ki dinga daurewa kina cin abinci sosai haka ne?" Kai ta gyada mata a hankali "To me kike tunanin zai faru idan mukaje ya gwadaki yaga babyn baiyi girman da zaki haihu ba?" "Zanci ama,don Allah kice masa kada yacemin ba yanzu ba,bana iya bacci ama,bana iya komai,dukana kawai yakeyi a ciki na,kullum dare a zaune nake....." Ta qarasa fada tana saka tafin hannunta guda tana share sabbin hawayen dake sauko mata. Tsananin tausayinta sai da ya sanya ama din taji qwalla sun sauko mata amma ta daukesu cikin dabara,saita miqa hannu tana dan bubbuga bayanta cikin dabara.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 22 Ganin ta zage tasha abun sosai sai ama ta yanke shawarar su qara nisan zango a tafiyarsu don ya saukar mata sosai,kada su koma gida da wuri ya dameta ko ya sanyata amai. Cikin salon jan hankali ama ke bata labarin Germany,har zuwa sanda sukazo giftawa ta wani baby shop. Har sun gota amma ta tsaya,sai a sannan ta tuna babu koda qyallem handkerchief da ta siya da sunan kayan haihuwa. Juyawa tayi ta dubi sultana "Mu shiga nan ki jirani nayi siyayya" bata musa ba ta sanya kai tana biye da ama din. Guri ta sanya ma'aikatan gurin suka bawa sultanan tace tayi zamanta,gudun kada tace tazo ta tayata zabe taje ta jangwalowa kanta,qilu ta jawo bau. Sosai ta nutsa cikin shagon,ta dinga zaben kaya designers masu tada da sukaja pounds sosai. Samun kanta tayi da daukar duk abinda ya bata sha'awa,musamman kayan baby girl. Har yanzu akwai wannan qawa zucin a jikinta da kuma zuciyarta,har yanzu tanason baby girls,don dai kawai lokacin haihuwarta ta fuskanci ya wuce ne. Sanda ta shiga bangaren overalls 'yan ubansu,saita tsinci kanta da zaben komai pink,haka kawai cikin zuciyarta taji tana da burin inama ace babyn ya zama mace?, murmushi ya subuce mata ba tare data shiryawa hakan ba. Daidai bangaren teddies ama ta ajeta. A nutse takebin wajen daki daki da kallo,komai na wajen me kyau ne,alamu dake nuna cewa komai na cikin shagon zaiyi tsada kenan. A hankali wani tsohon emotion nata ya fara taso mata. Nini dinta ta fado mata wadda har kwanan gobe batasan inda tayi ba. Allah ya zuba mata qaunar teddy,duk da wannan emotion din nata yaso mutuwa murus daga gangar jiki harma da ruhinta. Har ta zare idanunta daga kansu sai hankalinta ya fusgo mata wata kyakkyawar pink teddy. Maida dubanta tayi,ta miqa hannunta tana shafata. Sosai jikin teddy din yayi mata,haka ma fasalin da akayi mata "Ki dauka idan tayi miki" ta tsinci muryar ama daga bayanta. Da sauri ta waiwaya ta kalli ama dake riqe da wani babban kwando da ta cikashi taf da suturu,saita maida dubanta ga fuskar ama din tana girgiza kai alamun a'ah,sannan ta miqe a hankali da zummar barin wajen. Da kallo ama ta rakata sai kawai ita ta saka hannu ta zaro teddy din ta jefata a kwandon kayan. Har tayi gaba ta dawo da baya,ta zake zabar wasu guda biyar suka zama shida cif,sannan ta wuce wajen lissafi. Mamaki ne kawai ya kashe sultana sanda taga uban kayan da ama ta diba,ashe kwandon hannunta na daxun sauran kayanne kawai. Kamar ba da guminta take neman kudin ba,ta zare Pounds masu ciwo ta biya kudin kayan tas,sanann ta bada Adress din inda za'a kai mata suka fice abinsu daga shagon. Har ranta bataji komai ba,jinin maina ne kuma tsatsonta itama.......inda ana kyautar rai tabbas zata iya sadaukarma ahalinta,xata iya komai domin jininta,ita a yanzun ma da kwanakin cikin ke qara nisa sai takejin zumudi qauna da kuma soyayyar abinda ke cikin na sake kamata,taji ta dokanta da son ganin abinda ke cikin sultana din,ta matsu ya iso duniya. ********Sake duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ama tayi,mamaki ya sake kamata,me sultana din keyi shuru bata fito ba har yanzu?,bayan tasan inda zasuje din da kuma muhimmancin wajen. Kamar ta aika tanja sai kuma ta fasa,ta miqe tana ajjiye medium veil din hannunta mahadin doguwar rigar jikinta ta gyara zaman agogon hannun nata tana wucewa dakin sultanan. Zaune ta sameta saman stool a gaban madubi,daure take da babban farin towel,sumar kanta na nannade tsakiyar kanta. Tuni ta jima da zama qazama ta wannan fannin,bata yarda da abinda zaya taba mata kanta duk qanqantarsa,sai ama tayi da gasken gaske sannan ake wankeshi a kuma maidashi yadda yake. A nutse tare da sallama ama ta shiga dakin,waiwayowa sultana din tayi,hawaye ne shabe shabe kwance a fuskar tata "Ya salam" ama ta furta qasa qasa. Itadai tunda take bata taba ganin mutumin da kuka baya damunsa ba baya kuma yi masa wuya ba irin sultanar "Yanzun kuma kukan meye?" Ta tambayeta tana isa bayanta ta tsaya tana duban fuskarta cikin mudubi. Cikinta ta kalla,sai a sannan idanun ama yakai kai,ta yaye towel din dake jikinta,sai turtsetsen cikin a gaba kai kace saura satittika ta haihu "Menene?" Ama ta sake tambayarta cikin fargabar kada ta bata amsar wani abu ne ya samu cikin "Fasamin ciki zaiyi ama......sai dukana yakeyi nan da nan" ta bata amsar tana rushewa da kuka tare da nuna mata gefe da gefen cikinta da yatsanta. Ga dariya ga kuma tausayi,da gasken gaske sultana danya ce shataf,babu wani abu data sani dangane da ciki ko haihuwa,uwa uba auta kuma 'yar fari,wautar tata tayi yawa. Gaban sultana din ama ta zauna tana qoqarin fahimtar da ita cewa alama ce ta lafiyar abinda yake cikinta "Ni na tambayeshi yana lafiya?,ya mutu mana" ta fada tana buntsuro baki gaba "Subhanallahi" ama ta fadi tana zaro idanu,don sosai maganar ta daketa, jikinta yayi wani mugun sanyi,tsoro kuma ya shigeta. Kada dai ace zuciyarta ta taso da qeqashewa da qiyayyar abinda zata haifa din kamar yadda ta yiwa mahaifinsa muguwar tsana?. Wannan tunanin kadai ya sanya zuciyarta rawa,bata fatan kuma wannan ya zama qaddararta ta gaba,batasan yadda zata fuskaci wannan qaddarar ba kuma "Sultana?" Ta kirayeta a sanyaye tana kallon tsakiyar qwayar idanunta. Duban aman tayi amma sai ta janye kallonta daga kanta,karon farko da taji wani nauyi na aman,taji kuma nauyin kallon idanun aman,jikinta itama ya sanyaya,taji a jikinta kamar ta furta wani abu da ba dai dai ba. "Kinaso muyi fada dake?" Ta sake tambayarta with seriousness. Da sauri ta girgiza kai tana jin zuciyarta tana karyewa "To kada ki sake fada,kada na sake jin kinyi wannan furucin,akan kowa ma bare d'an cikinki,da yake kwana ya tashi a jikinki,bashi da wata uwa sai ke,ke kadai kika dauki cikinsa kikasan wahalarsa,mu nan dukka tayaki kawai mukeyi kinji ko?" Kai ta jinjinawa aman,sai tayi saurin kauda zancan ta hanyar cewa "Oya.....tashi ki qarasa shiryawa,idan munje wajen likita saiki kai masa qararsa,zai masa fada nasan,zai daina kuma dukanki" wannan 'yar maganar ta sanyayawa sultana rai,ta kuma miqe din ta shirya tsaf a gaban ama din kamar yadda ta saba shiryawar,ba wani nauyi ko kunya ko digo da takeji nata. Yauma sai da sukayi tattaki subway,sannan suka hau train zuwa asibitin. Dr abdur'razaq mansoor,cikakken likita dan asalin qasar Egypt shine likitan dake duba sultana,likita ne me matuqar kirki da kula da addini,yana da tausayi da kulawa sosai. Tun ranar farko da ya fara ganin sultanan tausayinta ya cikashi,ya fahimci yarinya ce qarama sosai da bata gama sanin rayuwa ba. Yanayin nutsuwar likitan da tausayin da ya gwada ma sultanan ya sanya ama bata boye masa komai ba "Zan bata kulawa in sha Allah,zata haihu kuma lafiya" a boye ya baiwa ama addu'o'in da zata dinga tofawa sultana din a ruwa,kuma ko sau daya aman batayi fashin tofa mata din ba ba tare da sultana ta sani ba. Duk wani gorar ruwa na gidan da tasan sultanan zata iya sha sai data budesu ta tofa din,daya daga cikin sirrikan abinda ya kawowa zuciyarta nutsuwa ya kuma sake tanqwara ta ya sanya mata dangana. A irin qasashe dake da ci gaba irin haka,zaiyi wuya kaje ganin likita ka samu cinkoson marasa lafiya suna jiran likita,hasalima lokuta da dama saidai ka samu likitan yana zaune kawai yana hutawa ko wani research da ya danganceshi. Don haka mace daya ce ta fito number dinsu tayi appearing jikin board na office dinsa don haka suka wuce ciki kai tsaye. Da fara'arshi da kuma sakin fuska ya musu maraba. Ya saba sam sultana bata magana har su gama ganinsa su tafi,amma hakan baya hanashi dan tsokanarta janta da wasa kadan don ta saki jiki da kuma tambayarta yanayin lafiyarta. Sai da ya gama mata dukka tambayoyin da aka saba,ya nemi jin ko akwai wata matsala da take fuskanta?. Murmushi ama tayi sannan cikin harshen France don sultana din taji ta gaya masa "Tace dukanta cikin yakeyi,ta gaji dashi yaushe zan karba?" Qaramar dariya Dr abdur'razaq mansoor ya saki "Yau zamu duba muga me yake faruwa sai a gaya masa ya fito haka momy ta gaji" shi da ama suka dan saki dariya,banda sultanan da take binsu kawai da kallo. Komai ya hada sannan ya bata umarnin hawa gadon scanning. Karon farko da za'a yi mata scanning din tun bayan wanzuwar cikin. Kusan daskarewa Dr abdur'razaq mansoor yayi yana ci gaba da yawo da na'urar saman cikinta "Subhanallah" kawai yake furtawa lokaci lokaci idanunsa qur bisa allon computer din. Subhanallah din da yake fada ta sanyawa ama fargaba,amma ita dinma saita dinga ambaton sunan Allahn kawai,don tunda taji baice komai ba qila babu buqatar yin maganar gaban sultana. Yana kammalawa ya danna wani madanni na kiran nurse,ba jimawa nurse din ta shigo,cikakkiyar baturiyar Austria,saidai ita dimma da alama macace me kirki da yawan fara'a. Cikin harshen German yace da ita ta kaita garden na masu juna biyu,sannan ya sake juya harshen nasa cikin yaren France ya yima sultanan magana. Ba musu ta miqe ta saki doguwar rigarta,ta kuma gyara yafen mayafin nata tabi bayan matar. Da idanu ya bisu,sai daya tabbatar da fitarsu sannan ya dawo da dubansa ga ama wadda ta tsurawa hoton scanning din dake jikin allon computer din idanu,kwanyarta nason rarrabe mata gaskiyar abinda idanunta ke gane mata. Hannu kawai ya miqa ya juyo mata da fuskar computer sosai yana kallon idanunta,cikin yaren faransanci yace mata "Ina tayaku murnan samun 'yan biyu,yarinyarki tagwaye ne a cikinta kamar yadda na jima ina zato" maganar tazo mata a mugun ba zata,cikin hanzari ta maida dubanta ga Dr abdur'razaq. Ya fahimci she was shocked,sai yayi murmushin nan nasa yana dora dukka hannuwansa kan computer din. Kai tsaye ya canza hoton da take gani zuwa 3D scanner,take fuskokin yaran dake kwance cikin mahaifar sultana din suka bayyana tarwai. Ko ina a jikinta ya dauki rawa,ta sanya hannuwanta dukka biyun tana rufe bakinta,bakin nata dakeson kama sunan Allah amma rawar da yakeyi ya sanya ta kasa,Dr abdur'razaq bai waiwayo ya dubeta ba yaci gaba da mata zooming fuskokin guda biyu da suka zama cikakkiyar fuskar bil'adama,fuskokin da suka cika suka kuma bayyanar da kamanninsu,suna rungume da junansu "Bacci sukeyi,inda idanunsu biyu zaki iya ganin motsawar kowannensu,kukansu ko walwalarsu" "Subhanallazi lam yattakiz waladan walam yakun lahu sharikun fil mulki walam yakun lahu waliyyun minazzull" ta furta wasu hawaye masu sanyi suna sauko mata. Tayi tunanin zasu tsaya amma basu tsaya din ba,haka suka dinga sauko mata daya bayan daya. Bai hanata ba Dr,yadai miqa mata tissue yana duba wasu ayyuka nashi har sai da zuciyarta tayi sanyi sannan suka dakata,ta gyara fuskarta ta kuma gyara zaman mayafinta sannan tace "Amma Dr ina tsoro,ta yaya sultana zata iya haifan tagwaye da kanta?" File din gabansa ya rufe yana dubanta "Bayanin da nakeson miki kenan,tayi qanqanta qwarai,don ko a yanzun girman da yaran keyi a cikinta ya bani mamaki,nauyinsu da na gani,lallai ita kanta ba qaramin qoqari takeyi ba,kuma tana da jarumta duk raunin nan nata da yawan koke koke,bakinta kuma na tabbatar duk da yawan qorafinta akwai abinda bata iya gaya miki,so ina kyautata zaton cikin yana shiga sati na talatin da shida za'a yi mata CS a cireshi......amma banason ki gaya mata hakan,saboda a yanzun dole a dinga monitoring blood pressure nata,a bata kwanciyar hankali sosai da nutsuwa don komai yazo yadda akeso". Sosai jikin ama ya qara sanyi,ya lura da hakan sai ya bata gwarin gwiwa sosai,qwarin gwiwar da ta sanya taji eh tabbas zasu iya fuskantar komai,kuma komai zaizo ya wuce da qudirar Allah kaman bai faru ba. A karo na Babu adadi bayan fitowarta daga office din Dr abdur'razaq ta ciro wayarta,kamar kowanne lokaci da idan abu irin hakan ta faru zatayi gajeran tex wa maina *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 23 A duk sanda wani abu ya faru sai ta rubuta ta tura masa tare da gargadinsa kan duk inda yake ya dawo. Ko sau daya bata taba samun tabbacin saqon yana isa ba,bata taba ganin alamu na maido amsa ba koda da digo,amma hakan bai hanata aika saqon ba. Cikin hanya kaf tunaninta na yadda zata sake dauke hankalin sultana,tare da yin handling komai idan lokaci yayi. Dukka qarfi da basirarta ta sanya don tabbatar da farincikin sultanan. Ta sake qirqirar abubuwan da tasan zasu dauke mata hankali. Tilas ta dinga siyan ticket na zuwa qasashen da suke maqwaftaka da Austria duk don ta faranta ranta,ta kuma sake don a samu a cimma nasara. ********Misalin qarfe tara na dare ta fito daga toilet din. Daure da babban towel take amma sam ya kasa ratsata saboda girman uban cikin dake gabanta. Da qyar take daga qafafunta,duk ta qarasa zama wata babba ta kuma kumbure har fuskarta. Dazu daxu kafin ta shiga wankan ta gama cikin kukanta,abinda ya ruruta idanunta kenan,ya kuma sanya fuskarta ta sake yin jazur. Kai tsaye ta isa gaban mudubin ta tsaya tana kallon kanta da kanta,wani zazzafan hawayen ya zake silmiyo mata,ganin kanta takeyi kamar ba ita ba,sau tari idan ta kalli fuskarta takanji kamar ba itace sultana ba,itakam a rayuwa tana jin hatta da shaidan saidai maina ya biyo bayan qiyayyarsa a zuciyarta. Batajin har abada zata iya yafe masa,batajin akwai wani wahala ko Azaba da zata ganshi a ciki da zai karya zuciyarta taji zata yafe masa. Kullum kwanan duniya fadi take fili da zuci "Allah ka sakamin". Hannu ta saka ta yaye towel din,tulelen cikinta dake rinjayarta ya bayyana,yayi girma qwarai ya kuma yi tsini sosai,ta dafe qasan mararta da nauyin da takeji yafi yawa a nan akan ko ina,Allah Allah takeyi kwanan watan da ama tace mata zata karbi babyn yayi,Allah Allah take a cire mata shi,ta hanci ne?,ta baki ne?,ta kunne ne oho itadai ba matsalarta bane. Matsalarta daya ta wayi gari ta jita wayau,ta jita ta tashi babu wadannan lalure laluren da uban nauyin da yake damunta. Turo qofar da akayi ya sanyata saurin sakin towel din. Ama ce ta kuma ga abinda ta tsaya din tana kalla amma sai tayi kamar bata gani ba,ta dauke kanta ta shigo dakin tana fadin "Bakijin sanyi sanyin garin nan daya fara busawa?" "Yanzu zan shirya" ta fadi da dakusashiyar muryar da har yau bata bude qwarai ba don ba maganar ma ta fiya yi ba bare ta bude yadda ya kamata. Tana kallon ama ta gefen ido ta jawo akwatin da kusan kullum sai taga tazo ta shiryashi,ta kuma sake zuba kaya,ita kadai cikin ranta take mamakin kayan da ama din keta narkawa akwatin,bayan tace mata dashi zasu tafi asibitin,to tabbata zasuyi cikin asibitin da aketa loda ma akwati kaya?,oho bata da wannan amsar,sai kawai ta jawo lotion ta fara shafawa a jikinta. *********Sanye da kayan theatre Dr abdur'razaq mansoor ke fitowa daga office dinsa. Gefansa wani gajeran likita ne baturen qasar Austria din,yana riqe da files a hannunsa suna magana da Dr abdur'razaq din cikin harshen German. Ama dake zaune saman kujerun dake daura da theatre room din ta miqe tsaye tana jiran qarasowarsa. Dab da zasu iso din ya sallami likitan ya shige dakin theatre din shi kuma ya amshi file din hannunsa yana qarasowa. Yaga fargaba,sarewa da kuma tsoro a tattare da ita,abinda bai tana gani ba kenan daga gareta tsahon watannin da sukayi suna zuwa gurin nasa. Tsayyayyar macace da ba komai ke firgitata ko kuma ya bata tsoro ba. Ya sani a irin situation din sultana dole ta fuskanci fargaba da tsoro,don haka ya sakar mata murmushin dake bada qwarin gwiwa,ya miqa mata file din yana kallon agogon hannunsa "Ki kiranta a nutse ki sanya hannu,sanya hannun shi zai bamu damar fiddo miki jikokinki nan da mintuna talatin kacal in sha Allah". Hannu tasa ta amsa,ta koma ta zauna kusa da tanja gwiwa a matuqar sanyaye,ta buda page din ta fara karantawar tana sanya hannu,saidai a duk inda ta sanya hannun,sai zuciyarta ta jaddada mata.....muddin aka samu akasi la shakka itace ta kashe sultana "Hasbunallahu wani'imal wakil" take bin mummunan tunanin da shi,har ta kammala ta rufe ta miqawa Dr abdur'razaq. Amsa yayi yana sake murmushi "Compte à rebours les minutes(ki irga mintunan)" ya fadi yana bata qwarin gwiwa cikin idanunsa,sannan ya taka zuwa qofar dakin theater din ya sanya kai bakinsa dauke da bismillah. Ragwaf ta koma ta zauna,ta dunqule dukka hannayenta cikin na juna tana jin jikinta yana mata wani yaarr,ta dinga maimaita kiran sunan Allah data samu bakinta ya fuzgo sanda tanja dake riqe da carbi take maimaitawa a fili don ta samu ama din ta kama kuma nutsuwarta ta dawo. Mintina biyar kacal ambaton sunan Allah ya saukar mata da nutsuwa,saita zaro wayarta as usual ta turawa maina tex akan current situation din da ake ciki,ta maida wayar tsakanin cinyoyinta kawai tana ci gaba da kiran Allah. Da ita da bibi batasan waye ya riga wani miqewa ba sanda qofar theater din ya bude ba,saboda mintunan da Dr abdur'razaq mansoor ya basu sun cika harma sun gota da wajen qarin mintuna wasu talatin din akai. Dr dinne da kansa,iya fara'ar saman fuskarsa kawai ta bayyana musu labarin me dadi ne,ya qaraso gabansu yana cire facemask din fuskarshi "Alhamdulillah,anyi nasara,an ciro mata tagwaye dukka YARA MATA" ya fadi yana duban tanja da ta qame cikin zallar farinciki. Batasan yaushe bane,ba kuma tasan ya akayi ba,itadai taji dukka gwiwoyinta sun zube izuwa qasa,kafin daga bisani fuskarta da goshinta su kafu a qasa "ALLAH kaine Allah,Allah ina me tuba izuwa gareka,Allah na tuba bisa dukka laifukana,Allah na tuba bisa dukka zunubaina,Allah na tuba bisa karan tsaye da nake yiwa al'amuranka, ubangiji a yau ka tabbatar min da qarfin ikonka,Allah ina godiya a gareka,Allah na gode mahaliccina na gode,ya hayyu ya qayyumu kasa yarannan rayayyu ne,duk wani dake boye da wanda ke a zahiri Allah ya daidaitashi cikin izza hikima da buwayarka,Allah ka bawa mahaifiyarsu dangana,ka bata haquri,ka taushi zuciyarta,ya hayyu ya qayyumu ka karkato da hankalin mahaifinsu gida,Allah kaine mafi sani,kafi kowa sanin hikimar data sanya ka wanzar da wannan al'amari,ya arhamar rahimeen ka sanya qarshen komai ya zamana da kyakkyawar cikawa" sannan ta cikashe da maimaita alhamdulillah har sau babu adadi. Itama tanjan sumbatun addu'a kawai ta dinga yi,hawaye ne itama cikin idanunta,yau 'yar lelen bibi ta zama uwa,yau 'yar lelen bibi da yara har biyu?,tabbas wannan haihuwa inda cikin gida nijer akayita batasan wanne irin cika yau asibitin nan zaiyi ba,batasan adadin farincikin da fuskokin mutane zasu nuna ba. Da suka buqaci ganinta ba'a hanasu ba,wata nurse ta musu jagora zuwa dakin hutun da aka bata wanda suna ciki ita da yaran da aka dawo dasu daga sashen yara yanzu yanzu bayan anyi musu gwaje gwaje da bin qwaqwafi irin na bature. Sakamakon da suka gani ya basu mamaki kodon qarancin shekarun uwar yaran. Sun jima basuga lafiyayyun yara irin yaran ba,ga wani irin girma kai baka ce daga cikin qaramar yarinya under 14yrs suka fito ba.(ai addu'a ba wasa bace,duk wanda ya gaza ganin tasirin addu'ar da yakeyi to baiyi addu'ar da kyau bane,ko bai cika sharuddanta ba,ko kuma baiyi addu'ar yana bawa Allah dukkan yaqininsa ba da yardarsa ba). Duk yadda taso taje ta fara ganin fuskar sultana dake bacci daga ita har tanja sun kasa,gaba dayansu gadon babies din suka nufa,hannun kowa yana rawa yana saurin isa garesu. "Ma sha Allahu la quwwata illa billa,ma sha Allah....tabarakallahu ahsanul khaliqeen....." Ama ta dinga maimaitawa bakinta yana rawa. Wasu irin fararen yara masu cikar zati da kyau,wasu irin jarirai masu tsananin kama da juna,kyawawan jariran da batasan ma kamannin waye zatace sun dauko ba. Farare tasssss tamkar iyayensu haifaffun Vienna ne ba nijer ba,nannade cikin fararen kaya masu tsananin taushi da daukan idanu. Yadda hannunta ke rawa ta tabbatar muddin ta daukesu tana iya yada su,hasalima bata iya gani sosai saboda uban hawayen dake narke cikin idanunta,saita sanya dogayen yatsunta ta riqe siraran yatsun yaran dake nannade cikin safar hannu. Duk yadda taso riqe kanta sai ta kasa,kuka ya balle mata,tayi qas da kanta tana kokawa,tanja tana bata baki. Ina maina ya tafi?,ina aliyyu yaje?,yazo ya gani a yau shima ya zama uba,a yau yabar yabanya,a yau ubangiji ya cika masa burinsa,mafarkinsa,kuma fatansa,burin da a sansa yake furtawar yana fada ne kawai ba tare da samun tabbacin fatansa zai cika ba _"duk randa nayi aure,matata ta haifami 'ya mace haihuwar fari ama ke zan bawa,in sha Allah sai na share miki kukan rashin haihuwar 'ya'ya mata,sai na dauke miki takaicin da ake sakaki na hanaki riqon 'ya'yan wasu"_ wasu daga cikin kalaman maina kenan a duk sanda yaga tana neman 'yar budurwar da zata riqe,ko kuma taje ta daukota akazo aka karbeta,ko kuma ta fara riqon taje hutu taqi dawowa. Yau gashi burin maina ya cika,bama yarinya daya ba,yara biyu reras a lokaci guda,itakam batasan me zata cewa Allah ba. Ko sau daya ama ta kasa motsawa daga gindin gadon,ta kasa dauke idanunta daga kan yaran,duk wani motsi da zasuyi saman idanunta ne,kamannin yaran sun baci ainun. Wata irin mahaukaciyar soyayyarsu ce ke ratsata tun sanda ta dora idanunta saman fuskarsu,sai takejin kamar a duniya bata taba son wata halitta ba tunda Allah ya halicceta sai a kansu.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 page 24 A hankali ta zare hannunta daga nasu bayan sunsha hoto,sun sha videos har batasan adadinsu ba,ta matsa kusa da sultana karo na biyu taga kota farka a baccin?. Har yanxu dai baccin takeyi lakadan,fuskarnan ta fada tayi kuyas,hakanan duk girman jikinnan ksmaryan zugeshi tare yaran,ta ragu sosai,qanqantarta ta soma dawowa. Sai data fuskanci lokacin sallar azahar yayi sannan ta tashi a wajen,ta shiga bandaki ta daura alwala tabar tanja a wajen. Sanda take idar da sallar sultana ta motsa,ta shafa addu'ar da sauri ta miqe ta nufi sultanan. Tun daga idanunta zuwa jikinta take jinsu wani iri,batayi yunqurin miqewa ba saboda nauyin da jikinta yayi mata,kanta ta mirgina gefe guda tana kiran Allah can qasan zuciyarta,zuciyar tana bata zaiyi wuya idan ba mutuwa tayi ba,don ba abinda zata iya tunawa,tadai jita daga qarshe kamar tana yawo cikin iska. Ama data hango tana tahowa ta tsurawa idanu. Da murmushi a fuskarta ta taqaraso,ta jawo doguwar stool dab da gadon nata ta zauna. Idanunsu cikin na juna Hannunta ta miqa ta riqe hannun sultana wanda babu qarin ruwa a jiki "Kin tashi?" Kai gyada mata tana ci gaba da duban ama din "Sannu" yauwa tace da ama,amma sautin baya fita sosai. "Me yake miki ciwo yanzu?" Kai ta girgiza alamun ba komai,hakan ya yiwa ama dadi,sai taci gaba da zama a nan din bata sake cewa komai ba kaman yadda sultana din itama bata sake magana ba,sai idanunta data mayar ta lumshe. Tana jin alamun cikinta empty babu komai,duk uban nauyin dake jibge tana jin ba komai a cikinsa,tasan dai kenan tabbas an cire baby din kamar yadda ama tace mata,to amma yana ina?, Ta yiwa kanta tambayar "Oho" ta sake baiwa kanta amsa "Kome meye na cika umarnin ama,nima ama ta cikamin alqawarina,ban mutu ba gani ina raye,baby dama nasu ne,na gama nawa aikin" ta gayawa kanta da kanta,don haka tayi relax daga kwancen,duk da tanajin ta soma gajiya da kwanciyar. Qushin qushin din qananun kukan jariri shi ya sanyata bude idanunta a hankali,saidai kuma bata yarda ta juyar da kanta sashen da take jiyo kukan ba "Hajja yaran nan fa da alama maciya ne,tun dazu sun kasa nutsuwa sai mutsu mutsu sukeyi,ya kamata a nema wani abun a basu,tunda naji kince likita yace idan sun nema din a basu" tanja dake rungume da daya daga cikinsu ta fada "Eh,ai bari nazo nayi musu addu'a cikin kunnensu" ta fada tana zame hannunta daga na sultana. "Har su nawa ne?" Sultana ta yiwa kanta tambayar can qasan zuciyarta,duk takun ama zuwa wajen yana qididdige a kunnenta "Wacece babba ne?" Tanja ta tambayi ama tana duban fuskokin yaran "Akwai alama da suka sanya a qafafunsu"aman ta fada tana duban qafafun yaran. "Ga hassana ga usaina" ama ta furta tana murmushi hadi da duban fuskansu. "Anya wannan nan gaba za'a dinga banbancesu?" Fuskokinsu ama ta duba sosai "Subhanallah subhanallah" aman ta fadi da sauri tare da yiwa tanja nuni da hannu. Daidai gefen kunnen hassana,wani digon baqi sak irin na maina "Tanja kin gane wannan?" Ama ta fadi muryarta tana dan rawa,abinda ya sanya sultana bude idanunta da sauri,ta kuma juyar da kanta sassan da su ama ke tsaye tana ware idanunta cikin fargaba "Allah hakimu,Allah me iko,irin digon baqin dake kunnen maina" da sauri sultana ta runtse idanunta saboda kiran sunan maina din, tsakiyar qahon zuciyarta taji kamar an caketa da wani qarfe. Tanason saka hannuwanta ta toshe kunnenta don kada ta sakeyin kuskuren jin sunansa ko wani abu da yayi kamanceceniya da shi,saidai a daidai lokacin ama ta yiwa tanja alama da idanu na kuskuren kiran sunan nasa da tayi,don haka tanja din bata sake cewa komai ba,sai ama data miqa hannu ta karbi yaran ta sanyasu cikin jikinta sosai,dumin jikinsu yana haduwa,wani irin qauna ta jini tana ratsata. Dukka addu'o'in da musulunci ya tanada tayi musu,ta kuma yi musu huduba cikin kunnuwansu,sannan ta basu suna kanta tsaye ba tare da shawara da kowa ba FATIMA BINTOU DA NADEEYA (mahaifiyar sultana da kakarsu aba). Hadasu tayi dukka ta sake rungumesu a jikinta tana sauke ajiyar zuciya. Ko yau ta mutu burinta ya cika,babu kuma abinda zata cewa ubangiji face godiya mara qarewa. "FATIMA BATOUL da NADEEYA BENAZEER" Ama ta fadi idanunta akan fuskarsu. Masu cikakken gata irin gata da ba kowanne bawa Allah ke tsagawa da rabonshi ba,amma sai gashi sunxo tsakiyar wata irin cudewa rikita rikita da kuma cakwakiya,saidai koma meye ita din ba zata bari komai ya shafi rayuwarsu ba,zata basu cikakken gatan da suka cancanci dashi,zata basu dukkan wata rayuwa da duk wani me tutiya da tunqahon gata zai sameta. Har likita ya bada umarnin sultana zata iya zama zata kuma iya miqewa,sannan ya bada umarnin duka a ranar za'a iya goge mata jikinta,za'a kuma iya nema mata wani abu me ruwa ruwa tasha bata tambayi yaran ba ko sau daya. Duk ama na ankara da ita,ko sashen da suke bata kalla,sai tayi mata shuru batace da ita komai ba,har sai data gama goge mata jikin,ta zaunar da ita tana bata abu me dumi. Dab da sultana din take zaune,ta miqa mata spoon bakinta sannan tace "Baki tambaya baby ba sultana uhmmmm" shuru ta danyi,sannan ta bude bakinta a hankali "Naki ne ama,dama kince ke zan bawa,na bakin ai" kai ama din ta jinjina tana jin ba dadi,kada dai ya zamana su rasa soyayyarta kamar yadda taketa tunani tun dazu. Rabuwa tayi da ita har sai data gama batan sannan ta maida bowl din. Ta qarasa inda yaran suke ta dauki batoul sannan tanja ta aza mata benazeer ta rungumosu a kafadanta. Da idanu sultana ta bita sanda take aza mata yaran saman cinyoyinta,bata budesu ba ta kalleta tana murmushi "Budesu ki gansu" cewar ama. Idanu biyu dukka sultana ta fiddo,sai kuma ga hawayen nan nata da bata gajiya da xubdashi "Har biyu ama?,ni ba guda daya kikacemin bane?,har guda biyu?, gaskiya ni guda daya ne.....guda daya ne Allah" mamakin tarin quruciya irin ta sultana da bata rabuwa da ita ya kama ama "To biyu Allah ya baki,yanzu a ciki wanne ne bake kika haifa ba?,wace bakyaso?,bude ki kalla ki zaba na zaba a bada dayan,dayar kuma saiki bata nono kinji kinga duk yunwa sukeji" kuka ne ya qwace mata "Ni banaso duka,banaso ama,kuma ba Wanda zan bawa......." Sai ta kasa qarasa fadin nonon ta sanya hannunta mara qarin ruwan tana janye zaninta,abinda ya sanya batoul ta gangaro sosai jikin benazeer,nauyinta kuma ya sanya benazeer ta gaza riqeta suka fara gangarowa. A gigice ama ta sanya hannayenta ta fada tallafe yaran zuciyarta na bugawa da tsananin tsoro,saboda ba qaramin shammatarta tayi ba,dukkansu yaran suka tsanyare da kuka a lokaci guda,da alama suma din sun tsorata dinne. Wani irin mummunan baci ran ama yayi,bata tabajin haushin sultana ba irin yau,bata taba jin rayukanta sun baci dama ko meye takeyi ba irin yau. "Ke sultana!" Ta kirayeta cikin tsawa,tsawar data kada zuciyar sultana din. Karo na farko a rayuwarta da tsawa ya taba hadasu da ama "Ashe baki da hankali?,don baki sonsu sai akace ki kashesu?,yaran da kika haifa a cikin cikinki?,ke haka kika ga bibi tana miki?,haka kika ga aba yana miki?, oncle bashar oncle umar?,uwa uba mahaifin nasu da kikaqi jini?,shi ya goyeki a gadon bayanshi,ya baki abinci da hannunsa,yayi maka wanka,wankin kashi da na fitsari,shine yanzun zaki gangaro qananun yara da ko kwana daya basuyi ba duniya?,to ke kika haifesu duka 'ya'yanki ne,idan ke kika haliccesu ki maidasu inda suka fito" ta qarasa fada cikin bacin rai tana debe yaran. Wani mugun mutuwa jikin sultanan yayi,dukka gabbanta sukayi sanyi,idanunta suka cicciko da sabbin hawaye,ranta ya dinga yi mata ba dadi da ganin bacin ran ama. A yau zuciyarta ke mata fadan da ya dace,bai kyautu ta yiwa ama haka ba,matar data tsaya da ita cikin wuya rintsi da dukka tsananin data fuskanta tsahon watanni goma,bata tana gajiya ba,bata taba sarewa ba,bata kuma taba ja da baya ba,bai kamata ta saka mata da wannan ba. Tana jin sanda ama ta fita ta siyo madara tazo ta hada ta bawa yaran,babu jimawa sukayi luf,bacci yayi awon gaba dasu. Ama bata sake saurarenta ba,iyakaci ta barta da tanja,tana ji tana gayawa tanja ita yanzun ta koma rainon jikokinta,ga diyarsu nan. Abun sai ya quntatawa sultana,a fakaice dai ama ta rabu da ita kenan?. Ko a washegari da mutane sukayita shigowa ganin twins duk wanda ya tambayi mamansu sai tace bacci takeyi,duk kuwa da idanunta biyu. Sosai turawan suka dinga shigowa ganin 'yan biyu,abinka da bature wanda baya raina abun kallo. Hotuna suka dinga yi da yaran,gif kuwa sai gashi sun cika wani sashe na dakin da gifts,har sai da ma'aikata suka kwashe aka kai musu ajiya dakin ajiya dake cikin asibitin. Wani irin kyau da murjewa yaran sukeyi,kusan kullum Allah ne da kullum amma indai rana zata fito ta fadi sai masu son ganin yaran sun shigo,kuma dukkansu turawa ne,duk wanda zai shigo kuma da gift dinsa,suna son yaran kamar su lashesu,akwai cikin ma'aikatansu da kullum a rana sai sun shigo kusan sau uku kawai saboda yaran,tamkar wadanda aka yiwa yayyafin farinjini,ita dai ama ta sani muddin suka dauko farinjinin iyayensu to lallai sai ta hada musu da addu'ar baki. Kwana uku kacal suka sallamesu,har a ranar aman bata sake mata maganarsu ko tayin basu nono ba,hasalima ita da yaran saidai taji muryoyinsu daga nesa,suna qushin qushin din kuka ko wani abu daban. Bata yarda ankai yaran ko ina na,cikin nan dakinsa tasa aka shirya musu gadajensu da komai da komai,komai nasu pink hot pink da baby pink,komai nasu designers ne,hatta da turaren jarirai na kamfanin Dior ta siya masu yawa ta ajjiye. Dukka kayan sawarsu kuwa cotton kaya ne masu kyau qwarai 'yan turkey,channel brand,h&m brand,zara brand,Lacoste fendi Balenciaga da sauran manyan brand. Tanason a san cewa tabbas daga tsatso da ahalin manyan iyali suka fito MAYAK'I FAMILY sannan jinin babbar 'yar kasuwar qasar nijer da kewayenta hamdiyya ABDU ME KANO ne. Tsaf ta shiryasu cikin wasu long sleeve body suit masu kyau da taushi na kamfanin channel,ta nade kowannensu cikin shawl me taushi sannan ta rungumosu kowacce ta kwantar da ita saman gadonta,ta daidaita qarfin AC din dakin,sannan ta fita zuwa kitchen don ta zuba ruwan zafi a flask dinsu ta hada musu madara. NADEEYA ALIYYU MAYAK'I (BENAZEER) FATIMA ALIYYU MAYAK'I (BATOUL) _SAI MUCE BARKANKU DA ISOWA TSAKANIN CAKWAKIYAR DADDY MAINA DA MOMMY SULTANA_😂😂😄*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 25 Ta dade a tsaye gaban madubi daure da towel,ita bata shirya ba ita bata zauna ba,haka kawai takejin zuciyarta wani irin empty,sai tarin karaya da rashin confidence. Sake shafa fuskarta tayi a karo na babu adadi tanason tuna fuskokin yaran,batasan me takeji a kansu ba,soyayya ko qiyayya?,har yanzu bata tantance ba,abu daya ta sani har yanzu tana iya tuna wahalar da tasha a kansu,ko yanzu da take goge jikinta sai data kalli wajen da aka yanka cikin cikinta saboda yaran "Mene makomata?" Tambayar da taketa yawaita yiwa kanta kenan,zata koma nijer ne taci gaba da fuskantar mutane?,taci gaba da fuskantar qawayenta a haka?,da wacce fuskar?,ita sultana me 'ya'ya har guda biyu?,duk da ama ta karbesu,duk da ama tace nata ne amma ta sani hakan bazai canzasu daga sunan 'ya'yanta ba tabbas!. Wanne bigire ta kama?,ina rayuwarta ta fuskanta?,bata sani ba!,bata sani ba sam sam sam......wannan itace amsar da take bawa kanta. Qas tayi da kanta, hawayen da batasan ranar daina zubarsu ba suka fara tsiyaya daga idanunta suna diga saman madubin. Sautin kukansu cikin muryar rigima sosai ita ta sanyata daga kan nata tana duban fuskarta ta cikin mudubin tamkar su din zata gani ta ciki. Idanunta ta maida ta lumshe kukan nasu na isketa har inda take,dukansu su biyun sun dage sai qyaqyata kuka sukeyi. Idanunta ta lumshe,batasan me yasa sam batason jin kukan ba,ta matsa daga gaban madubin,saita samu kanta da jawo babban mayafinta ta lullube dukkan jikinta,sannan ta taka a hankali ta murda qofarta ta fice. Daga dakin ama ne kukan ke fita,ci gaba tayi da nufar dakin amma gabanta yana dukan tara tara,wata zuciyar kuma na hanata zuwan,sai ta kasa dakatawa,har ta isa qofar dakin ta tura ta bude. Kanta ta fara zurawa tana leqensu,ba kowa cikin dakin sai su kadai,sun rude da kuka abinsu suna jejjefa qafa kamar zasu tashi sama "Ya salam ya Allah" ta fada qasa qasa saboda yadda taji zuciyarta na motsuwa. Batayi tunanin komai ba ta sanya kanta cikin dakin,ta taka a hankali zuwa gaban gadajensu. Fes kyawawan fuskokinsu suke,ba hawaye ko wani abu,harararsu tayi tana tura baki gaba,kamar an gaya musu wacece ita,kamar an sanar musu da matsayinta garesu sai kukan nasu yana baya sosai,da kadan da kadan yana ja baya,yayin da duk su biyun suka kafeta da idanunsu. Itama nata idanun ta zube musu, zuciyarta na ayyana mata abubuwa iri daban daban. Banda wahalar da ita daya tasan kalarta da tasha, tabbas da zatace ba yaranta bane. Dan mutum guda guda har guda biyu?. Murmushi ya subuce a saman fuskarta karon farko bayan shudewar watanni d'ai d'ai har kusan wata goma sha daya rabon da ya fita a fuskarta. Miqa musu yatsuntsa tayi d'ai d'ai kowanne ta cusa shi tsakiyar tattausan tafukan hannunsu. Mamaki ya kamata yadda taji caraf kowacce ta riqe suka sakeyin relaxing suna kallonta zaka rantse ba jariran kwanaki kadan bane. "Batoul?, benazeer?" Ta furta qasa qasa tana nuna kowacce da yatsa daidai,tanason ganin ta banbance sunayen kowaccensu?. Kai ta girgiza tana ganin kamar bata fadi dai dai ba,amma ta tuna taji ama tana cewa gefan kunnen babbar akwai alama irinta aliyyu. Wani daci ya ratsa harshenta da tuna sunansa kawai da tayi, qirjinta na quntata ta sanya hannu ta duba gefan fuskokinsu. Taga alamar da ama din ke fada,kuma haka yake,sak irin nashi,tawadar Allah,tasha tambayarsa meye wannan tare da nacin sai ta kankare masa "Nadeeya BENAZEER fatima BATOUL" ta sake maimaitawa kamar me gudun kada ta mance sunan. Sai taji sunan kuwa ya zauna daram a kwanya da zuciyarta. A nutse ama ta maida qofar ta rufe bayan ta gama kallon duk abinda takeyi. Sautin rufe qofar ya sanyata waiwayowa a dan razane gabanta yana faduwa. Ya akayi ta shigo haka ta sakankance ba tare da tunanin ama ko tanja wani cikinsu zai shigo ya ganta ba?. Kauda kai ama tayi sam kamar bata ganta cikin dakin ba,ta fiddo kyawawan feeders dinsu guda biyu ta dora saman bedside table tana nufar gadon nasu tare da fadin "Bansan kun qagu kusha ba,ashe yunwa kukeji my babies" ta fadi tana fara dauko benazeer da kukanta yafi na kowa,sannan ta dauko batoul ta iso dasu gaban gadon. Dole saidai ta fara bawa mutum daya,don tanja ke tayata bawa dayan tanjan kuma yanxu ta fita,don haka ta fara bawa benazeer sai kuma batoul ta fara qushin qushin. Da idanu sultana dake qame take satar kallonsu,shan madarar takeyi yarinyar sosai kamar zata hada da feeder din,da alama me cice sosai "Wai mutum mutumin sultana aka shigomin da shi ne?,zonan ki zauna ki taimakawa batoul idan zaki iya" ama ta fadi tana gyara zamanta. A kunyace a kuma mugun darare ta tako ta zauna. Sau biyu tana miqa hannu zata dauki batoul sai ta fasa "Har yanzu baki sonsu dinne?" Ama ta jefa mata tambayar da ta sanya babu shiri ta dauki BATOUL din ta aza saman cinyarta. Dumin jikin yarinyar ya sauka a dukka cinyoyinta,yarinyar kuma ta sake zuba mata idanu sosai kaman dazu,tamkar tasan yau ne ranar farko da mahaifiyarta ta azata zaman cinyarta,zata kuma shayar da ita da madara bawai da nonon jikinta ba. Dukka yadda taga ama tanayi haka tayi,har sai da ama din tace ta zare ya isa haka,ta basu ruwan zam zam da shine ya ruwam shansu,kuma shi zaici gaba da zama ruwan shansu cewar ama har sai sanda suka buda baki sukace sun gaji dashi muddin tana raye. "Sakata a kafada har sai tayi gyatsa" cikin tsoro ta dagatan ta sakatan,suka shiga shafa bayansu ita da ama din,sai a sannan ama ta magantu "A qalla idan baki sosu ba ko kulawa ki nuna musu,mafi qaranci dai zasu tashi da ganin kallon rahama daga idanun uwarsu.......maraici bashi da dadi,ke baki sanshi bane saboda an baki cikakken kulawa da gata,to kiyi qoqari su dinma koda sun rasa uba susan cewa suna da uwa a raye". Kasa cewa komai sultana tayi sai qas da tayi da kanta,wani abu yana dawainiya da zuciyarta. Sanda ama ta lura batoul din tayi bacci tace ta kwantar da ita,lokacin da zata kwantar da itan kusa da 'yaruwarta ji tayi kamar kada ta kwantar da ita din "zo ki zauna" ama ta sake fada kanta tsaye da daure fuska,daure fuskar da take sanya ma sultana shakkarta da kuma d'ari d'ari. A dararen ta zauna "Ki saki jikinki sosai mana,ki manta ni momynki ce?" Maganar tayi mata dadi sosai,amma sai taji zuciyarta ta raunana,inda ace uwa mahaifiya a gareta tana raye wala'alla zatafi fahimtar duk wani rauni da quncinta ko?. Kamar ama tasan abinda take tunani sai tace "Zuwa yanzu banajin akwai wanda ya fahimceki kamar ni,akwai wanda zaisan ciwonki da zaqinki kamar ni......daga yau inaso sultana ta fara sauyawa,inason na daina ganin wannan sultanar,me musu da taurin kai,inason sassauqar sultana me cewa "eh to" a dukka lamuranta,inaso ki canza zan tallafa miki duk wani ciwo na zuciyarki ya gushe idan kin shirya" kai ta gyadawa ama tana share hawayenta "Na shirya,kiyi haquri ama" ta fadi kuka yana tsinke mata. Cikin jikinta ta rungume sultana din tana rarrashinta. Sai takejin inama komai yazo ne a LOKACIN da ya dace,inama ace aliyyu baiyi gaggawa ba?,saidai idan ta tuns cewa rabonsu batoul......lokacin wanzuwarsu a duniya ne yayi shi yasa komai yazo a gaggauce irin haka,sai taji ta sake sallamawa lamarin ubangiji. Hamdiyya abdu kano,jajirtacciya uwa kuma tsayayya. Itace ta shimfida dukkanin tafukan hannayenta......ta sadaukar da dukkanin dukiyarta........ta bada lokacinta da rayuwarta ma rayuwar SULTANA BATOUL DA BENAZEER.....ta sadaukar musu da dukka komai nata,ta kula da yaran ta kuma kula da uwarsu. Dukkaninsu babu wanda ya samu naqasun kulawarta. Sau tari tanja kan zauna tayi shuruuu..... Eh lallai baka taba gama sanin halin mutum sai ka zauna dashi. Ashe wannan itace hamdiyya wato ama da sukewa kallon me izza,miskila saboda ganin ta mallaki maqudan kudade,wadda bata shiga shirgi ko sharafin kowa,ashe ita din me sadaukarwa ce,ashe ita din me sassauqar zuciya ce?. Kulawa da sultana kusan itace ta kwashe mafi yawancin lokutanta. Fitness center ta kaita me kyau da suke bawa jikin sultana kulawa cikin kula da CS dinta ba tare da ya samu matsala ba,tanason sultanan ta koma sultana dinta,harma tafi da,tunda zuwa yanzun idan ka ganta zaka tsammaci ta shiga shekara ta sha bakwai ne bawai sha hudu ba. A gida kuwa lafiyayyun abinci da dukka nau'in ganye da tasan zai maida sultana mutum,ya murje mata jiki kullum cikin research da hade hadensu take,ruwan ganyen gwanda daya zamewa ama aboki a baya yanzun ta tilastawa sultana shanshi sau biyu a rana(yana hada nuna tsufa,yana maintaining jiki,kiyi looking younger akan shekarunki)daya daga cikin sirrikanta da take taqama dasu. Sannu a hankali saiga sultana ta fara dawowa SULTANAN BIBI DA ABA,fatarta ta fara ninka kyanta,duk wata rama tata tana yin nata waje,komai yana komawa kan saitinsa. Tun usul dama damammen ciki gareta,don haka ko yanzunma ba zace ta taba daukan ciki a cikinta ba, stretch marks ne yaso fito mata dan kadan a fatar cikinta ama tace bataga ta zama ba. Kudi ta zuba sosai ta siya mata mayuka masu kyau da dan Karen tsadar da ko a can dimma saika ciza sannan zaka siya,sai gashi sun bace bat,babu su babu alamunsu,tunda dama bana halitt bane na ciki ne. Gyaran kai, manicure da pedicure akai akai,so take ta koma sultana cikakkiyar 'yar gayu,cikin kwana talatin da biyar cif da haihuwar sai gata ta canza,ba zakace itace me jego ba. Wani irin girma yaran sukeyi tamkar ba madara suke sha ba,wani irin wayo kai zaka ce sun doshi watanni uku ma. Bul bul dasu kamar ana hurasu, weather din Austria tamkar don saboda su aka halicceta. Wayo na masifa a cikinsu,sunsan idanun ama sunsan na tanja,don na sultana bai fiya ganuwa a garesu ba. Bata kyararsu,amma ba kasafai take shiga shirginsu ba,idan suna kuka dai takan daukesu idan ama bata wajen,amma indai tana wajen saidai ita ta dauka ko tanja. Cikin kwanakin talatin da biyar din taji dukka hankalinta ya fara komawa gida. Ta yita duba saqonninta na layinta da email ko zata ga saqon sakinta daga hamid(aba) duk da tasan abune me wuya amma bata gani ba,sai saqon roqon ta dawo ta email dinta har babu adadi daga aba,saddi atta harma da almu. Visa kawai ta shiga nema musu,tana ganin zuwa yanzu lokaci yayi da zasu koma. A yanzun zata koma da dukka qarfinta ne,zata sanya auduga ta toshe kunnuwanta,ta sanya duk wani effort nata ta nema inda maina yake,tana da buqatar danta,ba don komai ba kodon yaran da ya dasa baisan da wanzuwarsu ba,ya kamata su tashi da dumin ubansu. Ba zata sanya kowa neman maina ba,ita daya zata fuskanci komai,ita daya zatayi fadi tashinta,yadda suka dauki zafi dashi saidai suga dawowarsa gida......amma kuma hakan ba yana nufin itama ba zata hukuntashi ba bisa laifinsa,amma hukunci ta hanyar da ya dace. Sultana batace komai ba bayan ama ta miqa mata passport dinta dake dauke da visa din Nigeria. Ta danji sassaucin ganin qasar nigeria zasu fara shiga,kwata kwata nijer ta fita a kanta, batasan ma ta yaya zata fuskanci rayuwa ba a can. Zaman gida zatayi tayi rainon yara?,ko makaranta zata koma cikin qawayenta da a yanzu ita kanta tasan tabbas ta banbanta dasu?,dukka dai bata sani ba. ********Sun baro Austria cikin matuqar kewa, Vienna garin da suka shuka tarihi a ciki suka kuma binne,sun fito da benazeer da batoul da a yanzun suke da shaidar zama cikakkun 'yan qasar Austria halak malak,wanda sanadin haihuwarsu qasar ya basu wannan damar. Transit ne na kwana guda a Egypt cairo,sun sauke luggage dinsu a gajiye,amma ama tace su shirya su fita su zagaya,akwai guraren tarihi me kyau da yake da kyau suje din. Tanja na murna ta gama shirinta,ta kamawa ama shirya su benazeer daketa wutsil wutsil abinsu,kamar sunsan suna kan hanyar komawa qasarsu ne.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 26 Sanda ama ta fito sultana na zaune ta saka tv a gaba tana kallon news,wanda ama tayi imani ba wani fahimtar me akeyi takeyi ba,kawai tsabar zama miskilar qarfi da yaji da tayi ne duk ta koma haka,bata doguwar magana bare doguwar hira,dukka kalmominta taqaitatattu ne "Baki shirya ba sultana,ya kamata muje mu dawo da wuri mu kwanta don mu samu gobe mu tashi da wuri,jirgi baya jira" ama ta fadi tana taje doguwar sumarta "Ama na gaji,saikun dawo" waiwayawa tayi ta dubeta "Ahaaa?......kina da tabbacin sake samun dama irin haka?,baki da tabbas zaki sake ratsa qasarnan,oya tashi ki shirya" ta fadi tana dan dakewa. Tsam sultana din ta tashi,ama ta bita da kallo har ta shige bandaki. Sanda ta fito cikin ido sai ama taga tayi mata kyau ainun. Cikin doguwar rigar Dubai,tayi rolling kaman yadda ta saba shekarun baya. Ta cika tayi tsaf tamkar babu wani abu dake damunta. Yawo sukayi sosai gidajen tarihin dake cairo,sannu a hankali sai ta dinga jin zuciyarta na sakewa,damuwarta dake cunkushe a qirjinta tana raguwa sosai. Saidai duk inda duka gifta sai an tanka benazeer da batoul,abinda ya sanya dole ama ta sake lullubesu da kyau. Koda suka shiga daya bangaren na kayan tarihi sai ama ta miqawa sultana batoul. Waiwayawa tayi ta dubi ama din,sai kuma ta sanya hannunta ta karbi yarinyar ta rungumeta a kafada. Ajiyar zuciya ta saki a boye,wani abu taji ya zarta ta jininta sanda dumin jikin yarinyar dake cakude da daddadan qamshin turaren Dior ya sauka a hancinta. Sau tari cikin zuciyarta takanji yaran suna burgeta,irin burgewa da kake iyaji ga yaran da suke ba naka ba ko kake ganinsu daga nesa. Tun daga ranar da suka iso duniya cikin ado suke da kwalliya,koda a gida suke babu inda zasu fita to tabbas adonsu na dabanne,hatta kayan bacci idan ka gansu a cikinsu saisun dauki hankalinka. A asirce tanja ta saki murmushi tana kauda kai,wato dai so sone amma son kai yafi. Tuni ta lura da abinda ya sanya ama ta maqalawa sultana batoul,idanuwa ne sukayi yawa akan sultanar,duk da cewa ba wani sakewa a tattare da yanayinta ko fuskarta,amma ta fuskanci tana ta fusgar hankulan mazaje dake wajen. Duk inda ama taga wulgawar kayan yara saita saiwa su benazeer,kayan qyale qyale masu yawa,su kadai take tunawa,komai ta siya nasu ne. Sai cikin dare suka koma gida a gajiye,duk da haka ama bata gaji ba sai sata wanke yaran tsaf,nan suka shiga baccin gajiya. **********K'arfe daya na rana dai dai motar mallakin hajiya hamdiyya abdu me kano ke shiga makekiyar harabar gidanta dake garin abuja. Dukkansu ita da sultanan ba wanda bai saukar da boyayyar ajiyar zuciya ba. Kafatanin masu aikinta maza da mata dukkansu suna tsaitsaye a harabar gidan domin yi mata barka da isowa. Sanda motar ta tsaya bakin motar sukayo,kowanne zuciyarsa fal farinciki da annashuwa,tsoro da fargabar data mamayesu na bacewarta tsahon watanni tuni suka bar zukatansu daga jiya data shaida musu isowarta,tare da isowar ma'aikata sukayi musayen furniture na gidan,suka kuma shirya lafiyayyen daki wa benazeer da batoul. Bilki ce ta karbi batoul,uwa ta karbi benazeer kowa bakinsa fadi yake "Masha Allahu,ma sha Allah,barka da arziqi sultana" a lokacin da sultanan ke fitowa daga motar cikin wata baqar doguwar riga me azabar sulbi da daukan idanu. Fatarta da jikinta dukka sunyi kyau,ta dan murje,saidai qiba ce har yanzu babu ita ba dalilinta,ta zama slimy. A hankali idanun ama suka sauka kan baqin motoci da take gani a rumfar gidan,sai ta maida dubanta ga tasi'u "Malam Tasiu wadannan motocin fa?" A ladabce ya rusuna yana cewa "Yallabai ne suka zo shi da hajja bibi,yau kinsan ake bikin bude kamfaninsa na nan abuja" kai kawai ta gyada,ta san da company din,wanda ya dauki shekara da shekaru yana gininsa tare da tanadin ranar budesa,tabbatuwar kamfanin kuma zai iya sanyawa zamansu yafi yawa a Nigeria ne garin abuja saboda yawan hada hadar da a kullum aba din zai dinga gudanarwa. Ciki dukkansu suka dunguma,tana jinsu bilki sun barke da hira da tanja hirar yaushe gamo?,sunata kwasar tanjar wai ta sauya quruciyarta ta dawo,itakam sai dariya kawai take musu. Dukkan wani abu da zaiyi cikin watannin da sultana da ama sukayi baton dabo yana yinsu ne tuquru don wanke duk wani ciwo da radadi na batan sultana a zuciyar bibi. Ko a yanzun da duke dawowa su biyu rak cikin motar bayan ya karbi tuqin daga hannun driver dinsa ajiyar zuciya ta saki "Har yanzu hamidou zuciyata ta kasa nutsuwa,har yanzu ina ganin cewa nice silar faruwar komai,inda nasan sultana na buqatar cikin,inda nasan da gaske hamdiyya take tana da buqatarsa itama,da na ajjiye nufi na,ba hamdiyya ba sultana..... shima maina tunda ya tafi....." "Ki ajjiye batun maina,ba mune mukayi masa laifi ba,shi yayi mana laifi,sannan ya zabi tafiya ya barmu,koda kasheta yayi a yanayin da ya barta bashi da asara" ya furta maganar yana ciro wayarsa da yaji alamun kira ya shigo. Baikai ga daga wayar ba kiran ya katse,sai text din hamdiyya da ya shigo kusan awanni biyu baya,rububin taro ya sanya bai gani ba sai yanzun da ya samu ya sullubewa jama'a yayi bad da bami a mota daya ya taho gida kawo bibi ta hut sannan ya koma. Hannunsa har rawa yake sanda ya karanta layi guda kacal na saqon,ita dai bibi batasan me yake faruwa ba,taga dai ya qarawa motar uban gudu bayan ya aje wayar da hanzari a gefensa "Lafiya hamidou?" Bibi ta tambayeshi tana dubansa "Hamdiyya ce ta dawo,ina kyautata zaton suna nan cikin abuja" ya bata amsa yana sake bakwa kwalta hankalinsa sosai. Idanu bibi ta fidda cikin wani mugun zumudi da ba zata "Hamdiyya?,ita da sultanan?" "Eh na tabbatar tare suke" ya amsa mata yana sake qara tsula gudu abinda sam ba al'adarsa ba "Allahu qadiran Ala man yasha'u" bibin ta furta hankalinta yana daguwa,jinta takeyi kamar tayi tsuntsuwa ta isa gidan,sai kawai tayi luf jikin kujera tana kiran sunayen Allah a jejjere. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 27 "a hankali bibi" aba ya fada lokacin da yake tsaida motar tasa bibi na qoqarin budewa ta sauka. Ai bata saurareshi ba sai data tabbatar qafafunta sun taka qasa. Da sauri ya fita a motar yabi bayanta,yasan tana da ciwon qafafu,a yadda kuma take gaggawar kaiwa ga sultana yana gudun kada ta sarqe. Dukka muryarta ta ware tana doka sallama kamar baquwar gidan,ta daburce gaba daya,saboda batasan ta inda zata fara ganin sultana ba. Tana shirin shiga wanka taji kamar muryar bibinta,kamar muryar da kullum take mafarkin ji,sai kawai ta jawo babban mayafi ta yafa a kanta tana nufar qofar fita. Qarar bude qofar ya sanya bibi maida kallonta gurin,sultanarta ce,itama sultanan bibin take kallo,kallo kallon suka hau yiwa juna kamar wasu baqin juna,sai kuma daga bisani sultana din ta nufo bibi cikin sassarfa tana kiran sunanta da rawar murya. Jikin bibi ta fada bibi din ta maida hannayenta ta rufeta gam "Sultana?" Itama bibin ta dinga maimaitawa tana jin wani irin abu cikin zuciyarta,abinda ya karyar da zuciyartata kenan hawaye masu sanyi suka saukar mata. "Bibi" itama ta sake maimaitawa kowannensu hawaye yana fita a idanunsa. Da kyau bibi ta riqeta suka qarasa saman kujera,sai kawai sultana din ta kifa kanta saman kafadarta tana sakin sabon kukan. Ya zata iya kwatantawa bibi abubuwan data fuskanta?,baki bazai iya bayyanawa ba, gwagwarmayar data ratsa har ta kawo yau din ita kadai tasan abinda taji,ba mahalukin da zai iya fuskantarta,wannan din wani abune da yake tsakanin zuciya ruhi da kuma gangar jiki ne kawai. Kasa cewa komai da ita bibi tayi,sai sharar hawayen itama da takeyi aba yana tsaye a kansu yana basu baki,saidai fiye da rabin hankalinsa shima yana tsakanin falon da kuma qofofin da falon ke dauke dashi,yana son ganin ta inda ama zata bullo. Dukkaninsu taga shigowarsu ta cctv camera din dake hade da system din gefan gadonta,amma bata motsa ba,sai data kammala shirya yaran tsaf bayan ta musu wanka,ta nadesu cikin overall set da wasu irin huluna masu kyau da suka boye tattausan sumarsu me azabar baqi da sulbi,fuskokinsu sun fita tarwai da wani irin haiba da annuri. Nannadesu tayi cikin tausasan shawl sannna ta sanyasu a kafadarta hagu da dama,ta zura slippers dinta ta taka zuwa hanyar fita. Duk da cewa takunta baya bada wani sauti amma sai fitowarta din taja hankalin bibi da aba tamkar wadanda aka jonawa mayen qarfe. Kasa miqewa bibi tayi,daga ita har aba bin ama sukayi da kallo har zuwa sanda ta qaraso ainihin cikin falon da sallama a bakinta. Wuce aba tayi kaman ma bata ganshi ba,ta isa gaban bibi a nutse ta sauke yaran daga kafadarta tana kwantar dasu a gaban ama tana jeresu daya kusa da dayar,sannan ta miqa hannunta tana yaye shawls din da suka lullube fuskokinsu. Dukkaninsu suka kai idanunsu kan yaran,tamkar an jona musu shock haka sukaji cikin jikinsu "Subhanallahi wabi hamdihi, subhanallahil azeem" bakin aba ya furta yana tasowa da gaggawa daga tsaiwar da yayi daga jikin bango. Gaban yaran ya qaraso ya zube,yasa hannu ya tallafawa bibi da hannuwanta ke rawa tana son karbar yaran,ya dauki benazeer ya dora mata ita saman cinyarta. "Ya Allahu,ya assamadu" shine abinda take maimaitawa tana juya yaran qwalla na sauko mata "Astagfirullah, astagfirullah....." Ta sake maimaitawa tana jin qirjinta na mata nauyi,har cikin jini da zuciyarta takejin wani irin nauyin ubangiji,har ruhinta takejin wata irin kunya tana saukar mata,yanzu wadannan halittun da taso a murqushe?, yanzu wadannan ruhin taso a niqeshi yabi rariya?. "Allah na tuba,Allah ka yafemin,Allah kada ka barmu da soye soyen zukatanmu" ta dinga maimaitawa hawayenta yana qara yawa Hannu ta miqa tana shafa fuskokin yaran,idanuwanta a kansu tana sake tsarkake girman zatin Allah. "Ga jikokinku nan,kuma 'ya'yan jikoki,wadanda kukaso gushewar rayuwarsu kafin isowarsu duniya,nayi dukkan abinda nakega ya dace nayi,ga sultana nan na dawo muku da ita,yaran kuma zan riqesu,Allah ya rayaminsu" ama ta fadi hawaye yana cika idanunta taf ta sanya tafin hannunta tana sharewa "Inaaa hamdiyya,kece kika cancanci mu bawa haquri,kece kika cancanci wannan yabon,abinda ya kamata tunaninmu yakai kai ya gaza kaiwa kece naki tunanin yakai,kika fiddamu daga halaka zuwa hanyar tsira,inda ace na aikata abinda son zuciyata ya gayamin a sannan tabbas da zuwa yanzu ina cikin fushin Allah,ku yafemin 'ya'yannan da naso kasheku tun baku shaqi iskar duniya ba" bibi ta fadi tana sake kuka. Iya yadda bibi ta rame kadai ya isa ya gayama ama ba qaramin tashin hankali take ciki akan tafiyarsu ba. Cikin zuciyarta wani abu ya darsu me kama da tausayin bibi cikin ranta "Zo nan hamdiyya,yaki" Bibi ta furta tana miqawa ama hannu. A nutse ta qarasa gaban bibin,ta tsugunna,har a yanzun tana jinta a matsayin suruka,kuma har yanzu babu abinda ya sauya. Ta sani dukkan wata zuciya cike take da son rai,saidai idan Allah ya baka ikon fin qarfin zuciyar taka. "Allah yayi miki albarka,kiyi afuwa a gareni" bibi ta fadi tana dafa hannuwan ama. Qas tayi da kanta tana jin nauyin bibi din "Ya wuce bibi,ya wuce har abada" "Na gode hamdiyya" ta sake fadi tana sake duban fuskar yaran daya bayan daya,tare da tunanin da waye sukayi kama "Wanne suna kika basu?" Bibi tayi tambayar sanda ama ke tashi ta zauna sosai saman kujera kamar yadda bibi ta buqata a tare da ita "Nadeeya BENAZEER da Fatima BATOUL" a nutse aba ya daga kai ya dubeta karo na biyu yana jin kimarta na daduwa cikin ransa,yayi tsammanin zatayi zuciya ne,ta saka sunanta da kuma sunan duk wanda taga dama,sai gashi ta watsa komai a baya,ta sanya musu sunayen mutanen da suka kasance tsani na samuwarsu. A hankali aba yakai bakinsa kunnen kowaccensu yayi mata addu'a,ya sauke batoul a nutse saman cinyar ama sanda ta fara mutsu mutsu yana miqewa idanunsa suna satar kallon ama. Ya sani akwai zantuka da yawa wadanda a yanzun ba zasu fadu ba,ba kuma zasu yiwu a tattauna ba,zai jira lokacin da ya dace. Ta sani abinci suke da buqata a yanzun,don tunda suka taho daga Egypt bacci sukeyi abinsu basu buqaci madara ba,sai ama ta juya tana kallon tanja data rabe tana jin nauyi nauyin ama "A sama musu ruwan zafi zan hada musu madara" dubanta bibi tayi "Madara kaman yaya hamdiyya?,ko zasusha madara nono ai ya kamata a fara basu ko tukunna,idan basu qoshi ba saisu qara da madarar" Ama bata dubi bibi ba tace "Madarar sukesha,itace abincinsu" ta maidawa bibi amsa tana gyarawa benazeer kwanciya. "Ina nonon uwarsu?" Maganar ta zowa sultana a bazata saboda ta tsammaci bibi zata bar maganar ne,sai gashi kuma ya jefo da wata tambayar. Waiwayawa bibin tayi tana duban sultana,a hankali sultana din ta jawo gaban mayafin jikinta tana sake suturce qirjinta da bibi ke kalla "Hamdiyya kada dai kicemin hanasu nono tayi" bibin ta fada da wani irin zafi a muryarta abun yana tabata. Kai ama ta girgiza "A'ah,kawai dai bata taba gwadawa bane" "To yau kuwa zata gwada yau dinnan" bibi ta furta da gaske tana zunkudawa gaba. Dukka idanunta sultana ta fidda waje tana zarosu,nonon nata za'a zuqa kuma?,tashin hankali. "Aje a nemo min wannan maganin duk inda yake a garin abuja,a fiddo da dukka bournvita din dake gidan nan da madara,daga yau zuwa safiya nakeso ruwan nono yazo yara su kama abinsu" sosai sultana ta sake gwalalo ido gabanta yana faduwa "Da kin bari bibi,tunda sun riga sun saba da wannan ai..... Bakiga kuma yadda ya karbesu ba?" Ama fada tana tana fuskar bintou "Kinga hamdiyya ki daina bata bakinki,darajar nonon uwa daban da madarar bature,kinsan Allah?, billahillazi daga yau su da madara saidai a matsayin ciko" kuka sultana ta saki tsoro yana kamata,yanzun ace nononta zasu tsotsa?, fisabilillahi har mutum biyu?,ta ina?. "Don Allah bibi kiyi haquri" "Yo ai bansan baki da imani ba,haba sultana,kece za'a ce kiyi haquri dai,don nono kaman sun shashi sun gama" idanu sultanan ta wuwwulga a falon,ba wani sauran me cetonta,aba ne ya rage dama,shi kuma tunda aka fara batun shayarwar ya fice. Duk irin kukan da sultana keyi saboda tsananin tsoron shayarwar bai damu bibi ba,nan ta gwaggwafe hada wannan tsuma wancan,zuwa safiya sai ga nono yazo. Bibi da kanta ta taka ta amso benazeer da batoul daga wajen ama,wadda tuni tayi musu wanka ta shiryasu tsaf sunata tashin qamshi sai tsotsar baki suke,da alama dama a yunwace suke. Qin bin bibi ama tayi kada tausayin sultana ya mata tasiri ta hana abinda ita kanta tasan shine dai dai,abinda ya sanya bata taba tilastata ta basu din ba alqawarin hakan ta yiwa kanta,kuma bata fatan hakan ya haifar mata da wani raunin cikin zuciya,ko taga kaman aman tana biyewa soye soyen zuciyarta ne tunda ita din bataso,biyayya kawai takeyi.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 28 Idanunta fal ruwan hawaye take kallon bibi sanda ta fara aza mata benazeer akan cinya "Don Allah bibi,wallahi zafi zanji na sani,bazan iya basu ba" "Zaki koya ne,kowa ma ai da haka yake koya" bibin ta fadi tana hade rai babu alamun wasa saman fuskarta "Yalla, fito dashi ki basu ko nazo da kaina na basu,an baki shine don kiyi ado dashi a qirjinki dama?,fito dashi" bibin ta fada cikin fada da tsawa. Hannu ta saka tanason cirosu,amma rashin sabo ma ya sanya ta kasa yadda zata fiddosu din "Bari dai kiga" bibi tace tana motsawa kusa da ita. Kuka ta saki sanda benazeer ta cafki maman ta fara tsotso kaman dama ta saba. Idanun yarinyar qur kan fuskar sultana kaman tasan ba da son ranta take bata maman ba. Tasha kuwa sosai,bibi ta dauketa ta saka batoul itama ta kama guda daya. Kafin su gama hawaye shabe shabe akan fuskar sultana "Yauwa to ma sha Allah" bibi ta furta tana daga yaran. Sai yanzu zuciyarta ta samu nutsuwa,ta sanya batoul a kafada tayi gyatsa sannan ta saka benazeer. A nan saman gadon sultana din ta kwantar dasu,tanayi tana qananun mitoci,abun ya qonawa sultana rai sosai,yanzun kenan ko damuwa da damuwarta bibi ta daina?,bibi da bata barinta tayi kuka yau itake kallonta tana kuka amma bata ko dubeta ba bare ta lallasheta?. Bibi na fita ya tura qofar dakin ya shiga da sallama. Tana tsaye bakin mirror tana daura towel,tanason shiga tayi wanka tunda ta samu bibi ta dauki yaran kafin ta dawo mata dasu. Sau daya ta juyo ta kalleshi ta dauke kai tana ci gaba da abinda takeyi din. Ya taka ya matsa gabanta yana dubanta "Hamdiyya" ya kirayeta qasa qasa "Na'am" ta amsa masa ba tare data juyo ba,sai kuma shuru ya biyo baya A nutse ya qaraso,ya jingina ta a jikinsa ta baya "Har yanzu kina fushi ne?,kin daina ta tawa gaba daya sai ta jikokinki?" Bata dai waiwayo din ba ta bashi amsa "Fushin me zanyi?, bayan nina muku laifi?,amma aina wanke kaina ko?,tunda ga diyarku nan na dawo muku da ita ban gutsireta ba" "Ya isa" ya fada cikin son katse zancan,don gaba daya bayason ana maimaita maganar. Hannunta ya kama ya zaunar da ita sannan ya zauna a gabanta "Haqiqa kinyi abu me kyau,kinyi abinda kika cancanci a yaba miki da kika tseratar da Bibi daga rudani da kuma fadama nadama,na gode miki qwarai,kuma ina fata zaki yafemin bisa duka kusakurai na" ta tsammaci zaya sako zancan maina amma sai taji bai sako din ba,ya zuwa sannan zuciyarta ta qeqashe da takejin bata buqatar taimakon kowa sai nata ita d'ai,don haka itama bata tada masa zancan komai ba. Cikin kwanakin gaba daya tare da Bibi ake rainon yaran,sam sam ta hana a basu madara sai nono. Sultanan tayi kuka tayi kuka har idanunta ya dinga motsawa me ciwon amma hakan baisa bibi ta janye ba,duk sanda za'a basu nonon bibi ke tsaiwa a kanta saita tabbatar sun sha sun qoshi. Gaba daya jin abun take banbarakwai,abubuwan da take boyansu,abubuwan da take adonsu yau sun zama abebaden shan wadansu. Amma kuma abun mamakin da yaran sun kama sun fara sha sai taji zafin da takeji cikin zuciyarta yana sauka a hankali. Wadansu irin yara ne,masu tarin wayo da wani irin farinjini da kwarjini da Allah ya zuba musu. Idan kana kallon fuskarsu ba zakaso ka daina ba,sun iya kallon mutum kamar sun sanshi ,bibi takance "Wannan wayon da abinku aka haifeku,so kuke ma kufi uwarku wayo". Kwanansu uku kacal da dawowa saiga tawagar family din MAYAK'I sun iso. Kusan kaf kowa na gidan ba wanda aka bari acan. Duk wanda ya daga yaran sai yayi kamar bazai ajjiye ba. Sultana na daki kwance jikinta a mugun mace,ta kasa zama cikinsu,ta kuma kasa hada idanu da kowa,jinta take kamar bare a cikinsu,a dakin su aminata suka cimmata suna santin yaran "Wallahi kaman ba kece mamarsu ba sultana,don Allah ki barmuna su kawai" kanta ta juyar wani sashen tana cewa "Ku daukesu kawai na baku" dariya sosai yasmine ta saki "Wallahi qarya kike,wai ke irin bakiso dinnan,wa zai samu yarannan yace baiso?,ko ke bakiso na tabbatar yaa maina yana son kayanshi" a wani irin fusace ta juyo da fuskar nata data kawar dazu tana kallon yasmine. Ambatar sunansa kawai dai dai yake da kira mata uwa uba da duk wani da take gani da kima a mazaunin mahaifi ka zageshi. Tashi tayi ta zauna sosai daga kwanciyar da tayi dazun tana duban yasmine "Kada ki sake ki qara kiramin sunanshi a nan wajen yasmine,don ba wajen kiran sunansa bane nan din" tayi maganar kanta tsaye,idanunta na bayyana abinda ke danqare kai tsaye a zuciyarta. Sanyi jikin yasmine da aminata yayi,suka kalli juna,sai yasmine din ta koma ta zauna daga gefanta "Kiyi haquri,mantawa nayi,amma sultana.....baki tunanin a tsahon wannan lokacin ma a ina yake?,kina da tabbacin kawo yanzu yana raye ko ya mutu?,kinsan yaa maina....." "Yasmine ya isa da Allah....." Sultana ta fadi tana sanya yatsunta cikin kunnuwanta,da gaske take,batason jin komai da ya danganceshi,bata qaunar ambatar sunansa a gabanta. Ama ce ta bude qofar dai dai maganar yasmine na qarshe data kirayi sunan maina. Taji komai ta kuma ga komai,sai ta saki qofar ta tako a hankali tana shigowa ciki "Yasmine,kuje kuci abinci an kammala" miqewa sukayi dukansu,daya bayan daya suka fice a dakin,sai a sannan ama ta dawo da kallonta ga sultana. Takawa tayi a hankali,ta sanya sannu ta zare hannuwan sultanar daga kunnenta. A nutse ta soma warware idanun nata ta saukesu a fuskar ama. Taga gaskiya muraran saman fuskar sultanar na iya girman tsanar data yiwa mainan,ta kuma tabbatar da gasken gaske take,don daga fuskarta har cikin idanunta sun canza launi zuwa ja. Murmushi ama ta sake mata tana hadiye wani dunqulallen abu da ya tsaya mata a wuya. Habar sultanar ta dan riqe "Karki sake damuwa,ba wanda zaya sake miki maganarsa,an rufe babinsa kinji?,tashi kiyi joining 'yanuwanki kici abinci kema,ki sake a cikinsu,mutum kike kamar kowa,idan kina ganin abinda ya farun kamar ya rage daraja ko martabarki sam sam ba haka bane,a yanzunne ma kima da darajarki ta dagu,saboda kowa na miki kallon me hankali ne a yanzun,kina da abinda kaf 'ya'yan jikoki babu me shi sai ke,tashi kije". Da irin wadannan kalaman ama ta samu ta dinga rage mata kaifin abinda takeji cikin zuciyarta,ta dan sake dasu aminata tamkar suna gida tsahon kwanaki ukun da sukayi. *********Misalin bakwai da rabi na safiyar ranar lahadin,cikin gidan ama dake garin abuja,babban gid daya ginu ainun da wani irin tsari da kai tsaye idan ka kirashi da MANSION HOUSE bakayi kuskure ba. Cikin faffadan dakin da ya zama masaukinsu najma aminata da yasmine,dukkansu a zaune suke kaman ba safiya ba,saboda shirin komawa nijer da sukeyi a yau din. Najma tayi wanka,aminata na zaune tana jiran yasmine ta fito ta shiga,sultana dake zaune saman sofa gab da aminata,sanye da wata rigar bacci me taushi me gajeran hannu da iyakar tsahonta gwiwa tana kallonsu kawai. Jifa jifa aminata na sanyata a hirartasu,gaba daya amsarta bata wuce daya zuwa biyu idan tayi nisa uku. Sake kallonta aminata tayi,can qasan ranta tana mamakin sauyawar sultanar,a duniya duka idan akace mata wani lokaci zaizo da sultana zata zama miskila to tabbas zata musanta,musu kuma me tsanani,sai gashi dare daya sultanar ta tashi daga ainihin sultana ta zama wani abu daban. Sultana da a baya ko fada kakeyi da ita ta sanyaka kuka badai kai ka sakata kuka ba..... sultana da a baya idan ta fannin magana ne saidai ta cinyeka badai kai ka cinyeta ba.......saidai ka haqura kayi shuru ka barta......... saidai ka gaji kayi shuru badai ita ta gajiya ba.......yau sultana ce magana ke mata wuya,murmushi ya zama wani kayan gabas a wajenta "Don Allah sultee......ki canza please,wannan sabon halin naki nikam baiyimin ba,kuma bayamin dadi" aminata ta fada tana bata fuska. Fararen idanunta kawai ta daga ta kalli aminata din sai ta maidasu ta lumshe. Aminatan ba zata taba ganewa ba,ba zata taba fahimtar what she goes through ba......a yanzun a cikin ruhinta itama jinta takeyi kaman ba sultana ba. Kafin tace komai bibi ta shigo dakin,rungume take da wasu sabbin atamfofi wanda duk zuwa Nigeria sai an sayesu an tafi dasu,ayita ajiyarsu saboda tashin wata hidima ko kuma dinkin yaran gidan. Kusan al'ada ce da maina ya kafa saboda yadda ya tsani yawan ta'ammali da English wears da su sukeyi wanda ba komai bane kusan al'adarsu. Ama ke biye da ita dauke da wasu kayan masu yawa itama data ware zata rabawa su najma,kayayyaki ne da tasan suna qanfarsu a can. Turus bibi tayi tana dan duban sultana "Ya na ganki zaune kowa yana shiryawa?,bakisan tare zamu koma ba?,tunda shi hamidou komawarsu ba yanzun ba?" Idanu ta daga ta kalli bibi,sai kuma ta maida dubanta ga ama kafin ta janye duban nata idanun nata na cika da hawaye duk da basukai ga zubowa ba. Sam batajin zata iya komawa cikin qasar nijer taci gaba da rayuwa,a yanzun bata sha'awar hakan sam sam sam. Da wanne ido zata kalli jama'ar data sani a baya?,da wanne ido zata kalli mutane?,tace musu me?,batajin tana da rufin asirin da ya wuce mata rayuwa yanzu cikin Nigeria "Zan zauna a nan ne,bazan biku ba" qarasawa bibi tayi ta zube kayan hannunta baki bude tana duban sultana "Kamar yaya?,saboda me?" Hannu ta sanya ta dauke siririyar qwallar data ziraro mata "Nafiso nan, nafison na zauna a nan kawai,ki barni a nan don Allah bibi" ta qarashe fadi muryarta tana rawa. Baki buden bibi ta waiwaya tana duban ama,sai aman ta dagawa bibi hannu sannan ta tako kusa dasu "Tunda hakan takeso kiyi haquri bibi ki barta a nan din,in sha Allah zanci gaba da kula da ita,zan kuma riqe amanarki,duk lokacin da taji zata iya komawa can din,zan shiryata na maida miki ita har gida in sha Allah" zama bibi tayi tana duban ama "Yo na tafi a cuci wadannan bayin Allahn?,kina gani da idona ma ba wani nonon arziqi suke samu ba?" Da sauri ta dago kai tana duban bibi. Kaji wani sharri irin na bibi(sultana ta fadi a ranta),tun bayan abunma ba'a taba takurawa rayuwarta ba yadda bibin ke takura mata. Cikin dare zataje ta debo yaran,ta tasheta a bacci,haka zasu kwana jikinta,wani lokacin haka zata kwana tashinta wai ta basu nono,wani lokacin idan abun ya isheta saidai kawai ta sake mata kuka,ta maidata kamar wata saniya,amma yanzun cewa take ba nonon arziqi suke samu ba?. Murmushi ama ta saki me sanyi,makauniyar qaunar da taga bibi na yiwa yaran mamaki take bata,yadda yaran suke da saurin shiga zukatan mutane ta sani wani abune kawai daga Allah "Duk hakan ba zata faru ba in sha Allah,na miki alqawarin zan kula" "Idan naga sabanin haka,ko nazo naga yaran nan sun zube fa ba zanwa kowa ta dadi ba" bibin ta fadi cikin salon mita "Ba za'a yi hakan ba in sha Allah" ama ta sake tabbatarwa bibi. A ranar dukkansu suka tarkata suka wuce,sai gidan ya zamana daga ama sai tanja da Bibi tace ta barwa aman ta tayata kula da 'yan biyu duk da gidan akwai ma'aikata sosai,sai aba sai kuma sultanan. *********** Watansu hudu amma sunyi kubul kubul dasu kamar ana hurasu,ga nauyi da suka sakeyi saboda isashen nono da suke samu,tun sultanan najin wani banbarakwai idan tana shayar dasu,har ya zame mata tamkar wata hanya guda daya da zata samu kusanci da yaran,ta kuma qare musu kallo yadda take buqata,don bata wani sakewa ko cikakken kallo tayi musu gaban mutane koda kuwa ama ce.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 29 *_BAYAN SHEKARA DAYA_* K'awataccen falo ne da aka qawatashi da wasu irin resting chairs masu azabar kyau. Ba wani tarkace me yawa aka zubawa falon ba,kasancewar an yishi ne kawai domin hutawar baya buqatar tarin wasu tarkace masu yawa. Malale yake da carfet lallausa me kyau,sai wasu irin curtains da aka qawata bagunan gilasai manya na falon dasu. Daga can sashe daya na falon take zaune,sultana ce sanye d wani yadi me taushi ruwan madara da aka yiwa qawataccen dinkin sakakkiyar doguwar riga. Ta nade kanta da mayafin kayan me sauqin nauyi,daurin da tayishi ta yishi ne simple saboda kada tabar kan nata haka,amma sai ya zamana kamar ado a kanta ya zaina daras ya kuma boye tarin sassalkar sumar kanta. Game ce a hannunta take bugawa wadda ta zame mata abokiyar zama a duk lokacin da take da buqatar kadaici. . Tunda ama ta karanci hakan sai ya zamana bata da aiki sai siya mata games kala kala. wata guda baya ta cire benazeer da batoul daga nono. Ama bata hanata ba,saboda a shekara dayan da watanni yaran sun zama barden goyo,sun zama wasu dima diman da zakayi tsammanin sunyi shekara bibbiyu ne. A hankali ta cira kanta tana kallon saitin qofa inda ta jiyo ihun benazeer daga farfajiyar gidan. Kamar ta maida kanta saboda tasan zallar rigima ce da suka saba yi ita da batoul amma kuma sai ta kasa saboda qara sautinta da benazeer din keyi. Zame game din tayi ta ajjiye,ta sauke qafafunta qasa tana gyara daurin scarf dinta da santsin sumarta ya sanyashi sauka,ta tako a da dan hanzarinta zuwa wajen. Tana sako qafafunta wajen ama na fitowa a gaggauce ta qofar kitchen ta baya,hannunta dauke da ludayin miya. A duniya koda bacci takeyi taji wannan kukan nasu to sai katseshi. Ta gefan idanu ama ta hangi kamar inuwar sultana din. Murmushi ta saki qasan zuciyarta tana jin dadin yadda ta yunquro don duba kukan me sukeyi?,ba kaman kwanakin baya da idan suna kuka irin wannan ko motsawa batayi bare ta lalubi abinda yake faruwar har sai ama ko tanja wani a cikinsu yazo. Gilmawar ama data gani ya sanyata ja da baya ta boye bayan labule,saidai kuma daga nan inda take tsaye din tana hangen yaran da kuma hangen abinda yake faruwa. Su uku ne, benazeer batoul da kuma goumar dake dauke da wasu kyawawan kwalaye guda biyu da dukkansu kalolin baby pink ne "Dama kana wajen amma suke irin wannan kukan goumar?" Ama ta fada tana tsayawa turus hadi da duban hannun goumar din "Ama kin sani dai,kinsan halinsu,abu kadan ita wannan lutiyar qaramar saita bude baki tayita zabgawa mutum ihu kamar an saceta" ya amsa yana qoqarin bude kyakkyawar takardar da aka lullube akwatin farko da shi,yaran kuma na tsaye kyam a gabansa riqe da rigarsa,kowa yana hanqoro a bude abinda ke ciki a bashi "Shi wannan din daga ina?" Ama ta tambaya "Ban sani ba,muna nan ina sakasu cikin keke me delivery yayi sallama,wai aikoshi akayi ya kawo,tun last week ma wai bashi da cikakkiyar lafiya bai samu fita aiki ba" ya fadi yana qarasa yage ledar, kyakkyawar akwatin ta bayyana "Wata uku,wata shida,wata tara, shekara daya duka ina qidaye da kawo wannan saqon,wai me security na gidannan sukeyi da basu taba banbance wanda ke aikoma yarana gift ba?,a wannan yanayun na rashin tsaro da Nigeria ke dashi?" Ama ta furta cikin damuwa tana duban goumar,saidai shi goumar din baice komai ba yanata kici kicin bude akwatin. Gift ne tsadaddu masu matuqar daukan hankali da tsari. Wasu irin abun hannu guda uku uku na wani irin duwatsu masu tsada da daraja,komai na jiki sak da sak iri daya,an rubuta sunansu a tsakiyar kowanne dutse,tarin chocolate,sai wasu qananun jirage masu kyau,qaramin turare sai card na gaisuwa dake dauke da haruffan Happy birthday. Miqawa ama duka kayan goumar yayi bayan ya raba rigimar benazeer da batoul ya basu chocolates a cikin kayan. Hannu tasa ta amsa tana juyasu "Kada a sake amsar wadannan kayan goumar,ba'a san waye ke kawosu ba" "Nifa in kyautata zaton cikin masu ganin pics dinsu a Instagram ne ama" "Kawai kuma sai a lalubi address dinsu?" "Eh to da wannan kuma" goumar din ya fada yana shafa kansa. A nutse ta koma da baya ta zauna,sannan ta dauki game dinta taci gaba dayi. Daga nan inda take zaune din tana iya jiro darar goumar da su benazeer,wani irin sabo da shaquwa ne sosai a tsakaninsu,wanda har takai goumar din ba kasafai ya fiya zaman NIJER ba,yanzun haka kusan a gidan ama yake,karatunsa ma ya dawo cancakat university of ibadan,weekends yana abuja wajen ama,idan ya samu dama kuma yaje NIJER din ya dawo. Daidai sanda akayi mata game over taji hayaniyarsu batoul har saman kanta,ta daga kanta a nutse tana duban qofar sanda suke shigowa goumar na dauke dasu su duka. Idanu ta kawar tana qoqarin kashe game din ta sanya kata caji. Hakanan batason kallon goumar din sam,bata kuma son hada hanya dashi,dawowarsa gidanma ita sam sam baiyi mata ba,duk sanda ta kalli goumar din ba wanda ke dawo mata a rai sai MAINA. Kafin bacewarsa kusan duk inda zashi goumar na hannun damansa ne tare zaku gansu,shi yasa duk sanda taga gilmawarsa ko taji muryarsa sai ta dinga ganin kamar mainan ta gani. Shi kansa ya karanci yadda take kauce ma al'amuransa da dama,duk kuwa da cewa a baya abokiyar fadansa ne,kuma abokiyar wasanshi ne,kaf gidan ita tafi kowa zaqewa wajen kiransa da BAQIN BUZU,musamman da tafi kowa kyau da hasken fata a gidan. Muddin za'a yi zancan baqaqe sunansa take fara jefowa koda zaikai mata bugu,amma a yanzun duka babu wannan,tsakaninta dashi gaisuwa ce,sai kuma magana idan ta kama. "Maza ku hau bayan aunty mimi tayi muku doki" goumar ya fada yana sauke mata yaran bisa wuyanta batoul kuma a cinyarta. Bata kulasun ba kamar yadda ta saba saici gaba da tayi da zura charge na game dinta. Benazeer tafi batoul rawai kai, hannayenta dukka biyun ta sanya ta kama gashin sultana din da kyau ya riqe tana fadin "Doci....doci" da gwarancinta. Zafi taji sosai,ta miqa hannu cikin zafin nama ta buge mata hannun tana bata fuska,sai kuwa ta saki kuka sosai,daidai sanda ama ke shigowa da ummin aneesa. Maqociyarsu ce wadda tun ama na zuwa tana komawa nijer suke zumunci sosai. Tasu tazo daya ne saboda kamanceceniyar dabi'u da kuma halaye,hakanan macace itama me matuqar kirki da sanin ya kamata. Kusan duk wani da ya shafi ama yake hulda da ita ya santa da ummin aneesa,saidai ita din shekarunta basu qarasa na ama ba da kadan. Zaresu daga jikinta dukansu goumar yayi yana fadin "A'ah baki da gaskiya Benazeer,ya za'a yi ki jawa anty mimi gashi,da zafi fa" a shagwabe yarinyar ke sake bare bakin kuka,musamman data hangi ama na shigowa,sai ta fara dagawa aman hannu. Sanda ta iso zata dauketa suka hada ido da sultana,wani nauyinta sultanan taji,sai ta miqe a nutse tana kwashe tarkacenta hadi da cewa ummin aneesa "Barka da yamma,ina yini?" "Lafiya lau sultana,ya gida,su aneesa har sun gaji da tambayarki,nace ni kaina baki shigomin bare a saka ran ranar visiting ki rakani din muje tare da suketa naci" qaramin murmushin gefan baki ta saki kamar yadda yanzun ya zame mata al'ada,bata fiya maida magana ba,hakanan tafi ganewa ta amsa maka da murmushi kawai. Bata kuwa sake cewa komai din ba har takai bakin qofa,tana jiyo ama na fadin "Ina take zuwa?,nan nan shopping nace tazo aje sai tace bata zuwa,idan tana da sautu zata bayar" guri maman aneesa ta samu ta zauna,ita daya ce mutum bare wadda bata shafi rayuwar iyalin mayak'i ba da tasan ainihin meke faruwa cikin rayuwar mutanen gidan "Zaman shurun baya damunta hakanan?" Maman aneesa ta fada tana zama saman kujera "Shine abinda yaketa damuna aisha(asalin sunan maman aneesa),zaman hakanan bashi yiwuwa,inaso naga rayuwarta ta matsa zuwa wani mataki kuma,bai kamata ta zauna haka ba,ba karatu ba mijin,yaran ma kana kallonsu gasunan gasunan kawai tamkar ba naka ba,makaranta nakeson sanyata,koda bataso dole yanzu taso karatu,inason canzata daga ainihin sultana zuwa wata sultanar,kuma nasan babu abinda zaiyi wannan aikin da wurwuri irin ilimi,nigerian turkish zan kaita" ama ta qarasa fadi alamun damuwa suna bayyana qarara saman fuskarta. "Wanne irin Nigerian Turkish kuma?,kin manta da school din su aneesa ne?" Maman aneesa ta fadi tana duban ama. Kai ama ke jinjinawa sosai "Oh yes,yes,yes,anyi haka,tabbas kamar makarantar ita zata dace da irin sultanar" "Qwarai ma kuwa,kin manta taurin kan humeir da yadda ta dauko fara bani wahala,yanzu humeir zakice ita ce?" "Gaskiya,gaskiya,nayi mamaki wai humeir ce harda azumin tadawwu'i" dukkansu sai suka sanya dariya,saboda sauyawar humeir din ta musu dadi qwarai,don abune da basu taba tunanin faruwarsa ba,amma sai gashi daga fara zuwan yarinyar makarantar tearm guda kacal ta sauya. Sosai suka tattauna akan makarantar da yadda take matuqar tasiri wajen canzawar halaye da kuma dabi'un yaro "Duka duka sati biyu ya rage suyi hutu,idan sun dawo kuma hutun na wata daya ne za'a debi sabbin dalibai" "Shikenan,faduwa yazo dai dai da zama" ama ta fadi tana jin dadin shawarar. Ayadda taga makarantar tayi tasirima rayuwar yaran ummin aneesa din,sai taji tana da imani da yaqinin dari bisa dari sultanarta zata sauya,zata koma kalar sultanar da take da buqatar gani,zama koma uwa abar alfahari wa 'ya'yanta. Sati biyun yaran ummin aneesa suka dawo,suka kuma fara gudanar da hutunsu,a wannan zuwan ama ta sake saka idanu kan dabi'u da halayensu,sai ta sake samun gamsuwa dari bisa dari sultanan ta samu wajen karatu. Kai tsaye ta shaidawa aba,da farko cewa yayi "Amma kina ganin me yiwuwa ne mu dauketa mu kaita har kano makaranta bayan bata da kowa can?" *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 30 "Yaran ummin aneesan fa?,suma ba kano din suke tafiya ba?,don Allah aba kada ka hana,kada kuma ka bari ta gane zucoyarka tayi rawa akan al'amarin,muna da buqatar mu.maida sultana ainihin mutum,aikin da maina ya gagara yi inaso na aiwatar masa,koda baya raye na tabbatar hakan zai bashi sukuni cikin kushewarsa" ta qarasa fada zuciyarta na yin wani irin nauyi. Shuru yayi tun daga lokacin bai sake cewa komai ko ya nuna baiso din ba,hasalima da dukka kudinsa ya bayar akayi komai daya dace,itakam sultanan ma batasan meke faruwa ba,don rayuwar kebe kai tafi komai yi mata dadi a yanzun,sai ayi abu cikin gidan sau babu adadi amma bata sani ba. K'arfe tara na dare ta tura qofar dakin sultana din ta shigo. A lokacin benazeer na rungume a kafadarta tana taba rigima,batoul na cinyar aba tana bacci,don ita din ba kasafai ta fiya rigima ba. Da shanyayyun fararen idanunta ta waiwayo tana duban ama,kafin ta janye idanun nata ta dorasu akan benazeer da aman ta kwantar mata saman gadon,sai kuma ta dauke duban nata daga kan benazeer din ta sake maidawa fuskar ama "Hala shirin kwanciya kikeyi?" Ama ta tambaya tana sake qarema sultanan kallo. Ta sauya sosai,har yanzun dai batayi qiba ba,amma jikinta yayi kyau kai sai ka rantse bata taba sanin d'a namiji ba bare ayi zancan haihuwar 'yan biyu,wannan kyawun nata ya sake fita da wani irin sirri na cikar cikakkiyar mace,idanunta sun sake girma da haske,hatta da idonta dayan da ya samu dan matsalar da sai ta sanya masa glass babu lallai kai ka fahimci hakan saboda yadda suma suka bude fes dasu kaman dayan. Gashinta ya wani sake cika kamar kowacce gaba ta jikinta ke fara nuna girma na asali bawai girman da samuwar ciki ya tilasta zuwansa ba. "Eh ama" ta amsa mata tana bude man shafawarta sannan ta koma ta zauna saboda ta fahimci da magana ama din ta shigo. "Ya kamata,sultana" "Na'am ama" ta amsa mata a sanyaye tana fatan ba wani sabon abu bane kuma ya taso "Kinsan rayuwa babu abinda yakai ilimi dadi da daraja,babu kuma abinda yakai ilimi maidaka cikakken mutum haka ne?" Kai ta gyada a sanyaye karo na biyu "Mun yanke shawara,in sha Allah nan da sati biyu masu zuwa tare zaku wuce kano tare da yaran ummin aneesa,zaki fara makarantarsu,saidai mun roqi alfarmar koda daga j.s3 ne idan hakan ta samu" ama ta qarashe fadi tana zubawa sultana idanu. Kai ta jinjina,ita a yanzun batajin akwai wani abun da zai taba mata zuciya,ko ya sosa mata rai,batajin akwai wata tsana ta wani abu cikin zuciyarta da zatayi girman tasirin wutar tsana da qiyayyar dake ruruwa yanzu haka a zuciyarta "Allah ya kaimu" sultanan ta fadi a sauqaqe kai tsaye kuma ba tare da taji komai cikin zuciyarta game da batun ba. Sake kiran sunanta ama tayi a karo na biyu,sai ta kuma amsawa tana duban ama "Ki daure kiyi karatu sultana,banason wadanda suka sanki a shekarun baya su sake ganinki dai still yadda kike,ba wani ci gaba,babu kuma abinda ya canza daga gareki" murmushin qasan zuciya ne ya subuce mata,tadan murmusa ta yadda ita kanta ama din ba zata gani ba,ita wai meye ya ragewa rayuwarta?,bata da MANUFA burika da fata na rayuwarta dukka sun jima da bizne kansu cikin qarqashin duk wani buqatu na rayuwarta gaba daya. *********K'arfe takwas na safiya suna qofar gidan ama,yaran ummin aneesa da suka kasance 'yammata kamarta a shekaru ne. Anata zuba kayansu cikin mota,sunata kuma kai da kawowa cikin 'yar hargowa da rigingimu nasu irin na sako da sako. Daga gefe daya sultana na tsaye kawai,jingine jikin motar. Sanye take da uniform da yayi matuqar karbarta ainun,idanunta saye cikin farar kwalbar glass wanda ya zame mata tamkar ado,ba zaka taba tunanin lalurar idanu bane suka sanyata sakasu,sun amsheta ainun,sun kuma qarawa zagayayyun idanunta wani irin kyau da kuma kwarjini matuqa. Sai da aka gama komai tas sannan ta buda motar ta shiga,ama ta shiga gaba dauke da BATOUL, goumar ya buda gidan baya dauke da BENAZEER yanata cakularta da wasa tana qyaqyacewa da dariya. Shigowarsa gefanta ya sanyata daga shanyyun kewayayyun idanunta ta kalleshi dasu. Kusan tare suka kalli juna,wannan yayi sanadiyyar haduwar idanunsu guri guda. Hasken fararen idanunta ya dakeshi sosai,yayi saurin zare idanunsa shima yana ci gaba da tsokanar benazeer suna sake cikawa sultana kunne. Basu kuma bar kunnuwannata sun huta ba har suka isa airport. Wannan karon su aneesa nata murna,sun huta dogon zaman mota daga abuja zuwa kano,tafiyar jirgi ce cikin mintuna qalilan zasu isa. Basu kuwa dauki lokaci ba,duka duka mintuna qalilan suka sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano,daga can din kuma suka samu daya daga cikin motocin dake zirga zirga cikin airport din ta daukesu zuwa HASSAN IBRAHIM GWARZO. ****Motoci da dalibai fal qofan makarantar. A irin wannan lokacin akan samu cikowar mutane irin haka da ababen hawa. Cikin lokaci qalilan suka isa office na shugaban makarantar,ama tayi dukkan abinda ya dace goumar yana tsaye yana rungume da twins. Daga goumar din sai ama,su biyun kacal sukafi sakewa dasu fiye da kowa,sun gane goumar sosai kamar yadda suka gane ama din. Tattaki suka yima sultana har zuwa hanyar da zata sadata da bangaren mata. Iya ama da su benazeer,don goumar tun daga can mararrabar section din maza da na mata suka dakatar dashi. Haka tsarinsu yake,kome alaqarka da mutum ba zasu tabi bare ya tsallake wannan shingen ba muddin ba section din jinsinka bane. "Allah ya bada sa'ar karatu sultana,shikenan sai munzo visiting?" Ama ta fadi tana duban fuskarta. A sanyaye ta daga kai ba tare data dubi ama ba,hankalinta yana rarrabuwa akan yadda rayuwa zatazo mata cikin makarantar. Ta gani komai da ama ta shigar ta shigar dashi ne dai dai da na kowacce yarinya matashiya budurwa. "Shikenan,Allah ya bamu alkhairi" ama ta sake fadi,sai sultana din ta kuma jinjina kai kana ta fara taku daya biyu zata wuce ciki,saidai kuma batasan dalili ba,can qasan zuciyarta takejin wani irin nauyi yana mamayarta,kamar akwai abinda takeson aiwatarwa,kamar akwai abinda zuciyartata keso wanda ta gaza yi mata shi*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 31 "sultana" taji sautin muryar ama na kiranta. Waiwayowa tayi suka hada idanu,a hankali sai ta sauke idanunta akan batoul da benazeer. Sauko da batoul din ama tayi ta miqa mata ita,takowa tayi a hankali ta qaraso gaban ama din,hannayenta ta sanya duka biyun ta karbeta. A hankali ta dora idanunta saman fuskarta, fuskokinsu suka gauraya waje daya,sai yarinyar ta sakar mata dariya tana qoqarin kamo eye glasses dinta. Batasan ya akayi ba saita tsinci kanta da sakin wani siririn murmushi,ta saka nata hannun ta riqe dan qaramin hannunta. Daidai lokacin benazeer ta fara gwaranci. Sake daga kai tayi ta kalli benazeer din,hannu take miqa mata tana zillo kamar zata fado,maida BATOUL tayi daya side din ta amshi benazeer,sai ta hadasu dukka su biyun ta rungumesu a qirjinta ba tare data shiryawa hakan ba. Luf sukayi daga ita har su,yaran sunyi shuru cikin qirjinta kamar wadanda sukasan meke shirin faruwa,kamar wadanda sukasan tana shirin yin nesa dasu ne har na tsahon watanni uku. Cikin qirjinta taji zuciyarta tana bugawa da kyau,sai ta maida idanunta kawai ta lumshe. Idanun itama ama ta lumshe tana jin wani yanayi yana sauka a zuciyarta,tsakanin uwa da d'a sai rabbussamawati,koda kuwa dan na shege ne muddin akwai zuciya a qirjin uwar. Ta bude idanunta sanda sultana ke miqa mata su,sai dukkansu suka riqe gaban hijabin sultana din suna qyuyar sauka. Murmushi hade da hawaye ne suka subuce ma ama din,hakanan sultanar itama hawayen ne maqale a kuncinta. Cikin dabara da waqar da ama keyi musu ta samu ta amsosu,saidai har suka bar wajen idanuwansu da hankulansu yana kan mamarsu. Ta shiga dakinsu,ta kuma sameshi cikin tsafta da tsari. Yanayin dakunan da yadda ta samu daliban ciki kawai ya soma gaya mata inda tazo din waje ne na tarbiyya,waje ne na cikakken karatu,waje ne kuma bana wasa ba. Kintsattsun matasa kamarta,kowacce ta karbeta hannu bibbiyu,hakanan itama tayi iyakar bakin qoqarinta a ranar tata ta farko ta sake musu an gaisa da kyau,daga nan kuma ta kama kanta ta soma sabgogin gabanta da qoqarin fahimtar komai. *_3:45 am_* Tsakiyar baccin da bai jima da daukarta ba saboda tsananin tunanin da har yau batasan meye qarshe da mafitarsa ba taji ana tashinta cikin nutsuwa. A hankali ta buda idanunta tana qarewa dakin kallo, tunaninta ya dawo fes yana tuna mata a inda take din a yanzun. MAKARANTA kwanyarta ta tuna mata. Gefan da ake tabata din ta waiwaya. Tana zaune riqe da uniform dinta a hannu tana kallonta,fuskarta qunshe da murmushi. Fatima ahmad yusuf idan bata manta ba shine kiran data kirayi kanta dashi sanda suke gabatar da junansu. Kusan tafi kowa kusa da ita ita da ameena aleeyu dake maqwafataka da ita ta hannun hagunta. "Ki tashi,lokacin sallar asuba ya kusa,mu samu mu gama komai a nutse kafin captain ta fara counting" ta fadi mata tana ci gaba da harhada abubuwan da zata dauka. Idanu da baki sultana ta saki tana kallonta,saita maida dubanta ga qaramin agogon dake dakin. Sallar asubahin tun yanzu?, counting na meye za'a fara?. Bata ida wannan tunanin ba taga shigowar ameena aleeyu tsaf cikin uniform. Binta tayi da kallon mamaki,ko hudu na dare bai cika ba? ,A wannan daren me kuma sukeyi su din haka?. "Qarasa muje muyi alwala da wuri kada mu samu cinkoso muyi shigen ta jiya" ameena ta fada tana zama sanya hijabinta sannan tace "Kin tashi lafiya sultana?,mamaki nasan kikeyi ko?,dukkanmu haka mukayi kaman naki dinnan farkon zuwanmu makaranta,dole kowanne daliba ya tashi da wuri yaje yayi alwala ya wuce masallaci sallar asuba,muddin ka makara kuma.....hmmm akwai qura,ni da fatima ba zamu iya tuna randa muka makara din ba,saboda muna cikin dalibai masu kiyayewa" kai ta jinjina tana sake binsu da kallo kamar baqin halitta,kawai saita juya a hankali ta maida kanta ta kwanta tana lumshe idanuwanta hadi da cewa "Kuje zan taho" tare suka juyo gareta "Karkiyi haka,da zaki taso mu wuce zaifi fa" kanta ciwo yake sosai,don ko baccin awa biyu cikakke batayi ba,runtse idanun ta sakeyi tana jin kamar damunta kawai sukeson yi "Kuje kawai karku damu" shuru sukayi na wani lokaci suna duban juna,saboda sunsan horon da takeson jefa kanta din ba mai dadi bane,abune da kowanne dalibi cikin makarantar ke qoqarin kaucewa. To amma ba yadda suka iya kasancewar dukkansu ba masu son shishshigi ko hayaniya bane sai suka qyaleta. Duk da baccin bai dawo ya dauketa ba gaba daya amma ya soma fusgarta ta soma jin hayaniya sama sama,kowacce daliba tana tashi gami da kwasar uniform dinta a gurguje tana sanyawa. Idanunta ta qarasa budewa tsaf sanda wata kakkaifar murya ta soma fadin "One......two...... Three......" Jin kamar ana guje guje ya sanyata bude idanun nata. Dakin duka ya hargitse,kowa takai takai yakeyi wajen qoqarin saka uniform sannan kuma ya fice da gaggawa kafin a kammala qirgen. Haka kawai tsoro ya dirar mata,ta sauko da sauri cikin firgicin wanne abune me muni zai iya samunta idan suka fice suka barta a nan,sai ta lalubi hijabinta ta zura tabi bayansu ba tare data tsaya sanya uniform ba. Da gudu gudu wasu ke nufar gate dinsu na farko,tun kafin su isa ta jiyo shigen wancan muryar tana counting itama,saidai dab da zasu isa me lissafawan taja qofar ta bame,sai gani sultana tayi dalibai suna zubewa bisa gwiwoyinsu hadi da furta "Astagfirullah....... astagfirullah" cikin wani irin tashin hankali. Abun ya bata tsoro ya kuma daure mata kai,bata da zabi illa itama tabi sahunsu ta zube a wajen. Sai da suka gama neman gafara sannan suka zarce wajen daura alwala. Tasha wahalar kafin ta samu kan famfo din da zata daura alwalar,abinda nan duniya bata taba saninsa ba baya ga abinda ya faru da ita ba wato wahala wajen samun wani abu na duniya. Tana alwalar tana tuna adadin yawan kan famfo dake gidansu,wanda hatta tsuntsayen dake gittawa ta cikin gidan sai a inda suka zaba suke shan ruwa ballantana su,su dinma ita sultana shalelen bibi da aba. Ayarin ta sake bi suna nufar wani guri,bata karanci ina bane sai da suka qaraso,masallaci ne,shima anja gate din an rufe,dukkansu saida suka sake zaman yin istigfari sannan aka bude musu suka sanya kai ciki. Cikin wani irin tsari da burgewa kowa yahau sahun sallah,aka kabbara sallah. Mintuna kusan takwas sannan aka idar,tana niyyar miqewa taga ba wanda ya motsa sai qur'anai da ake budewa,kowa kuma yana lalubar 'yan ajinsu. Idanu ta shiga budewa tana waige waige,ba inda ta sani,ba kuma wanda take ganewa a wajen. Cikin haka Allah ya taimaketa ta hango fatima tana daga mata hannu. A sanyaye ta isa kusa dasu,ta miqa mata qur'anin,tasa hannu biyu ta karba,ta samu waje kusa da ita ta zauna. "Ki bude,recitation za'ayi,za'a yi mana qarin karatu kuma,sai qarfe bakwai sannan zamu koma hostel mu shirya shiga aji" kai ta jinjina qasan zuciyarta fal da mamaki,wacce irin makaranta ce ama ta kawota haka?. Buda qur'anin kawai tayi ta zuba masa idanu,saboda inda ake musun ita sam batazo wajen ba,yo inama tayi jumurin zuwa makarantar ballantana ta kawo nan,ta sani dai,ta kuma tabbatar su aminata da suke aji daya tare a baya sun wuce haka yanzun,saboda makarantar islmiyyarsu badai karatu ba,ita dince dai da bata sanya aka ba. Tana nan zaune aka gama biyawa aka soma karanta musu suna bi,duk sai taji ta muzanta,bata kuma ji dadi ba ganin kowa yana bi tar tar,ita kadai ke baza idanu. Kusan ita daya ce sabuwar daliba cikinsu,saboda dokan makarantar bata yarda da daukan dalibi daga kowanne mataki ba saidai matakin farko wato J.s one,ita dinma sa'a ta taka da kuma sanayya ya sanya suka kaita j.s3 din. Har akayi aka gama bata iya kama komai ba a ciki. Hakanan taji jikinta yayi sanyi qwarai,irin sanyin da bata taba ji ba wai akan karatu,ko don wannan din wani littafi ne na daban?,na musamman da ya banbanta da dukka sauran litattafai a duniya. Suna hanya ameena aleeyu da Fatima ahmad yusuf sunata hirarrakinsu,saidai abinda ta fuskanta a gurguje kowa ke yin tafiyar zuwa hostel. Tun tana binsu a hankali ta fuskanci zasu tsere mata don haka ta dan daga qafa ta taddosu. Waiwayota ameena aleeyu tayi tana murmushi "Saikin saba da dukka tsari da dokar makarantar nan sannan zaki zauna lafiya,yanzun zamu wuce hostel ne,ayi share share,sannan mu wuce kitchen yin breakfast" idanunta tadan fiddo,duk wannan wahalar da tayi,da kuma qoqarin da take ta koma ta wuce toilet ta sheqa wanka ake batun shara da cin abinci?. "Wanka kuma fa?" Ta tambaya tana dubansu. Dariya kadan sukayi "Ba batunsa,sai Allah ya kaimu biyu na rana idan an tashi class" cikin ranta takejin ba zata iya wannan rayuwar ba,itakam koma meye dole tayi wanka da safen kafin ta wuce aji,don ba haka ta saba ba. Suna isa labour perfect na raba aiki,kusan kowanne class da suke hade a hostel guda sunsan area din da zasu share,suna da yawan da ba'a kula da baquwar fuska bace ita,don haka ta nufi bangaren da toilets dinsu yake don yin wankan. Kowanne toilet a kulle yake gam,taja baya ta tsaya tana duban qofofin,ta kuma kalli bucket din hannunta. Da gaske kenan saidai ta koma sai qarfe biyun kamar yadda ameena aleeyu ta gaya mata. Ranta a bace take takawa zuwa sassan dakinsu cikin babban compound na hostel din nasu da yakai girman babban parking space,bayan football field da suke dashi dake hade da table tennis. "Ke!" Taji an kirata daga bayanta. Cak ta tsaya tana jin amsa kuwwar kiran cikin kunnenta,irin kiran data fi tsana duk duniya,kiran wulaqanci da yaa maina kadai keyi mata shi,a yanzun batasan kuma waye ya ara ya yafa ba. Waiwayawa tayi jin an sake ambatar "Ba dake nake ba?" Kafin tayi komai taga daya daga cikin daliban dake daura dasu ta saki tsintsiyar hannunta,ta kuma qarasa da sauri ta zube bisa gwiwoyinta tana fadin "Aunty gani". Mamaki sosai ya kama sultana,aunty kuma?,harda duqawa saman qafafu?,ita sam a wannan wajen bataga aunty ba,tunda duka duka ma autyn da ake kira dinma baifi ta bata tazarar shekara biyu ba "Ba dake nake ba,da wannan 'yar iskar nake" ta fadi cikin dagawa da izza tana nuna sultana. Wani abune yazowa sultana wuya ya tsaya mata,ta tattara dukka miyan bakinta ta hadiye,ranta yana sosuwa da sunan 'yar iska data kirata dashi. Waishin ma ita din wace da zata kirata da wannan sunan?,ta buda baki zatayi magana muryar Fatima ahmad ya gauraye gurin "Baquwa ce aunty,don Allah batasan tsarin komai ba,tana cikin sabbin daliban da aka kawo jiya" "Tambayarki nayi?,ita batasan wacce makaranta ta shigo ba?,uban meye takeyi da botiki a hannunta lokacin tsafta da gyara waje?" "Bata sani ba kiyi haquri aunty" "Samomin bulala" prefect din ta fadi tana bawa yarinyar dake durqushe a gabanta umarni. Tsaiwa cak sultana tayi tana jiran ganin ikon Allah,tanason ganin yau din wacece zata daketa?,wacce me tsautsayin ce?,batasan babu wani halitta da ya isa ya daketa ba bayan ruwan sama?. Cikin qasa da minti daya yarinyar ta iso,cikin ladabi irin nasu na makarantar daya zamewa kowanne dalibi tilas ya siffantu dashi ta duqa ta miqa mata "Zo nan" ta yiwa sultana umarni cikin tsawa "Kije don Allah,don Allah kije sultana" Fatima ke fadi cikin tsoro "Har saikin roqeta ma?,idan batazo bama zan qaraso da kaina" perfect din ta furta tana takowa gurin sultana din cikin izza,zuciyarta na gaya mata duk yadda akayi 'yar gidan uban wani ne daga wata qasar,don sam batayi zubin qabilun nigeria ba "Durqusa kikayi tsai kina qarewa mutane kallo!" Ta fadi cikin wata sabuwar tsawar*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 32 Ci gaba da duban tsakiyar idanunta sultana din tayi tana hadiye wani abu daya tsaya mata a maqoshi,wannan din ya sake tunzura prefect din,ta daga bulalar hannunta da nufin saukewa sultanan "Lafiya?,me kukeyi a nan carko carko?" Muryar Metrom din dake kula da shiyyar ta gauraye wajen. Cikin fushi perfect din ke maida jawabi,gurin yayi tsit har ta gama "Shikenan ya isa,kowa ya koma kan aikinsa,ke kuma huda kiyi haquri,baquwa ce,amma zan mata bayanin komai" wani irin tsuka wadda aka kira da hudan taja,alamu dake nuna takaicin dake ranta fal,don taci buri sosai na ladabtar da sultana. Kyawunta wani abune da ya bugi zuciyarta qwarai ya kuma sanyata kishi. Idanunta da suka dan jirkita ta lumshe sannan kuma ta budesu,ita kanta taso yarinyar da aka kira huda ta samu isowa gareta,ba shakka da ta barwa rayuwarta darasi. Don rayuwa ta cimmata hakan bai nufin komai da komai daga asalin sultana ya sauya ba,ba zata lamunci cin zarafi ko kuma qasqanci ba. "Taho muje" taji muryar Metrom din na fadi tana kama bucket din hannunta. Bata musa ba tabi bayanta har zuwa wani kebantaccen waje da Metron din kan zauna ko tayi ajiye ajiyen kayanta "Zauna,sultana mayak'i ko?" Ido ta daga ta dubeta tana mamakin yadda ta kama sunanta haka kai tsaye kuma lokaci guda. "Zauna" ta sake maimaitawa,ba musu ta samu waje ta zauna,itama Metron din ta zauna tana duban idonta "Sunana maama asabe,kina iya kira na maama ko asabe,da farko inason shaida miki,duk wani da kk da buqata ko menene shi kina iya shaidamin kai tsaye,za kuma ki sameshi in sha Allah" saita tsagaita tana kallonta. Mamakin sultana ya sake qaruwa,to meye hadi ko alaqarta da ita bayan yau ne ita karo na farko a rayuwarta ma data fara ganinta,ta yaya zata buqaci wani abu a wajen ma'aikaciyar da idan ita sultanan bata taimaketa ba ita din ba zata taimaketa ba "Kada kiji shakkar nema ko tambayar komai daga hannuna tamkar kina gida,don komai zai fito daga hannuna da zaki buqata din daga gidan yake.....makarantar nan tana da dokoki da qa'idoji masu tarin yawa,duk dalibin da kika gani a makarantar nan yana rayuwa ne a kansu,kina da wata kariya da alfarmar da ba lallai ki fahimci abinda zan ce ba,kawaidai abinda zan gaya miki shine,don Allah ki koyi kiyaye kowacce doka da qa'ida,ta yadda babu wani hukunci da zaya dinga hawa kanki,ni kuma zanyi dukka qoqarina wajen tafi da komai" shuru tayi tana jujjuya maganganun maama asabe dake tafe da wani irin surkullen zance data kasa fahimta,to wai shin maama asabe ta santa ne ko kuwa?,akwai harshen damo cikin maganganunta da bata fahimci ina ta sanya gaba ba,daga qarshe kawai ta yanke ta gyada mata kanta "Yauwa,yanzu lokacin tafiya kitchen yayi,kibi 'yan uwanki ku wuce" kai ta sake gyada mata,sannan ta miqe riqe da bucket dinta. Cikin uniform ba tare da wanka ba ta sami su fatima,ta lura da tuni sun saba da wannan yanayin,don shirin tafiya kawai sukeyi kitchen. Ameena ce ta kama hannunta "Don Allah ki kiyaye sultana,haka makarantar take,amma muddin kika kiyaye zaki fahimci rayuwa ce me dadi kike kai" bata ce da ameena komai ba,ta sunkuya qasan gadonta ta sauya takalminta. Wani irin takalmi ne me azabar tsada da kaf fadin makarantar.....duk kuwa da kasancewarta makarantar yaran masu hannu da shuni za'a samu me irinsa,ta dauki school bag dinta da tuntuni take dauke da litattafanta a tsare ta goya sannan tabi su fatima suka wuce kitchen. Babban hall ne da aka tsarashi da table da kuma kujerun cin abinci rukuni rukuni,kowanne rukunin table yana dauke da kujerun zama guda goma,kaman yadda yake a doka mutum goma ne ke zama kowanne table. Kafin isowarsu an shirya kowanne table da cooler din abinci, spoon cups da plates da kowanne dalibi zai buqata. Yadda taga kowa ya zauna haka itama ta zauna,ta dinga nazarin wajen da.idanu tare da cika da mamaki,mamakin yadda duk yawansu kowanne dalibi na zaune bisa kujerarsa cikin tsari,kowanne table kuma cups da sauran tarkacen kai a qididdige suke dai dai da yawan masu zama a wajen. Fatima ce ta miqe tayi saving nasu kamar yadda kowanne table mutum daya ke wakiltarsu. Tabi plate dinta da kallo sanda fatima ta gama ta koma ta zauna. Doya ce da qwai,sai kuma tea lafiyayye cikin kowanne cup,ta dauke idanunta ta fara bazashi a hall din sanda taji sun rude da addu'a duka lokaci guda. Addu'ar cin abinci ne,sai da suka sauke sannan kowa ya fara kaima cikinsu,a sannan hayaniya ta rude a wajen. Ko hannu batakai ta taba abincin ba,bawai don baiyi.mata bane ba,aah tsabar rashin sabo da cin abinci cikin gamayya haka,uwa uba kuma a gida ta saba,baa taba ajjiye musu breakfast qwaya daya tsura haka,a qalla akwai kalolin breakfast uku ake ajewa ka zabi son ranka. "Minti talatin kacal ake bayarwa,kiyi ki fara ci kafin a fara counting" ameena aleeyu ta fada tana kai cup din tea din bakinta. Tun asali a dabi'arta bata iya sauri wajen cin abinci ba,don haka tana tsaka da soma ci din taji an fara irge kwatankwacin irgen da taji anyi dazu da asuba wanda ya sanyasu zubewa suna istigfari. Ture abincin tayi sanda fatima ke gaya mata lokaci ya kusa cika,gaba daya abincin ya taru ya dunqule mata a qirji,ta sunkuya ta dauki handbag dinta "Baki dauki ruwanki ba" fatima tace da ita,kai ta girgiza alamun AA tana yin gaba,hakan bai hana Fatima daukan sassanyan ruwan ba tabi bayan sultana din dashi,tausayin sultanan yana kamata, saboda ta sani bata saba da irin rayuwar bane bisa dukkan alamu. Kaman hakan suma suka fara,sai gashi yau rayuwa ta fara koya musu yadda zasu rayu cikin dadi da kuma akasin hakan,hakan kuma ya zame musu jiki tamkar dama a haka rayuwar tasu ta taso. Sai da taji qishirwa da gasken gaske,ta kuma tabbatar babu wani sauran bottle water a nan wanda ta saba sha a gida sannan ta amsa daga wajen fatima ta sha. Kusan duk karatun da akayi cikin ajin shima nata idanu,bata fahimtar inda komai ya dosa,bata gane komai,tana jina rayuwarta kamar bata taba zama a aji ba. Haka kawai sai taji ta muzanta,ta kuma tsargu,kowa yana karsashi tare da qoqarin bada gwargwadon fahimtarsa cikin aji amma banda ita. A hankali ta dinga jin wani abu me kama da rashin jin dadi yana sauka a zuciyarta,ta dinga jin me ya hau kanta wancan lokacin?,me yasa bata tsaya tayi karatu ba?,tana gani yanzu a gaban idanunta tamkar ita daya ce bata gane komai cikin ajin. Koda kuwa akwai banbancij harshe da yare a tsakaninsu,amma tayi imanin inda ta tsaya tayi karatu a baya ayanzun batajin akwai abinda zaya gagareta,tunda ko a makarantar tasu ana koyar dasu harshen turanci sosai,kuma kaf gidan ba wanda ba zaya iya jefa maka turanci ba,bare larabci da ya zama yaren dukkan musulmin duniya. Sha daya aka fita break,masu sha'awar cin provision dinsu suka diba sukaci,ciki harda su fatima data fahimci ita da ameena aleeyu komai nasu a hade yake. Sukayi sukayi tazo suci abinci amma ta qiya,don bata sha'awar cin komai,hasalima dandanon bakinta ya dauke,ba abinda ke kai kawo a kwanyarta illa yadda zata tafiyar da baquwar rayuwar data fado mata rana tsaka ba tare data shirya ba. Biyu na rana aka tashi da classes. Tana kallon yadda dalibai keta walwala zuwa masallaci,kowa na sabgar gabansa,sai ta dinga jin inama ace itama tana daya daga cikinsu. A yanzu kawai tana jin gangar jikinta da ruhinta ne a wata baquwar duniyar,bawai irin duniyar data saba rayuwa a ciki ba. Sallah sukayi bisa jam'i a masallacin mata,abinda kaf rayuwarta zata iya cewa bata taba yi ba wato sallah cikin jam'i. Ta saba kammala sallarta a mintuna qalilan,yau sai gashi itace da tsaiwar sallah,sannan kuma bayan an idar sukayi zaman yi azkar na bayan kowacce sallar farilla,nan ma 'yar kallo ta zama,ta lumshe idanunta muryoyin daliban cikin NISHADI suna jeranta addu'o'in na shiga cikin kunnenta. A hankali ta dinga jin wani sanyi yana saukar mata,nutsuwa na zuwa ruhinta,qullin bacin ran dake danqare can wani kebantaccen saqo na zuciyarta yana neman hanyar fara kwaranyewa. Fuskokin benazeer da batoul suka gilma mata cikin idanunta,saita bude idanun da hanzari tana kiran sunan Allah. Daidai sanda suka kammala addu'an kowa ya soma miqewa domin kaiwa ga kitchen cin abincin rana. Kaman dai da safe,komai da kowa kan tsari,sunyi lunch da lafiyayyar jallope din taliya da kuma soyayyen kifi. Wannan karon tadan cakula ta barshi kaman dai da safen,duk kuwa da cewa girki ne me kyau da bashi da makusa kwata kwata. Sanda ta iske layin shiga wanka saita koma da baya kawai ta zauna,ta lumshe idanunta wani abu me kama da bacin rai nason sauko mata. Bakayi wanka ba tun safe,ka debo zafi da rana kazo da zummar ka wankesu kuma ka samu wannan layin da batasan ranar da zai ragu ba?. Tana nan zaune bisa layi tana duba qaramin agogo dake hannunta,mintuna goma kacal suka rage lokacin yin wanka ya cika,a yadda kuma ameena aleeyu ta gaya mata indai hakan ta kasance kuma wanka saidai da dare,lokacin baccin rana ne. Abinda ya matuqar daure mata kai da ta gaya mata koda bakajin baccin dole nefa ka qirqiroshi "Qangin bauta" hausar tazo mata a tsakiyar kai. Anya ama tayi mata dai dai kuwa?,wannan rayuwar da ama ta zabar mata tazo tayi da sunan makaranta irin rayuwar data dace da ita ne?,zata iya ci gaba kuwa?. Dukkan tsammaninta ya yanke ganin mintuna biyar kacal sukayi saura,koda ta samu shiga a sannan tasan zaiyi wuya ta samu abinda takeso,tunda a qalla wankanta yakan dauki mintuna goma sha biyar kafin ta kammalashi "Sultana mohmoud mayak'i" taji muryar Metrom asabe na kiranta. Waiwayawa tayi da fararen idanunta da suka fara laushi tana duban Metron asabe. Hannu ta sanya ta yafitota,dan jim tayi sannan ta fara takawa tana nufarta. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 33 "muje kiyi wankan kafin lokaci ya qure" Metron asabe ta fadi tana amsar mata bucket. Ba musu ta miqa mata,Metrom tayi gaba sultana na biye da ita. Duk sai su fatima suka bita da kallo,can qasan ranta itama sultanan tana mamakin yadda metrom din ta kebeta ita daya. Toilet dinsu da iya su yasu ta sanya muqulli ta bude ma sultanan ta shiga. Duk da a tsaftace yake amma sai ta dinga jin wani bawai. Sam baiyi koda rabin toilet din da ma'aikatan gidansu ma ke shiga ba. Hakanan tayi wankan a gaggauce saboda jaddada mata iya sauran lokacin da ya rage da Metron tayi. Koda ta isa hostel an fara counting an kusa kaiwa qarshe,hakanan tabi lafiyar gadonta ta kwanta. Bata wani matsawa kanta can bama baccin ya dauketa kasancewar tana da buqatar yinsa,don tsahon rayuwarta bata taba daukan lokaci haka yini guda tana a tsaye ba,bata jurewa wahala aam,shi yasa take gudun islamiyya kamar me?. Babban abinda ya sanya ta tsani boko kuwa baccin safe da take hana mata,ta tsani tana bacci a yanke mata shi,yanzun zakaga bacin ranta. Ilai kuwa tana tsaka da baccin sautin muryar fatima ta ratsa kunnenta. Bata gama wartsakewa daga bayanin fatiman ba taji wannan kakkaifar muryar wadda tamkar an halicceta ne don qididdige musu mintuna ta fara musu lissafi. A kasalance ta jawo hijab dinta na house wear ta zura,ta sauke qafafunta qasa tana saukowa daga saman gadon tana jan wani mugun malalacin tsaki. Kanta gaba daya sara mata yakeyi,wannan wanne irin stress ne haka?. Sallah suka sake wucewa sukayi cikin jam'i kamar dai ta azahar,sukayi dukkan azkar sannan suka wuce babban filin da suke zama don maimaicen karatun da akayi a ranar. Yana daya daga cikin dokoki da qa'idan makarantar. A bisa radin kansu kowanne zaiyi muraja'ar karatunsa,cikin rukuni,idan kuma anso awarwartsasu kowa shi kadai. Ajinsun ta lura suna da himmar karatu,team guda sukeyi suna yiwa juna tuni da qarin haske,a yanzun ma hannunta saman habarta,littafinta a bude amma kuma idanu ne nata. Ta baza dukkan hankali da nutsuwarta amma har yanzun bata fahimci komai ba,sai ta sauke ajiyar zuciya,wani abu yana darsuwa cikin zuciyarta,wani abu da bata taba jin irinsa ba sai a wannan karon. Sha'awar taga ta iya karatunta kaman kowaacce daliba,tana karantashi sosai kamar yadda taga Fatima ahmad da ameena aleeyu nayi,bisa dukkan alamu ma sune jagororin zaman,ta fahimci suna ganewa matuqa,sai suka dinga bata sha'awa ta dinga binsu da kallo. Karfe biyar suka koma hostel,masu wanka gyaran gado,saka net duka suna aikinsu,tana zaune tana sake nazarin kowa tare da bin kowa da kallo. Ameena aleeyu ta taba kafadarta tana kallonta "Ki gyara gadonki sultana,kinsan komai namu yana da qayyadadden lokaci,qarfe shida zamu fita a nan,idan ka wuce haka kuma sai kayi zaman istigfari,ga punishment" ta qarasa fada tana dariya saboda tuna makarar da Fatima ahmad tayi wata rana da lokaci ya qwace mata "Wai dama istigfari din da ake tsareka kayi shima wani azabar ne ban sani ba?,saika bude duk muryarka ka qwala da qarfi kamar wanda kake saka ran mutanen sama su tayaka lissafawa?" Maganar ke sanya ameena aleeyu dariya har yau,duk sanda kuman tayi dariyar fatiman tasan da ita take,to in sha Allah sai takai mata duka. Kamar yanzun ma dundu ta bita dashi tana sauke net dinta,ameenan ta qwace tana gocewa,sai Fatiman ta zarto gadon sultana tana cewa "Tashi na kama miki mu gyara muyi mu fita da wuri" ta fuskanci duk irin gatan da suke taqama dashi sultanan ta damesu,ta sake tabbatar da hakan sanda sultana ta kasa tabuka komai. Batasan ta yadda zata kama zanin gadon ta zaunar dashi sosai saman katifar ba ballantana net din da bata taba bacci qasan net irinsa ba,na saman gadonta ba irin wannan bane sam sam sam,aba ne ya siyo mata shi musamman daga turkey,daga gadon har net din,shi kansa duk da kyau da tsadarsa bata fiya shiga ciki ba,don gidan kwata kwata basusan wai wani abu da ake kira sauro ba bare sauran qwari,gida ne dake bisa tsari yake samun cikakkiyar kulawa daga ma'aikata kowanne lungu da saqo na gidan "Kaman haka a irin wannan lokacin muke gyara makwancinmu,duk lokaci irin wannan sai na tuna da talatu" fateema ta fadi tana dariya dariya "Suna qoqari sosai,a lokacin bakasan zafin abun ba,sai yanzu da rayuwar makaranta ta gaya maka" ameena itama ta fadi tana tata dariyar. Lokaci lokaci sukan zauna suyi hirar masu aikin gidajen nasu,zuwansu makarantar ya sanya suka qara ganin kima da matsayinsu da kuma girman hidimar da suke musu. Hannu kawai sultana ta sanya ta dafe goshinta,itama tanja ce ta fara fado mata,sau daya kuma koda wasa bata taba daga tsintsiya da sunan share dakinta ba,hatta suturarta idan ta cire tanja ke killace mata,me taci?,me zataci,dukka suna wuyan tanja,hatta panties nata washing machine ke hidimat wanke mata su,yau gata cikin rayuwar yiwa kai komai,ba kuma cikakken 'yancin lokaci,sai iya abinda aka qayyade maka. "Ya Allah" karon farko ta furta sunan ubangiji da a lokacin zuciyarta ke ayyana mata shine zai dafa mata,ta waiwaya ta sake kallon gadon tana mamakin yadda fateeman ta gyarashi tsaf,ita dinma kamarta kenan take ada?,dole ta sanyata koya?,ta yaya ta kuma ina ita zata fara nata koyon?. A masallacin sukayi magariba,suka sake komawa kitchen sukaci abincin dare,sukayi isha'i sukayi tilawar litattafan addini sannan suka wuce makwanci. Kamar jiya din,yauma da farko juyi ta dinga yi,gaba daya yininta na yau take nanatawa cikin ranta. Wata irin rayuwa data banbanta da rayuwarta,ta banbanta da rayuwar data saba yi,yau gata tsundum cikin makaranta, makarantar da babu abinda ta tsana sama da ita,yau sai gashi ba jeka ka dawo bama makarantar kwana ce. A Hankali tunaninta ya gangaro kan yadda rayuwar karatunsu take. Kowa kusan gwanine za'a ce cikin daliban,tana hangen yadda kowa ke zagewa ya kuma dage don ganin ya kai maqurar iya karatunsa,ta tuna yadda a kowanne darasi ta dinga baza idanu,nan da wani lokaci idan batayi da gaske ba zata zama cikin sahun dalibai na kashin baya,wadanda kowa zai fahimci qarancin ganewarsu. Wannan tunanin ya sanyata hantsilowa daga gadonta,wani abu yana dasa mata qaimi cikin zuciyarta,tana jin ba zata lamunci faduwa ko rashin iyawa ba. Ta saka hannu gefan gadonta inda qaramar locker dinta take ta fidda jakar makarantarta,ta zazzage dukka litattafan da a yau sukayisu,ta soma budesu daya bayan daya tana dubawa. Da qur'ani ta fara,ta dinga hada baqin yana guduwa,ta dinga qoqarin maimaita shafukan daidai,a haka ta kashe awa daya kusan da rabi kafin taji ta fara kama hanyar karatunta bisa qa'ida. Bata sare ba bata kuma gaji ba,tayita nacin maimaitawa har sai da taji ya zauna mata a harshenta,ta tabbatar zuwa gobe koda za'a ci gyaranta kadanne. Kowanne subject sai da tayi maimaicinsa,tun bata fahimtar abinda take ta faman karantawar har sai da taji kamar qwaqwalwarta tana budewa ne a hankali. Sanda ta duba agogo awa uku kacal ya rage lokacin tashinsu dsga bacci yayi. Sai ta zauna tsakiyar gadon tana son tuna addu'a daya daga cikin tarin addu'o'in da taji suna yi,yayin tashi a bacci,kwanciya bacci,cin abinci,shiga bandaki,shiga aji da komai ma na rayuwar daliban makarantar. Ba wani abu guda da taga wani dalibi yayi bs tare da yayi addu'a ba,tamkar ma ta shiga jinin jikinsu ne sun kuma saba. Duk sallolin da akayi yau din cikin jam'i abinda bata taba yi ba tsahon rayuwarta......duk sanda aka idar suka hada baki duk yawansu suna addu'o'in da akeyi bayan idar da sallah,sai taji wani sanyi dadi da nutsuwa suna shigarta,sai taji wani sukuni yana ratsata,har sai taji kamar ma kada lokaci ya cika, kamar kada su daina addu'ar. Waiwayawa tayi ta dubi su fatima dake bacci abinsu. Cikin ranta ta ajema kanta zasu zame mata mudubi in sha Allah cikin rayuwar makarantar,zata kuma yi qoqari tayi catching up na dukkan abinda suka tsere mata. Abunda ya bawa su fatima mamaki a yau ita ta tashesu maimakon jiya da sune suka tasheta,kafin kace meye ta kammala komai da sukeyi kafin fita masallaci sallar asuba. A bakin hostel din suka cimmata tsaye da metron asabe tana gaidata "Ina fatan baki da wata matsala ko?,idan kun kammala karatu kina da sha'awar wanka kafin ki wuce aji kiyimin magana saiki shiga kiyi" "Ba komai,zan jira har lokacin da kowa yakeyi,idan ban samu toilet ba zan miki magana sai nayi s gurarenku din" ta amsa mata tana rungume da qur'aninta cikin wata murya me sanyi. Da kallo metron asabe ta bita,bata taba zaton zata sameta da sauqin kai har haka ba,bata taba kawowa cewa zatayi saurin daukan shawararta ba,sai gashi daga jiya zuwa yau kacal tana qoqarin kiyaye dokar makarantar. Yadda ta dinga nacin bibiyar kowanne harafi da ake qara musu ya sauqaqa mata qwarai. Kafin akai ga tashi sai gashi ta iya karatun fes kamar kowa. Dadi sosai ta dinga ji cikin ranta,har kuma hakan ya nuna a fuskarta,duk da ba murmushi takeyi ba amma fuskarta a washe take sarai. Gurin sharar compound na hostel dinsu kuwa kamar kowa ta karbi tsintsiya. Metron asabe na cewa ta bari amma tace zata iya. Tana sharar tana mamakin meye dalilin metron asabe nason dauke mata wasu wahalhalu na makarantar ne?,me yasa take kawo mata hanyoyi sauqi da sauqaqawa?,ahalinta ne fa da hannunsu suka danqata a makarantar,komai na ama bisa manufa da tsari yake,ta tabbatar ba a banza ama ta aikata hakan ba,ba shakka akwai dalili,kuma akwai hujja. Koma meye ita dai ta barma ranta zata rayu kamar kowa,tayi alwashin zatayi irin rayuwar data samu cikin makarantar,zata rungumi kalar sabuwar K'ADDARAR da ta risketa. Can kuma qasan ranta takejin kamar dai ama ta kawota ne don tasan rayuwa?,kamar dai ama ta kawota ne don ta fahimci bayan duniyar da take rayuwa a ciki akwai wata duniyar ta daban?,kamar dai ta kawota ne saboda wasu abubuwa masu yawan da ita kanta bata gama fahimtarsu ba. Tana ankare da yadda labour prefect huda keta wani fusge fusge da sanya mutane aiki cikin izza da gadara. Duk wanda ta kira ita da team dinta da sassarfa yake isowa ya kuma zube yana kiran "Aunty gani" ladabi ne wannan na makarantar da dole kowanne dalibi ya koya ya kuma ginu akai,amma batajin zata iya zube musu har haka,hasalima batajin tana da LOKACIN shiga sharafinsu.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 34 Lokacin data sake kame kanta tare da takatsantsan da lamarin huda da sauran maqarrabanta ita kanta sai tayi mamakin kanta,har batasan sanda qaramin murmushi ya subuce mata ba abinda ta jima bata yishi ba,wai yau ita sultana ita ke kaucewa rigima da wasu,ita sultana da batajin tsoron rigima da ko waye,mace ko namiji,yaro ko babba,bata tsoron tunkararka ko qaddamar maka,lallai giwa tayi lafiya ta fadi qasan zuciyarta tana shafar gefan fuskarta,to ko hankali ta soma yi?,ta yiwa kanta tambayar data sanyata sakin wani murmushin. *****A hankali A hankali cikin wani irin yanayi sauyi na bazata ke ruskar rayuwarta. Ingatacce kuma gamsashen sauyin da yayi nasarar taba ainihin ruhi da zuciyarta. Cikin ba zatar da ita kanta bata sani ba ta tashi daga SULTANAn bibi,sultanan aba sultana ta nijer zuwa sultanan Nijeria,sultanan hassan Ibrahim gwarzo,sultanan fateema Ahmad da kuma ameena aleeyu. Ba wanda take bari ya huta tsakanin fateema Ahmad da ameena,kowannensu ta samu ta riqeshi to tabbas sai yayi mata qarin dukkan wani kwantan karatu da aka tsere mata,tashin cikin dare ya fara bin jikinta,a lokacin da kowa ya sanya haqarqarinsa yake bacci.....a lokacin take tashi bita da tilawar katatuttukanta. Cikin kowanne mataki na karatunta batajin akwai ya kamar ALQUR'ANI. Tana jinta wani fresh a sanda take karantasa,tana jin wani softness cikin zuciyarta,tana jin kuma nutsuwa tana shigarta,shi ya sanya cikin lokaci qanqani ta kamosu ta kuma hade da izifin baya da suka wurwuceta,abinda ya baiwa kowa mamaki,sauri da kaifin basirarta,duk da a farko sun mata kallon hadarin kaji,kallon dalibar da bazata wani basu matsala ba. Tana da rivals da yawa a ajin,matan da sukaci buri suke ganin sune na gaba gaba wajen samun yarda da amincin malamansu,sai gashi cikin dare daya wata baquwar haure na shirin yi musu shalll. Wata irin murya Allah ya mallaka mata me dadi,sai take sake qawatuwa da sautin karatun qur'ani da wani irin daddadan sauti. Bata da lokacin kowa,ba wanda take bi ta kansa,bata kuma hulda da kowa idan ka debe fateema da ameena. Muddin kaga hirarta sosai to da sune,idan kaga motsawa kumatu da labbanta to da ameena dinne,sun dinke sun zama kaman wasu 'yan uwa, dabi'a da yanayin sultana din su ke burgesu,suna mata kallon wadda gayu gata da shagwaba suka yiwa yawa shi yasa komai nata ya fita na dabanne. Kowanne kwanan duniya sai metron asabe ta tambayeta ko tana da wani buqatar?,amsarta daya ce A'ah,a nata tunanin tanason gwadawa ama zata iya rayuwar data zabar mata,zata kuma wanzuwa a kowanne bigire ko muhalli da rayuwa ta gangarata cikinsa. *_VISITING DAY_* Tun daren jiya daukacin daliban makarantar ke cikin farinciki da walwalar ganin ahalinsu a goben,kamar yadda fateema da ameena aleeyu suka bi sahun sauran dalibai. Safiyar yau din kowa shiryawa yakeyi don 'yan gidansu su ganshi fes..... sultana na zaune kusan sai da kowa yayi nisa wajen nashi shirin,wasuma suka soma fita sannan ta shiga tayi nata wankan da yau ta zabi tayi cikin tsaftatattun toilets dinsu ba nasu metron asabe yadda ta saba yi ba. Komai nata cikin wani sanyi da nutsuwa ya koma,babu sultanan nan ta anihi,haka ta tsaya gaban gadonta ta shirya kanta cikin house wear kaman kowa,bayan ta daure jelar manyan kitson da fateema da ameena sukayi taron dangi sukayi mata,saboda sulbinsa da tsahonsa ya sanya ba kasafai take kitso ba,koda anyim ma baya dogon zango yake warwarewa. Tayi kyau sosai,don sabbin house wear ta sanka,dinkin kuma ya zauna sosai ya qara fidda tsaho data qara,saidai kuma tadan fada kadan wanda hakan baya rasa nasaba da sabuwar rayuwar da take qoqarin daidaita kanta taga ta hauta bisa tsari. "Sultana mohmoud mayak'i" aka maimaita kiran sunanta har sau uku. Waiwayawa tayi tana duban me kiran nata,senior dinta ce cikin wadanda zasu fita makarantar a shekarar da ake ciki "Kina da baqo" ta fadima sultana din tana juyawa. Turarenta ta miqa hannu da sauri ta dauka ta fesa ta maidashi,sannan ta zura house shoe dinta ta soma tattakawa cikin wani irin zumudi tana ratsa hostel din nasu "Tacan zaki zagaya" dalibar ta fadi tana mata nuni da hannu sannan ta wuce gararin gabanta. Sosai take takawa da zumudinta shiyyar da ta nuna matan,qasan ranta cike fal da dokin ganin ama da aba,tasan kuma zaiyi wuya ace bibi batazo mata ba,BATOUL da BENAZEER......taji an kira mata sunan yaran daga can qasan zuciyarta,ta lumshe idanunta murmushi na subuce mata,wata irin mahaukaciyar kewar yaran ta taso ta lullubeta,karon farko daga can qasan ranta taji wani irin tausayinsu ya saukar mata. Tsaiwa tayi cak ganin tana ta cusa kai area din da babu motsin kowa babu kai kawon kowa. Ta tayi ta tsaya cak,wai mema dalibar tace mata ne "Kinyi baqo" ta tuna da abinda tace "Baqo......baqi...." Sai taji kwanyarta ta rikice. To ko aba ne shi daya ya samu zuwa?,idan hakane ai ba za'a barshi ya qaraso har gate na biyu na sashen mata ba,akwai askar da basa bari maza su wuce gurin,kuma bata nan ya kamata ya tsaya ganin nata ba. Wani mummunar bugawa zuciyarta tayi. Cikin jini tsoka da jikinta taji kamar ana fusgar hankali da kuma numfashinta sakamakon shaqar wannan qamshin.......wannan qamshin dai da hanci zuw qwaqwalwa ba zasu iya gaza fayyaceshi ba,wannan qamshin dai da yake da taushi dadi da laushi......amma a nata hancin kama yakeyi mata da qamshin MUTUWA.....Tabbas inda mutuwa tana da wani qamshi na daban......wannan qamshin shi ya dace a baiwa wannan sunan. Waige waige ta fara yi jikinta yanason fara rawa, hankalinta kuma nason yin qaura daga gangar jikinta "Ki nutsu,ba kowa a wajen nan,ba shi daya aka qerowa turaren ba,bashi daya kaf duniya yake siyan turaren ba......ki nutsu kada ki ruda kanki sultana" zuciyarta ta fara rada mata cikin kunnuwanta yayin da qirjinta ke wani irin bugawa da tsananin qarfi har numfashinta yana rarrabewa. "Sultana mohmoud mayak'i" ta sake ji an kirata,kiran sunan da ya hautsinata gaba daya ta waiwayo da wani irin sauri. Wata dalibar ce cikin daliban da suke ajin farko wato J.s one ke nufota. Hannunta riqe da wani babban abu da ya yima sultana zubi da kwali. Har ta iso gabanta sultana na dubanta qirjinta kuma bai fasa dagawa ba,sai ta miqa mata kwalin tana kallonta bayan ta rusunawa sultana din kamar yadda yake doka ne na makarantar dole na qasa ya rusunawa babba "Wai gashi" bin kwalin dake hannun yarinyar tayi da kallo sannan ta maida dubanta ga fuskarta tana tattaro ragowar miyau din bakinta,da qyar ta tambayeta "Wai inji wa?" Kai ta karkada yarinyar "Ban sani ba,nima wata daliba ce ta bani tace itama wata ce ta bata tace a baki" fuska tadan motsa kadan,abun yadan daure mata kai,tayi kaman ba zata karba ba,to amma yadda yarinyar ke rusune sai taga bai kamata ta barta a haka ba "Ya sunan wadda ko wanda ya bada?" "Nima na tambaya tace bata sani ba,wancan din tace me bada saqon sunanki kawai ya kama yace a baki" "Kodai aba ne yake sauri bazai iya tsaiwa ba ya bayar a kawo?" Wannan tunanin ya sanyata miqa hannu ta karba,yarinyar ta juya da sauri sauri tana barin gurin don kada azo mata ba'a sameta ba,sai itama sultana din ta soma takawa tana riqe da kwalin tana barin wajen zuwa nana aisha hostel,har a sannan hancinta yana jin qamshin nan data yiwa maqurar tsana*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 35 Tana tafe a hanya tana juya kwalin,ba qato bane hakanan ba qarami ba,yana da matsakaicin girma,amma kuma yana da dan nauyi. Kai tsaye ta koma hostel dinsu,sanda ta isa dakin da yawa an yoye,kowa ya fita waje,wasu gurin family dinsu,wasu kuma suna jiran tsammanin isowar 'yan uwan nasu. Gefan gadonta ta zauna a nutse,ta aza kwalin saman cinyarta ta fara budeshi. Sannu a hankali ta kammala yage takardar jiki tsaf,wani irin kwali ne na musamman tamkar qaramin akwati,sai daukan idanu yakeyi da wani irin santsi da tambarin dolce and Gabbana ko ina a manne a jiki. Doki ya kamata,muddin wannan kyautar daga hannun aba take to ko shakka batayi tafiya yayi ya kuma tuna da ita "Allah sarki ubana,maganin kukana" ta furta hawayen qaunar aba na cika mata idanu. Cak ta tsaya tana duban kyaututtukan da aka shirya cikin box din. Tarin tsagwaron chocolates,dukka kalolin wasu chocolate da takesha babu wadda ba'a zuba ba a cikinta. Wani siririn agogo da take da tabbacin zaiyi wuya chain dinsa idan ba gold bane a jiki. Turaren da take amfani dashi sanda tana sultana dinta wanda a yanzun ma tuni ta sauya zuwa wani kalar daban. Biro da wasu qananun notebook masu masifar kyau da tsari,sai wata memo itama daban da zata baka damar tsara komai na rayuwarka da date da komai,sai wani greeting card da duka rubutun jiki layi qwaya daya ne tal "Best wishes" kadai ke rubuce daga tsakiyansa. Bin budadden box din kawai takeyi da kallo,cikin jikinta ta dinga jin wannan kyautar ba daga hannun aba ta fito ba,batama dace da ace daga aba din take ba,to anya ba batan suna sukayi ba?,tunda dai daliban makarantar ba suna da yawa qwarai,kuma bazaiyiwu kaf makarantar ace ita daya ce qwallin qwal me suna sultana mahmoud ba. Juya bayan katin tayi,a nan ta samu amsar tambayarta,cikakken sunanta harda na qasarta ne rattabe a bayan,hakan yana nufin me aiken yanason bata tabbacin saqonshi ne. Wani abu me kama da bacin rai ya biyo bayan mamakinta,ta sake juya katin ko zataga alama koda ta sunan me saqonne amma babu,tsoro da shakka suka kamata,daidai sanda ameena aleeyu ta shigo da sassarfa "To kizo ga duka 'yan gidanku nan gaba daya,har mun gaisa da aba ma,ama nada maqurar kirki,atta da almu suna yanayi dake" ameena din tace da sultana cikin nuna zallar zumudi. Da sauri ta tashi hae box din dake saman cinyarta ya watse a wajen,sam batabi ta kansa ba tayi hanyar waje duk da tana jiyo ameena na fadin "Kinyi barna,wannan agogon me tsada .......Allah yasa baki fasa glass dinshi ba". Tana tafiya zuciyarta na nanata tambayarta daga ina wannan gift din ya fito?,indai har ga aba yazo to waye ko wace ta aiko da gift din?. "May be dai still aba dinne" zuciyar dake neman nutsuwarta ta fada tana bata tabbaci. Tun daga nesa data hangosu murmushi ya subucewa fuskarta,kasa jurewa tayi ta isa garesu a hankali sai ta dan saka da sassarfa,ta qarasa ga ama ya fada jikinta tana riqeta da kyau,bakinta har rawa yakeyi wajen fadin sunanta "Ama.....sannu da zuwa ama" "Wato ama dinki kawai kika gani ko?,ni baki ganni ba?" Muryar bibi ta doki kunnenta. Waiwayawa tayi da sauri tana duban bibin,sai ta saki ama ta nufeta itama ta fada jikinta tana qanqameta "Ban lura da bibi na ba,bibi tun daga nijer kikazo ganina?" Ta fadi tana murmushi. Harara ta balla mata "Kuma gashi an yanqwanani ko ganina ma ba'a yi ba?" Ta fadi tana yatsina baki,saidai kuma qasan zuciyarta na mata wani irin sanyi saboda sauyi muraran da take gani tattare da sultanarta. Baya taja tana duban bibin "Ni ya kamata nayi fushi bibi,kina can kina qiba abunki aba yana baki kayan dadi,ina nan kin barni da abinci da horon boarding" ta dan taba tsokanarta wanda abune da kusan dukkaninsu kunnuwansu sun manta rabon da su jishi daga bakinta,sai suka sanya dariya,wanda muryar aba ta fito a ciki,sai a sannan ta ankara dashi shima,abinda ya sanya tadan yi qas da kanta ta kuma nufeshi da hanzari. Zamewa tayi ta tsugunna a qasa tana gaidashi "Barka da warhaka aba,ina kwana?" Ba wanda bai dubeta ba yadda take komai cikin nutsuwa da tsantsar girmamawa. Yana dan saki murmushi ya amsa mata "Lafiya qalau sultana,tashi a qasa kada ki bata uniform dinki,ga abun zama can an shimfida mu qarasa" tanja ce ta riqe hannunta,saita waiwaya tana duban tanja din "Kina Nigeria ko kina nijer tanja?" Ta tambayeta bayan ta gaida tanjan itama cikin rusunawa,abinda sultana din bata taba mata shi ba koda wasa,kai kwata kwata ma ba zatace ga sanda sultanar ta taba gaidata ba,ba zata iya tunawa ba. "Inaaa......ina nan gurin iyayen dakina,in tafi nabar 'yan biyu?,ai bazan iya ba" ta amsa mata tana murmushi. Sai a sannan hankalinta yakai kai,bataga benazeer da batoul ba,idanu ta shiga warewa can qasan zuciyarta tana jin shauqin ganin yaran,amma ko me kama dasu bata gani ba. Duka sai taji zuciyarta ba dadi,ta dinga nacin kallon inda goumar yake amma bataga alamun suna tare ba,har goumar din ya lura da yawan kallon da takeyi,sai ya saki murmushi ya watsa mata hannuwansa,qasa qasa kuma yadda babu wanda zaiji yace da ita "Me na satar miki ne kuma yau?,mutumin da ko kallon fuskarsa ba'a sonyi yau shi aketa kalla?,ki bude baki kawai ki cewa ama ina 'ya'yanki ko?" Harara ta watsa masa gabanta yana faduwa,salon maganarsa sak yaa maina,kusan wasu abubuwan nasu suna bala'in kamanceceniya da juna,kamannin fuska ne sam Allah bai sanya sunyo daya ba. Qaramin tsaki taja tana dauke kanta ta maida ga sashen su ama daketa bata labarin abubuwan da suke wakana bayan batanan,sai muryar goumar ta motsa cikin dariya "Allah bibi wannan 'yar jikanyar taki ladabin qarya tayi muku,qanzo ne ya sanyata yin laushi,bata canza hali ba ashe rashin kunyar nan tana nan,yanzun nan ta gama min tsaki harda harara" ya qarasa fadi yana dariya sosai. Harara bibi ta watsa masa "Qaniyarka sarkin sharri,ta ina ta hararekan dukkanmu muna nan idanunmu suna gani?" "Wannan idon naki ai ya kusa rubewa,don inda kina gani sosai da a yanxun kinga wani abu da ni kadai nake hangowa" ya furta maganar yana kallon wani guri daban. Ba tare da Bibi din ta waiwayo ba tace "Kaji dashi ja'iri" saita jawo wani mazubi ta miqawa sultana,wanda ba komai ciki sai kayan ciye ciye da tasan tafiso. Cikin wata irin sassanyan nutsuwa ya maida wayar tashi me bango biyu ya manneta guri guda ya rufeta. Qirjinsa da zuciyarsa tana masa wani irin nauyi,da gaske goumar yakeyi bazai taba ganin yaran ba?,da gaske yake,yau din rana ce da zata iya sake nesantashi da damar sake ganin kowa da komai da ya shefeshi ko ahalinsa. Yayi kwadayi qwarai wajen sakasu a idanunsa,yaso ya samu wannan damar koda zata kasance dama ta qarshe a garesa,tunda bai san yaushe ba?,baisan sai wanne lokaci ba. Wannan babbar dama ce a gareshi da muddin ta gushe masa baisan sai yaushe zai sake samun wata damar makamanciyarta ba,zaiyi komai zaije zai kuma aiwatar dukka domin sa,domin ahalinsa. A hankali ya isa dab da motar da mutumin da idan baka matso kusa dashi qwarai ba zaka tsammaci mutum mutumi ne. Yana isowar ya sanya hannu ya bude masa bayan motar,ya zura gangar jikinsa cikin wata irin kasala da galabaita tamkar wanda yayi watanni yana aikin kauda duwatsu ba tare da ya huta ba. Wata wawiyar ajiyar zuciya ta subuce masa,ya lumshe kyawawan idanunsa yana jin kamar ajiyar zuciyar zata fita ne tare da zuciyar dake qirjinsa,ya maida bayansa jikin kujerar yayi relax yana jin yadda zuciyarsa ke tsananta bugawa sanda motar ke gangarawa tana barin wajen. Har ta rako su aba bakin mota,suka kuma fidda komai da komai da suka kawo mata cikin zuciyarta bata kasa juya batun box dinnan ba,daga ina yake?, itace tambayar da taketa nacin nanatawa. Tana nan tsaye har suka kammala shiga motar. Ama ya sauke glass din bangarenta ta miqa ma sultana wani box. Kallonsa tayi sannan ta sanya hannu ta amsa. Madararta ce,madara mafi soyuwa a gareta,madarar da tana begenta amma kuma tana nisantata da rayuwarta saboda tuna mata da takeyi dashi "Gashi inji benazeer da batoul da baki tambayesu ba,sunce suna gaidaki" wata irin kunya ce ta saukar mata,tanason tambayarsun amma batasan ta yaya zata fara tambayar tasu a gaban ama da aba din ba,uwa uba ga bibi a gefe,ga kuma dan sanya ido goumar "Ace ina gaidasu" ta fada da sassanyan muryarta "Basa amsawa,sai da aka roqa musu" goumar ya fadi cikin salon tsokana. Harara kawai ta samu damar binsa dashi saboda tashin da motar tayi bata samu daman maida masa raddi ba. Duk wata kujiba kujiban zuwan masu visiting lokaci yana yi aka rufe gate din makaranta,doka kuma taci gaba da aiki. Suna saman gadonsu kowa na kintsa wajensa da gyara kayayyakin da aka kawo masa daga gida,dakin nasu fal kaya saboda dukkansu kusan daga gidan iko da wadata kowacce ta fito,babu wadda ta fito daga qaramin family. Da wuri sultana ta gama komai,tana daga saman gadonta ameena aleeyu ta qaraso da box dinta ta miqa mata "Ga box dinki nan" binsa tayi da kallo tana jin shakkar amsa,sai ta maida dubanta ga ameena "Bansan waye ya aiko dashi ba,ki ajjiyemin kawai zan nema maishi saina karba" "To ya wuce saurayinki?" Ta tsokaneta tana dariya. Dukanta maganar tayi har tsakiyar zuciyarta,sai ta daga kai tana kallonta gami da jefa mata harara "Ba saurayi ba dattijo" ta fadi cikin hushi. Yanayin yadda tayi maganar gauraye da harshen qasar nijer cikin kuma fushi dukkansu ya basu dariya,bata sake ce musu komai ba ta janye qafafunta zuwa gadonta ta juya musu baya. Iyakar tunaninta kaf ta gaza canko wanda zai iya aiko mata da saqon "To kodai goumar ke yimin wasa da hankali?" Tayi tunanin haka daga qarshe,sai ta cije lebanta tana jin qamshin gaskiyar hasashenta. Tabbas da ta tuna hakan kafin su tafi saita yayyaba masa magana,ta fuskanci kamar yana yawan son yiwa rayuwarta shishshigi. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 36 **********Sannu a hankali rayuwa taci gaba da tafiyar mata,tana sake hankali tana kuma sake fahimtar me ainihin rayuwa ke nufi kadan kadan. Sosai kwanyarta take budewa,a hankali kuma ta fahimci gatan da ama tayi mata data kawota makarantar. Kafin takai ga zuwa ss3 ta zama wata sultana ta daban. Azkar ya kama bakinta ainun,karatun qur'ani da wata nutsuwa dake nuna sanin haqiqanin rayuwa. Tabbas! Ilimi wani irin haske ne da babu irinsa,wani abu ne dake busawa zuciya da rayuwa wani ruhi na musamman. Hatta da kamanninta sun sauya,sun cika da wata irin nutsuwa da wani sirtaccen kyau nata dake boye. Idan ka kalleta a sannan babu abinda zakaji cikin zuciyarka dangane da ita sai tsananin burgewa,saboda wata kamala annuri da kwarjini da ilimi ya zuba mata,komai nata sai ya zama cikin nutsuwa da kuma kamun kai. Kalaman bakinta sun canza sosai,hakanan mu'amalarta,saidai kuma tun wancan sanyin da tayi.....tun wancan sauyawar......tun a wancan lokacin har zuwa yanzu sai ta zama me matuqar sanyi,miskila mara yawan surutu hayaniya ko kuma kwarafniya kwata kwata. Tana S.S3 ama ta saka su benazeer a free nursery,surutu da wayonsu ya isa,wani irin wayo ne dasu da yafi na shekarunsu,duk da batoul nada kalar nata miskilancin,amma tun kafin shekarunsu su fara nisa kamanceceniyar halayya wajen yawan surutu rigima da rawar kai na sultanan can baya benazeer ta kwafe tsaf!,wannan ya sanya ama tafi maida hankali akan benazeer din sosai,tanaso dukka wadannan halaye da Tayo gadonsu su kasance kan tsari da kuma cikakkiyar kulawar tarbiyya. Saboda kwadayin ingantar tarbiyyar yaran ya sanya gaba daya ama ta daina tunanin komawa nijer,tafison a nan din inda suke suyi tasu quruciyar da wayon,saboda itace babbar shaidar banbancin tarbiyyar da qasashen biyu ke dashi. A shekararta ta qarshe a makaranta ta yiwa kanta gata me tarin yawa. Tayi joining classes da akeyi na musamman bayan wadanda suka zama wajibi. Litattafai ake musu na addini masu yawa,zazzafan karatu ne da ya sanya da yawa daliban basu fiya joining ba sai masu wayo da masifar nacin so karatu irin sultana. Yadda zazzafar qiyayyar karatu ta juye mata zuwa zazzafar soyayyar karatu tana bawa ama mamaki. A duk sanda sukayi hutu tazo gida yakan zamana kamar ba hutu ta samu ba. Duk bayan kowacce daqiqa tana maqale da litattafai,wani lokaci hadda takeyi wasu lokuta kuma tilawa. Ta samu hadisai sosai,wasu ta haddacesu ne,musamman wadanda keda alaqa da mu'amala da kuma rayuwa,wasu kuma a yayin da aka karanta mata ta iyasu a rubuce kuma tana tsintar wasu tana amfana dasu. Kosu benazeer bata basu lokacinta kamar yadda take bawa litattafanta. Sai ya zamana ba wata shaquwa bace can can a tsakaninsu da ita. Da ama suka budi idanu,ama itace mommansu,ita sultana AUNTY kawai suke kiranta,kuma suna mata kallon auty dinsu ce,saboda tsakaninsu hukuntawa ne da tsawatarwa idan za'a yi ba dai dai ba tamkar na qaramin yaro da babbar yayarsa. Watannin qarshe da suka rage musu a makarantar,dab da zasu fara jarabawa sukayi saukar alqur'ani me girma. Kyawawan qira'o'i dukka guda bakwai din da muke dasu babu wanda bata iya ba. Karatu take tartilan babu gargada,babu bata,zakayi tsammanin ta jima da saukeshin a yanzun maimaici kawai takeyi. Tana cikin zaqaquran dalibai guda goma na farko da aka fidda cikin ajinsu. Sanda suka fara jarrabawa dukka tunaninta sai ya sake fadada akan qara nisan zangon karatunta,batajin zata zauna haka,yanzunne ta soma jin gardin ilimi,ashe ilimi dadi ne dashi har haka?,ashe muddin kana da ilimi kuma kana aiki dashi basai an zauna ana fama wajen gyaraka da saitaka ba?. Sau tari idan su ameena aleeyu sukaga tana zaune guri daya tana murmushi sukan cika da mamakin meye yake sata nishadi yayin kadaicewa ita daya?. Murmushin ta kan fita ne a duk sanda ta tuna da quruciyarta,ta tuna da rayuwarta a niamy,ta tuna irin tabara da rashin hankali da zallar wauta data tafka,yadda ta qaunaci rawa,xuwa party zuwa birthday kamar hauka,a yanzun idan dukka ta tuna wannan sai kunya ta kamata. Ta sake tabbatarwa da lallai komai lokaci gareshi,komai kuma yana zuwa ya shude ne cikin rayuwa tamkar a allon majigi. Abu guda daya ke zuwa ya tsinke kyakkyawan zaren wannan tuna baya nata,idan ta tuna da MAINA. Komai yana shafewa a zuciya da ruhinta,komai yana shafewa daga tunaninta amma banda abu daya,banda MAINA banda yadda ya yiwa rayuwarta da mutuncinta dirar mikiya,banda yadda ya wargaza mata kyakkyawar rayuwa yabar mata wata rubutacciyar qaddara a rayuwarta,ya kuma shura qafafunsa ya bace battt daga sararin duniya tamkar zuwan walqiya da daukewarta. Komai ya sauya cikin rayuwarta amma wannan tabon yana nan a zane radam......wannan tsumammiyar qiyayyar tana nan a rubuce dara dara bata kauce ba,daga qarshe takan buge da xubda hawaye me tarin yawa. Takan jaye jikinta daga cikinsu fateema Ahmad duk lokuttan da suke hirar samarinsu,soyayya ko hirar data shafi 'yammatanci,saboda a sannan kowacce ta soma cika mace,takai kuma ganiyar 'yammatancinta. Cikin jiki da ruhinta takejin kwata kwata bata cikin sahunsu,to meye zai zaunar da ita a cikinsu ana hirar da ba layinta ba?. Su kuma dukkan wannan sun azashi ne cikin zallar miskilanci irin na sultana,son zaman kadaici da zaman shuru,kamewa da rashin son hayaniya. Takan saki siririn murmushi da jerarrun fararen haqoranta a duk sanda suke mata tsiya "Kin fiya shuru shuru wallahi,ke ba dama ki zauna ayi hirar arziqi dake." "Baku riski sultana a sanda take sultanan ta ba,kun samu sultanar nijeria ne,sultanar hassan Ibrahim gwarzo,sultanan ama,auntyn benazeer da batoul.......ba sultanan nijer ba,sultanan bibi da aba,da hirar tsiya ma duka sai anyi,saikun nema wajen fakewa daga gareta" takan raya haka ne cikin zuciyarta. Ta riqi sallah sosai,ta kuma koyi azumin litinin da alhamis a gida ko a makaranta,tun daga sanda suka karanta hadisin dake bayanin falalar azumin litinin ko alhamis basu taba ruskarta tana da cikakkiyar lafiya ba tare da tayi azumin nan ba. Saidai har yanzu jikin nan yana nan ba wata qiba,amma kai tsaye ba zakace a rame take ba,sai tsaho data qara,duk wata halitta tata ta qara cika,kyawun nan na cikakkiyar buzuwar asali,jinin NADEEYA MUHAMMAD MAYAK'I ya hudata sosai,ya zamana har hirarta akeyi sashi sashi cikin makarantar,domin kaf cikar makarantar da batsewarta babu wata diya mace data isa ta tsaya a tudun mizanin kyau tare da ita,wannan ya sanya take sake kame kanta da kuma fita a dukkan shirgin da ba nata ba. Sai kuma Allah ya zuba mata farinjini da kwarjini wajen juniors,bata da mugunta ko kadan,hasalima cikin sabbin shigowar nan duk yarinyar da ta gani ne rawar kai iyayi da surutu sai taji tana tausaya mata,wani lokaci kuma ta saki murmushi don suna tuna mata da shekarun baya da suka shude mata. *_GRADUATION DAY_* Rana ce me matuqar tarihi cikin rayuwarta,ranar data sanyata xubda hawaye me yawa,ranar data sakata dana sanin zaman da tayi ba karatu a wadancan shekarun,ranar kuma data sakata a godiyar Allah me tarin yawa daya fiddata daga duhu zuwa haske. Taro ne akayi gagarumi na saukar dalibai tare da yayesu,tana cikin dalibar farko da aka kira aka karramata har hawa uku gaban dubban al'umma,gaban familynta,gaban mutanen da suke tamkar iyaye a wajenta,gaban mutanen da suka debe tsammanin zamantowarta a yadda take a yanzun. Duk inda ta motsa kyaututtuka ne na yabawa da karramawa. Da yawa mutanen dake wajen da sukasan family din MAYAK'I sun mata kyaututtuka na alfarma,har sai da goumar ya taso ya dinga tayata karba. Data dawo mazauninta ta zauna kasa jurewa tayi,taja hijab dinta ciki ta boye fuskarta tana kuka. Abun mamakin sai batoul ta kalli benazeer cikin kwabe fuska kaman zata saki kuka "Benz(haka take kiranta don bata iya kiran full name din ya mata tsaho da nauyi),waye yasa aunty kuka?" Waiwayowa benazeer din tayi ta zubawa sultana idanu,itama sai ta kebe baki kamar zata sanya kukan tana duban goumar "Oncle.......ko itama aunty ta tuna da daddynmu da kace yayi tafiya?" Sosai maganar ta doki qirjin sultana,har batasan sanda ta fidda rabin fuskarta ba tana duban goumar. Kamar dama ya shiryawa hakan,shima ita yake kalla,suka zubawa juna idanu na wasu lokutta suna kallon kallo. Tanata hadiye bacin ranta da maganganun da takeson gaggaya masa saboda cikin bainar jama'a suke. Wato kebewar da yake da yaranta har gaya musu yakeyi suna da wani daddy da yayi tafiya?,waye ya sashi?,shi awa?,meye hadinsu da daddyn da yake musu maganarsa?, tabbas ba zata qyaleshi ba,sai tayi warning nasa,kada ya sake bari wannan maganar ta shiga kwanyar yaranta,bata buqatar hakan. Wannan maganar kawai ta dauke hawayen fuskarta,sai suya da zuciyarta keyi mata tana fakon goumar tana jira su samu matsawa daga wajen ta amayar masa da abinda ke cikin ranta. Bata samu wannan damar ba sai da suka tashi komawa gida,bayan taro ya watse,makaranta ta sallamesu sai kuma zuwa karbar result na exam dinsu. Ta gama koke koken rabuwa ita dasu fateema Ahmad da ameena aleeyu,aminan qwarai da ba zata taba mancewa dasu ba,sunyi exchanging phone numbers da full address nasu,har Adress dinta na nijer dukka ta basu saboda batasan me rayuwa ta tanadarwa gobenta ba, al'amuranta bata fiya basu amana ba,ta fahimci caccanjawa sukeyi a duk sanda sukazo hakan,koda yake umarni ne daga rabbussamawati. Ita da aminata,najma da yasmine su ya dauka a motarsa wadda bai jima da siyenta ba bayan kama aikinsa baya bayan nan da kammala karatunsa. Kusan duk wani hali da dabi'a na maina yana dasu. Har rabon motoci aba ya yiwa samarin cikin dangi yace bazai amsa ba,yafison ya fara hawa wadda ya siya da guminsa. Kusan aqidar maina ne,neman nakai,ya tsani a masa alfarma,ya tsani ya rabu da wani ya dinga cin albarkacinsa,wannan dalili ya sanya har yabar gida baida motan hawa na kanshi,duk da cewa akai akai yana bisa hanya duk kusan sati ko sati bibbiyu tsakanin niamy da marad'i. Ta fahimci akwai wata kyakkyawar alaqa tsakaninsa da najma,saidai a yanzun ba komai take magana akai ba shi yasa batace komai ba,amma tunda su aminata sukazo ta karanci akwai gulma fal bakinsu,bata dai tsaya ta basu lokaci bane,amma ta tabbatar sai sun fesa mata koda ba zata saurara ba. Kyawawan 'yammatan buzayen da suketa daukan hankulan jama'a suka jera reras su hudu bayan tashin motarsu aba suka wuce zuwa inda goumar ya ajjiye motar tasa. Hirar suke amma sultana bata fiya sanya musu baki ba,don burinta kawai ta fesarwa goumar abinda yake cikinta. Akwai takadda guda daya ta sultana da ya tafi karbowa don haka suka dan tsaya suna tattaunawa daga bakin motar tasa kafin ya iso ya bude musu. Yaro ne da duka duka bazai wuce shekara sha hudu ba ya iso gurin. Fari ne siriri,yana da dan tsaho kadan,yanayin zubin fuskarsa kadai zai shaida maka bafulatanine usul. Sanye yake da wata dakakkiyar shadda sai maiqo takeyi fara qal,kanshi sanye da jar dara sosai irin ta ainihin bare bari. Kana dubansa kasan daga gidan gata ya fito,kuma alamun jikinsa da fatarsa na nuna ainihin jin dadi da yake ciki. A gabansu ya tsaya yana sallama fuskarsa a sake. Dukkansu suka daga kai suna dubansa,aminata ta amsa masa,sai sultana ta maida kanta tana daidaita qananun litattafan azkar dinta data qarasa debowa daga drawer dinta ta jikin gadonta don bawa 'yan ss2 da zasu maye gurbinsu damar cin gadonsu da kyau. Gaishesu yayi sannan yace musu "Wai anason yin magana da wannan" ya fadi yana dan murmushi hadi da nuna sultana da yatsa. Kusan dukkaninsu sai da wuta ta dauke musu na wucin gadi,ba sultana kadai ba,su kansu saida tsoro da fargaba ya cika zukatansu. Suka zuba mata idanu dukkansu,yayin da ita kuma ta zubawa yaron nata idanun ba tare da sanin takamaimai amsar da zata bashi ba.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 37 ______________________________ https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr ____________________________ "wai inji wa?" Najma tayi qarfin halin tambaya da alamun sanyi qwarai cikin muryarta "My broz....gashican,yace idan ba damuwa zai qaraso.....don Allah aunty ya qaraso din,mun gaji so muke mu aurar dashi mu huta" ya fada yana qyalqyala dariya,da alama akwai sakewa sosai tsakaninsa da wanda ya aikoshi din. Dukkansu suka maida dubansu inda yaron ya nuna musu. Baiyi qarya ba,matashin saurayine fari tas da yayi zubin buzaye yarensu,saidai su da yake suna shaida duk wani da sukejin harshe daya dashi take suka shaida bafulatanine shima tamkar qaninsa. Yana sanye da shadda da hula sak irin ta qanin nasa,komai nasu irin daya kamar yadda suke kama da juna "Kaje kace masa matar wani ce" muryar goumar ta ratsa kokwanto da walagigin da zukatansu suka shiga na yadda zasu kaucema wannan kiran. A birkice ta daga kai tana kallon goumar "Matar wani?" Ta furta a fili amma a hankali. Juyowa goumar yayi wanda yaji fitar lafazin nata yana duban qwayoyin idanunta kamar yadda ta kafeshi da nata "Eh..... qarya nayi?" Ya fadi kanshi tsaye yana sake kafeta da kallonsa. Mummunan faduwa gabanta taji yayi. Tsahon kwanakin watannin da kuma shekarun bata taba tuna cewa wai har yanzun itadin matar aliyyu bace,bata sake tuna har yanzun a sunan matar aure take ba,bata sake tuna akwai igiyoyin aurensa guda uku qwarara a kanta ba.....to wai zaman meye takeyi da igiyoyin auren maqiyinta kuma makashinta?,me ta zauna tana yi dasu tsahon shekara hudu?. Kai ta jinjina tana zare kallonta daga kan goumar,taji daci qwarai har saman harshenta,saidai kuma taji dadi da yayi mata tuni da wani muhimmin al'amari da ya kamata ta tuna dashi ta kuma kawo qarshensa cikin rayuwarta gaba daya. A yanzun ita din wata sultana ce ta daban data fara sanin dadin rayuwa,kyawun rayuwa da kuma cikakken 'yanci da rayuwa ke dashi,tanaso tayi rayuwa kamar kowa,tana so tasan me duniya da rayuwa suka qunsa?,tanason ta fita tayi gwagwarmayar da al'umma zasu amfaneta,dole ta kawo qarshen wannan maqalallun igiyoyi da ko daya bataga amfanin barinsu a sarqafe ba. Najman ce a gaba dukkansu suna baya su uku,tana iya hango yadda fuskar saurayin ta canza sanda qaninsa ya iskeshi a sanyaye yana labarta masa,batasan ya suka qarke ba,tadai ga yabi bayan motarsu da kallo har suka fice daga makekiyar harabar makarantar. Cikin motar kanzil bata ce ba,aminata da yasmine sunta hirarsu,goumar da najma da batasan me suke fadi ba suma tasu hirar suke,sai ita daya da suka fari da hannu dafe da gefan kanta tanata zane saman bangon littafin dake cinyarta,wanda ita kanta batasan me take zanawa ba saboda tsabar tunani. Iska ta shaqa sosai da suka shiga tangamemiyar harabar gidan aba dake garin abuja bayan jirgi ya saukesu a airport. Tadan bi harabar gidan da kallo yadda ya qawatu matuqa da gaske. Sabon gida ne da basu jima da tarewa ba,duka duka sati biyu. Cikin shekarun nan wani irin tumbatsa arziqin aba dama na hamdiyya ABDU ME KANO wato ama keyi,kaman an sake yiwa dukiyarsu yayyafin albarka,mahaukatan kudi kowannensu yake samu. Yanzu haka sun budewa benazeer da batoul manyan manyan boutique cikin garin abuja har guda uku,wanda kowanne kudade ya lasa ba qananu ba,saboda girman boutique din ya kusa wani mini supermarket din B&B BABY DREAM. Komai nasu na dabanne saboda ana sarrafashi ne daga wani kebantaccen kamfani dake sanya tambarin B&B a kowanne kaya,shi yasa kayansu ya fara zama na daban,ya kuma samu karbuwa qwarai da gaske,karbuwar kuma tana da nasaba da yaran da Allah ya hore musu wani irin farinjinin mutane. Randa sultana tazo wani hutu ta amshi wayar yaran da ama ke musu amfani da ita tana duba account nasu na insta abun ya bata matuqar mamaki. Followers suke dasu masu yawan gaske. Account ne na musamman da ama ta bude kawai saboda yaran,ba abinda take dorawa sai hotunansu. Tun sultana tana kallon pics din har ta gaji saboda yawansu,ta aje wayar kawai tana murmushi "Kakar zamani" tayi gulmar ama a ranta tana dan dariya qasa qasa. Motar goumar ya tsayar a farfajiyar ajiyar motoci dake gidan wadda gari ne kusan guda,ya kalli najma "Samomin wani abu me dan sanyi,ki tahomin da BB(benazeer da batoul)zamu fita dasu wani guri" "Okay sir" ta fadi tana murmushi sannan ta bude motar ta fice. "Akwai abinda na riqe miki ne madam?" Goumar ya fadi yana gyara qaramin pillow din dake gefan kujerarsa. Sai data sanya qafafunta waje sannan ta waiwayo "Goumar" ta kirashi kai tsaye wani irin tsauri na fita daga cikin qwayar idanunta "Na'am madamme" ya amsa fuskarsa a sake ba komai "Karka bari ka barar da sauran mutuncin dake tsakaninmu" "Tofa!,ikon Allah,me kuma nayi?" "Da batoul da benazeer basu da wani abu a duniya yanzun,kayi qoqari ka daina yi musu tilawar abinda babu wanzuwarsa a duniya......haka nima......ni ba matar kowa bace,ba matar wani bace ni" wata siririyar dariya ya sake mata,ba abinda yake ganowa a idanu da fuskarta sai zallar quruciya da har yanzun shi baiga ta fita kwata kwata a jikinta ba "Basu da uba a duniya.....ke ba matar kowa bace to kece kika kashe musu uban?" A kaikaice ya waiwaya tana dubansa,maganar tasa ta sake tsaya mata a wuya kamar mulmulallen dutse. Gaba daya abinda ta fahimta goumar kallon shashasha kuma yarinya yakeyi mata,baima dauki maganarta da muhimmanci ba. "ko ya mutu koma ya rayu wannan duka ba abinda ya shafi sultana bane,abu daya sultana ta sani,bata da wani hadi ko alaqa ta kusa kota nesa dama ko waye" ta fadi da salon tsiwar nan tata data jima bata taba ba "Ashe dai da sauran bakin har yanzu" goumar ya fada qasa qasa yana dariya sanda take fita a motar. Ta jishi sarai,bata kuma gama fahimtar abinda yake nufi ba,saidai duk da haka ta juyo ta zabga masa harara,ta murguda qaramin bakinta tace "Baqin ba'abzine,Allah ya qara gwara da Allah ya barka a baqinka" ta buga murfin motar ranta yana suya da ambatar mata sunan maina tana qarawa gaba zuwa cikin gidan cikin sassarfa. Dariya sosai ya kwashe da ita yana duban hanyar da tabi "Baki gama laushi ba kenan,hali zanen dutse" ya fada a ransa yana gyada kai gami da ci gaba da dariyarsa sannan ya sanya hannu yana daga glass din motar zuwa sama tare da duban hanyar dawowar najma.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 38 Tunda sukayi maganar nan da goumar walwalarta ta sake daukewa tsaf,duk yadda ta motsa sai zancan goumar ya fado mata a rai "Matar wani" kalmar data dinga jin nauyinta qwarai,take kuma dugunxuma mata rai. Abun ya tsaye mata qwarai a rai,ashe duk duniya kallon da ake mata kenan?,ita din matar maina Aliyyu ce?. Cikin jikinta ta dinga jin qyamar danganta kanta da matar maina,ta dinga jin ranta da zuciyarta sunqi su yarda da wannan batun. ******K'arfe takwas ne da mintuna na dare, cikin kebantacciyar wajen da aka killace aka kuma zuba masa dining table na alfarma da daukan hankali. Ama ce keta qoqarin serving aba da bibi,wadda tunda tazo bata koma nijer din ba saboda wani likitan gargajiya da take gani cikin kano. Ciwon qafarta ne ya soma matsantawa ama tace ta zauna ayi masa magana,ta fara zuwa kuma alhamdulillah sauqi ya samu,a hakan rigimar komawa nijer takeyi nan da kwanaki masu zuwa. Magana suke tsakanin aba da bibi, benazeer da batoul nata hawa cinyar bibi su sauka su dane bayan ama. Ba wanda ya damu da zirga zirgar wasansu da sukeyi,sai ama dake qoqarin hanasu wani lokaci gudun kada daya daga cikinsu ya fadi. "Wadannan 'yan qaqur din.....wai ina tsohuwarku ne?" Bibi ta fada tana danqo benazeer da kirinkinta ya ninka na batoul,komai nata sak irin na sultana sanda tana qarama,har goumar ya saka mata wani suna wai little sultana "Tana daki bibi" "Ni me yarinyar nan keson xama?,anya kuwa kanta qalau?,ace kaine zaman daki ko gajiya bakayi?,ba zaka fito cikin al'ummar muhammadu rasulullahi fa ka zauna ayi tadi dakai?" Bibi ta fada cikin jajjabi. "Jeki kira uwarku" bibi tace da benazeer tana sakinta. Fuska benazeer din ta kyabe tana duban bibi "Wai aunty ce uwarmu?" "Da dawa nake ja'ira?" Dariya ta qyalqyale dashi sannan ta nufi hanyar lobby din da zai kaika dakunansu da gudunta. Awa guda cur ta kashe akan internet ta system din da ama ta bata kyautar graduation. Bincike kawai takeyi akan abinda ya shafi aikin jarida,haka kawai cikin kwanakin data tsananta addu'ar neman zabin Allah kan makarantar da zata tafi da kuma abinda zata karanta din taji ba abinda yafi kwanta mata a rai irin aikin jaridar. Lokaci guda ta tsinci zuciyarta hankalinta da dukka tunaninta ya karkata ga zama shararriyar 'yar jarida. Tayi d'ai d'ai a tsakiyar gado,tana sanye da wata maroon abaya,daya daga cikin dressing dinta da tafiyi a yanzu,dankwalin abayar me santsi ne wannan ya sanya ya gaza zama saman lallausar sumarta. Wani qamshi jikinta da dakin dukka yake fiddawa,a yanzun ba abinda ke burgeta sama da turare,komai nata qamshi yakeyi,hatta da abubuwan amfaninta na yau da kullum muddin tana ta'ammali dashi ko da yaushe sai kaji yana wannan sassanyan qamshin nata. Hutu da zama guri daya ya sanya fatarta yin matuqar yin fresh. Gazar gazar din gashin idanunta da na girarta sun sakeyin baqi sidik sun kuma kwanta a fuskarta luf,kamar yadda gefe da gefan fuskarta keda wani irin lafiyayyen kwantaccen gashi me santsi da duhu. K'ofar taji an murda sannan an budeta da qarfi ta daga fararen idanunta da sukayi laushi saboda kallon allon computer tana duban me shigowar. Idanu ta zubawa yarinyar sanda take shigowa,abinda ya sanyata nutsuwa da shiga taitayinta. Sam bata musu wasa kwata kwata,idan kaga warginsu to suna jikin ama,ko suna tsakanin aba ama bibi ko tanja,wani irin discipline take musu sosai wanda kallo kawai da idanu sun isa su sanyasu shiga taitayinsu. "Koma kiyi sallama" tace da ita cikin bata fuska da kuma dake rai. Sum sum ta saki qofar ta kuma koma da baya,saiga zazzaqar qaramar muryarta tana jero sallama fes. Amsa mata tayi tana sake qare mata kallo,kullum qara girma sukeyi suna wayo,wayonsu yafi qarfin shekarunsu sosai "Wai ki fito inji Bibi,za'a yi dinner" "Ok" tace mata tana gyada kai,sai ta juya tana komawa "Zonan" ta kirayi benazeer din,haka kawai taji tausayinsu yana saukar mata,hannu ta sanya gefan bedside drawer ta jawota ta fidda wani pink box me cike da chocolates. Tana siyansu ta ajjiye ne kawai saboda su,duk da ba ita da kanta take basu ba,duk sanda tayi niyya kawai tana dauka ta bawa tanja ta basu. Abun yana bawa tanja dariya,itakam ta rasa wannan abu na sultana,anaso ana kaiwa kasuwa?,ko cikakken kallo bata iya yima yaran idan cikin jama'a ne,saidai kuma duk burger banza ce,idan kayi tsinkaye da kyau xaka fahimci dukka motsin yaran bisa idanunta da lurarta yake. Hannu biyu tasa ta karba da qaramar muryar nan tata tace "An gode" "Madalla" ta amsa tana binta da kallo,saita cilla da gudun murna tana fita daga dakin,tana iya jiyota tana qwalawa batoul kira "B...B" murmushi yadan qwace mata ta girgiza kai,sai kuma a hankali murmushin ya soma bacewa fuskarta,ta miqe da sauri ta shiga toilet ta wanke fuskarta,ta dawo.ta shafa turare kaman yadda ta saba ta daura dankwalinta tana fita daga dakin. A nutse ta iso wajen,zuwa sannan aba da bibi sun fara cin abincinsu, benazeer da batoul kuma anata faman rikici ama tana sharia,saidai isowar sultana kawai ya sanya suka kama kansu suka hau cin abincin ba tare da sun sake koda tari ba. Sai datakai har qasa dukkansu tayi musu barka da gida sannan ta miqe taja kujera ta zauna. Da kanta tayi serving kanta,ta fara kai abincin bakinta amma kuma zuciyarta cike fal da tunanin ta inda zata fara sako zancan data quduri aniyar yau din zata fadeshi don a sauke mata nauyin dake bisa kanta ta huta,ta kuma sake cikin tabbaci da yaqinin ba wata alaqa tsakaninta da wani. Aba ne ya fara gamawa,sai ya koma bawa benazeer da batoul,muddin kuwa ya bawa batoul kafin yazo ga benazeer ta soma rigima,haka ya dinga dariya yana rarraba basu. Yana jin dadin irin wannan yanayin sosai,yaran sun zame musu wani tushe na farinciki da walwalarsu,yaran sun zama tamkar wani budi na alkhairi wa rayuwarsu,tunda aka haifesu al'amura daban daban na alkhairi ke samunsu,komai nasu yana sake bunqasa da ci gaba tamkar dama ragiwar rabonsu yana hannun yaranne sune zasu iso musu dashi. Duk lokacin da ya tuna da haka,ya kuma tuna da yunqurin zubda su da aka soyi a baya sai yayi istigfari. Yaga maganar malamai qarara da suke fadi,kowanne yaro da arziqinsa yake zuwa,hakanan bakasan wanda arziqinka ke a jikinsa ba,hikima ce wannan ta ubangiji. Sai daya gama da rigimarsu yana goge musu baki sannan yace da sultana "Kaman naga sanarwar fitowar exam dinku ko?" Kai ta gyada a nutse tana dan ture plate din abincin daga gabanta,duk da ba wani abinci taci me yawa ba "Eh aba,don fateema Ahmad ta fadamin dazun da safe ta dubo nata" "to ma sha Allah,Allah yayi jagora,kema sai amanki ko goumar wani ya duba miki naki,tunda sun fini iya shige shigen computer" "Ama din dai" ta fada qasa qasa yadda ba wanda zai jita,saidai duk da haka ama din ta jita. Ta rasa wanne irin rashin jituwa ne irin haka tsakaninta da goumar din,tana iya kashe wuninta dashi batace masa kanzil ba,shi kuma da yake ya saba a baya abokiyar dabinsa ce to in sha Allah sai ya samu abun tsokanarta,idan taga ya fara sai ta tattara ya nata ya nata tabar masa wajen,takance "Kaci kanka da kanka". "Alhamdulillah,yanzun wanne ecole kike buqatan yi?,kuma wanne cours(course) kike sha'awar yi?" Ajiyar zuciya ta sauke,aba ya soso mata inda yake mata qaiqayi,ya kuma dauko mata mafarin maganar da take juya ta inda zata fara yinta "journalisme(aikin jarida) shi nake so aba" murmushi aba din yayi,itace mutum ta farko kuma qwaya daya tal a cikin gidan mayak'i data zabi wannan aikin "To ma sha Allah,saidai kuma munyi magana da bibi,ina kyautata zaton akwai tafiya da zata samemu ni da ama dinku,kuma tafiya ce bata kwana daya ko wata daya ba,tafiya ce ta shekaru biyu ko uku,na samu kujera cikin gwamnatinmu duk da ba'a sanar ba officiellement (a hukumance) ba amma abun tabbatacce ne,so sai a tayamu da addu'a,duk abinda yafi alkhairi Allah ya zabar" kai ta jinjina "Allah yayi jagora aba ya zaba abinda yafi zama alkhairi" "Ameen ya rahman" kusan dukansu suka amsa. Shuru yadan ratsa tana ta dan juya hanunta. Cikin qasan ranta takejin kamar abinda zata fadi akwai nauyi,to amma komai nauyinsa abune daya kamata ta tunasar dasu idan sun manta. Dukkan juriyarta da qwarin gwiwarta ta tattaro sannan tace "Amma aba ina neman alfarma a wajenku" hankalinsa ya bata da kyau da ganin yadda tayi maganar,bama shi ba hatta bibi da ama,saboda baqon abune a wajensu,tun faruwar abun sultanar bata taba neman komai daga wajensu ba "Ina jinki sultana,fadi duk abinda kk son ki fadi,karkiji komai nidin mahaifi nake a wajenki kuma uba" kai tadan jinjina sannan tace "Inason a rabani da igiyar auren......ya maina dake kaina" ta danyi dabur dabur wajen furucin saboda yadda furta sunanta kadai yake haifar da wani abu me daci daga saman harshenta.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 39 Dif wuta ta daukewa kowa dake dakin. Tun daga tsakiyar kan ama har tafukan qafafunta sai da taji wani ya tsarga mata,ba wanda ya taba hasashe ko tunanin maganar da zata fada kenan. Kaf cikinsu kowa ya kasa furta komai,kimanin wasu sakanni har sultana ta debe tsammanin wani a cikinsu zaiyi magana sannan aba ya sauke ajiyar zuciya,kafin yace komai bibi ta furta "Sultana?.....me kike fada haka?" Hannu aba ya dagawa bibi yana kallonta,sai tayi shuru,tsam ama ta miqe ta zagayesu tana barin wajen,saboda batason jin duk wani hukunci da zai fito daga bakin aba,don ta tabbatar zaiyi wahala hukuncin ya dace da abinda ita takeson ji ko son ya kasance "Kinyi qoqari qwarai sultana da kika iya zama da igiyar auren mutumin da har yau ba wanda yasan inda yake,a raye ko a mace duk ba wanda ya sani,kika raini cikinsa kika haife,kika shiga makaranta kika gama,don yau kin buqaci hakan ba laifi bane,tashi kije zan nemeki in sha Allah,Allah ya yiwa rayuwarki albarka,idan kuma goumar ya shigo ya duba miki sakamakonki" "To aba,na gode qwarai" ta fadi tana miqewa daga zaman durquson da tayi. Tana shirin juyawa sashen dakunansu suka hada idanu da goumar dake tsaye daga can bakin qofar falon jingine da qofar,hannayensa goye a qirjinsa,da alama kuma yaji komai,don abinda ta gani cikin idanunsa ya karanta mata haka. Harara taso watsa masa amma saita shareshi kaman itama bata ganshi ba ta juya ta wuce lobby. "Amma dai hamid,kada kacemin ka amshi zancanta da gaske kana nufin yi mata abinda takeso din?" Bibi ta tambayeshi murya qasa qasa tana duban qwayar idanunsa. