[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ Karku manta wannan din shine littafina na farko kumin uzuri a inda na kuskure. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ *MOM TEEMAH* *AISHA HUMAIRA* *JIKAR HAJIYA* *CHIDA* Happy sallah to all muslim ummah, Ubangiji Allah ya karɓi ibadun mu, Ameen ```Page 1``` ***Kamar ko wacce rana yauma cike majalisar yake da samari,ba ka jin komai sai kace nace dake tashi a wajen ana musu kan ƙwallon ƙafan da aka kalla daren jiya,a ɗabi'a irin ta samari dama hakan na faruwa,musamman idan aka samu bambancin ra'ayi,ma'ana wane yana da club da yafi so shima wane haka,kuma abun takaicinma shi ne,a lokuta da yawa tare za'a je a kalla,a guri ɗaya majigi ɗaya amma idan an dawo dole sai anyi musu. Ƙarar taka burkin motar data faka daga can gefe ɗaya yasa ilahirin samarin dake gurin juya wasu na faɗin "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allah yasa ba accident aka samu ba.." Daga cikin motar data faka matashiyar budurwar ta fito kamar an cillota ta sha gaban ɗaya budurwar dake tafiya cikin kwalliya tana kwarkwasa,sake buɗe motar akai wata budurwa ta fito tana faɗin "Hafsat don Allah kada kice za ki takaleta da faɗa a gaban maza.." Ai bata gama rufe bakinta ba,faɗa ya kacame tsakaninsu babu zato bare tsammani,cikin kumfar baki ɗaya daga cikinsu harshenta har yana sarƙewa take faɗin "Ke har kin isa kiso saurayin da nike so? Me kike ji da shi? Me kike taƙama da shi? Wallahi in baki fita sabgar *ABDUL-KAREEM* ba sai na canza miki kamanni.." Tana huci taci gaba da cewa "na ga batun yau ba kike bibiyar shi dan maita,duk da ko sau ɗaya bai taɓa nuna ya san kina yi ba,wane irin maita ne wannan da baza ki fita sabgar shi ba!?" "Maitar data hana ki rabuwa da shi,duk da yanda yake yakice ki a kusa da shi,nima ita ta hana zuciyata rabuwa da shi" amsar da abokiyar faɗan nata ta bata kenan cikin haki suna ci gaba da kaiwa juna naushi,kaca² suka ci gaba da dambatuwa a filin Allah mutane na kallonsu,ganin al'amarin ya fara munana ne yasa mazan dake zaune a majalisar da abun ke faruwa tasowa suka shiga ƙoƙarin raba faɗan,suna faɗin "ku kuwa mene ne haka za ku tsaya faɗa da junanku a titi alhalin kuna mata?" Hafsat tace "ku rabu da mu yau mu fitar da raini ni da ita.. Ita har ta isa taso abunda nake so" ɗayar budurwar wani matashi ya kalla yana cewa "haba Nusaiba! Wannan ai ba girmanki bane,ina ke ina faɗa da wata a titi?" Nusaiba cikin jin zafin abunda Hafsat tayi mata tace "Sadeeq kuna dai kallo ta tare ni a hanya,bance mata ƙala ba ta nemi rufeni da duka,akan me? Ita ba uwata ba za tai min abu ban rama ba?" Haƙuri samarin ke basu duk da cewa inda sabo sun saba dan ba yaune karon farko da suka fara rabon fada na mata a majalisar tasu ba,amma kamar suna turasu,sai da ƙyal bayan sun yayyagema juna riga sannan aka rabasu,kowa ta tsaya tana kallon ƴar uwarta tana nishi kamar zakarun dambe,tabbas sun dambatu kuma sun goge raini,a wahalce dukansu suke maida ajiyar zuciya,daga mai kumburarren baki sai wacce aka naushe ma hanci. Wani matashi cikin masu rabon faɗan ya kallesu cikin takaici yace "kun san Allah ku rufama kanku asiri ku tattara kubar unguwar nan kafin *MAI JAMA'A* ya fito, "in ba haka ba kuma kun san sauran" cewar wani daga cikin samarin da suka raba faɗan,yana gama faɗa musu haka ya juya tare da shigewa cikin gidan da yake nan daura da majalisar tasu. Ƙawar Hafsat da tun farkon fitowarta a mota take cewa kada ta tankawa Nusaiba ce ta tallafeta bayan ta ɗauko ruwa a cikin mota tana cewa "kinga Hafsat kizo mu wuce,ni dai kin san ban son tashin hankali,ku kullum da kun haɗu ko a ina ne sai kun raba hali" tayi maganar tana zuba ruwa a hannunta tana wanke ma Hafsat ɗin fuskarta da aka fashe ma hanci jini sai zuba yake. "Kareema ki barni in koya ma yarinyar nan hankali,wani shegen ne yace mata ta fini son Mai Jama'a? Wallahi duk yanda take jin son shi na tabbatar na fita,dan kullum da shi nike kwana nike tashi a zuciyata,kuma wallahi yanzu na fara son Mai Jama'a,dole ta barni da masoyina.." Hafsat ta faɗa cikin kumfar baki,tsaki Kareema taja,cikin tarin jin haushi tace "ai kinji abunda kullum yake haɗani dake kenan,wai ke fisabilillahi yaushe za kiyi ma kanki karatun ta nutsu? ,ke ba masoya kika rasa ba,da kyanki da komai amma kin manne ma Abdul,wai ko kunya ba kyaji? Ni fa gani nike in baki girmi Abdul ba,to za ku zo kan²kan dashi,wallahi in kika ce haka za kici gaba da zubda ajinki akan shi,kina tare da wahala kuma zakice na faɗa miki hakan wata rana, dan tabbas kema kin san gaskiya nake faɗa. Yanzu ina amfanin abunda kuka aikata? Kuna mata ku tsaya dambe akan saurayi,kuma dan rashin kunya a ƙofar gidansu,ko kunyar tarin jama'ar dake wajen da masu wucewa baku ji ba? Yanzu duba yanda ta fasa miki hanci,faɗamin wani amsa za kiba mutanen gidanku idan suka tambayeki garin ya hakan ya faru?" Da ƙyar Hafsat ta ɗago kanta bayan jinin ya tsaya tana kallon ƙawarta tace "Kareema dan Allah ki ƙyaleni,ba na son yawan surutu, banajin zan iya tuki a halin da nike ciki kija motar mubar unguwar nan dan bana so Abdul ya fito ya taddani a nan,raina ƙara baci zai yi.." Taɓe baki Kareema tayi,ba tare da tace komai ba ta kamata zuwa gefen mai zaman banza ita kuma ta kewaya gefen direba taima motar key suka bar unguwar,to ita ma dai Nusaibar bata tsaya ba bayan matasan sun bata ruwa ta wanke bakinta daya fashe gidan su dake nan saman layin ta karasa dan itama bazata so ya fito ya ganta a haka da kumburarren baki ba, haka dai kowaccen su ta kama gaban ta ba tare da sunga mai Jama'an da suka yi faɗan akan shiba. Bayan wucersu haka samarin dake zaune a majalisar suka ci gaba da caccakar su,suna alawadai da halin ƴan matan, da kullum suka hadu sai sun tankama juna sannan babban abin takaicin shi wanda suke faɗan a kanshi babu wacce yake kallo da gashi a cikin su, dan wallahi da yana wajen sukayi wannan haukar karamin aikin shine ya sa belt din shi ya cicci musu uwa shiba ruwan shi, suma basa fara yin har gagin su muddin yana waje. *Mai Jama'a* kenan kullum mata ke binshi shi kuma bai gajiya da yarfa su. Ko da Sadeeq ya shiga cikin gida,kai tsaye inda yake da tabbacin zai samu mutumin nashi ya nufa,wato sashen Hajiya Innah,kishingiɗe kan doguwar kujerar 3 seater ya sameshi yana cin soyayyar gyaɗa,ko sallamar da yayi Innah bata amsa ba sai juyowar da tayi tana sababi "Oh ni Aminatu na ga abunda yafi zare tsayi,ace mutum ba shi da halin da zai yi ɗan abunshi na kwaɗayi yaci,sai kunzo kun baibayeshi kamar wasu sabbin mayu.. Shi wannan ɗan mai karfin ga shi yazo yamin sake² a falo,ko taya mishi gyaɗar nan banyi ba,amma kaga yanda ya wafce min kusan rabi,ga shi kaima zalo² ka biyo bayan shi,kuma yanzu dan Allah idan na hanaka gyaɗar nan baza ka koma gefe kana tsinemin a cikin zuciyarka ba?" Sadeeq dake ma Hajiya Innah wani kallo yace "yanzu nan Hajiya dama saboda soyayyar gyaɗa ne yasa ko sallamar da nayi kika ƙi amsamin?" Cikin jin haushi Hajiya Innah tace "ameen wa'alaikumus salam.. To na amsa sai me kuma?" Sadeeq yace "nifa dama zuwa nayi ince kije ki raba faɗa,dan inaga zuwa gaba ƴan matan jikanki kashe juna zasu fara,saboda hauka da kishin wanda bai san suna yi ba.." Salati Hajiya Inna ta fara tana tafe hannuwa "Muhammadur rasulullahi (S.A.W)!" Ta faɗa tana yunƙurawa har zanin ta na neman faɗuwa tace " Kai saddeequ! Fisabilillahi ina cikin gidan nan,amma dan cin amana har akaci aka siɗe baka zo ka kirani ba sai yanzu?" Sadeeq yace "Hajiya to ai kallo na tsaya dan in samu damar kawo miki rahoto da kyau, basai kin fita ba ai tuni suka gama dakuwa nasan yanzun sun riga sun wuce" Hajiya Innah tace "ɗan nema me yasa baka zo ka kirani tun ɗazu in fita mu daku da su ba? inji dalilin da yasa suke neman maida min kofar gida filin dambe" tai maganar yayin da take komawa kujerar data tashi ta zauna tana gyara zanin jikinta.. "Ni dai wannan abu na ci min tuwo a ƙwarya,yanzu ace duk cikin ƴaƴa da jikokina mata babu wacce ta ɗauko farin jinina har gara² ma ƴar wajen Jidda ita kam sak kamar ni lokacin ina yarinta na, a rasa wanda za'a ba farin jinin sai wannan mutumi mai ƙirar ƴan dambe,mutum a tsaye gansansan jiki duk a mummurɗe nayi² dashi ya raba kanshi da ɗaga waɗan can tsinannun karafunan yakiji, yanzun fisabillahi in tsautsayi ya gifta wata rana ba fata dai nike ba amma in suka kutto daga hannun shi suka dakar mishi kirji ba shike nan ba,to Allah ma dai ya kiyaye atoh nidai ba fata nike mishi ba, amma wai haka mata ke binshi su ko tausayin kansu basaji.. Ni fa kullum tunani nike ina zan samo mashi mata inya tashi aure,eh mana to mutumin da matan na binshi yana guduwa ai sai dai in nagaji da ganin shi a haka insa kayo min list na ƴan matan dake mishi layi kullum ka haɗomin kan hotunan su in duba mishi, kaga in ba'a dace ba sai in fantsama cikin gari ko a dace dan nidai ba mahaukaciya bane dazan ɗauki kasadar haɗashi da ɗaya daga cikin jikoki na atoh dan so nike in darzo mishi mai irin ƙirar jikinshi,kada in ɗauko wanda zai ƙwara.. Allah kuwa! Yo inba haka ba wannan ai zuwa ɗaya zaima mace ya tasheta aiki" Ƙyalƙyalewa da dariya Sadeeq yayi,shi ko gogan yanda kuka san ma bashi a falon,ko kallo basu isheshi ba gyaɗarshi kawai yake afawa a baki hankali kwance. Hajiya Innah ta ci gaba da cewa "kana ji koh Saddeequ,ni fa tsoro nike saboda a zamanin ƴan matancina tsabar farin jinina dole haka aka dunga ɓoyeni ko fita ba kasafai nike yinta ba domin fita 10 sai na samu saurayin da zai biyoni cewar sona yake,to farin jini ne dani duk inda na shiga sai masoya sun biyoni.. To wallahi ko Kakan ku ma darajar ƴan uwantaka yaci ya sameni da ƙyal,dan ni a lokacin manema na duk manyan mutane ne,rabon haihuwar iyayenku ne dai ya ajiyeni a Nigeria,na san da yanzun ina can kasashen larabawa.. Ko da yake shima fa Kakan naku mun kusa zagaye duniyar nan da shi gurin yawon buɗe ido,kafin ya mutu ya barni.." Sai kuma ta fara shessheƙa tana faɗin "ai ga irinta nan ABDUL-KHAREEMU ka tafi ka barni da yaran nan sun garƙameni a cikin gida kamar ƴar fursuna,nan da Habuja idan nace zanje sai na yi da gaske suke barina zuwa" ta ƙarasa faɗa tana face majina a cikin tissue, kamar ya samu TV haka Mai Jama'a ya gyara zama yana kallon dramar Hajiya Innah,ƙasa² ya furta "lallai matar nan" in ma ba kallon bakin shi kayi ba bai zama lallai ka gane mai ya faɗa ba. Gefenta Sadeeq ya koma ya zauna,cike da lallashi yace "yi haƙuri Hajiyana ki share hawayenki,In ABDUL-KHAREEMU ya wuce ai ga wasu jaruman mazan yabar miki masu jini a jika ma ba irin shi daya tsufa ba yanzu ki faɗamin wani ƙasa da wanne ƙasar kike son zuwa ni zan kai ki, kina wannan maganar gama na karfen naki nan a gefen ki Hajiyata kina damu ai baki da takaici wallahi umarni zaki bayar dole a cika !" Tunda suka fara magana bai yarda ya tsoma musu baki ba dan so yake yaga iya gudun ruwan su daga Hajiyar harshi kanshi Sadeeq ɗin da yake nema ya zama ɗan taya ɓera ɓari,to yanzun kam an kai matakin da dole sai ya tanka musu dan haka da wata irin kakkaurar murya yana juya idanunsa akan Sadeeq yace "ka kaita ina? Last month fa Hajiya ta dawo daga Dubai,kana sane da yanda ta hautsina min kai akan son zuwa dubai wai zata kaima kawarta ziyara, sannan yanzu daga dawowarta kace wai ta ƙara ƙetare ƙasa? Babu inda za taje kada ma tasa kai asarar kuɗin ticket.." "Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un.. *ABDUL-KHAREEMU!* Ashe kana cikin ƴan hassada na bani da masaniya? To dan ƙaniyarka naje Dubai ɗin,eh nace na je ɗin! Kuma komawa zan yi yanzuma,na ga dai iya kuɗin kuɗin jirgi ka biyamin kona shan ruwa a hanya da ake ba matafiyi baka bani sai wata shegiyar dubu 50 daka turamin wacce ko dan kenne bazata siyamin ba.. Ashe yanzu nan duk gatantaka da nike yi bita da ƙulli kakemin? To ta Allah ba taka ba,tashi maza² ka koma gidanku,dama ni na san ba zuwan Allah da Annabi kakema garin nan ba,zuwa kake saboda ɗan kayan daɗin da ƴaƴana suka taramin mu cinyesu da kai da askarawan daka tara min a kofar gida, kana nan kullum manne dani wai sunan ka gama makaranta amma kullum kana nan kamar nan ne gidan ubanka.. To tashi maza ka fice ka barmin gidan mijina,kullum haka zaka zo kana taramin jama'arka a ƙofar gida,sai kun zazzagemin buhunan abinci hankalinku yake kwanciya,idan za ka dawo kuwa haka nan kake zuwar min gida hannu na dukan cinya sai in naci sa'a ne kake ciko bayan motar ka da kayan abinci salon wani ya gani yace kai kake cidani, Haka kawai kazo gidana kuma ka nemi yimin iskanci,to uban kuturu yayi kaɗan.. Waiga bayan ka ga ƙofa nan,ta nan ka shigo ko? To maza bita ka fice min a ɗaki kafin in targaɗaka" Dariya Sadeeq ke yi domin indai rikici ne tsakanin Hajiya da Mai Jama'a,ba yau ne farau ba,kuma duk wanda yayi gigin shiga tsakani,tofa ya shiga ukun shi dan kanshi zata koma tace ana so a shiga tsakaninta da jikanta,dan anga duk cikin jikokinta shi ya ɗauko komai nata. Shi ko Mai Jama'a miƙewa yayi "nadai fada babu inda zaki" yana gama furta hakan ya fice kamar yanda ta buƙata,dan yau ba ya jin zai iya biye mata su raba hali da maraicen nan, Dan Hajiya bakinta baya gajiya da Masifa. Bayan fitar shi ta ɗauko sameerar da gyaɗarta ke ciki ta dankwafar a gefen Sadeeq tana cewa "To ga gyaɗar nan kaima kaci,karka ƙullaceni kace ina nuna bambanci.. Atoh! Ni ba ruwa na.. Yauwa! Faɗamin su waye ma kace sun yi dambe?" Sadeeq yace "Hafsa ce fa wannan yarinyar dai data nace mishi kin dai santa da yarinyar nan ƴar saman layin nan Nusaiba.." Hajiya tana yatsina fuska cikin takaici kamar ta ga abun ƙyama tace "tir! Yanzu su waɗannan danƙara²n ƴan mata,dan rashin daraja shi ne suka zage suna min dambe a ƙofar gida, ita dai wannan Hafsat to gaskiya dai banace uwarta tayi asarar aihuwa ba, amma ina tantama idan basuyi gadon maita a dangin suba, yarinya ta nace tuntale tale tunfa tana kwailarta take nan ta manne mashi dubi kaga yanzun yanda tayi wani uban ƙiba, nifa ranar da tazo nan tsoro naji kai anya yarinyar nan ba shaka fashe take shaba kuwa? kai bakaga yanda takoma ba? to wallahi ko wani nonon ta daya yayi girman kaina ga uban ɗuwawuka saida na kare mata kallo fes dan da fari nayi zaton ko ciko tayi, kai niko inba na koma Aminatun mahaukata ba ina zan yarda jikana ya auro min ita! wallahi irin su suke juya miji su sa yakijin maganar uwar data haifeshi ma balle kuma wata ni kakarshi, atoh nidai ko zannuwan data kawomin ranar babu wanda na ɗauka Jummai na kira nace tazo ta kwashe kaikoh kana nan zannuwa nefa duk babu wacce ta haura dubu ashirin kuma ma dai tsoro nike kar yazo kila ko tayi tsafe²n da yan mata keyi, Kaga nifa shi yasa banyi maraba da wannan majalisar da Mai Jama'a ya kafamin a ƙofar gida na mutanen shi ba,abu dai ya zama jaraba ko yana nan ko bashi sai ka samesu a ƙofar gidan nan ga shegun yan matan nan da kullum suke zaryar zuwamin gaisuwar munafunci, mutum shi ba shugaban ƙasa ba,shi kuma ba gomna ba,amma mutane su dunga binshi duk inda yayi ɗiyyy.. To ni dai ina nan ina mishi addu'a Allah yasa a cikin mutanen nashi babu na ɓoye,atoh kaiko farin jinin ai ya yi yawa.. Ka san shi yasa nayi tsayin daka wajen rabashi da zaman cikin makaranta nace ya dawo nan ya zauna a gabana,to kaiko duniyar ce ta lalace,ba mata kaɗai akema fyaɗe ba harda maza,haka kurum inzo ina nan kwance ina baccin asara cikin AC,aje can wasu kattin mata suma jikana fyaɗe in shiga uku.. Huuuuu! Aiko da ƙulli ya ci amanar kokoh" ta ƙarashe faɗa tana tsuke fuska,tace "Amma kaga nan duk rashin kunyar yarinya in tazo,ni zan takama ƴar banza burki,yo ina abun kisisina faso a ido? Bayan duk sun gama zubar da ajin,inba lalacewa ba wai mace kebin saurayi tana neman soyayyarshi kaji taɓewa fa salon su ruguza min tarbiyyar da nayi shekaru ina daura shi akai, ah ah nikam badani ba wallah .." ******"""" Masha Allah to gashi nan dai ina rokon ubangiji Allah yanda na fara rubutun nan lafiya ya bani ikon kaishi har karshe cikin amincin sa, #My first novel ina fatan zaku soshi🤍 #Ummiee~Zaria # 22/4/2023 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_KarKu manta wannan ɗin shine littafina na farko kumin uzuri a inda nayi kuskure. *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ *MOM TEEMAH* *AISHA HUMAIRA* *JIKAR HAJIYA* *CHIDA* ```Page 2 ***Shi dai Sadeeq dariyar ta kawai yake kwasa yanaci gaba da murkushe mata gyadar data gama goranta mishi kafin ta bashi, "Kai ya haka daga ɗan sammane kuma saika Kama ka wani tasamin gyada a gaba kayita tumur musa!? Nifa dan kar kaga rowata ne yasa na taya maka,Gaskiya dai ku canza hali dan Wannan ba halin musulmin kwarai bane atoh ina ma amfanin kwaɗayi!, Allah ma shedane Wannan kwaɗayin naku ba'a wajena kukayo gado ba can dangin iyayen ku mata kukayo gadon shi ku anayin gadon abun arziki ku kuna na tsiya" Bai tsaya jin karshen zancen taba ya cika hannun shi da gyaɗar sannan ya mike dan yasan kaɗan daga cikin aikin hajiya ne yanzun ta nemi tara mishi jama'a kamar ba itace ta bashi gyaɗar kan radin kanta dan ganin damanta ba. "Au to dan na fadi gaskiya shine kaima ka mike wato ga jarabab biyar tsohuwa ko wani mara mutunci a cikin ku dana fara mishi magana saiya tashi ya bani waje, To wallahi nikam da bakina ko uban ninku basu isa su hanani magana ba, Dan ma Allah ya taimakeni nayi tsaye akan ku da addu'a da da nefa yanda na soya gyadar nan haka zatayi batar dabo ko sama ko kasa ban kara ganin ta kun biyo dare kun min fashin ta sai dai tashin zance, To shikenan kuma sai ace bazanyi magana akan gaskiya taba! Da zarar nayi laku²fa cutata zakuyi su kuma iyayan ku da shegen son y'a'ya ko kunyi ba dai² ba basa iya saku a daki su ladafta sai suyi ta sanyi² kamar ma tsoron ku suke, Kuma idan ka fitan ka kiramin shima daya gagaren duk kuzo ku koma gaban iyayen ku, ban iya wahala biyu nayi na iyayen ku yanzun kuma gaku to bazaku karasa tsofar dani ba Haka kawai kuna bigewa da zuwa hutu kuna zuwa kuna taramin taron mutane a gida kun maida min gida kamar gidan baitil mali to gidan nan dai na mijina ne bana iyayen kuba," Haka taci gaba da sababi itafa idan jidalin ta ya motsa ko dogon numfashi bata shaka saita gama tayi ta numfarfashi, Kuma fa duk wannan fadan da take Sadeeq din da take dashi tuni ya dade da barin mata falon. Shiko *MAI JAMA'A* koda ya fito majalisar baiyi mamakin rashin ganin *HAFSA* da *NUSAIBA* ba dan yasan daman bazasu bari ya same su a wajen ba sai dai yaji bakin cikin yanda kullum suke zubar mishi da kima to wallahi basu kaɗai ba harda ma sauran yan wahalan duk saiya shata musu layi tunda basa tashi yin jakancin faɗar su sai a kofar gidan nan tunda duk doɗaɗɗiyar kwalwa garesu, sun ma maidashi wani ɗan iska tunda duk wanda yaga suna faɗar idan ya tambaya cewa za'ayi akan shi suke faɗar. Sallama yayi Sannan ya koma kan kujerar da take dimun da iman a matsayin tashi ya zauna, Karfa kuyi zaton majalisar irin ta yan zaman sa idon unguwane! Inah tashi majalisar ta ban²ta da tasu domin da yawan mutane ma *FADA* suke ce mata kamar yanda yake rubuce a jikin shagunan da suke laye a kofar gidan na Hajiya Innah wato *FADAR~MAI~JAMA'A* Hatta da shagunan idan kwatance zakayi sai ka Kira *FADAR* Kafin a gane, Manyan Shaguna ne da suka kunsa Shagon ɗinki na Mata da mazan ƴan gayu, Shagon aski na maza masu ji da kansu, Shagon saloon na ƴan matan da sukejin cewa sun isa , Shagon kayan masarufi,Babban Restaurant, Shagon karshe shine na kallon kwallo domin shi yafi sauran girma dan haka wajen kamar karamar kasuwa haka yake cika da mutane a koda yaushe, Sai kuma gefen da aka ware na buga table tennis dasu snooker , Gaskiya dai yanda aka tsara wajen dole ya burge mai kallo dan haka wajen bashi rabo da matasan yan gayu mata da maza. Kuma duka shagonan mallakin *ABDUL-KHAREEMU* ne jikan Hajiya Innah. Wato *Mai Jama'a* Ita kuma fadar tana daura da shagunan ne. Babbar falo ne sai dai ba ginin bulo aka mata ba anyi amfani da Aluminum da glass mai karfi ne wajen ginata sannan aka zagaye ta da burglary dan bata kariya ga yara masu kiriniya ta yanda ko sun jefa dutse bazai cimma glass din ba balle ya fasata, Hajiya dai tace fadace ta magulmata domin dai indai ba sun zuge glass din bane to kai na waje komin kwa²rka baka sanin wake ciki amma su duk Abunda ake a wajen a kan idon su yake faruwa. Sannan an kawata cikin ta da duk wani abun bukata da za'a iya samun shi a falo na alfarma tun daga kan Kujerun zama, Kayan kallo fridge don sanya² abubuwan sha kai hatta da labulayen da aka zagaye falon dashi abun kallo ne gaskiya dai an gyara wajen dai² da zamani, Duk da falon ya kasance majalisa ta maza domin duk wani abu na matasa idan ya tashi anan sukeyi tun daga kallon kwallo zaman meeting dama duk wani Abu mai mahim manci daka iya tasowa, Sai dai ita wannan Majalisar ba maza kadai take dauka ba harda zafafan yan matan dake ji da kansu, Wasu yan makaranta ne anyi karatu tare, wasu kuma yan wahalan fataucin soyayya ne da suke fakewa da kawo dinki ko saloon ko zuwa cin abinci dan suzo su gwada sa'ar su ko tarkon su zai kama kurciya, wasu kuma yan matan sauran yan majalisar ne wasu ko zuwa kawai sukeyi asha hira su wuce, To haka dai wajen yake kullum baya rabo da mutane ko uban gayyar na gari ko bashi akwai masu kula da Fadar shi sukuma masu shaguna suna harkar kasuwancin su. Haka dai suka kare zaman wannan rana ba tareda wani daga cikin su ya tada maganar abunda ya faru tsakanin *hafsa* da *Nusaiba* ba. *Wannan kenan* ******* Cikin garin zaria *Unguwar Malamai* note(nasa sunan unguwan ne kawai bawai dan akwaita ba). Unguwace ta manya kuma fitattun malaman da akeji dasu a cikin garin na Zaria, Gidan *malam Almustapha* wanda mafi yawan mutane sukafi Sanin shi da *Malam Almu* yana daya daga cikin manyan malaman da suke rayuwa a cikin unguwar tsayin shekaru, Babban gidane wanda suka gada tun fil'azal dan haka gidan ya kasance babban gidan daya kasu kashi² kowa da sashen shi. *MALAM ALMUSTAPHA*(Baba Malam) shine babba dan haka ya kasance shine matsayin uba a wannan gida tunma kafin gushewar iyayen su, Yana da mata biyu da yara mata 8 da maza 12 duk da kasancewar shi babban malami allah bai jarab ceshi da yawan aure² ba domin duka matan shi biyu auren zumunci ne uwar gidan shi mai suna *Ameena* yaran gidan ke kiranta da (innan mu) ita din yar uwar shice ta jini da mahaifinta dana malam iyayen su daya, Sai matar shi ta biyu mai Suna *Hadiza* (dije) itama dai yar uwace ta fannin uwar su mahaifiya. Malam yana da kanni 4 maza 2 mata 2 maibi mashi namiji shine *ADAMU*(Baba Adamu) Shima babban Malami ne a cikin gidan yake zaune da matar shi daya da yaran shi 3 maza 2 mace 1 sunan matar shi *MURJANATU* (Aunty Murja) Bashi da yara da yawa saboda baiyi aure da wuri ba , Mai bin shi ita kuma mace ne *AISHA*(Momin Abuja) ita kuma a Abuja take aure dan haka ita da iyalanta can suke zaune, Sai *Mukhtar* (BabaAuta) Shi kuma professor ne yana karantarwa KASU shima anan cikin gidan yake zaune da matar shi 1 *Hauwa'u* Jidda (Momi Hauwa) da yaran shi 8 maza 5 mata 3. Sai *Fatima*(Momi Zahra) itace autar su ita kuma tana Auren wani babban dan kasuwa ne a Kano, Ahalin malam duk da kasancewar su manyan malamai basu zauna haka ba suna Noma kuma suna hadawa da kasuwanci dan haka suke da rufi asiri sosai. Sai dai kuma Allah yayi malam Almu cikin mutane masu wata irin baud ɗaɗɗiyar hali sannan Allah ya mishi wata irin kwarjinin da mutane ke shakkar shi yana da kwarjinin da ba kowa yake iya hada ido dashi ba, Kai hatta da matan shi na aure suna bala'in tsoron saɓa mashi daga su har yaran su, Ya kasance shi mutum ne mai magana guda 1 inyace eh to eh din zai tsaya akai ko tama saura daɗi ko kartayi su suka jiyo, Malam mafaɗaci ne kwarai domin da zarar ya shigo gida duk wani mai guntun kiriniya dole ya natsu dan tun kafin ya iso gyarar muryar shi ke isarma na cikin gidan isharar gani nan tafe, Sannan bai yarda ya shigo gida ya iske matan shi zaune da yaran su a tsakar gida da sunan suna hira ba, yanzun zai Kama sababi cewa "sun tasa yara a gaba suna koya musu gulma da tsugudidi" Dan haka ko zaune suke da zarar sunji motsin shi kowacce zata shige daki kota Kama wani aikin, Hakan kuma bashi zaisa su tsiraba dan saiya duba ko ina duk inda ba'a share da kyauba ko kuma ya dawo ya cimma ba'a kammala abinci ba to aiko ya dunga surfa faɗa kenan, shi dai haka nan Allah ya yishi ya iya fada harda marar dalili dan wallahi ko kajin gidan suka dameshi da kyar kyara ko cara sanyawa yake a tattare su a yanke, Sai dai kuma duk wannan halin faɗar nashi Allah yama malam son jama'a yana kuma da farin jini wajen al'umah kodan yanda yake kyautata musu, yana kuma da kyauta sosai dan haka gidan shi ko yaushe basa rabo da baki gashi dason zumunci yana son yan uwan shi sosai alkhairin shi bai tsallake kowa ba harda jama'ar unguwa, Malam yana da wata akida wacce kusan kowa yasan shi da ita , ta kin ilimin boko sosai yake nuna kyamar shi ga duk wanda ya karkata ma ilimin boko da akida irinta nasara duk da cewa ilimin bokon ta yawaita sosai, Dan haka ya zamana tun daga kanshi har zuwa kannen shi basuyi karatun ba,sai dai ya yarda ya kashe ko nawa ne ya tura su zuwa kasashen musulunci domin nemo ilimin islama, ba'a samu sassauci ba har sai da Malam Adamu yayi tsayin daka wajen nunama malam cewa shima fa ilimin bokon yana da ranar shi domin shi *Malam Adamu* ba mazauni bane mutum ne mai yawace² gari² kasa² yake zuwa yawon neman ilimi fitan da yakeyi ne yasa ya fahimci a wannan rayuwa ba ilimin islama kadai mutum yake bukata ba ya dace a nema harda na zamani dan haka ya fantsama neman ilimin, Sanda yayi wani dawowa ne ya samu malam da maganar dakyar dai ya shawo kanshi ya yarda cewa ya yarjema yaran shi maza da kanin shi *Muktar* su fara zuwa shima iya secondary kadai da kyar ya yarda matan suma aka sanya su da sharaɗin primary kawai zasuyi kuma hakan ce ta kasance, badan malam yasoba yanaji yana gani *Adamu* ya kai yaran makaranta. A haka har wasu daga cikin su suka kammala aka aurar da matan mazan kuma shida kanshi ya rarrabasu zuwa kasheshen musulunci domin karo ilimin addini, Duk da Ana ganin cewa malam yayi sauƙi a lokacin amma koda ya tashi aurar da Autar su da kuma yaranshi mata da suka kai aure a lokacin bata canza zani ba, kamar yanda kowa yasan cewa baya bada auren yaran shi mata ga kowa sai yayan manyan malamai ko Kuma wani babban mutum ko yan kasuwa shi dai har yanzun bai yarda ya hada zuria da ahalin boko zallah ba, dan har yanzun baya shan inuwa guda da ƴan boko. Sannan kuma duka yaran shi dana yan'uwan shi dake zagaye dashi shine yake zaɓa musu mazajen aure kedai sai dai ace miki (ki shirya kina da baƙo) ko ya miki ko bai miki ba wannan ke kika jiyo domin dai wannan zuwan da baƙon yayi bazai kara dawowa ba sa ranar aurene zai biyo baya, maganar fahimtan juna bayan auren kwayishi a gidan ku. Sai dai adalci daya da yake musu shi baya tallan yaran shi ma kowa haka kuma baya fidda ma yarinya mijin aure sai ya jira ta samu manema akallah 3 sannan shi da kanshi zai bincika wayafi nagarta a cikin su wanda ya ciri tuta shi zaiba sauran suyi hakuri, Haka kuma shi baya bada auren mace kamar sadaqa a'ah duk wani Abu na neman aure sai yasa kayi shi kuma in an kawo wanda bai mashi ba zaisa a canza, sai dai bai yarda da zaryar zuwa zance ba, haka kuma baya amsan karamin sadaki domin yana kafa hujja da cewa y'a'yan yan boko ma da sukayi karatun zaman duniya basa aurar da yaransu da arha ballantana shi da zai aura maka mahad daciyar Alqur'ani mai tsarki. Sannan kuma shi a tsarin shi baya aurar da yaranshi ma talaka domin dai yace "bazai saida akuya ta dawo tanaci mishi danga ba" dan haka saiya duba mai rufin asirin da yasan zai iya rike mishi ɗiya da kyau kafin ya bada auren ta. Sai dai yana rangwame wa yaran shi maza shi namiji yana da damar auro yarinya komai talaucin babanta idan ma ya Kama shi malam din da kanshi yakan dauki nauyin komai da iyayenta zasu mata na kayan daki amma fa banda *y'ar boko*! Hakan kuma ba iya kan ƴa'ƴan shi ya tsaya ba harta da ƴa'ƴan yan uwa ko makota in uba bashi da hali shi yake tsayawa a matsayin waliyyi haka kuma shi zaiyi ma yarinyar kayan ɗaki, Shi dai Allah ya sani har gobe baya shiri da duk wani dan boko. Sai dai duk wannan taka tsan² din da yake wajen ganin ya katange iyalanshi daga shiga sabgar boko Abunda bai sani ba tuni kannan shi biyu sunyi zurfi ƙwarai a cikin shi, domin sun gane cewa tafiyar tafi armashi idan ka haɗa ilimin duka biyu domin sun faɗaɗa karatun su sama da iya sacandiren dashi Malam ya sharɗanta musu , Dan haka shima Mukhtar ya dage sosai ya maida hankali wajen karatun shi duka biyun, kuma acan wajen yawon neman ilimin nashi ne ya haɗu da *Hauwa'u*Jidda ita din ta kasance yar babban gidace wadanda suka jiku da ilimin boko da islama soyayya mai tsafta suke gudanarwa a tsakanin su ba tareda Sanin malam ba, burin mukhtar bai wuce ya dawo gida ya gabatar ma Malam da jidda ba danya nema mishi aurenta. Bai taba zaton neman auren Jidda zai zamo matsala tsakanin shi da malam ba domin tun tasowar shi yasan cewa malam yana son shi yana son duk abunda yake so domin shi Mukhtar kallon uba yakema yayan shi yana matukar girma mashi, Sai dai ya manta da ra'ayin riƙau irin na Malam akan yan boko, ga kuma laifi na 2 dashi Mukhtar din ya aikata nayin karatun bokon mai zurfi batareda Sanin malam ba. Bayan da Mukhtar ya kammala karatun shi kasa dawowa yayi saida ya jira ya'yan shi Adam dan so yake suna komawa a fara maganar auren shi da Jidda dan haka tare suka dawo gida harma da sauran yaran. Sai dai Abunda basu saniba shima malam a gefen shi ya fara nemawa dukan su biyun aure domin zuwa lokacin ya fara damuwa da rashin auren *Malam Adamu* domin kullum idan ya mashi maganar aure sai yace mishi "ba yanzun ba" dan haka ya gaji tare zai haɗasu ya aurar dan malam Adamu zuwa lokacin ya wuce a kirashi tuzuru dan ma yana da rufin asiri shi yasa girma bai nuna sosai a jikin shiba. Shiko malam Adamu a inda yake yayi kafuwar da yake tsoron ya matsa daga wajen yabar dukiyar shine saboda rashin amana da tayi yawa a wajen al'umah da kaɗan² yake so ya kwaso arzikin daya Tara acan idan ya dawo gida gaba ɗaya sai yayi aure dan duk yarinyar da yace zai aura yanzun zai shiga hakkinta da yawa tunda yana dadewa bai waiwayi gida ba. Ɗiyar wani babban Malami malam ya fara nemawa Mukhtar ba tare da shi ya sani ba, shi malam a wajen shi bazata ya shirya yi musu da sun dawo sai aure sai kuma gashi bayan dawowar su kafin malam ya gabatar musu da nashi bazatan su sun bashi nasu. Domin shi mukhtar da kanshi yaje ma malam da zancen Hauwa'u a matsayin matar da yake son aura, Malam yana son Mukhtar sosai a cikin kannin shi wannan dalilin shiya hanashi kawo mishi maganar murjanatu anashi zuciyar ya kudura cewa idan aka gama maganar jidda daga baya zai bijiro ma mukhtar din da nashi zabin daya mishi koba komai ai Namiji mijin mata 4 ne dan haka ya taushi kanshi. Abubuwa basu rikice ba sai da yasa a mishi bincike akan ita Jidda ɗin yar wasu ahali ne? Ranshi ya baci sosai ayayin da waɗan da ya wakilta akan su mishi bincike suka kawo mishi rahoto iri daya. Duk da yarinyar ta fito daga babban gida sannan sun bincika bata da wani nakasu tana da ilimin addini mai zurfi sai dai fa ita da ahalinta dukan su alhazi bokone domin binciken su ya nuna musu a kasar waje tayi karatunta na gaba da secondary saboda ilimin da Allah ya bata yanzun haka dai ta dawo kasane a matsayin likitan mata da ƙana nan yara. Ran Malam ya baci sosai taya mukhtar zai aikata haka? Ya rasa yarinyar da zai nema sai yar boko ita nata bokon ma tafi karfin tayi shi a gaban iyayenta har sai ta ketare ƙasar waje! Koda yake ai uwa batayi gudu yarta ta rarrafa ba waye zaice bai san ubanta *ABDUL~KHAREEM* Ba? Mutumin da kowa yasan rikakken dan boko ne naƙin ƙarawa shida ahalin shi! Kai ina ai wannan zagi kawai *Mukhtar* yake so yaja mishi wajen mahassada dan haka wanna magana ma bamai yuwuwa bane kuma ba a gidan shiba!. A wannan rana malam yayi faɗa kamar ya ari baki baiyi kasa a gwuiwa ba ya nemi ganin *Adamu* yace mishi ya taho tareda *Mukhtar* bayan sun iso duk son da yake ma *Mukhtar* ajiye shi yayi gefe ya mishi kacha² har Adamun bai shaba a wanna rana, karshe kuma ya fada mishi ya rufe maganar wata Jidda a cikin ahalin shi anan yake fada musu dama ya fara nema musu aure tun kafin dawowar su. #Share please # #My first novel ina fatan zaku soshi🤍 #Ummiee~Zaria #25/4/2023 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_# My first novel *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ *MOM TEEMAH* *AISHA HUMAIRA* *JIKAR HAJIYA* *CHIDA* ```Page 3 *Sosai hankalin *Mukhtar* ya tashi dan ba karamin so yakema *Hauwa'u Jidda* ba, tunani yake akan taya²ma zai tun kareta yanzun yace mata *ya fasa auren ta!* Kai ina gaskiya da sake. A takaice dai ankai ruwa rana sosai kuma rayuka sun baci saida *Mukhtar* yayi kamun kafa sosai wajen sauran iyayen su da suke raye da kuma manyan Malaman da yasan Malam yanajin nauyin su sannan da kyar suka shawo kan Malam. Sai dai kuma Malam yayi fushi sosai dan tunda yake da kannin shi bai taba kafa musu doka suka ƙetare ba, sai a wannan karan da *mukhtar* yake shirin ɗauko mashi yar boko ya kawo mishi cikin ahalin shi a matsayin suruka dan haka gaba ɗaya yaji ya baya ra'ayin ta, tun yanzun tana neman shiga tsakanin shi da kannan shi tana son raba haɗin kan dake tsakanin su *taya ma zai sota?* Ina har abada..... Dan haka ya kafama *mukhtar* dokan cewa bazai matsa ko ina da sunan zama ba dole anan cikin gidan zai zauna, To shima dai baijaba tunda har yasamu an shawo mishi kanshi ai komai zai biyo baya mai saukine dan haka cikin kankanin lokaci saboda tsoron kar zuwa gaba Malam ya kara botsarewa aka tada ginin da Amarya zata zauna anan cikin gidan kamar yanda malam ya buƙata, anyi ma gidan gyare² sosai ta yanda ya nuna lallai anma bikin shiri na musam man, kowa na ɗaukin wannan biki amma banda Malam domin komai na neman auren ma zame kanshi yayi ya wakilta *Malam Adamu* haka dai akaci gaba da shirin biki ba yabo ba fallasa domin kowa taka tsantsan yake karyama Malam laifi. Allah da ikon sa an daura aure lafiya amarya ta tare a dakin ta. Kowa yayi tunanin cewa bayan aure Malam zai sauko to ya sauko ɗin domin bai rage kanin nashi da komai ba, sai dai tsakanin shi da *jidda* ba wani abunda ya canza tsakanin ta da *Malam* gaisuwa ne kawai bayan shi baya shiga sabgarta bawai ƙiyayyarta yake nunawa ba amma dai gaskiya kowa yasan cewa baya wani yinta, Da farko yaso ya hanama iyalan shi shiga sashen ta saida *Mukhtar* ya nuna ɓacin ranshi sannan ya barsu suke mu'amalan tar juna, Itama tunda ta gane cewa ƴa'yan mijin nata baya yinta take taka tsan² bata shige mishi, Ko gefen matan shi bata zuwa indai yana gida sai dai su suje mata sannan rashin jituwarta da *Malam* baisa yaran gidan sun rainata ba, sai ma komawa shashen ta da wasu daga cikin su sukayi suka tare acan. Malam yasa ido ko zaiga wani sauyi na tarbiya daga wajen yaran sai dai baiga hakan ba dan dole ya kauda idon shi akan su. A haka rayuwa taci gaba da tafiya har zuwa sanda *Allah* yaba Jidda ciki haihuwar fari ta samu namiji aka sa mishi sunan mahaifin su Malam wato ~{{ UMAR FAROUQ }}~ haihuwarta na biyu shima Namiji ta kara samu aka sa mishi sunan Malam ~{{ MUSTAPHA }}~ na ukun shima Namiji Allah ya bata tayi zaton ko za'a mata kara a sanyawa yaron sunan Mahaifinta domin tana da cikin Allah yama Baban ta rasuwa, Tanaji tana gani haka yaro yaci sunan ~{{ ADAM }}~ taso ta nuna bacin ranta yan uwanta da mijinta suka bata hakuri, Koda ta kara samun wani cikin Allah da ikon sa wannan karon ma dai Namijin aka samu amma bana Malam yayi abun kai ya maida ma yaron sunan Baban ta yaro yaci suna ~{{ ABDUL KHAREEM}}~ ita da yan uwanta sunyi murna matuka dan haka sunyi hidima fiyeda wanda sukayi a haihuwar ta na baya. Bayan wannan haihuwar bata kara samun wani cikin ba sai bayan shekara goma sha daya, Zuwa wannan lokacin sun samu cigabar rayuwa ta maban²ta fuskoki Allah ya kara musu budi arziki ya ha'baka an buge gidan an sake mishi fasali an mishi gini dai² da zamani, A hankali zuwa wannan lokacin dayawa daga cikin tsauraran halayen malam sun ragu, domin da kadan² girma yana ta Kama shi sannan shima Malam Adamu ya dawo da dukiyar shi gida dan haka yanzun baya yawan yin tafiye²n da yakeyi, Da kyal dai aka shawo kan malam yaba jidda dama ta fara aikin ta na likitan ci, domin ta dade da samun aiki malam ya hana, Sai dai a gida mata suke zuwa tana dubasu kuma duk abunda ke faruwa Malam yana sane. (Kuji karfin iko da isa irinta Malam gaskiya dai malam akwai karfin hali, kayi iko da matan ka matan kanni ma basu tsira ba, gaskiya ba kowa zai yarda da wannan mulkin mallakan ba). Itama dai bata dagama mijinta hankali akan hakan ba domin yana tsaye akan buƙatun ta dana yaranta koda wani lokaci sannan yan uwanta ma tsaye suke akanta babu abunda ta rasa a hakan kuma itama tana taɓa kasuwanci. Kaf ahalin mijinta bata da matsala da kowa dukansu suna girma mata da kyautata mata kamar yanda itama take tsaye akan hidimar su, dan haka rashin kulawar da malam ke nuna mata bai taɓa damunta ba, dan koba komai yana nuna kulawar shi akan yaranta dan haka tuni ta cire damuwar shi a ranta koba komai ai bashi ke auren ta ba. Ana haka shima *Mukhtar* ya gaji da kumbiya²n da yakeyi na ɓoyema malam laifin daya dade da aikata mishi tsayin shekaru, kuma har zuwa wannan lokacin duk yaron daya kammala secondary shida Adamu suke ma yaran tsaye in an fiddasu waje don ganin sun samu ilimin boko da islama ba tareda Sanin Malam ba, Azaton su Shi malam yana nan yana hidimar shi bai san cewa tuni ahalin shi sun goge sun daɗe da zama yan boko ba. *Malam Adamu* ne ya mishi jagora suka jema malam da maganar, Sai dai ga mamakin su Ashe malam yasan komai tsayin shekarun nan ya daiyi bakam ne yana so yaga iya gudun ruwan su dan haka ya zuba musu ido, koda wasa bai taɓa gwada cewar yasan abunda yake faruwa ba, yasha mamaki da yaga baiga wani canji a wajen yaran dashi *Mukhtar* din ba dan shi da fari kallon yan iska yakema yan boko sai gashi a hankali yagane cewan shine yama abun gurguwar fahimta, Dan haka koda suka gama mishi bayani maimakon suga ya rufesu da faɗa kamar yanda ya saba idan aka aikata mishi ba dai² ba sai sukaga ya tsatstsare su da ido yana kallon su yana murmushi, Su kansu sun tsargu dan haka suka dunga bashi hakuri suna kara wayar mishi da kai da bashi misalai akan fa'idar ilimin bokon a yanzun, kuma shima bai katse musu hanzari ba sai da ya gamajin ta bakin su kafin ya daura dayi musu nasiha kana ya fada musu duk abunda suke ciki ya sani kuma ya yafe musu boye mashin da sukayi, Sai dai ya kara da cewa har yanzun yana kan ba kanshi ɗiya mace bazatayi karatun daya haura secondary a gida, ba bazai yarda yarinya tayi ta jera kafada da iyayenta mata a cikin gidaba idan anyi magana ace karatu takeyi. Basu kadai ba duk ahalin gidan sunyi mamakin abunda ya faru ayau, dan sunyi zaton sai ankai ruwa rana kafin a shawo kan malam dan haka suka cika da farin ciki lallai komai yanada lokaci kuma Allah yana iya canza mutum komai taurin kanshi ya koma mai sanyi. A kuma wannan lokacin ne ciki na biyar ya bayyana a jikin *Momi Hauwa* dan haka murna da farin cikin wannan ahali ya karu duba da tsayin shekarun data dauka rabon ta da haihuwar dan *Abdul~Khareem* ya girma tuni, basu gama wannan murnar ba wani ƙarin farin cikin ya same su domin a wannan lokacin ne shima *Baba Adamu* yayi aure da yarinyar nan *Murjanatu* da Malam ya nemar ma *Mukhtar* shekarun baya, idan baku manta ba! Tayi aure tun wancan lokacin to Allah yama mijin nata rasuwa sannan tsayin shekarun nan allah bai bata haihuwa ba dan haka bayan gama iddarta Malam ya nema wa *Adamu* aurenta kuma an bashi anyi aure lafiya amarya itama ta tare a sabon shashen da aka ware masu. ---+++---- Haihuwar jidda na 5 cikin ikon Allah wannan karan mace aka samu kyakyawar jaririya mai Kama da uwarta domin dukan yaranta fuskar Baban su suke daukowa sai wannan ce ta biyo uwa, Wanna yarinya tazo da farin jini sosai domin an daɗe ba'a samu ƙaruwar ƴa mace a gidan na malam ba sauran yan matan kuma duk an aurar da dasu sai samari suka rage dan haka kowa yake ɗaukin haihuwar. Allah da ikon shi sai ya ɗauki soyayyar wannan jaririya ya sanya shi cikin zuciyar Malam tunda ya kyallara idon shi akanta, duk haihuwar da jidda keyi bai ta ɓa taka ƙafar shi zuwa shashen ta da sunan ya mata barka ba sai wannan karan, kai hatta kayan barka na musamman ya haɗama wannan ƴa tun kafin suna yake aikawa a ɗauko mishi jaririyar a kawo mishi, abunda bai tab'a kwatan tashi akan nashi yaran ba, Malam fa ya cika zukatan mutanen gidan shi da mamaki gashi kuma ba wanda ya isa ya tare shi dan Sanin dalilin wannan sauyin! Koda yake dama yan magana cewa sukayi *abun cikin kwai yafi kwan dadi! Domin kowa yasan yanda malam keson *Mukhtar* kaf a cikin kannin shi to amma uwar y'ar fa? (wannan amsar a bakin Malam kaɗai zakujita) Bai karkare ba mutanen gidan mamaki ba har sai ranar sunan da jaririya taci Sunan Mahaifiyar su malam din wato *~{{ Aminatu }}~* manyan raguna biyu da jibgegen sa ya bada aka yanka sannan ya hada sha tara ta arziki ma jaririya Ameena, gaskiya dai yayi abunda kowa bai tsam mata ba duba da cewa matan shi sun haifa mishi yara mata ɗai² har 8 amma cikin su ba wacce yasama sunan Mahaifiyar shi, sai wannan da kowa ya shaida baya yin uwarta dan haka masu gulma dai sunyi ita dai uwar ƴa gaba ta kaita, koba komai itama an mata kara domin sunan uwarta itama *Amina* dan haka ba kare bin damo. An daiyi taron suna lafiya kowa ya koma gidan shi yana ma Amina fatan Allah ya raya, A wannan lokaci rainon Aminatu wacce suke ma lakabi da *Meenal* wasu kuma suke kiranta da *Meenat* kashi 3 ya rabu, kason farko mafi girma yana hannun Malam, kaso na 2 kuma hannun jama'ar gida domin kowa kauna yake nuna mata , suma suna ma Malam kara, sai kaso na 3 wajen uwarta da idan tayi kuka ake kai mata domin ta bata nono wani lokacin ma ko dawo da ita ba'ayi sai tayi bacci. Wannan bayya nan niyar soyayya da malam ke gwadama Meenal ya sanya duk wani halin ko in kula da malam ya nuna ma Jidda a baya gushewa a zuciyarta kun san shi mai ɗa wawane, domin abun a fili yake yanda Malam ya damu da al'amarin Meenal ko nashi ɗiyan na cikin shi basa samun kulawar shi hakan domin komai ya samo na Meenal ne shiga 10 fita 10 sai ya mata tsaraba, Itama kuma ta wayeshi sosai dan hatta Baban ta takan mishi kiwiya amma bata ma Malam, data fara wayau kuwa da zarar tayi laifi wajen Malam take gudu. *******"""""""******* Alhmadulillahi a haka rayuwa taci gaba da gungurawa wata rana Zuma wata ran madaci, Bayan haihuwar *Meenal* jidda da yara ke Kira (Momi Hauwa) ta kara haihuwar yara 3 biyu mata sai namjin ɗaya yanzun dai yaranta 8 cif, Matar Baba Adamu Aunty Murja itama ta haifi yara 3 matan Malam suma sun kara haihuwa banda kuma jikokin da suka cika gidan, domin samarin gidan manya suma duk sunyi aure sun haihu sai dai kamar yanda kuka sani har yanzun Malam bai amince kowa ya fita a gidan ba, dan haka kullum cikin kara sabunta gidan ake domin yanzun kam suma bokon ta fa huda jikin su ta bayyana kanta kunsan babbar arziki ne Allah ya azurta ka da ilimin boko da islama wacce take itace kan gaba ga kuma rufin asiri Allah ya musu dan haka sai kwarjinin su ya ƙaru, Dan ma Malam ya hana matasan rawar gaban hantsi da kafara rawar ƙafa zai saka a ɗaki yabika da wa'azi sai ka dawo hayyacin ka zai kyaleka. •••••••••••••••••√••••••√√ *Meenat* ƴar gaban goshin Malam. Shekarun *Meenal* 14 a yanzun haka tana aji 5 ne a matakin secondary wato ss1 fannin islamiya kuma tuni tayi saukan ta na hadda kunsan gidan Malam dai ba wasa balle ita uwar Malam dan haka komai nata yake na musamman An fa zama An mata dan haka rawar kai Salamu Alaikum domin dai kaf cikin gidan nan babu marajin magana irin *Meenal*kafiya da zuciya naci akan abunda take so jinini akan abunda bai taka kara ya karya ba sai *Meenal* Gaba daya haka take da rashin hakuri ga shegen son girma inda Allah ya taimake ta zuwa wannan lokacin ita ce babba a gidan domin yayyin ta maza basa ƙasar dan haka itace babba a yaran gidan na yanzun masu tasowa, dan haka dole yaro ko yarinya ya mata biyayya in baiyiba yasan sauran, in ko sauran yayyen ta suna nan tofa ba'a ga maciji domin dai ko laifi tayi bata buguwa (kai wani tsautsayi zai kaika taɓa uwar masu gida?). Dan Malam na raye bamai taɓa mishi uwa ya zauna lafiya har gara ma in mai sunan Malam din ne ya hukun tata ko kuma farouq *Meenal* yarinya ce mai farin jinin al'umah farin jinin nata ya samo asali ne saboda da irin kyan da Allah ya mata tun tana jaririyar ta kuwa, kum san yara masu kyau badai farin jini ba. Tana da wayau sai dai kuma bata da son shiga al'umah haka nan take kamar mai tsoron mutane, gata da ilimi Allah ya hore mata, tana da shiga rai da kuma saurin sabo in harta saki jiki da kai, Soyayyar da take samu a wajen malam yasa itama bata da wani mafi kusanci da ita kamar shi , tana iya rufema mahaifiyar ta damuwan ta amma bata rufema Malam ko kanta ke ciwo malam ke fara sani kafin Maman ta , kauna ce mai karfi tsakanin Malam da Meenal. Sai dai tunda girma yazo mata take fuskantar wani irin yanayi na matsanan cin ciwon mara, a duk lokacin yin al'adarta wanda idan ciwon ya tashi ba karamar wahala take shaba dan har suma takeyi dan tsananin ciwo, anyi magani kuma ana kanyi amma dai har yanzun ba'a dace ba duk da kasancewar Mamanta likitar mata kuwa. Wannan lalura yana cikin abubuwa mafiya girma da suke tada ma Malam hankali akoda yaushe, domin ciwo ne da baya ɓoyuwa da zarar ta fara tofa harta da makota sai sunji dan mutuniyar taku gwanace wajen raki, haka kowa yake fafutuka wajen nema mata magani, duk inda akaji mai maganin ciwon mara tafe suke wajen amsa a gwada ko za'a dace amma inah. Uwarta dai tasan miye maƙasudin ciwon amma tausaya mata takeyi domin kullum kallon karamar yarinya take ma Meenat ɗin duba da yanda har yanzun da shekarun ta suka kai 14 babu abunda ta iya na aikin gida uwa uba kuma girki domin firr Malam yake hana asata duk wani aikin wahala, duk da a hakan Momin tana tsaye a kanta wajen ganin ta iya wasu abubuwan. Zaune take kan kujerar tsuguno ta mata riga da wando ne a jikinta yan pakistan kafafuwanta a mimmike ta wara su, bokiti ne a tsakiyar kafar nata ta dage sai faman wanki take, under wears ɗinta ne take ta faman wanke wa kayan da dududu basu wuce 10 ba amma ta samu kujera tayi rashe rashe, wayarta dake gefe ajiye ne yaci gaba da kuka, karo na biyar kenan da kiran ke shigowa, kamar dai bazata ɗauka ba me tagani kuma ohon Mata dai, tsame hannun ta tayi daga cikin bokitin sai da ta ɗauki wani singilatin ta dake ajiye a gefe wanda bata jiƙa ba ta goge hannun dashi kafin ta ɗauki wayar kiran yana gab da ɗaukewa, Ba tareda ɓata lokaci ba ta fara balbale wacce tayi kiram da masifa "ke banson iskanci fa kike ta wani faman jera min kira kan kira bashin uban me naci miki kike neman tasomin rayuwa gaba? " bata sarara ba taci gaba da faɗin "ai saboda baki ɗaukeni a bakin komai ba shi yasa kika sa ƙafa kika bar Zaria har zuwa Kaduna bamu da labari daga ni har Meelat" Daga ɗayan gefen wacce ta kira tayi saurin katse ta da cewa "Beb please ki saurareni in miki bayani wallahi is not my fault nima banyi zaton za'ayi tafiyar dani ba sai a jiyan, kuma koda muka wuce tsabar farin cikin da nike ciki yasa na shafa'a in kiraku in faɗa muku koda muka sauka kuma kinsan irin yanayun da mutum yake shiga in ya shiga cikin family ɗinshi most expecially waɗanda suka daɗe basu haduba, amma please kuyi hakuri shi yasa tunda safe nike kiranki ke kuma dan kuturin wulakanci kika ƙi daukar min waya, wallahi da ina gida kin san har gidan zan biyoki in tuɓe mu daku yar wulakanci kawai" Ta karasa faɗa a kausashe itama, "dallah can toya KD ɗin da daɗi? Meenat ta tambaya, of course Beb KD fa wallahi tana da daɗi shi yasa bana son ina missing zuwa garin" ta bata amsa, " keni wanki nikeyi i will call you back idan na gama and dont you dare switch off your phone dan nasan halinki", Meenal tace mata da muryar bada umarni, "No ƙawata bazan yi haka ba" ta bata amsa, sannan suka yanke kiran. Bayan ta gama wankin da ƙar ciki ta koma kai tsaye tana ajiye bokitin ɗakin su ta wuce tana mitan ta gaji dan haka tana zuwa bajewa tayi akan gadon ta tayi ɗai² hannu ɗaya anan ɗaya a can hakama ƙafafun ta, tana kwancen nan haka kawai ta fara nazarin yanda duk yawancin school mate dinta da zarar lokacin hutun su yayi kowaccen su zata fara faɗin garin da zataje hutu, kuma aka sari zakaji sunce wajen yan uwan maman su zasuje. Ahankali ita da kanta tana kwancen ta fara nazarin me yasa sauran yaran gidan idan an samu hutu suma suke tafiya wajen yan uwan Maman , su Amma ita ko tayi magana Malam zai kawo wani dalilin dazai hanata zuwa, Tun tana yarinya Momi bata zuwa da ita unguwa saboda duk sanda Momi zata wani waje to ita tana tareda malam dan haka bata taɓa damuwa ba, Tasan Momi tana da yan uwa maza da mata domin suna zuwa nan wajen momi kuma itama in taje tudun wada gidan Hajiya Innah tana ganin su, harta da yaran su idan anyi hutu sukanzo musu hutu amma ita koda wasa bata taɓa zuwa garu ruwan suba balle tasan gidajen su, tasan dai gidajen su na nan garin amma su basu gajiya duk sallah sai sun mata aike duk da bata shiga cikin su a hakan suke nuna mata kauna, Sauda yawa ta kanso taje ko gidan Hajiya ne tayi mata kwana biyu tunda can gidan shima cike yake da yan uwan momin koda sallah haka in sunzo amma sai malam ya kawo wani uzurin dako taje bazata daɗe ba zata dawo gida, Amma in cikin gidajen ƙannin Malam din ne Malam bai taɓa hanasu zuwa hutu ba a cikin *dangin* ta na wajen uba babu wanda bata sani ba, na birni dana ƙauye domin sauda yawa idan malam zaije musu ziyara da ita yake tafiya, To amma *Danginta* na wajen uwa ɗai² kune ta sani suka Santa domin harta kannin ta sunfi ta sanin dangin momin dan su har hutun karshen sati sukan je suyi tareda su. magana ta gaskiya dai kamar yanda babu shakuwa sosai tsakanin ta da Momi haka ma babu wannan shakuwar tsakanin ta da yan uwan Momin, kuma duka wannan turbar Malam ne ya ɗaurata akai, amma yarinta yasa bazata iya gane hakan ba. "ko dai wannan dalilin shine yasa kullum Hajiya Inna take faɗa cewa malam ya hanani zumunci dasu !? " take tambayar kanta a bayyane, kowa zai bata amsar tambayan nata oho. Haka dai taci gaba da saƙa da warwara amma ta kasa gano bakin zaren, daga karshe dai ta yanke ma kanta hukuncin cewa itama zatayi kokari ta fara shiga cikin yan uwan Maman ta duk da halin masifar Hajiy innah yana ɗaya daga cikin dalilan da suka sa zuwa unguwar na Tudun Wada ya fice a ranta tun tana karamar ta, Momi bata daɗe da tafiya tudun wada ba family house din na su wai suna da meeting duk da ba wani abu takeyi ba amma koda momin ta tashi wucewa bata taya mata fitan taji ko zata bita ba sai ma kashedi data buga mata akan karta yarda ta dawo gidan ta samu bata wanke waɗancan kayan ba, Dan inda sabo momin ta saba tun *Meenal* na karama bata binta unguwa dan in ta matsa akan sai taje da Itama har suje inda zasu bazata dena kukaba har sai sun dawo gida inko tafiya ce ta kama na kwana to ciwo zatayi ta mata sai sun dawo gida take warwarewa dan haka tuni ta shafa ma kanta lafiya tunda dai Allah yasa ba ita kadai ta haifa ba. #My first novel ina fatan zaku soshi🤍 #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga ɗaukakin jama'ar da suke tsaye dan ganin littafin ya zaga a tsakanin makaranta, tun daga kan marubuta har masu karatun. *MAMAN YAR'SO* *IKEEN MAMA* *MUM SAYYED&NOOR* *ASMA BAFFA* *MAI DAMBU* DAMA WAƊANDA BAN KIRA SUNA BA NAGODE KWARAI 🤍 ```Page 4 *Dan haka ko yau din ma data tashi zuwa family house din nasu bata tayama Meenal din ba ta kwashi kannen Meenal din sukayi tafiyar su. Tana nan kwance a ɗakin take cigaba da saƙe² sai dai har zuwa lokacin bata gano dalilin da yasa malam yaki barin ta ta sake da yan uwanta *Danginta* na gefen Uwa har ta shaƙu dasu, kamar yanda ta shaƙu da yan uwanta *Danginta* na gefen Uba ba, kun san dama ance so hana ganin laifi dan haka tayi saurin watsar da sak'e²n da zuciyarta ke mata akan Malam ɗin tun da wuri dan bataga wani dalilin ma da zaisa ta kalubalanci Malam ɗinba. Raheenatu ce ta shigo ɗakin nasu da sallama dauke a bakinta *Raheenat* ita ce diyar Malam Adamu da Anty Murja ta farko kuma itace tsarar *Meenal* da suke kusan shekaru ɗaya a gidan dan haka itace suke kusan kan su daya, Gadon da Meenal din ke kwance ta karasa ta zauna akai itama tana me tambayan Meenal din cewa "Bakibi Momin Tudun wadan bane? " Ya mutsa fuska tayi "me akeyi a can din wai? Naga Momin duk ta kwashi y'ayanta ta tafi dasu amma ni ko tayin zuwan bata min ba kuma yau ina gidan nan tun safe dasu malam suka wuce wajen daurin aure zuntu, amma ba wanda yace min komai saima sallahun data barmin cewa kar in sake ta dawo ta samu banyi wankin can ba, " Ta tambayi Raheenat din domin magana ta gaskiya Raheenar tafita kusanci da Momin domin dai ita tun tashin ta komai nata Malam ne dan haka babu wani shakuwa tsakanin ta da Momin, ita kuma Momin tana kauda kai akanta ne duba da soyayyar jama'ar gidan data samu dan haka take musu Kara. " wai baki sani ba? Anty binta cefa yayan su Aisha zatayi aure, Kuma yaune Za'a kawo kayan lefen ta. (Aishan yarinyar ya'yan Momin ce Namiji) tsaya kar dai kicemin wai baki san kuna da biki ba bayan duk shirin dasu momin da Auntyn mu keyi na bikin har anko an mana fa dan bikin ai yau sauran sati daya insha Allah?" ta karasa fada tana tsare Meenal din da ido, Basarwa Meenal din tayi da fari kamar bazata tanka Raheenat din ba dan maganar gaskiya taji ɗacin hakan a zuciyarta ace ita da Momin ta haifa bata san meke faruwa a gidan su Momin ba har sai Raheenat ce ke bata labari kai gaskiya da sake. Sai kuma can tace "ke nifa mantawa da hidimar kowa nikeyi kinsan abubuwan dake gabana yawa garesu" ta fada tana kauda maganar da cewa me Anty ta dafa yau? Dan yunwa nikeji kuma ni banajin cin shinkafa. " Mutuniyar kice Waina sukayi basu ma gama suya ba na gudo dan kamshinta keta hawa min kai," innahlil lahi wa'innah ilaihir raju'un amma ke kam anyi baƙar marowaciya yasin, yanzun ace anyi waina a sashen ku amma ki ɗauko hanya ki tahomin nan hannu na dukan cinya dan cin amana, bayan kinsan kauna ce mai tsananin gaske tsakanina daAunty Waina! Ke waina fa ake magana , to wallahi kin ma kanki kuma sai naje na ciyo d'an bakin ciki sai dai ya mutu" ta kai karshen zance tana mikewa, a hanzar ce tayi hanyar fita tana bankama Raheenat ɗin harara. Itama Raheenat ɗin biyo bayanta tayi tana bata hakuri akan cewa dama ta bari su gama soya wainar ne sai ta ɗibo mata, dan tasan halin Meenal yanzun akan Wainar nan tana iya ɗaukar fushi da ita, Meenal bata kara sauraran Raheenat ba tayi wucewar ta kai tsaye zuwa Sashen nasu bata ko nemi Antyn ba ta wuce zuwa inda tasan suna suyan wainar, saida ta ɗauki 🍽 plate dinta da za'a sa mata wainar a ciki kafin ta karasa wajen ƴan aikin Anty Murjan dake suyar, su biyu ke aikin suyar wainar da tunda ta doso wajen kamshin ta tagama tado mata da yunwar cikin ta. sannu da aiki ta musu tana mai tambayar su ina Antyn? "Tana ciki" suka bata amsa sai da ta ɗiba wainar dai² yanda tasan zai kosar da ita sannan ta musu godiya ta wuce su kuma sunaci gaba da zolayarta da cewa dama sun san indai tana gidan nan to sai kamshin wainar ya jawo musu ita. Dan kusan kowa yasan yanda Meenal din Malam kesan waina kamar Baban ta Malam. Falon Aunty murja ta koma bayan ta dibi miyar wainar a kitchen miyan da rabi nama ne dan ita ta tsani kashi dan haka ko tantakwashi bata ci, bayan ta aje abincin da ruwan data dauko ne ta haura sama inda dakin Antyn yake da sallama ta shiga dakin ko gaishe da Antyn sama² tayi shi Yayin da ta iske Antyn cikin shiri da alama fita zatayi bata son cin abinci idan ya huce dan haka bata b'ata lokaci ba ta dawo ta zauna ta cigaba da ba baba uban ba'u hankali kwance, Ko rabin wainar batayi ba Ya'Sa'ad ya shigo (shi ɗin yaron Malam ne) da kyar ta iya amsa sallamar shi dan ta cika bakinta da nama a lokacin, kallon ta ya tsaya yi cike da mamakin yanda naman cikin abuncin yafi abincin yawa, dagowa tayi tana kallon shi saboda jin shiru da tayi bai motsa ba koda ta dago kai ita din dai yake kallo har yanzun. da idonta ta tambaye shi "ya akayi? " Girgiza kai yayi "ke yar malam allah ya shirye ki yanzun wannan waina kikeci ko nama? Dubi yanda kika cika plate da nama anya ba naman miyan duka kika kwaso ba yarinya kamar kura ke wallahi ko barbade aka miki a nama sai kinci? " Hade rai tayi bayan ta haɗiye abincin bakin ta "to kai y'ay'a aini bana cin ko wani abinci sai nayi bismillah kaga ko ai ko mutum yayi barbaden shi bai kamani, kuma dan allah shi kenan mutum bazai zage yaci abinda yake so a gidan uban shiba! bafa bakon waje naje nike ciba" ta karasa fada tana ci gaba dacin abuncin ta, To shima dai wuceta yayi dan yasan bakin ta bai tab'a mutuwa komai ka fada tana da amsar shi ita gata a haka ganin farko in ka mata zaka iya rantsewa da Allah cewa ko magana batayi saboda kamewar ta da salihar fuskar da Allah ya bata amma daka latso ɗayan gefen tofa ba kanta. Bai dade a wajen Anty Murja ba ya sauko har ya kusa fita daga falon ta Kira sunan shi, "ya sa'ad fita zakayi? Dan Allah in shirya ka ajeni a gidan Hajiya innah kaji dan Allah! " ta fada tana marai raicewa ba tareda ya juyo ba yana ci gaba da tafiya yace Mata ta shirya kafin yaci Abinci saiya sauketa dan PZ zaije. Cike da murna ta amsa domin yau dai ta kuduri aniyar bama kowa mamaki zatayi wato zuwa gidan Hajiya Innah bisa raɗin kanta ba tareda Momi ta aiketa ba ko kuma wani abun daban, ta riga tayi wanka tun ɗazun dan haka bata bukatar wani sabon shiri dan zata fita wayarta dake gefe ta ɗauka ta latso number din da tayi saving da *JAMEELATA* Ta danna mata Kira tana addu'ar Allah yasa tana kusa da wayar dan bata son ta bata mata lokaci. "kawata" Daga dayan gefen wacce ta kiraɗin ta fada da karfi cire wayar tayi daga kunnen ta ke wani kalan iskanci ne wannan zaki min ihu a kunne, "Me ruwan hodaaa" Jamilan ta bata amsa a iskance, wato shi iskancin ne mai ruwan hoda. Me kikeyi? Meenal ta tambaya, ke yanzun dama nike so ince kizo muje tudun wada zan kai mana ɗinki a *Fada* jameelar ta bata amsa. To ki shirya dama nima na kirane ince ki fito muje gidan hajiya innah ya'sa'ad zai sauke mu". "Ok to zan jiraku a bakin gate din mu, kawata akwai labari sai kin fito" jameelar ta fada tana yanke wayar, Sauri ² haka ta dunga cusa abincin tana korawa da ruwa bayan ta gama ta wanke hannun ta a kitchen din ta baya ta fice zuwa sashen su ba tareda tama Anty Murja sallama ba. Koda ta isa ɗakin su Raheenat ta samu kwance a gadon ta tana bacci domin ɗaki ɗaya suke kwana da Raheenan sai dai kowa da gadon shi ba tareda ta tashe taba kai tsaye ta shige bayi ta Kama ruwa ta kuma ɗauro alwallah sannan ta fito, domin sabonta ne in har zata fita saitayi shi, sai da taɗan ƙara mutstsuka man shafawa a fuska hannu da kafarta sannan ta ɗan shafa hoda kaɗan ta rufe maskin man fuskar nata, Bata kasance cikin ma'abota kwalliya ba dan haka bayan hodar kwalli kawai ta gogama idanuwanta sai Vaseline data shafa a labbanta komai da takeyi cikin hanzari takeyi dan tasan wallahi karamin aikin ya Sa'ad ne ya tafi ya barta inta b'ata mishi lokaci gyalen rigar jikinta data daura shi a kanta ta warware bayan ta ɗauko hular da yake blue kalar Abayar jikinta tasa a kantane sannan tayi rolling da gyalen, turare mara karfi tadan fesa domin kullum Malam yana mata faɗa akan yanda take bulbula turare takalmi da jakanta farare kalar zaren da akayi aiki ajikin rigar ta jawo harta gama kimtsawa Raheenah bata ko motsaba da alama dai Raheenar na tareda gajiya dan ba kullum take baccin rana ba dan haka batayi yinkurin tashin taba ta fice daga dakin. fitowarta kuma yayi dai² da kwala kiran sunan ta da taji anyi a tsakar gida ko bata tambaya ba tasan ko waye dan haka gudu² sauri² ta fice zuwa tsakar gidan , tsaye ta sameshi a kusa da motar shi yana magana waya Kare a kunnen shi hannu ta mishi alamar bari ta sallami mutanen gidan, dan haka da gudu ta shige ciki ita ko tsoron ta faɗi da shegen takalmi mai tsinin dake kafarta batayi, girgiza kai yayi a bayyane ya furta "ita yarinyar nan ban san yaushe zata fara hankali ba" yana ci gaba da wayar shi, koda ta shiga can ɗin ma bata b'ata lokaci ba tayi musu sallama akan zata je tudun wada gidan Hajiya Innah duk kansu da kallon mamaki suka bita baki bude a tunanin uwar gidan Malam ko kunnen tane baiji mai takwarar nata ta fadiba dan haka ta kara tambayar ta "ina zuwa"? "tudun wada" ta bata amsa kai tsaye ba tareda ta lura da yanayin mamakin da suke ciki ba, Bata tsaya sauraron ta bakin suba ta kara juyawa da gudu kamar yanda ta shigo ta barsu da kallon² suna mamakin yau wacce rana, "ah lallai takwara ta fara girma" cewar uwar gidan malam din. Zaune cikin mota ta sameshi kuma har zuwa lokacin bai yanke wayar da alamomi suka nuna soyayya yakeyi a cikin wayar ba dan haka koda ta shiga gabar motan itama bata isheshi da surutu ba ta Kama bakinta wayarta ne yayi kara tun dazun Meelat ke kiranta tasan cewa zatayi ta shanya ta dan haka ta yi saurin daukar wayar bata ba Meelat din damar magana ba tace "ke gamu nan ki fito waje" bata saurari abinda zatace ba ta yanke wayar sannan ta juya gefen da ya' Sa'ad ke driving "ya'ya zamu ɗauki Meelat please" tace tana marairaice fuska, shareta yayi ba tareda yace uffan ba, "y'a Sa'ad angon Anty bilkees" ta fada tana dariya "dan allah ya'ya kaima kayi² aure muma musha biki kaga an dade ba'ayi biki agidan nan ba kaji, Allah ni in ma kunya kakeji to ka aikeni wajen Baba Malam nizan faɗa mishi ka samu matar aure," girgiza kai yayi "lallai ma yarinyar nan wato ma dan kin rainani kece zakimin iso wajen baba to ban tashi auren ba tukun har sai na aurar daku" ya fada yana cin magani, Zaro idanuwan tayi a firgice "innalillahi kai ya'ya dan Allah ni inba neman magana kakeyi ba ni ina na isa aure fisabilillah kwata² fa shekaru na 14 kuma ss1 nike yanzun fa ko secondary ban gamaba waye zai min aure? A'ah wallahi nikam karatu zanyi nida nike so inyi karatu in zama babbar likita kamar Momi inyi kudi insiya katuwar mota irin ta Baba Auta (Baban ta) in gina ma Malam katon gida a Abuja, mu koma can nida shi indunga siyan mishi kayan Dadi yana ci ina ni ina aure yanzun? dan Allah y'a karka kara faɗa kar yan Ameen su amsa in shiga uku." "Ke mahaukaciya Auren ne shiga uku?" Ɓata fuska tayi kamar zatayi kuka "kai ya'ya nice mahaukaciyar bayan kamin fatan aure kuma harda mahaukaciya kacemin dan kaga Baba Malam bayanan" ta fada tana neman yin kuka, "Ke dallah baki san wasa bane bafa mahaukaciya zance ba mai hankali Uwar Baba kuma aure ai bani zan miki ba kina zaune Malam din da kanshi zai fidda miki mijin yarinya shekara nawa kwata² ya rage miki ki gama makaranta, in badai akan kine ke yar gaban goshi zai canza ra'ayi ba ni ai harna fara hango taron jama'ar daurin aure a kofar gidan nan," ihu tayi tana kai mishi duka ni ka saukeni nama fasa zuwa tudun wadan kuma saina faɗama Malam komai ince kace aure kake so." Shareta yayi bai kara kulata ba domin sun kawo kofar gidan su Meelart din dan haka itama bata kara maganar ba. Karasowa wajen motar Meelat din tayi ta shiga gidan baya saida ta zauna sannan ta gaida ya Sa'ad ɗin shi kuma ya kunna motar sukaci gaba da tafiya sun san bai cika son surutu ba dan haka ba wacce ta kara magana a cikin su sunyi nisa da tafiya sannan Meenal ta juyo ta kalli Meelart tana cewa "kawata kaza nike son ci yau gashin YAHUZA" "kedai kin zama kura wallahi" meelat ta amsa mata jin ya Sa'ad bai tankata bane yasa ta ciro wayarta a jaka ta latsa kiran number din Baba Malam ta sanya wayar a speaker yanda ko bata kai wayar kunnen ta ba zataji abinda ake cewa ta cikin wayar," Assalamu Alaikum" cewar Baba Malam daga gefen shi bayan ya dauki wayar "Ameen Alaikum salam Babana" ta ansa dashi "uwar Malam ya akayi ne?" "Baba dama wani labari zan baka ko ince albishir wallahi dama y'a....... Ai jin wannan magana ba shiri ya Sa'ad ya taka burki Allah ma ya taimakeshi ba akan babban titi yake tafiya ba da anyi batatta dan in bai bugama waniba shi inda wani a bayan shi yana iya buga mishi Meelat dake zaune a baya itama tana cakalar nata wayar ba tareda tasan abunda ke wakana a gaban motar ba sosai burkin da ya Sa'ad din ya taka ya kayar mata da gaba ta fara zazzaro ido tana tambayan "lafiya? Meya faru wa aka kabe?" Shiko maida hankali shi yayi wajen Meenal cikin marairaice murya yake lallabata domin tuni ta yanke kiran data ma Malam. "Haba uwar Malam me yasa baki san wasa bane ke wai? Nifa wasa nike miki yanzun fadamin me kike so kici kuma bayan kaza? Kome kike so kin san zan siya miki amma dai kiyi hakuri karki fadama Malam maganar nan". Juyowa tayi ta fuskance shi da kyau. "Yaya" Ta kira sunan shi tana Kara karkatowa ta fuskance shi da kyau, Ya'ya ka tuna maganar bikin Teacher Zahra da nayi maka kwanaki? A haf ai nasan ma Anty Bilkisu zata fada maka tunda sune kawaye to bikin dai yau saura sati 2," Saida ta kara marairaice murya sannan taci gaba da cewa "kuma gashi har yanzun nida Meelat bamu siya ankon ba kuma tunda na maka magana tun ranar baka kara cewa komai ba", ta karasa fada tana tsareshi da ido, Ajiyar zuciya ya sauke gamida cewa "Inda wannan anko din ne nayi magana da Billy yanzun haka ma suna hannun ta kuna so akai muku ɗinki ne ko a baku akwai inda zaku kai? Meelat dake baya ce tayi zakal cike da farin ciki tace "ya Sa'ad a bamu kawai zamu kai Fada sunfi iya ɗinki sai ka bamu kudin ɗinki", Ba tareda ya waigo ta ba yace "itama Fadar tace zata kai Amma bari mu karasa dai ya fada yana kunna motar sukaci gaba da tafiya basu dauki lokaci mai tsayiba suka karasa Tudun Wadan. family house din su Momi Hauwa zan sauke ne ko mu karasa gidan su Billy ku karbi kayan? "Mu karasa ya'ya" suka bashi amsa dan haka wuce wa yayi kai tsaye yana daga ma yan majalisar *MAI JAMA'A* dake zaune a wajen hannu koda suka isa kofar gidan su billyn sun samu dai² itama tana fitowa daga cikin gidan nasu ne ɗauke da wata babbar leda a hannun ta. Dan haka ya taka burki daga gefen gidan yana mata horn, Balle murfin motar Meenal tayi ta fita da gudunta ta karasa ta rungume Bilkisun tana ihun kiran sunan ta oyoyo Anty Billyn mu rungumeta Bilkin tayi itama fuskarta cike da fara'a dan batayi zaton da ita Sa'ad din zai taho ba. "Yau kuma kun koma M square kun tashi a triple M ne dan ku kam kune ake kira in ka gano wata kaga Zara, ina kuka baro ɗaya M din" ta fada a dai² sanda Meelat ta karaso wajen itama dan haka Meelat din ce ta bata amsa da cewa "Maryam taje KD suna biki amma nasan gobe zata dawo dan ba iya zama acan din zatayi ba" Horn din motar da Sa'ad ya danna shiya ankarar dasu cewa bafa su kadai bane a wajen kama hannun su tayi kamar wasu kana nan yara ta jasu suka karasa wajen motar. "Barka da zuwa" ta fada suna aikama juna da kallon kauna tsakanin ta da Sa'ad din "barka" ya amsa dashi yana basarwa ganin irin kallon dasu Meenal ke musu suna gulman su da ido, Shigo in sauke ku a shagon dan sauri nikeyi PZ zani ana jirana "ok" tace tana mai zagayawa gefen mai zaman banza ta zauna su kuma M square suka shige baya ba wanda ya kara cewa wani Abu har suka karasa wajen jerin Shagunan dake kofar gidan Hajiya Innah wato *Fadar Mai Jama'a* sannan ya nemi waje ya faka, "ku karasa shagon dasu dan sunce anan suma suke son nasu ɗinkin duk yanda kukayi dai zamuyi waya" yace bayan su Meenal sun fice daga motar kudi masu yawa ya bata da sunan kudin dinki sannan ya bude kofar gefen shi shima ya wuce inda Majalisar domin gaisawa da matasan dake zaune a wajen kamar kullum. Ledar hannun Billyn Meenal ta karba ta rike tana mitan cewa "Ni wallahi shi yasa ban son zuwa unguwar nan saboda wanna shegiyar majalisar yan sa idon" ta karasa fada tana tsaki billy ta kalleta tana cewa "Allah dai yasa *Dangin* kine masu zaman majalisar dan kin san ko majalisar waye! " "To ke Anty billy baki ganin wani rashin daraja ace zaman majalisa harda yan mata ni wallahi duk haushi suke bani ina ganin kokarin ku yan unguwar nan da kuke iya shiga da fita a gaban su duk su kure mutum da ido kamar mayu" dariya billyn tayi 'ai dan kema dai ba unguwar kike ba da haka nan dolen ki zaki saba ɗin tunda dai kusan dukan su yan unguwar nan ne kowa yasan kowa", "to wai su basu da aikin yine? Meenal din ta Kara tambaya "dukan su suna da ayyukan su bakiga shagunan dake jere bane ai koba majalisar wajen nan bazai rabu da kai da kawon mutane ba saboda yanda ake ma shagunan zirga² amma dai cikar majalisar nayau yana da nasaba da bak'in gidan da suka fara isowa tun yau da aka kawo lefe, ga kuma shima Mai Jama'an a gari kinga ko ai dole majalisi ya cika. Jin shirun Meelat yayi yawa ne yasa Meenal waiwayo ta jin tun ɗazun bata tsoma baki a hirar suba " kawata" ta Kira sunan ta "uhmm" Meelat din ta amsa dashi "ya dai ? Meenal ta tambaya Kuyi min sorry nasan kunyi ta zuba ido sai yanzun. #Share please # #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne gareku, *Aisha (AG)*ALKHAIRIN ALLAH YACIN MAKI HAR KASA MAI TSARKI* *OUM FATEEMA* *OUM ABDALLAH*UWAR MIJI* *NANA KHADI*RABIN RAI* INA SON KU MUTANE NA.... ```Page 5 *****Ke ba komai fa kawai ina kallon shagunan ne sun min kyau, gaskiya wajen ya tsaru kin san na daɗe ina jin labarin wajen nan a bakin mutane shi yasa nace zan kawo ɗinkin mu nan" ta karasa fada tana ma Meenal din nuni da ledar hannun ta. Ke kawata wai kaya kika siya mana shine baki fadamin ba ta faɗa fara'ar fuskanta na ƙaruwa " Aunty ce ta bamu, jiya da mukaje sabon shagon data bude a Sabon Gari". "Kai aiko mungode dole in je inyi godiya ubangiji Allah ya Kara arziki, ai kam carrot zan siya in kai mata tunda tana sonshi kin san yaba kyauta tukuici". Ganin sun tsaya wani firar yasa Billy shigewa shagon ta barsu a tsaye, Kofofin hancinan su suka buɗe suna shakar dadda d'ar kamshin turaren dake fitowa daga cikin shagon ɗinkin dake gaban su kofar shagon takalma ne kala² a gefen wajen na yan gayu da alama shagon ba'a shiga da takalmi. Meelat ce taja hannun Meenal daketa kalle²n yanda aka kara gyara wajen domin ita ai tana zuwa unguwar duk da ba sosai take zuwan ba, amma ai tasan da ba haka wajen yake ba an Kara gyara shi, sosai aka kawata shi fiye da Sanin datama wajen a baya. Cikin shagon suka shiga da sallama falone mai madai²cin girma a wajen wanda ya dauki set na kujera sai show glass din da ake rataye d'inkakkun kaya a ciki tun daga kan less shadda atamfa dama materials wasu a ɗinke wasu kuma basu da ɗinki da alama dai ba iya dinki akeyi a shagon ba, harma da kayan sawa suna sai dawa, gefe kuma ga wasu zafafafan riguna an makale su a hanga kai daka shigo kasan shagon ɗinki ka shigo sai dai a wannan shagon babu tarin kyallayen da aka saba gani a shagon teloli domin mad'inkan suna ciki ne nan din saiya zamana kamar falon tarban baki ne in sun kawo ko sunzo amsar ɗinki nan zasu tsaya . gaskiya dai wajen ya tsaru kalar burgewa saida Meenal ta gama kalle²n ta tsaf domin yaune karo na farko da itama din ta taɓa shiga shagon sauke idon da zatayi sai akan Aunty Hassana ya'yar Momin ta "lah! " ta furta tana karama idonta girma cike da mamaki da kuma farin cikin daya mamayeta lokaci d ɗaya. "Mommy" ta kira sunan tana karasawa da sauri inda mommyn ke zaune wanda kiran sunan ta da Meenal din tayi ne ya ankarar da sauran yan matan dake zaune a falon domin suma basu lura da shigowar su Meenal din ba hankalin su nakan d'inkunan da suke dubawa, Sai gashi tun kafin Meenal ta karasa wajen Mommyn yan matasan yan matan dake daura da ita sun taso da azama sun rungume Meenal din suna masu murnar ganin ta suma, Dan haka gaba daya sai shagon ya dauka da hayaniyar su har ba'a tantance me suke fada dan haka mommy ne ta katsesu da cewa "bazaku sakar min yarinya ta karaso inji dumin taba? " Dariya Meenal din tayi "dallah ku sakeni inje wajen uwata kun wani dakune ni kamar kwabo a hannun kuturu " karasawa wajen mommyn tayi. "Mommy Yaushe kika zo?" Ta tambaya "jiya" ta bata amsa sannan ta dora da cewa "ai dazun nan nagama fada da Jidda dan naga kowa ban gankiba", "To ai basu fadamin bane suka tafi suka barni shi yasa nace ya'yan mu ya kawo ni" Cewar Meenal din * Mommy kunzo lafiya ya hanya?" " Alhmadulillahi kowa lafiya Mamana" Mommy ta amsa dashi. "Kawata zoki gaisheda Mommy na" ta fada tana kallon Meelat, Dan haka Meelat din ta karaso cike da fara'a ta gaida mommy itama sannan suka koma inda Aisha da Maimoon suke Zaune suna cigaba da duba d'inkuna duka Meenal ta d'aka ma Maimoon a baya. " amma wallahi kudai yan cin amana ne zakuzo shine ba wacce ta kirani a cikin ku", Dukan itama Maimoon din takai mata "kefa wallahi muguwa ce dallah ba surprise muka shirya miki ba kuma ai gashi kwalliya ta biya kudin sabulu ko bakiyi murnar ganin muba? "Nayi wallahi sannun ku da zuwa ga kawata ku gaisa" ta fada tana jawo Meelat tsakiyar su "sunan ta Jamila amma Meelat ake kiranta, Masoyiya ta ce ita din kuma ku tayani son ta" ta fada tana zare musu ido, Dariya sukayi dukan su sannan ta juya wajen Meelat din "kawata wadannan yan uwana ne *DANGINA* na jini wannan sunan ta Maimoon amma Moon ake mata lakabi" ta fada tana taba maimoon din "sai Aisha shatu tsohuwa dafatan zaki so su kamar yanda suke sona? Duka suka kai mata suna dariya "wato ma ashe mu ke sonki ke bakya yin mu? Cewar Aisha suna cikin hirar wani kyakykyawan matashin ya shigo shagon dogo wankan tarwad'a mai kirar karfafa kai tsaye wajen da Mommy ke zaune ya karasa yana mai mika mata gaisuwa cikin girma mawa "kiyi hakuri Mommy mun d'an shiga cikin gari da yaron kine" Ya fada bayan ya gaisheta, "Tare da Mai Jama'an kuka dawo? Ta tambaya "eh gashi can a Fadar shi tareda su Sadeeq, "Ba laifi ai zai zo ya sameni , nike ta kiran shi baya dauka," "Bai fita da wayar ba a gida ya barta shi yasa baiga kiran naki ba" ya bata amsa kai tsaye, "basu kawo miki kayan bane? Bash" ya kwalama Kira sai gashi ya fito "barka da dawowa OGA"cewar bash din, " Ya akayi baku sallami Mommy ba? Ya tambayi bash din , "Mun sallame su Oga wasu kayan suka kawo, "ok to jeka koma bakin aikin ka nayi tsammanin ko baka san sun shigo bane ai, Mommy kije kawai ba wani damuwa zaki same su cikin lokaci" Anty Billy ce ta fara gaishe shi kafin su Maimoon suma suka haɗa baki wajen gaishe shi, suma ya amsa musu yana tsokanar billyn da sunan Amaryar su " Amaryar mu kema dinkin kika kawo ne? "Eh OGA Musty nawa da nasu Meenal ne ta fada tana mashi nuni dasu Meenal din, "Kai wa nike gani yau unguwar nan a shagona kamar takwarar Hajiya Innah jaririyar Aunty Jidda? Amma dai batan kai kikayi ne koh? Ya fada muryar shi cike da zolaya, Rufe fuska Meenal tayi da tafin hannun ta tana dariya domin tsaf ta gane shi dan suna zuwa wajen momin ta shida yayyen su Aisha. "kai dan Allah mai sunan baba Malam wai har yanzun bazaka dena cemin jaririya ba" Ai dole kiji kunya tunda kin san baki da gaskiya, kuma ni ai har yanzun kallon jaririyar nike miki shi yasa" "Nidai wallahi na girma" ta faɗa tana tura baki, Mommy ne ta katsesu da cewa su tashi su wuce gida "kije mommy zamu shigo gaba daya" Cewar Aisha, wucewa tayi ta barsu bayan Anty billy ta bada nata dinkin itama wucewa tayi tabarsu a shagon sai bayan wucewar ta sannan Meelat ta bada nasu itama kiran Bash yayi yace ya turo mishi Asiya ta dauki measurements din su "kawarki bata magana ne Meenal!? " ya tambaya yana kallon Meelat data dukar da kanta kasa saboda yanda taga ya kura mata ido, kallon Meelat din tayi sai taga kanta a kasa tana wasa da yan yatsun ta kamar wata wacce take gaban sirikin ta "kawata ya dai? Meenal din take tambaya ɗan dagowa tayi kadan ta kalli Meenal ba tareda ta iya cewa komai, "ko kunya na takeji? Cewar musty dariya Meenal tayi shi kuma ya samu waje gefen Meelat din ya zauna "An mata yane ko dai kodai²! Dariya dukan su suka fara Maimoon ne tace "Allah ya musty inaga dai kayi kasuwa ne, da gudu Meelat ta daga kanta tana hararar Moon din "kai dan allah ni yaushe mukayi haka dake? Meelat din ta fada tana kama hanyar barin shagon dariya dukan su sukeyi. '"To ai shikenan zokiyi zaman ki tunda ni banyi kasuwa ba ke kinyi zadai ku bani koh? Ya tambaya yana kallon su ai kamar hadin baki dan kusan a tare suka hada baki wajen cewa "da gudun besfa ma" fitowar Asiya ne ya katse su "Gani Oga" ta fada tana ajiye littafi tape da biron rubutun data fito dasu, karaso kizo ki dauki Measurements din su kun zabi style ne? "Ah ah" Meenal ta amsa mishi bari in Kira kawata ta fadi style din da za'a mana ɗin" ta fada tana mikewa zuwa waje tsaye ta samu Meelat a bakin kofar shagon tana waya dan haka ba tareda tayi mata magana ba taja hannun ta suka koma cikin shagon measurements din Meelat din Asiya ta fara dauka sannan ta dauki na Meenal sannan ta koma bakin aikinta a ciki ta barsu zaune a falon. "Me zakuci ko me zakusha? Musty ya tambaye su kallon kallo suka shigayi a tsakanin su Maimoon da Meelat sukace sudai sun koshi Meenal da Aisha kam drink suka ce suna so dan haka shida kanshi ya fita bai jimaba ya dawo da leda shake da snacks da drinks din ya damka a hannun Aisha "yanzun zaku wuce ko sai zuwa dare? Ya tambaya yana karema Meelat kallo Meenal ce ta amsa da cewa "sai zuwa anjima gidan hajiya zamu shiga yanzun" "oh baku dade da zuwaba kenan "eh" ta bashi amsa ok to nagode da ziyara to amma zaku tafi banji sunan kawar taki ba! "Jamila (Meelat) ta bashi amsa suna fita daga shagon shi kuma yayi ciki. *Moon ce ta kamo hannun Meelat din tana dariya bayan sun fita "ke An mata kinfayi kasuwa, dan allah irin kallon da naga Ya Musty na miki nasan da wata a kasa dan yan magana sunce in kaga kare na shinshina takalmi dauka zaiyi, ke kam ai kinyi sa'a wallahi d'inkin ki a bati style sai wanda kike so" cewar Aisha, "Ke kibari kawai ai inaga nikam d'inki duk wata sai nayi dan naga waje" cewar Meenal, hararar ta Meelat tayi "kawata bana son haka fa ke wai baki k'are mishi kallo bane? Abu jiki duk a murmurd'e keda ganin shi kinsan yana cin karfe, gidan ubanwa zan kai wannan katon? Dan allah ku rufamin asiri kubar maganar nan". "Anki abar maganar, ke yarinya karki raina min wayau fito fili kawai kice kin raina arzikin shi baki iya soyayya da tela inba haka ba ai wallahi ko hasidin iza hasada yasan mai sunan Malam hadaɗɗe ne karki bata min rai Ina ce a makaranta Head Boy sonki yake, koba kuɗin shi mukeci kullum ba? ta fada tana zazzarema Meelat din ido kamar zata kai mata duka, "Ke kifa kiyayeni inba so kike mu raba hali a wajen nan ba dan iskanci kike maganar Head Boy yo shi wannan Namiji ne? Yaron da sai ubanshi ya bashi kudin breakfast yake zuwa ya kashe min uban me zanyi dashi kema ai kinsan dan dai kar a raina mu shi yasa nike kulashi," Suko su Maimoon tsaye sukayi suna rarraba ido kamar marasa gaskiya tsoron su Allah kar yasa wani daga cikin yayyen su suji wannan hirar yau su shiga uku Aisha ce tayi karfin halin cewa "ke Meenal muna kusa dasu Ya Mai Jama'a nefa kuyi a hankali kar yaji ku, balla mata harara tayi "ke toni dama nace miki Ina tsoron wani ne? Dallah can ni ku daga kafa mu karasa inyi in bude ledar nan inga kayan dadin da mai sunan Malam ya siyamin, "kutmelesi ke tsaya naji kina wani cewa ya siya miki ba tare da kinyi jam'i ba in kin isa kici kayan nan ke kadai a canza mun suna daga Jamila zuwa salaha ke har kin ma isa dallah ni bani ledar ma in rike! Ai makalewa su Aisha sukayi baki bude suna kallon ikon Allah ah lallai shi yasa ake cewa ba'a kawance sai hali yazo daya dan sun dade da Sanin halin*Aminatu* na rikicin gangan ashe itama Jamilar ba tayar baya bace su dai fatan su shine su rufa musu asiri su samu su wuce majalisar nan lafiya atoh ina dalili suna neman sasu a shiga uku. Maimoon ce taja Meelat ita kuma Aisha taja Meenal dan Allah ya sani basu shirya shiga komar Mai Jama'a a yau ba, gara su dan zuwa anjima gida zasu gudu suko dole gida ɗaya zasu kwana da shi, tun basu karasa wajen majalisar ba mutuniyar ku ta fara kana nan surutu "Ke wai ita Hajiya duk bala'inta mai yasa akan mu ya kare ne ga yan zaman banza a kofar gidan ta amma ta kasa tarwatsa su ? "To ai ba laifi In kin shiga ciki sai ki tambayeta" cewar Aishatu "Ina wunin ku" suka hada baki wajen gaisar da matasan dake zaune a majalisar amma banda Meenal ita ko daga kai batayi ta kalli ko su waye a majalisar ba duk da tsungulin ta da Aisha keyi dan tayi gaisuwar kinyi tayi yau dai anyi sa'a ba mata mazan ne kawai, "Daga Ina kuke? Wata murya mara hayaniya a cikin ta ta doki dodon kunnen ta Aisha ce ta bada amsa da cewa "daga shagon Ya Musty muke, a dubaran ce a wayance Meenal ta dan dago idonta tana neman wanda yayi maganar hada ido sukayi dashi yana zaune hakimce akan kujera kamar sauran, wayace a hannun shi yake latsawa hararan ta yayi yana zazzare mata idanun shi da suke nan dakwa² tubar kallah ba bata lokaci itama ta bishi da katuwar harara harda alakoron murguda baki zare ido yayi yana binta da kallo cike da mamakin shine wannan jaririyar yarinyar ke harara harda murguda baki aiko sai ya fasa wannan bakin data murguda mishi, Sauri ta Kara tayi gaba tabar su Maimoon a baya dan haka nan taji kirjin ta yana bugawa kasan zuciyanta kuma tanajin kamar bata kyauta ba me yasa itama zata harare shi aida ta barshi da halin shi, abun kunya wai babba da tsokanar faɗa ai Allah ma sheda ne cewa shine nan da girman shi ya fara hararar ta, bayan ba girman ido yafita ba gaskiya dai anji kunya inda wani ne yace mata manya najan tsokana ba yarda zatayi ba, sai gashi ta gani da idon ta wato tunda yasan ya girme ta shine bari ya tsokane ta salon zuwa anjima inyaso cin zalin ta ya tare ta yace zai zane ta. Allah dai yana kallon mutum atoh # Share fisabillahi # #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah. ```Page 6 ***Ganin kanta a cikin gidan Hajiya Innah yasa tuni ta watsar da tunanin wani harara da murguɗa bakin data gamayi a waje, haka nan ta tsinci kanta cikin farin ciki domin abune da bata taɓayi ba tsayin rayuwar ta wato zuwa gidan bisa radin kanta ba tareda an aikota ko sunzo da yay'yinta ko Momi idan anayin wani abun ba. Ita kanta bazata ce ga ainihin dalilin da yake hanata zuwa gidan a wancan lokacin ba, abu guda ta sani shine ita bamai ra'ayin shiga cikin mutanen da batayi sabo dasu bane tafijin sakewa a cikin gidan su cikin *Danginta* wannan dalilin shi yasa ba ko ina take son zuwa ba daga gida sai Makaranta. rayuwar ta mafi yawa tareda Malam tayi shi dan yanzun nema data samu Jamila da Maryam har take iya barin gidan su taje musu hira kasance warsu cikin unguwa guda shima saida sukuyi ta mata mita tukun kafin ta fara zuwa musu. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke gaskiya tayi kewar gidan dama mutanen dake zaune a cikin shi domin indai ba mantawa tayi ba a kallah yanzun tayi kusan rabin shekara rabonta da gidan nan, gaskiya dole Hajiya tayi ta fada kullum dan itama sai yanzun take kara tabbatar ma kanta da rashin kyauta warta na rashin zuwa gidan, dan Allah ya sani taji zafin yanda aketa abubuwa a gidan amma Momy bata taɓa sata a lissafi ba, ace hidimar gidan nan da take matsayin jika a cikin shi wai sai a bakin Raheenat takeji fisabilillahi wannan ai abun kunya ne wallahi, dan haka ta kuduri niyyar toshe duk wata kafa na rashin kusanci tsakanin ta da *danginta* na wajen uwa data bari a baya Insha Allah saita ba kowa mamaki yanzun kam dan ai itama tana son su kamar yanda a kullum suma basa gajiyawa wajen nuna mata soyayya mazan su da matan su duk da cewa da yawan su ba mazauna garin Zaria bane amma duk sanda sukazo tsarabar ta daban ne suke ware mata daga cikin na yan uwanta, kuma har kwanan gobe duk wani abu da za suma ƴaƴan su tare suke hadawa da ita basa taba ban²n tawa haka suma ƴaƴan nasu indai sunzo garin can gidan su wajen mamanta suke tarewa basu cika zaman a gidan Hajiya ba saboda jarabar faɗanta sukan gwam mace zuwa wajen Momy Hauwa har su gama hutu su koma garuruwan su,domin dai kowa yasan zama da Hajiya da daɗi ba daɗi hakan nema yasa ta shaku dasu tunda ita dai bata taba zuwa garuruwan su da girmanta ba , Kamar yanda kowa ke son kakar shi haka itama take son Hajiya innah domin macece mai kirki ga ta da tsafta dan har yanzun data fara tsufa kullum tsaf zaka ganta cikin gayu yar gayuce ta gasken gaske dan ita gayunta basai zata fita unguwa takeyin shiba ko gidan ta kaje tsaf zaka sameta kullum kafarta baya rabo da lalle mai mata kitso ko duk sati ne wannan kam ba fashi dan haka yasa bata shiri da kazami ko bako tayi inhar ta raina tsaftar mutum bata barin ya shiga mata babban falon ta , tana da karamin falo na ganawa da duk wanda ta raina tsaftar shi. Hajiya tana da ilimin boko dana zamani mai zurfi domin a lokacin da mijinta yana raye ta rike manyan mukaman gomnati kashi², kasancewar mijin nata babban mutum fitacce wanda tako ina ake damawa dashi a gomnatan ce yasa sukayi fice, Hajiya nada buɗaɗɗen hannu domin ko sam bata da rowa akwaita da kyauta bata da kwauro in zata baka a wadace zata baka ga kuma san zumunci tana son yau ace ɗan uwanta ne daga waje kaza yazo mata ba karamin dadi hakan ke mata ba haka itama tana da kokarin ziyartar yan uwanta , Sai daifa duk wadan nan kyawawan halayan na Hajiya wallahi ba karamar mafadaciya bace masifaffiya ce ta gaban benci kwata² bata daukar raini gashi sam bata da hakuri bata iya ganin abu ta gyale duk wanda yayi ba dai² ba ko a inane ko waye kai tsaye zata fito ta tsage mishi domin ita yar gaskiya da gaskiya ce kai tsaye take abubuwan ta bata nuku² gata da shiga sabgar daba nata ba dan hatta su da suke matsayin jikokin ta basu tsira a hannun taba. har gara *Mai Jama'a* shi kam da yake shima masifaffen kanshi ne irinta to sinfi shiri,sannan kuma a bayyane take ga kowa na yanda Hajiya ta fifita son Mai Jama'a akan sauran jikokin ta dan ita babu ruwanta da wasan jika da kaka kana mata gara² zakaji kayau ta kai maka duka dan haka da zarar tazo waje kowa yake kama kanshi, wannan halin faɗan nata yana daga cikin dalilan da suke hana Meenal zuwa gidan tun wancan lokacin dan inhar taje gidan da zarar tayi ba dai²ba Hajiya ta hukunta ta ita kuma tana komawa gida zata fadama Malam shi kuma haka zai yita faɗa yace ta daina zuwa gidan tunda dukanta takeyi dan shi duk abinda zai taɓi lafiyar jikita ba son shi yake ba. ****" To yau dai gata ta kawo kanta gidan Hajiya Innah mai abun tsiya dana dana arziki , yanzun² zata iya nunama duniya cewa kaine komai nata ɗan gaban goshin ta hakan kuma bazai hana anjima kaɗan ta ɓata dakai ta dena yayin kaba, ga gori harda na bala'i gashi dai ta tsufa a shekaru amma ko kadan allah bai saka mata mantuwa ba dan duk abinda ta maka in wani abun ya haɗaku saita goranta maka wata rana.... Daga yanayin cinkowar gidan zaka tabbatar da cewa lallai akwai hidimar da ake a gidan duk da kasancewar gidan na jama'a ne a koda yaushe yau gidan ya banbanta da sauran ranaku duba da adadin motocin gidan da yawan su ya karu ga kuma sauran shashe²n gidajen da suke a buɗe alamun cewa masu gidan suna ciki kenan dan shima nan din dai babban gidane sosai kamar gidan Malam, sai dai yafi gidan malam kayan more rayuwa dan harma yafi gidan Malam haduwa da kuma gyale² na zamani. Da gudu ta kwasa zuwa cikin falon Hajiya innah tana kwala kiran sunan Anty Binta Anty Sady burinta kawai tayi tozali da yan uwanta data dade bata gani ba, dan tasan kila suma sun fara manta kamanni ta dan haka shaf ta manta ana sallama daga bakin kofa kafin a shiga waje , oho kawai fadawa tayi da gudunta da kullum Momy kemata fada akan ta daina tsabar zakwaɗi. Ke! Ke!! Ke!!! Wallahi tsawar da tsohuwar nan ta daka mata saida ƴan cikita suka cure waje guda dan gaba daya ta manta cewar tana iya samunta a falon zaune. "Fitamin a falon kiyo min sallama ko ki koma inda kika fito shikenan ƴara kamar ana kaɗaku da ƴaƴan hanji komai naku ba nutsuwa wai wacece ma nike gani kamar ƴar wajen Jidda? Kai Usman tayani gani ita dince kowa? Batar hanya kikayi ne kika fadomin nan ko ya akayi? Dan ba saba ganin ki a gidan nan nayi ba, to juya maza kiyomin sallama kafin ki faɗomin daki dan iskanci kuma haka nan kika shigomin falo da wannan shegen takalmin na kafarki salon ki koƙemin tayes, Yau ni naga jaraba da dai ina zaune kalau cikin gidan nan bakina alaikum amma tunda na farajin dirin motoci nace shikenan bani ba baccin safe inba jaraba ba abu yaufa bikin nan saura sati amma duk kunbi kun harhaɗo kayanku dana ƴaƴanku kunzo kun tare min a gida kamar a kanku aka fara bikin aure, na tabbata jarabar yaran ku sai yasani rama kafin ku wuce, yanzun fisabilillahi koni da sauran jama'ar arziki bazamuyi tsaye mu amshi kayan lefen ba sai kun wani baro gidajen ku da aiyukan ku kunzo kun taremin a gida? Tun fara kwakwazon ta Meenal tayi sadaf² tayi waje dan tasan yanda Hajiya ta furta ta koma ɗin nan to yasin sai ta koma inba haka ba a bala'inta tana iya kamo sunan Malam kai tsaye ta zaga. Tsaye cirko² ta samu su maimoon a kofar falon suna ganin ta fito suka fashe da dariya Aisha ce mai cewa"hala kin manta inda zaki shiga ne da farko? Ko kuma manta dokar hajjaju kikayi? yasin ki gode Allah da bata jefo kiba" Tura baki Meenal din tayi tana cika taba batsewa tace 'kun san Allah nifa shi yasa tuntuni bana son zuwa gidan nan saboda hajiya ba'a taɓa shan inuwa daya da ita ta daɗin rai sai ran mutum ya ɓaci kuma in bakazo ba tace baka son zumunci bula³ surutan ta da baya karewa. Dunguma sukayi dukan su suka shiga falon da sallama ita dai mutuniyar cewa tayi bama Hajiya tayi sallamar ba, Karasawa tayi wajen kawun ta da suke ta washe baki suna masu nuna farin cikin ganita dan haka itama cikin girma mawa ta bisu daya bayan daya ta gaidasu saida ta gama da mazan su da matan suna tambayan lafiyan ta dana mutanen gidan su tana amsawa kafin ta juya gefen da Hajiya ke hakimce tasha wanka ta wanku kamar yanda ta saba zama da kwalliya tana kamshi akoda yaushe, "Ina wuni Hajiya" ta fada tana tura baki ba tareda hajiyar ta amsa ba ta kara jefo mata tambayar data mata dazun "Nace wai hala ɓatan hanya kikayi? " "Niba ɓatan hanya nayi ba in kuma bakiyi maraba dani bane ai sai in koma inda na fito. meenal ta bata amsa tana kunkuni, "kun gani koh a gaban ku take min kunkuni amma ba wanda ya kwaba mata, ba tareda Meenal din tabi ta kanta ba ta haura sama dan su Moon tuni suka haura dan gudun kar Hajiya ta hada dasu. dakin da tasan zata samu su Anty binta a ciki ta bude da sallama ta shiga tana kwala kiran sunayen su aiko suma cike da farin cikin ganin nata a wannan lokacin suka rungume ta bayan sun zauna ta gaisheda sauran ƴaƴƴanta kannin ta data girma suma suka gaisheta waigawa tayi inda wasu matasa biyu da suke nan kusan kai daya a zaune "kai yaran nan baku ganni bane da bazaku gaisheni ba? Kusan a tare suka dago kan su suna kare mata kallo, dawa kikeyi? Daya daga ciki ya tambaya, da ku nikeyi! Ta bashi amsa ɗayan dabaiyi magana bane ya ansata wannan karan "lallai ma yarinyar nan wato mune zamu gaishe ki dallah ware kiba mutane waje waye tsarar ki anan? To dama ai kuba tsarana bane kanne na ne kuma dole babba ya taka karami ya wuce, " Innah " ta kwala kiran sunan aiko ba shiri suka mike "aike tsiyar ki kenan dama komai sai kin kira Hajiya" to ai gara tazo ta raba mana gaddama dan naga har yanzun baku yarda nice yayar kuba, ficewa sukayi a dakin sauran kannen su na musu dariya dan dama da zarar an hadu tsakanin su da Meenal yar tsama ne dan kowan nen su akwai shegen son girma ita Meenal ta girme su da watan nine amma ji take kamar wasu tarin shekaru ta basu. Bayan fitan su itama ficewa tayi zuwa dakin da yake matsayin nasu a nan ta iske su Meelat sun bude ledan da Musty ya basu ko wacce ta ɗauki abunda ranta ke muradi tana korawa da drink "cak tayi tsaye tana kallon su baki bude cike da tarin al'ajabi tace "kam bala'i amma wallahi yaran nan kun raina ma kanku hankali ma dan wulakanci nida na kakkaɓe idona daya tambaya nace zanci, kukaci darajata ya cikomin leda taf da abun arziki kuka barni nayi dakon ledar har kofar gida shine wato kuka kule a ɗaki dan cin amana kukayi kasafi ba tareda kun jira zuwa naba, to kunyi ma kanku dan wallahi kaza zanci anjima zanga ƴar rainin wayan da zata cishi" kamar kububuwa haka ta karasa inda suke ta tattare sauran meatpie din da ke cikin leda da sauran drink din tana cigaba da mita, Meelat ce ta musu alamar karsu kulata. Meenal taji dadin kasancewa cikin *Danginta* a wannan rana domin kowa sai nan² yakeyi da ita batun yauba dama tasan ana sonta a cikin wannan ahali dan haka yauma haka ta sake a cikin su harta Meelat in ka ganta zakayi zaton itama yar gidan ce dan dama ita bata da duhun kai tuni ta sake jiki a cikin su sai kuma Allah ya taimake su fita ya kama Hajiya dan suna ta son su sauko su bude kayan lefen su duba amma uwar gayyar tayi kane² a falo dan haka ba dama su sauko dan Hajiya bata yarda tana falo a dunga mata zarya ba. Dan haka saida ta fita sannan suka samu damar bude akwatunan suka musu ɗaiɗai suka duba, bayan haka suka shiga cikin sauran sashen dake cikin gidan duk sun shiga sun gaishe da sauran mutanen, itama momy tayi mamakin ganin ɗiyar nata a gidan nasu amma dai bata ce mata komai ba tun bayan tambayan data mata cewa waye ya kawo su? Bayan sun gama yawace²n su a cikin gidan kitchen din Hajiya suka kaima farmaki suka dunga ci mata mutuncin madara da sunan yin tuwon madara da iloka bisa shawarar Meenal, sunfa mata ta'asa a kitchen ba kadan ba, amma basu tsira ba dan sun kammala sun bararraje suna rabama kansu ta dawo gidan Allah yasa kuma kai tsaye da shigowarta kitchen din tayo dan dazun da safe Mai Jama'a ya kawo mata kilishi a kitchen din kuma ta ajeshi gashi mutane sun ma gidan yawa tana tsoron kar a mata ta'asa dan haka ba shiri ta dawo gidan, to dai ba'a mata ta'asan kilishi ba an mata na madara da sugar domin kusan suman tsaye tayi bayan shigowarta kitchen din. Kai! Kai!! Jama'a me nike shirin gani? Uban me kuka shigo kuna min a kitchen? Larai! Larai!! Ke larai wai gidan uban wa kika shige kika barmin kitchen a bude wadan nan yaran suka shigo suna min ta'asa a cikin shi? yara da shegen fitina kamar sauro. Dan risinawa Larai tayi bayan ta iso "Hajiya ina kara kimtsa falon ne", kintsa falo shi yasa kika sakar musu kitchen ɗina suka shigo suke min abunda suke so? " ayi hakuri Hajiya ban san sun shigo ba " cewar larai, fita ki kiramin *Mai Jama'a* a waje kice nace yazo yanzun nan yamin maganin su, Ai ba shiri su Aisha da Moon cikin su ya duri ruwa suka fara bata hakuri, Hajiya dan Allah kiyi hakuri Allah kuwa zamu biyaki madarar ki, " ban hakuri sai kun fadamin ubanda ya turoku ku shigar min kitchen dan kunga bana gidan wato ma dakon fitana kukeyi koh? " cewer Hajiya a harzuƙe. Larai fa tuni har takai bakin gate dan tasan in ma tatsaya bama Hajiya hakuri laifin duka kanta zai komo sai dai koda ta karasa majalisar bata samu *Mai Jama'a* ba sai Sadeeq dasu Musty ta samu ganin bashi a wajen yasa ba tareda tayi ma kowa magana ba ta juyo cikin gidan suma dai basu lura da ita ba, har ta kawo kusa da falon Hajiya ta hango shi tsaye tareda Baba Usman suna magana dan haka ta karasa wajen su. *Mai Jama'a* kazo inji hajiya" tace bayan ta isa inda suke, " meya faru hala? " ya tambaya Uhmn mai sunan tane ta wajen Jidda da su Aisha bayan fitan ta suka shiga kitchen suka kwashe mata madara sukayi iloka da tuwon madara shine tace in kiraka", " muje cikin" cewar Baba Usman dan haka suka rankaya zuwa cikin sashen Hajiyar amma dai larai bata bisu zuwa can ba aikinta taci gaba dayi na gyaran falon Hajiyar. Duk wannan sababin na hajiya bai hana Meenal kwashe kason ta dana Meelat ta zuzzuba musu a leda ta cusa a cikin jakarta ba dan ta dauki aniyar komai zai faru tuwon madarar nan bazai taba zama haramiyar ta ba . yo ina dalili fisabilillah inba fitinar Hajiya ba madarar nan fa gashi nan a store din ta daga na gwangani na ruwa harda manyan gwana²n na gari kawai dan sun dan yi amfani da wannan shine zata wani zo tana neman tara musu mutane kamar wasu barayi harda wani aikawa a kira mata wani *Mai Jama'a* su kuma waɗan nan lusaran duk sun wani firgice sai wani hakuri suke bata ba Mai Jama'a ba a kira mata *Dangin* ma gaba daya. Muryan Mai Jama'an ne ya katsema su Moon ban hakurin da suke ta ba Hajiya ita ko sai wani cika take tana batsewa a dole fa an bata mata rai kamar ba iyayen su ke siya mata madarar suna tara mata a store ba. "Meke faruwa anan?" Ya tambaya, yau wa ɗan nan karaso daga ciki ka tam bayamin dalilin da yasa suka shigomin cikin kitchen suka kwashe min madara suka barnatar min dashi a banza!. "Bafa barna mukayi ba tuwon madara da iloka mukayi" cewar Meenal tana wani turo baki a sakalce kota manta wake tsaye a wajen ne oho. "Shi Ilokan ubanki Malam ne ya siyo madarar ya aikomin da ita da zaki baro gidan ku kizo kitchen dina? Hajiyar tace a zafafafe. Kai hajiya! Kai hajiya dan nazo nan gidan nayi tuwon madara shine zaki faramin gori naga dai ai gidan nan gidan kakana ne ina da damar yin abunda nike so kuma wallahi nasan da Baban su Momy na raye shi bazai takura min kamar yanda kikemin ba ai dama tunda nazo bakiyi murna da zuwa naba kawata tashi mu tafi" ta karasa tana kamo hannun Meelat data kasa cewa wani abu ita mamaki kawai take irin masifar da Hajiya keyi akan madara bayan ga madarar nan da yawa a store ko itama fa gani. "Koma ciki" Mai Jama'a yayi maganar a dake a yayin da suka kawo inda yake tsaye suna shirin ficewa, shidai Baba Usman yana ta bakin kitchen din a tsaye kuma har yanzun hajiya bata san da wanzuwar shi a wajen ba. Komawa tayi tana cika tana batsewa dan wallahi tayi dana sanin zuwan gidan da tayi yau haka kawai Hajiya zata kama mata fada a gaban kawarta Allah ma ya rufa mata asiri ta dade daba kawar nata labarin kalar masifar Hajiyar ai da tasa ajinta ya zube yau, kai jama'a ina ma amfanin masifa dan Allah, Baba Usman ne yayi magana "Zo ka amso ma Hajiya madarar, da madara dame kukayi amfani dashi? "Yace yana kallon su, Suga da man gƴaɗa Moon ta bashi amsa, a zafafe hajiya ta waiga dan bata san da wan zuwar shi a wajen ba tun farko sai yanzun dataji muryar shi. "Kai kuma waya gayyatoka nan? Nidai nasan nace Larai tamin kiran *Mai Jama'a* amma nasan ban ambaci sunan kaba, wato ku iyayen son ƴa'ƴa yaran ku bazasuyi laifi a musu fadaba shine ka taso zalo² ka taho to waima a magana ta kaji nace a biyani madara ne? Ko koh tsabar daure ma karya gindi shine wato kai ubansu bari ka biya to ai bance maka bani da madara ba ina da madara cike a cikin store dan haka koma inda ka fito ban gayyato kaba, ko kaine ka gayyato min shi? Ta fada tana kallon Mai Jama'a, shareta yayi bai kulata ba kamar yanda shima Baba Usman din yabar wajen yana dariyar rikicin Hajiyar nasu da ba'a mata gwanin ta, Kai ku tattara kayan ku kubar mata kitchen din ta" ya fada yana kallon su fuska a daure, ina zasu kuma basu dibar min ilokar ba? Kana ganifa sukayi kasafin abunsu iyasu! kuma ai dai ido guba tunda na gani sai su diba min, "ilokar zaki sha?" to wai kina bukatar tuwon madarar dama kuma kike fadar sun ɓata miki madara?. To ina ruwan ka? Naga dai ai madarar tawa ce kuma kitchen dina ne, karamin kwano ta dauka ta diba tuwon madarar da ilokar kafin ta fice a kitchen din tabar shi da binta da kallo baki bude cike da mamaki girgiza kanshi kawai yayi ya juya shima ya fice daga kitchen din dan bashi da abun cewa kuma. Hajiya cefa inka biye mata sai ku wuni kuna jidali ita bata gajiya. #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ *MOM TEEMAH* *AISHA HUMAIRA* *JIKAR HAJIYA* *CHIDA* ```Page 7 Falo ya sameta zaune ta daura kafarta ɗaya kan ɗaya hankalin ta kwance take cin ilokarta, tsaye yayi mata akai hannun shi bibbiyun dafe da ƙugun shi ba tareda ya zauna ba yake mata kallon kasan ido cike da jin haushi yace " kinga hajiya gaskiya ki dena min irin haka, wannan ai salon kijamin raini a wajen yarane zaki wani sa a kirani akan wani soki burutsun zance, yanzun fisabillahi ko kunya wai abunda kika gama bala'i akanshi shine kika wafce musu kika dawo nan kika gyara zama kike ta sha, haba Hajiya gaskiya nidai bana so" ya fada yana ƙyacci. "Ah² kai ban gane ma wannan muzuran da kazo kamin tsaye a saman kai kana min ba, yo rashin kunya da rashin ta ido harna kaika, kaida kullum kake laya min jerin ƴan mata sahu² da anyi magana kuma kace ba wacce kake so cikin su ruwa tun bai tafasa ba har zai kone, wallahi dakai da suɗin lokaci nike nema na musamman da zan ci muku uwa, kai nidai Allah ya isana wallahi waɗannan shegun mata dai sun cuceni duk gashi nan sunsa gaba ɗaya baka ganin mata da gashi, ooooh tsaya ma wai kai nan saboda rashin imani zuwa kayi dan ka jibgar min jikokin ko ƙaƙa??? Iiiyee naga sai wani zakalkalewa kake faman yi, toni shike nan saboda gani Aminatun mahaukata kawai sai inyi kira akan kazo kasa min su a gaba da bugu kamar wadanda suka kashe mutum? Kawai dan na kiraka ka tambayan min su dalilin da yasa zasu shiga min kitchen bada izinina ba, kenan kai nan zuwa kayi ka kakkarye min su ko me ka raya a zuciyarka? To nidai ba hauka nikeyi da zan baka damar dukan wadancan kananan yaran ba fisabillahi yaushe har sukayi girman da zan kira Iliya ɗan mai karfi kamar ka ya hukunta su ah'ah wallahi da hankali na , yo ita waccen ƴar Jiddan in ka taɓata kuma ai ka janyo min jangwam, kana ganin yau Allah ya karya alkadarin ubanta da kafarta tazo gidan nan fa kai yaushe rabon da kaga haka? to in ka bugeta kuma ai ka maidamin hannun agogo baya duk sallah fa sai nayi addu'a Allah ya karkato min da hankalin ta kan mu ah'ah wallahi jeka kawai na yafe in ma sunyi laifin da yakai matakin duka nikam mai zai gagareni insa a zaromin zabori in zazzane musu jiki dashi. Ciki da waje," ta karasa fada tana hararar shi,baki sake yake binta da kallo cike da mamakin yanda ta rufe idanu take masifa kamar ba ita ta aika a kira mata shiba amma yanzun so take ta maida laifin kanshi. "Da zaborin ne zaki dake su? " ya tambaya, "kwarai miye a ciki? Ta bashi amsa. Ah lallai to ai ba laifi nidai na fada miki karki kara kirana dan yaran nan sun miki laifi inba haka ba hummmm, yafada yana ficewa daga falon rai bace. Duk abinda ke faruwa a falon suna daga kitchen suna jiyosu dan Hajiya bata iya fada da karamar murya ba, dan haka ta kofar baya suka fice daga kitchen din, kai tsaye sashen Momy Hauwa suka wuce domin dai itama din kamar sauran yaran gidan tana da sashen ta daban da take sauka idan tazo gidan kamar lokacin biki haka ko kuma wani sha'ani daya zamana dole saita kwana dan Hajiya ba ta yarda wani ya sauka a side dinta, har gara² ma jikokin ta yan mata suna da ɗakunan data ware musu suke sauka a ciki idan sunzo ba tareda iyayen suba, suma dai ba kasafai suka fiye son sauka a wajen taba saboda takuran ta dan in har ka kwana a side din Hajiya tofa tashin asuba dole babu fashi da zarar kun idar da sallah zata ware ma kowa aikin shi masu shiga kitchen daban , haka ma masu gyaran side ɗin da zarar an gama kuma sai wanka ko wani irin sanyi ake bata yarda mutum ya zauna mata baiyi wanka ba dan ita bata shiri da kazami. Khadija suka samu tana shirin fitowa daga side din hannun ta rike da wani ƙaton basket da aka jera wadansu kyawawan kuloli masu daukar hankali gwanin burgewa kai daga kallon su kasan masu tsada ne, "Khadi ina zuwa? " cewar moon, ita kuma ta amsa da cewa " Zan kaima Ƴa Abdul abincine, lah Meenat yaushe kikazo? " ta tambaya tana karasawa kusa da ita fuskarta cike da fara'a, "tun yaushe kikazo? Ta kara tambayan ta. Keni tun tuni nike cikin gidan nan kawai dai nan din ne bamu shigo ba muna sashen Al-masifatu" ta karasa fada tana harare² dan har yanzun bawai takaicin abinda Hajiya tayi musu ya saketa bane dan Allah ya gani yau hajiya ta gama kwance musu zani a kasuwa ta rasa wanda zata musu sai wancan ɗan damben bayan batun yauba tasan shi da shegen karfin tsiya dan bata manta wani zuwa gidan datayi lokacin baya ba, musun ƙwallon ƙafa ya sarƙe a majalisar shi abun har saida ya kaisu ga dambatuwa, a gaban idonta fa yama abokin faɗan nashi duka ɗaya wallahi kawai sai ganin kato tayi a kasa kwance bai kara motsi ba saida aka yayyafa mishi ruwa dan tsaf ya aika shi duniyar somammu in kukaga wanda ya somar din wallahi a tsaye da girman jiki duk ya fishi, shi wanda ya somen yayi zaton zai daki banza ne dan anata rirrike shi ana son a raba faɗar shi yana kwacewa sai kunfar baki yake akan a sake shi ya koya ma Mai Jama'an hankali yagan shi da kirar madara yayi zaton bai iya faɗa ba, atoh kun san yaran yan gayu ba wani son wahala suke ba . Ai ko shi da kanshi Mai Jama'an yace "dan girman Allah su sake shi yakaraso" mugun ashe ya shirya sumar dashi ne to dai mutumin nan bai dawo daga duniyar suma ba saida suka feshe shi da ruwa, fisabillahi shine zata wani aika a kira mata shi wato yazo ya kakkkarya kasusuwar su dama gasu kamar kudin guzuri duk kan su babu mai auki, gashi ɗazun nan dama ya gama hararar ta ita dai Allah yasa ma ya manta hummm lallaima Hajiyar nan tasan matsayin da zata ajiyeta daga yau, ita hajiya ko kunyar bakuwar fuska bataji ba jama'a a gaban ƙawarta fa ta kwance mata zani a kasuwa....... "Miye a cikin kulan hala? " Aisha ta tambaya "kema kin sani ai tuwo ne" Khadi ta amsa mata, hummm Allah ya kyauta da yamman nan inci tuwo ai shi yasa kullum yake kara murdewa bashi da abincin ci sai tuwo nikam ina tausaya ma matar shi dan ta shiga uku da tukin tuwo safe rana dare" cewar Moon Khadi kam cewa tayi " nidai ku karasa bari in mika mishi in dawo kafin ya biyo sahu ta fada tana ficewa zuwa side din samarin gidan. Bayan anyi sallan la'asar ne Anty Hassana ta aike su saman layin sukai mata sako, wasu kaya ne zasu kaima kawarta daga nan kuma ta musu umarnin su shishshiga makota su gaishe su kamar yanda suka saba duk in sunzo zasu shiga gidajen unguwan su gaishe su sannan sukai musu tsaraba domin duk yawancin mutanen unguwan zuri'a ɗaya ne, a lokacin ne kuma Meelat ta samu kira daga gida dan haka ta roki dasu rakata ta samu abun hawa ta wuce. Dan bazata samu damar binsu gidajen ba, bayan su Moon sun tabbatar mata da cewa Insha Allah suma bazasu kwana anan ba dazarar sun dawo zasu hado kayan su zasu taho tareda Meenat gida kamar yanda suka saba, suna shirin fita sukayi kicibus da ƴa Musty zai shigo gidan "ah² jikokin Hajja sai ina kuma? ya tambaya, zamu raka Meelat ne zata koma gida cewar Aisha, waiga wa gefen da take boyewa a bayan Meenal yayi "yanzun fisabillahi da ban ganku ba haka zan laluba inji kin wuce ba sallama kanwata? " ko ba'a dauke ni a matsayin ƴa'ƴan bane iyeh? " to ni dai da gaske nike dan haka muje in sauke ki dan bazan bari kije kiyi tsaye a bakin titi kina neman abun hawa ba" ya fada yana juyawa. (Cinyewa kin yake mu) suka haɗa baki wajen fada da karfi Moon ne mai cewa "bebs bana fada muku ba wallahi ko tantama banayi ƴa Musty ta zurma kunga irin kallon da yake mata kuwa? mutumin da in yana gaban mata yake daure fuska yana wani cin magani amma kuga yanda yake mata magana da kwantacciyar murya wai Allah dadi muma mun zama an mata", Iiiii huuu huuuu jama'a Alhamdulillah Allah nagode maka" Meenal tace da karfi tana tsalle cike da murna saida ta gama raye²n sannan ta dawo gefen da Meelat ke tsaye dan ita gaba ɗaya ma ta rasa na cewa, "ke wallahi kawata tsaya kiji karki yarda ki jefar mana da wannan damar da muka samu, ban kuma ce kiyi gaggawar bude zuciyar ki dan ki cusashi ba NO sai munja zaren mu, Wallahi in kika mishi sakwa² kikayi saurin kware mishi ba uban dazai hana ni in tube mu daku dake, mutanen da kullum mata ke musu layi suna binsu kamar ƙuda da mangwaro dan haka ba ɗagin ƙafa zuciyar shi zaki rikemin dakyau so nike mu banbance musu Banbancin kana nan yan mata da wadancan sakarkarun da kullum suke layin taya su zaman majalisa barima ki gani"ta faɗa tana bude jakarta ta fiddo kwalbar turare ta kama fashe Meelat din dashi, me su Moon zasuyi ai sai suka fara ihu suna kara kuranta ta, "Allah kuwa naku wasa ne bakusan irin bakin cikin dake kamani duk sanda