[8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ ~{{MY FAMILY }}~ ©® *UZ-2023.* *BOOK 2* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*✍🏼 *Bismillahir Rahmanir Rajeem* *Ina mai mik'a yabo da godiya na ga Allah mad'aukakin Sarki wanda bai hafa ba kuma ba'a haifeshi ba Ubangijin sammai da kassai, Sannan ina k'ara salati zuwaga shugaban mu d'an gatan Allah, Annabin mu Muhammad (S.A.W), tareda iyalansa da sahabban sa baki d'aya. *SADAUKAR WA* A wannan tafiyar gaba d'aya littafin tun daga farkon shi har zuwa karshen shi zai zamo sadaukarwa ne ga d'aukakin masoya da suka jure wajen bibiyar labarin in daga farko har zuwa yanzun, Ku d'in kun kasance abun alfaharina, na fara rubutu banyi zaton labarin zai zaga har zuwa inda banyi zato ba, sai gashi a sanadin littafin *DANGINA* na had'u da mutane kala² wasu iyayena wasu yayye wasu kanni, Lallai na yaba da kaunar ku gareni, tun daga kan Marubuta dama makaranta da a kullum kune ke bani gwarin gwuiwar ci gaba da rubutu, Kuna da yawan da bazai yuwu ince zan zano sunayen ku ba, ina dai so ku sani cewa na yaba matuk'a💘. *Ga masu buk'atar littafin daga farko zaku iya tuntub'ana kai tsaye da wannan number d'in* 08061358462. Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ma makaranta ba, dan haka karkuji d'ar kuba duk wanda kuke so. *Page 1* ``````` Tunda Allah yama Malam isowa da maraicen nan gaba d'aya bai samu zama ba, domin bayan tafiyar shi anyi wani rashi na d'aya daga cikin d'aluban shi da sukayi karatu a k'ark'ashin shi, dan haka koda ya iso babu jimawa ya shirya ya wuce can wajen iyalan mamacin domin yi musu ta'aziyya bashi ya samu sukuni ba dai har sai zuwa dare. A gefen Baba Adamu kuwa tun a sanda Baba Auta yama shi sallama akan zai wuce Abuja a ranshi yaji cewar gudun hijira ne kawai Adamun zaiyi dan baya son gamon su da Malam, domin dama tun zamanin k'uruciya ma in sukayi ma Malam d'in laifi shi Auta Hijira yake yabar gidan har sai Malam yayo bikon shi kafin ya dawo. Bai matsa mishi ko tambayan dalilin da yasa zai wuce d'in ba dan yasan Auta dannewa ne kawai yakeyi amma shi a matsayin shi na wanda yake gaba dashi yasan dole abunda ya faru ya dake shi, domin dai babu uban da zaiyi alfahari da kasancewar d'iyar shi bazawara, Malam bai shigo cikin gida ba har sai misalin karfe 9 da wasu mintuna na dare, a yayin da shi kuma Baba Adamu ya kasa ya tsare a farfajiyar gidan yana jiran isowar shi dan gara ya gabatar mishi da komai a daren nan dan Malam mai iya mishi sai Allah yana iya idan shi yace ya bari sai gobe ya tunkare shi da batun, shi kuma Malam d'in yahau shi da fad'a akan wani dalilin ne ya hana shi gabatar mishi da takardar a yau? "Ah ah Adamu kai kad'ai zaune a waje lafiya kuwa? Ko kodai jiran shigowa na kakeyi ne?" Malam ya tambaya a yayin da hankalin shi yakai kan Adamun dake zaune a kan d'aya daga cikin kujerun da aka ajiye dan zama a kofar falon Malam, "Eh Malam barka da dawowa an dawo lafiya ya hanya da gajiyar tafiya?" "Alhamdulillah lafiya lau muka iso, kai kuma kazo kayi zaune a nan kai kad'ai ai ko sauro bazasu barka ka sarara ba, da kasan kana jirana ai da ko a waya ka kirani, tunda dai ba komai nikeyi a wajen ba na dai tsaya ne muna gaisawa da makota tunda kwana biyu bana nan abubuwa sun d'an faffaru, kuma ai da ka bud'e falon ma ka shiga" "Ba komai Ya'ya na daiji zaman a nan d'in ne dama shi yasa ban shiga cikin ba" "To madallah bismillah mu shiga daga ciki koh!" Malam ya ambata a yayin da ya tura kofar falon da sallama suka shiga, Bayan sabuwar gaisuwar da suka sake da tambayar bayan saduwa ne malam ya d'aura da cewa, "D'azun auta ya kirani cewa sun wuce abuja shida mai d'akin shi zasu d'an kwana biyu kafin su dawo, wato dai Auta take taken shi so yake dai yabar gidan nan dama garin baki d'aya, ni ban san me mutane suke so su zama ba gaba d'aya dai da zarar mutum yaga ya d'an tara yan kud'ad'e sai kaga ya manta da gidan su sai ya ware kanshi can a gefe shi d'aya, niko gani nike mai yakai zama cikin ahalin ka dad'i fisabilillahi fa, amma yanzun da zarar nayi magana sai ayi min wata fassara ta d'aban, tunda aikin shi ya koma Kaduna ya fara wannan galantoyin tsakanin kaduna da zaria nasan cewa gaba kad'an zaice ya gaji da yawon zai kwashe iyalanshi ne su koma can, yanzun nan fisabilillahi in banda abun Muntari a kadunar har za'a samu wata makaranta data d'ara ita wannan ABU d'in daya bari ne? Ni dai bazan k'ara magana ba ma balle aci gaba da cewa na fiye takura" Duk surutun da Malam keyi Adamu baice komai ba sai dai d'an murmushi da yakeyi, "To ina ce dai lafiya? dafatan dai babu abunda ya faru a gidan bayan tafiya na? Koda yake ko wani abun ya faru nasan zaku magance shi basai kun jira dawowa na ba" Daga kanshi yayi ya kalli agogon dake mak'ale a jikin bangon falon nashi, "Ashsha ashe dare ya fara haka gashi gaba d'aya na manta dana ware tsarabar uwata ban ce yaran nan su mik'a mata ba harna fita, Baiwar Allah nasan babu mamaki ta shigo bata iskoni gida ba" Wayar shi dake gefe ya d'auka kafin ya lalubo Number din Innar yara kira d'aya biyu ta d'auka, "Na shigo fa tun d'azun amma babu wacce tazo dubani a cikin ku" Daga can gefen Ita kuma ta amsa mishi da cewa, "Ayi mana afuwa Malam ita Dije nan wajena ta amshi maganin ciwon kai tasha to nasan babu shakka bacci ne ya d'auketa ni kuma ban san ka shigo ba shi yasa amma zan iso yanzun" Sai da ya yanke wayar sannan yace da Adamu, "Kaga halin matan nan koh? Mata biyu amma na shigo tun d'azun an rasa wacce zata shigo ta bani abunci a cikin su" "Ayi musu uzuri ya'ya indai abinci ne ai koni sai in had'a maka tunda gashi can ai naga an ajiye" "Allah mai iko, aiko kaga ni sam ban kula da cewa an ajiye abincin ba, to d'auko sai ka zuba mana muci ai mun kwana biyu dama bamu samu damar cin tuwon dare tare ba" Duk da cewa Baba Adamu yaci nashi abincin hakan bai hana shi zuba musu wannan d'in ba suna ci suna hira a haka har Ameena ta shigo ta same su, Koda ta iskosu itama zama tayi sukaci gaba da hiran Malam na basu labarin yanda tafiyar shi zuwa Mai duguri ta kasance, [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *~{{MY FAMILY}}~BOOK 2* ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*✍🏼 *Page 2* A wannan dare sam Malam bai samu sukunin yin bacci cikin salama ba, domin kam sosai fa abun ya dake shi bai tab'a zato ko hasaso cewa hakan na iya faruwa a cikin ahalin shi ba sakin aure fa ake magana, auren kuma daya zama auren had'i na farko da suka had'a tsakanin yaran su da fatan karin dankon zumunci a tsakanin su, shine daga tafiya ya dawo ya cimma wannan irin k'atuwar iftila'in. Duba da cewa suma iyayen su basu kasance mazaje masu sakin aure ba, haka kuma suma da suke a matsayin iyayen nasu yaran sam babu wanda a cikin su ya tab'a tsinke igiyar d'aya daga cikin matan shi, Amma sai gashi yau an wayi gari nasu Yaron da suke kallo mai nutsuwa da hankali shine ya aikata hakan, Duk da jawabin da Adamu ya mishi na dalilin da yasa uwar gida tayi tsaye akayi sakin sam shifa bai wani gamsu ba, dan haka ya k'agara gari ya waye ya samu zama dashi Yaron dama iyayen shi, dan bazai yarda da d'abiar saki a cikin zuri'ar shiba, koda ko ace sakin ba akan Meenal ya fad'a ba dolene yabi kadun dalilin sakin balle kuma abu ya fad'o akan ta. Kamar yanda Malam ya buk'ata cewa Auta ya kira Hajiya akan a dawo mishi da Meenal gida, to dai shi Auta a wannan daren kasa kiran Hajiya yayi har sai washe gari, Washe garin ma bashine ya kirata ba Mommy ya rok'a domin dai koda kiran Malam din ya riske shi taji sakon da Malam din ya bayar tasan kuma shi Auta bazai iya kiran Hajiya ba dan haka ita da kanta ta kira ta take shaida mata cewar Malam yana son ganin Meenal din a gida saboda zasuyi zama, Hajiya ko dama tuni damar hakan ta dad'e tana jira dan haka babu musu ta amsa da cewa zasu isa gidan da wuri kamar yanda ya buk'ata, Duk da cewa Meenal din nada class din safe a ranar amma hanata zuwa Hajiya tayi domin a cewar ta, yanzun lokaci ne na kwatar y'ancin kai bawai lokacin karatu ba. Shima a bangaren Malam Sulaiman tun daren da kiran Malam ya riske shi sam ya kasa samun sukuni, Domin shi yasan halin Malam tunda har ya gaza hakurin wayewar gari ya kira shi a daren nan tabbas yasan ba komai bane illah sakon takardar Meenal daya dawo ya riska, Yayi fad'a sosai dan Wallahi shi dama yasan hakan yana iya biyo baya, dan haka tun daren yake ta kokarin kiran Sarki a waya domin ya shaida mishi cewa koma ina yake to yayi kokarin dawowa Zaria a washe gari dan shidai wallahi uwar gida da d'anta sunja mishi, yana zaman zaman shi bai san farkon matsala ba sai da suka jagwalgwala komai sannan yanzun sun d'auko shi sun sashi a tsakiya, yanzun haka gobe zaije gaban Malam yayi tsuru² fisabilillahi kai dai ka haifi mutum kawai amma baka haifi halin shiba, Rashin samun Sarki a waya hakan yasa dole a daren ya aika mishi da sakon Text message, Washe gari ma yana tashi haka yaci gaba da kiran Sarki a waya amma har zuwa lokacin wayar bata zuwa. Karfe goma sha d'aya 11am na safiyar wannan rana tayi ma, Malam Sulaiman, Uwar gida Baba Adamu Innar yara Hajiya Innah Meenal Dama shi kanshi Malam d'in ne a cikin falon shi inda kuma ya bama yaran ahalin maza kaf sallahun cewa dukan su yana neman su da Misalin 12 na wannan rana wato dai bayan ya gama da iyaye kan yaran zai koma. **** Malam Adamu ne ya bud'e taron da addu'a bayan anyi yan gaishe² ne Malam yayi gyaran murya kamar yanda ya saba, Duban shi ya maida kan Malam Sulaiman dake zaune daura dashi kanshi a duk'e kafin ya mayar kan uwar gida. "Sulaimanu hak'ika da kai da Matar ka kun bani mamaki matuk'a domin kun aikata min abunda ban tab'a tsammanin riskar shi daga gareku ba, musamman ma ke Uwar gida!" Ya k'arasa fad'a yana nuna ta da hannun shi manuniya. "Shin kun manta shekarun bayane da kuka dunga min zarya a wannan falon nawa kuna rok'on arzikin in d'auki auran Mamana in ba d'anku?" Ya karasa kalaman shi da tambayar su yana mai jiran jin amsar da zasu bashi, Malam Sulaiman ne ya amsa da cewa. "Ayi hakuri ayi mana aikin gafara Yaya, abunda ya faru baya nufin cewa mun manta da alfarmar da Kayi mana na bamu auren ita Mai sunan Hajiya duk da mun san cewa darajar zumunci mukaci, sai dai lamarin muma bamuyi zatan cewa zai juye zuwa gabar da muke kai a yanzun ba sai dai ka haifi mutum ne baka haifi halin shiba" Yana rufe baki itama Uwar gida ta karb'a da cewa, "Tabbas abunda ya faru ba abune mai dad'i ba, abune wanda dukan mu bamu tab'a tsammani ba, sai dai na sani cewa laifin duk nawa ne, Nice naso kaina da nayi zaton cewa idan na aura ma d'ana mata daga cikin Dangin shi hakan zai karkato da hankalin shi zuwa gareni dama yaran shi dake tare damu, Gaba d'aya son kusanci da d'an da nike ganin yamin nisa yasa na manta cewa rayuwar yarinyar da muka aura mishi zai iya zama cikin kunci, Nayi zaton cewa d'a mai biyayya na haifa wanda zaiso abunda na bashi ya kuma tattala abun koda zuciyar shi bata so, Sai dai ina ashe ba haka bane, domin ya nuna min cewa bako wacce zuciya ake cusa ma abinda bata muradi kuma ta k'arb'a hannu bibbiyu ba, Hakika nayi kuskure naso kaina domin a lokacin baya idanuwa na ya rufe ta yanda bana hango komai sai rayuwar d'ana banyi la'akari damai zaije ya dawo ba, Ashe shi ya amsa ne kawai dan yamin biyayya bawai dan yana soba wannan dalilin yasa koda muka aura mishi ita yakai ya ajiye ba tareda ya damu da kula da sauke hakkokin ta wadanda suka rataya a kanshi ba, mafi hatsarin kuma shine rashin sauke hakkin shimfid'a" Katseta Malam yayi da cewa, "Kenan kina nufin cewa dama tun da fari shi Sarki bai amsa batun auren ba kece kikayi ruwa kikayi tsaki kika dunga taso min keyar Mijin ki a gaba kuna min jele da rokon in baku auren uwata?" Malam ya tambaya. Ita ko Hajjaju dake gefe salati ta d'auka tana tafa hannuwa cike da mamaki take cewa. "La'ilaha illahlahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, Ke koh dai wagga mata akwai ki da son kai dama na zuciya! Yo ashe ba iya jikata kad'ai kuka tilastawa auren dole ba shima kanshi mijin cusa mishi ita kukayi! Yo ba dole tak'iyin daraja a wajen shi, ku a wajen ubanwa kukaji cewa anawa maza auren dole? kodan dai kunyi sabon yin ma yaran ku mata auren dole shine wannan karon kuka juya kan maza?, To dan Allah jama'a ku tayani ganin wannan al'amari fa inba son kai ba in d'anki yayi nesa dake saboda Allah ya had'ashi da wata can k'atuwar mushirika ta shiga tsakanin ku miye na jikata a ciki da zaki sakota cikin dambarwar gidan ki?, Kai wannan mata wannan mata da son kai kike, lallai ashe alhakin jikata ne ya bibiye ki shi yasa auren yak'i yayi danko, inba haka ba jama'a kina matsayin uwa ace d'anki na cikin jafa'i mai makon ki tashi tsaye kema ki yaki Matar tashi da karfin kudurar ubangiji kisa a taya shi da addu'a kema kuma ki dage, shine kike zaton yi mashi aure ne mafita bayan ita shed'aniyar Matar nashi na raye tare dashi?, Ashe konton b'auna kukayi min kuka sa na yarda da cewar za'ama jikata auren ne kawai saboda a samu mafitar ciwon marar dake damu ta a wancan lokaci, dan cin amana ashe shigo shigo babu zurfi aka min, yanzun shi yayi saki ya tattara yayi wucewar shi wajen Matar shi ita kuma jikata an barta da zawarci, niko yar iya harda dagewa na wajen nemo mishi maganin sammu, to kowa yaje da halin shi wallahi mu dai bamu nufi kowa da sharri ba wanda kuma ya kullace mu cikin shi tayi" Baba Adamu da Innar yara na suka dage wajen ba Hajiya hakuri dan sosai fa ta nemi burgewa sai faman maganganu take, Sai da tayi shiru sannan shi kuma Malam ya amsa da cewa. "Duk ma masu cewa munayi ma yaran mu mata auren dole ko kuma auren wuri, suna fadane kawai saboda jin dadin bakin su, Nidai abunda na sani shine hakkin ubana wato ya zab'o ma yarshi miji na gari, sannan ni a wajena ban tab'a hango illah a wajen aurar da ya mace da wuri ba, duba da zamanin da Allah ya kawo mu a yanzun, Bawai muna ma Allah wayau bane, ba kuma muna gadara akan kasancewar mu Malamai bane balle muyi tunkaho da hakan cewa mu yaran mu bazasu iya fadawa wani halin na rashin d'a'a ba, Ita ya mace tamkar glass take koda ka adana ta a waje d'aya tofa sai Kayi kata tsan tsan domin abun kadan ne zai iya ture ta ta fado ta tarwatse, Zaka iyayin ajiya na kayan kwaras na tsayin shekaru a waje d'aya amma fa duk ranar da tsautsayi ya amfa musu lallai zaka sha mamaki domin da zarar sun rushe fa babu wani tsafin da zakayi wanda zaisa su koma dai dai yanda suke tun farko, Alhamdulillah a hakan muke kokarin bama yaran mu mata kula har zuwa lokacin da muke ganin sunkai kun zalin da zamu aurar dasu su koma hannun mazajen su, su kuma su d'aura da nasu tarbiyar, Ita diya mace inka dubi rayuwarta kacokam zataga tun daga tashin ta har zuwa tsufanta komai nata a takaice yake, in an haifeta zata samu tarbiyar farko a gida, a tashin ta bata san kowa ba sai yan gidan su, ma'ana uwa uba yayye kanni da kuma sauran Dangin dake tare da ita, soyayyar farko da take tashi dashi shine na ahalin ta, Mataki na biyu tarbiya na biyu kuma sai ya koma a hannun mijin auren ta da nashi ahalin, a hakan muke bakin kokari wajen zab'o mai tarbiyar da muka san zaiyi daidai da namu tarbiyar da muka d'aurata akai, wanda shi kuma zai daura mata nashi ciki harda yanda zata so shi su kuma rayu a tare, Mataki na uku kuma shine matakin da mace zata fara hayayyafa itama, A sanda ta fara haihuwa itama zatayi kokari ne wajen ganin taba nata yaran kalar tarbiyar data samu tsayin rayuwar ta. Mace ta kasance halitta mai sanyi ta yanda duk abunda iyayen ta suka gabatar mata koda bashine ra'ayin ta ba, gudun b'ata musu kansa ta amshi abun da hannu biyu takuma rayu dashi tsayin rayuwa, Sab'anin namiji, Yara maza suna da taurin zuciyar da idan suka ki abun wasun su ba lallai ne su iya daga idanun su suyi duba da abun ko mai nene ba, Idan kuma an samu masu biyayya zasu amsa din kamar yanda shi Sarki yayi biyayya ya amsa amma daga karshe ya jingine ta duba da cewa ita d'in ba zabin shi bane na iyayene abunda ya zamar mishi dole dama shine yayi musu biyayya kuma yayi tunda ya amshi auren, Kwarai ina ma yarana mata auren wuri, Sai dai kuma kafin auren saina bincika waye shi mijin da zan d'auki yata inbashi? Shin ya cancanta ko kuma a'ah? Ya addinin shi? Ya kuma nasabar shi? Shin zaima iya rikemin ita ya faranta mata ya kula wajen sauke hakkokin ta? Sosai nake tsayawa in nazarci mutum kafin in bashi auren yata ciki kuma harda lura da halin ita yarinyar domin dai bazaka d'auko wuta da wuta ka had'a waje d'aya sannan Kayi zaton samun salama ba, Tsayin lokaci da muke auran yaran mu babu wacce ta tab'a fuskantar wani kalubalen daga wajen mijin da muka zab'a mata alhamdulillah muna alfahari da hakan, Amma abun mamaki sai auren da muka had'a a tsakanin yaranmu wanda zamu iya kira da tuwona maina shine a yau muka taru saboda shi, Wa'iyazubillah wannan abu sam baimun dad'i ba, Ba kuma na ganin laifin kowa sai ku dai ku biyun nan domin ni dai yata nasan kalar tarbiyar dana bata kuma Alhamdulillah duk da bason d'an ku takeyi ba tayi biyayyar zama dashi na tsayin shekaru ko sau d'aya batayi tunanin kawo min karar shiba" Ya k'ara sa fada yana nuna uwar gida da malam sulaman da hannu, Baki malam Sulaiman ya bude zaiyi magana amma malam ya tari numfashin shi da cewa. "Bana son jin ta bakin kowa tukun ku bari in gama nawa maganar, Ku kun sani cewa zumunci shine abunda na duba kafin in amince da batun bama danku auren yata domin ko babu komai shima din nawa ne dan ban manta cewa nine na amso mishi auren shi na farko ba, Duk da tarin nakasun dake gareshi haka na ture na biye muku na b'ata ran uwata badan ina soba sai dai nima a lokacin idanuna sun rufe da son ceto ta daga halin ciwon da likita ya tabbatar da cewa aure shine maganin shi, Kafin ku nuna kuna buk'atar a had'ata dashi wasun ku da dama sun fito sun nuna kwadayin su nason auren ta, Amma zumunci yasa haka nan na runtse ido naba na kusa dani nayi amfani da kalmar nan da yan magana ke cewa duk dadin inuwar gemu bai kaiga makogoro ba, A lokaci na farko dani da kaina na assasa auren zumunci a tsakanin yaran mu, a zatona hakan zai kara zumuntan da iyayen mu sukayi tsayin daka wajen ganin kafuwar shi a tareda mu. Babban abun bak'in cikin shine yanda ya zaman wai ku iyayen su mata kuka kasa gane wani irin zama yaran nan suke gudanarwa tsayin shekarun nan, Ni nayi ma yata aure a zatona auren nata zai zama waraka a gareta, ashe aikin banza ne shi mijin ajiyeta yayi kamar ka d'auki kudi ka zuba a asusu kasan babu mai tab'a maka har sai randa kai ka buk'ata, To Alhamdulillah dukan mu dai nufin alkhairi mukayi, na kuma gode Allah daya tsaremin uwata duk da halin da take ciki amma allah ya kiyaye ta bata fad'a cikin wani halin na daban wanda bai dace ba, Ke kuma bayan kin fahimci abunda ke faruwa dake da kakarta mai makon ku kawo mana maganar gaban mu mu iyayen su mu d'auki matakin daya dace a ah sai kuka nuna mana halin ku na mata kuka yanke hukunci kai tsaye, Ita ta d'auke jikarta zuwa gidan ta ke kuma kika sa naki d'an a gaba ya rubuta mata takardar saki, to shin wai ma kafin ya saketa d'in kin tuhume shi cewa yana son ta ko a'ah?" Ya kare maganar da maida tambayar shi akan uwar gida, "Ayi hakuri Malam amma nidai nayi la'akari ne da cewa inda yana son ta da ba'a d'auki tsayin shekarun nan suna tare kuma ace babu abunda ya shiga tsakani ba, domin ko ban tambaya ba a bayyane yake cewa harda rashin so ya shiga cikin al'amarin nasu" Uwar gida ta bashi amsa. "To ai ba shi kadai yake da hakki ba ita Meenal din kuma kinsan meye a nata zuciyar ne? Wata kila tana son shine shi yasa har tayi hakurin zama a hakan ba tareda ta sanar da kowa irin zaman da sukeyi ba" Mai makon uwar gida ta bashi amsa wannan karan Hajiya ce tayi tsalam da cewa, "Ah ah kam wallah akai gaba jikata ma ba son