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyara zamansa "Komai a musulunci bibi yana da iyaka,yana da doka,a shekarun da maina yayi baya nan ba wanda ke da tabbacij yana raye fa,kuma ko a musulunci miji yayi irin wannan bacewar ba tare da ya sake waiwayar matarsa ba ya halatta alqali ya raba auren ayi ma matar GAIBA ta auri wani.....bibi sultana yanzun ba qanqanuwar yarinya bace,ta iya yiwuwa tana da buqatar tayi aure shi yasa ta bijiro da wannan batun da ya kamata ace mu muka fara dubashi" zama tayi sosai tana jifan aba din da wani irin kallo hadi da gatsine fuska "Hamidou......ka fara kasheni tukunna saika tsinka auren maina kaji" "Subhanallahi bibi,abun baikai har can ba" "Ah to,yo Allah na tuba,don qaniyarta nawa take duka duka da har za'a ce waiko tana da buqatar aure?, ina cewa kwata kwata sha tara shekarun nata suke?,to ko labarin mutuwar maina aka samu ai bata isa tayi wani auren ba sai tayi masa idda" "Ya maina ma yana raye......" Goumar ya fada ".........in sha Allah,jikina yana bani haka" ya qarasa fadi ganin dukka sun waiwayo sun zuba masa idanu,sai ya sauke hannayensa yana ci gaba da takowa cikin falon "Bazamuyi masa fatan mutuwa ba aba baiga jininsa ba diyoyinsa,kai din ubane,a duk inda yake kaci gaba da yi masa addu'a Allah ya bayyanashi,ko kuma ubangiji ya karkato da hankalinsa gida" shuru sukayi su dukka jikinsu a a mace,saidai maganganun goumar dake cike da nutsuwa da kuma hankali sun ratsasu. Tunda ta shiga daki take nanata kowacce kalma data fita a bakinta,saida zuciyarta ta gamsar da ita bata aikata wani abu me muni ba,hakanan batayi amfani da tsauraran kalamai ba wajen bayyana musu yankewar igiyar aurensu takeso,hannu ta daga tana addu'a Allah yasa aba ya yanke hukunci da wurwuri,ta yadda zata samu cikakken 'yanci kamar kowacce mace,tayi karatunta iya yadda takeso ta kuma gamsu. Agogo ta dinga dubawa har sai data tabbatar da lokacin da goumar yake zama babban falon ama shi dasu benazeer su cikawa mutane kunne da karadi,sai ta dauki hijabinta ta sanya saman kayan baccinta donta gama shirin kwanciya,kasancewar bata fiya kaiwa dare can can batayi bacci ba. Takardunta ta diba ta sanya loppy tana fita a dakin. Yau din sabanin kullum ne,zaka samesu ko yaushe sun cika falon da hayaniya da wasanninsu,amma a yau din sai ta samu yaran duka sunyi bacci zube a tsakiyar ama da goumar din. Daga goumar din kuma har ama idanunsu na bisa tv. Motsinta ya sanya ama da goumar din juyowa duk suna kallonta. Idanun goumar bai sanyata jin komai ba,amma sai idanun ama taji sunyi mata mugun nauyi. Ta dinga jin kamar ana dabaibayeta,cikin gangar jikinta ta dinga jinta kamar me laifin da aka tsare. Miqewar ama din kafin ta iso tana daukar benazeer ya sanya ta dan sake ji wani iri tana cewa "Tanja zata zo ta dauki batoul,sai da safe" "Allah ya bamu Alkhairi ama" ta fada a kunyace "Ameen sultana" yadda ta amsa matan a sake sai ya rage mata tsarguwar da tayi,ta samu waje ta zauna tana duban fuskar batoul dake bacci. Bakinta gaje gaje da chocolate,tasan kuma ba aikin kowa bane sai na goumar,shi yasa yaran kullum qara habaka suke suna qiba mul mul abinsu,duk wanda ya gansu saiya tanka,wannan ya sanya duk sati ama ke sanyawa ana sauke musu qur'ani. Hannu ta sanya ta shafi cute face din batoul tana dauke mata gashin daya warware daga band din kanta don suma sunyo gadon gashi me tsaho da santsi irin na iyaye da kakanni "Ah waima,unuhunn......wai a haka fa sonta kikeyi ko?,bayan kin gama kashe musu uba da baki,kina kuma neman a sakeki" goumar da bakinsa baya shuru muddin shi da sultana ne ya fadi. Miskilin gaske ne a zahiri da fuska,amma indai shi da sultana ne dama tun tale tale sun saba. Idanuwa ta dago ta zabga masa hararar da bata samu daman sakar masa ba dazu "Wai kai meye yayi maka zafi da shiga sha'anina ne baqin buzu?" "Fadi ki sake fadi,baqin buzu nake me farar aniya da zuciya" "A hakan?,kaga ma ni ba wannan bane ya kawoni,don bani da lokacin wannan maganar,aba ne yace idan ka shigo ka dubamin exam dina" "Zan duba miki yanzun kuwa,don ni din me jin maganar magabatansa ne......exam kuma dai saidai a cirota a ajjiye don ba inda zaki sake tafiya,sanda akeson kiyi karatun bakiyi ba sai yanzun da kike matar wani?" Ya fadi kansa tsaye ba tare da damuwa da abinda zataji ba yana sanya hannu ya dauko laptop dinsa dake ajiye a gefansa wadda bai jima da gama aiki da ita ba. Tsam ta miqe,ba goumar ba,har wajen da take zaune a kansa sai da taji ta tsanesa. Hawaye fal idanunta tana dubansa dishi dishi,tana shirya kalaman da zata gaya masa da zata fanshe wannan maganganun da ya yaba mata,abu biyu ta iya gaya masa taji muryarta ta soma rawa,saita juya bata ida gaya masan ba,tana jinsa yana cewa ta kawo takardun ya cika aikin aba,ko waiwayoshi batayi ba bare ta saurareshi. Ko a jikinsa yaci gaba da aikinsa yana dariya qasa qasa cikin ransa hadi da cije lips dinsa na qasa. Tun daga lokacin bata sake bi ta kansa ba,bata kuma sake bari sun hada koda hanya cikin gidan ba bare mazauni,rainon maina ne,tasan kuma zai aikata abinda yafi hakan,duk zuciyar tasu iri daya ce ta gayawa kanta,shi yasa ta yanke hukuncin nesanta qwarai dashi. Aba ne da kansa ya kirata ya miqa mata hard copy na result dinta. Sanda ta karba hawaye ne ya kwance mata,ta samu fiye da marks din da ta tsammaci zata samu,ta cinye kowanne subject,abinda tayi hasashen zata samu ta samu fiye da hakan,ta kifa takardun saman fuskarta tana kiran sunan Allah,yau sultana ita keda wannan result din da abaya kaf gidansu koda cikin mafarki ba wanda ya taba kawo mata kwatankwacinsa saboda zallar qiyayyarta da karatu. Ba ama ba hatta aba abun ya faranta masa rai matuqa da gaske,bai kuma yi sanya ba ya bata option ta zabi duk kalar kyautar da takeso yayi mata,ya bata dogon takarda yace ta rubuta list. Hannunta rawa ya dinga yi,ta kasa rubuta komai,sai daga bisani cikin rawar bakin bayan ama ta matsa mata ta rubuta din tace "Umra nakeso aba" "Sau nawa?" Hawaye ya biyo kuncinta tana tuna adadin zuwanta,sau uku ne,amma saidai duk sanda taje din tana cikin rudu,tana asalin sultanarta,batasan muhimmancin wajen ba,batasan kuma dimbin falala da wajen yake dashi ba,taje ne kawai taji dadin jirgi,ta kuma shaqata a kantunan dake daura da harami,tasha chocolate laban da ice cream har sau babu adadi. Amma a yanzun da tasan muhimmanci da girman wajen sai shauqinsa yaketa kamata,yanzun da ilimi ya ratsata burinta kawai shine zuwa wajen sau babu adadi cikin rayuwarta "Sau nawa kikeson xuwa?" Aba ya tambayeta "Sau babu adadi" ta qarasa fadi tana rushewa da kuka "Kin samu in sha Allah" ya fadi yana nufin hakan har cikin zuciyarsa kuwa. Diyar mohmoud ce tafi qarfin komai,uwa uba ya samu sanyin idaniyarsa halittu mafi soyuwa a gareshi da silarta BENAZEER DA BATOUL. A arziqin da Allah yayi masa inda ana zuwa kullum kuma tana da buqatar zuwa din zai iya kaita. Ya mata alqawarin muddin yana raye din zata yita zuwa har sai sanda tace ta gaji. Ita kuwa tasan zata yita zuwa kenan muddin ranta,muddin akwai wadata wa aba,akwai lafiya cikin jikinta,saboda bata tunanin akwai ranar da zatazo tace ta gaji da zuwa wannan gurin. **. **. **. Randa bibi zata juya nijer sai taji haka kawai tana sha'awar zuwa. Tare suka tafin,da harda goumar ta kafe indai tare zasuyi tafiyar ita ta fasa,dole yayi gaba daga baya aba ya basu driver da escort uku. Sosai taji dadin xuwa nijer,ta ji har cikin ranta lallai a gida take,abu daya ke yawan takurata,duk sanda ta gilma wani guri da tasha dabdala a baya,ko guraren da maina yafi yawan zama sai taji duk walwalar da take ciki ta gushe,wannan ya sanya ta dinga kame kanta daga shiga wasu guraren,ciki harda nahiyar dakunan dake sassan bibi wanda anan me akkuwa ta auku. Wata guda ta shafe a nijer,daidai lokacin kuma muqamin aba ya tabbata,tafiya ta tabbata daga nijer to nijeria har zuwa qasar FRANCE!. *_TOFA MASU KARATU,DAB MUKE DA ISA GURIN😄,muna dab da mu qarasa gurin da na tabbatar kowa ya qagauta a isa_* *_FRANCE......NEW CHAPTER UNLOCKED_*🥰 *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 40 *FRANCE _(PARIS)_* *Charles de Gaulle Airport* *Avenue champs elysees* _8th arrondissements_ Cikin awa daya da saukesu da jirgin qatar airways yayi a airport din Charles de Gaulle suka iso champ elysees avenue. Unguwar dake da matuqar kyau tsari da kuma dadin zama,wadda take dauke da dukkan nau'ikan shop shop,malls restaurant da coffee shops harda makarantu. Unguwa ce me kyau qwarai da dadin rayuwa,wannan ta sanya aba ya zaba musu zama a cikinta. Cikin daya daga cikin apartment dake unguwar wanda gwamnatin nijer ta bashi. Babban apartment ne dake qunshe da dakunan bacci guda hudu,biyu ta gaban gidan inda zaka bulla har balcony zuwa harabar gidan, biyu kuma ta cikin gidan wanda suke hade da backyard na gidan. Kowa yasan ginin bature gini ne me matuqar kyau da daukan hankali,komai na gidan a tsare yake a kuma killace,sun iso cikin gidan bisa jagorancin wakilan qasar nijer a nan din da suka tarbesu a hukumance,suka yiwa aba duk wata tarba data kamata. Karfe hudu agogon paris suna cikin gidan,sun gama zagaya ko ina da duba ko ina. Sultana kam da ido take bin komai tana sake tabbatar da maganar hausawa da suke cewa tafiya mabudin ilimi,tun daga abuja zuwa gidan da suke ciki a yanzun take ganin mabanbantan al'amura. Benazeer da batoul kam sai tsalle tsallensu sukeyi,suna biye da ama duk inda ta sanya qafarta. Walwalar yaran data qaru kawai ta sanyawa ama farinciki,tana ji a ranta zaiyi wuya tabar qasar nan nan kusa,har sai yaran sun samu kalar ilimin da take musu kwadayin samu. Tanason su fita daban,su zama na musamman,kamar yadda gatan da suke samu ya banbanta da gatan duk wani d'iya dake familyn MAYAK'I,kamar kuma yadda suka zamo jikokin farko a wajensu aba din. A nutse ta taka izuwa babban curtains daya suturta babbar qofar glass na dakin da zai iya baka daman ganin cikin unguwar da kuma duk wanda ke zirga zirga ta street din nasu. Qofar ta murda ta fita zuwa balcony din,sassanyan yanayi na la'asar sakaliya dake gauraye da qamshin tsirrai da suka wadaci unguwar ya daki fuskarta,iskar ta shiga sosai cikin hancinta ta isa hunhunta ta sauketa a nutse tana kuma fidda wata me zafi. Ajiyar zuciya ta sauke,tana fatan taji ruhi da zuciyarta ta nutsu amma. Ta lumshe fararen kewayayyun idanunta da suke da wani irin qwalli kamar an diga mai a cikinsu,haka kawai taji bugun zuciyarta yana dan sauyawa a hankali yana qara gudu. Da hanzari ta ware idanun nata cikin mamakin abinda ya haifar mata da hakan,sai ta aza hannun nata saman qirjin nata tana qoqarin controlling sabon yanayin data tsinci kanta a ciki. Tsahon wasu mintuna babu sauyi,sake maida idanunta tayi zata lumshe karadin benazeer ya cika mata kunnuwa "Aunty......aunty kinga" hannayenta ta sauke tana waiwayowa zuwa ga yarinyar. Da gudunta take nufarta tana nuna nata wata qatotuwar teddy. Murmushi ta saki dan siriri tana tuna rayuwarta,yadda tayi yayin tara teddy kaman hauka,batajin cikinsu ma akwai wanda zai qaunaci teddy din yadda ta sota "Kizo inji ama" benazeer ta sake fadi tanata qoqarin ganin ta goya Teddy din,sai kuma ta juya da gudu gudu tana sauka hadi da kiran "B.....B" Juyawa tayi tana komawa cikin dakinta ta dauki mayafin gown din jikinta ta yafa tana bin bayansu. Daga qofar dakin da ama ke ciki din ta tsaya saboda rashin ganin dacewar shigarta dakin,don daki ne da ama ta zabawa aba,duk da cewa aba dinma baya nan ya fita tare da mutanen da suka yo masa rakiya zuwa nan din. Knocking tayi ama dake ciki tace ta shigo. Hakanan cikin jin nauyi ta murda qofar dakin tana shiga. Babban dakine da yafi kowanne girma da kyan furniture,aman tana tsaye da wani folder a hannunta tana dubawa,ta amsa sallamar tana kallon sultana sannan ta miqa mata takardun tana cewa "Ba hutu,ba zama,sun kusa gama daukar dalibai,aba yace ki duba,cikin universities din wacce ce tsarinsu yayi miki?" "Allah sarki ubana na kaina" ta fada hawaye yana cika idanunta. Hannu biyu tasa ta karba tana kallon folder din. Itakam dai kawai tayi rashin mahaifinta hamani ne,amma zata iya cewa iyayenta sun maye mata gurbinsa har fiye da haka,batasan wani abu waishi maraici ba,bata taba ji ko ganin zumunci irin nasu ba,tasan indai ana batun dacewa da family itakam ta dace "Amma ki kula ki duba location na kowacce university ki zabi wadda ba zaki dinga shan doguwar tafiya ba" "In sha Allah ama". Ta fadi farinciki yana cika zuciyarta fal,burinta ya kusa cika na zama 'yar jarida,ta rungume folder din tana fita daga dakin. Tsabar zumudi ya hanata tsaiwa ta kintsa dakin ta zauna duba jami'o'in,tanayi tana browsing a wayarta da babu layi a ciki duk kuwa da tsadar wayar,akwai wifi da suka samu a gidan don haka bata buqatar komai don research din. Har tanja ta gama abinda ya dace tayi ta biyo ta dakin tana nade tsakiyar gado tana aikin canki canki. Cikin zolaya tanja tace "Wai sultee kamar yanzu zaki fara zuwa makaranta a rayuwarki,wannan zumudi haka?,xuwa makarantar ma kamar yafi komai yi miki dadi" tashi tayi ta zauna tana yatsina fuska saboda yadda bayanta ya riqe sakamakon rub da cikin da tayi na kusan awa daya tana cewa "Ji nakeyi kamar yanzu aka haifeni tanja,kaman yanzu ne na soma rayuwa,ai da can ba rayuwa nakeyi ba tanja,rayuwar da babu ilimi a ciki?,meye marabarka da gawa?" "Irin wannan lokacin maina yakeson gani,shi yayita burin gani tattare da ke,ya Allahu ko ina wannan bawa naka ya shiga?" Qwaqwwaran motsi sultana batayi ba,sai tayi kaman bataji abinda tanja tace ba,inda sunsan adadin dimuwa da qyamatar da ruhinta ke yiwa sunansa kawai bama shi din kansa ba.......da babu wanda zaiyi kuskuren sake kiran sunansa a gabanta "Bari na kintsa miki wajen kafin ki gama" a hankali ta motsa labbanta tace "To" tana maida hankalinta ga wayarta cikin tsananin nutsuwa,yayin da zuciyarta taci gaba da motsa da wani irin sautin tsana da qiyayya duk sanda kunnuwanta suka tuna mata sautin kiran sunansa da tanja tayi. Satinsu daya suka gama huce gajiya,sai ama ta fara diban jikokinta suna fita shan iska. Kullum da inda zasu,sai idan sun dawo kaji labari cakwai a bakin benazeer,don ba kasafai batoul ke da surutu haka ba. Hasalima ita saita nema debo dabi'un abbanta sak da sak,tana da wani irin miskilanci da kuma basarwa. Haka kawai idan taso saita tashi da 'yan shirun, benazeer tayi hirar duniya taqi kulata,idan taga haka tasan tana nufin yau ba zasuyi wasa ba ko ifce ifcensu da suka saba ba sai tahau tsokanarta,ba kuwa zata qyaleta ba har sai ta sakata kuka,sau tari sai ama ta shiga tsakani,ko kuma idan suka cikawa sultana kunne ta leqo shikenan sai benazeer din tayi laqwas ta shiga taitayinta. A irin wannan lokacin ama kan zauna kawai tana binsu da kallo, zuciyarta tana mata haske tana kuma mata fari,wani lokaci kuma damuwa ta cika zuciyarta,dukkansu su biyun sun dauko attitude na mutum biyu ne, benazeer sak SULTANA tana yarinya,batoul kuwa MAINA ce har yabar gabansu. Duk da garine dake da ababen kallo sosai,gari ne dake da ababen sha'awa amma ita bata sha'awar fita ko ina. Zaman kadaicin da taketa yi ya sanyata karance karance a matsayinta na wadda keson fadawa harkar karatun jarida,a hankali har abun ya zame mata jiki. A nan taga wata makarantar koyar da girke girke na qasashe daban daban,koda ta duba kudin registration din sai taga yayi yawa,don haka ta maida site din ta rufe bata sake budeshi ba. Ranar ama ta karba aron ipad dinta taga ta soma register,ta fahimci yawan kudin ya hanata qarasawa. Murmushi ama tayi,sultana..... sultana,akwai barin kashi a ciki,ba zata taba bude baki tace ga matsala ko damuwarta ba,sai ta shiga site din ta qarasa komai ta biya kuma kudaden,sai gayawa sultana tayi ranar da zata fara zuwa. Nauyi da kunyar ama suka sake kamata,tana kunyar yadda ta azama kanta dukkan nauyinta,komai nata itace,bata qyashin kashe mata ko nawa ne, ba'a maganar su benazeer da suke fuskantar wani irin gata,idan akace gata ana nufin gata na qarshe,irin gatan da ake kwatance dashi. Komai nasu me tsada ne,komai nasu kuma na musamman ne,hatta kuwa da brush da zasu wanke haqoransu. Amma kuma duk da gatan da ake gwada musu hakan bai sanya sunyi lako lako da tarbiyyarsu ba. Sosai suke samun kulawa da tarbiyya,don ama da kanta take koya musu qur'ani. Da yake sunyi gadon kwanya,sai gashi da qananun shekarunsu sunyi nisa a alqur'ani,hadda kuma tartilan cikin qwaqwalensu. Ta siya musu kayan karatu kala kala da zasu taimaka musu, harshensu kuma ya fara juyewa da qira'ar sheik imam khusari. Makaranta me kyau aba ya duba ya sakasu,inda suke karatu da dukka harasa biyun, French da English harda qarin larabci. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 41 Cikin watanni biyu aba yayi settling komai ta fara zuwa makaranta. Qaramar mota ya siya mata daidai d'iya mace,ta kaita makarantar koyon tuqin mota ya zube kudi ta koyi tuqi da kyau suka bata license. Hakan ya mata dadi qwarai,don ta huta da tafiya railway ko kiran taxi. Shigarta makarantar ya sake sanya idanunta suka bude da rayuwa,ta qara sanin mece duniya?,tarin al'umma mabanbanta masu mabanbantan halaye da dabi'u. Ta sake sanin tabbas duniya tana da girma da fadi,taga kalolin tarbiyya iri iri al'adau dabi'u da kuma halaye,wanda kusan kullum idan ta dawo sai ta bawa ama labari. Murmushi kawai ama keyi,itama sai yanzu take sake tabbatar da quruciyarta,lallai a baya in banda quruciya da tabara babu abinda sultanan ta sani. Duk da haka suna biye kuma suna kula da ita,ko don girman igiyoyin dake saman kanta,wanda tun wancan lokacin da bibi tayi magana ba'a sake tada zancan ba. Suna exam semester farko aba ya ajjiye musu visa dinsu na zuwa umra. Ranar kasa bacci sultana tayi. Hakanan Allah ya jarabceta da son zuwa madina da makka,tun daga sanda ilimin addininta ya fara zurfi ta fahimci muhimmancin gurin gaba daya zuciyarta ta tafi can. Washegari goumar ya dira a Paris,sai a sannan tasan dashi za'a yi tafiyar. A sannan tana parlor tana duba wasu litattafai nata door bell tayi qara,tanja ta bude masa ya shigo riqe da jakarsa. Daga benazeer har batoul yarda abun wasan hannunsu sukayi sukayi kansa kamar zasu shide saboda murna,shi kuwa ya tattarasu duk da girmansu ya dagasu yana zagaye dasu. Har suka gama abinsu tana zaune bata daga kai ba,sai da suka nutsu suka zauna tanja ta ajjiye masa drinks da snacks tana gaya masa ama tana bandaki,sai ta fara tattare litattafanta da zummar barin wajen idanunta na kallon litattafan nata tace dashi "Ina yini,kana lafiya?" Gwanin tsokana baya fasa halinsa,tabe baki yayi yana cewa "Nidai ban roqi gaisuwa ba bare a wulaqantani ehe,meye wani ina yini kana lafiya?" Tsaiwa tayi da abinda takeyi ta xuba mishi fararen idanunta, kwanyarta na mata tariyar tarin kamanceceniyar halayya dai da uban dakinsa sarkin zalunci da mugunta wato maina kaman yadda ta rada masa "Kaidai ba'a iya maka wallahi,Allah ya sawwaqe" saita dauki kayayyakinta a hannu tana yin gaba "Ya kyauta mana gaba daya,mutum se shegen qunci da dacin rai kamar wanda aka kashewa diyan fari" ya qarasa fada yana galla mata harara. Tasan halin goumar,baiqi su kwana sunayi ba,don haka ko waiwayoshi batayi ba ta shige dakinta,amma ranta cike fal dashi,tana kuma tunanin hanyar da zata bi ta taka masa burki,yadda yake shige mata sharafi ya soma isarta hakanan. Bata qara bari sun gamu ba sai ranar da zasu wuce. Tafiyar tasu dukkansu ce,harda tanja,amma sai ya zamana duk cikinsu sultana din tafi zumudi saboda a wajenta tamkar zuwan farko ne. Tafiyar awanni tara bayan yada zango a wani qasar Wizz Air Malta ya saukesu a filin tashi da saukar jiragen sama dake garin madina don can suka fara sauka. Wata ajiyar zuciya me qarfi ta sauke kamar wadda aka finciki zuciyarta. Ta furzar da iska daga bakinta tana jin daukin ganinta cikin masallacin ma'aiki. Daga wankansu cin abincinsu a masaukinsu zuwa fitowarsu masallacin duk sai taji kaman basa sauri,ji take kamar duk duniya ita daya keda buqata,kamar duk duniya ita keda damuwa a qirjinta,kamar kowa baya da matsala sai ita kadai. Tana ganinta a raudha kuwa kuka ta saki sosai,saidai qasan ranta taji nutsuwa tana saukar mata,wannan ya taimaka ta samu nutsuwa tayi addu'a sosai. Dukka kwanakin da sukayi a madina babu wanda bata amfaneshi ba da tarin addu'o'in da ita kanta batasan adadinsa ba. Sai gata a yau wai itace da yiwa ummanta NAFESSA da mahaifinta HAMANI addu'ar samun rahamar ubangiji,lallai hankali da nutsuwa ya samu,madalla da wannan rayuwa data samu sauyinta. Randa suka sauka a garin makka kuwa kayanta kawai ta ajjiye tayi wanka ta fice,ko ama su benazeer ta barwa sallahu su gaya mata ita ta wuce harami. Ta kasa nutsuwa don masaukin nasu daga nan idan ta bude window din dakinsu tana gano harami sosai,saita dinga ji kamar ana fusgarta. Sanda suka fito ma ita ta bace cikin masallacin,don haka ama ta fara tata ibadar, benazeer da batoul ma sukayi nasu waje,wanda ama batasan ma ina sukaje ba sai da suka dawo hannu dumu dumu da siyayyan kayan zaqi,tunda kafin su fita dama already aba ya basu kudi a hannunsu. Da rigima suka dawo,mutuniyar batoul tayi kicin kicin da fuska tana harara benazeer,tambayar duniya taqi bayani sai ice cream da ta saka a gaba,ita kuwa benazeer ba abinda ya shafeta ta zauna ta bude abinta ta fara sha tana dariya. Da kallo ama ta bita,sak yadda sultana ke cakar da yara zamanin quruciyarta da shegen tsokana da yiwa yara dariya. Daqyar ama ta lallasota ta gaya mata "Mutane take kulawa ama,sai kuma tayita basu labari mu 'yan nijer nigeria da paris ne" waiwayawa aman tayi tana duban benazeer,suna hada idanu jikin benazeer din yayi sanyi saboda tasan kalar wannan kallon na ama "Bana hanaki dogon surutu irin haka ba benazeer?,kina so na saka wuqa na rage miki tsahon bakinki?" Da sauri ta girgiza kai idanunta na hada hawaye "To daga yau na hana,idan zakuje siyan abu kuje ku dawo,ba ruwanku da kowa kina jina?" Kai ta gyada mata tana lanqwashe qafafunta taci gaba da shan sanyinta. Dariya taso qwacewa ama,wato tsoratar da itan da tayin bazai hanata qarasa shan kayanta ba "Gado ba karambani ba" ta furta can qasa tana sake tuna mata da sultana da qananun shekarunta cikin qasar nijer mansion house na MAYAK'I family. Da wata irin kasala mutuwar jiki data zuciya rungume da dardumarta take fitowa daga masallacin. Idanunta sun tasa sun kuma yi jaa saboda yawan kukan da tayi a gaban ka'aba. Rabin kanta sarawa yakeyi saboda abincin da bataci ba wunin yau din gaba daya sai zam zam data dinga sha sosai kaman ba gobe. Sanye da baqar jallabiyya yake takawa a farfajiyar wajen. Tsahonsa bayananne ne,hakanan nannadaddiyar sumarsa. Bata lura dashi ba kamar yadda shima din da alama bai lura da ita ba yana cikin gaggawa ne,wannan yayi sanadin da saura kadan kafadunsu su hade waje guda,abinda ya sanya sultana janyewa gefe zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu saboda qamshin turarennan da hancinta ya shaqa qwarai da gaske fiye da yadda take jiyo qamshin daga nesa a mabanbantan gurare..........qamshin yaja hankalinta ta waiga a hargitse tana duban wanda ya giftata din........ *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 42 Rufewar da idanunta sukayi,da kuma irin bugun da zuciyarta keyi ya sanya idanunta suka nuna mata shi a matsayin maina,daga bisani kuma a hankali ganinta ya washe,ainihin kamanninsa suka fito mata "Sannu ko?,yi haquri don Allah" ya fada yana daga Mata hannu da sassauqar muryarsa dake bayyana zallar sauqin kansa,ya bata haqurinne da hausa kawai don baya tsammanin ko kadan zataji me zaya fada,don kuwa koda alama batayi masa kama da launin jinsin hausawa ba. Kanta ne yayi wani mummunar sarawa,sai data sake matsawa nesa kadan dashi sannan ta gyada kai tana furta "Ba komai" a wahale sannan ta juya da sasarfa tana barin gurin,don ko kusa bata qaunar sheqar qamshin wannan bala'e'en turaren "Uhmm......nace ba,don Allah ko zan iya sanin masaukinku?" Taji ya fadi a bayanta bayan ta baro wajen sosai,don tayi tsammanin ma inda suka tsaya din daga nan ba lallai ka hangoshi ba. Muryar tasa ta sanyata waiwayowa sai suka hada ido. Kai ta girgiza masa alamun a'ah,sai ya marairaice yana ci gaba da binta "Don Allah,kada kice a'ah" hannuwanta dukka ta sanya tana dage doguwar rigarta tana kuma qarawa qafafunta karsashin yin sauri,don burinta ta tsere masa daga wajen. Ba abinda yake sake hadsasawa zuciyarta sai wani irin bugawa "Please" ya sake fadi ba tare daya dakata da binta ba "Ka daina bina,nan din waje ne me alfarma" "Na sani,ni dinma alkhairi nake nufinki dashi,bata yadda zan miki magana a nan kuma zuciyata sharri ne a cikinta game dake" "Na gamaka da girman gurin da wanda ake bautawa a wajen ma dakata" ta sake fada daidai sanda ta hangi goumar yana nufo wajen,yana riqe da hannun BATOUL tana bashi labari,shima kuma da alama dukka hankalinsa yana kan batoul,saidai hango sultana da wani na biye da ita ya sanyashi dauke dukka hankalinsa a kan yarinyar ya maido kansu batoul. Bata fasa sassarfar tsere masa idanunta nakan fuskar Goumar data tabbatar sai yayi mata shishshigi,kaman yadda bai fasa binta yana mata magiya ba,hakanan goumar bai fasa nufosu ba fuskarsa da idanunsa na nuna wani irin emotion. Ta karanci abinda ke fuskar Goumar,kaman ma a fusace yake ainun,yau kam sai tayi maganinsa taga idan akwai abinda zai iya,don haka suna zuwa dab dashi ta dakata,ta kuma karantawa matashin Address na hotel harda number dakinta "Na gode sosai,sunana suhail kefa?" "Sultana" ta fadi a taqaice tana juyawa ta rabe goumar ta wuce. Sai data fara nisa da gurin suhail ya maida dubansa ga goumar da yayi tsam ya zuba masa wannan idanun nasu me matuqar kwarjini da haiba irin na maina,idanun buzaye dake da wani irin sirri da kuma launi na daban. A idanu suhail yaga suna kamanceceniya da sultana,saidai shi din baqi ne sosai kuwa akan kalar fatar sultana dake jazur kamar ta fito daha yankin larabawa,wannan kama da ya gani yasa ya miqa masa hannu yana fadin "Assalamualaikum" girman kalmar da sanin ma'anarta kadai ya hana goumar qin miqa masa hannu. Ya bashi hannun,saidai kuma ya bar masa saqo yana fadin "Ita din matar wani ne,kada kayi gangancin shiga gonar da ba taka bace,kada kuma kayi yunqurin keta dokar Allah" sosai sai jikin suhail yayi sanyi,amma a yadda karo daya yake jinta cikin kowanne sassa na zuciyarta daga kallon farko,sai yaji kalaman goumar basu shigeshi ba "Ni jikina sam bai bani haka ba,idan ma kai din rival ne saidai nace maka kayi haquri na riga na kamu,ma'assalama" ya fada yana yin gaba. Tun daga ranar sai goumar ya dauke mata wuta tsaf,ta daina ganin koda haqoransa,itakam hakan yafi mata dadi,don dama so take ya fita a sabgarta kuma ya fita din,takance a ranta "Aikin banza aikin wofi,koshi wanda kakeyin abun saboda shi bai isheni kallo ba,bai kuma isa yace zai damu rayuwata ba bare kai" Suhail kuwa tasha ganinshi a hanya ko cikin masaukin nasu da alama ita yake nema,saita bace masa kota koma har sai yabar wajen. A daidai lokacin lokacin ubangijinta kawai take dashi,ita kanta cikin zuciyarta taji nutsuwa da gamsuwar lallai tayi ibada iya yadda ubangiji ya bata iko,fatanta kawai ta zama karbabba,muddin kuwa ta karbun tayi imanin zata cimma dukkan nasara da kyautatuwar rayuwa. Sati uku sukayi suka koma Paris ta rungumi karatunta,wanda babu abinda take gani sai budi da nasara,duk wani nasibi da budi data roqo akan karatunta tana ganinsa,karatun tamkar ana buda kwanyarta ana zuba mata shi,nan da nan kafin ma su kammala ajin farko sunanta ya fara yin fice cikin makarantar tsakanin dubban dalibai dake department dinsu. Duk yadda takai ga janye jikinta da rashin son jama'a sai Allah ya bata farinjini sosai cikin makarantar,kowa ta zauna dashi dai ya qaunaceta,duk da miskilancinta bata iya wulaqanci ba sam,sannu sannu sai gashi ta fara dan sakewa da jama'a. Koda ba zatayi mu'amala dakai ba amma zata maka murmushi saman fuskarta,wannan sai ya sake zama abun burgewar jama'a a wajenta. Tun wannan zuwan da sukayi sai zuwa umrar ya zame musu tamkar jiki kamar yadda aba yayi mata alqawari. Abun sai ya zama kaman ya tsara musu kanshi da kanshi,duk sanda suka samu hutun makaranta ita dasu benazeer to a saudiyya suke yin abinsu,suyi wata guda suna ibada sannan su dawo kuma a soma shirye shiryen komawa bakin karatu. Ta riqi karatunta gam da matuqar muhimmanci,tana bashi dukkan lokacinta,saidai kuma hakan bai hanata ibada ko koyon wasu abubuwa da suka shafi rayuwa ba wandada tasan tana da naqasu ta bangaren,kaman koyon girke girke,hanyoyin kula da kai da kuma gyara kai da wata balarabiyar oman ke koya musu. Macace me baiwar sanin ilimin halittar diya mace,shiga ajin matar ya faranta mata ainun,don ya sake maidata wata irin 'yar gayu..... mace me aji,irin macen kuma da tasan kanta ciki da waje. Sai a sannan ta karanci ama cikin hikima. Wato ita ama ba'a banza ba ta fita daban a zuciyar aba,duk da cewa aure qaddarar wasu mazajen ce,to amma bata tunanin tana cikin qaddarar aba,wasu abubuwan ma da yadda take kula da rayuwarta da kuma kanta dukka sai yanzu hankali da ya game sultanan take karantarta,wasu abubuwan tayi qoqarin daukesu,wasu kuma su bata kunya. Abinda bata sani ba ama din ta fita zurfin nazari sanya idanu da qwaqwqwafi,tuni ta fahimci sultana,sai bata nuna mata ba,amma itama saita sakata a nata ajin na yadda mace zata amsa sunanta mace a idanun mata 'yan uwanta dama maza abokan cudayyarta. Ta sake salute na ama,ba banza ba ta sake fita daban da faccalolinta,tun tale tale komai na ama dabanne,she's so classy,har kuma a yanzun dabi'arnan tana nan,shekaru da fara zuwan girma bai sanya ta canza ba. Ta zame mata mentor sosai ta fanni da dama,ita kadai data kalla ya sake sanya mata sha'awar koyon girke girke iri daban daban. Ama din kamar half cast za'a kirata,uwa uba kuma ita din tayi zaman qasashe tun zamanin quruciya har zuwa yau,wannan ya sanya ta iya nau'ikan abinciccika kala daban daban,kuma da kadan da kadan sai da sultana da iya da yawa daga cikinsu. *_KOMAI NISAN DARE gari zai waye_* Cikin babban dakin taron dake mallakin makarantar,cike yake da dalibai irinsu sultana dake murnar amsar sakamakonsu na kammala karatun aikin jarida fanni daban daban,sai kuma manyan baqi iyaye da 'yan uwan daliban dake qasashe da kuma garuruwa daban daban cikin paris da wajenta. Tana sanye da academic regalia data dora saman wani tattausan lace da ya lashe kudade masu ciwo da ama ta siya mata,ta kuma bayar akayi masa dinki me aji. Lite make-up ne a fuskarta wanda zaka iya rantsuwa da Allah ba komai saman fuskarta saboda nutsuwa da kwanciyar da kwalliyar tayi a saman fuskartata. Tun daga takalmin qafarta har zuwa mini handbag da medium mayafinta idan akayi lissafi a qalla zasu tada jari me qarfi ga wani. Komai nata me sanyi da tsari,kaman yadda halittar ta take da daukan hankali da saukar da wani irin nutsuwa. Siririn kwallin da aka sanya ma fararen qwayoyin idanunta da kuma red lipstick da ta shafa ya fidda mata wata haiba da kwarjini na musamman. Tana zaune a inda aka tanada saboda dalibai,amma gaba daya hankalinta yana kan batoul da benazeer da aka yiwa kwalliya sosai cikin wata red gown da tayi masiiiifar kwanciya a lafiyayyar fatarsu da hutu da gata ya jiqa sosai. Sai kai kawo sukeyi suna 'yan guje gujensu tsakanin mutane,duk kuma inda zasu gifta din sai sunja hankulan mutane. Wasu su jasu suyi hotuna,wasu su basu qananun gift da ba'a raba baturen mutum dasu. Kiransun da aka fara yi daya bayan daya ya sanya dole ta haqura da lura da kai kawonsu,duk da tasan idanun aba ama goumar harma da bibi da tayi tattaki tun daga nijer domin ganin yadda gudaliyar tata a yau zata karbi sakamakon da zai bayyanata a cikakkiyar 'yar jarida. Sanda sunanta ya fita a cikin mic haka ta miqe tana ratsa mutane,kunya gami da nauyin idanuwan da sukayo kanta dukka suka cikata,haka ta dinga takawa cike da nutsuwa har takai saman step din da kowanne dalibi ke tsaiwa tana qasqantar da ganinta. Idanu sosai takeji cikin jikinta tamkar yawansu ya wuce yawan adadin jama'ar dake wajen kadai. Bayan gajeriyar gabatarwar dake nuna da qwazo da nagartarta,kwanya da kaifin ganewa da take dashi,da kuma kasancewarta daya daga cikin dalibai guda biyar da sukafi kowanne dalibi samun high mark. Ji ta dinga ji kamar zata fadi a wajen,gaba daya qafafunta sunyi laushi hawaye ya cika idanunta. A kowanne bigire na rayuwa data tsaya ba abinda take gani sai haske,wani irin budi take gani a duk matakin karatun data taka,batasan abinda ke nufi da hakan a gareta ba,me yiwuwa akwai hukimar ubangiji da ya sanya qiyayyar karatu me yawa a ranta a baya. Kuyi haquri dai,ku qara haquri,naso yau na kaiku inda ya kamata aje din,amma yau da gobe ta riqeni,duk da haka ku bini bashi gobe in sha Allah,na gode sosai *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 43 Hannu ta sanya ta amshi certificate dinta,wanda tayi tsammanin bayan ta karba din zata koma ta zauna ne kamar kowanne dalibi......amma kuma a'ah. Kyaututtuka na karramawa ne suka yita fitowa saboda qoqarin data nuna da hazaqa a guraren da suka danyi ayyuka dasu na neman qwarewa watannin da suka wuce da kuma cikin makarantar kanta,kasancewar su mutanene masu girmama mutum irinta,sunason suga mutum me talent qwarai da gaske. Sai ta dinga ji kamar tarihi yana maimaita kansa a hassan Ibrahim gwarzo makarantar da har yau take kewarta,take kuma jin tamkar ta koma can. Makarantar ta zame mata wani mabudi,ta kuma zamewa rayuwarta haske kuma fitila dan jagorarta daga duhu izuwa haske. Kafin a kammala taron duka ta bata fuskarta da koke koke,sai tissue da ama keta bata tana goge fuskar saboda hotuna da aketason dauka da ita,musamman su benazeer da suka ja hankulan mutane qwarai. Tana duqe tana qoqarin controlling hawayenta muryar benazeer ta karade hall din ta cikin mic. Da zazzaqar muryarta tayi sallama,sallamar data sanya kowa dake wajen murmusawa,ta kuma saka sultana dagowa da sauri. Tayi dare dare saman step din tana murmushi,cikin yaren france da ya kama harshenta matuqa da gaske tamkar yaren hausa da suke magana dashi yau da gobe a gida ta soma magana "Ina gaida aunty na.....ina gaida mommy na ama.... oncle goumar....kaka na aba.....sai daddy na.......daddy na ina gaisheka......muna kewarka daddy,yaushe zamu ganka?" Ta qarashe fada muryarta tana raunana. Tafi wajen ya dauka,yayin da maganar ta doki qirjin duk wani ahalin mayak'i dake a wajen. Sultana kam maida bayanta tayi makarin kujera ta jinginar tana rufe idanunta, qirjinta yana bugawa kusa da kusa. Goumar ya riga ya gama yiwa tunaninsu lahani,ya gama cusa musu wannan tunanin na mahaifinsu wanda batasan yaushe zaibar zukatansu ba. Kusan jikinta a sanyaye aka kammala taron,saidai dab da za'a kammala din saiga sanarwa daga wani gidan tv kai tsaye suke neman sultana zuwa channel dinsu zatayi interview,suka bata date wanda ya dauki makonni kusan hudu,dai dai da sanda suka kammala wasu gyare gyare na shirye shiryen da suke gabatarwa a channel din nasu. Wannan shine abinda ya wanke mata zuciyarta,farinciki ya kamata sosai,abinda bata taba tunani ba,yau ita sultana wani tashan talbijin dake a qasar turawa ke nemanta da kansu? "Alhamdulillah" kawai ta dinga maimaitawa tana jin farinciki yana ratsata,ko ta ina addu'arta ke karbuwa,cikin qaramin lokaci buri da muradinta ke dab da cika. Koda suka koma gida bacci tayi sosai na gajiya,bata tashi ba sai azahar,tana yin sallah ta sake komawa,don duka kwanakin zirga zirga sukeyi don tabbatuwar taron. Bayan sallar la'asar benazeer ta shigo,ta bita da kallon harara sannan ta zaunar da ita. Data fara yi mata fada akan abinda tayi dazun saita sakar mata kuka,abinda ya sanyata sakin baki kawai tana kallonta,sannan kuma cikin bacin rai tace "Oho.....tun bankai ga dukanki ba?,hala duka kike buqata ko?" Kai ta girgiza tana share hawayen fuskarta "We missed him mommy,uncle goumar yace yana nan amma bamu taba ganinsa ba,sai a hoto ya taba nuna mana shi sau daya" gabanta yayi mummunar faduwa,da gaske goumar yakeyi bazai bar shiga shirginta ba?,wato har wani nuni yake musu dashi a hoto "Tashi ki bani waje" ta fada tana watsa mata harara. Har ta miqe sai ta dawo a sanyaye,ta tsugunna gabanta murya a sanyaye "Kiyi haquri aunty" ta fadi tana mutsuka idanunta da qwalla ke fita. Ido tadan xuba mata na sakanni,tausayinsu su dukka yana ratsata,ita da yaran gaba dayansu ababen tausayi ne,sai itama taji nata idanun sun ciko,ta sanya hannu ta jawota ta rungumeta a jikinta. Ajiyar zuciya yarinyar ta saki tana yin luf a jikin nata,kasancewar basu fiya samun wannan damar ba,saida tayo controlling nata hawayen don kada ta gani sannan ta sake tana cewa "Kije wajen bibi naji kaman tanja na kiranki" "To" ta amsa tana miqewa da dan tsallenta tamkar komai bai faru ba,gashinta dake daure yanaya lilo a bayanta ta fice a dakin. Binta tayi da kallo har zuwa bakin qofar,sai a sannan taga ama dake tsaye hannayenta goye a qirjinta. Sauke hannuwan tayi ta tako cikin dakin,yau dai sau daya tak taji zata yima.sultana din magana,zafin qiyayyar aliyyu da take gani a idanunta sun fara bata tsoro,tayi tsammanin ilimi shekaru da kuma wayewa sata samu zasu goge komai,koda komai din bai gogu ba tayi zaton xai ragu ainun har ya zamana bai iya bayyanuwa a idanun mutane "Sai yaushe sultana?,sai yaushe zaki sassautama ranki wannan abun dake qulle cikun zuciyarki?" Karon farko tayi mata tambayar ido cikin ido. Qasa tayi da kanta,ba zata iya jurar kallon qwayar idanun ama ba,nauyin da dukka ruhi keji akan uwa game da d'anta ya saukar mata. Da alama abun ya zafafi ama a yau tunda har ta magantu,shine abinda sultana ta raya a ranta,kamar ta karanci abinda take rayawar sai ta bata amsa tana gyara zamanta "Kada ki dauka naji haushi ne ko nayi fushi ko kuma zanyi fushin,ko kadan,shekarun da muka dauka abinda nake gani cikin idanunki na saba ganin irinsun......amma yanzun rayuwa tana sauyawa ne,yaranki yaran aliyyu ne,bai kamata kina bari suna karantar wannan harshness din dake cikin idanuwa da kalamanki ba,wani abun bau cancanci 'ya'ya suna sani akan iyayensu ba,wata kakkaifa kuma qaqqarfar dangantaka ne da tafi qarfin kowa yayi shishshigi a cikinta.........zamu je umra cikin satinnan in sha Allah,daga can zamu wuce nijer sai bayan bikin aminata da yasmine zamu dawo,amma immediately saboda maganar gidan tv dincan" kai ta gyada hawaye suna son sauko mata,amma batason tayi kukan,kada ama ta zaci don ta mata fada ne "Kiyi haquri" tace da ama bayan aman ta miqe,a sanyaye ta waiwayo tana dubanta "Ke ya cancanci ayita bawa haquri sultana,ba za'a daki mutum a hanashi kuka ba,kawai dai kukan saffa saffa ya dace kayi,tunda kayi imanin ko meye ya sameka ko zai sameka daga Allah ne" kai ta sake kadawa a sanyaye. Hannuwanta dukka biyun ta sanya ta lullube fuskarta dasu tana sakin wani asirtaccen kuka. Ita kanta ciwon da qirjinta ke mata a kullum ta tuna da ita din wacece ya soma isarta,bataso,tanaso ta rayu da zuciya sakakkiya kamar kowa,ta rasa me yasa ta kasa watsar da komai,ta manta da komai?,ta manta da wanzuwarsa a duniya kamar yadda yayi nesa da rayuwarsu itama ta nesanta kanta da komai da yashafeshi "In sha Allah wannan zai zama jigon addu'a ta a wannan tafiyar......in sha Allah zan gayawa ubangiji na......zan roqeshi da dukkan sunan da yake amsa addu'a idan an kirashi da su,zan masa magiya ya sake nesantaka daga cikin tunani......daga cikin rayuwata ni da 'ya'yana......zan roqi ubangiji ya kawo silar tsinkewar igiyarka data daureni" ta yiwa kanta wadannan alqawuran. Tana takawa zuwa dakinta amma tunani ne fal zuciyarta. Duk da rakinta da ake gani.....duk da qin yarda da daukan qaddarar da wasu ke gani kaman ta gaza JARUMA ce sultanar,zama da igiyar wani da bakaso tsahon shekaru babban nauyi ne,ya kamata susan abunyi akai......amma wai ina maina?,INA MAINA YA SHIGA?,YANA RAYE KUWA ANYA?. Da wannan tunanin kadai saida zuciyarta ta buga,idan har ya mutu a ina?,a hannun wa?,waye ya sururta d'anta?. *_M A I N A_* Wani irin matsakaicin falo ne dake da wani irin atmosphere mai matuqar daukan hankali da tafiya da tunani. Komai dake wajen tun daga color da yanayin da aka tsarashi da kuma unguwar da ainihin ginin ma yake zakasan ya banbanta ya kuma yi nisa qwarai da kalar tamu rayuwar. Cikin daya daga cikin luxury sofas dake zagaye da falon yake zaune sosai,irin zaman da zakasan lallai yayi relaxing yadda ya kamata,bashi kuma da nufin tashi yanxu,hakanan da alama ba wani schedule dake a gabansa. Zabgegen farin ba'abzine,jazur tamkar ka sanya yatsa jini ya fito,dogo me murjajjen jiki,ma'abocin baqar sassalkar suma,tun daga saman kanshi,girarshi,gashin idanunsa har zuwa kumatunsa da aka yiwa sumar wani irin gyara dake zamewa fuskar mazaje ado na musamman me kama da gold a inda akasan daraja da kimarsa. Yanayin kayan dake jikinsa pajamas ne masu gajeran wando da kuma gajeran hannu,farare tassss tasu masu tsananin taushi da aka saqasu daga audiga mafi tsada da daraja. Dogoyan fararen qafafuwansa da hannayensa dukka lullube suke da gargasa baqa sidik saidai duk yawan gargasar bata hana bayyanuwar murdewa damtse da qafafunsa ba da kuma tsananin da fatarsa ke dashi wanda ke cakude da sirkin ja......duk da a zaune yake structure na jikinsa ya fita sosai a matsayin mutum ma'abicin shiga gym da daga qarafuna. Babu gilmawar annuri ko kadan saman fuskarsa,hannunsa na dauke da tab dinsa,a nutse kuma yana bin hotunan daya bayan daya yana kalla. A duniya bai taba jarabtuwa da soyayyar wani abu da baisan asalinsa ko tushensa ba irin yadda ya jarabtu da soyayyar wadannan twins din ba,a duk sanda yake kallon hotunan yaran yakanji tamkar ya cirosu daga jikin hotunan ya gansu a zahiri,yakanji har a ransa soyayyar d'ansa da goumar ya gaya masa sultana ta haifa tana hauhawa a ransa,yaron da ya tabbatar da gangan goumar yaqi bari ya gansa tsahon shekarun,duk wata jafa ko hanya da zaiga yaron goumar din ya tosheta,ya gaya masa.muddin yanasin ganinsa ya dawo gida,ya dawo cikin ahalinsa ya fuskanci ko ma meye. Abinda ya tabbatar goumar bazai fahimta ba a sannan,duk bayanin da zaiwa goumar bazai fahimceshi ba,shi daya yasan meke faruwa dashi,shi daya zai iya fahimtar damuwar da matsalar. Ya zuwa yanzun yana jin haqurinsa ya gaza...... tafiyarsan nan ta qarshe da ta zama cikamakin burikansa tazo masa da abubuwan ban mamaki masu tarin yawa,mafarkinsa yakai ga gaci,ya cimma nasarar rayuwar da a mafarki bai taba tunanin zata isar masa ba......yanajin yakai qarshe,ya kuma tuqe......yana da buqatar yayi gaba da gaba da ahalinsa......ya shirya karbar kowanne hukunci,ya kuma shirya fuskantar su dukka gaba daya. Yanason ganin d'ansa.....yana da buqatar ya bayyanawa d'ansa shi waye a wajensa,amma kuma dukka wadannan abubuwan me ya tanada?. "Ina da rabb" ya bawa kansa amsa,saboda yayi imani shi daya yasan me yake cikin zuciyarsa,shi daya yasan gwagwarmayar da ya fada shi daya yasan yadd ya rayu ya kawo wadannan shekarun har ya qarasa zama CIKAKKEN MUTUM ya fita a cikakken DR MAINA. Shawara guda daya tak zuciyarsa ta bashi yaji farinciki da gamsuwa. Yaji a ransa tabbas mafitarsa kenan,ya dangane da dakin Allah yakai masa kukansa kamar yadda ya saba,a wannan karon ya nemi qwarin gwiwar tunkarar ahalinsa,ya nemi jarumtar iya karbar kowanne hukunci da mahaifansa zasu yanke masa "Harda hukuncin rabuwa da sultana?" Mummunan tunanin da yaso birkitashi ya darsu a zuciyarsa lokaci guda. Kai ya dinga girgiza da sauri da sauri yana jin kowanne sashe na jikinsa na qaryata yiwuwar karbar hakan. Ya aza dukka qarfinsa ya tankwabe tunanin gefe,ya tattara hankalinsa akan sabon hotunan yaran. Murmushi ya dinga saki yana binsu da kallo gami da saukesu daya bayan daya akan tab din kamar yadda ya saba. Yana da hotunansu bila adadin dashi kansa baisan yawansu ba,abinda ya sani dai ba'a taba dora wani hoto nasu a personal Instagram account din yaran bai saukeshi ba. Yayi bincike yayi bincike amma ya kasa fahimtar 'yan wanne qasa ne?,ina ne asalinsu?, ba'a taba dora hoton wani abu ko hoton wani ba sai nasu,ba wani abu da aka tana dorawa da zai sanyaka fahimtar su din su waye. Sai daya gama saukesu tsaf sannan ya sauya wallpaper na iPhone da tab dinsa da sabon hoton nasu kaman yadda ya saba. Tsaiwa yayi yana kallon yadda hoton yayi kyau saman screen din wayar tasa,wani miskilin murmushi ya kubce masa. Mutanen da suke mu'amala dashi wansunsu da yawa suna tsammanin yaran 'yan uwansa ne,banda sunsan single yake da yawa zasu zaci nasa ne yaran saboda yawan hotunansu da yake dasu,da kuma yawan dorasun da yakeyi zaman dukka screen nasa da yake using dashi. Wasu lokutan shi kansa yakan gayawa kansa ya zaqe da yawa,to amma shi kansa baisan me yasa yake jinsu har cikin jininsa ba. Knocking da akayi a qofar falon dake waje hade da kada bell ya sanyashi daga kansa,ko ba'a yi magana ko ya duba camera ba yasan waye,ba wanda ke hada masa irin wannan rubdugun knocking da bell din idan ba suhail ba,sai ya aje tab din ya miqe zuwa bakin qofar. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 44 Yana bude masa qofar ya dawo ciki abinsa ya koma inda ya tashi ya zauna. Suhail din ya shigo kunnensa manne da waya yana amsawa. Hannun kujera ya samu ya zauna yana ci gaba da amsa wayar,yayin da maina ke sake ci gaba da kallon fuskokin yaran. "Haka Allah yake jarabtar bayinsa da qaunar wasu bayin nasa na daban da basusan da zamanka ba" suhail ya fada yana danna wayarsa. A nutse maina ya daga kai yana duban fuskar suhail cike da mamakin furucinsa. Yaune karon farko da yayi magana akan yaran cikin kwantar da harshe da kuma murya. Kusan ko yaushe yafi zabar tsokanarsa da yi masa iya shegen "Mutumina gwara kayi aure ka haife mana twins dinnan ko fuskokin yaran nan zasu huta" sau tari saidai yayi murmushi kawai ya shafi sumarsa. Har yanzu cikin suhail da ahmad bello da sukewa laqabi da sardauna.....mutanen da suka zame masa shaqiqai kuma makusanta bayan barinsa gida basu taba sanin ya taba aure harda yaro ba. Wani irin mutum ne shi tun asali me tsananin zurfin ciki,zaiyi wahala kaji qorafi ko wani zance daban a bakinsa. Tun a halittarshi yana da qaranta magana da surutu......a yanzun kuma sai abun ya zame masa ninki. Akwai yawa yawan mutane da sukayi tsammanin kurma ne shi din,rana ta farko kuma da yayi magana a gabansu a mamakance suke waiwayowa suna dubanshi saboda ranar ne suka fara jin lafazin bakinshi. Kallon da maina din yakewa suhail ya tabbatar tambaya ce cikin idanun nasa,amma yasan zaiyi wahala ya tambayeshin kai tsaye,don haka ya aza wayar saman qawataccen glass table din gabansa ya goye hannayensa a qirji yana duban idanun mainan "Na fada soyayya da kallo daya tak aliyyu......I don't know how to explain it....abun kamar shirin film,ganina daya tak da ita ta ban kuma ganinta ba,har yanzu ban mance fuskarta da kuma kamanninta ba.....ina jinta kusa da zuciyata qwarai,bazan kuma fasa nemanta ba a duk inda nake tunanin zan ganta". Kamar maina ya samu statue haka ya zuba masa idanunshi har ya kammala,suhail din ya fuskanci hakan,yasan halin mutumin qwarai da gaske,ba lallai ya fahimci dukka dogon bayanin nan nasa ba,don haka yaja dan qaramin tsaki yana daukar wayarsa "Bansan me yasa na zauna naketa maka bayani ba bayan zuciyarka ba'a halicceta don taso diya mace har tayi sha'awar aure ba.......abu daya naga kana yiwa mahaukacin so wadannan yaran da bakasan nahiyar ma da suke ba" ya qarashe maganar yana zuba idanunsa kan wayarsa. Maganar tasa ta sanya maina maida dubansa saman fuskar tab dinsa,sannan ya zame tab din ya ajjiye yana hade hannayensa guri guda "Me yasa ka yiwa zuciyata wannan fassarar?" Ya jefawa suhail tambayar da wani irin sound me taushi saidai kuma cikin tsakiyar taushin muryar tasa akwai wani irin deep amo me saurin isar da saqo kunnen me saurarensa koda baka shirya hakan ba. Sai da suhail ya waiwayo ya kalleshi sannan yace "Ah..... Mr man,nayi qarya ne?,ko iya yadda LAILAH keyi maka tsahon shekaru inajin ya kamata zuciyarka ta narke ka saurareta......amma fa banga alama ba,ba alamun zakayi giving up,ko kunyar sardauna baka ji?" Kai kawai ya kada yana kallon gefansa "Akwai abubuwa da yawa da baki bazai iya bayaninsu ba suhail......." "I see" ya maida masa cikin gatse,sai kuma ya tsaya cak yana sake duban maina "Kai.......if i can remember kamar naga face din yaran nan zuwa na umra last fa?" A nutse maina ya sake kallonsa ba tare da ya motsa ko yace komai ba,saidai cikin qasa da second biyu ya fahimci ba wasa bane irin na suhail,da gaske yake "Really?" Ya tambayeshi yana dage dukka girarshi biyun "Yes.....da gaske nake.....kaman a hannun rival dinnan da kaji ina bawa sardauna labari.....a harami ne tabbas" haka kawai ajiyar zuciyar da maina baisan dalilinta ba ta kufce masa,muryarsa so cool yace "Zuciyata gaba daya ta karkata zuwa umra,ka dubamin yadda zan samu ticket da wuri mana please" "Kai da ka fini xuwa akai akai ai kaman ka fini sanin masu siyan ticket da wuri ko?" "Baya nan man din.....baya kusa" ya amsa mishi da alamun zaquwa sosai cikin muryarsa,sannan shigowar Moses wanda ya fito daga kitchen dauke da breakfast tray na ogan nashi yaja hanakalinsu. Rusunawa yayi ya gaida suhail,suhail din ya amsa masa yana dan janshi da tsokana kadan sannan moses din ya wuce yana shirya dining "Amma zuwa nayi muji yaushe sardauna zai dawo,mu kammala lissafi saboda nasan kowa yana da nashi plan din ko?" "Bazan zauna jiran sardauna ba.......kuyi komai koda bananan ba matsala bane,tunda idan na dawo dinma duka duka bazan haura sati daya ba zan wuce paris......next month asibitin zai fara aiki in sha Allah" "Alright......ba matsala" suhail ya fadi yana lalubar wata number "Kwana nawa zakayi?" Idanunsa na a rufe,yatsansa guda daya ya dagawa suhail sannan labbansa suka motsa da "Month". Sai ya maida kansa ga dannar wayar,ya sani duk sanda maina ya shiga irin wannan mode din bai fiyason takura ko yawan magana ba,wannan ya sanya suke dauke masa qafa da kuma yi masa uzuri,duk da basusan taqamaimen damuwarsa ba har kwanan yau. ********Benazeer da batoul ke akan gaba janye da wasu kyawawan qananun qawatattun luggage dai dai su wanda ama ta bada order yinsu musamman saboda benazeer da batoul din tun daga dubai. Kowanne luggage na dauke da sunayensu a jiki da wani ruwan gold din rubutu. Abayar jikinsu ma haka ta kasance,gray color ce da tayi masifar dacewa da yanayin yaran. Kubul kubul dasu babu rama babu mummunar qiba,hutu jin dadi da zallar nutsuwa ta bayyana tattare dasu. Komai dake a jikin dayar akwai jikin dayar,abinda zai matuqar rudar dame kallonsu yayi tsammanin mutum daya ne aka tsagashi gida biyu,don hatta da rufaffen takalmin dake qafarsu na kamfanin D&G ba abinda ya banbantasu dana juna,haka siririn agogon gold dake hannuwansu. Suna gaba ama da sultana na biye dasu,su dinma abayar ce a jikinsu me matuqar tsada da daukan hankula. Batasan me ya sanya ba wannan karon tunda suka diro madeena gabbanta suke a sanyaye,tayita neman tsari daga sharrin shaidan koda shike da niyyar hanata ibada wannan karon tuquru kaman yadda ta saba,tunda shi din maqiyin duk wani dan adam ne,ta sanya hannunta ta gyara zaman glass dinta dake taimakawa ganinta,wanda akayi mata tun a wancan lokacin da idanunta suka samu raunin gani. Tun zuwansu Austria ama ta sanya aka sabunta mata shi,aka maidashi na ado sosai,a wancan lokacin qin yin amfani tayi dashi,sai a sannu data fara fahimtar inda rayuwarta ta sanya gaba ta nemeshi,ya zuwa yanzun kuwa tana nan dasu kala kala,dukkansu zaka dauka tana sakasu ne saboda ado. Ba yadda aba baiyi da ita ya fiddata a duba idanun ayi mata aiki me kyau ba amma ta qiya,tsoro takeji qwarai,tana ganin idan aka tabata ana iya rasa idanun duka ma. Kamar ko yaushe suna isa masauki tayi wanka taci abinci ta wuce masallaci,tayita zuba idanun ganinsu benazeer da batoul amma bata gansu ba,har ta kammala ta dawo bata gansu ba. Samunsu tayi cikin dakin sun baje kayan ciye ciye sunata fama,benazeer tafi batoul bawa abun muhimmanci,ita batoul da alama ta gama ta koma kan waya. Harara ta watsa musu dukkansu sai suka nutsu,bata ce musu komai ba har tashiga ta sake wanka ta fito,sai ta samu dakin wayam da alama sun gudu wajen ama,ta gyada kai tana jan qwafa ta koma saman gado ta nade ta fidda wayarta tana dan duba wasu abubuwa da suka shafi channel din da take sanya ran farawa aiki tare da dakon jiran shigowarsu. A qalla yanzun sun fara girma,shekara hudu cikin ta biyar ai sun san gabas sunsan yamma,ba zata barsu haka siddan su dinga zuwa waje me alfarma irin wannan ba tare da sunsan muhimmancinsa ba. Har ta gama jiran bacci ya saceta basu dawo ba,basu hadu ba sai data tashi sallar asuba,sai data kammala tata sallar sannan ta tashesu sukayi tasu,ta ritsasu tana tambayarsu me ya zaunar dasu jiya?. Inda inda suka fara mata,daga qarshe batoul ta sanya kuka, benazeer ce me bada haquri,ta musu kashedi sosai,wanda tana tsaka da yin ama ta shigo. Dariya ta dinga yi ciki ciki,ita tunda take bata taba ganin alaqar uwa da d'a irin ta sultana ba,gaba daya ta zame musu wata senior master bawai mummy ba. Da ama tabi ba'asi sultana ta gaya mata,sai ama taqi bin bayansu "Eh da gaskiyar auntynmu,daga yau a dinga qoqarin zuwa masjid kunji ko?,amma kuma auty ayi mana afuwa,a dinga tafiya daga baya zamu taho tunda munsan wajen kuma bamu da nisa,munyi alqawarin ba zamu sake zama daki ba,idan kuma mukace mun gaji a barmu mu dawo daki mu huta" ama ta fada tana hada hannayenta waje guda. Murmushi ne ya subucewa sultana hadi da nauyin ama,saita kada kai kawai,ama dai ta samu ta kwashe 'yan jikokinta suka fice hawaye shabe shabe. Tun daga ranar kuwa basu saba alqawari ba,kamar wasu manyan 'yammata,koda ta tafi zasu biyo bayanta,saidai kuma sai sun gama qailularsu,siye siyen chocolate da fadace fadacensu na tsakanin sako da sako. Satinsu guda kacal bibi itama ta iso,sukayi jiranta ta gama nata ibadar suka wuce makka. *_makka_* *_Al_ajyad street_* *_SWISSOTEL HOTEL MAKKA_* Kai tsaye motar kamfanin dake da alhakin tarbarsa ta wuce dashi swissotel,wanda kusan duk sanda ya shigo garin makka din bashi da hotel din da ya wuce wannan,hotel ne da yake jin dadin zama cikinsa sosai,saboda daga nan yana iya hangen haram tarwai,har wasu lokuta idan yayi tsaye daga bakin window din dakinsa yakan yi addu'o'i sosai kafin ya sake labule ya wuce. VIp suite suka bashi saboda cancantarsa da cab din,aka tabbatar da shigar da jakarsa ciki,da kuma tambayar abinda yake da buqata suka gabatar masa sannan suka danqa masa dakin a hannunsa. A nutse yake cire lallausar rigar saman kayan jikinsa,daya daga cikin shigar 'yan qasar hindu,riga ce me wando da top dinta qarama me budadden gaba,wadda an saqata ne da yadin zaren vicuna mai matuqar daraja da tsada. Da baya ya zauna saman sofa din dake dakin yana lumshe idanunsa,kanshi yana kallon sama yana furzar da numfashi da kadan da kadan ta cikin bakinsa da wata iska me zafi. Wata nutsuwa ke zagayashi,a duk sanda ya tsinci kansa cikin qasar sai ya dinga jin zuciya da qirjinsa wasai,saidai kuma hakan baya hanashi jin wani abu a jikinsa,irin jin da me nauyin laifi saman kansa yakanji a duk sanda ya gujewa laifinsa da ya aikata. Tsahon shekaru yana jin wannan abun a dukka wani motsi ko tattaki na rayuwarsa,ko sau daya koda na minti daya zuciya ruhi da kuma gangar jikinsa basu taba samun hutu ba game da hakan,a haka ya rayu.......darare da yawa bacci yana qauracewa idanunsa......lokutta da yawa yana sarayar da baccinsa ya zauna dangwargwar,sautukanta......furucinta da lafazzanta suna dawo masa sabbi fil cikin kansa..... zuciyarsa na tuhumarsa,tana sake maimaita tuhumrsa,me yasa?......don me ya gaza kai zuciyarsa nesa?,don me yasa ya kasa haquri ya dauke kai?,me yasa ta gaza cin albarkacin nafessa?,ya cika alqawari?,yayi abinda ya dace?,a yau inda nafessa zata dawo duniya zaya iya fuskantarta?. Bai sani ba shima.....baisan me yahau kansa ba,baisan me ya fusgeshi ba......kawai yaji har cikin ransa ya aikata,hakan kima shine dai dai.....shi zai sanyata nutsuwa,shi zai zama mafarin lanqwasuwarta da shigarta taitayinta. To ashe dukka yayi bahaguwar fahimta,ashe muqulli ya sanya zai kuma bude musu sabbin shafuka da qofofin qaddara masau tsauri da nisan zango irin wannan. Sai daya samu nutsuwa gabbansa suka huta sannan ya bude idanun nasa yana duban agogon dake manne a bango, mintuna qalilan suka rage a tayar da sallar isha'i,kuma yana da matuqar muradin samun sallar cikin jam'i,kamar yadda duk tsanani ko wuya ko a ina yake baya barin jam'in kowacce sallah ya WUCESHI,musamman asuba da isha'i saboda falala dake cikinsu. Kayan jikinsa ya fara ragewa,yana cirewar yana jin yadda wayarsa ke qugi. Baiyi koda attempting din tabata ba,saboda yaga wacece me kiran,yasan kuma ba Wanda ya shaida mata ya tabo nan din sai suhail,yanzun kuma ba lokacin wasa ko lokacin bata lokaci bane,duk da dama can ya bawa wajen muhimmanci me tarin yawa cikin rayuwarsa,da har baya iya daukan lokaci baizo ba,to amma yanzun buqatu gareshi masu nauyi,wani babban aiki ne a gabansa da yake da buqatar jajircewa yayi addu'a da kyau. Cikin kayansa ya fidda bathrobe ya rataya sannan ya wuce toilet abinsa. A gaggauce suka iso swissotel suka kuma gama komai suka karba maqullan dakuna guda biyu kamar yadda suka saba,daya na ama da aba,daya kuma nata da su benazeer da bibi,don haka classic room suka dauka me gadaje uku. Suna shiga ta duba lokaci,sannan ta sake duba babban agogon nan dake garin makka. Lokacin isha'i ya kusa yi,don haka a gaggauce ta cire kayanta don watsa ruwa,tanason a qalla takai tsakiyar dare gaban ka'aba,akwai tarin buqatu da take dasu,ta kuma tabbatar tayi imani tare da yaqinin amsasu a wajen kamar yankan wuqa yake,ba wata addu'a da tayi bataga karbuwarta ba,a yanxun ma tazo da kukan yankewar igiyar aure da tayi saura tsakaninta da maina,don bata da qwarin gwiwar sake fuskantar su aba da zan can. Tun tana kasa kunnuwa taji aba din ya nemeta harta fidda rai,kullum zancan yana a ranta,saboda xuwa yanzun tasan girma da nauyin igiyar dake kanta tsahon shekarun........ "Ku gama abinda kukeyi da wuri,da minti goma yau zan rigaku fita" ta fada tana daga musu yatsunta gami da shigewa toilet din,sai bibi ta bita da kallo tana kama baki,abun mamaki wai yau sultana ce da tsantseni da tsananta tarbiyya "Yar nema,kina kamarsu ma sanda kike zuwa daki kike kwance abinki har muje mu dawo kina bacci shine yanzun da wanan sirisirin hannuwan naki kike irga musu lokaci" qaramar dariya ta saki tana tsaka da brush,don fes taji abinda bibin ta fada. Itakam ta karanceta irin mutanen dake son jikoki da yayan jikoki ne fiye ma da yadda sukewa yaransu da suka haifa soyayya "Allah yabar mana ke bibi" ta fada qasa qasa tana tuna wasu lokuta na quruciyarta can shekarun baya murmushi ya sake subuce mata "Ba abinda bashi da iyaka sai ikon Allah" ta fadi a ranta *_KACIBUS..........😂INJI HAUSAWA DON BANA QARASA BA,SAI NACE KUZO MUJE*_ 🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️ *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 45 Sun dudduba benazeer sun kuma tabbatar masa ba komai,don dama faduwar ba wata babbar faduwa bace. Dariya ta dinga yima maina "Uncle......wai tsoro kaji?,banji ciwon komai bafa,faduwar ma kuma babu zafi" ta fadi tana dariya gami da tafa hannuwa. Idanunsa shidai carrr a kanta,sai ya saki qaramin murmushi sannan cikin tsokana yace "Na ganki 'yar lukuta ne,kuma lukutaye basu da qarfi,sannan ma ance mutum idan ya cika fari shima bashi da qwari wai" ya qarashe fadi yana dan tabe baki kaman zai saki kuka yadda yara qanana sukeyi. Wannan karon har batoul sai data qyalqyale da dariya,sai shima ya biye musu yana tayasu,suka amsa receipt suka fito daga pharmacy din. Shagunan ice cream ya nufa dasu,yaja kujera kawai yayi zamanshi abunsa kamar wanda bashi da sauran aikin yi yace su duba duk wanda sukeso. Aifa benazeer an samu abunyi,duk bayan daqiqa sai ya waiwayo ta dubeshi "Uncle a sakamin banana flavor?" "Eh a saka miki" sai ya amsata yana murmushi,bayan wata daqiqar saita waiwayo tace "Uncle vanilla fa?" Sai ya sake murmushi yace " A baki" at last ya fahimci sun saba da shansa ne,kuma suna sonsa sosai don haka yace da ma'aikacin wajen "A musu takeaway na dukka flavours din da suke dasu". Murna ya kama benazeer harda qaramar rawa,shikam yana zaune tamkar wanda ya samu tv dake bashi nishadi. Duk yadda suka sake dinnan dashi abinda ya bashi mamaki,qememe wani sukaqi bin wani balare da yace musu shagon gabansu zai siya musu gift na Pizza. Suka hau kallon kallo gami da maqale kafada suna kuma satan kallon maina din. Dariya suka bashi suka kuma burgeshi qwarai,dole sai nan ya siya ya kawo musu,a nan dinma maina ne yace su ansa,saboda yasan wajen wajene mai aminci,ba wani abu na cutarwa ko me cutarwa da zaiyi tasiri a wajen. Shi ya riqo musu ledan suka qarasa haram sukayi sallah tare dasu bayan kowacce ta gyara mayafin abayarta,ya dinga dariya sanda suke gardama tsakanin benazeer da batoul,ita batoul tace lallai sai benazeer ta sauya alwala saboda ta fadi,kuma ma tayi surutu da yawa,itama kuma ta dage kai da fata alwalarta ba abinda tayi,da qyar ya raba gardamar. Kiran wayarsa da akayi ya sanyashi miqewa don ya matsa gaba kadan ya amsa wayar saboda wajen da sukayi sallar yana ganin bai kyautu ya daga wajen ba. Yana Allah Allah yacemusu su tsaya ya maidasu masaukinsu amma number dake kiransa din tana da matuqar kima da martaba a wajensa,don haka ya taka a hankali yana qoqarin dagawa. Kallon benazeer batoul tayi tana miqewa "Mun dade B,nidai tafiya zanyi,kya taho" "Bamu yiwa uncle sallama ba" ta fada cikin yanayin damuwa tana kallon hanyar da yabi "Gobe sai muyi masa" ta bata amsa tana sanya takalmanta. Miqewa benazeer din tayi tana yarda da maganarta,suka gama sakawa suka dauki ledarsu sukayi hanyar da zata sadasu da swissotel hotel. Sassanyan turarenta ta feshe jikinta dashi bayan ta kammala sanya rigar baccin me taushi da rashin nauyi,ta maida turaren ta ajjiye tana satar kallon bibi dake kwance tana kallon tv. Daga kai tayi sai suka hada ido da sultana "Wai ina yarannan ne suka tsaya haka?" Bibi ta fadi tambayar kuma data yiwa sultana din dadi kenan. Abinda taketa lissafawa kenan cikin zuciyarta,sun dade fin yadda suka saba,duk da dama shiriritarsu yawa ne da ita amma basa kaiwa haka basu dawo ba. "Ban sani ba bibi,hala shiriritarsu suka tsaya" ta amsa mata cikin basarwa tana ninke abayar data cire "Ke kinga banson kidifirin banza....sanya jilbab dinki ki bisu,don kunga waje amintacce ne kunsan ba abinda zai faru dasu amma ai yana da kyau a dinga bibiyarsu ko?" Bata musa ba ta miqe ta saka hijab din nata,don dama abinda takeso tason yi kenan,kunya da kawaici ya hanata. Bata taba tsammanin akwai yaran cikun zuciyarta da rayuwarta gaba daya ba sai yanzu. "B fuskar uncle fa kamar ba santa Allah" benazeer ta fadi tana yamutse fuska irin na yara masu surutu da shegen wayo. Harara batoul ta balla mata tana tura baki gaba "A'ina kika sanshi,yau muka fara ganinsa fa,kuma Allah duk sai na gayawa auty da ama abinda kika dinga yi" ido ta zaro tana kallon batoul din "Me kuma nayi?" "Ba an hanaki surutu da kula wanda baki sani ba,shine kiketa bashi labarin school enmu ko da fada masa sunayenmu" "Kuma daga wannan shine zakice zaki gayawa aunty?,don Allah B kinji kada ki fada,kinga uncle ai yana da mutunci,kuma ai don ya bugeni ne na kulashi,bazamu sake ma ganinsa ba inajin tunda bamusan ina yake ba" "Sai an fada din" ta fada tana murguda baki tare da fitowa daga elevator din bayan ya tsaya a floor dinsu benazeer ta biyo bayanta tana magiya. "Meye ake cewa kada a fada?" Suka tsinci muryar sultana dake qoqarin shiga elevator ta fasa saboda ganinsu. Tsuru tsuru dukkansu sukayi,sai kuma suka hau kallon kallo. Idanunta ta zuba musu sosai yadda ta saba musu duk sanda takeson gano laifi ko gaskiyarsu,a hankali kuma ta maida dubanta ga ledar hannunsu "Daga ina kuke?,waye ya baku wannan kuma?" Tayi furucin tana nuna ledar "Uncle haidar ne" benazeer ta furta da shagwababbiyar muryar nan tasu data cakuda da sauti na tsoro. "Uncle haidar?,waye haidar kuma.?" Ta tambayesu gabanta na wani irin faduwa,sunaye ukun nan a duniya,duk lokacin da zata jisu sai sun barwa zuciyarta razani ALIYYU HAIDAR MAINA. "Mun taho masallaci na siya ice cream dina ya bugeni ya zube,shine ya kaini pharmacy aka dubani ya kuma siyo mana wannan" yadda suka tsorata ya sanya ta sassauto "Da nace kada a siyoshi sai anyi sallah shine bakuji ba?,ku wuce ku bani waje" ta fadi a dan fadace. Da sauri sauri har suna rige rigen wuceta a tsakaninsu suka bar wajen,tana nan tsaye sai data tabbatar sun shiga dakin sannan murmushi ya qwace mata. Tabbas idan bakayi da gaske ba yaran saisu maidaka wani abun wasansu. Kudin hannunta ta duba,akwai abinda takeson sauka qasa ta siya itama,don haka ta matsa gaban elevator din tana yunqurin kiranshi, saidai ta nuna mata akwai mutum ciki dake haurowa saman,wannan ya sanya ta tsaya daga gefe tana danna wayarta tana jiran isowarshi. Kansa yana qasa,shima kuma wayar yake dannawa,a haka ya fito itama idanun nata nakan waya ta sanya kai ciki. Lokacin da suke gifta juna......iskar data debo kowa ta bugi dan uwansa har cikin jini da jijiyoyinsu sai da sukaji wani irin yanayi. Turarensa shi ya fara bugar da ita ya kuma haifar mata da qaqqarfar faduwar gaban data fusgi hankalinta,ta kuma kawar da hankalin nata daga kan waya,ta daga kanta tana duban bayansa......yana takawa ne a hankali kamar bayasin taka qasar,tsayyayen namiji me cikakkiyar siffa da zati,kwantacciyar sumarsa dinnan na kwance luf daga qeyarsa da take iya hangowa, dogayen hannayensa dake dauke da wasu veins kawai take iya hangowa,ta zubama bayan nashi idanu tana jin mahaukacin bugun da zuciyarta keyi irin wanda bata taba ji tayi irinsa ba,tilas ta yiwa kanta da kanta tambayar a fili yadda iya labbanta ne kawai suka motsa "Waye wannan?" Ta furta idanunta bisa bayan nasa. Tayi imani ba'a banza zuciyarta ke wannan bugun ba,tayi yaqinin koma waye akwai wani abu me qarfi tsakaninsu,tabbas!!!!..... zuciyarta ba zatayi wannan bugun da ya sabawa qa'ida ba muddin ba wani abu mummuna ke shirin faruwa da ita ba,wanda wannan tunanin ya sake haukata bugun zuciyarta. Shi kansa yasan ya danyi nisan tazarar taku tsakaninsa da elevator din yana replying saqon da ya zame masa kaman dole ne ya amsa din bawai don yana so ba.......amma cikin kowanne jini dake harbawa jikinsa wani abu yaji yana bibiye da harbawar tasa zuwa qwaqwalwa da zuciyarsa. Cikin jikinsa yaji kamar akwai wasu idanuwa masu kaifin gaske dake kallonsa,akwai wani dake bibiye dashi daga bayansa,wannan ya sanya ya juyo a hankali zuwa saitin elevator din,daidai sanda ta gaji da barin kanta da kanta a hangame ta soma rufe kanta. Cikin idanuwanta idanunsa suka fada,haduwar idanuwa hudun da suka bada wani gigitaccen yanayi cikin zukata da qwaqwalensu. Dukkaninsu jinsu sukayi kamar daga wata duniya suka fado kwatsam ba tare da kowannensu ya shirya ba,babu wani dake iya cikakken motsi bare yunqurin janye idanunsa tsakanin shi da ita,har sai da qofar ta fara motsawa zata rufe din. Kamar wani magnet ya jashi haka yaji,ya fara takawa da wani irin sassarfa da hanzari yana nufar elevator din. Ruf ta rufe kanta kafin yakai ga isa,yana miqa hannu kuma ta fara sauka qasa dauke da sultana wadda ta kama qarfen jikin elevator din kam ta riqe gudun kada takai ga faduwa,saidai kuma duk da hakan zuciyarta da ruhinta dukka sun gaza samar mata da qarfin da zaya iya riqeta a tsayen,dole ta sulale a hankali cikin elevator din ta zauna dirshan tana jin kamar tana shirin fita a hayyacinta ne.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 46 Da sauri ya lalubi wani elevator din,ya kuwa samu a kurkusa dashi,ya iso ya shige,saidai ya kasa tsaiwa waje daya,yana jin kamar dakin ba tafiya yakeyi dasu ba,kamar a tsaye yake cak waje daya,cikin qwaqwalarsa wani abu ke masa yawo kaman ana yamutsata. Cancan nesa da hotel din nasu ta kai kanta,wani mayalwacin guri da babu kowa sai haske da tsirrai da aka qawata wajen dashi. Sulalewa tayi agun,ba ruwanta da wai a qasa take,ta zuba dukka hannuwanta saman fuskarta tana qoqarin maido da numfashinta daidai. Kokawa tsakaninta da zuciyarta ruhi da kuma numfashinta,tsahon wasu mintuna masu yawa kafin ta samu numfashin ya dai daita a qirjinta "Maina na gani?,haidar?,Aliyyu?,da gaske yana rayen kenan kamar yadda goumar yasha gaya mata?.......kenan hakan yana nufin watan watarana zai dawo zuwa cikin rayuwarsu?,ama tasan yana raye?,yana kuma kusa dasu?,aba fa?" Tambayoyin da sukayi mata tsaiwar mashi aka kenan,saidai daga bisani zuciyar ta bata tabbacin "Basu sani ba!,duka tambayarki amsarsu basu sani ba" kanta ta sanya tsakanin cinyoyinta,sai taji kawai babu abinda take sha'awar yi irin kuka,kuka data jima da ajeshi cikin rayuwarta,ta tattara duk wani koke koke tun daga sanda ta soma hankali cikin hassan Ibrahim gwarzo ta ajjiye ayau shi ya dawo mata sabo fil,ta sakeshi a hankali ya soma fita da wani zazzafan tsohon miki. Daga cikin swissotel tun daga first floor zuwa floor na qarshe baisan adadin sau nawa ya duba ba,daga nan ya sake maida qafafunsa zuwa cikin haram bayan zuciyarsa ta gaya masa ta tafi tayi addu'a,ya zagaye haram har qafafunsa suka soma gaya masa tafiyar ta soma yawa akan wadda ya saba yi. Duk wani tunaninsa ya kulle,abinda kawai yake iya tunawa sultana ya gani,kuma ita yakeson ya lalubo,baiji gajiyar zaryar da yakeyi ba har sai da zuciyarsa ta ladabtar da dukka gabansa,ya sulale ya samu waje cikin reception din gaba ya zauna bayan ya shafe awanni yana abu daya. Wayarsa kawai ya sake zarowa,ya lalubi number yayi kira. Cikin nauyin bacci suhail ya daga kiran ya saka a kunnensa "I thought kayi bacci tun tuni,ko murnar ganin dream twins dinka ya hanaka?" Idonsa ya lumshe yana jin bugawar da zuciyarsa takeyi,shi kam ya manta ma da batun yaga yaran,abinda ya gani yanzun duka ya shafe wannan "Inason kayima mutanen nan magana,nijer da Nigeria duka nakeson shiga,banzan ainihin inda zan sameta ba,a rage lokacin da aka dibamin,bazan iya kaiwa har sannan ba.......next week zan bar nan". Duka zantukan sai suhail ya kasa ganesu,don baisan komai akan abinda maina ke magana ba "Wacece zaka samo?,me zakayi a nijer kuma?" "Kayi yadda nace please,ayi arranging komai saboda idan na shiga bansan ranar fitowa ta ba sai Allah" yayi furucin duk wani qarfin gwiwa da yake tunanin zai samu yana narkewa daga zuciyarsa "Are u okay maina?" "Yes iam" ya bashi amsar dashi kansa yasan ba ita bace haqiqanin gaskiyar yana zare wayar daga kunnensa,sai kawai ya maida bayansa jikin kujera yayi relaxing,idanunsa naci gaba da bibiyar kai kawon mutane cikin wajen,yana jin kamar ya tabbata a wajen har sai ya gano ainihin location nata. Maida dubansa yayi ga ma'aikatan dake wajen,yayi imanin da zai bincika akwai komai nasu cikin hotel din muddin a nan din ta sauka,to amma bashi da yaqinin daga ina take?,ina ta tafi?,wajen wasu tazo?,duka bai samu wannan information din ba. Number goumar da ya rasa shine mafi girman rashi da yayi a wancan shekarar,ya daina jin komai,komai ya yanke,baisan kuma ta yaya zai sake samo wani abu da zai sadashi da goumar din ba. Abune me wahala su bada information na wani room,ba zasu bada ba,hasalima zai sanya sunyi zarginsa da wani abu. Wannan tunanin ya sakashi qarasa debe duk wani tsammani nasa,ya maida idanunsa ya lumshe,sai ya dinga jin sunayen Allah na zuwa kanshi. Fara maimaitasu yayi daya bayan daya,yana yi a hankali yana samun nutsuwar zuciya da kuma ta ruhi. Sosai taji yadda idanunta sukayi nauyi suke mata kuma mahaukacin radadi,ko da bata duba ba tasan sunyi kumburin da duk wanda ya kalleta zai fahimci kuka tayi ba na wasa ba. "Ya hayyu......ya qayyumu..... birahmtika astageesu....hasbiyallahu lailah illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ta dinga furtawa a fili,saidai can qasa ta yadda idan ba mugun kusanci bane a tsakaninka da ita kunnuwanka ba zasu iya jin abinda bakinta ke furtawa ba. Sanda ta duba agogon wayarta sai tayi mamakin yadda lokaci yaja dare kuma ya fara nisa,tasan zasuyi tsammanin ta koma haram ne saboda sun santa da nacin addu'a idan akazo wajen. Ta saba raba dare a wajen,baccinta kuma qalilanne,wannan dalilin tasan shine kadai ya sanya basu nemeta ba. Dukka wani kuzari da za'a samu jikin dan adam babu shi a jikinta,a haka ta dinga takawa har ta maida kanta swissotel. Ta samesu dukkansu sunyi bacci,yaran na jikin bibi duk su biyun,da alama tatsuniya ko labaran data saba basu take basu bacci ya daukesun. Taji dadin hakan qwarai,saita lallaba ta daura alwala,daga zaune tayi sallah raka'a biyu amma ta kasa roqar komai,ta maida kanta ta kwantar saman qafafunta wasu hawayen na zirarar mata. Wani irin wahalallen dare yayi cikin wani yanayi dashi kansa baisan taqaimemen inda ya dosa ba......baisan me gobensa ke tanadar masa ba,kuma har yanzu baisan da fuskar da zai kalli ama ba,ta bibi me sauqi ciki cikin sauqi ma......amma aba fa?. Yafi kowa sanin waye din aba,ya sanshi tamkar yunwar cikinsa,shekara biyar ba wasa bace.....ya sani aba bazai taba aminta da cewa ba GUDUN K'ADDARA yayi ba.....bazai taba yarda cewa SHIKE BIBIYAR QADDARAR BA.....cikin kowacce dama daya samu.....daidai da second daya bai taba daga qafa ba saidai idan DAMAR ta kubce masa. Yadda ta tashi da zazzabi me zafi haka ya tashi da mugun ciwon kai,saidai ko sau daya bai matsa daga bakin tafekeken window din dake dakin ba me kamanceceniya da qofa,idanunsa dukka cikin sashen harami,shine abu guda daya dake sanya masa nutsuwa da kuma juriya. Kiran sallar azahar daga masallacin haram shine abinda ya tasheta. Ta bude idanunta a hankali tana qarewa dakin kallo. Ta tabbatar cikin dakinsu take na hotel din,abinda ya bayyana mata inda ta ganta a yanzun mafarki tayi. Shareren fili ne dake dauke da wani irin farin yashi iya ganinka,ba kowa cikin filin daga ita sai maina din. Wasu fararen kaya ne a jikinsa farare qal matuqa da sukayi kusanci da yashin dake shimfide qasan qafafunsu. Sutura ce irin ta asalin buzaye,ya kuma qawata shigar tasa da nadi irin na asalin ba'abzine,nadin farin rawani shima tas dashi wanda ya sake qarawa fuskarsa wani madaukakin kyau da kwarjini. Tsakaninsu duka duka taku ne baifi biyar ba,ita dinma kuma cikin shigen shigarsa take na fararen kaya,kanta babu dankwali sai iska dake wasa da gashinta daga hagu zuwa dama. Suna tsaye carko carko,kallon kallo sukema juna su duka,a duk sanda maina yadan motsa sai ta matsa baya,sunyi hakan ya kusa sau goma,daga qarshe ta jita caraf a hannunsa,kafin kuma tayi kowanne yunquri ya lullubeta da faffadan qirjinsa. Mutsu mutsun qwatar kanta ta dinga yi amma hakan ya gagara,yanason rada mata wani abu a kunne ne amma taqi bashi dama,daga qarshe ta soma cizonsa tana yakushinsa amma tamkar ba jikinsa takema haka ba........sai muryar benazeer ta bayyana tana qwala mata kira,kiran nata da tayi shi ya sanyata farkawa daga baccin ya kuma yanke mata mafarkin. Sai data tattara nutsuwarta sannan ta miqe a hankali,ta zauna sosai tana duban jikinta da kyau. Haka kawai ta dinga jin kamar qamshinsa ne cikin jikinta,wannan ya sanya kanta yaso sarawa,ta saka dukka hannuwan nata ta dafe kan nata bacin rai yana ratsa zuciyarta. Ta tabbatar kuma jikinta yana bata masaukinsa yana a wahen,ko cikin hotel din ko kuma wajen hotel din,muddin kuwa haka ne ya zame mata dole tayi takatsantsan ta kuma kula da kyau harsu kammala kwanaki hudun da suka rage musu subar qasar. Ba zata taba bari wani yaji labarin wai ta ganshi ba,hakanan zatayi duk me yiwuwa ta tabbatar baiga yaranta ba. Wannan tunanin ma ya sanya ta janyo wayarta ta kira number ama. Bugu daya ta daga, muryarta adan dakushe tayi sallama "Kin tashi kenan?,mun dan fita siyayya kina bacci,zazzabin ya sauka?" Boyayyar ajiyar zuciya ta ya sauke "Ya sauka ama,batoul suna tare dake?" Tayi mata tambayar dake qasan ranta "Eh muna tare....." Ta bata amsa matuqar mamakin tambayar sultanar tana kama ama,saboda abune da bata taba yinsa ba "Akwai wani abu ne?" Ama ta kasa shuru ta tambayeta,da sauri ta girgiza kai kaman tana wajen "Ba komai,kawai jiya sai da na fita nemosu ne ama,suna nisan kiwo sosai" mamaki ya sake kama ama,yau sultana ke magana haka akansu batoul kai tsaye?. "Kinfi kowa sani muddin cikin haram ne ba abinda zai faru,just relax....." Aman ta fada murmushi yana subuce mata. Sautin murmushin ama din ya sanya kunya tadan kamata,saita wayance dayi musu adawo lafiya,ta maida wayar ta ajjiye gefanta tana sauke ajiyar zuciya. Har yanzun kallon kallon da suka yima junansu a daren jiya ya kasa barin idanu da kwanyarta,hakanan kallonsa na cikin mafarkin me kama dana jiya. Qatuwar tsaki taja,wani irin tsanarsa yana ratsata,ba abinda fuskarsa ke tuna mata sai zallar azaba qunci da jarrabawar daya afka rayuwarta a ciki. *_Masu karatu......marabanmu da isowa gaba😂😂😂.......wasan zaya fara,sai nace Allah ya hadamu ranar litinin muji_* *Waye zaiyi nasara?" *Waye zaiyi giving up?* *Ta yaya maina zai fuskanci mutum hudu zuwa biyar?* *Ama* *Aba* *Bibi* *Benazeer batoul* *Me gayya me aiki SULTANA?* _ASHA HUTUN QARSHEN MAKO LAFIYA_ *HUGUMANKU CE*🥰*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 47 A nutse ya rufe mas hafin qur'anin dake hannunsa,yayi addu'o'i na wasu sakanni sannan ya maidashi ya ajiye. Wayarsa ya jawo ya bude,makeken hoton benazeer da batoul dake saman screen din wayarsa ya bayyana. Sunyi matuqar kyau cikin wasu pink gown,komai dake jikinsu pink ne,hatta ribbon da aka musu adon ka dashi da qananun dan kunnayen azurfa masu pink din duwatsu ne. Ajiyar zuciya ya sauke karo na babu adadi,fuskoki ukun wunin yau duka su suka hanashi kuzari ko wani karsashi. Fuskokin yaran da baisan meye hadinsa dasu ba yakejinsu da wani irin qauna me zurfi a zuciyarsa,da kuma fuskar sultana. Yes,sultana ce,ba wani abu ba kuma wasu shekaru yanayi ko zamani da zai iya hanashi ganeta,halittar daya raina da hannunsa ya bata dukkan kulawa. Ko ina yaronsa?,da waye yake kama?,ya girmansa yanzu?,duk bai sani ba,yana kuma daya daga cikin burikansa a yanzun. Yayi zirga zirga yau din tsakanin haram zuwa cikin hotel tsakanin kowacce sallah amma baiga wani abu da yayi kamanceceniya da ita ba. Ciwon kan da yake fama dashi duka yau bai barshi zama a masallacin ba,dole idan ya idar da sallah yake dawowa daki ya kwanta,amma yanzun da ake shirye shiryen kiran sallar isha'i sai yaji yana da muradin sake fitan. Yanason sake ganin yaran,ko suma sun nemeshi oho?,ko a wanne hotel suka sauka?,duka bai sani ba. Alwala ya sake duk da wancan bai baci ba,ya feshe jikinsa da turarensa ya sanya qaramar hular da bahaushe ke kira tashi ka fiya naci saman kansa sai gashi ya fita a balarabe sak,ya sanya takalmansa ya fito a dakin. Yana takawa har zuwa cikin haramin zuciyarsa na masa saqe saqe iri iri,bakinsa da kuma zuciyar tasa duka ambaton Allah sukeyi. Zuwa yanzu yanajin kamar ya rufe ido ya bude ya ganshi a nijer,yana jin ya shirya facing duk wani challenge.....duk wani tuhuma da kuma kowanne hawa da sauka bore da kuma bijirewa daga gurin koma waye. Cikin tsantsan sawa kai nutsuwa da kushu'i akayi sallan isha'i da shi,ya kammala dukka addu'o'insa,sai ya samu kansa da zama a hanyar da sukayi clashing da yaran jiya,saman wata concrete chair. Yana lazumi a hankali iskar wajen kuma tana ratsashi, cikin ruhinsa kuma yana jin kewar yaran,sai ya dinga hango fuskokinsu a jiya,daga shi har cikin yaran a cikin nishadi suke,dukka moment da sukayi spending tare ya zame masa memorable. "Uncle haidar....... uncle haidar" ya jiyo muryar dab da shi. Kaf qasar a yanzun yasan su daya ne zasu kirashi da wannan sunan,don su kadai ya gayamawa wannan suna,a ko ina da aliyyu maina yake amfani,idan yaso ya qara da MAYAK'I. Idanuwansa ya bude yana waiwayawa,dukkansu suna sanye da jilbab daidai jikinsu da yayi matuqar haskasu ya kuma qara musu kwarjini. Daga benazeer me giggiwa har batoul miskila murmushi sukeyi masa,alamun dake nuna sunji dadin ganinsa qwarai da gaske. "U are highly welcome my BB" kafin ya gama kaiwa qarshen zancan ma benazeer ta zagayo tana neman gurin zama kusa dashi "Dama na cewa batoul zamu iya ganinka fa,tunda aunty bata kiramu ba mu duba ko zamu ganka kafin lokacin komawa gida yayi" murmushi ya saki yana juyawa wajen batoul,yayi mata alama da hannu kan ta taho. Bata musa din ba ta zauna a daya gefan nasa,ya basu hannu sukayi musabaha dukkansu yana gaidasu da larabci. Ga mamakinsa sai yaji sun responding masa,yadan zaro idanu "Wanne yare da wanne kukeji?" Dariya benazeer ta bushe dashi tana kallonsa,saita nuna masa yatsa hudu "Ehnn......wanne da wanne?" Ya tambayeta irin amazingly dinnan yana fidda murmushi "Hausa,english,arabic....... France small small" dariya sosai ta bashi da yadda ta fadi small small din tana daga qaramin yatsanta. Kai ya jinjina sosai suna sake burgeshi,da alama sun samu background me kyau ta kowanne fanni na rayuwa "Za'a yimin magana da kowanne?" Kai suka gyada kusan lokaci guda,sai ya saki murmushi yana gyara zamansa sosai a gaskiyarsu,yana jin zuciyarshi da ruhinsa yana masa wani irin dadi,yana jinsa tamkar a tsakiyar ahalinsa "Bari na gayawa kowa abinda zaice" yana rufe baki benazeer ta maida masa da arabic,sannan ta sakeyi da sauri ta maida da France,sannan ta sake maida masa da english "Daman da hausan ka fada" ta qarashe zancan da fadin hakan. Dariya ne ya kamashi,fararen haqoransa dake a jere ras suna sheqi suka bayyana. "Na yarda....yanzun muje na bada gift na wannan abun" ya furta yana miqewa. Duk sai yaga basu motsa ba,ya waiwaya yana dubansu "Oya...... muje" "Aunty zatayi fada uncle" batoul ta fada tana maqale kafada. Dawowa yayi ya zauna ya dafa kansu "Idan zatayi fada kuce uncle ne ya baku sabeel.....kun gane?" "Idan mukace haka ba zatayi fada ba?" Kai ya gyada yana murmushi,duk sai suka sauka da karsashinsu suka bisa. Kaman jiya ya musu siyayya,saidai yau din ya siya musu dai dai daidai yadda zasu iya cinyewa ma a gurin,gudun kada ya sanyawa iyayensu rashin nutsuwa a zuciyarsu da kuma ayar tambaya. Tsakiyarsun ya zauna sunata ciye ciyensu suna qananun fadansu da ba'a raba sako da sako,wani lokaci kuma su sakashi a ciki ya raba ko su jefashi a hirar su har suka gama. Sanda ya niyyaci rakasu suka fidda idanu,suna tsoron ya hadu da sultana,don ko jiyan susan banda sun iso da wuri data fito nemansun nan saita gansu,sun tabbatar kuma zasusha fada qila harda punishment "Uncle zamu iya zuwa da kanmu" idanunsa ya lumshe yana gyada kansa "Goodnight" "Goodnight uncle" suka maida masa,zukatansu dukkansu cike da shauqi,kowanne a cikinsu yana jin kamar kada ya rabu da dan uwansa. Sai daya qara wasu awanni a wajen,ya sake addu'a sosai yana neman ubangiji ya shiga lamarinsa. Sai kusan sanda dare ya raba sannan ya wuce masaukinsa. A dakin kusan abun jiya ya hanashi bacci. Fuskar sultana da a yau yayi mararin su sake ganin juna,da kuma yaran. Baisan wacce jarrabawa ce take bibiyarsa akan yaran ba,amma yana jin wata irin tsaftatacciya kuma tatacciyar qaunarsu cikin zuciya da ruhinsa. *******Dukka kwanakin da suka rage musu cikin makka din a darare take,kowanne motsi sai take ganin kamar zata ganshi a masaukinsu kowanne fita da yaran zasuyi sai taji kaman zasu hadu,kaman zai kwashe yaran a nemesu a rasa,kowanne fita tata cikin kaffa kaffa takeyi da lura da duk inda zata gifta din. Tun daga rabar bata sake bin elevator ba ta gwammace tayita bin stairs har takai qasa,wanda idan ta fita din sai tayi zamanta cikin masallaci,idan ta dawo ciki kuma ta dawo din kenan sai kuma washegari. Duk sanda tayi hanyar elevator sai taga kamar zasu sake haduwa,kaman zata sake ganinsa irin yadda ta ganshi rannan. Kwana hudu kacal da suka rage subar makka su wuce nijer sukayi wani irin sabo dashi,hakanan shima yayi wani sabo dasu ta yadda har bai tuna haduwa sukayi kuma kowanne lokaci shi ko kuma su wani zai iya tafiya yabar wani. A jikinsa yake jin kamar gurin zamansu daya,kamar wani family ne shi dasu dake rayuwa cikin gida daya,kamar a nan zasu dawwama da yaran. A kullum bayan sallar isha'i sai ya zauna ya jirayesu. Duk irin yadda yake girmama lokaci......duk irin yadda ya tsani jira cikin rayuwarsa,duk kamewa irin tasa da rashin shiga sharafin kowa.......duk uban miskilanci da tsananin ginshira irin nashi amma bayan sallar isha'i saiya bata wananna awa daya zuwa biyun. Ko yana zama su iso,ko yazo ya samesu zaune a wajen suma suna jiransa. Ice cream da chocolate sun sha har babu iyaka,masu tsada ya koma siya musu irin wanda canjin da ama ke sanya musu cikin jaka bazai isa su siya ba,babu kuma me biyewa ciye ciyensu a cikinsu bare ya bisu ya siya musu da nasa kudin,don dukkansu sunsan girman wajen,zaman masallacin yafi komai cinye lokacinsu a wuni guda. Tunda benazeer ta fahimci a ranar zuwa azahar jirginsu zai bar makka hankalinta ya soma dagawa,tasan dai ba zasu kai lokacin da suka saba haduwa da uncle ba bare suyi sallama,ta kuma gaya masa zasu tafin. Gaba daya sai ta kasa sukuni,tana cikin kujera a kwance tana ta kallon batoul dake cin chips da fork,tana ta son ta kalleta suyi shawarar yadda zasu ga uncle su gaya masa zasu tafi,shima yaushe zai tafi?,yaushe kuma zasu sake ganinsa?. Yawan surutu kuzari da karsashin batoul ya sanya kusan kowa ma ya fahimci tana da damuwa. Tuni sultana ta fahimta,amma saboda kawaici da batason fiya zaqewa cikin lamuran yaran bayan ga qashin bayansu nan jigonsu a gurin saita kauda kai,saidai kuma tanata monitoring komai nata,ta kuma karanci tsaf akwai abinda yake damunta ya kuma hana mata sukuni. Qaramar akwatinsu da ama ta shirya musu tsaraba a ciki tazo ta ajjiye,saita juya kadan tana kallon benazeer "B....me yake damunki yau?" Tayi tambayar cikin salon nuna muhimmancin tambayar saman fuskarta. Zamewa tayi ya sakeyin lamo cikin kujera,sannan ta motsa qaramin bakinta "Ba komai" " Da gaske?" Kai ta gyada a hankali "Ko kuma kayan shaye shayen sanyin nasu takeso ba,tunda na fahimci duk sun zama shazumamu,sunma fi uwarsu son shan jarabbaben zaqin nan ai" Dariya ama ta danyi,ta jawo purse dinta data shigo da ita ta fidda riyals tana cewa "Su kenan suka ragemin dama......aje a siyo na bankwana" ta furta tana murmushi. Idanu sultana ta dauke gefe zuciyarta na motsawa,zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba ganin soyayya tsakanin kaka da jikokinta ba irin ta ama da su batoul. Haqiqa bibi ta sota,ta qaunaceta,ta kuma nuna mata soyayya me yawan gaske.....amma akwai wasu kusakurai da ramuka masu yawa a hanyar,wadanda tasan ta tsallakesu ne kawai saboda qilan taci albarkaci ko darajar wani ne. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* * *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 48 Da sauri benazeer ta miqawa ama qaramin hijabinta ama din ta sanya mata, batoul ma ta ajjiye abincin tana sanya lausasan wasu rufaffun takalma masu kyau suka sanya kai suna ficewa riqe da hannun juna,ama ta bisu da "Ayi addu'a" "In sha Allah" suka hada baki wajen fada. Sai da benazeer ta tabbatar sun sauka sannan ta kalli batoul "Nifa uncle zan nemo na gaya masa mun tafi fa" ido batoul ta zaro tana kallonta "A ina zaki ganshi?" "A inda muke zama,muje mu siya ice cream sai mu dawo mu wuce ta wajen ko zamu ganshi" dan jim tayi kaman me nazari,sai kuma tayi murmushi "Muje to". Shop din da ya saba kaisu suka shiga,suka zabi kowa flavor din da yakeso,har ma'aikatan wajen suna tsokanarsu "Yau babu fada?,ina uncle din nasu?" Dariya sukayi, benazeer tace "Baizo ba?,nemansa muke" daya balaraben yace " Tare kuke zuwa, sai dare yake zuwa tare daku" basu wani fahimta ba,sundai gane kawai baizo ba don haka suka sanya kansu suka fice benazeer na cewa "Ma'assalama". Suna riqe da ice cream din suna sha suna kuma bin duk hanyar da suke ganin zasu iya ganin uncle haidar amma babu shi babu dalilinshi,har batoul ta gaji,taja tunga sanda aka soma kiran sallar azahar "Kizo mu tafi gida tunda bamu ganshi ba,kada aunty tayi mana fada,ama ma kuma tace fa mu dawo da wuri" juya idanuwa benazeer tayi kaman me shirin sakin kuka,ta sake waiwayawa bayanta kamar me fatan ta bude idanunta ta ganshi a wajen,saita dawo da kallonta ga batoul wadda itama dinma duk ranta ba dadi "Muje" ta fadi a sanyaye. Haka suka jera suna komawa hotel din ba um ba um um. Sanda suka isa dakin duk sun fice zuwa sallar azahar,amma kuma kayansun sun gama hadasu tsaf,kowacce saita samu waje tayi lamo ba wani me magana ko kuzari a cikinsu. Koda suna shirin fita a dakunan saida ama tayi qorafi "Anya lafiya kuke kuwa.yau dinnan?" Ta fadi tana taba wuyansu,sanyi taji ba alamun zazzabi ba komai,batoul ce tace mata ba komai "To Allah yasa alkhairi" aman ta furta,saboda tsahon tarenta da yaran bata taba ganin jikinsu ya mutu haka ba. Nannauyan numfashi ta sauke tana furzar da iska daga bakinta. Cikin ruhinta takejin wani salama da nutsuwa suna saukar mata,zuciyarta kuma tana gaya mata tayi masa nesa ta tsere masa. Ta window din take kallon fadin sararin airport din,tana jin kewar barin qasar kamar yadda ta saba,amma tana jin farinciki idan ta tuna ta tserema idanun maina,sannan nan gaba kadan zata dawo ta sake ziyartar dakin Allah. Tafiya miqaqqiya daga birnin makka har zuwa qasar nijer. Tafiyan awanni goma sha daya suka sauka a niamy,daga nan wani jirgin suka sake hawa suka wuce marad'i. Iska ta shaqa sosai ta qasar nijer sanda tayi relax cikin daya daga cikin lafiyayyun motocin mallakin aba da ama. Wasu emotions suna cakuduwa cikin zuciyarta,qamshin qasartata yana motsata tare da tuna mata abubuwa masu yawa,wanda kusan fiye da rabinsu quruciyarta ne......yarinta da zallar wauta da ta tafka a rayuwarta,wani abun ya sanyata murmushi wani ya bata takaicin da shima din dai murmushi ne na dole ke qwace mata. Tun barinta nijer zuwanta daya kacal......wannan shine zuwa na biyu da tayi,zuwan daya banbanta da zuwanta na farko. A yanzun ta sake dawowa qasarta a matsayin cikakkiyar sultana,me yara har guda biyu,wadda ta mallakin hankalin kanta......sannan masaniya cikakken sani a harkar ilimin jarida. Sultanar da a yanzun kai tsaye zaka iya kiranta da madam. Dukkan wata sura da halitta nata na kyawu ya gama cika,ya kuma cakuda da zallar kwarjini da hasken ilimi. Ta zama classy qwarai,ta banbanta da girman tazara da wancan sultanar me rawan kai yawan surutu fitsara da rashin kunya. Yanzun ta zama wata sultana me yawan shuru shuru,wadda ba shirgin kowa take shiga ba,abinda ya shafeta ma ba kowanne take daga idanu ta kalla ba har ta bashi lokutanta. Isowarsu qofar makeken gate din mansion house din mallakin MAYAK'I ya sanyata daga tsintsiyar hannunta tana gyara zaman siririn agogon gold din dake hannunta,lokaci ta duba murmushi ya subuce mata sanda hancin motarsu ke shiga harabar gidan. Ba wani abu ta tuna ba illa lokaci irin wannan da take hada dabar hira,sam qawaye mata a sannan ba damuwarta bane,maza ma sunfi mata dadin qawance qwarai,saboda su din zata musu tsiwa tayi musu fitsara kuma su daga mata qafa don suna kallon ita macace kamar sauran mata. Idanunta cikin farfajiyar gidan da ta sake qawatuwa qwarai,anyi mata gyara sosai,da alama kuma dukkan gyaran yana da nasaba da bikinsu aminata ne. Ko ina yayi fes,tamkar sabon gini,tamkar ba wannan tsohon ginin da qarfi d kuma qoqarin NADEEYA ya samar dashi shekarun baya ba. Ko kusa ko alama mamallakan gidan basu taba barin tsufa ko shekaru su cimmasa,saboda kusan koda yaushe cikin aikin gyaransa suke,duk wanda ya samu dama a cikin kawunnan nata saidai kawai mutanen gidan suji ana shelar a kwashe ko za'a yi aiki. Idanunta ta janye sanda suka sauka a wannan bigiren....muhalli ne da kusan yafi zama a cikinsa akan ko ina cikin gidan,waje ne da yake zama yana kula da shige ficensu yana kuma monitoring motsinsu da tarbiyyarsu. A duk sanda zata kalli wajen koda sau dubu ne sai taji ranta ya baci sau dubun,shi ya sanya zabinta daya kauda kai a irin wannan lokacin. Motarsu na tsaiwa kusan duk wanda ke wajen ya ankara da isowarsu. Kafin kace meye wannan mutanen dake cikin gida ma sun fara fitowa tarbarsu. Kusan kowa ya fito ta batoul da benazeer yake. Batoul sarkin rashin yarda da shegen miskilanci da taga ama ta kutsa kai cikin jama'a sai ta koma jikin sultana ta lafe. Abun sai ya soma baiwa sultana kunya,saboda idanuwa data ja mata,kowa sai ya matso ya tsokaneta ya kuma tsokani sultanar,wadda a sannan idan kaga batoul dake jikinta zatayi rantsuwa yayarsu ce bawai uwa mahaifiya ba. Ko kusa ko alama duk qwaqwafinka baka isa kaga alamun sultana ta isa ta mallaki tiqa tiqan yara har guda biyu kamar benazeer da batoul ba. Wata motar ce ta shigo,najma aminata da yasmine ne a ciki amare. Najma ke driving aminata da yasmine da houda cousin dinsu suna baya,a kujerar gaba kuma djamilla ce itama dukka kakanni daya suke dasu sultana. A gaggauce najma ta tsaida motar,dukkansu cike da farinciki suke qoqarin fitowa,saidai ta rigasu ma qarasowa,fuskarta dauke da nutsatsen murmushin nan nata,da muryartannan me sanyi tace "An fara yawon amarcinne?,amma ko a jirani?" Junansu suka kalla da dan mamaki,ba wanda ya kawo zata nema sakewa a cikinsu shi yasa wasu abubuwan ma basu tsara da sunanta ba "Zaki iya yawo a cikinmu?" Houda ta fadi tana 'yar qaramar dariya. Waiwayowa tayi tana dunan houda da murmushin da ya tsaya saman kumatunta tace "pourquoi pas?(me zai hana?)" Ta fadi tana kallon houda "Yar jarida ce ke yanzun a qasar France...... kinga dole muyi takatsantsan karmu shiga ajin da ba namu ba" dole ta sanya sultana sakin siririyar dariya,siraran jerarrun haqoranta suna bayyana "Banason sharri houda.....har yanzun baki sauya hali ba?" "Inaaaa......wannan canjin saiku......na rantse bada wasa ba ko.......ban ganeki ba sai da kika matso sosai" kada kai tayi tana murmushi,tasan halin houda da kyau,tun suna qanana,tasu tafi zuwa daya saboda halin tsokana irin nata na da da take dashi "Amma sœurs(yan uwana)su ba zasu kasa ganeni ba ai" "Nima canzawarki ta jawo" "Ku bani hanya naje naga babies dina,don idan aka biye taku naga alama zamu jima tsaye a nan" aminata ta fada tana maida headphone dinta qaramar handbag din dake hannunta. Rufe qofofin motar sukayi suka fara takawa gaba dayansu zuwa cikin gidan,suna tafe suna tattaunawa akan dame dame aka tsara yi a bikin. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 49 Sake duba agogon wayarsa yayi don bai fito da agogo ba. Wannan dubawar yana irge ita ta zame masa cimakin dubawa na goma sha biyar kenan. Zubawa fuskar wayar idanu yayi wadda ke dauke da hotunan yaran,yaja godon numfashi daya sauka har cikin huhunsa. Kanshi ya sake dagawa yana duban jama'ar dake shige da fice cikin haram din wai ko zai ga gilmawarsu,saidai ko twins guda daya bai gani ba bare ya sanya ran dasu a ciki. Ya fara sarewa da ganinsu yau,saboda tun wancan ranar da suka hadu din basu taba kaiwa warhaka basu iso wajen ba,basu taba latti kaman haka ba,kamar yadda basu bata fashin zuwa ba. Dauke kansa yayi ya maida idanun nasa qasa,sai ya samu kanshi ya tsawaita a addu'a cikin zuciyarsa na zuwan yaran a nan kurkusa. Bayajin zai samu nutsuwa ko qanqani idan bai gansu din ba,zuciyarsa da rayuwarsa a kwanakin jinsu yakeyi a rikice gaba daya,hatta da suhail da sardauna da basu kusa dashi suna iya fahimtar haka cikin mu'amalarsu dashi. Duk wata tattaunawa da ya shirya zasuyita through video call ya kasa halarta,wani lokacin ma sai sunyi sun gama zaiga miscal nasu. Idan sun matsa da yabi sai yace musu duk yadda suka yanke yayi. Duk kawaici na sardauna sai daya magantu "Kafi kowa sani daddy bazai amince da dukka abinda zamuje masa dashi ba saiya tabbatar bisa yarda da sahalewarka ne tunda dai kaine jagora......kuma ma,ta yaya zaka jagoranci harkar lafiya a qasar dake da tsari da doka kana cikin dimuwa haka? what's wrong with you ne maina?" Sumarshi kawai yakan shafa duk sanda suka masa tambaya irin wannan,don baisan amsar da zaya basu wadda zasu fahimceshi su kuma gamsu ba,abu daya ya sani,Allah yana sonshi da ya kawo masa irin wannan yanayin a wajen da dukkan dimautacciyar zuciya ke samun nutsuwa,a muhallin da amsa addu'a bashi da shamaki da ubangijin dake amsa roqon bayi,banda hakan shi kansa baisan a wanne yanayi zaya kasance ba. Miqewa yayi bayan ya fahimci ya sake qara wasu mintuna ashirin din masu kyau,ya zube hannayensa a aljihun kaftan abaya dinsa ruwan bula(navy blue)wadda ta sake fidda ainihin kyawunsa na cikakken ba'abzine kuma bafulatanin buzu,sai ya tsinci kansa da gangarawa bangaren shops din dake hada hadar saida ice cream da sauran kayan zaqi,wajen da yasan duk dare shi dasu suna zuwa. Kai kawo ya dinga yi yana duba ice cream din zuwa chocolates din,saidai kawai yana zaba ne shi kansa baisan me zaiyi dasu ba. Nan dinma ya kashe kusan awa guda amma baiga alamarsu ba,har yakai lokacin da.ya tabbatar a irinsa ne suke ce masa sun tafi,daha qarshe ya fidda riyals ya biya uban chocolate da ice cream din da ya zaba yace su kyautar wa duk yaran da suka shigo. Cikin wani irin nauyin jiki da na zuciya yake komawa swissotel, zuciyarsa a mugun quntace da wani irin rashin dadi,duka ya rasa target dinsa,ba sultana ba kuma yaran,sai ya dinga jin kamar lokaci yayi shima da zai bar wajen,lokaci yayi da zai cimma sultana,cikin nijer......cikin gidansu. Yana fitowa daga elevator wayarsa ta dauki tsuwwa,sanda ya fiddata yaga me kiran sai da yaji kamar ya kyautar da wayar,don baya cikin mode na amsa kowanne kira. To amma hausawa sukace wata fuskar tafi gaban mari,ko don sardauna kawai kafin akai kan daddy,dole ta sanya ya daga kiran ya kara a kunne. A yangance tayi masa sallama,da qyar ya hada kalmomin amsa sallamar tata,yana jin kamar numfashinsa baya sauka cikin hunhunsa da kyau "Am sorry,zan kiraki wani lokaci" dan jim tayi,kamar bataji dadin furucin nasa ba,amma kuma sai tace masa "Okay" a taqaice sannan suka ajjiye wayar kusan a tare. Kasa haquri yayi,kafin ya isa daki ya lalubi suhail. Komawa yayi ya jingina da qofar dakin bayan ya maida ya kulle,idanunsa a kulle,kunnuwansa na sauraron yadda kiran ks gangarawa wayar suhail,gefe daya kuma yana sauraron bugun zuciyarsa. Sama sama suka gaisa,kai tsaye ba kwana kwana ya gabatar masa da uzurinsa "Banason na wuce kwanaki biyar suhail ban isa nijer ba" "Why?,me yasa kake caccanzawa kamar wani wahainiya ne maina?" "je ne sais pas non plus(nima ban sani ba)"ya fadi da harshen faransanci "Me kace?" Suhail din da yaren turanci yafi yawa cikin nasa harshen ya tambayi maina abinda yace din "I don't know suhail...... I don't know why" "But amma kasan a yadda muka tsara zakayi koda one week ne a Paris a gama komai koda a tsaitsaye ne sai ka wuce" "Noooo suhail,no.....bazan iya ba,koma meye ya jiraci dawowata......na gaya maka.....kwana biyar kadai zan qara a nan din.....bazan canza ba" daga haka ya katse wayar don kada ma suhail din ya sake kawo masa wani hanzarin,don bayajin akwai wani abu a yanzun da zai iya dakatar dashi kai kanshi nijer din. *********Tunda suka sauka a nijer shirye shiryen biki kawai ake cikin gidan babu kama hannaun yaro. Da fari ta soma halinnata na dararewa da kebe kanta akan komai,daga bisani su aminata suka mata bore kan basu yarsa ba "Abinda yayiki shi ya yimu,kuma meye hujja ki dalilinki na tsame kanki daga cikinmu sultana?,bayan idan kin koma paris sai mun ganki fa" wannan dalilin ya sanya tayi qoqarin sakewa sosai a cikinsu. Duk wata hidima sai sun tsomata a ciki. A hankali saita fara warewa,wannan yanayin......wannnan yanayin......wannan lokacin da wancan zamanin dukka da ya dade da shudewa cikin rayuwa da mafarkanta sai ya dinga farfadowa. A hankali ta dinga samun nishadi cikin zuciyarta,wani nauyi dake qirjinta ya dinga raguwa kadan kadan. Son kadaicewa......jin kanta kamar ta banbanta dasu ya dinga raguwa sosai. Mutum daya ke neman matsanta mata,babu daman ya gansu sun fito sai ya matso gaban motarsu,idan anci sa'a ita keda driving ranar kafin ya iso take maka baqin glasses wa idonta ta finciki motar su fice,najma tayita mitan ta bari mana ko wajenta zayazo amma bata bi kanta,idan kuwa najma cw driver dinsu na ranar to ya samu yadda yakeso. A fakaice yake gasa mata maganar "Karki manta,tu es la femme de quelqu'un d'autre(ke matar wani ce)" Baisan iya adadin yadda kalmar ke motsa zuciyarta ba,sai ranar da abun ya qureta kawai taji hawaye ya tsinke mata. Cikin arashi kuwa a gaban idanun uncle bashar abbanshi,shi yayi masa tas yace su shige mota su tafi abinsu,Allah ya tsare. Daga ranar ta samu sauqinsa,saidai fa hausawa sunce me hali baya fasa halinsa,duk ko yaya ya samu dama sai ya sake fesa mata,duk hade ranta da dauke kanta bai dameshi ba. Siyayya sosai ama tayi musu na biki a dan tsakanin,kayan gargajiya na hausa sosai,ready made na atamfa da laces,don su benazeer din basu da wani kayan gargajiya sosai saboda yanayin inda suka taso. Kafin wani lokaci ama ta kammala musu komai,don wasu abubuwan amma matar uncle bashar ta kammale musu dama. **********Tun yammaci ta sanya driver ya dawo da ita gida ta baro su aminata suka wuce wajen booking musu lallen biki. Ba yadda batayi su cire sunanta ba amma najma tace "Sai kiyita yi" najma ta fadi tana jan motar, driver modu ya jata ya dawo gida da ita. Duka saurin da takeyi don ta amsarwa ama girkin aba. Tana sallar la'asar ta kammala komai,qarfe biyar aba ya aiko atta a fito musu da girkin wani kebataccen waje daga bayan gidan,da alama suna sa tattaunawa ne shi da uncle omar da oncle bashar. Tun daga nesa ta fahimci zaman na musamman ne,akwai invitation na daurin aure da yawa a wajen da sauran takardu. A nutse ta durqusa ta ajjiye musu komai akan tsari,sannu dukka suke mata. Iya 'yan kwanakin kawai kowanne mamakin sultanan yake,kamar ba sultanar data fita a gidan bace wata ce daban aka sauyota. "Allah yayi albarka,ya shirya miki zuri'arki" aba ya fadi cikin qauna da kuma tausayi "Ameen aba" ta amsa ranta yana mata fari sosai "Bashar......ka rubuta cikin calendrier (schedule) na abinda zamu tattauna.....mu duba yadda zamu warewa marainiyar Allahn nan igiyar wannan yaron daga kanta don mu bata damar rayuwa cikin 'yanci kamar kowacce yarinya...". Wani numfashi ta zuqa me zurfi da nauyi tana jin kowanne gaba ta jikinta na rawa, zuciyarta ta motsa sosai da wani irin matsanancin bugu,qafafunta na hardewa ta qara sauri tana barin wajen ba tare da ta jiyo amsar dasu oncle bashar suka bawa aba ba......*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 50 Da dan sassarfa ta qarasa sassan bibi don shi yafi qarancin mutane. Dakin bibin ta wuce don rabonta da dakinta har ta manta,tun wancan ranar sam bata iya shiga dakin ta zauna,saidai idan wani abu zata dauka kota ajiye,tana shiga kuma take fitowa. Sai datakai can quryar gadon sannan ta kwanta,rigingine tayi tana qoqarin ganin fitar numfashinta ya dai daita. Tsahon wasu mintuna sannan ta motsa bakinta a Hankali idanunta na runtse "Ya Allah.....ya rabbussamawati ka bawa wannan bawan naka ikon rabani da wannan alaqaqai din igiyar" tayi addu'a tana fita daga tsakiyar zuciyarta. Har cikin ranta taji addu'ar ta karbu da gaske,sai taji tadan samu nutsuwa,ta juya barin hannun damanta tana fadada tunaninta na yadda zata tafi da rayuwarta cikin 'yanci,tana sake fadada mafarkinta na zama fitacciyar 'yar jarida a duniya. Da wannan tunanin a hankali a hankali bacci yazo yayi awon gaba da ita. Washegari me qunshi ta musamman dakewa ama qunshi tazo yi mata. Su benazeer tace a fara yiwa. Da farko batoul taqi yarda wai tsoron lallen takeji,tunda ba'a taba yi musu ba tunda sukazo duniya. Bibi kaman ta ari baki,ta dinga fada "Haihuwar faransa rainon faransa.....ai dole,ba abinda kuka sani daya shafi al'adar africa.....don lalacewa atamfa nan murna wai yarannan suke zasu daura zani,laifin hamdiyya ne.......banga ta barinku ku tabbata a turai ba,gwara ku dawo nan kusan rayuwa" Dariya surukai da sauran 'yan uwa dai daiku da suke wajen suka dinga yi. Benazeer babu tsoro ita ta fara miqa hannunta akayi mata,sai da batoul taga benazeer din ta cire,lallen yayi matuqar kyau a fara tas din fatarta, benazeer din nata murna tana shafawa,abun yana bata sha'awa ita karan kanta sannan batoul ta yarda ayi mata. Matsawa batoul din tayi kusa da sultana dake shirya duka kayan da zasu sanya cikin bikin a wasu madaidaitan akwatuna guda biyu,ta zura mata hannun saitin fuskarta "Auty bakiga hannuna ba?,kaman ba nawa ba auty,kema ayi miki,zaiyi miki kyau aunty" tayi nisa a tunanin da ita kanta batasan na meye ba,haka kawai tun jiya gabanta ke yawaita faduwa,ta laluba kafff batasan dalili ba,saidai zuciyarta tafi raja'a akan kodai tana tunani akan wanne hukunci su aba suka yanke game da makomar igiyar auren dake kanta?,tayi winning ko batayi ba?. Fararen idanunta masu yalwataccen gashi ta daga ta kalli fuskar yarinyar,sannan ta maida ga hannun da taketa zura mata. Ita kanta hannun yarinyar ya burgeta,jan lallen ya kwanta saman jar fatarta kamar jan lalle saman hannun balarabiya "Ma sha Allah,tabarakar rahman......kinyi kyau sosai" farinciki sosai ya kamata,ta buga tsalle saman katifa tana kiran yaran da suke gurin sa'anni kamarta tana gaya musu "Kunji ko?,ko aunty ma tace nayi kyau". Washegari wuni sur basu zauna ba suna wajen lalle,qin yarda tayi ayi mata daga farko don batason me yawa,tafiso sai an yiwa kowa me lallen ta gaji sannan ayi mata. Dan kadan din akayi mata,janne itama har bayan hannu sai na cikin tafin hannu,na qafa ma duka kadan akayi mata,ikon Allah sai ta zamana kamae zabarta me lallen tayi,gashi dai yafi na kowa qaranci amma kuma yafi na kowa yin kyau,ai kuwa suka yiwa me lalle caaa,itadai dariya ta dinga yi matar tana cewa "Ba daga ni bane,daga me hannun ne......ina cewa kuna gani dai,fatarta tafi ta kowa kyau da haske" maganar matar dole ya sanya sultana murmusawa duk da jikinta da takeji wani iri babu dadi. Ranar laraba aka fara biki sosai,komai nasu bisa tsari da kuma tarbiyya suka shiryashi,ba wani abu da ya wucewa tsari. Duk wata shiga idan sultana din tayi sai ta fita daban,kallo kam ta shasu,ta tabbatar banda tana da yawan azkar tsaf baki zai kamata,komai nata me aji sanyi ds kuma nutsuwa. Wadanda suka jima basu ganta ba kuwa mamaki kowa yakeyi "Wai wannan sultana ce da gaske?,wadannan diyoyinta ne?" Abinda kusan dukka suke tambaya kenan,wasu riqe da baki wasu kima fuskokinsu cike fal da mamaki. Itakam saidai tayi dariya ta wuce. Benazeer abun nema ya samu,ba zama wai an saci dan barawo,idan ta fice cikin jama'a sau tari sai ama tasa an nemota,bata nan bata can,kusan ita din akafi sani akan batoul,saboda kwata kwata ita din bame hayaniya da surutu bane. Duk da kamannin da suke dashi yana rikita mutane,amma kuma dabi'unsu ya sanya ake saurin banbancesu. Yawan qawayen da benazeer din tayi cikin dangi sai abun ya baka dariya ds mamaki,duk wani team na yara idan kaga sun hadu sai kaga itace shugaba. Sak SULTANA saidai wasi banbance banbance a tsakaninsu. Benazeer ta samu kulawar ama qwarai,data fuskanci yanayin dabi'u da halayenta sai take tarbiyyantar da ita daidai da halin nata,wannan ya sanya duk surutu da rawan kanta take da matuqar ladabi,tana da kirki tana da kyauta tana kuma da tausayi,bata iya rashin kunya ba sam, kusan duk wanda zata gaisar sai takai har qasa,saidai fa za'a cikaka da surutu da kuma labari. Randa aka soma bikin goumar baya nan,sai dare ya dawo washegari kuwa me daure musu qarqashi ya dawo?,ai har batoul itama saita bazama,basa zama sam,wani lokaci ma sai sunyi bacci da dare za'a shigowa ama dasu,sai kuma wata safiyar idan rai ya kaimu. Duk inda za'a suna gaban motar goumar din,kowa yasan nan ne mazauninsu ma bame zama wajen,haka aka dinga gudanar da event din daya bayan daya,komai ya qawatar ya kuma bada sha'awa. Ranar juma'a itace ranar dinner. Qawatacciyar dinner da aka shiryata ga dukkan amaren da danginsu dana angwayen aminata da yasmine,ga dangin uwayensu mata,wannan ya sanya aka kama babban waje da zai dauki kowa da kowa a sake kuma akan tsari. Tun asubar juma'a din ta tashi da wani dan qaramin zazzabi,har cikin qashinta take jinsa,hakanan kanta bangare daya yana sara mata lokaci lokaci. Idanunta ta lumshe tana mamakin abinda ya saukar mata da wannan zazzabin hade da bacin rai. Tasan dai lafiya lau ta kwanta bayan sun dawo daga kamun amare da akayi alhamis,sannan ba wani zirga zirga tayi ba,don ama ta bata daya daga cikin motocinta tace tayi hidimarta da ita,ko a canma tana zaune waje daya,saboda yadda idanu ke mata yawa suna binta da kallo duk inda ta motsa ne bata so,abinda kuma ya sake bata mata rai ta samu waje ta zauna,daya daga cikin abokan ango da tazo wucewa ta gefansu zata bude motarta ta daukowa wasu friends din su aminata sevenniours. Ya jima yana binta da kallo duk inda ta gifta,shine mutumin da ya sanyata ta dinga zabga tsaki har babu adadi,a yanzun kuma da zata wuce ta shiyyarsu sai yace da ita murya can qasa "quelle douce odeur(qamshi me dadi)" har cikin ranta maganar da ya fada din taji ta soketa. Eh tabbas,ita kanta ta sani,tana amfani da wani irin mayen turare ne me masifar kama jiki da sanyin qamshi,qamshin da hatta su aminata sai da suka magantu akai,tana maitar son turaren wannan ya sanya ya gama kama jikinta,amma aiba huruminsa bane yayi magana akai ko?. Bata kulashi ba ko waiwayo batayi ba ta wuce abinta,saboda kulawa ma ai yabawa ne. Sanda ta sake dawowa bai haqura ba sai daya sake magana "Banyi mamaki ba don baki tanka ba.....ko makaho kukayi gaba da gaba dashi zaisan ke ta musamman ce......tu es une femme chic(macace ke me aji)" juyawa tayi tana dubansa,kamar zata tanka saita tuna hala dama tankawar nata yake da buqata,don haka saita sake masa wani siririn tsaki ta wuce abinta,abun haushin sai ta jishi cikin murmushi yana cewa "Merci bébé(na gode baby)" maganar data qular da ita kenan ta samu guri tayi zamanta. K'ofar aka taba alamun knocking,daga jin knocking din tasan bazai wuce benazeer ko batoul ba,sassanyan muryar nan tata can qasa tace "Entrez(shigo)" batoul ce sanye da wasu cotton sleeping dress. Tabi yarinyar da kallo,kullum da kalan kayan baccin da zata gani jikin yaran,itadai batasan adadin guda nawa suke dashi ba,ita kanta wasu abunuwan nasu batasan adadinsu ba,saboda ko yaushe ama cikin kashe musu kudi take,cikin musu siyaya take,bata kuma iya musu siyayyan abu me araha ba,komai sai ta zuba me daraja da tsada. Kullum sake girma sukeyi suna wani wayau,halittar da Allah ya musu kyautarta na sake bayyana,yadda taji ana zancan har kamar ma sunason juyewa kamanninta. "tante......ki fito inji ama kiyi breakfast,taji kaman su Yasmin suna cewa zaku fita" idanu tadan fidda tana dubanta "Yau kuma na koma tante,aunty din in English bai isa ba?" Dariya ta saki sosai irin me cike da quruciyar nan "Tante yafi dadi aunty......duka su aminata haka ake kiransu,kema a nan sunanki tante,saimun koma nigeria ko Paris zaki koma autyn" kai kawai sultana din ta gyada,ta fuskanci yau da surutu itama BATOUL ta tashi,don tanajin tanja tanata fama dasu daga cikin kitchen "Ganinan zuwa" "d'accord" ta amsa mata da farshen faransanci tana ficewa a dakin da dan tsallenta. Janye idanunta sultana tayi daga qofar tana jin wani yanayi yana shigarta,haka kawai takejin tausayin yaran yana shiga zuciyarta,dukka tayi qoqarin danne wannan,ta jawo qafafunta ta sauka ta wuce bandaki. Wanka ta sakeyi hade da brush don ta hada gumi saboda maganin saukar da zazzabin da tasha,kuma alhamdulillah sai taji ya sauka din,saidai kuma rashin qwarin jiki. Simple gown ta saka na wata cotton atamfa maras nauyi,don ita ta tsammaci ma material ne da farko da ama tasa aka dinka musu,ta lullube kanta da dankwali sannan ta dauki wayarta ta fito. Fuskarta tayi fayau,ba komai saman fuskar sai dan alamun rashin jin dadin jiki. Akwai baqi a falon,ta bisu ta gaidasu har qasa cikin girmamawa. Wannan dabi'ar tabi jikinta durqusawa yayin gaida manya,tana daya daga cikin dabi'un da aka horesu dashi a hassan gwarzo. A nutse har ta qarasa dining,ta taras da houda salamatu dukka cousins dinta ne,suka gaisa ta samu kujera ta zauna tana duba abinda zata iya ci. Tana ci suna hira a haka aminata ta fara shigowa "Kun gama shiryawa?" Houda ta fara amsawa "Mayafi na kawai zan dauko,Je pense salamatu est prêt(ins tunanin salamatu ma ta shirya)" ta fadi tana duban salma din,kai ta gyada alamun hakanne,aminata ta dubi sultana cikin kokwanto "Kefa?" Dan motsawa kadan tayi sannan tace "Ina ji fa sai dare zamu hadu gurin dinner din kawai" "Baki isa ba" aminta ta fada tafa hannuwa cikin bala'i. Cikin sa'a yasmine ta shigo dai dai lokacin,suka hadu duka dinga mata. Ba wanda ta tankawa,don maganarsu ma so take ta daga mata ciwon kanta,ta barsu sukayi iya yinsu,amma yadda suka tarar mata tasan bata da mafita,salin alin ta koma daki ta dauko mayafinta kayan da zatayi amfani dasu da key din motar ta fito suka wuce. Mutun bibbiyu sukayi, yasmine da salma a motar salma din,sultana da aminata a motar sultana. Katafaren beauty lounge ne da yayi suna cikin marad'i da kewayenta. Wajene da idan kinsan baki isa bama baki kai kanki wajen,service sukeyi na manyan mata tamkar a cikin gidanki. Tarba za'a miki da drinks lemo harda kalan abincin da kike buqata,itakam sultana dukka batabi takan wannan ba,sai ta wuce qurya salle de repos(resting room) nasu dake dauke da manyan sofas masu taushi tayi kwanciyarta. Tana jiyo duk wani karakainar su tana kuma hango motsinsu ta cikin babban glass da ya rabasu. Idonta ta lumshe haka kawai yau takejin ta rasa gane kanta da kanta,hannunta ta zura cikin jaka cikin sa'a taci karo da tasbaharta,saita maqalata a yatsa ta soma hailala don mugun faduwar da gabanta keyi yana bata tsoro. Awa biyu tsakani taji ta kasa nutsuwa,saita dauki wayarta ta soma kiran tanja. Har ta katse bata daga ba,da alama bata kusa,kasa jurewa tayi ta sake kiranta,bugu biyu ta dauka. Hayaniya ya fara cika kunnenta kafin muryar tanja "Benazeer da batoul fa?" Ts tambayi tanja kai tsaye,tambayar data bata dan mamaki,shigen tambayar data taba ma ama a makka,amma saita share mamakin tace "Suna lafiya.....suna tare da goumar" "Yayi......shikenan" ta fadi tana katse wayar,ajeta tayi saman kanta tana furzar da numfashi,duk sanda akace mata suna tare da goumar nutsuwar zuciya da ruhi take samu,duk da irin yadda shi goumar din baya gajiya da cakar da ita da kuma tsokanarta,tasan wannan a jininsa yake,kuma akanta kawai cikin yaran gidan yake haka,duk da ita ta fara sanadin sanya masa sunan BAQIN BUZU da tayi.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 51 Kaman kowanne event sai sun tsokaneta bayan kowa ya gama shiryawa,yanzunma sun buwayeta da ya akayi komai lite tayi amma yafi na kowa kintsuwa da yin kyau. Ta gaji da wannan zolayar tasi,ciwon kai kawai sukeson qara mata,don haka ta fita daga wajen ta koma mota ta zauna tana jiran isowar angwayen da zasu dauki amarensu su wuce gurin dinner gaba daya. Har a lokacin jinta kawai takeyi sama sama,basu jima ba kaman sunsan a qage take suka iso,dukka motocin suka tashi a tare suka wuce. *_MAINA_* A nutse nutsuwar dake bayyana a iya fuska takunsa da ayyukansa na zahiri kadai.....yake saukowa daga matakalar jirgin da yayi jigilarsu daga niamy zuwa nan marad'i bayan dogon zaman da yayi daga makka a jirgin Ethiopian airlines. Dogon ba'abzinen,Giant me wani irin qawataccen tsaho da murjajjen jiki......fari tas ma'aboci sassalkar cikakkiyar sumar da kai tsaye za'a kirata da sumar gado,sanye cikin wata farar shadda qal.....da aka zamanantar da dinkinta ya zauna a jikinsa tamkar don saboda shi shi kadai aka qirqiri dinkin. Dogon wando ne da gajeriyar riga ta ciki me gajeran hannu,saidai kuma an qawata shigar tasa da babbar riga da kuma dakakkiyar hular da bata rufa dukkan asirin sassalkar sumarsa ba. Daga nesa idan ka hangi tsahonsa da yanayin jikin gami da shigar tasa zaka dauka jinin hambararren shugaban qasar nijer ne wato mohamed bazoum,saidai kana kallon fuskar zata tabbatar wannan jinin MAYAK'I da jajirtacciyar tsohuwar yar kasuwa NADEEYA ne. Gujajjen D'a daga ainihin qasarsa ta haihuwa,daga ainihin gidansu abun alfaharinsu,daga ainihin garinsa ahalinsa da kowa nasa......yau gashi cikin qasar da ya barta ba tare da sanin zuwa wanne lokaci zai dawo ba?,yau gashi kan hanyar komawarsa gidan daya fita cikin fitar hayyaci da rashin sanin abinda zai biyo baya,yau gashi zai fuskanci ABA AMA BIBI DA D'ANSA DAMA MAHAIFIYAR YARON SULTANA. "Bienvenue Monsieur" yaji an fadi daga gefanshi da harshen faransanci ana yunqurin karbar luggage dinsa da suhail ne ya samu nutsuwar hada masa kayan nasa. Kai kawai ya gyada ya sakar masan,don already yasan waye,uniform din jikinsa ya sake gaya masa waye din,kuma aikin sardauna ne duka ya sani. Yana biye dashi har suka isa gaban wata Mercedes Benz baqa wul dake daukan idanu qirar wannan shekarar ce da suka siyeta su ukun,shi sardauna da kuma suhail. Kai tsaye yace a turo tasa nan,a ajjiye a kamfaninsu dake shirin fara aiki a qasar tasu. Yau ya fara ganin motar ido da ido,amma a yanzun bashi da cikakkiyar nutsuwar qare mata kallo,don haka shigewa kawai yayi back seat din da ya bude masa,ya maida motar ya rufe,ya shiga mazaunin driver ya tayar da motar suka dauki hanyar fita daga airport din. Baisan wanne yanayi zuciyarsa take ciki ba,baisan kuma meye yakeji a dukka jikinsa ba,abu daya tak ya sani,zai fuskanci babban QALUBALE......zai gamu da komai,zai ga komai zai kuma ji komai,amma koma meye ya dawo da dukka qarfinsa,ya kuma dawo da shirin fuskantar KOMAI DA KOWA. Unguwar tasu ya dinga bi da kallo,a tsahon shekarun akwai ci gaba sosai,komai ya sauya,ba wani abu da yaga yaci baya,har zuwa LOKACIN da ya driver din ya iso dab da gidansu. Lumsassun idanunsa ya ware,ya miqa hannu ya taba kafadar driver din,da muryarsa dake can qasa yace "arrêt(tsaya)" bai musa ba ya gangara gefe saboda ya bawa motoci biyun da suka biyo bayansa damar wucewa,ya tsaida motar daga gefe daya. "Bani maqullin,tu peux y aller(zaka iya tafiya)" "d'accord Monsieur(to yallabai)" ya fadi cikin girmamawa yana bude murfin ya fita kaman yadda ya buqata. A hankali ya fito daga bayan yana komawa seat din driver idanunsa bisa babban gate din mansion house din nasu,jikinsa yana bashi wani hidima akeyi cikin gidan don yaga alamun haka,zuciyarsa ta raya masa wani abu da tilas ya rufe idanunsa yana kiran sunan Allah sannan ya tayar da motar "Bana fatan na mutu ban gurfana gaban aba da ama ba......bana fatan na mutu da hakkinsu" ya furta a fili saidai can qasa bayan zuciyarsa ta raya masa kodai wani daga cikinsu ne ya rasu. Motoci biyun da suka wuce su yabi,dukkansu security suka budawa hanya suka wuce ciki,saidai kuma ana zuwa kanshi suka jaa qofan saboda kasancewar motar baquwa a idanunsu,sannan kuma basu tabbatar da motar waye ba,don haka ba zasu bata daman shiga ba har sai sunyi checking nata. Cikin dakewa da sanin makamar aiki daya daga cikin security din ke matsowa,idanu maina ya zuba masa,houdu ne,daya daga cikin security na gidan tun kafin barinsa gidan. Ya tabbatar shine mutum na farko da zaya fara shaidashi,saboda yasan fuskar tasa tun babu saje babu gemu,ya sanshi tun a sanda saje ne kawai dashi,a yanzun da gashi ke kwance luf bisa tsari na samuwar shekaru a tattare dashi bazai gaza shaidashi ba. Abu daya tak yayi,houdu na matsowa yana sake glass din motar,dai dai sanda ya iso dai dai sanda shima ya kammala saukewar,sai sukayi ido hudu da MAINA din. Duk wani connection na jikinsa ya katse cak na wasu mintuna,sannan second kadai ya dawo bisa saitinsa,idanunsa fes cikin nashi,sai yasa hannu yana cire hulan kanshi,sai maina ya dora hannunsa saman lips nashi dole houdu ya maida maganarsa cikin cikinsa,ya kuma juya ciki da sassarfa yana bawa saura umarnin su bude,ba musu tunda shine shugaba suka bude din ba tare da sanin waye cikin motar ba,ya dage glass dinsa ya danna hancin motar zuwa farfajiyar gidan bangaren ajiyar motoci bayan shekaru biyar da barinsa gidan........... *_WELCOME BACK MAINA_*😂😂😂 Sanda take wucewa falon aba dauke da saqon aba a hannunta kunnuwanta sukaji qarar shigowar wata motar. A ranta take dariyar mugunta,tana kyautata zaton goumar ne ya nemo najma data boye ya maidota gida,don ta barshi a can ranshi bace yana nemanta,yayi rantsuwa bazai barta a wajen ba. Ta rasa wanne irin kishi gareshi haka?,abun goumar yana daure mata kai,duk da migraine da take fama dashi amma itama sai data rama yau dubu cikin abinda yake mata "Ta can baya na ganta da wani farin buzu me irin tamu fatar" tayi furucin ko a jikinta tana bude motar ta cilla kayanta ta shiga tabar wajen tana hangensa ta madubi. Gun data fada din yakeson zuwa,amma ya dake yaqi nufar wajen yana tsoron ko tsiyarta ne yasa ta gaya masa hakan saboda yasan hali sarai,barin hali kuma sai mutuwa,ta kuma karanceshin itama haka ta dinga dariya cikin mota ita kadai har ta fice a wajen. Daga qafarta zata sanya a falon aba din yayi daidai da qarasa shigowar motar gidan,ba kasafai hankalinta ke kaiwa ga shigowar motoci gidan ba,amma wannan sai taji gabanta ya yanke ya fadi. Dan dafa saitin qirjinta kadan tayi tana cewa "Hasbiyallahu lailah illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" "Waye a nan?" Muryar aba daga cikin falon ya isketa daga nan inda take "Aba nice,saqon oncle sidi ne" ta amsashi tana qarasa shigowa ciki. Sai data shigo din taga bashi daya bane,kamar kusan kowacce rana,tunda aka fara hidimar bikin basa rabo da irin wannan zaman waje daya. Oncle bashar oncle umar da oncle issoufou,sai qani ga mahaifinsu da bai jima da dawowa nijer ba. Bakinsa dauke da sunayen Allah ya ajjiye motar kan tsari kaman sauran motocin gidan,ya kasheta ya kuma zura qafafunsa yana furta "Bismillah" ya taka dandagaryar qasan gidan. Sai daya kulleta sannan ya juyo,juyawar daya samu security na gidan tsaitsaye daga bayanshi suna kallonsa cikin tsantsar mamaki. Murmushi ya jefesu dashi,sannan ya juya yana fuskantar ainihin ginin gidan,zuciyarsa na shawarta masa INA YA DACE YA FARA NUFA?. sassa guda biyar din dukka sai sukayi masa kwarjini,daga qarshe zuciyarsa tayi masa ragama izuwa sassan AMA saboda tuna masa da tayi UWA CE,zata iya zame masa tsanin zuwan kowanne qalubale da sauqi. Kasancewar kusan kowa bai dawo daga wajen dinner din ba sai daidaiku,sai ya dinga tafiyarsa ba tare da yaci karo da kowa ba. Daf da qofar sassan ama din yaja burki kaman yadda wanda ya fito da hanzari dauke da gorar babban lemo a hannunsa shima ya tsaya cak kamar an tsaida mashi. Almu ne,wani irin kallon gigita da bazata yake bin maina dashi,sai gorar lemon hannun nasa ta sulale ta fadi qasa. A nutse maina din ya duqa ya dauko masa,ya bude tafukan hannayensa ya zura masa a ciki ya kuma damqe hannun cikin nasa,sannan cikin karyayyar muryarsa yace masa "Kaini wajen ama" maganar tasa saita zamewa almu kamar wahayi,bai musa ba don dama tun dacan ba musu tsakaninsu,bai kuma iya tambayarsa komai ba saboda tsananin mamaki ya wuce gaba maina yana biye dashi. Yasan inda ya baro ama din yanzun daya fito daga wajenta,tana falon farko wanda take da bedroom a wajen,ya barta suna hada shimfidun da za'a fitarma dakin baqi na gidan ita da tanja,don haka suna zuwa dai dai qofar dakin yaja ya tsaya yana bawa maina hanya,tamkar yana nufin "Ya maina na gama nawa" idanun almu din ya kalla,sai ya sake kama hannunsa ya riqe sosai "Ka jirani koda a nan ne,kada kaje ko ina" kamar mataccen qadangare almu dai ya gyada kai,yayin da maina ya sanya hannu ya murza handle din dakin ya sanya kai bakinsa dauke da cikakkiyar sallama........ *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 52 Sallamar tasa ta iske kunnuwansu dai dai sanda ama ta miqawa tanja blanket din tana cewa "Kowanne gado a canza don Allah kafin mutane sukai ga dawowa daga wajen dinne........." Cak sauran maganar ta tsaye mata a qasan maqoshinta,kowanne gaba na jikinta yayi wani irin mutuwa gami da yin sanyi kamar anabi ana zare mata laka. Sake maimaita sallamar tasa yayi cikin karyewar murya da zuciya gaba daya,wata irin qaqqarfan qaunar mahaifiya tarin madama da jin cewa shi cikakken me laifi ne yana taso masa. Gabanta na faduwa ta kalli tanja,tun bata yiwa tanjar tambayar ba tasan amsar tambayar tata,amma saboda tabbatarwa sai tace mata "Tanja?,muryar waye kunnuwa na sukeji?" Ta furta da wani irin sauti muryarta da mugun sanyi "Shine...." Tanja ta fadi itama kamar me tsoron gayawa ama din. Wata qatuwar ajiyar zuciya ce ta kufcewa ama din,ta runtse idanunta sannan ta budesu,taja numfashi sosai cikin hunhunta sannna ta fesar,sai ta durqusa tadauki wani madaidaicin blanket din ta sake miqawa tanja tana ci gaba da yi mata bayani tamkar ba wata halitta baquwa data wanzu a wajen "Ki ajjiyewa su bilkisu saiki dawo,akwai ragowar aiki a nan din" taci gaba da bayaninta. Iya yadda tayi wannan motsin ya tabbatarwa maina akwai qototuwar matsala,ya taka zuwa bayanta jiki a mutuqar sanyaye,ya sulale a hankali ya zube bisa gwiwoyinsa kanshi a qasa ya kasa furta komai. Cikin jikin nata taji alamun yana bayan nata,sannan satar kallon bayan nata da tanja takeyi yasa ta sake fahimtar a bayannata yake tsaye har yanzun. Wani nannauyan abu yana fusgar zuciyarta,dukka zuciyarta da kwanyarta na shirin shiga rudani,bataso ta waiwaya ta kalleshi......bataso ya saukar mata da rauni a a matsayinta na uwa,idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba tasan cewa kaf gidan gurinta ya fara dosowa kanshi tsaye.......ta tabbata ba wanda yasan da shigowarsa cikin gidan sai ita,akanme zata sassauta masa?,akan me zata bari zuciyarta tayi rauni cikin lokaci qalilan har haka?,tsugunnonsa da zamansa ba zata tana bari suyi mata tasiri ta kasa aiwatar da abinda ya kamata ace ta aiwatar din ba. Dukka kayan tanja ta dauka sannan ta soma takawa tana barin dakin,duk taku daya sai ta waiwaya ta kalli maina har ta fice,yayin da ama kuma ta soma hada wasu kayan,duk da batasan ainihin me zatayi da kayan ba ita kanta. Cikin jikinta takejin wani irin yanayi,karyewar zuciya da mutuwar kowanne sashe na jikinta,yadda yanayin bugun zuciyarta ya sauya ta tabbatar akwai fushi me tsanani kwance a qasanta "Assalamu alaikum.......don Allah ama koda ba zaki kulani ba ki amsa koda sallamata,ki amsa min da neman aminci da albarkar ubangiji da na rasa tsahon shekaru" maganar tasa sai ta zame mata kamar famin wani tsohon miki dake danqare qasan zuciyarta. Watsar da kayan hannun nata tayi sannan ta gewayeshi da hanzari zata fita a dakin. Cikin wani irin zafi irin na namiji yasha gabanta,sai ya sake zubewa a gabanta yana riqe da dukka qafafunta da hannayensa "Don Allah ama......na roqeki......ko sallamata kawai ama ki amsa min" janye qafafunta baya tayi da sauri,karon farko ta watsawa fuskarsa wani irin kallo .......wani rauni ya sake mamayarta. Mainan ta ne......ya zama cikakken mutum......mainanta ne.....ya zama babban mutum.....aliyyu ne da ya bar gabansu tsahon shekaru,yanzu gashi duqe gabanta cikin qoshin lafiya da dukkan alamu na nutsuwa da kwanciyar hankali tattare dashi "Waye kai?,nace kai din waye?,don kaga na qyaleka a matsayinka na bare ka shigo har cikin dakina shine zaka zaqe da yawa haka?" Ta jefa masa tambayar da murya me cike da fushi. Sosai kalaman nata suka daki zuciyarta,suka kuma so tarwatsata zuwa piece's. Yau din shi ama ke barrantawa daga gareta?,shi ta maida bare?,wanda bata masan fuskarsa ba?. Ya hadiye wani qatoton abu daya tsaya masa a wuya,muddin ama tace zata qalubalanceshi ta haka bayajin zai iya dauka,ya shirya fuskantar kowanne irin fada da ladabtarwa,koda kuwa suka ne,amma bazai iya jurar shariyarsu da wofantar dashi haka ba. "Danki ne ama,ba wani bane daban,aliyyu ne ama......maina ne......danki bijirarre gujajje.....me tarin laifuka a gareku.......don martabar manzon Allah S A W ama kada kice ta wannan hanyar zaki horani" girman roqon da yayi mata yayi matuqar tasirin wajen rauna mata zuciya,amma hakan bai sanya ta kasa sake janyewa baya ba ta kuma nufi qofa da sauri tana jin kamar hawayen da take riqewa zasu balle kansu da kansu saboda girma da nauyin dake danqare cikin qirjinta.......ta jima da sarewa.....ta dade da fidda rai daga samun rayuwarsa,tana raye ne kawai tabarwa kanta abinda zuciya ke yawan raya mata a kanshi.....amma sam bata taba hasashen rayuwar aliyyu na nan tabbace saman doron qasa ba. "Indai kazo ne na goya maka baya......na tayaka binne laifinka ba zaka samu haka ba aliyyu......nice mutum ta qarshe da zaka fuskanta,hukunci na shine hukuncinna qarshe da zaka karbanan din ba shine mihallin da zaka fara fuskanta ba" abinda ta gaya masa kenan a gaggauce ta fice a dakin,wani irin abu yana zagayawa cikin jini da zuciyarta,tunaninta yana rarrabuwa. Tasan tabbas!,Allah ne ya amsa addu'arta......amma me dawowarsa ke nufi?,meye kuma zai faru a nan gaba?,wannan dukka bata da masaniya. Taja numfashi da kyau ta kuma fiddoshi waje,ga mamakinta sai taji dunqulallen abunnan daya tsaye mata a maqoshi tsahon shekaru......wanda ta gaza gane meye shi tsahon wancan lokacin yana narkewa a hankali yana sauka. A lokacin yana jin dukka jikinsa ya masa nauyi,yana jin kamar bazai iya motsawa daga wajen ba......yana jin kamar kwanyarsa ta daina tunani dai dai,saidai kuma a hankali ya kama sunan Allah,ya fusgeshi da matuqar qarfi "Alhayyu alqayyumu" ya fara maimaitawa,a hankali sai dukka qwarin gwiwarsa yaji yana dawowa,ya kuma sake kiran "Allah!" Da qarfin zuciya yana miqewa,ya nufi qofar dakin ya bude ya fice. Inda ya tsayar da almu a nan ya sameshi,suna hada ido almu din ya sunkuyar da kai "Ina zan samu su aba?" Da hannu almu ya masa nuni da hanya tamkar wani kurma,maina din ya karanci me yake nufi,sai shima ya masa nuni da hannu akan suje din,almu yayi gaba,shi kuma yaci gaba da bibiyar sahun almu din dake masa jagora zuwa falon. Gaban aba ta qarasa ta durqusa kamar kullum tana musu barka da warhaka. Dukkansu suka amsa cikin kulawa,ta sanya hannu ta dauki ledar tana miqawa aba fuskarta fadade da murmushi "yauwa ma sha Allah,ya cika alqawari,ungo wannan" aba ya fadi sanda yake warware kilishin da sultana ta kawo masa. Murmushi tayi ta sanya hannu biyu ta karba tana cewa "To na gode aba sosai" "Madalla" ya amsa mata,sannan ta yunqura tana miqewa "Kinga sultana.......ki shiga ki gayawa mariya su duba abinda yayi ragowa a kayan amfanin gobe" oncle umar ya fada "To uncle" ta amsashi tana nufar qofar tana ji aba yana tsokanarsu kan cewa boye kilishinsa zaiyi,diyarsa kadai zai iya bawa. Murmushi ta saki qasan zuciyarta,ba abinda zata ce ma Allah sai godiya,itakam batasan maraicin uwa da uba ba. Tsam almu ya tsaya daga bakin qofa ba tare da maina ya buqaci hakan ba, cikin jikinsa yaji bazai iya jerawa da maina ba,yana jin bazai iya jure hukuncin kallo kadai da maina zai iya fara maraba dashi daga dukka iyayen nasu ba. Bai waiwaya ya kalli almu ba,kaman ma baisan almun ya tsaya ba ya doshi babbar qofar falon. Ya tube tsadajjen sau cikin qafarsa,ya sanya qafafunsa dake saye da safa cikin falon yana janye labulen gefe bakinsa kuma dauke da cikakkiyar sallamar "Assalamualaikum warahmatullah". Wani dogon numfashi almu ya saki yana qamewa jikin bango gami da runtse idanunsa. Ya rantse da Allah.....tabbas inda shine ya maina bazai iya sanya kansa ga falon nan ba,ya rantse da Allah bazai iya fuskantarsu ba saidai idan tara tara za'a yi masa,wanne irin qarfin zuciya dakiya da jarumta ke gareshi?,ko kuwa dai baisan girman laifinsa bane a garesu?. "Wa'alaikumussalam warahmatullah" sukayi hadin bakin amsawa,saidai kuma ba dukkansu bane suka samu cikakkiyar lada da daman amsa sallamar.......kamar yankewa zubar ruwan sama sauran amsa sallama ta tsaya saman harshen aba......yayin da oncle umar shima sauran furucin suka tsaye masa cak. Wani irin rawa zuciyar aba tayi bayan daukewar sallamar daga bakinsa,a nutse kuma sai ya dauke kansa daga kallon qofar falon ya maida ga takardar kilishinsa ya soma qoqarin nannadeshi. Cikin qasa da second biyu da shigowarsa dakin da fitar sallamar daga bakinsa idanunsu suka gauraya waje daya. Haduwar idanun data zame musu wani abu na bazata dukkaninsu. Batayi zaton ganinsa ba.....baiyi tsammanin samunta a wajen ba......hasashe ko tunaninta bai kawo.mata ganinsa a nan kurkusa ba. Wani wawan birki taja a matuqar Hautsine,a hankali taji hankalinta yana neman firgita,nutsuwarta na shirin yin qaura daga ganganr jikinta. Wannan haduwar dai dai take da MUGUN GANI a wajenta...... mummunar rana da kuma mummunan lokaci......maina cikin gidan?,a wannan daren?,a kuma irin wannan lokacin?. Tambayoyin da suka kusan tsayar mata da gudun numfashi tsakanin qirjinta da zuciyarta zuwa hunhunta kenan. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 53 Dukkan zagayayyun lion eyes dinnan nasa ya kafeta dashi. Karon farko......lokaci na farko da sukayi gaba da gaba dashi. Karon farko yau gashi tsaye a gabanta,a gaban wata sultanar da ko kusa ko alama baiga tayi masa kama da wancan sultanar da ya bari shekaru biyar baya ba. Wani irin qaton abu yake ji yana gangarowa daga zuciyarsa me matuqar nauyi yana kwaranyewa zuwa sassan jikinsa. Da wani zazzafan karsashi ta janye idanuwanta,wata irin wuta na ruruwa cikin qahon zuciyarta. Har tsakiyar qirjinta takejin wani irin zafi yana sauka,ta soma takawa cikin bawa kai qwarin gwiwa ta kewayeshi tana nufin fita daga dakin, zuciyarta na jaddada mata bata da hadi dashi,ruhinta na gaya mata cewa bata sanshi ba......bata ma taba saninsa a rayuwarta ba,tana kuma sake bawa kanta yaqinin bata da wata alaqa dashi. Dukkan kowanne sashe na zuciyarsa muradin binta da kallo yakeyi,abinda ya gani qasa da second goma cikin qwayar idanunsa ya matuqar razanashi,to amma sanin da yayi cewa abinda ke gabansa da kuma mutanen dake zaune cikin falon din dai dai yake da tunkarowar yaqi cikin rayuwarsa sai ya tattara dukka wani abu daya taso ya tsaye masa a wuya yayi musu muguwar hadiya,hadiyewar daya haifar da ciwo a qirjinsa da kuma jirkicewar ainihin launin qwayar idanunsa. Tamkar gagarumin me laifin dake takawa zuwa gaban alqalin da zai yanke masa hukuncin mutuwa ko rayuwa haka yaci gaba da daga qafafunsa da kuma saukesu yana tunkarar mutanen da ya tabbatar suke da matsayar ci gaba da fuskantar rayuwarsa a yanayin daya kamata ko akasin haka. Dukkaninsu idan ka dauke mutum daya tal wato ABA idanunsu yana kanshi,kowa yana dubansa ne da zallar tarin mamaki da kuma bazatar bayyanarsa a irin wannan lokacin. Dai dai sanda ya zube a tsakaninsu aba ya miqe,ko sau daya ko alama bai nuna yasan da shigowarsa ko wanzuwarsa cikin dakin ba "Issoufou idan kun gama ka sanya yara su shiga dakincan su fidda komai,zan din shiga ciki na kwanta goben ina tunanin zan riga kowa fita don ina da baqi a gidan baqi na". Ba maina kawai ba,dukkansu sunsan wannan miqewar da yayi bawai ya yita bane saboda yana nufin abinda ya fada din,ya yita ne kawai saboda baya buqatar hada numfashi da maina,ya yita ne saboda isowar maina gurin,don a zaman tattaunawar da sukayi duka duka basuci koda rabin abinda suka zauna su tattauna saboda shi din ba. Kaman yadda ya yiwa ama haka ya miqe cikin zafin nama ya tari gaban aba sannan ya sulale a gaban nasa. "Waye wannan?,ku gaya masa ya matsa daga gabana!" Aba ya furta da wata irin kakkausar murya da duk sanda ta fita da irin wannan sautin......duk wanda ya sanshi to yasan cewa yakai maqurar fushinsa kenan "Don Allah aba.....don girman Allah......!" Bai barshi ya qarasa magiyarsa ba sai saukar zazzafan mari da sautinsa ya karade falon. Kaf dinsu jini ya dauke a jikinsu,don ba wanda ya tsammaci irin wannan zazzafan hukuncin haka tashin farko daga wajen aba,kasancewarsa mutum ne bame yawan kaiwa koda yara hannu ba bare maina da a yanzun ya zama cikakken mutum "Kaci gaba da tsayamin bisa hanya kaga yadda zamu kwashe dakai mahaukacin banza!......zaka matsamin ko sai na tattakaka a wajen?" Aba din ya kuma fadi cikin fushi. Cikin hanzari oncle umar ya miqe ya janye maina wanda ko gezau baiyi ba,hasalima baiso oncle umar din ya janyeshi ba,zaifi masa dadi ya barshi a wajen aba yaci gaba da dukansa wataqila ita daya ce sassauqar hanyar da aba din zaiyi saurin sassautowa ya saurareshi. "Zauna nan,kada ka sake tsaiwa masa a hanya aliyyu" oncle umar da zuciyarsa shima ta fara motsawa ya fada cikin nasa fushin. Kafeshi oncle umar din yayi da idanu,kaman yadda oncle bashar da oncle issoufou suka kasa motsawa,idanunsu dukka akan maina din,saboda wani abu ne da yazo musu a bazata gaba dayansu. A hankali idanuwansa suke sauya launi saboda abinda ke motsa masa cikin zuciya,wani irin yanayi maras dadi qunci da zafin zuciyar da shi daya yasan me yake fuskanta. "Yaushe ka dawo?, yaushe ka shigo gidan?" Oncle bashar yayi qarfin halin tambayar maina. Sanda ya dago fuskanshi da zummar amsa masa dukkansu saida kowa yasha jinin jikinsa. Wani irin yanayi fuskar tasa ta sauya,gaba daya kamanninsa sun canza. "Yanxu oncle......yanxu na shigo,ama taqi saurarona tace saidai na sameku...... shima aba haka" "Ba zasu saurareka din ba,don bakayi abinda zasu saurareka haka ta sauqi ba aliyyu" oncle umar ya fadi da wannan yanayin nasa dake nuna zafinsa. Idanu maina ya maida kan oncle umar din yana da zafi shima qwarai,har wani lokaci bibi ke ganin ta wajenshi ya gado zafi da kafiya,saidai nashi zafin da ya tashi ya ninka na dukka uwayen nasa. Duk da zafinsa idan ya gama spark ya sauka yana da budaddiyar zuciya,yana da zuciyar sauraro dake iya fahimtar mutum ta kuma bashi uzuri,yana da kafiya da qoqarin fahimtar da aba harma da bibi a duk sanda suka hau dokin naqi,ya hangi nasara ya idanuwa da bangarensa,don haka ya zamo a hankali ya gurfanar da kansa a gabansu "Bansan da wanne baki zan fara baku haquri ba......bansan wadanne kalmomi ne zasuyi tasiri a kanku wajen wanke fushina dake zuciyarku ba...... abinda zan iya fada kawai shine......ina me neman afuwa da yafiyarku akan yanayin dana sanya zukatanku.....zullumi da fargaba dukka.......sannan gani a gabanku kuyimin dukka hukuncin da kuke ganin ya dace kan cutarwar da na yiwa jikarku" kalamansa sun dakesu sosai sun kuma sanyayar da jikkunansu. Dakin ya dauki shuru,kaman yadda basuce komai ba hakanan shima bai motsa daga tsugunnon da yayi ba,har sai da oncle umar ya magantu "Koma ka zauna maina" kasa motsawar yayi yana jin nauyi da kunyarsu,yanajin nauyin abinda ya aikata din da yayi sanadin barinsa gida,yanajin kamar a yanzune komai ya faru,har sai da oncle issoufou ya kama hannunsa sannan ya matsa gefe ya sake zama sosai. Fada sosai oncle umar ya balle masa dashi,don dama shidin baya barin ko ta kwana,sha yanzu magani yanzune ko akan waye,sai da yayi mai isarsa bashar da issoufou suna tayashi sannan ya rufe da fadin "Abinda ya faru tsakaninka da matarka za'a iya cewa me sauqi ne inda ka zauna baka nuna ragwantaka ba...... za'a iya cewa rabo ne ya kawo haka,shi kuwa rabo baya tsallake rana da loakcinsa......ba kuma wanda ya isa ya hana wannan rabon fita sai ya fita a sanda ubangiji ya tsara......abu mafi muni shine tafiyarka,tafiya bata sati daya ko biyu ba,bata wata daya ko biyu ba,bata shekara daya ko biyu ba.....shekaru aliyyu,shekaru a qalla biyar?,wanne irin rago ne aliyyu?me yasa ba zaka tsaya ka fuskanci koma meye ba?,duk tsiya ba haramun dinka ka afkawa ba,me yasa ka tafi?" Ya jefa masa tambayar da alama tafiyar tasa tana daya daga cikin abinda ya sosai zuciyarsa. Tabbas yasan cikin bacin ran dake danqare aran oncle umar ne kadai ya sanyashi ya jefeshi da kalmar RAGWANTAKA......saboda duk gidan yafi kowa sanin TSORO yana daya daga cikin abubuwan da bai baiwa muhimmanci a rayuwarsa ba JA DA BAYA basa daga cikin kafatanin dabi'unsa,duk yadda zai musu bayanin yadda yaji a sanda abun ya faru.....duk yadda zai kwatanta musu yadda qaddara ta dinga janshi tana tilasta masa ficewa daga gidan ba zasu gane ba.......daga bayan barinsa gidan kome daya faru dashi ya sakashi a mizanin wannan QADDARAR da tayi sanadin fitarsa a gida..... wanda yayi imanin banda hakan ta faru......da tuni a yanzun ba shine ALIYYU MAYAK'I da ake magana a kai ba,da tuni ba shine MAINA da yaketa qoqarin binne daukaka da matsayin da ya samu ba,bayan tarin qalubalen da ya gamu dashi sanadin fitarsa a gida "Dukka ka yiwa kowa laifi,amma tamu me sauqi ce,kuma mun yafe maka,a yanzun babban qalubalenka, zamuyi iya abinda zamu iya wajen nema maka sasaauci,amma saukowarsu wannan tana hannunka,tunda bamu isa mu tilasta musu su yafe maka ko mu goge abinda ke ransu ba......" Ko iya wadannan kalaman na oncle umar kadai sun samar da wani sasaauci cikin gurbin zuciyarsa,sun kuma haifar da wani dan qaramin hope Baisan ta yadda zai gode musu ba, matsayin nagartattun kawunnai a wajensa,ya miqe da zummar barin falon,yana kuma wassafa ta inda zai fara tunkarar wannan gundumemiyar matsalar........ babban yaqi da zai zama madubin rayuwarsa muddin ya cimma nasara. "Kaje zuwa da safe koma meye zamu qarasa magana akai......gobe daurin auren qannenka biyu" "Waye da waye?" Ya samu kansa da jefawa oncle umar tambayar saboda wani fargaba daya kamashi. Dukka sai suka dan tsaya suna dubansa kafin oncle umar din ya bashi amsa "Aminata da yasmine" qas yayi da kansa kuma yana jin nauyinsu,yana jin kamar yayi tambaya akan makomar aurensa da sultana......to amma kuma hakan kamar zai zama da gaggawa,karbarsa da sukayi bawai yana nufin yanzun shi bame laifi bane a wajen kowa ba...... a'ah......yasan sun karbeshi ne saboda tsananin zumunci irin nasu da yadda suka tashi da soyayyar junansu data yaran da suka fita daga tsatsonsu. "Aliyyu" oncle issoufou ya kirayeshi da sassaucin nan nasa,don shi din mutum ne da bashi da zafi sam,duk cikinsu yafi kowa sanyin hali "Ka kama bibi,ka tabbatar ta zame maka tsani" kai ya girgiza wani busashen murmushi na fita daga saman labbansa,tamkar oncle issoufou din ya shiga zuciyarsa,bibi ce kawai last hope dinsa da yayi imanin tana da power din da zata maida komai bisa saiti,ko meye zatayi duk wani borenta bazai bari ya dameshi ba,zai runtse idanunsa,zai kuma gwada mata shi dan yau ne,domin yasan halin bibi sarai,zuma ce sai da wuta,amma kuma yana da babban yaqini a kanta. Daidai inda sukayi kacibus ya kalla sanda yake fita a falon,yaja dogon numfashi daya sauka har tsakiyar hunhu da zuciyarsa "SULTANA" ya maimaita sunan kamar yaune ya fara jinsa. Akwai babban game tsakaninsa da ita,yana tunanin itace abu na qarshe da zai cimma,a yadda ya tsara itace zata kasance matakalar qarshe,yaya zaije mata?,ta yaya zai risketa?,dukka bai san wannan ba......abu daya ya sani,ya kuma haqiqancewa kansa shine........duk RINTSI......duk yadda za'a je a dawo ba zaya taba yarda da abinda zai shafi igiyoyinsa ba "Idan suna nan har yanzu?" Wani sashe na zuciyarsa ya jefa masa tambayar data tilasta masa riqe hannun almu dake zaune zuwa yanzu a gefan qofar falon saman wasu qananun kujeru dake wajen don ya gaji da tsaiwar jiransa "Idan har yanzu sashe na yana nan......ina buqatarsa,ka gyaramin koda iya wajen da zan ajjiye kayana" ya fada adan birkice,don har yanzun bayajin cikakkiyar nutsuwa a jikinsa. Kai almu ya gyada yana miqewa,har yayi taku biyu mainan ya kirashi,sai ya dawo ya tsaya cak gaban maina yana kallonsa "Bayan tafiyata ciwon kurumta ko bebantaka ya sameka ne?" Ya masa tambayar yana duban idanunsa. Kai ya girgiza sannan ya matso taku hudu da sauri ya fada jikin mainan yana cewa "Barka da dawowa ya maina,Tu nous manques(munyi kewarka)" "merci(na gode)" ya ambata da raunanniyar muryar nan yana daga almu daga jikinsa yana kallonsa. Shima almu din kallon fuskar maina yakeyi,yana mamakin yadda ya mainan nasu ya sake komawa. Babban mutum da wani irin shinfidadden kwarjini da nutsuwa saman fuskarsa. Abinda shima maina ke wassafawa a ransa kenan,almu din da ya tafi ya bari da sauran quruciya ya zama saurayi "Ka girma almu,ina fata zaka taimaka wajen kawo wani haske komai qanqantarsa tsakanina da ama" "je promets in sha Allah(nayi alqawari in sha Allah)" kai maina ya jinjina,yana a tsaye har almu ya tunkari tsohon sashensa da baiga wani abu daya sauya ba ta wajen,saima gyara da wajen ya samu da kuma kulawa. A yadda idanunta suke a rufe sam bataga bibi dake zaune cikin falon ba tana kallo saboda raguwar jama'a daga sassan nata. Sanda ta shigo din daga kai kawai bibi tayi ta bita da kallo,yanayin taku da tafiyar sultanar dukka ba sune tattare da ita ba "Ikon Allah" bibi ta fadi har zuwa sanda ta tura qofar dakin dake kusa da ainihin dakinta ta shige "Allah ya kyauta.......itama wannan ja'irar na fuskanci ta zama baudaddiya" ta fadi a bayyane tana maida toothpick din data zaro bakinta taci gaba da sakacenta. Kamar daga sama taji sallamarsa,saita maida dubanta da hanzari bakin qofar qawataccen falon nata. Yadda ya zuba mata idanu haka itama ta zuba masa tana jin kamar cikin mafarki take ko kuma majigi take kalla "Wannan kamar maina" ta fadi cikin tantama duk da yaqininta yafi yawa akan tabbas shi dinne. Qafafunta dake saman kujera ta sauke,har yanzu bata dauke dubanta daga kanshi ba kamar wadda taga fatalwa. Ta waiwaya kadan tana qwala kiran sunan "Tanja!,ke tanja!!" Tanja tana kusa,don tana kitchen din bibi din zata zuba abinci taci,saita saki abinda takeyi din,don yanayin kiran da bibi ke qwala matan baiyi kama da kiran lafiya ba,uwa uba kuma tanata juya dawowar maina a daidai wannan lokaci. Dashi idanunta suka fara cin karo,yana tsaye abinsa qyam daga bakin qofar,a dan rude ta kalli tanja "Wancan dake bakin qofar a tsaye ba aliyyu maina bane?" Tayi tambayar bihaqqi tana neman sani. Tanja bata ma dubi wajen ba ta bawa bibi amsa "Shine" kammala fitar haruffan guda biyar yayi daidai da miqewar bibi tamkar bame fama da ciwon qafa lokaci lokaci ba,sai kawai ta soma jan zaninta tana daurin qirji dashi idanunta fes bisa fuskar maina da sai data miqe din take sake qare masa kallo abinda daga maina din har tanja suka gaza gane abinda take nufi da hakan *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 54 Idanunsa fes bisa kanta,yasan dukkan wani kalar rigimarta,yasan meye zata iya aikatawa da wanda ba zata iya aikatawa ba,yasan kuma lagonta qwarai da gaske. "Billhuwallazi lailah illa huwa idan ma fatalwa ce ba aliyyu ba ni bibi nafi qarfinta.......idan kuma har da gaske kaine.......da idanuwanka guda biyu a bude na rashin kunya ka iya dawo mana cikin gida to dai dai nake dakai,shege ka fasa ni da kai" ta fadi cikin daukaka murya tana sake gyara daurin zaninta da kyau tamkar me shirin yin dambe dashi. Dolen dole badon yaso ba murmushi ya subuce masa yana kallonta,da gaske take tattara dukkan qarfinta kamar wadda ke shirin yin dambe da qaddararta. A yanzun ba bibi kadai ba, kusan duk wanda keda ruwa da tsaki da rayuwarsa yasan a tunzure yake dashi,bazaiyi wani abu kuma da zai sake tunzurata din ba don yanzun tamkar itace sitiyarin gidan gaba daya,samun kanta shine samun kan kowanne mutum dake cikin gidan,don haka yaci gana da takawa yana nufarta "Au......ba zaka dakatamin a nan ba?,la'ilaha illallahu......da gaske dai aliyyu ne!, jama'a kuzo ku ganemin ikon ubangiji na" ta sake fada cikin daga murya tamkar tanasom tara masa jama'ar gidan gaba daya "Bibi kibi a hankali,ba fatalwa bane na gaya miki maina ne" tanja ta furta adan daburce ganin yadda bibi ta dage lallai saita hada masa jama'ar gidan. Shikam ko gezau be fasa takawa zuwa wajenta ba,yayin da taci gaba da kwakwazo da jan salati iri daban daban. Yana isa dab da ita baiyi wata wata ba ya sanya hannu ya riqeta da kyau "Sakeni,sakeni nace" ta fadi yana qoqarin qwace hannunta daga nasa cikin fada da hargagi "Kiyi a hankali,tunda dai baki samu damar hadamin jama'ar da kikayi niyya ba aisai ki haqura ki zubawa sarautar Allah ido ko?" Ya fadi yana qoqarin zaunar da ita. Dukka sauran qarfinta ta sanya ta tureshi cikin fusata tana cewa "Gafara can ka bani waje,wato nice marainiyar wayonka,ka tsallake katanga.ka shigowa mutane cikin gida a sirrance zaka zo.ka cuceni,banga alamar akwai wanda yasan da shigowarka cikin gidan nan ba" qaramin murmushi ya saki yana sake yunqurin riqota "Allah ya kiyaye.......da lalacewa ta sameni,na gudu daga gida......na tashi dawowa na biyo ta katanga?.....ai kuwa da nayi asarar suna,kuma da daga yau na ajjiye sunan Aliyyu na koma aliya" "Ahaf.......lalacewa kuma ta nawa?,duk dan da zai tsallake albarkar iyayensa yabar gida shekara da shekaru ai lalacewa ta gama samunsa" ta fada tana sake qoqarin tureshi . Har cikin zuciyarsa maganar tata ta bashi dariya,saidai boren nata yayi imanin mataki ne na nasara,nasarar da ya tabbata tana da alaqa da addu'ar da ya tsananta yi tun kafin ya sanya qafafunsa cikin gidan. "Kina batan lokaci ki zauna ki marabceni kawai" ya fadi yana sanya qarfinsa cikin tausasawa ya maidata ya zaunar saman kujera,sai ya waiwaya yana duban tanja "Jeki abunki kija mana qofa miji zai gana da matarsa" dan qaramin murmushi me hade da hawaye ya qwacewa tanja,tayi missing maina qwarai,bama ita ba,kowa dake gidan idan zaiyi magana ta tsakani da Allah zai fadi haka. Duk da zamantowarsa me zafi fushi da kuma zuciya......amma kuma shi din mutum ne me dadin mu'amala qwarai da gaske. Gadon bayansa ta kaiwa dundu da dukka qarfinta tana fadin "Allah ya kiyaye Allah ya sawwaqe nayi miji da kai,mijina jarumi ne,bai tana ja da baya ba" ta fadi tana yarfa hannunta,don dukan data kai masan ba shine yaji zafin ba itace taji,ita dimma bata ankara da wautar da tayi ba na kai masa dukan sai daya zauna ya babbake a gabanta sannan ta qare masa kallo tsaf. Ya zama ingarma dake da wani irin ginanne kuma tsayyen jiki da nuna zallar qoshin lafiya da cikakken qarfi,ko ina a murde alamun daga qarfe sosai sun bayyana ga jikinsa,duk da cewa cikin sutura yake cikakkiya. "Bafa mainan da kika sani a baya bane kike dukana haka bibi?" "Na sani mana.....wannan wani shashashan maina ne,gudajje daga gidan iyayensa bayan yaso ya kashe 'yarsa kuma 'yaruwarsa sannan matarsa" ta fadi masa cikin fushin zuciya,tana jin takaicin yadda bata da cikakken qarfin tureshi ta tashi a wajen ta daina kallonsa. Wani qasaitaccen murmushi ya saki yana sadda kanshi qasa kafin ya dagoshi "Kowa na gudu.....kowa guduwa nayi.......bien(da kyau),duk kuci gaba da fada,ba laifi tunda abinda idanu suka gani kenan,amma nan gaba kadan zan tabbatar muku da sabanin fahimtarku" ya qarashe maganar yana jan siririn hancinta me tudu kadan wanda kusan dukansu irinsa suka gado,wani irin hanci me kyau dake qarawa fuska kyawu. Hannunta ta saka ta buge hannunsa tana cewa "Ka fita ka bani waje tun banci mutuncinka ba,ko kuma na kira ubanka ya fiddamin da kai,tunda naga alama shi kake tsoro" idanu ya fiddo waje,sai ya sulale qasa yana riqe dukka qafafunta hadi da dora kansa saman qafafunta,yayi laushi qwarai da muryarsa cikin sigar tausayi "Indai ba bindigeni kikeso aba yayi ba kiyi haquri kada ki kiramin shi,dazun nan ya gama kwakwadamin mari,bibi kaman zai tsinemin,ama taqi koda kallo na,kema nazo kin juyamin baya bayan ko meye ya faru ke kika dauremin qarqashin aikatawa......." Bakinsa ta kaiwa bugu da sauri,saidai kuma bata sameshi ba don ya kauce yana boye dariyar dake subucewa tun daga zuciyarsa,fiye da rabin tsoro razani da quncin da yake ciki a yanzun baya jinsa tunda gangar jikinsa ta gamsu da cewa yana cikin gida...... yana cikin family dinsa,yana cikin ahalinsa iyalinsa "Ni nace kaje ka yiwa diyar mutane fyade?,ka kusa kasheta?,ka illata mata idanu maina?" Ta fadi adan rude. Maganarta ta qarshe ita ta dakeshi,har ta sanyashi daga idonsa yana kallonta,dan siririn murmushin da ya soma samu saboda tubura bibi da yakeyi ya bace bat daga saman fuskarsa "Illata idanu bibi?, yaushe?,garin yaya?" Tambayar tasa ta sanyata daga hannuwanta dukka biyun ta zuba masa ranqwashi da qasusuwan yatsunta da dukka qarfinta,ta yadda tazan zafin zai ratsa tarin sumarsa ya kuma isa ga ainihin tsakiyar kansa. Idanunsa ya runtse gam,saboda da gaske zafin ya isa har fiye da inda taso yaje din "Ni zaka yiwa tambayar yaushe ka illatata din?,sanda ka aikata aika aikarka wa kayi shawara dashi?,oh.....ni 'yar nan naga ta kaina......ban sake yarda lallai baka da kunya ba sai yau aliyyu......tashi ka bani waje,kada ka sake shigomin guri,ban gayyaceka ba,daka dawo bani ka dawowa ba,tashi nace" ta fada tana tureshi da gasken gaske. Yaga fushi da motsuwar bacin rai saman fuskarta,amma kuma ta wani sashen da batayi zato ba akwai farincikin ganinsa danqare qasan zuciyarta wanda batasan wannan hasken yana bayyana akan fuskarta ba. Tsam ya miqe din yana dubanta na wasu sakanni ya qare mata kallo,sai ya zuba hannayensa a aljihun wandonsa yana magana a nutse,duk da qasan ransa akwai razanin jin cewa ya yiwa idanun sultana illa,saidai yana mamakin ta ina?,don baiga wani nakasu cikin fararen zagayayyun idanun nata data jefa masa kallo dasu a makka da kuma dazu dazu ba cikin falon aba "Zan tafi bibi,amma bawai na tafi kenan ba,zan dawo koda zaki yayyanka ni ki sakani a tukunya.......kafin na karbi kowanne hukunci ya kamata a bani damar magana koda ta minti daya ne,zan bayyanar da kaina a gobe gaban kowa,zan kuma karba kowanne hukunci da kuke tunanin na cancanci ns karbeshi" daga wannan ya soma takawa don barin falon,amma kuma idanunsa manne da bakin qofar dakin,dakin da bazai taba mancewa dashi ba......dakin da yasha mafarkin gashi a cikinsa.....wancan din daya faru yana maimaita kansa har sau babu adadi.....cikin kowanne dare da zaizo ya shude. Cikin jikinsa ya dinga ji tana cikin dakin,amma koda wasa bibi na wajen bazaiyi gangancin shiga ba,a yadda take a fusace ya tabbatar tana iya tayar da boren da a yau aba da bibi ma basu isa sunyi bacci cikin gidan ba. Dai dai lokacin daya fita din ta sulale qasa tana jingina bayanta da qofar dakin bayan ta gama kallon komai dake faruwa tsakaninsa da bibita qaramar hudar da akayi don hangen wanda ke waje. Tana ganinsun,amma kuma bata iya jin abinda duke fadi a tsakaninsu. Tun dazun hawaye ya gama wanke mata fuskarta gaba daya,saita qarasa zama dirshan qasan dakin tana rufe fuskarta da dukka tafukan hannayenta. Duk da batajin me bibi ke gaya masa amma kuma sai tayi mamakin yadda bibin ta tsaya saurarensa koda kuwa kanainayetan yayi. Ta dauka zata sanya qafa tayi fatali dashi,ta zaci zata sanya madoki tayita dukansa har sai ya fice musu a daki da qafafunsa,duk wani action na bibi bai burgeta ba duk data fuskanci bore tayi masa,so tayi bibin ta masa irin tarbar da zaiji baya da sauran sha'awar sake zaman gidan. "Ke sultana!.....,kukan meye kikeyi?,kin manta yanzun ke ba sultanar baya bace?,kin manta a yanzun ke wata sultana ce ta daban?,a baya min xubda masa hawaye,a yanzun bai cancanci kici gaba da xubda masa wannan hawayen ba,ki qarafafawa kanki gwiwa,ki gayawa kanki da kanki a yanzun damuwa bata cancanceki ba.......kiyi moving forward,kada ki bari ya sake maidoki inda kika riga kika wuce" kaifafan maganganun da suka dinga kai komo kenan a tsakiyar qwaqwalwarta. Sosai taji ta gamsu,ta yadda yanzun shi din ba kowan kowa bane cikin rayuwarta,bashi da kaso ko misqala zarratin a rayuwarta,me yasa zata bari ya dameta?. Da wannan tunanin ta isa gaban madubi tana kallon kanta da kanta. Da gaske ta canza,da gaske ba sultana yarinya qanqanuwa bace wadda zai yiwa qarfa qarfa......wadda zai yiwa.kama.karya......wadda zai yiwa dukkan abinda yaga dama yakeso,a yanzun ta girma......ta kuma mallaki hanakalin kanta,koda jama'ar dake kewaye da ita wadanda zata rayu dasu sai wadanda taga damar zama dasu ta kuma zabesu. "Dole ya sani ya kuma shaidawa kansa da kansa da da yanzu ba daya bane" ta furta a fili qasa qasa tana motsa jajayen labbanta. Bandaki ta shiga,ta raba kanta da kayan jikinta ta watsa ruwa hade da alwala. Sakakkun kayan bacci ta saka don tafi sakewa,duk wani motsi nata tana furta "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" saboda zuciyarta tayi sanyi. Hijab ta sanya har qasa,ta isa qofar dakin nata ta murza key don kada ma su dawo su dameta,tun dacan dama bata kwana da kowa dakinta don batason takura ko hayaniya,yanzun ma bata son kowa ya dameta shi yasa ta rufe dakin,ta shimfida abun sallah tahau ta kabbara salla shafai ds wuturi sannan ta dora da nafiloli. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 55 Idanunsa suna kan kowanne sashe na sassan nasa,yana nan kaman yadda yake,ba abinda aka sauya ba kuma wani abu daya lalace kamar bai dauki wadannan shekarun baya nan ba. Duk inda ya gifta ba abinda ke dawo masa sai shekarun samartakarsa, abubuwa da yawa ya dinga tunawa har ya ratsa falonsa yakai ainihin bedroom dinsa. Yana shiga almu yana ajjiye mop stick din daya gama goge masa tiles din wajen,suka hada idanu da maina din,sai yadan sadda kansa kadan. Abun almu din yana dan bawa maina mamaki,duk ya maidashi wani baqo qarfi da yaji,duk da ko a baya ba sakewa tsakaninsu sai desipline,amma kuma yana tunanin kaman a baqon almu yake kallonsa. "Ina goumar?" Ya tambayeshi, tambayar data sanyashi daga kai ya kalleshi,don a nasa lissafin maina din bai wani san goumar can can ba "Sunje niamy.....amma gobe da sassafe jirginsu zai iso da angon yaaya aminata" kai ya jinjina,shuru na wasu 'yan mintuna ya biyo baya,sai ya gyada kai "Shikenan jeka,sai da safe" "Akwai wani abu da kake buqata?" Almu din ya tambayi maina,har qasan zuciyarsa yana jin tausayinsa,duk da baikai wayon haka ba sanda yabar gida amma kuma yana iya tuna kulawa da yake basu,sa'annan a yanzun ya san cewa gagarumin qalubalen dake gaban yaa aliyyun,duk wata kulawa bazai sameta daga iyayensu ba "Babu" ya amsa masa a taqaice "Merci" ya sake fadi yana jin dadin yadda almu din ya nuna masa kulawa. A yadda yakeji din baya jin zai buqaci wani abu,nutsuwa kawai yake da buqata da kuma kebe kansa har zuwa safiya. Don haka almun yana fita ya soma zagayawa cikin dakin,yayi 'yan dube dubensa. Komai yana nan hatta da suturunsa ba abinda aka taba,ya maidasu waje daya ya killace,don a yanzun bazai iya amfani da ko daya daga cikinsu ba. Kayan jikinsa ya cire ya daura towel ya wuce bandaki. Ya jima yana dumama jikinsa sosai, tunani cunkushe a kwanyarsa. Baisan yaya safiyar gobe zata waye masa ba,baisan da wanne ido da kuma wanne hannu zasuci gaba da tarbarsa,saidai koma meye yana bawa kansa tabbacin juriya da dagewa hadi da jajircewa. Kayansa da yazo da su ya bude,ya fidda pajamas marasa nauyi ya saka,kwanciya yakesonyi amma bayajin zai iya kwanciyar,don haka ya shimfida abun sallah shima ya kabbara sallah da tarin buqatu dake cikin ransa. *********Tun asuba hayaniyar cikin gidan ta qaru saboda yawan jama'a da kuma hada hadar daurin aure da aka fara yi,wanda duka daurin auren su biyun zai gudana ne a babban masallacin alhj Mohammed mayak'i dake farkon street din nasu. Tana idar da sallah ko hijabin jikinta bata fidda ba ta koma saman gado,idanunta fal da bacci don a jiya bata samu cikakken bacci ba. Batasan adadin awannin data shafe tana bacci ba,ta daiji anata knocking sama sama amma bata ko motsa ba,don tasan mutane ne kawai zasu dameta,saidai a yanzun bugun da ake mata yasha banban da wadancan,don yanzun kamar za'a tsinke qofar a shigo,dole ta miqe tana lalubar dankwalinta da ya zame ta sanyawa kanta,sannan ta sauko daga saman gadon ta nufi qofar. Yasime ne a tsaye,tayi kyau cikin shigar wani arnen farin lace da ya wadatu da ado da duwatsu masu qyalli,kana kallonta basai an gaya maka ba amarya ce, fuskarta ta dauki makeup sosai wadda ta sake bayyana ainihin kyan nan nasu da sukayi gado. Houda na tsaye a gefanta cikin army green shadda da sukayi anko dukkansu 'yammatan amare suka tsara zasu sanya a yau din. Wata harara ta jefa mata "Wai bacci ma kikey?" Hannu ta sanya tadan dafe kanta "Da ciwon kai na kwana Yasmin,don Allah karkiyi qorafi" ta fadi tana karya murya. Dariya ta bawa Yasmin din "Kiyi ki shirya don Allah,kada azo daukan hoto bake a ciki" "In sha Allah" ta amsa mata,wanda ita kanta tasan ta amsa mata ne kawai,amma sam yau bata sha'awar fita ko nan da can. Harabar gidan gaba daya bata burgeta,ta tabbatar a yau din kusan labarin da zaiyi trending cikin gidan shine labarin dawowar maina. Suna juyawa tana shirin maida qofar ta rufe tanja ta qaraso "Ama tace na dubaki kin tashi?" "Na tashi tanja......don Allah tea nakeso me dumi sosai,madara da sugar kadan" "Tea kawai?" Kanta ta gyada mata tana lumshe fararen idanunta,bakinta babu test kwata kwata,shima tea din zata sha ne kawai maganin yunwa. Tanja tana fita ta juya ciki ta soma zare kayanta ta fada wanka. Koda ta fito tanja ta aje mata tea din,sai ta zauna ta fara kurba a hankali tana dumama cikinta. A hankali sai tunaninta ya koma daren jiya,wata siririyar faduwar gaba ta ratsa qirjinta,ta maida idanunta ta lumshe tana son kauda surar fuskarsa dake gilma idanunta. Benazeer da batoul ta tuna,wannan ya sanyata ajiye cup din a hankali,ta jawo hijab ta zura ta nufi qofa. Tana gab da fita a dakin wata murya daga can qasan zuciyarta ta jefa mata tambaya "Idan kinje gurinsun me zakiyi?,zaki hanasu yawo ne bayan gidan cike yake da yara?,kada kiyi abinda mutane ko shi kansa zaiyi tsammanin kin damu da sha'aninsa ne,bake daya ba,akwai dakaru a gabanki da bai isa yace zaya dauki yaran ko ya aiwatar da wani abu ba" ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta dawo da baya jiki a salube,daga tsaye ta dauki tea din ta kurbe,saita koma wajen drawer dinta ta soma duba kayan da zata saka, zuciyarta da tunaninta haka kawai ya raja'a akan yaran. Tun asuba yayi alwala ya kuma fita sallar asuba kamar yadda kowanne namiji dake gidan yakeyi tun gabanin barinsa gida,har kuma yanzun babu abinda ya sauya. Yana qoqarin fita daga makeken gate din gidan sukayi kacibus da aba adan hanzarce,da alama shima yaso ya makara ne. Idanu suka hada da aba din,sai ya janye idonsa tamkar ma baisan mainan ba,ya kuma qara taku ya wuceshi a sanda maina ke yunqurin yi masa magana. Ajiyar zuciya me sanyi ya sauke yana lumshe ido hadi da budeshi,wannan abun idan aba yana masa shi yana sanyashi jin tamkar zai mutu. Ba haka ya saba masa ba,a shekarun baya kafin komai ya faru idan sukayi kacibus irin hakan da hannu yake masa nuni da ya matso,idan ya matso din kuma sukan wuce masallaci tare da aba din kafada da kafada,a yanzu da yake ganin akasin hakan sai yakejin kamar zuciyarsa zata tsinke daga qirjinsa,bazai iya jurar wannan halin ko in kula na aba ba. A baya yaci gaba da bibiyarsa har suka isa masallacin,sanda aba ke qoqarin kafa sahu cikin zafin nama ya tsaya daga gefansa,ya kuma daidaita sahunsa dana aba din. Yayi zaton zaiyi wani motsi amma sai yaga ko daga kai ya dubeshi baiyi ba,tamkar ma baisan dashi suka hada sahu tare ba. Suna idar da sallar aba din yadan ja gaba ya fita a sahun,sannan ya zauna sosai ya fara azkar din daya zame masa.jiki duk safiya muddin yana da lafiya,idan kuma baya dan jin dadi yana komawa gida yayi cikin falonsa balcony ko bedroom dinsa. Daidaikun mutane da sukasan maina sai suka dinga matsowa suna gaisawa dashi tare da tambayarsa yaushe ya dawo qasar,saidai ya danyi murmushi yace musu "Jiya" yadda suka dinga masa barka ya alamta masa lallai sunyi zaton karatu ya tafi. A hankali a hankali yana gaisawa dasu har zuwa sanda suka kammala,ya dan juya idonsa kadan ya saci kallon aba. Yadda yake tun dazun har yanzu a haka yake a zaune,yaja numfashi sosai,sannan ya miqe cikin mazantaka ya taka izuwa garesa. A gabansa ya zube gwiwoyinsa,muryarsa cike da girmamawa da kuma rusunawa ya furta "Barka da asuba aba" idan carbin dake hannunsa ya amsa shi shima haka,sai yaci gaba da jan tasbaharsa baiko motsa ba bare maina ya sanya ran ya jishi. Sake maimaita gaisuwar yayi,wanda yana direta aba din ya yunqura ya miqe yana durfafar qofa,baiyi qasa a gwiwa ba ya take masa baya,saidai kafin ya cimmasa har ya sanya slippers dinsa masu tsananin taushi ya soma barin farfajiyar masallacin. Dab da zai fita ya cimmasa,ya sake taresa karyar da wuya dama murya gaba daya "Aba.......na roqeka don......" "Bakaji abinda na gaya maka ba jiya?,kai wanne irin mahaukacin yaro ne?, meye alaqata da kai da zaka dinga bibiyata haka?,ni bani da wani d'a me kamanceceniya dakai,ka fita daga harkata tun kafin na saka hukuma su kamamin kai" yayi maganar a fusace yana nunashi da yatsa,sannan ya kewayeshi yana wuceshi bayan yaja dogon tsaki. Sosai jikin maina yayi sanyi,abinda yake gani a idanun aba din me girma ne,anya zaici gaba da tunkarar aba?,anya ba bibi bace kadai tsaninsa kaman yadda oncle issoufou ya gaya masa?. Cikin qarfin hali yaci gaba da takawa cikin gidan. Koda yakai bai koma sassansa ba sai ya zarce sashen ama. Can dinma mutanen daya samu a sassanta wadanda suka tattashi sallah dukka basu koma ba binsa suka dinga yi da kallon yaushe gamo?,ya gaisa da wadanda zai iya gaisawa dasu,ya tambayi bilki me aikinta ta gaya masa yanzun ta shiga daki. Sau uku yana knocking sannan ya murda qofar,bakinsa dauke da sallama,qasan zuciyarsa cike fal da addu'a. Da ita ya fara tozali,tana zaune saman tattausan abun sallarta dinnan,jikinta sanye da ustazah hijab da skirt dukkansu kala me haske. Tsananin tsafta da gayunta ya santa kusan komai nata me hasken kala ne,sai dai daiku masu duhun kala. A nutse ya qaraso cikin dakin,ya kuma yiwa kansa mazauni a qasan dandagaryar turkey carfet din dake malale a dakin wanda ya qarawa dakin kyau da kuma tsari. Hannayenta a sama tana addu'a,sai shima ya buda nasa tafukan hannayen,sanda ta kammala suka shafa a tare,sannan ta waiwayo suka hada idanu. Kwarjinin nan nata yana nan,gaba daya fuskarta ta cika da hasken ibada sanin kima da martabar kai. Wani lokaci su uncle abdulhakeem kan bata lokaci kan cecekucen kwarjinin da yayo gadonsa yayi,amma basusan tsakanin hamid da hamdiyya waye yafi wani kwarjini ba?. Sai data gama zuba masa dukka dafin kwarjinin idanunta sannan ta janye daga kallonsa. Zuciyarta na hira a kansa ita kadai. Mainan nata ya girma,ya zama cikakken mutum wanda ta tabbatar akwai maganganu masu yawa da labarai cikin tafiyarsa da kuma dawowarsa,saman kowacce fuska akwai labari......cikin kuma kowanne littafi nan ma tasan akwai labari,amma a yanzu bata jin zata bashi wannan qofar ko damar haka a kurkusa. Kaman yasan niyyan tashi ta bashi waje takeyi sai yayi caraf da dukka hannayenta ya kuma hanata miqewar,koda ta daga kai ta kalleshi sai ta tsinci hawaye fal idanunsa. Kuka a idanun aliyyu?,abinda zata iya cewa kaf rayuwarta bata taba gani ba,tun yana qaraminsa kuka abune me wuya a wajensa bare kuma sanda ya mallaki hankalin kansa,yana da tsananin fushi kafiya da zuciya,wannan ya sanya ko yara sa'anninsa basu fiya takalar fada dashi ba,idan kuwa kayi gangancin yin hakan kaine zakasha qasa "Don martabar fiyayyen halitta ama kada kiyimin haka,aba haka yakemin tun jiya,kema haka zakiyimin ama?,idan duk duniya sun gaza fahimtata ama na dauka ke zaki riga kowa fahimtata,ke zaki fara sauke fukafukan jin qanki a kaina ama?,ban tafi don wata manufa ba,banyi nesa daku saboda na rainaku ba.....hasalima nayi nesa daku ne saboda kunyar keta maganarku......saboda kunyar na aikata abinda ya kamata ace ya zama sirri ne tsakanina da ita saidai nayi ta yadda ya zai fita,na tafi ne saboda bansan da idanun da zan kalleku ba,bansan da bakin da zanyi muku bayani ba......ama....... wallahi wallahi wallahi ban tafi da nufin na tafi daga gareku kenan gaba daya ba.......na tafi ne da niyyar idan kun huce zan dawo......a raina ban taba sakawa zan tafi nayi koda wata guda ba.......sai kuma gashi komai ya sauya......ina biye daku ama......ina biye da duk wani motsinku ama.......ban yanke daga shiga rayuwar sultana tare da sanin hakinda take ciki ba ama......amma kuma saidai a cikin tarko nake......ina cikin wani dauri da muddin na bayyana a gareku rayuwata na cikin hadarin da bani da gatan da zai fiddani.... Lokacin kuma da nake tunanin na zama free......ina da 'yanci sai yayi dai dai da lokacin da zan cika BURIN ABA.....MAFARKIN ABA.....burin dana tabbata a duk sanda na bayyana a gabanki babu shi kema zaki qalubalanceni BABBAN LIKITAN ZUCIYA kuma DAN KASUWA CIKAKKE.....Na hadu da jarrabawar da na tabbatar barinku ne sila......na kuma hadu da lalurar da afuwarku da kuma yafiyarku ne kawai zai bani maganinta......" Hannu ta daga masa tana yin qasa da kanta,batason yaga zallar rauni da karaya daya zubawa zuciyarta,batason yaga tausayin daya lullube qirjinta,irin tausayin da dukka uwa keji akan d'anta komai girman laifi ko kuskurensa,saboda kasantuwar zuciyar mahaifiya ta banbanta da zukatan mutane gaba daya,koda kuwa ita wannan uwar wata halitta ce daban bata dan adam ba...... "Banason naji komai daya faru dakai,koda zanjin zanji ne a tare a kuma lokaci guda da mahaifinka,kaje ka nema yarda mutum ukunnan.......sannan ka dawo gareni" sai ta zame hannunta tana miqewa. Shima bai zauna din ba sai ya miqe yayi tsaye yana kallonta tana barin dakin "Kiyimin alfarmar amsa gaisuwata ama.....koda iya ita kadai na roqeki" har ya fidda rai don takawa take tana barin dakin,kamar kuma ba zata amsa ba,dab da zata fita din tace masa "Nayi maka" cikin dubunnan nauyikan dake qirjinsa yaji kaman an cire daya,ya fesar da iska me nauyin gaske da ya fusgota daga cikin cikinsa yana aza tafin hannunsa saman fuskarsa wani farinciki yana dan ratsashi,sa'annan yana jin qwarin gwiwarsa ya sake qaruwa. Sai daya ji ya nutsu sannan ya soma fita a dakin,cikin takunsa me cike da qasaita,saidai kuma a yau din a sanyaye yake takawar. Bangaren bibi ya nufata kai tsaye,shikam a yau yakeson gamawa da bibi din,don dama bai azata a ma'aunin matsala ba,ya duba agogo dab da zai shiga sashen,ya kwasarwa drama dinta awa daya kacal,don yanason ya koma bangarensa ya sake runtsawa koda na awa daya ne sannan ya shirya ya fito,don yanason ayi daurin auren 'yan uwansa dashi. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 56 A falo ya sameta riqe da tasbaharta da masu aikin sassanta. Cikin girmamawa suka gaidashi sauran da jiya basu ganshi ba sai yanzu sunata satar kallonsa hadi da mamakin ganinsa da sauyawarsa lokaci guda. Da daya da daya suka zame a falon kamar yadda suka saba a baya,sai ya zamana daga shi sai ita a falon. Zamowa yayi ya zauna a gabanta yana dan matsa mata qafafunta daya tabbatar suna dan mata ciwo kadan kadan,ya kuma fahimci haka ne a rigimarsu ta jiya. Saurin janye qafafun nata tayi tana jifansa da harara,yayi amfani da wannan damar ya sakar mata murmushi sannan yace "Barka da safiya da fatan kin tashi lafiya uwar gida ran gida" harara ta sake jefa masa tana hade rai da gaske "Kaga ka fita a ido na,ni ba sa'ar wasanka bace,uwarka da ubanka ma duka basu isheni kallo ba bare kai mara kunya fitsararre" tana kaiwa qarshe ta fara yunqurin tashi,bai hanata ba,ta miqe tsam ta wuce bedroom dinta tana mita kaman zata ari baki. Biye yake da ita bata sani ba,sai data shiga dakin tana shirin maida qofa ya shigo "Me ka shigo yimin daki?" "Ba komai,nazo mu fahimci juna ni dake" "Lallai aliyu raini ya shigo tsakaninmu,waishin me yasa baka tunkari uwarka da ubanka ba?,sai khadeeja marainiyar wayonka ko?,to na fika tijara" daga haka ta samu waje tayi zamanta. Qarasowa yayi gabanta ya zauna,duk wani yanayi da yasan zai bata ta tausaya masa amma taqi ma kulashi bare ya sanya ran samun wani ci gaba. Zuwa lokacin har maqoshinsa ya bushe kasancewarsa mutum bame yawan son dogon magana ba,yaja numfashi yana lumshe idonsa,qirjinsa wani zafi zafi yakeyi yi masa,ya kallo agogo yaga yana shirin cinye awa dayan da ya bawa bibi amma babu canji. Tsam ya miqe yana tattare hannun rigarsa idonsa a kanta "Allah ya gani nayi duk yadda zanyi na fahimtar dake kinqi fahimtata,shikenan zan tafi......kuma idan na tafin bawai zaki sake ganina bane,ba zaki sake ganina na ba har abada" yana fadin haka ya soma takawa. Da idanu ta bishi zuciyarta na rawa,tasan halinsa,aliyyu ne ba wani ba,komai ya fada yana aiwatar dashi,tsanani ko wahala basa sanyashi sauyawa,yana gab da fita taji bakinta ya fusgi kalmar "Ina zaka?" Cak ya tsaya yana jin ranshi yana masa dadi,bai waiwayo ba yace da ita "Zan koma inda na fito mana,tunda dukkanku kunqi bani dama na fadi abinda nakeson fada din" "Yo kaje mana,me jiya tayi ballantana yau......" Bai bari ta qarasa ba ya sanya qafarsa daya waje,sai kalaman nata suka sauya da "Amma dai kasan hukuncin me bijirewa iyayensa ko?,kasan hukuncin gudajjen bawa ma bare gudajjen d'a ga iyayensa" idonsa ya lumshe hawaye na taruwar masa,ya godewa Allah.......tabbas ya samu baiwar soyayya daga iyaye da 'yan uwansa,wannan reaction din kawai na bibi ya bashi qwarin gwiwa matuqa fiye da kowacce sa'a da daqiqa,yasan a yanzun ya cimma kaso hamsin cikin dari,hamsin kadai ya rage masa,shima kuma yasan ta yadda zaya biyo masa. Dawowa yayi da baya cikin wani irin sanyi da ita kanta bibi ta lura dashi,tsugunnawa yayi a gabanta ya sanya fuskarsa tsakiyar hannayenta daya kama "Ku yafemin bibi,ku yafemin.....na tafi na barku tsahon shekaru bayan nidin me laifi ne a wajenku" sanyi jikinta yayi sosai da taji damshin hawayen aliyyu,ganin fitar hawaye a idonsa ba qanqanin lamarj bane,sai dai ita dinma tanaji a zuciyarta bai kamata tanuna masa goyon baya ko.karaya tun yanzu yanzu ba,don haka ta janye hannayenta tana cewa "Ka tashi kaje kaci gaba da neman afuwar wadanda sukafi cancanta,zamu qarasa magana ko zuwa anjima" bayan hannunta kawai ya juya ya sumbanta ya miqe a nutse yana ficewa batare da sake cewa komai ba,don zuciyarsa tayi nauyi,bata yadda zai iya sake cewa wani abu. Tunda sukaga dinkin dogayen rigunan atamfar da akayi musu da zasu sanya ranar daurin auren suketa tsalle da murna,hakanan suka dami ama da cewa ranar yaushe za'a saka wannan kayan?. Tana sane take tambayarsu sunan kayan don bakinsu bai iya fadin ATAMFA da kyau ba,saboda bawai saninta sukayi sosai ba,saidai suyita qoqarin pronouncing dinta da suna kala kala,ama kuma tayita dariya. Suna daya daga cikin ababen dake sanyata nishadi da debe mata kewa da damuwa qwarai,a yanzun cikun rayuwarta bata jin akwai wani abu na biyunsu me daraja a gurinta,ko almu atta da saddi dai kawai ta haifesu ne,amma soyayyar benazeer da batoul daban take a ranta,bama ita daya ba,duk wanda ya kalli yaran haka kawai sai Allah ya jarabceshi da sonsu,suna da matuqar maqurar shiga rai. Tun takwas na safe suke zaune a dakinta suna jiran ta shiryasu cikin kayansu da qananun mayafai masu tsada data musu order tun daga dubai,hakanan qananun hand bags nasu hade sukazo da takalmansu na musamman data zabi wanda za'a yi musun,kuma dukka samples ne na kayan da take zubawa a qatoton boutique dinta dake dauke da kaya designers a garuruwa daban daban. Dole ta ajjiye kudin da take sanyawa yaran da zasu yi mata clearance din kayanta ta dauki waya ta kira tanja tace ta shiryasu. Nan ma wajen wanda za'a fara yiwa wanka suka gama fadace fadace,anayi ana rigima a haka tanja ta gama shiryasu. Ita kanta tanja baya taja tana kallan yaran tare da tsarkake girma da buwayar ubangiji daya samar da yaran cikin taqaitaccen lokaci cikin mahaifar mahaifiyarsu,ya kuma basu tsaro da kariya,sannan aka haifesu da wani irin kwarjini farinjini da kyau. Dariyar yadda suketa kallon kansu kayan na burgesu ta dinga yi,kana ganin yadda sukeyi kasan sanya atamfar ba sabonsu bane. Ana tsaka da fadan sanya turare wanda ama ta riga ta saba musu da sanyashi goumar yayi sallama yana murda qofar,yazo kuwa a dai dai,duk sai suka watsar da turarukan suka ruga wajensa suna masa oyoyo "Maaa shaaaa Allahhhhhh BB na.......wai,wai wai" ya fadi saboda yadda kwalliyar tayima yaran kyau qwarai yana bude musu hannayensa. A tare suka isa suka fada,ya hadasu ya rungume. Benazeer ce ta fara mitan ya tafi ya barsu yau kwana wajen biyu,yadan saki dariya kadan yana lakuce bakinta data turo,shima sultana yake gani a yawancin lokuta,amma kuma lokaci bayan lokaci idan tayi wani abun dan uwansa MAINA take tuna masa "Yanzun ai gashi na dawo ko?,am back" "Ayi mana hoto,dama ama tace sai ka dawo" "Tom an gama,kwana biyu nayi checking account dinku banga ama ta saka mana update na african twins BB ba" . A gaba ya sanyasu,yau kowacce taqi yarda ya dauketa wai kada ya bata mata kwalliya,su a dole ga 'yammata. Ta baya can ya fita dasu,don ya tabbatar idan yabi dasu ta gaban gidan yadda sukayi kyau haka za'a bata musu loakcine,kuma ba za'a barshi ya musu hoton da kyau ba. Cikin rumfar da aba ya sanya aka yiwa bibi saboda zama lokacin zafi suka tsaya. Guri ne da aka qawatashi sosai da zubin ginin gargajiyar qasar nijer,ya tabbata wajen zai bada background me kyau. A nutse suka fara hotunan,kowanne idan ya dauka sai yaga yafi dayan kyau,suka gama tsaf,sai ya samu kujera daya a wajen ya zauna yana duba duka hotunan zai turama ama ta watsapp. Hannayensa dukka zube cikin aljihun rigarshi yake takawa a nutse,sassalkan gashinsa dinnan me santsi da duhu yadan cakude kadan saboda baiyi combing nasa ba bayan yayi alwala. Yanayin da zuciyarsa ke ciki ya sanya fuskarsa ta danyi ja kadan,hakanan idanunsa daketa qoqarin saye abinda ke yawo a qirjinsa. Duk yana jin ba dadi cikin jikinsa,saboda ya saba kowanne lokaci kusan warhaka ya dawo daga gym ne yana shaqar daddadar iskar balcony din dake gaban dakinsa,a yanzu duk sai kasala da yanayin da zuciyarsa ke ciki suke son kashe masa jiki. Kamar a iska yake jiyo muryoyinsu,yana ci gaba da takawa yana kasa kunnensa don yanason tabbatarwa muryar yaranne ko ba nasu ba?,yana tsoron kada tsananin damuwa da yaran da ba nashi ba,baisan me yaran waye ba ya sanya su fara shiga rayuwarsa har haka?,kada ya soma halin da ba nashi ba wato damuwa da abinda bai shafeshi ba. Yana sake kusanto wajen yana sake jin tashin muryarsu,a hankali a hankali kamar almara sai ya fara hangensu yana kuma dab da isa inda suke. Suna tsaye su biyun suna gwada yin selfie, benazeer ta matse batoul da yawa, batoul din na mita tana qoqarin banbare hannun benazeer daga wuyanta. Ta samu sa'a kuwa ta cire din,sai taja da baya tana tura baki gaba hadi da hararta "Kina gani kina shaqemin wuyana?....bazanyi hoton ba ai uncle........." Bata iya qarasawa ba saboda dan juyawar da tayin idanunta ya fada kan maina. Dukka idanunta ta fiddo waje kamar zasu fado,ba wani jiran komai ta qwala kiran sunansa "Uncle haidar!!!!....... benazeer kinga......zo kiga uncle haidar a gidanmu......" Da wani mugun sauri benazeer din ta juyo kuwa tana jin daukin ganinsa, zuciyarta na raya mata qarya batoul keyi mata. Bata iya jiran benazeer ba ta kwasa da gudu tana tattare doguwar rigarta ta nufeshi tana jin wani irin farinciki. Da siririyar muryarta itama ta kwatsa wata irin ihu,abun tana jinsa kamar a carton da suke kalla,sannan ta diba da gudu itama tayi kansa LOKACIN tuni batoul ta dade a jikinsa,harfa fara qwallar da ita kanta batasan dalilinta ba. Qarar batoul ita ta fara zuwa kunnenta,ta kuma ji qarar kamar daga baya wajen window din dakinta,taja qaramin tsaki,yaran sun sake da yawa,tabaransu kawai sukeyi cikin gidan,kowa soyayya qauna da kulawa yake basu,tana tsoron su sangarce da yawa da ganin yawan gatan da suke samu,saita ware dankwalinta tana daurawa da zummar idan ta fita zata kirasu taja musu kunne da kokaye kokayen banza,su nutsu cikin mutane suke. Saidai kuma bata sauke wannan tunanin ba muryar benazeer ta sake iskota. Dogon tsaki ta saki tana soke daurin dankwalin gefen kanta ta juya ta nufi window din ranta adan bace da ihun da suke sakima mutane. Da zafin nama ta zuge labulen,saidai kuma abinda idonta ya gane matan ya kusa sanyata sulalewa a qasa. Benazeer da batoul rungume da maina,wata irin runguma dake nuna zallar shauqi da tsumammiyar qauna dake tasowa daga zukatan iyaye,ya dagasu daga jikinsa yana riqe da hannayensu,fuskarsa na fidda wani irin murmushi kaman yadda idanunsa ke jifansu da wani irin kallo na tausasawa. Tambaya yakeson musu kamar yadda suma suka cikashi da tambayoyin,to amma sai yakejin cikin jikinsa kamar akwai wani idon dake kallonsa,tashin farko kuma idon nasa ya canki daga inda ake kallon nasa. Sake haduwa idanunsu sukayi a karo na biyu,ko second biyu cikakke bata qara ba ta saki labulen da hanzari tana komawa da baya,zuciyarta na wani irin mahaukacin bugu kamar zata fito daga qirjinta,yayin da ranta ke mata wani suya Meye hadinsa dasu? Yaushe ya sansu? Waye ya shaida masa su din yaransa ne? Don me zai shiga rayuwarsu? Shin ance masa suna sa buqatarsa? Dukka tambayoyin da takewa kanta kenan a zafafe ba tare da samun wanda zai amsa mata ba. *_muje zuwa_* *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 57 https://chat.whatsapp.com/IQ6XVJntkTj5FFJ66euAIR Hey everyone.. Assalamu Alaikum. let's build our business together. join our whatsapp group, ladies only Zamu kawo kwararru a bangaren business da zasu yi mana bayanin yadda suka samu cigaba a kasuwancin su,yaya zaka yi tallan kayan ki online ki saida online, ta ya zaki samu riba a kasuwancin ki? Yaya ake marketing da branding da sauran su. Wanda kuma suke son fara sana'ar amma basu san taya ba, in sha Allah you will find something to start with Lets grow together. ______________________________ Har ta zame tabar wajen bai daina kallon window din ba,shi kadai yasan me yakeji a zuciyarsa game da ita,yadda tausayinta yayi shekara da shekaru yana masa didibniya cikin zuciyarsa shi kadai yasan yadda ya luguiguta shi,ya kuma yi masa kyakkyawan kamun da zuciyarsa tayi wani mugun laushi. Takun goumar shine ya ja hankalinsa yadan dauke idanunsa daga wajen ya maida ga goumar din,suka hada idanu sai goumar din ya sakarwa maina murmushi,murmushin dake nuna tsananin farincikin dake kwance qasan zuciyarsa da dawowar dan uwansa cikin ahalinsa "Ya maina....bansan a irin wannan lokacin ka shirya dawowa ba ai,da banyi nesa ba,da na zama mutum na farko da zan dauko ka na kawoka cikin gidan. Harara ya jefeshi da ita da lion eyes dinnan nasa,dole goumar yadan dauke dubansa daga cikin nasa saboda yadda idanun sukayi masa kwarjini "Kayimin dukka qoqari goumar,amma kuma daga qarshe ka yanke alaqata dakai,ka barni ni kadai ins fakan fakan.......ba uwa ba uba ba mata......ka hanani ganin fuskar yaro na fafur......ko sunansa ka hanani sani bayan ina cikin asibitin ranar da za'a fiddoshi daga ciki" idanu goumar ya dora kansu benazeer,da alama har yanzu bai samu masaniyar sune 'ya'yan nasa ba,sune wadanda cikinsu yazo cikin gagggawa zazzafan rabo wanda ko cikin tarihi ba'a fiya samun irinsa ba,yaji dadin hakan,zai kuma ci gaba da wasa ba hankalinsa har sai yaji ciwo cikinnzuciyarsa shima,yanason a ranar da zai san su benazeer yaransa ne yasan hakan yana jin ciwon shekarun da ya dauka yana mutuwar sonsu ba tare da yasan mallakinsa bane su "Yanzun tunda ka dawo ai zaka san komai ba?" "Ina d'ana goumar?,inason ganinsa,na tabbatar duk gidan nan babu me yimin maganarsa,kai kadaine nake da fata a kanka" tsaiwarsa goumar ya gyara yana harde hannunsa a qirjinsa "Yaronnan baya cikin gidan nan yanzu haka, infact ma banjin yana nijer gaba daya" "Nigeria suka kaishi?" Ya jefawa goumar tambayar cikin damuwa,har hakan ya bayyana qarara saman fuskarsa "Ban sani ba,but amma zan tambayi ama naji" miqewa tsaye maina yayi,har yanzu suna riqe da hannun juna shi dasu benazeer "Alright......akwai maganganu da yawa da nakeso mu tattauna,inason nasan abubuwa da yawa bayan wadanda na sani akan sultana" "Saboda me?" Goumar ya jefa masa tambayar. Kallon da maina din ya jefa masa ya sanyashi shiga taitayinsa,ya kuma tuna cewa har yanzun fa shine din dai ALIYYU MAINA HAIDAR ba abinda ya canza daga wancan halin nasa,don haka ya gyara zancansa cikin basarwa "Sanin komai akan sultana yana da tsada matuqa,nawa ne farashin?" "Daga million daya har million goma kayi requesting......zaka sameta cikin account dinka" yayi maganar yana fidda wayarsa saboda shigowar kira. Goumar yana dariya shi kuma dukka hankalinsa yana kan wayar. Yana jin nauyin yaqi daga wayarta amma kuma ya rasa me yasa ta gaza fahimtar take takensa ta yiwa kanta fassara ba tare data wahalar da kanta har haka ba?. Daddy da sardauna mutanene da bazai taba iya butulce musu ba......bazai kuma taba iya wulaqanta jininsu ba,don haka ya danne zuciyarsa da duk wani emotion nashi ya daga kiran "Hello.......Yaa maina kana jina?" Ta furta daga can bangaren murya can qasa "Ina jinki laila.......ya akayi?" Zamewa tayi sosai ta kwanta daga can inda take tana narkewa,iya sautin muryarsa kadai yana tafiyar da dukka damuwarta ya qara mata walwala da kuzari,yana da wani irin husky voice dake ratsa zuciya qwarai da tunani,wani lokaci recording takeyi na taqaitacciyar hirarsu tayita kunnata tana saurara duk sanda take tsananin kewarsa kaman haka. Ta fahimci yana cikin jerin sahun mazan da su baki lokacinsu abune dake musu wuya,duk da ta bayyana kanta bata tsaya boye boye ba,amma hakan bataga ya canza wata mu'amala a tsakaninsu ba,abinda har kullum yake sanyata kokwanto "Ya akayi kuma yaa maina?,bayan ka wuce nijer ka manta dani?,last wayarmu kace zaka kirani amma shuruuu" boyayyar ajiyar zuciya ya sauke,bata qaunar saba alqawari ko kadan,amma shi sam ya manta ma sunyi zaiyi kiran nata. Yanayin da yake ciki yanzu yana buqatar lokaci da kuma nutsuwa,don haka ya gyara tsaiwarsa "Afwan na saba alqawari,amma ina cikin wani muhimmin aiki dana tabbata sardauna zai iya dan gaya miki muhimmancinsa a taqaice,ina tare da family na muna kashe wani issue......amma in sha Allah idan na zama normal zamuyi waya" sosai maganar tasa tayi mata wani iri,amma da yake ita din me yawan bada uzuri ce sai ta gyada kai "Tou yayi...... Allah ya taimaka,i missed you" "Thanks,but......kina iya kira duk sanda kk buqatar hakan" ya fadi don ya sassauta mata abinda ke yawo a zuciyarta,don ya fahimci kaman maganar batayi mata dadi ba "Na gode da wannan karramawar" "U r welcome" ya sake fada yana katse wayar ya jefata a aljihu. Idanu suka hada da goumar,sai yadan dauke kai kaman baiji wayarsa ba "Yaran waye a family dinnan?" Ya jefawa goumar tambayar da baiyi zato ba. Idanu kadan ya zuba masa yana tunanin amsar da zai bashi,sai kuma ya janye yana cewa "Ba zakasan waye mama da babansu ba saina zauna na maka bayani,kuma qilan ka manta fuskarsu ma yanzun.......zan wuce dasu na maidasu kada ayita nemansu ansan tare muka fito" ya fada yana riqe hannun batoul da tafi kusa dashi. Idanu ya sakawa goumar din yana jin kamar maganar tasa bata hau ma'auni ba,tunani ne iri iri cikin kansa,don haka ya ture wannan,ya durqusa a tausashe yayi kissing goshinsu daya da daya sannan ya dubesu yana murmushi "Zan shirya zan fito..... anjima akwai shan ice cream?" Ya tambaya yana kallon fuskar benazeer. Qaramin ihun murna ta saki tana tsalle,sai batoul itama tabi sahu,don itama wannan karon sosai takejin dadin ganin uncle haidar din,har bataso yabar inda suke. Tare suka wuce da goumar sunata bashi labarin haduwarsu a makka,tausayinsu su dukka ya dinga ratsashi,ya dinga jin kamar ya koma ya bayyana musu gaskiyar su din waye wa junansu?,amma kuma sai yaji bai kamata yasan yaran su waye a wajensa ta cikin sauqi ba. Ya samu kira daga wajen najjashi mutumin da sardauna ya hadashi dashi don ya masa hidima yana tambayarsa ko yana buqatar breakfast ko wani abu me kama da haka?,yace masa a'ah,don ya samu almu ya shirya masa breakfast din,komai da komai,yayi tsaye yana mamakin yadda almu zai iya shirya abinci sosai kaman haka,amma kuma daya dinga qarewa salon jera kwanukan kallo da kuma yadda aka shirya abincin sai yaji jikinsa yana bashi tabbas daga hannun ama aka aiko dasu. Ya debi abincin yaci sama sama don bai fiya cin abu me nauyi da safe da kuma dare ba,ya wuce bandaki yayi wankansa na kusan minti talatin yadda ya saba,sannan ya fito ya shirya. Cikin wata shegiyan danyar gezna off-white ya shirya kansa,sai maiqo take da daukan idanu,dinkin babbar riga wanda da 'yar ciki,hular daya sanya a kansa baqa ce wadda ta dace da rufaffen baqin takalmin qafarsa me matuqar kyau da jan hankali qirar kamfanin WEITZMAN,fatarsa kawai idan ka kalla zakasan ba qananun kudi ne suka mallaka masa shi ba. Sassanyan turarensan nan daya kasa rabuwa dashi tsahon shekaru......sai kamfani kawai daya sauya amma da dsame qamshin shi ya fesa,yana fesawar yana kallon fuskarsa cikin mudubi. Tabbas shekaru ba qarya bane,a yanzun fuskarsa kadai ta zama cikakkiya wadda ke bayyana zuwan gejin girma da hankali a tare dashi,ya ajjiye turaren yana qoqarin daura agogon fatar kamfanin blancpain sai yaji muryoyi a falonsa. Ko bai fita ba yasan cousins nasa ne,daga bangaren aba da ama gaba daya. Baima gama tunanin ba yaji ana knocking qofan bedroom din. Muryar attahir ne,ya lumshe ido yana murmushi kana ya budesu saman madubi,attahir sunsan juna kaman yadda sukasan yunwar cikinsu,abokin fadanshi abokin adawarsa,shi fushi da zuciya attahir kuma tsokana,haka zasuyita bugata saidai idan baije nigeria ba,d'a ne ga uncle abdulhakeem babban d'ansa ATTAHIR ABDULHAKEEM ME KANO. "Malam kada ka balla min qofa fa?" Ya fada yana gyara zaman agogon a hannunsa "Idan kaqi fitowa tsaf zamu balla qofar......." Muryar bilal ya ratsa ta attahir. Dole murmushi ya subuce masa,ya zari handkerchief ya fito. Dukkansu cousin nasa ne kaman yadda yayi zato daga bangaren aba din da ama,kuma dukkansu sa'anin haihuwarsa ne da kusan tare aka taso. Dukkansu kaman dai shi,sun zama cikakkun samari,wasu a cikinsu ma basu jima da angwancewa ba. Rudu iya rudu suka hada a falon nasa,don ma dai shi din ba gwanin magana bane amma duk da haka sai da sukayi yadda suka saba,sannan daga qarshe suka fice can masallaci suna takawa da qafafunsu domin shaida daurin auren. Kafin sukai ga fita din haka ya dinga bi yana gaida kowa,kowa kuma barka da dawowa yake masa,a haka suka isa masallacin suka kuma hade da tawagar angwaye suka tsaya karbar daurin auren. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 58 Kusan duk inda suka gilma sai sun debi kallon jama'a,kana ganinsu zakasan samari ne masu jini a jika wadanda ilimi da hutu suka ratsasu,amma duk da hakan daban maina ya fita a cikinsu,saboda yadan fisu tsaho da kauri hakanan sumarsa tafi tasu nannadewa,kaman yadda fatarsa ta dara tasu gogewa. Cikin qasa da minti talatin aka kammala siga aka daura aure,sauran hidimomi ne suka biyo baya kafin daga bisani a wuce babban hall na gidan da aka ginashi musamman saboda lokaci irin wannan. Reception sukayi a ciki wanda family din MAYAK'I suka shirya,kusan duk biki suna yiwa dangin ango wannan karramawar komai wadatarsu kuwa. Daga nan cikin gidan suka yi don gaida iyayen amarya. Tana idar da sallar azahar houda na sanyo kai cikin dakin "Ki fito za'a yi hoton family......ama tace nayi kiranki" kusan hoton hotone me muhimmanci ga dukkan dan gidan,don ana maidashi enlargement ne a ajjiyesu,kuma kowanne biki kusan sai anyi hakan. "Kice mata bana danjin dadi....." "Kinsan Allah saikin fito, bazanje na gaya mata ba" houda ta fadi kanta tsaye tana jawo mata mayafinta. Ko kadan bata qaunar fita farfajiyar gidan saboda dalilai biyu na farko bata son ta ganshi sam sam,duk da tana ji a jikinta zai wuya ta sameshi a wajen saboda shi din bamai shiga ire iren wadannan abubuwan bane,na biyu kuma bata qaunar kallo,ta rasa wanne irin kallo ne mutane ke binta dashi haka?,kamar ita daya ce Diya cikin dangin?. Gaban madubi ta tsaya ta shafa powder ta maida lipgloss din da houda ta matso mata,sannan ta maida daurinta ta lulluba mayafinta a saman ka "Kin saje da amaren ai wannan" houda ta fadi tana dariya,harara ta balla mata "Zan fasa wallahi" "Na tuba" ta maida mata amsar dai tana dariya. Plate shoe ta saka wanda ya dace qwarai da kayan jikinta,ta fito suka jera da houda din. Duk inda ta gifta sai an Mata magana,wasu sunata mamaki dama tana ciki?,tana amsa musu da eh ta tashi ne yau bata jin dadi,da haka da haka sannu sannu har suka fara fita qatuwar harabar gidan. Tanata raba idanu taga benazeer ko batoul amma babu wanda ta gani a wajen,harma ta haqura ta koma hirar da houda ke mata tana biye mata. Qoqarin saita tsarin hoton akeyi yana daga zaune saman kujerun dake wajen yana maidawa suhail reply din saqon daya turo masa,yana gaya masa yana sanya ran shigowa NIJER nan da kwana uku. Ya san suhail din nada family a nan amma ba masu yawa ba,to sai bai saki jiki sunyi wani hirarsu ba saboda bayason Susan daga wanne yanki ya fito,yasan kuma zaiyi wahala ya ambaci family dinshi suhail din bai sani ba duk da ba wai yana yawan shigowa bane. Har tsakiyar kansa yake jin hayaniyar tana damunsa,banda son ya farantawa su bibi da aba dake wajen da tuni ya fice yabar wajen,don kwata kwata kanshi baya iya daukar hayaniya haka. Shigowarsu wajen sai ya zamana kamar sun taho da daukewar surutun dake tashi a wajen. Baya ga shirun da baisan meye ya haifar da shi ba,cikin jikinsa ya dinga jin wani baqon yanayi,tilas yadan dauke idanunsa daga fuskar wayar yana maidashi cikin farfajiyar wajen. Gani daya biyu ana uku idanunsa suka fada kanta. Dan mitsitsin bakin nan dake dauke da wasu irin pink lips......bakin daya saba da tsiwa a baya yana motsawa a hankali tamkar bataso,ta zube fararen idanunta akan fuskar houda da alama wani magana suke me muhimmanci a wajensu. Wani irin zuzzurfan kallo ya samu kansa da yi mata,yana karantar kowanne motsi nata. A nutse ta jingina da wata qaramar bishiya dake a wajen ta kuma goye hannayenta a qirji, kyawawan fararen idanun nata nata da abaya yasan ta qware wajen yin fari dasu idan tana jin rashin kunya a yanzun sun rusuna qwarai,sun zama wasu irin lumsassun idanuwa dake qawace da eyelashes,sun kuma qara girma kewayayyun idanun masu dauke da fararen qwayar idanuwa. Kwantaccen gashinnan da ya sani a gefe da gefen kunnenta zuwa gaban goshinsa ya sake qawata fuskarta qwarai,ya sake cika da sake kwanciya luf luf abinda ya zame mata kamar wani adon dawisu. Yadda ta nutsu tana sauraron houda kadai ya isa ya gaya maka tarin nutsuwa da rayuwarta ta samu,zallar aji da kamala dake tattare da ita. Gyara zamanshi yayi sosai cikin kujerar,sam yama manta da waje ko muhallin da yake,don sai yanzunne yakema sultanar kallon tsanaki kuma kallon tsaf,yake kuma ganin canji ga rayuwarta me mugun nisan tazara,irin sauyin da yayi mata kwadayin samu,irin canjin da ya dinga fatan ta samu,amma kuma komai sai ya sauya,komai sai yazo ta bahaguwar hanyar da baiyi zato ba. Gilmawar wani ta gabansu da kuma dawowarsa gurin tsaiwarsa yaja hankalinsa. A nutse ya maida dubansa sashen,har zaya dauke kai saboda baiga wani abun kallo a wajen ba sai idanunsa suka hango masa mutum uku cikinsu. Mutum ukun da suka hade kai waje guda suna qus qus,dukkansu idanunsu suna inda houda da sultana ke tsaye. Tashi yayi ya zauna sosai sanda zuciyarsa ta fara bugawa,adadin gudunta yana son ya sauya daga yadda qa'idarsa yake. Kallo suke mata irin kallon nan da ake kira na qurilla "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya fada yana jin yadda numfashinsa yake rawa. Ko shakka babu ita suke kallo,maganarta kuma sukeyi,yana da saurin fahimta da kuma nacin gane me kake fadi koda daga nesa ne ta hanyar karantar motsawar labbanka. Ya fuskanci shirin tunkararta suke ba shiri ya miqe don baya jin zai iya tsaiwa ya kallesu koda a gefenta ne bare suyi mata magana,bayajin zai kasa taka musu burki koda kowa zaiji bai cancani yayi hakan ba. Murmushi ne ya kubce daga fuskar Goumar wanda ya gama karantar komai daga fuskar maina,duk kuwa da cewa yana nesa kadan daga inda yake din,ba kuma lallai ya ganshi. Wani irin zazzafan abu yake gani a fuskar maina din,mahaukacin baqin kishi,tun kafin yau,tun yana haidar dinsa dan makaranta a niamy.....tun yana saurayinsa me qananun shekaru dama mutum ne shi me matuqar kishi na gaske,wannan dalili ya sanya yayi ruwa yayuntsaki wajen kula da tarbiyyar qannensa mata kamar me?......wannan dalili ya sanya tyj suna da qananunnshekaru ya haranta musu sanya qananun kaya saidai atamfa da manyan riguna masu rufe jiki......wannan dalili kuma still shine ya zama silar samun rashin jittuwa tsana da qiyayya me gurma tsakaninsa da SULTANA.....yana kishin dukka yan uwansa mata qwarai,yayin da ita kuma sultana take kallon hakan a matsayin takurawa da kuma tsangwama,don a sannan hankalinta baikai ta gamo girma da matsayin gatan da yakeyi musu ba. Taku biyu kacal yayi sai ya hangi goumar har ya isa gabansu sultana din. Maganar da takewa houda ta katse,ta daga kai tana duban goumar da kallo me kama da hararara harara "Me kuma ya faru?" Ta jefa masa tambayar tana hade girar sama data qasa. Tun kafin ma ta ajjiye harshenta maganar data tsani ya fada mata ita ya gaya matan "Kefa matar wani ce,duk wajen nan kuma kusan mazan wajen ke suke kallo" sosai ranta ya baci,yakai qololuwar baci ma "Baqin buzu......wai oncle umar baiyi mana tsakani dakai ba?" "Don yayi mana tsakani saina tsaya na kasa tunasar dake girman nauyi da haqqin dake kanki?" "Nauyi?,haqqi?, dukka na waye?,ba haqqin kowa kaina, goumar ka dameni......ka shafamin lafiya,wai idan nace aure zan daura yau ko gobe ka isa ka hanani?" Shi dinma dan uwan maina dinne wajen kishi,maganar tata sai yaji ta zafafeshi tamkar shike da igiyar auren nata a hannunsa "Baki isa ba.....kema kin sani,saidai kiyi aure akan aure,wanda kuma badai cikin family dinnan ba" "Haka kace?,zaka gani kuwa yanzu,badai taqamarka igiyarsa ba?,to yau zata zo qarshe naga da meye zakamin taqama" ta fadi a zafafe sannan ta zagaye houda tana nufar hanyar ficewa,tanata qoqarin riqe fushi da hawayenta amma ta kasa,ita kanta batasan meye ya zafafi zuciyarta har haka ba. Bayanta houda tabi tana kiranta, kiran nata da takeyi sai taji ya qarasa karya mata gwiwa,don haka ta soma takawa da sasaarfa tanason kubucewa ganinta. Tunda aba da oncle issoufou suka nufo wajen,wadanda barinsu gurin sunje suyi sallama da wasu baqin aba dinne su dawo suka hangi tahowar sultana da houda. Sam sultana bata gansu ba saboda yadda idanunta suke a qasa,har sai data ci tuntube da aba sannan ta dakata. Saurin riqo hannunta aba din yayi yana fadin "Subhanallahi.......lafiya kike?" Idanunta da suka cika taf da qwalla ta daga suka hada ido dashi,sai kuka kawai ya taho mata gaba daya,ta sanya daya hannun nata ta riqe hannun aba da kyau tana sakin kuka me sauti. "Subhanallah......ya salam......ke houda.....me yake faruwa?" Aba yayi mata tambayar yana jin tuhumar maina cikin ransa. Dan daburcewa tayi saida oncle issoufou ya maimaita mata sannan ta gaya masa komai. Sosai ran aba yaji ya baci matuqa.....ta kowanne fanni gani yakeyi kaman basa yiwa yarinyar adalci,zuwa yanzu ko a musulunci tana da haqqin zabawa kanta abinda takeso,to don me yasa su zasu tauyeta?,me yasa zasu bari a dameta akan abinda bai zame mata dole ba?,me yasa za'a dinga dukanta kuma ana hanata kuka?,shi me laifin waye ya dameshi?,waye yake sanyashi kuka tunda ya shigo gidan kusan awani arba'in da takwas?. Hannunta ya kama yana juyawa zuwa hanyar sassansa,oncle issoufou yana biye dashi. A yadda aba din ya fusata ya sani zai iya kowanne hukunci shi yasa bai barshi ya wuce shi kadai ba. Yana ganin aba din ya zaro wayarsa daga aljihun babban rigarsa shima ya zaro tashi,a gaggauce ya turawa oncle bashar tex _"mu hadu a falon yaaya yanzu yanzu don Allah karka wuce wadannan mintunan komai na iya faruwa"_ ya tura masa ya maida wayar nasa aljihun,dai dai lokacin yaji aba din yana magana "Kazo inason ganinka yanzu yanzu,ka taho da kuma wanda ya sanyaka ka gaggaya mata maganar.... Eh aliyyun nake nufi" ya fadi a hasale sai ya maida wayar aljihu yana jan wani dogon tsaki zuciyarsa na masa zafi..... *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 59 "koma ka dauko mata ruwa me sanyi" aba ya fadi sanda suke shiga falon,atta da ya gama sanya masa turaren wutar da ama ta bashi ya saka din yana shirin fitowa sukayi kacibus. Da kallo yadan bisu sannan ya koma ya ajjiye kwalbar turaren ya bude fridge ya ciro ruwan,ya hado da kufunan gilasan da suka zamewa saman freezer din ado,ya qaraso gaban sultana da kanta ke duqe a qasa,hawaye yana layi saman fuskarta. Fuskartata har ta dan hada ja,abinka da farin mutum "Gashi aunty sultana" atta ya fadi yana miqa mata ruwan. Cikin ransa tausayinsu dukka yakeji,duk da baisan har yanzu ainihin abinda ya sanya ya maina barin gida ba,bai kuma san abinda ya hadasun ba,amma yadda suke ganin komai ya sauya a shekarun sun tabbatar ba na dadi bane. Hannun tasa ta karba,muryarta na rawa tace dashi "Na gode" bai iya amsawa ba ya miqe,ya dauki turarensa yana barin falon. Ko zama aba baiyi ba sai kai kawo da yakeyi tsakanin oncle issoufou da sultana da suke zaune,zuciyarsa na masa lissafin wahala fadi tashi dawainiya da mohmoud yayi dasu,jininsa bai cancanci zubda hawaye ba. Baiji ko d'ar ba sansa goumar ya gama gaya masa saqon aba yana kiransu "Amma ya maina......me zai hana ka fice,zan gaya masa yanzu yanzu kuka fita dasu tahir" idanunsa ya daga ya watsa saman fuskar Goumar "Na fita goumar?,na sake fita a gidannan?,na gama fita goumar......kasan sunan da nafi tsana a duniya?,kasan abinda nafi tsana a wajen d'a namiji?,RAGWANTAKA.....kalmar da ban yarda a kirani da ita ba kenan......don meye zanta guje guje akan halas dina?,meye zai sanya na yita guduwa?,kasan meye ma'anar sunan HAIDAR?,fassararshi na nufin jaririn ZAKI,ka taba ganin zaki ya gujewa wata masifa?,to haka nake goumar.....wancan da ya faru na yarda yana cikin babin qaddarata.....ba kuma wai nayi GUDUN K'ADDARA bane...... a'ah.....rubutacce ne dole sai na fita nabar gida na wannan shekarun kafin na zama abinda na zama a yanzu....muje goumar,zan iya fuskantar aba" bai sake bawa goumar second chance da zaiyi magana ba ya fusgi hannunsa,har cikin ransa yana jin wani karsashi yana cikashi. Shima ya gaji,yafison ayita baro baro......yafison su fidda duk kalar hukuncin da suka yanke masa,yafison yaji meye matsayinsa?,yasan daga inda zaya fara. Mamakin tsananin jarumta da yadda yake takawa ta kama goumar,sai ya kasa tabuka komai sai kallo da yake binsa dashi,ya kuma ci gaba da binsa tamkar raqumi da akala. Sai da suka isa qofar falon sannan ya saki goumar din,ya durqusa ya sabule takalman qafarsa ya sanya qafars a falon bakinsa dauke da cikakkiyar sallama,dukkan wata gaba ta jikinsa tana bayyana nutsuwar zuciyarsa. Oncle issoufou ne ya amsa masa yana binsa da kallo. Bai tsaya ko ina ba sai daya dangane da gaban aba sannan ya durqusa, goumar ya biyo bayansa shima ya tsugunna gabansa. Cak aba ya tsaya a gabansu su dukka biyun,saidai kuma goumar yake kalla "Ina cewa kwanaki umar ya maka gargadin kiranta da matar wani?,wanin da ba'asan a wacce nahiya yake ba?,......ko yanzun kuma da akasan nahiyar da yake bashi da nagartar rayuwa da d'iyata....... inason naji shi ya aikeka ka sake maimaita mata?!" "Nine aba" maina ya furta cikin qanqan da murya da kuma nuna tsananin girmamawa "Goumar kai nake tambaya!" Aba ya kuma maimaitawa fushinsa yana motsuwa. Abun ya taba oncle issoufou sosai,bai taba ganin zallar madarar fushi akan fuskar aba irin na wannan lokacin ba,don haka ya sake fidda wayarsa. Wannan karon direct ya kirayi bashar,akayi sa'a ya daga,baice masa komai ba yabarshi speaker bude,yadda yasan zaiyi sautin aba din. Yaji din kuwa take hanakalinsa ya dawo jikinsa,ya katse kiran, oncle issoufou din yana ganin ya katse sai ya sake rubutawa oncle umar gajeran saqo yasan shi din zaiyi wuya bai gani akan lokaci ba saboda yana yawan mu'amala da waya _idan zai yiwu ka shigo da bibi da kawu_ ya rubuta masa daga qarshe. Ya nemi tallafinsu ne saboda yana gudun kada ayi aika aika,yadda yau din fushin aba ke hauhawa bayajin shi daya a matsayinsa na autansu zai iya controlling nasa. "Abokin wasanku zaku maidani kai dashi din?......." Ya fada yana sake fusata saboda yadda kowa ke son maida laifin kansa kusan minti biyu kenan. Basu amsa masa ba don haka yayi taku biyu baya ya dauki qaramar jotting paper da pen dake maqale a jiki ya wurgawa maina,ba bata lokaci ya sauka a fuskarsa "Maza maza rubutawa diyata saki......saki ukku kuma nake buqata bawai daya ko biyu ba". A razane ya dago kansa,karon farko ya kalli fuskar aba da idanunsa da suka sauya launi "Eh abinda na fada din nake nufi...... girman idanunka ba zasu razanani da komai ba,ka rubuta mata sakinta guda uku......" "A'ah yaaya ba za'a yi haka ba,wannan hukuncin ai yayi girma da yawa" oncle issoufou ya taso yana son riqe hannun aba "Kada ka dakatar Dani issoufou.....me za'a jira?,meye amfanin igiyarsa?,ya gama shekarunsa dai ya dawo ba?,to ya sallamarmin diya zan zaba mata miji na kere sa'a,me tarbiyya wanda yasan mutuncin na gaba dashi" kamar ya zanya tsinin qaho ya caki qirjinsa haka yaji,wannan radadi da ciwon da qirjinsa keyi masa lokaci bayan lokaci.....ciwon da tunda ya fara zuwa gaban ka'aba yana shan zam zam shi da azababben ciwon cikinsa suka shafa masa lafiya a yau din kalaman aba sai yaji suna shirin tayar masa dasu "Don Allah yaaya ka daina....." "Sai ya saketa don bata dace dashi ba" ya sake maimaitawa,kalaman da suka sanyashi zamewa ya zauna sosai saman carfet,sallamar oncle umar da oncle bashar ta baqunci wajen. Oncle umar ya duba bibi din bai ganta ba,don haka sukayo gaba shi da oncle bashar,don saqon issoufou din ya nuna musu ba lafiya ba "Bazan iya sakinta ba aba.......bazan iya sakin diyar NAFESSA ba!" Ya furta cikin dakiya da jarumta. Sak aba din yayi,don bai taba tunanin maina zaiyi masa musu ba. "Sai yanzu kasan diyar nafessa dince?,sai yanzu kasan da haka?" "Na yarda da dukkan wani laifi da kuke tuhumata dashi aba.....na yarda da duk wani kalar suna da zaku laqabamin......na kuma yarda da kowanne hukunci amma na roqeka da girman mahaliccinmu banda saki" "Saboda?" Ya tambayeshi yana matsowa gabansa "Bazan iya sakinta ba!,ina qaunarta.......ina qaunar jinin nafessa!" Ya fadi wasu siraran hawaye na biyo gefan idanunsa "Zan yita baku haquri ku da ita iya adadin numfashin da ya ragemin.......aba koda nayi ma sultana laifi banajin yakai a yankemin hukuncin rabuwa da ita........naku laifin da nayi muku gani a qasa ina roqon afuwa da yafiyarku!" "Kasan yadda ta rayu tsakanin shekarun?,kasan da yadda aka samu rayuwarta?,ka tafi ka barta da dawainiyar cikin yara har biyu?,don bakasan yadda mata sukeyi ba idan suna tare da juna biyu?,baka da tausayi bakasan ya rayuwarsu take komawa ba?,yara biyu da qananun shekaru irin nata?,wannan shine qaunar?,wannan shine tausayin?" A hautsine ya daga jajayen idanunsa yana kallon goumar "Yara biyu?,twins?" Ya yiwa goumar tambayar idanunsa a kanshi,da alamun ya zaqu matuqa yaji cikakken bayani,kamar ma ya manta a gaban waye yake,kamar ma ya manta cikin kotun aba yake. Ganin goumar bai dago ya dubeshi ba sai ya dafa kafadarsa da qarfi "BENAZEER DA BATOUL?" Ya fadi muryarsa tana shacking "Ka bani amsa goumar!...... benazeer da batoul?,nadeeya da BINTOU?" Ya kuma fadi cikin yanayin matuqar rudewa,rudewar da sai data sanya kowa dake wajen zuba masa idanu. Kiran sunayen nasu da yayi sai ya zamana kamar kiransu yayi,sai gasu da gudu daya tana bin daya, benazeer ce ta qwace Sweet din nadeeya ita kuma ya biyota kan lallai sai ta bata. Sun cire duk wani kayan adon da aka saka musu dazu,kama daga abun hannu sarqa harda takalmansu,sai wani sock's me kyau da aman tace a saka musu don tasan ba lallai su iya wuni da high hill ba. Ko dankwalin kansu dukka sun yar,gashinsu kawai da yasha gyara yake matse a band ne jelar keta yawo a bayansu. "Benazeer,batoul" ya kirasu yana kallonsu da idanunsa da zuwa yanzu suka koma kamar an diga musu jini. Suna hada ido dashi suka manta da rigimar da sukeyi sai kawo sukayo kansa kowacce nason ta riga 'yar uwarta isowa. Tafukan hannayensa ya bude musu,ba bata lokaci suka shige,ya maida hannuwan nasa ya lullubesu tsakiyar qirjinsa,ya matsesu gam yana boye fuskarsa tsakanin kafadunsu,sun lullubeshi da surutu,yayin da shi kuma wani zazzafan hawaye ya qwace masa,hawayen da bazaiso kowa ya gani ba. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 60 "ka sake mata yara ka rubuta mata takardarta" aba ya fadi yana hadiye abinda yake taso masa "Bazan iya ba aba..... I can't" ya fadi da rawar murya,yayin da benazeer da batoul sukayi tsuru tsuru a jikinsa,don basusan abinda yake faruwa ba,basu shaida komai ba "Baka isa ba kuwa......ba abinda zai hana ka sakarmin diya" aban ya furta cikin hargagi "Kai hamidou,meye hake faruwa ne?" Muryar kawu ta halarcin gurin yana takowa zuwa falon bayan ya cire takalmansa. Dubansu suka maida kansu,har cikin ran aba baiso shigowar kawu a wajen ba,don yasan zaiyi wuya bai karya masa budget ba. Yanaso a barshi ne shida maina kadai,akwai lesson da yawa da yakeson ya koya masa. "Samu waje ku zauna.....kai aliyyu,ku zauna sosai" kawu ya fadi yana zama kujerar dake tsakiya. Dole kowa din ya zauna,shuru ya ratsa wajen na wasu mintuna,sai batoul da benazeer dake faman kallon fuskar maina,kaman yadda shima yake kallon nasu fuskokin,yana jin wata soyayya da qauna da qaunarsu na ratsa kowane sassa na jikinsa. Kiran sunan maina din kawu yayi,ya amsa masa kanshi a qasa. "Abinda ka aikatama matarka baikai girman kuskuren barinka gida da kuma rashin waiwayosu ba" ya fada shima yana nuna bacin ranshi sosai "Akwai dalili kawu.....ba haka kawai bane ba" ya fadi muryarsa a karye. "Wanne dalili indai har kana raye kuma cikin hankalinka?......" Fada sosai ya tsinke dayi masa,har sai daya fidda dukkan abinda ke zuciyarsa dama wanda ya fahimci yana narke cikin zuciyar aba din. Tsahon wasu mintuna ya dauka,har ya gama ba wanda yace komai a cikinsu,sai daya kammala sannan ya maida dubansa ga aba "Hamidou,abinda ya faru ya riga ya faru,tunda har Allah ya dawo dashi lafiya,fatan kawai da za'a yi shine, ubangiji ya sanya hakan yaci gaba da zama silar alkhairi wa kowa....." "Nifa dama kawu ba abinda yayimin,d'a dama idan ka haifeshi ai ka gama naka.......abu daya nakeso yanzu ya sakarmin diyata" ajiyar zuciya kawu ya fidda,ya sani shima aba din ba baya bane wajen taurin kai da kafiya,yasan kuma tunda ya kafe din saukeshi daga abinda ya niyyata din sai babban abu "Ta yaya zaka ce haka?,bayan yace shi bazai iya sakinta ba?" "Idan bazai iya sakinta ba ai kawu ita ba sonshi takeyi ba" ido maina ya lumshe yana ganin qiyayyarsa quru quru cikin idanun aba,wanne irin abune haka?,duk yadda yakai ga son sultana baya jin zai sota kamar shi din,gudan jininsa,kuma dansa na fari da ya fara mallaka a duniya "Waye ya gaya maka?......ke sultana......karki duba girman laifin mijinki,kada kuma ki duba mu mu dukkanmu da muke a nan wajen,aliyyu mijinki ne,kuma uban yaranki da a yanzun baku da kamarsa,kina son mijinki ko kuwa a'ah?" Duk wanda yake wajen yasan cewa kawu yayi tambayar ganganci ne saboda bashi da masaniyar yadda sultana ta dauki maina.......a wajen maina din kuwa,ji yayi kamar ya maida tambayar data fita a bakin kawun......don ya sani abune me wuya yaji abinda yake da muradin ji din daga wajenta "Bana sonsa kawu......na rantse da Allah bana sonsa" ta furta muryarta tana rawa,fuskarsa na tsakanin dankwalin data warwareshi tana tsane siraran hawayen dake sauko mata. Saukar wani abu me tsini yaji tsakiyar zuciyarsa kamar saukar mashi,kalaman nata yaji sun matuqar yi masa girma a zuci da gangar jiki gaba daya. Kalmar QIYAYYA ba qaramar kalma bace dake raunatar da mutum gaba daya, qiyayyar ma kuma da aka sanar da ita cikin bainar jama'a,a gaban idanuwan mutane,ba mutum daya ba biyu ba,iyayensa da yaran cikinsa,ya ilahi wannan wanne irin qiyayya ne?,bazaici darajar koda mutum daya a wajen ba!? . "Shikenan,duk da kince baki sonsa amma hakan bazai sanya ayi gaggawar cewa ya sakeki ba sultana,ki sake nazari,kowace mace na iya fuskantar irin wannan bacin ran,amma bayan zukata sunyi sanyi ana iya fahimtar juna" "Sai yaushe zuciyata zatayi sanyi?,sai yaushe zan fahimci maina?,bana jin hakan zata kasance har abada,kullum tsanarsa ninkuwa takeyi cikin raina,kullum burina na bude idanuna naga nayi nesa da rayuwarsa shima yayi nesa da tawa,kullum neman hanyar da zata qara nisantani dashi nakeyi" abinda ta fadi kenan cikin zuciyarta tana dunqulewa waje daya sabon kuka yana kubce mata "Kawu,inda za'a dubi rayuwarta ayi mata adalci shine......ya bata takardarta tukunna,duk wani fahimtar juna da ake buqata a sameshi daga baya" "Yaaya..... inaga ayi haquri a gwada maganar kawu tukunna" oncle umar ya fadi yana duban aba cikin girmamawa "A'ah,ku rabu dashi,ai dan kanshi ne,sai yayi yadda yakeso kaman yadda zuciyarsa takeso" muryar bibi data shigo afujajan ta fada,wadda almu ne ya isketa cikin gida ya shaida mata saqon oncle umar,kuma tazo akan gaba. Gurin zama suke qoqarin bata amma bata bi ta kansu ba,sai data dangane da kujerar dake gaban aba ta zame ta zauna a qasa a gabansa tana kallonsa "Kafin ka kashe wannan auren inason ka fara kasheni ne hamidou kaman yadda na taba gaya maka" ta furta kanta tsaye da qarfin gwiwarsa. "Subhanallahi" kawu dasu oncle umar suka fadi,yayin da aba ya zame qasa kusa da ita babu shiri ya zauna yana dubanta a matuqar ladabce "Bibi.....me yasa kk irin wannan maganar?" Kafin ta sake cewa komai oncle umar ya dubesu "Goumar......ka dauki benazeer,maina dauki batoul ku wuce ciki" tuni goumar ya gaji da ganin wannan tashin hankalin dama,don haka a gaggauce ya miqe ya dauki benazeer,ya miqawa batoul hannu,ga mamakinsa saita maqale kafada tana sake dafe maina tana kallon fuskarshi. Wani siririn murmushi ne ya subuce masa duk da yanayin da zuciyarsa take ciki,ya miqe a nutse ya dagata bisa kafadarsa,sai benazeer itama ta zame daga hannun goumar tana jin kishin bai dauketa ba,ya duqa a tausashe ya azata saman daya kafadar tasa ba tare da yaji nauyinsu ba sam sam suka fara takawa suna barin dakin oncle umar da issoufou da kawu suka bisu da kallo kowa tausayin yadda qaddara ta samar dasu tana ratsashi "To eh mana...... tunda muke da ubanku har yabar duniya ban taba yaji ba bare akai ga batun saki,hakanan tunda na kafa zuri'ata ba'a taba sakin kowa ba a cikinta......sai yanzu za'a fara daga kan maina da sultana?,su zasu kafa baqin tarihi cikin zuri'ata?" Maganar saita zafafi sultana dake zaune a tsakanin kujeru,wato a nan bibi tana nufin tayita dakon aurensa?,ko tana nufin taci gaba da zama dashi?, abinda har abada bata jin zata iya koda a mafarki kuwa,a taqaice dai kaman ma goyon bayan mainan takeyi?,ta manta dukkan wasu azabu da wahalhalu da tasha?,ta manta da qyar ta samu rayuwarta ta daidaita?,da qyar ta tsira da ranta?,ranta ya sake baci sai ta miqe tsam tana barin wajen tana raba hanya. A nutse yake takawa dauke da yaran,kunnuwansa sunata jiye masa surutun da suke zubawa su da goumar,alamun sabo da shaquwa me qarfi na nunawa a tsakaninsu. Abubuwan da suka wanzu a yanzun ne kawai ke kai kawo a zuciyarsa,tunda suka fito daga dakin ya kasa furta koda kalma guda daya,sai kunnuwansa dake tsintar surutan yaran. Haka kawai yaji gidan ya quntace masa,yana buqatar nutsuwa da kuma kadaicewa,yanason ya kalli yaransa son ranshi,yanason ya sake sosai da yaransa wanda yasan muddin cikin gidanne bazai yiwu ba,da wannan tunanin sai kawai ya wuce parking lot na gidan,kafin su qarasa kuwa sunsha kallo shi da yaran,sunyi wani kyau a jikinsa,sai a sannan kamanni kadan kadan suke bayyana tsakaninshi dasu da suka jera dashi. BMW dinsa ya bude,ya kuma bude gidan baya ya saukesu suka shige suna murna,kamar wani sakarai yayi tsaye yana kallonsu har suka gama shiga ya rufe musu qofar,ya koma mazaunin driver ya shiga,daidai sanda goumar ya bude seat din kusa dashi ya shige shima. "Me yasa kayimin qarya?,me yasa ka boyemin kyautar da Allah yayimin?" Ya jefawa goumar tambayar ba tare daya kalleshi ba yana qoqarin tayar da motar. Kallonsa goumar yayi sannan ya maida dubansa gaban motar "Bai kamata zuciyarta ita kadai ta wahala ba,bai kamata ace ita daya tasha wannan azabar ba......taci wahalar da babu wanda ya zatar mata rayuwa,duk wani information da nake baka kana jina ne kawai,amma bahaushe yace gani ya kori ji......banda wasu dalilai.......banda kuma wasu hujjoji tabbas bazan bari ka dawo ka sameta da aurenka ba...... tabbas da na......" "Goumarrrr!!!" Ya kira sunansa da wani irin sauti me qarfi. Waiwayowa goumar yayi yana dubansa,idanun nan da suka sauya launi tun dazun yanzun sunfi haka jirkicewa, murmushi can qasan zuciyarsa ya qwace masa,yana sane ya gaya masa hakan, yanason ya motsa masa zuciyarsa da kyau a kanta,yana kuma son shima ya dandani koda kadan cikin quncin da zuciyarta ta wanzu akai. Duk yadda yake takurata yake tsokanarta......amma yana jin babu dadi da yanayin da haidar din ya sanyata ciki "Karkayi tunanin don kana dan uwana..... kuma ka yimin wata rana hakan ya baka daman shiga gonar da ba taka ba" yayi maganar fuskarsa nayin jaaa. Qaramin murmushi goumar ya sauke,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya zura qafafunsa waje sannan ya waiwayo yana kallonsa ""Ban fada da zummar cin zarafi ba,Allah ya baka haquri" daga haka ya fita a motar salin alin ya rufe masa. Kaman jiran fitar nasa yakeyi ya bawa motar wuta,ya juya kanta da zafi zafi ya nufi gate yana sakewa security horn,cikin iya aiki da cika umarni suka bude masa gate din ya fice da mugun gudu har yana cin taya. Sanda ya saitu a saman titin batoul ta saqalo hannunta ta wuyansa,abinda ya sanyashi sauke wata ajiyar zuciya me sanyi "Uncle haidar.....me ya sanyaka hawaye dazun kai da auty?" Tambayar tazo masa a bazata,sai ya dinga juya amsar da zai bata din. Baisan yadda zai gaya mata yadda zaga fahimta ba,hakanan kuma bayason ya mata qarya "Ko aba ya dokeku ne?,kuma shi ai baya duka,bai taba dukanmu ba" batoul din ta sake fadi sanda benazeer ta zuro hannu tana shafa gashin habarsa dake da santsi cika da kuma baqi sidik. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 61 Kai ya girgiza qaramin murmushi yana subuce masa,ko da basu fada ba,kallo daya zaka yi musu kasan sun samu gata gami da tsantsar kulawa me tarin yawa "Aba be dokeni ba,autynku nakeso......ita kuma tace bata sona" ido suka hada yaran suna hangame baki,qwaqwalwarsu bata gama fahimtar ainihin ma'anar maganar ba,amma kuma sunsan meye so a suna bawai a ma'ana ba "Uncle babu kyau,Allah ya hana acewa mutum ba'a sonshi ko?" Benazeer ta furta har tana leqowa fuskarsa. Hannu daya ya sanya ya shafa sumarta yana sake sakin wani murmushin,har cikin zuciyarsa yana jin suna sake zama jinin dake harbawa a zuciyar tasa suna narkewa da kyau "Ba kyau beenaz......zaki gaya mata ta daina fada?" "Eh Uncle" "Kefa batoul?" "Eh nima haka uncle" "Am not Uncle.....am dad" ya furta a hankali yana duban yanayin fuskokinsu ta madubin gaban motar. Sak yaga sunyi suna sake kallon junansu,sai suka kasa fadin komai saboda kwanyarsu kamar tana mamakin maganarsa "Kun taba ganin daddynku?" Ya sake jefa musu tambayar. A tare suka hada baki wajen cewa "Eh...." Batoul ta daga yatsanta daya tana cewa "Amma fa sau daya" "Nayi kama dashi?" Ya fadi yana nuna kanshi. Tsit suka sakeyi suna duban fuskar nashi ta cikin mudubi su dukka biyun,kowanne kwanyarsa na dawo masa da surar abban nasu da goumar ya taba nuna musu shi har sau biyu "Kuna kama sosai uncle....." Benazeer ta fadi "Kaman kai ma" batoul ta sake fada tana Dora hannun a qirjinsa tana qaramar dariya. Shuru yayi shima yana murmushi,zuciyarsa na masa sanyi,komai daya sameshi a baya a yanzun sai yaji kaman bai sameshi ba,komai sai yaji yana sauka masa a zuciya,wani farinciki na ratsashi da kadan da kadan. Kalaman bibi suka dawo masa,ya tabbatar da izinin Allah komai ya kusa zuwa qarshe,kuma tunda bibi na goyon bayan barin igiyar aurensa.......yana da yaqinin shike da nasara...... matsalar aba kuma zata zo masa da sauqi tunda dai da bibi a gefansa,rigima da kuma daru ne yasan zaya shashi "Sultana fa?" Zuciyarsa da tun dazun take motsawa ta jefa masa tambayar dai dai sanda yake karya kan motar zuwa titin dake dauke da hotels da kuma guest in. Ya gama karantar lamarin sultana,yana da kuma plan guda uku zuwa hudu dukka a kanta,yana kuma kyautata zaton bazai hau dukkan matakan ya sauka babu nasara ba. A yanzu yanaso yayi calling attention dinta ne har ta tsaya dashi,bayan ta tsaya din maganar fatar baki ta hadasu,wannan shine matakin farko da yake da buqata,saidai kuma ya fuskanci shine abu mafi wahala a dukka tafiyar. Tunda yazo qasar ko kalmar A bata taba hadasu ba,ta yaya zai samu ya tsaidata suyi magana shi da ita?. Kai tsaye ya gama zagayen titin,ya kuma zaba musu hotel me kyau. Bayan sun bashi key bai isa dakin ba,sai daya daukesu suka tafi yawon siyan kayan maqulashe. Ci wannan ci wancan,duk abunda suka nuna sona so sai ya siya musu,haka suka dawo masaukinsu da tsaraba fal,suka yada zango a dakinsu. Da kansa ya musu wanka,ya kuma shiryasu cikin wasu baby pink din pyjamas masu ratsin maroon sannan shima ya shiga yayi nasa wankan,daya fito cikin irin nasu pyjamas din ya shirya,ya feshe jikinsa da tattausan turarensa ya kuma gyara lallausar sumarsa ya maidata baya,sai ya sanya slipper din da ya siyo,ya kunna musu tv yace zaije yayi sallah,bazai jima ba kada suje ko ina. Su din ba baqin abun bane already sun saba,don haka har yaje ya dawo suna zaune abinsu. Dukka kayan ciye ciyen ya sake baje musu sukaci iya cinsu suka bar na bari,sai ya tattara komai ya dawo ya zauna a tsakiyarsu. "Kuzo kuga daddynku" ya fadi yana buda wata folder daya adana dukkan tsaffin hotunansu,wasu da yan gidansu wasu da aba ama,wani shi da sultana sanda suna dasawa qwarai. Kallon hotunan sukeyi suna kuma duban fuskarsa,kaman yadda duk inda akazo wajen da take a ciki sai ya tambayesu waye wannan?sai suce "Kaine" "Shine daddynmu" batoul take yawan nanatawa sai ya daga musu kai yana murmushi. Sai da suka gama kalla tsaf sannan yace "Bari daddynku ya baku labarin mommynku" kwance sukayi a jikinsa fuskokinsu cike da farinciki,sun kanainayeshi gaba daya suna maimaita "Uncle haidar......kaine daddynmu?" Da alama abun yana bugar da tunaninsu yana kuma basu mamaki "Baru na kira muku uncle goumar a tambayeshi" "Yes" benazeer ta fada tana miqewa ta zauna sosai a gabansa gami da tanqwashe qafa,ta kuma tsireshi da idanun nan nata. Sak abun sai ya masa kama da yadda sultana ke masa,ya saki siririn murmushi ya soma laluben number goumar. Sau uku tana sanya hijab dinta tana zareshi kana sai ta koma ta zauna a wajen data tashi. Ta sake duba agogo,still dai dare yana dada yi,ba motsin benazeer ba na batoul,ta kuma lura tunda ya fita dasu daga falon aba ne. Taga goumar har kusan sau biyu,bata ganshi da yaran ba,sannan bataji kowa yana maganar yaran ba. Idanunta ta lumshe zuciyarta tana bugawa,tun dazun abu daya zuciyarta ke raya mata,kada fa ya gudar mata da yara?,kada fa a sake nemansa a rasa da yaran?,tunda dai shi din mugu ne dama,mugunta bai dauketa a bakin komai ba. Zumbur ta sake miqewa a karo na hudu zuciyarta na tsunkularta ta maida hijabinta,saidai kuma tana takawa zuwa waje tana tunanin waye zata kaima qara ko ta tuhuma?. Tana tsananin kunyar ama ba zata iya tunkararta ba,aba kuwa batason sake assasa qiyayyar da yake nunawa diyan cikinsa qarara a kanta,bibi kuwa ta fara sallama lamarin bibi,duk da bata fito kai tsaye ta nuna tana yi da maina ba,amma kuma ta fuskanci ta karkata gareshi "Goumar" zuciyarta ta gaya mata, tabbas shi daya ne zaisan inda suke,tunda zuwa yanzu ta fahimci tun asali munafukinsa ne,kamar akwai wata boyayyar alaqa tsakaninsu. Gidan yayi shuru saboda raguwar 'yan biki,don tun magariba aka kai amare aka dawo,amaren da bata samu daman zuwa kaisu ba. A nutse take taka farfajiyar gidan,zuciyarta na mata fargabar amsar da zataji daga goumar. Har ta nufi hanyar dakunansu sai ta fasa,ta dawo da baya tana nufar bakin gate din farko na gidan. A bakin motarsa ta sameshi a tsaye yana amsa waya da qaramar wayarshi,saita nufeshi kai tsaye tana saita nutsuwarta. Sanda yaji ana nufoshi waigawa yayi kadan,sai yayi qoqarin yin sallama da wanda ke kan layin dab da sanda ta iso gareshi. "Ina yara na?" Ta tambayeshi tana shan mur idanunta a kansa. Qaramar dariya ce ta qwace masa,ya gyara tsaiwarsa yana kallonta,kamar ya tsokaneta yace daman kina sonsu har haka?,sai kuma ya fasa kada qilu ta jawo bau,ya hada nutsuwarsa da kyau sannan yace "Bansan ina suke ba,amma dai sunbi mahaifinsu" haushi kalmar mahaifin ta bata har ta gaza jurewa ta jefa masa wata tambayar "Dama suna da wani mahaifi ne?" Shigowar kiran wayar goumar sai ya zamana kamar amsar tambayarta,sai ya hadiye amsar da yayi shirin bata ya zaro wayar yana dubawa. Murmushi ne ya qwace masa,abun yazo masa a dai dai,don haka sai ya miqawa sultana wayar kai tsaye yana duban qwayar idanunta "Ga mahifin nasu,saiki gaya masa ya dawo miki dasu ko?" "Kana tunanin bazan iya bane?,ko kana tunanin jiya yau ce?" Ta furta da zafi zafinta tana fusgar wayar daga hannun goumar cikin fushi. Dagawa tayi ta kuma sanya wayar a kunnenta. A nutse yayi cikakkiyar sallama "Assalamualaikum" ya ajjiye sallamar a hankali,saidai kuma a maimakon yaji muryar goumar sai wannan sautin......sautinnan da bai taba gushewa daga kunnuwa da memory dinsa ba,sautin nan dake tsaye tsakanin zuciyarsa da jinin jikinsa,sautin nan da yayi matuqar kewa.......yake kuma son yaji koda sau daya tak ne ya mamayi qirjinsa da kunnuwansa "Ka dawomin da 'ya'yana,kada kuma ka yarda komai na cutarwa ya samesu,don baka da hurumin tabamin yarana" idonsa ya lumshe wani abu yana kwarara tsakiyar zuciyarsa,ya tabbatar idan bai tsokaneta ba,bai kuma tunzurata ba maganarta dashi ta qare,don haka yace "Wadannan kam sun zama nawa,saidai ki haifi wasu" ji tayi kaman ya doka mata guduma saman kai,idanunta suka rufe,tana son yayyaba masa maganganu amma kuma idanun goumar na bisa kanta,batason kuma ta sauka da yawa daga control dinta "Wannan duka cikin matsalarka ce,nidai na gaya maka ka dawomin da 'ya'yana.......mtsewwe" ta rufe da jan tsaki kaman zata tsinke harshenta sannan ta zare wayar a kunnenta tana miqawa goumar. Lips dinsa na qasa ya cije sosai yana rintse idanunsa saboda yadda sautin tsakin ya rasashi matuqa. Tsaki?,ta manta yana cikin abubuwa biyun daya tsana?,tsaki da gunaguni?,har cikin ransa yaji saukarsa matuqa,sai ya gaza bude idanunsa har zuwa sanda yaji muryar goumar ta maye gurbin tsakin nata "Yaa haidar" ya fadi zuciyarsa ba dadi na tsakin da tayi masa "Goumar" ya kirashi kai tsaye "Kay...." "Shshshsh.......wannan ba huruminka bane,kayi kaman bakaji ba,zanyi handling abun...... BINTOU da NADEEYA keson sanin waye daddynsu?" Ya masa tambayar yana maida wayar free. Murmushi mai sauti ya fito daga bakin goumar har sautin nasa yana bayyana "Kaine daddynsu....... wanda na taba nuna musu uncle haidar shine daddy maina daddy aliyyu,ya dawo daga tafiyar da yayi,kuma dama ya musu alqawarin zai dawo din" kamar shiri kamar hadin bala'i dukkansu suka saki qaramin ihu suna ruqunqumeshi. Kashe wayar yayi yana murmushi ya hadasu dukka shima ya rungumesu. A nan saman cinyarsa suka kwanta,ya shiga basu labarin quruciyarsa da na sultana saidai kuma iya abubuwa masu kyau da zasu basu dariya ko suyi musu dadi yake gaya musu. Sannu sannu dukkansu bacci ya daukesu,ya miqe ya kwashesu gaba daya ya maidasu saman gado ya kwantar,sai ya kasa tashi,ya sanyasu a gaba yana kallonsu,hannunsa cikin tafukan hannayensu. Tunda Allah ya jarabceshi da soyayyar yaran yake tambayar kansa why?,me yasa yake mutuwar sonsu haka?, duk tarin twins din dake Instagram me yasa sai su?,jikinsa yasha bashi ba'a banza ba, zuciyarsa kuma ta taba raya masa sau daya TABBAS YANA DA DANGANTA DASU TA KUSA KOTA NESA,saidai kuma ya qaryata hakan, din yayi lalubensa kaf baiga ta inda zasu hada dangantaka ba. Murmushi ya sake kufce masa,ashe ubangijinsa ya cika masa muradinsa ba tare daya sani ba?,yara matan da yasha alwashi ya kuma jima yana yiwa ama alqawarin kyautar mata dasu ashe Allah ya jima da cika masa burinsa?,ya sani koda ba'a gaya masa ba sunsha gata da kalar kulawar da ba kowanne yaro ke samu ba. Tsakinta na dazu ya sake dawo masa fes a kunnensa,sake cije lips din nasa yayi ya girgiza kansa kadan,bata canza bane ko da saura?, Ya jefawa kansa tambayar. Lallai zai dauki komai amma banda raini, wadannan tsakin akwai buqatar nuna mata bai kamaci tayi masa shi ba,tabbas......... *_maina sarkin son girma😂,me karatu kada fa ya qara b'aro wani aikin muzo mu hadu da wasu twins din?,ba ruwan HUGUMA dai_* *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 62 Cikin jikinsa yaja yaransa bayan ya gama shafa'i da wuturi,ya rungumesu tsam suna jin dumin juna yana sauke ajiyar zuciya. Sai yanzu yake sake tabbatarwa lallai jininsa ne,lallai wani bangare ne na jikinsa. Ni'imtaccen bacci yayi wanda ya jima baiyi irinsa ba cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,haka yaran suma,babu wadda ta motsa a cikinsu haka suka qarar da daren. Juyi kawai ta dinga yi tana tuna yaran,sam bacci ua qauracewa idanunta,tana tsoron kada ya aiwatar sa abinda ya fada din,don ta gama sallamawa shegen kaifin maganarsa guda daya kafiya da taurin kansa. Batasan haka take qaunar yaran har cikin jininta, batasan haka zuciyarta ke mutuwar qaunar yaran nata ba,bata taba kuma kawowa haka take jinsu a ranta ba sai a wannan daren,ta jima tana juyi kafin daga bisani baccin yayi awon gaba da ita. ********Tunda sukayi sallar asuba washegari basu koma ba,shi dasu zaman hira sukayi,duk wata tambaya idan sukayi masa haka zai amsa musu,hakanan shima ya sakasu gaba da tambayoyi. A nan din ya samu information sosai akan sultana,wasu abubuwan da bai sansu ba sakamakon yankewar sadarwa tsakaninsa da goumar dukka yaji a bakinsu benazeer. Shuru yayi yana sauke boyayyar ajiyar zuciya,tausayinta yana sake illata masa zuciya. Yana da buri sosai a kanta,burin da yasha banban da burinsa na baya,amma kuma dukka abinda zai gudanar dole saida hadin kanta. Yana tsaka da wannan tunanin wayarsa ta dauki tsuwwa,batoul dake game a ciki ta miqo masa a nutse yasa hannu ya karba yana mata murmushi. Daddy ne,alhj Bello Muhammad mahaifin sardauna......mahaifin kuma laila..... Mutumin da ya zame masa bango jigo kuma makwafin mahaifi. Tashi yayi ya zauna sosai yana jin wani iri,bai kyauta ba kwata kwata,duk kansa ya shiga kawuna,sam baiyi kiran daddy din ba tsahon kwanaki,abinda kuma bai saba ba. Yana qoqarin gaidashi shi kuma yana qoqarin tambayar lafiyarsa "Lafiya alhamdulillah daddy" "To ma sha Allah......'yar rigimarka ce ta sakani a gaba,wai na binciki lafiya kake?,ka zama wani mugun busy kwana biyu" sumarsa ya yamutsa,laila tana daureshi da jijiyar jikinsa,duk sanda ta hada lamarinsu da daddy din a ciki sai ya zamana kamar ta masa dabibayi ne. Ko dazun bayan asubah da ya tashi yaga saqonta,yayi mata reply ne ya zame masa jidali har kawo yanzu. "Lafiya alhamdulillah nazo wajen family nane.....ina da buqatar lokaci ne daddy,akwai matsaloli da nakeson gyarawa" ajiyar zuciya ya saki yana jin farinciki yana ratsashi. Tunda suke da maina din tsahon shekaru uku bai taba zancan gida ba,hakanan shima bai taba tilastashi game da komai nasa ba,amma a matsayinsa na uba kuma mahaifi ko yaushe yana da wannan tunanin a ransa,dole kuwa a yanzu yayi farinciki "Ma sha Allah, alhamdulillah,to Allah ya yaye damuwa ya shiga lamarin" "Ameen ya hayyu ya qayyumu daddy na gode sosai " ya fadi har qasan ransa yana jin kimarsa tana sake qaruwa. Mutum ne me tsananin dattako,kamili na gaske wanda yasan abinda ya kamata "Gashi karbi" daddy ya fada yana miqawa laila wayar. A dan kunyace ta karba sannan ta miqe tana barin wajen,ta tabbatar yau din zata samu kulawa data d'ara wadda ta saba samu. "Yaa maina.......barka da warhaka" ta furta tana karyar da murya "Barka kadai laila......kina lafiya?" "Uhmmm......to, lafiya alhamdulillah,amma ba lafiya sosai ba" "Me yake faruwa?" Ya tambayeta cikin son nuna kulawa "I missed you so much yaa haidar,and it's killing me wallahi" tayi maganar tana fita daga tsakiyar zuciyarta da gasken gaske. Ido ya lumshe sannan ya budesu,bayason yadda kullum kwanan duniya take sake zurmawa cikin soyayyarsa,baisan ta yaya akayi ta fara sonshi ba,baisan kuma yaushe ba,tabbas ba shakka da bazai barta ta fara ba. Har yanzu zuciyarsa jaririya ce akan soyayya,yana jin kamar rainonta yake, zuciyarsa batayi fadi da girman amsar kalolin soyayya ba "Ina gida as i said......ina wajen family na......ga 'ya'yana su gaisheki" ya furta da zummar cimma manufar dake qasan ranshi "Yayanka?,when...... yaushe ka haihu?" Murmushi me sauti ya fidda "It's a long story........ batoul ga aunty laila" ya fadi yana hadasu da wayar yayin da ya koma yayi relaxing jikin kujera yana kallonsu. A qalla sun kusa mintuna biyu kafin su miqa masa Wayar,ya karba ya saka a kunnensa "Yayanka ko yaran cousins naka ko yaran sisters dinka?" "My biological daughters" d'if tayi na wasu sakanni kafin ta furzar d numfashi "Okay...... okay,it's ok,see you later?,zaka kirani?,ko ni zan kira?" Ta tambayeshi tana karyar d wuya,maganarsa ta yanzu kuma tana dukan zuciyarta "Idan kinji shuru zaki iya kiran nawa na bada dama" qaramin murmushi ta saki "Thanks,bye.....ka kula da kanka please" "Na gode" ya amsa mata a taqaice,sai ya zame wayar yana kallonta. Yayi tsammanin daya gaya mata wannan zata rude ne,ya dauka zata katse wayar,ya kira kuma taqi dagawa,ya zaci zatayi fushi,sai yaga dukka babu wannan a tattare da ita. Har rana yayi kawai yana zaune cikinsu suna sabgoginsu,yayi musu doki,ya dora wani a bayansa wani a qafafunsa,suyi wasan buya dukka. Abinda ya sake haifar da wani irin shaquwa tsakaninsu qasa da awa ashirin da hudu. Sukayi wani mugun sakewa da shi,qauna da soyayyar nan dake tsakanin mahaifi da 'ya'yansa ta sake bubbuga sosai,duk wata soyayya ta motsa qwarai. La'asar liqis suka baro hotel din,ba kuma gida ya nufa dasu kai tsaye ba,yayi kiran hadiminsa ya bashi jan motar suka wuce wani qaton mall dake garin marad'i. Siyayya ya dinga yi musu harda ta hauka,sosai yake jin kansa a matsayin mahaifi,yake kuma son ya soma taka wannan rawar,yake muradin ya amsa sunansa na mahaifi din. Sanda yake musu 'yan tambayoyi don sanin abubuwan da ba lallai ya jisu daga bakin ama ko wani a gidan ba.....sai zuciyarsa dukka ta raunata,ya fahimci tsantsar gatan da ama ta nuna musu,kulawa da sadaukarwar da aba ya musu. Ya sani koshi ne a wajen ba lallai ya musu irin wannan gatan da suke samu, zuciyarsa sai ta sake rauni,qauna da soyayyar mahaifiyarsa ta sake cika masa zuciya. Ita din ta daban ce......mahaifiya soyayyart daban ce kamar yadda take ta daban. Yawan siyayyar motarsu tayi kadan ba zata iya cinyewa badon haka suka zuba abinda zasu iya dauka,sauran kuma ya bada location dinsa sukace zai taras da kayansa har qofar gida in sha Allah. Daga nan ya sake biyewa dasu ya cikasu da kayan maqulashe,hakanan ya tsinci kansa da yiwa driver umarni suka dauki hanyar wajen tsohon me namansu da bibi da ama ke so sosai,bama su kadai ba harda aba din. Suna dosar wajen komai yana dawo masa sabo,wajen da yayi silar wanzuwar komai cikin rayuwarsu,muhalli da daga nan aka fara qulla zaren saqar K'ADDARARsu,daga nan komai ya fara. Daga nesa kadan ya sanya yayi parking,yace su benazeer su zauna cikin motar,sai suka maqale wuya "Daddy ba zaka dade ba?" Kai ya jinjina yana murmushi "In sha Allah" ya fadi yana shafa sumarsu,shi kansa yana jin inda zaiyiwu ko na second daya bazaiyi nesa dasu ba,ya janye jikinsa driver ya maida murfin ya rufe. Lokacin da yayi sallama yana kan hadar hadar killace naman da aka samu gasawa,bayan dadin da namansu ke dashi suna da matuqar tsafta qwarai,wannan ya sanya maina din duk iyayinsa da zabe zaben abinci da yake dashi bai taba challenging namansu ba. Idanu ya zuba masa sanda yake amsa sallamar,kamannin maina din suna masa yawo a ido,saidai wannan din ba yaro maina bane yake gani,cikakken saurayi da Hankali ya game jikinsa,me cikar zati halitta da wani uban kwarjini dake yawo saman fuskarsa "Ka ganeni?" Ya tambayeshi yana qaramin murmushi "Eh to.....magana ta domin Allah naso na shaidaka,amma kuma ina tantama idan kaine din,kamar dai maina ko?,dan gidan alhj hamidou mayak'i?" Kai ya jinjina yana murmushi. Murna ta cikashi ya ajjiye kayan hannusa yana cewa "Kai,Allahu akhbar....... ashe rai kanga rai,shuru babu kai ba dattijuwar arziqi?" Mamaki yadan kamashi,kenan bibi ma tabar aikowa a siya mata kenan tun bayan da yabar gidan?. Gaya masa yadda yakeso ayi masa yayi yace ya aiko masa dashi mota yanzu zai jirashi. Jikin yahuza na rawa ya soma aiwatarwa,don ya tabbatar yau qila dukka kudin namansa ne zasu fito daga jikin maina din. Kamar yadda ya zata din kuwa,don sai waiwayowa yayi kawai yaga ya ajjiye masa bandir daya da CFA,wanda yayi imanin sun ninka kudin namansa ma,don haka ya zage shima ya cikashi da naman da yafi yawan wanda ya buqata,yana sake jinjina kyauta irin ta jinin 'yan gidan da kirkinsu. Yinin ranar duka cikin rashin sukuni ta yishi,ta kasa zaune ta kasa tsaye tsakanin sashen bibi dana ama,damuwa ce sosai cikin rai da fuskarta,wanda sai kana da mugun nazari zaka kula da haka. Ta dauka da sassafe aba ama ko bibi zasu tasashi gaba da sababi ya kawo mata yaranta,ko kuma shidin ya kawosun amma sai taga ba wanda ma yayi batun yaran. Sanda taga har azahar ta shigo tana shirin ficewa damuwarsa da fargabarta sai ya qaru,idan ma barin qasar ne tasan zuwa yanzu sun jima da ficewa. Qaruwar damuwar ya ankarar da ama,tana sane,tasan ya kwashesu tun jiyan bai kuma dawo dasu ba,ta fahimci kuma sultana din a dame take,tayi shuru ne saboda ko yaya dai a bashi chance shi da su da zasusan shine mahaifinsu,susan suna da mahaifi,ya kuma yi duk hirar da yakeson yayi dasu din. Idan shi me laifi ne su ai basuyi laifin komai ba,basusan kuma komai ba,bai kamata a lullube musu ubansu ba, shi kadai yayi laifi,shi kadai zai amshi hukunci,abinda ke tsakaninsa da mommynsu kuma ba hurumin yaran bane bare a tsundumasu a ciki basuji ba basu gani ba,bayan suma kawosu akayi cikin rigimar da basusan da zamanta ba. Yamma lis ta sameta a kitchen tana qoqarin diban abincin rana da bataci ba,don ko na safenma dai tsakurarsa tayi. A iya safen zuwa yanzun aman ta fahimci itama me qulafucin yara ne,wani dalili ne kawai dama yake sawa take nuna halin ko in kula dasu,amma tana qididdige da dukka motsinsu da takunsu. "Lafiya kike yau kuwa sultana?,ko bakya jin dadi?" Kai ta girgiza,sai taji zuciyarta tadan tsinke,aman bata san abinda ke damunta ba kenan "Lafiya lau nake ama,kawai kasala nakeji" "To Allah ya qara lafiya,Alla ya rufa asiri" ta amsata tana ajjiye plate din data shigo dasu ta gama abinda zatayi sultana din na satar kallonta qasa qasa har ta juya ta fice. Ajiyar zuciya ta sauke tana ajjiye abincin data debo din,ta rungume hannayenta ranta na sake baci,magariba na dosowa ya kwashe mata yara tun jiya har yanzu ba duriyarsu?, bacin ran ya sanyata jin qwalla ta cika mata ido,sai tayi qarfin halin son maidasu amma duk da haka sai da suka zubo,ta daukesu tana yiwa kanta fadan "Ashe har kwanan gobe shike cin nasara a kanki tunda baki daina masa kuka ba,bai daina saka hawayenki zuba ba" wannan maganar ta sanya dole ta jawo jarumta ta azama zuciyarta,ta zuba abinci me yawa kaman da gaske zata iya cinyewa sannan ta juya ta fice. Ana kiran magariba suna isa qofar gidan,kaman ko yaushe ya sallami driver din ya karbi tuqin motar ya nufo bakin gate din da ita. Horn daya hudu ya qaraso,yaja da baya cikin girmamawa ya bude masa ya shige da motar. Parking lot na gidan gaba daya cike da motocin 'yan gidan,alamu dake gwada kusan kowa yana gida kenan. Ya tsaida tasa motar ya juyo yana kallonsu benazeer "Zaku shiga ciki,kuje wajen ama da bibi kuce dukkansu ina gaidasu, benazeer ki bawa ama wannan, batoul ke kuma bibi,zanyi sallar magariba zan shigo daga nan" "Kada ka dade daddy" batoul ta fadi a raunane. Murmushi ya saki,tausayinta yaji ya ratsashi, yarinyar da alama tana da tsananin qulafuci akan abinda takeso,kamar dai yadda yake,yana fata kada Allah ya bawa mamansu galaba a kanshi,zayaso su rayu tare cikin aminci "Kada ki damu B na,magarib da isha'i zanyi,zanzo muci abinci tare a wajen ama ko bibi" dan qaramin ihun murna suka saki, murmushi ya kubce masa,sai ya sauka ya bude musu qofar motar suka fice sukayi cikin gidan. Yana shirin kulle motar yaji maganarsa a bayansa, goumar ne da alama shima masallacin zashi,ya qaraso yana dubansa cikin bashi girma kuma yace "Barka da yamma" yayi gaisuwar yana karantarsa. Daga jiya zuwa yau daya dauki yaran kadai walwalarsa ta qaru,kai idan ma idanunsa sun gani da kyau nutsuwarsa ma ta ninka ta jiyan "Barka kadai malam oumar me qarya" ya qarasa fada yana dagowa daga rufe motar da yakeyi. Sunan da ya bashin ya sanyashi bushewa da dariya harda dan ranqwafawa,wannan ya bawa maina daman buga masa duka a tsakiyar bayansa, goumar ya gantsare yana jin zafi yana ratsashi. Tun ba yau ba sunsan hannun yaa maina bashi da dadi,shi yasa ba kasafai suka fiya son yi masa laifi ba "Bayana yaa maina" "Eh,ai bansan me zanyi maka na huce ba,ashe kaima da nake ganinka me imani ba imanin gareka ba,twins fa?,ashe nawa ne?,nayita kwana ina tashi da begensu?,kacemin yaro guda ta haifamin,ashe jaruma ce ita din" ba shiri goumar ya qyalqyale da dariya. Wato har wani sunan jarumta ya bawa sultanan,saboda baisan ainihin fadi tashin da akasha kafin yaran su rayu ba a cikin mahaifarta,tashin hankalin data dinga yi,saidai duk da haka yanason bashi abinda zai karya lagon bibi sosai "Eh to,zaka iya kiranta da hakan......amma kasan banda tsananin rabo da tuni bibi ta sanya an markade maka yara tun suna 'yan tayi?" Dif wuta ta dauke masa,Girarsa ya tsuke saboda kasa fahimtar abinda goumar ke shirin gaya masa "Kaman yaaya?" Ya tambayi goumar din yana sakin wuyanshi da ya riqe,miqewa tsaye sosai goumar din yayi yana gyara rigarsa "Eh,so tayi a zubda cikin,wai sultana tayi qanqanta,wannan ai shine silar tafiyarsu Austria da nace maka sunyi a sace" Ajiyar zuciya ya sauke tamkar zata fito hade da zuciyarsa,sai yaji qafafunsa sun kasa daukarsa,ya koma ya jingina da motarsa. Ba komai goumar yake gayanmasa ba kenan,akwai abubuwa da yawa da bai bashi information akai ba. Inda bibi ta aikata masa hakan ya tabbatar babu wani abu da zatayi wanda zata wanke kanta,kuma yasan tabbas a lokacin da goumar ya gaya masa abinda bibi ke shirin yi kenan......yayi imani duk yadda yake aboye to sai ya bayyana kansa "Alhamdulillah lillahil lazi bi'ni'imatihi tatimmus salihat......lallai bibi Allah ya taimakeki" ya furta a fili yana jinjina kai. Dariya sosai abun ya bawa goumar "Cool down yaa maina,ya wuce ai" idanunsa ya zubawa goumar din yana jin ciwon abun a ransa kaman yanzu ya faru,kafin ya sake cewa komai sai suka hangi fitowar aba da oncle issoufou,wannan ya sanya suka saita kansu. Dab da zasu gotasu ya russuna yana gaidasu, oncle issoufou ne ya amsa cikin kulawa,yayin da aba ya kalleshi sai ya dauke kai yana yin gaba,sannan kuma ya amsa gaisuwar tasa da qyar. Murmushi yayi yana miqewa,iya hakanma ya masa dadi,ya tabbatar kuma yabi maganar kawu ne kawai. "Muje masallaci kada lokaci ya qwace,akwai maganganun da nace maka zamuyi" ya fadi yana duba kwantaccen agogon Rolex dake daure a hannunsa "Okay to" sai suka fara jerawa suna takawa a hankali "Sultana fa?" Ya jefawa goumar tambayar duk da yanata qoqarin controlling harshensa kada ya tambayeshin don bayason ya samu lagonsa ko ya soma rainashi. Dan satar kallon maina din yayi sannan ya qunshe dariyarsa,abinda bai sani ba mainan ya ganshi amma yayi kaman bai gani ba "Da yammar nan naga fitarta,ta shiga gidan alhj hamza duba matarshi" kai ya jinjina,komai zayazo masa da sauqi kenan. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 63 Da gudu suka isa sassan ama suna qwala mata kira,idar da sallarta kenan,ta miqe tana duban ta inda zata ga sun bullo. Tun jiyan suna ranta,tana kuma sane da fitarsu da rashin dawowar tasu,saidai kuma bataso tace komai ko ta shiga hurumin d'a da ubansa. Ta sani tafiyar tasu ce kawai zata samawa maina nutsuwa a ranshi,hakanan su kansu yaran fitar da zasuyi dashi ta tabbatar zuciyarsu zata ginu da sanin waye mahaifinsu. Tun daga jiya zuwa yau din ba abinda take juyawa a ranta irin hikimar ubangiji da ya hadasu tun kafin susan su din waye a wajen junansu?,suka kuma yi wani irin sabo cikin lokaci qanqani haka,wannan kadai yana sanyawa gwiwarta tayi sanyi,ta kuma sake yin imani da al'amarin ubangiji,yadda yake saqa faruwar abubuwa cikin hikimarsa da buwayarsa. Sai da suka isketa a dakin sannan suka daina kwaroroton kiranta din,sukayi turus suna dariya,ta jefa musu hararar wasa kaman yadda suka saba yi lokaci lokaci. Dariya dukansu suka saki,yayin da mutuniyar benazeer ta taho da sauri tana haye mata kafada "Amanmu" "Ba wani nan,bayan kunga abbanku kun manta da ama din?" "Ashe da gaske daddynmu ne din?" Batoul da har yanzu mamaki da murna basu barta ba ta tambayi ama kai tsaye tana kallon idanunta. Murmushi aman tayi,sunan maina matsayin uba,ubanma na yara har biyu yana faranta mata rai matuqa da gaske,yana sata jin wani iri,yana kuma sakata din farinciki. Wani kyauta ne ta ba zata da Allah yayi musu,duk kuwa da cewa akwai madaci sosai da aka tauna kafin zuwan wannan lokaci "Daddynku.....shine abbanku" Alamun murna suna bayyana saman fuskar batoul sosai,yayi da benazeer ta sake maqaleta da kyau,sai ta saki dariya itama tana saukota daga wuyanta "Karki ballani tunda ubanki yazo" ta qarashe fadi suna yin dariya dukansu. Bayan sunyi sallar magariba din cikin masallacin suka zauna shida goumar,yana tambayarsa abubuwan da suka faru da bai sansu ba bayan ya tafi. Wasu abubuwan su sanyayar masa da jiki,wasu su sakashi murmushin dole,a haka har lokacin isha'i yayi,suka sake tada jam'i suka yita suka idar,sai ya samu kansa da sake tsaiwa gaban ubangiji yana neman afuwa da yafiya,yana neman sauqi sassauci da kuma rangwame hadi da zuwan komai da sauqi tsakaninsa da sultana. Koda ya idar sai suka jero zuwa gida,saidai gab da zasu isa gidan kira ya shigo wayar goumar,ya daga yana duban maina "Zan koma titi,akwai abokina da ya iso yanason ganina" kai maina din ya daga,goumar ya juya yana komawa da baya,shi kuma yaci gaba da takowa cikin gidan. A nutse ya wuce gate din farko ya shigo na biyu sukayi kacibus da saddi,ya rusuna cikin girmamawa da matsayinsa na babban wa a garesu ya gaidashi,ya amsa masa yana fadin "Sultana ta shigo?" "Bata shigo ba,taje dubiya maqota amma bata dade da fita din ba" kai ya jinjina yana lumshe idanunsa. Yana ji sosai cikin jikinsa yana da shauqin ganinta,yana da shauqin magana da ita,koda kuwa bazata tanka masa ba,koda ba zatace komai ba,koda tsiwa zata masa,don haka ya taka a hankali ya isa wani gefe can daban da muddin zata wuce sai tabi ta wajen,dab da qofar falon daya daga cikin saukar baqinsu na gida ya zauna saman qananun concrete chairs guda uku dake wajen tsakanin shukokin da suma taka rawa wajen qawata harabar gidan. Wayarsa ya fidda,sai yaci karo da saqonnin laila birjik, numfashi yaja,bayan fatan taci gaba da jarabtuwa da sonshi,duk da ya fahimci kusan kullum kaman tana sake zurfi ne a ciki,duk da yadda yake jan jiki da kuma yin baya baya da ita. Dole ya buda yana dubawa,saboda aqalla bai kamaci ace a duk yawan saqonnin bata samu amsa guda daya daga gareshi ba. A nutse take takowa zuwa harabar gidan. Sanye take da simple gown na atamfa da aka yiwa yalwataccen dinki,dinkin daya tafi da sigarta da kuma murjajjen jikin nan nata,kanta ba dankwali tadai yafi madaidaicin mayafi baqin sidik wanda ya qarawa fuskarta kyau ya kuma fidda ainihin kamanninta na cikakkiyar ba'abzina. Idanunta a fede babu kwalli,hakanan fuskarta fes take babu digon komai,amma kuma hakan bai hana sassanyan qamshin nan nata na har abada ba fita daga jikinta. Wata siririyar waya ce a hannunta wadda aba ya bata ita gift na gama makaranta. Waya takeyi da daya daga cikin ma'aikatan gidan tv din da zata fara aiki dasu,suna sake gaya mata ainihin date din da zasu fara zuwa aiki,da kuma ainihin program din da sukeso ta fara gabatar musu,wanda ya shafi al'adun a yankin africa. Yadda hanakalinsa ya dauku akan wayarsa nata yafi haka daukuwa. Sosai take qaunar wannan aikin har cikin jininta,hakanan kuma sosai take zumudin farashi. Tasan yana daya daga cikin abinda zai samar mata ragowar farinciki da kuma walwalarta data rasa. Takawa ta fara yi slow sama da yadda ta shigo gidan qirjinta yana bugawa. Wucewar qamshin kawai ta kafofin hancinta suka sanya zuciyarta motsawa,a hankali sai harshenta yadan fara sarqewa da bashi amsa da yaren faransanci da suke magana. Qoqarin baza idanunta takeyi don hango daga wanne bangare yake ta kaucewa rabar wajen,saidai yadda hankalinta yadan tashi ya sanya ta gaza ganoshi dab da flowers din dake gefanta. Rashin gano taqamaimen location din da yake ya sanyata ta jita bata da tsaro,ta gwammace ta tsaya cak a wajen,don bata qaunar haduwarsu koda na wucewar second daya ne,bata kuma da tabbacin idan taci gaba da takawar ba zata ci karo dashi ba,gwara ta tsaya daga nan ta gano daga inda yake sai ta zabi sashen da zata wuce,sassan bibi ko na ama din. Sautinta da suka isa kunnuwanshi su suka ankarar dashi isowarta wajen,a nutse ba tare daya daga kanshi ba ya kashe wayar yana maidata aljihu sannan ya miqe cak yana zuba hannayen nasa a aljihun nasa,ya kuma fara takowa inda take a tsayen. Tana qoqarin yin sallama da mutumin don ta tattara hankalinta waje daya,gefe guda kuma iska na qoqarin yaye lullubin kanta,wanda dole ta kasa hankalinta biyu,saidai bata cimma nasarar riqe mayafin ba saboda ta bada qarfi wajen kashe kiran iskar ta debi mayafin ta kuma yi cilli dashi gefe guda,baqar sumarta me santsi yawa da tsaho ta warwatsu saman fuskarta,hakan sai ya zamana tamkar ado ga saman fuskartata,qamshin hair mist din da take using dashi shima ya fara fita tare da iskar. Qaramin tsaki taja idanunta akan wayar "Allah yasa a cikin gida ne da na cutu" ta furta tana qoqarin saving number, idanunta kuma akan wayar tana takawa direction din da taga mayafin ya tafi ya fadi da zummar ta dauka ta wuce cikin. Yana sane,ya kuma ga tahowarta,don haka ya taka a nutse idanunsa a kanta har ya isa gaban mayafin,ya kuma tsugunna ya sanya hannayensa ya dauki mayafin. Hannu ta miqa ba tare data kalli wajen ba,saboda ta gama gane inda mayafin yake,can qasan zuciyarta kuma tana wani irin bugu saboda mugun qamshin turarensa da takeji dab da ita sosai. Qasa taji ta debo,wannan ya sanyata barin saving number din don dole ta maida dubanta ga wajen. Sauka idanunta sukayi kan zaratan qafafunsa dake sanye cikin wani flip floppy masu taushin gaske, charcoal color da suka haska farin skin dinsa sosai. Da sauri ta miqe cikin rashin sanin yana dab da ita, hakan ya sanya tayi gware da katafaren qirjinsa da ya mamaye tsahonta. Haduwar jikinta da qirjinsa yayi sanadin sa saura kadan numfashinta ya kubce mata,da wani irin hanzari taja da baya tana watsa masa wani irin kallo,tuhuma da bacin rai fal bisa fuskarta. Abinda bata sani ba manyan fararen idanunta da take jifansa da kallon tsana ya dinga ji suna ratsa kowanne sashe na jikinsa,sai yakejin kallon kamar wani kallo ne na musamman bawai na bacin rai ba,idanunsa suka shagala da kallon sassalkan gashinta da yake tunanin shekaru da hankali data qara suma abun ya shafesu,don ya qara cika tsaho da kuma santsi. Kafeta da yayi da lion eyes dinsa sai taji kaman yana watsa mata wuta ne cikin sashen jikinta,ba abinda idanuwansa ke tuna mata sai waccar ranar da wancan LOKACIN. Ba abinda suke tuna mata sai yadda ya gwada mata zallar qarfi da rashin imani......baya tuna mata komai sai sanda take jifansa da kalaman da take tsammanin zasu sanyashi fusatar da zaya rabu da ita ba tare da yayi mata komai ba,ashe a nata rashin sanin......a nata rashin wayon rashin imaninsa yakai har inda baya jin kiran. Bata qaunar koda hada idanuwa daya dashi bare wata magana ta hadasu,ta gwammaci ta koma cikin gida a haka akan tayi masa maganar ya bata mayafin,ta sanya hannunta ta maida gashin dake tsone mata idanu baya,sannan tayi taku biyu gefe da zummar kewayeshi ta wuce,don ya tokare kowacce hanya daga gabanta da zata bata damar wucewar. Cikin sauke qafafunta da tayi sau biyun tare suka sauke shi da ita,a fusace ta daga idonta zata sauke masa,saidai kuma yana tsaye kaman wani zane ya sake kafeta da kakkaifan kallon nasa da suke sanya kowacce laka ta jikinta zarewa a shekarun baya,suke kuma cire mata duk wani taurin kai qwarin gwiwa da tsiwar data tsammaci yi. Ga mamakinta ko a yanzun ma tasirin wadannan idanun masa masu kama da idanun zaki basu fasa galaba a kanta ba, saidai kuma bacin rai dake sidar zuciyarta ya rage kaifin tasirinsu. Hannun hagunta ta sake takawa don neman hanya still ya sake tareta,wannan karon ya motsa siraran labbansan nan dake da wani irin color me birgewa "J'ai besoin que tu m'écoutes s'il te plaît(ina buqatar ki saurareni don Allah)" ya fadi cikin tattaccen harshen faransanci da zai nuna maka zallar qwarewarsa a ciki da kuma nuna da yaren yayi saman harshensa "ne bloque pas la route(kar a taremin hanya)" ta maida da harshen da sukafi magana dashi din dai still,cikin lafuzzanta akwai kakkaifan sound na gargadi tayi kuma maganar ne ba tare data kalli idanunshi ba,don ko kusa ko alama bata da sha'awar hakan. Bai damu da wannan ba,don lokaci da hankalinta kawai yake da buqata "je cherche des faveurs(ina neman alfarma)" ya sake fada yana zaro hannayensa daga aljihun wandonsa ya hadesu guri daya👏🏽. "Ka matsamin na wuce nace!" Tayi maganar da tsawa zuciyarta na mata zafi. Tsam ya runtse idanunsa yana jin saukar siririyar muryarta har tsakiyar kanta. A nutse ya bude idanun nasa sanda yaji tana takawa da gaske zata wuce ciki. Kai tsaye ya sanya hannu yayi caraf da tsintsiyar hannunta,abinda ya bata shock qwarai,ta kuma tsaya cak da tafiyar da takeyi,ta waiwayo tana kallon tsintsiyar hannunta dake cikin tafukan hannunsa daya runtse tsam. Maida dubanta tayi ga fuskarsa "Ka sakarmin hannuna.....baka da hurumin tabani" ta fada tana qoqarin controlling hawayen daketa turereniya suna son bayyana kansu take son hanawa,batason ko sau daya ta sake kuka a gabansa a rayuwarta,tanason nuna masa she's strong......fiye da yadda yake tunani "corrige tes mots(ki gyara kalamanki)" ya maida mata amsa. Maganar tasa sai taji zallar raini ce a ciki,ta tattara dukkan qarfinta da nufin son zame hannunta saidai kuma inaaaa......wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ita kanta tasan ba abu bane me yiwuwa don riqon bana ragwagwen maza bane. Shi kam yana tsaye hankalinsa kwance,yanata qare mata kallo da kuma yadda take fafutukar qwace kanta "Kinyimin tsaki jiya.....saboda na qyaleki shine yau kika dora da yimin tsawa?,Ai-je ton âge ?(ni tsaranki ne?" "Je ne sais pas, parce que c'est ton souci et pas le mien(Ban sani ba, domin matsalarka ce ba tawa ba!") Ta amsa masa still da tsawa hawayen da take boyewa suka sillobo ta gefen oily eyes dinta da hawayen suka qarawa sheqi " assez !(ya isa!)" Ya fadi cikin tsawar data bada amsa kuwwa a dukka wajen da husky and deep voice dinnan nasa,zuciyarsa nason hasala da harzuqa,idanunsa a hankali na son fara sauya launi,tabbacin ya fara shiga bacin rai kenan. Kaman an watsa ma sassan jikinta ruwan sanyi haka tsawar tasa ta saukar mata,tayi mugun ratsata fiye da yadda take tsammani,har dai data kaita ga runtse idanunta gam saboda yadda sautin ya shiga kunnenta da kyau "Wuce ki zauna!" Ya sake fadi cikin gigita,sai kuma ya kasa tsaiwa jiranta,ya sake sanya hannunsa ya riqe nata hannun da kyau ya soma yin gaba. Sai a sannan ta bude idanunta,so take ta tirje masa amma kuma qarfinta da gabbanta ke dashi sun gaza bata hadin kai,da sauri sauri yake riqe da ita har zuwa qofar babban falon,ya sanya qafa ya tura qofar da dan zafinsa ya shige yana jan hannunta zuwa ciki "Ka sakeni nace!" Ta sake fadi itama tana bude muryarta da kyau,zuwa lokacin hawaye ya gama wanke mata fuska "Cool down maina......kabi a hankali.....kabi a sannu" abinda zuciyarsa ta soma nanata masa kenan. Sai ya fara furzar da iska da sauri sauri daga bakinsa yana fatan zuciyarsa ta saisaita,daidai sanda ta sake juyawa da sassarfa,sumar kanta na lullube fuskarta ta nufi qofa. Taku biyu rak ya cimmata,ya rigata dora hannu akan handle din,ya maida qofar ya kulle ya murza key ya zare ya jefa aljihunsa,falon ya qara duhu,shuru ya sake ziyartar wajen,ba motsin komai sai bugun zuciyoyinsu guda biyu,abinda ya darsa tsoro a zuciyarta kenan,ta shiga tuna wadancan ranakun da abinda ya faru da ita,sai taja da baya tsoro yana cika zuciyarta,amma tana qoqarin bawa kanta qwarin gwiwa. Ta ritsashi da dukka idanunta kamar yadda shima ya ritsata da da shanyayyun idanunsan nan da suke birkice,birkicewar da taso yima sultana kama da birkicewar wancan lokacin,abinda ya dinga qara adadin tsoronsa cikin zuciyarta kenan. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 64 Kaifin idanunsa ya rage mata ta hanyar lumshesu,yayi qoqarin yin gyaran murya koda kalaman da yakeson gaya matan zasu fita dai dai "Zan barki ki wuce ciki ne kawai SULTANA idan kika tsaya kika saurareni mukayi magana" ya fada da muryarsa data lanqwashe qwarai tayi wani irin sanyi. Kai ta girgiza tana jin tsanarsa na sake kai mata iyaka,to me zai ce da ita?,me zai gaya mata ma?,wanne bayani garesa?,batajin akwai wata kalma da zata fita daga bakinsa wadda zata yi daraja ko ta samu matakin yarda a wajenta "Bazan saurareka ba Aliyu,bazan taba sauraronka a nan dakin ba,don kai ba abun yarda bane......da shigen wannan salon ka cutar da rayuwata a baya" ta furta kukan gaske yana qwace mata ba hawaye ba irin na dazu "Cutar dake kaman yaaya?" Ya fadi da sigar tambaya fuskarsa na nuna gaskiyar rashin sanin cutarwar. Wani kallo ta bishi dashi harara takeson gasa masa 'yar gaske da zai fahimci a yanzun shi ba kowan kowa bane cikin rayuwarta amma kuma idanunta sunqi bata hadin kai "Kince fyade nayi miki wancan karon,amma zuwa yanzu ina fatan kinyi gamsuwar da zaki fahimci haqqina na na karba......tunda da gumina......da kudina a matsayina na dan makaranta na biya sadaki.......zan iya yarda idan kikace nayi abun ne ta yarda ya dara shekarunki......but har a gurin Allah bani da laifi.......wannan kuma bazai zama hujjar da a yanzun zan dinga baki dama kina gayamin dukka maganganun da suka zo kanki ba,bazanyi tolerating rubbish ba.......dole dole kisan matsayin da Allah ya bani a kanki......ina buqatar zama muyi magana dake ta fahimtar juna.......zan nema afuwa a duk guraren da kike ganin na saba miki" batayi shirin zama ba amma sai data koma da baya ta zauna saman kujera,batayi tunanin yana da zarra da qarfin hali har haka ba,batayi tunanin akwai lokacin da zayazo ma ya tsaya a gabanta ba bare ya fadi mata ire iren wadannan maganganun,yanzun yana ganin laifinsa da qanqanta har haka?. Kaman yasan me take saqawa a ranta sai ya maida hannayensa yana goyesu a bayansa,sannan ya fara takowa zuwa kujerar da take zaune a kai, tahowar tasa data sanya hanjinta kadawa,zuciyarta kuma na saqa mata tsaf zai iya maimaita aikata abinda ya aikata a baya. Wani irin hautsinawa tayi gefe,sai gata ta sauka a qasa,zata miqe ya cimmata,ya sulale shima a hankali ya tsugunna a gabanta,tsugunnon da ya basu kusanci qwarai "Kar ka aikata" ta fadi kuka yana qwace mata sanda ya miqa hannu da nufin janye mata gashinta daya warwatsu har kusa da idonta "Halalina ce fa" ya fada calmly "Bani da wani miji.....ni ba matar kowa bace!" Ta fadi tana jin zafin kiranta da matarsa da sukeson gwada mata qarfa qarfa shi da goumar "Am really sorry.......kowanne kalan ban haquri kikeso ki fadi zan miki shi SULTANA" Kaf gidan yafi kowa iya furta sunanta,kaman saboda shi aka halicci sunan,kaman sunan yasan shine wanda ya zaba mata shi. "Bana buqatarka a rayuwata......ka fitamina a rayuwa" "Am so sorry sultana.......ni benazeer da batoul muna da buqatarki......kiyi haquri ki yafemin,let build a home ni dake for our kids please" sosai ta bude fararen idanunta da suka koma kalan manja a kansa "Which kids?,baka da wasu yara,yara yaranane......kaman yadda ni ba matar kowa bane.......zasu samu wani iban,nima zan rayu da duk mijin da na zabawa kaina wanda yasan darajar rayuwa da mutuwa" wani ciwo maganar take ji masa a zuciyarsa har yanajin kamar bazai iya ci gaba da dauka ba "don't say that please 🙏" ya fada idanunsa a rufe gam "Bazan daina fada ba!.....bazan daina ba,that's my truth!" Dole ya sake bude idon nasa a kanta a Karo kusan na uku "Baki canza ba har yanzu sultana?,da gaske akwai sauran wani gyaran?" Tambayar da yayi mata kaman ya sanya sarqa ya kulleta ne,tanason ta fahimci abinda yakeson cewa ta kuma gaza fahimta din,sai kawai ta sanya hannayenta duka biyun ta dafe qasa taja da baya sannan ta miqe tana son dosar qofa "Ba abinda zai canza a maganata hukuncina da kuma ra'ayina,you better to stay away from me........" "How can I do that?,dukka rayuwata tana tattare da ke,'ya'yana gudan jinina......matata....." "Baka da mata.......kalamanka ba zasu taba rusunar da zuciyata ba........ saboda kai din azzalumi ne.......me take......" Labbanta basukai ga qarasa cewa komai ba suka tsinci kansu tsakiyan tausasan nasa labban,kafin tayi kowanne yunquri ya hadeta da bango sosai ya kuma sakar mata qarfinsa,sannan ya sanya hannayensa ya riqe kanta da kyau yana sake kamo labbanta sosai cikin bakinsa. Kamar ya samu sweet haka ya dinga sarrafasu daga lips nata har zuwa harshenta. Wata muguwar gigicewa tayi,saboda yadda abun yazo mata a bazata,ta sanya hannayenta ta dinga dukan qirjinsa da yunqurin qwacewa amma sam bai saurara ba bai kuma dakata ba,duk abinda tasan zatayi don ta dakatar dashi tayin amma hakan baiyi tasiri ba,sai kawai ta tattara dukka yawun bakinta ta tura masa bisa tsammanin zai janye. Zut taji ya zuqeshi gaba daya,ya kuma sake zura harshensa cikin bakin nata kaman ma me neman qarin yawun nata,abun sai ya zafafeta ta fashe da kuka gaba daya. Sai daya tabbatar dukkan tsoro da mutuwar jiki sun mamayeta sannan ya zame bakinsa daga nata,tana zaton zata tureshi ta zille sai ya riqe qugunta sosai yana kallonta da lion eyes dinsa da sukayi matuqar yin laushi. Sosai qirjinsa ke bugawa fat fat har kana iya hangen hakan ta saman rigar kaftan din jikinsa,hawaye sun wanke mata fuska sosai,yayi mata riqon da ba abinda ke faruwa sai musayar numfashi da sukeyi shi da ita,ya fidda nasa ta zuqa ta fidda nata ya shanye,idan kuma ta kawar da fuskarta wani gefen ya sanya hannun ya tallafota,tanata bitar kalma guda da zata gaya masa da zata sanyashi jin haushi ta qona masa zuciya ya saketa ko bai shirya ba,tana kuma tunanin abinda zata fada din me zaya haifar mata "Idan baka sakeni ba zan maka ihu na rantse da Allah" duk ya yadda idanunsa ke lullumshewa amma sai da maganar ta sanyashi fidda wani sassanyan murmushi me qaramin sauti,riqonta ya qarayi da kyau yana duban tsakiyar qwayar idanunta. A hankali yakai yatsansa gefen idonta guda dayan yana rayawa a ransa wataqila wannan shine tabon da ya kusa illata mata idanu. Idon nata ta runtse hawaye sabbi suna fita. Sosai yaji zuciyarsa ta matse,yaji zafin kansa da kansa sosai,shaidan tabbas yayi tasiri a lokacin,ya kuma iza masa wutar zafin kai data zuciya sosai a sannan,but......yayi alqawarin shafe wannan tabon dama lalurar gaba daya muddin yana numfashi "Da kin kyautamin,kin kuma gajarcemin wahala......anyways......daga yau duk sanda kika taba lips dinki ko kika kalleshi a madubi zaki tuna cewa ke matar aure ce,kuma uban jarumin uban 'ya'yanki yana nan......na yarda ni din me laifi ne......duk wata tuhuma zan karbeta hannu bibbiyu......but tsiwa......da barranta kanki da yarana daga gareni wani abune da zuciyata ba zaya iya dauka ba" harara sosai take balla masa wannan karon,ta sake tattar qarfinta ta tureshi tana rushewa da kuka sai ya saketa wannan karon babu ja,ta nufi qofa yana yunqurin budewa "Nop.....jirana zakiyi ai tare zamu shiga cikin gidan" ya bata amsa yana tattare hannun rigarsa sannan ya bude toilet din falon ya shige. Sulalewa tayi ta koma gefe ta zauna tana sake sakin kukan,gaba daya abun nasa yazo mata da rainin hankali,ta yaya shike da babban laifi ko tace manyan laifuka irin wadannan dukka ya zauna yana qanqantar dasu a idanunta?,yana abu kaman baisan girman abinda yayi mata ba?. Ya jima cikin toilet din yana ajiyar numfashi idanunsa kan fuskarsa daya bayyana tar gaban madubi,emotions da yawa yake gani saman fuskarsa "Alhamdulillah" ya furta can qasa amma a fili,lallai addu'a ba abun banza bane,bare addu'a gaban dakin ka'aba?. Ya tsammaci bore fiye da wannan daga wajenta,sai gashi komai da alama zayazo masa da sauqi (Nidai nace uhmmm malam aliyyu haidara,ba girin girin ba dai tayi Mai,kabi a hankali da sultana😂). Alwala ya dauro sannan ya fito yana warware hannun rigarsa, idanunsa yakai kanta,sai baice komai ba ya fara takawa yana nufar qofar. Key ya zura ya bude qofar sannan ya waiwaya a nutse ya dubeta "êtes-vous prêt à aller?" Ya tambayeta yana tsareta da kallonsa hadi da miqa mata mayafinta. Kaman ba zata karba ba amma ta daure ta miqa hannu,sai ya gaza zare idanunsa daga dogayen hannun nata dake dauke da farar fatar da kamar ka wanke hannu kafin ka taba. Ganin kamar baida niyyan bata sai ta saka hannu tana zare shi daga hannunsa,dab da zata kammala zarewar yayi caraf ya riqe mayafin yana duban cikin idanunta "Daga yau......kada ki sake fita bada izini na ba" haushi takaici,kaman tayita zunduma ihu haka taji,ta gaza jurewa sai data watsa masa wani kallo. Koda batayi magana ba yasan sarai meye a cikin ranta,shi ya raineta,duk wani motsi nata koda batayi magana ba yana fahimta,don haka ya sake riqe mayafin da kyau cikin hannunsa yana kuma sakar mata wani kallon da ya tabbatar sai ya isa har tsakiyar zuciyarta "Idan da ba'asan inda nake ba,kuma ba laifi idan kinyi hakan,a yanzun ina nan,kuma ina shirye da sauke duk wani hakkina.....kema kuma dole ki sauke hakkinki" "Dole?" Ta tambaya cikin salon mamaki tana kallonsa da rinannun idanunta,kai ya daga mata don son tabbatarwa "Qwarai kuwa" so takeyi ta gaggaya masa maganganun da zasu yiwa zuciyarsa nauyi amma tata zuciyar sai ta kwabeta "Kada ki fara,a nan din daga ke saishi.....karki maimaita kuskuren da kikayi a baya" wannan ya sanya ta tattaro dukka kalamanta ta hadiyesu,sannan ta sake zare mayafin sai ya sakar mata. Yana tsaye ya tsareta da kallonshi har ta lullube kanta saidai baiga ta motsa ba,ya fahimci me take buqata,don haka ya matsa daga bakin qofar yana cewa "Bismillah" a nutse ta tako zuwa shiyyar ta kuma giftashi, iskar data kwaso din ta watsa masa lallausan qamshin jikinta wanda ya sanyashi sakin wata ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa tamkar yaron da yayi kukan neman mamarshi har ya gaji. Ko kafin ya bude idanunsa sai ya taras har ta fice ta kuma fara nisa da inda yake,sassarfa takeyi tamkar wadda ke gudun tserewa mayunwacin zaki. Murmushi ya qwace masa,kwata kwata sauri bai dace da tsarin halittarta ba,amma sai yayi tsaye,sai data qurewa saurinta,sai gashi a qididdigaggun taku ya cimmata. Kamar ko yaushe,qamshinsa kadai ya sanya ta fahimci yana dab da ita,koda ta waiwaya ta ganshi saita fara qaramin gudu tana nufar sassan bibi,abinda ya bashi mamaki kenan,sai ya qara saurin tafiyarsa yana biye da ita......baisan me bibin zata dauka ba idan ta gansu a hakan sun shigo tare,koma meye a yanzun zatace ko zatayi bibin ko a kwalar rigarsa,kome dai meye she's his wife......kuma bazai taba bari damarshi ta kubce masa ba. A shirye yake ya fuskanci kowanne qalubale ta dalilin haka......komai tsanani,komai runtsi...... _maina fa da gaske yake_😂 *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 65 Bibi na daga tsaye tana qoqarin karbar daffafiyar nonon raqumi me dumi da takansha daga hannun bilki taji sautin sheshsheqar sultana din,ko kafin ta waiwayo ta iske bibi din ta kuma rungumota ta baya tana sauke kanta a bayan bibin tana kuma sake fashewa da wani kukan. "Meye haka?,lafiyarki?" Ta jefa mata tambayar dai dai sanda maina ke shigowa falon. Idanunshi a kansu kaman yadda bibi itama take kallonsa,saita rasa bakin magana,ta dubi bilki "Ajjiyemin madarar ki tafi abinki" ta amsa mata cikin girmamawa,ta qarasa kan daya daga cikin tables na glass dake tsakanin kowacce kusurwa ta kujerun falon ta aza akai sannan ta wuce. A nutse abinsa ya qaraso cikin falon,ya samu daya daga cikin kujerun ya zauna ya kuma miqa hannu ya dauki daffafiyar madarar ya kurba. Sosai yayi missing al'adunsu,sosai yayi missing komai da ya shafi abzinawa,sai yanzu yakejin komai din yana dawowa cikin jikinsa "Me kayi mata?" Bibi ta tambayi maina tana dubansa ganin yadda kukan sultana ke qara yawa. Sauke cup din da yakai bakinsa yayi yana dan juyashi a hannu sannan yace "Ki tambayeta mana bibi.....nidai bansan wani abu da nayi mata ba......" "Aliyyu" bibi ta kira sunansa na aihini kai tsaye "Banason a samu matsala ko maimaicen kuskure" "Ba za'a zamu ba bibi......ba wani abu nayi mata ba,kawai nasan na ja mata kunne ne kadan,tana yimin tsaki tana kuma gayan magana ba ta hanyar data kamata ba,ina cewa kun koya mana girmama babba ko?......to don Allah bibi ki sake karanta mata kafin ta fara zaman aure cikin gidanta ta gyara dukka wadannan dabi'un" maganar tasa saita zama kamar turin wuta,da sauri ya daga fuskarta daga kafadar bibi zuciyarta tana zugi cikin kuma muryar kuka tace "Kinji ko?,kinji ko bibi?,ki gaya masa ya fita sabgata ya fita rayuwata,don ba abinda ya hadani dashi,bani da wata alaqa dashi,kuma ni ba matarsa bace na gaya masa,yaje ya nema matarsa,ki gaya masa yayi nesa da lamurana,tunda nidai ban shiga nasa hurumin ba" tana kaiwa nan ta saki bibin ta wuce ciki da sassarfa tana ci gaba da sakin kukanta. Da kallo dukkansu suka bita,saidai sanda bibi ke dawowa daga nata kallon shi ya dauke idanu ya fuske din baiso ma bibin ta gani. Rai ta hade tsam tana dubansa "Waikai din wanne irin yaro ne?,ka dawo da wannan manya manyan laifukan kuma kake tunanin kawai kai tsaye zamu baka ita?" Idanu ya zubewa bibin ga mamakinta sai taga ya saki murmushi "To bibi idan baku bani ita ba dafata zakuyi ku cinye?,ni kadaine zan iya da ita bibi,sannan bugu da qari ma ai nasan kuna buqatar ganin wasu twins din ko?" Turqashi!,bibi ta fadi a ranta,yaushe aliyu ya soma komawa haka?. Bai taba gwada magana irin wannan ba don haka duk furucin sai ya sanyata ta daburce "Qaniyarka.....ni kake gayawa irin wannan maganar aliyyu?,zaka maimaitata ne a gaban hamidou kuwa,kaga shi sai ya dauketa ya bakan" siriryar dariya ya saki,yasan a nan wajen bibi din nasararsa take "To kece bibi mana,kun dameni da cewa na tafka laifi,laifina daya na rashin bayyana kaina ga kowa na karbi laifina a bayyane,amma duka sauran abinda ake tuhumata akai ban karba ba ban kuma yarda ba,ke kika sanya su aba da oncle bashar suka bani lasisin aikata komai fa,sannan a yanzun ki dawo kina min qorafi bayan abinda kikeson ji da gani kenan,gashi kinji kin gani harda result ma" "La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam" bibi ta jawo dogon salati kai kace mutuwa ce akayi mata "To da alama wannan shari'ar nema takeyi tafi qarfina,bari ka gani" ta fadi adan diririce tana juyawa kaman zata bar falon. Cikin zafin nama ya miqe ya tareta,ya kuma riqeta da kyau yana cewa "Haba bibita......zo kiji,ai ba za'a yi haka ba" ya qarashe maganar yana zaunar da ita saman kujera,shi kuma ya koma saitin qafafunta ya zauna yana dan tausa mata qafar a tausashe. Idanu ta zuba masa,sai yayi mata shuru ya qyaleta har sai da tayi hararar me isarta sannan ya sake matsowa kadan murya a tausashe "Duk ki gama hararata bibi..... Allah dai ya rufa miki asiri kawai da baki zubda min cikin yara ba,da wataqila yanzun ina nan ina shari'a dake" baki ta bude galala,kunya kuma tana dabibayeta,saita watsa masa daquwa "Ungo nan.....qaniyarka,wanne shaidanin ne ya gaya maka wannan maganar......nasan ba aikin kowa bane wannan saina wancan dan banzan goumar baqin buzu" yadda a yau din tayi amfani da sunan da sultana tafi kiransa dashi ya sanyashi sakin murmushi me sauti "Kinyi zaton bana bibiye da rayuwar sultana?,kin dauka na watsar da ku da ita ne gaba daya?" Tambayar da ya jefa mata ta sanyata tsaiwa kawai tana dubansa "To bari na baki labari" sai ya sauke qafafunta qasa,ya kuma fara gaya mata abubuwan da tayi imanin da gasken yana tare dasu,da gasken yana bibiye da motsin sultana lokutta da yawa. Haihuwarta tafiyarta Hassan gwarzo,metron asabe da ya bawa kwangilar kula da sultana da duk abinda takeso tsahon shekarun da zatayi ta kammala,wanda daga nan ne sadarwashi da ita ta yanke,ya tafi karatun da ya dauki alqawarin ma daddy daya kubutar dashi daga hannun mutanen da suka so tilastashi shiga aikin S.S.....ya kuma zo ya rasa number goumar tun ranar da shima yaje visiting hassan gwarzo "Kowa bai ganni ba amma goumar ya ganni,har yayi wata magana a sannan da na tsammaci zaki dauki haske(inama kina iya ganin abinda nake gani)" fes maganar ta dawowa bibi,ta kuma tuna sanda goumar ya fadi hakan yana kallon wani guri daban,duka ta zaci iya shegensa ne kawai,ashe magana yake mata me harshen damo. Hirarsu dashi din a yanzun ta sanyayawa bibi jiki,ta kuma fahimci a kame yake a hannun wasu da sukayi masa dauri me kamar sake don su sakashi cikin aikin da baiso qarfi da yaji. Ajiyar zuciya ta saki tana lanqwasa yatsunta sannan a nutse tace "Duk na fahimceka,kuma ka sani bana goyon bayan raba aurenka da sultana....... saidai ko kadan bazan tilastata zama da kai ba,bazan kuma baka izinin takurata ba,kabi hanyar data kamata ka shawo kanta ka amintar da ita,sannan kuma uwa uba ka sanya soyayyarka a zuciyarta". ********Tun daga wancan ranar da abun ya faru ta yima kanta alqawari ya daina ganin koda gilmawarta bare ya samu qwarin gwiwar tsareta da wasu kalamanta da sam basu da tasiri a gareta. Ta gwammace ta kwanana a daki sannan tayi wuninta gaba daya a dakin. A yanzun hatta da gilmawar benazeer da batoul ya ragu sosai cikin gidan,saboda bini bini suna tare da maina din,tana sane da komai,amma ta barsu ne ta zuba masa idanu taga iya gudun ruwansa. Abinda yafi komai yi mata dadi shine,kwanakin da zasuyi cikin gidan ba masu yawa bane,tasan komai ya kusa zuwa qarshe,da zarar ta wuce Paris ina zaya ganta bare ya gallabeta?. Bataga wani sakewa tsakaninsa da ama ba bare ta sanya ran zata zauna tayi dogon zancan da ya shafeta dashi,su benazeer kuwa ko kadan bata taba bari sun san lokacin komawarsun ba,don tasan su kadaine hope dinsa da zaiji komai daga garesu,musamman benazeer da bakinta bayaniya shuru,rawan kanta akan daddynta kuma ya fara bawa suktanan tsoro,ko shigowa sukayi gaidata in sha Allah kafin su fita a dakin sai ta mata zancansa,saidai ta koreta ko ta rakata da harara sannan ne zata ja bakinta tayi shuru. A zaman da takeyi ta maida kai sosai wajem research yadda zata zama good presenter akan program dinta, research akan abubuwan da suka shafi al'adun qabilu daban daban,saidai ta fi bada qarfi akan qasarta ta nijer,don da ita take son farawa,wannan ya sanya duk sanda ta fahimci bibi ita daya ce a zaune zata je ta dameta da tambayoyi da son sanin wasu tsaffin al'adu da ita batasan su ba. Duk wata magana da maina din ya gaya mata a wancan ranar ta azata a mizanin qarya ne,don bataga wata hanya guda daya zancansa zai zama gaskiya ba. A yanzun ba maina take kallo ba,aliyyu take kalla,duk wata kalmar damuwa da ita da yake furtawa tana kallonta ne a mazaunin labarin qanzon kurege,ko kadan zuciyarta ma bata qaunar wani lamari da ya shafeshi,a yanzun da zai sake bacewa bat kaman wancan karon tayi imani dari bisa dari itace number ta daya a gidan da zata fara murna da hakan. Su aminata sunyi mita sun kuma yi qorafin rashin zuwanta gidansu har sun gaji,abinda basu sani ba shine,ita ba zuwa gidansu ne matsalarta ba,damuwarta ta fita farfajiyar gidan tsautsayi ya hadata dashi. **********K'arfe takwas na daren ranar tana tsaye cikin kitchen din ama tana qoqarin kammala miyar tuwon aba. Tun safiyar yau data shigo gaida ama don ba'a sassanta take kwana ba kwana biyu ta karanci ama din bata jin dadi,wannan ya sanya da yammaci liqis ta fito ta karbi girkin aba wanda bata baiwa kowa yayi masa sai ita da kanta sai kuma sultanan. Bata kuma baro sassan bibi ba sai data tabbatar baya gidan shi dasu batoul da a yanzun suka zama qafar yawo,kowacce rana akwai inda suka nufa,guraren shaqatawa daban daban cikin marad'i harma da niamy kamar wadanda suka kawo yawo duniya. Abun yana bata haushi, musamman yadda taga kowa cikin gidan ya xuba musu idanu,kamar ma sun samu goyon baya kenan,wani gun idan sunje su kwana,wani su dawo a ranar, goumar idan yana free kuma shima ya zama dan rakiya dan iza wuta. Haka zata zauna tayita baqin rai,abun da yake sake bata haushi hatta da bibi tana yin kamar bata san me yake damunta ba,kusan tanja ce kawai ke tankata,ita dimma tana bin tanja da ba komai,don tana ganin idan ta furta wani abu game da yaran kaman tayi rashin kunya ne,amma yana da kyau a dinga duba mata basai tayi magana ba. Lafiyayyen tuwon shinkafa tayi masa miyar shuwaka da taji agushi. Tadan qara yawan abincin saboda ama tace tana da buqatar tuwon itama. Ta kammala komai tana shiryawa cikin warmer's tanja tana tayata. A nutse yake takowa zuwa sassan ama daga nashi sassan don yayi dinner,yana sanye da wata baqar hoodie abaya ta maza wadda aka yiwa adon golden din zare,bai sanya hular saman kanshi ba,wannan ya sanya baqin nannadadden gashinsa na asalin buzaye ya bayyana bisa tsari saman kansa. Suma ce da ba'a gajiya da gyaranta da kuma kashe mata muggan kudade gurin siyan kayan gyaranta,kama daga mayuka hair mist da sauran tarkacen kula da gashi na maza. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 02 page 66 Duk inda ya gifta sai yabar sassanyan qamshin nan nasa me kwantar da zuciya wanda yakan jima a waje kafin yabar wajen. Tunaninsa da kuma hankalinsa suna karkasuwa,ya gama noticing nata tsaf,duk wani zaman daki da boyewar da takeyi ya tabbatar don saboda shi ne,shi kuma yana ji cikin jikinsa akwai wani abu da zai girgizashi ko ya sanyashi janyewa daga qudurinsa. Duk kuwa da cewa ba wani sauyi daga wajen aba,gaisuwa ce kawai take hadasu, gaisuwar ma zaya amsa masa ita ne da qyar,bibi kuwa tana ji tana gani ya mata qarfa qarfa,duk abinda zaiyi wanda zai saka ta kulashi shi yakeyi,to kuwa koda batayi niyyar kulashin ba sai ta kashi. Ama kam zata amsa masa gaisuwa ne ba yabo ba fallasa,daga haka koda zaman awa nawa zasuyi a wajen muddin dai bai sake cewa komai ba itama bata sake cewa. Zuciyarsa ba zata iya daukan hakan daga ama ba koda kowa zaiyi masa,don haka ya soke kawo mishi dinner da akeyi har sassansa,ya tsiri zuwa suyi dinner tare koda ba abinda zai hadasu har su gama. To bare zaiyi wuya su gama dinner din sun tashi haka,musamman da yake su benazeer suna zuwa ayi tare dasu,sai ya soma ganin alamun zuciyarta tana sanyi daga daukan zafin da tayi,saidai tanata boyewa ne taqi ta bayyana hakan akan fuskarta,to koda bata bayyana ba shidai hakan ma ya masa dadi,ya sani kuma tsakanin uwa da danta sai Allah,tabbas zata sassauto kaman yadda yake fata. Sanda ya shiga falon babu kowa,baiyi mamaki ba saboda dukka masu aikin cikin gidan daga kowanne sashe daga magariba tayi suke komawa sassansu,saidai idan kuma an buqacesu,sai na jiki sosai irinsu tanja da ba'a rabo dasu. Fes falon yake wanda girmansa ya sanya yake dauke da rukunin kujeru biyu,amma duk da hakan sai yake neman rainsu,ko ina qamshi yake fiddawa dake gauraye da sanyin a.c. qatuwar tv plasma din dake girke ce kadai keta aikinta. Takawa yayi a hankali ya dauki remote yana rage sautin ta,yayin da hancinsa ke shaqo masa daddadan qamshin miyar shuwakan. Ajjiye remote din yayi yana duba lokaci. Bakwai da hamsin da takwas,masallatai dake sallah da wuri dukka sun idar. Kewar yaran gaba daya ta isheshi,tun dazun suka fita da goumar da yammaci yawonsu saboda yau din shi bai samu fita ba yana daki yana duba wasu takardu da sardauna ya turo masa ta email dinsa,gashi har yanzun basu dawo din ba. Bude wayan yayi ya kira goumar din "Mun kusa da gida,nasan yaranka ka biyo" abinda goumar ya furta kenan yana qaramar dariya cikin salon tsokana. Qaramin murmushi ya subuce masa,yadan cije lips nashi kadan yana katse wayar. Shi goumar din baisan banda shi ba ba wanda zai iya lamuncewa yaran har a fita dasu daga gidan har haka su dade ba?. Number ama ya laluba ya kira,bugu biyu ta daga,muryarta a qasa tayi sallama,ya amsa mata cikin tsananin kulawa a ladabce "Na shigo ban ganki ba ama" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke. Haidar dinnan dai me tsananin nuna mata kulawa da kuma kula da damuwarta,har yanzun shine dai,komai har yanzun halayen da dabi'unsa game da ita da take tunanin sun barshi suna nan ba inda suka je "Zan fito yanzu zan shiga wanka ne" "A fito lafiya" ya bata amsa yana komawa saman kujerar dake facing dining area ya zauna yana dan sauke idanunsa a wajen. Yanason duba me suka dafa din yau amma sai yaji yana gandar haka,ya bude wayarsa ya kunna data dinsa,sai ya shiga IG yana duba hotunansu benazeer da baya gajiya da kalla. Kiranta shi ya katse masa kallon hotunan da yakeyi "Sister" shine sunan da ya bata,wanda ya tabbatar bata taba ganin hakan ya sanya mata ba. Doguwar numfashi yaja ya sauke qafansa da a dazu take daya saman daya ya gyara zamansa yana tunanin yadda zai kaucewa doguwar waya da ita,don a yanzun yana da buqatar lokacinsa qwarai,akwai abubuwa kuma masu muhimmanci da har yanzu bai gamasu ba. Yana shirin dagawa ta katse,yana kuma yunqurin bin kiran wani kiran nata ya shigo,sai ya daga yana saka wayar a kunnensa "Hello" ta fada cikin karyayyar muryarta "Assalamualaikum" ya furta kaman yadda ya saba a duk sanda zai daga waya. Gyaran murya tayi kadan tana tuno kuskurenta,yasha gyara mata amma saboda sabo tana mantawa. "Wa'alaikumussalam........zuciyata tanata gayamin cewa da gaske yaa maina bai damu dani ba" ta fadi har tsakiyar zuciyarta kalaman suna fita,tana kuma ji da gasken bai damu da ita din ba. "Kada kice haka mana.......ya mummy take?" "Tana lafiya,amma wunin yau na cikata taf da qorafi a kanka,har sai da daddy ma yaji hakan" idonsa yadan rufe kadan,bayason abinda mahaifinta zai ga kaman bai damu da rayuwar diyarsa ba,diyarsa mace guda daya daya dorawa dukkan buri da gatan duniya "Me yasa?" Ya tambayeta shima "Saboda abinda idanu da zuciyata suke gani kenan.......yaa maina......inaso ka bani dama na shiga rayuwarka sosai......nayi maka alqawarin baka dukkan farinciki da kuma soyayya,ka bani dama na soka yadda ya kamata,soyayyata kadai zata samar maka da kalar farincikin da baka taba riskar irinsa ba" A yadda take maganar ya shanshano tana fesar dasu ne da gaske daga zuciyarta,yaji mata babu dadi sosai,ya kuma kasa gane sai yaushe zata fahimci inda shi yafi karkata ne?,sai yaushe zata fahimci pretending da reality?. "Wannan damar da kike magana a kanta sai nake gani kamar na baki ko?......but duk da haka kiyi tunani da kyau laila....karkiyi pushing kanki zuwa abinda zai dinga hurting mind dinki..... please laila" ya fada cikin kwantar da murya yana fatan kalamansa masu harshen damo zasu warware cikin kwanyarta har ta fuskanci ina ya sanya gaba. "Ya maina" ta furta a marairaice "Laila" shima ya kirata da salon murya kaman me begging wanda ya furta sunan ne yana bude dukka idanuwansa,idanuwan da basu sauka a ko ina ba sai a kanta sanda take fitowa da qawataccen kwandon da aka saqashi da wani kalar ciyawar turawa me azabar kyau kalar green. Sanda ta sanya dukka qafafunta waje zuwa cikin falon taji fitar sunan fes daga bakinsa,bata gama fahimtar waye a wajen ba sai data kammala fitowar daidai lokacin da ya aza nasa idanun cikin nata. Janye kallon nata tayi daga kansa,ta kuma dauke kanta zuwa gefe zuciyarta na ayyana mata yau tayi baqar rana. "Zan kiraki later" ya furta a nutse "Is okay....... but ka cika alqawari" "Zan qoqarta" ya sake amsa mata a gajarce yana zame wayar daga kunnensa. Zuwa lokacin har ta kusa qofar falon da nutsatsen takunta tamkar ma batasan da wata halitta a falon ba. Bai debe idanunsa daga kallonta ba har sai data kammala ficewar,sai ya maida idon nasa ya lumshe yana jin wani iri a zuciyarsa. Ko ba komai,koda bata kuma sanshi ba gaba ai take dashi ko?,kuma ya cancanci gaisuwa "Kana nan har yanzu?" Ya tsinci muryar ama abinda ya sanyashi ware idanunsa a hankali sannan kuma ya miqe tsaye yana duban ama din "Ina jiran fitowarki ama" "Lafiya" ta jefa masa tambayar tana duban qwayar idanunsa da ta sauya launi,alama qwaya daya tak dake nuna somi somin bacin ransa kenan "No.....ba komai, I can't take my lunch bakya kusa" ya fadi yana shafa sumar kansa. Komai da ya faru kusan a kan idanunta ya kasance,tun fitowar sultana daga kitchen har zuwa ficewarta daga falon. Idan akwai abu daya da ama keson sultana da gyara a yanzun shine gaida maina,badon komai ba sai don idanun su batoul,kuma batajin zata bar haka yaci gaba da tafiya kodon tarbiyyar yaran "To bismillah mana" ta furta tana nuna masa table din ba tare da tasan tayi hakan ba. Da sauri ya daga idanunsa ya dubeta,yau din ama ke masa magana haka a tausashe tamkar shekarun baya da yake little maina dinsa?. Wani abu me sanyi ya tsarga ta tsakiyar bacin ransa,sai yaji zafin da zuciyarsa ta fara yana raguwa. "To mu qarasa ama" ya amsa mata yana janye mata wata qaraman kujera daga hanya. Fuska yaga tadan bata "Ka fara yin gaba mana". Yadda tayi maganar ya kusa bashi dariya,wato ta gano kanta da kanta,wannan tausayin dake danqare a zuciyarta yana don fallasa kanta,ita kuma ba yanzu ba,yanzun bata shirya barinsa ya fahimci haka ba,tanaso yasan martabar sultana sosai.....tanason yaji ciwo akan 'ya'yansa,tana so kuma PLAN dinta da zai kaishi ga jin wannan ciwon ya tafi dai dai. Shikam ko iya haka a wannan daren ta biyashi,don haka ya soma takawa har zuwa wajen dining din,yaja mata kujera yana jiran isowarta ba tare da shi ya zauna ba. Key ta zura ta bude sassan aba tunda tasan baya nan,ta dauki kwandon tana shiga falon da sallama duk kuwa da tasan ba kowa a ciki. Tana qoqarin jera ma aba abinci fuskarsa tana mata yawo cikin idanunta "Ya salam.....ya salam" ta furta tana yarfar da hannu,ko kadan ko alama batason tunawa da sunansa bare ta dinga ganin gilmawar fuskarsa,wannan ya sanya take jin dadi sosai yadda take killace kanta "Mugu" ta fadi qasa qasa tana murguda qaramin bakinta,tamkar wanda takeyi don shi yana zaune a wajen. _"Laila........zan kiraki later"_.ta tuna kalaman guda biyu da taji yana furtawa sanda take fitowar. Siririn tsaki taja tana tabe baki "Yo daman mutumin da yabar gida ya tafi yawon duniya shekara biyar aiba abun mamaki bane hakan ta faru dashi" ta samu kanta da fadi qasan zuciyarta. Sai kuma ta sake jan tsakin zuciyarta na mata wani sabon qunar "Me ya kaika jiyo abinda bais shafeka ba?" Tace da kunnenta cikin jin haushi jiyo sautinsa ma da tayi har ta jiyo wadannan kalaman. Tsakin dai ta kuma,ita in banda ama da bata jera mata nata tuwon ba bataga abinda zai maidata sassan ba,amma dole ta koma din,ama ta cancanci dukkan wata kulawa,domin itama babu wani nau'in kulawa da bata bata ba sanda take da matuqar buqatar hakan. "Ama me zan zuba miki?" Ya tambayeta bayan ya tabbatar ta zauna. Wannan din al'adarsa ce dama tun ba yau ba,daya dawo kuma bai manta da ita ba yaci gaba "Nan duk abinda zanci yanzu diyata zata kawomin tuwon data yi min". Maganarta kaman jirwaye me kama da wanka tayi masa,ko bata fada ba yasan tana nufin sultana,don haka sai ya koma ya zauna ya rungume hannayensa yana jiran dawowarta. Da wannan muryartata dai da bata taba bacewa kunnuwansa da kuma mafarkansa ba ta sake sallama a falon. Dukka tsokar zuciyarsa ta motsa,don kafin ta iso jarabbaben qamshin nan nata da baisan yaushe ta juye haka ba y soma riskarsa. Kamar zuciyarsa tana narkewa haka yaji sanda takunta ke isowa inda suke,yana muradin juyawa ya kalli takunta da kyau......yanason ganin takun tafiyar wannan sultanar shine har yanzu ko kuma ya sauya?,amma haka kawai cikin jikinsa yake jin kamar ama na ankare da duk motsinsa,wannan ya sanya dole ya cinye wannan da jawo wayarsa ya buda yana ci gaba da duba Instagram dinsa. "Kin kammala?" Ama ta tambayeta sanda ta iso wajen tana maida al'amarinsa gefe guda gami da tattara hankalinta akan ama kawai "Eh ama" ta bata amsa tana ajiye na ama din data fito dasu daga kitchen ta ajjiye qasan dining din "Sannu da qoqari,ban kula bama ashe abincin yana kusa dani" dan qaramin murmushi maras sauti tayi tana bude warmer's din "Sultana" ama ta kira sunanta da wani sauti da yaja hankulansu dukka su biyun,saidai still dai shi din bai kallesu ba yana ci gaba da danna wayarsa tare da qoqarin kokawa da sabon yanayin da yakeji a dukka sassan jiki da zuciyarsa "Naama ama" "Kin tuna?,duk garin kafiran da ma'aiki yaci da yaqi yana ci gaba da girmamawa dattawan kafiran?,ya kuma ce maja duk wanda baya girmama manya baya kuma tausayin qanana na qasa dashi tabbas baya cikinmu?" Fes ta karanci karatun ama din,saita sadda kai a karon farko taji kunyar ama din ta dan kamata "Kiyi haquri ama" "Ba laifi kikayi ba" ta tareta da wannan amsar fuskarta Na bayyanar da zallar jin dadinta. Cikin jin wani irin nauyi da takura tadan juya jikinta sassansa kadan. A zahiri wayarsa yake dannawa,yanayinsa sai ya tuna mata da shekarun baya,sanda take gaidashi yake bawa banza ajiyarta,bata gaidashi ba kuma ya zam wani laifi me girma,a zuciyarta ta dinga jin kamar ta bace daga wajen don ta kubucewa gaidashin,amma kuma ama tafi gaban haka daga gareta "Barka da dare.....ina yini" ta hada gaisuwar dukka gaba daya. Kansa ya daga yana kafeta da lion eyes dinsa "Barka kadai alhmdlh" ya amsa mata shima,sai shigowar batoul da benazeer ya kawo qarshen gaisuwar qeqe da qeqen. Kamar ko yaushe da rigimarsu suka shigo,ama ce ta karbi rabiyar fadan. Tanaso ta wuce tabar wajen amma sai taga rashin dacewar hakan. Da qyar ama ta raba fadan,yana zaune yana murmushi,saboda hakan bai tuna masa komai ba sai fadan attah da almu. Bata ko bi ta kansu warning daya take basu a sannan,amma sai gata yanzun tana lalacewa wajen raba fadan jikoki,wannan kadai ya isa ya gaya masa yawan adadin son da take ma yaran. Ta qasan idanunsa yake satar kallonta yana kuma qare mata kallo son ranshi ba tare da kowa dake wajen ya karanci hakan ba. Totally wannan ba sultana bane hatta da zara zaran yatsun hannunta sun sauya. Ta zama wata miskila ta gaske ba da ruwanta da abinda ke faruwa a kewayenta,don ko yanxun ma a zaune take tsaf saman kujera tana danna waya sanda ama ke rabon rigimar yaran. Qarar wayarsa ne ya katse masa daddadan yanayin,iya morewa kallonta kawai daya fara ya saukar masa da nishadi. A kasalance ya sanya hannu ya dauki wayar dake gabansa,sai ta tsinci kanta da satar wayar da kallo,ta janye idanunta da sauri tana miqewa. Buqatarta tabar wajen,sam batason kunnuwanta su dinga ma sha'aninsa shishshigi,hakan tamkar tana batawa kanta da tunaninta lokaci ne,da hakan gwara taje ta karanta abu qwaya daya da zai zameta jagora a aikin jaridarta "Na fara jin bacci ne ama" yaji tana bawa ama din amsa sanda ta tambayeta sai ina?,sai ya janye idanunsa yana maidawa kan wayar. Suhail ne yake kira,ya kara wayar a kunnensa lokacin da take sauka a hankali daga step din area din,ya dauka dubansa daga kanta a hankali daya fahimci tana shirin hardewa "Surprise" suhail ya soma fada yana dan dariya "For what?" "Ina nijer" "Bana wasa dakai" ya fadi kansa tsaye "Tuwo ne a idonka da baka fahimci code din NIJER ne a number na ba?" "Ma sha Allah..... but munyi da kai ni xan daukoka a airport fa?" "Kada ka damu,tunda na sauka a qasar nan karsashina ya qaru......haka kawai jikina yake bani kaman zanga crush dina fa, yarinyar haram" dogon tsaki maina yaja,har ransa yana jin haushin tada zancan,baisan me yasa ba,amma yana haushin yaga namiji na yima mata rawan qafa. A nashi ra'ayin ba kowacce mace namiji ya kamata ya budewa zuciyarsa ba,qalilan ne suka cancanta "Zaka iya qaryata zancena ko ka gasgata,nidai gaskiya na gaya maka......ka turon Adress zan taddaka har gida,zan baro niamy gobe in sha Allah" "Karka damu,kana isowa airport ka kirani zanzo na daukeka" "Yayi......godiya,sai na qaraso". *_Tofa,ga suhail nan zuwa,ko ya zata kaya?_**_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 page 67 Tsaye yake jikin motarshi dake cikin tashi da saukar jirage na garin marad'i cikin shigar cikakken buzu da ta fidda sigar kyau da cikakkiyar kamalar da yake dashi,yadda rawanin ya zaunawa kansa kadai abun burgewa ne,kyawawan idanunsa da hancinsa da bai cika tsaho ba sun zauna das saman fuskarsa. Sumar fuskarsa na kwance luf, zakayi tsammanin usulinsa balarabe ne bawai ba'abzine ba. Wayarsa ce a hannunsa yana sauraren laila,sam ya rasa amsar da zaya bata,daga jiya zuwa yau gaba daya ta soma rikice masa kamar wadda ake mintsinin zuciyarta "Na fara kaiwa stage din da bazan iya juriya ba......ban taba cewa inason kowanne namiji ba saikai please maina......ina gaya maka da gaske ne,i really love you......kuma zaka iya ganina a nijer any moment" zagayayyun lion eyes dinsa yadan fidda kadan,tazo nijer ta qara wuta fetur?,yana kan lallaba aba fa har yanzu?,yace masa meye?. "Cool down laila.....na fahimceki,amma banason kina zafafawa haka da yawa......kibi komai a sannu" idanunta ta lumshe tana dora hannunta saman qirjinta hadi da fidda siririyar iska daga bakinta "Don bakasan yadda nakeji bane ya haidar......shi yasa kake cewa haka,ni dama kawai nake buqata ka bani cikij rayuwarka,basai ka tayani ba" "Ki nutsu please......ga suhail can ya iso,zan daukeshi mu wuce gida,zamuyi waya in sha Allah" "Nadai kiraka as usual" ta fadi murmushin yaqe yana fita daga fuskarta,sai ya rasa amsar da zaya bata. Cikin kafatanin rayuwarsa sam sam bai bata soyayya ba,bai kuma san ta yadda zai tattaro wannan kaya da laila keson aza masa ba,shi dukka dabararsa akan aikinsa take,a kanta ta qare,so baqo ne shi ta wannan fannin "Ba damuwa,kiranma wata damar ce,na gode da ita,bye......take care dear" ta furta a hankali tana katse kiran. Iska ya furzar shima yana gimtse kiran,ya sake daga kai yana hango tahowar suhail,sai ya dan tashi daga jikin motar ya soma nufarsa tare da qoqarin sanya murmushi kan fuskarsa. Wayar ta ajjiye gefe tana cusa yatsunta cikin sumarta hadi da jan iska sosai cikin hunhunta. A hankali Sarah ta miqa hannu ta dafa ta "Duka wannan daga qafan da zagaye zagayen idan nice bazan iya shi ba......aliyyu yana ganin kima da martabar mahaifinki ya yayanki,me yasa ba zakiyi amfani dasu ba?,ina kyautata zaton wannan kadai ce hanya da zaki samu yadda kikeso ba wani dogon kwana kwana,ba cutar dashi kikayi ba ai,sonshi kike,kuma kina da tabbas a soyayyar da kikeyi masa,sannan kuma zaki bashi duk wata kulawa data dace,anayin aurenku ya samu yadda yakeso namiji ne fa,nan da nan zai mance matsayarsa ya biye miki kuyi soyayyarku me dadi" daga fuskarta Laila tayi tana duban sarah "Nafison ya nutsu ya gamsu da kanshi kafin akai wannan matakin sarah......amma kuma na fara sarewa da haka, zuciya ta ina jin tana min ciwo lokaci lokaci,inajin zaiyi wuya gaba kadan muddin ban shawo kanshi ba......komai zai ya samuna" ido sarah ta fiddo "Me yasa?,da gatanki?,kuma da chance hundred percent na samunsa a hannunki ki bari ciwo ya kamaki?,ni zan gayawa mummy maganar nan tabbas" ta fadi tana miqewa. Caraf sarah tayi ta riqo hannunta "Kada kiyi haka sarah don Allah,aminci na dake yasa na gaya miki sirrin da ya shafeni,a zaton mummy yayi accepting soyayya na ne, soyayya mukeyi,please ki barsu a haka" a sanyaye ta dawo ta zauna,saita kasa cewa komai daga ita har laila din. Hannu ya miqawa suhail sukayi shacking,idanun suhail a kanshi ya soma magana "Kai mutumina......ya naga kaman nijer na shirin karbarka fiye da ko ina?,kaga yadda kake zama fresh?" Dan tureshi baya kadan yayi yana amsar luggage dinsa ya soma ja sannan ya bashi amsa "Indai kaine zaka fadi fiye da haka,ka wuce muje ko na tafi da iya jakarka" ya amsashi yana fara takawa don barin wajen "Baqonka annabinka dai,muddin kace zakamin wannan halin naka zan koma inda na fito" "Ga fili ga me doki ai" ya kuma bashi amsa,sai suhail din ya saki dariya sosai. Indai shida maina ne sun saba irin haka,sardauna ne sam baya jurewa irin wannan wasan,wani lokacima shi yake zama dan rabiyar fada a tsakaninsu. "Bayan wancan BMW din wannan kuma yaushe ka siyeta?" Suhail ya furta bayan ya zauna a seat me zaman banza yana shafa gaban motar,saboda sosai ta tafi dashi,sabuwar shigowa ce da duka duka batayi wata biyar da bayyana ba "A satinnan,wannan ne hawa na na biyu gaba daya" ya amsa amsa yana tada motar,sai suka zarce da hirar motar,qirar motar na sake burge suhail din don shima ma'abocin son hawa motoci ne. Hayaniyarsu benazeer ne ya farkar da ita daga baccin data koma a sassan ama,hayaniyar tasun ce kuma ta sanyata baro sassan bibi tunda safe ta dawo sashen ama din,sai gashi bata tsira ba sun sake biyota da kalar rigimarsu. Qaramin tsaki taja tana saukowa daga gado,ta jawo hularta data dace da cotton night gown dinta me kauri ta lullube gashinta me santsi,ta zura flip floppy dinta ta miqe tana nufar qofa,sai tayi punishing nasu yau,tabarar da sukeyi tanason ta fara yawa hakanan. Tana bude qofar dakin nata ta hangesu suna fita daga lobby din,duka su biyun kamar ko yaushe kamar kuma kowanne lokaci sanye da pink pyjamas masu wando kawunansu fake da tafkeken pink ribbon da yazo cikin mahadin kayan, qafafunsu wasu lausasan slippers ne rufaffu duka cikin set din kayan sukazo,wannan kusan shine shigarsu daga dare zuwa safiya,tana kuma kalla tasan lallai basuyi wanka ba sai uban karadi da suka cika gidan dashi,basa ma duba cewa ama bata jin dadin. Maida qofar tayi ta rufe bayan ta fito daga dakin,kai tsaye tabi qofar fita daga lobby din inda zata sadata da falo. A tsaye ta hangesu a dining area kowannensu dauke da mug dinsa wanda ke dauke da sunansa baro baro a jiki,tanja na tsaye tana qoqarin hada musu juya madarar data zuba musu a oat,su kuma baki abun magana sai sambada mata zance sukeyi *BB" ta kirasu da sunan da goumar ne ya fara rada musu,zaiyi kuma wahala kaji ta kirasu dashi din. A tare suka daga kai suna dubanta,sai ta daga hannu ta yafitosu,ba jinkiri suka soma saukowa daga dining din suna nufota. Kamar yadda suka koya suka kuma tashi dashi,dukkansu rusunawa sukayi suna gaidata da harshen faransanci da ya zauna a bakunansu "bonjour, tu t'es réveillé sain et sauf ?" "bonne santé" ta amsa musu tana murza goshinta saboda hatta gaisuwan ma kowa so yake yaga shine ya fara yi mata "Ihun mene ne kukeyi haka?,kowa yana bacci?" Junansu suka kalla,don a wajensu yanzun sha dayan safiya ba za'a kirata safiya ba,basu iya baccin safe ba Sam,barsu da baccin rana dai "Batoul ce......" "Allah bani bace aunty........bena" "c'est assez(ya isa haka)" ta fadi yana daga musu dogayen yatsunta,don ta tabbatar idannta tsaya tana kallonsu sunyita yi kenan. "Banason na sakejin hayaniya,yau zamuje gidan tante aminata da tante yasmine......but.....duk wanda ya qara cika mana kunne zaiyi gidan gidan nan ne" murna sosai ta kamasu harda tsallensu,duk kuwa da cewa already goumar ya kaisu. Qarasowa tanja tayi tana murmushi "Ai gwara kije din gaskiya kafin lokaci ya qure" "In sha Allah yau zanbi mutanen gidan......ina kwana tanja?" "Kin tashi lafiya?" "Lafiya alhamdulillah ya yaran?" Ta tambayi tanja data fara raba musu oat din,don kullum tanjan takan tambaya kwanansu tare dayi musu sannu ko ita ko ama "Lafiya qalau alhmdlh" "Ma sha Allah......ama bata samu fitowa bane?" "Tana ciki kam,tunda ta fito tare dasu batoul ta barsu a nan" "Badai jikin ba?" Ta tambayi tanja cikin kulawa tana takawa zuwa tsakiyar falon tana qoqarin daukan madarar dake ajjiye tana tsatsafar sanyi,da alama an ajjiyeta ne tasha iska. A kwanakin shan madarar ne yakeson dawo mata sosai,wani abu data bawa shekaru sosai rabonta dashi "A'ah jiki alhamdulillah mana,naji ma tana waya dazun kamar tace zata leqa shagonsu benazeer don tana da lissafe lissafe dasu" "To alhamdulillah,bari na dubata " ta furta tana wucewa kai tsaye zuwa dakinta dake benen saman sashen,don tasan aba baya nan,tun daren jiya sukayi sallama akwai gajeruwar seminar da zasuyi,koda kuma yana nan din sunfi zama a sassansa dake manne da babban falon ama din. Da sallama ta tura dakin ta shiga,ama dake zare tattausan socks din dake qafarta ta amsa mata,idanunta akan sultana din. Duk sanda zata kalli fuskarta sai ta samu kanta da yi mata addu'a,Allah ya dawwamar da farinciki cikin rayuwarta,dukkan wani qalubale da cakwakiya da basu da mafita a kanta Allah ya bada hanyar warewarta. Da kwantacciyar fara'arnan me laushi saman fuskarta ta qarasa gefan sofa bed din ama ta rusuna har qasa kaman yadda ya zame mata al'ada tana gaidata,can qasan zuciyarta tana jin wani dan nauyinta da a yanzun takanji kuma har yanzun batasan meye dalilin hakan ba,tadai alaqanta hakan da girma da kuma gankali dake sake lulluneta kullum kwanan duniya,sannan uwa uba takan tuna da wasu abubuwa da suka faru tun kan cikinsu benazeer din zuwa haifesu da tayi. Bayan bibi da tanja da tayi rainonta duk gidan ama itace mace ta biyu data taba ganin jikinta zahiri,tayi biqinta ta kuma yi jegonta kamar jaririya.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 68 sannan ta bita da tambayar jikin nata "Alhamdulillah na samu sauqi" itama ta amsata cikin kulawa "Allah ya qara afuwa yasa kaffara" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ama ta amsa mata tana shafa cleanser a fatarta,da alama shirin shiga wanka takeyi. Tadan dauki mintuna suna tattaunawa da ama din wanda kusan duka akan komawarsu ne da kwanaki kadan suka rage,sannan ta miqe tana cewa "Zanyi wanka ama,yau din naji kaman yaran gidan nan suna cewa zasu gidansu aminata,zan daure na leqa kada mu wuce banje ba,bansan kuma sai yaushe zan dawo ba" kai ama ta gyada "Eh gaskiya yana da kyau,saura kadan atta ya karbi key din motar da kike hawa,na hanashi nace ya dauki wata wannan din duk bubbugemin mota yakeyi,bai iya tuqi a hankali ba" murmushi ta danyi kadan "Da kin bar masa ama,nima tunani nakeyi nabi motocin gida" "A'ah bashi yiwuwa,nex time idan mun dawo ma dole a siya mota a ajjiye miki,ko don su benazeer da suke tasowa" ama tayi maganar tana cirar key din ta miqa mata "Idan bakijin driving ma ai almu yana nan,saiku fita tare" hannu biyu ta saka ta karba,koda yaushe kulawar ama a kanta daban take,ta banbanta da wadda take bawa 'ya'yan cikinta ma. Tana komawa daki ta wuce bandaki,don tana fitowa suka hadu da ummeeta dake shaida mata "Tante.....ba zamu wuce sha biyu zuwa daya ba zamu dawo" tace da ita. Cikin nutsuwa ta fidda bath set dinta,tsadajjen shower gel da sauran tarkacen wanka wanda kusan ama ce nauyin komai,sai daga bisani da tayi hankali ta soma saving abinda take samu take wuf tayi wasu hidindimun kafin ama din takai ga yi mata. A nutse ya wuce gate din farko na gidan,ya kuma zarce sashen ajiyar motoci dake gidan ya fara yiwa motar tasa mazauni. Tunda suka shigo gidan suhail ya kasa cewa komai,yana dai bin sassa sassa na gidan da kallo yana mamakin ya za'a yi mutumin da ya fito daga mansion house na alfarma irin wannan ya zabi yayi rayuwa qarqashin wani kuma yazo masa a yaronsa?. Sanda ya kashe motar yake qoqarin cire seatbelt suhail ya kasa haquri lokacin da wasu security dake sanye da uniform suka gaidashi suka wuce "Mamaki na yaketa kamani fa haidar,na kasa nayi shuru" qaramin murmushi na gefan baki maina ya saki,ya sani dole ne suyi mamaki,tsahon zamansu tare shekara kusan hudu ba wanda yasan asalin wayeshi,ba kuma wanda yasan komai daya danganceshi,illa dai ama aba da sunan sultana da suka sani,shima din cikin mafarkanshi ne da yakeyi wadanda sukan bayyana masana a zahiri wani lokaci idan yana baccin har ya ambaci sunansu. "Zaka sani ai yanzun ko?" "Sardauna zaifi kowa yin mamaki" suhail ya fadi yana bude murfin motar kamar yadda maina ya bude na bangarensa. Cikin atamfa ta shirya kanta riga da skirt me launin army green da adon light orange kadan a jiki,ya lullube kanta da Chantilly veil daya dace da shigarta,siraran abun hannu da wuya ta sanya da sue mahadi da agogon da zoben hannunta,kaman yadda jakarta da takalminta dukka suka kasance na kamfanin Hermes brand hakanan turarenta dukka na kamfanin ne. Kusan komai nata tafi ta'ammali da wadannan Brand din guda biyu Hermes ko saint Laurent. Sosai fuskarta ta fita das cikin daurinta data kawoshi gaban goshi,qirar jikinta ta fita da kyau saboda yadda driver din ya qware sosai wajen fidda shape din dinki,ta fita a bahaushiyar nigeria zam,ta kuma yi kyau ainun,saboda shiga ce da ba kasafai ta fiya yinta ba. Tafi ganewa dogayen riguna a yanzun abayas sai English wears masu skirt ko budadden wando irinsu palazzo. A nutse ta fito daga dakinta ta samu ama tana shirin yin makararren breakfast dinta saboda bata sauko da wuri ba. Dubanta ama din tayi,a yau din karon farko taji kishi ya darsu a ranta. Irin kyan da sultana din tayi tasan ba kowanne namiji bane zai iya dora idanu a kanta yaso janyewa ba tare daya sake marmarin kallonta ba,komai nata cif da cif Masha Allah,kama daga yanayin tsaho da halittar qibar jiki,batayi qiba ba kaman yadda sam sam bata da rama,idanunta sun sake fitowa sun kuma qara wani haske sosai,santala santalan qafafunta da hannayenta dake dauke da shimfidaddiyar fata dake nuna zallar hutu da ta samu "Tun dazun suke jiranki,amma nace musu suyi gaba baki kammala shiryawa ba,su benazeer din ma maybe sun bisu,don an shiryasu,nasan kuma zaiyi wuya su iya tsayawa jiranki" "Shikenan kam,na huta da rabiyar fada" ta furta tana dariya. Murmushi ama ta saki tana mata fatan dawowa lafiya tare da binta da kallo. Ajiyar zuciya ama ta sauke sanda ta fita din,a wannan yanayin ta tabbatar idan haidar ya ganta zaiyi wuya ya iya shanyewa,tasan tsananin kishinsa,wanda shine yayi musabbabin tilastawa qannensa sanya atamfa ya kuma sanya aka bayar da duk wani English wears nasu,suka kuma dinga fada da samun sabani da sultana. "Mu wuce ka fara hutawa tukunna saika shiga cikin gidan" maina yace da suhail yana nufar sassansa "A'ah,a ina ake haka?,kazo baqunta kaqi fara duba kowa?,fara kaini wajen grandma tukunna sai mu wuce wajen ama din" qaramin murmushi maina ya saki "Bibi rigima,Allah yasa ta barmu mu fito da wuri,kasan dai zuwa yamma zamu shiga company mu duba engines dinnan ko?" "Ina sane" "Alright" ya furta a taqaice,sai yayi kiran daya daga cikin security din gidan,ya bashi luggage din hade da key din sassan nasa yace ya saka masa a ciki yabar gurin a bude yanzu zai shiga. Tare suka jero har suka isa sasaan bibi,sun sameta a falo tana ta fada,fadan kuma da maina yasan rigima ce kawai irin tata,kayan sawa take warewa tana fadin wannan batason ayi musu guga,a qyale mata abunta haka "Ayita danawa kaya wuta b gaira ba dalili" ta sake jaddada mitarta daidai sanda suka shigo falon,ta daga kai tana amsa sallamarsu. Tun asali mutum ce meson baqi da kuma girmamasu,wannan ya sanya ganin maina tare da wani saita dan saki fuska,maina din ya qaraso kan kayan yana duban yaron dake musu gugar "Kwashe kayan gaba daya,kaje ka fidda duk wanda tace bataso a goge din a dawo dashi ciki" "In sha Allah" matashin ma'aikacin ya fadi yana duqawa ya tattare kayan yana fita dasu,sai ta koma ta zauna idanunta akan suhail "A ina ka sake samo mana bafullatani?" Maganar ta bawa suhail mamaki, baiyi zaton zata gano bafulatani bane shi nan da nan,lallai tsohuwar nada kula sosai "Hala bai baki labarina ba?" "Shin kaine suhail?" Ta jefa masa tambayar sai ya qarasa sakin murmushi "Nine bibi,barka da warhaka" ya soma gaidata cikin girmamawa yana murmushi,qarasa sakin fuskarta tayi tana amsawa,sai tahau shelanta kiran masu aikinta "Nayi baqo,a kawo masa abun tabawa". Tace da masu aikin nata. Yadda suke gaisawar kamar sun jima da sanin juna ya bawa maina mamaki,daga dai yanayin yadda ta saki jiki da suhail har hira na gudana tsakaninsu ya tabbatarwa maina haduwar jini ta qullu tsakanin bibi da suhail,sai maina kawai ya sanya kunne abinsa yana jin yadda suhail ke kwasar bibi suna hira,da yake shima gwanin barkwanci ne idan taku tazo daya,itama kuma ama din tana da son barkwancin. Har ta sanya key ta bude motar ta kuma zura jakarta a ciki sai ta tuna aminata tace tana da ajjiya wajen bibi. Murfin ta maida ta rufe,ta soma takawa zuwa cikin gidan tana gyara yafen mayafinta. Dab da zata shiga sasaan bilki data karbo maqullan sassan baqi a wajen bibin za'a gyara ta fito,ta bawa sultana hanya tana fadin "Kece qarshen tafiya kuma kece wadda kadai bata taba zuwa ba" murmushi sultana ta saki "Yanzun zan wuce in sha Allah,yauwa......don Allah ina samun daffafiyar madara idan na dawo?" "In sha Allah za'a hadata" "Na gode,bari na qarasa" ta fadi tana sanya kai falon. "Shekar kusan hudu bibi wannan jikan naki gashinan,bai tab......." Maganar ta tsaye masa a maqoshi sanda sassanyan muryarta tayi sallama cikin falon. Kusan a tare idanunsu suka sauka a kanta,suhail da maina,mabanbantan feelings kuma suka sauka saman zuciyar kowannensu. Da kallo daya tak ya gama karance shigar dake a jikinta,don shi din mutum ne me kaifin basirar dauke komai hadi da ankara,sai ya maida idanunsa ya lumshe zuciyarsa tana bugawa,wani irin kishi yana mintsinarsa har kaman zai kasa controlling kansa. Suhail kuwa gaba daya idanunsa ya zube mata,sam bata lura dasu ba dukka su biyun har sai data qaraso tsakiyar falon. Kasa haquri yayi yakai hannu yana tabo maina zuciyarsa tana bugawa. Fes ya bude idanun nasa,saidai basu sauka a ko ina ba sai akan sultanar. Sarqewa da tafiyarta ya fara yi ya tabbatar mata da idanu da yawa a kanta,tun shigowarta falon qamshinsa ya shaida mata akwai mutum ta wajen,inma yazo ya tafu ko yana zaune a wajen,ta watsa fararen idanunta cikin falon don batason tabi ta gefan da yake yayin da take cema bibi "Bibi ta.....zan wuce duk sun tafi sun barni,saqon aminata". Kaiwa qarshen maganarta yayi daidai da tuntube da tayi hakanan "Subhanallah......kula kada ki fadi" suhail ya fada da hanzari har yana dagowa daga saman kujerar da yake kai kaman zai tallafe ta. Maganar da yayin yasa ta lura da zamansa a wajen,ta juya fuskarta sashensa ta masa kallo daya tak sannan ta janye idanunta tana ji a jikinta kamar tasan fuskar,kamar sun taba haduwa a wani waje daban taci gaba da takawa gaban bibi. Dukka kaifafan idanunsa ya zubewa suhail,motsin da yayi kadai a yanzun ya harbawa maina kokwanto da shakka a kansa cikin zuciyarsa "Why he was so bothered?,don tayi tuntube meye na nuna damuwa qarara haka?" Ya fadi a ransa yana duban tsakiyar qwayar idanun suhail din. Idan ya lura,idan kuma idanunsa da gaske suke nuna masa to tabbas kallonsa nakan sultana,kuma idanunsa na manne da ita tana zama a gefen bibi *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 69 "Dama ni ke nake jira,ki shiga dakina daga cikin cupboards din kusa da bandaki ki bude zakiga baqin leda ki ciro,bansan meye ne a ciki ba aka qulleshi haka" murmushi ta saki wanda ya sake qarawa fuskarta ainihin kyau,murmushin da ya sanya suhail murmusawa shima yana jin tana qara burgeshi da duk wani motsinta,ya kuma sanya maina lumshe ido yana jin bugun zuciyarsa yana qaruwa musamman da ya maida kallonsa kan suhail yaga yadda ya maida hankali a kanta "Ba fada meye ya kawo gaba?" Suhail ya kasa jurewa ya furta,maganar tashi a karo na biyu ta sakata waiwayowa tana kallonsa "Sorry?" Ta furta da alamun rashin ganeshi qarara a fuskarta,saita juya zata wuce ciki amma idanunta sukayi kuskuren fadawa cikin na maina. Janye idon nata tayi da sauri hadi da fadin "Barka da rana,ina wuni" ta furta masa sabo tunawa da girman ama a wajenta,gaisuwar duk a hade lokaci guda tana wucewa ciki "Alhamdulillah" yayi qarfin halin fada yana ci gaba da monitoring suhail har sanda ta wuce ciki. Ajiyar zuciyar da suhail din ya saki dukka tsakanin bibi da maina saida suka dubeshi "Lafiya ko?" Bibi ta wani abu ya darsu a ranta ta fada tan kallon suhail, murmushin qarfin hali ya saki yana shafa kansa "Ba komai,kawai akwai wani abuna ne daya bata nake tunanin kamar na tuno inda yake" "to alhamdulillah,ai haka akeso" bibi ta fadi tana kawar da maganar gami da jefa masa wata tambayar,ya nutsu kuwa yana bata amsa tare da sake qanqan da kanshi,don yana da tabbacin zaiyi wuya sultana ba jikar bibi bace,daga kuma yadda bibi din ta amsheshi o bibbiyu tabbas alamu sun nuna yana cikin nasara. Ya matsu ta sake fitowa daga dakin ya samu yabi bayanta,a yau basai gobe ba zai sake gabatar mata da kanshi. Yadda ta kalleshi dai ya nuna sam bata ganeshi ba,amma jikinsa bai bashi haka ba yana ganin kawai jan aji ne irin na isassun mata irinta. Zafin da zuciyarsa ke masa ya sanyashi kasa ci gaba da zama a wajen,sai ya miqe tsam yana zube hannayensa a aljihun rigarshi "Ina zuwa?" Bibi ta daga kai tana kallonsa qwayar idanunsa na nuna tasirin fushi kadan kadan daga zuciyarsa "Zan samu ruwa nasha" ya bata amsa yana nufar hanyar kitchen. Taso ta dago wani abu,saboda indai ruwa ne gashinan a nan wajen gaban suhail,ta san maina din sosai,tasan kuma akwai abinda ya tadashi,uwa uba kuma ta karanci mugun kishin nan nasa kwance cikin idanunsa,taga kallon da suhail yabi sultana dashi,tayi imani wala'alla abinda take ganowa cikin idanun nasa yana da tasiri da wannan. Tasan halin 'yan kayanta sarai,tsoronta daya kada sanadin kallon ya sanya ya yiwa dan mutane diban karen mahaukaciya duk da matsayinsa na baqonsa. Freezer din ya bude ya ciro ruwan gora me sanyi har yana tsatsafa,ya balle murfin ya kafa kai ya soma kwankwada. Duk kuwa da cewa shan ruwan sanyi sam baya cikin dabi'arsa amma sai daya shanye shi tasa sannan ya buga ribar ta daki kitchen cabinet din ta fado qasa,sanyin da yakeson ji a zuciyarsa bai sameshi ba kwata kwata,ya furzar da iska ya ciro handkerchief daga aljihunsa yana share zufan data tsatstsafo masa a goshinsa,sai ya juya kawai gadan gadan zuciya tana ingizashi yana fita a kitchen din. Daga qofar kitchen din yana hango bibi da suhail suna ci gaba da hirarsu abinsu. Wani abu ya tsaya masa a wuya daga kallon fuskar suhail kawai,abinda bai taba ji ba tsahon zaman tarensu. Kanshi ya kawar sannan ya nufi sashen dakin bibi din kansa tsaye,babu tsoro ko shayin bibi ta ganshi ko wani cikin masu aikinta. A nutse ya murda handle din qofar dakin sannan ya tura yana shiga. Tana duqe tana qoqarin jawo ledar tana mita qasa qasa yadda bakajin abinda take fada din sai dan sound na lallausar muryarta dake dan motsawa cikin dakin. Jingina yayi da qofa yana qare ma qugunta kallo wanda ya turo sosai saboda duqawar da tayi,gaba daya qamshinta ya cika dakin,wani irin lallausan qamshi me kwantar da zuciyan. Baisan ya akayi ba sai siriryar ajiyar zuciya data kubce masa,wani mahaukacin kishinta ya sake taso masa ya dinga ji kaman zuciyarsa zata zauce,wannan ya sakashi sakin hannayensa daya goye a qirjinsa ya soma takowa cikin dakin zuwa inda ta ajjiye handbag dinta da key din motar. Shaqar iska ta gaba da zatayi saita gauraya da qamshinsa,abinda ya haddasa mata mummunar faduwar gaba,ba shiri ta saki ledar data jawo din,ta miqe tsaye sosai sannan ta waiwayo a nutse fuskarta a dinke tsaf. Yana tsaye daga bayan nata,duka duka taku shida ne adadin tazarar dake tsakaninsu su. Idanunsu suka gauraya waje daya kaman yadda qamshin jikinsu ya cika dakin bibi din. Yadda take kallonsa fuska a hade haka shima,asalin fuskar maina take gani yanzun a tattare dashi. Dakiyar nan da hadaddiyar girar nan da yakan cure guri guda duk sanda zai musu hukunci,bakinsa yakan tsuke kadan a wancan LOKACIN to yanzun ma haka,saidai wannan karon siraran labban nasa dake da wani irin launi me kyau zagaye suke da gyarraren saje daga qasan habarsa zuwa qasan hancinsa. Haka kawai taji bugun zuciyarta ya sauya,sai ta janye idanunta tana gargadar zuciyarta da kada ta kuskura taji shakka ko tsoronsa,don haka sai ta juya tana yunqurin ci gaba da jawo ledar ba tare data ce masa kanzil ba,duk da yadda tsoro ya mamayeta,kwarjininsa a yau yakeson mamayar dukka qarfinta yakai qafafunta qas,abinda bata jin zata bada damar ya faru "Waye kika tambaya da kike shirin fita baki nemi izini na ba?" Har cikin kwanyarta taji tambayar ta mata banbarakwai,ta ciro ledar daidai lokacin,don haka ta miqe tsaye riqe da ledar tana fuskantarsa "Izinin wa kika nema?,ko kina rayuwa ne on your own?" Ya maimaita mata tambayar a karo na biyu. Dara daran fararen idanunta da hasken qwayayen dakin bibi ya qara haskawa,suka kuma fidda ainihin oily eyes dinta ta zuba saman fuskarsa. Qaramin bakinta ta motsa da niyyar maida masa da dumi,sai kuma dukka kalmomin data tattara don yaba masa suka fara sulalewa sunayin nasu guri,saboda takowar da yakeyi zuwa gareta ya haifar mata da fargaba. Batason ya sake taba jikinta ko ya sake kusanto inda yake,to amma kuma tana jin asarar tsaiwa bashi amsa. Duk taku daya idan yayi fargabarta ce take daduwa,amma kuma kaman wadda aka kafe a wajen ko aka qullewa baki taqi cewa dashi kanzil. Sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sosai sannan ya miqa hannunsa,miqawar data sanyata qanqame jikinta a tsorace. Tsaiwa yayi da abinda yayi niyyar yi din yana qarewa fuskarta kallo. Baby face dake dawo masa da shekarun baya fes cikin kwanyarsa, fuskar sultana sosai ta bayyana,har baisan sanda wani siririn murmushi maras sauti ya qwace masa ba,ga tsoro ga ban tsoro,ga tsiwa ga kuma tsoron hukunci. Tas ya zare mayafin daga jikinta,tana tsaye tana jin yadda kowanne sashe na mayafin ke fita a jikinta yana barinta gaya,sai daya gama zareshi duka sannan ya dunquleshi cikin hannunsa,yayi kaman zai cillar sai ya fasa,ya sanyashi saman kafadarsa, lallausan qamshinta kuwa yace salamu alaikum,yadan lumshe ido ya bude "Wannan din ba mayafin yafawa bane,duk randa kuma na sake ganinki dashi na rantse da Allah sai na hukuntaki ko a gaban waye" daga haka ya juya yana takawa a hankali,sai a sannan ta samu nasarar bude idanunta da suka cika da hawayen takaici tana binsa da kallo,tana mamakin kuma me zaiyi ta qofar bayan sassan bibi?,bazai fita ta normal qofa yadda kowa ke fita ba?,salon ayi zaton suna tare a dakin?,to ta yaya ma zata iya iya fita a haka ba mayafi,wanne kallo bibi da baqonta zasuyi mata?,bayan kuma ta tabbatar sunga shigowarsa?. Duk sai taji kunyar fita a hakan,ta koma ta bude wardrobe din bibi tana bincike ko zata samu wani abu da zata yafa itama tabi ta qofan bayan ta fice,don dai ba zata iya fita a haka ba. Allah ya taimaketa ta samu wani sabon mayafi a ledarsa,da alama cikin kyaututtukan da akewa bibi dinne cikin 'ya'yan 'yan uwa da kuma surukai saboda qarfafa zumunci. Sosai ya dace da kayan jikinta tamkar dama ta ajjiye ne saboda ita,ta farke ta yafa,sai taga yafi haskata ma akan wancan. Da sauri ta zari handbag dinta da ledar aminata ba tare data tsaya duba key din motar ba,burinta ta isa gidan ta kuma dawo da wuri,Allah Allah take kwanakin da zasu bar nijer ta cika ta fice daga qasar,ta gaji da ganinsa kwata kwata,ya soma shiga rayuwarta wanda ita kuma ba zata lamunta ba. Da yake tabar qofofin a bude ne sai ta bude front seat,ta zura hannunta da zummar ajjiye ledan,wanne tudu wanne gangare ta tsinci kanta a ciki, kafin ta gama daidaita nutsuwarta ya miqo hanunsa har yana shafar qirjinta ya jawo qofar ya rufe,abinda ya sanya numfashinta daukewa na wucin gadi. Wutar jikinsa ce shima ta dauke tsaf!,sai wani irin shock da ya ratsa kowacce jijiya ta jikinta yabi jininta,ya furzar da zazzafar iska daga bakinsa yana qoqarin dage dukka baqaqen glass din motar sama. Tsaf ya dagesu ya miqa hannu a kasalance ya kunna ac din motar sannan ya fara yunqurin tayar da ita. Sai a sannan hankalinta ya dawo gangar jikinta,tsoro sosai ya mamayeta,qamshinsu da numfashinsu kawai ke karakaina cikin motar,sai bugun da zuciyarta keyi wanda take kyautata zaton shi dake zauna a seat dinsa tana iya jiyowa. *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 70 Dukka dauriyarta ta tattaro cikin dakiya da son ragewa kanta tsoron dake damunta "Ban fahimci abinda kike shirin yi ba?,ina zaka kaini?" Ta tambayeshi tana qoqarin duban tsakiyar idanunsa. Da idanunsa da sukayi laushi qwarai saboda yadda qamshinta ke kassarashi ya kalleta "Shshshs......fyade zan miki" ya furta kalmar gatse gatse kansa tsaye. Karon farko ta janye idanunta daga kanshi tana jin wani nauyi yana ratsata. Karom farko da taji nauyi da girman kalmar har tsakiyar kanta,irin girma da nauyin da bata taba ji tayi mata ba,bugun zuciyarta ya sake daduwa har taji kaman iska tana mata wahalar shaqa. Ya zaci zata ce wani abu amma sai yaji batace komai ba,duk da yana iya ganin yadda qirjinta yake dagawa ta saman mayafin jikinta. Tana ji tana gani ya tayar da motar,maganganu ne fal cikin bakinta takeson furta masa su masu tsananin zafi,saidai duk sanda ta motsa labbanta da nufin tofar masa sai wancan ranar ta dawo mata,sai taji kaman abunda ya faru wancan karon shine zai sake maimaita kansa,haka ta runtsen ido kawai tana jin yadda motar ke gangarawa tana ficewa daga gidan zuciyarta na mata tsananin zafi. Sanda yahau kwalta sosai sai ya figi motar kamar me tashi sama,irin dai tuqin nan nasa daya saba a baya,dama shi din bai iya yiwa abun hawa ta sauqi ba. Shuru ne ya ratsa motar sosai,ba me cewa da dan uwansa wani abu. Ita din tayi shuru taga iyakar gudun ruwansa ne,yayin da shi kuma yake fatan taci gaba da zama a haka cikin laqwas din da tayi,wannan ce kadai damarsa da zai samu furta dukan abinda yakeso ya furta din ya kuma aiwatar "Sulthana" ya kirayeta da wani irin sauti daya sanya jinin jikinta harbawa da gudu. Sake runtse idonta tayi tana jiyo yadda qasan zuciyarta ke zafi akansa,yana kuma tuna mata da abubuwa masu yawa da suka shude. Bakinsa ya bude zai kuma kiran nata saidai kuma kiran wayar laila ya dakatar dashi. Shuru yayi yana jin wayar tana ringing har ta katse,ta sake kira,dole ya danna accept ya kuma maida wayar a free. "Hello dear....." Ta furta da salon karyar da murya tana langabe kai daga can barin da take tana jin zuciyarta na sake samun rashin madafa game dashi,wanda muddin hakan yaci gaba da kasancewa tasan tabbas......indai tanason tsira da rayuwarta to takai batun gaba bro da daddy. Muryar tata ta fita tas ta kuma karade motar har kaman tana amsa kuwa. "Am on the way laila......i will call you" ido ta runtse,wannan kalmar ta gama haddaceta tsaf a bakin maina,kuma ta fahimci dukka salo ne na koreta daga yin doguwar waya dashi. "Alright" ta amsa masa a taqaice tana katse kiran. Gaba daya ji take kaman ta sauke glass din ta fita ta window din motar,laila.....laila.....bashi da aiki sai zancanta?,shi ko kunya ma bayaji?,ya gama yawon duniyarsa ya dawo da abokiyar shashanci har ya bari ta dinga kiransa?. "Mtseww" taja tsaki tana gyara yafen mayafinta. Sam sam bata dauka tsakin zaya fito ba,saidai ya fita din da sautinsa sosai. Ido ya runtse yana jin kaifin tsakin kamar an zura masa abu cikin kunnuwa. A nutse ya rage gudun motar,sai ya koma tafiya slow kafin ya sanya signal ya fara sauka gefan titi. Mamaki ya cikata ganin yana qoqarin parking qasan wata bishiya cikin bishiyoyin da aka qawata gefan titin dasu. Bataga wani shop ko masu saida wani abu a wajen ba bare tayi tsammanin wani abu zai siya. Sanda ya tsaida motar cak ya kuma kasheta sai mamaki ya hanata sukuni,sai data juyo tana dubansa da fararen idanunta. A lokacin ya nutsu ne gaba daya ya zuba mata lion eyes dinsa yana kallonta,dauke idanun nata tayi tana kauda kanta hadi da hadiye abinda takeson fada. Tana ganin bata bakinta da lokacinta ne ma ta tsaya yi masa magana,shuru shi yafi dacewa dashi. "Waye kika yima tsaki?" Kasa bashi amsa tayi sai qeya data juya kasa,kwantankwacin abinda takeyi masa a shekarun quruciyarta sosai duk sanda yake mata fada "Look!" Ya fada da kakkausar muryarsa "Kinyi tsaki na farko a waya.....nayi warning dinki,kinyi na biyu yanzu a gabana......karkiyi kuskuren maimaita na uku......am not your mate..... uban 'ya'yanki ne....yayanki kuma mijinki,hope i made it clear to you?" Wani haushi ya sake saukar ma zuciyarta,yadda yaketa jero wadannan bayanan da matsayinsa mataki mataki tana jin kamar ta fasa motar ta fice,saidai tunda suka shiga taji qarar saka security a kulle take. Bai damu da amsarta ba don yasan tsiyar daya qulla mata a yau din,sai ya juya sosai ya soma kwantar da kujerar motar ya miqe qafarsa ya kuma yi relaxing bayansa abinsa bayan ya kunna sauti can qasa. Shurun da taji yayi yawa ba motsinsa ba kuma alamun kunna motar shi ya sanya ta fara tambayar kanta da kanta ko lafiya?,banda sauti da AC din da ya bari a kunne ba abinda ke motsi cikin motar. Ta dinga qoqarin kallonsa ta gefan idanu,saboda batason ta juya ta kalleshi ta bada kanta,da qyar ta hangeshia a kwance abinsa sambal tamkar yana cikin dakinsa a kan gadonsa "Wannan wanne irin mulkin mallaka ne?" Ta tambayi kanta da kanta bayan ta duba agogonta taqa a qalla sun share mintuna talatin a wajen shi bai motsa ba itama bata ce masa ta tafas ba. Ci gaba tayi da duba agogonta akai akai,taci alwashin ba zata masa magana ba har dai ya gaji da kansa ya tashi motar sun tafi,saidai kuma duk sanda ta kalli agogon sai ranta ya kuma baci akan wancan bacin ran. Wanne irin mulkin mallaka ne wannan?,hankalinsa kwance yanata sauya tattausan busar guitar din dake tashi a motar xuwa nau'i daban daban?,ita ya barta zaune ya kuma tsareta?,bai barta ta tafi ba bayan bata gayyatoshi cikin rayuwarta ba?. "Zaka iya bani key din motata ka sauka ni na wuce,ina da wajen zuwa" ta karya billenta daga qarshe ta furta murya a cunkushe kamar wadda aka yiwa cushen tsumma. Sirrintaccen murmushi daga can qasan zuciyarsa ne ya subuce masa,dama so yake gaya iya nata taurin kan da kafiyar,batasan yanzu aka soma ba "Ni bani da abunyi.....don mun kwana a nan ma ba damuwata bane indai ba zaki koyi manner na magana dani ba" sake baci ranta yayi,me yake nufi?,ta qasqantar masa da kanta kenan ko.meye?,lallai tarin neman fitina ce kawai qasan ransa,banda haka na meye zai dinga shiga gonarta har haka?. Sai daya mula don kansa sannan ya miqe ya zauna sosai,yasa zara zaran yatsunsa yana maida sumarsa baya,sannan kuma a nutse bakinsa yana ambatar "Bismillah" ya tayar da motar,saidai a yanzun ya rage gudun da yakeyi sosai dukka hannuwansa dafe da sitiyarin motar. Idanunta nakan hanya,tana kallon shimfidaddiyar kwaltar zuciyarta kuma cike fal da tunani iri daba daban. A hankali ta fara lura hanyar da yake bi din kamar ba hanyar gidan amaren bace,don ta riqe kwatancen da dunan street din nasu. Tsoro ya sake kamata,wannan karon kuma kai tsaye ta kasa shuru ta magantu "Ina zaka kaini?,nan ba hanyar bace" juyowa yayi idanunsu suka hadu waje daya "Nace miki fyade zanje nayi miki karo na biyu tunda wancan ya amsa sunansa" yayi maganar yana dauke kan motar suka shiga wani titi na daban da wani irin zafin nama. Ido kawai ta zuba suna ci gaba da wuce wurare har suka iso babban ginin daya tsaya a gabanshi yana karbar binciken security kafin wucewarsa ciki. Idanunta ta daga tana qarewa ginin kallo,sunan data gani daga qarshen sunan dake kafe a tsororuwar babban ginin ya sanya gabanta harbawa "Hotel?,to me sukazo yi s hotel?" Ta tambayi kanta da kanta. Kafin ta lalubi amsa har ya gama da security ya wuce cikin babban harabar hotel din. Ko ba'a gaya mata ba da ganin tsari da girman wajen tasan hotel ne na manyan mutane masu hannu da shuni,komai bisa tsari tun daga farfajiyar har tsarin ginin wajen *_KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 71 Bayan ya daidaita tsaiwar motar,ya zare seatbelt dinsa yana dubanta,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude side dinsa ya fice. D Bata koda kalli sassan da yake ba har sai da taji ya maida murfin ya rufe, second biyu ta bayar ta waiwaya da kanta tana duban gefanta. Cikin takun nan nasa me cike da ginshira da qasaita yake takawa zuwa main entrance na hotel din,hannunsa guda daya zube a aljihun wandonsa,daya hannun kuma wayarshi da key din motar ya riqe. Idanunta ta kawar tana tabe tana jan tsaki,tana mamakin irin qarfin halinsa,yanayin komai kamar baisan ya aikata komai ba,kamar kuma bame laifin komai ba,yanata maimaita kalmar fyade zaiyi mata kamar wata kyakkyawar kalma me dadin ji da sauraro?,baya ma ko kunyar idanunta bare abinda ya aikata a baya da ita har yanzun sunan fyade ta bashi?,duk da ta fahimci da gasken ba fyaden bane,sadakinsa na saifa daya bayar ya sauyawa abun suna a musulunce. Yanxun daya kawota nan din me zaiyi a ciki?, Tambayar data yiwa kanta kenan kuma bata da amsarta. Tunaninta ya katse sanda kira ya shigo wayarta,ta bude handbag dinta ta zaro wayar tana gyara ajiyar cards dinta masu amfani dake ciki. Yasmin ce sarkin zaquwa da gaggawa "Shuru.....shuru sultana lamarinki sam babu kara fa" yasmine ta fadi cikin zumudi "Afwan yasmine...... kin ganni nan......" Da sauri ta katse abinda da farko tayi niyyar fadi,sam ta mance,tana shirin dabawa kanta da kanta wuqa "Ina hanya bazan wuce awa daya ba in sha Allah" "Shikenan,ina jira,aminata ma ke take tsumayi" "In sha Allah" ta amsa mata tana lumshe ido saboda bacin rai daya taso.mata. gaba daya ya sauya mata akalar tafiya?,wai anya ma ba sassauci ya gani saman fuskarta yake neman rainata har haka ba?. Tana katse kiran tare da qoqarin sauka daga call logs dinta taji ya bude murfin motar a hankali. Sam batasan da isowarsa wajen ba don hankalinta baya kai. Idanunta ta daga a hankali ta sauke dubanta a kansa. Yana tsaye gabanta,cikin cikakkiyar tsaiwar nan tasa dake sake fidda diga da zatinsa. Cikakken tsayayyen ba'abzine dogo fari tas. Shima ita din yake kalla,hasken rana daya haska qwayar idanunta dake da sheqi kamar an diga zaiba sai ya bada wani irin haske me kyau,abinda ya masa kwarjini qwarai,mazantakarsa ta sanyashi shanyewa,ya sassauta kafin nasa qwayar idanun cikin nata kadan,sannan ya rusuna yana dauke handbag din take saman cinyarta,wanda kafin tayi kowanne yunquri ya soma takawa yana barin wajen "Taso mu qarasa" "ina?" Ta tambayi kanta tana fidda ido waje. Ganin bai waiwayo ba ci gaba yakeyi da shiga ciki,ga idanu da sukayi yawa a kanta dole ta zura qafafunta waje tabi bayansa. Tana biye dashi saidai ta cika tayi fam da bacin rai da baqinciki "Wai me wannan yakeji dashi ne?