nazo naga mata zaune a kofar gidan nan ba, kai Allah dai ya isa an zubda mana daraja wai mace ke zuwa neman soyayya muna nan daku duk sai nacicci musu uwa, Dan Allah karki bari wannan damar ta kubuce mana" inji Moon ita kuma Aisha ta daura da "karki bamu kunya kawata" ke in kika bani kunya wallahi kai tsaye zan miki Allah ya isa dan kinja mana asara ne babba cewar Meenat basu barta ba saida suka gama fanfata sannan suka fito, koda suka fito daga gidan ƙasa kaɗan suka hango motar shi a fake da alama su yake jira dan haka ba ɓata lokaci suka karasa inda motar ke fake Meenal ce tayi saurin bude mata gaban Motar tace ta shiga basu wani tsaya ba suka musu fatan sauka lafiya suka juyo. Cikin gidan suka koma a farfajiya suka tadda su Anty sadiya da Anty fati duk dai yan matan gidan sun fito "ina kukaje? " Anty fati ke tambayan su, rakiyar Meelat mukayi ta tafi gida' suka bata amsa to ai sai ku juya muje ko ma samu mu dawo da wuri, juyawa sukayi da niyyar fita "kai ina kuma zaku" cewar Anty Sas, ba tafiya zamuyi ba? Aisha ta tambaya to waye zai kwashi kayan nan? Anty Sas din ta kara tambaya, Kai dan Allah baga yara nan ba su dauka mana" ku dai zaku dauke shi dan badasu zamuje ba, suna kunkuni suna komai haka suka dauki kayan ita dai Meenat makalewa tayi a gefe a cewarta bata ma kowa dakon kaya haka dai suka rankaya suka fito sun kumayi sa'a majalisar kamar anyi ruwa an dauke dan ba mutane sai tsiraru, haka dai suka tafi duk inda ya kamata su shiga sun shiga kuma sun raba musu tsarabar gidan karshe da suka shiga shine gidan ƙawar Anty Hassana kuma gidan su Nusaiba masoyiyar Mai Jama'a koda suka isa gidan haka ta dunga rawar jiki tana nan² dasu ina ka saka ina ka aje ita a dole ga kannin saurayi sunzo gidan su batasan wannan rawar jikin nata haushi yake ba su Moon ba su dai su Anty Sas da basu san miye a kasa ba sunyi zaton ko tsabar son jama'a ne yasa ta sake dasu haka basu san tana kamun kafa bane, duk inda tayi haka Meenal ke binta da ido so take saita gano munin ta sai dai kuma Masha Allah Nusaibar fa tana da dan kyanta ba laifi kuma yar masu kudine dan tun daga bakin gate in ka shigo gidan zaka san an tara ba laifi duk ta gama karanceta tsaf amma duk wannan kyan cewa tayi wai Nusaibar bata haɗu ba, jira take subar gidan ta samu damar fesar da abunda ta kunsa, dan haka ta riga kowa tashi dan ko kayan ciye²n da aka jera musu bata yarda taci komai ba haka kuma ta hana sauran ci dan dama su Anty fati sunce suna da koshi, "ku muje koh" tace bayan ta mike "Haba dai da wuri haka ku zauna mu danyi hira mana gashi ma bakuci komai ba" cewar Nusaiba, Ah ba komai muna da koshi gashi magrib ta kawo kai gara mu koma Anty Sas ta amsa mata, to bari in sa muku a leda kuje dashi gaskiya in kunje gidan sai kuci"Nusaiban ta kara fada tana shigewa ciki saida ta kira mamanta cewa zasu wuce sannan ta dauko leda ta juye musu duk kayan dake wajen ita kuma Mamanta kayan zaki ta hada a wata ledar ta mika ma Aisha "ku ce mata nagode nima gobe zan shigo gidan in Allah ya kaimu nagode kunji ku gaida gida". Suna fitowa a gidan tun basuyi nisa ba suka fara gulmar Nusaiba Meenal ce mai cewa "ke Moon wai da gaske ita wannan figaggiyar itace keson wancan Iliya ɗan mai karfin? Kai innalillahi gaskiya dai girma ya fadi yanzun ita duk kyanta kawai ta rasa wanda zata so sai Mai Jama'a" "Wacece? " su Anty Sas suka tambaya, kawar ku mana cewar Meenal "ke kawar wa Anty Fati ta tambaya tana kallon Anty Sas a zaton ta ko wata kawar Anty Sas din suke magana akai Aisha ce ta basu amsa da cewa" Nusaibar nan fa da muka fito gidan su ita ce keson Ƴa AK kuma harda danbe ma sukeyi akan shi haka naji hajiya tana fada" "Meee" suka fada cike da mamaki, "waiyo Allah yarinya ta kamu da mugun abu innalillahi wallahi harta bani tausayi ita wani hau din ne ya hauta ta rasa abun so sai Ƴa AK mutumin da gida da makaranta kullum mata kebi" cewar Anty Sas. gata kyakyawa da ita tubarkhallah" cewer Anty fati cike da jimami "to Allah ya yaye mata dan ko kaffara banayi bazai saurareta ba, suwai basa ganin komu da muke kannen shi ba saurara mana yakeba shegen girman kai ko daga ido ya kalli mutane baya iyawa, duk su suke kara mishi girman kai ai tunda duk inda ya shiga matan ke binshi kamar mayu mtws wallahi duk tama siremin a haka gata kamar mai hankali" haka suka cigaba da caccakar Mai Jama'a da yan matan da kullum suke binshi shi kuma yana yarfa su har suka kusan karasawa gida. Moon ce ta hango majalisar dankam cike da mutane sabanin dazun da suka wuce ba jama'a "to wallahi kuyi shiru dan gashi can a zaune. #kuna ina fans ɗin mai jama'a kuna jin dai yanda ake caccake muku shi ko🥳🥳 #Ummiee~Zaria Jikar lerawa💞 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ *Maman ƴar'so* *Ikeen Mama* *Mom Sayeed & Noor* ```Page 8 Kamar dai kar Maimoon tayi magana dan nan take gaban Meenal yayi wani irin faduwa na rashin dalili gaba daya sai ta dunga jin nutsuwar ta na watsewa yana barin ta, Sauran ma dif su kayi ba wacce ta kara samun zarafin magana dan tsoro suke kar suce wani abu iska ya ɗauki maganar zuwa kunnen shi, dan shikam haka yake kamar maciji indai wajen jin magana ne. Kasan cewar yamma tayi dan haka majalisar tayi dam da jama'a sabanin ɗazun domin daga inda suke takowa suna iya shako zafafan kamshin turarukan da mazauna wajen sukayi amfani dashi domin kowa inya dawo daga aiki sai ya ɗau wanka ya wanku kafin ya iso fada gaskiya dai kaf cikin su ba kazami dan kowa bayason a raina shi, to maza ma suka iya fesa turare balle iyayen kwalisa mata! Ke daga nesa idan kika hango su abun na farko dazai fara zuwa kanki shine kodai zaman meeting sukeyi! Sai dai ba hakan bane su a wajen su suna zaman majalisar ne dan ɗebema juna kewa su dai ba ƴan iska bane basa yawon zuwa club kaf cikin su kuma babu wanda yake shaye² zama dai sukeyi suyita labarai suci susha abunda suke so in lokacin sallah yayi akwai masallaci da zarar sun idar kuma zasu dawo su ɗaura daga inda suka tsaya ba'a watsewa har sai dare ya raba, mazan kenan matan kuma daga 9:30pm zuwa 10:00pm Mai Jama'a yake sallamar su ko wacce ta nemi hanyar gidan ubanta domin yawancin matan saboda shi suke zuwa. Suna kara isa wajen bakin ciki yana kara yawa a zuciyar ta saboda hango wasu zafafan ƴan mata da tayi a tsaye gefen da AK yake zaune akan bayan wata mota su kuma sun sashi a tsakiya suna mishi surutu ko uwar me suke karanta mishi oho abun mamaki kullum yake bata ace mutum kamar shi kadai ne namiji a dangi yana da yayye maza fa kafin shi amma duk gidan babu wanda Allah yama farin jini wajen jama'a sai shi tun daga kan tsoffi dattawa matasa samari yan mata kai hardama yara shi kowa nashine, duk inda yake sai ka samu mutane a kewaye dashi ita dai babban bakin cikin ta yanda mata ke binshi kamar wani shine autan maza, shi kuma sai uban wulakaci da girman kai cike da ciki dan tunda mata ke binshi shike nan dan wulakanci sai ya tattara matan ya musu kudin goro gani yake duk mata haka suke basu da aji kuma basa iya rike abu a cikin zuciyar su, su da ganin mutum kawai sai su wani kware mishi dan haka ba halittar daya raina irin mata. mata ko na gidan su baya shan inuwa guda dasu in yana cikin jama'ar shi a waje zai sake yayi ta wasa da dariya da mutane amma daya shigo gida zai daure wai dan kar na gidan suma suce son shi suke kamar yanda yaga sauran suna mishi, sannan da anyi maganar soyayya yanzun zai fara kumburi yana cika baki shi Allah ya kyauta a cewar shi wai ai ita soyayyar wanda ta raina take kamawa a tsammanin shi yafi karfinta ne shi yasa har yanzun bata iya kamashi ba,(kuji wata farsafa daga bakin mai jama'a fa) Hannun Moon ta riko domin kafafuwanta ta dunga jin suna har hardewa kamar zasu kadata saboda tsabar yanda ta tsargu ji take kamar ita kadai maza da matan wajen ke kallo dan Allah ya sani ita dai ta tsane zaman majalisar nan wallahi da ace Iliya ɗan mai karfi baya wajen da dago kanta zatayi duk ta harare su to tsoro take karta dago kai su hada ido irin na ɗazun . Kamar masu tsoron kar suyi laifi haka suka hada baki wajen gaisheda mutanen majisar kafin ma su karasa wajen ogan Meenal dai ko uhumm bata ceba dan tsine musu ma takeyi a zuciyarta to ina dalili kawai ta tsaya tana wani gaida gaddawa, suko yan majalisar harda masu tsokanar Anty binta da cewa Amarya! Amarya suko matan sai wani washe baki suke sukarkarun kamar kwarto ya hango wawan zama. "Daga ina kuke? " mai Jama'a ya tambaya bayan sun isa inda yake zaune kallon Meenal kawai yake cike da mamaki domin in bai manta ba dazun jaririyar yarinyar nan bata gaishe suba yanzun ma yana lura da ita tsaf wallahi bata gaishe suba sai ma wani dukar da kai data keyi na munafunci, tun basu kai ga bashi amsa ba ta cire hannun ta daga cikin na Moon fuuuuu ta wuce kamar wata kububuwa ta shige gidan Hajiya, Duk yana ankare da taki gaidashi da kuma yanda ta shige a fusace lallai zai ware lokaci ya zanema jaririyar nan jiki tsaf dan alamu sun nuna gata ya mata yawa, "ita kuma wancan meke damunta! ? Ya tambaya muryar shi cike da mamaki yana kallon Maimoon "Um umm wai fitsarine ya matseta" ta fada tana kau dakai dan bata son su haɗa ido ya gane karya takeyi. "Ku wuce gida" yace ba tareda ya karabi ta kansu ba ya duro daga saman motar yana nufa hanyar FADAR shi yan matan nan biyu suka take mashi baya. Ita kam tana shiga side din Momy Hauwa ta nufa ba kowa a falon dan haka ta nemi waje ta zauna tana warware naɗin gyalen da tayi dan ji take kamar yana shake mata wuya. "Ke Ameenatu meya same ki? " zuciyarta take tambayarta "oho" ta amsa a fili to wai ina ruwana ma dasu, mikewa tayi ta isa wajen fridge din dake gefe ta bude ta dauko goran ruwa masu sanyi bata tsaya neman kofi ba ta bude goran ta kafa ruwan a baki dan ji tayi gaba daya miyon bakin ta ya kafe, a dai² lokacin kuma su Aisha suka shigo "kina lafiya? " Anty fati ta tambaya tana tsareta da ido, "lafiya lau me kika gani? " itama ta jefa mata tambaya, naga kin shige a fusace kamar an maki wani abu!" fitsari nefa ya matse ni ga kuma kishi inaji. Ok kawai ta amsa mata dashi a yayin da take zama akan kujera itama. Ku shirya mu wuce fa ni bazanyi sallah a gidan nan ba nasan ma yanzun Baba Malam ya dawo kuma nasan zai nemeni" ta fada tana kallon su Aisha, Ba anan zaki kwana ba dama? Anty Sas ta tambaya "tab nikam wallahi ban kwana kawai waccan tsohuwar tasa mutum a gaba tayi ta mishi masifa gida zan koma ba ruwa na. "Ubanki ne masifaffen" momy hauwa da fitowarta kenan ta tsinkayi maganarta ta amsa mata dashi, "dama uban waye ya gayyato ki nan zoki tattara ki wuce gidan ku mara mutunci" ai bata bari momy hauwa ta karaso inda take ba tayi wani kutubal ta yayimi ledar da aka basu daga gidan su Nusaiba gyale da jakarta kafin su an kara sai gata a kofar falo, suko me zasuyi inba dariya ba domin ko su basu lura da fitowan Momyn ba muryarta kawai sukaji, tana daga bakin kofar take fadin kun gani ko wallahi ko kuzo mu tafi ko inyi tafiyata kwazo daga baya, mikewa sukayi suka rufa mata baya Anty Sas na kiranta akan ta kawo ledar su dibi nasu rabon amma tayi kunnen uwar shegu dasu ta bace daga wajen bayan ta bata amsa da cewa ai sunce sun koshi, Komawa tayi can bakin gata wajen wasu kujeru da aka ajiye a wajen na zama tayi zaune tana jiran su Moon su kwaso kayan su daga sashen Hajiya suzo su wuce dan ita kam ba abunda zai kara mai data side din,bata juma da zaman ba aka buɗe kofar gidan aka shigo, ko bata ɗaga kanta ta kalla ba daga jin takun tafiyar shi da kuma kamshin turaren shi tasan shine, da dahali tashi zatayi kafin ya kai ga karasowa gefen da take dan ta gudu, sai dai ina tasan kota tashi tsalle ɗaya zaiyi ya cafko ta dan haka ta ke bakin kokarin ta wajen ganin bata biyewa idon ta daye neman cin karfin ta akan taɗan daga ko yayane ta kalle shiba, mai makon hakan sai ma wayarta ta ciro daga jaka tayi kiran ƴa Sa'ad domin dama yawanci shi yake kaita waje in ta gama ya dauko ta wannan umarnin Malam ne "Ƴa'yana dan Allah kana ina? " meya faru? Ya tambaya, "gida zamu koma" ta bashi amsa, keda wa kuma ba naga Meelat ta dawo ba? "Eh ta dawo nida su Maimoon ne" ta bashi amsa 'to gani a kofar gidan Hajiya amma ku bari ayi sallah sai mu wuce, Dan Allah ka kaimu yanzun sai ka dawo kaga nasan yanzun Baba Malam ya dawo kuma kasan zai nemeni bana nan kaji" "Naji to ku fito mu tafi" yauwa shi yasa kullum nike maka addu'a allah ya baka Anty Billy kuma ai baka manta da Kazata ba koh?"tace kasa² a dai² sanda Mai Jama'a yaci burki a wajen wani police ɗaya daga cikin security ɗin dake gadin gidan. "Ke wai me yasa kin cika fitina kamar sauro ne? " Sauro kuma niɗin? Bai bata amsa ba ya yanke wayar Aiko saita fara cika tana batsewa wai yace mata sauro wai ita Amina itace sauro hummn aiko saita faɗama Malam. Tana wannan kumbure² su Aisha suka fito su biyu ita da Moon kowacce dauke da kayanta "muje tace" dasu "kuma dai baku manta da tsaraba taba koh? Dan yasin in kuka manta baku da rabo anan ta fada tana musu nuni da ledar hannun ta, ke dallah ya zamu manta sai dai kin san bamuyi tsarabar da Meelat ba ya za'ayi kenan? Cewar Aisha "karku damu nawan zamu raba kuma baga wannan ba kunga harda ilokarta ma ta manta dashi, yanzun dai to ku ware tsarabar a gefe dan so nike mu sauka a gidan su sauran kayan sai Ƴa'ya ya karasa dashi gida dan nasan in muka shiga gida ba lallai mu fito ba, kuma kunga kayan da muka kawo ɗinki dazun Mom dinta ce ta siya mana ina so inje in mata godiya. "To" suka amsa dashi haka kuwa sukayi suka ware kayan tsarabar a gefe. Har yazo zai gifta su bayan ya gama magana da police ɗin meya gani kuma dai oho, dawowa yayi baya kaɗan zuwa inda suke "kai ina zaku je da yamman nan? Aisha ce tayi karfin halin bashi amsa dan ita Meenat duk a takure take jin kanta dan tsayuwar da yayi a wajen kusa da ita wani irin abu takeji yana bin jikin ta da bata gane kan shi ba. "gidan su Meenat zamu tafi" cewar Aishar, "ku koma gida bazaku fita da yamman nan ba in Auntyn zata koma sai ku bita ku wuce gaba ɗaya" ganin dai da gaske korasu gidan yake son yi yasa Meenal buɗe baki badan taso ba tace "to ai Ya Sa'ad ne zai kaimu kuma yana bakin gate ma mu kawai yake jira mu tafi" Ba tareda ya kara cewa komai ba ya juya zai tafi "Ya AK mu tafi? Moon ta tambaya, "Allah ya tsare hanya a sauka lafiya " yace yana ci gaba da tafiya, dan haka suma suka yi gaba da niyyar ficewa har sun kai bakin gate Meenat ta kasa jurewa a zaton ta yayi nisa koda ta juyo da niyyar taɗan kalla ta gani koya kule sai gashi cikin rashin tsammani idon ta ya faɗa cikin nashi kyam yana tsaye yana kallon ta ba shiri ta ruga da gudu bata kara waigowa ba ta fice a gidan, girgiza kanshi yayi yana tabe baki kafin shima ya wuce zuwa uzurin gaban shi, koda suka fito bakin gate din kamar yanda tayi zato zaune ta hango shi cikin mota shida wani abokin shi Mukhtar, shida kanshi ya fito ya bude musu murfin motar sai da suka gaishe shi sannan suka shiga wanda yake zaune a gaban ne wa juyo inda take yana tsokanar ta "Maman Malam yau kuma Hajiya kika kawoma ziyara? " . "lah Babana kaine a gaban motar ashe! Ina wuni suka gaishe shi, "Lafiya lau" ya amsa musu yana cigaba da cewa to ke ai kamata yayi ki kwana bawai kizo ki musu wayau su biki ku koma can gida ba, kai Baba ai Momy ce ta koreni wai in koma gidan ubana kawai dan nace hajiya masifaffiya kuma ai kowa yasan gaskiya na fada dan haka ban kara zuwa, ta fada tana tura baki, "Ah ah diyata ba'a haka wayace miki ana fushi da iyaye kuma keda kikayi niyyar alkhairi ai bai dace ki janye ba ko kin manta menene makomar wanda ya yanke zumunci ne? Ya tambaya, "ban mantaba Babana" ta bashi amsa, to in haka ne ni zan dauke ma Ya'yan ku nauyin duk sanda kika shirya zuwa kimin magana zan kawo ki kinji? "Eh naji nagode" yauwa diyar Albarkha. Haka sukaci gaba da hira har suka bar tudun wada "ƴa'ƴa" na'am kanwar ƴa'ƴa "kazar" ta bashi amsa, "ban manta ba" shima ya amsa mata, to ƴa' gidan su meelat zaka sauke mu dan Allah su Moon ne zasu bata tsaraba kuma kaga in muka shiga gida baza a bari mu fito ba kaji dan Allah saika karasa da kayan su dan Allah, "naji amma dai karku daɗe a gidan kunga magarib tayi, bazamu dade ba Moon ta bashi amsa wannan karan, Koda suka karasa unguwar su a kofar gidan su Meelat din da yake farkon shiga layin suka faka ya sauke su yana kara jaddada musu cewa su koma gida da wuri shi kuma ya wuce. ************ Malam kam lokacin da Meenal ta kirashi da rana yana cikin Jama'a domin daurin aure sukaje yi a zuntu hayaniyar Jama'a shiya hanashi kiranta dan yasanta da shiririta kilama ba wani kira bane mai mahim manci dan haka take yi ko yana gida ma taga damar ta daga waya ta kira shi in sun gaisa saita kashe, to dai shima bai samu kanshi ba gaba daya wunin ranar dan basu samu damar dawowa Zaria ba sai da yamma liss bayan dawowar nashi kuma yayi zaton zata zo tarban shi kamar yanda ta saba tun tuna yarinya inyayi tafiya tana jin kukan motar shi komai takeyi zata bari ta fito tarbar shi bata komawa kuma saiya bata tsarabarta dan har gobe ita kam bata girma da cin tsaraba ba, (yar gatan Malam kenan). Sai gashi shiru har sauran yaran suka shigo suka gaishe shi bai ganta ba, bai iya tambaya ba har saida uwar gidan shi ta shigo bayan ta gama jera mishi abinci ne yake tambayar ta "ina uwata ta shige ne? Banji motsin taba tunda na dawo" sai bayan data gama zuba mishi abincin sannan ta amsa da cewa"ai yau Mai babban suna tudun wada ta yini, kasan bikin gidan yau saura mako guda yaune kuma ake kawo lefe nima nayi mamaki data shigo take sallar mu cewa tazaje tudun wada nace oh su Yar Malam an girma" Tudun wada fa? Malam ya maimaita fuskar shi fal mamaki "to Allah ya dawo da ita lafiya nasan dai indai ɗiyar Malam ce anjima kadan kin ganta a gidan nan ta dawo, Ai malam yau tamayi bazata ita da bata zuwa ko ina kamar daddawar ɗaka, ina dai ta mata addu'a Allah ya bata mijinta anan kusa damu dan bazataji daɗin auren nesa ba. Murmushi Malam yayi yana mai cewa "aiko auren nesan ne ya kama haka zatayi hakuri amma nima bazan yarda akai min uwa nesa ba gara ina ganin ta kusa dani hankalin na zaifi kwanciya, kin ma tuna min Malam Abakar fa ya kara tada maganar da yamin lokutan baya na batun yaron wajen shi Sufyan da yake son in bashi uwata" ya karasa fada fuskar shi kadaran kadaham, "to kai me kace dashi Malam? "Eh to na dai ce dash ya&han kara hakuri tukun har zuwa gaba" Nagode Allah da bakayi saurin amsawa ba Malam dan nidai labaran da nike samu akan matar yaron nan gaba ɗaya basu da daɗi dan kaf ba wanda ta ragama ina tsoron ka ɗauki mai sunan manya kaba shi azo a samu matsala, duk da dai shidin kowa ya shede shi yaron kwarai ne, amma nidai haka nan nikejin fargaba, "Allah yayi mata zabi mafi alkhairi" cewar malam ita kuma ta amsa mishi da ameen Haka dai sukayi ta zantawa akan halin Meenal na rashin son shiga cikin mutane duk da yanda mutane ke nan² da ita kowa so yake ta raɓe shi amma ita kamar mai tsoron su dan ko baki akayi a gidan kiriniyar ta na raguwa shi yasa Jama'a da dama basu san halin ta na rashin ji ba. ****** Tofa akwai chakwakiya fa, wacce take lissafin tayi karatu ta zama likita inta fara aiki ta siya gida ta kuma gina ma Malam gida a Abuja itace ake maganar auren ta. Akwai magana a gaba fa...... Kar a manta aci gaba da sharing ana haɗawa da comment #Ummiee~Zaria jikar lerawa [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _*Ina baran addu'a ga duk wanda ya karanta page ɗin nan yasa sister ɗina Fauziya a addu'a tana fama da rashin lafiya ubangiji Allah ya yaye mata. ```Page 9 Koda Sa'ad ya sauke su kai tsaye cikin gidan nasu Meelat suka shige, Babban gida ne mai kyau ginin zamani wanda aka kawata farfajiyar shi da fulawoyi masu kyan kallo saɓanin gidan Malam da yake sassa² wannan ɗin ya kasance a dunkule ne ta yanda hakan ya nuna cewar mazauna gidan basu da yawa, duk cewa dayau ne karon farko dasu Maimoon suka fara zuwa gidan hakan baisa sun maida hankali wajen ƙarema gidan kallo ba domin dukkan su babu wacce take da duhun kai a cikin su, dan in aka kwatanta wannan gidan da nasu gidajen iyayen wannan ɗin ba komai bane. "Ah² Uwar Manya ce yau a gidan?" cewar mai gadin gidan bayan ya amsa gaisuwar dasu Meenal ɗin sukai mishi, " Kai Baba Ayuba ko jiyafa nazo gidan nan ɗazun ma nazo shigowa ne dai kawai banyi ba", " to barkan ku da zuwa a fito lafiya" ya faɗa a yayin da suke wucewa zuwa cikin gidan, koda suka karasa cikin falon Hajiya Kausar suka samu Mahaifiyar Meelat tareda ɗaya daga cikin yayyin Meelat din Namiji mai suna Mashkur suna duba wasu kaya, da sallama ɗauke a bakunan su suka karasa shiga cikin falon sai da dukan su suka gaishe su sannan Meenat tama su Maimoon nuni da kujerun falon "ku zauna" tace dasu, "Ƴar Malam yau kuma ziyarar dare aka kawo mana? Gara da kika shigo ma dan dama yanzun nike shirin inba ya'yan ku saƙo in yana wucewa ya miƙama Hajiya Jidda waɗan nan kayan" ta karasa faɗa tana mata nuni da wasu lesuka data ware su a gefe cikin kayan dake gaban ta, "To ai Momin bata dawo ba can muka barota a Tudun Wada" Meenat ɗin ta faɗa tana karasawa inda kayan suke "Anty wannan kayan wai duk na Momy ne? to amma dai ba nata ita kaɗaiba harda nikoh? " Take tambaya, "to ƴar jarida aida kin adana tambayoyin naki har ki kai mata kayan tukun dan nidai nan bani da amsar tambayan ki, kin ajiye baƙi a kujera ko ruwa baki dauko musu ba, Jameela" ta kwalama kira "Na'am Anty ina zuwa" Jameelar ta amsa daga ɗakinta, "Ni ban san me kikeyi a cikin ɗaki tun dazun ba to fito kiba baƙi ruwa dan wannan mashiririciyar yanda ta tsareni da tambayoyi anan ba damuwa da basu ruwan zatayi ba, "Anty ni zan wuce ga lokacin sallah ya karato zuwa goben kafin in wuce shago zan shigo mu karasa lissafin" Ya Mashkur ya faɗa a yayin da yake mikewa "ok to ba damuwa saida safen ka gaishe min da Aslam" ta faɗa itama tana mikewa "Ya mashkur kace ma Anty zan zo mata yawo gobe kaji amma a soyamin kaza", cewar Meenat "ke raba kanki ki rasa wajen zuwa sai gidan waccan marowaciyar da bata ƙaunar kowa yaje mata gida saboda tsabar rowa har kaje gidan nan ka fito ko ruwa bazata maka tayin shiba balle kasa rai da abinci mtsw ina ma amfanin rowa" Antyn tace sannan tasa kai ta wuce ciki ba tareda ta karabi ta kansu ba, "Goben da ƙarfe nawa zakuzo? " ya tambaya, "Ya'ya in zamuzo zan kiraka"ta bashi amsa "ok to saida safen ku sai naji ki" ya fada sannan yasa kai ya wuce. Falon ya rage saura su uku, kai ku tashi mu shiga ciki waccan ƴar rainin wayan bansan uwar me take a ɗakin daya hanata fitowa ba! Jagora ta musu zuwa ɗakin Meelat ɗin koda suka isa zaune suka sameta kan kujerar mirrow da waya a hannun ta, jin motsin bude kofar ne yasa tayi hanzarin ɗago kanta daga kallon wayar da take ta maida kallon nata zuwa bakin kofar, "ke wai wani salon wulakanci ne sabo kika samu kina jin motsin mu a falo kikaƙi fitowa kuma bawai bacci kike ba! ", cewar Meenat "Ke dallah ai nasan dole zaki shigo bagashi yanzun kin karaso ba ta faɗa tana mikewa "Moon Aisha bismillan ku ku zauna mana please ku dena biyema wannan Autar Malam ɗin bari in kawo muku ruwa" ta karasa faɗa tana shirin barin ɗakin " ke in akwai meatpie ki ɗibomin zanje gida dashi" inji Meenat, Bazan ɗibo ɗinba ai kila ni ƴar aikin kice kin ma rainan wayau! ta karasa faɗa tana hararar Meenat ɗin, Haba abar kauna nice fa"Meenat ta faɗa tana marai raicewa Meelat bata ƙara bi ta kanta ba tasa kai ta wuce, kan mirrow inda Mealat tabar wayarta Meenat ta karasa ɗaukar wayar tayi sannan ta nemi waje a gefen gadon ta zauna tana cire naɗin gyalen dake kanta, call log ta fara dubawa idanuwan ta suka ci karo da wata special Number wacce itace number ta karshe da aka amsa kira daga gareta akallah kuma wanda ya kiraɗin yayi Magana da Meelat din na kusan mintuna 40,fita daga wajen tayi ta koma wajen ajiye saƙo anan ma taci karo da sakonni biyu dukan su kuma daga waccan number ɗin ne sai dai duka sakon ba wacce Meelat din ta bada reply akanta, "Bebs ku matso ku gani yasin tarkon mu ya kama Zakara dan mu dai munfi karfin muyima kurciya tarko wallahi" Cewar Meenat tana matsawa kusa dasu Moon sosai yanda zasuga abinda take son nuna musun, "Dan Allah dai kice munyi sara akan gaba Sister? " cewar Moon, "ah kwarai kuwa to muɗin ai ba na wasa bane, "da fari dai bayan doguwar magana a waya ta kusan awa guda ga sakon nin da suka biyo baya " dariya tayi sannan ta kara da cewa " bari mu karanta sakon soyayya atoh da muna ganin wasu nayi yanzun muma yazo kanmu" "Ke dallah kiyi ki karanta kina jamin rai na matsu inji me sakon ya ƙunsa" cewar Aisha cikin zakuwa, juyowa Meenat tayi tana hararar ta "ko kimin shiru ko inƙi karantawa wallahi tam" kara gyara zama dukan su su kayi ke in kika gansu zakice ko wani abu mai matukar mahimmanci zasu karanto a cikin sakon, Ga abinda sakon farko ya kunsa: Assalamu Alaikum Mai Kyau, Meelat akwai Matsala fa! dan ina zaton akwai abunda na rasa a jikina bayan rabuwar mu! Ki tayani nema idan kin ganshi ki adana min shi a wajen ki domin kece mafi dacewa da ajiyar shi dama, Ki kasance cikin farin ciki daga yanzun har zuwa karshen numfashi. *El~Mustapha* Kallon² suka tsaya yi a tsakanin su bayan Meenat ta gama karanto musu saƙon, Bebs kun gane me sakon ke nufi kuwa? Meenat ɗin ta tambaya, tana mai kara maimaita karanta saƙon a karo na biyu, Aisha ce ta mike ta fara rawa su kuma suna kallon ta suna murmushi saida ta gama rawar sannan ta dawo ta zauna, a dai² lokacin ne kuma Meelat ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da katon farantin data gero plates ɗin abinci ruwa dasu drink kan mirrow ta karasa ta ajiye shi sannan ta dawo tsakar ɗakin tana kallon su kamar yanda suma ɗin suke cigaba da kallon ta, "Nidai karku tambayeni komai yanzun ku bari har muyi sallah tukun sai in baku labari dan nasan wallahi harda jin gulma yasa kukazo" ta faɗa tana hararar Meenat, Ke Baby inani Aminatu ina bacci banji ya aka kwana ba bayan nasan baiwar da Allah yama kawata nidai zoki taimaka ki shafamin labarin abinda ya faru karkisa inyi sallah ba cikin nutsuwa ba kinji dai yanzun nema ake kiran Sallah ɗin" cewar Meenat, shareta Meelat ɗin tayi ta juya inda ta aje farantin data shigo dashi ta ɗauko ruwa da drink tazo ta ajiyema Moon da Aisha a gaban su " kusha ruwa ta faɗa sannan ta juya ta shige bayi batareda ta kara bi takan Meenat ba, "kutmelesi ke ni zakima iskanci kika shige kika barni, da kyau eh ba laifi yarinya to yasin ban barin gidan nan sai kin bani labari inba haka ba yanzun nan in maida mishi amsoshin sakon nin shi kin dai san halina tsaf bakya buƙatar karin bayani," "kin daɗe baki tura ɗinba" cewar Meelat tana shigewa makewayin, komawa tayi ta zauna "ke Aisha baki faɗa mana abunda kika fahimta ba" cewar Moon bayan ta cire goran drink ɗin da take sha a bakin ta, "humm wallahi Ya Musty son Jamila yakeyi ku gane mana wai cewa fa yayi ya rasa wani abu a jikin shi, kuma wai inta gani ta adana, to na rantse zuciyar shi yake nufin ya rasa ta adana wato ta haɗa zuciyar shi da nata zuciyar wai shinan mai wayau bazai fito kai tsaye yace yana son ta ba" "ke barshi dan Allah ai tunda aka fara haka duk taurin kanshi wata rana sai ya furta muje zuwa dai, Kai ku tsaya nifa wallahi tsoro nikeji" cewar Moon, tsoron me? Suka haɗa baki wajen tambayan ta, gyara zama tayi sannan ta ɗaura da cewa "wai ku bakwajin tsoron a gida a gane kuna kula samari? Ke wani saurayin muka kula? Meenal ta tambaya tana tsareta da ido, "shi Ya Musty ɗin mana!" Moon ta bata amsa, ke dallah ware wani munafikin ne zaije yakai labarin cewa Ya Musty nason Meelat a cikin mu? ta faɗa tana tsatsatsare su da ido, "ah² ni wallahi bazan faɗa ba",cewar Moon "to da dai yafi miki kuma ai wannan abun dukan mu zai amfana dan wallahi kuna ganin bikin nan in bakuyi wasa ba yan aiki zaku zama, kunaji dai ɗazun ake cewa wai wajen reception ba yara wai mune yaran suke nufi fa, amma kunga in muna da Ya Musty ai ba fashi sai munje dan kunsan wallahi indai Iliya ɗan Mai karfi ne ba bari zaiyi muje ba" Ke wai waye Iliya ɗan mai karfin?" Meelat data ɗauro alwallah ta tambaya, Ya Abdul mana ta fada tana mikewa domin zuwa ɗauro alwallah itama, "kr wai wanda hajiya tasa aka kira mata dazun? Eh to ba laifi yaci sunan"ta karasa faɗa tana dariya, Saida suka idar da sallah dukan su sannan sukayi zaman cin abincin da Meelat ta shigo musu dashi bayan sun zama ci Meenat ce ta janye farantin gefe, "ke kawata dan Allah ki bani labari meya faru a hanya ciniki ya faɗa kuwa?" "Ai in ban baki labari ba na tabbata har mafarki sai kinyi yau to gyara zama kisha labari, amma dai kafin nan bani tuwon madara da ilokata sai inji daɗin baki labarin" Mika hannu tayi ta ɗauko jakarta ilokar ta ciro ta mika mata gashi ni ban son jinini, Abinda ya faru...... Bayan su Meenat sun wuce. Ina yini" Meelat ta gaishe shi, "lafiya lau kanwata amma dai kin san saura kada) n kisa zuciyata ta tsaya cak koh? Waigowa tayi taɗan saci kallon shi, "yes kalleni da kyau ba wasa nike miki ba Allah da kin tafi batareda kin min sallama ba ba abunda zai hana ni suma", Kai Ya Musty suma kuma ana zaune kalau? Waiyo Allah Momina kinji wata murya mai daɗin amoh dan Allah kara kiran suna na a bakin ki inji, ban taɓa jin daɗin sunan ba sai yau" hannu takai kan fuskarta ta rufe tana murmushi, "kai dan Allah amma dai wasa kakeyi koh", ki taimake ni ki dena rufe fuskar nan Allah dan bakiga yanda murmushin ki ya kara kawata fuskar bane Allah cutar dani zakiyi muddin kikaci gaba da rufemin ita dan ni banki in gangare gefen hanya in faka kawai dan inci gaba da kallon fuskar mai kyau ba. "Ah ah nidai kar kayi haka kaga jirana akeyi a gida" To yane an mata bani labari na samu shiga kuwa? dan kawance nike so mu kullah, kin san kowa yana son mu'amalah da abu mai kyau toya zaki iya kawance dani? " Kai Ya Musty to ai ba'a kawance tsakanin Namiji da Mace, " Ke mai kyau waya faɗa miki? Nidai na sani ai"itama ta bashi amsa, "To yanzun kina nufin ban samu karbuwa ba kenan? " ya fada da karyayyar murya, Ah ah ni ai bance ba" ta bashi amsa batareda ta kalleshi ba, "to in haka ne na samu shiga kenan, to dafari dai domin abota tayi karko ina bukatar phone number ɗinki ta yanda zan samu damar kiranki aduk sanda naso jin muryar ki, bani wayar ki " Ciro wayar tayi daga cikin jaka ta mika mishi bayan ya loda number din shi akan wayar nata sai da ya kira wayar sannan ya waigo gefen ta "da wani suna zan miki saving number ɗin? Ya tambaya, Zanyi saving da kaina" ta bashi amsa "oh right nidai Mai Kyau zansa a nawa Kinga duk wanda ya dauki wayar yasan mai kyau ce ke kirana, Bai barta ta sarara ba haka yasa karamar yarinya a gaba yana ta bulaleta da kalamai a tsanake a haka har suka iso kofar gidan su Meelat ɗin sannan ya sauketa, ko a kofar gidan nasu ya ɓata lokaci sosai kafin ya juya ya koma ita kuma ta shige gida, To kunji abunda ya faru....... "Kawata faɗamin wani abu kin kware mai ko ah ah? Meenat ta tambaya tana kallon Meelat ɗin, ke dallah can ai kema kin san ko giyar wake nasha bazanyi saurin kware mai ba, koba a bakin ku naji kuna faɗar yanda mata ke musu layi ba? Yanzun ni fisabillahi ina ni ina sa kaina a shiga uku dududu fa shekarun mu basu kai 15 ba har yanzun shi yasa na kasa bashi amsar saƙon nin shi, kin san dai gidan nan har yanzun kallon jaririya sukemin shi yasa na kosa ingama sakandire ko sa faramin kallon matashiyar budurwa, " Yauwa yanzun dai bazaki bashi amsar saƙon shi ko ɗaya ba in yayi magana kuma kice baki fahimci abinda saƙon nashi ya kunsa ba, karki sake koda wasa yazo gidan nan da sunan zance wallahi inba so kike acicci mana uwa ba toh, kidai rike mana shi a waya kaɗai ya wadatar inya matsa yana san ganin ki sai kizo gidan mu in yazo sai ku gaisa fakat, Aisha karanto mana ɗaya sakon muji shi kuma meya ƙunsa "ta faɗa tana mikama Aisha wayar Meelat ɗin. Sai kuma sako na biyu shima ga abunda ya kunsa..... ****Gaskiyar yan magana da sukama wannan rana laƙabi da Jummu'at babbar rana, domin nima ayau naci alfarmarta daga cikin nasabarta nayi katarin samun abunda ya girgizamin zuciyata, wato haɗuwa dake da nayi ayau. Ki karanta da murmushi domin hakan yana karama kyan ki kyau, El~Mustapha Huhuhuhu kunji wani salo dan Allah gaskiya Ya Musty na kawo wuta, dan littafi zan nema in dunga rubuta kalaman nan ina adana ma future husband, oh my future husband were are you sai nan da shekara nawa zamu haɗu ne? Kayi ta kulamin da kanka kafin haɗuwar mu," cewar Meenal tana murmusawa. Haka suka shantake suka dunga tsara yanda suma zasuyi shagalin bikin Anty binta ba tareda sun takura kansu ba, a haka har lokaci ya fara ja basu ankara ba, Hajiya Kausar ne jin shiru² basu fito ba yasata lekowa taga mai sukeyi. Meenal halan dai yau kwana zakiyi a gidan nan Malam baya gari ne hala? Cewar Anty, La'ilaha Illallah Muhammadur Rasoulullah (s,a,w) Meenat ta faɗa tana wantsalowa daga kan gadon da take kwance, tsakani da Allah itafa ta manta da cewa ba'a gidan su take ba hira tayi daɗi ta manta cewar Malam tabbas zai neme ta, rarumar jakarta tayi ta lalubo wayarta 2 missed call ta gani daga Malam sai 3 missed call na Ya Sa'ad 1 missed call na Momin ta, kai ku tashi mu wuce gida wallahi Malam ya kira take faɗa a firgice, murumshi Anty tayi tana rufe kofar ɗakin take faɗin ai "dama nasan kuna nan kuna shuririta kin manta zakuje gida to kuzo ku wuce dai dare yayi kema bisu ku barni in sarara, ke Meenat karki Manta da kayan nan gasu nan a falo" daga haka ta koma ɗakin ta, Moon ne tace "Meelat ga tsarabar ki kiyi hakuri ba yawa" cike da murna ta karɓa tana godiya, muma Anty ma tace in biku muje can gidan in kwana bari in dauki kayana" karamar jaka ta dauko ta zuba duk wani abunda tasan zata bukata a ciki Aisha ce ta ɗaukar mata jakar ita kuma ta ɗauki farantin data kawo musu abinci sannan suka fita daga dakin kitchen ta wuce su kuma Meenat ta musu jagora zuwa ɗakin Anty bayan Antyn ta musu izinin shiga, "Anty zamu wuce saida safe" to ƴaƴan Albarkha sannun ku angode da zumunci Allah yayi Albarkha ke Ƴar gidan Malam baƙi kukayi ne hala? " Antyn ta tambaya "eh yaran yayyen Momi ne da sukazo yau" ah masha Allah to sannun ku kunji nagode kwarai Allah ya kara haɗa kanku" Ameen suka amsa mata dashi, Meelat ne ta shigo ɗakin hannun ta dauke da ledar tsarabar da suka kawo mata zazzage kayan tayi kusa da inda Antyn ke zaune cike da jindaɗi tace "Anty kinga tsarabar da suka kawo min, kuma fa yau muka san juna dasu", Kai Masha Allah sannun ku da ɗawainiya kunji angode, Meenat ce ta rike ƙugu tana hararar Meelat ɗin "ke wai wannan godiyar da kike tun ɗazun na miye? nifa bana son haka duk kinsa naji wani iri, to nima ku tayani godiya aina faɗa muku kayan ɗazun Anty ce ta siya mana koh? ta karasa faɗa tana kallon su Moon, su kuma kamar wasu masu jiran umarni suka haɗa baki wajen cewa "angode Anty ubangiji Allah ya kara arziki" Ameen, Sai da Anty ta rako su har bakin gate bayan ta sa Meelat ta ɗauki kayan da zasu kaima Momi Hauwa sannan ta koma cikin gida. Sai bayan sun fito sannan tabi bayan kiran Ya Sa'ad, "ina kika ajiye wayar ne? " ya tambaya bayan ya ɗauka, sallah nikeyi Ƴa'ya ta bashi amsa tana istigfari a cikin zuciya na ƙaryar data sharara mishi "ok to ya maganar kazar a siyo ko kin koshi?" Kai ya'yan mu bafa ni kaɗai nasa raiba harda su Aisha ma sunsa rai ga kuma Jamilata itama yau a gidan mu zata kwana dan Allah ka siyo mana kaga sai ya tayamu hira wallahi Allah ne kaɗai yasan ladar da zaka samu in kai wannan taimakon yau kaji Angon Anty Billy" bata kara sauraran jin me zaice ba ta yanke wayar a dai² kofar wani shago dake cikin layin nasu ta hango shi zaune gefen shi dama da hagu waɗansu irin ɗika ɗikan karnuka ne sunci sun koshi gwanin firgitarwa gamai kallon su gefe guda kuma yaran shine suke dafa shayi a cikin irin kananun butocin nan na buzaye, Meenal ga ɗan gidan kinan fa, cewar Meelat data matso kusa da ita, "yaushe ya dawo kuma ni Amina? " oho in kin matsa kusa kya tambaye shi. Ganin suna kara matsawa inda suke yasa karnukan fara haushi, wani irin haushi suke mai bada tsoro, tsukuikuye juna sukayi tsabar tsoro, suko samarin dake gefe me zasuyi ba dariya ba, "Shutup" ya daka ma karnukan tsawa sai gasu duk sunyi kwance sunyi shiru sun natsu, ku kuma miye na dariya anan" ya faɗa yana kallon samarin fuska ɗaure, ayi hakuri Sarki" suka haɗa baki wajen faɗa, Daga ina kuke da daren nan? Ya tambaya babu alamun fara'a a fuskar shi, Meelat ce ta iya bashi amsa da cewa "daga gidan mu muke". Kuma sai baku iya gaisuwa ba koh? Ya tambaya "mun iya" suka haɗa baki wajen faɗa kamar wasu gaulaye, "oho to ina wunin ku" Kayi hakuri Ya'ya Sufyaan ina wuni ka dawo lafiya ya aiki barka da zuwa" haka suka dunga jero gaisuwa domin duk sun riga sun gama ruɗewa, "lafiya lau" ya amsa musu dashi a takaice yana kauda kai. "Kuzo ku wuce kai kwaro zoka rakasu, yace cikin wata irin buɗaɗɗiyar muryar shi da sam bata rikuwa duk sanda yaso ya rageta da niyyar yayi magana a tsanake baya iyawa dan muryar nashi tana da amo sosai da zarar yay magana harna nesa dashi sai yaji. Huhuhu gafa Sarki ya bayyana🤕 ina fatan kun shirya tsaf dan yanzun zamu shiga cikin labarin kaain da naain. #Share and Comment #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _Bazan taɓa mantawa da ku ba aminan ƙwarai,ina kuma alfahari da kasancewa ta cikinku,ko ban kira suna ba kun san kanku,mutanen Family House. Na gode³ ƙwarai da ƙarfin gwuiwar da kuka bani,wajen rubutun littafin *DANGINA* ubangiji ya biya da aljannah._ ```Page 10 #No editing "Angama Sarki" wanda ya kira da sunan kwaro ya amsa dashi yana tasowa shima ɗin saurayine cikakke yana sanye da plain ɗin white shirt sai gajeren wandon sojoji a jikin shi, "muje ko yan mata" ya faɗa yana mai nuna musu hanya, haka sukaci gaba da tafiya har saida suka kusa isa gidan Malam sannan ya buɗe baki yace "ku dunga kiyaye fita gida da dare fa tunda sarki ya dawo kunsan zai dunga sakin karnukan shi, yauma kunyi sa'a ne da kunkai karfe 9 da kun zama nama" ya faɗa fuskar shi ba fara'a sam, waiyo Allah kinji ko Meenat wallahi dama nasha faɗa miki karnukan nan da wuya inba naman mutane ake basu suna ciba, yanzun shikenan yaufa da sun cinyemu" Meelat take faɗa a tsorace dan ita dama shegen tsoro gareta abu kankani ke firgita ta, shiko ya faɗa musu hakan ne dan su kiyaye fitan dare. Gab da kofar gidan ya dakata "na kawo ku gida koh? " eh Malam mun gode, cewar Meenat "to ku karasa ina hangen ku daga nan" ai gudu² sauri² suka wuce shi kuma bai wuce ba har saida yaga shigar su cikin gidan sannan ya juya. Dukan su kamar waɗanda sukayi gudu haka suka dunga sauke ajiyar zuciya bamai iyama wani magana a cikin su har suka ƙarasa cikin farfajiyar gidan, karar da wayar Meenat dake cikin jakarta tayi ne ya sanya Meenat ɗin kallon parking lot ɗin gidan aiko sai idonta ya sauka akan motar Momi Hauwa, "waiyo Momi ta dawo tun ɗazun kenan " ta faɗa a baiyane "ku ƙarasa ciki please zanje in duba Baba Malam ko zakuje? Ta tambaya "No kije zamu shiga da safe Insha Allah ", Ok to ga wayata Meelat in Ƴa'Sa'ad ya kira ki ɗauka kuce ma Momi na shiga wajen Baba" ta faɗa tana mikama Meelat ɗin wayar da jakarta su sukayi gaba ita kuma ta juya akalarta zuwa sashen Malam dan tasan yanzun yana gabda tashin magidan tan da suke karatun dare a wajen shi, kamar ta shige ciki wajen matan shi sai kuma dai ta wuce falon shi kai tsaye, kamar yanda ta zata ɗin haka ta tarar ba kowa a falon dan haka guri ta samu ta zauna hango kulolin abincin da aka jera mishi a gefe ya sanyata mikewa ta karasa inda suke saida ta buɗe ko wacce kula taga abinda aka shirya mishi kamar yanda ta saba duk sanda ta shigo bata tarda shi ba takan ɗibi abincin iya wanda zata iya cinyewa taci, in kuma ta sameshi to tare suke cin abincin ko kuma in bataci ba zaici yabar mata saura dan yasan dai inhar lafiya lau take ba shakka sai tazo tayashi hirar dare, da zarar bai gantaba shima hankalin shi baya kwanciya yasan ba kalau take ba, dan haka ta ɗibi abinda take muradi duk da tana da koshi ta koma kan kujerar data tashi taci gaba da cin abincin ta hankali a kwance tana yi tana kallon Agogo, zuwa can ta fara jin mitsi da gyarar muryar Malam ɗin da yake nan kamar ƙa'idah domin inhar yazo waje kafin sallama sai yayi gyaran murya, plate din abincin ta ajiye a gefe sannan ta mike tsaye domin nuna girma mawa, da sallama ɗauke a bakin shi ya shigo fuskar shi cike da annuri, karasawa inda yake tayi tana amsa sallamar da yayi, "Uwata idon ki kenan? " ya faɗa a yayin da take amsar littafan dake ɗauke a hannun shi, juyawa tayi tana rufe fuska da littafan alamun jin kunya, "to aini har saura kaɗan in bada cigiya naji shiru² banji ɗuriyar ki ba, harna fara cewa to ko Hajiya Amina tayimin garkuwa dake ne so take in kai mata ƴan kuɗaɗe kafin ta sakomin ke? ", Baba ai mun dawo tun ɗazun mun shiga gidan su Jameelata ne mun karɓoma Momi saƙo yanzun ma saida Ƴa sufyaan yasa wani ya rakomu kofar gida, ni ban san ya dawo ba ai da bamu daɗe a gidan ba" ta karasa faɗa tana tura baki, "Too haka akayi? To lallai Malam Sufyan ya kyauta tunda yasa aka rakomin uwata gida Allah dai ya saka mishi da alkhairi dan nima dai hankalina bai kwanta ba dan nasan karfe 9 ake sakin karnukan gashi banga uwata ta dawo ba, to barka tunda Allah ya dawomin dake lafiya" karasawa kan kujerar shi dake gefe yayi ya zauna "kinci abincin kuwa? dan kinga yau mun ɗan kara lokacin tashin karatun namu nasan kila kinji yunwa", eh gashi na ɗiba ina kanci nema" karasowa tayi kusa dashi ta zauna a kasa gabda kafafun shi bayan ta adana littafan data amsa a cikin ma'ajiyar su, Ina wuni Baba, ka dawo lafiya, ya gajiyar hanya ya mutanen Zuntun? Kun ɗaura auren lafiya? Ubangiji Allah ya basu zaman lafiya!. Lafiya kalau na wuni uwata, kuma na dawo lafiya dan harda tsaraba ma nayi miki, mutanen zuntu suna nan kalau duk sunce suna gaisheda Uwar Malam, Alhamdulillah kuma mun ɗaura aure lafiya dan har an wuce da Amarya gidan ta tuni sai fatan zaman lafiya kamar yanda kikayi. In kawo maka abincin nan ne ko saika huta zakaci? To da yake ma dai bani da wani yunwa sosai inaga kiɗan ɗibomin kaɗan dai haka a faranti sai in gani ko zai shiga" to ta amsa dashi tana mikewa zuwa inda abincin yake saida ta tsatsatsakuri duk wani abunda tasan zaiso sannan ta haɗo da ruwa da zoɓo drink ta kawo, Saukowa kasa yayi ya zauna da kyau sannan ya fara cin abincin, Baba ashe karnukan Ƴa Sufyan suna cin naman mutum? ta jefo mishi tambaya dan abinda yake ta cizon ranta kenan tun ɗazun, Tofa uwata ke waya faɗa miki? "Toba wannan da yasa ya rakomu bane yace wai yau da mun kara lokaci har aka saki karnukan da sunci nama, wai karnukan ne zasuci naman mu, kaji shifa. "Ah³ babbar magana to kinji koh ai shi yasa bana son kuna fitar daren nan yanzun da sun cizamin uwa yake nan? Kai lallai to uwata ki kiyaye fitan nan kin san ance hanyar lafiya a bita da shekara kinsan dai ko banza sojoji ba kirki ke garesu ba balle kuma karnukan su da suka sha training suka koshi, To Baba haka za'a bar karen su dunga cizon mutane baza'ace su mai dasu can inda suka ɗauko suba? " Ina Za'ayi haka uwata bakiga su karnukan sunayi mana gadi a unguwa bane? Aisu waɗan nan karnukan sune maganin yaran nan marasa kunya yan sara suka masu sa babba zabgawa da gudu ko bai shirya ba inya gansu, ko kin manta yanda kwanan baya suka so su fara shigo mana unguwa da sunan shara, kai ubangiji Allah dai ya shirya mana zuri'a kana nan yara su dunga ɗaukar makami suna shiga unguwan ni haka kawai duk wanda suka gani yaro ko babba tsoho ko tsohuwa mace ko namiji sai subi su sassare sai dai in ka hango su kafarka ta kwace ka, dan rashin hankali da sharrin kwayoyin da suke sha in an kamasu sai kaji suna cewa wai ai su sunje shara ne, To saboda sune yasa ai Malam Sufyan yayi Magana a kawo mana sojijin da zasu dunga mana gadi su kuma waɗan nan karnukan ai nashi ne in yazo unguwar ne yakan sallami waɗancan sojojin suje su huta nashi yaran sojojin da karnukan suke kwana gadin mu ai mu muna cikin gidajen mu muna bacci, kinga ko ai abun a yaba mishi ne koh? Allah dai ya saka mishi da Alkhairi, " Ciki² ta iya daurewa ta amsa mashi da ameen badan taso ba, dan ita bata san me yasa Malam yake son mutumin nan ba ko kaɗan baya son laifi ko tace Ƴa Sufyan yayi kaza sai ya nemo wani abunda zai wanke shi dashi, ita dai Allah ya sani ta tsani karnukan can masu shigen kama da zakuna, shegun karnuka dako gefen gidan kaje wucewa indai sunji motsin ka sai kukan su ya firgita ka, kawai su dai ana ɗaukar alhakin su duk sonta da zuwa tsinko mangwaro da gwaiba a gidan na Malam Ladan ɗin yanzun ba hali sabida sheggun karnukan nan insha Allah sai ta nemo poison ta basu sunci sun mutu. Uwata ya dai tunanin me kike kuma? Malam ya katse mata tunanin ta, kafin ta bashi amsa uwar gidan shi ta shigo da sallama. Bayan ta shigo tun kafin takai zaune tal farama Meenal ɗin tsiya da cewa " gaskiya fa gidan nan karara ake nunamin ban²ci ashe kin dawo tun dazun wato Baban ki kaɗai kika nema niko oho, to ai ba komai bari lokacin aure yayi mugani ko shi Malam ɗin binki zaiyi ku tare acan, " Taran numfashin ta tayi da cewa " barka da dare Innan mu, so nike fa in natashi daga nan dama in shigo, ai kinsan ban iya bacci saina ganki ko Baba" "Kwarai kuwa uwata"cewar malam. Ah² Malam ai kai daman kullum goyon bayan mai sunan manya kakeyi to barka da dawowa ya kika baro kakar naku da sauran mutanen gidan? " Dukan su suna lafiya kuma sunce a gaishe ku tare muka dawo dasu Aisha ma," ta karasa fada a yayinda take mikewa bayan ta gama cin abincin datake ci, "Badai har kingama yima Baban naki hirar ba? Naga kin mike alamun tafiya! " Eh Innan mu akwai saƙon da zanba Momi ne kinsan ita da wuri take bacci shi yasa" Malam ne yayi gyaran murya hakan ya maida hankalin su a kanshi Kayataccen murmushine kwance a fuskar shi a yayin da yake cewa "Innan su inaga fa maganar ki keson ya zama gaskiya, yau wacce rana kinga fa uwata ta shigo har tana shirin wucewa batayi tambaya akan tsarabar ta kamar yanda ta saba ba" Dariya tayi tana mai amsa mishi da cewa aina faɗa maka ƴata ta girma, Tsumewa Meenal tayi a tsaye ita kanta mamakin kanta takeyi, "Allah Baba karnukan can na Ya Sufyaan ne duk suka firgitani" ta fadi hakan a yayin da take komawa ta zauna a kusa da Malam tana leke²n inda zata hango ledar tsarabar nata, "ina yake tsarabar nawa?" Gefen shi ya mika hannu ya yawo wata leda bag "gashi ta nan asha lafiya jeki huta kuma sai da safe" Haba malam ka mika mata kuma duka baka bani na ɗibi kasona a ciki ba shi yasa fa nace kuna wareni gashi kuwa! " ta faɗa tana juyar dakai gefe alamar tayi fushi, Dariya Meenal takeyi tana mai cewa "Allah innan mu ke wai sai kice muna wani wareki, nidai ba ruwa na inma duka kike so gashi in kuma ɗiba zakiyi duka dai" mika mata ledar tayi ita kuma Innar tasa hannu ta ɗauki apple guda ɗaya a cikin ledan "nagode wannan ma ya isa yi maza kije nasan suna nan suna jiran ki" Ficewa tayi tana musu saida safe. A wannan rana dai kusan kwanan zaune su Meenal sukayi suna hira, domin koda ta koma ta samu Ya Sa'ad ya siyo musu kazar har biyu dakwa² ya kawo musu harda su ice cream kamar yanda yayi alkawari, basu suka rintsa ba har saida Momi Hauwa ta gaji dajin motsin su tazo ta sanya su baccin dole. **washe gari ma da wuri Momi Hauwa tabar gidan dan ta samu kira na gaggawa daga asibity dan haka ta wuce bayan ta rarraba ma su Meelat ɗin aiki sannan ta doka musu warning cewar karsu yarda ta dawo ta cimma sun mata ɓarna a kitchen dan tana sane da abunda ya faru tsakanin su da hajiya, To suma dai basu damu ba domin tun jiyan sun gama tsara cewa yau ɗin gidan Ya Mashkur zasu in sungama da can kuma zasu wuce gidan su Maryam dan ta kirasu da safen akan tana kan hanyar dawowa daga KD. Da wurwuri suka gama gyaran gidan tsaf sannan sukayi wanka suka shirya da niyyar ficewa, saida suka fara shiga sashen Anty Murja suka gaisheta ita da Baba Adamu kafin suka wuce sasan Matan Malam suma suka miƙa musu nasu gaisuwar haka sauran sassan sirikan gidan saida suka zaga ko ina kafin suka yada zangon su a falon Baba Malam, to anan ɗin ma basu wani daɗe ba Meenat ɗin ta nemi izinin fita a wajen Malam kamar yanda ta saba akoda yaushe indai yana gida, to shima tunda yasan bawai yawon fitan ta cika ba shi yasa duk sanda ta nemi izinin fitan bai fiye hanata ba, dan haka yaudin ma fatan dawowa lafiya yayi musu da kuma gargaɗin su kula da kansu #2k ya cire ya basu da sunan ko zasuga wani abin a hanya. *** Kira Anty kiji ko Ya Mashkur yazo gida" cewar Meenat tana kallon Meelat, "kuma fa haka ne Allah yasa ma ya fita dan wallahi bana son muje gidan nan mu sameshi, dan wallahi yau duk abinda Nafi tamin ramawa zanyi" ta faɗa tana ciro wayar ta a jaka ta danna ma Aunty kira, wayar bata daɗe tana ringin ba Auntyn ta ɗauka, "Autar Aunty badai har kinyi kowata ba? ta fada muryarta cike da kewar ɗiyar tata, dariya Meelat ɗin tayi "Anty ina kwana" Lafiya lau, ya kwanan mutanen gidan? "Kowa lafiya lau Aunty dama na kirane in tambaya ko Ya mashkur ya shigo dan kinsan Meenat tace zamuje gidan yau" To bai dai riga ya zo nan ɗinba, kardai kuje gidan ku zauna kinji koh Auta dakun gaisheta kubar mata gidan ta, ni dan ma kunki jin ta nawane da bazakuje ba" Allah kuwa Anty bazamu daɗe ba zamu dawo bye" ta faɗa tana kashe wayar, hahaha tayi dariya tana kallon Meenat kinji Anty Allah bata son muje gidan nan kuma yau dai saidai tayi hakuri in mun dawo ma bata labarin yanda ta kaya. "Ai wallahi Nafisan nan munafuka ce inta ganka a cikin mutane sai tayi ta maka fara'a kamar da gaske ta dunga fadin wai bama son zuwa gidanta bayan daka taka kafarka a gidan take canza fuska to yau dai gamu nan tafe gareki uwar Aslam kuma wallahi yau sai munci mun ture koya kukace? " Ah kwarai kuwa Rabin rai fadi ki kara muda gidan Ya'yan mu ai dole mu sarara, duk wannan hirar da sukeyi suna kan tafiya ne sukeyin shi. Wow tubarkhallah masha Allah gaskiya gidan nan ya wuce da kwatar zuciyata," Moon ta fada tana ɗaura hannun ta a kirji idanuwan ta a waje tana mai karema gidan kallo, Gaskiya ba hassada nidai gidan nan yamin kyau ko a kasar waje sai haka, Gaskiya indai irin gidan nan za'a kaini wallahi na shirya ayimini aure na hakura da karatun bokon" Ta fada tana rungume Meenat cike da shauƙi, sororo Aishat ta tsaya tana kallon ikon Allah "ke Maimoon yaushe kika zama yar iska bani da labari dan ubanki daga ganin gida tun baki san meshi ba zaki wani ce kin shirya a miki aure! To shi mai gidan zaki aura kowa! " Tafaɗa cike da takaicin Moon ɗin, Inda kasan Meenat ta rufeta da duka haka takeji dan haka tayi kicin² da fuska dan abun yakai mata ko ina, ita ko Meelat inta kalli Moon saita koma ta maida kallon ta ga Moon sai kuma ta kyalkyale da dariya, "Ke wai wani dariyar iskanci ne wannan kikeyi kamar wata taɓaɓɓiya ke kuma in baki rufemin baki da batun gidan nan ba kuka wuce muka tafi duk sai na muku rashin mutunci wallahi mtws koba gida ba kawai daga ganin gida dan hauka sai ki fara warwarewa kina sambatu" Katseta Moon ɗin tayi da cewa "ke Meenat kiji tsoron Allah wallahi komin hassadar mutum yasan gidan nan ya gama haɗuwa, kinga fa yasin ko rantsuwa bazanyi ba nasan ginin mace gudane wannan gidan oh allah Allahumma Arzugni ya Allah" ta karasa addu'ar tana shafawa a fuskarta. Ganin haukar na Moon da Meelat ba karewa zaiyi ba yasa fuuuu tayi gaba cike da takaici karo taci da mutum shi ya fito daga gidan cikin hanzari ita kuma adai dai lokacin burinta shine taga tabar kofar gidan, kanta ne ya bugi kirjin shi a take wayar hannun shi ta faɗi sai akan kafarta, "waiyi Allah Baba Malam za'a fasa maka kaina ta faɗa tana dafe goshin ta daya daki kirjin shi tana shirin yin kuka chak yayi tsaye yana binta da kallo dan gaba daya gabban jikin shi yaji sun sake. "Ke karki sake kimin kuka a wajen nan" ya faɗa cikin muryar shi mai amo sosai ganin yanda tasa hannu tana mutsutsuka ido alamar gab take da fashewa da kuka. "To bakai bane kawai ina tafiya na kashiga gabana ba waya sani ma ko goshina ya fashe"ta fada tana turo baki, "ai da yike kinsan da dutse kikayi karo dazai fasa miki goshin koh, come on duƙa ki mikomin wayata da kika yar min kuma tana fashewa sai kin biyani" Dukawa tayi badan taso ba ta dauko wayar dake gefen kafarta ta mika mishi ba tareda ta ɗaga kai ta kalle shiba, karbar wayar yayi ya dudduba ta cikin sa'a dai wayar bata fashe ba, "Allah yasoki da sai kin koma gida kin faso asusunki kin gyaramin wayata, ba tareda tace komai ba ta ɗaga kafarta da niyyar tafiya cikin zuciyarta koh ba kalar kunkunin da batayi ba, daga kafarta yayi dai² da buɗe makeken gate ɗin gidan da akayi wata motar hilux ta fito daga cikin gidan ashe ba iya motar bane kadai harda waɗan nan sheggun karnukan nashi masu kama da zakuna a bayan motar fit haka karnukan nan da gudu kamar an korosu suna haushin su na rashin dalili, Lura da fitowar karnukan da yayi yasa shi juyawa cikin zafin nama da niyyar ya kamota dan yasan yanda take jin tsoron su, aiko juyawar da zaiyi sai jinta yayi a cikin jikin shi ta wani irin rukun kume shi kamar wacce ke shirin komawa cikin jikin shi tama kasa ihun data saba na neman ceto duk sanda ta gansu sai ma numfashin ta da take wani irin jan shi da kyar, jikin ta ko babu inda baya rawa sai faman kara kankame shi take, ga kuma karnukan da suka kewaye su sukayi tsaitaye suna dararo harshen su ganin uban gidan su tsaye a kofar gidan, Zuwan da tayi ta faɗa cikin jikin shi ba tareda tsammani ba yasa harta da fatar bakin shi yaji sun mishi wani irin nauyin daya kasa motsa su, Sai ma runtse idon shi da yayi yana jin yanda take kara shigewa jikin shi tana gogga mishi abubuwan dake kirjin ta waɗanda suke karasa jinin shi yana kara daskarewa, duk yanda yaso ya cireta a cikin jikin shi abun ya faskara dan gani take da zarar ya cireta a jikin shin to karnukan shi zai mikama ita suyi kalacin hantsi dan haka taki yarda ta fita a jikin shi, Da kyar ya samu ya buɗe bakin shi "ki nutsu mana baki ganin suma sun nutsu, sakeni ki gani bazasu miki komai ba" Girgiza kanta tayi alamun bazata sake shi ɗin ba karamin murmushi yayi "oh dadin kwanciyar kikeji a jikin nawa kenan da kike ta wani kara kankame ni" Dan ɗago kanta kaɗan tayi domin ta tantance shin wai a jikin nashi taken kamar yanda yace ɗin? wani irin kunya neya kamata dayasa fita daga cikin jikin nashi babu shiri tana duddukar dakai gefen shi ta koma bayan ta kama hannun shi ta rike gam, To kace musu su koma ciki nidai tsoron su nikeji ance suna cin naman mutane" Kur yama fuskarta yana kallon yanda take motsa labban ta tana magana a shagwaban ce, "Kaji" tace ganin yayi shiru kuma bai kora karnukan nashi zuwa gidan kamar yanda ta bukata ba sai ma zagaye su da karnukan sukeyi suna kaɗa bindi, kara manne wa da jikin shi tayi a sanda wata karya tazo dab da kafarta tayi kwance, "waiyo Allah dan Allah ka koreta ai kaga dai wallahi bada gangan nayi karo dakai har wayar ka ta faɗi ba Allah da nasan ma kana gidan nan da bance mu biyo tanan ba" Alama yayi ma karnukan dasu wuce cikin gidan ganin yanda har yanzun jikinta bai daina rawa ba, "ki natsu nace wai me yasa kin cika tsoro ne Ameenatu" Dago kanta tayi cike da mamaki take kallon shi dan tsawon rayuwarta bata taɓa sanin wai yasan sunan ta ba dan koda wasa bata taɓa jin ya kira sunan taba sai yau, "Kibar kallo na Malama" "To kaima ba tun ɗazun kaketa kallona kuma bance komai ba ta faɗa tana juyar da kanta gefe "ina su Moon? Ta fada a bayyane tana juyawa dan sai yanzun take tuna cewa ba ita kadai ta fito gida ba, can ta hango su a baya sunyi carko² duk da halin tsoron itama ba gama sakin ta yayi ba amma wallahi sun bata dariyar yanda sukayi tsamo² kamar waɗanda ruwa ya daka aiko sai ta kyalkyale da dariya, daga kai yayi shima yabi inda take kallo da ido dan yaga dalilin dariyar nata, ɗan murmushi yayi dan shima sun bashi dariyar saima girziza kai da yayi yana ci gaba da binta da kallon "Ya Sufyaan kalle su kagani dan Allah matsorata dasu kawai" "Ai garasu tunda nasu tsoron baisa sun rungume wani sun tada mishi tarxoma ba" Na'am tace tana kallon shi, shareta yayi "ina zaku ne ma wai? Ku me yasa bakwa gajiya da yawo ne? " Bafa yawo zamu ba gidan Ya Mashkur ɗin su Meelat zamuje' Kara sowa su Maimoon sukayi "Ina kwana" suka hada baki wajen mika gaisuwar su gareshi "lafiya" yace a takaice juyawa cikin gidan yayi ya fasa fitar da yayi niyya dan yarinyar nan ta rusa mishi tsari kuma. #karku manta dan Allah kusa Sister ɗina a addu'a, Allah ya baki lafiya Fauzy #Share and Comment #Ummiee~Zaria[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne gareku mutanen gidan uwata Mai Dambu, most especially Oum Khadija💙, NAgode sosai da comment *Surayyahms* *Binta Umar Abbale* Nagode da kulawa. ```Page11 Ba ita ta dena binshi da kallo ba har sai sanda ya kulle ta dena ganin shi tukun,doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana mai maida dubanta zuwaga su Moon katuwar hararar tabi dukan su dashi tana mai cewa "ai wallahi kulli yaci amanar koko daga yau daga yanzun ɗin nan nasan zamana daku, shine dan cin amana kuka barni a gaba wato ashe ma tsayuwa kukaci gaba dayi kuna gulma,yanzun fisabilillah da Ya Sarki baya wajen nan fa haka karnukan nan zasuyi partyn kalacin hantsi da nama a wajen nan,gaskiya dai Allah ya isana," Meelat na danne dariyar da takeyi kasa² gudun kar Meenal ta gani ta dangwalo ma kanta wani jangwal ɗin tace "haba kawata kema kinsan bazamu miki haka ba,kuma ma waye a cikin mu yayi zaton karnukan suna gidan nan tunda mun san ba anan ake ajiye suba,kuma karon ki da Sarki ai naga laifin kine tunda ke kika kai mishi karo kika gaure shi koh? ta karasa faɗa tana kallon su Aisha "eh wallahi mu bamu san kinyi nisa bama", " Yauwa kinji koh kuma ba gashi yauma Sarki ya kara cecenki a hannun karnukan shiba". "Dallah yimin shiru ai wallahi nasan dake ce sai kinyi fitsari a wando da shegen tsoron kin nan," cigaba da tafiya sukayi ba tareda wata a cikin su ta kara cewa komai ba dan sunga alamar mutuniyar nasu fa ta shaƙa da yawa. can dai Moon ta kasa daurewa tace "Bebs tsakanin ku da Allah gayen nan bai burgeku ba? kuma fa kamar mutumin da yasa aka rakamu gida jiya koh? duk da dai jiyan ba wani ƙare mishi kallo nayi ba dan Allah shike da gidan nan koh? Oh ya rabbi yau dai inga a sa'a na tashi shi yasa nike ta gane² nidai wallahi ya burgeni,ku baku gani ba duk tsayin Meenal fa wallahi nidai gani nayi kamar a iya kugun shi ta tsaya,oh Allah yau she za'a aurar damu ne kar maza masu kyau su gama karewa a barmu da kwarababbu masu kama da mata" Takalmin dake kafar Meenal ta cire ta fara bin Moon ɗin dashi tana son lallai saita bugeta,faɗi take cewa "badai kin zama yar iskaba zaman lagos ya lalata ki kema kin iskance,to yasin duk ki gama iskancin ki ki ɗauka cewa kinyi shuka a idon makarwa ne domin kamar a kunnen Hajiya maganar nan" ta karasa faɗa tana dafa Aisha da yau mamakin Moon itama yake ta neman kasheta wai Moon ce take ta maganganu haka kamar wata wacce tasha kwaya, so take tajawo musu bala'in daba iya kanta zai tsayaba dan dukan su zai shafa in yayyen su maza sukaji batun nan karma Iliya ɗan mai karfi yaji labari tasan shi kenan su kuma sun tashi aiki. Cike da nishaɗi Moon tace" wai ke ƴar Malam miye matsalar ki shikenan mutum inyaga abu ya burgeshi bazai faɗa ba,to wallahi nikam na fada na kara gidan damai gidan duk sun burgeni,Allah da ace na isa aurema cewa zanyi ina son shi to miye a ciki". Itafa tsakanin ta da Allah bata ɗauki hakan a bakin komai ba. "Innalillahi wa'ainnah ilaihir'raju'un kai jama'a yau kuma boyayyun aljannu ne ke shirin bayyana a jikin yarinyar nan ne koya? " Ke yana da mata fa" cewar Meelat dan ita Meenal ai nihin yau ne taga abunda ya isheta dan haka da ido kawai take bin Moon ɗin,. "And so sai me dan yana da mata sai inƙi son shi kome?ko akwai inda aka rubuta kar aso mai mata ne? Na rantse da Allah in bazaku zo mu tafi ba zanyi komawa ta gida ban son iskanci,ke dan makiyin ubanki har kike wani cewa miye dan kince kina son shi,to ai baida damuwa ko yanzun kina iya shiga ki faɗa mishi cewa kina son nashi,ai da nasan cewa iskancin Lagos jinin mutane yake bi dako ke bazan dunga sakar miki fuska ba iskancin banza mutumin dako dariya baya yi kullum fuskar shi a ɗaure shine zaki wani ce kina so tirr wallahi kin dai faɗi kasa ba nauyi wallahi,duk inda zai shiga fa haka zakiga yaran shi na binshi shine zaki wani ce kina so to sai kije kiyi ta kaya ai,shin zakuzo ku wuce ne ko tsayawa zakuci gaba dayi kuna kallon bakina". Easy mana Meenal wannan zafin da kika ɗauka ai yayi yawa miye laifin ta dan ta faɗi abunda ke cikin zuciyar ta,ke shike nan dan baya burgeki sai kice kar wata ta gani ta yaba kuma"cewar Meelat bayan ta rike hannun Meenal suna cigaba da tafiya. Wai halan ya kuke dashi ne Meenal? Aisha ta tambaya. Hahaha yan mata ai inda Meenal ce bata faɗa miki, bari dai mu karasa gidan ya Mashkur sai in baku labarin ko waye shi Sarki kenan Mai Zamani kuma shi ɗin ɗan adawar Kawata ne shi yasa nima baya burgeni, Ah ah wallahi bamu musha tun dazafin shi,dan daga ganin gidan nan kowa yasan bana karamin mutum bane gida kamar a turai aka kerashi aka ɗauko aka kawo nan aka ajiye, "wallahi nayi mamaki da naji wai shike da gidan nan ashe dai warrgajejen mai kuɗi ne"cewar Aisha. "Eh wallahi nima nayi mamaki" itama Moon ta faɗa,"to ai mun kawo gidan ku bari dai mu shiga ciki mu zauna kusha labari. A farfajiyar gidan suka haɗe da Ya Mashkur yana shirin shiga cikin motar shi cikin shirin fita,"ah ah yan matan Aunty ai nayi zaton ko kun fasa zuwa ne shi yasa nace bari in fice kunsan Aunty na jirana,karasawa kusa dashi sukayi suna gaidashi bayan ya amsa ne ya kara cewa "zaku jirani in dawo kafin ku wuce koh? Dan matar gidan ma bata nan amma nasan itama bazata jima ba,ku shiga daga ciki mana" Ya Mashkur meka ajiye mana? cewar Meelat. "Ai kunsan nidai ba mace bace balle kusa ran in shiga kitchen in muku girki kamar wani ɗan daudu Sarah na nan a ciki taji daku komai kuke bukata akwai a store you can serve your self." Ya karasa fada yana shigewa cikin motar shi gamida bata wuta yayin da mai gadin shi ya buɗe mishi gate ya fice, Huhhuu lallai yau zamuci karen mu babu babbaka a gidan nan tunda matar gidan bata nan"cewar Meelat cikin farin ciki dan ba karamin daɗin hakan taji ba dan tasan in matar gidan nanan bazata barsu su wala yanda suke soba dan karamin aikin tane ko ruwan gidan taga damar ta hanasu in sunyi magana tace fita unguwa zatayi. To yane Bebs let's get inside" ta faɗa tana musu jagora zuwa cikin gidan ko iso basu nema ba kai tsaye sunayin sallama suka shige cikin falon gidan. Sarah! Sarah!! Sarah kina ina yau gamu a gidan ku" da hanzari wacce Meenal ta kira da suna Sarah ta fito tana washe baki cike da jin daɗi tace "wai wasa ko gaske dan Allah ku ɗin ne dai nike gani kai gaskiya kun min bazata,ku zauna mana sannun ku da zuwa kai gaskiya naji dadin zuwan ku wallahi" haka ta dunga nan nan dasu cike da farin cikin ganin su, Kai amma dai halan kunsan Aunty Feenah bata nan shi yasa kuka zo,bari dai in kawo muku ruwa" Ke dallah wai miye haka sai wani rawar jiki kikeyi,kuma ai mu kinsan ko tana nan ko bata inta mela mana zuwa zamuyi gidan Ya Mashkur nefa mu ina ruwan mu da ita, kuma karki damu kanki yawon zamunci yau mukazo dan haka wallahi bamu shan ruwa domin dai ko Ya Mashkur bai bamu go ahead akan muci abunda muke soba kin san ci zamuyi balle kuma ya bamu" Bebs mai zaku sha? dan Allah ku saki jikin ku gidan Ya Mashkur mukazo ba baƙon waje ba". Cewar Meelat, "ke Auta nidai ku rufamin asiri kunsan in Anty ta dawo ni zatama faɗa baku ba imma wani abu zakiyi ku bari harta dawo dan Allah" cewar Sarah. Ke wallahi bazamu jira ba bari ma ki gani wai ina Sweat heart ɗina Aslam ya shige ne ko har yanzun bai tashi a bacci bane?",ina dalili mutum yazo gidan ɗan uwan shi a wani fara kafa mishi dokoki,to ni nabi takan dokar nata na wuce asa wuƙa a yanka ni.cewar Meelat a yayin data Mike zuwa neman Aslam ɗin dan tasan sau da yawa a gida uwar ke barin shi ta fice harkokin ta. Ai tareda maman shi suka fita" Sarah ta bata amsa tana juyawa zuwa cikin kitchen ɗin data fito, Zazzaune sukayi akan kujerun dake falon, "keni dan Allah ki bani labarin mai gidan yan gayun can na matsu inji waye shi" cewar Moon. " yau naga abunda yafi zare tsayi wannan wani irin jidali ne haka Maimoon ance miki mutum yana da mata amma still kin dage sai maganar shi kikeyi to in ma sonshi kike tun wuri gara ki kama kanki dan ba samun shi zakiyi ba,ke ina ke ina soja fisabilillah kifa kiyayeni" Cewar Aisha da tuntuni mamakin Moon ɗin yasa ta kasa cewa wani abu sai yanzun.a dai² lokacin ne kuma Sarah ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke da farantin data jero musu kayan motsa baki ta kawo ta ajiye musu, "Ga ruwa nan kusha" ta faɗa itama tana zama a gefen Meelat "maganar me kukeyi halan? Uhm yama sunan ki? Moon ta tambaya, "Sarah" ita kuma ta bata amsa "dan Allah in tambayeki tsakanin ki da Allah wancan gidan mai Ash and Black ɗin penti ɗin dasai an wuce kafin azo nan ki fadamin tsakanin ki da Allah in kikazo wuceshi bakyajin ina ma ace gidan nan ya zama naki,ina nufin ki zauna matsayin mata a gidan?". " Wai gidan Sarki kike nufi ? Wallahi³ kinji rantsuwar musulmi ko to gidan nan ko hasidin izah hasada bazai kushe shiba dan yasan bashi da makusa balle kuma irina mai addu'ar Allah ya bani makaman cin shi,ke gidan nan fa ya gama haɗewa yasin dan ma iya wajen kika gani bakiga cikin shiba dasai kinfi haka ruɗewa,bani labari mai ya faru kike tambaya akan gidan?" Hannu Moon ɗin ta mika ma Sarah "Salamu Alaikum mu gaisa ƴar uwa, kina ji koh waifa kawai dan munzo wucewa na tsaya koɗa kyan da gidan yamin shine fa duk suka wani hayayyako suna neman cinyeni ɗanye,dan Allah kin taba ganin me gidan?", Kai gani sosai ma gidan Sarki nefa,ga ƴar uwar shi a gefen ki kike neman wanda ya sanshi" ta faɗa tana mata nuni da Meenal dake cin doughnut da drink kamar bata san akan me suke magana ba. "Wai da gaske ɗan uwan sune? Ah ashe ma ɗan uwan mune", Ta faɗa tana kaima Meenal duka a cinya, "Zan cicci miki idan kika ƙara sani a maganar nan ƴar kalan dangi kawai a gidan ubanwa ya zama ɗan uwan naki ? Kinji kunya wallahi mtwss" Eh naji ba komai dai cigaba da bani labari Sarah, "Toni me zance dan nima ba wani sanin shi nayi ba kawai dai nasan matar shi kawar Aunty Feenah ce kuma ita ya gina ma gidan amma tace ita bazata taɓa barin lagos ta dawo Zaria da zama ba sai dai ya mata gini a Abuja ko Kaduna,iya abunda na sani kenan dan lokacin da sukayi rikicin har Aunty Feenah saida tasa baki amma tace wallahi bata dawowa sai dai ya saida gidan ya siya mata wani a inda ta keso,shi kuma yayi alwashin bazai siyar ba sai dai tayi ta zama a lagos ɗin gashi yanzun ita tana can shi kuma ya dawo KD da aiki kunsan dai dama yanda Aiki Soja yake. Tabdijan to ita bata tsoron ya ƙara wani auren a nan ne yasa matar a cikin gidan? Aisha ta tambaya tana jinjina kai, Oho mata" ta faɗa cikin rashin damuwa. Dan Allah fadamin ya zumuncin su yake dasu Meenal? cewar Moon, "wai ba gata nan ba ki tambayeta mana" No ai kema kinsan bazata fadaba tunda batayi niyya ba. "Ke bakiga daga gidan su Ya Sufyaan ɗin sai nasu Meenal ba to ai Dangi ɗaya suke yayan yaya da kani ne iyayen su,ina nufin kakan su Meenal da nasu Ya Sufyaan ɗin. Ok yanzun na fahimta" cewar Moon ɗin.wai ke Meenat me yasa a komai sai kinyi zari ne kin tasa abu a gaba kamar ke kaɗai aka kawoma sai faman ci kike", Oh to bari inƙi ci in tsaya biye muku da banzan surutun ku" kallon Sarah tayi "ke yarinya gidan nan baku da kaza ne naga sai kayan fulawa kika jibgo mana salan muci mu kunbura irin matar gidan,muje kitchen ɗin ai wallahi an bamu go ahead muci duk abunda muke muradi, Atakaice dai a wannan gidan sukayi kusan rabin wunin su bayan sun shiga kitchen sun dafa abunda suke so sunci sunyi nak harda zuguri ma sunyi dan mai gidan ya kira ya faɗa musu bazai samu damar dawowa da wuri ba ya shiga cikin gari,gashi kuma daɗin daɗawa har sukaci suka suɗe matar gidan bata dawo ba dan dama ita haka take wuyar ta dai tasa kafa tabar gidan tofa sai sanda Allah yayi dawowar ta.basu tashi barin gidan ba saida sukayi sallar azahar sannan sukama Sarah sallama wacce ta rako su har bakin gate ɗin gidan kafin ta juya su kuma sukayi gaba. ****** Bari mu waiwaya gefen Sarki muji dalilin daya mai dashi cikin gidan shi bayan ya fito, Bayan shigar shi cikin gidan kai tsaye falon nashi dake buɗe ya wuce ba tareda ya kula abokin shi dake zaune a falon wanda ganin shigowar nashi yasa yake tambayar shi "Sarki ya haka bakaje ɗin bane kuma? Da alama dai fitan da yayi daga gidan wani wajen yayi niyyar zuwa, Ba tareda ya iya buɗe baki yayi magana ya amsa ma mai tambayar dakai kawai ya wuce shi yana mai haurawa zuwa sama inda ɗakunan gidan suke,a daddafe yaci gaba da haurawa hannun shi guda akan marar shi yana tallabe da ita kamar mai tsoron kar marar ta fita daga jikin shi,koda ya kai kanshi zuwa ɗakin baccin nashi wajen window ya nufa ɗan Jan labulen yayi kaɗan wanda hakan ya bashi damar kallon su Meenat kai tsaye daga nan inda yake tsaye,cigaba da kallon su yayi duk da bawai yanajin abinda suke cewa bane har sai da suka wuce kafin ya koma yayi ruf da ciki akan gadon ɗakin daga ganin shi dai kasan bayajin daɗin kwanciyar a dole yayi ta duba da yanda yaketa faman juye ² akan gadon kamar mai nakuda. Ganin dai abun bana karau bane yasa ya mike a dudduƙe yakai kanshi bakin mirror wani magani dake ajiye a wajen haɗewa da ruwa ya ɗauka yasha sannan ya shige bayi ya samu ya watso ruwa kafin ya dawo kan gadon yaci gaba da kwanciya. *Shin wai wanene Sufyaan inkiya Sarki Mai Zamani ma?* Nasan kuna son sanin wanene shi kuma. A baya munyi magana akan ahalin Malam sai dai bamuyi magana akan yan uwan shi dake kewaye dashi a cikin unguwan ba,dan in baku manta ba na faɗa muku yawancin mazauna unguwar ahali ɗaya ne, Bari mu fara da gidan su Sufyaan Sarki sauran a hankali duk zasu fito a cikin labarin. Gidan Malam Ladan shine inkiyar sunan da akeyiwa gidan nasu Sufyaan kasancewar Kakan su Sufyaan ɗin shine Babban ladanin masallacin unguwar tun fil'azal ,kamar kuma yanda na faɗa a baya suma dai gidan su na malamai ne Zumunci ne mai karfi tsakanin su da gidan Malam domin dai dukan su asalin su ɗaya iyayen su uwa ɗaya uba ɗaya suke dan haka ko bayan shuɗewar iyayen su sukaci gaba da rike zumuncin su har ya zuwa yanzun,shima nan ɗin babban gidan ne sai dai sabanin gidan Malam nan ɗin mazajen gidan daga mai mace biyu ne sai sama da haka domin ko shi Mahaifin Sufyaan ɗin mai suna Sulaiman matan shi hudu ne kuma Sufyaan ɗin shine Babban ɗan shi namiji kafin shi akwai mata amma tunda matayen suna gidajen auren su hakan yasa gaba ɗaya girman ya koma kanshi, Sai dai kuma matan gidan saɓanin gidan Malam sukam sun kasance wasu irin mata masu zafin kishi ko wacce a cikin su cike take da kishin ƴar uwarta idan ka cire uwar gidan Malam ɗin Mai suna Hajara wacce ahalin gidan ke kira da uwar gida,dan tana bakin kokarin ta wajen ganin kishin matan gidan bai raba tsakanin yaran gidan ba kuma duk yanda kishiyoyi dama facalolin nata ke haukar su bata taɓa daga kai ta kalle su dan bata lokacin su,to suma dai iskancin nasu a gefe sukeyi basu fiye yin mata hawan ƙawara ba. Sufyaan ya taso ne a matsayin natsatstsen yaro ta yanda har wasu iyayen sukan bama nasu yaran misali dashi,yaro ne mai tarin ilimin boko dana addini saboda hakan yasa baban shi jawo shi a jikin shi sosai ya cusa shi cikin har kokin kasuwan cin shi Allah da ikon shi kuma sai gashi ya zama mai nasibi domin bayan shigar dashi cikin harkokin nasu sai sukayi ta samun cigaba sosai kasancewar dama harkar kasuwan cin ya karanta kuma yana son kasuwancin sosai,wannan cigaba daya samu yasan ya Baban shi akoda yaushe yake ƙara alfahari dashi sai dai abunda bai saniba shine matan shi guda biyu ba karamin bakin ciki sukeji da faruwar hakan ba, domin duk cikin su babu wacce Allah yama arzikin samun ɗa namiji sai mace, dan haka suka haɗa hannu wajen lallai sai sunga bayan Sufyaan dama mahaifiyar shi data zame musu ciwon ido dan batun yauba suke ta Neman yanda zasuyi da ita sai dai tako ina tafi karfin su kasancewar ta fito daga cikin gidan sarauta kuma sunan Baban ta aka sanyama Sufyaan ɗin dan haka suke kiran shi da Sarki. Kun san yan magana na cewa tsafi gaskiyar mai shi domin dai da kaɗan² abubuwa suka fara kwabewa ta fannin Sufyaan da farko gaba daya suka cire zuciyar shi akan harkokin Mahaifin nashi dama nashin gaba daya,dan kwata² ya dena zuwa kasuwa zai shirya ya fice daga gidan amma kuma ba can ɗin ya nufa ba,da wannan damar sukayi amfani suka dunga kai sukar shi a wajen Mahaifin shi, Mahaifiyar shice ta fara lura da canjin da yayi dan ba haka ta saba ganin ɗan nata ba dan haka ta Mike tsaye wajen sanya shi cikin addu'o'in ta,Allah kuma yaji kanta dan abun bai daɗe yana tasiri a jikin shiba ya sake shi dan har ya koma kan kasuwancin shi,ganin cewa basu dace ta wannan fannin bane yasa suka canza shiri wannan karan so suke bama iyayen shi kadai ba harta sauran jama'ar dake bama yaran su misali dashi su tsine mishi.a hankali sai ga Sufyaan ya fara shaye² tun yanayi a boye har Allah yasa ranar Mahaifiyar shi ta ganshi,tsabar tashin hankali suma ne kawai ya rage batayi ba dan wallahi da wani ne ya faɗa mata cewa zatayi sharri akema Sarki dan iya sanin ta tasan ɗanta ko warin sigari baya so balle kuma azo ga batun shanta sai gashi yau Sarki ne da shan kayan maye Innalillahi wa'ainnah ilaihir'raju'un me yake shirin faruwa da ahalin ta,shine abunda bakinta ya iya furtawa dan haka ko Mahaifin shi bata bari ya sani ba ta kira ɗan uwanta ta zayyana mishi abunda yake faruwa,washe gari yasata ta tura mishi Sufyaan ɗin can inda yake zaune a Abuja sukayi ta neman taimako da kuma addu'ar uwa Allah yasa wannan karan ma suka karya kadarin ba wanda yaji koya gani,bayan komai ya lafane ɗan uwan nata ya bata shawara a kan yana ganin gara Sarki yabar garin dan yana tsoron abinda zai faru zuwa gaba kuma dan in wadanda suke mishi hakan sunga basuga abunda suke tsammani ba yana tsoron mugun abunda zasu aikata mishi a gaba,kuma shi kawun Sufyaan ɗin shine yama Baban Sufyaan ɗin bayani akan halin da ake ciki da kuma shawarar daya kawo na barin Sufyaan ɗin garin gaba ɗaya,babu bata lokaci ya amince domin koba komai bazai so rayuwar ɗanshi babba ta lalace ba.dan haka daga wannan lokacin rayuwar Sufyaan ta koma Abuja inda yaci gaba da karatun shi daga bayane da taimakon kawu yusif ya nemi aikin soja Allah kuma yasa ya samu a yanzun haka shiɗin sojan ruwa ne, yanayin aikin shine ya kaishi Lagos inda Allah ya haɗa shi da uban gida mai mutunci Brig,Gen,Abubakar ya rike Sufyaan kamar ɗanshi saboda kwazon shi a wajen aiki wannan dalilin ne yasa Sufyaan komawa gidan Brig da zama ,ya taka matakan nasara da dama sanadiyyar General dan yanda ya ɗauke shi kamar ɗa haka shima yake mishi kallon uba, Yaran Brig su hudu Allah ya bashi 3 mata 1 namiji wanda shine karamin cikin su babbar ƴar shi mace ba a 9ja take karatu ba dan haka bata san Sufyaan ba sai dai kullum tana jin sunan shi sai kuma a hoto,sai dai kuma Allah da ikon shi tun ranar farko da taga hoton shi taji bata da gwani sai shi,dan haka tun tana can tasa baban ta ya tura mata Number ɗin shi ta fara yaɗa manufofin ta akan shi,kunsan yan magana na cewa da zafi² akan daki karfe to hakika kusan hakan ne ya faru domin dai saida tayi duk yanda tayi wajen ganin ta yaɗa manufofin ta akan shi ya zamana harta da iyayen ta sun san ra'ayin ta akan Sufyaan ɗin,duk da ilimin addinin da Sufyaan ke dashi shiɗin mutum ne mai son wayayyar mace ƴar gayun data san kanta wacce bazaiji nauyin nunata a duk inda hakan ta kama ba,sai gashi a ganin shi hakan yazo mishi cikin sauki dan haka bazancen Jan aji tuni ya bada kai sukaci gaba daba fulawa ruwa har zuwa sanda Fatima ta dawo, ba'a dauki wani dogon lokaci ba aka fara maganar auren su. Zuwa wannan lokacin shima Sufyaan ɗin a hankali ya fara taka manyan matsayi ta fannin aikin shi ga kuma kasuwancin shi da yake gudanarwa a gefe guda dan haka ba ƙaramin shiri yama bikin nashi ba,sanin da yama Teemah na rashin son zaman cikin barikin nasu yasa dole ya nemi wani gida a wajen barikin mai kyau madai'daici na zaman mace ɗaya ya siya dan su zauna a can subar barikin saboda tsabar yanda yasan Rabin ran nashi ta tsani zaman barikin ne yasa ta bijire wajen yin karatu a 9ja, sosai ya gyara gidan nashi a kokarin shi na ganin ya faranta ran masoyiyar nashi dan gaskiya ba so na wasa yake mata ba sosai ya sanyata a zuciyar shi da alama dai inba Teemah ba sai rijiya. A can gidan su a Zaria kuma duniya sabuwa wajen kishiyoyin uwar shi domin su rashin shi a gari gaba ta kaisu koba komai bazasuci gaba da ganin shi rayukan su tana ɓaci ba,dan su a zaton su aikin sune yaci shi yasa gudun abun kunya yasa uwar shi tasa shi barin garin dan haka suka koma wajen da suke zuwa akan a dan kwafar musu dashi acan karma ya ƙara marmarin dawowa gidan ma, rashin dawowar nashi yasa suke zaton aikin sune yaci dan haka sukaci gaba da sha'anin su, Sai dai abunda basu sani ba shine a yanzun yafi jin daɗin rayuwar shi a inda yake fiye da c nan ɗin sannan duk sanda iyayen shi suka so ganin shi sukan kai mishi ziyara haka shima duk sanda aiki ya kawo shi arewa yakan zo yaga iyayen nashi sai dai maimakon yazo ido na ganin ido sai ya maida zuwan nashi na dare,har sai yazo ma yayi abunda zaiyi ya wuce wani bai san shine ba, Iyayen shi maza sun san meke faruwa sai dai Malam Babba ya kwabi kowa akan yin maganar da mai ɗakin shi, Sai gashi kwatsam bayan wasu shekaru maganar auren Sufyaan ɗin ya taso da yike bikin a can lagos ɗin za'ayi ba anan ba dan haka basu san wacece zai aura ba shi yasa ba wacce ta damu, a ganin su ai gara yayi auren ma ya dauwa ma acan ko ba komai sun san abinda sukayi na kafeshi a can,(a zaton su fa). Su Malam ne suka niƙa gari har lagos wajen Neman aure da duk wani al'adar da ake gabatarwa na neman aure, Wata ɗaya akasa yayin da Mahaifiyar shi da yan uwanta sukayi tsaye wajen ganin sun haɗa mishi kayan aure na fita kunya,sai dai matsala na farko daya fara kunno kai kafin auren shine batun kayan lefe duk da yan uwanta sun yaba kwarai amma fa kawayen Teemahn yan gayu kuma yan karya irin ta suna zuwa suka fara kushe kayan a cewar su kayan ba ajinta bane a kokarin su nason ganin sun kaskantar da Sufyaan ɗin dan tun abun bai bata haushi ba har saida ranta ya bacci ,dan batun yau ba suke kokarin nuna mata cewar tafi karfin Sufyaan ɗin ita matar manya ce ina laifin ma in auren zatayi ta samu wanda ya zarce Mahaifin ta arziki amma abun takaici ta kare a yaron Baban ta,sun daiyi maganganu iya iyawar su wajen ganin sun ɗaurata akan keken ɓera amma dai tasirin da son shi yayi a zuciyar ta yasa basu samu daman yin galaba a kanta ba. Koda bikin ya rage saura sati uku da ta mishi magana akan gidan da zasu zauna saboda kayan ta da za'a kai gidan saboda har lokacin bai kaita gidan daya siyaba saboda ayyukan su da suka ɗan sha mishi kai a lokacin key ɗin gidan ya bata sannan yace mata duk sanda ta shirya zuwa tama yaron shi Ibrahim kwaro magana zai kaita gidan. A wannan ranar bayan ya wuce gidan shi dake barikin inda ya koma da zama a yanzun ne kasancewar zai zama sirikin gidan na General yasa ya tattara kayan shi ya koma nashi gidan dan ba karamin kunyan su yakeji ba a matsayin su na surukan shi, a daren taso takaima Anty Rahma (Mahaifiyar ta) makullin koda taje kai matan bata sameta a ɗakin ta ba dan haka ta wuce gefen Brig dan tasan tana can ɗin dan yana gida a lokacin,koda ta isa ta iske su suna ta magana ne akan auren nata,ba kunya ta zauna suka cigaba da tsara abubuwan su na yanda suke son bikin ya kasance daga karshe ne ta gabatar musu da key ɗin gidan da Sufyaan ɗin ya bata,amsar keys ɗin Brig yayi daga hannun ta a cikin daren kuma ya kira Sufyaan ɗin akan yazo a daren yana son ganin shi su haɗu a wani waje a cikin barikin akwai inda zai raka shi,babu bata lokaci yaje ya same shi suka tafi zuwa inda yace zai mishi rakiya ɗin basu zame ko ina ba sai wata unguwa na manyan mutane masu daraja,a zaton Sufyaan ko wani zasu ganin a unguwar sai dai kuma bayan sun faka a inda Brigadier general ya bukaci ya faka ga mamakin shi sai yaga kai tsaye cikin gidan suke shige ba tareda neman iso ko an basu izinin shiga ba,bayan sun zauna ne brig da kanshi ya dauko musu lemu mai sanyi duk da yanda yaga Sufyaan ɗin yana kallon gidan baibi ta kanshi ba dan gaskiya dai ancicci mutuncin Nairori a wannan gidan dan an dandaƙema kuɗaɗe kai wallahi,kai jama'a masu layya nacin nama ayi ta gine² kamar baza'a mace ba. haka yaci gaba da Jan shi da hira akan aikin su,kafin daga karshe ya gabatar ma Sufyaan ɗin da keys ɗin gidan a matsayin gift ɗin shi na aure wanda shi brig ɗin a matsayin shi na Mahaifi ya mishi,abun yaxoma Sufyaan ɗin a bazata sannan kuma general ya toshe duk wata kafa da Sufyaan ɗin zaiki amsar kyautar nashi dan daga karshe da yaga yana son turjewa akan bazai amshi kyautar ba Malam ya kira yake faɗa mishi cewa Sufyaan ya nuna mishi cewa bai ɗaukeshi uba ba, Hakika Malam ya jinjina karamci irin na Brigadier general dan haka ya taya Sufyaan ɗin godiya bayan brig ya roki Alfarma kan yana son maganar gidan ya tsaya a tsakanin su kawai ba tareda kowa ya sani ba. Wannan abu ba karamin kima ya ƙaramar General a idon Malam dama shi kanshi Sufyaan ɗin ba dan haka Malam ya kara yima Sufyaan nasiha akan ya rike Teemah da amana kodan Albarkacin iyayen ta. Basu bar gidan ba sai da ya damka mishi duk takardun gidan sannan ya mishi jagora suka zagaya gidan sak yanda Teemah ke fatan gidan ta ya kasance haka uban nata yasa aka tsara mishi gidan saboda ya faranta mata. Kar a manta aci gaba da sharing please. #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page12 Anyi auren Sufyaan da Amaryar shi Rabin ran shi Teemah lafiya, kasancewar auren na soyayya yasa suke dage wajen cinye soyayyar nasu ba kama hannun yaro kamar su mai da juna cikin cikin su haka sukeji dan tun bayan auren da sati ɗaya suka ketare kasa zuwa honey moon, Sai dai kuma ba anan gizo ke sakar ba domin tun daga dawowar su chakwakiyar ya fara. dafarko yawan zuwan gidan da kawayen ta sukeyi shine abu na farko daya fara ɓata mishi rai sai dai baiyi saurin yin magana ba a zaton shi ai dama in amarya tana sabuwa mutane kanyi zaryar zuwa kawo mata ziyara,Sai dai kawayen ta maida gidan sukayi kamar wani joint na jin daɗin su nan zasu zo ko wacce taci abunda take so tayi abinda take so,har ya zamana tun abun bai ɗaɗashi da kasa ba har ranshi ya fara ɓaci da hakan,dan basujin ɗar ko shakkar yin ma gidan nashi zuwan duku² sau da yawa inya dawo daga masallaci yakan wuce wajen training idan ya dawo kuma yakan so ya kusanci iyalin shi ta bashi energy yanda zai samu karfin fita,sai dai abun haushi sai sanda wasa yayi wasa yan wasu sun dau harama duka kan duka kowa nakai naushi kawai sai su farajin karar karar rawa inko Allah yasa yayi mantuwa bai kulle kofar falon ba haka zasu shigo kai tsaye in basu samu kowa a falon ba babu wani dogon tunani kawai tafiya zasuyi zuwa ɗakin ta,hakan yasha faruwa ba sau ɗaya ko sau biyu ba sannan abun haushin da zarar taji motsin su tofa shike nan wasa ya kare dan bazata bari ya sauke tashin hankalin daya ɗibo ba in yayi magana kuma sai tace,wai ita kunya take karsu gane yayi wasan danbe da ita. da abun yakai mishi ko ina yayi magana ba karamin rikici suka so suyi ba,domin dai ita Teemah tun tashin ta a gidan su bame takura mata abunda take so shi akeyi mata sai gashi daga aure zai fara tsiro mata da wani tsirfa. Ganin tadau zafi yasa ya koma rarrashin ta dan baya ƙaunar abinda zai taɓa mishi ran gimbiyar tashi dan haka a daren maganar ta wuce,ya akayi ya ba'ayi ba dai oho domin a lokacin kawayen nata sun ɗan rage zuwa gidan dan ya zuba ido yaga ko zata musu magana akan zuwan mishi gida da sassafe amma baiga tayi hakan ba dan haka yama mai gadin gidan kashedi akan karya kara barin su suna zuwa mishi gida da sassafe, Rashin zuwan kawayen nata yasa ta tsiro da yawan fita unguwa naba gaira babu dalili domin ko a kullum ba fashi sai ta fita ko yana gari ko baya gari ko yana gida ko bashi haka zatasa kafa ta tsallake shi tayi tafiyar ta wajen yawo dan har lokacin bata fara aiki ba,wani lokacin ma ko yana gidan bazai san ta ficeba sai in ya nemeta bai sameta ba,ga kuma wani hali data tsiro na rashin gyaran muhalli abinda bai sani ba shine dama kawayen nata sune ke ɗan kan kanta mata gidan in sunzo dan ita kam shegen san jikin ta bai barin ta ko tsinke ta ɗage to yanzun sun dena zuwa dan haka a hankali gidan ya fara sukurkucewa, kullum Kafin ya tafi aiki shike kimtsa gidan fess tun daga kan shara wanke² ita gimbiyar nacan kwance tana bacci sai dai inta gaji da baccin inta tashi ta fesa wanka ta feffesa turare a kuma fente fuska da kwalliya wannan kam ba fashi indai batun gyaran jikine amma ɗakin ta in ka shiga Sam bashi da daɗin kallo dan yanda take watsa kaya ko ina,shine ma inya shigo yake daurewa ya gyara mata ya ware na wanki ya fitar sannan ya gyara mata ɗaki duk abunda yake mata bai ɗauke shi a matsayin komai ba sai kyauta tawa tsabar son da yake mata yasa ya kasa gane cewa hakan bai dace ba domin shidai a rayuwar shi bai ƙaunar abinda zai mata ta ɓata rai harta raba shimfiɗa dashi dan ba karamin daɗin ta yakeji ta wannan fannin ba gashi kuma Allah yasa itama ɗin jaruma ce, Kun san mu mata bamu iya samun waje ba haka nan ma mukan tsula tsiya muyita wulakanci balle kuma in an bamu dama, Dan haka gaba ɗaya ganin cewa ai mijinta yana son ta dan gashi ko laifi ta aikata mishi da zarar ta ɓata rai dole yake neman sulhu yasanya tasa kafa ta fara kwallo da duk wasu hakkoki daya kamata macen aure ta kiyaye su akanta,suko kawayenta dama ba ƙaramin bakin cikin auren data rigasu yi sukeyi ba dan haka ko sunga tayi ba dai² ba babu mai kwaɓa mata a cikin su, Abunda ta sani kawai in gari ya waye tayi wanka ta ɓata lokaci wajen shiryawa inta gama ta fito in Sarki yayi girki kafin ya fita taci in bai girka ba kuma zayi order ɗin abinda take muraɗi taci sannan itama ta kama gaban ta,domin dai a dole Sarki ya koyi girke² dan shi Allah yayishi mutum ne shi mai tsagina gini bako ina yake iyacin abinci ba,yanzun kuma da yake auren Teemah bazai yuwu yaje gidan brig gen cin abinci ba dan haka ya dage da koyan girke² kala² a kokarin shi na ganin ya faranta ma Rabin ran shi dan su zauna lafiya,to ita kuma hakan data gani yasa ta ƙara sakan kancewa da irin son da yake mata dan gaba ɗaya bata shiga kitchen bawai kuma dan bata iya girkin bane NO tsabar gayune a ganin ta tafi karfin shiga kitchen sannan bata yarda da batun ɗaukar mai aiki ba saboda kishin mijin ta da takeyi,in Sarki baya gari kannin ta take daukowa su dawo gidan da zama har ya dawo kuma su zasuci gaba da kula da gidan da duk wani abu daya kamata.sun share shekaru biyu da aure amma babu wani alama na bullowar ciki daga jikin ta sannan har zuwa wannan lokacin a halayyar ta babu abunda ya canza sai ma wadanda suka ƙaru domin ta fara aiki dan haka ta kara haɗuwa da kawaye yan gayun da sukayi dai² da ra'ayin ta saukin ɗaya dai yasamu yanzun shine ɗaya daga cikin yaran shi mai suna Ibrahim kwaro shine yake kula da tsaftar cikin gidan dama girkin abincin da zasuci abinda ya shafi tsakar gidan kuma sauran yaran nashi suke kula dashi amma har kwanan gobe shike gyara ɗakin shi ya kuma gyara mata nata a matsayin ta na ƴar gaban goshi,har zuwa wannan lokacin kuma ko sau ɗaya bata taɓa taka kafarta a Zaria da sunan taje taga asalin shiba duk sanda bukatar hakan ta taso to saita kirkiri wani babban dalilin dazai katangeta da zuwa sai dai yaje shi kaɗai ya dawo,sannan koda yan uwan shine suka zo Mahaifiyar shi ko cikin kanne ko yayyen shi babu ruwan ta dasu sha'anin gaban ta shi zatayi in mutum yaji yunwa ne dole ya nemi hanyar kitchen macen da bata dafama mijinta bane zata dafa dan wani baƙo. A irin hakan ne wata rana kanwar Sufyaan ɗin mai suna Hindatu sukazo garin ita da mijin ta kasancewar aikine ya kawo mijin nata garin hakan yasa ta rokeshi arzikin ya barta taje gidan ɗan uwan ta taɗan kwana biyu maimakon zaman dazata dungayi koda yaushe a cikin ɗakin hotel ɗin da sukayi masauki,hakika kam tayi zuwa a sa'a kuma tayi kyawawan ganin da in a labarine tuni zatayi watsi dasu wajen cewa karya ne domin zaman auren da ake gudanarwa tsakanin Sarki da matar shi ko gidan turawa albarkha domin ita dai a kwana biyu da tayi a gidan sau ɗaya ne sukayi ido biyu da matar gidan tun ranar data iso gidan suka gaisa ta shige ciki ta barta da ɗan uwanta suna gaisawa bata karajin motsin taba sai dai in taji yunwa ta shiga kitchen ta dafa abunda take muradi taci dan Ibrahim kwaro sau ɗaya yake musu girki a rana,ta dai naɗi abubuwa ma'ishi waɗanda Allah² take ta koma Arewa dan taje ta fesama Uwar gida labarin halin da gidan Sarki yake ciki,wannan irin kwamacala har ina. Bayan mijinta ya gama abunda ya kawo shi sun koma bata tsaya ɓata lokaci ba taje ta zayyana ma uwar su irin mulkin da Teemah keyi a gidan ɗanta harma da ƙari (lol su dangin miji an iya sharri), Hankalin Uwar gida ya tashi matuka tsoron ta shine Allah yasa bawai ɗanta ya faɗa komar mata marasa tsoron Allah bane dan haka a satin ta kirashi akan duk abinda yakeyi ya bari ya tattaro shida mai ɗakin shi su taho Zaria karshen wata dan akwai bikin da za'ayi dama a nan cikin gidan ta kara da cewa bata bukatar jin wani uzuri umarni ta bashi dole yazo. A sanda ya samu kiran ba karamin tashin hankali ya shiga ba domin yana kan shirye²n fita kasar wajene zuwa hutawa shida rabin ranshi wacce ita Teemah ce ta bukaci fitar a cewar ta ta gaji da zaman 9ja tana so su fita su ɗan sarara,aiko ba karamin tashin hankali sukayi ba a lokacin da yazo mata da batun tafiyar nasu,dan amsa na farko data bashi shine cewa ai yana sane da batun fitan su dan haka ba wani Zaria da zata kokari take ta rarrage wasu aiyuka a office kafin su tafi yayi zaton zai shawo kanta da sauki sai dai ina a kullum kawayen ta cikin zugata suke akan ba itaba koshi ta nemi yanda zata hanashi shigema yan uwan shi da yakeyi dan idan yana zuwa gunsu tabbas wata rana bashi daya zai dawo ba sai dai ta ga sun haɗoshi da wata matar ita bata san halin mazan Arewa bane dason tara mata barin ma shi da Baban shi yake da mata 4 dan haka ta kiyaye. To dai haka da kyar da siɗin goshi ya samu ya lallasheta suka tafi kasancewar a lokacin bai mallaki muhallin shiba sai ɗakin shi na samar taka daya gyara wanda yakan sauka a cikin shi lokaci lokaci yasa koda suka isa dole sai sashin uwar gida aka sauketa duk da gidan ya kasance ginin zamani kuma an kawata shi domin dai kaf matan gidan babu wacce side ɗinta yakai na uwar gida tsaruwa,amma hakan bai burge ƴar gaban goshi ba,sai ma fargaban ta daya ƙaru a sanda aka dunga gabatar mata da jama'ar gidan bata ƙara tantance zancen kawayenta da suke faɗa mata cewar mazan Arewa na tara mata ba sai zuwan ta Zaria domin bayan nan gidan su Sufyaan ɗin da aka dunga nun nuna mata wacce kishiyar wacce sauran gidajen ma dai duk kanwar ja ce dan haka ta tsorata sosai dan haka taci alwashin dakushe mijinta daga zuwa garin sauran yan uwan shi dake mata jele a gidanta ma duk zatayi maganin su ne,tun fitan da tayi na ranar da uwar gida tasa a mata jagora zuwa gaishe² bata yarda ta kara zuwa ko ina ba koda yaushe tana cikin ɗakin da aka sauke ta dan harta uwar mijin nata sai dai inta so ganin ta ko magana da ita ta leko ɗakin ko tasa a kira mata ita sai ta gama Jan aji kafin ta fito taji dalilin kiranta da akayi bata komai sai dai taci tayi bacci domin abincin gidan ma bata sakin jikinta taci sai dai ta kira Sarki ta faɗa mishi abunda take so shi kuma jikina rawa yaka zai kawo mata. A wannan kwanaki kam Uwar gida tayi ganin abubuwa kala² a kuma lokacin ne ta kuduri aniyar dole ne Sarki ya kara aure dan bazata yarda Teemah taci gaba da juya mata yaro sai abinda taso zaiyi ba dan taga alamar a yanzun in ta matsa tace ya saketa tofa kunya zai bata dan bazai saketa ɗin ba dan haka zatabi komai a hankali. To dai kamar Teemah tasan abinda uwar gida take shiryawa dan suna komawa itama bata samu sa'ida ba saida ta zayyane ma kawayen ta abinda ta tarar a Zaria su kuma suka ƙara ɗaurata a hanya dan haka tun daga wannan zuwan gaba ɗaya Sufyaan ya dauke kafa da zuwa Zaria koda aiki ya kaishi Arewa baya iya zuwa kullum in yayi waya dasu zaiyi ta cewa yana tafe amma shiru kakeji.a cikin shekaru 3 da watanni da auren sune Teemah ta samu ciki bisaga shawarar kawayen ta domin dama tun farko su suka ɗaurata akan karta yarda tayi ciki da wuri dan da zarar ta samu ciki tofa tsufa ne zai fara ƙonƙosa mata ƙofa kuma son da Sarki yake mata raguwa zaiyi,ita kuma a duniya tana taƙama da kuma alfahari da irin son da Sarki ke mata bazata so wani abu yasa wannan soyayyar raguwa ko kuma ace son ya gushe ba,a yanzun data tabbatar ma kanta da cewa Sarki nata ne ita kaɗai ga kuma matsayi da tarin arzikin daya tara shine suka bata shawara akan ta haihu yanda komai zai mata daga ita sai ya'yan ta. Lokacin data samu ciki ba ƙaramin murna Sarki yayi ba a ranar duk wani makusan cinshi ya shaida hakan lokacin da watar haihuwar ta kama kasar suka bari dan acewar ta bazata iya haihuwa a 9ja ba duk da cewa tun kafin cikin nata ya tsafa Uwar gida tamishi magana akan ya dawo da ita Zaria inta haihu ayi suna a can amma ƴar gaban goshi ta kekashe kasa cewa bata zuwa dole sai hakuri yaba uwar gida,ɗiya mace ta haifa suka sanya mata sunan uwar Teemah Ramlat,a jejjere dai sai da tayi aihuwa uku duka kuma Allah ya bata duk da batayi farin ciki da hakan ba dan Allah ya sani ita yara maza taso samu ta yanda zata samu kwanciyar hankali cewa zuwa gaba komai na Sarki ita zatayi iko dashi ba yan uwan shi ba,dan zuwa lokacin a babu yanda zatayi dole tanaji tana gani Sarki ke tafiya Zaria yaje yayi kwanaki duk da tayi yanda tayi ta hana yan uwan shi zuwa gidan Amma hankalin ta bai kwanta ba kullum tsoron ta karsu haɗashi da wata a can ɗin duk da tasan mijin ta tana son ta da wuya ya iya kula wata amma ai ance har maza ma ana musu auren dole a Arewa, Ana hakane kuma ya samu canjin wajen aiki zuwa KD wanda kafin faruwar hakan ne ya siya fili anan cikin unguwan su ya ɗauko masu aiki tafiyayya tun daga wata kasa sukazo suka ɗanɗasa mishi ginin nan da kowa ke maganar shi saboda kuɗaɗen da ginin yaci,ya kashe manyan kuɗi a tunanin shi in taga ginin zata yarda ta dawo gidan ba tareda anyi tashin hankali ba,sai dai ina a banza wai an tsikari kakkausa dan a lokacin da yake nuna mata pic da vid ɗin gidan ta yaba kwarai harma take ce mishi irin gidan zai gina musu in zai canza musu gidan zama,ganin yanda ya yaba da tsaruwar gidan yasa bai ɓata lokaci ba wajen faɗa mata cewa gidan nashi ne kuma yasan zata so gidan shi yasa yayi amfani da komai bisa ra'ayin ta dan yana son wannan karon dasu zai wuce,saboda duk sanda ya samu canji na wajen aiki shi kaɗai yake tafiya bata yarda tabishi har gara² takan kai mishi ziyara in taso. Aiko tamkar dukar guduma haka taji zancen wai itace zata koma Zaria da zama ita da yaran ta,to ai ito ko abuja sai dai ta zauna aba yanda ta iya Zaria fa tab. #kuyi hakuri ba yawa naso in kai karshen labarin sarki a page ɗin nan amma na kasa wallahi kaina ke ciwo,zanyi kokari mu gama dashi a page na gaba dan mu koma kansu Ameenatu, kafin na uban gayya jikan Hajiya ya biyo baya*Mai Jama'a* #Team Sarki #Team Mai Jama'a #Sheikh Naseer🥳 #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ # Free Book ne ```Page13 Duk yanda Sarki ya hasaso abin ya zarce tunanin shi domin tun sunayi iyasu sai da maganar ta koma gidan Brig domin Teemah ta samu ɗaurin gindi daga wajen uwarta,domin a lokacin Brig baya kasa shi kuma Sarki gudun kar in maganar yaje kunnen Brig gimbiyar tashi ta karayin fushi fiye da wanda take kai a yanzun yasa bai iya kiran Baban nata ya faɗa mishi ba,to dai koda maganar ya koma wajen Hajiya Ramlat itama bin bayan yarta tayi suka kafa hujja da cewa karatun yaran zai dakushe ga kuma aikin da Teemah ɗin keyi a lagos ɗin. Haka nan yanaji yana kallo dai dole ya tattara yabaro su a Lagos shi kuma ya dawo Kaduna inda yaci gaba da aikin shi,sabida ya nuna mata rashin jin dadin shi akan abinda tayi yasa a lokacin sai da ya kwashe wata 5 bai koma Lagos ɗin ba sai dai duk karshen wata a Zaria take mishi. Wannan nisa da juna da sukayi yasa a hankali saboda yawan ziyara da yakan kaima abokan shi yake ganin yanda suke tafiyar da al'amuran su na zaman takewar aure tsakani su da matan su da kuma yanda matan ke kaffa² da komai daya shafi mazajen nasu hakan yasa duk sai ya fara tsarguwa domin idan ya ɗauko nashi zaman auren ya kara dana abokan shi sai yaga ina ko kusa basu dai² taba, wanda ada shi bai taɓa ɗaukar cewa sakewa da damam makin da yaba Teemah take yin abinda ranta keso a matsayin wani abuba sai tsabar soyayya,bai san cewa wuka ya ɗauka ya daɓa ma cikinshi ba sai yanzun domin gashi dai har ankai matakin da yanaji yana gani bai isa yace ga abinda yake buƙata tayishi cikin daɗin rai ba,ko kuma yace yau ya kafa doka akan wani abu. duk bashi da waɗannan daman ta yanda sai abinda taso taga dama takeyi, kula dashi da adacan baya takeyi a filin wasan dambe shima tuni ta tattara ta watsar a cewar ta wai yawan dambacewa na tsofar da mace dan haka inba ita tayi ra'ayin kawo mishi kanta ba koya nema bata bashi shi kuma ya kuduri aniyar bazai taɓa yi mata dole ba dan haka ya koma koda yaushe cikin azumi yake sannan kuma yana matukar kauracema duk wani abu dazai danganta shi da hurɗa da duk wata mace a tsoron shi na faɗawa harkar neman mata duk kuwa da yanda yake fama da ciwon mara lokaci lokaci. Ganin tsayin watan nin daya ɗauka ba tareda ya dawo ba yasa taɗan fara damuwa,domin dai ita babban tashin hankalin ta shine kar yaje can iyayen shi su sanya shi ya kara aure, sai dai duk sanda tayi maganar da kawayen ta suke kwantar mata da hankali akan cewa ta tsaya akan bakin ta in kuma ya matsa to ta faɗa mishi ya saida wannan gidan ya siya mata wani a Abuja ko anan KD ɗin, Koda ta tunkare shi da Maganar bata samu yanda take soba,dan kai tsaye shima ya faɗa mata bai amince da hakan ba in bazata zauna a Zaria ba to taci gaba da zaman ta a Lagos . ɓacin ran rashin samun biyan bukatar ta yasa ta tattara shi ta watsar dan tasan ko giyar wake yake sha bai isa ya mata kishiya ba. duk wannan rikicin da sukeyi yan uwan shi basu sani ba ciki kuwa harda mahaifiyar shi domin hatta da ginin gidan da akayi har aka gama ba kowa yasani ba daga mahaifin shi sai Malam sai kuma mahaifiyar shi duk yanda ginin gidan yaja hankalin mutane sukayi ta cece kuce a kanshi wasu na yabawa wasu na kushewa babu wanda yasan ko gidan na waye domin aikin ginin company keyin shi sannan kafin a fara ginin saida aka zagaye filin da kwano aka mishi katanga da idon mutane,lokacin da aka kammala ginin ko da aka cire wannan katanga ba irin surutan da mutane basuyi ba dan da yawa ganin su almabazzaranci ne kawai wannan gidan duniya da a kullum zaka iya tafiya ka barta. ganin har an gama ginin gidan Sarki baiyi magana akan dawowar iyalin nashi gidan bane yasa Uwar gida da kanta ta tareshi da zancen dan koba komai zata so ace da iyalin shi zai tare a cikin gidan,sai dai bai boye mata yanda ta kaya akan batun dawowar su Zarian ba tayi zaton hakan dama dan haka a matsayin ta na uwa taga ya dace ta shiga maganar dan tayi sasanci,dan ko ba komai tasan ɗan nata na ɓukatar iyalan shi a kusa dashi hakan yasa tayi kiran wayar Teemah ɗin a gaban Sarki a zaton ta ko kila in tasa baki taji nauyin ta ta yarda da batun dawowar, sai da tayi mata kira biyu kafin ta ɗauka a kira na uku wayar tana gab da tsinkewa, Bayan sun gaisa ta tambayeta yara da kuma mutanen can gidan su ita kuma Teemah ta amsa mata da cewa "lafiya lau suke" sannan Uwar gida tayi gyaran murya ta ɗaura da cewa "Fatima dama na kirane inji ya maganar tahowar ku Zaria domin dai aikin gida ya daɗe da kammala komai na bukatar ku an zuba,ga bikin kannen Sarki da yake ta gaba towa nasan kina da labarin bikin kuma so samu ace ku iso da wuri koba komai kinga Sarki dai shine Babban ya'ya yana da kyau ke a matsayin ki na matar shi ki iso da wuri dan ayi komai dake" shiru tayi tana jiran jin amsa daga bakin Teemah ɗin domin tasan ko maganar nata ya samu karbuwa ko a"ah "hello kina jina kuwa" ta tambaya jin shirun yayi yawa,sai dai ga mamakin su sai ɗin ɗin ɗin sukaji alamar daga can gefen Teemah ɗin ce ta yanke kiran,cike da mamakin hakan Uwar gida ta daga ido ta kalli Sarki dake zaune ranshi In yayi dubu ya ɓaci kokari yake ta yanda zai danne fushin dake tasowa daga cikin zuciyar shi,wato abinda take mishi a duk sanda yake mata wani maganar da bai gamsheta ba shine yau ma ta yanke ma Uwar shi Mahaifiyar shi waya. Kara dialled ɗin number ɗin nata Uwar gida tayi sai dai wannan karon ko arzikin ɗaukar wayar bata samu ba.ba tareda ta iya cewa komai ba ta tattara wayar ta tayi cikin ɗaki ta barshi nan zaune bayan ta kira ɗaya daga cikin kannen shi akan ta kawo ma Sarki ruwa mai sanyi,bai tsaya jiran komai ba shima ya tattara ya fice a gidan rai ɓace gaba ɗaya kanshi kullewa yayi a wannan lokacin baya son ya ɗauki mataki akan Teemah cikin gaggawa domin duk abubuwan da takeyi darajar mahaifin ta yasa yake kauda ido dan su zauna lafiya,amma wannan karan zai bata mamaki. a wannan lokacin bai jira komai ba ya ɗauki hanyar komawa KD tun da yabar gidan kuma yake ta faman kiran layu kanta tun yana kira wayar na ringing har daga karshe ya dena samun ta dan ta kashe wayoyin,bai yarda ya kara kwana a KD ba a ranar ya dira Lagos sai dai kuma abin haushi bai isketa a gidan ba mai gadin shi ke shaida mishi cewar kusan satin ta biyu kenan bata gidan amma dai yaran tun kafin ta tafi ƙanwarta Aziza tazo ta kwashe su zuwa barikin su,ba tareda ya huta ba ya kama hanya zuwa gidan Brigadier inda can ɗin ma bai samu Uwar matar tashi ba dan tabi mijinta zuwa US yaran ne kawai a gida sai nashi yaran, a wajen kannen Teemah ɗin ne yake jin cewa wai ta tafi Makodi yin wani aikine na wata ɗaya saura 2 weeks yanzun ya rage mata kafin ta dawo,wannan abu ya kara tunzura shi duk da ba wannan ne karo na farko da take tsallakewa ta tafi wata kasa ko wani state da sunan aiki ba tareda sanin shiba,kayan yaran yasa ta haɗa mishi ya iza keyar su bayan ya tattaro kayan su dake can gidan da duk wani abun bukata nasu dan ankai matsayin da bayajin zai iya cigaba da sakar mata ragamar tarbiyar yaran shi ita bata damu dasu ba can kuma inda ta kaisu shima babu mai sawa bare hanawa, Washe gari ya iso garin na Zaria shida yaran shi dake ta murnar za'a kaisu wajen kakan nin su dan tun tasowar su basu san kowa ba dan Uwar su dai bataje ba balle taje dasu su kuma yan uwan Sarki baƙin halin Teemah yasa suka dena zuwa inda yake sai dai shike bin su, Koda Uwar gida ta ganshi da yaran bata iya cewa komai dan dama tasa ran hakan na iya faruwa ta daɗe tana sa ran ko zai dawo hankalin shi in giyar soyayya ta sake shi to gashi dai bayan shekaru yau yayi abin kwarai,ɗaki guda aka ware ma yaran anan sashen ta bayan ya ajiye musu komai da zasu buƙata ya koma bakin aikin shi. Koda ya koma bakin aiki bai ƙara kiran Teemah ba dan yasan dole inta dawo zata nemeshi da kanta akan batun yaran ta,hakan ce kuwa ya kasance dan tun kafin ta kammala abinda ya kaita ta samu labarin abinda ya faru awajen ƙanwarta Aziza a daddafe ta samu ta kammala ta duro garin na Lagos bayan ta tabbatar da abinda taji a waya tayi ta kiran number ɗin shi bai ɗauka ba dan haka ba kunya ta daga waya ta kira Uwar gida,lallai Fatima ta cika mara ta ido domin tsawon shekaru da take auren Sarki dai² da rana ɗaya bata taɓa ɗaukar wayar ta tayi kiran Uwar gida da sunan gaisuwa ko kuma wani abu na mutuntawa ba,sai gashi yau dan an kwaso mata yara ta iya kiran waya kota manta tarin kiran da ita tayi mata ne oho. Maida komai ba komai ba tayi a matsayin ta na babba ta ɗauki wayar ba tareda wani gaisuwa ko nuna mutunta war cewa da uwar mijinta take magana ba kai tsaye taje ga dalilin da yasa tayi kiran wayar "na kirane dama inji in yarana suna wajen ki" Too dama baki san da batun ɗauko sun da yayi bane ko bai faɗa miki inda zai kai su bane dama? Itama Uwar gida ta tambayeta,amsa ta bata da cewa "inya faɗamin ai bazan ɗaga waya da sunan kira in tambaya ba,tabbaci kawai nike nema in suna nan ɗin ne inzo in kwashe su dan bazan iya barin yara na suyi rayuwa nesa dani ba",amsa mata Uwar gida tayi da cewa "ai ba laifi kina iya zuwa ki kwashe su duk sanda kika so hakan tunda kece mai iko dasu dama ba uban suba" tana gama faɗin hakan ta yanke wayar tana mai jinjina rashin kunyan Fatima lokaci yayi daya kamata ta nunama yarinyar nan cewa bafa son ɗanta bane batayi data bar mata shi tsayin shekarun nan tana ta kwallo dashi kamar tamola,bata faɗa ma kowa yanda sukayi da Fatima ba sai Amina Uwar gidan Malam ita kuma tace mata su zuba ido su gani ɗin ko zata zo ɗin kamar yanda tace, Aiko ga mamakin su sai gata a Zaria a cikin satin da ake bikin gidan inda ta samu rakiyar kawayen ta mutum biyu wannan zuwa nata ya haifar da mummunan saɓani tsakanin ta da Sarki dan fa sunzo sun tata rashin mutunci iya iyawar su ita da kawayen ta Allah ne kawai ya kiyaye dan tabbas Sarki taso ace iyayen shi sun barshi ya tsinke koda igiya 1 ne daga cikin igiyoyinta dake wuyar shi sai dai sam Malam ya shiga maganar ya hana sai dai Uwar gida tayi rantsuwa ko bayan ranta bata yarda yaran su koma hannun Uwar suba,dan yanda ta nuna musu rashin tarbiyar ta haka zata tarbiyar tar da yaran ma,har zuwa wannan lokacin kuma Brigadier bai san halin da ake ciki ba domin Malam sam ya hana Sarki ya faɗa mishi a cewar shi koba komai dole Fatima taci albarkhacin mahaifin ta. Haka ta tattara ta koma lagos cike da ɓacin ran rashin sanin matsayin da auren ta yake kai,suko kawayen ta ba haka suka so ba domin dama su sun mata rakiyane ta yanda zasu zigeta tayi abinda dole a raba auren ta da Sarki dan ba karamin bakin cikin dacen miji da tayi kamar Sarki sukeyi ba,domin kaf cikin su babu wacce ta ke abinda take so kamar ta. Bayan komawar ta duk yanda taso ta hasaso cewar abinda ta aikata bai dace ba shegun kawayen ta sunki bata dama gashi kuma Sarki gaba ɗaya ya tattara ta ya watsar kota kira baya ɗauka daga ƙarshe dai saida ta dunga kamun kafa daga wajen abokan shi kafin ta samu ya sauko ya fara kulata dan Allah ya sani cewa tana mutuwar son mijinta ba ƙaramin cutuwa takeyi da shariyar da yake nuna mata ba,ta ina ma zata fara rayuwar da babu Sarkin ta a cikin shi, tayi ta lallaɓa shi akan ya siya mata gida ko a KD ne ta dawo yaƙiya saboda yasan yanda ta tsani zaman bariki ne yasa shi ce mata sai dai ta dawo suci gaba da zama a bariki,to kun dai san halin yar gaban goshin dan haka taki yarda ta dawo har yanzun sai dai takan ɗanzo ta mishi weekend in taga dama wani lokacin kuma yakan ɗauko mata yaran in tazo kd su tayata zama. Tun wannan lokacin Uwar gida ta kuduri aniyar cewa dole Sarki ya ƙara aure tasan cewa shi bamai shiga harkar mata bane dan haka wannan aikin ita da kanta zata yishi ba kuma zata yarda ta ɗauko wata bare ba a cikin yan uwan ta kona mahaifin shi zata duba tasan in ta zaɓa mishi bazai mata musu ba,tofa a cikin tantancewar nata ne ƙuri'a ya faɗa kan *Ameenatu* bayan ta yanke hukunci kai tsaye ta samu mijin ta da maganar domin tasan cewa inta tsaya sanya sai dai a kawo musu goron sa ranar auren Meenal ɗin dan kowa dai yasan cewa auren wuri suke ma yaran su mata,koda taje mishi da batun shima baiƙi ba domin dama yasa idone yaga ta yanda za'aci gaba dagudanar da auratayya mata na kudu miji na arewa, Dan da karfin gwuiwar shi yaje ma Malam da Maganar dan wannan shine Aure na farko da yake fatan su kulla na zumunci atsakanin su dan kaf yaran su babu wanda suka taɓayi ma auren zumunci daga mazan su har matan. Koda yaje bai rufema Malam komai na dangane da irin zaman da Sarki yakeyi da matar shi ba duk da cewa yasan Malam ɗin na sane,In baku manta ba Malam shi yayi jagorancin neman auren Sarki a wancan lokacin. a sanda Malam Sulaiman yaje ma Malam da Maganar kuma ita Amina ko shekara 14 bata kaiba,kafin zuwan shi kuma dama akwai mutane biyu da sukayi magana suna so aba yaran su sai dai su ɗin ba yan uwa bane,dan haka Malam bai amsa da cewa ya bayar ko zai bayar ba yadai ce mishi suje suyi ta addu'a Allah yayi zabin alkhairi in matar shice zuwa sanda zata gama makarata sai ayi amma dai subar Maganar tukun na. Bayan ya tafi Malam ya daɗe yana nazari dan shi dai gaskiya bawai auren dangine baya soba,a'ah tsoron abinda ka iya biyowa baya in auren baiyi daɗi ba yakeji dan shi baya son abinda zai taɓa zumuncin shi da yan uwan shi dan haka bai tattauna maganar da kowa ba, Sai gashi bayan kwanaki Uwar gida da kanta ta wanke kafa taje da sunan samun Malam akan maganar sai dai tayi rashin sa'a koda ta isa ya riga ya fita,dan haka ta zarce wajen Uwar gidan shi a can take faɗa mata abinda ta yanke nason a haɗa auren Sarki da Meenat dan ita dai tana son Aminatu sosai, sun daɗe suna tattaunawa kafin ta koma gida,yayin da ta tafi tabar matar Malam da dogon nazari ta yama za'a haɗa karamar yarinya kamar Meenat da Sarki wanda a haife ya haifeta,duk bama wannan ba fisabilillahi ai rashin imani nema ace an aurar da ita a gidan mai kishiya balle kuma kishiya irin Fatima wacce tafi karfin mijinta, kai inah gaskiya wannan son kaine,bata taɓa sa baki akan auren ko wacce yarinya a gidan ba amma kam gaskiya bazata bari ama Uwar Malam irin wannan auren ba, Gaba ɗaya wunin ranar kasa sukuni tayi Allah² takeyi Malam ya dawo taji ta bakin shi taji me ya yanke akan maganar. Koda ya dawo kuwa batayi kasa a gwuiwa ba duk da cewa ba ranar girkin ta bane,kai tsaye ta faɗa mishi zuwan da uwar gida tayi da kuma dalilin zuwan nata harma da abinda suka tattauna Malam yana saura ranta ba tareda yace mata komai ba,ganin bai ba zancen nata mahimmanci bane yasa ta gyara zama ta zayyane ma shi duk abubuwan da suka faru dama waɗanda ke kan faruwa a gidan Sarki tsakanin shi da matar shi duk a kokarin ta nunama Malam irin cutar war da auren zai zama akan Meenat dan kowa yasan Sarki na son matar shi duk da tasan Malam yasan da yawa daga cikin abubuwan data lissafa mishi,sai dai duk yanda taso taji wani abu daga bakin Malam hakan ya faskara amsa ɗaya dai ya bata cewa taje tayi addu'a Allah yama Meenal ɗin zaɓi mafi alkhairi,haka ta koma sashen ta jiki ba kwari duk tausayin Meenat ɗin ya rufeta,lokaci² kuma haka Malam Sulaiman ke zuwa wajen yin ma Malam tuni akan maganar su, Kuma Uwar gida ta nemi ganin Sarki bayan yazo ta zaunar dashi akan aure take so ya ƙara,wannan magana ba ƙaramin tashin hankalin ya zama a wajen Sarki ba dan shi a ganin shi ina shi ina kara wani aure kuma fisabilillahi guda ɗaya ma kullum cikin sa mishi ciwon kai take balle kuma biyu,bai ƙara tabbatar da cewa lallai Uwar gida so take hawan jini ya kamashi ba sai da ta faɗa mishi wai yar gaban goshin Malam ta zaɓa mishi fisabilillahi kwata² nawa Meenat ko Meenal ne yaji suke kiranta take,wallahi ko rantsuwa bazaiyi ba yasan tsaf da yayi auren wuri zai ajiye wacce tafita girma,amma ya zaiyi yasan dai ko shaye² yakeyi bai isa ya kalli idon Uwar gida yace mata bai son zabin taɓa,dan haka bai iya mata musu ba haka nan ya amsa mata da toh cikin zuciyar shi kuwa ji yake kamar babbakewa takeyi dan shi dai rayuwar shi kaf bai taɓa hasaso kanshi a tsakanin mata biyu ba.ga kuma sharaɗin da uwar gida ta gindaya mishi na ya janyo yarinyar a jikin shi dan Malam ya tabbatar da gaske sukeyi. Wannan shine takaitaccen bayanin Sarki da abinda rayuwar shi ya kunsa,ina fatan kun rike cewa shine na uku a cikin manema auren Aminatu a yanzun da take matsayin kwaila nasan zuwa gaba sai sunkai 10 ko kuma waya sani ko itace zatayi gadon farin jinin kakarta Hajiya innah😂,mun gama da wannan fannin bari mu koma kan su Moon budurwar Sarki. ******** Bayan sun bar kofar gidan ya mashkur takaddama ce ta kaure a tsakanin su Meelat da Moon suna cewa a wuce gidan su Maryam su kuma Meenal da Aisha na cewa a wuce bayan layi wajen siyo awara mai kwai ɗin da Meenat ta basu labari jiya in suna dawowa sai su wuce gidan su Maryam ɗin,kafiyar da Meenat tayi akan zuwa bayan layin ne yasa dole suka hakura akan aje a siyo awarar dan haka suka yanke hanya,a cikin tafiyar nasu ne Aisha ke tambayar Meelat akan meya haɗa Sarki da Meenat da ɗazun Meelat ɗin tace Meenat batayin shi shiyasa ita ma batayin shi, "Kai kema Aisha wallahi kin iya tambayan gangan ke yanzun dan Meenat batayin wani har sai kin tambayi dalilin hakan bayan kinsan ta haka take kamar mai iskokai ita ai bata neman dalilin so ko ƙi akan wani abu, Kin san mutuniyar ki da ci,to bayan dawowar Sarki da aiki a KD duk weekend nan yake dawowa yayi shi kamar yanda kuka ganshi yanzun to idan yazo yana zaman karatun da akeyi na maza a masallacin Malam wani zubin kuma a cikin gida sukeyi to in sun gama karatun sai Malam yace ya shiga suci abinci a falon shi to kuma kun san mutuniyar kota koshi sai taje ta ciyo na Malam to zuwan da Sarki keyi yana rage mata bojet dan haka ta fara adawa dashi wai yana zuwa kwaɗayi a gidan su,shine fa kawai ba wani dalili mai ƙarfi ba sai kuma wani lokacin yakan tsareta akan ta kwaso takardun ta tazo yaga ni ko tanayin abinda ya dace a school abuna ƙarshe dai waɗannan karnukan daya kawo waɗanda suke hana mutane sukuni,ina fatan yanzun kin gamsu zaki barni in huta da tambayiyin kin nan" ta karasa faɗa tana haɗa hannayen ta biyu alamun roko,dariya duka sukayi banda mutuniyar data ɗaure fuska dan ita ko maganar shi bata so ayi a kusa da ita. Sunzo wucewa ta kofar wani gida suka hangi wata mata rike da yaro sai faman tsaga kuka yake duk yanda take lallashin shi yaron nan yaki yin shiru,sunzo dai² kofar gidan da niyyar su wuce su yaron ya kara fasa kuka kamar wanda ake yanka naman jikin shi,ina wuni suka gaisheta haka nan ta amsa su hankalin ta ya kasu biyu rabi a kansu rabi akan yaron da take lallashin "wai bazaka min shiru ba dame zanji da jarabar kukan ka koda aikin gidan zanji shi uban naka ai yana kallon kana kukan ya tsallake yabar gidan gashi na leko bashi ba dalilin shi,yau ko yaran dake wasa a unguwar ma babu balle In samu mai rikemin kai inje in karasa girkina,yan mata nace ko zaku ɗan rika min shi ya muku rakiya? Kunga wallahi aiki nike duk ya gama ruɗani nasan kafin ku dawo na gama aikina shima kukan wanda zai fita dashi yakeyi" Mika hannun ta Meenat tayi ta karɓe shi aiko kamar aikin asiri sai gashi yayi shiru ya lafe a jikin ta sai ajiyar zuciyar da yake faman saukewa na kukan da yasha, "Kun gani koh! Dama na faɗa bari in miko miki zanin goyon shi da feeder ɗin shi,ai wallahi nagode miki na samu in karasa aikina a tsanake" ta karasa fadar hakan a yayi data juya cikin gidan da saurin ta bata jima ba ta dawo da showel na goyo da wata yar madaidai ciyar jaka data zuba kayan bukata na kula da yaro tana ta musu godiya ta basu kayan sannan ta juya cikin gidan Tafiya sukaci gaba dayi ba tareda wata tace komai ba zuwa can Meelat ta kalli Meenat dake saɓe da yaron a kafaɗarta ba tareda ta goya shin ba tace "Beb wai ina zaki kai yaron nan da kika karɓo shi a hannun Uwar shi? "Ya akayi hala? Itama ta maida mata amsa da tambaya,"nasan baki fiye son ɗaukar yara ba sai naga kin karɓe shi,me kike shirin yi? Dariya Meenal ɗin tayi,"yarinya lallai zuwa yanzun kin sanni da kyau to tsaya kiji kinga can" ta fadi can ɗin tana mata nuni da hannun ta,kallon inda take nunawan dukan su sukayi, a tare suka haɗa baki wajen cewa police station suna masu zaro idon su cike da tsoro, "Kwarai Ganuwa Police Station aka rubuta,can zan kaishi wai hala bakuji abinda Uwar tace bane?" Bata jira amsar suba ta ɗaura da cewa " cewafa tayi mijin ta tsallakewa yayi ya fice ya barta da yaro yana mata kuka duk da tarin aikin dake gaban ta bai sa ya tausaya ya taya ta aikin dan ta gama da wuri taji da ɗanshi ba ko kuma ya ɗauki yaron ya fito dashi dan ta samu damar kasara aikin gaban ta cikin kwanciyar hankali,ku duba kuga yanda duk kukan yaron ya ruɗata tayi rarrashi shima ɗan Baban shi yaƙi shiru,saboda tsabar rashin tausayi irin na uban matar nan ta ɗauki ciki wata Tara koma fiye da haka duk tsayin watan nin nan ita kaɗai tayi ta fama da lafiya ko babu tazo tasha wahalar nakuda Allah ya ceceta tasha da kyar yanzun da lokacin dazai tallafa mata wajen kula da yaron yayi shine ya tsallake yabar gidan wato ita yar wahalar tayi ta fama koh? To ya gamo yawon nashi ya dawo yazo ya ɗauki yaron nashi a police station" ta faɗa tana yin gaba hankali kwance kamar ba tashin hankali take shirin ballo musu ba, Moon ne tayi saurin shan gaban ta, "Meenat kawo shi dan Allah mu mayar ma Uwar shi karki kaishi wajen can please" Wallahi sai na kaishi in tsoro kukeji kubi tanan lungun ku fita ta can ku jirani idan na kaishi zan fito in same ku muje wajen mai awarar," Muje in rakaki" cewar Meelat, Ke Jamila ashe kema bakida hankali irin ta nidai wallahi ba ruwa na Aisha zo mu ƙara gaba mu jira su" lungun da Meenat ta nuna mata suka bi su kuma kai tsaye suka wuce police station ɗin, Mutum biyu suka samu cikin police ɗin sai da suka gaishe su cike ladabi sannan Meelat ta ɗaura da cewa," muna cikin tafiya ne zamu wuce ta layin Sule Ajasco munzo dai dai kofar wani gida shine muka haɗu da wata mata tace mu riƙe mata wannan yaron taba ma kawata shi wai zata ɗauko abu a gida tayi mantuwa,to dama koda muka ganta yaron yana ta kukane koda ta bamu shi kuma bai dena ba,shine ta bamu harda wannan ta faɗa tana mika musu jakar tarkacen su feeder ɗin yaron da zanin goyo,shiko yaron ganin su maza yasa yaketa washe baki yana mika musu hannu hakan yasa Meenat ta mikama su yaron sannan Meelat taci gaba da cewa, " Munyi tsoron kar azo sato shi tayi dan mun daɗe a tsaye wajen bamu ga ta dawo ba da muka bi lungun kuma sai mukaga ashe hanyace kawai ba gida ko ɗaya a wajen balle mu shiga mu tambaya mu kuma ba yan nan unguwar bane daga tudun jukun mukazo neman gidan wata yar makarantar mu kuma bamu gane kwatancen ba, shine mukace gara mu kawo shi nan tunda bamu san gidan mai unguwa ba, Su kuma police ɗin kamar Allah ya rufe musu baki basu wani tsanan ta bincike ba suna kallon su suka wuce a dai² kofar police station ɗin ne sukayi karo da Ibrahim kwaro yayin fitan su dukkan su basuyi tsammanin ganin shi a wajen ba dan haka sosai suka tsorota amma tsabar Jan wuyanci sai basu nuna ba sai ma gaishe shi da sukayi suka wuce dan sun san dai shike nan aikin su ya buɗe. 🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Wannan tar gaban goshin Malam ɗin fa sai kun mike da addu'a dan wallahi batajin magana. Domin jin yanda zata kaya sai ku Tara a page na gaba. Gaskiya mutane na bakwa comment anya bazan ajiye alkalamina ba kuwa?