shi take ba, zaman hakuri dai tayi dashi yanzun kuma mai afkuwa ta afku aure ya k'are dan haka kowa yayi ta kanshi, Kee Meenal bazaki bud'i baki ki fada musu cewa ba kya son shiba sai sun kara k'ak'aba miki shi abu dai kamar dole?" Ta fada a tsawace tana kallon meenal din, "Eh Baba Allah kuwa nima bana son shi dan Allah karku matsa min cewa saina koma, kuyi hakuri in kun bani umarni bazank'i biba sai dai zan koma zama dashi ne kawai badan ina soba kamar yanda shima ya tabbatar min da cewa har yanzun ban canza daga matsayin k'anwa a wajen shiba" Ta k'arasa fad'a cikin muryar rok'o adanuwan ta a kasa batareda ta iya kallon kowa a cikin suba. "To kun daiji da kunnuwan ku atoh itama jikar tawa bata so, da dai an mata dole amma yanzun kam babu mai karayi mata dole akan auren wanda tace bata so shima kuma din ba son nata yake ba, Yanzun kuma kai ka gama jawabin cewa kana bada auren yaran ka mata ne ga mazajen da suka cancan ta, dukan mu nan kuma mun shaida cewa yaran nan basa bukatar auren, saki kuma ya tabbata" "Tashi kije ciki Mamana babu wanda zai miki dole tunda bakya so, Allah ya miki zabi mafi alkhairi, Allah kuma ya albarkacin rayuwar ki hakika ina alfahari dake" Da ameen sauran jama'ar dake wajen suka amsa. Dan haka itama Meenal din ta mik'e da niyyar barin falon, "Ke jirani mu tafi kinji dan dama ba wani karin arziki nayi ba, gara in koma gida in samu inci in koshi tunda Allah ya taimakeni komai yazo karshe yau dai kam bacci zanyi babu jimami" "Meenal bazata koma tare dake ba Hajiya nan dai gidan ubanta zata ci gaba da zama inda ta rayu tun bayan haihuwar ta, yanzun kuma dan auren ta ya mutu hakan baya nufin zan barta ta koma wani wajen daban da zama, dan a wajena ita din har yanzun yarinya ne dole ta dawo gaban mu muci gaba da kula da tarbiyar ta kafin allah ya fiddo mata wani mijin tayi wani auren" Kafar wanda ya zabge fuskar Hajiya da mari haka taji saukar maganar shi a cikin kunnuwan ta, K'ifi k'ifi ta farayi da ido harshen ta har yana hardewa wajen furta cewa. "Kai Malam Almu ka kiyayeni ka fita idona in rufe tun wuri, Harni ce zaka kira gidana da wani wajen, kace wai jikata bazata je wani wajen ta tareba, Nafa gaji da mulkin mallakar da kake gwadamin tsakanina na jikokina, In mantawa Kayi bari in tuna maka cewa ni nan dai Hajiya Aminatu da kakeji da gani nice nan na haifo Hauwa'u Jidda uwar data tsugunna ta haifo Meenal, yanda nike da iko da Jidda haka nike dashi akan yaranta, Tun tuni da nake kauda ido akan hukuncin da kake yankewa a rayuwar yarinyar nan darajar Mukhtar kake ci, Amma yanzun kam tabbas idan ka matsa a shirye nake domin yin fito na fito da kai, wato taci gaba da zama anan haka nan ita zata k'are rayuwarta bazata samu kula na musamman daga gefen uwa mace ba, Tunda aka haifo yar nan ka kankame ko ina ka hanata shakuwa da uwarta, Wanda rashin shakuwar nasu shi ya taka rawa wajen lalacewar auren da kuka mata dan da ace akwai shakuwa tsakanin ta da uwarta tabbas bazataki shaida mata halin da take ciki a zaman auren ta ba, Ko kai dan kana ganin kafi kowa kusanci da ita a naka zaton duk wani damuwarta idan ta taso kai zata tunkara kai tsaye, To ga karamin misali nan ai ka gani tunda ga damuwar nan amma duk ta tsallake ku duk yawanku a gidan nan ta bini can wani wajen daka kira ta maida min damuwar ta, Dan haka komawar Meenal gidana kamar anyi an gama dan koshi uban daya haifeta shi Auta bai isa ya hana ni rikon taba wannan karan atoh" Baba Adamu ne ya shiga maganar da cewa, "Kiyi hakuri Hajiya bazamu hana ta zama a wajen kiba tunda kin bukaci hakan Allah ya tayaki riko, Ya'ya Kayi hakuri dan Allah su tafi d'in koba komai a yanzun nasan ita Meenal din zatafi sakewa acan fiye danan, da in ta zauna tunani ma na iya sata a gaba kuma muma bazamu so ganin ta a wani yanayi ba" "To sai dai ta zauna na wani d'an lokaci amma ba wai zaman din din din ba, kai ka sani yaran mu basa tab'a zama a wani wajen aure kadai shike rabamu dasu" "Ka daiji da shi" hajiya ta fad'a a yayinda ta riko hannun meenal da niyyar barin falon, Har takai bakin kofar falon ta juyo tana kallon uwar gida, "Nace ba! Kar kuce ban fad'a muku ba cikin satin nan zan tura a kwaso min kayanta dake can gidan, dan ba'a barsu babu kowa a gida kayan makudan kud'i su lalace a iska ba" Suna fita daga falon motar Hajiyar da direban ta ya tuko su suka shiga ya k'ara jansu domin komawa inda suka fito, A hanya ko sai mita take akan bazata k'ara yarda Malam yaci gaba da mulki akan jikokin ta kamar wani shine uban su ba, Yayin da a can falon kuma bayan fitar su Hajiyan suma uwar gida da mai gidan ta hakuri suka k'ara ba Malam din da rokon cewa suna fatan bazai rikesu a zuciya ba balle har hakan ya tab'a zumuncin su, Malam ya musu nasiha sosai sannan ya k'ara jan hankalin su akan kula da addu'a akan yara, kar kaga cewa yaran ka sun girma Kayi zaton cewa shike nan sunyi hankalin da zasu kula da kansu balle kuma hakan ya d'auke hankalin ka akan yi musu addu'a da nema musu kariya akan sharrin masu sharri, Domin koda Allah ya hada miji da mata nagari tofa yakan iya haduwa da shedanun abokai, Shedaniyar kishiya, Shedanun kawaye, Mahassada dai suna a ko ina wasu ma yawanci dasu muke rayuwa amma bama tab'a sanin hakan har sai ranar da Allah ya kaddara tonuwar asirin su, Dan haka ya kamata iyaye suyi tsaye wajen koyama yara addu'a tun daga yarinta har zuwa girma, A kuma dunga kiyaye azkar safe da maraici, sannan sadaqa tana maganin masifa Allah kuma ya tsare mu da tsarewar sa ameen, Ya dai musu matashiya sosai sun kuma yaba sunyi godiya kafin suka mishi sallama suka wuce zuwa gida, Itama kuma Innar yara ta koma cikin gida, Karfe 12 kamar yanda ya buk'ata duka yaran gidan maza da masu aure da marasa shi ba iya kuma yan cikin gidan nashi ba duk yaran ahalin maza yasa aka kira mishi illah wadanda basa gari ne kawai basu hallata a wannan kiran na Malam ba, Bayan taruwar su yayi amfani da wannan damar bayan ya shaida musu barakar data kunno kai a cikin a halin na mutuwar auren Meenal wanda babu wanda yaji dadin hakan a cikin su, Yaja musu kunne sosai tunda masu auren harma da samarin cewa duk fa wanda yasan zaiyi aure to ya d'aura damarar zama da Matar har zuwa sanda mai rabawa zai raba domin su dai a ahalin su ba'a musu tambari ko shaida akan sakin auren ba tun daga kan kakannin su har zuwa kan iyayen su da kuma sudin kan su, Ba kuma zasu zuba ido hakan ya faru akan yaran suba, Na Sarki da Meenal sun d'auke shi a matsayin kaddara amma sufa sauran kar suyi duba da cewa ai sarki ya bude musu kofa ne suyi zaton cewa suma zasubi sahun shi babu wannan maganar, Domin dai su dama yaran maza ba kamar mata bane ko wanne ana bashi damar ya zab'o Matar data mishi ne kafin a aura mishi, Daga karshe suma Malam ya musu tuni akan rike ibada da kula da addu'a kana kuma ya k'ara jan hankalin su akan rike zumuncin dake tsakanin junan su, Domin yana fatan zaman lafiya da fahimtar juna ya tabbata a cikin ahalin shi ko bayan kasa ya rufe mishi ido, Haka dai a ka tashi wannan taro jiki a sanyaye kowa na mamakin ya akayi auren Sarki da Meenal ya mutu, A wannan rana dai mutuwar auren shine ya zama labari mafi zafin daya dunga watsuwa a tsakanin ahalin. #No aditing 😒 #Team AK #Team Sheikh Naseer #Team Hajiya #Team Malam *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *~{{ MY FAMILY}}~ BOOK 2* ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{{UMMIEE ZARIA}}~*✍🏼 *Page 3.* *AK d'an mai karfi, da Yusuf wase* kuwa kasancewar basu bar garin Kaduna da wuri ba hakan yasa basu samu damar shigowa cikin garin na Zaria ba sai gaban nin magariba, Hakan nema kuma yasa koda suka iso basu samu damar shiga gidan na Hajiya ba sakamakon tsayawa gaisawa da matasan majalisar nasu da sukayi, wanda gaisuwan nasu shiya kai su har zuwa lokacin sallan Magriba to bayan an idar da Sallah din ma da kyar Mai Jama'a ya samu ya zare jikin shi a cikin jama'ar shi domin Yusuf dama suna fitowa daga masallaci ya wuce cikin gidan bai tsaya a wajen ba. Kamar wanda magnet ke janshi haka ya samu kanshi da d'aukin zuwa sashen na Hajiya fatan shi dai kawai shine Allah yasa yarinyar nan itace abu na farko da zai fara yin tozali da ita a sashen, Dan haka gudu gudu sauri sauri haka ya fad'a sashen shi turaren shi ya dauka ya k'ara feffesawa had'ida gyara zaman hulan shi kafin ya fito kai tsaye zuwa sashen na Hajiya cike da takun shi na mazajen dake ji da kansu, Sai dai tun kafin ya k'arasa ya farajin hayaniyar Hajiya inda take cewa... "Shike nan duniya ace mutum bazaici abincin kwarai ba rayuwa sai mace tasha tea da safe tea da rana tea da dare uwa dai wata jinin larabawa ko buzaye? Takwara indai baso kike ki k'arasa karmashewa ta yanda ubanki Almu zaiji dad'in fadamin maganar banza ba ai kamata yayi ki ceci kanki ki bani had'in kai ki dunga cin abunci masu gina jiki ta yarda ko mak'iyi yaganki yasan cewa zawarci ya amshe ki, ke bakiga mazan yanzun sun fison mace mai d'an mulmulallan jiki ba, ina amfanin mace ta zauna a rame uwa wata mai cutar yunwa, to nidai Allah ya sani gidan nan babu kishirwa bare ayi batun yunwa, so kike dai sai ubanki ya samu hanyar fad'amin maganar banza in ya ganki a bushe" Murmushi ne ya subuce mishi a zuciyar shi yake cewa, kuji min tsohuwar nan fa, towa yace mata ni yar lukata nike so matata ta zama me?" Mai makon yabi ta kofar falon sai ya juya akalar shi zuwa tacan baya yabi ta kofar kitchen, kamar yanda ko yayi tsammani a bud'e kofar take ba'a kulle ta da makulli kamar ko yaushe ba, dan haka ya bud'eta kai tsaye ya shige ciki. Koda ya bullo cikin falon ta wajen dinning duk Sallamar da yake Hajiya da idon ta ya fure take tama meenal mita wacce ke zaune a kan kafet din dake tsakiyar falon manyan littafan tane na karatu kewaye da ita sai wani littafin dake yin jotting abubuwan da take tsinta a cikin littafan gefe d'aya kuma kofin shayi ne sai wani k'aramin bowl dake d'auke da dambun nama a cikin shi, Lallai hausa sunyi gaskiya a yayin da sukace kubar rai da abunda yake so, Domin ko hakance ta faru da Mai Jama'a tun bayan wanzuwar shi a cikin falon idanun shi basu sauka a ko inaba kai tsaye sai akan abar kaunar shi wacce daman ita din itace abunda yake da buri da fatan yin tozali da ita a daidai wannan lokacin, Bai san yayi kewarta da yawa ba sai lokacin domin kuwa mai makon ya k'arasa inda suke duk da alamu sun nuna cewa sud'in basuji shigowar shi ba, Ah ah kawai sai ya samu kanshi da gyara tsayuwar shi bayan daya jingina jikin shi da dinning din dake wajen kawai yaci gaba da bin fuskarta da kallo, bakin ta kawai yake kallo a yayinda take amsa ma Hajiya da cewa, "Wai ke Hajiya waye ma yace miki yawan cin abunci shike sa mutum yin kiba ne? Kuma ni Allah ma ya sani cewa ko kadan bana son k'ibar da kike ambata min shi yasa ma yayo ni haka" Daga kan bakin ta ya maida kallon shi zuwa kan dogon hancin ta dake nan d'an zuwat abunshi sai kuma kyawawan idanuwan ta dake kyalli akoda yaushe sakama kon ruwan dake cikin su hakan nema yasa abu kadan kesata kuka, Kanta da babu d'an kwali sai wani d'an karamin hankaci da tayi amfani dashi ta dan daure kan dashi, saboda kasancewar hankacin karami ne kuma hakan yasa sai bai rufe mata gashin kan nata dake tsefe da kyau ba, sakamakon tea din da take Shane kuma zafin da tea din yake dashi hakan yasa zufa tsatsafowa a goshinta har ya zama silar da gashin dake kwance goshin ta kwanciya lambam a gaban goshin nata, Mik'a tayi na alamar gajiya da zaman da tayi a wajen, mik'ar data nemi tarwatse mishi dan nutsuwar daya samu a yan kwanakin sakamakon bankaro k'irjinta da tayi zuwa gaba, gashi kuma dama ba wata rigar arziki bace a jikin nata half best ce a ciki sai kuma ta d'auko wata fibgilar shimi dake nan shara shara ta d'aura akan half best din wanda hakan bai wani rufe komai na daga ainihin surar jikin taba sai ma k'ara fitowa da surar nata yayi a zahiri, tasan cewa ba kasafai a yanzun hajiya ke samun bak'i mazaba tunda Mai Jama'a ya dena zama a garin sai bakin gidan suka ragu dan haka koda ta dawo gidan take zama a sashen na hajiya bata da shamaki shigar data keso shi takeyi sai dai yawancin lokuta in zata zauna a falon sai ta kullo kofar falon saboda gudun fad'owar wani cikin falon ba tareda ta kimtsa ba, yau kuma ganin dare ya fara kuma kofar falon yana rufe dan haka ta fito a bunta dan akwai abu mai mahimmanci da take son yin nazari akan shi, tun kafin magrib take zaune sakamakon fashin sallan da takeyi shi yasa koda lokacin sallan yayi bata tashi ba dan hatta da tea din da take sha Larai ta rok'a ta had'o ta kawo mata dan bata son abunda zai katse mata abunda takeyi din tafison sai ta kammala sai ta tashi gaba d'aya. Runtse kwayar idanuwan shi yayi gam yana karanto kalmar innalillahi wa innah ilaihir raju'un, yasin inda ace yarinyar nan tasan da tsayuwar shi a wajen to da sai yace da gayya tayi mik'ar dan taga yana kallon ta, to amma ai koba kowa bai dace mace ta saki jiki tana wani gantsaro kirji da sunan mik'a ba😒 dan hakan d'aukar alhaki ne, kawai daga zuwan shi tana neman had'o mishi tarzoma, *Ita ko Meenal* da fari kamshin turaren shi data dad'e da haddacewa ne ya fara sumame zuwa hancin ta, taso ta share dan a zaton ta kamshin ne kawai irin yanda wani lokacin idan mutum na zaune sai ya dunga jin kamshin abubuwa, sai dai kuma daga baya tsigar jikin tane taji yana tashi gaba d'aya sai takejin ta tsargi kanta kamar dai akwai idon dake yawo a jikin ta, Dan haka sai ta d'ago kanta zuwa ga wajen Hajiya dan taga ko itace ke kallon ta, sai dai kuma sai ta iske gaba d'aya hankalin Hajiyar nakan shirin da ake gabatarwa ne a tv hannun ta kuma rik'e da carbin ta da take ja sakamakon azkar din da takeyi duk bayan idar da sallar magrib, Da kad'an da kadan ta fara yawo da kwayar idonta a cikin falon har zuwa lokacin kuma tsigar jikinta bai bar tashi ba, kurrr idanuwan ta suka shige cikin nashi ga mamakin ta sai taga yana mata murmushi, A zaton ta gizo ne yake mata dan haka sai tayi kokari wajen fusgar nata idanuwan daga cikin nashi ta runtse su da karfi sai dai kuma ilai dai koda ta bud'e shi din dai taci gaba da gani tsaye ya rungume hannayen shi a kirji yana sakar mata murmushin shi kai kayatarwa, Baya baya tayi kafin ta bud'e bakin ta ta kwad'a ihu tana mai nuna inda yake da hannu, "fatalwa Hajiya! Fatalwa!! Wallahi fatalwa ne a falon nan" Ta fad'a a yayin da ta isa wajen Hajiya da rarrafe ta wani irin cumuimuye kanta a cikin jikin Hajiyar, "Fatalwar lafiya! Ke kin taba ganin fatalwa ne a gaske dan ubanki, kuma shi fatalwar duk ta rasa wajen zuwa sai falona da kullum yake cike da tsarki, dallah can ni cikani" "Wallahi Allah da gaske nikeyi Hajiya ba gashi can a tsaye wajen dinning table dinki ba" Kai duban ta zuwa wajen Hajiya tayi, "Wannan ne fatalwar? Ikon Allah aiko da sai ince lalacewar zamani takai inda takai tafale da ado da kwalliya, kiga mutum a tsaye da kafafu biyu kice wani fatalwa, to waini uban wa ma na kashe da zaimin fatalwa? Yo ni ko shedanun aljannu ai sai sun shirya kafin su nufo inda nike balle wata tsiya can wai fatalwa," "Hajiya kalli fuskar shifa murmushi yakeyi wallahi" "Ikon Allah, kai kuma dan mak'iyin uban mutum wani salon iya shegen ne wannan zaka fad'omin daki daga sama kamar wani dan aljannu? Kai tsaya ma ina fatan dai ba zuwa Kayi kaima ka amso shegiyar layan nan ta k'arya da ake cewa ana b'ata in an latsata ba?" Dariya dukan su suka bashi, Dan haka ya shiga kyakyatawa ba kakkautawa a yayinda yake karasowa wajen su, Da kallo Meenal ta bishi domin dai wallahi tsayin rayuwarta ita bata tab'a ganin shi yana dariya harda kyakyatawa irin hakan ba, dan haka sai ta kure shi da kallo tana ganin yanda dariyar ya mishi kyau matuk'a sakamakon fararen hakoran shi da suke jere reras ga wushirya a tsakanin su sama da k'asa, "Wai kema tsoron kikaji kamar wannan zabuwar jikar taki Hajjaju ta?" "Allah ya sawake in tsaya jin tsoron wani abun halitta can da yawar ka" Ta k'arasa fad'a tana aika mishi da harara. "Ke kuma mai kikeyi a gidan nan?" Ya tambaya a yayinda yakai zaune a kasan shima kamar yanda suma suke zaune, "Oh wai meenal kake magana? Ai Allah yayi dai bana na kwato ta daga hannun wancan uban nata dake musu mulkin mallaka dan haka ta dawo hannuna, fata nike Allah ya fiddo mata da d'an dashe shen miji na nuna ma sa'a kwanan nan in wanke ta in kai mishi ita" "Allah ya sawak'e ni bazan k'ara yin wani aure yanzun ba" Meenal ta amsa dashi tana murgud'a baki. "Ah ah wallahi karma Kiyi ka kanki mugun baki, aure ai ya zama dole, to so kike in saki a gaba inyi ta kallo bayan tako ina kinkai minzalin auren? Ina ce suma kawayen naki batun aurar dasu iyayen su sukeyi to so kike su suyi auren ke kuma kici gaba da zama a gaban mu salon Almu yasamu dalilin da zai kullaceni da kyau kinga kin bashi damar fad'amin magana kenan, zaice na baro ki daga gida na kawo nan kuma na d'aure miki gindi kinki aure, Ah ah wallahi aure kam bari dai ki gani mijin dai ya fito" "Hajiya tunda tace bata son auren ki barta mana har sanda ta shirya!" "Kai matsa can bani waje, kai in ana maganar aure har ma kana da bakin tsomawa? Ka daiyi ta zama har mutuwa tazo tayi wuf da kai baka ajiye mana wanda zamu gani mu dunga fad'in cewa oh ga d'an Abdul Khareemu ba, kana nan kana sha shanci mtws duk dai ka gama tara kudin kana mutuwa kasafin su za'a mana muci kaji kaiko kana can an turbud'e a karkashin kasa" "To wai dama ni Hajiya na taba zama dake ne nace miki bazanyi aure ba?" "Oh to ka samu lafiyan kenan kwanan baya ai cemin kayi baka da lafiya yin aure saboda nika d'auka shashasha" Shiru yayi wannan karan ba amsa, Kuji hajiya fa tana neman tona mishi asiri a gaban yarinyar nan, Sad'af sad'af Meenal ta mike a yayinda ta tuna cewa bafa kayan kwarai bane a jikin ta dan siket din dake jikin tama ko gwuiwar ta bai k'arasa ba dan haka ta bayan kujerun falon ta dunga bi harta fada cikin daya daga cikin dakunan dake nan k'asa dan bazai yuwu ta wuce zuwa sama da kayan dake jikinta ba alhalin shi din yana zaune a falon dan ba kadan ba duk take jin ta tsargu, haka kawai ya wani shigo ma mutane babu sallama. Sabon gaisuwa sukayi shida Hajiyar bayan ta bace ma ganin shi, kafin suka d'aura da hira anan kuma Hajiya ta bud'e babin bashi labarin abubuwan da suka faru a cikin kwanakin da suka wuce da bashi a cikin gidan. Suna kuma cikin hirar ne Yusuf ya shigo shida Musty wanda shima bai dad'e da isowa daga Abuja ba, dan haka suma suka zauna akaci gaba da hirar dasu har zuwa lokacin da akayi kiran sallan ishsha'i, hakan ne kuma yasa dole suka tsagaita da hirar da suke suka tashi da nufin zuwa su gabatar da nasu sallan, har sun kai bakin kofa Yusuf ya dawo baya, "Hajiya yau fa ina da labari mai tsada da zan baki amma sai kin bani goron albishir kafin nan kuma yunwa nikeji😞" Ya k'arasa fada yana narke fuska, [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *~{{MY FAMILY}}~BOOK 2* ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*✍🏼 ~~~*Page 4* Allah yasa albishir da haihuwan Saniyata zakamin, dan satin daya wuce danaje gidan gonar na samu guda a cikin su da ciki tsoho kuma Zakariya yace min suna saran haihuwar ta cikin satin nan" Hajiya ta fad'a tana washe baki, "Ah ah kam wannan albishir din nawa wanda kika dade kina jira ne kedai kawai ki tanadi goron ki na albishir ni kuma idan na dawo in baki shi da zafin shi," Yana gama fad'in hakan ya take ma su Musty baya wadanda suka fice tuni, Da gudu gudu ya samu ya cimmusu, kamar dama AK jiran isarshi ya ke ya wani bishi da kallo yana cin magani, "Yusuf³" Ya kira sunan Yusuf din har sau uku shima kuma Yusuf din yaci gaba da amsawa ba tareda ya gajiya ba. "Wallahi in ka fada Allah ya isa na" "Kai dallah can ware, ai wallahi kaji dai nama Kara rantsewa yasin sai na fad'a" 'Oh amanata zakaci bayan na yarda da kai?" AK ya tambaya