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar. Yadda suka dinga wuce security ana checking nasu duk inda suka wuce ya sanya ta sake shiga nutsuwarta sosai amma kuma ranta cike yake fal da fargabar shigarta wajen,batasan me yazo yi ba,batasan me ya kawosu yi ba. Elevator taga ya nufa,ya danna ta bude ta shige,sai a sannan ya waiwaya yana kallonta. Ja tayi ta tsaya,abun ya isheta haka,ya maidata kaman wata raqumi da akala?. Yana tsaye daga bakin qofar ta yadda bazai bata daman rufewa ba ya kuma tsareta da ido. "Idan kika qara minti daya a nan wannan karon nine zan miki ihu na kuma tara miki mutane kaman yadda kika yimin wancan karon" hanjin cikinta taji ya dunqule guri daya,daga yadda taga wajen yadda yake cike da matakan tsaro idan ya aikata mata hakan ta kade daga ita har ganyenta "Idan kin damqani a hannun police har na kwana ni a hannun da zan damqaki ko?......." Bai qarasa ba illa yatsansa daya nunata dashi wani shu'umin murmushi na mugunta na kubcewa daga saman labbansa. Babu shiri tayi taku biyu xuwa gaba,sai yayi taku biyu baya har ta shiga elevator din ya rufe dasu suka fara wucewa zuwa floor din daya zabar musu. Tana tsaye daga bakin qofar dakin take qarewa dakin kallo. Babban daki ne wanda aka wadatashi da komai na alatun rayuwa. Kana ganinsa kasan vip suit ne na isassun mutane. Idanunta ta dauke daga kallon dakin ta maida kansa sanda yake qarasawa ciki yana ajjiye key din motar saman bedside drawer din dake dauke da bed lamp. Wani abu ta sake hadiyewa me tauri daya tsaya mata a wuya tun dazun "Amma dai kasan inda zanje ko?" Ta jefa masa tambayar muryarta na bayyanar da bacin ranta "Na sani......ina da buqatar na huta tukunna kafin mu wuce" "Bana buqatar wani hutu.. wannan abun da kakeyimin ya isheni haka,ka bani key dina na tafi,idan kaso ka bari sai wata shekarar sai ka taho wannan ba damuwar sultana bace" ta fada tana yarfa hannu cikin fusata. Sosai ya zauna saman sofan dake dakin,ya kuma dora qafanshi daya saman daya yana qare mata kallo tsaf har takai aya. Murmushin gefen baki ya saki yana kada kai "Taurin kai da rashin kunyar nan naga alama da sauranta har yanzu......yayi kyau......haka nakeson gani" ya fadi yana sauke qafafunsa qasa,sai ya miqe cak abinsa ya qarasa bakin window din dakin,ya zuge labulen yana hangen view me kyau daga nan cikin dakin. Abun sai ya fusata ta,wato ya maidata wata mahaukaciya ma,ta hasala sosai,kawai sai ta fara masifa idanu rufe. Yi yayi kaman baiji ba har minti kusan biyu. Ya saki labulen ya juyo a tsanake. Kallo days yayi mata sai yakau da kai,ya sanya hannunsa a nutse ya fara balle botiran rigarsa. Da farko bata ankara ba har sai daya gama ballesu tas,fara qal din vest dinsa dake ciki ta bayyana kanta,ya saka hannunsa ya fara zare rigar a nutse,ya cireta tsaf ya ajjiyeta a gefe. Kallo daya tayi ma qirar jikinsa wata shakkarsa me qarfin gaske ta shigeta. Murdadden jiki me cike da baqa sidik din gargasa. Ba tare da yace mata kanzil ba sai gashi dukka maganganun da take zubarwa tana musu muhalli tare da maidasu cikin cikinta ragowar da bata ida furtasu ba. Tsoro sosai ya shigeta sanda ya zare ragowar vest din data rage a jikinsa ya waiwayo kuma yana dubanta. Guri daya idanunsu suka sarqe,ya lumshe idanun nasa yana mata nuni da dogon wandon jikinsa yana riqe hannunsa a qugunsa. Ba qaramar yarinya bace ita,hakanan tun ba yau ba yayi mata sabo da body language,don haka sarai ta fahimci me yake nufi. Cikin dakiya ta aje masa wani kallo zuciyarta na tsananta gudu kaman zata fasa qirjinta ta fito "Muqulli na kawai nake da buqata......kada ka yarda kaci gaba da shiga hurumin........" Bata qarasa ba ta tsinceshi gabanta,yayi mata katanga da faffadan qirjinsa. Dukka tsahonta ya shanyeshi,bata kuma tsaya ko ina ba sai daidai qirjinsa dake a waje cikin ni'imatacciyar lallausar suma. Baya tayi niyyar ja da sauri,saidai kuma kafin takai ga aiwatar da hakan ya sanya hannu daya ya fusgota. Batayi masauki ko ina ba sai saman qirjinsa,fuskarta ta samu kyakkyawar tarba tsakiyar kwantacciyar sumar qirjinsa. Wani dogon matsoracin numfashi taja wanda ke cakude da sassanyan qamshin dake fita daga cikin gargasar tasar. Kafin tayi tunani na biyu ya sanya dukka hannuwansa biyu ya warware mayafinta tas.....bai barta ta gama nutsuwa ko tattara hankalinta waje daya ba ya sauke mata dankwalinta,wanda cikin sa'a ya hada harda ribbon dinta,abinda ya bawa doguwar sumarta daman bajewa gaban fuskarta zuwa gadon bayanta. Tana cikin qoqarin tattara sumar nata cikin tashin hankali da tunanin me yake shirin aikatawa,fit......taji ya sauke zip din gaban rigarta gaba daya tun daga sama har qasa,abinda ya sakata sakin gashin nata kenan a muqar gigicewa da kuma razanin yadda ya iya aikata hakan kamar qiftawar idanu "Mm......meyeh.....haka?,wanne abunne wannan?" Ta tambayeshi a gigice tana qoqarin tattaro gaban rigar tata don hana bayyanuwar jikinta muraran "Ladabi zan sakeyi miki,don na fahimci yara biyun ma da kika haifa basu sanya kin sauya hali ba...... karatu kawai kikayi ba ilimi ba, yanzun zan baki cikakken ilimi,and yanzun yara uku nakeso na baki ajiya!" "Maina!...... don't......" taja sunansa da wani irin amon sauti me dauke da tashin hankali......Sai ta kasa qarasa fadin abinda takeson fada din saboda tsintar tausasan tafukan hannayensa da tayi cikin ainihin fatar jikinta yana yawo dasu daga saman cikinta ya zagaya har zuwa gadon bayanta sannan ya zarce yana neman maballin bra dinta "Don't what?.......ehhh?,ba zaki daina bani warning akan abinda yake halali na ba?,karki damu wannan karon nayi hankali nima,na sake girma.......you will enjoy it......babbabn ALBISHIR dinma tare zamuyi rainon cikin,tare kuma zamu shiga labour room din". Rawa dukka jikinta ya dauka cikin matsanancin tashin hankali,bakinta ya kulle gam,sai kawai ta sakar masa muka sanda taji d'as! Ya balle bra din. Jikinta ta cukuikuye waje guda tana girgiza masa kai sanda taji yana qoqarin zare rigar da bra din duka daga jikinta,yana nufin ya ganta a tsurarta kenan?,abinda bata taba yi ba gaban wani d'a namiji "Please......don Allah,i beg you.....kayi haquri" ta jefa masa roqon ba tare data shiryawa hakan ba tana girgiza kai kaman ba gobe. Cak ya dakata daga abinda yake shirin yi,yayi komai ne akan plan da son cimma wani abu na sanyata ta sakeyin laushi,amma kuma sai abun ke neman zame masa na gaske,don ba wata kafa a jikinsa da bata mutu ba,gaurayuwar jikinsu waje daya da kuma yadda fatarta keda tsananin taushi sulbi da wani irin qamshi na musamman sun masa wata irin mummunar illar da basuyi masa a baya ba cikin qasa da minti daya. Sake mata komai yayi sannan ya juya a nutse abinsa yana wucewa toilet. Da gudu gudu sauri sauri ta dinga maida komai muhallinsa,ta mayar din amma kuma komai a hargitse ta maidashi,ta lullube jikinta da mayafinta,saita sulale a wajen tana sakin qaqqarfan kukan da take ta riqewa. Ya jima sosai a bandakin sannan ya fito,sanye da gajeran wando zalla abinda ya sanyata sake cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana jin wani bacin rai da weakness suna ratsata. Baice da ita komai ba ya isa ga windows din dakin dukka ya sauke labulayen,abinda ya qarawa dakin duhu kenan,ya isa ga makashin qwayaye dukka ya kashesu,sannan ya qarasa saman gadon a matuqar kasalance yabi lafiyarsa yana cewa "Zan huta na wasu mintuna daga bisani na kaiki.....ki kwanta ki huta kema" ya furta yana tattare pillows din saman gadon ya matsesu gam a jikinsa yana sauke numfashi a wahale. Bata amsa masa ba,hakanan bata motsa ba,taci gaba da rera kukan bacin rai a hankali. A qalla mintuna ashirin da daukan shirun da dakin yayi,wayarta data watse a gefe ta soma haske. Kaman ba zata daga ba sai kuma ta miqa hannu ta janyota "Ama ta" shine sunan dake yawo saman screen din. Riqe kukanta tayi da kyau tama share hawayenta da bayan hannunta sannan ta daga kiran "Karki jima sultana sosai,ki dawo da wuri ki fara hada kayanku,kwana biyu kawai ya rage mana zamu koma" kamar bushara haka taji maganar ama,ta bude idanunta da suka jiqe da hawaye tana hangensa daga inda take a zaune,wani irin farinciki ya soma mamaye damuwarta,lokaci yayi da zata sake masa nisa,nisan da idan tayishi ba zata sake bashi daman zuwa kusa da kta ba bare ya dinga walagigi da rayuwarta yana mata Iko yadda ranshi yakeso ba "In sha Allah ama" har ama din ta buda baki zata tambayeta inda ta tsaya don yasmine tace bata qarasa ba sai kuma ta fasa ta yanke kiran. Wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki fuskarta na kallon sama "Alhamdulillah" ta samu kanta da furtawa,tana ji a nan kusa zata yakiceshi ta huta. Bashi da communication me kyau da ama bare aba ballantana ya isketa a inda take din. Sai ta miqe a hankali ta taka zuwa qofar toilet din tana ji har jikinta da zuciyarta ta samu qwarin gwiwa. _ba'a nan naso tsaiwa ba,amma yanayin yazo a haka,in sha Allah idan na samu yadda nakeso hutun zai kasance asabar da lahadi ne zuwa litinin kawai,daga nan zamu dora_ _da alama qullalliya sultana ke shirin qullawa maina ta hanyar amfani da ama ba tare da ama din tasan da haka ba,shin ya zata kasance?_ _ayi sallah lafiya cikin aminci,ubangiji ya maimaita mana ya karbi ibadunmu ameen ya hayyu ya qayyumu_*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE page 72 Alwala ta daura ta goge fuskarta da kyau cikin toilet din,ta fidda powder da bata rabo da ita ta shafa,ta kuma gyara lips dinta. Har cikin zuciyarta tana jin sanyi,bacin ranshi kuma ya ragu sosai,tunda tasan kwanaki biyu rak suka rage mata tayi adabo dashi. Tayi zaton data fito zata sameshi a shirye ko yana ma shirin su tafi din,maimakon haka samunsa tayi a kwance lakadan abinsa,kamar ma wanda ke bacci. Ta saci kallonsa sai tayi hanzarin kauda kai,saboda ta tunashi da shegen saurin karantar mutum. Taci alwashin ba zata ce dashi komai ba,don haka ta koma saman kujera ta zauna,ta fidda wayarta daidai sanda take ringing kira ya shigo. Ko data duba sai taga kiran yasmine ne still "Ya salam" ta furta cikin damuwa,don batasan amsar da zata bata ba "Oya..... bani wayar nan" muryarsa can qasa kaman wanda yasha wani abu ya ratsa kunnenta. Tadan tsorata don ta tsammaci bacci yakeyi,amma sai ta tada kai tana dubansa. Bai ko kalli wajen ba,amma hannunsa suna saitinta yana jira ta kawo din. Har tsakiyar zuciyarta taji zallar raini kawai yayi mata,banda haka meye hadinsa da wayarta dama ita kanta da zai dinga qoqarin control dinta da komai nata "Kada na maimaita fa?" Ya furta har yanzun muryarsa da wani mugun laushi. Bacin rai ya kawo mata iya wuya,ta motsa qaramin bakinta da niyyar masa tsiwa kuma saita maida dukka maganganunta ta hadiye,don tasan furtasu bazai haifar mata da d'a me ido ba,kuma a wannan wajen da suke komai ma zai iyayi mata babu me ganin laifinsa. Wannam tunanin ya sanya ta tattara duk wata tsiwa tata da bacin ranta ta hadiye,ta kuma yunqura a nutse tana isa inda yake din. Wayar ta miqa kamar yadda ya miqa hannunsa ba tare da tace masa komai ba,tana kuma qudurcewa a ranta ba zata ce masa ta iso ba,duk sanda ya juyo ya ganta. Hannunta da aka cafka ya sanya zaren tunaninta katsewa,kafin ta sake tuna komai ya jawota zuwa saman gadon ita da wayar gaba daya. Birkitota yayi sosai yana zare wayar a hannunta ya danna switch ya kasheta,idanunsa a lullumshe muryarsa na dauke da wani irin lallausan amo yana cewa "Ba zuwa nayi kawai na kashe kudin daki kina niamy ina marad'i ba.....dole ki tayani hutawa,bacci nakeji sosai.......baccin da kikayi shekara da shekaru bakya barina inyisa cikin nutsuwa.......duk sanda na jefar da kaina na kwanta to tabbas sai wannan muryar taki me cike da tsiwa ta biyoni har cikin mafarkina tana sake jaddadamin abinda ta gayamin a baya......zaimin fyade.....Allah ya isa ban yafe ba...... it's so annoyed" ya qarashe fadi da salon muryartata sannan ya cusata tsakiyar qirjinsa a tausashe yana maida hannuwansa ya lullubeta da kyau. Wani irin abune taji ya mamayi dukka ilahirin jikinta wanda ya haifar mata da tsatstsafowar gumi ta kowacce kafa ta jikinta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta jikinta yana rawa,wani irin tashin hankali yana rufto mata "Shshshsh!" Ya fadi da qaqqarfan sauti yana dora yatsansa saman lips dinta,wanda a sannan fuskokinsu sunyi matuqar kusaci da juna. Ji tayi kaman zata shide sanda ya busa.mata iskar bakinsa a fuskarta,iskar dake dauke da qamshin mint na mouthwash ne kona meye bata sani ba. Dukka qarfinta ta tattaro ta turashi baya,sai ya ware lion eyes dinsa yana kallonta "Ehnnm......bance miki fyade zan miki ba dama?,yanzun wa zaki kira cikin wadanda ke tare miki?,uhmmm?" Ya sauke maganar yana duban tsakiyar idanunta dake kawo gudunmawar hawaye. Labbanta rawa suke tanason fidda maganar dake zuciyarta tare da qoqarin qwatar kanta,sai kawai ya saki siririn murmushi ya maida kansa ya kwanta bayan ya tabbatar ya zagayeta da hannayensa. Ya barta taci gaba da yunqurin qwatar kanta,bai hanata ba bata fasa ba har sai da dukka qarfinta ya qare,yayi amfani da wannan damar ya jata jikinsa sosai,sai ta fashe da kuka ganin babu sauran wata dama data rage mata kenan,bata da sauran zabi sai hada numfashi dashi,ba wata mafita ko garkuwa saita hada gangar jiki dashi,abinda bata sake mafarkin faruwarsa ba,abunda take gani bazai taba hadata dashi ba har qarshen numfashinta. Wanne irin tsaurin ido gareshi haka.,wanne irin taurin kai da kafiya ce dashi da har ya ya iya zare duk wani tanadi data yiwa haduwarta dashi?,ya yake neman rusa komai ya kuma ci galaba a kanta?. Abune da ba zata taba bari ya faru ba yayi iya yinsa na yau ne kadai,saidai duk yadda yakai ga qwarewarsa wajen yaudara bai isa yakai inda yake hari ba. _nikam nace mmmm🤐 Tun tana lissafa minti biyu biya har goma sai gashi ta tafi lissafin awa daya,sannu a hankali awar tana shudewa tana zarcewa awa ta biyu. Idanunta fes tana zagaye da cikin dakin tana muma biye da fitar numfashinsa da kuma bugun zuciyarsa. Ko yaya ta motsa da zummar zare kanta sai taji ya sake maqaleta da kyau,murya can qasa kuma ya furta "No" har abun ya fara bata tsoro,a qa'ida ya kamata idan baccinsa yayi nisa dukkan gabbansa su saki ta yadda zata iya zare kanta,amma nasa qawa zucin bai bar hakan ya faru ba. Tayi kuka tayi kuka har dantsensa daya dora kanta akai ya jiqe,idanunta dukka suka tasa saboda tsabar bacin ran da takeji cikin ranta,ga wayarta daya kama ya kashe mata,tsoronta daya kada hankalinsu ya tashi da neman inda take tunda dai ita bataje gidansu aminata din ba,sannan kuma bata koma gida ba. Dai dai sanda muhtarin sallar la'asar ya shiga ya motsa. A hankali ya bude zagayyayun idanunsa da duka qara girma suka. Dan kada kadan ya zubesu akan fuskarta. Kamar an qara mata qarfi saboda yadda zuciyarta ta motsa da rainin hankalinsa,shi ashe ma baccinsa yakeyi da gaske?. Sanda yake qoqarin tashi saita rigashi tashin,tana tunanin shammatarsa ne batasan miqewa shima zaiyi ba. Tsam ta miqe tana gyara dankwalinta da mayafinta,sai ya miqe a nutse ya zauna ya zuba mata idanunsa. Can qasan ransa dariya ce sosai take kamashi,yasan ya gama da ita,wannan din wani assignment ne ya bawa zuciyarta da gangar jikinta,ya basu wani aiki ya kuma ajjiye musu wani yanayi da zaiyita kai kawo cikin kwanyarta koda batason hakan. Abu na biyu yadda taketa wani gyara jikinta tana gyara yafen mayafinta tamkar wadda taga wani muharraminta. Taurin kanta da yadda har yanzu take masa kallon ba mijinta ba yana burgeshi,don yana hango ranar da zai sanyata ta qaryata hakan da kanta,ba da bakinta ba,zata qaryata ne tun daga qasan zuciyarta har ya bayyana a dukka ayyukanta. Kau da kansa yayi kaman baiga abinda takeyi ba ya miqe a nutsensa ya wuce toilet yana boye dariyarsa,ya azawa fuskarsa wata muguwar daurawa da cin mur. Har ya fito ya maida rigarsa ya dauki key zai fita tana zaune,sai da taga da gasken yayi hanyar fita sannan tayi hanzarin miqewa "Ina zaka tafi ka barni?" Tayi masa tambayar wadda a zahiri murya da fuskarta dukka sun juye sun koma kalar shagwaba,irin tsohuwar shagwabar nan tata da take tatawa sanda take ganiyarta,yayin da can qasan zuciyarta kuma ba shagwabar bace. Wata tsana da haushinsa ke yunqurin hallaka zuciyarta. Muryartata saita kashe masa jiki gaba daya,ya daki handle din ya tsaya sosai yana kallonta,kaman zaiyi magana sai wani abu ya fado a ransa,sai yasa hannu yaja qofar ya rufe yayi gaba. Duk taku daya kunnuwansa na cikin dakin yana wani murmushin mugunta,zayaso wannan LOKACIN ya qaraso,sanda zai dafa zuciyarta da gangar jikinta da soyayyarsa,yana tausaya mata,daga mata qafan da yakeyi a yanzun yana yinsa ne kawai saboda yanason ya fara sauke zafin kanta da kuma zafin fushin da zuciyarta ke ciki a kansa. Yadda ya zata hakance kuwa ta faru,sulalewa tayi a wajen qwalla masu zafi suna fita mata a fuska,wannan wacce irin baqar rana ce gaba daya a wajenta?,tayi nadaman fitowa a yau,inda tasan wannan ranar zata qareta dashi ne qarqashin daki guda,zata gwammace ta wuni a daki da zazzabi a jikinta,tasan koma meye duk inda za'a je a dawo shi zazzabi kankarar zunubi yakeyi. Baiyi mamaki ba daya dawo ya sameta a wajen,shima yi yayi kaman bai ganta ba a wajen,ya koma ya zauna ya gama azkar dinsa na yammaci,yana ankare da ita baiga ta tashi tayi sallah ba. "Ki tashi kiyi alwala kiyi sallah" ya furta yana miqewa sanda ya hangi wani a bakin qofar dakin yana jiran a bude mishi ta cctv din dake maqale a qofar dakin. Bayansa ta ballawa harara siraran hawaye na karyo mata,ta sanya hannu ta daukesu a zuciyarta tana cewa "Ba za'a yi sallan ba,sai kace da can kaike sakani sallar" amma yana waiwayowa ta kwashe kallonta daga kansa zuciyarta nadan bugawa tamkar tana tsoron yaga tana harararsa ne "Allah ya kiyaye ni.ba tsoronsa nakeji ba" ta baiwa kanta da kanta amsa cikin fushi. "Bazan zake maimaita kije ki sallah ba........kawai nasan idan na tashi zan saki kiyita koma ta yaya ne" ya fadi yana bude makararren lunch din da aka kawo musu "Fashi nakeyi......" Ta furta a dan tsiwace tana tura baki gaba rai bace,na meye zai takura lallai sai yaji sirrinta. Tsaiwa yayi daga abinda yakeyi yana dubanta "Fashi kaman yaaya?,kina nufin har yanzu baki daina wasa da sallah ba ashe?" Ya fadi seriously "Menstruation......" Ta furta da sauri harda dan daga murya hawaye na balle mata ganin yana niyyar yi mata mummunar fassara. Siririn murmushi ya kubce masa duk da bai shirya ba,dama abinda yakeso yaji kenan daga bakinta duk da ya fahimci tun farko abinda take nufi. Waskewa yayi yana shafa tattausar sumarsa "Oh..... okay,ashe ma a bule kike kiketa wani tutturjemin....." Kasa riqe bacin ranta tayi sai kawai ta rushe da kuka,abinda ya sanyashi boye kansa tsakiyar tafukan hannunsa kenan yana sakin asirtacciyar dariya. Ya yadda babba babba ne kuma duk wanda ya girmeka ya riga ya girmeka,duk yadda yaketa qoqarin hargitsata dinnan bata fahimci da biyu yake komai ba,sai quruciya da suka sanyata a gaba taketa sake tunzura. Sau uku yana mata maganan tazo taci abinci taqi,sai ya qyaleta ya bude yaci.nashi,duk da shima din ba wani me yawa bane. Magariba tayi taga ya daura alwala ya fice,ya dawo yaci gaba da sabgarshi abinshi. Yana haramar fita Isha'i ta sanya masa kuka. Kunya takeji da kuma nauyin dukka jama'ar gidan. Duk duniya duk wanda ya gansu tare babu wanda bazai fassara da goyon bayanta ba kuma tana sane ta biyoshi. Ta tabbatar kuma zuwa yanzun nemanta kowa keyi, musamman da wayarta ke a kashe. Yasan me yake damunta,amma yaci alwashin ba zasu tafi ba har sai ta buda baki ta roqi su tafi, zaiga qarshen gudun ruwanta. Abu daya ke damunsa yadda taqi yarda taci ko tasha komai kaman me azumi. Yana hanyar dawowa masallacin kiran suhail ya shigo,kusan kira na biyar kenan da yayi masa yana shareshi. Sai daya hadiyi wani abu yakai kuma zuciyarsa nesa,yaja numfashi har cikin hunhunsa sannan ya daga kiran "Ina ka tafi ne haka?,haka ake tarbar baqo a gurinkun?" Ya fadi cikin muryarsa akwai alamun wani abu yakeci "Komai kake da buqata nasan ka sameshi......wani uzuri ne ya fiddani amma ina hanyar dawowa ko yaushe" "Uhunn......yayi kyau,banda Allah ya hadani da tsohuwar nan me kirki da kuma dattijuwar arziqi ama haka zaka kwasoni ka yasar ko?......kasha zamanka ma ni na samu abokiyar hira me kirki ba me shegen baqin rai irinka ba......amma kasan wani abu?"*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 73 "Nop" ya fada a gajarce don ba abinda ke dawo masa sai kallon da ya dinga bin sultana dashi dazu" "Na samu komai......amma wannan balarabiyar sister din naka......kasan itace naketa nema tsahon wannan shekarun......tunda na ganta a haram ban sake ganinta ba sai yau a gidanku?,kuma tunda naga ta shige dakin bibi nayi imanin kuna da qaqqarfar alaq......." "Wait mana......wai me bibi ta baka kasha ne kaketa zuba haka kaman lalataccen famfo?" Dariya suhail ya tuntsire da ita "Giyar soyayya nasha....... maganar gaskiya ina neman taimakon ka haidar....... I really really love her,na kamu sosai" "Stop mana suhail.......soyayya kazo neman nijer ko zumunci da aiki ya kawoka?" "Dukka ukun" ya maida masa amsa muryarsa tana komawa serious. Dif maina yayi yana karanto yadda suhail ya koma magana da gaskensa ba kamar daxun da yake magana da wasa wasa a ciki ba "Alright......sai ka nema mai taimaka maka,ka kuma nema wata matan ba wannan ba...." "Why?" Ya tambayeshi a mamakance "Saboda bazan iya ba" "Gashi kuma ni ita nakeso.....ita na jima inaso,na ganta kuma saika haramta min ita?" Ido ya lumshe yana jin zuciyarshi kamar zata fashe duk sanda suhail yace masa ita yakeso "Meye dalilinka haidar?,ko kaima kana sonta?,idan sonta kake hakan bazai hana a bawa wani dama ba,tunda mace allura ce a cikin ruwa ko?." "U are very stupid suhail,damnit!" Ya furta a fusace yana katse wayar. Sauran kadan yayi cilli da wayar sai kuma Allah yasa ya jefata cikin aljihunsa. Baisan wanne tsautsayin ne ya kawo suhail nijer ba,amma yayi imanin muddin zaici gaba da fadin wadannan maganganun akan sultana komai zai iya faruwa tsakaninsu. Bai koma cikin dakin ba saboda bayason ta ganshi a wannan mode din,sai daya zauna na wasu mintuna masu yawa a waje ya daidaita kanshi sannan ya samu qarasawa ciki. Yana bude dakin kiran goumar yana shigowa wayarsa. Da sallama ya daga kiran goumar din ya amsa "Ina kyautata zaton tana tare da kai yaa maina right?" "Yeah,me ya faru?" Ajiyar zuciya ya sauke "An fara nemanta fa......har an sanarwa aba.....don bataje gidan yasmine ba bare aminata,wayanta kuma switched off,kayi qoqari ku dawo please kafin su ankara kaine ka dauketa,kasan har yanzu aba ba'a huce yake ba,itama ama din haka" siririyar iska ya fidda daga bakinsa. Me yasa ake masa hakan?,kamar dai ya saci diyar mutane?,ko kuma ya dauki diyar da ba muharramarsa ba?,bai manta bafa har yanxu,ba wanda ya bari ko a sannan ya biya mishi sadaki,da kudin school dinsa ya biya sadakinta...... Me yasa suke manta wannan?. Gefe guda kuma goumar din masoyi ne,yasan yana cikin masu sonsa cikin gidan,kome zaiyi yana yine saboda kawo gyara da daidaito,don haka ya sassauta fushinsa ya amsa shi a gajarce "Okay" kai goumar din ya jinjina "Na gode da fahimta" sai ya sauke wayar. Yana takawa zuwa dakin yana ji a ransa inama zasu gansun su fusata da hakan?,shi kam da yafi kowa jin dadi,yafiso su fahimta ma da kansu shikam bazai taba iya yi musu abinda sukeso ba idanma kora da hali suke masa a kanta. Wannan karon a dakensa ya shiga dakin,ya kuma kasa ya tsare da tsukakkiyar girar nan tasa da idan baiso ba yake juyewa wata irin fuska me ban tsoro. Abincin ya jawo ya bude yace kuma ta taso taci,kaman yasan me ta qudurta yi ya dora da "Duk musu daya da zakiyi kuma dai dai yake da kwananmu nan wajen,dama kudin kwana din na biya,choose wisely.....but zanfi so kiyi taurin kan" ya qarashe maganar yana buda dukka hannayensa ya dora saman makarin kujerar yana yakuma yi relaxing bayansa jikin makarin kujerar bayan ya miqe qafafunsa sosai. A yadda yayin ta tabbatar ya fadi ne har cikin zuciyarsa. Dole taja abincin ta kuma juya masa baya taci spoon uku da qyar. Data maida masa sai daya mula don kansa sannan ya miqe ya tattara komai da yasan nasa ne sannan ya bude dakin ya fice ta bishi a baya tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida. Shuru ne ya ratsa motar,shi da ita din babu me cewa komai. Itakam ko qwaqwaqwaran motsi batayi,ta gama yarda maina kawai ya qaro ta'addanci ne,a yanxun idanunsa sun sake soyewa fiye da baya,ta tabbatar zai iya aikata komai,koma dai meye Allah ya kusa nesantata dashi. A nutse kuma hankali kwance yake tuqinsa,yasan yau din ya samawa kansa memory masu dadi,duk wani motsi laushin fatarta da kuma qamshinta ne yake dawo masa sabo,zaqin da laushin labbanta sai yakejin kamar a duniya babu wani abu da yakai lips dinta sulbi. Cikin qwarewa ya sauka daga saman titin ya gangara layin nasu dake shimfide da tsararriyar kwalta. Dai dai qofar gate din mansion house din nasu ya tsaya ya kuma danna horn daya tak saiga daya daga cikin security na gidan ya bayyana tamkar dama dawowarsa ake jira. Tsaf ya wangale qofar,hasken fitilar gaban motar da ya sanyata a full light ya haske masa farfajiyar farko ta gidan da kuma mutanen dake tsaye a wajen. Shi da ita dukkansu zubawa wajen idanu sukayi,tata zuciyar ta tsinke ta fara luguden bugu cikin firgita,yayin da tashi zuciyar take a nutse tamkar ma baiga komai ba,ya sanya hannunsa saman steering din ya soma murzashi a nutse kuma cikin qwarewa yana sanya hancin motar cikin gidan game da rage kaifin hasken motar. Tsananin hasken ne yana hankulansu dukka zuwa bakin qofar,ama ce tsaye sai aba da goumar kusa dashi,sai kuma oncle issoufou da alamu ke nuna yanzun nan suka suka shigo gidan shi da aba. Idanu dukka suka zuba musu,har zuwa sanda ya isa da motar parking lot na gidan,ya daidaita ya kasheta ya zare key din. Juyowar da zaiyi sai suka hada idanu da ita,hawaye ne kwance cikin idanun nata,ta kuma zuba masa ido kafin ta janye kallonta ta maida gefansu inda su ama ke tsaye,kuma dukkansu hankulansu suna kan motar kamar masu jira suga wanda zai fito daga ciki. Ya fahimci me take nufi,wani murmushi ya taso masa daga qasan zuciyarsa,shi kam wannan incident din yake da buqata ako da yaushe,sai ya dage mata dukka girarsa biyun yana tambayarta da idanunsa "Kaga irin abinda zaka janyomin ko?,yanzu me kakeso nace musu?,waye zaice ba nice na bika ba?,wanne irin shiga haqqine wannan?" Ta jefa masa tambayar muryarta yana rawa kukan da takeson daqilewa ya fara yin kansa da kansa. Hannayensa dukka biyu ya daga yana kallonta da zagayayyun idanunsa daya fiddo waje "No.....kinga kada ki sake shafamin baqin jini banda wanda na diba......idan suka qaraso yanzun kuma sukaga kina kuka,ba rape zasuce nayi miki ba tunda sunsan an riga na wuce wajen tunda ga result nan kin basu......i think wannan karon kidney dinki zakice musu naje na saida ko?" Haushi kaman ta dora hannu ta rusa ihu,amma ba zata iya hakan ba don batason asan tana ciki tare dashi,don haka idanunta sai suka zarme da jefa masa harara cikin maqurar bacin rai "Gyara kallonki babe.....if not wallahi zakisha mamaki a gabansu...... okay har kin manta dokan dana kafa miki saboda kin dawo gaban masu sangartaki ko?" Ba shiri ta janye idanun nata saita maida bakin qofar,still suna tsaye saidai magana aba yakewa ama wanda batasan me yake ce mata ba. Kafin ta ankara ya bude murfin motar ya fita,ta zaro idanu saboda data lura da kyau handbag dinta na hannunsa,baiko waiwayo ba,hakanan kuma ko a jikinsa yake takawa yana nufarsu. Fitowar tasa taja hankulansu,shi kuma ya basar yana takowa dai dai har ya iso dab dasu. "Ama barka da dare" ya fadi a ladabce yana rusunawa "Yauwa" ta amsa shi a taqaice. Ya waiwaya wajen aba ya buda baki da zummar gaidashi sai yayi hanzarin juyawa yana duban almu da ya iso wajen yanzu "Ka bude bayan motata ta fiddowa bibi cukui kakai mata" "Attah......kaima sultana handbag dinnan nata tana fitowa yanzu" maina ya fadi da biyu cikin dan taqaicewa,don bayason aba yabar wajen baiji abinda ya fada ba. Sarai aba din yaji abinda yace din,amma sai yaci gaba da takawa yana wucewa ciki baiko waiwayo ba. Yana miqawa atta jakar ama ta bita da idanu,sai suka hada ido dashi,nauyi yaji yadan saukar masa,ya sanya tafin hannunsa yana shafa kwantaccen sumar dake qeyarsa yana dan basarwa. Itama nata idon ta janye,daidai sanda sultana ke takowa wajen,don dole saita wucesu zata isa qofar sassan ama din ko sassan bibi. Dukka idanunta qasa suke kalla,don batasan yadda zata iya hada idanu da ama din ba duk da tana jin idanunta a kanta,haushi takaici da baqincikin maina ya kamata,cuta yau kam ya riga ya gama da ita ya kuma cuceta,amma daga yau ai zata yiwa tufkar hanci,da wanne ido zata kalli ama?,da kuma wanne baki zata yi mata bayanin yadda suka hada tafiya da maina?. Ta karanci fuskarta fes,don haka tun kafin takai ga isowa sai ama din ta juya abinta ta wuce ciki itama,wannan ya sauqaqa tsananin nauyi da kunyar da takeji din,kallonsa kuma sai ya koma kanta,yana kallonta tsaye kallon tsaf,yadda take takawa cike da kunya sai abun yaji ya masa,ta masifar tafiya dashi gami da burgeshi,kamar ya dauketa su kuma suci gaba da kasancewa tare kaman dazun,koda ba zata buda baki tayi masa magana ba,koda zata masa tsiwa ne,koda masifa zatayi masa "Ki tafi a hankali mana please" ya furta a tausashe sanda take giftawa ta gabanshi. Ji tayi kaman ta sanya abu ta tureshi ya fadi,a sanda ya hada wata cakwakiya me zafi sai yasan yadda ya zame kanshi,sai yasan yadda ya maida komai ba komai ba,yasan duk yadda zai sauke laifi duk girmansa izuwa qaramin mataki.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 74 Sassanyan murmushi ya saki yana furzar da iska me sanyi daga bakinsa,ba qaramin dadi yaji ba da ganinsun da aba da ama sukayi,wani abu ya darsu a ransa sanda yake wucewa zuwa sassansa yana sake sakin qaramin murmushin,yakai hannunsa ya shafa lallausar sumarsa yana cije lips dinsa na qasa. Nishadi da farincikin da zuciyarsa ta samu wunin yau kawai ya wadatar dashi lafiyayyen bacci a daren yau me cike da kwanciyar hankali. Kai tsaye ya fidda kayan jikinsa bayan isarsa bedroom dinsa,ya hada ruwa me zafi ya shige cikin bathtub dinsa yana rufe idanunsa,dumin ruwan yana ratsashi zuciyarsa na masa haske. Koda ya fito a nutse ya sharce kansa ya kuma shirya cikin wata cotton doguwar riga ta maza maras nauyi saqar qasar india,kewar benazeer da batoul yakeyi sosai,yasan kuma ko su din sun nemeshi,yanzun haka yana da tabbacin sunyi barci,to amma kuma bazai iya kwanciya har zuwa safiya bai gansu ba,don haka ya zura wasu slipper nashi masu taushi off-white kalan rigar yana fita a dakin. Daga sassan bibi har na ama suna da dakunan kwanansu a ciki da komai da komai,ko ina suna iya kwana cikin gidan,don haka ya rasa wanne sashe suke. Daga bangaren ama harna bibi din ba wanda yakeson shiga,sassan ama yana dan jin nauyin abun dazu ne, sassan bibi kuma bayason ya taras da suhail a can,ko yaya yayi misbehaving masa yasan sai bibi ta tanka,don ya fuskanci ta karbeshi hannu bibbiyu. Kamar an jeho masa saddi,ya tako a hankali ganin yayan nasu tsaye a wajen,yadan rusuna cikin ban girma yana fadin "Barka da dare" "Barka saddi,BB fa?" "Suna sassan ama" ya amsa masa yana masa nuni da sashen da yatsansa "Yayi jeka abunka" ya furta yana nufar sashen. Duka a rude take sanda ta wucesu,ta rasa ina zata dosa wajen ama ko bibi?. Idan ta tafi wajen bibi hakan yana nufin fa kenan ya tabbata ita din me laifi ce,amma kuma zuwanta wajen ama din kuma fa?,kunya takeji yau din matuqa, tilas ta hadiye tunda tana jinta aba me laifi ba tayi sassan ama din,ta bude dakinta ta tura ta shiga. Sai data maida qofar sannan ta fidda numfashi tana jinta safe,ta soma tariyo abinda ya faru dukka wanin yau din,sai taja dogon tsaki "Bazan sake bashi daman da zai ganni ba bare ya rainamin hankali haka ba" ta fada tana jin zafin walagigi da ya dinga yi yau din da ita. Wanka ta shiga itama don gaba daya kayanta da jikinta taji sun fita mata a rai,don ba abinda sukeyi sai qamshin wannan mayataccen turaren nasa,tana ciresu ta jefasu a laundry basket ta fiddashi qofar dakinta,tasan me hada musu kayan wanki zuwa gobe da ssfe zata iso tayi gaba dasu zuwa laundry room dinsu. Tsaye tayi gaban madubi,lallausan gashinta da yaji ruwa ya kwanta mata lambas a goshinta zuwa wuya,ta goge fuskarta da qaramin towel sannan ta jawo cream dinta ta fara matsa tana shafawa. Sanda tazo daidai bakinta saita tsaya tana zagaya yatsunta akai,turo lips din tayi gaba ta kuma jan qaramin tsaki tana dauke ido daga saman kyakkyawar fuskar tata. Sai yanzun takejin wai yama akayi ta tsaya yayi mata dukka irin wadannan abubuwan kaman me jin tsoronsa?,ya raina mata wayo da yawa, sa'a dai kawai tasan ya taka,amma tabbas nan gaba ko meye zaiyi mata bazai sake samun dama a kanta irin haka ba. Wasu pink pyjamas ta zaqulo masu hade da cap ta sanya,ta taje gashinta da kyau ta nannadeshi ba tare da ta sanya band ba saboda batason abinda zai takurata idan zata kwanta,tabi dukka jikinta dukka da sassanyan body body mist me qamshin strawberry,ta zauna daga saman stool ta dauki wayarta da zummar turawa aminata da yasmine apology tex akan rashin xuwanta,sai benazeer da batoul suka fado mata a rai. Zura wayar tayi cikin dan qaramin aljihun pyjamas dinta dake maqale ta qasan rigar,kwana biyun sai takejin wani sabuwar qauna da kewar yaran,ta sanya takalmanta ta rage hasken dakinta ta fito. Ta tabbatar suna sassan,don yawanci irin wannan ranar sunfi kwana sasssn ama,don itama a sassan take kwana,ba kasafai ta fiya zuwa sassan aba ba a irin wannan ranar,su kuma sunfi son su kwana idan tana cikin sashen. Ba kowa falon ama din har ya ratsa ya isa dakin yaran,ya murza handle din ya tura ya shiga,dim light ne duka dakin,ya gauraye da sassanyan qamshin da kusan ya kama jikinsu da ma dakin zuwa sassan ama gaba daya. Makunnin babbar fitila ya laluba ya kunna. Tarwai fuskokinsu suka fito,ruqunqume da juna cikin duvet kamar wadanda aka ce za'a rabasu. Murmushi ya subuce masa,qaunarsu da alfahari da yaran yana ratsashi,a yadda yake ganin sun damu matuqa da al'amuran juna da tsananin kama da juna da sukeyi yana kyautata zaton a mahaifa daya suka rayu. A nutse ya qarasa ya haura saman gado,tsakiyarsu ya zauna sosai,ya miqa hannu yana shafa fuskarsu sannan ya gyarawa kowacce kwanciya,ya hada hannayensu biyu waje daya ya musu addu'o'i ya shafa musu. Hannunsa saman kan batoul,yana jin wata soyayya tana sake ratsashi. Shi kadai yasan me yaji sanda ya fahimci mamansu na dauke da cikinsu,a lokacin da bashi da iko ko daman taimaka mata da komai,a lokacin da kowa ke masa kallon ya gudu ne da gangan,a lokacin da kowa ke kallon yayi komai ne akan bada qarfi,ba wanda ya kalli K'ADDARA cikin lamarin. Zamannan da yayi a tsakaninsu sai yaji tamkar yana hira ne a tsakanin zukata biyunsu da tashi zuciyar,tamkar yana gaya musu damuwarsa wadda kowa ya kasa fahimtar sa,kowa yaqi bashi uzuri tamkar su din suna fahimta suna kuma tayashi alhini. Bude idanunsa yayi a hankali,cikin jikinsa yakejin kamar tana tahowa dakin saboda yadda bugun zuciyarsa ke qara yawa,sai ya miqe tsam,ya tafi bayan qofa yayi tsaiwarsa,don ya tabbatar muddin ta ganshi ba zata qaraso ba,shi kuma yana da buqatar ganinta da gaske,ganin da zai zame masa dan rakiya har zuwa gadon baccinsa. Can qasan maqoshinta tayi sallama da siriryar muryarta duk da tana da tabbacin sunyi bacci "Ya akayi sukabar wuta akunne kuma?" Ta fadi da tattausar muryarta tana takowa zuwa ciki. Fes yake qare mata kallo cikin pyjamas din da suka fidda shatin bra da kuma pant dinta, yalwataccen gashinta nata sheqi a hasken qwan dakin,qamshin strawberry body mist dinta ya gauraye dakin duka ya sauya masa qamshi. Wani yaarr taji yaji tun daga yatsun qafarsa har tsakiyar kwanyarsa lokacin da take takawa a nutse tana nufar bed din yaran. Kowanne sashe na jikinta motsawa yakeyi da salon tafiyarta tamkar wadda takeyin tafiyar a qididdige ko kuma take motsa jikin nata da gayya. Baby sultanansa ta bude sosai ta zama babbar mace,irin isassun matan nan da qirar jikinsu keda wahalar samu,duk da kusan a rurrufe yake ganin komai har yanzu,amma shi din a yanzun ba yaro bane qarami,yayi yawo a duniya yaga halittan mata kala kala,uwa uba likita ne shi din dake mu'amala da kowanne irin jinsi ko yare. Wani irin kishi ya taso ya saukar masa,maza nawa ne sukaga irin haka a tattare da ita?,ko dai abinda suhail ya gani din kenan ya rude masa har haka a kanta?, tambayar data ida rikita mode dinsa gaba daya,yaji kaman zai fita hayyacinsa saboda wani irin kishi daya sauko masa,hakan ya sanyashi kulle idanunsa yana zuqar iska sosai don takai hunhunsa, rufe idanun da suka sanya har ta musu nata addu'o'in ba tare da tasan yayi musu ba ta sake rufesu ta juyo zata bar dakin bai sani ba,sai da tazo dab da qofar ya shaqi qamshinta da kyau ya miqa hannunsa a tausashe ya fusgota zuwa inda yake tsaye din. Bata zaci haka ba kwata kwata,don haka abin ya matuqar tsoratar da ita,ta kira sunan Allah da qarfi abinda ya saukar mata da nutsuwa kenan nan da nan. A tare suka ware idanunsu akan juna,cike da zafin nama ta sanya hannu zata turasa baya,ya nuna mata namiji gaban mace yake ta hanyar kamo qugunta ya riqe sosai,ya kuma janyota jikinsa ya hade qugunsa guri guda,abinda yayi sanadiyyar daukewar numfashinta na wucin gadi saboda saqon daya aika mata a fakaice. Dukka jikinta ya soma rawa kamar wadda aka tsoma cikin ruwan qanqara,tsoratar tata sai ta sake qarawa idanunta kyau a idonsa,ya saki boyayyen murmushi don yasan saqon da yakeson ya aika din ya isa,ya gyara tsaiwarsa da kyau yana duban tsakiyar idanunta suna musayar numfashi "Ina roqonki..... please..... please,daga yau ki dinga saka jilbab idan zaki fita.....bazan iya jurewa ba naga ana kallonki.......you are not a baby now......kin zama babbar mace.....zuciyata ba zata iya dauka ba.....ki killacemin please" "N killace maka me?,waima......meye hadinka da dukka rayuwata iyeee...... please stay away from me" ta fadi da qwarin gwiwa tana son banbare hannunsa daga qugunta,don wani mummunan saqo me tsayawa a zuciya da qwaqwalwa kawai yake aikewa gangar jikinta a haka. Tana jin wayarta na vibration amma bata ma da qarfin duba me kiran. Hankalinsa kwance yake kallon qwayoyin idanunta,akwai wani kakkaifan abu a ciki da yake sanyashi nazari yadda zai kaudashi daga zuciyarta,ta riqi abubuwa masu yawa a ranta da alama,and shi kuma bazai iya kallonsu tattare da ita ba,dole ya kawo qarshensu. Sakinta din yayi a hankali saidai kuma ba salin alin ba,don sai daya zira hannunsa cikin aljihun rigar tata ya zare wayarta,wanda bata lura da hakan ba sai daya daga wayar yana qoqarin cire code din kai. A tsiwace ta bude bakinta zatayi magana amma sai maganar ta koma inda tafito sakamakon turo qofar dakin da akayi da dan sauri. A tarw suka juya suna duban bakin qofar,ama ce sanye da qaramin hijab mahadin pyjamas dinta,fuskarta tayi kyau qwarai cikin kalolin kayan,sun kuma fidda quruciyarta sosai saika dauka duka duka bata wuce shekara talatin ba. Wani irin abu sultana taji kaman an watsa mata cikin jikinta "Subhanallah" ama ta furta qasa qasa da sauri,sai sultana din tayi hanzarin ja baya cikin zafin nama tana nesanta jikinta daga maina. Zuciyarta na bugawa kamar wadda aka kama da laifin sata dumu dumu,idanunta dukka sun nuna tsantsar tsoronta da ganin da ama tayi musu tsaye cikin mugun kusanci da juna ita da maina din. Daga subhanallah ama bata qara komai ba ta saki handle din ta juya tana ficewa daga dakin cikin abinda duka bai wuce second biyar ba,dama zuwa tayi taga yanayin yaran ta wuce itama ta kwanta,wanda hakan sabonta ne,duk dare takan dubasu kusan sau hudu ko biyar,musamman idan aiki yama tanja yawa ko ba'a nan zata kwana dasu ba. A fusace ta juyo tana duban maina wanda ko dis babu wani alamun tashin hankali tattare dashi,hasalima sai taga kaman wani tattausan murmushi ne yake fita daga saman fuskarsa. A yadda taga hankalinsa na akwance tasan ko meye zata fada ma batawa kanta lokaci ne kawai zatayi,sai kawai ta juya da gaggawa tabi bayan ama kamar wadda keson cimmata. Wani murmushin ya kuma saki bayan ta bacewa ganinsa,ya matsa gaban yaran ya sake dubasu,ya saita musu ac din dakin sannan ya kashe duk wasu kayan wuta ya rufe musu ya fice abinsa. Yana ratsa farfajiyar gidan iskar dake kadawa tana sake sanya masa nishadi har cikin zuciyarsa,idanunsa ya dinga lumshewa yana tuna qamshinta da laushin fatarta,wani irin dumi da fatarta ke dashi wanda kusan ya jima da haddace wannan,tun tana mitsitsiyarta ma......lokaci na farko da ya fara saninta a matsayin diya mace,sanda tana sultana qwaila. Wani murmushin ya sake subuce masa daya tuna ranar,rana ce da tazo musu a rikice ba tare da shiri ba,rana ce da bai taba hasashen faruwar abinda ya faru din ba a sannan,tana dauke da wani irin memories masu nauyi da bazaiyiwu zuciya ko kwanya su manta dashi ba.....amma duk da haka yakan tuna wasu baiwawwaki da ya sameta dasu da suka girmi shekarunta. "Lafiya kake murmushi kai daya?" Muryar suhail dake zaune cikin falon yana duba wata jaridar qasar France ya fadi yana kallon fuskar maina. Sai a sannan ya lura dashi,yayi qoqarin gyara mode na fuskarshi yana neman wajen zama "Lafiya mana....." Tashi suhail yayi sosai ya zauna yana ajjiye newspaper din "A'ah,inafa lafiya,kafimin kama da mutumin da soyayya ta yiwa mummunan kamu fa malam" harara ya watsa masa yana qoqarin bude wayar sultana din daya taho mata da ita "Hakane.....tunda kowa ma irinka ne wanda bashi da aikinyi sai soyayya" sai ya gyara zamansa sosai yana shiga cikin wayar ya soma dube dubensa. Baku suhail ya sake yana kallonsa kafin ya saki murmushi daga baya "Ni ka tunamin,i got her phone number......bari na gwada kiranta" kaman an fusgeshi ya daga idanu yana duban suhail,so yake ya tambayeshi wacece amma kuma ya kasa,sai idanu kawai daya zuba masa,zuciyarsa na harbawa kadan kadan. "Yeey.....ta shiga" ya furta with excitement yana gyara zamansa. Ga mamakinsa wayar sultanan dake hannunsa ne ya fara harbawa,a nutse ya dauke dubansa daga kan suhail ya maida kan wayar,saiga numbers a jere reras suna harbawa. Iya adadin yadda suke harbawar haka zuciyarsa ke bugawa fiye da kima,a nutse ya maida dubansa ga suhail bayan kiran ya katse yana sake qoqarin kuma kira. Kaman dai dazun haka yaga kiran ya sake shigowa,da gaske ne wannan ba wasa ba, numbers din sultana ke gareshi,kuma ita din yake kira,waye ya bashi number wayarta cikin gidan?,ya yiwa kansa tambayar da baisan amsarta ba "Still dai taqi dagawa.......tana da aji da yawa,da gaske sai nayi yaqi da gasken gaske zan sameta...... lemme try again" ya furta yana duban screen din wayarsa yana sake qoqarin kiran. Hannu ya sanya ya latse wayar gaba daya ya kasheta duka yana jin wani abu yana riqe masa waya "Oh no!" Ya sake ji suhail ya fada da sautin damuwa cikin muryarsa "Ta kashe wayar.......wai man.....me yasa ba zaka shigemin gaba ba?,na tabbatar sister dinka ce don akwai kamanni a tsakaninku......i love her wallahi with all my heart.....zan kula da ita i promise" "Mahaukacin da ya baka digit nata bai gaya maka matar aure bace!" Ya fadi a tsawace har sautin tsawar nasa na fita farfajiyar corridor dinsa. A mamakance suhail ya fidda idanu yana duban maina,kafin daga bisani ya rage kaifin kallonsa a kanshi,ya kuma tattaro dukka jarumatarsa yana masa duba nakai tsaye*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 75 "Please banason irin wannan wasan,wanne magana kake haka?,matar aure kamar yaya?,ta ina ta zama matar aure?,ina mijin?" "Eh.....yes matar aure ce harda yaranta" dariya suhail ya saki yana doka qafanshi a qasa "Kaga,cool down man.....kawai kacemin kaima kana cikin 'yan takara bawai kayimin qaryar matar aure bace...." "Na taba maka qarya?" Ya jefa masa tambayar yana jin zafin jifansa da qaryar da yayi "No.....amma akan mace ai ba abinda mu maza ba zamu iyayi ba muddin dai muna sonta" "Shut your mouth please suhail......sultana matata ce..... benazeer da batoul are my kids!" Yakai qarshen maganar yana dukan hannun kujerar da yake kai. Sak suhail yayi yana kallonsa cikin mamaki,yayin da shima maina din suhail yake kalla fuskarsa na sake bayyana zallar kishinsa. Qaramin dariya suhail ya saki yana komawa baya ya zauna sosai "Nasan ka qware wajen dakiya,cin magani,zafin zuciya da kuma zallar miskilanci......to amma bansan sanda ka zama dan wasan kwaikwayo ba,yaushe kukayi auren?,har ta haifa maka wadannan bula bulan twins din ma sha Allah tubarkalla,son kowa qin wanda ya rasa?,idan su din yaranka ne me yasa tsahon shekarun kaketa begensu kake sonsu amma kuma muke yawan maganar bakasan inda suke ba a fadin duniya?,ko nufinka duk cikin rainin hankalinka ne?" Ya amsa tambayar cikin salo na shashantarwa. Tsam ya miqe daga inda yake zaune din "Duka wannan bani da lokacin maka bayaninsa,kaje wanda ya baka phone number din ya maka bayanin,kuma ka gaya masa nace ya warware maka komai ta yadda a Karan kanka zakasan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane.......zan iya jure komai amma banda abinda zai tabamin mutuncin iyali na.......kada ka kuskura mu ssmu matsala dakai akan haka,je répète(na sake maimaitawa)sultane est ma femme(sultana matata ce),reste loin d'elle(ka fita hanyarta)" daga nan ya tsugunna a nutse ya dauki wayoyinsa da nata ya soma takawa kai tsaye zuwa bedroom dinsa. "Wannan duka matsalarka ce,ko ba wajenka ba zan zauna a gidan MAYAK'I,sannan idanma kayi hakanne don ka hanani sonta so yanzu na fara sonta......" Maganar ta sakashi cin burki sanda ya sanya qafarsa a dakin ya waiwayo ya zuba masa wani kallo me cike da kashedi da gargadi ba tare daya sake tofa masa kanzil ba ya juya ya qarasa shigewa ciki. Saman bedside drawer ya zube wayoyinsa,ya cusa hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata,wanne irin jarrabawa ce wannan takeson kutso kai tsakaninsa da abokinsa na kusan shekaru hudu?,Ta yaya zai iya ci gaba da mu'amala dashi?,yanason matarsa?,uwar 'ya'yansa?,me yasa suhail yaqi yarda da bayaninsa ne?,bayan yasan tsahon zamansu da shekarun da sukayi tare bai taba kwatanta yi masa qarya ba?. Kiran sunan Allah yayi a jejjere yana fatan zugin da zuciyarsa ke masa ya sassauta. Bayason yayi treating suhail in a wrong way,koba komai kusan qarfin zuwansa marad'i saboda shine,ya baro familynsa a niamy ya zabi zuwa wajensa,bai dace ace yayi masa wani ba dai dai ba,amma shima ya dace ya fahimceshi,ya fahimci maganarsa da kyakkyawar fahimta. ***********Kaman wata maras gaskiya haka take takowa zuwa dakin ama,tun daren jiya data samu ta shige daki ko motsi me qarfi bata sakeyi ba saboda nauyi da kunyar ama din. Batasan me zata ce mata ba,duk da komai data gani kawai yazo ne ba zata,amma sai abun ya zamana kamar an tsarashi ne,bataso ama ko wani cikin gidan ya fahimceta bai bai. Wata off-white gown ne a jikinta chiffon da aka yiwa budadden dinki,sosai kalan yayi mata fatarta kyau wadda keta fidda qamshin milk cream nata da take amfani dashi. Da safen sumarta ya dameta,ta zauna bayan ta fito daga toilet ta rabashi gida biyu ta kalbace kowanne,sai jelar ya biyo ta bayan kunnenta, fuskarta yayi wani irin kyau kai kace daga qasar hindu ta fito. A falon ama din su zuwaira keta kai kawo suna kawar da abubuwan dake buqatar a kauda su din,tabbacin dai da gaske goben tafiya ta tabbatar musu. Don duk wani abu da zai iya datti ko qura anata cireshi ana alkintashi. Ta gaisa dasu cikin mutuntatawa suka amsa mata cikin girmamawa da kuma qauna da sanin darajar juna,sai ta zarce dakin ama, wanda tun daga bakin qofa takejin muryoyinsu benazeer,da alama yauma sammakon tashi sukayi kenan. A kunyace ta tura qofar dakin bakinta dauke da sallama. Ama dake yiwa batoul stretching da mini stretcher dinsu ta amsa tana waiwayowa. Suna hada idanu sultana tayi saurin dauke idanunta saboda sosai takejin nauyin ama,itama ama din saita basar taci gaba da tsaga sumar batoul tana cewa "Uhm.......sai kuma me ya faru?" Da zumudi take ci gaba da bata labarin,wanda sai data zauna sannan ta fahimci labarin daddynsu take bawa ama din,ita kuma ta tattara dukka hankalinta tana saurararta. "Barka da safiya ama" ta fadi kaman wata baquwa "Barka kadai.....mun tashi lpy?" Ta amsa mata yadda suka saba gaisawa ba tare data juyowa ba "Lafiya alhamdulillah" zamowa dukka benazeer da batoul sukayi suka gaidata,ta amsa musu tana dan dubansu. A kullum cikin zuciyarta sake jin alfahari takeyi da yaran,a kullum kwanan duniya wani kusanci zuciyarta take samu da yaran,ko yaushe nutsuwa da tarbiyyar da suke samu yi mata dadi takeyi a rai,ba wani guri da zasu baqunta su zauna ko su gifta saisun samu masoya,wani irin farinjini garesu,sai kuma Allah ya hukunta suka zama wasu irin nutsatstsu masu hankali,idan ka dauke surutun benazeer wanda shi din kaman a halittarta yake,saidai kuma duk surutun nata yana da limit,bata soki burutsu KO maganganun da suka shallake shekarunta. "Dame dame ama za'a hada?" Sai a sannan tadan waiwayo "Ni kuma?,ai na kammala komai,saidai ke,abinda kikasan baki hada din ba ki hada,goben in sha Allah by 10 zamu tashi zuwa Nigeria,four kuma zamu wuce in sha Allah" ta fadi sanda benazeer da batoul keta hayaniyarsu basuji ma me take fada ba. Kunya tadan sake kamata,ta sadda kai qasa tana matsa hannayenta,sai ta miqe sum sum "Zamuje lalle,ba zakije ba?" Ama ta tambayeta. Batajin zata iya hada wajen zama da ama na wasu awanni,don ame laifin take jin kanta,don haka tace da ita "A tahomin da kayan hadin kawai duka,koda mun isa can zan saka da kaina" "To yayi" ta amsa mata tana qoqarin hadewa batoul gashinta guri guda. Agogon fata na kamfanin D&G shine abu na qarshe daya daura a hannunsa,kuma shine cikamakin kwalliyar da yayi cikin bugaggiyar shaddar qasar mali fara qal dake jikinsa. Shadda ce da aka zubawa wani irin kwantaccen aiki daya dace da kalar dakakkiyar hular kansa,ya daga zagayyayun lion eyes dinsa yana duban fuskarsa ma'abociyar sassanyan kyau da wani irin shinfidadden kwarjini wadda ta qawatu da baqiqirin gashi daga gefe da gefen kumatunsa zuwa habarsa. Comb ya dauka yana sake gyara gashin fuskar tasa da kyau,duk kuwa da cewa a kwance yake yana sheqi,sheqin da zai gaya maka qololuwar tsafta da kulawar da yake samu. Siririn murmushi ne ya subuce saman labbansa dake da wani irin color me jan hankali daya qarawa habarsa da kyakkyawan hancinsa kyau,daren jiya ya tuna,yayi mafarki sosai da ita,mafarkin da ya sakar masa da matsananciyar sha'awarta me cakude da wata iriyar narkakkiyar qauna da ya tashi da ita da safennan. Wani irin so ne me nauyi da yaji tamkar an qara mizanin nauyin zuciyarsa,t bashi memory me dadi da ya tabbatar zaiyi masa rakiya zuwa niamy ya bashi kuma dukkan karsashi har yaje ya dawo. Abu daya zuciyarsa ta tsaida masa,wanann tafiyar idan yaje ya dawo,zaya zauna ayi komai ya qare tsakaninsa da aba ama harma da sultana din. Bazai juri yana rayuwa da ita gida daya ba amma batasan girma da nauyin igiyarta dake kansa ba. Knocking qofar da kuma fitar sautin suhail shi ya Katse masa komai "nous allons rater le vol(zamu rasa jirgi)" ya fadi da harshen faransanci. Bai amsa masa ba sai ajjiye comb din da yayi,ya dauki wayarta data kwana a hannunsa ya zura a aljihunsa,sannan ya saka hannu ya jawo luggage dinsa dake dauke da kayan sawarsa na kwana daya tak da zasuyi ya fito. Zuciyarsa yakai nesa sosai ya miqawa suhail hannu. Ga mamakinsa shi kaman ma komai bai faru ba ya bashi hannu shima suka gaisa yadda suka saba "petit-déjeuner(breakfast)" suhail ya fada yana nuna masa warmer din kayan karin kumallon da Bibi tasa aka shirya musu. Kai ya kada alamun a'ah "Kasan yayi safiya yanzun,zan shiga muyi sallama da su ama" "Saika fito don ni already ma munyi,har 'yar tsohuwa ma ta bani wata kyauta wallahi,naji dadin.kyautar nan" ya fadi yana murmushi gami da satar kallon maina. Sarai ya ganshi,amma sai ya share kaman bai ganshi din ba,ya taka a nutse yana fita daga sassan nasa.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 76 A gaggauce yake amsa gaisuwar masu aikin saboda shi kansa yasan lokaci yana dab da qauracewa. Sanda yake duban agogonsa yana nufar dakin ama kai tsaye lokacin ta sanya santala santalan fararen qafafunta da suka dan nuna ta qasan material din jikinta. Qafafun nata ya soma gani kafin ya kai idanunsa har zuwa qaurinta don rigar bata sauka har qasa sosai ba. Tsigar jikinsa ya zuba,wani abu ya tsarga mishi har cikin jininsa da ganin kwantaccen baqin gashi saman qaurinta,wanda bame yawa bane,wannan din sai ya zama tamkar ado saman farar fatarta. Da sauri ta kauce masa sanda yake sauke idanunshi a kanta. Kalbar kanta ta dauki hankalinsa sosai lokacin da take giftashi da hanzarinta,don batason ma wani abu ya hadasu. Da kallo ya bita har ta bacewa ganinsa,sai ya maida idanunsa ya lumshe,yana jin tsananin kewar tattausan qamshin da jikinta ke fiddawa,ya qarasa ya murza handle din dakin ama ya shiga. Tana amsa sallamarshi ta dauke kanta tana ci gaba da hada hadarta,ta fahimci gaba daya kaman kunya ce takeson yin qaura daga jikinsa,shi yasa ta hade ranta da kyau. Daga benazeer har batoul basu barshi ya qarasa shigowa dakin ba suka taho da gudu,kowacce na qoqarin fara hawa jikinsa. Murmushi ya subuce masa,wani farinciki yana ratsa zuciyarsa,ko iya wadannan princess din da sultana ta bashi kadai ya isa ya siya mata matsayin da bayajin duk duniya baya ga ama akwai wata mace data isa ta sameshi,ya tsugunna dukkansu ya basu daman hawa kanshi da kyau kamar bai damu da farar shaddar dake jikinsa ba,sannan ya miqe dauke dasu yana qarasawa wajen ama. Har qasa ya tsugunna bayan ya ajjiyesu yana gaidata,ta amsa masa ba yabo ba fallasa,shuru ya biyo baya sai kokaye kokayen benazeer da batoul. Agogonsa ya kalla yana cewa "Akwai aikin bude wani company din ubangidana a niamy da zamuje ama,kwana daya zamuyi gobe zan dawo in sha Allah,ayimin addu'a" maganar taji tayi mata banbarakwai har ta kasa hadiyewa,ta waiwayo tana duban idanunsa "Company din uban gidanka?" Ta tambayeshi cike da mamaki. Kai ya gyada "Eh ama" "Kana jinin gidan mayak'i?,jikan ABDU ME KANO?,ubangida fa aliyyu?" Ta kuma furtawa tana jinjina abun. Qasa yayi da kansa,yasan sarai dukka tambayoyinta abinda suke nufi,ya kuma san meye ya taba zuciyarta,to amma kuma shidin ya riga ya yiwa kansa alqawari ne,zaya dawo musu a cikakken mutum me dogaro da kansa,wanda yasan zafin nema da rashin,wanda bai dogara da kowa ba,wanda kuma bai aza nauyin rayuwarsa akan kowa ba. "Allah ya bada sa'a" kawai tace dashi a taqaice "Na gode" ya amsa mata yana miqewa dukka jikinsa a sanyaye. Ya sani don dai sunqi bashi cikakkiyar damar da yake da buqata ne,amma akwai abubuwa masu tarin yawa da suke buqatar su sanar da juna su kuma fahimtar da juna,saidai komai lokaci ne,yana sanya ran zuwa da wucewar komai a kurkusa. A gaban benazeer da batoul ya tsugunna ya kama hannayensu ya sanya cikin nasa "Ayima daddy Addu'a zaiyi tafiya" murmushi dukka sukayi,benazeer ta hade hannayenta waje daya ta fara karanto ire iren addu'o'in da ake koya musu. Murmushi ya dinga yi yana amsawa da ameen,har sai data gama suka shafa a tare,ya durqusa yayi kissing goshin kowaccensu sannan ya soma tafiya da baya da baya yana daga musu hannu suna maida masa,tamkar yasan idan yaje ya dawo din ba lallai ya taddasu,a haka ya fice a dakin. Kamar zai wuce amma sai taji kaman ana jansa da magnet zuwa dakin nata,a nutse ya juya akalar tafiyar tasa zuwa dakin nata. A tausashe ya murza handle din ya tura,tana tsaye gaban madubi da madaidaicin mug dauke coffee me dumi tana kurba a hankali. Har cikin jiki da zuciyarta taji shigowar tasa,amma wata zuciyar ta bata shawarar dakewa,don haka ta basar,tayi kaman bata ganshi ba tana ci gaba da kurbar coffe din nata da a yanzun taste dinsa ya sauya gaba daya a bakinta. Maida qofar yayi ya rufe sannan ya murza key yana qarasowa cikin dakin hannayensa zube a aljihun wandon rigarsa. Ta qasan idanu take satar kallonsa,zuciyarta taci gaba da harbawa tana qoqarin dannewa. Karon faro taji ya mata kwarjini sosai,shigar ta sake sakashi ya zama babban mutum kuma magidanci zam,taci gaba da dannewa cikin nuna dakiya da juriya,shi kuma yaci gaba da qarasowa,bai kuma tsaya ba har sai da yazo dab da bayanta. Cikin zafin nama taso zillewa,saidai ina ya fita ta wannan fannin,caraf ya riqota,ya kuma sanyata cikin jikinsa da kyau yana dora habarsa saman kafadarta,wannan ya bashi damar sakar mata numfashin da ya sanya dukkan wata tsiga ta jikinta tashi. Kici kicin qwacewa ta fara yi,ya mata namijin riqo muryarsa can qasa da wani irin laushi tamkar wanda ciwo ya yiwa sassan jikinsa illa yace "Relax mana......zuwa nayi muyi sallama zan danyi tafiya,ayimin addu'a" "Meye hadina da tafiyar ka?,wancan karon da zaka tafi din ka gayaminne?,yanzun ma Allah yasa kafi ruwa gudu" wata malalaciyar dariya ya saki wadda ta sanyashi sakinta yaja da baya qaramar dariyarshi nadan fidda sauti. Muddin a yadda yakeji a jikinsan nan yanzu da yadda lokaci ya qure musu yace zaya biye mata tafiyar ba zata yiwu ba,yana da burin ya jigatata ainun ta yadda zata rasa bakin maida masa martani "Na fahimci tafiyata ta wancan lokacin ta miki zafi sosai......" "Allah ya sawwaqe" ta maida masa a tsiwace. Murmushi ya sake qwace masa,shi daya yasan tanadin da yayi mata yana tarata ne kawai,sai ya kalli agogon hannunsa sannan ya maida dubansa tsakiyar fararen idanunta "Idan ta miki idanma bata miki ba.....duk ba damuwa.....Allah ya dawo dani zan wanke kaina yadda ya dace" ya fadi yana dage mata girarsa guda daya. Kai ta dauke da sauri saboda wani nauyi da ya aje mata ta cikin idanunsa,ta soma nufar qofar toilet ba don tana da abunyi a can din ba "Basai idan ka taras dani ba?" Har ya soma taku sai ya tsaya cak ya waiwayo a nutse yana dubanta,wani abu ya darsu a zuciyarsa,ya sauke numfashi sannan a nutse cikin jerarrun kalamansa da kuma wani yanayin sound dazai nuna maka da gasken gaske yake magana ya furta "Idan kina ganin kin bacewa ganina a wancan karon......wannan lokacin kiyi gudu dukka iya yanda kike ganin zaki iyayi cikin fadin duniya.....ni aliyyu maina mayak'i ina me baki tabbacin zan taddoki na kuma zaquloki......i promise" ya furta yana daga yatsunsa. Da idanunta fes take kallonsa daga qofar bandaki,bai qara daga haka ba ya juya a dan gaggauce yana ficewa a dakin bayan ya aje mata wayarta saman sofa bed. *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 77 Numfashi taja me qarfi matuqa daga hancinta zuwa cikinta sannan ta fesar,yanayin yadda yayi magana ya ratsata qwarai,har taji kowacce kalma na sauka a kowanne gaba na jikinta,ta dinga jin abinda ya fadi din kamar dahir ne,amma kuma wani sashe na zuciyarta sai taji ya kasa aminta da hakan. Ta ina zai zaqulota?,ta yaya zai taddota?,bayan inda zata shiga din zata guje masa ne da nisan tazarar tafiyar awanni da kwanaki ma?,ba zata taba bari ya zaqulota ba, tabbas!.....itama zata tabbatar ta cika wannan alwashin da taci. Da wannan tunanin ta fito daga bakin bandakin don dama bawai wani abu zatayi a ciki ba,mafaka kawai take nema,ta dawo cikin dakin jikinta na neman mutuwa amma ta bawa kanta qwarin gwiwa,ta sauke suit case dinta guda biyu,ta soma hada komai nata waje daya,tana ji a ranta da zuciyarta muddin yana nijer batasan ranar sake zuwanta ba. Shi daya cikin mota suna a hanya amma dukka jikinsa ya mutu murus,irin qiyayya da tsanar da yake hanga cikin idanunta tana taba zuciyarsa sosai,baisan me take buqata daga gareshi ba wanda zai wanke dukka laifin da yayi mata. Kamar me magana a radio din yasan me yake tattaunawa cikin ransa ya soma magana kaman haka _ba kowacce matsala ce tsakanin masoya sulhu ke maganceta ba,wani lokaci sai ayi fada,wani lokacin sai anyi qarfa qarfa an saka qarfin iko_ a nutse ya lumshe idanunsa yana digesting maganar a kwanyarsa,tsahon mintuna kusan talatin kafin wani murmushi ya subuce masa "Na fahimta" ya furta can qasa yana jinjina kai. "Me ka fahimta yallabai?" Suhail dake zaune gefansa yana duba newspaper da alama shidin makarancin labarai ne ya fadi yana duban maina. Juyowa yayi suka hada idanu dashi ta cikin eye glasses dinsa "It's not your own business" idanu suhail din ya dan fiddo sai kuma ya maidasu yana rufe jaridan "U right.....abinda yafi damuna rashin samun layin crush dina......kaine nake ganin zaka taimaka min kana neman watsa min qasa a idanu,ka qirqiri wasu labarai duk don ka nesantata dani......ni kuma nayi alqawarin bazan bar marad'i ba sai da soyayyarta" ya fadi yana dunqule hannunsa guri guda. Da qyar maina yawu ya wuce ta maqoshin maina,ya dauke kansa a hankali yana qoqarin tausar zuciyarsa kan kada ya yiwa suhail mugun bugu cikin motar,muddin yace zai daki suhail to saidai buzunsa,don ko a qirar jiki suhail din dan kalankashi ne me jikin fulani. Hannunsa ya tura cikin qaramar jakarsa ya fiddo headphones ya dora saman kansa ya toshe kunnuwansa,yayi connecting da wayarsa ya soma sauraren wani abu na daban,sai suhail yayi sak yana kallonsa kafin daga bisani ya dauke kallonsa yana girgiza kai. **********Washegari sukayi sallama da dukkan wani family din MAYAK'I suka wuce airport suka bar al'ummar gidan cike da kewar iyalan ama musamman BB. Bibi harda qananun qwallar wucewar yaran "An daukesu an dauke uwarsu" ta fadi cikin falon nata tana qananun qwalla. Kusan dariya ta bawa kowa,bibi din bata iya sabo da mutum ba idan ta tashi sabo dashi din,bare sultana da take tamkar wani bangare na jikinta,ga yaran suma sun dosano farinjininta da kuma soyayyar data samu din. "Sai da nace ki shirya mu wuce tare bibi,yanzun a miki shiri ki biyo bayanmu?" Ama ta furta cikin lallashi. Kai bibi ta girgiza "A'ah hamdiyya,barni a nan cikin ahalina,shekaruna turawa sukeyi,na gaji da yawo a qarfen nasara,irin haka ne mutuwa zata riskeka a qasar wasu azo ayita tiri tiri da gawarka,ko mutuwa ne gwara ka mutu cikin sutura a dakinka" maganar tata sai tadan taba zuciyar kowa amma sai suka bita da dariya,sultana tace "Mutuwa bibi ba yanzu ba,Allah ya qara miki dogon kwana me amfani" "Ameen" aba dake duqe shima a gabanta ya amsa. Nutsuwa sukayi bibi ta musu addu'o'i sosai sannan suka miqe,har sun fita ta sanya aka kira mata aba,ya dawo gabanta ya tsugunna "Hamidou" "Na'am bibi?" "Rayuwa bata da tabbas,hakanan duk dan adam bai wuce kuskure ba,shine cikar dan adam din,abinda nakeso dakai don Allah ina roqonka ka sassautawa yaron nan koda a iya fuska ne,ya dawo da dukka qwarin gwiwarsa da kuma daidaita rayuwarsa,bai kamata mu rushe komai nasa ba akan kuskuren da ya riga ya afku,kuma Allah ya kawo yankewar komai ba tare da an samu mummunan sakamakon lalacewar rayuwar wani cikin su biyun ba" kai ya gyada a ladabce "In sha Allah bibi" "Allah ya albarkaci rayuwarku gaba daya" ya amsa da ameen. Lokacin da jirginsu ya daidaita a sararin samaniya sai ta furta "Alhamdulillah" cikin wata cikakkiyar nutsuwa,ta rufe idanunta tana jinta ta zama comfortable, murmushi ya kufce mata,can qasan maqoshinta ta fadi "Naga ta inda zaka nemo ni" tayi maganar cikin mugunta da jin ta tsere masa har abada. A nutse ama ta dauke dubanta daga fuskarta tana sauke tata ajiyar zuciyar,tun daxun ta fahimci yadda take cikin walwala da barowarsu nijer,ta sani koma meye zai sakata walwala baya rasa nasaba da gujewa maina,batasan yadda wannan qaddara ta samo asali ba,kuma Allah shine masanin lokacin qarewarta,bata taba ganin irin wannan mummunar rashin jituwar kamar tasu ba,tun abun be damunta har ya soma tabata,abu daya ya rage mata wannan addu'ar zata ci gaba dayi "Allahumma khir li wakhtarli". Maida dubanta ta sakeyi ga benazeer da batoul,basuyi sallama da mahaifinsu ba don basusan inda zasu koma din wani guri ne da zasu jima basu ganshi ba,duka lissafinsu Nigeria zasu sake zuwa suyi wani hutun na kwana daya ko biyu kafin daddynsu shima ya dawo daga tafiya. Iska ta kuma furzarwa,Allah ya sani taqi shaida masa ne saboda tana son ya sake sanin maqurar muhimmancin mace a wajen d'a namiji,tanason yasha wahalar samo kanta wadda bai sha ba sanda aka aura masa ita sama taka yana zaune cikin inuwa,tanason ya jigata yadda bazaiyi wasa da ita ba,bazai kuma yi wasa wajen nemo soyayyarta ba. Murmushi yadan qwace mata tana hangoshi sanda zai duba kaf gidan yaga ba ita ba benazeer ba batoul ba kuma sultana din. Ta tabbatar sai yayi musu qaramar hauka,to amma kuma tana dan shakkar anya zaya dauki lokaci mai tsaho me gano inda suke ba?. Ta sanshi farin sani tas ma kuwa,tunda dai ya fita daga jikinta ne,yana da naci da bin qwaqwafi akan dukkan abinda yakeson aiwatarwa ya kuma sanya a gaba,uwa uba ko da can yana da wata fikira da basirar saurin gano abu,to amma koda ya gano inda suke din,tasan bazai gano su a banza ba,dole energy da kudaden aljihunsa suyi aiki,idan yazo kuma ya kawo mata kanshi,don ba zata zake bari yayi aiki qarqashin wasu ba,bayan a abinda kakanninsa ita da aba suka tara masa yana da dukiyar zai dauki mutum Dari aiki a qarqashinsa da cikakken albashin da zai riqe kowanne ma'aikaci da iyalinsa. Kwana daya rak suka daidaita cikin qasar France a garin paris. Ba wani dauda ko qura me yawa suka samu,don haka cikin awanni qalilan suka gyare komai,komai kuma ya koma kan muhallinsa,abu na gaba data fara shiri shine fara aikinta a sati na gaba a gidan tv ta qasar paris,wanda zata zama jagorar shirin daya shafi al'adun africa gaba daya. A satin suka tura mata kudade masu yawa daga gidan tv din na wardrobe allowance. Bata da buqata ba abinda kuma zatayi dasu,don suttura kam wata ma sai ta shekara biyu bata sakata ba. Ta bangaren aikinta da zata fara kuwa komai aba ya tanadar mata,ga ama itama a gefe data tsaya mata kan ta lissafa duk abinda take da buqata ko takeso,buqata kam saidai idan bata fadi wadda takeso ba,don haka hanakalinta kwance take shirye shiryen kama aikinta. *_MAINA FA?_**_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 78 *ALIYYU MAINA* Cikin qwazo da kuma qwarewa ya jagorancin aikin duba kamfanin da gabatar da abubuwan da suka zama dole a buqata a cikinsa don samun ingantattun abubuwa da zasu dinga fitarwa. Haka kawai ya samu hankalinsa da tunaninsa suna karkasuwa kashi kashi,wani a niamy wani a marad'i,duk bayan wasu lokuta sai benazeer da batoul sun fado masa a rai,ta wani gefen kuma sultanan ce gaba daya tayi masa tsaye a rai,yana tuna abubuwa masu yawa da suka faru a tsakaninsu,bama iya sultana kawai ba hatta da yaran,wani abun ya saki murmushi wani ya girgiza kai,daga qarshe yakai tafin hannunsa saman qur'aninsa saitin zuciyarsa ya dafe yana fidda wani sihirtaccen murmushi. Ya yadda yayi imani sannan kuma ya tabbatar a yanzun sune rayuwarsa,sune Kuma duniyarsa gaba daya,bayajin zaya iya rayuwa ba tare dasu ba,haqurin da yayi na wancan shekarun,ya rayu babu su,a wannan karon baya jin zuciyarsa zata dauke wannan. Wannan tunanin ya sanyashi yin overwork a ranar,suhail nata mitar ya gaji,ba sauri sukeyi ba,me zaya hana su isa masauki su kwanta, gobe su qarasa zuwa jibi,ko gata ne sa koma marad'i din,ai suna da enough time. Juyawa yayi kawai ya kalleshi,shi daya yasan me yakeji a zuciyarsa,yana ji kaman ya raba zuciyarsa ne gida biyu yabar rabi a marad'i,a wannin da yaketa spending a nan din yana ji kaman ya maidosu marad'i,bazai taba iya kaiwa jibi a niamy ba,yana buqatar komawa ya hada kan iyalinshi waje guda,ayi duk abinda za'a yi a gama,zai rungumi kowanne irin tsanani,don wannan karon bawi da wasa yakeson maidota cikin rayuwarsa ba. "Ban hanaka zuwa ka kwanta ba......abinda na sani dai kawai shine,gobe in sha Allah a marad'i zan kwana,ko mun gama ko bamu gama ba,bare ma inda tabbacin na sanya dukkan effort dina,gobe azahar yayi yawa mun gama in sha Allah.....idan ka gaji kaje ka huta zan iya kammalawa" bai sake cewa komai ba ya maida kansa yaci gaba da magana da ma'aikatan. Satar kallon maina din kawai yakeyi,he's so hardworking,tun farkon haduwarsu abinda yaja raayinsa game dashi kenan,bashi da wasa,ko meye ya saka a gabansa sai ya cimma nasararsa. Iya wannan daya tuna din,sai shima ya kakkabe dukkan wata guntuwar kasala ya miqe sosai suka ci gaba da aikin tare. Kaman yadda ya yiwa kansa alqawari washegarin qarfe sha biyu na rana sun kammala komai,zuwa qarfe daya ya kammala rubutawa daddy report ya tura masa ya kuma turawa sardauna ragowar,kai tsaye suka koma masauki,ya koma toilet ya sake watsa ruwa,ya kuma shirya tsaf cikin wani lallausan farin yadi,saidai kuma dukka wannan gaggawar tashi dole ya jira akwai ragowar lokaci,don jirginsu sai qarfe hudu zai tashi,yana ji yana gani ya fita corridor din dake manne da dakinsu ya zauna samam couch yana duban suhail dake zaune d'ai d'ai abinsa ba alamun shiri tattare dashi. Kanshi ya dauke yana zuqar numfashi,zayaso suhail din yayi zamansa a nan ba tare daya bishi marad'i din ba,duk da haka sai ya danne zuciyarsa ya tambayeshin yana duban wani guri na daban "Hala ka dawo gida kenan?" "Me ka gani?" Suhail dake shan yoghurt ya fadi "Banga alamun tafiya tattare dakai ba,na dauka zaka kammala hutunka a nan,zamu hade kawai a France" "Inaaaa" ya furta yana miqewa da hanzari kamar wanda aka mintsina,har sai da maina dole ya juyo ya kalleshi. Fararen danunsa fes cikin na maina din yana kallonsa "Banga ta zama ba,ka manta har yanxu ko cikakken magana bamuyi da crush dina ba?,yaya zan koma ban samu soyayyata ba?" Idanunsa ya mayar ya lumshe. yanajin kamar suhail yana diga masa wani abu saman zuciyarsa,baisan me yasa ba,ba halin suhail bane qin fahimtar mutum da gangan ba,amma sai yaga kaman idanunsa ya rufe a wannan karon "Idan ma akwai wanda ya sanyaka kakemin haka......ina me baka shawarar kabi a hankali,idan har ka bari na fusata zan manta da matsayinka a wajena,na gaya maka ina kuma sake gaya maka,sultana is my wife......" Yana kaiwa nan ya miqe a nutse yana bar masa wajen. Da kallo suhail ya bishi,shi fa har yanzu yana tantama akan hakan,ta yaya hakan zata kasance?,shekarunsu nawa dashi?,amma koda wasa bai taba zancan wata ba?,yaran da yake iqirarin nashin ne sau nawa suna zancan baisan yaran wanne qasa bane?. Kai ya girgiza,shi kam har yanzu bai gamsu da zancansa ba. Kafin lokacin ya cika sai ga suhail din ya shirya tsaf harda jakanshi da wasu kayan daya musanyo daga ainihin masaukinsa gidan kakanninsa. Maina din baice masa komai ba,don haka ko cikin jirgi ma kowa sabgar gabanshi yakeyi. Awa biyu rak ta iso dasu marad'i,cikin drivers na gidan mayak'i daya daga ciki yazo ya daukesu daga airport cikin daya daga cikin motocin maina dake gidan. "Wanne kalan malalacin tuqi kakeyi ne?" Maina ya tambayi driver din yana kallonsa ta cikin madubin. Waiwayowa suhail dake qoqarin kunna wayarsa yayi ya kalli maina,sai ya maida dubansa ga driver din wanda yake qoqarin take motar ya qara mata gudu "Kada ka damu tuqinka yayi dai dai ba laifi,muje a haka" sai ya juya ga maina. Ya fahimci kaman bashi da nutsuwa daga jiyan zuwa yau "Fake wife din naka ka matsu ka gani ne?" Ya tambayeshi cikin muryarsa akwai sautin tsokana me yawa. Wannan karon gaza daurewa maina yayi,ya kaima suhail wani mummunan duka a kafadarsa,saiga suhail din ya gantsare yana runtse idanu hadi dayi masa nuni da driver dake cikin motar. Dukka girarsa ya daga yana nuna masa ko a jikinsa "Gaba idan ina sabgogi na nida iyalina ka sake shiga,na rantse da Allah da Allah saidai su sardauna suzo su daukeka a kakkarye" "Amma dai kai mugu ne wallahi,koda yake na fuskanci inda ka dosa,kishi ne yake dawainiya dakai,kuma kada ka manta......ba sauke kafada ba,ko meye zaka yimin idan tace saini saini din" tafin hannunsa kawai ya sanya ya lullube fuskarsa,ya fuskanci ko meye zai cewa suhail bazai daina fadin abinda ke ransa ba,tun ba yau ba,yasan shi din dan kai tsaye ne,amma yanzun ya soma fahimtar abinda yakeyi masan kamar akwai wata a qasa. Ana kiraye kirayen magarib motar ta daidaita a farfajiyar babban gidan nasu,ya sauke ajiyar zuciya yana dan yawo da idanunsa wai ko zai hangi benazeer ko batoul. Yanason shiga ciki ya gansu,to amma kuma muddin ya shiga din zai iya rasa jam'in sallah,don haka ya daure ya cire agogonsa da sauran kayayyakinsa ya miqawa attah yace ya shiga masa dashi wajen ama. Atta din nason masa bayanin saidai ya kaiwa bibi yaga har ya juya yana amsar ruwan alwala daga hannun daya daga cikin ma'aikatan gidan,don yace bazai qarasa famfunan dake jere a farfajiyar gidan. Tare suka wuce masallacin shi da suhail almu atta da saddi. Sukayi sahu daya har aka idar,bai zauna azkar ba yasan kafin ya isa gida ya kammalasu a hanya,suka sake rankayawa cikin gida tare. Sassan ama ya soma wucewa kai tsaye,saidai tun bai isa ba ya fuskanci sashen a kulle yake,ya dubi almu da suke tare "Ina ama?"*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 79 "bata nan" ya amsa masa yana dan sosa kanshi,don shi bashi yaso ya shaida masa tafiyar tashi ba kada ya debo rigimar da tafi qarfin shekarunshi. Ido yadan qanqance yana kallonsa "Kuma aka rufe sashen gaba daya haka?" "Eh...... zata.....zata danyi kwana biyu ne" dan jim yayi yana jinjina abun,har yanzu ama fushi takeyi ne dashi haka da har zatayi wata muhimmiyar tafiyar da zatayi kwana biyu amma bata gaya masa ba?. Kai ya gyada yana juyawa a hankali,har yayi taku biyu kuma sai ya waiwayo "Ita da waye tayi tafiyar?,na ganku dukka a gida kai dasu saddi?" "Benazeer da batoul sai mamarsu......a gida dama mu muke,ba zamu iya dadewar da sukeyi a can ba" ya amsawa maina kai tsaye duk da kaucewar da yaso yi. Duka maganar saita dunqulewa maina waje daya,wanne irin dadewa sukeyi?,a ina kuma suke dadewar?,ina suka tafi?. "Ina suka tafi?" Ya tambayeshi yana jin fargaba cikin ranshi,don maganar data gaya masa ta qarshe ce ke dawo masa ka "Da dai Austria suka fara zuwa,amma daga baya sun canza qasa,ban dai tantance ba" "Hasbunallahu wani'imal wakil" ya fadi cikin ransa,indai hakane kenan ama ta sake debe masa iyali sun yi nesa?,nesan da baisan waye zai masa cikakken bayani cikin gidan ba?. "Amma wanne iri ne kai?,ta yaya mahaifiyarka zatayi nesa dakai irin haka amma kuma bakasan wanne qasa take ba?" "Bata gayamana ba ya maina...." "Okay saita gaya maka?!" Ya tambayeshi a tsawace,tsawar data ratsashi sosai. Qas yayi da kansa yana dan ja baya gudun kada yakai masa duka "U are not serious at all" ya fadi yana juyawa zuciyarsa na masa susa. Yana takawa zuwa cikin sashen bibi amma gaba daya hankalinsa a dagule yake,da gaske take kenan da tace basai ya dawo ya sameta ba?,wanann din duka plan ne kenan?,plan kuma harda saka hannun ama?,kenan ama tafi son sultana a kanshi?,tafison farincikin sultana akan nashi farincikin?. Da wannan tunanin a ransa yayi sallama murya can ciki a falon bibi,idanunshi a kanta tana zaune tana amsa waya da wayar hamaissa ta sashen oncle umar. Zamewa yarinyar tayi ta gaidashi ta soma barin falon,duk da bai jima da dawowa cikinsu ba amma halinsa ba baqo bane sannane ne,kuma har yanzu babu wani abu daya sauya game da halin nasa tunda suna gani. Zamewa yayi ya zauna sosai gaban bibi kanshi a qasa,kunnuwansa suna sauraren wayar da bibi din takeyi,amma kuma saidai gaba daya hankalinsa yayi nisa da wajen,saidai ya fahimci waya takeyi hankalinta kwance,kenan babu abinda ya shalleta ko ya dameta?. Kokawa yaketayi da zuciyarsa da kuma harshensa don kada fushi ya sanyashi fadin abinda bai kamata ba. Yana zaune bai motsa ba har ta ida wayar ta aje gefanta tana dubansa. Bacin rai fushi da kuma motsuwar zuciyarsa baya boyuwa a idanunta. Bata kai ga magana ba ya daga idanunsa da shi kansa yakejin sun sauya launi "Abinda akeyimin bibi ya fara kaini maqura......ayimin hukunci kawai a wuce wajen amma ba'a yimin ba?,sai a dinga yimin wani irin bahagon horo?,zuciyata akeso ta buga?, saboda inata kawaici?" Bude baki bibi tayi kawai tana kallonsa,kafin ta tattara mamakinta tsaf ta alkinta bayan ta tuna waye ALIYYUN "yanzu wannan baqi da farin da kazo kana ja da waye kake?" Ta furta fana jefa masa wani kallo a kaikaice "Kun tattaramin matata da 'ya'yana kun cillasu wata duniya,bada sanina ba,bada izini na ba,wannan dai dai ne?" Ya qarashe maganar yana duban bibin. Motsawa tayi tana sake daukar wayar gefanta "Af.....wannan zancan ai hamidou ya kamata na kira maka saika gaya masa kai tsaye,kasan waqa a bakin me ita tafi dadi ko?" Ta fadi tana lalube cikin wayar. A nutse ya sanya hannu ya zare wayar daga hannunta,saita bishi da kallo sanda yake aje wayar gefe "Meye na gaggawa bibi?,zan fadi mishi a sanda na lalubosu da kaina ba tare da neman taimakon kowa ko qarin haske daga gurin kowa ba.....zan tabbatar muku ina matuqar qaunarsu,kuma su din jinina ne....... numfashi na sannan kuma rayuwata.......saidai kuma,daga sanda na nemosu da kaina,a barni da matata saboda halalina ce ita din.....,inason ki isarmin da wannan saqon" baki bibi ta kama tana kallonsa,dukka ya gama sanyata jin kunya da nauyin kalamansa,data rasa abunyi sai kawai ta buge masa da borin kunya "Nice marainiyar wayonka kenan kazo ka zauna ka sakani a gaba kake gayamin?" Wani malalacin murmushi ya saki,don yanzun bashi da kowanne energy na biyewa bibi akan maganarta,sai ya miqe tsam,ya matsa gaba ya kama hannunta yayi kissing bayan hannun nata a kasalance yana cewa "Karki rigima dani,don nima gobe zan koma inda na fito in sha Allah" yana ganin yadda jikinta yayi sanyi saboda maganarshi ta qarshe,ya juya a nutse ya fita a dakin. Bai samu suhail cikin dakin ba,amma kuma yaji tashin muryarsa a harabar gidan shi da security,yasan halinsa dan rudu ne,yanzun haka wata hirar ya samu a can shi yasa yayi zamansa,dadewarsa da yawa kuma ya bashi tabbacin qilan ya wuce wajen mutuniyar tasa wato bibi. Sanda almu ya kawo masa abinci ya tabbatar masa da haka. Ba wani taste yaji a abincin ba,don ba abincin ba hatta gidan a daren salam yake jinsa,kafin suhail ya shigo dakin tuni ya kade passport dinsa ya sanya a yanka masa ticket,gwara ya koma Paris ya soma rage wasu abubuwan kafin binciken inda sukayi ya kammala,don yaci alwashi yadda yayi mata alqawari to sai ya cika,sai ya zaqulota ko a ina take cikin fadin duniya. Yayi sa'a qwarai ya samu ticket na jirgin da zai tashi daga abuja zuwa Paris direct kwanaki biyun da zasu zo a gaba,ba haka yaso ba, yaso ya samu wanda zai tashi a gobe,to amma haka dole ya haqura ya karba a haka,saidai iuma yaji yafi masa sauqi ya wuce Abuja gidan daya daga cikin kawunnan nasa ya jira kwanakin, uncle abdulhakeem ko uncle tahir. Sai washegari da safe yake gayawa suhail zai koma,yayi mamaki suhail din ya kuma tambayeshi me ya kawo wannan tafiyar haka ta gaggawa "Lokacine yayi" kawai ya amsa masa a taqaice "Alright,yayi,ni zan qarashe weekend dina a nan gidan,kasan gidan masoyi dadi gareshi,ga kuma sabuwar granny na samu,ina jin kusan sai sabon wata zan taddaka a Paris" "Allah ya kaimu" ya amsa masa a taqaice. Ya lura akwai damuwa me yawa cikin idanun maina din,to amma yasan hali sarai,ba lallai bane ya bashi amsa idan ya tambayeshi,don haka sai kawai ya tayashi da addu'a cikin ransa. ***********Jiran mintuna kadan yayi bayan ya shaidawa uncle tahir yana cikin filin sauka da tashin jiragen sama na garin abuja aka kirashi da wata baquwar number. Cikin matuqar yauqi da iyayi take magana ta cikin wayar "Hello......mr haidar?" "Yes" ya amsa a taqaice "Sunana ayana tahir me kano......kana ta wanne guri?,ina jiranka zanyi picking naka" "Gani nan qarasowa" ya amsa mata a taqaice daga inda yake yana hangota. Idanunsa ya sauke daga kanta,duk da ya jima rabon daya ganta,tun batafi shekara sha takwas ba amma hakan bai hanashi ganeta ba,saboda tsananin kama da sukayi da uncle tahir din. Straight gown ne a jikinta na wani yadi wine color,ta yane kanta da mayafi gray color me haske. Kana kallonta zakasan ta hada jini da abzinawa sosai,sai ya sanya wayarsh a aljihu ya jawo luggage dinsa yana nufarta. Garin waiwayen neman ta inda zaya bullo idanunta suka fada kanshi,sai ta tsaya cak tana goye hannayenta a qirji, murmushin da bata shirya ba ya subuce mata "Tun ba yau ba,na jima ina fadin ya hadu,ya hadu,ya hadu......maganata ta tabbata bayan shekaru bakwai rabona dashi" ta furta cikin zuciyarta saidai kuma labbanta suna motsawa,hakanan murmushi yana fita daga saman fuskarta. "U are welcome" ta fadi cikin karairaya sanda ta iskeshi a hanya tana amsar luggage din hannunsa. Hannunsa ya zame yana bar mata tare da danyin gaba yana amsa mata da "Thanks" "Saura kadan na wuce ai daddy yace na tsaya lallai na dauko yaya na" ta fadi tana murmushi sanda take bude masa side dinsa. Dan qaramin murmushi da yafi kama dana yaqe ya saki yana girgiza kai "Lallai naci sa'a kenan" "Sosai ma kuwa" ta fadi da zaqi da kuma kambama abun. Shiga kawai yayi ba tare da ya sake cewa komai ba,ta zagaya ta shiga itama ta rufe motar tana qoqarin tashinta. Ko cikin motar ta dameshi ta hira,tana ta sako mishi hirar da yake ganin sam bata shafeshi ba,hasalima ba lissafinta bane a gabanshi a yanzun. Sam yadda yayi bakam ita bai dameta ba,abubuwa da yawa take shiryawa ranta a kanshi,take kuma tsara yadda komai zaya kasance. Bayan tsahon shekarun batayi tsammanin koda rabin haka zaya kai ba,sai gashi ya zarta dukka tunaninta a ganin data yi masa,ya darata kyau ya darata ilimi,kaman yadda take da tabbacin dukka gatan da take gani tana dashi ya darata,saidai duk ba damuwa bane wannan a wajenta. Sai daya fara shiga a tsaitsaye ya gaisa da matar uncle tahir sannan ayana tayi masa jagora zuwa dakin da aka saukeshi. Komai sai data tsaya ta masa bayani dalla dalla tamkar yace mata yana da buqata,minti sha biyar kacal ta bashi ta dawo dauke da kayan abinci ta shirya masa komai, yayi tsammanin zata tafi ta barshi ne amma sai yaga tayi sabon zama,surutunta ya fara damunsa,don bacci yakeso yayi isashe,hutu yake da buqatar samu wanda zai bashi daman aiwatar da komai tsakanin kwanaki biyun da zaiyi a Nigeria zuwa tafiyarsa paris,amma ya fuskanci ba zata barshi ba "Zan iya samun space please,ina buqatar hutu" "Oh sorry,bari na barka ka huta,na sha'afa inata zumudin ganin dan uwa.....daddy baya nan,amma na tabbatan gobe war haka yana gida......idan kana da buqatar wani abu ka kirani,kada ka damu, number dana kiraka dazu a airport itace number na......a huta lafiya" ta furta tana murmushi hadi da waving hannunta. Kai kawai ya daga mata ya maida idanunsa ya rufe,yana irge da takunta a haka har xuwa sanda ya fuskanci ta fita,ya miqe da hanzari ya isa bakin qofar ya murza key ya rufe yana furzar da iska daga bakinsa "Muddin a gidansu wannan yarinyar zaiyi kwana biyun nan to tabbas zata sabauta masa kunnuwa da dan banzan surutunta,wannan da suhail tafi dacewa" ya fadi qasan ransa hannayensa zube a aljihun wandonsa yana komawa inda ya jona system dinsa da yakeson ya fara aikun binciken location na ama ko sultana..*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 80 Bashi yabar kan system din ba sai da yaji ana kiraye kirayen sallar magariba,duk da yaji an masa knocking kusau sau uku,sannan kuma yaga musicals na ayana amma ba wanda yabi takai. Wanka ya soma sakewa,ya canza kayansa suwa abaya na Maza,ya Sanya slippers da ya gani a sashen wanda ya tabbatar an ajjiyeshi ne saboda baqi ya wuce masallaci. Magariba da ishai duka acan yayi,bai dawo ba sai bayan ishai din. A farfajiyar gidan ya zauna yana amsa wayar suhail. Tun daga nesa ya hangeta sanye da English wears riga da skirt da suka zauna mata daidai jikinta,ta yane kanta da qaramin scarf kunneta manne da earpiece,kansa ya dauke kadan kamar bai ganta ba yana ci gaba da wayarsa. Baisan ya akayi ta hangoshi ba,ta iso wajen fuskarta dauke da fara'a "Ashe kana ta nan kana hutawa,nayita knocking na jika shuru" . Dan shuru suhail yayi daga bangarensa sannan yace "Wacce babe ke magana?" "Excuse me,zan kiraka" maina ya fadi yana katse kiran,don bayason taratsin suhail,yanzu sai ya qara masa damuwa. A nutse ya daga kai ya dubeta,saita sakar masa murmushi "Nayi disturbing naka ko?,am sorry bansan waya kake bane" ta sake fadi tana neman wajen zama kusa dashi. Miqewa yayi yana maida wayarsa aljihu "Zan shiga ciki" "In qaraso na tayaka hira idan ba matsala?" Ta tambayeshi tana karyar da kai,har cikin zuciyarta tana jin wani abu yana mata suka game dashi "Idan ba zaki damu ba kiyi zamanku a nan,akwai aikin da nakeyi ne a ciki,but idan na gama i will let you know" yace da ita yana dan soma takawa "Alright" ta amsa masa a sanyaye tana binsa da kallo. Sai da ya bace mata sannan ta sauke ajiyar zuciya "Ya hadu,ya isa mijin aure" ta furta qasa qasa tana sakewa kanta murmushi,addu'a takeyi cikin ranta Alllah yasa zai dade cikin gidan nasu,wala'alla ta samu damar da zata gabatar da qudurinta cikin sauqi a kanta. Ta tabbatar komai zaizo da sauqi,tunda dai jini daya suke ita dashi din. _ni kuwa nace hmmmm,hala bata yiwa aliyyun cikakken sani ba_ Washegari dukkansu suna dining suna cin abincin dare,shi uncle tahir daya dawo tunda yammaci daga tafiyar da yayi din,sai kuma ayana da qannenta mata guda biyu,hajar da nusaiba. Gaba daya tabi ta addabi motsinsa,ko yaya ya motsa sai tace "Akwai wani abu da kakeso ne?" Saidai kawai ya girgiza mata kai. A haka har sukayi nisa da cin abincin nasu,suna dan taba hira da uncle tahir din kadan kadan. "Ina zaka koma yanzun?" "Paris daddy" "Wow......paris?,daddy na samu abokin tafiya kenan" ayana ta tari zancan tana nuna zaquwa da murna cikin muryarta. Da alama uncle tahir din dan boko ne na gaske,sai ya saki murmushi yana duban maina "Ashe fa qanwarka cikin watannan itama zata wuce paris din,kaga shikenan na samu me kulamin da wasu al'amuran nata ko?" Uncle tahir din ya fada yana murmushi. "Ma sha Allah" kawai maina ya iya fadi,amma shikam baiga ta inda zai hada sabganshi da ayana ba,bama ayana din ba,shi kwata kwata idan ka debe yaran gidansu bashi da wani hadi da mata,ba harkarshi bace,wannan dalilin ya sanya har yanzu laila ta kasa saito kanshi,shima kuma ya kasa sanin yadda zaiyi da ita cikin ruwan sanyi,saboda girmamawa ga iyayenta da yayanta sardauna. ***********Washegari uncle tahir da kanshi ya rakashi airport,ayana na maqale dasu don ita tayi driving nasu ma zuwa airport din. "Don Allah yaa haidar.......kar ka manta dani,kana da number na,kayi qoqari ka kirani idan kun sauka,inaso mu fara sabawa ne tun yanzun" ta furta tana langabe kai idanunta a kansa sanda yake sanye da wata lafiyayyar suit da aka saqata da zaren vicuna. Wani irin kwantaccen kyau take hanga tattare dashi,wanda tayi imani shi kansa baisan yana dashi ba,komai nasa a tsare yake cikin aji,wanda tayi imanin muddin ta mallaki maina din Allah ya gama sallamarta cikin gidan duniya dai. Tasha ji mummynta na labarin kyan da family din MAYAK'I inda auty hamdiyyan ke aure,amma da yake ta jima basu hadu ba ba zata iya hasashen fuskarsu a zahiri ba. "Zan qoqarta" ya amsa mata a taqaice,don gaba daya surutunta yakai masa iya wuya,dabi'ace da sam baya sonta,tana daya daga cikin abinda ya dinga hadasu fada da sultana a baya. Sosai yayi relaxing cikin jirgin,kyawawan lion eyes dinsa a rufe,yayi nisa cikin tunani,amma kuma kunnuwansa na jiye masa 'yan surutai dake tashi cikin jirgin qasa qasa daga passengers dake magana da mabanbantan yaruka. Basu jima ba aka daidaita komai,aka kuma bada sanarwar tashin jirgin,ya jawo belt ya daurawa jikinsa ba tare da ya bude idanunsa ba. Sanda jirgin ya daidaita a sararin subhana sai ajiyar zuciya ta kufce masa,wani sasauci yakeji daga cikin zuciyarsa,abinda bai taba hasashe ba haka kawai sai ya tsinci zuciyarsa da samun sukuni,kurkukun da yakejin kamar yana ciki sai yaji kaman an zareshi daga ita "Alhamdulillah ala kulli haal" ya fadi qasa qasa. Wayarsa ya jawo ya bude,kyakkyawan hoton benazeer da batoul da ya mamaye fuskar wayar ya bayyana,ya saki murmushi yakai hannunsa yana shafa hoton,kewarsu sosai tana taso masa,kwana uku kacal da yayi bai gansu ba sai ya dinga jin kamar shekaru uku yayi "Am on the way.......zan fiddoku duk inda kuke indai cikin duniyar nan ne" ya fadi cikin ransa yana sake sakin wani murmushin. *PARIS* *champs elysees paris* *8th arrondissements* Tun shigowarsu unguwar yakejin tayi masa,yanayi da tsarin unguwar gaba daya ya dace da yanayinnsa da tsarinsa. A nutse yake bin ko ina da kallo,daddy din karimi ne na gasken gaske,tsakaninsu da sardauna suhail har zuwa shi kansa da yake bare a tsakaninsu riqo daya yake musu,kallo kuma daya yakeyi musu,ba wani banbanci da yake nunawa duk qanqantarsa. Ko ba'a gaya mishi ba ya sani 8 arrondissements din na cikin unguwar masu matsakaicin matakin rayuwa qwarai da gaske,kuma daddyn duka yayi hakanne saboda shi,saboda jin dadinsa,asibitinsa da zaya fara aiki a ranar litinin yana kusa sosai da nan din,sai kuma yafi masa sauqin gabatar da komai. A nutse baturen faransan me suna Ahmad ya tsaida motar gaban gidan,a hankali ya zuro qafafunsa waje ya fito yana ambatar "Bismillah,Allahumma anzilni munzalan mubarakan wa anta khairul munzaleen" ya qarashe fada yana shaqar fresh air din dake kai kawo a tsakanin layukan dake da wadatar tsirrai iri daban daban,idanunsa akan ginin gidan,tsarin ya masa sosai duk da bai shiga ciki ba,abinda ya fuskanta dukka gine ginen dake wajen iri daya ne,abinda ya sake qawata unguwar kenan. Ahmad da dayan yaron daya kasance Christa su suka shiga masa da komai nasa ciki yana biye dasu a baya. Sanda suka kammala komai sun sameshi a falon gidan,ahmad ya miqa masa muqullan ko ina yana ce masa cikin harshen faransanci "je suis disponible quand tu as besoin de moi(duk sanda kake buqatata zaka sameni)" "merci(na gode)" maina ya fadi yana karbar key din "Il y a un employé qui fait le ménage et cuisine qui viendra plus tard(akwai ma'aikata masu tsaftace waje da dafa abinci zasuzo daga baya)" "pas de soucis(ba damuwa)" ya amsa musu cikin jin dadin jigila da hidimar da sukayi dashi. Sallama sukayi masa sannan suka juya suka fice,abinda ya bashi daman wucewa cikin bedroom din daya zabi zama a ciki cikin bedroom uku da gidan yake dashi. A gajiye yake sosai,don haka ya sabule kayan jikinsa ya fada wanka,koda ya fito zama yayi ya nema number daddy ya shaida masa isowarsa "To Allah ya huta gajiya,ka huta sosai saboda ka samu energy din yin aiki yadda ya dace,karka shaidawa laila ka dawo,don ba zata barka ka huta yadda ya kamaya ba" daddy din ya fada yana murmushi me sauti. Kunya da kuma nauyin daddy dinne ya saukar masa,baisan ya zai kalli idanunsa watarana yace masa babu soyayyar laila ko daya cikin zuciyarsa ba,yana kunyar randa zaice masa yana mata soyayya ne kawai irin ta yaya da qanwarsa. Sardauna ya kira bayan sun gama da daddy,sannan daga qarshe ya kira suhail. Zancan daya fara masa ya sakashi katse wayar,ya fara sansano akwai wata a qasa game da batun suhail akan sultana,wannan ya sanya zafin zuciyarsa akan batun da suhail din ya koma kashi hamsin zuwa dari,saidai yayi rantsuwa duk sanda hasashensa ya zama gaske sai suhail ya raina kanshi. Tunawa yayi da uncle tahir,ya kamaci ace ya kirashi shima,sai ya soma duban number dinsa. Bugu biyu aka daga,saidai kuma muryar ayana ce ta fara fita daga wayar. Kanshi ya dafe da hannunsa,an riga an daga bare ya kashe,dole hakanan yayi sallama bayan ta cika masa kunne da fadin "Hello.....hello...... who's on the line?" "Assalamualaikum warahmatullah" "Yes........yaa haidar?, thanks for calling,zancanka yanzu nakeyi" ta fadi da zaqewar nan tata da surutu daya fahimci baya mata yawa. Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai yaji uncle tahir ya karbi wayar "Thank God" ya furta a fili can qasa qasa,sallamar uncle tahir din ya maida hankalinsa jikinsa,suka gaisa sosai ya kuma yi masa barka da hanya "Nasan u are tired......ka huta tukunna,mamanka da ayana suna gaidaka" har cikin ransa yaji dadin hanata wayar da uncle yayi,don haka ya amsa da "Ina amsawa,ina gaidasu sosai" daga hakan ya samu ya katse kiran yana furzar da iska yana latse wayar zuwa yanayin kasheta gaba daya,duk da yana buqatar yin magana da goumar wanda tunda ya dawo daga niamy aka ce masa yayi tafiya,bai kuma san inda yake din ba,bai samu kuma sukunin nemansa ba,amma a yanzun yafi buqatar kashe wayar don kada wani ya dameshi. Yana shirin shiga wanka yana auna yadda ayana din ke zaqewa rayuwarsa da yawa,duk wani motsinta ya gama fallasa masa me takeson kutsa kanta a ciki,ya lumshe idanunsa sanda yake watsawa kansa ruwa "Sultana" ya furta sunanta,ita daya ce matsalarsa a yanzun,ya kuma yi alqawarin zaiyi mata shigar ba zata ne,bazaiyi mata da sauqi ba wannan karon,dolen dole ta tsaya ta fuskanceshi koda bata shiryawa hakan ba,ya shiryawa komai da kowa ma. Wannan tunanin ya sakashi kammala wankansa a gaggauce,yanason ya kammala binciken da ya fara yi,bayason abun ya daukeshi da nisa,yanajin nasara cikin jikinsa,yana jin cewa tabbas addu'o'insa ba zasu tashi a banza ba.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 81 *_SULTHANA_* **********Dukka wani mayuka zuwa qananun engines na gyaran gashi ta zube cikin bathroom dinta tana hidimar gyara dogon gashinta. Dole ta zama wata 'yar gayu ta musamman,komai nata ya canza,wani irin feleqe gareta yauqi da ya hade da wani irin aji kyau da kuma zallar kulawa na gyara da take samu. Zama da ama din ya zame mata kamar wata jami'a ta musamman,tayi naso da dabi'unta masu tarin yawa. Tana tsaka da taje kanta ta soma jiyo hayaniyarsu,sharewa tayi taci gaba da abinda takeyi saidai kuma hayaniyar tasu kaman qaruwa yakeyi,dole ta ajjiye comb din ta dauki qaramin towel ta rufe kanta ta fito. Tsaiwa kawai tayi riqe da qugunta tana kallonsa,harda ama,tana cikinsu,sun baje kaya masu uban yawa tsakiyar falon sunata zabe zabe. Batoul ce ta fara ganinta,tana ta dariya ta kalleta "Guess what mummy?" Sunan mummy din data kirata dashi ya sanyata tayar da kai ta kalleta sosai. Sau daya suka taba fadi ta hanasu, w sunce daddynsu ne yace mummynsu ne,sunanta mummy not aunty. Haushinsa ya kamata a sannan,meye nashi da wani shishshigi zai sauya mata suna daga sunan da yaran suka saba kiranta "Mummy ki canka" benazeer ta fada da qarfi tana boye abu a bayanta. Wannan yaja hankalin ama daketa tara kaya gefe guda ta waiwaya tana kallonta "Ki canka din mana.......suna birthday month dinsu ne,saiki gaya mana date muga idan kin riqe" ta fadi tana ciro wani kwali dake dauke da wasu kids wears designers na wani kamfani ta aje gefe. Murmushi tayi tana dan jin kunyan ama din,saita qaraso din ta zauna,sun sanyata a tunani "Yau 25th......kaman......kaman on 28ne" "Kaman ko kuma haka ne?" "Hakanne ama,28 sixs years kenan?" Ta fadi cikin mamaki tana dan fidda idanu. Murmushi ama tayi,taji dadi cikin ranta,don batayi tsammanin ta riqe ranar ba "Wanne kaya zaki saka mummy,ama zata hada mana birthday party?" Benazeer ta tambayeta cikin murna "No......ranar da na fara zuwa aiki washegari ne zakuyi,maybe ma ina gurin aikin...... but zan bada gift na" fuska suka bata dukkansu su biyun, benazeer ta karyar da kai "Please mummy" waiwayowa tayi ta zaro mata idanu "Ni ko ama?,......ama ne mummy" "Ama grandma kece mummy" ta amsa mata tana nunata da yatsa. Ama da ta kauda kai kaman bata gani dariya ya kamata,yayin da mamaki ya kama sultana sosai,wato duka yayi brainwashing yaran?. Bata gama wannan mamakin ba ta sake ballo mata wani ruwan "Daddy fa zaizo?,uncle goumar yace zaki gayyato mana shi" ai batasan sanda ta qarasa fiddo idanun nata dukka waje ba,wannan din kuma bai hana benazeer ci gaba da zubo da surutunta ba "Na daukama dashi zamuzo?,don Allah mummy ki gayyaceshi,we missed him a lot......ko batoul?" Tayi tambayar tana juyawa wajen batoul din. Da sauri yarinyar ta gyada kai itama,qarasa daburcewa tayi,sai kawai ta juya ta wuce ciki ba tare data samu amsar basu ba. Guri ta samu ta zauna,ta kasa qarasawa toilet din,wai anya kuwa maina zaibar rayuwarsu yadda ya kamata?,tana tsoron faruwar wasu abubuwa nan gaba. Dukka kayan da tasan sunyi cakudedeniya dashi a nijer ta waresu guri guda,don duk wanda ta dauko babu abinda takeji a jiki sai qamshinsa. An wankesu kusan sau uku kenan,amma bata daina ji ba,kawai saita sanya kuka tana rufe fuskarta,kukan da ita kanta batasan meye dalilinsa ba. *_MONDAY_* Da dukka karsashi da qwarin gwiwa ya tashi ranar duk don kada yayi disappointing daddy. Ya shirya tsaf shi da sardauna da zai wakilci daddy ranan farko da za'a fara amfani da asibitin. *_SULTANA_* Ta bawa ranar muhimmanci me yawa cikin tarihin rayuwarta,ranar nasara kuma ranar sa'a a wajenta. Tun bayan sallar asuba bata koma ba,ta kasa zaune ta kasa tsaye,hatta da kayan da zata sanya daga gida zuwa tv station din,da wanda zata saka yayin gabatar da program din a dakin da aka tanada don buqata irin wannan. Qasa ce ba irin tamu ba,suna matuqar bawa lokaci muhimmanci,don haka kafin cikar lokacin dukka iyalan hamdiyya abdu me kano suka isa gidan tv din don yiwa sultana rakiya a ranar farko ta kama aikinta,a matsayin cikakkiyar 'yar jarida da zata shugabanci sashen al'adu na gidan tv din. Ama aba benazeer da kuma batoul din dukkansu,sauka ta musamman akayi musu,bayan tattaunawa a wani qaramin hall na musamman dasu ama din a matsayinsu na iyayenta,sun basu tabbacin cewa zata samu dukkan kulawa da mutuntawa data dace da addininta da al'adarta da kuma mutuncinta,uwa uba kuma sun sani tana da qananun shekarun da take buqatar hakan,daga qarshe suka rankaya tare aka sadar dasu zuwa ga office dinta. Sam bakin sultana ya kasa rufuwa, murmushi ne zalla kwance saman kyakkyawar fuskarta,kyawawan tausasan labbanta sun fadada qwarai da mayalwacin murmushi. Madaidaicin office ne dake dauke da toilet da kuma balcony domin shan iska,ga spare din daki don changing kaya,an zuba mata komai don qawata wajen da kuma bata damar gudanar da aikinta hankali kwance. Aqalla sun kusa awa daya wajen,aba ya mata addu'o'insa sosai ya kuma bata taqaitacciyar nasiha data ratsata sosai ta kuma sanyaya mata jiki,sannan ya fiddo key din mota ya ajjiye mata a gabanta "Don sauqaqa zirga zirga,ranakun da kikejin qyuya kuma zaki iya bin train" hawaye ne suka fara digo mata,ta zame zuwa qasa saman gwiwarta sai ya dakatar da ita "Tashi ki koma ki zauna,kada kicemin komai,jinin mohmoud yafi qarfin komai a wajena,rayuwarsa mohmoud ya sadaukarmin,banda Mahmoud da yanzun haka ba'a san waye hamidou bama,abu daya zakiyimin shine,ki kula da kanki,ki karemin tarbiyyarki da mutuncinki.....bazan lamunci duk wani abu da zai zama cutarwa ko cin zarafi a tattare dake ba" dan dubansa kadan ama tayi,sai taji kaman yana magana a fakaice ne akan aliyyu,amma sai ta share zancan daga ranta,tunda bai kama suna ko kwatance da zai nuna shine ba. Duka suka tattara suka tafi suka barta ta fuskanci ayyukanta,wanda sai kusan yamma sannan zata dawo gida. A nutse ya maida qofar ya rufe yana ajiyar numfashi,baro mutanen da wajen hayaniyar da yayi sai yakejin kamar ya tserewa wani mugun abu. Kwata kwata baya son hayaniya ko surutu me yawa,yanzunne kanshi zai fara yi masa ciwo. A hankali ya zare suit dinsa na saman ya maqale,ya wuce toilet ya daura alwala ko zaiji mode dinsa ya daidaita,kasancewarsa kuma mutum da baya rabo da zama da alwala(hakan yana da matuqar muhimmanci,don tana bawa mutum kariya sosai daga dukkan sharrin wani abu me sharri mutum ko aljan). Saman sofa din da aka shirya daga wani sashe daban na office din ya zauna,yayi relaxing sosai yana fidda numfashi da kyau,har sai da yaji ya fara komawa dai dai. Qafafunsa ya sauke yana lissafa adadin kwanakinsa a paris,yana ganin kamar yayi nawar gano inda ama suke,don haka ya sanya hannu cikin zafin nama ya jawo system dinsa dake aje saman table ya bude. Aiki sosai ya shiga yi da ita,lokaci lokaci yana magana ta wayarsa,sau biyu ana masa knocking yana neman excuse akan wani aiki yakeyi me muhimmanci. Kimanin awa guda da wasu mintuna kusan arba'in din kafin hannunsa ya tsaya cak saman board din system din,yana duban sunan qasar dake yawo saman screen din. A fili fuskarsa shimfide da wani shauqi da farinciki,zuciyarsa fari tas ya furta "Paris!" Sunan ya fita tar a bakinsa da wani irin accent tattacce. Baya ya koma ya jingina sosai da kujerar yana tallafe da qeyarsa,wani sassanyan abu ke masa yawo cikin zuciyarsa,ama benazeer da batoul dinsa dukka suna Paris?,suna qasa daya?,jaha daya?,wannan shine dalilin da ya sanya yakejin raguwar qunci kenan daga zuciyarsa tunda ya sauka a qasar?,wannan shine dalilin da yasa ya dinga jin ya nutsu sosai da qasar?. "Komai yazo qarshe,zai kuma zo da sauqi" ya furta a fili yana jin kaman ya gansu ya gama. Knocking da akeyi shine ya katse masa tunaninsa,sai kuma kira ya shigo daga wajen sardauna "Am done.....yallabai a daure a budemin qofan" ya fada da sauqin kan nan nasa har sai daya bawa maina dariya,ya aje wayar baice komai ba ya tashi ya nufi qofar. "Done and dusted" sardauna ya furta yana saluting maina. Murmushi ya sakeyi,ya miqawa sardauna hannu "Daddy ya kamata ka bawa wannan salute din sardauna...... he's our mentor" "Harda kaima haidar......mafarkan daddy na shekara da shekaru dana gaza cika masa su yanzun ka zama silar cikarsu........ thanks for coming into our lives" jijjiga hannun sardauna yayi ya jashi zuwa kujera "Kowacce kaddara da silarta sardauna.......sanda duk wani abu ya sameka qila sila ce kuma ta samuwa ko faruwar wani abu ga rayuwarka,Allah shine abun godiya" kai sardauna ya jinjina "Haka maganar take......kunyi waya da suhail" "Karka ambatarmin shi,tunda ya bini ciwon kai kawai yake bani,na rantse saina ragargaza maka dan uwa watarana" dariya ya kubcewa sardauna,ba kasafai maina yake biyewa suhail ba,amma kuma duk randa ta hadosu to da zafi zafi abun yake zuwa "Indai suhail ne kayi duk yadda kakeso dashi,hasalima ni zan tayaka" ya bawa maina amsa yana isa gaban babbar tv plasma dake maqale a bango ya tsugunna ya kunnata,sannan ya juya zuwa wajen fridge yana cewa "Bari muga me zamu samu a office din likitan zuciya" cikin dan tsokana da jan wasa. Sanda ya bude bakinsa zai bashi amsa,daidai lokacin muryarta ta karade dakin,cikin tattausar muryarta me dauke da tataccen harshen France,wanda daji kasan ba tsintarsa tayi a hanya ba,don ya kama bakinta radam. Idanunsa nakan wayarsa a sannan yana duba saqonnin ayana da na laila da suka kusan yin gware wajen shigowa wayarsa,kowacce na tura masa saqon fatan alkhairi ne da fatan nasara. Da sauri ya cira kansa daga screen din wayar zuwa screen din tv din,idanunsa sukayi kuwa kyakkyawan gani. Beautiful sultana,farar ba'abziniya wadda dukka kamanninta sukafi karkata da jinin arab,fara sol me wata irin ni'imtacciyar fata me azabar sulbi da sheqi,sanye cikin ainihin kayansu na al'ada,kayan da aka san kowacce mace ba'abziniya da sakasu,kalar shuni da sukayi masifar fidda kyawunta suka dace da jikinta,hatta da kyawawan qwayoyin idanunta a yau sun fidda kyansu,brown din qwayar idanu me wani irin sheqi tamkar an diga mai a cikinsu,siraran labbanta sunsha nasu adon,kamar yadda zara zaran yatsunta da hannayenta suka sha adon banguls na azurfa da tagulla da wasu irin duwatsu irin nasu. Gashinta kawai bai fito ba,ta sayashi cikin daurin kallabin dake kanta. Da qyar ya zuqo numfashinsa,da mugun wahala da kokawa da rai ya zaquloshi ya maidoshi cikin qirjinsa. Me yake shirin gani haka? "Ba sultana bace" wani sashe na qwaqwalwarsa ya gaya masa "No" ya furta a sarari wanda banda hankalin sardauna nakan wayar da yake amsawa fes zai jishi. Sultana ce,babu wani yanayi da zai hanashi gane sultana,babu shi a duniya!,tsanani wahala ko dadi. "Ma sha Allah,wannan kamar shigar gargajiyarku ko haidar?,da alama presenter din expert ce......wannan program din zaija jama'a gaskiya" sardauna ya fadi bayan ya dauke idonsa daga saman tv din yana lalubar wajen zama. Kasa hadiye abinda ya taso masa yayi,ya sanya remote ya kashe tv din gaba daya. Dago kai sardauna yayi da zummar tambayarsa me yasa ya kashe?,ya barshi suga gargajiyar nijer a paris mana?,sai maina din ya rigashi tambaya "Wanne gidan tv ne wannan?,a ina kuma yake?" _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 page 82 "ga logo dinsu can a sama,kaman national TV ne ai ko?" Sardauna ya fadi yana kai cup din bakinsa. Remote din ya ajjiye ya sake daukar wayarsa cikin karsashi,gefe guda yana jin ranshi yana sosuwa,yana hasaso dubban miliyoyin jama'ar dake kallonta yanzu haka live "Ya salamu ya Allah" ya furta qasa qasa bayan dukka bayananta sun fito a page din gidan tv din a matsayin sabuwar ma'aikaciyarsu ta sashen al'adu. Iska ya sake furzarwa,kusan ya gama samun komai,a yanzun samun adress nata ba shine a gabansa ba,don yasan bazai zama damuwarsa ba. Bai sauka ba sai daya gama bincika dukkan abinda yake da buqatar bincikawar,wanda ya daukeshi dogon lokaci,don har sai da sardauna ya tafi ya bashi cikin office din. A nutse take driving cikin takatsantsan dabin dokokin qasar,gefe guda kuma ranta fes,nishadi takeji sosai a ranar,komai yayi successful,su kansu suna yabawa da yadda ta gabatar da program din cikin zaar qwarewa,babu wani abu da zai sanya kayi tunanin farin shiga ce ita din,ta samu yabo sosai,hakanan a iya ranar kawai gidan tv din ya sake samun qarin viewers da sukw bibiyarsa ta kafafen sada zumunta da sauran kafafen sadarwa. Ta cikin speaker din motar ta jona take sauraron VN din aminata da ta bibiyi shirin sanda ake gabatar dashi. Kalmomin yabo ne sosai da kuma alfahari da ita da family MAYAK'I keyi,ba aminata kadai ba,ta samu saqonnin cousins dinta da yawa da ayanzun take saurara yake kuma sake sanyata nishadi, kyakkyawan fuskarta tattausan murmushi kawai take fiddawa wanda yake qara mata wani irin kyau da kuma kwarjini. A nutse ta isa qofan gidan,ta ajjiye motar a muhallin da gwamnati ta aminta da ajjiye ababen hawa,ta bude motar a nutse ta cire wayarta tana daukan hand bag dinta idanunta ya sauka akan pack na snacks da abokiyar aikinta 'yar qasar nijer ta bata dioura. Zuwan sultana ya yiwa dioura dadi sosai,don sai ta jita tamkar a gida nijer,ta samu 'yar uwa abokiyar aiki. Wunin ranar nan nan ta dinga yi da sultana,ganin farko dama Allah ya hada jininsu,gashi kuma suna qasa daya. Daukan pack din tayi tana murmushi tana tuna kirkin dioura,a yau din tana jin duk wani baqinciki da bacin rai dake ranta ya goge fes,sai ta soma takawa cikin gidan riqe da Jakarta. Sau daya tak ta danna bell aka bude kaman ana jiranta ne dama. Wani abu taji an watsa mata tadan kauda kai kafin ta bude idanunta tana duban benazeer da batoul dake tsalle a gabanta "Happy happy mommy,first day a gidan tv" benazeer dake fama tsalle ta fada "Mun ganki mommy Allah" batoul itama ta fada tana dariya. Murmushi ya qwace mata,abun nan da bahaushe ke cewa diyoyin sanyin idaniyar iyayensu shine ya saukar mata,tadan saci kallon ama dake tsaye tana murmushi,saita ajjiye kayan hannunta ta tsugunna ta rungumesu dukansu "Thank you,na gode sosai" sai kuma ta miqe a kunyace ta qarasa gaban ama tana kallon dam decoration din da suka yiwa falon da rubutun congratulations "Barka da warhaka ama,ya gida ya yara?" "Barkanki dai ma fille('yata),tu as travaillé dur(kinyi aiki sosai),nayi alfahari sosai dake yau,ina fata Allah ya qara haska miki rayuwa,ya haska miki kuma dukkan kyakkyawan abu,ya haneki da fadawa hanyar da ba dai dai ba" ama tayi mata dukkan wadannan addu'o'in tana dafa kanta. Kunya ta sake kamata,ta rusuna tana sunkuyar da kanta qasa,sai ama din ta dan janye baya. "Ki shiga ciki ki huta kafin aba dinku ya dawo ki bamu labarin yadda aikin ya kasance" "To ama na gode" ta amsa mata. Da kallo ama din ta bita,dai dai da rana daya bakinta bai tana gajiya ba wajen roqon ubangiji ya daidata dukkan al'amuran rayuwarta,kai ta kada tana maida dubanta cikin falon,saita nufi benazeer da batoul da suka tasa cake din da ta sa aka kawowa sultana din a matsayin gift a gabansu suna lakata suna ci ta soma musu tsiya "Tofa ga shazumamu me bakin shan zaqi" *_Aliyyu maina_* Sake juya fuskar system din masa yayi a karo na babu adadi wai ko arrow din dake masa nuni da direction din arean da phone number din yake aiki zai sauya akala,saidai fa ina,duka adress din da arrow din suna masa nuni ne da gidan dake kallon nasa gidan. Tsananin mamakinsa ya qaru,ya kashe system din ya sake kunnata,ya koma kan aikin nasa still abu daya yake nuna masa. Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya sauke qafafunsa a hankali,ya zura takalmansa ya taka a nutse har ya isa gaban babban window din dake facing gidan da arrow din ke nuna masa. Hannu biyu ya saka ya yaye labulen yana sauke idanunsa akan gidan. Kamar kowanne gida dake qasarma gaba daya zai iya cewa,a rufe yake ruf baya iya hangen komai da zai bashi satar amsar tambayarsa. Dukkanin idanunsa ya zubawa gidan kamar yana fatan ganin gilmawar wani,saidai shuru ba motsi ko gilmin komai. A qalla ya kusa kashe awa biyu kenan daga aikin zuwa tsaiwarsa a wajen yana neman hujja,tunda ya dawo daga office bai bar gurin ba,ko abinci bai nema ba daga wajensu Ahmad,ruwan lemo kawai yake dirkawa cikinsa. Sakin labulen yayi da zummar komawa ya sake bincikawa,amma sai kuma yaji zuciyarsa ta kasa yarda da qaryata binciken da takeyi. Sake juyawa yayi ya kalli gidan,sai ya taka a hankali ya koma mazauninsa ya dauki wayarsa ya fara laluben number ahmad. Bugu biyu kacal ya dauka,komawa yayi ya zauna yana amsa gaisuwarsa da harshen faransanci "Ina da aike da zanyi maqota,akwai dan aike da zan samu?" "Eh akwai,nan da mintuna biyar zai iso yallabai" "Da kyau,na gode" "Ba godiya yallabai" ahmad din ya fada yana murmushi. Shi daya yasan zallar karamci irin na maina,ya jima bai hadu da mutum me karamcinsa ba,amma kuma da sardauna yake gaya masa halin dattako irin nasa sai gaba daya ya qara sallamawa lamarinsa. A nutse ya miqe yana binciken me zai aika dashi gidan a mazaunin saqo?,me zaya bada wanda zai bashi damar fahimtar su waye mazauna gidan?. Tunawa da yayi da su benazeer ya sakashi bude fridge yana laluben chocolate din da ahmad ya zuba tun randa yazo gidan,shi din ba gwanin shan zaqi bane,wannan ya sanya ya manta da lamarinsu gaba daya. Dukka kwalayen ya debo ya shiryasu saman table,dai dai sanda yaji ana danna bell sai ya taka ya bude qofan. Matashin saurayin bature ne dogo siriri,ya gaidashi cikin girmamawa,ya amsa masa yana masa nuni da kwalayen,sannan cikin yaran faransanci ya nuna masa gidan da zai miqa din. Bakin window din ya koma ya sake budewa yana dafe window din da hannayensa,yana biye da takun matashin har ya isa qofar gidan ya kuma soma danna qaraurawa. Tana zaune tsakiyar benazeer din da batoul tana musu adon gashinsu. Dole suka sakata gaba akan ita zata gyara musu kansu saboda goben sunsan zata fita aiki ne tun da safe. Ama na zaune a gefe tana duba wani littafi daya shafi hikayoyin gargajiya da aka rubutashi da yaren faransanci,sultana ta yunqura zata miqe saboda qarar door bell din,sai ama ta ajjiye littafin tana cewa "Yi zamanki" ta jawo wani madaidaicin farin hijab ta sanya ta miqe tana nufar qofar,a nutse ta murza key din sannan ta Murda handle din ta bude. Tarwai fuskar ama dinsa ta bayyana a gaban qofar,ya lumshe lion eyes dinsa yana jin wani abu yana tsarga masa,ya sake budesu da sauri dai dai sanda ta waiwaya bayanta tana magana,da alama da sultana take magana,yadda kuma take kallon saqon bayan ya miqo mata ya bashi tabbacin ta dago haske ne,ko kuma ranta ya darsa mata wani abu. "Merci" ta furta da yaran faransanci bayan ta karbi kwalin dake da sanyi alamun daga gidan sanyi aka cirosu. Tunda ta karbi kwalin jiki da zuciyarta ke raya mata wani abu,alamu da motsin aliyyunta takeji all over her heart......tana jin kamar yana kusa dasu ne,tana da yaqini kaso tamanin cikin dari cewa daga hannunsa wannan ya fito. "To idan bashi ba waye?" Ta tambayi kanta sanda zuciyarta ta soma mata wasi wasi. Daga ita har sultana ba wanda yayi ordering wani abu daga waje,hasalima sun gama siyan komai na birthday din yaran,goumar baya nan bare tace shine, after all shi daya yake wannan gift din ma yaran,tun sanda ma yake mutumin boye. "Indai kuwa shine tabbas d'ana ya cika sadauki......ya kuma cika namiji sannan ya nuna mazantaka daya lalubo family dinsa da kansa" ta furta qasan ranta murmushi yana qwace mata a sirrance,don tana da yaqinin bai samu goumar ba kwata kwata ko a waya ballantana tace shine ya bashi haske. Dukka idanun yaran yana kan kwalin saboda ganin masoyiyarsu wato kayan zaqi "Ama namu ne?" Benazeer ta tambayi ama. Rasa amsar da zata basu tayi,batason tayi wata magana da zata razana sultana ko ta sanyata dasa zargi a ranta kamar yadda zargin ya dasu a nata ruhin "Naku ne,ku diba kadan ku sanya raguwar a fridge karku sha ya muku yawa" cikin murna suka amsa din suka baje suna zaba. Ama na zaune tana binsu da kallo tare da hasaso ta ina maina zai bullo indai shine?. Yayin da sultana ma sam bata kawo komai cikin ranta ba,saboda tayi imani dari bisa darin cewa bai isa ya cimmata ba. Tattare kayan kitson ta farayi,don tanason ta shiga daki ta qarasa abubuwan dake gabanta ta kwanta da wuri,don tanason fita aiki da cikakken energy da kuma nutsuwa. "Nikam na gaji,tunda kun samu abunyi sai da safenku" "Goodnight mommy" suka amsa mata a kusan tare ba damuwa tunda sun samu abun maqulashe. Da baya da baya ya koma ya zauna a hankali yana furta "Alhamdulillah" murmushi ya qwace masa saman fuskarsa,dukkansu yayi missing dinsu,yayi kewarsu kaman hauka,shi kadai kuma yasan me yakeji. Agogo ya kalla,dare ya fara yi,amma kuma yana da muradi,yanason ya isketa a wannan daren,idan da hali idan kuma zai yiwu,yana sha'awar raba dare da ita,ya kamata a karon farko ya bata wani lesson me wuyar mantawa,ya bata wani babban karatu da kowanne motsinta zai dinga tuna mata "She's belong to him" Hannunsa ya damqe qam qam guri guda tsigar jikinsa na zubawa saboda tunawa da yayi da komai nata,lallausar fatarta me qamshin nan,lips dinta dake da wani irin sulbi da sanyi,sassalkar sumarta dake da wani irin sulbi,uwa uba dumin jikinta dake da wani irin tasiri cikin qasusuwansa tun tana mitsitsiyarta. Sake duba lokaci yayi,sai ya miqe a nutse yana komawa bakin window din,zuwa yanzu babu haske kwata kwata da yake iya hangowa,tabbacin sun wuce zuwa ga kwanciya,uwa uba qarin mota guda daya daya gani ya bashi tabbaci aba ya riga da ya dawo. Juyawa yayi cikin nishadi ya wuce bedroom dinsa. Wayoyinsa ya kashe dukka gaba daya,ya jawo drawer din madubin ya zubasu,sannan ya soma zare kayan jikinsa ya wuce zuwa toilet ya hada ruwa me yawa da dumi. Kwanciya sosai yayi cikin bathtub,yana shirya komai cikin kwanyarsa,dole yau ta tsaya ta fuskancesa ko kuma yayi forcing nataa ta fuskanceshi ta dolen dole.....zabi ne guda biyu.✌🏽 _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂. *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 83 Sai data dan sake bata lokaci gefen gado tana duba aikinta na yau,tare da dan qaramin research kan program dinta na wani satin da zata fara practicing dinsa tun daga gobe. Ta kusa awa daya sannan ta kashe system din ta mayar ta ajjiye,ta miqe tana miqa saboda gajiyar dake bin sassan jikinta. Tunda ta tashi yau din bata huta ba,yawan mutanen da yau tayi magana dasu da murmushinta a yau ya zarta na kullum. Mutane ne su masu son mutumin da yake da talent,wannan ya sanya suka yita zuwa ganinta tare da yabawa program din a iya yau kawai,dole kuma ta sakarwa kusan kowa a fuska kaman yadda ama tayi mata fadan haka sosai. Kayan jikinta dukka ta zare ta daura babban towel,ta bude jakarta ta ciro sabbin bath set dinta daya hada da shower gel bath mist da sauransu,ta zare ribbon dinta ta azashi saman madubi,ta dauki qaramin towel ta dora saman kanta don tasan wankan tsarki zatayi,don kafin ta fita dinner ta duba taga al'adarta ya dauke. Ta zura slippers dinta na wanka ta wuce toilet bayan ta daidaita sanyin dakin. Tun tana wankan takejin idanunta suna mata nauyi kaman zasu rufe saboda bacci da kuma gajiya,wata irin kasala takeji tana bin duka sassan jikinta,wannan ya sanya ta jima sosai a toilet din fiye da yadda ta saba dadewa. A hankali ya tura qofar dakin ya shigo,sanye yake da wasu fararen hoodie pyjamas masu matuqar taushi da sulbi,ya dora hulan saman kanshi amma hakan bai hana bayyanuwar sumar nan tashi me tsaho sulbi da kuma baqi ba. Duk da kayan farare ne amma yayi wani irin sassanyan kyau,fuskarshi tayi fes tayi tarwai kaman an qara masa hasken fata ne. Hannayensa duka biyun zube a aljihun wandon pyjamas din nasa,yana qarewa dakin kallo a nutse. Hankali kwance kuma yake shaqar daddadan qamshin da dakin yake fesarwa,qamshin wani irin freshener ne da ya cakuda da qamshin sassanyan turaren nan nata da yake mutuwar so. A nutse yaci gaba da nazarin dakin,daga qarshe idanunsa ya sauka saman gadonta dake dame a gyare abun sha'awa game kallo. Saman gadon nata ta yasar da fari qal din under skirt dinta hade da brazier dinta data zare. Cike da nutsuwar nan tamkar ba kutse yayi cikin gidan jama'a ba tare da saninsu ko izininsu ba ya soma takawa zuwa gefan gadon. Dab da kayan ya zauna,ya miqa hannunsa ya dagasu yana kallo. Qamshi suie fitarwa tamkar bata sanyasu ta fita zirga zirga dasu ba,ya lumshe idanunsa yana jin wani abu yana fara sauka masa yarr a jikinsa. Hannu ya miqa,ya dauki remote dake controlling dukka qwayayen dakin ya kashesu,sai guda daya daya bari wanda yake daura da mirror dinta. Gaba daya qamshinta ya gama kashe masa jiki,a hankali ya koma da baya yayi relaxing saman pillow din dake ajiiye fuskan gadon,ya daga undies din a hankali ya aza saman fuskarsa yana shaqar qamshin dake fita a jiki. Dadewar da tayi ya sanyata fitowa a dan gaggauce,kanta daure da towel din tana yamutsa sumarta da takeso ta ragewa danshi saboda batajin zata iya tsaiwar sanya drayer ta busar dashi. Dan qara kadan da qofar toilet din ta bayar ya sakashi juya kanshi sashen bandakin. Da dan sauri sauri taja qofar,tana takowa zuwa tsakiyar dakin. Jajaye lips dinta ke motsawa a nutse,da alama akwai abinda take karantawa. Lumshe idonsa yayi yana jin wani nauyi na raguwa a qirjinsa,gudun zuciyarsa kuma yana sake qaruwa. Cikin kallo me kama dana qurilla ya soma sauke qwayoyin idanunsa daga saman lips dinta zuwa fararen kafadunta masu sulbi da suka kasa riqe ruwan da tayi wankan dashi saboda santsin fatarta. Sarqafewa idanunsa sukayi a saman qirjinta data daureshi da towel,wanda sosai tudu da tsaiwarsu kyam ta nuna ta saman towel din. Yadda yaji yana neman fara kokawa da numfashinsa ya sanyashi qarawa kallonsa gaba,yanason ya more kallonta da kyau kafin lokacin da zata Ankara da wanzuwarsa a dakin. Santala santalan cinyoyinta suka sanya tsigar jikinsa zubawa,suka kuma tuna masa da wani dadadden yanayi da ya kasa manta irin duniyar da ya tsinci kansa a ciki,dole ya miqe ya zauna,sannan ya tattara dukka qarfinsa ya tashi ya soma takawa zuwa inda take tsaye. Ko kusa ko alama jikinta bai bata da mutum cikin dakin ba,tunda tasan qasa ce dake da doka da qa'idar da ba wanda ya isa ya haure maka gida,uwa uba kuma ta sani hatta su benazeer basu shigo mata daki sai sunyi knocking bare ama da bama shigowar takeyi ba idan ba kamawa tayi ba. Abu daya hancinta ya iya fahimta,kamar atmosphere na dakin ya sauya,da kadan da kadan taji kaman qamshin sake mamaye dakin yake,sai taja qaramin tsaki. Batasan me yasa hancinta ke yawan saurin tantance qamshinsa ba,batasan me yasa hancinta yake gane kowanne qamshi nasa ba,ta tsani wannan saurin gane duk wani qamshi na jikinsa,sai ta miqa hannu ta dauki comb ta zame towel din saman kanta ta zummar fara taje sumarta don ta samu tasha iska da wuri. Comb din taji an riqe kafin kuma ya kama qugunta yadda ya saba ya manne da jikinsa. Muguwar razana tayi wadda kadan ya rage ta fadi banda ya tallafota da hanzari "Ya salam.......take it easy mana......bakiyi zaton zuwa na bane?" Ya furta mata cikin kunnenta da wani sound da ya sanya ta kusa loosing control nata. Idanunta kawai ta mayar ta lumshe tana kiran sunayen Allah tare da qoqarin daidaita bugun zuciyarta,don kowacce laka ta jikinta tsoratar da tayi yabi ya kassarashi,taja numfashi da kyau sannan ta tattara dukka sauran qarfinta ta turashi. Abun takaicin ko gezau baiyi ba,sai hannuwan nata ma daya riqe da kyau yana dubanta. Fuskarsa a nutse tsaf yake dubanta "Cool down......ba fada nazo nayi muyi ba......duk da kinyimin laifin da ki wajen Allah idan baki nema afuwata ba sai Allah ya qonaki" ya fadi a tausashe,qamshin man data wanke kanta zuwa qamshin da jikinta ke fiddawa yana son fara rarraba masa hankali. Maganar tashi taji ta mata nauyi qwarai,wani abu me zafi ya tsaya mata a wuya,tanason ta fesar masa da maganganu ne to amma tana jinta a tozarce da yadda take tsaye haka a gabansa daga ita sai towel,duk wani sashe na jikinta yana nuna kansa. "Ka sakeni" ta fadi idanunta a lumshe da tsiwa cikin muryarta "I said calm down.......ki zauna ki fahimceni" "Bazan fahimceka ba,ta hauro mana gida ka.ketomin daki,ka tsaidani a gabanka kana qarema tsiraicina kallo?,kana tunanin idan nayi qararka akan hakan ba za'a karba min haqqina ba?" "Tsiraici?......haqqi?......,for sure kin manta waye ni cikin dictionary din kanki?" "Who are you?" Ta furta tana ware masa fararen idanunta. "You asked in the right place" abinda kunnuwanta suka jiye mata kenan,abu na gaba data iya ji shine damqar towel dinta da soma warwareshi tsaf daga jikinta. Iya gigicewa ta riga ta yishi,tayi imanin muddin ya cimma muradinsa na rabata da dan towel din da shine kawai garkuwar da ya mata katanga daga bayyanar jikinta ta kade,ta tattara dukka qarfinta cikin tashin hankali tana fadin "Stop it....." Baiko nuna kumnuwansa suna ji ba bare ta sanya ran ya fahimta,gigicewarta ya hanata fahimtar hakan,bakinta ya gaza kama kowacce kalma sai fadin "Stop it" "Stop it" data dinga maimaitawa,wanda duk fitar kalma guda daya daga bakinta kamar yana daidai da warwarewar towel din jikinta nata. Hawa daya tak ya rage masa ya kammala zareshi,bakinta na rawa ta sake maimaita masa kalmar cikin furucin da take sanya ran shine na qarshe da wata raunanniyar murya "Stop it......pleeeeassseee" kalmar qarshe din sai ta zamana kamar wata gaba ta karya lago a wajensa,ya dakata cak yana maida numfashi. Baya jin a yau zai iya barin sultanar.......baya tunanin zai iya qyaleta ko ya daga mata qafa,kowanne sashe na jikinsa muradinta yakeyi,hakanan yana son ya tuna mata wani abu data manta,yanason yabar mata abinda zata dinga jin kanta ko yaushe a MATAR AURE ce ita din kaman kowacce mace. Ragowar towel din da kowanne ya riqe a hannunsa yana son hana dan uwansa cikar burinsa ya jawo da wani irin zafin nama,sai gata gaba daya cikin jikinsa,sauran abinda kuma ya rage na towel din ya zame yayi nasa waje,abinda ya haukata kwanyar maina cikin qasa da second biyu,ya kuma gigita sultana gaba daya data fahimci garkuwarta ya fadi,ba wani sauran abu da ya rage da zata rufe tsiraicinta dashi,sai kawai ta dunqule cikin jikinsa kuka yana qwace mata. Dunqulewar da tayi a jikin nasa da zummar samun kariya sai ya zamana kamar turi tayi masa,tamkar fami ne ta yiwa wani tsohon miki kamar kuma susa ce ta yiwa kowanne gaba ta jikinsa,ragowar nutsuwar da tayi saura a jikinsa ta soma sulalewa,ya soma gagara kama hankalinsa........ _tom......qaqa qara qaqa_ _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 84 Kyakkyawan tarba yayi mata cikin faffadan qirjinsa,ya lullubeta tsaf irin lullubar da inda zuciyarta a sake take zata jita cikin aminci ne da nutsuwa tamkar kwanciyar d'a cikin mahaifiyarsa. Cusa kansa yayi tsakanin fuskarta da kafadunta "Calmez vous s'il vous plait(ina roqonki ki nutsu)" ya furta mata cikin taushi dason bata nutsuwa,maimakon nutsuwa sai maganar tasa ta qarasa hautsinata,don yana sauke mata hucin numfashinsa da tasirin muryar nan tasa da tun ba yau ba suke daya daga cikin abinda ke sanya mata tsananin shakkarsa. Yadda yaga taba sake curewar jikinta ko ina yana rawa ya bashi tabbacin ta tsorata ne,yana buqatar nutsuwarta fiye da kowanne lokaci,bayason ya maimaita abinda zataji ya qarasa fice mata a rai,baya son taci gaba da kallon mu'amalar aure a wani abu me kama da horo azaba ko wahala cikin rayuwar diya mace,he needs to show her me ainihin mu'amalar ke nufi,yanason shi da kansa ya tabbatar mata isn't a rape.......ba abinda take tunani bane. Tayi imanin zamanta cikin jikinsa a irin wannan yanayin kuskure ne babba,amma bata da wani sauran mafaka daya wuce wannan,zuciyarta ta gaya mata ta gwada masa barazans ko zai qyaleta,muryarta na shacking sosai kaman wadda sanyi ya kada tace "laisse-moi(ka rabu dani),ama da aba dukka suna kusa.......ihu daya zai kawos......su dakin.....na,ka sani ai" ta fada da qarfi tana daga murya wai ko zaiji abun ya tabashi ya barta. Siririn murmushi ya saki a galabaice,sai ya sauketa saman sofa bed,ya sanya hannunsa yana qoqarin banbare hannunta data cukuikuyeshi dashi. Sam taqi sakin nasa,saboda ta fuskanci janyewa zaiyi daga gareta alhalin bai bata wani abu da zata maye gurbin jikinta dashi ba. Tsaiwa yayi cak yana murmushi "Ahaaannn......kince na fita na tafi,but kuma kin riqeni......idan kuma nace zanyi abun kice nayi raping dinki.......cela montre qu'il y a quelque chose que tu veux(yana nuna cewa akwai abinda kikeso)"ya qarasa fadi da harshen faransanci "You missed me the way I missed you" ya sake fada da muryarsa na sake qanqancewa,yana jin kamar tana fita ne daga maqoshinsa da qyar saboda yadda jijiyoyin jininsa ke sake budewa,suna kuma aika jinin da sauri da sauri zuwa ga kowanne sashe na jikinsa. "Nooo....." Ta furta da muryar kuka. Kai ya girgiza mata shima alamar a'ah,cikin wani irin taushi ya zame jikinsa don yana da buqatar ganin abinda take boye masan gani na zahiri. Tunda yake idanunsa basu taba ganin wani abu daya fusgi dukkan hankali tunani da nutsuwarsa ba irin jikin sultanar,komai ya bayyana muraran,wani irin tashin hankali ya sauko mata ta fara qoqarin samun wajen buya tsakanin pillows da duvet. Da wani irin zafin nama ya cimmata a tausashe ya riqota,ya dagata gaba daya ya sauketa cikin jikinsa yana qoqarin cusa hannunsa tsakanin wuyanta zuwa qirjinta. "Nooooo pleeeeassseee" ta sake fada da sheshsheqar kuka,saboda iya riqon da yayi mata kawai ya soma gaya mata lallai abinda ya faru shekara biyar zuwa shida baya ne yake shirin maimaita kansa. Dukka haqurinsa yaji yana sulalewa,rashin haqurin nan nasa na asalin halittarsa ya fara taso masa yana tasiri wa ruhinsa,yadda take kame jikinta guri daya da kyau tana dukkan qoqarinta na ganin ta hana hannuwansa isa inda yake da muradi...... ta hanashi yakai gurbin da suka fi ko ina tsone masa idanu......ba haka ya sansu ba.....ko a wancan lokacin da komai ya faru cikin fushi zafin rai da fitar hayyaci amma kuma yana iya tunasu......ba haka suke ba,yaushe suka koma haka?,sun maida kansu yadda yake gani cikin mafarkinsa,sun koma yadda yake buri da muradi,burinsa a kansu masu yawa ne,yana cikin jerin mazan da suke da haushin wannan wajen,suke kuma da tanadi me yawa a kansu,tsananin kamun mai da zallar miskilancinsa ya sanya kosu suhail da sukan taba zantuka irin wannan bai taba sanya musu baki ba,basu kuma taba sanin kowanne plan nasa akan kalar matar aurensa ba. Juyeta yayi kawai saman tattausar katifar,ya kuma yi mata wata da faffadan qirjinsa cikin salon da bazai hanashi kallon fuskarta da qwayoyin idanunta da suka qara sheqi saboda ruwan hawayen dake kwance a ciki. Da gaske ihu takeso tayi masa amma sai takejin kamar an kame harshenta an riqe,a wannan yanayin idan tayi masa ihu ama ko aba suka kawo mata daukin da take da buqata da wanne idanu zata kallesu a gobe?. Fuskarta ya kawo cikin tafin hannunsa,ta sanya hannunta da ture hannun tana kauda fuskartata,cikin zafin nama ya kama hannuwan nata ya aza musu nauyinsa,sai ya zamana bata da wani sauran abu da zata kare kanta dashi,shi kuma yi ya bash damar zube hannuwansa a inda yaketa harin. Abinda ya sanya ya qarasa birkicewa gaba daya,muryarsa ta sarqe gaba daya,sultana kuma ta sake masa kuka na gasken gaske,tana jin wani abu yana yawo cikin sassan jikinta. Har tsakiyar kansa ya dinga jin saukar sautin kukanta,sautin daya dinga so ya tuna masa da abinda ya faru five yrs back,cikin birkitacciyar muryarsa data qanqance kamar wanda mura ta yiwa kamu ya fara magana,yana yi yana jan numfashinsa da kyau don yana jin kaman zai qwace masa ne. "s'il te plaît(please)Sultan give me a chance....no more aba,no more ama..... Aliyyu haidar kawai.....ki fahimceshi......ki bashi zuciyarki da tunaninki......all this while sultana zuciyata bata taba samun hutu ba,ban taba hutawa ba sultana......ban taba kwanciya nayi bacci cikin nutsuwa ba dukka shekarun nan saikin hanamin sukuni cikin bacci na......ban taba samun cikakken nutsuwar ruhi ba dukka shekarun nan......,pleeeeassseee sultana,ki yafemin......dukka laifin da kike tuhuma na dashi na yarda na dauka......zan gyara kuma.....ki bani Chance mu gina gobenmu......ki bani Chance na koya miki soyayyata,ki bani chance na inganta rayuwarmu data 'ya'yanmu" "Bana sonka.......bana......i hate you...." Ta fada cikin gunjin kuka sanda ya mata wata wawiyar runguma tamkar zai tsagata gida biyu. "You are a liar.......idanma da gaske kike daga yau zan koya miki yadda zaki fara sona" daga wannan bai sake bata daman magana ba,ya toshe labbanta da harshenta da nasa bakin da wani irin salon kiss.....wani irin tsotsa yakema lips nata da harshenta,sai daya tabbatar ta galabaita ta kuma haqura da yunqurin magana da takeyi,duk wani cizo da take kai masa da haqorinta ya shanye,bai qyaleta ba sai daya zuqe duk wani yawan bakinta tas,ya tabbatar numfashin dake kai kawo a qirjinta ya soma sauyawa sannan ya gangaro zuwa wuyanta. Wani irin zazzafan numfashi ya dinga sauke mata yana sansana wuyan kamar zai hadiyeta,saqonnin da yake sakar mata a iya wuyan kadai suka fara qoqarin rikita mata lissafi,ta bude baki zatayi magana amma numfashinta rawa yakeyi yana kai kawo tsakanin qirjinta da zuwa maqogaronta,koda zatayi maganar ma ta tabbatar ba wani sauti me kyau da zata bayar. Ita ce macen farko kaf rayuwarsa da ya fara sani a matsayin diya mace......amma kuma yana da sani me yawa akan mata.......duk wani sani nasa daya tara tashin shekaru saboda ita a ranar ya bude mata su babi babi,zafafan saqonni dake tafi da imanin me imani,ya kuma sauke dukka zafin kai da na zuciyar kowacce irin diya mace......izza taqama da kuma qasaitarta. Tun tana qoqarin qaryata abinda gabbanta keji har ta fara tsoron maina din......ya hanata kowanne motsi,zafafan 'yan aike kawai yake tura mata da suka sanya kwanyarta ta fara zafi,hannunsa zuwa harshensa kawai takeji suna yawo all over her body.......bai qyaleta ba sai daya tabbatar kowacce gaba a jikinta ya aje mata saqo me dumi da gigita tunani......a sanda kunnuwanta suka soma dodewa ta daina fahimtar kowanne sauti daidai,sanda gangar jikinta tayi nisan nisa cikin wata duniya daban da maina ya aikata......lokacin da ta soma tunanin dama tana da irin wannan feeings din cikin jikinta?,wanne irin shaidani ne mainan har haka da yakeson fiddata daga saitin hankali zuwa wani layi da yafi kama da mutumin da yasha wani abun bugarwa ya bugu?,sanda tayi nisa wajen tunanin ta yaya zata dakatar dashi......a lokacin ta jishi yana yunqurin kaita azababbiyar duniyar daya taba kaita tsahon shekaru biyar da suka shude......duniyar data aje ma rayuwarta tarihi.....duniyar da ko sau daya bata taba gushewa ko ta subucewa tunaninta ba. Daidai lokacin hankalinta yayi mummunan tashi,ta kuma yi azamar dawowa daga inda ya kaita din,cikin galabaitacciyar muryar da ko maqoshinta bata kaiwa ta soma magana kai kace magen data sha wahala a hannun yara "Don Allah.......kayi haquri...... please Allah bazan sake komai ba....suis désolé pleeeeassseee" ta qarashe maganar tana jan wani dogon numfashi sanda ya cimma gaci. Daga shi har ita ba wanda zai iya tantance meye ya biyo baya,kimanin wasu mintuna ta sake dawowa hayyacinta karo na biyu,ta fara sauka daga layin amasar saqonninsa,ta soma hawa wancan layin da take tsoro. Zuwa lokacin bashi da katabus din kansa bare nata,tuni ya sake mata hannayenta,wanda dasu tayi amfani ta tattarasu saman qirjinsa tana turashi "Leave me......i beg you.....don Allah" ta kuma fadi hawaye karo na biyu suka soma cika mata idanu. Me yasa tayi gangancin qyaleshi har yakai ga wajen? Taji wata tuhuma daga can qasan zuciyarta. "Don Allah ya maina...." Ta sake fada tana sakin kuka. Yana iya jiyo muryarta sama sama cikin kansa,amma kuma qwaqwalwarsa bata aikin da zata rarrabe me take fada. Sake qanqameta yayi da kyau muryarsa na rarrabewa kamar zai shide mata "Don Allah sultana......." Shima ya fadi yana sake qanqameta kamar za'a rabashi da ita,tamkar zata bacewa ganinsa. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 85 Abinda bata lura ba duk sanda sautin muryarta ya fita sai ya zamana kaman qara masa qaimi takeyi,abun ya soma bata tsoro saboda ta fara karbar gashi yadda ya kamata,zuciyarta ta cika da fargaba,ta tuna yadda ta qwaci rayuwarta da qyar a wancan lokacin,sai ta saki kuka da gasken gaske,yayin da ya sake tattarata zuwa jikinsa sosai muryarsa na sake yin rawa kamar wanda aka yiwa wanka da ruwan qanqara yana fusgar kalmar "Am sorry.......am sorry please help me......" Idanunta ta maida ta kulle gam tanayin surrender,ta sani yau ma Allah ne kadai macecinta. Dakatawarta daga dukkan wani yunquri ya sake bashi nutsuwa qwarai da gaske,ya kuma zame masa tamkar wani taimako a gareshi da zai isa wata duniya me matuqar tarihi cikin rayuwarsa. Ji tayi kamar zata amayar da 'yan hanjinta lokacin da ya sake rungumeta tamkar zai ballata gida biyu "Wayyo Allah" ta fada murya a karye hawaye masu dumi suna sauko mata. Har cikin jikinta taji zafin yadda ya matsetan. Da sauri ya sassauta riqon,ya kuma daga fuskarsa da ta sauya launi,zagayayyun lion eyes dinsa sun wani jirkice,jirkicewar da bazata iya kallonsu ba,saita maida qwayar idanunta ta lumshe. Hannunsa ya Sanya da sauri saman idanun nata,gumin daya jiqe masa fuska yana diga saman fatarta "Please open your eyes.......ban ji miki ciwo ba ko?" Ya fadi a dan rude yana tsoron maimaituwar wancan tsautsayin. Wani nauyi takeji a zuciyarta,kunya haushi da takaici dukka sun cikata,wannan ya qara yawan ruwan hawayen dake bulbula ta qasan idanunta. Sosai ya rude,da sauri kuma ya rage mata nauyinsa daya aza mata dukka. Fuskarta ya dago da kyau yana duban fuskarta da take fes tarwai,babu komai sai digon guminsa da nata da suka gauraya waje daya. Ko a haka da idanunta ke a rufe yana iya hangen zallar kyan da suke dashi "Sultana" ya kirata da wani sauti me matuqar sanyi da sanin yadda ake furta ainihin sunan "Please open your eyes.. kalleni sultana" "Idan ka gama zaka iya wucewa" abinda tace dashi kenan cikin muryar kuka. Wani abu ya hadiye,sannan kuma yayi qoqarin daidaita kanshi "Ban gama ba.......and bazan gama ba muddin ni dake muna raye......ki soni ki koyi haquri dani,wannan shine shawaran da zan baki" daga hakan bai tsaya saurararta ba ya yunqura ya miqe cikin mazantaka duk da yadda jikinsa yake a mugun mace. Cak taji yayi sama da ita,abinda ya tilastata bude idanun nata kenan tana kallonsa "Ka saukeni......" "Shshshs" yace da ita yana hade fuskarsa,irin hade ran nan da ya zama jinin jikinsa,tamkar ba shine a yanzun ya gama rawar jiki da roqon ganin qwayoyin idanun nata ba "Kada kice zaki fiya sa'insa dani......idan kika daga murya da yawa ma akaji aka shigo ba raping naki nayi dis time ba.......dan aike na aika kika kuma karbeshi hannu bibbiyu" . Wayyo ina rami ta shiga ta huta?,ina wuta kuma ta cilla maina?,wanne sauka tayi daga layi har zai fara goranta mata?,tabbas ya gama da ita,batasan kuma me zatayi masa ta huce ba,kawai sai ta saki kuka sosai harda shashsheqa. Ko ta kanta baibi ba sai daya tabbatar ya sanyata cikin bathtub dake cike da ruwa me dumin gaske. Sai ya juya ya fara zare ragowar abinda yayi saura a jikinsa. Ta matuqar kaduwa da ganin zai qarasa bayyana mata abinda bata iya buda idanu ta kalla ba,ta qame gaba daya cikin bathtub din zuciyarta na mugun harbawa. Ya juyo yaga kuma yadda tayi, silently ya saki murmushi,shima baiyi niyyar shiga ba,sai ya wuce Jacuzzi abinsa ya kunna shower ba tare da yace da ita komai ba. Tsaf yayi wankansa ya gama,duk wani motsinsa idanunshi a kanta,a tsorace take da gasken gaske,don tunda ta rufe idanunta bata bude ba. Ya jima ruwan yana sauka a kansa yana morewa kallon fuskarta da tayi jazur saboda kuka,wani irin yanayi yakeji cikin gangar jikinsa da zuciyarsa,duk yadda ya hasaso zai samu pleasure abun ya wuce nan,yana mamakin kansa qwarai idan ya tuna wai baby sultanarshi ce ta tsaye ma rayuwarsa?,ita din wadda ya raina da hannunsa ce ke son juya akalar zuciyarsa dama rayuwarsa gaba daya?. Da babban towel ya daure qugunsa,ya qaraso inda tayi mutuwar zaune,ba zato ba tsammani ta jishi cikin ruwan yana tsiyaye na ciki yana kuma tara wani,saita sake hade jikinta tana kuma sakar masa kuka "Ka fita ka bani waje......Allah zankai qararka.....zankai qararka wajen Allah" idanu ya zaro yana kallonta "Da nayi miki me?,don kawai na taimakeki na miki abinda kikeso?,karki manta kema fa kindan san dadin abun......ko kin manta shi ya sakaki suma" ji tayi kaman ta hadiyi zuciya ta huta,maina ya gama kasheta yau gaba daya bata da sauran abinda xata masa a yanzu dai ta huce. Zata masa gardama ya fidda mata idanunsa yayi warning nata "Duk taurin kai ko musu guda daya yana dai dai da na sake raping naki ne cikin toilet dinnan tunda sunan rape kika bawa abun ko?,wanka kuma ai ba yau na fara yi miki shi ba" Yadda yake mata maganar kai tsaye ya saka shakkarsa cikin ranta,tanaji tana gani ya wanketa tas kamar wata baby doll,ya kuma daukota zuwa bedroom ya laluba Wardrobe dinta ya fidda kayan bacci ya saka mata. Kwanciya ya sanyata yi ta dole,don ba zata iya zama taci gaba da kallonsa ba,hawaye kam yaqi barin fuskarta,gashi dukka gabbanta ciwo sukeyi mata,ita kuwa me ta yima yaa haidar haka kaf cikin zuri'arsu yafi sanya ma rayuwarta idanu?. Tana jinsa ya koma toilet din,yayi alwala ya dawo ya shimfida abun sallarta,ya sake matsawa gaban madubinta ya dauki tutarenta ya fesa,sannan ya kabbara salla abinsa cikin nutsuwa. Raka'a biyu rak yayi,amma kuma ta kusa daukansa mini talatin kafin ya kammalata zuwa addu'o'i,ya shafa ya miqe yana dubanta. Tana nannade cikin duvet tana jin zuciyarta kaman zata fashe,daga pillow din har duvet din qamshinsa suke fiddawa,zataso ta miqe ta sauya daki ma gaba daya ba pillow case da duvet ba,to amma da wanne ido zata miqe su kalli juna?,yau din ya ganta haihuwar mahaifiyarta?,ya ganta ganin da rabon da yayi mata irinsa tun kafin takai munzali. A tausashe yake takowa gareta,yaso qwarai ta fahimceshi ya bata first night dinta me dadi a wannan ranar,saidai ya gama fahimtar da gaske har yanzu sultana zuma ce sai da wuta,jan ido yafi sanyata tayi laushi wasu lokutan. Saman kanta ya tsaya,ya miqa tattausan tafin hannunsa saman sumarta,ya sunkuya ya bata wani hot kiss a wuyanta da goshinta,muryarsa da wani irin sanyi yace "merci pour cette belle nuit(na gode wannan dare)" ido ta lumshe sauran hawayen dake maqale suka zubo mata. Ba dole yayi mata godiya ba?,ya gama tozartata har cikin dakin baccinta?,tsakanin ama da aba da yaranta "Ki rage wannan kukan kada da safe mutanen gidan su fahimci abinda ya faru,thought dai zanso su fahimta din,may be su gane cewa kin balaga sosai,kina buqatar namiji kusa dake......and bafa raping naki nayi ba in jaddada miki.....nasan bakisan bada kanki kikayi ba" ya fadi yana danne dariyar dake qasan ranshi,don yasan wannan kalmar kadai zata tabata,yana kuma kaiwa qarshe ya juya yana furta "Have a sweet sleep" ya maida qofar a nutse ya rufe mata. Kanta ta cusa cikin pillow tana sake sakin wani tsumammen kukan. "Wayyo Allah na" ta furta can qasa tana jin qamshinsa tako ina,hakanan kowanne sashe da hannunsa yakai a jikinta tana jin tamkar yanzu ne komai yake faruwa,ya akayi ya shigo gidan?,shine babbar tambayar data dinga yiwa kanta. Ta jima tana sharar hawaye,sai data tabbatar bazai maganta mata da komai ba sannan ta miqe tana cije labba saboda yadda jikinta ke dada ciwo. Toilet ta koma ta zare kayan jikin nata ta musanya da wasu,ta dawo ta zare komai dake saman gadon tabar katifar da pillow din ta koma ta kwanta tana kyautata zaton qamshinsa zai tafi,saidai kuma babu wani abu daya canza. Daga qarshe saita sauke pillow din qasa ta koma can ta kwanta. A can dinma dai duk ba wani sauyi da taji,saita miqe ta zauna kawai ta rushe da wani kukan. Tayi kuka sosai har sai dataji ba dadi sannan ta haqura,a hankali bacci ya soma rinjayar idanunta,tun tana sharar hawaye a sannu a sannu har bacci ya rinjayeta. Yayi zaton zaya samu bacci yadda ya kamata,amma kuma sai ta sake tsaye masa rai duka daren,duk wani juyi da zaiyi ita yake hangowa cikin idanunsa,irin pleasure din daya samu da wata irin nutsuwa da bai taba samun kamarta ba daga gareta. Knocking din ama ne ya sanyata bude idanunta da taji sun fara mata nauyi "Anyi sallar asuba sultana banji motsinki ba" ama din ta fadi daga bakin qofar tana juyawa ba tare data shiga dakin ba. "Alhamdulillahil lazi ahyana ba'a da ma amatana wa ilaihin nushur" ta furta can qasa tana motsa labbanta. Juyawa tayi hannun damanta,idanunta ya sauka kan wayarta,sai taga wayar tana haske,ta miqa hannunta da yayi mata nauyi tana jawo wayar. Text ne daga number da bata santa ba,kaman zata ajjiye sai kuma ta bude. Tun kafin ta qarasa karanta saqon ta fahimci daga ina ya fito *_Stay at home_* Maimaita saqon tayi har kusan sau biyu,to me yake nufi?,kada taje wajen aikinta?,kada taje wajen aikinta sai yaushe?,yana son yace ta ajjiye aiki ne fakaice?. "Tabdijan" ta fada qasa qasa,ta tattara dukka qarfinta ta miqe ta zauna sosai,ko zata lamunci komai banda abinda ya shafi aikinta,cikar burinta?,burinta na shekara da shekaru?,burin data cimma cikin wani irin yanayi da baisan ya akayi takai ba?,ba zata lamunta ba ko kusa ko alama,aikinta alfaharinta ne.....cikar farincikinta kuma. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 86 Ko Ina a jikinta ciwo yake mata,zata kuma buqaci hutu a qa'ida,amma ko don ta nuna masa iyakarshi sai ta fita aikin,ba zata zauna ba,don bataga meye alaqarsa da aikinta ba. Sau uku tana attempting tashi amma ta kasa,an hudun ta miqe tana cije labba,dukka jikinta ya mata tsami,ta soma takawa a hankali tana wucewa bandaki. Tana shiga idanunta ya sauka a inda ya tsaya, Jacuzzi da bathtub din daya wanketa tsaf a ciki,idanun nata ta janye tana jan qaramin tsaki,haushi ya cikata,wai me yasa ma bata tada masa ama da aba din ba?,tunda dai tasan duk tsiya idan ta tashesun ita keda gaskiya,kunya kuma sai ya fita ji?. Ruwa me mugun dumi ta hada ta shige bathtub din tana sake gasa jikinta da kyau,ta dade a ciki har sai da taji dadin jikinta sannan ta fito. Zaune kawai tayi gaban madubi daure da towel,batajin dadin yanayinta gaba daya,sake jan qaramin tsaki tayi,shi ya jawo mata komai,me yasa dole saiya cusa rayuwarsa cikin nata?,bayan ita ba damuwa tayi da lamuransa ba?. Agogon dake manne a bango dai dai saman mirror dinta ta kalla,mamaki ya kamata saita dan fidda idanu,ta miqa hannu zata dauki cream dinta sai ama ta turo qofar. A nutse tayi sallama,idanun ama din a kanta,amma saita samu kanta wannan safiyar da kasa kallon fuskar ama din,ta kauda idonta tana dan sunkui da kanta qasa. Kallo daya aman tayi mata taga sauyin yanayi a tattare da sultana din,mutuwar jiki da rashin kuzari,hakanan fuskarta ta dan tasa kadan ta danyi jaa kuma "Hala yau ba aiki sultana?" Kai ta girgiza "Makara nayi ama" "Yauwa nifa ince,koda asuba baki leqo ba,har su batoul sun wuce school" bata iya amsa mata ba sai rusunawa da tayi ta gaidata,har yanzun dai taqi su hada idanu,gani take tana kallon ama din aman zata fahimci abinda ya faru da ita daren jiyan. "Lafiya Lau mun tashi lafiya?" Ta amsa mata tana shirin zama gefan gadon,sai kuma ta fasa tayi sak tana kallon gadon yadda ya yamutse gaba daya,hatta da bedsheet din ba'a dai dai yake ba,pillows din dukka a qasa. Abune da bata taba gani ba wajen sultana,saita kwanta a gado ta kuma tashi ka ganshi lafiya Lau,don akwai tsafta,ba zaka taba ganin gadonta a yamutse ba,wanann ne ya sanya ko su benazeer bata bari su hau mata gado musamman idan ta gyarashi. "Lafiya....lau ama" ta amsa mata tana dan daburcewa saboda yadda ta fahimci idanunta na saman gadon,gabanta yana dan faduwa,kada dai ta dago wani abu,Allah yasa ba wani abu saman gadon da zai tona mata asiri,ta fadi cikin ranta da dan fargaba "Lafiya kika kwana ko?" Ta tambayeta a fakaice don son tabbatar da ba wani abu ne ya sameta na lalura ba "Lafiya.....lafiya qalau ama" ta sake fadi tana sake kauda idanunta sosai daga kanta. "To ma sha Allah,idan kin kammala ina parlor saiki fito kici wani abu kafin ki wuce ko?" Ta furta qasan ranta tana kokwanto,sinqe sinqen da sultana keyi na meye?,saidai kuma tunda tace mata lafiya lau din ai lafiyarce,don dama ita ke buya,don haka ta miqe ta fice daga dakin. Dogon numfashi ta sauke kamar me laifin da ya kubuta daga hannun alqali,ta maida idanunta saman gadon,ya yamutse qwarai,kuma dole ama taga abun wani iri,harda towel dinta na jiya daya zare ya watsar,warin dan kunnenta da kuma pant dinta. Ta miqe a hankali ta isa gadon,ta sanya hannu ta tattare bedsheet din,sai takeji ya fita a kanta,ta hada duka da pillow case din data cire jiya ta watsa a laundry basket,ta duba wardrobe dinta ta ciro wani ta sauya. A gurguje ta gyara dakin,abinda ya sanyata ta sake makara kenan,ta sake buda wardrobe dinta ta fidda wasu English wear skirt and blouse na yadin chiffon me dan kauri ta shirya kanta tsaf,ta yane kanta da madaidaicin scarf daya sake fidda kyawun fuskarta wadda a yau daya taga fuskartata tadan ciko,tayi dam tsakiyar scarf din,har sai data sake duban kanta. Cikowar da fuskar tayi ya qara sawa idanunta labbanta da hancinta dukka sun sake fitowa sunyi kyai,ta dauki turare ta fesa,sannan ta daura agogon fata na kamfanin blancpain,da hand bag nata da takalminta dukka set ne daga kamfanin Hermes da suka siya a nan French cikin shagonsu,gift ne kuma daga aba cikin siye siyen fara zuwa aikinta. Wani mahaukacin sassanyan kyau tayi,wanda ko mai hassada idan ya kalleta bazaiyiwu ya dauke idanunsa a kallon farko ba,ko makaho ya shafata yasan lallai komai na rayuwa ta hada,ba abinda ya rage mata sai neman lahira. Dakin ta jawo ta rufeshi ba tare da ta saka key ba don bata sakawar. A nutse take tafiya cikin yanayin kasala zuwa parlor din tana duba saqonnin data taras cikin wayarta,duk inda ta gifta sai tayi ajiyar sassanyan qamshinta,a haka ta isa dining area saidai batakai ga zama ba saboda bataga ama ba,tana a tsayen tana replying massages din wayarta aka danna qararrawa. Ta daga kai tana duban qofar da zummar tambayar waye taga an turo qofar da alama ba'a rufeta ba gaba daya. Itace abu na farko da idanunsa ya fara kaiwa kanta,kamar yadda itama dashi ta fara tozali, zagayayyun lion eyes nashin nan da taga sunyi wani irin haske a safiyar,kamar kuma an qara musu girma. Sassanyan kyansa dake kwance saman ba'abzinar fuskar nan tasa dake wannan kwarjinin na tun asali,tun duniya na kwance,gayun nan dai da duk wanda yasan aliyyu maina na kwance a yanxunma a jikinsa,irin gayun dake nuna zallar wayewa kwanciyar hankali da kuma tarin ilimin da ya mallaka,ilimin da ya qarawa fuskarsa kwarjini,ya kuma haifar da zallar nutsuwa cikin kowanne taku da kuma motsi nashi. Suit din jikin nashi tamkar kamfanin sun qirqireta ne kawai saboda shi,idan ka kalleshi babu abinda zaya hanaka rantsewa wani balarabe ne. Sai da yaji kamar an harbi zuciyarsa da ganinta a tsaye,kyanta ya bugeshi sosai,ya kuma motsa masa ainihin kishinsa da yaketa qoqarin dannewa a kanta. TAURIN KANTA da sauransa kenan har yanxu?,bazai gaya mata taji ba?,sai ya gyada kai,shi daya yasan me ya shirya mata. Sake maimaita sallamarsa yayi yana tsugunnawa a nutse yana sabule tsadajjen sau cikinsa daya sakaya qafafunsa a ciki. Kafin ya dago yaji muryar ama tana amsawa,wanda sai data iso cikin falon sosai sannan ta fahimci waye?. Dagowa yayi suka hada idanu da ama, murmushi zai kubce mata ta danne,saita buge da fadin "Kaine?" Nasa murmushin ya sake mata,wai ala dole sai tayi fushi itama da fushin wani?,banda abun ama meye alaqar dake tsakanin dangantakarsa da ita da kuma dangantakar sultana dashi?. Duk da haka sai ya dake shima,yana sake dauke idanunsa sosai daga sultana kaman baisan da tsaiwarta a wajen ba "Nine ama......ko na koma?". Baki tadan tabe "Banason sanabe,idan zaka qaraso ka qaraso,kaga abanka?" Kai ya girgiza duk kuwa da cewa yaga wucewarsa,to amma yanzun bai shirya haduwa dashi ba,so yakeyi su hadu ranar da zai kasheshi da mamaki "No,bamu hadu ba" "Yanzun nan ya fita" ta fada tana nufar dining. Qasan ranta sai takejin wani sanyi da dadi suna ratsata,amma kuma bata bari hakan ya nuna a kan fuskarta ba. Kanshi tsaye shima dining din ya nufa,don bazai bari yayi Missing abincin ama dinsa ba. Tana qame a wajen har ya qaraso,ya jawo kujerar dake kusa da tata ya zauna yana fadin "Barka da safiya ama,fatan kun tashi lafiya,ashe nan ne location naku" "Lafiya alhamdulillah" "Ya hanya?,bansan zaku taho ba ama......har yanzun baki dawo dani bane cikin 'ya'yanki?" Yayi maganar cikin karyewar murya da nuna rauni. Batajin yanzunne right time da zasuyi irin wannan maganar dashi,don haka ta bashi amsa a dunqule da cewa "Kai kaso....in ka shirya cin abinci ne bismillah,tunda ka iskemu magana ya qare ai" murmushi ya saki,ya fahimci inda tasa gaba,don haka baice komai ba ya miqa hannu yaja butar shayi "Amma zan wuce" ta fadi tana jinta duk a takure. Mamakin qarfin halinsa takeyi,kaman ba shine ya hauro musu gida daren jiya ba yazo ya muqurqusheta,amma yanzun don qarfin hali da qwarewa a rainin wayo wai shine yake tambayar ashe nan ne location nasu?. Ita kanta yadda ya dubeta a gaban ama din ba zaka dauka cewa ya taba ganinta ba,ya basar yayi zamansa "Ban gane zaki wuce ba?, c'mon zauna kici abinci,haka akace miki ana zuwa aiki da empty stomach?" A hankali ta matso tana jan next chair,ta haqura da wadda ta fara ja din saboda tayi kusa dashi sosai "Ina kwana" ta furta a hankali kaman wadda batason yin magana sanda take shirin zama. Sai daya daga kanshi suka hada idanu,ya faki idanun ama ta yadda ba zata ganshi ba ya sake mata wani irin narkakken kallo yana lumshe idanunsa sannan yace "Alhamdulillah" labbansa na wani irin motsawa. Ta fahimci ma'anar gaisuwar tasa,saita kau da kai taja itama butar coffee din ta soma zubawa. Sam kaman baisan da ita a wajen ba,dukka hankalinsa ya tattara yana jan ama da hira,tadan soma dojewa daga baya tadan sake masa kadan. Yayi kaman ya manta da ita ne,amma duk wani spoon ko mug da zatakai bakinta yana lissafe da adadin. Har yanzun tana nan da wannan halin na yiwa abinci riqon sakainar kashi. Sanda ya fahimci dab take da qoshi sai ya fiddo wayarsa daga side pocket din jikin rigarsa. Saqo ya tura mata cikin hikima ta yadda ama ba zata fahimta ba,ya maida wayar ya ajjiye yana ci gaba da duban ama cikin tsananin kulawa yadda ya saba mata. Tayi zaton wani Tex ne me muhimmanci,wannan ya sanya ta jawo wayar ta buda *_zanyi warning naki a karo na qarshe,muddin kikayi kuskuren fita aiki.......bazan gaya miki what's going to happen ba.......but zaki gani a aikace_*. Maimaita saqon ta sakeyi tana satar kallonshi,abu nashi taga alama yama wuce gona da iri,wai ana dole ne?,lallai sai ya maidota cikin rayuwarsa?,lallai sai ta maidashi itama cikin rayuwarta?. Tsaf ya karanci meke reading saman fuskarta,sai ya miqe a nutse "Nayi mantuwa ina zuwa" yadan sauka daga wajen yana fita da 'yar sassarfa. Ajjiye pork din hannunta tayi ama ta bita da kallo tana furta "Ma sha Allah" qasan ranta,sai yanzun sultana ke zama cikakkiyar mace,shekarunta suke kaiwa dai dai shekarun cikar 'ya mace,ita kanta tayi mata kyau sosai "Na qoshi ama,zan tafi yau na makara sosai,akwai abubuwan da zan duba na program dinmu na next week" "Allah ya taimaka,saikin dawo" har ta fara barin wajen idanun aman yana kanta "Ki kula da kanki sultana" ama din ta fadi. Sai taji maganan ya ratsata sosai,har sai daya waiwayo ta kalli ama sannan a sanyaye tace "In sha Allah" juyawan da zatayi ya shigo,bata yarda ta kalleshi ba ta sanya kai zuwa ba. Lips dinsa ya cije yana sakin wani boyayyen siririn murmushi,yaro man kaza ya fadi a ransa,hankalinsa kuma kwance yake dawowa wajen amansa,don sosai yakejin dadin hira da ita a wannan safiyar,ta dan sake masa ba kaman yadda take masa a baya ba. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 87 A nutse ta bude motar ta ta shiga tana ajjiye hand bag dinta daga gefe,ta tattara hankalinta ta sanya muqulli ta kunnata sannan ta tayar da ita ta soma barin unguwar a nutse. Radio ta kunna don ta rage mata kewa,zantukan ama ke dawo mata da wasu tunanuka da suka shafeshi keson kutso mata kai wanda bata da buqatarsu. Tana mamakin qarfin halinsa da yadda yake abubuwan kanshi tsaye,duk da halinsa da dabi'unsa ba ta jima da saninsu,amma a yanzun yana shirin zame mata sabon mutum. Yadda ya sake girma ya sake zama cikakken mutum haka take sake ganin wasu sabbi da baqin halayya daga gareshi,koma meye dai oho,damuwarshi ne,ita ba wannan ne a gabanta ba,gina kanta takeyi a yanzun,lokaci ne da shekarunta suke dai dai da sanda kowanne dan adam ya kamata ya maida hankali ya gina gobensa,tanason ta sake yiwa rayuwarta ta baya nisan tazara sosai fiye da tazarar da tayi mata a yanzu. Daren jiyan ya fado mata a rai,tsaki taja,har yanzu haushi da baiken kanta take gani,tana ganin kaman tayi sakaci da har haka ya faru da ita,abun ya maqale mata a rai,tana jin tayi abun kunya da har tayi saken da ta sake hada jiki dashi,yadda akayi yaci galaba a kanta abune da bazata iya tunawa ba,ta sanya yatsanta guda daya a baki tanason second guda daya daya bashi dama ya shawo kanta amma ta kasa tunawa. Dan dukan steering din motar tayi tana tura baki gaba cikin alamun jin haushi tamkar yana a gabanta. Batayi wani nisa ba can danja ta tsaidasu,ta tsaya kaman yadda dokar qasar yake,tana yi tana duba adadin mintunan da suka rage a basu daman wucewa. Tsaki ta kuma ja,duk shi yaja mata koma meye,wannan lattin batasonshi,bataso ta fara aikinta da saba alqawari da kuma saba lokaci,tunda ta sani,su din mutane ne masu girmama lokaci da kuma alqawari. Gefan hannun damanta tadan kalla,har ta dauke kai tayi saurin maida dubanta wajen. Maina ne,zaune cikin motarsa hankalinsa kwance,ya manne qwayar idanunsa da baqin eye glasses wanda suka yiwa farar fatarsa mugun kyau. Kallo daya zaka masa kasan cool guy ne a ido,amma a idanun sultana can qasan zuciyarta sai ta furta "Wicked" sannan ta dannan madanni tana dage glass din side din,don bata qauna ko fatan ya ganta ma,kowa tashi ta fishsheshi,hanyar jirgi daban ta mota daban. Ana sakinsu kuwa taja motarta tana dan qara speed kadan akan na dazu duk kuwa da yadda take tsoron gudu a mota,koda kuwa driving nata akeyi bare ace ita keyi da kanta. A nutse take dan bin waqar da suka sanyo cikin gidan radio din da harshen faransanci,saita waqar ta dinga tuna mata shekarun baya,sanda tana sultanar bibi,me bala'in son rawa da waqa,me bin duk wani gida da ake shagali walau gida ko hotel. Waqar na daya daga cikin waqoqin da take mutuwar so, murmushi ya dinga kubce mata a hankali tana bibiyar waqar. Dan speed ta qara ganin ta hau doguwar hanyar nan wadda daga ita zata shiga titin gidan tv dinsu,hanyar ta fiya shuru,ita kuma tun dacan tana da tsoron wajen daya fiya shuru haka. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta tana zaro idanu lokacin da gudun motar ya fara ja baya,ta kuma fara tafiya slow. Dukka idanunta ta fiddo waje ciki tsananin fargaba tana duba ma'ajiyar dake nuna dadin man fetur dake cikin motar. Mamaki ya kamata qwarai ganin cewa wai mai ne ya qare,bayan shekaran jiya aba yayi mata full tank da motar tata. Bata saku damar kai motar gefan hanya ba ta mace mata,ta sake kiran sunan Allah tsoro da fargaba yana cikata,ta kalli hagu da dama dukka ba motsin kowa sai kukan tsintsaye da iskar dake kada dogayen bishiyun da suka yiwa hanyar qawa. Hannayenta ta hada waje daya ta karanta addu'o'i ta shafa a jikinta,ta bude murfin motar a darare tana fitowa wai ta duba gaban motar ko zata gane inda matsalar take,duk da cewa ba wani abu data sani akan matsalar data shafi mota,don shi kansa driving ma bata dade da farawa ba,ko ina zata akwai mai kaita akwai me daukota. Koda ta bude kaman yadda ta zata bata fahimci komai ba,haka ta qarewa wayoyi kallo ta mayar ta rufe,saita jingina da motar zuciyarta na bugawa tana kiran sunan Allah. Waige waige taci gaba dayi,mintuna kusan goma amma bataga gilmawar kowa ba,ta lumshe ido ta juya da sauri ta bude motar,ta dauko jakarta ta fidda wayarta da zummar kiran ama ko aba ko can tv station din nasu ko akwai wani dauki da zasu iya kawo mata. Wayam ta gani,babu komai cikin jakar sai dan tarkacenmu na mata da bama rabo dashi,kulle idanunta tayi da qarfi tana cewa "Innalillahi" tabbas saman dining din ama ta manta wayar. Zuciyarta dukka ta karye,ta koma ta window tana cilla jakar,daidai sanda ta soma jiyo sautin tahowar mota "Alhamdulillah" ta fadi tana gyara yafen scarf dinta,ta matso bisa titin sosai ta sanya hannu sanda motar ke dab da isowa inda take tsayen,saidai abun haushin wucewa motar tayi. Cikin sarewa ta sake komawa ta tsaya tana fatan samun dauki,cikin sa'a ta sake jiyo wata motar,sai ta sake matsowa tana saka hannu wannan karon harda bayani "s'il vous plaît, aidez(please help)". Murmushi ya kamashi amma ya danne,har yanzun halayyar nan ta tsoro tans nan bata barta ba?,target dinsa ya fada a dai dai kenan. Yana sane yadan take motar kamar zai wuce,har yayi gaba sai ya rage gudu,ya danna reverse ya dawo da baya da gudu. "Alhamdulillah" ta fada tana aje numfashi ganin motar data wuce din ta fidda ran tsaiwarta itama tana dawowa. Ganin an tsaida motar kuma ba'a fito ba saita soma takawa zuwa gaban motar,duk dadai a tsorace take amma tana da yaqinin qasa ce me aminci da iren iren abubuwa masu cutarwa haka basu fiya faruwa da mutane ba,uwa uba kafin ta fito daga gida tayi addu'a,tana da tabbacin tana cikin kariyar ubangiji. Yana zaune daga cikin motar yana qare mata kallo son ranshi,idanunsa da kansu suka dinga rusunawa suna budewa,yadda take takowa zuwa gareshin yana sake tada masa wani sabon tsumammen feelings a kanta,tamkar daren jiya dama baiyi komai ba. Yana iya ganinta tarwai,amma ita bata iya ganinsa saboda baqin glass ne dashi. Sanda ta tsaya jikin window din ta masa knocking sai yayi kaman baiji ba,yana ganin yadda fuskarta ta nuna alamun qosawa,ta sake knocking glass din,sai yadan sauke glass din kadan ta yadda zai iya jinta kawai ba tare da taga fuskanshi ba "Pouvez-vous m'aider? La voiture ne fonctionnait plus(zaka iya taimako na?,motata ce ta daina aiki)" kai kawai ya gyada,ya maida glass din ya kulle. Sak tayi tana tsammanin mamallakin motar na shirin yin gaba ne abunsa,sai taga an bude murfin side din da yake,ya zura qafafunsa ya fito gaba daya. Baya taja da sauri tana dubanshi yayin da shi kuma ke gyara zaman suit din jikinsa kamar ma bai santa ba. Sake ja tayi da baya sanda ya fara takawa yana nufar motar . Turqashi!,ita sam batasan shi bane tunda batasan wanne kala ne motarsa ba,tsoro ya hanata motsawa,har ya bude gaban motar ya gama tabe tabensa,ba kuma tare daya kalleta ba yace "Wannan motar bazai tashi ba yanzu ya tafi hutu,ki nema abun hawa ki wuce" ya fadi yana karkade hannayensa kaman wanda yayi wani abun arziqi. Tayi zaton zaice mata ta taho suje,amma sai taga yana nufar motarsa,har yanxun kuma bai kalleta ba, sanda ya shige ya maida murfin ya rufe ta tabbatar tafiyar fa zaiyi,saita kalli hagunta da damanta,su kadai suka rage a wajen,dole ta sake matsowa gaba da sauri ta daga masa hannu. Kaman bazaiyi kowanne motsi ba sai kuma taga yana sake sauke glass din har ya kammala saukeshi tas,idanunsa a kanta,ya sanya hannu a nutse ya zare baqin eye glasses dinsa "Ya akayi?" Ya jefa mata tambayar yana mata wani irin kallo. Idanunsa sun fiya dafi da yawa,sai ta kauda kanta gefe sannan tace "Ka qarasa dani bakin hanya...... please" ta qarasa maganar tana jin dacin neman alfarma yau a wajensa. Kaman ya qyalqyale da dariya to amma yanzun ba muhallinta bane,don yana hango yadda roqon ya mata daci. Murya can qasa ya amsa mata yana maida glass dinsa "Bismillah" yace da ita. Rai a bace ta qarasa wajen motar tata ta fidda kayayyakinta,ta tako cikin nutsuwar nan tata zuwa bakin motar. Bayan motar take da muradin shiga,to amma kuma tun duniya tana kwance tasan halinsa sarai,dole badon taso ba ta bude gaban motar ta shiga,ta maida murfin ta rufe,ya saki boyayyen murmushi cikin ranshi yana cewa "Mission accomplished" ya tayar da motar a nutse yana qarawa fuskarsa daurewa,daurewan da ya qara mata wani irin kwarjini daya fitar da ainihin kyanshi. _su maina sarkin wayo,ina zuwa?_ _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 88 Cikin nutsuwa yake driving motar,wani irin calmness yana nunawa saman fuskarsa. A jikinsa yakejin addu'a tana mugun tasiri ga bawa baya ga irin sa'arshi a rayuwa,yanajin wani sukuni idan ya tuna tana a gefansa,ta shiga kuma tarkonsa sai yadda yayi da ita a yau dinma,amma idan ka kalleshi zakayi tunanin yana wani lissafi ne daban bawai tana a gabansa bane. Tafiyar mintuna goma kacal suka fita a titin,sai ta sauke ajiyar zuciya tana jin sasaauci a ranta,sun wuce wajen da take mutuwar tsoron,kuma a nan ya ajjiyeta hakan ya mata. Tadan motsa kadan tana tunanin zai faka motan ne gefan hanya ya ajjiyeta,sai kuma taga yaci gaba da tafiyarsa lafiya lau kaman ba kowa cikin motan sai shi kadai. Kusan hanyar tasu daya ce,don haka bata fuskanci wani hannun ya dauka ba sai da sukazo dai dai titin da zaka tadda TV station din nasu,maimakon ya saka signal ya shiga sai taga ya wuce. "Zaka iya ajjiye ni a nan" ta furta tana gyara riqon jakarta "Kinyi zaton driver kika samu da zaki tsaidashi a duk sanda kika so?,na riga dana wuce,sai kuma idan na dawo" ya fadi yana basarwa ba tare daya kalli fuskarta ba. Fuska tadan motsa tana maida idanunta ciki,kai tsaye take dubansa,bata fahimci abinda yake nufi ba,ta hadiye maganar dake ci mata a rai tace "Bance ka qarasa dani ba,zan iya kai kaina daga nan" ta amsa masa da dan qwarin gwiwarta "Shut your mouth mrs maina" ya fadi yana saka signal zuwa hannun hagunshi titin da asibitinsa yake. "Mrs maina?" Ta maimaita sunan a fili saidai can qasa tana jin abun banbarakawai "Yes......maina MAYAK'I", ya qarasa mata ba tare da ya waiwayo ba. Shuru tayi yatsunta qasan habarta tanason wassafo zallar rainin hankalin da yakeson yi mata. Maganganu ne cikin ranta na bacin rai masu yawa da takeson gaya masa amms kuma tana jin wata shakkarsa tana ratsata. Bata manta yadda ta gurzu ba a jiya,wanda tasan wani abun da gayya yayi mata,ta kuma ji a jikin nata,don har yanzun akwai guraren da basu daina ciwo ba a jikinta. To amma ita bata nema komai daga wajensa ba banda rage hanya. "Kada dai ace hanata zuwa aikin yayi niyyar yi da gaske kaman yadda ya haramta mata zuwa gidansu aminata har ta baro nijer?" Ta tambayi kanta sanda ya tsaya bakin gate din katafaren asibitin yana neman izinin shiga. Ranta yayi qololuwar baci sanda ta cusa hancin motar zuwa harabar asibitin,ya tsaida motar a wajen ajiyar motoci na musamman dake asibitin. Qasa ya danyi da glass dinsa,ma'aikatan dake wajen suka fara qarasowa suna gaidashi cikin girmamawa. Wasunsu da harshen France,wasunsu da English,wasunsu da Arabic,sai wasu masu yare biyu daban da batasan wanne yare sukeyi ba,amma kuma da mamaki da taji maina din ya iya. Zare key din motar yayi ya juyo kaman zai kalleta sai kuma ya dauke kai,ya bude side dinsa ya fito ya zagaya nata seat din. Hannunsa ya zura ya sauke glass din motar sosai,hakan ya bashi damar dogara gwiwar hannunsa saman window din idanunsa zube fes cikin nata idanun da hasken rana ya sanya sheqin qwayar idanunta fita sosai,ta kuma sake fidda kyan idanuwan,saidai kuma rauni da karaya me tarin yawa ya hanga cikin idanun nata. "Zaki fito salin alin?,ba tare da mun tarawa kanmu jama'a ba?,ko kuma in sauqaqe miki na daukeki zuwa ciki a hannuwana?" Tsoro maganar tasa ta bata,hae ta zaro qwayar idanunta waje ba tare data shirya ba. Ya fahimci me take nufi,sai ya dage dukka girarsa yana sake kafeta da shu'umin kallon nan nasa da zagayayyun lion eyes dinsa "Yes........ya halatta a nan qasar koda ba couples bane mu,ballanta ne da kike halaliyata,ko a cikin motar nan na buqaci ki bani haqqina indai kinason kaucema tsinuwar mala'iku haka zaki gyar........." "Subhanallah" ta fadi a fili tana kuma janye idanunta daga cikin nasa numfashinta yana neman sauyawa saboda fargaba da mamaki. Kalamansa sun mata matuqar tsauri,Wani abu me kama da nauyinsa taji ya saukar mata tun daga saman zuciyarta,don haka ta janye idanunta gefe. Shi ko sau daya bai taba jin nauyij gaya mata irin wadannan kalaman ba?,shi baya jin kalaman cike suke da tsauri da kuma nauyi?,ya sake lalacewa daga ya maina din data sani sanda tana nijer,sultanar nijer wadda batasan rayuwa ba,sultanar nijer da bata taba zuwa ko ina ba banda Nigeria. "Fito....." Ya fadi yana ja baya,ya kama murfin motar ya bude mata yana tsaye ata wajen. Bata sake cewa komai ba saboda shawarar da zuciyarta ta bata,ta bishi ta lalama ko ta zuba masa idanu taga iya gudun ruwansa,ta miqa hannu zata dauka jakarta ya miqa nasa hannun sai ta janye nata hannun,ya riqe jakan ta sako qafafunta ta fito daga motar. Murfin ya maida ya rufe,taku uku ya iso gabanta,bata tsammani ba sai taji tafin hannunta cikin nashi soft and warm tafin hannun. Wani yarrr taji kaman an watsa mata kiyashi "Karkiyi taurin kai.......banason musu,i hate it.....indai da musu tsakanina dake ba zakiji dadi na ba sultana" lips dinta na qasa ta dan cije kadan,ga maganganu fal cikin ranta,amma yanzun neman kubuta daga hannunsa takeyi kada abun jiya ya maimaita kansa. Abinda ta lura dashi kafin su isa reception din yadda idanu suka yi musu yawa a ka,eh su ba qabilarsu bane......amma kuma mutane ne kaman kowa,idanun haka na meye?. Bata da amsa saita taqaita ganinta kawai,bata da wani sauran kuzari saboda abinda takeji a jikinta. Tunda ya sanya hannunshi cikin nata yake yamutsa hannun a hankali,fatar tafin hannunshi yana gogar bata softly,sau uku tana qoqarin janyewa yana warning nata da idanunsa,sai tayi sak kawai tanason taga iya gudun ruwansa. Tun daga reception taga kalar girmamawar da ake masa,wani girma ake bashi na musamman wanda ya tabbatar mata tabbas shi din wani ne cikin asibitin. Duk wanda ya gaidashin kuma sai ya kafeta da kallo,kwarjininsa ya hanasu tambayarsa ita din wace?,at last suna dab da shiga elevator sukayi kacibus da daya daga cikin doctors na asibitin. Da alama shima babba ne cikin asibitin,saidai kuma yana da shekaru ba kaman maina din ba,shi dinne yayi qarfin halin tambayarsa,murmushi yadan saki yana gaya masa matarsa ce. Murmushi sosai likitan ya saki ya juya yana gaidata,daurewa tayi ta saki murmushin yaqe tana amsa masa,sukayi sallama ya sama musu elevator suka shige. Ko kammala rufe kanta elevator din batayi ba ta zame hannunta cikin zafin nama,batasan me yasa ba amma tunda ya soma murza mata tafin hannuwa gaba daya nutsuwar jikinta ya fara yin qaura,wani abu me kama da yanayin data tsinci kanta a daren jiya yake mata yawo a jiki,kasala da mutuwar jiki tana mamaye dukka gabbanta,har idanunta tana jin sun fara wani iri. Baice komai ba sai tsaiwa da yayi a gabanta da dukka tsahonsa,ya zube hannayensa cikin aljihun trouser na suit dinsa,ya kafeta da mayatattun idanunsa dinnan da har yau bataga idanun da suka kai nashi nauyi ba. Baya taja kadan saboda yadda tsahonsa ya kere nata sosai,karon farko data fahimci lallai da gaske yaa maina din yana da tsohon da murjewar jikinsa yake hanawa a gani. Cikin rashin sa'a taku biyu kacal tayi ta tokare da qarfen elevator din,saita juya baya da sauri,no more space kenan?,sai ta sake taku biyu Left side dinta don burinta kawai ta bashi tazara. Duk hanzarinta batakai shi ba,batakai ga aje sawayenta ba ya tare gurin da hannu yayi mata katanga,ya qara taku biyu kawai sai ya hade gap din dake tsakaninsu gaba daya. Musayar numfashi suka fara yi,daya daga cikin abinda ya karanci yana cikin weakness dinta tun a daren jiya. Hannayensa ya sanya dukka ya kamo hannayenta cikin nasa ya riqesu da kyau,ya kuma yi musu matsaya saman qirjinta still yana riqe dasu,wannan ya bawa bayan hannunsa damar gogar qirjinnata a dabarance. Cikin magudanar kowanne jini na jikinta ya sakar mata wani irin feeling na babu zato wanda ke cakude da fargaba kafiya da taurin kai,fes yaga komai cikin idanunta,wannan taurin kan ya tsana,yanason ya qarasa cisgeshi gaba daya daga ruhi da gangar jikinta,don haka ya danna hannayensun duka da kyau cikin qirjinnata,abinda ya sanyashi tabo muhallin sosai,hakanan itama saqon ya sake isa ga sassan jikinta fiye dazu,lamarin daya sanya zuciyarta karyewa saboda komai ya fara kai mata ko ina,wannan ya karya zuciyarta,oily eyes dinta suka fara hidimar tara ruwan hawaye ta fara girgiza masa kai don abinda ta soma gani cikin qwayar idanunsa tana jin kamar zai kassarata,sauyawar kalolin qwayar idanunsa kadai abun tsoro ne a wajenta,yadda ya kafeta da idanunsan nan masu kaifi ya sake kassara duk wani kuzari da karsashinta. Abinda bayan hannunsa ke iya ji din su suka zama jagoran baiwa dukka sassan jikinsa wani irin feeling me matuqar qarfi,har yana jin kamar bazai iya skipping minti daya ba a haka,numfashinsa ke son fara masa wasa,yayin da cikinsa ya harba,ya tabbatar somi somi ne na murdawar ciwon cikinsa,matsanancin ciwon cikin da tun daga wancan ranar daya fara saninta diya mace yake zame masa barazana a rayuwarsa. Duk inda zaya samu magani magana daya suke gaya masa,yana buqatar mace by his side. Ya riga ya fara yiwa halittarsa dan dani haukaci,tarin sha'awar da take cikin jini da halittarsa ya fara mata hanya daga bisani kuma hanyar ta datse,yana ganin komai cikin kowanne mafarki,yana ganin komai cikin kowanne dare,amma a zahiri bashi aikatuwa. Bai tana sha'awar zina ba,koda wasa kuma bai taba sha'awar tana diyan kowa bada sunnar annabi Muhammad ba,wannan ya sanya yake cikin azaba tsahon shekarun. Daga baya ya gayawa kansa,ciwon cikin yana daya daga cikin hukuncin da Allah zai masa ne tun a duniya na nesantar gida da yayi,har yanzun kuma yana aza ciwon a mizanin hukuncin Allah a kansa. Sauqin daya samu zuwansa umra biyu na qarshe daya yawaita addu'a,sannan kuma yasha zam zam sosai,sai gashi a wannan rana a kuma wannan lokacin yana niyyar tasan masa. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 89 A hankali jikinsa ya fara shacking abinda ya tilas masa sake mata hannu,ya kuma yi amfani da hannayen nasa ya jawota cikin jikinsa sosai sanda take neman yadda zata qwace,saidai ko kusa ko alama ya hanata hakan,dai dai sanda elevator dinsu ya isa floor din da ya buqata,sai ya jawota gefen qugunsa sosai ya riqota da kyau ya soma takawa da ita a hankali suna fitowa daga elevator din. Dogon lobby ne dake dauke da office a jere cikin tsari da tsafta da kuma wadatar haske,waje ne dake da cikakkiyar nutsuwa don babu hayaniya ko kadan a wajen,a nutse yake takawa da ita bai saketa ba hakanan bai sassauta mata riqon da yayi matan ba,sai dan cije lips dinsa kadan da yakeyi saboda yadda yaji mararsa na murdawa,da gasken gaske ciwon keson motsa masa kenan. Inda so samu ne,kuma inda ciwon yayi shawara dashi bazai taba bari ya motsa a irin wannan lokacin ba,saboda shi kansa yana tsoron zuwa irin ranar akan kowacce diya mace ma game dashi,yasan baqar wuyar da yakesha a baya,irinta dinne ya tabbatar duk sanda ya sameshi zai juye akan koma wacece. A nutse duk da yadda jikinsa keson ya fara shacking ya bude qofar office na uku dake jere cikin jerin office din,yana riqe da ita da daya hannun ya tura qofar ya shige,sannan ya maida qofar ya kulle ya juya a hankali yana dubanta. Tana tsaye a tsorace,ta raba hankalinta biyu,da farko tayi zaton office ne kaman kowanne office,sai da suka shigo sai ta fahimci office ne amma kuma na musamman dake dauke da wasu kujeru da kake iya maidasu gado a duk sanda kk da buqatar hakan,akwai lallausan carpet daya mamaye ko ina, kyakkyawan table dake dauke da takardu,fridge da manyan throw pillows masu taushi farare qal, corridor daga waje sai toilet daga ciki,gefe guda kuma kayan tarkace cups ne cikin wani drawer na glass a shirye,harda plates da spoons masu azabar kyau duka gold color. Basarwa tayi ta kama scarf dinta tana gyara zamansa saboda dan zamewa da yayi. Hannuwansa ya goye a qirjinsa yana takowa inda tadan bashi baya. Sam bataji tahowar tasa ba saboda lallausan carpet din dake wajen,saiji da tayi yayi caraf da hannunta a tausashe. Juyowa tayi adan hasale,saidai kuma Kallon da yake mata ya banbanta da na kullum,mamaki da dan tsoro yadan kamata ganin yadda idanunsa sukayi laushi cikin lokaci kadan,a hankali idanunsa suna lumshewa suna kuma budewa kusan lokaci guda,sai ya sanya hannuwansa ya soma warware scarf din dake kanta "Am burning with jealousy.......am envying sultana" ya qarasa fada muryarsa a tsananin karye,ya kama hannunta da daya hannun nasa yana kaiwa saitin qirjinsa daidai zuciyarsa, idanunsa cikin nata. Hannunta taso janyewa,amma kuma sai taji bugun zuciyar tasa da gaske ya wuce kima,dukka wata laka ta jikinta ta fara tsinkewa,sai ta gaza aiwatar da komai sai idanunta dake qirjinsa data zubawa idanu "Am a cardiologist......kinji yadda bugun zuciyata ya banbanta da na masu lafiya ko?.......inaji a jikina indai haka yaci gaba da faruwa......zan iya samun heart failure sultana" ya qarasa maganar ta sigar rada yana lumshe mayatattun idanunsan nan tamkar wadda bacci ya yiwa illa. Mutsu mutsu ta fara yi da hannun nata tana son qwace kanta,yanason yayi amfani ne kawai da harshensu na maza da suka qware wajen zaqin zance yasa ta mance yadda yayi rugu rugu da rayuwarta,ta dinga daukan rayuwarta da zuciyarta a pieces da qyar ta iya hadeta waje daya,sai kuma bayan ta tsallake kowanne tsanani,tayi moving forward yakeso ya dawo ya sake rabar rayuwarta?. "Me yasa kika sake fita sultana bayan na gaya miki banaso?" Ya jefa mata tambayar yana qoqarin komawa mode dinsa na dazu. Fararen Idanunta ta daga ta kalleshi abubuwa da yawa cikin ranta. "I can't take it......duk duniya suna kallonki,fuskanki,muryarki dama mo......." Kasa qarasawa yayi saboda ciwon daya mugun murda masa,sai kawai ya sanyata cikin jikinsa gaba daya ya dunqulesu waje daya har sai data ce "Wayyo Allah na bayana" saboda wawiyar rungumar da yayi mata,kusan mintuna biyar sunana haka yaqi sakinta,ya kuma hanata motsawa,kamar yadda itama tsoron gudun da zuciyarsa takeyi ya hanata aiwatar da komai,tana jin yadda take bugawa sosai har saman qasusuwan qirjinsa. Idanu ta shiga rabawa saboda gumin da taji yana ratso sumarsa yana gogar gefan wuyanta,shiri ne ko da gaske ne?. Ta tambayi kanta,da sauri ta zare jikinta daga nashi tana dan turasa kadan,abinda ya sanyashi yin baya yayi kaman zai fada saboda yadda jikinsa yayi laushi,sai ya sanya hannayensanya dafe bayan kujerar yana yin qas da kansa gami da runtse idanunsa da kyau. Labbansa na motsawa yana kiran sunan Allah yayin da sautin baya fita da kyau,shi kadai yasan abinda ke yawo tsakanin mararsa da jikinsa Bata lura ba don gaba daya yadda yake behaving dinta ya sanya lissafinya na neman kwancewa,saita qarasa saman table inda ya yiwa jakarta ma'ajjiya ta dauka tana gyara riqonta gami da fadin "Ka budemin na wuce na makara" ganin bai ko motsa ba saita tuna taga key din saman table,ta koma da sauri ta dauka ta dawo ta zura tana qoqarin budewar. Lausasan tafukan hannayensa taga ya saka ya riqe hannuwanta dake murza key din,ya dagasu a nutse yana zare muqullin daga tsakiyarsu "I need you......i really need you" ya fadi yana yin jifa da key din,kai tsaye kuma ya fada wani guri ko irinsa bata gani. Fuska a narke ta dauke idanunta daga key din daya bacewa ganinta ta maida kansa,yayin da yake tsare ya tsareta da nasa idanun "Amma......hanya kawai nace ka ragemin,ka daukoni ka kawoni nan" ta fadi zuciyarta na karyewa. Tana tsoron haduwa dashi,iya jiya kawai tasan zaren ba kalar yadin bane........fitinar dake idanunsa a yanzu kuma suna sake nuna mata yana da buqatar qarin wani abu na daban. Maimakon ya amsa mata sai ya saki wani tattausan murmushi,ya kamo fuskarta yana duban qwayar idanunta da ko yaushe suke tafiya dashi,tun da can,tun yana matsayin uncle dinta idanunta yasan na dabanne,bare yanzun da suke haifar masa da wani yanayi mai matuqar gaske a jikinsa "How can you turn me on so much just for looking at me?". Fidda idanun nata waje tayi tana mamakin abinda yace din,sharri kenan zaiyi mata?. Buda masa idanun da tayi sai ya sake kunnashi din "Ya salam" ya furta yana yarfar da hannu, tsigar jikinsa tana tashi,yafiso duk sanda zasu kasance din a tare ya zamana tana cikin shauqinsa kamar shi,ko yanzun ji yakeyi kaman yayi mata yadda zuciyarsa ke raya masa,amma ba wannan yake da buqata ba,ba jikinta kawai yakeso ba,yanason harda zuciyarta nutsuwarta dama yardarya,yardar ce kadai yasan zatayi masa wahala muddin ta kai tsaye ce "Let me go......" Ta fadi tana son tsaurara muryarta "No.....ba zaki shigamin mota a bati ba,kinsan ba'a aikin banza dai ko?" "Me kakeso na biyaka dashi?" Can qasa yayi da muryarsa yana jifarta da wani irin kallo,kamar me rada kamar kuma wanda bayason kowa yaji me yake cewa,ya qara taku yana hade tazarar tsakaninsu "Money?" Ya tambayeta yana dage mata gira,tayi taku biyu zata ja baya ya sake hadr gap dinsu "Inason wani abu da yafimin kudi daraja......yafi duk wani abu me daraja daraja a wajena......." Sai ya sake tausasa muryarsa yana qoqarin saita kansa saboda ciwon cikinsa dake qara gaba "I need to re_taste that body of yours.....i can't wait to kiss every inch of your body.......my hand wants to feel every inch of you". Maganganunsa gaba daya suka sanya taji qafafunta ba zasu iya daukan gangar jikinta ba,sai tayi qasa ta sulale tana dunqulewa waje daya. Bai qyaleta ba,don abinda yakeson ya samu kenan lagonta,sai ya bita suka qarasa sulalewa gaba daya,ya jawota jikinsa ya mata wani irin kyakkyawan riqo yana fusgar numfashinsa da qyar saboda tsananta da ciwonsa yayi,magani kawai yake nema,don haka cikin qasa da second uku ya zame mata kamar wani mahaukaci ko mayunwacin zaki. Saboda wasu irin saqonni masu mantar da dan adam sashen tunani da tuna abinda ya kamata na qwaqwalwarsa ya shiga aike mata. A zafafe,a yunwace a kuma shauqance. Duk yadda taso kaucewa wani saqo nashi abun ya faskara,duk yadda taso ta kauce kada ya lalata mata tunani abun yafi qarfinta "Yaaya maina ne wannan?,ya haidar ne?" Tambayar da zuciya da kwanyarta suka hadu suna aike mata kenan a sanda yake dab da fiddata daga hayyacinta. Ba zatace ga yadda aka fara ba,dukkansu daga ita sai shi sai bude idanunsu sukayi sukaga komai ya wakana a nan gurin,dab da bakin qofa,sauqin abun carfet din wajen me tsananin taushi ne,sannan wajen office ne na musamman da akayi musu bayan office dinsu na ainihi dake first floor,wannan din kaman ya zamana wajen hutawa ne kawai a garesu su manyan likitoci. Ko motsin kirki ta kasa tayi bare ta yarda ma su hada idanu,sai hawaye kawai da take tsiyayarwa,wanne irin yaudara ne haka yake mata?,wacce irin shammata ce wannan?,wanne irin kuma rashin adalci da qarfa qarfa yake mata?. Dariyarsa yake qunshewa kawai,shi daya yasan yadda ya sanyata ta sauka daga kan layi,shi daya yasan me yaji me kuma ya gani?,duk da yadda take dojewa a hakan saboda kafiya da taurin kai irin nata,amma koma meye ya sani yayi winning,ta kuma sama masa magani yau cikin qasa da mintuna goma,abinda a baya sai ya shafe kwanaki yana kwance saboda babu matallafi,babu me tayashi fidda cutar dake danqare a mararsa. Har ya fito a wanka tana duqunqune a wajen,ta cure cikin lallausan blanket har baka iya hangota,sai sheshsheqar kukanta. Tsaye yayi gaban madubi yana kallon fuskarsa,ita kanta fuskar tasa tayi wani fresh ta qara haske,irin haske da qyallim goshin da ake cewa angwaye sunayi,wani murmushi yasubuce masa ya miqa hannunsa zuwa lallausar sumarsa da tasha ruwa har yake diga ruwan,yanxun yana mata magana yasan rigime masa zatayi,solution shine kawai yayi mata yadda ya saba. Tsane kansa yayi da kyau ya maida trouser dinsa da shirt din ciki ta suit dinsa,ya balle maballan rigar yana nannadesu,sannan ya taka zuwa gabanta. Tsugunnawa yayi sosai yana bada qarfinsa a qafar damansa,tsugunnon sai ya masa kyau yana sake nuna cikar zatinsa da haibarsa. "Kukan nan ya isheni, gate up kije kiyi wanka,ina cewa aiki na miki kika biyani........I didn't do it by force" ido ta rufe da kyau,zai sake raina mata wayo irin na rannan kenan?. "Ko meye ka yimin Allah zai saka min" ta fadi qasa qasa,saidai mugun ji gareshi din haka ya jiyota "What?" Ya fada dariya na qwace masa "Kinga malama,ji mana,ni zaki rainama wayo?,inda bakiso me ya hana ki qwace kanki koda ta qarfi ne?,ba abinda kika tsinana sai cewa da kikeyi 'ka bari mana,banaso' kuma nasan it is hypocrisy, gate up idan ba haka ba na wankeki tas........abun ma da ba wani dadi da yayi?" Ya qarasa fada yana miqewa. Batasan me yasa maganarsa ta qarshe ta sauka a kunnuwanta da ciwo fiye da dukka maganganunsa ba,sai kawai ta saki kuka me sauti,sautin daya dinga jinsa yana masa dadi don ya jima baiji kukanta me sauti kama haka ba,sautin yana tuna masa da yadda yasha fama da its lokacin quruciya,koke koken banza da tsokana,idan kuma akafi qarfinta ranan aka zaneta ta buwayi kowa cikin gidan. "Idan nayi counting daga daya zuwa goma baki wuce toilet ba,na rantse yanzu zan tube mu tafi second round,kuma second round dina bashi da dadi ni kaina na sani......it will take more than twenty to thirty minutes" ba shiri ta tattara blanket din tana boye kanta a ciki,ta soma takawa zuwa bandakin,har yanxu bata bar kukan da take ba. Da idanu ya bita yana jin wata zazzafar qauna da tausayinta cikin zuciyarsa. Xayaso shi zai mata wankan,ya lullubeta cikin qirjinsa,ya shiryata,yayi mata tausa a dukka guraren da yasan ya wahalar da ita,to amma ita din zuma ce sai da wuta,qilau zata iya jawo bau,gwara dai ya bita a haka. Sai data shige toilet din ya dauke idanunsa yana fidda iska daga bakinsa,yana mata uzuri sau da dama,kowa da yadda Allah ya halicci zuciyarsa,wani mutumin yana da saurin manta abu ya wuce,wani kuma koda ya yafe abu baya saurin barin zuciyarsa,bashi da mantuwa kwata kwata,kuma hakan ba yana nufin bai yafe ba,any way yaci alwashin sai ya sanyata tayi rushing zuwa gareshi sooner or later. Yanason ya fara gyara wasu abubuwa da yakejin lokaci yayi da zasu gyarun,don haka ya miqa hannunsa ya dauki jakarta,ya kuma fiddo wayarta ya bude, zuciyarsa fes,ruhinsa tas.......... _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 90 Mobile app nashi ya bude bayan ya gama caje wayar ya lalubi account number dinta,kudi ya tura mata masu yawa,ya kuma zuba mata numbers dinsa dukka yayi saving da "Dad BB" wasu kuma ya saka sunan masoyi da yaren faransanci,wata kuma ya saka sunanshi haka nan. Duk abinda yake da buqata,kama daga pictures dinta da sauransu ya tura sannan ya maida wayar aljihunsa. Ta jima tsaye a bakin qofar lullube ruf da towel tana jin nauyin fita,batasan da wanne ido zata kalleshi ba,wani irin kunya takeji ba dan kadan ba,ta dinga juya kalamansa a kunnenta _idan bakiso me ya hana ki qwace kanki koda ta qarfi ne?,nasan it's hypocrisy_ idanunta sukayi rau rau da hawaye tanason tuna da meye da meye ma tayi a lokacin,saidai kuma oho ta kasa tuns komai. Hakanan tayi shahada ta murda handle din ta sanyo qafafunta waje. Yana tsaye kyam yana fuskantar qofar tamkar me gadinta,dukka idanunsa ya zuba mata, murmushi yana son qwace masa,gaba daya ta tsargu,sai ta koma ta bayansa tana cire towel din da sauri tana maida dankwalin kanta. "Nooo" ya fadi yana ajjiye wayoyin hannunsa saman mirror,fara takowa yayi wajenta yayin da tayi tsuru tsuru tana kallonsa. Ita totally a firgice take dashi,ko qanqani batason ya matso kusa da ita,saboda ta fahimci ko yaya jikinsu ya samu connection sai mode dinsa ya sauya,sai ya buqaci kuma kebewa da ita. Ta bayanta ya tsaya,ya sanya hannu ya zare scarf din yana cewa "Bai bushe ba ta yaya zaki rufeshi?" Kafin tace komai har ya sanya hannayensa biyu ya fara ware gashin zuwa gadon bayanta wani kuma zuwa fuskarta. Da sauri ta miqa hannu ta riqe hannun nasa,sai ya kada kai "Ko ki sakarmin hannu ko kiga matakin da zan dauka....." Ba shiri ta sakar masa hannun idanunta na sake hada hawaye. Ta gaji da hawaye,batason kuma tayita zub dasu tunda bataga ranar tsaiwarsu ba. Kaman yaji abinda ta raya itama ya sake tabbatar mata yana sake janyota cikin jikinsa "Ki rage yawan kuka kada ki rasa hawayen xubadawa a labour room". Qarasa kashe mata bakinta yayi,ta rasa ma meye zata ce masa taji dadi,sai kawai ta gwammaci tsuke bakinta amma ta kasa tsaida hawayen idanun nata. Janta yayi ya zaunar gaban madubi,yasa drayer ya busar mata da kan nata,yana aikin yana cewa "Tunda nine silar jiqewarsa ai gwara na gyara abuna kada laifin nawa yayi yawa" harara takeson watsa masa amma tana shakkar abinda zaya biyo baya a matsayin horo,ta tabbatar idan yace zai sake wani round din a yanzu babu abinda zai hanata ziyartar gadon asibiti,don dukka gabobinta motsi sukeyi mata yanzun da wani irin ciwo,mada ma cinyoyinta suji labari,haka nan lips dinta da suka sha tsotso kaman babu gobe. Kanta ta dauke gefe tana tsuke bakinta gefe,bakin da zuciyar fal da tsiwa,amma tana tsoro ta furta,so take ya fiddata daga wannan office din,batasan wanne tsautsayi bane ya sanya tayi trusting nashi ta shiga motarsa ba,bayan ko jinyar jiya bata gama yiwa jikinta ba,gashi yanzun ya sake hada mata wata gajiyar. Tsaf ya gyare mata kan,ya kuma dameshi da band dinta. "See" ya furta yana dan ja baya kadan cikin murmushi yana duban fuskarta ta cikin madubin,fuskartata ta fito sosai tayi fes,kyawunta ya sake fita ainun,hakanan oily eyes dinta sun sakeyin haske sosai. Sau daya ta daga kai ta kalla na duka duka baifi second biyu ba ta dauke kanta. Ita kanta taga yadda yayi qoqari,kyan yayi kyau kaman an mata retouch ne. "Ni dama badon ke nayi ba,koki yabani ko karki yabani.....dama aikina ne tun kina 'yar mitsitsiyarki" yayi maganar yana kama hancinta. Tana shirin kauda fuskarta kira ya shigo wayarsa,sai ya sake mata hancin yana duba me kiran. Tare idanunsu shi da ita suka kai kan screen din wayar "Laila" ya furta bayan duka sun karanta sunan dake saman screen din a zukatansu. Ta gefen idanu yake kallonta a sace,kanta yaga ta dauke tamkar ma bata ga komai ba. Murmushi ya saki dan qarami,ya haye saman dressing table din qafarsa na gogar tata sannan ya daga wayar yana sanyata a handsfree "Hello nijer man......" Laila ta fadi cikin sanyin murya da mutuwar jiki gaba daya. Yana sane ya danyi delay na amsawar,sai ta sake magantuwa "Hello........dear" ta sake fadi cikin lanqwasa murya har tafi ta dazu zaqi da qarfi. "Hi......kina lafiya?" Narke murya tayi "Yanzu kuma?......dear ban cancanci hakan ba,me yasa?" Yasan sarau akan me zatayi complain,ya fara satar kallon sultana sannan yace "Am sorry.....,am was so busy ne,but....zanyi qoqari naga na gyara" "Kayi alqawari?" "Zan duba in sha Allah.....ina fata ranki bai baci ba?" Ya fadi da gayya yana kuma sane. Tsam ta miqe tana maida scarf dinta saman kanta,ta tsani jin sunan yarinyar gaba daya,ba don komai ba sai don yadda ta fahimci a yawon duniyarsa ya hadu da ita,babu kunya kuma a tattare dashi yake ci gaba da mu'amala da ita?,ko babu komai ita din ba d'iya ko qanwa take a wajensa ba?,wanda ya kamata ace kome zaiyi ya kaucewa idanun sani ai. Ji tayi an jawota an kuma zaunar da ita,wanda bata zauna ko ina ba sai saman cinyarsa,don juyota yayi sosai ya kuma yi mata masauki a nan din. Hannuwansa taso zamewa amma yayi mata riqon tsauri yana kuma ci gaba da wayar,tana iya jin sanda lailan ta bashi amsa "Ba'a fushi ai da masoyi......yana da wani daraja da ya cancanci ayi haquri dashi a kowanne situation" hannu ya sanya yana juyo da fuskar sultana gareshi lafazin laila yana ratsashi. Idanu suka hada,ta kauda kanta tana jin zuciyarta na mata susa. Ne meye zai riqeta haka?,lallai dole sai taji zancansa da yarinyar da ta tabbatar bata da kamun kai?. "Thanks.....na gode sosai, za'a yimin uzuri yanzun?" "Me zai hana.....ba damuwa bane" "Thanks my little sister" murmushi tayi tana jin dadin hirarsu,yau din sai taji ya sake mata sosai ba kaman yadda ya saba amsa mata a daddake ba,ya sauke wayar tana kissing dinta,tana tunanin nan da next week ta siya ticket gaskiya taje ta ganshi,me yiwuwa addu'ar ta ne Allah ya amsa mata. A nutse kaman baiyi komai ba ya aje wayar a gefe,ya dauki tata wayar yana buda tafukan hannayenta,taso damqesu amma tasan wahalar banza zatayi da ranta,qarfinsu ma ba daya bane,ya sanya mata sannan ya dubi idanunta "As from today.....ki gayawa ama da aba,bana buqatar su sake miki komai,ke ko su benazeer,dukka nauyinku a wuyana yake,ko abinci zanso kuci daga wanda na siya da kudina......amma shima din with time zaku koma qarqashina" sam ko kadan abun baiyi mata ba,sai ta soma qoqarin zame jikinta daga kan cinyarsa ranta na baci sosai. Bai hanata ba har ta gama zamewar. Tazara ta bayar tsakaninta dashi tana dubansa "Shekara nawa munaci daga taskar tasu?,ka taba tunawa da mu?" Ta fadi wani abu me tsauri yana nunawa daga qasan idanunta. Tsakiyar idanunta yake kalla,ko kadan maganar bata bata masa rai ba,a yau sai yake gano wani abu daga tsakiyar idanun nata,wani abu daya sake sanya masa hope sosai a kanta,sai ya maidata kaman tv sanda take motsa dan qaramin bakinta. Tsiwa takeyi amma batasan idanunta suna tona wasu sirrika da yayi imanin ita kanta batasan dasu ba, murmushin gefan baki ya subuce masa,ya maida hannuwansa ya goye a qirjinsa "Na lura tafiya ta tana miki zafi da yawa a rai right?" Ya qarashe da sigar tambaya yana dage mata dukka girarsa "Saboda me zan damu?,bayan sai daka tabbatar na mutu ne sannan ka gudu ka barni" "Ya salam......" Ya fadi yana kuma saki qaramin murmushi "Yes.......kudadenka basa nufin komai a wajena......bani ya dace na cisu ba,yammatanka sune sukafi dacewa dasu" dole wani murmushin ya sake qwace masa. Kishi!,ya fita sosai cikin zantukanta,so yake taci gaba da maganar,saboda ya tabbatar tana fitar da duk wani ciwo da rauni Dake qirjinta,maganar yakeso tayi tuntuni amma ta qiya,shi yasa ta gaza hucewa,amma a yanzun maganarta tana zame masa tamkar wata nasara a tattare dashi. "Cool down.....ki gayan hukuncin da kikeso na yiwa kaina da kaina" "Leave me alone please, stay away from me...... that's all i want" ta furta da wani irin zafi. Bai barta ta sauke numfashin data debo ba yayi mata wani kyakkyawan kamu,bai kuma bata second chance ba ya mata masauki cikin jikinsa,ya mata riqon tsauri yana same tsotse lips dintan nan masu sulbi da baya gajiya dasu. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* Book 2 page 91 Hawaye kawai take fiddawa ta gaza aiwatar da komai,itakam me ya maidata ne?,tun daga sanda suka hadu a France bashi ds aiki sai luguguitata,ya maidata kamar wani babyn wasa?,meye ya rage ne a jikinta bai taba ba?,meye ya rage a jikinta hannunsa da bakinsa baikai wajen ba. Bata da qarfin qwatar kanta don haka hawaye da idanu sune kawai nata,har sai da yayi me isarsa ya gama,ya saketa yana maida numfashi amma kukan da yaga tanayi ya sanyashi sake kamota har zuwa saman sofa din dake dakin. Qafafunsa ya raba ya sanyata a tsakiya,bayanta ya jingina da qirjinsa yana sauke numfashi a hankali idanunsa a lumshe,har sai daya daidaita numfashin nasa ta yadda zai iya magana. "Inata tabaki bakiso ko?, I can't control my heart.......if you know what double means to soyayyarki ce.....na soki tun kina zallar jini a jikin nafessa.......na soki lokacin da kika wanzu a mahaifarta,na soki sanda kika shaqi iskar duniya,na kuma dora da sonki tun daga wannan ranar kawo yau........abinda ya faru tsakaninmu na tabbatar ubangiji ya hukunta hakan saboda ya mallakamin ke......banda hakan ya faru da bazan taba ganewa cewa ina sonki so na soyayya ba......bazan taba gane ina sonki so na auratayya ba,zanta dauka cewa so nake miki na 'yan uwantaka,so irin na uba da 'yarsa ne kawai,zan yita fafutukar mallaka miki miji na gari ne ba tare da nasan cewa ni din nine nafi cancanta dake ba.....ke jinina ce sultana kuma ruhina,ko baki sona,koki yarda ko kada ki yarda ke din BUGUN ZUCIYATA CE......I can't stop loving you till my last breath........Tu es mon bonheur, tu es ma vie(kece farincikina kece rayuwata" ya furta yana sakin gauron numfashi da ya motsa zuciyarsa. Wani irin takejin kalamansa cikin zuciya da jikinta,gaba daya yanzun bata fahimtar kusan komai,siririn kukanta kawai ke fita yana ratsa kunnuwa da zuciyarsa,duk sanda take kuka irin wannan wannan kukan nata na quruciya yake tunawa,wanann kukan data dinga yi masa sanda ya karbe jaririn budurcinta da bai gama cika ba "Me kikeso?" Ya tambayeta calmly don bai qaunar kukan "Ka maidani....." "Ya isa.....muje" ya fadi a taqaice yana miqewa. Tsam ta miqe itama,cikin jin nauyi da kuma jin tur da abinda ya faru ta tsinci kayanta da suke d'ai d'ai cikin dakin. Jikinta ba qwari ta maida scarf dinta saman kai,ta lalubo hand bag dinta da sauran tarkacen agogo da dankunnenta da ya ciresu daya bayan daya ba tare ma da yasan yayi ba. Dukka bata da lokacin maidasu jikinta,don haka ta tattarasu ta watsa cikin jakar,ta xura takalminta tayi tsaye a bakin qofa tana jiransa,kamar wadda za'a ce ket ta zura da gudu A nutse ya isa wajen saqale suit,suit dinnasa ya dauka ya maidasu jikinsa,ya gyara musu zama sosai a jikinsa,ya tsaya gaban mirror din dake saqale a kusurwar office din saman dressing table ya dauki comb yana gyara hair style dinsa. Cikin second goma ya koma tsaf abinsa,tana tsaye tana satar kallonsa,cikin ranta tana gulmarsa sanda yake daura agogon hannunsa saman lafiyayyar fatarsa me wadatar gargasa "Har yanzun wanann shegen iyayin da gwallin kamar mace yana nan" ta fadi a ranta tana tuna sanda yana maina dinsa,dan jami'a cikin jami'ar niamy,yama akayi ne ya zama likitan zuciya?,bayan ya taso a matsayin soja kuma likita?. Murmushi me sanyi ya saki ta gefen bakinsa yana daura agogon,ya kamata sosai tana satar kallonshi amma ita din bata sani ba,sai ya kauda kai har sai daya gama daura agogon nasa sannan yadan yardar da hannunsa yana cewa "Idan baki qoshi da kallona din ba...... ni ba sauri nakeyi ba,mu zauna ki qarasa saimu wuce", mugun firgita tayi dataji ya fadi hakan,ta wani basar tana juya masa baya,ko zata yarda da kowanne sharri nasa amma banda wannan,bakinta ta murguda cikin jin haushin me zata kalla?. "Allah ya sawwaqe,me zan kalla?" "To ni na sani ne?,kinsan ance tsakanin miji da mata ai sai Allah ko?,na sani ko kewar......." Kaman tasan me zaya fada tayi hanzarin tararsa da fadin "Pleeeeassseee......." Tana dora hannunta saman kunnenta gami da runtse idonta da kyau. Tilas siririyar dariya ta kubce masa,ya dauki wayarta data manta ya fara takowa har ya iso bakin qofar,sai yasa dukka hannunsa saman kafadarta yadan matsar da ita gefe,ya zura hannunsa cikin Jakarta ya ajjiye mata wayar sannan ya zura key din daya lalubo yana bude qofar,dukka idanunsa bisa fuskarta yana hango yan qananun kamanni tsakaninta da su batoul can qasa qasa,yayin da idanun nata suke a rufe,amma kuma tana iya feeling idanun nasa cikin jikinta. Nishadi yakeji sosai cikin ransa tare da wani energy cikin jikinsa,don haka ya saka slow music dake tashi da wani sassanyan sarewa,wannan ya taimaka qwarai wajen kashe mata jiki,tayi relaxing sosai jikin kujerar tana aje numfashi,qamshinsa da takeji duka ya buwayi hancinta,ko ina na jikinta idan ta motsa qamshinsa yake bata. Idanunta a rufe saidai batasan inda suka nufa ba,tadai dauka zaya kaita ne TV station din. Duk bayan wasu mintuna sai ya juya yadan kalleta,hira yakeso suyi koda fada ne,koda tsonakarta yayi amma kuma yadda ta tsume din yasan ba zatayi magana ba,don haka yana sane ya dauke kan motar zuwa babban titin dake da yawaitar shops a wajen. Daya daga cikin shop din da yafi siyayya a ciki ya tsaida motar,sai a sanann ta bude fararen idanunta a hankali,ta zauna sosai tana duban wajen,sai taji zuciyarta na narkewa. Da gasken yake bazai kaita ba,kalaman bakinta dukka ya qarar dasu,batasan ta yadda ma zata fara roqarsa ba. Dubansa tayi sanda ya zagayo ya miqa mata hannunshi. "Koda sau daya ya kamata mu siya gift na birthday din su benazeer tare......ko don farincikinsu......na tabbatar zasuji dadi" kanta ta kawar gefe,kaman ba zata ce komai ba,kaman kuma ba zata motsa ba,sai kuma ta juya a hankali ta zura qafafunta waje yasa hannunsa ya riqe hannun data hanashin "Kada ki zama marowaciya mana......i need these soft hands" ya furta yana laluban hannayenta ya matsesu gam cikin nashi. Babban shop ne da suke saida kowanne irin nau'inkan kaya da suka shafi yara. Kaya masu kyau da daukan hankali. Sukayi tsaye a bangaren chocolates yana goye da hannayensa bayan ya zame hannunsa daga nata a nutse "For the first time daddy da mommy zasuyiwa yaransu siyayya" ya fadi yana kashe mata ido gami da dage mata gira guda daya. Kanta ta kawar gefe tana jin wani iri,kalmar daddy da mommy din tana mata girma da yawa. A tausashe yaja hannunta "Oya.....choisissez la bonne chose pour eux(zabar musu abinda ya dace)" ya fadi yana daukan cart. Dole ta fara takawa tana duba kayan. Dab da dab yake da ita,kusan ko cikakken taku daya babu na tazara a tsakaninsu,yana bibiye da ita. Duk sanda jikinsa ya gogi nata sai taji wani iri,shikam kamar ma ko a jikinsa ko kuma da gayya yakeyi ne bata sani ba. Duk sai ya nemi sukurkuta nutsuwarta,har ta dinga zaben wasu abubuwan ba dai dai ba "Huta kawai,suis-moi(biyo ni)" komawa baya tayi tana biye dashi,tana noticing nasa komai zai dauka me tsada ne,komai nasa me kyau yake zaba hakanan wanda yake bada kala da nutsatstsen nau'i,hakanan komai ya dauka din sai taji yayi mata dari bisa dari,batasan dalili ba,ko har yanzu wannan chemistry din dake tsakaninsu yana nan?,don ko a baya kusan zabinsu akan komai daya ne. A karan kanta taga siyayyar ta fara yawa,amma kuma batason masa magana kan hakan. Sanda ya fara jidar musu turare saita koma baya kawai ta zubawa sarautar Allah Ido "Ba abinda yaran suka rasa,wannan abun kamar almubazzaranci ne ai" cart na uku daya cika ya saki ya waiwayo,sai suka hada idanu "Bance kice komai ba,m'as-tu entendu?(kinji ni?" Ya furta da sigar seriousness cikin maganarsa "Nima shishshigi na" ta fadi can qasan zuciyarta tana dauke kanta. Murmushi kawai ya saki,yasan taji haushi ne da tsaidatan da yayi,baya jin ko meye zai kashewa yaran zai biya zai kuma sauke haqqinsu dake kanshi,a dukka tsahon shekarun yana jin kamar ya dawo dasu yayita hidima musu ita dasu din gaba daya. Kusan awa guda suka kashe cikin shop din,suka kuma cika bot din motar da siyayya me yawan gaske. Sake zubawa sarautar Allah ido ta sakeyi sanda suka dauki hanya,saidai ga mamakinta TV station Street ya hau. Batace masa uffan ba tana jira taga me zayayi,sannu a hankali sai gasu cikin harabar gidan,ya samu parking lot ya tsaida motar,ya kasheta ya waiwayo yana dubanta "Kije ki dauki excuse" maganar yadan bata mamaki. Yadda take kallonsa ya tabbatar masa tana da buqatar qarin bayani,sai ya dage mata dukka girarsa "Wannan shine adalcin kawai da zan iyayi miki,kada ki wuce mintuna sha biyar......." Ya fadi yana duba agogon hannunsa kana ya dauke dubansa daga kanta kaman baiga kallon zallar mamakinsa da take jifansa dashi ba "vous perdez votre temps(kina bata lokacinki)" ya fadi still ba tare daya dubeta ba. Ba sanin jiya ko yau tayi masa ba,hakanan a sanin yau dinma wasu sabbin halaye da kuma dabi'u yake fitarwa,kulashi din tamkar baiwa kanta horo ne kaman yadda ya alqawarta mata,dole ta bude murfin motar tana fushi tana kumburi ta fice,saidai kuma itama zata d'ana masa,wannan mulkin mallakar da yakeyi mata ba zata bari ba. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 92 Minti goma kacal ta dawo,fuskarta a dan daure,don gaba daya abinda aka tsara zasuyi a yau din yayi silar rushewarsa,sai uzurin tana da maras lafiya ta basu. Qofar motar na bude don haka yayi tsammanin shigowarta,maimakon haka sai yaga ta cake daga bakin qofa. Tana da yaqinin yanzun haka gida zaice zai kaita,ita kuma ba zata taba lamunta a gansu tare ba kaman yadda aka gansu a nijer,idan aka gansun tare wanne sauran dalili gareta?,me zata cewa ama ko aba?, infact ma ita batason kowa cikinsu ya ganta dashi. "Excuse me.......baki gaji da zaman Tv station din bane?" Ya tambayeta cikin zolaya ta window din motar "Let's go......lokaci yana qurewa.....na tabbatar batoul zasuyi kewanki if kika je musu late" "A motata zan koma gida tunda a ita na fito" ta fadi tana basarwa. Dan nazarinta yayi na wasu daqiqu,sai ya amsa da "Is okay,yayi" yana buda murfin motar ya fito. Wayarsa ya ciro daga aljihu bayan ya haye bayan motar,yakuma yi magana da bata wuce ta minti daya ba kacal sannan ya kashe ya maida wayar aljihunsa. Baice mata komai ba ya fidda daya wayar tashi yana latsawa,ba'a cika mintuna ba babban qofar station din ya bude motarta ta shigo. Motar tabi da kallo tana mamaki,sam ita ta manta ma da batun motar tunda tsoro ya kamata a lokacin. A nutse ya sauka daga motar ya doshi farin bafaransen da ya fito daga motar. Key ya karba daga hannunsa ya miqa masa wani key din,sannan ya juya a nutse ya dubeta "Bismillah" ya fadi yana bude mata front seat. Idanunsu suka hadu waje daya,ya zuba mata ido yana sauke mata nannauyan kallo da idanunsa. Zare idanunta tayi daga kansa,lallai sai qafarta qafarsa?,ta yaya zata musa masa?,bata sani ba,don haka dole ta sauke hannuwanta ta soma takawa a nutse tana nufar motar. Da wani sassanyan kallo yake qarewa takunta kallo,komai nata a nutse kamar ba baby sultanarshi gwanar rawar kai ba,komai nata ya canza,yana hangen tasirin fushi kadan kadan daga can tsakiyar idanunta,withtime zai wanke komai daga cikin zuciyarta kamar komai bai faru ba,yana sanya ran hakan in sha Allah. Maida murfin yayi ya rufe,sannan ya zagaya seat din driver ya shiga,ya kunna motar amma bai tasheta ba,ta mirror tana iya hangen yadda suke debo kayan suna maidawa boot din tata motar. Sai da suka kammala sannan yayi bismillah,ya tayar da motar a nutse suka fice daga gurin. Daga can farkon street din nasu ya gangara gefe a hankali ya ajiye motar,ya juya barin da take zaune din yana jifanta da wani sassanyan kallo. Cikin jikinta take jin dukka idanun nasa,amma qemene taqi dubansa,har sai da wayarsa dake ajiye a tsakiyarsu ta kada. Kaman an fusgi hankalinta ta juyo da dan hanzari,sunan AYANA shi yake yawo kan screen din. Sai daya gama qarewa sunan kallo sannan ya miqa hannu ya kashe sound din ya maida wayar silent,sannan a hankali ya maida idanunsa kanta. Sabanin daxun yanxun waje take kalla ta window din motar. Sai kuma ta sanya hannu ta bude motar tana ficewa daga ciki ba tare data bari yaga fuskarta ba. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 93 Ayana ce,ya saki qaramin murmushi saboda kiran yazo masa a dai dai. Da muryar nan tasa dake matuqar tafiya da ita yayi mata sallama,ta amsa cikin zumudi da kuma karadin nan nata "Yaa maina......ba call ba tex,why na?" "Munyi wannan dake?" Ya tambayeta a dake,don ya fahimci rawan kanta yayi mugun yawa. Yayi imani bata sanshi bane a baya da duka batayi irin wannan abun da takeyi yanzu ba "Nooo...." Ta fada murya a karye tana karyar da wuya "I think zan samu kulawa tun yanzu,coz next week in sha Allah Ina tahowa nan,zakuyi magana da daddy,naji kaman yace ba cikin school zan zauna ba" "Alright..... yayi,karbi nan" yace da suhail yana kallonsa. "Karbi mana,maza ka tayata hira,she's my sister also" ya fada yana cin serious kaman wani abbansa. Dariya tasi kama suhail din,sai kawai yasa hannu ya karba wayar,maina din kuma ya juya zai shige ciki. "Kunyi magana ne da laila?,tacemin cikin satinnan zata shigo Paris,tanason zuwa ta gaidaka......tayi missing naka,I was surprised da kalamanta,ina ji a jikina anya ba wani abu a boye?" Tsaiwa yayi cak sannan ya juyo yana duban sardauna,kalaman zuwan ayana da zuwan laila suna masa yawo saman kai "Did she tell you something?" Ya tambayi sardauna,kai ya girgiza yana tabe baki "No.....kawai yadda take bawa komai naka muhimmanci ne yasa na saka ayar tambaya" murmushi maina yayi, sardauna yana da kara da alkunya,amma rashin maganatuwar laila ga kowa tsakanin daddy da sardauna hakan ya masa,don fadi musun da zatayi tamkar ta masa wani dabaibayi ne "Kada kayi mata shishshigi to malam ka turata ga abinda ba shine zabinta ba.....wataqila akwai wani a boye cikin rayuwarta" kai sardauna ya girgiza sai maina yaci gaba da wucewa ciki "Kada ka jima a wankan nan naka,don akwai gurin da zamuje" sardauna ya fadi "In sha Allah" ya amsa musu a gajarce. Sama sama ta dinga jin hayaniya da kuma knocking duka lokaci guda,nauyin baccin da tayi ya bata mamaki,taja lokaci sosai,amma kuma ba abun mamaki bane saboda ita kanta tasan gajiya ce sosai a jikinta. Dankwalinta ta dauka ta daura sannan ta sauko daga saman gadon,tasa hannu ta murza key din ta bude qofar ta jawota baya. Benazeer ce da batoul sanye da fararen singlet da gajeran pant,da alama shiri ake musu na birthday din,don gyaran gashin dake kansu kadai ya gaya mata hakan. Dukkansu ita suke kallo ba wanda yayi magana a cikinsu,tadan fiddo idanu waje tana dubansu "What's happening?" Tayi maganar da muryar bacci,cikin idanunsu take kalla,sai take ganin idanun nasu tamkar na maina "Mommy an kusa a fara fa.....mummy baki shirya ba" benazeer ta fadi a shagwabe "Bacci nayi yanzun zan fito,shikenan?" Kai suka gyada a tare "Yes mummy" kasa maida qofar tayi ta rufe har suka wuce,girma yaran sukeyi sosai,idan ka gansu zakayi tsammanin sun girmi shekarunsu. Da kadan da kadan wasu abubuwan nasu suke juyewa zuwa na babansu. Shape din idanunsun sak irin nasa lion eyes din data sakawa suna,data kalli qafafunsu kuma yanzun sai ta sake gani tamkar nashi "Ya akayi har kika haddace qafarsa?" Wata zuciyar ta tuhumeta,sai taja tsaki tana jin haushin kanta da kanta,don itama bata san ya akayi hakan ya faru ba,ta maida qofar ta kulle ta taka tana komawa ciki,sannan tazarce direct zuwa toilet. Ruwa ta hada me yawa ta hada me yawa tayi wanka,ta gasa jikinta da kyau da ruwa me dumi sosai,sai taji dama dama,gabbanta suka saki ciwon da take danji ya ragu. A nutse ta zauna ta soma shiryawa gaban madubi,haka kawai yau din taji tana sha'awar shiga party din yaran wanda tsahon shekarun da aka dauka ana celebrating birthday din nasu bata taba wani daukan abun da muhimmanci ba. Kafin ta kammala sun mata knocking ya kusa sau uku. Atamfa taji tana sha'awar sanyawa,wanda ta jima sosai rabonta da ita. Ta bude Wardrobe dinta ta tsaya tsaf tana qarewa kayan kallo kafin daga bisani ta jawo wata straight gown ta atamfa da aka yiwa adon shawbrosky tun daga samanta har qasa. Dinkin ya zauna mata das a jikinta,hakanan kalar atamfar ta haskata ainun,don data gama ta dora dankwalin saman kanta zakayi tsammanin daga maqwafciyar qasar take. Sosai qirar jikinta ta fita,shape dinta dukka ya gama fita,ita kanta data kalli kanta a mudubi saida shigar ta qayatar da ita. Duk wani salon ado da sanya atamfa zamanta da ama ya sanya ta iyashi,ba zata iya qididdige yawan adadin abubuwan data koya wajen ama ba. Har zata sanya qaramin mayafinta saita fasa,haka kawai taji idan ta saka mayafin kamar ta bata adonta,yau daya tanason ta sake sosai cikin yaran,tana jin cewa idan batayi da gaske ba tsaf aliyyu zai iya janye mata yara,yanayin yadda taga suna maqale masa da yadda suke yawaita zancansa har basa maganarta kamar haka. Baqanqe plate shoe da suka haskaka fatar qafarta ta saka,ta shafe jikinta da tsadajjen perfume dinta sannan ta dauki wayarta tana fita zuwa falon da take jiyo 'yan qananun hayaniya da tashin kida maras qarfi da yawa. "Wow,ma sha Allah" ta fadi cikin ranta,irin yadda akayi decorating parlor din dole ya burgeka,ba zaka taba tsammanin cikin parlor din bane. Idanunta akansu benazeer,wani irin ado akayi musu irin na larabawa,takanas ama ta dauko matar ita ta shiryasu. Uwa me dadi,duk jama'ar gurin amma haka suka tattare gown din suka nufota,ta durqusa tana murmushi gami da bude hannayenta tana jiran isowarsu,daidai lokacin stella maqociyarsu 'yar asalin qasar england ta bude qofar falon da akayi qaraurawa,ya sanyo qafarsa cikin falon sanye da trouser din da baqar shirt wadda ta fidda ainihin hasken fatarsa me cakude da sirkin jaja jaja. Ita ya fara hangowa kaman yadda itama nata idanun a kanshi suka fara sauka. Ita ta fara dauke kai sai shima ya dauke nashi kan tamkar ma a wunin ranar ba qani abu saya sake hadasu baya ga gaisuwar da sukayi da safiya. Zamewa sukayi daga jikinta sanda suka hangoshi yana takowa zuwa cikin falon da tsahon nan nasa dake cakude da murjajjen jiki da ya zamewa tsahon nasa ado sosai. Idan ka kirashi dogon namiji kai tsaye bakayi kuskure ba,sumarshi ta zauna sosai a kanshi tana ta qyalli. Kai tsaye ya wuce wajen ama dake zaune guri dayayayin da benazeer da batoul ke rige rigen isowa wajensa don sun ganshi ne a bazata,basu taba tunanin da gasken zaizo ba kamar yadda uncle goumar ya gaya musu. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 94 Sosai ya zauna daidai qafafun ama kamar zai shige cikinta ko kuma qanqanin yaro,irin wannan zaman a baya yakeyi a gaban ama din,yana kuma matuqar jin kewar yin hakan duk sanda ya tuna. "Barka da warhaka ama" ya fadi sanda ya zauna daidai, batoul da benazeer kuma suka haye jikinsa suna masa hayaniya. "Barka kade,mun yini lafiya?" Ta amsa masa da dan sakewa har abun ya sake sanya zuciyarsa yin fari. "Alhamdulillah,ya fama da yara?" Ya furta yana kallonsu benazeer daketa cusa masa alawa a hannu da baki "Alhamdulillah" ta fada a nutse tana duban fuskarsa,sam sai yaqi yarda ya kalli aman saboda tambayar tata da yayi shi kansa yasan tana da nauyi,to amma ya quduri aniyar gyaran komai ne shi yasa ya shirya fara tunkarar gyaran. Cikin yaran ta shige abinta tana fama dasu,ta fidda wayarta tana musu hotuna da qananun videos gaban manyan cakes dake dauke da hotunan su benazeer da batoul din. Kallo daya tak zakasan cake din ya lashi kudi,duk daya hawa shida gareshi. A zahiri yana fama ne da qiriniyarsu batoul,wanda tunda suka ganshi sukaqi komawa wajen baqinsu,sun cikashi da tambaye tambaye "Daddy ashe zakazo...... Daddy mummy ce tayi inviting dinka?,daddy munyi missing dinka......har uncle goumar ma muka gayawa,yace mana dama zakazo" ya biye musu sosai,duk gift din da suka karbo shi suke kawowa yana ajjiye musu,saidai kuma fiye da rabin hankalinsa yana kanta. Duk wani motsi nata idanunsa yana kai,wani shauqi ke fusgar zuciyarsa,duk sanda ta gilmashi sai yaji kaman ya jawota zuwa jikinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Bugun zuciyarsa yana qaruwa haka idanunsa ke sake qanqancewa......baisan me yakeji me zafi haka tattare da ita ba,baisan wanne irin maganadisu ne yake janshi a kanta ba,kamar ba dazu dazu suka kasance tare da juna ba,har sai daya fara tilastawa kanshi qoqarin controlling abinda yakeji game da ita. Komai tana yine bisa dakiya da dauriya,don batason barin wajen kota sauya abinda tayi niyya don kada ya dauka saboda shi ne,wannan ya sanya yadda ya bagarar da ita itama sai ta bagarar dashi kamar bata ganshi ba ko batasan da wanzuwarsa a wajen ba,saidai kuma can qasan ranta batasan me yasa takejin haushin yadda ya wani basar ba,kamar bai ganta ba,kamar kuma baisan da ita a wajen ba,kamar ba dazunnan ya gama jagwalgwalata kaman tsohon maye ba?. Amsar da zuciyarta ta bata raina mata wayon da yayi yana pretending ma duniya kaman ba komai tsakaninsu shine abinda yafi bata haushin. "Meye naki don ya nuna haka?,dama haka kikeso ai yaci gaba dayin walau a zahiri ko a badini ko?" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa,sai taja qaramin tsaki,tana jin ba wannan tunanin ya kamata tayi ba,tunanin yadda zata fita aikinta gobe hankali kwance ba tare data hadu dashi ba shi ya kamata ya dameta,ta sake jan wani tsakin still dai sanda take gyara ma wata yarinya 'yar qasan Bangladesh gashinta da ya kwance daga jikin ribbon saboda santsi. "Lokaci yayi" maman yarinyar ta furta da yaren France tana kallon ama tana murmushi "To bismillah,ni 'yar kallo ce ai,na gama nawa aikin" ama ta maidawa matar amsa. Duka duka ayeesha ba zata haura shekarun haidar ba,amma jininsu ya hadu sosai da ama,kaf neighbor's dinsu su sukafi mu'amala da juna "Ku taso birthday girls" ayeesha ta fada tana murmushi gami da kallon su benazeer da suketa dabdalarsu akan maina. Gyara daurin igiyar straight gown dinta takeyi tana tsaye daga tsakiyar yaran,eye glasses din data mannawa idanunta ya qara fidda sirrin kyanta. A hankali ta waiwaya wai taga ko su benazeer din sun taso,sai idanunsu suka shiga cikin na juna. Cikin wani irin salon ya kafe idanun nata a cikin nasa yana aike mata da saqo ta nan inda yake zaunen,duk yadda taso ta janye idanun nata ta kasa,har sai daya tabbatar bugun zuciyarta ya qaru yadda yakeso,sannan ya sake mata wani shu'umin murmushi yana dauke kallonsa daga kanta. Dole ta koma baya ta zauna a hankali saboda wata kasala daya sake mata,kanta ta dan dafe kadan tana ayyana "Mugu" cikin ranta. Da shigen kallon yake punishing dinsu a gida tun yana yaa maina,dan makaranta,yaa maina me shekarun da basu rufa talatin ba. Dauke hannun tayi da sauri sanda ta tuna yana dai falon,batason ya karanci lagonta,saidai still ta sake kamashi yana mata wannan mayen kallon nasa. Wanann karon bata bari ya riqeta ba ta janye dubanta da sauri, murmushi ya kubce masa wanda iyakarsa saman labbansa "Inda kin isa ki tsaya mana kici gaba da kallon nawa ki gani idan ban saki kin magantu a gaban kowa ba" ya fadi daga can qasar zuciyarsa. Yasan dukkan wani salo ko lago da zai iya kamata red handed ta kowanne fanni da yake da buqata,to amma kuma yana daga mata qafa ne saboda yanason ya dafata yadda ya kamata. A sace take kallon kowa dake falon,ba wanda ya lura da abinda yakeyi din,wannan ya sanya taja numfashi da kyau ta furta sannan ta miqe tana zare glass din idanunta. Idan ma yazo ne don ya hanata sakewa itakam ba zata lamunci haka ba,don itama bata shiga rayuwarsa ba na meye xai shiga tata. Cikin mintuna gurin ya dauki saiti yadda ya kamata,'yan abubuwan da ayeesha ta tsara saboda yara a wajen qananun games dukka akayi aka gama,sai aka fara karban gift,sai a sannan ya fidda wayarsa yayi kira duka duka da baikai na second biyar ba. Ba jimawa akayi knocking,da kanshi ya miqe ya bude. Ma'aikata ne na wani kamfanin sarrafa kayan qarau da kayan yara sanye da rigunan wajen aikinsun suka fara shigowa da kwalaye suna jerawa,a sannu a sannu saiga kwalaye sun kusa guda ashirin suka kammala suka juya suka fice. Ama na daga zaune tana kallo komai amma batace komai din ba,kuma bata motsa ba,ya juyo suka hada idanu da ita saita kau da kai,batason yaci gaba da karya mata da kuma tsinka mata zuciya,soyayyar yaran da take gani cikin idanunsu har kamar ma taso tafi qarfin kalar soyayyar da su suka gwada masa sanda yana yaro. "voici un cadeau de papa(ga kyauta daga baba)" ya fadi yana duban yaran. Sai da suka kalli ama sanna suka kalleshi,kaman hadin baki suka rungumeshi dukka su biyun suna fadin "Merci papa" tattaresu yayi cikin jikinsa yana sauke boyayyara ajiyar zuciya,bayajin duk duniya akwai me iya fahimtar yadda yake son yaran. Tsbaar zumudi sai suka kasa jira,dukka aka tattaru wajen bude kwalayen. Sutturu ne kala kala daga manyan kamfanin kaya na duniya dake samar da kayan yara designers masu quality da tsada. Kamfanin da ama din kawai ta gani ya sanya ta jinijina abun,ita din uwace me fahimtar yaren d'a koda bada harshen dake furta kalma yayi maganar ba. Ita din 'yar kasuwa ce da kusan kowanne kaya ta gani tasan a wanne aji yake,ko ba tare sukayi siyayyan ba amma ta sani kudade ya kashewa yaran masu ciwo. Kowanne kwali da abinda ya qunsa,na sutturu takalma kayan kitso agoguna da sauransu kowanne kwali goma goma benazeer din da batoul. A nutse ta dan juya idanunta tana satar kallon sultana,a guri daya take zaune sam bata cikin sahun masu kallon gift din. "Sultana" ama ta kira sunanta,ta dauke idanunta daga wayarta da take latsawa tana duban ama din "Na'am ama" gauraya idanunsu sukayi waje daya,haka kawai sultana din taji nauyi yadan kamata "Ki duba kitchen an kawo order na abinda za'a ci,ki dinga shirya komai yadda za'a iya dauka ayeesha ta tayaki fitowa dasu,kallon gift dinnan bazaiyiwu a gamashi a lokaci qanqani haka ba" "Okay" ta amsawa ama din tana qoqarin ajjiye wayarta. Duk da dukka kalamanta cikin gajerun furuci ne amma hakan bai hanashi hango kyawun labbanta ba,kwadayinsu ya kamashi har sai daya hadiye yawu a bakinsa a hankali. Ta fara wucewa zuwa kitchen,yadda tayin yasan hali,zai wuya ta basu gift din daya cika mata bayan mota dashi. Murmushi ya saki a boye,idan tasan wata batasan wata ba ai. Duqawa yayi a nutse daidai saitin kunnen benazeer ya gaya mata wani abu,ta daga kai da sauri tana fidda idanu waje "Good daddy....." Bata qara minti daya bama ta daga murya duk da slow music din dake falon amma saida sautinta ya fito saboda zazzaqar murya gareta "Mummy...... Ina gift namu?" Cak ta tsaya sannan ta waiwayo tana bakin qoqarin hana idanunta kallon fuskarsa,don tasan saitin bigiren da yake tsaye,ta fidda fararen idanunta waje da kyau tana duban benazeer yayin da takejin idanunsa na yawo saman fuskarta amma ta share "wanne gift?" Ta tambayi yarinyar tana kallonsu duka ita da batoul da suka zuba mata idanu,kai ta karyar "Ki tuna dai mummy.....na dazu fa.....daddy yace kin saya mana da yawa" dole a sanann ta kalleshin ba don taso ba. Kwata kwata kaman baya wajen ma,don ya maida dukka hankalinsa akan wayarsa ne kaman baiji me benazeer ma ta fada ba. Kafeshi tayi da kallo waiko zayaji a jikinsa ya daga kanshi,amma sai taga ma ya sake gyara zamansa yana bawa wayar hankalinsa. Duk qiftawar idanunta a kanshi yana ji a jikinsa,saidai ya basar din kaman baisan me yake faruwa ba,saima ya fara sakin qaramin murmushi still fuskarsa nakan wayar. Haka kawai taji ranta yadan sosu,tayi imani ba yadda za'a yi ta kalleshi jar hakan baiji a jikinsa ba,yana daya daga cikun abinda ta haddace sanda suna 'ya'yan bibi,tana tashen jin takai matsayin sultana,yana jin hakai aliyyu haidar dinsa. Yasha cewa saiya tsone mata idanu,don a sannan tana da dabi'ar tsureshi da kallo a duk sanda tayi laifi "Dauken wadannan idanun magen naki a gun!" Saboda tsaban yadda yake damunta da fadin hakan sai da takai duk magen data gani saita tsaya ta qarema idanunta kallo,tanason taga wanne irin idanu ne da ita haka da yake goranta mata dasu,wannan ya sanya itama ya baida qaimi wajen kiransa da "Me idanun zakuna" tun baisan tana fadi ba har sunan yazo kunnenshi,a ranar tasha horo sosai,amma maimakon ta daina saima ta sake maida kai wajen kiranshi da hakan,sunan da duk gidan ita daya ke fadinsa. "Laila" sunan ya fado mata a rai,taja qaramin tsaki zuciyarta na raya mata qilan dasu yake chart "Sai me?" Ta tambayi kanta,shi yaga zaya iya "Amma yana cikin yaranshi suna hidima me muhimmanci a wajensu?" Wani sashe na zuciyarta ya furta. Ranta ta sakejin ya quntata da taga yana gyara Bluetooth din kunnensa da alama kiran waya ne ya shigo masa "Ta yiwu ayana ko laila ce" can wani bangare na zuciyarta ya sake fadi "Sai meye ne?" Ta sake gayawa kanta a tsawacen da sai da taja numfashi ta daidaita kanta. "Bansan suna ciki ba.....idan na gama abinda nakeyi na baku key kuje ku dauka" ta fada tana juyawa ranta na mata wani zafin da batasan dalili ba tana wucewa hanyar kitchen din. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 95 Boyayyan murmushi ya saki yana satan kallonta ta qasan idanunsa,salon kallon da duk qwqwarka ba zaka taba zaton ita din yake kalla ba,yadan cije lips dinsa na qasa sannan ya buda muryarsa cikin qasaitar nan tasa data jima bata jita ba ya kira sunanta "Sulthana" har inda take sautin ya isketa,ya riski kunnenta da wani irin amo daya sanya tsigar jikinta tashi,duk yadda taso ta qaryata kunnuwanta dake jin zaqin sunan a bakinsa amma hakan ya kasa gamsar da zuciyarta. Kamar kada ta tsaya ko kuma kada ta juyo,to amma cikin jikinta tana ji ama tana ankare da komai,don haka ya tsaya sannan ta juyo tana dauke fararen idanunta daga kanshi "take the keys and bring them the gifts" ya fadi da muryar bada umarni nakai tsaye muryarsa a dake da wani irin deepness me tsayawa a zuciyar wanda ake bawa saqo. Idanunta dake da yalwar eyelash ta lumshe sannan kuma ta budesu,abinda yayi matuqar yi masa kyau,sai suka zama tamkar wani ado na musamman saman fuskarta,ya janye dubansa daga gareta yana sake hade rai,hade ran daya fidda ainihin miskilancinsa da ta sanshi dashi na asali. Juyawa tayi tana guna guni cikin ranta ta nufi dakinta. Saman bedside drawer ta dauko key din,har ta isa qofa ta fasa,ta dawo da baya saboda tuna wani abu da tayi,ta bude Wardrobe dinta ta fidda mayafi medium dake da kauri ta lulluba saman kanta. Sosai mayafin ya sake qara mata kwarjini,ya kuma cikasa kwalliyata,ta fita sosai da kamanninta. Tana takowa waje tana wara maqullan tana laluba na motar,har yanzun mita takeyi qasan ranta. A saman idanunsa ta fito daga dakin,ya saki wata siririyar ajiyar zuciya,mayafin data sanya din ya masa dadi sosai,bai tsammaci zata saka din ba,sai gashi ta rufe jikinta yadda ya kamata. Ratasu tayi a nutse har ta fice daga falon,ta maida qofar ta sakayata. Numfashi ya kuma ajewa,sai kuma yayi saurin daidaita kansa don ya tuna a inda yake,ya dan juya sashen ama,basu hada idanu ba amma kuma yaga sanda take maida dubanta wani guri na daban. Haka kawai jikinsa ya bashi duk abinda yakeyi din ta ganshi,sai ya danji nauyi ya kamashi,don haka ya miqe,idan ya fita waje tamkar ya bita ne,don haka kawai sau ya wuce kitchen yana cewa "Bari na samo ruwa" batace masa komai ba don nunawa tayi ma kaman bata ganshi ba,ya miqe zuwa kitchen din yana dan shafa sumarsa kunya na tabashi. Tana tsaka da mitarta sanda take bude motar taji muryarsa. Goumar ne,ta juya tana kallonsa,da alama a gurguje yake saboda yadda yake tafiyan da sassarfa "Mommyn twins me za'a dauko mana ne?" Ya furta cikin tsokana. Harara ta watsa masa sannan ta juya tana jefa masa key "Sarkin bin qwaqwqwafi......ka bude boot ka tayani mu kwashe kayan ciki" "Angama matar babban yaaya" ya kirata da sunan daya jima bai kirata din ba. Tayi tsammanin zataji zafin nan da takeji cikin zuciyarta a baya idan ya kirata da wannan sunan,ta dauka zataji qunci a zuciyarta kaman yadda takeji a wancan lokacin,sabanin hakan bataji wannan ba,saidai taji kaman furucinsa ya taba zuciyarta,ta jefa masa harara tana cewa "Wallahi yaa goumar ka bini a hankali,idan ba haka ba har najma ka shafa mata wallahi" "Tuba mukeyi kar a hadamu da babban yaaya" ya fadi yana qyalqyalewa da dariya. Shine ya taimaka mata tana fiddo kayan yana kwashewa har suka kammala tas. Kafin ta isa falon benazeer da batoul sun cikashi da karadin murna. Yau mummynsu ta basu gifts din da bata taba basu irinsu ba. Da gudu suka qaraso sanda take shigowa,suka rungumeta da kyau kaman yadda suka yiwa maina "Mommy mun gode,thank you,thank you" yadda suka rungumeta din suna murna sai taji wani abu me sanyi yana sauka qasan zuciyarta,ta miqa hannunta ta dora a hankali saman sassalkan gashinsu da yasha gyara "Allah yayi muku albarka" ta samu kanta da furtawa zuciyarta tana motsawa. Ajiyar zuciya ama ta sauke tana jin wani alfahari da iyalan nata yana kamata,tayi qas da kanta tana yawaita addu'a cikin zuciyarta a kansu gaba daya "Mummyn twins ina tunanin saidai ki fiddo abincin nan,idan nabar yaran nan a wajen nan barna zasuyi mana" ayeesha dake tsakiyar yaran ta fadi. Juyawa sultana tayi,sai tadan saki murmushi tana gyadawa ayeesha kai ta wuce zuwa kitchen din. Yana saman freezer dake daga bakin qofa,duk me shigowa babu lallai ya lura dashi, musamman idan hankalinsa bai wajen. Apple ce a hannunsa yake gutsira a hankali yana jefa qafafunsa tamkar qaramin yaro, nishadi yakeji sosai har cikin ransa. Fes ya ganta lokacin data shigo din,amma sai yayi biris ya kuma sake rage motsinsa don kada ta ankara dashi a wajen. Idanunshi a kanta sanda ta zare mayafinta ta ajjiye, murmushi ya kufce masa jin tana qananun mitoci "Yanzu zanyi maganinta" ya fadi cikin ransa yana ajjiye apple din a gefen freezer din sannan ya sauka daga saman nashi a hankali ba tare da sautin takun sawayensa ya fita ba saboda socks ne a qafarsa. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 96 Cikin nutsuwa ya tsaya dab da bayanta,ya zura hannunsa saman ruwan cikinta ya jawota jikinsa sosai ya adanata tsakiyar qirjinsa,don dukka tsahonta bata wuce tsakiyar qirjin nasa ba,wannan ya bata damar samun kyakkyawan masauki cikin jikinsa. A ba zata abun yazo mata,saidai kafin takai ga cewa komai ya Sanya hannu ya juyo da fuskarta gefensa yana fadin "Yarinyar nan har yanzu na fahimci sai a hankali,akwai sauran ladabtarwata......." "Wai baka da wani punishment sai ta haka?" Ta fadi da sauri tana katsar numfashinsa,muryarta na nuna zallar tsorota da tayi. Dole siririyar dariya ta kubce masa,a karon farko tsoro ya bayyana muraran cikin muryarta,wannan shine abinda yakeson gani,wannan shine abinda yakeson fahimta dama tattare da ita "Ashe da gaske horo na yana isa inda ya kamata yaje kenan" ya furta hakan yana dora hannunsa saman dogon dokin wuyanta,sai ya fara neman hanya yana zarcewa qirjinta. Numfashinta yaso daukewa jin har ya fara isa samansu,tayi caraf ta saka hannu ta riqe hannayen nasa tana cewa "Ni ba tsoron......" "Ba tsoron abun kikeyi ba?" Ya qarashe mata yana sanya hannunsa ya juyo da ita gaba daya suka koma suna fuskantar juna. Musayar numfashi suka shiga yi,idanunsu sarqe dana juna,ya sanya hannu yana jawota qugunta cikin jikinsa sosai yana cewa "Tunda ke jaruma ce a sake gwadawa mana........" Kai ta fara girgizawa tana dunqule hannunta saman qirjinsa "Ni......niwai......" Ta fara magana cikin in ina,don maganar Allah ta sani,shi din ba kanwar lasa bane,duk da zuwa yanzun tana jin wani irin sauyi itama,saidai ba zata iya bari ya fahimta komai daga gareta ba,don babu babban abun kunyar da yafi wannan. Sanda hankalinta yake neman yin wani gefen yayi amfani da wannan damar ya zame hannun nasa,bata ankara ba ta tsinci lallausan tafin hannun nasa a tsakiyar dukiyar fulanin nata. Abun yazo mata a bazata don haka ta dan zabura,bata kuma shirya ba ta fada jikinsa gaba daya tana qanqameshi sosai wai ko zata samu ya saketa. Ajiyar zuciya ta kubce masa,shi hakan data masa ya masa dadi sosai,sai kawai ya tayata qanqamewa cikin faffadan qirjinnasa dake fidda sassanyan qamshin turare da wani irin dumi da nutsuwa ta musamman. "Na maimaita miki ko mutuwa tana tsoron idon mahaifi......ki sassauta min ko don ama....ko kina zaton bata sona ne?" Ya jefa mata tambayar yana yamutsata da kyau. Ba tare data shirya ba ta saki wani zazzafan hucin da siririyar qara,abinda ya qara masa shauqi kenan,ya saki murmushi qasan ransa yana fadin "Daya kenan" "Ka sakeni please,kada wani ya shigo kasan dai gurine na jama'a" "If not fa?" "Zan kwarara maka ihu" ta fadi "Ihu?,wow......abinda sai bada citta..... bismillah mana,kinga daga nan kin ragemin nauyin wahalar yiwa mutane bayanin ina qaunar matata......ina sha'awarta...... inason kasancewa da ita.......ina buqatar........" "Enough please....." Ta fada da wani irin tune saboda bala'in da yake kunna mata cikin jikinta,ga kuma qarin kalamansa da suke matuqar mata nauyi. "noooo please"shima ya fadi da narkakkiyar murya cikin salon kwaikwayon muryarta yana sake matsata da kyau sake da sanyata cikin jikinta kamar me tsoron wani zai qwaceta daga gareshi. Kansa ya soma qoqarin cusawa a tsakanin dukiyar fulanin nata,ba shiri ta riqe kanshi da kyau,tanason roqonsa amma labbanta dake rawa sunqi bata wannan hadin kan. Motsin tahowar da akeyi zuwa cikin kitchen din shine ya ceceta,ya saketa da hanzari yayi taku biyu baya yana qoqarin daidaita mode dinsa,yayin da itama ta taka gaban sink tana qoqarin daidaita numfashinta gami da gyara zaman rigar jikinta. Dai dai sannnan ama ta qarasa shigowa kitchen din tana fadin "Anya sultana?,meye ya tsaidaki haka?" Tayi maganar idanunta akan sultana dake qoqarin bude famfo jikin sink din. Dan tsaiwa ama tayi tana kallonta,yadda hannayenta suke rawa sai abun ya bata mamaki. A hankali kuma ta waiwaya bangaren hannun damanta saboda qamshin turarensa data shaqa. Suna hada idanu sai ya juya yana yana shafa sumar kanshi a hankali,sai kuma ya taka a hankali yabi ta gefen ama din yana fita daga kitchen din. Batace komai ba ko bayan ya fita din,saita dubi Sultanan "Kiyi qoqari ki fiddo abincin don lokacin tashi ya kusa" "Tohm" ta amsa muryarta a shaqe ba tare data yarda ta juya sun hada ido da ama din ba,itama saita dauki ruwa kawai tana fita daga kitchen din ba tare da tabi ba'asin komai, jikinta dai ya bata akwai wata a qasa. Da qyar ta samu ta saita kanta ta fara fita da abincin,saidai duk fitar da zatayi bata taba yadda su hada ido da ama,hasalima ko maina rin taqi duban sashen da yake,tasan dai kawai zai ja Mata zargine a zuciyar aman,duk abubuwa da yakeyi din a waje basu isheshi ba,a cikin gida ma sai ya biyota yayi?. Qwafa taja kadan, cikin ranta tana raya cewa zata yiwa tufkar hanci. A matuqar gajiye ta isa dakinta don fiye da rabin gift da suka samu sai da suka budesu,don qememe suka hanata tafiya ta kwanta abinda taso tayi kenan,don tana sanya ran tashi da wuri ta fece wajen aiki kafin yakai ga iskota. Tun ba'a tashi daga party din ba ta nemeshi ta rasa shi da goumar, batasan Ina sukaje ba,hakanan sai tayi dabarar qin xama a falon a bude gifts din gudun kada yaje ya dawo ya taras da ita,so batasan ya dawo ba ko bai dawo ba. Ruwa me zafi ta hada tayi wanka kawai,ta hada kayan da zata fita dasu goben waje daya sannan ta isa bakin qofa,key din jikin qofar da tunda tazo gidan bata taba amfani dashi ba ta murza ta rufe qofan,wannan shi daya zai bata nutsuwa,tunda dai batasan ta yadda yake shigowa dakin ba,to ta tabbatar kodai aljanine shi bazai iya buda qofan ba,hankalinta kwance ta kashe wutar dakin tabi lafiyar gado tana karanto addu'o'in bacci. A nutse ta gama ta hura saman tafin hannunta tabi kowanne sashe na jikinta da ita,taja duvet ta shige ciki tana lumshe fararen idanunta. A hankali komai da ya faru wunin yau ya soma dawo mata kwanya,duk kuwa da cewa muradin bacci take dashi amma sai taji idanunta suna neman qeqashewa. A hankali komai komai daya wakana cikin office din ya fara dawo mata sabo,ta qanqame jikinta duk a yunqurin hanawa kanta jin abinda take ji din. "Wai meye hakan?" Ta tambayi kanta da kanta,bata taba sanin wannan abun zai taba dadata da qasa ko da sau daya ba a duniya,duba da irin wahalar data gamu da ita a karo na farko na faruwar abun cikin rayuwarta. Bude idanunta tayi da sauri waiko zata daina ganin abinda take gani din cikin duhuwar idanunta,nan ma dai baby wani sauqi sai a wajen Allah,ta kira sunan Allah zuciyarta tana karyewa,kada dai ace ya goga mata cutar addiction da abinda tasan temporary ne,tana dan da daukan mataki akan hakan?. Daidai lokacin da yake tsaye cikin balcony din gidan nasa dake facing gidan ama. Idanunsa tar akan gidan,yana tuna tunda yazo qasar bai bari aba yasan da zamansa a cikinta ba bare maqotakar dake tsakaninsu,kuma ya tabbatar zaiyi wuya ace ama ya gaya masa. Idanunsa ya sake kaiwa kan wayarsa daketa burari kira wani yana bin wani,sai ya dauke kansa daga kan wayar yana maidawa kan mug din hannunsa ya zuqe ragowar madarar dake ciki yana shimfide idanunsa akan window din dakinta. Yanayin rashin wadataccen haske daga window din dake da alaqa da dakin ya tabbatar masa ta kwanta koma ta jima da yin bacci,cikin kowanne gaba na jikinsa yakejin kewarta,yana jin shauqi izuwa gareta, xayaso yaje yayi mata kyakkyawan good night,amma koda ya duba agogo sai yaga ya kamata ya barta ta huta,ya tabbatar yau din ta sha zirga zirga,dole ya danne zuciyarsa,ya saki ajiyar zuciya ya sanya hannunsa yana debe wayoyinsa tare da kashesu gaba daya,don ya gaji da jarabar kiran yaran su biyun,kowacce cikinsu akwai albarkacin da take ci yake dage mata qafa. *********Da qyar ta tashi tayi sallar asuba saboda yadda takejin gajiya a sassan jikinta da kuma rashin samun wadataccen baccin da batayi ba a daren jiya,a daddafe tayi sallar asuba,bacci yanason dibanta amma ta gana hakan faruwa saboda plan din d atake dashi na kubce masa da kuma hanashi yi mata karantsaye a aikinta,ta hada ruwa me dumi sosai ta deba kayan wankanta ta wuce toilet. Karfe bakwai ta gama shiryawa cikin dubai abaya dake da zip yun daga samanta har qasa,da iya mayafin abayar kawai amfani tayi rolling bayan ta nade gashinta dukka ta cikin dankwalin da ribbon me fadi,da hand bag dinta da takalminta me dan tsinin dunduniya dukka na kamfanin gucci ne masu asalin tsada da tsari,yau kam tayi amfani da sun glasses daya sake maidata balarabiya sak,bata tsaya saka tarkacen kayan qawa da yawa ba banda dan earrings me wani irin dutse mai daukan idanu da kuma agogon data daurawa tsintsiyar hannunta na kamfanin Rolex. Dimple dressing tayi amma kuma yayi matuqar karbarta,ta fito da wani irin sassanyan kyau. A nutse take taku har ta fito falon,ga mamakinta sai ta samu benazeer da batoul da kuma tanja suna ci gaba da qarasa aikin jiya "Tanja biye musu kikayi?,ke din da kika sha hanya ba zasu barki ki kwanta ki huta ba?" Murmushi tanja ta saki "Aikinsu ai shine nawa,har kin fito haka yau da wirwuri?,gashi ko karin safe ban gama ba" "Ba komai tanja,idan ama ta farka kice mata na wuce,zanyi break a office" ta bawa tanja sallahu tana amsa gaisuwar yaran sannan kai tsaye ta wuce zuwa waje _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 97 Akan qofar gidan idanunta suka fara sauka,saita dauke kai tana dan tabe baki,yau kam taga ta yadda zaiyi mata karan tsaye,ta riga ta kufce masa,zuwa aiki kam babu fashi. Sanda motar ta saitu saman hanya saita saki ajiyar zuciya,tana jin cewa lallai tayi escaping. Hannu ta miqa ta kunna gidan radion qasa dake paris,tana da sha'awar sauran labaran duniya sosai,wannan yana daya daga cikin abinda ya motsa mata sha'awar aikin jarida a baya. Cikin qwarewa sa tataccen harshen faransanci aka soma watso labaran,tana biye dasu yayin data raba hankalinta akan titi,har zuwa sanda ta sanya signal ta fada saman doguwar hanyar. Tana sake nisa cikin hanyar tana tuna abinda ya faru jiyan. Murmushi ys qwace mata sanda tazo dai dai inda abun ya faru. Can wani saqo na zuciyarta yana cika da mamaki,duk sanda yayi wani abu saita dinga jin kamar ba ya maina ba,ya maina dai wanda ko dariyarsa ke musu wahalar gani,me azabar bada punishment dinnan wanda bashi da sasaauci ko sauqi ko kadan,wacce KADDARA CE ta gauraya rayuwarsu haka waje daya?. A yau din karon farko kawai taji tana yiwa kanta wannan tambayar. Kawar da zancan tayi daga ranta,tana sake maida hankalinta ga titi sanda take dab da fadawa Street na tv station din. A nutse ta ajjiye motarta,ta zagayo tana daukan jakanta. Harabar maaikatar tasu babu wadatar zirga zirgar jama'a sosai saboda zuwan wurin da tayi,ita kanta yau tasan tayi sammako,ta kalli agogonta sanda take tafiya cikin nutsatstsen takunta dinnan ga hanyar da zata sadata da floor din da office dinta yake. Kafin ta qarasa ta hadu da ma'aikatan da sukayi shigowar wuri irinta,dole ta dorawa fuskarta murmushi kaman yadda ama tayi mata Elevator ne ya ajjiyeta,ta fito tana takawa a nutse hadi da qoqarin fidda wayarta. Yasmine ce,ta saki siririn murmushi,itakam ko kudin da ake janye mata na kira sam bata ji,koda yake yanzun ta zama 'yar kasuwa sosai yanzun. Sanda ta daga da muryar bibi taci karo,murmushinta ya sake qaruwa,har yanzu tana son bibinta,tana ji da ita,bata kuma taba manta gatan data gwada mata,duk da ya zame mata matsala,ya kuma so ya zama silar samun tasgaro ga rayuwarta,amma da yake tayi komai ne da kyakkyawan nufi bawai don rayuwartata ta samu damuwa ba sai gashi komai yazo cikin sauqi. Tana tafiya a lobby din zuwa office din nata tana waya da bibi,jifa jifa suna gaisawa sa staff's din da suke cin karo dasu,har takai bakin office din,ta fidda card na bude qofan ya karashi jikin qofar,ya bada sauti na alamun tsaro ya bude kansa,ta murza handle din tana tura qofar gami da fadin "Karki bata bibi,sai na zauna sosai cikin office na zama comfortable sannan zan kirata" "To ya rage ya naku,ungo ni" bibi ta fadi tana miqawa Yasmine wayar,jin hakan ya sanya sultana qit ta kashe kiran tana dariya,don ta san qarshen zancan,qorafi ne kawai yasmine din zata cikata da shi. Tsaf murmushin dake saman fuskarta ya dauke saboda abinda idanunta suka gani. Maina ne,aliyyu haidar,yana zaune tsaf abinsa saman kujerarta ta office,yayi relax sosai abinsa,ya zare eye glasses dinsa key da wayarsa duka suna saman table din,daga gefe kuma madaidaicin tray ne dauke da wasu qananun bowls da butar shayi. Yayi wani masifaffen kyau cikin tsadaddar suit din jikinsa da aka saqata da zare da auduga me daraja. A nutse kuma tsaf ya watsa mata lion eyes dinnan nasa da ayau ta gansu sun rusuna qwarai fiye da kullum "Come in" ya furta calmly yana tsareta da idanunshi da suke shigar mata da wani magnet me qarfi cikin jikinta. Tayi tsaye ne kawai cike da mamaki,ita bata shiga ba kuma ita bata fita ba. Wai ta yaya yake samun access da komai nata?,bayan tayi imanin bashi da wani mabudi nata?,yaushe ya shigo?,yaushe ma ya taho gaba daya?,ya akayi yasan da wannan plan din nata bayan duk duniya daga ita sai zuciyarta suka yanke wannan shawarar?. Bataga tahowarsa ba sai isowarsa bakin qofar,dav da ita ya tsaya idanunsa cikin nata,hancinta ya shaqi qamshinsa da kyau daya ratsa ta qwaqwalwarta ya sauka a zuciyarta. Tamkar zai gogo jikinta ya fidda hannunsa guda daya daga aljihun wandonsa ya maida qofar ya rufe still dai bai zare idanunsa daga nata ba. Sosai ya tsaya a gabanta,irin tsaiwar da idan yayi kyakkyawan motsi zai iya hade tazarar dake tsakaninsu. Tsaiwarsa a gabanta ya qara masa mugun kwarjini cikin idanunta,irin kwarjinin data jima bataji irinsa ba,ya tokare mata ko ina da tsahonnan nasa, hakanan ya hana qwayar idanunta sukuni ko motsin kirki kwata kwata "Kina mamaki ne?" Ya jefa mata tambayar kai tsaye da muryarsan nan me ratsa kunnuwa "Kin manta wannan din uncle maina ne?,wanda ya raineki da wadannan hannayen....." Yayi furucin yana daga mata hannunsa qwaya daya bayan ya zaroshi daga aljihunsa. "........yadda maina ya sanki yasan halinki bana tunanin kin san kanki haka,yasan me zaki aikata da abinda ha zaki aikata ba..... fuskanki kawai tana iya bani labarin abinda yake cikin qirjinki da zuciyarki......" Ya furta yana hade gap din dake tsakaninsu. "Kada ki tsorata.......ba wani abu zaki bani ba......bacci kawai nazo ki tayani......jiya ban samu isashen bacci ba" ya furta yana sabule jakar kafadarta ya ajeta a gefe. Sake miqa hannu yayi ya zare pin din data maqale rolling din kanta dashi,a hankali mayafin ya soma ware kanshi da kanshi,ya riqe hannayenta cikin nasa wannan ya sanya bata da damar tsaidashi har ya gama ware kansa ya zame ya fadi qasa. Baqar lallausar sumarta da tasha mayuka da gyara ta bayyana,kyakkyawar fuskarta ta fito tarwai,sai ya sakar mata hannu daya ya miqa hannun masa guda dayan ya soma zuge zip din gaban abayar tata. Hannu dayan da ya sakar mata ta saka ta riqe hannunsa tsam adan razane,muddin yaci gaba da zuge zip din to ba makawa komai nata zai bayyana ne, don bata sanya vest ba ganin rigar me kauri ce, underwear ne kawai a jikinta. Da idanunta da suka qara laushi ya kalleta, muryarsa a dan sarqe yace "No" yana girgiza mata kai,sai ya shammaceta ya zuge zip din gar zuwa gwiwarta. Dukka numfashinsa yaso yayi qaura,farar bra din jikinta zuwa farin underwear dinta sun sauka sun xauna kuma dai dai saman farar lallausar fatarta da a kullum take cikin gyara da kulawa. Albarkatun qirjinta dukka suka tsone masa idanu,ya kasa janye dubansa daga kansu,cikin wani irin zafin nama ya jawota zuwa jikin nasa numfashinsa yana kai komo. Kyakkyawar runguma yayi mata,ya miqa hannu yana ware band din kanta,hakan ya bawa sumar kanta damar bajewa saman kansu shi da ita gaba daya. Cusa kansa yayi tsakanin wuyanta,da muryar rada yace mata "Karkiyimin gardama please,i want a peace please,am sleepy" daga haka bai barta ta qara sukuni ba ya dauketa cak ya nufi sofa da ita rigar da mayafin da takalminta dukka suka zame a wajen. Sosai ya kwanta saman cinyarta hankalinsa kwance bayan ya cire suit din jikinsa sai fara qal din vest dake jikinsa dake fidda lallausan qamshi,gaba daya yayi mata kane kane saman cinya tamkar yaro yaso rigima saman cinyar mamansa. Hankalinta gaba daya a rarrabe yake,yanzun idan akayi mata knocking fa?,wanne amsa zata basu?. Idan kuma tsautsayi yasa akayi tsammanin shurun da za'a ji bana lafiya bane akayi attempting shigowa fa?. "Don Allah...... nan din fa ba gida bane wajen aiki ne" "Ban gaya miki stay at home ba?,na baki izinin fitowa?......duk wanda ya miki knocking ki gaya masa kina tare da mijinki" yayi lafazin yana yin wani irin juyi,ya koma rub da ciki yana gyara kwanciyar kansa saman cinyarta tare da miqa hannunsa ya zagaye qugunta ta baya. Idanu ta sake fiddawa tana mamakin qarfin hali irin nasa,saidai kuma tana tsoron cewa wani abu,don gwara wanann punishment din nasa akan me gaba dayan. Bata gama wanann tunanin ba taji ya kamo hannunta ya dora tafin hannun nata saman tattausar sumarsa yana cewa "Bacci......bacci nakeyi mummyn twins" ya qarashe fada yana lumshe idanunsa yana jin yayi comfortable yadda ya kamata. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 98 Yadda yayi ruf da ciki saman cinyarta ya sanya take iya jin bugun zuciyarsa sosai. Bugawa takeyi fiye da kima,sai hakan ya zama tamkar wani Aiken saqo ne zuwa ga gangar jikikta gaba daya. Sannu a hankali taji bugun zuciyar tasa yana dai daita zuwa matakin da kowacce zuciya ke bugawa,a hankali taji numfashinsa yana fita a hankali,ya soma sauke numfashi da wani irin nutsuwa,saidai lokaci lokaci yana sauke ajiyar zuciya tamkar wanda yayi tsaren gudu,ga kuma qanqame qugunta da yayi sosai kamar zata bace masa. Nauyi da nutsuwar daya qara yi saman cinyoyinta ya tabbatar mata bacci ya daukeshi,hannuwanta dake saman tattausar sumarsa ta kalla,ta kasa janyesu,sai kallon yatsunta da suka nutse cikin sumar tasa takeyi. A hankali ta soma motsa yatsun nata suna sake nutsewa cikin sumar tasa,wani irin taushi da santsi take dashi. Sannu sannu yadda hannunta ke shigewa cikin sumar sai ya tuna mata da wasu shekaru can baya da suka shude,lokacin da yake daukanta saman wuyansa,ta riqe gashinsa da kyau tana dariya,duk da tasan akwai zafi amma baya nuna mata hakan,lokacin da yake kwanciya saman pillow tayita jagwalgwalata da sunan kitso zatayi masa,wani lokaci ta hanashi bacci har sai ya tashi,wani lokaci kuma yayi baccin dole da bai shirya ba. Wata ajiyar zuciya ce ta kufce mata,sai ta dauke hannuwan nata a hankali tana maida kanta saman makarin kujerar,duk jikinta ya mutu murus,babu wani sauran laka a jikinta itama,ya gama saukar mata da kasala me yawan gaske,gefe guda ga sammakon da tayi itama bayan kuma bata samu yin isashen bacci ba a daren jiya. Idanunta a lumshe taji vibration na wayarsa dake ajjiye dab da cinyarta kusa da kanshi. Bude idanun nata tayi a nutse tana kallon wayar.......sunan laila ne ya fito radau saman wayar. Batasan me yasa ba sai taji an motsa zuciyarta,ta zubawa sunan ido yanata yawo saman wayar,tanason ta dauke kai da idanunta amma ta kasa,wai wacece wannan laila din?,tanason sanin wacece,haka kawai takeso ta sani din,tanason taji muryarta koma wacece ita. Zuciyarta na gargadarta akan ta dauke kanta daga wayarsa amma ta kasa,haka ta miqa hannu ta dauki wayar daketa fidda qamshin tsumammen turarensa daya kama jikin komai da yake tu'ammali dashi. Tayi shipping ta daga kiran sannan ta sanya wayar a kunne, zuciyarta haka kurum na wani irin luguden duka "Helloooo dear...... good morning,ina hanya in sha Allah,bazan wuce awa daya ko biyu ba zan iso paris......amma champs elysees din ko zaka sa azo a daukeni please ko ka qaraso da kanka?" Ta qarasa maganar a shagwabe da kuma karyar da murya da alama tanason karya taurin kansa ne "Bacci yakeyi saman cinyata" ta samu kanta da fadi zuciyarta na mata zafi,ranta kuma yana raya mata abubuwa da dama. Dif laila tayi daga daya bangaren,dukka wutarta ta dauke daga bayyanar sautin muryar sultana dake bayyana zallar kamun kai da ajin dame muryar ta mallaka. Qarfin hali tayi ta tattara dukka dauriyarta gabanta yana faduwa tare da mamakin wacece wannan da zatace yaa haidar yana bacci saman cinyarta?,ba zata tana mummunan tunani a kansa ba,don ita kadai shaida ce akan tsarkin zuciyarsa,tsahon zamansu da shekarun da sukayi tare dashi ko kallon banza bai taba yi mata ba bare akai ga batun wani maganar banza "Ke din wacece?" Laila ta jefawa sultana tambayar. Tambayar saita zowa sultana da salon rainin hankali,ita din zata kalla tace wacece? "Idan ya tashi kina iya tambayarsa" ta amsa mata a taqaice,sannan ta saki siririn tsaki tana katse wayar?. Kasa aje wayar tayi ta dinga kallon number din,sai taji tana da sha'awar duba cikin wayar,to amma kuma ta riga ta shiga security wayan. To wacace wannan laila din?,zata iso paris nan da awa daya ko biyu?,it means kenan akwai wani boyayyar alaqa a tsakaninsu?,me zatazo tayi masa tana baligar mace yana baligin namiji tun daga wani waje?,a gidansa zai sauketa?. Tambayoyin dukka taji sun mata girma da yawa,ranta yana sake baci,ta motsa kadan tana leqa fuskarsa. Fayau take dauke da wani irin kwantaccen kyau,komai na fuskarshi na aje cikin tsari da baiwar iya halitta ta ubangiji. Mix take gani na kamannin batoul da benazeer saman fuskarsa,abinda duk tsahon shekarun bata taba gani ba sai yanzun. Kamar jira suke ya dawo rayuwansu dama,suna ta juyewa zuwa kamanninsa. "Ki rage fada please" taji ya fada qasa qasa kaman me mayen bacci "Ki maida wayan silent,ki kuma daina picking mini call" ya sake fada yana gyara kwanciyarsa sosai hankali kwance. Mamaki yadan kamata,kada dai ace yana sauraren abinda duk take fadi?,bai bata dama ta biyu ba ya saka hannu ya jawo hannunta sai gata gaba daya ta kifo saman kansa tayi masa rumfa "Sleep please......na sani kema baki samu cikakken bacci ba" ya hanata motsawa ya hanata sakat,haka taci gaba da yi masa rumfar,tun tana qananun tunanuka har idanunta suka soma mata nauyi,sannu a hankali bacci yayi awan gaba da ita. A haka suka shafe awa guda da rabi,gaba dayansu jikkunansu da numfashinsu sun gama gauraya da juna. Shine ya fara farkawa,ya bude idanunsa a hankali yana dubanta. Kyakkyawar fuskar rigimammiyar qanwarsan nan baby sultana,yau din ta zama madam sultana,duk wani sirrin kyau nata ya bayyana,irin kyawun da bai taba gani ba tsahon zamansa da ita. Hannu ya miqa saman lips dinta,yana da muradin taba bakin tsiwa. Cikin jikinta taji yanayin da take ciki ya sauya sosai,ta bude idanunta a hankali,sai kuma ta qarasa budesu da sauri,a lokaci guda kuma tayi wani irin hantsilawa a tsorace sai gata ta zauna sosai sama sofa din. Idanu take bubbudewa cike da mamaki,ita dake a zaune kanshi a saman cinyarta ya akayi ta koma a kwance,ta matse sosai cikin jikinsa saman doguwar sofa guda daya,wanda koda da yaro ka kwanta sai jikkunanku sun matsi na juna?. Yadda ya zauna calmly yana qarewa santala santalan hannayenta da dogon wuyanta kallo,yadda baqar sumarta me tsaho da santsi ta baje a sassan jikinta ta sake zama ado a tattare da ita ya tuna mata jikinta ba kaya,ba komai sai bra da underwear. Da azama ta cure waje daya tana kifa kanta saman cinyarta,itakam wannan wanne irin abun zub da mutunci yake jawo mata?. Siririn murmushi ya saki yana kada kai,duk da bai gaji da kallonta ba bazai kuma gaji din ba,amma dazun kafin ta farka daga bacci ya morewa idanunsa kallonta yadda ya kamata,ta kuma tayar masa da feelings dinsa qwarai,to amma bayason ya cika zaqe mata ko matsarta da yawa dashen da yake da niyyar yi cikin zuciyarta ya rasa kyakkyawan gurbi da muhallin da yake fata. Tsam ya miqe yana fadin "Tashi ki bani abinci......am starving" yayi maganar yana dosar toilet dinta. Ta tsakanin gashin kanta da ya lullubeta take satar kallonsa har ya shige toilet din,ta miqe da mugun hanzarin ta doshi bakin qofa ta rarumi abayanta ta maida,saita soma laluben key din office din bayan ta dauki handbag dinta. Sama da qasa ta rasa maqullin,sai a sannan zuciyarta ta soma raya mata ya boye ne,cak ta tsaya,tabbas xai aikata,tunda har yana iya gane komai saman fuskarta data shirya,kaman yadda yasan tsaf meye zata aikata da wanda ba zata iya yi ba. Dole ta koma saman kujerar ta zauna tana furzar da iska,saita daga kanta a nutse tana duban agogo _nan da awa daya ko biyu zan iso paris.....ko zaka qaraso da kanka ka daukeni please_ muryar laila ta fado mata a rai. Agogon ta jefawa harara ta janye idanunta tana jan tsaki. "Rashin kamun kan yayi yawa" ta fadi qasan ranta tana kuma jan qwafa,ta maida dubanta ga wayarsa kamar me jiran shigowar wani kiran. Can qasan zuciyarta kuma sai takejin babu me laifi sai shi,don meye?,don meye ya fito daga family na mutunci zai dinga jaye jaye?. Lumshe ido tayi abun yana tsaye mata a rai,yanason bata musu sunan family kenan? "Sunan family ko sunan 'ya'yanku?" Ta jiyo sautin tambayar data sanyata bude idanunta gaba daya tana neman amsarta. Sosai ya hakimce mata saman sofa din,ta dinga zirga zirgan debo abincin dake shirye cikin tray wanda batasan ma ya akayi ya samu shigowa office din ba,harda kuma wai abincin da ta tabbatar daga kitchen na station dinnasu aka kawo mishi. Ta qasan idanu yake qare mata kallo,bata da abun cewa sam bakinta ya kullu,to meye ma zata ce masa?,ya riga ya gama kulle mata baki,itakam zuwa yanzun ma tsoro yake bata,ta yadda duk yadda tayi qoqarin kaucema qaddarar haduwa dashi hakan bashi samuwa. Lallabawa takeyi ya fice gurin lafiya lau ba tare daya daura mata jinyar ciwon jiki ba(nace gulmammiya,anaso ana kaiwa kasuwa). "Koma ki zauna" ya fadi sanda ta ajjiye abincin a gabansa,yana zaune sosai saman dan center carpet dan madaidaici da aka qawata office din dashi. Dubansa tayi kaman zata saki kuka,to amma yadda yake dubanta ya sanyata zamewa ta zauna sosai a a gabansa. "Oya.....saka hannunki....", Ya bata umarni yana tattare dogon hannun shirt din suit dinsa,ya sanya nasa hannun cikin abincin ya fara kaiwa baki a nutse. Kasa motsawa tayi,cin abinci tare dashi cikin kwano daya wani tsohon al'ada ne data manta rabonta dashi,batajin zata iya sam,don haka taci gaba da duban kwanon sanda yake kai abincin cikinsa hankali kwance. Wani mugun nishadi ne ma yake saukar masa,duk sanda zasu kasance qarqashin inuwa daya kaman hakan,yakanji kaman ya tsaida lokaci ya hanashi motsi,abinda ya kasa bawa kansa amsa har yanzu shine,wai dama can wannan matsanancin son yakewa sultana?,ko kuma bayan faruwar wancan abun a wancan lokacinne mahaukaciyar soyayyarta ke yagalgalashi?. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 99 "idan kika bari na rigaki gama cin abincin nan.......dura zanyi miki" ya fadi yana kada yatsansa dan manuni. Itakam a yanzun ko meye yace zaiyi zai aikata ta sani,don haka ta rufawa kanta asiri ta matso,ta sanya hannu ta dauki spoon. Hannunsa ya miqa ya karbe yana fadin "Um um......yau da hannu zamuci,mu samu albarkaci junanmu" cikin ranta ta tabe baki "Wanne albarka mutumin da yake da side chics dinsa?" Ta fadi qasan ranta "Me kika ce?" Ya jefa mata tambayar yana tsareta da idanu "Ba komai" ta fadi qasa qasa tana tura baki gaba. Murmushi ya saki,lallai da gasken tsoro ya sanya ta fara gyara wasu abubuwan,ya sani akwai abinda tace,amma shakkar tasa ya saka ta kasa fadi masa a sarari,wanda inda ada ne ya tabbatar zata fadi mashi ne,ko meye zaiyi saidai yayi. Koda ya gama sai ya koma da baya yayi relaxing yana kallon taunarta,idanunsa can qasa,ba zaka taba kawowa ita din yake kallo ba. Wayarsa ya jawo sanda ta fara ringing,ya saki murmushi ganin sunan goumar,yana dagawa muryar benazeer da batoul ne ya soma masa sallama. A handsfree ya sanya wayar yana fitar da murmushi,muryarsu fes cike da doki da zumudin mahaifinsu. Hira suke masa sosai hayaniya hadi da shirmensu,ya sakankance sosai ya biye musu "Daddy munyi missing naka,uncle goumar yace mu tambaya zai kawo mu office dinka?" Tsaiwa tayi da hadiyar lomar tana kallonsa qirjinta nadan bugawa,ko kusa ko alama batasan kowa yasan suna tare,kowa dinma irin goumar?,ta tabbatar daga ranar ta kade daga ita har ganyenta,kai wala'alla ma bakinsa bazaiyi shuru ba saiya gayawa ama, itakam ai da ta kade,da wanne ido zata kalleta?. Shima din ita yake kalla,kuma salon kallon da yakeyi mata tamkar yana jefa mata tambayar na basu izinin zuwa?ne a fakaice. Rau rau tayi da idanunta tana tsame hannunta daga abincin,sai ya zame idanunsa yana cewa "No kuyi zamanku,nayi alqawari anjima kadan zamu kasance tare" ihun murna suka saki,yanata sakin lallausan murmushinnan nasa kafin daga bisani yace su bawa goumar wayar. Magana sukayi kadan sannan ya kashe wayar,ya miqe ya nufi inda suit dinsa take ya saka,ya maida takalminsa,yana daura agogonsa ya dubeta "Zaki wuce gida yanzun......daga yau kuma duk sanda kika sake fita bada izinina ba......" Sai bai qarasa ba ya maida kansa ga daura agogonsa. Afakaice ta harareshi,kaman yaji hakan cikin jikinsa sai ya waiwayo,saura kadan su hada idanu tayi hanzari dauke kanta ta maida ga agogon bangon office din nata. Lokacin yayi daidai da sanda yarinyar tace zata iso paris,hakanan taji wani abu ya tsaye mata a wuya.....lokacin tashinsu daga aiki da saura,don meye don zaije ya dauko wata can daban zai matsa mata tabar office yanzu?, bayan ya hana mata yin duk wani aiki,har yanzu program din da zata next week bata shirya komai game dashi ba,saboda ya hana mata sakat,ya hanata motsi,ya kuma hanata nutsuwar da zatayi aikinta. "Are you with me?" Ya tambayeta yana qoqarin daukan wayarsa. Wani tunani da yazo mata ya sanyata miqewa ba tare data kalleshi ba "Zanje na danyi submitting wani abu,bazan wuce minti biyu ba" ta fadi tana jin dacin yadda wai saita nema excuse a gurinsa kafin tama fita "Hope ba wajen namiji bane?" Tambayar ta quleta,sai taji kaman kada ta amsa masa,amma tana tsoron hukunci,don haka ta gyada masa kai kawai. Sai data tsaya tsaf ta maida komai nata inda yake sannan ya barta ta fita din. Qwafa taja bayan ta fita tana cewa "Ai idan kasan wata bakasan wata ba" office na qarshe a lobby din ta shiga,tasamu baturiyar matar cikin aiki kace kace,amma kasancewar suna girmamata saita tsaida komai ta saurareta. Dan qaramin hutu ta buqata a kwanakin,ta basu uzurin tanason ta shiryama next program sosai a gida,don mamanta ita zata taimaka mata da wasu research akan culture din da zasuyi magana akai. Ba wani damuwa ta tura request akan buqatarta,ta kuma bata dama a take ta rubuta letter ta tura,sukayi sallama ta fita a office din. Fes takejin ranta sanda ta baro office din,kome zaiyi daga nan zuwa gida ba zataji haushinsa ba,don tasan abinda ta shirya din shi daya zai mata maganinsa. Ko a cikin motar yaga ta saki fuskanta sosai,bata damu kaman yadda take damuwa wancan lokacin ba idan ya yanke zasu wuce gida tare a motarsa. Duk da hankalinta ya dauke daga kanshi,amma lokaci lokaci sai ta dinga duba agogon hannunta,abu daya ranta dai keci gaba da bata zayaje daukota,tanaso tayi tsaki amma tana gudun yinsa a sarari. Kama ko yaushe ya tsaya daga farkon street din nasu ya bude ya fito ya zagayo inda take zaune yana miqa mata key din "What do you want to me to do to you tonight?" Ya tambayeta yana dage masa girarsa guda daya hadi da kashe mata ido. Wani abu ya zubawa gangar jikinta,saboda tsananin kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,abinda take gani kuma a idanunsa yana son shallake yadda ta daukeshi "Ki gayyaceni mana yau dai daya da kanki please madam" ya sake fadi yana sassauta mata murya da salon dake narka zuciya. Saura kadan ya dauke mata numfashi da wani irin tsananin kunya da kuma nauyi daya saukar mata. Ya fahimci ne taji,don haka ya miqe daga durquson da yayi ta jikin window din yana watsa hannayensa gami da dage girarsa sama "I don't know what's wrong with me,am so addicted to you.....see you tonight" ya fadi da tataccen turancinsa tamkar baisan wani abu waishi yaren faransa ba. Takowanne bangare gwanine,Allah ya bashi baiwar harshe qwarai da kuma salon sarrafa kowanne harshe,idan France yakeyi zaka zaci shine kadai yaren da ya sani,hakanan idan ya juya English. "Tonight?" Ta maimaita kalmar bayan ta soma gangara motar sosai cikin layinsu. Kai ta gyada murmushin mugunta yana qwace mata "You will see tonight kuwa" ta sake fada qasa qasa. Hannayensa ya saki yana juyawa zuwa inda matashin ya aje masa motarsa kamar kullum. Daidai nan wayarsa ta dauki flute ringing me sanyi. Ranshi yadan hade kadan,sai kuma ya daga kiran yana sanyawa a kunnensa. "Almost over one hour ina jiranka yaa haidar.......bakasan na iso ba ko?" "Me yasa kika taho laila?,aunty din tana Paris dinne?" Ya tambayeta don baiga ta inda zai bari tayi masa masauki cikin gida ba. Ajiyar zuciya ta saki,har yanxu tana jin dacin maganar da matar data daga wayanshi dazu ta gaya mata,so amma yanzun ba muhallin da zata tambayeshi bane "Tacemin yau suna hanya in sha Allah,so ko zakamin alfarmar zama cikin gidanka na wasu awanni kafin su iso?" A yadda sautin nata ya fito ya nuna kaman wani abu ya sosa zuciyarta. Sardauna da daddy sune mutanen daya tuna,ya kuma tuna halacci da gudunmawar da suka taka a rayuwarsa "Ki tsaya a wajen,zanzo nayi picking naki" "Alright, thank you" ta fadi. Ya sauke wayar tausayinta yana dan kamashi,shi da ita dukka yana tunanin jirgi daya ne yayi jigilarsu,son maso wani da hausawa ke kira da qoshin wahala,ya juya a nutse ya koma matar yana tayar da ita idanunsa kan hanyar da sultana ta wuce. Daure da babban towel da kuma qarami ta fito daga toilet. Haka kawai tunda ta dawo gidan gaba daya hankalinta yana kansa,duk kuwa da cewa duka duka basu zarce awa biyu da rabuwa ba. Duk bayan wasu mintuna sai ta tuna da kiran LAILA. Sunan da ma yarinyar gaba daya sun tsaye mata a rai,tayi masifa tayi fada ita da zuciyarta dama ranta gaba daya kan shiga shirgin da bai shafeta ba amma abun yaqi barin zuciyarta. Tanata ture tunanin tana shirya kanta cikin wani sassanqan material,so take tayi keeping kanta busy yau sosai,tanason ta zauna cikinsu ama da yaran ta basu lokacinta,daga magrib zuwa ishai kuma tana sanya ran ta qarar dashi wajen binciken al'adun qabila daya cikin tarin qabilun Nigeria wato qabilar KANURI. Fes fuskarta ta fita ta tsakiyar turban cap data sanya fara qal,ta matsa jikin bed Side drawer dinta dake daura da window dinta,haka kawai sai taji sha'awar bude window din. A nutse ta miqa hannunta ta yaye labulen,ta kuma sake zura hannunta ta janye glass din. Fes ta cikin window din take hangar gidan,gidan da take da tabbacin cikinsa yake rayuwa. Tana qoqarin sakin labulen motarsa ta tsaya qofar gidan,sai ta samu kanta da gaza sauke hannun nata, idanunta tamkar wadanda aka yiwa majanyi suka bi qofofin motar da kallo,dai dai sanda shi da laila dukka suka fitowa daga cikin motar, suhail ya bude back seat shima ya fito. Da qasaitaccen takunsa yabar jikin motor din,ya haura zuwa qofar gidan ya saka key ya bude gidan,ya tura qofar sannan yaja da baya yana bata hanya. Takowa tayi cikin murmushi, zuciyarta yau din tana mata wani dadi,yau itace ya haidar din da kansa ya daukota daga airport?,bayan haka ma sai daya biya da ita wajen cin abinci taci abinci ya taho mata da takeaway wai don kada taji yunwa,zata iya mantawa da wannan ranar kuwa?. Anya ba nasara da sa'a bane ya kawota paris?,kodai da gaske hasashen da Sara tayi mata zai tabbata?,zata jarraba......tana fatan dacewa. Sanda ta saka kai gidan ya mara mata baya labulen ya subuce daga hannunta,tayi qas da kanta tana son gayawa kanta da kanta da sabganta bane,ba abinda ya dameta bane,ta soma qoqarin buda kwalin turaren amma sai ta fahimci hannuwanta rawa sukeyi,taja wani dogon tsaki a matuqar fusace,ta miqa hannu tana maida window din ta kullesu gam ba tare data sake bari idanunta sun kalli gidan ba "Bazan sake budeshi ba har mubar Paris" ta gayawa kanta da kanta a fusace tamkar wani ne yayi mata. Gagara bude turaren tayi don hannuwanta sai tajisu kamar an bugesu,cilli tayi da turaren saman gadon,saita koma saman madubinta ta fesa wanda ya samu kawai,ta dauki wayarta tana fita a dakin can qasan ranta tana qoqarin controlling kanta da kanta,don bataga abun damuwa ba a abinda ta gani,meye sha'aninta a ciki?. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 100 Fitowarta ta musu dadi sosai,suka sanyata a tsakiya da karadinsu da basa gajiya. Duk da shuru shurun batoul amma benazeer tanason koya mata surutu. Jinsu kawai takeyi,amma sai takejin hankalinta da tunaninta baya tare dasu. "Mummy yau kiyi mana kwalliya.......daddy yace zaizo mu fita dashi......me zamu siyo miki?" Batoul ta tambayi sultana tana kallon fuskarta. Dan kallon yarinyar tayi fuskarta tana tuna mata da tashi fuskar,yadda yayi bacci saman cinyoyinta dazu lakadan kaman bashi ba......amma kuma yanzun sai gashi yana shiga da wata macen cikin gidansa shi da wani. "Ba komai batoul" ta fadi tana shafa kan yarinyar zuciyarta tana karyewa. "Mummy to ki shirya muje tare dake mana?,.......ama don Allah ta bimu?" Ta maida tambayar ga ama dake a zaune waje daya,tana karantar sultana din a fakaice,cikin kwanakin tana fuskantar canje canje daga gareta,saidai har yanzun batakai gacin gano sauyin na menene ba "Na gaji ni bazan iya sake wani fita ba...... infact ma ina da aiki da zanyi na program dina......saikun dawo,tanja zata shiryaku" ta basu amsa tana miqewa don dab ake da shiga lokacin sallar. Dukansu suka bita da kallo,fuskokin yaran tayi rau rau da alama basuji dadin hakan ba,ama ta kira sunansu tana yafitosu da hannu,suka taso dukansu suka zauna gabanta,saita riqe hannayensu tana dubansu "Idan mummynku tace ba zatayi wani abu ba ku daina tursasata kunji?,tana fita aiki,kuma tana dawowa a gajiye,kunaso tayita ciwon jiki?" Kai suka girgiza a tare "Yauwa......yanzun ku yiwa uncle goumar waya ya dawo da wuri sai kuje tare" hakan data fada sai ya saka suka saki ransu,suka suri wayarta suna qoqarin gano lambarsa su kirashi din. Duk abinda ama din ta fada ma yaran akan kunnenta ne,don tsaye tayi jikin bakin qofarta. Gwiwoyinta sukayi sanyi,tausayinsu taji yanason kamata,ta daga qafafunta da qyar tana wucewa ciki,idanunta akan agogo. Tanaji a jikinta babu ma lallai ya tuna da yaran tunda wancan laila din tazo,duk zumudin fita dashi din da zasuyi tasan ba lallai ya tuna dasu ba. Ta sake maida idanunta tana kallon window din kamar zata iya hango cikin gidan,saidai kuma zuciyarta ta gargadarta kada ta soma budewa,don haka ta juya tana wucewa toilet don dauro alwala. Sanda ta fito sai tayi deciding ta kira yaran wajenta suyi sallah da azkar tare,wani sashen na zuciyarta yana gaya mata "Kinaso kiga baban nasu zaya fita dasu ne?,ko kina son gasgara zarginki?" Tsaki taja tana qaryata wannan hasashen na zuciyarta,sai ma ta fasa fita,ta dauki wayarta ta kira tanja tana tambayar yaran "Gasunan suna alwala zasu wajen ama suyi sallah" "Turomin su" "Tom" tanja ta amsa mata. Fasa shimfida qaramin abun sallarta tayi,ta sanya musu wadatacciyar dadduma,ta sanya ustazah dinta da ya fidda kyan fuskarta ta fuskanci gabas,daidai sannan suka shigo suma kowa sanye da wadataccen hijabi. Fuskokinsu kawai sun sanya zuciyarta yin sanyi,ta lumshe idanunta ta kuma budesu,ta qarasa saman dressing table dinta ta dauko tutarenta,ta matsa dab dasu ta feffesa musu duk kuwa da cewa ko yaushe cikin qamshin suke,don suna da personal turarensu. Hakan ya musu dadi,kuma ya nuna har saman fuskarsu. "Oya assalaat" ta furta tana maida turaren,duk sai suka matso suka hau saman abun sallar. Gefen hannun damanta ta tsaidasu suka tada sallar cikin nutsuwa. Kusan a shekarunsu sun iya komai na sallah,koda akwai gyara bazai wuce wasu qananun abubuwa ba,da haka suka kammala sallar,suka daga hannu yadda sukaga tayi sukayi addu'a tare suka shafa. Agogo ta sake kalla, lokacin dai yanata tafiya,zuciyarta taji ta sake matsewa,sai tayi qoqarin saita kanta ta maida dubanta kansu "Yaudai karatun islamiyyan kowa zanji" da zumudinsu suka gyara zama,cikin dabara da hilata ta dauke musu hankali da karatun,duk da hakan tanayi tana duba lokaci,har sannan bataji wani motsinsa ba,bata kuma ji ance su fito su tafi daddynsu yazo ba. Tunda suka shiga gidan ya wuce bedroom dinsa ya barta da suhail a falo suna hira,wadda kusan indai suhail ne sun saba da irin wannan doguwar hirar shida laila din,don ba baqin juna bane. Har kafin ma a fahimcesu ana zaton soyayya sukeyi,saidai daga bisani sai aka fahimci haduwar jini ne kawai ba wai soyayya ba. A dakin ya kashe dukka awannin saman system,sanda magariba tayi ya leqo yayi musu magana,suhail ya wuce daura alwala don su hada jam'i,ita kuma ta gyara zamanta tana fadin "Ina fashin salla ne yaa maina" kanshi ya dauke kaman baiji ba,baisan me yasa takeson bayyana masa komai ba,akwai abubuwan da yasha jin basu dace ta gaya masa ba amma haka kai tsaye take gaya masa. Tana nan zaune har suka kammala sallar,yayi zaman azkar dinsa har isha'i tayi suka sake jam'i suka idar. Tun yana sallar yake zuba idanu yaji ta jira aunty din tata,amma sai baiji ba,don haka bayan ya kammala azkar dinsa a nutse ya shafa,ya miqe yana nade carpet din da sukayi sallar. "Dare yanayi......call them mana kiji idan sun iso,ya kamata ki wuce tun yanzun" ya fadi da sarautar nan tasa da takan motsa masa time to time,wadda me masifar qara masa kwarjini ainun da haiba. Dan kame kame ta farayi,abinda ya sanyashi zama saman one sitter sofa din dake falon ya hade qafafunsa daya saman daya yana kallon idanunta "Banjin fa sun iso......amma dai, lemme call" ta furta da sauri sauri tana zuge jakarta ta fiddo wayarta. Cikin motsinta da idanunta ya gano qaryarta,taso tahowa ne kawai taqi jiran lokacin da zasu dawo saboda ta matsu ta ganshi shi yasa tayi qaryar yau din zasu dawo "Sakata a handsfree" ya bata umarni nakai tsaye yana ajjiye carbin hannunsa a side table. "Okay" ta amsa qasa qasa,wayar ta fara ringing, muryar aunty din ta fito tarwai. Tun daga yanayin yadda suka gaisa ya tabbatar masa basu da masaniyar tahowarta ma "Yaushe xaku iso aunty?" Tayi qarfin halin tambaya,don ko ba'a gaya mata ba koda bata kalleshi ba ta sani jifanta yakeyi da kallo da wannan fitinannun idanun nasa "Next week by now in sha Allah muna gida" "Alright.....saikun iso" "Yauwa.....byee,ki gaida nenne(mamarta)" sauke wayar tayi daga kunnuwanta amma sam taqi yarda ta kalleshi,shi dinma yasan ba zata iya hada idanu dashi ba,don ba abinda yafi qin jini irin qarya. "Ina da alqawarin fita dasu BB suhail,can u please help me?,ka dauketa ka sama mata daki for one week?" Da sauri ta dago idanunta ba tare data shirya ba, muryarta a raunane tace "Amma yaa haidar..... nan din fa akwai spare din daki,meye laifi don an barni cikin guda daya?tunda dai daddy da nenne dukkansu sun yarda dakai?" Kafeta yayi da wani irin kallo,ya yadda duk iya zamansa dasu yarinyar bata gama sanin halinsa ba tabbas "es-tu dans ton sens ?(kina da hankali?)" Ya tambayeta da harshen faransanci saboda ranshi da ya fara baci. Qasa tayi da kanta,ya jima yana dubanta kafin ya janye idanunsa daga kanta "Wannan ba tarbiyyarki bace kema kuma kin sani,ba zaki kuma fara yanzu ba,pack your stuff za'a kama miki masauki......" Ya fadi mata yana daukan counter dinsa. Daidai nan wayarsa ta dauki tsuwwa. Daddy ne yake kira sai ya koma ya zauna yana daga kiran _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 101 Cikin girmamawa da mutuntawa ya gaidashi,bawan Allahn yana daya daga cikin mutanen da yake ganin girmansu qwarai. "Lafiya alhamdulillah aliyyu,kaga baquwa ko?,sardauna nata fadan me yasa aka barta ta taho,mamana rigimammiya ce,kuma na yarda dakai,na tabbatar she's safe a wajenka" dan murmushi kadan ya fidda yana cewa "In sha Allah daddy" "To ma sha Allah,kada ta wuce ona week,tacemin gidan aunty surayya zata sauka ko?" Kallonta yayi,sai ta marairaice masa alamun kada ya fada ya rufa mata asiri "Eh haka tace" ya bawa daddyn amsa,don bazai taba iya mara mata baya tayi qarya ba,don qaryar tana cikin dabi'un da bai iya ba,hasalima abune da idan kanason ganin tsananin bacin ransa kayi mata ita,idan ya gane shikenan,idan bai gane ba Allah ya taimaketa "Tow yayi,kada ka barta ta wuce one week kaji haidar?" "In sha Allah daddy" "Allah yayi muku albarka......ya aikin?" Ya sauka daga kan wancan maganar ya koma masa hirar wajen aiki. Sun dan tattauna da daddy din a taqaice sannan sukayi sallama,ya ajjiye wayar yana dubanta ransa na sake baci da kalar qaryarta "Kina so ki xama maqaryaciya ko?" Kai ta girgiza da sauri,don ta sanshi farin sani akan yin qarya,duk yadda kake dashi yanzu yanzu zaku bata,yanzu za'a ji kanku akan qarya (Don Allah,don Allah iyaye mu kula,mu tsaya tsayin daka game da tarbiyyar yaranmu,wallahi wallahi qarya masifa ce,itace silar rugujewar komai da kuma dukkan wahalhalun rayuwa da mukesha,wasu qarairayin kuma daga wajenmu yayanmu suke koya,kiyi qaramar qarya kina ganin batakai ta kawo ba wallahi tana affecting tunanin yaro sosai,misali ungo nan,zo ka ka karba,jeka dauko takalminka mu tafi sai ya dawo ya tarar kin gudu kin barshi,duk da irin haka suke farawa,zasuga au ashe idan na fadi magana kaza ba daidai yadda abu kaza yake ba ashe akwai wani abu da ake cimmawa,ko babansu ya dawo ki karkace ki shirga masa qarya don ki Kare kanki bayan duk suna kallo,da haka saimu wayi gari muga mun cika al'umma da maqaryata,muyita mamaki ina suka samo wannan dabi'a,bayan ba daga ko ina bane daga wajejenmu ne,Allah ya bamu ikon gyarawa ameen). Siririn tsaki yaja yana kauda kanshi gefe,sai kuma yayi wami gajeran tunani,daddyn ya riga ya damqa amanarta a hannunsa,dole ya kula ma dashi kansa hotel din da zaya sauketa,kafin gobe ya laluba mata inda zata zauna cikin gidajen abokan aiki,don bayason xaman hotel ga mace baliga babu muharrami,don haka ya miqe tsaye yana kallonta,yama fasa suhail din ya kaita,gwara ya kaita da kanshi,fatansa su rabu 'yar mutane ta koma gidansu lafiya "Wuce muje" ya fadi a dake. Dakewarsa bata dameta ba saboda kaita din da zaiyi da kansa ya mata dadi,hakanma daraja ce,sai yayi gaba yana barwa suhail din sallahun ya jirashi yanzun zai dawo. Yana fitowa idanunsa suna kan gidan,daidai saitin window din nata, hankalinsa yana kan yaran,bayason ya musu alqawari ya gaza cikawa,don yanason su tashi da dabi'ar cika alqawari. Seat din driver ya shiga ya tayar da motar. Full light din da ya yiwa motar yana kunnawa sau biyu yana kashewa sai taji tamkar da ita ake sanda take tsakiyar yaran tana qoqarin su qara assignment dinsu. A nutse ta daga kanta ta kalli window din gabanta yana dan tsinkewa, zuciyarta ta bata ko shine zaya dauki yaran?,amma kuma zai kunna mota tun yanzun bayan da qafa zai shigo?. Wannan tunanin ya sanyata kauda kai ta sadda kanta qasa. Duk yadda akayi zai fita ne da wancan yarinyar, that's why bazai iya zuwa ya kwashi yaran ba,iya wannan tunanin ya saukar mata da qunci a zuciyarta. Kaman goumar yasan tambayar da taketa yiwa kanta kenan saiga muryarsa yana baiwa ama saqo "Yanzun naga ya maina zasu fita da laila......yacemin zai zo ya dauki su benazeer" "Sai ya iso" ama ta amsa,don bai boye mata wacece laila ba ta riga ta Santa. Sosai ranta ya qara baci,ta dinga jin koda yazo ma ba zata bari yaran suje ba,tunda laila gaba take da 'ya'yansa,saita sake karkata hankalinta akan yaran,daidai sanda akayi knocking qofar dakin nata. "Goumar ne" ya fadi tun bata tambaya ba,daya daga cikin dabi'unsa masu kyau baya taba shiga waje ko inane ba tare daya nema izini ba "Baqin buzu?" Ta tambaya yau daya tana jin sha'awar tsokanarsa "Ban sani ba mummyn twins" qaramin murmushi ya qwacewa kyakkyawan fuskarta,inda yasan yanzun sunan baya bata haushi,dadi ma yakeyi mata da bai dinga fadi da zummar ya tsokaneta ba "Indai ka yarda da baqin buzu sunanka ka shigo,idan baka yarda da sunan ba ka koma" "Indai kin yarda da matar babban yaaya,matar maina MAYAK'I kike to tabbas zan shigo" dif wuta ta dauke mata,ta xubawa qofan idanu kafin kuma ta sauke idanun nata akan yaran. Kamar suma suna fahimtar abinda yake fada din dalla dalla,dukkansu sun gwalalo mata fararen idanun nan nasu masu wani irin kala irin na ubansu "Kallon kuma na meye?" Ta jefa musu tambayar tana kallonsu,dariya duka suka saki sai suka maida kansu ga rubutun nasu, daidai nan goumar ya tura qofar ya shigo. Kamar ko yaushe suka miqe suka maqaleshi ya daukesu sannan suka koma suka zauna. Yawancin lokuta idan ya musu hakan saita tuna sanda maina yake yaya kuma uba a wajenta,fiye da wannan kusancin ne a tsakaninsu. Daga qarshe dai komawa tayi 'yar kallo,suka gama assignment suka shiga shirmensu su da goumar din,wanda dukansu basa gajiya dashi,sannan tanja ta shigo musu da abinci sukaci,a hankali kuma bacci ya kwashesu suka zube a wajen. Da murmushi yake dubansu sannan yace "Yara kun looser......yau ba fita da daddy kenan". Maganar goumar saita zame mata tamkar fami cikin zuciyarta,ta daga idanunta ta kallesu,saita maida kanta ga tattara karikicen karatunsu. Yadan saci kallonta sai ya fahimci maganar da zaiyi ma kamar ba zata samu gurbin zama a wajenta ba,don haka ya miqe,ya dauki yaran da daya da daya ya fita dasu zuwa dakinsu. Sanda ya dawo tana bakin qofa yana shirin kulle dakin,ya dubeta yasan saki murmushi. Tunda taga yayi murmushin ta tabbatar tsokana ce ta dawo dashi,sai ta dan tsuke gira tana cewa "Sai kuma me?" "A'ah,gulman mijinki nazo gaya miki,sai kuma na ganshi da wata bafulatana mazauniyar France zasu fita yawon shaqatawa ke kina cikin gida a zaune" harara ta balla masa, goumar din duk yadda zai bata takaici ya iya "To sai me?,su wuce the great wall ma,sukai qarshenta su dawwama a can" saita ja qofarta tana rufewa. Tana jiyo dariyarsa daga bakin qofar harda durqusawa,sai ta kasa barin qofa,lokacin yadan daga murya yana cewa "Kinci bashi wallahi......amma dai ina gaya miki,tabbas mijinki rububinsa ake,abu daya da Allah ya rufa miki asiri shine bame fuskar da za'a tareshi bane,nima kuma ki godemin,don na tsare miki kishiyoyi da yawa" tanason yaba masa baqar magana amma kuma batason yasan ma taji abinda yake fada,saita juya zuwa ciki taja jan tsaki kamar zata tsinke harshenta. Haka kawai taji komai ya quntace mata,daga bisani ta dinga masifa ita daya da ranta kaman an mata wani abu. Ta gama shirin kwanciyarta kaf,ta matsa bakin qofar dakin ta murza key ta barshi a jiki,don haka kawai jikinta yake bata zaya shigo. **Daure da towel a qugunsa ya fito daga wanka,faffadan qirjin nan nasa me cike da gargasa sun kwanta luf sunbi jikinsa sosai,sai suka sake fidda qirarsa ta qaqqarfan namiji ma'abocin motsa jiki da daga qarfe. Agogo ya kalla,sai yaja siririn tsaki,sosai yarinyar ta bata masa lokaci yau,kwata kwata yayi niyyar kama mata wajen kwana ne kawai,amma ta dinga amfani da damarta don tasan matsayin daddy da sardauna a wajensa har sai data tsaya taci abinci,ta saka order din wasu kayan amfanin,wannan ya bata masa lokaci har sukayi dare haka. Cikin lallausan pyjamas ya shirya kansa,ya wuce kitchen riqe da wayarsa,ya kunna coffee Maker ya hada coffee me zafi sosai saboda iska da take dan kadawa me dadi a daren,iskar data haifar masa da kasala da kewarta me yawa. Koda ya juye a cup sai ya fita zuwa balcony dinsa,inda zai samu daman kallon gidan sosai. Yana kurba jifa jifa yana duba wayarsa,rabin hankalinsa kuma yana kan gidan dake dauke da halittu mafi soyuwa a wajensa a duk fadin duniya. Ya kusa minti goma sha biyar kafin ya shanye din,ya ajjiye mug din yana jin kewarta tana qaruwa cikin ransa,gaba daya zuciyarsa da ruhinsa yafi karkata ga yaje yaji duminta,koda na awa daya ko biyu ne,ya tabbatar muddin baije din ba,babu shi babu bacci me dadi,bama lallai ya samu baccin,don haka ya miqe ya ajjiye wayoyinsa gaba daya,ya zura slippers dinsa dake ajjiye a gefe ya fito cikin nutsuwa yana saka hannayensa cikin aljihun pyjamas dinsa. Batasan adadin sau nawa taji juyi ba daga kwanciyarta zuwa wannan lokacin,wani irin qunci takeji cikin qirjinta sosai wanda ita kanta batasan meye dalilin hakan ba. Jin da gaske baccin yaqi zuwa saita miqe tana maida cap dinta ta bacci,ta zuro qafafunta qasan gadon tana shirin yunqurawa sai taji ana taba qofar dakin. Da farko ta tsorata sosai,amma daga bisani hancinta ya fara dauko mata qamshinsa yana aiko mata dashi. Zuqar qamshin tayi da kyau,sai taji wani kaso na qullewar da qirjinta yayi yana sassautawa,sai kuma murmushi ya subuce mata,tadan cije lips dinta,hasashenta yayi daidai kenan,dama tasan zaiyi wahala baizo ba,kawai sai ta koma saman gadon abinta ta nannade cikin duvet tana fidda murmushi tana kuma jiyo motsinsa sama sama. Bayan wasu mintuna taga wayarta tana haske,koda ta duba sai sunan da yayi mata saving dashi ya bayyana,maida wayar tayi ta ajjiye tana murmushin,har tayi iya yinta ta katse. Iska me dumi ya furzar daga hunhunsa yana maida wayarsa da dole ta sanyashi fita ya daukota cikin aljihunsa,bayason ya matsanta kan sai ya shiga,duk da idan yaso zai shiga din,to amma bayason tada kowa cikin gidan. Kwata kwata issue din laila ya sanyashi baiyi wani dogon nazari akanta ba,inda a nutse yake tabbas zai gano zata aikata hakan,ya watsa hannayensa yana daga kafadarsa,lallai bazai qyaleta ba,wannan abun da ta ciwa kanta bashi ne. Murmushi me dan qaramin sauti ta saki sanda taji shuru,ta tabbatar ya gaji ya wuce,ko iya yau kadai ta dan rama kadan daga cusa matan da yakeyi ya kuma hanata katabus,da wannan murmushin saman fuskarta bacci ya dauketa. ********Cikin kwanaki biyar din data dauki hutu ko qofar gida bata fita,tana daki zuwa parlor tana hada ayyukanta. Da zarar anyi knocking Bell zata tattara komai ta wuce daki kafin a shigo,wannan ya sanya tsahon kwana uku basu hadu ba,har sai rana ta hudu,ranar da benazeer ta tashi da zazzabi. Da yammaci ne dukkansu suna zaune a falon, benazeer din an rakwarkwabe jikin ama anata zuba shagwaba,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka,sultana na zaune da system saman cinyarta,gefe kuma kayan sawa na asalin qabilar KANURI,ta gama shirinta tsaf, gobe kawai idan Allah ya kaimu take jira. Door bell aka kada,sai ta daga kanta daga aikin da takeyi ta maida ga qofar,yau din bata da sauran option dole itace me budewa, benazeer na cinyar ama, batoul tsahonta baya kaiwa,dom haka ta tattare tarkacen dake saman cinyarta ta miqe tana gyara top din jikinta hadi da gyara daurin scarf dinta da santsinsa yasa ya kusa faduwa ta nufi qofar. Adan darare ta bude,don jikinta yana bata shine. Kaman yadda ta zata din kuwa shine,yana tsaye qyam daga bakin qofar,sanye da baqin trouser da baqar shirt short sleeve data fidda qirar damtsensa sosai. Ya sakaye idanunsa cikin baqin glasses daya fitar da tsananin kyawun fuskarsa,hannayensa dukka cikin aljihun trouser dinsa,wannan ya sanya ya sake cika qofar gaba daya. Wani mugun kwarjini taji yayi mata,gabanta ya yanke y fadi. Ga mamakinta sai taga tamkar bai ganta ba,ya dauke kansa yana shigowa cikin falon kamar bata wanzu a wajen ba. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 102 Dukka hankalinsa yana kan yarinyar,wadda itama tana ganinsa ta sake narkewa jikin ama. Cikin nutsuwa da kuma girmamawa ya qaraso gaban kujerar da ama din ke zaune akai ya zauna sosai a qasa yana miqawa benazeer din hannu. Nata hannun ta miqa masa sai ya jata cikin jikinsa yana jin yadda nata jikin yayi dumi sosai "Barka da warhaka ama" ya gaidata cikin girmamawa. Ajiyar Zuciya ta saki tana gyara zamanta,ita daya tasan me take tunawa "Barka kadai" "Ya gida yame jikin?" "Alhamdulillah da sauqi,ta karba magunguna ai,amma da yammar nan za'a maidata su sake gwada jininta" shuru yayi hannunsa saman sumar yarinyar yana shafawa,tausayinta sosai yakeji haka kawai yana ratsashi "Akwai inda yake miki ciwo yanzun?" Ya tambayeta cikin nuna kulawa,kai ta gyada masa tana nuna masa kanta,kan ya kama a nutse ya karanta mata addu'o'i,sannan ya zare idanunsa ya maida ga ama "Wanne asibiti ne?,yanzun lokacin zuwa ganin likitan yayi?" Ya tambayi ama din "Mamarsu ta sani.….." ta furta tana dan duban sultana,wadda tunda ta bude qofan ta zauna a hannun kujerar dake daura da qofar. Haka kawai takejin jikinta dukka a mace,batason kuma wucewa daki don kada ama taji ba dadi game da hakan da zatayin "Alright" ya amsawa ama a taqaice. Miqewa yayi yana daukanta saman kafadarsa yace da ama "Tanja tana kusa?,ta fiddo mata takalminta" ya amsa yana yin hanyar waje. "Ki dauki takalminta cikin shoe rack,kisa mayafinki kuje" ama ta bata dukka umarnin lokaci guda tana miqewa daga zaman da tayi don dauke batoul da bacci ya dauketa a wajen. Kawai take dari dari dashi da kuma tsoro tsoro,kaman ta dojewa ama din amma kuma sam ba zata iya ba,ala dole tayi yadda ama dij tace,ta fito sanye da wani mini hijab data dora saman doguwar rigar jikinta. A seat din kusa dashi ya zaunar da benazeer din,tanata zuba tabararta,yau aiki ya samu shi kuma yana biye mata,tasa hannu ta bude seat din baya ta shige ba tare da tace komai ba,shima din bai tanka ba ya kunna motar ya soma motsata suna barin layin. Dukka dakiyarta da dauriyarta ta tattaro sannan ta hada kalaman "Ina yini" lion eyes dinsan nan ya daga,ya kalleta ta cikin glass din gaban motar. Kamar idanuwanta sunsan ita yake kalla itama takai nata duban ga mirror din,take idanunsu suka hadu waje guda. Shi ya fara janye kallonsa daga kanta yana amsa mata murya ciki ciki "Lafiya" yadda ya amsa mata din sai ya tsaye mata a rai,yayi mata kama da lokuttan baya ko tace shekarun baya s nijer,sanda yake mata ire iren wadannan abubuwan a duk sanda sarautar tashi ta motsa. Daga haka bai sake cewa da ita komai ba,itama bata sake fada din ba,to me zatace bayan ma tasan bata da abun fada din. Yana driving yana hira da yarinyarshi,sam kaman ma bata cikin motar,duk da benazeer na zazzabi amma baki bai mutu ba,surutu kuma ba'a daina ba,a haka suka isa asibitin. Kaman dazu yanzun ma daukarta yayi sukayi gaba,tana biye dasu a baya har suka isa reception. Shi ya gabatar da abinda zasuyi da tattacen faransancinsa,suka bashi number ya tafi daga gaban office din yana jiran number su ya nuna. Sanda number ya fito wayarsa tayi ringing,ya katse kiran suka shiga office din likitan. Yar asalin qasar faransa,me yawan fara'a da kirki da kuma son yara,tana ta jan benazeer da wasa,saita daga kai tana murmushi ta dubesu "beau couple,vous êtes parfaits l'un pour l'autre(kyakkyawan ahali,kun dace da juna)" ta qarasa fada tana kallon fuskar sultana. Dan qaramin murmushi ta saki tana satar kallonshi ta gefan idanunsa,sai taga shi duka hankalinsa ma yana kan wayarshi. Haka kawai taji ranta ya quntatar mata,wataqila wannan yarinyar fa yake magana da ita?. Bata qarasa wannan tunanin ba taji yana cewa "Je suis désolé, quand ils auront fini, ils me trouveront dehors, je lancerai un appel d'urgence au téléphone(Yi hakuri, idan sun gama za su same ni a waje, zan yi kiran gaggawa a waya)" murmushi tayi "aucun problème monsieur(babu matsala yallabai)". Matsawa yayi ya shafa sumar benazeer yana cewa "Il n'y a pas de contestation(banda taurin kai),ba zasuyi miki allura ba kinji my angel?,see you soon" ya qarasa fada yana dan jan kumatunta. Murmushi tayi tana bashi peck a bayan hannunsa. Juyawa yayi ya fice a nutse yana sanya wayar a kunnensa. Idanunta ta lumshe tana jan numfashi da kyau saboda wani motsuwa da ranta yayi,ta zaci uzurin lalurar benazeer din tafi dukkan wayar da zai daga din muhimmanci?. Kiran sunanta da likitar tayi shi ya dawo da hankalinta,ta sauka daga kujerar da take kai ta koma saman wadda ta tashi tunda tafi kusa da likitan,tayi qoqarin tattara hankalinta don suyi abinda ya kawosu su gama. Cikin minti ashirin da biyar suka gama komai,ta karba dukkan sauran magungunan da zataci gaba da amfani dasu. Sun fara fitowa zuwa haraban asibitin benazeer taja tunga ta tsaya. Ta juya tana kallonta,sai babbata fuska takeyi "Lafiya kuma?" "Mummy ni ki daukeni" idanu sultana ta fiddo waje tana kallonta "Dauka benazeer?,bakiga kinyi nauyi ba?, infact ma kin girma fa" narke mata tayi tana shirin sakar mata kuka "Mummy amma bani da lafiya fa,bakiga daddy dauka yakeyi ba?" Sak ta tsaya tana dubanta,wayo ya fara sangartasu kenan?,to ita din ba zata lamunta ba,don haka ta hade rai tsam tana dubanta "Ba zan daukeki ba don kin fara wayau ai,ki wuce mu tafi ko kuma ki jira daddy din naki yazo ya daukeki" qafa ta soma bugawa zata tabare mata,wannan din ya fusatatata ta daka mata tsawa sosai. Har inda yake tsawan ya taddashi,sai ya leqo da kanshi daga seat din driver da yake zaune qafafunsa a waje yana amsa waya ta handsfree. A kansu idanunsa ya sauka,sai ya dauke kallonsa ya maida kan diyarshi. Hawaye takeyi sosai tana share fuskanta da bayan hannunta,suna hada ido ta tako da gudu ta qaraso wajensa ta fada jikinsa. "Daddy mummy ce...... " Benazeer din ta fada cikin shesheqar kuka. Cikin jikinsa ya sanyata sosai yana fadin "Am sorry,cool down B" ta samu abinda takeso saita lafe tana goge hawayen. Fuska a hade tana sake kama kanta ta bude back seat kaman yadda sukazo ta shiga,tana shirin maida murfin ta rufe muryar data dade da haddace ta waye taji ta cika motar,da alama waya yakeyi,ya kuma jona wayar da speaker din motar "Halan waye ya taba B?" Laila ta fada tana fidda murmushi me sauti. Ware idanu benazeer tayi wadda itama batasan waya akeyi ba,ta kalli maina sannan ta kalli speaker din "Mummy ce" "Rabu da mummy,sai an zaneta ko?" Laila da batasan alaqarsa da benazeer ba ta fadi. Murmushi benazeer ta saki tana leqen sultana dake baya. Ba benazeer ba,ko maina bai isheta kallo ba. Saidai wani abu da yazo ya tsaye mata a wuyanta me matuqar tauri da zafi. Dama da yace zai amsa kiran gaggawa wayo zaizo yi cikin motar da wannan yarinyar?,ashe su ya rainawa.hankali,kenan ciwon bai dadashi da qasa ba?,kawai sai taji idanunta sun fara mata yaji yaji,alamun suna neman dalilin da zasu fidda qwalla,saidai kuma cikin tsananin dakiya sa jarumtarta ta girgiza kai alamun a'ah,akan meye zatayi qwalla?,shi din waye da zatayi masa qwalla "Am on my way" "Saika qaraso dear........" Ta fadi tana katse kiran da sauri kaman wadda tasan tayi laifi. Sallamarta ta qarshe sai ta dinga mata amsa kuwwa cikin kunne,tana ji ya tayar da motar suka fara fita daga asibitin,batace komai ba,bata motsa ba kuma bata bude idanunta ba. Tana jin hirarsu daya bayan daya,wanda duk kalamansa a nan zallar qauna kulawa da soyayyar da yakema yaran suke nuna kansu. Batasan me yasa shariyarsa take mata ciwo a zuciya ba,bayan irin wannan abun ta jima tana buqatar ya dinga yi mata,a yanzun data samu kuma batasan me yasa ta kasa jin hakan dai dai bane. "Bari naga wata" maina din ya fada yana rage gudun motar tashi,sannan kuma a hankali ya soma gangarawa gefen titi kusa da wasu shops yana neman area din da ake parking "Alhamdulillah" ya fadi bayan ya tsaida motar,ya kasheta yana bude side dinsa ya zura qafafunsa waje. Kamar a mafarki cikin rufaffun idanunta taji muryar yarinyar dab dasu,gabanta yayi wani mummunar faduwa,hakanan ba tare data shirya ba ta soma ware idanun nata sanda muryarta me karadi ke tashi "Na gode sosai da ka bani damar ganin B......B.....how far?,ya jikin?" Ta fadi da murmushi sosai saman fuskarta tana yunqurin xagayawa side din kujerar benazeer. Sisiririyar bafulatana sanye da gown na chiffon da bata sauka idanun sawunta ba,ta sanya qaramin scarf ta manne idanunta da baqin sun glasses,qafafunta saye da takalmi sneakers daya dace da material din. A shekaru zata iya bata shekara uku,a kyawun sura kuwa tabbas koda wasa ba zatayi gigin shiga sahun da sultana take ciki ba, ba'a maganar diri da structure na jiki,amma a idanun sultana sai taga gaba daya ta kowanne fanni ma kamar ta kere mata. Sanda ta bude side din benazeer din ta sako kanta tana bawa benazeer hannu tare da tambayarta jikinta duk dai taji kaman iskan wajen yana neman yi mata kadan. A nutse ta dauki wayarta da qaramar jakarta,ta sanya hannu ta bude murfin motar ta sanyo santala santalan fararen qafafunta waje tana fita a motar,wannan motsin ya sanya laila ta ankara da zaman mutum a seat din bayan. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 103 Qamshinta da motsinta yaja hankalin laila,ta daga kanta tana bin bayanta da kallo. Bataga fuskarta ba amma gabanta yayi wani mugun faduwa "Mummy karki tafi ki barni" benazeer da taga fitan sultana ta fadi. Sosai tayi qoqarin daidaita mode na fuskarta sannan ta waiwayo,sai a lokacin laila da take binta da kallo ta samu daman ganin fuskarta da kyau. New TV show presenter Sultana mohmoud,ta shaida fuskarta,tun a ranar data fara program din,a ranar aka fara ganinsa da ita,a ranar kuma taji tayi matuqar burgeta,har ta dinga jin tamkar itama ta sauya hannu ta koma aikin jarida. Qwarewarta kawai zai sanya kayi tunanin ta dade a harkar,kyanta ya burge laila qwarai ya kuma bugar da ita,to amma kuma me takeyi a mota tare da maina?. Saurin kauda tunanin daya darsu a zuciyarta tayi,muddin ya kasance wata alaqa ce data danganci soyayya tsakaninsu to tayi imanin kashinta ya bushe,don ita kanta da take mace tahi imanin wanda yake da sultana babu abinda zaiyi da ita. "Zan shiga in sha coffee" ta bawa benazeer amsa tana shiga shagon coffee dake daura dasu. Jakarta kawai ta daura saman table din,ta kuma order din coffee din,yanata zuba tururi da qamshi a gabanta amma batasan meye zatayi dashi ba,haka kawai zuciyarta dukka taqe a quntace, idanunta nakan qofan Glass din da ta yiwa wajen qawanya,wadda bata hana wanda ke ciki hango kai kawon jama'ar waje. Agogonta ta duba,a qalla mintuna goma da shigowarta wajen kenan,sanda zata daga kai daga agogon benazeer ta shigo "Mummy kizo wai mu tafi, za'a ajjiye aunty laila a hanya" "Aunty laila?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar tana duban idanun benazeer. Kai ta gyada tana kallon sultana din. Numfashi ta ajiye tana qoqarin controlling kanta "Ku wuce zan biyo ku a baya" ta bata amsa tana jawo cup din takai bakinta wai ko hakan zai rage mata abinda takeji. Kaman ba zata motsa ba yarinyar sai kuma ta juya tana fita a wajen a sanyaye. Yana jingine da jikin motar yayi crossing qafafunsa ya kuma goye hannayensa a qirji yaga fitowarta ita kadai,idanunshi a kanta har ta qaraso "Daddy tace wai mu wuce zata taho".idonsa ya lumshe gami da budesu duka lokaci daya "Me kikace mata?" Ya tambayeta "Da waye kikace mata zamu tafi?" Ya sake gyara tambayar yadda zata fahimta "Da aunty laila....."idanu yadan zaro sai kuma ya saki murmushi. Ya samarwa laila taxi kuma har ta wuce,don shima bawai yanason yadda take rabarsa bane,kawaidai yana tuna karamcin daddy da mutuncin sardauna,tanacin darajar mutum biyu. Mota ya budewa benazeer ya kwnatar mata da kujera sannan yace "Zauna,karki fito har sai na dawo,ki zauna kiyi game ko ki kwanta" ya fadi yana fiddo mata wata mini game wadda dama ya ajeta cikin motar ne sabodasu. Baki ta washe tana karba da sauri,ta kwanta abinta kuwa tana maida hankalinta ga game din. Hannun rigarsa ya gyara sannan ya fara takawa zuwa cikin coffee bar din. Tunda ta kurba sau daya bata qara ba,ta ajjiyeshi a gabanta tana juya tea din da spoon,tayi nisa a duniyar tunanin da batasan ina ta tafi bama,sai inuwarsa ta gani saman kanta. Yayi qyam a gabanta da wanna tsahon nasa da dakiyarsa,fuskar nan ta fito a asalin sunansa na aliyyu haidar,ya motsa bakinsa cikin wata ginshira da izza data jima rabon data ganta tattare dashi "Kin shiya tafiya da qafafunki ko kuma ni kike jira na daukeki?" Ya mata kwarjini sosai ta yadda ba zata iya kallon cikin idanunsa ba,amma duk da haka tayi namijin qoqarin kauda fuskarta gefe "Idan kika qara minti daya zaune a wajen nan da hannayena xan daukeki,kuma kinsan hukuncinki basai na gaya miki ba......and benazeer ba zata hana aiwatar da komai ba" yayi maganar yana gyara hannun rigarsa. Ba shiri ta suri handbag dinta tana miqewa tsaye. Hannu ya miqa mata yana tsareta da idanu,ta fahimci abinda yake nufi,don haka ba musu ta miqa masa hand bag din,ya sakata a gaba suka fice daga wajen bayan yaje ya biya kudin abinda ta karba din. Da kansa ya bude mata gidan gaba yana basarwa,tadan dubi benazeer da tayi kwanciyarta a baya,ta shiga a hankali ta rufe,ya daidaita zamansa ya tayar da motar. Bai ajesu gida ba sai daya gama yawon yima yaransa siyayya kaf,kaman ta sanya hannu aka ta saki ihu,don sam zaman cikin motar ya gama gallabarta,shi da benazeer kawai suke sabgarsu,yaqi sakata ma a cikin hirarsu gaba daya. Koda ya ajesun ma bai shiga gidan ba ya juya abinsa bayan ya raka benazeer da sayayyarsu har bakin qofa,ya tsugunna yayi kissing nata ya wuce. Itama dauke kai tayi ta wuce ciki,saidai kuma can qasan ranta tana jin wani qunci yana saukar mata. Ba abinda idanunta ke nuna mata sai yadda yake hira sosai da wancan yarinyar tashi,wai wacece ita?,meye ne alqarsa da ita?. "To ke menene sha'aninki da ita?,suje su qarata mana" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata,saita ja tsaki tana qoqarin fincike komai daga ranta, tsakin da ya sanya ama waiwayowa ta kalleta,tayi sauri ta dake ta dauki jakarta tana wucewa ciki. Duk yadda taso fidda abun daga ranta tayi amma a banxa,don sanda ta kwanta saman gadonta,sanda garin ya sake daukan shuru,dare ya fara nisa sai komai yake neman kwance mata,ta dinga laluba murmushi guda daya tak da yayi mata a yau din ta rasa,magana tsakaninta dashi bata iya tuna guda daya ba,hirarsa kaf da yarinyarsa sukayi suka gama har suka rabu. A daren yau din saita samu kanta da sauraren bakin qofarta wai ko zataji kusurkusur ko motsinsa,ta dinga juyi saman gadon ita daya,daga hannun dama zuwa hagu. Bacci taketa buri da fatan tayi amma yaqi zuwa mata,gefe guda ga wani muguwar kasala da mutuwar jiki data saukar mata,sai kace wadda aka yiwa dukan tsiya,ko ina na jikinta ta dinga ji yana mata ciwo,duk burin da taci nayin bacci isashe don ta samu gabatar da program dinta a gobe cikin karsashi da fara'a dukka ya zagwanye. Bata taba ji jikinta na mata ciwo irin haka ba,ba kuma wai bata da lafiya bane,batasan meye dalili ba. Wannan abu biyun su suka taru sukayi mata rubdugu suka nakasa baccinta,don ba itace bacci ya dauka ba sai da biyu na dare ya raba. Da sassafe taso fita a washegari wai ta shammaceshi kaman wancan karon,to saidai yanayin da takeji jikinta na kasala ya sakata shiryawarta dama komai nata ya zama a sanyaye. Koda ta buda break din da tanja ta hada mata sai taji cikinta ya cushe ta kasa ci,don haka taja tissue kawai ta goge hannunta,ta dauki key dinta da hand bag tayi hanyar fita,daidai sannan ta kalli agogo. Duk saurintama ya tashi a banza,don a irin wannan lokacin yake shigowa gidan. Amma kuma sam bataga alamun gidan a bude ba ko kuma da mutum a ciki. Tana shirin tashin motar kiran bibi ya shigo,ta zauna daga gaban motar tana amsa wayar, jifa jifa idanunta nakan qofar gidan,tamkar wadda ke tsammanin fitowar wani ko wata,saidai qasan zuciyarta ta tabbatarwa kanta babu wanda take tsimaye. Sukayi sallama da bibi,ta ajjiye wayar a gefanta tana sake kallon qofar gidan,sai taja siririn tsaki ta tayar da motar a kasalance tana barin layin nasu. Sanda ta isa tv station din ta samu ma'aikata sosai,don yau batayi sammakon da tayi jiya ba,duk inda ta gifta saita gaisa da mutane,batasan da wanne irin farinjini ta shigo tv station din ba,qauna suke nuna mata sosai,duk kuwa da cewa ba ita daya bace 'yar Africa a wajen. Bugun zuciyarta ne ya dinga qaruwa sanda take lalubar key tana qoqarin bude office din,sai takeji har cikin zuciyarta kaman zata taras da wani a cikin office din,kamar wancan lokacin......kamar waccar ranar..... "Maina?" Wata zuciyar ta tambayeta "Ban sani ba" tayi saurin amsawa kanta da kanta rana murguda baki kaman ita da wani ne. Sanda qofar ta bata sautin ta budu daita aza hannunta saman qofar tana jin yadda bugun zuciyarta yake qaruwa,sai data kulle idanun nata taja numfashi da kyau sannan ta tura qofar a hankali ta sanya qafafunta. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 104 Dukka idanun ta wara sanda ta shiga office din, zuciyarta na bada sautin bugun da har ya take iya jinsa ga kunnenta. Office din fetal yake,babu kowa babu ma alamun an shigo tun bayan gama gyara mata shi da akayi. Sosai ta wara hancinta wai ko zata jiyo wani baqon qamshi daban,ba qamshin komai saina freshner da ake mata using nata cikin office din. Jinta tayi kaman an buge mata gwiwarta,haka kawai taji ta sare,qwarin gwiwarta ya sake raguwa,dannkarsashin data samu daga qasa zuwa hawowanta sama dukka babu ya zagwanye. Jikinta a sanyaye ta isa cikin office din,ta ajjiye tarkacen hannunta taja kujera ta zauna tana maida numfashi. Ta sake bude idanunta,sai suka sauka saman kujerar,inda ya zame duk kayan jikinta da inda ya zaunar da ita,tsigar jikinta tayi wani irin tashi,ta runtse idanunta tana kiran sunan Allah hadi da lullube fuskarta da tafin hannunta. Sosai takejin zafi cikin zuciyarta,tayi imani yarinyar ce ta tareshi,qilan ma yanzun haka suna tare,ai hakan bai taba faruwa ba sai yanzu,sai yanzu da tazo qasar. "Idan yazo meye zaiyi miki?,ina ruwanki dashi?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar "Aifa" ta sake bawa kanta amsa. Knocking din da akeyi ya sanyata miqewa tana nufar qofar,gabanta nadan faduwa tana tunanin ganin wani abu da zai wanke mata wannan kai kawon da zuciyarta keyi. Saidai kuma sanda ta bude din da Dioura ce da fuskar nan tata ma'abociyar fara'a. Qoqari tayi ta tattaro dukka fara'ar dake kan fuskarta dama qasan zuciyarta tana mata sannu da zuwa cikin harshen abzinanci. Ta amsa mata itama ta bata waje ta shigo. Shigowar dioura ya debe mata kewa sosai,qarasa tattaunawa da kuma tsara daukan program din suka qarasa yi. Ita daya cikin dakin sauya tufafin na musamman da aka tanadar mata a cikin office dinta,tayi wani fitinannen kyau cikin laffayar me azabar kyau da tsada,idan ka ganta a sannan zakayi tsammani shuwa ce,duk suturan data sanya yana karbarta ainun haka jikinta yake. Fuskarta take kalla,tanason bawa kanta qwarin gwiwar shiga studio din. Ta jima tana zumudin randa zata gabatar da al'adun kanuri saboda yadda abubuwansu suke burgeta,yau ranar yazo,amma kaf ta rasa duk wani walwala da nishadi da take da buqata. Ga kasalar da take sake saukar mata,tana jin kanta da idanunta tamkar wadda ta tara bacci na shekaru aru aru a kanta. Siririn tsaki taja sanda akayi knocking qofar dakin,sannan kuma tace "Ina fitowa" ta sake juyawa tana gyara fuskarta,tana ambaton sunan Allah a hankali a hankali wai ko zata samu sassauci daga dukkan abinda takeji din. "Wow......bansan wanne shiga bane yafiyi miki kyau,na last week ne ko na wannan satin?" Dioura ta fadi da kwantaccen murmushi da gurbatacciyar hausarta tana kallon sultana. Dan murmushi da yafi kama da na yaqe ta saki tana maida abubuwan hannunta data cire cikin jaka. Har sun soma ficewa ita da dioura saita tsaya,tana buqatar wani abu da zai dawo mata da karsashinta cikin jikinta,idan ta fita a haka tabbas ba zata taba bada abinda program din yake buqata ba. A nutse ta koma ta zauna,ta fidda wayarta ta soma kiran layin ama. Dab da zata katse ta daga da sallama a bakinta "Good morning ama" "Morning sultana,ban tashi da wuri ba yau din,tanja tacemin har kin wuce" "Eh ama......" "To ma sha Allah.....ina fatan komai lafiya?" Ta tambayeta saboda yanayi muryarta daya bata kaman akwai wani abu "Lafiya alhamdulillah,zan shiga program.......ina buqatar addu'a" ta qarasa fada muryarta na danson yin rawa. Tausayinta sai ya saukarwa ama,ta dinga ji a ranta inda mahaifiyarta tana raye tabbas ita zata kira ta nema addu'a kaman haka,maraici ba dadi komai gatan da zaka samu,gatan uwa daban yake,mahaifiya kuma ba madadinta. Sai muryar ama da jikinta dukka sukayi sanyi,cikin nuna kulawa tace "Allah ya bada sa'a,yasa a gama lafiya.......zaki magana dasu batoul ne?" "Eh ama" ta fadi qasa qasa cikin dan jin nauyi "Gasu" ta fadi tana miqawa yaran wayar. Da zumudinsu suka soma magana da ita don yau basuje school ba saboda jikin benazeer,koda batoul taje ita daya ba lallai ta zauna,shi yasa ama tace a barsu duka,ta dinga murmushi tana biye musu,a qalla sun kusa mintuna goma da ita tana biye dasu kafin tace su bawa ama wayar sukayi sallama. Iska ta furzar daga bakinta tana kallon fuskar wayar,ta samu relief kaso hamsin cikin dari,amma ta rasa gane dalilin da ya sanya wannan gurbin ya gaza cikewa,ta rasa me yasa ta kasa samun satisfaction dari bisa dari?. Idanunta ta rufe tana karanto addu'o'i,tana jin zatayi managing da 50% din data samu,don haka ta miqe tana fita daga office din. Ita kadai tasan yadda tayi forcing kanta tayi program din,a fuska ne kawai take da karsashi da kuma kuzari,amma cikin zuciyarta da gangar jikinta wani irin emptiness take ji. Ita daya ta koma office ta zare dukka kayan data gabatar da program din dasu duk da cewa sun zama mallakinta. Haka kawai taji bata da buqatar barinsu a jikinta,ta maida kayanta data taho dasu ta koma saman sofa tana maida numfashi. Kanta ta juya tana kallon agogon wayarta,ta gama abinda ya shigo da ita gidan don haka tana tunanin komawa zatayi gida,don kasalar dake jikinta koda ta zauna ba zata barta tayi komai ba. Komai nata ta tattare tayi sign-in ta wuce parking lot,ta zuba duka tarkacenta cikin motar ta shiga ta tayar da ita ta fice daga gidan. ^^^^Motsa jiki yayi a safiyar na tsahon mintuna talatin da biyar,sosai yake jin kanshi fresh a safiyar,don jiya ya samu yayi bacci isashe ba laifi. Direct ya wuce toilet yayi wanka,ya dawo ya shirya kansa cikin long sleeve shirt da dogon trouser. Yayi wani fresh sosai kaman yadda zuciyarsa yake jinta da sauqin damuwa a ciki. Ta falo ya dawo yana duba abubuwan da suhail yayi kafin ya fita a gidan,bai jima ba yaron dake musu share share ya qaraso,sai ya matsa bakin window ya bashi space don ya gyara gidan. Idanunsa saman gidan,yana kallon abun hawa aba,abinda yake tabbatar masa da aba bai fita ba kenan. Yanason shiga yaga batoul da benazeer,ya kuma gaida ama,amma bayason aba din yasan da wanzuwarsa a unguwar,har yanzu wannan lokacin baiyi ba, yafison yayi nesa dashi,ya tabbatar hakan zai sanyata yaci gaba da jin kewarsa. Idanunsa ya mayar side din window dinta,idan ya rantse bazaiyi kaffara ba ya tabbatar ta wuce wajen aiki ne,barin hali sai mutuwa,sai kuma yanzun da ya tasamma sauyata. Murmushi ya kubce masa sanda ya tuna yanayinta a jiyan,indai har da gaske ne abinda yake gani cikin idanunta kishi ne hakan yana nufin akwai soyayyarshi koda bame yawa bace a zuciyarta?. Ajiyar zuciya ya saki,yana jin kewarta sosai cikin kowacce jijiya dake dauke da alhakin zagayawar jini a jikinta,to amma yanajin dole yadanyi step down kadan don yayi taste akan irin nata soyayyar a kanshi. Matsawa yayi daga jikin window din sanda wayarsa ta dauki tsuwwa,ya juya a hankali yana nufar wajen wayar,a yadda ya tsara din yau gaba daya bazai fita ba saboda shirye shiryen tafiyar da zasuyi shida suhail na sati uku. Haka kawai bayason yin tafiyar,don bayason yayi nesa da ama da twins dinshi,to amma kuma hakan ya zama dole,don daddy ya nema alfarma a wajensu su wakilceshi,daddyn kuma yafi qarfin kowacce kalar alfarma a wajensu. Tunda ya fita ya dawo ma bai duba wayar ba sai yanzun,tarin miscals ya samu,ciki harda na ayana wanda ya kusa guda goma. Yadan tsuke gira kadan,yana shirin yayi deleting na miscals din wani kiran na ayana ya sake shigowa. Hakanan ya daga ba don ranshi yana so ba,surutunta har hawan masa kai yakeyi,baisan inda ta gaji surutu ba,tunda dai shi yasan uncle tahir ba haka yake ba. Da dakakkiyar muryar nan tashi yayi sallama,sallamar data sanya ayana shiga taitayinta,murya ce me ratsa zuciya da qwaqwalwar wanda ake magana dashi "Good morning yaa haidar" "Morning,kina lafiya?" "Lafiya Lau nake,na kira ne na gaya maka yanzu haka ina airport,yau ne taho wana,transit daya zamuyi kuma,ina saka ran nan da wajen dare anan paris in sha Allah ina Paris" "Yayi kyau,Allah ya tsare hanya....." "Amma ya haidar......baka manta dai da alfarman da daddy ya nema min ba ko?" "Name?" Ya tamabayeta don shi bilhaqqi ya manta "Habba ya haidar........daddy fa ya gaya maka,kaine wakili na......ya wakiltaka akan al'amurana a cikin Paris" "Oh......,karki damu,muna tare da ama,kuma nasan She will do her best to take care of you.......ina da harkoki da yawa,ba komai ne zan iya concentrating akai ba" shuru ta danyi jikinta yana sanyaya,anya abinda take gani me sauqi ne zayazo da sauqin kuwa?. "I know yaa haidar....but kulan mace da namiji ba daya bane......" "She's the one who raised me......so that tana iya kula da 'ya'ya dari ma" ya datsi numfashinta. Yanajin yadda ta aje numfashi,sannan muryar qasa qasa tace "It's okay,saina qaraso" "Safe flight" "Thank you" ta amsashi tana jin dadin fatansa na qarshe a gareta. Iska ya furzar,ya soma gajiya da wadannan abubuwan,ga laila sai kuma ga ayana ta taho......ayana me sauqi ce a gareshi,laila dince yake komai da takatsantsan a kanta,ta yadda komai idan ya tashi qarewa tsakaninsu za'a yishi cikin girma da mutunci. Wayarsa ya mayar aljihu,ya koma bakin window din ya duba,ba motar aba,hakan kuma yana alamta mishi ya fita kenan,don haka ya koma ya zura lallausan fluffy dinsa yana fitowa daga gidan,yana buqatar ganin ama. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 105 Ya samu qofan a bude,don haka ya turata kawai ya shiga da sallama. Suna saman carfet sanye da wasu pink loungwear,an raba musu sumarsu me tsaho gida biyu,kowacce an kameta da pink din ribbon da ya dace da kayan jikinsu,sun yiwa building blocks baja baja a falon sunata qoqarin hadawa. Ama na zaune saman kujera,gabanta dan madaidaicin table ne da system akai,da alama wannan lissafe lissafen nata da ya santa dashi shekara da shekaru takeyi,akwai madaidaicin tray daga gefanta,da alama late breakfast zatayi ko kuma takeyi din. Building blocks din dake saman cinyarsu suka watsar sunata qoqarin tararsa. Tsaiwa yayi yana kallonsu murmushi ya subuce masa,kafin su iso sai ya goce,sannan kuma ya miqa hannu ya dauki benazeer. Baya batoul tayi tana kyabe baki alamar zata saki kuka "Daddy nifa?" "Benazeer ce bata da lafiya,baki gani ba har wadannan kumatun sun zazzage?....." Ya fada yana jan kumatunta wadanda da gaske sundan ragu,sai kuma ya dora da cewa "Kin manta kuma ke din babbace,qanwarki ce ita fa" hakan daya fada sai ya faranta mata ta fara tsalle,ya saku murmushi ya duqa yana miqa mata hannunsa,saita riqe ta tattakashi itama ta haye kafadarsa suka nufo ama,wadda a haka zaka dauka batasan me yake faruwa ba,saidai tana karance dasu. Duk sanda irin hakan zata faru ita kadai tasan farincikin da takeji, addu'a daya takeyi Allah ya sanyaya zuciyar sultana,tana da matuqar buqatar tarin jikoki,musamman da bata haihu da yawa ba,takanji kamar ta yiwa almu da saddi aure,saidai sunyi qanqanta sosai,amma tana ji a jikinta ko shekarun maina ba zasukai ba zata aurar dasu da ikon Allah. Da qyar suka bari ya gaisa da ama,suja tattaro masa blocks din sukace lallai shima ya hada nasa aga waye zaiyi abu me kyau. Yanata murmushi ya fara diban nasa,yana sane ya dinga hada shirme sunata masa ihu,sai ya narke fuska shima kaman qaramin yaro ya dubi ama "Ama kinga abinda sukema danki ko?" Tun bata kulasu har dole ta dinga sanya baki a ciki,ita ta dinga raba maki ba yadda ta iya. A daidai lokacin qararrawar qofa ta buga,tanja ta baro kitchen zata bude yace ta koma taci gaba da aikinta,ya tashi yana gyara hannun rigarsa daya tattare ya nufi qofar. Bata kawo komai ba sanda ta danna bell,don haka tana tsaye sosai tana jira a bude mata,duk ta qagauta ta qarasa cikin gidan,kwanciya kawai take da buqatar yi ko zata samu mode dinta da abinda takeji a jikinta ya koma daidai. Shi da ita duka basu tsammaci ganin juna ba,idanunsu suka sarqe waje guda,kowannensu sai ya kasa janye nashi idon,kamar masu kallon quda na wani sakanni,sai yayi hanzari janye idanunsa yana juya ciki jikinsa a mace. Duk wani feeling nashi da yake qoqarin dannewa yana controlling nasa tasa kakkaifar qwayar idanunta cikin qasa da second sittin ta rusashi,gaba daya ta saukar masa da kasala,ta tayar masa da wani irin abu cikin sassan jikinsa,amma duk da haka da yake namijinne da gaske, sai ya yaqi hakan saman fuskarsa,ya koma cikin yaran ya zauna sosai abinsa kamar dazu. Da qyar ta daga qafanta ta sanyo kai cikin falon tana yin sallama,kallo daya ama tayi mata ta karanci ba cikin daidai dinta take ba "Sannu da gida ama" ta furta tana qoqarin qaqalo murmushi,don ita kanta taji idanunsa har cikin tsakiyar jikinta,wani kakkaifan kallo daya tayar da kowacce tsiga ta jikinta,ya aike mata da wani irin saqo me nauyi,saqon da taji inama ace zaya shimfida mata kyakkyawan qirjinsa ta samu masauki a ciki,tana ji tana kuma tsammani a nan ne kawai zata samu sassaucin abinda takeji,a nan ne kawai zata samu nutsuwar da take da buqata. "Yauwa sultana......lafiya kuwa?" Ta tambayeta tana tattara hankalinta a kanta sanda ta matso kusa da ama din tana kwashe mata takardunta da suka zube a qasa "Laf.....fiya ama,na gama abinda najeyi ne" amsar data bawa ama din sai data sanyashi lumshe kyawawan idanunsa. Yanzu haka a wannan safiyar miliyoyin maza nawa ne suka kalle masa fuskarta?,anya zai qyaleta a haka kuwa?,zai iya ci gaba da yi mata wannan zurun?. "Gajiya ce kenan?" Ta sake tambayarta,saita gyada kai kawai ba tare da tace komai ba "Saiki shiga ciki ki kwanta ai ki huta sosai,may be idan kika samu bacci zakiji kin ware" "To ama" ta amsata tana riqe kayanta da kyau. Sai sannan benazeer da batoul da hankalinsu yayi nisa a wasa da daddynsu sukayi mata sannu da zuwa. Tadan saci kallonsa na abinda yayi qasa da second biyu sannan ta watsa musu harara "Sai yanzu kuka ganni?,banason sannu da zuwan" murmushi ya qwacewa ama,har sai data dora hannunta saman bakinta kadan ta maida jikinta bayan kujera tana lumshe ido "Yaro man kaza" ama din ta fada qasan ranta. Tanajin yaran suna fadin "Am sorry mommy.....am sorry mommy". "Naji" ta fadi,cikin dakewar da takeson nuna tsananin kamun kanta tace "Barka da rana" saidai tayi maganar ne tana kallon gabanta. Kamar baijita ba haka yayi mata,yasan daya daga cikin abinda bataso kenan. "Ina wuni" ta sake maimaitawa wani abu yana tsaya mata a wuya "Maina bakai ake gaidawa ba?" Ama tayi saurin kawo qarshen drama din "Oh.....sorry ban ganta ba,kina lafiya?" Ya amsa yana duba letter A cikin tarkacen building blocks din. Kasa amsa masa tayi,don tayi imanin idan ta bude baki kuka zata sake masa,sai kawai ta qara wuta ta wuce dakinta. Tana maida qofar suka hada idanu da ama,har tayi kaman ta jefa masa harara sai kuma ta dauke kai saboda wani tunani da tayi,bata harareshi ba amma ya fahimci harara taso jefa masan,sai ya qunshe dariyarsa yana dauke kai,ya maida kai ga yaransa. Tana ajjiye jakarta saman gado taji damshin hawaye ta eyelashes dinta,takai hannu ta tabosu,ta dawo da dubanta kan yatsun nata "Kuka kuma?,na me?" Ta tambayi kanta cikin qarfin hali,duk kuwa dacewa sosai takeji wani abu yana damunta a zuciya "No" ta fadi tana girgiza kai,tana gayawa kanta kada tayi kukan,tayi qoqarin hadiye komai,sai kuma taji zuciyarta tana bala'in tashi. Gefan gadon ta samu ta zauna,ta dinga jan numfashi me zurfi tana kuma fesar da wani,dukka a qoqarinta na daidaita damuwarta. Ta kusa kashe minti ashirin a haka sannan ta danji dama dama,sai ta tashi ta cire kayan jikinta,ta nemo riga da skirt free size masu taushi ta saka. Idan zata iya tunawa wunin yau babu abinda ta sanyawa cikinta,bata kuma jin yunwar kwata kwata,a cushe takejin cikinta,to amma kuma koma meye bai kamata takai har irin wannan lokacin ba tare da taci komai ba,don haka ta sanya baby hijab saman kayan ta fito kitchen ko zata samu wani abu taci. Qin yarda tayi kwata kwata ta kalli sashen da suke,ta maida dubanta ga qofar kitchen din da take tunkara,saidai duk da haka hakan bai hanata jiyoshi yana gayawa ama saqo ba "Zuwa dare idan Allah ya kaimu ayana zata iso,nace bari na gaya miki,zanje daukota around 8,don munyi magana da uncle tahir ya bani ita........" Bata bari ta gama jin sauran abinda yake fada ba ta shige kitchen din da sassarfa,ayana.....tasan ayana sosai,kusan mate ne ita da ayana din,duk a sannan ayana din ta bawa sultana shekara daya. Ama nason ayana don 'yar yayanta ne uwa daya uba daya,sannan a baya tasha jin uncle tahir yana tsokanar maina zai bashi ayana.....tun maina din yana dan makaranta. A birkice ta dauko fresh milk,ta bude da zummar tasha ko zata wuce da abinda ya tsaya mata a maqoshi,amma data sanya baki sai taji ba zata iya ba,don haka ta dauki qaramar tukunya ta juyeta a ciki,ta jefa citta da kanunfari da cardamom da kuma mint fresh mint leaves da basa rabo dashi,ta rage wutar can qasa,ta goye hannayenta a qirji ta zubawa tukunyar idanu tunaninta kuma yana lulawa wata duniyar ta daban. Sanda ama ta tashi tana shiga dakinta dauko wasu files ya samu ya miqe yana miqawa batoul gidan daya hada mata "Ina zuwa,bari na samo ruwa" ya fadi yana gyara bottom na rigarshi,ya soma takawa zuwa kitchen din. Tunda ta wuce hankalinsa yayi can,yadda ya karanci sultana yayi imani koda mahaifiyarta a yanzu da zata dawo duniya ba zatayi mata karatun da yayi mata ba,ya tabbatar daga jikinta har zuciyarta bata jin dadinsu,to amma wannan hanyar daya biyo ita daya ce sassauqar hanyar da zata kawo musu qarshen komai,don dukka wata jarrabawa da zaiyi game da ita ya gama yinta,ya kuma gama fahimtar inda ta dosa gaba dayanta. Tun kafin ya qaraso yaga madarar ta cika tukunyar tana kuma zubewa,yayi mamakin ganin tana tsaye a wajen amma bata lura da hakan ba,yadan qara sauri kadan ya isa bakin gas din ya kashe. Gilmawarsa ta sanyata ankara da shigowarsa amma saita gaza motsawa daga wajen,tana kallonsa ya dauki rariya da cup ya tace madarar,ya dawo kusa da kitchen cabinet inda take tsaye,ya bude ya dauko zuma ya zuba ya sanya spoon ya barta a wajen. Ya qarasa bakin freezer dake daya side din ya fiddo ruwa mara sanyi cancan sannan ya juya yana barin kitchen din. Samun kanta tayi da binsa da kallo,yana qarasa ficewa sai taji hawaye ya silalo mata,ta shafo hawayen tana kallonsu "Again?" Ta tambayi kanta muryarta tana rawa,kawai saiga wasu hawayen sabbi suna sake fitowa. "No.....no" ta fadi sau biyu a jere tana girgiza kanta,saita matsa gaban fanfo dake kafe a sink ta kunna,ta fara tarar ruwan tana wanke fuskarta dashi. A qalla ta kusa mintuna biyar a haka kafin ta samu nasarar tsaida hawayen,saidai abinda takeji a cikin zuciyarta bai sauya ba. Da kadan kadan take kurbar madarar,sai taji tana zauna mata sosai,a hankali ta shanye,wanda tun kafin takai ga ajjiye kofin jikinta ya sakeyin weak,wani kasala ya sake sauko mata,saita ajjiye cup din a daddafe ta fice a kitchen din. Yaga fitarta,ya rakata da idanu har ta shige dakinta saiya fidda ajiyar zuciya a sirrance yana dauke kanshi. Sosai ta duqunqune cikin duvet tana jin sanyi cikin qashinta kamar wadda zazzabin cikin qashi yake neman kamawa,ta lumshe idonta tana fidda numfashi,ita kanta zuwa yanzu ta tabbatar ba lafiya lau take ba,ta dinga karanto addu'o'i cikin ranta,cikin ikon Allah sannu sannu wani irin mahaukacin bacci yazo yayi awon gaba da ita. Batasan tsahon lokacin data dauka ba,itadai ta farka ta jiyo maganganu sama sama daga falo,da alama baqi ke dasu a gidan. Ta kalli agogo,saita miqe da dan hanzarinta zata wuce toilet,mararta taji ta murda,tadan dafeta tana yamutsa fuska,a hankali kuma saita saki,ta miqe ta wuce bandaki don daura alwala ta biya bashin sallar da yake kanta. Koda ta idar bandakin ta koma,tayi wanka da ruwa me dumi sosai sannan ta shirya cikin wata doguwar rigan kayan bacci me taushi. Ta taje gashinta da kyau ta dameshi cikin band,saita tsaya tana kallon fuskarta. Skin dinta ya sake fresh sosai,hakanan idanunta ma kaman sun qara girma da haske. Yunwa taji tana dan ji,hakan kuma ya mata dadi,don tanaso taci abincin sha'awar cinne bata jinsa. Juyawa tayi ta dauki wayarta ba tare data daura dankwali ba ta nufi falon,sam ta manta da batun zuwan ayana,hakan wannan lokacin tasan lokacine da daga su saisu a gidan. Sai data bude qofan ta soma isa falon sannan tunaninta na daxun ya fara dawo mata. Benazeer da batoul da kuma maina suna zaune saman carfet,sun sake sosai sun kuma yiwa wajen abinda suke so,sun batashi da abinci,ayana na duqe a gabansu tana qara musu miya da lettuce. Muryarta da tasu benazeer kadai ke tashi,alamun da zai bayyana maka lallai ita din ba baya bace wajen surutu da karadi. Yayin da hannun maina na hagu ke riqe da waya yana daddanawa tamkar hankalinsa baya kansu. Idanunta dukka ta zube akan ayana din, shirt ce a jikinta inner da top me budadden gaba,sai palazzo madadin kayan,wata irin hula ce kawai saman kanta,wannan ya sanya sumar da ta danyi gadonta ta fito ta qasan hular. Tayi kusanci da yawa da maina,ko luma bata sani ba idanunta ne suka nuna mata hakan?,koma mene sai taji ci gaba da kallonsu bashi da wani alfanu face wani abu me zafi da yake saukar mata saman zuciyarta. Tana zare idanunta daga kansu yana dago kansa suka hada idanu,tun fitowarta fitinannen qamshinta ya ziyarci.hancinsa. Kanta ta dauke,daidai sanda ayana itama ke qoqarin dauke kanta daga kan fuskar sultana, fuskar data rudar da ita da kwantaccen zallar sassanyan kyau. Tun sultana batakai haka ba tasan ita din me kyau ce,don kaf iyalin MAYAK'I ba wanda ya kamo qafarta, mutum daya ne suke gogayya,ya haidar din,aliyyu maina,to amma a yanzun zallar kyau aji da kuma nutsuwa me cakude da kwarjini da take gani tattare da ita yaso firgita zuciyarta. *_tofa,wanne ne ba wanne ba?,ga sultanar ama?,ga AYANA da take matsayin diya a wajen ama,wacce AMA da MAINA zasu zaba?