🤕 Share please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _*Ina mai bada hakuri sakamakon jina shiru da kuma yi* gashi nan dai aci da hakuri..... ```Page14 Tafiya suke suna waige alamun rashin gaskiya duk da yanda sukayi mursisi kuwa dan Allah ya sani jinin su a kumba yake Allah² suke suga sun ɓace a wajen kafin ɗaya daga cikin police ɗin nan ya fito neman su,dan haka suka canza hanya izuwa wata lungu daba a fiye binta ba har saida suka kule cikin lungun kafin Meenat ta juya cike da fargana tana kallon Meelat tace "kawata Allah ya cece mu! Waiyo Allah kinji yanda nike jin zuciya ta tana tsalle kuwa? na rantse da Allah banyi zaton zamu sha ba,ke wai uwar me ma ya kawo wannan sojan wajen nan ? Shike nan mun shiga uku dan nasan da zarar yasan abinda ya faru yana komawa gida zaiba Sarki labari. Dukewa tayi dafe da kirjin ta,kamar kuma wacce aka tsikara sai gashi ta zabura "kina ji koh shiru zamuyi karki sake ki faɗama su Moon abinda ya faru dan wallahi suna sani tofa magana ta ƙare ba lallai su iya shiru da bakin suba dan shegen tsoro garesu,shiru kawai zamuyi mu jira abinda zai biyo baya dan mai afkuwa dai ta riga ta afku". Duk wannan surutan da Meenat keyi a ruɗe Meelat bata iya tofa ko 'A' a maganar ba dan ita harga Allah ta sadaƙar dan harta fara hango kansu a gaban Sarki ya saki sheggun karnukan nan nashi sun yagalgala naman jikin su, Waiyo Allah ashe ita kuma nata kalar mutuwar a hannun karnuka zatayi,yanzun waye zai saurareta ta balle harta sheda mishi cewa itafa iya rakiya kawai tayi, Meenat itace wacce ta shirya komai tsakanin ta da zuciyar ta kuma ta gabatar,ita fa dan dai bazata iya ganin kawarta ta taro aradu ta barta ta ɗauka ita kaɗai bane yasa ta rakata,sai gashi tsabar rashin sa'a tun basu fita daga station ɗin ba sunyi karo da wancan kwaɗo ne ko kwaro taji ana ce mishi,ita fa wallahi tasan muddin maganar nan ya koma gidan su tofa ba shakka yayyen ta maza sai sun haɗa partyn cin ƙaniyar ta.shine abinda take ta lissafawa a zuciyar ta. "Waiyo Allah tsautsayi yasa na yarda na biye miki akan a fara zuwa siyan awarar kafin muje gidan su Besty gashi nan kin taro mana hau ɗin da yafi ƙarfin mu, kai innalillahi wa'innah ilaihir raju'un police station fa ga kuma Soja a gefe" cewar Meelat cike da taraddadi da alama sai yanzun take kara hasaso kalar katoɓarar da sukayi na miƙa ɗan mutane hannun police, matsawa kusa da ita Meenat tayi hannu wanta duka biyun ta ɗaura a kafadun Meelat ɗin sannan ta jijjigata da karfi tana mai cewa, "ke miye haka dallah ki nutsu babu ma abinda zai faru abinda police ɗin ba sanin mu sukayi ba,shi kuma wancan Sojan nasan bazai wani ce musu komai ba dan haka ki share kawai". Buge hannun ta Meelat tayi a zafafe tace, "In share fa? Inshare ma kike ce mun ɗan mutane fa ƙaramin yaron dako magana bayayi na biye miki muka kaishi hannun polisawa, Ke Meenat amma kin san dai baki kyauta ba koh? Me yasa zaki kai yaron mutane police station nifa dan kar ranki ya ɓaci shi yasa na raka ki,amma ke kullum hankalin ki bai kwanciya sai kinja mana duka, nan fa ba makaranta bane da aka saba kai mu ƙara koda yaushe, office ɗin principal ɗin makaranta daban fa dan wannan police station fa ake magana" ta karasa faɗa tana ɗaura hannayenta duka biyun akai ta fara zagaye ɗan filin wajen "kin kashe mu wallahi yasin yau ko shaye² nikeyi ban isa in koma gida ba,dan haka gidan ku zanci gaba da tarewa gidan ku zan ƙara kwana nasan duk bala'i Malam bazai bari a kulle mu a police station ba,waiyo Allah ga police ga soldier mala'ikun duniya, police duka da mucciya sojoji tsallen gwaɗo. "Ke dallah ki nutsu kina haka sai kin tona mana asiri tukun hankalin ki zai kwanta kinga saiki shirya kwana a cikin cell da hujja amma nikam wallah ba uban da ya isa ya kaini cell, dallah ni muje da shegen mugun fatan ki har kinsa na fara rasa kwarin gwuiwa ta, "Kin tabbata babu abinda zai biyo baya kawata? Meelat ta tambaya, "Me ko zai biyo baya! Iya kacin in ma antada maganar tambaya cefa kawai za'a mana,toke bakin ki na ciwo ne da bazaki iya basu amsa ba? To tsaya kiji nidai nasan bai wuce in ma shi wancan ya buɗe mana aiki ace aje neman muba bari kiji mai zai faru, Daga police station kai tsaye nasan gidan mu zasu,in sun isa nasan kowa zaiyi mamakin mai kuma ya kawo police gidan Malam dan sojoji aka saba gani a unguwar ba su ba,in sunyi katari sun cinma Malam nasan baza'aja maganar da tsayi ba , akasin hakan ko duk wanda suka cimma tsakanin Baba Adamu ko Baba Auta nasan abinda zasu fara tambaya shine " ina muke? dan haka cikin gida za'a shiga a tambaya su kuma sun san bama gida dan haka kowa zai bada shedar cewa bama gidan tun safe, police zasuyi tambaya cewa "ina muka je? Su kuma zasu ce, " munje gidan ya Mashkur" nasan ba zasu hakura ba zasuyi zaton ko daga police station can zamu koma dan haka zasu kwasa su tafi,in kuma shi wancan Kwaron ya kaima Sarki labari to nasan da Sarki zasu isa gidan ko wasu daga cikin yaran shi in kuma yayi mutunci nasan zai ce dasu su koma bakin aiki shi zai neme mu, amma kafin nan dole wani daga cikin gidan zai kira wayar ɗaya daga cikin mu in bamu ɗauka ba zasu gidan acan kuma za'a basu tabbacin bama nan, Daga can kuma gidan su Besty zasu nufa,dan haka zuwa gidan su Besty cancel ba wannan maganar a yanzun, daga nan muna gama siyan awarar Tudun Wada zamu koma dan Gara muje muyi hakuri da halin Hajiya damu koma Sarki ya haɗamu kwana ɗaki guda da karnukan shi dan wallahi ban kwanan cell nikam. Huhuhhu chakwakiya kenan an gujema police da soja za'a fada hannun iliya ɗan mai karfi😂🥳, Hausawa sunce da babu Gara ba daɗi shi yasa na daure na baku babu dai yawa gobe in Allah ya kaimu da rai da lafiya ma ɗaura. Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _*Ina mai bada hakuri sakamakon jina shiru da kukayi, to gani na dawo insha Allah zamu cigaba daga inda muka tsaya, Nagode. *********/////////. Page 15 *Mai Jama'a* Cikakken sunan shi, shine *Abdul Khareem Ahmad*{A,K,A Mai Jama'a} ɗa na uku a cikin jerin gwanon yara 5 ɗin da iyayen shi suka mallaka, sannan ya zamto ɗa mafi kololuwar soyuwa a wajen uwar shi Aminatu wacce ta kasance yar Babban ahali masu tsatson Naira domin sosai ahalin ta suke da *Kunbar Susa* Littafin Surayyahm. wacce a kullum take takaicin yanda Hajiya Innah ta janye mata shi daga gareta domin dai tun bayan daya kammala matakin karatun shi na sakandire Hajiya tayi mata awon gaba dashi zuwa Zaria sakama kon yanayin kasuwan cin Abba Ahmad mahaifin shi daya mai dashi kasar Saudiya, a babu yanda mahaifiyar shi Amina zatayine yasa ta iya tsallakewa ta tafi ta barshi bawai dan taso hakan ba sai dan tasan Hajiya zata kula mata da Abdul fiye da kanta. Bayan dawowar shi zaria ne ya jona karatun shi a ABU Zaria dashi da abokan shi 2 Sadeeq da Musty waɗanda suka kasance abokan shi ne suɗin tun na yarinta sai Yusif wanda shi kuma a nan ABU suka haɗu har suka zama Abokai kasancewa shima ɗin ɗan sharholiya ne irin su AK dan haka tuni ya saje dasu suka cigaba da bada wuta. Ak, Musty, Sadeeq, Yusif sun kasance the hottest young billionaires dake tashe a cikin makarantar ABU a wancan lokacin sun kasance masu class kyau gata gamida wayewa tareda ilimi atako wanni fannin dan haka a kullum mata suke kan kawo musu hari saboda kasancewar irin mazajen dako wacce mace ke fatan samu. Sun ɗauki karatun su da matuƙar mahimmanci matuka dan haka koda yaushe cikin burgewa da class ɗin su suke, sai dai duk cikin su huɗun babu wanda ya kama kafar AK domin Shi dai haka Allah yayi shi da wani irin izzah da kwarjini duk da bai haɗa jini da sarauta ba sai dai izzar kuɗi tuni ta daɗe da huda jinin jikin shi domin shiɗin dan gata ne gaba da bayan shi. Rata ne mai matukar tsayi tsakanin shi da talauci, sai dai duk wannan arzikin daya buɗe ido a cikin shi baisa ya zama cikin wasu matasan masu kuɗin da suke wulakanta marasa shi ba sannan kuɗin gidan su baisa ya zaman to cima zaune cikin matasan da babu ruwan su da tunanin dogara da kansu ba, daga shi har abokan shi duk da kasancewar su ɗalibai a wancan lokacin hakan bai hanasu neman halaliyar su ba duk wata harka da za'ayi kuɗi na halak su shigo sun san shi dan sosai suka kware wajen iya juya biyar ta zama goma domin dukan su kasuwanci suke karanta kasan tuwar su yaran manya shima ya taka rawar gani matuka wajen habakar kasuwancin su, abokan takar su sukeyi gwanin burgewa babu munafunci balle kuma hassada suna farin ciki da farin cikin dayan su haka kuma suke baƙin ciki da baƙin cikin dayan su duk da halayan su daya banbanta kuwa domin Sadeeq da Musty mutane ne masu fara'a sosai suke da sakewa basa da ɗaure fuska, Shiko Yusif miskiline kafi mahaukaci ban haushi amma shi miskilancin nashi ya hada da sarautar dake yawo a jinin shine kasancewar shi ɗan sarkin Wase. Shiko AK a fuskar shi in ka kalle shi kai tsaye ba zaka sashi cikin mutane marasa fara'a ba saboda yanda baida sake fuska matukar ba tareda su Sadeeq yake ba indai a cikin School ne bazaka taɓa ganin dariyar shiba balle harya kalli wata macen koya nemeta, ina sam dan tsabar ya raina ma mata da aji ko course mate ɗin shi mata baya sakar musu fuska balle ya sake dasu saboda tsabar gudun raini domin a kullum yana daraja girma da class ɗin shi, uwa uba kuma ego da yake ji dashi akan ganin matsayin sa kyawunsa da kuma dukiyar sa hakan yasa yake ganin shiɗin dole komai girma, kyau, class, gata, ilimi, da kuma dukiyar mace dole ta kallesa ta ƙara kallon sa duk da a rayuwar sa babu halittar daya raina wayan su kaman mata a ganin shi mata basu da darajar da har shi zai kallesu balle yaji yana son su,gani yake lalacewa ta same shi duk ranar da ya fara son wata Ƴa to hakika dole yakai kanshi asibity dan yasan baya cikin hankalin shi, dan haka babu waɗanda yake ma kallon zararru waɗanda suke buƙatar a mikasu dawanau irin masoya banda kallon taɓaɓɓu harda kallon makaryata ma yake musu inba karya ba mai zaka dunga faɗama yarinya. yanda yake ganin sauran abokan shi na kiran yan mata su share a wanni suna waya mtws wannan ma ai tsabar zubar da ajine shi wallahi kullum cikin takaicin su yake, shi dai gaba ɗaya baiga abun burgewa a cikin soyayya ba dan haka kullum cikin neman tsari yake da soyayya tayi gabas shi kuma yayi yamma. Shi ina shi ina mata fisabilillahi domin a ganin shi su ɗin basu ɗauki kansu da darajaba dan tun bai san kanshi ba yake ganin yanda mata ke ribibin shi har gobe kuma dai bata canza zani ba. Sauda dama idan su Sadeeq suna fadin cewa har yanzun akwai matan da suke tare da budurcin su ma'ana basu taɓa kusantar wani namijin ba yakan kallesu ne kawai saboda iya hange dai baya tunanin akwai su, kai ko akwai ma yana ganin badai cikin gari ba sai dai daji wanda suke can ɗin ma yasan duhun kaine da rashin yancin kai yasa haka, Kamar dai yanda aka sani kudu garuruwan su da mutanen cikin su da tsananin wayewa yayin da wani wayewar harta zarta tunanin mai hankali ta zama iya shege tsagwaron ta domin da yawa daga cikin ɗabi'un su anan arewar mu da zarar ka gwada aikata daya daga cikin nasu dabi'ar to fa kai tsaye ne za'a kiraka da sunan DAN ISKA KO YAR ISKA da babban baki kuwa. (Dan uwatai ko ubanwa yace mai tarbiyar yaran Arewa ɗaya yake dana yan kudu oho😒) Saboda shidai tunda ya tashi yayi wayau a garinda aka raine shi yake ganin yanda ake wata irin badakala ta yanda yarinya zata baro gidan ubanta tazo ta tare a wajen saurayi koda ko saurayin yana zaune tare da iyayen shi ne hakan bazai sa yaki dura mata ciki ba, wani ma haka zai ajiye macen harta hayayyafa daga karshe kuma kaga basuyi aure ba har tsufan su yayin da wasu kuma matan nasu iskancin ma a gaban iyayen su sukeyin kayan su , shi kanshi tun tasowar shi yake gwagwar maya da migayun halittun nan Mata kullum cikin binshi suke suna mararin shi da dama a cikin su basu iya boye mishi tarin maitar sonyin mu'amala ta banza dashi sai dai kuma shi Allah yasa mishi kyamar su, sai dai har kwanan gobe bai daina fuskan tar hare²n matan da suke son yayi harkallah ta banza dasu ba, dan haka a ganin shi wani sauran daraja ya rage na mata da zai gani kuma tunda gashi a kullum cikin binshi suke duk inda yasa kafa sai mata sun maida nasu, Shidai Allah yayi shi cikin mutane masu sa'ar rayuwa domin kaf rayuwar shi baisan wani abu waishi damuwa ko bakin ciki ba ballan tana kuma wani abu waishi takura inba na matan da suke maitar shiba, kwata² bai san zafin rashi na komai ba dan bai taɓa nema ya rasa ba, ga kuma gata da yake samu wajen dangi na uwa da uba karma asa mutan gari a lissafi iya ahalin shi kadai ma sun isa, domin tun yana ciki Allah yasanya ma iyayen shi matukar kaunar shi haihuwar shi kuma ta kama a dai² ranar sallan layya bayan dangi na nesa dana kusa sun hadu wannan dalili yasa tun ranar daya fito duniya ya samu sunan Mai Jama'a, sunan daya zama linzamin farin jinin shi a wajen al'ummah domin kam ya amsa sunan dan yana da kyawawan hali da kuma saukin kan da inhar ka zauna dashi koda na mintocine sai kaji ya burgeka, sai dai daga in kana nesa dashi bazaka mishi kallon mutum mai saukin kai ba gashi dason taimako sannan shi ko alkhairi zai maka bazai taba barin wani ya sani ba ko kai da yamawa bazai bari ka sani ba domij yana da wakilan da suke mishi irin wadan nan aiyukan in ana neman taimako, Da fari ba karamin dizgi da yankwana wa ya dinga ma yan matan dake binshi a cikin makaranta ba sai dai kuma su matan da alama hakan ma burgesu yakeyi bai sha fama kanshi lafiya ba har saida yaga suna neman mai dashi mahaukaci sannan dan dole ya koyi iya zama a cikin su a bashi da yanda zaiyi dole ya koyama kanshi yanda zai dunga tolerating din su sai dai fa duk da hakan bai yarda ya sakar musu fuskan da zasu mai dashi kamar wani abokin wasa ba duk yanda yake ganin girman ki da zarar yaga zaki zame mishi cingum zai kakkabe ki ne tsaf dan shi baya son naci wallahi, sai dai fa duk yanda yaso Hafsa da Nusaiba yaran nan biyu shi bai taba ganin marasa zuciya irin suba, ita dai Hafsat makaranta ɗaya sukayi tun daga matakin sakandire amma tsabar jaraba da kuma kasancewarta yar gata kyankyasar inji yar dady da momy sai da tayi yanda ta shawo kan iyayen ta a maimakon kasar waje da suka so turata tayi karatu ta dawo arewa tayi joining ABU saboda tsabar son da takema AK gani take da zarar yayi mata nisa tofa wata daban zai so ba ita ba, koda tazo ABU maimakon karatun Law ɗin da kowa yasan cewa shine burin rayuwarta ajiye shi tayi itama ta ɗauki course ɗin masoyinta a burinta na kasancewa dashi akoda yaushe,sai dai a banza wai an tsikari kakkausa duk da yasan dalilin ta nayin hakan kwata² hakan da tayi bai burge shiba sai ma kara zubewa da class dinta yayi a wajen shi dan a cewar shi indai soyayya gaskiya ne ai namiji ne ya dace yaje yayi ta fataucin ta a wajen mace, batun yau tasan halin kayanta ba dan haka tuni ta koyama kanta kiyaye duk abubuwan da tasan baya so, sai dai a gefe guda kuma kullum cikin tashin hankali take da sauran mata akan shi dan ba karamin kishin shi take ba dan haka koba zancen so in taga mace na zakewa akan AK take yin fito na fito da ita, duk da yana sane da haukan da take akan shi hakan bai taba sawa ya kalleta da sunan soyayya ba shifa kallon aboki ma yake mata class ɗaya fa sukayi rayuwa a sakandire tun daga Js har zuwa Ss class to shi made &in shi zaima kallon budurwa kamar mai fama da bakin iyaye fisabilillahi sai dai yana daga mata kafa koba komai yanda take kiyayewa bata fiye zake mishi ba hakan yasa shima yake ɗaga mata kafan yasan dai duk tsiya dole inta gama makaranta ta tattara ta koma gaban iyayen ta, shi hauka yake da zai auri tsarar shi, Ita kuma Nusaiba da farko kallon mai hankali yake mata saboda ba karya tana da nutsuwa yarinyar gata da yawan gaisuwa hakan yasa duk dashi bame yawan wasa da mata bane haka dai yake daurewa yana mata raha dan yana matukar son a dunga girma mashi shine saboda taga yana sake mata fuska yarinyar nan ta kwance mishi zani a kasuwa ta wani samu Musty da batun wai son Mai Jama'a takeyi, to dai tundaga ranar itama dai ta kabar da daman daya bata amma munafukar kullum sai ta fake da wani abun take nema ta biyo ta inda tasan zata ganshi a cikin school in kuma lokacin weakend ne bata da sukuni haka zatayi ta zarya a cikin unguwa , abun fa bana wasa bane domin dai yan matan nan da tun anayin abun a cikin makaranta sai gashi sun fara biyo shi gidan da suke zaune a offcampus da sunan wani abu ya shige musu duhu ta fannin karatu kasancewar su guraye a fannin karatun su dama su Musty basu da matsala da yan matan todai a hankali a hankali gidan su ya zama wani karamin hall din karatu sai ya zamana ko wani abune daya shafi student ya tashi a can za'ayi. Tun AK na nuna bacin rai har sai da ya kawo na mujiya ya zuba musu na dole. Yawan ziyarar da hajiya ke kai musu a duk sanda taso ne yasa ta fara ganin canje² domin dai duk zuwan da zatayi sai ta cin ma gidan da students ba kuma iya maza ba duk da a gaban idon ta tasan abinda ya shafi karatun sune yake kawo su gidan amma hakan bai sa ta samu kwanciyar hankali ba duba da yanda zamani ya lalace tana tsoron Allah tana tsoron yaran zamani atoh duk da dai duk weakend a tudun wada Ak yakeyi wani lokacin ma su duka huɗun ke zuwa amma dai ita sam hankalin ta bai kwanta da yanda yan mata ke zarya a gidan ba, Tasan halin jikanta sarai mutum ne mai kyankyami da son cin abinci yana da bala'in tsafta ta jiki dama ta muhali domin koda yaushe tsaf zaka ganshi yasha wanka yana bulbula kamshi sai dai fa shidin ƙaton zero 0 ne indai a wajen kula da tsaftar muhalli ne bai iya komai na gyaran waje ba duk abinda ya shafe shi tun yana gida dama uwar shi ke kula mishi dashi dan haka koda ya zo Zaria Yar Aikin Hajiya ta amana Larai ke kula mishi da ɗakin shi, abinci dama ba'a ko ina yake iya ciba duk da bashi da zaben abinci amma shidin ma'abocin son tuwo ne sosai yake son cin abinci mai nauyi dan haka baya rabuwa da motsa jiki a koda yaushe, sam Hajiya bata so yanda yaki zaman gidan ta ya zabi zama a cikin samaru ba amma bata da yanda ta iya haka ta kyale shi to ko yanzun ma dai kula da komai nashi akan abokan shi ya rataya domin shi dai babu ruwan shi a duk inda yaga dama nan zai watsa kayan shi sai dai su su dage su adana gyaran gado da komai daya shafi kula da dakin shi Sadeeq ke yi mashi dan haka ko wani abu yake nema nashi kai tsaye shi yake tun kara tunda komai shike mishi, batun girki ko wannan Musty da yusif da suke kira wase sune incharge wani lokacin kuma yan matan dake zuwa gidan ke dafa musu suci ko su fita su siyo ko kuma suje gidan hajiya suci Allah ya sani Hajiya na tsoron abinda zai samar mata jika domin dai tun wani zuwan da tayi ta samu Hafsat a kitchen ta dage da girki kamar gidan mijin wai ita ke dafa abincin da jikanta zaici tsoro ya kamata tana sane da cewa Son shi Hafsat din keyi sannan ita gaba daya madai zubin munafukai yarinyar take mata dan haka tana gudun kar wata rana ta ma jikanta barbade a kokarin ta nason shawo kanshi dan yan matan yanzun sun zama abun tsoro tsaf suke shake wuyar saurayi da asiri ita ko da ranta da lafiyarta ina dalili da tanaji tana gani yan iskan mata su shigar mata rayuwar jika suyi kane² ai dole ma ta kira uwar shi ita dake kasa mai tsarki ta dunga zuwa tana ma danta dawafi duk sati tana neman mishi tsari a dakin Allah. dan haka wannan dalilin yasa ta botsare akan cewa dole sai dai ya dawo gidan ta, shi kuma sanin halin ta da yayi cewa infa ya dawo gidan nan ba wani sauki zai samu ba dan shi dai halin Hajiya kuma ai sai dai yaba wani labari dan halin hajiya hatta shi da a bayyane take fifita shi akan jikokin ta bawai daga mishi kafa takeyi ba yasan walllahi raba mishi hankali kawai zatayi da fitinar ta dan haka shima ya shafa ma fuskar shi toka ya kiya, an dai kai matsaya akan kullum zata dunga ba driver dinta abincin shi yana kawo mashi dan bata yarda ya dunga cin abincin da matan dake zuwa gidan suke dafawa ba, domin a zauna lafiya yasan ya shi amsawa da cewa ya amince amma duk da haka yawanci ita da kanta take kawo abincin sai kuma tasa shi a gaba taga yaci sannan hankalin ta ke kwanciya , dan ba haka nan take dafa abincin ba sai ta barbade shi da magungunan baki dana kambun baka harda na tsari, dan tasan mutanen da yake tarawa bai zama lallai ace dukan su tsakani da Allah suke tareda shi ba dan haka ita dai bazata taba barin wani tsinanne ko tsinanniya su taso mata rayuwar jika gaba da ranta da lafiyar taba, domin duk da ake mata kallon yar boko tasan inda ke mata ciwo. A haka dai akayi ta tafiya har zuwa sanda suka kammala degree din su na farko, yakan kaima iyayen shi ziyara a kasa mai tsarki lokaci² kuma yawan cin zuwan tare sukeyi da Hajiya. #ina mai Kara bada hakuri, Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ _*Ina mai bada hakuri sakamakon jina shiru da kukayi, to gani na dawo insha Allah zamu cigaba daga inda muka tsaya, Nagode. *********/////////. `````` Page 16 *Zuwa wannan lokacin sosai suka karayin suna kana kuma sukayi fice akan har kokin kasuwan cin su. Sadeeq, Yusuf, Musty, dukan su ukun sun Kama ayukanyi na gomnati duba da cewa dama su yaran masu (Kunbar susa; littafin Surayyahms) tun kafin su kammala nasu karatun daman iyayen su kan tanadar musu da guraban aiki a inda ya dace, to su ma dai da yike yaran gaban goshin ne, Dan haka tuni nasu iyayen suma suka nuna bajinta su wajen samar musu da guraben aiyukan yi na garari, sai dai sam Mai Gayya mai aiki ya nuna baya wani bukatar yin aiki a karkashin gobnati yafi muradin kasuwan cin shi dan ta hakan ne zai iya taimakawa al ummah kai tsaye ba tareda ya jira umarni daga na sama dashi ba. Dan haka baiyi kasa a gwuiwa ba wajen Kara habbaka kasuwancin shi bayan kamfanin su da suka kaddamar Wanda yake na hadin gwuiwa tsakanin su hudun. Mai Jama'a yana da Manya²n plaza daya gina a filin da Kakan shi na wajen uwa ya Mallaka mishi bayan Kasuwan cin da sukeyi na gwala²i wanda Ummi ke turo mishi su daga Saudiya, Sannan ga wasu daga cikin Kasuwan cin Dadyn shi wadanda shine yake kula musu dashi. Hakan yasa ya zama busy sosai yau baya nan gobe baya can duk da cewa yana da mutane na amana wadanda suke kula mishi da wadansu abubuwan, duk da rashin samun lokacin hutun da yake fama dashi hakan bai hanashi Kara komawa makaranta ba yaci gaba da karatu shida Wase dan Musty da Sadeeq fir sukaki acewar su basuzo duniya dan bautar boko ba wanda sukayi Allah yasa mishi Albarkha su yanzun next agenda din su shine aure kuma, Oho shidai bai damu dasu ba Dan shi idan har ya riga yasa kanshi yin abu tofa ko kanshi baya saurara har sai ya aiwatar, su basu san so yake ya maida kanshi busy ba dan komai ba kuwa har sai Dan saboda kwata² har yanzun bayajin lokaci yayi dazai kula wata diya balle akai batun aure, dan zuwa lokacin Ummi ta fara tuntubar shi akan batun auren dan yayyen shi maza biyu da yake bi sun fidda nasu matan har ma ana batun a hada auren nasu ayishi lokaci daya dan haka ta fara tuntubar shi taji ko zai yarda a hada da nashi ayi a lokaci daya. Kuji wani neman magana irin na Ummi fa shi dan Allah yaushe har ya isa aure? To yaji in ma sunce ya kai auren in sun mishi auren wazai kula da matar? Dan shi dai lokacin kanshi ma ba samu yake ba balle ya kula da wata! To in ma tace aure to shi fa har yanzun kaf cikin matan da suke rububin shi baiga ta aure ba, kai wama ya sani ko kilama har yanzun ba'a haifi matar tashi ba. Oho su dai wadanda suka isa auren su sukaga zasu iya sai suje Suyi ta kaya amma shikam a rufa mishi asiri a shafa mishi lafiya. Duk yanda Ummi takai gason ganin ta shawo kanshi hakan ya faskara dole ta hakura har zuwa lokacin da bikini su Mudassir da Saleem yayi suka baro Saudiya suka dawo aka sha biki dasu kafin suka koma, Saleem yana aiki da NNPC ne a Lagos amma matar daya aura yar arewa ce jihar Kaduna shi kuma Mudassir Abuja yake aiki. A gaskiya dai tako wani gefe Mai Jama'a ya kafu da kafafuwan shi Dan haka baya fadin komai sai Hamdala, domin arzikin dama akwai shi ko ba'a cigaba da nema ba an riga an tara sai kuma ya tadda inda akasan dadin shi ake kuma amfani dashi wajen daga marasa karfi Dan suma su dogara da kansu, sau tari Hajiya kan mashi tsiya cewar bata san me zaiyi da kudiba kuma inba dai rijiya zai haka ya dunga zuba kudin ba Ina zai kaisu, shiko sai dai yayi dariya in kuma taci sa'a yakan bata da cewa, "Hajiyata aiko sabida ke kadai dole in nemi kudi so kike wata rana ki tambayeni kudin siyan tikitin jirgin zuwa Saudi ziyara in nace babu kimin saki uku? No! No!! No!!! Hajiya ta kudi fa abin nema ne kedai kawai kiyita min addu'a Allah yayi ta bamu masu albarkha, Dan su kudi dadine dasu kobaka nema dan kanka ba Ka nema Dan mabukata. Daga karshe dai Hajiya ta samu ta shawo kanshi da kyar da sidin goshi ya dawo gidan ta da zama bayan kammala degree din shi na biyu wanda hakan ne yayi dalilin dawowar shi Tudun Wada gaba daya da zama duk da cewar harkokin Kasuwan cin shi sunfi yawa a kudu duk inda yaje ya dawo dai gidan Hajiya ne masaukin shi, Yusif da Sadeeq zaman su yafi yawa a Abuja sai dai duk ranar Friday suke dawowa Zaria su koma Abuja on Friday Domin dukan su can suke aiki sai Musty shi kuma nashi Aikin a Kaduna yake yin shi dan haka duk ranar aikI zuwa yakeyi yana dawowa danshi ke kula musu da Kasuwan cin su na cikin gari, A kullum shakuwa da kaunar junan su karuwa yakeyi domin komai daya daga cikin su zaiyi sai da shawarar sauran, Bazamuce basa samun sabani kai tsaye ba, sai dai suna da matukar fahimtan junan da koda sun samu sabani basa bari yayi tasirin da zaisa suyi fushi da juna duk da sau tari ma dai Ak ne yake shigar musu hanci da kudun kune wani lokacin a wani wajen can za'a bato mishi rai in bai samu ya sauke a can ba to Wallahi sai ya dawo wajen su da gangan zai janyo wani abun da zai sa dukan su ransu ya baci a banza sabida tsabar mugunta, inko aka fara musu dashi tofa ko abu farine zai kife kaine yace jane sai dai kai mai musun Ka gaji ka barshi, inko a cikin abokan su ne wani ya bata mishi rai rana guda zai ware yace yasa musu wasan kwallo to Insha Allah ko a cikin filin zai kirkiri wani mugunta da zaima wanda ya bata mishi ran ta yanda in ya kaishi injury sai yayi jinyar jikin shi, Wallahi AK bakin mugune duk wani hanyar mugunta a ruwan sanyi ya santa ta yanda zaiyi Abu da gayya amma babu wanda zaiyi zaton da gangan yayi saboda tsabar iya kisan mummuke sai dai kaji Ana cewa Wallahi tsautsayi yasa yau wane kaza yaji targade koya goce a filin ball, Dan shi gani yake zuwa yanzun ai yafi karfin ya tube riga dan yin dambe da wani No a ruwan sanyi zai maka muguntar da zakayi sati ko fiye da haka baka iya fita yawo ba. Komawar shi tudun wada yasa majalisar shi ta koma can dalilin da yayi ginin fadar shi kenan Domin ko sunan ya gama makaranta ne kawai amma koda yaushe yana tarene da daliban makaranta ta yanda in har ya samu lokaci yakanje ya musu lecture jefi². Har yanzun kuma Hafsa bata hakura tayi aure ba, kullum cikin binshi take a kokarin ta na ganin ta fahimtar dashi cewa itafa shi take jira, amma kullum amsar shi a gareta shine. Shifa ba yanzun zaiyi aure ba. To itadai ta daura ma kanta dakon wahala Dan kuwa dai bawai masoyan ta rasa ba, amma dai ta yarda zuciyar kare ya dauka, Haka Nusaiba itama take fama, su biyun nan dai da kowa yasan yanda suka mato akan AK tofa kullum cikin dambace wa suke a duk inda suka yi kacibis kamar dai yanda suka dambatu ranar a kofar gidan Hajiya abun haushin kuma shi dai har yanzun babu wacce yake ma kallon mace a cikin su, Duk yanda AK keda kyakyawar alaqa tsakanin shi da mutanen waje tofa kar kuce ya banbance matsayin yan matan family din su da sauran yan matan dake mishi naci a waje ne, dan suma basu tsiraba domin duk yanda yake dason yara tofa da zarar diya mace ta dan fara tasawa shike nan kuma tsakanin shi da ita tosai dai kuma in tayi laifi ya zane mata jiki dan sosai yake daure musu fuska a ganin shi suma idan ya sake musu da yawa ba mamaki cikin su a samu mai tsaurin idon da zatace sonshi take dan yasan dai koda ganganci baza'a danganta shi da wata diya da sunan auren zumunci ba. wannan dalilin yasa suma suke tsoron shi suke kaf² da alamarin shi, duk da zamu iya cewa kaf cikin yaran family din maza babu mai kyauta da kyautatawa kannen shi kamar shi, domin duk abunda Ka nema a wajen shi ba zaka rasa ba, sau da yawa ma yaran basu fiya tunkarar iyayen su da wani bukata ba sai Ya Ak yana da kyakyawar alaqa da kannen shi harda ma yayyen sai dai rashin daukar raini. Saukin abun ma da kusan dukan su ba gari daya suke ba kowa yana inda yake amma hakan bai taba hadasu zumunci domin duk hutu Zaria sukeyin shi wani lokacin koba hutuma sukan zoma hajiya weakened. *bari mu takaita bayani akan Mai Jama'a anan dan tafiyar mu da nisa kuma har yanzun bamuyi komai ba tukun* Gaskiya in bakwayin comment ku sani posting zai koma sai yanda hali yayi😒. Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page 17 *Mu koma gefen su Ameenatu* Idan mai karu bai manta ba a page 14 mun tsaya a inda Ameenatu ke cewa. "Daga can kuma gidan su Besty zamu nufa, dan haka zuwa gidan su Besty cancel ba wannan maganar a yanzun, Daga nan muna gama siyan awarar Tudun Wada zamu koma dan gara muje muyi hakuri da halin Hajiya damu koma Sarki ya hadamu kwana daki guda da karnukan shi dan Wallahi bani ba kwanan cell nikam" *Hajiya gamu nan tafe gareki* ta fadi hakan a yayin da ta damki hannun Meelat sukaci gaba da tafiya zuwa inda su Moon suke, Can suka hango su gaban kaskon mai awarar dake ta aikin suya awarar tana sallamar masu siya. "Kun siya awarar ne? " Meelat ta tambaya a yayin da suka karasa wajen. "Wanda ta kwashe bai kai na kudin muba dan koda muka zo akwai layi saida ta sallami na gaban mu tukun na, amma inta kwashe wannan kaskon zai ishemu" Aisha ta bata amsa, Tsugunno Meelat da Meenat sukayi a gaban kaskon duk kuwa da Cewar akwai tebiri na zama da aka tanadar ga masu siyan awarar musamman masu bukatar ci a wajen. Hannu ta mika cikin karamin kwandon da take zuba awarar inta kwaso shi daga mai dan ya tsane ta dauki guda biyu sannan ta dan gwali yaji ako wannen su, Mikama Meelat daya daga cikin awarar tayi sannan ta cusa dayar itama a baki duk da yankar awarar suna da girma ba laifi ba tareda damuwar cewa akwai Abu a cikin bakin taba ta mike dan karasawa kan bencin dasu Moon ke zaune tana mai cewa, "Ke Moon ..... Tudunnn wada faa...... zamuu... wucce daga nan dan an yanka ta tashi" Haka maganar ke fita a har harde dan tana magana ne tana kuma taunar awarar dake cikin bakin nata. "Ke dai wallahi kalar ki daban ne Meenal to sai kace wani dole sai kinyi maganar kin cusa awara a baki kina magana kamar wacce aka shake ni ban ma fahimci abinda kikace da kyauba, naji kamar kince Tudun Wada komai ma ohon miki dai" Aisha ke cewa tana hararar Meenal din, Bata amsata ba sai bayan data gama hadiyar awarar tukun ta bata amsa da cewa, "Eh cewa nayi Tudun wada zamu wuce daga nan" Ba tareda Moon ta bari takai karshen maganar ba ta katseta da cewa "yin me kuma a gidan Hajiya? Kin sani sarai cewa tsohuwar nan da zarar Ka rabi inda take saita kirkiro wani abunda zatayi wanda ran mutum zai baci a banza ya su Aunty Sas su kuma suyi tasa mutane yin wadansu unnecessary ayuka, ni bazan hanaki zuwa ba inkin tashi amma nidai bada niba, Kuma bari kiji inma tsoro ne yasa zaki gudu can to wallahi Ina fada miki gara miki gidan Malam koba komai nasan komai kika taro zaiyi tsaye wajen kareki dan in har gidan Hajiya ne to Ina miki albishir da cewa kowaye zai tsaya miki Ya AK bazaiji kunya ko nauyin rugurguza kasusuwan jikin ki a gaban su Baba Usman ba" Moon takai karshen jawabin ta tana mai mikewa tsaye, "Mai awara ki kwashe mana sauran haka ni bana son wanda ya soyu sosai kuma yajin a Leda zaki kulla mana kuma karki mana kauron yaji dan yau dai mu muka siye miki awarar shima Albasa da kabejin daban² zaki kullasu karki hada su waje daya" Da "to" mai awarar ta amsa tana ci gaba da kirga musu awarar dan yau dai kam ita tafito a sa'a awarar dubu da dari biyar suka siyafa ko Ina zasu kaita oho, bata yi nawa wajen hade musu komai a cikin Leda ba Sannan ta mika ma Moon. Bayan tashin Moon ko Aisha ne ta fuskanci Meenat tana mai cewa. "Kin san Allah Sister komai zai faru gara ayishi anan muddin muka kwasa jiki zuwa gidan can tofa yau sunan mu sorry dama ace Dan Mai Karfi baya nan ne da sauki amma wallahi a yanzun kam gidan nan baya ziyuwa ke dan baki taba shiga komar Ya AK bane shi yasa har kike mararin zuwa can a yayin da kika tono kura to ki sani in tsoron ki kare can in kika je hannun mayun wacin zaki zaki afka, Meelat tashi mu tafi" Ta fada tana sauke ajiyar zuciya. Cigaba da tafiya sukayi batareda daya cikin su ta Kara tankawa ba har saida suka danyi nisa kadan daga wajen mai awarar, Moon ce ta jefo tambaya kai tsaye jin babu wacce tace wani abu cikin su. "Baku bamu labarin abunda ya faru a station din bayan kun kai yaron ba? Ko kuma su police din haka nan suka amshe shi ba tareda sun bincike juba? " Gama tambayar nata keda wuya taja ta tsaya tana mai karema su biyun kallo, Kauda kai Meenal tayi batare da ta bata amsa ba, Meelat ce tayi karfin halin zayyana musu yanda abun ya faru harda ma haduwar su da kwaro yayin fitowar su a station din. Hummm kawai Moon ta iya cewa kafin wata cikin su ta samu zarafin magana wayar Aisha dake rike a hannun ta ya fara ringing ba kowa ke Kira ba sai Momy Hauwa, "Wake kiran ki? " Meenal ta tambaya. "Momy Hauwa" Aishan ta bata amsa, "Dauka kiji me zata ce" Meenal din ta bata umarni, "Assalamu Alaikum Momy" Acan gefen kuma bayan Momy ta amsane ta daura da cewa "Kuna Ina ne wai harna dawo tun dazun banga kun dawo ba, badai kuma daga gidan mashkur din wani wajen daban Meenal taja ku zuwa ba dan ga Maryam nan tazo tun dazun wai take kiran wayoyin su bata samu nima kuma na gwada kira baije ba, ku dawo gida haka yawon ya isa" "To" Aisha ta amsa dashi tana mai yanke wayar, "Momy tace mu koma gida dan Maryam tana gidan tun dazun ta Kira wayar ku duba bata samu ba, kuma da alama dai babu abinda yake faruwa a gidan, Ina nufin banji alamun bacin rai a muryan Momyn ba dan nasan da abinda ya faru yakai gidan to tabbas dole ranta zai baci, Dan haka muje gidan kawai ai dama hausawa sunce in zakasha giya kasha ta dubu, Kuma da kuka kashe wayoyi taya zaku san abinda ke faruwa" Jiyawa tayi ta kalli Meenal sannan ta daura da cewa ni ai nayi zaton cewa gwaskiya bata tsoron kowa Ashe dai akuyace da fatar kura" Ta karasa fadan hakan cikin dariya, "Wai ma hijira zuwa gidan Hajiya turkashi lallai Babyn nan har yanzun labarin Mai Jama'a kawai kikeji, kin dauki dan mutane kin kaima police da sunan tsuntuwa sannan dan wani ya ganki shine kike zaton neman tsira a gidan mai shara'a! Lallai wanna shine ganganci Marin mace da magariba, Toya yanzun kin shirya komawa gidan ne ko har yanzun kina kan bakanki na tafiya Tudun wadan? Dan in sani kinga sai in diba miki awarar ki kiyi guzurin tafiya ala bashshi in kinje jiki ya miki tsami sai muzo mu dunga miki tuwon kasa" Dariya su ukun suka sa Itako gwaskiyar dogon tsaki taja, "Kuzo mu wuce gida kar awarar nan ta huce" Ta fadi hakan a sa'ilin da ta ciro wayarta daga cikin jakarta ta kunna, Meelat ce tace "Meenal bai kamata mu wuce ba tareda sanin halin da yaron nan yake ciki bafa, Duk da nasan bazai yuwu mu koma station dinba amma nidai bazan so mu tafi mu barshi a can ba Ina ganin zaifi dacewa ko wani ne mu wakilta ya leka mana station din kinji" Ta karasa fada cikin sanyin jiki. "To ya kike ganin za'ayi? " Meenal din ta tambaya, "Mu shiga gidan su Sakina in tana nan sai mu wakilta ta taje ta dubo kin san Yayan ta Lawal police ne kamar ma anan ganuwa yake aiki dan haka nasan shiga cikin station din bazai bata wahala ba kuma suma police din bazasu zargeta ba. "To mu karasa gidan Allah yasa tana nan" Cesar Meenat. Da yike gidan baida tazara mai tsayi da inda suke nan da nan suka Samu isa gidan, sun kumayi sa'a sun isketa basu bata lokaci ba dan ko zama basuyi ba da yike ma Allah ya taimake su mutanen gidan basa nan ita ma Sakinar tace musu bata dade da dawowa ba wai sunje kwarbai biki ne, babu bata lokaci suka zaiyane mata kaf din abinda ya faru da kuma abinda suke bukatar tayi musu na zuwa station din danta binciko musu halin da ake ciki, To da yike dai dama ita dasu din duk zamu ne ta tadda muje mu ba tareda wani nazari ba amsa bukatar su dan haka suka kara rankaya wa zuwa station din........ Kar a manta a dunga sharing please 🤍 #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page 18 ******* A cikin wani lungu da yake nan daura da gidan su Sakina kafin a karasa ga police station din Meenat! Meela!! da Aisha suka labe yayin da Sakina da Moon suka karasa cikin station din, Batareda da ko dar ba kai tsaye suka shige station din domin dama ita Sakina ta saba da police din wajen saboda Yayan ta dake aiki a wajen abunda yasa ta samu karfin zuwa din ma dan tasan baya wajen ne domin tare suka dawo daga kwarbai bayan ya sauke tane ya wuce unguwan kaya zai kai wata yayar su gida. Da sallama suka shiga kasancewar ta hango su Musa ne yanzu a bakin aiki, Bayan gaisuwa ya biyo bayane take tambayar su cewar, "Ya'yana yana ciki kuwa ? Ina ta kiran wayar shi bata shiga" "Tab ai rabon shi da office tun safe, ya akayi hala?" Musa ya tambaya, "no dama zai mai dani kwarbai ne kuma nayi ta kiran wayar shi bai shiga ba shi yasa nace bari inzo in same shi anan to ashe ma baya nan din" "Baya nan kam gaskiya, Kice baku gama bikin ba kenan? itama wannan bakuwar bikin tazo kenan? Ah to ai in haka ne inshi officer baya nan ga wani Ya'yan koni basai in wakilce shi in mai daku gidan bikin ba". Dariyar rainin hankali Moon tayi tana mai rufe fuskarta a zuciyarta tace hooo maza kenan ai dama ance in kina da kishi kar ki yarda kiyi soyayya da wadan nan mutanen, mawaki ko jarumin film, Likita, police,Telan mata da kuma banker. A fili kuwa cewa tayi.. "Haba Ya officer ya zamu dauke Ka a bakin aiki kuma kaida ke on duty kaga ni bama can zan komaba ita kadaice mai komawa rakota nayi ta duba shi, dan dama ni gida zan wuce daga nan, Mu wuce Sakina tunda bamu same shiba," Har sun juya da niyyar ficewa daga wajen kuma sai Moon ta juyo idon ta kirr cikin na officer Musa fuskarta cike da alhini take cewa, "Ya Officer niko dazun a saman layin mu naji ana cewa wai wasu sun tsinci wani yaro kamar ma ance nan aka kawo yaron koh? " "Subhanallah yaro kuma aka tsinta koya bace ne bai gane gida ba? " Sakina ta jefo ma Moon tambayar itama fuskanta cike da alhinin abunda Moon din tace na tsuntuwar yaro. "Ke karamin yaro nefa akace nidai ban ganshi ba, amma ance nan aka kawo shi dan wai wadanda suka tsince shi din ba yan nan unguwan bane akace ko Ya officer?". Eh! Eh!! Eh wallahi haka ne kuma wallahi bakuga yaron ba, karamin yarone mai shan nono duk da koda suka kawo shi mu bama nan" Ya fada a dan rikice dan shi so yayi dama da yace zai mai dasu kwarbai yadan yad'a manufar shi a wajen wannan kyaky kyawar furen da Sakina ta kawo musu office yau dan shifa wallahi ya kyasa ai in bai yad'a manufarshi bama lallai zai tabbata marar rabo, gashi tun bai gama kare mata kallo ba ta fara fadin su tafi. Ba tareda Moon tabar shi ya karashe basu labarin ba ta katse shi da sallallami, Muhamnadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wa Sallam , kinji koh wallahi ashe da gaske ne dai, oh Allah sarki wallahi har ya bani tausayi nasan itama uwar shi tana can cikin tashin hankali dan wallahi bacewar yaro ba dadi, to ina yaron yake ko an gano iyayen nashi ne? "Ayya ai da yake ma abun yazo da sauki wai ashe ma yaron dan nan layin da sukace matar ta basu shine, dan yaron ma dan makotar su Azumi mai shinkafa ne ashe , dazun nan kafin ku shigo Baban shi yazo shida wasu ya karbe shi," Wai ah to masha Allah tunda anga iyayen shi" Sakina ta fadi hakan tana ma Moon signa akan su tafi, To Ya officer bari mu wuce" suka fada a yayin da suke juyawa da niyyar barin station din. "Bakiji ba" ya fada yana sosa keya, juyowa sukayi suna kallon shi, "Dama cewa zanyi muje in taka muku" Ok tunda ka bukata godiya muke" Signal yama abokin aikin shi kafin ya rufa musu baya. "Ya sunan kawar takine Sakina? "Maimoon" ta bashi amsa a yayin da su biyun sukaja burki. Allah Ya officer daka koma kawai karmu takura ka, nizan taka mata kadan kafin in samu abun hawa" cewar Sakina. To Malama Maimoon a gaida gida sai dai inba damuwa zanba kawarki sako zuwa gobe, mungode da ziyara fa" Ya karasa fada yayin da ya sanya hannu cikin aljihu ya ciro kudi yan dubu² guda biyu ya mikama Sakina, "To ga wannan ku hau mashin," Nokewa tayi ba tareda ta amsa ba take cewa, "kai Ya Musa wallahi kabar kudin ka mungode" "Ki amsa malama bana son musu" Tana amsa kuwa ya juya ya koma bakin aikin shi yana mai dagama Moon hannu alamun bye bye. Murza kudin Sakina tayi domin Kara tabbatar wa, shin dubu biyu ne ko dari biyar ² ne guda biyu, dan tsayin rayuwarta daga lokacin da tasan Musa zuwa jiya bai taba mata kyauta koda ta naira biyar bace kuwa, lallai maza ma sai a barsu wato tunda yaga kyakykyawar fulawa bari ya bata cin hanci aiko ya fadi kasa ba nauyi wallahi dan wallahi da kudin shi yau zataci tsiren Dan Asabe me nama, dan Allah me yakai yin abota da abu mai kyau dadi, Murmushin daya kasa yankewa a fuskarta ne yasa Moon magantawa, "Yane hala? Naga sai faman murmusawa kike! " "Ke Moon wallahi maza muna fukai ne masu fiffike, Wai kin san mutumin nan tun da nike dashi ko kwandala tashi ban taba ciba shine yau dan ya ganki harda mana kyautar 2k, Dubu biyu fa Allah na tabbata yau sai yayi zazzabin kudin nan daya fitar, saukin tama ba Kara ganin ki zaiyi ba ko banza munci banza wallahi" Raba kudin tayi ta dauki dubu taba Moon dubu daya, Bayan sun karasa wajen da suka bar su Meenal kaf abunda ya faru a station din suka zaiyana musu da alama dai maganar bata koma can gidan Malam ba a zaton su, Nan suka rabu da Sakina ta koma gida suma suka dauki hanya. "Dan Allah mubi ta kofar gidan sarki in Kara kallon gidan one last time please" Cewar Moon. Mtwss Meenal taja dogon tsaki "ai kuma sai kiyi mayya kawai ga hanya nan in kinkai sai kiyima masu gadin gidan magana su bude miki gidan ki zauna" A kofar masallaci suka hango Ibrahim Kwaro da Sarki da wani da basu san kowaye ba zaune, "Kai innalillahi Allah yasa Kwaro bai fadama Sarki ya ganmu a station ba" Cewar Meelat. Kiran sunan Sarki da tayi kwarai yasa gaban Meelat faduwa amma ta dake batareda nuna razana ba ta amsa mata da cewa, "To sai me dan ya fada Ina cewa dai Sarkin ba mala'ikan daukar rai bane? Ni ku daga kafa please awarar nan fa ta fara sanyi wallahi" "Oh ke ta awara ma kike? Allah yasa dai ki kika amshi dan mutane kika mikashi police station ninawa rakiya ne kawai su kuma su Aisha yan kallo ne kinga ko ai ko hukunci za'a mana naki sai yafi namu yawa". ***** Kuzo nan" A firgice suka juya dan ganin wake kiran su, dan wallahi cece kucen da sukeyi gaba daya ya dauke musu hankali har sun gota Sarki batareda sun lura ba, "Naan naa'aam" Eh kuzo nan nace ku biyun nan ku kuwuce gida" Kwaro ya basu amsa. Kallon kallo sukayi a tsakanin su sannan Meenat ta mikama Moon ledar awarar dake hannun ta da Jakarta, "Ku wuce da wannan karkuce ma kowa komai muma zamu shigo yanzun in ya gama nashi binciken" Juyawa sukayi zuwa gidan cikin jimami, Hannun su cikin na juna suka karasa inda su Sarkin ke zaune, Kai Jama'a ina ma amfanin kinji wallahi dakewa kawai sukayi amma dukan su a tsorace suke, "Ina wunin ku" Sukayi saurin fadi dan gudun karsu karama kansu laifi, "Lafiya"Sarki ya amsa dashi yana mai kauda kanshi zuwa gefen da dayan mutumin yake sunaci gaba da tattaunawa, "Nine ai nayi kiran ku ku matso nan" Kwaro ya fada, Matsawa inda yaken sukayi kamar yanda ya bukata harda rage tsayi zuwa tsugun no kamar wasu na Allah, "Me kukaje yi a ganuwa dazun dana ganku? " Shiru sukayi aka rasa mai bashi amsa a cikin su, "Daku nike magana fa kuma na tabbata kuba kurame bane koh? Ku fadamin mai karamin yaro ya muku kuka kaishi police station da sunan tsintuwa alhalin ba hakan bane?" Ya Kara jefo musu tambayar, "Mufa tsintar shi mukayi" Meenal ta bashi amsa, "Karya kukeyi, ku fadamin me yasa kuka aikata abinda kuka aikata din? In ba haka ba jikin ku zai fada muku, " "Kayi hakuri dan Allah wallahi mun dena daga yau bazamu karaba" Cewar Meelat dan itafa a duniya bata kaunar abinda zai tabi lafiyar jikin ta wallah, "Ni ai ba hakurin ku na nema ba dalilin dayasa kukayi hakan nike son sani" Meenal ce ta amsa mishi da cewa, "Aini dama koda na kai yaron can nayi hakan ne saboda in Baban shi ya amso shi gobe koda bacci Maman yaron keyi in yaron na kuka bazai tsallake su ya fice a gidan ya barta da dawainiyar yaron ita kadai ba, kuma ai dan ma mu ne taba yaron fisabilillahi da ace masu Satan yarane taba shi bashi kenan ba, kawai daga ganin mu zamu wuce ta kofar gidan ta saita dauki danta ta bamu, yanzun ai sai suje su sulhunta yanda zasuci gaba da rainon yaron atoh, gobe ai bazata Kara bama wasu shiba ko kukan me yake kuwa shima Uban kuma dole ya koyi raino daga yau" Ta karasa fada tana kauda kanta gefe, Ba Kwaro ne kadai ya cika da zallar mamakin karfin halin yarinyar ba harda Meelat ma kallon mamaki take mata. "Me yake faruwa anan? " Cewar Sarki daya maido hankalin shi kansu bayan tashin dayan mutumin, "Ku sai yanzun kuke dawowa tun fitar safe da kukayi? " Ya Kara tambaya, "To ai ya Mashkur ne yace mu jirashi ya dawo sai mu wuce gida kuma ko yanzun ma bai dawo ba muka taho," Meelat ta bashi amsa, ita ko Meenal a dubarance take ma Kwaro magiya akan ya rufa musu asiri karya fadama Sarki abinda suka aikata. Kuje har gida zuwa gobe kuba matar hakuri, kuma in bakuje ba nida kune wallahi" Cewar Kwaro, a yayin da ya amsa Meenal da kai cewar bazai fadama Sarki ba, Ku tashi ku wuce gida" Sarki ya basu umarni, Kamar wadanda suke kan kaya haka suka zabura ba tareda bata lokaci ba suka bace awajen Wai Allah ansha da kyar. Koda suka shiga gida kuwa koda wasa basu tada maganar ba, Abubuwa da yawa sun faru a wannan kwanakin ciki su harda zuwa gidan Zainab din Bala uwar yaro bada hakuri duk da basuje a ranar da Kwaro yace ba, Sannan ba fashi kullum sai sunje tudun wada, dasu aketa hidimar biki sai dai boyewa suke da sunga an fara taso su gaba da yawan aike, Tsakanin Meelat da Musty kuwa kullum ko basuga juna ba sukan zanta ta waya ko sakon text albarkhacin shi yasa duk wani program da aka shirya na biki sai da suka samu halarta kamar yanda suka tsara. An gama hidimar biki lafiya su Maimoon sun koma garuruwan su sai dai koda yaushe sukan zanta a waya, sukanji nishadi a sa'ilin da suka tuna irin shirmen da suka shuka na zuwan su wannan biki da bashi goguwa a cikin tarihin rayuwar su, wanda ya kasance biki na farko da Meenal ta taba shiga ciki akayi komai da ita ba kamar lokacin baya da takeyi kamar me tsoro mutane ba, babban abinda in suka tuna suke kara sadaqarwa da iya shegen Meenal shine ranar yinin bikin da tasa ma yan matan da sukazo ma Mai Jama'a biki maganin amai a cikin Lemun 5alive suka sha suka dunga competition din amai gwanin tausayi daga karshe sai cewa akayi wai lemun ne yayi expired bayan ba hakan bane. Ana daurewa ana comment da sharing please. #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page 19 ........... Zaune take akan kujerar daya kasance mazaunin ta na din-din-din a cikin ajin nasu yayin da ta yada kanta akan tebur din dake gaban ta sai faman ciccije bakin ta take sakama koh mararta data kejin tana ta kara daure mata kamar yanda ta saba mata aduk sanda lokacin yin hailarta yazo, kwata² batayi zaton zuwan nashi a wannan lokacin ba domin a lissafin ta ko zaizo mata sai sati na gaba dan haka bata fito da shiri kamar yanda ta saba shirya ma zuwan bakon nata ba, dan hatta da pad da take yawo dashi aduk sa'ilin datake tsammatan zuwan period din nata yawancin lokuta a cikin jakanta domin yin kunzugu yau bata da koh daya a cikin jakar nata, gashi a hankali mai makon ciwon ya ragu sai karuwa takejin yanayi alhalin lafiya lau ta fito daga gida, agogon hannun ta takallah sai dai har yanzun akwai sauran lokaci akallah kusan awa uku kafin lokacin tashin su zuwa gida, Tasani sarai cewa ba lallai ta iya jure zafin ciwon zuwa anjima gashi kuma daga Jamila har Maryam basa ajin dan a cikin su ita ce kadai ke science, "Amina Mukhtar" Malamin chemistry din nasu ya kira sunan ta, Bata iya amsawa ba illah dago kanta da tayi ta kalleshi da idanuwan ta da suka farayin ja alamun dake tabbatar da cewa akwai abinda ke damunta. "Are You alright? " Ya tambaya. Bata iya bashi amsa da baki ba illah girgiza kanta da tayi kawai ta Kara maida kan nata, To shima dai ganin cewa in ma ciwo take ai tasan inda zataje ta amshi magani yasa bai Kara bi takanta ba har ya gama koyarwar shi ya fita a cikin class din, Sakina ce ta baro sit dinta zuwa na Meenal dan tun tuni take lura da ita ta tabbatar da wuya inba ciwon cikin ta na fama bane ya tashi mata ba. "Meenal ya kamata ki tashi kije gida fa tun kafin ki galabaita muje in raka ki ki dauki permission dan nasan bazaki iya jurewa har a tashi ba" cewar Sakina, "Kira min su Maryam" inji Meenal din, "Ah-ah tashi dai ki gani in kamaki" Ta furta hakan a yayin da ta mika hannu ta dauko jakar Meenal din na makaranta dake gefe, sauran yan ajin ne suka taso kowa na tambayan meya samu Meenal din, ita dai Sakina bata da lafiya kawai ta iya ce musu, "to mu kaita clinic mana" cewar daya daga cikin daliban yayin da sauran sai faman Sannu suke mata da addu'ar samun lafiya, Da kyar ta samu ta iya mikewa bayan sakina da wata yarinya sun tallabo ta, "karku kaini clinic gida zanje" ta samu ta iya furtawa da kyar dan zuwa lokacin dauriya kawai take amma gaba daya ji take kamar ana sanya igiya ana daure mata marar nata tsabagen yanda take jin ciwon, bafa karamin dauriya takeyi ba wajen hana kanta kuka a halin da take ciki, dauriya na duniya ta aro ta daura ma kanta gudun kar tayi kuka da ihu a gaban yan ajin su su rainata illah dai matsar hawaye kawai da takeyi su kuma suna Kara mata sannun a haka har suka samu suka karasa Staff room domin daukar permission, Aunty Hajara daya daga cikin Malaman su mata kawai su ka samu a wajen tanayin marking din wasu littafai, Da kulawa ta dago tana kallon su ganin kusan gaba daya yan ajin ne suka rako Meenal din "lafiya meya sameta? " ta tambaya a yayin da tabar abinda takeyi ta taso zuwa inda suke rirrike da Aminatun da take ta kokarin dukewa zuwa kasa, "Lukman Kira Malam Sa'idu yazo ya wuce da ita gida" A tsinke su Maryam suka shigo cikin office din "Meenal meya sameki? Ciwon cikin ne ya tashi?"suke tambaya duk sun gigice dan su ganau ne ba jiyau ba na irin yanda take wahala da ciwon marar ta duk wata, "Aunty Hajara kin Kira Mommy ne? " Maryam ta tambaya, "Ban Kira kowa ba nadai tura Lukman ya Kira Malam Sa'idu sai ya kaita gida" Wayarta dake gefe ta dauko dan ya kamata ta tambayi Maman Aminan taji ko za'a wuce da Aminan asibiti ne sai dai kuma Kira uku ta mata amma duk kiran basu jeba, "Ban samu Maman ta a waya ba" Maryam ce tace to tunda ba'a sameta ba akai Meenal din gida kawai, Lukman ne ya shigo Malam Sa'idu biye dashi a baya. "Ku fito da ita ku kuma ku koma class" yace a yayin da ya juya zuwa inda motar shi ke ajiye, Fita sauran student din sukayi bayan sun mata fatan samun lafiya su kuma su Jamila da Aunty Hajara suka kama Meenal din da zuwa yanzun ko iya mikewa batayi balle harta tsaya akan kafafun ta, haka dai suka tallabeta zuwa cikin Motan, Aiko dai uwar Malam kamar jira take a shigar da ita cikin motar dan tun basu bar cikin makarantar ba ta fara ihun kuka tana tumurmusa a jikin su Maryam kamar wata mai nakuda, Fadi take tana karawa cikin ihun kuka... waiyo Allah cikin ta tun tana kiran ciki har ta koma fadin waiyo Allah mararta zai balle shike nan mutuwa zatayi, haka dai ta dunga sambatu barkatai dan dama hakan yake mata gaba daya in ciwonya taso saita fice a hayyacin ta tayi ta surutai marasa kan gado, tun su Meelat na mata sannu har suma dai ganin wahalar da take sha yasa suka fashe da kuka suna kwantar mata da hankalin cewa bazata mutu ba zataji sauki ne, gaba daya haka suka cika motar da ihun kukan su yanda kasan duka su ukun ne masu ciwon, "Dan Allah ni kumin shiru yan rainin wayau kawai ku barni inyi kuka na kunzo kuna ta cikamin kunne da naku ihun kukan, Ko ubanwa yace muku naku kukan zai ragemin ciwon ne, Waiyo Allah Baba Malam dan Allah driver ka tuka motar nan da sauri kafin mala'ikun mutuwa su karaso" tana damke da marar nata fa amma sai gashi tana bude kofofin hancin ta tana shin shine shin shine, "Bakuji kamshin turaren al miski ba? Allah kuwa suna kusa da motar nan, ni kayi sauri ka kaini gida direba Ina jin ina kusa gab da suma, saura fa kadan in some karku barni in suma wallahi suma kanin mutuwa ne, ka kara gudu karsu Kara so su dauki raina ban roki yan gidan mu gafara ba, kunga fa kana nan yaran dake gidan mu dukan su nikeyi in sunmin laifi kar fa yazo ace wata rana sun min Allah ya isa a bayan idona." Kara fashewa tayi da kuka, "Waiyo Allah ni Aminatu Ashe mutuwa na a kusa yake shi yasa kwana biyu niketa mafarkan koraye da fararen furanni," cikin kuka sosai sakama kon marar nata data Kara murda mata taci gaba da cewa. "Allah sarki ni Ashe mutuwa zanyi tun ban gama sakandire ba, jama'a in na mutu wazai ginama Baba Malam gida a Abuja? Waiyo Allah zan mutu ko saudiya banje ba,banje hajji ba balle umara, banje na ziyarci ka'aba ba balle har in taka madina, Hajiya innah ke kikace wannan shekarar dani zaki inyo umara in zaki duba Abba Ahmad, waiyo Allah sarkar zinare ta dana aje sai da sallah zansa" (Kai jama'a, ku matsofa inga rabon gado uwar Malam zata yi karta manta damu a lissafi 🥳) Cikin sheshshekar kuka Maryam tace "Meenal kiyi shiru dan Allah kince mu daina kuka dan bazai rage miki ciwo ba, amma ke kuma baki dena naki kukan ba bayan kuma kin san naki kukan ke jawo wa muma muyi kuka dan Allah ki dena surutan nan babu kyau kiyi Addu'a" Sai da taja majina sannan ta maida kallon ta inda Meelat da itama fuskarta yayi jagab da hawaye tana kwabe fuska tace, "Besty kina jinta koh zagina fa take son yi da wayau, So take tace na fiye raki kuma wallahi ba raki bane sosai marar kemin ciwo fa, sa hannun ki kiji yanda fatar wajen tayi Zafi waya sani ma ko gobarace ta kama a ciki" Kamo hannun Meelat din tayi ta kai kan marar nata ta matse, "Ki danna min dan Allah karya fashe" Kafin su isa gida gaba daya ta riga ta gama fita hayyacin ta, har cikin farfajiyar gidan Malam Sa'idu ya shigar da motar shi da yike ranar aiki ne kuma gaba daya yaran gidan suna makaranta hakan yasa ba yaro ko daya a harabar gidan, Kashe motar yayi bayan ya faka sannan ya juyo yana tambayan su Maryam cewa wanne ne sasan su Aminan? "Wajen Baba Malam zamu shiga da ita dan dazun da safe tace min Mommy taje Kaduna kuma nasan bai isa ace ta dawo ba" Allah da ikon shi suna cikin maganar saiga shigowar Sarki cikin gidan da alama yazoma Malam sallama zai koma bakin aikine domin ko shirye yake tsaf cikin kakin shi na aiki, baima lura dasu ba har sai da ya nemi gifta su dan koda ya shigo dama wayace a kunnen shi, "Assalamu Alaikum bawan Allah nace ko zaka taimaka naga kamar cikin gidan zaka shiga, Amina Mukhtar ce bata da lafiya ni din Malamin makarantar sune" Ya karashe fada A yayin da ya mikama Sarki hannu domin suyi musabaha. Duk yanda su Meelat ke tsoron shi yau ba wannan batu domin suna an Karewa dashi a wajen tauni sukayi azamar fitowa daga motar, "Ya Sarki dan Allah ka taimake mu Meenal zata mutu zoka gani ta dena motsi" Jan hannun shi Meelat tayi suka zagaya ta daya gefen inda Maryam ke rungume da Meenal din data dena motsi zuwa lokacin sai faman jijjigata takeyi tana fadin ta tashi karta mutu ta barsu, ita ko Aunty Hajara tsabar rudewa yasa gaba daya ta kasa aiwatar da komai zaune kawai take a cikin motar itama tana hawaye, dan tsayin rayuwarta bata taba ganin inda ciwon mara ke galabaitar da mace irin haka ba, Ashe haka wasu mata ke faman shan wahala, lallai duk mace da period ke zuwa mata ba tareda ko wani kalar laulayi ba to taci gaba da mika godiyarta zuwaga ubangijin al'arshi. "Ibrahim! Ibrahim!! Kai Kwaro!!!!!! Wai kana cikin rijiyane da baka jin Kira" da gudu kwaro ya shigo gidan, "A fuwan Sarki " Bai tsaya sauraron abinda kwaro zaice ba yace ya kunna mota yanzun nan, shi kuma ya zura hannayen shi cikin motar ya dauko Meenal da batama san wainar da ake toya waba yanzun kam. Sai gata wata yar tsurut a hannun shi Kwala kiran sunan Kwaro da yayi da muryar shi da dama koya yayi magana da ita na nesa dashi ma yana iyaji balle kuma yau daya budeta masha Allah, Wannan dalili yasa tuni hankalin mutanen gidan ya dawo zuwa farfajiyar gidan domin ko ba'a fada musu ba sun san muryar waye amon muryar tashi kuma karara ta nuna cewa ba lafiya ba, Malam ne ya fara fitowa kafin sauran jama'ar gidan a dai dai sanda Sarki ya ciro Meenal daga cikin motar Malam Sa'idu, ba tareda ya tsaya yinma kowa bayani ba yayi waje abinshi cike da zafin naman da akasan sojiji dashi, su Meelat suka rufa mishi baya suna kuka, Aunty Hajara ce ta fito daga cikin motar tana mai gabatar musu da kanta a matsayin Malamar makarantar su Meenal din da kuma abinda ya samu Meenal sannan ta mikama yan gidan jakan Meenal din a sa'ilin da suke masu fatan Allah yaba Meenal din lafiya su kuma suka juya, "Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un" Malam ya fada a yayin da yakai zaune a wata kujera, Allah kadai yasan yanda yakeji a lokacin nan. "Malam ai ba zama zakayi ba kamata yayi mubi bayan su, bakaga yanda Sarki ya fita da ita bane ko motsi fa batayi, kai innalillahi jama'a yaushe yarinyar nan zata huta da ciwon nan da yake neman zaman mata tamkar mahadin rayuwa? Ace duk wata babu fashi sai tayi shi" Ta karasa fada tana matsan kwalla, dan wallahi ji take da tana da halin da zata raba Aminatu da ciwon nan da tuni tayi. Dagowa Malam yayi a zafafe yana mata wani irin kallo yace, "Oh kema kin zama karamar yarinya kenan da zaki zo ki sani gaba kina min kuka a gaban sirikan ki" Maida duban shi yayi zuwa kan sauran jama'ar gidan da duk sukayi cirko² yasan tabbas da baya gidan da tuni sunbi bayan Sarki. "Tsayuwar me kukeyi toh ku koma ciki zanbi bayan su yanzun" "Ah² Malam karkace zakayi tuki da kanka bari dai a Kira wani cikin yaran nan suzo su tukaka inyaso mu ma biyo bayan ku zuwa anjima, kaji" Aunty Murja data kara waya tana magana basu san kowa ta Kira bane, bayan ta sauke wayar take cewa. "Na Kira Yayan su Sa'eed zai zo yanzun bari in dauko mayafi sai mu biyoku a baya dan Allah Baba Malam karka hanamu zuwa komun zauna hankulan mu bazasu kwanta ba" Tana karasa fadin hakan ta juya sasanta tana goge hawaye, suma sauran matan haka suka juya kowaccen su jikin su a mace. Ficewa Baba Malam yayi zuwa waje dan ya jira zuwan Sa'eed. A gefen Sarki ko koda ya fito waje dauke da Aminatu ya iske Kwaro ya kunna motar dan haka bai bata lokaci ba ya shige gidan baya, Meelat da Maryam dake biye dashi a bayane suma suka bude gaban motar dukan su biyun suka shige a yayin da suka kasa dauke idanuwan su akan Meenal kuma har zuwa lokacin basu bar kukan da suke ba, Wata uwar tsawa ya daka musu mai kad'a hantar ciki wanda yasa suka shige cikin jikin juna suka cikwuikuye kansu, Tsawar da harta Kwaro dake tuki sai da ya kusan sakin kambun motar. "In bazaku min shiru ba ku fice in daina jin muryoyin ku kai kuma Malam kar ka maida hankali akan tukin ka ka dage ka watsar damu kaga sai muyi mutuwar kasko tunda haka kake muradi in kuma tukin ne baka iyawa kaima ka fice ni zanja motar bana son shiririta". Aiko gum su Meelat sukayi ba wacce ta karayin koda nishi mai karfi ne a cikin su. Sorry for am late😒 #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu Wannan page din zato da sammatsi idan mai karatu yazo karatu ya tsallake duka na saman ya koma can kan na karshen shine cikakken page 20 ayi hakuri. a daure a dunga comment atoh. ```Page 20 can na kasan karshe zaku karanta ba sauran ba. ................. **** Ina zamu nufa Sarki?" Kwaro ya tambaya a yayin da suka fice daga cikin layin suka nausa kan babban titi, "Asibitin Dr Mubarak" Ya bashi amsa a takaice, Kuri Sarki ya kafe fuskar Meenal da kallo a son shi na gano ko tana numfashi ko kuma numfashin nata ya dauke! dan shifa tsakanin shi da Allah bazai so daga taimako yar mutane ta mace mishi a cikin mota ba, in ma macewar zatayi gara ta bari ya mikata hannun likitoci tukun, atoh dan bazai yarda tasa shi a bakin duniya ba. "Wai Ibrahim ba nace ka kara gudun motar nan bane? Numfashin yarinyar nan fa banga yana fita da kyau ba karta mace min a cikin mota," Maida duban shi yayi inda su Meelat suke rungume da juna "Ku fadamin wai ma meke damunta ne haka, wani irin ciwo ne wannan? Banji jikinta yayi zafi ba amma gashi sai zufa take hadawa,ko dama haka take nata ciwon? " To shi yanzun fisabilillahi so yake su fada mishi gaskiya ko ka'ka, kai jama'a ina ai gaskiyar nan kam bata faduwa a wannan lokacin dan ko *tuntuben harshe* by Surayyah.... Sukayi sukace ma Sarki period ke sata haka, lallai za'ayi balbalin bala'i tsakanin su da Meenal inta farka, yo sukam da kunya ta haifa Ina ma zasu iya fada mishi gaskiya. Dan haka sai suka fara kallon kallo a tsakanin su wannan na dungurin wannan an rasa mai bashi amsa a cikin su, "Baku nan ku suna ciwone kuma din ko wani kalan iskanci ne nike magana kuka kyaleni? " Ya tambaya a kausashe, Umm'ummm umm damaa damaaa muma muna cafeteria ne aka ce, akace mana wai waii Amina bata da lafiya, Suka hada baki wajen bashi amsa, sai Maryam ce ta kara da cewa, "Kuma wallahi muma bamu san mike damunta ba lafiya lau tazo makaranta da safe, har zuwa lokacin da akayi break bamuga alamar bata da lafiya ba koh Jamila? " "Eh Wallahi koni banga alamar ciwo a tareda ita ba, sai dai sai dai dama ummm dama tanayin irin wannan ciwon kuma Baba Malam ne ke mata Addu'a Mommy Hauwa kuma ta bata magani". Sai kuma suka fashe da kuka cikin kukan nasu sukaci gaba da fadin waiyo su Allah shi kenan Meenal zata mutu ta barsu. **** Sarki da kanshi ne ya cirota daga cikin motar bayan sun isa cikin asibitin, bai tsaya jiran wani abuba yayi cikin asibitin da ita dauke a hannun shi su Maryam suka rufa mishi baya, Ma'aikatan asibitin ne sukayi saurin taran shi a kokarin su nason su karbeta a hannun shi sai dai bai basu dama ba yaci gaba da kutsawa suna mishi jagora har zuwa emergency inda ya shimfideta a daya daga cikin gadajen dake dakin sannan ya juya ya fito domin ya basu damar gudanar da aikin su. Suko su Meelat gaba daya kasa zama sukayi gashi kaf cikin su babu mai waya a tareda ita dan dokar makarantar ne ba'a yarda dalibai suje da waya ba, inko kaje da ita har aka kwace tofa kai kajiyo, Kwaro daya biyo bayan su ne ganin su a tsats tsaye cikin rashin rashin sukuni yasa shi umartar su akan su samu waje su zauna yana mai Kara kwantar musu da hankali akan zata samu lafiya, Shiko Sarki fitowar shi daga emergency din yayi dai dai da karar da wayar shi ta dauka alamun Kira, "Malam" Ya ambata a bayyane kafin ya amsa kiran, "Assalamu Alaikum" a can bangaran Malam yake tambayar shi cewar suna wani asibiti ne dan gasu a hanyar zuwa, "Malam ai da bakayi wahalar fitowa ba, tunda Ina tare da ita zan kula da komai da za'a bukata dan yanzun haka ma tana ciki ana dubata nasan insha Allah zata samu lafiya bada dadewa ba" "Angode da kokari Malam Sufyan amma ai baza'ayi haka ba, kaida Kake kan hanyar komawa bakin aikin ka, ya kuma zakaje ka tare a asibity da sunan kula da mara lafiya kamar ba dangi a gari? Iyi ai bazai yuwu kai kuma ka tauye kanka ba koh, yanzun dai kuna wani asibitin ne dan gani nan tafe da Sa'eed " "Muna Asibitin Dr Mubarak" Sarki ya amsa ma Malam dashi gamida yanke kiran, yaso Malam ya zauna basai yaba kanshi wahalar zuwa ba domin dai ko zuwan yayi ba wani Abu zaiyi ba, sai dai yasan Malam bazai taba iya zama a gida cikin kwanciyar hankali ba alhalin Aminatu na asibiti kwance, yarinya kamar ita kadaice d'iya a cikin dangi, Ba'a dauki mintoci ba su Malam suka iso. "Malam Sufyan ai gara kuzo ku kama hanya kar kuyi dare duk da kace gobe jirgin hantsi zakabi zuwa Lagos nasan bazaka rasa yan kimtse²n da zakayi ayau inka isa Kaduna ba". To Baba Malam bari likitan ya fito muji ko ta farka in naga jikin da sauki sai mu kama hanya in kuma abun yayi tsanani sai a canza asibiti," "To ba laifi hakan ma, sannu da dawainiya kaji Allah dai ya maka albarkha ita kuma Allah ya bata lafiya, wallahi haka take fama da wannan ciwon na mara duk karshen wata magani dai babu kalar wanda bamuyi mata ba, kullum nida sauran mutan gidan tafe muke wajen nema mata maganin ciwon nan amma kaga dai har yanzun shiru, hatta uwarta dake kuri ita likitar mata ta gaza a al'amarin ciwon nan, kuma Innan su ta shaidamin tun fara al'adarta take fuskantar wannan kalubalen na ciwon mara mai tsanani, dama ni shirina nace nida kaina zan daukota zuwa asibiti dan so nike likitocin sumin Karin bayani akan ciwon nata dan gaskiya abun bana wasa bane, ita kuma uwar gaba daya banga alamar ta damu da wahalar da y'ar kesha ba dan har yanzun banji gamsas shiyar bayani daga gareta akan ciwon ba" Sai da ya dan goge zufan daya tsatstsafo wanda take nuna alamun cewa shima din a dame yake kwarai kafin yaci gaba da cewa, "Tun tashin yarinyar nan ita bamai yawan laulayi bane shi yasa in ciwon ya tashi duk sai tabi ta firgice, Allah Kasai yasan azabar da take sha yar karamar yarinya da ita" Fitowar daya daga cikin Nurse din dake kula da Aminatun ne yasa su Maryam mikewa sukayo wajen ta suna mai tambayar ta da cewa... "Ya jikin ta? Ta tashi kuwa? Meya sameta? " Haka sukaci gaba da jero ma nurse din tambayoyi ba kakkautawa, "Ah ah sister's ku kwantar da hankalin ku ya'r uwar ku zata samu lafiya nan bada jimawa ba Insha Allah dan yanzun hakama ta farka" Karasawa wajen Sarki tayi. "Ga wannan abubuwan da ake bukata ne ku amso zamuyi mata amfani dashi kafin Dr ya fito daga labour room" Alamu ya mata da hannu cewar ta mikama Kwaro takardar, Mikewa Sa'eed yayi "bani takardar in anso! Tana mika mishi takardar ita kuma ta koma ciki, Jin cewa Meenal ta farka yasa suka danji sa'ida a cikin zukatan su, nan da nan Sa'eed ya dawo, Nurse din dazun ne ta Kara fitowa ta amshi kayan ta koma ciki, Ba'a dauki lokaci ba su Aunty Murja suka iso asibitin gayya guda kamar wadan su masu kai Amarya, Da mamaki Malam yake kallon su, inba haukaba ya zasu kwaso iyalan gida gaba daya su taho suzo su tare a asibiti subar gida ba kowa alhalin yaran su na gab da dawowa daga makaranta, yanzun kuma Idan yace zaiyi magana sai sugar laifin shi suce ya fiye fada ko yanzun dai sunci albarkhacin Sarki ne amma Ana basu damar ganin Aminatun zai korasu su koma gida asibiti aiba gidan biki bane, dan haka bai iya ce musu komai ba Allah kauda kanshi ma da yayi ya mike da niyyar barin musu wajen, sai dai kuma had yayi taku daya biyu ya juyo garesu, "Ina fatan cewa babu wacce tayi gigin kiran Hauwa'u ko auta a cikin ku? " Dukan su dukar da kansu sukayi aka rasa mai bashi amsa dan ba wacce Zata so ya sauke haushin ganin su diyyy din da yayi a kanta, shifa Malam mai iya mishi sai Allah dai wallahi ko shakka babu da basu biyo bayan su ba ko ace wasu suzo wasu su zauna tabbas saiya samun abun magana cewa dan ba cikin yaransu ne d'aya ke ciwo ba shi yasa suka zauna a gida wato inta mutu ma oho, Amma gashi yanzun sun kwaso jiki sunzo sai wani daure fuska yakeyi Malam ho. Uwar gidan shi ne ta wakilci sauran da cewa, "Bamu kira Auta ba itama kuma Jiddan mun kirane dama muji ko Aminatun nada sauran maganin da take sha a gida dan mu taho dashi sai dai kuma bamu samu wayar nata ba har muka taho, ya jikin nagta? ta farka kuwa? " Bai tsaya bata amsa ba yasa kai ya fice su kuma sauran matan suka samu wajen zama suna tambayan su Maryam yaya jikin na Aminatu, Bayan zaman shiru da jiran tsammani da sukayi na wani lokaci Shannan ne wannan Nurse din ta Kara zuwa take fada musu cewar an canza ma Aminatun daki sai dai kuma sun mata allurar bacci bazsu so kuma hayani ya yasa ta farka da wuri ba, "Zamu iya ganin likitan daya kula da ita? " Sarki ya tambayi Nurse din, "Eh to bari in mishi magana, ku biyoni in nuna muku inda aka maida ita" Tace a yayin da ta juya zuwa wani hanyar daban ba wandavta fito daga ciki ba. "Kira Baba sai muje yaga likitan koh? " Sarki yace da Sa'eed, "To Ya'ya" Ya amsa a yayin da ya juya zuwa waje su kuma su Meelat tuni sun rufama Nurse baya zuwa dakin da aka kwantar da Meenal. #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page 20 ................. **** Ina zamu nufa Sarki?" Kwaro ya tambaya a yayin da suka fice daga cikin layin suka nausa kan babban titi, "Asibitin Dr Mubarak" Ya bashi amsa a takaice, Kuri Sarki ya kafe fuskar Meenal da kallo a son shi na gano ko tana numfashi ko kuma numfashin nata ya dauke! dan shifa tsakanin shi da Allah bazai so daga taimako yar mutane ta mace mishi a cikin mota ba, in ma macewar zatayi gara ta bari ya mikata hannun likitoci tukun, atoh dan bazai yarda tasa shi a bakin duniya ba. "Wai Ibrahim ba nace ka kara gudun motar nan bane? Numfashin yarinyar nan fa banga yana fita da kyau ba karta mace min a cikin mota," Maida duban shi yayi inda su Meelat suke rungume da juna "Ku fadamin wai ma meke damunta ne haka, wani irin ciwo ne wannan? Banji jikinta yayi zafi ba amma gashi sai zufa take hadawa,ko dama haka take nata ciwon? " To shi yanzun fisabilillahi so yake su fada mishi gaskiya ko ka'ka, kai jama'a ina ai gaskiyar nan kam bata faduwa a wannan lokacin dan ko *tuntuben harshe* by Surayyah.... Sukayi sukace ma Sarki period ke sata haka, lallai za'ayi balbalin bala'i tsakanin su da Meenal inta farka, yo sukam da kunya ta haifa Ina ma zasu iya fada mishi gaskiya. Dan haka sai suka fara kallon kallo a tsakanin su wannan na dungurin wannan an rasa mai bashi amsa a cikin su, "Baku nan ku suna ciwone kuma din ko wani kalan iskanci ne nike magana kuka kyaleni? " Ya tambaya a kausashe, Umm'ummm umm damaa damaaa muma muna cafeteria ne aka ce, akace mana wai waii Amina bata da lafiya, Suka hada baki wajen bashi amsa, sai Maryam ce ta kara da cewa, "Kuma wallahi muma bamu san mike damunta ba lafiya lau tazo makaranta da safe, har zuwa lokacin da akayi break bamuga alamar bata da lafiya ba koh Jamila? " "Eh Wallahi koni banga alamar ciwo a tareda ita ba, sai dai sai dai dama ummm dama tanayin irin wannan ciwon kuma Baba Malam ne ke mata Addu'a Mommy Hauwa kuma ta bata magani". Sai kuma suka fashe da kuka cikin kukan nasu sukaci gaba da fadin waiyo su Allah shi kenan Meenal zata mutu ta barsu. **** Sarki da kanshi ne ya cirota daga cikin motar bayan sun isa cikin asibitin, bai tsaya jiran wani abuba yayi cikin asibitin da ita dauke a hannun shi su Maryam suka rufa mishi baya, Ma'aikatan asibitin ne sukayi saurin taran shi a kokarin su nason su karbeta a hannun shi sai dai bai basu dama ba yaci gaba da kutsawa suna mishi jagora har zuwa emergency inda ya shimfideta a daya daga cikin gadajen dake dakin sannan ya juya ya fito domin ya basu damar gudanar da aikin su. Suko su Meelat gaba daya kasa zama sukayi gashi kaf cikin su babu mai waya a tareda ita dan dokar makarantar ne ba'a yarda dalibai suje da waya ba, inko kaje da ita har aka kwace tofa kai kajiyo, Kwaro daya biyo bayan su ne ganin su a tsats tsaye cikin rashin rashin sukuni yasa shi umartar su akan su samu waje su zauna yana mai Kara kwantar musu da hankali akan zata samu lafiya, Shiko Sarki fitowar shi daga emergency din yayi dai dai da karar da wayar shi ta dauka alamun Kira, "Malam" Ya ambata a bayyane kafin ya amsa kiran, "Assalamu Alaikum" a can bangaran Malam yake tambayar shi cewar suna wani asibiti ne dan gasu a hanyar zuwa, "Malam ai da bakayi wahalar fitowa ba, tunda Ina tare da ita zan kula da komai da za'a bukata dan yanzun haka ma tana ciki ana dubata nasan insha Allah zata samu lafiya bada dadewa ba" "Angode da kokari Malam Sufyan amma ai baza'ayi haka ba, kaida Kake kan hanyar komawa bakin aikin ka, ya kuma zakaje ka tare a asibity da sunan kula da mara lafiya kamar ba dangi a gari? Iyi ai bazai yuwu kai kuma ka tauye kanka ba koh, yanzun dai kuna wani asibitin ne dan gani nan tafe da Sa'eed " "Muna Asibitin Dr Mubarak" Sarki ya amsa ma Malam dashi gamida yanke kiran, yaso Malam ya zauna basai yaba kanshi wahalar zuwa ba domin dai ko zuwan yayi ba wani Abu zaiyi ba, sai dai yasan Malam bazai taba iya zama a gida cikin kwanciyar hankali ba alhalin Aminatu na asibiti kwance, yarinya kamar ita kadaice d'iya a cikin dangi, Ba'a dauki mintoci ba su Malam suka iso. "Malam Sufyan ai gara kuzo ku kama hanya kar kuyi dare duk da kace gobe jirgin hantsi zakabi zuwa Lagos nasan bazaka rasa yan kimtse²n da zakayi ayau inka isa Kaduna ba". To Baba Malam bari likitan ya fito muji ko ta farka in naga jikin da sauki sai mu kama hanya in kuma abun yayi tsanani sai a canza asibiti," "To ba laifi hakan ma, sannu da dawainiya kaji Allah dai ya maka albarkha ita kuma Allah ya bata lafiya, wallahi haka take fama da wannan ciwon na mara duk karshen wata magani dai babu kalar wanda bamuyi mata ba, kullum nida sauran mutan gidan tafe muke wajen nema mata maganin ciwon nan amma kaga dai har yanzun shiru, hatta uwarta dake kuri ita likitar mata ta gaza a al'amarin ciwon nan, kuma Innan su ta shaidamin tun fara al'adarta take fuskantar wannan kalubalen na ciwon mara mai tsanani, dama ni shirina nace nida kaina zan daukota zuwa asibiti dan so nike likitocin sumin Karin bayani akan ciwon nata dan gaskiya abun bana wasa bane, ita kuma uwar gaba daya banga alamar ta damu da wahalar da y'ar kesha ba dan har yanzun banji gamsas shiyar bayani daga gareta akan ciwon ba" Sai da ya dan goge zufan daya tsatstsafo wanda take nuna alamun cewa shima din a dame yake kwarai kafin yaci gaba da cewa, "Tun tashin yarinyar nan ita bamai yawan laulayi bane shi yasa in ciwon ya tashi duk sai tabi ta firgice, Allah Kasai yasan azabar da take sha yar karamar yarinya da ita" Fitowar daya daga cikin Nurse din dake kula da Aminatun ne yasa su Maryam mikewa sukayo wajen ta suna mai tambayar ta da cewa... "Ya jikin ta? Ta tashi kuwa? Meya sameta? " Haka sukaci gaba da jero ma nurse din tambayoyi ba kakkautawa, "Ah ah sister's ku kwantar da hankalin ku ya'r uwar ku zata samu lafiya nan bada jimawa ba Insha Allah dan yanzun hakama ta farka" Karasawa wajen Sarki tayi. "Ga wannan abubuwan da ake bukata ne ku amso zamuyi mata amfani dashi kafin Dr ya fito daga labour room" Alamu ya mata da hannu cewar ta mikama Kwaro takardar, Mikewa Sa'eed yayi "bani takardar in anso! Tana mika mishi takardar ita kuma ta koma ciki, Jin cewa Meenal ta farka yasa suka danji sa'ida a cikin zukatan su, nan da nan Sa'eed ya dawo, Nurse din dazun ne ta Kara fitowa ta amshi kayan ta koma ciki, Ba'a dauki lokaci ba su Aunty Murja suka iso asibitin gayya guda kamar wadan su masu kai Amarya, Da mamaki Malam yake kallon su, inba haukaba ya zasu kwaso iyalan gida gaba daya su taho suzo su tare a asibiti subar gida ba kowa alhalin yaran su na gab da dawowa daga makaranta, yanzun kuma Idan yace zaiyi magana sai sugar laifin shi suce ya fiye fada ko yanzun dai sunci albarkhacin Sarki ne amma Ana basu damar ganin Aminatun zai korasu su koma gida asibiti aiba gidan biki bane, dan haka bai iya ce musu komai ba Allah kauda kanshi ma da yayi ya mike da niyyar barin musu wajen, sai dai kuma had yayi taku daya biyu ya juyo garesu, "Ina fatan cewa babu wacce tayi gigin kiran Hauwa'u ko auta a cikin ku? " Dukan su dukar da kansu sukayi aka rasa mai bashi amsa dan ba wacce Zata so ya sauke haushin ganin su diyyy din da yayi a kanta, shifa Malam mai iya mishi sai Allah dai wallahi ko shakka babu da basu biyo bayan su ba ko ace wasu suzo wasu su zauna tabbas saiya samun abun magana cewa dan ba cikin yaransu ne d'aya ke ciwo ba shi yasa suka zauna a gida wato inta mutu ma oho, Amma gashi yanzun sun kwaso jiki sunzo sai wani daure fuska yakeyi Malam ho. Uwar gidan shi ne ta wakilci sauran da cewa, "Bamu kira Auta ba itama kuma Jiddan mun kirane dama muji ko Aminatun nada sauran maganin da take sha a gida dan mu taho dashi sai dai kuma bamu samu wayar nata ba har muka taho, ya jikin nagta? ta farka kuwa? " Bai tsaya bata amsa ba yasa kai ya fice su kuma sauran matan suka samu wajen zama suna tambayan su Maryam yaya jikin na Aminatu, Bayan zaman shiru da jiran tsammani da sukayi na wani lokaci Shannan ne wannan Nurse din ta Kara zuwa take fada musu cewar an canza ma Aminatun daki sai dai kuma sun mata allurar bacci bazsu so kuma hayani ya yasa ta farka da wuri ba, "Zamu iya ganin likitan daya kula da ita? " Sarki ya tambayi Nurse din, "Eh to bari in mishi magana, ku biyoni in nuna muku inda aka maida ita" Tace a yayin da ta juya zuwa wani hanyar daban ba wandavta fito daga ciki ba. "Kira Baba sai muje yaga likitan koh? " Sarki yace da Sa'eed, "To Ya'ya" Ya amsa a yayin da ya juya zuwa waje, su kuma su Meelat tuni suka rufama Nurse din baya zuwa dakin da aka kwantar da Meenal. Babu bata lokaci su ka dawo Malam ne kan gaba kamar zai hada da gudu Sa'eed kuma yana biye dashi a baya, "Ya jikin nata ta farka din ne mai likitan yace #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page 20 ................. **** Ina zamu nufa Sarki?" Kwaro ya tambaya a yayin da suka fice daga cikin layin suka nausa kan babban titi, "Asibitin Dr Mubarak" Ya bashi amsa a takaice, Kuri Sarki ya kafe fuskar Meenal da kallo a son shi na gano ko tana numfashi ko kuma numfashin nata ya dauke! dan shifa tsakanin shi da Allah bazai so daga taimako yar mutane ta mace mishi a cikin mota ba, in ma macewar zatayi gara ta bari ya mikata hannun likitoci tukun, atoh dan bazai yarda tasa shi a bakin duniya ba. "Wai Ibrahim ba nace ka kara gudun motar nan bane? Numfashin yarinyar nan fa banga yana fita da kyau ba karta mace min a cikin mota," Maida duban shi yayi inda su Meelat suke rungume da juna "Ku fadamin wai ma meke damunta ne haka, wani irin ciwo ne wannan? Banji jikinta yayi zafi ba amma gashi sai zufa take hadawa,ko dama haka take nata ciwon? " To shi yanzun fisabilillahi so yake su fada mishi gaskiya ko ka'ka, kai jama'a ina ai gaskiyar nan kam bata faduwa a wannan lokacin dan ko *tuntuben harshe* by Surayyah.... Sukayi sukace ma Sarki period ke sata haka, lallai za'ayi balbalin bala'i tsakanin su da Meenal inta farka, yo sukam da kunya ta haifa Ina ma zasu iya fada mishi gaskiya. Dan haka sai suka fara kallon kallo a tsakanin su wannan na dungurin wannan an rasa mai bashi amsa a cikin su, "Baku nan ku suna ciwone kuma din ko wani kalan iskanci ne nike magana kuka kyaleni? " Ya tambaya a kausashe, Umm'ummm umm damaa damaaa muma muna cafeteria ne aka ce, akace mana wai waii Amina bata da lafiya, Suka hada baki wajen bashi amsa, sai Maryam ce ta kara da cewa, "Kuma wallahi muma bamu san mike damunta ba lafiya lau tazo makaranta da safe, har zuwa lokacin da akayi break bamuga alamar bata da lafiya ba koh Jamila? " "Eh Wallahi koni banga alamar ciwo a tareda ita ba, sai dai sai dai dama ummm dama tanayin irin wannan ciwon kuma Baba Malam ne ke mata Addu'a Mommy Hauwa kuma ta bata magani". Sai kuma suka fashe da kuka cikin kukan nasu sukaci gaba da fadin waiyo su Allah shi kenan Meenal zata mutu ta barsu. **** Sarki da kanshi ne ya cirota daga cikin motar bayan sun isa cikin asibitin, bai tsaya jiran wani abuba yayi cikin asibitin da ita dauke a hannun shi su Maryam suka rufa mishi baya, Ma'aikatan asibitin ne sukayi saurin taran shi a kokarin su nason su karbeta a hannun shi sai dai bai basu dama ba yaci gaba da kutsawa suna mishi jagora har zuwa emergency inda ya shimfideta a daya daga cikin gadajen dake dakin sannan ya juya ya fito domin ya basu damar gudanar da aikin su. Suko su Meelat gaba daya kasa zama sukayi gashi kaf cikin su babu mai waya a tareda ita dan dokar makarantar ne ba'a yarda dalibai suje da waya ba, inko kaje da ita har aka kwace tofa kai kajiyo, Kwaro daya biyo bayan su ne ganin su a tsats tsaye cikin rashin rashin sukuni yasa shi umartar su akan su samu waje su zauna yana mai Kara kwantar musu da hankali akan zata samu lafiya, Shiko Sarki fitowar shi daga emergency din yayi dai dai da karar da wayar shi ta dauka alamun Kira, "Malam" Ya ambata a bayyane kafin ya amsa kiran, "Assalamu Alaikum" a can bangaran Malam yake tambayar shi cewar suna wani asibiti ne dan gasu a hanyar zuwa, "Malam ai da bakayi wahalar fitowa ba, tunda Ina tare da ita zan kula da komai da za'a bukata dan yanzun haka ma tana ciki ana dubata nasan insha Allah zata samu lafiya bada dadewa ba" "Angode da kokari Malam Sufyan amma ai baza'ayi haka ba, kaida Kake kan hanyar komawa bakin aikin ka, ya kuma zakaje ka tare a asibity da sunan kula da mara lafiya kamar ba dangi a gari? Iyi ai bazai yuwu kai kuma ka tauye kanka ba koh, yanzun dai kuna wani asibitin ne dan gani nan tafe da Sa'eed " "Muna Asibitin Dr Mubarak" Sarki ya amsa ma Malam dashi gamida yanke kiran, yaso Malam ya zauna basai yaba kanshi wahalar zuwa ba domin dai ko zuwan yayi ba wani Abu zaiyi ba, sai dai yasan Malam bazai taba iya zama a gida cikin kwanciyar hankali ba alhalin Aminatu na asibiti kwance, yarinya kamar ita kadaice d'iya a cikin dangi, Ba'a dauki mintoci ba su Malam suka iso. "Malam Sufyan ai gara kuzo ku kama hanya kar kuyi dare duk da kace gobe jirgin hantsi zakabi zuwa Lagos nasan bazaka rasa yan kimtse²n da zakayi ayau inka isa Kaduna ba". To Baba Malam bari likitan ya fito muji ko ta farka in naga jikin da sauki sai mu kama hanya in kuma abun yayi tsanani sai a canza asibiti," "To ba laifi hakan ma, sannu da dawainiya kaji Allah dai ya maka albarkha ita kuma Allah ya bata lafiya, wallahi haka take fama da wannan ciwon na mara duk karshen wata magani dai babu kalar wanda bamuyi mata ba, kullum nida sauran mutan gidan tafe muke wajen nema mata maganin ciwon nan amma kaga dai har yanzun shiru, hatta uwarta dake kuri ita likitar mata ta gaza a al'amarin ciwon nan, kuma Innan su ta shaidamin tun fara al'adarta take fuskantar wannan kalubalen na ciwon mara mai tsanani, dama ni shirina nace nida kaina zan daukota zuwa asibiti dan so nike likitocin sumin Karin bayani akan ciwon nata dan gaskiya abun bana wasa bane, ita kuma uwar gaba daya banga alamar ta damu da wahalar da y'ar kesha ba dan har yanzun banji gamsas shiyar bayani daga gareta akan ciwon ba" Sai da ya dan goge zufan daya tsatstsafo wanda take nuna alamun cewa shima din a dame yake kwarai kafin yaci gaba da cewa, "Tun tashin yarinyar nan ita bamai yawan laulayi bane shi yasa in ciwon ya tashi duk sai tabi ta firgice, Allah Kasai yasan azabar da take sha yar karamar yarinya da ita" Fitowar daya daga cikin Nurse din dake kula da Aminatun ne yasa su Maryam mikewa sukayo wajen ta suna mai tambayar ta da cewa... "Ya jikin ta? Ta tashi kuwa? Meya sameta? " Haka sukaci gaba da jero ma nurse din tambayoyi ba kakkautawa, "Ah ah sister's ku kwantar da hankalin ku ya'r uwar ku zata samu lafiya nan bada jimawa ba Insha Allah dan yanzun hakama ta farka" Karasawa wajen Sarki tayi. "Ga wannan abubuwan da ake bukata ne ku amso zamuyi mata amfani dashi kafin Dr ya fito daga labour room" Alamu ya mata da hannu cewar ta mikama Kwaro takardar, Mikewa Sa'eed yayi "bani takardar in anso! Tana mika mishi takardar ita kuma ta koma ciki, Jin cewa Meenal ta farka yasa suka danji sa'ida a cikin zukatan su, nan da nan Sa'eed ya dawo, Nurse din dazun ne ta Kara fitowa ta amshi kayan ta koma ciki, Ba'a dauki lokaci ba su Aunty Murja suka iso asibitin gayya guda kamar wadan su masu kai Amarya, Da mamaki Malam yake kallon su, inba haukaba ya zasu kwaso iyalan gida gaba daya su taho suzo su tare a asibiti subar gida ba kowa alhalin yaran su na gab da dawowa daga makaranta, yanzun kuma Idan yace zaiyi magana sai sugar laifin shi suce ya fiye fada ko yanzun dai sunci albarkhacin Sarki ne amma Ana basu damar ganin Aminatun zai korasu su koma gida asibiti aiba gidan biki bane, dan haka bai iya ce musu komai ba Allah kauda kanshi ma da yayi ya mike da niyyar barin musu wajen, sai dai kuma had yayi taku daya biyu ya juyo garesu, "Ina fatan cewa babu wacce tayi gigin kiran Hauwa'u ko auta a cikin ku? " Dukan su dukar da kansu sukayi aka rasa mai bashi amsa dan ba wacce Zata so ya sauke haushin ganin su diyyy din da yayi a kanta, shifa Malam mai iya mishi sai Allah dai wallahi ko shakka babu da basu biyo bayan su ba ko ace wasu suzo wasu su zauna tabbas saiya samun abun magana cewa dan ba cikin yaransu ne d'aya ke ciwo ba shi yasa suka zauna a gida wato inta mutu ma oho, Amma gashi yanzun sun kwaso jiki sunzo sai wani daure fuska yakeyi Malam ho. Uwar gidan shi ne ta wakilci sauran da cewa, "Bamu kira Auta ba itama kuma Jiddan mun kirane dama muji ko Aminatun nada sauran maganin da take sha a gida dan mu taho dashi sai dai kuma bamu samu wayar nata ba har muka taho, ya jikin nagta? ta farka kuwa? " Bai tsaya bata amsa ba yasa kai ya fice su kuma sauran matan suka samu wajen zama suna tambayan su Maryam yaya jikin na Aminatu, Bayan zaman shiru da jiran tsammani da sukayi na wani lokaci Shannan ne wannan Nurse din ta Kara zuwa take fada musu cewar an canza ma Aminatun daki sai dai kuma sun mata allurar bacci bazsu so kuma hayani ya yasa ta farka da wuri ba, "Zamu iya ganin likitan daya kula da ita? " Sarki ya tambayi Nurse din, "Eh to bari in mishi magana, ku biyoni in nuna muku inda aka maida ita" Tace a yayin da ta juya zuwa wani hanyar daban ba wandavta fito daga ciki ba. "Kira Baba sai muje yaga likitan koh? " Sarki yace da Sa'eed, "To Ya'ya" Ya amsa a yayin da ya juya zuwa waje su kuma su Meelat tuni sun rufama Nurse baya zuwa dakin da aka kwantar da Meenal. #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page 20 ................. **** Ina zamu nufa Sarki?" Kwaro ya tambaya a yayin da suka fice daga cikin layin suka nausa kan babban titi, "Asibitin Dr Mubarak" Ya bashi amsa a takaice, Kuri Sarki ya kafe fuskar Meenal da kallo a son shi na gano ko tana numfashi ko kuma numfashin nata ya dauke! dan shifa tsakanin shi da Allah bazai so daga taimako yar mutane ta mace mishi a cikin mota ba, in ma macewar zatayi gara ta bari ya mikata hannun likitoci tukun, atoh dan bazai yarda tasa shi a bakin duniya ba. "Wai Ibrahim ba nace ka kara gudun motar nan bane? Numfashin yarinyar nan fa banga yana fita da kyau ba karta mace min a cikin mota," Maida duban shi yayi inda su Meelat suke rungume da juna "Ku fadamin wai ma meke damunta ne haka, wani irin ciwo ne wannan? Banji jikinta yayi zafi ba amma gashi sai zufa take hadawa,ko dama haka take nata ciwon? " To shi yanzun fisabilillahi so yake su fada mishi gaskiya ko ka'ka, kai jama'a ina ai gaskiyar nan kam bata faduwa a wannan lokacin dan ko *tuntuben harshe* by Surayyah.... Sukayi sukace ma Sarki period ke sata haka, lallai za'ayi balbalin bala'i tsakanin su da Meenal inta farka, yo sukam da kunya ta haifa Ina ma zasu iya fada mishi gaskiya. Dan haka sai suka fara kallon kallo a tsakanin su wannan na dungurin wannan an rasa mai bashi amsa a cikin su, "Baku nan ku suna ciwone kuma din ko wani kalan iskanci ne nike magana kuka kyaleni? " Ya tambaya a kausashe, Umm'ummm umm damaa damaaa muma muna cafeteria ne aka ce, akace mana wai waii Amina bata da lafiya, Suka hada baki wajen bashi amsa, sai Maryam ce ta kara da cewa, "Kuma wallahi muma bamu san mike damunta ba lafiya lau tazo makaranta da safe, har zuwa lokacin da akayi break bamuga alamar bata da lafiya ba koh Jamila? " "Eh Wallahi koni banga alamar ciwo a tareda ita ba, sai dai sai dai dama ummm dama tanayin irin wannan ciwon kuma Baba Malam ne ke mata Addu'a Mommy Hauwa kuma ta bata magani". Sai kuma suka fashe da kuka cikin kukan nasu sukaci gaba da fadin waiyo su Allah shi kenan Meenal zata mutu ta barsu. **** Sarki da kanshi ne ya cirota daga cikin motar bayan sun isa cikin asibitin, bai tsaya jiran wani abu ba yayi cikin asibitin da ita dauke a hannun shi su Maryam suka rufa mishi baya, Ma'aikatan asibitin ne sukayi saurin taran shi a kokarin su nason su karbeta a hannun shi sai dai bai basu dama ba yaci gaba da kutsawa suna mishi jagora har zuwa emergency inda ya shimfideta a daya daga cikin gadajen dake dakin sannan ya juya ya fito domin ya basu damar gudanar da aikin su. Suko su Meelat gaba daya kasa zama sukayi gashi kaf cikin su babu mai waya a tareda ita dan dokar makarantar ne ba'a yarda dalibai suje da waya ba, inko kaje da ita har aka kwace tofa kai kajiyo, Kwaro daya biyo bayan su ne ganin su a tsats tsaye cikin halin rashin sukuni yasa shi umartar su akan su samu waje su zauna yana mai Kara kwantar musu da hankali akan zata samu lafiya, Shiko Sarki fitowar shi daga emergency din yayi dai dai da karar da wayar shi ta dauka alamun Kira, "Malam" Ya ambata a bayyane kafin ya amsa kiran, "Assalamu Alaikum" a can bangaran Malam yake tambayar shi cewar suna wani asibiti ne dan gasu a hanyar zuwa, "Malam ai da bakayi wahalar fitowa ba, tunda Ina tare da ita zan kula da komai da za'a bukata dan yanzun haka ma Malaman asibitin suna ciki suna dubata nasan insha Allah zata samu lafiya bada dadewa ba" "Angode da kokari Malam Sufyan amma ai baza'ayi haka ba, kaida Kake kan hanyar komawa bakin aikin ka, ya kuma zakaje ka tare a asibiti da sunan kula da mara lafiya kamar ba dangi a gari? Iyi ai bazai yuwu kai kuma ka tauye kanka ba koh, yanzun dai kuna wani asibitin ne dan gani nan tafe da Sa'eed " "Muna Asibitin Dr Mubarak" Sarki ya amsa ma Malam dashi gamida yanke kiran, yaso Malam ya zauna basai yaba kanshi wahalar zuwa ba domin dai ko zuwan yayi ba wani Abu zaiyi ba, sai dai yasan Malam bazai taba iya zama a gida cikin kwanciyar hankali ba alhalin Aminatu na asibiti kwance, yarinya kamar ita kadaice d'iya a cikin dangi, Ba'a dauki mintoci ba su Malam suka iso. "Malam Sufyan ai gara kuzo ku kama hanya kar kuyi dare duk da kace gobe jirgin hantsi zakabi zuwa Lagos nasan bazaka rasa yan kimtse²n da zakayi ayau inka isa Kaduna ba". To Baba Malam bari likitan ya fito muji ko ta farka in naga jikin da sauki sai mu kama hanya in kuma abun yayi tsanani sai a canza asibiti," "To ba laifi hakan ma amma babu bukatar canjin asibiti wannan din ma ya wadatar , sannu da dawainiya kaji Allah dai ya maka albarkha ita kuma Allah ya bata lafiya, wallahi haka take fama da wannan ciwon na mara duk karshen wata magani dai babu kalar wanda bamuyi mata ba, kullum nida sauran mutan gidan tafe muke wajen nema mata maganin ciwon nan amma kaga dai har yanzun shiru, hatta uwarta dake kuri ita likitar mata ta gaza a al'amarin ciwon nan, kuma Innan su ta shaidamin tun fara al'adarta take fuskantar wannan kalubalen na ciwon mara mai tsanani, dama ni shirya nace nida kaina zan daukota zuwa asibiti dan so nike likitocin sumin Karin bayani akan ciwon nata dan gaskiya abun bana wasa bane, ita kuma uwar gaba daya banga alamar ta damu da wahalar da y'ar kesha ba dan har yanzun banji gamsas shiyar bayani daga gareta akan ciwon ba" Sai da ya dan goge zufan daya tsatstsafo masa wanda take nuna alamun cewa shima din a dame yake kwarai kafin yaci gaba da cewa, "Tun tashin yarinyar nan ita bamai yawan laulayi bane shi yasa in ciwon ya tashi duk sai tabi ta firgice, Allah Kadai yasan azabar da take sha yar karamar yarinya da ita" Fitowar daya daga cikin Nurse din dake kula da Aminatun ne yasa su Maryam mikewa sukayo wajen ta suna mai tambayar ta da cewa... "Ya jikin ta? Ta tashi kuwa? Meya sameta? " Haka sukaci gaba da jero ma nurse din tambayoyi ba kakkautawa, "Ah ah sister's ku kwantar da hankalin ku ya'r uwar ku zata samu lafiya nan bada jimawa ba Insha Allah dan yanzun hakama ta farka" Karasawa wajen Sarki tayi. "Ga wannan abubuwan da ake bukata ne ku amso zamuyi mata amfani dashi kafin Dr ya fito daga labour room" Alamu ya mata da hannu cewar ta mikama Kwaro takardar, Mikewa Sa'eed yayi "bani takardar in anso! Tana mika mishi takardar ita kuma ta koma ciki, Jin cewa Meenal ta farka yasa suka danji sa'ida a cikin zukatan su, nan da nan Sa'eed ya dawo, Nurse din dazun ne ta Kara fitowa ta amshi kayan ta koma ciki, Ba'a dauki lokaci ba su Aunty Murja suka iso asibitin gayya guda kamar wadan su masu kai Amarya, Da mamaki Malam yake kallon su, inba haukaba ya zasu kwaso iyalan gida gaba daya su taho suzo su tare a asibiti subar gida ba kowa alhalin yaran su na gab da dawowa daga makaranta, yanzun kuma Idan yace zaiyi magana sai sugar laifin shi suce ya fiye fada ko yanzun dai sunci albarkhacin Sarki, ne amma Ana basu damar ganin Aminatun zai korasu su koma gida asibiti aiba gidan biki bane, dan haka bai iya ce musu komai ba illah kauda kanshi ma da yayi ya mike da niyyar barin musu wajen, sai dai kuma har yayi taku daya biyu ya juyo garesu, "Ina fatan cewa babu wacce tayi gigin kiran Hauwa'u ko auta a cikin ku? " Dukan su dukar da kansu sukayi aka rasa mai bashi amsa dan ba wacce Zata so ya sauke haushin ganin su diyyy din da yayi a kanta, shifa Malam mai iya mishi sai Allah dan wallahi ko shakka babu da basu biyo bayan su ba ko ace wasu suzo wasu su zauna tabbas saiya samun abun magana cewa dan ba cikin yaransu ne d'aya ke ciwo ba shi yasa suka zauna a gida wato inta mutu ma oho, Amma gashi yanzun sun kwaso jiki sunzo sai wani daure fuska yakeyi Malam ho. Uwar gidan shi ne ta wakilci sauran da cewa, "Bamu kira Auta ba itama kuma Jiddan mun kirane dama muji ko Aminatun nada sauran maganin da take sha a gida dan mu taho dashi sai dai kuma bamu samu wayar nata ba har muka taho, ya jikin nata? ta farka kuwa? " Bai tsaya bata amsa ba yasa kai ya fice su kuma sauran matan suka samu wajen zama suna tambayan su Maryam yaya jikin na Aminatu, Bayan zaman shiru da jiran tsammani da sukayi na wani lokaci Sannan ne wannan Nurse din ta Kara zuwa take fada musu cewar an canza ma Aminatun daki sai dai kuma sun mata allurar bacci basu so kuma hayani ya yasa ta farka da wuri ba, "Zamu iya ganin likitan daya kula da ita? " Sarki ya tambayi Nurse din, "Eh to bari in mishi magana, ku biyoni in nuna muku inda aka maida ita" Tace a yayin da ta juya zuwa wani hanyar daban ba wanda ta fito daga ciki ba. "Kira Baba sai muje yaga likitan koh? " Sarki yace da Sa'eed, "To Ya'ya" Ya amsa a yayin da ya juya zuwa waje, su kuma su Meelat tuni suka rufama Nurse din baya zuwa dakin da aka kwantar da Meenal. Babu bata lokaci su ka dawo Malam ne kan gaba kamar zai hada da gudu Sa'eed kuma yana biye dashi a baya, "Ya jikin nata ta farka din kuwa mai likitan yace? #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen._ *Ga masu tambayar littafin daga farko zaku iya tuntuɓata kai tsaye da wannan number ɗin 08061358462,* Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ba dan haka karkuji ɗar kuba duk wanda kuke so. Free book ne yan bati a dage da karatu a daure a dunga comment atoh. ```Page 21 °°°°°°°°°°°°° £h ta farka dan har ma sun canza mata d'aki, sai dai kuma sunce sun mata allurar bacci saboda ta samu wadatac cen hutu ana saran idan ta farka zataji saukin ciwon insha Allah " Cewar sarki, "To sai mu karasa can din koh! Kai kuma ina ganin ya kamata ku wuce tunda gasu Hadiza sun karaso,kar a tauyeka da yawa sannu da kokari kaji Allah dai ya saka maka da alkhairi Allah yayi Albarkha , " Su Kwarone suka amsa da ameen. Shi kuma ya amsa ma Malam da, "Eh zamu wuce so dai nike muga likitan tukun inji idan babu wata damuwa , dan namayi kokarin Kira wayar Dr din bai amsa kiran nawa ba," Cigaba da tafiya sukayi zuwa d'akin da Meenal ke ciki, suna isowa Dr din yana fitowa daga d'akin. "Soja mazan fama wai dama kana gari ko dai shigowar kenan? dan kai ana cewa gida biyu maganin gobara kai kam naka gidajen ba iyaka, yanzun gaka a Zaria anjima Kaduna gobe Lagos gata kuma sai yanda hali yayi" Ya karasa fada a yayin da ya iso inda su Sarki ke tsaye, Hannu ya mika musu sukayi musabaha fuskar shi cike da fara'a yake tambayar su cewa, "Ah² shin kodai kune kuka kawo Amina Mukhtar? " Ya karashe tambayar yana mai nuni da hannun shi zuwa dakin da ya fito, "Dalilin ma da yasa nayi Kiran ka kenan". Sai da Dr din ya duka har kasa ya gaishe da Malam kafin yace "Baba harda kai suka taho? ai da kayi zaman ka a gida jikin da sauki ai" "Likita ai ban iya zama gida uwata na asibiti gara dai in taho ayi komai a gaban idona, ya jikin nata? " "Jiki Alhamdulillah Baba muna saran samun saukinta da zarar ta farka, bismillah mu karasa ku ganta" Jagora yayi musu zuwa cikin dakin inda suka sameta kwance akan gado ga karin ruwan da aka daura mata, Karasawa wajen gadon Malam yayi yana mai binta da kallo, "Sannu uwata, sannu kinji wannan ciwon Allah yasa ya zama kaffara a gareki, Allah ya kawo sanadiyar rabuwar ki dashi ki huta" Ya karasa fada yana gyara mata zaman hijjab din dake wuyan ta ya rufe mata kafadunta da suke waje sakama kon zamewar da kafadar rigarta yayi. "Sarki mu karasa office dina, nurse ikleema tace kuna son gani na" "Ok" kawai Sarki ya amsa mishi dashi, juyowa gefen da Malam yake yayi yanda yaga Malam ya tsare Meenal da kallo ne yasa shi jin ba dadi dan yasan haka Malam zai takura kanshi har sai sanda yaga ta warware tukun kafin shima ya samu salama, kauda kanshi daga kan Malam yayi zuwa kan Meenal din, kallo daya ya mata ya kauda kai dan shi kullum mamaki yake akan hukuncin da uwar gida ta yanke waishi ne za'aba auren wannan karamar yarinyar dan a kallon daya mata yanzun ba abunda ya hango illah zallar kuruciyar ta daya kara fitowa. "Muje koh" Dr ya fadi hakan a yayin da yake barin d'akin wanda hakan ne ya yanke ma Sarki sakar zucin da yakeyi. "Baba mu karasa office din Likitan" "Toh Madallah Malam Sufyan bismillah" Malam ya fada yana binsu a baya duka suka fito daga cikin dakin, fitar nasu shi yaba matan daman shiga cikin dakin bayan Malam ya kora musu gargadi akan kar suyi hayaniyar da zasu tasheta a bacci. Malam da Sarki ne Kasai suka isa office din likitan, Dr yayi kokari sosai wajen kwantar ma Malam da hankali akan ciwon na Meenal, duk da Malam ya mashi bayanin tsayin lokacin data sauka tana fama da ciwon da kuma irin yanda take wahaltuwa da ciwon, harda ma irin yanda suke fad'i tashin neman mata magani amma Allah baisa an dace ba, Ganin da likitan yayi cewa babu bukatar wani boye ² tsakanin Dr da mai jinya balle yanda yaga Malam duk ya damu yasan ya shi fadama Malam gaskiyar cewa lalurar ciwon mara irin na Aminatu gaskiya maganin shi d'aya ne cikin biyu idan kuma har ba'a dace ba to sai acigaba da neman magani har zuwa sanda Allah zai yaye ma mace ciwon, duk da dai a ganin shi sosai Aminatu tayi kankanta da aure a shekarun ta da kuma irin kalubalen da auren wurin kan haifar ga matan da ake aurar dasu basu kai matakin ba, Amma hakan baisa yakiyi ma Malam bayanin cewa Aure shine sahihin maganin da yake sarai cewar in akama ta zata rabu da ciwon, duk da cewar wasu matan ko sunyi auren ciwon baya saurin tafiya sai dai yakan ragu har zuwa sanda mace zata fara haihuwa a hankali kuma sai a nemi ciwon a jikin mace a rasa. Malam ya jinjina wannan al'amari matuka bawai dan bai son aurar da itan bane , sai dai kuma sanin kanshi ne yanda kullum take cin burin yin karatun likitanci, yasan Aminatu tana da burika da yawa wanda bata tab'a kawo cewa akwai wani abu dazai shiga tsakanin ta da burikan nata ba, To amma kuma da irin wannan wahalar da take sha duk wata yana ganin ai gara auren duk da shima Allah ya gani bai so ya aurar da ita din da wuri ba . dan hakan nema yasa kaf cikin maneman da suka fito nata yaki bama kowa dama har yanzun sai dai kuma yana tsoron kada rashin yin mata auren yasa su rasata wata rana duk da a kwanakin yaga yanda aketa fuskantar kalubale ga matan dake kamuwa da ciwon yoyon fitsari a sanadin auren wurin kamar yanda likita ya fad'a, A takaice dai wani damuwar kuma Malam ya kara shiga Wanda zamu iya kira da ga koshi ga kwanan yunwa, daga karshe dai ya yanke shawarar zaije yaci gaba da istihara in auren ne mafi alkhairi to Allah ya tabbatar. Bayan sun fito daga wajen likitan Malam da kanshi yama iyalan nashi umarni akan su koma gida haka, dan likitan yace koda ta farka bazai basu sallama yau ba har sai sunga yanda jikin nata ya karaji dan haka su koma gida ita Innar su inta koma gida saita hada abubuwan da zasu bukata na zaman jinya, sai ta dawo ta zauna da Meenal din, Fatan samun sauki suka mata sannan suka Kama hanya dan har dasu Jamila Sarki yace kwaro ya mai dasu makaranta, cikin dakin Malam ya koma yayin da shi kuma Sarki ya koma office din Dr sai da yayi settling din komai da yasan zasu bukata a zaman da zatayi a asibitin sannan ya baro office din. Harabar asibitin ya koma, koba komai ya kamata ya kira Uwar gida dan tasan cewa har yanzun yana cikin Zaria bai wuce kaduna kamar yanda ya mata sallama a yayinda yabar gida ba. Da fara'a a muryar ta ta amsa sallamar daya mata, "Sarki badai har kun sauka ba? amma dai gudu kasa Ibrahim yayi da motar koh? Kuma kullum Ina fada maka ka dena sa d'an mutane yana gudu da Mota, atoh ba fata ba ai gara kai ko yanzun ka mace kabar baya shiko har yanzun ko auren farko baiyi ba ! " Sai da yayi murmushi sannan ya bata amsa da cewa "muna cikin Zaria ai bamu samu damar wuce wa bama" "Subhanallah to meya faru kuma? " anan ne ya mata bayanin abinda ake ciki kana ya kara da cewa yanzun hakama yana cikin asibitin shida Baba Malam. Daga yanayin yanda yake jiyo muryar ta cike da annashuwa yasan cewa koda bata fito fili ta fadaba hakika tayi farin ciki da abunda ya aikata. "To kai babban mutum haka akeyi ai kamata yayi ka kirani tun dazun ka shaida min muma mu taho asibitin to amma ko yanzun bata baci ba bari insa a hada abinci sai in taho musu dashi, Kai kuma kayi abunda ya dace Allah ya maka albarkha, kafin kabar asibitin kuma sai kayi musu cefanen kayan jinya koh yan kayan tea dasu kayan marmari haka," Jin yayi shiru yasa ta kara da cewa "kana jina kuwa?" "Eh inaji" ya Bata amsa, "To nace ba, inaga tafiyar ka dole zaka barshi sai zuwa yamma kenan dan dole ka zauna muga yanda jikin nata zai kara ji zuwa yamman! " "To amma Hajiya tun dazun fa Malam yake cewa ya kamata in wuce haka tunda dai kinsan yasan yau zan koma dama kuma akwai shirin dazan karasa idan na isa" Bata bari ya karasa ba ta katseshi da cewa "to kai kuma dan yace ka tafi shike nan saika kama hanya gilu² ka tafi ka barshi da dawainiyar Aminatun? Sarki Ana magana nefa akan yarinyar da ake nema maka da aure! To in baka nuna kulawarka a kanta ba fisabilillahi kana ganin zai samu kwarin gwuiwar baka ita ka aura ne? Kar kayi la'akari da cewa itadin kanwar kace yasa kayi zaton cewa Malam zaiji nauyi na kona mahaifin ka wajen daukar Aminatu ya baka muddin baiga alamar cewa zata samu kulawar daya dace a wajen kaba, dan haka kafin ma in iso ka tabbatar ka aiwatar da abunda na saka kuma suma sauran yan uwanka zan fada musu suzo su dubata" Tana gama fadin hakan ta yanke wayarta dan tasan dai tabbas bazai bar asibitin ba har sai yamman kamar yanda tace, Kuri yabi wayar da kallo yana kara mamakin Uwar gida yanda ta fututtuke wai shi da girman shine ake shirin yima auren dole fisabilillahi shida yake da kamar Teemah mai zaiyi da wannan karamar yarinyar. "Allah ka bani mafita mafi alkhairi "ya fada a bayyane. Malam ko zaman shi a dakin Baba Adamu da Baba Auta ya fara kira ya shaida musu abinda ke faruwa kafin yaci gaba da kiran sauran dangi, sai dai duk kiraye²n da yayi bai kira Mommy Hauwa ba dan yasan matan gida zasu Kira su fada mata, koda lokacin sallah yayi saida ya Kira nurse din dake kula da Meenal din ta zauna da ita Sannan ya wuce masallacin. shiko Sarki mortar Dr Mubarak ya ara ya shiga gari dan aikata umarnin da uwar gida ta bashi na siyo kayan jinya haka ko ya kwaso harda su drink dasu ruwa duk wani abunda yasan zasu bukata sai da ya siya koda ya dawo Malam yana Masallaci, sai dai ya cimma Kwaro da Sa'eed a d'akin, su yasa suka kwaso sauran kayan suka kawo dakin sai da ya kirga kudade yaba Sa'eed da sunan ya rike a hannun shi koda za'a bukaci wani abun sannan yaja mishi kunne cewa karya fadama Malam sannan yace ma Kwaro ya tashi su kama hanya dan bazai so Uwar gida ta iso asibitin ta iske shiba dan tana iya kara ballo mishi wani ruwan kuma. Sai da sukama Malam sallama tukun kafin suka kama hanya, tafiyar su babu dadewa su uwar gida suka iso tare da sauran matan gidan Malam Ladan din. A wannan rana dai su kansu yan asibitin sun san an kawo musu yar dangi jinya domin tako ina haka ake zuwa dubiya cikin yan dubiya kuwa, harda Hajiya Innah da nata gayyar wadanda suka samu isowa asibitin da dare bayan ishsha'i zuwa lokacin kuma su Baba auta sun Samu sun lallaba Malam ya koma gida Mommy Hauwa da Innar yara sune a asibitin kuma Alhamdulillah koda Meenal din ta farka jikin nata da sauki sosai domin period din yazo mata, Dama in ya riga yazo ciwon yakan ragu, har ta Samu ma tayi wanka ta canza kayanta daga na makaranta zuwa na gida. mota guda Hajiya sukayo ita da ahalin gidan ta gefe Guda kuma gasu Mai Jama'a, Musty, da kuma Sadeeq. Koda suka iso sun Samu Mommy Hauwa da Innar yara a waje ne suna fira , yayin da suka bar Maryam da Meelat a ciki tareda Meenal din a Cewar su wai su zasu kwana da ita. Bayan gaisuwa ne suka dunguma zuwa ciki dan duba mai jikin, sun same su duka su ukun zaune akan gadon mai jinya suna hira, sai da Hajiya ta kare musu kallo tsaf sannan ta rike hab'a tana kallon Mommy Hauwa "Jidda nace mutum nawa ne ke ciwon hala? nidai mutum uku na hango a gadon marar lafiyar ko an fara hada mutum uku a gado daya ne? " Sauka daga gadon su Maryam sukayi suna dariya yayinda ita kuma Meenal ta koma ta kwantar a maimakon zaunen da take haka kafin Hajiya tayi magana, ita dai Allah ya gani ta gaji haka mutum zaiyi ta zama a asibiti mutane suna mishi jele da sunan gaisuwa , itafa Allah ya sani wallahi ta tsani zaman asibiti dan da za'aji ta nata da gida zata koma tunda dai aiko yanzun taji sauki inyaso sai taci gaba da shan magani ta warware a gida abinta, dazun ta fara magana Malam yace a'ah, haka kawai ka kwanta asibiti maye da mayya suyi ta maka jele salon a lashe maka kurwa, Sannu takwara ya jikin? Kekam wannan girma naki baizo miki da sauki ba sam wallahi, ace mace in zatayi al'adah sam ba sirri " Dago idonta tayi da niyyar kallon Hajiya bakinta cike da magana sai akayi sabani idonta ya fada cikin na Dan Mai karfi aiko ta daddage ta watsa mishi hararar da tayi niyyar bama hajiya ita akan Sari, "Kai" ya furta cine da mamaki yana nuna kanshi da yatsa......... #Ameenatu. 