yana marairaice wa, "Amana ta nawa kuma? Amana ta wuce wacce ka cinye tsakanin ka da zuciyar ka, malam ni mafita kawai nike nemo maka saboda ina kaunar ka da yawa bazan so inga kana wahala ba" "Kai wai ku tsaya kunfa sani a duhu ban gane ba, meke faruwa ne anan?" Musty ya tambaya yana shiga tsakaiyar su, "Ni dai Allah ya isa na wallahi, kuma ma laifina ne dana fada maka damuwa ta" Cewar AK a yayin da yayi gaba ya fice daga gidan ya barsu a baya Yusuf na mishi dariya. "Wai Baban Affan bazaka fadamin abunda yake faruwa ba?" "Me zai hana in shafa maka, amma dai gaskiya labarin mai tsada ne wallahi bazan fada muku ba sai naji saukar alert mai nauyi cikin asusuna," "Ah haba Baaba kar muyi haka mana nine fa Mustyn ka" "Koma dai miye na dai fada maka amma ga Satan amsa zan baka, *abokin ka ya fad'a soyyaya*" Wata irin fashewa da dariya Musty yayi kafin ya tsagaita da dariyar anan inda suke tsayen yayi ruku'u na nuna godiyar shi a wajen Allah subhanahu wata'alah, "Ai dole kayi ruku'u wallahi" Rungume Yusuf yayi tsamtsam bayan ya dago cike da tarin murna da farin cikin da suka sauka mishi ya sanya duka karfin shi ya d'aga Yusuf din sama yana juyawa dashi irin yanda akewa yara, Dan koba komai dama shi Musty din yafi Yusuf din jiki kasancewar Yusuf din bafulatani sai ya zamana hatta da jikin shi irin na fulanin ne, "Kai miye haka dallah ni saukeni ya zaka wani dunga juyi dani kamar ka dauki karamin yaro, dan allah saukeni juwa nike gani" Ya fada yana dukan kirjin Mustyn a kokarin shi na ganin ya sauke shi, Ajiye shin yayi yana dariya shi kuma saiya rike Mustyn sakamakon jirin da yakejin yana neman kadashi, "Kai dan iskane wallahi musty taya zaka wani dunga juyi dani a filin Allah dan kawai kana takamar ka fini girman jiki to yasin kayi ma kanka bazan baka labarin ba" "Kama isa ka shafa min mai abaki sannan kace bazaka fadamin ba, wacece dan Allah?, kai amma wallahi AK dan rainin wayau ne wai dama soyayyar ce duk tasa ya firgice uwa wanda ya shekara rashin lafiya? Oh Allah na gode maka ashe zanga wannan ranar da AK zaiso wata macen sab'anin matan da kullum sune suke binshi" Dafa kafadar shi Yusuf, "Kaga Malam muje kafin mu rasa jam'i kardai ka manta kanun labarin kawai na fad'a maka cikakken labarin sai naji alert tukun a hakan ma kuma har sai Sadeeq ya dawo zuwa gobe tukun dan yace min zai shigo gobe" "Fad'i ko nawa kake buk'ata wallahi zan tura maka a yau din nan in dai zaka bani labarin nan, Allah Yusuf in kaki fadamin jinina yana iya hawa kafin safe" "Oho in ka kashe kanka ai Jameela ce zatayi a Asara kaga kana mutuwa ni kuma zuwa zanyi in roki alfarma a matsayina na abokin ka a bani ita in aura basai an canza ranar auren da aka sanya ba, dan haka kama kanka Malam" Duk yanda musty yaso Yusuf ya bashi labarin wacece yaushe kuma abokin nasu ya fara soyayyar k'iyawa yayi har sukaje sallan suka fito, Wannan karan AK bai jira sun jera ba yayi gaba abunshi dan da gaske haushin wase yakeji, Ya daga fada mishi sirrin shi dan wulakanci zai wani zo ya nemi baza labarin shi a faranti yana tallah dashi. Sai da ya sake sabon wanka kafin kiran Musty ya same shi akan shifa suke jira ya shigo suci abunci suna sashen Hajiya, "Oh dama acan sashen Hajiyar kuka saba cin abunci ba anan ba? Ko koh tsabar son ayi munafunci na a bayan idona shi yasa kuka wuce can? Wallahi nidai ban yafe ba duk wanda yayi gulma na" "Ai sai kayi shegen mita kamar goyon mace kuma anyi gulmar naka kayi abunda zakayi, malam in zakazo muci abinci bismillah in kuma baka zuwa ma duk cikin ka tayi atoh" Ya k'arasa fad'a tareda tsinke wayar nashi, Hajiya, Meenal, Musty, Yusuf dukan su su hud'un zaune suke a kan dinning table din falon na Hajiya ko wanne da plate din abunci a gaban shi, sab'anin Meenal da nata plate din ke dauke da meat pie guda biyu sai lemun kunun aya mai sanyi data tsiyaya a cikin kofin tambulan tana cin meat pie din tare dashi, Doguwar riga ce a jikinta shigar datafi ta'amali dashi a koda yaushe sai dan kwalin rigar data daura shi akan nata ba tare da ta d'aure ba, Hira suke gudanarwa wanda kuma rabin hirar akan tsare tsaren bikin Musty ne wanda a yanzun bikin nashi ko wata biyu bai kaiba, Da sallama ya shigo d'akin kuma yanzun din ma dai kamar d'azun ta kofar bayan ya Kara biyowa ya shigo, Hajiya ce ta dago kai bayan sun amsa sallamar, "Wai kai Abdul wannan kofar ta kitchen itace kake so ka mayarmin da ita kofar shiga da fitar ka ko ya yah? Karfa kaga dan d'azun ka shigo tanan bance komai ba kayi zaton kyaleka nayi, Wannan ai salon ka nuna ma barayi hanya ne, ke tashi kije kisama kofar key ki kuma ciro key din ki kawo min nan sai inga ta inda zaibi kuma idan ya tashi fita" Shidai bai tankata ba har sai da ya samu kujera wacce take kallon kujerar da Meenal ke zauna yaja shima ya zauna, zaman nashi kuma yayi dai dai da mikewar Meenal taje ta kulle kofar ta kuma ciro key din kamar yanda hajiya ta buk'ata, Sai dai kuma tashin ta na zuwa da dawowa duk tayi sune idanuwan AK yana kanta dan itama dai sabon wanka tayi tadan feffesa turare kawai kuma sai zuciyar shi ke raya mishi cewa wai tayine saboda shi, kujimin wani kwala kai a faranti fa irin na jikan innan🤨. "Hajiya k'ofa dukan su sunan su kofa, dan na biyo ta nan kuma ai ba laifi bane tunda naga dai ni din ba bako bane" "Kace haka mana dama, amma ai a gaban idon ka d'azun ka firgita takwara kasa ta fara kiramin fatalwa ana zaune kalau" "To Kiyi hak'uri zan kiyaye" "Da dai yafi maka kam, ke kuma sai an rok'a ne kafin ki zuba mishi abuncin?" "Toni nasan wanda yake son cine hajiya? Kuma ai baice azuba mishi bama!" "Amma dai kin iya jin baki da neman magana inba haka ba har zaki kwana ki hantse a gidan nan sannan kice min wai baki san me zaici ba bayan kinga dukan mu anan tuwon muke ci in bake da shegen tsurfa ba da kika maida kanki wata iri bazaki zage kici abunci mai nauyi ba" Hannun shi ya mik'a ya dauki plate, "Kyaleta Hajiya zan zuba da kaina" Shiru sukayi kowa yaci gaba dacin abunda ke gaban shi har suka kammala, kafin suka dunguma suka koma falon na Hajiya yayinda Hajiya taci gaba daba Wase labarin gidan gonar su Yusuf din dake samaru wanda suke tayata kiwon nata dabobin. Musty ne ya jefo ma meenal tambaya da cewa, "Bestyn ki fa tace min ke suke jira batun cire anko wai tunda kika zo gidan nan baki zuwa ko ina daga makaranta sai gida shi yasa baku samu damar zuwa kasuwa ba" Mai makon Meenal ta bashi amsa sai Hajiya ne ta amsa mishi da cewa, To kai Musty ta ina macen dake iddah zan saketa sakaka ta kama yawo salon ubanta ya sani a bakin duniya, A'ah wallahi koma miye zasuyi su jin kirta har zuwa gaba kadan in kuma ya zama dole ita Jamilan basai suje ita da Maryam su fito da ankon ba, cire anko dai ba wata tsiya ba," "Hajiya kasuwa kawai fa zamu awa nawa ne mun siyo mun dawo?" Cewar Meenal. "Eh fa kasuwar koma minti daya ne nidai nace a'a dan dole inyi kaffa kaffa dan kar kiyi mamaki ace ubanki yana nan yasa masu kula mishi da shiga da fitan ki dan kinsan dole na mishi kike zaune a gidan nan badan yana so ba kamar wani shine yama yata nakudar ki" Cike da haushi ta tashi fuuuu kamar wata kububuwa ta haye sama tana turo baki, "Ai sai dai Kiyi ta fushin ki amma babu abunda zai canza in fad'a miki, aini kuma shi kenan na d'auko ma kaina jangwam magana daya biyu ki wani dunga turomin baki dan kaniyar ki, da dai ina zamana abuna baki na Alaikum yanzun banda halin in zauna shiru a cikin gidan nan sai dai in kina makaranta, ai dole ma Kiyi aure da wuri wallahi tun kafin a ganmu a rana a mana gwai Allah" Ita fa Meenal bawai saboda abunda Hajiya tace bane yasa ta wuce sama ah ah tadai tuna cewa bata da pad din da zata canza cikin dare ne dan a kayan data kwaso a gidan Sarki pad guda daya kawai ta gani, Dan haka koda ta shiga cikin dakin kudi taso d'aukowa domin ta fita shagon dake waje ta siyo saboda gidan na hajiya dai babu yara balle ta aiki wani daga cikin su, Sai dai kuma tana shiga dakin kira ya shigo wayar ta koda ta duba kuma sai taga malam ne ya dawo mata da kiran da tayi mishi d'azun bai dauka ba dan tunda ta dawo gidan kullum ne zai kirata dan ya tambayi ya take da fatan hajiya bata matsa mata kamar wata wacce hajiyar zata dafa ta cinye, To anyi rashin sa'a yau din gaba daya basuyi yawa ba dan tayi sammakon zuwa makaranta wanda hakan yaja harta mance da wayarta data kashe tasa a caji, Sun dade suna hira bayan sunyi gaisuwa kafin ya mata saida safe ya kashe wayar, Gyalen dake kanta kwai ta gyara ta d'auko kudin ta sauko, babu kowa a falon sai Sadeeq dake waya, AK da Musty duk bata san ina sukayi ba garama hajiya taji motsin bude kofar dakin ta d'azun da alama ciki ta shige, "Ah ah an matan Hajiya sai ina kuma?" Sadeeq ya tambaya yana dan kauda wayar daga bakin shi, "Kofar gida zani zan d'an siyo abu a shagone yanzun zan dawo" "Kawo in amso miki Kiyi zaman ki dare ya farayi" Kai😳" ta furta tana zaro ido, ina ita ina aiken Sadeeq siyo pad fisabilillahi, "Ya akayi ?"ya tambaya "Ah ah ka barshi dan Allah wallahi yanzun zan dawo kaga ai waya kakeyi" "Kawarkice ko in baki ku gaisa ne?" Bata tsaya ba tana ficewa daga falon take cewa "ah ah kace ina gaisheta" Koda ta fito babu kowa a harabar gidan sai hasken wutar lantarkin daya haska ko ina ya fito fes kamar ba dare ba, daga can bakin gate kuma masu gadine zaune suna hira a tsakanin su, Karasawan da tayi kusan sune kuma hakan yasa daya daga cikin su mai suna Isah tasowa, "Zakiyi aike ne Hajiya?" "Ah ah ya Isah ba bu wani abu jeka zauna kawai zan amso da kaina" "Haba Hajiya gamu zaune ba wani abun mukeyi ba ai da nauyi mu barki kije siyan wani abu da kanki da girman kujeran ki ranki ya dade" Da murmushi a fuskanta ta amsa mishi da cewa, "Allah kuwa ka koma ni da kaina zanje ai ba zama zanyi ba kafin ka sani na siyo na dawo" "To shi kenan ranki ya dade tunda kince haka a dawo lafiya" Ya k'arasa ya bude mata kofar ita kuma ta fice a gidan, Duk da cewa a wasu unguwan nin za'a iya cewa dare ya farayi ta yanda zirga zirgan mutane zakaga ya ragu su nan ba haka abun yake ba domin yawancin darare a cike wajen yake kasancewa da mutane sakamakon wadannan shagunan da suke raya unguwar akoda yaushe baya rabo da jama'a inba tsakiyar dare ba, Bata tsaya bata lokaci ba taje chemist din dake nan ta siyo pad din guda d'aya kafin idan taje asibiti gobe zata dibo wasu, Tana siya din kuma ta dawo gida, wannan karan ma Isah ne ya bude mata domin tana tsaye harta je ta dawo, AK ta hango zaune a cikin motar shi ya kunna fitilar cikin motar sautin kid'a na tashi kadan kadan shi kuma yana zaune a mazaunin driver sai dai bai kulle kofar motar ba domin kafar duka biyun ma ata wajen motar suke yana danna waya, Murmushi tayi, kasa kasa take cewa, "Mutum bashi da aiki sai na cire manyan kudade yana siyan manyan motoci to muma dai baza'a mana Kuri ba atoh," Key din motar ta na wajen Sarki dake rike a hannun ta wanda dama ta fito dashi ne da niyyar idan zaka koma ciki ta bud'e kofar motar akwai sakon da Meelat ta bata d'azun a makaranta shi take son dauka a cikin motar, Sai da ta jinjina mukullin da kyau sannan ta matsa luck daga inda take tayi unlucky din motar, har wani canza tafiya take a yayin da take k'arasa wa zuwa wajen motar, Shi kuma AK dake zaune yana amsa waya ta Bluetooth din dake kunnen shi daya wayar dake hannun shi kuma yana duba sakon ni karar da motar tayi ne yaja hankalin shi zuwa gareta dan sam bai san da wanzuwar ta a wajen ba, Kallo yake binta dashi cike da burgewa domin shi dai a yanzun kam allah ya sani babu wani abun halittan da baya gajiya da kallo wanda kullum yake fatan ya dauwama yana kallo kodan samuwar farin cikin zuciyar shi irin yarinyar nan, Shi dai yasan bai taba jin son wata yarinya irin yanda yake jin sonta a cikin ko wani fitar numfashin shi, Ji yakeyi kamar inbai sameta yana iya rasa numfashin shi, Wallahi ko nawa za'a nema a wajen shi zai bada koda ko kafatanin dukiyar shine dan dai kawai ta zama mallakin shi. Dan haka da kallo yaci gaba da binta yana jin wani yanayi mafi kololuwar dadi na lullube shi, har zuwa sanda ta isa wajen motar ta wani bude ta da still, Murmushi yayi a bayyane ya furta cewa "da alama dai yar kauye tayi agogo shine ake mana kaud'i" Kallon ta yaci gaba dayi yayin da ita kuma ta shiga cikin motar ta zauna, saida tayi warming motar da kyau kafin ta fito daga ciki ba tareda ta kashe motar ba ta zagaya ta bud'e bayan motar ta cire sakon da take son d'auka sannan ta maida booth din ta rufe ta Kara komawa cikin motar ta zauna itama kafafuwan duka guda biyun suna waje kamar yanda ya zauna, "I will call you back John please excuse me" Ya furta cikin harshen turanci bai kuma jira amsar John din ba ya yanke wayar, Takowa yayi zuwa inda nata motar yake bayan ya tura murfin nashi kofar motar ba tareda ya kashe ba har ya iso inda take, Tun tasowar shi idanuwan ta ke kanshi tana mishi kallon kasan ido ba tareda tayi yanda zai gane cewa kallon nashi takeyi ba, har ya iso inda take, yana karasawo kuwa kamshin turaren shi gaba d'aya ya lullube wajen, wanda dole saida ta runtse ido tana mai bude kofofin hancin ta dan taba turaren nashi damar isa cikin kwalwarta da kyau...... *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/20, 8:48 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *~{{MY FAMILY}}~ BOOK 2.* ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~* *Page 5.* Ke farar kura wai me yasa kika raina nine?" "Ni kuma fisabilillahi to me kuma nayi maka yau daga dawowar ka?" Itama ta maida mishi da tambaya. "Oh baki ma san me kikayi min ba kike cewa?" "Eh" ta bashi amsa a takaice. "Da kyau amma kin san dai tunda na shigo ko gaisuwa bai had'ani dake ba koh? Ko shima gaisuwar ban kai darajar da zan same shi daga gareki bane?" Ya k'ara tambaya yana kureta da kallo. A yayinda ita kuma kunya ya rufeta, dan sosai taji rashin kyautawar hakan, "Kayi hakuri na manta ne ban gaisheka ba,Ina wuni ya hanya dafatan ka dawo lafiya?" "Lafiya kalau alhamdulillah, ko kefa!" "kuma ma ai laifin Kane tunda kaine ka shigo ta kofar baya ka bani tsoro yasin nayi zaton aljanine!" "Oh shi yasa kika kirani da suna fatalwa dan kawai na biyo ta kofar kitchen? Kuma ai nayi sallama keda kakarki da kuke ta surutu ne bakuji ba" Sai da ta maida kanta k'asa saboda abunda take son fadi tasan bazata iya fadar shi a yayinda take kallon cikin idon shiba kafin tace. "To ai manyan kaya naga kasa kuma fa sai faman murmushi kake tayi shi yasa kawai nayi zaton ba kai bane, amma da kayi magana aina gane cewa kai din ne dai da gaske," "Manyan kaya! Murmushi?" Ya tambaya yana dage mata giran shi guda daya a yayinda ta d'an d'ago nata kan tana kallon shi kad'an kad'an, Sai da tayi yar karamar murmushin ta dake bala'in burgeshi kafin ta amsa mishi da cewa... "Eh mana Allah kuwa nidai banfa tab'a ganin kasa manyan kaya harda hula irin yauba, ko lokacin bikin su Aunty Sas da Anty Fati duk kana nan kaya kasa, kuma kai ai kullum fuskarka a murd'e take" "Kamar fuskar shanu ko?" Ya tambaya yana tsare ta da ido, Sai da ta kauda kai kafin ta amsa da cewa, "Eh mana sai yau kawai naga kanata murmushi harda dariya da kyakyatawa ka dunga yifa,shi yasa ni kuma nace fatalwa. Dan ma ba kaga yanda manyan kayan da murmushin fuskar ka suka sa ka k'ara kyau kamar wani ango bane, allah da kullum bazaka yarda ka dunga d'aure fuska ba," "Ango dai!" Ya tambaya da mamaki, Ita kuma ta amsa da cewa "Allah kuwa koda yike kuma gara dai ka dunga d'aure fuskan naka saboda yan matan dake nacin binka kamar wani namar kasuwa" Ta k'ara furucin ta da d'aure fuska sab'anin farkon zancen data d'auko shi da murmushi a fuskar nata, Murmushi yaci gaba dayi, yana jin wani irin farin ciki da dad'i mara musaltuwa, domin dama ai shi abunda yake muradine wato ta yaba kwalliyar kuma gashi ta yaba d'in duk da dai cewa ita bata san manufar shi nayin kwalliyar ba, in ko haka ne ai shi abubuwa zasu zo mishi da sauk'i koba komai ai gashi yanzun ma ta bashi wani k'arin haske, akan yanda zai samu damar kwamushe zuciyar ta a saukake, Dan haka a can kasan zuciyar shi ya tsinci kanshi da furta cewa, "Anything for you my ❤️ love " Dan haka fuska cike da murmushi kana kuma yana girgiza kanshi ya nunata da yatsar shi manuniya duk a lokaci d'aya. "Ke wallahi yarinyar nan fitinan niyace, oh kice k'aremin kallo kawai kikayi a d'azun din bawai tsoron fatalwa ba, to tunda har kika samu damar kallona a arha sai kin biya farashin kallon, Toma wai waye yace miki nid'in bana dariya neh? Inda bana dariya zakiga mutane na bina ne? Ko kin manta in kiyata ne *MAI JAMA'A*? " K'ara matsar da jikin shi zuwa kofar motar yayi ya wani jingina kafadar shi da kofar motar ta inda take zaune yayi tsayuwar a karkace gamida d'an rage tsayin shi ta yanda tsayin nashi zai dai da ita da ita dake zaune, hannun shi duka biyun kuma goye suke a kirjin shi, ya kuma karkato gaba daya ya rufe ta kafin yace.. "Fad'amin yarinya kenan dai na miki kyau, koda yike ai kin riga kin fad'ama miye nawa na tambaya kuma" Dariya ta fashe dashi irin dariyar ban haushin nan tana nuna shi tace. "To sai me dan nace kayi kyau ko bakayi kyau ba,halan baka yarda da kanka bane? ai dai kasan ni ba abokiyar adawar ka bace ba kuma zanyi maka hassada ba koba komai ai nima mai kyan ce ba kuma fina kyau d'in kayi ba,balle inyi kishi dan kawai nace manyan kaya da murmushi na maka kyau bawai yana nufin na yaba bane, kawai dai ka d'auki hakan a matsayin shawara ina ganin idan ka rike hakan a gaba zaiyi tasiri ga matar da zaka nema kasan wasu matan sun iya jefa kansu a had'ari wajen auren abu mai kyau" Katseta yayi da cewa "Kefa? Ke baki son abu mai kyau d'in ne?" "Tab aini matsala na da namiji mai kyau bai tab'a zama mijin mace d'aya, domin ko bai nemi mace ba su matan zasu neme shi kaga kuma ni mijina nike da burin aure bawai mijin wata ba dan haka babu maza masu kyau a lissafina sai wanda na tabbatar da cewa shi d'in zai kasance nawa ne bana kowa ba🤷🏻‍♀️ ina nufin bazan tab'a rabashi da wata macen ba zai dauwama ne a matsayin mijina ni kadai" "Hummm" ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, "Kenan in irina ya nuna yana sonki ba zaki amince ba?" "Zan amince idan na tabbatar da gasken gaske yake son nawa kuma bashi bayi min kishiya" ta k'arasa fad'a tana karkata kai, Dariya ma ta bashi wallahi dan haka yako kama dariyar abunshi dan ya tabbatar har yanzun da yarinta sosai akan yarinyar nan, a cikin dariyar nashi ne yake cewa. "Ashema karamar kwalwa gareki yarinya tunda har zaki yarda idan namiji ya miki dadin bakin cewa dake kadai zai dauwama har karshen rayuwar shi, to ma idan ya miki alkawarin kuma zuwa gaba allah ya kaddara cewa dole saiya k'ara auren ya kenan zakiyi?" "Sai ince ya sakeni" ta fad'a tana bata fuska da turo baki. "Ai kaji matsalar yarintar ba, to idan kin fito kina da tabbacin samun wani mijin single wanda bai da mata kuma shima kina da tabbacin zai iya zama bai miki kishiya ba? Ko koh haka zakiyi ta aure kina fitowa da zarar miji yace zai k'ara aure? Koda yike muma bar hirar nan dan bazaki gane me nike nufi ba, yanzun fad'amin ya zaman gidan ina fatan kina jin dadin shi tunda kika zab'i dawowa cikin shi ki zauna? " "To wai kai dan Allah laifina kake gani?" Ta tambaya muryar ta cike da rauni, "Ah ah ni bance ba, nasan dai zama da Hajiya ne kamar yanda zuwa yanzun nasan kin fara tantancewa" Dariya tayi sannan ta daura da cewa "Hajiya hooo wannan matar Allah dai ya yafe mata yanda duk tabi tasa min ido bani da katabus harta abincin da zanci so take tace sai wanda ta zab'amin zanci kamar a cikinta zansa abincin, nama gode Allah daba uni nikeyi a gidan ba, kasan Allah da naga ta fara sababin ta nike sulalewa inyi makaranta koda ko bani da lecture" Dariya suka sa dukan su ita dashi din, "Hajiyar ce yar sa ido koh? Aiko sai na fad'a mata," "Amma