_* *_tayi masauki cikin gidansu,kuma kusa da gidan MAINANTA,ya zata kaya?_* _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂 *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 106 Daga ayana har shi ta bawa banza ajiyarsu,taci gaba da takawa da nutsuwarta har ta isa dining area sannan ta dubi batoul cikin muryartan nan dake saurin janye hankalin me sauraro "Ina ama?" "Ta shiga wanka" benazeer sarkin karadi ta baiwa sultana amsa. Kai kawai ta gyada,saita maida idanunta ga kayan abincin dake saman dining din tana nazarinsu,daidai lokacin tanja ta fito daga kitchen dauke da nata kwanaon abincin. "Uwar daki kin tashi kenan" wani qaramin murmushi da baikai zuci ba sultana tayi tana dan shafa kwantaccen gashinta,murmushin da ya kusa sanya maina kasa controlling kanshi,don tunda ta fito ta wafci hankalinsa da tunaninsa,kowacce gaba dake jikinsa tana amsa kallon da yayi mata sau daya tak "Wallahi tanja......yunwa nakeji,kuma na rasa meye zanci a ciki" tayi maganar tana taba warmer din da tafi kusa da ita. "Ba zaki rasa ba kam,bari na bude miki ki gani" "Na gode tanja" sultana ta fadi cikin girmamawa da qauna. Matar ta jima tana hidima wa rayuwarta,ta dade tana nunawa rayuwarta kulawa da soyayya. Dukka abincin ta bude,ta zuba musu ido tana ci gaba da nazari kafin tace "Inajin pepper soup din catfish dincan zanci" "Yauwa nasan ba zaki rasa ba" tanja ta fada tana daukan plate ta soma zuba mata tana bata labarin program dinta na yau data kalla. Murmushi kawai takema tanja din,don sai taji haka kawai batason dogon magana,duk da taci gaba da surutanta da yaran,amma jikin sultana yana bata daga ita har maina din hankalinsu yana kanta,wanda ko sau daya bata waiwaya sashensu bama bare ta basu damar tunanin tasan sunayi. "Da kin zauna ai" sultana tace da tanja wadda ke nufin sauka tabar wajen "To ai sai na tayaki hirar" tanja din ta fada tana jan kujera ta zauna. A hankali da kuma kadan da kadan take diban pepper soup din tana sawa a bakinta suna hira da tanja. Duk da bakinta babu dadi amma sai taji ta samu appetit sosai,kafin wani lokaci sai gashi ta cinye tas "Yayi dadi tanja,xan samu qari?" "Me zai hana?" Ta amsata tana murmushi,sai tana plate din ta sake qara mata harma yafi na farko yawa "Zan iya cinyewa kuwa?" "Mummy zanci......" "Nima mummy zanci" muryoyin benazeer da batoul suka bata amsa. Baki tadan bude tana dubansu ba tare data bari ta hada idanu da wani tsakanin maina da ayana ba. Kafin ma tace komai har sun iso saman dining din,suka sanya hannu suka fara ci,sai batace komai ba ta maida kai tana cin tana musu qananun mitoci "Idan kika cinyemin ban qoshi ba tam,ni daku ne" tanja na zaune tana dariya,gami da mamakin cin kifin sultana,don ba abune data fiya damuwa dashi ba,dashi da nama duka basu wani dameta ba da zatayi musu cin qoshi. Nannauyan ajiyar zuciya ayana ta saki a boye,ita kadao tasan me takeji cikin qirjinta. Duk yadda takeso kada ta saci kallon sultana koda a boye ne amma ta kasa,ta kalleta ta kalleta har ta dinga jin ta raina kanta da kanta,a yanxun da take xaune tsakiyar yaran nata suna cin kifin saita dinga jin inama ace itace?,inama ace yaranta ne ita da maina?. Babu wanda zai kalleta yace itace mamarsu,haihuwace irin ta quruciya,quruciyarma iya quruciya ko ciwon kai ba'a gama sani ba bare ayi maganar girma. Tana jin kamar zata sare da maina din amma wata zuciyar tana bata qwarin gwiwa,abu daya ne da bata sani ba......har yanxun yana nan a matsayin mijinta,tana nan a matsayin matarsa ko kuwa?,bata da amsa,batasan kuma waye zata tambaya ba ta samu hasken da zai haska mata kalan takun da zatayi. Maida hankalinta tayi ga maina tanason janshi da fira,saidai kuma hausawa sukace miskili kafi mahaukaci ban haushi,gaba daya attention din da take buqata daga garesa ta gaza samunsa,wayarsa ya bawa kusan dukka a hankalinsa a idanunta,amma kuma ta wani gefen sultana ke daukan hankalinsa. Ya qware qwarai wajen iya satar kallo,wannan ya sanya ba lallai ka fahimci ita yake kalla din ba. "Alhamdulillah,ku matsa ku bani waje na wuce" sultana ta fada tana miqewa daga saman dining din bayan ta kammala cin kifin. "Idan ama ta fito kice mata na koma daki,zan duba program na next week in sha Allah" "To ba laifi" tanja ta fada tana matsa mata hanya. Tana sauka daga dining area din ama na fitowa,cikin shigar BOUBOU na wani material sassauqa ruwan bula wanda ya zauna mata sosai,ya kuma boye shekarunta,tamkar ba itace ta haifi maina ba,daya daga cikin dabi'un ama din dake burgeta qwarai wato ado da kwalliya,ta kuma tasirantu sosai dasu a iya tsahon zamanta da ita "Ama zan wuce daki,sai da safe" sulta tayi saurin fada sanda taga ama din tana kallonta "Zan duba wasu ayyuka" ta sake bawa ama uzuri don batason tace mata ma ta zauna a falon "To Allah ya taimaka.......ayana......ga yayarki kun gaisa kuwa?" Ama dake shirin zama saman kujera ta fadi. "Sultana ga ayana" aman ta kuma maimaitawa ganin sultana kamar bataji ba tana nufin wucewa ciki. Tsaiwa tayi da tafiyar ta juyo,idanunsu suka gauraya waje guda karon farko tun shigowarta falon. Zubin halittar idanun sultanar na dabanne,suna da wani irin kyau da koke mace kika kallesu sai sun burgeki,sun kuma bar miki kishi me yawa a zuci muddin akwai abinda ya hada tarayyarku ta fannin kishin "Barka da dare kina lafiya?" Ayana ta fadi tana qaqalo murmushin dole "Sannu ya kike?,ya garin?" Sultana din ta fada itama tana qoqarin arowa fuskarta sakewa. "Lafiya qalau,ya paris?" Ayana ta sake tambaya "Paris normal alhamdulillah.......kema gaki a cikinta" "Yes....... gaskiya ne,Allah dai yasa tana da dadi" ta sake fadi tana kuma karantar duk wani motsi na sultana. Qaramin murmushi ta saki mata,ta gaji da wannan tambayoyin marasa fa'ida da bataga ma'anarsu ba illa kawai bata mata lokaci da sukeyi,so take ta wuce daki gaba daya kifin da taci ma kaman yazo mata wuya ya zauns ne,bugu da qari wani abu daban kuma yaja hana numfashinta fita yadda ya kamata "Me na gaggawar tamabaya?,gaki a cikinta?,nan da sati daya ma qilan ke xaki bawa wasu labari" ta qarashe da wani murmushin. Idanu ta kada tana duban maina "Allah yasa haka......amma ya maina saika kawo taimako......tunda dai bansan ko ina ba ka sani.......sultana ki sanya baki ki tayani roqarshi kada yace a'ah" ta qarashe fadi a shagwabe. Har tsakiyar ranta taji abun,amma kuma har yanzun tana yaudarar kanta da ba wata alaqa tsakaninta da maina din "Sultana bare ce fa......kunfi kusa gaki gashi,ina da abinyi a ciki,lokaci kinsan yanzun sauri yakeyi,ko kai ka yankeshi ko kuma shi ya yankeka,goodnight, enjoy ur new home" ta fadi tana juyawa tayi ciki abinta. Da kallo ya bita ta qasan idanu har ta wuce ciki,qaramin boyayyen murmushin gefen baki ya saki,dole yau yayi rarrashi koda indirect ne,ya hangi abubuwa masu kaifi cikin idanunta da batasan tana fiddasu ba,uwa uba kuma fushi dake lasar zuciyarta. Ayana ba damuwarsa bace,shi yasan maganinta,hakama laila,amma zuwansu sai yake neman zame masa alkhairi,kaman sun pushing nata ne wajen matso abinda batasan yana ajjiye cikun zuciyarta ba,abinda taketa qoqarin yima kanta qaryar babu shi sam tattare da ita. Ta kusa minti biyar tanason controlling kanta da zuciyarta,ta zuqi numfashi ta fesar har batasan adadi ba amma abinda takeji yaqi ya sauka,gaba daya abincin da taci a wuyanta take jinsa,daga qarshe ta gasgata tabbas idan ba amayar dashi tayi ba ba zata samu sassauci ba,don haka ta wuce toilet kai tsaye,ta sanya brush a bakinta,zunguri daya kuma ta soma kelayashi kaman zata fidda 'yan hanjinta gaba daya a waje. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 107 Ta dade dafe da sink tana maida numfashi kafin fa samu numfashin nata ya daidaita,ta daga idanu tana kallon fuskarta da tayi jazur a mudubi. Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata,tasa hannu ta share,ta ware famfon ta tara hannuwanta tana wanke fuskarta gami da daura alwala. Gefan gadon ta zauna tana lumshe idanunta,tasa qaramin towel ta share fuskarta tana sauke ajiyar zuciya kaman jaririn da ya kwana yana kuka yake kuma buqatar lallashi. Saman gadon ta koma ta kwanta rigingine,ta rungume pillow tsam a qirjinta,idanunta a rufe amma batasan me take tunawa ba,tun tana a matsayin fakare har bacci yayi awon gaba da ita cike da wata irin kasala. Ficewarta daga falon sai yaji gaba daya zaman falon ya gundureshi,ya duba agogo a hankali sannan ya maida hankalinsa yana duban batoul da benazeer "Daddy zai gudu.....kuxo muyi sallama" ya fada yana miqa musu hannu. "Naga dare kaman baiyi ba ya haidar......tun yanzun?" Ayana ta fada tana kallon agogon hannunta itama "Ina da busy gobe in sha Allah" ya bata amsa yana miqewa tsaye,ya saka wayarsa a aljihun wandonsa hannunsa guda daya cikin hannun batoul da benazeer. Durqusawa yayi yayi kissing hannayensu,ya dago yana duban ama "Ama zan wuce...." Ya fadi yana duban idanunta "Allah ya bada sa'a ya kiyaye,Allah ya bamu alkhairi" ama din ta fada,daga tsakiyar idanunsa ta karanci addu'a yakeso,kawai yana mata kawaicin magana a kai ne. "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ya fadi yana juyawa "Bari na rakaka......ya haidar baka gayyaceni naga gidan ba" ta furta a shagwabe tana karya wuya "No,na yafe dare yayi...... goodnight" ya fadi yana nufar waje. Jikinta a mace ta koma ta zauna tana kallon hanyar da ya wuce din. "Ya kamata ki kwanta ki huta ayana......goben sai kiji dadin shiga school da wuri ko?" Ama ta fadi tana tarkata kan su benazeer da suka zube sunason fara bacci a gurin. ^^^^^Cikin farare qal din pyjamas yake takowa zuwa cikin dakin,hannayensa dukka biyun zube a aljihun wandonsa. Jikinsa na fidda sassanyan qamshin turarensa. A nutse ya maida qofar ya rufe yana jin wani shauqi yana ratsashi,yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Duk da dim light dakin yake dashi amma hakan bai hanashi hangota ba. Tana kwance miqe saman sofa da matsakaicin tsahon nan nata,ta rungume pillow tsam a qirjinta. Idanunshi fes a kanta har ya isa dab da ita,saitin kanta ya tsugunna yana kallon fuskarta,kallo daya yayi mata ya fahimci tunda ta shigo dakin a dazu bacci yayi awon gaba da ita. Gashinta dukka ya barbaxu saman pillow din kujerar da ta dora kanta. Dan qaramin bakin nan nata me labba masu sulbi ta turoshi gaba kadan,kana kallonta kasan cikin fushi tayi baccin. Murmushi ya saki yana tuna quruciyarta,wannan kwanciyar irinta takeyi masa shi ko bibi idan tana fushi,ba kuma me shawo kanta sai shi ko bibi din ko madararta,madarar da baisan har yanzu me ya rabata da ita ba,tasha gaya masa "Uncle......ko nayi aure ai zaka siyamin motar madara na tafi da ita ko?,kuma kaima tare xamu tafi ba zan tafi ni kadai ba kaman yadda aka yiwa su aunty chamsiyya" tayi tambayar ne a sannan cike da quruciya,tayi tambayar ne a lokacin ba tare da sanin me ma aure yake nufi ba,ashe shine mijin.......shine abokin rayuwarm.....Mallakinsa ce". Wannan tunanin da yayi ya haifar da raurawar zuciyarsa da kuma haihuwar wani abu me nauyi cikin qirjinsa da zuciyarsa,ya miqa hannu a hankali yana matsar mata da gashin da yake son rufe mata hancinta. Zama yayi sosai gabanta yana morewa kallonta,kallo irin me haifar da kusanci qwarai tsakanin zukata. Bayan wucewar kowacce daqiqa soyayyarta ke sake haukacewa cikin zuciyarsa,feeling sosai kallonta ke tayar masa,shi kansa yasan yayi mugun haqurin rashinta a kusa dashi, abinda bai taba kawowa zai iya ba. Cikin baccinta ta dinga jin qamshin nan nasa yana isa har cikin kwanyarta,ta dinga motsa idanu a hankali,hankalinta da yayi nesa da gangar jikinta ya fara dawowa. Shuru tayi bata nuna ta farka din ba,ta nutsu sosai wai ko xataji wani motsi daya danganceshi?. Cikin ranta ta dinga fatan jin motsin ko yaya ne,duk da har yanxu batasan meye silar da yasa takeson taji motsin nasa ba "Bs kowa,ke kadai ce dai" zuciyarta ta gaya mata. Qasan ranta taja tsaki,ta motsa tana son gyara kwanciyarta,saidai kuma batakai ga aikata hakan ba taji tattausan hannunsa ya lullube kafadunta. Har cikin ranta taji saukar tafukan hannayen nasa,da mugun sauri ta ware fararen idanunta da suka sauya launi kadan saboda bacci ta watsasu a kanshi. Tabbas shine,farin qaqqarfan ba'abzinen nan daya qaurace mata tsahon kwanaki,qauracewar da tayi awon gaba da dukka nutsuwarta...... qauracewar da batasan dalilin da ya sanya ta dameta ba har ya wuce iyaka. Da sauri tayi niyyar miqewa amma sai ya nuna mata mazantaka ya maidata kwancen,ya maye gurbin pillow din da take rungume dashi bayan ya zareshi ya aza mata nauyinsa. Kallon tsakiyar idanu yakeyi mata wanda shi ya kassarata,ya kuma zare mata duk wata laka daga jikinta,bai daina duban tsakiyar qwayar idanunta ba kamar kuma yadda bai dagata ba,numfashinsa da nata sukaci gaba da gauraya waje daya,hakan ya haifar musu da wani irin yanayi me matuqar nauyi cikin gangar jiki da zukatansu. Cikin qarfin hali ta soma yunqurin tureshi,amma sai yayi mata wani mahaukacin riqo,muryarsa da numfashinsa yana rarrabewa ya soma magana da ita cikin muryar can qasa "ita yake sharewa amma shike amsar hukuncin fiye da ita.....Allah ne kadai yasan yadda ya wuce dararen nan.......awanni da sa'o'i masu tsaho da suka zame masa tamkar shekarun da suke wanzuwa rayuwar dan adam cikin tsanani.......kekam wai babu zuciya ne a qirjinki......ko sau daya mana ki gayamin cewa MAINA NAYI MISSING DINKA YADDA KAYI KEWATA NIMA" ya qarasa fada da wata iri murya yana kuma hade fuskokinsu guri guda,hancinsa yana gugar nata. Idanunta kawai ta mayar ta rufe saboda abubuwan daya aike ma jikinta ita kanta tasan bata isa ta kauce musu ba. Hakan yake nema dama daga gareta,ya kuma fahimci aikinsa na farko ya fara isar masa da saqon yadda yakeso,don haka ya zura hannunsa ta gefen kunnenta ya shafo wuyanta da wani irin salo da ya sanya ajiyar zuciyar da bata shirya fitarta ba kubce mata "Ke bakya kewar mijinki?" Ya sake jefa mata tambayar yana lalubar bakinta. Batasan amsar da zata bashi ba,baima kuma bata daman yin hakan ba ya bame bakinta cikin nasa. Wani irin zazzafan saqo ya shiga aike mata,wanda girmansa ya Sanya sofa din da suke kai ta gagara daukarsu shi da ita,suka zame a hankali zuwa qasan carfet din,jikinsa gaba daya rawa yakeyi,kaman yadda nata jikin ya dauki kakkarwa,tanata yunqurin janye hannunsa amma ina bai bata wannan damar ba,sake shigewa jikinta yakeyi yana kuma sake boye fuskarshi sosai cikin jikinta a duk inda yaga yayi masa,a kuma wajen da duk yake da muradin hakan. Bata tayashi da komai ba,amma kuma ya samu cikakken hadin kan da bai taba samu daga gareta ba,ko a guri daya bata yi yunqurin hanashi ko dakatar dashi ba daga abinda ya nufa. Ita a karan kanta batajin zata iya hanashin,jikinta ya sauka daga dukkan wani tsari data dorashi akai,tahau wani bigire da ita kanta batasan yaushe ta soma hawa wannan layin ba,saqonsa ya isketa fiye da yadda ta saba jinsa. Kuka ta sake masa tana juya baya bayan komai ya kammala. Dariya ce taso qwace masa,ya cusa kansa a tsakiyar bayanta tana fidda qaramin sauti gami da janye bargon data duqunqune a ciki. "zo kiji mummy twins" ya furta yana qoqarin birkitota. Jikinta ta hade guri guda taqi bashi wannan damar,da gaske rigima takeyi masa,don ya gama sanyata ta kunyata iya kunyata,ita kanta tasan ta saki layi fiye da yadda ya dace,batasan da wanne ido zata kalleshi,ya sakata shallake iyakoki sosai. Har yanxu dariyar ke cinsa,ya sani shi da kansa yasan yau din baibi mata ta sauqi ba,ya sani duk dauriyarta......duk kafiyarta......koda wani irin mahaukacin qiyayya take masa a yau din layin da ya dorata akai dole tabi. "Ba wani kunya mummyn twins......ba wanda yasan fa me ya faru.......daga ni saike fa.....kome kikayi lada za'a rubuta miki......kuma kome kika fada na miki uzuri nasan cikin yanayi kik......." "Me kuma nace?" Ta tambayeshi da sauri,sai ya saki dariya har yana cusa kansa a pillow. Dariyar tasa ta sanyata ta tsargu,itakam yau ta shiga uku,ba zata iya tuna da meye da meye ta fada ba bare tayi gyara,Allah ne kadai yasan irin baran baramar da tayi kenan,sai kawai ta sake fashewa da kuka tana cusa kanta a qafafunta. Har tsakiyar zuciyarsa yakejin sautin kukanta,ya lumshe idanu yana dakewa sosai "Tashi muyi magana......" "Banaso......ka barmin dakina" ta fadi tana kuka da gasken gaske "Bazan fita ba indai baki tsaya munyi magana ba.....hasalima a nan din zan kwana kinji na rantse" yana kaiwa nan ya hantsilo daga gadon, cikin nishadi da kuma jin kansa da yakeyi fresh ya shige bandakinta. Kasaqe tayi tana sauraren saukar ruwansa a bayi. Abinda bai taba yi ba kenan,ga qoshi ga kwanan yunwa,tasanshi farin sani,kuma ita zata fada bada labari a kansa,baya rantsuwa bai cika ba,da gasken idan bata saurareshi din ba xai kwana a dakin nata?,baya tsoron ama ko aba su ganshi?,baya tsoro ko kunyar idanun kowa?. Wadannan tambayoyin suka tsaye mata a rai,ta rasa wanne zata zaba,ta murje kunyarta ta saurari abinda zaice ko kuma ta barshi taga iya gudun ruwanshin,da gaske zai iya kwana din?,to meye ma wai zaya gaya mata bayan ya gama sanyata ta barar da mutuncinta?. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 108 Tana jin motsin fitowarsa ta maida idanunta ta kulle,ita batajin zata iya sake hada idanu dashi. Ta cure waje daya tana neman gurin cusa kanta taji anyi cak da ita "Leave me please......ka sakeni......banaso" birkitota yayi ya lullubeta tsakiyar qirjinsa yana cewa "Da alama baki biya bashin nan da kyau ba,shi yasa bakinki yake iya magana har haka" ya qarasa maganar yana laluben bakinta. Bam ta bameshi ta cusa dukka labbanta cikin bakinta. Qaramar dariya ya saki,yayi maganin mitarta hankali kwance. Duk ta firgice kada yace shi zaya wanketa yadda yakeyi mata,itakam yanxun ma gaba daya lamuransa tsoro suke bata,nema yake ita kanta ya sauyata,so yakeyi yayi mata dole ya kuma shiga rayuwarta ta qarfin gaske. Sai daya gama hada mata komai,hatta towel da zata buqata idan ta gama sannan ya soma ficewa daga toilet din da baya da baya yana cewa "Karki dade a ciki.....idan ki gama ki kirani" ya hada hannayensa biyu ya mata sign na heart sannan ya juya yana ficewa. Wata doguwar ajiyar zuciya taja tamkar zata tsinke jijiyoyin zuciyar dake jikinta,ta sauke numfashi tana bude idanunta taba duban hanyar daya fice din. Batasan me yakeson sauyata ba kwata kwata,da gaske yake rikita mata tunani bayan ita a yanzun bata shirya faruwar hakan ba. Tana wankan qwaqwalwarta ta dawo mata da komai daya faru tsakaninta dashi mintunan da suka shude,ita daya a toilet din ta dinga jin wani mugun nauyi da kunyar kanta da kanta,komai na jikinta a yanzun ta tabbatar babu abinda baisan gwajin yawansa tudunsa zurfinsa da kuma fadinsa ba. "Innalillahi" ta fadi tana tara ruwan hawaye,me yasa ta barshi tun sanda ya fara abun batakaj qararsa ba?. "Wajen wa?" Ta samu kanta da tambayar kanta da kanta "Ama ko aba?" Ta sake tambayar kanta. Kai ta girgiza,abunma sam baiyi ma'ana ba,takai qararsa tace me?,yana shigowa gidan?,yana kuma shigowa dakinta?,idan ya shiga to meye yayi mata daya cancanci takai qarar?. "Tace gana k....." "Subhanallahi" ta fadi a ranta da sauri,ba zata iya gayawa ama da aba wannan maganar ba,kenan koda zatakai qarar ma yana da hujjar musa mata?,yana da kuma hujjar kare kanshi tunda ita din dai bata da wata qwaqwqwarar hujja. Wankan ta farayi amma har a sannan bata haqura ba,so takeyi lallai ta samo hanyar da zata yakiceshi,tana tunanin kamar zata iya din,kaman yin nesa dashi din ba komai bane a wajenta,batasan ya riga yayi mata dashen da rayuwarta ma ta soma dogara da fitar numfashinsa ba. Tana yi tana zancan zuci ita kadai,tana wassafa yadda zata fita daga toilet din "Wai ta yaya ma zaki iya kai qararshi wajen ama?.....shin kin manta cewa ita din uwa ce?" Tambayar data sanyata tsaiwa cak daga goge sumarta da takeyi da towel. Gabanta ya fadi tana maimaita kalmar uwa,saita koma da baya ta zauna kawai a toilet seat. Dukka zamannan sam sam ta manta da batun ama ba ita ta haifa ba MAINA ta haifa. Ta manta da zancan cewa ba zata taba qin maina ba saboda ita,wannan yana nufin duk abinda takewa maina kenan ama tana jun haushin hakan?,to amma me yasa?,me yasa ama din bata taba nuna mata ba ko a fuska?,wacce irin jarumar uwa ce ita dake iya shanye qiyayyar da ake nunawa dan cikinta?. Ta dade xaune a haka tana son tuno wanne iri da wanne irin rashin kyautawa ta yiwa maina a gaban ama tsahon zamansu,to amma abun da yawa, lokacin da tsaho ba zata iya riqewa gaba daya ba,dole ta gaji ta miqe tana daure bathrobe din jikinta sosai da nufin idan ta koma daki ta sauya kaya. Idanu ta fidda sosai ganinsa kwance dai dai abinsa saman gadonta,da alama ma ya fara bacci ne abinsa. Tsoro sosai ya kamata,ta kalli agogo,uku saura na dare,ta yaya zaiyi mata bacci a daki?,bata tsoron asuba ta riskeshi suje suyi kacibus da wani cikin gidan?. Cikin sanda ta dinga takowa har ta iso gefan gadon ta zauna. Idanunta suka sauka saman kyakkyawar fuskar nan tasa dake da wani irin kwarjini,ta qura mishi idanu tana kallon fuskokin su benazeer cikin tashi,wani lokaci kuma sai ta dinga hangen tata fuskar kadan kadan. A baya sanda yake matsayin uncle mafi soyuwa a gareta tafi kowa jin dadi idan akace suna kama,amma daga baya sai ya zamana muddin zaka ce suna kama da yaa maina to ka tarowa kanka masifa,ranan babu me rabata da kai sai Allah,ta dingi mita har sai bibi tayi kaman ta bugeta,amma sai gashi a yau din da idanunta tana hangen gaskiyar maganar quru quru. Idanun ta janye daga kallonsa,tayi masa kallon da bazata iya tuna lokaci na qarshe data yi masa shi ba,idanunsa na ganin kyawunsa zuciyarta nata avoiding,zuciyar kuma na karbar wani saqo da batasan daga wanne guri ya taso ba.......amma taurin kanta da jin cewa ba komai game da ita daya shafeshi ya hanata yarda da hakan. Maida dubanta ta sakeyi,da gaske lokaci yana tafiya,kuma awanni kadan suka rage lokacin sallar asubahi yayi,tayi imani kuma muddin ama ta samu maina a dakinta a yau dai ba ita ba kwanan paris,tana kyautata zaton saidai ta kwana a nijer. Hannu takai zata tasheshi sai kuma ta janye zuciyarta na gargadarta da kuskuren tabashi,ta dunqule hannun nata tana wassafa yadda zata tasheshin,bata da wata mafita don haka ta sake kai hannu,saidai yanzun ma kuma janye hannun nata tayi kamar me tsoron taba wuta. Sake kallon agogon tayi, tafiyarsa yakeyi bai fasa rage tsahon mitunan da suka rage musu ba,sai ta sakejin hankalinta ya kuma tashi. Motsi ta jiyo daga bakin qofarta kaman ana shirin mata knocking,ai batasan sanda ta sake kai hannu da zummar tashin nasa ba. Tattausan hannunsa da yayi wani dumi ya miqa ya jawo hannun nata da sauri ya aza saman kuncinsa sannan ya lullube bayan hannun nata da tafukan hannayensa. Da sauri ta dauke kanta daga kallon qofa da ta tafi yi ta dawo dashi kansa,saita samu zagayayyun lion eyes dinshin nan fes saman fuskarta yana kallonta da narkakkun idanun nan nasa da a yanzun suke matuqar bata tsoro. Kallon kallo suka yiwa juna na wasu sakanni,yana lumshe idanunsa yana kuma budesu dukka lokaci guda,shi daya yasan me yakeji a kanta,bai taba tsammanin watarana zai jarabtu da soyayyar 'yarshi ba,koda kuwa a wasa ne.....wancan lokacin..... wancan ranar da komai ya afku ya zame masa alkhairi. Kalmar FYADE shikam zai iya cewa alkhairi ce a tattare dashi,banda furtatan da tayi yayi imani da tuni a yanzun ita din ta zama mallakin wani. "Kinason kallona amma gulma ya hanaki ko?......am aliyyu maina,not yaa maina da kika sani shekarun baya.....ni naki ne yanzun.......ba maina yayanki kuma uncle dinki da kika sani ba" sosai kalamanshi suka sauka a zuciyarta,amma kuma tana cikin tsoron da bata da nutsuwa "Don Allah...... please na roqeka,ka tashi ka tafi tunda ka gama abinda ya kawoka..... inajin motsi kada wani ya shigo ya sameka a nan" ta fada a mugun narke sannan kuma a karye tana daga hannunta guda daya da bai samu ya riqe ba alamun roqo. Sanda taga ya motsa ta zaci tashi zaiyi ya tafi,sai taga ma ashe dogara gwiwar hannunsa yayi saman gadon,ya kuma tallafe kumatunsa yana sake qare mata kallo. Yadda tayi masa shagwabar nan ta sake tsumashi sosai,ta kuma sake tuna mashi da little sultanarshi,wani shauqinta yakeji kamar ya dauketa ya boyeta a inda idanuwa basu isa sukai wajen ba "Pleeeeassseee ya mai......" "Uhmmm.......say it.....i missed the way you are calling me YAA MAINA" Ya fada yana lumshe idanunsa dake kafe har yanzu a kanta yana fidda murmushi. Kanta ta kawar, calmly yake magananshi kaman baisan wanzuwarsa a wajen bai dace ba,ta fahimci abinda ma take hange shikam bashi yake hange ba "Please" ta sake fada a mugun karye ba tare data kalleshi ba. Hannunta dake cikin nashi ya matsa "I love it......inaso naji kina begging dina......but ba'a irin wannan yanayin ba,ba kuma a irin wannan muhallin ba.........inason wata rana tazo da zaki dinga begging dina kaman haka akan kinaso na kasance dake......,mu raye wani dare......." Wani zabura tayi a gigice kaman wadda aka watsawa kunama,abinda ya sanya zancansa yankewa ba tare daya shirya ba saboda dariyan da yaso kamashi,waishi baya jin nauyin fadin maganganu har haka?,yana mantawa ita din wacece?,qaramar sultanar nan daya raineta?,yana mantawa ne wai?. "Already na gaya miki af first,idan baki saurareni ba a nan zan kwana ai ko, right?" Da sauri ta juyo a hargitse da firigitattun idanun nan nata tana dubansa "Na saurareka,tell me please" tsareta yayi da idanu kafin ya saki wani tattausan murmushi "It's too late madam sultana......baki saurareni ba saboda rad'in kanki,kin saurareni ne don tsoron kada azo a ganki da kwartonki ko me miki fyade kullum?" Ya furta da wani qaramin murmushin,saboda xuwa yanzun kalmar ta zame masa wani abu na daban cikin rayuwarsa. "No....." Ta fadi cikin nuna karaya "Oya.....zo muyi bacci.....bazan iya gaya miki komai ba yanzun don bacci nakeji,kin gajiyar dani" ya furta duka lokaci daya yana birkitota cikin jikinsa. Wani kyakkyawan boyo yayi mata cikin qirjinsa,ya bata skin to skin contact me kyau wanda ya sanyaya mata kowacce gaba ta jikinta,tsoron kada ya zamana wani ne a bakin qofar dakinta ya sanya bata ko motsa ba tayi luf,saidai kuma qirjinta bai fasa bugawa ba da tunanin ta yaya zai kwana mata a daki kuma ya fice daga gidan salin alin ba tare da kowa ya ganshi ba?,ta sanshi shi din fada da cikawa ne,tunda ya dauki aniyar kwana tayi imanin bata isa ta sauya masa ra'ayi ba,sai kawai ta maida idanunta ta rufe tana ambaton "Rabbi sallim sallim" cikin qasar zuciyarta,tana jinsa sanda ya saki wata wawiyar ajiyar zuciya yana furta "Thanks" da tausasashen sauti,yana tsammanin tayi shuru ne don ta bashi hadin kan samun nutsuwa da bacci me kyau,baisan meke yawo cikin zuciyarta ba,hanyar da zai fita daga gidan ba tare da ya kunyatata ya tona musu asiri ba.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 109 Tun kafin a kira sallar asuba ta tashi,ta daura alwala ta zauna tana raba idanu,amma a zahiri ta nuna kaman tana jiran ayi kiran sallar assalatu ne,a qasan zuciyarta kuwa tana fata ya tashi ne yayi alwala ya fice,ita koda baiyi alwala bama din indai zaibar mata daki buqatarta ya biya. Yayi likimo kaman baisan meke faruwa ba amma yana sane din,ya danne dariyarshi kawai yana mamakin yadda tsabar rigimarta ta hana mishi barci itama kuma ta hana kanta,tanayin abune kamar wadda ta kawo kwarto. Yana sane ya sake miqewa sosai cikin duvet,bai kuma tashi ba sai da aka kira assalatu. Hankalinshi kwance ya wuce toilet dinta,bai jima can can ba ya fito daure da alwala,ta bishi da kallo tana addu'ar ya fita amma sai taji yana bata umarnin ta shimfida musu darduma ya jasu jam'i. Da hanzarinta tayi komai tana zaton zai tafi idan sun idar,amma da suka idar din sai taga yayi zaman yin azkar din safiya. Nutsuwarta ta fara yin qaura daga gangar jikinta sanda taga alfijir yana neman ketowa,ta kasa azkar dinma gaba daya,sai idanu da take fama binsa dashi tana satar kallonshi. "Ki nutsu kiyi azkar dinki,nima nan din gidanmu nefa,bawai baqo bane" ya bata amsa da dakiyar nan tasa yana kallon qibla ba tare daya dubeta ba. Duk yadda taso ta nutsu din ta kasa,saita soma sarewa sanda taji wucewar tanja har sau biyu zuwa kitchen. Dukka dauriyarta ta qare sanda taga ga kammala azkar din,ya miqe yana sake wucewa zuwa gadonta. Muryarta ta dauki rawa ta dubeshi "Amma...... amma fa safiya yayi.....baka kalli agogo ba?" Girarsa ya dage mata dukka biyun sanda ya jingina da fuskar gadon "Wannan ce gaisuwan barka da safiyan?" Nauyinsa kuma taji ya kamata,abinda ya kamata ace tayi ne batayi ba,sai tayi qasa da kanta don yadda ya tsareta da idanun ya mata nauyi "Barka da safiya,ina kwana?" Murmushi ya sake kadan,yanajin inama zasu tabbata a haka ita dashi,sai ya miqa mata hannuwansa daga nan inda yake yana cewa "Gaisuwan nesan nan bana sonta,zo kiji" ya furta yana lumshe idanunsa,feelings da yake samu a duk lokaci irin wannan yana motsa masa. Maslaha take nema,so take ta lallabashi ya fita tun aba da ama idanunsu baikai kai ba,don haka ta miqe a sanyaye tana takawa gareshi. Da idanu yake bin kowanne taku nata,kowanne sashe na jikinta yana motsawa cikin wani salo kamar wanda ake bawa umarni,idanunsa suka qara qanqancewa,kishinta ya wani cikashi har ya dinga jin kamar zuciyarsa na matsewa. A hijab yaga dukka kyakkyawan surarta,ina ga sanda take cikin veil ko scarf?,ina ga sanda ta sanya abaya ko gown,anya kuwa zai iya ci gaba da xuba idanu?,xai kuwa iya tausa zuciyarsa yadda yaso yayi daga baya akan ya qyaleta ta mori karatunta?,aikin gidan tv fa?,abune da yake international ba iya state daya ba ba jaha daya ba na qasa baki daya. Hannunsa ya sanya ya riqe dogayen siraran yatsunta yana kallonta,muryarsa tayi laushi sosai da wani irin duka da kishi yayi masa "Please......ko menene,ko yaya ne sultana.....ki taimakeni,ki rufamin asiri ki killacemin kanki.....i swear bazan iya dauka ba,zuciyata me rauni ce a kanki,bazan iya jurewa ba naga wani ko wasu suna kallemin ke......" Bata yarda abinda yake fadi da gaske bane dai da yaja hannunta saitin qirjinsa,da gaske zuciyarsa bugawa takeyi,har abun ya bata tsoro ta janye hannunta da sauri tana kallon fuskarsa. Raunannen murmushi ya sakar mata yana kallon cikin idanunta "Har yanzu maina shine nada,ba abinda yake sanyashi sauya magana.....so that kada ki damu da zamana dakinki don sai na qarasa hutawa.....karki damu ya waye zai ganni?,yaushe zan fita?,duk kada ki damu,ina da ragowar lokaci kafin na fita,zaki iya joining dina kafin lokacin walaha,karkiyi stressing kanki too much da tunani..... please" ya qarasa fada yana hade hannayensa waje guda alamun roqo. Eh tabbas yaa maina na baya shine yanzun,wasu dalilai yasa take gani kamar ya canza amma bai canza ba din da gaske,ta saki baki tana kallonsa sanda ya shige duvet yana sake qudunduna da kyau,muryarsa can qasa ya sake cewa "Join me please mummy twins" ji tayi kaman da gayya ma yake roqonta, saita dauke kai tana zamewa a wajen ta zauna sosai kaman me gadinsa,itadai tasan ya gama da ita,lallai yau da alama ranar shan kunyar su ne daga ita har shi ya kama,to amma zata iya cewa ita daya din,tunda shi koma meye zai faru shi ya jawo,kuma tunda yayi hakan tasan akwai abinsa ya taka. Duk wucewar mituna tana irge dashi,rana na sake fitowa fargabarta yana qaruwa,ta dora kanta saman gadon a hankali tana kiran sunan Allah,fatanta daya ya tashi ya fice salin alin. Knocking akayi wanda ya sanya 'yan hanjinta hautsinewa,tayi qoqari da qyar ta gyara muryarta qasa qasa,ta kalli inda yake kwance baima san anyi knocking din ba,ta sake maida dubanta ga qofar sanda ake qwanqwasawa Karo na biyu "Waye?" Ta tambaya adan tsorace "Mummy mune.....BB" "Get out ko CC ne,da safen nan?,to ban tashi ba" "Mummy ki bude mana don Allah,yau Halloween party ki duba mana kayan nan" "Benazeer.......sa'arki ce ni?,zaku bacen a wajen ko sai na fito na bubbugeku?" Ta fadi a harzuqe tamkar su suka sanya daddynsu yayi kwance kwance a dakinta😂. Tana jinsu suka juya jiki a sanyaye,ta zuqi iskar ta fesar tana ware idanunta,cikin ranta tana addu'ar Allah yasa kada yaran su matsa da yawa,kuma kada Allah ya kawo wani. Sau biyu taji sun sake wucewa da tanja zuwa kitchen,saidai ko motsi me qarfi taqiyi bare suyi tunanin idanunta biyu. Awa guda ba kadan aka sake buga qofan,yanzunma dai a hasale ta soma magana "Batoul ku fita a ido na fa?" " Da sukayi me?" Taji muryar ama tana tambayarta daga bakin qofar. Wani gumi taji ya karyo mata "Innalillahi" ta fadi da muryar rad'a tana ware idanu "Tashina sukeson yi ama.... Kuma....." "..... Kuma me?,yau baki da aiki ne?" "Na dauki hutu ama sai next week ana gobe zan sake program" ta fada tana hadiye wani yawu me kauri a maqoshinta "To yayi,kizo aba dinku yana kiranki......but kada ki wuce minti talatin don fita zaiyi" "Gani nan ama" ta fada da sauri. Yadda take amsawar ya bawa ama mamaki,tadan tsaya jim "Are you okay?" Ta tambayeta tana kallon qofar dakin "Yes am....ama" "Budemin qofar dai" ta fada tana jin bata gamsu da yadda muryarta ke fita ba kaman a tsorace. Maida dubanta tayi ga maina a tsorace,hankalinsa kwance,hasken safiyar ya haske fuskarshi ta wani sake fresh. "Sultana" ama ta sake kiran sunanta "Gani nan ama ina saukowa daga gado ne....." "Alright.....daga baccin kika tashi ashe.....karki zauna kizo kiran aba dinku" sai taji ama din ta juya tana barin wajen. Ido ta lumshe tana yada kanta gefe hadi da sakin ajiyar zuciya "Matsoraciya" taji ya fada da muryar bacci. Da sauri ta daga kai cikin mamakin dama duk abinda akeyi yana jinsu?. Tun bugun dasu benazeer sukayi suka katse masa baccinsa,sai baccin ya zama ba wani me nauyi ba,yanajin komai amma kwanciyar ta masa dadi shi yasa yaqi tashi. Idanunsa ya bude sai idanunta cikin nasa,ya ture duvet din ya miqe yana zama sosai saman gadon. "Am starving......me zan samu?" Ya fadi yana lumshe idanunsa. Gaba daya zuciyarta ta karye,ya qarasa gigitata,sai kawai ta sakar masa hawaye. Ta yaya zaice zaici wani abu?,salon ta fita dauko masa wani ya shigo?. Tsaiwa yayi yana kallonta,kaman bazaiyi magana ba sai ya rusunar da idanunsa yana cewa "Banason kuka.......tashi ki shirya kije kiran aba" "Ni a shirye nake" ta tari numfashinsa,sai kuma hankalinta ya dawo jikinta sanda taga yana bin jikinta da kallo. Tabbas yamutsewarta da yamutsewar jikinta kadai zai sanya ka saka mata ayar tambaya. Baice komai ba ya sauko ya a nutse daga gadon yana wucewa toilet,sai tayi amfani da wannan damar ta wuce wardrobe dinta tana laluba abinda zata sauya din. Allah ya taimaketa ta shirya cikin sauri, doguwar riga ta saka daga ciki sannan ta dora babban hijab har qasa. Tana gyara madaurin fuskar hijab din ya fito daga toilet din,ta gefan ido ta saci kallonsa sai akaci sa'a shima ita yake kalla din,ta masa kyau qwarai,hijab din ya wani qara mata kwarjini sosai,ta dauke idonta tana qoqarin gyara igiyar,sai yayi taku hudu ya qaraso gareta. Hannunsa ya sanya saman nata,dumin hannunsa ya ratsata,sai ta zame hannunta da sauri,hakan ya bashi daman gyara igiyar ya daura mata ita saman tulin gashinta data nannade ya zamana kamar ribbon ta sanya. Ta saman kafadunta ya zura kanshi yana kallon kyawawan idanunta ta cikin madubi "Zaki tafi baki sake tambaya na me nakeson gaya miki ba.......well,na cinye abuna nima......yanzun ace aba ya tambayeki idan kinje......me ya kawo aliyyu dakinki yake kwana wanne amsa zaki bashi?" Ji tayi kaman a gaske aba dinne yayi mata tambayar,saita juyo a rude suka hada idanu,ta dauke kanta kuma da sauri tana jin tana dirircewa. Murmushin gefan baki ya saki, yayi taku biyu da baya da baya "If kuma ya tambayeki kinason maina?,zaki koma dakin mijinki?,wanne amsa zaki bashi?" Ya jefa mata tambayar yana kallon reaction nata ta cikin madubi. Qin daga idanunta tayi bare ya samu damar kallon qwayar idanunta,abu daya taji har cikin jininta ya jefeta da wata magana me girma. Ta qarasa ta zira slippers dinta ta soma takawa a hankali shi kuma idanunsa yana biye da ita,ta tsaya cak sanda ta isa bakin qofa,ba kuma tare data waiwayo ta dubeshi ba tace "Zan gaya masa bana sonshi......ban kuma taba sonshi ba,bazan kuma koma ba.....idan zaka fita daga dakinnan kayi qoqari kada wani ya ganka please" daga hakan kamar wadda ke tsoron za'a kamata ta taka da sauri tana fita a dakin. Qas yayi da kansa yana jin maganarta na shiga ranshi,baiga fuskarta ba bare ya karanceta ta cikin idanunta,saboda haka bashi da tabbas din abinnan da take gaya masa gaskiya ce ko qarya tsagwaronta,koma meye take fada yaji saukar furucinta sosai,wani qaramin murmushi da baisan a wanne gida ya ajeshi ba ya qwace masa "Saina sanyaki kin qaryata kanki da kanki da bakinki......wallah.....indai na haifu jinin aba......saikin qaryata kanki cikin mutane sababin yadda kika fadi maganarki a sirrance" ya fadi a fili murya a qasa. Ya fahimci abu na qarshe da bataso shine asan yana cikin gidan cikin dakin,kanshi tsaye hannayensa zube a aljihun wandonsa ya fara dosar fita daga dakin gaba gadi,kanshi kuma tsaye,duk da yana jiyo muryar ama benazeer da batoul daga falon.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 110 Cikin nutsuwar data roqa Allah ya bata kada wani cikin gidan ya gano komai tattare da ita take fitowa a dakin. Ayana itace ta farko da suka fara kacibus,tana tsaye tana kurbar wani abu cikin mug,jikinta sanye da pajamas masu dogon hannu da dogon wando,kanta sanye da qaramar hula. Sultana ce ta fara dauke idanunta daga kan ayana din. Haka kawai batason wannan kallon da take tsireta dashi,kuma sam tana jin jininta dana ayana bai hadu ba kwata kwata,tana da zaqewa hali guda daya da sultana taqi jininsa kenan. Ci gaba tayi da fitowa cikin falon,ta gota ayana din ba tare data waiwayeta ba. Wani abu me tauri ayana ta hadiya hade da madarar da takesha,ita kadai tasan yadda takejin matsanancin kishin sultana cikin ranta,bayan kishi tana kishin yadda ta fita da komai,duk kuma yadda taso gano makusar sultana ko aibunta ta gaza ganowa,hasalima duk wani move nata sai yakeson ya dinga burgeta,kama daga yanayin takunta,salon yadda take magana da kums kallo,komai bisa aji da wani irin tsari. "Good morning" ayana tace da sultanar sanda take giftata, saboda tayi imani ama zatace ta gaida matar yayanta ne,sunan matar da ama ke bawa ayana yana sanyata a nazari,da auren ko babu?,idan da auren bataga alamar wani good relationship tsakaninsu ba. Adan dake sultana ta juya tana qoqarin dora murmushin dole kan fuskarta "Kin tashi lpy baquwar Paris?" "Alhamdulillah" ayana ta amsa tana lumshe ido jin yadda sunan PARIS din ya fita a bakin sultana tarwai kaman don ita aka sanyama garin sunan. Daga haka sultanan bata qara ba tayi gaba wajen yaran da ama. Tana riqe da hannun benazeer da batoul suna gaidata,amsa musu takeyi amma kaf hankalinta ba'a kansu yake ba. Gani takeyi kaman zai fito yabar dakin,tasan halinsa komai ma zai iyayi,bashi da tsoro,hakanan ba abinda yake canza masa maganarsa. Waiwayawa tayi suka hada idanu da ama,saita samu kanta da sulalewa har qasa tana gaidata,duk da saita rusuna sosai din take gaidata kullum kwanan duniya,amma gaisuwar yau din ta banbanta da ta kullum. "Lafiya alhamdulillah" ama din ta amsa mata tana dauke kanta daga gareta "Batoul riqewa aba wannan muje" ama ta fadi tana miqawa batoul wasu qananun cups biyu "Ni ba za'a bani na riqe masa ba?" Benazer ta fada tana karya wuya gami da maqale kafada "Batoul yace a bawa,next time sai a baki kema" ama ta amsata tana daukan warmer ta soma yin gaba. 'Yar qaramar sautin da qofofin dakunan ke bayarwa a duk sanda aka budesu yaja hankalin ayana dake zaune cikin falon tana satar kallon sultana da yaranta cike da kishi. Mutuwar zaune tayi ganin wanda ke fitowa daga dakin sanye da kayan bacci da suke bada tabbacin ko a nan ya kwana,ko kuma ya shigo da asuba yayi bacci cikin dakin,don yanayin fuskarsa ta nuna lallai daga baccin ya tashi. Kasa motsi tayi,sai idanu data zuba masa,qwaqwalwarta ta kasa tuna ko tantance komai. Ya haidar ne ya fito daga dakin sultana, dakin da tana a tsaye itama sultanar ta fito daga ciki?. Wani irin abu taji yana mata yawo dukka sassan jikinta,ta kasa controlling yadda zuciyarta ke mata zafi,saita dinga qoqarin dauke kanta daga sashen da yake don tana gudun abinda zuciyarta zata iya ci gaba da raya mata a kansu. Sam baima lura da wanzuwarta a wajen ba,dukka hankalinsa yana kansu,yana jingine jikin qofar dakin yana murmushi gami da kallon dukka drama din da akeyi tsakanin ama dasu din hannayensa nade a qirjinsa. Dama haka akeji duk safiya sanda ka wayi gari cikin familynka?. Baya benazeer taja alamun taji haushi,sultana da takeson kowa da kowa yabar falon koda zai fito ta juya tana zare mata idanu "Ba za'a gaya miki magana ki haqura ba?,oya wuce muje" baki ta kyabe kaman zata saki kuka sannan tayi gaban,sultana ta bita da kallo ta soma takawa tana bin bayansu itama. Bakin qofar ya bari shima yana nufar hanyar fita,saidai kuma kafin takai ga bacewa cikin jikinta ta dinga jin kaman ana kallonta,wannan ya sanyata waiwayo babu shiri. Mutum biyu ta gani a falon,tanja dake fitowa a kitchen da kuma maina din dake qare mata kallo tamkar yau ya fara ganinta,sai ayana da itama ke kallonsu kamar idanunta zasu fado d wani mahaukacin kishi. Wani gumi ya yanko mata,ta firgice gaba daya tana fidda fararen idanunta "Barka da safiya" tanja ta fada tana dan rusunar da kanta "Ina kwana tanja,mun tashi lafiya" "Lpy alhamdulillah" ta amsa masa tana wucewa dining area da dan sauri sauri da alama tanason aje abun hannunta ne ta wuce tabar musu falon,hakan ke alamta kenan ta fahimci daga inda ya fito?, sultana ta tambayi kanta da kanta. Ga ayana da tayi imanin taga fitowarsa,don ta karanceta da alama zatayi qwaqwafi da sanya idanu akan lamuran da basu shafeta ba. Kallonta ta maida kan tanja,amma sai taga tanja din fuskarta bata nuna komai ba,bata gamsu ba,tunda tasan tanja farin sani,daga ita har maina din tanja ta haddace halin kowa,tunda ba wai yau ko jiya take tare dasu ba,tun tale tale da quruciya cikin jikkunansu. Ganin tanja ta soma barin wajen ya sanya itama ta qara sauri da zummar barin wajen,sai kuma muryar benazeer tayi mata birki "Laaa.......daddy a nan ka kwana?" Faf ta buge bakin benazeer ba tare data shirya ba,ta kuma juyata da sauri tana saita mata hanya. Tayi imani idan ta bari wannan akun ta isa wajenshi to ba wanda ya isa ya rufa asirinsu sai Allah. Idanunsa ya runtse har cikin zuciyarsa yana jin zafin bugun da ta yiwa benazeer din,ta riga da tabar wajen,koda yayi magana ta bacewa ganinsa bazaiji ba. Ya kusa minti biyu tsaye a wajen sannan ya juya yana ficewa daga gidan,amma ranshi yana masa susa har yanxun na dukan yarinyar da tayi. Ji yayi ya kasa jurewa,har ya isa bakin qofar gidanshi suhail ya bude masa sai yace "Ina zuwa" ya juya yana komawa cikin gidan,duk da yaci alwashi bayason aba yasan da zamansa cikin paris ko zuwansa cikin gidan,amma yau yana jin bazai bar gidan ba sai ya mata gargadi na gaske,tafiya zaiyi na sati uku,haka zai tafi tana dukan masa yara?. Da qyar ayana taja numfashi takai hunhunta,ji tayi babu sauran space da zata iya zama cikin falon tana kallonsu,bayan ba abinda take ganowa cikin idanuwansu illa zallar soyayya me masifar zafi da akan jarabci zukata da ita,saidai kuma qasan zuciyar akwai wani abu da yakeson lallai saiya murqushe soyayyar ya hanata bayyana kanta. Duk kuwa da idanuwa suna qaryata hakan,ta cikin idanunsu kawai zaka iya karantar kome,saita miqe da sauri saurinta tana wucewa daki tun kafin ta rasa ragowar numfashin da zata shaqa,zuciyarta tana karyewa,tana jin kamar tana dab da rasa dukka damarta ne. Tunga taja ta tsaya a hanya tana tsare batoul da ido,ta tabbatar sukaje wajen aba a haka tana kuka zai tambayi ba'asi,kuma lallai indai benazeer ce me bakin bada labari ba zata kasa gaya masa ba, musamman ita din,tatabbatar indai ta fadi aba zaya lallasheta ne,yakuma hadata da chocolate ko sweet "Bana hanaki surutu akan duk abinda kika gani ba?,ban hanaki bada labarin abu koda tambayarki akayi ba bare ba'a tambayeki ba?" Ta fadi tana tsare yarinyar da idanu fuskarta a daure. "Kinaso na daina kulaki kwata kwata?" Da sauri benazeer ta girgiza kai kukanta yana tsayawa tana duban sultana a tsorace "To daga yau indai baki bar wannan halin ba ruwana dake" "Na daina mummy" ta fada tana qwalla "Naji......goge hawayen" ta fadi mata tana dubanta. Da kanta ta saka gefan hijabinta ta goge mata fuskar,ta tabbatar ta koma normal sannan suka wuce. Ta samu aba tuni ya fara breakfast shi da batoul, benazeer tayi joining dinsu,ita kuma ta zauna suna hira kadan kadan da aba din tana tattare duk inda su batoul suka bata har suka kammala. Aikenta yayi saman study table dinsa ta dauko wasu takardu,ya budesu ya miqa mata "Wadannan fa aba?" Ta tambayeshi idanunta a waje "Nakine sultana, mohmoud baya raye,duk abinda na raya a raina inda yana raye zanyi masa to ke ya cancanta na yiwa" jikinta gaba daya yayi sanyi,ta kasa cewa komai sai ama datake kalla kamar tana jira ta bata umarnin yin magana "Kinga ama" ta fadi tana dorawa ama takardun a cinya. Murmushi ama ta saki,duk duniya batasan me zasuyiwa jinin mohmoud su saka masa ba,alkhairi keta bibiyarsu ta sanadin sadaukarwarsa da kuma jininsa daya bari a duniya,ita ko da benazeer da batoul ta tsira daga jinin mohmoud bata da abun cewa "Na gani sultana,aba muna godiya Allah ya qara budi da arziqi" tayima aba godiya don ta bawa sultana qwarin gwiwa. Qwalla taji ta cika mata idanu,batasan adadin dukiyar data mallaka ba daga hannun aba,komai ya rarumo sai ya rubuta mallaka da sunanta,tamkar baisan ciwon kudin ba. Muryarta na rawa take masa godiya,yayi murmushi yana janta da tsokana,bari barta ta tashi a wajen ba sai data sake. Ita ta fara fitowa ta barsu,don muddin aba yayi irin wannan zaman benazeer da batoul na gefansa to tashinsa a wajen ba yanzu ba. Dam bata lura dashi ba,don hankalinta yana kan takardun hannunta tana sake shiryasu,saidai kuma abinka da aikin jini,tana qarasa fitowa falon dukka jikinta ya dauka,saita dan rage saurin tafiyarta tana maida hankalinta gabanta. Ya nutse sosai cikin kujera yana fuskantar tv,a haka idan ka kalleshi zakayi tsammanin bacci yake,amma kuma ba baccin yakeyi ba,yana kallon komai fes,yana kuma ankare da kowa. Fitowarta ya sanyashi dan qarawa idanunsa girma,wannan ne ya bata daman sake tantance idanunsa biyu. Yunqurawa yayi ya zauna sosai,daidai sanda ama ke fitowa daga wajen aba din. Fuskarshi a matuqar daure,daurewar data haifar mata da tsoronsa,irin tsohon tsoron nan da take masa a baya,sanda yake tamkar wani mai gadin motsin kowa na gidan,ya zamewa gidan katanga,idanunsa akan tarbiyya da shige da ficen kowa. "Daga yau......kada ki sake gangancin dukarmin yarinya a fuska ko a baki,idan ba haka ba zakisha mamaki na wallahi" ya fadi mata yana bude dukka idanunsa. Saida gabanta yayi mummunan faduwa,don ta jima bataga fuskarshi da idanunsa cikin irin wannan yanayin ba. Kanta ta kawar da sauri, zuciyarta na raya mata kodai maganar daxun itace ta tunzurashi?,banda haka dukan data yima benazeer baici ace ya dagi hankalinsa ko ya bata masa rai har haka ba. Sum sum ta wuce zuwa ciki,sai a sannan yaga ama dake tsaye a bayanta. Idanunsa ya lumshe sanda suka hada idanu da ama din,yanajin bacin rai sosai cikin zuciyarsa "Ina kwana ama?" Ya fadi cikin rusunawa da girmamawa "Lafiya qalau" ta amsa masa tana nazarin fuskarsa. Zuwa yanzun tana jin zuciyarta tana quntata da yawa,haqurinta yana shirin gazawa,ta fahimci daga maina sultana har aba zuru da zuba idanu ba zatayi musu aiki ba,wacce irin rayuwa ce suke shirin tanadarwa gobensu?. "Ka gaida aba?" Tayi masa tambayar tana zama saman kujera tana kuma qureshi da kallon nan da yake sanyashi jin shi din tsantsar me laifi ne "Zanje ama,kiyimin afuwa sai na dawo daga tafiya,ina buqatar adduarki,yau zan wuce los Angeles,sati uku kawai zanyi in sha Allah,idan na dawo komai zai daidaita......na miki alqawari,amma da taimakon adduarki" shuru ta danyi tana karatu akan muryarsa, muryarsa tayi rauni da yawa,ta tabbatar akwai damuwa sosai cikin zuciyarsa "Allah yasa,Allah ya tsare ya bada sa'a" "Ameen ya Allah na gode" ya fadi yana tashi,hanyar waje ya kama,kamar tace ya tsaya yayi breakfast dasu amma ta sani ba lallai ya iya ci din,ranshi a bace yake,kuma muddin yana cikin bacin rai irin haka baya iya cin komai. "Aliyyu" ta kirashi da sunansa,sai ya dakata ya waiwayo "Ka dinga qoqarin rage bacin ranka akan sultana......karka manta har yanzun rainonka ce ita,kafi kowa sanin yadda zaka tafi da ita" karon farko ta sanya baki akan abinda ya shafeshi shi da ita,sai yaji cikin tsakiyar zuciyarsa kaman an cire wani dutse an maida gurbin wajen da dutsen qanqara,har ajiyar zuciya tana subuce masa. Wato har yanzun dai sultana nada wannan matsayin cikin rayuwa da zukatansu,har yanxun basa ganin laifinta cancan,harda ita kanta ama din ma,bata taba yaba ma juriyarsa da kawaicinsa ba,amma ya yiwa diyarta fada sau daya ta kasa haquri?. Murmushi ya subuce masa yadan girgiza kai "In sha Allah ama,na gode" ya qarasa fada yana ficewa da sassarfa. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 111 Binsa da kallo suhail yayi sanda yake shigowa,yana kwance a qaramar kujera "Wai a ina ka kwana ka barni ni kadai cikin gida?" Yana balle bottoms na rigarshi ya kalli suhail din "Wajen matata.....ko ance maka kowa ma gauro ne irinka?" Hantsilowa suhail yayi ya zauna dai dai tana dubansa "ne dis pas de bêtises(kada ka gayamin maganar banza),yaushe kayi matar?,ko leqe leqe ka fara ban sani ba nayi saurin gayawa ama a nemo maka mata?.don ni......." Bai samu qarasawa ba saboda saukar maqullin maina a fuskarshi. Yaji zafi sosai ya dafe wajen yana kallonsa baki bude "Na lura baqin kishinka ya fara yawa,na samu labarin crush dinmu daya dakai,shine kakeson yimin tabo a fuska salon idan ta tashi tace kai takeso bani ba?" Yana kaiwa qarshe hucin naushin maina ya wuce ta fuskarsa,mugun hantsilawa suhail yayi yana salati ya dira ta bayan kujera "Anya ba gamo kayi ba?,see dis man jama'a,ko sai na nemo taimako?" Sosai maina ya nunashi da dogon yatsansa "Zan maimaita maka amma a karo na qarshe,idanma iya shege kakeyi kaida bibi da kuka qulla abinku ku kiyayi kanku,sultana matata ce..... benazeer da batoul 'ya'yana ne.......daga yau koda wasa ka sake kiranta da crush dinka......kasan Allah saidai a saka maka wasu haqoran badai baka na haihuwa ba" yana gama fadi ya sauke qafafunsa qasa. Dariya sosai suhail ya saki harda kama cikinsa,lallai bibi ta iya hada tsiya,ya tabbatar duk yadda bibi ke zaton maina din ya wuce haka akan sultana. Ya miqe yayi caraf ya kamo maina dake shirin wucewa bedroom dinsa "ne dis pas de bêtises(zo abokina)" waiwayawa yayi ya watsa masa harara "viens mon ami(sakeni)" zagayowa suhail yayi gabansa ya tsaya "Karmuyi haka dakai,daga yau bani da wani crush da ya ragemin,ko dama can baya na cire haka a raina,a baya dai na sota sanda bansan wacece ita ba,amma daga ranar da ka gayan matsayinta a raina,babu sauran soyayya sai respect da nake bata.....inda da gaske ita din nakeso ta yaya zan zauna Ina fadi iya baki ba'a aikace ba?...... shirin bibi ne,itace tace naci gaba da aikina" ya qarasa fada yana sake qyalqyalewa da dariya. Hannu maina ya sanya ya turashi gefe yana wucewa daki. Yana cire kayanshi yana tuna maganar suhail,yayi tsaye a gaban madubi sai murmushi ya subuce masa,shi bibin zata yiwa haka?,banda Allah yasa ya fahimta abun da wurwuri kenan da sai sun haukatashi ita da suhail din zasu barshi?. Tabbas bibi bataci bulus ba,daga ita har suhail din sai ya rama abinda suka masan. Toilet ya shiga ya sake wanka da kyau,ya dawo dakinsa ya duba luggage dinsa,zama yayi ya shirya komai,abinda yake buqatar ya saka ko ya cire dukka yayi hakan. Yana aikin amma fiye da rabin hankalinsa yana kanta,duk wani daqiqa guda daya da suka share a daren jiya da ita ba wanda bai tuna ba. Tsaf ya gama gyaran,ya wuce closet dinsa ya shirya cikin wani lafiyayyen trouser da shirt dinsa dukkansu na kamfanin gucci. Yayi kyau qwarai kai kace wani jarumi ne daga cikin jerin jaruman qasar india. Idanunsa ya sauka kan dan qaramin frame daya kafe me dauke da kyakkyawan hoton benazeer da batoul,ya miqa hannu ya dauka yana kallon fuskokinsu,diyoyinsa abubuwa mafi soyuwa a ranshi,kyautar da ubangiji yayi masa kaf rayuwarsa ta ba zata, kyautar da bai taba tunani ko tsammanin samuwarta ba,baya ga ama da ita kanta mamarsu bayajin anyi wata halitta da yakeso sama da yaran,bai sani ba ko a nan gaba zata haifa masa makwafinsu. Iya wannan tunanin nasa na qarshe ya haifar da kyakkyawan murmushi saman fuskarsa. Ya lumshe idanu yana budewa,sai ya samu kansa da motsa jajayen labbansa yana fidda addu'a daga bakinsa "Ya rabb.....kana amsa addu'ar matafiyi......ina roqonka yadda kayimin waccar kyauta cikin ba zata......wannan ma ina roqonka ka azurtani da wasu bayin naka a matsayin diyoyina kuma mallakina" ya qarashe addu'ar yana rataya qaraman jakarshi a kafada,ya kalli gabas ya karanta addu'o'insa ya shafa,haka kawai sai yaji abun ya darsu a ransa,idanunsa suka dinga nuna masa sultanan tashi a matsayin me juna biyu. Murmushi ya kuma saki,shi kansa baisan irin kulawar da zai bata ba,baisan wanne irin soyayya zai gwada mata ba,a karon farko zaiso suyi rainon ciki tare,su kuma raba wuya da dadinsa tare,ya tallafi rauninta,ya goge laifinsa ta hanyar bata kulawar da wata 'ya mace bata taba hasashen samu daga wajen mijinta ba. Wannan tunanin ya haifar da sakin fuskarsa sosai,wannan daurewar da daskararren miskilancinnan yau kam babu shi. Ya samu suhail tsaye a bakin qofa yana faman duba agogo,da alama jiransa yakeyi. Sai ya bishi da kallo yana mamakin me ya sanya walwala me yawa haka a fuskarsa?. Idanunsa akan gidan sanda motar ke tashi dasu zuwa airport,yanaso xai kuma so yayi sallama da yarannasa,so amma yana da plan da dole ya tafin ba tare da yayi sallamar dasu ba,dama baya ta sultanar,tunda dukka plan din nata ne dama. ****wunin ranar gaba daya sai ya zame mata tamkar jarrabawa,duk sanda ta zauna shuru na mintu biyu koda zummar tayi wani aikin sai tunaninsa ya addabeta. Kallo na qarshe data yima fuskarsa dake dauke da bacin rai wanda tun bayan dawowarsa bataga irinsa ba. Kalmar data gaya masa na qarshe "Bana sonka,kuma bazan taba sonka ba" ta tsaye mata cak a zuciya,batasan dalili ba,daga bisani wani sashe na zuciyarta ya fara raya mata rashin dacewar fadin hakan da tayi,wani sashen kuma na nuna mata ba aibu bane,ya shiga rayuwarta da yawa,ya kuma matsa mata. Wunin duka bata bari sun hada guri da ayana ba,sam taqi yarda su hada waje,yawan kallon da take binta dashi da kuma yadda take yawan sanya mata idanu a dukka motsinta ne bataso,da tunaninsa da matsalar ayana dukka tayi yunqurin zubda su,ta tarkata kayan aikinta da system dinta ta fita can backyard na gidan tayi zamanta,duk kuwa da cewa ba wajen zamanta bane. Batasan dukka qoqarin da tayi na yakice tunaninsa a banza tayi ba sai da aka kirayi sallar magariba,batasan ya akayi ba ta samu kanta da jiran jin door bell,tun daga sallar magariba har zuwa sanda tayi isha'i. Harta sallame ba motsin wani baqo,ama ce da ayana da yaran a falo suketa sabgarsu. Wanka ta shiga tayi,ta kuma shirya cikin kayan bacci don tanaso tayi bacci da wuri kuma isashe,tana jin jikinta dukka a mace,amma kuma idanun basa jin bacci,ta yanke cewa tana kwanciya wala'alla baccin yazo. Wayarta kawai ta dauka,don a yadda ta shirya tana gama cin abinci xata dawo dakin ta qarasa aikinta a system dinta,ta jona system din a charge sannan ta fice a dakin. Fitar tata a yanxun ma dai kallon kallo ne. Ta dauke kanta tana jin wani iri da yadda damuwar ayana a kanta yake qara yawa,ama nata tsokanarta ta daki ta fito,ta qarasa dining ta zuba abinci ta fara ci. Batayi wani nisa da cin abincin ba taji ya fita a kanta,ta tureshi ta zuba lemon da aka matse strawberry aka samar dashi. Tanason lemon,ta kuma koya ne wajen ama,amma sai ya zamana har taso tafi ama din iyawa. Ama din irin matan nan ne da sukasan yadda ake sarrafa nau'ikan abinci iri iri,hakanan ba kasafai take shiri da lemukan roba kwali ko gwangwani ba,tafi ganewa tayi da kanta,don haka sultana din ta wannan bangaren ma ta qaru da ita qwarai. Daki taso wucewa amma saita samu kanta da zaman falon,hankalinta ta raba gida uku,wani yana kan waya wani akan tv,wani akan motsin yaran da suke dan sanyota a rigimar su da basa rabo da ita. Agogo ta kalla,goma na dare a qasar Paris. Ba sabonta bane zaman falo har wannan lokacin,yau din batasan me ya zaunar da ita ba,me take jira?,itama bata sani ba,sai taja sirirj tsaki da ya sanya ayana daga kai ta kalleta,tana jin tsarguwa har ranta,tana jin kamar da ita take. "Ama zan wuce ciki sai da safe" dan murmushi ama din ta saki "Kinyi qoqari ma yau ai,Allah ya bamu alkhairi" "Ameen" ta amsa tana wucewa ciki bayan ta amsa goodnight din da su benazeer sukeyi mata. Ta kusa sha biyu na dare amma ba bacci a idanunta,a haka ta tattara komai ta kwanta. Kamar jira kwanyarta takeyi ta kwanta din sai komai ya soma dawo mata,dukkan wata daqiqa da mintuna da suka taba shude musu a tare da juna. Ta bude idanunta ta kuma kulle yafi sau a qirga,taja tsaki har babu adadi,ta jawo pillow cikin jikinta tana qanqameshi da kyau,sallah takeso ta tashi tayi amma 'yar banzar kasalar da batasan dalilin samuwarta ba a jikinta ta hanata motsi,sai taji gaba daya dakin kamar ba nata ba,ta sake rufe idonta tana ambaton sunan Allah. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 112 Kadan kadan tana motsa bakinta cikin addu'a har wani bacci me dadi yazo ya saceta. Tun baccin nata baici talata da laraba ba ta fada duniyarshi......duniyar mafarkinsa,duniyar ds bataga kowa a ciki ba daga ita saishi,saman wata tattausan shimfida ta wani lallausan carfet me gashi a jikinsa sosai,daga shimfidar har zuwa tufafin jikinsu dukka farare ne. Daga gefensu kuma yara ne qananu suketa wasa,a qalla sun kusa goma sha biyu,ba fuskan wanda ta gane a ciki,daga benazeer sai batoul kadai. Guje guje suketa yi a tsakaninsu,daga baya kuma suka samu waje suka zauna dukkansu suka zuba musu ido, benazeer da batoul kuma suna can ta bayansu a zaune. Shi ya maida dubansa kanta,sai ya sakar mata wannan murmushin nasa data sanshi dashi a zahiri,ya miqo mata hannu yana cewa "Zo kiga......ke suke kalla,wai kaman kina fushi" ya fadi yana dage mata gira. Da farko harta noqe kafada,sai kuma ta waiwaya tana duban yaran. Har yanzu ita suke kalla,zuwa lokacin kuma fuskokinsu sun sake nuna damuwa da bacin rai sosai,sai ta miqa masa hannun ya miqa mata nasa ya jata zuwa cikin jikinsa,daidai nan kuma dukka yaran suka bace,daga ita saishi a wajen. Hannu ya zura cikin rigarta ya fara mata mata tafiyar tsutsa, abinda ya sanyata kasa jurewa ta riqe hannunsa suna dariya sosai,sai ya miqe yana dagata cak,yana daga qafafunsa sai kuma yayi tuntube,suka tafi luuu dukka zasu zube saman farin rairayin dake wajen...... Firgigit ta farka,ta miqe zaune da hanzarinta tana dube dube cikin dimlight na dakin,hannu ta miqa ta kunna fitila,haske ya wadaci dakin. Ba kowa a ciki,daga ita sai ita kaman yadda ta kwanta,sai taja wani irin dogon numfashi tana fesarwa,sannan ta sanya dukka tafukan hannunta tana lullube fuskarta tana kuma jin damshin dake goshinta da alama gumi takeyi. Ta jima zaune a haka tana kiran "Ya hakeem" qasa qasa sannan numfashi da bugun zuciyarta ya daidaita,ta daga kai tana duban agogo, lokacin sallar asuba ya kusa saura kadan,hannunta ta saka tana ture duvet dinta tasoma yunqurin sauka,lallai ba abinda ya sanyata yin mafarkinsa sai kwanciya da tayi da tunaninsa cikin ranta,to amma wai meye damuwarta dashi?,me yasa cikin lokuttan komai yake son sauyawa?,kwanyarta ke qoqarin damuwa da mummunan dabi'ar yawan tunashi?,bayan bataga wani dalili da zai sanyata hakan ba?. Alwala ta daura tazo ta gabatar da nafilfilu,tayi shuru saman abun sallar tana jiran lokacin assalatu ya qarasa shiga,amma kuma mayyar zuciyarta da mayyar qwaqwalwarta shi din suke sake tuno mata "Why?" Ta tambayi kanta, yanzun nan fa ta gama addu'ar yayewar hakan daga gareta amma kaman bata roqi komai akan hakan ba?,kaman qari ta roqa ayi mata?. Idanunta da suka rusuna saboda rashin samun wadataccen bacci ta daga a hankali tana kallon window dinta, window din dake duban fuskar gidan nashi,tayi tsai da idanunta ata wajen,kamar wadda ke fatan ganin gilmawa ko motsinsa "Rabbi yassir wala ta'asir,wa tammim bilkhair" ta furta a hankali tana maida idanunta ta lumshesu,daidai lokacin wayarta ta kada alarm na kiran sallah,saita miqe kawai tana wasu addu'o'i cikin zuciyarta. *_BAYAN AWANNI_* Tsaye take gaban madubi tana duban fuskarta kamar wadda aka bawa contract na kallon kanta da kanta,yadda fuskarta take qara glowing yake bata mamaki,itadai tasan products din da take amfani dasu sune dai,bawai ta canza wasu bane,paris kuma zamanta a cikinta wancan karon ai batayi kyan da tayi wannan karon ba,meye banbacin wancan lokacin da yanxu?. Ajiyar zuciya ta saki,ta kasa gano komai,kawai dai taji dadin dogon baccin data samu,don badon Allah ya taimaketa ta samu baccin ba tabbas da yau din tasan akwai matsala. Qarar wayarta ya sanyata barin gaban madubin,ta dauki wayar tana duba me kiran,sai ta samu waje ta zauna tana amsa wayar. Kafin ta kammala kiran tanja ta shigo dubata inji ama,saita yanke kiran tana bin bayan tanja. Ba kowa gidan, benazeer sun tafi school,ayana itama ta tafi nasu school din ta qarasa abubuwan da batayi ba. Tun abincinta na safe tanja ta dumama mata ta dawo mata dashi,ta jawo gabanta ta fara ci,to amma kuma abincin kwata kwata bai mata dadi ba,ba taste haka take jinsa,dole ta haqura dashi tana maida tray din gefe. "Yadai?" Ama da take ganin sultana din wani iri iri haka ta tambayeta "Ba komai,na qoshi kawai ama" ta fadi tana dubanta "Ai an kusa gama lunch,saikici,dumame breakfast dama ya zaiyi miki dadi?" "Okay" kawai tace. A maimakon komawa daki da takeyi kamar yadda ta saba,saita samu kanta da zamewa nan cikin kujera ta kwanta lamo tana taya ama kallon News,duk da bawai burgeta labaran tashar yakeyi ba,tunda labarai ne na duniya,hasalima bata fahimtar me suke haskowa,tana dai jin ama time to time tana salati ko qorafi. Wayarta da kuma bakin qofar da take yawan kalla sune suka janye hankalinta. Mintuna suka yita shudewa suna bada awanni amma tana kwancen a nan,can qasan ran ama tanata mamakin abinda ya zaunar da sultana din,tunda zaiyi wuya ka shigo gidan ka sameta a falo. Door bell na kadawa gabanta ya yanke ya fadi,ta lumshe idonta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,lamo tayi taqi tashi,don zuciyarta na raya mata shine,har sai da tanja ta fito ta bude qofan sanda ama ta qwala mata kira tana gaya mata ta bude din sultana bacci ya dauketa. Qasa qasa ta bude idanunta sanda su benazeer ke shigowa da school uniform,sunata fada akan wani dan qaramin notebook. Soror tayi,haka kawai kuma tana jin ba wai,bata tsammaci su bane,kawai zuciyarta tana raya mata shine,daya zamana kuma bashi din bane duk sai taji abun wani iri. Maida idanuntan kawai tayi ta sake rufewa,a hankali a hankali tun tana jiyo hayaniyarsu ama nata fama dasu har wani bacci ya sake saceta. Bata farka ba sai da aka sake buga qaraurawan. Ta bude idanunta tana kallon tanja dake bude qofar. Ayana ce,tanja ta matsa ta bata waje ta shigo,saita zube takardun hannunta nan tsakiyar falon tana kallon ama a marairaice "Ama aikin babbane,ba sauran abubuwa da bas qarasamin bane,ya maina babu abinda yayi min,ashe yace musu ne zanzo nayi komai da kaina don nasan darajar karatun" ta qarasa fadi kaman zatayi kuka "Yanzu idan bai tausayamin ba waye zai tausayawa?,sannan ama harda samarmin wajen zama,ya barni mana na zauna a nan" ta qarasa maganar muryarta na nuna bacin rai. Kai sultana ta dauke,don dukansu tasan ba lura da farkawarta,sai kawai ta maida idanunta ta kulle ba tare da tace komai ba, saidai kuma kunnuwanta suna jin komai. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 113 "bai kyauta ba..... tun farko sai yayi bayani baiyi komai ba ki samu ki shiga da wuri ki gama aikinki.......har yanzu haidar yana nan da halinsa.....amma kuma na tabbatar tunda yafiso ki zauna cikin dalibai yana da dalilin hakan,nasan halinsa sarai" y ayana tayi tana sake ajiyar zuciya,ta dauka ama zatabi bayanta ne,don kwata kwata batason tayi nesa da gidan,ko ba komai idan tana zaune a nan din hakan zai kawo kusanci tsakaninsu,kusancin kuma da take fata ya tabbatar mata da burinta. A yanzun tana gayawa kanta tayi gefe da matsalar sultana,kowa yaji da kanshi kawai,kuma wanda ya iya allonsa ya wanke. Bata sake cewa komai ba,sai falon ya danyi shuru sai hayaniyar yaran daketa hada litattafansu na islamiyya,don malaminsu dake daukarsu karatun addini yana dab da isowa. Sosai suke karatun addini ama bata bari sun zauna haka ba,kudi ta kashe me yawa take biyan malamin,yanzu haka suna da haddar izifi goma goma cas a kansu. Yaran nada wani irin budaddiyar qwaqwalwa da kuma baiwa data sanya ama tsaiwa tsayin daka akan karatunsu na addini,don duk bokonta bata yarda da tsurar karatun boko ba,wannan ya sanya cikin family house na mayaki komai na ama dana yaranta tun usul ya fita daban. Ama ce ta miqe ta wuce ciki saboda wayarta dake ringing,wannan ya bawa sultana damar bude idanunta a hankali ta kuma miqe ta zauna sosai, benazeer da batoul suka matso suna cikata da surutun sun dawo tun dazu tana bacci. Qaramin murmushi ta saki kawai tana shafa kawunansu. "Ga ya shaik can ya qaraso" ta fadi musu sanda bell din ta kada "Allah ya bada sa'a" ta fadi zuciyarta cike da qaunarsu sanda suke rige rigen zuwa su bude qofan. Suna fita ta miqe tana wuce dakinta,ayana ta bita da satar kallo. Duk yadda takeso ta amintar da kanta ta daina jin d'ar game da sultana din amma ta gaza haquri,muddin xasu hada inuwa daya koda sultana cikin kayan bacci take sai taji ta raina kanta,duk kuwa da yadda qawaye da samarinta ke kambama kyanta da ajinta,bata tana tunanin zataga wata diya mace taji ta raina duka wadannan abubuwan nata ba. Duk yadda batason zaman falon ko don ayana amma ranar a falon ta wuni. Dukka hankalinta yana kan qofa da duk wata bell da za'a kada don neman izinin shigowa gidan,batasan tana yi ba ita a karan kanta sai daga baya ta fahimci kamar akwai wani abu da takeyi out of dabi'arta data saba da ita a gidan. Ta lalubi kanta kaf don neman ba'asin wannan qwaqwafi da takeyi amma ta rasa amsa,koda wani sashe na zuciyarta ya gaya mata nashi hasashen sai ta bashi amsa da "Wannan babbar qarya ce!" Abinda ta gayawa kanta da kanta kenan. Ta aza hakan kawai akan ta gaji da zaman waje daya,tana buqatar sabbin mutane da sabon waje,saidai kuma har a cikin zuciyarta wannan dalilin yaqi gamsar da ruhi da kuma zuciyarta. Har fargabar zuwan dare ta dinga yi,don batasan yadda zai risketa ba. Daren jiya tasha wahala sosai,bayan kasalar jiki zuciyarta da ruhinta dukka tamkar jinya sukeyi,bata da qarfi a jiki da kuma zuciyarta gaba daya,wannan ya sanya daren ranar yafi zuwa mata da tsananin da yafi na jiya. Don a daren data tashi donyin alwala tayi sallah kaman jiya,kawai saita samu kanta da fashewa da kuka,kukan da ita kanta ba zatace ga dalilin zuwansa ba,kawai tana jinta cikin wani matsanancin kadaici da batasan dalilin samuwarsa ba,tana jinta a matsayin wata gajiyayya da bata da sauran qarfin jiki dana zuciyarta,jikinta da zuciyarta dukka ba dadi,tana jin kamar an toshe dukka wasu qofofinta na walwala. Washegari saita tashi a sukurkuce gaba daya,nutsuwarta qalilan ce,damuwa tana neman yi mata yawa,tana jin wani mugun kadaici baya ga kasalar data zanyataya gaba,sai ta dinga jin kamar ita daya ke rayuwa cikin duniyar ma gaba daya ba cikin gidan ba. Abinda tayi noticing shine,tamkar rashin zuwansa gidan cikin kwanaki ukun yana damunta,kamar tana ankare da kowanne motsi nasa kenan indai rashin zuwansa gidan ya dameta?,bataji wani ko wata kuma koda sau daya ya ambaceshi cikin kwanaki ukun ba,suna sane da dalilin rashin xuwan nasa kenan?,ko kuma suma basu sani ba?,sun watsar da lamarinsa ne kamar yadda ya watsar da nasu?. Wani lokaci sai tayita kallon benazeer da batoul,kamar tanason yin wata magana data shafi daddynsu da su,sai kuma wata zuciyar ta gargadeta "Koma ina yaje ya daina xuwa gidan yana sane.....akwai mahaifiyarsa akwai yaransa a ciki kin manta?" Abinda yakan xo mata akai kenan,sai ta share maganar tayita qoqarin dora walwala saman fuskarta. A satin da ake fuskanta program dinta zaiyi magana ne kan wani yare dake qasan Ethiopia,dukka sai abubuwan suketa zuwa mata a slow,tana kadaice kanta don ta samu damar yin aikin,amma kuma sai hakan ya zame mata kamar wani sabon tashin hankali,don duk sanda ta kadaice da zummar tayi aikin sai tunaninsa tare da wani mutuwar jiki ta saukar mata,saidai ta tattare komai ta bawa tunanin lokacinsa,sannan ta samu da qarfi da yaji tadan taba aikin kadan. *********Kwanaki biyu suka rage ranar program ya zagayo,gashi kuma bata tsinana wani abun azo a gani ba. Tana kyautata zaton muddin satin yazo ya sameta a haka sam ba zata iya bada abinda ake buqata cikin program din ba,don haka ranar wani alhamis,qarfe takwas na safe ta shirya da zummar tafiya office,qila acan din idan tana ganin gilmawar mutane ta samu karsashin hada aikinta. Uwa uba kuma ga dioura da take da tabbacin zata taimaka mata. Qarfe tara saura ta yiwa ama sallama,tayi kyau cikin wata wata doguwar rigar Indonesia me launin baqi da adon sea green,ta fita sosai a muslim girl dinta,amma idan ka ganta zakayi tsammani daya daga cikin musulman wata qasar da bata shafi Africa bane. Ayana na zaune take ficewa daga falon,taja numfashi tana dauke idanu daga kan sultana din. Tana bala'in kishin kyau da ajin da Allah ya zubawa yarinyar,ta rasa da wacce hanya zata doke tauraruwarta gaba daya?,tana ji inama ace itace sultanar,wai mema sultana ta rasa a rayuwa?,wannan itace tambayar da ayana kullum ke yiwa kanta,sai kuma qwaqwafin son jin tsakaninta da yaa maina din akwai aure ko babu?. Ama nada tsare gida idan taso, mutum ce kuma mara son tsurku ko mutum ya dinga shiga lamuran da basu shafeshi ba,wannan ya sanya take shakkar sako mata maganar. Bismillah tayi tana xura muqulli don bude qofar motar,sai idanunta suka fada kan gidan. Daidai lokacin laila daketa knocking gami da danna bell ta gaji,ta juyo a hankali tana saukowa daga saman 3step din dake qofar gidan. Idanu suka hada da sultana,har cikin ran laila sai data ji wani abu. Tana da wani irin aji da kyau dake qara mata kwarjini,tana kishin halittar sosai,duk da har yau batasan meye ainihin alqarta da haidar ba,to amma a yanzun da takeson ganin yaa haidar din da yayi mata batan dabo kusan kwanaki shida kenan,tana jin ita kadai zata tambaya inda yake din. Tun a kallon farko sultana din ta janye kallonta daga kanta,batasan me yasa take mugun qin jinin yarinyar ba,a qalla batajin haka akan ayana,nata abun baikai har can ba,bata sani ba ko don ayana din tana da nasaba da jinin ama dake da kima a idanunta. Taji takun takalmanta masu tsaho,kuma jikinta ya bata tana nufo direction dinta ne,don haka adan gaggauce ta qarasa bude motar ta shiga ta maida murfin ta rufe. Dab da laila din zata qaraso wajen ta dage dukka glass din windows dinta,ta tayar da motar. Tana tsaye daga gaban motar tayi reverse ta bata wuta tana barin wajen. Ta madubin gaban motar take hangenta,tana tsaye tana bin sawun motar da idanu kafin ta maida dubanta ga motar gaba daya. Idanunta ta janye tana jan wani mugun tsaki kamar zata tsinke harshenta. Karon farko taji wani mugun haushin maina ya kamata. Na meye zai dinga bari wai mata suna bibiyarsa?,inda ya kame kansa hakan zata faru?. "Kinfi kowa saninsa ai.....ayana jininsa ne ba yadda zaiyi da ita,wannan kuma itama akwai tabbacin ba banza ba ya rangwanta mata har take samun daman biyar sawunshi" wata zuciyar ta karanta mata hakan cikin nutsuwa "To meye alaqarsu?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar "Allah masani" zuciyarta ta sake bata masa. Tambayar data rasa amsar tata tafi tsaye mata a rai,ta sake jan tsaki wani tsumammen bacin rai da batasan na meye ba ya taso yana shirin rufeta. Bacin ran ganin laila?,ko bacin ran ganin laila din tazo nemansa?,ko baqincikin rashin ganinsa na tsahon kwanaki ba tare da tasan ina ya tafi ba?,duk batasan wannan amsar ba,tambayoyin da wasu daga cikinsu ma bata yarda da wanzuwarsu cikin dalilan sauyawar mode dinta ba. Iska laila ta furzar tana jin zafin kanta da kanta data dosheta ma,dama tun ganinta na farko da ita ya kamata ace ta fahimci zatayi girman kai,irin kyau da take dashi da tasirin ilimin daya bayyana a jikinta kawai ya isheka ka fahimci zatayi ji da kai. Ta kalli kanta daga saman har qasa. Yau ita laila bello wata mace ta disga?,laila bellon da kaf fadin abuja duk diyar da take jin kanta ta isa mace neman qulla alaqa takeyi da ita?. "Laifi nane" ta bawa kanta amsa. Maida kallonta tayi tana nazarin gidan data fahimci kamar daga nan ta fito. Suhail yace mamanshi a nan gidanta yake,saidai kuma shi maina din bai taba zancan da ita ba bare ya bata fuskar zuwa,haka kawai taji hankalinta yana bata a wannan gidan take,don haka sai kawai ta fara takawa tana nufar gidan. Tana driving din amma gaba daya hankalinta yana wani wajen,wannan ya sanya kafin takai gidan tv din sai da akaci tararta a hanya saboda sabawa doka da tayi. Koda ta isa ma kulle kanta tayi a office,aqalla saida ta dauki awa guda tana sauraren qur'ani cikin wayarta,tayi wasu daga cikin addu'o'i sannan ta samu confidence. Ta daga waya ta kira dioura ta gaya mata ta shigo,tana kuma buqatar taimakonta "Gani nan madam" ta gaya mata da rababbiyar hausarta. Ama da tanja suna kitchen ama din tana duba kayan cefanen da yayi qasa da wanda ya qare,don yau goumar zai shigo Paris,shi daya ne kuma ke iya mata siyayya yadda takeso,don ita kanta bata jurewa zuwa supermarket,kasancewar ta saba,a nijer da Nigeria gaba daya komai ana kawo musu ne daga manyan supermarket n can,saidai ayi bill ta biya. Ayana ce taji qaraurawar,ta sauke wayarta wadda take turawa maina saqo ta manhajar watsapp duk da bata da tabbacin samun amsa,don bai fiya bashi muhimmanci ba,ta miqe da saurin taje ta dawo ta qarasa ta tura masa. Kallon kallo sukayi a tsakaninsu na wasu sakanni,dukkansu hakanan suka ji basu yarda da juna ba,sai laila tayi qoqarin sake fuskarta tana kallon ayana don taga alamun akwai alamun jinin haidar a jikinta "Ama tana nan?" Kaman ba zata amsata ba,sai kuma tace "Tana ciki" ta saki qofar tana juyawa ciki ba tare data sake kallon laila ba. Itama bata damu ba ta sako kai tana biye da ayana din.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 114 Batayi mata tayin zama ba,hakanan bata kuma cewa da ita komai ba ta koma ta zauna tana ci gaba da danne dannen wayarta. Dan kallonta kadan laila tayi tana mamakin wacce 'yar wulaqancin still ta sake haduwa da ita?,kodai dukka jininsa haka suke da miskilanci irin nasa?,a haka zata rayu a cikinsu?,ta yiwa kanta tamabayar. Sanda ama ta fito idanun akan laila dake tsaye ya fara sauka "Baquwa garemu?" Ama tayi tambayar saboda kallo da laila kebin ama din dashi. Da sauri laila ta saki tunanin da takeyi tana sakin fara'a,koda ba'a gaya mata ba wannan din tabbas itace uwa ga abun sonta,itace ta haifa yaa haidar,kamanninsu sun nuna haka,saidai kuma abinda ya bata mamaki,kwata kwata shekarun ama basuyi kama da na matar da zata aje d'a kaman maina ba "Baquwa ce ama" sai kuma tadan sunkui da kanta. "Ayana ya zaki bar baqo a tsaye?,ga guri zauna" ama ta fadi tana nunawa laila waje. Kame kame ayanan ta soma yi,tasan halin ama din sarai akan hakan zata iya saba mata "Na dauka ta zauna ai" harara ama ta jefa mata,saita samu waje ta zauna tana fuskantar laila. Tana dan sussunne kai wanda ya sake haskawa ayana lallai da wani abu,abinda ya sake tunxurata ta gyara zamanta taji da wacce uwar tazo,saidai kuma waya take dannawa kaman batasan me akeyi cikin falon ba. Bayan gaisuwar shuru yadan biyo baya "Ban gane fuskar ki ba yammata" ama ta fadi sanda tanja ta gama ajjiyewa laila ruwa da lemo "Laila ce ama......qanwar sardauna" murmushi aman tadan saki,suka sake gaisawa sai kuma wani shurun ya sake shigowa. Ama din bata yau bace ba kuma ta jiya ba,sannan ita din uwace data taso gidan dake da yara mabanbantan halaye,yara irin maina da sultana,kuma kowanne take iya fahimtar yaren da yake magana dashi,bawai iya maganar baki kawai ba "Kina lafiya ko?" Ama ta sake tambayarta "Lafiya qalau,nazo inata knocking ne sai kuma naji gidan shuru,kwana wajen takwas bamuyi waya da yaa haidar ba,ban kuma ganshi ba" a fusace ayana ta daga kanta,abinda ama ta riga ya ganta don kusan tana bangaren da dole aman zata gani,amma saita kawar da kanta ta tattara hankalinta akan laila. "Ayyah,tafiyace ta taso masa" "Okay,ban sani ba wallahi" ta fada tana dan jan mayafinta kadan,daidai nan ayana ta miqe tana wucewa zuwa daki da wani irin saurin da ya sanya dukkansu suka bita da kallo. Sai data bacewa ganinsu sannan ama ta maida dubanta ga laila "A wacce makaranta kike karatu cikin Paris din?" Dan daga kai tayi ta kalli ama "Ba karatu nakeyi ba" sai ama ta dage girarta "Ayyah,me kike a Paris to ke kadai?" Dan daburcewa laila din tayi,gabanta ya dinga faduwa,kada dai ta fassarata da wata ma'ana ta daban,ita dake buqatar yabo da soyayyarta "Hutu nazo.....sai na samu aunty na bata dawo ba ita da mijinta......amma jibi nake kyautata zaton zasu dawo,ina can masauki ina jiransu......ya haidar ne ya kamamin safe place" boyayyen numfashi ama din ta saki,bata tantama akan tarbiyyarsa da kamewarsa,amma dan adam ne shi kaman kowa,shaidan kuma game da mace bashi da amana sam "Yayi qoqari......amma a yadda yake da kishin nan ko 'ya'yansa bazai kamawa masauki ba bare sultana matarsa,aikin gidan Tv din ma da takeyi na tabbatar temporary ne kafin ya hutsance mana" ama din ta fadi babu damuwa sam saman fuskarta "Mata?,yaya?" Laila ta samu kanta da fadi tana duban ama kai tsaye. Murmushi ama din ta saki,don ta samo amsar abinda takeson sani,ta kuma isar da saqon da takeson isarwa din duka lokaci guda "Eh,yana da tsananin kishi tun yana qanqaninsa" wuta ce ta daukewa laila tsaf.......duk wani gaba da zata sadar da fitar furuci daga bakinta ya dauke,shurun yaci gaba da wanzuwa a falon,yadda bata sake cewa komai ba haka ama bata sake magana ba,saita maida kanta ga wayarta tana amsa kira. Dole.laila ta miqe tana mata sallama,sai ama ta tsaidata ta sanya tanja ta dauko mata wata leda a daki. Lace ne me matuqar tsada cikin irin wanda take yin order,tarkacen turaruka da hijabai masu kyau ta hada mata,kayan ba masu yawa bane amma kudinsu suna da nauyi,ita kanta lailan ta sani. "Na gode" laila ta fadi a sanyaye "Ki gaida gida" ama ta furta cikin fara'a ta taka mata har qofar falon. Maida qofar tayi ta rufe tana furzar da iska,saita dawo saman kujera ta zauna hankalinta ta lulawa ga tunani. Dole ta girmama laila don sun riqe mata danta bai fada wata hanya ba,sun kuma bashi kulawa da gata cikin mutuntawa bakin gwargwado. Da laila da ayana dukkansu ta karanci kowaccensu,manufarsu guda daya ce. Maina mijin mace hudu ne,kuma yana da damar ya auri dukkan macen da musulunci ya halasta masa,amma yanzun lokaci ne daya kamata ya shiga rububi da rigimar 'ya'ya mata da kowaccensu take a shirye don mallakarsa?. Ita kuma sultana fa?,me yasa hankalin sultana yayi nisan kiwon data kasa hango abinda ita taketa hango mata?. Tambayar data yiwa ama tsaiwar mashi kenan cikin kwanyarta wunin ranar gaba daya,duk inda ta juya taga gilmawar benazeer da batoul sai taji abun ya fado mata. Su din 'ya'ya mata ne da zasufi kowa jin dadi idan suka tashi sukaga mahaifinsu da mahaifiyarsu a tare suna rayuwa qarqashin inuwar aure. ++Don aiki a ranar tayi aiki sosai,ta kuma kammala duk abinda ya dace ace ta gama din da taimakon dioura. Amma irin gajiyar da takeji a gabbanta ta wuce qa'idar aikin da tayi,don daga qarshe tare suka fito daga gidan da dioura,ita tayi driving nasu,basu rabu ba sai da sukazo traffic jam,ta bata motar ita kuma ta tsaida taxi ta wuce. Hannunta dukka ta bude tana tarbar benazeer da batoul da suka taho da gudunsu,ta zauna tana yiwa ama barka da gida,sai aman ta bita da kallo. Komai na sultana kaman yana sauyawa,kuzarinta ta fahimci kamar tana loosing dinsa,sannan kaman akwai boyayyar damuwa qasan zuciyarta da take qoqarin dannewa. A yanzun sultana ta riga ta zamewa ama wani sashe na rayuwarta,ko babu auren maina bisa kanta,ko babu benazeer da batoul shekarun da sukayi da sultana tana jinta kamar su saddi da almu. "Lafiya kike?" Ta yiwa sultana tambayar wadda ta shiga nazarin falon ko zataga wani abu da zai gaya mata anyi wani baqo a gidan bayan fitarta. Da sauri tayi qoqarin tattara hankalinta,tadan saki murmushi tana cewa "Alhamdulillah ama,aiki nayi yau sosai me yawa" "Allah yayi jagora" "Ameen,bari na shiga na huta" har ta kusa isa dakinta ta waiwayo "Benazeer.....maza gayawa tanja,don Allah idan akwai fulawa,zata iya soyamin waina?,da manja da albasa da yawa" cak ama dake qoqarin gyara sabbin kayansu benazeer data yi musu order ta daga kai ta kalleta. Suna hada idanu haka kawai sai sultana din taji wani iri "Na gaji da abinciccikanmu ama,na dade banci waina ba" "Akwai kayan a kitchen,indai tanja ce akan aikinki bata nawa" ama ta fadi tana maida kanta ga abinda takeyi, juyawa tayi tana wucewa dakinta,yayin da benazeer ta fella da gudu don Isar da saqon sultana din. A daren dukka juriyarta ta qare,ba shiri ta sauka daga saman gadon,ta xura hijabinta ta fito. Dakin ama kai tsaye ta wuce inda yaran suke kwana tun xuwan ayana. Ta samesu tanja na shiryasu xasu kwanta,don benazeer ma harta kwanta din,ama na qoqarin daidaita musu sanyin ac din dakin. Dukkansu suka juya suna kallonta,tun tun dazu data gama cin wainar fulawa tace bacci takeji ta wuce daki. "Ama aronsu benazeer zaki bani,zasu tayani kwana" duk sai suka zuba mata idanu,saboda abune da bai taba faruwa ba tunda ta haifi yaran. Idanunsu harda na yaran taji ya mata nauyi,kallon da suke binta dashi ya sanyata komawa gefan gadonsu ta zauna. Cikin kawaicin nan na ama da takejin yana dab da qurewa,cikin halin ko in kula tace "Gasunan ai,tafaddal" dukkansu murna suke yaran,tuni banazeer ta diro daga gadon tana rarumar blanket dinsu "Ajjiye wannan mana hajjaju" sultana din ta fada tana murmushi,cikin zuciyarta tana jin tana samun sassauci. Kayan wankansu harda towels da bathrobe da brushes dinsu ta sanya tanja ta hado musu suka wuce dakin. Zaune tayi kawai tana kallonsu,sunata zuba mata surutu,har zuwa sanda bacci ya daukesu daya bayan daya. A gaba ta sanyasu tana kallon fuskokinsu, fuskarshi take gani cikin tasu,dogayen yatsunsu irin nasa,harma da tsagar kyakkyawan labbannan nasa. Sai da tayi alwala sannan ta haura gadon,ta tofesu da addu'o'i ta shiga tsakiyarsu ta kwanta tana jansu cikin jikinta sosai. Numfashi ta fesar me sanyi,tana jin relief sosai cikin qirjinta,ta lumshe idanunta tana jin dumin jikinsu yana shiga jikinta.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 115 Kafin takwas dukansu sun shirya,suna dining ita da yaran,tsaye kawai tayi tana duban abincin,babu abinda ya kwanta mata a ciki,tana kallon su benazeer sunata lodawa cikinsu,da yake ba laifi basa wasa da abinci,wannan ya sanya kullum qibarsu suke,ga gata ga cima me kyau,ba abinda ya damesu sai qiba da fari da suke sake ajewa,kubul kubul dasu,wani lokaci takanji goumar yana tsonakarsu "Kumatun benazeer ko na batoul zamu cire mu saida mu siyo Sweet ko chocolate?" . "Ya kike a tsaye kuma uwar dakina?" Tanja data fito zata aje ruwan zafi ta fada tana kallon sultana. Dan yamutsa fuska tayi "Banajin cin komai wallahi tanja" "Ashsha.....hala bakijin dadi ne?" "Wallahi bakina ba taste ma kwata kwata" "Ai da kinyi magana tun dazun sai a dafa miki abinda kikeso" tanja ta sake fadi tana duban sultana "Nifa da zan samu wainar fulawa irin na jiya ko dumamamme ne ci zanyi" Batoul da benazeer ne suka bushe da dariya suna duban sultana din "Mummy dumamen kalallaba fa?,tabdi......ga abinci sabo Allah mummy yayi dadi kici kiji" kai ta kawar tana dan hararar benazeer dake kora wannan jawabin "To ki bada minti goma mana ayi miki ki tafi dashi,akwai komai ai" agogonta ta kalla,sai taja kujera ta zauna tana cewa "Da kuwa naji dadi...... benazeer kubu school bus,gobe idan Allah ya kaimu saimu fita tare" ba haka sukaso ba,don sun saka rai sosai su fita tare da ita,amma haka suka gama sukabi motar makaranta. Sau uku ana dora mata camera ana saukewa. Tayi shuru tana jin bugun zuciyarta yana qaruwa,fuskarsa kawai take mata yawo cikin qwayar idanu,da kuma maganar da ya gaya mata darensu na qarshe _please,ko yaya ne ko menene sultana....ki taimakeni ki rufamin asiri ki killacemin kanki,i swear bazan iya dauka ba,zuciyata me rauni ce a kanki bazan iya jurewa ba naga wani ko wasu suna kallemin ke_. Kalamanne suka dinga mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,sai da tayi da gaske sosai sannan ta samu ta gabatar da shirin. Shirin ya qayatar kamar kullum,saidai gaba daya yau din ta rasa farincikin da take samu duk sanda ta gama program dinta successful,hatta da wayoyin mutane da aka saba ana dagawa cikin shirin yau bata samu dagawa ba,tana gamawa tasa sukayi off din camera ta kuma wuce zuwa office dinta. Saman table dinta ta dora qirjinta zuwa kanta tana maida numfashi,tana jin zuciyarta kamar an rataye ta cikin wani kurkuku,ta dinga fesar da numfashi tsahon rabin sa'a sannan ta samu ta maida hankalinta waje daya. Muguwar yunwar da takeji kaman an mata satar 'ya'yan hanjinta ya sanyata miqewa dole,ta shiga toilet ta wanke hannunta ta kuma dawo ta zauna ta jawo flasks din wainar ta soma ci. Ita kanta sai data kammala sannan tabi kwanon da kallo,tanata tantamar ita ta cinyeta duka yawanta?. "Kece mana" ta bawa kanta amsa,tunda dai ita kadaice a falon bare tace da wani sukaci. Ta wanke hannunta kenan ta dawo zata zauna akace mata tana da baqo,mamaki sosai ya kamata,ta tabbatar ba shi bane......don bai taba neman izini wai don zaya shigo office dinta ba,saidai kawai ta ganshi gaba gadi,ta qaraci lissafinta kaf ta rasa gane waye,sai kawai tace a barshi ya shigo. Goumar ne cikin shigar suit,sanda yake sallama daga bakin qofar office din sai taga yana juye mata maina. Ta tsareshi da idanu,har sai da yayi ciki ciki da idanunsa sannan yace "Madam......stop starring at me.......ba oga maina bane,wannan baqin buzu ne,angon najma......" Maganarsa tayi tasiri qwarai wajen ankarar da ita ta dawo sautinta,akwai similarities sosai na wasu abubuwan tsakaninsa da maina,amma saita dake ta kums murje idanunta tana watsa masa harara "Waye kuma maina?,sannan waye baqin buzu?,duk ba wanda na sani a cikinsu, Mr disturber me ka biyoni office kayimin?" Dariya sosai ta taso masa,komai wahala bata rasa confidence wanda yake ta'allaqe da tsananin taurin kai da kafiya da take dashi. "Zuwa nayi na taimaka miki na daukeki mu dauko yara mu koma gida.....naje gidan naji shuru,ba abokiyar rigima ba kuma yarana.......maimakon ki fara tambayata ma saukar yaushe saiki soma min masifa da tsiwa......ke wannan yarinyar anya zaki iya riqe miji kuwa?,kada halinki fa ya sanya ayo miki kishiyoyi tun bakici talatarki da laraba ba". Idanunta kamar xasu fado ta watsa masa su "Me aure akewa kishiya ai,kuma wadda keson miji ke kishinsa...kumsma wai don Allah nace ina buqatar taimako?" "Oh.....really?,ashe bakisonshi har yanzu ko?" Yayi mata tambayar yana kafeta da idanunsa. Amsar da zata bashi taji ta mata nauyi,ta kuma tsargu iyakar tsarguwa. Kodai yana sane da yadda mainan ke biyo dare ya turmusheta?,da kuma sakin layin data taba yi?. "Ta ina?" Ta yiwa kanta tambayar,saboda ta sani sam maina baya layin maza masu bayyana sirri,sirri koda yaro qarami ne yayi dashi babu meji bare nashi,sam ma bame surutu bane bare ace garin yawan maganarsa ya tonawa kansa asiri,yanzunne rashin maganarsa ma ke dan raguwa saboda yanayin rayuwa da kuma gwagwarmaya da mutane. "Tunda baki sonshi zamu sanya ya auro wadda ke sonshi....." "Stop it" yaji an fada ta cikin Bluetooth din kunnensa,sai ya miqa hannunsa yadan tabashi kadan murmushi yana qwace masa. "Taimako kuma tsakanina dake ai ya zama dole tunda qanwata kike" ya qarasa fadi yana shiga sosai cikin office din. Fara tattara mata kayanta yayi,saita kasa hanashi don gaba daya jikinta a mace yake,ji takeyi ma kaman tace ya matso da motar cikin office din kawai ta shige,tsiwarta dukka ta qarfin hali ce kawai,taji dadin zuwan nasa sosai,to amma fa wannan halin nasu ita da goumar sai an rabashi sannan zasuji dadi. Sassanyan ajiyar zuciya ya saki sanda yaji fitarsu a office din,ya maida bayansa jikin kujera yayi relaxing yana lumshe idanunsa. Badai zata daina nunawa duniya bata sonshi ba?,ba zata daina nuna cewa bata damu dashi ba?. Bude idanunsa yayi ya kalli calendar,akwai kusan kwana goma sha biyu a gabansa kafin ya dawo,yana jin kamar yayi tsuntsuwa ya baro komai ya dawo din. Tunda har take nuna komai da zafinta,shima yaci alwashin sai ya sanyata ta kusa haukacewa a kanshi,yayi alqawari sai ya sanyata ta fidda duk wani sirri dake cikin zuciyarta ba tare data iya boye koda abu daya ba. Ya mata dukka dagin qafar da zaiyi mata,a zatonsa zata fidda komai da bakinta,tunda ta zabi ya turara zuciyarta da kyau to shima a shirye yake,har yanxu ya tabbatar batasan ainihin waye maina ba.....but a wannan karon zata gani......yazo qarshe ya kuma kai bango.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 116 To zuwan goumar a wannan karon sai ya zame mata na daban akan kowanne zuwa da ya saba yi,tun suna Austria har zamansu a Paris. Don ita kanta sai ta dinga jin dadin zuwan nasa cikin gidan,kewa ta dinga ji yana debe mata,duk kuwa da cewa bata sanya kai cikin shirmensu da shirginsu da su benazeer,amma dai tana wajen suke bidirinsu. Dole ta soma zaman parlor ganin yadda zaman daki yake neman fin qarfinta,yake kuma neman maidata zautacciya. Bata da ikon zama ita daya sai ta zurfafa a wasu tunanuka na daban da suka shafeshi. Koda tana cikin jama'a ma bata rufa minti talatin bai fado mata a rai ba "Wai ina ya tafi?,ina ya shiga?" Wannan tambayar itace tafi tsaye mata a rai. Hatta goumar bata taba gani suna waya dashi ba,suma yaran har ama ba wanda taji yayi zance ko cigiyarsa. Dukka wannan abun sai dare yayi tazo kwanciya sai bacci ya gagareta,suyita fafatawa da idanunta amma tunani yace baisan wannan ba. Sau tari saidai ta hada benazeer da batoul duk biyun ta rungumesu a jikinta sannan take samun sa'idar zuwan bacci. Banda zaman data koya qarfi da yaji a falo ta tabbatar qila da yanxun ta fara samun dimuwa. Sauqin abun daya ayana bata fiya zama a gidan ba sosai,ko tana nan dinma bata fiya zama a falon ba muddin ita da yaran da goumar suna ciki. Abinda ta lura ba wata jituwa tsakaninta da goumar,batasan meye dalili ba,amma gaisuwa itace kadai tsakaninsu. Tayi mamakin hakan kasancewar goumar bame irin wannan halin bane sam,bashi da fada wulaqanci ko qyamatar mutum,amma dai miskilinne shima tamkar yayansa. Ayana din tana da dan daukar kai,don haka ba ruwansa da lamarinta. *******Da yammacin da yayi dai dai da sati biyu da kwana daya da tafiyar maina din. Suna daga gaban gidan,benazeer goumar da batoul suna dan buga qwallon qafa bame zurfi ba sosai. Ya dage lallai sai ya koya musu,suma din kuma suna so,don haka daga ita har ama sai ganinsu sukayi da Jersey masu kyau da ball dinma kanta. Baki ama ta kama tana kallonsa "Kana da daurewa qarya qarqashi uncle goumar,yara mata da football?" "Eh mana ama...... tunda mamansu taqi bamu baby boy......kinga gwara na maida mata yara maza qila tayi zuciya" sanda ya fadi maganar tana zaune saman kujera,ta gama shan kankana kenan wadda tun safe itace abinda ta sanya a cikinta saboda rashin sha'awar cin abinci dake damunta,ga kuma cushewar ciki. Har cikin qashinta taji wani irin sanyin kunya yana ratsata, maganar tayi mata girman da ya sanya ko kanta ta kasa dagawa "Na shiga uku..... innalillahi goumar?" Ta fadi cikin ranta kawai tana ci gaba da latsa wayarta tamkar bata a wajen. Ama ma abun ya mata nauyi amma kuma saita saci kallon fuskar sultana din,bata samu nasarar ganin kowanne reaction nata ba,don haka batace komai ba ta juya tana wucewar ciki. Allah Allah dama takeyi ama din ta juya,ta jefa wayarta gefe tana kallonsa idanunta awarwaje zata sauke masa. Hannunsa ya dora saman lips yana zare mata idanu kamar yana magana da qaramar yarinya "Wallahi kina cewa tak zan dawo da ama,kuma idan tazo cewa zanyi kema kince kin qosa ki samo mana din......don dai kawai sunqi fahimtar haka su maidaki dakin yaa maina" qamewa kawai tayi tana dubansa,mamaki ya cikata,tayi imanin zai aikata tsaf,ta rasa mw zata masa ta rama,sai ta miqe kawai ta kwashe tarkacenta tana cewa "qanin maina dinne ai,zaka aikata,in sha Allah sai an qara shekara daya akan ranar aurenka da najma" ta murguda baki tana wucewa dakinta. Tana jiyoshi yana qyalqyala dariya harda kwanciya,batoul da lokacin suka dawo parlor din suna tambayarsa "Uncle goumar meye?". Lokaci lokacin tana dan daga kai taga yadda suke buga ball din,sannan ta maida kanta ga system dinta da take research a ciki. Fayau takejin cikinta ba uban komai,amma kuma batason cin komai din,ta kuma soma gajiya da saka tanja ta soya mata wainar fulawa,wanda kullum sai goumar ya tasata a gaba yana fadin "Ni banga abun dadi a fulawa da mai da albasa ba,salon kwadayi ne kawai wannan,daga yanzu ama na daina siyo fulawa a list na shopping din gidan nan" Bata da amsar bayarwa,don ita kanta tana mamakin yadda ta maqale mata. Ama kuwa da idanu kawai take binta,ba abinda yake damunta irin yadda duk wani kuzari nata ya ragu,ga kuma ramewa da takeyi a tsaye haka kawai, addu'a takeyi cikin ranta, ubangiji ya sanya hankalinta ne ya soma karkata akan mijinta. Sanda taji dariyar goumar da batoul suna yiwa benazeer dariyar an cinyeta wayarsa dake ajiye gefanta ya dauki tsuwwa,ya saki ball din yazo ya daga wayar yana dubawa,sai ya sanya Bluetooth dinsa a kunne yana fadin "Good evening bros....." Maida kanta tayi a hankali kan system dinta tana ayyana mintunan da zata tashi a wajen ta shiga ciki koda tsiya ta samu wani abu ta tilastawa kanta cinsa. Zama goumar din yayi yana amsa wayar,yaran suka dawo gabansa suka zauna suma. A hankali sai zuciyarta da kunnuwanta ke fusgar wayar goumar din. Sannu sannu take bin maganar da yakeyi cikin wayar,gabanta yayi wani mugun faduwa lokacin data fahimci da maina yake magana. "He's safe dama?,yana ta wani wajen ne?" Ta yiwa kanta tambayar. A hankali sai taji ranta yana baci,duk yadda taso yage kunnuwanta daga jin hirarsu amma haka ya gagara. "Gasu a gabana ma.......dama tun jiya suke mitan kace zaka sake kira baka sake kiransu ba har sukayi bacci.......BB ga daddy..." Sai ya miqa musu wayar yana sanyata a handsfree,ya matsa gaba yana kwashe ball dinsu da takalmansu da suka zubar hankalinsa kwance kaman sultanan bata wajen. Fes muryarnan tasa dake da wani irin amo me saurin isar da saqo da kuma tsayawa cikin zukata ke fita ta speaker din wayar goumar. Hira yake sosai da yaransa,irin hirar da kana ji zakasan ba wai yau ya fara kiransu ba daga sanda yayi tafiyar,don sunata tambayarsa abubuwa yana basu amsa. Hira irin ta d'a da uban da suka shiqu,yaran suka dinga dariya suna kwanciya saman grass carfet saboda tsokanar da yake musu. Kadan kadan taji wani abu yana tsaya mata a wuya,ranta ya dinga motsuwa da kadan kadan yana baci. Kasa jurewa ci gaba da zama a wajen tayi sanda taji ya tambayi ama sannan kuma ya hada da tambayar ayana,ya kuma kashe wayarshi ba tare da ita ya tambayeta ba,saita wuce ciki a gaggauce bata ko waiwayosu ba. Saman gado ta zube tana qoqarin gayawa kanta kada ta soma kuskuren damuwa dashi,kada ta yarda wani abu me suna damuwa a kanshi ya shiga zuciyarta,meye ma hadinsu?,ya tafi yayi shekara kusan biyar bata damu ba sai yanzu?,me yasa zata damu ne?. A haka tayi sallar magariba,tayi isha'i,dole bayan isha'i ta fito don neman abinda zataci ganin yunwa na neman halakata,ga wata azababbiyar yunwa kamar bata taba cin komai ba a duniya. Motsin fitowarta falon yaja hankalin ama,ta daga kai tana binta da kallo bayan ta musu sannu da gida ta wuce kitchen. Sanda ta fito da cup data hada madara da cornflakes sai ama ta kasa jurewa ta kirata. Qasan carfet ta zauna,don tana jin jikinta dukka ba qwari "Baki da lafiya sultana" ama tafadi kanta tsaye. Tanaso cewa ama din lafiyarta qalau,don ita bata yarda bata da lafiya ba,amma sai wani mugun rauni ya mamayi zuciyarta,take kuma hawaye ya cika mata qwayar idanu,daga ama din har goumar da yaran dake wajen sai suka zuba mata idanu. Kallonsu gareta ya sanya ta aro juriya,tana qoqarin shanye hawayen muryarta na rawa kadan tace "Lafiyata qalau ama" "Ban yarda ba.....bakiga yadda kiketa rama a tsaye ba kaman kin hadiyi allura?,sai uban haske fau?,ko aba dinku da ba zama yake ba jiya sai da yayi complain kan ramar da kikeyi,ya tasani gaba akan lallai lallai na tambayeki ko kina da damuwa?" Dan shuru tayi kanta a qasa,batasan me zata ce da ama ba,kuma fadin ba komai din ta tabbatar ba zata taba yarda da hakan ba "Bana iya cin abinci ne ama" "Me yasa?" Ta jefa mata tambayar tana tsareta da idanu "Ina tunanin aiki ne da ban saba dashi ba.....amma komai zai warware in sha Allah" ta fada tana jin karayar zuciya sosai. Shuru ama ta danyi kaman bata gamsu ba,sai kuma ta dubeta "Rashin cin abinci indai ba da ciwo ba to akwai matsala,ki dinga qoqari kina cin abinci,aiki ba uzuri bane kuma ya zamana harda rama a ciki ma" "In sha Allah " ta fadi tana jin dadin ta kufcewa tuhumomin ama din. Tana zaune saman sofa cikin dakin tanja ta shigo mata da yaran,ta shiryasu tsaf suka haye gado tayi musu sallama ta fice. Sama sama takejin qananun hirarrakinsu,wani shirme na yarinta wani kuma fal quruciya,tana zaune kawai tana dafe da kanta saboda yadda madarar data sha din ke taso mata,tanata qoqarin ganin ta danne aman da takeji,amma daga qarshe sai da yaci galaba a kanta. Da sassarfa ta miqe ta wuce bandaki tana yunquri,abinda yaja hankalin batoul da benazeer,dukka suka miqe saman gadon suka zauna suna kallon juna, sukayi carko carko suna jiyo nishin yunqurin amanta,sai kuma suka sauka kusan lokaci guda suka nufi bandakin da gudu gudunsu.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 117 Sai data amayar da duk abinda yake cikinta tas,ta dafe sink tana fidda numfashin wahala "Sannu mummy....." Taji muryar batoul,wanda tana waiwayowa benazeer itama ta jeho mata tata tambayar "Mummy dama baki da lafiya?" Yadda suka rutsata da idanu haka itama take kallonsu,tama rasa amsar da zata basu,sam ta mance suna cikin dakin. Numfashi ta sauke ta juya tana kuskure bakinta hadi da wanke fuskarta,sannan ta tako ta kama hannuwansu suna fitowa daga bandakin. "Lafiyata qalau,bana dan jin dadi ne" "Na kirawo ama sai mu tafi asibiti?" Batoul ta tambaya fuskarta na nuna damuwa sosai. Kai ta girgiza da sauri "Kada wanda ya gaya mata koda gobe da safe ne,ai naji sauqi,ku koma ku kwanta maza". Sai data tabbatar sun kwanta din sannan ta koma saman sofa bed ta nade da wani blanket din daban. Ta cure sosai waje daya saboda sanyin da takeji yana ratsa qasusuwanta,ta kwantar da fuskarta saman cinyarta tana lumshe idanunta. Sosai takejin wani kewa yana ratsata,tana jinta incomplete tun daga zuciyarta zuwa gangar jikinta. Allah ya taimaketa washegarin ba wanda ya tayar da maganar cikin yaran,saidai ta lura gaba daya sun damu,bini bini idanunsu yana kanta. Batason dorawa ama damuwa me yawa a kanta,don haka sai taqi zaman falon gaba daya ta tattare a bedroom. Hakan ya taimaka mata sosai,don dama jikinta bata jin wani qwari da zata iya dogon zama ko hira cikin mutane. Ranae ta kira bibinta,sun jima suna hira da bibi din,doguwar wayar da suka dade basuyi irinta ba. Maganar bibi ta qarshe da ita ta kashe waya tana juya maganar cikin ranta "Daga ke har aliyyu har yanzu babu wanda ya yiwa kansa fada?" Dan jim tayi tana hade fuska kaman bibi tana wajen. Itakam zancan aliyyu ya isheta,har yanzun basusan zai iya sanya qafa ya tsallake yayi tafiyarsa ya barta ba?,har yanzu basusan bai dauketa a bakin komai ba?,basusan har yanzu bayajin komai don ya tafi ya barta ba?. "Wanne aliyyu?" Ta tambayi bibi. "Qaniyarki ja'irar banza ja'irar wofi" bibi ta fadi tana watsa hannuwa kaman zata kamo sultana "Kubar ganin kunyimin nisa daga ke har maina din zan sanya a maidomin ku gabana nayi maganinku.....kina jina ko?" "Allah ya baki haquri" kawai ta fadi a sanyaye,tunda dai tsahon zamanta da bibi ba zata iya tuna sanda ta zageta har haka ba. Ji tayi bibin ta kashe wayarta don haka itama ta aje wayar tana maida kanta saman filo hadi da fidda numfashi,ta lumshe ido tana jin zuciyarta tana mata suya sosai. Kaf matsalar rayuwarta maina ne,kuma still dai har yanzu shi dinne,batasan me yasa ya tsayewa rayuwarta har haka ba......ta fara gajiya itama,tana buqatar hutu a rayuwarta gaba daya. Zuwa yanzu ta fahimci ko taqi ko taso yanason zamewa rayuwarta jarrabawa,wata jarrabawa da babu yadda zata iya shallake mata. Abinda takeji a kwanakin nan dukka yana son sauya tunaninta.....duk yadda takai ga kafiya da sauya ma'anar tunaninta tana ji a sannu a sannu komai yana canzawa,tana jin tana qaryata kanta da kanta,uzurorin da take bawa kanta da kanta game dashi tana jin zuwa yanzu zuciyarta ta daina gamsuwa ta kuma daina karbar uzurin sam. Kanta ta sake gyarawa tana goge qwallar data ziraro mata,sai taji an turo qofar ana shigowa. A hankali ta juya bayan ta sake goge danshin idanunta da kyau. Ama ce,idanunta dukka akan sultanar,hakan ya sanya sultana yunqurin tashi ta zauna sosai. "Yau duka na jiki shuru baki fito ba,na tambayi yara suncemin kina kwance tun safen?,anya kuwa sultana?" Ta qarasa tambayar tana samun waje dab da sultana din ta zauna. Qasa tayi da kanta,zuciyarta nason karyewa amma tana bawa kanta qwarin gwiwa "Jikina ne ba qwari,amma lafiya nake" dubanta kadan ama tayi tana qaryata zancanta,don ko kusa ko alama bata gamsu ba. Yadda take ramewa yafi komai daukan hankalin ama din,wasu dabi'u nata da yawa sun sauya,saidai hankalinta ya kasa kaiwa inda zuciyarta keson kaita,saboda tana da dalilai da ta tabbatar hakan bazai kasance ba "Dama ta yaya jiki zaiyi qwari kinqi abinci?, bari aliyyu ya dawo maganin cin abinci xan sanya ya rubuta miki,idan ma ulcer keson hanaki cin abinci,kina fita aiki sannan kuma ba zaki zauna kici abinci ba?". Kai ta daga ta kalli ama sai kuma ya sauke,kiran sunan aliyyun ya haifar mata da wani abu a gangar jiki da zuciyarta,kamar akwai tambayar da takeson yiwa ama din amma ta kasa. Rasa me zatace da ama din tayi,har tayi mitarta ta gama ta miqe "Ya kamata ki fito hakanan,shima zaman kadaicin kashe jiki ai yakeyi tunda ba wani aiki kike yi ba" "To" ta amsa mata a sanyaye. Numfashi ta aje,har ga Allah batason fita bare su hadu da ayana,amma dole ta daure ko don cika umarnin ama. Toilet ta shiga ta sake wanka wai ko zataji dadin jikinta,ta sauya kaya zuwa wasu riga da skirt na material marasa nauyi,ta sanya dan siririn Gyale ta lullube sumarta data hade cikin wani qaramin band. Sosai fuskarta ta fito fes,tayi fayau da ita,ta sirance sai mugun haske data qara,kayan sun amsheta qwarai da gaske,duk kuwa da cewa ba wani kwalliya ta yiwa fuskartata ba,sai sassanyan qamshin turaren da jikinta yake fiddawa daya dade da kama fatarta. Su biyar ne cikin falon,ama benazeer batoul goumar uban gayya,sai tanja dake zaune daga gefe tana gyara lettuce da zata yiwa ama hadin salad dashi. Fuskar kowa ta kalla,sai taga kaman kowa din cikin farinciki yake,kamar kowa yana cikin walwala banda ita,kamar ita kadai ta rasa walwala cikin gidan. Sannu da gida ta yiwa tanja da tun safe basu sake haduwa ba,ta amsa tana dan duban sultana din,don ita kanta tana ganin rama a tattare da ita. Tana zaune suna dan hira da tanja jifa jifa,tayi hakanne don ama din taji dadi ta sake bawai don tanason hirar ba. "Hadin salad za'a yi mana?" "Ko kina sha'awa a hada dake?" Tanja ta jefa mata tambayar tana jin tausayinta qasan ranta. " A haka dai sai nakejin ya burgeni,amma ban sani ba ko zan iya ci?,cikin nawa dai kaman ulcer keson cushemin shi" ta fadi tana dan yamutsa fuska. Murmushi kawai tanja tayi tana girgiza kai "Bari na kammala saiki gwada ci din" ta bata amsa ba tare data kalli fuskarta ba. Tsaf ta gama hadin salad din ta kawowa ama,ta isa gaban sultana ta aje wani dan bowl din tana cewa "To bismillah" "Na gode" ta amsa tana jin dadin yadda tanja ke kulawa da lamuranta,sosai take qaunarta qauna ta fisabilillahi. Zamowa tayi daga saman kujerar ta zauna sosai a qasa,ta bude bowl din zata fara ci dan neman rigimar ya sako benazeer da batoul daga bayansa wadanda yakewa doki "Kuje ku taya mummy twins cin abinci" "Aah suzo ga nasu" tanja tayi saurin tarewa. Dariya ya saki yana fadin "So nayi ki barsu suci tare,ita matar nan mafa bansan meye yake damunta ba,kunyace ko Kara?,wai sai taqicin abinci da yaran nan?" Harara ta gasa masa don bata da bakin magana a wajen tunda ama tana nan. Tanja ce tayi dariya "Kaidai anyi babban kwabo goumar,baka girma da jaye jayen rigima?,lallai saita kulaka kunyi?" Dariya ya sake saki yana jawa yaran kwanon salad din,don shi bai dameshi ba.. Sosai ta dinga jin dadin potatoe salad din,sannu sannu sai gashi ta cinye tas ta riga kowa ma cinyewa. "Ko a qara miki?" Tanja ta tambayeta,kai ta girgiza "Na gode tanja ya isa haka alhamdulillah" daidai lokacin ayana ke fitowa daga dakinta. Riga da wandone a jikinta,wandon yana da fadi amma kuma rigar me hannun vest ne, kunnenta maqale da earpiece tana amsa waya. Sai wani kwantar da murya takeyi cikin tsananta ladabtarwata,kallo daya goumar da sultanar sukayi mata suka dauke idanunsu,yayin data nufi ama kai tsaye tana fadin "Am sorry yaaya....... a'ah wlh,am sorry ya haidar.......ga ama din" ta fadi tana miqawa ama wayar da dama earpiece din. Cire earpiece din aman tayi ta karba wayar "Wai yanata kiran wayarki baki dauka ba,nace may be kin barta a bedroom ne" ayana ta fadi cikin jin alfahari idanunta suna satar kallon sultana. Kau da kai tayi kaman batasan me ayana ke fadi ba,saita maida hankalinta kan labarin abinda benazeer tayi jiya da tanja ke bata,ta sanyawa fuskarta dariya sosai kamar tana jin nishadi ko fahimtar abinda tanja ke fada,saidai duka ba wannan ba,ba abinda take fahimta sosai game da abinda tanja din ke fada,amma kuma batason maida hankalinta daga sashen da ayana ke zaune.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 118 Tsam ta miqe daga wajen sanda ta fahimci akwai wani abu qasan ran ayana,kuma dashi ta fito "Wardrobe dina nakeso na gyara tun last week tanja....bari naje na duba" "Da kin barshi uwar daki,ke da bakya jin dadi sosai?" "Qyaleta tanja,daki takeso ta gudu,ta shiga ta shirya kema ki shirya kuzo muje wani guri,na samo mana wani guri me kyau....... daughters aje a zabo kayan fita me kyau" ya qarasa maganar yana kallon benazeer da batoul. Wani wawan tsalle suka buga sukayi daki da gudu daya nabin daya,su dama ba abinda sukeso irin suji uncle goumar yace za'a fita,sunsan ranar sai sun qurewa yawo har illa ma sha Allah. Haka nan taji maganar goumar ya mata dadi da yace ta shirya su fita,yau din ba harara ba tsokana ba tsiwa,ta shiga ta shirya din kamar yadda goumar yace. Tayi kyau cikin tsadaddiyar abayar tata,daya daga cikin abayas nata da take ji dasu saboda yadda takejin dadinta a jiki idan ta saka. Ta samu ayana a falo kusa da ama,waya take dannawa amma zuciyarta fal da bacin ran yadda goumar din sam bai dauketa da wani daraja ba,baya bata dukkan girman da take buqata ace ya bata ba,ta fahimci goumar din yana da kusanci da maina da yawa,ya kamata ace ita yake dama dama da ita bawai sultanar ba "Sai illa ma sha Allah kenan ko?" Ama ta fadi tana kallonsu. Murmushi sultana tayi,itama kanta tasan yau sai inda man goumar ya tsaya,yana da son zuwa park park kamar baya gajiya,kamar kuma baisan zafin kudinshi ba. Sallama sukayiwa ama dukkansu suka fice suka barta daga ita sai ayana daketa baqin rai. Suna tafe a hanya amma zuciyarta tayi nisa wajen tunanin da abinda yake haifar mata dashi illa bacin rai. Meye hadinsa da ayana?,yana waya da ita kenan?,yana kuma kiranta?,yana kiran kowa ma na gidan banda ita?,ita daya tak?,to me hakan yake nufi?,hakan yana sake tabbatar mata da abinda ke saman harshensa yake kuma furta mata ba shine cikin zuciyarsa ba......bata da wani sauran amfani a wajensa sai na biyan buqatarsa?,a yanzun yayi nesa da ita,bashi da wata buqata don haka bai da amfani kenan ya nemeta.....indai hakanne ya tabbata baya sonta.....baya kuma qaunarta,wannan muguwar tsanar da yayi mata tun a farkon tarayyarsu tana nan zuciyarsa babu abinda ya kankareta. Yana da buqatar kowa amma banda ita,saboda ita din bata kai ba,bata kuma da matsayin komai cikin rayuwarsa. Wannan tunanin ya haifar mata da illa sosai cikin zuciyarta,ya kuma ji mata rauni me nauyi da radadi. Har cikin zuciyarta ta dinga ji eh yes da gaske bata da sauran amfani cikin rayuwarsa saina ssuke sha'awarsa......da gaske baya da buqatarta bata da muhimmanci sai idan zai sauke lalurarsa. Ta dinga goge hawayen da yakeson kunno mata kai,tanata qoqarin hadiye karyewar da zuciyarta tayi don kada ta ragema su benazeer da tanja jin dadin fitar,ta kuma sacewa goumar gwiwa wanda ta tabbatar ya qirqiri fitar ne musamman saboda ita. Koda bai fada ba dukka ayyukansa sun nuna haka. Goumar din dan uwa ne daya da daya,a baya da suke yawan samun sabani da kuma tsonakar juna bata taba zaton akwai ranar ra zatazo zai zame mata wani jigo kuma masharar hawaye kuma me qoqarin dauke mata damuwa ba. Duk da quncin da zuciyarta ke ciki tayi qoqari ta danne, guraren cin abinci uku ya kaisu,amma sai a guda daya ta zabi abu daya,da qyar ta iya zabar abu daya taci,shima bata kammala ba taci gaba daya ya fita a kanta. Sosai zuciyarta ta dinga tashi,ta dinga yatsina fuska saboda yadda yake taso mata "Lafiya uwar daki?" Tanja ta tambayeta. Daidaita kanta tayi qoqarin yi sannan ta amsa "Abincin na yake min yawo" "Anya uwar daki?,lafiyar nan taki da sauqi fa,ni banga kinci komai ba tunda mukazo sai abu daya,shima kince yana damunki,anya ba zakije asibiti ayi cakin dinki ba a dubaki da kyau?" Kai ta mirginar gefe,ita kanta batasan abinda yake damunta ba,saidai kawai tasan bata jin dadin komai ma,hakanan rayuwarta take jinta ta zama upsidedown. Bata iya baiwa tanja amsa ba,amma kuma maganarta ta tsaye mata a rai. Sosai goumar yayi yawo dasu,basu koma gida ba saida suka gaji tubus. Sunga gurare da dama wanda tun zuwansu Paris basu taba zuwa wajen ba. Ita kanta taji dadi,duk da yadda kasala ta dinga mata cikas,wasu guraren ma zamanta takeyi a mota su shiga su fito su taras da ita zaune. Daga qarshe goumar ya gaji ya kalleta cikin salon tsokanar nan tashi "Ke ba qiba kika qara ba ba komai ba amma kin koyi wani son jiki mara dalili?" Yayi maganar da son tsokanota. Murmushi kawai tayi ta dauke kai,taqi ce masa uffan,ganin hakan ya sanyashi shima bai sake cewa komai ba sukayi gaba,daman wani ice cream ya kawosu siya su wuce. Suna komawa yau kam ko wankan dare basuyi ba,banda sultana din da ko ina yake mata ciwo,ta hada ruwa me zafi tayi wanka sannan ta kwanta. Saidai kuma kwanciyar batayi nisa ba zazzafan amai ya taso mata. Kaman jiya dukka yaran suka tashi,sukayi carko carko. Ta gama ta fito ta samesu yau harda hawaye "Kuje ku kwanta,banaso ku tayarwa da ama hankali,zansha magani gobe in sha Allah" da haka ta lallabasu. Kwanaki uku kenan duk dare da kuma safiya sai tayi wannan asababben aman,ta kuma hana yaran su gayawa ama,tana ganin ulcer dince kawai tazo mata da wani salo na daban,don komai da takeji a jikinta na alamu ulcer yana kawo hakan,tayi duk wani qoqarin ganin ta daina wannan aman ta kuma samu energy a jikinta amma haka ya gagara. ********Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ta fito daga dakin nata,tana sanye da doguwar riga ta atamfa data bude sosai daga qasa. Shiga ce da ba kasafai ta fiya yinta ba,amma kuma duk sanda tayin tana bala'in yi mata kyau a jiki sosai. Medium mayafi ta yafa saman kanta, daga takalmin qafarta har hand bag dinta dukka designers ne daga kamfanin Hermes. Ko mace 'yar uwarta idan fa kalleta dole yanayin adonta da kamewarta ya burgeta bare namiji,tayi wani irin kyau saidai sirancewa da tayi da haske data qara. Idanunta akan fuskokin benazeer da batoul dake kwance saman cinyar ama,sanda ta fito ta fuskanci akwai abinda suke gaya mata,amma fitowartata ya sanyasu yin shuru suka bita da idanu kaman yadda itama ta bisu da ido. Abinda bata lura dashi ba ama itama kallonta takeyi,har ta qaraso ta rusuna tana gaidata "Sai ina?" Murmusawa kadan tayi "Zan leqa office.....zan rage wasu ayyukan" "Allah ya taimaka.......amma sultana......kina kallon kanki a madubi kuwa?" Ama tayi mata tambayar yau kai tsaye idanunta cikin nata. Jikinta sultana ta kalla sannan ta maida dubanta ga ama din "Me nayi ama?" "Bakiga yadda kike qashin wuya ba?,ko baki fuskanci kayan sawarki sun fara miki yawa ba?". Gyara yafen mayafinta tayi tana dan jingina da kujera saboda yadda takejin kaman iska zata kayar da ita saboda yadda take jinta fayau,ta rasa me zatace da ama din "Allah ya tsare" aman ta bita dashi. Tanason ganin iya gudun ruwanta ne,yaro baya qarya amma ba zata gasgatasu kai tsaye ba,saidai kuma shi ciwo ai ba'a isa a boyeshi ba. Jikinta a sanyaye ta fita,ta tayar da motar tana jin zuciyarta na karyewa idanunta akan gidan data fuskanci ko budeshi ma ba'a yi,alamar me gidan yayi nisan kiwo kenan. Sai kuma ta dauke idanunta da sauri tana jin haushin kanta da kanta. Don meye zata tsaya tana kallon gidan mutumin da bai damu da ita ba?,bai damu data rayu ko ta mutu ba?,farincikinsa ba damuwarsa bane sai biyan buqatar kansa kawai da ya sani?. A guje ta tashi motar tana ficewa a layin tare da tilastawa hawayen da yake qoqarin digowa komawa inda ya fito. Sosai ta dinga qoqarin sakewa cikin ma'aikatan wai koda iya na yau ne kawai ko zata samu sassaucin abinda takeji,saidai kuma kome takeyi tana jinta ne sama sama kaman me tafiya akan iska. Qarfe biyu na azahar ta samu taci chips da kaza sai dan black tea kadan,zuwa qarfe uku taji dukka dauriyarta ya qare,do haka tayi musu sallama ta wuce gida. Ta ajjiye motarta a inda sukan bar motocinsu,ta bude motar ta fito idanunta akan motar aba tana mamakin ganinsa yau a gida haka da wuri. Tun zuwansu qasar aba bai fiya zama a gida ba,harkoki ne kawai suketa bude masa,wani lokacinma yana cikin paris din amma wani garin,sai yayi kwana biyu a can kafin ya qaraso gida. Kauda wannan tunanin tayi ta fara takawa zuwa qofar gidan. Sau biyu rak ta danna bell aka bude. Batoul ce,hannu dumu dumu da cream na cake. Ko ba'a gaya mata ba tasan yau ranar zuba fitinarsu ne a gida,me daure musu qarqashi aba yana gida. Da sallama ta shiga falon,amma ragowar sallamar ta maqale mata saboda warin tafasar shinkafa daya taso daga kitchen ya iske hancinta. Ta hadiye wani abu da qyar,yawu kuma ya cika mata baki sai taji kanta na neman juyawa,dole ta samu kujerar da tafi kusa da inda take ta zauna tana tunanin yadda zata hadiye yawun bakinta saboda ama dake wajen. Idanunta ta runtse da qyar ta hadiye,sai ya tsaye mata a qirji ya soma taso mata,ya kuma hadu da warin dahuwan shinkafar ya soma dagula mata lissafi. Cikin minti daya amai ya fara taso mata,wannan ya sanya a gaggauce ta miqe tana fadin "Bari na sauya kaya nazo mu gaisa da ab......." Bata iya qarasawa ba wani irin jiri ya maidata ya zaunar "Subhanallahi" ama ta fadi da hanzari tana yowa kanta,qasan ranta tana godewa Allah da ya sanya ba'a qasa ta fadi ba "Sultana.....kina jina?" Ama din tana rufe baki zazzafan amai ya taso mata. Tun tana amayar da chips da naman da taci har ya zamana yunqurin kawai takeyi cikin babu uban komai,sai yawu da wani irin yellow din abu dake fitowa. Fara fita hayyacinta tayi,don qirjinta ya riqe sosai da kalar yunqurin da takeyi,ama ta fahimci haka,tasa hannu ta dafe mata qirjin da kyau hankalinta a mugun tashe tana mata sannu. Sai data galabaice gaba daya sannan yunqurin ya tsaya,zuwa sannan kowa yana tsaye saman kanta harda aba dake can daki. Benazeer da batoul ma na tsaye a gefe suna sharar qwalla,haka nan goumar da shigowarsa kenan yana tsaye shima,sai ya jawo yaran hana shafa kawunansu. Daga idanunta har fuskarta dukka sunyi jajur,hawayen da batasan na meye ba ya tsinke mata. Tanja ta kawo roba da ruwa ama ta riqe mata ta kuskure bakinta. Haka kawai gaba dayanta take jinta a tsarge,ta gama tanja ta karbi roban ta wuce don ta zubar. "Sannu sultana......nakega hamdiyya taje taga likita mana ko?" "Eh in sha Allah aba" ama ta fadi jikinta a sanyaye,hankalinta kuma yana rabuwa gida biyu. Aba ne ya fara juyawa yana komawa ciki tare da qara yi mata sannu,sai ama ta kalli goumar "Jasu ku koma ciki......tanja duba mata wasu kayan ta cire wadannan,ki dafa mata madara ki kawo ta fara sha tukunna kafin na yiwa asibitin waya" dukka suka amsa mata suna juyawa ciki,sai falon ya zama ba kowa daga ita sai ama din. Sai da ama ta qare mata kallo sosai,irin kallon da ake kira da kallon qurilla,kallon data jima bata yi mata irinsa ba,sai take ganin kamar sultana ce a gabanta ta shekaru shidan da suka shude,sultanar dake laulayin cikinsu benazeer,amma a yanzun ya za'a yi hakan ta kasance?,bayan ta bada tazara tsakaninta dashi tazara me tsahon da wanda ke nesa ma ya shaida haka bare su da suke a kusa. "Zan tambayeki,ruwanki ki gayamin gaskiya ruwanki ki boyemin kaman yadda kiketa rufata tunda baki daukeni uwa ba" ama ta fadi tana zama kujerar dake kallon tata. Hawaye ne ya balle mata da jin abinda ama din ta fada,ta sani tabbas ba zataji dadi ba,ta tambayeta yafi sau shurin masaki akan lafiyarta,amma kulluma amsa daya take bata lafiyarta qalau. "Already yara sun gayamin,kullum baki da lafiya a haka kike kwana,kwananki nawa kina wannan aman?" "Bai wuce kwana biyar ko shida ba" ta fada da shagwababbiyar muryar nan data tunawa ama cewa sultanar bibi ce fa har yanzu,a wasu dabi'u nata basu canza ba,wasu halaye nata har yanzu suna nan "Shine kika gwammaci ki xauna a haka kiyita fita aiki kamar wadda aka gaji da ita ko bata da gata?" Ama ta jefa mata tambayar tana tsareta da ido ranta yana baci. Tana dauka a ranta cewa sultana dolenta ce a rayuwa gaba daya,tana ji a jikinta kamar itace ta tsugunna tayi naqudarta,bataso ko qaunar dukkana abinda zai cutar da ita,kaman yadda bataso ace sultana tana boye mata komai. Kasa bata amsa tayi,sai qasa da tayi da kanta tana matsar qwalla. Tanja ta qaraso da kayan,ama tace da ita "Bata ta shiga dakina ta canza ta fito,ki cewa goumar ya dauko mota,yabar miki su benazeer muje mu dawo" "Tom" tanja ta fadi tana juyawa,can qasan ranta tana jin dadi da Allah ya kawo dalilin da dole aje asibitin,ita kanta kawai dai tana addu'ar Allah yasa a kurkusa ama din ta tursasa aje din,siririn murmushi ya kubce mata tana jin farinciki sosai,tana kuma ayyana drama da za'a yi a gidan nan gaba kadan.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 119 A gida suka bar yaran da tanja,sun yarda sun xauna ne saboda aba yana gidan. Ita da goumar da ama ne kadai cikin motar,sai motar ta dauki shuru,wannan dalilin ya sanya goumar danna fefan waqensa na soyayya yana bi kadan kadan. Idanunta ta lumshe tana jin kalaman dake fita daga ciki kamar da ita ake,can qasan ranta kuma tana jin wata fargaba haka kawai game da zuwansu asibitin. Kai tsaye emergency suka amsheta,don jikinta yayi weak sosai,duk da ba wani galabaita tayi na fitar hayyaci ba,to amma qasashe ne da basa wasa da lafiyar mutum,hakanan ciwo komai qanqantarsa suna bashi kulawa ta musamman. Drip suka fara sanya mata don qarfin jikinta ya dawo,ba'a jima da saka mata drip din ba wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita. Ama na gefanta goumar na daya gefan,yana danna wayarsa a hankali kiran maina ya shigo. Disconnecting na wifi yayi sannan ya daga kiran yana miqewa tare da dosar hanyar fita. Cikin girmamawa goumar ya gaidashi "Lafiya Lau,ya akayi yau banji BB ba?" "Bama tare ni nan ina asibiti" saman center table din dake gabansa ya miqe qafafunsa yana zama sosai "Asibiti?,waye ba lafiya?" Yayi tambayar cikin tsananin kulawa yanayin fuskarshi yana canzawa "Mummyn twins" "Ya salam" ya dora da fadi goumar yana ajiye bayaninsa. Hannunsa ya aza saman sumarshi yana shafawa,har cikin zuciyarsa yana jin damuwa sosai "Kada kacemin damuwa ce?" Dan murmushi kadan goumar ya saki "Gayen nan yasan takan d'ana tarko" yayi gulmar maina qasan ranshi "To akwai damuwar ma dai.....amma basuyi gwaji ba,naji likitar tace sai drip din da aka sa mata ya qare" "What?,drip?" Ya tambaya a dan rude "Yayi worst ne jikin?" Ya sake jefawa goumar tambayar muryarsa na nuna damuwa ainun. "No,bawai tsanani yayi ba,jikinta yayi weak ne sosai......" "Kaga goumar ya isa haka......gobe inajin zan biyo jirgin yamma,kazo da Allah airport ka daukeni......komai ya kamata yazo qarshe hakanan" "Yes sir" goumar ya fadi da girmamawa,amma kuma yana danne dariyarshi qasan ranshi. Ya jima baiga masoyan dake bawa juna punishment irin maina da sultanar ba. Kowa a cikinsu yana ji a jikinsa,amma sunqi bawa jikkunansu da zuciyoyinsu hutu,to aqalla dai har gwara maina din,yana son ya matsa gyada ne tayi mai koda bata shirya ba "Please ka kula da ita..... banason ayimin ganganci da mata koda wasa" "An gama big bro" ya fadi murmushin da yake boyewa yana fita a dole. "Kana cikin hankalinka?" Maina din ya fadi a dake,take goumar ya shiga nutsuwarsa don yasan abinda tambayar tasa ke nufi "Afwan yaa haidar" ya fada yana daidaita nutsuwarsa,akan haka sukayi sallama ya juya ciki. Da dan sauri ruwan ke shiga shi yasa yake tafiya da saurin. Ya dubi ama yana tamabayarta ko akwai abinda suke buqata?,sai ta girgiza kai "Ba komai,ai Allah ya kawo mana sauqi,likitan neighbor dinmu ce,zasu dauki sauran test din da za'a mata,tace saimu wuce gida,gobe idan ta tashi daga aiki zata shigo da result din,idanma akwai wani treatment da zata buqata duk ba damuwa bane" kai ya jinjina ya koma saman kujerarsa ya zauna. Ruwan yana qarewa ta farka tamkar tare suka tafiya da baccin nata. Likitar nada kirki sosai,ta zare mata allurar tana mata sannu,ta dauki sample na jininta dana fitsari,suka dan sake cewa ta huta duk da taji dadin jikinta sosai da drip din da suka sanya mata,sai kuma yunwa da takeji kaman taci babu, goumar na tsokanarta ya fita na mata abinci "Kodai mayu ne suka kamata ama?,akwai mayu a qasar masu jajayen kunne?" Ya kalli ama yana tamabayarta. Waiwayowa tayi tana dauke kanta daga kan sultana da taketa nazarta ta jefeshi da harara don iya shegen goumar ba wanda ya bari "Ka tambayi 'yan qasar idan kaje siyo abincin.....xaka tafi ko so kake muyi dare cikin asibiti?" Yana dariya ya fice,saita maida dubanta ga sultana,tana kallon tafukan hannayenta dake zube kan cinyarta tana lissafa wurudin da takeyi bayan ta idar da biyan bashin sallolin dake kanta. Gaba daya hannayenta sun dashe,sosai suke nunawa ama alamomi da yawa,saidai har yanzu taqi gamsuwa,ta kalli qafafunta ta kuma sake maida dubanta ga qwayar idanunta,duk abu daya suke gayawa ama,amma taqi gamsuwa sa hakan,daga qarshe ta tattara tunanin ta maidashi baya,ta miqe tana maida qananun kayayyakinsu cikin qaraman jaka tana jiran dawowar goumar,tasan zuwa sanda zata gama cin abincin mitunan da sukace ta qara din sun cika sai wucewa gida kawai. Kamar kowanne lokaci idan bata da lafiya,kamar kuma kowacce uwa haka ama ta tsaya a kanta. Sanda suka iso gida ta tabbatar tasha maganin ciwon jiki da suka fara bata,tayi wanka da ruwa me dumi sosai,ta kuma saka tanja ta dafa mata madara kaman dazu. Sai data tabbatar tasha,sannan ta sanya aka kawo mata su benazeer kaman yadda aka saba. Don tun daga ranar data fara daukansu su kwanan mata kullum dakin suke kwana,koda wani abu ya dauke mata hankali bata zo daukansu ba,ama zata sanya su taho ko tanja ta kawo mata su. Hakan da ta fara yi da kanta ya yiwa ama dadi sosai,don tsuntsu biyu ta jefa da dutse daya,kuma yadda take dibansu tayata kwana ta tabbatar ruwa baya tsami banza,ta tabbatar akwai wani kusanci na daban tsakanin zukata biyu dakan iya motsawa. Sunyi rigata yin bacci yaran,sanda ta gama komai ta kwanta daga bayansun kamar yadda ta saba sun jima dayin nasu baccin. Ta rufe idanunta tana sakin ajiyar zuciya,tana jin raguwar ciwon da gabbanta sukeyi mata sosai,saidai har yanzun zuciyarta bataji ta samu sukuni da nutsuwar daya kamata ace ta samu ba. Vibration na wayarta dake saman kanta ya tilasta mata bude idanuwan nata. A mamakance take kallon qaramin agogon dake ajjiye saman bedside dinta tana duba lokaci tare da mamakin waye yake kiranta a irin lokaci irin wannan?. Wayar ta dauko saita maida kanta saman pillow tana duba kiran. Baquwar number ce,babu ita cikin list na contact dinta,wannan ya sanya ta maida wayar ta ajjiye. Tana ji tana ci gaba da bugawa,duk motsin wayar tana qididdige dashi,har zuwa sanda ta gama vibration dinta ta yanke. Kamar wadda ke jiran ta yanke din saita sake maida idanunta ta rufe,yadda wayar ta dinga burari ya dinga dawo mata akai,bata kammala ba wani kiran ya sake shigowa. Ba kasafai ta fiya maida kai ga kiraye kirayen da batasan waye ba,amma koda ta sake duba kiran taga dai still wannan number dinne saita gaza ajjiyewa,ta daga kiran ta kara a kunnenta tana daga kwancen. Wannan husky voice din nashi cikin wani irin softness da ita ya cika kunnuwanta da cikakkiyar sallamar data zare kowanne irin kuzari da yayi saura a jikinta. Tun daga yatsun qafarta har zuwa tsakiyar kanta taji wani abu ya zuba mata yarrr har sai data dunqule hannunta da kyau tana curewa waje daya. Shuru ya ratsa tsakaninsu,sai ya sake motsa labbansa yana sake maimaita mata sallamar,da alama yana da buqatar amsawarta kenan "Wa'alaikummussalam warahmatullah" ta motsa labbanta tana furta amsawar da bata da yaqinin yaji ko baiji ba. Shuru ya sake wanzuwa,saidai kowannensu yana iya jin fitar numfashin dan uwansa ta cikin wayar,abinda ya haifar da mutuwar jikkunansu gaba daya. Kira ne da bata taba zaton samunshi daga gareta ba,to amma kuma zuciya na gaya mata sai yau zaya nemeta?,dukka tsahon wannan lokacin sai yanzu zai tuna da ita?. "Hellooo..... sulthana" ya kirata a tausashe muryarsa can qasa fiye da kullum. Ya gama kassara kunnuwanta da fitar sautinsa,don haka ta kasa amsa masa "Nasan kina jina......kina fushi ko?" Ya jefa mata tambayar. So take tace masa NO don kada ya gano lagonta,to amma yadda zuciyarta tayi wani irin laushi, idanunta suka fara tattara ruwan hawaye sai harshenta ya gaza aiwatar da komai "Mummy twins" ya kuma kiranta still yana haifar da wani irin amo cikin muryarsa "Kina buqatata a kusa?" Tambayar data qarasa ruguza dukka sauran qarfin zuciyarta,suka tilastawa hawaye biyowa hanyarsu. Shuru ya sake giftawa,yana iya bibiyar bugun zuciyarta daga cikin wayar da kuma sauyawar fitar numfashinta "I know you want me.......but i want you to tell me....." "Okay.... lemme tell you ni tunda ke ba zaki gayamin ba.....i want you and I want you forever" sautin kukanne ya kufce mata,sai tayi hanzarin hanging up na wayar,tayi switching dinta off gaba daya,ta maida kanta cikin pillow tana boye kukanta gudun tashin wani cikinsu benazeer ko batoul.*_ *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 120 Abu mafi ban mamaki sai ta dinga jin duk wani qunci daya lullube zuciyarta da kuma zuzzurfar kewa suna sulalewa suna kuma zagwanyewa. Hawayen dai kawai take zubarwa,amma kuma babu wannan quncin da takurar zuciyar. Sakin ajiyar zuciya ta dinga yi a jajjere,ta mirgina tabar sashen dasu benazeer suke zuwa daya sashen gadon,ta kama pillow ta rungumeshi tsam a qirjinta,sautin muryarsa ta dinga yi mata amsa kuwwa a kunne. Tattausar muryar nan me dauke da wani irin sauti me dadi.......lallausar muryar nan da yake iya bada tsoro da ita a duk sanda yaso yin hakan..... muryar nan da a baya koda bacci takeyi take farkar da ita koda bata shirya hakan ba.......muryar nan data zauna daram cikin rayuwarta,ta shiga kowanne motsi na second da mintuna na rayuwar tata. A hankali a hankali tun tana goge qananun hawaye har hawayen suka soma ja baya,fuskarta ta bushe sarai,ta dinga sakin ajiyar zuciya kamar yaron daya gaji da neman mamarsa,a hankali har bacci ya dauketa. Koda ta tashi da asuba jikinta da zuciyarta dukka taji sauqinsu,saita samu kanta da duba wayarta,ta rasa meye take nema?,kira ko saqo,amma daga wajen wa?,itama bata sani ba. Tun tana dubawa har ta gaji,ta maida wayar ta ajjiye tana tura baki gaba gami da kwantar da kanta saman cinyoyinta a hankali,a haka bacci yayi awon gaba da ita ba tare data sani ba. Hayaniyar benazeer da batoul ne saman kanta ya tayar da ita,ta bude idanunta a hankali tana kallonsu. Ama ce ta aikosu su tasheta hakanan ta samu abinci taci sai suka buge da fadan waye zai fara tashinta a cikinsu. "Ku matsa daga kaina kada ku sakamin ciwon kai" ta fadi tana korarsu. Miqa tayi sosai tana duba lokaci,har sha daya da rabi na safe,ta shafa cikinta saboda yadda taji wata wawuyar yunwa tana sakadar cikinta. Bandaki takeso taje ta fara yin wanka amma sai taji ba zata iya jurewa ba,don haka ta jawo hularta ta saka,ta maida kimono din sleeping dress din jikinta tana wucewa kitchen,cikin ranta fal mamakin me ya sameta haka?,don tunda take bata taba jin yunwa kaf rayuwarta irin na wannan lokacin ba. Ta samesu sunyi dama dama da kitchen,anata soya awara suna cinyewa. Mamakin inda suka samo awara a qasar ya kamata,tabi goumar da kallo wanda ya cika plate da miyan source na vegetable ya saka benazeer a gaba da batoul sunata kaiwa cikinsu "Wannan nasan aikinka ne,saboda qwalama a qasar nan sai daka zaqulo awara?" Ta fadi yawunta yana tsinkewa,saidai kuma tana tsoron taci,don ta fuskanci duk sanda taci wani abu solid sai ya dawo mata. "Bakisan awara tayi matsayi a duniya ba?,ba inda ba'a santa ba,suna nan suna saidata a supermarket matar babban yaaya" ya qarasa fada yana cika bakinsa da awarar. Harara ta balla masa,yanason bata kunya gaban ama da zai dinga kiranta da wannan sunan?,sai ta matsa kawai tana cirar cup saboda hango kunun gyada da tayi fari qal da yayi masifar tsinkar mata da yawu. Gefan ama ta tsaya ta soma gaidata saboda sanda ta shigo kitchen din waya takeyi,a dan mamakance ama ta waiwayo tana dubanta tana kuma amsa gaisuwar,saidai kuma nazarinta takeyi cikin mamaki,wanne irin ciwo ne wannan?,jiya a galabaice harda zuwa asibiti qarin ruwa?,yau kuma gata har kitchen da qafafunta "Ya jikin naki?" "Da sauqi alhamdulillah" ta bata amsa tana miqawa tanja cup din ta cika mata da kunun gyadar. Waje daya ta samu ta zauna sai gata ta tashi dashi,ta sake cika cup din shima ta tashi dashi. Ta ajjiye tana daukan ruwa ta Kora,take taji ta soma ganin daidai,tayi hamdala tana mamakin yawan kunun da tasha. Duk kuma sai ya kashe mata jiki,tanason zama cikinsu amma ta kasa,idanunta suka dinga lumshewa,kasalar nan tanason dawo mata. Dukka ama na ankare da ita,gaba daya zaren tunaninta ya gama kuncewa,duk yadda taso kawar da tunaninta kan abinda zuciyarta keta bata amma hakan ya gagara. Saidai kuma taqi gasgata tunanin nata,saboda abu ne a duqunqune da zai zamo da zallar firgici da kuma ayar tambaya "Ki wuce ki kwanta sultana" ama ta fadi ganin yadda ta dafe goshinta tana qoqarin amsa surutansu benazeer,amma kuma launin idanun nata ya sauya,hakanan muryarta ma tayi laushi sosai. Murmushi kawai ta yiwa ama tanason dakewa,a haka a daddafe ta bari qarfe daya na rana tayi,ta wuce daki tana layi saboda tsabar bacci. Tasan muddin ta sake ta kwanta tofa ba lallai ta samu sallar azahar ba akan lokaci,don haka ta fara shiga toilet tayi alwala tayi sallar azahar din tata tunda mukhtari ya shiga. A nan inda ta idar ta zube,tanata qoqarin cijewa tanason gama addu'o'inta amma kuma bacci yace baisan wannan ba,bata tsinci kanta a ko ina ba sai a duniyar bacci. *_ABUN B'OYE_* Tun k'arfe biyu na rana goumar ya sanya tanja ta shirya benazeer da batoul don zuwa airport. Dukkansu cikin shiga iri daya. Wandon jeans da rigar chiffon da tayi matuqar dacewa da wandon. Sosai tanja ta qware itama wajen gyaran gashinsu,idan ka gani zaka dauka me gyaran gashi na musamman ama ta aje musu. Takanas tanja din ta zauna ta koyi komai da komai,wannan yana daya daga cikin abubuwan da ya sanya tanja ke sake shiga zuciyar ama Bibi dama sauran 'yan gidan,komai da ake da buqata daga wajen 'yar aiki tana qoqarin ganin ta koyo,zuwa yanzun tanja ta wuce me aiki a wajensu,saidai su kirayeta kakarsu tamkar ama,a wajen sultana ma kuwa uwa ce dungurun gum. Cikin tashi shigar ta shirt da trouser ya iso falon,yayi fes dashi yana fidda salon nashi qamshin. "Sai ina kuma sarakan yawo?" Murmushi ya saki yana sanya maballan hannun shirt dinsa "Kin manta daddyn twins zai dawo?" "Oh..... okay" ta furta tana gyada kai "Allah ya tsare hanya" ta musu addu'a sanda suke fita. Sai da suka bacewa ganinta ta dawo da dubanta cikin falon tana sauke ajiyar zuciya. Addu'a takeyi sosai cikin ranta, addu'ar data kwana da ita ta kuma tashi da ita cikin ranta. Basu jima da fita ba taji ana danna bell,ta tashi ta duba,sai taga aba ne tsaye. Mamaki yadan kamata,saboda yau din suna da tafiya daya daga cikin state din dake France. Buda masa qofar tayi da sauri da dan mamaki saman fuskarta. Ta miqa hannu tana karbar briefcase dinsa "Barka da dawowa" "Yauwa hamdeee......kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana murmushi "Fargaba dai aba,Allah yasa lafiya" "Lafiya qalau,anyi cancel flight dinne......sai jibi in sha Allah tafiyar" "To alhamdulillah,Allah yasa hakanne yafi alkhairi,da sun shaida maka ma da baka sha wahala ba......" "Laifi nane,tun tura ta email hankalina ya dauku kan wani aiki ban samu damar dubawa ba" ya bata amsa yana wucewa hanyar da zata sadashi da dakinsa. Har zai shiga ya dakata yana dubanta "Gidan shuru,ko sarkin yawo ya debesu?" Murmushi ama tayi,sam ba dama aba din ya shigo gidan yaji baiji su batoul ba ya dinga tambaya kenan,idan kuma har ya jima ciki basu dawo ba ya soma qananun mita da qorafi kenan har sai an nemosu duk inda suke sun dawo gida "Yanzun nan suka fita..... amma yau ba nisa sukayi ba" ta bashi amsa a dunqule ba tare data masa zancan dawowar maina ba. Tuni tayi cancel din yi masa batun maina,kwata kwata ta daina masa magana kan duk wani abu da ya shafeshi. Dan dubanta kawai yayi,kaman zaiyi magana sai kuma ya sanya kai ya wuce ciki. Ya lura akwai maganganu da yawa data daina yi dashi,ta daina hira dashi kan abubuwa masu yawa,tanason fadi masa abubuwa da yawa nan ma ta daina.....har yanzu yana tunanin akwai wani side nasa da bata gama sani ba,abinda bata sani ba,shi din komai na iyalinsa kusan akan tsarinsa yake,saidai abu ya kubce masa ba tare da saninsa ba. Komai da yake da buqata ta shirya masa,sunayi suna hirarrakinsu da suka shafesu,wanda kusan fiye da rabi akan business nasu ne,nata da na yara su batoul boutique boutique dinsu,yadda kullum suke sake fadada suna buda rassa a garuruwa da qasashe na kurkusa da nijer din "To ni sai yaushe za'a bani manager a BB boutique din?" Qaramar dariya ama ta saki sanda take cire masa maballan gaban rigarsa "Haba aba.....da wanne zakaji fisabilillahi?,ga shekaru suna sake hawanka,kada bibi tace nice na sukurkuta mata d'a...Kai kanka sabgoginka neman matallafi kake fa ka manta?" Sai datakai qarshen maganar sai taji kaman bai dace tayi ta ba,bataso yaji ko kusa a ranshi tana nemawa maina sassauci ne daga bangarensa,tanaso sai ranar daya gama dukka cije cijensa akan d'ansa ya fito yayi duk hukuncin da zai sanya fushinsa ya gama fashewa gaba daya a wuce wajen, fushin nasa da ta tabbatar dai dai yake da fadan gwaggo a kofa,duk wani dagiyarsa da cijewarsa ta gama ganin lagonsa. Baice komai ba kuwa,saidai ta fahimci fuskarsa tadan bada wani reaction,don yanayinsa ya sauya kadan,sai ta bagarar da wancan zancan ta dauko masa wani zancan na daban. Yunwa ita ta fara tashinta kamar mahaukaciya,a gigice ta kuskure bakinta tana mamakin yadda ta jiqe haka da gumi,wanka take buqatar tayi amma yunwar cikinta tafi damunta,ta kalli agogo saura kadan hudu ta cika,sai kawai ta fice kitchen a gaggauce. Tanja tanata tambayarta me takeso amma ta kasa mata cikakken bayani,sai kawai tanja din ta matsa ta bude wani mazubi ta zuba kunun gyada me kyau daya cup din madara me dumi ta ajjiye mata a gefanta "Na gode tanja" ta fadi tana fara daukan cup din kunun gyadar ta soma kurba a hankali. Tsaiwa tanja tayi tana kallonta yadda take lumshe idanu tana enjoying kunun kamar batasha ba dazu. Qamshi qamshin lemon tsamin yake sake bata nishadi sosai,ta gama tas dashi ta dauki cup din madarar "Allah tanja ulcer ke neman yimin illa,qarfi da yaji tanason maidani wata acici ga shegen lalaci me yayi zafi?,wannan ai aikina sai ya samu damuwa" ta fada a shagwabe tamkar sultanar data sani can shekarun baya "Haqqun" kawai tanja tace da ita tana duban fuskarta, cikin zuciyarta tana sake haqiqancewa tabbas lallai dai yaro a koda yaushe yaro ne,kowacce mace da irin lokacin da quruciya take barinta koda kuwa yara nawa ta haifa,kallon sultana din kawai takeyi,tanata aika madara cikinta. A*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 121 Itama sai data gama tas da ita sannan ta dire cup din tana fadin "Alhamdulillah" ta miqe tana cewa "Bari nayi wanka nayi sallah,in sha Allah yau bazanyi baccin wuri ba saina kammala research dina" ta furta tana maida dubanta kan tanja "Lafiya tanja?" Sultanar ta tambayeta tana kallonta. Murmushi ta saki tana girgiza kai,tana kuma qoqarin danne dariyar dake cin ranta "Aah ba komai,a fito lafiya" "Allah yasa,kin samu ladana ai" ta fada tana fita a kitchen din tana duba miscals din data gani cikin wayarta data bari kunne sanda take bacci. Har zata wuce dakinta taji ana danna bell,ta daga kai daga duban wayan tana sauya akalar tafiyarta zuwa bakin qofa,ta bude tana ja da baya. Likitar jiya ce,maqociyarsu da tayi alqawarin tahowa da result din gwajin sultanan. Matar nada fara'a da kuma kirki sosai,da murmushi take tambayar sultana ama "Tana ciki,shigo nayi miki magana da ita" ta amsa mata tana qoqarin mayarwa matar murmushin da take faman doka mata. Haka kawai ganinta ya sanya gabanta yankewa ya fadi,ita ta manta ma jiya sunje asibiti,tunda dai taji dadin jikinta na meye sai an damesu da duba result?. Wajen zama ta bata sannan ta nufi hanyar dakin ama,sai kuma ta tuna bata ciki,don taji tanja na fadin aba ya shigo gida,don haka ta dawo ta zauna tana kiran layin ama. Bugu biyu ta dauka,saita fara isar mata da saqon zuwan matar "Ba damuwa,a bata drinks da snacks,tadan jirani kadan aba yana toilet idan ya fito zan sameta a falon.....ku debe mata kewa" "Toh ama" ta amsa mata tana sauke wayar. Hada idanu sukayi da matar,ta sakar mata murmushi sai itama tayi saurin gayyato murmushin ta jefeta dashi,haka kawai takejin zuwan matar cikin gidan bai kwanta mata ba,ta daure cikin harshen faransanci tayi mata bayani "Ba komai,ta kammala a nutse". Miqewa sultana tayi,ba zata iya zama tare da ita ba,hasalima wanka takeson yi zafi kuma takeji,don haka ta wuce kitchen kawai ta yiwa tanja bayanin anyi baquwa ama tace akai snacks. Tasan tanja din ta iya yaren France daidai gwargwado da zata iya hira da likitar,wannan ya sanya kawai ta wuce daki kai tsaye,ta fidda kayanta ta fada wanka. Cikin kyakkyawar shigar farar long sleeve shirt da farin trouser masu matsakaicin kauri da wani irin sulbi mallakin kamfanin Calvin yake. Komai nashi fari ne qal,tun daga kan undies dinsa na ciki har zuwa kayan jikin nasa,takalmi agogon fata luggage da kuma wani zagayyen farin eye glasses da ya fidda kyawun qwayar idanuwansa data sanyawa suna da lion eyes. Wani irin sassanyan kyau yake fitarwa,wanda hasken rana maras zafi da yake tsaye a cikinta yake sake tona asirin kyan nashi ta hanyar fidda kyawun baqar nannadaddiyar sumarsa ta asalin ba'abzine dake karban gyara da kuma zallar kulawa. Sumar ta qawatashi matuqa da gaske,ta fidda sirrin kyakkyawar fuskar nan da shekarun da ya samu da kuma hutu ke sake bayyana cikar kamalarshi. A 'yar tafiyar ta sati uku kacal ya sakeyin fresh,ya kuma sake cika,cikar data dace da tsahon nan tasa dake nunawa a dukka gabbansa koda a zaune yake. Yana tsaye yayi crossing qafafunsa,idanunsa nakan wayarshi,amma kuma tsaiwarsa a wajen ta fusgi hankali da zukatan mata da yawa dake wajen ba tare da yakai hankalinsa kai bama. "Daddy......daddy" ya fara jiyo muryoyinsu benazeer sama sama,duk kuwa da nisan da hankalinsa yayi hakan bai hanashi jiyosu din ba. Cira kansa yayi a hankali yana duban direction din da yake jiyo muryoyinsu daga wajen. Dole sassanyan murmushin nan nasa ya subuce masa ba tare daya shirya ba,ya miqe ya tsaya sosai kaman me bayyanawa wadanda ke satar kallonshi ainihin tsahonsa,ya maida wayarsa aljihu,ya soma tattare hannuwan rigarsa zuwa gwiwar hannunsa,don yasan dole yasha cafa yau,sai ya goye hannun nasa a qirji yana sakin murmushi idanunshi a kansu yana dakon isowarsu "Oh god.....damn it" wata baturiya da tun dazun ta mace a kansa ta furta tana rufe idanunta,ya gama tafiya da ita ainun,ta kuma yarda itama da kanta wajen kyan sura da kuma iya sace zukatan 'yan maza,to amma a yau din ta hadu da mutumin da takejin wani mugun kwarjini da shakkar tunkararsa,tayita attempting ta taddashi inda yake tsaye tun dazu amma ta kasa. Batoul yau ita ta riga benazeer isowa,ita ya fara dagawa sama sannan ya sauke ya dauki benazeer,duk kallo sai ya koma kansu, saboda yadda sukayi bala'in daukan hankalin mutane. Suna da kyakkyawar surar da idan ka kalla dole ka sake kalla,tsafta da kuma iya sanya sutura data zamewa yaran ado tun suna jarirai. Da surutu suka barke masa,yaji a jikinsa ido.yayi yawa a wajen,don haka ya dakatar dasu,ya waiwaya yana kallon goumar "Samin luggage a mota mu wuce" ya kama hannuwansu yana yin gaba,goumar ya jawo luggage din suna barin wajen. Sai data ajjiyewa aba baqin coffee dinsa sannan ta dubeshi "Dr ta kawo result na sultana,barin je na karba" "Ba laifi,gwara da aka kawo da wuri,ya kamata asan wanne ciwo ne ayi masa rigakafi da wuri" "Gaskiya kam....." Ama ta amsa masa tana zura dan madaidacin hajib ta dauki wayarta ta fice. Da fara'a ama ta bawa doctor hannu suka gaisa,sai tanja ta matsa gefe ta basu waje,itama bakinta ya huta da gwagwarmayar France din da taketa hadawa don suyi hira da matar. Yar gajeruwar gaisuwa ta baki suka sakeyi,ama na tambayarta aiki ta amsa mata da "Alhamdulillah" tunda musulma ce,shuru nadan sakanni ya biyo baya tana qoqarin fidda takardar gwajin daga cikin takardunta data taho dasu. "Ina tayaku murna madam......" Ta fadi da fara'a tana miqawa ama takardun. Daurewa kan ama yayi,amma sai tayi tunanin kamar bataji abinda ta fadi bane da kyau,ta miqa hannu tana karbar takardun sanda take sake cewa "Dole tayi haquri da wasu canje canje da zata dinga ji,daga wadannan satittikan har zuwa sati sha biyu sha biyar har sati na ashirin ga wasu matan" idanu kawai ama ta zuba mata,mamakinta yana sake ninkuwa,ita sam bata fahimci inda zanca dr ya dosa ba,saboda bayanan dr kaman tana bayani ne ga mutumin dake kiwon kaji?. "Kaman yaya dr?" Ama data kasa buda takardun ta tambayeta "Votre fille est enceinte(yarku tana da juna biyu)" wani duka maganar tayi saman kunnuwan ama da wani dirar mikiya naban mamaki "quoi ?(what?)" Bakinta yayi subutar fadi ba tare data shirya tambayar ba. Kai dr ke gyada mata har yanzu fuskarta da murmushi,don ta yarda da tarbiyyar mutanen dattako da nutsuwarsu harma da kamewar yarinyar,tayi imanin cikin da ta gani tattare da yarinyar zaiyi wahala ya biyo ta baragurbin hanya "Eh madam". Tattaro dukka wani busashen yawu dake bakinta ama tayi,ta kuma aro murmushi ta jefi dr dashi "Na gode sosai da wannan albishir dr" "Ba komai.....sai a kula da ita da kyau,duk sanda akaji wani abu kuma da ba'a yarda dashi ba hanya a bude take kada ayi jinkiri a sanarmin koda bana gida" "In sha Allah,na gode" ama ta sake jaddada godiyarta,tana bin dr kawai da kallo. Duk yadda taso yi mata tattaki koda zuwa bakin qofar falonne ta kasa,tana jin qafafunta sun mata nauyi da wani irin dan banzan mamaki mara adadi. Saida dr ta fita sannan taji tana da muradin kiran sultana,amma sai taji kamar muryarta ba zata kai ba. Sai a yanzu ta samu kanta da wani matsanancin fargaba da wani mummunan tunani daya rikito mata "Ciki?,na waye?, yarinyar data shekara shida rabonta da d'a namiji?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un..... Sultana ba zata taba aikata alfasha ba,amma kuma cikin waye a jikinta?,shin akwai boyayyar alaqa tsakaninta da maina?" Dukka wadannan tunaninkan suka dinga bugun kan ama har ta rasa hanyar da zata kira sultana din ma "Ya Allah.....Allah kasa boyayyar alaqar ce" ama ta samu kanta da furtawa a sarari bakinta yana rawa,tsoro da fargaba kamar zasu dulmiyar da ita a wajen. Sai sannan idanunta ya fada kan tanja,ta tabbatar zaiyi wuya ta fahimci duk maganar da sukayi da dr tunda kaf da harshen faransanci ne,wanda nata harshen baiyi nunar da zata fahimci duka komai ba "Tanja kiramin sultana" ta fada tana fasa kiran nata datayi niyya,wayarma saita sulale daga hannunta. Da dan mamaki saman fuskar tanja din ta miqe tana nufar dakin sultana. Ta gama salla kenan da hijabinta a jiki tanja ta isar mata da saqon,gabanta ya sake faduwa kaman dazu,sai ta miqe kawai ba tare da tsaiko ba tabi bayan tanja. Tunda ta sanya qafafunta ta fito daga dakin ama ta soma qureta da wani irin asababben kallo da bata taba ganin tana mata irinsa ba,abinda ya sake qara yawan faduwar gabanta,ya kuma saka dukka gwiwoyinta sanyi,a haka ta isa gaban ama,sai ta samu kanta da sulalewa ta zauna sosai a gabanta. Kasa cewa sultanar komai tayi saici gaba da kallonta da tayi,don ta rasa da wanne harshe ma zatayi tambayar,da hausa koda turancin ko kuma da faransanci ko da yarensu na abzinanci?. "Sultana" ama ta kirata sosai "N....na'am" ta amsa mata tana dan daburcewa,don sosai takejin shigar kallonta "Cikin waye a jikinki?,kuma wata nawa?" Kamar da wadda ta yiwa magana da yarbanci haka taji,don kwata kwata sai taji sautin ama kamar me koyon magana a yau din. Gefe guda kuma kamar an sharara mata ruwan zafi haka taji,wannan ya sanya ta dago a firgice tanason tabbatarwa ita ama kewa wannan tambayar?, don tana jin kamar bata da alaqa da tambayar,meye hadinta juna biyu kuma?. Idanun ne suka sauka kan takardar gwajin quru quru kafin takai ga kallon ama din,abinda yayi gaggawar fusgo tunaninta da hankalinta ya maido mata jikinta,maina ya fado mata a rai,dararensu dama sauran ranakunsu da BOYAYYAR ALAQARSU...... *_huguma ta gantale ko?,😂, afuwan,Allah kadai yasan nake squeezing nake muku rubutun nan,Allah ya saka muku da aljanna mutanen kirki da haqurinku gareni,in sha Allah muma mun kusa yin sauka,na gode_**_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 122 Kamar an kaba labbanta na sama da qasa an datse haka taji,gaba daya kowanne harafi da zatayi bayani dashi ji tayi yayi qaura daga bakinta. Wani mugun nauyin ama da bata taba jin makamancinsa ba ya saukar mata,taji koda wasa koda sau daya ba zata iya hada idanu da ama din ba,sai tayi qasa da qwayoyin idanunta da basa Gani da kyau saboda ruwan hawayen da ya cikasu. Jinta takeyi tamkar ba zaune take cikin falon ba,kamar gangar jikinta ce kadai a zaune a wajen,amma ruhinta baya tare da gangar jiki nata gaba daya. Har yanzu idanun ama suna kan sultana,kaman yadda zuciyarta da qirjinta basu bar bugawa ba. Bata zargin sultana,amma kuma tana fatan taji wani abu daga bakin sultana da zai sake bata nutsuwar zuciya. Jiki a sanyaye ama ta waiwaya bayanta jin takun mutum. Aba ne sanye da jallabiyya hannunsa dauke da key din motarsa,da alama yayi mantuwa ne a ciki zai fita ya dauko. Yadda ama ta bishi da idanu haka shima ya bisu da kallo,fuskarsa na bayyanar da zallar mamaki a cikinta "Ya dai?,me ya sameta hamdiyya?" Yayi tambayar yana duban fuskar ama da alamun tuhuma sosai a ciki. Kallon tuhumar da yake mata ya sanya ta kasa cewa komai,sai kawai ta zare takardun gwajin dake zube saman cinyarta ta miqa masa,ta hada hannayenta kawai ta rungume ba tare da tace komai ba. Yana kaiwa qarshe ya zare glass din idanunsa,sannan kuma ya samu kujerar da tafi kusa dashi saboda wani iri da yaji jikinsa yayi masa. Sai daya zauna sosai sannan ya iya maida idanunsa akan fuskar sultanan "Yi shuru,daina kuka hakanan......ki nutsu" muryar aba din sai ya zame mata kamar fami ga zuciyarta da kuma raunin dake ruhinta. Wai da gaske cikin ya maina ne a jikinta a karo na biyu?. Totally tayi disappointing dukkan wani qoqari na aba kenan?,da gaske ta bulawa aba qasa a idanu?,to wai da wanne bakin zatayi bayani?,da meye zata kare kanta?. A qalla mintuna biyar aka sake sharewa cikin falon ba wanda ya iya cewa uffan,shidai aba ya bata space ne akan ta nutsu aji ta bakinta,gefe daya kuma zuciyarsa nata nanata masa sunan "Maina ne....maina ne" to amma Ina maina din?,a ina ya ganta?,idan bai manta ba tun a Nigeria da suka rabu bai sake ganin alama ko samun information din yana qasar bama gaba daya bare ya sanya a ransa shine ya lallabo ya sake aikata wannan aika aikar a karo na biyu. Ganin kamar ta daidaita kanta ya sanyashi gyara zamansa yana duban ama. Hada idanu sukayi,sai ama din tadan dauke kanta gefa,don tanajin kamar case din yana son ya fita daga hannunta,don gaba daya jikinta ya gama bata inda komai ya dosa,to amma kuma tanaso sultana tayi bayanin da dukansu zasu fita daga duhu,cikin saukar da murya da tausasa harshe ta sake maimaita "Sultana.....ya akayi hakan ya faru?,juna biyun maina ne ko?" Ama ta bata tambayar me hade da amsa. "Nawa ne ama......salamu alaikum warahmatullah" muryarsa ta bayyana tar a falon da bayyanannen amo daya wadaci dukkan falon. Da aba da ama dukkansu suka waiwaya zuwa bakin qofar,yana shigowa ne riqe da hannun batoul da benazeer hagu da damansa,bayansa kuma goumar ne janye da luggage. Sautinsa da amsarsa kusan lokaci guda suka daki zuciyarta dama kunnenta,ta daga jiqaqqun idanunta itama tayi duba zuwa qofar falon. Aliyyu haidar MAYAK'I,jinin abzinawan nijer,mutumin da ta kwashe sati uku cif! Bata sakashi cikin qwayar idanunta ba,mutumin da duk yabi ya gallabi rayuwarta,yayi dashe a kowanne lungu da saqo na rayuwarta,ya maida kansa jinin dake gudana cikin jiki da jiyoyinta ta qarfi da yaji,ya dasa wani irin alaqa me matuqar qarfi tsakaninta dashi,irin alaqar da duk yadda taso ta kankareta kota gogeta HAR ABADA! Ba zata taba goguwa ba,ya maida dukkan rayuwarta tashi,fitar numfashinta da dukka motsinta. Ama ce ta fara kauda kai tana jin kamar dariya ko murmushi zai kubce mata don nata mamakin gajere ne qwarai. Ita ta haifi abinta,tasan duk abinda zai aikata dama wanda bazai aikata ba,tayi shuru ne kawai ta sanyawa kowa idanu,amma jikinta ya jima yana bata,saidai kawai hausawa sunce dan yau ka haifeshi ne ba tare da ka haifi halinsa ba......sannan wayo da dabara ta yarda dukka ya nuna mata irin nasu na 'ya'yan zamani,amma ta jima tana suspecting haka,ta dade hasashenta yana bata,abubuwa da dama sun jima suna bata alamomi da sai yau haskensu ya fito tarwai. Idanu aba ya bishi dashi kamar yaga wata sabuwar halitta,sai kuma ya janye kallon nasa daga kan maina din yana dawo dashi cikin falon kan sultana,ya zuba mata idanu kawai kamar me tunanin abinda zai gaya mata. Tana jin idanun aba ainun a kanta,duk wata kunyar duniya da nauyi sun tarar mata. Tana tsammanin idan yazo zata samu sassauci da rangwamen kunyar data yi mata rubdugu,amma shigowar nasa bai rage mata komai ba saima nauyin daya qara mata da irin amsar da ya basu ta hanyar kai tsaye babu kwaskwarima. Kwata kwata aba ya rasa me zaice?,ya rasa me zaya fada?,gaba daya kalmomin bakinsa sun dauke tsaf,ya rasa hukunci zaiyi ko meye?,idan hukunci yace zaiyi akan waye zaiyi?,kuma akan wanne dalili?,wanne kuma laifi aka aikata da za'a yi hukunci a kansa?. Abu daya da yazo masa a rai shine,babu uwa kamar bibi,me hangen abinda zai wakana shekaru goma ma gaba. Tun daga bakin qofa ya tsugunna yana zare takalman qafarsa,sai yara suka duqa suna tayashi cire guda dayan,ya daga kai ya kallesu ya sakar musu murmushi,kowacce ta dauki guda daya suka soma takawa zuwa gaban aba. Zubewa yayi a gaban aba din saman dukka gwiwoyinsa,ya zube kansa a qasa ya kuma hade hannayensa waje daya "Indai faruwar hakan laifi ne aba.....gani a gabanka ka yanke dukka hukuncin daya dace dani......saidai don Allah ina roqonka,kowanne irin hukunci ne ya zama taqaitacce aba.....kada yayi yawan da zai sake ruguza kowanne irin gini da nake yunqurin ganin na aza..." Qafarsa yadan janye,gaba daya kunya ta masa wani irin dabaibayi,ya sake dan ja baya kadan sannan ya miqe yana dubansu benazeer "Muje ciki ku tayani hira,tun dazu nake dakon dawowarku,na ajjiye muku abun dadi" Da murnarsu suka ajjiye takalmin suna bin bayansa,sai daya sanya yaran gaba suka wuce sannan aba din ya tsaya,ba tare da ya waiwayo ba ya furta cikin muryar bada umarni "Ka dauki matarka ku tafi duk inda zakuje mara kunyar banza" daga haka ya taka zuwa gaba yana bin bayan yaran. Dauke idanunta ama tayi daga kan aba din tana sake danne dariyar da a yanzun ta tabbatar idan batayi da gaske ba saita kufce mata. Sai kuma idanunta ya fada kan maina dake duqe a inda aba ya barshi. Kunya ce ta kamata itama da nauyi,ga idanunshin nan daya tsareta dasu,saita sake tsuke fuska da kyau itama "Meye kake kallona?,bakaji abinda yace dakai ba?" "Naji ama" ya fada a mugun marairaice kamar marayan daya rasa danginsa gaba daya. Saidai kuma can qasan zuciyarsa wani irin mahaukacin farinciki ke ratsashi "D great victory ✌️! Da sauri haka?,wannan d'a ko 'ya tabbas ba qaramin qaunarsa suke ba......yana da hope na samun cikin,amma kuma babu tabbaci sam sam sai addu'a". Kasa ce masa komai tayi sai kawai ta kwashe wayarta tabi bayan mijinta. *_Allah sarki sultanarmu ta mutunci_*🥹😥😥*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 123 Tuni tanja tabar falon tun shigowar aba,don ita wannan gwaji ya biyata,ya kuma gama yi mata komai. Don haka a yanzu sai falon ya zamana ba kowa,daga shi sai ita,sai kuma ayana dake maqale bayan labulen dakin. Tun fara drama din ta farka daga baccin data kwanta tayi bayan ta dawo daga makaranta. Idanunta tamkar su fado haka takeji,kaman yadda zuciyarta ke wani irin bugu cike da mahaukacin kishi,kebewarsun yanzun ya sanyata sake lafewa da kyau tanason kunnuwanta su ida jin abinda zai sake gudana tsakaninsu. Tsaye kawai tayi yana nade hannayensa a qirji yana qare mata kallo da zagayayyun lion eyes dinshi da a yau suke lumshewa da kansu suna budewa sau babu adadi,ya zuba mata dukka idanuwan yana kallonta,wani irin narkakken kallo dake cike da shauqin soyayya da tsumammiyar qauna irin wadda ta jima da narka zuciya gami da yi mata illa. Yanajin sautin kukanta har cikin zuciyarsa da ruhinsa,saidai kuma bayason abinda zai katse kallonta da yakeyi. Yayi kewarta......yayi kewarta kamar hauka........yayi mutuwar kewarta har baisan iya adadi ba......yayi kewarta kamar ya karya tsari da lokutan daya diba kafin ta sake ganinsa,shi da ita baisan waye yafi wani gasuwa ba. Kunnuwansa ke sake dawo masa da furucin aba "Ka dauki matarka ku tafi duk inda zakuje....." Sai wani tattausan murmushi ya kubuce ma kumatunsa. Zai iya cewa kawo zuwansa duniya zuwa yau bai taba jin wani umarni me gardin wannan ba.......qwaqwalwarsa ta lula wani irin tunani me zurfi,yana laluben wai a duniya a wanne shiyya zai ajjiyeta?,a wanne muhallin ne zaciyoyinsu zasu samu dukkan hutu da salama?,a wanne tsibiri tudu ko tsauni ne zaiyi shimfidar rayuwarsa da sultanarsa?, diyarshi?,rainonshi......matarshi?,uwar 'ya'yanshi?. Dukka wadannan tunanikan yana daga tsaye yake tsarasu cikin qwaqwalwarsa,kafin ya sauke hannuwan nasa yana takawa zuwa gareta. Yanaso ya dakatar da wannan kukan,sai ya dinga ji kaman abinda ke kwance qasan mararta ma tayata kukan yakeyi,ya gaji.......yanason tsaida wannan hawayen da sukayi shekara da shekaru suna zuba,ya kamata su tsaya hakanan. Gabanta ya qarasa cikin nutsatstsen takunsa dinnan, baiyi qasa a gwiwa ba ya zauna sosai sannan ya tanqwashe qafarsa yana fuskantar ta har gwiwarsa tana taba tashi. Taji isowarsa,ta kuma ji hucin dumin jikinsa,sai lallausan qamshin nan nasa da a yau takejin ya zama sabo cikin hancinta,har sai da qamshin ya tilasta mata fidda BOYAYYAR ajiyar zuciya,tana jin kaman ta shaqi wani abu me sanyi da ya dinga sauka har saman zuciyarta yana wanke mata zaciyarta. "Sulthana" ya kirayeta a tausashe yana qoqarin leqa fuskarta ta qasan hijabinta. Ta fahimci me yakeso,fuskarta yakeson gani,sai ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta da kyau saboda ta hanashi wannan damar. Wani qaramin murmushi ne ya subuce masa daga siraran labbansa,hakan da tayi sai ya tuna masa da little sultanarshi ta shekarun baya,ya sanya tafukan hannunsa cikin na juna yana mutstsukawa a hankali cikin wani salon nishadi,idanunshi kuma a kanta "Am so sorry......ya maina bai kyauta ba.....don me zaiyita zura qwallo a raga ba tare da permission din goal ba?" Hakan da ya fada sai ya zama kamar tiri a gareta,ta kuwa sake sakin kuka mai qarfi tana jin takaicin sa. Ya sanyata abun kunya,irin abun kunyar da bazata taba mantawa dashi ba,ya goga mata kashin kaji,shi kuma nan ba ruwanshi gashi nan,da wanne baki zata kare kanta ne wai?,mutanen da suketa fadi tashi a kanta suke qoqarin ganin sun qwato mata 'yancinta?. "Ki daina kuka please baby sultana(ya kirata da tsohon sunan da yake kiranta tun lokacin da batafi girmansu benazeer ba ".....nima duk kunya ta kamani,ashe ina tsallakesu ina tafiya dakin 'yarsu ina turmusheta" ya qarasa fadi yana kashe ido daya dariya nason taso masa. Kalmarshi ta qarshe ta mata girma ta kuma sake tunzurata,ta rasa ma meye zatayi masa ta huce,saita fara shureshi da qafa. Kamo qafafun nata yayi ya aza saman cinyarsa yana cewa "Indai wannan zai sanyaki ki huce sultana yita shureni har sai zuciyarki tayi sanyi......kiyi iya son ranki......eheenn" ya fadi yana sakin jikinsa da kyau. Ba haka takeso ba,tanason masa abinda zaiji zafi ne,amma it seems ma bai damu ba ko kadan?,muddin taci gaba da zama a wajen haukatata zaiyi,don haka ta miqe tsam taba kubce masa tayi hanyar daki. "Ina zaki?,bayan aba ya bani damar tafiya da matata?" Ya jefa mata tambayar. Ji tayi ba zata iya jurewa ba wanann karon don haka ta waiwayo tana kallonshi da fararen idanun da suka jiqe sharkaf da hawaye "Ba inda zan bika,ni ba mara kunya bane" yadda tayi maganar da zallar quruciya dukka da yarinta a mode dinta yaso bashi dariya,amma a yanzun yana jin ba lokacin dariya ko wasa bane,lokaci ne da zai nuna mata qarfin qwanjinsa,ya kuma murda tashi mazantakar,aba da ama sune rauninsa,idanunsu ke masa gate suke kuma kawo masa tsaiko wajen maidata qarqashin umarni mulki da kuma ginin gidansa,a yanzun kuma ya samu cikakken izini koda da gatse aba ya fada,koda ba da son ranshi ba. "Ni kuma ba kunya gareni ba......don aba kanshi yasan haka,yasan waye haidar......muddin yaci gaba da riqe masa mata yanzun ba juna biyu kika samu ba?,to idan ana daukan ciki kafin a haife wani zakiyita daukan ciki a gabansu........bana iya barin abinda nakeso.......zuciyata bata iya son abu da wasa ba kota fara so tayi sassauci a ciki......saboda idan ta fara son tana yin wannan soyayyar ne da gaske......batasan wasa ko ha'inci ba" ya gama kashe mata duk wani qwarin gwiwa da kafiya da takeji tana dashi,saqon kuma da idanunsa ke isar mata yafi wanda yake furta mata da bakinsa tsanani da kuma tarin kaifi,don haka ta juya da nufin ta isa dakinta ta kulle kanta da kanta,don duk tsanani ba zata iya binsa haka siddan don aba ya fadi wannan maganar ba,wala'alla ma yayi ne don ya gwadata,daga ya fadi magana sau daya sai ta tattara ta bishi kaman dama tana jira?. Abinda ta manta shine maina din tamkar uba yake a wajenta?,haifanta ne kadai baiyi ba,amma dukka halayenta ya gama da saninsu daya bayan daya,don haka ya kausasa murya yana bata umarni nakai tsaye wanda ba wasa ko sassauci a cikinsa "Kikayi kuskuren kulle qofa bayan kin shiga zaki gane baki da wayau kwata kwata......zaki fahimci kuma maina aliyyu ne,bashi da sassauci......ina fatan baki manta yadda ya dinga iskeki duk dare ba koda bayan kin rufe qofa ne....." Ya isar mata da saqon da ya sanya ta kasa maida qofar ta kulle kaman yadda ta niyyata,sai kawai ta buge da wucewa dakin da gudu gudu,ta kuma fada saman gado tana fashewa da kuka. Gaba daya ya sanyata a tsaka me wuya,jin laifi takeyi a kowanne sashe na jikinta,tasan koda zata hadiyi qur'ani ama da aba ba zasu taba gasgatata cewa ba ita ke kawo aliyyu ko kuma ita ta bashi fuska ba. Abun kamar almara?,wai ciki a jikinta?,cikin maina again?,bayan duk wahala da fadi tashin cikinsu benazeer da ba zata taba mantawa dashi ba?. Idanunsa ya lumshe yana furzar da numfashi,sai kuma wani murmushin ya sake kubce masa. Wannan karon koda bori zata hau.....koda aljanu zata tayar sai ya tabbatar mata da cewa shi din likitane,zai banbance mata zaqin soyayya da kuma banbancin kulawarshi a kanta sama da kulawar kowacce halitta.......wannan soyayyar da yayi nasarar haukatata tayi bishiya me manyan jijiyoyi da rassa tsakiyar qwaryar zuciyarta cikin sati uku kaman yadda ya tsara kuma lissafinsa ya tafi dai dai.......zai finciko wannan qaunar.......zai tasheta daga dukkan wani bacci da tayi. Ya sake lumshe idanunsa yana budesu murmushi na sake fita akan fuskarsa kamar me aljannun murmushi. Iya abinda qwayar idanunta ya gaya masa a kanta,baiyi tsammanin aikinsa zaiyi wannan uban tarin nasarar a sati uku kacal ba,tanata wahal da kanta......tanata qaryata kanta akan abinda gaskiyarshi kenan,ita dole ba zata yarda ta kamu ba?,ba zata taba yarda ta fara mahaukacin son maina d'a ga hamid da hamdiyya ba? "Zakisha mamaki" ya fadi a fili siririyar dariya tana kubce masa. Miqewa yayi a nutse daya tuna shigarta daki ba abinda zai sameta tanayi sai kuka tabbas kuwa,kukan kuma a matsayinsa na likita yasan baya haifar da d'a me ido ga mace me yaron ciki kamarta "Tana buqatar kulawa da kwanciyar hankali......ina buqatar healthy baby" yayi wannan maganar shi da zuciyarsa "Baby ko babies?" Ya tambayi kansa "Ya rabbb......babies girls or boys.....ko mix dukka inaso" dukka shi kadai yake maganar can qasan ransa kamar wani zautacce,sai ya sake yima kanshi da kanshi murmushi. Bai taba sanin haka yake da son yara ba sai yanzu,koda yake d'an kanka daban yake da komai,zaka yita mamaki ace wannan wani yanki ne daga gareka?. Qofar dakin ya maida ya kulle,sannan ya isa a hankali gabanta yana kallonta,sai ya zare hannuwansa daga aljihun wandonsa,ya zauna daga gefan gadon,ya sanya hannunsa dukka biyun yana qoqarin dagota zaune "Tashi muyi magana......ki tsaida wannan kukan....." Yadda yayi maganar da sassaucin murya da kuma girman nan da tasan yana mata shi a baya yasa ta sassauta kukan. Dakin ya dan dauki shuru,sannan yayi gyaran murya ya jefa mata tambayar "Me kike da buqata?" Muryarsa ta daki zuciyarta sosai,har wata yar shesheqa ta fita daga hunhu zuwa hancinta a sanyaye,tanason ko yaya ne shima yaji bacin ran data ji,rana tsaka ya jawo aba ya mata koran kare a gidansa?,ama kuma da alama itama bayi bayansa?. "Bana sonka" ta furta zuciyarta na qaryatata amma labbanta sunason cewa gaskiyarta ta fadi. Har qahon zuciyarsa yaji maganar,karo na biyu kenan data gaya masa kalmar gatse gatse,takuma sokeshi qwarai da gaske. Yadan cije lips dinsa,sannan ba tare daya dubeta ba yace "I will slap you sultana......ni ba sa'anki bane,duk ranar da kika sake cewa you hate me ko?......" Sai kawai ya jinjina kai yana jin zuciyarsa tana motsawa "Am just asking you me kikeso,saiki ce wani you hate me?.....ba rannan kin fada ba?,yanzun ma kin maimaita ko?,well.....karki maimaita na uku.......nima din na janye kalman i love you....i hate you..... shikenan?" Ya jefeta da tambayar yana dubanta. Ko sau daya,koda wasa kuma bata taba kawowa a ranta zataji zafi idan ya gaya mata baya sonta ba,amma sai taji wani abu me tauri yazo ya tsaye mata a wuya kamar ma tana neman rasa numfashin shaqa "So stop telling me......ina da wadanda suke sona,zanyi focusing a kansu.....now ki dauka kina tare da uncle dinki......nemi hijab ki saka muje,dole kibar musu gidansu yadda suka buqata" sai ya miqe kawai ya bude Wardrobe dinta. Duk abinda yaga ya kamata ya dauka kawai yake dauka din,baima nuna yaji kukanta ba,har sai daya gama hada komai,yana daga tsaye ya fiddo waya ya kira goumar. Kamar me jiran kiran nasa ya dauka "Qaraso ciki kazo ka fitarmin da kayan nan" "Okay sir" goumar din ya fadi dadi yana cikashi. Wayar ya mayar aljihu ya waiwaya gefansa yana kallonta "Idan kina zaton zan nema wani abu a wajenki ki daina wannan tunanin......zanje na kula da ajiyata.....idan kika sauke ya rage naki......yanzun na koma uncle dinki kamar baya,live your life.....banason na sake maimaicen magana dake,ki saka jilbab mu wuce" daidai nan goumar yayi knocking maina ya bashi daman shigowa. Idanunsa akan sultana gulma tana cinsa,maina yana ankare dashi don yasan halin mutanen nashi,ya jefa masa harara yana masa nuni da kayan,sai ya dauke kanshi yana qusnhe dariya ya daga luggage din ya soma janta,maina ya kira shi ya waiwayo ya jefa masa key din motarsa ya cafe sannan ya juya yana ficewa.