🧕🏻 #Team Sarki. 🤴🏼 #Team Mai Jama'a. 🤵🏻‍ #Sheikh Naseer.👨🏻‍💻 #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 22 "Kaiii" ya furta a fili yana mai zaro ido cike da mamaki ya nuna kanshi da yatsa. Ita kuwa yallabiyar kauda kanta tayi kamar ma bata san da wanzuwar shi a wajen ba tawani gyara kwanciyar ta abunta ta juya musu baya, Zanyi maganin kine yarinya baki san nidin maganin tsageru bane irin ki, Yake aiyanawa a zuciya yana mai dage kafadun shi duka biyu alamun ke zakiji a jikin ki, Karasawa wajen gadon yayi kamar abun arziki ya nemi gefen gadon ya zauna, bai tsaya wata² ba ya cusa hannun shi cikin bargon data rufe jikin ta dashi ya manna mata wani irin shegen tsunguli mai dan Karen zafi, Bata tab'a tsam manin cewa shine ya zauna a kan gadon ba sakamakon juya bayan da tayi. tsananin azabar zafin mintsilin daya tafi kai tsaye ya kai sako zuwa kwakwal warta a bazata ne yasata sakin firgitaccen kara a yayin da ta wani irin zubarar da bata sauka akan kowa ba sai akan shi, Cacume shi tayi da kyau tana burgima da kiran ta shiga uku kunama ta cijeta, "Waiyo Allah kunama ta cijeni, ku cire min ita karta shigemin cikin jiki,tana wannan ihun take cigaba da yakushin shi a wuya, waiyo Allah Baba Malam" Haka ta dunga ihu tana burgima tun tanayin burgiman akan gadon har ta sauko kasa duk ta yamutsa gadon ta watso komai a kasa, Amma fa dan walakanci irin na Meenal duk wannan ihun da haukar tsalle tsallen da take rike take gam da jikin Mai Jama'a riko kuma bana wasa ba, Bawan Allah duk ta gama cimimiye mishi shaddar jikin shi duk ta yamutsa shi dan dole ya koma kamar wanda yayi fada da zaki, dan ba rikon wasa ta mishi ba abundai kamar da gayya ko kuma daukar fansa, dan kuwa duk yanda yake tsammanin zai iya yakice ta a jikin shi abun ya faskara, Sai fadi yake "ke! ke!! ke ki tsaya a duba mana, dallah ni sakeni kinbi kin wani shakemin wuya in mutuwa kike muradi ki mace ke daya mana amma kin wani shakeni in baki sakeni ba sai na karya miki hannuwa" "ke yar nan kunama kuma ana zaune kalau daga zuwa dubiya kuma sai ace kunama ta halbi mai jinya, Haka kawai salon ace mune da muka shigo yanzun mukazo da ita salon kisa a dunga nuna ni da baki anayi damu a gari? Ah ah wallahi wannan tareren bankadar bada niba, atoh na kwaso yayan mutane akan suzo mu samu ladar ziyarar mara lafiya tare dasu kar kija musu sharri, Nima kaina gudun dai kar a kullace ni daga nan har karshen duniya ne yasani zuwa inba haka ba miya jamin fita cikin daren nan daya dace ace ina can gaban kafcecen TV na ina canza tasha ko kuma nayi kwance a gadona na rufa da lallausar bargo AC na hura ni, To nidai bari in koma daga waje ai an ma gode Allah tunda ga maza nan ko yanzun zuwana yayi amfani tunda haka nan kuke babu namiji ko daya, Kai Saddeequ aiki ya same ku ai sai kuma d'akin juyin masa ku zaluko Kunamar nan in Allah yasa kun kasheta sai ku fito mu tafi Allah ya bamu ladar aikin alkhairi " Sai da takai bakin kofa tana shirin ficewa sannan ta dakata, Juyowa tayi cike da taraddadi take cigaba da cewa, "Kai jama'a Ina amfanin kwakwazo yarinya duk ta firgita kanta ta firgita yan jinya, To kunga dai dama kazace nasa larai ta dafa mata nace in taho mata da ita, duk da dai nasan tun tana kankanuwar ta ko ciwo da suma take ba cin abinci take ba, ton kardai ayi abun kunya zuwa dubiyar jika hannu na dukan cinya shi yasa nace ayi mata dan farfesu mai romo ko zata iyaci, To gashi nazo ko wajen dazan aza duwaiwuka na ma in zauna ban samu ba duk na firgice ina shirin komawa da abin arziki todai kar ace dama ta leko ta koma nazo yi gashi dai taci ta tada kafada cikin kajin da Hassana ta aiko min ne nace a dafa mata itama taci arziki ai kayan uwarta ne." Tana gama fadin abunda zata fada ta ajiye kullar anan bakin kofan ta fice daga dakin tana kara jaddada musu cewar sufa duba da kyau, kar yazo kunamar ta makale a wani wajen. Lallai ma yarinyar nan taci uwar rainin wayau daga dan mintsilin ta da yayi shine ta wani cacume shi haka duk ta gama yage mishi fatar wuya da faratan ta inya cinka dai dai wato da gayya ta rukun kume shi. Suko su Musty sun dage sai d'ad d'age kayan wajen suke a dole kunama suke nema, Innar yara ne ta matso inda Meenal din ke nan kanannade jikin AK, "Meenal! Ke Meenal sake shi kizo induba inda abun ya cijeki kilan dai cinnaka ne dan babu wani alama na kunama a cikin dakin nan, In banda abunki ta Ina ma kunama zata samu hanyar shigowa ko ina a killace, Taho in gani dai" Da kyar ta banbaro ta a jikin shi, A gefen shi shikam zuwa lokacin wallahi abu dayane yasa bai yayyaka ma yarinyar nan marin da sai ta some ba, wato wanzuwar Mommy Jidda a dakin dan su Maryam tunda ta yanka ihun kiran kunama dama suka koma bakin kofa Hajiya na ficewa kuwa suka take mata baya. Zaunar da ita a kan gadon Innar su tayi bayan ta kara gyara shimfidar gadon, ruwa ta mika mata ta umarce ta da tasha, babu musu koh ta amshi ruwan tasha tana sauke ajiyar zuciya, Wallahi wannan dan karamin gumurzun da tayi a jikin shi ji take duk gabobin jikinta sun sage d'an karfin data fara samu duk tabi ta sadaukar dashi wajen daukar fansa, humm wai shi yayi zaton zai shata musullah ne bayan haduwar su na karshe lafiyayyen rankwashi ya bata akai wanda saida ta kwana ta uni tana ciwon kai saboda tsabar cin zalin, Wato yaga yasha wancan karan bata dauki fansa ta rama ba shine yau saboda tsabar rashin tsoron Allah tana kwance a gadon jinya zai biyota har cikin asibiti ya nemi kwaye mata fata. To wallahi ita dashi ne dan bazata mishi sakwa² ya raina taba, kuma Allah dan dai Malam ya hanata yin Allah ya isa ma kowa ne amma wallahi da dabaka ken bak'u zata ja mishi nashi Allah ya isan mugu kawai wanda ko gyaran gadon baccin shi bai iyaba sai yasa an mishi, *Abinda ya hadasu ya rankwashe ta last haduwar su kuwa shine* Ranar wata asabar ne da safe, ta gama shirin ta dan sunyi niyyar zuwa gidan su wata kawar su a makaranta me suna Zulaihat dan su kureta domin kullum in tazo makaranta da kalar karyar da zata zabgaga musu cewar ita yar masu kudine, da baban ta a abuja yake aiki daga baya ne aka dawo dashi zaria, Kuma su gidan su komai yi musu ake ita bata dadema data fara yin wanka da kanta ba, dan dukan su a Cesar ta suna da nanny masu kula dasu, wato dai yarinyar nan inta samu waje babu kalar karyar da bata bulala musu na yau daban na gobe daban, dafarko tun suna dan yarda da ita daga karshe dai sun buga ma duk maganganunta alamar tambaya, Kunsan student da iya kure da kuma bin kwakwakafi, To suma dai hakan take a wajen su duk abunda kika fada so suke sai sun tabbatar barin ma in abun ya hada da 3full M wato su Meenal kenan, dan yanda kullum take bada labarin gidan su hakan ya sanya su son zuwa gidan dan su ganema idon su abunda take labarta musu kullum, Amma makarya ciyar yarinyar nan duk ranar da suka shirya zuwa saita nemo wani sankacecen karyar da zata gilla musu wanda zai hanasu zuwa, to daga karshe dai da suka gane bafa tason suje gidan nasu ne suma sai suka fita harkar ta dan sun kuduri aniyar kureta, harsu zata mayar wawaye kullum tazo ta dunga sharara musu karya, lallai sai sun koya mata hankali naga wasa ne. dan haka a boye suketa binciken inda gidan nasu Zulaihat din yake domin su kai mata ziyarar bazata su mata dirar mikiya, Todai bayan bincike sun gano gidan dai ashe a unguwar Alkali take, dan haka suka sanya ranar asabar a matsayin ranar da zasu kai sumame a cewar ai dama in mage data Kama b'era natsuwa takeyi. sai dai shirin su ya rushe ne sanadiyyar zuwa gidan Hajiya daya kama Meenal na dole a wannan ranar hakan yasa batun zuwan su can din ya rushe. Domin ta gama shirin ta tsaf da niyyyar tafiya Mommy ta shigo dakin ta bata sakon wani maganin ciwon kafar da Hajiyar ke amfani dashi akan Meenal din takai mata, Haka a babu yanda ta iya badan taso ba haka ta amsa sakon wannan abu koh bai musu dadiba ita da yan koranta, gashi ba hanya d'aya bane balle tace suzo su tafi in sun kai sakon Hajiya sai suje gidan su Zulaihat din, Ta isa gidan lafiya taba Hajiya sakon fa tana Allah Allah tabar gidan ta dawo su tafi inda sukayi niyya kawai Hajiya ta wani bijiro mata da cewar taje ta gyarama Dan Mai karfi d'aki baya gari domin a kano suka kwana cikin abokan shi guda ke aure yau zasu taho da Amaryar, to kuma tun jiyan yanda ya tafi yabar dakin haka nan yake, dan dama Larai ce mai kula mishi da tsaftar dakin sai ko Sadeeq in yana nan to kuma duk tare suka tafi, ita kuma larai tun jiyan taje Hanwa da sunan gaisuwar mutuwa sai kuma ta iske ana sha'anin biki dan haka ta zauna bata dawoba, Rukayya kuma ita da Hajiya Jummai suma sunje pambeguwa wajen wani biki, shi kuma gashi da tsirfar bala'i sai yace ba kowa yake son yana shiga mishi d'aki ba, Dan haka zuwan Meenal yasa Hajiya turata dakin domin ta gyara mishi, Ita hajiya bata san cewa tsakanin AK da Meenal banbancin jinsi bane kawai domin itama Meenal din babu abunda ta iya na kimtsa waje balle kuma ace wankin bayi da sauran su, Koda Meenal ta fito fili ta fadama Hajiya cewar bata iyaba gwasaleta tayi da cewa tsabar kiwuya ne kuma duk abinta ko da jan gwuiwa ne saita gyara dakin nan. A zaton ta aikin ne Meenal din bata so dan harda gori saida ta mata akan ita dai an cuceta a rasa wacce za'a bata takwara sai ita da take nan sululu kamar wacce ruwa yaci yarinya sam ba kama jiki, Inah ita wallah koda tayi yarintar ta aiki babu kalar wanda yake gagarar ta dan haka tama b'ace mata da gani gyaran daki ne sai tayi. Meenal kam ta kulu iya kuluwa dan haka tayi alwashin bazatayi shi da kyau ba, Gaskiya dai kuma mutumin ku fada ya canza hali, Domin dai koda ta isa dakin bashi da wani datti sai dan kurar da yayi amma fa duk gefen da kika jefa idon ki kayane a watse dan hatta da man daya shafa yana ajiye ne a kan gadon a bude ko rufeshi baiyi ba haka ya barshi towel din da yayi amfani dashi ma yana kan gadon ga kayan daya hargitso ya watso su kasa daga cikin wardrobe hatta da kofar wardrobe din bai kulle ba kai komai dai na d'akin yana bukatar kimtsi, Yanzun fisabilillahi ita da nata kayan ma Raheenat ce keyin tsaye wajen kan kanta mata su shine yau Hajiya ta wani turota dakin wannan mutumin da sunan ta gyara, haba jama'a daki kamar na yaran da basada mafadi...... To wallahi zaiga aiki ganin idon shi kuwa. Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 23 To wallahi zaiga aiki ganin idon shi kuwa domin ko ita da ake ganin ta fiye nawa a hakan inta sa kanta tana kankanta waje yayi tsaf abunta, Kan mirror din shi ta karasa bayan ta gama karema d'akin kallo, turarukan dake jere a wajen wad'anda batun yau ba take da fushin su, dan ta dad'e tana ayyana yanda zata shiga d'akin ta saci turaren bata samu mafita ba sai yau Allah ya taimake ta tsuntsu daga sama gasas she dan haka sai ma ta zab'a ta darje wallahi, Sai da tabi turarukan nan daya bayan daya ta dunga feffesa su dan ta tantance kamshin wanda tafi muradi sannan ta ware wasu kwalabe guda uku da sukafi kwanta mata a rai, Sai dai bata san sud'in sune favorite din AK ba duk cikin turarukan yafi son su kuma sunfi sauran tsada domin ko, Koda kudin d'aya daga ciki aka baka ya isa kayi jari ka kama kasuwanci, ciresu tayi daga cikin kwalayen su ta adana su da kyau a cikin jakarta wacce dama da ita ta shigo d'akin sannan ta maida kwalayen turaren a inda suke ta yanda bazakayi zaton cewa babu komai a cikin suba, kayan wardrobe din daya watso kasa ta fara kwashewa babu ruwanta da wani zancen ninke su haka nan ta dunga kwasa tana watsa mishi su a cikin wardrobe din, da kyar ta iya rufe kofar saboda yanda kayan suka yamutse sai basu zauna da kyau ba, dan kana bude kofar zasu biyo kofar ne su zubo, oho ita Ina ruwan ta dan sauri take ta gama da dakin ta fece, Gyaran gadon ma babu wani zancen kakkabewa haka tajajja gefe² n zanin gadon ta cuccusa , abun dai bako kyan kallo bargon ko daya kasance jibgegen gaske dama ko kusa ko alama bata ba kanta wahalar ninke shi ba illah ma yayiban shi da tayi ta maka shi haka nan a yamutsen shi akan gadon, tanayi tana nishi bayan ta gama gyaran gado kuwa babu zancen shara ta hau mopping din dakin, haka tayi cab'a cab'a da ruwa a ko ina tanayi tana mitar bayan ta ya rike gashi ko wankin bayi batayi ba. Bayan gama mopping din kuwa gadon shi ta haye tayi shane² ita nan a dole saita huta sannan zata karasa sauran aikin, Kamshin turarukan shi dana room freshener din daya kama d'akin kai hatta da gadon kanshi kamshin shi na musamman ne, hakan yasa daga kishin gid'a da sunan hutu bayan ta gama kalle hotunan shi dake kafe a bang on d'akin ne ta kure 1 daga cikin hotunan shi da kallo wanda duk ciki shi yafi daukar hankalin ta, tana kallon hoton ne amma tana mitar cewa "shegen kyau kamar mace, shi yasa ake cewa abu in ya cika kyau hadari ne dashi, ciki kuma harda auren namiji mai kyau, dan auren Namiji mai kyau tofa ki shirya shan maganin hawan jini, gashi nan shi dan yaga yana da kyau da kuma kud'in da mata keso shi yasa yake wulakanci son ranshi" Ganin ta kasa raba idon ta da kallon hoton nashi ne yasa ta runtse idanuwan ta bata son ya kayi ba dan kuwa wani daddadar baccine ya sad'ado ya saceta ba tareda ta shirya ma hakan ba . Ba ita ta farka ba sai da Allah ya taimaketa kiran da Meelat ke mata ya tasheta dan Jamila fa badai nacin kiran waya ba inta fara jera kira sai tayi ma mutum Kira 50 a lokaci daya bata gaji ba. Dan dole ta tashi badan baccin ya isheta ba ta karasa zuwa inda jakar nata ke ajiye kan mirror ta d'auki wayar. "Kin dawo daga tudun wadan kuwa? " "Ban dawoba bacci nema ya daukeni ban sani ba garama da kika kira, zuwa anjima kadan dai zan dawo kina gida ai? " "Eh Ina gida, sai kin dawo din to" bayin ta wuce kai tsaye bayan ta yanke wayar leka cikin bayin tayi, shi din ma dai babu wani alamun datti dan ko Ina kal yake har yana daukar ido sai dai shima kamar cikin d'akin ne kayan amfanin cikin bayin duk a yamutse ya barsu kayan wanki ma daya cire bai iya sasu a basket ba gefe ya watsa su, jawo kofar tayi ta koma cikin dakin, abayar data daura akan doguwar riga mai hannun shimin dake jikinta irin masu lafewa mutum a jikin nan ta cire harda dan kwalin, sannan ta kara komawa cikin bayin, Hhhhhh mata fa zasuyi aiki. Ta daiyi kokari wannan karan ta tsaya ta kwashe kayan wankin ta cusa su a basket din data gani, su showel gel da sauran kayan amfanin shiko sai da tabisu daya bayan daya ta duba dan ta tabbatar ma da kanta cewa bilicin yakeyi shi yasa kullum fatar shi ke kara walkiya. Sai dai kuma duk ta duba jikin su bata ga inda aka rubuta cewar sabulan suna sanya hasken fata ba. Bawai dan tayi na'am da hakan bane tadai mayar dasu ta ajiye ne kawai, shima kuma sai da ta zabi wasu shower gel guda biyu a cikin wadanda bai bud'e ba a wajen . dan bafa zatayi aikin banza ba ta tike tama shi gyaran daki ba lada bare la'adah, Ganin cewa bayin babu wani dattin da zata b'atama kanta lokaci wajen wanke wa yasa ruwa kawai ta wau watsa ta dauraye bayin, Bayan ta gama sai da ta nemi Leda ta zuba shower gel din nan dan tasan ganganci ne ta shiga dakin Hajiya dashi dan tana gani zata mata tereren ban kad'ane. abayar ta ta maida sannan ta fito daga d'akin ta maida kofar ta rufe kuma har lokacin mopping din da tayi bai gama bushewa ba,sai ma wani wajen duk yayi jirwaye. Can cikin wasu fulawan da aka kawata gidan dasu ta nemi waje mai duhu ta boye ledar kafin ta koma wajen Hajjaju, Jin motsin shigowar ta ne yasa Hajiya lekowa daga cikin kitchen din da take ta aikin girki yau dambun shinkafa take son ci gashi kuma Larai bata nan dan haka ita da kanta take aikinta dan dama har gobe intaso ita da kanta ke shiga kitchen ta girka abunda take muradin ci, "Ke y'ar nan badai har yanzun kina gidan nan baki koma gidan kuba? Nifa ban son kwadayi wallahi in ma dan kinga ina dambu ne yasa kika tsaya sai kinci kafin ki tafi to wallahi kadan zan sammiki dan masu jiran dambun nan yawa garesu" Itafa Hajiya gaba daya ta manta cewar tasa Meenal ta gyara ma AK daki,,,, "Aiko wallahi ban tafiya sai naci shi kodan ladan gyaran d'akin da kika sani, Gashi nan duk jikina ma ciwo yake" "Innalillahi wa'innah ilaihir raju'un oh ni Aminatu badai tuntuni kina dakin Dan mai karfi ba ? wani irin sharan kirkine zai dauke ki awanni baki kammala ba? " Sai da ta zuka numfashi da kyau dan ta tabbatar da kanshin da hancin ta ke jiyo mata sannan ta karasa kusa da Meenal din dan gazgata zargin ta. "Amina tunda kika shigo falon nan naji kamshin turaren wutan da nasa ya dakushe, Fadamin badai wanka kikaje kikayi da turarukan Abdul khareemu ba? " Ta karasa fada tana tsatsare aminatun da idanu, "Ni ba wanka dashi nayi ba kadan na fesa" "Eh to lallai zoki tattara ki kama hanyar gidan ku dan wallahi ba kirki Abdul khareemu ya cika ba, kibar ganin Ina kusa kiyi zaton idan yaji kamshin turaren shi a jikin ki bazai nad'a miki na jaki ba, kuma nikam ba hanashi zanyi ba dan shara kad'ai na turaki kiyi, Allah yasa ma dai baki mishi wani barnar ba" "Niba abunda na mishi, kuma Allah kuwa ban tafiya sai naci dambun nan" "Da kyau ai wanda baiji bariba yan magana sukace zaiji hoho" Cewar Hajiya tana gama fadin hakan ko ta koma cikin kitchen dinta tabar Meenal din a falon. Waje ta nema ta zauna akan kujera abunta domin ita dai ko a jikin ta, jin shiru Hajiya bata fito bane yasata mikewa ta bita kitchen din, Ba irin korar da Hajiya bata mata akan tafa wuce gidaba itako uwar taurin kan ta kiya, a haka har Hajiya ta sauke dambunta ta kasafta shi kamar yanda tace masu jiran dambun nada yawa hakan ne kuwa dan kaf dambun ya kare. Ita dai tunda ta samu Hajiya ta zuba mata nata ta dauka ta koma falo taci gaba daba ciki hakkin shi, Bayan ta gama ci alwallah taje ta daura ta gabatar da sallan azahar dan wasu masallatai sunyi kira, bayan ta idar tadan kara gyagy gyarawa sannan ta fito ta iske Hajiya itama akan daddumar da tayi nata sallah din anan falon, "Ke Meenal shiga kitchen din nan ki dauko dambun cikin jar kullar nan dana ware a gefe ki mikata gidan su Balkisu ki kaima Turai, kuma sauran kije ki zauna kina mik'a mata ki dawo kizo ki wuce gida" Batayi musu ba ta wuce kitchen din dan koba komai tana son zuwa wajen tsohuwar nan dan ita sam ba irin halin Hajiya Innah gareta ba, dan sosai take sakin musu fuska kuma duk in kaje saita nemi wani abun ta baka. tana daukowa kuwa ta fice daga falon na Hajiya dama gidan baki daya, Da yike rana ta bude sosai hakan yasa babu yalwar jama'a a fadar yan sa idon kofar gidan, Batama kanta sabon gaishe da kowa a wajen ba dan haka yanzun ma wucewar ta tayi abunta kamar bata san da wanzuwar kowa a wajen ba, a hakan kuma sai da aka samu wadanda suka rakata da kallo dan bala'i, A farfajiyar gidan ta had'u da Aunty Billyn Ya Sa'eed tana kwashe kayan wankin dake jikin igiyar shanya, "Oyoyo Aunty na" ta fada tana mai rungume Billyn. "Oyoyo Meenalin Baba Malam, yau kin tuna damu kenan? " "Toda wa yace na manta daku bayan kullum sai nace ma Y'aya yace ina gaisheki, ko baya fada miki sakona ne? " "Yana fada kai, nima Ina nufin kin dauke kafa ne a unguwar kwana biyu! " "To ai gani yau nazo me aka ajiyemin? Bari dai in mikama Dada turai Dambun nan in fito nasan ba'a rasa kayan dadi a wajen ki Auntyn mu" "Bari nima in ajiye kayan nan a ciki in biyoki dan dani za'aci dambun nan kam" Karasawa sashin Dada Meenal tayi tana mai kwala kiran sunan Dadan kamar yanda takeyi duk in tazo gidan, "Dadah! Dadah!! Dadan Hajiya innah, in baki fito kin tarbeni bafa komawa zanyi da abun dad'in dana kawo miki incema Hajiya bakya nan" Daga cikin bedroom din Dadan ta amsa da cewa, "Kujimin takadiran ci irin na yaran zamani, yarinya a baki sako ki kawomin shine saboda rashin son gaskiya kike batun komawa dashi kije kice bana nan, to aiko da kinyi ma kanki dan nima akwai abunda na tana da miki kinga nima sai in hanaki" Ta karasa fada tana fitowa daga cikin dakin nata zuwa falo, Itama dai kai tsaye ba zamu iya kiranta da sunan tsohuwa ba domin dai Masha Allah har yanzun tana nan a tsaye kyar kyakyawar farar bafulatanar ta wanda gayunta ya lullube tsufar , wanda tsabar hasken fatar tanema yasa tun tana yarinyar ta ake kiranta da sunan turai amma asalin sunan ta shine Fatima. "Me Kakar taki ta baki ki kawomin ne? " Ta tambaya a sa'ilin da takai zaune bisa kujerar falon, Matsowa inda ta zauna Meenal tayi, "Dambu ta girka shine tace in kawo miki" "Madallah aiko Hajiya ta kyauta kamar tasan ina kwadayin shi, shiga kitchen ki dauko min plate da cokali ki gani yanzun zanbi ta kanshi" Meenal na dariya ta mike taka cewa "Dadah kuma wallahi yayi dad'i dambun sai ma kinci zaki tabbatar" "Ahaf yarinya ai nice zan baki labarin zakin Hannun Amina dan tun muna makaranta ita ke mana girki" Fitowa daga kitchen din Meenal tayi dauke da plate har da ruwa da drink ta dauko dan tasan Dadah zata bukace su. Fitowar ta yayi dai² da shigowar Billy falon, "Ai kaji tsiyar yaran gidan nan yanzun nan fisabilillahi daga ganin wulkin kulan abinci shine sai da kika biyo sahu? Wato kudai bazaku tab'a barin mutum yaci abu shi kadaiba balle yayi kiba irin na sauran Hajiyoyi to karkiji da wai wannan dambun yau dagani sai mijina keda rabo a cikin shi, dan haka juya baya ki koma inda kika fito " Idan naga comment zan saki wani page din anjima in kuma kunyi shiru nima kujini shiru😎 Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. 💓💓 Wannan page din naki ne Aunty Binta Umar Abbale, Ina miki fatan alkhairi ubangiji Allah ya kara basira. Wancan page din danayi posting d'azun nayi mistake mai makon 23 saina kara sa 22, ```Page 24 Gefen kujerar da Dadah ke zaune nan itama Billyn ta karasa ta zauna, "Dadah kullum fa kece ke fada mana cewa ido gubane kuma rabon mutum kesa harya iskoka kana cin wani abun, Zaifi dacewa inka taya mishi har sai dai in shine ya nuna baya ra'ayi to tanan wajen kai kuma ka fita hakkin shi, To amma kuma Dadah yau nida kene za'aji kanmu akan dambun Hajiya? Kema kinsan daba abincin Hajiya bane ko kallon shi bazanyi ba balle har ya shigar min ido, amma wannan dambun tun banyi ido biyu dashi ba ya shigar min rai, dan Allah ki sammun koba da yawa ba in maida yawu kar alhakina ya kamaki, kin san dai kobanza dama dambu na shake mutum" Katseta Dadah tayi da cewa " ke tsaya Malama naji kina dambu na shake mutum, to albishirin ki lafiya lau zanci nawa dambun harma in kora shi da ruwa kuwa, sai dai ke kuma kici kanki badan halin kiba dai zan sammiki amma ai jiya jiya nan na aika kizo ki kunsa min lalle a kafa kika k'i zuwa dan kina wajen hira da samarin da har yanzun kin kasa tsaida tsayayye kina nan kina ruwan ido gashi nan kannin bayan ki duk sunyi aure sun haihu, anya Balkisu lamarin ki basai nayi da gaske ba kuwa? dan dai gaskiya wannan nauyin jinin naki badai a dangin muba kila dai can kika kwaso shi" Mikewa Billyn tayi fuuuu tayi waje cike da haushi, ita Dadah bazaku tab'a zama kuyi hira ta arziki da ita ba saita jangwalo wani tsegumin kuma, Su jama'a shike nan da zarar a kace a cikin gidan ku ko cikin Dangi kannin ki sun fara aure tofa duk idanuwa da bakin jama'a kanki zai dawo, Sam basa la'akari da cewa kowacce mace kalar hasken tauraron farin jininta daban dana yar uwarta, Kawai dan Allah yasa kannin ta mata yaran kishiyar maman ta sun samu mazajen aure tun kafin su kammala sacandire, suna gamawa kuma aka musu aure sukaci gaba da karatu a dakunan su, shi kenan fa ta fara fuskantar wata kalar rayuwa ta daban a cikin gidan su dama wajen dangi, domin da wasa wasa sai gashi duk wasu tsararrakin ta tuni sunyi auren su wasu ma har sun hayayyafa, A cikin dangi ko yanzun hatta kannin bayanta an aurar dasu tuni, Kuma itafa bawai ta rasa maneman bane Ah'ah abun nedai baya lasting dan da zarar tayi saurayi karkarinta suyi wata biyu a tare ko sama da haka zaiyi batar dabo, Sunyi kuka sunyi Addu'a ita da Ummanta dama duk wasu masoyanta amma dai shiru har yanzun sai dai tana da yakinin cewa addu'ar su bazai taba faduwa kasa a banza ba, Yanzun nema da Sa'eed ke neman ta taga har yanzun bai daina zuwa ba dan a kallah sunyi kusan shekara a tare sai dai kuma kullum shima in ta mishi zancen ya fito ya nuna kanshi a gidan su domin iyayenta susan da zaman shi, amma kullum sai yace mata ta dakace shi tukun akwai abinda yake jirane, To me mutane suke so tayi ne? Wai su mutane a zaton su itama jin dadin tane zaman gidan da takeyi bayan ga kannin bayanta nan da yaransu, Sai dai ya zatayi duk yanda taso aure ai dai ba itace mai alhakin aurar da kanta ba. In hakan ne ai a cikin Danginsu har yanzun akwai maza tun daga kan samarin har masu matan, amma kaf cikin masu surutun dayi mata gorin taki aure ta tsaya jiran mai kudi babu wacce ta kwatanta hadata aure da d'anta, To su mazan basuzo sunce suna sonta ba so ake ita ta fara bin mazan tana cewa tana son su ta yanda zata wulakanta kanta ko ya suke so tayi? Ai tasha fada musu ita a shirye take ko auren dolen nema su mata, amma kuma babu wani yunkuri da sukayi har zuwa yanzun da takai kusan shekara 30 da haihuwa tuni ta kammala degree dinta har aiki ta fara, duk wani dawainiyar ta yanzun a kaso 100 ita Kema kanta kaso 70 duk dan ta ragema iyayenta wasu dawainiyar, Amma hakan baisa ta tsira daga zagin da ake mata da sauran habaice habaice ba, dan hatta kannin ta mata da sukayi aure sosai suka raina ta saboda daurin gindin da uwar su ta musu. Kullum cikin fadama Allah damuwar ta take akan ya mata zabi mafi alkhairi kuma tana da yakinin cewa addu'ar ta bazata fadi kasa banza ba. **** Bayan fitan Billy... Rufe baki Dadah tayi da duka hannuwanta guda 2, "Oh ya Allah maiya kaini wannan subutar bakin ni Turai yanzun sai yarinyar nan ta kullaceni tayi zaton ko nima ina cikin sahun makiyanta, Allah kadai gani kullum sallah ta biyar indan na daga hannuna saina roke ka akan kabaiwa wannan jika tawa miji na gari mijin nunawa sa'a, Allah badan halina ba Allah ka nuna min auren Balkisu in mikata d'akin auren ta da kaina Ya Allah" Sai da ta shafa addu'ar a fuskarta bayan ta kammala sannan ta maida dubanta kan Meenal dake tsaye a gefe, dan itama yanda Billyn ta fita a fusace ya tab'ata dan tana da masaniyar yanda ake hantarar ta akan taki aure, Shi yasa tayi matukar farin ciki sanda ta fahimci alakar soyayyar dake tsakanin Bilkisun da Sa'eed, kuma ko yanzun ta kuduri aniyar zata kaima Malam zancen dan tana da yakinin cewa son gaskiya Sa'eed din ke mata sai dai wani ra'ayin nashi can ne ya hanashi aure bawai dan babu halin yin auren ba, wai shi zaman cikin family house ne bai so shi yasa yaketa wani kwale² bayan yasan cewa ko yafi kuturu naci Malam bazai barshi ya zauna a wani wajen daban ba. "Amina zoki dibar mata dambun a wannan plate din da kika kawo min kinji, kuma karki wuce daga can ki dawo akwai sakon dazan baki" "To" ta amsa dashi sannan ta karasa ta diba dambun ta fice daga falon bayan ta dauko wani plate din daban ta rufe dambun dashi. Bayan ta gaisa da mutanen gidan dakin Billyn ta nufa dan tunda bata ganta a falon ba tasan tana can a dakin ta. Duk sallamar da takeyi Billyn bata iya amsa mata yanda zatajiyo taba sakamakon kukan da takeyi, Itama Meenal din bata damu da jiran amsar ba ta shige dakin dan tana jiyo sheshsheka na kuka a ciki, Ilai kuwa kwance ta sameta a gadon ta rufe fuskar ta da pillow, akan drawer din gadon dake gefe ta ajiye plate din dambun sannan ta koma da baya ta tura kofar d'akin data bari a bud'e, Saman gadon ta haura har zuwa inda Billyn ke kwance, ga dai d'akin tubarkhallah yaji komai daya dace a sameshi a dakin yar gata, sai dai kuma ita ma mallakiyar d'akin bata cikin kwanciyar hankali kasan cewar d'akin ba d'akin auren ta bane, tafi fata da burin kasancewa koda a cikin kango ne indai har tasamu yancin da zata iya kiran kangon da d'akin auren ta. Dago kanta Meenal tayi daga kan katifar ta maida kan a cinyarta, tafikan hannun ta tayi amfani dashi wajen share hawayen dake gudana a fuskar Billyn kafin ta daura da cewa. "Aunty Billy dan Allah kiyi shiru kukan ya isa haka, dan nasan da kukane zai magance miki damuwar ki toda tuni kin manta komai kin dade a d'akin mijin ki, kuma nasan Dadah bata fadi hakan dan ranki ya baci ba domin duk masoyan ki zasuso su ganki a d'akin mijin ki" Katse ta Billyn tayi da cewa, "Meenal mantawa sukeyi cewa banice nike da ikon tsarawa kaina kalar rayuwar da nike so inyiba, idon su ya riga ya rufe akan son ganin aurena gani suke kamar nice nike korar masu zuwa suce suna sona, alhalin tunda nike bantaba wulakanta wani saurayin dazai tun kareni da sunan soyayya ba, tunda na taso nasan ba'a yarjema yaran familin nan mata tsayuwa da samari ba har sai kin kammala sakandire, Ni kuma Allah yasa tun Ina junior sakandire na fara samun masoya, tsoron kar a gane a gida a hukunta ni yasa bana sake musu fuska da kazo da zancen soyayya nike taka maka burki, har zuwa sanda nakai matakin aji 5 na sakandire ban dena samun masu cewa suna sona ba, Amma kin san meya faru Meenal? " Bata saurara dan jin amsar Meenal dinba ta daura da cewa, "Tunda na shiga aji shida wato shekarar karshe dazan kammala secondary dina abubuwa suka canza min, duk masu bibiyata da suke jiran ingama makaranta su gabatar da kansu da daya² suka zare jiki na nemesu na rasa, a haka har na kammala karatuna nayi zaman jiran result babu wani tsayayyen dazan nuna ince shi din saurayi nane, Ganin shiru miji bai fitoba yasa Abban mu ya siyamin admission na koma makaranta naci gaba da karatu, to kingani dai gashi na gama makarantar tuni har aikina samu amma babu mijin aure har yanzun, bawai kuma dan babu masu cewa suna sona bane a'ah sai dai yawancin su da muguwar manufa suke zuwa min, daga Wanda in an kwana biyu zai fara tambayana Baby abokina wane yana birthday ki shirya muje mishi, sai mai cewa Baby zaki rakani waje kaza ko kuma ina waje kaza kizo ki sameni , mazan yanzun ba kunya ba tsoron Allah in bakiyi taka tsan² ba zasu afka miki, dubeni ki gani Meenal koda ban fito na furta ba kowa yasan a shekaru na dole nima ina so ace Ina gidan mijina ne bawai gidan iyayena ba, Amma Ina kowa ya kulle idon shi duk sun tattara laifin sun daura a kaina gani suke nike koron mazan, wasu kuma na cewa dan naga Ina da kyau shi yasa nike jiran mai kudi, sun manta cewa aure da mutuwa dukan su boyayyun sirri ne wanda ubangiji ne kadai yabarwa kanshi sani" Kara maida kanta tayi ta kwantar a cinyar Meenal din tana ci gaba da sheshsheka. "Aunty Billy Ya'yana fa, me yasa bazakice ya fito ba? Wallahi yana son ki, kuma nasan idan ya aureki zai kula dake" Murmushin yak'e Bilkisun tayi, "Humm Meenal kenan ke din har yanzun yarinya ce shi yasa, nasan bai zama lallai ki fahimceni ba" "Na fahimta Aunty tunda gashi ai Ina gani duka kannen ki dake gidan nan mata sunyi auren sun barki dan haka nasan dole kina cikin kadaici koda ace ba'a takura miki da batun auren ba kuwa" Zirgiza kanta kawai Billyn tayi. "Meenal kenan kin san tun yaushe nasan Sa'eed kuwa? To bari kiji na sanshi da dadewa amma bai iya bude bakin shi ya fadamin kalmar so tun a sannan ba sai a watan nin baya ne ya furta min yana sona, yayanki ba karamin yaro bane da in yana son aurena ni zan tunkare shi kai tsaye, domin koba komai duk wanda yake tare dani a kallah yasan damuwa ta, Bari in baki karamin missali da Mai Jama'a Ina son ki fad'amin daga tasowar ki zuwa yanzun fadamin yan mata nawa kikasan suna crushing akan shi? wadanda duka a cikin su babu wacce bata shirya mutuwa akan shiba indai zai aureta, fadamin guda nawa ya aura a cikin su? amsar shine ba ko daya, cikin su ni babu wacce nafi tausayama irin Nusaiba ki duba ki gani da gatanta da komai amma kalli yanda son wanda bai damu da wanzuwar taba yake wahalda ita, sai dai duk wahalar da take sha a banza domin har yanzun data dauki shekaru tana tura soyayyarta a gareshi bata samu sa'ar da soyayyar zata matsa ko inaba, domin ko a fuska bai taba banbanta ta da sauran matan dake kawo mishi cafka ba, to kenan in naci gaba da nuna naci na akan Sa'eed nima irin sakama kon dazan samu kenan" Da sauri Meenal ta katseta da cewa, "Oho musu su wadan nan ai basu da ajine kuma basu san ciwon kansu ba domin koni da nike karamar nan bazan iya cewa Ina son namiji ba" Ta karasa fada tana wani hada rai da turo baki gaba, "Yauwa to kin gani, Ashe kenan nima idan na tunkari yayan ki da batun cewa ya fito ya aureni na zama mara aji irin su" "Ah ah Aunty aike son gaskiya kikema Yayana, kuma dan kince mishi ya turo ai hakan baya nufin zubar da aji ko wani abun daban, kinji dan Allah ki bashi dama ki mishi magana ko sau daya ne" "Meenal ya zanyi toh domin shima har yanzun bai nemi damar ko sau daya daga gareniba, ko kin san cewa har yanzun gidan nan basu san da zaman soyayyar muba saboda bai bukaci su sanin ba! Ki sani shifa abunda kake so burin ka akanshi bai wuce yanda zakayi saurin mallakar shi dan karya kubuce makaba, amma shifa? Ko a jikin shi bai damu ba ko sau daya bai taba neman dama dan ya gana da iyayena da sunan ya gabatar da kanshi a matsayin masoyin yarsu ba" Haka dai sukayi ta tattauna al'amarin duk da cewar sosai Bilkisu ta girme ma Meenal nesa ba kusa ba amma taji dadin hirar daya gudana a tsakanin su, koba komai yau ta samu damar amayar da abubuwan da suka dade suna danne mata zuciya sakamakon kasancewar ta mace daya tilo a cikin dakin su, hakan yasa bata da wani abokin hira na sirri dan ita bata iya zama da kawa ta bude mata duka sirrin rayuwarta ba. Badan hirar ta kareba dole ganin yamma na kunno kai yasa tayi sallama da Billyn wacce saida ta mata kyautar kayan zaki su sweet sannan ta hada mata da wasu kaya kala biyu wanda ta bada dinki aka samu matsala kayan basu shigeta ba, tun a lokacin dama ta kuduri aniyar Meenal din zataba kayan, Sai da ta rakota har kofar d'akin Dadah sannan ta juya ta koma sashen su, Meenal bata zauna ba koda ta shiga sakon da Dadan tace zata bata kawai ta amsa, sannan ta mata sallama bayan Dadan ta bata 1k da sunan tayi kudin mota. Tun daga nesa kafin ka karaso majalisar hayaniyar matasan dake wajen zai baka tabbacin cewa masu wajen nanan, kamar yanda ita ma Meenal hayaniyar nasu ne ya shaida mata cewa yan anacen sun dawo, Abun haushin kuma shine yau ba zallah bakin fuska bane kawai a wajen harda su Musty Sadeeq Wase dama wasu da bata sani ba, Sai gashi duk rashin son gaisuwarta yau dole sai da ta musu gaisuwar duk da jam'i ta mika musu ita, dadin tama AK da baya wajen, Addu'a take Allah yasa baya cikin gidan domin tana shiga kayanta kawai zata dauka ta gudu gida wallahi. Sai dai kash tana bude get din gidan ta hange shi zaune akan kujera waya kare a kunnen shi kuma nan inda yake zaunen nan wajen ta boye shower gel dinshi data dauko a dakin shi, Kauda kai tayi tana karfafa ma kanta gwuiwa da cewa ta maze kawai ta wuceshi abinta, Shiko tun shigowar ta gidan karar da kofar tayi shiya an karar dashi, sai dai bai nuna ko wani alama dazai nuna cewar yasan wani ya shigo gidan ba, kallon da yake mata ta kasan ido kuma bai zama lallai tajishi ba bare kuma ta gane yana kallon ta din. Sai dai ga mamakin shi yauma din dai kamar kullum zuwa tayi ta gifta shi kamar dutse ne a wajen bashi AK Mai Jama'a ba, Katse wayar yayi ganin abun fa na yarinyar nan yafara wuce tunani yana zaton inbai tantance mata aya da tsakuwa ba bazata shiga hayyacin ta ba, dan haka ya bude bakin shi cike da isa ya kirata. "Keee zonan" Taso tayi kamar bataji shiba ta wuce sai dai kuma kafin ma ta kara daga kafarta ya kara cewa, "Koda wasa kika kara daga kafar nan da sunan barin wajen nan sai na karyaki" Juyowa tayi tana zaro ido tace "ka karya ni, to nime na maka? Ai kee ka Kira ni kuma ba suna na kenan ba" Galala ya tsaya yana kallon ta lallaima yarinyar nan, Shikoh shi dai waishi yarinyar nan take so ta raina haka kowa? Shida manyan mata ma idan yana gaban su zakaga har rawar jiki sukeyi shine ita take da kwarin gwuiwar raina mishi da wayau, aiko in batayi hankali ba kafin tabar gidan nan saiya zane mata jiki tsaf in takamar ta rashin kunya ne shi shine Baban ta....... Tofa🤣 Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. Wannan page din naku ne mutanen Family house, Rukayya Saudath Hajiyayye Jikar hajiya (goyon kaka) Har dama wadanda ban Kira sunan suba, ina fa son ku da yawa mutane na❤‍🔥 ```Page 25 Aiko in batayi hankali ba kafin tabar gidan nan saiya zane mata jiki tsaf wallahi dan in tak'amarta rashin kunya toshi shine Baban ta, Karasowa tayi tana wani ciccijewa kamar wacce ake jawowa da igiya. "Gani" "Aina ganki, ko kinga alamun inada ciwon makanta ne? zauna anan tambayan ki zanyi" Gefen shi ya mata nuni da hannu a matsayin inda zata zauna d'in, Kuri ta kafeshi da ido ita da zuciyarta suna tafka muhawara akan ta zauna din ne ko ta zabga da gudu ta fice a gidan, sai dai kuma tasan ko tace tayi gudun a banza dan tsaf in yayi tsalle daya zai cafkota , a babu yanda zatayi dai ta nemi waje d'an nesa kadan dashi ta zauna. "Menene Sunan ki? " Kai jama'a kujimin wani rainin hankali fisabilillahi wai sunan ta yake tambaya, to dan Allah inba neman rigima ba dan dai tambayar suna aida sai ya tambayetan kawai basai ya wani daure fuska wajen bata umarnin zama ba, dan ita harta fara hasaso laifin gyarar datama d'akin shine zai hukun tata akan shi. A zaton ta na cewar ta kubuta yasa wannan Karon cikin d'an sakin fuska ta bashi amsa da "Ameena shine suna na amma Meenal ko Meenat ake kirana dashi a gida da makaranta" Saida ya kauda kanshi gefe sannan yace, "Ni kinsan suna na? " Shiru tayi tana wuki² da ido a zuciyarta kuma cewa take, kuji wani maganar yan kwaya wai nice ban san sunan shi ba, to wani sunan ne a ciki ban sani ba, Abdul Khareem din ko Iliya dan mai karfi, ko Mai Jama'a ko kuma Ak. A fili ko cewa tayi "Na sani Mana sunan ka Ya'ya Abdul Khareem" "Oh ashe kin san suna na? "Ya tambayeta yana mai dage giraren shi, "Eh" ta bashi amsa. "da kyau kinyi kokari, Tambaya na biyu so nike ki fadamin ya alaqata dake take" "Alaqa kuma? kawai dai ai kai d'an Kawuna ne Yaron Ya'yan Mommy" "Ok idan na kasance Yaron kawun ki nidin menene matsayi na kenan a wajen ki? " Babu bata lokaci ta bashi amsa da cewa, "Ya'yana mana! kuma ai cewa akayi d'an mace da d'an namiji abokan wasan juna ne" Ba tareda wani damuwa a cikin furucin nata ba ta kara da cewa, "to kaga kenan nima abokiyar wasar ka ce" Ta karasa fada da murmushi a fuskarta. Kai innalillahi wa innah ilaihur raju'un, kai jama'a wai shi wani tsautsayi nema yasa shi kiran yarinyar nan, kuji wani rainin wayau fa da take fada mishi wai shine abokin wasan ta, bayan shi koda yayyen ta maza ma ba wasa yake ba sai ita da take nan kamar alakoro ne zata kalle shi ta kirashi da abokin wasan ta. Katse shi tayi da cewa "in tafi? ana jira na a gida ko baka gama tambayoyin ba? " "Kika tashi a wajen nan saina tokare ki ta yanda in kika kifa sai an nemo masu d'aukar ki, lallai ma yarinyar nan wato saboda kin daukeni a matsayin abokin wasan ki shi yasa kikamin rainin dakoh gaisheni bakya iyayi koh? Ko a gidan kune ba'a koya miki gaisheda na gaba dake ba? " Bata fuska sosai tayi ganin daga maganar arziki abun yana nemar komawa cin fuska, dan Allah jama'a bashi ya tambayeta ba ita kuma ta bashi amsa, kuma ita ai sam a cikin d'abi'un ta babu fadar karya, in har ka tambayeta gaskiyar zata fada maka wala ta maka dad'i ko kuma akasin hakan wannan kuma kai ka jiyo, shine dan wulakanci zaice wai ko a gida ba'a koya mata gaisuwa ba. "Ba dake nike magana bane? " Ciki-ciki ta amsa da cewar "an koya min mana! " "Oh ashe an koyamiki to meyasa ni baki tab'a gaisheni ba? Ko a cikin wadanda akace ki gaisar din babu suna nane?" "Ah'ah kayi hakuri " "No yarinya aiba maganar inyi hakuri bane so nike inji dalilin da yasa ko sau nawa zaki ganni saima kin daure fuska kin kauda kai kafin ki wuceni kamar kinga kashi, ko ina miki wari ne? " "La'ilah" ta fada tana zaro ido gamida cewa "ni din? " "Kwarai kedin fa ko cemiki akayi bana lura dake a duk sanda zamu hadu?" Bata da amsar bashi dan haka tayi shiru, saima dukar da kanta da tayi tana wasa da ledar dake hannun ta, "Uhummm ke nikejira" "To... to.... toow nidai kayi hakuri, ba kai bane duk sanda mutum zai ganka kana cikin jama'ar ka, in ma an ganka kai kadai to waya kakeyi ni kuma shi yasa nike wucewa bana gaisheka" "Wato in mutum yana cikin mutane bazaki gaishe shiba kenan? amma ai a hakan kike gaisheda su Musty su kuma miye alaqar ki dasu? Bata bashi amsar tambayar farko daya mata ba sai ta biyun, inda tace "to ai shi Musty sunan Baba Malam yakeda" Saida ta gyara zaman takalmin kafarta ta kuma rike ledar hannun ta da kyau sannan ta daura da cewa, "Kuma su ai dukan su suna da sakin fuska suna ma mutane dariya kai koh fuskarka kullum kamar ta shanu" Tana gama fadar hakan kamin kiftawar ido ya hangota ta falfala da gudu zuwa sashen Hajiya. Baki da hanci ya bude yana kallon ikon Allah, Wato ma shi yarinyar nan ta Kira da mai fuskar shanu, Da gaske dai kenan abokin wasan nata ta dauke shi. Girgiza kanshi kawai yayi fuskar shi dauke da karamin murmushi, "Allah ya shirye ki" Baiyi yunkurin bin bayan ta ba sai ma sashen shi daya wuce dan koba komai hakika yana bukatar hutu dan haka zaije yadan watsa ruwa kafin yaci abinci. Sai dai me? Yana bude d'akin nashi anan bakin kofar ya tsaya ya cire takalmi da safar dake sanye a kafar shi, sai dai kash domin ko baiyi taku mai nisa ba Allah ya hadashi da gamon shi, wato k'afa yar hutu wacce bata dauke da faso ko kauje ga kuma danshin safa ne ya hade da santsin tayes sakama kon ruwan da har yanzun bai gama bushewa ba, aiko dai kafin ya ankara ji kake suuuuu tabb duwawun shi ya maku da kasa dan ainihin faduwar da ake kira faduwar yan bori shi yayi, "Innalillahi Wa'innah Ilaihir Raju'un, waiyo Allah na wash bayana subhanallah" Kalmomin daya dunga maimaita wa kenan cike da azaba dan wallahi yafa maku da kasa da kyau bawai faduwar wasa ba, bai iya tashi a wajen ba saida yaji rad'ad'in da jikin shi ya dauka ya ragu tukun na, sannan ne ya lallaba da rarrafe ya karasa cikin dakin shi, wajen wardrobe din shi ya wuce da niyyar ya ciro kayan da zai canza domin na jikin shi dai sun gama nad'e sauran ruwan dake wajen, sai dai me? Yana bude kofar kayan da dama jira suke a bud'e kofar su zubo suka biyo kofar gaba daya haka suka danne shi da yake a duke yake, Kaya! kaya haka dai ya samu yayi watsi da kayan a gefe, cike da jin haushi ya koma gefe ya zauna ranshi a bace can kuma ya fara bin d'akin da kallo dan ya tabbatar ba haka ya fita ya barshi ba to waye Hajiya taba key din dakin shi har aka shigo mishi, dan yasan dai Wallahi wannan ba aikin Larai bane, to " waye? " ya tambaya a bayya ne, zuciyar shice ta bashi amsa da cewar "yarinyar nan", kai anya kuwa? Yes itace dan tabbas dazun yaji kamshin turaren shi a jikinta, "To kenan ita ta shigo min d'aki? Meya kawota dakina? Aiko zata sani wallahi" Ganin sakar zucin bazai fishsheni bane hakan yasa shi daddafawa ya mike, dan gara yayi sauri yaje ya ritsata kafin tabar gidan, bai jira komai ba ya wuce gefen Hajiya hannun shi daya dafe da kwankwason shi. ***** Da gudun ta tafado falon na Hajiya dan a zaton ta yana iya biyota, Kiririf ta maida kofar falon ta rufe harda murza makulli. Ke! Ke!! Ke uban waye ya biyo ki kika fadomin falo haka kamar wacce mutuwa ta biyo, ah gaskiya baki da kyakykyawar d'abia wallahi nidai kin dauki alhakina haka kawai ana zaman kalau zaki fadomin daki kamar an jeho ki mtws Kuma ki koma ki budemin kofa dan ina kallon masu min shiga da fita ne tunda mutanen gidan basa nan, Ita dai bata kula Hajiyar ba saima karasawa inda jakarta yake da tayi, "Ita Turan da kika kai mata dambun sunan ubana ta kira ta zaga koh ya'ya ? dan banji kince min tace ta gode ba! " "Kai Hajiya ba yanzun na shigo ba ko zama fa banyi ba, ai kin san dai dole zatayi godiyar kuma harda ma kaya Aunty Billy ta bani Dadah kuma ta bani wani sak'o wai in kaima diyarki" "Wacece kuma Aunty Billy a gidan? Bakuwa sukayi? " "Hajiya Bilkisu fa nike nufi ba wata ba" "Allah Sarki itace ta baki kyautar kaya? " "Eh Hajiya wai telan ne ya matasu sun matseta shine ta bani kin gansu! " Ciro kayan tayi daga cikin ledar tana nuna ma Hajiya, "Ah lallai kinsha godiya kuma kayan masu tsada ne, to Allah ya mata albarkha Allah kuma ya dubi zuciyarta ya fito mata da miji na kwarai tayi aurenta ta huta, dan nidai tausayi take bani yarinya bata rasa komai ba na diya mace amma ace miji ya gagara samuwa, aini dai dan kar inyi shish shigi ne dana nema mata miji wallahi, to yanzun abun alkhairin nema baya dorewa kar in hadata da wani in abu baiyi dad'iba ace nice sila, amma inba haka ba aiko yaron kirkin nan Saddeequ nace ya nemi aureta nasan bazai kiba tunda masha Allah yarinya ce mai kyau wallahi sak kakarta turai to tsoro nike shi yasa ban mishi maganar taba" Katseta Meenal tayi da cewa "Hajiya Ya' Sa'eed ke neman tafa, kuma aurenta yake sonyi" "Kai madallah, madallah too kice duk mune aiko na mata murna wallahi miji irin Sa'idu ai idan ka samu saika rike abinka kayi ta riritawa, to aiko zan samu Dadah da batun gara ace ya fito a musu aure tun kafin shima a neme shi a rasa" Kwankwasa kofar da akeyi ne ya katse musu hirar da suke. "Kinji koh? Shi yasa nace ki budemin kofata dazun amma da yike kunnen kashi gareki kikamin kunnen uwar shegu yanzun ai kya bude" "Waye? " Meenal ta tambaya a yayinda take bude kofar, bata samu amsar tambayar nata ba idon ta yayi tozali da AK da tambayar nata ya kara fusata shi, Zaro ido tayi ganin shine, "Waiyo Allah dan Allah kayi hakuri wallahi bazan kara ba" Baice mata komai ba illah janyo hannun ta da yayi suka koma cikin falon. "Hajiya me yarinyar nan taje yimin a d'akina? " Ya fada a sanda suka karasa inda Hajiyar ke zaune tana kallon su, "Mai kuwa zai kaita banda ta gyara maka d'akin tunda ba kowa a gidan, wani abune ya faru? " Bai iya bata amsa ba illah juyawa da yayi ya jawo Meenal zuwa gaban shi baiyi wata wata ba ya sauke mata wani irin lafiyayyen rankwashin da sai da yasa takai kasa bayan ta fashe da k'ara nan kuma kukanta ya cika d'akin, "Kai Abdul ka kiyayeni fa wani irin rashin mutunci ne zaka kawo yarinya har gaba na sannan kaci zalin dinta, na tambaye ka meta maka baka bani amsa ba shine kake kokarin bula mata kwakwalwa da gudumar hannun ka? To kasan dai ko banyi Allah ya isaba sai Allah ya saka mata tunda dai ni na ce taje ta gyara dakin....... Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. Ina ma d'aukakin al'umman musulmai barka da sallah tareda fatan Allah ya maimaita mana🥰 Here is your sallah gift, kuyi karatu har ku gaji😂😂 ```Page 26 Ai kasan dai ko banyi Allah ya isaba sai Allah ya saka mata, tunda dai ni nace taje ta gyara d'akin, shine dan bak'in mugunta zaka kama musu yarinya kana neman kwankwashe mata kwalwa , zonan takwara in gani Allah yasa dai bai rusa miki kai ba? Ke dama gaki nan kullum kamar wata kalallab'a". ta fad'a tana janyo Meenal din dake ta kwarara ihu tana murje² a kasan tile's kamar wacce ake yankawa zuwa jikin ta, "Yi hakuri kinji barshi da halin shi ai tsabar mugunta ne ke damun shi to jama'a inba mugunta ba mai zai d'iba a jikin wannan lab'ub'uwar yarinyar ? in mutum tak'amar shi karfi basai ya fita cikin maza ko yaje gidan damben dake Sabon Gari ya tub'e su daku da mazan ba, shine zai huce haushin shi akan jikata, yi shiru kinji uban shi zan kira yajama d'an shi kunne ya shata layi tsakanin mu in kuma ba haka ba wallahi koni ina iya mishi kud'in jirgi in tarkata mishi kaf kayan tsiyar shi dake gidan nan in kuma had'a shi da police su rakamin keyar shi zuwa airport ya tafi can inda iyayen shi nima in huta atoh haba Jama'a ina ma dalilin wannan kwazzaba nikam." Har ya juya da niyyar barin falon jin abinda Hajiya ta fad'a yasa shi juyowa yana mata wani irin kallon dashi ba harara ba shi kuma bai rufe idanun ba, kasa² dai yakeyin kallon. "Hajiya! Hajiya!! Hajiya kin san dai bako yaushe nike son ana shiga gonata ba koh, kuma kud'in jirgin da zakimin ki tsakura a ciki ki siyama jikar ki paracetamol" Yana gama fad'in hakan yasa kafa ya fice ko waigen su bai karayi ba, Astagfirullahi ya Allah kasa inga annabi jama'a me nike shirin gani yau ni Aminatu? Ke takwara kinga abinda ya faru a falon nan nawa yau kuwa? Nagode Allah a gaban ki akai komai kema kin isheni shaida dan babu abunda zai hana ni kiran uwar shi dan dolenta ta baro Saudi tazo ta dauki takadirin d'an ta dan wannan shara'ar tafi karfin ayita a cikin waya sai ido da ido, dan in ban mike tsayeba zuwa gaba yaron nan yana iya shigomin har falon nan ya kashemin fuska da mari" Hajiya duba min kaina Allah kuwa ya rotsamin kai! " gyale da hular dake kanta dama tuni suka kama gaban su, "Ke da Allah ba wani fa shafewar da kanki yayi ni banason haya gaga irin naki, tashi maza ki shirya ki koma gidan ku Allah ya bada ladan zumunci ameen" Diff kukan Meenal ya dauke a yayin da ta tsaya tana kallon Hajiya cike da mamaki, "Hajiya" Ba wani Hajiya zoki wuce ai tun d'azun nike fama dake kikayi kunnen uwar shegu dani, kinga yanzun ai kya nemi inda dare yayi miki" sai da ta turo baki gaba tana mutsts tsuke idanu sannan tace "Hajiya kaina!" Ita kuma hajiya tace "to ina ce dai nayi miki sannu? naga dai shi mugun ko kallo baki isheshi ba ya fice bayan ya gama kwashemin albarka" "To aini maganin ciwon kai zaki bani inba haka ba kaina rabewa biyu zaiyi" "Ah ah wallahi ba'a gidana ba, bari in ma tarwatsewa zaiyi ya tarwatse d'in bayan kin koma gidan ku kafin kisa a farayi dani a radio cewa jika tazo gidan kaka kanta ya tarwatse a'ah wallahi badani ba, maganin ciwon kai dai ai bazan rasa shi a gidan nan ba jirani in d'auko miki" ta fadi hakan a yayin da take mikewa zuwa ciki. "Nidai kud'in zaki bani idan na fita in siya maganin" "Me naji kin ambata? Kamar kud'i naji kin kira yarnan! Oh kice fashi zakimin da ranar Allah to kama gaban ki yarinya,dan banci nanin ba nanin bata cina ke tsaya ma! Wai mema kika aikata mishi a cikin d'akin daya harzuka shi haka? " "Ni banyi komai ba" Inma kinyi ai jikin ki dai ya gyaya miki" Ciki Hajiya ta wuce bata jima ba ta dawo da maganin ciwon kan, saboda yanda take jin ciwon kan yasa batayi jayayya da Hajiyar ba ta amshi maganin tasha, "Muje wajen in ma daya daga cikin samarin nan magana su kaimin ke gida" "Ni bana so bazan hau motar kowa ba, zan je bakin titi in samu mota" "Kedai kika sani mutum na miki abun arziki kina gwasale shi" Shiru Meenal ta mata ganin Hajiyar ta koma Ciki da niyyar dauko mayafine yasa ta ficewa a falon da sauri ta karasa wajen fulawoyin nan da ta ajiye shower gel d'in data kwamuso a d'akin shi ta dauke su ta cusa a cikin ledar kayan da Billy ta bata can kasa ta yanda babu mai gane cewar akwai shi a ciki, yanzun nan fisabilillahi da ace batayi sama da fad'i da turaren shi da wannan shower gel d'inba dashi kenan fa ya rankwashi banza kenan? "Kut ai wallahi bai isa ba koba dad'e koba jima saina rama" ta fad'i hakan a bayyane, Hajiya ce ta karaso wajen tana mita, "ke kuma daga in shiga in dauko mayafi shine kikayi fitowar ki? Nayi zaton kin wuce ne ai? "To aini na fad'a miki ni bazan hau motar suba tafiya na zanyi tunda basu suka kawoni ba dama" "Kyadai ji dashi!" Hajiya ta bata amsa. Koda suka fito kofar gidan Yusuf wase da Mai Jama'a ne kad'ai a majalisar sai kuma wasu bakin fuska. "Kai Abdul taso ka mikamin yarinyar nan gidan su in samu mu rabu lafiya da ita! " "Dama ni na kawota ne dazan mai data? tunda ta kawo kanta ai tasan hanyar komawa, kuma ni ko man petroleum ma babu a motana" Baki bude Hajiya ke kallon shi, "Kai Abdul Khareemu ashe bakajin tsoron kwanciyar kabari cikin duhu? da girman ka da komai kake kallon tsabar idona kana shekamin karya, ince kazo ka maida musu Y'a gida kacemin motar ka ba mai, to ai da hakan gara ka fito gaba gid'i kace min ke Amina bazan kaita ba kiyi abinda zakiyi" Bai gama sauraren abunda take cewa ba ya mike ya wuce zuwa cikin Restaurant d'in dake wajen. "Kai kai kai Abdul ina kuma zakaje me zakayi anan , karfa kamai dani wata shashasha, in tashi tunda farar safiya in had'a abinci shine saboda baka tausayi na kake neman zuwa wajen matar nan mai shafe² wai can zaka cin abinci to wallahi Allah dai yana kallon ka atoh dan bazaka mai dani wahalalla ba, aiko dan wahalar da nayi ka dawo kaci dambun nan, mutane da yawa ke son shi amma na hanasu na aje maka shine dan iskanci kake neman kwance min zane a kasuwa" Juyowa yayi ba tareda yace mata komai ba ya kama hannun Wase suka wuce cikin gidan. "To ya daifi kam ke kuma Takwara ki jira ya fito da motar saiya mik'aki gida" Sai dai me? Koda ta juya wayam babu Aminatu ba alamarta domin ko dama tun fitowar su ta kama hanya tayi tafiyarta tabar Hajiyar na b'ab'atu ita da bakin ta baya gajiya da surutu. Wannan rankwashi shi yayi sanadiyyar da sai da Meenal ta kwana da ciwon kai dalilin hakan yasa basu samu damar zuwa gidan su Zulaihat d'in da sukaci alwashiba, To kuma dan Allah shine saboda tsabar rashin imani yau ya wani biyota har gadon asibity ya mintsileta, tab ai wallahi su zuba shida ita hege ka fasa dan halak sai yanka, Kwana hud'u Meenal tayi a asibiti suka sallameta a kwana 4 nan kuwa tab'ara sai kalar data manta, sannan kullum Malam da Hajiya sai sunzo asibitin suma da nasu kalar wasan kwaikwayon dan Malam dai zuwa dubiyar ta haka ya maidashi kamar biyan bashi akan kowa, tsaf yake lissafe da wadanda basuzo sun duba mishi uwaba. Itako Hajiya innah nata idon akan masu zuwa dubiya babu kayan dubiya yake haka dai akayi ta fama har sanda akayi sallama kowa ya koma kan harkokin shi. ***** Dalilin ciwon laulayin cikin da Teemah keyi a wannan karan yasa dole Sarki ya zauna da ita,abunda take da bukata kenan dama domin koh sosai ta tubure mishi akan cewa rashin sone yasa yanzun bai damu da damuwarta ba, dan haka ita bazata iya wahala ba domin a gaskiya sosai takejin jiki dalilin hakan yasa duk abubuwan ta suka tsaya tadai fada mishi in bai zauna da itaba to hakika zuwa zatayi ta cire cikin dan bata iya wahala da cikin da uban cikin bai damu da itaba, To kun san dai dama can sai ya ciza da kyar yake iya daure zuciyar shi ya mata babu dad'i balle kuma yanzun da take shirin bashi sabon Baby dan haka dole ya d'auki hutu dan ya samu ya shawo kanta to dai suna can suna ba fulawa ruwa. Bayan wani lokaci........ Abubuwa da dama sun faru wasu sun tafi dai² bisa tsarin da yayi dai² da zuciyoyi wasu kuma sun kasance akasin hakan , A yanzun haka dai saura yan watan ni su Meenal su zana jarabawar gama secondary sunfa zama yan mata sosai Masha Allah komai yaji, Dan haka nema wasa² dai samari suka fara rububi a kanta sai dai da yike ta iya takunta da kuma kasancewar akwai waya a hannun ta yasa babu wanda ya fahimci halin da take ciki, domin dai duk kwakwar nacin mutum bata tab'a yarda yasan unguwar suma balle kuma gidan su saboda tsabar gudun tonuwar asirinta komai a cikin tsari take binshi, Alfarma daya dai takema wadanda take ji dasu a cikin samarin shine idan suka matsa da son ganin ta zataje can Tudun wada gidan Hajiya su had'u acan kuma ko hajiyar bata san da hakan ba, wato dai duk yanda zata raina ma mutune hankali ta b'atar musu da tunani a kanta ta sanshi, domin dai kullum a gida ikirarin ta shine likita zata zama dan haka babu batun wani soyayya da aure, hakan yasa babu wanda zai zargeta cewar tana kula samari. Sai dai bata san cewa tana shuka a idon makarwa bane, domin ko duk halin da take ciki na janyo samarin ta zuwa gidan Hajiya Mai Jama'a tuni yake ankare da hakan domin har farfajiyar gidan na Hajiya take shigo da samarin su zauna suyi hira, Shi mamakin shi a kullum shine, su samarin da suke biyon tan mahaukatan wani kasa ne? Su basa ganin kankantar tane dahar suke iya tsayawa da ita da sunan zance? , Kome ma suke cewa in suna zancen oho, dan yasan shirme da yarinta dai shi zatayi ta musu kala² dan rawan kanta yayi yawa. Jama'a fisabilillahi in soyayyar cema ka nemi cikakkiyar mace mai hankali mana ba wannan yar birin wasan ba. Kuma zai same tane wallahi in bata dena kawo musu maza gidan suba saiya had'a ita da samarin yacicci musu mutunci tunda ita bata da kunya wallahi, Dan shifa sosai abun yake bashi takaici dan cikin samarin nata inka duba zakaga bawai irin yan kuca kucan yaran nan bane, ah ah cikakkun samari take samu wayayyu dan alama ya nuna saita darje kafin ta baka damar zuwa inda take, Barin ma wani sakarai daya lura da cewa yafi sauran dake zuwa rawar k'afa a kanta, kuma yasan gayen Lukman Dan gidan Master ne, sosai yaron suke da arziki a gidan su to zaija mishi kunne ne kar yayi amfani da arzikin shi yama yarinyar mutane wayau. yadai tsaya sosai yayi nazarin cewa saboda taga ta fara zama budurwa shi yasa kullum take k'ara raina shi,domin da gaskefa ta maidashi abokin wasan nata dan ko bai takaleta ba ita sai ta takaleshi, domin dai har yanzun kullum babu shiri a tsakanin su sai dai in bata zo gidan ba, inshi yaje gidan su wajen Mommy Hauwa tofa bata da katabus, domin yafi samun damar cin zalin d'inta acan da kyau dan datayi wani motsi da niyyar ramawa Jidda ke taka mata burki akan bata son raini aishi yayan ta ne, amma in a gidan Hajiya ne yana mata itama take huce haushi a d'akin shi dan dai shi baya buguwa, kuma ita dai bazata mishi Allah ya isa ba sannan ba zata yafe ba wallahi, dan tuni saida tayi yanda tasan inda Hajiya ke ajiye key din d'akin shi, dazarar ya mata ba dai² ba take sace key din taje d'akin ta huce haushin ta akan kayan shi. Tsaf yasan cewa ita ke daukar mishi turare da sauran abubuwan dan kullum a jikinta yakejin kamshin da ba irin turaren shi su Sadeeq ke amfani dashi ba, sai dai yana nan yana dakunta duk ranar daya kamata a hannu dumu² zata gyawa aya zakin ta. Gefen Meelat da Musty ko soyayya suke zubawa ruwa² domin tuni aka san da zaman shi a gidan su Meelat d'in duk da akan soyayyar nasu har fad'a saida sukayi da Ak a cewar Ak din shi Musty yana haukane duk cikin Nigeria ya rasa yarinyar dazai nema sai wannan yar jaririyar, wato ashe shi yasa yaran nan suke mishi gani gani dan haka wallahi duk ranar da giyar soyayya ta kwashe shi yaje zance wajen yarinyar nan inhar ya sake ya kira sunan shi a wajen to bai yafe ba. Maryam dai itama irin na Meenal take duk samarin ta a iya waya hirarsu take karewa dan ita dai tasan a gidan su koda wasa ma a kasan tana kula wani jikinta ne zai fad'a mata. Su Moon da Aisha ma ko wacce tana inda take sai dai kullum Moon ta kira Meenal saita tambayeta ya labarin mai gidan yan gayu dafatan yana lafiya, tofa daman da zarar ta ambato shi hirar su ta wannan rana ta kare sai kuma wani lokacin, da alama dai Moon fa ta kamu 🤔 yarinya keda Teemah dan wannan fadar yafi karfina. Batun ciwon marar ta kuwa Alhamdulillah duk da cewar badai ta warke bane amma in ya tashi mata yanzun akwai wani taimako da Malam ya amso mata wanda da zarar ciwon ya taso in tasha bacci zai dauke ta, hakan yasa wahalar nata ya ragu. A gefen Malam kuma kullum cikin istikhara yake akan maneman Aminatun da zuwa yanzun suke ta kara yawa, domin a yanzun haka wadanda sukayi mashi magana akanta a da din su ya haura mutum goma sannan dukan su babu wanda inda hali bazai iya hanashi bashi auren Aminatun ba, dan haka dole yaci gaba dayi mata Addu'a domin neman zabin Allah a cikin al'amarin dan ya yanke hukuncin gara ya aurar da ita d'in kawai kodan samun lafiyar jikin ta itama, in yaso karatun nata tayi shi bayan aure. ************ A gefen Masoya biyu kuwa wato Sarki da Sarauniyar shi zamu iya cewa duniyace sabuwa ta bud'e musu domin dai tuni mutuniyar tashi ta tashi tsaya wajen ganin ta shiga ta fita ta gyara tsakanin ta da mijin ta kuma sosai yanzun kam ta samo kanshi take kuma juyashi yanda take so harma fiye da shekarun baya, Firrr yanzun kam ta hanashi zuwa zaria komai akeyi bai zuwa sai dai aike hatta da yaran shi dake hannun uwar gida yanzun bai wani damuwa da al'amarin su ta uwar su kadai yakeyi. Ita ko Teemah duniya tayi mata dad'i domin dama tuni abunda take so kenan taga Sarki yazama mata mijin kan tace, gashi kam ta samu dan yanzun dai sunan kawai yana aiki a KD ne amma duk sati yana Lagos bayan haihuwar ta kuwa hutu tasa shi d'auka na musamman dole ya koma Lagos sukayi jegon tare, ganin cewa yanzun shi kanshi da komai daya shafeshi yana karkashin ikon tane yasa gaba daya harta da yaran ta dake Zaria bata tunawa dasu balle kuma acewar ta yanzun ta haihu tunda ta haifo Namiji. Al'amarin Sarki wannan karan ba uwar gida kad'ai ya dama ba hatta da ubanshi mahaifi dama sauran yan uwan shi kwarai abun ya damesu, domin dai suma sunata nasu kokarin bakin gwargwadon nason ganin ya dawo hayyacin shi sai dai ina, domin sosai Teemah ta rike wuta wannan karan. Daga karshe dai sun tsaya akan matsaya d'aya cewa dole dai su k'arayi mai aure a wannan lokacin domin indai yana da wata matar anan Zaria dole ko baizo garin dan iyayen shi da yaran ba ya zo kodan matar shi. Hhhhhh naku wasa ne, wanda bai tuna da uwar shi bane zai tuna da wata mata. A hakan dai sosai uwar gida ta matsama Malam Sulaiman akan maganar cewa yaje ma Malam dan Susan wani mataki suke kai yanzun duba da cewa su Meenal din na gab da kammala makaranta, Gaskiya Malam yana cikin halin k'ak'ani kayi, domin dai sosai abubuwa suka rikice mishi domin dai tsayin lokaci daya d'auka yana Addu'a akan nemawa Aminatu zab'i mafi alkhairi bai tab'ajin kin had'in aure tsakanin ta da Sarki ba, sai dai shi abunda yake hangowa idan yabada ta aure ma Sarki meye zai iya biyowa baya? Domin dai tsaf yana sane da chakwakiyar da ake ciki hatta shi da kanshi sosai yake tsaye wajen yin ma Sufyan d'in Addu'a dan ganin ya dawo hayyacin shi domin a bayyane take cewar a yanzun kam Fateemah tasha kan Sufyan, to amma in yak'i auren yaba ma wani Aminatun ba lallai Malam Sulaiman da Uwar gida su mishi uzuri ba, dan haka yana ganin gara ayi auren in yaso sai su bisu da Addu'a kawai, To amma Aminatu fa? Hakuri zatayi koba komai ai Sufyan d'an uwanta ne koba komai yasan bazata k'ishi ba tunda ba wasu samarin take kulawa ba dama balle har tasan abinda take so....... Hhhhhhhhh akwai gwarama fa. Domin ko dai Malam ya amsa cewa yabama Sarki Aminatu su iyayen Sarki suje su shirya sai dai ya kwab'e su akan Sam koda wasa baya son maganar neman auren ya fita waje dan haka dole komai na neman haka suka gudanar dashi a sirance domin Malam ya tabbatar ma kanshi da cewa bayan shedaniyar mata da Allah ya had'a sarki da ita tofa ba tantama akwai na kusa dashi da suke mishi bita da kulli, lokaci yana ta tafiya har ya rage baifi wata d'aya dasu Aminatu zasu fara jarabawar su ta fita ba, Kai jama'a Malam bazai tab'a iya dena halin shiba, domin dai wannan karan ma a kokarin shi na ganin cewa bai kuntata ma Meenal ba yasa ya yanke hukuncin aurar da Raheenat da y'ar wajen shi Sa'adatu wadanda suke gudanar da rayuwar su cikin kwanciyar hankali ba tareda tsammanin zancen auren su zai taso nan kusa ba domin dai dama duk cikin su Meenal ta girme su sun san ko auren za'ayi sai dai ita amma me? Kwatsam ranar wata Juma'a kamar yanda suka saba zuwa islamiyar safe kafin a dawo ayi shirin tafiya makarantar boko, suna isowa kofar gidan suka fara ganin cincirin don mutane, iya hasashen su sun gaza gane ko taron jama'ar na menene domin dai ba'aiyi haihuwa a kusan nan ba balle suce taron suna! Basu ga kuma alamun bak'in ciki ko alhini a fuskar mutanen ba balle suce taron mutuwa ake, to me ya faru? Sai dai kuma babu mai basu amsa hakan yasa dole sukaja kafafuwar su suka shige cikin gida. A farfajiyar ko ba taron komai akeyi ba saina baikon auren Raheenat da Sa'adat wad'anda Malam ya duba a cikin wad'anda suka fito neman auren Aminatu ya musu madadi da kannen ta. Soyayyar da Malam yakema Aminatu soyayya ce mafi kololuwar girma wanda hakan yasa koshi baya son yazama sanadiyyar k'uncin ta balle kuma wani, sai dai soyayyar ta rufe mishi ido sosai ta yanda baik'i wasu su shiga wani yanayi ba indai ita zata samu sassaucin damuwa a zuciyarta, Hakan nema yasa shi yanke hukuncin ya hadesu ukun ya aurar sannan a maimakon ita kad'ai a cikin su ta auri mai mata da yara hudu ya yanke hukuncin suma sauran duk masu mata da yaran zasu aura, sai dai a maimakon ita mai yara 4 su nasu mazajen yaran su sun zarta hakan, dalilin shi na kara rufe zancen auren ta tuntuni kuma shine dan kartaji ba dad'i amma yanzun inta samu labarin auren sauran ko nata yazo bazataji damuwa mai yawa a zuciyarta ba, dan zataga cewar ai an aurar da kannen tama balle kuma ita, Duk yanda suka so suji taron me ake gudanarwa hakan bai samu ba daga karshe ma Ya Sa'eed ne ya kwashe su zuwa Kano a wannan ranar suka kaima Maman Kano ziyara da sunan washe gari zasu dawo, babu wacce tayi tunanin wani abu daban domin dama sun dad'e basu je kanon ziyara ba dan haka tuni suka sake jikin su suka dunga yawace yawace. ''''''''''*******''''''''''''' Uwar gidan Malam Innan yara ce zaune a falon na Malam sai dai lokaci lokaci takan d'aga kai ta duba agogon dake manne jikin bango domin tasan dai zuwa yanzun tuni su Malam suka tashi a wajen karatun da sukeyi na dare shida magidan tan dake zuwa d'aukar karatun, sai dai kuma gashi shiru har yanzun bai shigo ba har ana neman karfe 10 na dare yanzun. Jin motsin shi da kuma gyarar muryar shin nan daya zamar mishi (Bakandamiya) littafin Surayyahms🥰. hakan yasa ta kara gyara zama, domin tabbas yau bata iya bacci saita tattauna da Malam akan batun baikon yaran nan da aka gudanar dashi da safe Wanda su iyayen gidan ko alama basuji kamshin maganar ba sai baiko dasa rana kawai ne ya musu dirar mikiya, domin dai aiko ada can baya kafin baiko sai Malam d'in ya turo mane man sun gana da yaran kafin asa ranar aure, Da sallama ya shigo. "Innar yara kece zaune? ashe na barki da jira mun d'an tsaya tat tauna wani batu ne da Sa'eed akan batun nashi auren dan so nike a had'e shi gaba d'aya dana yaran nan ayishi a huta koya kikace? " Ya Kara she tambayar nashi a yayin da yakai zaune. "Nima abinda ya kawoni kenan Malam" "Ah to madallah amma yanzun dai fara zuba min abinci tukun ni kuma bari in d'an shiga daga ciki in canza kayan nan kin san an fara zafi a gari." "To Malam a fito lafiya" Har ya kai bakin kofar d'akin shi kana ya waigo gyarar muryar shi yayi wanda hakan ya maida hankalin ta kanshi. "Nace ina fatan kin tahomin da nawa kason kunnun tamban dan d'azun naji yara na cewa kin dama kunun tamba? Murnushi tayi tana cigaba da shirya mishi abincin, shi kuma ya shige ciki yana ayyana cewa mata kenan, wato daga jin batun baikon yayan su shine ta kwaso jiki tazo dan ta tutsiye shi ya fad'a mata dalilin yin hakan, alhalin kosu Adamu da Auta babu wanda ya bude baki cikin su yace mishi mai yasa yayi haka? Mata hooo komin tsufan su dai basa tab'a ganin sun girma, girgixa kanshi kawai yayi ya shige makewayi dan ya watsa ruwa. Bayan fitowar shi bata tada maganar ba har sai sanda ya kammala cin abincin shi ta gyara wajen sannan ta dawo ta zauna, "Malam mike faruwa a gidan nan bamu da masaniya haka? " "Wani abune ya faru a gidan hala? " Shima ya maida mata da tambaya maimakon ya bata amsa, "Ah ah ina magana akan baikon da akayi da safe ne nasu Raheena da Sa'adatu, kawai kuma sai mukaga ana taro bamu da masaniyar komai akan hakan! " "Allah sarki eh wallahi baiko ne akayi harma da sa ranar auren da zarar an samu hutu domin so nike kowa ya samu damar halattar bikin auren koba komai ai mun dad'e bamu aurar da yan mata ba a gidan koh?" Katseshi tayi da cewa, "Amma Malam yaran fa" Hannu ya daga mata yana mai daure fuska shima yace "dakata Ameenah indai akan batun nan ne zan fad'a miki gaskiya inhar ba Addu'a zakiyi Allah yasa albarkha ya kuma tabbatar da alkhairi ba to ina ganin zaifiye miki alkhairi kiyi shiru da bakin ki, in kuma ban baki zakiyi to zaifi kyau kije kiyi ma iyayen yaran bawai niba domin na riga na yanke hukunci" "Allah ya baka hakuri Malam amma ni dama gani nayi su yaran suna da mazajen da suka nuna suna bukatar auren su anan cikin gida, kuma koba komai yan magana na cewa gida bai koshi ba aiba'aba dawa nama ba! Kaga ita Raheena ai Abubakar ke neman ta tun zuwan shi garin nan domin a sashena ma sukeyin zance, ita kuma Sa'adatu Farouq ke neman ta ban fad'a maka bane saboda nasan ba yanzun zaka aurar dasu ba, " (Abubakar yaron Maman Kano ne aikine ya dawo dashi Zaria yana aikin Banki, shi kuma Farouq yayan Meenal ne) "To ai gashi nan nauyin bakin naki yaja musu kinga kenan koba komai ni bani da laifi, domin dama ai wani baya auren matar wani sud'in ba matan su bane dan haka sai suyi hakuri su nema a wani wajen domin dai kin san bazai yuwu ince an fasaba tunda na riga na basu, kuma abunda baki saniba shine duk su ukun zan aurar harda uwata suma mazan zan tuntub'esu in akwai wanda ya shirya auren a cikin su duk a had'a ayishi lokaci daya a huta" "Meenal d'in itama auren zaka mata? " "Oh bakiji abinda nace da kyau bane hala? To bari in maimaita auren itama zan mata ina kuma fatan cewa baki manta da neman auren nata da uwar gida da Sulaiman suke tamin jele akan shi tsayin shekarun nan ba? To Alhamdulillah yanzun kam lokacin auren yazo dan dazarar sun kammala jarabawa bikin zai gudana, ina fatan kuma yanzun bazaki ce nayi son kai ba? " Galala Innan yara ta saki baki tana kallon Malam cike da mamaki, lallai hakika yan magana sunyi gaskiya da suke cewa hali zanen dutse to ita kam yanzun me zatace tunda harta da yar gaban goshin shi a wannan karon bata tsira ba, "Innalillahi Wa'innah Ilaihir Raju'un" Sai da ta maimata sau uku a cikin zuciyarta tamkar wacce aka aikoma da sakon mutuwa sannan tace, "Malam Sarki zaka aurama Meenal? Malam Sufyan fa! Wanda kowa yasan yanda matar shi take, ta gagare shi amma dan bala'i kalli yanda ta zame mishi matar jaraba ta yanda har yanzun ya kasa rabuwa da ita, gashi yanzun har an kai matakin data rabashi da iyayen shi ciki kuwa harda yaranta wanda itace uwar su ba yayan riko ba! Malam Meenal din zaka aurar gidan kishiya mai tsafi? Dan babu tantama tsafi yarinyar nan keyi shi yasa ta gagari kowa,Malam Meenal din kafa kake neman ka sadaukar a inda baka san kalar rayuwar kuncin da zata gudanar in anyi auren ba domin ko Wanda bai damu da yayan cikin shi dama iyayen shiba ina tabbatar maka itama ba zatayi daraja a idon shiba, Malam na rokeka ka soke batun had'in aure tsakanin ta da Sarki in ma auren nata a yanzun ya zama dole saboda lalurar ciwon ta Malam ka duba koda cikin yaran d'akina ne kona Dije ka hadata da wani, inba haka ba Malam zaka cutar da ita" Bai bari ya barta ta karasa ba ya katseta a tsawace da kiran sunan ta "Ameenahhh wai ba nace in bazaki fad'i Alkhairi akan auren nan kimin shiru ba? Ko ke kin san gaibu ne? fad'amin kinsan abunda ka iya faruwa anjima ko gobe? Ah ah koko dan Allah ya had'a shi aure da shaid'aniyar mace shike nan sai mu yanke tsammanin mu akan shi mu sakar mata shi kamar yanda takeso taci gaba da mulkarshi kamar Sarki da Bafade iye? Ko koh dan bakece kika haifeshi ba shi yasa kike kalubalantar auren? Fadamin idan a cikin yaran ki Allah ya jarabta da samun mace irin haka shin komawa gefe zakiyi ki rungume hannu ki zuba ido kina jiran ikon Allah ko koh zaki tashi tsaye ne da Addu'a domin neman ma kanki mafita? Aminatu ban sanki da son kai ba, koba komai uwar yaron nan kawarki ce ta kusa kinga ko inda kara dan kawarki ai nakine! Sannan uban yaron nan fa dan uwan kine tako ina dai Sarki dolen kine dan haka ban son in karajin wata magana a bakin ki sab'anin addu'ar sanya alkhairi domin mu bazamu gaji da fad'ama Allah ya kawo mana d'auki a wannan al'amarin ba" "Kayi hakuri Malam nima insha Allah bazan k'ara kalu balantar zancen auren ba, ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya kuma kad'e fitina," "Ameen" Malam ya amsa dashi kana yaci gaba da cewa "munyi magana da yaron ki gobe su Auta zasuje gidan iyayen yarinyar dan haka sai ku fara shiri" "Malam aini keda shiri nida keda auren yan mata uku ai ba zama kuma Allah dai ya bamu aron rai in mik'asu d'akunan su cikin aminci kamar yanda na mik'a sauran yan uwan su. " *Bayan wasu kwanaki * Maryam, Jameela, Aminatu duk sun fara zana jarabawar fita yayin da a gefen su Aisha da Moon suma hakan take duk sai d'auki suke akan su gama su taho Zaria domin yanzun kam ba fashi duk hutu a zaria sukeyin shi, dan yanzun an samu cigaba suma Meenal duk ta jajje gidajen su, dan an samu cigaba sosai ta fannin Meenal din dan yanzun ta sake sosai da yan uwan ta *Danginta* na wajen uwa sosai take jin dad'in yanda suke mu'amalan tarta suke nuna kulawar su akanta, Sunyi jimami matuka a sanda zancen auren su Raheenat ya fito domin abun ya dake su matuk'a, wai su da koh sakandire basu gama bane za'a aurar, amma ya suka iya biyayya ga Baba Malam wannan kam tilass ne, ba amaren kadai bane sukaji rashin dad'i harda Meenal sai dai koda tajema Malam da maganar amsar daya bata shi yasata dole tasha jinin jikin ta ta koma ba amaren hakuri barin ma Raheenat da suke kwana d'aki daya, sosai tasan yanda Raheena da ya Abubakar suke kaunar junan su Wanda kusan duk jama'ar dake gidan sun san da hakan. Dan sosai ya shiga ciki tashin hankali a yayinda labarin ya iskeshi dan babu wanda koda wasa yayi zaton Malam zai aurar dasu Raheenat din a yanzun, da yasan abinda zai faru kenan da tuni ya gabatar da kanshi a wajen Malam sai dai kuma yanzun kam bakin alkalami ya riga ya bushe sai dai hakuri kawai da zaiyi shi akan dole, Shirye ² aure fa yana ta kankama su Meenal sune amarori kirjin biki dan itace gaba² akan komai daya shafi amaren. Duk abunda ke gudana fa nasa rana ku sani hatta da uwar Meenal bata sani ba domin dai Baba Auta gaba d'aya kwarin gwuiwar dazai tun kareta da batun nema ya nema ya rasa, to me zaice mata, ta shirya Malam zai aurar da Meenal nan da yan satikai ko ya zaice mata, Yaje har wajen Innar yara akan ta taimake shi tazo ta fad'ama Jiddah din abinda ake ciki amma matar nan firrr tak'i a cewarta bata kar zomo ba wallahi baza'a bata rata ya ba, ya koma dai yasan ta yanda zai fad'a mata ai matar shine domin dai yasan aure ba fashi garama ya fad'a matan dan kullum kwanakin kara kusantowa sukeyi........... Kun daiga yanda na daure na zuba muku tarin Read more saboda ina son yayi sauri koh? To yasin in banga comment ba shiru zakuji gobe🤨🤨 Aci gaba sa Sharing dinshi please 🙏 . #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 27 Tunda ya baro wajen Innan yara yake ta famar sak'a da warwara, Allah ya sani ba karamin kunyar Jidda yakeji ba dan hakika yasan ba'a kyauta mata ba sai dai koshi da yake matsayin uban Meenal babu wani abunda zai iyayi dan dakatar da batun auren. Ganin cewa shirun bazai kawo maslaha ba yasa koda ya shigo kai tsaye d'akin Jiddah ya wuce domin gara ayi ta a kare yau kawai. Waya ya sameta tanayi dan haka ya nemi gefen gadon da take zaune shima ya zauna, sallama tayi ma wanda suke wayar sannan ta juya gareshi, "Barka da shigowa! yanzun ka shigo ko tun d'azun? na dan tsaya gyara kayane shi yasa banji shigowar naka ba" Bai iya bata amsa ba illah kamo hannu wanta da yayi duka bibbiyun ya zare wayar dake rike a hannun nata sannan ya runtse hannun a cikin nashi hannuwan yana d'an mur murzasu ta yanda bazata ji zafi ba. Daga kanta tayi gamida maida kallonta zuwa fuskar shi tana karantar yanayin da yake ciki domin karara ta karanto tarin damuwa kwance a fuskar nashi, "Abban su me yake faruwa ne? Kasani koda baka fito fili ka fad'amin ba ina lura da yanayin da kake ciki tunda da aka fara maganar auren yaran nan domin nasan damuwar taka tana da alak'a da batun auren! " Ajiyar numfashi ta sauke tana shafa tafin hannun shi ta d'aura da cewa, "Meye abun damuwa akan abunda ba yau aka fara ba! Naga dai tun tale tale dama haka kuke aurar da yaran ku da kananun shekarun su balle kuma yanzun da su d'in zamu iya kiransu kai tsaye da suna yan mata, gashi Alhamdulillah duka mazajen nasu ai babu yaro balle suyima yaran garaje, ina ganin gara kabar duk wata damuwa kabisu da Addu'ar fatan alkhairi sai kaga nan da wani d'an lokaci mun samu k'arin jikoki a gidan" ta karasa fad'in hakan tana mai sanya murmushi a fuskarta duk dai dan taga ta rage mishi damuwar dake kwance a fuskar shi. Duk abinda take cewa kallonta kawai yakeyi batareda yayi yunkurin katseta ba harta kai aya, sannan ya d'an k'ara janyota zuwa kusa dashi sosai yana mai kwantar da kanta akan kafadun shi, "Hauwa'u Jiddah"ya kira sunan ta yana mai kallon cikin idon ta, Dago kanta tayi ta kalle shi dan an dad'e rabon da taji ya kira cikakken sunan ta haka, dan ko sunan nata zai kira sai dai yace maman wane ko kuma ya kira ta da Jidda amma yau ya kira ta da Hauwa'u Jidda, Sai da ya k'ara kwantar da kanta da kyau yana d'an bubbuga gefen kafadarta a hankali sannan yaci gaba da cewa. " da fari ina mai neman afuwar ki akan abunda zai fito daga cikin bakina zuwa cikin kunnuwan ki, Jidda ki sani a kullum ina alfahari da kasancewar ki matar aurena kuma uwar yarana, tsayin shekarun auren mu bazan iya tuna rana guda da kika tab'a b'ata min rai ba, duk da nasan cewa ni d'in lokuta da dama nakan b'ata miki amma baki tab'a fushi kika juyamin baya ba, dan haka yauma ina fatan zakimin uzuri akan abinda zakiji daga gareni" Waiyo Allah wallahi da yasan yanda kalaman nan nashi ke rugurguza mata zuciya da yayi gaggawar fadin mata abunda zai fada. "Abban su ka taimakeni ka fad'amin abunda ke faruwa, ko dai wani laifin ne mai girma na maka ban sani ba? " "Bakimin laifin komai ba Jidda nine dai da Ahalina muka aikata miki laifi mai girma, hakan nema yasa nike kara neman afuwar ki, kiyi hakuri ki kuma kara hakuri," "Dan Allah Abban su ka fito ka fad'amin abunda ke faruwa, ko dai rasuwa akayi ne? Fadamin waye ya rasu kake boyemin? " "Ah ah ba rasuwa bane, Akan lalurar da Meenal take fama dashi ne na ciwon mara" Saida ta sauke nannauyan ajiyar zuciya saboda jin cewa ba wani mugun abun bane ya faru. "Nasan baki manta kwanciyar da tayi a asibitin Dr Mubarak ba? " Bai jira ta bashi amsa ba ya d'aura da cewa, "a lokacin Dr yama Malam bayani akan cewa Meenal bazata rabu da ciwon ba har sai sanda tayi aure in Allah yasa an dace zata rabu da ciwon gaba daya in ma bai wuce lokaci daya ba dai zai ragu har ta dena ciwon ma gaba daya wata rana, Wanda kuma ina da tabbacin kema kin san da hakan a matsayin ki na likitan mata sai dai nasan dalilin ki na boyewar bai wuce duba da karancin shekarunta da kuma burinta data taso dashi na zama likita kamar kiba, Jidda kece kika d'auki cikin Meenal har zuwa haihuwarta dan haka nasan kinfi kowa sanin zafinta, amma zan miki tuni da Abu guda Malam Uba yake a wajena domin ya zarce matakin da zan kira shi da sunan wana ko in kira shi da Ya'yana, domin tun tasowa ta nike samun kulawa ta musamman a wajen shi na sani Malam ya nuna rashin amincewar shi a lokacin auren mu, wannan kuma na dauke shi a matsayin halin dan adam dan tuni na goge hakan daga cikin zuciyata abunda nike son ki gane anan shine Malam yana da iko dani balle kuma yaran dana haifa cikin su kuwa harda Meenal da kowa yasan cewa koni da nike matsayin mahaifinta banfi Malam kaunarta ba, domin a bayyane yake ta yadda ko makaho yasan Meenal takai kololuwar matsayin da Malam bai had'ata da kowa ba a wajen shi kema kuma kin sheda hakan, kamar yanda Malam ya amsa sunan uba a wajen Ameenatu tun daga haihuwarta har zuwa yanzun ki sani yanzun din ma ya kara tabbatar da matsayin shi wajen sauke hakkin dake rataye a wuyar shi matsayin uba domin ko *Malam ya fidda ma Ameenatu miji harma ansa ranar auren atakaice dai dukan su ukun zamu aurar rana daya*" "Innalillahi wa'innah Ilaihir Raju'un"shi tayi ta mai maitawa ba adadi domin kalmar shi ta karshen daya fada shi yayi tayi mata amsa kuwwa a cikin kunnen ta, Sosai ya kara kankameta a jikin shi dan tabbas yasan dama maganar dole zata daketa. "Kiyi hakuri"kawai yayi ta maimaita mata, kuka sosai ta fashe mishi dashi dan gaskiya Allah ya gani bazata iya daurewa ba, dan sosai takejin wani irin kuna da bacin rai yana taso mata. "Aure! Aure!! Aure!!! Meenal din ta ne za'ayima aure shine saboda tsabar ba'a dauketa da daraja ba a matsayin ta na uwar Meenal sai yau da biki ya rage ko sati uku bai kaiba ne za'a fada mata, sannan saboda tsabar son kai shine Mukhtar zai wani zo yana mata dadin baki, to harma akwai wani wanda zaiso Meenal sama da ita uwarta ne? Itafa ta kawo Meenal din duniya da bata haifota ba har shi Malam din zai sota ne, kai soyayyar ma taci uwarta wani irin sone wannan za'a tauyema yarinya hakkin ta sannan ace wai soyayya. Murje murje ta farayi a kokarin ta nason ta kwace daga rikon daya mata, "Ka cikani nace, ka cikani yau sai Malam ya fad'amin in shi yayimin nakudar Meenal, kullum yana min abubuwa ina shanyewa saboda kai kanin shi da kuma darajar jinin dana had'a dakai shine yau kuma Meenal wai ita zai aurar saboda tsabar kiyayyar shi gareni hakan yasa tun tasowar yarinyar nan sai da yasan yanda ya juya mata kai ya cire zuciyarta kwata² akan yan uwana, Nina haifeta amma yafini sanin damuwar ta, ce muku akayi hakan bayamin zafine ko a tunanin ku bana son tane dana kauda kai akanta na bar mishi yana yanda yake so da rayuwarta nayi hakan ne saboda in daraja shi a matsayin shi na yayan mijina, wai aure! Aure fa amma sai yau ake fadamin ni uwar ta ashe ni bani da wata daraja kenan sai na haihuwarta da nayi, naga su sauran yaran tuni aka sanar da iyayen su batun auren su." Mikewa tayi daga kasan da take zaune tana ta murje² tana zuba rikici ta koma inda yake zaune ya zabga tagumi yana binta da kallo, "Wa zaku aurama yarinya ta? waye mijin? Badai tsohon itama za'a aura mata kamar sauran ba? Abban su ka bani amsa waye mijin Meenal d'ina? " Shidai yau ya shiga ukun shi, shi bai kar zomoba amma rataya ya zame mishi dole, gashi komai akan shi yake karewa, ya dad'e baiga Jidda ta fice a saiti ba wannan dalilin yasa ya kasa tun karanta da batun auren. "Sufyan ne zai aureta! " "Wanene kuma wani Sufyan? Kayimin gwari² yanda zan gane Abban su dan wallahi bazan zuba ido a nakasamin rayuwar yarinya a aura mata tsoho ba!" "Sufyan din mu Sarki dai da kika sani yaron Uwar gida da Y'aya Sulaiman" Ai kamar wacce ya caka da allura haka ta wani irin zabura ta fara kai kawo a cikin d'akin sai faman mai maita sunan takeyi da alama ta manta waye ma ake kira da Sarki sai zuwa can kuma sai gashi tayi tsaye cak kamar wacce aka danna ma Pause ⏸ "Sufyan Sarki" ta maimaita sunan tana zaro idanuwa, "Wai Sarki dai naku Sojan ruwa kake magana akan shi ko wani daban? Bai iya amsa mata da fatar bakiba illah gyada mata kai da yayi alamun eh shifa. "Sarki dai dakoh iyayen shi yanzun baya tunawa da sha'anin su balle kuma yaran daya haifa Wanda suke hannun uwar shi shid'in kuke shirin aurama yata taje tayi Kishi da mushrika Wanda kowa yasan da karfin asiri ta dauke hankalin shi akan kowa? To indai shine ko bazan taba yarda Meenal taje gidan da sunan zaman aure ba balle har tayi Kishi da matar shi, akan hakan kuma na shirya batawa da kowa ciki kuma harda kai daka Haifeta, in auren ya zama dole ku bata wani in ma baku dashi niko a cikin yaran yan uwana zan had'a ta da wani amma bazan yarda Meenal ta auri Sarki ba" Tana gama fadin hakan ta fice daga dakin nata zuwa nasu Meenal........ Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 28 Bata tsaya jiran komai ba ta bankad'a kofar d'akin ta shiga sai dai kuma tayi rashin sa'a domin ko babu kowa a cikin d'akin, Shiko Baba Auta data fito ta bari a zaune yana sakar zuci, domin tunda ta rikice din nan salati kawai yake yana sanar ma ubangiji akan Allah ya sanyaya mata zuciyarta yasan duk abunda ta fada akan gaskiyarta ta fad'e shi amma a yanzun kam baya tunanin akwai wani abun dazai hana faruwar auren nan anan kusa hakuri kawai zasuyi subi yarsu da Addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, tunanin cewa karfa Jidda taje ta samu Malam garan gatsau d'in nan tace bata amince da batun auren ba yasa shi mikewa ba shiri ya fita daga d'akin sai dai yana fitowan itama ta fito daga d'akin su Meenal, bata kulashi ba ta dawo fuuu ta kara komawa cikin d'akin ta da niyyar d'aukar waya ta kira Meenal din, ganin ta koma cikin dakin sai shima ya bita dan gara komai za'ayi ayishi cikin d'aki koba komai d'aki yafi waje sirri ai, "karki kira Meenal domin bata san da maganar ba, bama ita kadai ba kaf gidan ba kowa ya sani ba illah mu, kimin wannan alfarmar karki fada mata yanzun in lokacin yayi nida kaina zan fada mata" Durkushewa tayi a wajen tana cigaba da fidda hawaye take cewa, "Ba'a kyauta min ba wallahi wannan ba adalci bane Abban su, ni bazan yarda da wannan tsarin naku ba domin kaf a tsarin auren nan kowa yasan yata ce zata cutu, Meenal dina zakuma auren cushe zaku kaita inda kuka san kishiyarta bazata bari tayi daraja a idon mijin ta ba, sannan ace wai soyayya shi Malam in son gaskiya yakema Meenal aishi ya kamata ya dakatar da zancen auren bawai ya hada auren ba, nidai ban yarda ba bazan bada Meenal anakasa min ita a banza ba" Dagota yayi daga kasa zuwa cikin jikin shi yanaci gaba da rarrashi, "Kiyi hakuri Jidda nasan dole ranki zai baci hakan yasa saida na nemi afuwar ki kafin in fad'a miki abunda ke faruwa, na b'ata darare masu yawa ina kasa bacci saboda tunanin mako mar Meenal da kuma yanda zan tunkare ki da batun, sai dai ki sani ina da yakini akan Malam bazai tab'a yanke hukuncin da zai cutar da Meenal ba, sannan ina mai k'ara baki hakuri kamar yanda kika saba yimin biyayya wannan karon ma ki k'ara akan nada domin bana son ganin ki cikin tashin hankali, ki dauka wannan auren kaddarar Meenal ne sai kibita da Addu'ar Allah ya bata ikon jure ma zafin kaddarar Allah kuma ya tabbatar da alkhairi a cikin auren ya kauda fitina" "Abban su so kakeyi kace inyi shiru insa ido akaimin yarinya gidan kishiya mai asiri?" "Komai asirin ta Jidda bata isa tayi abunda Allah bai kaddara faruwar shiba, duk abunda Allah ya tsara zai faru a cikin rayuwar Meenal ko tana gaban mu wannan abun saiya sameta, ki duba irin wahalar da yarinyar nan take sha na ciwon mara duk wata yayin al'adarta kodan shi ya kamata ki mata fatan alkhairi kinji Jiddatulkhair" Kunsan ance tsakanin mata da miji sai Allah domin ko haka Baba Auta yasa Mommy Hauwa a gaba sai da ya rarrashi matar shi tsaf ya kwantar mata da hankalin cewa babu abunda zai faru domin ko a nan gidan Sarki na cikin unguwan Meenal din zata zauna, dan yaga alamar zaman Meenal din da kishiyarta ne ke tada mata hankali, "Amma dai Abban su kai zakaje ka gayama hajiya batun auren koh? Dan wallahi nidai bazan je insha fada akan laifin dabani ce na aikata ba! " Ta fad'i hakan tana mai kureshi da ido, murmishi yayi a cikin zuciyar shiko cewa yayi uwar Meenal ma ta amince balle kuma kakarta, amma a sarari sai ya bata amsa da cewa "Koni bani da kwarin gwuiwar tun karar Hajiya a yanzun abu daya dai zanyi shine zan kira Usman in fad'a mishi halin da ake ciki shi kuma sai ya isar da sak'on kunnen ta dan hakan zaifi sauk'i, ke kuma sai ki kira sauran yan uwanki ki shaida musu halin da ake ciki" "Abban su sati uku fa biki kuma ban shirya komai ba! " "Shirin auren diya mace ai dama na ubane kin san kuma koda ace ba Meenal bace Malam zai aurar shi mai d'aukar dawainiyar komai daya danganci bikin auren ne balle kuma auren Yar gaban goshin shi dan haka kisa ranki a inuwa ki koma gefe ki zama yar kallo" "Wani irin in koma gefe in zama yar kallo kuma ai kasan dai ba'a biki ace uwa bata fitar da nata kayan ba" "Baida komai tunda kin dage zan tura miki kud'i sai kiyi naki siyayyar, ina fatan hakan yayi miki? " "Eh hakan yayi nagode Allah ya kara arziki bari in kira su Ya'ya in fada musu, to amma ita Meenal din fa? " Ta tambaya a marairaice dan Allah ya sani gaskiya tana fa tausayama Meenal wallahi. "Wannan kuma kece zakiyi duk yanda zakiyi dan karta gane komai har zuwa lokacin bikin dan ban son tashin hankali " A wannan ranar ba'a kwana ba sai da Jidda ta kira kaf yan uwanta ta shaida musu batun auren Meenal din sai dai bata shaida musu kalubalen dake gaban Meenal d'inba ta bari sai sun iso sai su tattauna, a kuma ranar Baba Usman shima yayi kiran Hajiya Innah ya shaida mata abunda ake ciki, Wuhuhu ina wuta ta saka Malam kuma Kunsan wacece Hajiya dan haka tayi fada tayi fada kamar ta cinna ma kanta wuta, bata iya hakuri ba saida ta dauko mota da kanta ta tuko kanta zuwa gidan Malam dan taji dalilin wannan dibar albarkha daya shirya mata, a cewar ta so yake yaga iyakarta inba haka ba har itace zaisa ranar auren jikanta bata da labari sai dai kwatsam taji wai biki saura sati uku kamar wani a wasan kwaikwayo, So yake wato yaga karshen arzikinta ta kasa fitar da jikarta kunya to wallahi ahirrr din shi dan su kudi suke binsu suna guje musu insha Allah bazata ji kunya ba komai da akema yar gata shi za'ama jikarta wato shi mai Dangi shine ya dauki jikarta yaba dan kannin shi bayan itama gata nan da zabga zabgan jikoki wanke hannu ka tab'a. Koda ta isa gidan tun daga fitowarta daga mota ta fara abunda tafi kwarewa akai wato jidalin fadanta na kullum sosai fa ta burkice ta zuba tijara son ranta ta kira sunan Malam ta kira shi da Babban kwabo wato tunda yasan uban Meenal bazaija da hukuncin shiba shine yasa zai aurar mata da jikarta babu notice tafa tata nata iya iyawarta sai dai kash bata taki sa'ar samun Malam din a gida ba sai Baba Adamu ta samu ta kuma kafe kaida fata cewar bata zuwa ko ina sai taga Malam ido da ido taji dalilin daya yanke hukuncin aurar mata da jikarta bada yawunta ba, komai isar shi dai ai ita itace ta haifi uwar Meenal kuma da Jidda bata haifi Meenal din ba ai isar shi a iya kan nashi yaran zai tsaya, Da kyat dai Baba Adamu ya samu ya bata hakuri sannan yasa cikin yaran gidan suka maidata gida, bata tafi ba saida tabar ma Baba Adamun kashedin cewa gobe²n nan take bukatar a kawo mata Jikarta gidan ta tazo ta zauna da ita na tsayin kwanakin daya rage kafin auren dan itama tana da hakki akan jikan ta, to dai Baba Adamun ya mata alkawarin goben za'a kawo mata Meenal din sannan kuma ya fada mata cewa Meenal din ma bata san da batun auren ba, Wannan jidalin na Hajiya shiya tona halin da ake ciki na auren Meenal a gidan har jama'ar gidan dama makota sukaji labarin cewa Sarki ne zai auri Meenal, Yan bakin ciki dai sunyi haka ma yan farin ciki sun yi, bayan dawowar Malam sai da ya tara kaf ahalin gidan yaja musu kunne akan cewa koda wasa baya son suyi kuskuren har da zaisa Meenal tasan da batun auren Wannan kenan. To gadai Meenal zata koma gidan Hajiya da zama na tsayin satikai, shin koya zaman nasu zai kasance ita da abokin fadan ta AK mai jama'a ga kuma hajiya a gefe, Ina labarin mutanen Lagos Sarki da matar shi, ana dai ta Shirin biki angon ma bai san meke faruwa ba, Ga kuma Teemah uwar Kishi a gefe itada ta lashi takobin cewa bata ba zama da kishiya, Moon budurwar mai gidan yan gayu, koya zataji in akace gidan nan Meenal ne zata zauna a cikin shi matsayin matar gidan? Huhuhuhh ga kuma uwar gayya Meenal ta dage sai shirye shiryen bikin kanne takeyi bata san cewa itama amaryar bace ko ya zatayi in ta samu labari ohooooo, Kowa ya hasaso amsar 🤣🤣🤣🤣 Babu editing 😰 Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 29 *A gurguje* Washe gari kamar yanda Hajiya ta bukata haka Mommy Hauwa ta had'a Meenal da kayan ta zuwa gidan Hajiya, hakika hakan baima Meenal din dad'iba domin a cewar ta zirga zirgan zai mata yawa a matsayin ta na Babbar ya'yar amare, dan ma Allah ya taimake ta sun riga sun kamala exam's din su gaba daya, Koda bukatar Hajiya na komawarta can Tudun wada yaje kunnen Malam baiyi musu akan hakan ba domin koba komai yasan zamanta acan din shima zaifi mishi kwanciyar hankali domin tabbas intana nan sai an samu mai dogon bakin dazai furta batun auren nata a gaban ta. Ita ko Hajiya kaf yayan ta saida ta kira takai musu karar cewa Malam ya nuna mata mulki da isa akan jikarta ya nuna mata bata da wani matsayi dan haka tana bukatar ganin su in ma bazasu samu damar zuwa ba tofa kowa ya turo da nashi gudun mawar dan tama fi bukatar kudaden da zasu turo akan zuwan nasu domin kayan yar gata takeso ta hadama jikarta dan Malam yasan cewa kullum cikin shiri take ita batayi gadon tsiya ba, to dai suma tunda Allah yasa sun san ko sunzo a lokacin ba wani tsiyar zasuyi ba domin infa Hajiya ta kafe ta kafe kenan yasa sai kudaden data bukata suka tura mata, ita kuma taci gaba da shirye shiryen ta na auren jika, Tsaf ta shiga ta fita tabi kwakwafin wanda za'a aurama jikar tata acan ne kuma tajiyo abinda batayi tsammani ba, wato ashe kiyayyar da Malam kema Jiddan ta har ya kai ya dauki yar Jidda yaba yaron dan uwan shi da matar shi ta gagari kowa! Yanzun da ace bata raye kenan haka za'ayi auren ba tareda an shirya Meenal din ba gayarta za'a dauka akaima kishiya wato taji dadin nakasa ta da kyau, to ai in sun san wata basu san wata ba ita kam da ranta da lafiyarta bazata sadaukar da rayuwar Takwarar ta, dan haka tuni itama ta zage damtse wajen neman ma Meenal din duk wani maganin da tasan na tsarin jiki ne sai da ta tanade shi, Satin farko na komawar Meenal gidan bata fuskanci ko wani damuwa ba, domin dai Hajiya bata takura mata kuma duk inda suke bukatar zuwa yawon rabon anko da katin biki Dan gidan Master ne ke zuwa yana kaisu dan sosai yakeji da Meenal din a kokarin shi nason ta bashi dama ya gabatar da kanshi a gidan su tunda gashi allah yasa har za'a aurar da kannin ta yasan koya nema baza'a hanashi ba domin shi baiki ba wallahi a hada bikin ma dana kannin nata, amma yasan Hajiyar tashi ba yarda zatayi da hakan ba sosai fa ta samu yanda take so a wajen Dan gidan Master dan sosai ya bud'e mata bakin aljihu take ta dandake kan nerori domin dai duk abunda take so jiki na rawa yake mata shi, Gashi kuma kwanan nan ta lura ba Malam kadai ba yanzun harta da Mommy Hauwa sosai take sake mata fiyeda lokutan baya domin abun mamaki kulum cikin tambayan ta abunda take so take ga yawan daukarta da sukeyi zuwa kasuwa ita dasu Meelat zuwa siyayyar kayan da take zaton nasu Raheenat ce domin dai dama ko yayyin su maza in zasuyi auren Mommy ne ke hada musu kayan auren, dan haka sai bata damu ba a zaton tasan kila dan Mommy tasan in tace su Raheenat din suzo suje kasuwar tasan ba lallai su sake jiki su zab'i abubuwan da suke bukataba shi yasa, dan haka ta zage damtse da zuciya d'aya ta maida hankali ta dunga d'aukar duk abunda taga ya mata kyau dan tasan dai auren dole ne za'ama kannen ta to amma inta bada nata gudun mawar wajen ganin an shirya musu dakunan su da kyau tasan hakan zai rage musu damuwa, Bawai kananan siyayya kadaiba hatta da kayan gado dasu kurjeru komai ita ta zaba musu sai dai abunda bata sani ba harda nata kayan ta zaba'a domin komai itama sai an tambayeta choice din ta, cikin sauk'i dai abubuwa sukaci gaba da tafiya, Biki ya rage saura sati biyu Mai Jama'a ya duro Zaria domin duk wainar da ake toyawa baya gari yaje Lagos akan wasu harkokin su, ita kuma Hajiya hidindumun data sa a gaban ta sun sha mata kai dan haka ko a waya bata tuna ta bashi labarin abunda ke faruwa ba, a kuma sati biyu da bikin ne Hajiya tasama Aminatu takun kumin fita domin zuwa lokacin ta gama hada duk wani tanadi da tayi domin gyarar jikar nata, ta kuma fad'ama harta da masu gadin gidan cewa koda wasa suka kara barin Meenal din ta fita saita b'ata musu rai wallahi. Ganin cewar Meenal ba had'in kai zata bata ba yasa ta fada mata cewar maganin ciwon marar tane ta amso mata kuma ka'idar maganin sati biyu ake shanshi kuma in an fara amfani dashi ba'a zuwa ko ina gida ake zama dalilin ma da yasa tace Jidda ta maido mata da ita nan kenan, in kuma bata bukatar ta warke ga kofa nan tana iya komawa gidan su, Saida Meenal ta kirga kwanakin daya rage mata kafin zuwan al'adarta sai taga kwanakin duka basufi goma ba, to kenan in har tabi umarnin Hajiya ta zauna tayi amfani da maganin tana sa ran kenan wannan watan lafiya lau zatayi al'adarta kamar na sauran mata, gashi kuma dama tsoron da take ji kenan domin lokacin zuwan nashi a lissafin ta zaizo a cikin bikin ne dan Haka ba komai zata jure zama dai na kwana kin a gidan Hajiya ai mai sauki ne in aka hada da wahalar da take sha duk wata, sai dai gaskiya za'a takura mata dan bata gama rabon katin biki ba amma ba damuwa tunda gasu Moon zasu iso ga kuma su Meelat a gefe, sai dai kuma ya zatayi da yan anacen samarin ta da bata amshi kudaden data yanka musu na anko ba? Wannan ma ba damuwa tunda dai ga waya shi dai Dan Master tasan shegen kwakwa gareshi dole sai yazo inda take dan ma ta gode Allah iliya dan mai karfi bayanan balle yasa mata ido, Ita fa gaba daya bata damu ba domin dad'inta kawai takeji cewa zatayi bikin kannen ta cikin koshin lafiya batareda mutane sun taru akanta suna faman yi mata sannu kamar mai ciwon mutuwa ba. Bayan dawowar AK yayi mamakin ganin Meenal kwana 1&2 a gidan batareda ta koma gidan suba dan iya sanin shi yasa inba dai Moon sunzo ba tofa bata yarda ta kwana a gidan ranar dai ya gaji da ganin nata dan Allah ya sani yarinyar nan fa ba karamin takura mishi takeyi in yana waje ba, dan yanzun ma wani sabon iskanci ta tsira da zarar ta hango shi saita fara mishi wakar da in tanayi yake jin kamar ya shako wuyarta har saita daina numfashi kafin ya saketa, wai shi yarinyar nan take ma wakar.. .. .. Turun turun tuzuru wai yaushe zaka auree. Tuzuru wai yaushe zaka aure.... Wai shi shi din nan da girman shi da mutunci da komai amma tsabar rainin da yarinyar nan ta mishine yasa har take mishi wakar tuzuru wai yaushe zaiyi aure, insha Allah duk ranar daya riketa sai ya fada mata taje gida ta tambaya shekarar Baban ta Adamu nawa yayi a duniya ba tareda mata ba in yaso sai tazo ta hada shekarun da nashi aga wayafi wani zama tuzuru a lokacin! Suna zaune a falon Hajiya tuwo yake ci kamar yanda kowa yasan yafi son cin abinci mai nauyi, "kinyi wanka da ruwan maganin dana hada miki? " Hajiya ta tambaya Meenal wacce fitowarta kenan daga dakin da Hajiya ta sauke ta, "eh nayi"ta bata amsa tana wucewa cikin kitchen da plate din dataci abinci a hannun ta, Saida yaga kulewar ta sannan ya waigo gefen Hajiya, "Me yarinyar nan takeyi a gidan nan wai?" "Ban gane me takeyi a gidan ba!" "Eh na tambaya ne saboda nasan ba zuwa takeyi haka nan ba balle kuma harta kwana gashi kuma tunda na dawo nike ganin ta a gidan kuma na tambayi bala yace min tayi kusan sati a gidan ko laifi tayi a gidan su ta gudo nan? " "Kai dai ka sani da neman ba'asin ka, yarinya ita da gidan kakan nin ta ka kama tambayar me takeyi gaskiya dai ka canza hali wallahi" Ta fada tana karkata dan kwalin kanta zuwa gefe a dai dai lokacin ne kuma Meenal din ta fito daga kitchen waya kare a kunnen ta amma cikin su babu mai iya jin abinda take cewa a wayar harta wuce su ta koma d'aki, Sai da Hajiya ta tabbatar ta shige sannan ta baro kujerar da take zaune ta koma wacce mai jama'an yake kai, duk wannan kusancin da suka samu bai wadace taba sai da tayi kasa da muryar ta sosai tana kara kallon kofar dakin da Meenal ta shiga kai da ganin yanda takeyi ko ba'a fada maka ba kasan cewar irin gulmar nan dako kuda ba'a son yaji shi take Shirin yi. "Aure fa uban ta zai mata karshen watan nan.... " Wani irin mummunar shaka romon daya surb'a a lokacin ya mishi domin har cikin kwakwalwar shi romon ya wuce, aiko sai tari ya biyo baya domin a lokaci guda yaji kurjin shi ta dauka da wani irin radadi kamar na wanda aka watsama barkono akan ciwo, dan haka tari yace bani wajen, tari yake cikin azaba idanuwan shi har sai da suka zubda hawayen azabar da yakeji, "Subhanallah innalillahi sannu sannu sannu Abdul sannu, haka Hajiya ta dunga jera mishi sannu ba kakkautawa sannan ta mika mishi ruwa ya samu yasha kafin ya samu tarin ya lafa mishi da kyar, "Sannu yajine ya tsarke ka koh ai Saida na fadama takwara ta rage attarugun data zuba dan kar yayi yaji amma tace min farfesu in baiji yajiba baya dad'i wannan ai daukar Alhakine, Kara shan ruwan zakaji ya sake ka" Karbar ruwan yayi ya kara sha yana mai jama'a jingina kanshi a jikin kurerar, ba tareda ya iya cema hajiya komai ba duk sannun da take mishi kuwa dan so yake ya tuna abinda yaji ta furta wanda yayi silar da yasa roman nan haura mishi saman kai, Saida yaji yadan sarara sannan ya kamo hannun hajiya guda dake kisa dashi, jajayen idanuwar shi da basu koma dai dai ba har yanzun da jansu ya zuba mata. "Hajiya mai kikace d'azun? " "Umm bari kai dai Mai gida ai wallahi nasan dole ka tayani jimami, kai ma kajishi wani bambara gwai koh? Wai Yar wajen Jidda fa za'ama aure karshen watan nan yau dai saura yan kwanaki" Bai bari takai karshen zancen taba ya tari numfashin ta da cewa"wai wancan yarinyar ce za'ama aure?" Sai da kara gyara zama ya fuskance ta da kyau sannan ya kara cewa"wai auren gaske ko na wasa kike magana akai Hajiya" Wani kallon karfa ka raina min wayau Hajiya ta mishi sannan ta bashi amsa da cewa "dama akwai auren wasa ne Abdul Khareemu? Kuma kayi kasa da muryar ka karka tadamin balli dan ita kanta yarinyar bata san da zancen auren ba dalilin da yasa ta dawo gidan nan da zama kenan har zuwa lokacin bikin dan ba'a son ta sani," Sai da ta bata fuska cike da jimami ta daura da cewa "kuma kaji wani cin amana Soja fa zasu aura mata Sojan ma mai mata harda yaran shi 4 ba kuma iya nan tashin hankalin ya tsaya ba domin dai ita matar sojan in fada maka babu ubanda bai san yanda ta shanye mijin ba sai yanda taga dama taje juyashi ko iyayen shi baya tunawa dasu, amma dan cin amana aka dauki jikata aka bashi, fadamin dan Allah inba sun shirya ganin bayan jikata ba mai zai sa suyi haka yarinyar dako ruwan zafi bata iya dafawa ba, shi yasa kaga na kasa zaune na kasa tsaye ina ta faman shiga da fita wajen neman mata magungunan tsarin jiki, atoh ban nemi kowa da sharri ba duk wanda ya nufamin jika da sharri shi zaiga abunshi, To bagashi ba daukotan da nayi yayi amfani tunda a yan kwanakin nan fa tare muke shiga kitchen ina nuna mata abubuwa dan Sam Jidda bata koya mata komai ba kuma a haka suke son aurar da ita, nayi magana iyayen ka sunce wai babu ruwana ai iyayen ta sun fini iko da ita, to fisabilillahi so suke insa ido a nakasa min rayuwar jika? " Shidai tunda ta fara magana fuskan ta kawai ya kafe da kallo wai aure Aurefa wai za'ama waccen jinjirar wannan aure za'a mata ko raino dai za'a kaima mijin? Ga manya manyan yan mata nan ba'a aurar dasu ba sai wannan yar tatsitsitar hanci duk majina kai cike da rashin kunya, Allah ya sani ya tausaya mata ya kuma tausaya ma wanda za'a daurama auren ta dan yasan zai sha fama. Babban abun da yake kara daure mishi kai kuma shine cewar da Hajiya tayi wai yarinyar bata san da batun auren ba, to kenan dai auren dole iyayen ta zasu mata? Shifa tsakanin shi da Allah sosai abun ya daure mishi kai domin shidai kullum yakanji ana maganar auren dole bai taba gani ba sai gashi yau a kusa dashi, haka nan kawai kuma sai ya farajin tausayin yarinyar yana shigar shi, karamar yarinya a rasa ma mijin da za'a aura mata sai soja kuma ma mai mata harda yara koya zataji duk ranar da taji batun auren? "Lallai akwai rikici " ya fad'a a bayyane, "Akwai shi kam sai dai muyi fatan Allah yasa auren shine mafi alkhairi a gareta" "Ameen" ya amsa dashi yana yunkurawa da niyyar barin wajen domin a yanzun kam bayajin zai iya cin wani abu kuma dan gaba daya abincin ya fita akan shi. "Tafiya zakayi kuma baka gama cin abincin ba? " "Nakoshi Hajiya sai da safe" ya fad'a yana ficewa daga side din gaba daya, sai da ta kwashe kayan sannan itama ta shige. Satin biki. Tako ina fa kowa ya shirya ranar auren kawai ake jira, Su Aisha Moon da iyayen su duk sun iso garin Zaria, sai dai suma komai da sukeyi cikin taka tsantsan sukeyin shi domin dai kar a fasa maganar harta koma kunnen Meenal, Hajiyar ku ko ta dage da shan magani domin duk abinda hajiya ta bata amfani take dashi a sonta na ganin anyi hidimar biki da ita lafiya, samarin ta kuma tuni ta amshi kudaden ankon data yanka musu, wasu sukan zo har nan gidan ne in sunzo takan saci jiki ta fita ko kuma ta tura Rukayya ko su Meelat su amso mata in tana bukatar wani abu a gida kuma cikin yayyen ta wani ke kawo mata domin shima dai ya sa'eed yayi busy da nashi shirin bikin, Zuwa yanzun kam ba karamin tausayi Meenal keba AK ba domin dai shi Allah ya sani har yanzun bai fara mata kallon mace ba balle kuma wai ace matar aure, hakan nema yasa yau da ta fito daga sashen Hajiya zata sashen Hajiya jummai ya kura mata ido, Kai jama'a Allah dai ya tsine ma shedan la'anan ne inba shedan da kitsama mutum mugun abu a zuciya ba dan Allah yana zaman zaman shifa a kofar gida cikin abokan shi kirar wayar shi da wani abokin kasuwancin yayi ne hakan yasa dole ya shigo gidan dan ya samu damar amsa wayar a tsanake ya gama wayar nefa sai ya dan zauna dan akwai wani number din da abokin zai tura mishi shine fa kafin shigowar number din yarinyar nan ta fito tana waya, kuma yasan dai wayar nan bazai wuce da shegen yaron nan Bash Dan gidan master ba dan yanzun yaga yabar kofar gidan bayan ya sauke daya daga cikin kannen shi ta shigo gidan, yana mamakin ta yanda har yanzun saurayin nata bai san da batun auren da za'a mata ba, koda yake abune anatayin shi a munafunce, da farko dai yanda take ta fara'a har fararen hakoranta dake jere gwanin sha'awane ya dauki hankalin shi har yabi fuskar nata da kallo, tofa a kokarin shi na ganin ya dauke fuskar shi akanta ne yayi kasa da idon shi, shine dan wulakanci irin na sharrin shedan idanuwan shi suka wani ja burki suka tsaya akan kirjin ta doguwar rigar atamfa ce da akayi ma dinkin fitetgown ga shi kuma dinkin yayi dai² da jikin ta kuma dan iskanci haka nan ta wani fito a bunta ko lillibi babu, shi dai bai son yanda akayi daga kallon fuska ya koma karewa sauran sassan jikin ta kallo ba, Allah ma yaga zuciyar shi bai kalleta da wani manufa ba sai dai sharrin shedan yasa ya kasa dauke idon shi a kanta dan koda ta wuce shi ya zamana ta juya mishi baya haka yaci gaba da kallon ta zuwa lokacin kuma sai yaga kamar ma da gangan takeyin wani abun saboda yanda duk inta motsa shima jikinta yake motsawa gaba daya kasa katabus yayi har sai da ya dena ganin ta bayan ta kule ma ganin shi, a rayuwar zai iya rantsewa da Allah cewa yaune rana ta farko daya tsaya ya karema halittan wata diya mace kallo domin duk wadanda ke binshi baima da lokacin su balle har ya bata lokaci wajen kallon surar ta, Inba shedana irin na shedan ba duk wannan kallon bai wadatar da shiba har Saida zuciyar shi ke raya mishi wai duk wannan abubuwan da ya gani fa a jikin yarinyar nan a hakan ma fa wai dan bata gama girma bane to in tafi haka kuma ya zata zama kenen? Haka kawai shedan ya fara hasko mishi ita a matsayin cikakkiyar budurwa, bakon al'amarin da ba kasafai yafiye samun shiba sai ga shi yau da rana tsaka sharri irin na shedan yana so yasa shi a shiga uku domin dai sai ga shi gaba daya tsigogin jikin shi da duk wata jijiyar da jini ke yawo a jikin shi ta motsa domin dai alkalim rubutun shi da koshi bayace ga ranar da yaga ta tashi tsaye car cikin kwanciyar hankali bane yau ta nemi farayi mashi hankoro, shida baya taba iya shiga irin yanayin da yake ciki a yanzun inba sanyi yayi sanyi ba koshi din ma sai in kamar yana kallo haka yaci karo da masu fararen kunnuwan nan da allah bai yi halittan kunya ajikin su ba suna aikata aikin nan da Allah ya hana har sai ka biya sadaki ba shine kawai yake jin irin hakan amma yau a banza a hofi shedan yana neman ya kaishi ya baro shi. Runtse idon shi yayi da karfi bayan ya kai hannu ya danne alkalamin dake shirin tona mishi asiri a tsakar gidan fa jama'a, auzubillahi minal shaidanir rajeem haka yaci gaba da mai maita wa, a kokarin shi nason fitowa daga halin da shedan ya jefe shi, wallahi wani irin kunya yaji ya sauko ya lullube shi, Allah dai ya isa kuma bazai daina Addu'ar Allah ya mashi katangar karfe tsakanin shi da shaidan ba, yanzun nan dan Allah da wani yazo ya ganshi a haka mai zaice mishi? Shike nan sai a fara mishi kallon wani dan iska fa, Lallabawa yayi ya shige sashen shi kuma har lokacin bai daina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan ba. Dan wallahi yau da shedan din nan mutum ne babu ubanda zai hanashi ya faffashe mishi fuska wallahi, amma yayi alwashin har yarinyar nan tabar gidan nan bazai kara bari su hadu ba. *** Bari mu leka gidan uwar gida. Daga ita har yaranta sunyi kokar dan ganin cewa kota waya ne sun samu Sarki sai dai ina kwata² hakan yaki samuwa domin ko duk ya watsa number din su a inda ko sun kira shi bazasu samu ba, Haka dai suka had'a karfi da karfe suke ta hidimar shirin auren da dukiyoyin su domin harta gyaran gidan shi su suka dauki nauyi sun kuma yi bajin ta kwarai dan sunyi komai fiyema da wanda shidin zai iyayi dan ganin cewa sun faranta ran uwar gida, Ganin cewa biki yana ta matsowa babu labarin ango yasa suka shirya cewa daya daga cikin kannin shi ya shirya ya tafi har Lagos din ya shaida mashi cewa Uwar gida fa bata da lafiya kuma tace tana bukatar ganin shi, ita kuka Dr Mubarak suka kira yazo gida ya daura mata ruwa domin a zahiri dama tana bukatar shi dan gaba daya taki kwantar da hankalin ta ganin takeyi kamar in Sarki bai k'ara auren nan ba tofa shike nan zata rasa shine gaba daya. Kunsan duk abunda kakeyi sai ka samu mai maka bacci da ido daya domin ko ashe tun bayan zuwan da Hajiya tayi gidan Malam tayi tijarar da yasa maganar auren na Meenal fitowa cikin kishiyoyin Uwar gida aka samu wacce ta kira Teemah saboda tsabar kwarewa a iya munafunci wai ta kirane ta mata Allah ya sanya alkhairi na Karin arzikin da mijinta ya samu, sosai teemah tayi mamakin kiran domin ita dai iya sanin ta bata san wani abun alkhairin daya samu sarki wanda har mutanen zaria zasu kira su taya ta murna akan shi ba dalilin hakan ne yasa ta tambayar me yake faruwa domin dai su Lagos lafiya lau suke, To dai uwar gula dama abunda take so kenan dan haka ta fad'ama teemah cewar ai aure akaba Sarki anan cikin family harma an tsaida rana yanzun haka ma an gama komai na shirin biki, Sosai abun ya kadama Teemah zuciya amma da yake yar barikice bata bari ta nuna cewar ta jijjiga dajin zancen ba sai ma Addu'ar Allah sanya alkhairi da tayi ta yanke wayar ta. Wani irin katoton ashariya ta lailayo ta maka akan ahalin Sarki tundaga kan manyan harda wadanda basuzo duniyar ba duk saida ta tabbatar ta kwashe ma kowa albarkha, tafayi hauka son ranta sai dai tayi alwashin cewa aure koh! Ita bazata hana shi aure ba tunda har aure suke so ayi auren saboda tanan nema zata kara tabbatar musu da cewa ita din taci dubu sai ceto Allah ya kaimu lokacin biki lafiya, tafa cije kwarai ta yanda hatta kawayen ta babu wacce ta fadama cewar mijin ta zai mata kishiya kai in ma ta bari akaji ai taji kunya wallahi wai Ita Teemah ita ce har uwar miji zata ma kishiya dan wannan ai bazata ce mijin ta zai mata kishiya ba dan a yanzun kam tasan wallahi ko cocaine Sarki ke shak'a bai iya yace zai mata kishiya, to su shirya zata aje kowa a matsayin shi kamar yanda ta saba, a zaton su tana raye har zata zuba ido wata karamar yarinya ta shigo mata gida harma ta kwanta mata da miji tayi ciki itama ta haihu God forbid over her death body ai gara ace bara raye da dai taga zuwan wannan ranar. Koda dan sako ya iso daga zaria akan cewar uwar gida bata da lafiya tana bukatar ganin Sarki ko kadan bata tada hankalin taba sai ma dama data ba Sarkin akan in ya isa yasa a gyara mata gidan ta itama in an kwana biyu zata zo ta duba jikin Uwar gidan, yaji dadin furucinta sosai a ganin shi ta fara saukowa tunda har gashi ita da kanta yau ta furta zataje duba jikin mahaifiyar shi, bai san cewa ita tayi hakan bane saboda ta samu lokacin da zata shirya ma zuwan kishiyar nata da kyau. A ranar da suka isa zaria hankalin Sarki ya tashi matuka a yanda ya samu mahaifiyar shi domin kwanciya tayi nakwa nakwa tamkar wacce tayi doguwar jinya, ganin ta a cikin wannan hali sosai ya daga mishi hankali ya faraji a jikin shi cewar bai kyauta ba, ga kuma yanda hatta da yaran shi suke ta mamman ne mishi saboda ko suma sunyi kewar shi, hakan nan a kasar zuciyar shi yakejin bai kyauta ba sai dai koshi bai san dalilin daya hanashi zuwa garesu ba, shifa zaima iya cewa gaba daya ma mantawa yayi dasu wallahi. Ganin da uwar gida tayi cewar jikin shi yayi sanyi kwarai yasa ta bijiro mishi da bukatar ta cewa son take a daura auren shi da Aminatu kamar yanda ta fada mishi tun tuni dan tana son taga auren kafin ta mutu dan a cewarta tasan ciwon ta bana tashi bane, sosai dai tayi mishi hannun ka mai sanda had'e da nasiha a matsayin wasiyyarta a gareshi, Da yake abinda ke dawainiya dashi yafi yin tasiri ne a sanda yake tare da Teemah hakan yasa cikin kwanakin ya maida hankalin shi kachokan wajen ganin ya kula da mahaifiyar shi da kuma son ya cika mata burin ta na auren da take son yayi duk da allah ya sani wallahi ba ya bukatar Karin kowani aure a yanzun dai, to shi mai yake nema a yanzun da baya samun shi a wajen matar shi? Su dai kawai dan basa son teemah ne shi yasa suka kasa yi mata uzuri, amma tunda sun dage da maganar auren zaiyi kowa ma hankalin shi sai ya kwanta, to amma Teemah fa? Zuciyar shi ta tambaye shi, ya gode Allah ma da tace zata zo inya so in tazo zaiyi kokarin fahimtar da ita yanda abun yake, shifa yanzun damuwar shima yanda suka tashi suka zubama yarinyar can da suke kira matar da zai aura kaya a gidan sama da kasa duk kayan tane ga kuma Teemah tace a gidan zata sauka shi dai kawai nema suke su sakashi cikin damuwa, ga kuma wata magana da uwar gida keyi na cewan wai yaje ya samu yarinyar yaji ko tana bukatar wani abun na sha'anin biki, yanzun fisabilillahi shi da girman shi da komai sai yaje yasa a mishi sallama da yarinyar can dako hankali bai isheta ba wai da sunan yazo wajen ta, kai ina ai sai dai ya nemi wani ya aika, shi babban damuwar shi ma yanda duk suka wani kira abokan aikin shi dana kasuwancin shi suka fad'a musu maganar bikin yanzun haka zasu zo suga amarya wata yar ficika a wajen bayan kowa yasan tsarin shi. (Jama'ah Sarkin nan mafa dan rainin wayau ne ku fad'a mishi da babbar murya cewar muma auren dole za'a mana ba son shi mukeyi ba🙄). isowar su Moon sosai ya kara sa Meenal ta sake jikin ta suke abubuwan su ita da kawayen ta kullum kuma tana lissafin kwanakin da suka rage mata ta koma gida aci gaba da hidima da ita da yike ma ba wani shagalin biki za'ayi ba walima ce kawai aka shirya za'ayi su kuma sun shirya yin zaman yinin su a gidan su Meelat yanda zasu fi sakewa, Tun ranar da shedan ya nemi sa AK yayi abun kunya ya kama kanshi ya kiyaye duk abunda zai had'a shi da Meenal a cewar shi amarya tsautsayi gareta dan a yanda ya tara ta da yawa din nan yasan inya riketa tofa bazata sha ta dad'i a hannun shi, Sai dai a yan kwanakin sosai su Moon suka matsa mishi akan alkawarin wayar daya musu da dad'ewa akan in sun gama secondary zai siya musu manyan wayoyi dan so suke suci biki da wayoyin su a hannu yanda zasu samu daukar hotunan biki. Share Please #Ummiee~Zaria⚜️🔱 FAMILY HOUSE ⚜️🔱 ~{{ȶֆɨռȶֆɨʏǟ ʍǟƊǟʊʀɨռӄɨ Ɗǟʏǟ}}~ *©®UZ-2023.