aini dai kaine ka tambayeni ni kuma na baka amsa" Ta fada tana tab'e baki a shagwabe, "Wai akwai bak'in da akayi a cikin gidan nan ne?" Ya tambaya "Babu kowa fa daga ni sai Hajiya dan Hajiya Jummai ma ta tafi Abuja jiya, me kagani ne kake tambaya hala?" "Ok nayi zaton ko anyi bak'ine danaga wannan motar ai" "Wannan motar wai? Mota tace fa bayan tafiyar ka aka kawo min!" "Motar ki😳?" Ya tambaya da mamaki a cikin muryar shi zuwa kan fuskar shi duba da yanda yayi tambayar yana k'ara ma idanuwan shi girma. "Eh tawa kuwa ko ance maka dama kaine kad'ai aka yarjema hawa manyan motoci ka dunga yawo a gari," Ta fadi hakan kasa kasa sosai ta yanda a zatonta bazaiji maita furta ba sai dai kuma cikin rashin sa'a tsaf yaji me tace d'in. "Waya siya miki mota?" "Lallai ma kenan da kai kallon talaka kake min bani da kudin siyan mota kome?" "Ki dai bani amsa tukun, eh kuma nasan baki da kudin siyan motar tunda kika kasa iya siyan turare da kudin ki uwar mak'o dake ne zaki cire kud'i masu nauyin da zasu siya motar nan?" "Nagode tunda gorin turaren da kake siyamin ina fesawa yau kake min, kuma tunda abun ya zama haka ka fad'amin kud'in turaren naka dana fesa ni kuma zanyi lissafin adadin kwalaben daka siyamin in biyaka kudin ka, dan in tabbatar maka da cewa nima mai arziki ce," Ta fad'a fuska a daure, kana kuma sai ta gyara zaman ta ta maida duka kafafuwan ta duka biyun cikin motar ta mik'a hannu ta kwaso sakon data ciro a booth d'in motar da pad d'in data ajiye duka a kujerar mai zaman banza, Key d'in motar ta cire bayan ta kashe motar, tana kokarin fita sai dai kuma shid'in da a yanzun ya mik'e daga kishingid'ar da yayi a jikin motar a d'azun yanzun saiya zamana gaba d'aya ya babbake bakin kofar, "Kabani hanya zan shige ciki dare yayi" "To ya muna hira zaki shige ciki kuma ko kinyi fushine dan na tambayi wanda ya siya miki mota?" "Eh nayi fushin ai wannan ma tambayar rainin wayau ne, wato ni gidan mu babu mai arzikin da zai iya siyamin mota ya bani kenan kake nufi, naga dai kafin wannan motar na hau wasu wancan ma in baka manta ba motatace" Ta fad'a tana nuna d'ayar motar ta. "Kuma kafin ita nahau wata, in kuma son sanin wanda ya siya min kake to mai sona ne ya siyamin dan wanda keson Kane kadai yake maka kyautar da har abada bazai maka gori ba" "Ke wai ya kike wasu maganganu kamar wacce dama take jirana ne, nifa kawai tambaya nayi, laifine dan nayi tambaya akan motar da ban san da zaman ta a inda nike da iko ba? Shine zaki kalli idona kice min wani wai mai sonki ne ya siya miki motar to kenan ni kallon mak'iyi kike min, kawai daga tambaya duk kin wani bi kin b'ata rai, To kiyi hakuri ni banyi tambayar dan ranki ya baci ba" Bata hanya yayi ta fito, Tana shirin tura kofar motar da niyyar rufewa ne kuma kayan dake hannun ta suka watse a kasa ciki harda ledan pad din da take ta b'oyo dan kar ya gani, Duk'awar shi da niyyar ya kwaso mata kayan yayi dai dai da sanda itama ta duka dan haka a bazata goshin su ya had'u dana juna ji kake kummm, "Waiyo Allah goshi na," Ta fad'a dan haka shima babu shiri ya d'ago, Kamo kanta yayi da hannun shi guda, d'ayan hannun kuma ya fara amfani dashi da niyyar ya murza mata goshin nata data bugu, Kici kicin kwacewa takeyi tana bori take cewa. "Nidai ka sakar min kaina ai kaine kaja mukayi karo, waiyo Allah nidai ka kyaleni wallahi akwai zafi idan na shiga zan goga mishi Robb," "Oh so kike in bar miki kan yayi tsini uwa goshin jirgi? Salon in gari ya waye hajiya ta nemi ba'asi" "Eh nidai bana so ka bari zanyi da kaina" Bai yarda ya saketa ba duk da yanda take harbin shi da kafarta tana dukan shi da hannayen ta sai da ya murza mata goshin ita ko harda kwalla sai da tayi, kafin ya saketa, Dafe goshin tayi da hannu guda d'ayan hannun kuma tana murza idon ta dashi a dole nan wai ita kuka takeyi, Shi kuma ganin hakan sai ya duk'a kasa ya tattaro mata kayan. "Ke wai ma ina kikaje ne da kika fito? " "Shago" ta bashi amsa da shagwababbiyar muryarta, Ledan dake hannun shi ya bud'e wanda pad d'in ke ciki kafin yace "bari muga mai aka siyo nasan bazai wuce kayan kwadayi ba," budewar ko yayi ba tareda ya jira amsar taba, "Wallahi Allah nidai karka bud'emin abuna, aiba kai ka aikeni ba ina ruwan ka da abunda na siyo, ka bani abunna karka budemin bana so" Sai dai duk har gaginta a banza danya riga ya bud'e, dan son ya k'ara kular da itama sai kawai ya wani cire pad d'in daga cikin ledan, ya d'aga pad d'in sama zuwa wajen fuskar shi yana k'are mishi kallo da kyau, "Miye wannan d'in wai naji shi da taushi ko buredi ne, bakya son inci ne kike wani b'oyewa ba akwai buredi a cikin gidanba shine kikaje kika siyo wani" "Koba buredi ba nidai kaban kayana bacci nike ji inba haka ba saina had'a ka da Hajiya" "Allah ya baki hakuri ga kayan ki, karki manta kuma idan kin shiga ki kulle kofar," Mika mata yayi, harya juya da niyyar tafiya kuma sai ya juyo. "Ke..." Bata amsa ba duk da kuwa tasan da ita yakeyi. "Kina jina fa" "Ni ai suna na Ameenatu in ya maka nauyin fad'a ka kirani da Meenal ko Meenat" "Ai na fad'a miki sunan Mamana ne kike da dan haka bazan iya kiraba, kuma dole duk sunan dana kiraka dashi ki amsa, Duk bama wannan ba, karki yarda in k'ara ganin ki da yan iskan kayan dana sameki dasu a jikin ki d'azun, bazan hanaki zama tsirara in kina cikin d'akinki ba amma koda wasa karkice zakici gaba da fitowa da wannan shigar zuwa falon Hajiya dan bake kad'ai bane a gidan, ke ko kunya ma bakyaji bayan kinsan bak'i na iya zuwama Hajiya ko wani lokaci" "To aikai ka shigo mana babu sallama tunda kafin in zauna sai da na kulle kofar falon" "Na dai fad'a miki kar in kara gani," Yana gama fad'in hakan yayi gaba ita kuma ta take mishi baya babu wanda ya k'ara cewa komai a cikin su har suka kai kofar falon yana tsaye harta shige ciki ta kulle kofar falon da key kafin shima ya juya zuwa nashi sashen. *** *WASHE GARI* Kamar yanda Sadeeq ya fad'ama Yusuf cewa zai shigo garin na Zaria hakan ce kuwa ta faru, domin kuwa da duku²n asuba tun gari bai gama waye ba ya baro garin abuja dan tun jiyan dama Musty ya kyankyasa mishi cewar abokin su fa ya fad'a soyyaya dan haka a zak'e ya kwana yana fatan yaga asuba dan ya kama hanya, Su ukun suke Zaune a Fadar na mai jama'an wanda yake nan kofar gidan wato, Yusuf Musty Da kuma Sadeeq din, "Wase ka dubi girman Allah ka bamu labarin nan! Kasan cewar daren jiya bacci barawo ne kawai ya saceni amma k'arfe 4 tana bugawa na bud'e ido na fara shirin tahowa, sai yanzun kuma na iso ka wani tsaya kana ja mana rai, Gaskiya wallahi alhakin mu kawai kake d'auka" "Ba wani d'aukar alhaki ai na riga na rantse cewa bazan fad'a muku ba sai kun bani tukuici" "Munji fad'a tukuicin me kake so Allah kuwa zamu baka" Cewar Musty da yakejin cewa da da hali cikin zuciyar Yusuf din kawai zai shige dan yajiyo ko me nene cikin sauk'i dan Yusuf din tun safe yake mishi iya shege ko satar amsa ma yaki bashi balle ya gane ko wacece abokin nasu yake so, Paper Yusuf ya dauka da biro ya rubuta musu account number din shi yayi rubutun manya ta yanda dukan su zasu iya hange daga inda suke, Sannan ya ajiye musu a tsakiyar su, "Gashi nan in fara ganin saukar alert masu nauyi a account dina tukun ni kuma in fad'e muku biri har wutsiya" Yana fad'a yana yarfe hannuwa alamun ko a jikin shi dan haka sai ma ya d'auki remote din tv ya fara canza channels, Tsaki mai kauri dukan su biyun sukaja kamar masu shirin rufe shi da duka, "Eh kuyi tsakin ku gama na dai fad'a muku sharadina," Kusan a jere karar shigowar sakon nin ya sauka a wayar shi dake ajiye akan center table, Dan haka babu b'ata lokaci ya mika hannu ya d'auko wayar alert din ne kuwa, "Oh dama kun gama shawara akan nawa zaku siya labarin nawa ne da naga kun turo min amount d'aya a tare?" "Kai Yusuf idan kud'in basu maka dawo min da kayana d'an fashin tsakar rana kawai inma banda rashin tsoron Allah muda keda hidimar biki a gaban mu mune wai zaka tasa kana mana sata" Cewar Musty. "Oh sata nema? To dan uban mutum nine nace mutum yaje ya tattago aure? In kasan baka tara kudin hidima ba ai sai kace su d'aga auren kawai, Kunga ni bacci ma nike ji bari in koma ciki idan kun shirya jin labarin sai ku tasoni" "In ka isa shege nike, mune zaka maida wasu yan iska bayan ka danni kud'i a account dinka ne zakace kuma bacci kakeji" Sadeeq ya fad'a a yayin da ya mike yana huci yaje ya rufo kofar falon harda murza key, "Allah ya baka hakuri, atoh bawai dan kunga kun fini girman jiki bane zaka wani rufo kofa waton kuci min uwa babu mai kwata na, to zoka zauna in baku labarin komai dan musan ta yanda zamu bullowa abun dan gaskiya nidai bana son muyi sanya gudun samun ko wacce irin tangard'a daka iya tasowa" Ya k'arasa fad'a yana gyara zaman shi bayan yaci serious sosai, Kowama Sadeeq din yayi ya zauna suka sa Yusuf din a tsakiyar su, "Nasan dukan ku kun lura da canjin da AK yayi wanda a lukuta da dama munsha tambayar shi amma sai yace mana wai stress ne?" "Kwarai anyi haka" Suka amsa mishi dashi, "Tun a shekarun baya nina lura da cewa AK yana da damuwa, na kumayi iya bincike na ban gane miye silar damuwar nashi ba sai daga baya na lura da cewa yawancin lokuta yakan shiga damuwan ne idan yazo garin nan, Wanda idan kun lura a lokacin zakuga cewa sam koda wani abun ya taso anan bazai zoba sai dai cikin ni daku wani ya wakilce shi, Daga baya kuma sai abun yayi kamar yayi sauk'i duk da ni na tabbatar da cewa yana kokarin boyewa ne kawai a duk lokacin da muke tare saboda gudun amsa tambayoyin da yasan zamu mishi, Sai dai duk yanda ya boye ni na san damuwar nashi tabbas tana da alaqa da soyayya sai dai nima ban matsa mishi ba amma ina dai ta binshi da addu'a," "Wai kana nufin tsawon lokacin nan dama son wata ya mace ne yake faman wahal dashi? " Musty ya tambaya. "Kwarai kuwa ina da tabbacin hakan domin da farko daya fara sonta shima kanshi bai gane son ta yake ba, A lokuta da dama idan naga yanda yake mata nakan tsaya inyi ta kallon shi dan na gane cewa yar tsamar dake gudana a tsakanin su sosai yake sashi nishad'i, Amma ban ce mishi komai ba dan nasan da zarar nayi magana musamin zaiyi ko kuma yama fita a sabgar ita yarinyar, Dan haka a boye wani lokacin nakan aika a kirata dan tazo inda yake dan nasan baza'a kwashe lafiya ba dan ita ma bata da hakuri kuma ita ce kadai macen da naga tana da zarar tsayawa a gaban shi ta mishi maganar da taga dama amma kuma sai ya kasa d'aukar ko wani mataki a kanta sab'anin hakan ma sai dai kawai yayi ta binta da kallo idan kuma ta tafi sai yayi ta murmushin da ba halin shi bane," "Ikon Allah" Sadeeq ya fad'a yana rike baki, "Kana mamaki koh?" Cewar Yusuf. "Ci gaba please Yusuf so nike in san ina aka kwana" Musty ya Fad'i hakan yana dungure ma Sadeeq hannun daya dafe hab'ar shi dashi, "A dai dai lokacin da shi yake rainon soyayyar ta, a lokacin da canji ya shigo rayuwar shi kawai sai rana d'aya muka tsinci mummunar labarin cewa Baban yarinyar ya fidda mata mijin aure, wanda a lokacin shi kuma a boye AK yake ta yak'i da samarin yarinyar dan ya rabata dasu, Kun san me?" "Ah ah sai ka fad'a" "Wallahi lokacin har k'aramin ciwo sai da yayi ninayi jinyar shi a asibiti na kwana biyu ko Hajiya bata sani ba balle ku, duk da kuwa cewa ko a wancan lokacin yaki yarda ya fad'amin dalilin ciwon nima kuma ban iyace mishi komai ba, dan ban san ta inda zan fara rarrashin shiba, bayan yaji sauk'i ne kuma ya tattara yabar kasar gaba da goyon bayana dan nasan idan baya kasar yawan tunata da yakeyi zai ragu sab'anin idan yana nan da zaici gaba da ganin ta ciwon sonta yana taso mishi alhalin ita d'in kuma matar wani ne" "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un" Suka tsinci bakunan su da maimaitawa, Musty ne yayi k'arfin halin bude baki ya jefama Yusuf tambayar dake cikin zuciyar shi cewa, "Kenan matar aure yako so?" "Ah ah ba matar aure bane domin kuwa a yanzun dai auren nata ya mutu sun rabu da mijin nata" "Alhamdulillah kenan dai akwai hope dake nufin cewa Abokin mu zai iya samunta a matsayin mata?" Sadeeq ya tambaya yana kallon Yusuf. "Eh kusan hakan ne if we act quickly, idan kuma muka tsaya sanya tofa tabbas zamuji a salan sane dan ita yarinyar baban ta shike zab'ar ma yaran shi mata miji a yanda wanda nasa shi yamin bincike ya tabbatar min da hakan, Sannan kuma shima din adai yanda ni daku muka sani ba lallai bane ya iya tunkaranta kai tsaye ya furta mata cewa yana son ta ba, Wannan nema dalilin da yasa nace kuzo mu tattauna dan musan ta yanda zamu bullo ma al'amarin, jiya naso inyi maganar da Hajiya sai kuma dai nace bari in farayin magana daku biyun tukun, ya kuke ganin zamuyi?" "Wai kenan kana nufin har yanzun bai gayama yarinyar cewa yana sonta ba?" Sadeeq ya k'ara tambaya da mamaki, "Eh bai fad'aba" Shiko musty cewa yayi "Ikon Allah lallai AK son gaskiya yake ma yarinyar nan inba haka ba mace taje tayi aure a wani wajen harta fito amma ka kasa cireta a cikin zuciyar ka yanzun data riga ta zama bazawara, wai ma wacece yarinyar nan ne?" Dariya Yusuf yayi yana kallon musty yace "mamaki kakeyi kenan, to ai soyyaya tafi gaban nan kuma ita yarinyar inda zaka ganta yanzun a gaban ka na tabbatar da cewa kana iya d'aura alwallah ka dafa qur'ani akan cewa budurwa ce, dan yarinya ce k'arama har yanzun dan tana da yarinta sosai akayi mata auren ba kuma son juna suke ita da mijin ba dan haka nema shi sakaran ya sakota ba tareda ko sanin ta a matsayin mace yayi ba, wannan labarin kuma duka a safiyar yau na same shi a wajen wanda nasa ya bincikamin, duk da kuwa ita yarinyar yar uwar AK ce ta kusa" "Kai tsaya dan Allah Yusuf wai badai akan Meenal kake magana ba? " Cewar Musty a yayinda ya mik'e tsaye ya fara kaida kawo a cikin falon. "Ita fa jikar hajiya yarinyar aunty Jidda wacce yanzun haka take zaune tareda Hajiya" Yusuf ya bashi amsa. "Ikon Allah wai meenal ce dama AK keso?" Sadeeq ya fada cike da tarin mamaki, "Babu wai a cikin maganar nan" Yusuf ya bashi amsa. "To amma me yasa mu bamu gane hakan ba tuntuni? " "Saboda baku sa kanku zaku gane ba amma ni tuni na harbo jirgin shi" Dariya sosai suka fashe dashi, Musty ne mai cewa "Shegen gora mutumin dake cewa allah ya kyauta yayi soyayya da karamar yarinya, Wai kum ma san da sunan da yake kiranta? Jaririya fa yake ce mata saboda tana da sunan maman shi shi kuma yafi karfin ya kirata da meenal," Ya k'arasa fada yana dariya sosai, "Aiko sai naci uban shi wallahi yanda ya dunga mana maganar banza muma gashi alhaki ya kamashi zai kare a karamar yarinya bazawara ma" Inji musty "Kai wallahi in kana ce maka bazawara matsala zaku samu, Dan jiya cemin yayi ba zawara ba ko duniya ta haifa shi dai yana sonta a haka balle kuma itama din budurwa ce," "Kai gaskiya naji dadin labarin nan sosai gaskiya koba komai shima ya samu abunda zuciyar shi keso zanso kuma ace wannan karan ya mallaketa a matsayin mata karta k'ara kucce mishi kuma mu shiga uku dan yasin AK yana iya haukacewa idan ya rasa ta" "Kwarai kuwa, amma dai yanzun muyi hakuri zuwa gaba kadan duk da dai bawai zatayi iddah bane amma mud'an jinkirta har abun ya saketa tukun, Hajiya kuma ni zan mata bayani da kaina, shi kuma na mishi bayani akan yayi kokari ya dunga jan yarinyar a jiki bawai irin yanda ya saba d'aurema yan matan shi fuska zai mata ba, kuma muma zamu taya shi wannan yak'in a bayan fage dan Wallahi wannan yarinyar yanda take nasan da zarar maza suka gane bata da aure tofa bashi kadai ba muma mun shiga ukun mu dan ba matar yara bace wallahi" "Wai shi yana ina ma?" Sadeeq ya tambaya, "Ina zaka ganshi yana can falon Hajiya tun safe daya d'auki wanka can yaje ya kasa ya tsare yana kallon rabin ran shi" Fashewa sukayi da dariya, lallai aiki ya samu ga masuyi, To Allah ya sanya alkhairi, sun dade suna tattaunawa.... Yayinda suke nan suna tattaunawa shi kuma gogan yau tunda safe ya k'ara d'aukar wani wankan cikin wasu fararen kayan wani yadi mai d'an karan taushi uwa auduga idanun ka kad'ai sun isa sheda wajen fada maka cewan tsadadden yadine, kasancewar shi mara nauyin shi da kasancewar shi mara kaurine yasa ake iya hango best din daya saka a ciki, kamar koda yaushe kuma sai da ya tabbatar da cewa ya feshe jikin shi da turare kafin ya doshi sashin Hajjaju to dai tunda ya shiga dama yake ta faman ware idon dan son ganin ta inda gwanar nashi zata fito sai dai kuma harya share kusan minti Biyar baiji motsin saukowar taba, Dan haka ya tashi kai tsaye ya nufi kitchen sai dai koda ya lek'a Larai ce kadai a kitchen din, Bayan sun gaisa yake tambayar ta "mutanen gidan basu tashi bacci bane? Ita kuma ta bashi amsa da cewar sun tashi basu dai sauko bane duk da dai ita Meenal bata jima data sauko ta had'a tea ta koma saman ba, Komawa da baya yayi kafin ya haye saman, d'akin Hajiya ya shiga da sallama sai dai ita kuma a gado ya hangota lullub'e da bargo tana bacci, Gudun karya tashe tane kuma hakan yasa ya koma da baya ya fita daga d'akin ya rufe mata kofa, Har yayi gaba da niyar sauka sai kuma zuciyar shi ta kasa bashi had'in kai dan haka sai kawai ya koma da baya ya murd'a kofar d'in nata da sallama d'auke a bakin shi, sai da yayi sallama sau uku kafin a amsa mishi ana hud'u shi kuma jin ta amsa hakan ya bashi damar Sakai cikin dakin ba tareda jiran izinin shiga daga mai d'akin ba, Shigar da sai da yayi dana sani kwando dubu cewar daya sani da baima shigo Sashen ba balle har ya hauro saman........ *Allah kuwa idan banga comment ba babu na dare*🤷🏻‍♀️. Kuma banyi editing ba😜 *UMMIEE ZARIA*✍🏼 #Mai Jama'a #Sheikh Naseer #Meenal #Hajiya #Malam [8/21, 9:44 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *~{{MY FAMILY}}~BOOK 2 ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*✍🏼 ----- *Page 5* Da wani irin sauri mai cike da zafin nama irin na zaratan maza ya juya ya fito daga d'akin nata idanuwan shi a rufe ruf, bayan ya runtse idanuwan shima sai da yayi amfani da hannun shi ya k'ara rufe fuskar shi da tafukan hannun nashi, Sai dai kuma har zuwa lokacin bai daina ganin hoton abunda yaci karo dashi a cikin kwayar idanun shiba, to wai shi me zai kira wannan ganin? Farin gani ko bak'in gani, "Subhanallah Masha Allah lallai Allah yayi halitta a wajen can wai wai wai dank'ari", Gaba daya fa ya rud'e dan bai tab'a zato ko tsammanin cewar gamon da zaiyi kenan a cikin d'akin ba, rawan da jikin shi keyi ne kuma hakan yasa dole ya kasa tsayuwa har saida lalube yasamu ya lalubo jikin bango ya jingina kafin ya sulale zuwa k'asa yana mai had'e jikin shi waje d'aya, Kafin ya wani k'ara cusa fuskar shi cikin tafin hannun yana mai matse cinyoyin shi waje d'aya,kamar wani wanda yake cikin matsanan cin tsoro. Yasan bazai taba iya kai kanshi d'aki a hakan da yake ba hakan nema yasa koda wasa baiyi gigin sauka matakalar da sunan sauka k'asa ba dan yasan wallahi yana iya missing step ya mulmula zuwa k'asan yaji ma kanshi ciwo a banza, ya dad'e zaune a wajen a kallah dai sai da yayi zama na wajen mintuna goma yana k'ok'arin ganin ya samar ma kanshi nutsuwar daya rasa a lokacin, sai dai kuma hoton dake cikin kwalwalwar shifa sam ya kasa gogeshi dan har yanzun hoton yawo miki mishi a cikin kwayar ido kamar dai har yanzun d'in itace dai a gaban nashi a yanda ya ganta, Tafin hannun shi daya rufe fuskar shi dashi yad'an fara warewa kad'an kad'an yana lek'o idon shi ta tsakanin yatsun dan yagani ko ta fito ne ko tana ciki sakamakon motsin da kofar dakin nata yayi, ganin cewar ba itace ta fito ba hakan yasa ya dafa dakyar ya samu ya mik'e a dudduke ya samu ya shige d'akin da yake gefen nata wanda shine yafi kusa dashi, "Wannan yarinyar in banyi wasa ba saita sa zuciyata ta buga na mace tun lokacin mutuwar nawa baiyi ba" Ya samu damar furtawa a bayyane a yayinda ya samu yakai kanshi zuwa ga gadon dake cikin d'akin ya kwanta a wahalce. Ita ko mutuniyar a gefen ta tun bayan data had'o tea dinta a kitchen a gurguje tasha tea d'in dan so take ta fita da wuri dan tama hajiya k'aryar cewa tana da lecture din safe ne alhalin su kuma kasuwa suka shirya zuwa yau d'in ita dasu Meelat dan Wallahi bata zama gida haka kawai Hajiya sai faman wani kimeta takeyi a cikin gida ita ba matar aure ba alhalin koda take da auren shi mijin ba kulle yake mata ba, Yanzun kuma da take ganin ta samu free ta zama sakakkiyar tsuntsuwa shine kawai Hajiya zata wani k'irk'iro mata da wani zaman idan ganin ido wanda kowa yasan babu ta inda iddan ya kamata, haba ina ma dalili ai in hajiya tasan wata tofa bata san wata ba dan Wallahi babu abun da zai mata sha maki da shirin bikin da sukeyi na Meelat, Bayan ta gama shan shayin d'akin Hajiya ta lek'a, ganin ta kwance rashe rashe a gado hakan yasa ta dawo da baya ta fad'a daki da gudu ta shek'o wanka a gurguje, Tofa ta fito ne tana shafa mai ta farajin sallama tsakani da Allah kuma ita bata d'auki ko muryar waye bane, dalilin kin amsawarta da wuri kuma ita tayi zaton cewa ko Hajiyar ne shi yasa da farko ta shareta duk da tana jin sallamar tak'i amsawa har sai a sallamar k'arshe, Bata tab'a zaton cewa wai idan AK ya hauro saman zai iya yunkurin shigowa d'akin ta ba dan bai tab'a kwatanta aikata mata hakan ba, domin ko zaman da tayi a gidan shekarun baya ko saman baya haurowa, hakan nema yasa koda taji motsin bud'e kofar d'akin bata wani damu da son d'ago kai dan ganin ko waye mai shigowan ba dan sau da yawa Hajiyar kan biyota d'akin su sha hirar su, Sai gashi yau saboda rashin sa'a wani k'aton ya fad'o mata cikin d'aki a d'ai dai lokacin da take kok'arin sa riga alhalin yau ko bra bata saba, Saboda dama ita idan tana period to bata babu bra dan nonuwan ta kan cicciko ne su kama mata ciwo na rashin dalili ko rigar da zai matseta bata sawa balle kuma bra, Allah ma ya taimaketa ta riga ta zura dogon wandon skin tight a jikin ta aida yaci amanar ta da yawa wallahi kuma ko yanzun saita Allah kawai amma fa wallahi bata yafe ba, Domin yafa shammace ta da yawa shigowar nashi d'akin yayi dai dai ne da sanda ta d'aga hannun ta sama da niyyar zura rigar ta, motsin shigowar ne kuma yasata juyowa a zaton ta Hajiya ce, wanda motsin juyin nata ne kuma yaba albarkatun k'irjinta daman juyawan da k'arfi suma, hakan kuma duka akan idon bawan Allah ya faru, karon farko a rayuwar shi da yaga halittar mace a waje b'aro b'aro bawai a tv ko kuma hoto ba, Ita kuma ta juyo da zummar ganin Hajiya kawai sai tayi gamo da wani bak'on halittan yau a cikin d'akin nata wanda ya fad'o mata ba tareda gayyata ba ko neman izinin shiga ba, Zaku sha dariya in kuka hango yanda ta buga wani uban tsalle gaba d'aya uwa wacce taga dodon da zai iya cinyeta a take, wanda tsallen nata shi kuma ya k'ara haifar mishi da wani sabon tashin hankali a cikin ruhi da jiki, dan haka babu shiri shima ya juya, Ita kuma jikin ta ya shiga mazari kamar wata wacce ta kwana a waje a lokacin hunturu, Da gudu ta k'arasa wajen kofar ta tura shi da k'arfi ta murza mishi key kafin ta sulale a jikin kofar itama ta zauna, Ajiyar zuciya kawai take faman saukewa, kafin ta fara bori anan wajen daga zaune ta fara watsa k'afafuwa tana buga hannayenta a k'asa, "Wallahi Allah sai ya saka min kawai shi kenan mutum sai ya wani shigomin d'aki babu izini duk ya gama ganina babu kaya" Kukan tab'ara taci gaba da yi tana cigaba da fad'in, "Allah dai ya isana wallahi shi kenan ya gama kalle min Mamaa," Mai da duban ta kan k'irjin nata tayi, kamar kuma wacce aka tsikara sai ta k'ara fashewa da kuka yayinda tasa hannuwan ta ta kare su dashi domin dai tuni dama tayi watsi da rigarta a can gefe, "Nidai wallahi ban yafema ganina da babu riga da akayi ba kuma Allah ma sai ya sakamin" Ta fad'a tana share tsilli tsillin hawayen da suka taru a idon ta, Ta dad'e zaune a wajen kafin ta rarrafa ta d'auko rigar sai da ta kakkab'e shi tana cigaba da mitar cewa bata yafeba kafin ta zura rigar sai kuma ta nemi waje ta zauna domin dai duk saurin da take wallahi bazata tab'a yarda ta sauka k'asa ba a yanzun balle kuma tsautsayi yasa su had'u dan bata san da idon da zata kalle shiba, dan tasan yana ganin ta yanzun Maman ta kawai zai dunga hangowa koda ko daga nesa ne, Wannan hasashen nata kad'ai ba k'aramin kunya da bak'in ciki ya k'ara mata ba, dan haka sai kawai ta koma ta kwanta ta janyo wayarta ta kira Maryam akan subar tafiyar sai zuwa anjima, domin tasan ba zaman gidan sosai yafiye yiba in yana gari, a nata nufin wai in ya fita itama sai ta fice kunga kenan bazasu had'u ba. Shiko jikan innah can ya mak'ale a d'aki sai faman burgima yake a gado, Pillow biyu ya rungume d'aya a tsakanin cinyoyin shi d'ayan kuma ya rungume shi a k'irji, da kyar ya samu bacci b'arawo ya silalo ya yi wuf dashi. *CIKIN MAFARKI* A cikin mota suke tafe shida ita sai dai kuma yanda yake tuk'in motar kamar mai shirin shiga rami ne abunda zai baka mamaki, domin kowa yasan yanda baya d'aga k'afa wajen bama mota wuta a duk sanda ya zama na shine matuk'in motar, Da wannan tukin nashi suka samu suka k'araso cikin gidan na Hajiya har zuwa lokacin kuma tana ankare da yanda hankalin shi ya rabu biyu rabi a kanta rabi kuma akan tuk'in da yakeyi, Can cikin lungu a wajen da ake parking motocin gidan ya k'arasa da motar duk da yanda wajen yake da d'an duhuwa saboda bishiyoyin dake wajen sab'anin ainihin wajen parking d'in da yake da haske sosai, Koda ta yaka motar batayi yunkurin fita daga cikin motar ba, haka shima daya gyara zaman shi yana mai binta da kallo kamar ya lasheta haka yake ji a lokacin kuma ya kasa furta mata koda kalma d'aya ne, Har sai da suka shafe a kalla tsayin mintuna 10 suna bin juna da mayen kallo, kafin ta bud'e baki tana ci gaba da kallon nashi tace, "Me yasa kayi parking anan sab'anin bayan mu inda kowa ke ajiye nashi motar?" "Bana son kowa ya ganin min ke shi yasa na yanke hukuncin tsayawa anan har sai kowa ya shige ciki" Ya bata amsa. "Saboda me to yasa hakan?" Ta k'ara tambaya tana mai cigaba da binshi da ido, wani irin kallo take mishi mai sa mutuwar gab'ob'i, "Saboda ina kishin abunda nike so mana bakiga wad'ancan masu gadin yanda sukayi tsai-tsaye kamar wasu masu gadin fada bane!" Ya fad'i hakan a yayinda yake mata nuni da glass din gaban driver na cikin motar wanda ta ciki yake iya kallon abunda akeyi a cikin gidan. Murmushi tayi tana kauda fuska gefe bayan ta rufe fuskar da tafukan hannayen ta alamun jin kunya, "Kin san me?" Girgiza kanta tayi alamun Ah ah ba tareda ta bashi amsa da baki ba. "A kullum fatana shine in dauwama tare dake har zuwa karshen numfashi na" sai kuma yayi shiru, Dan haka itama sai tayi shiru bata iya cewa bata iya cewa komai ba, Shirun da motar yayi ga kuma sanyin ac da kamshin turaren jikin sune suka had'u suka bada wani irin daddad'an yanayi, Wanda hakan ne kuma ya haifar da mutuwar gabb'an jikin kowannen su, ji yake ina ma zai iya daya jawota cikin jikin shi ya k'ank'ame kozai samu sa'idah akan yanda yake jin jinin jikin shi yana yamutsawa, "Shshshshuuuu" Taja dogon iska ta bakinta sakamakon sanyin data kejin yana huda tsigar jikinta yana ratsa tsokarta yana shiga mata cikin k'ashi, Sai dai kuma fitar iskar bakin ta zama yayi kamar wani d'an sak'o ko kuma ince abunda akayi shi da gayya domin kuwa kai tsaye ya wuce cikin kunnen AK ya ratsa har zuwa cikin zuciyar dake bugawa a cikin k'irjin shi, Jikin shi a mace ya jefa mata tambaya da cewa. "Miye wannan?" Bai jira ta amsa ba yaci gaba da cewa.. "Ko kinajin sanyi ne in kashe ac?" Shiru tayi bata amsa ba, can kuma sai ta zura hannunta a cikin handbag dinta dake ajiye akan tsinyoyin ta, Ta ciro jambaki sai da ta kunna hasken gaban motar ta kuma karkato da glass din dake wajen yanda zata iya ganin fuskarta da kyau ta cikin shi sannan ta goga janbakin a saman kyawawan lab'b'anta, Chocolate ta ciro a cikin Jakar bayan ta maida janbakin, saida ta bud'e shi ta gutsira taci sannan ta mik'a mishi, Shiko komawa yayi kamar wani sakago wajen kallon ta dan suma ne kad'ai ya rage mishi a yanda dai yake kallon bakin data bi ta shafe tass da jambaki ga kuma yanda take wani taunar chocolate din cike da jan rai, Dan Allah inba neman fitina ba miye na wani shafa jambaki da daren nan fisabilillahi, binta yaci gaba dayi da kallo yayinda wasu miyagun miyan kwadayi suka cika mishi baki har sai da kyar yake iya had'esu, Hasasowa kawai yake na yanda zai cinye bakin nan nata idan ya kamata. Chocolate din ta mik'a mishi, "Zakaci chocolate din ne kayi shiru?" Murya a rarrabe cike da ininan daya fara a yanzun yanzun ya amsa mata da cewa. "Ah ah ah niba chocolate nike soba" "Mi kake so to?" "Bakin" Ya tsinci kanshi da furtawa cikin tuntub'en harshe, Shiru tayi ba tareda ta kalleshi ba taci gaba dacin chocolate d'inta kamar bataji shiba, A cikin zuciyar ta kuwa cewa take "haba malam ashe dai baka shigo hannu da kyau ba har yanzun da sauran ka to shi kenan muje zuwa" Kallonta shima yaci gaba dayi can kuma dai ya kasa daurewa dan haka ya kira sunan ta a sanyaye yanzun din ma dai kamar d'azun muryar tashi da ininan da bata sanshi da ita ba ya kira sunan da yake kiranta dashi. "💞 Heart" Hummm ta amsa, "Zan iya sumbatar ki" "kwafal kwafal" Wani munafukin tari ya sark'eta a bazata sakamakon shak'ewar da tayi da chocolate din bakin ta, "Ki barni please in sumbace ki sau d'aya kawai, sau d'aya kacal" Ya fad'a cike da rok'o yana marairaice wa, "Tofa anzo wajen" ta fad'a a cikin zuciyar ta, a bayyane koh cewa tayi. "Heart amma hakan fa sam sam babu kyau🙅🏻‍♀️" Ta furta tana mai duk'ar da kanta cike da kunya, "To shike nan tunda kin hanani" Ya fad'a da karyayyen muryar dake nuna alamun sam baiji dad'iba, Har yayi shiru kamar ya hak'ura sai kuma can ya juyo, "Dan Allah Heart sau d'aya kawai please 🙏" "Ka tabbata sau d'ayan kacal ne?" "Eh na tabbata" ya fada yana mai matso da jikin shi zuwa kujerar da take sosai, Yana binta ita kuma tana k'ara zuwa baya gashi kuma ta wani k'ankame jikinta sosai ta cure a waje d'aya, Duk'owa yayi sosai zuwa jikin ta ba kuma wai ya had'e jikin nasu bane, a rashin sani hannun shi guda 1 daya dafe sitiyari dashi ya danna horn din motar ji kake motar ta bada sautin biiiiieeee da k'arfi. "Waiyo waiyo waiyo wallahi Allah ni babu ruwana shine" Meenal ta furta a firgice, Cike da zafin nama shi kuma ya koma inda ya taso yana wani babbasarwa bayan ya lek'a dan ganin ko wani yayo tanan inda suke a cikin masu gadin gidan sai dai kuma babu wanda yake tahowa, "Na sumbace ki!" Ya fad'a hankali kwance, "A yaushe?" Ta tambaya, "D'azun mana!" "A ina?" Ta kara tambaya. "A kumatun ki da goshin ki" Ya bata amsa. "Kai 😳" Ta furta tana zare ido, Kafin ta janyo jikinta zuwa inda yake. "Ke miye hakan?" Ya tambaya yana makalewa a jikin kofa, "Ki koma mazaunin ki ni wasa nike miki" "Wasa?🤨 ok ni kuma da gaske nikeyi in fad'a maka muahhh" ta sake mishi sumba mai k'ara a fatar bakin shi, karar sumbar kai tsaye ya wuce cikin kunne ya cake shi a kahon zuciya, dan haka luuu yayi baya uwa wanda yake shirin somewa, Ganin hakan yasa ita kuma ta koma kujerar ta tana fashewa da dariyar yanda taga yayi, yunkurowa yayi da niyyar cafkota sai dai kuma kafin ta ankare ita kuma ta balle murfin kofan gefen ta ta fice daga motar tana nuna shi tana kuma ci gaba da dariya a lokaci daya, "Dawo mana kinji tsoro ne?" "Ah tsoro halal ne" "Dan Allah kizo please 🙏" "Kai Heart kai bakajin kunya nane? wai" "Kunya fa naji kina magana akai bayan kinsa na rasa kunyar tawa a yanzun nan, me yayi saura kuma?" "Aure" ta bashi amsa tana rufe fuska, kafin ta juya taci gaba da tafiya duk kiran da yake mata da cewar da yakeyi ta jira shi hakan bai sa ta tsaya ba, "Kai Abdul! Kai Abdul!! Mai Jama'a fa, wai baka jina ne bazaka tashi ba kazo ka kwanta kamar wani mai shafar aljannu sai wani faman kiran sunan Heart kakeyi a'ah ba heart ba zuciya, dallah can tashi, ni anya kuwa Yaron nan ba dagaske bane kuwa da ake cewa ko aljannah ce ta aure ka shi yasa kake k'in kula yan mata ba kuwa?, To inba haka ba miye wani na kwanciya kana mafarki da kiran sunan Heart da rana tsaka? Tashi da Allah ni bana son lalaci kana namiji kana baccin hantsi" Duk surutan da Hajiya keyi tsaf yake jin duk abunda take cewa sai dai kuma gaba d'aya bashi da karfin dazai yunkura ya tashi, dan hatta labban shi ma ji yayi sun mishi nauyi ta yanda ya kasa bud'esu balle ya tanka mata ko sau daya ne dan tasan ya tashi. Kuyi hakuri da guda 1 bamu da wuta ne wallahi kuma na cinye cajin wayar tun safe shi yasa. Babu editing fa🤨 *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/22, 7:00 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *~{{MY FAMILY}}~ BOOK 2* ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* * ~{Ummiee Zaria}~*✍🏼 ___*Page 7* Kuyi hak'uri jiya nayi mistake wajen rubuta number mai makon insa page 6 saina k'ara maimaita number 5, ***Kai Abdul shin wai kodai dannau d'in dake danne mutane in suna baccine ya danneka shi yasa ka kasa tashi ne ban sani ba?" Ganin cewa babu mai bata amsa a d'akin kuma shima da take magana dashi d'in bai nuna alamun cewa yana jinta bane hakan yasa ta koma da baya ta shiga cikin bathroom din dake d'akin, wani k'aramin roba ta ciko da ruwa sannan ta fito, Ta gefen kanshi ta koma tayi tsaye tana k'are mishi kallo, can kuma sai tasa hannun ta ta zare pillow d'in da kanshi ke kai ta zauna a wajen sai ta maida kanshi akan cinyoyin ta, Ruwan data d'ibo ta d'auko daga kan side drawer din data ajiye shi sai da ta karanto addu'o'i ta tofa a ruwan kafin ta dunga d'iban ruwan da hannun ta na dama tana shafa mishi bakin ta kuma yana karanto ayatul kursiyyu tana tofa mishi duka a lokaci d'aya, Shigar ta da kuma fitowar ta cikin bayin duka akan kunnuwan shi hakan ya faru sai dai kuma har zuwa lokacin yak'i bud'e idon shine a nashi zaton in taga bai tashi ba zata fice ne ta bashi waje, kenan idan ta fita shima sai ya lallab'a ya fice a Sashen salin alin ba tareda tasashi a gaba da tambayoyin data fara jera mishi tun yanzun ba, Sai gashi mai makon yaji ta fice daga d'akin ah ah sai ma saukan sassanyan ruwan da yake da tabbacin a cikin bayin ta dibo shi yaji a kan fatar fuskar shi wanda dole hakan yasa ya dunga sauke a jiyar zuciya dan sosai sanyin ruwan ya ratsa shi, a hankali sai ya dunga jin gabobin shi suna mikewa sab'anin d'azun daya rasa karfin jikin shi gaba d'aya, dan haka sai ma kawai ya wani k'ara gyara kwanciyar nashi da kyau akan cinyar na Hajiya,yayinda ita kuma hakan ya bata damar bud'e mab'allan gaban rigar shi taci gaba da shafa mishi ruwan harta cikin jikin shi wato daga kan kafad'un shi kirji zuwa cikin shi, "Abdul" Hajiya ta kira sunan shi dan ta gani ko dannau d'in ya sake shi yanzun . "Na'am Hajiya ta " "Ya kakeji yanzun ?" "Lafiya lau nike ji babu abunda yake damuna ni dama ai" Ture kanshi tayi daga kan cinyarta tana sababin cewa. "Aikin banza babu abunda ke damun ka dama shine kazo kamin Shane Shane a gado uwa wata mai jego sabuwar haihuwa, nifa nayi zaton ko dannau ne ya danne ka shi yasa harna tsaya ina wahalda kaina" Ta fadi hakan a yayinda ta yunkura da niyyar tashi a inda take zaunen, Ganin hakan ne shi kuma yasa ya k'ara murginowa ya maida kan nashi akan cinyar nata, "Ina zakije kuma bayan kin tasheni ina cikin bacci na mai dad'i da mafarkin da nike fatan ina ma ace a gaske ne hakan ya faru kawai kika wani shigo kika katse min komai" "Ai ni nasan dama bazai wuce mafarkin ba dama tundaga waje fa nike jin kana ta faman kwala kiran Heart 💞 Heart" "Da gaske Hajiya kinjini ina kiran sunan ta?" "To in banji kaba zan shigo ne? nifa tsoro ma naji dan a iya sani na dai nasan mu biyu kacal muka kwana a cikin Sashen nan nawa dagani sai takwara shine kawai daga fitowana na fara jin ana kiramin sunan Heart a cikin gida ai dole in leko inga ko lafiya, Wai bama wannan ba wacece kakeyin mafarki da itane? Dan wallahi nifa lamarin ka ya fara bani tsoro, kasan fa ance dama ita aljanah idan ta auri namiji mafarkin ta kawai zai dungayi a hakan sai kaji wai ta hayayyafa a rayuwar dashi yake ganin yana mu'amala da ita a mafarkin, niko in aljanah ta aureka har kuka tara yara a cikin baccin da ba komai zaka gane ba aita cuceni Wallahi. haka kawai ina zaman zamana a haifomin tattab'a kunne da aljannuh" Dariya ma ta bashi dan haka yako fara dariya sosai yana daga kwancen, "Oh mahaukaciya ka d'aukeni ina fad'a maka gaskiyar zance kana dariya?, Wallahi indai kasan kana mafarkin saduwa da mace harta haifo yara to gara tun wuri ka fad'amin gaskiya in tashi tsaye in yak'eta da karfin ikon Allah," "To ke Hajiya wai waye ma yace miki ni aljannah ta aure nine?" "Ai ba wani ne zai fad'amin ba nice kawai nike ta hasashen hakan, Fisabilillahi inba shafar aljannu ba d'an nan shekaru sunja amma ace har yanzun baka da wata tsayayyar budurwar da za'a nuna ace wacce ne budurwar da kake nema, Naga suma masu biyoka gidan duk kamar anyi ruwa an d'auke duk sunsha fama kansu lafiya sun dena zuwa yanzun, Ga Yusufu dai harda yara 3 Mustapha ma angwancewa zaiyi kwanan nan shi Sadeeq kuma duk da dai ba'asa ranar auren ba amma dai gara shi ko babu komai ai munsan yana da tsayayya, To kaifa? Iye nace kaifa? Shiru ko maganar matan ma baka zama ayi dakai ba dole inyi tunanin ko da gaske aljanar ce da kaiba, Ko ce maka akayi inajin dadin yanda kake zaune hakan ne bayan ba kudin auren ka rasa ba, ko kwanan baya da uwar ka ta matsa da maganar kayi min k'aryar cewa baka da lafiya na dai gyale Kane kawai dan bana son kaga kamar ina matsa maka, dan ban sani ba ko jira kakeyi sai na mutu ne kafin kayi auren?" "Ki dena wannan maganar Hajiya insha Allah ko zaki mutu ba yanzun ba sai kin goya yarana kamar yanda nima kika goyani" "To in haka ne ka fito da matar kayi auren mana, ko da gaske kana da aljanar ne?" "Aljannah kuma dai Hajiya, ni babu wata aljana a tare dani ki yarda dani lokacin auren ne kawai baizo ba a shekarun da suka gaba ta da kuma nima da ban shirya ma auren ba" Tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna yana fuskantar ta kafin yaci gaba da cewa, "Zanyi aure kwanan nan Hajiya ta, ko badan kaina ba kodan in dena ganin damuwa akan kyakyawar fuskar nan naki" Ya k'arasa fada da murmushi a yayin da ya mik'a hannun shi ya shafo fuskar nata, Hannun ta guda ta d'aura akan nashi hannun dake fuskarta tana shafawa da murmushin itama tace, "Ah ah Abdul so nike kayi aure dan ra'ayin kanka dan kana son matan bawai dan ni ina son kayi aure ba, domin so nike inganka cikin farin ciki da matar da nasan zaku kula da junan ku ko bayan bana raye, kaga kuwa hakan bazai samu ba sai ya kasance dukan ku kuna son juna, shi yasa kaga tun tuni ban tilasta ka akan kayi auren ba duk da nasan idan na kawo maka matar zaka amsa, sai dai nafi son naka zab'in wato macen da zuciyar ka tayi maka na'am da ita, ni kuma zan baka goyon baya na d'ari bisa dari har sai ka mallaketa ko wacece ita kuwa!" "Ko wacece Hajiya kin tabbata zaki tsayamin har sai na mallaketa?" Ya tambayeta yana mai tsare ta da ido. "To wacece ma zataga jikana son kowa kin wanda ya rasa tubarkhallah tace wai bata so, kana da asali da na saba mai kyau, kana kuma da rufin asirin da zaka iya rike mata hud'u ma idan kaso hakan balle kuma mace daya,kaf a cikin halayen ka babu na banza dan haka ina da tabbacin babu macen da zatace bata son ka" Wai dan Allah dama ashe haka mutum yakeji aduk sanda za'a zauna ana kwarzanta shi? Eh Alhamdulillah yasan shi din Allah bai rage shi da komai ba, haka kuma bai tab'a neman wani abun buk'ata a rayuwa ya rasa ba, mutane da dama kuma sun dad'e suna kwarzanta shi, Amma yabawar yau da yaji daga bakin hajiya ya k'ara sawa yaji cewa lallai zai iya samun cikar burin shi, "Wai Malam bazaka fad'amin ko wacece yarinyar dan in taya ka kamfe ba?" "Hajiya saurin me kikeyi ne?" "Har sai ka tambayeni bayan yanzun na gama