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 124 Idanunta akan gidan,ta tsammanin can zataga ya wuce amma sai taga ya nufi motarsa. Goumar da ya jima da sanya luggage din a ciki yana tsaye jingine da motar. Zai bude mata maina ya daga masa hannu,yasa hannunsa ya bude mata gidan gaba ba tare da yace komai da ita ba. Kai ta daga ta kalleshi,sai kuma ta maida dubanta zuwa ga cikin motar, zuciyarta na karyewa ta saka kai tana shiga,rauni yana ziyartarta,tana ji a ranta zai nesantata da kowa nata,ta yaya zata iya tafiya tabar ama?,ta yaya zata iya nesa da benazeer da batoul yaran da kwanan da suka dinga yi tare dasu a dan tsakanin ya haifar da wata mahaukaciyar shaquwa a tsakaninsu. "Banyi sallama da ama ba,banyi sallama da aba ba,benazeer da batoul" ta furta muryarta na rawa,sabon kuka yana so ya qwace mata sanda ya shiga motar seat din driver yana niyyar rufewa. Sai ya fasa tayar da motar,Iska ya furzar yana dan buga steering motar da yatsunsa dake samanshi. Tausayinta yaji ya kamashi,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fiddo jikinsa waje gaba daya yana nufar qofar gidan da zummar komawa ciki. *_ABA_* Abu uku ke turereniya a zuciyar ama sanda take barinsu a falo tana bin sahun aba zuwa nashi falon. Na farko mamaki dariya kunya da kuma tausayin sultana,dukka sauran abubuwan kuma wa aba takewa. Lallai gaskiyar hausawa da suke cewa ba'a shaidar d'an yau,ta godewa Allah da bata zafafa da yawa cikin lamarin maina da sultana ba lallai tabbas da yau taji kunya,ta sake godewa Allah da aba yabar batun raba auren,inda ya kafe akan hakan Allah ne kadai yasan me zai faru. Cikin biyu dai dole ayi daya,ko ayi cikin a waje wa'iyaxubillahi tunda dai rabo ya rantse,ko kuma aba din ya rasu kuma suci gaba da zaman aurensu. Dariya ta kusa subuce mata sanda ta isa falon ta sameshi dirshan tsakiyar jikokinsa yana aikin bare musu sweet,abinda duk soyayyarsa da yara baya jurewa,zai dai siya,amma saidai ama goumar ko tanja suyi aikin budewa,yau sau gashi da bare leda ya kusa nawa,idan ya barewa batoul sai ya barewa benazeer. Ya amsa sallamarta yana daga idonsa a kanta,suna hada ido wata dariyar tazo mata saita kauda kai kaman tana neman wajen zama. Jinjina kai kawai yayi qasan ransa murmushi yana subuce masa,ya sani,dariya take masa,kuma bama ita ba duk wanda yaji zancan shi da ya zaqe da yawa cikin lamarin zai fara yiwa dariya. "Ku dauki ragowar kukai tanja ta boye muku.....ta saka muku house wear a cire wannan kayan" aba din ya fada yana tattara musu tarkacensu. Sanda suka fice sai falon yayi shuru daga ita sai shi,sai aka koma satar kallo tsakaninta da shi. A karo na kusan ashirin da suke satar kallon juna daga qarshe suka kama juna,dole murmushin ama me sauti ya fita tana danne dariya kada ta biyo baya "Aba....how far?" Tayi maganar tana kashe ido hadi da maqe murya. Dariya dole ta kamashi shima "Hamdi ni kikewa dariya?" "A'ah,aba ai dole nayi dariya,kaga aikin 'yan zamani ko?" "Na gani hamdiyya,me na isa yanzu nace?,shi yasa nace ya tattara matarsa su tafi,bansan kuma da wanne ido zan sake muzurai da cika baki akan 'yar marainiyar da naketa haqilo ba" "You learn a lesson aba......tsakanin miji da mata fa sai Allah,ma'auratan da dukka sun balaga harda 'ya'ya a tsakaninsu,haka kawai sai a turke kowannensu kamar dutse?" Murmushi yakeyi yana girgiza kai "A'ah......ni na tabbatar daga yadda diyata ke kuka fin qarfi yayi mata..." "Rape still?,wallahi aba wannan karon bazan yarda a jefawa dana kalman fyade ba,wancan karon nayi kawaici......amma dis time around nima murje idona zanyi......ahaaan......sanda suka daidaita kansu da inda suke jonewa ma baka sani ba aba,amma kazo kana yabonta.....saifa bango ya tsage qadangare yake samun wajen fakewa" ta fadi tana shan mur kamar da gaske. Dariya sosai ta bawa aba,abun dukka sai ya juye masa nishadi musamman idan ya tuna wai BB nada qani ko qanwa a hanya. "Maida wannan dogon hancin naki kada ya tashi sama.....wait......ashe dama baki da kara har haka hamdiyya?" "A nan dai bani da aba.....,yarinya ta kawo maka result.... Ina laifin ma a yabawa d'ana shima?" Dariyar da tafi ta dazu ama ta bawa aba "Fitinannen dankin nan ba,shekaru shidan da suka wuce da suna tare na tabbata for now mun gani da daukan jikoki ko?" Sai a nan kunya tadan kama ama,ta kauda kai tana dariya qasa qasa gami da cewa "Oho.....koma dai meye,Allah dai ya sakawa Bibi da alkhairi" "Ameen ya hayyu ya qayyumu "aba din ya fadi yana jinjina abun qasan ranshi. Wato wani irin rabo ne me zafi a tsakaninsu wanda duk idan ya tashi zuwa baya zuwa da sauqi,ya godewa Allah da rabon baiyi ajalinsa ba. Ama na zolayarsa yasan amsar da zai bawa mutane batoul ta dawo. "Ama wai kizo" kaman zata tambaya waye sai kuma ta fasa,ta miqe tsam tana bin bayan batoul suka fito. Yana tsaye tsakiyar falon hannayensa goye a bayansa. Suka hada idanu da ama,yau din shima sai yaji kunya ta dabaibayeshi,yadan yi qasa da kansa,ama din ta gyara tsaiwarta tana hade rai "Meye kuma?" Kanshi ya sake dagawa a karo na biyu,saidai kuma ya gaza hada idanu da ita,ya karyar da murya yana cewa "Ama.....kuka take,tace ba zata tafi ba bakuyi sallama ba" tausayin sultana din ya saukar mata,tasan halin d'a namiji,bata kuma cire har d'an cikinta ba,sun qware wajen iya yaudarar diya mace da kalamai,sun muma qware wajen karyo dake su samu biyan buqatunsu idan suka so komai kafiya zafin kai da jajircewarki,ballantana sultana......sultanar da take tashi......sultanar da jinin jikinta ya gaurayu da nashi,sultanar da tayi amanna koda wanin maina ta aura a rayuwarta zai wuya yayi controlling nata yadda maina zaiyi,ta zama shi ya zama ita......kominsu daya ne.....girma da sauyin dabi'unta ya kawo jirkicewar komai a tsakaninsu. Hijab dinta dake aje saman kujera ta dauka ta zura tayi gaba ba tare data ko kalleshi ba,sai yaji dadi ya saukar masa ganin tayi accepting abinda yakeson gaya mata tun kafin ma ya gabatar mata dashi. Bai bita ba,sai ya doje daga bakin qofar gidan,yana kallon ama sanda ta isa gaban motar ta sanya hannu ta bude murfin motar ta shige. Sanda taji an bude motar ta dauka shine,don haka tayi banza da ranta tana ci gaba da rera kukanta. Zama sosai ama tayi a seat din driver din tana kallonta. Qamshin turaren ama ya fallasata,saita daga kai da sauri,suna hada ido da aman ta gaza ci gaba da kallonta saboda kayan kunyar da takeji ta debo "Au.....kuka kika zauna kinayi?,cikin shege kikayi ne sultana?" Maganar ta sanyata maido dubanta kan ama,tanason ta tabbatar da gaske ama bata dauki wani abu ba?,da gaske ba komai bane wajen ama din. "Ko bashi da uba yana da kaka,auren sunna ne har abada tsakaninki da haidar haka ne?" Wani sanyi ya soma sauka mata cikin zuciya,ta shiga gyada kai hawaye na sake yawa cikin idanunta. "Ki goge hawayen muyi magana ko na fita na barku" da sauri taja gefan hijabinta tana goge idanun nata tare da tattarawa ama hankalinta. Tun maina da suka shanya a waje yana kallon motar har ya koma kallon agogon hannunsa yana irga lokaci. "Wannan maganan yayi tsaho" ya sake fadi a karo na kusan biyar. Goumar yana gefe dariya kaman ya kasheshi,wai dama haka ya mainan yake mutuwar son sultanarshi?,da gaske irinsa dama soyayya haukatasu takeyi a mafi yawancin lokuta?. "Goumar....ko zaka......" Sai kuma abinda zai gayawa goumar din ya yanke ganin ama na fitowa daga motar. Tun kafin ta qaraso ya miqe yana jiran isowarta,gaba daya ama din ta zame masa wata boss. Tana isowa goumar ya matsa ya basu waje "She's pregnant ka sani,akwai wasu canje canjen halaye wajen me ciki.....saurin fushi yawan kuka duk zata iya fuskantarsu,cin abincinta ya qaru,kowanne lokaci tana iya buqatar abinci......gata nan kaman ajiya ce.....kada kaga ance ka tafi da ita ziqau ka dauka ruwa tasha ko kaci bulus.....da sauran gatanta,kuma komai na 'yar gata zamuyi mata kaman kowacce mace.....cikin jikinta ne kawai zai kawo tsaikon wasu abubuwan....." "Na shiga uku ni maina" ya fadi qasa qasa "Baka shiga uku ba saika kasa kula da ita" ama ta bashi amsa idanunta cikin nasa "Bamu hanaka saitata ba......da qin biyema kuskurenta ko son zuciya,tsawatarwa duk yana da kyau......amma ta yanda ya dace....ka cika mata zuciya da soyayyarka......banason na haifi d'an da mace zata kasa mutuwa a soyayyarshi" ama din ta fada kanta tsaye. Mutum ce me matuqar son soyayya,tana martaba soyayya saboda tasan dadinta. Yana daya daga cikin dalilan da yasa ko mutuwa take fata ta fara daukanta ko ta daukesu tare da aba..... namiji da tasan an jima ba'a yi kama tasa ba cikin duniyar iya nunawa matarsa soyayya.....girma shekaru ko tsufa basu sanya ya wofantar da hakan ba......ba wasu shekaru da suka dakushe salon nuna mata kulawa da yakeyi ko kuma soyayya,wannan ya sanya kullum kwanan duniya aba yake na daban a zuciyarta dama rayuwarta gaba daya (Zuciyar mace 'yar son soyayya ce,komai tsufa da shekarunki kinaso kiga mijinki ya mato a kanki,yana tattalin farinciki da baki lokacinsa da dukka kulawarshi,ba abinda yakai wanann morewa a rayuwar mace). Yana murmushi yana dosar motar,indai ta fannin winning zuciyar mace ne yayi winning zukatan matan da ba soyayya ne ya hadasu bama ina ga sultana......a nan koda sakewa sultana yayi yace tayi rayuwarta,yayi imanin ba zata taba kubuta daga sharrin tsumammiyar soyayyar daya dasa mata ba.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 125 A nutse ya shiga motar,yayi bismillah ya kunnata,ya tasheta suna fita a layin sannu a hankali. Cikin motar ya dauki shuru,ba kuka takeyi ba,amma kuma baya iya ganin fuskarta,ta cure waje daya kaman maijin sanyi,wannan ya sanyashi miqa hannunsa ya kashe ac din motar gaba daya,ya kuma sake dage glass din sama. Tana iya jin kowanne motsi nashi kaman yadda qamshin turarensa daya cika motar yake shiga hancinta cikin kowanne numfashi da zata shaqa. Idanunta ta dinga lumshewa,tana mamakin yadda takejin matuqar dadin qamshin fiye da kowanne lokaci. Maganganun da sukayi da ama suna dawo mata daya bayan daya tana sarrafasu cikin kanta. Bata taba tunanin haka ama ta shahara wajen kara ba......haka ama ke kallonta dama?,amma koda a motsin 'yan yatsunta bata taba nuna mata komai ba..... kullum tana bayanta.....kullum goyon bayanta kuma takeyi,hakanan kullum farincikinta takeso. Duka duka tafiyar minti goma ya bulla wani titi,titi ne dake dauke da wadatar shops iri iri da ke saida abubuwan buqata iri daban daban. Ya ganganara muhallin da aka kebance don yin parking ya ajjiye motar a hankali sannan ya kasheta,ya zare key din,yadan waiwaya ya kalleta. Har yanzu taqi kalonsa,taqi juyawa sashen da yake gaba daya. "Zaki magantu,zakiyi bayani" ya fadi qasan ransa yana tunanin me ama ta gaya mata haka da ya tsaida kukanta a lokaci guda haka?. A nutse ya bude murfin motar ya fice,saita samu kanta da satar kallonshi. Yadda yaketa dake mata da yadda fuskarshi keson koma mata aliyyun nan na maradi ke bata mamaki "Hey madam.....gani ta nan" taji an fadi daga gefanta. Juyowa tayi ga mamakinta yana ta bakin window din da take zaune. Suka hada idanu saita dauke kai don nashi idanun duka suna kanta. Ita batasan ya zagayo ba,da ba yadda za'a yi tabi bayanshi da kallo. Rumfa taji ya mata gaba daya,ta daga idanu a dan tsorace tana tunanin me zaiyi mata?. Oily eyes dinta suka hadu da lion eyes dinsa suka sarqe waja guda. Tana jin dumin numfashinsa sosai yana sauka saman fuskarta yana kuma gogayya da nata numfashin. Hannunsa ya miqe yana sauke mata kujerar sosai yadda zata iya jingina ta huta yadda ba zata takura ba,faffadan qirjinsa yana gugar nata a hankali,ya lumshe idanun nasa yanayin numfashinsa yana sauyawa. Shi kadai yasan idanunta kadai ke iya illata dukka jarumtarsa.....ina ga kyakkyawan jikinta dake dauke da wani irin sinadari dake kassara duk wani qwarin gwiwa nashi "Bi a hankali 'yammata,idanuna basu da kyau......kince baki sona.....so ina baki shawara karki yarda ki fada tarkon so na" yayi maganar softly kaman me rada. Kanta ta kawar gefe saboda yadda zuciyarta ke wani irin bugawa. Tana iya jin sautin fitar murmushinsa,ya miqe yana maida mata qofar ya rufe "Mugu" ta fadi cikin zuciyarta tana lumshe idanunta,qamshinsa yana sake sanya mata nutsuwa a ranta,maganarta da ama tana sake kwantar mata da hankali,duk quncin da take tunanin shiga tana jin babu kaso hamsin cikin darinsa. Duka duka bai wuce mintuna ashirin ba taji ana bude butt din motar. Ta glass din motar take hango sanda ake zuba siyayya a ciki,ya sallamesu ya dawo ya tayar da motar. Tafiya suke a nutse kaman bai shirya zuwa inda zasuje din ba. Sun kusa mintuna talatin saman hanya kafin su isa inda suka nufa din. Daya daga cikin unguwanni ce dake dauke gine gine masu irin wani fasali dake da ban sha'awa kaman cikin qasar turkey. Idanunta qasa qasa amma tana kallon unguwar da duk wani tsari da yanayinta me kyau. Kaman ko ina cikin qasar,itama a tsaftace take cikin tsari,sannu a hankali har ya isa qofar wani madaidaicin gidan dake da madaidaiciyar harabar me qananun katangun da kana iya hangen ainihin ginin gidan dake tsakiya,harabar da aka qawatata ainun kamar wani qaramin garden. Da kanshi ya sauka ya bude motar,sannan ya saka wani siririn key ya bude gajeran gate din,sannan ya dawo ya shiga da hancin motar ya kuma ajjiyeta daga hannun hagun harabar inda aka saka qaramar rumfa mara girma don ajiye motaocin da bazasufi biyu zuwa uku ba. "Alhamdulillah" taji ya furta cakude da fitar numfashinsa yana zare key din motar. A nutse ya ciro wayarshi,yadanyi danne danne sannan kuma yayi kira. Cikin qasa da second biyar aka daga kiran. Kiran sunan suhail da yayi ya tabbatar mata suhail ne "No...je n'ai besoin de rien(bana buqatar komai)" ya fada a taqaice "Near Rue de rivoli" ya sake fadi. Dan satar dubanshi kadan tayi,ta fahimci kaman yana gaya masa adress na unguwar ne,don a hanya taga symbol na wannan sunan,saita mayar da kanta gefe. Zuciyarta na qiyasta mata wanne bigiren kuma rayuwa zata kaita yanzu?,a ina rayuwa zata ajjiyeta?,ta yaya zata zauna dashi?,yaya zasu rayu?,a matsayin miji?,ko a matsayin yaaya kaman yadda yayi iqirari?. Tana jinsa ya bude motan ya fita bayan ya gama wayar,da idanu dai take ci gaba da satar kallonshi har ya isa qaraman veranda,ya sanya maqulli ya bude qofar da zata sadaka da ainihin cikin gidan ya shige. Ko ina lullube da duhu,sai ya dinga takawa a hankali yana kunna kowacce fitila ta gidan. Ko ina na gidan tsaf yake kuma fes kaman yadda ya zata,don ya ajjiye me kula dashi na musamman duk bayan kwana bibbiyu. Sai daya gama zagaye ko ina ya tabbatar komai yana kan order sannan ya dawo tsakiyar falon. Yayi tsaye hannayensa cikin aljihun wandonshi yana kallon babban hoton benazeer da batoul da ya mamaye kusan rabin bango ga tsaho ga fadi kamar zasuyi magana. Saidai kuma ba ainihin photo bane,qwararren me zane ne ya zanasu irin zanen da kana kallon frame din kawai kasan yaci kudi bare akai ga farashin zanen kansa. Wani irin tsarin gini me matuqar tsari da dukan hankali aka yiwa gidan. Gida ne daya ginashi da guminsa da kuma jinin jikinsa. Gida ne daya ginashi tun bai sanya ran ci gaba da rayuwarsa kaman kowanne mutum ba,kamar yadda hoton dake maqale a bangon hoto ne da aka zanashi tun baisan benazeer da batoul mallakinsa bane.....jininsa bane ....kuma 'ya'yansa bane. Tsananin soyayyar da yakewa yaran ya sakashi aka masa zanen ya sanya a cikin gidan da ko sau daya bai taba kwana a cikinsa ba. Sardauna yasha tambayarsa me zaiyi da wannan gidan da har ya kashe maqudan kudade don ya mallakeshi a qasar da ba tasa ba?. murmushi kawai yakeyi,don shi kansa a lokacin baisan me zaiyi dashi din ba,saidai kuma zuciya da gangar jikinsa suna yawan gaya masa ya gina gidanne don iyalinsa "Wanne iyalin?,iyalin da babu su?" Sai wani sashe na zuciyarsa ya tuhumeshi da wannan,saidai kuma bai taba sarewa ba......yau gashi ashe akwai ranar da wannan tunani nasa zai cika. Gidan yasha burgeshi shi a karan kanshi,yasha jin kaman ya kwana a gidan.....amma kuma hakanan sai yaga bai cancanci kwanan a ciki ba. Gini ne daya dace da dukka tsarinsa da yanayin rayuwarsa,don ko suhail ma bai taba zuwa gidan ba. Juyawa yayi a nutse yana fita a falon bayan ya kashe dukka ac din gidan,don ya fahimci kaman sanyi yana takurata. Yana fitowa ta maida idanunta ta rufe,ya ganta amma sai yayi shima kaman bai gani ba,don yasan meye ya shirya mata,ya saka hannu ya bude murfin motar,sai kawai ya zura jikinsa gaba daya ya daukota cak daga cikin motar. Tsoro ya kamata sosai irin tsoron da yaro kanji a sanda babba ya daukeshi yana gudun kada ya yada shi,ba tare data shirya ba ta saqalo wuyansa da duka hannayenta tana zaro idanu waje zuciyarta kuma tana karyewa. "Shshshs" yace da ita ba tare daya kalli idanunta ba,don yasan me yiwuwa dole tace wani abu. Kanta tayi qasa dashi,tana tuna alqawarin data yiwa ama ba za tana musu ba don yanzun matsayin yayanta kuma uba yake a gareta,tsohon matsayi ne da bai canza ba yanzun ya dawo sabo. A nutse ya dinga wuce gurare har sai daya dangana da daya daga cikin bedroom din. Dream bedroom dinsa ne a duniya ya tabbatar da wanzuwarsa a wajen. Ya kashe kudade ba qananu ba wajen ganin bedroom din ya zama kamar yadda yake a yanzun. Saidai ko sau daya bai taba iya dogon zama a ciki ba,saboda duk inda ya juya yana reflecting masa rayuwar auren da a wannan lokacin bashi da wanda zai tayashi rayata. Yana da tsananin kamun kan da ba abinda ya tsana irin zina,don haka ya nisanci dakin gudun galabar shedan. Duk da idanunta suna kulle amma suna shiga dakin ta tabbatar ta shigo wani guri na musamman daya banbanta da duk guraren da suka gilma cikin gidan. Saman wata zagayayyr sofa ya ajjiyeta wadda ta nutse sosai saboda laushinta. Bai tsaya ba ya juya yana ficewa a dakin. Taji alamun fitarshi wannan ya sanyata bude idanunta a nutse tana qarewa dakin kallo. "Ma sha Allah" ta fada a zuciyarta duk yadda take basarwa. Iya canopy bed din dake dakin kadai ya isa ya sanya maka sha'awar kayi bacci. Ta gama bin ko ina da kallo,ko ina din yana burgeta. Har yanzu maina din na dabanne,ba abinda ya sauya nashi saima sake gaba da yayi. Yasan me gayu yake nufi kaman yadda tsafta da ado suka zame masa jinin jikinsa,yadda ya fita daban a family din MAYAK'I haka ya fita daban da dabi'unsa dama komai nasa. A qalla mintuna arba'in yayi kafin ya dawo,duk lokacin nan tana jiyo motsinsa a can babban falo,wanda daga shi zaka taras da matsakaicin falon da aka shiryasu saboda zaman karatu ko shan coffee ko kuma shan iska ko hantsi,sannan kabi lobby din dake shirye da dakunan bacci har guda hudu dake nesa da juna. Ba kayan dazu bane a jikinsa,yanzu wata shirt ce a jikinsa wadda bata da nauyi ko kadan,hakanan wandon jikinsa ya sauko amma baikai masa idon sahu ba,kayan duka black ne wannan ya sanya suka haskashi sosai. "Kina buqatan wani abu?" Ya fadi gently muryarsa na nuna rauni da gajiya a cikinta. "Babu" ta fadi qasa qasa tana yin qasa da kanta. Idanu yadan zuba mata,gajiya yakeji yanzun bayason debo rigima,amma da tabbas yadda take amsashin da sai yayi maganinta,sai kuma ya birkitata. Sakin wannan tunanin yayi ya tako ciki,ya isa gaban build in wardrobe din dake dakin,ya zugeta a nutse,take komai dake ciki ya bayyana. Kayan sawa ne cike a ciki na mata,takalma,mayafi harma da hijabai. Ya riga ya zuba komai a gidan,don dama ya qudurce a ransa muddin ya dawo daga tafiyar zaiyi terminating komai,sai kuma Allah ya taimakeshi komai yazo a sauqi. "Kiyi wanka ga kaya nan ki saka....... banason qazanta aikin sani?" Ya qarashe maganar da sigar tambaya. Fararen Idanunta ta daga tana dubansa cikin mamaki,ita zai cewa bayason qazanta bayan yafi kowa sanin halinta tun ba yau ba?,kuma ya wani hade rai yana gaya mata umarni,kamar ma itace tayi masa laifi ba shine yayi mata ba?,bayan ya rabota da gida tana tsakiyar rayuwarta da mutane......ya finciketa da qarfi ya sanyata barin gida a lokacin da ko da wasa tunaninta bai taba kawo mata irin haka zata faru ba. Wannan tunanin ya sanya qwalla ta tarar mata,amma duk da haka sai ta miqe tana zare takalmin qafarta,ta sanya wasu lausasan flipflops data gani a gefan wajen tana dosar qofar da ta tabbatar toilet ne. "Wait" taji yace yana qare mata kallo. Kukanta wani irin horo ne da takewa zuciyarsa ba tare data sani ba,baisan me zaiyi ya tsaida wadannan hawayen daga idanunta ba,duk da a yanzun bai shirya zuwa mata da lalama ba,amna dole ya hanata yawan wannan kukan ko don saboda abinda take dauke dashi.....ya qarasa raya hakan yana sauke idanunsa akan shafaffen cikinta da yake kaman zai manne da bayanta. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 126 Murmushi ya subuce masa can qasan ransa ba tare da ya bari fuskar ta nuna ba. Duk second daya da zai wuce muddin zai tuna cewa yana dab da sake zama baba sai farincikinsa ya sake ninkuwa. Yana burin ganin wannan tulelen cikin a jikin sultanarshi kaman waccan lokaci. Yanason yaga shagawabbiyar sultanarshi dinnan da juna biyu irin na kowacce diya mace,yanason ya bata daman baje kolin dukka sauran tabararta da batayi ba a shekarun baya,dum wata shagwaba da shine ya zama silar yankewarta da manna mata juna biyun benazeer da batoul da yayi ba tare da dukkansu sun shirya ba. Bayanta ya tsaya,sai ya duqa a hankali ya zura hannayensa ta bayantan ta qasan mayafin nata. Jin hannunsa tayi kawai saman fatar bayanta, numfashinta ya fusga da qarfi yana shirin qwace mata saboda wani irin abu da yayi tasiri cikin gangar jikinta. Qaramar sheshsheqa ya saki da dumin skin dinta daya ratsashi ta tsakiyar tafin hannunsa. Lullubin kanta ya fara warewa a hankali yana duban fuskarta. Hannu ta daga kaman zata riqe mayafin,sai kuma ta tuna da alqawarin da ama ta sanya tayi mata,don haka ga sauke hannu a hankali tana maida idanunta masu zara zaran eye lashes ta kulle. Sai daya gama cirewa ya ajiye gefe,sannan ya sake hade tazarar dake tsakaninsu yana dora hannunsa saman zip din rigarta,idanunshi saman fuskarta yana kallon reaction dinta. Hakan bai masa ba,qwayar idanunta yakeson gani,itace fitilarsa dake fallasa masa halin da zuciyarta ke ciki,bayason kulle idamun da tayi,yanaso ya gani da gaske tayi kewarsa koda tanason qaryata kanta da kanta akan hakan?,yanaso ga gani da gaske tana da feelings a kansa kamar yadda yakejin wani mahaukacin feelings a kanta ko kuwa?,don haka ya matsa da bakinsa daidai fuskarta ya busa mata wata sassanyan iska saman fuskarta. Kaman zata shide haka taji,taja numfashi me qarfi ta kuma dinga fesar dashi a hankali a hankali tana jin zuciyarta na wani riqewa. Boyayyen murmushi ya saki,kafiyarta da taurin kanta wani zubin suna burgeshi,alamu ne na inda an barta takai shekarun da maza zasu shiga gasar neman aurenta......tabbas zata jasu a qasa,hakanan ba za'a iya juya akalarta ko samun zuciyarta cikin sauqi ba. "Bude idanunki kije kiyi wanka......na fadi ba qazanta a gidan nan" ya fadi yana shan mur..... shima yanason ko yaya ne yadan taba zuciyarta,a yadda ya zura hannunsa yana zare zip din rigarta yayi imanin zuciyarta sai ta raya mata samun romance ko yaya daga wajensa,sai gashi yabar mata zip dinta cak tsakiya baikai qasa ba bai kuma rufeshi ba gaba daya,yayi sauri ya juya yana hadiye yawun bakinsa,bayason ta fahimci yana da feelings a kanta yanzun,yanaso ko yaya ta dandani abinda yake dandana. Idanun nata ta ware a hankali da suka sauya launi tana kallon hanyar daya fita. Haka kawai qasan ranta taji wani iri da hakan da yayi,jikinta a mugun mace ta sabule rigar ta maida gurbinta da towel taja qafafunta zuwa bandakin. Tsaye tayi a gaban madubi tana kallin fuskarta tana kuma jin yadda kowacce gaba a jikinta take aiki,ta lumshe idanunta ta kuma bude tanason tabbatarwa da kanta da gaske ne abinda takeji a jikinta game dashi?. "Ya Allah.....ya assamad" ta fadi tana kama kanta da hannunta. Me yasa zata tsinci kanta a haka?,bata shirya ba sam sam.....meye ya kawo mata wannan yanayin?,ta shiga tuhumar kanta tanason maida kanta mode dinta na ainihi ta qarfi da yaji. Dole daga qarshe ta gaji,ta hada ruwa me dumin da har ya wuce yadda take wanka ta soma zubawa jikinta duk a qoqarinta na ganin ta fidda komai daga jiki da zuciyarta. Babban towel ta dauro ta kuma yafa wani saman kanta sannan ta fito daga bandakin. Tana tafe tana jin yadda kasala ke luguguitata,hakanan jikinta dake da wani buqata shima yana sake taimakawa wajen wanzuwar kasalar. Ta samu abinci a jere a wajen saman wani dan zagayyen rug,sai ta dauke kanta gefe,don gaba daya bata da wani buqatar abinci a a yanzu,hasalima tasan bata isa taci ba,koda taci kuwa sai ya dawo. Ruwan jikinta ta goge tas sannan ta tsaya gaban dressing table tana binsa da kallo. Komai akwai akai,abun mamakin ma duk wani nau'in product da take amfani dashi ne. Ya akayi yasan zabinta?,hatta da turare irin nata ne bare powder qaramin alhaki. Ta miqa hannu ta daukeshi tana juyawa,irinsa ne tabbas,amma tsadarsa ya zarta nata. Daga gefe taga nashi turaren,ta miqa hannu a hankali ta dauka tana dubawa. Qaramin murmushi ya subuce mata ba tare data shirya ba,dole turaren ya dinga tsaye mata a rai da zuciya,ba qaramin turare bane. Bude murfin tayi tana sansanawa kaman ranar ta fara jin qamshin. Ido ta lumshe tana jin wata nutsuwa tana shigarta, cikin duhun idanunta ta dinga ganin tamkar shine a gabanta,batasan me yasa ta jarabtu da son qamshin ba,sai kawai ta fara fesa turaren qirjinta zuwa wuyanta ba tare data bude idanunta ba. Caraf taji an riqe hannun nata tare da hana mata damar ci gaba da fesa turaren,wannan ya sanyata bude idanunta da sauri. Shine a tsaye a gabanta taba duban face dinta. Fuska a hade,ya kama hannun nata ya riqe cikin nasa da kyau,sannan ya saka daya hannun yana zare turaren daga hannunta "Irin wannan fesa turare haka?" Ya qarasa maganar yana dage mata girarshi duk biyun. Nauyi da kunya suka kamata,bata fiyason yana kamata tana shiga shirgin lamuran da suka shafi rayuwarsa ba,wannan ya sanya ta motsa nata kambun,ta zare hannun nata tana jin nauyi da takura da yadda yakebin qirjinta da kallo "Ni bansan turarenka bane......shi yasa naji baimin dadi bama....." "Ashe?......me qarya,?......" Yayi maganar dariya na taso masa amma ya kanne. Qin bashi amsa tayi fafur,saita juya zuwa wajen wardrobe dinta tana. Tana jin yadda idanunsa ke binta da kallo. Batayi qarya ba,don gaba daya ya sauke zazzafan kallonsa a kanta,qugunta yana juyawa a hankali tamake wadda keyi da gayya,yayin da ita kuma taji ta qagu ta isa ga wardrobe din,tana jin baiken kanta ma,me yasa ta saki jiki cikin dakin bayan tasan cewa ko yaushe yana iya shigowa. Bayansa ya jingina da dressing table din yana harde hannunsa a qirji yana ci gaba da jifanta da mayataccen kallon nan nasa tamkar maye yaga nema. Ko Ina ajikinsa take aikewa saqo ba tare data sani ba. Yana jin inama zai iya riqe lokaci su tabbata a haka?. Kayan da hannunta ya fara kaiwa kawai ta zaro,ta riqesu a hannunta tana juyawa kawai ba tare data waiwayo ba. Tayi imanin kallonta yake,kuma muddin ta juya tabbas qirjinta zai fara aza idanunsa akai. Batasan me yasa sam bashi da kunya ta wannan gefen ba,waishi baya ma kunyar tabasu?,baya kunyar kusancin dake tsakaninsu?,me yasa yake manta shi din kamar uba ko kawu yake a wajenta?. Ta tabbatar tsaiwar ba zata haifar da d'a me ido ba,don wala'alla su dauki dogon lokaci haka baice mata ci kanki ba. Tun a wancan shekarun ta sani miskilancinsa yafi gaban haka,don haka ta cije tace "Ina buqatar dakin zan sauya kaya" "Me na tsare miki?,ki canza abinki mana,beside ma ni banda abun kalla a nan wajen" yayi maganar yana dan tabe baki kadan hadi da nuna halin ko in kula saman fuskarsa. " A gabanka?" Ta fadi cikin jin haushin maganarsa "Yes......me kike boyewa?,kin manta na miki tsarkin fitsari na cire miki majina.......ni nake siyo miki pant..... boom short,har aka fara half vest aka koma bra......." "Na shiga uku" ta fada a mugun raunane,don duk iya tsiwarta akwai abubuwan da yayi mata da batason tunasu,suna sakata taji kaman ta nutse,amma shi sai ta fahimci abun dadi yake masa. "Baki shiga ba tukunna" ya raya a ransa yana wassafa randa zai manna mata haukan da zata fito da bakinta ta bayyana masa ta kuma bayyanawa duniya matsanancin son da take masa. Lallausan busar piano dake a mazaunin ring tone dinsa ne ya katse muhawarar. Ya juya gefansa a hankali ya kalli me kiran. Laila ce,sai yadan tada idanunsa kadan ya saci kallonta. Ya dauke idon nasa yana cije lips dinsa hadi da sakin murmushin mugunta. "Bazan lamunci wasa da abinci ba ko don lafiyar baby na..... ki shirya ki zauna kici abinci" ya fadi yana daga kiran,ya kara a kunnensa hankali kwance yana fadin "Hi laila....." Dai dai sanda yake fita a dakin.. Kaman wadda ya fusgi hankalinta da kiran sunan kadai da yayi,ta bude kyawawan fararen Idanunta da kyau tana binsa da kallo sunan LAILA yana amsa kuwwa cikin kunnenta. Ta tsani sunan tsana ta haqiqa,kuma bata da tabbacin tsanar data yiwa sunan bai shafi me sunan ba.....bata ko qaunar jin sunan da yayi mata da wannan sunan......wai wacece ita?,tambayar da har yau bata sani ba kuma takeson tasan amsarta. Dumin da taji saman fuskarta ya sanyata miqa hannu,data shafa sai taji hawaye "No sultana.....kuka?,me yasa?" Ta fadi a fili wasa qasa tana mamakin kanta da dalilin fitar hawayen idanunta duk da tana jin radadi kamar ana tsaga zuciyarta. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 127 Komawa tayi ta zauna a wajen tana ci gaba da girgiza kai. " Bai kamata na damu ba tunda na amsa bana sonshi,bai kamata naji ciwo ba......na barshi yayi rayuwarshi nima nayi tawa" ta dinga fadi qasa qasa ita daya "Da cikinsa a jikinkin?' wata zuciyar ta jefa mata tambayar,abinda ya qara raunin zuciyarta kenan,ta miqa hannu saman plate tummy dinta tana shafawa. "Yanzun wata halittar ne a nan?,me kama da benazeer ko batoul?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar tana jinjina lamarin a ranta. Tanason tasan wacece lailan nan,ba wata diya mace da ta taba tsaya mata a rai sama da laila din,sai ta miqe tana qoqarin baiwa kanta jarumta da qwarin gwiwa,ta sauya kayan jikinta,ta koma inda ta tashi ta zauna still hannunta saman mararta kamar tanason taji motsi ko alaman wani abu da xai tabbatar mata ciki ne manne a jikinta. Yunwa takeji sosai,amma ta kasa samun qwarin gwiwar da zata kalli abincin ma,ta lumshe idonta tana tura tarin wahalhalu da tiri tiri da tayi da kanta da rayuwarta lokacin cikinsu benazeer,sai taji wasu sabbin qwalla na zubo mata,don bata da tabbacin wanne hali zata shiga a yanzu?. Saman daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana fidda iska a bakinsa "You know what?" Ya yiwa laila tambayar a dake. Mamaki ya kamata,yanzun nan ya kira sunanta da kulawa da taushi,har tanajin hakan cikin zuciyarta,to meye kuma ya sauyashi nan da nan? "A'ah ya haidar" "Daga yau banaso kici gaba da wahalar kirana......magidanci ne ni yanzun,kina iya kirana sanda iyalina ke kusa.....i will call u duk sanda buqatar hakan ta taso" wani tsawa taji ya fashe mata saman kanta. Kada dai ace da gaske hasashenta ne zaya zama gaskiya,kada dai ace SULTANA HAMANI MOHMOUD MAYAK'I,sabuwar 'yar jaridar gidan tvn nan matarshi ce kaman yadda ta soma ji da ganin qishin qishin din haka?. Muddin ko haka ne......ita laila bello ina zata iua goga kafada da ita,sultana ake magana fa?,matar data shiga media da wani irin mugun farinjini?,matar da ko ke mace idan kika kalleta saita burgeki?,indai itace matarsa,BB twins yaransa lallai bata da wani gurbi ko muhalli cikin rayuwarsa. To amma ta yaya zata bari tayi loosing hope har haka?,ta yaya zata bari ya subuce mata a dare daya?,ta yaya zata kashewa kanta qwarin gwiwa alhalin bai fito qarara ya bayyana mata hakan ba?. Salube wayar tayi tana jin kamar wani zazzabi zai saukar mata. A duk sanda tayi tunanin akwai wata mace a rayuwarsa,kwanyarta tafi hasko mata ayana tahir cousin dinsa,don ta tabbatar indai ta hangi sultana a wannan gurbin bata da wani sauran abinda zata nuna a gabanta. Wayar ya dinga juyawa a hannunsa. Yana buqatan Peace zuwa yanzu,ayana da laila dukka zasu zame masa matsala su hanashi sukuni su kuma dagula lissafinsa. Yadan waiwaya kadan yana duban bakin qofar dakin,dukka hankalinsa yana can,yana kanta,yanason komawa ko don ya tabbatar taci abinci,amma kuma yayi wuri ya koma yanzun,don haka yaci gaba da zama a wajen hankalinsa yana rarrabuwa,ganin haka sai kawai ya danna numbers din goumar ya kirashi. Su batoul ya buqaci ya bashi,suna kusa dashi don haka ya hadasu ya koma gefe ya basu wuri. Hira da yaran ya dauke hankalinsa,a qalla sai da ya kwashe musan mintuna ashirin sannan ya katse kiran,ya miqe yana wucewa dakin. Qamshinsan nan daya soma zame mata jarraba zuwa yanzun shi ya fara gaya mata shigowarsa,daga inda take zaunen kamar wadda aka dasa ta daga idanunta da suka sauya launi saboda yunwa da kuma tabuwar da zuciyarta tayi ya zube masa su. Dauke kai yayi yana basarwa,saidai kuma idanun nasa yana kan hannunta dake saman cikinta. Cikin qasaitaccen takunsa ya qarasa gaban kayan abincin,ya kallesu sannan ya maida dubansa a kanta,kaman zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya tsugunna a hankali,ya buda komai ya zuba daidai yadda ya dace ya hada saman tray ya isa inda take ya sabule takalmin qafarsa ya zauna sosai saman rug din wajen "Oya......sauko kici abinci" idanunta ta aza a kansa sai kuma ta janye,wani irin zafinsa takeji,waya yaje yayi da wata ya jima haka,ya barta zaune a daki bayan ya rabota da ama dinta,ya kuma danqara mata cikin da ta tabbatar shi yake sanyata jin gigitacciyar yunwar da tunda tazo duniya bata taba jin yanayi irin wannan ba. "Bana ci" ta bashi amsa murya a dakushe. Cikin qasa da second biyu yanayin fuskarta ya sauya tas.......wannan lion eyes din nasa ya zube mata yana maida fuskar nan ta ALIYYU HAIDAR saman fuskarsa "Nasan ke kin qoshi......ki sauko ki bawa baby na abinci,that's what i wanta......." Zuciyarta taji na neman karyewa,wato bata tata yake ba,ta d'ansa yake,tunda ita din ba diya bace kota mutu ko tayi rai ba damuwarsa bace. Yadda ya zuba mata nauyin idanunta da kwarjininta ya sanya ta kasa cewa komai,ta zamo qasa a hankali har yanzu tana dafe da cikinta ta zauna sosai. Hannun ya sake bi da kallo,wanne irin tsaro takewa cikin haka?,Allah yasa soyayyarsa ce ta shigeta da gaske ba qiyayyar data gwadawa cikin benazeer da batoul bane. "Hope ba damunki yayi ba...... don babu batun abortion a nan" ya fada cikin salon basarwa. Da sauri ta daga kai ta kalleshi,suka hada ido sanda yake tura mata dukka palates din gabanta. Kau da kai tayi gefe zuciyarta tana raurawa,waishi waye yake bashin labarin komai?,labarin abubuwan duk da akayi alhalin baya tare dasu?. _"a sannan duk wani motsinki,faduwarki da nasararki a gaban idanuna kika yita,ba wani second na rayuwarki da ya wuce ba tare da nasan me yake gudana ba.....baccinki da tashinki.....kukanki da kuma sakewarki don ba dariya a dairy din qwaqwalwarki a sannan"_ ta tuna da maganar daya taba gaya mata. A sannan ta dauka ya fada ne kawai don ya wanke kanshi,amma yanzun ta tabbatar da gaskiyar abinda ya fadi din. "Bismillah" taji yace. Koda ta waiwayo sai taga abincin ya debo cikin spoon ya biyo bakinta dashi. Duk yadda zata masa bayanin ba zataci ba bazai gane ba,bazai kuma yarda ba,don haka ta cire idanunta daga cikin nasa,tasa hannu zata karba spoon din. Kansa ya girgiza yana janye cokalin baya "For my baby......idan ya gama ci sai na baki kici naki da kanki......amma yanzun dai ki barni nayi aikina,ke kyaci naki da kanki,don dama bazan iya aikin mutum biyu ba" "Ahaaaann" ta fadi qasan ranta,indai xaiyiwu harara me zafi takeson watsa masa,komai baby komai baby?,ita ba mutum bace wai?,me yasa bazai nuna kulawa a kanta ba?,me yasa ya daina nuna mata kulawa?,me yasa ya daina nuna damuwa da ita?" Wannan ya tsaye mata a rai,amma haka ta daure,ta buda qaramin bakinta tana karbar abincin kadan kadan. Yadda lips nata ke juyawa sanda take tauna abincin ya tayar masa da tsigar jikinsa,all the way kawai yaji yana muradin siraran lips nata masu sulbi,saidai kuma yanason ya bata tazara tsakaninsu don ta sake aminta ta kuma gamsu ita yakeso ba gangar jikinta ba. Yadda yake bata abincin tana karbar wani tana kuma qin karbar wani har sai ya hade rai sai ya tuna masa da some years ago.......sanda tana baby sultanarshi da sai ya lallasheta zataci abinci,sai ta kuma zabi irin abinda takeso taci dina. Abincin da taci a lokacin ita kanta tayi mamaki,tanata fatan kada ya dawo mata kaman yadda ta cishi,saidai har sanda ta gama shirin kwanciya ta kwanta tana qudunduna a blanket bataji alamun xai taso mata ba. Idanunta lumshe zuciyarta na bugawa kadan kadan. Ta lumsassun idanunta take satar kallonshi. Bashi da niyya ko alamun fita a dakin,don ya nade abinsa cikin sofa bed yayi kyau cikin wasu pyjamas da suka bayyanar da kwantaccen lallausan gargasar dake lullube da qirjinsa. Idanunsa duka akan wani dan qaramin littafi da bata iya gane na meye ba saboda yadda qarami ne. Tadan sauke numfashi kadan tana motsawa,har yanzu yana nan da dabi'arsa ta karance karance kenan. Tun tana zaton zataga yayi wani motsi har ta gaji. Haka kawai ta samu kanta da juyi daga wannan hannun zuwa wani hannun,tana jin wani eagerness a hankali yana ratsata,cikin jiki da zuciyarta ta dinga jin wani feeling kaman she's waiting for something.....akwai abinda take jiran tsammani. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 128 Sake qara yawan motsinta tayi daga hagu zuwa dama duk bayan wasu mintuna. Cikin ranta taji ta kasa samun calmness........ Yadda yake zaune cikin nutsuwa yana buda littafin shafi bayan shafi ya bata mamaki,ta kasa jin ta yarda da cewa baiji motsinta ba,baiga duk wani juyi da takeyi ba. Yadda taketa mutsu mutsu koda ba daura da ita yake ba ya kamata ya fahimci ai ba'a kwance take waje daya ba,kodai halin ko in kula din daya koyi nuna matanne yake sake nuna mata a yanzun?,sai ta jawo pillow ta qanqame,tana ji har cikin bargonta runguma takeso,tanaso wani abu da zatayi hugging nashi ko shi yayi hugging nata,zuciyarta tana da buqatar home..... abinda ake kira da ainihin home bawai wannan da take ciki ba. Tsuka taja qarama wadda bata shirya fitowarta ba,da sauri ta kalli inda yake zaunen tana dan ware idanunta kadan,don ta sani babu abinda ya tsana irin tsaki,fata take baijita ba,tana kuma fata koda yaji kada yace dashi take. Ga mamakinta baiko motsa ba bare alamu su nuna ya jita. Ta matsar da idanunta zuwa ga kunnuwansa tana dubawa wai ko earpiece ya sakawa kunnen nasa?. Ba wani earpiece,sai hankalinsa daya tattarawa littafin. Wani abu me tauri taji ya tsaya mata a wuya,mode dinta na neman attention daga wani ya sake hauhaww,taji zuciyarta kaman zata zautu,kana zaune da mutum daki daya amma baka monitoring mode dinsa?,meye hakan?. Hawaye zuciyarta keson zubarwa amma ta dake,tayi gyaran murya kadan wai ko zai daga kanshi,amma tamkar tana zaune da kurma a dakin. Ta sake motsawa kadan tana jefo pillow qasan qafafunta,nan ma dai duk ko a jikinsa,saima qafafunsa daya dauke daga qasa ya aza saman sofa yana sake gyara zamanshi alamun zama ya masa dadi. "Ni ban iya bacci da wuta a kunne ba" ta furta cikin qufula alhalin bata da abu guda daya da zata ambata yayi mata da sunan laifi. Shanyayyun idanunsa da suka rusuna ya dago ya zube mata su a nutse,dan hasken dake dakin yana haske farin kwalbar computer glass din daya maqala a idanunsa. Kallon kallo suka fara yiwa juna,kowa da abinda yake rayawa cikin ranshi. Ita tafara janyewa don nan da nan taji ba zata iya jurewa dogon kallo a tsakaninsu ba,ko a iya haka aka tsaya ya sake rusunar mata da zuciyarta da wani irin mode da rauni me yawa. Kaman bazai magana ba saboda qasaitarsa data lura ta motsa sai kuma yace "Me kike buqata?" Yayi tambayar a taqaice "A kashemin hasken dakin" ta amsa masa tana lumshe idonta don batason qwallar da taji ya fara taruwa ya samu nasarar cika mata idanu. Qafafunsa ya sauke qasa ya sake tashi ya zauna sosai yana kallonta "Ikon Allah,nan dinfa dakin aro ne......dakin matar gidanne me zuwa,aro na baki zuwa wani lokaci,so kinga dole kiyi haquri da isa da dakin da zakiga ana nuna miki" bata shirya zuwan kuka ba amma sai gashi ya taho,ta juya da sauri tana saka kanta cikin pillow tana jin wani irin loneliness yana mamayarta. Gilashin fuskarsa ya zare yana fidda idanu waje "What?.....me kuma nayi?,daga magana?,kince baki sona,na miki alqawarin zama dake a matsayin uncle.....yanzun don nace dakin akwai maishi nayi laifi?" Maganarsa kamar tiri ta zame mata,ba wadda ke yawo a kanta sai laila....laila yake nufi kenan?,ita kuwa me zataci da dakin laila?. Tanaso ta miqe tabar dakin amma kuma kunya ta dabaibayeta,kunyar yadda akayi ta bari har ya fahimci wai taji haushi don yace aron daki ya bata. "Withtime yarinya.....muje zuwa" ya fadi yana miqewa a hankali gami da rufe littafin,ya dora eye glasses dinsa akan littafin. Ko batayi magana ba ya gama karantar me takeso,skin to skin contact. Shi take mutuwar buqata a lokacin,ya gama karantar mode dinta,tun juyinta na farko ya gama fahimtarta,yana sane yayi biris da ita. Pyjamas dinsa ya zare yana murmushi ya wuce toilet ya daura alwala ya fito,har yanzu tana kife ya kuma tabbatar hawaye takeyi. Ya dauke kansa yana qunshe dariya. Wahala bata sakata giving up da wuri,ya lumshe idanunsa yana sake sakin boyayyen murmushi,wala'alla ubangiji ya dubi zuciyarsa da haqurinsa ne ya sanya mata wannan yanayin. Wani irin yanayi ne da ciki zai iya kawoshi duk dare tattare da wasu matan. Zuciyarsa yaji tana sake sanyi,yayi amanna komai yana kusa da zuwa qarshe. Wutan ya gama kashewa gaba daya,sai ya haura gadon ya dage blanket din yana shigewa ciki,ya sanya dukka hannuwansa yana jawota cikin jikinsa. Zamewa ta soma yunqurin yi,sai ya gwada mata banbancin mace da namiji,yayi mata wani kyakkyawan riqo da hannunsa,ya saka daya hannun nasa yana yage rigar baccin jikinta,ya manna fatar jikinsu guri daya. Shi da ita ba wanda yasan ya fidda ajiyar zuciya sai bayan ta fita daga jikkunansu a lokaci guda,muryarsa nadan sarqewa yace "You are not strong enough at all madam......don xan taimakeki na baki relief ma sai kinyimin taurin kai,taimako ne fa?,a qa'ida ma saikin biya" kaman ta mutu saboda haushi,saita cusa kanta qirjinsa ala dole tana son goge damshin hawayen idanunta cikin gashin qirjinsa. Haushin kanta da kanta takeji,me zai hana tayi kwanciyarta ita daya?,da datake kwanciyarta shekarun baya meye ya sauya?,me yasa yanzun ta damu da son jinta jikin wani?,yanzu ba gashi yana gaya mata baqar magana a fakaice ba. Minti guda yayi yawa nutsuwa ta fara saukar mata,kukan da take tsammani zata dade tana yi sai gashi yana yin nasa guri. Shuru ya ratsa dakin,sai sautin bugun zuciyoyinsu da wani irin dumin jikin juna dake ratsasu. A hankali wani irin ni'imtaccen bacci yayi awon gaba da ita,ya gyara mata kwanciya sanda ya fahimci bacci ya dauketa,ya leqa fuskarta kadan yana kalla. Duk da baya iya ganinta da kyau amma sai da qaramar dariya ta subuce masa. Ta riga ta fada ruwa tsundum amma tanata yunqurin qaryata kanta da kanta,taqi bada kai.....amma a sannu a sannu zaici gaba da matsata har sai ta bayyanawa duniya bama shi kadai ba. Sake mata mazauni yayi sosai cikin jikinsa,ya cusa kansa tsakiyar gashinta yana shaqar daddadan qamshin hair mist da take using dashi. Wani irin scent me laushin qamshi,ya lumshe idonsa tana jin feeling din da yaketa qoqarin dannewa tana tasowa. Ko ina na jikinsa ya soma amsawa,ya sakeyi mata kyakkyawan riqo ainun. Shi daya yasan me yakeji a jikinsa,sati ukun nan ba qaramin qoqari da kuma yaqi yayi da kansa ba tsahon kwanakin. Ba gangar jikinsa kadai ba,hatta jinin dake zagayawa a jikinsa yayi kewarta. Bayason ya karya shirginsa......yanasin ya nisanci neman komai daga wajenta saboda ya wanke zuciyarta yadda ya kamata daga tunanin gangar jikinta kawai yakeso......yanason ya tabbatar mata da sahihiyar qaunar da yake mata......yanason ya bata tabbacin ita sultana yakeso gaba dayanta bawai wani abu daban daya danganceta ba. A hankali ya dinga murza fuskarsa cikin gashinta yana sauke zazzafan numfashi,kowanne saqo na jikinsa ya shiga fidda gumi,kaman yadda numfashinsa ya dinga fita a wani irin birkice. A hankali dumin numfashin ya dinga ratsa fatar kanta yana aika saqo zuwa qwaqwalwarta. Wannan ya sanya katsewar baccinta,ta bude idanunta a hankali,turarensa kuma daya gauraya da nata ya zama abu na farko data fara sheqa. Yadda numfashinsa ke fita wani iri ya bata tsoro sosai,tayi qoqarin banbarewa daga jikinsa don ta kalli fuskarsa don tabbatar da lafiyarsa saidai kuma ya hanata wannan damar,don wata wawiyar runguma yayi mata jikinsa ko ina ya dauki rawa. Mararsa ke murdawa sosai,ya lumshe idanunsa yana ambaton "Ya Allah......ya rahman" gabanta ya fadi sosai,tsoro ya kamata jin yadda hatta da gashin qirjinsa ke fidda damshin gumi "Kada dai wani abune ya sameshi mummuna,idan hakan ta kasance ya zanyi dashi?" Tambayar data dinga yiwa kanta kenan cikin zuciyarta. Samun kanta itama tayi da karanto addu'o'i,ta sake yunqurin zame kanta a karo na biyu,muryarsa cikin rawa har labbansa suna rawa yace "No.....please......stay with me,don't......" Sai ya kasa qarasawa yayi mata wani kyakkyawan riqo yana sauke wani numfashi me matuqar qarfi da nauyi. Idanunta ta lumshe tana cije lips dinta itama tana sakin nishin wahalar tsatstsauran riqon da yayi mata,don sai da taji kaman qashinta zai amsa. A hankali kuma ya sassauta riqon yana sake cusa fuskarsa cikin gashinta,jikinsa ya saki gaba daya,gumin jikinsa kuma yaci gaba da tsatstsafowa,sai ya sassauta riqon sosai amma saita kasa matsawa daga jikinsa kunnenta saman qirjinsa tana sauraren bugun da zuciyarsa keyi wadda sannu a hankali ya fara daidaita. Shuru yaci gaba da wanzuwa,bai sake motsawa ba har kusan mintuna biyar. Ajiyar zuciya ya saki yana miqewa,a hankali ya zareta daga jikinsa,ya dora mata kanta saman pillow ya maida duvet ya rufeta sosai sannan yaja jikinsa yana sauka daga saman gadon a sanyaye. Da idanu ta bishi ta qasan duvet din,har zuwa sanda ya isa toilet ya tura qofan ya shige ya maidata ya kulle. Idanunta ta dauke daga wajen,gaba daya kanta ya kulle,me ya sameshi haka?,yana da wani ciwo ne da ba'asan dashi ba?,yadda bugun zuciyarsa yake da kuma fitar numfashinsa da irin riqon tsaurin da yayi mata ya bata tsoro. Ta maida idanunta ta lumshe tana jin qarar ruwa daga bandakin. Mintuna kusan sha biyar taji alamun fitowarsa,tadan ware idanunta tana kallon fuskarsa a sace. Yana daure da rigar towel wadda ta fidda ingarman qirjinsa waje,gargasar duka ta jiqe da damshin ruwa kamar yadda sumar kanshi ke digar ruwa, qaramin towel ne a hannunsa yake rage ruwan yana matsawa zuwa gaban stool. Caraf ya kama idanunta tana satar kallonshi,a gigice ta dauke idanunta wata matsananciyar kunya tana kamata. Basarwa yayi kamar bai gani ba,ya juya yana ajjiye towel din hannunsa,ya kuma kama zaren bathrobe din yana warewa,ya sanya boxers ya feshe jikinsa da turare sannan ya sake dawowa zuwa gadon. Kaman dazu haka ya maidata jikinsa,ya dora hannunsa a hankali saman sumarta yana shafa sassalkan gashinta. Yadda yayi matan ya haifar mata da faduwar gaba,muryarsa can qasan maqoshi taji ya furta "Shshshsh......relax......relax" idanunta ta maida ta lumshe tana qoqarin daidaita bugun zuciyarta. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 129 Daga ita har shi ba wanda yasan lokacin da bacci yayi awon gaba dashi ba. Saidai lokaci yana yi na sallar asuba suka farka kusan lokaci daya. Ita ya fara yiwa umarni ta shiga tayi alwala sannan shima ya shiga yayi,ya jasu jam'i sukayi sallar asuba bayan kowa yayi raka'atanil fajri. Ya juyo ya zauna sosai yaja duban fuskarta,ya xube mata idanunsa dake a lullumshe wanda suke nuna akwai alamun bacci a cikinsu. Taqi yarda ko sau daya su hada ido,saboda duk sanda ta tuna yadda suka kwana jiya saita dinga jin kamar ta aikata wani babban zunubi ko laifi. Wani kasalallen miskilin murmushi ya saki na gefen baki. Ta gama cukuikuyeshi ta gama sunnewa a jikinsa amma yanzun tana wani basarwa kaman ba ita ta aikata ba, ya tabbatar da zai nuna mata yadda ta dinga maqalewa cikin jikinsa tana matsowa a duk sanda ya motsa tana sake shigewa jikinsa.....ya tabbatar sai ta kusa narkewa. Zara zaran hannunsa ya miqa mata kaman meson suyi musabaha. Ta daga ido a hankali ta kalli hannun sai ta dauke idanunta tana boye hannuwanta cikin hijab kamar me tsoron kada ya kamata "Good morning mom twins" ya fadi da muryarsa can qasan maqoshi da tayi wani irin laushi yana lullumshe ido,saboda shi daya yasan irin feelings da yanayi da kuma lokaci irin wannan yake saka masa. "Ina kwana?" Ta fadi qasa qasa itama,sai ya maida hannunsa yana hadesu guri guda idanunshi a kanta "Lafiya qalau alhamdulillah" ya bata amsa a nutse har yanxu ya kasa dauke idonshi a kanta. Sosai ta kuma dauke kanta,kunya yake sanyata ji abinda batayi niyya ba. Saita kwantar da kanta saman cinyoyinta tana lumshe ido. Yunwa takeji sosai,amma kuma batason ta nuna masa,batason ta bayar da kanta,saidai kuma da gaske yunwar qara gaba takeyi. Qara qudundunewa tayi,tana shirin jingina jikinta da sofa din dake kusa da ita,sai taji ya sunkuya ya dagata cak. Idanu tadan fitar qamshinsa yana shiga hancinta. Bai ajeta ko ina ba sai gefen gadon,ya sauketa a hankali yana mata rumfa da faffadan qirjinsa,ya miqa hannu ya dauko pillow ya saka mata a bayanta,ya jawo mata blanket yana lullube mata qafafunta. A nutse ya miqe,saita daga idanunta,suka hada ido,shima ita yake kallo yana aje mata kallon nan nasa da kowacce rana yake barazanar sauke zuciyarta gaba daya. Baice komai ba sai ya juya yana fita a dakin. Ajiyar zuciya ta sauke tana rungume pillow da kyau a qirjinta,ta kuma kanta ta kwantar. Batasan tunanin me takeyi ba,amma dukka hankalinta yana tare dashi bayan fitarsa, zuciyarta ta dinga bugawa a hankali kunnuwanta kuma sukayi nisa da sauraren kowannw motsi dake gilmawa cikin gidan,kamar dai tana qididdigen takunsa daga inda ya fita din zuwa cikin dakin. Sanda taji an bude qofar dakin sai data sauke qaramar ajiyar zuciya,duka duka fitarsa da mintuna kadan amma sai take jinta ta takura,duk dakin takeji kamar an sauya masa yanayi. A nutse ya iso gabanta,ya tsugunna a hankali daga gefe ya dauko wani abu. Koda ya bude saiga dan madadaicin tray table. Hannu ya miqa ya bubbuga pillow din da take kai. Ya sani idanunta biyu,don koda qafa tayi motsi yana fahimta,amma har zuwa sannan taqi daga idanunta a kanshi. Kunyarsa takeji sosai ta yadda batason hada idanu dashi,yana jifanta da wani kallo ne da zuciyarta bata iya jurewa,shi yasa take matuqar qoqarin kaucewa duk wani eye contact dashi,don abune da bashi da sauqi sam. Da ido ya mata nuni ta gyara zamanta. Bata musa ba ta gyara,saboda qamshin da takeji daga tray din da ya ajjiye yana qara mata kwadayi,yawunta ya shiga tsinkewa shi daya ba tare da taga meye a ciki ba. A nutse ya saka table din daga saman qafafunta,ya dauko tray din dake dauke da qananun cups da bowl ya ajjiye ya fara buda mata komai. Ya kammala ya hau saman gadon ya zauna sosai,ya dauki qaramin spoon yana cewa "Haaaa" sai data kalli spoon din sannan ta kalleshi. Ya dage mata dukka girarshi biyu yana fadin "Aikina na uncle nake cikawa,sannan duk kina cikin baquncina ne......baby na nakema kuma.....banason zama da yunwa right?" Yayi maganar gently da irin dakiyar nan tasa dake qara masa kwarjini. Bata tsaye sa'insa dashi ba ta bude bakinta ya fara bata,kaman jiya sai daya tabbatar takai geji sannan ya tattara komai ya fita dashi. Bayanta ta mayar jikin gado ta jingina tana fidda numfashi,bata san wanne sihiri bane a hannunsa?,wacce baiwa gareshi da ya haddace duk abinda take matuqar so,hakanan duk abinda taci din baya dawo mata,ba kaman a gida ba da bata isa taci solid abu ba,gashi daga jiya zuwa yau taci abinci da kyau ba tare da ya dameta ba. Minti biyar goma ashirin taketa tsammanin sake jin dawowarsa,saidai ko motsinsa bata qara ji ba. Kasala takeji gadan gadan da wata irin mahaukaciyar kewa da takeji kamar ba zata barta ba. Tana buqatar ta jita jikin wani abu......tana da buqatar dumi a tattare da ita. Sannu sannu sai gashi ta buge da duba agogo,har zuwa sanda lokaci yayi nisa, zuciyarta ta dinga zafi,ta kasa zama guri daya,sai ta miqa hannu ta jawo wayarta. Numbers ta dinga bi tana tunanin waye zata kira?,a hankali a hankali har ya isa kan number bibi,sai kawai hannunta ya zarce da kiran bibi din. Tayita ringing kamar ba za'a daga ba,wannan ya sake sakawa zuciyarta tazo iya wuya,ta cika ta cika tayi fam,dai dai sanda bibin ta daga wayar da sallama a bikinta. Bakinta ta bude zata amsa sallamar amma saita kasa,wani abu ya tsaye mata a wuya,sai kawai ta fashe da kuka,kukan da ya daga hankalin bibi ainun. "Ke meye ne haka da fara safiyar nan?,.......ke sultana?.....me ya faru?,waye ya mutu?" Tanason buda bakinta ta yiwa bibi magana amma ta kasa "Na shiga uku,me ya samu diyar mutane?" Bibi dake zaune saman abun sallah ta fada. Jikarta khadeeja diyar uncle bashir ta waiwayo tana kallon bibin "Lafiya bibi?" "Kinga kiramin hamidou ko hamdiyya,banga ta zama ba" ta fadi a dan rude. Ajiyar zuciya khadeeja ta saki tana lalubowa Bibi number aba. Cikin rashin sa'a a kashe wayar, dubanta khadeeja tayi "Bibi a kashe yake wayarsa" "Kiramin hamdiyya" ta fada idanunta akan wayar kamar zata fada ciki. Sanda ama din ta gama komai take shirin shiga kitchen ta samu tanja ta duba abinda za'a dafa da safen wayarta dake hannunta ta dauki kuka. Ta danyi mamakin kiran bibi a lokaci,don bata saba yin hakan ba saida dalili muhimmi. Dakatawa tayi tana daga kiran,hankalinta dukka akan bibi din "Barka da safiya bibi" "Barka kadai hamdiyya....kowa lafiya ko?" "Lafiya qalau alhamdulillah" ta bata amsa cikin girmamawa "Amma nace....me ya samu sultana?" "Me ya faru bibi?" Dan ajiyar zuciya ta saki hankalinta yadan fara kwanciya,da alama iya shegen sultanar da tabararta ne ya motsa "Naga kiranta,dana daga kuma sai naji ta sakarmin kuka 'yar banten uba" murmushi me sauti ama ta saki duk da batasan me ya farun ba amma don ta kwantarwa da bibi hankali,saita fara takawa tana wucewa kitchen saboda nutsuwar data samu "Ban sani ba bibi......bansan me ya sameta ba,don bamu kwana tare da ita ba,tana can tare da aliyyu" "A'ah ikon Allah,aliyyu kuma?" Bibi ta tambaya zuciyarta na fatan Allah yasa abinda take hasashe ne "Eh aliyyu.....jiya dare ne yayi,naso kiranki na gaya miki abinda ya faru" "Daina yimin kwana kwana ke hamdiyya,me ya faru?" Tana dan jin nauyi ace ta fitowa da ama baro baro abinda ya faru,don haka a sakaye tace "Aliyyun ya sake yiwa aba laifi ne.....don haka yace ya dauki matarsa su bashi gidansa" maganar tadan yiwa bibi sarqaqiya don haka tace "Wanne irin shirmen banza ne wannan?,da aliyyu yayi laifi itama sultanar laifin me tayi da zai hadasu?" Rasa me zata cewa bibi tayi,sai kawai ta miqawa tanja wayar. Tanja na dariya ta karba ta saka wayar a kunennta tana gaida bibi "Dakata da gaisuwar nan......nasan iya shegen aliyyu da kafirin taurin kai da zuciyarsa,sun bashi marainiyar Allah Allah yasa ba wata uban yake mata ba ta kirani da safe tana min kuka......tanja gayamin wanne laifi aliyyu ya sake yiwa hamidou ya koreshi?" Dariya kaman tanja tayi me,ta dakatar da ita da qyar saboda masifa da bibi ta fara "Ki kwantar da hankalinki bibi,kawai aliyyun naki ya rantse ba zaki bar duniya ba sai kinga 'ya'yansa da sultana turmus......juna biyu aka samu,kun samu qaruwa ko kuma ince mun samu qaruwa" qirji bibi ta dafe tana zaro idanu waje,saidai kuma fuskarta lullube take da murmushin data jima batayi irinsa ba "Saboda ma'aiki tanja?,kada kisa na biya miki umara fa a banza?" "Bibi na taba yi miki irin wannan wasan?" Tunda tanja take da bibi bata taba jinta tana guda ba,yau sai ga bibin ta taqarqare tana zankada guda. Khadeeja dake zaune a gefe batasan meke faruwa ba tayi sakato tana kallon bibi "Dan halak kenan.....ah.....ai nasan za'a rina,ina idanun wannan tsohon nasa wanda yayi gadon kafirin taurin kai a wajensa,yanxu ya yarda da cewa ja'irin yaro ya haifa ko wanda ya fishi kafiya da iya shege" kalaman sunyi matuqar bawa ama da tanja dariya,don ama ma juyawa tayi tana barin kitchen din,don tasan bibi yanxun nan zata baro maganar da zata kasa hada ido da tanja idan batayi wasa ba "To amma banda ja'iri ne me juna biyu meye zakayi mata da farar safiya haka ka sakata kuka?, bayan lallashi take buqata?,bari na kira ja'irin naji" bibi ta fadi cikin zumudi tana katse kiran. "Kamomin yayanku haidar maza maza hadeeza". Itadai khadeeja nata cika aiki,haka ta maida akalar nemanta number maina da bibi tayi saving da ALIYYU PARIS. Sosai iskar wajen ke masa dadi tana kuma ratsa dukka qofofin shan iska dake jikinsa. Yawan furanni da koreyen tsirrai dake wajen ya sake sakawa zuciyarsa tayi fresh. Zamantowarsa likita daya jibanci abinda ya shafi fannin zuciya yasa yake da hanyoyin da zai samawa zuciyarsa yanayin da zai iya bashi nishadi har zuwa qarshen wuni. Duk yadda ya kebe kansa daga gareta don ya samu cika alwashin da ya dauka kansa a kanta hakan bai hana zuciyarsa jinta cikin matsanancin kewarta ba. Iya qamshinta kadai yakan haifarwa da zuciyarsa wani mummunan tabo,duk sanda zaya kalleta sai ta yiwa zuciyarsa illa,baisan adadi ba......baisan girma da nauyin mizanin son da yakeyi mata ba. Sassanyan sarewar dake a mazaunin ring tone na wayarsa ta fara busawa. Yana shirin dagawa matashin da isowarsa qofar gidan kenan ya soma neman izinin shigowa yar harabar gidan. Da hannu maina ya masa nuni,sai ya cire sakatar yana qarasowa cikin nutsuwa. Hankalinsa nakan duba number waye yayi kiransa matashin ya qaraso. Baqin fata ne da zaiyi wuya ya wuce mallakin qasata Nigeria,saidai ko a idanu baiyi kama da matasan hausa fulani ko kanuri ba. Tsaf tsaf yake cikin shigar qananun kaya,tun daga nesa kadan ya fidda takalman qafarsa,yana goye da jaka ya qaraso inda maina yake. Abdulhamid kenan,dan asalin qabilar igala dake aikin kula da gidan gaba daya,duk bayan kwana biyu shike zuwa ya gyare gidan gaba daya banda bedroom dinsan nan qwaya daya tak,shike kula da dukka shukoki da furannin da suka qawata harabar gidan kowacce rana. Da harshen turanci ya fara gaida maina,cikin qasan zuciyarsa yana murnar ganin ubangidan nasa da alama a nan ya kwana. Cike da mutunta dan adam ya amsa masa "Ka fara da gyara nan harabar,idan ka gama kayimin magana nayi maka iso ciki don yanzun akwai matan aure a ciki......" Fara'ar abdulhamid ya qaru,yanason ya tambayi maina "Oga kayi aure ne?" Amma kuma yana tsoron tambayar,tunda yasan halinsa sarai, mutum ne da baya jurar shishshigi. A girmame ya amsa masa yana miqewa don kama aikinsa,daidai nan kiran bibi ya sake shigowa a karo na uku kenan bayan kiran farko datayi masa "Wannan tsohuwar Allah yasa dai lafiya" ya fadi can qasa yana motsa labbansa tare da gyara zamansa yana daga wayar. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 130 "aliyyu kana ina?" Itace tambayar da bibi ta fara jefa masa tana wani hade rai "Ina gidana mana" ya bata amsa calmly. "Eh ai na sani basai ka gayamin ba, yarinyar mutane da aka baka amana fa ka barta a daki tana kuka?" Yadda take maganar cikin haqiqancewa sai ya bashi dariya,yadan saki murmushi me qaramin sauti yana miqe qafafunsa saman table "Me haidar yayi mata?,banda soyayyarsa da tayi mata mugun kamu kuma taqi barin zuciyarta ta bayyana hakan?,ki gaya mata ita zuciya ba'a tilastata ta boye soyayyar wanda takeso" ya fadi maganar hankalinsa kwance "Iyeee......ni kake bawa wannan saqon?" Kafadunsa dukka biyu ya daga yana dariya "Bani nakar zomon ba,rataya aka bani......kawai ki tuna mata dukka 'ya'ya mazan da suka fito da tsatsonki zafafa ne.......mace bata iya kubcewa soyayyarsu......idan ta manta soyayyar aba da ama ki tuna mata" "La'ilaha illallahu........aliyyu wai ni kake gayawa magana haka kanka tsaye?,......aliyyu ko kasha wani abunne?" Dariya ta kusa qwace masa,yanason yayi maganin bibi ne gaba daya kuma hankali kwance,don bayason taci gaba da saka baki cikin harkar gidansa,kada a samu akasi wannan tsohuwar soyayyar da takewa sultana ta janyo ta dinga bin bayanta koda kuwa kuskure ta aikata. "Ba abinda nasha sai giyar soyayya.....bibi ita zanci gaba da sha.....amma shawara bibi,indai bakison ki jini cikin mayen soyayya irin haka.....ta daina kawo miki qarar maina kina kiranshi kai tsaye haka" "Haidar?,eh lallai,biri yayi kama da mutum" bibi ta fada tana tafa hannu kaman yana gabanta "Wallahi bata inda sukayi kama bibi,dadinta dai wannan cikin tana nesa bare kice aje a zubar?" "....aliyyu ai tun ba yau ba nasan tatacce ne kai.......amma zakasan ni ka kwarewa baya,inacan ina hanqilo a kanka na tsaya maka saboda 'yancinka ni ashe ka yimin tanadin cin mutunci" bibi ta fadi cikin jajjabi. Wannan karon siririn sautin dariyarsa kasa boyuwa yayi,ya saki dariyar yana cewa "Ba za'a yi haka ba.......kawai shawara na baki bibi ta ta kaina..... Ke kika yimin silar samun wannan alkahirin fa?,duk da dai ba don Allah kikayi ba..... wai kina tsoron kada na yiwa jikarki fyade .....bakisan alkhairi zai zame mata ba" "Kaci ubanka maina......ubanka nace.......zaka tashi a wajen kaje ka dubo yarinya tana can tana sharban kuka ko sai na ragargaje maka kai dan kusun uwa?" Ta fada cikin hargagi ganin xai kwance mata zani a kasuwa,zai tado tsohon zance. Dariya ya saki sosai wannan karon harda duqawa,ko a ina zata ganshi har ta ragargaje masa kan kamar gaske,matar da qarfin arziqi bai isheta ba. "Naji me ran qarfe" "Da ubanka hamidou kake dan baqinciki,yanxu muka fara rayuwa a duniya" tana kaiwa nan ta kashe kiran. Sosai ya sake darawa da maganar bibi, wai matar data doshi shekara tamanin da wani abu ita ke zancan yanzu suka fara rayuwa. Itama yasan halinta,dole ne ya biyo mata ta bayan gida sannan zai barta ta sarara,idan ba haka ba ya sani tsaf zata buwayeshi ta zuge masa matar da yake ganin ya fara dorata bisa saiti. Hankalinsa kuma sai yayi dakin,to kukan meye takeyi?,duk wani motsinsa a wajen tana ransa,rana yake so tadan sake dagawa ko zuwa yammaci ya sanyata ta shirya,akwai guraren da yakeso suje a yau din. Tsaye yayi a bakin qofa yana qare mata kallo,duk wani yanayin jikinta ya nuna emotion na zuciyarta. Boyayyen murmushi ya saki,koda batayi kowanne action ba yayi imani hug take da buqata,ya gani cikin qwayar idanunta,dukka nutsuwarta tana neman barin gangar jikinta "Allah ka tabbatar da ita a haka .....indai hakan ta kasance wannan juna biyun ya sake xame min Alkahiri kan alkhairi" ya furta a zuciyarsa. Sallama yayi qasan maqoshinsa,wadda tana jin sautinsa ta waiwayo da sauri,suka hada ido ta kauda kai tana gyara kwanciyarta gami da bawa qofa baya. Batason yaga hawayenta bare ya zargi wani abu. Ya sake sakin murmushin kallonki kawai nakeyi,ya taka ya isa gaban gadon inda ta juyar da fuskarta. A nutse ya tsugunna a gabanta fuskarta data dan yi ja taba bayyana tarwai cikin idanunsa. Ya tsareta da ido yana kallon zara zaran eyelashes dinta data kulle idanunta taqi yarda ta kalleshi. Kowanne sashe na jikinsa yana muradinta, zuciyarsa kuma na sake narkewa cikin soyayyarta. Gyaran murya yayi yana dan hade rai sannan yace "Kukan me kikeyi?,me akayi miki?,idan yunwa kikeji sai sakiyi magana ko?,baki zauna kuka ba.....mema nayi miki?" Jin tambayar tasa tayi kamar wani rainin wayo ne da zallar gatse,tana ganin ya kamata yayi mata abinda ya kamata ba har sai taji damuwa akan haka ba, zuciyarta taso hasala amma wani sashen na zuciyarta yace da ita "Ke kikace ya nisanceki.....bakison kusancin dake tsakaninku,duk da haka ma ya sammiki dumin jikinsa wanda dashi kikayi bacci,yanxun kuma me zaya yi miki bayan ya tabbatar kin qoshi?". A shurun daya gilma tsakaninsu wayarsa ta dauki wani qarar kiran. Koda ya duba sai yaga ama ce "Ya salam" ya furta a fili,abinda ya sanyata bude idanunta ta watsa a kansa gabanta yana faduwa,don zuciyar tuni ta raya mata wannan yarinyar LAILA ita ke kiransa,waya sani ma fitan da yayi da zaman da yayi a waje ba tare daya dawo ba ko yana can suna waya ne kaman jiya?. Idonsa ya nutsar sosai cikin nata,ya motsa jajayen labbansa yana furta "Qarata kika kakkai wajen al'umma?" Ya qarashe maganar yana dage mata girarshi dukka biyun. Ya riga ya gama luguguitata zuciyarta ya kuma karyata da salon kallon da yake jifanta dashi,batasan ya akayi ba, cikin narkewa da salon karyewar da take masa magana shekarun baya can sanda tana little sultana dinta ta girgiza masa kai tana turo lebanta na qasa. Lips din yabi da kallo yana jin kaman ya kamashi ya tsotse saboda yadda ya bashi sha'awa,amma kuma sai ya fuske,yana jiran ranar da zatasan muhimmancin haduwar jikkunansu guri guda qarqashin umarni da kulawar zukatansu da kuma soyayyarsu. Wayarsa kawai ya daga yana nuna mata screen din. Taga sunan ama itama,sai taji dukka ba dadi,bai kamata a irin wanna lokacin daga tahowarta jiya ace sun wayi gari haka ba. Ta tsurawa wayar idanu yayin da shi kuma ita ya tsurawa nashi idanun,sainya saki wayar ya aje mata kawai a gabanta,murya can qasa yace "Pick" tada kanta tayi sosai saman pillows data jera,saita miqa hannu ta dauki wayar ta daga sannan ta kara a kunnenta. Sosai ta sakawa ranta wani irin dakiya da juriya. Suka gaisa da ama tanata qoqarin controlling voice dinta da mode dinta "Hope komai lafiya ko?" Ama ta tambaya daga qarshe jin batace komai ba,hakanan muryarta fresh na wani alamun kuka ko wani abu "Lafiya qalau ama" "To ma sha Allah" ta amsa mata tana jin dadin amsar data bata "Bashi wayar" aman ta fada. Daga wayar tayi daga kunnenta ta miqa masa wayar,ya hada da hannunta ya riqe tsam sannan ya miqe daga tsugunnon da yayi ya koma soman gadon har kafadunta suna gogar nashi,sannan ya sanya daya hannun ya zare wayar ba tare daya saki hannun nata ba,ya hada tafukan hannunsu ya game waje guda yana amsa kiran ama. A tausashe yake gaida ama din,itama ta amsa masa cikin kulawa,bata iya jin me take gaya masa,amma da to kawai yake amsa mata,gefe daya yana murza tafin hannunsa cikin nata abinda yake sake luguguita zuciyarta da gangar jikinta kenan,yake sake haifar mata da kasala,take kuma jin tana buqatar wani abu da zai lullubeta ya zame mata garkuwa. Waiwayowa yayi ya kafeta da idanu bayan ya gama amsa wayar "Ta yaya uncle haidar zai baki skin contact da rana?,idan ba jaraba irin ta sultana ba?" Yayi maganar yana wani tsare gida,bayan shi kansa jikinsa yana da buqatar kusanci irin na jiya. Tabbas banda kwarjinin da yayi mata,banda ido daya cika mata ba abinda zata huce dashi irin ta kama lallausan gashinsa taja da kyau yadda zaiji zafi har kwanyarsa. Yanzun itace jarababbiya?,to ai a samu jarababbiya tsakanin ita dashi,shi da tsabar maitarsa take iya karantar sirrin dake kwance qasan zuciyarta?. Dukka qarfinta ta tattara ta saka hannunta zata tureshi,saidai dukka hannayenta ya kama din,ya jata a jikinsa yana bata kyakkyawan dumin jikin da ya tabbatar zai bata cikakkiyar nutsuwa. Sannu a hankali duk ita dashi sai dukayi collapse,kamar kowanne lokaci irin wannan bugun zukatansu sai suka zama kamar abokan hirarsu. *_B A Y A N A W A N N I_* Kusan mintuna aqalla goma da yayi zaune cikin motar yana jiranta ko sau daya bai dauke idanunsa daga bakin qofar ba. A hankali ta sake bude qofar ta fito a karo na biyar,fuskarta a hade bacin rai yana dan bayyana kanshi da qananun fushi. Tun daga yatsan qafarta ya fara qare mata kallo har zuwa girarta. Wannan shine shiga ta biyar da tayi yana maidata. Duk shigar da tayi idan ta fito sai yaga tayi masa wani mahaukacin kyau,tamkar a ranar ya fara ganinta,kamar kuma a ranar ya fara sonta. Tunda take shiga tana fita ba abinda zuciyarsa ke nanata mamaki a kai. Wai sultanarshi ce wannan?,me wani irin zubabben kamala da nutsuwa me cakude da kwarjini me matuqar yawa saman fuskarta. Duk yadda kakai ga jin isa idan ta tunkaroka sai kaji wani irin kwarjini ya dakeka..... sultanar da dukkansu a baya ke tsoron zamowarta wata mace ta daban saboda yadda suka qulla alaqa da zumunci me kyau da hotel hotel da guraren sharholiyar biki da birthday "Tabbas likulli ajalin kitab" ya fadi a ransa sanda tazo dab da motar "Wannan fa?" Ta fada tana turo baki,don batason saita shiga sannan y sake fiddota. Sake binta da kallon qwaqwafi yayi from head to toe,a cikin jikinta har sai da taji kallon yayi yawa. "La ba'as..... amma dai.....is okay" ya fada yana dage kafadunsa. Tanata tura baki ta bude gidan gaba ta shige,saita dauke kanta dukka gefe ta maida bangaren window. Tanata jira taji ya tada mota shuru sammakal,har sai data gaji da sauraro ta waiwayo sashensa. Ashe kwantar da kujerar yayi abinsa ma yanata danne danne a waya. Ido duka hada ya matse fuskarsa don ya fahimci me takeson tambaya "You know what?,......ba driver kika dauko ba da zaki zauna kina juyan qeya......if kin shirya tafiya ki gyara zamanki dai dai da yadda kowa yakeyi,Si vous n'êtes pas prêt à partir, cela ne me dérange pas de rester ici(idan baki shirya tafiya ba ni bazan damu muyita zama a nan ba)" "Wai Allah na" ta fada qasan zuciyarta,mulkin mallakarshi yayi yawa,hatta da zama ma sai wanda ya aminta dashi zatayi?,ya Allah" ta sake fada tana fitar da numfashi. Dole ta motsa,ta gyara zaman nata tana bada attention dinta cikin motar. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 131 Boyayyen murmushi ya saki,yana tausaya mata ne kawai,saboda kowanne minti da second soyayyarshi yayi imani tana ninkuwa ne cikin ranta,kuma zatakai matakin da nan gaba sai ta yiwa kowanne sashe na jiki da zuciyarta illa,don ita soyayya ba'a hanata fidda kanta daga zuciya. Wani slow music ya saka musu,daya daga cikin waqoqin wani shararren mawaqi dan qasar France. Cikin waqoqin da take mutuwar so a shekarun baya,waqan daya sanya saita dinga tuna mata quruciyarta,ta dinga tuna mata wani moment daya dade da shudewa,ta rufe idanunta kuma tana tuna abubuwa masu yawa da suka shude cikin rayuwarta. Bata bude idonta ba har sai da taji ya kashe motar. Ta bude idanunta a hankali tana duban wajen. Asibitinsu ne ya kawota,daya daga cikin private hospital na musamman a garin. Kamar kowanne lokaci shi ya bude mata qofar,yakuma bata hannunshi,dole ta aza nata akai,ya hadesu guri daya yana tallafe da hannun har ta fito ya rufe motar suka jera zuwa ciki. Duk inda suka gifta sai sun dauki hankula,shi din sanannen likita ne cikin asibitin,don shine shugaban likitocin dukka asibitin gaba daya,amma ganinsa da kyakkyawar mace kaman sultana yaja masa wani kallon na daban. Kowa ya sani turawa mutanene da basu iya munafurci ko boye abinda ya burgesu ba,cikin reception haka nurses ma'aikatan gurin suka dinga gaidashi suna kuma tambayar wacece?. Kai tsaye yake amsa musu matarsa ce,suka dinga kodasu suna sha'awar hadin,har zuwa sanda ya isa bakin wata qofa dake dauke da sunan mamallakiyar office din,har a lokacin kuma yana riqe da hannunta tsam kamar za'a qwaceta. Knocking kawai yayi aka bashi izinin shiga,ya Murda handle din ya bawa sultanan dama ta fara shiga sannan yabi bayanta. Babbar macace farar fata,wadda a qalla ta kusa shekara hamsin. Kamila ce sosai,kana kallonta kuma zakasan cewa musulma ce,don ta nannade kanta da scarf ba'a iya ganin gashinta. Fuskarta ta wadata da murmushi tana yiwa maina sannu da shigowa,da alama akwai fahimtar juna da sabo sosai tsakaninsu. Dr Camille tadan miqe tana dubansa,cikin tataccen faransancinta ta kasa shuru idanunta tsakanin fuskar maina dana sultana tace "Yar uwarka ka kawomin ne Dr?" Tayi maganar cikin fara'a. Juyawa yayi kadan yana murmushi shima ya kali sultana,sai kuma ya dawo da dubansa kan Dr Camille "Yata qanwata kuma matata" idanu sultana tadan rufe kadan tana bitar adadin sunayen da ya bata dukka ita kadai. Dr tadan saki dariya tana gyara ma sultana kujera "Da gaske Dr?,ashe kai din me iyali ne?,amma kuna tsananin kama Dr.....tunda naji kace diyarka kuma qanwarka na tabbatar auren zumunci ne,haka ne?" Murmushi ya kuma saki,dr Camille ce kaf asibitin suke hira irin haka,itama yana mata kallo ne kaman na ama,saboda tana da tsananin kamun kai da kirki na gaske,sa'annan ita din ba yarinya bace "Haka ne Dr" "Duk family dinku masu kyau ne Dr da alama, za'a samu kuma kyawawan 'ya'ya sosai madam" ta qarasa maganar still tana murmushi tana kuma kallon sultana. Murmushi tayi qoqarin kawowa saman fuskarta,hakanan taji matar ta kwanta mata,bata da hayaniya tana kuma da tsananin kula da alama. Yadda ya tsareta da ido yanason yaji amsar da zata bawa Dr Camille ya sanyata jin nauyi,saita kauda kanta kawai ba tare data amsa din ba. Sai daya zauna a kujerarsa sannan ya sake mata hannu,ta damqe hannun nata tana jin dumin jikinsa har yanzu yana ratsata, hakanan tafin hannun nata ya wadata da qamshinsa. Hira kadan duka taba sanann ya maida nutsuwarsa yana yiwa Dr Camille bayani "Na kawota ne a dubamin ita da kyau......Dr inason tayi register dake,ke kadai na yarda ki dinga dubamin lafiyarta......ina tsananin sonta.....ina kuma tsananin qaunar abinda yake jikinta......don Allah Dr ki basu dukkan kulawa da ya kamata.....su din rayuwata ne" ya qarashe maganar yana dan rusunar da idanunsa. Wani murmushi Dr Camille ta saki,tana jin maina din yana burgeta,da gaske bata taba tsammanin mutanen Africa sun iya soyayya can can har haka ba,idanunsa kadai sun gaya mata gaskiyar abinda yake cikin zuciyarsa yake gaya mata. "Na tayaka murna Dr da samun qaruwa,in sha Allah zan bata dukka kulawar data dace........madam" ta furta tana duban sultana "Ina tayaki murna da samun miji kamar Dr maina.......shi din nagartaccen mutum ne da muke matuqar alfahari da shi" dan murmushi ta yiwa dr Camille tace "Na gode". A nan ya zauna cikin office din,ya kasa ya tsare yana kallon yadda Dr Camille ke gudanar da gwaje gwajenta. Sultana kamar ta fasa ihu saboda yadda suka tsareta da bincike,duba wannan duba wancan,binciken qwaqwafi har sai data gaji kafin a kammala. Tana jin sanda Dr Camille ke masa bayani filla filla cikin yanayin bayanansu na likitoci yadda zai fahimta. Shi kuma ya tattara dukka nutsuwarsa akan Dr Camille yana sauraronta. "Wata nawa ne cikin?" Yayi ma Dr tambayar da yafi matsuwa yaji amsarta "Sati goma......" Ajiyar zuciya ya saki yana fadin "Kenan akwai sauran jira kafin na hadu da little angel dina?" Murmushi ya qwacewa Dr Camille,kulawarsa akan sultana da cikin yayi yawaa "Amma fa bamu gama dubata ba,don akwai abinda na gani cikin scanning da nayi mata,inason cikin ya qara nisa kamar ya shiga sati takwas haka sai mu sake dubawa" idanu yadan fitar waje "Da matsala ne?" Murmushi ta sakeyi "Ba matsala sai alkhairi" ajiyar zuciya ya fitar "Shikenan,godiya nakeyi' "Ba wannan a tsakaninmu" ta amsa masa tana miqa masa folder din sultanar da aka bude da bayanan komai da komai a ciki,sannan ta juya ga sultana "Duk idan kikaji wani abu,ko kina da wata matsala karki ji nauyin kirana ki sanar min,zan iskeki a duk inda nake in sha Allah" "Na gode Dr" ta amsa mata,har cikin ranta taji dadin yadda tayi matan,ta karramata qwarai ta kuma nuna mata damuwarta a kanta. Sai daya dage dukka gilasan motar ya kunna ac a madaidaicin sanyi sannan ya juyo gaba daya yana zube mata idanunshin nan dake mata nauyi yanxu "Me dame kike buqata?,me kike son ci?,me kike sha'awa?" Ya jera mata dukka tambayar. A yanxun babban burinsa shine ya bata kulawar da ba kowacce 'ya mace ta samu gatanta ba,yana jin wani qaqqarfan abu a kanta,yana jin wata soyayya ta daban game da ita da abinda yake cikinta. Shuru ta danyi,duk kuwa da cewa akwai abubuwan da taji tana sha'awa da yawa. "Ba komai" ta fada qasa qasa tana lanqwasa yatsun hannunta. Idanunsa ya janye daga kanta yana dan lumshesu "You are a liar" ya furta qasa qasa yana qoqarin tayar da motar. Guri guri ya dinga kaita,guraren cin abinci da saida kayan maqulashe da kwadayi iri daban daban. Duk iya yawonta a Paris duk kuma iya qwarewar goumar a paris basu taba yawo irin hakan nan ba. Can qasan ranta ta dinga ji zuciyarta tana sakewa,amma kuma tana dakewa a saman fuskarta. Duk sanda ya kalli fuskarta sai dariya tazo masa,saboda yasan fake reaction ne,real one din yana danqare saman zuciyarta. Tana sane ta dinga wasa da hankalinsa,duk inda sukaje sai tace wajen ko abincin waje baiyi mata ba,dariya ta dinga bashi,ya sani tana sane,ta kuma shiryawa hakanne,saidai abinda ita bata sani ba shi ya fita shiryawa,don haka ya dinga canza mata guri,har suka iso daya daga cikin manyan guraren cin abinci dake anguwar. A qalla an zube mata kalolin abinci da na kwadayi sun kusa guda ashirin. Yanayi na ciki ya taso mata,sai idanunta suka rufe,shaf tama wani manta da maina dake wajen,ta dinga jaye jayen bowl da plates. Ci wannan ci wancan har sai data ji komai yana neman fita a kanta sannan ta dawo hayyacinta. Tana ajjiye spoon ta tuna ashe yana zaune opposite dinta. Wannan ya sanyata daga kai da sauri don taga shin ita yake kallo?. Motsinta qwaya tak ya gaya masa abinda zatayi kafin takai ga kallon nasa,don haka tun kafin idanunta ya sauka a kanshi ya daga magazine da ya sanya suka bashi ya rufe idanunsa. Boyayyar ajiyar zuciya ta saki tana jin dadi,ashe ma ba ita yake kalla ba,don haka saita goge bakinta da tissue ta kuma ja rai ta hade tsam tana kallonshi qasa qasa. Ta sama yake kallonta ba tare data lura ba,sai ya maida magazine din ya ajiye ganin ta gama ya miqe yana fadin "Let's go". Ta zaci gida zaya kaita amma sai taga ya wuce wasu guraren da ita. Classes yaje ya mata register na rainon ciki,da kuma matan dake zuwa har gida su duba yadda lafiyarki da tsaftarki da kuma yanayin yadda kike rainon cikinki yake gudana. Ita kanta abun sai ya fara bata mamaki,damuwar da kulawar da yake bawa cikin kamar yaso ya wuce iyaka. Daga can kuma still sai suka koma yawon park,guda biyu kawai sukaje tace masa ta gaji. Gurare ne da suka qayatar da ita,suka kuma bata kyakkyawar iska da yanayi me kyau,suka dinga tayar da wasu matattun abubuwa dake zuciyarta,basu bar wajen ba sai ana dab da shigar loton sallar magariba. Bashi kadai da yake driving din ba.....hatta ita dake zaune a gefe tana jin yadda jikinta ke amsawa da gajiyar yawon da sukayi idanunta yaga abinda ke tsaye qofar gidansu. Full light ya saka,abinda ya sake nuna musu ita tarwai kaman da rana. Ayana ce zaune saman wata concrete chair dake opposite da gidan nasu. Tana sanye da wasu English wears da warakin hijabin da iyakarsa kafadunta. Daga qasa kuma a gefanta kwando ne me kyau lullube da wani farin yanki,hannunta riqe da wayarta tana dannawa,amma kuma motar data yi mata full light ya santa daga kanta da sauri tana kare fuskarta da hannunta. Wani abune daya tsaya mata a wuya a tsahon xaman jiran dawowarsun da takeyi ya sauka xuwa cikin cikinta sanda ta fahimci motarshi ke shigowa layin. Ta miqe a hankali tana goye hannuwanta a qirji tana jiran isowarsa,wani zazzafan kishi yana tafasa zuciyarta don ta tabbatar duk tsahon awannin da tayi tana jiransu yana tare da ita ne........tunaninta guda daya.....yadda zata karya wannan katangar me danqo ta rugurguzata ta kuma kafa tata gwamnatin......... _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 132 Ci gaba tayi da bibiyarsu da idanu har zuwa sanda ya isa cikin gargajiyar gidan da motar,ya kasheta yana cire seatbelts din jikinsa. Juyawa yayi yana qoqarin kallon fuskarta don yayi imani taga abinda ya gani shima,saidai taqi juyowa bare su hada idanu,ya miqa hannu yana qoqarin cire mata seatbelt din,sai ta rigashi,ta sanya hannu ta zareta,ta kuma bude murfin motar ta zura qafafunta tana fita daga motar adan gaggauce. Daidai sanda ayana ke shigowa dauke da kwandon,akan idanunta sultanan ta fito,ta kuma tsaya gaban qofar mashigar gidan tana rungume da hannayenta ta kuma basu baya. Shu'umin murmushi murmushi ta saki tana kallon bayan sultana din,tanaso ko sau daya ko iya yau kawai ta cusa mata haushin da zata kasa cikakken bacci,kaman yadda takejin zuciyarta cikin qunci duk sanda ta tuna maina yana tare da wata,aliyyun da take matuqar so yana tare da wata mace. "Yayaaa" ta furta tana dan daga muryarta a shagwabe kamar qaramar yarinya harda karya wuya. Bai barta ta qaraso ba ya rufe motar yana dauke kanshi daga kanta,idanunsa akan key din da ya sanya yana kulle motar sannan ya fito daga wajen. Kallo daya yayi mata duk wani rawar kai da karsashinta ya zagwanye. A yau fuskarsa tana tuna mata ainihin fuskar aliyyun da tasha jin daddy dinta yana fada lokaci bayan lokaci. Fuskar da bai taba gwada mata ita ba saboda darajar ama da kuma uncle tahir da suke dashi a idanunsa,kuma baya ganin ta tsallake limit,amma zuwa yanzun ya karanci abun kamar gaba gaba yakeyi. "Me kikeyi a nan din da daren nan?,waye ya baki adress?" Ya jefa mata tambayar yana zura hannayensa a aljihun wandonsa. Tambayar daya tsaya ma ayana din sai sultanar taji kaman ta muzanta,tana tsaye ne tana jiransa ya bude mata qofa,amma saboda bayason ranta ya baci kenan shine ya tsaya ya fara ji da ita?. Dan siririn murmushi ta saki tana kallon kwandon hannunta "Banda abun yaa maina.....jini wasa ne?, goumar ya kawoni,naxo kawo maka abincin dare ne wanda muka dafa ni da ama" tsaiwarsa ya gyara,ya fahimci abubuwa da yawa cikin idanunta "Ama din ce tace ki kawo ko kuma ra'ayin kanki?" "Ra'ayin mu nida ama" ta fada tana kuma sakin murmushi,don bataso a yadda ta juya bayan ta zaci ba maganar lumana yake mata ba "Yayi,kawo ki wuce gida dare yana qara yi" "Goumar yace zai dawo ya daukeni" ta amsa masa da sauri,don tana burin shiga cikin gidan taga meye da meye a ciki. Tabbas ita shaida ce maina ya hadu,tayi imanin komai daya shafeshi din zai kasance na musamman,ta yaya zata bari wannan damar ta kubce mata?. Bayason tsawaita magana da ita,ga sultana da yake da tabbacin ta gaji,don haka ya taka zuwa gaban gidan,wannan ya bata daman binsa tana karadin yabon gidan. Gefe ta matsa masa wajen da zai sanya key din tana kauda kanta gefe. Yadan dubeta shima saiya kauda kanshi don yadda yaga fuskarta yasan ta qulu ne. Ya bude qofar yana tura mata ita yadda zata shiga,saita waiwayo dukanta tana duban bayanta. Fes ta zubewa ayana fararen idanunta masu kyau da daukan hankali,cikin wani nutsuwa kuma ta miqa mata hannunta tana fadin "Ki yiwa ama godiya da ban gajiya......ki kawo basket din kina iya juyawa daga haka". Baisan sanda yaja da baya yana zuqar wata iska yana fesarwa ba. Zai iya cewa ya dauki shekaru masu tsaho baiga abinda ya burgeshi irin wannan salon nata na yau ba,ji yakeyi kaman zai narke a wajen,yau shine sultana ta birkice haka cikin qasa da mintuna a kanshi?. "Dukkanmu mun gaji kuma hutawa muke da buqata" ta qara mata da bayanin ganin ta xube mata itama idanu tamkar bata da niyyar bata kwandon. Maina ayana ta kalla,sai ya dage dukka kafadunsa alamun ba ruwanshi,yana nufin kenan ya goyi bayan matarsa?,ya goyi bayan abinda tace?. Kafin ta dawo daga wannan radadin horn din motar goumar da yake a fusace kan sakashi fitowanbda tayi a daren da shegen nacinta ya cika wajen,a matuqar sanyaye ta miqa mata kwandon ta kuma sauka da dan sassarfa tana barin qofar gidan,yayin da sultana ta karba tana kuma takawa a nutse ta shige falon tana jin wata izza tana ratsata gami da wani qarfin zuciya tare da alfahari. Tana isa falon ta dire kwandon,taja wani mugun tsaki kamar zata cire harshenta, zuciyarta na mata zafi sosai. Ta fita daga harkar ayana,ta baro musu gidansu amma ba zata barta tayi jinya ta raini cikinta cikin salama ba?,da wannan bacin ran ta wuce bedroom ko tsayawa ta gaisa da goumar batayi ba. Bacin rai fal zuciyarta ta maida qofar ta saka key don batason ma ya shigo yaga wani sauyi tattare da ita. Ta soma zare kayanta da takeji sun isheta,har yanzu ranta yana suya,ta shiga bandaki ta tara ruwa ta shige bathtub. Tana ta jin knocking dinsa har ta gama wankan ta fito. Sanda tana shiryawa dinma taji knocking dinsa,amma ta basar kaman bata ciki. A nutse ta gama shiryawa cikin tattausan kayan bacci riga da wando masu gajeran hannu,saidai kuma sun sauko sun rufe mata jikinta sosai. Yunwa takeji kaman kaman me amma kuma batason bude qofar. Qaramin tsaki taja,abinda takeji a zuciyarta tafi tunanin mode swing ne kawai ke damunta irin na ciki,ba zata ce ba don ba zata iya tantance komai ba akan cikinsu benazeer. Cikine da yazo mata da wata irin wahala da damuwa da bazata taba mancewa da ita ba. Cikinta ta shafa tana sake jin ba komai a ciki. Knocking ta kuma ji yayi amma sai tayi biris,da gaske haushinsa takeji sosai,duk da bata da wani dalili da zata bayar akan hakan. Wayarta dake gefe ce ta fara haske,ta waiwaya tana dubanta,kamar kada ta daga sai kuma ta miqa hannu ta daga ta sanya wayar a kunnenta "Idan kika sake na sake knocking qofar nan sai ranki yayi mummunan baci" ya furta da husky voice dinsan nan dake da ban tsoro a yawancin lokuta. Rau rau tayi sai kuma ta ajiye wayar,ta miqe tana nufar qofar ba tare data damu da lullube kanta ba. A hankali taja qofar baya,sai ta maqale a bayan qofar kaman yaron da ya yiwa mamanshi rashin gaskiya. Wayace a kunnensa wadda yanzun akayi kiransa,sunan sardauna kuma daya kira ya bata tabbacin dashi suke wayar. Idanu ya watsa mata sannan ya qarasa shigowa da kwanukan abinci,ya qarasa kan qaramin rug din dake dakin ya tsugunna yana fidda komai wayar tana maqale a kunnensa. Sai daya zuba komai kaman yadda ya saba mata sannan ya koma ya zauna,ya sanyata a gaba yana kuma ritsata da idanun nan nashi bayan ya dora qafarsa daya akan daya yana mata magana da idanu. Ta fahimci sarai abinda yake nufi,amma duk sai taji abun bai mata armashi ba,ta zauna tsakiyar rug din ta jawo plate din ta soma juya abincin. Biyu uku taci taji duka bai mata taste ba,ta langabe wuya tanason sakin kuka. Wai me yasa komai nasa yake mata daidai da ra'ayinta?,me yasa komai yayi mata sai taji ya dace da ita?,idan ita tayi kuma sai taji totally wrong?. A jiya da ya kasance shine yake bata abincin sai taji yafi tafiya yadda ya kamata,yafi kuma dadi taste dinsa ya banbanta da wannan,amma a yanzun da takeci da nata hannun komai ma baiyi mata ba,anya kuwa ba sihiri ya fara ta'ammali dashi ba?,ta yiwa kanta da kanta tambayar da tasan hasashe ne kawai mara dalili. Duk sanda ta tsaya sai ya kafeta da idanunsa,dole haka ta dinga qoqarin ci har sai da ya tabbatar iya abinda zata iya ci kenan. Wayar ya kashe ya saka a aljihu,sannan ya zamo a hankali ya tattara kwanukan ya fice dasu. Ci gaba tayi da zama a wajen ba tare data motsa ba,tsoron tafiya ma takeyi ta kwanta gaba daya,don ta tabbatar a yadda wata irin kasala ke lullubeta zaiyi wahala bataji tana buqatar wannan hugging nasa dake bata wata irin nutsuwa ba. Cikin ranta ta samu kanta da tuhumar "Me yakeyi bai shigo dakin ba har yanzu?" Tana duban agogo,a qalla ta share mintuna kusan talatin a zaune,dole ta qarfafa jikinta ta wuce zuwa gado tana rage hasken wutar dakin tare da laluben me zatayi da zai dauke mata kewa?. Komai ta dauko sai taji baiyi mata ba,kaman jiya duk idanunta kunnuwanta nutsuwarta da motsin da duk zataji tana bibiye dashi. At last ta yaye bargon,tana jin maqoshinta ya bushe,ruwa take da buqata me sanyi kadan. Ta laluba inda ya saba aje mata ruwa tsakanin jiya da yau ba komai wajen, zuciyarta tadan karaya,sai taji kaman yanason sake ninka halinsa na daina damuwa da al'amuranta. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 133 Kamar me sanda take takowa zuwa falon gidan,hannayenta rungume a qirjinta idanunta kan saitin fridge din tana mamakin ganin cups da ruwa da drink ragowa saman center table din falon. Kaman ta kwashe sai kuma ta fasa tunda bata sani ba ko shine yake amfani dashi don haka kai tsaye ta wuce side din da fridge din yake. Ta bude a nutse tana duba ruwan da baiyi sanyi sosai ba,sai ta dinga jin kaman magana qasa qasa. Ta share tana tsammanin daga waje ne,amma kuma sai ta dinga jin kamar dukka muryoyin biyu ta sansu. Ruwan ta aza saman fridge din ta waiwaya zuwa bakin qofar shigowa falon,saita ganta a bude. Ta danyi mamaki tunda ba al'adarsu bane barin gida a bude,ta fara matsawa a hankali da zummar rufe qofar,amma kuma muryar wadda takeji ta sanya gabanta yankewa yayi mummunan faduwa "Ina sonka......wallahi ina tsananin sonka.....kuma ko yaya ne zan iya zama dakai ya maina..........kaima kuma nasan kana sona......don ba wanda zai dinga respecting abinda baya so" "Laila......." Ya kira sunanta dai dai sanda sultana ta isa bakin qofar. Shi da lailan ne,tsaye suna fuskantar juna saidai kuma akwai tazara tsakaninsu. Dukka jikinta ne ya dauki rawa,ta saki qofar a hankali tana nufin juyawa,saidai kuma garin gaggawar barin wajen hannunta yadan daki qofar,sautin da ya sanyashi juyawa ya ganta amma kafin ya gama ganin nata gaba daya ta bace a wajen. Bai wani kawo abun da komai ba ya maida dubansa ga laila wadda zuwa yanzun ranshi ya soma baci da ita. "Next week zaki wuce Nigeria,wannan umarnina ne kuma umarnin daddy......duk wannan shirmen da kikeyi banason ki kaini bango,ina respecting sardauna......dole nayi respecting naki......ina girmama daddy......dole na girmamaki don ke din jininsa ne" ya qarasa maganar yana kara waya a kunnensa "Sardauna kazo ku tafi......zan kwanta sai da safe" ya fadi duka lokaci daya. "Ba matsala gani a qofar gidan" sardaunan ya amsa masa daidai sanda lailan ke sakin kuka ta kuma nemi wajen zama a wajen. Wayarsa ya jefa aljihu yana komawa cikin gidan,yana kunyar sardauna,bazai iya ci gaba da tsaiwa har sardaunan yazo ya iske qanwarshi a haka ba. Har ya gota fridge din ya ganshi a bude,sai ya koma ya cire ruwa guda daya me sanyi ya rufe fridge din yana mamakin barinsa a buden da akayi. Saman kujera ya koma,ya zauna yana bude murfin gorar ya kafata a bakinsa yana shanye ruwan da sauri da sauri. Tsaf ya gama dashi,yayi wulli da robar yana fidda wani zazzafan numfashi daya gauraya da sanyin bakinsa "AYANA LAILA" a yanzun sune manya manyan matsalarsa.......dukkansu kuma suna da wata martaba a idanunsa da bazai iya wancakali dasu lokaci guda irin yadda ya dace ba,ANYA KUWA BAZAIYI ABINDA YA DACE A KANSU DUKKA SU BIYUN BA?" ya tambayi kansa da kansa. Wani dan gajeran tunani yayi,sai ya girgiza kanshi "BA HARAMUN BANE" ya bawa kansa da kansa amsa,amsar data zaburar dashi ya miqe a hankali yana tuna ta leqo dazu,ta kuma juya da gaggawa,don haka ya miqe yana kashe na'uarorin falon ya wuce zuwa bedroom din. Yadda ya sameta cikin duvet tayi luf sai yayi tsammanin bacci ne ya dauketa,ya zube wayoyinsa ya sake rage hasken dakin,sai ya zare rigarshi ta sama ya shiga toilet yayi alwala. Shafa'i da wuturi yayi sannan ya haa dukka addu'o'insa. Ya jawo wayarsa yana duban numbers dinsu duka su biyun,kamar ya rubuta gajeran saqo ya aika musu,sai kuma ya fasa,ya ajjiye wayar ya kammala shirinsa ya wuce saman gadon. A tausashe ya jawota cikin jikinsa,saidai kuma ta sanya duka hannuwanta biyu ta nesanta kanta dashi. Mamaki yadan kamashi,yayi zaton bacci takeyi,ya sake kamota don bata wannan yanayin daya fuskanci tafi buqata amma ta sake masa hakan. Sautin kukan da yaji ta fashe dashi ya sakashi miqewa yana kunna bedside lamp. "Me haka?,me ya sameki?,ar you okay?" Kamar dama tana jiransa ne,muryarta na rawa saboda uban kukan da tayi tace "Stay away from me!" A kausashe. Idanu ya zuba mata sosai,ranshi yadan motsu "Ki gogeni daga rayuwarki mana idan zaki iya?" "Bazan iya ba but i hate you!,baka da aiki saidai mata su dinga binka har cikin gida?,shin ba zasu iya jira ka fita ba?" Dan yamutse fuska yayi maganarta na bashi mamaki "Bana sonka,kabar rayuwata ta huta" a wannan karon! Yaji dukka wani haquri nasa yakai bango,a wannan karon yaji ya kamata yayi mata me gaba daya!, A wannan lokacin yana jin cewa ya kamata komai yazo qarshe,sai ya soma sauka daga gadon a hankali zuciyarsa na wani irin tafasa,har sai daya kammala sauka gaba daya,sannan ya tsaya sosai a gabanta yana kallonta da dukka idanunsa fes........ _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 134 "Tu m'as dit que tu ne m'aimais pas d'innombrables fois(kin gayamin baki sona sau babu adadi),inajin yanzun ya kamata nayi nesa dake din kaman yadda kika buqata......but zan auri wadanda suke sona......soon in sha Allah" yayi maganar babu hargagi balle fada,saidai kuma shi kadai yasan me yakeji qasan zuciyarsa,meye zaiyi ya burgeta?,me zaiyi da zai sanyaya dukka zuciyarta ta fito masa da zallar soyayyar da taketa boyo qasan zuciyarta?,ya rabu da ita din kaman yadda tace?,ko ya biyo mata ta bayan gida?" Maganganun daya dinga tattaunawa cikin ransa kenan shi daya zaune cikin balcony din gaban gidan. Duk da yadda dare ya tsala amma baiga hakan ba,radadi sosai yakeji cikin zuciyarsa,baya jin bacci kwata kwata a cikin idanunsa,mode swing ne ke damun sultana kamar yadda ama tace?,ko kuma wannan kafaffen halinne daga zuciyarta?,meye ma ya tunzurata haka?. Ya dinga yiwa kanshi tambayar. Peaceful man ne shi,baya qaunar tashin hankali sam,kuma shidin mutum ne da yake buqatar tattaunawa tsakaninsa da duk wani mutum da suke mu'amala,me yasa ba zata fuskanci halinsa ba?,bayan ita din ba baquwar saninsa bace?. Yadda ya dinga juyi a waje haka ta dinga juyi cikin dakin. Yanayin yadda yabar mata dakin salin alin ya dinga nuqurqusar zuciyarta. Wani sashen na zuciyarta yana gaya mata bata kyauta ba......wani sashen kuma yana laluben meye tayi na rashin kyautawa a ciki?. Mutumin da ya jawo mata 'yammata har biyu cikin gidanta na sunna?,ta gama da wata saiga wata?,ta tabbatar yasan da zuwansu,me ya hana ya dakatar dasu?,tunda dai yayi waya da sardauna,tabbacin yasan suna zuwa. Da qyar ya miqe yana komawa cikin gidan saboda wani mugun ciwon mara daya sarqeshi,ga wani zazzabi da yaji yana shirin kamashi,wannan ya sanya ya dinga jin sanyi sosai yana ratsashi har cikin qashinsa. Daya daga cikin bedrooms din dake gidan wanda baima taba budesu ba yau dole ta sakashi ya bude,yanason bata tazarar kaman yadda tace taji idan har hakan zai dace da rayuwarta. Bata samu bacci ba har dai dab da asuba,wannan ya sanya ta makara sallar asuba. Sanda ta tashi da idanu ta dinga bin dakin,tayi tsammanin ganinshi a ciki,saidai bataga alamun ma ya sake komowa dakin ba. Jiki a mace ta shiga toilet,ta daura alwala ta dawo ta tayar da sallah. Duk sai take jinta wani iri,har ta kammala sallar ta koma ta zauna tana lazumi. Duk bayan wasu mintuna sai ta daga kai ta kallo lokaci. Lokaci yanata garawa amma babu motsinsa ko alama. Ta lumshe idanunta tana jin wannan baqar yunwar da take fama da ita duk bayan kowacce awa cikin duniyarta,sai taji hawaye yana shirin zubo mata. Tun jiya take tauna abun cikin ranta,tanaso ta tantance kyautawarta da rashin kyautawarta. Idan bata kyauta ba ai shi dinma haka,ko banza ko bata hada alaqa dashi ba a matsayinta na jininsa,mai matsayi tamkar Diya a wajensa,uwar yaransa kuma qanwarsa ya kamata ya kaucewa barin kowacce mace shiga rayuwarsu. Haka ta dinga dakon lokaci,qarfe shida bakwai takwas tara haqurinta ya gagara,yunwa ta cita sosai,haka ta miqe tana maida hijabinta tana layi ta,ta sanya slippers ta murda qofar dakin tana fitowa. Da qyar ya janyo wayarsa dake vibration saman kanshi idanunshi a rurrufe ya daga kiran ya kara a kunnensa. Abdulhamid ne,ya gaidashi cikin tsantsar ladabi sannan ya shaida masa ya iso. A qa'ida bayason ya bawa abdulhamid din damar shigowa gidan kai tsaye,don yanzun yasan bashi daya ke rayuwa cikin gidan ba,amma kuma akwai buqatar a tsaftace gidan,uwa uba yasan zuwa yanzun tana da tsananin buqatar abinci. Ciwon da cikinsa keyi da kuma zazzabin jikinsa bazai barshi ya samar mata komai ba,don haka yace dashi murya qasa qasa "Ka gyara harabar gidan da parlor,kayi da sauri,ka qarasa kitchen ka hada simple breakfast wa madam.....idan ka gama kayimin magana na fito" "Okay sir" ya amsa masa a ladabce. Wayar ya katse yana shirin maidata mazauninta,saidai kuma yaci karo da tarin miscals harda na Dr Camille a ciki. Bayason hayaniya ko doguwar magana don haka ba kiran wanda yabi din,ya maida wayar silent ya ajjiyeta yana maida kanshi saman pillow yana jin yadda kanshi yake sarawa. Dai dai sanda abdulhamid yake tsaka da share sharensa a falon bayan ya kammala da harabar gidan. Yadan ja baya kadan kamar yadda itama adan tsorace ta dakata da nufar kitchen din da takeyi,ta tsorata saboda tayi tsammanin shine a falon sai kuma taga akasin hakan. Kafin tayi yunqurin komai ya rusuna yana gaidata cikin harshen turanci da yake kyautata zaton shi takeji. Amsa masa tayi tana masa kallon rashin sani,sai kuma ta dauke kai tana wucewa kitchen. Raba idanu ta shiga yi tana tunanin meye ma zata dafa da zai zauna mata a cikinta?,ta manta rabonta da shiga kitchen ko girki,tadan kwana biyu. Tukunya ta dauraye ta dora saman gas,sai taji takunshi da sallamarsa. Waiwayowa tayi,yadan russuna yana cewa "Madam na gama, abincin dama zan dora miki,ban dauka zaki tashi da wuri ba" da idanu ta bishi,sai kuma ta motsa labbanta tana cewa "Waye kai?" Baiyi mamakin tambayar ba saboda yasan bata sanshi din bane "Nine nake kula da gidan gaba daya,mu biyu ne akwai abdulgaffar......amma yaje gida,zai dawo soon in sha Allah" kai ta jinjina,daga yanayinsa tasan dan Nigeria ne "Ba damuwa kaje zan dafa" "Okay maa" ya amsa mata sannan ya juya yana fita daga kitchen din. Sai data kwashe wasu mintuna tana kame kame kafin ta tsaida abinda zata dafa din. Kafin ta kammala duk sai taji kaman ta jigata,iska na neman kayar da ita. Ta samu ta gama da qyar,ta shirya a tray kaman yadda yakeyi mata,taja stool ta zauna,ta dauki spoon ta fara diba. Daga taste har abincin duka sai taji baiyi mata,tsaki taja,ta sake diba karo na biyu tana zaton zata iya daurewa,nan ma still taji abincin ya tsaya mata a wuya,tilas ta tureshi ta soma tunanin meye abunyi?. Wata tukunyar ta sake azawa tana canza wani abincin,saidai shima koda ta kammala din kaman wancan haka taji yayi mata. Tayi rau rau da idanu,hala tana cikin matan da idan suna da juna biyu ba kasafai suke iya cin abincin hannunsu ba?. Dukka dauriyarta ta tattaro ta sake aza wani girkin,saidai shima still tana fara ci ma taji amai ya taso mata,da qyar ta samu ya kwanta mata,sai kawai ta soma hawaye. Tafin hannunta ta saka tana gogewa,gidan shuru, kitchen din ba dadi,dakin ma ba dadi,haka duk girkin ba dadi,yaya zatayi ne?.. Fahimtar cewa indai ba shine ya bata abincin ko daga hannunsa ya fito ba to lallai ba shakka bazai zauna mata a cikinta ba,don haka ta haqura gaba daya,ta dafa Madara tasha sosai ta koma daki tana ci gaba da kwanciya. Da azahar tana kwance taji an kira wayarta,baquwar number ce amma ta qasar Paris din. Kaman ba zata daga ba ta danne zuciyarta ta daga din. Daya daga cikin gidajen abinci ne dake daura dasu suke tambayarta meye da meye take buqata na lunch dinta?. Ido ta lumshe tana budewa,sosai taji zuciyarta ta tabu "Qui a ordonné qu’on apporte de la nourriture ?(wanene ya bada umarnin a kawo abinci?)" Ta jefa musu tambayar. Dan dauke wuta tayi saboda tana duba sunan wanda ya bada order din,sai daga bisani ta furta "Monsieur aliyyu maina(yallabai)" ta kira sunan nasa da rashin iya furta sunan da kyau "Ku barshi ba buqata" ta fadi tana jin ciwo a ranta. Bazai iya tsaiwa ya bata kulawa ba? "Je suis désolé monsieur, il a déjà payé la nourriture, donnez-nous une chance de vous l'apporter.(kiyi haquri madam,ya riga ya biya kudin abincin,ki bamu dama mu kawo miki)" ta fada cikin girmamawa. Shuru tayi kuka yanason zuwar mata,batasan kuma me dame zatace su kawo ba,don haka tace musu abincin africa,yankin Sahel ta datse kiran. Ba jimawa suka iso,ta bude qofar ta karba idanunta akan qofar dakin. Tanajin kamar ta zauna a falon,sai kuma ta wuce zuwa cikin dakin. Ko takan abincin bata biba,sai data tabbatar yunwa na gab dayi mata illa. Wunin gaba daya a kwance yayishi,salla kawai ke tayar dashi,don ko abinci baibi ta kansa ba banda ruwan fresh milk da yake dirkawa kansa saboda yiwa kansa garkuwa daga yunwa. Saidai duk da haka hankalinshi yana kanta,baya son kuma kai kawon abdulhamid a cikin gidan a matsayinsa na baligi ga kuma matar aure a ciki,don haka yayi mata order din abincin da kansa. Bai samu sassauci daga zazzabin ba sai kusan qarfe goma na dare. Ya sake jawo Madara yasha sosai ya wuce toilet don yin wanka jikinsa ka fidda gumin saukar da zazzabin yayi. Sai a sannan ya samu yayi sallar isha'i,ya cire bathrobe ya sanya doguwar riga mara nauyi wine color saqar qasar morocco. Sai a sannan ya samu ya duba tarin kiraye kirayen da suka cika masa waya. Daya bayan ya dinga bin mutanen dake da muhimmanci yana kiransu. Ciki harda Dr Camille wadda ta zama itace ya qarshe,tace ta kira ne tahi ya jikin madam komai lafiya ko?. "Alhamdulillah" yace da ita yana jin hankalinsa yana karkata wajenta "Muryarka tayi qasa da yawa Dr lafiya kake?" "Ciwon nan dai Dr" ya gaya mata. Kusan Dr Camille na daya daga cikin mutane biyun da yake gani lokaci bayan lokaci kan ciwon cikinsa. "Ya salam,amma baka kirani ko ka kira Dr Muhammad ba?" "je vais bien maintenant(na lafiya yanzu),kada ki damu" "Allah ya qara lafiya,but idan ta yiwu goben sai a dubaka" akan haka suka rabu da Dr Camille. Wayar yake juyawa a hannunsa,har cikin zuciyarsa yaji yana da buqatar ganin suhail da sardauna kan batun ayana dama lailan duka idan hakan ta yiwu,don haka ya maida akalar kiran nasa zuwa garesu. Sardauna ya fara kira,kuma nan da nan suka gama waya dashi da yake he is serious ba kaman suhail ba,ya kuma bashi tabbacin goben zai shigo,sai ya danna kiran suhail "Baka da kirki mutumina.....angonci ne ya sanya ka daina koda daga kiran mutane?" "Ban sani ba,idan na sake angoncewa soon zaki fahimci komai" "Ban gane ba?" Suhail ya masa tambayar cikin mamaki "Zaka gane, gobe inason magana dakai kai da sardauna,ina da damuwa da zamu tattauna,zaka shigo kamar qarfe nawa?" "Ina fatan lafiya?" Suhail ya tambaya cikin kulawa "Khair in sha Allah" ya bashi amsa "Ameen.....duk sanda sardauna ya taso kayimin magana sai nayi qoqari dukka mu shigo lokaci daya" ya amsashi "Fine..... hakan yayi..... goodnight" ya katse wayar,sai ya ajeta saman pillow ya miqe yana son zuwa ya leqa lafiyarta. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 135 Ji tayi gaba daya kanta yana neman kasa daukar yanayin da take ciki. Ba shiri ta kunna data ta kuma kirayi goumar ta waya. "Goumar kana gida?" "Ikon Allah,yau kuma babu baqin buzun?" Bata cikin mode na tsokana wasa ko zolayarsa,don haka taqi bi takai "If kana gida don Allah zan kira ka bani su batoul mu gaisa" "So soon haka?" Ya fadi yana mata dariyar shaqiyanci,bai damu data amsa ko kada ta amsa ba ya dora da cewa "Har kin fara missing nasu matar oga?,na zaci you don't care fa gaba daya" ido ta lumshe,karon farko yau dai tayi Allah wadai da zallar tsokana irin ta goumar "Goumar...... goumar" "Yes ma" ya amsa mata "Zaka bani su ko na haqura?" "Na isa?,inje ki hadani da oga ya janyemin subsides?,biki yana matsowa shi nakeso yamin walicci kada yace ya fasa" "Kai ka jiyo" ta amsa masa tana zaquwa ya daga video call din data fara. Wata nannauyan ajiyar zuciya ta saki sanda fuskokinsu ya bayyana cikin screen din. Suka fara murnar ganinta suma,da alama sun fara kewarta kamar yadda ta fara nasu. Yadda suke murnar ganinta ya sake sanyayar mata da jiki,takai hannu a hankali tana shafa qasan mararta da wata halittar ubangiji ke kwance a ciki. Lallai d'a da uwa sai Allah,ta yarda babu wani yanayi ko rintsin daya isa ya tsinke wannan kakkaifar soyayyar dake tsakaninsu. Tunda take dasu bata bata dadewa dasu haka suna hira irin wannan lokacin ba. A yau din gaba daya fuskarsa take gani cikin nasu,wani motsinsu da wasu dabi'un nasu a yau take ganin zallar kamanceceniya da mahaifinsu. Sun debe mata kewa matuqa kaso hamsin cikin dari,sun kuma sanyata farinciki. A hankali ta dinga tuna wasu daga cikin hadisai da suka karanta a makaranta na 'ya'ya mata rahama ne. Sunyi treating nata kamar sunsan damuwar dake zuciyarta duk da qarancin shekarunsu,wanda ta tabbatar inda namiji ne ba lallai ya iya hakan. Wannan nutsuwar ya bata damar samun bacci,wando yazo ya dauketa ba tare data shirya ba da wayar a hannunta. Yayi mamaki daya tura qofan dakin ya jita a bude,mamakinsa ya sake qaruwa da ya ganta a kwance amma kuma dukka fitilun dakin a kunne. A hankali ya isa gaban gadon,ya tsugunna idanunsa saman fuskarta yana jin wani abu yana fusgarsa game da ita. Wunin yau duka da bai ganta ba yanajin tamkar ya shekara bai ganta ba,amma dole yayi hakan,don ya sake tabbatarwa kansa zuma ce saida wuta da kuma dabaru kafin komai ya gama daidaita. Ya gaji shima so yake komai yazo qarshe. Wayar hannunta ya fara zarewa,sai ya bude yana duba waye ta kira?. Murmushi ya saki bayan yaga da waye ta gama wayar,ya maida idanunsa kanta yana sake sakin murmushi. Yaran da ake kawarwa da kai,yaran da akaqi shayar dasu.....yaran da akaso turewa tun suna kwanan farko a duniya,yaran da akace ba'a so an barwa duniya yau su ake bege har haka?.. qaramar dariya ya saki,al'amuran sultanan akwai ban dariya wani lokaci. A nutse ya tashi ya dagata cikin hikima ya gyara mata kwanciya da kyau,yaja mata duvet ya rufeta sannan ya sanya mata pillow daga gabanta. Yana zare hannu ta miqa hannun nata ta yiwa pillow din kyakkyawar runguma tana cusa kanta a qasansa. Dariya ta bashi da kuma tausayi,ya saki murmushi yana ci gaba da kallonta har sai data nutsu ta daina mutsu mutsu gaba daya,ya sani tana buqatar dumin wani ne a kusa da ita,amma tsabar fitina ya hanata tsaiwa ta fahimci inda zuciyarta ta dosa. A nutse ya busa mata addu'a yadda bazai tasheta ba ya kashe mata fitilar dakin gaba daya yaja mata qofar ya rufe yana ficewa. *W A S H E G A R I* Tun sha biyu na rana taji gaba daya cikinta an yasheshi tas,kamar bata san wani abu waishi abinci ba a duniya. Ta jima tsaye gaban madubi tana duban kanta cikin jin tausayin kanta da kanta. A jiya da yau tana jin kamar ita daya ke rayuwa cikin gidan. Jiya duka bataga koda gilmawarsa ba,a yau tayi tunanin zai leqo amma shuru,saidai ta samu breakfast daga wajen abdulhamid kuma yau din da yake ba ita tayi girkin ba ta samu ta danci wani abun. Ba zata iya maimaita cin abincin dazu ba,don haka yanayin nata kuma yazo mata dashi,dole ta yafa mayafin baqar abayar jikinta 'yar qasae Egypt dake fidda wani qyallin tsadajjen yadin da aka saqa rigar dashi da kuma adon duwatsun da akayi mata. Fuskarta tayi fayau ta kuma yi haske ainun,saidai kuma tadan fada kadan saboda yanayin laulayi da take fama dashi. Isarta falon kawai hancinta ya tabbatar mata yana a wajen. Ta shaqi iskar falon da kyau idanunta nason lalubo daga inda yake a zaune. Cikin qawatattun sofas da suka yiwa falon qawanya,gabansa dauke da madaidaicin tray,saman cinyarsa kuma system ce da hasken screen din ke haske gilashin idanun daya sakaya qwayar idanunsa a ciki. Cikin jikinsa yaji ana kallonsa,a hankali ya shammaceta yayi caraf ya kamata,tayi wani wawan dauke kai gabanta yana faduwa,sai ta maida kanta hanyar kitchen cikin ranta tana tambayar kanta da kanta meye ya sameshi haka ya fada?. Kaman zata zagaye sai kuma ta biyo ta hanyar da yake zaune. "bon après-midi(barka da rana)" "Comment vas-tu?(ya kike?)" Shima ya tambayeta a taqaice,duk kuwa da cewa kwanciyarta da tashinta dukka yana monitoring,ya saita komai ta cikin laptop dinsa da CCTV din da dakin yake dashi "Lafiya qalau" ya fadi tana wucewa kitchen. Cikin ranta kamar ta tamabyeshi,amma sai taga na meye?,ita dake dauke da cikinsa ma ya ajjiyeta a gefe?. Abinda take tunanin zata iya ci ta hado,ta dauko a tray tana jin kamar ta juye duka cikin cikinta duk da tayi imani zaiyi wuya ta iya ci. Muryar Dr Camille ce ta daki kunnenta sanda take fitowa,dole ta aro fara'a ta aza saman fuskarta tana nufar Dr din dauke da tray din hannunta "Lallai maman baby lafiya kike" Dr Camille ta tsokaneta. Tsokanar data sanyata sakin murmushi,ta qarasa gabansu kawai ta dire dukka abinda ta fito dashi tana samun waje ta zauna tana gaidata cikin girmamawa ita da baqon likitan da suke tare. Da idanu yaketa monitoring dinta,yadda taketa qoqarin karramasu dr Camille tamkar ta sansu,tanata qoqarin musu fara'a da basu tarba ta girmamawa. Duk da taurin kanta da kuma kafiyarta tun a shekarun baya tana da wasu dabi'u da da yawa ba'a sanya mata rai dasu. Na farko mutum ce me mugun tausayin da nan da nan ta yiwa mutum kuka saboda tausayi ba komai bane. Na biyu tana da son taimako,a lokacin komai yawan kudi ko tsadar suttura ko wani abu na amfani da za'a bata muddin taga mutum nada buqatar wannan abun zata sadaukar masa. Har wani lokaci 'yan gidan kanyi mata shaguben batasan ciwon dukiya ba. Duk da abinda ta kawowa su Dr Camille din ba cimarsu bane amma sunci sun kuma yana sosai da abincin africa. Bayan sun gama dinne Dr Muhammad ya fara dubashi,ya gama masa tambayoyi da qananun gwaje gwaje "Kafi kowa sanin history na ciwonka......ya kamata ka kiyaye Dr aliyyu" Dr Muhammad ya fada yana komawa mazauninsa. Sultana dake wasa da yatsunta ta daga kanta kadan ta saci kallonsa,wanne irin ciwo ne wannan?. A hankali kuma sai tunaninta ya dawo kan darensu na rannan,yadda ya dinga wani abu daya firgitata ainun "Dama yana da ciwo har haka amma bai taba gayamin ba?" Ta tambayi kanta da kanta,sai kuma ta tuna yanayin da suke ciki,don haka ta kauda wannan tunanin. Tana zaune Dr Muhammad ya bashi shawarwari, shawarwarin da ta dinga jin sun mata nauyi, kunya ta kamata sosai,da yake bature ne shi din, kuma akan aikinsa yake don haka bai damu ba,kanshi tsaye yake masa bayani. Taso rakasu Dr Camille har bakin mota amma dr din tace tayi zamanta,ita dinma hakan ya mata,don yunwa gaba daya ta kashe mata jiki,batasan kuma zuwa yanzun me zataci ba,shu daya ke iya sarrafa mata abu ya bata ya zauna mata lafiya lau. Ama ce tazo ranta,tabbas a wajenta kawai zata samu yadda takeso,sai kawai ta fidda waya ta turawa aman saqon neman abincin gargajiya daga wajenta,don tana kunyar kiranta kai tsaye. Motarsu Dr Camille na tashi taji sautin shigowar wata motar, ba'a yi minti biyu ba muryoyinsu ya karade farfajiyar gidan. Suhail da sardauna,dukkansu ta dauki muryoyinsu "A nan ya kamata mu zauna don tattaunawar nada muhimmanci sosai" "Shiga ka fito,kazo kuma ka gayamin ma'anar zaka sake angwancewa muji mu muna nan zaune gardawan banza kakeson maidamu ko?" "Ku kuka so shegen banza" ya maidawa suhail amsa yana dawowa ciki don ya dauka musu drinks. Tunda suhail yayi maganar taji kunnuwanta kaman sun dan toshe na wucin gadi,tayi shuru tana sauraren muryarsu sanda sardauna ke sake tambayar suhail din. Waje daya idanunta ke kalla,don haka har ya shigo ya dauki wayar ya fice bata ma lura dashi ba,tadai jiyoshi yana musu jagoranci zuwa saman kujerun concrete dake filin 'yar farfajiyar tasu. *_masu siyan anko da masu zuwa dannar qirji duk ku shirya_*🧐🧐 *_ni nayi nan saikun taho_* *_sauka on the way in sha Allah_* _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 136 Abinda ta sake shiryawa saman tray ta ajjiye jikinta a sanyaye saman stool. Gaba daya hankalinta taji ya koma wajen inda suke zaune. Duk da bata iya jiyo komai amma sai ta kasa zama waje daya. Ta bude abincin da zummar taci duk sai taji gaba daya ta qoshi. Mayarwa tayi ta rufe,ta jawo wayarta ta bude,zuciyarta na bata shawara ta kira bibi ko su batoul su debe mata kewa,nan ma taji koda ta kirasu din kamar ba zara iya magana ba,don haka ta ajjiye wayar,ta maida idanunta ta aza saman tv wadda keta aikinta ba tare da volume ba. Sosai kunnuwanta sukayi nisa da son jin abinda suke magana akai,amma kuma bata iya jiyo komai din sai dan guna guninsu wanda bata iya tantance ko meye suke cewa. Baya ta zame ta kwanta tana dora kanta saman pillow. Wata irin kasala na sake rufeta,tana jin batason daga koda yatsanta ne "Me suke tattaunawa?,da gaske zai barta tayi rayuwarta kamar yadda taketa nanata masa?,da gaske bata da buqatarsa?,da gaske zata iya rayuwa babu shi?" Har tsakiyar ranta takejin amsar da tafi dacewa da ita kamar NO ce fiye da YES,ta soma wassafa rayuwarta ita daya ba tare dashi ba,sai kawai taji kanta ya kasa dauka,ta dauke kanta gefe tana girgiza kai,batasan me takeji ba,bata kuma san me zata fuskanta ba. Ta kusa mintuna ashirin a haka kafin taji muryoyinsu sun fara tashi,kamar musu sukeyi,kamar kuma rigima sukeyi,abu guda kunnenta ya iya jiyowa, muryar maina sanda yake fadin "Da laila da ayana dukansu......." Sai ta gaza jin abinda yake fadi daga qarshen. Iya jin sunyensu kadai a bakinsa sai daga sanya gabanta tsananta faduwa,ta runtse idanunta tana qoqarin daidaita bugun zuciyarta. Fargabarta tana sake qaruwa,kada dai ace ya aminta da zancanta,ya kuma yarda da abinda ta fada din?. Idanunta ta sake lumshewa da suke mata yaji yaji kaman hawaye na shirin fita. Har yanzu tana jin tashin muryoyinsu,tsahon lokaci tana jinsu kafin daga bisani taji hayaniyar ta lafa,sai kuma maganganunsu qasa qasa da dariyar suhail da sardauna. "Hasbunallahu wani'imal wakil" ta fada tana gyara kwanciyarta. Komai qwace mata yayi,sai hawaye kadan kadan da suke fita mata daga qasan idanunta tana sharewa,daga qarshe ta dinga furta "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" kadan kadan tana neman daukin ubangiji. Mintuna kusan talatin taji an buda qofar dakin,ta ware idanunta da suka sauya launi. Akan fuskarsa suka sauka sanda yake takowa cikin dakin,shima ita yake kalla,ranshi ba dadi da yadda yaga fuskarta alamun ta danyi kuka don har fuskar tadan kada tayi ja,dole sai an tauna madaci wasu lokutan ake samun maslaha,don haka ya kauda kanshi kaman bai gani ba qasan zuciyarsa tana masa ba dadi,ya wuce zuwa inda ta ajiye kayan abincin. Zama yayi ya bude komai ya qare musu kallo sannan ya ja qaramin bowl din data ajjiye ya zuba ya sanya cokali ya sauka qasa ya ajjiye a gabansa. Lion eyes dinsa da suka rusuna saboda zafin zazzabi ya daga ya zube mata su,yadan lumshesu kadan sannan ta motsa bakinsa a nutse yana miqa mata hannu "Taso nan" jiqaqqun idanunta ta daga ta kalleshi,sai ta saukesu qasa a hankali,ta yunqura da karyayyiyar zuciya jikinta a mace,ta fara takawa a hankali. Idanu ya bita dashi yana kallon takunta,tausayinta yana ratsashi a hankali a hankali,sai ya miqa mata hannu kafin ta qaraso yana gyara mata inda zata zauna. Sosai ra zauna a gabansa ya gyara mata skirt din jikinta,ya dago bowl din ya ciro cokalin ciki ya debo abincin yakai bakinta "Bismillah" ya furta,saita maimaita itama ta bude bakinsa ya saka mata. Ta runtse idonta tana tauna abincin a hankali. Da gaske komai da zai fito daga hannunsa dabanne a wajenta da bakinta,me hakan yake nunawa?. Duk yadda take ganin zata iya,zata iya ci ita kadai zata iya gamsar da kanta da buqatunta a hankali a hankali sai komai yake neman qaryatata. Me yasa take gazawa akan komai?,me yasa kasawarta ke fito akan komai da komai? "Ba zaki iya ba sai dashi" wani sashe na zuciyarta ya bata amsa kai tsaye cikin sallamawa daga lamarin gaba daya. Maganar ta tsaye mata a rai,da gaske hakanne ko kuwa?. Tana tsaka da wannan tunanin ta daga idanunta,sai taga ashe ita yake kallo shima,ya ritsata da idanunsan nan da a yau kallon cikinsu ya haifar mata da wani irin abu da bata taba jinsa ba,a take kuma idanunta suka hada hawaye fal har hakan ya nuna cikin qwayar idanunta masu sheqi. "No...... don't cry" ya fadi a tausashe,sai ya zaro tissue daga gefansu yana miqa mata. Bata musa ba ta saka hannu ta karba ta fara tsane idanunta "Kin qoshi?" Ya tambayeta yana dubanta. Kanta ta gyada a hankali "Good" ya fadi yana maida ragowar tissue din cikin kwalin. Ruwa ya tsiyaya ya miqa mata,ta miqa hannunta zata karba hannunsu ya hadu waje daya. Dukansu shida ita babu wanda baiji wani abu a jikinsa ba,yayi saurin sakar mata ruwan wanda saura kadan itama ya subuce daga hannunta. Kamar kullum ya hada kan kayan guri guda,ta bishi da satar kallo ta gefan ido. Tana jin kamar tace masa kada ya fita daga dakin,amma kuna tana jin nauyin fadan haka. Bayanta ta mayar jikin kujera tana lumshe idanunta gami da fidda numfashi a hankali.tanason tuna daidanta da kuma kuskurenta,a cikin wannan tunanin nannauyan bacci yayi awon gaba da ita,dukka jikinta ya sake saboda qoshin da tayi,wanda tun ranar qarshe daya bata abincin rabonta data qoshi haka. Lokacin da ta farka tayi mamaki sosai ganinta kwance saman gado kuma lullube cikin duvet,ta dudduba jikinta a hankali mamakin dai bar barta ba haka ta sauka tana duba lokacin sallar azahar. Lokacin bai qure ba amma dab yake da fita,wannan ya sanya ta qara azamar shiga toilet. Tana idar da sallah wayarta ta dauki tsuwwa,ta miqa hannu a nutse tana jawo wayar. Number goumar ne,don haka ta daga kiran. Muryar batoul ta fara ji,cike da karsashi take magana "Mummy assalamualaikum" murmushi ya subuce mata,muryarsu na daya daga cikin abubuwan da suke sanya mata nutsuwa a wannan lokacin "Wa'alaikummussalam B" murmushi ya qwacewa yarinyar,har tana jin sautinsa ta wayar "Mummy ina kwana?" Karyar da kai sultanar tayi tana jin dadin jin muryarta "Lafiya lau B.....amma yanzun ba safiya bace,ko bacci ama ta barku kuka dinga yi?" Dariya ta qyalqyale dashi "A'ah,yanzun nan mamy tanja ta gama gasa mana cake.... uncle goumar yaje ga siyo mana whipping cream strawberry flavor ta saka a ciki" murmushi ya qwace mata,yaran badai son cin dadi ba,bakinsu yasan kwadayi qwarai,ko don sun saba tun suna qananu?,saidai kuma duk da hakan bai sanya an barsu sun sangarce ko kuma sun miqe da samun duk abinda sukeso ba "Ma sha Allah,a yiwa mamy tanja godiya sosai" "Mummy.....we missed you.....don Allah ama tace mu tambayeki muzo mu ganki?" Maganar ta sanya sultana jin nauyi da kunya,me ama ke nufi?,ya zata hana yaran zuwa?,ita kanta marmarin ganinsu takeyi,inda da hali ma kuma da zaiyiwu aman ta bata dasu zatafi kowa farinciki da hakan,amma ta sani wannan magana bame yiwuwa bane,koda wasa kuma ko a mafarki ba zata ce a bata su batoul ba,don sun zama halak malak din ama da aba,mallakinsu ne ko duniya ta shaida "You are welcome BB" ta fada a gajarce don batasan ko ama tana wajen ba. Ihunsu taji daga cikin wayar da muryar mutumin nasu goumar,sai kawai ta ajjiye wayar tana murmushi. Batasan wanne qarfin qauna goumar din yakewa yaran ba,ba wani abu da yake barinsu su nema su rasa,real definition of uncle ne shi din. Samun kanta tayi da tunanin me zata samawa yaran suci a matsayin barka da zuwansu?. Ta dinga tunani daga qarshe ta yanke abinda zata basun,tasan ba abinda suke so irin kayan maqulashe,don haka ta qarfafa jikinta ta miqe tana zare hijab dinta ta lullube kanta da madaidaicin mayafin daya dace da rigar jikinta. Har cikin ranta takejin walwala sosai,ta dinga takawa cikin lobby din don ta wuce zuwa kitchen din,daidai sanda taga qofar dakin dake daura da nata a bude. Idanunta saman qofar dakin tana qiyasta a nan ya koma kwana kenan. Dab da zata gifta dakin ta soma jin sautin muryarsa,cikin calmness dinnan nashi "In sha Allah next week ko upper week zamu shigo Niger din......" "Lafiya ko?" Daga cikin wayar ta jiyo sautin muryar uncle umar yana tambayarsa "Neman aure oncle......nigeria da kuma niamy in sha Allah" "Hasbunallah" ta fadi tana gifta dakin da sassarfa tana jin qafafunta kaman ba'a jikinta suke ba.......tana qoqarin sarrafa tashin hankalin da takeji cikin zuciyarta tana kuma tuhumar kanta me ya kaita tsaiwa jin maganarshi cikin waya. Da qyar ta qarasa kitchen,ta samu stool ta zauna saiga hawaye kamar ana tunkudosu.......auren zaiyi da gaske?,meye makomarta kenan?, meye matsayinta a gurinshi?,a ina ya ajjiyeta?. "Sultana......ki fitar da kanki daga sabgar nan......kiyi ta kanki kiyi ta rayuwarki......taki qaddarar ce qila kiyita haifa masa yara babu cikakken zaman aure.....ki sauke wannan daga nan ki samawa kanki mafita...... zaiyi aure saboda baki da wani matsayin komai a wajensa....baki kuma isa komai ba.......ki zama jaruma....ki zama jajirtacciya......ya hado laila ayana da dukka danginsa ya aura mana" zuciyarta ke gaya mata hakan cikin tsawatarwa. Kokawa sosai ta dinga yi da zuciyarta tana wassafa yadda zata iya handling maganar. Maganar tafiya neman aure kenan ya kira suhail da sardauna yayi musu?,zasuyi masa rakiya kenan?,su zasu zame masa abokan ango?. Kifa kanta tayi a tafukan hannayenta tana wassafa girman tashin hankalin da takeji cikin zuciyarta,yayin da tsoro ya mamayi zuciyarta,anya zata iya jurewa wadannan abubuwa?,tana tsoron kada wani abu ya samu dan tayin halittar dake kwance qasan mararta......halittar da takejin wani matsanancin soyayyarsa banbanci da abinda taji a cikinsu benazeer,ko don su din bata gama sanin me ake nufi da gundarin abinda kalmar d'a ke nufi ba?,ko don a sannan batasan ciwon kanta ba?. Ta sake shafa mararta a karo na biyu tana sake addu'ar ubangiji ya tsare duk abinda take dauke dashi. Mamakinta kuma yana sake linkuwa,me zata haifa haka da duk irin tashin hankalin da takeji daga zuciyarta zuwa gangar jikimta bata taba jin wani alama na akwai wani mummunan abu da yake faruwa dashi ba?,bata taba jin alamun girgiza daga zamansa qasan mararta ba?,tabbacin wata ajiya ce ta ubangiji dashi kadai ya barwa kansa sani. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂GUDUN KADDARA Chapter: B00K O2 PAGE 137 *_GUDUN KADDARA_* *HUGUMA* 'ya'yanta data tuna ya bata wani irin qwarin gwiwar cilli da kuma tunkude kowacce kalar damuwa. Ta mige tana garfafawa kanta gwiwa ta soma duba duk wani abu da takeso tana hadawa waje guda. Girki tayi sosal irin wanda ta jima batayi irinsa ba, duk da yadda gamshin wasu abubuwan ke neman galabaltar da ita amma tuna benazeer din da batoul kadal yana saka mata qwarin gwiwa. Koda ta gama bata fidda komai ba ta barshi cikin kitchen din, ta gyara komal yayi mata yadda takeso, sannan cikin kasala ta juya zata fice a kitchen din. Yana tsaye ya harde hannayensa yana kallonta, kuma dukkan alamu sun nuna yadan jima tsaye a wajen don har ya jingina sosal da bakin gofa. Suna hada ido ta kauda kai, batason taci gaba da kallonsa bare gazawa ko rauni ya mamayeta. Ci gaba tayi da takowa, yayin da yaci gaba da kallonta yakuma d'ana mata tarko har zuwa lokacin data iso dab dashi. Sosai yaso dauke kanshi daga gareta, ya ja numfashi har zuwa cikin hunhunsa amma zuciyar. tagi daidaita daidal da matakin da yakeso. Ba tare daya shiryawa hakan ba, ba kuma tare da yaso hakanta kasance ba ya sanya hannunsa ya fusgota cikin jikinsa. Sanda ta isa ga faffadan girjinsa sai taji kamar an yaye mata wani abu dake lullube a girjinta. Sassanyan gamshin nan nasa da a yanzu a duk duniya babu abinda takeso take kuma gaunar shaga... gamshin ainihin fatarsa laushinta da duminta ya mamayeta. "Kin gama kuka dazun......yanzun kuma kinzo kina girki..... banason dukka wadannan dabi'un please.... ko meye kikeyi abinda yake cikinki yana sane dashi" kaman jira takeyi dama yace wani abun ko kuma yayi wani motsi sai kawai ta cusa kanta cikin gir jinsa ta fashe da wani irin kuka. Kuka me wani irin sauti daya rudashi ya kuma daki zuciyarsa lokaci guda. Ya dagata daga jikinsa yana rige kafadunta da dukka hannayensa biyu "What's happening?....mene kuma?" Ba zata iya cewa komal ba don tana ganin ta katse kukan bame yiwuwa bane...... yaga alamun hakan shima, don haka bai sake tambayarta ba ya rigeta da kyau ya fita da ita falon. Saman kujera ya azata ya koma yasa a gabanta ya zauna dirshan yana kallonta. Bai rogeta ta tsaida kukan ba, saboda yadda take kukan kadal ya tabbatar masa daga zuciya ne. Bai ce da ita komal ba sai daya tabbatar dai dai lokacin zuciyarta tayi sanyi "Me ne kuma ya faru?, ko har yanzun dal na matsa miki?, ina takuraki?, ko kina bugatar wani space dinne sama da haka?" Dukka tambayoyinsa sai suka bata masifan haushi, tama rasa gane masa gaba daya?, me yasa bazai fahimceta ba?, baya ganewa ne?, baya gane yanayinta ne?, anya ba da gangan yakeyi ba?, bayan kuma ya tabbata yafi kowanne mutum iya karantar badininta daga tsakiyar idanunta?. "Kina da wata matsalar dani ne?, idan akwai ki gayamin zanyi gogarin kauce ma hanyarki...... na miki algawari ne kuma ina gogarin cikawa.... please let me know idan akwai wani matsala". Dukka maganganunsa suna nuna bai fahimta komai ba, da gangan ne ko kuma iya gaskiyarsa kenan ita bata sani ba, abu daya ta sani, dukka wadannan maganganun ba su take burin ji daga bakinsa "Kaine matsala!" Shine abinda taketa son gaya masa amma kuma batasan da wacce siga zata fasa mishi maganar ba. Bayan hannunta ta saka tana sake goge fuskarta,sai ya sanya dukka hannunsa biyu ya zuba tagumi yana kallonta. Can gasan ransa kaman ya saki mata dariya amma yana cijewa. Ka nema abu da kanka amma kuma kazo ka buge da bawa kanka punishment?, shi kam bai taba ganin wannan abu irin na sultana ba. Gajeruwar hanya me saugi amma ta maidata doguwar tafiya. Shi din mutum ne daya ci burin samun ingantacciyar soyayya zazzafa daga wajen matarsa... ....ba kowacce kalar soyayya ba wadda bata amsa sunanta ba, so me sunan so wanda ya gunshi sadaukarwa abota da kyakkyawar fahimtar juna .....wannan ya sanya a tarihinsa bai taba budurwa ba a baya.....ba wanda ya isa yace ga budurrsa..... don kowacce mace ya kalla sal yaga kaman ba zata bashi abinda yake bugata ba ta hanyar haquri dashi ta kuma mallaka masa zuciyarta da rayuwarta dama gangar jikinta gaba daya...... auren dole yana daya daga cikin abinda ya yiwa mummunar tsana......ya kuma yiwa kansa algawarin bazai taba auren macen da babu soyayyarsa cikin zuciyarta ba "Ki sake gayamin me kk bugata haidar zai kiyaye...." "Idan nace kai nake bugata nayi daidai banyi kuskure ba?" Ta gwada fadi cikin zuciyarta, saidal a fili kuma idanunta ta lumshe. Batasan ya zatayi masa bayani ba.....batasan yadda zai fahimceta ba ba tare data furta komai ba. Bell din da aka kada ita ta katse komal a tsakaninsu, ya waiwaya a hankali yana duban qofar kafin ya dawo da dubansa kanta "Wipe your tears please baby gurl.... kada na je su ama ne ki sanya suyimin dukan tsiya..... naga har yanzu basa yina kedin dai ke sukeyi" ya fada yana dan ranqwafawa kadan ta saman kanta kamar me rada mata bayason wani yaji abinda yake fada din. Jikinta ya bata su batoul ne, don kamar tana dan din muryarsu kadan kadan, ta jawo tissue tana sake tsane idanunta tare da gyara zaman mayafin kanta tare da gyara zamanta. Ihun da suka saki yaran ya sanyata duban bakin qofar bata shirya ba, dukka sun saki kayan hannunsu sun dane uban, shi kuma ya dagasu dukka su biyun kamar bayajin nauyi da girman da suke sakeyi kullum. Ya diresu suna gaidashi, benazeer tadan bata fuska tana cewa "Ina mummy?" Da yatsa ya nuna musu ita, sannan ya ranqwafa a tsakiyarsu gasa gasa yana cewa "Kuyi magana a hankali mummyn batason hayaniya......kuzo mujeku tayani bata haquri, wai haushina takeji" ya furta shima kaman garamin yaro yana dan bata fuska. Agaba ya sakasu har suka isa gabanta, sun tsareta da idanu kamar yadda itama ta tsaresu da idanun, sai ta bude musu hannuwanta, da gudu kuwa suka fada kanta. "fais-le soigneusement (yi a hankali), karku buge baby" ya fada yana janyesu daga saman gafafunta. RA Batoul sarkin magana ce ta daga kai da hanzari ta kalleshi "Daddy ina babyn?" Ta fadi tana zare idanu. Hannunsa ya dora daman cikinsa sannan ya nuna mata sultana. Tsalle ta buga tana rigeshi da kyau "Baby zata siyo mana daddy, mu xama mu haka?" Ta fadi tana daga yatsunta guda hudu. "In sha Allah" ya fada yana murmushi. Harara sultana ta jefawa benazeer sanda ta juyo da niyyar mata tata tambayar, hararar ta sanya benazeer ta tsuke bakinta tsaf, daidai nan goumar ya shigo da sallama. Zuwan nasu shi ya sake debe mata damuwa me yawa, tayi yogarin sakin jiki dasu, yayin da goumar uban tsokana yaketa son kwasarta amma kuma idanun maina ya hanashi. Duk motsinta akan idanunsa yake, ya lura kuma tana sane tana basarwa ne, kaman batason kallon idanunshi ne bataso kuma shima ya kalli nata. Tare sukayi sallar magariba cikin falon dukansu, yana kuma sane ya hanasu tafiya da wuri ya jasu har magaribar saboda ita. Bayan sallar magaribar abincin da yayi musu order daga wani gidan abinci ya iso. Kowa da zabinsa, ta mige ta wuce kitchen yaran suka bita don dauko spoons da plates, sai ya bisu da kallo yanaji a ransa Inama wannan yanayin ya dore har abada?. Sanda ya dauke idanunsa sai suka hada ido da goumar, dariya ta tasowa goumar din amma ya toshe fuskarsa da wayarsa, sai ya zabga masa harara yana dauke kanshi. "Ka shirya Next week ko upper week zamu wuce Nigeria, ina tunanin adadin bukukuwan zasu dadu, so nake a hade bikin duka lokaci daya idan zai yiwu" maina ya fadi yana bude wayarsa da sago ya stigo, daidai sanda kuma take fitowa ita da yaran daga kitchen din "Bukukuwa yaa maina.....bikin waye?" "Ka fito da passport dinka kawai, ka gayama ama ta fiddo nasu benazeer zan duba mana ticket, idan munje zaka gani"….*_GUDUN KADDARA_* *HUGUMA* B00K 02 PAGE 138 Goumar daya ga isowarta gurin ya daga kanshi ya kalleta, suka hada idanu saita kauda kai tana ajjiye abincin data dauko musu a hankali. "Mun gode" goumar ya fadi cikin sanyin jiki. Dukka juriyarta da yogarinta ta tattaro ta aza saman fuskarta ta kuma fidda murmushi "Aunty najma zata biya bagin buzu" duk da yana cikin yanayi na rashin Jin dadin zuciyarsa amma sai daya maida mata murmushinta. A nutse kaman bataji komal ba ta juya, duk kuwa da cewa zuciyarta na wani irin rawa. "Zan shiga daki zaku zauna wajen uncle goumar?" "Zamu biki dakin" benazeer tayl saurin fada. Bata hanasu ba suka bita a baya, benazeer tana gaba batoul na binta a baya ita kuma tana bayansu. Ko cikin dakin sun sake abinsu sunata dara, tana zaune kawai tana binsu da kallo, yayin da zuciyarta tayi nisa sosal da gangar jikinta. Tana jin wani rauni yana mamayarta, da gangar ya kasa fatimtar ta?, ko kuma da gaske yake bai fahimceta din ba?, zata kuwa iya jurewa wannan hukuncin da ya yanke musu me gaba daya ita dashi?. Qarar wayarta ya dawo da ita hayyacinta, ta kalli wayar daga inda take zaune, abun mamaki sai taga goumar ne, ranta ya bata ko akwai wani abu me muhimmanci ne ya sanyashi kiranta. Da sallama a bakinta cikin raunanniyar muryarta, ya amsa sal kuma shuru ya biyo baya tsakaninsu "Sultana" ya kirayeta da sunan data manta rabonshi da kiranta. "Na'am" ta amsa masa a sanyaye. "Kinsan waye maina kuwa?" Yayi mata tambayar da ta rasa abinda zata ce masa, sal shuru daya ratsa a tsakaninsu "Why sultana?..... me yasa ba zaki yafe ba?, me yasa komal bazai wuce ba?, me yasa ba zaki bayyana masa soyyaya ba?.. kinsanadadin yadda yaa maina yake mutuwar sonki?, kinsan yadda ya daukeki a rayuwa?, kinsan adadin soyayyar da ya baki?, kinsan iya matsayinki da matakinki a rayuwarshi?....... yana bugatar wata soyayya wadda bata uwa ba....yana bugatar wata soyayya wadda bata 'ya' yanshi ba.. ...sultana pl...... Maganarsa ta yanke sanda take jiyo muryar maina ta cikin wayar, da alama ya shigo gurin da goumar din yake zaune, alamu kuma sun nuna baya wajen sanda yayi kiranta "Ki turo su batoul zamu fita" goumar ya rufe maganar tashi da wannan. Sauke wayar tayi tana jin idanunta suna mata zafi, kuka takeso tayi amma kuma batason ta karya farincikin da yaran suka samu ta sanadinta. "Kowa ya sanya cap dinshi, uncle goumar yana kira" da saurinsu suka maida p_caps dinsu da suka cire garin tsalle tsallensu, suka kuma ruga suna rige rigen fita daga dakin. Rub da ciki tayi qwalla na silalo mata, da gaske ne dukkan abinda goumar ya fadi mata?, da gaske ne komal goumar ya fadi a kanshi tattare da ita?, ta yaya ya kamata ta fuskanceshi?. Da wannan tunanin ta dinga juyi saman gadon tana tuna abubuwa da yawa cikin kanta. Tun tana zuba ido tana lissafin sanda zataji motsin dawowarsu har taga dadewar tayi yawa, tun tana kawaici har sai data daga waya ta kira goumar. "Yanzun muka wuce gida, ama tace mu dawo dare yayi" "Ku gaisheta" ta bawa goumar amsa tana aje wayar. Minti goma minti ashirin minti arbain shuru bata ji motsin dawowarsa ba, har ta share awa daya awa ta biyu ta wuce. A hankali wannan kasalar tayi mata rubdugu a jikinta, wani nannauyan bacci da bata shiryawa zuwansa ba ya ziyarceta, baccin da bata farka ba sai washegari daidal sallar asuba. Ko da akayi sallar asuba ma wani irin bacci ne ya sake surarta, saidai duka duka bata wuce awa biyu ba ta farka. Toilet ta shiga tayi wanka, ta tito ta tsaya gaban madubi tana duban lotion din da take amfani dashi. Ta budesti amma kuma ta kasa tabuka komal, qwagwalwarta tanata wassafa mata yadda zata fuskanceshi. Handle din dakin ta ji an murza sannan aka tura gofar aka shigo. Aliyyu maina ne cikin wasu suit da suka karbeshi matuga da gaske. Tsahonshi da mur jewar jikinsa dukka sun bayyana. Sumarnan baga sidik tanata shegi saboda gyaran da take samu a kowanne lokaci. Lion eyes dinnan nasa yau fes suke, sun sake wani haske da kuma girma kaman ya diga musu wani abun. Sallama yayi yana motsa jajayen labbansan nan masu daukan hankali idanunsa tsaye car saman girjinta da ya zauna sosal, gefe guda kuma yana kokawar dauke idon nasa gudun kada ya kasa sauke abinda ya niyyata. Muryarsa kawal ta saka zuciyarta tayi rauni, amma duk da haka ta hana hakan bayyanuwa saman fuskarta. Ta jawo towel tana dorawa saman kanta ta yadda zai lullube mata kafadunta da girjinta da suka fito tana amsa sallamar. Rarasawa yayi a nutse ya ajJiye complete kayan breakfast din daya shigo mata dasu kaman yadda ya saba "Ina kwana?" Ta gaidashi tana fatan samun damar yin wata maganar daban dashi bayan galsuwar "Kin tashi lafiya?" Ya bata amsa cikin nuna kulawa, can yasan ransa kuma yana jin ba dadi kan yadda ta haramta masa ganin kyakkyawan fatarta dake gara wani sulbi da "Athamdulillat" "Zan fita..... •zan zama busy sosal a kwanannan.....idan kina da wata damuwa ko wata bugata kiyi magana akai" ya furta cikin salo na bada dama gareta. Bakinta ta motsa tanason tayi magana amma sai ta kasa furta komai din, ya motsa kadan yana cewa "Abdulhamid zai kula da abincinki in sha Allah, duk sanda kk da bugatar wani abu let me know... zaki iya serving abincinki da kankiko?, ina sauri zan iya makara" kai ta gyada masa, sai ya juya a hankali yana furta "Fi amanillah" da idanu ta bishi har ya fice daga dakin, tana jin kamar ta dawo dashi ta zaunar dashi a waje daya. *****Kamar yadda yace mata ne, cikin kwanakin duka busy din yayi. Amma hakan bai hanashi dubata da safe ba. Sau tari kuma Lokacin da zai dawo wani kasalallen bacci yayi awon gaba da ita, don haka bata sanin lokacin da yake dawowar. Duk yadda takeson space takeso kuma ya bata sai wannan abun ya gundureta, ta dinga blaming kanta da kanta, me yasa?, wal me yasa?. Duk da yanayin da take ciki me wahala amma hakan bal hanata hada program dinta ba. A ranar da ya zamana washegari ne ranar da zata shiga Tv station, takai har garfe goma na dare a zaune tana hada komai cikin laptop dinta. Ta kammala ta tattara komal ta aje gefe tana duba agogo, baccin da takeyi da wuri ne kenan ya sanya bata gane daren da yakey kafin ya dawo gidan ba?. "To ina yake zuwa?, har yakeyin dare?" Ta yiwa kanta tambayar. "Laila......ayana" ta tuna sunayensu, wani abu kuma ya darsu a zuciyarta, abinda ya sanyata taji kanta ya Sara kenan, ta saka hannunta daya tadan tallafi kan nata tana lumshe idanunta. Tsation mintuna goma sha biyar tana zaune a haka ta ji garar motarsa. Ta sauke hannunta a hankali tana kallon yadda hasken fitilun motar ke ratso labulayen dakin nata. Tana iya jin muryarsa gasa yasa da alamu waya yakeyi, ranta ta ji ya sosu, ta maida idanunta ta lumshe sai kuma ta mige tana wucewa toilet. Fitsari tayi don a yanzun ba wani rige fitsari takeyi sosai ba, sai kuma ta daura alwala kaman yadda ta saba duk sanda take da niyyar yin bacci, ta dauko garamin towel don tsane damshi sannan ta nufo waje. Yana tsaye tsakiyar dakin, hannunsa guda cikin al jihun wandonsa, dayan kuma dauke da wayarsa yana dannawa. Suit dinshi na saman yana rataye a kafadarsa. Haske wayar ya haske mata gajiyayyun qwayar idanunsa da suka rusuna saboda gajiya "Sannu da zuwa" ta fadi a hankali tana sake takowa xuwa bakin gadon. A jyar zuciya ya sauke yana saka wayar a aljihunsa "Yauwa, fatan kin wuni lafiya" "Alhamdulillah" ta bashi amsa "Yau bakiyi bacci da wuri ba kenan?" Ya tambayeta yana duba abincin da abdulhamid ya dafa yau din. Baki ta murguda tana harararshi gasa gasa. Bashi da aiki sai labta mata abinci?, ya temperature din jikinta yake?, yata wuni?, tasha maganinta ko a'ah, wannan duka suje abinda take da bugata? baisan yadda tayi missing gamshinsa ba?, baisan yadda tayi missing dumin fatarsa ba?, baisan yadda tayi missing air jinsa ba?, zazzafar rungumar dake bata peaceful sleep data jima bata sameshi ba?. Bata wani ci abun kirki ba, sal ya dago wayar idanun nan nashi masu kwarjini yana dubanta sanda take amsa masa ciki ciki da cewa "Eh "Me yasa bakici abinci yadda ya kamata ba?, kinaso ki haifa baby garami?" Ya mata tambayar seriously. Yadda ya tambayetan da kaifafanidanunsa ya sanya ya mata kwar jini, ta kuma ji wani nauyi ya saukar mata, saita kauda kanta ba tare data amsa masa ba "Lafiya kike yau?" "Eh" ta sake amsa masa a tagaice, shima sai ya jin jina kai kawai "Ba wani abu?" "Eh" ta kuma ce masa wannan karon har sai daya tada kai ya kalleta sosai. Idanu ya zuba mata, kamar zalyi magana sal kuma ya fasa, ya juya a hankali yana cewa "Allah ya bamu alkhair... well" ... sleep "Ina da aiki gobe" ta fada tana rige gugunta da hannu daya, ta fadi kai tsaye ne da haushin ya kasa fahimtar ta, ta kuma fada kai tsaye da fatan haushi da bacin ran da takeji cikin zuciyarta shima ya ji irinsa. Ta dade da sanin ba abinda yakewa yiyayya irin aikinta, shine kadal kuma abinda zal bata ranshi. Juyowa yayi kadan ya kalleta sai kuma yace "Allah ya kaimu, Allah ya kiyaye hanya" ya taka a hankali yana ficewa daga dakin.GUDUN KDDARA Chapter: B00K O2 PAGE 139 *_GUDUN KADDARA_* *HUGUMA* BOOK OZ PAGE 139 Da kallo yabi bayanshi har ya fice, sai abun yayi mata banbarakwal. Bata taba zaton haka daga gareshi ba, bata taba zaton zaya ce mata ta je haka kai tsaye cikin saugi ba, saita zame tana zama daga gefan gadon tana hadiyar wani abu ranta yana sake baci. ** **Ita daya ta gama shirinta washegari cikin gidan, don ko abdultamid bai bari ba, yana gama ayyukanshi ya sanyashi a gaba, sai daya fita sannan shima ya fice. Tana dining area tana wassafa yadda zataci abincin, duka ranta a jagule yake kiran goumar ya shigo mata. "Ki fito na saukeki, ina gofar gida" ya furta, mamaki yadan kamata, motarta na gidan ama, tayì zaton zatabi train ne kawai ko bus, tana kyautata zaton shine ya aiko goumar din. AjJiye yin breakfast din tayi ta dauki handbag dinta da sauran tarkacenta ta tito. Kaman basuyi kowacce magana ba jiya suka gaisa da goumar, saidai kuma ba wani karsashi tsakanin shi da ita ko wani dogon hira ko tsokana kaman yadda suka saba ya dauki hanya da ita. Har office sai daya tabbatar ya rakata, sannan ya karbi time da zata tashi ya fice yabar ma aikatar. Ta tabbata ta kuma yarda yau din a rude take, tarin kusakural ta dinga tafkawa wa jen alwatar da shirin, ta rasa nutsuwarta sam, wannan ya sanya dole aka haqura da sanya saka sabon shirin suka sanya malmalci na wancan satin. Daidai lokacin daya dakatar da duk wani aiki da yakeyi cikin office din, ya kuma kunna tv zuciyarsa na wani irin zafin tururin kishi, yana wassafa wanne irin kyau ne yau zatayi?, mutum million nawa ne a fadin duniya zasu kalleta?, zasuji muryarta?, za kuma su kira suyi magana da ita. Maimaicin da yaga an sanya ya bashi mamaki tare da tambayar kansa me yake faruwa, ya dinga sauke a jiyar zuciya shi daya kaman yaron da yayi kuka ya ga ji. Agalla ya samu relief tunda ba ita din bace live kamar yadda aka saba. Banda kakkauran warning din aba gareshi ko duk duniya zasu taru baiga wanda zai sanyashi barinta yin wannan aikin ba. Kasa kashe tv din yayi, yana kallonta kallon daya jima bai mata shi shi da ita ba. Ya fidda wayarsa ya fara kiran goumar. Yau ko dioura kasa doguwar hira tayi da ita, tadai tabbatar musu bata da lafiya. Hankalinsu duka ya tashi don basu taba ganin irin wannan yanayin tattare da ita ba. Ita daya ta wuce office din tana yogarin daidaita kanta. Ba jimawa kiran goumar ya shigo mata, ta bashi tabbacin ya shigo kawai su tati. **** ***Kusan tafiya ce data shafi dukkansu, aba ama dashi kanshi maina din. Sati biyu kacal ya rage bikin goumar din da najma, goumar din kuma yafi garfin aike a wajen ama. Yana cikin mutane dake da muhimmancida daraja a wajenta, don haka ta yanke datse komal nata su kuma wuce nijer da wurwuri don a shirya komal tare da ita. Sosal tayi mamaki da maina ya gaya mata zasu wuce ni jer tun a satin, sun tattauna sosal dashi,ya kuma shaida mata da benazeer da batoul da goumar din duka zasu wuce. Ganin kusan kamar cikin ayari ne tafiyar ya sanya ama tayi cancel din nata schedule din, ta siya nata ticket din, wanda tuni aba yayi gaba don akwai abubuwan da zai gabatar a Nigeria cikin abuja. Ita dinma an samu banbacin lokacin tashinsu da kwana daya, ama zata riga tashi, su kuma washegari nasu jirgin zai tashi. *** ** **A hankali take takowa cikin shigar bagar abaya me sulbi da tayi mata wani irin mahaukacin kyau, kyau irin na yaron ciki da kuma kyau irin na asalin halitta ga wanda Allah ya bawa. Duk jikinta bata jin dadinsa wannan ya sake sabbaba yaugi a yanga a komal nata wanda zaka zaci tana sane takeyi. Har yanzun jikinta yana bata tabbas tafiyarsu Niger ba haka siddan bane. Uwa uba yawan wayar da suketa yi da suhail da kuma sardauna abun ya wuce yadda suka saba. Dukkansu haushinsu takeji, tana danne zuciyarta ne kawai suna galsawa dasuidan har sun hadu bisa dole. Tayita zuba kunnuwa da ido ko zataji wani abu daga wajen ama amma shuru... hakanan tayita kasa kunne kozataji aba ya kirata shima bataji komai daga gareshi ba. Gefe bibi da take sanya ran tace wani abu itama shuru, kosu aminata da take sanya ran samun wani information daga garasu duka satinma basuyi waya ba, don sun shiga cikin sabgar bikin najma gadan gadan. Abinda ya sake rikita mata lissafi kenan, dai dal da goumar jira takeyi taga kiransa koda kuwa tsokanarta zalyi amma dif. Lissafinta ya fara bata kada dal ace kowa goyon bayan abun yakey!?, kada dal ace dukkansu sunyi hadaka wajen boye mata abinda komai sun goyi bayan maina dinsu?. Yana zaune bayan motar hayar da zata migasu airport yana amsa waya, saidal fitowarta kuma ta fusgi hankalinsa. Tayi masa wani irin kyau da ya sanya ya gaza dauke idanunshi daga kanta, har ta iso bakin motar ta bude ta shiga a hankali. sau biyu kafin su isa sardauna da suhall na kiransa, abinda ta fahimta ma kamar gaba daya zasu wuce, kamar Jirginsu daya kenan dasu?, turgashi ta fada gasan ranta tana jin wani zafi yana taso mata. Wayoyinsa yakeyi har zuwa sanda suka isa airport din. Dan dakatawa yayi kadan yana qarewa zirga zirgar jama'a dake wajen kallo. Akwai mutane da yawa dake kai kawo, alamun cewa yau din akwai matafiya masu yawa dake tafiya wasu kuma suke dawowa kenan. Ajiyar zuciya ya dan saki, har cikin ranshi yana jin kishi yadda zasu fita haka. Yayi imanin idanu ne zasuyi yawa a kanta, shi kansa yau din shigarsa tayi masifar tafiya dashi, yana jin wani irin kishi har tsakiyar zuciyarsa. Ta motsa zata bude motar ta fice ya furta "Wait" da sauri yana kama hannunta ya rige gam cikin nasa ba tare da yasan yayi hakan ba yana tsaka da neman number din goumar. "Eh mun garaso.....zo don Allat" daga haka ya kashe wayar yana gogarin kulleta. Idanunta ta sauke saman dogayen yatsunsa da suka ratsa nata hannun. Komai nashi ta kalla masu kyau ne, kaman yadda kusan komai nasa shi su batoul suka debo. Janye idanunta tayi don kada ya kamata tana kallonshi, bugu da gari kuma wani irin kishinsa taji yana motsa zuciyarta. Saida goumar ya iso ya fidda luggage dinsu sannan ya bude ya fita, ya zagaya ya bude mata ya bata hannunsa yana rige hannunta cikin nashi sannan ta fito. "Biyomu a baya" ya bawa goumar umarni, dariya ta tasowa goumar din ya gintseta. Abun ya motsa kenan, kishin aliyyu ba sabon abu bane ga duk wanda ya sanshi, ya kirashi ne kenan saboda yayi musu bodyguard?, goumar ya raya a ranshi. Tun kafin ta garasa shiga departure lounge ta Jiyo muryan benazeer da batoul. Tadan saki boyayyen murmushi, yau kam tasan kowa zia shigesu da surutu.....ba sukuni yau za'a nijer?, bibi taga ta kanta a hannunsu. Su suka fara ganinta, suka bar komal suka rugo zuwa wajenta, wanda dab da zasu iso maina yayi hanzarin shiga tsakaninsu da sultana yana daga hannu "Be careful mana BB, ban hanaku irin wannan welcoming din ba......ku taho a hankali" ya fada yana nuna cikinsa. Dariya yaran suka ayalqyale dashi sannan suka sassauta gudun zuwa sassarfa "Good girls" ya fada yana matsawa daga tsakaninsu. Wani irin kunya ce ta kamata ganin akwai jamá'a da yawa a wajen, saugin abun kusan da yawansu ba yaren sukeji ba, tabbas da a nijer ko Nigeria hakan ya faru sai ta kusa faduwa saboda idanu, saidai duk da hakan tana jin kaman akwai idanuwa a kanta. Ta canka daidal, idanunta basu zame ko ina ba sai kyakkyawan gani da sukayi saman fuskar laila da ayana, kowaccensu saman kujera daban, suna kuma rige da wayoyinsu a hannunsu amma dukkansu idanunsu yana kanta. Samun kanta da faduwar gaba tayi, tayi namijin gogarin dauke idanunta daga sashensu cikin nuna sam sam ma bata gansu ba, to amma me sukeyi a nan?, dasu za'a yi tafiyar? ¡dan dasu za'a yi tafiyar me zasuje nijer suyi?, meye alagarsu da familynsu?, indai duka tambayoyin nan akwai amsoshinsu, kuma amsoshin suka zama daidai da hasashenta hakan yana nufin... ...". Kasa garasa hasashen da zuciyarta tayi mata tayi saboda wata fargaba da taji ta saukar mata, saita soma takawa a hankali tana budewa benazeer da batoul hannuwanta tana yogarin canza mode nata saboda idanun da takeji suna kewaye da ita.