* *👨‍👩‍👧‍👦DANGINA!👨‍👩‍👧‍👦* _{{ℳℽ ℱᗅℳⅈℒℽ}}_ ⱤɄ฿Ʉ₮₳₩₳. *ZAINAB USMAN* _{Uɱɱιҽҽ~Zαɾια}_ *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *₲₳฿₳₮₳Ɽ₩₳* _Yabo da godiya da'iman wa abadan na Allah ne. Salati da sallama sune na ɗan gatan Allah fiyayyen halitta Annabi Muhammad (s.a.w),tare da iyalansa da sahabban sa baki ɗaya._ *₴₳Đ₳Ʉ₭₳Ɽ₩₳* _Gaba ɗaya kacokan ɗin labarin nan sadaukarwa ne gareku ababen alfaharina._ *JAMILA MUSA* {{Meelat Musa}} *HAUWA MUH'D USMAN* {{Real Smasher}} *H UMAR* {{Admin Beneficial}} & *SAJIDA* {{🇳🇪 NIGER}} *₮Ʉ₭Ʉł₵ł* _Wannan shafin tukuici ne ga gidaje biyu masu albarka,BENEFICIAL WRITERS ASSO,tare da gidanmu na gado abun alfahari FAMILY HOUSE,Allah ya ƙara haɗin kai ameen. ```Page 29 kuyi hakuri wannan page din yayi double in kunzo karatu , ku karanta na can k'asan shine cikakken page ba sauran na zaman ba. Washe garin ranar kamar yanda Hajiya ta buk'ata haka Mommy Hauwa ta had'a Meenal da kayan ta zuwa gidan Hajiyan,Bayan ta fad'a mata cewar magani zataje sha a gidan, hakika hakan baima Meenal din dad'i ba domin a cewar ta zirga zirgan zai mata yawa a matsayin ta na Babbar ya'yar amare ga kuma ya sa'eed daya kamata ace itace zata tsaya akan batun komai na bikin shi domin dai itace taje ta zaiyana ma Malam halin da Billy take ciki saboda ganin da tayi shi Sa'eed d'in baiyi yunkurin komai ba har yanzun , dan ma Allah ya taimake ta sun riga sun kamala exam's din su gaba daya ai da hidimar ta mata yawa wallahi, Koda bukatar Hajiya na komawarta can Tudun wada yaje kunnen Malam baiyi musu akan hakan ba domin koba komai yasan zamanta acan din shima zaifi mishi kwanciyar hankali domin tabbas intana nan sai an samu mai dogon bakin dazai furta batun auren nata a gaban ta wanda shi kuma bai shirya fuskantar ta da maganar a yanzun ba. Ita ko Hajiya kaf yayan ta saida ta kira takai musu karar cewa Malam ya nuna mata mulki da isa akan jikarta ya nuna mata bata da wani matsayi ta yanda har ya iya sanya auren jikarta ba tareda sanin taba, dan haka tana bukatar ganin su in ma bazasu samu damar zuwa ba tofa kowa ya turo da nashi gudun mawar dan tama fi bukatar kud'ad'en da zasu turo akan zuwan nasu domin kayan yar gata takeso ta had'ama jikarta kodan Malam yasan cewa kullum cikin shiri take ita batayi gadon tsiya ba, to dai suma tunda Allah ya sa sun san ko sunzo a lokacin ba wani tsiyar zasuyi ba domin infa Hajiya ta kafe ta kafe kenan yasa sai kud'ad'en data buk'ata suka tura mata, ita kuma taci gaba da shirye shiryen ta na auren jika, Tsaf ta shiga ta fita tabi kwakwafin wanda za'a aurama jikar tata, acan ne kuma tajiyo abinda batayi tsammani ba, wato ashe kiyayyar da Malam kema Jiddan ta har ya kai ya d'auki yar Jidda yaba yaron dan uwan shi da matar shi ta gagari uban kowa! Yanzun da ace bata raye kenan haka za'ayi auren ba tareda an shirya Meenal din ba gayarta za'a dauka akaima kishiya wato taji dadin nakasa ta da kyau tunda an mata auren gani kasheni, to ai in sun san wata basu san wata ba ita kam da ranta da lafiyarta bazata sadaukar da rayuwar Takwarar ta a banza ba wallahi , dan haka tuni itama ta zage damtse wajen neman ma Meenal din duk wani maganin da tasan na tsarin jiki ne sai da ta tanade shi atoh maye yaci kanshi ba dai jikarta ba, Satin farko na komawar Meenal gidan bata fuskanci ko wani damuwa ba, domin dai Hajiya bata takura mata sai ma nan nan da takeyi da ita wajen ganin ta jata a jiki dan Wallahi in tana mata wani abun sai taga kamar ba Hajiyar data sani bace wannan wata daban ce, dan a yan kwanakin sosai Hajiya ta tsiri yawon zaga dangi da ita ga janta da takeyi suna shiga kitchen tare tana koya mata kalolin girke girke, harma da sauran ayyukan gida kuma duk inda suke bukatar zuwa yawon rabon anko da katin biki Dan gidan Master ne ke zuwa yana kaisu kuma Hajiyar bata hanawa dan sosai yakeji da Meenal d'in a kokarin shi nason ta bashi dama ya gabatar da kanshi a gidan su tunda gashi allah yasa har za'a aurar da k'annin ta yasan koya nema baza'a hanashi ba domin shi baik'i ba wallahi a had'a bikin ma dana kannin nata, amma yasan Hajiyar tashi ba yarda zatayi da hakan ba sosai fa ta samu yanda take so a wajen Dan gidan Master dan sosai ya bud'e mata bakin aljihu take ta dandake kan nerori domin dai duk abunda take so jiki na rawa yake mata shi, shi dai yana son Aminatu sai dai duk nacin shi har yanzun Meenal bata yarda ko Hajiya ya shiga ya gaisheta ba, Gashi kuma kwanan nan ta lura ba Hajiya da Malam kadai ba yanzun harta da Mommy Hauwa sosai take sake mata fiyeda lokutan baya domin abun mamaki kulum cikin tambayan ta abunda take so take ga yawan daukarta da sukeyi zuwa kasuwa ita dasu Meelat zuwa siyayyar kayan da take zaton nasu Raheenat ce domin dai dama ko yayyin su maza in zasuyi auren Mommy ne ke had'a musu kayan auren, dan haka sai bata damu ba a zaton ta tasan kila dan Mommy tasan in tace su Raheenat d'in suzo suje kasuwar tasan ba lallai su sake jiki su zab'i abubuwan da suke bukataba shi yasa, dan haka ta zage damtse da zuciya d'aya ta maida hankali ta dunga d'aukar duk abunda taga ya mata kyau dan tasan dai auren dole ne za'ama kannen ta to amma inta bada nata gudun mawar wajen ganin an shirya musu dakunan su da kyau tasan hakan zai rage musu damuwa, Bawai k'ana nan siyayya kad'aiba hatta da kayan gado dasu kujeru komai ita ta zab'a musu sai dai abunda bata sani ba harda nata kayan ta zaba'a domin komai itama sai an tambayeta choice din ta, cikin sauk'i dai abubuwa sukaci gaba da tafiya, Biki ya rage saura sati biyu Mai Jama'a ya duro Zaria domin duk wainar da ake toyawa baya gari yaje Lagos akan wasu harkokin su dan haka bashi da masaniya akan abinda ake ciki , ita kuma Hajiya hidindumun data sa a gaban ta sun sha mata kai dan ga kuma bikin Billy jikar Turai dan haka ko a waya bata tuna ta bashi labarin abunda ke faruwa ba, a kuma sati biyu da bikin ne Hajiya ta sama Aminatu takun kumin fita domin zuwa lokacin ta gama hada duk wani tanadi da tayi domin gyarar jikar nata, ta kuma fad'ama harta da masu gadin gidan cewa koda wasa suka k'ara barin Meenal din ta fita saita b'ata musu rai wallahi. Ganin cewar Meenal ba had'in kai zata bata ba yasa ta fada mata cewar maganin ciwon marar tane ta amso mata kuma ka'idar maganin sati biyu ake shanshi kuma in an fara amfani dashi ba'a zuwa ko ina gida ake zama dalilin ma da yasa tace Jidda ta maido mata da ita nan kenan, in kuma bata buk'atar ta warke ga kofa nan tana iya komawa gidan su, Saida Meenal ta kirga kwanakin daya rage mata kafin zuwan al'adarta sai taga kwanakin duka basufi goma ba, to kenan in har tabi umarnin Hajiya ta zauna tayi amfani da maganin tana sa ran kenan wannan watan lafiya lau zatayi al'adarta kamar na sauran mata, gashi kuma dama tsoron da take ji kenan domin lokacin zuwan nashi a lissafin ta zaizo a cikin bikin ne dan Haka ba komai zata jure zama dai na kwana kin a gidan Hajiya ai mai sauk'i ne in aka hada da wahalar da take sha duk wata, sai dai gaskiya za'a takura mata dan bata gama rabon katin biki ba amma ba damuwa tunda gasu Moon zasu iso ga kuma su Meelat a gefe, sai dai kuma ya zatayi da yan anacen samarin ta da bata amshi kudaden data yanka musu na anko ba?dan fa kaf dinsu kowanne da harajin data d'aura mishi, Wannan ma ba damuwa tunda dai ga waya shi dai D'an Master tasan shegen kwakwa gareshi dole sai yazo inda take dan ma ta gode Allah iliya dan mai karfi bayanan balle yasa mata ido, dan kwanaki ya buga mata kashedi akan inya k'ara ganin ta da wani saurayi da sunan yazo wajenta to yasin a gaban saurayin zai kakkafta mata mari, kuji wata magana fa irinta masu afa kwaya dan Allah shida yake tara yan mata a kofar gidan su waya mishi magana sai ita dan yana mata bak'in ciki yaga tauraron ta ya fara haskawa to ai bashi kad'ai bane mai farin jini wallahi. Ita fa gaba d'aya bata damu ba domin dad'inta kawai takeji cewa zatayi bikin kannen ta cikin koshin lafiya batareda mutane sun taru akanta suna faman yi mata sannu kamar mai ciwon mutuwa ba. *** Bayan dawowar AK yayi mamakin ganin Meenal kwana 1&2 a gidan batareda ta koma gidan suba dan iya sanin shi yasan inba dai su Moon sunzo ba tofa bata yarda ta kwana a gidan ranar dai ya gaji da ganin nata dan Allah ya sani yarinyar nan fa ba karamin takura mishi takeyi in yana waje ba, dan yanzun ma wani sabon iskanci ta tsira da zarar ta hango shi saita fara mishi wakar da in tanayi yake jin kamar ya shako wuyarta har saita daina numfashi kafin ya saketa, wai shi yarinyar nan take ma wakar.. .. .. Turun turun tuzuru wai yaushe zaka auree... Tuzuru wai yaushe zaka aure.... Tanayi tana gyada kai. Wai shiii, shidai shi din nan da girman shi da mutuncin shi da gemun shi da komai amma tsabar rainin da yarinyar nan ta mishine yasa har take mishi wakar tuzuru wai yaushe zaiyi aure, insha Allah duk ranar daya riketa sai ya fada mata taje gida ta tambaya shekarar Baban ta Adamu nawa yayi a duniya ba tareda mata ba in yaso sai tazo ta had'a shekarun da nashi aga wayafi wani zama tuzuru a lokacin! (Kai jama'a dan Allah ku dunga ma jikan Hajiya fad'a dan ya iya dukan kwano, insha Allah ni kuma saina tuna maka wannan maganar zuwa gaba) Suna zaune a falon Hajiya tuwo yake ci kamar yanda kowa yasan yafi son cin abinci mai nauyi, "kinyi wanka da ruwan maganin dana hada miki? " Hajiya ta tambaya Meenal wacce fitowarta kenan daga d'akin da Hajiya ta sauke ta a ciki, "eh nayi"ta bata amsa tana wucewa cikin kitchen da plate d'in dataci abinci a hannun ta, Saida yaga kulewar ta sannan ya waigo gefen Hajiya, "Me yarinyar nan takeyi a gidan nan wai?" "Ban gane me takeyi a gidan ba! naga nan ma ai gidan sune" "Eh na tambaya ne saboda na san ba zuwa takeyi haka nan ba balle kuma harta kwana gashi kuma tunda na dawo nike ganin ta a gidan kuma na tambayi bala yace min tayi kusan sati a gidan ko laifi tayi a gidan su ta gudo nan? " "Kai dai ka sani da neman ba'asin ka, yarinya ita da gidan kakan nin ta ka kama tambayar me takeyi gaskiya dai ka canza hali wallahi" Ta fada tana karkata dan kwalin kanta zuwa gefe a dai dai lokacin ne kuma Meenal din ta fito daga kitchen waya kare a kunnen ta amma cikin su babu mai iya jin abinda take cewa a wayar harta wuce su ta koma d'aki, Sai da Hajiya ta tabbatar ta shige sannan ta baro kujerar da take zaune ta koma wacce mai jama'an yake kai, duk wannan kusancin da suka samu bai wadace taba sai da tayi kasa da muryar ta sosai tana kara kallon kofar dakin da Meenal ta shiga kai da ganin yanda takeyi ko ba'a fad'a maka ba kasan cewar irin gulmar nan dako kud'a ba'a son yaji abinda za'ace shi take Shirin yi. "Aure fa uban ta zai mata karshen watan nan.... " Wani irin mummunar shaka romon daya surb'a a lokacin ya mishi domin har cikin kwakwalwar shi romon ya wuce, aiko sai tari ya biyo baya domin a lokaci guda yaji kirjin shi ya d'auka da wani irin rad'ad'i kamar na wanda aka watsama barkono akan ciwo, dan haka tari yace bani wajen, tari yake mai cike azaba idanuwan shi har sai da suka zubda hawaye dan azabar da yakeji, "Subhanallah innalillahi sannu ! sannu!! sannu!!! Abdul sannu, haka Hajiya ta dunga jera mishi sannu ba k'ak'k'autawa sannan ta mik'a mishi ruwa ya samu yasha kafin ya samu tarin ya lafa mishi da kyar, "Sannu yajine ya tsarke ka koh ai Saida na fad'ama takwara ta rage attarugun data zuba dan kar yayi yaji amma tace min farfesu in baiji yajiba baya dad'i wannan ai daukar Alhakine, Kara shan ruwan zakaji ya sake ka" Karbar ruwan yayi ya kara sha yana mai jingina kanshi a jikin kurerar, ba tareda ya iya cema hajiya komai ba duk sannun da take mishi kuwa dan so yake ya tuna abinda yaji ta furta wanda yayi silar da yasa roman nan haura mishi saman kai, Saida yaji yadan sarara sannan ya kamo hannun Hajiya guda dake kusa dashi, jajayen idanuwan shi da basu koma dai dai ba har yanzun da jansu ya zuba mata. "Hajiya mai kikace d'azun? " "Umm bari kai dai Mai gida ai wallahi nasan dole ka tayani jimami, kai ma kajishi wani bambara gwai koh? Wai Yar wajen Jidda fa za'ama aure karshen watan nan yau dai saura yan kwanaki" Bai bari takai karshen zancen taba ya tari numfashin ta da cewa "wai wancan yarinyar ce za'ama auren?" Ya fad'i hakan yana nuni da hannu zuwa d'akin da Meenal ta shiga, Saida ya k'ara gyara zama ya fuskance ta da kyau sannan ya k'ara cewa "wai auren gaske ko na wasa kike magana akai Hajiya" Wani kallon karfa ka raina min wayau Hajiya ta mishi sannan ta bashi amsa da cewa "dama akwai auren wasa ne Abdul Khareemu? Kuma kayi kasa da muryar ka karka tadamin b'alli dan ita kanta yarinyar bata san da zancen auren ba dalilin da yasa ta dawo gidan nan da zama kenan har zuwa lokacin bikin dan ba'a son ta sani," Sai da ta b'ata fuska cike da jimami ta d'aura da cewa "kuma kaji wani cin amana Soja fa zasu aura mata Sojan ma mai mata harda yaran shi 4 ba kuma iya nan tashin hankalin ya tsaya ba domin dai ita matar sojan in fad'a maka babu ubanda bai san yanda ta shanye mijin ba sai yanda taga dama take juyashi ko iyayen shi baya tunawa dasu saboda ta gama shanye shi ta sud'e tass wallahi , amma dan cin amana aka d'auki jikata aka bashi, fadamin dan Allah inba sun shirya ganin bayan jikata ba mai zai sa suyi haka yarinyar dako ruwan zafi bata iya dafawa ba sai da tazo gidan, shi yasa kaga na kasa zaune na kasa tsaye ina ta faman shiga da fita wajen neman mata magungunan tsarin jiki, atoh ban nemi kowa da sharri ba duk wanda ya nufamin jika da sharri shi zaiga abunshi, To bagashi ba d'aukotan da nayi yayi amfani tunda a yan kwanakin nan fa tare muke shiga kitchen ina nuna mata abubuwa dan Sam Jidda bata koya mata komai ba kamar dai bani naba jidda tarbiya ba wallahi kuma a haka suke son aurar da ita, nayi magana iyayen ka sunce wai babu ruwana ai iyayen ta sun fini iko da ita, to fisabilillahi so suke insa ido a nakasa min rayuwar jika? " Shidai tunda ta fara magana fuskan ta kawai ya kafe da kallo wai aure Aurefa wai za'ama waccen jinjirar wannan aure za'a mata ko raino dai za'a kaima mijin? Ga manya manyan yan mata nan ba'a aurar dasu ba sai wannan yar tatsitsitar hanci duk majina kai cike da rashin kunya, Allah ya sani ya tausaya mata ya kuma tausaya ma wanda za'a daurama auren ta dan yasan zai sha fama. Babban abun da yake k'ara d'aure mishi kai kuma shine cewar da Hajiya tayi wai yarinyar bata san da batun auren ba, to kenan dai auren dole iyayen ta zasu mata? Shifa tsakanin shi da Allah sosai abun ya daure mishi kai domin shidai kullum yakanji ana maganar auren dole bai taba gani ba sai gashi yau a kusa dashi, haka nan kawai kuma sai ya farajin tausayin yarinyar yana shigar shi, karamar yarinya a rasa ma mijin da za'a aura mata sai soja kuma ma mai mata harda yara koya zataji duk ranar da taji batun auren? "Lallai akwai rikici " ya fad'a a bayyane, "Akwai shi kam sai dai muyi fatan Allah yasa auren shine mafi alkhairi a gareta" Hajiya ta amsa mishi dashi "Ameen" ya amsa dashi yana yunk'urawa da niyyar barin wajen domin a yanzun kam bayajin zai iya cin wani abu kuma dan gaba daya abincin ya fita akan shi. "Tafiya zakayi kuma baka gama cin abincin ba? " "Nakoshi Hajiya sai da safe" ya fad'a yana ficewa daga side d'in gaba daya, sai da ta kwashe kayan sannan itama ta shige. *Satin biki.* Tako ina fa kowa ya shirya ranar auren kawai ake jira, Su Aisha Moon da iyayen su duk sun iso garin Zaria, sai dai suma komai da sukeyi cikin taka tsantsan sukeyin shi domin dai kar a fasa maganar harta koma kunnen Meenal saboda su sun samu labarin bikin auren harda Meenal amma iyayen su sun kwab'esu akan su kama bakin su, Hajiyar ku ko ta dage da shan magani domin duk abinda hajiya ta bata amfani take dashi a sonta na ganin anyi hidimar biki da ita lafiya, samarin ta kuma tuni ta amshi kud'ad'en ankon data yanka musu, wasu sukan zo har nan gidan ne in sunzo takan saci jiki ta fita ko kuma ta tura Rukayya ko su Meelat su amso mata in tana buk'atar wani abu a gida kuma cikin yayyen ta wani ke kawo mata domin shima dai ya sa'eed yayi busy da nashi shirin bikin, Zuwa yanzun kam ba karamin tausayi Meenal keba AK ba domin dai shi Allah ya sani har yanzun bai fara mata kallon mace ba balle kuma wai ace matar aure, hakan nema yasa yau da ta fito daga sashen Hajiya zata sashen Hajiya jummai ya k'ura mata ido cike da tausayinta, Kai jama'a Allah dai ya tsine ma shed'an la'anan ne inba shed'an da kitsama mutum mugun abu a zuciya ba dan Allah yana zaman zaman shifa a kofar gida cikin abokan shi kirar wayar shi da wani abokin kasuwancin shi yayi ne hakan yasa dole ya shigo gidan dan ya samu damar amsa wayar a tsanake, bayan ya gama wayar ne fa sai ya d'an zauna dan akwai wani number d'in da abokin zai turo mishi shine fa kafin shigowar number d'in yarinyar nan ta fito tana waya, kuma yasan dai wayar nan bazai wuce da shegen yaron nan Bash D'an gidan Master ba dan yanzun yaga ya bar k'ofar gidan nan bayan ya sauke d'aya daga cikin kannen shi ta shigo gidan, yana mamakin ta yanda har yanzun saurayin nata bai san da batun auren da za'a mata ba, koda yake abune anatayin shi a munafunce, da farko dai yanda take ta fara'a har fararen hakoranta dake jere gwanin sha'awane ya d'auki hankalin shi har yabi fuskar nata da kallo, tofa a kokarin shi na ganin ya dauke fuskar shi akanta ne yayi k'asa da idon shi, shine dan wulakanci irin na sharrin shedan idanuwan shi suka wani ja burki suka tsaya kyam akan kirjin ta doguwar rigar atamfa ce da akayi ma dinkin fitetgown a jikin ta ga shi kuma d'inkin yayi dai² da jikin ta kuma dan iskanci haka nan ta wani fito a binta ko lullib'i babu, shi dai bai san yanda akayi daga kallon fuska ya koma karewa sauran sassan jikin ta kallo ba, Allah ma yaga zuciyar shi bai kalleta da wani manufa ba sai dai sharrin shed'an yasa ya kasa d'auke idon shi a kanta dan koda ta wuce shi ya zamana ta juya mishi baya haka yaci gaba da kallon ta zuwa lokacin kuma sai yaga kamar ma da gangan takeyin wani abun saboda yanda duk inta motsa shima jikinta yake motsawa gaba d'aya kasa katabus yayi har sai da ya dena ganin ta bayan ta kule ma ganin shi, a rayuwar zai iya rantsewa da Allah cewa yaune rana ta farko daya tsaya ya karema halittan wata d'iya mace kallo domin duk wad'anda ke binshi baima da lokacin su balle har ya bata lokaci wajen kallon surar wata a cikin su, Inba shed'ana irin na shed'an ba duk wannan kallon bai wadatar da shiba har Saida zuciyar shi ke raya mishi wai duk wannan abubuwan da ya gani fa a jikin yarinyar nan a hakan ma fa wai dan bata gama girma bane to in tafi haka kuma ya zata zama kenen? Haka kawai shed'an ya fara hasko mishi ita a matsayin cikakkiyar budurwa, bakon al'amarin da ba kasafai yafiye samun shiba, sai ga shi yau da rana tsaka sharri irin na shed'an yana so yasa shi a shiga uku domin dai sai ga shi gaba d'aya tsigogin jikin shi da duk wata jijiyar da jini ke yawo a jikin shi ta motsa domin dai alkalamin rubutun shi da koshi bayace ga ranar da yaga ta tashi tsaye car cikin kwanciyar hankali bane yau ta nemi farayi mashi hankoro, shida baya tab'a iya shiga irin yanayin da yake ciki a yanzun inba sanyi yayi sanyi ba koshi din ma sai in kamar yana kallo haka yaci karo da masu fararen kunnuwan nan da allah bai yi halittan kunya ajikin su ba suna aikata aikin nan da Allah ya hana har sai ka biya sadaki ba, shine kawai yake jin irin hakan amma yau a banza a hofi shedan yana neman ya kaishi ya baro shi. Runtse idon shi yayi da karfi bayan ya kai hannu ya danne alkalamin dake shirin tona mishi asiri a tsakar gidan fa jama'a, auzubillahi minal shaidanir rajeem haka yaci gaba da mai maita wa, a kokarin shi nason fitowa daga halin da shedan ya jefe shi, wallahi wani irin kunya yaji ya sauko ya lullube shi, Allah dai ya isa kuma bazai daina Addu'ar Allah ya mashi katangar karfe tsakanin shi da shaidan ba, yanzun nan dan Allah da wani yazo ya ganshi a haka mai zaice mishi? Shike nan sai a fara mishi kallon wani dan iska fa, Lallabawa yayi ya shige sashen shi kuma har lokacin bai daina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan ba. Dan wallahi yau da shedan din nan mutum ne babu ubanda zai hanashi ya shak'o wuyar shi ya faffashe mishi fuska wallahi, amma yayi alwashin har yarinyar nan tabar gidan nan bazai kara bari su hadu ba. *** Bari mu leka gidan uwar gida. Daga ita har yaranta sunyi kokari dan ganin cewa kota waya ne sun samu Sarki sai dai ina kwata² hakan yak'i samuwa domin ko abinda basu sani ba shine tuni Teemah duk ta watsa number d'in su a inda ko sun kira shi bazasu samu ba, Haka dai suka had'a karfi da karfe suke ta hidimar shirin auren da dukiyoyin su domin harta gyaran gidan shi su suka d'auki nauyi sun kuma yi bajin ta kwarai dan sunyi komai fiyema da yanda shid'in zai iyayi dan ganin cewa sun faranta ran uwar gida, Ganin cewa biki yana ta matsowa babu labarin ango yasa suka shirya cewa daya daga cikin k'annin shi ya shirya ya tafi har Lagos d'in ya shaida mashi cewa Uwar gida fa bata da lafiya kuma tace tana bukatar ganin shi, Dr Mubarak suka kira yazo gida ya daura mata ruwa domin a zahiri dama tana bukatar shi dan gaba d'aya tak'i kwantar da hankalin ta ganin takeyi kamar in Sarki bai k'ara auren nan ba tofa shike nan zata rasa shine gaba daya. Kunsan duk abunda kakeyi sai ka samu mai maka bacci da ido d'aya domin ko ashe tun bayan zuwan da Hajiya tayi gidan Malam tayi tijarar da yasa maganar auren na Meenal fitowa cikin kishiyoyin Uwar gida aka samu wacce ta kira Teemah saboda tsabar kwarewa a iya munafunci wai ta kirane ta mata Allah ya sanya alkhairi na Karin arzikin da mijinta ya samu, sosai teemah tayi mamakin kiran domin ita dai iya sanin ta bata san wani abun alkhairin daya samu Sarki wanda har mutanen Zaria zasu kira su taya ta murna akan shi ba, dalilin hakan ne yasa ta tambayar me yake faruwa ? domin dai su Lagos lafiya lau suke, To dai uwar gulma dama abunda take so kenan dan haka ta fad'ama teemah cewar ai aure akaba Sarki anan cikin family harma an tsaida rana yanzun haka ma an gama komai na shirin biki, Sosai abun ya kad'ama Teemah zuciya amma da yake yar barikice bata bari ta nuna cewar ta jijjiga dajin zancen ba sai ma Addu'ar Allah sanya alkhairi da tayi ta yanke wayar ta. Wani irin katoton ashariya ta lailayo ta maka akan ahalin Sarki tundaga kan manyan harda wadanda ma basuzo duniyar ba duk saida ta tabbatar ta kwashe ma kowa albarkha, tafayi hauka son ranta a gidan ta ita kad'ai sai dai tayi alwashin cewa aure koh! Ita bazata hana shi aure ba tunda har aure suke so ayi auren saboda tanan nema zata kara tabbatar musu da cewa ita d'in taci dubu sai ceto Allah ya kaimu lokacin biki lafiya, tafa cije kwarai ta yanda hatta kawayen ta babu wacce ta fad'ama cewar mijin ta zai mata kishiya kai in ma ta bari akaji ai taji kunya wallahi wai Ita Teemah ita ce har uwar miji zata ma kishiya dan wannan ai bazata ce mijin ta zai mata kishiya ba dan a yanzun kam tasan wallahi ko cocaine Sarki ke shak'a bai isa yace zai mata kishiya rana tsaka kamar saukar aradu ba, to su shirya zata aje kowa a matsayin shi kamar yanda ta saba, a zaton su tana raye har zata zuba ido wata karamar yarinya ta shigo mata gida harma ta kwanta mata da miji tayi ciki itama ta haihu God forbid bad thing over her death body ai gara ace bata raye da dai taga zuwan wannan ranar. Koda d'an sak'o ya iso daga zaria akan cewar uwar gida bata da lafiya tana bukatar ganin Sarki ko kadan bata tada hankalin taba sai ma dama data ba Sarkin akan in ya isa yasa a gyara mata gidan ta itama in an kwana biyu zata zo ta duba jikin Uwar gidan, yaji dad'in furucinta sosai a ganin shi ta fara saukowa tunda har gashi ita da kanta yau ta furta zataje duba jikin mahaifiyar shi, bai san cewa ita tayi hakan bane saboda ta samu lokacin da zata shirya ma zuwan kishiyar nata da kyau. A ranar da suka isa zaria hankalin Sarki ya tashi matuka a yanda ya samu mahaifiyar shi domin kwanciya tayi nakwa nakwa tamkar wacce tayi doguwar jinya, ganin ta a cikin wannan hali sosai ya d'aga mishi hankali ya faraji a jikin shi cewar bai kyauta ba, ga kuma yanda hatta da yaran shi suke ta mamman ne mishi saboda ko suma sunyi kewar shi sosai dan ko a waya basajin duriyar shi balle kuma na uwar su, hakan nan a kasar zuciyar shi yakejin bai kyauta ba sai dai koshi bai san dalilin daya hanashi zuwa garesu ba, shifa zaima iya cewa gaba daya ma mantawa yayi dasu wallahi. Ganin da uwar gida tayi cewar jikin shi yayi sanyi kwarai yasa ta bijiro mishi da bukatar ta cewa son take a daura auren shi da Aminatu kamar yanda ta fada mishi tun tuni dan tana son taga auren kafin ta mutu dan a cewarta tasan ciwon ta bana tashi bane, sosai dai tayi mishi hannun ka mai sanda had'e da nasiha a matsayin wasiyyarta a gareshi, Da yake abinda ke dawainiya dashi yafi yin tasiri ne a sanda yake tare da Teemah hakan yasa cikin kwanakin ya maida hankalin shi kachokan wajen ganin ya kula da mahaifiyar shi da kuma son ya cika mata burin ta na auren da take son yayi duk da allah ya sani wallahi ba ya bukatar K'arin kowani aure a yanzun dai, to shi mai yake nema a yanzun da baya samun shi a wajen matar shi? Su dai kawai dan basa son teemah ne shi yasa suka kasa yi mata uzuri, amma tunda sun dage da maganar auren zaiyi kowa ma hankalin shi sai ya kwanta, to amma Teemah fa? Zuciyar shi ta tambaye shi, ya gode Allah ma da tace zata zo inya so in tazo zaiyi kokarin fahimtar da ita yanda abun yake, shifa yanzun damuwar shima yanda suka tashi suka zubama yarinyar can da suke kira matar da zai aura kaya a gidan sama da kasa duk kayan tane ga kuma Teemah tace a gidan zata sauka shi dai kawai nema suke su sakashi cikin damuwa, ga kuma wata magana da uwar gida keyi na cewan wai yaje ya samu yarinyar yaji ko tana bukatar wani abun na sha'anin biki, yanzun fisabilillahi shi da girman shi da komai sai yaje yasa a mishi sallama da yarinyar can dako hankali bai isheta ba wai da sunan yazo wajen ta, kai ina ai sai dai ya nemi wani ya aika, shi babban damuwar shi ma yanda duk suka wani kira abokan aikin shi dana kasuwancin shi suka fad'a musu maganar bikin yanzun haka zasu zo suga amarya wata yar ficika a wajen bayan kowa yasan tsarin shi. (Jama'ah Sarkin nan mafa dan rainin wayau ne ku fad'a mishi da babbar murya cewar muma auren dole za'a mana ba son shi mukeyi ba🙄). isowar su Moon sosai ya kara sa Meenal ta sake jikin ta suke abubuwan su ita da kawayen ta kullum kuma tana lissafin kwanakin da suka rage mata ta koma gida aci gaba da hidima da ita da yike ma ba wani shagalin biki za'ayi ba walima ce kawai aka shirya za'ayi su kuma sun shirya yin zaman yinin su a gidan su Meelat yanda zasu fi sakewa, Tun ranar da shedan ya nemi sa AK yayi abun kunya ya kama kanshi ya kiyaye duk abunda zai had'a shi da Meenal a cewar shi amarya tsautsayi gareta dan a yanda ya tara ta da yawa din nan yasan inya riketa tofa bazata sha ta dad'i ba a hannun shi, Sai dai a yan kwanakin sosai su Moon suka matsa mishi akan alkawarin wayar daya musu da dad'ewa akan in sun gama secondary zai siya musu manyan wayoyi dan so suke suci biki da wayoyin su a hannu yanda zasu samu daukar hotunan biki. Share Please #Ummiee~Zaria [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦*DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ """""Page 30 Meenal kuzo muje Ya Ak yana kiran mu, d'ago kanta data d'aura akan pillow tana waya da D'an gidan Master tayi tana maida duban ta zuwa ga Moon dake maganar, "In kunje kuce mishi nayi bacci" ta fad'i hakan k'ara maida hankalin ta kan wayar da takeyi dan sosai takejin dad'in waya da Bash dan tsaf yake maida kanshi karamin yaro yayi ta biyema shirmen ta. " kutmelesi lallai nema Babin nan Kin ma isa kisa inyi k'arya! Wallahi inya tambaya cewa zanyi kince baki zuwa, Moon taso muje waya sani ma ko alkhairi ke kiran mu" Banza Meenal tayi da ita su kuma ganin hakan suka sa kai suka fice basu k'ara bi ta kanta ba. Tana nan a kwance tana ci gaba da wayar har suka dawo, da gudun besfa suka shigo d'akin suna ihun murna suka wani kankame ta suna cigaba da ihu, "Ke dallah ki yanke wayar nan haka, alkhairin Allah ya same mu da rana tsakar nan" Aisha ta fad'i hakan tana karb'e wayar Meenal d'in ta kashe ta gaba d'aya, "Ke miye haka bamu gama maganar da mukeyi ba fa kike kashe min waya dan Allah, Ni bani wayata kina ganin ina zaman zamana Bash yana neman ya kwanto min kurar da zata cinye ni har kasusuwa na" Babu wacce tabi takan abinda take cewa a cikin su sai ma kwalayen dake hannuwan su da suka mik'a mata a tare. Surprise suka had'a baki wajen fad'a cikin ihu. "Ke Beb please bar wannan zancen a gefe duba kiga abunda muka samo" cewar Aisha, bin kwalin wayar Meenal tayi da kallo a yayin da ta wuntsulo babu shiri zuwa inda suke " ke Sister kamar fa kwalin waya nike gani,ko idanuwa na ne basa gani da kyau?" Hannuwan ta bibbiyun ta mik'a ta karb'i kwalayen a hannun su, Aisha ce mai taya ta bud'ewa dan Moon gaba d'aya tsabar zumud'i yasa ko zama ta kasa murna kawai takeyi ji take tamkar ta lashi tafin kafarta tsabar dad'i, Bayan sun fidda wayar daga cikin kwalayen su kuwa haka suka dunga kallon wayoyin kamar wasu sabbin shiga, "Ke Moon wallahi wannan irin wayar dake hannun Aunty Sas ce, wooo mu yan mata muma mun faso gari, Allah dai ya k'ara arziki Mai Jama'a wallahi Ya'ya ya dad'e bai burgeni irin yau ba, ashe da rabon muma zamu rike babbar waya yar shafa" kashewa sukayi ita da Moon cike da farin ciki gefen Aisha Moon ta zauna, "ke Sister ai wallahi Ya AK dan aljannah ne kin san Allah dayace muzo cikina harya d'ura ruwa all my thought nayi zaton ko waccen mai zubin yan ruwan ta fad'a mishi tsokanarta da Meenal tayi d'azun ne shi yasa nike ta rara gefe, Allah dai yabar mana Yayan mu ya nuna mana ranar auren shi ku kwakw kwaso Alanta da shoki wallahi" "Kaiii.. wai ban fa gane ba ,ku tsaya mu nawa ne a wajen nan? " Meenal ta tambaya. "Uku" suka had'a baki wajen bata amsa. "To mu uku amma kuma naga wayoyin kwaya biyu kacal tawa wayar fa? " ta tambaya tana daure fuska, "nifa ban son halin wariya da nuna yan ubanci ya zai baku waya bai bada nawa ku kawomin ba?" "Dallah rufema mutane baki Malama ba saida mukace miki yana kiran muba? Fad'amin wani amsa kika bani ? cewa fa kikayi muce kinyi bacci, to badan halin kiba dai yace in kin tashi kije yana neman ki" "To aini da nace kuce ina baccin nayi zaton an kai mishi gulma nane, kunga karku kunna wayoyin bari inje in amso nawa in dawo, kuma Malamai bari inje in dawo in baku labari D'an gidan master zai ballo min ruwa wai zai tura iyayen shi wajen Malam a mishi tambayar aurena " "Tambaya? " suka had'a baki wajen furtawa suna masu zaro idanuwa waje, Moon ne ta kalli Aisha sannan ta d'aura da cewa "neman aure cikin neman aure kenan fa? Tab" Meenal batabi takan abunda Moon tace ba ta fice daga d'akin tana mai cewa bari taje ta dawo, har ta fita kuma ta dawo ta d'auko wani zumbulelen Hijjabin Aisha ta zumbula ta fice daga d'akin, Bayan fitar ta Aisha ne ta kalli Moon, "Waike mai yasa bakin ki bashi da kintsi ne? Yanzun da kikace neman aure cikin neman aure data fahimci wani abun kuma mai zakice mata? " Shiru Moon tayi ba tareda taba Aisha amsa ba sai can ta nisa kafin tace, "Aisha wallahi ina matuk'ar jin tausayin Meenal ban san ya zataji a yayinda batun auren ta kai tsaye zai isa zuwa gareta ba? karfin hali kawai nikeyi wajen danne harshe na amma ni banji dad'in da aka boye mata ba, auren mutum yau sauran kwanaki amma ace mutum bai sani ba! Kalli yanda take ta shirye shiryen ta hankali kwance, kina jin fa saurayin ma da take ikirarin tana so d'in ma ta kasa bashi daman zuwa gaban iyayen ta saboda ya nuna auren yake so da wuri" ta karasa fad'a hawaye na taruwa a idon ta, Matsowa kusa da ita Aisha tayi, "Moon duk yanda kikeji nima inajin kwatan kwacin hakan to amma ya zamuyi tunda iyayen mune suka zab'i su boye mata nasan suna da nasu dalilin nayin hakan, nidai Addu'a na Allah yasa mijin yana son ta nasan in shi yana son ta komai zaizo da sauk'i domin shi zaiyi k'ok'arin cusa mata soyayyar shi a hankali², kuma ai su dama gidan su kinsan da wuri ake musu aure sai dai gaskiya nima inajin tausayin Bash dan na lura kaf cikin samarin ta yafi sauran sonta itama kuma naga alamar kamar tana d'an son shi duk da dai kullum tana cewa bata wani son shi nasan karya takeyi. Amma dai kiyi hakuri ki rufa ma kanki asiri karkiyi katobaran da maganar auren nan Meenal zataji shi a bakin ki tunda har su Meelat suka kasa fad'a mata to kema kisa ido" Bayan fitowarta kai tsaye d'akin shi ta wuce dan tasan ba lallai ace harya koma majalisar shi ba dan tana lura bai fiye zama a wajen da rana fatse fatse ba, Jiyo karar TV yana aiki a falon hakan yasa dole sai da ta bud'e murya ta kwad'a sallama yanda zai jiyota, Daga ciki shi kuma bayan ya amsa Sallamar kana ya bata umarni akan ta shigo, Su uku ne a falon, Musty, Yusuf Wase, sai kuma shi Dan mai k'arfin, kamar wata ta Allah haka ta durkusa har kasa tana gaishe su kamar malamar islamiya, su dai sauran amsawa kawai sukayi ba tareda sun raya komai a cikin ran suba, shiko gogan k'are mata kallo kawai yakeyi da mamaki yau kuma bayan dogon hijjabin data aro harda wani gaisuwar munafunci kuma har k'asa. kai shifa yaga alamar shi kad'ai yarinyar nan ta raina ma wayau wato saboda tasan abun da ta aikata d'azun shine yanzun ta wani zo kamar wata ta Allah, to shidai bazai biye mata su zama d'aya ba. "Zauna mana kin ma mutane tsaye a Saman kai" ya fad'a yana mata nuni da kujerar dake gefen shi,waje ta nema ta zauna d'in kamar yanda ya buk'ata, "Ya Musty an gama mana d'inkin mu kuwa? Kasan gobe zan koma gida! " "Haba Bestyn mu kayan Amarya guda ai dole a had'a shi da wuri, Mai kyau bata fad'a miki nakai mata su wajen ta jiya bane? " "No bamuyi waya ba yau dan dama tace min yau bazata shigo nan ba sai da yamma" Katse su AK yayi da cewa. "Malam idan kana son magana da itane ka bari in sallameta tukun na, amma yanzun nina kirata! " Ba tareda Musty ya tanka abunda AK d'in yace ba, ya mik'e ya shige ciki yana cema Wase "Yusuf in zaka fita ka tasheni please". "Gani Ya'yan mu" tace jin shiru bai kara cewa komai ba. "Miye ma sunan ki? " Dagowa tayi ta kalle shi, Dan Allah jama'a inba neman magana ba kuji min wani tambaya fa, "Wai yauma ka k'ara manta sunan nawa? " Shiru yayi bai bata amsa ba, ita kuma dan a zauna lafiya burinta dai ya bata wayarta ta samu damar fecewa a d'akin in yaso sai ya ciji kanshi ma in yaso, hakan yasa ta bashi Amsa da cewa "Meenat, Meenal, Ameenatu yar Baba Malam" "Shekarun ki nawa? " "Saura kad'an in cika 17" Sai da ya d'ago idanuwan shi yayi mata kallon mintoci sannan yana ci gaba da kallon nata yace "mai ya had'aki da wacce tazo nema na d'azun har kika mata rashin kunya? " Saida ta wani d'auke kai tana hararar gefe sannan tace "to ba ita bace kawai zata wani shigoma mutane gida kai tsaye kamar gidan, su kuma kawai daga gani na kamar wata nid'in yar aiken ta ce zata wani cemin (Kee shiga ki kiramin Abdul) ta fad'i hakan tana kwaikwayon muryar Hafsan, To shine ni kuma nace mata ba ke ba sai dai Keke, to kawai daga nace haka shine zata wani tasomin tana min masifa harfa kamar zata rufeni da duka ta ringayi wai na mata rashin kunya ni kuma nace mata ai da bata baro gidan su tazo gidan su saurayi ba da nima ban ganta ba balle in mata rashin kunyan" Shiru tayi bayan takai nan a labarin da take bashi, jin ta tona ma kanta asiri, itafa matsalarta d'aya shine bata iya shirga karya ba, atoh gaskiyarta take fadi sai dai uban kowa ya mutu. "Uhummn ina jinki cigaba ai ba iya nan aka tsaya ba sai kuma kikace mata me inajin ki? " Shiru tayi tana rarraba idanu, "Kimin magana" ya fad'i hakan a yayin da ya d'auko kwalin wayar dake gefen shi wanda tunda ta shigo falon idon ta ke kan kwalin kuma tsaf yake ankare da ita, "Kinyi shiru ko iya abunda ya faru kenan? " "To ba ita bane tazo gidan mutane kuma ta kama musu masifa, in ma aikena zatayi ai sai tace min kanwata shiga ki kiramin Yayan ki Abdul in yana ciki,cikin lalama koba komai ai tunda ta haifeni ai bazan k'i zuwa ba, to ni kuma da naji haushi ne nace mata ai itama gashi nan ta zama tuzuruwa kullum tana yawon zuwa wajen saurayi bayan tasan ba auren ta zaiyi ba" Zumbur ta mik'e ta koma can bakin kofa, "Wallahi kika sake kika bar d'akin nan kin ma kanki" ya fad'i hakan a yayin da yake nunata da kwalin wayar hannun shi, bubbuga kafafuwan ta ta farayi a k'asa cike da shagwaba irin na sakakkun yara sannan tace "ai wannan d'aukar alhaki da jan raine in dai dan Allah zakama mutum abu ai basai ka tsaya ka fara tono tsofaffin laifukan da yayi maka ba, kuma dai ai koba komai Allah yana son mutum mai yafiya mai maida komai ba komai ba, kuma ni ai taimakon ta nayi dan Manson Allah S, A, W cewa yayi in kaga mutum yana aikata ba dai² ba ka fad'a mishi gaskiya in yaso ko baiyi amfani da abunda ka fad'a ba kai dai ka fita hakkin shi, kuma ai kowa yasan cewa ciwon y'a mace na y'a mace ne, itama inaga ta rasa mafad'a ne shi yasa basu fad'a mata cewar ta hakura dakai haka nan ba tunda dai kai ba auren ta zakayi ba. "Keee ni nace miki budurwa tace ita dama harda zakice min ba auren ta zanyi ba?" "Allah kuwa budurwar kane tunda itace kullum take zuwa wajen ka harma fad'a takeyi da sauran yan matan ka, nidai in saboda itane dan na fad'a mata gaskiya kake fushi to kayi hakuri " Yusuf wase dake zaune a falon tuntuni duk da hankalin shi yana kan film din da yake kallo a Tv amma tsaf kunnuwan shi yake Jiyo mishi tattaunawar da akeyi tsakanin AK da yarinyar data lissafo sunayen ta har guda hud'u kuma wai duka ita ke amsa sunayen ne yayi dariyar da har saida sautin dariyar tashi ta fito fili, lallai Allah da iko yake ashe yana raye zaiga ranar da wata d'iya zata iya fuskantar abokin shi irin haka gaba da gaba yana fadar magana tana maida mishi da amsa ba tareda tsoro ko fargaba a cikin muryar taba? Wacece wannan yarinyar da har AK ya zauna yake mata magana a hankali haka bada taratsi ko hargagin daya saba ba, Dan haka ya dago kanshi dan ya kare mata kallo, ga mamakin shi sai ya hango wata yar karamar yarinya wacce in ba karya idanuwan shi suke mishi ba kai tsaye zai iya cewa shi kamannin ta ma tsaf yake mishi kama dana abokin shi sai dai kawai dan ita mace ce, cire duban shi yayi daga kanta ya mayar kan fuskar AK dan ya kara tantancewa sai akayi sa'a suka had'a ido shima AK din kallon shi yakeyi, Gira d'aya Wase ya d'age ma AK alamun lafiya? "Dariyar me kakayi? " AK ya tambaya. "An hana dariya ne? " Shima ya maida mishi da tambaya maimakon ya bashi amsa, "Malam tashi kabar min falo ka wuce ciki! " "Kai harka ma isa kace in tashi, dan uban ka bakaga ina kallo bane? " "Kaje ciki kayi kallon" "Kai banfa zuwa ko ina wallahi anan nayi niyyar zama garama kayi ta kanka" Muryarta ne ya katse su yayin da, Ta kira sunan AK da wata irin shagwababbiyar murya "Ya Abdul" "Ai nace miki ki dawo ki zauna koh? " "Bazaka duke niba? " "Dama na tab'a dukan ki? " "Ah ah" "To zoki zauna" Sai da ta maida duban ta wajen Wase sannan tace "Abokin Yaya kana sheda yace bazai duke Niba koh?" Shima da yike miskilin ne bai iya amsa mata da baki ba illah kai daya gyad'a mata kawai yaci gaba da kallon shi ita kuma ta dawo ta zauna a kujerar dake kusa da AK sabanin d'azun data zauna nesa dashi sosai. "Yayan mu dan Allah kayi hakuri kaga ni gobe ma zan koma gidan mu in bar muku gidan ku" "Eh ki bar nan kuma kije gidan mijin shima kici gaba dayi mishi rashin kunyan da kika saba koh? Allah dai yasa baya duka dan zama dake in mutum nada saurin hannu wata rana saiya karya ki" Ba tareda ta bama abunda ya fad'a mahimmanci ba tace "kai Yayan mu Kannina su Raheenat nefa za'ama aure ni sai na gama makaranta" Maganar da tayi ne yasa ya tuna cewa ashefa duk wainar da toyawa a b'oye akeyi ita shashashar batama san wainar da ake toyawa ba, Allah sarki haka nan kuma sai yaji ya tausaya mata,yanzun ace shine za'ama irin auren nan yanaga ai sai yayi kanin mutuwa wallahi amma sai ya kauda maganar da cewa, "ki tabbatar kuma baki shigo kin d'auke min turare ba kafin kibar gidan nan" Dariya ta kyalkyale dashi irin dariyar dabai tab'a ganin tayi ba "Eh kin d'auka cewa ban san kece me d'auke min turare da shower gel d'ina ba? Kallon ki kawai nikeyi" "To kayi hakuri ni ai kamshin ne yake min dad'i ina son kamshin sosai" "Eh kina son kamshin amma bakya son mai turaren! " "Na'am" ta amsa dashi domin kasa² kwarai yayi maganar ta yanda ba kowa ne zai iya jiba. Paper bag d'in dake gefen shi ya d'auko sannan ya saka kwalin wayar dake hannun shi a ciki, "ga nawa gudun mawar bikin nan Allah ya bada zaman lafiya" ya fadi hakan yana mik'a mata, "In bud'e inga miye a ciki? " "Ah ah ki bari sai kinje ciki sai ki bude kinji" Harta yunkura zata fice daga falon ya kira sunan ta. " *AMMINA* " Juyowa tayi tana kallon shi har yanzun murmushinta mai kyau take aika mishi. "Kiyi hakuri da duk yanda rayuwa ta juya miki, karkice zakiyi fushi kik'i yin biyayya ma iyayen ki kinji? Allah ya baku zaman lafiya ki kula da kanki" Oho ita fa wallahi bata wani fahimci abunda ya fad'aba dan haka da ameen kawai ta amsa tana ficewa daga falon da sauri shima dai dan karta ruga da gudu ne yayi mata fad'a. Shiko da kallo ya bita jikin shi duk yayi sanyi, Dan yan kwanakin nan da yayi tareda ita a gida d'aya sosai yarinyar ta tsaya mishi a zuciya sosai yakejin tausayin ta, karamar yarinya da ita za'a tauye mata rayuwa, Mai da bayan shi yayi ya kwantar cikin kujeran yana mai sauke ajiyar zuciya, "ya dai? " wase ya tambaya "dai dai" shi kuma ya maida mishi da amsa. Sosai sukayi celebrating din samun sabbin waya k'arin dadi kuma gashi harda kyautar turare da wani set din d'an kunne da sarka mai kyau da Ak ya mata. Washe gari ranar da zata koma gida, bayan sun gama karyawa Rukayya ce ta shigo tace mata taje Baba Usman yana kiranta a falon shi, Ba tareda tunanin komai ba ta bi bayan Rukayyar dan zuwa amsa kiran, Duka Yayyan maman ta mazan su da matan duka ta samu a falon suna zazzaune kafin su iso falon tabbas hira taji suna tayi sai dai kuma tana shiga kowa sai yayi shiru aka rasa mai magana har saida ta fara gaishe su tukun na, bayan gaisuwa, Aunty Hassana ce ta kirata da cewa "Meenat My daughter zoki zauna anan kusa dani" dan haka can kusa da ita din Meenal ta zauna, Baba Usman ne ya fara magana kamar haka. "Mai sunan Hajiya kuma ya naga yau kin fi kullum fara'a ne kodan yau zaki gudu gidan ku kibar Takwarar taki? " Murmushi tayi "Baba ai na dade a gidan nan fa kuma ana ta shirin biki ni ina nan kuma jibi ne Daurin aurefa shi yasa zan tafi da wuri inje mu karasa shiri," "Ah lallai kam gara kiyi harama, Sai da yayi gyaran murya sannan ya d'aura da cewa "Meenal " "Na"am"ta amsa dashi. Shi kuma yace idan na tambayeki zaki bani amsa, " Sai da ta gyad'a kai sannan ta bud'e baki tace "eh Baba" "Yauwa d'iyar kirki, so nike ki fad'amin kaf fad'in duniyar nan wanene kike ganin yafi kowa sonki? " Ba tareda wani fargaba ba ta bashi amsa da cewa "Babana Malam sai Mommy da Baba Auta" "Masha Allah to kenan ashe wanda yake matukar kaunar ki kamar yanda Malam ke son ki zai iya yanke ko wani irin hukunci a rayuwar ki? " Wannan karan ma bata b'ata lokaci ba ta amsa da cewa " eh " "Yayi kyau amsar da nike son inji kenan dama a bakin ki, amma ina so in miki nasiha da cewa shi bawa bashi ke tsara rayuwar shi sannan ta tafi mashi a yanda yake soba, ina fatan duk abinda kikaji kuma gani a gidan ku idan kin koma bazaki bari yayi tasiri a cikin zuciyar ki ta yanda zaisa ki manta cewa su wadanda suka yanke wannan hukuncin akan ki sunfi kowa sonki ba, ina fatan ki d'auki abin a sannu kuma kiyima iyayen ki damu ma biyayya kinji, Allah ya miki albarkha" Duk da kasancewar ba komai take sawa a zuciyarta ba balle ya dameta ba amma dai wad'an nan kalaman na Baba Usman masu kama da gugar zana sun sa ta farajin wani iri a cikin jikin ta, shin kodai wani abu na faruwa ne wanda ita bata da masaniya? "Baba akwai wani abun da yake faruwa ne wanda ya kamata ace na sani kuma ban sani ba? " Ta tambaye shi da sanyin jiki, Bai iya bata amsa ba sai Dady Ahmad ne ya amsa mata da cewa ba komai mai sunan Hajiya tashi kije ki k'arasa shirin ki gaba d'aya zaku wuce dasu Momin ki can gidan naku, Bayan fitan ta haka sukaci gaba da tattaunawar su duk dai akan batun auren na Meenal. "Zuwa k'arfe nawa ne shi Mijin nata zaizo? " Dady Ahmad ya tambaya, "To jiya dai Mukhtar cemin yayi da safe zaizo" To Allah ya kawo shi lafiya bari in koma ciki akwai abinda nikeyi in sun k'araso sai amin magana. *** Koda 11 na safe ta buga su Meenal sun dad'e da isa Unguwan Malamai sai dai kuma saida ta sauke tarkacen ta a gidan su Meelat a cewarta ta dawo gidan su Meelat din kenan har sai an watse biki, Wani ikon Allah kuma sai gashi wannan karon sai ganin al'adarta tayi kawai babu ciwon marar kwata² hakan kuma ba karamin dad'i ya mata ba, a cewar ta zata sakata ta wala a bikin nan babu ciwon mara babu fargaban wanke make-up in zatayi sallah dan haka gayu Salamu Alaikum. Bayan ta huta a gidan su Meelat suna cikin shan hirar su misalin karfe 1 Maman Kano da wata mata d'aya daga cikin kannin Malam suka shigo gidan nasu Meelat a cewar su wai tunda aka fara biki basuga Meenal d'in ba shine sukazo tafiya da ita dan ga Amare can ana musu kunshi itama taje a mata, Babu yanda Meenal batayi dasu Moon akan suzo suje can gidan tare ba amma sukak'i acewar su taje kawai zasu zo daga baya dan Maryam ta kira musu wata Sadiya ita zata zo ta musu, Haka suka tasa keyarta har gida, tun a hanya duk wad'anda suka had'u dasu sai taji suna fad'in Amarya amarya ita dai bata damu ba in an kirata da sunan sai dai ta washe baki a zaton ta kila basu san cewa banda ita a cikin wad'anda za'a aurar bane. Sai dai kuma harta a cikin gidan nasu ma dake cike dam da baki na nesa dana kusa wadanda suka fara hallara nan dinma duk inda suka wuce suma dai amaryar kawai suke ta fad'i, sashen su taso ta fara wucewa bayan sun shigo domin su Maman kano sashen matan Malam suka wuce bayan sun ce mata in sun gaisa da Mamanta tazo ta same su a wajen innar su a mata kunshi, Da murnar ta ta shiga sassan nasu dan gidan fa ko ina masha Allah dan hatta da yaran gidan mata dake aure nesa duk sun iso mazan dake kasar waje ma duk sun dawo dan haka mai makon ta wuce wajen Mommy Hauwa sai ta juya akalarta zuwa inda Yayyenta sai da ta bisu duk sukayi gaisuwar yaushe gamo sannan ta karasa sashen su, tunda ta shigo take kwala kiran sunan Mommy Hauwa "Mommy! Mommy!! Mommy!!! Mommy na dawo" daga saman bene Mommy Hauwa ta amsa da cewa "eh aifa kin dawo kam dan inba keba babu mai kwalamin kira irin haka sai ke uwata" Ta fad'a tana murmushi domin dai ko ita tsayin kwanakin nan tayi kewar Meenal din ga kuma aure yanzun dazai d'auke mata ita saukin tama kusa da ita zata zauna, Da gudu Meenal ta haura sama tana jero ma Mommyn sunayen Yayyen ta wadanda suka gaisa yanzun kafin ta shigo, "Mommy wallahi maganin Hajiya ya karbe ni kin gani wannan karan ina period d'ina lafiya lau babu ciwon mara ko d'aya kuma tun jiya yazo min" ta karasa fad'a tana tsalle² cike da nishad'i dan abun ba karamin farin ciki ya k'ara mata ba wai yau ita ke period lafiya lau babu matsalar komai, Sai da ta gama tsalle²n ta sannan ta kwantar da kanta a kafadar Mommy "Mommy wai fa su yan bikin nan sun d'auka ko harda ni za'ayin ma aure tun da muka fito gidan su Besty dasu Maman Kano ake ta wani cemin amarya, ni dariya ma suke bani ko basu gane ni bane? " Sai da ta daga fuskanta sama tana kallon Mommy sannan ta kara jefa mata tambaya da cewa "mommy na canza ne wai? Kema kinga na k'ara kyau koh? " bata tsaya jiran amsa ba tace "wallahi dai Hajiya wannan karan inaga taji wa'azin malamai ne Kinga fa ko masifarta fa yanzun ta daina! Allah ko zatayi fad'arta nidai wannan karan bata min sai dai tana ma su Moon" "Matsa ki bani waje! Wato bazaki dena cema uwata masifaffiya bako Meenal? " "Yi hakuri mommy na dena ai bazan kara ce mata haka ba tunda tamin magani ciwon marana gashi na warke in an gama biki ma zan amsa kud'i a hannun Baba Malam in kai mata ta k'ara amso min wani maganin kafin wannan yayi expired" "Kinje kin gaishe da Baban naki? " "Banje ba naga d'akin shi a kulle bayan kuma jiya nace mishi yau da wuri zan dawo shine bai jirani ba! " Ta karasa fada tana tura baki, "To yanzun dai sauka kije ki samu su Raheenat din a wajen innar ku kema a miki kunshin in Baban naki ya dawo sai kiji dad'in nuna mishi, Tunda Meenal ta shiga sashen Innar su inda aka keb'e domin gyaran amare bata kara taka kafarta a kofar gida ba, har akayi kunshi aka gama aka d'aura da dan gyaran jikin da ba'a rasa ba domin dai Hajiya ta riga ta gyara jikarta tsaf. Misalin karfe 10 saura Malam ya bada izinin a kawo mishi Amaren domin daman in zai aurar da yara tun kafin d'aurin auren yake zaunar dasu ya musu Nasiha, Dashi da Baba Adamu sai Yara Maza na gidan Manya sune suka musu nasiha, nasiha mai shiga jiki kuwa domin dai hatta da Meenal da bata san tana cikin sahun amare ba wannan nasiha ya ratsata domin nasiha ne suka musu akan biyayya ma'ana biyayya ma iyaye kafin ma akai ga biyayyar miji, wannan nasiha shi ya goge rashin adalcin da Meenal take ganin kamar anyi ma kannen ta su Raheenat na auren wuri harma a cikin zuciyar ta take musu fatan Allah ya basu ikon cin ribar biyayyar da sukayi ma iyayen su. Sai da Malam ya sallami kowa, kowa ya kama gaban shi zuwa makwanci amma banda Meenal data gyara zama domin a satikan da tayi bata a gidan ba sosai ta tara labaran da take son bama Malam, shiko bayan fitan su cikin d'akin shi ya shiga ya fito da wasu kana nun gora masu d'auke da ruwan rubutu a cikin su, bayau ya fara bata ruwan rubutu tana shaba dan haka nayau ma batayi musu ba ta amsa ta shanye dan dama tunda aka kaita sashen Innar su take ta bata magunguna tana sha duk a zaton ta dai maganin ciwon marar tane dan dama hakane tun kafin yazo ake fara bata maguguna. Sai bayan da Malam ya bari ta gama bashi labaran dake bakin ta tsaf harda na kyautar da Abdul ya mata sannan ya kira sunan ta. "Aminatu " Wallahi sai da gabanta yayi kwance kwance ya fad'i dan Wallahi ita dai tsayin rayuwar ta bata tab'ajin Malam ya kira sunan taba sai yau hakan nema yasa ta kasa amsawa sai tana ganin kamar ba ita yake kira ba, har sai da ya k'ara mai maita kiran sunan nata, "Na'am "ta amsa dashi bayan ta tabbatar da cewa da ita dai yakeyi. "Aminatu nayi miki laifi dan haka nema nike neman afuwar ki ki yafemin nasan na aikata miki ba dai dai ba," Wallahi wani irin dumm haka taji a cikin kunnuwan ta kamar wacce ta gwauru da bango, Ta bud'e baki da niyyar yin magana ya tari numfashin ta da cewa "karkice komai tukun ki bari in gama magana tukun, Uwata tundaga ranar dana yanke hukuncin nan nike jin kunyar had'a ido dake, na tabbata da wani daga cikin iyayen ki ne suka yanke hukuncin dana yanke akan ki hakika dasai na sab'a musu sai gashi ni dakai na ne nake shirin b'ata miki rai, ina so ki yafe min laifin dana aikata ko zan samu in denaji a raina cewa ban kyauta miki ba" Da rarrafe ta karasa inda yake fuskarta na zubda hawaye, "Babana me yasa zaka aikata min haka? Wacece ni da har zan zauna a gaban ka ka dunga neman afuwa na bayan kai din kai kafi kowa iko dani, hatta dani kaina bani da iko da kaina kaine ke iko dani, Baba babu wani abunda zaka aikata min wanda har zai sa inyi fushi ko wata banzar tsoka a cikin kirji ma'ana zuciyata ta rayamin cewa baka kyauta min ba, wallahi duk hukuncin daka d'auka akan rayuwata ka isa dani ne shi yasa ka zaratar dashi, wacece ni da bazan maka biyayya ba? Kaine Baban Meenal wa nake dashi sama dakai da har zan juya maka baya ko in k'aluba lanceka Babana, ai ka wuce ka nemi yafiya a wajena sai dai ni in durk'usa maka, kamin aikin gafara in na aikata wani laifin ne Babana" Ta karasa fad'ar hakan cikin kuka dan Wallahi sosai kam hankalin ta ya tashi, Kamota Malam yayi ya jingina da jikin shi, ruwan dake gefen shi na gora ya bud'e yakai Mata baki, kadan ta iya sha, "Meenal gobe idan Allah ya kaimu za'a d'aura auren ki tareda na K'annin ki su Raheenat! Ina fatan zaki min biyayya kamar yanda kikace kuma bazaki bani kunya ba? " Wani irin shuuuuuu ta ringaji a cikin kunnen ta kamar kana sauraron Radio network ya d'auke musu, "Kiyi hakuri nasan burin ki shine karatu, ki sani cewa bazan tab'a aura miki mijin da nasan bazai tayani wajen ganin cikar burin kiba, bazan tab'a rusa miki burin ki na zama likita ba insha Allah wata rana ko bana raye sai an kiraki da suna Dr Aminatu dan jarabawar ku na fitowa nida kaina zan kaiki makaranta kamar yanda na saba," Da kyar ta iya bud'e baki tace "Baba aure zakamin nima? Ashe shi yasa mutane suke ta cemin amarya! Wa zan aura to? Ni ai duk samari na ban turo ko d'aya cikin su wajen ba ka kullum ce musu nakeyi karatu zanyi, harshi ma Bash din gidan master da kullum yake matsamun na fad'a mishi ni karatu zanyi" "Ba d'aya daga cikin samarin ki bane uwata, Yayan ku Sufyan Sarki shine mijin dana zab'a miki ina fatan kuma zaki karb'eshi hannu bibbiyu? " "Baba Sarki mai karnuka ne zan aura?" Kwarai taso ta danne duk wani tashin hankalin da take ciki sai dai kuma ina shekarun ta basu kai ta yanda zata iya sarrafa abinda takeji a cikin jikin ta da kuma zuciyarta ba, Wani irin jiri jiri haxo hazo haka ta dunga gani sai ganin ta ya koma kamar irin nefa Suna wasa da wuta tsakar dare a inda babu haske ko kad'an din nan, domin dai wal wal ta dunga ganin haske da duhu na zuwa mata a tare ga kuma mararta datayi wani irin kullewa lokaci daya, Da lalube ta samu ta riko hannun Malam "Babana Suma zanyi, Suma wallahi suman yana kusa, bana gani Baba ka kunna haske duhu nike gani tun tana sambatu dai har tayi dif............ ❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 Naso ace anyi Daurin auren nan yau wallahi wayata babu caji, shi yasa, sai yanzun suka kawo mana wuta. Kuyi hakuri nasan da yawan ku bakwason auren Sarki da yar gidan Malam sai dai ina mai baku hakuri kar kuce saboda haka zaku ajiye karatun littafin Dangina domin dai ba'ayi komai ba tukun, Kusha ruwan sanyi ku sarara. Team Sarki😟 Team Mai Jama'a 😰 Ummiee Zaria ✍🏼[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA! * 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 ''''''Page 31 *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* **************31 Farouq Malam ya kira ya d'auke ta zuwa wajen Mommy Hauwa, yasani daman cewar bazasu kwasa ta dad'iba hakan nema yasa yayi ma Dr Mubarak magana, shi ya bashi maganin baccin daya zuba mata a cikin ruwa tasha domin in har ba hakan yayi ba yasan ba lallai bane ta iya kwantar da hankalin ta balle harta samu yin bacci yau, yasan koda Allah yakai rai gobe zatayi bori sosai ba. A ranar da Meenal ta baro Gidan Hajiya shi kuma Sarki da Abokan shi isa gidan domin gabawa da ita, kamar yanda Uwar gida ta bashi umarnin zuwa ya gana da ita, Sanin cewar har zuwa wannan lokacin bata san da zancen auren ba kuma zuwan nashi na iya haifar da wani abun yasa Hajiya ta ha'da Meenal d'in da iyayen ta mata suka wuce da wuri domin sosai Hajiya ta shirya tarban angon Takwarar nata a cewar ta dole ta gindaya mishi dokar da mudun ya takata zata wanke kafafuwar ta taje har inda yake ta karta mishi rashin daraja, dan karma yaga an d'auki jikarta an bashi yayi zaton ko sun gaji da ita ne. Misalin karfe 1 saura su Sarki suka isa kofar gidan koda suka isa an fara kiran Sallah a masallacin dake kofar gidan dan haka basu shiga ciki ba har saida suka gabatar da farali tukun, Bayan sun idar da masallaci a kofar gidan bakin gate sukaja burki domin neman wanda zai musu iso zuwa cikin gidan kasancewar su na bak'i bazai yuwu su wuce ciki kai tsaye ba. Fitowar Yusuf wase daga masallaci kenan yazo da niyyar shiga ciki Kwaro ya mishi sallama. "Bawan Allah kamar cikin gidan nan zaka shiga koh? " ya tambaya bayan sun gama gaisawa dasu Sarki. "Eh ciki zan shiga" "Alhamdulillah tazo mana gidan sauk'i kenan, mu bak'ine ko kuma a tak'aice dai ince sirikin gidan ne yazo gaisuwa, inba damuwa zamu so kayi mana iso zuwa ciki duk da dai an san da zuwan namu amma kaga ai bai kyautu mu shiga kai tsaye ba! " "Ba damuwa kuna iya shigowa ai" Rufa mishi baya sukayi zuwa farfajiyar gidan, ganin cewa sunce su sirikan gidan ne yasa shi yanke shawarar kai su falon Hajiya tunda itace uwar kowa a gidan. Sai da suka karasa gab da falon sannan ya juyo garesu "bari in shiga in isar musu da sak'on isowar naku koh? " "Ba damuwa muna jira anan" suka bashi amsa shi kuma yasa kai cikin falon. Da sallama ya shiga, ya kumayi sa'ar samun Hajiya da iyalanta maza dukan su zaune a falon, "Karaso daga ciki mana yusufa, ga wajen zama ai kadai zauna koh? ga kuma abinci duka in kana da bukata" "Nagode Hajiya dama bak'i ne akayi suka buk'aci inyi musu iso, sunce sirikan gidan ne gasu a nan bakin kofa" "To Allah ya musu isowa kenan barkan su da zuwa to ai ce musu su shigo kawai dan dama zaman nan daka gani zaman jiran zuwan su akeyi" Ta fad'a tana jawo mayafin ta dake gefen ta ta rufe jikinta dashi, "Larai! Ke larai!! Waini anya larai basai na dangana ki da asibitin ABU ba kuwa? Jama'a kayi ta ihu kana kiran sunan mutum kamar wanda yake cikin rijiya nan da kitchen ace mutum baiji kira ba, ah ² wallahi wankin kunne zan kaiki a miki waya sani ko dattin kunne ne yasa bakijin magana sai anyi ta miki ihu duk kisa makwogoron mutum ya tsatsage wajen d'aga murya" "Ayi hakuri hajiya ina ta baya ne" Larai ta fad'i hakan a yayin da ta iso falon, "to ai sanin hali yafi sanin kama yar'nan yanzun dai fito da abubuwan da aka tanadar na taron bak'i domin gasu nan sun iso atoh kar suce sunzo gidan surukai ba'atare su da komai ba" Tana rufe bakin ta bak'in suka fara sallama su uku ne sai Sarki angon cikon na hud'un su. Bayan gaisuwa da yan tambayoyi dasu Baba Usman sukayi ma Sarki duk Hajiya na zaune tana karema Sarki kallo dan tunda abokanan shi suka gabatar dashi a matsayin Mijin takwarar ta take mishi kallon ciki da waje. Jin sun fara sallama zasu wuce yasata dakatar dasu da cewa "Nace ba! " Juyowa sukayi suna sauraron ta. "Ku d'an bani Aron abokin naku na yan mintoci", Ba damuwa Hajiya suka amsa dashi a yayin da suke ficewa, maida kallon ta kan su Baba Usman tayi "kuma ku bani waje sirri nike son yi da mijin takwara ta" "To Hajiya" suka had'a baki wajen fad'a duk da basu so hakan ba dan suna gudun kartayi wani maganar daba ita kenan ba domin dai ko d'azun nan babu abunda ta mance bata fad'a ba akan shiga hakkin jikarta da akayi wajen yi mata auren wuri, amma haka nan dukan su suka fice suka bar mata falon ta suna fatan Allah yasa kartayi katobara. "Kace sunan ka Sufyan ko? " "Eh Hajiya Sunan kenan Sufyan Sulaiman Ladan" "Masha Allah, sunce min matar ka d'aya da yara 4 koh? " "Eh haka ne" "To dama so nike in tambaye ka inji ya zaman naku zai kasance duba da cewar aikin ka a KD yake ita kuma uwar gidan ka ance tana can Lagos itama yanayin aikin tane ya hanata dawowa nan ta zauna a kusa da kai koh? " "Eh Hajiya a Kaduna aikina yake a yanzun duk da dai yanayin aikin yakan d'aukeni zuwa wasu state d'in inje inyi kwanaki ko wata ma haka, kuma itama iyalin nawa kamar yanda aka fad'a miki yanayin aikin tane yasa bata dawo nan din ba amma in ta samu hutu takan zo nan din nima kuma duk karshen wata a can nike yin shi" "Da kyau to dama abunda yasa na tambaya dan inji ainihin inda zaka ajiyemin jikane, anan Zaria ne ko a Kaduna inda kake aiki? " " anan zata zauna Hajiya saboda a can d'in cikin barracks nike zaune kuma gaskiya ni bana da ra'ayin ajiye iyalina a cikin bariki dan haka nan zata zauna ni kuma zanyi kokarin in ringa zuwa dubata duk sanda na samu lokaci" "To hakan ma ba laifi, Sai dai kuma gashi gidan ka na nan d'in daka ce jikata zata zauna naga gidan ginin zaman mace guda ne gashi kuma kace ita uwar gidan naka takan zo maka hutu nan, to yanzun daka ke shirin auren jikata ita kuma matar taka idan tazo a ina zaka sauketa kenan? Dan dai rashin adalcine kace zaka sauke ta a gidan da jikata take ciki! " Sai da ya nisa dan Wallahi wadan nan tambayoyin da tsohuwar nan ke mishi sun fara hawa mishi kai, to fisabilillahi ina ruwanta da sha'anin gidan shi, inace dai gidan nan nashi ne koba matar shi ta aure ba yana da damar da zai sauke duk wanda yake so a gidan balle kuma matar shi da daman saboda ita ya gina gidan, amma dai dan su rabu lafiya sai ya amsa mata da cewa. "Eh ai da yike ita Fateemah ko tazo a KD can tare dani take zama kota shigo nan d'in ba zama takeyi ba" "Eh ba shakka to aini dai daman saboda gudun abunda ka iya tada wani fitinar a gaba nikeyi, koba komai dai kaga ita takwara ta bata da iko da gidan ka dake can lagos, na kaduna kuma tunda ka nuna baka bukatar matan ka su zauna a wajen nasan ba zaka d'auketa ka kai can ba, shine dama yasa nake so ince tunda abun haka ne karfa wata rana ita uwar gidan ka tazo nan kace zaka sauke ta anan inda jikata gudun wani abun ya biyo baya kaga ai gara ayima kowa adalci koh? Saboda a samu zaman lafiya kaga dai ita wannan karamar yarinya ce domin dai a haife wallahi tsaf nasan ka haifeta, in ma banda had'in dangi ai nasan ko kai ido da kunya ma ka kalleta kace kana so balle ayi zancen aure, to karamar yarinya ce dai dududu bata wuce 17 ba Inma fa takai kenan, sai kuma abu na gaba" Ta fada tana mai mashi kallon ido cikin ido duk dashi d'in yana ta kokarin yanda zai cire nashi idon a cikin nata a mtsayin ta na kakar matar da ake shirin aura mishi. "To dai rokon ka zanyi ko kuma ince alfarma zan nema, wato kaga dai ita yarinya nan wallahi kankanuwar yarinya ce in ma dai banda cewa yaran yanzun suna da kufan jiki wama zai kalleta yace ya kalli mace! To nidai dan Allah karkaga tayi saurin girman nan ko ina a ciccike kayi zaton wata uwar mata ne wallahi ba iyawa zatayi dakai ba, dalilin hakan nema yasa nace bari in roki arziki dan Allah ka daure ka d'auke idanuwan ka akan ta ka bari harta k'ara girma tayi kwarin da zata iya d'aukar dawainiyar ka kafin kace zaka haike mata dan nasan ku maza baku iya kawaici ta wannan gefen ba, ita kuma kaga yarinya ce karama zuwa d'aya zaka mata ka tasheta a aiki, to tunda har Allah ma yasa kana da wata matar inaga Ai komai zaizo da sauki ko? Ina fatan ka fahimci abunda nike magana akai domin dai magana na gaskiya bari in maka b'aro² yarinyar nan fa bason auren nan take ba ubanta Malam shine ya shirya ya kuma gabatar da komai ba tareda yayi shawara da kowa ba, harta ninan dana haifi uwar ta dama ita kanta uwar nata bamu samu labari ba saida ya riga ya zartar da komai in fad'a maka karewa ma hatta dai ita amaryar taka yanzun haka da nike magana dakai a matsayin gobe za'a daura mata aure tofa labarin auren bai kaiga isa kunnen taba, dalilin ma da yasa baka sameta a gidan nan ba kenan" Yau dai Sarki shi yake ganin ikon Allah jama'a to wai ita matar nan bata san cewa ba iya jikarta ce kad'ai akama dole a batun auren nan ba harta shi da girman shi da komai biyayya kawai zaiyi ma uwar shi domin yaga sun rabu lafiya yasa dole ya amshi auren badan yana bukata ba! Shine tun ba'a daura ba har an fara kafa mishi dokoki, shi aiko shaye shaye yakeyi to ba karamin sha zaiyi wanda har zai iya kaishi ga kusantar yarinyar nan ba, balle kuma shi rabon shi da zuke² ai tun lokacin da bai san ciwon kan shiba, dan Allah jama'a Inma yace zaijema yarinyar nan a matsayin miji ai zalinta kawai zaici hakan kuma ai shi gani yake bama karamin zunubi bane, yarinyar dakoh autar su ta girme mata sosai, yaso ya d'aga ido ya kalli Hajiya yace mata ke Hajiya nima fa auren nan ba dan ina so ake shirin daura min shiba, kamar dai jikar ki nima auren biyayya zanyi, amma ina bazai iyaba dan sa'insa da babba ba dabi'ar shi bace balle kuma su Sojoji da aka san su da biyayya komai sai dai suce *yes sir* Dan haka sai ya kara dukar dakan shi kasa yana mai amsa mata da cewa. "Hajiya insha Allah zanyi kokarin kula da ita bazan cutar da itaba koba komai ita d'in kanwata ce dan haka zan kula da ita kamar yanda zan kula da kannena ko kuma yarana na cikina" "Kai madallah madallah kaji Allah dai yasanya Albarkha da alkhairi a wannan aure ya kuma baku zaman lafiya, to abu na karshe da banyi magana akan shiba shine batun karatun ta nasan ba lallai iyayen ta su tada maganar ba, amma ka sani tana da burin ganin ta zama likita kamar mahaifiyarta, kuma ni nayi mata alkawarin dafa mata wajen ganin cikar burin ta, nagode Allah kuma da yasa kaima mijin nata ba mazauni bane kaga hakan zai bata damar da zatayi karatun ta a tsanake cikin kwanciyar hankali, dan haka da zarar jarabawar su ta fito za'anema mata admission taci gaba da karatun ta ina fatan bazaka hana ba" Ta karasa fad'a tana kallon shi dan so take ta fahimci shin zai amince ko k'ak'a, "Ba damuwa insha Allah domin nima nasan dad'in karatu dan haka bazan tauyeta wajen hanata cikar burin taba". "To Alhamdulillah yanzun kam kana iya zuwa ka samu abokan ka ku wuce Allah yasa ayi taron biki lafiya, a kuma daure a gunda yin Addu'a da yawan sadaka maganin bala'i dan makiya da mahassada ako ina suna nan wasu ma tare ake bacci dasu ayi tayin azkar ba gajiyawa kaji" "Insha Allah za'a kiyaye Hajiya Nagode Allah ya kara lafiya da nisan kwana" "Ameen ameen Allah ya muku albarkha muje in taka maka dan dama zuwan kune yasa ban fita ba nima aminyata ke aurar da jikanta matar da kanin ka Sa'eed dan wajen Malam zai aura kasan jikar Aminiya ta ce can nike son lekawa tunda nidai nan ba taron komai zanyi ba duk matan gidan suna can sun kwasa sun tafi unguwar naku" A bakin kofa tayi karo da kwalayen su drinks da buhu nan kayan abinci, Larai ta kwalama kira tana tambayan wannan kayan kuma daga ina ya fito aka ajiye mata su a bakin kofa? "Bak'inne suka kawo Hajiya" Larai ta bata amsa, "shine tun tuni baki sanar dani ba har saida suke shirin tafiya, fisabilillahi ai sai ki sanar dani inyi musu godiya koh, irin wannan dawainiya haka" Ita dai Larai komawa ciki tayi tabar ta. *WASHE GARI* Meenal bata samu damar tashi ba har sai zuwa karfe 12 na rana kasancewar Mommy Hauwa tasan tana al'adah hakan yasa bata damu kanta wajen ganin ta tashin ba sai dai lokaci lokaci takan duba yanayin numfashin ta, A yayinda ta farka abubuwan da suka faru a daren jiyane suka fara dawo mata amma sai take ganin inah wannan ai sharrin mafarki ne dan a mafarki ne kawai kake ganin abubuwan da kaima kasan ba lallai bane su auku a zahiri ba,ta ina ma wai ita za'ace za'ayi auren ta har a gama komai bata da labari bayan kullum cikin lallab'a d'an gidan master daya damu kanshi dason turo iyayen shi gidan su take yi akan ya bari tukun har sai zuwa gaba, shine kawai shirmen mafarki zaice wai za'a mata aure da wani. dan haka ma ta watsar da tunanin ta tashi ta shige cikin bayi domin dai a jikin ta takejin yanda pad din dake jikin ta ya jike sosai. Lerowar da mommy Hauwa ta k'arayi a karo na ba adadi ne ganin bata a gadon da take kwance kamar ko yaushe hakan yasa tasan ta farka kenan, Kayan data ware domin Meenal din tayi amfani dashi ayau a d'auko ta ajiye mata shi akan gadon dama duk wani abunda tasan zata buk'ata, Babu jimawa Meenal ta fito, "Mommy ina kwana" "lafiya lau Meenal kin tashi lafiya?" "Lafiya lau " ta amsa dashi tana karasowa inda mommy ke zaune sai da ta jingina kanta da jikin Momin sannan tace "yunwa nikeji wallahi kamar wacce tayi sati bataci komai ba" "Tashi kisa kaya to sai in had'o miki abun karin" Harta yunkura da niyyar tashin sai kuma ta koma ta zauna riko hannun Mommy tayi "Mommy yau nayi wani irin mafarki mara dad'i wai Baba Malam zaiyi min aure ban saniba ko kila dazan kwanta na manta banyi addu'a bane, sharrin shaidan ne koh Mommy? " Shiru mommy tayi kamar bazata amsa mata ba sai kuma can tace "tashi kisa kaya tun d'azun su Moon suke zuwa dubawa ko kin tashi bari in kawo miki abunda zaki karya karki fita ki jirani anan" Bayan Mommy ta kawo mata abinci ta karya ita da kanta ta tayata shiryawa, tsaye Meenal din take a gaban Mirror tana karema kanta kallo sai ta juya nan ta juya can sai hutuna take d'aukar kanta wai zata turama Bash yaga wankan da tayi, Juyowa tayi sai taga Mommy tayi mata Kuri da ido tana kallon ta, "Mommy nayi kyau ko bari in zo in mana hoto" ta fadi hakan tana mai kara sawa inda Mommyn ke zaune taci gaba da d'aukar su hotuna. "Meenal natsu ki bani hankalin ki nan" Natsuwar ko tayi kamar yanda Mommy ta bukata. "Meenal kince min kinyi mafarki koh? " "Eh Mommy" "Fad'amin idan mafarkin nan da kikayi ya zama gaskiya shin ya zakiyi? Zakiyi ma Malam damu biyayya ki karbi zab'in da mukayi miki da hannu bibbiyu ko kuwa bijire mana zakiyi wajen nuna k'in amince warki akan auren?" Shiru tayi tana kallon Mommy dake maganar a sanyaye, A hankali kuma sai kiran da su Baba Usman sukayi mata a safiyar jiya da maganganun da suka fad'a mata da kuma yanda tun shigowar su unguwan mutanen gidan da sukayi ta kiranta da suna amarya harda ma zuwan su falon Malam dama komai daya faru ya dawo mata tsaf cikin kanta, Aiko babu shiri ta kwalla wata uwar kara wanda da ace d'akin da suke ciki ba irin ginin nan bane dake rike sauti babu abunda zai hana sauran jama'ar cikin gidan jiyo karar data yi. "Innalillahi da gaske ne! da gaske ne!! da gaskene aure za'amin yau, Waiyo Allah na shiga uku za'amin auren dole *Bari muje a gurguje*⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA! * 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 ''''''Page 31 *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* **************31 Farouq Malam ya kira ya d'auke ta zuwa wajen Mommy Hauwa, yasani daman cewar bazasu kwasa ta dad'iba hakan nema yasa yayi ma Dr Mubarak magana, shi ya bashi maganin baccin daya zuba mata a cikin ruwa tasha domin in har ba hakan yayi ba yasan ba lallai bane ta iya kwantar da hankalin ta balle harta samu yin bacci ayau, yasan koda Allah yakai rai gobe ba zatayi bori sosai ba. A ranar da Meenal ta baro Gidan Hajiya shi kuma Sarki da Abokan shi suka isa gidan domin ganawa da ita, kamar yanda Uwar gida ta bashi umarnin zuwa ya gana da ita, Sanin cewar har zuwa wannan lokacin bata san da zancen auren ba kuma zuwan nashi na iya haifar da wani abun hakan ne yasa Hajiya ta ha'da Meenal d'in da iyayen ta mata suka wuce da wuri domin sosai Hajiya ta shirya tarban angon Takwarar nata a cewar ta dole ta gindaya mishi dokar da mudun ya takata zata wanke kafafuwar ta taje har inda yake ta karta mishi rashin daraja, dan karma yaga an d'auki jikarta an bashi yayi zaton ko sun gaji da ita ne. Misalin karfe 1 saura su Sarki suka isa kofar gidan koda suka isa an fara kiran Sallah a masallacin dake kofar gidan dan haka basu shiga ciki ba har saida suka gabatar da farali tukun, Bayan sun idar da sallah a kofar gidan bakin gate sukaja burki domin neman wanda zai musu iso zuwa cikin gidan kasancewar su na bak'i bazai yuwu su wuce ciki kai tsaye ba. Fitowar Yusuf wase daga masallaci kenan yazo da niyyar shiga ciki Kwaro ya mishi sallama. "Bawan Allah kamar cikin gidan nan zaka shiga koh? " ya tambaya bayan sun gama gaisawa dasu Sarki. "Eh ciki zan shiga" "Alhamdulillah tazo mana gidan sauk'i kenan, mu bak'ine ko kuma a tak'aice dai ince sirikin gidan ne yazo gaisuwa, inba damuwa zamu so kayi mana iso zuwa ciki duk da dai an san da zuwan namu amma kaga ai bai kyautu mu shiga kai tsaye ba! " "Ba damuwa kuna iya shigowa ai" Rufa mishi baya sukayi zuwa farfajiyar gidan, ganin cewa sunce su sirikan gidan ne yasa shi yanke shawarar kai su falon Hajiya tunda itace uwar kowa a gidan. Sai da suka karasa gab da falon sannan ya juyo garesu "bari in shiga in isar musu da sak'on isowar naku koh? " "Ba damuwa muna jira anan" suka bashi amsa shi kuma yasa kai cikin falon. Da sallama ya shiga, ya kumayi sa'ar samun Hajiya da iyalanta maza dukan su zaune a falon, "Karaso daga ciki mana yusufa, ga wajen zama ai kadai zauna koh? ga kuma abinci duka in kana da bukata" "Nagode Hajiya dama bak'i ne akayi suka buk'aci inyi musu iso, sunce sirikan gidan ne gasu a nan bakin kofa" "To Allah ya musu isowa kenan barkan su da zuwa to ai ce musu su shigo kawai dan dama zaman nan daka gani zaman jiran zuwan su akeyi" Ta fad'a tana jawo mayafin ta dake gefen ta ta rufe jikinta dashi, "Larai! Ke larai!! Waini anya Larai basai na dangana ki da asibitin kurame ba kuwa? Jama'a kayi ta ihu kana kiran sunan mutum kamar wanda yake cikin rijiya nan da kitchen ace mutum baiji kira ba, ah ² wallahi wankin kunne zan kaiki a miki waya sani ko dattin kunne ne yasa bakijin magana sai anyi ta miki ihu duk kisa makwogoron mutum ya tsatsage wajen d'aga murya" "Ayi hakuri hajiya ina ta baya ne" Larai ta fad'i hakan a yayin da ta iso falon, "to ai sanin hali yafi sanin kama yar'nan yanzun dai fito da abubuwan da aka tanadar na taron bak'i domin gasu nan sun iso atoh kar suce sunzo gidan surukai ba'atare su da komai ba" Tana rufe bakin ta bak'in suka fara sallama su uku ne sai Sarki angon cikon na hud'un su. Bayan gaisuwa da yan tambayoyi dasu Baba Usman sukayi ma Sarki duk Hajiya na zaune tana karema Sarki kallo dan tunda abokanan shi suka gabatar dashi a matsayin Mijin takwarar ta take mishi kallon ciki da waje. Jin sun fara sallama zasu wuce yasata dakatar dasu da cewa "Nace ba! " Juyowa sukayi suna sauraron ta. "Ku d'an bani Aron abokin naku na yan mintoci", Ba damuwa Hajiya suka amsa dashi a yayin da suke ficewa, maida kallon ta kan su Baba Usman tayi "kuma ku bani waje sirri nike son yi da mijin takwara ta" "To Hajiya" suka had'a baki wajen fad'a duk da basu so hakan ba dan suna gudun kartayi wani maganar daba ita kenan ba domin dai ko d'azun nan babu abunda ta mance bata fad'a ba akan shiga hakkin jikarta da akayi wajen yi mata auren wuri, amma haka nan dukan su suka fice suka bar mata falon ta suna fatan Allah yasa kartayi katobara. "Kace sunan ka Sufyan ko? " "Eh Hajiya Sunan kenan Sufyan Sulaiman Ladan" "Masha Allah, sunce min matar ka d'aya da yara 4 koh? " "Eh haka ne" "To dama so nike in tambaye ka inji ya zaman naku zai kasance duba da cewar aikin ka a KD yake ita kuma uwar gidan ka ance tana can Lagos itama yanayin aikin tane ya hanata dawowa nan ta zauna a kusa da kai koh? " "Eh Hajiya a Kaduna aikina yake a yanzun duk da dai yanayin aikin yakan d'aukeni zuwa wasu state d'in inje inyi kwanaki ko wata ma haka, kuma itama iyalin nawa kamar yanda aka fad'a miki yanayin aikin tane yasa bata dawo nan d'in ba amma in ta samu hutu takan zo nan d'in nima kuma duk karshen wata a can nike yin shi" "Da kyau to dama abunda yasa na tambaya dan inji ainihin inda zaka ajiyemin jikane, anan Zaria ne ko a Kaduna inda kake aiki? " " anan zata zauna Hajiya saboda a can d'in cikin barracks nike zaune kuma gaskiya ni bana da ra'ayin ajiye iyalina a cikin bariki dan haka nan zata zauna ni kuma zanyi kokarin in ringa zuwa dubata duk sanda na samu lokaci" "To hakan ma ba laifi, Sai dai kuma gashi gidan ka na nan d'in daka ce jikata zata zauna naga gidan ginin zaman mace guda ne gashi kuma kace ita uwar gidan naka takan zo maka hutu nan, to yanzun daka ke shirin auren jikata ita kuma matar taka idan tazo a ina zaka sauketa kenan? Dan dai rashin adalcine kace zaka sauke ta a gidan da jikata take ciki! " Sai da ya nisa dan Wallahi wadan nan tambayoyin da tsohuwar nan ke mishi sun fara hawa mishi kai, to fisabilillahi ina ruwanta da sha'anin gidan shi, inace dai gidan nan nashi ne koba matar shi ta aure ba yana da damar da zai sauke duk wanda yake so a gidan balle kuma matar shi da daman saboda ita ya gina gidan, amma dai dan su rabu lafiya sai ya amsa mata da cewa. "Eh ai da yike ita Fateemah ko tazo a KD can tare dani take zama kota shigo nan d'in ba zama takeyi ba" "Eh ba shakka to aini dai daman saboda gudun abunda ka iya tada wani fitinar a gaba nikeyi, koba komai dai kaga ita takwara ta bata da iko da gidan ka dake can lagos, na kaduna kuma tunda ka nuna baka bukatar matan ka su zauna a wajen nasan ba zaka d'auketa ka kai can ba, shine dama yasa nake so ince tunda abun haka ne karfa wata rana ita uwar gidan ka tazo nan kace zaka sauke ta anan inda jikata gudun wani abun ya biyo baya kaga ai gara ayima kowa adalci koh? Saboda a samu zaman lafiya kaga dai ita wannan karamar yarinya ce domin dai a haife wallahi tsaf nasan ka haife wacce ta fita, in ma banda had'in dangi ai nasan ko kai ido da kunya ma ka kalleta kace kana so balle ayi zancen aure, to karamar yarinya ce fa wacce dai dududu bata wuce 17 ba Inma fa takai kenan, sai kuma abu na gaba" Ta fada tana mai mashi kallon ido cikin ido duk dashi d'in yana ta k'ok'arin yanda zai cire nashi idon a cikin nata a matsayin ta na kakar matar da ake shirin aura mishi. "To dai rokon ka zanyi ko kuma ince alfarma zan nema, wato kaga dai ita yarinya nan wallahi kankanuwar yarinya ce in ma dai banda cewa yaran yanzun suna da kufan jiki wama zai kalleta yace ya kalli mace! To nidai dan Allah karkaga tayi saurin girman nan ko ina a ciccike kayi zaton wata uwar mata ne wallahi ba iyawa zatayi dakai ba, dalilin hakan nema yasa nace bari in roki arziki dan Allah ka daure ka d'auke idanuwan ka akan ta ka bari harta k'ara girma tayi kwarin da zata iya d'aukar dawainiyar ka kafin kace zaka haike mata dan nasan ku maza baku iya kawaici ta wannan gefen ba, ita kuma kaga yarinya ce karama zuwa d'aya zaka mata ka tasheta a aiki,karshen ta in an sab'a number kaji ana fad'in wacce ai auren wuri ne yayi sanadin data kamu da yoyon fitsari, to kaga to tunda har Allah ma yasa kana da wata matar inaga Ai komai zaizo da sauki ko? Ina fatan ka fahimci abunda nike magana akai domin dai magana na gaskiya bari in maka b'aro² yarinyar nan fa bason auren nan take ba ubanta Malam shine ya shirya ya kuma gabatar da komai ba tareda yayi shawara da kowa ba, harta ninan dana haifi uwar ta dama ita kanta uwar nata bamu samu labari ba saida ya riga ya zartar da komai in fad'a maka karewa ma hatta dai ita amaryar taka yanzun haka da nike magana dakai a matsayin gobe za'a daura mata aure tofa labarin auren bai kaiga isa kunnen taba, dalilin ma da yasa baka sameta a gidan nan ba kenan dan zuwan naka na iya sanyawa ta hasaso wani abun" Yau dai Sarki shi yake ganin ikon Allah jama'a to wai ita matar nan bata san cewa ba iya jikarta ce kad'ai akama dole a batun auren nan ba harta shi da girman shi da komai biyayya kawai zaiyi ma uwar shi domin yaga sun rabu lafiya yasa dole ya amshi auren badan yana bukata ba! Shine tun ba'a daura ba har an fara kafa mishi dokoki, shi aiko shaye shaye yakeyi to ba kana nan kayan maye zaisha wanda har zai iya kaishi ga kusantar yarinyar nan ba, balle kuma shi rabon shi da zuke² ai tun lokacin da bai san ciwon kan shiba, dan Allah jama'a Inma yace zaijema yarinyar nan a matsayin miji ai zalinta kawai zaici hakan kuma ai shi gani yake bama karamin zunubi bane, yarinyar dakoh autar su ta girme mata sosai, yaso ya d'aga ido ya kalli Hajiya yace mata ke Hajiya nima fa auren nan ba dan ina so ake shirin daura min shiba, kamar dai jikar ki nima auren biyayya zanyi, amma ina bazai iyaba dan sa'insa da babba ba dabi'ar shi bace balle kuma su Sojoji da aka san su da biyayya komai sai dai suce *yes sir* Dan haka sai ya k'ara dukar dakan shi kasa yana mai amsa mata da cewa. "Hajiya insha Allah zanyi kokarin kula da ita bazan cutar da itaba koba komai ita d'in kanwata ce dan haka zan kula da ita kamar yanda zan kula da kannena ko kuma yarana na cikina" "Kai madallah madallah kaji Allah dai yasanya Albarkha da alkhairi a wannan aure ya kuma baku zaman lafiya, to abu na karshe da banyi magana akan shiba shine batun karatun ta nasan ba lallai iyayen ta su tada maganar ba, amma ka sani tana da burin ganin ta zama likita kamar mahaifiyarta, kuma ni nayi mata alkawarin dafa mata wajen ganin cikar burin ta, nagode Allah kuma da yasa kaima mijin nata ba mazauni bane kaga hakan zai bata damar da zatayi karatun ta a tsanake cikin kwanciyar hankali, dan haka da zarar jarabawar su ta fito za'anema mata admission taci gaba da karatun ta ina fatan bazaka hana ba" Ta karasa fad'a tana kallon shi dan so take ta fahimci shin zai amince ko k'ak'a, "Ba damuwa insha Allah domin nima nasan dad'in karatu dan haka bazan tauyeta wajen hanata cikar burin taba". "To Alhamdulillah yanzun kam kana iya zuwa ka samu abokan ka ku wuce Allah yasa ayi taron biki lafiya, a kuma daure a gunda yin Addu'a da yawan sadaka maganin bala'i dan makiya da mahassada ako ina suna nan wasu ma tare ake bacci dasu ayi tayin azkar ba gajiyawa kaji" "Insha Allah za'a kiyaye Hajiya Nagode Allah ya kara lafiya da nisan kwana" "Ameen ameen Allah ya muku albarkha muje in taka maka dan dama zuwan kune yasa ban fita ba nima aminyata ke aurar da jikanta matar da kanin ka Sa'eed dan wajen Malam zai aura kasan jikar Aminiya ta ce can nike son lekawa tunda nidai nan ba taron komai zanyi ba duk matan gidan suna can sun kwasa sun tafi unguwar naku" A bakin kofa tayi karo da kwalayen su drinks da buhu nan kayan abinci, Larai ta kwalama kira tana tambayan wannan kayan kuma daga ina ya fito aka ajiye mata su a bakin kofa? "Bak'inne suka kawo Hajiya" Larai ta bata amsa, "shine tun tuni baki sanar dani ba har saida suke shirin tafiya, fisabilillahi ai sai ki sanar dani inyi musu godiya koh, irin wannan dawainiya haka" Ita dai Larai komawa ciki tayi tabar ta. *WASHE GARI* Meenal bata samu damar tashi ba har sai zuwa karfe 12 na rana kasancewar Mommy Hauwa tasan tana al'adah hakan yasa bata damu kanta wajen ganin ta tashin ba sai dai lokaci lokaci takan duba yanayin numfashin ta, A yayinda ta farka abubuwan da suka faru a daren jiyane suka fara dawo mata amma sai take ganin inah wannan ai sharrin mafarki ne dan a mafarki ne kawai kake ganin abubuwan da kaima kasan ba lallai bane su auku a zahiri ba,ta ina ma wai ita za'ace za'ayi auren ta har a gama komai bata da labari bayan kullum cikin lallab'a d'an gidan master daya damu kanshi dason turo iyayen shi gidan su take yi akan ya bari tukun har sai zuwa gaba, shine kawai shirmen mafarki zaice wai za'a mata aure da wani. dan haka ma ta watsar da tunanin ta tashi ta shige cikin bayi domin dai a jikin ta takejin yanda pad din dake jikin ta ya jike sosai. Lekowar da mommy Hauwa ta k'arayi a karo na ba adadi ne ganin bata a gadon da take kwance kamar ko yaushe hakan yasa tasan ta farka kenan, Kayan data ware domin Meenal din tayi amfani dashi ayau ta d'auko ta ajiye mata shi akan gadon dama duk wani abunda tasan zata buk'ata, Babu jimawa Meenal ta fito, "Mommy ina kwana" "lafiya lau Meenal kin tashi lafiya?" "Lafiya lau " ta amsa dashi tana karasowa inda mommy ke zaune sai da ta jingina kanta da jikin Momin sannan tace "yunwa nikeji wallahi kamar wacce tayi sati bataci komai ba" "Tashi kisa kaya to sai in had'o miki abun karin" Harta yunkura da niyyar tashin sai kuma ta koma ta zauna riko hannun Mommy tayi "Mommy yau nayi wani irin mafarki mara dad'i wai Baba Malam zaiyi min aure ban saniba ko kila dazan kwanta na manta banyi addu'a bane, sharrin shaidan ne koh Mommy? " Shiru mommy tayi kamar bazata amsa mata ba sai kuma can tace "tashi kisa kaya tun d'azun su Moon suke zuwa dubawa ko kin tashi bari in kawo miki abunda zaki karya karki fita ki jirani anan" Bayan Mommy ta kawo mata abinci ta karya ita da kanta ta tayata shiryawa, tsaye Meenal din take a gaban Mirror tana karema kanta kallo sai ta juya nan ta juya can sai hotuna take d'aukar kanta a sabuwar wayar da Mai Jama'a ya bata wai zata turama Bash yaga wankan da tayi, Juyowa tayi sai taga Mommy tayi mata Kuri da ido tana kallon ta, "Mommy nayi kyau ko bari in zo in mana hoto" ta fadi hakan tana mai kara sawa inda Mommyn ke zaune taci gaba da d'aukar su hotuna. "Meenal natsu ki bani hankalin ki nan" Natsuwar ko tayi kamar yanda Mommy ta bukata. "Meenal kince min kinyi mafarki koh? " "Eh Mommy" "Fad'amin idan mafarkin nan da kikayi ya zama gaskiya shin ya zakiyi? Zakiyi ma Malam damu biyayya ki karbi zab'in da mukayi miki da hannu bibbiyu ko kuwa bijire mana zakiyi wajen nuna k'in amince warki akan auren?" Shiru tayi tana kallon Mommy dake maganar a sanyaye, A hankali kuma sai kiran da su Baba Usman sukayi mata a safiyar jiya da maganganun da suka fad'a mata da kuma yanda tun shigowar su unguwan mutanen gidan da sukayi ta kiranta da suna amarya harda ma zuwan su falon Malam dama komai daya faru ya dawo mata tsaf cikin kanta, Aiko babu shiri ta kwalla wata uwar kara wanda da ace d'akin da suke ciki ba irin ginin nan bane dake rike sauti babu abunda zai hana sauran jama'ar cikin gidan jiyo karar data yi. "Innalillahi da gaske ne! da gaske ne!! da gaskene aure za'amin yau, Waiyo Allah na shiga uku za'amin auren dole *kuyi hakuri ga biyan bashin page d'in jiya kamar yanda nayi alkawari page din yau zai biyo baya daga yanzun har zuwa dare idan naga comment d'inku. Wai nace kun amso kayan ankon ku a wajen dinki kuwa ko adawar auren yasa ko ankon bikin bakuyi ba🤔.. Ummiee Zaria ✍🏼✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 """"""32 "Mommy kice min ba dagaske bane! kice min wasa kuke min! me nayi? laifin me na aikata da za'a aurar dani tun yanzun? , Mommy kin manta buri nane? Ina da buri fa karatu nike so zanyi niba aure nike soba," Kamota Mommyn tayi ta zaunar "Meenal ina ce Yaya Usman Jiya kafin ku taho saida ya zaunar dake yayi miki nasiha akan abun da zaki dawo gidan nan ki tarar? " "Yayi min nasiha Mommy amma ni ai baice min aurena za'ayi yau ba wallahi da bazan dawo ba" ta fad'a a yayin da hawaye yaci gaba da bin kuncin ta, k'aramin murmishi Mommy tayi "Meenal kenan to ai shi aure ko a ina kike za'a iya d'aura maka shi ko kina gidan nan ko baki hakan bazai canza komai ba" "Mommy aure fa kuma ni ai banyi kwantai ba ina da samari na da kulumm suke cewa suna sona fa! ai dan karkiyi fad'a shi yasa na hanasu zuwa gidan nan kuma kullum sai Bashar yamin magana akan ya turo a tambaya mishi na hana shi" sai kuma ta k'arama kukun nata volume tana kallon Mommy taci gaba da cewa "yanzun shike nan Mommy an rabani da Bash kenan? Yanzun shikenan nima na zama mayau dariyar da ake cewa?, Mommy Bash fa kullum yana cemin yana sona sosai duk ranar daya rasani bai san ya zaiyi rayuwa ba, gashi zakumin aure bada sanin shiba, Allah sarki Bash kila dai haukacewa zaiyi shima ya fara tsince² a bola irin na mahaukata" cike da ihu sosai ta kwara da cewa "shi kenan ni Meenal za'a sani d'aukar alhalin daba nawa Bash zai haukace idan ya rasani, shi kenan kowa zai koma yimin kallon mayaudariya" "Ke Meenal" Mommy ta kira sunan ta a tsawace, "Idan baki rabani da wad'an nan surutan iya shegen naki da basu da amfani ba sai na sab'a miki kamanni , zaki bani hankalin ki nan muyi magana na fahimtar juna ko a'ah? waima da izinin wa kike kula samarin a waje da har kike ikirarin wani can zai haukace dan ya rasaki? Fad'amin shid'in matsayin shi har yafi na mu iyayenki ne da zaki kasa bin umarnin mu dan kina gudun karya haukace? To ba hauka ba yama rataye kanshi ya mutu inya so, sakarcin banza da wofi kawai kuma wallahi ki yimin shiru da kukan nan naki kafin in tattaka ki" Jin yanda Mommy ta fututtuke take ta fad'a yasa ta yin shirun na dole dan tasan yanda ba kowa daga ita sai Mommyn a d'akin tofa yasin tana iya zagewa ta nad'a mata na jaki kafin wani yazo kwatar ta ta tabbatar taji jiki, Kasa kasa tayi da murya kafin tace "Mommy to in auren zaku min basai kuce in fito da miji ba shine kawai za'a had'ani da Ya Sufyan" Ta fad'i hakan da sheshshekar kuka tana turo baki. "Oh baki gode Allah bama ashe da kika samu Sufyan d'in su kuma kannen ki da aka had'asu da wadancan iyayen nasu kinji wacce ta kalubalanci batun auren a cikin su? Sai ke shafaffiya da mai da kike shirin nuna mana cewar bamu isa ba, Wato saboda Malam yana d'aure miki gindi Meenal shine yasa kike ganin kamar babu wanda ya isa dake koh Meenal? To ki sani mune iyayen ki dan haka aure kuma kamar an d'aura nagode Allah ma daya sa shine mijin kin kuma san ba wasa yakeyi daku ba, dan haka kije kiyi mishi shirme ya banka miki kashin bala'i wallahi kin kuma san kina da kishiya dan haka gara ki kama kanki tun wuri" Shigowar Aunty Hassana d'akin ne yasanya Mommy Hauwa yin shiru daga karshe ma ta fice a d'akin. Tasowa tayi ta rungume Aunty Hassana kukan ta yana dawowa,dan sosai abun ke k'ara tukota a kirji "Mommy kinji wai auren dole zasu min kuma ni ina da wanda yake sona, kuma ko jiya sai da ya rokeni yana son ya turo iyayen shi na hana shi shine kawai yau za'ace aurena za'a d'aura da wani bayan shi kuma na riga na gayyace shi, dan Allah Mommy mai zan fad'a mishi yanzun ya yarda cewar ba yaudarar shi nayi ba? Bash yana sona Ban san wani hali zai shiga ba kinga fa koda na tashi d'azun tarin miss call din shi na samu a wayata, ni wallahi ban san ya zanyi ba" Haka Aunty Hassana ta zaunar da Meenal tana ta bata baki daga karshe kuma ta amshi Number Bash din a wajen Meenal d'in akan cewar ita da kanta zata kira shi yazo su iyayen ta su fad'a mishi abunda yake faruwa dan yasan cewa ita d'in bata da laifi kuma bata yaudare shiba. *Bari mubar amaryar Sarki haka mu lek'a halin da uwar gida sarautar mata Teemah take ciki* Tun bayan barin Sarki Lagos take ta faman fad'i tashi na ganin yanda zata bullowa al'amarin domin dai wannan yak'in nata ne dan haka bazata sanya kowa a ciki ba dan kamar yanda ta k'udiri aniyar babu wanda zai san da batun auren cikin kawayen ta, tofa hakan take so ya kasance sai dai kuma tasan hakan bazai samu ba dole sai tayi kamar tanayi, ta dai tattaro bala'in gabas da yamma kudu da arewa wanda take da tabbacin kamar yanda bokayen ta suka tabbatar mata da cewar auren bamai dorewa bane tofa hakan ne zata kasance domin dai basu tab'ayi mata alkawari suka sab'a ba, taso a daukar mata mataki mafi tsauri akan yarinyar data yarda zata aurar mata miji sai dai hakan ta bai cimma ruwa ba domin dai an fad'a mata komai zatayi bazata samu sa'a akan yarinyar ba, sannan shima Sarki barin gefenta da yayi hakan ya jawo nakasu sosai akan abubuwan dake jikin shi ga kuma alamu sun nuna cewar akwai wanda yake b'ata musu aiki dan haka suka had'a mata abubuwan da zatayi mishi amfani dashi in ta isa gareshi wanda dole itace zatayi su da kanta, sannan kuma sun kara da jan kunnen ta akan cewar koda wasa in taje karta yarda tayi wani abun da zai iya kawo wani sab'ani tsakanin ta da Sarki dan hakan na iya b'ata musu aiki. To dai ta shirya tsaf akan da zarar biki ya rage kwana biyu zata musu dirar mikiya, hakan ne kuma ya faru dan ko shi Sarki bata fad'a mishi cewar ta taso ba har sai sanda ta iso kaduna sannan ta kira shi cewar gata fa a kaduna amma inta huta ko zuwa yamma ne zata wuto Zaria, ko kusa ko alama tsayin kwanakin nan bata tab'a nuna mishi cewar ta san abunda ke faruwa na batun auren da yake shirin yiba, Shi kuma harga Allah abubuwa ne suka sha mishi kai da kuma cewar da tayi zata zo yasa ya yanke hukuncin in ta iso sai suyi ga da ga. Yaji wani iri sosai bayan ya gama amsa kiran nata ta yanda har yakejin cewa bai kyauta mata ba, gashi yanzun ta baro aikin ta da duk abubuwan dake gaban ta masu mahimmanci a wajen ta tazo dan ta duba jikin mahaifiyar shi amma su kullum yan uwan shi bak'inta kawai suke gani komai tayi bata burgesu, yana dai Addu'ar Allah yasa ya shawo kanta cikin sauk'i domin dai yasan ba'a kyauta mata ba. Shi yanzun babban damuwar shima inda zai sauke ta dan yasan bata son sauka a gidan su gidan shi kuma daya gina domin ta gashi yanzun wata harta maye gurbin ta ga kuma yanda sukayi da Hajiyar can dake amsa sunan kakar yarinyar, dan haka yana ga hotel kawai zai sauke ta yasan itama zata fi son hakan tunda bata iya sakewa a cikin yan uwan shi. ****** Duk yanda Aunty Hassana taso Meenal ta fito daga d'akin nan ta koma wajen su Raheenat k'i tayi, a cewar ta tunda kowa baya son ta babu inda zata taka k'afarta domin dai harta kayan data sanya d'azun tub'e su tayi sannan ta koma toilet ta sake sabon wanka duk ta wanke kwalliyar da tayi a d'azun ta dawo kan gadon taci gaba da kwanciya daga ita sai wata tsohuwar doguwar riga kamar wata mai jinya. A haka su Moon suka shigo suka sameta, "Kunga ku kwashi sheggun kafafuwan ku d'aya bayan d'aya ku ficemin a d'akin nan dan banga uwar da kukazo yimin ba jajayen munafukai kawai, badai har daku za'a had'a kai aci amana taba, kuje ku da Allah alhakina kuma yana kanku, dan haka sai ku koma gefe ku zuba ruwa a kasa kusha, ace wai duk yanda na d'auke ku ku rasa abunda zaku sakamin dashi sai wannan, daku fa muka dunga gantalin rabon ankon biki da raba cingum, ina ta yawo a gari ina fad'in k'anne na zasuyi aure kullum jimami nike saboda nasan yanda auren nan yazo ma yaran nan, ashe basu bane abun tausayi nid'in dai da nike tausar su nike basu baki akan suyi biyayya nice abar tausayin da aka tsaida ranar aurena ba tareda sani naba, ashe su gata aka musu tunda koba komai an sanar musu sannan aka had'asu da mazajen nasu da suke ta rawar jiki a kansu nifa? A rasa da wanda za'a had'ani aure sai Sarki ko waccen su mazajen su sunzo sun gana dasu amma ni har yanzun da ya rage awanni kad'an in tabbata a matsayin matar aure bamuyi ido biyu da mijin ba, kenan dai shima dole aka mishi badan yana soba tunda ko nema na ya kasayi, Ku kuma wallahi duk nasan matsayin dazan ajiye ko waccen ku munafukai kawai kuma insha Allah dukan ku kuma auren dolen za'a muku kuji inda dad'i" Allah sarki Meenal wallahi basu ba hatta ni kaina na tausaya mata, Amma kuma ya bawa ya iya? Kaddara fa ba'a iya guje mata sai hakuri, Masu karatu ina mai k'ara baku hak'uri nasan bakwa son auren, kuyi hakuri please 🙏. Karasawa inda take sukayi ko waccen su jikin ta a sanyaye Meelat da Maryam kan kasa rike kukan su sukayi wanda kukan nasu shi ya kara tada kukun Meenal din sai gashi duk sun taru suna kukan babu mai ba wani hakuri, Kiyi hakuri Meenal to mema zamuce miki bayan mai afkuwa ya riga ya afku, mun san ko mun fad'a miki hankalin ki kawai zaki tada wanda hakan bashi zaisa a fasa auren ba, sannan kuma an gargad'e mu da karmu fad'a miki dan Allah kiyi hakuri muma munajin babu dad'i kamar yanda kikeji" "Karya ne baku san ya nikeji ba, tunda baku za'a dauka akai gidan mijiba, koba komai har yanzun a gaban iyayen ku kuke kuma a gaban su zakuci gaba da zama har zuwa sanda lokacin naku auren zai zo, na tabbata kuma su bazasu rufe muku komai ba hasalima sai wanda kuka fidda cewa kuna so zasu baku ku aura, Nifa? Ku kirgamin a wanni nawa suka ragemin inyi a cikin gidan nan domin dai nasan ko suma nike ana shafamin ruwa tofa babu mai bari in k'ara kwana a cikin gidan nan domin yanzun kaf gidan babu mai kaunata babu wanda ya damu da damuwa ta, Tun safe nike d'akin nan amma kamar wata agola a wajen rabon gado haka na kasance babu wanda ya shigo ya dubani ko a wayata babu wanda ya kirani hatta Malam da kullum nake ganin yafi kowa sona yau bai tuna da wani hali nike cikiba, shin kun ma san da kiran wa na fara cin karo a wayata bayan na tashi daga dogon baccin dana tabbatar bana lafiya bane? " Bata sarara domin jin amsar suba ta d'aura da cewa, " Bashar ya kirani sau adadin da bazan iya tunawa ba tsoro nike shin ko har maganar yaje kunnen shine? Fisabilillahi wani amsa zan bashi da wani kalami zanyi amfani wajen fad'a mishi cewar komai daya faru bani da masaniya ta yanda zai yarda dani?" Kuka ta fashe dashi sosai su kuma suna ci gaba da bata hakuri. Duk halin da Meenal ta tsinci kanta a ciki hakan bai hana jama'ar gidan cigaba da gudanar da harkokin su cikin farin ciki ba, hasalima duk wanda ya tambayi ina take cewa akeyi bata gidan. *An daura aure lafiya* aure kuma ya dauru😟 masu fatan alkhairi sunyi akasin hakan kuma dai sun barma zuciyoyin su, Tunda Magrib ya gabato Mommy Hauwa da kanta ta shigo d'akin ta tasa Meenal a gaba har zuwa ban d'aki tayi sabon wanka bayan sun fito kuma tayi tsaye a kanta har sai da ta shirya sannan ta fice daga d'akin ita ko Meenal har zuwa wannan lokacin babu abunda takeyi sai aikin kuka idanuwan ta ko kallo guda zaka musu kaji baka sha'awar k'ara kallon su, Daga ita har kawayen ta dukan su babu mai walwala bikin aure da akeyi cikin nishad'i to nata dai komawa yayi kamar wani bikin mutuwa, barin ma da yamman nan da taga ana ta kara haramar mik'a su Raheenat d'akunan su dan ita Raheenat Kaduna za'a kaita dan haka da wuri suka wuce da ita ko sallama Malam bai bari tayi da Meenal ba, ita ko Sa'adatu da yike cikin garin Zaria ne anan cikin GRA yasa sai gab Magrib d'in suka wuce ya rage saura Meenal kad'ai da za'a mik'a gidan Malam Ladan dake makotaka da gidan Malam d'in kafin a wuce da ita d'akin ta, kasan cewar ita kusa ne hakan yasa sauran jama'ar sukayi ma sauran amaren rakiya, anayin sallar ishsha'i babu jimawa itama Billyn ya Sa'eed aka kawo ta a kuma lokacin ne Malam ya bada izinin a fito da Meenal din itama a mik'ata nata d'akin amma kafin a fita da ita sai da aka sadata da falon malam inda iyayen ta suke suka k'ara yin mata nasiha da kuma ban hakuri, Amma Mommy Hauwa kam b'oye kanta tayi itama tana nata kukan dan bata da k'arfin zuciyar da zatayi sallama da Meenal d'in tadai riga tayi mata nasiha a matsayin ta na uwa dan haka sai dai ta bita da addu'a kuma. Meenal tasha kuka, kukan nata koh ba karamin tab'a jama'ar gidan yayi ba sai dai ya zasuyi tunda dai ai dama ko ba dade koba jima ita ya mace dole aure za'a mata ta tafi nata gidan, Malam ko bai iya cewa komai ba illah hakuri daya ringa bata da kuma sa albarkha har aka fita da ita daga gidan a cikin motar dasu Kwaro suka kawo duk da kasancewar tsakanin gidan Malam da gidan su Sarki babu wani tazara amma haka suka laya manya manyan motocin su kamar wasu masu shirin barin gari sojojin nan duk sun sako kakin su na aiki dan su tabbatar ma da jama'a cewar bikin fa nasu ne, Tarba ta girma da arziki suka samu a wajen Uwar gida da nata ahalin wanda anan din ma dai nasiha suka yima Ameenatun da alkhawarin zasu riketa amana domin ko babu aure ita d'in dolen suce, daga nan kuma ka sada Amaryar Sarki da gidan auren ta. To a can din ma dai komai da zasu bukata na daga abinci da ruwan sha da sauran su duk an tanadar musu, tunda ake bikin aure a gidan Malam ba'a tab'a kai amarya yan kaita su kwana a gidan ba sai akan Meenal domin da ankai ta ake juyawa amma sai ga shi ita uwar Malam tsabar gata duk da kasancewar ta cikin unguwa Malam bai hana kowa kwana ba saima umarni daya bayar akan a samu wadanda zasu zauna tare da ita su d'ebe mata kewa kar tunani ya mata yawa, a gidajen amare da yawa in kawaye sun kwana zaka samu cewa sun raya daren ne cike da farin ciki dan wasu ma kusan kwanar zaune sukeyi suna hira, sab'anin gidan Meenal daya kasance shiru babu wani kara kaina dan ita dama ganin kukanta yayi yawa yasa tun kafin su fito da Aunty Hassana ta tsareta taci abinci ta hada mata da maganin bacci dan haka koda suka iso gidan da aka mik'ata d'akin ta umarni Aunty Hassana ta bayar akan su koma falo domin zuwa lokacin bacci ya fara cin karfin Meenal din, Su kuma kawayen waje can suka koma wajen abokanan ango suna daddalewa domin dai tunda aka fara hidimar bikin babu wanda ya nemi wani a cikin su gashi har amarya ta tare a d'akin ta koda suka nemi ganin ango uzuri abokan suka basu akan cewa shima bayajin dad'i shi yasa bai zo tare dasu ba, sai dai abokan sunyi musu sallama ta girma a matsayin su na kawayen amarya kafin suka juya suka koma masaukin su bayan kawayen sun tabbatar musu da cewa basa bukatar komai aka bar wasu daga cikin yaran Sarkin domin su kula da gidan. *Jama'a wai ina Angon ya shige ne?