shaida maka cewa auren ka nike son gani kafin in mutu" "Nifa har yanzun ma ban fad'a mata cewa ina sonta ba!" "Baka fad'a mata ba to uban me kake jira, so kake sai wani can ya maka shigar sauri ko me?" "Hajiya yarinya cefa wallahi har yanzun ba wani hankali take dashi sosai ba, yanzun idan naje nace mata ina sonta kai tsaye ai rainani kawai zata k'arayi dama can kuma ba wani tsorona takejiba," Galala Hajiya tayi da idanuwa da baki tana binshi da kallo, Can kuma sai ta fara tafa hannuwa da alama abun yakai mata ko ina, "Amma kai dai kam Allah yayi shashasha a wajen nan ko sakarai zan kira Kane ma oho, Oh wai ita wacce kake son ma har yanzun baka riga ka gabatar mata da kanka a matsayin masoyi ba tukun na amma kake nan kwance kana faman mafarke mafarke na banza da hofi, to kwanta a gida kaci gaba da bacci baki bud'e kaga duk sanda ka farka sai kaji ana sanarwar d'aurin auren ta, Kuji min wani zancen banza fa, kasan karamar ce kuma ka fara son ta, in kana tsoron raini ai da tun farko sai kayi kokarin tankwara zuciyar ka ka hana kanka sonta, to wai ma dama duk shekarun nan jira kakeyi idan ka tashi aure ka d'auko min gansamemiyar mace mai irin k'irar ka? Ako dai da nayi turr dakai dan bazaka mori mata ba, kasan ni shekara nawa ne tsakanina da mijina kakan ka? To a kallah shekarun kusan goma sha Biyar ne ko fiye ma da hakan a tsakanin mu, tunda baka son ta raina ka ai sai kayi ta zama kana kallo wani can zaizo wanda shi yarintar nata ma shine zaiga ya burgeshi har yaji kwadayin auren ta" Tana gama fad'in hakan ta mik'e da niyyar barin dakin, "Hajiya ya kuma zaki wuce bamu gama shawara ba?" "Wacce shawarar kuma ta rage ban baka ba? Tunda k'arama ce ai sai kaje kayi ta raino koh!" Ficewa tayi a d'akin tana kana nan surutai, Yayin da shi kuma ya koma da baya ya kwanta kanshi na kallon saman d'akin, "To yanzun fisabilillahi ita Hajiya so take in tari yarinyar tun yanzun, to me zance mata idan na tare ta? , oh ya Allah ka bani kwarin gwuiwar da zan tunkareta dan Wallahi yanzun kam ni kaina nasan ina da bukatar ta a rayuwata dan an kai matakin da nike buk'atar kusanci da macen aure na" Ganin zaman d'akin bazai bashi mafitar da yake nema ba, sai kawai ya mik'e ya fice a cikin d'akin koda ya fito tsaye yayi yana kallon kofar d'akin ta da murmushi akan fuskar shi, Kafin ya gangara ya sauka daga matakalan zuwa k'asa Hajiya ce kadai a falon tana zaune tana cin abinci akan dinning wanda yake da tabbacin cewa yanzun take yin nata karin safen kenan, yanda yaga tana watso mishi harara yasan idan ya zauna tofa ba lallai su kwashe ta a dadin raiba sai kawai yasa kai ya fice daga Sashen nata dama gidan baki d'aya yana fitowa ya kira, Unaiza daya daga cikin yan matan dake aiki a restaurant din dake nan wajen ya fad'a mata abunda yake buk'ata ta kawo mishi yana gama karin kuma wani abokin shi yazo da mota ya d'auke shi suka bar unguwar gaba d'aya. Baccine ya kwashe Meenal a cikin d'aki ba ita ta farka ba har sai wuraren 1 saura na rana, dan haka tana tashi sai kawai ta fad'a bayi sai da tayi tsarki kafin ta d'auro alwallah, nasan wasu zasuyi tunanin cewa mai yasa bata k'ara yin sabon wanka ba? To ita dai jikar Hajjaju a ka'idar ta sau biyu takeyin wanka a rana idan tayi na safe tofa sai kuma na kwanciyar bacci, inba dai irin taje makaranta ta dawo a wahale bane shine inta dawo zatayi wani sabon wanka amma inba haka ba ita bata takura ma kanta da cewa dole dole sai tayi wanka sau uku a rana🤨, Bayan ta fito wasu takardu ta fara harhad'awa ta cusa su a cikin jakarta kafin ta fiddo wata atamfa da akayi ma d'inkin doguwar riga pitted gown kalar navy blue da gyalen da zai shiga da atamfar ta ajiye su a gefe kayan jikin ta ta cire ta maida wannan rigar jikin ta, agogon dakin ta kallah jin ana ta kiraye kirayen Sallah dan haka sai kawai ta shimfid'a dadduma ta zura hijjabi ta tada Sallah, Bayan ta idar hoda yar kad'an kawai ta shafa a fuskarta dan ya rufe maskin man data dan murza ko kwalli bata goga a cikin idon taba sai mascara da tayi amfani dash tad'an taje gashin idon ta suka tsaya da kyau, Girarta tsararre ne dan haka bata buk'atar bata lokacin wajen gyarar ta, jan baki kuma dama ita baya cikin tsarin rayuwar ta iya karta Vaseline to yau ma shi ta murza a bakin nata, Ba wani iya d'aurin d'an kwali tayi ba domin kowa yasan daman yawancin kayan ta dogayen rigunan abaya ne sai English wear, dan haka ko yanzun bata tsaya b'ata ma kanta lokaci ba d'aurin nan na gargajiya wato ture kaga arziki tayi, Bata tsaya duba mirror dan ganin tayi ko da gyara ba kawai ta feffesawa jikin ta turare ta kwashi jaka da gyalenta da takalmin duk a hannu tayi waje tana jin yanda wayar ta ke vibration amma bata damu da cewa sai ta duba ba, Sai dai kuma koda ta fito daga dakin tsaye tayi dan sai yanzun kuma taji tanajin shakkar sauka kasan kar yazo ace wancan mutumin na nan a falon, dan haka sai ta juya bayan ta kad'an ta bude kofar dakin hajiya bakinta dauke da sallama ta lek'a, Babu kowa akan gadon dan gadon da Hajiyar ma ta tashi tuni ta gyare abunta tsaf kamar ba itace kwance akai d'azun ba, Ganin babu hajiyar a dakin ne yasata komawa da baya sad'af sad'af haka ta dunga tafiya gudun kar ajiyo takun ta daga saman bene take lekowa kasa dan taga waye da waye a cikin falon, harta gama kalle kallen ta bata ga kowa ba dan haka sai taji kwarin gwuiwar saukowar cikin sand'a, kenan dai baya cikin Sashen, To amma kuma ai bata da tabbacin cewa baya a harabar gidan dan ta sanshi yawanci a nan yake zama yana amsa wayoyin shi na fama da baya gajiya, Itafa Allah ya sani kawai bata shirya yin ido biyu dashi a yanzun bane shi yasa take ta wannan kame kamen inba haka ba ina ruwan ta dashi ai da tuni tasan inda dare yayi mata, Tana tura baki da kunkuni ta nufi window din falon shima ta yaye labulen wajen tana lek'a wajen duk da cewa ba komai take iya gani ba amma dai bataga alamar shi a wajen, A yau dai kam tayi da na sani akan rashin mallakar number din ko mutum d'aya daga cikin masu gadin gidan, Yanzun dan Allah da tana da number din wani a cikin su ba kira zatayi ba kawai ta tambaya taji ko AK na gidan koya fice, amma gashi yanzun sai wani kame kame takeyi, "Mtwsss" Taja tsaki mai tsayi. "Allah kuwa fitana zanyi ai ba tsoron shi nike ji ba inma kunya ne ai shine zai biye kanshi tunda ya aikata abun kunya ya shigomin daki ba tareda izini ba" Da kwarin gwuiwar data aro ma kanta ta fito, "Ke wai dama tun safe kina cikin gidan nan bakije makarantan ba?" Ta jiyo muryar hajiya daga gefen ta, Waigawa tayi sai taga hajiyar zaune akan dadduma daura da kofar falon ta baje wasu takardu kona minene oho, "Ban tafi ba Hajiya na samu kira da safen cewa an canza lokacin da zamuyi lecture din ne sai da ranar nan shi yasa zan tafi yanzun, na lek'a dakin ki ban ganki ba dama ince miki zan fita dan nasan bazan dawo da wuri ba sai can yamma" "To Allah ya tsare kidai kula da kanki in kin fitan kuma dai nasha fad'a miki banda kula samari atoh," Wucewa tayi bayan ta amsa ma hajiyar da cewa "to insha Allah hajiya sai na dawo" Bata fita a gidan ba sai da ta tsaya ta k'arbi number din Isah daya daga cikin masu gadin gidan tayi saving a wayarta. *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/22, 10:33 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *~{{MY FAMILY}}~BOOK 2* ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *~{Ummiee Zaria}~*✍🏼 ..... *Page 8* Acan makaranta Meenal ta iske su Meelat bayan tayi submitting abunda take buk'ata ne kuma suka rankaya zuwa kasuwar sabon gari can Babban shagon Ya Mashkur dan su duba ankon da zasu fitar, Tafe suke suna k'ara tattauna wa akan batun ankon, Meenal na fad'in atamfar a fidda mai haske wacce zata d'auki kalar fatar kowa in yaso less din kuma sai a fitar da peach color saboda shima yana ma bak'ar fata kyau, ita kuma Amarya dama shigar farare zatayi har a gama biki dan farar kala dama shine zabin Meelat din, Tattaunawa suke tayi dai in Maryam tace kaza za'ayi meenal kuma tace ah ah kaza dai za'ayi a haka har suka isa kofar shagon nashi, can gefe suka faka, "Bebs wai kun lura da motar nan dake bayan mu kuwa?" Maryam ne ke tambayar su, bayan sun faka. "Wace motar?" Meelat ta tambaya itama a yayinda ta juya baya tana leke dan taga motar dan dama itace a baya su kuma suna zaune a gaban motar ne Meenal na tuk'i Maryam kuma na zaune a kujerar mai zaman banza hankali kwance sukeci gaba da hirar su kamar ba'a cikin mota suke ba dan Meenal gyalen tama a gefen sitiyari ta ajiye shi kuma glass din gefen ta ma ta sauke shi kusan rabi, "Wai wannan farar motar dake bayan mu kike magana akai?" Ta tambaya bayan ta dawo da kallon ta kan Maryam din, "Ita fa inata lura da motar tun d'azun take bin mu nayi tunanin ko kila anyi katari ne ko kila waje d'aya zamu nufa da mai motar sai yanzun na k'ara tabbatar da cewa mu dai yake bi" "Dallah can kyale koma waye bashi da aikin yine," cewar meenal a yayinda ta dauko gyalen ta gyara zaman gyalenta a saman kanta ta bud'e kofar gefen ta tana shirin fita, "Ke Meenal karki fita ga mai motar nan fa ya fito kuma wallahi nan suke nufowa su biyu"inji Meelat "To sai me in nan yake zuwa ina ruwan mu dasu? Ina ce dukan ku dai kuna da mazajen aure to uwar me zaku musu? Kunga Malamai dallah ku fita muje ni bani da lokacin b'atawa kunsan abunda ke gabana gobe a makaranta,ina ga in mun gama danan ma can zan koma ko zan samu ganin Na'eem yasan yanda za'ayi in rubuta shegen test din nan mu kaishi office din shi mu ajiye, naji haushi sosai wallahi da kukace Sir Emma yayi shegen test d'inshin nan yau kuma duk wancan mugun ne yajamin rashin zuwa makaranta da wuri yau, ga Emmanuel din nan wallahi ni ko hanya bana son ina had'awa dashi yanzun nasan jira yake gobe zanje in dunga rok'on shi yana yarfani, Allah sai ya saka min wallahi" Ta k'arasa fad'a yanayin fuskarta na canzawa zuwa fuskar damuwa, "To wai ke meya hanaki fitowa da wuri to bayan kuma dama mun shirya fitowa tun safen?" Meelat ta tambaya. "Ba wancan Dan mai karfin bane yajamin!" Ta bata amsa tana tab'e baki, "Ban gane yaja miki ba, miye had'aku?" Meelat ta kara tambaya. Dariya Maryam keyi kafin tace "wa yaga qawata a gaban Mr Emma tana rokon shi" "Ke ai wallahi bama zani ba balle ya samu damar fadamin maganar banza irin yanda ya saba yima wadanda ya raina" "Kingani koh aina fad'a miki da bakiyi mata ba to tsaf zata murje idone tace bazataje ta roke shiba" Cewar Meelat, "Lah wai Maryam dan Allah kin min da gaske? Kai masoyiya allah ya jefa min ke a cikin aljannah" Ta fada fuskarta na washe wa, Knock knock karar glass din window din gefen mai zaman banza, Dukan su suka maida hankali a wajen, "Kungani koh wallahi masu motar can ne ai dama nace muku mu suke bi gashi kuma kun gani🤷🏻‍♀️" "Kisan yanda zaki damk'o mana wuyar koma waye zuwa cikin shagon nan mu tatse mishi yan canjin dake jikin shi, Allah dai yasa ba yaron oga bane aka aika ya biyo bayan mu, aiko da na mishi rashin daraja wallahi" Inji Meenal, "Kee a wani dalilin zakice in kula shi bayan yanzun kika gama tunamin cewa ina da nawa mijin auren a hannu, in haka ne ai kece yan zun for sale" Zuge glass d'in gefen nata Maryam tayi zuwa k'asa, kafin tace komai wanda yayi knocking din ya riga ta da cewa, "Assalamu Alaikum yan mata kuyi hakuri please Allah yasa dai ban katse muku hanzari ba?" Ya furta fuskar shi cike da fara'a, "Eh to kusan hakan dan muma uzuri ne ya kawo mu nan gashi kuma ka tsaida mu Allah yasa dai lafiya?" "Lafiya kalau Alhamdulillah, nace to ko za'a dan min alfarma a cikin lokacin naku ad'an d'iba min kad'an a ciki dan jin mai ke tafe dani? " Maimakon Maryam ta bashi amsa sai ta juya fuskarta gefen da Meenal ke zaune tana faman latsa waya tamak'i d'agowa ta kalli ko waye gaba d'aya, "Bebs kunji me yace" "Meenal mu shiga daga ciki sai mu basu waje su tattauna koh" Meelat tace a yayin da ta bud'e kofar motar ta fice hakan ne kuma yaba itama Meenal din damar ficewa daga motar da jakarta a hannu, Koda suka fita a motar babu wacce ta kalli gefen da yake tsaye shida abokin shi da shima ya k'araso wajen, har suka shige katafaren shagon na Ya Mashkur, har lokacin kuma gyalen na Meenal na nan saman kai ta d'aura shi ta mishi yafi irin na matan aure sab'anin d'azun da take tuk'in ko gyalen ma babu a jikin ta kuma ta sauke glass din gefen ta duk da bawai duka ta sauke ba amma tsaf wanda ke waje zai tantance ko wacece ita, Suna shigewa cikin shagon Meelat ta fara maka mata harara, "Ke wannan iskancin kuma fa kin wani kama gyale kin d'aura akai uwa wata matar mamaci, kefa ba matar aure bace yanzun, ko kina nufin a haka da zabga zabgan gyalen da kike yafawa ne zamu cinye sauran lokacin daya rage min a matsayin budurwa kafin zuwan lokacin bikin, Gaskiya wannan cin amana ne wallahi dan haka daga nan gidan Hajiya zamu wallahi dole kima canza dressing kawata, duk tsoffin kayan ki kyauta zamuyi dasu ko kin manta wai ke din har yanzun budurwa ne? Kina wannan shigar fisabilillahi waye zai gani ya yaba?" Shekek'e meenal ke kallon ta, "Me kike nufi? Oh wato ga yar iska tunda aurena na ya mutu sai in koma yawo da kaya half naked koh?" "Karkimin iskanci yaushe nace kiyi yawo halfnaked, amma dai kin san dole zaki komayin normal dressing ba kamar shigar da kikeyi lokacin da kike da aure ba, kar dai ki manta yan matan cin da kika rasa a baya shi zakiyi yanzun, ki gane mana so nike inga kina shiga irin na manyan yan matan da in maza suka gansu dole gaban su ya fad'i ai ba sai kinyi shiga kin fidda tsaraici bane yake nufin kin kai karshen wanka hajiya ta, shiga mai daga darajar ya mace nike nufi," "Mtwss yar rainin wayau kawai to in kinga dama daga yau karki k'ara fita dani tunda ban iya sa kaya ba" Tana gama fadar hakan tayi gaba tabar Meelat a tsaye a wajen, Bayau ne ranar farko da suka fara zuwa shagon ba domin kusan kaf yaran shagon sun san su, Dan haka tuni ta shige gaba ta fara duba kayan da suke ta gabatar mata wadanda suke ganin zasu bada kala in aka fitar dasu a matsayin anko, Meelat na taya ta, har suka gama zab'en wadanda suke buk'ata kuma Maryam bata fito ba, shigowar Ya Mashkur ne kuma yasa suka k'ara shantakewa dan Meenal bata tuna cewa tana jin yunwa ba sai da ta ganshi, da yayi maganar ya aika a siyo musu abinci kuma sai cewa tayi ah ah bafa abinci ba domin a hanyar da suke zuwa ne ta hangi wani waje da ake ta faman gashin Hajiya kaza kuma ranta ya biya sai dai kuma bata tsaya bane dan ba a hannun ta wajen yake ba dole sai taje gaba tayo u turn in tana son zuwa wajen dalilin da yasa ta yanke shawarar biyawa kenan in zasu koma gida, Kuma wallahi a ribar da Ya Mashkur din zaici dasu na siyayyar da sukayi zata fanshe, "To me kike sonci uwar malam?" "Kaga Yayan mu Allah kaza naga ana gasawa a can k'asa kafin mu iso nan shi nike son mu siya idan zamu koma" "Kawai kice kwad'ayin ne ya motsa zaki sauke shi a kaina" "To dan Allah in bamu tambayeka abunda muke so ka mana ba wa muke dashi anan da zamu nema a wajen shi?" "Naji karki min wata doguwar farsafa in kun tashi tafiya zan baku" Hannun ta tasa cikin juna tana dan jujjuya jikin ta irin yanda yara keyi in suna so a musu abu kafin tace, "Nidai Allah Ya Mashkur ka bani kawai a hannuna kar in mun tashi tafiya ka manta ko kuma ni inji kunyar tuna maka" Ta k'arasa fada tana dariya k'asa kasa, "Oh Aminatu badai zaki tab'a canza waba wallahi, wai ma karkiji kunyar tambaya, wai kece zakiji kunyar amsar kud'i a hannuna ai ina ganin in ban baki kudin nan ba kina iya bina bashi sai na biya kafin in huta da mitan ki," Dan haka sai yasa hannu a aljihu ya ciro wallet din shi, dubu goma ya kirga kafin ya miko mata, "Zasu iya ko a kara?" Sai da ta mik'a hannu ta amsa kafin ta furta cewa. "Ba komai yayan mu ko basu cika ba ai mu sai mu cika Allah dai ya k'ara arziki Allah kuma ya baka ikon k'ara aure wallahi" Ta k'arasa fad'a da dariya, shima dariyar kawai yayi yasa kai ya wuce dan yasan magana kawai take son sashi. Duk abunda sukeyi Meelat nacan ana buga mata lissafin kud'in kayan su, Karasawa wurin ta Meenal tayi "Wai kinga Maryam shiru dan mak'iyin ubanta har yanzun bata sallame suba balle ta shigo," Wayarta ta ciro daga cikin jaka ta dannama Maryam din kira, Tana d'auka ta rufeta da sababin cewa, "Ke wai me kikeyi ne a wajen har yanzun mun riga mun gama zab'a fa kuma wallahi baki isa kizo kice mana wanda muka d'auka basuyi ba tunda kika k'i zuwa ki tayamu zab'en" "Yi hakuri gani nan zuwa" "Na dai fad'a miki ki shak'o mana wuyan su suzo su biya kudin biyo bayan mu da sukayi koh? To wallahi karma ki fara ki shigo wajen nan ke d'aya atoh" Sai gashi kamar jiran kiran nata Maryam keyi domin cikin kankanin lokaci sai gata da mazajen nan biyu a bayan ta d'ayan kusan a jere suke tafiya da ita shi kuma d'ayan yana bin su a baya, Gefe meenal ta koma tana musu kallon kasan ido, Bafa yara bane dan zama mu iya kiran su da suna magidan ta dan sun d'an fara manyan ta sai dai alamu sun nuna cewa dukan su biyun idon su a bud'e yake da ganin su kaga mayun mata, "Aiko zakuci uban ku wallahi wato kun hango kyawawan yan mata wanke hannu ka tab'a shine kuka biyo bayan mu, to ai ba laifi dan motar da naga kun tuk'o ta isa shedar cewa kun tara" Cewar meenal kasa kasa tana murmushin mugunta, Suna k'ara dosowa inda suke a gaban kanta ita da Meelat da style ta sauke gyalen ta daga saman kai zuwa kafad'a ta yanda babu wanda zai gane cewa da gangan tayi hakan, nan danan kuwa ta aro murmushi ta yafa a fuskar nata, "Wai har kun gama siyayyar da wuri haka?" Cewar wanda suka jero tare da Maryam ita kuma Maryam din kayan take dubawa tana yaba kyan su, Dan haka Meenal ce ta amsa mishi da cewa, "Eh wallahi yallabai, mun kammala fa, kayi hakuri na katse muku hira bana son mu gama bata zo ta duba bane shi yasa na kirata ina fatan ban shiga hakkin kaba?" "Ah haba dai ai girman kine wallahi aini godiya ma ya kamata in miki na aron kawarki da kika bani" "Babu komai wallahi yallaibai, Maryam in kin gama dubawan ku biya su kudin su had'a mana kayan mu tafi dan Allah wallahi na gaji zan kuma tsaya in siya abinci a hanya dan bazan iya d'aura wani abunci idan na koma gida ba wallahi" Daga Maryam din har Meelat kallon mamaki suke mata, ita ko ta wani fuske abunta, daga inda take tana ankare da kallon da d'ayan mutumin yake binta dashi tunda ya shigo kuma baice ma kowa komai ba har yanzun. "Ah haba ayi haka kuma maza na tsaye subar mata da biyan kudin siyayyar da bata taka kara ta karya ba, ai sai girma ya fad'i, malam ka gama lissafa kudin kayan nasu?" Ya tambayi yaron shagon dake lissafin kudin kayan, "Eh na gama" Wuf tayi ta matsa kusa dashi tana cewa "haba Yayana ya haka daga zuwa kuma zakace zaka biya mana kud'in kayan bayan kasan cewa tunda mukazo shagon da niyyar siyayya dole zamu riko kudin biyan kayan ai, ya kuma zamu d'aura maka wata dawainiya daga had'uwa. Oh ya Allah jama'a farawa da iyawa yar malam zata fara cin kudin samari tun bata gama iddah ba, Kuyi hakuri naso page din yafi haka tsayi sai dai kuma kallon film ya d'auke min hankali. *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/23, 6:57 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *~{{MY FAMILY}}~BOOK 2* ©® *UZ-2023.* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~*✍🏼 ,,, *Page 9* Mai makon shi wanda suke magana da Meenal d'in ya biya kud'in kamar yanda ya buk'ata, ah ah sai gashi abokin tafiyar shi dake gefe shine ya matsa wajen biyan kud'in ya biya tun su Meenal basu gama nasu muhawaran ba, Babu b'ata lokaci haka mutumin nan ya lale kud'ad'en kayan da suka siya tsaf ya biya kud'in, Ita ko Meelat kallon Meenal kawai takeyi cike da mamaki, Dan batun yau ba zadu iya cewa Meenal itace hatimin nasarar su dan ata dalilin ta sun dad'e suna cin yan kud'ad'e na samari tun kafin auren ta, bayan auren kuma da suka fara karatu duk wanda ya yunk'uro idan suka ce matar aure ne sai ya nemi lab'ewa a tsakanin ita Meelat d'in ko Maryam a haka zasuyi ta musu hidima har sai in sun gaji dasu sanemi hanyar sallama su salin alin, Kai itafa idan ma tace batayi farin cikin mutuwar Meenal yasin k'arya takeyi sai dai kawai dan darajar dake cikin aure yafi k'arfin ace za'a nuna mad'aukakin farin ciki a fili bayan mutuwar shi, Amma ba komai tasan cewa yanzun kam qawarta zata samu damar data rasa a shekarun baya na tsaya ta zab'ar ma kanta abokin rayuwar da take ganin ya dace da tsarin ta, hakan nema yasa take ganin wannan lokacin na musamman ne a awaken su da zasu kasance a tare dukan su babu wacce keda igiyar auren wani akan ta balle hakan ya musu shamaki akan wani abun, To gashi tun daga yau da alama wasar zai fara, idan suka had'a ido sai Meelat d'in ta girgiza kai ita kuma Meenal k'asa kasa take binta da murmushi, Tsaf aka had'e musu kayan da suka siya yaran shagon suka raka su dashi har mota ko Sallama Meenal bata yarda d'aya daga cikin su tama Ya Mashkur ba dan allah ma sheda ne cewa Allah Allah kawai takeyi akan suyi subar wajen kafin ya fito dan tasan mawuyaci ne idan Maryam ta fad'a ma mutanen sunan su na gaskiya dan haka sukeyi dama batun yau ba in suka had'u da samari irin haka to suna da inkiyar da suke kiran sunan junan su sab'anin ainihin sunayen su na gaskiya. Har wani ajiyar zuciya ta sauke yayinda taga sun fito daga shagon salin alin ba tareda an samu matsala ba, shiko wancan mutumin da suka shigo tare da Maryam bakin shi ko gajiya bayayi da surutu, d'ayan dai da alama miskiline dan bai iya tanka musu ba sai bayan sun fito ne sannan ya matso inda suke, "Sannu koh yan mata!" "Yauwa sannu Maryam da Meelat suka amsa mishi dashi domin ita gwanar ko kallo bai isheta ba saima gaba da tayi abunta bayan ta kulle booth din motar ta da aka sa kayan da suka siyo, ta juya da niyar shiga motar kenan shi kuma ya tare ta da cewa, "Yan mata nace ba!" Ya fad'i hakan a yayinda yasha gabanta ya tare hanyar da zata wuce, D'aga kai tayi batareda ta kalli fuskar shiba ta amsa mishi da cewa, "Kace me? Oh na manta ban maka godiyar dawainiyar da kayi damu yanzun ba, mun gode fa Allah ya k'ara arziki ya jikan iyaye" "Ameen nagode da addu'a duk da dai bawai nayi bane dan a gode min d'in ba, Bama wannan ba shinko zan samu gimbiyar tad'an bani aron lokacin ta In ba damuwa ina son mud'an tattauna," Sai da tasa hannu ta gyara zaman gyalenta zuwa saman kai kafin ta bashi amsa da cewa, "Yar uwata bata gaya maka cewa ina da aure bane hala?" "Hakan dai tace min da farko kafin daga baya kuma sai ta fad'amin cewa tadai fad'ane kawai amma baki da aure," Ya k'arasa fad'a yana kureta da kallo, Turo baki tayi ita kuma tana juya mishi baya "Oh da gaske dai baki da auren kenan?"ya k'ara tambaya "Injiwa yace maka? Nidai ai nace maka ina da aure koh" "Yanda kikayin ne ya nuna min cewa da gaske d'in baki da aure, dan haka in babu damuwa ko zaki bani dama mu k'arasa zuwa gidan ku, dan gaskiya ina buk'atar magana dake kinga kuma dani dake duka ba girman mu bane mu tsaya muna hira a titi, shine nike ganin ko zaku mana jagora in yaso mu sai ku biyo ku a baya zuwa gidan ku ? Dan yau nike son komawa Abuja bazan so kuma in wuce bamu tattauna ba gaskiya please 🙏" Kam buhu yau Allah ya had'ani da d'an anace daga taimako shine saboda tsabar maita wato bazai yarda mu rabu anan ba shine yake son lallai sai ya rakamu har gida, jama'a ina ma laifin yace ta bashi number in yaso koma dai miye alakar ta tsaya a iya waya kawai in yaso sai ta bashi koda number din wayarta da ba kullum take amfani dashi ba, "Kinyi shiru?" "Umm umm to aini tsoro nikeji dan mu a gidan mu ba'a barin namiji zuwa wajen mace sai ya nemi izini kaga kuma ni karatu fa nikeyi a yanzun shi yasa ba'a barni na fara tsayuwa da kowa ba tukun"ta k'arasa fad'a tana wik'i wik'i da ido, "To yanzun ya kenan?" "Kayi hakuri sai dai muyi waya zuwa wani lokacin idan ka k'ara shigowa ni kuma zan san yanda zamuga juna koda a gidan d'aya daga cikin yayye nane, zaka iya zuwa ka sameni ai" "Mai zai hana kuwa kin tab'a ganin inda mai nema yayi fushi ne? Kafin nan dai bari in gabatar miki da kaina, Suna na Al'ameen Adam Rano, bakano neni amma kuma mazaunin abuja" "Allah sarki ni kuma suna na Zubaidat Ibrahim amma Ikram ake kirana, kamar yanda ka gani kuma ni d'in yar Zaria ce mazauniyar cikin ta kuma" "To karmu b'ata muku lokaci ga wannan katina ne dan Allah kiyi kokari idan kun isa gida ki kirani," Ya fad'a bayan ya mik'a mata katin nashi ita kuma ta amsa, Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke dan da alama ta tsira. "Mu zamu wuce nagode da lokacin da kika bani" "Ah haba Yallabai ai muke da godiya da dawainiyar da akayi damu" Sai da ya rakata har bakin motar ta ya bud'e mata ta shiga ya kuma maida mata kofar ya rufe sannan sukayi sallama da su Meelat ita kuma taja motar sukayi gaba suka bar su anan wajen suna d'aga masu hannu, Sai da sukayi nisa da sosai kafin dukan su suka fashe da dariya, "Kun san abunda ake cema dakyar nasha yafi ace da kyar aka kamani? To wallahi shine ya faru yau, haka kawai mutumin nan zai wani ce wai zasu bimu a baya suga gida kamar wani body guide dina" ta fad'a ta tareda ta dena dariyar da takeyi ba "Kai Beb wallahi baki da kyau, yanzun yanzun kin wanki mutanen nan kusan dubu d'ari biyu fa, wallahi shi yasa nike son fita dake zuwa waje irin wannan dan zuwan ki alkhairi ne, wai haka dama yace zasu bimu tab lallai ma?" Jakarta dake gefe ta d'auka ta mik'ama Meelat din "duba cikin Jakar zakiga katin daya bani fito dashi kimin gutsi gutsi dashi ki watsa shi ta window" "Ah haba dai kina nufin ko sau d'aya bazaki kirashi ba?" Cewar Maryam itama tana dariya. "Wai hala dai idanuwan ku sun samu matsalar da basa gani da kyau ne? Ku daganin wannan mutumin ai kun san mijin wasu ne wallahi dan tabbas da ganin idon shi bazai yarda ya zauna da mace d'aya a gidan shiba to niko inba bakin iyaye ke bina ba uban me zanyi dashi, mtwss dallah ni karku bani haushi ma" "Eh ai baki da uban da zakiyi dashi amma kina da uwar da zakiyi da kud'in shi" Maryam ta fada tana dariya, "Aini ban tura mishi katin gayyata ba, idanuwan shi ne suka gano mishi ruwan da yayi zaton suna iyayi mishi wanka, bai san cewa wannan ruwan maliya bane in ya sake ya shiga bai zama dole ya fito a raye ba,ina fatan dai baki fada mishi ainihin suna na ba?" Tayi tambayar tana kallon Maryam. "Kina da wani sunan da yafi Zuwairat ne a duk lokacin da tarko ya kama kurciya dama?" Itama ta tambaya tana dariya, Dariya suka kara fashewa dashi, "Kai Zubaida ashe baki manta sunan nawa ba?" Inji Meenal. "Ke wai ma da muka barki tare dasu me wancan yake fad'a miki?" "Ah ah ai shi rakiya kawai yayi abokin ne ya gano abinda ya gano shine yasa suka biyo mu a baya, shi dai yace min sunan shi Auwal kuma wai d'an Malali ne a garin gomna (kd take nufi)" Basu isa gidan hajiya ba sai da suka tsaya Meenal ta siya kajin da ta amshi kudin su a hannun Ya Mashkur, Bayan ta faka motar nata a harabar gidan baya ta koma ta tambayi Isah, "Mai Jama'a yana gida koya fita?" "Ai Hajiya tun fitan da yayi na safe ina tabbatar miki da cewa har yanzun bai dawo ba, su Sadeeq ne kawai a gidan suma d'azun nan suka shigo" Juyawa kawai tayi bayan ta gama sauraron abunda yake cewa domin su Meelat sunyi gaba zuwa Sashen na Hajiya dama, Sai da sukayi shagalin cin kajin nan kafin suyi zaman ware kayayyakin kowacce ta d'auki nata suka cirema Moon da Aisha nasu, dan a gobe suke so su fara rabon ankon, Suna cikin ware kayan ne kuma Allah yama Hajiya shigowa dan ta shiga wajen Dada Turai kakar Billyn Ya Sa'eed, "Wa nake gani yau a gidan kamar Amaryar Mustafa na?" Da dariya Meelat ta tareta tana cewa, "Wallahi Hajiya kamar kin san cewa ke nike jira dama" "To ai gani na dawo ya akayi ne hala" Ta tambaya a sanda take zama a kan kujera, "Hajiya yaushe za'a kwaso kayan Meenal na can gidan ne? In kuma ba'asa ranar kwasowan ba ki bani key dan Allah muje gidan nida Maryam mu d'ibo cikin kayan ta wad'anda bata dinka ba, mukai mata d'inki, ki kalli shigar da takeyi fa har yanzun Hajiya bayan ita din a yanzun da bata da aure kamata yayi ta canza kalar shigar ta," "Eh to kema kince wani abu dama so nayi in hayaniyar Sakin ya lafa sai insa a kwaso kayan, amma yanzun bari in d'auko muku mukullin sai kuje ku d'auko abunda kuke buk'ata din kafin a kwaso kayan" "Yauwa Hajiya aiko mun gode, kinga ko ga kayan ankon ki kema na ware miki dan kema ai k'awar amarya ce" Sun kai har bayan la'asar a gidan suna ci gaba da tattauna wa sai yamma liss Musty ya kwashe su ya mai da gida kafin su tafi kuma sai da Meelat ta amsa key d'in da tayi ma Hajiya magana aikai, har lokacin kuma AK bai dawo ba dan tun Meenal na d'ar dar da tunanin haduwar su har ta sake taci gaba da harkokin ta, A wannan ranar dai basu ba had'u da AK din ba dan da wuri ta haye sama ta kulle d'akin ta bata kara gigin Saukowa ba har dare, kuma ranar dashi dasu Sadeeq dukan su anan Sashen Hajiyar sukayi hirar dare, Tunda baiga wulkin Meenal din ba yasan kunyar ganin shine ya hanata Saukowa dan haka sai kawai ya share shima, *BAYAN KWANA HUDU* A gefen Meenal sosai ta d'auki matakin hana kanta zama a falon Hajiya inko har zata zauna tofa saita tabbatar da cewa ta rufo kofar falon dana kitchen, Anayin knocking kuma da bazata bud'e ba sai ta tambayi waye, inko har taji muryar AK ne tofa bazata bud'e mishi kofar ba juyawa zatayi ta koma d'aki idan kuma anyi katari Larai na kusa ita ke bud'e mishi kofar Yanzun, Ya kuma yi tambaya akan dalilin menene yasa yanzun ba'a barin kofar a bud'e ? Larai kuma ta fad'a mishi Hajiya k'arama ce ke kulle kofar, Tun daga ranar ya gane cewa da biyu take kulle kofar kenan hakan na nufin cewa har yanzun kunyan had'uwa dashi takeyi, Sai dai kuma gaskiya shi tana matuk'ar cutar dashi ta wannan hanyar, ita bata san cewa saboda itane yazo garin nan har ya kwana biyu ba amma haka nan ta tsiri hora shi da rashin ganin ta, Kwana biyun nan kama kanshi fa kawai yakeyi akan rashin ganin ta dan ma yakan lab'e daga falon shi aduk sanda zata fita haka zaiyi ta kallon ta har saita fice, gashi gobe yake son yin tafiya zuwa Jos a kallah kuma zaiyi kusan sati baya nan, A haka a babu yanda zaiyi din haka ya shirya washe gari yabar mata garin, Yana tafiya ita kuma ta koma kan harkokin ta kamar yanda ta saba a baya, Duk wannan abun a idon hajiya yake faruwa dan itama tasha tambayar dalilin da yasa meenal din take kulle mata kofar falo amma bata samu amsa gamsasshiya ba, sai dai kuma bata matsa mata ba ta kyaleta, Yusuf kuma yakai ma Hajiya Ziyara na musamman a wani dare bayan ya tabbatar Meenal na cikin d'akin ta shi kuma Ak baya ma unguwar gaba d'aya a lokacin dan sun gama yanke hukunci shida su Musty aka cewa gara ya sanar da Hajiyan komai kawai tun yanzun kar in abu ya lalace a gaba tace dan me yasa basu sanar da ita tun da wuri ba, To dai koma me suka tattauna zamuji shi zuwa gaba, ta amince ko ah ah nima dai ban sani ba, dan washe gari Yusuf din da AK suka wuce Jos Musty da Sadeeq kuma suka koma bakin aiki suma duk da dai yanzun Musty baya wani zama Sosai a Kaduna saboda hankalin shi dake kan ginin gidan da Meelat zata zauna a ciki da yaketa faman kokarin ganin ya kammala kafin lokacin bikin da kullum k'ara matsowa yakeyi, Wannan kenan, *BARI MU LEK'O SARKI* Yauma kamar kullum tunda ya dawo daga wajen aikin daya kawo shi garin yake zaune a cikin d'akin shi na cikin barrack din da aka sauke su, Zaune akan kujera mai mazaunin mutum d'aya ya mik'e duka k'afunshi sai ya daura su akan center table din daya jawo zuwa gaban shi kad'an, Laptop ne a kan cinyar shi yana cigaba da duba hotunan gidajen da yayi magana da wani abokin shi dake can ZARIA ya turo mishi akan Maganar gidan da sukayi da Meenal cewa tana son ta siya ma Malam gida, Domin bai baro garin ba a ranar sai da ya bada cigiya akan yana son gidan, kamar yanda yaba Salman umarnin kawo mata motar a ranar, Tun zuwan shi bai samu zaman da zai duba hotunan ba duk da cewa abokin nashi yasha kiran shi dan yaji ko ya duba gidajen daya tura mishin domin duka a kasuwa suke, Mamaki yake son bata dan haka sai ya yanke hukuncin turama Sa'eed hotunan Kawai akan ya taya shi zab'en gidan, sai da ya aika mishi hotunan kafin ya kirashi ya bashi umarnin son yake ya zab'a mishi d'aya a cikin gidajen daya tura mishin, Rufe Laptop din yayi ya ajiye shi a gefe dan sai lokacin ne ya tuna da tonunan da Meenal din tace ta tura mishi a cikin wayar, Dan haka sai ya d'auko wayar ya gyara zama bayan ya shiga cikin ma'ajiyar hotuna ya fara bincike, Hotunan daya gani kusan kala 10 ne kuma dukan su na mutum d'aya ne sai guda biyun da sukayi ita da Meenal din ne hakan ya tabbatar mishi da cewa sune wanda meenal din ta tura mishi dan haka sai ya fara bin su d'aya bayan d'aya yana karema hotunan kallo, Ya dad'e yana kallon hotunan bai iya furta komai ba sai kuma zuwa can yace, "Meenal kenan wato saboda taga Teemah tana da d'an jiki kad'an shine yasa take son had'ani da wannan kenan?" Eh kam gaskiya yarinyar cikin hoton tadan d'auki hankalin shi duk da a iya hoto ya ganta amma yana jin cewa zatayi dai dai da tsarin shi dan ya lurada cewa ta mallaki dukkan abunda yake buk'ata a wajen macen da zai zauna da ita a matsayin matar shi na aure, wato wayewa kyan fuska cikakken diri da wasu abubuwan wadanda shi ya barma kanshi sani, A bayyane kuma ya k'ara furta cewa, "Koma batayi ba ai dole in amsa haka da hannu bibbiyu ma kuwa tunda ta fito daga wajen abunda nike matuk'ar girmamawa a yanzun, Inma batayin ba duk ni zan saita ta zuwa tsarin da nike muradin ta kasance min. *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/23, 9:51 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *BOOK 2* *PAGE 10* Shi kam a Yanzun gani yake bashi da kalmar da zaiyi amfani wajen nuna godiyar shi ga Meenal, Domin dai duk da kasancewar ta yarinya k'arama da ya tabbatar da cewa a haife zai iya haifan ta sai gashi ta sanadin ta ne yau ya kasance cikin nutsuwar daya rasa tsayin wasu shekaru a yanzun Allah da ikon sa zai kwanta yayi bacci lafiyar Allah kuma ya tashi ba tareda yayi wani mugun mafarki ba sab'anin lokutan baya da baya samun isshen bacci, rashin baccin nashi kuma bazai sa yace ya tashi ya gabatar da nafila koda raka'a biyu bane, domin a lokacin nema yake jin wata irin muguwar kasala haka zai b'ata dare a banza shi baiyi bacci mai dad'i ba shi kuma bai raya daren ba, sai gashi yanzun Allah da ikon sa a cikin k'asa da wata d'aya komai ya canza ciki kuwa harda ibadan shi dan ya k'ara kusanta kanshi ga mahaliccin shi sosai ga kuma azkar da yakeyi akoda yaushe, yasan kuma yawan farin cikin da yakeji a zuciyar shi duk suna da na saba ne da hakan, Yasan ya aikata kura kurai da dama a baya, domin dai adah can baya tunawa da damuwar kowa sai na matar shi kad'ai baik'i yab'ata da kowa ba indai har ita zatayi farin ciki to bazai tab'a damuwa ba wanda dalilin hakan ya b'ata mu'amalan shi da mutane da yawa bayaga abokan shi da sukayi kokarin ganin sun dawo dashi kan hanya ciki harda wasu daga cikin yan uwan shi wad'anda ya shatawa layi duk akan matar shi sai yanzun ne kuma yake jin bak'in cikin hakan ya kuma d'aura aniyar gyara kuskuren shi da yardar Allah, Adah can baya yakan manta cewa akwai hak'k'in uwa da uba ya'ya da kuma k'anne ciki harda hak'kin ita kanta matar da iyaye suka aura mishi da take zaune cikin gidan shi a matsayin matar shi, ya nisan ta da kowa babu mu'amala mai kyau balle akai batun shak'uwa dan harta yaran daya haifa duk da a Yanzun sunyi girman da zuwa gaba kad'an yasan maganar auren su za'a fara amma suma bai samu damar da zai zauna ya jasu a jikin shiba balle har yasan damuwar su da kuma abunda suke buk'ata na yau da kullum dan a lokacin uwar yaran ita kad'ai ce a gaban shi ta yanda baya iya tuna kowa sai ita, ita kad'ai dai itace a lokacin yake gani kamar duk wani farin cikin shi yana tare ne da ita, Sai gashi Yanzun Alhamdulillah dan ba iya nutsuwar zuciya yake jin cewa yasamu ba harma da nutsuwa ta cikin gangar jiki domin a Yanzun mazan takar shi ta dawo ta yanda akoda yaushe yake jin kanshi a matsayin cikakken namiji kamar wani saurayin da yake cikin lokacin kuruciyar shi sab'anin shekarun baya da inba yana tare da Teemah bane bayama tuna cewa shi din namiji ne, Abun mamaki ashe abundai daya raina itace warakar shi zai fito a sanadin ta, dan hakan yasa yake ganin me nene ma wanda Meenal zata nema a wajen shi har ya kasa cika mata shi? Dan a Yanzun ta wuce neman abu a gunshi shi dai da yake matsayin Babban yayan ta shine zaiyi tsayin daka wajen ganin cewa bata rasa komai na buk'atar rayuwa ba, Duk da ko a Yanzun bawai matsayin daya bata ya canza bane, Ah ah sai dai yana d'aukar al'amarin ta da girma ne sosai ya kumayi imanin cewa ita d'in tun farko dama ba matar tashi bace shi yasa yake mata fatan Allah ya had'ata da wanda zai kaunaceta kamar fitar numfashin shi, Ya d'ade zaune yana cigaba da kallon hotunan Moon tunawa da paper din da Meenal ta rubuta mishi sunan yarinyar ne yasa shi mik'ewa dan tun a ranar yana dawowa ya cire shi a cikin aljihu ya saka shi a cikin wallet din shi gudun kar ya salwanta, Inda wallet din yake ajiye akan side drawer ya nufa yana budewa ko ya zaro shi a inda ya soke shi, Babu b'ata lokaci ya bud'e ya karanto, a bayyane ya furta, "Maimoon, Lagos, ah lallai zuwa Lagos ya kamani," Address dinta da Meenal din ta tura mishi ya k'ara dubawa, kafin ya d'auko wayar shi yayi saving number din dake rubuce a jikin takardar da sunan "Moon" Sai da yayi kamar ya danna ma number d'in kira sai kuma ya fasa, domin kafin komai ya fara shiga tsakanin su zai so ya Santa da kyau ta yanda zai san ta inda zai fara dan ganin ya kamo zuciyar ta cikin kwanciyar hankali, kuma ma gani yake ai yanzun yayi wuri ace ya kirata. Komawa kan kujerar daya taso yayi ya zauna yana k'are mata kallo, "Wannan yarinyar da wuya itama inba irin halin kawarta take da ba, daga ganin bakin nan nata sai tayi yawan surutu, wai zata ma so tsoho kamata kuwa?, Allah ka dafamin in samu shawo kanta cikin sauki" Ya fad'a a bayyane, can kuma kamar wanda aka tsungula sai ya fita daga wajen hotunan ya koma wajen ajiyar lambobi, Number din da yayi saving da suna Joseph ya aikama kira, Number din bata dade da shiga ba aka d'auki wayar da harshen turanci suka gaisa, Da harshen kuma sukaci gaba da magana inda shi Sarki yake tambayar Joseph din cewa yana gari kuwa? Shi kuma Joseph din ya amsa da cewa eh yana nan, "Zan turo maka pic din wata yarinya da address a kanta ina son sanin komai a kanta, idan nace komai ina nufin komai", ya jaddada mishi, "Babu damuwa sir duk abunda kake buk'ata zaka sani akanta cikin kwana biyu" "Ok zan tura maka pic da address din yanzun" Bayan Joseph ya amsa ne kuma Sarki ya yanke wayar sannan ya tura mishi, "Ina ganin lokaci yayi da zan waiwayi Lagos" Ya furta a bayyane domin tun kafin faruwar komai dama ya dad'e baije garin ba, ga shi kuma yanzun Zaria bata zuwuwa gaskiya dan ido da kunya wallahi, Bai san da wani idon zai kalli baban shi da Malam ba idan yaje dan ta uwar gida mai sauki ne domin tuni suka dai daita tsakanin su, ba iya ita kad'aiba ma harda yan uwan shi yanzun shida kanshi yake kok'arin kiran su, Shima kuma baban nashi suna waya dan shine ma ya shaida mishi komai daya wakana bayan ya gama mishi wankan tass a randa shi Sarkin ya kira shi, ya kuma ce mishi ya kira Malam ya bashi hak'uri, Ranar daya kira Malam d'in sai Allah ya rufa mishi asiri wayar bataje ba dan wayar Malam din yana rufe, Ranar daya k'ara kira kuma ya samu malam d'in yayi zaton zaiyi mishi fad'a ne ko ya nuna b'acin ranshi kamar yanda Baban shi yayi, Sai malam ya bashi mamaki dan nasiha Kawai yayi mishi sosai mai shiga jiki ya kuma