*_GUDUN KADDARA_* *HUGUMA* BOOK O2 PAGE 140 Daga ayana har laila babu wanda bai hangi tsantsar dacewa me girma tsakanin maina da sultana ba. Wani irin matching da ba kasafai aka fiya samunsa tsakanin ma aurata ba. Wasu irin couples da suka dinga daukan hankulan mutane, tun daga shogowarsu airport din har zuwa wait lounge din. Kamannin dake tsakaninsu ita da maina din sai ya zama wani abu na musamman kuma na daban da ba kasafai ake samun irinsa ba. Tsakaninita da mainan saika rasa waye yaf kyau?, duk da a zahiri nata kyan ya dara nashi, saboda natan ya hadu da ado da gayu irin na diya mace. Daga laila har ayana ba wanda bai sake duban jikinsa ba... ba wanda baiji ya muzanta ba, ba kuma wadda bataga tarin fifiko dake tsakaninta da sultana ba, wauta ce ko ganganci shiga gonarta?, ko ratsa huruminta?, ko kuma hadakar masoyi da ita?. Sultanar irin mutanen nan ne da bangiji ya sanya suna da rabon abubuwa masu tarin yawa a rayuwarsu, kyau ilimi dukiya gata da kuma miji na kerewa sa'a, ga albarka ya'ya na gani na fada har guda biyu sukutum da guda tunda sauran quruciya sharkaf a jikinta. Wannan ya sanya duk wanda zai kalli su batoul baya taba kawo cewa su din wai 'ya' yanta ne, kallon gannenta kawai ake musu, don ko zaka kwana kana rantsuwa indai ba da qwaqwawaran hujja ba babu me yarda dakai akan hakan ba, ba kuma wadda bataga tarin fifiko dake tsakaninta da sultana ba, wauta ce ko ganganci shiga gonarta?, ko ratsa huruminta?, ko kuma hadakar masoyi da ita?. Tsam suka rungume gafafunta dukkansu, ta saki murmushi a nutse tana shafa kansu. Sunyi kyau matuga da gaske cikin wandunan jeans da shirt dinsu data dace da wandon. Rafafunsu sanye da rufaffun takalma, komal nasu iri daya ne kuma kala daya ne, ama bata taba yarda koda zaren ya rabasu, don haka hatta agogon dake magale a hannuwansu da kayan adon gashi da aka yima gashinsu ado iri daya ne sak da sak. Hannuwansa ta rige suna takawa zuwa rukunin wasu kujerun daban da basa kusa da inda su laila ke zaune, saidal duk da hakan bata jin ta tserewa ganinsu. Dukka hankalinta ta karkata akan yaran, sunata mata surutu tana biye musu, saidai fiye da rabin hankalinta gaba daya yana kan duk wani motsin maina da su suhail, wadanda tunda suka zauna suke qus qus, ba kuma zatace ga abinda suke tattaunawa ba. Abu guda daya ne kacal da zata iya cewa yayi mata dadi,bataga yaje inda su ayana suke ba, haka suma basuje ba, kawal dal zata iya ganin sanda ya daga musu hannu suma suka daga masa, sannan ya samu waje ya zauna cikinsu suhail din. Hannu takaita shafa cikinta jin yayi wayam kamar anyi yasa, ta daga agogon hannunta ta kalla, agalla akwai kusan awa guda a gabansu kafin tashin jirginsu, ita kuma bata jin zata iya jurewa har zuwa sanda zasu shiga jirgi a basu in flight meal ba. Benazeer ta kalla tayi gasa gasa da murya "Kiramin uncle goumar" amsa mata tayi tana sauka daga saman kujerar, ta kuma nufi inda goumar yake wanda yayi zaune yana waya da najma. Duk motsinta idanunshi yana kai, zakayi tsammanin baya gani ko baisan abinda ke faruwa ba, saidal har jininsa yana jin ita din priority dinsa ce. Har suka gama qus qus da goumar ya juya yana laluben hanyar fita don ya sama mata abinda zata ci din idanunshi a kai, sai yasa hannu ya yafici goumar din. A girmame ya davo yadan ranqwafo gabansa "Ina zuwa?" Ya tambayeshi yana kallon idonsa "Mummyn twins ce take jin yunwa, so zan sama mata abinda zataci kafin lokacin tashi". "Waye ya saka?, ba aikinka bane tafi ka bani guri" ya fada cikin kurari. Abun ya bashi dariya sosal, don suhail da sardauna dake gefe basuji ma abinda yake gaya masa ba, ya qunshe dariyarsa yana komawa mazauninsa, cikin ransa yana fadin "Dama nasan za'a rina, ina zaman zamana an jawomin kora da hali". Dubansa ya malda inda suke zaune din, akayi sa'a Idanunsu suka hadu guri guda. Cikin ido da fuskarta yaga rauni sosal, da gasken gaske take jin yunwa da alama, yadan motsa idanun nasa da wani salo na magana da ido, sai ta dan janye idonta kadan daga kanshi saboda qwayar idanunshi kadai suna sanyata jin abubuwa gasan zuciyarta da take gani bai dace ta ji a kansa ba. Kamar tana zurfafawa tana kuma zafafawar da bai kamata ace haka tayi ba. A nutse ya mige yana basu excuse ya nufi hanyar fita. Bai wuce minti goma ba duka duka ya dawo. Kai tsaye ya nufi kujerun da suke zaune bayan ya ja kujera guda daya ya a je gabanta. "Oya ku matsa mamanku da baby zasuci abinci" yace da benazeer da batoul wadanda sukayi kane kane saman cinyarta. Kai kawal ta daga ta dubesti, batasan me yasa baya kunyar yin zancan cikin da yaran ba kwata kwata, itakam ba zata ya ba, ko a yanzu ma kunyar yadda zata shiga nijer da wani cikin takeyi, bayan tsayin dukka shekarun da kuma irin kai ruwa rana da aka dinga yi tsakaninta dashi, yanzu ta dubiidonsu tace me?, bibi ma kawai tasan ta isheta. Suna dariya kuwa suka matsa din, yayin da idanu suka gara yawa a kansu. Saman gafafunsa ya dora abincin sannan ya bude, ya sanya spoon yana kallonta "Bismillat" ya fada yana tsareta da idanu. Ya lura kaman bata zama comfortable da cin abinci a gurin ba, don haka ya sake jawo kujerarsa gabanta. Sunyi kusa ainun kamar zasu hade gaba daya, amma kuma hakan ya zame mata garkuwa ya kuma bata nutsuwar fara cin abincin a hankali, har sai data goshi sannan ya janye jikinsa. Ko a cikin jirgi tana ankare da komal, saidal kuma ko a tuska bata nuna ba. Lailan da ayana seat dinsu daya, sai suhail da sardauna suma seat daya suke. Benazeer da batoul suna seat din gabanta. Kusan shine na garshe, ya garaso a nutse ya zaua seat din usa da nata bayan ya dudduba benazeer da batoul ya tabbatar komai lafiya. "Akwai wata matsala?" Ya jefawa sultana tambayar yana zaro wayarsa a aljihu don kasheta. "Alhamdulillah" ta amsa masa tana sake hade ranta, ta fahimci yadda ayana ke yawan waiwayowa tana kallonsu, ta tsani wannan bala in kallon da take dashi wanda batasan meye dallinsa ba. Sanda jirgi ya daidaita a sararin subhana sal dukka ga jiya da kasala suka saukar mata, ta cure jikinta guri daya bayan ta gama cin abinda zata iya ci daga in flight meal din da duka gabatar musu. Yana karance da ita,ya kuma fahimceta, ya sanya hannu ya dauko mini blanket ya ware ya lulluba mata. Wannan ya sake kashe mata jiki sosal, ta bishi da idanu, idanuwansu ya hadu guri guda. Ya karanci godiya takeson masa, Itace magale a bakinta, sai ya dauke kanshi a hankali yana maida idanunsa kan screen dake gaban kujerarsa yana duban map da awannin dake gabansu kafin saukarsu a niamy. Bazatace ga yadda tafiyar ta kaya, ba kuma zatace ga yadda akayi ba, tadal farka ta ganta kwance cikin air jinsa, ya mata wata irin kyakkyawar runguma data jima tana kewa, wanda kuma tayi imanin wannan hug din data samu shi ya sanya baccinta yin lasting har haka. Bataso ta motsa har yasan ta farka, don batasan da wanne ido zata kalleshi ba, awa nawa ta share oho...... kamar sunsan me take tunani sanarwa ta fara karade cikin Jirgin akan isowarsu niamy din. Tunda ta farka yaji haka a cikin jikinsa amma shima yagi ya nuna don ta samu nutsuwa da kyau. Hakanan shi shaida ne akan ta samu bacci me kyau na dukka awannin, baccin dashi kansa yayi mamakin yadda ta cinye awannin tana yinsa. A hankali ta zare jikinta, bai barta ta gama daidaituwa a zamanta ba ya soma qoqarin daura mata belt. Idanunta akan hannunsa sanda yake hakan, hucin numfashinsa da gamshin tattausan turarensa yana ratsa hancinta, take ta ji Jikinta gaba daya ya amsa, sai ta kawar da kanta gefe zuciyarta na gara yawan bugawar da takeyi. *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 141 Kusan tun daga nan bata sake ganin ayana da laila ba,hakanan suhail da sardauna. Suna zaune dasu benazeer maina din ya qaraso,ya dubi goumar "Nan da one hour flight din da zashi maradi zai tashi,so ina ganin is better ku zauna jirashi a nan,gobe in sha Allah morning flight muma zamu biyo" ya fadi yana kallon agogon hannunsa. "Yeah hakan yayi,awa dayan ai kamar yanzu ne" goumar ya fadi yana duba lokaci shima. "BB......see you tomorrow ko?" Maina ya fada yana duban benazeer da batoul. Qarasowa sukayi suka rungumeshi,sannan suka matsa jikin sultana dake tsaye wadda bata gama fahimtar abinda maina yake nufi ba. "Gaskiya zan bisu......banason kwana a niamy" sultana ta fadi tana gintse fuska. Waiwayowa yayi ya kalleta sau daya tak,sai ya maida kansa yana ci gaba da tafiya. Sak ta tsaya ranta yana baci,ta waiwaya sai suka hada idanu da goumar. Da ido yayi mata nuni da ta bishi,tayi kaman bata gane ba,dole ya buda baki "Why are you like this mummy twins?" Ya tambayeta cikin ranta yana jinjina soyayyar da maina keyi mata. Yadda ya sauka a boss mainan nan tunda ya shaqi iskar niamy kafin sukai ga shiga maradi ya tabbatar inda wani ne cikin shi ko su almu ko su aminata da tuni ya gamu da nasa tashin hankalin,amma da yake shalele ce bai tanka ba yadai soma nuni ne kawai da ido. Yaran ta kalla taga sun dan zuba mata idanu,kai ta kada,ba zataso ta dinga jayyaya da daddynsu a gabansu ba, zuciyarta a raunace tace "Ku gaida su bibi kafin mu qaraso" saita qarasa tana tana kumatunsu benazeer "Kuce nace ta tanadarmin abun dadi" dariya sukayi dukansu "Allah yasa ta baki,don itama bibi kwadayinta baya barinta ajjiye wani abun dadi" "Qaniyarku,uwatace dai" ta fada tana dan zare musu ido. Cikin sabuwa kar din fara BMW ta sameshi a zaune,ta bude baya kusa dashi ta shiga ta maida qofar ta rufe,driver ya tashi motar suna ficewa daga airport din. Hannunta taji ya kama a hankali ya sanya cikin nasa,yadan matsa har dai da taji zafi,ta saki qaramar qara tana kallonshi bakinta a gaba. Ba ita yake kalla ba sam,hasalima idanunsa suna kan titi "Taurin kai.....har yanzu wannan halin bai canza ba?......muna niamy zamu wuce maradi gobe.......kina da chance sultana...... Think twice" abinda ya fada kenan da muryarsa da tayi sanyi can qasa kamar wadda yayi jiyya. Da idanu ta kafeshi,tayita kallonsa ba qaqqautawa,tanason ta tantance me yakeson cewa. Cikin ba zata ya waiwayo suka hada idanu,ga mamakinta sai ya sakar mata murmushi duk kuwa da yadda taga yanayin fuska da idanunsa sun sauya,da alama wani abu yana ci masa rai "Inaso na huta sosai kafin mu sauka a maradi......i need your assistance" ya kuma fadi da muryarsa me laushi. Rasa me zatace masa tayi,dukka maganganunshi guda biyun kamar ya sanyata ne a duhu a kansu,sai ta zabi kawai tayi shuru akan ta furta komai,amma kuma maganarsa nacan qasan ranta tana kai kawo. Tun daga zuciyarta har gangar jikinta ita daya tasan abinda takeji,tanaso ya fahimceta a hakan da take,ya kamata kuma ace yayi hakan a matsayinsa na wanda ya raineta,rainonsa ce ita. Wani babban maison d'hôtes(guest house) sukayi masauki. Daga yadda aka karbesu ya tabbatar mata yana da matuqar kima da daraja a wajen. Daki na musamman aka basu,wanda suka taras da komai an shirya cikan dakin. Ba alatun cikin dakin bane ya dameta,abincin data gani kawai shine a gabanta. Tayita qoqarin mazewa har zuwa sanda ya wuce toilet,ta tabbatar wanka zaiyi zai kuma jima kafin ya fito,tunda tun ba yau ba ta sanshi da jimawa gurin wanka. Bata jira ya wani fito ya bata abinci yadda ya saba ba ta zagw ta hau qaramin table da aka shirya komai akai. An jima ba'a hadu ba, abincin qasarsu ta gado,yau ko tashin amai da tashin zuciyar ma bataji,ta dinga diban abincin tana aunawa cikinta,wanda batasan ma ta jima zaune tana aikin ciki ba sai da taji cikinta ya dauka,ta ajjiye robar madarar tana hamdala. Waiwayar da zatayi ta ganshi tsaye bakin qofar toilet,yana sanye da bathrobe data bayyana ni'imtacciyar sumar qirjinsa. Wani irin nauyi taji ya kamata,da alama ya jima yana qare mata kallo,sai kace wata kwancen yunwa?. Yadda tayi tsuru tsuru ya bashi dariya sosai,amma ya danne,yaci gaba da takowa,yanason yaga yau qarshen basarwarta. Daidai kanta ya tsaya yana duban yadda ta yiwa table din kaca kaca,sai ya miqa hannu yana daukan kwalin madarar data shanye har guda uku yana juyata a hannunsa. Madararta ta asali,madarar da akayi rainonta da ita,madarar data zame mata tamkar uwa......madarar da jama'a da dama suke jin haushinta saboda ita. "Inajin nan gaba ni zaki fara cinyewa idan kina jin yunwa......bari na rufawa kaina asiri" ya furta yan jawo wayarsa. Mutum biyu ya kira,duka kiran bai wuce na minti biyar ba,sai ya kashe wayar,yaja kujera ya zauna yana kafeta da idanunshi. Kai ta dauke,kallon da yake binta dashi yayi mata nauyi da yawa,amma da alama shi sam bayajin haka. Sau uku tana waiwayowa suna hada idanu,ana hudun taga ya miqe yana ja baya,ya wuce wajen qaramar luggage dinsu ya bude yana fidda kaya. Kafin yakai ga fara saka kayan tayi wuf ta fada bandaki,gaban mudubi ta tsaya tana fidda idanu kunya tana kamata,ta ware hannayenta tana kallonsu,ita kanta batasan haka taci abincin ba,madarar kuwa a baya kwali daya kawai take iya sha,amma yau gata da shanye kwali uku,ta lumshe ido tana tande baki,sosai madarar tayi mata dadi a harshenta,ta manta rabonta da shan madarar kwata kwata,a yanzun sai takeji ta koma mata sabuwa. Kafin ta fito ya gama shiryawa yaci abinda zaici ya kuma gyara wajen. Tana fitowa idanunta akan kwalayen dake jibge tsakiyar dakin,mamaki ya kamata,madarartace da take mutuwar so kwali kwali masu yawan data tabbatar zata iya gama rainon cikinta da ita. Ta fara takowa a hankali yana kwance saman sofa bed,bedside lamp ya haske idanunsa don duhun magariba daya fara shigowa. "Nayi rigakafi?" Ya tambayeta yana kallon kwalayen da idanu. Kunya ta sanyata juyawa baya da sauri tana komawa can bakin window din dakin. *********Tun daga gate din gidan ta dinga sakin ajiyar zuciya. MAYAK'I mansion house....... gidan da yake da dimbin tarihi cikin rayuwarta,tarihin da bazai taba goguwa ba a rayuwarta. Komai yana nan yadda yake,sai kyau da gidan yake dadawa ko yaushe saboda tsantsar kulawa da yake samu daga mamallakan gidan. Akwai alamun baqi jifa jifa tun daga farfajiyar gidan,abinda ya sake bata tabbacin da gaske kawai hidima cikin gidan,abinda kuma ya ninka fargabarta,tunani iri iri ya dinga darsuwa a ranta. Sanda ta shiga falon bibi tsohuwa me ran qarfe,ta sameta zaune ana duba sabbin dinkunan da aka kawo mata ita da masu aikin sassanta. Tana nan yadda take,sai tsufa data qara yi kadan,don a haka tana samun kulawa ta musamman daga 'ya'yanta,kowanne ba baya bane wajen bata kulawa. Baki bibi din ta kama tana kallon sultana da maina dake biye a bayanta wanda ita sam sultana dinma batasan yana bayanta ba "Idonku kenan?,tsabar salo ku iso qasar nan ku wani yada zango a niamy,nan din ta muku kadan kenan?" Tayi tambayar tana jifan maina da harara. Itadai sultana Allah Allah take ta qarasa gab da bibi ta samu waje ta qunshe kanta,don gani takeyi kamar bibin na ganin abinda ke tattare da ita,rashin sani batasan tuni bibi ta dade da sani ba,hasalima da abun take kwana take kuma tashi cikin ranta,kullum addu'arta ubangiji wannan karon ka baiwa wannan 'yar marainiyar taka da sauqi,ya ubangiji ka zama gantanta,ka fanshe mata wahalarta ta wancan karon. Hardewa tayi garin sauri,ta tafi tayi taga taga zata fadi,kafin hakan ya faru tuni maina ya cimmata da wani irin zafin nama ya kuma riqeta tsam,yayin da bibi ma duk da ciwon da qafafunta keyi ta miqe tana zabga salati kamar ba ita ke lanqwashe tana ciwon qafafu ba. Kafeta yayi da idanu qwayar idanunsa na nuna yadda yayi matuqar tsorata da yadda ta tafi zata fadin, muryarsa a maqoshi ya furta "Sannu......ki dinga kula.....don Allah.... Please" maganar data tabbatar daga tsakiyar zuciyarsa ya furtata,da alama ya kadu sosai da faduwar tata. Zame jikinta tayi a dabarance saboda idanu na kansu,kowa kuma sannu yakeyi mata,ta gyara lullubin kanta tana mamakin yadda bibi keta sababin batasan ciwon kanta ba har yanzu?,me yasa ba zata dinga abu a hankali ba?. "Don Allah bibi daga isowata?,ku duminki baki bari naji ba?" Ta furta a shagwabe tana narke murya,irin shagwabar nan data saba yi mata sanda tana sultana baby dinta. "Yo ba dole ayi miki fada ba,irin wannan gaggawar ai bata masu juna biyu bace" "Shikenan na shiga uku" ta fada tana jin kamar bibin ta dora mata dala da gauron dutse,ta tona mata asiri gaba jama'a,harda wanda baisan ma me yake faruwa ba yau ya sani,sauta juya da hanzari tana wucewa hanyar bedroom din bibin tana mita cikin ranta. Zamewa yayi ya zauna sosai yana gaida bibi din,shima bai tsira daga rigimarta ba,don meye bazai dinga saitata ba bayan yanzu ba ita daya bace?. Zukudi yayi yana kallonta,yau din da alama bibin da rigima ta tashi. Abun mamaki,mainan da ake hanashi ladabtar da sultana......yau shi ake bawa wuqa da naman hukunta sultana?,wato kowa dai yana son abinda ya fito daga tsatsonsa,kowa yana son abinda ya shafeshi,da gaske kuma bibin tanason ganin zuri'arsa masu yawa?. _KWANKWASON JIMINA_* *_TSUTSAR NAMA_* *_AMEENATOU_* *_GUDUN KADDARA_* _DUKKA AYARIN LITATTAFAN KUDINSU YA KAMA KAMAR HAKA_* LITTAFI DAYA_400 BIYU_800 UKU_900 HUDU_1200 _IDAN TA BANKI NE ZAKI SANYA KUDINKI A WANNAN ASUSUN_ 6019473875 Musaa Abdullahi safiya Keystone bank _ANTAYA SHAIDAR BIYANKI ZUWA GA WANNAN NUMBER_ 09166221261 *Masu tura katin waya ko vtu kuma kai tsaye wannan number zaku tuntuba* 09134848107 *Maqotanmu kuma al'ummar qasar nijer zaku tuntubi wannan number dinne kai tsaye don biyan naku kudin* 09033181070 *ZAFAFA FAMILY na maraba daku*🫂🫂🫂🫂🫂*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 142 "dakin bibi me dadi" ta fada tana sakin murmushi sanda ta shiga dakin. Ta furta haka ne saboda tuna mata abubuwa masu yawan gaske da dakin yayi. Gudun makaranta,boko da islamiyya gaba daya,gudun dukan yaa maina......neman wajen buya duka cikin dakinne. Murmushi ta sake saki tana hayewa gadon bibin,har cikin ruhinta da jikinta ta dinga jin wani dadi yana ratsata,tabbas kowa yabar gida gida ya barshi,quruciya kuma abune me dadi da tunashi yakan bawa zuciya farinciki da walwala. Hannu takai qasan gadon bibi,ta taba wata Locker nata da take ajjiye ajjiye. Kaman wasa ta saka hannu ta jawo locker din "Bibi da alqawari" ta furta tana murmushi. Komai nata da take ajjiyewa yana cikin locker din tun wancan shekarun,ba kasafai bibi take bari ake sauya mata furniture ba saboda duk sanda za'a canza din sai an siya me matuqar tsada,takan ce "A barsu basu tsufa ba,jikin da zashi cikin kabari qarqashin qasan qasa ya kwanta meye na buri kuma?" A nutse ta dinga fidda kayan ciki, murmushi na qwace mata,komai kuma tana tuna sanda ta ajjiyeshi a wajen,har zuwa sanda hannunta yakai kan wani kwalban turare. Ba komai a ciki,turaren ciki ya qare ya kuma bushe dai kwalbar kawai. Riqe kwalbar tayi da kyau cikin tsakiyar hannunta tana sakin murmushi,kwanyarta kuma tana dawo mata da sanda ta kawo turaren nan ta boye. Turaren ya maina ne,sanda yana ainihin zakinsa cikin gidan,sanda yana maina dan makarantar sojoji a niamy.......sanda ya kwashe mata teddies dinta karo na biyu,ta rasa meye itama zata dauke masa da zai bata masa rai,sai ta tuna da cewa mayen turare ne,kuma duk cikin turarukansa ba turaren da yafi so irin wannan. A sannan ta maqale ta window din dakinsa sanda yake neman turaren,ya dinga hargitse kayansa,yayi nema yayi nema cikin dakin har ya gaji,tana maqale a window tana masa dariya,tsautsayi ya sanyashi yaji dariyarta,ya kuma zagaya ya damqota. Koda yayi nufi hukuntata a sannan bibi tsohuwa me ran qarfe ta dire tace bata yarda ba,shi ya faye zafin zuciya,don kawai ya ganta a window din dakinsa sai yace ita ta dauka?. Bata mantawa haka ta taqarqare ta dinga sheqa rantsuwa harda qananun hawaye akan itafa ba itace ta dauka ba. Sanda tunaninta yakai qarshe dariyar dole ta qwace mata "Astgafirullah" ta furta a fili,ita kanta a yanzun idan tana tuna kalar quruciyarta abun dariya yake bata,komai nada lokacinsa a rayuwa. "Irin wannan murmushi haka?,ko bayan an rabu da oga kuma taninsa aka kebe anayi?" Muryar aminta ta ratsa kunnenta. Da sauri ta dago,suka hada idanu da aminata,dukkansu sai suka sanya dariya,aminata da tayi nauyi sosai ta qaraso tana hayewa gefan gadon bibi itama. "Boss yau ya iso gidan nan,tun baiyi magana ba naga kowa yana shiga hayyacinsa...." Aminata ta fada tana tuna waye maina din da yadda ya saita rayuwarsu. "Baki manta ba kenan?" Sultana ta fada tana duban aminata cikin dariya,tanason mata tsiyar nauyin da tayi tana tsoron kada taje ta tonowa kanta tata tsohuwar ajiyar "Inaaaa......waye zai manta da yaa maina?,ko su djamilla da suke tasowa yanzun baya zaune a gidan ai sun sani bare mu da muka rayu dashi" tana shirin tambayar yasmine sai gata tare da amarya najma. Bacci taso yi amma suka kashe dukka awannin a dakin bibi suna hirar yaushe gamo,basu suka bar dakin ba sai yamma liqis sannan balkissa me aikin bibi ta shigo ta gyara dakin,daidai sanda bibi din ke gyaran fallen alqur'aninta tana mitar jikokinta na gidan da suka ara suka lalata mata. "Don Allah balkissa idan kin gama gyaran dakin a maida canopéé din gadon nan yadda zanji dadin yin bacci" idanu bibi ta wurga mata "A ina?,ba dakina ba ehe.......ban iya diban zunubi ba kwana da matar wani a dakina" idanu Sultana tabi bibi dashi tana mamaki,yau ita bibi ke hanawa kwanan dakinta?. Ba ruwan bibi,don bata ma tsaya taji ta bakinta ba tayi gaba abinta. Wanka tayi ta sauya kaya,tana idar da sallar magariba taci abinci sosai irin abincinsu na gargajiya wanda a baya bata damu dashi ba. Madararta takeson sha matuqa,to amma batasan inda zataga maina ba bare ta karba,don tunda suka iso gidan bata sake ganin gilmawarsa ba. Dole ta haqura,ta yafa mayafinta ta wuce cikin gidan da bata samu shiga ba. Sassan oncle bashar uncle umar uncle issofou dukka tabi daya bayan daya suka gaisa. Sassan uncle umar da yake sassansu goumar tasan samu mutane don haka tafi jimawa a can. Tana can din taji ama ta dawo,tunda suka shigo gidan basu sameta ba,tasan kuma duk tana can wajen hidimar auren dan gaban goshinta ne. Ta iske sashen surukar tata kuma uwa a gareta fes cikin tsari fiye da kowanne sashe na gidan kamar dai yadda aka saba. Masu aikinta keta zirga zirgar shirya mata abinci,ita kuma tana nata dakin tana wanka. Tana zama batoul da benazeer suka fito wadanda tanja ta sanyasu sukayi wanka suka sauya kayan bacci,don ama tace kada su haura tara na dare yau basu kwanta mata ba. Yawon wunin yau kaf dasu tayi gaban mota. Su suka zauna suna rage mata lokaci da shirmen hirarsu. Duk idanunta sun daddaure don ita kanta a mugun gajiye take jinta,ga abincin da taci ya qarasa kashe mata jiki gaba daya. A shirye tsaf ama ta fito,idanunta da kulawarta dukka suna kan familynta sultana da yaranta. Tana yiwa ama din sannu itama tana yi mata sannu,duk kunya saita kama sultanan. A nan qasa ama ta sanya aka sauke mata abincin, sultana ta dinga zuba musu don cikinta babu space,madara kawai take da buqata kuma bataga me batan ba. Ama nacin abincin suna tattauna tafiyar tasu,har zuwa sanda zuwaira me aikinta ta qaraso tana mata sallama zata wuce sassan 'yan aiki. "Kafin ki wuce,ki tabbatar kin nemo almu ko saddi,su bude tsohon sassan yayansu su gyarashi don inajin yau dai a gidan zasu kwana,naga kuma jikin sultana ya fara nauyi zaiyi wuya bata kwanta da wuri ba" "To ama in sha Allah" ta amsa mata "Yayi da jiki don Allah" ta sake jaddadawa zuwaira "Yanzun kuwa in sha Allah". Nauyi da kunya suka sake kama sultana,tayi qasa da kanta tana wasa da serving spoon din hannunta. Ko a jikin ama taci gaba da sabgar gabanta,har zuwa sanda su batoul suka gama cin nasu abincin suka musu sallama suka wuce dakinsu dake manne dana ama. Kamar jira yakeyi su fita ya sako qafafunsa cikin falon. Yana sanye da wata kaftan abaya na maza kalar Navy blue. Kalar tayi matuqar haska farar fatarshi,yau din harda wata qaramar hula saman kanshi sample din tashi ka fiya naci,sai fuskarsa ta fita sak kamar wani baqin balarabe. Tare suka amsa sallamarshi da ama,amma ita saita dauke dubanta daga wajensa gabanta yana faduwa da wani irin kishinsa da taji yana taso mata. Shikam bai iya janye nasa idanun ba daga kanta,yayita qoqarin kiranta yaji ta samu abinci yadda ya kamata?,amma bai sameta ba,ya kira su almu atta da saddi dukkansu sunce basu ganta ba,haka yayita musu fada kaman su suka boyeta. Sai da yayi da gaske yayi controlling idanunshi, already ama ta ganshi,saita kame kanta da kyau itama tana basarwa. A gaban ama ya zauna yana tanqwashe qafafunsa ya soma gaidata. Ta amsa masa tana tura masa kwanukan abinci gabansa. Bai musa ba bai kuma ja ba saboda a mugun yunwace yake,ga tarin gajiya a jikinsa,tunda suka shigo garin bai zauna ba,ya jawo ya buda ya fara zubawa. Kadan ya zuba saboda dare ya riga ya fara yi, bayason cika cikinsa da yawa da abinci,ya fara ci suna ci gaba da magana da ama,duk sai sultana ta jita a wajen kamar a takure. Atta ne yayi sallama da maqullai a hannunsa "Kaine kayi aikin?" Ama ta tambayeshi. Kai ya gyada mata "Eh na gama" "Yauwa,tashi ya rakaki kije ki kwanta sultana,kada ki yarda don kin shigo cikin mutane ki dinga stressing kanki da yawa,kuje idan akwai abinda kike buqata ki gaya masa zai kawo miki" kaman zata nutse a wajen ta miqe tana mata sai da safe. Suna tafe a hanya ita da atta suna hira,hirar duka data shafesu ne abubuwan da suka faru da basa kusa,har suka isa qofar sassan yayi mata sallama ya juya ya koma. Kusan wanna shine karon farko da zata fara kwana a sassansa,duk sai ta jita wani iri,ta samu saman sofa ta takure tana qarewa sassan kallo. Sassa ne dake basu fargaba a baya,ba kuma kowa ke sbigarsa ba don me wajen bayason hayaniya ballantana shirme. An gyarashi fiye da zato,an qawatashi an kuma sake zuba komai sabo,bata sani ba aikin ama ne kona me sashen. Tana tsaka da wannan saqe saqen ya murda handle din yayi sallama,hannunsa dauke da 'yan qananun abubuwan amfani,kanta a kwance saman cinyarta tana jinta kamar a baqon waje ta amsa sallamar,sai ya qarasa yana ajjiye komai a muhallinsa,sannan ya tattako a nutse zuwa inda take zaune,saiji tayi ya dauketa cak daga saman kujerar yana fadin "Wannan zaman kin takura da yawa" bai mata masauki ba ko ina sai saman gadonsa,yasa hannu yana zare mayafin wuyanta,tadan motsa zata riqe ya girgiza mata kai "Ki kwanta kiyi bacci,nina na gaji,karki sake gajiyar dani da musunkinnan" daga haka ya juya yana ficewa daga dakin. Aqalla ya kusan mintuna talatin kafin ya dawo dakin,ta cikun dim light take kallonsa,ya dauki pillow ya haye saman sofa ya zube a hankali sabida gajiya yana ambatar sunan Allah saboda tsantsar gajiya. Tun tana sauraren saukar numfashinsa a hankali har itama baccin yazo yayi awon gaba da ita. *******Tana zaune daga gefan gado,yayin da yake tsaye daga gaban madubi yana sanya links na rigarsa. Wata zubabbiyar dakakkiyar shadda ce a jikinsa ya sanya wadda ta amsa sunanta wajen kyau da tsantsar tsadar da basai an gaya maka ba. Yana danyin komai a gaggauce ne,alamu suna nuna jiransa akeyi,minti bayan minti yana duba agogon Rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa. Tunda ya dora babbar rigar kayan saman jikinsa komai ya ida tsinke mata. Yayi wani irin fitinannen kyau,mahaukacin kishin da batasan tana dashi ba ya soma taso mata kamar zatayi amansa ta bakinta. Dafaffiyar madara take sha amma sai takejinta kamar ruwan madaci. Ya kammala shirinsa tsaf,ya kuma wadata jikinsa da sassanyan turarensan nan me tsayawa a zuciya. A nutse ya tako gabanta yana kallonta da narkakkun idanunsa dinnan dake nuna bai samu isashen bacci ba daren jiya. Taji tashinsa yakai sau nawa,taji shigarsa toilet ya kusa sau uku,duk fitowa kuma da alwalarsa yake fitowa,wannan ya sanyata samun yankakken bacci itama. Tana tsoron kada yayi ciwo irin wanda yayi a paris. Cikin kulawa ya duba mug din tea din dake ajjiye a gefanta,shi ya sanya aka dafo madarar,don ko yaya yake sauri yanason duk lokutan cin abinci ya zamana shi ya fara sanya mata wani abu a cikinta,hakan yana jin kamar yana wanke kansa ne daga tarin yunwa amai da wahala daya barta a cikin lokacin cikinsu benazeer. "Are you okay?" Ya tambayeta yana kallon qwayar idanunta. Har tsakiyar zuciyarta takejin wannan tambayar idan yayi mata,me yasa wai bazai tsaya ya kalli qwayar idanunta ba?,me yasa wai bazai karanci komai daga idanunta ba?. Kai ta gyada masa tana kuma basarwa tare da qin yarda ta kalli idonsa. Ture mug din yayi gefe,ya sanya hannu a aljihunsa ya fidda sabbi CFA masu yawa ya ajjiye mata yana fadin "Zamuje Nigeria gidan uncle tahir,ni da Sardauna da oncle issofou da oncle umar......amma ina sanya rai a yau din in sha Allah zamu dawo". Mummuar faduwa gabanta yayi,taji zuciyarta na wani irin rige rigen bugawa. "Me zasuje yi?,gidansu ayana?,nema masa auren ayana ko me?,da gaske yake?,......d gaske ya daga mata qafa?,da gaske ya barta kenan?,da gaske ya zabi AYANA DA LAILA a kanta?,kada dai ya zamana tsaiwar da sukayi da niamy auren LAILA ya karba?". Duk sauran abinda yake fada bata jishi ba,abu daya taji na qarshe saukar tattausan lips dinsa me sanyi saman goshinta,sai kuma qarar rufe qofar bayan fitarsa. Ji tayi kaman zata dimauce,duk yadda taso ta zauna a dakin ita kadai ta kasa,duk yadda take tunanin babu soyayyarsa ko digo a zuciyarta a yau din ta qaryata kanta sau babu adadi.....a yau kuma ta tabbatarwa kanta tarin TSANA DA QIYAYYAR da take tunanin tanayi masa ba komai bace face zallar soyayya fara sol mara sofane.......wajen waye zataje taji dadi?,waye zai rage mata abinda takeji a ranta?. Idanunta a rurrufe ta zura slippers a inda suke aje slippers nasu ta nufi hanyar fita,saita samu kanta da wucewa zuwa sassan bibi kai tsaye,tana jin itace dama me tallafar damuwarta,a yanzun ma ita zata taya idaniya da zuciyarta kokawa. Aba oncle issofou da oncle umar harda oncle bashar da shi kansa maina dinne zaune a falon,sun kammala karin kumallo suna yin sallama da ama da sauran dan maganganu da suka shafi yan uwa. Daga gefe su aminata ne da yasmine suke tsaye atta da saddi suna musu gyaran daya daga cikin freezer din bibi suna kwashe ruwa da lemukan ciki don sunaso suyi snacks su ajjiyeshu fresh,don dukkansu basu kadai bane,kuma kamar sultana suma basa iya jure yunwa,a nan sassan bibi ne kawai kuma suke da tabbacin zai tsira. Yadda ta shigo din kusan yaja hankalin kowa a falon,banda bibi daketa faman mita wa maina. Ita dinma idanunta basu gane mata kowa ba,ba wanda ta gani sai bibi kadai wadda hankalin da tunanin dama zuciyar gaba daya dama sun taho ne dominta. "Yauwa yaki nan" bibi ta fada tana yafitota. Dukka hankalinta ba abinda ya bata sai bibi ta kirata ne ta qara jaddada mata batun auren ayana da laila da maina zaiyi tare da bikinsu najma "Wai ke kika bawa wannan ja'irin damar tafiya Nigeria zuwa........." "Wallahi bani bace bibi........bani bace,bibi don Allah ki hanashi......ki gaya masa kada yaje.......inasonsa wallahi......ina qaunarsa bibi.......zuciyata ba zata iya jurar ganinsa da kowa ba......ina sonsa......kice masa nace ina sonsa,ina mutuwar sonshi fiye da yadda yake sona.....nafi sonshi bibi akan son da yakeyimin......yace aure zai qara.......laila da ayana yakeso yanzu......zaije Nigeria neman auren laila bayan ayana kuma...... wallahi bibi bazan iya jurewa ba" ta qarasa fadi hawaye yana sauko mata. Dif wajen yayi,kunya ta kama aba qwarai da gaske har ya kasa motsi,yayin da bibi mamaki ya kamata,sai kuma a sannan ta fahimci lallai hankalin sultana yayi gaba,bata kula da kowa a cikin falon ba sai ita. "Zo nan ja'iri,don qaniyarka abinda ka gaya mata dama kenan?,baka ko lura da ba'a gayawa masu juna biyu tashin hankali irin haka ba.?" Zancan bibi ya sanya aba zare jikinsa cikin dabara ya lalubi hanyar barin falon tun kafin sultana ta watsatsake ta sameshi a wajen. Wani irin sassanyan abu ya soma ratsa zuciyarsa yana narkar da wannan dunqulallen abun me zafi da quna daya tsaye masa a wuya tun ranar farko data soma ware idanunta ta kalleshi tace "Bana sonka!,bana qaunarka!,i hate you" "Dakai nake kaketa fama murmushi kaman wanda aka bawa tallan maclien" "Bibi" ya kirata a tausashe da wata irin murya da farinciki yake gauraye da ita "Ni nace mata ina neman auren ayana ma bare laila?......da bakina na taba gaya mata haka?…...sultana" ya kira sunanta yana takowa gabanta "Yau da zan fita na gaya miki ni zan nemawa kaina auren laila?......bibi kaman bakisan zancan suhail da sardauna akeyi ba kin manta?" Dif wuta ta dauke mata,a hankali idanunta suka fara washewa daga rufewar da sukayi,ta fara hango uncle bashar da yayi qasa da kansa,gefe oncle issofou ga kuma oncle umar.........*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 143 Dukkansu suka lula wata duniya......duniyar da basa gane kowa sai kawunansu,duniyar da a lokacin suka manta da kowa da kuma komai. Sirrikan zuciya ne kawai ke tona kawunansu cikin wani irin jirkitaccen yanayi wanda dukkansu su biyun basu taba fuskantarsa ba. Gigicewar qwaqwalwa da dimaucewar tunani.....ba abinda ke tasiri sai QAUNA me wani irin matuqar qarfi dake wanke laifuka ga zukata,ta kuma goge kowanne irin tabo bacin rai da kuma quncin zuciya. Suna tsakiyar wannan yanayin wayarsa ta fasa qara. Cikin zafin nama ya miqa hannu da zummar kasheta don baya buqatar komai da zai katse masa wannan yanayi me matuqar tsada a gareshi...... yanayi mafi soyuwa a gareshi fiye da dararen farko ga angwaye. Akayi rashin sa'a ya daga kiran a maimakon kashewa harda guzurin shigar da wayar handsfree. Muryar suhail ta fito fes ta cika dakin,cikin wata muguwar kasala ya zare jikinsa daga gareta a hankali yana sauke numfashi a jejjere kaman wanda yayi tseren gudu da dawakai "Zamuyi missing flight fa......kana duba time kuwa?" Lion eyes dinsa da suka qara girma suka kuma sauya kala ya lumshe yana furzar da iska,qoqarinsa ya daidaita numfashinsa kada yayi magana suhail ya fahimci yanayin da yake ciki "Hello.....maina" "Ina jinka" yayi qoqarin fadi "Wulaqancin naka ne ya motsa?,don baqinciki saida layi yazo kaina sannan zaka tsiri mugun halinka?" "Ni kake gayawa haka?" Ya furta calmly yana nuna qirjinsa da yatsarsa. "An gaya maka waye kai?" Ya fada da sautin dariyar da ake qoqarin boyewa. "Alright......to na fasa zuwa bazanje ba......kayi duk abinda zakayi,Allah yasa su hanaka lailan muga ta tsiya...." "Mugu saboda kai ka samu?....." Bai tsaya ya gama jin abinda zaice ba ya katse kiran gaba daya ya kuma kife wayar. Bai taba kawowa dukkansu zasu amshi batun laila da ayana haka da muhimmanci ba,koda yake ya sani wani abu ne kawai da ubangiji ya shiga cikinsa, bayan dimbin tarin addu'a daya dinga yi dare sur akan ubangiji ya kawo daidaito a tsakaninsu. Already an bashi laila,amma kuma madaurin aurensu yana Nigeria,sai suka yanke zuwa gaidashi hade da nemawa sardauna ayana. To amma shi suhail dinma yafi sardauna matsuwa da damuwa,kamar wanda akace an fasa bashi lailan. Da wani irin narkakken kallo ya waiwaya gareta,bai samu ganin fuskarta ba don ta duqunqune waje guda,ya sanya hannu ya birkitota,daidai sannan aka soma knocking qofar. Wani wawan tsaki ya saki yana sake adanata a qirjinsa da kyau,tana jin yadda zuciyarsa ke fat fat fat,ta lumshe ido tana jin sautin cikin kunnenta "Sulthana" ya kirayeta da wannan salon kiran da tayi imani duk duniya babu wanda ya kaishi iyawa "Anya zan iya ci gaba da zama cikin gidannan?,.a tabbatar bazasu barmu mu mori amarcinmu ba?" Kunyace ta kamata da abinda ya fada,wanne irin amarci da yara biyu ga tsarabar wani cikin ma?. Kafin wani a cikinsu ya sake magana aka sake knocking qofar sosai. Wani dogon tsakin da yaf na dazu ya kuma saki,jikinsa a matuqar mace ya miqe yana maida bottom na rigar shaddarsa da tuni tayi squeezing sosai,ya taka a hankali ya fita yana mita a fili. Numfashi taja sosai tana qanqame pillow tana jin yadda mararta ta daure sosai. Har ga Allah itama an shiga nata haqqin,kowanne bangare a jikinta yana buqatarsa,batasan haka tayi mahaukacin kewarsa ba sai yanzu,batasan haka ta zama addicted to him ba sai yanzu. A zafafe ya bude qofar,almu yaja da baya yana rabewa,ya sani ko ada ba mutum bane meson a yawaita masa knocking ba. Jirkitattun idanunsa ya kafeshi dasu,har sai shakka da tsoronsa suka saukarwa almu. "Ama tace na gaya maka aunty sultana ta shirya,ga dr noor nan zata shigo ta dubata" idanunsa ya maida ya lumshe yana dora hannunsa saman goshinsa. Bayajin zamansu cikin gidan zaici gaba da dorewa gaskiya,yasan muddin suna zaune ko iya kulawar ama garesu ba zata basu cikakken lokaci ba. Qofar ya tura kadan sannan ya taka yana komawa ciki. Yadda yayin. Ya ishi almu amsa,don haka ya juya yana barin wajen gami da sakin ajiyar zuciya "Allah ya soni". Ya fada a fili yana yiwa kanshi dariya qasa qasa. Cak ya dagota yana kallon qwayar idanunta ita kuma tana qoqarin boyewa,ya saki dariya a hankali yana tura fuskarshi cikin fuskarta yana laluben kunnenta "Baby yayi missing daddynshi?...." Riqeshi tayi da kyau kunya tana dawainiya da ita tana kuma boye fuskarta a jikinsa "Wait....." Ya furta yana qoqarin dagota,saita hanashi,wannan ya sanya hankali kwance ya sauketa gami da zaunar da ita saman sofa. Tana qoqarin kwanciya ya tallabota ta zauna sosai,sai ya sulale a gabanta ya duqa bisa dukka gwiwoyinsa,yasa tattausan tafin hannunsa ya riqe hannuwanta yana kallon tsakiyar qwayar idanunta "Sulthana" da fararen idanuwanta ta amsa masa,abinda ya sanyashi hadiyar yawu da qyar,ya tarkato sauran nutsuwar data rage masa yaja numfashi sosai sannan yace "A bedroom...... sulthana nakeso gani zahirinta...kin fahimta?" Wuya ta langabar tana narke masa fuska gami da turo lips dinta na qasa saita girgiza kai kadan "Ya salammmm" ya fadi da sauri yana runtse idanunshi. Yadda tayi masan gaba daya ta sake tsomoshi,sai yaji yana craving nata qwarai da gaske,kamar ya toshe kowacce qofa da zata sada jama'a dasu "Exactly wannan sultanar!" Ya fadi da karsashinsa yana nunata da yatsansa idanunsa cikin nata. "Sultana shagwababbiya....... sulthana sakakkiya........sultana mara jin magana........ sulthana mara kunya.......amma dukka a bedroom dina.......akan gado na......." Sai kuma ya sassauta murya can qasa "......idan mun fita waje kuma ki zama mummyn twins.......matar aliyyu maina.....the owner of my heart,my life and my breath.....kiyimin alqawari" ya fadi idanunsa yana lullumshewa. Kai tsaye a yanzun ta kalleshi da fari qal din qwayar idonta. "Ka fadi ko meye kakeso......ka fadi ko meye kake da buqata daga wajen sulthana......nayi maka alqawarin zaka samu fiye dashi" fuskarsa ya kifa tsakiyar tafin hannunta,hannunsa ya shaqi wani irin launin qamshi daya banbanta da qamshin jikinta,ya daga kansa a hankali yana sake kallonta da narkakkun idanunsa "Kiyimin alqawarin bani sabon ruhi......kiyi alqawarin bani sabuwar rayuwa......kiyi alqawarin lullube rayuwata da tsaftatacciyar soyayya..... kiyimin alqawarin rayuwa dani har abada..........ki sadaukarmin da raywarki sulthana gaba daya". Gaba daya kalamansa sun qarasa kashe mata jiki,har taji kaman qwalla zata fito daga idanunta,sai kawai ta zamo daga saman kujerar itama tana riqe da hannuwan nasa "Rayuwar sulthana naka ne yaa maina......ka manta da wadannan hannuwan ka raineta?,ka manta kaine ka kafa tubalin rayuwarta?,ka manta kaine ka bata dukkan wata rayuwa data dace da ita?,kaine ka bata qwarin gwiwar rayuwa ka kula da komai nata......kaine sulthana......kaine rayuwa da komai na sulthana,kaine numfashinta.....ka manta jininka ke yawo a jikin sulthana?,ka manta jininka aka zubawa sulthana ta miqe taci gaba da rayuwa?...." Idonsa ya sake lumshewa yana jinsa tamkar yana yawo cikin iska.......yana jin wani abu daya zarta farinciki yana dawainiya dashi "Zan baka fiye da rayuwar daka sanya rai a kanta.....zan baka sama da farincikin da kake mafarkin samu......zan zame maka tamkar uwa.....zan zame maka tamkar 'ya zan kuma zame maka mata......in sha Allah".. Duk dauriyarsa ta qare,babu wani sauran juriya ko dagiya tattare dashi ya jawota yayi mata wata wawiyar runguma. Sai digar hawayensa taji kawai tsakiyar kanta daya ratsa sassalkan gashinta dake tarwatse a gadon bayanta. Zuciyarta tayi wani irin laushi,jikinta ya mutu murus. Ya haidar da babu wani abu da za'a ce ya taba sanyashi kuka a iya tsahon sanin da akayi masa?,yau shine yake kuka a kanta har karo na biyu?,ya haidar me kafiya da tsaiwa akan raayi,me kuma tsatstsauran ra'ayin da baya canzawa yau shine duqe a gabanta yake kuka?. "Ba GUDUN QADDARA nayi ba sulthana.......ki yafemin......please......bansan da wanne idanu bane zan kalli su aba da bibi......na taba marainiyarsu......na taba ajiyar da suke riritawa......na taba halittar da sukewa masifaffen so......muddin na zauna a lokacin fushin aba zai iya lalata rayuwata,don bansan da wanne furuci zai jefeni ba......motsa zuciyar ama da nayi a sannan sannan kuma tana ci gaba da kallona zai iya saukar da fushinta a kaina......na tafi ne da zummar sai kowa ya huce sannan na dawo,ashe wata QADDARAR tana biye da dukanmu.....ashe ke din nabar mikia ajiyar bayin Allah cikinki......ni kuma qaddarar mutanen da zasu kamaji su nemi shigar dani kalar aikinsu yana bibiyata.....da qyar na kubuta daga hannunsu,sunmin daurin talala,sun barni inje dui inda zani,amma duk takuna qwaya daya tak suna biye dashi.....ashe bazanga girman daddyn sardauna ba?,me yasa bazan girmama musu laila ba?,shine silar kubutata daga hannunsu,ya daukeni ya bani kalar rayuwar da nake buri,duk kuwa da cewa......daga ranar dana aikata miki abinda ya farun duk wani buri na na zama soja ya zagwanye ya fita a kaina......na kalli kaina a madubi yafi sau shurin masaki ina gayawa kaina tabbas bani da imani......aikin soja bai dace dani ba.....tunda har na iya haikewa wannan 'yar qaramar babyn ta bibi......na iya sauke mata huqatuna masu girma da nauyi na shekara da shekaru ba tare dana duba qanqantarta ba......ashe dai wannan babyn itace rayuwata.....mabudin farinciki na...... wannan babyn ita zata zama mummy..... Mummyn twins da upcoming triples in sha Allah......." Ya qarasa fadi murmushin farinciki da nasara yana kubce masa. Duka idanunta ta zaro waje tana kallonsa,sai kuma ta shagwabe masa kwatankwacin yadda take masa a baya "Do you know how i survived yaa maina.....na kusa mutuwa fa kafin na haif......." Yatsansa ya dora mata saman lips dinta yana fadin "Shshshsh......." A tausashe "Nasan komai sulthana..... kowanne motsi na rayuwarki ina da information akai har zuwa rana ta qarshe a hassan gwarzo.....kina cikin depression da anxiety a lokacin...... yanzu kuma ga beloved person a gefanki.....Likitanki,duk da ba bangarena bane amma na miki alqawarin baki kalar kulawar data banbanta data kowa.......ke kika dasamin son twins sulthana......daga ranar dana fara ganin hotunansu benazeer suka zama jarrabawar rayuwata.....Allah ya jarabceni da soyayyarsu irin wadda bayan ke ban taba jin irinta akan kowa ba idan kika cire ama........ashe su din nawa ne......daga randa kuma nasan cewa nawa ne......a ranar burikana suka ninninku....Wallahi,Allah sulthana burina a duniya kiyita haifa min uku uku bibbiyu" hannunsa ta kama tana dariya ta aza saman goshinta,ta buda baki zatayi magana sautin wayarsa ya katsesu.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 144 Sunan ama ke yawo saman screen din wayar,ya saki sultana yana daga wayar. "Me kakeyi haka ne aliyyu?,ban gaya maka ga Dr Noor nan ba?" "Afwan ama....." Ya fada. A tausashe,bata sake cewa komai ba ta katse wayar,shima sai ya kashe yana ajjiyeta a gefen sa. Ido ya zubawa sultana kaman bazai dauke idanun nasa ba sai kuma yace "Get ready......yau ko gobe zamu bar gidan nan......zamu tare a namu gidan sulthana bazan iya zama a nan kusa ba" dubansa tayi,tana mamakin hakan da yace,don tayi tsammanin zai rayu cikin gidanne kamar sauran kawunnansu. Kai ya jinjina mata yana miqewa ya nufi toilet. Tsarki yayi yayi alwala sannan ya fito itama yace taje tayi,ya zare shaddar jikinsa data gama yamutsewa ya sauyasu da wani tattausan yadin vicuna me asalin tsada da aka yiwa aikin kufta na zamani. Ita kanta data fito sai daya dauki hankalinta,ta fahimci gayunshi ya ninka sosai,idan batayi da gaske ba da alama zai nuna mata feleqe da iya ado. Jawota yayi ya karata da jikinsa yana murmushi "Idan baki gaji da kallona ba mu zauna,sai na bawa Dr Noor haquri,mu shanye fadan ama tare dake" rau rau tayi da idonta. Duk sanda taga Dr noor sai ta tuna wahalan da tasha cikinsu benazeer,bata tunanin akwai wani guri dake daukan allura a jikinta da ba'a bulashi ba "Don Allah yaa maina......kace mata kada tayimin allura,ko magunguna kadan don Allah"ta fadi tana narke fuska. Murmushi ya qwace masa,ya saka tafukan hannayensa biyun duka ya kamo fuskarta tsakiyarsu yana matso da fuskarta dai dai tasa "Ki yarda dani....duk cikin da za'a raineshi cikin soyyaya da kwanciyar hankali daban yake da wanda ba'a raineshi ta haka ba,zakiyi lafiyayyen ciki fiye dana baya......ba allura ba tarin magunguna ba kwanciya asibiti........in sha Allah" da iya kalaman bakinsa kadai sun saukar mata da nutsuwa,ya sanya mata hijab ya kama hannunta suna wucewa falon. Bata tashi jin kunya ba sai da suka hada ido da Dr Noor. Ta tuna abubuwa da dama da suka wuce lokacin cikinsu benazeer,wai yau sai gata zaune gaban dr noor din da wani cikin. Ta dubata sosai ta kuma tabbatar da komai lafiya,amma tace "A kula da ita sosai,don cikin kamar wancan ne nake tunani" sai ya tuna maganar Dr Camille,satin da tace su koma tahowarsu nijer ya tashi basu koma ba,ya barshi ne da zummar zasu je din idan sun koma paris. "Wannan karon kamar kinfi jarumta ma.....kamar 'yan uku nake hasashe......" Dr Noor ta fadi cikin salon tsokanar nan nata "Amma sir maina yaci gari......don ba haka mukayi dake ba......" "Please don Allah Dr Noor" sultana ta fada tana qunshe bakinta cikin matsananciyar kunya,ta tabbatar tsiya Dr noor zatayi mata,zata tuna mata maganganun data dinga fada ne cikin quruciya da kuma damuwar da ta ninkawa kanta saboda cikinsu batoul. "Wani abu ne Dr?" Maina dake son ya samu abun tsonakarta ya tambayi Dr noor "A'ah sir.....abar kaza cikin gashinta" Dr noor ta fadi tana dariya dariya "Zan iya siyan labarin?" Ya tambayi Dr noor yana duban sultana data marairaice masa dariya nason zuwa masa,ya tabbatar ta sheqa quruciya me yawa shi yasa bataso aji. "Idan farashin yayi mani sai na siyar" Dr noor ta kuma fadi bayan ta gama hade komai nata "Dollar dari uku yayi?" "Ma sha Allah labari yayi tsada......tace ba zata sake ma aure ba bare ta haihu,ta gama haihuwa har abada.....su wadannan ma ita ba ita tayi cikinsu ba su sukazo suka shiga cikinta bata sani ba......kana zaman zamanka abu ya shige maka ciki yayita hura maka ciki cikinka yana zama qato don mugunta bayan kai ko abinci baka iya ci?.......at last kuma ta fashe da kuka......na shiga tausayinta a ranar irin tausayin da ban taba yiwa wani patient nawa ba". Da farko dariya tazo masa,amma maganar Dr noor ta qarshe ta narkar masa da zuciya har ya kasa dauriya ya sanya hannunshi ya lalubi hannun sultana ya riqe sosai cikin nasa. Bashi ba har dr noor din ma data tuna da labarin kana kallon fuskarta zakaga ta sauya. Ita kuwa murmushi kawai takeyi qasa qasa kanta a qasa, quruciya da wautar data tafka ke dawo mata. Koda ya bawa Dr Noor Dollar din qin karba tayi,amma ya sanya almu yabita da ita har motarta ya saka mata a seat din baya. Shuru ya ratsa bayan fitar Dr Noor,ya kasa cewa komai sai murza tafin hannunta kawai da yakeyi,yana hango irin jarumtar da tayi duk da quruciyarta,har yanzu ya kasa hasashen abinda zaiyi mata ya biyata "Am really sorry sulthana.....har yanzu sai naji kamar idan nace miki kiyi haquri bai wadatar ba" "Sorry for what ya maina?.....qaddararmu ce.....akwai wanda ya isa YA GUJEWA QADDARARSA,gudun qaddara fa guzurin tarar da ita". Kai ya jinjina yana mamakin yadda taji hausa haka,koda yake Nigeria ta zame musu kamar gida kuma uwa. Yaso zamansu ya dore a falon amma hakan bai yuwu ba,a hankali a hankali sai ga masu dubiya cikin gidan da baqi sunata shigowa. Dole badon yaso ba ya tattare falon yayi qaura yabar musu nan. Baisan bayanin da Dr noor ta yiwa ama ba,amma wani sabon salon jinya yaga an fiddo dashi. Ama din ta shigo da kanta sunyi maganganu da sultana,baisan me suka tattauna ba,amma ya damu mutane su janye yaji meye ama ta fadi?. Tanja ta aiko sashen ta soma gyaran wani bedroom din daban,da alama kuma umarni tanja ta samu,duk wani motsi na sultana tana kula dashi,sun hanata komai,komai tana daga zaune akeyi mata shi wunin ranar. Baya falon amma yana bibiye da komai shima ta CCTV camera din dake cikin falon. Yadda sultana din ta sake cikin mutane ya masa dadi,amma kuma yana jin su nesantashi da ita. Yana jin lokacin cin amarcinsa ne amma sunason kawo masa cikas. Wani abu da yayi masa dadi yadda ya fahimci time to time tana duban sashen dakinsa. Hakan ya masa dadi sosai,mutum ne shi me matuqar son a nuna soyyaya a gareshi,musamman ga abinda shima zuciyarsa ke matuqar so din. Sanda ya idar da sallar la'asar cikin masallacin layinsu sai yayi zamanshi daga gurin da shekarun baya yafi zama cikin gidan. Iskar wajen tana masa dadi qwarai tana kuma saka masa nutsuwa sosai. Kira ya shigo wayarsa,koda ya duba sai yaga sardauna ne. Sau biyu yana kira bai sameshi ba,don dama bai kira suhail ba,yasan idan ya kira xasu taba rigima yadda suka saba. "Boss.....sir.....surukina" duka sardauna ya fada lokaci guda. Murmushin nan nasa me sanyi ya qwace masa "Kaima yau?" "Ai dole,ba sake tabbatarwa da nayi dacen dan uwa ba irin wannan lokacin,familyn ama akwai karamci da mutunci,na dace da samun ayana......an bani ayana halak malak" "Alhamdulillah" maina ya furta a fili. Har cikin zuciyarsa yana jin farinciki yana ratsashi. Duk da sun soshi basu sameshi ba,amma kuma ya musu silar samun mazaje tamkarsa,yayi silar danganasu da inda yake tabbacin za'a riqesu kaman yadda zaiyi nasa qoqarin. "Saika qara masa da bayanin kawu ya karbeni hannu bibbiyu,laila ta zama tawa" ya jiyo muryar suhail daga gefe. Maganar tasa ta saka dole murmushin ya sake kubcewa maina,ya girgiza kai kawai yana fadin "Zamuyi waya anjima,amma wannan surukin naka ka samu majanyi da kyau ka daure masa wannan kan nashi dake fama rawa" dariya sardauna ya saki shima suka katse wayar a tare. Wayar ya mayar gefe yana dora idanunsa ga bangaren sashensa. Yana kallon yadda masu dubiya ke shiga suna fita,ya sake ajiyar zuciya. Bazai iya jurewa ba gaskiya,tunaninsa ya karkata yadda zai dauketa subar gidan.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 145 Koda ya koma sashen bayan sallar magariba still ba ita kadai bace. Daki ya wuce yana kumburi shi kadai,shi ya rasa wannan zaman na meye?,ko haihuwa akace tayi iyaka kenan ko?. Wannan abun ya sanya ya fara yanke shawarwarin bazai ma barta ta haihu a nijer ba,ya tabbatar idan ya barta haihuwa a nan shikam ya kade,tashi ta qare. Kafin ya fita sallan isha'i ya gwada kiran wayarta,tanata ringing amma bata daga ba,daya duba CCTV din daki sai ya samu wayar saman madubi,da alama a nan ta barta. Yaja gajeran tsaki,ya maida akalar kiran nasa zuwa ga yaronsa. "A gyara gidan da kyau,duk abinda babu ko ake da buqata a cikin gidan ka yiwa cha'aibou magana a zuba" "Okay sir" ya amsa masa da girmamawa. Bazai iya jurewa ba,sunzo gida hutu kuma ace an buge dayi masa haka?,haqurinsa a yanzu gajere ainun,gwara komai ta fanjama fanjam. Daya dawo sallar isha'i ma sai ya samu bata a sassan. Ranshi yaso baci amma daya tuna babu me aikata haka sai ama saiya hadiye abinsa. Ko ina fes an gyara,amma kuma bata ciki,duka sai yaji sashen ya masa zafi,don haka ya wuce toilet kai tsaye. Wanka yayi ya fito ya shirya cikin wani material cotton transparent na India da aka yiwa dinkin zamani me kyau. Sosai kayan suka karbeshi,turaren nan nasa me sanyin qamshi ya wadata jikinsa dashi,ya dauki wayoyinsa yana duba lokaci. Shi wato kota tashi ba'a yi ma bare a nemeshi a baci abinci?,rabonsa da abinci tun azahar,ya gyada kai,har yanzu fadar sultana kenan bata gama mutuwa ba. Sai daya shiga sashen bibi ya bata kusan awa daya,suyi hirar arziqi idan abun ya motsa ayi tsiya,har ya gama zamanshi ya miqe yana wucewa sashen ama,don dukka hankalinsa yana can. Kusan dukkan wata kulawa data bata lokacin haihuwar benazeer da batoul ita ama keson dawowa da ita a yanzun,itama tanata mamaki can qasan ranta, meye Dr noor ta gaya mata daya sanyata takatsantsan da ita irin haka?. Tunda ama tayi kiranta sashen nata ta kuma sanyata ta fadi da meye da meye takeso aje a dauko mata daga sashenta ta dinga tunanin to meye zatayi?. Daga sanda ta fahimci ama na nufin a sassanta zata zauna sai dukka jikinta yayi sanyi,ta lafe cikin kujerun ama kamar mejin bacci,saidai idonta biyu tana jin yadda aka tashi hankalin tsohon dakinta da gyara. Wannan karon ko daya bataji farinciki ba,bawai don batason zama da ama ba,ko kuma bata shaida kirki ko jin dadin da ama ke bata ba da dukkan wani nau'in kulawa da riritawa ba..... a'ah,zuciyarce kawai a wanann karon taqi yarda ta karbi nesantata da akeson yi da halitta mafi soyuwa a cikinta.........mutum guda daya tak.....amma daya tamkar da dubu a gareta wato ALIYYU MAINA. idanunta suna hango yanayin da zai shiga,a yadda ta hangi abubuwa bila'adadin cikin idanunsa akanta.....tasan hakan ba qaramin tabashi zaiyi ba. Bama maina ba,ita kanta bata da tabbas din zata iya jurewa?,zata iya karbar yanayin?. Wani tsohon tsumammen abu ke taso.mata a zuciyarta game dashi,wanda zata iya cewa bata taba jin wani abu irinsa ba a zuciyarta game dashi a wannan lokacin ba. Zuciyarta ta saba da sassanyan qamshin nan nasa data tsana,a yanzu tana jin kamar ta dawwama tana shaqarsa,dumin faffadan yawaltaccen qirjinsa,laushin da taushin gargasar dake kwance a ciki,dumin jikinsa da kuma dumin numfashinsa dukkansu wani abu ne da idan ta tuna takejin kowacce tsiga a jikinta ta tashi. Sanda take kaiwa qarshen duka wannan tunanin ta zuqi numfashi kafin ta aje nutsatstsiyar muryarsa dinnan tayi sallama cikin falon. Dukka jikinta taji kaman an zuba mata wani abu,zuciyarta ta soma sanyi,ta ware fararen manyan idanunta a kanshi. Cikin jikinsa yaji tana a wajen,ya wurga idanunshi kadan take suka fada kanta. Kamar yau suka fara ganin juna,wani shauqi yana fusgar kowannensu,ta cikin idanuwansu kowanne yake aikewa dan uwansa zazzafan saqo,ya dan qanqance idanunsa kadan kamar me tambayarta wani abu,sai ya sauya akalar tafiyarsa zuwa direction din da take. Duk taku idan yayi jikinta marabtarta yakeyi,duk motsinsa zuwa gareta sai bugun zuciyarta ya qaru da wani irin dokin zuwanshi gareta. Saidai kafin yakai ga isowar sautin muryar ama ya sanyashi tsaiwa cak sanda take magana ita da tanja suna fitowa daga kitchen din tanja tana biye da ita. Cikin hikima ya juya tamkar ba wajen yayo ba,saidai akace uwa uwace,kallo daya tak tayi masa ta fahimci ina ya dosa,amma ita dinma sai ta bishi a haka. Ta wuce zuwa saman kujera ta zauna tana tambayarsa yaushe ya shigo?,tanja kuma ta wuce wajen sultana tana miqa mata bowl cike da kankana da madara. "Na gode" ta fadi tana karba,ta sauke qafafunta qasa ta aza bowl din saman cinyarta ta fara kaiwa bakinta a hankali. Tun batayi nisa ba batoul da benazeer suka shigo,kai tsaye kowacce ta nema cokalinta zata sanya ciki. Maza maza ama ta korasu tana cewa "Wanann na mummy ne ita kadai,kuje tanja ta hada muku wani" tanja ta dinga musu dariya tana dan jan kumatunsu "Tun yanzu yayinku ya fara wucewa,ama ta fara daina yayinku yara" batoul dariya ta dinga yi, benazeer ce ta dan bata rai,don batason ace ama ta daina yayinsu. Yadda hankalinsa ke a kanta haka itama,ta gefan idanu take satar kallonshi tana tuna abinda ya faru dazun tana dan jin kunya kuma. Dama haka kishi yake da ciwo?,haka yake da radadi?,ash haka yake rufe maka idanu?. Batasan yaushe ta fara qaunar yaa maina ba har haka,amma maganar gaskiya bata jin zata iya rabashi sharing nasa da kowacce mace a duniya,tabbas a gaida matan dake da abokan zama,mazaje ne a ma'anar kalma. A nan tasa balkissa ta sauke musu abincin dare. Tayi tayi su batoul su taso suci suka qiya,an samu abun kwadayi. Ita da maina din suka fara yin dinner din. Yana ci suna hira jifa jifa da ama din,amma dai still hankalin da tunanin yana ta wani waje. Ganin goma ta gota ya sanyashi duba agogonsa. Ya saci kallon ama sannan ya saci kallon sultana. Wani tausayinta yaji yana saukar masa,ya tabbatar koda zatayi bacci ba irin baccin da takeso ba,yanason ya bata matsananciyar kulawa kamar 'yar tsanar roba.....yanzunne kuma dai dai wannan lokacin daya dace tunda ya mallaki dukka soyayyarta zuciyarta dama rayuwarta. "Sultana ki tafi ki kwanta hakanan.....jikinki bashi da wani qwari naga alama tun dazun,kamar qarfin hali kawai kikeyi" ama ta fada cikin tausayawa da kulawa. Murmushi kawai ta saki me kama da yaqe,ta yunqura ta miqe,sai ama din tace "Akai miki yaran daki,saisu tayaki kwana" "Baci gaba kenan?" Ta raya a ranta,don ba abinda take tunawa sai lokacin da maina yayi mata batan dabo a Paris,sanda take kwasarsu tayata kwana su debe mata kewar mahaifinsu da batasan tsumammiyar soyayyarshi ke walagigi da ita ba. Tana shirin wucewa sai suka hada idanu,ya saci idanun ama ya narke mata,ya wani koma kalar tausayi sosai,tadan kauda kanta gudun kada suyi abun kunya gaba ama din. Duk takunta daya zuwa daki sai yaji kamar ana gutsirar wani abu daga sashen zuciyarsa,duk takunta daya sai yaji kaman tana nesantar rayuwarsa ne,ya dinga qoqarin danne abinda yakeji din,amma sanda yaga sun gama shigewa dakin gaba daya sun yiwa idanunsa nisa sai ya gaza daurewa "Ama......am......" Yadan tsaya yana sosa qeya bayan ya kira sunanta. Ido ta zuba masa da kyau*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 146 Tana kallonsa,ta riga ta fahimci inda ya dosa,amma tanason taji meye zaya ce "Na'am ina jinka" "Nace wai....sultanar a nan zata kwana ne?" "Eh meye ya faru?" Ta sake jefa masa tambayar,kanshi yadan kawar gefe,yana matuqar kunyar ama,amma zuciyarsa na azalzalarsa,yayi imanin idan yayi kawaici daga shi har sultana din zasu cutu ne kawai matuqar cutuwa. "Ba komai.....kawai ba kasafai take iya bacci ba......" Sai kuma ya kasa qarasawa. Kobai qarasa ba ta fahimta,daga yadda take faman narkewa cikin kujera tasan dawar garin,tasan akwai ciki me matuqar son jiki,ta tabbatar kuma abinda ya samu sultana din kenan. "Wani ciwo ne da ita?" Kanshi ya shafa,yasan ama tana sane "Babu ama.....lafiya take" "To madalla......ni xan wuce ciki" ta fadi tana miqewa,don batason taci gaba da zama yaci galaba a kanta ko ya kashe mata zuciya ma. "In zaka fita ka yiwa tanja magana a rage electronics dinnan kada a barsu su kwana a kunne" baice komai ba sai ya miqe kawai,kaman xai yiwa ama din kuka,ya tabbatar inda shi din mace ne da kuka zai fashe mata dashi ko zata fuskanceshi,laifin ita sultanan da bata nuna komai ba. Yana tsaye har ama tabar falon tana wucewa sassan aba,ya dauke kai yana ji har cikin jikinsa tabbas ana nuna masa 'yan ubanci ne kawai. Zamanshi yayi a falon abinsa ya sauya tasha,tun tanja na leqowa za'a kashe wutar wajen har ta haqura,shima daga qarshe yace mata taje kawai zaiji dasu. Sai daya mula don kansa ya kashe komai,ya kuma saita komai ta yadda zayajin dadin shigowa a saquqe. Parking lot na gidan ya wuce,ya zabi mota daya cikin motocinsa ya fita da ita waje yayi parking dinta. A nutse ya jefa key dinsa da wayoyinsu aljihunsa sanda agogo ke nuna masa sha biyu daidai na dare. Ya tako a hankali yana barin sashen nasa bayan ya saka key ya rufe ko ina. Kai tsaye ya ratsa falon da babu motsin komai a cikinsa,ya dinga tafiya cikin nutsuwa kuma hankalinsa kwance har ya isa qofar dakin nata. Murzawa yayi ya tura ya shige,idanunsa suka fara sauka akan tanja dake kwance saman rug din dakin ta lulluba da babban duvet. Daga saman gadon fuskokin batoul da benazeer ne cikin duvet. Babu ita a gadon,amma qarar bude qofar toilet ya dauki hankalinsa yakai wajen. Itace sanye cikin wata tattausan rigar bacci off white data saukar mata har zuwa qaurinta amma basu qarasa rufe mata qafafunta ba. Kanta sanye da wata qaramar hula me kyau mahadin rigar wadda ta bawa sassalkan gashinta damar fitowa ta qasan wuyanta da gefan kunnuwanta. Sake zuba mata ido yayi kaman zai cinyeta danya,yayin da ita kuma ta narke masa hadi da shagwabe masa gaba daya tamkar benazeer ko batoul. Bawai ado tayi ba,amna sosai ta sake tafiya da imaninshi,Idanunta sun sake wani haske me daukan hankali,da alama cikin zai matuqar qara mata kyau. Hannuwansa dukka biyun ya bude mata,tamkar me jira ta tako da sassarfa ta fada qirjinsan nan da take matuqar kewa. Kyakkyawan masauki yayi mata,ya maida hannuwansa duka biyun ya lullubeta dasu,ta aza kanta sosai saman qirjin,sai ta sake masa wani irin shagwababben kuka "Shshshsh.......ya isa,yanzu zamu wuce,bazan iya jure kewarki ba....." "Tanja fa?" "Koda zata tashi ko idanunta biyu a gaban idanunta zan wuce dake.....oya take your jilbab" ya fadi yana sakinta. Tausayi taso bashi ganin yadda jikinta yake rawa wajen daukan hijabi,yayi imanin da lafiya lau take,sultanarshi me shegen dakiya da cinye abu bazatayi masa haka ba,duk da shi hakan ya masa,ya samu tabbacin yau zaya morewa amarcinsa yadda ya kamata. "Wait.....wait" yace da ita yana zare hijabin daga hannunta,ya juyashi daidai yana sakin murmushi "Babyn nan yana matuqar son daddynshi da yawa,kada fa yazo yafi su batoul son daddy" ta fahimci sarai me yake nufi,saita fada qirjinsa tana boye fuskarta "Allah......Allah ka bari" "Allah Allah dadi nakeji idan na tsokani baby sultana" ya maida mata amsa da irin muryarta da ta masa magana yanzun da ita. Banda wayarta bai bari ta dauki komai ba,ya riqe hannunta tsam cikin nasa suka fara takawa suna ficewa daga dakin. Fetal farfajiyar gidan,ba kowa banda security na gidan mutum biyu dake on duty ranar. "A sauka lafiya yallabai" shine abinda ya hadashi dasu,ya amsa musu suna ficewa,fitar data sakashi sakin murmushi,don ta tuna masa da wani abu,har ya kasa shuru,ya waiwaya yana kallonta sanda ta zauna sosai saman seat dinta shima ya miqa hannu zai tayar da motar "Lokaci makamancin haka na fice a firgice ina tunanin makomar rayuwata,da makomar rayuwar baby sultana......na fice da dimbin qiyayyata dana bari a zuciyar sulthana ta....yau sai gashi cikin wani tsohon dare zan gudu da wannan baby sultanar......amma a yanzun maman twins ce maman unborn sannan kuma wannan zuciyar a yanzu cike take da soyayyar mijinta..... uncle dinta kuma yayanta" murmushi me sanyi wanda ke cakude da kunya ya kufce mata,saita aza kanta saman cinyoyinta tana sakinsa a hankali "Ashe haka soyayya take da dadi?" Ta jefawa kanta tambayar "Ni ban taba qin yaa maina na ba...... Kawai dai nasan inajin haushinsa......ina kuma qyamar halayensa a zatona baida halin qwarai .....ashe zallar wauta da qurucciya ce ta cikamin kaina a lokacin". Wani irin murmushi ya kubce masa,kalamanta sai yakejin kamar sun qara masa qaimi da karsashi a dukka jiki zuwa zuciyarsa. Kasa jurewa yayi,ya miqa hannunsa a hankali ya lalubo tattausan hannunta ya maqale cikin nasa,yana driving da hannu daya,daya hannun kuma yana murza tafukan hannayensu guri guda,kadan kadan da wata irin lallausar murya yana farke mata dukkan wani sirri dake zuciyarsa game da ita. Ta kasa komai kaman yadda ta kasa cewa komai,sai idanu kawai da take lumshewa,kunnuwanta na sauraren kalamai mafiya dadi ga kunnuwan nata cikin muryar da har yau bataji wani sauti da yakai sound na muryarsa dadi da kuma ratsa zuciya ba. Ji takeyi kaman zata narke sabida yadda yake qara aza mata nauyin soyayyarshi,wanda kafin sukai gidan ya cire mata kowacce laka dake jikinta,ya kuma zare mata komai daga zuciyarta face zallar son kasancewa dashi. Daga qofar gidan kadai zakasan anyi gini na qasaita,gini na masu ilimi da ya cakuda da hankali,gidan ya tsaru da wata irin fikira......ba babba bane tangameme,amma a wadace yake irim wadatar da kai tsaye za'a iya a kirashi da babban gida. Tun daga falo suka zube warwas,daga shi har ita ba wanda yake da ikon sarrafa kansa ko yiwa kansa waigi,dukkaninsu burinsu shine junansu,a nan suka baje kolin duk wata tsohuwar soyayyar da aka fara ginata akan tubalin quruciya,soyayyar da akayi tsammanin ta uba da 'ya ce kota kawu da diyarshi,ashe tsumammiyar soyayya ce da zata juye musu zuwa wannan fuskar. A yau yarinyar da yakewa kallon yarinya ta gigitashi fiye da yadda duk wani hasashe nashi yake bashi. Ta kaishi wajen da tabbas yayi imanin inda abune wanda ubangiji bai hukuntashi a matsayin sirri ba ba shakka da yayi matuqar jin kunyar da baisan da wanne idanu zaici gaba da kallon kowa ba,sai Allah ya sanya suna cikin wata sirrintacciyar duniya ce,wadda daga ALIYYU MAINA sai SULTANA HAMANI. Koda komai ya daidaita sai ya rasa nau'in abinda zai zama sakayya ce a gareta,bakinsa ya gaza furta komai,sai qwalla data cika idanunsa har kuma damshinta ya taba gefa fuskar sultana. Sake lafewa tayi cikin jikinsa,me yasa aliyyun yake saurin yin kukan a kanta?,bai taba kuka akan kowacce diya mace ba,kuma ita din shaidace,amma yayi kuka a kanta karo na kusan hudu ko biyar a iya abinda zata iya riqewa kenan,kodai yana cikin nau'in mazan da tsananin soyayyar mace ke saka jarumtarsu guduwa?. "Maina bashi da wata jarumta indai akan sultanar ne,zaki iya kiran maina ragon namiji indai akan sultana ne......kina mamaki idan kikaga hawaye na a kanki?" Ya jefa mata tambayar yana wasa da sumarta. Kasa amsa masa tayi tanason auna mizanin son da yake matan "Soyayyarki cikin jinina take sultana tun ba'a haifeki ba......kin taba jin ka fara son abinda babu shi?......inajin daga kaina aka fara,tun ba'a haifeki ba na fara jin ina sonki sulthana......ya zuwa yanzu kuma mahaukacin so nake miki wanda bansan yanda zan fasalta miki ba......ki soni kawai ki kuma gwadamin a aikace wanna kadai shine qila zai gamsar dani" ya fadi yana sake riqeta ga jikinsa sosai. Kasa amsa masa tayi illa bugun zuciyoyinsu dake tafiya lokaci guda da ya dinga shiga kunnenta,sannu a hankali jikinsu dukka ya ida mutuwa, Allah yasa sun sauya masauki zuwa bedroom dinsa. Wani irin bedroom da ta dinga kallon tsarinsa da fasalinsa yana bata mamaki. Tana ji ya jawo duvet ya qarasa lullubesu gaba daya yana sauke ajiyar zuciya me nauyi tare da maida idanunsa ya rufe. ******Tun da asuba da tanja ta tashi sallar asuba taga bata ga sultana ba. Da fari ta tsammaci tana toilet dinta,ta zauna tayita jiranta shuru,ta dauka wani uzuri ne ya riqeta,don haka saita bar dakin ta shiga wani ta kama ruwa ta daura alwala ta dawo. Har ta idar da salla ta kammala azkar dinta shuru ba ita ba motsinta,wannan yaja hankalinta ta duba bandakin wayam. Tunaninta sai ya karkata akan ta koma dakin ama acan ta kwana qila tunda ama tana sassan aba. Bata damu ba ta tayar dasu batoul sukayi alwala sukayi sallah. Xuwa sanda gari yayi shaa tayi musu duk hidimar data saba,suka fice kitchen ta tarda su bilkissa suna hidimar hada breakfast. Haka sassan ama yake duk lokacin cin abinci. Girki akeyi sosai,saboda bata daukewa duk meson abincin sassanta ba zuwa ya diba yaci,wannan ya qara siya mata qauna da soyayya da kuma girmamawa ta yaran gidan,duk kuwa da cewa kowanne sassa na gidan wadace yake da abinci,kuma ba inda zaka shiga bakaci ka qoshi ba. Ana kammala breakfast din ama ta shigo. Kaman kowacce safiya da kwalliyarta suke ganinta,ba zaka taba ganinta haka ba. Suka soma gaisawa cikin girmamawa ita kuma cikin mutuntawa. "Yau kun kwana da mommy,Allah yasa kun barta ta samu bacci" ama ta fadi tana jan su batoul da wasa. "Ai inajin sun matsa mata ne ma yasa ta gudu dakinki cikin dare" tanja ta fada tana dariya "Dakina kuma?" Ama ta tambayi tanja cikin mamaki,don ta biya ta dakin ta shirya kafin ta iso nan,amma bataga alamar ma an shiga dakin ba "Eh bata kwana dasu ba" mamaki yadan kama ama,saita juya tana duban zuwaira "Dubamin wajen bibi sultana tana can?" "To" zuwaira ta fadi tana sakin suyar chips da takeyi ta fita a kitchen din. Ba dadewa ta dawo ta gaya mata tun jiya bibi bata ganta ba,tace ma ta turo mata ita idan ta tashi a bacci. Kai ta jinjina kawai tana sallamar zuwaira,tana juyawa suka hada ido da tanja. Dariya tanja keson saki amma ta cinye,saidai duk da haka ama ta ganota "Kin gane abinda yaron nan yayi kenan ko?" Dole dariyar tanja ta kubce "Kiyi haquri ama,yaran zamani?" Kai ama ta gyada "Zaici qaniyarsa.....baisan shi akewa ba?,ni dashi ne" ta fadi tana ciro wayarta daga aljihun doguwar rigar jikinta. _to ama dai da kinyi haquri cikin wanga sha'ani_ _na fara jin qamshin gama littafi,wata tace wai na yiwa Allah kada na yanke,alqur'an saidai kuyi haquri na rubutu jama'a 😂_*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 147 Kiran wayar ama ta shigo wayarsa daidai sanda yake bare mata kwalin madara ta biyu ya miqa mata. Da hannu biyu ya tallabe kumatunsa yana kallonta,kowanne motsi da zatayi a yanzun ba abinda yake tuna masa sai wannan little sultanar tashi daya raineta da hannunsa. Yadda takecin abinci na daya daga cikin abinda yake bashi mamaki,don ya sani,ita din ba gwanar abinci bace,shine daya tilo dake tursasata cin abinci a yawancin lokuta. Amma yanzun zaka rantse bata taba cin abinci a rayuwarta ba sai yanzu. "Ki ragemin don Allah mana" ya fadi yana langwabe kai sanda ta dauki ragowar apple din da yayi saura guda daya "Wannan din?", Ta fada tana daga masa shi sama. Kai ya gyada yana dubanta "Ka gyara zamanka ma idan na cinye ban qoshi ba dakai zan hada" gefe ya janye qafafunsa yana dariya "Ai na sani,zaki iya aikatawa,wannan cin abincin naki kamar keda wasu kike ci?" "Nida wasu ne mana" ta fadi tana dariya qasa qasa gami da dora yatsanta saman cikinta. Idanu ya fidda yana murmushi "Kema kinason sake haifan twins?" Kai ta gyada tana murmushi. "Ban taba so ko sha'awar ba duk da gidansu kakan ummana gadon hakan sukayi..... Ina ganin haifan 'yan biyu a wani abu me ban tsoro da wahala......basa ban sha'awa......kwatsam sai ga batoul da benazeer da sukazo a lokacin da ban shirya zuwan nasu ba......na gigice akan hakan ashe su din sanyin idaniya zasu zamemin....." Murmushi ya saki yana lumshe idanu. Tun baya tun asali can yana mutuwar son wannan muryar tata,ko sanda take magana din idanunsa nakan jajayen lips dinta dake motsawa da wani irin yanayi, yanayin da ya tuna masa da daren jiya. Daren jiyan kuma ya shiga cikin tarihin manyan darare masu daraja a wajensa da bazai taba iya mantawa dashi ba. Hannunsa ya miqa yana riqo zara zaran yatsunta yana dubansu,sai kuma ya maida kallonshi kanta "Kinsan irin kyautar da kika bani kuwa daren jiya?" Ya jefa mata tambayar muryarsa da wani irin laushi kamar ba aliyyu maina ba. Kunya ta sauko mata,don ita kanta a karan kanta batason tunawa,ita kanta tasan ta taka rawar gani ba kadan ba,saita kauda fuskarta gefe "Sulthana" ya kirayeta da wani irin sound da ya sanyata ta gaza jurewa ta miqe zumbur,amma sai ya sanya hannu da zafin nama ya fincikota jikinsa yana qyalqyala dariyar kunyar da yaga ta dabaibayeta. Bai mata matsugunni ako ina ba sai a saman cinyarsa,ya riqota sosai yana cusa kansa tsakanin wuyanta da kunnuwanta,kiran wayar ama ya katse masa hanzarinsa. Ganin sunan ama ya sanyashi dole ya saketa,yayi gyaran murya yana gyara throat dinshi da kyau don kada ama din taji wani abu,sannan ya daga kiran yana yin sallama. "Barka da safiya ama" "Aikai zan yiwa barka maina.....sannu da yin gaban kanka.....daka daukemin yarinya ka gayamin?" A handsfree take,sai ya waiwaya yana kallon sultana data zame ta zauna a qasa tunda taji ya kira sunan ama "Am sorry ama.......na shiga daki na sameta ta kasa bacci.......kuma ma.....na gaya miki bata iya bacci ama......idan na barta ita daya ba zata samu bacci ba......kuma yana da hatsari ga lafiyarta da lafiyar juna biyunta....ki tambayeta she's fine ama......i promise zan kula da ita......zan kula da ita da duka iyawata,bazanyi hurting nata ba....." Ya bawa ama amsar takai tsaye,tunda ya rasa ta wacce hanya zai gaya mata yadda zata fahimceshi. "Ya isa" ama ta fadi da sauri tana katseshi gudun kada ya fadi wani abun da zaifi qarfin kunnuwanta. "Kasan me Dr Noor ta fada?" Kai ya girgiza da sauri "Tana tunanin yara uku ne a cikinta,so dole a kula da ita sosai,bata buqatar takura tana son hutu sosai.......inda zai yiwu ayi keeping nata daban a gef......" "Allah ama bazan iya ba" ya fada da sauri yana katse hanzarin ama "Bazan iya yin nesa da ita ba......amma nayi alqawari bazan takurata ba ama har zuwa sanda kika iyakance....." Nauyi ta danji kadan,saboda akwai abinda takeson nusashshe dashi. Wayar taji an zare daga kunnenta,koda ta waiwayo sai taga aba ne "Aliyyu" muryar aba yaji ta maye gurbin ta ama "Barka da asuba aba" ya fadi yana dan rusunar da kanshi gami da sosa tsakiyar kan nasa,can qasan ransa yana jin zuciyarsa fal nadamar zuwa nijer,inama yayi zamanshi da ita a can,wannan damar datazo masa zatafi kyau a Paris,nan din da alama za'a matsanta musu ne a hanashi samun duk wani abu da yakeso,a hanamishi ginin da yakeso ya sake yiwa zuciyarta da rayuwarta. "Alhamdulillah....... Kayi zamanka da matarka.......ka kula da ita,babu me rabaku.......amma tana buqatar hutu sosai,ka bata hutu,karka matsanta mata kada ka takura mata saboda kare lafiyar abinda yake cikinta,ka daga mata qafa please ka fahimci abinda nake magana akai ai ko?" Bai taba jin kunyar aba irin yau ba, abinda ama keta son fada masa kenan ashe taketa gewaye gewaye?,yau din muryarsa har wani dan nauyi tayi saboda kunya "Na fahimta aba,Allah ya qara girma" aba din bai amsa masa ba ya kashe wayar,sai ya juyo yana kallon ama da tayi tsaye a tsakiyar kitchen din bayan kowa ya fice ya barsu da aman. "Yanzu da kanka kayi masa bayanin aba?" Ama ta fadi tana qaramin murmushi,can qasan ranta kuma tana jin farincikinta yana dawo mata. Bata da tashin hankali kullum kwanan duniya idan ta kalli aba ta kalli maina taga babu cikakkiyar fahimtar juna jituwa da shaquwa shi da babban dansa,babban dan nasa da zai zama kamar magaji a wajensa. Murmushi aba ya saki,bai bata amsa ba sai daya matso kusa da ita,ya lalubi hannunta ya damqa mata wayar sannan yace "A qyale aliyyu haka......ya cika d'a na halak.......yayi dukkan qoqari yayi kuma biyayya......ya dauki dukkan sharadi da qa'ida da doka dana sanya masa koda akan gaskiyarshi ne......for now aliyyu zai huta....... shima ya jishi magidanci kamar kowa...." Tsaiwa yayi ya maida numfashi sannan ya sake matsa hannun ama din "A yanzu ne ya samu abinda yake da buqata,so nayi imanin bazaiji ba bazai gani ba,saidai ki masa dabara kaman yadda nayi masa,ki kumayi addu'ar Allah ya tsare abinda yake cikin nata.......she will be fine in sha Allah......amma aliyyunki dai saikinmasa uzuri......ba lallai ma su dawo gidan nan kwana kusa" ya qarasa fada yana sakin murmushi me sauti hadi da jan hancin ama. Riqe hannuna ama tayi tana dariya dariya "Wato like father like son ko?" Kai ya girgiza yana dariya "No......wannan ba haka bane....." Qasa qasa yayi da murya kaman wani zaijishi "Twins yake badawa wanann ga triples suna tafe.......abbanshi daya daya ya dinga bayarwa,da aka karbi uku ma sai akace an daina karba haka nan" kunya tadan kamata,ta masa hararar wasa tana cewa "Basai ka kawo danya shakaf ta qaro maka wasu ba" dariya ya sake "Inaaaaaa...... hamidou mijin mace daya ne in sha Allah....... Har yau bai manta wahalar da yasha kafin ya samu hamdiyya ba,am belongs to you forever" murmushin jin dadi ta saki,har jiya har yau har kuma gobe lafuzzan aba a kanta saika zaci yau din ya fara saninta. Ido ya lumshe yana jin dadin maganar da suka gama da aba din. Yau din aba ya gama biyanshi dari bisa dari,ya bashi license ya sake sakar masa ragamar komai,ya bashi cikakken 'yanci. Ya saki murmushi sanda ya hangi sultana na juya kai cike da kunya. Tsam ya miqe ya isa gareta,ya sanya hannu ya sureta yana dariya "Waike kunya ko?, zakiyi bayani ne.....donma bance masa ke kika dinga roqona Allah annabi nazo na daukeki mu gudu ba" kukan shagwaba ta fashe masa dashi tana dan dukan qirjinsa,sai kuma ta riqe wuyanshi da kyau takai masa cizo a lips dinsa. Qaramar qara ya saki shima yana sane ya fara murza lips din nasa yana fadin bazai yarda ba sai ya rama. Ta dinga qyalqyalewa da dariya tana boye kanta a jikinsa. A fannin rayuwa raino da kuma nunawa juna zallar soyayya sultana din za'a iya cewa tsohuwar dalibarsa ce. Halayyarta da nashi kusan ba baqin juna bane. Raino da kulawarsa a gareta ba sabon abu bane,banda qaddara data gifta tayi kuma sanadin tarwatsewar komai tare da manta zallar sadaukarwa rayuwarsa da lokacinsa a kanta.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 148 Wata sabuwar rayuwa ya soma shimfidawa ruhinta. Wa ta rayuwa ya fara tsara musu,irin rayuwar da yakewa kanshi mafarki,irin rayuwar daya jima yana yiwa sultana sha'awa,irin rayuwar da a baya yakan zauna yana tsarawa bibi itace irin rayuwar da yakeso sultana tayi a gidan aurenta,irin rayuwar da itace mafarkinsa akan sultana. Rayuwar ta dinga wanke da goge komai daya faru a rayuwarsu ta baya,rayuwar data dinga tuno da tsohuwar dangantakar nan dake tsakaninsu,dangantaka me matuqar danqo,wadda ta shimfidu cikin jini da jijiyarsu tun kafin zuwanta duniyar ma gaba daya. Irin kulawar da yake buri da fatan sakawa a tsakiyar tafin hannun 'yar nafessa. Duk wani sauran tausayi da jin qai da yakewa nafessa din ya juyewa sultana shi tasss.......duk wata riritawa da kulawa da yakewa sultana fata dukka ya juyeshi. Ba abinda yakeso ya tabata,bayason tayi motsin komai,bayason ta rasa komai koda na daqiqa daya ne. Ta soma irin rainon cikin da yake cika mata baki akai,dukka wani kulawa da riritawa data samu daga wajen ama lokacin cikinsu benazeer saita zama lami.....ta kuma zama ba komai ba akan salon nashi kulawar. Soyayyarsa wani irin abune dake ratsa jini da jijiyarta,ya dinga narka mata duk wata kafar jini da zuciyarta,ta dinga juya tsananin kulawa da tattalinsa a gareta. Tayi dukkan yunqurin ganin ta taka rawa itama don ta bashi kulawa amma ya hanata wannan,saita tattara dukka tunaninta da akalarta wajen bashi kyakkyawan kulawa a shimfidarsa. Kulawar tata saita zama abu mafi tasiri kaf cikin rayuwarsa,kulawar tata ta zama wani abu daya dinga hudashi yana gigita tunaninsa,ta kuma zama abu mafi soyuwa a gareshi,ta sake zama sila kuma sanadin sake liqe mata da kwadayin son kasancewa tare da ita ako yaushe,duk kuwa da warning din aba......amma aduk sanda ta kusanceshi da tarin soyayyar nan tasa me narka zuciya sai yaji ya manta da kowa da komai. Hankalinsa ya fara dawowa jikinsa a wani dare bayan komai ya kammala,ta dafe mararta data fara mata ciwo,ya kula da hakan duk da basarwa data dinga yi amma sai da yabi ba'asi. Duk da ba wani tsanani yayin ba,qullewa ne amma hakan ya daga masa hankali,ya sanyata a jikinsa yana mata sannu kaman zaiyi kuka "Idan wani abu ya sameki ko ya samu baby na bazan iya yafewa kaina ba" ya fada yana kallon qwayar idanunta. Paracetamol tasha cikin mintuna qalilan ta ware,ya dinga sakin ajiyar zuciya hankalinsa a kanta,da safe kuwa a asibiti suka dira. An mata checkup sosai har ta dinga qorafi "Am fine fa daddyn twins" ta fada a shagwabe sanda suka dawo cikin mota zasu wuce gida. Da lion eyes dinnan nashi masu kwarjini ya kafeta yana sauke ajiyar zuciya har sai data gaji da yadda yake kallonta. Takai hannu ta shafi fuskarshin nan da KO yaushe take cike da wani irin kwarjini "Wadannan idanuwan.......suna kasheni......suna kasheni sosai" idanun ya lumshe mata yana murmushi "Kinsan inda ace me yiwuwa ne,zan cire idanunkin nan masu kama da zaiba.......na sanyasu cikin aljihuna nayita kalla a duk sanda naji kewarki?" Murmushi ya subuce mata sosai,duk lokacin da maina zaiyi wata magana da ita,zaqin kalamansa sukan ratsata qwarai,har taji kaman ta zaro zuciyarta daga qirjinta gaba daya ta aza masa saman tafin hannunsa "Idanuna basukai na wannan baby sultana din kyau ba.....ni da nake da lion eyes?,idanun lion suna da kyau?" Kunya ta kamata ta boye fuskarta cikin tafin hannunsa tana dariya "Inason idanunka ya maina ko a baya.... Kwarjini sukeyimin kuma tsoro suke bani yaa maina......suna firgitani Ashe bansan ajiyayyar soyayya bace danqare qasan ruhina" bibbiyu ya riqe hannayenta yana sakin murmushi "Ki daina haukatani haka sultana na roqeki.......banason na wuce gona da iri a kanki aba ya qwace license din daya bani" idanunta ta fiddo waje sai kuma ta shagwabe masa "Ya maina......." "Kece sultana......kece kike sake hauka maina.......bana iya sarrafa kaina a kanki sulthana.......am like crazy wollah" ya fadi yana sassauta muryarsa gami da sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa. "ina sonka da dukka zuciyata" ta furta itama tana jin yadda nata bugun zuciyar yake motsawa "Ina sonki da dukka rayuwata sulthana" ya furta yana maida idanunsa ya lumshesu. Waiwaya tayi a hankali tana kallonsa da kyau. Da gaske tako ina idan zai gwada mata yadda yake sonta......ko yaya zai ya fifita soyayyar da yake mata akan wadda take masa,da gaske ya fita sonta ko kuma ya fita iya bayyana soyyayyar ne. "Kin qoshi da kallon nawa?,ko baki gamsu ba?,zan iya tsaiwa har adadin lokacin da kikeso kici gaba da kallon nawa" ya qarasa maganar yana ware mata manyan idanunsa. Kunya ta danji,sai ta dan kauda kanta tana boye murmushinta. Murmushin shima ya saki sannan ya tayar da motar suka fara barin asibitin. A hankali a hankali taga yana daukan hanyar gidansu,ta waiwayo ta kalleshi,sai shima ya kalleta yana kashe mata ido daya. "Nayi missing ama......nayi missing BB" "i missed them too....but" saita narke masa tana kallonsa "Dauke idanun nan mommy twins kada na watsar damu a kwalta......menene buqatar?" Ya tambayeta kai tsaye. Murmushi ta sakeyi,wani mayen so yakewa idanunta ta sani tun tana qaramarta "Kunya nakeji bloodline" "Oh my god......da gaske kinaso na kasa driving dinnan soulsis......wait,mene ne abun kunya?" Idanu ta narke tana nuna cikinta da yatsanta. Dariya ya kwashe da ita yana dan dukan steering "Baby......ribar aure ne fa?" Sake marairaice masa tayi "Amma fa bloodline......sanda zamu fita a gidan fa bamuyi musu sallama ba,sai yanzu bayan almost ten days muje?" "Baby........gudu mukayi zuwa halinlinmu fa......ba saceki nayi ba don naje na miki fyade......" Dariya ya sake qyalqyalewa da ita,yayin da taci mur sosai "Banason kalmar nan bloodline" ta qarashe fadi kaman zata saki kuka "Duk yadda na tsaneta yanzun ina masifar sonta indai a kanki ne......saboda kinsan me?....." Bai jira amsarta ba ya dora "Like play like play sai gashi ta zama silar mallakamin ke" ya bata amsa daidai sanda ya tsaya qofar tangamemen gate din MAYAK'I family house din. Daya daga cikin security din da duke da duty a ranar ya taso,cikin girmamawa ya dage masa gate din,don plate number din family din MAYAK'I daban suke. Tun kafin ya qarasa parking space na gidan ya sauke glass din motar yana gaisuwa da security din har ya isa,ya kashe motar ya waiwayo yana kallonta "Kada kiji tsoro,am by your side" kai ta gyada sannan ya zagaya a nutse ya bude mata qofar,ya bata hannunsa saita noqe kafada "What?" Ya tambayeta yana duban tsakiyar qwayar idanunta "Zasu ganni ya maina.....Nidai Allah yasa kada naga su oncle bare aba" hannu ya sanya yana toshe bakinsa don kada taga dariyar da yakeyi mata. Ya tuna ranar data bayyana soyayyarsa gaban kowa,gaba kowanne ahali na gidan,irin bayyanawar dashi kansa baisan zata kai haka ba. "Ko na daukeki na goyaki?,ko kuma na daukeki na boyeki a qirjina don kada su ganki har na kaiki ciki?,ki zabi daya" ya tamabayeta yana duba agogonsa. Idanu ta fiddo waje,bata ma iya bashi amsa ba ta fito a gaggauce. Bai matsa mata ta bashi hannunta ba,sai yaja baya yana bata hanya,ya maida motar ya rufe suka wuce cikin gidan.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 149 Falon ama suka fara shiga,tana sanya qafafunta taji tamkar ta nutse. Ashe baqine a gidan da yawa,sam ta manta da wani lissafin a satin biki suke,don koda yasmine ta dameta da tsokana kasa bata amsa tayi. Tunda maina ya dauketa sukabar gidan ta wani manta da lissafin kwanakin biki da suka rage,da daya da daya suka dinga barin falon suna basu guri har sai daya zamana daga su sai ama sai batoul da benazeer da suka maqale daddynsu sunata bashi labarin irin kayan da ama ta dinka musu. Dukka labarinsu atamfa tafi birgesu,sultana ta dinga murmushi qasa qasa. Da gaske basu san wani atamfa can can ba,amma kuma suna mutuwar son atamfa,don ko yanzun kayan jikinsu kaftan ne na atamfar. Ta dinga tuna sanda maina yake yaqi da ita akan ta koyi sanya atamfa,a lokacin tana jin duk duniya bata maqiyi sama dashi,tana jin ba wanda ya tsani rayuwarta kamar shi din,tayi kuka har batasan adadi ba akan hanata fita da yakeyi don bata saka atamfa ba,har sai data tsaneta saboda haka,sai gashi yanzun Allah ya azurtashi da yara wadanda su kuma babu abinda suke matuqar so din sai ita. Duk da ya hanata tuna wasu abubuwan da ta masa marasa dadi,bayason ma ta dauko zancan,amma ita a karan kanta idan ta tuna wasu abubuwan takanji nauyi. Kamar yanzun data tuna yadda yasha gwagwarmaya wajen ganin ta suturce al'aurarta,ta kame kanta daga mu'amala da maza da zuwa matattarar rawa ko party. Saita daga idanunta tana satar kallonshi sanda suke magana da ama. Har yanzu yana nan da nutsuwar nan tashi,soyayayarta ce kadai ke sauyashi a duk sanda suka kebe sai ya koma kamar ba ya haidar ba. Masoyi ne na gaske,masoyi ne na gani kasheni,a wannan qarnin da muke ciki bata zaton akwai masoyi irin nata. Ta zuba masa ido sosai tana kallonshi amma a sace,wata qaunarsa na sake narka mata zuciya,batasan yadda zata fahimtar dashi tarin soyayyar da take masa ba,koda ta bude baki ta bayyana masa din,nashi kalaman guda uku rak sai taji ya rushe nata gaba daya. Cikin jikinsa yaji ana kallon nasa,yadan waiwaya kaman zai sosai wuyansa sai suka hada ido. Ya sha'afa a gaban ama yake,da idanu ya soma mata alamar kota gaji ya taso su tafi?,saita sake masa murmushi kawai tana.kauda kanta. Gyaran murya ama tayi kadan abinda ya dawo da hankalinsa kanta kenan "Komai dai lafiya ko?" Ta jefa musu tambayar "Alhamdulillah ama,ba wani damuwa" "Ma sha Allah,aba yace na gaya maka dama,yanaso ku zauna dashi,nima kuma inaso muyi magana dakai,amma......zuwaira!"ama ta qwala kiran sunan zuwairan,ba jimawa ta shigo. "Kuje keda su batoul su nuna miki jakar kayan mamansu ki dauko" amsa mata tayi benazeer ta miqe ta rakata. Ba dadewa suka dawo da.jakar,ta sanya zuwaira ta zauna ta bude komai a ciki ta zazzage mata "Ga ankonki nan da sauran kayan da akayi yaran gida zasu saka" kunya ta kamata,ama suruka kuma uwa ta gari ce,hatta da kalar mayafin da duk wani dan MAYAK'I zai sanya ta tanadar mata a shirye a jakar. Ita tama manta da wani batun anko,cikin matuqar girmamawa ta soma yi mata godiya,ta kuma miqe zata basu guri jin tace zasuyi magana da maina din "Yi zamanki,keda aliyyu ban taba ganin banbanci a idanuna bama bare zuciyata" komawa tayi ta zauna tana yin qasa da kanta, batoul da benazeer na gefe suna hirarsu da kusan rabi quruciya ce a ciki,ranar bikin oncle goumar kaza,ranar bikin oncle goumar kaza. "Nasan duk maganar da aba zaiyi maka iri daya ce da tawa ko shigenta......dani da aba duka duka ina kyautata zaton watanni bakwai suka rage mana mu gama zaman Paris mu dawo nijer ko Nigeria......akwai dukiyarka a hannuna me tarin yawa da tafiyarka ta kawo rashin baka ita......inason na damqa maka komai naka,saddi da almu suma inason na sakar musu harkokin dake hannuna,saboda haka horar dasu yana wuyanka,saika tsara yadda komai zai yiwu" shuru yayi yana jin nauyi na sake hawa kanshi. Bai samu ganin aba ba,bai kuma fiya son dogon zaman ba saboda yasan yanayin sultanar,ta zama wata me masifaffen son jiki,duk wani motsinta tafi ganeshi a jikinta,don haka suka yiwa ama sallama bayan ya aika batoul sukayi kiranta cikinsu najma. "Bloodline" ta kirashi a shagwabe sanda zai tayar da motar "Ya akayi?" Ya tambayeta "Nayi missing su BB,don Allah ko zamuje dasu?" Wuyansa ya karyar,yasan abune me wahala ama ta bada su "Don Allah muje ka rakani na roqi ama ta bamu su" shuru ya danyi sannan ya furzar da iska daga bakinsa "Okay...... let's go" ya fadi yana fita a motar. Tun kafin su isa sassan aman ta koma bayanshi ta boye,tana biye dashi kamar mara gaskiya,yana karance da ita tsaf,yana boye dariyarsa har zuwa sanda suka isa cikin falon nata. A inda ya barta a nan ya sameta,ta daga idanu tana binsu da kallo yadda suka dawo daga fitarsu ga sultanan biye dashi a baya "Lafiya?" Ta tambaya tana duban idanunsu. Bayansa ta sake komawa ta lafe sosai. Idanun aman sukayi masa nauyi da kwarjini,yadan shafa sumarsa dake kwance lub saman kanshi "Dama..... batoul da benazeer mukeso a bamu......." "Naku ne dama?" Ta katseshi tun bai qarasa ba "No ama......bawai duka ba,aro ko soulsis?" Ya fadi yana waiwayen sultana dake boye a bayanshi. Rigarsa ta riqe ta baya tana sake buya,sai dariyar dole taso kubce masa amma ya danneta da qarfi. Wato a fakaice wayo tayi masa,ta turoshi neman alfarma saboda ita ba zata iya ba. "Ina sultanan?,kin manta dama kince kin bani halak malak...... batoul da benazeer ba naku bane,ba aro ba dani,Allah ya bamu alkhairi" ta fadi tana miqewa ta dauki wayarta "Salon daga haka ku riqemin 'ya'ya...." Ta qara fada da salon mita tana wucewa ciki. Sai data tabbatar ama tabar wajen sannan ta fito daga bayanshi tana kallonshi ido a narke. Hannayensa ya watsa yana dage kafadunsa duka biyun gami da tabe bakinsa alamun nayi iya yina,yadda ta karyar da kai saita sake bashi dariya,ya bude mata hannayensa ta shige,ya dora hannunsa gadon bayanta yana shafawa a hankali,kafin ya saka hannu ya sureta gaba daya yana fadin "Ga wasu Allah ya bamu,muje muyi rainonsu soulsis.......wancan na ama ne halak malak ba aro ba dani" dariya ta saki "Na yarda......don da kaina na bayar.......amma a saukeni please kada muci karo da aba" "Yau duka da kanki kike tattaki,ba zaki sake taka qasa ba sai gobe in sha Allah" ya fadi yana bata kiss a goshi. Kaman yadda yace din kuwa bai barta ta sake taka ko ina ba,sai daya tabbatar ya gama mata dukkan abinda ya kamata,yana shirin ja mata duvet ta riqe hannunsa "Uncle maina....." Tayi kiransa da wani tsohon suna da take kiransa shekarun baya. Idanunsan nan dake kasheta ko yaushe ya daga ya kalleta "Me yasa ba zaka barni nayi hidima cikin gidana ba kamar kowacce mace?,bakaso na samu irin ladan da kowacce mace ke samu cikin gidanta?,zuciyata ba zata nutsu ba,inason naga ina hidima maka da hannuwana kaman yadda kake yimin" Murmushi ya saki,sai ya koma sosai ya zauna saman gadon "Zakiyi soulsis.......but a yanzun lafiyarki ita muke da buqata,beside ma......hidiman da kikeyi tafimin kowacce kalar hidima muhimmanci" "Wacce kenan bayan bana komai?" Ta tambayeshi tana ware masa fararen idanunta. Qasa qasa ya gaya mata wani abu daya sanyata jin matsananciyar kunya,ta danna kanta cikin pillow tana cewa "Allah bloodline......wai baka Jin kunyata?,kana manta wace ni?,babynka dinnan fa daka raina.....baby sultanarka?" "A nan wajen duka wannan abubuwan da kika lissafa mantawa nakeyi dasu......bana iya tuna komai" ya bata amsa yana dariya hadi da wucewa toilet. *********Gadan gadan aka shiga hidimar bikin goumar,komai ya hanata zuwa,qiri qiri saidai taga komai ta waya. Bata samu ya barta ta taka gidan bikin ba sai ranar kamun amare,a ranar ma aba ya buqaci ganinsa,ya barta cikin gidan suka fita shi da aba din. Ganin har lokacin tafiya gurin kamu yayi bai dawo ba sai wanann ya bata dama ta bisu abinta hankali kwance. Sunje gurare da yawa shi da aba din,ya kuma nuna masa kadarorinsa da yawa wanda shi mainan baisan mallakinsa bane. Qauna irin ta d'a da mahaifi ta dinga zaga jininsa,dukkansu shida ama sunyi fushi dashi ne a baki kadai,amma tsahon shekarun suna tattala duk wata kadara da sukasan tashi ce,hakanan zuciyar tana damfare da tunaninsa. Duk tsahon awannin da suka dauka da aba amma zuciyar da hankalin suna tare da ita, kowacce daqiqa idan ya samu chance sai yayi kiran wayarta,amma ta shiga tanata ringing bata dauka ba,don already ma a gida tabar wayar. Bata sani ba,ciki ne ya jawo haka?,ko tsohon tsimi ne ya tashi,haka siddan yau din taketa murna zata shiga taron mutane da yawa cikin family,abinda ya dade da mutuwa daga cikin ruhinta,ta kuma dade da ajjiyeshi tare da cireshi daga tsarin rayuwarta gaba daya. Zuwa wani lokaci haqurinsa ya qare,ya daina gane abinda aba yake fadi sosai,Allah ya taimakeshi wani abokin aba din ya buqaci ganinsa,ya matsa ya basu guri,sai kawai ya wuce inda ya ajjiye motarsa ya shiga ya nufi gida. Kaf gidan aka duba mishi ita bata a nan,daga qarshe matar oncle issofou da ita daya ta rage a gidan maman najma din ta gaya masa sun wuce wajen taron tare. Ajiyar zuciya ya saki me nauyi yana jin kishinsa yana motsawa,ji yakeyi kamar kowa na wajen ita zaiyita kalla,kamar kowa hankalinsa zai zama a kanta ne,ya tayar da motar da zafin nama yana fita a gidan,yana jin kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a wajen. *_second to the last page zamu shiga in sha Allah_**_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 150 Ganinta cikin jama'a ya tuna mata da baya sosai,ta dinga kallon masu kai kawo da masu taka rawa a wajen tana ayyanawa cikin ranta itama da haka take?,da hama takeyi?. Kunyar kanta da kanta ta kamata,tayi qas da kanta zuciyarta na rawa,zuciyarta na ayyano mata girma da martabar maina a ranta. Ashe duka haka yake hango mata?,ashe haka yakeso ta zama yadda take yanzun?,ashe ciwo yakeji cikin ransa?. Cikin zuciyarta taji wanne sakamako zata yiwa bawan Allahn nan?,dame zata saka masa?,tabbas itama bata sani ba,amma tanaji zatayi iya qoqarinta tuquru,xata sadaukar masa da rayuwarta har zuwa qarshen numfashi kamar yadda shima ya sadaukar mata. Akwai friends nata da yawa data jima rabonta dasu,wasu ma kwata kwata rayuwa ta sanya ta manta dasu,sai gasu sun hadu a wajen. Kowannensu mamaki yakeyi,kowannens kallon sultana yakeyi "Sultana hamani mohmoud?" Suke fadi. Duk da da yawansu sunsan a yanzun ita din wacece,Tv show presenter ta qasar paris. Kowa ya kalli benazeer da batoul ya kalli sultana din sai suyita mamakin idan tace yaranta ne,da yawansu ma qaryatata suka dinga yi,saboda basusan meye ya faru a rayuwarta ba,kawaidai sun tsinci ta daina zuwa makaranta rana tsaka,daga bisani kuma ta bace musu daga nijer gaba daya,sai suka samu labarin bata qasar. Yadda yaran keta daukan hankulan jama'a a wajen yadan dagi hankalin sultana,saboda sun zama popular a Instagram sosai,babu twins dake tsananin kama da juna dake trending a Instagram irinsu. Tasan ama ta musu addu'a tabbas kafin su fito,amma duk da haka ta sani bakin uwa daban yake,don haka ya kirasu ta jasu gefe ta sake tofesu. "Wai da gaske sultana hamani ce?,sultanan ya maina?,sultana 'yar madara fa?" Wata qawarsu dijama ta fadi tana dariya ganin zallar nutsuwa da kamalar da sultanar ta siffantu dashi a yanzu. Ta sake zama wata cikakkiyar mace,kwarjini da wani irin zallar kyau lullube da ita. Murmushi ta sakarwa dijama "Shafa mana kiji,halin fa yana nan raguwa yayi bawai na daina ba" ta fada tana dan gatsina baki. Dukkansu sai suka kwashe da dariya,wannan haduwar ta musu dadi qwarai,don rabuwa ce ta shekara da shekaru ba'a kuma yi zaton za'a sake haduwa ba. "Nidai ki bani twins dinnan don Allah sultana?" Daya qawar tasu ta fada cikin tsananin son yaran da burgewa. "Turqashi!"aminata ta fada tana dariya. "Ba zasu bani ba ko?" Ta fadi tana kallon aminata "Ko ubansu bai isa yace a bashi su ba bare uwasu bare wani,yara halalin ama ne ama kuwa ko mutuwa tayi inda da hali a hadata dasu" ta qarashe fada tana dariya. Dariya sultana tayi tana kauda kai "Nidai ba ruwana,Allah yasa ta jiki" kauda kan da tayi saita hango almu yana tahowa. Ya qaraso daf da ita yayi qasa qasa da kansa "Ya maina yana Jiranki ta waje fa" almun ya fadi yana dubanta. Idanu ta fidda waje,shaf ta mance ma bata gaya mishin zata bisu ba,ta kuma san halinshi sarai. Tsam ta miqe tana ce musu "Ina zuwa" "Ki gaida gida dai" aminata dake dariya ta furta "Don nasan wannan Romeo din naki bazai barki ki dawo ba" harara ta watsa mata "Sai na gaya masa abinda kika fada" ta furta tana yin gaba "Ki yiwa Allah kiyi haquri" itama tayi mata magiya tana hada hannayenta biyu waje daya alamar roqo. A nutse ya daga idanunsa yana duban hanya don yaga kota taho?. A hankali a hankali take takowa kamar me tsoron cin karo da wani abun tsoro,tana tafiyar tana sunne kai da hade jikinta guri guda. Ya zuba mata idanu sosai,sai kuma ajiyar zuciya gami da dariya suka subuce masa ba tare da ya shirya ba. Ya tuna shekarun baya da idan tayi wani laifi,irin wannan tafiyar takeyi kafin ta kawo gareshi,ko a yanzun da take tafiyar sai ya hango sultana 'yar shekara sha hudu. Gaza jurewa yayi ya fita da hanzarinsa,bata ankara ba taji yayi sama da ita "Kinaso ki wahalarmin da zuciyata ko?,kinason ki raban wannan kyakkyawar fuskar da wasu?,sai da naji zuciyata kamar zata narke sultana" ya fadi yana ajjiyeta cikin motar. Maqaleshi tayi ta hanashi ajjiyeta,ya daga idanunsa ya aza cikin nata. Ta shagwabe masa fuskar nan da irin nau'in shagwabar dake tafi da hankalinsa "What?" Ya tambayeta yana jin jikinsa yana saki gaba daya "Am sorry" ta fada a tausashe. Yatsansa kawai ya dora saman labbansa "You are already forgiven" ya amsa mata da wani irin shauqi dake fita daga qwayar idanunsa,kanshi yakai a hankali zuwa labbanta da goshinta ya aje mata wani tattausan kiss. Hanyar gida kawai ya wuce da ita,ta juyar da kanta a hankali tana dubansa "Bloodline......na dauka zaka barni gidan ama ne,tunda gobe daurin aure?" Idanunsa duka ya waro waje yadan saci kallonta a hargitse "Bazan iya ba soulsis....." Sai ya fara irga mata da yatsansa. ".......awa daya,awa biyu.....awa uku......awa hudu,har awa nawa?,it can't" ya qarasa fada yana girgiza kai. Bata sake ce masa komai ba,don ita dinma kawai tana sha'awar komawa gidanne,amma tasan ba tabbas ta iya bacci,ta maida kanta saman kafadarsa a hankali ta kwantar tana lumshe idanunta,sai ya sake sauke wata ajiyar zuciya wadda kusan sultana ta saba da jinta,batasan wanne irin ciwo soyayyarta take masa a zuciyarsa har haka ba. Bai iya sake barinta zuwa gidan bikin ba kwata kwata,suna gida ana bude sabuwar rayuwa,dukkansu sun budewa junansu idanu da wata irin soyayya me tsayawa a zukata,duk dare sai sun fita tadan motsa jikinta,ya kuma kaita guraren da yasan a baya tana da shauqin zuwa cikin nijer,guraren da a baya yake hanata zuwa da kuma kusantarsu,a yanzun shine ya zame mata dan jagora. Duk inda sukaje din sai ta tuna komai,kunya tayita kamata tana sunne kai,sai yayi fuska kawai kaman bai fahimci abinda takewa kunyar ba. Wasu guraren sai hawayen farinciki yazo mata,a yanzun data mallaki cikakken hankalinta,ta kuma samu ilimin addini dana boko isashe sai take ganin cikakken baiken rashin kasantuwar diya mace a wajen. Da gaske maina yayi mata gatan da ko uba mahaifi iya gatan da zaiyi mata kenan,yayi tsaiwar daka akanta irin tsaiwar da uwa ce kadai ke yiwa diyarta. Daga qarshe guri na qarshe da sukaje,taga yara irinta irinta nata tiqa rawa irin rawar da a baya bata da abun burgewa da takeso taji tana yi sai ita,saita kamo hannuwansa ta sanya cikin nata tana duban idanunshi "Bloodline......ka yafemin don Allah?" Wayarsa da yake amsa kiran suhail ya ajjiye gefe yana bata duka hankalinsa "Me kuma ya faru?,kinason sakani a damuwa sultana.....menene?" Sosai idanuntan nan masu sheqi suka hada hawaye "Nayi maka abubuwa da dama na rashin kyautawa,na kalleka ta fuskar abokin gaba,maqiyina wanda bayason walwalata ko ci gaba na,nayi maka mummunar fassara......na dauki duka qiyayyar duniya na aza maka......bayan dukka gata kakemin,duk duniya kuma bani da masoyi sama dakai......ya maina......ka yafen....." "Shshshsh.......ya isa soulsis mana....eheennnn......goge hawayen" ta fada yana sarqafe yatsunshi da nata. A hankali ta fara goge fuskarta da bayan hannun nata. Ya saki wani siririn murmushi na gefan baki wanda ya qara masa kyau sosai,ya motsa jajayen labbansa da tattausan muryarsa dinnan ya fara mata wata waqa cikin harshen France. Waqa ce da yake mata tun tale tale,tun tana zanin goyo sanda yake rainonta. Ta tuna waqar fes,ita ta dinga sakata sakin murmushi daga qarshe dariyar kunya ta qwace mata,ta kifa kanta saman table din da suke zaune tana boye qwayar idanunta. "Sultana na ta zama me wani irin kunya" ya fada a hankali yana dan taba saman qafarta da qafarsa dake cikin socks ta qarqashin table din,saita janye qafartata da sauri tana qyalqyala dariya. Da gaske wani irin kunyarsa takeji kam,sosai idan yayi wani abu saita dinga gani kaman ba uncle maina dinta ba?,wanda yake kaman uba a gareta?. Inda Allah ya taimaketa......da sun kebe sun shiga da'irar da yakeso saita manta da komai,shima kuma ta dulmiyashi cikin shauqi ta kuma kaishi wata duniya me nisan nisa. Dole ta zage ta karkade duk wani salo na ama da karatun ama,ta kuma sake zurfafa bincike da neman sanin hanyoyin kama miji,kamar yadda taji ama tana yawan gaya mata "Karki sake kada kuma ki yarda ki zauna haka sakaka,duk soyayyar da mijinki ke nuna miki saikin dinga fadada hanyoyin riqeshi da faranta masa da kawo sabbin abubuwa cikin zamantakewarku,sannan uwa uba addu'a.......kada kiyi sake......ina maimaita Miki kada kiyi sake ki kuma miqe qafa don miji yana sonki ki gaza yawaita addu'a akan Allah ya dawwamar da wannan soyayyar taki cikin zuciyarsa,addu'a takobi ce...... addu'a gata ce.....sannan kuma addu'a tanadi ce" "Ya Allah ka maida jin aliyyu,ka maida ganin aliyyu,ka maida tunanin aliyyu ya zama SULTANA ce" wannan shine addu'arta a duk sanda ta sanya goshinta qasa. Batasan tana tsananin kishin aliyyu ba sai yanxu,batasan tana da kishi me tsanani ba sai yanzu,wannan ya sanya addu'arta a kullum "Ya Allah,ka mallakamin aliyyu ni kadai,Allah ka sanya ni kadaice matarshi a duniya,ni kuma Allah ka bani ikon zama baiwa a gareshi,ya ubangiji kada ka bani iko na cutar dashi ko na tauyeshi cikin haqqinsa,Allah ka kiyayemin jinsa ganinsa da zuciyarsa daga kowacce 'ya mace". Aba dakeson ya sake ganinsa su qarasa tattaunawa ya sake kiransa,ranar ne suka koma gidan bayan an share biki. Bibi tayita kwasarsu shi da ita tana musu tsiya "Ji'irai biyu,sun gama yaqin da dauki ba dadi tsakanin dangi,sun hanawa kowa zama lafiya amma sai gasu yau bulunbuqui dasu,kaga idanun ja'irai" "Bibi......kiyimin ni kadai ki qyale matata ta huta" maina ya fada yana duban bibi. Baki ta riqe tana dubanshi,can qasan ranta ita daya tasan me takeji,ita kadai tasan farincikin da takeji,amma a zahiri saita tamke rai "Sannu me mata,matar da sai dana saka aka mata tara tara kai da ita?,ni zaka gayawa wai mata?,naci gidanku kai da matar" saita watsa masa daquwa. Qasa yayi da kansa yana dariya,bibi tafi gaban komai a wajensa,ta masa gatan da har ya mutu bazai manta ba. "Yo ai nima wannan cikin idan aka sauke ni ya kamata a baiwa sannan ku fara tara naku ma" ta fada tana miqe qafafunta wanda suke sake matsanta mata da ciwo,duk kuwa da cewa cikin magani da kulawa kullum ake. Ido ya zaro waje yana dubanta,sai kuma ya shiga girgiza kai "Bazan iya ba,haba bibi kaman companyn buga jarirai nake da?" Yadda ya fadi maganar sai ya bata dariya sosai,har shima ya tayata suka dara. Sati guda kacal da share biki suka tattara suka koma paris,saidai koda suka koma din kusan shirye shirye ya dinga yi gadan gadan na dawowarsa qasarsa a watanni bakwai masu zuwa adadin sanda ama zasu gama nasu wa'adin,bawai kuma da nufin yabar paris har abada ba,a'ah....zamansa zai koma nijer ko Nigeria ne guraren daya yanke kafa business dinsa da kuma inda ama ta aje nata business din,da inda plazas na BB MAYAK'I suke.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 151 Yayita zuba idanu yaga sanda sultana din zata koma aikinta,amma saboda yadda baya samun zama sosai tunda suka dawo sai hankalinsa ya dauke daga kan hakan. Yasan dai tabbas bata zuwa din,tunda ba zata taba fita ba tare da izininsa ba,bata kuma sake tayar masa da maganar ba. A wani dare,yana zaune cikin falo sanye da abaya ta maza me gajeran hannu,yana zaune saman sofa dake falon,amma kuma qafafunsa suna miqe a qasa. System da tarin takardu ne a gabansa. Kusan kullum cikin wannan hidimar yake,yanason fidda duk wata dukiyar daddyn sardauna daga hannunsa yayi musu handing over,kama daga asibitinsu da suka damqawa ragamarsa zuwa sabon company dinsu dake aiki a niamy. Dauke da varnish tray take takowa daga cikin kitchen din zuwa inda yake zaune. Tana iya hangen fuskar nan tashi me yawan kwarjini da cikar kamala musamman idan yana zaune irin haka yana aiwatar da wani abu me muhimmanci. Sumarsa ta sanyata sakin murmushi,dukka a cakude take,alamun da zai nuna maka lallai aiki yasha kansa sosai. Skirt da blouse ne a jikinta amma sakakku,duk da sakewarsu hakan bazai hanaka ganin cikin jikinta ba. Cikin wata biyar amma sai ka dauka yayi watanni takwas ko tara dinsa ma. Wani irin girma yakeyi,duk da Dr Camille tayi mata dukkan bincike,kuma bakinsu yazo daya da Dr Noor, triples suke sanya mata ran samu. Jikinta yayi sanyi tana tuna wahalar cikin twins ma ina ga wannan?,amma tsaiwar gwarzon namiji irin aliyyu a gefanta ya sanyata ta koma jin koda yara biyar ne ma zata iya haifewa. Kulawarshi a kanta ya danne dukka tsoro da fargabarta,soyayyarsa a ranta kuma ya bata wata irin nutsuwa da qaunar koma meye zata haifa din. Iya dososhi da tayi kadai yaji a jikinsa tana tahowa,da sauri ya sauke system din kan cinyarsa yana miqewa ya kuma nufota yana kama qugunsa "Me ciki na'am.....gani nan tafe.....me ciki na'am gani nan tafe" yadda yakeyi din ya sanyata sheqewa da dariya da gaske,shima yana tayata,ya kuma matsa yana karbar tray din hannun nata,ya saka daya hannun ya riqo hannun nata. Zaunar da ita yayi ya ajjiye tray din,sannan ya zauna sosai a gabanta dirshan yana tanqwashe qafarsa "Me yasa dole dole saikin wahal min da kanki?,ko nauyin abinda kike dauke dashi bakiji soulsis?" Murmushi ta saki,ta miqa hannu tana shafa tudun cikin nata. Iya nauyi tana jinsa,amma har yau taqi yarda ta nuna masa,ta sanshi da damuwa da yawa akan lamuranta,tasan kuma yawan ayyukan da sukayi masa rubdugu,yanzu yanzu sai ya kasa yin komai ya aza damuwarshi a kanta,bayan kuma lafiyarta qalau take jinta,nauyinne da sauran lalure lalure da ama kan gaya mata dama me ciki ba'a rabata dasu. "Ni bana jin komai,ko tsere ne zan iyayi dakai kuma na wuceka" "A hakan?" Ya fadi yana dariya gami da kallon tulelen cikinta. Cikin qwarin gwiwa ta daga kai "Sosai" "Naga alama......ni na isa na wuceki daman?,Allah ya taimakeki" ya fadi yana dunqule hannunsa tamkar meyi mata jinjinar sarauta. Dariya suka saki gaba daya,ta soma zamowa da zummar sauka qasa tayi serving nashi. Sauri yayi ya matsar da tray din "Dakata...... zauna kawai ke kin gama aikinki" ya fadi da sauri ya soma zuba musu abincin. Idan yaci spoon daya sai ya bata daya,da haka da haka har suka kammala,ya ajjiye spoon din ya zuba mata idanu "Ina mamakin wai yaushe baby sultana ta iya wadannan zaqaqan girkin?,kinsan kin batarmin da kowanne taste din abinci daga bakina idan ba naki ba?" Ya qarashe fadi yana dage mata dukka girarsa biyun, maganar kuma yana fadinta da gaske daga qasan zuciyarsa. Murmushi ta saki tana jin qaunar ama me qarfi a ranta,ta koyar da ita komai na rayuwa,duk abinda ya kamata diya mace ta iya ta sani kota fahimta don zamowarta cikakkiyar mace ama tayi mata shi "Aikin uwa ta gari ce.....ama" idonsa ya lumshe ya kuma bude lokaci guda. Mahaifiya daban take,dukka tayi wadannan abubuwan sabodashi,saboda yaji dadi,saboda ya samu abinda kowanne da namiji ke fatan samu daga wajen iyalinsa. Ta gefe guda kuma ta inganta duniya da lahirar marainiyar Allah. *******Washegari yana shirin fita yaga itama tana shiryawa "Aikin zaki koma?" Idanu ta fidda sai kuma ta saki murmushi "Zuciyata ba zata taba nutsuwa da aikin da ina yinsa mijina yana cikin kishi da rashin nutsuwa ba......na ajjiye aiki a bangaren gabatar da kowanne shiri muddin za'a doramin camera" ta qarasa fada tana zama gefan gado saboda nauyi sai taji tsaiwar ta mata wahala. Hankalinsa dukka ya tattara a kanta yana dubanta da wata irin narkakkiyar qauna. Duk yadda takai ga qaunar wannana aikin?,duk yadda takai ga shan gwagwarmaya don cimma wannan burin?,anya ya yiwa kansa adalci idan ta aje aikinta dukka saboda shi?. "Baki nema izini ba sultana?,me yasa?" Yayi tuhumar a sanyaye "Yardar Allah nake nema da kuma yardarka bloodline" ta bashi amsa itama a sanyaye "Sun roqi naci gaba da aiki dasu a bangaren culture din.......koda iya research ne da tsara program din nayi na tura musu,zasu samu sabuwar presenter.....nace su dan yimin haquri har na haihu.....koda na koma qasata zan iya wannan" ta bashi bayanin da ya sanyashi ajjiye comb din hannunsa ya dawo gefanta ya zauna. Idanu kawai ya zuba mata ya rasa abun cewa,saita saki murmushi tana waving hannunta saman fuskarshi "Wake-up bloodline" murmushi ya saki kawai,ya kama dukka hannayenta ya saka cikin nasa ya damqe,yayi kissing dinsu a tausashe "Allah yayi miki albarka" ya qarshe dashi. "Wajensu ama nakeso na yini yau" "Kina da dama.....kwana ne kawai bazan iya bari ba soulsis" dariya ta tuntsire masa dashi. Yasha cewa taje din,to amma ita damuwarta tace idan taje ta tabbatar su batoul ba zasu barta tayi baccin ranarta ba,zasu cikata da tambayoyi ne kawai da labarai na school,sai kuma tambayar daddynsu. Tun a bakin qofa suka dinga ihun ganinta,tambayoyi kam haka suka dinga jera mata su akan cikinta,har sai data kusa buge benazeer sannan ta nutsu. Sunyi hira sosai da ama,tana ta nan nan da ita,duk inda suka gifta ita da yaran sai farinciki ya kama ama "Alhamdulillah" da take maimaitawa cikin zuciyarta har batasan adadi ba. Hikimar ubangiji gaba daya yawa ne da ita,shi yasa kome ubangiji yayi ba'a son ka cika qyamarsa,me yiwuwa akwai hikimarsa a ciki. Sultanar dai ashe ita aka haifawa?,ashe dai daga qarshe sultana tata ce,itace tushen zuri'arta da kafuwarta?. Dafa wannan ajjiye wannan haka me aikin bibi ta dinga jerewa sultana. Duk yawan cin abincinta har sai data ture,kafin wani lokaci jikinta ya mutu bacci yazo. Ama tanata lura da ita, tausayinta ma gaba daya ita takeji. Tana qanqanuwarta amma Allah ya qaddara mata haihuwan yara bibbiyu uku uku,gadon dangin mahaifiyarta. "Ku raka mummy daki ta kwanta ta huta hakanan" ama tace dasu benazeer. Suna gaba tana biye dasu a baya har suka isa dakinsu,saita samu dakin turmus da kaya. "Kayan qannenmu ne wai inji ama" benazeer ta fadi tana murna sosai harda juyawa kamar zata taka rawa. Dariya taso qwace sultanar,taja qaramin tsaki tana ture pillows din dake saman gadon batoul ta yada kanta idanunta akan kayan dake jibge. Sai yanzu take sake yarda,komai nata ba halayya benazeer ta dauko,batoul kuma maina ce a wasu abubuwan da dama. "Ku fita ku bani waje bacci zanyi" "Idan kin tashi zamuyi hirar?" Batoul dake tsaye a gabanta ta fada. Dole suka bata dariya,ta saka hannu ta riqe hannayensu tana murmushi "Eh zamuyi" idanunta a kansu har suka fice,sai ta sake maida kallonta ga kayan. Ko ba'a gaya mata ba ta fahimci irin haukan siyayyar da ama ta yiwa su batoul shine zata yima wanann cikin,kaya har sunfi nasi batoul yawa,ta kuma san bawai ta gama siya bane. Ko ba'a fadi ba tasan Allah ya zubawa ama son 'yaya,ko daga yadda ta dinga dauko riqon yayan yan uwa ana hanata,da yadda takema yaran gidan tun sultana na sultanarta,bare kuma yanzun data samu mallakinta halak malak. Sallah kawai ama ke tashinta tayi ta koma,ba ita ta wartsake gaba daya ba sai da tayi magariba. Me aikin ama ta shirya dining,basukai ga fara ci ba maina din ya iso. Sau daya ta dubi qwayar idanunsa ta fahimci yauma a gajiye yake tulus. Bataji kunya ko nauyi ba,ta yunqura duk nauyinta ta tarbeshi,ta kuma ajjiye masa ruwa da sauran abinda tasan yakan buqata idan ya shigo gidan. Abun ya yiwa ama dadi sosai,idanunsa shima a kanta ta furta "Allah yayi miki albarka" yanason kulawa,kuma ya sameta har fiye da yadda yakeso. Tare kuma cikin kwano daya sukaci abinci da yaran,surutu har ya rasa na waye zai amsa,kusan benazeer ta fara koyawa batoul surutu,basu barshi ba har sai daya kusa qwarewa. Sulthana na gefe tana musu dariya,shine yake hanata hana benazeer yawan maganar nan tata "Ki barsu,alamu ne na budewar qwaqwalwa wa yaro,duk yaro me yawan magana zai wahala ki sameshi baida basira......iya kanki kawai ni ya isheni misali na gani.... haquri ake dasu ayita amsa musu tambayoyin,inda sukayi mistake ko tambaya mara ma'ana kuma gyara musu akeyi". Abinda yake yawan gaya mata kenan. Qwarewar da yayin sai duka suka nutsu,suka dinga jera masa sannu hankalinsu tashe,ya saki murmushi yana cewa "Naji sauqi,mu qarasa cin abincinmu". Basu bar gidan ama ba sai kusan sha biyu saura,saboda aba ya sameshi, kuma sun tattauna dukka su ukun,wanda duka dai baya wuce kan dawowarsu qasa nijer. *_akwai dinner in sha Allah,ku shirya_**_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 152 ********A hankali take takawa tana fitowa daga toilet din tallafe da cikinta da yayi matuqar girma da tsini kamar zai fado qasa. Jin alamun fitowarta ya sanyashi daga kansa daga akwatin da yake shiryawa,wanda ya gama shirya guda daya,dayanne a gabansa cike fal da kayan babies. Dukka qarfin halinta ta tattaro ta sakar masa murmushi tana kallon qwayar idanunsa. Rauni zallah,kai tsaye ma zata iya cewa ita dake facing yanayin ta fishi qwarin gwiwa da kuma dakiya "Bloodline saida tanja tace ka bari ta shirya kayan fa,wasu abubuwan na hidimarmu ya kamata ace kana hutawa,abun sai yayi maka yawa fa" ta fada a narke da shagwabarta wadda a yau ta motsa zuciyarsa da wani irin rauni. Duk tsanani duk kuma halin da take ciki qoqari take ta boye komai,qoqari takeyi ta nuna masa everything is fine koda kuwa can cikin jiki da zuciyarta ba haka bane. Shi daya yasan da yadda take bacci take kuma iya yini dauke da wannan qatoton cikin,ya gaji da gani shi yasa yayi deciding gwara a cireshi yana da sati talatin da biyar itama ta huta. Dama kuma ko can Dr Camille tace saidai Cs din,tunda haihuwan farko CS ne,yanzun kuma ba yaro daya bane a cikin,koda yaro daya ne a irin qasashen nan basa bari ka dauki wannan kasadar koda sau daya aka taba yankaka. "Inda zai yiwu soulsis......koda numfashi ma yi miki zan dinga yi.....dani da yara na muna wahalar dake da yawa" ya furta yana kamo dogayen yatsunta da a yanzu suka ninka nauyinsu yana murzawa a hankali cikin tausasawa. Murmushi ta saki sosai,ta tsugunna a hankali tana zama sosai a gabansa,ta saka hannu ta jawo wani set na bodysuit da kamfanin BB dinsu ya fidda sample dinsa "Kowanne minti na guda daya cikin bautar ubangiji yake bloodline......ba wahalar banza nakeyi ba,duk macen data mutu ta wannan hanyar ka tuna tayi shahada?" Kalmar mutuwar data furta gaba daya saita kashe masa qwarin gwiwarsa,ya sanya daya hannun nasa ya riqe dukka hannayenta biyu cikin nasa,sai a sannan ta lura idanunsa har sun sauya kala "Ki daina ambatar me raba masoya......me yanke jin dadi.....ba yanzh ba in sha Allah,na rantse miki da Allah sulthana bazan iya rayuwa cikin duniyar da babu ke ba,bazan iya qara cikakkiyar awa guda cikin duniyar da babu ke ba" murmushi ta saki tana son bashi qwarin gwiwa. Gaba daya ya koma macen,itace namijin,akan dukka abinda ya shafeta sam sam bashi da juriya batasan me yasa ba,rago ne ta wannan fannin na gaske kuwa. "Ina fata har jikokinsu batoul sai mun gani in sha Allah......" Don kauda maganar sai ta sake daga bodysuit din "Bloodline......har yanzun baka gayamin me zan haifa ba?" Dan qaramin Murmushi ya saki bayan ga ambato sunayen Allah gaba daya,ambaton da ya saukar masa da nutsuwa "Kinsan wani ikon Allah?" Kai ta girgiza "A'ah" "Har yanxu babu wanda Allah ya bawa ikon fadin jinsin da zamu samu" dan sama ta kalla kadan alamun nazari,sannan ta gyada kai. Ita kanta sai yanzu ta tuna,tabbas babu wanda kam a cikinsu daya fadin musu sex na yaran. Habarta ta kama ta riqe tana kallonsa,sai yadda tayi din ya bashi dariya,yasa hannu ya tungule hannun yana dariya,tayashi tayi itama,yadan jawota kafadarta ya rabata yana cewa "Qiri qiri wadannan yara sun hanani rungumar matata yadda ya kamata" yayi maganar da sigar qorafi shima yana narke mata yadda take masa hadi da nuna dogon cikinta da yatsansa. Dariya tadan saki,ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Ban taba sha'awar naji abinda zaki haifamin ba sulthana soulsis.......duk abinda kika haifamin inaso......idan ana haifar rabin d'a idan kika haifamin inaso sulthana" kanta ta kwantar saman kafadarta,hawaye yanason balle mata amma kuma ta hanashi fita din,don tasan yanzun zata daga masa hankali. Itadai tayi imanin ta samu miji wanda ba irinsa a wannan zamanin sai anyi dogon nazari da kuma bincike. Rana ce da Dr Camille ta sanya musu don yiwa sulthana din Cs,amma yayi qoqarin maidata rana me muhimmanci a garesu gaba daya. Ya hanata zaman damuwa ko tunani kamar yadda itama taketa qoqarin hanashi wannan. Hudu na yamma suka tsara barin gida,amma ama tace su jirayeta ita da kanta zata shigo ta daukesu. Ta tabbatar a ranar aliyyu bashi da sauran nutsuwar da zai iya wani abun kirki. Ta sanshi sarai,tasan halinsa,ko itace bata da lafiya ba wani iya kuzari yake ba a ranar. Kafin ama din ta iso sun kammala komai,don haka tana isowar suka wuce asibitin. Tun daga bakin gate din asibitin har ciki haba haba kowa yakeyi da ita,kasancewarta matar babban likita a asibitin kuma likitan da suke matuqar so,wanda duka duka wata uku ya rage masa yabar asibitin nasu. Kulawa ta musamman suka bata,sukayi mata dukan abinda kuma ya dace. Batasan goumar da najma suna gurin ba sai data baro dakin likita "Baqin buzu da amaryarsa" ta fadi cikin sigar tsokanar nan tasa. A yau din yadda goumar ke mata magana sai taga shima jikinsa gaba daya a sanyaye yake,najma ce me qarfin halin. Murmushi kawai itama tayi,tana mamakin rauninsu haka a kanta. Tana zaune cikin dakin har aka sanya mata cannula da komai,tsakanin mintuna goma sha biyar sai shigowar bibi sukaji. Bataji zuciyarta ta raunata ba sai da taga bibi afujajan,ta rungume bibi din sai dukansu kuka ya kubce musu. "Kuyi mata a hankali kada jininta ya hau" Dr Camille ta fadi maina ya yiwa bibi bayani,wannan shi ya kawo nutsuwar. Dukkansu abun ya zame musu tamkar sabo,kasancewar sanda akayi nasu benazeer daga ita sai ama din kadai ne. Duk wani abu da sukeji yanzun a wancan lokacin ama ita daya ta shanyeshi,lallai ama ta cika jarumar mace,ta kuma cancanci dukkan yabawa. Macace me kamar maza,wadda tayi abinda kaf family din MAYAK'I ba zasu taba mantawa da ita ba. Da taimakon aba komai ya daidaita,sai aka koma hira kadan kadan,amma duk da haka maina ya kasa zaune ya kasa tsaye. Kamar ma ya manta da kowa a cikin dakin,don duk bayan minti kadan ko second kadan sai ya tambayeta "Ba wani abu?" "Ba komai" take amsa masa,har ta fara jin Kunyar yadda yakeyi din,don kamar ya raina kulawar da kowa ke qoqarin bata ne. Sanda nurse ta shigo tafiya da ita kasa tsaiwa yayi a wajen,don yana jin yadda idanunsa sukeson fidda hawaye,yanason fita amma qafafunsa sun riqeshi "Muje daga waje ta qarasa shiryawa" aba daya lura da yanayinsa yace dasu,duk sai suka juya suna ficewa,dakin ya zamana daga shi sai ita sai nurse din da zata bata rigan da zata saka. A zafafe ya sanya hannu ya jawota jikinsa,zuciyarsa tana wani irin bugawa da qarfin gaske,hawayen nan da yake son riqewa suka biyo ta gefan idanunsa. Tsam ya riqeta cikin jikinsa,murya a tausashe ya soma mata magana can qasa "You will be fine in sha Allah,you will make it in sha Allah.....ki yafemin please sultana....am sorry for my past....a irin wannan lokacin daya kamata na tsaya dake.....amma ya zamana bana kusa dake,bani da ikon bayyana kaina.....ina miki fatan alkhairi soulsis". Hannu bibbiyu tasa tana dauke masa hawayen,tata zuciyar tana son tayi rauni amma tana bawa kanta qwarin gwiwa. Shi ya karba kayan,yayi dressing nata da kyau,ya tsaya ta bayanta ya cusa doguwar sassalkan sumarta cikin hular da suka bayar. Hannunta ya kama yana juyo da ita idanunsu cikin na juna. Murmushi ya sakar mata,kayan sun mata kyau kamar don kwalliya akayisu "You look so gorgeous my baby sultana" dariya ta kufce mata "Still baby ce?,duk da babies din da take bayarwa?" "Yes.....baby ce,tu continueras toujours à être un bébé pour moi(zakici gaba da zama baby a wajena)". Abun sai ya burge nurse din,ta saki murmushi sannan ta danyi gyaran murya ganin kamar sun manta da ita a wajen, dukansu suka juya suna kallonta don da gaske sun manta da ita din "Yallabai ga kujera ko zata hau mu wuce?" Hannu sultana ta saka ta tura kujerar baya,sannan ta maqale a kafadar maina din sosai. Dariya ya saki yar qarama,ya gama fahimtar abinda take nufi,don haka ya waiwaya ya kalli nurse din "Kije zan rakota yanzu" "To yallabai" ta amsa masa tana dariya ta tura kujerar ta fice abinta. Yana riqe da ita a kafadarsa hannunsu cikin na juna har suka is qofar theater room din,ya juyo da ita yayi kissing nata sai ya juya a hankali yana barin wajen. Bata iya taka qafafunta ba har sai data daina ganinsa,sannan ta juya ta wuce ciki tana karanto dukka addu'o'in data sani da wadanda ya gaya mata tayin a dazu. Ji ya dinga yi kaman dunuyarsa ta tsaya cak,ya dinga ji kamar rayuwarsa ce take a tsaye guri guda,kowanne minti daya daidai yake da awa goma a wajensa,wani irin jira me cin rai wanda tsahon rayuwarsa bai taba jira me wahalar wannan ba. Duk da qoqarin yakicewa da sukeyi dukkansu kowa hankalinsa nakan dakin theater din yana jiran jin sakamako. Dukkansu counter ne a hannunsu suna ja kadan kadan. Sanda danjar dake saman dakin ta sauya zuwa launin kore sai dukkansu suka miqe. Duk yadda yaso riqe kanshi kada yayi azarbabi ya zama daga gaba ya kasa. Shine na farko daga bakin qofar,ya hade hannayensa waje daya yaba murzasu,labbansa suna haduwa suna kuma rabuwa yana kiran sunayen Allah duk wanda yazo bakinsa. A nutse aka bude qofar,nurses biyu suka bayyana fuskokinsu dauke da murmushi "Le CS a-t-il été complété avec succès ?(an kammala CS din cikin nasara?)" Ama ta tambaya cikin son jin lafiyar sultana din. Kai ta gyada "Oui madame, les bébés sont en sécurité, leur mère est également en sécurité.(eh madam,jarirai suna lafiya mahaifiyarsu ma tana lafiya)" "Alhamdulillah" kusan dukkansu suka hada baki wajen fadi "à quoi a-t-elle accouché ?(me ta haifa?)" Najma ta tambaya cikin zumudi.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 153 Yatsunta uku nurse din ta daga sannan tace "triplés" Dan qaramin ihu najma ta saki,har cikin ranta tana jin wacce irin me sa'a ce sultana?. Goumar yadan jefa mata harara sanda wajen ya kaure da fadin "Alhamdulillah" "Bakiji abinda kowa yake fada ba zaki mana ihu?" "Yaa goumar......don Allah kayi mana addu'a,Allah yasa kaima hakan take" idanu yadan fiddo yana kallonta,Allah ma yasa qasa qasa tayi magana "Au daga yaa maina dinne ma?" "Nidai haka nake gani" ta fadi a shagwabe,abunda ya sanyashi sakin dariyar da bai shirya mata ba. Daya nabin daya suka shiga dakin bayan an fito da ita,tana daga kwance tana hutawa ruwan da ake qara mata yana shiga jikinta a hankali. Yaran suna kwance daga gefanta cikin gadajensu da aka killacesu da kyau. Kowanne nannade cikin fararen kaya masu matuqar haske da daukan idanu saqar qasar turkey na kamfanin firstcray. Kiran sunan Allah ne kawai a bakunansu da tsarkake girmansa. Bibi kuka takeyi wiwi ana miqa mata yaran daya bayan daya tana dauka. Biyun cikin blue din kaya wanda ke nuna maza ne,dayan kuma cikin pink color wanda ke bayyanar da jinsin mace ne "Ko yau na mutu na godewa Allah,sultana da diyoyi har biyar,wayyo Allah na,Allah na gode maka,inama yau ace mohmoud yana da rai?,yazo yaga jikokinsa bayan ya rasa nafessarsa,ko yau na mutu na godewa Allah" "Haba bibi,ya da fadar haka kuma bayan nima nawa twins din suna tafe?,aisai kin gansu in sha Allah" goumar ya fada yana zolayarta. Fuskarta da hancinta ta goge da tissue din da maina ya warwaro mata,wanda dukka hankalinsa yana kan sultanarshi wadda take bin kowa da idanu,da alama bacci ne yakeson fusgarta "Kayya goumar,kayya.......sai me yawan rai" "To Allah ya ara mana" yayi saurin yin addu'ar,wanda duka dakin suka amsa da "Ameen". Sanda yaran suka iso hannun ama sai da ta goge hawaye sosai,yau itama dauriyarta ta qare,abun kamar a mafarki,abinda koda wasa bata taba kawoshi ba,wai sultana ce ta zama jini da tsoka kuma zuciyar kafuwar zuri'arta,yau diyar nafessa.....nafessan da aka haifa ita daya qwal......ta haifi sultana ita daya qwal itama yau itace taketa tara mata zuri'a haka. Allah al hakeem kenan......ba ruwansa,mulkinsa da ikonsa ne abun dubawa,d'a guda daya yana iya yara gari guda,duk cikin hikimarsa ce haka. Idonta ta maida ga sultana,sai taga bacci tuni ya dauketa,maina da har yanzu bai sanya yaran a idanunsa ba yana gefanta yana gyara mata rufa. Sai da suka tabbatar komai yayi settle sannan suka bar asibitin,ama ce kawai ta rage,don bata jin zata iya tafiya. Goumar ya dauki bibi da najma suka wuce gida,amma zuwa anjima yace zai dawo ya kawo musu abinci,sai ya taho da benazeer da batoul dake wajen tanja suga qannensu. Aikoda suka isa gidan shine ya fara musu albishir,wani irin tsalle da suka hadu suka daka suka daneshi tabbas banda namiji ne da sai sun kaishi qasa. Fafur suka dage sufa sai ya tashi kawai ya koma ga kaisu asibitin,da qyar da lallama najma da tanja suka lallabasu akan za'a dafa musua abinci sai suje akai musu. "fatabarakallahu ahsanul khaliqeen........maina ya dinga maimaitawa yana juya yaran a hannunshi daya bayan daya. Tun dazun da bibi ke sambatu akan yaran yana jinta,amma da yake dukka hankalin yana kan uwar yaran bai bada hankali ba. Da gaske ne,komai nashi yaran sun dauke,hatta da yatsun qafarsu irin nashi ne. Zama yayi dirshan yana qare musu kallo,hatta da safar qafafunsu sai daya cire, hakanan hulunan kansu, kasancewar dakin babu kowa saishi kadai da kuma Sultana dake bacci. Ganin komai yakeyi kamar a mafarki,wai shine baban yaran?,mahaifinsu?,bayan su benazeer su biyu da Allah ya bashi?,me zai cewa Allah?. Zuciyarsa ta karye sosai,yau sultanarshi ita ta zama.uwar 'ya'yanshi,ashe kanshi ya yiwa rainon?,ashe shi yasa yakejin ciwo zafi da radadi a kanta idan tayi wani abu a baya fiye dana kowanne yaro cikin gidan?. Ta jima da bude idanunta,idanun nata suna kanshi,yadda ya sanya yaran a gaba yana qare musu kallo ya dinga bata dariya. Ta dinga murmushi tana kallonshi tana kuma kallonsu,duk da cewa bata iya ganinsu amma tana jin wata soyayyarsu tana fusgarta har cikin jinin dake zagayawa dukka jikinta. "Uncle maina" ta kirayeshi da jaririyar muryar nan tata data fusgi hankalinsa. Ya maida dubanshi gareta, kyakkyawan murmushin nan nasa na saman labba suka subuce masa,ya tsareta da idanu yana kallonta,sai kuma ya ajjiye yaran a hankali yana takowa dab da ita. Hannunta ya riqe yana murzawa a hankali cikin nuna tsananin shauqi da kulawa "Welcome back honey.......am glad to see you feeling better" ya furta yana ranqwafawa saman kanta a tausashe ya sakar mata lallausan kiss a goshinta. Idanunta ta lumshe hancinta yana shaqar mata tattausan qamshin nan nashi dake saukar mata da nutsuwa cikin kowanne irin yanayi take ciki "Daddy of five" ta fadi tana kallon qwayar idanunsa da Murmushin tsokana. Qaramar dariya ya saki "Ke kika maidani hakan matata abar alfaharina". Kafin ta sake cewa komai nurse ta shigo. Ta duba komai,ta tabbatar da komai lafiya sannan tace zata iya tashi ta zauna,a bata ruwan lipton me dumi. Rubuce rubuce tayi,daidai nan ama ta shigo hankalinta itama akan sultanan,ta matsa ta duba yaran sannan ta qaraso wajen nurse din suna magana da ita. Dole ama ta sakar masa komai ta koma wajen jikokinta "Wannan karon bai kamata kiyi wahala ba kwata kwata ama,ya kamata kema ki huta da wancan dawaniniyar ta farko da kikayi kadai ta isa,Allah shine zai biyaki" abinda ya dinga fadi kenan cikin ranshi. Sai daya tabbatar ta jita comfortable sannan ya koma ya fara dauko mata yaran yana miqa mata daya bayan daya yana tambayarta kowanne "Da wa yayi kama?" Duk wanda ta kalla sai taga fuskarshi take gani bata wani ba. Baby girl din ta qarshe data dauka ya gaza boye dariyarshi,cikin sautin dariya yace "Ita dinma na dauka zatayi miki kara tayi kamanninki......Allah sarki sai gashi ta zabi daddynta itama" ya qarasa fada da sigar tausayi. Idanu ta zubawa yarinyar sosai saita daga kai fuskarta a narke ta maida kallonta fuskarsa,ta tabe baki kamar zata sakar masa kuka. Wayarta ama ta miqa hannu ta dauka kawai,ta samu tabi ta bayansu ta fice daga dakin tun ba'a saki layi ba tana zaune a wajen. "Nifa ban yarda da wannan wayon ba,su BB ma duka ai kaine,haka akeyi tsakani da Allah?" Dariyarshi ce ta fito fili,ya hadasu gaba daya ya rungumesu yana dariya "Karki damu,mu tara Next time,hudu zakiyo dukka masu kama dake" idanu ta waro waje tana fadin "Kayi haquri uncle maina ban shirya ba" sosai ta sake bashi dariya "Ba ruwan aliyyu daga Allah ne". Shigowarsu batoul ya katse wannan ganawar,tunda duka shigo suka durfafi jariran,gaba daya suka hana kowa ya tabasu,akan baby girl din akaso ayi rigima. Batoul tace ita tafi son a bata ita haka benazeer,daga qarshe aka ce batoul taci girma ta barwa benazeer,ta saki kuka tace ita kuwa saidai a bata sauran guda biyun. "An baki yaaya babba" goumar dake dariyar rigimar tasu ya fadi. Aiki fa sai meshi inji bahaushe,da gaske raino sukazo yi,da gaske kuma sunyi qanne,don qiri qiri sukaqi matsawa daga jikin yaran,hakanan qiri qiri suka hana a daukesu,kowacce ta saka nata a gaba wai raino takeyi,abun ya dinga bawa kowa dariya. Koda za'a fara gwadawa yaran nono zama sukayi,saida sultana ta zare musu idanu sannan suka fice. Duk saita dirirce,na farko rashin sabo,don zata iya cewa su benazeer ba wani shayar dasu tayi na azo a gani ba,na biyu kuma ga master aliyyu ya tasata a gaba,a lallai sai yaga yadda sultanarshi zata bawa yaranshi nono. Gaba daya ama taji zaman dakin yafi qarfinta,a ranta ta dinga shawarwarin wucewa ta barshi da matarsa,don da alama ya iya komai,hakanan bataga amfanin zamanta gaba daya cikin asibitin ba,don komai shike yi. Ko wajen shayarwa dimma shi ya dinga tayata,gyara can tallafe mata can,a haka kowannensu ya dana shan,duk da ruwan bai wani zo sosai ba. Uwa uba dole a hada musu da Madara saboda yanayin aikin da akayi matan bazai bawa ruwan mama damar zuwa da wuri ba. *_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 154 Da suka tashi tafiya saida goumar ya lallaba su benazeer ya tabbatar musu kuma gobe xai dawo dasu sannan suka yarda suka bishi. Sai da maina yakai zuciyarsa nesa sosai sannan ya iya tafiya yabar asibitin. Ranar gidan ama ya kwana,ya kwashi su benazeer su suka tayashi kwana cikin dakin mamarsu. Washegari da wuri suka yiwa asibitin dirar mikiya suka dora daga inda suka aka tsaya. Kwana uku kacal asibiti ya sallamesu,zuwa lokacin yaran sun sake washewa sosai,kyansu da kamanninsu da daddynsu ya fita sosai,ba macen ba ba mazan ba gaba dayansu MAINA NE. Kanshi tsaye ya kusa tarewa a dakin,gaba daya sai ya zamana ama ke jin kunyar ma,ta tabbatar sunyi gangancin dauko masa mata da 'ya'ya kam,shi yasa take kaucewa zaman falon,ta tattara al'amarinsu ta damqawa tanja,idan ka ganta dakin sultana to bai iso gidan ba,daya iso komai nasu ya koma hannunshi har sai zai tafi. A kwana na shida bayan sallar magariba ne,bayan ya gama riqe mata babban daketa rigima,ta goge jikinta sosai,ya tayata ta shirya cikin wani cotton material,ya tabbatar ta zauna taci abinci daidai yadda zai dace da lafiyarta,sai ya aza mata shi saman cinyarta. Tasan me yake nufi,tun tana kunyarsa da nauyin zaro maman a gabansa har ta soma sabawa. Tadan kauda kanta kadan gefe sannan ta ciro ta fara bashi ya soma sha. Wata nannauyan ajiyar zuciya ya saki yana kallon yaron,ya miqa hannu ya shafa sumarsa me laushi da santsi irin ta jarirai,wadda kuma ta biyo gadon jinin ABZINAWA "Ku taimaki daddynku ku rage masa shima......Allah bai gama qoshi ba kuka iso" yadda yayi maganar cikin karyar da kai da murya duk sai ya bata kunya ga dariya dake cinta. Zata iya rantsuwa wannan din ba uncle maina bane,ba aliyyu MAYAK'I bane,tana ganin aliyyu haidar kuma maina MAYAK'I ne kadai idan ya fita waje,amma duk sanda suka kebe irin haka wani mutum na daban yake zamar mata "Zanje naga aba......ya kamata a basu suna,banji yace komai ba" ido ta zaro "Bloodline......kada fa aga rashin kunya a abun,shi aba yasani ai,har yau bamuyi kwana bakwai ba" sumar kanshi ya shafa "Allah na kasa controlling kaina,inajin kamar na hadiyeku na huta da azababben son da nakeji ina muku......bari naje dai......ina dawowa....." Har yayi gaba sai ya dawo,ya rusuna daidai kunnenta ya sassauta murya "Yau dai please adan tanadin min wani abu da zan dan rage zafi kadan" yana kaiwa nan ya sakar mata kiss a wuya daya sanyata jin tsigar jikinta ta zuba. Ta bishi da kallon mamakin meye abun nema a wajenta a haka tana jego?,shi kuwa ko a jikinsa ya wuce abinsa ya fice. Cikin sa'a ya samu aba a falon yana dinner,ya danji nauyin ganinsa da yayi ya fito daga dakin,sai yadan kauda kai yana sake shafa sassalkar sumarshi. Basarwa aba din yayi yana ci gaba da magana da ama kamar ma bai ganshi ba. "Bismillah" aba din ya masa tayin abincin. Duk da a qoshe yake sunci abinci tare da sultanar amma borin kunya ya sanyashi zama dole yaja plate din. Sai daya kammala cin abincin ama tana gyara wajen ya kalleshi "Ya akayi angon qarni?" Da gaske kunyar aba din yanzu yakeji,yadan murmusawa yana dan basarwa,sai yayi gyaran murya "Aba cewa nayi kaman ya kamata a bawa yaran nan suna ko?" Idanu aba ya zuba masa sannan ya saki murmushi "To kai banda abinka aliyyu ina ruwan aba a nan?,shine uban?,na baka wuqa da nama,ka saka musu duk sunan da kaga ya kamata" Kunya ta sake kamashi,har yanzun halin aba yana nan na bawa yara 'yancinsu,ba takura ba shiga haqqi muddin baka sabawa addini ba. Yayi shuru kaman bazaiyi magana ba,akwai sunayen da yawa da suka cancanci ace an sanyasu,baisan wanne zai dauka a ciki yabar wani ba. "Feel free,yancinka ne,kada kaji nauyina" aba ya fadi ya jawo wayarsa yana budewa. Zamansa ya gyara sannan yace "Mohmoud da hamid,sai kuma khadeejatou(bibi)" "A'ah,mohmoud hamid da hamdiyya dai aliyyu" suka tsinci muryar bibi da basusan ta fito ba tana fadi. Dukkansu suka waiwaya suna kallonta tana takowa a hankali saboda ciwon qafafunta. Aba ne ya miqe yana gyara mata kujera,daidai fitowar ama itama "Bibi ya za'a miki takwara kice bakiso?" Ama ta fadi bayan bibin ta zauna. Kai ta daga ta kalli ama "Ke kikafi cancanta a yiwa takwara hamdiyya,kece jarumar.....kece kika sauya komai daga inda yake zuwa yadda ya zamana a yanzun.....ke kikayi gwagwarmayar hamdiyya....ke kikafi cancanta......a yanzu na yafe takwara,na amince a yiwa hamdiyya" ta fadi cikin raunin murya. Zuciyar ama itama raunin tayi,ba shakka bibi ta nuna dattako ta nuna kuma karamci "Shikenan kai aliyyu kaji,saika maye hamdiyya a madadin khadeeja,Allah ya rayasu yayi musu albarka". Dukkansu sai suka kasa barin gurin,sukayi zaman hira ana tuna abubuwa da suka wuce,wasu ayi dariya wasu a jajanta. A washegari ne najma ta baiwa kowannensu wakilin suna,ta zauna ta duba sunaye sannan ta daga Mahmoud daya kasance babban "Mohmoud aseem" ta daga usaininshi "Hamid Waseem" ta ajjiye ta daga gambonsu "Hajiya ama kenan,hamdiyya BIRRA" "ASEEM,WASEEM,BIRRA" Goumar dake zaune yana biye mata ya maimaita sunayen a jere. Kwanaki bakwai jikinta sultana yayi kyau,ta fara maida jikinta saboda samun isashiyar kulawa da takeyi. A zagayowar sati na biyu gaba daya yaran suka fara wani hawa,wanda yake nuna zaiyi wahala idan ba irin jikinsu batoul suka dauko ba. Daga benazeer har batoul sun maida dakin wajen wuninsu da kwanansu,wani irin so sukewa yaran,kamar su hadiyesu,qauna sosai irin ta dan uwa da dan uwansa. Watansu biyu suka kammala komai dukkaninsu suka dunguma zuwa Nigeria. Hutu sosai suka sakeyi a Nigeria din,ta fahimci kuma akwai abinda ya saukar dasu Nigeria din,saidai bata zafafa sanya kanta akan abubuwan da ba'a nemi ta shiga ba. Zaman da sukayi a nan ayana tazo musu sosai,da farko babu sakewa tsakaninta da sultana,saidai kuma ita ayana gaba daya ta kasa jurewa,don sosai 'yan ukun sultana ke tafiya da ita. Yara ne masu wani irin farinjini kamar 'yan uwansu,musamman da yake abune da ba'a saba gani ba a al'umma,yan uku abune me matuqar jan hankali a cikin al'umma,bare yaran lafiyayyu ne,ga tsananin tsafta da suke samu. Duk kayan da zasu sanya kuwa designer ne wanda mafi yawa sabon design ne da bai gama shigowa cikin jama'a ba. Rainon mamarsu ya amshesu sosai,komai na yaran dabanne. Koda tazo bata iya cikakken kwana biyar bata dawo gidan ba saboda yaran. Sannu sannu hira tadan fara shiga tsakaninta da sultanan,don dama ita sultanan tun bayan faruwar abun bata riqi waninsu a rai ba,ko laila ko ita. Birra na kwance cikin jikin ayana din tana barci abinta lakadan cikin tattausan kayan bacci. Sultana na gefe tana amsa wayar maina wanda duka kusan qorafi yake mata akan me yasa zata yarda ama tana boye masa ita?,koda bata fama warkewa ba yana buqatar kulawarta. Da qyar ta samu ta lallabashi,ta sauke wayar tana sauke numfashi gami da furzar da iska. Murmushi ayana ta saki tana duban sultana "Duk macen da tayi gigin auren maina tasha wahala,don zata zama 'yar kallo" idanu Sultana ta daga tana kallon ayana,sai dariya ta kubce mata "Innalillahi,ya kike haka?,so kike ki kashema mijina kasuwa?" "Ai gwara na gaya musu gaskiya wallahi.....mijinki na dabanne kamar yadda soyayyarku take ta daban,ko mu a baya rashin sani ya sanyamu gigin son saka kanmu a muhallin da ba namu ba......amma mu kanmu mun fahimci gangan ce" dariya sosai ta bawa sultana,daga nan sai kuma hira ta barke a tsakaninsu. Bayan komai ya kammala ta fahimci katafaren kamfani ne na hadin gwiwa tsakanin aba maina da ama sai saddi da almu. Basu bar Nigeria ba sai da komai ya daidaita,yaran suka fahimci komai duk da qarancin shekarunsu bisa jagoranci uncle tahir. Kafin su wuce saida maina ya tabbatar da kammaluwar ginin mansion house dinsa daya bawa kowa mamaki. Yanason Nigeria kuma yana sha'awar zama cikinta shi yasa ya aje irin wannan gidan,wanda a nijer dinma irinsa yake dab da kammaluwa. *_CONCLUSION_*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 155 *_Bayan shekara BIYU_* K'arfe hudu na yammaci jirgin saudi airlines ya sauke jerin gwanon fasinjojin daya dauko daga qasa me tsarki zuwa qasaf nijer cikin garin maradi. Cikin iyalan daya samu nasarar debowa,akwai familyn hamdiyya abdu me kano(ama),sannan kuma iyali jinin Aliyyu hamidou MAYAK'I(maina). Lokacin da aka sauke matakalar da zata sadasu xuwa ga shakadeden filin,Bintou aliyyu hamidou(batoul),Nadeeya aliyyu hamidou(benazeer), khadeeja aliyyu hamidou(BIRRA),hamid aliyyu hamid(waseem),mohmoud aliyyu hamid(aseem) haka suka biyo baya daya bayan daya. Kyawawan 'yammatan twins din masu tsananin kama da juna sune xaka fara gani a gaba,daya a gefan daya. Daga nesa kawai zaka fahimci me yawan surutun wato benazeer, batoul me halin daddynta kuwa nata saurare,sai fararen qwayoyin idanunta da suke kama dana mamanta wanda ta boyesu cikin brown sunglasses daya qara musu kyau su duka biyun. Sai da suka kai qasa sannan birra ta juya bayan taja tunga ta tsaya, batoul ce ta fara ganinta ta waiwaya a nutse cikin tataccen harshen faransanci daya kama bakinsu take mata magana "Wuce mana muje". Kafada tadan maqale ta narke fuskar nan me tsananin kama data maina,tamkar an dauko fuskarsa an aza a tata "Mummy nake jira" "Eh na sani ai maqalemata.....kinsan tare zasu fito da daddy ko?" Ta qarasa maganar akwai seriousness dinnan irin na maina akan fuskarta. Kafin su qarasa cewa komai ma'auratan guda biyu suka fara sanyo qafafunsu zuwa qasa. Aliyyu hamidou MAYAK'I da sulthana hamani mohmoud. Ma'aurata mafiya dacewa da juna ta fannin halitta....kamanni halaye da kuma dabi'a. Mummy sultana......wadda a yanzun duba daya zakayi mata ka kirata da CIKAKKIYAR MACE,wadda auren wuri da haihuwar wuri suka zame ma rayuwarta ado da kuma gata. Da za'a yi maka tambaya su waye benazeer da batoul a wajenta?,tashin farko cike da qwarin gwiwa zaka bada amsa da "Qannenta ne" ba wata alama ta kusa kota nesa da zata sanya kayi zaton cewa daga jikinta suka fito. Ko a yanzun da hannayenta ke cikin na masoyinta kuma mijinta da baya gajiya da dawainiya da ita,da kuma jurewa wasu halaye nata da dama tun usul yasan kayarshi dasu. Sanye take cikin wata baqar abaya me azabar kyau da sulbi saqar qasar oman,budaddiya da bata fidda wannan kyakkyawan shape din nata ko kadan ba. Idanunta itama saye cikin baqin sun glasses daya sake qawata fuskarta ya kuma fidda kyawunta da quruciyarta muraran. Qaramar handbag ce ta kamfanin Hermes a daya hannun nata da kuma carbin counter. A yadda take din,macace me matuqar sakewa da barkwanci ga iyalanta,me yawan jansu a jiki,musamman benazeer da batoul da a qalla zuwa yanzu suka doshi shekara sha uku,amma girman jikinsu yasa zakayi zaton sunkai shekaru sha biyar,sun doshi shekarun fara girma,shekaru masu hadari a rayuwar yarinya. Tasan illar irin wannan lokacin,tasan kuma matsalolinsa,wannan ya sanya ta sake musu ainun duk da cewa basu hannunta,suna hannun matar da ita kanta fiye da rabun tarbiyyarta a wajenta ta tsotsa wato AMA da suka maidawa suna AMOUR wato LOVE a turance. Ta cancanci sunan,don ta zame musu bango abun jingina,ita din madogara ce ta gaske. Wani irin matsanancin so takewa jikokin nata,soyayya fiye da son da takewa kanta,son da take musu bata hadashi dana kowa,soyayyar da take musu a bayyane take,gata take musu irin gatan daya amsa sunansa gata,saidai kuma duk da hakan.....bata yarda ba,bata kuma lamunci sangarta ko sauka daga hanyar data kamata ba. "Soulsis" maina ya kira sunanta qasa qasa. Idanunta dake saye a glass ta daga ta kalleshi "Are you okay?" Yayi mata tambayar da daga jiya zuwa yau batasan adadin sau nawa yayi mata ita ba. Qarfin hali tayi sosai wajen tattaro dauriyarta ta sakar masa murmushi "Am okay daddy" idanun nan nasa ya kafeta dasu yanason gano gaskiyarta ko akasin haka,sai ya kasa jurewa,ya miqa hannu ya zare glass din fuskarta,take qwayar idanunta da take hanashi gani tun jiya suka bayyana. Da sauri tayi qas dasu,saboda tasan muddin ya kalla din zai fahimci bata jinta daidai,wanda hakan kuma daidai yake da zuwan tashi nutsuwar "Qarya soulsis?" Ya tambayeta a sanyaye "Ba qarya nayi maka ba daddy......bansan me yake damuna ba.....banajin dadin zuciyata gaba daya,jikina kuma ina jin wani irin zazzabi ta cikin qashi na" ta bashi amsa takai tsaye. "Ya salam.......ko rashin lafiyar bibi kika saka a ranki?,amma kin manta ama tace jikinta da sauqi sosai?,saboda wanann damuwar taki ya sanya na rage kwanakin zamanmu a makka fa?" Haka kawai taji zuciyarta ta karaya,amma ta hana kanta bayyana hakan,ta dubeshi da guntun murmushi saman fuskarta "Nafi tunanin zazzabin dake damun jikina ne fa bloodline" dan zuba mata idanu yayi sannan kuma ya janye daga kallon nata badon ya gamsu ba "Asibiti zaka wuce damu" ya furta ta hanyar amsa kiran driver dinsu ta Bluetooth din kunnensa. "Asibiti kuma daddy?" Ta furta a shagwabe. Da idanu yayi mata nuni da yara dake tsaye daga gabansu kadan wadanda sukka suka zuba mata idanu cikin damuwar ko wani abune yake damun mummyn nasu. Tun suna can batoul ta fara yiwa benazeer complain na daukewar fara'ar mummyn nasu da kuma raguwar kuzarinta. Suna hada idanu da yaran sai tayi qoqarin komawa kan control dinta,ta waiwayo suka hada ido sai ya kashe mata ido daya gami da daga mata gira. Ta fahimceshi,dole kenan ta bada kai su zarce asibitin. Sam baya wasa da lafiyarsu,ko yaya abu yake zaice aje aga likita,wannan ma ya sanya abubuwa da yawa bata gaya masa saboda gudun daga masa hankali akan ciwon da baikai ya kawo ba. Babbar motar dake da wani irin kwarjini da daukan idanu ta daukesu gaba daya. Sabuwar qira ce da duka duka bata kai watanni uku da bayyana ba daga qasar Dubai. Duk abinnan birra na jikinta, batoul tayi tayi amma tace ita tana wajen momma dole ta rabu da ita. Suna cikin motar amma haka kawai tunaninta yake lulawa wajen bibi. Kwana uku kenan da sukayi waya da ita,doguwar wayar da bazata iya tuna kaf tsahon rayuwarta yaushe suka taba irinta ba,tun tana sultanar bibi har ta koma ta maina. Sunyi wata irin hira data tsayawa sultana a rai,ta kuma kasa mancewa da kowacce kalma data gaya mata. Haka kawai hirar ke yawan fado.mata a rai,take kuma nanata kowacce kalma dake ciki. Me abu da abinsa,asibitin nasu ne,don haka da shigarsu da gama ganinta duka ba'a haura minti arba'in ba. Sakamako kuwa ya fito da kyansa,ta samo tsarabar saudiyya,juna biyu na iya dadin watanni biyunsu a can. Baisan alaqarsa da son yara ba,baisan me yasa Allah ya jarabceshi da son haihuwa ba,ko don ama bata da yara da yawa?,ko don itama ama din hakanan Allah ya halicci zuciyarta a wajenta sukayi gado?. Duk yadda yaso daurewa saida idanunsa suka fidda qwallar farinciki. Ya tsugunna gabanta,ya riqr hannunta sosai yana hadiyar wani abu ya kasa cewa da ita komai,at last muryarsa ta fita bakinsa ya budu "Allah yayi miki albarka,ya jiqan mahaifanki" shine abinda ya iya furta mata. Ita kam jin komai take kaman a mafarki,ta zaci haihuwar sunyi sallama da ita,tunda gasu birra nada shekara biyar a duniya. Ta sani zata ga farinciki fiye ma da wanda ta gani a tattare dashi,don tsahon shekarun su birra da waseem da aseem kullum zancansa "Soulsis.......i need more" "Name bloodline?" "Twins ko triple" sau da dama dariya take masa,har ranar ya gaji bayan ta fito daga wanka tana daure da towel,ranar duka sun wuni ne wajen ama,data masa dariyar ya riqota sosai "Zakisan kinmin dariya,in sha Allah a watannan saina tabbatar na baki ajiyar 'ya'yana" kaman ya fadi da bakin mala'iku,bat samu a watan ba,amma watanni biyun kenan da wanann maganar sai ga cikin. So yayi yayi mata lallabawar daya saba mata shekarun baya,suna isa gida yaso ya fara killaceta yana bata kulawa,ta kama qugunsa ta riqe kaman yadda yake riqe da nata "Daddy kullum fa girma mukeyi,yanzun nidin uwa ce,mother of five,zan iya kula da kaina na kula da yarana na kuma kula da mijina da gidana.....bare ma meye aikin daddy?,gidan duka cike yake da ma'aikata,ka wadatani da masu yimin komai,nauyin dake kaina bashi da yawa". Sai data masa dabara da kyau sannan ya fahimceta. Zagewa tayi ita da yaran suka gyara dukka sassan da bata bari masu aiki su shiga mata,duk zirga zirgar da takeyi idanunsa da hankalinsa suna kanta,yayin da nata hankalin gaba daya yake kan bibi. Bayan kowanne minti sai taji ta fado mata a rai,ta dinga qoqarin yakice aikin ta kira ta gaya ma ama sun sauka ta kuma ji jikin bibi amma bata samu dama ba. Don tanason ta kammala komai da tasan maina zai buqata. Sanda ta kammala komai din kuma tana yin wanka sai zazzabi ya rufeta,daga bisani wani nannauyan bacci mara dadi yayi awon gaba da ita.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 156 Tsakiyar dare baccin nata ya yanke da wani irin mafarki da ya sanyayar mata da jiki. Ta miqe a hankali tana kiran sunan Allah, jikinta sosai ya jiqe da gumi,ta juya da nufin canza side na kwanciyarta sai idanunta ya fada a kansa yana zaune sosai saman abun sallah. Ido suka zubawa juna ita dashi,ta sani ma'abocin tashi sallar dare ne,jajirtacce wanda addu'arsa kullum kan iyalinsa suke,baya gajiya da musu addu'a da nema musu kariyar ubangiji,amma a yau din sai yake ganin wani abu na daban saman fuskarsa. Tanason masa magana sai ta kasa,taja jikinta a hankali ta sauka daga saman gadon ta wuce toilet,fitsari tayi ta daura alwala wai ko zataji dadin jikinta,ta dawo ta bude ruwa tasha sosai,sannan ta taka ta isa gabansa ta zauna. Hannuwansa ta kama ta riqe sai taji sunyi sanyi,ta kalli tsakiyar idanunsa saita hangi wani abu. "Daddy...." "Shshshsh......koma ki kwanta" ya fadi mata a raunane. Haka kawai ta kasa masa musu,ta miqe ta koma saman gadon ta kwanta din. Ta rufe idanunta yafi sau shurin masaki amma ko alamar wani abu me kama da bacci bata ji ba,sai kawai ta bude idanun nata ta azasu a kanshi wanda yana zaune ne saman abun sallah amma kanshi yana qasa. Batasan adadin lokacin da suka dauka a haka ba,tadaiji kiran sallah. Tana nan har ya miqe ya sake alwala "Ki shirya Idan na dawo daga masallaci zamu fita" kasa tambayarsa tayi har ya juya ya fice. Kawai dai taji jikinta gaba daya yayi sanyi kamar an zare mata laka. Duk da tana da alwala amma saita koma ta sake dauro wata. Tana idar da sallar kawai taji kuka ya qwace mata,kukan da batasan dalilin zuwansa ba,ta kuma kasa tsaidashi. Ko sanda taji ya bude qofar ta kasa daga kanta ta kalleshi,tana jinsa ya dauki key da wayarsa ya jefa a aljihu,sai ya miqa mata hannu ya tayar da ita "Sulthana" ya kirayi sunanta kai tsaye abinda ya jima baiyi ba. Daga kanta tayi ta kalleshi "Kukan na meye kuma?,uhmmmm?" "Inaji a jikina akwai abinda yake faruwa" ta fada muryarta a rarrabe da muryar kuka. Jikinsa ya jawota ya rungumeta tsam yana kiran sunayen Allah daya bayan daya. Yadda taji zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri ta tabbatar ba lafiya ba,amma albarkacin kiran sunayen Allahn sai taji nutsuwa ta saukar mata. Kusan mintuna goma sukayi a haka sannan yaja hannunta,ya bude ma'ajiyar takalmanta ya bata takalmi yaja hannunta suna ficewa daga dakin. Bai tashi kowa ba cikin gidan,kamar yadda yaran ba wanda ya tashi,koda birra da ba kasafai ta fiya baccin safe ba. Daya daga cikin motocinsa qanana ya bude ya tabbatar ta shiga seat din driver sannan shima ya zagaya ya shiga ya zauna ya tayar da motar. Baiyi horn ba daya daga cikin security dake gadin mansion house din nasu yana bakin aiki,don haka ya zuge masa gate din suka fice a hankali. Tun a farkon MAYAK'I street take ganin motoci kadan kadan har suka isa qofar babban gate din da zai sadaka da cikin gidan. Gabanta ya yanke ya fadi,tunda take tun kuma tasowarta bata taba ganin gate din gidan nasu a wangale haka ba,sai taji gaba daya hankalinta yayi cikin gidan kamar ana tunzurata. Ya fahimci hakan,don haka yayi parking dole a waje,yaje ya bude mata ya kama hannunta zuwa ciki. Idanunta sunga almu sunga atta sun kuma ga saddi, kowannensu kuma kuka taga yanayi,duk kamar an wanke mata kai ta bisu da kallo daga bisani zuciyarta tayi wani irin bugawa data sanyata saurin kama kalmar "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, astgafirullah ya Allah" ta dinga maimaitawa. "Wa muka rasa?,waye ya rasu?,karkuce aba,kada kuce ama,kada kuma kucemin bibi!" Ta tsaresu atta da tambaya. Kiran sunan bibi din ya sanyasu juyawa,hakan ya sanyata neman birkicewa. Isowar inna murjana 'yaruwa ga Bintou kakarta wajen ya sanyashi sakin qatuwar ajiyar zuciya baisan ta yadda zasu fuskanci wannan babban tashin hankalin ba,shi ko sultana. Ita ta riqeta,sai ta bita kamar raqumi da akala har suka wuce sassan bibi din. Duk wanda yake falon tabi da kallo,kowa yana nan,kowa ya hadu,dukka uncle's dinnata dama yaran gidan kowa zata iya cewa ta ganshi a falon,inna murjana taci gaba da jagorantarta har bedroom din bibi. Bai yarda ya barsu ba sai yabi bayansu. Dukka matan su oncle issofou suna wajen,tana dauke idanunta daga kansu sai ya sauka akan abinda ya dimautata gaba daya. Tana kwance cikin lullubin farin abun rufa,wanda a take zuciyarta ta gaya mata bibi ce,babu wadda ke kwance a wannan wajen sai bibi,taga kowa a gidan banda ita. Taga fuskar kowa amma bata ga ta bibi ba,duk wata jijiya dake jikinta ta gama shaida mata hakan,don haka bata tsaya jira ko sauraren kowa ba ta nufi inda take kwancen. Tana daga mayafin saman fuskarta ta fita tarwai. Cak taji komai nata yana neman tsayawa,kama daga bugun zuciyarta zuwa fitar numfashinta. "Alhayyul qayyumu!" Ta fusgi sunan da wani irin qarfi,cikin cikakkiyar ma'anar sunan nashi kuwa sai numfashinta ya dawo daidai,saidai gaba daya jikinta yayi rauni don haka ta zube ta saitin kan nata "A yanayin da naji jikina na tabbatar wani bangare na rayuwata ya tafi,na rasa wani sashe na rayuwata,wani mummunan abu zai faru dani,ashe kece zaki tafi bibi,ke zaki tafi ki barni,me yasa bibi?,ban shirya rasaki ba.....ban shirya rayuwa babu ke ba......ashe da kikace min aliyyu ne madadinki?,maina ne makwafinki abinda kike nufi kenan?,ashe da kikace kin barwa Aliyyu ni wasiyya ce kike yimin?,ashe tafiya zakiyi da gaske ki barni?.......me zan miki bibi idan ba addu'a ba?" Take kaman an zuba mata wani abu tasirin hassan gwarzo ya dawo mata,tarin addu'o'in da aka koya musu da yadda ya kamata ka yiwa mamaci. "Ya ubangiji gata nan.....me yawan zumunci ce.....me jin qan marayu ce......me kula da bayinta ne......wadda bata yarda zumunci ya samu tasgaro,ya ubangiji kajiqanta da mafi girman jin qai,kayi mata rahama cikin tarin rahamarka......ya Allah......ta kula da maraicina.......dama na sauran marayun dangi wanda ta sani da wanda bata sani ba......ya Allah,ka cika mata alqawarin nan da annabin rahama ya yiwa duk wanda ke kula da marayu na zama maqoci ga shugaban halitta a aljanna......Allah kasa kabarinta ya zama dausayi daga dausayin aljannah......Ya Allah ka san ita wacece a wajena.......Allah kafi kowa sanin irin girman rashin da nayi.....Allah ka bani ikon jurewa......bibi ki yafemin dukkan wani bacin rai da fargaba dana sakaki,daga randa kika karbeni a tsumman goyo har zuwa yanzun nan......Allah ka sanyamin dangana da haquri akan rasa bibi.....rashi na har abada......" Daga nan numfashinta ya qwace mata,ta tafi luuu ta kifa saman fuskar bibi da tayi wani haske kamar ka kirata ta amsa. Kafin kowa ya isa wajen shi ya isa,ya saka hannunsa gaba daya ya dagota luuuu. Gaba daya jikinta ya cika,ba alamun numfashi a tattare dashi. Kiran sunanta ya fara yi yana jijjigata cikin tashin hankali,sai kuma ya fara keta mutane da sassarfa yana fita daga dakin ba tare da yana fahimtar abinda suke fadi ba. Sai daya zagayo zai shiga motar bayan ya sanyata a ciki ya lura tuni almu na mazaunin driver,aminata na bayan tana kuka sai kawai ya koma ya umarci aminata ta koma gaba ya maye gurbin aminata yana sanyata a jikinsa. Gudu almu yake tsalawa amma gani yakeyi kamar tafiyar hawainiya yake. Bai dauke idonsa kona minti guda ba a kanta har suka isa babban private hospital da suke zuwa. Suna dagata don shiga da ita ciki saiga jini ta qasan doguwar rigar baccin jikinta,abinda ya sanyashi sulalewa ya zauna cikin reception yana kiran sunan Allah. Neman agajin ubangiji yakeyi,ko menene zaya faru ubangiji ya bashi qwarin zuciyar karba da hannu bibbiyu. Cikin qasa da minti.biyar wannan zuciyar ta aliyyu haidar ta dawo ganganr jikinsa,ya yunqura cikin matuqar jarumta kai tsaye ya wuce dakin da suka shigar da ita. Dashi akayi komai,kuma shima da kanshi ya fahimci cikin ne yake barazanar zubewa,dole ya amince akayi mata daurin mahaifa. Dr Noor ta qara masa haske da bayanin yadda za'a kula da ita,ta samu hutu sosai ake buqata da kuma zama waje daya. Basu wuce awa biyu ba wasu daga cikin yan gidan sukazo ganin yadda take,ama bata samu fitowa ba amma ta kirashi kusan sau biyu. Zuwa lokacin ya tabbatar an binne bibi,sai ya zauna kawai yana nazarin rayuwa "Yanzu bibi ta zama tarihi?" Ya tambayi kansa da kansa. Ta yaya zai mance da bibi?,itace qashin bayan nasararsa a rayuwa,itace qashin bayan komai,itace tushiya masomin dawa. Da kuka ta farka,hankalinsa ya sake tashi saboda ba'a son wanann tashin hankalin daga gareta. Oncle issofou yana gurin da oncle tahir,su suke da qwarin gwiwar fara dorata akan bigiren tayar da imaninta ta fannin yarda da qaddara. Bawai bata yarda da QADDARA ba,amma tana ganin komai kamar ba haka bane,kamar a mafarki ne,yau cikin duniya babu bibinta,uwa kuma kaka sannan mahaifiyar kaka duka a wajenta. Dole aka dakatar da masu zuwa dubiya,aka barshi daga shi sai ita. Ya bata dama sosai tayi kuka,har shima ya dinga hadiyar zuciya yana sauke ajiyar zuciyar a jejjere. Sai daya tabbatar ta samu sassauci da rangwame duk da yasan mutuwar bibi abune da ba zaya taba barin zuciyarsu da rayuwarsu ba,sannan ya fara lallashinta da kalaman da suka sake zabge wani kaso na zallar tashin hankali da damuwarta. "Zan zame miki bibi kamar yadda na zame miki momma nafessa da abba hamani da abba mohmoud...... nayi miki wannan alqawarin ba zaki sake kukan rashin bibi ba daga yau,saidai ki tunata kiyi kewa ki mata addu'a" hannayensa ta kamo ta riqe da kyau "Kayimin alqawarin ko meye na haifa indai mace ne khadeeja ce kuma bibi" "Ko biyar kika haifa kikeso a saka musu sunan shi za'a saka musu,amma muddin kinaso ki cika wannan burin saikin kwantar da hankalinki,lafiyar abinda yake cikinki ya inganta,ki haifota da cikakkiyar lafiyarta wadda ita zata bada wannan damar ta sanya sunanta" wata ajiyar zuciya me qarfi ta furzar tana kwantar da kanta saman kafadarsa tana kuma sake gayawa kanya dole ta samawa zuciyarta nutsuwa,tana da buqatar haifarwa bibi ta kwata yadda sunan zaici gaba da wanzuwa a ahalinta. Washegari suka sallamesu don ta tilastawa kanta haqurin dole kodon lafiyar abinda yake cikinta. Ta koma gida akaci gaba da karbar gaisuwa da ita,tayi qoqarin cika zuciyarta da tawakkali,saidai ko sassan bibi ta kasa shiga har akayi komai aka gama. Duk abinda Sharia tace game da rabon gado da sauransu aka aiwatar,inda aka samu kaso tsoka da bibi din ta ware ta rubuta da sunan sultana koda bayan ranta. Dukkansu sunfi qarfin haka,sultana kuma tafi qarfin komai a wajensu,aka tattara dukkan abinda ta bata din aka damqa mata,saidai tashin hankali ya hanata daga idanu ta karba,sai maina ne ya tsaya akan komai.*_GUDUN ƘADDARA_* *H U G U M A* BOOK 02 PAGE 157 *_Bayan shekara uku_* Kyakkyawar farfajiya ce da ake wareta cikin wani sashe daga sassan MAINA HAMIDOU mansion house aka mata wani irin yanayi na musamman da fararen duwatsu masu daraja da tsada,aka sanya mata rumfa da kujeru na kaba masu dadin zama da baiwa zuciya nutsuwa da ruhi. Kyakkyawar farar ba'abziniyar nan,ma'abociyar shimfidadden kyau me matuqar jan hankali da wani qira ta jiki da baya nuna tsufa ko adadin shekaru wato SULTANA HAMANI 'yar jaridan gidan Tv paris amma ta bayan fage wadda camera bata nuna fuskarta,amma ayyukanta da sunanta ya warwatsu a ko ina. Takardu da suka system ne masu yawa warwatse a gabanta tana aikin daya janye mata hankali,saidai duk da hakan daga nan inda take tana iya jiyo daddadan muryar benazeer tana karanta suratuttauba,surar dake dauke da bankadar asirin manufukan madeena da suka cutar da ma'aiki S A W sosai. Daya daga cikin yanayi da lokuta kenan da take yawaita godewa Allah da godewa ama data kaita makarantar data qara fahimtar da ita addini ta kuma fahimci alqur'ani da kyau har tana iya fahimtar ma'anarsa sanda ake karantashi,ta kuma cusa mata qaunar qur'ani ta yadda batayi sake ba har sai data tabbatar benazeer da batoul din sun kasance cikin mahaddata qur'ani suna da shekaru sha uku uku a duniya,yanzun shekaru biyu kenan. Benazeer da batoul sune suka zama madubin aseem waseem da birra,wadanda keda shekara takwas takwas a duniya,suke kuma da haddar izifi talatin kowannensu bisa jagorancin malaminsu na islamiyya da kuma taimakawar benazeer da batoul. Ta muskuta tana gyara zamanta kenan ta hangi tahowar batoul. Matashiyar budurwar buzuwar nijer usul data gado tsaho da kuma murjewar jiki. Ta qasan idanu take karantarta,tafi kowa kwaso dabi'u na mahaifinta,komai nata a nutse yake har ta iso gabanta ta ajjiye tray din hannunta saman table din gefan sultana din tana murmushi. Murmushin itama ta saki ta ajjiye takardun hannunta ta zauna sosai,ta saka hannu ta bude tray din da aka lullube tana fadin "Bari muga me besty yau ta girka.....anata karatu besty tanata girki" sultanar ta qarasa fada tana dariya. Sunayen data basu kenan ita da benazeer saboda tsantsar sabo dake a tsakaninsu. Duk da 'ya'yan ama ne halak malak,amma duk weekend na duniya indai suna qasar wajensu sukeyi,bama su benazeer ba,kusan duka yaran sunfi ganewa zama wajen ama din,don saisu kwashi sati biyu ma basa gidansu suna gidan ama ko family house na MAYAK'I. "Delicious.....anya ba catering zaki koma ba?" Ama ta fadi tana gutsirar pizza din dake gabanta. Dariya batoul ta qyalqyale da ita tana cewa "Mummy ko asa miki waigi santi kikeyi?" Sai ta saki dariyar itama. "Bibi!bibi!" Muryar birra ta karade kunnuwansu da kiran sunan KHADEEJATU BIBI da takeyi. Dukkansu suka waiwaya inda suke jiyo sautinta. Birra din ce ta biyo yarinyar da gudu gudu wadda duka duka ba zata haura shekara biyu da rabi ba. Hannun yarinyar cukuikuye da jilbab dinta tanata tsala gudu,bata kuma tsaya ba har ta iso gaban sultana ta fada jikinta tana ruqunmeta,kafin daga bisani birra ta iso cikin fushi ta tsaya a gaban sultana tana haki. "Me kuma ya faru?" Sultana ta tambayeta hannunta saman lallausar sumar bibi "Mummy.....wallahi yarinyar nan batason makaranta kwata kwata,tun dazu nake maimaita mata ayar da anty B tace na koya mata amma taqi fada?" "Gado ba karambani ba" muryarsa ta ratsa wajen. Dukkansu suka waiwaya suna dubanshi fuskokinsu dauke da murmushi,yayin da bibi dake kwance cinyar sultana tuni ta fincike ta tsinka da gudu ta nufeshi. Aliyyu hamidou MAYAK'I,a responsible father.....uba ba ga 'yayanshi kawai ba.....hatta ga matarshi da sauran ahalin MAYAK'I. Cikin shigar ba'abzinen asali harda rawaninsa,shigar da take qara mata soyayyarshi,take kuma sake fidda sigar kyansa haiba kamala harda kwarjininsa. Tun da safe da zai fita yayi shigar take masa tsiya. "Wannan kakar tawa ta musamman ce.....ku barmin abata,gadon qin son ecolé tayi,ku barta da sannu zata fara so tunda 'yanuwanta suna so". Kafada birra ta maqale "Dama tace ba zaka bari ayi punishing nata ba daddy" "A'ah zanyi kuwa muddin taci gaba da qin makaranta" ya fadi yana kama kumatunta,ita kuma ta qyalqyale da dariya tana boye kanta,daidai sanda 'yan samarin tagwayen guda biyu aseem da waseem sanye da shiga sak irin ta mahaifinsu suka shigo hannunsu dauke da leda. "Ku kaiwa anty batoul ko anty benazeer ta bawa kowa nashi" ya fadi bayan ya karbi leda daya ya sauke musu birra. Ciki suka dunguma sunata hayaniya irin ta 'yan uwa a tsakaninsu,dashi da ita suka bisu da kallo cikin jin alfahari da yaran nasu har suka bacewa ganinsu. Ajiyar zuciya ya sauke yana matsawa saman kujerar da take kai ya zauna daura da ita fuskarshi shimfide da murmushi ya miqa mata tattausan hannunsa me dauke da zara zaran yatsun hannu "Barka da gida rabbatul_bait" nata hannun ta cire ta miqa masa,ya sanyashi tsakiyar nasa hannun,dumi da taushin tafin hannun nata ya ratsashi. Komai nata na dabanne na musamman kuma,ya tabbatar ko iya yanzun da zai shanshana tafin hannunsa ya gogi wannan lallausan qamshin da tafin hannunta baya rabo dashi "Barka kadai abul_bait......barka da dawowa cikin iyalinsa" murmushi ya subuce masa yana shaqar daddadan qamshin KABBASA da kowacce sutura tata takeyi (Sirrina kenan) "Na gode......har yanzun kinqi gayan sirrin wannan qamshin,qamshin da nake fita dashi cikin qwaqwalwata na dawo kuma na tarar dashi" murmushi ta sake masa,yanason qamshin turaren matuqa,kuma koda ta sauya wajen siya saiya gane "Tafiyayye ne daga Nigeria,NAI perfumes" "Hajiya na'ima kenan?" Ya jefa mata tambayar,don kusan yasan matar saboda tsananin kirkinta da yadda take masifar son yaranshi,hakanan khumrarta da turarenta na dabanne,hatta da su benazeer turarenta ya fara kama jikinsu, ba'a zancan bedrooms dinsu dama zuwa parlor (Nima dashi nake using,kabbasa ko khumra duka,karkiyi missing sister,wanda ya sanni a zahiri yasan hakan,me buqatar tuntubarta ga number dinta nan +234 803 212 7953,it's not paid advertisement,na kawo muku ne kawai don qaruwarku,zan saka muku sample a status dina ku gani). "Ita,me kawo sabbin design na laces tare da ama?" Murmushi ya saki "Taya zan manta wadda ta qawata gidana da jikin matata da sasanayan qamshin dake bani nutsuwa?,anya ba mallaka a qamshin nan?" Sosai ya bata dariya yadda taga yana wani narke mata hadi da lullumshe ido,ta saki sassanyan dariyarta ta kama hancinsa taja "Kaiko?" "Keko?" Shima ya rama suka saki dariya gaba daya. "Me muka samu?,zakkar ce za'a fitar mu kawowa hajjaju account numbers dinmu?" Dariya ya sake bata,ta dago takardun tana kalla "Daddy ina zakakai kudi haka?,lissafin shagunan BB ne,sai kuma kudaden dana ware inason a ginawa bibi masallatai da makarantu da rijiyoyi a nijer da Nigeria,sadaqatul jariya" "Ma sha Allah,kin rigani a fili na rigaki a zuci" sai ya gyara zamansa "Za'a yi da naki kudin,nima zanyi nawa in sha Allah,Allah ya sanya kabarinta dausayi daga dausayin aljanna" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" ta amsa masa har yanzu tana jin kewa da rashin bibi a ranta. "BB kuma ai kin cika mana gidan da masu B,so dole za'a fadada shagunan dama.kamfanin,inason sakawa Birra Da little Bibi nasu share din,amma bansan ya za'a maida sunan ba,B din ya zama uku" murmushi tayi "Wannan aikin ama ne,na tabbatar zata fitar" kai ya gyada "Gaskiya ne,inajin jibi tasneem din sardauna da muzaffar din suhail zasuyi party na gama primary section,zamuje duka da yaran,saimu barsu a can mu qarasa wajen ama,auren atta da almu da saddi duka takeso a hada Next month in sha Allah" yayi maganar yana kallon agogon Rolex dake hannunshi "Ma sha Allah,abun ba wuya,Allah ya nuna mana ya rayasu su kuma,lallai akwai babbar hidima kenan" "Ameen ya hayyu ya qayyumu,ama zata qarasa cika burinta.....amma fa ina da complain" ya fadi sanda take miqewa don su wuce cikin gida ta bashi kulawa yadda ta saba. Barin abinda takeyi tayi ta waiwayo tana dubansa cikin kulawa "Na me fa bloodline?" Murya qasa qasa yace "An yiwa kowa takwara...... yaushe ni za'a yiwa aliyyu haidar takwara?" Dariya ke cinta tana dannewa,kusan sati guda kenan tayi PT ya nuna mata positive,amma taqi gaya masa,kaman kuma yasan da hakan ya dameta da zancan samun wani cikin,shi ko dan qin haihuwar nan ma ta matasan zamani baya cikinta. Sai data gama tattara komai tana murmushi idanunshi shi kuma suna kanta ya kasa gajiya da kallonta,ya kuma kasa dauke idanunsa,sannan ta daga fararen idanunta nan da bibi ce tayo irinsu sak tace "Biyoni ciki na gaya maka" tana fadi ta juya da dan sauri sauri tana dariya tayi cikin. Qaramin ihu ya saki na farinciki,ya tabbatar dole akwai abinda ta tanadar masa,sai ya dauki wayarsa yabi bayanta da 'yar sassarfa yanason cimmata fuskarsa fes da farincikin da yanzun baya rabo dashi,kuma itace silar wanzuwarsa a ciki yana fatan kuma har qiyama. *_Tammat bihamdillah_* *_Dukkan yabo godiya da jinjina sun tabbata ga Allah me kowa me komai daya bani ikon kammala wannan littafi 17/08/2024_* *_tsira da aminci su qara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad S W A_* *_haqiqa na yaba muku fans,masoyana bisa haquri da juriyar bibiyata,duba da yadda wannan karom rubutun yazo min da matsaloli da yawa wadanda ban san zasu kunno kai ba,ban kuma shriyawa zuwansu ba,amma duk da haka ubangiji yayi riqo da hannayena,da taimakonsa da qarfafawar gwiwar masoya har muka kawo qarshen littafin nan a yau,haqiqa na gode muku qwarai da gaske,masoya masu bani qwarin gwiwa,masu qoqarin bani uzuri da fahimtata,ina fatan Allah ya baku uzuri a ranar da kowa yake da buqatar hakan daga wajensa_* *_Da yawa sun jure,sun danne qorafinsu sai supporting da encouraging,Allah ya qara zumunci ya hadaku da dukkan alkhairi_* *_masoya mabiyana na kafar AREWABOOKS na yaba qwarai da juriya da haqurinku,ubangiji ya cika muku hannuwanku da rayuwarku da alkhairi maras yankewa, MASU FIDDA MANA Allah ya ganar daku,ya wanke muku zakatanku daga cutar da suka samu zukatanku na daqile ci gaban wani_* *_ina roqon duk wanda na batawa kona masa ba daidai ba ya yafemin,ina fatan Allah ya sadamu da alkhairinsa a gaba_* *Zafafabiyar na matuqar godiya a gareku,duk da tarin kusakuransu da ajizancinsu amma kun musu uzuri irin wanda masoyi kan yiwa masoyinsa, ubangiji ya dafawa lamuranku damu gaba daya* *_subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astgafiruka wa'atubu ilaika_*