* Kwaro Sarki yaba mota ya je ya d'auko Teemah a Kaduna a wannan ranar basu shigo Zaria ba sai gabanin Magriba, kai tsaye kuma Hotel din daya kama domin ta yayi ma Kwaro umarnin wucewa da ita domin yafi son ya fara ganawa da ita kafin ta isa gidan su, Dan haka koda Kwaro ya kaita d'akin da Sarki ya kama ya rakata da akwatin ta, bai kuma tsaya ba yayi sallama da Sarki ya koma domin shi ke kula da bak'in su dake zuwa dama duk wani zirga² na bikin. Kasan cewar bata da wani gajiya a tareda ita hakan yasa Sarki ya fara gabatar mata da abinci, sai da taci tayi nak sannan ta fara tambayan shi "ya mai jikin ta k'araji suna gida ne ko asibitin? " "Jiki da sauki tana gida domin a gida likitan ke zuwa yana dubata" "Allah ya k'ara lafiya sai mu tafi yanzun ai ko inje in duba jikin nata dan shine mak'asudin zuwa na garin!" "Yaran kifa? Bakya d'aukin son zuwa kigan su? Kin san dai sunyi kewar ki suma!" "Hhhh ko sunyi kewata ya zasuyi tunda haka uban su ya zab'ar musu, an nuna min kaka tafi uwa mahimmanci na gode Allah dabai yoni a matsayin juyaba tunda gashi harna haifo wani d'an, kasan ko ai dama koba komai shi d'a namiji kason mata biyu yake ci dan haka ban yi fad'uwar bak'ar tasa ba" Shareta yayi jin tana son tsokalo wani maganar daban kuma. "Zamu tafi can d'in amma dai kafin nan ina bukatar matata, koba komai ai an san nayi kewa" ya k'arasa fad'a yana d'age mata giraren shi, Ji tayi kamar ta waftoshi ta kikkifa mishi mari, wato ga dokin shi ta iso saura sukuwa koh? Shida ake batun aura mishi sabuwar budurwa ne dan bashi da kunya zai wani ce yayi kewarta bayan abunda yake shirin aikata mata? Wallahi da badan akwai aikin da aka bata wanda sharad'in shi shine dole sai yayi amfani da ita da abun a jikin taba da bazata bari ya kusanci jikin ta a yanzun ba da saita hora shi har ya koma yana rokon ta allah annabi tukun na dan ta nuna mishi cewa ita ba Teemar banza da hofi bane, amma ba komai a jure zuwa rafi koba komai ai durkusa ma wada ba gajiyawa bane, hakan nema yasa ta murmusa cike da kissa ita ma tace, "Nima nayi kewar kakkarfan jarumi kuma Sarki a fadar zuciyata, amma kafin a shiga filin wasa a dan barni in d'an gyagygyara domin bawa wasan damar samun armashi, Shi kuma sokon gado ya koma a dole yana jiran ta shiryo a shiga filin wasa aci gaba da fafatawa, Sai da ta d'auki kayan aikin da take bukata ta shige cikin makewayi tayi amfani dana matsawa daga gogawa harma dana feffesawa sannan ta fito, Allah da ikon sa yau dai sab'anin sauran kwanakin da take jan ra'ayin shi harma ta mantar dashi Addu'ar da aka koyar damu na ma'aurata yayin saduwa da iyali yau dai Allah ya bashi ikon karantowa kafin su fara fafatawa. Sunfa dambatu iya dambatuwa domin dai dama dukan su jarumai ne a wannan fagen, Bayan komai ya kammala kamar wani soko haka Sarki ya saki baki ya dunga ratata ma Teemah zancen abun dake faruwa na batun auren da uwar shi ta bashi umarni akan dole, ya kumayi mata alkawarin Karin auren shi bazai taba sawa ya canza mata ba domin dai shi din nata ne har gaban abada, ya daiyi b'ab'atun shi duk a son shi na fahimtar da ita cewar babu laifin shi kuma bama son yarinyar yake ba, ita kuma gudun karya yi tunanin wani abun daban hakan yasa tadan nuna bacin ranta akan yanda kai tsaye zaiyi mata kishiya ba tareda sanarwa ba. Kai jama'a yasin na gaji😰😰 Mu had'e gobe idan Allah ya kaimu da rayuwa, Ummiee Zaria ce✍🏼 💗💗💗 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *Free Book ga masu buk'ata daga farko zasu iya tuntub'ana kai tsaye 08061358462* """"Page 33 *Masoya masu juriyar bibiyar labarina Ina mai baku hakurin rashin ganin posting kullum,I am very sorry for that abubuwan ne da yawa,masu kira da masu ajiyemin sak'o na fatan alkhairi Ina godiya matuk'a da kaunar ku a gareni,domin ku ke k'aramin kwarin gwuiwa nagode kwarai* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _infection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_ _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ *08089965176* *07084653262* ****** Sosai ya zauna yayi ta aikin lallashin ta kafin ma ta nuna ta sauko daga fushinta, ta kuma nuna mishi cewar komai ya wuce koba komai ai tunda umarnin uwar shine ita ma zata tayashi ganin yayi ma uwar na shi biyayya, hakan da tayi ba kad'an ba ya k'ara kankaro mata mutunci a idanun shi. Shi yayi mata jagora har zuwa gidan su domin dai tace bata kwana sai taje ta duba yanda mai jiki ta k'araji, Hak'ik'a ta shayar da mutanen gidan matuk'ar mamakin ganin ta a wannan daren, domin dai koda wasa babu wanda yayi tsammanin zuwan nata a wannan lokacin duba da dad'ewar da tayi bata zo d'in ba , ga kuma wani sabon salon sauyi da suka gani k'arara a wajen ta domin dai tunda ta iso ta aro wata sabuwar d'abi'a na ladabi ga kula nan² da takeyi akan uwar gida dama sauran jama'ar gidan abinda ya zame ma yan gidan bak'o dan ba halin ta bane damin sun sani cewar sau tari intaga dama ko zuwan tayi har tayi zaman ta ta koma ba lallai wani ya ganta ba amma yau duka sassan gidan saida ta shiga ta gaishe su har da tsaraba abunda bata tab'ayiba tsayin shekarun aurenta da Sarki kuwa! , Sai dai kuma duk wannan rawar jikin nata ko kusa ko alama y'a ranta dake gidan kaf d'insu babu wacce ta kusanci inda uwar tasu take, domin dai ko d'aukin da yaro kan nuna na ganin uwar daya dad'e bai ganta ba kwata² yaran nan basu nuna hakan ba domin koda uwar gida tace suje su gaida maman su daga bakin kofa sukayi tsaye babu wacce ta matsa inda take suka mik'a mata gaisuwar kuma sukayi komawar su kan harkokin su domin ko acan baya ma fa suke hannunta babu wata shak'uwa a tsakanin su balle kuma yanzun day suke nesa da juna. Inda ace itad'in wata mai hankali ne tun daga yanda yaran data haifa da cikin ta suka wofantar da ita bayan tsayin lokacin da suka d'auka basu ga juna domin dai har an kai matakin dako ta shigo KD bata yarda Sarki yakai mata su a cewar ta bata son damuwa, wanda kamata yayi ace a yanzun da suka ganta su rugo da gudu cike da murnar ganin ta su rungumeta, amma ina ita shashashar ko a jikin ta dan K'annin Sarki ma da suka ma yaran magana cewar "bazaku je kuyi hira da mamar kuba, cewa tayi a barsu itama bata son suzo su dameta tana tare da gajiya, ****** Washe gari da safe kasancewar a gidan ta kwana, duk a kokarin ta na nunama Sarki cewan tana buk'atar kusanci da *Dangin shi* sannan dan ta k'ara tabbatar mishi da cewar tafa canza ba Teemar daya sani a shekarun baya bane wanna, Dan haka koda gari ya waye ma shigewa tayi cikin mutanen gidan aka cigaba da gudanar da abubuwa tare da ita sab'anin lokutan baya dako me za'ayi bata sanya kanta koda yaushe tana d'aki uwa wata sarauniya saboda tsabar jinkai da kuma kallon rainin da takema ahalin a ganinta tafi k'arfin shiga cikinsu sai dai ita su biyota. Sai dai kuma hakan da tayi yad'an sanyaya Uwar gida domin a yanayin yanda suka ga ta sake dasu wannan karon sai suke ganin kamar dai ba'a kyauta mata ba gashi tazo ta cimma bak'i cike da gida ana ta shirin bikin auren mijin ta wanda alamu suka nuna cewar bata da masaniya akan hakan! Domin sun san inda tasan ko taron me akeyi a gidan tofa daba wannan maganar akeyi ba a yanzun. Koda Uwar gida ta zaunar da ita tad'anyi mata yan nasihohi kafin ta shaida mata abunda ke faruwa, bata wani tada hankalin ta ba, illah ma nunawa da tayi ita bata da wani matsala da hakan, dan hakan ma k'arin arziki ne Allah dai ya basu zaman lafiya, da ita akayi ta shagalin biki domin tayi kokari matuka wajen danne wutar kishin dake ruruwa a cikin zuciyarta sosai kuma jama'ar gidan suka yaba da namijin kokarin ta harma da yawa daga cikin wad'anda suke adawa da ita fushin ta yad'an sauka a zukatan su, tunda ta ga an fara shirye² kawo amarya bayan magrib dan an shaida mata nan gidan za'a fara kawo yarinyar kafin a wuce da ita gidan ta, Kwarai taso ta tsaya a karb'i yarinyar da ita sai dai kuma a yanda takejin zuciyarta na yunk'urin biyowa bakinta yayo waje tasan bazata iya jure cigaba da basarwar da takeyi a cikin mutane bayan zuciyarta tana konewa a cikiba, kai bama fa lallai ta iya jure wa wajen hana kanta wafto wuyan yarinyar nan da za'a gabatar mata a matsayin kishiyarta ba, in hakan ko ya faru ai itake da fad'uwa domin ginin data fara ginawa ne zai rushe tun bata tabbatar da ingancin shiba. Dan haka ta d'auki excuse cewar bata jin dad'in jikinta ta koma Hotel d'in data sauka tsabar kishin dake nukurkusar tane yasa zazzabi ya sauko yayi mata rubdugun da dole sai da Sarki yaje ya zauna da ita domin dama koba zazzabin ta kuduri aniyar cewa Sarki bazai kwana a gidan shiba balle kuma har su samu daman keb'ewa da amaryar shi a ranar, to can dai Sarki ya lalace dan sosai suka raya daren cike da soyayya domin dai wani sabon amarci sukayi a karo na biyu aka bar Meenal da kwana da nata kawayen. *** Washe gari kuwa duk wani abunda ake gabatar ma wad'anda suke taya amarya kwana sai da aka gabatar ma su Meelat dashi kasancewar kuma abu ya zama unguwa guda yasa tunda gari ya waye sukaci gaba da amsar bak'i yan ganin d'aki, A gidan Malam ko bak'i na nesa kuwa tuni suka fara komawa garuruwan su, Ganin dai babu wani abunda ya canza domin dai bayan tabbatuwar aure gashi dai har an kawota gidan da koh a mafarki aka nuna mata shi a matsayin gidan mijin da zata rayu a cikin shi tofa saima ta tub'e kafin ta tattaro k'arfin da zata daku da duk ma wanda ya gabatar mata da hakan amma gashi wai a gaske hakan dai ya faru ba mafarkin da take ta tsammanin zata iya farkawa ko wani lokaci ba hakan yasa dole ta aro jarumta ta d'aura ma zuciyarta, to me yayi saura kuma hukuncin Malam nefa da dai ace wani daban ne ya d'auki nauyin shiryawa da gabatar wa ba shiba to da ta dage kwarai wajen nuna turjiyanta akan hakan dan tasan zata samu goyon baya daga Ma'am dan haka yanzun kam kuka ai bashi da amfani kuma sai dai ta zuba ido taga yanda rayuwa zataci gaba da juyawa, dan haka tuni ta hak'a rami acan k'ark'ashin zuciyarta ta bunne damuwarta harta da wacce ke kan fuskanta tayi kokarin maidashi ta aro ma kanta jarumta. Sai dai kuma har yanzun shiru take bakin nan nata kam ya mutu murus sai idanuwa da take bin mutane da shi ko abokan wasan ta da ta saba jansu suyi ta raha wannan karan kam ba dama, K'arin haushin kuma shine tun jiya da yamma taga an cire mata layukan ta dake cikin wayar ta sai fankon wayar aka bar mata, ita babban tashin hankalin ta shine so take taji wani hali dan gidan master yake ciki amma tasan hakan bazai yuwu ba domin dai ita ba jahila bace tasan hakkin dake rataye akan ta na auren wani yanzun, tana dai mishi fatan alkhairi Allah ya bashi wacce ta fita, tasan dai Allah ne kad'ai zai wanke ta akan kallon dazai dunga mata a matsayin wacce ta yaudare shi. *Bayan kwana biyu* Tun dai Meenal na zaman d'ar d'ar na jiran tsammanin shiga wata rayuwar sabuwa yanzun kam harta saba , domin dai yan biki duk sun koma gida jen su, domin dai zaman ta a wannan gida zamane na babu mai takura mata bamai sawa balle hanata domin dai abunda ransu ya raya musu shi sukeyi ita da kawayen ta, su dafa abunda suke muradin ci suci duk dakoh cewar kullum ana aiko mata da abinci daga gidan su Sarki dama nasu gidan amma indai su Moon sun shigo wajenta sai sun jata kitchen sun had'a wani abun wani lokacin ma har kusan 10 na dare sukan kai a gidan suna d'ebe mata kewa gari na wayewa kuma kannin Sarki ke shigowa suna tayata tsaftace gidan, dan haka sai kewar gidan su ya zama sauk'ak'ka a gareta domin tana samun masu shigowa dubata kuma kullum sai sunyi waya da sauran. Allah ma ya taimake ta da yike ana hutu hakan yasa gaba d'aya bata da wata damuwa miji dai ba ganin shi takeyi ba balle ta tsan gwami kanta, Shi dai ango tunda aka d'aura aure har yau Allah bai sa sunyi ido biyu dashi ba domin dai baya shigowa gidan in ma yana da bukatar wani abun da zai d'auka sai cikin dare ko kuma ya aiko Kwaro ya d'aukar mishi abinda yake bukata yana can ya b'oye fulawar shi a d'akin Hotel suna gwangwaje wa a filin wasa, dan jama'ar gidan su Sarkin ma har sunyi zaton ko ta koma ne babu sallama kamar yanda ta saba, sai dai ita a gefenta har yanzun bata saku kwarin gwuiwar da zata iya fuskantar amaryar nata bane, kwanciyar hankalin data k'ara samu kuwa ganin cewa gaba d'aya bataga d'aukin auren a wajen Sarki ba domin ko ya'ya ta d'auko zancen amaryar sai Sarki ya nuna baya bukatar zancen. °°°°°°° Zaune take akan kujerar 3sitter d'in dake cikin d'akin Hotel d'in da suka maida matsayin gida a yanzun, A yayin da ta d'aura duka kafafuwan ta dake mik'e sambal akan center table d'in data jawo zuwa gaban kujerar wayar tace a hannun ta guda 1 tana latse² yayinda d'ayar hannun nata kuma take amfani dashi wajen tausa mishi gashin kanshi, kasancewar shi kwance yayi pillow da cinyoyinta sala² dake waje sai shek'i sukeyi wanda hakan ke nuna zallar hutu da fatar ke d'auke dashi sakama kon kasancewarta sanye cikin kananun kaya wato gajeren wando da wata shed'aniyar half vest wacce an dai satane kawai amma bawai dan ta rufe wani abuba, Irin wadan nan shigar sune mafiya soyuwa a wajen sarki a duk sanda zai kasance tare da ita dan haka ita kuma tunda ta gane lagonshi ta rike mishi wuya taci gaba daci mishi uwa, Dan yanzun kam ta k'ara tabbatar da cewar mijinta nata ne ita d'aya. "Sarki ina son zan koma Lagos zuwa gobe fa domin akwai wani workshop din da zamu gabatar cikin satin nan kuma komai yana hannu na, sun kirani suna tambaya akan mai ake ciki kuma gashi ni ina nan, kaga kuma ya kamata dai kafin in tafi inje inga kanwata domin bai kamata ace har in koma baka gabatar damu a wajen juna ba, gashi kuma kai ka tare anan nasan tanacan cikin kewa" "Haba Gimbiya nayi zaton kin d'auki hutu ne zamu d'an kwana biyu a tare ashe kwalele kikazo kiyi min" Wata irin dariyar kissa take binshi dashi k'asa² cike da barikan ci tace "Haba Sarki na, ni harna isa inzo in maka kwalele kai da gonarka, sai dai ai kasan kodan saboda Boy dole in koma duk da dai nasan hannun dana barshi za'a kula dashi fiye da yanda zasu kulama da nasu dan kasan yanzun fa Boy ya doke matsayin kowa a gidan mu amma gara dai ace ina kusa da kayana, kai kuma dan ka bini mun koma tare aiba laifi bane! naga dai ko ka zauna ita amaryar taka ba wata tsiyar zata iya tsina na maka ba domin dai Sarki ai sai Gimbiyar shi" "Tunda haka kikace zan duba in gani ko bamu tafi a tare goben ba in yaso zanyi kokari in biyo ki a baya cikin satin nan dama ko ba'ayi haka ba akwai abunda zai kaini Lagos d'in balle kuma kinzo kin min d'and'ani haukaci gashi duk kin wani kasa sakewa ki kula dani da kyau" "Ah ah fa Sarki na bafa laifina bane domin dai kaine baka iya rik'e kanka da zarar an shiga filin wasa duk sai kabi ka rikice ka nemi fara kururuwa kaga kuma nan bafa gidan mu bane Hotel ne kasan kuma ina da kishi bazan so wani ko wata yajiyo muryarka a irin yanayin dani kad'aice ya dace naji shiba" "Ohh haka ne wato ma ni kadaine bana iya rik'e kaina to bari mu gani yanzun waye zai gaza iya rike kanshi a wannan karan" Ya fad'i hakan a yayinda ya yunkuro da nufin wawurar ta, gane nufin shi yasa babu shiri ta zabura suka fara zagaye d'akin daga karshe dai har yayi nasarar damk'ota yaci gaba da d'aura mata karatu. Da yamma liss kuwa suka shirya shida ita kamar yanda ta buk'ata suka kama hanyar zuwa wajen Amarya, Sai da suka fara shiga gidan su Sarki tayi ma mutanen gidan sallama wannan karan dai tsabar ta shirya ma abun harda gidan Malam sai da ta shiga ta kuma bi kaf sassan gidan suma ta gaishe su a karo na farko da dayawan sirikan gidan wadanda basu santa ba sukayi tozali da ita, ciki kuma harda sashen Mommy Hauwa saida ta shiga d'akin Malam shine na k'arshe inda ya had'asu ita fa Sarki ya musu nasiha akan suji tsoron Allah su kuma zauna da juna lafiya Allah kuma ya had'a kawunan su, Itako a cikin zuciyarta babu kalar tsinuwar da batayi ma Malam ba domin tsaf labarin komai ya dawo kunnen ta na cewar ashe yarinyar ma auren dole yayi mata Dan hakan tasan bazata sha wahala ba wajen ajiyeta a matsayin ta, shine dan bak'in munafunci ya ajiyesu a gaban shi yana karanta musu suji tsoron Allah, to shi d'in yaji tsoron Allah ne wajen auren ma mijinta yarshi akayi mata kishiya babu shiri? Ko wani shegen ne yace mishi ita d'in irin matan su na Arewa ne da ake jerawa kishiyoyi kuma harma a zauna lafiya, hummm badai aure ba bismillah ayi zaman auren ta gani indai da mijinta ne, Ummiee Zaria✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *It's a free book ga masu buk'ata daga zasu iya tuntub'ana kai tsaye*08061358462 """"""Page 34 Yauma dai kamar kullum gidan na Amarya Meenal ya samu ziyarar su Aisha, Maimoon, Maryam, Jameela harma da Rukayya, Tun jiya Meenal d'in ke magana akan faten shinkafa take sha'awa dan yau d'in faten shinkafan suka girka wanda Maryam ce ta jagoranci girkin kasancewar kaf cikin su hannun ta yafi fad'awa a wajen sarrafa abincin gargajiya, su dai sauran barsu wajen iya sarrafa kayan kwalam da makulashe, Zazzaune suke a kasan carpets d'in dake shimfide a tsakiyar falon sun zagaye farantin faten dake tsakiyar su, suna sha suna hira. Sai da Moon ta had'iye lomar dake cikin bakin ta sannan ta gyad'a kai gefe cikin kasalalliyar muryar da al'ajabi ya cika take cewa " wani dan Allah ku bakwajin mamaki kamar ya kashe ku?" Bata jira cewar su ba ta maida cokalin hannun ta cikin faranti tana mai k'ara gyara zamanta karamin murmushi ne kwance fuskarta sai da ta gama k'are musu kallo sannan ta bud'e baki tace, "wai Allah mai iko wallahi kullum in nazo kofar gidan nan na wuto bakin gate har na k'araso ciki na iske Meenal zaune sai inyi ta mamaki wai Meenalin Malam ne a cikin gidan nan Matar Sarki kuma! , kai jama'a dan Allah inba Allah ba waye ya isa ya yanke hukuncin nan kai tsaye ai sai dai shi,! " Kallon ta ta maida kan Meenal sannan ta had'e hannuwan ta guda biyun 🙏 alamun ban hakuri tana maida dubanta kan Meenal din taci gaba da cewa "Nidai please³ 🙏 sister kiyi hakuri da duk shiriritar da nayi a baya ba laifina bane sharrin yarinta ne duk wanda ya kalleni ai dama yasan girman jikine kawai ba shekaru, Allah kuwa girma ne kawai ya riga hankali zuwa inba haka ba ina ni ina Sarki ai kowa ya san yafi k'arfina" hannu wanta ta maida kan kunnuwan ta ta rike su suma sannan ta tashi daga zaunen da take ta tsugun na still dai hannayenta rike suke da kunnen ta saita d'an duk'e kamar zata kai goshin ta k'asa sai kuma ta d'ago zuwa ga tsugun nin da take "kiyafe min sister! Ki yafe min³!! Kar kici gaba da kallona a matsayin wacce ke son mijin auren ki wallahi ni dama ban sa shi a zuciyata ba duk abunda nikeyi inayi ne kawai a lokacin dan in tsokane ki tunda naga bakyason ana miki maganar shi, Allah ya gani ko a mafarki ban tab'a zaton zaki zama matar Sarki ba wata rana". Sake da baki Meenal ke binta da kallo yayin da su kuma sauran ke dariya k'asa² dan tun da aka gama biki babu wacce ta tada maganar yanda abun ya kasance dan babu wacce ke son ta kwanto ma kanta kura tunda ita uwar gayyar ta nuna musu bata son maganar dan haka sukaja bakunan su suka tsuke, Kallon Aisha Meenal tayi "Ke Aisha hala dai yarinyar nan ta fara zuk'e² da kurb'e²n kayan maye ba tareda sanin kowa bane? Ko kuma Ah² tsabar iskancin Lagos ne ya biyota har nan? Ashe ba k'arya Hajiya takeyi ba da tace kaji tsoron Allah ka kuma ji tsoron yan iskan Lagos, to na rantse in kika k'aramin maganar banza anan bazan k'ara kulaki ba har kibar garin nan tam! bama Sarki ba ah ah Saraki" ta k'arasa fad'in hakan a zuciye tana jan kwafa taci gaba da shan faten ta, Babu wacce ta k'ara tada maganar har suka kammala suka kuma gyara wajen sannan suka koma saman kujerun falon sukaci gaba da sha'anin su. //////Babu sallama balle ayi zaton neman izinin shiga Teemah ta bud'e kofar falon kai tsaye ta shige, kasantuwar dukan su hankulan su ya d'auku akan kallon film din da sukeyi hakan yasa basuji motsin shigowarta ba har sai da ta iso tsakiyar falon, kwas! kwas! Kwas d'in da takun takalmin ta yake badawa akan tile's d'in falon ne yajawo hankalin Meenal dake buga game da wayarta dan ita ba kallon film d'in take yiba, sai dai kallon matar kawai taci gaba dayi ba tareda ta iya ce mata komai ba, to jama'a me zata ce mata? haka kawai mutum ya fad'o maka cikin gida babu koh sallama sannan kuma yanayin shigar matar babu ta inda ya nuna cewar tana da tabuwar hankali balle tace ko mahaukaciya ce ta kutto daga wani wajen ta fad'o nan ko kuma to kila dai makuwa tayi! Dan haka da ido taci gaba da bin ta har zuwa sanda ta nemi d'aya daga cikin kujerun falon takai zaune tako d'aura kafarta d'aya kan d'aya abunta tana mai bin falon da kallon kurullah domin ai tunda aka gina gidan bata tab'a shigowa cikin shiba tadai ga gidan a hoto da video d'in da Sarki yayi ya kai mata a lokacin da ya so ta dawo gidan tak'i, Ganin zaman nata a falon bai wadatar ba yasa ta mik'ewa ta fara zagaye falon, da kallo duka su Meelat suka bita dan sai yanzun suka lura da ita suna tambayar Meenal da "wacece" ita koh dage musu kafad'a tayi alamun oho bata sani ba, Maryam ce tayi k'arfin halin gaisheta da cewa "ina wuni" amma ko alama matar nan bata nuna taji abunda Maryam d'in tace ba sai ma basar da ita da tayi ta k'arasa wajen dinning table din dake gefe tana karema wajen kallo domin yanda ya k'awatu a idon mai kallo kwarai gwanin ban sha'awa ga mai kallo, gaba tayi ta k'arasa hanyar da zai sadata da kitchen ta bud'e kofar ta tura kanta ciki ba tareda ta zura gangar jikinta gaba d'aya ba, shima dai sai da ta k'are mishi kallo a zuciyar ta tana mamakin dukiyar da aka narka ma yarinyar nan, anya ma ba kud'in mijinta suka samu sukayi facaka dashi haka ba? Inba haka ba ai ita bataga alamar cewa sun mallaki dukiyar da zasu kashe ma yarinyar mak'udan kud'i har hakaba! Bayan kuma ba ita kad'ai suka aurar ba waya sani ma ko baashi suka ciyo saboda gudun kar suji kunya dan ai daga ganin tsarin gidan duk wanda ya shigo dama yasan gidan yafi k'arfin a zuba mishi k'ananun kaya, to in ma dai baashin ne to su shirya maidawa mai kayan kayan shi in ya so a basu kud'in su su rage zafi, dan Wallahi babu shegiyar da zata zauna mata a gidan da aka gina da sunan ta, baza tayi saurin korata a yanzun ba domin hakan yana iya b'ata mata tsarin ginin ta data d'aura amma yanzun d'in ma sai dai yarinyar ta zauna mata a matsayin yar gadin gida badai matar gida ba. Fitowa tayi daga wajen taci gaba da zagayen d'akunan dake k'asa sai da ta gama ta juyo tana k'are musu kallo ganin su a tsatstsaye suna binta da kallo banda Meenal wacce ke zaune tanaci gaba da game d'inta kamar ma bata san meke faruwa a falon ba. Sai da ta k'are musu kallon tsaf Addu'ar ta d'aya shine Allah dai yasa ba waccan yarinyar bace dai kishiyar nata! Domin tun kallon farko data mata taji gaban ta ya yanke ya fad'i, Kallon su taci gaba dayi daya bayan d'aya kamar yanda suma suke kallon ta cike da mamakin karfin halin ta, sannan ta bud'e bakinta da wani irin girman kai da isa tace "Ita matar gidan bata iya fitowa ne a sanda bak'i suka shigo mata?" Babu wacce tayi zaton cewa Meenal zata bata amsa a dai² wannan lokacin har sai da kunnuwan su ya jiyo musu muryar ta a yayin da take ba Teemah amsa da cewa, "ita matar gidan takan tari b'akin da tasan da zuwan sune kad'ai bawai masu fad'owa daga sama babu gayyata ba," sai da ta d'ago kanta suka ma juna kallon ido cikin ido ita da Teemah sannan taci gaba da cewa... "baiwar Allah ina ganin kamar makuwa kikayi dan haka ki d'an koma ta gefen hannun damar ki inaga kamar tanan kika biyo koh? Bismillah kina iya komawa inda kika fito mun gode da gaisuwa" Zaburo wa Teemah tayi kamar mai shirin rufeta da duka sannan cike da jin haushin abinda yarinyar tace mata itama ta maida mata martani da cewa, "Ke din wacece da har zan shigo gidan mijina uban yarana kice wai in fita? gaki k'aramar yarinya dake amma alamu sun nuna baki da tarbiya" Yunkurowa itama Meenal d'in tayi domin sosai itama kalmar karshe na matar ya b'ata mata rai wai itace bata da tarbiya dan haka ta maida mata martani da cewa "tarbiyar ne yasa naga an shigo gidan matar aure babu sallama" Suna cikin wannan cacar bakin Sarki ya shigo falon Kwaro na take mishi baya, "Mike faruwa anan? " ya tambaya ganin su a tsaye kamar wasu zakarun dambe. Simi² su Meelat sukaja hannu wan juna suka shige d'aya daga cikin d'akunan dake kasan suka rufo kansu harda murza key, domin dai wannan ai family issue ne sukam basu da ruwa a ciki, ganin hakan yasa ita ma Meenal din juyawa da niyyar barin falon sai dai kuma tana takawa Sarki ya tsaida ta da cewa "dawo nan! ya ina magana daku kike shirin tafiya kuma" Teemah ce ta tari numfashin shi da cewa... "Baban Boy kar dai kacemin wannan mara kunyar yarinyar ce amaryar da ake ikirarin an aura maka?" Bata jira amsar tambayar nata ba ta d'aura da cewa.. "Sarki wani kalar abin kunya kake shirin jawomin, karasa matar da zaka auro ka had'amu kishi akan ka sai wannan yar kankanuwar yarinyar? ana ta cewa k'aramar yarinya nayi zaton zan ganta cikakkiyar budurwar da zamu goga zaman kishi da ita sai naga wannan abar... yanzun fisabilillahi a hakan ka iya nunata ma abokan ka yarinyar da a haife ka haifeta? Lallai yau na k'ara tabbatar da halin ku na ya'ya maza da kullum ake fad'a" Zagayen falon ta farayi takai gauro takai mari hannuwan ta duka a saman kanta kamar wata wacce aka aikowa sak'on mutuwar uwa da uba a lokaci d'aya. "Calm down please mana Teemah" Ya fad'a yana shirin kamota dan sai wani abu take kamar wata mai shirin tada aljannuh, ita koh tashin hankalin ta shine ganin abinda batayi tsammani ba, tabbas an bata labarin cewa k'aramar yarinya ce, to amma ita idanuwan ta abunda suka gane mata shine cikakkiyar budurwa mai mulmulallan jiki da cikakken dirin da bako wani namiji bane zai iya mata kallo guda ya d'auke kanshi, bayan wannan kuma ga wani irin masifaffen kyau data gano a fuskan yarinyar wanda ita kanta bata iya mata kallo guda ta d'auke kaiba ina kuma ga namiji irin mijinta da dama babu abunda yake bala'in burgeshi irin mace mai kyau kuma dirarra, wanda sanin kanta ne wad'an nan abubuwan su suka k'ara taimaka mata wajen shawo kanshi a lokacin data nuna tana son shi, domin shi dai mutum ne mai son matar fita kunya da hakan kuma take k'ara amfani da nata kyan da kuma salon kissa da kisisina ga kuma kulawa da kanta da takeyi duk dan kar dai ya hango wata a waje, shine yanzun aka wani d'auki wannan yarinyar mai siffan aljannun ruwa aka aura mishi gata kuma da kana nan shekaru, kai inahhh wallahi da sake dan bazata zuba ido aikin data fara ya lalace ba, ta sani sarai cewar babu kalar munafuncin da maza basu iyaba inhar ta barshi da yarinyar nan tofa yana iya mai data wata dankalin hausa a gefe yazo ya dunga hutawa da yarinyar nan domin dai akwai kayan hutun tabbas, ai ko da kulli yaci amanar koko wallahi. "Teemah calm down please ki saurareni ina ce mun riga mun gama maganar nan already" "No no no please don't tell me to calm down, ashe kaga irin kalar da kake so shi yasa dan bak'in munafunci tunda kasa k'afa ka baro Lagos ko a waya baka iya kyankyasa min abunda yake faruwa ba, Wato ga Teemar banza da wofi tunda ni ka gama cinyeni ka zazzage ni tas na haifo maka yara daya biyu har hud'u wato na tashi aiki bari ka gudo gida cikin *DANGINKA* Ka nemi karamar yarinya ka aura, kuka wani had'a baki da kai da muna fukan *DANGINKA* suka baka auren yar shilar da da'ace ban biyoka na taho ba sai dai inji zancen auren a shanun tallah" bai bari ta karasa ba ya katseta a tsawace... " will you please short up your mouth before..... " A zafafen ita ma ta katse shi da cewa... "Before what Sarki? Nace before what? are going to raise your hands on me? Oh saboda kayi aure yau kuma duka na zakayi tun baka riga ka tare da amaryar ba? " Sai kuma ta juya gefen da Meenal ke tsaye tana kallon ikon Allah dan kwaro dai shi kam tun fara hayaniyar su yayi sif³ sif ya fice daga falon, Damk'a tayi shirin kaima Meenal ita kuma Allah ya bata ikon zillewa bata yarda Teemah ta kai hannunta gareta ba. "Karki tab'a yarinyar nan Fateemah!" ya fad'a a tsawace da muryar nan tashi mai amso amo in baku manta ba dama shi din muryar shi masha Allah balle kuma yana cikin bacin rai. "Ka barni in rik'eta ta fad'amin da wani kalar asirin sukayi amfani wajen aure min miji, mai suka kulla da yasa tun ba'aje ko ina ba har ka faramin ihu, asiri suka maka wallahi ban yarda da yarinyar nan ba har dama iyayen ta dan anga Allah ya rufa maka asiri ne suka had'aku dan suma su dan gwali arziki" Anzo gab'ar da mutuniyar fa bata iya daurewa, atoh dai bazai yuwu wata can so called kishiya ta shigo mata cikin gida kuma sannan ta nemi cin fuskanta dama na iyayen ta ba dan haka ta maida mata martani da cewa. "Allah ya tsaremu da nufar wani da sharri balle har son zuciya ta kaimu ga aikata Babban sab'o wato yin asiri ga wani, inaga dai ita mai maganar bata yarda da Allah ba ko kuma dai abune wanda akai sabo dayi shi yasa akayi saurin tsarguwa! Alhamdulillah kuma ni iyayena ba makwad'aita bane balle son abun duniyar su yasa su bada aurena ga wani dan abun hannun shi, Inma kuma hakan ta kasance ai ba laifi bane koba komai ai kowa yasan dama son sone amma kuma son kai yafi wata ma daga waje can wata uwa duniya ta aure shi take cin arzikin shi balle kuma ni *Jinin shi DANGIN SHI* ko kin manta ne cewar wata kusan tafi wata kusan naga ai nikam dai koda aure ko babu ina iya had'a kayana in dawo gidan nan dan in dangwali arzikin Ya'yana balle kuma gashi yanzun darajojin sun k'aru, domin dai tuni na fara amsa sunan *Matar Sarki* nima" Ta karashe fad'a tana wani marmar da ido uwa wata babbar mace, A gefen Teemah ko kai tsaye zamu iya kiran kafewar da tayi a waje guda da mutuwar tsaye, domin sosai kalaman bakin yarinyar nan suka dake ta, duka kuma irin na mamayar da yazo mata a bazata, dan batayi zaton yarinyar tana da confident d'in da har zata iya tsayawa a gaban ta ta maida mata martani har haka ba, sai ga shi a gaban Sarki akayi komai amma ko sau d'aya baiyi yunkurin takama yarinyar burki ba sai ma waje daya nema kawai ya zauna abunshi. Shiko ya zauna ne saboda tabbacin da yake dashi cewa infa yaci gaba da tsayuwa tofa bazaiji wahalar takawa wajen damk'o su ya gwara kawunan su waje guda ba ya sumar ko ya denajin cece kucen su, dan hakan nema yasa tun zaman nashi ya lazamci maimaita fad'in kalmar innalillahi wa'innah ilaihir raju'un, sai da yad'an lafa, sannan ya bud'e baki cike da bada umarni yace... "In kungama cacan bakin kunemi waje ku zauna" Zaman dukan su sukayi kowacce nama yar'uwarta kallon hadarin kaji. Ganin sun zauna d'in shi kuma sai ya mik'e ya kufi inda dispenser ke ajiye sai da ya latsa ya cika kofi da ruwa masu sanyi ya shanye har sau biyu sannan ya k'ara d'aukar wasu kofunan suma ya tsiyayo ruwan a cikin su ya nufo inda suke zaune, Mik'ama dukan su ruwan yayi ba tareda yace komai ba, Koda bai furta ba sun san cewa dai yana nufin su shane, ita dai Meenal kad'an ta kurb'a dan ba wai k'ishin take ji ba, amma Teemah kam duka ta shanye har sai da ta k'ara dana hannun shi saboda yanda bama-baman kishi ke mata tashi a cikin kirjinta suna kai mata harin bazata. Babu wanda ya k'ara ko tari a cikin su sai ma Meenal dake cin apple d'in da tun d'azun ta ciro shi daga fridges saboda yayi sanyi da yawa dama shi yasa ta ajiye shi a gefe dan ya huce, yanzun kam da ya rage sanyi hankalinta kwance ta d'auki abinta tana yankawa da yar karamar wuk'a tana ci, kamar ma ta manta da mutane a falon. "Uhumm-uhmmm" yayi gyaran murya yana mai k'ara gyara zaman shi, kafin ya maida kallon shi akan Teemah. "Abinda kike bukatar yi kenan dama anan shi yasa kikace in kawo ki?" Shiru tayi ba amsa dan sai yanzun data sha ruwan nan hankalin ta ya dawo jikin ta sannan ta tuno da gargad'in da aka mata cewar karta takale shin da sab'ani zai shiga tsakanin su, Dan haka sai tayi k'asa da kanta cikin sassanyar murya tana kokarin boye bacin ranta tace. "Kayi min afuwa Baban Boy sharrin shedan ne! Hakan bazai kuma faruwa ba" Har cikin zuciyar shi yaji dad'in furucin nata amma sai ya dake bai nuna hakan ba ko a fuska, Ita ko mutuniyar ku duk da bawai kai tsaye take kallon taba amma k'asa k'asa take faman aika mata harara jin da tayi kuma tace wai sharrin shedan ne yasa itama cikin kasa da murya sosai tace. "ai kece shaidaniyar mai shigoma mutane gida ba sallama" Gefen Meenal ya kaida duban shi, "Ke kuma haka aka koya miki karb'an bak'i? Kinyi bak'uwa ko ruwa baki iya bata ba kun k'are da fad'a bayan kuma ita d'in ba tsarar ki bace, ko bakiga ita d'in ta girme kiba?" Kyar ta daga fararen idonanuwan ta tana mishi kallon ido cikin ido ta yamutsa fuska tana mai turo bakin ta tace, "To ai ko a musulunci babu inda akace bak'o ya shigo gidan mutane babu sallama balle kuma gidan matan aure, kuma fa har mara tarbiya ta kirani bayan kuma ai abunda yayi ka nima shi yayi ni, in tarbiya ne ita Babban ai a wajenta zan gani har in d'auka amma ta shigo gida kamar wata pastor bayan ko gidan arna ana nocking" Ta karasa fad'a tana mai da kai gefe. "To naji bata kyauta ba ta shigo gida ba sallama, amma kuma itama d'in ai gidan tane nan d'in tunda gidan mijinta ne! " Ba zato ba tsamnani yaji ta bashi amsa da cewa, "Ah ah kam gidan ta yana Lagos nan kam tuni ya amsa sunan Gidan Meenal tun ranar da aka d'aura aure aka kawoni cikin shi, in kuma mutum yana tantama zai iya fita daga waje ko yaro ya samu yana iya tara ya tambaye shi cewar gidan waye nan d'in dan ya tabbatar, koma ba wannan ba tsayin shekaru gidan nan ai kowa ya tabbatar ba'a ajiye ko wacce macen aure a cikin shiba sai yanzun, mai yasa tun wancan zamanin bata dawo gidan ta zauna ba sai yau ne za'ace min gidan mijin ta, nan gidan Mijin Aminatu ne can kuma inda take shine gidan mijin ta" Kai innalillahi jama'a wai dama yarinyar nan haka take? Ko kuma yanzun ne ta dawo haka? Ya tambayi kanshi sai dai kuma babu wanda zai bashi amsa a tareda shi, Ita ko Teemah yanda kuka san wata gunkiya haka ta koma domin dai ita zata iya cewa anan d'in da take zaune iya zuciyarta ne kad'ai yake bugawa amma hatta da jinin jikinta batajin yana zagawa a cikin jijiyoyin ta lallai tayi sake da yawa da har wata ke iya kiran sunan mijinta da sunan nata a kuma gaban idon ta, tana raye tun bata mace ba. Dan haka da kyar ta iya bud'e bakin ta tace. "baki da labarin cewa shi gidan mijin da kike ikirarin naki , shi mijin auren cushe aka mishi dake ma'ana auren dole? " "Fateemah" sarki ya kira sunan ta a kokarin shi na ya dakatar da ita, "Kar kace komai ka bari in fad'a mata tasan matsayin ta cewar ba sonta kakeyi ba ka aureta ne kawai dan kayima iyayen ku biyayya" Abun ya daki Meenal kwarai amma ta danne dan bata son ta nuna gazawarta tun yanzun, "Ai ba mijin kine akayi ma auren dole ba face ni da nike da kananun shekaru amma aka nakashe min rayuwa wajen had'ani da tsoho, Dan koba komai shi tsohon tunda ya samu sabon jinin da yasan zaiyi tafiyar dogon zango da ita ai dama bazaik'i ya amsa ba, amma nifa? Bari in miki tuni akan maganar d'azun da kikace cewar bani da tarbiya, to ki sani tarbiyyar dana samune yasa harna iya daure zuciyata na amshi tayin auren tsohon mijin ki dan in bancin biyayya ba kema kin san babu yanda za'ayi in k'are da auren tsoho kalleni da kyau ki gani" Ta fad'i hakan a yayin da ta mike tsaye tayi taku d'aya biyu sannan ta k'ara juyowa ta bada wasu takun,gyas gyas gyas sautin yatsun babba da da d'an tsakiya data had'a ta kyasta, "Ya kika gani ai Aminatu kowa ya gani yasan tafi k'arfin yaro sai dai baban yaro, hakan nema ya bani kwarin gwuiwar naji zan iya zama da mijin ki dan haka ki koma can inda kika fito kisa ido kisha kallon yanda zan wanke shi ya koma dai dai dani, bari in fad'a miki ita sutura in kinga tayi saurin tsufa wanki da gugane basu wadace taba" Komawa kujerar data tashi tayi bayan ta gama karkad'a musu kayan alatu ta maida kafafuwanta ta d'aura daya kan daya. Da kallo sarki yayi ta binta mamaki yana neman sumar dashi a zaune, Ashe haka take? Sai da Sarki yayi da gaske sannan suka nutsu da habaice²n da suke jifan juna dashi. Tashi muje in mai dake masaukin ki" "No anan zan kwana" Ta fad'a tana mikewa zuwa inda matakalar benen dake cikin falon yake da nufin haurawa sama, "Wani gidan? Badai gidan nan ba!" Cewar Meenal itama tana mikewar. "Oh bakiji abunda nace bane? Yau a gidan mijina zan kwana" "Teemah mai yasa kikeyin haka ne wai? Ok let me make one thing clear, ki sani duk sanda zaki zo garin nan baki da masauki a gidan nan kamar yanda in itama taje inda kike bata da masauki a naki gidan, na riga na yanke hukunci dan haka ki wuce mu tafi," Sororo ta tsaya tana kallon shi, kujimin wani sab'o fa da Sarki yake furtawa wannan ma ai zunubin gangancine wallahi, wai gidan daya gina domin tane zaice bata da masauki a cikin shi, ko dai mutumin nan ya fara korawa ne bata da labari? Kai anya kuwa kodai asiri akai mishi? Eh gaskiya sai dai asirin ai dama ance indai asirine yan zaria sai a barsu🙄 (nidai nace k'arya ne). 😂😂😂😂😂Nace ba Hajiya fa ta iya kashedi wallah gashi dai yau kashedin ta ya kwatar ma jikarta yanci atoh da wa yasan abunda Teemah ta shirya aiwatar wa ayau, Ummiee Zaria ✍🏼✍🏼 Share and comment please, [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *Free book ne ga masu buk'ata daga farko zaku iya magana dani kai tsaye* 08061358462 *Rubutawa* *Ummiee Zaria*✍🏼 Page 35...... A babu yanda ta iya haka ya mata jagora, uwa wata rak'uma haka ta bishi a baya suka bar gidan,badan ranta ya so hakan ba, Wallahi dan dai dare yayi a lokacin ne amma da babu abunda zaisa ta k'ara kwana a Zaria, sai dai ita d'in babu mafi kololuwar abunda take tsoro irin Night travel balle kuma anan da ba garinta ba. Bayan fitar su daga gidan komawa Meenal tayi ta zauna tana jiran tsammani dan a zaton ta zai raka matar tashi zuwa mota ne ita kuma ya dawo ya zane mata jiki, sai dai ga mamakin ta sai tashin motar su ta jiyo sun bar gidan. D'aga muryar ta tayi ta kwala ma su Meelat da suka kulle kansu a d'aki kira.... "Ku dallah can ku fito ya wuce fa" Sif² haka suka bud'e kofar d'akin suka fito, "Ke Meenal amma dai wallahi kina da k'arfin hali da har kika iya tsayawa a gaban matar nan tana fad'a kina bata amsa inda ta miki duka fa? " Cewar Maryam. " tab d'ijan duka dai lallai ma, Oh so kike inyi zaune kamar wata kujera tazo ta haye kaina ta zauna? Ai in tsoho baiji kunyar hawa jaki ba shima jakin bazaiji kunyar kayar dashi ba" "Kunga nidai ku tashi mu tafi gaskiya karya dawo ya taddamu yace muna zuga mishi mata" Cewar Aisha da duk cikin su tad'an fisu hankali, "ta sannu uwar iya" Meenal ta fad'a a yayin da ta mik'e tsam mutuniyar ta taje ta murzama kofar falon key ta kulle sannan ta cusa key d'in a cikin bra din ta, "Sai inga ta kofar da zaku bi ku tafi, wallahi babu gidan ubanda zaku muna nan daku!" Ta fad'i hakan a yayin da take shirin hayewa sama, Haka suka dunga rok'on ta akan tayiwa girman Allah tazo ta bud'e musu kofar su kama gaban su amma tayi hayewarta sama taba banza ajiyar su koda ta shiga d'akin da take kwana ma kulle shi tayi dan karsu dameta, *Bayan wasu kwana ki* Zuwan da Sarki yayi gidan a waccan ranar bai canza komai ba, domin dai tun fitar da yayi da matar shi bai k'ara komawa ba can ya lalace wajen matar shi sukayi sulhu kafin su wuce Kaduna tare a washe garin ranar daga can ita kuma ta wuce Lagos shi kuma sai washe gari ya dawo, Bayan tafiyar na Teemah dole gidan ya dawo da kwana sai dai kuma hakan babu abunda ya canza domin dai kowa harkar gaban shi yakeyi shi yana sashen shi da inba yaga dama bane har gari ya waye rana ta fad'i daga ita harshi babu mai ganin wani, Shi bai neme inda take ba ita kuma dama bashi bane a gaban ta damuwarta dai shine Allah ya nuna mata fitowar result d'insu lafiya dan Wallahi dai ta fara gajiya da zaman gidan gashi babu damar ta fita dan Mommy ta kwad'a mata warning cewa karta yarda ta ganta a gida, Saukin tama lokaci lokaci uwar gida kan turo K'annin Sarki ko ita da kanta tazo ta duba ta. Malam ma yazo gidan sau d'aya dan ya duba ya take abinda bai tab'a yima sauran yaran gidan ba wato zuwa d'akunan auren su. hutun auren da Sarki ya d'auka ya k'are dan haka tuni ya tattara ya koma bakin aikin shi duk da ba wata uwa yake tsinana ma Meenal d'inba amma dai taji kewar rashin zaman nashi a gidan domin yanzun ba kasafai take samun bak'i kamar daba dan su Moon sun koma garuruwan su , su Meelat ma yanzun ba kullum suke shigowa ba sai gidan ya zamana daga ita sai masu gadin dake bakin gate, sai dai in tayi kallo ta gaji ta d'auko kujera ta dawo dashi kofar falon ta ta zauna tana kallon masu gadin dake kaida kawowa ko kuma ta koma sama ta zauna a balcony d'inta dake saman tacan takan iya ganin kaida kawon jama'ar unguwar dake zirga². Bata da Matsala na komai a yanzun kam domin dai komai an tanadar mata, kuma shi kanshi Sarkin bai bar garin ba sai da ya sauke mata wasu yan kud'ade ko zata buk'aci wani abun, ga sakon abubuwan ci na sha'awa da ake mata daga gidajen biyu , domin dai har gobe indai Malam ya dawo daga tafiya kamar yanda ya saba zai bada tsarabar ta a kawo mata, A watan ta na uku da aurene ta rok'i Sarki ya barta ta koma Islamiyar su wanda dama a cikin unguwan yake sannan shima ganin yanda take rayuwa cikin gidan ita d'aya yasa ya sauk'aka mata , wajen bata umarnin fita zuwa wani wajen in baya gari a duk sanda hakan ta kama dan ta d'auke ma kanta kewa, dan yasan wani abun na iya tasowa a sanda zata neme shi a waya kuma ba lallai ne ta same shiba. Abun mamaki kuma a cikin watan nin nan ko sau d'aya batayi irin ciwon marar nan da takeyi mai tsanani ba, koda period d'in zaizo kad'an kad'an ciwon yake mata ba tareda ya takura mata kamar lokutan baya ba. Rayuwa nata tafiya cike da tarin nasarori tako wani gefen, gefen Meenal dai a zuwa yanzun kam bata da wani damuwa tuni ta cire komai a zuciyar ta taci gaba da harkokin ta, Sarki yakan yi kokari yazo ya ganta duk bayan wani lokaci gudun shiga hakki sai dai fa babu wani cigaba da aka samu ta fannin auratayya, in yazo dai zai kirata yaji ko tana da buk'atar wani abun, in akwai zata fad'a mishi in babu kuma in ya tashi komawa zai bata kud'ade ta rike a hannun ta,a haka suke zaman bata k'ara jin duriyar kishiyarta ba balle ta damu kanta dan haka gaba d'aya ma wallahi mantawa take wai tana da kishiya, to mijin ma har yanzun bai amsa sunan miji ba balle kuma wata aba wai kishiya. Jarabawar su duka biyu sun fito cike da tarin nasarori, kamar kuma yanda Malam yayi alkawari shida kanshi ya kira Sarki ya fad'a mishi cewar Aminatun zata koma makaranta, baija da batun ba domin dai a cewar shi bashi da hujjar yin hakan sai ma fatan alkhairi da yayi, ya so ace shine ya d'auki nauyin karatun nata domin a cewar shi hakkin hakan a wuyar shi ya rataya yanzun, sai dai Sam Malam yak'i bashi wannan daman. Aminatu, Maryam, Jamila sun fara karatu cike da karsashi domin dai Malam yayi abunda ya saba naba kowa mamaki wajen gwangwaje d'iyar shi da sabuwar mota domin zirga²n zuwa makaranta, babu b'ata lokaci kam Ya Sa'eed ya shige gaba wajen koya mata motar har zuwa sanda ya tabbatar da kwarewar ta, Alhamdulillah burin ta na farko ya cika na ganin kanta a matakin gaba da sakandire wanda shi take kallo a matsayin tsanin da zai kaita ga cika sauran burukan nata, kamar yanda suke tafiya sakandire su uku wannan karanma hakan sukeyi ita da Aminanta su Meelat wad'anda babu abinda ya canza a kawancen su sai ma abunda yayi gaba. Rayuwa yana ta tafiya a 360 abubuwa nata faruwa a cikin shekarar farko Billyn ya sa'eed ta samu karuwar d'a Namiji watan ni kad'an baya ita ma Raheenat ta haihu wanda su Meenal sukaje suna har KD sai da suka kwana biyu suka dawo, ba'a jima sosai ba ita ma Sa'adatu ta haifo nata jaririyar, Wannan k'aruwa da aka samu shiya fara karkato da hankalin *DANGI* akan zaman auren Meenal da Sarki domin dai har wasu sun fara yad'a cewa Mommy ne take ba Meenal maganin hana d'aukar ciki saboda karya yanke mata karatun ta a yanzun, Sai gashi babu damar Meenal d'in tayi koda ciwon kaine sai kowa ya fara sa ran ko ciki ne, ita dai ko a jikinta. A fannin uwar gida ko ita da kanta tasha zuwa ta amso taimako ta kawo ma Meenal d'in domin su abunda suka d'auka shine kila ciwon marar tane yasa har yanzun bata dauki cikin ba, (ko ce musu akayi a ruwa ake shan cikin oho)... Ita dai Mommy bata tab'a zaunar da Meenal dan taji yaya take tafiyar da zaman auren taba, domin tsayin lokacin nan dai itama Meenal bata tab'a kawo karar Sarki da sunan ya mata wani abun ba, koda ta tambaye ta ya take? Amsarta kullum shine "ina lafiya, " kai da ganin yanda ta kara mumulewa gabobin jikin ta suka k'ara budewa ma basai ka tambaya ba kasan bata da matsala sai wacce ba'a rasawa, domin dai ta k'ara cikar kyau da girman jiki, ga kuma gogewa data k'ara samu ta fannin mu'amalah da jama'a dama yanda zata kula da kanta a yanzun kam ita kanta tasan bata da matsalar komai saina karatun data sa a gaban ta dan miji dai zaman nasu kullum jiya iyau ne, cigaban dai daza ace an samu shine yanzun in yazo gari yana zama yaci abincin ta in ma bata had'a mishi takai ba yakan zo har sashen ta yaci sannan lokaci lokaci ko baya gari yakan kirata a waya yaji ya lafiyar jikin ta, Su Meelat da suka san irin yanda auren nata ke tafiya sun sha zaunar da ita suyi mata hud'uba akan zuwa yanzun ya kamata fa ta watsar da komai ta rungumi mijinta, sai dai ita kuma tsaf ta kuduri cewar inhar bashi bane ya sauko dan ra'ayin kanshi yaga cewar ya dace su fuskanci rayuwar auren da kyau ba, ita wallahi bazata tab'a kai mishi kanta ba. Shi kuma a gefen shi bawai kin auren yakeyi ba, ah ah wani lalura dai yake fama dashi na d'aukewar sha'awa aduk sanda ya shigo garin bazaiji shi ya koma cikakken Namiji ba har sai yabar garin, sai dai kuma kwata² bai dauki hakan da mahim manci ba balle har yasan matakin d'auka dan shi dama a yanda ya yanke ma kanshi shine baizai tabbatar da ita a matsayin Matar shi na aure ba har sai zuwa sanda ta kammala karatun ta yasan zuwa lokacin tayi girman da zata iya dashi, amma yanzun idan ya nemeta allah yasa rabon haihuwa yana kusa ai ganin yake ya shiga hakk'in ta dame zataji? da kulawa da buk'atun shi, rainon ciki ko kuma karatun dan haka yake ganin ai rashin sha'awan ma normal ne. *Bari mu waiwayi uwar gida Teemah* Tun bayan koma warta hankalin ta bai kwanta ba har saida ta shiga ta fita tayi kullin da aka tabbatar mata da cewa muddin Sarki ya taka Zaria tofa zai zauna ne a matsayin mace domin dai bazai tab'a jin sha'awar saduwa da mace ba har sai sanda yabar garin sannan zai koma yaci gaba da amsa sunan Namiji, Ita a yanda taso, so tayi a sakamar ma Meenal zubar jini, ko warin jab'a ko kuma a cusa mummunar tsanar ta a zuciyar Sarki, sai dai shi bokan nata ya tabbatar mata da cewar hakan bazai samu ba domin dai bazasu iya cimma yarinyar ba, taso ita kuma a cusa mata kiyayyar Sarkin taji cewar bazata iya rayuwa a karkashin inuwar auren shiba sai dai shima hakan kuma shima bai samu ba, alwashin da taci na cewar babu wacce zata aure mata miji ta zauna lafiya yasa badan taso ba ta yarda da shawarar bokan ta na kashe gaban Sarki a duk sanda ya taka Zaria,ai koba komai sai yana da lafiya ne zai iya kusantar ta batayi tunanin mai ka iya faruwa ba a sanda ita Meenal din zata iya zuwa ta same shi a wani wajen daban. *Tudun wada gidan Hajiya* Kasan tuwar kwana biyu Hajiyar bataji dad'iba hakan yasa Meenal ta yanke zuwa dubata in ta taso daga Makaranta, Kamar ko yaushe da gudu ta shigo unguwar domin dai tunda ta kware a driving tofa Sam bata tuk'i a hankali barin ma inta hau kan titin dake da karancin abin hawa, Tunda ta doso kofar gidan bakin ta ya gaza shiru har sai da ta furta abunda ke ranta "Na rantse da Allah dan dai ban iya azumin kaffara na wanda yayi kisan kaine, amma da take motar nan zanyi inje in haye kan wad'an can yan zaman kashe wandon" "Kai Meenal yanzun tsakanin ki da Allah da babu wani hukunci akan wanda yayi kisan rai sai kije ki haye kan nasu?" Maryam dake bayan motar ta tambaya tana dariya. "Mai zai hana harma sai na nemi shawarar wata a cikin ku" Harara Meelat ke banka mata, "amma wallahi baki da mutunci qawata wato ke tunda kinyi aure kin shige daga ciki ni bari ki kashe min nawa mijin tun kafin aure, " "Eh ai dole kice haka tunda da saurayin ki ake zaman majalisar kullum, wai bazaki mishi wa'azi su dena zaman wajen ba" Cewar Maryam "Ina ruwan ki tunda dai ba'a kanku suke zaune ba ku shafa musu lafiya Alhamdulillah kowa ma yasan ba zaman banza sukeyi ba tunda dukan su babu wanda bashi da abunyi a cikin su" "Dallah Maryam kyaleta ai bata son laifin su kwata²" Cewar Meenal "Naga alama kam. Koda suk k'arasa kofar gidan babu b'ata lokaci aka bud'e musu gate suka shige, gidan na nan a yanda yake sai ma abunda ya k'aru na gyare gyaren da ake mishi a koda yaushe. "Ku shiga zan biyo ku a baya, ina son k'arema fuskar future husband d'ina kallo da kyaune, kun san kwana biyu baya gari" Cewar Meelat "Mayya kawai yar wahalar soyyaya" Meenal ta fad'i hakan cike da jin haushi ta bude bayan motar ta cire ledar kayan fruits d'in data kawoma Hajiya na dubiya. Ita dai Meelat bata kulata ba, Maryam ko jakarta kawai ta d'auka tayi gaba dan dama tun a school take ce musu tanajin fitsari, Da sallama suka shiga falon na Hajjaju Masifaffiya, su biyu suka cimma ita da jikanta na hannun damanta zaune suna hirar yaushe gamo, domin dai shima a yanzun gaba d'aya baya samun damar zama a Zaria kamar da , saboda tsabar son kud'in shi yasa yau bashi nan gobe bashi can. Sallamar nasu ne yasa shi dago kai yakai duban shi kofar shigowa domin dai wannan muryar aiko a magagin mutuwa ya jiyota yasan kunnuwan shi bazasu gaza gano mishi mai mallakin muryar ba, ilai kuwa ita d'ince kamar yanda ya tsam mata yarinyar dake neman ta d'imauta mishi rayuwa dan gaba d'aya a watannin baya kamar wani mai shafar aljannu haka ya nemi komawa, ba damar yaga mace da jallabiya sai yarinyar nan ta fad'o mishi arai yana ta jimamin wani hali take ciki a gidan mijin nata amma ita jibita wallahi inba k'arya idanuwan shi suka mishi ba girma yaga ta k'ara babu alamun damuwa ko kad'an a tare da ita, shi yana nan kullum cikin jimami. Da kyar ya iya kwato idanuwan shi daga kallon da yake binta dashi yana korar shed'an a zuciyar shi, dan gaba d'aya sai yake jin kamar ya dauwama yana kallon ta dan wani sanyi mai cike da nutsuwa ne yaji yana lullub'e shi. Wata irin zazzafar ajiyar zuciya ya sauke wanda har saida sautin fitar ta yasa Hajiya maida duban ta gareshi, "Kana lafiya? " hajiya ta tambaya. "Yes yes yes am fine" ya bata amsa yana mai sosa k'eyar shi da hannun shi na hagu, Har ya yunk'ura da niyyar barin wajen kenan Meenal ta iso kujerar da yake zaune, kan hannun kujerar ta zauna ita kuma Maryam ta shige ciki dan sosai fitsarin da takeji ya matseta, "Mai jama'a barka da war haka yaushe a gari?ashe ka dawo? Oh kar in manta... Barka fa da arzik'i ashe wancan cingum d'in naka Nusaiba kuma lokaci yayi, gaskiya na maka murna ita kuma Allah ya bata zaman lafiya ya kuma sanya mata dangana yasa k'arshen wahalarta akan soyayya kenan, gaskiya dai na mata murna Wallahi gashi kuma ance mijin da aka bata d'in mai kud'i ne kuma sosai yake sonta, Ni kuma nace oh Allah rashin sani yafi dare duhu dan Wallahi na tabbata da tasan tsarin da Allah ya mata na samun wannan mijin da bata tsaya b'ata shekarun nan tana dakon jiran ka amshi soyayyar taba, ups sorry fa Brother wannan dai ta samu tasha da kyar saura d'ayar guzuman itama ina fatan Allah ya bata lafiya ta warke daga halin makuwar da take ciki" Tunda ta fara surutan ta bakin ta kawai yake kallo a zuciyar shi ko ayyana wa yake cewa, lallai ashe dai ba gaskiya bane da ake cewa in akama mutum aure yana hankali! To gashi dai yaga girman jikin ya k'aru amma fa hankalin har yanzun da saura, "Ke wai sai yaushe zaki san kin girma ne? An miki auren ma amma har yanzun kin kasa hankali, dama munyi dake cewa zan aure tane? Ko mun tab'a zama dake nace miki akwai wacce nike so a cikin su? Tashi a wajen nan kafin in kifar dake mara kunya kawai" Zaro ido tayi tana mai tashi daga kan hannun kujerar. "Allah ya baka hakuri mai yayi zafi harda zaka kifar dani, tab aini yanzun mai kai hannun shi jikina tofa sai ya tabbatar ma kanshi da cewar ya shirya kwanan guardroom" "Oh saboda kina auren soja koh? To tsaya ki gani in yaso idan na karya kin sai yazo ya d'aureni" Ya fad'i hakan a yayin daya mike yakai mata cafka, aiko babu shiri ta kwasa sai bayan Hajiya. "Wai takwara kinzo dubani ne ko kinzo tsokanar fad'a?" "To Hajiya laifine dan na taya shi murnar auren macen daya nuna baya so bayan tsayin shekarun data d'auka tana nace mishi?aini gani nayi abun a taya shi murna ne, kuma wallahi in mutum baiyi hankali ba sai alhakin mata ya kama shi" Mtsw yaja tsaki. "Yarinya kiji da kanki Keda akama auren dole! " "Eh irin auren dolen da aka min nima nike Addu'ar a d'auko wata y'ar daga kauye a had'aku, sai kaji yanda abun yake" Juyawa yayi da niyyar barin falon dan yarinyar nan fa bazai zauna ta mai dashi mahaukaci ba, "Taubashi na nace bah! Nace turaren nan da kakan d'an ajiye min a d'aki kwana biyu na duba ban gani ba nace ko ka manta ne? " "Kai" ya fad'a da d'an karfi cike da mamakin k'arfin halin ta yana juyowa, "Oh wato ga mai kud'in banza koh? Da mijin ki da komai sai in cigaba da siya miki turare kina fesawa saboda gani dan iskan da bai san zafin dukiyar shiba" "Kai yayan mu dan Allah miye a cikin kyautar turare dai, naga su wadancan da suke zuwa maka kullum a kallah abincin nawa kake siya musu bayan ba wani lada zaka samu ba! Niko ai koba komai bayan ladan kyauta harda ma ladan zumunta zaka samu, nidai muje Allah ko gyaran d'aki ka sani yau zanyi maka shi da kyau indai zaka bani turaren" "Hajiya kifa jama yarinyar nan kunne yasin ko a kofar d'akina na ganta sai na zane ta tom kar kice ban mata warning ba" Banza dashi Hajiya tayi ganin hakan shi kuma yasa kai ya fice a d'akin.... "Dan Allah Hajiya ku mishi auren dole, shima yaji inda dad'i....... Ummiee Zaria ✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *Free book ne ga masu buk'ata daga farko zaku iya magana dani kai tsaye* 08061358462 *Rubutawa* *Ummiee~Zaria*✍🏼 Page 36..... "Dan Allah Hajiya kuyi mishi auren dole shima yaji inda dad'i, ai ba iya mata kad'ai ake ma auren dole ba, inba haka ba ni karamar yarinya dani haka nan fa kuka had'a kai saboda kun gaji da ganina kuka aurar dani sai shi k'aton tuzuru amma ba wanda ya matsa mishi yace sai yayi aure, to gashi nan dai ai yan matan nashi sun fara watsewa tunda sun gaji da gafara sa basuga k'aho ba, Allah in bai wasa ba zuwa gaba a sanda zai buk'aci auren babu macen da zata saurare shi, badai dan yaga yana da kyau kuma yana da kud'i shi yasa yake wulak'anci ba" Kyacci tayi tana hararar hanyar da yabi ya wuce. "Ke Meenal wai me yasa ne ke in kinzo waje gaba d'aya bakya son kiga an zauna lafiya sai kin nemi wani zancen hankalin ki ke kwanciya ne? Kin dai san halin shi karkiga wai kina da aure in kika kureshi kin san jikin kine zai fad'a miki, kuma wama ya fad'a miki cewar irin su akewa auren dole? to yasin ko rantsuwa nayi nasan kaffara bazata hau kaina ba wannan in aka mishi auren dole tun a wajen taron d'aurin auren zai ma matar saki uku kwarara kuwa! " Cewar Hajiya. Turo baki Meenal tayi gaba sannan ta d'aura da cewa... "aike Hajiya dama bakya tab'a ganin laifin shi komai yayi dai² ne in dai a wajen kine kamar shi kad'aine jikan ki mu kuma yan karere, ni bama wannan ba mi kuka dafa a gidan nan dan Wallahi yunwa nikeji da safe ban samu nayi girki ba na fito koda naje makaranta kuma kame² kawai na dunga yi banci wani abincin kwarai ba, wai Hajiya Jummai har yanzun bata dawo daga Kauru d'in bane? Lallai a gaisheta kawai taje kauye tayi zaman ta kamar wata wacce taje Abuja" "Ke dai wallahi kin cika shegen surutu kamar aku, tunda kika shigo kike zuba uwa wata lalatacciyar famfo, ni na rasa Ina kikayo wannan mugun gadon na surutu wallahi, tunda kika shigo kike zuba tad'i kamar ana zuge zogale" Zaro ido Meenal tayi cike da mamaki "Hajiya wai nice mai shegen surutun? " ta tambaya tana dariya. "Lallai ma toni dan nayi surutu har a tsaya neman dalili ko tambayar wajen wa nayi gado bayan gaki! Minene ya rage naki wanda banyi gado ba? Kinga dai naci gadon sunan ki ni kad'ai a cikin *DANGI*. Na kuma d'auko fuskar ki da hasken fatar ki, surutu kuma ai bama sai na baki amsa ba, ga kuma farin jini masha Allah, yauwa Hajiya nace wai dan Allah su maza basa gane banbancin budurwa da kuma macen aure ne?" Ta tambaya tana maida hankalin ta kacho kan a wajen Hajiyar dan da gaske so take taji amsa daga bakin ta, Fitowar Maryam tana gaishe da Hajiyan ne ya d'an tsaida ta, sai kuma ta maida idon ta kan Maryam d'in "Besty wai kin san ko d'azun da safe da muka rabu daku sai da mutumin nan na shekaran jiya ya k'ara tsareni bayan a gaban ku shekaran jiyan na shaida mishi cewar ni matar aure ce! Wallahi kawai Ina tafiya sai gashi nidai karfin haline kawai yasa dana ganshi ban zura da gudu ba to nasan koma na gudun aikin banza ne dan tsalle daya ne zai kamo ni, Sai fa da na duk'a har kasa na dunga had'ashi da Allah akan ya rufa min asiri ni matar aure ce amma d'an iskan mutumin nan wai fa cewa yayi ai dama mu mata in bama son alaqa da mutum haka muke cewa bayan yasan cewa ni ba matar aure bane kawai kora da hali nike mishi, Kin san me yasa ban d'ud'dura ma uwatai zagi a lokacin ba? Wallahi tsoro nikeji dan kamar an hana mutane bin hanyar ba kowa dagani sai shi kin san ko yasin ko yankani zaiyi yana iya gama fed'ewa wani bai biyo ba balle ya ceceni" Dariya kawai Maryam keyi dan sosai alamun Meenal ya nuna ta tsorata. "Dallah ke banzane wallahi Ina miki magana serious kina neman mai dani wata tababb'iya, nifa tsoro nike kar wani abunda zai shafi karatuna ya gifta kin san in da lokacin baya ne wallahi shida kafafun shi zai gudu" Amsa Maryam d'in ta bata da cewa.. "Ai na fad'a miki ki nemi dogayen hijabai masu rufewa har suna jan k'asa ki kuma had'a da niqab amma kinkiji ba dole su biki ba tunda yan matan ma ai suna sa irin hijjaban da kike sawa, amma dai shima d'in dan iskane tunda ai mun fad'a mishi ke matar aure ce ya kamata ya yarda, in ya k'ara tareki wallahi k'arar shi zamu kai" Juyawa tayi wajen Hajiya bayan ta gama hararar Maryam d'in dake magana tana dariya, dan tafa bata haushi da gaske, "Bari in debo abinci inzo ki bani amsa kinji Hajjaju, Allah kuwa Hajiya in kikayi ciwo lafiya kike k'arawa masifar duk sai mu nemeta mu rasa itama ciwo ya korata!" "Eh amma ai a lissafin da kika gama d'azun banji kinsa harda masifar ba, kuma Kitchen d'in nan inba wani sabon girkin zaki d'aura ba tofa ba lallai ki samu abunda kike so ba dan tuwo mukayi kin san shi yafi ta'amali da abunci mai nauyi, Jummai kuma kin san taje zaman jegon jikarta ne data haihu nasan da bazaki rasa abunda zakici a can wajen taba, Larai kuma na aiketa kasuwa" "Tuwo kuma" ta fad'a tana b'ata fuska jin an kira makiyin ta, " kai innalillahi wai shi mutumin nan da zarar yana gari dole ne cimar gidan nan ya canza ne? Haba dan Allah shi kenan dan shi yana son tuwo kuma sai ku wani dunga biye mishi, ni wallahi in nice matar shi dole ma ya sauke ma kanshi wannan tsurfan atoh kullum tuwo, kullum tuwo kamar a prison" "Wannan kuma ke kika jiyo in yunwan kikeji da gaske sai ki fita ki siyo anan wajen matar can mai bleaching dan suma dai girkin nasu babu laifi, inaga hakan zaifi miki sauk'i" Hajiya ta k'arasa fad'a tana kauda kai gefe, Yaraf Meenal ta dawo ta zauna a kujerar data tashi, "Wallahi yunwa nikeji!" Ta fad'i hakan tana b'ata fuska da matse cikin ta daya k'ara lafewa saboda bai samu abu mai nauyi ya d'auka ba. "Bari in fita sai in amso mana, me kike so?" Maryam ta tambaya a yayin da ta mik'e dan zuwa Restaurant d'in dake kofar gidan kamar yanda Hajiya ta basu shawara. "Ke ni komai ma ki amso min amma banda tuwo " "To" ta amsa mata dashi tasa kai da niyyar barin falon. "Ki shiga kitchen ki d'auko kulan da zaki zubo abincin a ciki mana koh!" Cewar Hajiya "Ki barshi kawai Hajiya zan amso a takeaway" Bayan fitar Maryam kacokam Hajiya ta mai da hankalin ta kan Meenal, "Dawo nan muyi magana" ta fad'a cike da bada umarni tana mata nuni da gefen kujerar da take zaune, Babu musu koh ta tashi ta koma wajen. "Hajiya ya jikin naki? Koda yake naga kin warware tunda mijin ki ya dawo" Murmushi Hajiya tayi, "jiki Alhamdulillah kam naji sauk'i sosai fa, shi kuma adawa kike da dawowan nashi ko meya faru? dan na dad'e da sanin sosai kike kishi dashi, tsakanina da Abdul Khareem ko mai shiga tsakani sai ya shirya gara ma kiyi ta kanki, ya kike kema da naki ciwon marar koda yake yanzun kam banji kina yawan kuka dashi ba! D alama ya dai tafi kenan?" "Bai tafi bafa amma dai ya rage sosai ba kamar da can baya ba" "To ya mai gidan naki dama wajen ita kishiyar naki duk dai kowa lafiya koh?" "Shi dai nasan Lafiya lau yake dan d'azun ma dana kira shi nace mishi zanzo duba ki banji wani alamun ciwo a tare dashi ba dan shima ya shigo garin jiya da dare" "To shi kuma haka akeyi? Kalar nashi rayuwar kenan da bazai zo ya duba kakar matar shiba? Ko baki fad'a mishi bani da lafiya ba ai yaci ace yazo ya dubani, Rabon shi da gidan nan fa tun ana saura kwana biyu auren ku!, Shin wai ma wani irin zama kukeyi ke da shi ne takwara? , ya kamata ace zuwa yanzun dai kema ki fara laulayin nan da mata keyi in sun d'auki ciki, amma shiru nikeji har yanzun ba labari ga k'annin ki ma da ake zaton cewa basu isa auren ba duk sun haihu, Kodai akwai wani abu a k'asane wanda bamu da masaniya akan shi?" Shiru Meenal tayi ba amsa, to jama'a fisabilillahi wani amsa zata bata, ah ah wallah ita kam ba'ajin mutuwar Sarki a bakin ta. "Shirun nan naki shike k'ara tabbatar min da cewa har yanzun dai baki amshi auren ba kenan?" Da sauri ta amsa Hajiya da cewa... "Ah ah Hajiya ni wallahi ba laifina bane, kuma da ban amshi auren ba ai bazanyi ta zama har yanzun a gidan ba shekara biyu fa da watanni yanzun.... " Katseta Hajiya tayi da cewa "Kenan laifin shine tunda kince ba naki ba?" Shiru tayi bata cema Hajiyar komai ba, "Wai shin yama tab'a neman ki a shimfid'a kuwa?" Innalillahi jama'a wannan wani irin magana ne, Wani irin kunya ne ya sauko daga sama ya lullubeta kai Hajiya miye kuma na zakule zakule fisabilillahi. "Ina magana dake kina wani duddukar min da kai uwa kwarton da aka ritsa a d'akin sabuwar amaryar da ango bai kwana da ita ba, Nace kun tab'a had'a shimfid'a tun bayan auren ko a'a? In kuma so kike in fito miki a mutum ta yanda zaki gane to! Ina magana ne akan kwanciyar aure tsakanin miji da mata nasan kin san wannan, shi mijin naki ya tab'a neman ki kun raya sunnar ma'aiki ko a'ah? Dan ya kamata in sani. Ina tambaya ne saboda insan ta inda zan kamo bakin zaren, kinga in ma bashi da lafiya ne mu sani dan mu d'auki mataki, koda yake Ina mara lafiya zai haife yara har Biyar, Shin ko kuma dai kece kikayi wani siddabarun dazai hanaki d'aukar cikin dan karki haihu tun yanzun?" Ta karashe tambayar tana tsatsare Meenal d'in da idanuwan ta. "Ni wallahi banyi komai dan kar inyi ciki ba, to bama sai an kwanta da miji bane akeyin cikin ni kuma ai har yanzun bamu tab'a kwana d'aki daya ba, haka ma fa kwanaki Uwar gida tazo tana tambayan wai in Ina shan wani abune dan Allah in dena karya bani matsala zuwa gaba, bayan ni bana shan komai, maganin ciwon marana mafa yanzun bana shan shi kuma tunda ciwon ya ragu" "Iyee.. " Hajiya ta furta da k'arfi cike da mamaki tana dafe k'irjinta da duka hannayen ta, Kafin ta koma salati da sallallami tana tafa hannuwa, "La'ilah ha illah lahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, oh ni Ameenatu yan ninaga abunda yafi zare tsayi, Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, " Hannun ta ta maida kan habarta ta tallafe cike da jimami, can kuma tace, "Anya kuwa jama'ah? Ah wallah babu lafiya a wannan harka, um umm aure shekara biyu da watan ni babu ci gaba, wani irin rashin rabone wannan a wanke maka karamar yarinya mai jini a jika a kaimaka amma ace miji ya zuba mata ido tsayin lokaci babu abunda ya shiga tsakani" Sai kuma ta koma kan Meenal. "Ke takwara kiji tsoron Allah ki fad'amin gaskiya, karki sa in fara tsine mishi alhalin bashi da alhaki! Ya'ya za'a daura miki aura miki shekara biyu da yan watanni kina zaune a gidan mijin nan kuma duk bayan lokaci yana zuwa kuyi rayuwa a gida d'aya harna tsayin kwanakin dazai d'auka kafin ya koma ace babu wani abunda ya gifta a tsakanin ku. Anya kuwa fad'amin gaskiya dai hala tsoro kikeji shi yasa in ya nemeki bakya yarda? " Ta tambaya tana tsatstsare ta da idanuwan ta, "Wallahi Allah kuwa Hajiya ni bai tab'a nema naba balle ink'i yarda dashi, abinda ko d'akin shima baya barifa Ina shiga, kuma kullum in yazo in zan dafa abinci harda shi nikeyi kuma harma d'akin shi nike gyara mishi amma ko Ina ciki bazai shiga ba har sai na fita" "Turk'ashi, lallai to indai haka ne akwai matsala kenan, dawa kuka tab'a yin irin hirar nan?" "Ba kowa! Ni ban tab'a fad'ama kowa ba" "Madallah dan ko yanzun ma shiru zakici gaba dayi da bakin ki, kin san dai kuma nace miki ki dage dayin azkar kullum safe da maraice koh?" "Kullum ina yi ai Hajiya" "To Allah ya k'ara tsarewa" Rufe bakin Hajiya yayi dai² da dawowar Maryam wacce suka shigo tareda Meelat sa kuma Musty da Sadeeq na take musu baya. Suna shigowa Hajiya ta mike zumbur, "Yau ni naga jaraba nifa likita na cewa yayi in dunga samun isashen hutu in raba kaina da hayaniya, amma shine fisabilillahi kuka kwaso jiki wato kuga zakarun da suka biyo kaji, su suna a gaba ku kuna take musu baya, to ga falon nan dan bazan zauna ku sakamin ciwon kai ba wallahi, dan yanzun in nace ku fitar min a falo sai kuce nayi rashin kirki na koreku, to ni dai so nike in gama da kowa lafiya atoh, Ke takwara in kingama cin abincin ki duba cikin freezer akwai kajin da mai gida ya kawo ki taimakeni ki cire biyu a ciki kimin dambun kaza kafin ki wuce" "Babu wani dambun da zan miki tafiya zamuyi tunda kin koremu" "Ah ah fa kiji tsoron kwanciyar ki a kabari kar kimin sharri Allah ya gani ba Koran ku nayi ba, in kuma kinfi son kullum inyi ta fama da ciwo ai sai in dawo in zauna, dama mai yayi saura ai tsufa tuni ya dad'e da buga min kofa wadanda basu kaini bama suka mutu balle kuma ni da dama kullum cikin istigfari nike Ina fatan cikawa da imani, ki dai taimaki tsufana kimin dambun nan dan jiya har mafarkin shi saida nayi," Mai da dubanta kan Meelat tayi, "Sannu Jamila tare kuke ashe? Hala wannan mai d'aga karfen ne ya tsareki a waje ya hanaki shigowa ki dubani tun d'azun? To kiji dai da kyau karki wani ce aure sai kin gama makaranta in dai da gaske yakeyi gara ki bashi dama ya tura ki shige d'akin ki kema hankalin ki ya kwanta, Allah dai ya rufama Yusufu Wase asiri shi uwar shi ta nema mishi mata da yike d'an mutunci ne haka ya amsheta hannu hurhud'u su kuma suna nan har yanzun sun kasa zab'ar wacce ta dace, To ku kuma ai mun gaisa daku d'azun koh?" Ta tambaya tana kallon su Sadeeq. Basu amsa mata ba sai ma wajen zama da suka nema, to Hajiya cefa waye zai fad'a musu halinta ai su sai dai suba wani labari, Maida budanta tayi kan Maryam, "Maryam wannan ledar da qawarki ta kawo ban dai san ko miye a ciki ba tunda bata gabatar min dashi ba ki shigar min dashi ciki" "To Hajiya ai har dambun ma sai in miki" Taba Hajiya amsa, Sadeeq ne ya katseta da cewa... "Muje kitchen din to in tayaki aikin" Hajiya bata k'ara kulasu ba tayi hayewar ta sama abinta. "Bestyn mu ashe ana ganin ku? Aida cewa zanyi ko Soja ya hanaki yawon ziyara ne?" Musty ya tambaya yana kallon Meenal. "Kai Babana taya zai hanani ziyara kawai dai kune da bakwa zama sosai yanzun shi yasa mukan dad'e bamu had'uba kuma ai Ina cema qawata ta gaishe ka" "Gaskiya ne kam dan tasha fad'amin," "Ba kullum kana zuwa tad'iba amma ko sau d'aya baka tab'a neman Indan nike ba, dukan kuma" Ta fad'i hakan tana b'ata rai alamun abunda sukayin ya k'ona mata rai, "Tofa kai Sadeeq kaji wani batu, to ke yanzun fisabilillahi Ina kika tab'a ganin yayye sun kama zarya zuwa gidan kanwar su balle kuma ni uba guda? To amma dai tunda kinyi korafi zamu gyara insha Allah zamu zo wata rana, Ganin Maryam ta d'auki abincin ta tayi hanyar kitchen shi kuma Sadeeq ya take mata bayane yasa ita ma ta mike ta da'auki wayarta da nata ledan takeaway d'in ta fice daga falon, tabar Meelat da Musty a falon. Kai tsaye wajen da ta faka motar ta ta wuce ta bu'de gidan gaba ta shiga kunna motar tayi sai ta d'an kwantar da kujeran ta kunna ac da radio din motan ta rage volume, ledan abincin ta bu'de ta faraci hankali kwance, tana cikin motar a zaune taji motsin alamar ana shirin fita da motar dake gefen ta wacce ta tabbatar da motar na AK ne dan kaf gidan shike iya cire manyan kud'ade wajen siyan manyan motoci kamar wanda bai san zafin naira ba, Ilai kuwa shi din ne a ciki kasancewar motar da take ciki gilasanta a d'age suke kuma suna da duhu sosai hakan yasa bai lura da ita ba har ya kunna motar masu gadin gate suka bud'e mishi ya fice. "Alhamdulillah" ta furta a bayyane, dan hakan ma wani dama ne ta yanda zataje ta d'auki turare dama sauran abubuwan da take buk'ata kafin ya dawo, Dan fa Allah ya sani bawai bata da kud'in da zata cire ta siya turaren bane, No tana dashi amma tsakani da Allah bazata iya cire makudan kud'i ta siya turaren da kud'inta ba duk da dai ba aikin wahala tayi ta samu kud'in ba hasali ma cuwa² irin na student kullum takeyi tana tara kud'ad'enta dan insha Allah in har zata siya handout ko wani abun da zata siya ko take buk'ata na fannin karatun ta tofa babu d'aga double take amsa a hannun iyayen ta, zata amsa a hannun Malam ta kuma amsa a hannun Baba Auta, Baba Adamu kai harda ma iyayen ta mata takan amsa a hannun su hakan kuma bazai sa tak'i amsa a hannun Sarki da wajen sauran yayyen ta ba dan haka maganar gaskiya bata talauci, amma tattala abinta takeyi dan so take ta kud'ance kafin ta gama makaranta ta samu aiki ta riga ta tara kud'in siyan ma Malam fili dan data fara aiki kud'in ginin zatayi tanadi, ita wallahi bata san haka ake samun kud'i da cuwa² in kana karatu ba sai da ta fara, to gadai kud'in a asusun banki amma fa ranar da sukaje kasuwa ta gwada tambayan kud'in turaren nan da sunan ta siya ma kanta wallahi da mai turaren ya kira kud'in juwa taji kamar yana neman ya d'auketa ya nana da k'asa, ashe tsadadden turarene take ma feshin ala tsine bisa rashin sani, to daga karshe dai dole turarukan cikin akwatin auren ta ta d'auko taci gaba da amfani dasu amma Sam ko kusa ko alama basu kama kafar waccen d'in ba, dan haka ta kuduri aniyar zata kwantar da kai indai AK zai cigaba da bata turaren dan lokacin data fad'ama Sarki sunan turaren wani daban mai sunan shi ya siyo mata amma kamshin su ba iri guda bane. Barin duk abinda takeyi a cikin motar tayi ta fito, sai da ta wanke hannun ta sannan ta waige ta tabbata babu wanda ke ankare da ita sannan ta k'arasa bakin kofar inda suke ajiye key d'in ta duba, amma ga mamakin ta babu makullin a wajen, har ta fara tunanin juyawa dan jikin ta yayi sanyi da alama dai yau ba sa'a sai kuma ta karasa ta tab'a kofar wai ko Allah zai sa ya manta bai kulle ba, Aiko tana murd'awa ta tura sai kofar ta bude, Taji dadi matuk'a dan harda tsallen murna tayi tana jin jinama kanta, Babu b'ata lokaci ta shige ciki sannan ta mai da kofar ta shige, Bata tsaya wani kalle kalle a falon ba gudun b'ata lokaci kawai ta amfa cikin bedroom din dan gara ta d'auki abunda zata d'auka ta fice kafin wani cikin su Musty ya shigo ya ganta a d'akin tunda dai shi ya fice, Kan mirror ta wuce kai tsaye kamar yanda tayi tsammani ga koh turaren nan har kwalba uku a ajiye, D'aukar d'aya daga ciki tayi ta cire shi a kwalin shi ta mishi feshin huce haushi na kewar shi da tayi tsayin watanni tana sauke ajiyar zuciya cike da shauki, "Kai gaskiya dai mutumin nan duk yanda akayi d'an Aljannah ne Allah kuwa, Allah dai ya k'ara arziki bari gobe tuwo zan kokarta in tuk'o in kawo mishi tukuicin turaren nan," Guda biyu ta d'auka tabar mishi guda d'aya can kuma kamar wacce akayi ma tuni sai ta shige cikin bathroom din shi, yau ma showel gel din ta d'auko harda wasu mayukan wanke kai dama duk wani abunda taga ya mata ta fito niki² kamar wacce tazo shopping, sai da ta zube kayan akan gadon shi da yau Allah yasa gadon a kimtse yake yaji gyara harya gaji ga d'akin sai kamshi yake zubawa, dibi dibi ta farayi tana neman leda sai dai kuma bata samu ledar ba duk binciken ta a d'akin, daga karshe dai ta yanke hukuncin cire gyalen data rufe jikinta dashi kasancewar yana da girma sai tayi rolling dashi ya rufe jikin nata da kyau, dan tana ganin hakan zaifi sauki in ya so in ta isa mota tasan bazata rasa ledar zubasu ba, ko bata samu bama ba laifi dan yanzun in tace ta barsu taje mota dubo leda tofa yana iya dawowa ya isketa. Dan haka zuciyar ta d'aya tunda dai tasan cewa daga ita sai itane a d'akin hankali kwance ta balle fin d'in data mak'ale gyalen dashi ta warware gyalen ta shimfide shi akan gadon ta fara zuba kayan akai tana gama wa ta daure shi da kyau gudun kar wani abu daga ciki ya fad'i. "Masha Allah" ta furta a yayin data gama kullewa ta juya da niyar d'auko hulan kanta daya fad'i a gefe a yayin da take warware gyalen, sai dai mai tana dagowa daga duken da tayi kamar almara kamar a mafarki idanuwan ta suka fad'a cikin na mutumin da bata san da wani suna zata kira shiba, Aljani zatace ko kuma fatalwa, domin dai ai mai d'akin ta tabbata ya fita a gidan da mota, kuma sanda ta shigo ta tabbatar cewa babu kowa a cikin d'akin dan haka bata tsaya wata ² ba ta fasa ihu had'ada tsalle tsalle tana kiran aljanni, "Waiyo Allah na shiga ukuna, dan Allah dan annabi aljani kayi hak'uri, Wallahi niba barauniya bace ba sata nazo yiba, wallahi niba barauniya bace, dan Allah kayi hak'uri, waiyo Allah Hajiya, Jamila Maryam Sadeeq Musty, dan Allah kuzo d'akin Mai Jama'a ku kawo min d'auki nayi gamo da mutanen boye, K'alu innalillahi wa innah ilaihir raju'un, Allahu la'ilah ilah huwa innahu min sulaimana wa innahu........ A uuzubillahi mina shaidanir rajeem." Sosai fa ta firgita dan Allah ya sani gaba daya ta riga ta sadakar cewa aljannun d'akin ne suka gaji da zuwa d'akin da takeyi tana sama da fad'i da kayan mai d'akin shine yasa suke shirin hukun tata, Tafa tsorata matuk'a dan sosai take karkarwa addu'a kam yau babu kalar wacce batayi ba, tayi rantsuwar cewa ita ba barauniya bace yafi cikin tirela marasa adadi, alqawari koh tayi ta k'ara cewa daga yau ko hanyar d'akin bazata k'ara kallo ba balle tazo da sunan d'aukar turare. Har kasa takai idanuwan ta a runtse tana fad'in dan Allah dan annabi aljani yayi hak'uri ya barta ta tafi, wallahi tayi alkawarin ta bari daga yau bata karawa, 🤣🤣🤣🤣😂 Abinda bata sani ba shine babu wani aljani mai d'akin da take zaton ya fice a gidan ne ya dawo domin dama fitar ba mai nisa bane ya fita da motar ne yaba wani yaron shi ita dan ya wanke mishi dan kwana kin nan da baya nan motar tayi kura, jiya kuma daya kira mechanic din shi yazo ya duba motocin gidan ya manta yace su wanke motocin gashi kuma yana da wajen zuwa anjima. Koda ya dawo gidan baiyi tunanin k'ara komawa wajen Hajiya ba, dan bai san dalilin da yasa a yan kwanakin nan ko tunowa yayi da yarinyar nan sautin zuciyar shi ke sauya bugu ba, Dalilin hakan ne ya yanke hukuncin ya shigo ciki ko wani abun yayi wanda zai dauke mishi hankali, koda ya shigo Sam bai lura da takalman taba, har ya shigo cikin d'akin ya nemi kujera ya zauna yana yan k'ana nan tunane tunanen da bazai iya cewa ga katamai man abinda yake tunanin ba, Tabbas yaji kamshin turare a d'akin ya k'aru ba kamar yanda ya fita yabar d'akin ba, amma ko kusa bauyi zaton wani ne ya shigo d'akin ba duba da cewa dama duk inda aka ajiye turare kamshi baya barin wajen ne yasa ya kauda tunanin daga karshe ma sai ya d'auki wayar shi ya shiga latse latse, Babu jimawa ya fara jin motsi, sanin shi kad'ai ne a cikin d'akin yasa ya so ya share sai dai kuma yawan motsin daya k'ara karfine yasa shi dago kai ya maida duban shi inda motsin yake fitowa, Da fari shima ya d'auka dai ko gizo ne yarinyar nan ta fara mishi, to inba ciwon hauka keson kama shiba taya zai dunga ganin ta a wurare daban daban, lallai in ya riketa zai buga mata warning in ma wani abun ta mishi gara ta karya dan shi ba wasa yakeyi da yara ba, Sai dai kuma abun mamaki koda ya kulle ido ya bud'e ita din dai yaci gaba da gani ta jido abubuwa daga cikin bayin ta fito kamar wacce ta dawo daga shopping, sai dai da alama itama bata san da wanzuwar shi a d'akin ba hakan nema yasa yaci gaba da zuba mata ido dan yaga iya inda ruwan nata zai tsaya da gudu, Kallon ta yake harzuwa sanda ta warware lullubin data rufe asirin jikin ta dashi wanda a wannan lokacin shima ji yayi kamar asirin dake cikin zuciyar shi take warware wa, yayi kokarin ganin ya raba kanshi da kallon abunda yasa ya haramta gareshi amma Ina bai samu wannan kwarin gwuiwar ba dan haka yaci gaba da k'are mata kallo har zuwa sanda ta duk'a da niyyar d'auko hulanta dake kasa, kasancewar a wannan lokacin ta fuskanci ainihin inda yike ga kuma dukawar da tayi hakan yaba wuyan rigar jikin ta damar zazzagowa hakan yasa daga inda yake zaune tsaf yake Ina hango lafiyayyun na shanun ta da suke nan kamar an d'auko an dasa mata su, I zuwa wannan lokacin kam ko kifta idanuwan shi daga kanta baya iyawa, hakan nema ya zama sanadin da tana d'agowa suka h'ada ido da ita, Duk wannan iface iface da sambatun da takeyi tsaf yake jinta, ga abun dariya amma halin da yake ciki yasa bazai iyayi ba dan wani irin kullewa cikin shi yayi irin kullewar da bazai iya yaushe yayi irin shi ba yana daga zaunen nan tsabar azaba bai san sanda ya nemi kifewa yana dafe cikin nashi ba, ga azabar da yakeji da kuma ihun yarinyar nan data bud'e murya tana mishi hauka, ganin Infa baya taka mata burki bane tana iya fashe mishi dodon kunne hakan yasa shi cike da dauriyar daya aro ma kanshi ya d'ago kanshi yana korar shaidan a cikin zuciyar shi. Wata irin tsawa ya daka mata wacce tasa ta komawa ta kankame jikin ta waje guda, "Ki rufemin baki a wajen nan, ki kuma zo ki fita min a d'aki kafin in k'araso wajen nan wallahi zane ki zanyi ciki da wajen ki, Kai wai ubanwa ma ya baki izinin shigowa d'akin nan ne iye?" Ya tambaya cike da hargagi, "Ba dake nike magana ba, uban waye yace ki shigomin d'akin iye, wato ashe rashin hankalin ki da nike gani ya wuce tunani na, zaki kama hanya ki shigo d'akin namiji kamar wani d'akin mijin ki dan iskanci har kin samu zarrar cike lullubi ba tareda tunanin cewa wani na iya shigowa ya sameki babu lullubin ba" Ita dai Allah ya sani ta samu sa'idah ne kawai a sanda ta tabbatar da cewar ashe dai mai d'akin ne ba aljanin da tayi tsammani ba, Jin yana ta b'abatu bata da niyyar tashi yasa shi Kara daka mata tsawa. "Wallahi ³ idan na mike sai kinji ba dadi tashi ki fitar min a d'aki mara wayau kawai, kuma Allah yasa in kara ganin kin fito gidan ki bada dogon hijabi da kyakyawan shiga ba, tunda shi mijin naki ya zama sakaran namiji shi yasa ya sanya miki ido kina shigar da kikaga dama kina fita, shima sakarai dabai kishin iyalin shi, to ni nan zan gyara mishi zama wallahi" Sif Sif Sif ta mike jiki ba kwari, dan tasan yanda ya rufe ido yana bala'in nan ba sauraren hakurin da zata bashi zaiyi ba, Harta kai bakin kofa tana shirin ficewa ya kara daka mata tsawa da cewa. "Shi wancan kullin kayan naki wani shegen ne kika barma zaki zo ki d'auka ki fitar min dashi daga d'aki ko sai nazo na had'a kanki da bango? " Baya baya ta dawo jiki duk ba lakka, tasan cewa AK jarababbene amma batayi zaton ya iya masifa haka ba, Haka dai ta dauki kayan harta kai tsakiyar falon taji ya kira sunan ta, Wanda hakan yasa dole ta tsaya cak ba tareda ta iya amsawa ba, "Wallahi in na k'ara ganin kafar ki a gidan nan nan kusa sai na zane ki, kuma zansa a samin ido akan ki ki tabbatar bakya zuwa ko Ina daga Makaranta sai gida, inba haka ba ni zan biyoki har gidan naki in gyara miki zama tunda shi mijin naki naga alamar dan kwali ya kamata ya koma d'aurawa ba hula ba" Sif Sif ta fice daga falon, Duk magan ganun daya gaya mata bataji zafin suba sai da ta fito, aiko a bakin kofar ta tsaya ta bare baki tana kuka, yana daga ciki kuma yana jinta dan shima fa kanshi da ace yana da hali ihun zaiyi ta kwararawa wallahi, Muguwar yarinya kawai, inda yasan tana d'akin ai koda wasa bazai shigo ba, ita bata san yana kauce mata bane saboda gudun take iyakoki........... *Babu editing atoh* inda kukaga kuskure ku wuce shi kawai kuje gaba *Ummiee Zaria*✍🏼✍🏼✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *Free book ga masu buk'ata daga farko zaku iya magana dani kai tsaye* 08061358462 *Rubutawa* *Ummiee Zaria*✍🏼 '''''Page 37. Alhamdulillah rayuwa fa yana ta tafiya, karatun su Meenal yayi nisa sosai domin yanzun haka dai shekara 1 kachal yayi saura su kammala wanda hakan ne zai basu daman amsa sunan likitoci kai tsaye ba tareda shamaki ba, a kuma wannan lokacin ne aka tsaida ranar auren Meelat da Musty duk da dai ita Meelat taso yayi hak'uri har sanda zata kammala karatun ta amma ya nuna mata gara ayi a wuce wajen kawai, Maryam dai kam duk yanda Sadeeq ya so akan ta yarda shima ayi nasu bikin kafin ta kammala, k'iyawa tayi a cewarta bazata iya had'a hidimar karatun ta dana aure ba, dan haka badan yaso ba haka nan dai ya hak'ura dan yasha fama sosai kafin ta amshi tayin soyayyar shi, A gefen uban gayyar shiko dai D'an mai karfi har yanzun dai babu wata tsayayya, domin ta gefen shi tsakanin shi da mata babu wani abunda ya canza, dan harta da su Meelat da suke matsayin yan matan manyan abokan shi ba wani sake musu fuska yake yiba, Kwata kwatama yanzun halayyar shi k'ara juyewa yayi ya zamana ko yana gari ma ba kasafai zaka ganshi a majalisar shi ba, matan da ke zuwa wajen kuma domin shi tuni ya warware musu zaren rashin mutuncin shi tass ya musu hauka akan duk ma yarinyar data k'ara kallon su da suffa ta burgewa harta rayama zuciyarta cewa tana son shi to wallahi ta kuka da kanta, Hafsa ko bata shafama kanta lafiya ba har sai sai wata rana data cika mishi ciki, a lokacin yayi tafiya kusan na wata uku baya gari sabon shine muddin yayi tafiya zuwa wata k'asar ko ka kirashi a waya ba lallai ya d'auka ba zaifi sauki ma in ace sako ka ajiye mishi ba kirar waya ba, to a wannan tafiyar nashi haka yarinyar nan ta taso mishi rayuwa a gaba domin a kallah kullum sai ta mishi kira sama da hamsin amma tsabar wulakanci mutumin nan ko sau d'aya bai amsa kiran ba, kuma bai kirata yaji dalilin kiran ba. Ganin bazai dauki kiran bane yasa taje gidan Hajiya ta tasa ta a gaba da kuka aka cewa ta rufa mata asiri tasa baki AK ya fito suyi aure domin a lokacin itama a gefen ta sosai abubuwa suka kwab'e mata, Domin dai d'aya daga cikin tsoffin samarin da suka dad'e suna mata hidimane, wanda shi dai yaji ya gani yana sonta kuma auren ta yake son yi, dan dai itama d'in bata rasa komai ba tana da kyanta ga kuma diri irin na manyan mata data mallaka, toshi dai ganin shekara da shekaru yana mata hidima amma kullum yayi mata maganar aure sai ta zame bayan tun tana karatu yake naci a kanta harta gama tuni tana aikin ta kuma yayi bincike ya gano cewar shegen yaron da tanace ma so akan shi kwata kwata babu mata a gaban shi balle kuma ita da kusan tare suka taso, A yanda yake son ta inda ace shi wanda take so d'in yana sonta tofa babu shakka zai hak'urane ya barta ta aure shi, amma binciken da yayi akan yaron ya tabbatar yaron bazai aure taba, tunda ko shi ba auren ta zaiyi ba ai gara shi yayi duk yanda zaiyi ya aureta yakai d'aki ya adana dan sonta yake da gasken gaske. Bai tsaya jiran jin ta bakinta ba koh ya tura iyayen shi wajen nata iyayen kafin ta an kara har sun kalmashe bakin zaren, Tayi hauka sosai cewar tana da wanda take so, jin wannan kalmar a bakin ta ba bak'on abu bane domin dai kaf ahalin ta sun san yanda take hauka akan AK dan inhar kana son kayi shiri da Hafsat tofa sai ka nuna kana son AK anan ne zakaci moriyarta, Dama suka bata akan cewar tunda bata son Anas d'in da ya fito neman auren ta tofa sun bata wata uku ta fad'a ma AK d'in ya fito, in kuma hakan bai faruba tofa ta sani su kuma nan da wata Biyar suka yanke ranar bikin ta, Su kuma sunyi hakan ne dan su bata dama kartaga kamar sunyi son kai sun aurar da ita ga wanda bashi take so ba, domin dai sun san tunda wad'ancan shekarun suka shud'e AK bai so tan dahar zai nemi auren ta ba, tofa wata uku bazai canza komai ba, Dalilin hakan duk tabi ta tashi hankalin ta ta tayar ma wadanda ke tareda ita da nasu hankalin, Domin dai tayi iya bakin kokarinta akan yanda zatayi magana dashi ta fad'a mishi halin da take ciki amma hakan ya gagara kira kan kira har bata san sau adadin kiran data mishi ba amma yaki amsa wayar ta, Tabi dukkanin abokan shi dan su h'adasu amma shi kuma mugun dukan su ya musu warning akan koda wasa karsu yarda su kira shi a sanda suke tare da ita, Tofa ganin bata dace a ta fannin su bane hakan yasa ta yanke hukuncin tunkarar Hajiya tasan AK yana ganin girman ta sosai kila in hajiya tasa baki zai yarda ya aureta, Ita ta yarda zata zauna dashi duk da baya son ta tasan soyayyar da take mishi zai wadace su. Taje gaban Hajiya tayi kuka tayi roko wanda har saida Hajiya ta tausaya mata, ta kuma bata shawara akan taje tayi ta addu'a in auren ta da AK alkhairi ne allah ya tabbatar, Taji sanyi sosai a yanda hajiya ta zaunar da ita ta mata nasiha ta kuma ce mata zatayi magana da AK din, Bata bar gidan ba sai da taba masu gadin gidan sallahun cewa in ya dawo su kirata, ta basu number d'inta sannan ta musu alkhairi kamar yanda ta saba duk zuwan da zatayi gida. Sai dai kuma dawowan na AK bai zamo mata alkhairi ba domin a sanda labarin dawowar nashi ya riske ta batayi k'asa a gwuiwa ba ta d'auko mota ta taho, Koda ta iso ta iske shi a cikin jama'ar shi na majalisa suna ta hirar su ta yau da kullum, Zumud'i da murnar dawowar shi yasa kashi hamsin cikin d'ari na tashin hankalin da take ciki ya kwaranye, domin AK fa namijin gaskene burin ko wacce mace, Tunda ta shigo unguwar ya na hango motar ta ya b'ata fuska, kafin ta k'araso wajen kuwa bayan tayi parking a gefe ya tashi tsam a majalisar ya wuce cikin fadar shi, taji dad'in hakan sosai domin koba komai zata so dama su tattauna abunda ya kawota wajen shin a sirrance, bata bi ta kan yan wajen ba ta take mishi baya. "Kiran me kikayi ta min ne da kullum sai kin kirani sama da sau ashirin bayan kin san na tsani yawan kira? " Ya tambaya ba tareda ya nemi guri ya zauna ba, "Ka zauna please Abdul!" Ta fad'a cike da marairaice wa a tsammanin ta ko hakan zaisa ya taimaka ya saurare ta. Kujerar shi yaje ya zauna kamar yanda ta buk'ata, "Ina jinki! Meke faruwa? " Bata iya zama akan kujera kamar yanda ya zauna ba sai ma k'arasawa kusa dashi da tayi ta zauna a kasa tana fuskantar shi wato dai zama irin na d'alibi a gaban Malami, Kaf halin da take ciki na auren ta da ake shiryawa da damar da iyayen ta suka bata akan shi ta zayyano mishi, Daga karshe ta k'are da rokon cewa ya rufa mata asiri ya aureta ita wallahi ko baya sonta yaji ta gani zata iya zama dashi a hakan yardar shi kawai take nema, "AK ka dubi girman Allah da kaunar da nike maka ka taimaka ka aure ni, wallahi Ina son ka son da na tabbatar ma kaina cewar idan na rasaka tabbas zan iya rasa lafiya ta" Duk kalaman bakin ta saida tayi kokarin amfani dasu dan ganin ta shawo kan AK amma a banza, daga karshe dai tun sunayin zancen a sirri sai da abu ya fito fili domin kuka sosai tasa mishi tana rokon shi Allah annabi ya ji tausayin ta ya aureta amma gayen nan saboda bak'ar zuciya ko a jikin shi, yadai fad'a mata cewar aishi dama tuntuni yace mata taba samarin ta dama tayi auren ta itace tak'i domin shi dai dama bai tab'a kallon ta ta fuskar soba balle akai batun aure, A takaice dai abubuwa gaba d'aya basuyi dad'i ba dan fitowa tayi ta dunga rokon jama'ar dake majalisan akan susa baki ya yarda ya aureta, shi kuma hakan ne ya tunzura shi harda cire belt yana neman zane mata jiki, dakyar da ban baki aka cusata a mota wani daga cikin su yaja motar suka bar unguwar da ita, tun daga ranar kuma yasa kafar cin uban duk yan matan dake zuwa majalisar indai yana nan, hakan ne kuma yasa ya kara maida kanshi busy sosai domin duk ragamar kasuwancin su a hannun shi yake hakan kuma bai hana shi karatun da yakeyi wanda kullum Hajiya take mita akai ba, a cewarta kwalayen da yake tarawa indai ba tikitin ketare sirad'i bane tofa ya rufama kanshi asiri ya bar karatun nan haka dan in karatu fa yayi yawa yana tab'a kwalwar mutu, shidai ko tana surutun ta baya kulata dan yanzun ya maida azumi kamar sallar farillah, hajiya tasha tsare shi da tambayar cewa ko kisan kai yayi ne bata da labari akan yawan azumin da yakeyi, wanda shi kuma yana azumin ne saboda ya rage ma kanshi bala'in da yake jin yana kara kusanto shi a kullum, daga karshe dai har sai da aka kai matakin da ko Zaria bai son zuwa dan daya rufe idanuwa wasu hotuna ke haska kansu a cikin idon nashi, memory d'in da kullum yake fatan Allah ya goge mishi su a cikin zuciyar shi dan zaman su a rayuwar shi gani yake bala'ine kawai dan ko kusa bazai kusan ta hakan da alkhairi ba. **** Kasancewar aski in yazo gaban goshi dama akace yafi zafi hakan yasa kwata² yanzun Meenal bata da lokacin kanta balle na zaman gida dan hatta da baccin ta a yanzun ya zama ragagge ko islamiya ma tuni ta sallama shi duk da yanda take son karatun nata kuwa, sai dai takanyi kokari once in a while taje wajen Malam suna hira suna d'an duba wasu littafan dan wani zubin hatta da weakened bata samun lokacin kanta sai na karatun data sa gaba kawai domin kowa dai yasan yanayin karatun likita ba karatu ne da zakace zakayi mishi sakwa² ba, Tuni kuma batun rashin haihuwarta yayi tambari a dangi tun wasu nayi a bayan fage har aka kai matakin da akeyin shi kai tsaye sai dai a kullum cewa suke maganin hana haihuwa takesha tunda gashi yanzun Billy nada yara uku duka maza Raheenat ma ukun gareta Sa'adatu ce dai mai biyu itama dan tayi b'ari ne,dan harta da wad'anda sukayi aure a bayan su tuni sun haife. Malam yasan cewa Meenal bazata wani sha wani abu dan karta haihu ba domin kowa yasan yanda take da son yara balle kuma yanzun da su Raheenat suka hayayyafa dan haka shi yafi tunanin ko dai lalurar da tayi ta fama dashi a lokacin da take gidane na ciwon mara ya janyo matsalar rashin haihuwar dan haka shi da kanshi yake had'a mata magunguna yana kai mata, sai dai ko kusa bata tab'a amfani dasu ba, hatta Mommy Hauwa tasha rubuta mata magunguna da sunan ta amsa ta gwada sai dai ita ta kasa fayyace ma Mommy gaskiyar abunda ke faruwa tun sanda Hajiya ta kwabeta akan cewar karta fad'ama kowa. Ita dai Allah ya sani duk surutan da mutane keyi bai tab'a damunta ba, domin ta riga ta tabbatar ma kanta da cewa son ta ne kawai Sarki bayayi, kamar yanda itama har yanzun bata tab'ajin wani abu ya tab'a zuciyarta akan shiba, ita da take ta karatun ta ina ita ina d'aurama kanta damuwa, can da yawar shi, Ai koda bai fad'a mata baki da baki ba ta sani baya sonta zama dai yake da ita na dole kawai dan bashi da yanda zaiyi shi yasa tsayin shekarun nan bai tab'a d'aga kai ya kalleta a matsayin mace ba, duk da sau tari takan so ta kafa ayan tambaya akan wani kalma da Maman Boy ta tab'a fad'a mata wani zuwa Zaria da tayi bikin d'aya daga cikin kannin Sarki inda ta shigo har gidan ta jefeta da kalmar "yar gadin gida a haka zakiyi ta zama har ki gaji ki fad'ama iyayen ki su rabaki da mijina, domin dai nasan yanzun in yarinta ne yasa kike zaune da mijin da har yau bai iya had'a shimfid'a dake ba, nasan akwai lokacin dake da kanki zaki buk'aci kasancewa da d'a namiji in kuma baki samu a gida ba kina iya fita waje ki nema, ni kuma bazan zuba ido a kawo min shege cikin zuria taba" Wannan kalaman na Teemah sun dad'e suna buga karar rawa a cikin kan Meenal, To kenan hakan yana nufin matar shi tasan cewa Sarki bai tab'a neman taba? Tsabar yarinta yasa Meenal ta watsar da zancen a gefe taci gaba da harkokin ta kosu Meelat bata ba labari ba dan tasan idan ta fad'a musu suna iya cewa ita taje gareshi abunda ita kuma bazata tab'ayi ba kenan. Teemah fa da gaske ta shirya tsaf ma wasa tsakanin ta da ahalin Sarki domin dai yanzun kam tuni ta canza tsarin ta dan komai akeyi a garin haka zata baro aikin ta ta biyo jirgi daga Lagos tazo ayi da ita bayan ta dank'aro uwar tsarabar da zata taho dashi dan ta siye dangin mijin nata dashi, Kwarai kuwa taga alfanun wannan sabon salon nata domin dai yanzun sunan dai basa gari d'ayane kawai amma komai da yake wakana a cikin gidan Meenal d'in yan rahoton ta na kai mata labari, Tayi amfani da arzikin da take samu a jikin Sarki wajen siye yan uwan shi da suke yan uba dama matan Baban nashi wanda ada tasan basa kaunar ta ita da mijin ta, a yanzun kam da zarar ta iso haka zakaga ana rawar jiki akan ta da yaron ta, dan har yanzun Allah bai k'ara bata wani haihuwan ba duk da har gobe neman haihuwar take ido rufe dan a cewarta kason namiji 1 bazai rik'eta ba, Kaf gidan kowa na nan² da itama amma dai tsakanin ta da yan uwan Sarki wad'anda suke ciki d'aya har yanzun dai sama sama ne, Domin dai ance idan maye ya manta uwar d'a baici ta mance ba, haka ma ita uwar mijin nasu,har yanzun bata wani sake mata sai dai akwai sassauci kwarai a tsakanin su. zamu iya cewa dai yanzun da sauki sosai a bisa dah amma bawai irin so close suke ba. Tofa a wani zuwa bikin da sukayi ne wata rana duk da kamar yanda Sarki ya shard'anta ba gidan Meenal take sauka ba, domin dai yanzun a cikin gidan su tuni ya mata tamfatsetsen gini dai² da yanda take buk'ata in tazo garin can take tarewa ita da yan koranta, wanda ta gama barbadewa da asiri suka lashe suke binta kamar wasu karnukan farautan ta. Da sassafe ta buga sammakon zuwa gidan Meenal, saboda dai yau so take taje ta gane ma idanuwan ta abubuwan da take buk'atar Karin tabbaci a kansu, dan haka ko wanka bata tsaya yiba, dan asubahin fari mugun mafarkin da tayi cewar wai Sarki ya tare da Meenal har tayi ciki ta haifo yara maza hud'u a haihuwar farko ne yasa badan ta kai karshen baccin nata ba dole ta farka a mugun gigice tana sambatun fad'in karya ne wallahi. "Ina karya ne wallahi sai dai bayan bana numfashi shine har wata macen zata had'a gado da mijina ba yanzun da nike raye ba" Wannan mugun mafarkin da tayi shine dalilin da yasa koda ta tashi bata tuna da wani batun sallah ba faka faka ta fad'a bayi ta d'aurayo fuska ko brush bata samu damar yiba illah kurkure bakin da tayi kawai ta fito daga bayin ta zura hijjabin data gani a d'akin wanda batama da tabbacin ko mallakin waye ta fice daga d'akin. Meenal dake zaune akan daddumar data idar da sallah ne har zuwa lokacin, domin koda ta kammala azkar d'inta na safe littafan ta ta d'auko tana dubawa dan aranar tana da test karfe 11 na safe kokari take ta duba abunda take ganin zai fito musu kafin ta fara aikin gidan dan in har Sarki na gari fa to shi kenan ita kuma bata da hutu, dan wulakanci wani lokacin ma ko tana makaranta haka zai kirata ya bata sallahun cewa inta koma gida ta dafa mishi abu kaza kamar wata yar aikin shi, domin yauma dai tun daren jiya ya shigo d'akin kawai dan ya bata sallahun abunda zata had'a mishi na breakfast harta fara bacci ya tashe ta, tayi zaton wani abun ne amma wai d'an bawan Allan nan bayan ta tashi babu lallami ba komai sai ma cewa da yayi, "Ina buk'atar inkin tashi da safe gobe ki had'amin kunun gyad'a da alale,in ma zaki dafa wani abun daban bayan wannan ba laifi dan Ina son ki kammala kafin ki fita dan Ina da bak'in da zasu zo kuma anan zasu karya" Galala tayi da baki da idanuwa tana kallon shi, jin bata amsa shi bane yasa shi cewa, "Kinji abunda nace kuwa?" Ita kuma ta bashi amsa da cewa "Amma gobe fa Ina da test da safe, ga kuma aikin gidan da zanyi kafin in fita, fisabilillahi yaushe har zan gama har inje makaranta?, nidai gaskiya sai dai kayi magana ayi maka a gida a kawo maka ko kuma tunda itama tazo sai ta had'a maka suje can suci" Ta k'arashe fadar hakan tana tura baki da kauda fuskarta gefe, Lallai ne ma wallahi mutumin nan yama maida ita wata yar aiki, gaba d'aya fa baya tunawa da ita a gidan sai in yana buk'atar wani abu ne zai d'aga waya ya kirata da wannan k'aton muryar nashi haka zakuji yace "ki dafa min abu kaza! Ko ki gyara min d'aki ko ki shirya kibi su wacce waje kaza anayin abu kaza" Kai itafa wallahi ta gaji! tagaji!! Ta gaji!!! Wani irin rayuwa ne wai wannan shi kenan ita haka zataci gaba da zama a gidan da bata da wani amfani sai na gyaran gida da girki magana mai dad'i bazai had'ata da mijiba sai dai umarni kawai da kullum yake bata kai tsaye ko ya d'auka itama matar shi kamar yanda yake ba yaran shi umarni haka ya kamata ya mata ? In fa matar shi tazo garin nan tunda aka gama ginin daya mata a gidan su to insha Allah ita data sanya shi a cikin idon ta har sai cingum d'in nashi ta koma, Fisabilillahi koda ba kwana yakeyi a d'akin taba ai ya dace ace in tazo sai ya raba kwanakin saboda gudun magana, dan Wallahi ita batama san baya kwana a gidan ba har sai da matar k'anin shi da suke uba d'aya kwanaki ta wanko kafafuwan ta tazo har gidan take tambayan ta wai me yasa take barin Sarki yake tarewa a wajen Maman Boy duk in tazo, Tun daga nan ta gane cewa lallai kenan kallon mara matsayi a wajen miji kawai suke mata, saboda gudun jan maganar hakan yasa ta amsa ma Rayhan d'in data kawo mata zancen da cewa.. "Ita ta tsara hakan tunda ita Teemah ba sosai take zuwa ba shima kuma ba duk k'arshen wata yake zuwa mata Lagos ba koda yaushe yana zaria, shi yasa in tazo ita kuma saita bar mata mijin harta koma" Ta dai bata amsar hakan ne kawai duk da tasan cewa itama Rayhan d'in tasan bako yaushe Sarkin ke zuwa Zarian ba dan wani lokacin ma yakan share wata 1 baizo ba.......... Sorry😰😰 nasan duK kunyi bacci yanzun kam. Nadai cika alkawari Ummiee Zaria ✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ ~{{My Family}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *Ummiee Zaria*✍🏼 """""Page 38..... Bam! Bam!! Bam!!!.... ........ Haka Teemah taci gaba da dukan kofar falon da iya k'arfin ta, dan ta tabbatar dai koda ace ita yar gadin gidan bata tashi bacci ba shi mai gidan tana da tabbacin cewa yana cikin gidan dan an idar da sallah tuni. Sosai zuciyar ta ke azazzalarta, harma take jin da ace akwai wani siddabarun da zatayi wanda zaisa ta b'ace b'at ta ganta a cikin gidan da tuni bata b'ata lokacin ta wajen tsayawa jiran azo a bud'e mata kofa ba, sosai fa take jin tashin hankali mai had'e da tsoro, ba tsoron komai ba sai tsoron kardai ace da gaske Sarki kwanan da yayi a gidan jiyane ya samu damar kwanciya da yarinyar nan, domin sai yanzun ta tuna cewa kwana biyu bata lek'a wajen OBA domin a sabunta aikin jikin Sarki ba, hakan kuma yana nufin aikinta zai iya lalacewa!, Kenan in aikinta ya lalace mafarkin da tayi ne zai zama gaskiya? A gefen Meenal ko gaba d'ayan hankalin ta kacokan ta maida kan karatun ta da take Allah ² ta kammala dan so take ta shiga kitchen ta had'ama Sarki kunun gyad'a da alalen da yayi requesting jiya, dan tayi alwashin iyashi d'in zatayi dan bazata maida kanta tamkar wata jaka ba wallahi, Domin ba yau ya fara mata haka ba kullum in zaiyi bak'i shi da kanshi zai lissafa mata abunda yake buk'atar ta tanadar ma bak'in na abinci ba kuma kala d'aya ko biyu a'ah so yake yaga an cika mishi dinning table tsaf da kalolin abinci saboda ya burge bak'in nashi, wani lokacin in aikin ya mata yawa dole sai ta nemo masu tayata, amma insha Allah in ta gama abincin nan haka zai kwasa yayi sashen shi dashi babu wani zancen sannu bare nagode , kai hatta bak'in nashi sai dai ta hange su ta window domin bai tab'a kiranta da sunan wai ta fito su gaisa da abokan shiba, sai sun wuce zai zo ya bata umarnin zuwa ta kwaso kayan ta, dan haka wallahi yau zai sha mamaki badai harda wani cewa in ma zata k'ara dafa wani abin babu laifi ba, Irin ga kuku mai mishi girki, ita tayi mamakin ma abunda ya hana shi zuwa can wajen matar shi ya kwana jiya. Kamar wasa ta fara jin dukan kofar tun anayi a hankali har abun ya wuce misali dan sosai karar ta cika gidan, D'aga kai tayi ta maida kallon ta zuwa kan agogon dake cikin d'akin ga mamakin ta karfe 6 ne da kusan rabi, "Lafiya kuwa? Waye da sassafen nan haka yake bugun kofa?" Ganin dai kota zauna babu mai bata amsa sannan kuma yanda ake bugun ya tabbatar mata da cewa ba lafiya ba! Domin lafiyar Allah dai ai mutum bazaiyo asubanci yazo gidan mutane ba, Kife littafin tayi ta zura hijjabin ta data ajiye a gefe ta fice daga d'akin, tun kafin ta isa cikin falon ta fara amsawa mai bugun kofar da cewa "wanene Ina zuwa" duk da ta tabbatar koma waye yaji abunda ta fad'a amma abun haushi hakan bai sa an dena dukan kofar ba, Sai dai isowarta cikin falon yayi dai² da shigowar da Sarki yayi falon shima, "Waye da sassafen nan haka yake dukan kofa?" Ya tambaya yana kallon ta, "Nima ban sani ba nayi magana ba'a amsa min ba" Tana gama fad'in hakan ta juya da niyyar komawa ciki, "Ya zaki koma kuma baki duba ko waye ba" Ba tareda ta tsaya daga tafiyar da take ba ta bashi amsa da cewa.. "Da dai ace baka gidan ne, amma dai yanzun kam tunda ka fito kuma ai ka fanshe ni" Shigewar ta tayi bata tsaya jiran jin abunda zai biyo baya ba, sai dai mai makon ta koma d'akin ta lafewa tayi a corridor d'in dan tasan kota koma ciki hankalin ta ba kwanciya zaiyi ba har sai taji waye kuma me ake nema da asuban nan. Yarinyar nan fa haka take kamar wata mai aljannu wani lokaci ka ganta shiru² koda an mata abunda ya kamata ta tanka bazata tanka ba, amma abunda bai kamata ta tanka din ba wani lokacin anan tafi zakalkalewa, ya ayyana hakan a ranshi yana girgiza kai idanuwan shi akan hanyar da tabi ta koma inda ta fito. Ganin cewa dai da gaske juyawa tayi ta koma cikin ta barshi da bud'e kofar waton in ma menene shi ya same shi, hakan yasa shi k'arasawa bakin kofar ya bud'e, Kamar wacce aka koro haka Teemah ta fad'o cikin falon idanuwan ta akan shi bata ko kyaftawa. "Lafiya? meya faru? Maiya sameki? Wani ne babu lafiya? " Haka shima yaci gaba da jero mata tambayoyi domin Sam baiyi zaton ganin ta a gidan a dai² wannan lokacin ba. Duk tambayoyin da yake mata batajin cewa akwai d'aya daga cikin su wanda zata iya amsa mishi domin dai ita basune a gaban ta ba, Dan haka mai makon ta bashi amsa sai ta fara zagaye shi tana k'are mishi kallo daga sama zuwa k'asa kamar wata mai neman inda aka gutsura a jikin shi, Sai da ta zama zagaye shi tas sannan taja burki a gaban shi.. "Kana lafiya, babu abunda ya sameka? A Ina ka kwana?" Haka ta jero tambayoyin. "Ina lafiya babu abunda ya sameni kuma a gidan nan na kwana, meya faru ke kuma kika fito da asuban nan?" Bata bashi amsar tambayar ba sai ma cewa da tayi, "Muje d'akin ka please 🙏" Shima baiyi musu ba illah ma juyawa da yayi ita kuma ta take mishi baya, Koda suka isa, d'akin ta fara k'arema kallo domin so take ta tabbatar da cewa shi kad'aine ya kwana a d'akin ko kuma shida yarinyar can ne suka kwana tare kamar yanda mafarkin ta ya nuna mata? , Sai dai babu wani alama domin dai d'akin a gyare yake tsaf harta da gadon kanshi bazakace wani yayi bacci ma a saman shiba, domin dai in baku manta ba dama Sarki gwanine indai wajen kula da muhalli ne balle kuma d'akin shi, Ganin babu wani alama anan d'in yasa kai tsaye ta nufi bayin shi nan d'in ma dai ba kowa. "Wai me kike nema ne? Eyeh" Bata bashi amsa ba sai ma tambayar data jefa mishi itama, "A ina yarinyar can ta kwana?" "Wani irin tambaya ne wannan! A Ina zata kwana kuwa inba a cikin d'akin taba!" Ya amsa mata dashi. "Ok kenan ba'anan kuka kwana tare ba?" "Wai dama ni nace miki mun tab'a kwana d'aki daya ne da kikemin wad'an nan tambayoyin" Juyawa tayi sai da takai bakin kofar d'akin sannan ta juyo ganin shi a tsaye cak, "Muje ka nuna min d'akin ta! " "Me zakiyi mata?" "Babu wani abunda zan mata dan Allah ka rakani please 🙏" Tinkis tinkis haka ya mata jagora kamar wani sakarai har zuwa bedroom d'in Meenal. Ita koh Meenal a sanda ta lab'e tana jiran ganin mai shigowa, Ganin Teemah ne yasa taja dogon tsaki. "Mtws Allah ya isa na wallahi , Kawai mutum yana cikin karatun shi kawai ansa yakatse ya taso, jarababbiyar mata kawai, wato saboda mijinta baije ya kwana da ita ba daren jiya shine ita ta bugo asubanci ta biyoshi ya sosa mata inda yake mata k'aik'ayi, an daiji kunya wallahi an girma ba'a san an girma ba" Koda ta koma ciki bata iya komawa kan karatun ba gyaran gado ta fara dan so take ta fara kimtsa d'akin kafin ta wuce kitchen, Kamar wacce aka tsikara haka ta tsaya cak daga abunda takeyi, wani tunani ne ya fad'o mata a rai, Waima me zai hana ta koma kan gadon nan ta nad'e tayi k'aryar ciwo tunda ga matar shi ta shigo, tasan dai komai rashin imanin shi bazaice ta tashi daga ciwon taje kitchen ta dafa mishi abincin da bak'in zasu ciba ga kuma matar shi da tasan in har fa ta dafa itama sai taci, K'ara mai cike da ihun jin dad'i ta saki "what a wonderful idea,woow ni Aminatu wallahi shi kenan na huta ko gyaran gidan ma bazanyi ba, ai dama na dad'e banyi baccin safe ba, in ya so inya fita sai in shirya nima in wuce makaranta dan nasan shima ba zama a gidan zaiyi ba, eh wallahi hakan ma zanyi, ai in yasan wata bai san wata ba" Sosai taji dad'in shawarar da zuciyarta ta bata, hakan nema yasa Tana gama yanke hukunci shaf² ta fada bayi tayi fitsari, rigar da tayi bacci jiya dama shine a jikin ta dan haka bata tsaya b'ata lokaci ba ta kakkab'e gadon ta haye bayan ta k'ara gudun AC taja bargo ta rufe jikinta har zuwa saman kanta. Babu Sallama Nocking ko jiran iso Teemah ta bud'e kofar d'akin Meenal din ta shige Sarki na biye da ita, Turus taja ta tsaya kamar wacce aka danna ma paused ⏸, jikin ta na makyarkyata, shi kenan ta faru ta k'are ashe bonono takeyi aikin ta ya tashi tuni, Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, wani kalar masifa ne wannan ya sameta da asubahin nan, yanzun nan fisabilillahi da gaske kwanciya da yarinyar nan Sarki yayi, Yuuuuw haka juya ya kwashe ta yana shirin makata da k'asa, Da azama irin nasu na Sojoji Sarki yayi amfani wajen tarota daga fad'uwar da take shirin yi zuwa jikin shi, "Ke miye haka meya same ki? Wai me yake faruwa ne? " Da kyar ta iya bude idon ta ta d'aura akan fuskan shi kafin tayi amfani da d'an sauran k'arfin daya rage mata ta finciko jikinta daga rik'on daya mata, Zallar bakin ciki, kishi, bacin rai sune suka cika idonta ta yanda har saida wani irin zazzafar hawaye ya fara biyo kwarmin idon nata yana gangarowa zuwa kan kumatun ta, bata damu da tsaida kukan ko kuma share hawayen ba A zafafe a kuma tsawace ta d'aga muryar ta dake kakkarye wa cikin muryar kuka dan batajin yau dai zata iya tankwasa kanta, to me yayi saura? Abunda take ta kokarin ganin ta hana kasantuwar shi tsayin shekaru yau dare d'aya Sarki ya b'ata komai, yau kawai tayi sakacin da aikin ta na shekaru ya lalace, Sarki fa Mijinta shine yau ya kwanta da wata kwanciya irin na aure, ya tab'a yarinyar nan ya bud'e tsakanin cinyarta ya ratsa ya shiga itama yau yasanta a matsayin d'iya mace, shi kenan yanzun ta zama cikakkiyar matar shi, "Bazai yuwuba! Bazai yuwuba!! Bazai yuwuba!!!" Juyawa tayi ta cakumo wuyar rigar jallabiyar dake jikin shi tana jijjigawa, "Me kayi ma yarinyar nan Sarki? Itama kwanciyar kayi da ita kamar yanda kake kwanciya dani? Me yasa zaka kwanta da ita Sarki? Mena rageka dashi ? Gindine ko nonuwa? Wani kalar kulawa ne ya rage wanda bana maka? Sarki wani irin cine baka mun?, Ashe kai k'aton munafukine ban sani ba? Saboda dare d'aya da ban baka ba shine ka taho wajen yarinyar nan? Bayan daka nema sai da na shaida maka cewa bana cikin tsarki, naga dai a banza ma kakan jurema rashina na tsayin watanni balle kuma na yan kwanaki, Wallahi ka cuceni ba kuma zan tab'a yafe muku ba, daga kai har ita ku jira abunda zai biyo baya,bazan tab'a barin ku ku zauna lafiya a bayan cin amanata ba" A sanda suka shigo d'akin ita Meenal tayi zaton ko shine ya shigo dan yayi mata maganar shiga kitchen, Hakan nema yasa ta k'ara lafewa abinta dan fa ta shirya wallahi yau dai duk tsiyar shi bazata biyun mishi ta dad'i ba, sai dai kuma mai makon taji muryar shi sai sambatun Matar shi ta fara jin yana tashi murya sama² kamar ma kuka takeyi,ko kuma ciwon tane yauma ya tashi oho Amma dai kalaman na Teemah ne suka d'aure mata kai hakan nema yasa ta tashi daga kwancen da take ta zauna dangalgal tana kallon su, ba tareda ta iya tofa ko uffan ba tunda ai ba'asata a ciki ba, sai dai daga zaunen da take, takema kalmomin teemah fassara daya bayan daya, wato dai inta fahimta dai² ita anata zaton gani take kamar tunda Sarki baije wajenta ya kwana ba kenan a wajenta ya kwana!. To amma kuma sauran maganganun ne suka d'aure mata kai, to wai ma me matar nan take nufi ne? Ko kuma tace me ta d'auke ta? Tana mata kallon wacce bata isa kwanciya da miji bane ko me?, Mijin nan fa mijin tane itama, kwanciyar aure dashi kuma halattaccen abune a gareta, shine har ita take musu ikirarin cewa zasu ga abunda zai biyo baya! Duk yanda Sarki ya so ta tsaya su fahimci juna k'iyawa tayi har saida suka k'arasa falon Meenal, sannan ya rike ta kam dan a haukacen da take haka take shirin barin gidan. "Ka sakeni kasakeni in tafi nace! Me yayi saura? Nace me yayi saura? Eyeh mai zaka fad'amin, bayan karairayin da ka dad'e kana min cewa ba sonta kake ba darajar iyayen ku yasa har yanzun ka kasa sallaman ta ta koma gaban su, Cemin fa kayi bazaka tab'a iya had'a jiki da wata ba ni d'in nan na isheka koba haka kake fad'amin kullum ba?" A zafafe shima ya katseta da cewa... "Zakiyi min shiru a wajen nan ki saurareni ko kuma hauka zakici gaba dayi min?, Kin kama hanya kin taho ma mutane gida da sassafe kamar wacce wani tashin hankalin ya koro sannan kin zo kina min hauka, shin ita yarinyar da kike magana a kanta kin manta ne cewar ita din nan *MATATA CE* Ina da ikon dazan kwanta da ita aduk sanda naso? Oh kin d'auka wani dalilin daban ne ya hanani had'a shimfid'a da ita? To bari kiji, ni nan mijinta nine banga damar amsar hakkina a wajen taba, saboda har yanzun ban shirya ma hakan ba, kuma in zan kwanta da ita Ina ganin ai babu bukatar neman izini daga gareki domin sanda na fara kwanciyar aure dake ban nemi izinin kowa ba, kai tunda iya shegen da kike son tsurowa dashi kenan ma to bari kiji ni kuma insha Allah zan tabbatar na nemeta na maida ta cikakkiyar matar aure ba tareda na jira harta gama karatun ta kamar yanda naso a baya gudun raba mata hankali ba, in yaso sai kiyi yanda zakiyin da hujja sakarya kawai" Ya karasa fad'a a tsawace sosai dan sosai fa ranshi ya baci, "Karya kakeyi wallahi baka isa ba, Sarki harni ce zaka cema yarinyar can matar kace har kana min kurari, to ka sani bazan bari ka k'ara kusan tarta ba domin bazan tab'a yarda in wulakanta a cikin kawaye na ba, kamar yanda ba kowa yasan cewa mijina yayi aure ba haka auren zai dauwama har sai ka gaji da ganin ta ka saketa, sannan kuma kamar yanda ka canza shawara nima na canza nawa shawaran na barin ta zauna da kai a matsayin yar aikin gida, yanzun kam tabbas dole ta koma gidan ubanta. Wannan safiya dai abubuwa ne marasa dad'in fad'uwa ko a baki suka afku a gidan Sarki, Teemah tayi alwashin raba auren Meenal da mijinta yayinda shi kuma yaci alwashin cigaba da zama da matar shi harma da kudurin maida ita cikakkiyar macen aure, Rai babu dad'i Teemah tabar gidan a kuma ranar ta tattara ta koma Lagos ba tareda tayi sallama da kowa ba. 🤣🤣🤣Nace mu fad'ama teemah gaskiya ne ko kuma mu barta da halin ta? 🤔. Please I really need to see your comment akan abunda ya faru #team Sarki🥰 #team AK #Aminatu & Teemah *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 """"Page 39.... Gaba d'aya tunani sun cin kushe mata kwalwa, domin dai duk yanda taso ture kalaman na Teemah abun ya gagara, harta da baccin da takeji kafin shigowar su yanzun kam tsaf shima baccin guduwa yayi ya kama gaban shi, "To kodai da gaske ne kenan da mutane ke cewa kishiya nama kishiya asiri? Ko kuma ta raba ta da mijin ma gaba d'aya, dan kwana kin baya bata mantaba haka wata kawarta a makaranta ta dunga ciwon da aka rasa gane kanshi, sai da tayi kamar zata shek'e dan maganin asibity ake tayi ya zamana ana magani daban cuta daban, da allah dai ya nufa cewar kwanan ta na gaba tana warkewa ita kuma kishiyar ta kwanta wani irin kazantaccen jinya, jinyar nata ne kuma ya zama sanadin tonuwar komai. kuma wallahi kishiyar nata malama ce sosai kowa yake ganin girman ta. To itafa allah ya sani ba komai take tsoro ba, illah dai kar azo a turo mata wani mugun abun duk da komai ya samu bawa nufin Allah ne kuma hakan yana daga cikin kaddarar shi, dan haka wannan karan kam dole ta magantu ko ba tama kanta yak'iba dole zatama d'an uwanta ko badan alak'ar aure ba shi d'in jinin tane. ya kamata ta samu wanda zata tattauna maganar nan dashi ko dan ta samu mafita tasan ta yanda zata bullo ma al'amarin, domin dai shi wancan Sojan tun zuwan ta gidan nan tana lura ana idar da sallah yake tahowa gida abunshi, bata tunanin yana tsayawa domin yin azkar bata sani ba ko inya dawo gida dai yana yin shi a d'akin shi, to dan Allah mutum ya tsare azkar d'in ma basai Allah ya kareba, balle kuma ace bakayi gaba d'aya, Ita dai yanzun damuwarta shine to wa zata tunkara kai tsaye? Malam shine mafi kusanci da ita a koda yaushe in tana da wani damuwa koda ko a fannin karatun tane har gobe shine kan gaba a al'amuranta, to amma yanzun kam batajin zata iya tunkarar shi da maganar nan, to jama'a in taje me zata ce mai?, cewa zatayi tun auren su har yau mijinta bai tab'a kwanciyar aure da ita ba ko me zata ce? Su Meelat kuma tasan ko ta fad'a musu babu wani mafitan da zasu samar mata,dan su kullum laifinta suke gani, a cewar su wai inshi bai neme taba ita taja hankalin shi mana tunda Allah dai ya albarkaceta da kayan alatu, kuji wani rashin mutunci wai itace suke nufin takai mishi kanta kut, jama'a wannan abun kunyan ma in duniya taji ai bata ba k'ara fita gida wallahi to Ina zata kai abun kunya fisabilillahi shi da yake namiji ya iya rik'e kanshi sai ita kamar wata yar wiwi, to ai ko bushe bushe ta fara batajin zata iya aikata wannan aiki irin na tsofaffin dilolin kayan marisa. "Mommy " Zuciyar ta ta ambata mata, "Eh Mommy ya kamata ta tunkara to amma ta Ina zata fara mata bayani bayan basu saba hira da ita akan komai daya shafeta ba, "Hajiya Innah" Yes Hajiya inna zata dosa kai tsaye koba komai dama ita tasan abinda ake ciki tun tuni in yaso shi kuma Malam zatace mishi dai yasa Sarki a addu'a, tasan in ta fad'a mishi hakan ba lallai ya tsanan ta bincike ba, Komawa tayi ta kwanta tana ta faman sak'a da warwara, Kai jama'a Ina ma amfanin auren mijin wata!, Yanzun nan fisabilillah inda saurayi aka aura mata ina zata fuskanci wadan nan abubuwan, aure shekara da shekaru babu wani cigaban da aka samu, wai dan mafa ba gari d'aya suke da wancan mahaukaciyar matar ba dan tasan da gari d'aya suke tofa da tuni anyi wacce za'ayi kowa yasan matsayin shi, dubi fa yanda da sanyin safiyar nan tazo ta hautsina mata kwalwa da hayaniyarta na banza, ko ita ce mata akayi shi mijin nata yana gaban tane ko koh? Ai wallahi Allah yasa ta k'ara gigin maimaita zuwa mata gida da asuban fari yasin sai ta d'auki mataki da kanta tunda shi mijin tsoron ta yakeji, Gaba daya ma sai taji zaman gidan ya sire mata arai dan wallahi dama tun tuni tana tausar kanta ne dan dai ta samu taga ta kammala karatun ta dan tasan koba komai igiyar aure darajar shi katangace ga d'iya mace indai zata rik'e darajar da kyau, tasan inda bata da aure tofa ko hidimar samari na iya sawa hankalin ta ya rabu gida biyu, amma yanzun hankali kwance take karatun ta dan ta kama kanta sosai babu wanda zaiga fuskar ma da zai tareta da batun wani shashanci, Amma kam tabbas tana gama karatun ta maganar rabuwa ne! , tunda ba sonta yake ba falillahil hamdu gara su sallami juna atoh batayi lalacewar da zata rasa mijin aure ba, a baya can ma daba cikakken hankali da nutsuwa take daba anyi rububin ta balle kuma yanzun ai tasan sai ta h'ada go slow, Sauka daga kan gadon tayi ta isa gaban pic dinta da suke mak'ale jikin bango, sai da ta gama k'are musu kallo tsaf sannan ta juya zuwa gaban mirror nan ma taci gaba da kallon kanta da irin suffar da Allah ya mata, Fari da idanuwan tayi yayin da ta k'awata fuskarta cike da murmushi, A bayyane ta furta. "Oh Allah na gode maka da kayoni kyakyawa son kowa k'in masu hassada," Hannun ta ta maida kan gashinta dake tufke a tsakiyar kanta ta d'aure shi da ribom, kamo ribom din tayi ta janye shi kamar jira gashin keyi domin tana cirewa kuwa gashin ya watsu a bayan ta wasu kuma suka dawo ta gefen fuskan ta. Duk'ar da wuyan ta zuwa baya kad'an tayi sai ta girgiza kan nata wanda hakan yaba sauran gashin da suka zubo a fuskan ta damar komawa baya suka had'e da sauran suma. Lallai zanyi wulakanci zan kuma gwara kan yan maza a duk ranar da allah yayi na samu yancin da wannan auren jeka nayin kan ya guntule, Domin kam babu ni babu kuma auren mai mata rashin auren mai matan kuma bayana nufin k'in kulasu bane, No zan dai rike musu zuciya da aljuhu ne ta yanda zanyi ta walagigi dasu har sai na gaji dan radin kaina kafin in sallama su! K'alu bale gareku matan dake ikirarin cewar basu ba zama da kishiya, domin alqawari nane sai na firgita muku rayuwa, abun nan da kuke ikirarin cewa da kishiyar gida gara ta waje dashi zanyi amfani wajen tabbatar muku cewar da kishiyar waje gara ta cikin gida. Dan haka ga shawara kyauta zan baku ko wacce mace ta rike wuyan mijinta dam, dan yana kuccewa ya shigo hannu na ya kad'e, domin ni din nan.. Zan zoma duniya da sabon salon zawarci, domin dole in gigita yan maza da salona, tsoho ko magidanci basu a layina, bazan k'ara mai maita kuskuren da nayi na farko wajen auren mijin wata ba, wannan karan nida kaina zanyi yak'in ganin na tsamo wanda ya cancanta, bana son ragon namiji ba kuma nason wanda ya cika fara'a ko kuma mai yawan wasa, Cikakken namiji nike so mai cikakkiyar izza da aji, in son samu ne zanfi son wanda mata ke shakkar tun karar shi ta yanda ko bayan aure zan samu salama nasan zuciyata bazatayi ta bugawa saboda tsoron halin da zai kasance a duk sanda ya fito waje ni ina gida ba. Komawa tayi ta zauna a gefen gadon tana murmushi. "To yaushe auren zai mutu da har zaki samu cikar burin ki?" wata zuciya ta tambaye ta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi tana tallabe fuskanta cike da rud'ani ta amsa da cewa. "Duk ma yanda zanyi auren ya mutu sai nayi, auren biyayya ne dama kuma nayi biyayyar tuni, a yanzun kam bamai mani dole akan in zauna a wajen da ba'a tab'a kallo na da daraja ba" Sallamar Sarki tareda shigowar shi cikin d'akin kai tsaye ne yayi silar katsewar hirar dake gudana tsakanin ta da zuciyarta. Gefen gadon shima ya nema ya zauna inda take zaune yana mai kare mata kallo, Kamar yanda itama take binshi da kallo tun shigowar shi har zuwa zaman da yayi a gefen ta dan abune wanda bai tab'a faruwa ba wai Sarki ya shigo d'akin ta harma ya nemi waje ya zauna, domin dai sau tari dama in kunga ya shigo d'akin to sallahun wani aikin zai bata a tsaye kuma yake tsaya mata har ya fad'i sakon, baya kara b'ata lokaci kuma Bayan hakan yake komawa inda ya fito, tun daga shekarar auren su har zuwa yau din nan kuwa. Shine ya yanke shirun nasu da cewa. "Abinda ya faru a gidan nan yau, Ina son ya tsaya a cikin gidan nan, ma'ana bana son kowa ya samu labarin komai daya farun, Ina fatan kin gane bayani na?" Galala tabi shi da ido tana kallo. Lallai nema mutumin nan kujimin wani k'arfin hali fa, wato so yake tayi shiru da bakin ta karta fad'ama kowa har sai matar shi taje ta had'o wani mugun abunta akan su, ita in abun a iya kanshi zai tsaya mai zai dame ta? To amma wannan batun fa akanta akeyin shi dan haka wallahi bazatayi shiru ba ita kam. "Waike mai yasa kika raina mutane ne? Sai mutum ya dunga magana dake kina mishi banza!" Tsam ta tashi daga inda yake ta koma can karshen gadon, "To aini ba nice na b'ata maka raiba balle kazo ka sauke a kaina, kuma ai ita matar taka ba yau ta fara zuwa gidan nan ta fad'amin magana ba, kaji na tab'a kai karar ta a wani waje ne? Kuma nidai kaja mata kunne ta dena zuwa min gida in ma neman ka take ai akwai waya basai ta kiraka ba, shine zata zo ta hana mutane baccin safe, kuma miji indai nata ne nima bana so atoh gara ma mutum ya sani tunda shima baya so to a sallami juna kawai kowa yaje yayi rayuwar shi," Ta k'arasa fad'a da kunkuni, Sai dai kunkunin nata bai hanashi jin abinda take cewa ba, duk wata kalma data furta tsaf ta shiga kunnen shi. "Dawo nan inda kika tashi ki zauna!" "Nidai ka tashi ka tafi nifa ko lafiya ma bana da ita bacci zanyi kafin anjima" "Likitoci na ciwo ne dama?" Ya tambaye ta "To ai likita ba mala'ika bane da zaik'i yin ciwo" "To in kin kwanta wazai had'a kayan karin?" Babu b'ata lokaci ta bashi amsa da "matar ka mana" "Oh ke kenan?" "Aini yar gadin gida ce, ita dai Gimbiyar nike nufi" Bai k'ara tofa komai a maganar taba ya mike da niyyar yabar d'akin dan yaga alamar itama wannan hautsina mishi kai zatayi inya biye mata. "Kisha magani to kafin ki kwantan, Allah ya k'ara lafiya" Bayan fitar shi mai makon ta kwanta din kawai sai taci gaba da aikin gyaran d'akin data fara a haka har ta gyara duk inda yake buk'atar gyara a gidan Bayan ta gama kitchen ta fad'a ta dafa ruwan tea ta soya kwai ta dawo falon ta karya sannan ta koma d'akin ta ta shirya ta fice a gidan domin shima gogan ya fice a gidan tuni tasan kila yana can wajen lallashin Gimbiyar dan kartayi bindiga, Sau uku ta gwada kiran number din Hajiya amma babu Kira d'aya wanda yaje, a gurguje ta shiga gidan su ta gaisa da mutanen gidan bata shiga sashen suba dan tasan bazata iske Mommy ba taso ganin Malam sai dai shima yayi fitar safe zuwa wajen wani sa suna kuma bai dawo ba, tasan kuma inta zauna jiran shi zata iya yin latti dan karfe 10 ake nema yanzun, ga kiran dasu Meelat ke mata tun d'azun. Bawai dan ta gama abinda zatayi bane a cikin makarantan ba, sai dai uzurin da take dashi nason zuwa wajen Hajiya kuma so samu dai tayi zuwan ita d'aya dan su samu damar tattaunawar su da kyau, bawai kuma dan bata son su Maryam su san maike faruwa bane, ah ah tasan in sun sani a yanzun tabbas hanata zuwa zasuyi, dan haka sai ce musu tayi bata jin dad'i tana son zataje ta amshi wani magani a hannun Hajiya daga can kuma akwai inda zasuje da Mommy Hauwa, sunyi mata fatan samuwar lafiya yayin da suka rakora har bakin motar ta sai da ta bace ma ganin su sannan suka koma cikin makaranta. A hanya ma tayi ta kiran number din sai da kyar ta sameta, "Hajiya kina gida kuwa?" Ta tambaya Bayan sun gaisa, "Ina nan me zaki kawo mun?" "Ni babu abunda zan kawo miki ganin nan dai a hanya" "To Allah ya kawo ki lafiya," Koda ta isa sashen Hajiya Jummai ta fara wuce wa acan tayi sallah taci abinci sannan ta k'arasa sashen Hajiya, Yau dai da alama Hajiya zaman d'akin ne ya motsa domin dai bata falon ta inda ta saba zama, can kuwa ta isketa a d'akin ta ta baje wad'an su takardu kona miye oho, Waje ta nema ta zauna, "Hajiya ya d'akin naki yau naji ya d'ume da gumi ne? Bakya jin zafi kike zaune baki kunna ko fanka ba," "Ai dole kice zafi tunda kin fito falon Jummai dake bulbula ac da fanka duka suyi ta aiki ita ko tsoron kar sanyi ya kamata batayi, Niko da tsufana bazan yarda in k'ara gayyato ma kaina wani ciwon da yarana zasuyi ta faman jinya ba, insha Allah da kwari na zan mutu, Ya akayi ne nasan tunda kika kirani kafin kizo nasan akwai wani abun, meya faru?" "Akwai Hajiya kuma abubuwa sun faru yau, sai dai kuma kafin in fito shi Ya Sarki yazo har d'aki ya sameni aka cewa abunda ya faru in barshi a cikin gidan ma'ana kar in fad'ama kowa" "Yace miki karki fad'ama kowa kuma shine ni kika d'auko kafa kikazo dan ki fad'amin? To amma tunda kinzo ai bazan kore kiba miya faru ne haka?" Gyara zama Meenal tayi ta koro ma Hajiya tsaf abinda ya faru harda ma maganganun da Teemah take fad'a mata aduk sanda suka had'u, dama ikirarin da tayi yau cewa zasuga abunda zai biyo baya. Salati da sallallami Hajiya ta d'auka tana kankance ido cike da masifa take cewa. "Amma dai ke koh Aminatu kinji haushi, wallahi kin dai ji haushi albasa batayi halin ruwa ba, Ina ce komai nawa kikayi gado kamar yanda kikaci gadon sunan, Innah ashe da saura, yanzun nan ki zauna har wata kishiya tayi asubancin shigo miki gida ta fetsa kalar nata rashin mutuncin kina cikin gidan a raye kina kallon ta baki shek'a da gudu zuwa cikin kitchen din ki kika d'auko tabarya kikayi ma kanta fashin kwakwa inya so duk abunda zai faru ya faru ba, Ah gaskiya baki kyauta min ba, ni da wannan zancen da kika kawo min ai zanfi farin ciki in kirana zaman sulhu akayi police station Bayan kin rotse mata kai wallahi, Ke wai ma tsaya, Ina magungunan da kwanakin baya nace ki dunga zubawa a binci in zakiyi girki? Kar dai kice min duk uban wahalar da nasha wajen ganin an kammala had'a muku maganin nan a banza ya tashi bakiyi amfani dashi ko sau daya ba?" Ta tambaya tana tsare Meenal din da kallo, Ita ko soshe² ta kamayi alamun rashin gaskiya, hakan ne kuma yaba Hajiya amsar tambayar ta cewa Meenal din batayi amfani da maganin ba. "Wai a Ina kikayo gadon sakarcine Meenal? Kin san maganin miye na baki kuwa? Maganin karin ko wani irin asirine fa, da zarar Allah yasa aka dace sai kiga da mutum yayi amfani dashi duk wani mugun abun dake jikin shi sai ya warware cikin kankanin lokaci kuma insha Allah wani bazai k'ara cin galaba akan ka ba, Tun wancan lokacin da kika bani tabbacin babu abinda ya shiga tsakanin ku nike tsaye kanki dan ubanki wajen amsar miki taimako ashe ni kikema kallon sha² Ina ta gantalin ganin Allah ya tsareki daga sharrin kishiya, Ka tseta Meenal tayi da cewa, "Allah Hajiya duk wanda kika bani dan ni inyi amfani dashi nayi, na wajen nashi ne kawai tsoro yasa ban zuba mishi ba gudun kar wata rana ya gani yayi zaton ko Ina da nufin cutar dashi ne" "Eh ke baki da nufin cutar shi amma ai shi gashi ya cusa ki a cikin gida ya kafe kamar hoton enlargement, baki mishi amfanin komai saina gyaran gida da girki, Ita kuma dan ubanta ki barni da ita badai takamar ta matsafa ba, to mu bama tsafi amma mun yarda da kudurar ubangiji, dan haka lokaci yayi da nata wasan zanje karshe, su magungunan da nike bakin ya kikeyi dasu? " Suna nan a cikin magunguna na, To abunda za'ayi yanzun tashi kije maza ki had'amin kansu, zan aiko a amsa min anjima ko kuma kilama in shigo unguwar naku da kaina dan na dad'e banje ba, kuma bance ki fad'ama kowa abinda yake faruwa ba" "Hajiya" Ta kira sunan sai kuma tayi shiru, "Ya akayi akwai wani abun ne kuma?" Hajiya ta tambayeta. "Hajiya ni so nike ya sakeni, kinga baya sona nima kuma ba son shi nikeyi ba, nidai gara ya sakeni kawai zaman da nayi da Allah ya bada lada," A dar dar tayi maganan dan bata san yanda Hajiya zata fassara maganar nata ba. "Baki fara son shi ba kike nufi duk wannan shekarun da kukayi da aure? " "Hajiya ni ban tab'a jin son shi a zuciyata ko sau d'aya ba" "To Ina amfanin ka zauna da wanda baka so har karshen rayuwa, ai tunda har kin tabbata bakya son shi kwantar da hankali yar nan indai Ina raye an gama miki dole, wannan aure kam sunan shi matacce insha Allah dama kaddara ce tasa aka d'aura zaren to yanzun kam nice zanyi tsayin daka wajen tsinke shi, amma dai karki tada hankalin ki a yanzun dan dole mubi komai a sannu, dan in muka matsa ita waccan matar tashi gani zatayi kamar ta samu nasara akanki kenan, Yanzun abunda zaifi shine mu maida hankali wajen karya kadarin ta, kinji ko yar albarkha, ni dan dai ma kince baki sone da sai ince kiyi hak'uri kiyi zaman ki a gidan ki, dan yanzun dai ko kin fito ya riga ya b'ata miki suna kowa kallon bazawara zai dunga miki" "Nidai Hajiya koma me za'a kirani na yarda amma na gaji da auren nan haka" "Yo yar nan tunda kikace kin ganji yanzun kam ai babu dole, Allah dai yayi maki zab'i mafi alkhairi. Bayan baro warta gidan Hajiya koda ta dawo gidan su Sarkin ta shiga suka gaisa da jama'ar gidan kafin ta fito ta shiga gidan Malam, Tun tana gidan su take ganin kiran Sarki a wayar ta amma tayi kememe tak'i d'auka dan tasan bazai wuce yace abinci yake nema ko wani abun yake buk'ata ba, Sun dan taba hira da Malam a cikin hirar ne kuma ta sako mishi zancen addu'ar da take so ayi ma Sarki, Shiru yayi yana nazarin ta, amma ganin bata mishi wani k'arin bayani ba yasa shi amsa mata da cewa za'ayi insha Allah, Bayan ta shigo gidan ta dakin ta ta wuce kai tsaye taje ta ajiye tarkacen data shigo dasu sannan ta kama hanyar zuwa wajen Sarki, Da sallama ta shiga sai dai kuma bashi a falo, tayi kamar zata juya sai kuma zuciyar ta ta mata ishara da cewar ta duba dakin baccin shi, Tun daga cikin corridor d'in da zai sadaka da d'akin nashi ta fara jin wani irin nishi nishi wanda ta rasa gane kanshi, A haka dai tayi karfin halin k'arasawa ta bud'e kofar d'akin ta shiga bakin ta dauke da sallama, Abunda idanuwan ta yayi tozali dashi ne yasa zuciyar yayi kwance kwance ya yanke ya fad'i har wayar hannun ta da Hajiya ke kira ita kuma take kokarin Amsawa ya kucce daga hannun ta zuwa kass........... Babu editing duk inda kukayi karo da mistake please ignore it 🤨. Huhuhuhh, bafa ayi komai ba tukun yanzun ne wasan zai soma. Toya kukaji page din yau, Jiya banga comment da yawa bafa🙄 *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!* 👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY }}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 `````` *Page 40*.... Da gudu ta k'arasa shiga cikin d'akin bakin ta na faurta kalmar Innalillahi wa'innah ilairir raju'un.... Haka taci gaba da maimaita wa, a rud'e ta doshi inda yake kwance yana ta faman mulmule akan tile's d'in d'akin domin alamu sun nuna cewar tsabar azabar ciwone yasa shi fad'owa daga kan gadon badan ya shirya ma hakan ba. "Ya'ya! Ya'ya!! Ya'ya mai ya same ka? waiyo Allah na dan Allah ka tashi meke maka ciwo?, innalillahi dan Allah ya'ya ka tashi dan Allah muje asibiti, yama zaka zauna a gida Bayan kasan baka da lafiya! Ni ai ban san cewa ciwo kakeyi shi yasa kake ta kirana ba da nazo tun d'azun, kasha magani kuwa? Ina kake ajiye maganin ka in d'auko maka? meke maka ciwo ka fad'amin sai in d'auko maka maganin a d'akina in baka dashi anan" Take tambayan shi cikin kuka domin duk ta rud'e wannan shine karo na farko da take ganin zafin ciwo yasa Babban Namiji mulmula a kasa, Shiko tsabar azabar ciwo ne yasa gaba d'aya ma baya gane mai take cewa, dan sosai yake jin ciwon bada wasa ba, Shi bai san me yasa a cikin kwanakin nan yake yawan fama da sha'awa ba,domin dai a iya sanin shi har yazo garin nan ya gama kwanakin da zaiyi lafiya lau yake komawa ba tareda ko sau daya yaji cewar yana buk'atar keb'ewa da ita ba, dan sau tari sai ma inya koma Kadunan ne abun ke damun shi har sai yaje Lagos ya sauke damuwar shi sannan yake jin dai², To amma yanzun kam abubuwa sun canza mishi domin wata rana sai yaji kamar yaje ya nemi yarinyar nan sai kuma ya rasa kwarin gwuiwar shi, yayi zaton in Teemah tazo zai sauke a kanta sai dai hakan bai samu ba, wannan dalilin nema yasa ranar ya nemi Teemah sai kuma akayi rashin sa'a bata cikin tsarki, yasan za'a iya samun matsala inya kwana a wajen ta shi yasama ya gwammace ya dawo gida ya kwana a ranar, Ita kuma tayi zaton daya kwana a gida ya nemi Meenal ne shi yasa tazo tayi nata kalar haukan daga karshe kuma gashi ta tattara ta tafi ta barshi da bala'in da bai san inda zai samo mafita ba. Shi dai ba dan iska bane domin dai a can baya da yayi rashin ji ma ba'a hayyacin shi yayi ba kuma a iya shaye² ya tsaya baiyi neman mata ba har zuwa sanda yayi aure, balle kuma yanzun da har yake da yara sun zama yan mata, to shida keda yan mata Ina zai yarda ya tab'a yar wata a rama akan nashi. To yau dai abun ya gagara domin daren jiya ma bai samu yayi bacci wadatacce ba saboda tsabar ciwon daya kwana dashi, yau kuma yayi zaton ko in ya shiga cikin mutane ko abun zai lafa sai dai kuma abunfa ba sauk'i. Ganin yana neman mutuwa ne fa yasa ya dawo gida a zaton shi ko Meenal bataje makaranta ba tunda ai da safe tace mishi bata da lafiya, So yayi yazo ya lallab'ata yau dai yaji ya gani ya kuma amshi auren sai dai kuma tun shigowar shi falon ya tabbatar da cewar bafa ta cikin gidan domin dai baiji kamshin girki ba dan dai yasan tana dawowa daga makaranta indai yana garin take fad'awa kitchen domin had'a mishi abincin rana, tanan wajen kam yana respecting dinta dan kai tsaye zaice abinda ya rasane a wajen Teemah ita yake samu a wajen ta, Yaso kwarai ya daure sai dai yaufa abinda yakeji a jikin shi bamai dannuwa bane ganin cewa zai iya cutar da kanshi domin dai har magani ya sha amma ba sauk'i hakan yasa ya yanke shawarar gara kawai ya kirata ta dawo gida in yaso komai ta fanjama fanjam domin dai aiba abun kunya zai aikata ba ta dawo kawai ta bashi hakkin shi, dalilin da yasa yayi ta danna mata kira kenan har zuwa sanda ciwon yaci k'arfin shi ya mulmulo ya dawo kasa yana jiran ta Allah ta kasance, Sama² ya dunga jin tana kiran sunan shi cikin kuka, sai kokari take ta d'ago shi daga inda yake kwance sai dai kuma inah! Wane ita ta iya d'aukar shi! Soja nefa tsayayye wanda ko a tsaye yake bazata iya ture shiba balle kuma yana kwance sharbam, Ba karamin salaamah ya samu a yayin da ya tabbatar cewa ita dince ta shigo dakin ba, domin ko babu komai bazaiyi wasa da wannan damar ba, zaiyi amfani da ita yanda ya dace dan yasan dai inba haka ba tofa koda ace macewa yayi sai dai yazam cewa ya mace a banza indai ta itane yayan shine kadai zasu zama marayu, tunda ita dai ba fad'in shi ta sani ba duba da cewar koda safen yau saida ta maimaita mishi cewar ya saketa kowa yaje yayi harkar shi. Sauran karfin daya rage mishi yasa wajen jawota ta fado cikin jikin shi, shi kuma yayi amfani da hannayen shi wajen nad'eta a jikin nashi ta yanda ya tabbatar bazata iya mikewa ba. kam² ya damketa damka bata wasa ba, yayinda zafin damkar yasa ta fasa ihu ita a zaton ta ko zafin ciwon ne yasa ya damketa, tunda itama in tana ciwon mara duk wanda ta samu damkewa takeyi, Iya kokarin ta tayi dan ta kucce daga jikin shi sai dai d'an bawan Allah keme me yakiya, sai ma k'ara mamaye ta da yakeyi yana cusa kanshi a cikin k'irjinta. "Ya'ya ka cikani inje dakina in kawo maka magani kasha, insha Allah kana sha zaka warke garas kamar ba kai ba" Shiru ba amsa sai ma hannun shi guda daya fara amfani dashi wajen shafo gadon bayan ta zuwa wajen kwankwason ta, Kamar wacce aka kwashe fuskarta da mari haka ta zabura jin yakai hannun shi kasa yana tattaro rigar jikinta data kasance doguwa yanayo sama dashi, "Innalillahi yaya dan Allah ka dena nice fa Meenal ba Maman boy ba!, nidai dan Allah ka cikani in kira wani ya kamamin mu kaika asibity dan kana bukatar ganin likita" Ta fadi hakan a yayin da take ta kiciniyar kwacewa daga jikin shi, Shiko kamar dutse haka ya koma mata dan yasan dai duk tsiyar ta bata iya kwacewa a hannun shi, dan haka sai ma ci gaba da yayi wajen ganin ya samar ma kanshi nutsuwa, Hannun shi data rike ya danne wanda hakan ne ya bashi nasarar jawo rigar har zuwa saman cikin ta, Dambe sosai take kokarin yi dashi dan ganin ta kwaci kanta a hannun shi fad'i take.... "Yaya kayima girman Allah dan darajar iyayen ka kayi hak'uri, Inma dan d'azun ban had'a maka abun kari bane yasa kake fushi dan Allah ka yafemin wallahi bazan kara ba, nidai dan Allah kayi hak'uri kaji wayata ke k'ara kuma wallahi Hajiya Innah ce ke kirana zata aiko a karb'a mata sak'o, nidai dan ka dena wallahi bana so" Sosai jikinta yaci gaba da rawa zuwa lokacin ko ai inda za'a auna jinin ta ba k'aramin hawa za'aga yayi ba, To jama'a fisabilillahi Ina dalili aure shekara sama da Biyar miji bai tab'a neman kaba sai yau kawai daga taimako yana neman haik'e mata, so yake yace mata tsayin shekarun nan mantawa yayi da hakkin ta wanda har hakan yasa mutane ke mata kallon tana shaye shayen maganin hana d'aukar ciki sai yau ya tuno da hakkin nata ko ya'ya abun yake, Da kyar ya iya fusgo kalmar bakin shi ya iya furtawa a fili da muryar shin nan da zafin ciwo yasa ta k'ara komawa masha Allah... "Ki tsaya fa karkisa inji miki ciwo!" "Iyyehh kuwa jama'a ku kawo min d'auki waiyo Allah Ya Sarki dan soyayyar ka da manzon Allah ka rufamin asiri wallahi tallahi ban shirya ba" Ihu sosai take mishi da kururuwar cewa itafa bata shirya ba, shiko mugun ko takan ta baibi ba illah ma maida hankali shi da yayi wajen ci gaba da cakuda mata jiki, sai dai kuma duk yanda yaso samun damar had'e bakin su saboda ihun da take tak'i yarda bori kawai take uwa wata wacce ke shirin tada aljannu tana neman dauki, Jin saukar bakin shi akan ajiyar da Allah yayi a kirjin ta yasata fasa wani uban ihu tana fad'in kalmar shahada kamar wacce ke gargaren mutuwa, "La'alaha illallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, Shi kenan kwanan ki ya k'are Aminatu tun baki ga auren Besty din kiba, shi kenan Aminatun Malam zata mace tun bata zama cikakkiyar likita ba, Allah Sarki Malam za'a kashe makani tun ban gina maka gidan sama mai hawa biyu ba, waiyo Allah Yayan mu to aima ba haka akeyi ba, babu sallah ba kaza a farma amarya Sam wannan baya cikin shika shikan kwanciyar aure, ni wallahi bazan yarda ba ai nasan ita matar ka ba haka kaje mata babu kayan siyan baki ba, saini da ba'a so ne za'ama fashin budurci da rana tsaka, wallahi nidai tunda uwata ta haifeni banji inda aka tab'a nemar amarya da rana tsaka ba" (Nidai nace Meenal kila bakin nan bazai mutu ba sai an shiga daga ciki) Ture kanshi take ta kokarin yi dan sosai fa take jin ciwon yanda shiba jaririba amma ya wani kafa mata bakin shi dake cike reras da jerin hakoran shi a inda tunda tayi wayau take boyesu ga kowa, dan Allah jama'a maiya had'a babba da kayan da jarirai kesha, ga wani uban zafi da take jin suna mata wanda yasa babu shiru ta fara mishi k'ananun kuka a zaton ta wai ko zai tausaya yaji k'anta ya kyaleta, Sai dai mai makon hakan sai ma mirginata da yayi ya mai data kasan shi yaci gaba daya mutsa mata jiki, "Dan Allah dan Annabi karkayi a kasan tile's, ko wacce amarya a saman gado ake mata shi da lallashi shine ni za'a bajeni a tiles saboda dama ba sona kakeyi ba wato bari ka kasheni ka huta," "Zaki tsaya to in na mai dake saman gadon?" Ya tambaya ba tareda ya tsagaita da aikin da yakeyi ba, Kuka ta fashe dashi sosai. "Wai dan Allah da gaske kakeyi? Nifa Ina ce baka da lafiya ne shi yasa na shigo" "Maganin nike so ki bani ai!" Cak ya daga ta zuwa gadon, yana ko ajiyeta babu b'ata lokaci ta daka wani shegen tsalle ta dira ta d'ayan gefen tana sauke rigarta daya tattare, "Ina kike tunanin zaki gudu kije? Ke aiko wani ne yace miki zan barki ayau keda kanki zaki ce mishi k'arya ne kalli nan ki gani fa" Ya fad'i hakan yana mata nuni da gaban jallabiyar dake jikin shi daya taso, Ai da gudu ta maida idon ta ta rufe jikin ta na rawa taci gaba da rokon shi akan ya rufa mata asiri ya kyaleta, Komawa yayi ya duk'e dan tab'atan nan da yayi mai makon yaji sauki Ina sai ma k'ara kunnuwa yaji yayi, "Kizo nace" "Ai wallahi bazan zo ka kasheni da ranar Allah ba" Ta bashi amsa tun ma bai rufe baki ba, sannan ta d'aura da cewa... "Kuma wallahi kana k'ara tab'ani zanje in fad'ama Malam" Duk da yanda yake jin ciwo amma saida ta bashi dariya kuji fa wani shirme wai zata fad'ama Malam. "Me zaki ce mishi?" Ya tambaya. "Umm umm nidai kawai ka barni in tafi Ina ma ruwan ka da abinda zan ce mishi" Ganin tana k'ara ja mishi rai akan abinda baifi ya danneta ya kwata ta karfi bane yasa shi yunk'urawa da niyyar ya zafko ta sai dai kuma a dai dai lokacin cikin nashi ya k'ara mishi wani irin mugun kullin da dole sai da yakai kwance yana salati, Ita kuma a zaton ta wayau yake mata dan ta matsa kusa dashi, Da sand'a ta samu ta wuce inda yake kwance ta wani irin zabgaga da uban gudu ta fice a d'akin dan gara ta fita ta duba ko zata samu wanda zaizo ya fito mata dashi su kaishi asibiti, A bakin kofar falon ta suka kusan cin karo da Hajiya dake shirin shiga falon. "Ke kuma lafiya kike fitowa da gudu kamar wata wacce mutuwa ta biyo? " "Hajiya sarki ya Sarki ne baida lafiya wallahi mutuwa zaiyi in ba'a kaishi asibity ba dan Allah muje ki kamo min shi mu kaishi asibiti" Jan hannun Hajiyar ta fara da niyyar suje ciki, "Subhanallah meke damun shi? Tun yaushe ne bashi da lafiyan Ina ce yaune kukayi gurmin to yaushe ya fara ciwon" "Nidai Hajiya duk ban sani ba na dawo dai na same shi ya fado daga kan gado yana ta nishi kamar zai mutu" Matsawa baya kad'an Hajiya tayi tana k'arewa Meenal din kallo... "To ke kuma miya sameki haka naganki duk wani a yamutse kamar wacce ta kutto daga bakin kura? Kalle kifa duk kin wani yamutse" "To ba naje d'agashi mu fito bane kuma shine na kasa shi yasa na fito in kira masu gadi ai" "To ai ko yanzun sai mun nemo masu ceto Ina ni Ina iya d'aukar wannan mijin naki mai k'irar mutanen farko, koma daga ciki ki d'an gyara shi bari in ma Dan mai k'arfi magana yau ga ranar shi, dan nasan shi kad'ai keda zarrar d'auko shi ya fito mana dashi zuwa waje" Komawa cikin tayi kamar yanda Hajiya ta buk'ata yana nan kamar yanda ta fita ta barshi... "Ya'ya zamu tafi asibitin gasu Hajiya nan sun shigo" Hannun shi kawai ya iya mik'a mata yana mata ishara da cewa ta rik'ashi ya mik'e tsaye, "Ke takwara kuna ta inane? Ina d'akin mijin naki yake?" "Gamu nan Hajiya" Ta amsa ma Hajiyar tana fita daga d'akin. Hajiya ne a gaba shi kuma AK a bayan ta, fuska d'aure da alama dai dole Hajiya tayi mishi bawai da son ranshi ya shigo gidan ba, "To shiga daga ciki ka fito dashi ko! Ke kuma gyara mishi a hanya dan wannan aikin na maza ne ba iyawa zakiyi ba, nidai gani nayi da ace masu gadi da baku had'a komai dasu ba su shigo su gane miki sirrin gida ai gara shi koh? Naga dai ai koba komai shi d'an uwan kine, dan duniya yanzun ba gaskiya ka shigo da mutum yazo ga gama gane maka tsarin gida sai dare yayi a taho harda shi a yaye ka tass wallahi, nawa kuma akayi" Ita dai Meenal bata tsaya sauraron Hajiya ba itama tabi bayan shi cikin d'akin, Abunku da namiji yana zuwa haka ya d'ago shi ta gefe ya rataya hannun shi a kafad'ar shi sukaci gaba da taku sannu sannu har suka fice daga d'akin Hajiya na famar jera ma Sarki sannu da fatan Allah ya sawake, Motar da AK yazo da ita ya nufa dan dama kafin ya shiga gidan saida ya bude kofofin motar ya barsu bud'e, dan haka suna k'arasawa ya taimaka ma Sarki ya shiga, ganin fitowar sune kuma yasa sauran ma'aikatan gidan tasowa suna tambayan Lafiya, "Bashi da Lafiya"shine amsar da AK ya iya basu a takaice, gaban motar Hajiya ta shiga tayi ma kanta mazauni, ita kuma Meenal ta zagaya ta d'aya gefen da niyyar shigewa motar ita ma, "Keeee!!!! Gidan ubanwa zaki bimu a haka? da wannan shegen rigar na jikin ki kai ko kallabi babu karki sake ki shigar min mota na fad'a miki, k" Ya fad'a a matukar fusace, sai kuma ya juya inda ma'aikatan gidan sukayi cirko cirko "Ku kuma kuna iya komawa bakin aikin ku an gode" "To Ya AK dan Allah ka jirani in canzo kaya sai in fito mu tafi tare" "Eh na Jiraki mana tunda ga direban gidan ku, kinga kafin ki fito shi kuma ya mutu koh! Come on jare bace min anan" Hajiya ne tasa baki da cewa.. "Ah ah ka bari ta Sanyo ko hijabi ne sai mu tafi tare Ina zai yiwu mu barta ita d'aya" Jin Hajiya tasa bak'ine yasa ta samu kwarin gwuiwar falfalawa da gudu zuwa ciki, Shi kuma ya bita da kallo yana jin uwa zuciyar dake kirjin shi tana shirin fitowa, mai da duban shi yayi inda ma'aikatan gidan suke da ya tabbatar ba ita suke kallo ba sannan ya samu salama, Kamar yanda ta shiga da gudun hakan ta k'ara fitowa, Lokacin harya juya motar an ma bud'e mishi gate, Tun bata gyara zamanta a cikin motar da kyau ba ya gaza daurewa sai da ya furta, "Bana hanaki wannan yawan gudun da kikeyi ba? Ke me yasa har yanzun wai baki san kin girma bane, Abu kad'an gudu kamar wata shil shila" "Sorry" kawai ta iya furtawa, tana maida hankalin ta kan Sarki dake rik'e da cikin shi sai dai yanzun baya wannan nishin na d'azun bata sani ba ko ciwon ya ragune ko kuma ganin idon su Hajiya ne yasa ya kama jikin shi oho. "Wani asibity kuke zuwa?" "Dr Mubarak" Ta bashi amsa, Babu b'ata lokaci suka isa asibitin, kamar yanda ya tallafo shi daga cikin d'akin shi zuwa waje haka ya k'ara tallafa mishi suka fito a cikin motan kafin ma'aikatan asibitin su kawo kujerar da aka daura shi suka shige dashi ciki, Ganin an shige dashi ne hakan yasa Meenal nufa office din Dr Mubarak dan ta shaida mishi wanzuwar su a cikin asibitin, tunda ta mik'e yake binta da kallo ga mamakin shi sai yaga ta nufi office din da aka rubuta sunan maishi a saman kofar d'akin, "Keee" Ya d'aga murya yana kiranta, Juya tayi dan rainin wayau kuma wai sai itama take tambayar shi da cewa "ni" tana nuna kanta. "Eh kefa Ina zakije anan wajen?" Ya fad'a shima yana nuni da office din da take shirin shiga, "Dr zan gani" "Ke kadai?" Bata gane mai yake nufi ba dan haka bata iya bashi amsa ba. "Dawo nan ki zauna!" Kwabe fuska tayi kamar wata mai shirin yin kuka, "Hajiya kice mishi ya barni in shiga Dr din fa abokin Ya Sarki ne zan fad'a mishi ne saboda yaje ya duba shi" Kafin Hajiya tace wani abu sai ga Dr ya bullo da alama kiran shi akayi, "Dr Mubarak" Meenal ta kira shi tana k'arasawa inda yake tun bata jira ya amsa mata ba, "Ah ah Aminatu keda waye anan? Waye ba lafiya?" "Dr Ya Sarki ne babu lafiya yana can d'akin an shiga dashi nayi zaton ko kana cikin office din ka ne naso inje in sanar dakai sai kuma gaka" "Subhanallah Sufyan da kanshi! Tun yaushe ne bashi da lafiyan?" "Nima ban sani ba naje makaranta ne na dawo na sameshi a haka" "Subhanallah to bari inje in duba shi keda waye kuka zo?" Nuna mishi Hajiya da AK tayi, "Kakata da Yayan mu" Sai da ya gaisa dasu sannan ya juya zuwa duba halin da sarki ke ciki......... Ita kuma ta koma gefe AK ta zauna, "Ke saboda baki da kai shine zakije office din wani k'aton ke kad'ai koh?" Yayi maganar kasa kasa dan baya son Hajiya taji shi, "To ai shi d'in abokin mijina ne" Kamal saukar dalma akan gyambo haka yaji saukar kalmar a zuciyar shi, lallai ma yarinyar nan abun nata ya bunk'asa har shi zata cema wai wani abokin mijinta ne, Bayan ganin idon shi ai yaga abinda ke wahalar da mijin nata dan da taje gidan bai ganta ba amma yanda Hajiya ta dunga zabga f'ada tana ba Hajiya Jummai labari yasa ya fahimci komai tass................. To dai Sarki bai mutu ba masu mashi fatan mutuwa sai kuyi hak'uri ku cinye gumbar da kuka daka atoh. *ummiee Zaria*✍🏼[8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY}}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA* ````` *Page 41*.... "To ke yar nan ai sai ki kira mutanen gidan ku kona gidan su shi mijin naki dan su san abinda yake faruwa koh? Dan yanda muka kawo shi ranga rangan nan nasan indai likitocin nan na gaskiya ne tofa bazasu yarda su sallame shi ya koma gida ya mace a banza ba, dole rik'eshi zasuyi har jikin nashi ya dai'daita, Wai ke tsayama ! Shin ina kike cire rigar likitancin naki kika rataye wai da baki tsaya kin duba shiba? Kin daiji kunya wallahi kina likita a gida anma kin kasa tab'uka komai" "Uhmm nidai Hajiya dan Allah kiyi shiru asibiti mukefa ba gida ba, ke a ko ina ma sai kiyi ta surutu, kuma ni nama manta da wayata a gida ban d'aukoba da zamu taho sai dai ki bani Aron taki in kira dashi" "Kujimin wani zancen banza wajen yar wajen Jidda fa, to wallahi kiyi ta kanki dan nidai kin san da zarar naga ba dai dai ba tofa sai na tofa, daga cewa ki kira shine zaki hayayyak'o min kice sai dai in baki wayata salon kin cinye min katin wayar, badan halin kiba dai gata ki kira iyayen mijin na ki dan gara suzo su tsaya akan d'an su dan dai nida jikana ba zaman jinya zamuyi ba taimakon musulunci ne ma yasa na matsa mishi ya shiga ya fito dashi muka kawo shi asibitin nan, taimako dai ba wata abun tsiya ba to kin dai san sha'anin asibiti kar sugan mu da k'atuwar mota su fara lissafo abubuwan da zasu mishi amfani dashi dan nidai kudin jakata uzurin da zanyi dasu daban bana hidimar asibity bane, Atoh ina dalili za'a sani zubin adashin da babu kwasa bayan shi mijin naki ba gidana yake zuwa ba balle ince ya tab'a kawo min wani abun ko hakan zaisa yau in mishi kara, naki wasa ne yarinya bari ki gani uwarki zan kira ita tasa mayafin ta shiga gidan nasu fad'a musu" AK dake ta danne danne a waya ne ya amsa ma Hajiyar da cewa... "Ba sai kin kirata ba na riga na turama Sa'eed sak'o nasan zai kirani" AK ya bata amsa yana b'ata rai dan shima surutan ta sun fara sha mishi kai, inba abun Hajiya bama waye ya tambayeta ta bada ko kwabon tane, Kawai fa dan shi Sarki baya zuwa gidan ta balle ta samu damar more mishi aljihu shine yasa take duk wannan maganganun, Kiran Sa'eed daya shigo cikin wayar AK ne yasa shi tashi ya barsu a wajen yana nufar hanyan wajen asibitin dan ya tarbi Sa'eed din bayan ya amsa wayar. Dr Mubarak yad'an jima kad'an kafin ya fito daga inda Sarki yake, "Sannun ku da zama Hajiya" "Yauwa sannu Dr yamai jikin ya k'ara ji?" "Jiki alhamdulillah zai samu lafiya insha Allah dan zuwa anjima in ya k'ara warware wa ma kuna iya komawa gida dashi, amma Hajiya inba damuwa zanso mu d'an karasa daga cikin office d'ina domin akwai abinda nike so mud'an tattauna, akan ciwon nashi," "Ah ah dani kuma zaka tattauna? ai dai gara in ma wani abun ne ka jira har yan uwan shi su iso dan sune dolen shi, kaga nifa ba wata uwa na had'a dashi ba kawai dai ni uwar Jidda ce mahaifiyar matar shi amma bacin haka ni ban had'a komai dashi ba sai dai zumunta irin na musulunci da kuma auren shi da ke rataye a wuyan jikata, atoh Allah dai yasa ba wani abun bane ya taso, dan kaga ni dai bada shirin zuwa asibity na fito ba dan haka jakata ma yan kud'ad'en cikin ta basu taka k'ara sun karya ba," A zuciyar shi yace 😮 wow wanga tsohuwar daga gani yar jidalice, a fili kuwa dariya ya d'anyi, sannan ya daura da cewa.. "Hajiya dama ba wani abu bane domin maganar dama da ita matar nashi ya kamata inyi to amma tunda gaki a kusa shi yasa nike so kema kisa baki dan nasan zata fi jin maganar ki fiye da nawa inke kika fad'a mata" "Tooo subhanallah ciwon nashi kuma ya shafeta? Kai likita badai wani mugun ciwon yake dauk'e dashi daya gogama jikata ba dai koh?" "Ah ah Hajiya ko d'aya baya dauke dako wacce cutar da zai goga mata, mu k'arasa daga ciki dai sai mu tattauna da kyau" "Ke takwara tashi muje dan nikam gwuiwa ta ta fara sanyi kedai wannan aure naki dai toh Allah dai yasa kaffara ne, dan kina kan bautuwa" Tare suka jera har zuwa office din sannan Dr yayi musu nuni da kujerun dake gaban teburin shi suka zauna shima ya zagaya ya zauna. "Hajiya ko kina buk'atar wani abin a kawo miki? ruwa ko lemu wanne kike da buk'ata" "Ah ah wallahi na gode, kaga nikam da ruwan nan gara kayi gaggawar shaidamin abinda kenan dan insan wani sabon iftila'in ne kuma yake tunkarar jikata" Hannu ya mik'a ya zare glass din dake sanye a idon shi sannan yayi amfani da wani hankaci daya ciro daga aljihun rigar shi ya share fuskar shi, Kafin ya gyara zaman a kujerar da yake zaune kana ya d'aura da cewa.. "Hajiya a binciken da mukayi akan ciwon nashi mun gano cewar ba komai ne yayi sanadin ciwon ba face, hali na matsanan cin sha'awar da yake ciki domin ko rashin samun biyan bukatar da zai gusar da sha'awar ne yasa har ciwon ya taso mishi haka sosai, Abinda yasa nace ina son magana daku ba komai bane sai dan inyi ma ita matar shi nasiha, wala'allah ko sun samu sab'anin da yasa kila koda ya nemeta tak'i bashi had'in kai wanda hakan ne kila yakai shi a wannan halin da yake ciki, Domin dai inba haka ba wannan dole yaxam abun d'aure kai duba da cewa magidanci kamar shi ace yana fama da ciwon sha'awa alhalin kowa yasan yana da mace har biyu, na aure" Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yaci gaba da jawabin shi... "Nafi ta'allaka matsalar a wajen ita Aminatu duba da cewa anan dai itace a tare dashi" Juya gefen Meenal yayi ya fuskanceta da kyau, Ita ko Allah ya sani da tasan abinda zai biyo bayan shigowa office din kenan wallahi da bata shigo ba, kuji min sharri kawai zai wani ce wai laifin daga ita, ita ina ruwan ta da ciwon shi tuntuni bai san bashi da lafiya ba sai da yaga matar shi tayi komawar tane zai wani kama ciwo! "Meenal "ya kira sunan ta Bata iya amsawa ba tadai dago kanta kad'an, "Meenal meya had'aki da mijin ki wanda har yasa kike hanashi samun natsuwa dake?bayan kin san hakkin hakan a wuyar ki ya rataya! " Ji tayi kamar ace tayi wani siddabarun da zata bace b'at a wajen. To jama'a fisabilillahi wani amsa zata bashi? Hajiya ce ta amsa mishi da cewa, "Masha Allahu anzo inda nike so azo! Dan nan kace ciwon sha'awa ke damun shi koh?" "Eh Hajiya gaskiyar kenan" Waigawa tayi inda Meenal ke zaune sai faman mutsu² takeyi gaba daya ta kasa zama da kyau akan kujerar da take, "Ke takwara fad'amin shekarun ku nawa da aure yanzun?" Bata iya d'ago kanta ba ta amsa ma Hajiyar da cewa "shekara 6" "To kaji shekarun su 6" "Yauwa to fad'amin a tsayin shekarun nan sau nawa mijin ki ya nemeki a shimfid'a?" Zumbur Meenal ta mik'e da niyyar barin office d'in jin wani sabon tonon asiri da Hajiya ke shirin mata a gaban Dr Mubarak. "Kina dai fita a d'akin nan kin san wa zaki tarar a wajen dan haka zaifi sauk'i ki dawo ke ai Allah ne ma ya miki gata yake son warware mana komai cikin sauki" Badan taso ba tana tura baki tana komai haka ta koma a kan kujerar data tashi ta zauna. Shi dai Dr kallo kawai yake bin Hajiya dashi jin wani zance daban da take son kawowa. "Uhummn bashi amsar tambayan da nayi miki" "To Hajiya kema ba kin sani ba" ta fad'i hakan cikin turo bakin ta gaba, "Ni idan na sani shi likitan yasan gaskiya ne? Koba a gaban ki kinaji yake neman d'aura miki laifin da ni dake mun san ba naki bane, dan haka nike son yaji komai a bakin ki ta yanda zai zama min shaida a gaban iyayen ki, dan haka fad'a mishi don ya sani" "Ni tunda mukayi aure babu abinda ya h'adamu kowa a d'akin shi yake kwana" "To kadaiji da kunnen ka koh? Kaji kuma daga bakin ta ba daga bakina ba balle kace ko k'arya na shek'a maka, to Alhamdulillah Dr ai nan d'in dai asibitin Kane koh? dan haka duk ranar da zaka bada sheda ya zagayo ni da kaina zansa azo a tahomin da kai ka kafamin sheda, Yanzun kuma sai kasan maganin da zaka bashi wanda zai d'auke mishi sha'awar har ya ririta ta yaje ya sauke ma wancan matar nashi ita na k'arfen ita kuma jikata tunda Allah ya mata gata har tayi dakon igiyoyi uku na aure tsayin shekarun nan ba tareda ta tsallake sirad'in auren ba aini abun inje in siya dabino in raba sadaqa ne dan jama'a su taya mu murna, kai Jama'a! kai Jama'a!! Ke takwara wannan mijin naki tabbas kiyayyar shi gareki bayya nan niyace, Ashe mu ya maida yan iska ni ina can ina ta kissima cewar ko kishiyace ta shiga tsakanin ku yo ashe shi kam rass yake da lafiyar shi da komai, to aiko tunda har rashin kauna takai haka ni nan zan nuna ma kowa na isa tashi mu tafi" Ta k'arasa fad'a a fusace tana mik'ewa, "Hajiya kiyi hak'uri ki zauna dan ban gane me yake faruwa ba?" Tarar numfashin shi tayi da cewa,,, "kaga duk tarin tambayoyin ka gara ka nemi littafi ka rubuta in yaso inshi ya tashi sai ka jero mashi su ya baka amsa, ni kam na riga na samu amsar abinda na d'ade ina nema a wajen ka, kana iya kiran yan uwan shi suzo su zauna dashi mu mun tafi" Cike da dumbin mamaki Dr Mubarak ya raka hajiya data rike hannun Meenal dam kamar wani ne zai kwaceta a hannun ta har suka bar office din yana bin su da kallo ne kawai kanshi a d'aure, Kenan idan ya fahimta dai dai duk wannan shekarun Sarki bai tab'a kusantar yarinyar nan ba kenan? To me yasa? Ganin bashi da mai bashi amsa dole ya mik'e ya fito dan yana buk'atar tabbatar da cewa tafiyan zasuyi kamar yanda Hajiya tace ko kuwa, Hajiya ko suna fitowa daga office din ta samu AK da Sa'eed a bakin kofar d'akin Sarki, hakan kuma yayi dai² da isowar wasu daga cikin kannin Sarki mata da maza, in baku manta ba dama akwai hidimar bikin da akayi a gidan nasu Sarki kuma bawai an gama watsewa bane, Hajiya bata saurari kowa a cikin su ba taci gaba da jan hannun Meenal zuwa waje, sai da suka kusa kulewa sannan ta juyo, "Kai Abdul Khareem kazo ka tukamu mubar asibitin nan in kuma baka tashi ba mu k'arasa titi mu samu abun hawa" Tana kuma gama fad'in hakan taja hannun Meenal suka fice bata jira jin ta bakin shiba, duk juyawa sukayi suna bin ta da kallon mamaki sai dai babu wanda ya iya tankawa a cikin su, Sallama yayima Sa'eed shima ya take musu baya, dan yasan indai Hajiya ce tsaf zataje ta nemi wani abun hawan suyi tafiyar su su barshi a asibitin. Hakan kuma bazai hana ta d'ibi laifin duniyar nan ta jibge mishi ba.... Sorry yau dai page din ba tsayi aci da hak'uri ayi bacci🥰 *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY }}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ``````Page42.... A bakin motar ya same su tsai-tsaye, Hajiya dai sai uban gyacci takeyi bala'i na cinta, dan sosai ranta ya b'aci da bayanin da Dr ya mata cewar Sarki ciwon sha'awa ke damun shi. Sanin cewa infa ya kulata suna iya raba hali a titi yasa baice mata ci kanki ba sai ma bud'e musu kofofin motar da yayi shi kuma ya koma mazaunin direba ya kunna motar suka fice daga harabar asibitin, " kai Jama'a ke takwara amma ban tab'a sanin mijin ki digirgirarren mara mutunci bane sai yau, wallahi da ace ba'a gabana likita ya rattafo jawaban nan ba dad'e duniya babu abinda zai hana in karyata duk uban da zai kawo min labari koda ko kece, ace ni ina nan a gefe ina ta mishi kallon tausayi ina mishin kallon mijin da mata tayi ram dashi sai yanda taso take juya mishi akalar rayuwa, dan mak'iyin uban shi ashe qalau yake tsayin shekarun nan ya kafe min jika a gida Bata da aiki saina gyaran gida da girki, matan aure nata haihuwa ita ko ashe ko tsallake sirad'in farko batayi ba! " Sai da ta tafa hannuwa cike da jimami dan fa sosai abun ya dake ta, bata tab'a tsammanin hakan ba, dan haka ta ci gaba da cewa.. "To ni yanzun laifin wama zan gani? Iyii laifin iyayen ki da suka dauke ki suka mik'aki gidan shi a zaton su na samar miki sauk'i akan lalurar da Allah ne ya aza miki ko kuma shi sokon da aka wanke mishi yarinya d'anya shakaf aka mik'a mishi amma ya wofantar, Oh ni Ameenatu yanzun ashe da banyi tsayuwar daka wajen nema miki maganin ciwon maran nan naki ba da tuni ashe kin dad'e da zama gawa, to gawa mana jama'a tunda dai likita ya tabbatar musu cewa da an miki aure kin fara kwanciya da miji ciwon zai gudu, Ni wallahi ba abun inyi Allah ya isa ba to ban san ma katamam men wanda ya dace da Allah ya isar nawa ba, Iyayen ki da suka miki auren cushe suka mik'a min ke inda ba'a tab'a kallon ki da daraja ba koshi mijin daya ajiyeki a gida ya maida min ke baiwa, to duka dai ko ban fad'iba dama sai Allah ya saka miki cutar da aka miki,na tabbatar da ace Vida kike tsayin shekarun nan Allah yasan kalar mazajen da zasu dunga gware wajen fafutukar neman auren ki, yanda kike tsoka d'aya a miyar nan ai ba k'aramin mai sa'a bane zai tsamoki wallahi, ni kuma sai na tankad'e su na rairaye kafin in tayaki zab'ar dankwalele a cikin su" "Hajiya dan Allah kiyi hak'uri kiyi shiru, nidai tunda kin san komai kawai kisa ya sakeni, in baya sona nima ai ba son shi nikeyi ba, lokacin da akayi auren da ace na bujure ai kowa gani zaiyi kamar bani da tarbiya, to da bani da hakki ba ga abinda ya biyo baya ba" Katseta Hajiya tayi da cewa.. "Yo ke yar nan har sai ma kin fadamin yanda zanyi? Ai an daiyi d'aya ba k'ari wani lalacewar ce ta sameni dazan zuba ido ina kallo ki koma gidan nan kici gaba da zama kamar wata hoto, ah ah wallah anyi na farko kuma na k'arshe ba k'ari na baya ma allah yasa ya zame miki kankaren zunubi ya kuma baki ladan zama" Sai kuma tamai da Hankalin ta kan AK, "Kai dan mai karfi kaji min wani bala'in da yake neman yimin karan tsaye a rayuwar jika?kana fa jina tuntuni ina sababi inba zaka sanya baki ka tayani jimami ba ina laifin ka bani hakuri tunda dai kasan an b'atamin! " Bata jira ya amsa ba ta d'aura da cewa, "Wai shi wancan sojan mijin nata da muka kai asibiti ne likita yace min wai ciwon sha'awa ke damun shi, kaji min wani zunubin ganganci wajen marar rabon can fa, mai mata kamar jikata a gida, amma ya iya zuba mata ido tsayin shekarun nan" Gefen titi ya gangare da motar sai da ya kasheta sannan ya juyo, Kan Meenal ya fara jefa kallon shi sai yaga ta juya fuska tana kallon waje ta window din motar a yayin da ta kudundine a cikin hijjabin jikinta, sannan ya maida kallon shi kan Hajiya bayan ya d'aure fuskan shi sosai, "Hajiya wai ke mai yasa kika fiye son shiga cikin abinda babu ruwan kine?" "Kai dakatamin dan Allah" Hajiya ta fad'a tana katse shi, "Karfa kace zaka fad'amin maganar banza akan abinda kowa yasan akan gaskiya ta nike, Ana fa magana ne akan rayuwar auren jikata au kenan wato tunda ni nazama tsohuwar kawai so kake in koma gefe in rungume hannun inci gaba da kallon yanda rayuwar jikata zaiyi ta walagigi, ita ba budurwa ba ita ba zawara ba ita kuma ba cikakkiyar macen aure ba, To wallahi kayi ta kanka domin kasan ni dai ko kaine ka auro mace ka ajiye yar mutane a gida babu sauke hak'k'i ni mai iya mata jagora ta maka ka a kotune a nema mata hakkin ta balle kuma rayuwar jikata mace ake magana, dan haka bawai ra'ayin ka nike nema anan ba yita kanka kawai, to nima in banda abuna ma miye nawa nasaka a cikin zancen cikakkun mutane kaida ko tsayayyar budurwa baka da ita mtws" Ta karashe da jan tsaki.. "Koma dai menene karki shiga batun nan balle kice zaki raba shi da matan shi" "Kai kaci uban ka, har nice zaka fad'ama abinda zanyi?" "Amma Hajiya ai baki san hujjan shi nayin hakan ba koh," "A zaton ka har wani hujja gareshi wanda zan tsaya nema?, to nikam koda hujjar ko babu magana taje karshe wannan aure a yanzun kam yazo karshe indai ina raye zanyi tsaye wajen kwatoma jikata hakkin ta" Sanin da yayi cewar duk fa abinda zai fad'ama Hajiyar ba lallai ta fahimta bane yasa shi kunna motar sukaci gaba da tafiya, "Gidan ta zaka mai damu ta kwashi kayan ta mu wuce tare dan ta gama kwana a shegen gidan can" Dara dam dam haka zuciyar ta wani irin bugawa, Taya ma shida yaketa kokarin K'ara nesan ta kanshi da yarinyar nan Hajiya zata ce wai gidan ta zata koma, A fili ko sai ya ce "Amma Hajiya tun kafin mu taho na fad'a miki cewa inada nawa uzurin nima, in kin matsa sai tabar mishi gidan aiga gidan su nan a cikin unguwan ta koma can ta zauna mana miye kuma kice wai gidan ki zata koma da zama, bayan ga iyayen ta a raye, ki tuna cewa kafa Kakarta ce kawai! " "Sannu ubana! Eh nace sannu ubana!! to bata komawa gidan nasu kafata kafarta, in kuma ni ban isa insa ka abu kayi ba kana iya juyemu ko anan tsakiyar titi ne kayi tafiyar ka, Kaga ka fita a idona in rufe fa, tunfa da nace ka kaini gidan ta kakemin kananun kunkuni, naga dai ita shegiyar motar tun kan a haifo uwar ka nike shiga ina tuk'awa balle kamin tijara," "Eh koma mai zakice sai dai kice amma ni bazan je inyi jira da sunan d'auke matar wani bayan mijinta yana asibiti kwance ba, nama zama babban banza kenan zan dai sauke ku ai itama tana da mota sai kuyi amfani da natan kuje duk inda zaku" Sosai Hajiya ta dunga sababi yanda kuka san ko shi AK ne Sarkin daya b'ata mata rai, kamar yanda ya fad'adin kuwa yana sauke su bai b'ata lokaci ba ya juya yabar unguwan, Sai da yayi nisa da unguwar sannan ya nemi gefen hanya a kofar wani shago ya faka, bude kofar motar yayi ya fita ya k'arasa cikin shagon, bai bata lokaci a ciki ba ya fito da ruwan gora mai sanyi a hannun shi, yana kawowa wajen motar ya bud'e murfin gorar ya jefar, d'aga kanshi sama yayi ya fara duldula ruwan a cikin bakin shi yana shan ruwan, sai da yasha kusan rabi sannan ya dan duk'a kad'an ya maida gorar ta saman kanshi yaci gaba da duldula ruwan akan shi yayin da ruwan ke gangarawa har cikin jikin shi, jifa yayi da goran a gefe bayan ruwan ciki ya k'are sannan ya bud'e kofar motar ya shiga ciki yana faman sauke ajiyar zuciya a jejjere kamar wanda yayi wasan tseren gudu. "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un³, waiyo Allah zuciya ta" Ya fad'a yana danne zuciyar nashi da yake jin tana mishi zafi sosai ta ciki da hannun shi, "Waiyo Allah na wai me yake shirin faruwa dani ne? Me yake damu na ne? Astagfirullahi ya Allah na tuba ka yafeni, ya Allah kayi min maganin damuwa ta, Allah ka san wahalar da nike sha alhalin tana nesa dani, mutuwa kawai zanyi inta dawo kusa dani, bazan iya rike abinda nike ji yana min yawo a cikin jini na akan taba, Allah ka kawo min mafita na alkhairi, Allah karka bani ikon sab'a maka wajen aikata aikin ashsha, waiyo Allah zuciyata " Ya k'arasa fad'a hawaye na gangarowa daga cikin idanun shi zuwa kan fuskar shi,gwanin tausayi, in wani yace soyayya zai narka zuciyar *ABDUL KHAREEM AHMAD MAI JAMA'A* Har ma ya zubda hawaye tofa ko duniya ba lallai su yarda da hakan ba, amma ku kalle shi yanzun yanda ya koma cikin dan kankanin lokaci wai a hakan ma dannewa yakeyi. ****** Ku sani cewa ita soyayya ba k'irk'iranta akeyi ba, Asalima itace takeyin kanta, Haka zalika idan ta fad'awa *Mace* ko *Namiji* mai rauni ba'a jimawa in ba'ayi dace ba tofa sai dai ku tsince *shi* / *ta* a wani kalar mawuyacin hali, domin ita soyayya babu ta inda bata iya kutsawa dan ganin ta girgiza rayuwar maiyin ta, *Soyayya* ba kamar bacci bane da zaizo maka ba tareda *ka*/ *ki* n san yazo ba. Ita *soyayya* aduk inda zata shiga tofa saita sanar domin saita tab'a duk wani abu mai mahimmanci dake tare da *ke*/ *kai* tun daga kan *zuciya*, *lokaci*, *tunani*, kai in ba'ayi dace ba tana iya taba harda ma lafiyan maiyin ta, in ba'ayi sa'a ba sai ku tsinci mutum a dawanau yana shan magani. *kai* ko *ke* babu wanda yafi yafi karfin soyayya domin ita ba shawara take nema ba a yayin kasantuwar ta, afkuwa kawai takeyi a sanda maiyi baiyi zato ba, *ita soyayya batayin duba da matsayi*, *arziki*, *nasaba* ko kuma wani abu makamancin hakan yayin afkuwarta, Abu d'aya tafi dogara akai shine *silar faruwan ta*, A zaton AK mutum shike zab'ar ma zuciyar shi abinda zata so dama wacce bai kamata taso ba, a nashi hasashen gani yake cewar shine zai zab'ama kanshi kalar macen daya kamata yaso, ana shi ganin zuciyar shi tana da karfin da zata iya kare kanta daga ko wani irin harin soyayya da wata zuciyar ka iya kai mata, Ya dad'e yana taka tsantsan, ya dad'e yana kokarin kare zuciyar shi daga cutar daka inya janyo mishi rauni ko fad'uwa, ya dad'e yana ikirarin cewar shi yafi k'arfin so, *me akayi akayi soyayyar ma da har shi zata nemi hana shi sukuni* Sai dai kuma takan tsan tsan, wayau da dubarun shi basu canza komai ba na daga cikin kaddarar da Allah ya tsara mishi akan *Soyayya*. Wanda hakan ya zama abun bakin ciki a gare shi wanda yake da tabbacin cewa duk fa ranar da asirin shi ya tonu tofa hak'ika shike da jin kunya, domin a bin takaici ne ace soyayyar ta fallasa aka k'aramar yarinya, Yayi iya bakin kokari wajen danne abun a zuciyar shi ya kuma hana kan shi kusan ci da abar son nashi a yunkurin shi na yakice son, A sanda abar son nashi ta kucce kuma sai yayi zaton cewar ai hakan ma nasarar shice koba komai zai iya kiran hakan da *TA FARU TA K'ARE* tunda bai fallasa halin da yake ciki ba balle kunyar duniya ta dame shi, Sai dai kuma mai makon samun sauk'i sai yawan tunani ya kunno mishi kai domin a kullum inya zauna bashi da abin tattaunawa da zuciyar shi sai hasashen wani hali ita abar son nashi take ciki a inda aka mik'a ta, Sau dayawa tausayin ta kan kama shi harma yakan ga laifin kanshi na cewa mai yasa a lokacin baiyi kwani yunkuri ba! Mai yasa a lokacin ya gazayin yak'i akan abar son nashi, yasan da yayi yak'i inda rabo a lokacin data zama nashi, inko ta zama nashin Koba komai zata kasance cikin farin ciki inya zamana cewa a *Gidan shi* take ba a gidan wanda bai san darajar taba, Haka dai yayi ta fama wajen ganin ya yajice yawan tunanin ta domin abinda yake da tabbaci akai shine *Soyayyar ta* ba kamun wasa tayi ma zuciyar shi dazai iya cirewa kai tsaye ba, Sai dai yakan gode Allah akoda yaushe domin a dalilin ta shima ya d'andana d'aya daga cikin gefen soyayya mafi kuna, wato kaso wanda baima san kanayi ba, kai kuma bakama san ta yanda zaka nuna mishi son ba, Hakika ya yarda yana cikin jarabawar rayuwa mafi zafi a zuciya, Dan babu abu mafi ciwo irin kaci gaba da son abinda kasan ba zaka tab'a samu ba, mafi hatsarin ma shine *Soyayyar Matar Wani* yayi azumi ! yayi sallah !! yayi salati!!! yiyi rok'o zuwa wajen ubangijin al'arshi akan ya cire mishi ita a zuciyar shi amma ko abun yayi sauk'i da zarar ya ganta tofa sai ciwon nashi ya dawo sabo fil, Hakan nema yasa gaba d'aya yake k'aurace ma duk wani abun da yasan zai ha'dasu, A da can baya yakan ji fasuwar kai da alfahari aduk sanda yaga mata na bibiyar shi da k'okon barar Soyayyar su. Hakan yakan sashi alfahari har yake jin girman kai a ganin shi ai mata sune ya dace subi shi domin dai babu abinda ya rasa a cikin abubuwan da mata keso, Amma a yanzun sosai yake tausaya ma matan yakan kuma zaunar dasu ya fad'a musu cewar suyi hak'uri, yanda sukeji akan shi shima d'in yana jin sama da hakan akan wata, tunda kuma ya rasata ya yardar ma kanshi cewa a fannin soyayyar ne bai da sa'a dan haka ya K'ara kulle zuciyar shi gudun karma wata zuciyar ta k'ara samun damar shiga dan zuciyar shi tana iya tarwatsewa in hakan ya faru. Shi da yake ta bakin kokarin ganin yaba komai baya fisabilillahi shine kuma kwatsam wai Hajiya ke shirin kwaso yar mutane ta kawo gidan da yake rayuwa ta ajiye bayan tasan abu mai mahimmanci ne ya zaunar da shi a garin nan bai wuce kan nashi harkokin ba, Shifa bawai bak'in ciki yakeyi ko kuma murna ba, ah ah halin dai dazai iya kasancewa a ciki yake tsoro, domin yasan a cikin su uku shine zaifi cutuwa a yanzun. Bai bar wajen ba har sai da ya samu kira daga Yusuf wase cewar yana gida yana jiran shi. ***** Koda AK ya sauke su ciki suka shige, "Maza shiga ciki ki harhad'omin duk wani abun da kika san zaki buk'ata anan kusa," "To" Meenal ta amsa dashi sai dai kuma a yanayin ta kai tsaye bazaka iya fassara halin da take ciki ba, sai dai kuma gaba d'aya bata da kuzari, Tsaf Hajiya ta taya ta suka shirya kayan tun daga kan takaddun karatun ta, kayan ta na sawa dama sauran su, saida suka cika bayan mota taf da kaya sannan Hajiya ta kaso wutar gidan ta kuma kulle duk d'akunan da kayana Meenal suke ta ciro makullayen suna shirin fita a gidan ne shigowar uwar gida ya tsaida su. **** Abinda ya faru a can asibiti kuwa bayan fitan su Hajiya kananun maganganu ne suka fara tashi, a cewar su taya ita Meenal a matsayin ta na matar shi daya kamata ta tsaya akan shi zata tsallake tayi tafiyar ta, To abun gulma dai baya kad'an dan haka tuni suka fara kiraye kirayen waya suna kai rahoto, Haka sukaci gaba da zaman asibitin har zuwa sanda itama uwar gida ta iso asibitin tare dasu Innar yara, "Ina Meenal?" Innar yara ta tambaya dan su basu san cewa bata asibitin ba, Tsagal d'aya daga cikin kannen Sarkin wanda suke uba guda ta bata amsa da cewa, "Meenal tunda muka shigo nan ko zama bamuyi ba suka fice anan ita da kakarta har yanzun kuma bata dawo ba" Amsa mata Innar yara tayi da cewa, "to kila dai taje d'auko wani abun a gida ne, kuma ai ko tana nan din ma dama ba wani abun zatayi ba tunda ga yayan su," Duk wannan surutun uwar gida bata tofa musu kalma ko daya ba, tun bayan gaisuwar da sukayi ta tambaye su mai jiki suka amsa mata ciki suka lek'a suka iske shi yana bacci shine dalilin da yasa suka dawo nan d'in suka zauna, "Sa'eed ka samu ganin Dr Mubarak din ne?" Uwar gida ta tambaya, "Ah ah ban samu ganin shi ba domin lokacin dana iso yana tare da Hajiya innah da Meenal," "Muje ka rakani ina son ganin shi" Ta fad'a tana mikewa, Tashi suma kannin sarki sukayi da niyyar rufa mata baya. "Ku zauna bana buk'atar rakiyar ku, muje Sa'eed" Komawa sukayi suka zauna din badan sun soba dan tabbas sunso suje su jiyo abinda yake damun shi, Jagora Sa'eed ya mata zuwa office din na Dr sun iske shi yana ta faman cike ciken wasu takaddu, Da sallama suka shiga bayan nocking din farko da Sa'eed yayi Dr ya basu damar shiga, Mikewa yayi daga kan kujerar da yake zaune yana ma uwar gida barka da zuwa, "Kai Sa'eed haka akeyi? Ya zaka wahal dasu su taho bayan nace maka suma wadancan ka sallame su su koma gida dan shima insha Allah ina saran daya tashi zamu bashi damar komawa gida," "Kai DR kamar baka san halin suba, kaima kasan bazasu zauna ba" Sa'eed ya bashi amsa. "Ba laifin shi bane likita, ai gara muzo dai muga halin da yake ciki dan Babana ba gwanin ciwo bane nasan ba abu kad'an bane zai kawo shi kwanciya asibiti" "Bismillah to ku zauna" Zaman sukayi kamar yanda ya buk'ata, "Meke damun shine Dr?" Numfasawa yayi sannan ya maida duban shi kan Sa'eed,, "Dan bamu waje ina son magana da ita! " "Babu buk'atar fitar nashi domin da Sarki da Sa'eed duka yara nane, kuma Sa'eed ba yaro bane balle inyi fargaban cewa in yaji wani abun zai yad'a a waje, dan haka fadamin meke faruwa kanka tsaye karka boyemin komai" Kamar yanda ya korama Hajiya bayani haka ita ma ya fada mata silar ciwon na Sarki harda abinda Hajiya ta fad'a mishi kafin taja Meenal su bar asibitin duk sai da ya kora mata komai daya faru, "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un³ abinda yaron nan ya aikata kenan,? " Shi kawai uwar gida ta samu damar cigaba da maimaitawa, yayin da shi kuma Sa'eed mamakin maganar yayi mashi mugun dukan daya koma kamar hoto sai kallon Dr Mubarak kawai yake cike da mamaki,,, "Nagode Dr" Uwar gida ta furta a yayinda ta mik'e, tana gama furta hakan kuma ta fice Sa'eed na take mata baya, "Ku tashi mu tafi jikin nashi da sauk'i Dr yace da zarar ya farka zasu sallame shi," Haka ta tasa k'eyar su duka sai Salman kawai aka bari k'anin Sarki ne shi din, Tace mishi ya zauna in Sarkin ya farka sai su dawo gida tare, Bayan dawowar su kowa gida ya shiga amma ita kai tsaye gidan Sarkin ta wuce, Tayi sa'a tana shiga motar Meenal na shirin ficewa daga gidan, wanda ganin uwar gidan ne yasa Meenal din daka tawa tana fad'ama hajiya cewa "ga maman Ya Sarki nan" "To me zamuyi mata, ko sunje asibitin ne basu ganki ba ta biyo dan taji dalili, to ni ai dai dai nike da kowa kashe motan dan in samu bata sak'o da kyau atoh" Zagawa gefen da Hajiya ke hakimce uwar gida tayi, "Barka da yammaci Hajiya" "Barka kadai yame jikin?" "Alhamdulillah Dr ma yace zuwa anjima zasu bashi sallama saurin da nike tayi kenan dama in iske ku" "Allah sarki ai kuwa da kin b'ata lokaci bazaki same muba, ina fatan kuma shi likitan ya shaida miki komai kamar yanda nima ya fad'amin?" "Kwarai Hajiya na samu labarin komai, kuma banzo nan dan in hanaki tafiya da ita ba, nazo ne dai dan in banki hakuri wallahi ban san duk abubuwan da suke faruwa ba kenan tsayin shekarun nan, Kuma insha Allah tunda har ya nuna baya muradin ta ni nan da kaina zan amso mata takardar ta kamar yanda na zama silar had'a auren" "Ah ah to madallah! Madallah!! Abu yayi kyau dan dama nima shawarar dana yanke kenan, yanzun dai in Allah yasa ya rubuta sakin sai kibayar a kawomin can gidana, in kuma babu hali nima da kaina ina iya dawowa gobe in amsa tun da kince anjima zai dawo, kuma kiyi iya bakin kokarin ki ki hana iyayen su maza jin batun nan dan nasan tsaf zasu hana suce bazaiyi sakin ba, kuma in hakan ta faru nidai ba hakuri zanyi ba daga karshe ma ina iya ganin laifin ki wallahi tunda dai kece uwar shi, jikata dai hakuri iya hakuri tayi shi to allah ya bada lada ya kuma had'a kowa da rabon sa, ke Meenal tuk'a mota muje yamma na dad'a yi" Ficewa sukayi daga gidan ita kuma uwar gida ta karasa wajen masu gadi, Gargadi ta musu sosai akan koma waye yazo gidan karsu barshi ya shiga indai ba mai gidan bane, sannan karsu sake su fadama kowa cewar Meenal bata gidan....... *Ummiee Zaria*✍🏼 🥰🥰🥰 Son so my people [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ````` *Page 43*..... Bayan Uwar gida ta koma gida wayar Salman ta kira ta fad'a mishi cewar da zarar an sallame su su taho nan gidan ne kai tsaye bawai gidan Sarki ba, Sauran yaranta dake nan gida wadanda basu gama komawa nasu gidajen ba sun so su kawo suka akan dalilin da yasa Meenal tayi tafiyar ta tabar Sarki a asibitin a matsayin ta na matar shi, ganin suna son suga laifin Meenal din data biyema kakarta ta tafi, hakan yasa ta taka musu burki akan cewa ita ma Meenal din bata da lafiya ne shi yasa bata zauna ba, wasu daga cikin su sunyi Na'am da hakan wasu ko sun daijita ne kawai, domin dama dai ba komai ne in kayi zaka burge wani ba. Bayan isar su Hajiya gida, masu gadin gidan tayima magana suka kwaso mata kayan Meenal zuwa cikin sashen ta, dakin dake kusa da nata suka sa kayan, Ita ko Hajiya tun bata zauna ba ta d'auki waya ta fara kiran Turai (kakar billyn ya Sa'eed in baku manta taba). Babu b'ata lokaci bayan Turai ta d'auki wayar hajiya tace "Turai komai kikeyi dan Allah ki sake shi ki taho gidana ina buk'atar ganin ki da gaggawa" Bata tsaya jin ta bakin Turai ba ta yanke wayar, Hajiya Jummai ne ta shigo sashen da sallama. "Hajiya barkan ku da dawowa, ina daga falona naga ana sauke kaya daga motar Meenal shine ma yasa nace bari in taho in gani ko bak'i mukayi?" "Bari! Bari!! Bari kawai Jummai aini yau ni naga abinda yafi zare tsayi, ai dama ko baki shigoba nida kaina zanyi kiranki ki taho muyi jimamin tare, To gata nan dai na taho da abata gida tunda zaman gidan mijin ni dai banga ranar shiba" Tunda Meenal taji Hajiya zata fara rattaba zance ta mike tsam, ta haye sama, dan haka nan sai take jin zuciyarta Sam ba dad'i, "Banfa gane ba Hajiya! Auren nata ne ya mutu bayan barin ta nan gidan d'azun ? Ina ce d'azun nan tabar gidan nan, to koma warta gidan ne har akayi saki ko yaya?" "Ji Jummai da wani batu, toni in sakin akayi har zan damu kaina ne! Kawai mugunta da bak'in hali irin na soja mutumin nan yaje ya kafe min jika a gida yana kallon ta kamar hoto" "Banfa gane ba wallahi Hajiya" "Aifa Jummai ba ganewa zakiyi ba tunda ban miki bayani ba, ke dai nemi wajen zama dan in kin ji abinda ya faru kina iya yanke jiki ki fad'i," In kunga yanda Hajiya keyi zakuyi zaton wani k'aton zunubi Sarki ya aikata🤣. Wurjanjan haka Turai ta iso falon na Hajjaju ko damar yin sallama bata samu ba, "Innah lafiya kuwa meya faru kingan nifa haka na fito daga gida zuwa nan takalmi na wari da wari? wane ne ya mutu hala? dan daga yanda naji kina magana na tabbatar ba lafiya ba" Wajen zama Hajiya ta nuna mata da hannu batareda ta ce k'ala ba, Zaman ko tayi a gefen data nuna mata. "To masha Allah anan kusa dai gidan duniya kune kad'ai zan kira da shakikai na wadanda zan fad'amu duk wani abun da ke damuna in na kuka ne muyi tare haka ma in dariyar ce muyi tare, Nasan dai dukan ku baku manta yanda auren Takwara ta yar wajen Jidda ya kasance ba?" "Kwarai bamu mance ba" Suka had'a baki wajen bata amsa, "Masha Allah, kuna dai sane da yanda aka munafunce ni aka bayar da jikata har a kasa ranar aure ban samu labari ba sai da biki ya rage saura sati 3, ku biyun nan ku kukayi tsayin daka a sanda naso in botsare cewar ban yarda ayiwa jikata auren dole ba, kuka bani hakuri inaji ina gani aka d'auki karamar yarinyar nan aka aurama Soja mai mata harda yara 4 a lokacin dan kawai ya kasance dan uwanta" "Kwarai kuwa haka akayi" Turai ta fad'a tana kara gyara zaman ta dan sosai ta k'agu taji me ya faru. "To dai yarinyar nan a hakan kowa ya shaidane domin dai taba marad'a kunya wajen yima iyayen ta biyayya ta kuma amshi auren duk da bason mijin take ba, hasali ma ashe tana da wanda take so daban amma burinta nayin karatu yasa ta kasa bashi dama ya gabatar da kanshi, To ku bud'e kunne kujini da kyau, wai kun san cewa tsayin shekarun nan 6 da watanni da auren su amma shi mijin bai tab'a kusantar taba!" "La'ilah ha'ilallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, innalillahi wa innah ilaihir raju'un, lahaulah wala kuwwata illah billah to shi dama bashi da lafiya ne kuma ya yarda aka aura mishi ita, ko ya abun yake?" Jummai ta tambaya cike da jimami, ita ko Turai salati kawai takeyi tana sanar ma ubangiji, "Ke Innah wai wannan maganar naki gaskiya ko wasa?" Turai ta tambaya itama dan wannan batu kam ai yafi kama da tatsuniya, jama'a inba tatsuniya ba a ina za'a kaima namiji mace kamar Meenal ace wai shekara da shekaru bai tab'a taba, "To dai kuma zaku gama jimami ne ku fuskanci gaskiya, domin ni tun shekarun baya na san da batun, to a lokacin tsakani da Allah na ta'allaqa hakan ne da sharrin matar shi dan kowa dai yayi mata shedar tsafe tsafe, bayan na qara binciken ita Meenal din ta tabbatar min da cewa ko d'aki guda basu tab'a had'awa ba sai na fara neman musu maganin karin asiri dana tsarin jiki, Bayan ni na saki jiki cewar ita tayi musu amfani da maganin kamar yanda na fad'a mata ashe ita shashashan iya wanda na ware a matsayin nata kawai tayi amfani dasu sauran kuma ta ajiye a gefe, to nidai tun sannan ban K'ara tambayan ta ya ake ciki ba, tunda dai kullum na tambayeta ya suke zaune cemin take lafiya lau, to indai yanke muku zance, Ke Jummai ai wajen ki ta fara sauka data shigo d'azun daga makaranta koh?" "Eh kwarai kuwa wajena taci abinci tayi sallah ma kafin ta iso nan" "Madallah to ashe wai bikin da akayi na k'annen mijinta ita kishiyar nata tazo kamar yanda ta saba...... Kaf abinda ya faru a yau din na zuwan Teemah gidan da kuma komawar da tayi gida ta cimma Sarki ba lafiya dama abinda likitan ya shaida musu harda had'uwar su da uwar gida kafin su baro gidan meenal tsaf ta kwashe ta rattafa musu " Koda ta gama koro musu bayanin shiru tayi suma ta basu damar tofa nasu albarkacin bakin, "ku dakata ban san ko kun hango abinda ni nike hasashe ba,"jummai ta fada, "Me kike hasashe ne?" Suka tambaya suna kallon ta dason jin me hasashen nata ya k'unsa, "A nawa hangen sai nike ganin wannan abun fa ba haka banza bane ya auku, tabbas akwai wata a kasa, tunda tun farko dama kowa yasan cewar matar shi matsafiya ce, bakwa ganin kamar itace ta aikata wani abun ta yanda shi bazai tab'a jin sha'awar ita Meenal din ba?" Turai ne ta amsa da cewa, "Ah ah Jummai babu wani batun asiri rashin soyayya ne kawai tunda gashi har likita ya tabbatar da cewa ciwon sha'awa ne ke damun shi, ita dai Meenal din itace ya jingine tunda ai gashi nan baro baro cewa da lafiyar shi" "Banki ta naki ba Aunty Turai amma nima nawa maganar tana kan hanya, saboda dai komai kiyayyar da miji yakewa mace akwai ranar da in sha'awa ta kamashi dole zai ture zancen wannan kiyayyar a gefe ne ya nemeta domin itafa sha'awa bata san yaren rashin soba inba haka ba dan me ake cewa ruwan kashe gobara basai mai kyau ba, Ko kun manta ne cewa in ana son a shiga tsakanin ma'aurata babu ta inda ba'a bi, *misali* *Wasu zakuga an sakar ma ita matar warin jiki*, *Wata matar kuma jini ake sake mata* *Wata ko tsoron mijin za'asa mata ta dunga kallon shi kamar dodo*, *Shi kuma wani mijin a duk sanda yaje kwanciya da matar sai ya rasa kuzarin shi na d'a namiji ta yanda bazai iya kusantar taba*, *Ko kuma ita mace a mata asirin da in mijin yaje neman ta sai gaban ta ya koma irin na namijin ko kuma wajen ma ya shafe gaba d'aya*, akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dashi wajen dakushe alaqar aure tsakanin mata da miji, To ita dai Meenal din ina ganin in ba'a samu daya daga cikin abinda na lissafa a kanta ba to sai dai insha mijin ne akayi nasarar cire mishi sha'awar ta a duk sanda yake tare da ita.bari in kira Meenal din muji ta bakin ta" "Meenal" Hajiya ta kwalama kira, Jin shiru bata amsa bane yasa ta kiran Larai, "Larai haura sama ki kiramin Meenal ku sauko tare" Taren ko suka sauko. "Meenal zoki zauna anan tambayar ki zanyi" Hajiya Jummai tace, Zaman Meenal tayi kamar yanda ta buk'ata, "Ke takwara ina fatan dai baki kira kowa kika shaida mishi cewa kina gidan nan na d'auko kiba koh? " Hajiya innah ta tambaya tana kallon Meenal din. "Ban fadama kowa ba" "To kin kyauta ma kanki, kuma ki jini da kyau koda uwar kice ta kiraki bance ki d'auka ba dan nasan suna samun labarin bakya gidan zasu fara kira suji ba'asi kin san kuma ba uzuri zasu miki ba iyakacin suce ki koma, in kin koma koh kin san abinda kika baro nedai zaki tarar dan yanda shi mijin bai damu dake ba suma iyayen naki bana tunanin sun damu dake tunda har suka iya banzatar dake tsayin shekarun nan babu wanda a cikin su ya damu da sanin yanda kike rayuwa a gidan mijin da suka zab'a miki, gaba d'aya ma sun manta cewar auren dole suka mashi, to wallahi kinji dai na fad'a miki dan haka ko malam nema ya kiraki karki sake ki koma, in kuma kinsan kasa zaki watsanin a ido kina son mijin ki to tun kafin dare yayi ko kuma kizo daga baya ki kullaceni gara ki shaida min gasu Jummai nan su mai dake gidan ki atoh, dan ku yaran yanzun wani abun za'ayi dan a muku gata ku kuma sai kuga kamar cutar ku akeyi" "To ni Hajiya nace miki zan koma ne dama?" "Baki ceba amma ai gara in kara tabbatar wa a gaban su Jummai dan sumin sheda in magana ya tashi dan yanzun na tabbatar laifin duniya akaina kowa zai daura gani zasuyi kamar nice keson kashe miki aure, nasan babu wanda zaiyi la'akari da zaman da kikayi a gidan ba tareda wani abu ya gifta tsakanin ki da mijin ba, Kaini ai nagode allah da Allah yasa kaf cikin yarana da jikokin babu dan iska, Ku duba ku gani fa yanzun dan Allah in wata yarce aka ma irin auren nan hakan ya biyo baya mai kuke zaton zai faru? Ai wallahi tikitin iskanci ta samu kyauta, sai gashi jikata ko karar shi bata tab'a kaiwa wajen wani dan ya danne mata hakki ba, matan yanzun da ko mijin suka samu baya kai musu yanda suke so sai dai ku tsinci maganar a kotu anje gaban alkali batun kashe aure, in Kuma hakan bai samu ba shi kenan sai mace ta fara rab'e rab'e tana bin wasu mazan, allah dai ya shirya mana zuria" Ameen duk suka amsa mata dashi baki daya. "Meenal nace wani irin zama kikayi da mijin ki tsayin shekarun nan? So nike ki fad'amana komai bakin gaskiyar ki munan dukan mu babu wacce bazatayi tsaye wajen kwato miki hakkin kiba in munga za'a tauye ki, Fad'amin shi din kina jin tsoron shine shi yasa koya neme ki bakya yarda ko ya abun yake" Jummai ne ke tambayar ta. "To aini bai tab'a nema na ba wallahi, abinda shekarun baya ma ko sashena baya shigowa daga baya nefa inya shigo ya fadamin abinda yake buk'ata sai ya koma d'akin shi," "To ke da baya zuwa mai yasa bakya binshi can nashi d'akin?" "Kai" Meenal ta fad'a tana zaro ido waje, "Eh baki san in miji baizo inda mace take ba ita macen ba laifi bane dan ta bishi, ai babu laifi akan hakan ko kin tab'a zuwa ne ya koroki?" "Ah ah ni gaskiya ban taba zuwa ba, Kuma fa ko abu yace in kawo mishi da nakai yake cemin Ina iya tafiya" "Kenan dai kina so kice baku tab'a samun kusanci dashi ba kwata²? " "Eh gaskiya bamu tab'a ba" "To me ya faru ayau da har yayi sanadin da ciwon shi ya tashi tunda dai likita yace ciwon sha'awa ne ya kama shi" Shiru Meenal tayi ba amsa. "Karkiji kunya ki fadamin gaskiyar abinda ya faru" A daburce ta fara ba da labarin yanda ta iske shi a kwance a kasan tile's yana murgine murgine dama yanda yaso kusantarta tak'i duk da bawai ta bud'e musu komai bane amma haka take magana kunya duk ya gama rufe ta. "Tashi ki koma d'akin ki" Jummai ta bata umarni bayan ta gama sauraren ta, aiko kamar jira take dama domin tuni tayi bacewar b'at a wajen. "Kun fahimci wani abu a labarin ta" "Yo mu me zamu fahimta ko , bayan kinsata a gaba kina mata tambayoyi irin naku na tsofaffin lauyoyi," Cewar Hajiya Turai, Yar karamar dariya Hajiya tayi sannan ta d'aura da cewa, "Kamar dai yanda na fad'a muku ne d'azun ni nafi zargin akwai shiga tsakani a zaman auren yaran nan to hakan ne, domin dai a bayanan ta na gane cewar kwata kwata shi mijin nata baya son kusanci a tsakanin su, yanzun Kuma da aka samu canji ina da tabbacin cewa tabbas akwai inda aka samu tangarda kodai asirin ya karye ko kuma an canza sabon salo," "Ba shakka hakan yana iya zama gaskiya, to yanzun wani mataki za'a d'auka?" Turai ke tambayan Jummai. "Da farko dai zanso a fara kokarin karya komai dake tareda mijin, sannan sai a d'aura shi akan magunguna na kariya, koda yake magani baya aiki sai mutum ya had'a da addu'a gashi shi kuma bamu san ya yake ba wajen kula da ibada, babbar damuwar ma yanzun yanda Hajiya ta d'auko Aminatu daga gidan ta, kunga koba komai da tana can komai zaifi zuwa mana a sauk'ake," "Ko yanzun bazai gagara ba dan jikata dai na d'auko kayata kuma bata komawa gidan nan, magani kuma tunda dama nayi niyya da zuciya d'aya nida kaina zai kai in damk'a a hannun uwar shi ita sai tasan ta yanda zatabi dashi har yayi amfani dashi, saki ne dai sai ya saki takwara ta karma kowa ya bani hak'uri" "Aunty Turai bakice komai ba" "To me zance Jummai bayan aikin gama ya riga ya gama! Tunda tace sai yayi sakin ai sai muyi fatan ita yarinyar Allah ya mata canji na alkhairi shi kuma allah yasa iya wahalar kenan, ita kuma matar indai ya tabbata ita keda hannu allah ya shirya ta" Sun tattauna sosai kafin taron ya watse, *** Salman bai d'auko sarki sun dawo gida ba sai bayan ishsha'i zuwa lokacin kuma jikin na Sarki alhamdulillah sosai yaji sauki kamar ma bashine aka kwasa ranga ranga zuwa asibiti d'azun ba, D'akin shi dake sashen Teemah ya shiga sai da yayi wanka sannan ya samu damar jero sallolin da ake binshi, Ba kowa yasan yana gidan ba sai iya yan d'akin su, sai da uwar gida ta tabbatar yaci abincin da tasa aka kai mishi ya kuma huta sannan taje d'akin ta same shi. Bayan sun gaisa ta mishi ya jiki ya kuma amsa mata da jiki yayi sauki ne ta miko mishi takarda da biron dake rike a hannun ta wanda dasu dama ta shigo d'akin, D'aure fuska tayi sosai dad'e duniya bata tab'a sanin yanda akeyin dariya ba. "Sufyaan ³" Sai da ta kira sunan shi sau uku yana amsawa da "na'am" Sannan ta daura da cewa, "A duniyar nan kana da wata uwa data fini matsayi a wajen ka?" Duk da yanda zuciyar shi ke dakan lugude bai gaza amsa mata da cewa.. "Babu Hajiya" "Da kyau, kenan ina da ikon da zansa ka abu kayimin kenan?" "Kina da ikon kisani komai kike so inyi miki shi kai tsaye Hajiya indai hakan bai sab'awa shara'a ba" Kara bata tayi sosai alamun ba wasa, sannan ta matsar mishi da takardar da biron zuwa gaban shi, "Gashi nan sau nike in k'ara baka umarni kamar yanda na baka a lokacin da naso auren ka da yar uwar ka, yau ma ni din dai mahaifiyar ka ina mai baka umarni daka rubuta ma Aminatu takardar saki, domin yanke alaqar auren dani nayi silar had'ashi a tsakanin ku daga k'arshe kai kuma ka nuna min ban isa ba dalilin hakan ka ajiye yar mutane a gidan ka tsayin shekaru ba tareda ka tuna hakkin auren ta dake kanka ba, dan haka yauni zan sauke maka nauyin daka kasa d'auka, rubuta mata sakinta yanzun ka bani, bakuma nason saki d'aya ko biyu saki uku reras nike so ka zana a takardar gaban ka ka miko min nan, inyaso gobe sai ka had'a kayan ka kabi bayan matar so, na kuma gode maka allah ya saka maka da alkhairi ubana, ni dai bazan tab'ayi maka baki ba sai dai ina son in tuna maka cewa kana da yara mata gasunan saiti bida bi har su uku, ina fatan kar zunuban ku kaida uwar su ya shafi rayuwar su" Shiru gaba d'aya Sarki ya d'auke wuta dan bai tab'a hasaso ko tsammanin zuwan wannan ranar ba. "Ya ina magana dakai kamin shiru?" "Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri ki gafarceni, insha Allah na miki alkawarin gyara tsakanina da ita, karkice in saketa ban san da wani idon zan kalli Baba Malam ba........ Kuci shi da hak'uri in anci karo da mistake a tsallake dan banyi editing ba, *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ```` *Page 44*..... "Dan Allah Hajiya hakuri ki gafarceni,nasan ni mai laifine a gareku,na kuma cancanci amsar hukunci daga gareku na abinda na aikata,amma insha Allah na muku alkawarin gyara tsakanina da ita,zanci gaba da zaman aure da ita a matsayin cikakkun miji da mata, ina rok'on alfarman ku karkuce zaku shige gaba wajen raba auren nan, in hakan ya faru ban san da wani idon zan kalli Baba Malam ba." Katse shi uwar gida tayi a fusace jin wani sabon salon rainin wayau da yake shirin bijiro mata dashi, inba rainin wayau ba da can daya ajiye d'iyar mutane a gidan nashi ya kuma wofantar da ita da wani idon yake kallon iyayen ta? "Oh sai yanzun ne ka tuna da wani idon zaka kalli shi wanda ya baka ita a matsayin matar?, Ka daiji kunya wallahi Sufyaan ka fad'i kasa ba nauyi, a zatona koda ace ni banci darajar haihuwar kaba shi Malam zai iya cin darajar da Allah ya bashi na zamowa tamkar uba a gareka duk da cewa bashi ne ya haifeka ba, yarinyar nan kowa ya shaida kaunarta da Malam keyi amma a cikin jerin maneman da suka fito neman auren ta duk ya shallake sauran ya baka ita, Kasan tsayin shekaru nawa mukayi nida mahaifin ka mukayi muna bibiyar shi akan ya baka auren ta kafin ya amince? Nayi zaton cewa ba Aminatu da take matsayin yar uwa kuma kanwarka ba koda ace acan gefe na koma na d'auko maka wata nakasasshiya kai mai tara hannuwan ka bibbiyu ne ka amsa ka kuma riketa da amana, Kullum akayi haihuwa a cikin Dangi sai anyi batun Aminatu wasu na ganin cewar Allah ne bai kawo nata haihuwar ba yayinda wasu suka ta'allak'a rashin haihuwar nata da tsarin rashin haihuwa takeyi, Surutai babu irin wanda ba'ayi ba yakai tun anajin kunyan ayi shi a gaban makusan ta sai gashi ya koma harta da uwarta mahaifiya bata tsira ba, Kasan meye abun takaicin? Ni din nan da kaina nasha zuwa inje in amso taimakon neman haihuwar in kai mata har gida, wanda ni a nawa zaton ko ciwon da kowa yasanta dashi na mara shine dalilin jinkirin haihuwar nata, Idan na tuna hakan a yanzun har kunyar kaina nikejin yana kamani, idan ba ita d'inba wace yarinyar ce zata yarda a zauna a gaban idon ta a yad'a mata maganganu irin wanda yan uwanka ke mata akan cewar tak'i haihuwa, Amma yarinyar nan da yike takance matar rufin asiri ko sau daya bata tab'a tunanin cewar zata tona abinda ke binne a tsakanin ku na tsayin shekaru ba ta gwammaci tayi ta had'iye komai ita d'aya, dan haka wallahi bazan k'ara yarda in jagoranci cin zalin d'in daka mata a baya ba domin ko inda ace d'aya daga cikin k'annen Kane hakan ya sama kaima nasan bazaka bari ba, Ba kuma nazo jin ra'ayin bakin ka bane ko kuma ban hakurin ka nike buk'ata ba! Ah ah takarda dai zaka rubuta min yanzun basai an kwana gari ya waye ba, in yaso daga goben kana iya bude kofa ma masu zuwa maka jaje domin kaine ka tafka asara ita kam murna ya dace aje mata dan ina mata fatan samun wanda ya fika kodan albarkacin biyayyar da ta d'aure tayi ma iyayen ta na zama a gidan ka tsayin shekaru ba tareda ta nuna gazawa ko kuma ta ce zata bud'e sirrin ta ma wani, kai koh ni bazan maka baki ba sai dai ka sani yan magana kance ruwa cikin cokali ya isa mai Hankali wanka" Duk yanda Sarki yaso ya k'are kanshi da son ta fahimce shi Sam uwar gida ta rufe ido tama hana shi magana, to me zaice mata bayan ya gama nunawa duniya cewar ita din bata isa ba, domin ai d'an daka isa dashi bazai maka haka ba, Saki d'aya ya zana a takardar sab'anin ukun data buk'ata, copy biyu tasa ya rubuta ta rik'e daya a hannun ta d'ayan kuma tace ya rik'e a hannun shi gobe in gari ya waye yayi sammakon zuwa Tudun wada yakai ma Meenal d'in domin dai tuni tayi gaba Allah kuma yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu, bata bar d'akin ba sai da ta k'ara jaddada mishi cewar karya sake wani yaji zancen sakin nan har sai bayan ya isar ma Meenal da takardar ta, kuma ko bayan hakan bata yarda in magana ya tashi iyaye sunce ya maida ta ya amsa cewar ya mayar da ita d'in ba gara ma ya h'ada ina shi inashi yabar garin a goben, Wannan dare a wajen Sarki da uwar gida kai tsaye zamu iya kiran shi da bakin dare, Domin dai kaf a tarihin rayuwar ahalin su ba'a tab'a samun kaddarar data gifta na sakin aure ba, tun daga kan mazan su har matan su, domin kowa ya musu shaidar cewa in sun auro ko sun aurar tofa sai dai mutuwa ta raba, Sai gashi yau Allah ya kawo mutuwar auren daya kasance na *Dangi* daya ahali d'aya, auren farko da aka fara h'adawa a cikin dangi shine bai kai ko ina ba har ya mutu, innalillahi wa innah ilaihir raju'un, sosai uwar gida fa take cikin bakin ciki da bacin rai, domin laifin gaba d'aya ta d'auka ta d'aura a kanta a ganin ta itace ta jawo komai, da ace tun farko bata dage wajen nemawa danta auren Meenal ba da hakan bata faruba, tasan dad'e duniya yanzun bata da mafita domin yanzun kam mak'iyan ta sun samu sahihiyar damar da zasuci tuwo a kanta, Ganin da tayi cewa tunani da rashin nutsuwar zuciya bazasu barta ta samu bacci cikin salama ba hakan yasa ta koma cikin makewayin ta tayo alwallah bayan ta fito ta haye kan sallaya ta fara gabatar da nafiloli, haka ta dunga ibada inta gaji ta zauna tayi karatun qur'ani shima inta tab'a kad'an sai ta ajiye taci gaba da Sallah tana kaima Allah kukan ta ba akan kowa kuma ba sai akan Sarki,roko take tana qarawa akan Allah ya tsare mata shi akan sharrin dukan wani abun k'i, Allah ya kawo daidaito a cikin al'amuran shi, Lallai uwa uwace inba uwa ba wacece d'anta zai b'ata mata amma ta koma gaban ubangiji tana nema mishi dacewa, Lallai yan magana sunyi gaskiya da sukace hannun ka baya tab'a rubewa ka yanke shi ka yar ( nidai nace k'arya ne wallah aka yanke k'afa ma balle kuma hannu😒). To shima gafen Sarki hakan ne ta kasance domin gaba d'aya zuciyar shi a k'untace take har ma Allah Allah yakeyi gari ya waye ya tattara nashi ya nashi ya tsallake yabar garin, dan Wallahi sai yanzun yake jin nauyi da kunyar abinda ya aikata, ace da girman shi da komai har yarinyar da bata wuce yar cikin ba ta fishi hankali da hangen nesa, Yanzun shi da wani kalmar zaiyi amfani ma wajen kare kanshi bayan abinda ya aikata, ace yarinya k'arama ta iya amsar auren ta kuma rik'e hannu bibbiyu duk tsayin zaman shi da ita idan yace ga wani abunda ta aikata mishi na rashin tarbiya yayi k'arya yasan sau da yawa yakan kirkiro wani abun dan ya b'ata mata amma ko ranta ya bacin haka zata danne bata tab'a kai karanshi wajen kowa cewa ya aikata mata ba dai dai ba, haka dai yayi ta sake sake bashi ya samu damar rintsawa ba har sai zuwa gaban nin asuba. *** Washe gari daga masallaci Sarki ya wuce gidan shi, Yana zuwa kuwa kayan amfanin shi na yau da kullum ya har had'a yanayi yana kai su cikin motar shi domin yasan in yabar garin tofa bai san lokacin dazai waiwayo ba, Bayan ya gama sai da yayi wanka ya shirya tsaf sannan ya koma gidan su, shashen Malam Sulaiman mahaifin shi ya fara isa, ya iske shi yana batun karyawa a lokacin dan haka koda ya taya mishi bai musa ba suka zauna tare sukayi karin gaba daya, bayan kammala karin nasu ne kuma ya gabatar ma mahaifin nashi da zancen tafiyar gaggawar da ya taso mishi a daren jiya zuwa Calaba Cross River, Malam Sulaiman man bai kawo komai ba domin bayau ne karon farko da tafiyar gaggawa take kama Sufyaan d'in ba, sai dai korafi da yayi akan cewa shida aka sallama daga asibiti yammacin jiya ina yaga kwarin jikin da zaiyi tafiya mai nisa haka?, Daga karshe kuma ya mishi fatan alkhairi dafatan da cewa akan abinda aka sa gaba, Yanda yayin da addu'ar da yaketa jeroma Sarki nasa albarkha sai jikin Sarki yayi sanyi, harya fara tunanin yanzun kuma ya mahaifin nashi zaiji in zancen sakin auren su ya bayyana bayan ya wuce, lallai shi yasa akace abinda babba ya hango yaro ko ya hau dala da gwauron dutse bazai iya hango waba, domin dai bacin ran dazai biyo baya na uwar gida ta gudar mishi shi yasa kenan tace ya shirya bayar garin, gaba d'aya kuma sai yaji tausayin iyayen nashi ya kama shi, Daga sashen Malam Sulaiman na uwar gida ya wuce gaisuwar kad'ai ta iya amsawa kafin ta jefo mishi tambaya da cewa "ina fatan can ka nufa daga nan?" "Eh" Ya amsa mata a yayin da yaran shi suka baibaye shi kowacce na lissafa mishi abubuwan da take buk'ata bai bar gidan ba sai da ya sauke musu komai na kayan buk'atun su na yau da kullum ya kuma ba Salman sallahun cewar yaje gidan shi anjima su kwaso kayan abincin dake cikin store saboda kar a barsu su lalace, Tsabar kunyar dake d'awainiya dashi ita ta hana shi shiga gidan Malam bayan fitan shi daga gidan su, Domin a tsarge yake kwarai sai yakejin kamar duk wanda ya kalleshi abinda ya aikata yake kallo a tare dashi, Gidan Hajiya ba bak'on waje bane, duk da cewar ba zuwa yake ba amma yasan bazai rasa gane gidan ba dan haka shi kad'ai yama kanshi jagora zuwa gidan yana tafe gaban shi yana fad'uwa, Dan Allah ya sani shidai tun kafin auren su a had'uwar su na farko da Hajiyar yake jin shakkar matar tun ranar data gindaya mishi sharad'odin zama da jikarta, to gashi kuma yau zai kaima jikarta takardar saki a gidan ta, addu'a yakeyi, fata yakeyi cewa allah ya ceceshi ace harya shiga ya fita a gidan nan basu had'u da ita ba, Bayan isar shi unguwar a kofar gidan ya faka motar shi sannan ya k'arasa bakin gate din gidan yama masu gadin gidan Sallama, Sun gaisa a mutunce kafin ya sanar musu cewar wajen Meenal yazo inba damuwa yana buk'atar su mishi kiranta, Daya daga cikin sune ya amsa mishi, Shi kuma ya nemi kujera cikin kujerun da aka kirkira dan zama a cikin harabar gidan ya zauna yana tsumayen ganin wanda zai fito cikin ita ko k'akarta. ****a gafen Meenal ko tun bayan da Hajiya Jummai ta sallame ta da cewa ta koma d'aki a jiya tunda ta haura har safen yau bata yarda ta sauko ba, ba kuma komai takeyi a d'akin ba sai dai kuma gaba daya itama bazata iya cewa ga kata maiman abinda takeji a jikin ta ba, abinda ta sani kawai shine bata cikin walwala, harta abincin dare dama na safen yau can d'akin Larai takai ta sameta dashi, Duk abinda takeyi tsaf hajiya take ankare sai dai itama shareta kawai tayi, domin dai aiko mak'iyin Kane ka rabu dashi na rana d'aya sai kaji kewar shi balle kuma mijin aure, tun jiyan taje ta amshi magungunan dake hannun Meenal din ta ware wadanda take buk'ata ta barma Meenal din sauran bayan ta jaddada mata cewar ta dage taci gaba da amfani dasu, A daren kuma ta amshi number din uwar gida a hannun Meenal din ta kuma kirata ta shaida mata cewar tana son zata shigo wajen ta da safe, sai dai bata shaidama uwar gidan abinda zai kawota wajen taba, Sai ma cikin kokonto data barta da tunanin cewar zata biyo bayan takardar sakin ne kamar yanda ta ambata mata a yammacin jiyan. Koda Hajiya ta shirya ficewar ta kawai tayi da safen batareda tabi takan Meenal data maida kanta daddawar d'aka ba, Fitan nata kuma sai ya zama hannun riga tsakanin ta da Sarki domin dai ita tana barin unguwar ne shi kuma yana shigowa. Larai mai gadi yaba sak'on cewa Meenal nada bak'o, ita kuma bata tsaya bin diddigi ba ta haura sama ta shaida ma Meenal din. "Waye?" Meenal ta tambaya, "Gaskiya ban sani ba dan ban tambaya ba, "Kije ina zuwa" Shine amsar da Meenal din ta bata, "Ko za'a shigo dashi cikine Hajiya karama?" Larai ta tambaya, "Duk yanda kikayi" Juyawa Larai tayi ta fito daga d'akin duk da bawai wani farin sani tama mijin Meenal din ba amma a ganin ta da Sarki jikinta ya bata cewa shine mijin na Meenal, Dan haka tun kafin ta karasa inda yake ta fara gulmar shi a zuciyar ta. "Gashi dai namiji cikakke son kowa kin wanda bai samu ba amma ace an wanke gangariyar mace kamar Hajiya karama an kai mishi tsayin shekaru ya kasa tab'uka komai, domin dai kowa yasan cewa indai badai akwai wani abun a k'asa ba tofa cikakken Namiji kamar shi bazai yuwu ace ya kasa sarrafa mace ba koda yake dai jiya taji Hajiya Jummai na fad'in cewa aikin asiri ne,. "Hajiya karama tace ayi maka iso zuwa ciki" Ta fad'a bayan ta isa inda yake, Bayan ta yabi a yayin da take mishi jagora har zuwa falon na Hajjaju, A nashi gefen ko duk da yanda zuciyar shi ke kad'awa haka ya cije, Ya nemi wajen zama ita kuma ta wuce kitchen ba tareda tunanin ya karya a gida ba ta had'o wani kayan karin ta kawo mishi, wanda hakan yayi dai dai da saukowar Meenal bata kula dashi ba har sai da ta kawo matakala na k'arshe, can ta tsaya kafin kuma tayi yunkurin komawa a zaton ta ko bai ganta ba, "K'araso mana ya kike kokarin juyawa kuma? Wajen ki fa nazo" Tura baki gaba tayi tana k'arasawa inda yake cikin kun kuni tace, "to kai ba kwance kake a gadon asibiti ba mai kuma kazoyi nan, Allah nidai in ma zuwa kayi ka tafi dani bazan bika ba," "Waye yace miki nazo in tafi dake ne?" "To baga kanan ba, me kazoyi to?" Mikewa yayi daga inda yake zaune ya tarbota, Hannun ta ya kamo abinda bai tab'a aikatawa ba tsayin shekarun da suka kwashe a matsayin ma'aurata sai yau, "Sallama nazo miki tafiya zanyi kuma ban san tsayin lokacin da zai d'aukeni ba kafin in dawo, ko laifi ne dan nazo miki sallama" Ya k'arasa fad'a a yayin da ya zaunar da ita a kujerar daya tashi shima kuma ya zauna a gefenta. "Meenal" ya kira sunan ta, Bata iya amsawa ba illah maida hankalin ta da tayi kan kayan karin da Larai ta ajiye mishi, "Bakaci komai ba?" Ta tambaya tana kallon shi, "Yanzun na karya kafin inzo nan bana tareda yunwa, Hajiya bata nan ne?" "Hajiya ta fita bada jimawa ba" "Meenal " ya k'ara kiran sunan ta a karo na biyu, Shima din bata iya amsawa ba sai kallo data bishi dashi, k'ara riko hannuwan ta yayi cikin nashi, "Meenal fadamin da gaskene kinfi so mu rabu kowa yaje yayi rayuwar shi? Karki boye min ra'ayin ki ki fadamin kinji" Ya fad'a cikin yin k'asa da muryar shi, "To ai ni dakai dukan mu ba son juna mukeyi ba, kuma na sani cewa kaima auren dole aka maka kamar yanda nima aka mun" "Amma ni ai bance bana sonki ba, kokin manta ni dake *Dangi* daya ne?" "Ah ah ni ban manta ba amma ai matar ka bata sona" "To amma ai ba ita ke auren kiba nine mijin ki" "To ai sai baka nan take zuwa gidan ta fad'amin maganar banza, dan dai bana fad'ama kowa ne shi yasa kaima baka sani ba" "To naji ina kuma neman afuwar ki akan komai dani ko ita muka aikata miki tun daga ranar da aka daura auren mu zuwa yanzun da muke zaune anan ina fatan zaki yafe mana?" Shiru tayi bata amsa mishi ba, "Baki ce kin yafe ba" "To aini kai bakamin laifi da yawa ba" "To kadan din ma da nayi baki san cewa in baki yafe ba Allah yana iya kamani da hakkin ki, shi yasa nike neman yafiyar ki Kinga tafiya ce a gaba na yau in baki yafemin ba wani abu ya faru dani a hanya na mutu kinga ai zan mutune da hakkin ki" Runtse hannun shi tayi sosai. "Ah ah nidai babu abinda zai sameka ai ba yau ka fara yin tafiya kuma Kaje ka dawo lafiya ba," "Eh amma kuma kin san Allah babu ta inda baya iyayin ikon shi akan bawa koh!" "To nidai ka dena cewa zaka mutu, na yafe ma kowa duk wanda ya b'atamin na yafe mishi duniya da lahira, amma nima ka yafe min kaji" Ta k'arasa fada tana kallon shi, "Mai kika aikata kike neman yafiya na kuma?" Dariya tadan yi kasa kasa, tana kauda kanta gefe, Da yatsar shi babba yayi amfani wajen karkato da fuskarta zuwa gareshi, "Fadamin mana" Ya fada shima da dan murmushin da bai bayyana a fuskar nashi ba. "To ba ina ta tara kud'in da zan siyama Baba Malam Babban fili in gina mishi gida bane, shi yasa ni kuma Nike ta amsan yan kud'ade a wajen ku" Ta karasa fada tana duk'ar da kanta cike da kunya, sai kuma ta kara shagwabe fuskarta kamar mai shirin yin kuka tace, "To kuma shine kai kake maganar rabuwa tun kudin nawa basu gama cika ba, kaga ai saura kad'an in zama cikakkiyar likita, zuwa lokacin suma kudad'en asusuna zasu kai in siya ma Babana k'aton fili, kuma harda katuwar motar hawa Nike so in canza taka din nan dama nace sai na fara aiki kafin in fara ginin gidan," Ta karasa cike da muryar kuka, Duk yanda Sarki yaso ya matse wannan karan sai da dariyar shi ya fito fili. "To ai shi kenan tunda ma dariya na baka" "Allah ya baki hakuri, yanzun billion nawa kika tarane, Kinga ai in cikon babu yawa koni basai inyi kundun bala in cika miki mu siya mishi gidan ba, bar batun fili dan hidimar gini yawa gareshi, mota kuma ai daman kayan miji na mata ne dan haka daga yanzun ta tashi a matsayin nawa ta koma naki, sai kuma me kike so fad'amin shima yanzun in cika miki shi?" Dad'ifa ya kashe mutuniyar ku amma dai da yike yanzun ba kamar da bane an d'anyi hankali dan haka sai ta dake abunta bata wani nuna d'aukin ta a fili ba, "Kinyi shiru" "Nidai kabar kayan ka, kar mutane suce ka kwashe kudin ka da mota ka bani" Ta karasa fada tana juyar da kanta gefe cike da tsiwa, "Kema ai kince kayana, baki san cewa ko gidan nan kikace kina so zan baki ba?" "Tab lallai ma ni wallahi babu ruwa na, kai baka san yanda har yanzun mutane basu dena surutu akan gidan nan bane," D'aure fuskar shi yayi yaci serious sosai, Hannu ya mik'a ya d'auki ruwan dake ajiye yasha sannan ya maida hannun shi guda cikin aljihu ya zaro wasu envelope 📨 guda biyu ya rik'o hannun ta ya damk'a mata, "Meenal ina ganin lokaci yayi daya kamata in barki ko kema Allah zai had'aki da wani mijin wanda zai k'aunace ki yanda ya kamata miji ya k'aunaci matar shi, kiyi hak'uri nasan ban kyauta ba nasaki cikin jerin zawarawa alhalin kedin baki cancanci amsa sunan zawara ba, sai dai nasan ba kowa za'a shaida ma hakan ya yarda ba kamar yanda nima bazan iya cewa ga katamai man dalilin da yasa na kasa mai dake cikakkiyar matar aure ba tsayin shekarun nan, Abinda na yarda dashi kawai shine cewa ke din iya zaman da Allah yayi zamuyi da juna a tare kenan, ina kuma fatan hakan bazai sa ki kullaceni ba dan hakan nema yasa na nemi gafarar ki tun fari, ina miki fatan alkhairi a rayuwar da zakiyi nan gaba sannan ina rokon ki kar rabuwar auren mu yasa kice zaki yanke alaqar dake tsakanin mu, ki kirani kai tsaye ko sak'on waya aduk sanda kike bukatar' wani abu ni kuma zan miki shi kamar yanda na saba akoda yaushe" Zuwa wannan lokacin sosai Meenal ta fashe mishi da kuka, Cikin kuka ta furta mishi "yanzun shike nan kana nufin sakina zakayi? Nima zawara za'a dunga kirana bayan kasan babu wacce auren ta ya tab'a mutuwa a *Dangina*" "Kiyi hak'uri ki yafemin" Sai da yayi aikin lallashin ta sosai kafin ta tsagaita da kukan da take mishi, "Kace in tambaye ka duk abinda Nike so koh?" "Eh haka nace kuma koba yanzun ba duk abinda kike so zan miki shi" "Komai nake so?" "Eh komai Ameenatu" Hannu tasa ta zaro wayar shi dake makwale cikin aljihun gaban rigar shi sai kuma ta mik'a mishi, "Budemin key din" Amsa yayi ya cire wayar a key kamar yanda ta buk'ata, Nata wayar ta bude itama shi dai yana kallon ta tana aikin danne danne a wayar har ta gama sannan ta maida mishi nashi wayan a inda ta zarota wato cikin aljihun shi, K'aramin 🗒 memo din data gani akan stool din gefen kujerar da suke zaune ta d'auko, number waya, sunan mamallakiyar number din da kuma address ta rubuta sai da ta nan nad'e takardar kafin ta tura mishi a cikin aljihu, shi dai da kallo kawai yake binta, "Na tura maka pic a wayar ka ina son duk sanda Allah yasa ka samu lokaci ka bud'osu ka duba kaji dan Allah please 🙏 " Ta fad'a hakan tana mai hade hannuwan ta alamun roko, "Sunan ta da inda zaka sameta duka suna cikin takardar da nasa a cikin aljihun ka, Ita din jinina ce sai dai a shekarun baya can ta tab'a furta cewar kana matukar burgeta harma tana jin zata iya auren ka, Kafin alakar aure ta ratsa tsakanina da kai kullum in nayi magana da ita saita tambaye ni ya kake? Kana gari ko baka zoba? Duk da a lokacin tasan ba son hirar ka nikeyi ba saboda ni a lokacin haushin kusan cin dake tsakanin ka da Baba Malam nikeji gani nike kamar kana son ka kwace min matsayin da Nike dashi a wajen shi domin duk sanda kamin ba dai daiba idan na gaya mishi sai ya nemi hanyar da zai kareka duk dan dai kar inga bak'in ka, Nasan saboda ni ne ta cire duk abinda takeji akan ka, hakan bai wadatar da ita ba har saida ta nemi afuwata bayan auren mu, tunda na aureka kuma take tsallake zuwa inda Nike indai ance mata kana gari, Ba ina nufin dole sai ka sota ba, koda kuma kasota din ina neman alfarman karka shaida mata cewar ina da masaniya akan komai, dan haka na baka dama daga ranar da kaji a zuciyar ka cewa kana sonta zaka iya rayuwar aure da ita ka nemeta kar kuma ka gajiya har sai ka shawo kanta, ina fatan kuma bazaka watsamin kasa a cikin idona ba, nima kuma ina maka fatan alkhairi da fatan samun nasarar rayuwa nagode da kulawa. Tana k'arasa fad'in hakan ta mik'e, "Muje in taka maka zuwa kofar gida" Bai iya cewa komai ba illah mikewa da yayi haka suka jera yana gaba tana bin bayan shi har suka fice a sashen, A tsakar gidan sukayi kicibus da AK wanda tun barin gidan da yayi jiya bai dawo ba sai yanzun, Koda ya hango su so yayi ya juya ya koma sai dai kuma sun rigada sunyi ido biyu da Sarki, "Assalamu Alaikum" sarki ya mashi sallama gamida bashi hannu sukayi musabaha, "Thank You for yesterday, Allah ya saka da alkhairi" Da kyar AK ya iya bud'e baki ya amsa da cewa, "Ba komai yiwa kaine ya jikin naka, Allah ya kara lafiya" "Ameen jiki alhamdulillah" Gaba sukayi shi kuma shige sashen na Hajiya, har bakin motar shi Meenal ta raka shi saida taga ya shiga sannan ta fara matsar kwalla, "Wanene shi?" Sarki ya tambaya, "Shi wa?" "Wanda muka gaisa dashi yanzun" "Yaron yayan mamana" "Anan gidan yake zaune?" "Eh" "Ki kula dashi yana da kirki kar kice zaki dunga mishi tsiwar da kika saba kinji" Kauda kai tayi gefe tana murgud'a baki. "Ai kai dan baka san halin shi bane shi yasa kace haka, amma shi din harma akwai wanda yakai shi rashin kirki ne" "To allah ya baki hakuri zan wuce in hajiya ta dawo ki gaisheta na kuma gode da yanda kika tsaya kika saurareni muka fahimci juna, zansa Salman ya kawo miki motar anjima, maganar gidan Malam kuma zan bincika idan an samu zan tuntube ki a ina kike son gidan?" "Ni duka bana so, bana son komai sai anjima" Ta fad'a tana juyawa ta shige cikin gidan ta barshi anan, Yad'an jima kad'an kafin ya kunna motar ya bata wuta yabar layin, Ita ko tunma kafin ta k'arasa cikin falon Hajiya ta fara kuka, Kuka kuma bawai irin kukan tabarar data sabayi ba a'ah takeyi sosai domin tsakani da allah sakin aure fa ba abune na wasa ba, Shigar ta cikin falon yayi dai’ dai da fitowar da AK yake shirin yi, Bata tsaya wata wata ba takai mishi wata iriyar wawiyar runguma tana cigaba da ihun kukan ta kamar wacce akama ruwan bula lai, "Shi kenan na zama bazawara ya sakeni, ya sakeni nima na zama sakakkiya, waiyo Allah na zama bazawara aure na ya mutu....." Hihihihi haka ta dunga rusa kuka, kankame a jikin AK ko bata san wata rungume bane oho . Kam kam ya k'ara rungume ta domin wallahi tunda yaji ta furta kalmar "ya sakeni" ya fara jin hajijiya na nema maka shi da kasa, Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, yayi ta maimaitawa yayin da jin fitar kalmar a bakin shine yasa itama ta kama sukaci gaba da maimaita a tare ba kuma dan tabar kukan da takeyi ba, Haka yaci gaba da riketa a jikin shi har zuwa sanda kukan nata ya lafa sai hawaye da suka kasa tsaya mata, Janta yayi sukayi zaune a kujerar dake kusa dasu, koda suka zauna d'in bata yarda ta raba jikin suba, domin idon ta ya rufe inda zata jingina taji dama dama kawai take nema. "Larai" ya kira, dake gefen kitchen din rakube tana kallon su itama tana nata matsar kwallan, "Jeki kiramin Hajiya Jummai yanzun nan" "To" ta amsa dashi ta wuce, "Kiyi hakuri kiyi shiru haka, kukan ya isa, baki san duniyar nan a lokacin da wani yak'ika shi kuma lokacin wani yakejin cewa ko ranshi ne zai iya badawa dan ya faranta miki ba, me yasa zakiyi kuka dan kin rabu da mutumin daya nuna ma duniya cewar baya sonki, bayan dubu sau dubu a bayan shi kullum mafarkin son suyi rayuwa tare dake suke?" "Saki na yayifa kuma yanzun ai kowa kallon bazawara zai min" "To sai me dan an miki kallon bazawara? Iyeh baki san wata macen nata auren bai tashi mutuwa ba har sai sanda tsufa ya fara cimmata, kuma a hakan zakiga maza na rububinta har sai mai rantsatstsan rabone zai d'auka balle kuma ke, Kiyi shiru kukan ya isa haka dan in kika sa kanki a damuwa muma zamu shiga damuwar shiko Kinga ai can wajen d'aya matar shi zai koma ya manta dake" Kuka ta k'ara fashewa dashi, A haka hajiya Jummai ta shigo ta same su, "Mai ke faruwa anan?" *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ````` *Page 45*..... "Me yake faruwa anan?" Hajiya Jummai ta tambaya tana binsu da kallo, Kamar mai jiran iso warta haka Meenal taje da gudu ta shige jikinta, tana ci gaba da rusa ihun kuka. "Hajiya aure! Yau aurena ya mutu, Ya Sarki ya shigo har gidan nan ya kawo min takarda ta, ashe da gaske ne baya sona, hajiya ya sarki bai tab'a sona ba, ya dai zauna danine kawai dan babu yanda zaiyi waiyo Allah na shike nan na zama bazawara" Take fad'a cikin kuka mai tsuma zuciya, "Innalillahi wa innah ilaihir raju'un³ ubangiji Allah kai mana maganin abinda kasan bazamu iyaba," Ta fad'i hakan tana mai dan dukan gadon bayan Meenal din alamun lallashi cike da jimami. "Kiyi shiru Meenal kukan ya isa haka, ai bake ce ya kamata kiyi kuka ba shi da yayi rashin mace kamar ki shi kamata ya shige cikin d'aki yayi kuka, ke ai abun ki d'aga hannu ne ki gode Allah tunda har shi da kanshi ya sallame ki salin alin, kwana nawa ne zakiyi a gidan kafin wasu mazajen su fara tururuwar kawo miki cafka," Wannan kalmar nata kamar fitar kibiya haka taje kai tsaye ta caki zuciyar AK wanda dole ya daga kanshi yana mata wani kalar kallo mai kama da shi kenan so take ta kasheni, Ita ko ba tareda damuwa ba a kokarin ta shawo kan kukan da meenal din keyi ne taci gaba da cewa "share hawayen nan naki ni bana son ganin su,indai kukane akan namiji insha Allah kiyi d'aya bazaki k'arayin na biyun shiba, inba ma kaddara ba ai dama shi din ba sa'an auren ki bane dan yayi miki tsufa me ma zakiyi da mijin wata? Kai kuma tashi ka d'auko min ruwa masu sanyi in bata tasha ko ta samu sanyin zuciya, ka wani zo ka zauna ka tasata a gaban ka kamar ka samu TV ita kuma saboda rashin sanin ciwon kai ta wani dage da kuka akan mutumin daba kaunar ta yake ba amma ka kasa hanata" Zaunar da Meenal din tayi sannan ta yago tissue paper ta shiga goge mata hawayen ta dake ta faman shatata uwa ana korosu, "Kinga nifa in baki kama kanki kin dena kukan nan ba to a gaskiya ba zamu shirya ba da wuri zamu raba jaha dan nidai banga dalilin da zaki tsaya kuka akan mutumin da bai san darajar kiba, in kuma kina ganin kamar baki iya rayuwa ne dole sai tare dashi to ai sai ki mik'e muje ni da kaina zan mai dake d'akin ki in duk'a har kass in roke shi ya mai dake d'akin ki tunda naga kamar son shi kike da yawa ta yanda sai dashi zakiyi numfashi dole" "Aini dai bance zan koma ba!, amma ni ai ban san me zan fad'a a gida ba,shi yasa nike kukan kinga fa ban mishi laifin komai ba ya biyoni har gidan nan ya kawo min takarda ta, fisabilillahi kaf cikin *Dangina* wacece auren ta ya tab'a mutuwa idan bani ba?, aini wallahi kunya zanji a dunga nunani ana cewa aurena ya mutu" "Mtwsw" AK yaja wata irin doguwar tsaki mai shegen k'ara, dungure musu ruwan yayi cike da fusata, ya fara nuna ta da yatsa, "Na rantse da Allah in baki rufama mutane baki da wannan kukan iskancin da kikeyi tun d'azun ana lallashin ki kina ci gaba da iskanci ba saina zane miki jiki tass wallahi, kujimin wani sabon gulma da munafunci, oh dama kin san kina son nashi kika biyema Hajiya kika taho nan gidan, mai yasa tun jiya da nasa baki baki bijire mata kinyi zaman ki a gidan kiba? In bama hauka ba mijinki na kwance a gadon asibiti yana jinya kika tsallake shi kikayi tafiyar ki sai yau dan ya biyoki da takarda ne zaki samu a gaba kina mana kukan iskanci da rainin wayau, Larai" Ya kwala ma kira da karfi, sai ko gata a falon tsulum dan dama tsaye take daga bakin kofar kitchen tun d'azun tana jimamin wannan mutuwa na auren Meenal din. "Haura sama ki d'auko min akwatin kayan yarinyar nan ni nan nida kaina zan maidata gidan mijinta, tunda tana son shi taje can ta k'arata," Hajiya Jummai ce tasa baki da cewa, "Bank'i ta taka ba Mai Jama'a amma ina ganin daka jira dawowar Hajiya" "Au haka zan zuba mata ido kenan taci gaba da tujaramu, Hajiya ki barni kawai in mai data tunda ta zab'i zama dashi cikin ko wani hali" Zumbur Meenal ta mik'e tana k'ifi k'ifi da ido, "Ni wallahi bazan koma ba, to shi kenan dan kawai aurena ya mutu sai ace kar inyi kuka, in kuma banyi kukan ba sai a juya min zance ace ina murna ne da mutuwar auren, to wallahi bazan koma ba lallai ma, sai dai in kaine zaka koma can ka zauna amma bani ba, wato saboda kai bakayi auren kaji yanda yake ba shine zakace in koma" Goran ruwan daya kawo da sunan tasha ya wawura kafin kowa ya ankara ya seta ta yako jefeta dashi, wani irin zuk'ewa tayi a yayin da goron ruwan ya nufota, da gudu ta kwasa tabi ta cikin kitchen ta fice a sashen, Waje ya nema ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, "Me kakeyi ne haka Mai Jama'a?" "Hajiya ita bakiga abubuwan data ajiye mutane tana masu bane? Jiya fa akan maganar ne yasa na zame na baro Hajiya acan data dage cewar sai ta taho da ita, to data taho da itan ba gashi sanadin hakan ya biyota da takarda ba inba raini ba me yasa ta barshi ya tafi bayan saida ta mishi rakiya har kofar gida Eyeh daba sai ta tsaida shi ta kwashi kayan ta ta bishi suyi tafiyar su su k'arata can ba, wato mune ta raina sai da fa ya tafi sannan ta wani shigo ta sani a gaba tana min kukan rashin munafunci da rashin dalili, allah data tsaya da sai na zaneta" Fuuuu haka ya fice daga sashen shima yana cika yana batsewa. Hajiya ko da kallon mamaki kawai ta bishi, wai Mai Jama'an data sani ne ko wani daban aka canzo musu ne?, Ganin dai duk sun watse sun barta da bin bayan su da kallo hakan yasa itama taja nata kafafuwan tareda envelop ✉️ guda biyun data gani a wajen ta fice daga side din zuwa nata, Shiko Ak tunda ya koma d'akin shi ya kasa zaune ya kasa tsaye, Wallahi da ace yasan abinda zai zo ya tarar a gidan nan kenan dabai dawo ba, Domin dai jiya tun bayan daya sauke su a gidan Meenal, sabon gari ya wuce gidan wani abokin shi shima marar mata ne irin shi, acan ya kwana ko su Sadeeq da sukayi ta kiran shi bai shaida musu inda yake ba, da gari ya waye ne ganin yad'an samu nutsuwa ba kamar jiyan ba shine fa yace bari ya dawo gida da niyyar ya had'a komatsan shi ya wuce kd dan daman can kuma harkokin shi sukafi karkata yanzun, To gashi dai daga dawowar shi ya kuma cimma wani babban al'amarin da bai san fassarar daya dace yama abinda ya faru d'in ba, murna zaiyi ko bakin ciki zai tayata ya rasa wanne ne a ciki yafi cancanta yayi, Sai gashi wai dan rashin mutunci a gaban shi yarinyar nan ke wasu maganganu na banza, shiko ina zai iya zama a gidan nan yanzun ai gidan nan kuma yafi k'arfin shi dan ya tabbata idan yayi kuskuren cigaba da zama a cikin shi tofa takaicin yarinyar nan na iya sawa wata rana a wayi gari zuciyar shi tayi bindiga wallahi, Dan haka zaiyi nesa da ita domin ya bata lokaci ta yanda zata warke rad'adin bulalar sakin data zabgeta da safen nan, in yaso daga baya zai dawo ya fara dora nashi sabon ginin, Abubuwan da yasan zai bukata masu mahimmanci kadai ya d'auka bai d'auki suturar sawa ko d'aya ba haka ya fito daga sashen nashi har ya fice daga gidan bai k'ara wai wayen kowa ba. ************* A gefen Hajiya kam kamar yanda tayi niyya gidan Malam ladan ta wuce kai tsaye, Tarba kuma ta girma da girmamawa ta samu daga Uwar gida duk da dai duk kayan motsa bakin da aka tareta dashi bata iya tab'a komai a ciki ba, bayan sun gama sai suwa ne Hajiya ta bud'e baki tace, "Ina fatan dai sashen naki ana iyayin sirri a cikin shi? Domin abinda ke tafe dani abune da bai kamata ace kowa yaji ba duba da cewa yanzun sai ka share shekaru kana rayuwa da mak'iyin ka ba tareda ka ankare da hakan ba, " Ta karasa fad'a tana dan waige waige kamar wata mai shirin yin tsegumi, "To mu shiga daga ciki mana Hajiya inaga acan zaki fi sakewa" "To hakan dai yafi kam baki alekum" Dakin uwar gidan tayi ma Hajiya iso, shima duk da hakan bayan Hajiya ta zauna sai da uwar gida ta koma daga baya ta kulle kofar harda murza key. "Masha Allah," Hajiya ta furta a bayyane sabon gaisuwa suka k'ara hajiya harda tambayar yame jiki ya k'ara ji, "Jiki alhamdulillah ai kun mayi hannun rigane domin na tabbata cewa yanzun haka ya isa can gidan ki," "Allah sarki aiko kinga zuwan nan nawa nashi ne nayi shi takanas taka no, atoh koya abu yakai ga lalacewa dai ai an dad'e da zama d'aya, koda ace baiyi auren takwara ta ba ai shidin dai kamar jikana ne in an duba gefen Jidda, to kinga ko ai in ina raye yanda bazan iya zuba ido rayuwar d'iyan Jidda ya tagayyara ba shima bai kamata in zuba ido ma halin da ake ciki ba," Jakar da take rike shi a cinyar ta ta bud'e ta fara fito da magungunan dake ciki, tana mai cigaba da cewa, "Ban sani ba ko a matsayin ki na uwa kin iya hango duhun dake lullub'e da rayuwar d'anki, ko kuma kin fahimta kuma kin nemi taimako wajen Allah amma lokacin wucewar komai ne bai zoba, to nidai kiyimin aikin gafara dan nidai ban iya gani in kauda kai, wadan nan magun gunan da kike gani kudi na zube zunzurutu na nemo su, taimako ne da yake karya duk wani tsafi ko asirin dake jikin mutum komai karfin shi kuwa, insha Allah da zarar mutum yayi amfani dashi in allah yaso sai kuga an dace," Sai kuma ta k'ara wasu daga cikin magangunan. "Kinga su kuma wadannan na tsari ne, da izinin allah indai mutum ya kiyayesu allah zai kare shi daga sharrin dukanin masu sharri na daga aljannu da mutane, na nemi maganin nan ne tun shekarun baya da na fahimci zaman da yaran nan keyi, domin a lokacin hankali na ya karkata ne ga tunanin ko uwar gidan shine ta shige tsakanin su dan tsaf nike da labarin yanda tayi shuhura, To dai da allah baiyi cewa a lokacin ne komai zaizo karshe ba ita Meenal dana damk'a mata sai ta tattara su tayi waje ta adana su, iya wadanda na ware nata kadai tayi amfani dasu, Ni kuma ban tab'a bin didigin inji ya ake ciki ba domin dai kullum idan na tambayeta takan cemin lafiya lau suke zaune, ban tashi an karewa akan abinda ya faru kenan ba har sai jiya data iskeni a gida," Labarin abinda ya faru na zuwa gidan da teemah tayi Hajiya taba Uwar gida harda komai daya faru na zuwan da sukayi suka samu sarki babu lafiya da kaishi asibity duk sai da ta k'ara maimaita mata, "To kinji abinda ya faru, faruwan hakan ne kuma yasa naji azuciyata cewa d'anki ya samu lafiya rashin sone kawai ya hana shi kula wajen sauke hakkin iyalin shi, kinga koh ni a matsayina ba babba bazai yuwu in zuba ido aci gaba da cutar min da jika ba, wadan nan magungunan dai tunda allah yasa nayi niyya kuma tun farko da sunan shi na amso shi yasa nace bari In kawo miki su da kaina ke kuma ya rage naki kisanya shi yayi amfani dasu nidai nayi iya abinda zan iya, ina fatan kuma dai kin amsa min takardar kamar yanda kika alqawarta jiya?" Tashi uwar gida tayi ta bud'e cikin wardrobe din ta ta fiddo daya copy din takardar, Ajiyewa tayi a gefen Hajiya, "Gashi nan kamar yanda na fad'a tun jiya na sashi ya rubuta, har guda biyu na hannun shi shine zai kaima Meenal wannan kuma nine zan ba mahaifin shi sai ya mik'ata zuwa wajen Baba Malam, ina kuma k'ara bada hakuri akan abinda ya aikata da fatan hakan bazai zamo Silar lalacewar zumunci ba" Sunci gaba da tattaunawa kafin Hajiya ta mata bayanin yanda ake amfani da maganin ta fito, har kofar gida Uwar gida ta raka Hajiya har zuwa sanda ta shiga motar ta driver ya tuk'a suka bar unguwar yau ma kuma bata shiga gidan Malam ba. *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGIDA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ ~{{MY FAMILY}}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE~ZARIA*✍🏼 ````` *Page 46* Bayan komawar Uwar gida cikin gida, kuwa falo ta zauna kafin ta danna ma Sarki kira a waya tana mai fatan Allah yasa dai bawai harya wuce bane dan in so samu ne akwai bukatar dole tayi tsaye akan ganin yayi amfani da maganin nan a gaban idanunta yanda ya kamata, to sai dai kuma yanzun da sakin nan ya tabbata bazata so fitar maganar da zagayawar shi kunnuwan *Dangi* batare da ta cimma matsaya ko kuma ganin kamun ludayin al'amurah ba, dan gashi harta fara dana sanin matsa mishi da tayi yayi sakin nan da ace ta d'an kara mishi lokaci tana ganin kila da za'a iya dacewa wajen samun daidai tuwan abubuwa a tsakanin su, to amma kuma in abubuwan basu dai daita ba still dai ita yarinyar ita ce ake cutarwa tunda shi dai koba komai ai yana da wata matar ita ko fa? Da dai ace wani abu ya biyo baya gwanda ace gara da hakan ya faru, Ayayinda shi din baya gari, dan tasan dole maganganu dai ba fasa yinsu za'ayi ba, Idan baya nan tasan ihu ne kawai jama'a zasuyi bayan hari, to yanzun mai ya kamata tayi? Ta tsaida tafiyar nashi ne? , kana kuma ta roki Hajiya alfarma akan rufe batun sakin har zuwa sanda Sarki zai gama amfani da maganin nan ya bar gari ko kuwa, to amma kuma tsayawar nashi na iya janyo wa mutane su gane cewar Meenal din bata gidan ta, Kai jama'a abin duniya dai duk ya taru ya cunkushe ma Uwar gida inda tasan da batun maganin nan tun farko da bata tsaya akan lallai sai yayi sakin a jiya ba da ta barshi tukun har suga kamun ludayin abubuwa,to kodai wannan dalilin ne yasa Baba D'an magori yayi kiran Sarki zuwa gidan shi sannan bayan magungunan daya basu acan ya kuma k'ara aiko mishi da wasu? to amma ai shi baiyi musu k'arin bayani akan komai ba daga ita har Sarkin kuma ta tabbata kota tambayi mai martaba Mahaifinta bazai fad'a mata komai ba, Kai yasa shi yasa ake cewa gaggawa aikin shaid'an, tadai faru ta k'are kuma yanzun kam ta tabbata kuskure d'aya ne zai k'ara dagula komai, ita dai fatan ta shine Allah yasa mutane su fahimceta kar hakan ya zama silar tab'a zumunci su. To ko dai shiryawa zatayi ta bishi zuwa kaduna in ya gama amfani da maganin ita sai ta dawo? Tafa dad'e zaune tana faman sak'a da warwarar neman mafita ta yanda komai zai gudana a kan tsari ba tareda an samu b'acin rai daga ko wani gefe ba, daga karshe dai ta yanke bin Sarki d'in kawai zuwa kaduna in ya so inta dawo ayi duk wacce za'ayi, bayan ta danna ma layin Sarki kira ringing d'aya biyu yayi shi kuma ya yanke kiran nata daga can gefen shi sai ya maido mata kiran domin shi din irin mutanen nan ne da koda suna ganin shigowar kiranka bazasu d'auka ba har sai naka kiran ya katse sannan shi ya kiraka daga baya. A can gefen shi kiran wayar ya shigone a yayin da yake zaune cikin motar shi a kofar gidan Hajiya bayan Meenal ta shige cikin gidan ta barshi a waje, "Assalamu Alaikum" Sarki ya mata sallama, "Kana ina ne?" Ita kuma ta tambaya. "Ina Tudun wada yanzun nike shirin juyowa," Ya bata amsa. "Ok to sai ka k'araso ina jiran iso war ka yanzun". Mik'ewa tayi ta shige cikin d'akin ta kaf magungunan da hajiya ta kawo mata dama wadanda aka aiko mata daga masarautar su sak'o na musamman daga wajen Baba dan magori, domin kuwa a wani zuwan da sukayi yayin gabatar da bikin auren wasu daga cikin yaran yayyenta wanda hakan yayi dai dai da zuwan Sarki garin dan haka tare suka tafi garin ita da yaranta harma da meenal kamar yanda sukeyi in wani sha'ani daya shafeta ya taso, a kuma wannan lokacin bikin nan ne Allah yasa sukayi katarin had'uwa da Baba D'an magori, shi din ya kasance cikin jama'ar da Allah yama wata irin baiwa ta yanda suke ganin wasu abubuwan a tare da mutum,ba kuma dan ya kasance boka ko kuma matsafi ba, domin ada can baya kafin yanzun mutane da yawa sun sha jifan shi da k'azafin maita, saboda baiwar da allah ya mishi na hango abinda ke lullub'e wala'allah asiri ne aka ma wani, ko maitane mutum ke tare dashi ko kuma maye ya kama wani, ko kuma iskokai ke tare da mutum, Baba dan magori yakan dad'e bai ziyarci d'an tsohon aminin shi ba wato mai martaba, sai gashi kwatsam a wannan rana shida kanshi yayi tattaki zuwa fada domin sau tari idan wani abun ya taso sai dai yayi aike ayi mishi kiran maimartaba yaje can gidan shi ya iske shi to amma da Allah ya k'addara cewar zasu had'u da Sarki sai gashi shine da kanshi yayi tattaki bisa ga jagorancin daya daga cikin jikokin shi zuwa fadar mai martaba, Koda isarsu suna kan tattaunawa babu dad'ewa sai ga isowar iyalan Uwar gida dama ita kanta zuwa falon mai martaba din ciki kuwa harda Sarki da Aminatu, bayan gaisuwa anyi hirar yaushe rabo domin dai an dad'e ba'aga juna ba tsakanin uwar gida da baba d'an magori, domin rabon shi da ita shekarun da dama dan haka ma da yawa daga cikin yaranta ba sanin su yayi ba kasancewar shi mai yawan yin tafiye tafiye hakan yasa ko garin sukazo basu fiye samun shiba balle kuma shi in zaiyi tafiyar balaguron shi bawai yanayin sallama da mutane bane balle kuma ya shaida musu inda ya dosa, haka nan yake kamar sammatsi inda kake zaton samun shi ba nan yake ba, Duk zaman hirar da sukayi a gaban mai martaba idanuwan shi suna kan Sarki, inya kalle shi sai kuma ya maida duban nashi kan Meenal yanayi yana gyad'a kai, sai dai kuma kallo yake musu irin wanda ko kai da ake kallon ba lallai ne ka gane cewar ana kallon naka ba, bai iya furta komai ba har sai sanda su Uwar gida suka mik'e da niyyar tafiya sannan ya dakatar dasu da cewa.. "Kai Babban mutum kafin ku tafi ka nemi wanda zai kawo ka gidana zuwa anjima dan mu samu daman tattaunawa" Daga mai martaba har uwar gida kallon su suka maida kan Baban d'an magori, babu dai wanda ta tofa a cikin su sai shi Sarki daya amsa da cewa " to insha Allah zan k'araso tsoho" daga haka yasa kai suka fice, Bayan fitar su mai martaba mai da duban shi yayi wajen Baba dan magori, sai dai shi kuma dan magori bai bashi damar magana ba illah ma tarar numfashin shi da yayi da cewa, "kar ka damu ba wani babban abu bane insha Allah babu abinda yafi karfin Allah, sharri ne kawai ya had'u dashi irin na mace da kuma wasu ma dake gefe tare dashi, amma insha Allah komai yazo karshe Allah zai mana maganin su, ita kuma waccen da kuka gabatar a matsayin matar shi to sai dai fa kuyi hakuri dan ba matar da zaiyi rayuwa da ita bace, ita dai Allah yasata shiga rayuwar shine dan ta zame mishi garkuwa, dan haka ko wani abun ya taso zuwa gaba karku matsa kuce sai sun zauna tare, dan zaman nasu takaitacceni daga wajen ubangiji dama, sannan ita waccen matar nashi na wancan gari komai zai faru kar yace zai rabu da ita a kuma yi mishi tuni akan yawaita addu'a yawan sadaqa ma kuma yana maganin fitintunu" Daga haka Baba dan magori bai k'arayi ma mai martaba k'arin bayani akan komai ba harya mishi sallama ya tafi, a wannan ranar Sarki bashi kadai yaje ga baba dan magori ba domin uwar gida ce da kanta ta mishi jagora zuwa can din, kuma itama duk yanda taso ya bata k'arin haske k'iyawa yayi yadai had'a maganguna ya damk'a a hannun ta cewa da zarar sun isa gida tayi ma Sarki amfani dasu a kuma nan take shima yasa Sarki yayi amfani da wasu daga ciki kafin su baro can ya kuma fadama uwar gida cewar zai aiko da sako, Sanadiyyar wadannan magunguna ne yasa Sarki ya fara samun sauye² na yawan jin buk'ata sab'anin yanda a shekarun baya har yazo yayi zaman shi a garin ya koma baya tunawa da batun ko wani buk'ata, sosai yake cikin yanayi sai dai kuma ko yaushe in yayi yunkurin zuwa ga Meenal sai ya kasa saboda rashin sanin yanda zai tun kareta ko kuma ita a yanda zata tarbe shi a wannan lokacin, yayi nazari sosai akan dalilin daya hana kanshi kusan tanta amma ya rasa gano bakin zaren, duk da koda yake jin bukatuwar bawai hakan yana nufin cewa ya fara jin wani abu a kanta bane, inah har yanzun dai kallon ta yake a matsayin yar karamar kanwar shi, a haka dai yaci gaba da dannewa har zuwa sanda Teemah tazo sai kuma akayi rashin sa'a ita ma wajen ta babu labari, wannan dalilin na rashin samun biyan buk'ata shine ya zama silar ciwon shi da har yayi tsamarin da yake jin gara ya ture komai ya rungumi yar matar nan dai dake zaune cikin gidan tsayin shekaru. (Masu karatu ina fatan kun gane inda muka dosa domin naga wasu nata k'orafin cewa, "shi kenan teemah taci nasara akan su, tunda ta raba auren" ku sani sam wannan sakin baya nufin nasarar teemah domin da ace nasarar tace tofa da tuni auren bai kawo wadan nan shekarun ba, ina fatan ba zaku gajiya wajen bibiyar labarin ba? Domin dai muna da sauran chakwakiyar rigima sosai a gaba) Sashen Malam Sulaiman uwar gida ta nufa tare da magungunan data kwasa, dan dole a wannan karan tana buk'atar ya bata daman bin Sarki zuwa Kaduna har zuwa sanda zai gama amfani da magungunan ita kuma sai ta dawo gida, Ta sameshi yana shirin fita, sai dai hakan bai hanata neman wajen zama ba kafin ta gabatar mishi da buk'atar ta nason bin Sarki, "Abban su magana nazo muyi gashi kuma naga kana shirin fita ne!" "Eh kafin ki shigo kam shirin fita nikeyi, amma yanzun bayan shigowar ki dole nane in zauna in saurari mai Uwar gida ke tafe dashi dan na tabbata ko mai nene yana da mahimmanci sosai" Ya karasa fada da murmushi a yayinda ya isa gareta shima ya zauna har jikin su na gogan juna, "Fad'amin wani abun ne ya faru?" "Eh to kusan hakan domin abubuwa da dama sun faru kam suna ma kan faruwa, amma dai yanzun duk ba lokacin da zanyi maka bayanin su bane" Magungunan ta fiddo ta fara mishi bayanin su d'aya bayan d'aya domin ko tuni yasan da batun magungunan wajen Baba dan magori, "Na yanke shawarar in bishi can ne saboda kaga anan dai bazai yiwu ince inyi ta jelen zuwa gidan shi kullum ba, kuma shima bazai yuwuba ace anan gidan ne zaiyi amfani dasuba, kuma kona bashi ina da tabbacin cewar ba lallai bane ya maida hankali akan amfani dasu ba, amma kaga a can dole zan tabbatar yayi amfani dasu yanda ya dace" Sun tattauna sosai kafin Sarki ya iso gidan harta koma sashen ta tayi shirin tafiya yana isowa gidan ko kai tsaye ba boye boye ta shaida mishi cewar binshi zatayi su tafi kadunan tare ita da kanta zata kula da batun magungunan shi da Baba dan magori ya aiko dama wanda aka kawo mata yau sai dai bata fad'a mishi cewar Hajiya ce ta kawo ba, (Allah sarki iyayen mu mata ubangiji Allah ya k'are ku da lafiya, wadanda suka rasa nasu kuma allah ya jikan su, ameen). Dan Allah duk wacce ta karanta page din nan tasamin mahaifiyata a cikin addu'a domin bata da koshin lafiya, ina fatan Allah ya bata lafiya mai dorewa da jinkiri mai amfani da albarkha, To dai uwar gida tayi nasarar iza k'eyar dan ta zuwa kaduna garin gomna, A gidan Hajiya kuma shima jarumin mu gari ya mishi zafi dan haka shima tuni ya sai ta hanya zuwa gudun hijira, to ita uwar gayyar ko kwana nawa zatayi tana jimamin nata mutuwar auren? To ga kuma malam da bai san wainar da ake toyawa ba har yanzun, bari mu koma gefen Gimbiyar Sarki Teemah muji ita kuma tana yar wanne munji ta shiru kwana biyu, ********* A ranar da komai ya faru a gidan Meenal, Bayan teemah tabar gidan kai tsaye tana zuwa gida ta tattara kaf abubuwan ta na amfani motar da Sarki ya bata wacce take amfani da ita in tazo garin da ita tayi amfani tabar garin sai da ta tsaya a kaduna nan ma ta kwashe komai nata tsaf sannan ta nufi Lagos garage ta nemi driver din dazai tuk'ata suka tsadance yaja ta tun daga kaduna zuwa Lagos a mota abinda bata taba kwatan tawa ba, tsayin rayuwar ta amma tashin hankalin da take ciki yasa gaba d'aya bata iya tunawa da batun hawa jirgi ba, teemah bata tab'a tabbar da zancen yan magana dake cewa tafiya yankin azaba ce ba har sai a wannan ranar domin dai tayi wuji wuji ta kuma galabaita sosai haka ta dunga kwarara amai kafin su isa duk ta gama firgicewa, address din gidan Brigadier general taba driver din motan dan haka can suka nufa, Shidai driver dama Allah Allah yake yaga sun isa lafiya batareda ta mace mishi a cikin mota ba dan haka suna isa bayan ya tabbatar gidan su ya kaita shima ya kama gaban shi domin dama ta riga ta tura mishi kud'in shi a cikin account tun ma kafin su taso, Ganin halin da take ciki na ciwo yasa babu b'ata lokaci Aunty da autan su suka kwashe ta sai asibiti dan kamar jira jikin nata yake su isa gida jini ya tsinke mata, To ta dai sha dakyar kafin likitoci su gano cewar cikin dake jikinta ne ke neman hanyar fita wanda ko ita uwar cikin bata san da zaman shiba, dan ita bayan data dawo hayyacin ta Aunty ke mata batun cikin ma musawa tayi da cewa al'ada takeyi har sai da likitan ya zauna ya mata bayanin cewa ba al'adah bane cikin ne dai dama tun farko bai zauna a cikin mahaifan taba amma dai yanzun sunyi kokari sun mai dashi dan haka zasuci gaba da rikon ta a asibitin har zuwa lokacin da cikin zaiyi kwari sosai domin basa bukatar tayi ko wani aiki hutu kawai take buk'ata kuma hakan bazai samu ba sai tana cikin asibitin, Badan taso ba haka nan dai a babu yanda zatayi ta amince da zaman asibitin saboda soyayyar ta nason haihuwar d'a namiji, duk da babban kudurin ta na dawowan shine zuwa takaima OBA ziyara dan ya D'aukar mata matakin gaggawa akan Sarki da Meenal, Tunawa da batun Sarki da Aminatu cewa suna can fa suna cin amarcin su da tsinke a yayin da ita kuma ta kasance kwance a gadon asibiti har tana shirin rasa cikin da take fatan ya zame mata sanyin idaniya inya kasance d'a namiji, wannan tunani da damuwar data d'aurawa kanta shiya k'ara sawa jikin nata ya rikice. *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 ~{{MY FAMILY}}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ```` *Page 47* A yawancin lokata da dama mukan tsinci kan mu da son ganin mun nesanta zukatan mu akan yawan tunanin wasu tunanun nukan da dama wadanda muke ganin sun addabe zuciyar mu, Sai dai kuma sau tari duk yanda zamuyi kokari wajen nuna juriyar mu dan ganin mun danne tunanin ko muyi kokarin gogeshi dan kar ya zamana abinda zamu ringa tunawa akoda yaushe hakan sai ya faskara a garemu, domin kuwa wani yankin tunanin yakan zama dauwa mam mene tun daga cikin kwalwa harma a cikin zuciyar mu, Hakan ne kuma ya faru da AK a kokarin shi na son ganin ya ture duk wani tunanin Meenal bayan komawar shi Kaduna kan har kokin shi, sai dai ina abun fa sam ya gagara, domin sau tari yakan so ya maida kanshi irin so busy d'in da bazai iya tunanin komai ba sai abinda yakeyin amma sai kaga tun kafin aje da nisa ya gaza tab'uka komai, tun yana iya kokarin shi wajen ganin ya boye komai a cikin zuciyar shi kamar yanda ya saba sai gashi kafin ya ankara hakan ya tab'a tunani dama kuzarin shi, Sadeeq, Musty, Yusuf sun sha zaunar dashi dan son suji takai maiman abinda ke damun shi amma sam ya kasa fad'a musu, kullum in sun matsa mishi da tambaya sai dai yace musu gajiyar aiki ne kawai, gashi kuma sunyi sunyi dashi akan ya koma gida ya huta su zasu ci gaba da kula da komai yak'i, To kwana biyun nan dai haka nan yake jin jikin shi kamar wanda ciwo keson kamawa dan haka yau ya yanke hukuncin zama a gida ya huta, Sai dai koda ya kwanta da sunan hutun zuciya da kwalwa basu bashi had'in kai ba domin ko tsaf ya nemi bacci daga cikin idanun shi ya rasa, haka nan yake jin zuciyar shi sam babu dad'i duniyar gaba d'aya ta mishi k'unci, inda wani zai tambaye shi mai yake da bukata a yanzun? Shi kanshi yasan bashi da wannan amsar sai dai kuma acan k'asar zuciyar shi yake jin sautin sunan Yarinyar nan na mishi amsa kuwa, sosai kunnuwan shi suke buk'ace da son jin muryar ta, muryar da aduk sanda ta shiga kunnen shi sai tsigogin jikin shi sun mik'e, haka ma sosai idanuwan shi ke cike da maraicin son ganin kyakyawan fuskarta, fuskar da komai kuncin da yake ciki idan ya kalleta sai yaji ya samu sassauci, Ga dai number din wayarta daya lalubo a cikin group dinsu na *Dangi* da suka bud'e domin tattaunawa wanda shima yana ciki, Sai dai kuma gaba d'aya ya rasa kuzari da gwarin gwuiwar kiranta kai tsaye domin hakan bai tab'a faruwa ba a tsakanin su, kamar yanda bata tab'a kiran shiba haka shima bai tab'a kiranta ba koda wasa, Sai dai lokaci lokaci yakan zauna ya bud'o hoton ta data d'aura a dp dinta na WhatsApp da takan canza lokaci lokaci yayi ta kallo har sai yaji ya gamsu sai ya rufe wayar, to yanzun kam an kai matakin da ba hoton yake buk'atar cigaba da kallo ba ah ah ita d'in dai kaco kam yake son gani koda koh ace bazasuyi ma juna magana ba, sai dai kuma a yanzun sosai yake tsoron abinda kusancin nasu zai iya haifar mashi, Ganin cewa bashi da wata mafita hakan yasa shi yanke hukuncin d'aukar wayar shi dan ya kira Hajiya, ya tabbatar da cewa indai yarinyar nan tana gida tofa babu shakka za'a sameta ne tare da Hajiyar a yanzun dan kwana biyun nan ya gane cewa sam hajiya tabar yayin kowa sai Yarinyar, Kira ya danna ma number din Hajiya, kiran farko haka wayar taci gaba da ringing had'e da bugawar zuciyar shi, amma abun haushi har wayar ta gama k'ara ba'a d'aga kiran ba, K'ara maida wani kiran yayi shima d'in dai ba'a d'auka ba, kamar dai ya hak'ura sai kuma ya kasa, dan haka sai ma ya k'ara kiran wayar a karo na uku, kiran na gab da yankewa aka d'aga daga can gefen, "Assalamu Alaikum Hajiya bata kusa inta dawo za'a fad'a mata an kira!" Tana gama fad'in hakan k'it ta yanke kiran ba tareda ta saurari abinda wanda ya kira d'in zai ceba, "Hummm " yaja wata irin dogowar ajiyar zuciya mai cike da tarin sinadaran dake ba mutum nutsuwar daya rasa tsayin lokaci, Murmushi mai kama da dariya yayi kafin ya furta a bayyane cewa, "Marajin magana, wato tunda ta isar da sak'on shi kenan sai kawai ta wani yanke wayar ta, to dama wa yace mata muryar Hajiya nike son jine?" Kara kiran wayar yayi a karo na hud'u, kuma wannan karon ma bata d'auka ba sai da wayar take gab da katsewar, "Ke yarinya waye yace miki ki yanke min waya tun banyi magana bane? in Hajiya bata nan ke bazaki iya amsar sakon ba, kawai kin d'auki waya ko gaisuwa ma babu kuma kika yanke min waya hala baki iya karatu bane da baki karanta sunan wanda ya kira wayar ba?" "Wake magana?" Ta tambaya kai tsaye babu ko d'ar a cikin muryar ta, "Kaiii" ya fad'a yana zaro idon shi waje dan baiyi tsammanin amsar da zata bashi ba kenan, kai yarinyar nan wai mai take nema dashi ne? Har shine ma wai zatace ma wake magana, "Wanene ke magana nace?" Ta kara tambaya, "Baki iya karatu bane?ko kuma muryar tawa ce ta zamar miki bak'uwa ayau" Ya maida mata da amsa, "Baka amsa min tambayar da nayi ba, kaga malam in bazaka fad'amin ko waye ba zan yanke kiran ne aina fad'a maka cewar Hajiya bata nan, kuma nufin ka dan naga suna shi kenan bazan tambayi ko waye ba!" Ta fad'a cikin kunkunin data saba, "Ni kuma na rantse miki da Allah in kika yanke min waya sai nazo har inda kike na zane ki, inga k'aryar rashin kunya" "Eh ai dama kai kullum maganar ka kenan zaka zane mutum, in karfin gaske kake tak'ama dashi ka kama hanya zuwa sabon gari mana aiga gidan yan danbe can sai kaje ka dambace son ranka, badai dan kaji Hajiya nace maka d'an mai karfi shi yasa kake k'ara bubud'ewa kana ma mutane barazana ba, ni kuma insha Allah duk sanda ka tab'ani yayan mage zan hayo su taremin kai a hanya su min maganin ka" Lallai ma yarinyar nan wato kenan dai tsabar neman magana ne yasa take tambayan shi cewa wake magana tsaf ta gane shi ashe, a bayyane ko amsa ya bata da cewa.. "Oh ashe ke d'in yar sara suka ce bani da labari?" "Ban fara ba amma a kanka zan gwada" "Ai ban san yar ta'addace ke zaune tareda Hajiya ta ba da tuni na miki cinne, amma yanzun tunda kin tona kanki to tun wuri ki tattara naki ya naki kodai ki koma gidan ku ko kuma daga nan ki wuce d'akin mijin ki da kika gudo kai tsaye," "Haba taubashin tuzuru ai sai ka fito kawai kanka tsaye kace bak'in ciki kakeji saboda na dawo gidan Hajiya zan hanaka rawan gaban Hantsi kaida ala koron yan matan ka, ba shakka Ashe shi yasa ka tattara ka fece ko sallama babu tun ranar da mukayi ido biyu da kai, to bari in baka albishir, nan dai gidan da kaima kake tak'ama dashi ka sani cewa irin wannan tak'amar naka nikeji akan shi, dan haka yanzun da nike cikin shi kai kuma kakajin haushi koh? to sai ka share waje kayi zaman ka acan inda kake dan gidan nan zama na a cikin babu fashi," "Ke wai nine dai kike cema tuzuru koh?" ya tambaya "To naga dai ai ba karya nayi ba, koba tuzurun bane? " "To tuzuruwa nasan naki tuzurancin nema yasa har kike jin haushi na, dan haka kema ga gidan nan ki share domin zaman zawarci!" Ya karasa fad'a da dariya a muryar shi, Kuka ta fashe mishi dashi sosai ta wayar. "Ni wallahi ba bazawara bace allah ya kiyaye min in zama bazawara," take fad'a da muryar kuka, "Oh inba zawara ba me cece? fad'amin yarinya ce ke ko budurwa ko kuma matar aure?" "Ni ka kyaleni ina ma ruwan ka dani inma mecece aini ya shafa," "Ah ah wallah nima ya shafeni, bakiga shi yasa na kasa sukuni ba........" Shiru yayi yana rufe bakin shi da hannun shi jin yana shirin yin katob'ara, "Miye ya shafeka?" "Ke kin isheni da surutu idan Hajiya ta shigo ki fad'a mata na kira, ko kuma kima barshi kawai zan kirata anjima" Kit ya tsinke kiran bai k'ara sauraren jin ta bakin taba, mirginawa yayi sannan ya janyo filo ya rungume a k'irjin shi tsam tsam, cike da shaukin soyayyar daya dade baiji shi a tare dashi ba, A wannan lokacin ita kuma haka taci gaba da danna mishi kira da number din Hajiya babu k'akk'autawa amma harta k'ari kiran ta gama bai d'auki wayar ba, dan yasan koya d'auka fadar dai zasuci gaba dayi, shi kuma yanzun nutsuwa yake buk'atar samar ma zuciyar shi ba hargitsi ba, Yana a cikin wannan yanayin har Yusuf daya shigo gidan ya iso har cikin d'akin bai sani ba, Shima Yusuf din ganin halin da AK din yake ciki hakan yasa kawai sai ya nemi kujera ya zauna yaci gaba da kallon shi yana kuma nazartar shi, dan shi tuni ya fara harbo jirgin abokin nashi duk da kuwa yanda yake b'oye musu hakan bai hanashi gano cewar ya fad'a soyayya ba, Cigaba da mulmule mulmule AK yayi akan gadon domin Shifa tuni ya fita daga cikin duniyar mutane ya haura can sama kololuwa cikin furannin soyayya, Shiko wase yana dai zaune yana ci gaba da kallon ikon Allah dan dama tunda ya shigo ya kunna record a wayar shi ya ajiye saboda maganin musu, Juyowar da AK yayi ne idon shi ya sauka akan Yusuf din dake zaune akan kujera abunshi ya zuba mishi, ido, "Mtws" yaja tsaki a bayyane, kafin yace "Wase wani kalar iskancine wannan zaka fad'omin cikin d'aki babu notice? Kasan dai hakan haramun ne ko a musulunce ko?" "Eh ai dan uban mutum tunda nasan ba mata gareka ba me zai hana ni shigowa kuwa bayan nayi sallama baka amsa ba? Ko ka fara danne yan mata ne a cikin gidan bani da labari? Aikin banza ka wani kama pillow ka kankame a kirji kamar ka samu mace, mtsw" Ya karashe fada da jan tsaki, "Kai banza ne wallahi kawai ina cikin yanayi mai dad'i kazo ka katse min, mema ya kawo ka gidan nan? Ai nace muku yau hutawa zanyi babu inda zanje" "Wannan kuma kai ka jiyo amma kam tunda har na iya baro nawa iyalin na taho kasan dolen ka fita wallahi, dan kira nasamu daga wajen mutanen can na Barnawa," "Oh my God to shine bazakuje kuji dasu ba dole ne sai kun takura min," "Hakuri zakayi ka shirya muje inka dawo sai ka huta dan na musu alkawarin cewar zamu zo" Badan yaso ba haka dai ya shirya din suka tafi, ba su suka dawo gidan ba sai yamma liss, koda suka shigo abincin da suka siyo a hanya suka bud'e, Hankalin Yusuf kacokam ya mai da kan AK dake cin abincin shi hankali kwance, "Wai kasan me yasa some time bana son zuwa garin nan?" ya tambayi AK "Ina ko zan sani tunda ba tsibbu na fara ba," Shima ya bashi amsa. "Ai kai banza ne wallahi dan Allah dan annabi ka taimakeni ko dan ni kayi aure, wallahi ka sani Allah ne shaida na cewa da ciwon yunwa nike komawa gida duk sanda nazo garin nan, saboda bana samun cin abunci da kyau, haba dan Allah ina ma amfani k'aton namiji kullum sai yaje siyan abinci, amma fisabilillahi in kana da mata ni har zanji wani d'ar nema tunda koba komai nasan zanci mai d'adi koda bai kai na matana ba, ni wallahi ina mamakin inda ka kai kyankyamin ka bayan nasan ba a ko ina kake iyacin abinci ba ada amma yanzun a garin nan da alama kaf gidan abincin su ka sanshi," Ajiye cokalin shi yayi yana bin Yusuf da kallo, "Kai amma wallahi Wase kama raina min wayau, banyi aure dan buk'atar kaina ba sai dan saboda in kazo gidan nan kaci abinci zanyi? To kenan kuku zan auro a matsayin matana in ajiye maka ko ya kake so inyi ne iyeh Abba Ahmadu?" "Ai kai kaji tsiyar ka, sam ba zaka tsaya ayi maganar arziki da kai ba" "Eh na tsiya na iya can nafi kwarewa, aure kuma layine idan nima yazo kaina zanyi shine koda kuwa ban shirya ba, ba kuma wani ne ke cidani ba balle yace ya gaji" "Ai kai a duniya indai musu ne babu wanda ya kaika, ga bak'ar zurfin cikin da in bakayi wasa ba sai ya zama ajalin ka, badai ka iya tara damuwa a cikin kirjin kaba ka zauna a wajen harka rasa abinda zuciyar naka ke muradi kaga ka huta ai" "Ohhh ashe ka fara maita ban sani ba tunda har ka iya gane cewa ina da wata damuwa, to malamin duba fad'amin ya gobe na zata kasance?" Wayar da yayi record din d'azun ya d'auko kunno record din yayi ya ajiye a gaban Ak "Can you explain this to me?" Hannu ya mik'a ya d'auko wayar yana kallo, "Miye wannan d'in?" Ak ya tambaya. "Kai dai zaka bani amsar akan abinda ya jefa ka cikin shauk'i haka da har na shigo cikin d'akin tsayin lokaci baka sani ba!" Hummmm" ya sauke doguwar ajiyar zuciya kafin ya d'aura da cewa, "Wase yaushe ka koma dan sa ido ne bani da labari, ko kuma dai ka fara aikin binciken sirri akaina ne?" Serious sosai Yusuf yaci kafin ya kira sunan Ak "Abdul Khareem Ahmad, yaushe muka fara b'oye ma juna damuwar mu?, bani kad'ai ba dukan mu munsan kana da damuwa duk da kana ta kokarin boye mana, wanda kuma hakan ba sabon mu bane boye damuwar juna, a ganin ka mu bazamu iya tallafa maka bane idan har ka shaida mana halin da kake ciki? Su sauran sun sa maka idone dan suga iya gudun ruwan ka amma ni yau na gaza bazan iya barin garin nan ba har sai nasan abinda yake damun ka, in kuma ban kai matsayin da zan sani ba to, duk da jikina yana bani cewa damuwar naka tana da alak'a da mace, na kuma k'ara samun tabbacin hakan ne saboda yanda na sameka a d'azun, Fad'amin wata mai sa'ar ce tayi nasarar samun ka, ka sani ko yar waye mu din masu tsaya maka ne har sai mun d'auko ta mun kaimaka ita cikin d'akin ka zama na din din din a matsayin mata, ina rokon ka karka b'oyemin komai" Shiru falon ya d'auka kamar babu wani abu mai rai a cikin shi kafin zuwa can AK ya yanke shirun da cewa " wata karamar yarinya ce take shirin sa kaina ya tarwatse da tunanin ta Yusuf!" Sai kuma yayi shiru tsayin lokaci bai kara cewa komai ba, shi ma kuma Yusuf din bai tofa ba dan so yake ya amayar da duk abinda ke cikin shi, ba tareda shi ya takura mishi da yawan tambaya ba. "Yusuf karamar yarinya cefa ni banma san ta yanda zan iya tunkarar taba balle har kuma in gabatar mata da kaina a matsayin masoyi, kaima kasan hakan bai tab'a faruwa dani ba, ban saba tarar mace dan ingabatar mata da kaina ba a kullum matan ne ke tarana suna gabatar da kansu da bukatar su gareni dan haka ban san ta ina zan fara ba, kawai dai ina tsintar kaina a ciki farin ciki sosai a duk sanda na ganta ko naji muryar ta, haka kuma nike kasancewa cikin kewa da kad'aici a duk sanda na nesan ta kaina da ita, ban san dalili ba amma ji nikeyi a cikin zuciya ta cewa ita kad'ai nike muradi ita din zata wadatar dani in zauna da ita kad'ai a matsayin mata a yanzun shine kadai muradi na, sai dai kuma ban san ta ya'ya hakan zai faru ba" "Kenan dai kana so kace min har yanzun bata san cewa kana sonta ba?" "Bata sani ba dan ban tab'a nuna mata koda alama ba, hasalima auren ta bai dade da mutuwa ba amma wallahi kullum da tsoron kar in k'ara rasata a karo na biyu nike kwana nike tashi" "Bazawara" Wase ya ambata cike da mamaki, "Eh bazawara amma kuma wacce a zahiri ne ta amsa sunan a bad'ini kuwa budurwa za'a kirata" "Kai malam karka wani yi mata kwaskwarima duk macen da akama aure indai an d'aura tofa sunan ta bazawara ne" Katse shi AK yayi da cewa,,, "ban damu ba Yusuf koda wani suna za'a kirata, tunda har zuciyata tana sonta ko a ya na sameta hakan zanci gaba da zama da ita balle kuma abinda na shaida maka Ina da tabbaci akan shi" "Wacece ita? ma'ana ina nufin yar inace miye sunan ta ina ne garin su su waye iyayen ta? Duk ina son in sani!" "Karka damu kanka ita din ai ba bak'uwar ka bace," "Eh amma ai in baka fad'amin ba bazan san ko wacece ba!" "Sunan ta Amina amma Meenal suke ce mata yarinyar Aunty Jidda dake Unguwar Malamai zaria" "Kaiii" Yusuf ya ambata, "Kai mai jama'a badai yarinyar nan da akayi ma auren dole kwanan baya? Koba mai kiranka tuzuru ba?" "Ita fa" "Kai amma kun dace fa yasin kuwa ina fad'ama dan ni dama tun lokacin can naso inyi maka tsegumi amma sanin halin ka yasa na basar, to ya akayi auren nata ya mace ne?" "Sakaran miji ta samu mana, ya kaita gida ya kafe kamar wanda yakai ajiyar kud'i a banki" "Ahaf to ai mu Alhamdulillah indai haka ne gaba ta kaimu mai ya rage yanzun ai fad'awa kawai zakayi ayi faka faka a wuce wajen, dan wallahi yarinyar nan mai zafice da zarar kayi wasa sai dai ka fara ganin daka dakan motoci na layi alhaji," "Kai ban son wulakanci ya muna maganar arziki kai kuma kana sako wasa ne," "Ba zancen wasa ba Allah koni da ace baka ciki tofa tuni zanje inyi kamun k'afa a wajen Hajiya a bani ita in adana kogi ai baya k'in k'ari" Mtws Mai Jama'a yaja tsaki yana yunk'urawa da shirin barin mishi wajen, "Sorry sorry am just kidding, ni mai zanyi da k'arin wata mace kuma Allah na tuba, amma dai seriously zama bai ganka anan ba, can din dai daka guda zaka koma domin kasan yan magana sunce kula da kaya yafi ban cigiya, kar ka zauna anan ka saki baki acan kuma sai ka koma kaji ana wani zancen daban" "To idan na koma taya zan tun kareta, sanin kanka ne cewa soyayyar nan ni bak'onta ne, ban tab'a yin so ba balle in san yanda zan sarrafa ta wajen aika sakon inda ya kamata," "Karkaji komai indai soyayya ne matakan ta ai ba tsaurara kamar yanda kake zato bane, mataki na farko da zaka fara takawa shine jawota a jiki, Kaga duk wannan muzuran naka da kiran zan zane miki jiki da kakeyi, tofa duk ajiye su zakayi a gefe ka koyo tausasan kalamai wajen yin magana da ita," "Kai ban gane tausasan kalamai ba? D'an daudu kake son in zama a gabanta ne ko me? Kana ganin ta fa itama a taitsaye take kamar shinkafar da aka jik'a da ruwan zafi aka tsame, ita ba tafashe ba ita kuma ba dahuwa ba, yarinyar nan da zafina ma ba tsorona take ba in kuma naje mata a sanyi sanyi aishi kenan sai ta karasa maida ni mahaukaci," "Oh to a tsai-tsaye zaka tafiyar na naka salon soyayyar kenan, to ai yayi dama irin salon ai yafi bada citta, nidai ai mafita nike baka, indai kana son ta tofa dole ka ajiye duk wani girman kanka a gefe ka jawota a jikin ka har ta shak'u dakai, idan hakan ya kasance tofa bazaka sha wahala wajen yad'a manufofin kaba, jawo ta jikin naka kuma ya had'a harda d'aukarta kana d'an fita da ita yin siyayya haka ko kuma shan ice cream in ban manta ba tun a shekarun baya na Santa da son cin kaza, nasan ka gane mai nike nufi ta wannan gefen, amma tsakani da Allah karma kace ban fad'a maka ba zaka sha fama, dan kalarta ne kalar macen da suka kasance burin kowane cikakken namiji, Dan haka sai ka shirya ma yak'i da wadanda zasu fito rububin neman auren ta suma, yanzun dai inaga tunda kwana biyu kai ma baka lek'a ba ai ka tashi mu wuce Zarian kawai tunda mun gama uzurin da yake nan d'in dan dama nima gobe nike son in wuce Wase amma ba kwana zanyi ba. *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ ~{{MY FAMILY}}~ *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ```` *Page 48*..... *Masu ajiyemin sak'o a WhatsApp da masu kiran waya dan suji ya jikin mama ta k'araji, ina mai farin cikin sanar daku cewa Alhamdulillah jiki yayi sauki sosai wallahi nagode kwarai da gaske da kulawar ku gareni ubangiji Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci* ********* Ba tareda wani b'ata lokaci ba Mai Jama'a ya shige ciki, cike da zumud'i domin ji yake kamar wanda yayi shekaru bai sanyata a cikin idanuwan shiba,wani bak'on al'amari yakeji a tare dashi, ada shike nesanta kanshi da kusantar duk wani abu daya shafeta, amma yanzun zuciyar shi cike take da kwad'ayin son kasancewa tare da ita aduk wani saukar numfashi nashi, a cikin zuciyar shi yake fatan Allah yasa yana zuwa ita ce zata tareshi tayi mishi maraba,sosai ya kudura a ranshi cewa zaiyi yaki da koma waye wajen samar ma zuciyar shi abinda take so bazai tab'a gazawa ba har sai ya mallaketa, dan haka sabon wanka ya shek'a bayan ya fito kuma yad'an murza ma jikin shi mai kana kuma ya feffesawa sassan jikin shi turaren jiki, cikin kayan shi na sawa ya zakulo wani lafiyayyen yadi black blue da akama d'inki dai dai da zamani, manyan kaya ba wani burgeshi sukeyi ba dan haka nema yafi ta'amali da kananun kaya ko kuma suits, amma haka nan yau yaji yana ra'ayin sanyan kayan dan ya burgeta yana kuma fatan ta yaba koda a cikin zuciyar tane, wata bata tab'a kwalliyar daya yaba mata ba amma haka nan yake fatan ita da yayi kwalliyar domin ta ta yaba mishi. mata ma na d'aukar wanka dan sujawo hankalin mazaje kansu to me zai hana shima ya gwada, dan batun yauba yasan mutane da yawa na tankawa aduk sanda zaiyi shiga ta manyan kaya, shima ya shaida yanda yake ma manyan kayan kyau aduk sanda ya sanya su, yau kuma ra'ayin kanshi ne yasa zaiyi shigar dan ya burge budurwa, Tsaye yayi a gaban mirror yana k'arema kanshi kallo fuska cike da murmushin shi daba kowa ke samun sa'ar gani ba, Wai shi! Shidai ba wani daban ba! Shifa Abdul Khareem Ahmad Mai Jama'a shine yau yayi shiri na musamman badan komai ba kuma sai dan ya burge budurwa, Oh Allah shi yasa jama'a kance kar Allah ya kawo abinda bazai wuce ba, dan shima kanshi bai daina mamaki ba, to ya kuma sauran jama'a zasuji a randa komai ya fito sarari? Shi kadai ya kyalkyale da dariya yana nuna kanshi daya ke kallo a jikin mirror, "Ka daiji kunya AK an dai fad'i k'asa ba nauyi wallahi, wai duk wannan gayun dan mace kayi shi" Juyawa yayi ya koma inda ya ke tara hulunan shi, shifa rabon ma daya d'aura hula akan shi inba facing cap ba yasin tun bikin Wase dan ko d'aurin aure zasu inya kama dole in su Musty sun matsa to zai d'auki hulan ne sai ya rik'eta a hannun shi inma ya d'aurata akan shi tofa na d'an kankanin lokaci ne zai cire, sai da ya b'ata lokaci wajen zab'o wacce tafi da cewa da kayan daya sanya kafin ya mata kari ya kafa ta a kanshi ya wani cakota zuwa gaban goshi, (Hohoho jama'a ku hasko min kyau a wajen nan, kyau iya kyau wanka iya wanka, yau AK ne ke gayu dan ganin ya wafto zuciyar yarinya kota halin k'ak'a) Yafa wanku ya kuma d'auku kaya kuma sunbi jiki sai zabgaga kamshin yan gayu kawai yake abunshi , turaren shi da yasan Meenal na matuk'ar kauna ya d'auko, feeeee feeee feeee haka ya dunga feshema jikin shi turaren nan kamar ba kud'ade masu nauyi yasa wajen siya ba, agogon ya d'auko ya d'aura sai glass din shi shima kalar kayan jikin shi takalmin shi kuma half cover ya sanya, D'as ya fito a AK d'in shi namijin da yan mata ke marari, babu abinda ya d'auka sai mukullin mota da wayoyi da kuma jakar laptop, fitar shi daga cikin d'akin yayi dai dai da fitowar Yusuf daga cikin d'akin da yake sauka in yazo gidan shima, kamewa yayi kam kamar gunkin da aka sassaka aka ajiye a gidan tarihi idanuwa a waje baki a hangame, kallon kurillah yake bin AK dashi cike da mamakin wannan sauyi na farat d'aya da yake kan gani a tare dashi, Lallai ya yarda so na sauya mutum dan kuwa ga tabbaci nan a gaban shi zahiri yana kallo, girgiza kai yayi cike da mamaki yakai hannun shi guda d'aya ya mari gefen fuskar shi, "Kai jama'a wallahi dai ashe ba mafarki nikeyi ba, Ah lallai da gaske kake mutumina wannan kalar gayu har ina eh gaskiya na yarda lamarin nan bana wasa bane, da gaske aure kake so bana kam irin wannan kamshi kamar mai shirin tada gari" Cogewa shima AK yayi yana zabga ma Yusuf din harara cike da haushi yace.... "Amma dai kasan agwagwa tayi kad'an tace zatayi ma kwad'o gorin wanka, shiga kuma ra'ayina ne sanin kowa ne cewa tun ba yau ba dama ina sanya sutura duk kalar da nike buk'ata a sanda naso domin jin dad'in kaina, kar kayi zaton dan na fara son wata hakan zai sa in canza tsarin rayuwata ne" ya fad'i hakan yana hararar shi fuska a cunkushe, "Ah ah yaro ina abun kisisina faso a ido, kana batun tsarin rayuwa, ai tuni tsarin rayuwar ka kam yanzun sai dai muyi fatan Allah ya dai'daita al'amura dan kai kam tunda aka fara da haka allah yasa kar zuwa gaba muga kana tafiya kana sambatu, Ko ka manta a yanda na same ka d'azun ne? Kai kadai a gado ka wani uban matse filo uwa ka matse mace....." AK bai bari ya gama furta abinda yake son fad'a ba ya wawuri fillow din kujeran dake kusa dashi ya jefe shi dashi, "Kasan Allah Yusuf bana son wulakanci, kar kaga na zauna na fad'a maka damuwa na ka nemi mai dani wani d'an iska, ba gara ni ba kai ka manta ne lokacin da Saraki yayi maganar auren ka har ciwon k'arya saida kayi amma dan ubanka ana kai maka ita ko wata 9 cif bata cika ba ta haihu, kuma wallahi sirrina amana ne a gareka ko su Musty ka fad'ama Allah ya isana" ..... "Ah kwarai kam ai dole kace amana tunda kasan abun kunyar da kake guje musu shi kaima ka jajibo ma kanka, kai aini in ban ma fad'ama gayun nan wannan zazzafar labarin ba ai inaga ni kaina sai na zagi kaina wallahi, kaji ma da kyau labarin soyayyar ka labari ne mafi zafin da bazan bayar dashi ba sai an sauke min manyan kud'ade kafin in fesa ma duk wanda yake muradin saurara, Kana daga zaune zakaga yanda zan kud'ance akan labarin soyayyar ka da yarinyar can" Dariya harda na mugunta haka Yusuf ya duke yana kyakyatawa, "Labarin soyayyar tawa ce zaka kasa a faranti kana sai dawa?" AK ya tambaya cikin sanyin gwuiwa, "Me za'a fasa Malam mutuwar ko hisabi bari ma kaji in rantse, wallahi ni Yusuf sai ma su Sadeeq sun biyani da tsada kafin in sam musu labarin soyayyar ka dan ba duka zan basu ba gutsura musu kad'an zanyi, atoh alhaki kuma waya bari Malam kazo kana ta yima mutane dad'in bakin cewa kai ka girmi kana nan yara manyan matan ma sai ka zab'a to yane yanzun fa?" Ya karasa tambayar yana dage mishi giraren shi guda biyu, "Allah ya isa na wallahi" Cewar AK da bakin shi ya mace murus "Allah kam ai isashe ne indai wannan ne nima kaina shaida ne, dan gashi ya nuna isar nashi akan ka ta yanda har ka kasa lankwasa zuciyar ka kayi saken da har ta kamu da son jaririyar yarinyar can da aka haifa a gaban idanun ka, amma dai ko bani ba kowa ya ganka yasan shigar ka ta yau tasha bam bam dana baya, ko ka mantane cewa kai din fa d'aurin aure ne kad'ai kesa kayi shigar manyan kaya haka, dan kai dai ko gaisuwar sirikai zamu ba kasafai kake sanya irin wadan nan kayan ba, dan hakama Babaa karka wani raina ma kanka wayau, to miye a ciki dan ka ma abinda kake so gayu ai ta isa ne duk da kai d'in aiko babu gayun ma mai kyaune, amma ka kira Hajiya ka fad'a mata kana hanyan zuwa kuwa?" "Kai wai Yusuf ya kake min haka ne!" Ya fad'a a yayin da ya coge hannayen shi duk biyun dafe da kunkumin shi, "Gidan mufa zani miye kuma na wani sai na kira Hajiya cewa ina tafe?" Ya karasa fad'a yana harar Yusuf din. "Ai kaji tsiyar to ai kai dane kake da damar yima gidan shigar tsinke yanzun kam ai farauta zaka, naga kuwa zuwan ai bana Hajiya bane, kai ina fad'a maka fa indai kana son buk'atar ka ta biya cikin rufin asiri ba tareda ka kamu da hawan jini ba tofa ba iya yarinyar nan zaka lallab'a ba, yasin kai tsaye zan fad'a maka kayi takan tsantsan da lamarin Hajiya so samu ka nunnunka kulawar da kake bata fiye da lokutan baya,kasan dai Hajiya yar rashawa ce yasin kar kaga cewa kai na gida ne na tabbatar da cewa in baka damkowa da nauyi kana mik'awa tofa, abun nan da ake kira gida bai koshi ba shine zai K'ara faruwa, sannan kayi kokarin duk sanda kuka kasance tare ka dunga sako mata hirar yarinyar a wayan ce haka, ta yanda ita da kanta a hankali zata fahimci manufarka akan yarinyar nasan in har ka shawo kan Hajjaju tofa kaci rabin yak'in sauran ko daga kwance mu zamu karasa maka Allah kuwa, ina fad'a maka hakan ne dan na tabbatar da cewa yanda Hajiya tayi tsayuwar daka wajen ganin bayan auren nan tofa a yanzun kam bazata yarda a K'ara ba yarinyar wanda bata so ba, ka kuma san Hajiya bata goyon bayan rashin gaskiya wallahi karkayi zaton in yarinyar nan bata bada goyon baya ba Hajiya zata mata dole. " Ya fad'a a yayin da ya mik'a hannuwan shi ya d'aura akan kafadar AK d'in gamida jijjiga shi. "To angon yarinya muje koh, kuma dan Allah kayi kokarin kama kanka in mun isa saboda kar zak'ewar ka tayi yawan da zata fara tunanin ko murna kakeyi da mutuwar auren ta a dai bada kulawa sama ² daga yanzun har zuwa sanda zata sake da kai, ina fatan ka gama kintsawa ko kuma akwai abinda bai kammalu bane?" Ya tambaya yana nuna mishi kofar fita daga falon. ****** Bayan Hajiya ta isa gida a farfajiyar gidan suka had'e da Hajiya Jummai wacce dama tuntuni zaman jiran dawowar Hajiyan takeyi dalilin ma da yasa ta d'auko kujera ta ajiye a kofar sashen ta kenan takardu na envelope 📨 biyun nan kuma na tare da ita har lokacin koda alama ba tayi gigin budewa ba, "Ah Jummai kamar wacce dama take jiran dawowa na?" Hajiya ta tambaya. "Babu shakka dawowar naki nike jira Aunty shi yasama na kasa zaman ciki na dawo waje ina jiran ki" "To gani ai, Allah yamin dawowa Yaron nan tsohon Mijin Aminatu yazo nan gidan kuwa?", (Kuji hajiya da wani batu fa wai tsohon Mijin Aminatu kamar irin wanda sukayi shekaru da rabuwa🤣 Hajjaju tam) Cigaba da magana tayi bata jira amsar da Jummai zata bata ba.. " dan saurin da nike tayi kenan inyi in dawo kar yazo bai iskeni ba bayan ni kuma a kwai jawaban da nike so in karanta mishi, dan uwar shi tace min ta izo keyar shi tuntuni yayo nan" Envelop din nan biyu Jummai ta mik'a mata ba tareda tace komai ba, "Ah ah ya haka nida na tambayeki kuma kina mikomin wasu envelope daban". "Eh ai saboda suna kunshe da duka amsar da kike buk'atar sani shi yasa na mik'a miki, Yaron yazo kam dan sab'ani ma kuka samu kin fita kenan ya iso nan, mu k'ara sa ciki sai in miki sauran bayani" Hajiya bata amshi takardar ba kuma bata iya cewa komai ba illah gaba da tayi Jummai ta rufa mata baya, Sai da ta nemi waje ta zauna ta natsu kafin tace "Uhumm ina jinki bani labarin wani kalar diban albarkan yazo ya bar bad'a muku dan da ganin idanuwan shin nan tsai-tsaye ba kirki zaiyi ba shi yasa naso ace munyi ga da ga ni dashi," "To ya za'ayi Aunty ai sai dai hakuri yanzun kam kuma nima koda ya shigo bamuga juna ido da ido ba dan Aminatun yasa aka kira mishi ita yaba sakon" Ta fadi hakan tana k'ara ajiye ma Hajiya takardun a gefen ta. "Ah ah nikam kar ki ajiye min bafa tikitin aljannah bane dazan bud'e in karanta cike da farin ciki, Ke dai da kika saba karance karancen korafin masu k'ara a kotu sai ki karanto" Envelop din dake da nauyin shi ta fara d'auka ta balle shi, rappers ne na dalolin amurka jere a cikin shi bata tsaya duba ko guda nawa bane ta mik'ama Hajiya. "Kud'ine fa a cikin wannan" Ta fad'a cike da al'ajabi. "Kudi kuma? To kudin mene ne wannan din zazzage shi a k'asa mu gani, halan ce mishi akayi nid'in yar rashawa ce da zai kawo min cin hanci ya d'inke min baki da daloli," Idonta ta maida kan kud'aden cike da mamaki, "Jummai kud'ine fa masu yawa, anya kuwa Yaron nan bayan aikin Sojan baya had'awa da fashi da makami kuwa?" Ta tambaya tana faman zare ido a yayin da Jummai ta zazzage su kamar yanda ta buk'ata, ita kuma taci gaba da k'ara daddaga kudaden dan gaskiya kudine masu nauyi, "Ga wata yar takarda nan bud'e ta muji abinda ya rubuta" Cewar Hajiya. Babu musu kuwa Jummai ta d'auko takardar dan itama ta zaku taji ko wadannan tarin kudin na menene, "A fili fa zaki karanto" Inji hajiya. Ga abinda sakon ya kunsa. *Aminatu Meenal ina da tabbacin cewa a yayin da zaki kasance kina mai karanta wannan sakon nawa tabbas ba zaki karanta shi cikin farin ciki ba, na sani cewa ni mai laifine a gareki dama sauran Dangi da suka d'au yardar su suka bani wajen aura min ke dan suna da yak'inin cewa ni din zan kula musu dake, ayau na kasance ina mai jin kunyar kaina ina kuma jin kunyar kafatanin ahali na bama iyayen mu kadai ba, nasan ni d'in nayi asara mai girma wanda a kullum na tuna zanci gaba da ko kawa, domin nayi asarar macen rufin asiri, Aminatu ke din mace ce wanda ko wani irin namiji zaiyi fatan dauwa mammiyar zama tare dake, kin min halacci halaccin da bana zaton za'a samu wata macen da zata iya kwatanta zama na shekaru a gidan Mijin da yake matsayin Mijin auren ta amma ya yi watsi da ita kamar yanda na aikata a gareki , kuma wai harma ta daure ta kuma ci gaba da zama dashi ba tareda kowa yaji ba, dan haka nike k'ara rokon alfarmar ki ki yafe min hakkin ki dana danne tsayin shekarun auren mu domin bani da wani kalma da zanyi amfani dashi wajen kare kaina tabbas ban kyauta miki ba, sai dai na d'auki hakan a matsayin kaddarar mu,* *ina fatan Allah ya miki sauyi mafificin alkhairi a rayuwar ki, Allah ya baki Mijin da zai kula dake kamar yanda zai kula da rayuwar shi, zanci gaba da kallon ki a matsayin kanwata na kuma tabbata cewa zanyi matuk'ar kewar da d'ad'an abincin ki, Allah yasa rabuwar mu bazai sauya matsayina na yaya a gareki ba, ki kula da kanki fiye da yanda kika saba ina miki fatan alkhairi* *Sufyaan Sulaiman Ladan {Sarki}* "Mtwsssss...... " Hajiya taja wani uban dogon tsaki, a yayin da Jummai takai karshen takardar "Oh wato kudin girkin daya sa ta dunga mishi yana cinye wane ya biya? To yayi ma kanshi dan wannan kyautar dai babu ladane kuma babu zunubi, Miji kuma yana raye zaiga d'and'a shashen Mijin da takwara zata aura insha Allah shi dai kam shi yayi asarar mace, Budemin ita kuma dayar takardar inji saki nawa ya rubuta, dan kar yazo zuwa gaba yana cewa matar shi yake so dan Wallahi dai ko yafi maye maita takwarata ta tsallake rijiya da baya bata komawa gidan shi," Ta k'arasa fada tana sauke ajiyar zuciya. Bude d'ayar takardar Jummai tayi, Yar karamar takarda ce a ciki, Bata damu da jawaban dake cikin rubutun ba adadin sakin kawai ta duba, "Saki d'aya ne Aunty" "Saki daya kuma? Wani irin saki daya nida nike sarai da saki uku, to dai yayi ma kanshi ya tafi can gayyar tsiya anna a idi, duk su ke b'atawa auren cikin Dangi suna, gashi nan dai anyi daya ba k'ari ina ita kuma take?", Labarin abinda ya faru bayan wucewar Sarki Jummai taba Hajiya. "Muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam yanzun nan ita Meenal din ne ta zauna tana kuka uwa mai bakin uwa dan an saketa a auren jeka nayi ka, To wai shi kuma kawai sai ya zauna yayi ta kallon ta uwa ya samu majigi, bai nad'a mata dukan da idan na dawo zan dafa ruwan zafi in gasa mata jiki ba, oh ni Aminatu an daici amanata wallahi, yanzun nan fisabilillahi inda a can gidan su ta aikata wannan ta'addancin ba shi kenan sai a d'aureni har sai igiya tayi rara ba, ubanwa zan kalla ince bani ce silar mutuwar auren ba ya yarda dani? To taje dan kanta nidai dama dan Allah nikeyi inko ta matsa tsaf sai in zame hannuna kaf a kanta," "Ayi hakuri dai magana kuma ai ya k'are sai dai ayi fatan mafi alkhairi a gaba" "To ai yayi, yanzun ya za'ayi kenan kin san dai yarinyar nan ba iddah ne ya hau kanta ba, amma duk da hakan bazamu saketa saka ka uwa tunkiya ba, su kuma iyayen ta nidai babu wanda zan kira a cikin su da sunan in shaida musu abinda ke faruwa, su can dai sai su k'arata tunda uwar shi tanuna min daya copy din takardar sai su gabatar ma da iyayen ta, dan nasan ina zuwa ma Malam da batun nan sai yayi tsalle kafin ya dire akan nina kashe mishi auren y'a, dan haka ina nan a gida na suje can su k'arata. ****** A wannan rana da yamma kamar yanda Sarki ya fad'a Salman ya kawo ma meenal motar da takardun ta da komai, Kyautar data gigita Hajiya da Meenal dan ita dai Meenal gaba daya bata sa akaba, hajiya ko tukuicin naira dubu 20 ta ba Salman, a cikin lokaci kankani sai ga Hajiyar ku na fama sama Sarki albarka. A can kaduna kuwa tunda su Uwar gida suka isa bata sarara ba tana tsaye akan kafarta wajen ganin cewa Sarki yayi amfani da maganin yanda ya dace, ranar farko da ya fara amfani dashi sosai ya galabaita dan wani irin amai ya dungayi mara kyan gani kafin daga baya jikin shi ya d'ume da wani irin zazzafar zazzabi, sai da ya kwana biyu a gida baya iya fita ko ina hatta da Sallah a cikin gida yakeyi, hakan kuma baisa uwar gida ta tsagaita ba dan dama Baba d'an magori ya shaida mata cewa duk abinda ya biyo baya karta damu, Allah da ikon shi dai a hakan tun in yasha maganin yana sashi amai da zafin jiki har a hankali yazo ya daina, ta kumayi tsaye a kanshi wajen ganin ya kiyaye azakhar din safe da yamma ga kuma nafilfilin dare da ita da kanta take ta dashi a ko wani dare, Lallai wanda duk ya rike allah bazai tab'a tab'ewa ba domin ko a hankali Sarki ya dunga jin wani kalar nutsuwa yana shigar shi, sai yaji shi ya koma kamar wani jariri sabon haihuwar da bashi da damuwar komai, sosai yaji dadin kasancewa da mahaifiyar shi a wannan lokacin domin sosai take bashi kulawa kamar k'aramin yaro, ita kuma sosai tayi amfani da wannan damar wajen janshi a jiki tana kuma yi mashi nasiha, Tsayin kwanakin nan kuma ko sau d'aya uwar gida bata sako mishi zancen Teemah ko na meenal ba, shi kuma gaba d'aya kamar wanda aka gogewa tunanin komai, Acan Lagos ko Teemah nacan ta cika tayi dam kamar ta fashe domin dai kullum sai ta duba wayarta ko zataga kiran sarki dan dai ita tayi ma kanta alkawarin cewa bazata kira shi ba domin dai ta saba aduk sanda suka samu sab'ani shine ke neman sulhu koda ko ace itace bata da gaskiya, tayi zaton zaiyi ta kiran ta ne kamar ko yaushe ita kuma inya kira baza d'auka ba har sai ya baro komai ya taho dan ya rarrasheta, To gashi dai shiru bai kiraba kuma baizo ba ita kuma tace bazata kira ba, karin takaicin kuma jikin ta da har yanzun yaki dawo mata da lafiya bashi babu halin fita zuwa wajen OBA shi kuma ba wayace dashi ba balle ta kira shi ta sanar dashi halin da take ciki, Koda uwarta ta tambayeta cewar ta shaida ma Sarki batun rashin laifiyar nata k'arya tayi mata da cewa baya k'asa yayi tafiya, dan ta kuduri aniyar ita kadai zatama kanta yaki, bata buk'atar abokin tafiya. *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/7, 11:53 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ ~{{MY FAMILY}}~ *Free Book* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 *Ga masu buk'ata daga farko zaku iya tuntub'ana kai tsaye ta wannan number d'in 08061358462*. ```` *page 49*...... A kwana a tashi babu wuya a wajen ubangijin al'arshi domin kuwa yanzun hakan an kwarari kusan kwana goma da komawar Meenal gidan Hajiya, zaman ta a gidan kuma bai hanata zuwa makaranta ba domin tsaye Hajiya take akanta wajen ganin bata d'aura ma kanta damuwa ba, da zarar Hajiya taga ta zauna zata fara wasu tunane tunane na banza a cewar ta take k'akalo mata wani aikin ko hirar da zai d'auke mata hankali, dan Hajiya tace bataga abun tuni dan auren jeka nayi ka ya balle ba. har zuwa lokacin kuma Allah da iyawar sa a can unguwar su babu wanda hankalin shi yakai kan cewa meenal bata gidan ta domin yawancin lokuta dama in karatu yasha mata kai takan d'an daga kafa da zuwa gidan su sai dai takanyi kokarin kiran su a waya su gaisa, su kuma tunda sun san ba kasafai take wuni a gida ba, saiya zamana babu wanda ya damu ya lek'ata dan sun samu labarin cewa Sarki ya koma bakin aikin shi, Malam kuma da idan shiru yayi yawa yakan tura a lek'o mishi ita a cikin satin tafiya ta kama shi zuwa garin Maiduguri kuma dama in tafiya takai shi can yakan yi kwanaki bai dawo ba sai dai suyi ta waya da meenal din, Lokaci lokaci meenal d'in kan kira mommy Hauwa da Innar yara dan su gaisa amma bata yarda ta nuna wata alama da zai nuna musu cewar akwai wani abun da yake faruwa ba, Meelat da Maryam su kad'ai ne ta fad'ama halin da ake ciki, suma kuma saboda yawan tamba yoyin da suka dunga jera mata ne akan dalilin daya maida ta zama gidan Hajiya, zahiri sunyi bak'in ciki kwarai sun kuma taya k'awar tasu jimamin abinda ya sameta daga k'arshe kuma suka mata fatan Allah yasa hakan ya zama mafificin alkhairi a gareta, ita ko Maryam d'aurawa tayi da cewa garama hakan ko banza zata samu daman warwasawa a bikin Meelat aure bazai mata shamaki da kowa ba. Hajiya dai ta kame kanta a gidan ta, Yayin da a gefe guda kuma ta kasa kunne ne taji ta ina maganar mutuwar auren Meenal zai fara fitowa, tasan dai dole in maganar ta fasu dole kowa zaiji, ita kuma ta shirya gwabzawa da kowa akan maganar nan. ***** Alhamdulillah jikin Sarki yayi sauki sosai hakan yasa uwar gida ta tattaro kayan ta ta dawo Zaria domin fuskantar abunda ke gabanta na gabatar da takardar sakin Meenal zuwaga iyayen ta, Shi kuma Sarki bayan wucewar ta shima shirin wucewa Calaba yayi a wannan ranar kuma har zuwa lokacin bai kira teemah ba domin sosai ya d'auki fushi da ita, (To Sarki sai muce Allah yasa karshen wahalar kenan Allah kuma ya kiyaye na gaba). Tun da Uwar gida ta dawo take cikin taraddadi da jimanin yanda zata gabatar ma Malam Sulaiman da takardar nan, a haka har dare ya riske ta, kasancewar ita ta amshi girki bayan dawowar ta hakan yasa da wuri ta shirya bayan ta kammala komai ta wuce zuwa turaka. Sak'a da warwara ta dungayi dan bata san a yanda shi kuma zai kalli hukuncin nata ba, Tana cikin wannan halin na rashin makama har ya shigo ta gabatar mishi da abunci, Duk da ya fahimci halin rashin nutsuwar da take ciki bai tanka mata ba har saida sukazo kwanciya, yana ta zuba ido yaji tace mishi wani abun amma shiru, gashi ta kwanta din amma gaba d'aya ta kasa nutsuwa sai juye juye kawai takeyi alamun akwai abunda ke damun ta, gajiya yayi ganin tak'i cewa dashi komai yasa shi ya tanka da cewa. "Ya kika baro Dan naki? Koda yake d'azun ya kirani cewa yana Calaba!" "Alhamdulillah dan dama koda na baro can shima ya shirya wucewa a lokacin bayan ya sauka kuma ya shaidamin cewa ya isa lafiya" Ta amsa mishi. "To Allah ya tsare na gaba ya kuma cigaba da karewa" "Ameen" ta amsa dashi can kuma sai ta k'arayin shiru, "Gimbiya meke faruwa ne? Ina lura dake tun d'azun akwai abunda yake damunki amma kin kasa furtawa ko wani abun ya farune kuma a zaman ki dashi?" "Hummm" Ta sauke ajiyar zuciya, "Kin san bazan samu nutsuwa ba har sai na saurari abun dake damunki, fad'amin maiya faru?" Shiru tayi tana ta tauna maganar da zata furta ta yanda zai mata kyakyawan fahimta, "Ina jinki!" Riko hannun shi tayi a cikin nata kanta a duk'e ba tareda ta yarda sun had'a ido ba tace, "Ina rokon alfarmar cewar zaka tsaya ka fahimci dalilina na aikata abunda na aikata, zanso ace koda kowa bai fahimci dalilina na yanke wannan hukuncin ba kai kamin kyakyawan fahimta, nima ba dan naso ba na yanke hakan sai dan ganin cewa hakan shine mafita duba da halin da ita Meenal zata iya shiga zuwa gaba".... "Na fahimce ki dan nasan bazaki aikata wani abun dan son zuciya ba koma menene nasan kina da dalili mai karfi na aikata shi" Hannu ta zura a karkashin pillow ta zaro takardar, mik'a mishi tayi ba tareda tace komai ba, Duk da yanda gaban shi yake fad'uwa hakan bai hana shi bud'e takardar bayan ya amsa ba, rubutun dake Zane a jikin takardar ya ke bi da kallo yana karantawa daki daki kamar mai koyon karatu, jikin shi a sanyaye.. "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, Innalillahi wa'innah ilairir raju'un, Innalillahi wa'innah ilairir raju'un ya Allah ka shiga al'amarin nan" Yake maimaitawa jiki a sanyaye yayin da tashin hankali k'arara ya baiyana a yanayin muryar shi zuwa kan fuskar shi, Saukowa uwar gida tayi daga kan gadon zuwa k'asa ta maida gwuiwar ta a k'asa, "Dan Allah ka tsaya ka saurareni kafin ka yanke hukunci, hakika nasan ko wani uba bazaiyi alfahari a yayin da d'an da ya haifa ya saki macen da yake aure ba, Na yarda Sarki yayi laifi, amma a wannan karon laifin duk nawa ne, nice idona ya rufe na manta da cewa bawa baya gujema kaddarar shi, idona ya rufe na manta cewa komai yayi farko yana da karshe, Idona ya rufe a lokacin da nike ganin cewa k'arin aure shine kadai hanyar da zan samu kusanci tsakanina da d'ana, Na manta cewa d'iya mace itace kadai ake iya tilastawa auren dole ta kuma yi biyayya ta zauna tsayin rayuwa koda ko batajin dadin kasancewa da Mijin da aka aura mata, sab'anin d'a namiji da yake da hanyoyi da dama na kuntata ma matar da aka tisalta mishi ya aura koda ko babu duka ba zagi, sai dai kuma ganin kusancin dake tsakanin su hakan yasa nayi tunanin cewa koda yak'ita a farko akwai yuwuwar cewa zuwa gaba zaiso ta harma yayi alfaharin auren damu muka mishi, sai dai kuma ashe duk hasashe nakeyi " Dago kanta tayi tana kallon shi fuska a raunane taci gaba da cewa, "Nayi dana sani kwarai na dagewar da nayi har akayi auren yaran nan,ni ban san gaibu ba da ace Allah yana bamu sani akan abunda zamu riska a gaba da banja tunga na tsaya wajen ganin tabbatuwar auren ba yanzun da wani idon zan kalli jama'a?" Kamo hannunta yayi ya zaunar a gefen shi, "Maiya faru har hakan ya kasance bani da labari, kafin ki aikata komai daya shafeki ko yaranki, nine mutum na farko da kike fara tuntub'a don neman shawara, mai ya shiga kanki kai tsaye kikayi saurin yanke hukuncin raba auren da kika sa na shige gaba wajen neman shi, ki fad'amin komai, dan kinsan ko ban furta ba ina cikin bakin ciki mara misaltuwa na abunda ya faru, kedai kin san komai dan gane da jelen dana dungayi wajen Malam kafin ya amsa batun auren nan, Babu irin nacin da ban mishi ba kafin ya amsa mana, ba kuma dan komai ba na tabbar abunda ka iya biyo baya shima yake dubawa a lokacin amma a hakan ya daure zuciyar shi badan yarinyar nan taso ba ya d'auke ta ya bamu, yanzun kuma fisabilillahi bayan shekaru 6 sai in d'auki takardar sakin ta in tun kare shi dashi! Da wani idon ma zan kalleshi? , karki manta fa wannan shine aure na farko da muka fara d'aurawa a cikin ahalin mu a matsayin *AUREN DANGI* sai gashi ya zama aure na farko da sakama kon shi ya zama mafi muni a garemu, Sakin aure fa ake magana abinda ya zama bak'o a garemu domin bamu saba jin saki ba kaf a ahalin mu, A duk cikin yaran da muka aurar babu wacce kaddarar aurenta ya kaita ga batun saki, ya kike tunanin zanji da kuma wani idon zan kalli yan uwana, cewa d'an dana haifa ne ya saki yar da suka aura mishi a karon farko da zamu samu bazawara a cikin *DANGINA* kuma ta silar auren *DANGI*" Saida ta k'arayin k'asa da kanta dan sosai take jin nauyin abunda zata fad'a mishi a yanzun, dan sosai take ganin laifin kanta ayau na jajircewan da tayi na tabbatuwar auren a shekarun baya, "Aminatu bata amsa sunan bazawara ba domin tsayin shekarun nan Mijin da muka aura mata bai tab'a kallonta a matsayin matar shi na aure ba balle har yayi tunanin sauke hakkin ta dake kanshi a shimfid'ar auren su matsayin ta na matar shi" "Mai kike son cewa ne?" Ya tambaya. "Eh Sarki bai kusanci Aminatu ba ko sau d'aya a zaman da sukayi" "Kin san da hakan kuma kikayi shiru baki tab'a fad'amin ba tsayin lokacin nan sai yanzun kike zuwa min da takardar saki dan kun raina min wayau dake da d'anki?" Ya k'arasa fad'a fusace. "Kayi hakuri nima kaina banda masaniyar komai akan hakan, dan daga ita harshi babu wanda ya nuna cewar akwai wata matsala a cikin zaman auren su, shi yana zaune da itane kawai a matsayin matar da muka bashi umarnin aure badan yana soba, dan haka yaci gaba da zama da ita yana kallon ta a matsayin kanwa ko kuma wani abun daban wanda shima bai san dalili ba, Ita kuma a matsayin ta na mace budurwa da aka sani mai kunya taji nauyin yanda zata kawo maganar garemu ne shi yasa tayi shiru take ci gaba da zama dashi duk kuwa da irin maganganu da cin fuskan da yaran gidan nan ke mata akan tak'i haihuwa, Ni bazan d'auki laifin in d'aura shi duka akan shaidaniyar matar shi ba domin na tabbata asiri ma yana cimma hali, in ma matar shi tayi nata siddabarun dan ta shiga tsakanin su tofa shima baya son Meenal d'in domin da ace akwai so bazai zuba mata ido yayi ta kallo tsayin shekarun nan ba, Sai dai ita kakar yarinyar ta hango matsalar a shekarun baya, ta kuma yi kokarin d'aukar mataki sai akayi rashin sa'a allah kuma ya rubuta cewa karshen abun baizo ba a wancan lokacin, Tiryan tiryan ta karanta ma Malam Sulaiman komai daya faru tun wancan lokacin har zuwa ranar da tasa Sarki ya rubuta takardar sakin. "Nasan wasu da yawa ba lallai su fahimce niba, sai dai kuma ni na aikata abunda na aikata ne saboda koda nice na haifi meenal bazan amince taci gaba da zama da Mijin da bata da wani matsayi a wajen shiba, Domin dai shi namiji ne yana kuma da damar da zai auro wasu matan biyu a bayan ta, amma ita mace namiji guda ne kachal ya halatta a gareta, sannan mutum ce ita kamar sauran mutane, na tabbatar da cewa idan a shekarun baya ta iya danne kanta a lokacin da bukatar kasancewa da abokin tarayya ya ke taso mata, tofa shekarun da zasu zo mata a yanzun ba lallai ne ta iya daurewa hakan ba, kaga kenan dai tako wani gefe itace take cutuwa domin shi dai yana da wata matar bayan ita, wannan shine babban dalilin da yasa na yanke hukuncin raba auren su, da fatan ita kuma Allah ya bata wanda yafi shi, Alhamdulillah kuma sai gashi tun ba'aje ko ina ba a sanadin ta sanadin rabuwar su d'ana ya dawo gareni, Kayi hakuri Abban su, kayi fatan hakan ya zama hukunci mafi alkhairi da muka yanke akan su" Shiru yayi ba tareda ya iya tankawa ba, to me zaice mata kuma bayan mai afkuwa ya riga ya afku, "Baka ce komai ba!" "To mai zance miki bayan kintasa k'eyar d'anki ya wuce garin arna, mai yasa tunda yayi sakin baki tasa k'eyarshi kuka kai takardar sakin zuwa inda ya dace ba? Yanzun ni kike nufin in tunkari Malam da takardar sakin auren Yarinyar nan da kowa yasan kololuwar kaunar da yake mata, kai innalilahi wa'innah ilairir raju'un, ni yanzun fisabilillahi keda d'anki kun kyauta min kenan? To ai sai ki shirya tun karar Malam din da kanki" Ya furta kana kuma ya koma yayi kwanciyar shi yana mai juya mata baya. "Haba Abban su taya nida nike mace ace nice mai kai takarda kuma, kadaiyi hak'uri tunda Allah ya kaddara babu yanda zamuyi" Gwuiwa a sanyaye ta tashi itam ta kwanta jin yayi mata banza bai k'ara kulata ba, kwanciyar dai tayi tana mai ci gaba da sake sake. Washe gari da asuba bayan Malam Sulaiman ya fito masallaci, gaba da masallacin can ya tsaya yana jiran fitowar Baba Adamu, domin har zuwa lokacin Malam bai dawo daga tafiyar da yayi ba, tsakani da Allah kuma ido da kunya koda ace Malam yana gari bayajin zai iya tunkaran shi da takardar sakin nan. Bai dade da tsayuwar ba Baba Adamu da Baba Auta suka iso inda yake, "Malam Sulaiman lafiya kuwa kake tsaye nan kai kad'ai?" Adamu ya tambaya. "Alhamdulillah Adamu kai nike jira wallahi," Gaisawa sukayi da juna kafin Baba Auta ya wuce ya barsu nan. "Ya'ya ko zamu k'arasa cikin gidane?" Adamu ya tambaya. "Ah ah Adamu mudai koma cikin masallacin tunda naga jama'a sun watse," "Allah yasa dai lafiya!" Adamu ya fad'a a yayin da suke komawa cikin masallacin. Takardar ya ciro daga cikin aljuhun sa ya ajiyema Adamu a gaban shi bayan sun zauna, "Abune mafi girman muni ya same mu Adamu, ban san da wani idon zan iya kallo ko tun karar Baba Malam ko kuma Auta ba, shi yasa na yanke hukuncin tun karar ka," D'aukar takardar Adamu yayi cike da dakiyar zuciya ya bud'e takardar. "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un³ me yayi zafi haka Ya'ya?" "Kayi hak'uri Adamu amma yanda kaga takardar nan haka nima na ganta, na kuma ji d'aci sama da d'acin da kakeji a zuciyar ka a yanzun haka, Yaron nan Sufyaan ya bamu kunya domin ya aikata abunda babu wani cikin mu da yayi tsammanin zai aikata, sai kuma fushin zuciya yasa mahaifiyar shi tsare shi harya rubuta takardar sakin ba tareda sani ba," kaf abinda ya faru na irin zaman auren daya gudana a tsakanin Sarki da Meenal shima ya zaiyana ma Baba Adamu kamar yanda Uwar gida ta sanar dashi a daren jiya. "To kaji halin da ake ciki, shi kuma tun d'azun nike kokarin neman shi a waya dan in bashi umarnin mai da auren amma ban same shi a wayar ba" "Subhanallah gaskiya abu baiyi dadi ba sam, amma kuma ya muka iya kaddarar bawa bata wuce kanshi, haka Allah ya kaddara dama, shi kuma kar kace zaka mishi dole cewa sai ya maidata d'akin ta kayi hakuri mugani zuwa gaba in Allah yace akwai sauran zama a tsakanin su sai kaga shi da kanshi yazo ya nemi sulhu sun koma dan yanzun in ka matsa tofa gidan jiya za'a koma, ina fatan kuma zaka saukaka ma kanka yawan damuwa domin dukan mu munsan aure rai gareshi, maganar tun karar malam kuma ni da kaina zan tunkare shi, nasan dai dole abun bazai mishi dadi ba amma dole yayi hakuri shima dan nasan ko zaiyi fushi na d'an lokaci ne" Sun dade suna tattaunawa kafin suka fito daga cikin masallacin kowa ya nufi gidan shi, Baba Adamu bayan ya shigo gida wayar Baba Auta ya kira ya bashi umarnin zuwa ya same shi a sashen shi. Bayan zuwan Baba Auta sai da suka d'an tab'a hira sukayi harda karin kumalo duka a sashen na Baba Adamu, Takardar shima ya gabatar mishi kafin ya d'aura da mishi bayanin komai daya faru har ya kaiga afkuwan sakin, Shi dai duk bayanin da Adamun ke mishi bai iya cewa komai ba illah "Allah ya kyauta yasa kuma hakan shine mafi alkhairi a garesu baki d'aya" "Ameen" Baba Adamu ya amsa dashi kafin yace mishi, "Ka turomin ita Jiddan idan ka koma" "To" ya amsa dashi, dan gara dai shi Adamun yamata bayani da kanshi dan Wallahi shi dai bai san ta ina zai fara ba, ga kuma Malam da yake hanyar dawowa yau, ai wallahi shi kam tafiya zaiyi dama yana da zuwa Abuja gobe ne yakamata ace ya tafi amma yanzun kam ba maganar ya jira har gobe yau d'innan zai tattara nashi ya nashi shirya d'auki matar shi su tafi, Koda ya koma ya cimma Mommy Hauwa ta gama shirinta tsaf na wucewa office, dan yara tuni sun wuce makaranta sukam. Dole ya kama kanshi ya shanye damuwar dake kan fuskar shi, "Kai Mommyn su yanzun da ban dawoba ficewa zakiyi ki barni?" "Ah ah fa Abban su taya zan fice ban sallame kaba, tunda naji shiru ai nasan wani abun ne ya rik'e ka kaga ni kuma yau ina da ayyukan da zan duba kafin gobe sannan kuma ina son biyawa in dubo Hajiya kwana biyu banje gidan ba," "Ita uwata baza'a biya a dubo min ita ba?" "Wai Meenal ai dan tasan cewa Baban ta baya nan shi yasa baka ganta ba, amma yana dawowa zataci gaba da zarya" "Oh shi kenan kuma in bata zoba babu mai dubo min ita ga baki ga hanci? To ai shi kenan ni idan na shirya zan biya in ganta, ina tunanin kuma yau zamu wuce abuja, dan haka sai ki dawo da wuri dan kin san bana son tafiyar dare, kin sani" "To amma abban su ai gobe ne tafiyar ya kama ba yauba ko ka manta lissafin ne?" "Kedai kika manta, zan shirya maki kayan ki kafin in fita ki biya kuma ta wajen Yaya Adamu yace in turo mishi ke yanzun, kafin ki wuce" Yana k'arasa fad'ar hakan yasa kai ya wuce sama zuwa d'akin shi, Bayan shi tabi da kallo domin duk yanda yake kokarin boye damuwar da yake ciki ita ta hango damuwar a tattare dashi, "Meke faruwa to?" Ta tambaya a sarari, ganin babu mai bata amsa hakan yasa ta fice daga sashen zuwa wajen Baba Adamu, Bayan sun gaisane ya shiga mata nasiha, "Mommyn yara nasa mai gidan ki ya turomin ke nan ne saboda wani al'amari mara dad'i daya same mu, kiyi hak'uri na sani cewa tun shigowar ki cikin mu kike fuskantar abubuwa, kuma a hakan kike shanye duka bacin ran da muke sanyaki, kike kuma rike da auren ki da dad'i ba dadi, Meenal yarkice da kika haifa da cikin ki, duk soyayyar da wani zai nuna ma d'a bayan uwace, amma a hakan kike runtse idon ki akan duk wani abunda ya shafeta, mai dad'i ko akasin hakan baki tab'a tankawa ba, Dan haka nike rokon alfarmar ki ayau ma ina son ki k'ara hakuri akan kaddarar data afkawa Mamana domin kowa yasan cewa bawa bai isa ya gujema kaddarar shiba" Ita dai tana zaune ne kawai shiru kamar wacce ruwa yaci, sai dai kuma a kage take da son jin mai kuma ya samu Meenal dinta a wannan karon, Takardar ya ajiye a tebur din dake gaban shi kafin ya d'aura da cewa, "Wannan takardar sakin aure ne tsakanin Mamana da Sufyaan, sakin auren da akayi shi tun kusan sati biyu daya wuce batareda mu mun sani ba ciki kuwa harda mahaifin Sufyan din, kuma tun lokacin ita Maman nawa ashe Hajiyar Tudun wada ta mai da ita can gidan ta, Kiyi hak'uri ki kuma yi mata fatan allah yasa hakan ya zama alkhairi a gareta" Turkashi...... "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un" Shi kawai Jidda ke ambata a cikin zuciyar ta yayin da a sarari kuma zufa ya dunga keto mata kamar wacce ke gaban kaskon wuta, Ganin tayi shiru bata ce komai bane yasa shi kara cewa, "Kiyi hakuri Hauwa'u, Murjaa.... " Ya kwala kiran sunan matar shi, wacce ke cikin d'akin ta tun bayan shigowar Auta ta wuce ta basu waje dan su tattauna, "Na'am " ta amsa dashi tana fitowa, "Zo dan Allah ki kama Jidda zuwa sashen ta" Da sauri ta k'araso tana tambayar . "Mai ya same ta ne Abban Raheenat? Mommy yara tashi mu shiga daga ciki" Ta fad'a tana kamo Jidda din zuwa d'akin ta, ganin hakan shi kuma sai ya fice daga sashen gaba daya bayan ya d'auke takardar . "Auren Meenal d'ina ya mutu Murja!....... Sufyan ya maida min yarinya bazawara, tun farko sai da na nuna kin auren nan amma babu wanda ya saurareni gashi ya sakomin ita, Ina amfanin auren dole ita dake mace ta iya jure zama dashi amma shi ya gaza rikemin amanarta, Tsayin shekarun nan yarinyar nan bata tab'a kawo min karar shiba kullum idan na tambaye ta ya suke cemin take lafiya lau, Ki duba irin yanda yan uwan shi ke jifanta da maganganu akan shi harta ni danike uwarta basa shakkar fad'amin maganar daya shafeta ashe cutar min da ita yake, fisabilillahi nawa Meenal take da zai jeramin ita cikin sahun zawarawa, Kaf gidan nan babu wacce aka sako daga gidan miji sai nawa y'ar wacce ko ni uwarta banyi zawarci ba sai ita k'aramar yarinya, wani irin *DANGI NE* wannan? Indai haka auren *dangin* yake to daga kan Meenal an gama yin shi a cikin ahali na insha Allah ita da ta zama farko to itace k'arshe," Ta k'arasa fada cikin kuka...... Wanda kalamanta su suka karya ma Aunty Murja nata zuciyar ta rungumeta sukaci gaba da kukan tare,,,,,, Sun dad'e suna kokawa kafin Jidda ta yunk'ura, "Auntyn su bari inje Tudun wada ina son jin dalilin sakin nan domin Baba Adamu yace min meenal din na tare da Hajiya tun ranar da Sarki yayi rashin lafiya," "To zaki iya driving ko in kira cikin yaran gidan wani ya tuk'aki?" "Kar ki damu zan iya" Ta fad'a tana ficewa daga d'akin, Murja batayi yunkurin binta zuwa wajen hajiya bane saboda tasan ko babu komai idan taje can zasu so su zanta akan al'amarin shi yasa ta zauna, sai dai kuma itama sosai batun sakin ya daketa, ace yarinya karama kamar Meenal itace take shirin amsa sunan bazawara fisabilillahi Allah dai ya dai dai ta al'amarin ba tareda rayuka sun baci ba, Koda Jidda ta isa falon ta bata nemi Baba Auta ba Jakar ta dake nan falon kawai ta d'auka ta fito daga sashen ta shiga mota ta fice a gidan. Ikon Allah da tsarewar shi ne kawai ya kaita gidan Hajiya lafiya, koda ta isa bata tsaya yin parking mai kyau ba ta kashe motar ta nufi sashen Hajiya, Zaune ta iske su akan dinning table da alama sai a lokacin suke karyawa, Kasancewar sallamar da tayi k'asa kasa tayi shi kuma kofar na Hajiya koda yaushe a bud'e yake shi yasa basuyi saurin an karewa da ita ba, har sai da ta shigo tsakiyar falon, "Ke Jidda wani sabon hali kuma kika tsiro dashi na shigoma mutane gida babu sallama?" Hajiya ta fad'a a sanda hankalin ta yakai kan Jidda, "Oyoyo Mommy na wallahi I miss you" Meenal ta fadi hakan tana tashi daga kujeran da take zaune da gudu ta k'arasa ta rungume Mommyn, Ita kuma jin Meenal din a cikin jikin ta gaba d'aya sai taji rauni da tausayin Meenal din sun sauko sun lullubeta, dan haka kawai sai ta saki kukan da take ta faman rikewa, Kuka takeyi irin na wanda abu ya b'ata mishi rai sosai, ta kuma kasa magana........ *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/9, 2:46 PM] Zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ ~{{MY FAMILY}}~ *FREE BOOK* *RUBUTAWA* *UMMIEE ZARIA*✍🏼 ```` *Page 50*...... *END OF BOOK 1* Kuka takeyi sosai har zuwa lokacin kuma rungume take da Meenal d'in a jikinta ba tareda ta sake taba, Cikin hanzari Hajiya ta taso daga kujerar da take zaune a kai ta iso inda suke tsaye Meenal na faman tambayan Jiddan me ya sameta? "Mommy mai ya faru, wani ne ya mutu, ko baki da lafiya ne mu tafi asibiti yanzun? Shiru Jidda bata iya furta komai ba. "Wannan ai d'abiar banza ne, ya zaki shigo min gida ki fasa kuka kamar wacce aka aikawa sak'on mutuwa na, To in ma wani ne ya miki k'aryar cewa na mutu ba gani kin ganni a raye tsaye kan kafafuwana ba, ai sai ki kira koma waye ki zagi uban shi kice mai k'aryane gani a raye, bawai kimin tsaye a tsakiyar falo kina min ihun kuka ba, ko wani can ne a gidan naku ya mutu? Ke kuma kin wani k'an k'ameta bazaki saketa ku nemi wajen zama ta bamu labarin iftila'in daya auko tazomin gida da ihu ba" Hajiya ta ke fad'a a yayin da take yunkurin janye Meenal d'in a jikin Mommy Hauwa, Duk da ta rabasu hakan bai sa Jidda ta saki meenal din ba sai ma kamo hannun ta da tayi ta rike a cikin nata, har zuwa lokacin kuma idanuwan ta basu daina zubar da hawaye ba sai dai ihun kukan ta daya d'auke, Janta Hajiya tayi ta zaunar a kan kujerar dake kusa dasu, "Ke Meenal mik'o mata ruwa tasha" Zame hannun ta meenal din tayi daga cikin na Jidda kamar yanda Hajiya ta umarta taje ta d'auko ruwan, harta dawo idon mommy Hauwa na kanta tana k'are mata kallo, kallo take mata kamar wacce keson gano ko Meenal din ta rasa wani abu a jikin ta, "Ga ruwan Mommy" Meenal ta furta a yayin da take mik'a mata ruwan jikinta a sanyaye itama tana fidda yan k'ana nan hawaye, dan dai wallahi da wayanta bazata iya tuna ranar da taga Mommyn tana kuka ba. "Wai Jidda zaki amshi ruwan nan kisha ko saina kakkafta miki mari kila zaki dawo hayyacin ki, kisha ruwa ki fad'amin ubanda ya koroki nan gidan kika zo da sassafen nan kina min ihu salon kisa zuciyata ta buga shi kenan yarana sunyi asara" "Kai Hajiya dan Allah ki barta tasha ruwan mana ai zata fad'amiki komai tunda tazo wajen ki" Cewar Meenal. Badan Jiddan taso ba haka tama ruwan nan shan dole, Sai da ta share hawayen ta kafin ta iya furta cewa, "Meenal shiga daga ciki ki bamu waje zanyi magana da Hajiya" "Ah ah fa ni bana son bak'in hali wallahi, to ita meenal din bare ce a cikin mu da bazaki iya yin maganar da zakiyi a gaban taba? Bafa wata can daban bane Meenal ce dai yarinyar da kika haifa kukayi min takwara kinga ko ai abunda ya shafeni ya shafeki, abun kuma daya shafeki itama ya shafeta, a wani dalilin zakice ta tafi, waike Jidda sai yaushe zakiyi hankalin da zakija d'iyar ki a jiki ta yanda zaki dunga jin damuwar ta? wallahi nidai in kina wani abun sai in dunga ganin kamar ba nakudanta kikayi ba fad'owa kawai tayi, ina ma amfani ace mace ta haifi d'a amma ta sakar ma wasu can ragamar rayuwar ta........ " Mommy Hauwa bata bar hajiya ta k'arasa surutun taba ta katseta da cewa, "Auren Meenal d'ina ya mutu Hajiya, Sarki ya saki meenal Hajiya, shi kenan ya maida min yarinya bazawara Hajiya shi kenan ita bazata mori kuruciyar ta taji dad'in rayuwa kamar sauran yara ba Hajiya?" "Mmmttttwwwsssss" Hajiya taja wani uban dogon tsaki tana me kallon Jidda shekek'e cike da takaici, "Kai amma dai wallahi Jidda kinci amana ta, abinci fa kika shigo kika iske inaci, saboda tsabar rashin mutunci kika d'aga min hankali kika sa na tsamo hannuna na iso gunki a firgice duk a zatona ko wani mugun abun be ya k'ara faruwa, Ke yanzun nan saboda rashin sanin ciwon kai shine har dan wannan auren na da babu gwara ba dad'i ya mutu kikazo kika tasamu kina kuka? Nida nike zaton in kinji labari zaki yo hayan DJ suzo da manyan sifiku su kunna muyi celebration yarki ta samu freedom, To wallahi kama kanki tun kamin kisa in kullace ki, ina abun bak'in ciki anan fisabilillahi," "Hajiya auren Meenal nefa nace miki ya mutu" "Eh auren Meenal d'infa, yo shi dama auren nata irin kowani aurene da kuke tunanin zai dauwama, to ki godewa Allah domin da auren ya dauwama ina mai tabbatar miki cewa itama yar naki zata dauwama ne cikin kunci da bakin ciki domin dai tsayin zaman ta a gidan nan har zuwa ranar da na d'auko ta na kawo nan sunan ta na budurwa bai canza ba dan dai shi Mijin zuwa yayi ya jingine, ban san uwar da yake jira da ita daya ajiyeta yana kallo babu sauke hakkin aure ba, su iyayen nasu basu fad'a miki dalilin mutuwar auren bane?" Kasak'e Jidda tayi tana sauraron jawabin hajiya batareda tayi yunkurin katseta ba har sai da Hajiyar ta bukaci jin ta bakin ta, "Hajiya ni ban san komai ba d'azun ne Abban su daya shigo yake cemin Ya'ya Adamu yana son ganina, to dana jene shine ya nuna min takardar yace min takardar sakin Meenal ne kuma ita Meenal din tana nan tare dake tun tuni shine nazo" "Ikon Allah to kenan kice sai yau sukaga daman gabatar da takardar sakin, to barka da zuwa! Wato dai kinzo jin k'arin tabbaci akan batun sakin ne koh? To ina zuwa" Hajiya bata jira komai ba ta wuce zuwa d'akin ta, cikin kankanin lokaci ta dawo da takardar sakin a hannun ta, "Ina ga waccan ai iya takardar kika gani koh? To ga wata sai ki bud'e ki karanta abunda ta kunsa" Ta k'arasa fada tana mik'a mata ita kuma Hajiyar ta juya ta koma kan dinning table tana mitar ita dai an d'auki alhakin ta an yanke mata cin abinci har shayinta yayi sanyi. Mikewa Meenal tayi ta fice daga falon a sanyaye dan sosai taji babu dadi ganin Mommy na kuka a dalilin mutuwar auren ta, Dole muji babu d'adi idan wanda muke so ya rabu damu amma ba akan wanda ya auremu ya jingine a gida ba, Tasan bata son Sarki sai dai kuma hakan bashi ke nufin ta tsane shiba, saboda a iya zaman da sukayi bazata ce ga wani abu gagarumi daya aikata mata ba, sai dai kuma kowa yasan ba rabuwa ake ma kuka ba sabo ne abun kokawa, To itama dai wannan sabon na tsakanin su shi takeji a yanzun ba kuma iya kewar shi takeyi ba tana kewar abubuwa da yawa data samu ta dalilin shi, domin a sanadin shi ta samu gida, gidan da ake kira da suna *Gidan Meenal* gidan da yake nan ne take zama ta sakata ta wala tayi duk abunda take so ba tareda wani ya takura ta ko yasa mata ido ba, falon ta, kitchen d'inta, d'akin data ware danyin karatun ta, daku nan baccin ta, kayan kallon ta, da kayan jin kid'anta a lokacin da take cikin nishad'i, garden din da takanje ita da kawayen ta su zauna dan hutawa, swimming pool din gidan wanda dashi ta koyi yanda ake yin Iyo a cikin ruwa, Duka wadannan abubuwan da suke a matsayin nata, a kwanakin baya shi kenan yanzun ta rasa su saka makon mutuwar auren ta, Ita dai a wajen ta wadan nan abubuwan sune inta tuna suke mata tsaye a rai, bawai kuma dan gidan su babu ba sai dan banbancin dake tsakanin kalmomin nan guda biyu, Wato *GIDANA* da kuma *GIDAN MU* da can a gidan su ta rayu, kafin a samu ci gaba ta koma zama a gidan da ake kira nata yanzun kuma mai makon wad'ancan gidajen sai gashi ta dawo zama a gidan Hajiya, bata rasa komai na buk'ata anan d'in ba ba kuma ta fuskantar ko wani irin takura, sai ma nan nan da Hajiya keyi da ita, amma ku sani akwai banbanci mai nisa tsakanin gidan auren ki da kuma gidan ku, to itama irin wannan banbancin takeji a yanzun. *Bayan Meenal ta fice* Hajiya na daga kan kujerar da take cin abincin ta ta d'ago kai tana kallon Mommy Hauwa data kafe takardar nan da kallo hawaye naci gaba da zarya a idon ta, "To idan kin gama kukan ki k'araso nan in baki amso shin tambayoyin ki" Goge hawayen tayi sannan ta tashi itama taja kujerar da Meenal ta tashi wanda yake daura dana Hajiya ta zauna, "Ga tea nan na had'a miki zauna kisha dan nasan yanzun haka baki karya ba kika fito" "Bana jin yunwa Hajiya, nidai dan Allah ki fad'amin mai ya faru?" Daga hannunta hajiya tayi tama Jidda nuni da kofar falon, "Wancan kofar itace inda kika biyo kika shigo koh?" Bata jira amsa ba ta d'ora da cewa, "Dama kinzo jin tabbacin batun sakin ne ai dama koh? To ga dai takardar nan kin ma karanta dan haka kwashi kafafuwan ki ki koma can inda takardar ta fito sai suyi miki bayanin dalilin sakin wanda suka manta basu rubuta a jikin takardar ba, dan bazaki zo har gidana ki nemi mai dani wata shashasha ba kamar akan yarki aka fara sakin aure" Tea din ta d'auka da zafin shi da komai amma hakan nan ta kafa shi a baki bata sauke kofin ba har saida ta shanye shi tass, Hakan kuma bai sa hajiya ta k'ara bi takan taba illah ma abincin ta data maida kai taci gaba daci, sai da taci ta koshi sannan tayi hamdala, kana taja kujerar ta baya ta fita daga wajen dinning din ta koma falo ta kunna TV tayi zaman ta tana mai maida hankalin ta kacho kam akan kallon da takeyi, kamar bata san da zaman Jidda a falon ba. Bayan tashin Hajiya ita kuma Jidda kayan wajen ta tattara takai kitchen daga can ta tsaya ta wanko fuskarta kafin ta dawo falon ita ma ta nemi wajen zama, Sunyi zama na kusan minti 15 kafin hajiya ta mulla dan kanta ta d'ago kai, "Taso ki dawo nan muyi magana" Tashi Jidda tayi zuwa inda ta nuna mata domin ai dama ita abunda take buk'ata kenan, Sai da Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin ta fara magana a tsanake kamar haka. "Hauwa'u kinji babu d'adi a sanda wan Mijin ki ya gabatar miki da takardar shedar mutuwar auren yar da kika haifa koh?" Shiru Jidda tayi bata amsa ba sai ma idanuwanta da suka cika da hawaye, "Nifa bance kimin kuka ba, in kin san kukan kuma zakiyi kije gida duk randa kika natsa sai kizo in fad'a miki abinda kike son ji," "Kiyi hakuri Hajiya na shirya, na daiji babu dadi ne kasancewar Meenal karamar yarinya kuma mace ta farko da kaddarar zawarci ya fadawa a kaf cikin Danginta," "Nasan kina jin babu dadi Jidda amma ba meenal ba kowama bai wuce kaddarar shi, mu gode Allah da nata kaddarar bai kasance mummunar kaddara ba domin a zaman da tayi na tsayin shekaru a gidan ta ba tareda kuma data samu kulawar kusanci da Mijin auren taba da Allah yaso sai ya ratso wani mummunar abunda zai zama abu mafi muni a garemu, sai gashi Allah ya kare mana ita ta iya ci gaba da rike kanta har zuwa wannan lokacin da komai yazo karshe, dan haka godiyar mu ya kamata mu gabatar wajen ubangiji ba kuka ba," Shiru Jidda tayi tana sauraron Hajiya. "Jidda nice na haifeki amma ni kaina ina mamakin wasu daga cikin halayenki na halin ko in kula da kike nuna ma yarinyar nan Meenal, Badan komai ba sai dan yanda kike wofantar da duk wani abunda ya shafeta, yarinyar nan fa ba d'iyarki ta farko bace amma sai gashi kusancin da d'anki na fari yake samu dake ita ko rabin shi bata samu a wajen ki ba, lokuta da dama sai inga kamar kikan manta da cewa kece uwarta, domin baki damu ba sam da son sanin, Wani hali take ciki? , Miye damuwar ta? , tun tana yarinya kika saki ragamar ki a matsayin uwa zuwa ga wasu daban, sam baki nuna mata cewa ke d'in bango ne majin gina a gareta ba balle ta samu damar jinginar ki a yayinda take buk'atar mai lallashin ta, komai kin sake ma mutanen gidan ku da kuma yayan ubanta, Ni ko a nawa ganin ai duk son da wani zai nuna ma d'a baiyi kamar uwa ba domin dai uwa ita tafi kowa sanin ciwon abinda ta haifa, Yarinyar nan bakijata a jikin ki tana k'arama ba, Baki jata a jikin ki tana matsayin budurwa ba, Haka kuma da kuka aurar da ita sai kika k'ara nesan ta kanki da ita, Fad'amin tunda kike da ita ta tab'a tun karar ki da wani damuwar da take buk'atar kece zaki mata maganin ta?" Shiru Jidda tayi. "Kinyi shiru saboda hakan bai tab'a faruwa ba, ku dai kun aurar da ita kun mik'a babu wanda yake bin sahun ta balle wani ya hango nakasun dake cikin rayuwar auren dake gudana tsakanin ta da Mijin da kuka aura mata, shekara 1,2,3 har zuwa tsayin shekaru 6 babu b'atan wata babu bari balle akai ga batun haihuwa alhalin ga kannen Bayan ta nan duk sun haihu, Fada min kin tab'a zaunar da ita a matsayin ki na likita ki bincike ta? A cire matsayin uwa a gefe" "Kiyi hakuri Hajiya nayi kuskure" "Kin san me Hauwa'u? Ni ana ganin yawan fad'ana ne kawai amma duk da hakan komai akeyi baya wuce gani da jin kunnuwa na, bazan b'oye miki ba kinyi sake sosai domin dai gaki a raye amma hakan bai sa yar da kika haifa tasan dadin ki a matsayin ki na uwa mace ba, Karki manta in ma kinayin hakan dan Kiyi ma sauran mutanen gidan ku dashi malam kara ne, shi din fa namiji ne, akwai abubuwa masu yawa wanda komai kusancin dake tsakanin Meenal da malam bazata iya fad'a mishi suba, Su kuma sauran matan gidan ku Karki manta ba sune iyayen ta ba dan haka babu wannan shakuwar da zata tunkare su da damuwar ta a koda yaushe, ni kuma ba unguwa daya muke daku ba dan haka inba zuwa tayi ba ba komai nike iya fahimta akan zaman ta da Mijin ta ba," Sosai hajiya ta tsage Jidda akan yanda take mu'amalantar Meenal kafin daga karshe ta d'aura da bata labarin irin zaman da Meenal tayi a gidan ta harma da dalilin da yasa Hajiyar wutowa da ita gidan ta daga asibiti kafin batun saki ya biyo baya, "Nasan komai zai faru babu uwar da zata so ace yau yarta ta k'ara dawowa gabanta da sunan zaman zawarci, wata kilama zuciyar ki tana nan tana raya miki cewa tunda saki d'aya ne a dai'daita ta koma d'akin ta, To wallahi wannan karan na shirya muku tass tundaga kanki ke uwarta har zuwa shi wancan mai nuna yafi kowa iko da ita d'in duk dai dai nake daku, dan tunda har yarinyar nan ta nuna ta gama auren tofa ta gama shi kenan koda ko ace shi Mijin naso balle kuma shima baya muradi, yarinyar nan dai ba yara ta to tara a gidan ba balle ace ta koma tayi hakurin zama saboda su, ba kuma tsohuwa bace balle ace tayi zaman tsufa inta fito babu mai auren ta, Kin daiji na fada miki in zaki farka daga baccin asarar da kikeyi gara ki farka, kina iya tafiya na gama dake saura kuma shi d'ayan uban nata nashi sammacin Nike jira dan nayi mamakin da naji shiru banga ya biyoni gidan nan ba ashe sak'on ne bai kai hannun ku ba sai yau" "Malam baya nan amma yau zai dawo" cewar Jidda, "Kai masha Allah to allah ya kawo shi lafiya" ****** Bayan Jidda ta isa gida, Baba Auta ta samu zaune a falo, Bata kulashi ba duk da tambayan da yake mata cewar yayi kiran wayarta bata d'auka ba, Ganin ta wuce shi zuwa ciki hakan yasa shima ya yunk'ura yabi Bayan ta zuwa d'akin nata, Ita ko da shigan ta d'akin mayafinta kawai ta cire ta haye gado ta runtse ido tana fatan Allah yasa idan tayi bacci ta farka taga komai ya zama mafarki, wani yace mata mafarki takeyi ba Meenal dinta bane aka saka ba. Shigowa yayi ya zauna a gefen ta, ita kuma duk da taji motsin shi bata nuna tasan da zaman shi a wajen ba. "Kiyi hakuri Hauwa'u kinji bana son kisa maganar nan a ranki balle wani abu ya sameki, Kiyi fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, ki tashi ki shirya mu wuce na riga na had'a kayan tafiyar" "Eh ai dama kullum aka cuceni abunda kake cemin kenan inyi hakuri, tunda na haifi yarinyar nan nake fuskantar abubuwa Kala Kala akan ta, a tunanin ku bana son tane? Nice fa uwarta nina haifeta nafi kowa sanin zafin ta amma a hakan kullum nike kauda kai kar aga zak'ewata, Ko ka manta cewa auren dole kuka mata, haka kuma nayi shiru na hak'ura badan naso ba, amma kawai sai ya sako min ita, fisabilillahi da yasan baya sonta mai yasa ya aureta, Suma kuma iyayen shi sun san baya son aure suka matsa mishi ya aureta wannan ai son kaine tunda gashi nan komai a kanta ya k'are" To dai Bayan dogon lallashi baba Auta ya lallab'a matar shi sun wuce zuwa Abuja, Yayin da shi kuma Malam yayi ma garin na zaria shigowar la'asar sakaliya, *Tofa ya abubuwan zasu kasance kenan?* Bari in muku wani tuni, in baku manta ba kunji cewar Malam mutum ne mafad'aci, a wancan lokacin harda kajin gidan shi in suka matsa mishi umarni yake ba yarwa duk a kame su a yanke, Sai gashi yau zai dawo ya iske takardar mutuwar auren Meenal din shi yarinyar da yake ma kololuwar soyayyar da allah ne kad'ai yasan adadin ta, In baku manta ba saboda gudun abunda ka iya tab'a zumuncin shi da yan uwan shi hakan yasa ya d'auki lokaci Mai tsayi bai amince cewa zaiba Sarki auren Meenal din ba, Sai gashi daga yin aure Bayan shekara 6 aure ya mutu an b'ata ma maman shi suna daga budurwa zuwa bazawara, Koya ya zaiji in wannan bakin labari ya iske shi? Wani mataki zai d'auka gudun kar hakan ya k'ara faruwa akan wata daga cikin ahalin Bayan Meenal. Haha haha, wai ina labarin gwarzon mu Abdul Khareem Ahmad Mai Jama'a ne? Shiru dai har yanzun bai iso zaria ba. Shin AK zai samu cikar burin shi na auren Meenal cikin sauk'i kamar yanda yake hangowa kuwa? Yaya soyayyar su zata kasance ne, zatayi saurin amsa mishi intama ta fada soyayyar shi ko wani ne zai zo yayi ma nata zuciyar kutse? Yaya teemah zataji a sanda labarin mutuwar auren mijinta zai isketa? Wani mataki zata d'auka dan hana shigowar wata gidan ta Bayan Meenal? Shin Sarki zaije ya nemi yarinyar da Meenal ta bashi number da adireshin? Ko kuma hakura zaiyi yaci gaba da zama da Gimbiyar shi? Wadan nan tambayoyi dama wadansu masu tarin yawa duka zaku samu amso shin sune a cikin littafin *DANGINA* kashi na biyu, Wanda zaici gaba da zuwa muku nan bada jimawa ba insha Allah. Ina mika godiya zuwa gareku yan uwa makaranta da kuka b'ata lokacin ku wajen karatun littafi na, Nagode kwarai da yanda kuka dunga k'arfafa min gwuiwa da fari nayi zaton cewa bazan iya ba amma kuka tsaya a kaina wajen ganin ban dakata ba, Nagode da soyayyar ku a gareni, Kuna da yawan da bazai yuwu ince zan tsaya lissafo sunayen kuba, Sai dai ako ina nike zan kasance mai alfahari daku akoda yaushe, Son so fisabilillahi ina fatan Allah ya had'amu a littafi na biyu cikin aminci da sallama, *Domin yin gyara shawara ko matashiya akan wani abunda na manta zaku iya magana dani kai tsaye a wannan number din 08061358462 Nagode* *Alhamdulillahi* *Ummiee Zaria*✍🏼