tunasar dashi akan rik'e ibada daga k'arshe kuma ya kora mishi warning akan ko kusa ko alama koda wasa shi Malam din yaji cewa Sarki ya saki Teemah tofa babu shi bashi, Dan bayan mutuwar auren da maganar ta fita su dangi duka kowa tsinuwar shi akan Teemah ya k'are a zaton su ko itace silar da auren ya mutu shi yasa duk suke ganin laifin ta, yasan kuma tunda uwar gida tasa ya saki Meenal tana iya cewa ita ma Teemah sai ya saketa, dan haka Malam ya fad'a mishi cewa yayi na farko yayi na k'arshe idan ya samu matsala da matar shi inyaga cewa abin yafi k'arfin shi to yakai maganar gaban mahaifin ta tunda Allah yasa har yanzun yana raye, Sannan ko dan darajar ubanta yaci a d'aga mata k'afa ga kuma yara har 4 Allah ya basu a matsayin zuri'a dan haka shi Sarki yayi hakuri daduk abunda ya faru a baya sai kuma a kori gaba, Wannan abu sosai ya k'arama Malam kima a idon Sarki, domin dai a wannan lokacin da muke ciki bako wani uba bane za'a cutar da yarshi ya kauda kai balle kuma har ya rok'ama wacce ta cutar da yar nashi arzikin cigaba da zama da mijin data raba da yarshi alhalin yasa yana da ikon rabata da nata mijin itama, To dai shima Sarki har yanzun fa bawai ya dena son matar nashi bane, domin dai ita d'in ita ce mace ta farko da zuciyar shi ta fara mata wankakkiyar kaunar da babu algus a cikin ta har yanzun kuma baya dena son nata bane, Sai dai muce kaunar ta sauka daga kaso d'ari zuwa kashi 45, Ya yanke hukuncin hukunta ta shi yasa ma har yanzun bai gwada neman ta ko a waya ba, tunda ya binciki mai gadin gidanta ya shaida mishi cewa bata gidan yasan tana gidan su dan haka bai damuba dan shima yana buk'atar suba juna space kowa ya sarara, dan yasan idan ya tunkareta a yanzun ana iya haihuwar uwar da bata da ido, To gashi kuma yanzun uzurin zuwa Lagos ya kamashi dan yau d'ai daga ganin hoton yarinyar nan yaji ya zak'u yakai gareta dan ya ganta a fili dan yasan zatafi kyan kallo a zahiri, kwana biyun da Joseph yace mishi zaiyi dai dai da sanda shima zai koma KD dan haka yana komawa Lagos zai wuce, Bai tashi daga wannan sak'ar zucin ba har sai da kirar Sa'eed ya riske shi inda yake ce mishi ya dawo mishi da zab'in gidan da yake ganin yafi dacewa, Babu b'ata lokaci ko ya k'ara jawo laptop d'in ya kunna, a wannan daren dai bai kwanta ba sai da ya kira wanda batun gidan ke hannun shi ya kuma tura mishi Number din Sa'eed akan ya kirashi a gobe suje dashi yaga gidan sai suyi ciniki duk yanda akayi sai su fad'a mishi, ya kuma turama Sa'eed din number din mutumin shima. Bayan kwana biyu, Ya samu damar kammala aikin daya kaishi Calaba lafiya lau cikida tarin nasarori, dan haka ya tattara zuwa Kaduna, baiyi yunkurin zuwa Zaria ba yadai kira Sa'eed din shida Salman akan suzo su same shi, Dan haka a randa ya iso suma suka isa kadunar sun samu wancan mutumin ma da za'a siya gidan a hannun shi har ya rigasu zuwa ma, koda suka isa su d'in ya aika bank suka ciro kud'in gidan millions of Naira, abunda ya Sa'eed matuk'ar mamaki shine ganin takardun gidan d'auke da sunan Aminatu b'aro b'aro, hakan yasa bayan wucewar wanda aka siya gidan a hannun shi Sa'eed ya kasa shiru sai da yayi magana da cewa. "Sarki kunyi mantuwa fa wajen suna a takardun" "Bamuyi mantuwa ba Sa'eed sunan da ka gani akan takardar na mamallakiyar gidan ne a yanzun" "Meenal?" Sa'eed ya anbata da alamar tambaya. "Kwarai ita d'in dai domin ta cancan ta shi yasa na siya mata, itama kuma kyauta zatayi dashi ko zaka cemin baka san buri kanta bane?" Cike da mamakin dabai saki Sa'eed din ba ya amsa da cewa, "Burin ta uku, Zama likita Hawa babbar motar da zata kasance mallakinta Na ukun kuma shine idan tayi kud'i ta ginama Baba Malam k'aton gida ya koma can shi kad'ai yabar family house" "Madallah ashe baka manta burukan kanwar taka ba, to cikon na ukun ne na cika mata, sai dai ina rokon alfarmar maganar ta tsaya a tsakanin ni da kai sai ita Meenal din shi yasa kaga na aiki Salman ban bashi daman dazai san komai akan maganar ba dan bana son matsala dan ina gudun kar hassada ya shiga tsakanin ta da yan uwana na yarda da kai shi yasa na damk'a komai a hannun ka, idan ka kai mata ita zata gabatar ma Baba Malam dashi a matsayin daga wajen ta ya fito, Ban san yaushe zatayi hakan ba amma ina fatan zaka tayani rufe maganar nan?" "Insha Allah Ya'ya kamar yanda ka yarda dani bazakaga sab'anin abunda kake zato daga wajena ba, mungode ubangiji Allah ya k'ara arziki dan ba Meenal ce kad'ai zatayi godiya ba harda ni nima dan ba ita kad'ai ce take da burin canza ma Malam muhallin zama ba harda mu muna sai dai duk bamuyi yunkurin yin hakan bane saboda munsan bazai amince ba amma idan abun ya fito daga wajen ta tabbas bazai k'i amsa ba dan shima yasan ta rayu da burin gina mishi gidan dama tun tana k'aramar ta, Mungode kwarai ubangiji Allah ya cigaba da bud'e maka kofofi na alkhairi yasa ka gama da iyaye lafiya, Allah ya raya iyali ya kuma kareka daga sharrin Makiya" Ya k'arasa fad'a yana dukewa zuwa kasa, "Kai miye haka tashi mana so kake Salman ya shigo ya fara tambayar ba'asi, dan Allah tashi ko ka manta nima yaron Malam ne tun kafin a haifo ku?" Bayan dawowar Salman daya aika kasuwa yin siyayyar abubuwan da yasan za'a buk'ata a gidan ne kuma ya had'a musu da tsarabar daya taho dashi daga Calaba, sai da ya ware na gidan su dana gidan Malam sannan suma d'in ya jik'asu da nera sukayi Sallama da juna suka kamo hanya dan jirgin yamma zaibi zuwa Lagos dan haka yana buk'atar hutu sosai kafin yamma. *UMMIEE ZARIA*✍🏼[8/27, 5:20 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *BOOK 2* *PAGE 11* Tun safe Sarki ya k'ira d'aya daga cikin yaran shi dake can Lagos d'in ya bashi umarni akan su gyara mishi gidan kafin ya iso, Domin dai dama koda ma ace matar gidan tana gidan idan yayi tafiyan daya dad'e baije Lagos din ba to kafin ya dawo su yake turawa su kintsa mishi gidan dan ita dai Teemah haka Allah yayi ta da rashin iya gyaran waje baya tunanin kuma zata iya canzawa, ita dai barta a tsaftar jikin ta tsaftar muhalli ne dai bata da katabus, dan zata iya wanka sau goma a rana amma ba tareda damu da sharan d'aki ko sau d'aya a rana ba, dan dama tun bayan barin shi Lagos da aka maida shi KD aiki ya zamana ta samu freedom dan haka tuni ta d'auki yar aikin dake mata komai daya shafi aikin gida sai in Sarki yazo garine shine mai aikin ke dena zuwa idan ya koma kuma saita dawo da ita, duk da yanda zuciyar shi ke azalzalan shi akan ya kirata domin ya shaida mata zuwan nashi k'iyawa yayi, dan tun bayan barin ta zaria dama yayi alwashin cewa bazai kirata ba har sai in itace ta kirashi da kanta tunda har ta iya tsallakewa tabar garin bada izinin shiba, yasan fushin rashin gaskiyar data sabayi a duk sanda suka samu sab'ani koda ko ace shine mai gaskiya ba itaba shi takeyi a yanzun d'in ma, jira take ya kirata ya kaskantar dakai yana bata hak'uri kamar yanda ta saba ita kuma sai taji dad'in kafa mishi tarin sharud'an da baya iya tsallakewa a wancan lokacin yanzun kam ko kusa bayajin zai iya zubar da kanshi akan abunda yasan cewa koda ya aikata aiba haramun ya aikata ba, tunda ita yarinyar da take tunanin ya kwanta da ita d'in ai matar shice ta aure wanda ya biya sadaki kamar yanda ya biya nata sadakin itama, Ana cewa mata na kishi amma gaskiya wani kishin yana zarce ka'ida dan kishin teemah akan shi in batayi wasa ba sai ta d'aura ma kanta lalurar da babu mai mata maganin shi, Duk da yasan cewa a ayyukan da take aikatawa shima yana da nashi kason laifin domin shine tun farko ya sake mata, ta yanda ta samu damar aikata duk abunda take so batare daya takura taba, Ya sani cewa yana son matar shi sosai domin shi din irin mutanen nan ne da basa iya cusa ma kansu son abunda baiyi dai dai da ra'ayin suba, Teemar shi itace mace ta farko daya fara so, Yaso ta da dukkan zuciyar shi sai dai baiyi zaton cewa zatayi amfani da soyayyan da yake mata wajen juya akalar rayuwar shiba,bai sani ba ko soyayyar da yake nuna mata ne yayi yawan da take ganin kamar bazai tab'a iya rayuwa da ko wacce mace ba sai ita, ta manta cewar shi d'in namiji ne musulmi kuma wanda Allah ya halatta ma yin mace sama da biyu ma tunda yana da halin da zai auro su, duk da cewa yana da tabbacin cewa ita ma d'in tana matuk'ar kaunar shi, koba komai ai duk inda kaga kishi tofa yana tafe ne a cike da soyayya, matsalarta d'aya da bata iya sarrafa kishinta a duk sanda ya motsa mata sai kuma daraja da matsayin da miji yake dashi a wajen matar shi wanda ita bata duba wannan darajar in ta tashi magana dashi kai tsaye takeyi babu wani girmamawa ko ladabi, bata san inta aikata ba dai daiba ta duk'ar da kai ta nemi afuwa, ah ah a kullum ita gani take cewa ita dai itace akan dai dai. Zaije Lagos da kuduri ne guda biyu, na farko dan ya samu dai daito tsakanin shi da matar shi, dan a yanzun bayajin zai iya d'aukar wani sabon kalubalen da zata iya kawo mishi, dan haka zaiyi bakin kokarin shi wajen saita ta ta dawo kamar ko wacce macen kwaran da miji zaiyi alfahari da ita, Miye matsalar ta? Kud'i sune abunda tafi bawa mahimmanci fiye da auren ta, shima kuma Allah ya wadata shi yana da kud'in dan haka zai sakar mata su inhar zata dawo mishi kalar matar da yake fata, maganar aikin ta a can kuma duk yanda take son shi dole zata hak'ura ne ta dawo KD taci gaba da aikin zai nemar mata transfer in kuma tace a'ah tofa zai bata zab'ine yasan a yanda take son shi bazata yarda ta zab'i aikin ta akan shi ba, idan sun dawo nan Kaduna kuma zasuje suba uwar gida hak'uri ta dawo musu da yaran su a hannun su dan yana buk'atar had'e kan ahalin shi waje d'aya yana son yaran shi su taso da so da kaunar junar da yataso a cikin shi tsakanin shi da nashi k'annen, Sai kudurin shi na biyu, dan zuwa yaga Moon yarinyar da tunda yayi tozali da hotunan ta suka kafe mishi a kahon zuciya, Joseph ya Kira shi akan ya kammala duk wani binciken daya sashi yayi a kanta, yanzun sauran aikin nashi ne, shi dai a gefen shi ta mishi % percent bai san koshi d'in zai samu karb'uwa a wajen taba, sai dai kuma zaiyi iya bakin kokarin shi wajen shawo kanta harta amince dashi ba tareda ya nemi taimako daga wajen Meenal ba shi kadai zaiyi ma kanshi yak'i saboda ba iya farin cikin shi yason ya inganta ba harda na Mahaifiyar shi yasan cewa zataji dad'i kwarai inta samu labarin yana neman aure balle kuma idan taji cewa yarinyar tana da alaqa da Meenal, ×××××× Alhamdulillah ya samu isa garin na Lagos lafiya, Joseph daya Kira tun kafin ya taso ya shaida mishi lokacin isowar shi, Shi d'in ne ya d'auko shi daga Airport sai da suka tsaya a wani restaurant sukayi takeaway kafin suka k'arasa gidan shi, Envelope d'in da yake kunshe da bayanan binciken da Joseph yayi mishi akan Moon ya gabatar mishi sama sama ya mishi bayani akan ta domin suna cikin tattaunawar ne shi Joseph din ya samu Kira na gaggawa akan an wuce da matar shi asibiti zata haihu, wannan kiran shiya katse komai duk da Joseph d'in yaso Sarki ya zauna dan ya huta shi yaje asibitin amma Sarki ya nuna mishi cewa babu komai su tafi taren kawai, Dan haka suka rankaya zuwa asibitin, motar Joseph a gaba motar Sarki da d'aya daga cikin sojojin dake gadin gidan yake ja kuma suna binshi a baya a haka har suka isa asibitin, koda suka je sun samu an shiga da Matar Joseph din d'akin haihuwa sai iyayen matar dana Joseph din ne a wajen suna zaman jiran tsammani, Basu yi tsayuwa na mintuna 20 a wajen ba ya farajin muryar d'an shi Abubakar da suke Kira da Boy yana kwala kiran sunan shi, "Daddy! Daddy!! Daddy oyoyo ga dady" Yaron yake fad'a da harshen turanci a yayin da ya k'araso da gudu cike da murna ya rungume uban nashi, Wanda shima Sarki mamaki yake akan su kuma me sukazo yi a asibitin da daren nan, duk da mamakin da yake ciki hakan bai sa ya kasa nuna farin cikin shi na ganin sanyin idaniyar shi a dai dai wannan lokacin ba koba komai shima yayi kewar yaron nashi, dan haka sai yasa hannu ya d'ago shi yana jefa shi sama yana cafewa, "Oh my Boy kaida waye kuka fito da daren nan daya kamata ace kana kan gado kaima kana bacci?" Sarki ya tambaya, sai dai mai makon Boy ya bashi amsa sai shima ya jefo mishi tambaya kamar haka, "Daddy kaima kazo duba Baby da Smole Mom tace Momy zata haifa ne koh" Ya tambaya yana shafa fuskar baban cike da farin cikin ganin baban nashi da yayi a lokacin, "Sabon Baby na Momyn ka kuma? Ita kuma Momyn naka tana ina?" Ba tareda yaron ya damu ba ya amsa mishi da cewa, "Ai tana ciki kuma kullum ma anan take kwana ko nace ta tashi mu koma gida bata zuwa" Sosai kan sarki ya d'aure dan bai fahimci surutan da Boy ke mishi ba inya fahimta dai dai fa yaron yana nufin Teemah tana nan asibitin kuma wai anan take kwana bata komawa gida, ga sabon Baby da yaji Boy d'in ya ambata, to kenan Teemah nada ciki kenan? "Kai da waye kukazo nan?" "Smole Momy" ya amsa yana nuna mishi inda Aziza ke can gefe tana amsa waya da alama bata san cewa Boy ya sulale a wajen ba, shi kuma sarki dama tunda yaji yaron ya ambaci smole Momy yasan ita yake nufi dan duka yaran haka suke kiranta, Excusing kanshi yayi daga nan inda su Joseph suke ya kama hannun yaron suka k'arasa inda Aziza take, Da gudu Boy ya k'arasa wajen yana fad'a mata cewa ga dadin shi yazo ganin Momy da baby, Gaisuwa sukayi tsakanin ta da Sarki cike da girmamawa tana mishi barka da zuwa, bai iyace mata komai ba harta mishi jagora zuwa d'akin da Teemah take, wanda isar su yayi dai dai da fitowar Brigadier general Abubakar da matar shi Aunty Rahma daga d'akin na Teemah, Dan haka babu b'ata lokaci Sarki ya zube zuwa k'asa domin nuna girmamawa ga sirikan nashi da suka rik'eshi tamkar d'ansu, Anty ce kawai ta amsa gaisuwar nashi tana tambayar shi yanzun ya iso? Shiko General k'arasawa yayi ya kamo hannun shi ya mik'ar dashi tsaye, "Baban Junior bana hakana duk'amin irin haka ba," "Ayi hak'uri zan cigaba da kiyayewa mun same ku lafiya? Ya mai jikin ta k'araji?" "Alhamdulillah mai jiki tana samun kulawa dan d'azun danayi magana da Dr yace min zuwa gaba kad'an zasu bamu ita mu koma gida har sai in lokacin haihuwar yazo gab sai mu dawo, ai jiki alhamdulillah taji sauk'i sosai fa, ya hanya da wajen aikin ka kuma?" "Lafiya lau, ita kuma Allah ya bata lafiya," "Ameen" Brig ya amsa dashi kafin ya d'aura da cewa, "Gashi kana zuwa mu kuma muna shirin tafiya, ko zamu jiraka idan ka dubata sai mu wuce gida gaba d'aya kaga sai ka samu kaci abunci dan nasan kila bakaci komai ba kayo nan, kasan sunan basa barin yan jinya na kwana" "Ai babu damuwa kuyi gaba kawai Sir na riga naci abinci kafin in fito kuma bani kad'ai bane tare muke da Friend dina shima matar shi na d'akin haihuwa," "Oh Allah sarki to allah ya raba lafiya mu bari muyi gaba to sai da safe" Juyawa yayi sai da ya raka su har mota kafin su wuce kuma sai da suka duba matar Joseph sai dai har lokacin bata sauka ba tana dai ta fama, Duk yanda suka so Boy yabi su ko kuma yabi Aziza da mijinta Imran yazo d'aukarta k'iyawa yayi akan shi wajen Daddy zai tsaya dole haka suka hakura suka wuce shi kuma ya koma ciki rungume da Boy din dake ta bashi labarai, Da sallama d'auke a bakin shi ya bud'e kofar d'akin ya shiga, Kwance saman gadon da aka tanadar dan marasa lafiya take kwance tundaga kafafuwanta zuwa saman cikin ta rufe da farin lallausan bargo ita kuma kuma tana kwance ne amma fuskanta na kallon kofar shigowa, Domin tun isowar shi wajen taji muryar shi, bata da k'arfin da zata yunk'ura ta fito wajen dan ta tabbatar ko shi d'inne shi yasa kawai taci gaba da kwanciya tana kallon kofar shigowar, Bayan ta dena jin motsin su a wajen kuma sosai tsoro ya kamata Allah yasa dai ba juyawa yayi suka tafi tareda su Aunty ba, kenan har abunda ta aikata yakai matakin da Sarki zai shigo cikin asibitin amma ya kasa shigowa ya dubata shine ya juya ya koma? Kenan bai damu da halin da take ciki ba komai yake shirin faruwa da ita? Tunda ta dawo fa ko sau d'aya batayi sakacin da wayarta ta rasa caji ko kuma wayar tayi nisa da ita ba duk dai a tsammanin ta na ganin kiran shi, amma kullum haka Gari zai waye rana ta k'ara fad'uwa babu amo ba labari, A sanda batun Sakin Meenal ya risketa a gadon asibitin nan duk da tana kwance ne cikin ciwo amma ta samu sauk'in nauyin da zuciyar ta ke mata na yawan tunanin da take cewa mijinta nacan tare da wata suna cin soyayya ita kuma gata nan a gadon asibiti ciwo ya hanata sakat, Tayi zaton tunda akayi sakin zai tattaro ya dawo wajen tane sai kuma taji shiru, shine kuma yau d'in daya iso ya kasa shigowa dubata ya juya, Tana cikin wannan bak'in cikin ne ta k'ara jiyo muryoyin su shida Boy sai kuma gasu sun shigo d'in, ashe dai har yanzun mijinta na sonta, Hakan kuma yana nufin cewa ita dai Fateemah itace kad'ai zata dauwama a matsayin matar mijin ta, lallai idan taji sauk'i ziyara na musamman zata kaima OBA dan tasan wannan aikin nashi ne, ashe bai manta da ita ba duk da dad'ewar da tayi bata ziyarce shiba gashi kuma shi baya rik'e waya balle ta kirashi. ***** A gefen Meelat ko tun washe garin ranar da ta amshi key din gidan Sarki a wajen Hajiya suka isa gidan ita da Maryam kamar yanda suka tsara, Zama sukayi suka ware suturun na Meenal tsaf suka musu screening suka ware mata wad'anda sukafi buk'atar tayi amfani dasu, sauran kuma suka kimtsa mata su a gefe, duk wani abunda suka san zata buk'ata saida suka d'aukar mata tundaga kan gyale, takalma da jakun kuna, dan sai da suka mak'are manyan akwatuna biyu da kaya, da suka kuma kawo mata kayan harta da kayan ta na nan gidan Hajiyar suma sai da suka tantance su, basu huta ba haka washe gari suka k'ara shiga kasuwa suka sissiyo abubuwan da suke buk'ata, Badai su sarara ba sai da suka kaddamar da shirin su akanta na ganin ta canza tsarin shigar ta itama ta fito a yanda suke so, tako fito d'in domin dama tun tuni Meenal ba baya bace wajen iya d'aukar wanka matsalarta d'aya dai ita ba ruwan ta da shafe shafe da dangwale dangwalen su jambaki, dasu bar bad'a kumatu k'ure kwalliyan ta shine ta goga kwali sai mascaran da take amfani da ita dan daidaita tsayuwar gashin idon ta, a tsarin ta ko jagira bata ja dan girarta a tsare take, To dai itama tunda suka dage akan ganin canjin nata da kuma goyon bayan Hajiya hakan yasa itama ta canza d'in ta koma fiyema da Meenal din da kuka sani a baya wajen iya d'aukar wanka, Sai gashi hakan ya zama kamar wani makulline na bud'e kofar farin jinin ta, dan kusan kullum ne in sun fita sai sun samu wanda zai taya domin dukan su yanzun basa zama suna ta faman shirin biki ne yawon raba kati da anko, Kamar yanda kuma Hajiya ta fad'a a cikin satin ita da kanta ta jagoranci zuwa gidan Sarki da masu siyan kaya dan tace bata buk'atar kayan su iso gidan ta kona Malam dan haka duk wani abu mai daraja wanda ya had'a daga kan gadaje kujeru duk ta had'a ta siyar wadanda kuma tasan bazasuyi d'araja ba da wad'anda suka tsufa duk rabasu tayi wa mabuk'ata wasu kayan kuma ta aika dasu gidan Malam, kuma tass tama gidan ko tsinke basu barma Sarki ba dan ita cewa ma tayi ya gode Allah da Allah yasa shine ya zuba kayan Sashen shi da kud'in shi inba haka ba da duka harda na Sashen nashi zata kwashe wallahi, Duk wannan budurin rabon kayan da kwashe kayan Malam yana da labarin komai ido kawai ya kawo ya zuba batareda yace komai ba dan ya lura magana kawai Hajiya take nema shi kuma bazai biye mata ba, Ita ko Hajiya kan kud'in kayan ta had'a da kud'in da Sarki yaba Meenal wanda tuni Hajiyar tasa aka canzo mata ta tura su can Saudiya wajen Amina Mahaifiyar Mai Jama'a ta siyo mata dank'ara dank'aran qwalaqwalai ta aiko mata dasu ita kuma ta adana ma Meenal d'in a cewar Hajiyar wai in Meenal ta samu sabon Miji su za'a siyar a mata wasu kayan d'akin. *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/27, 10:31 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *BOOK 2* *PAGE 12* A hankali yaci gaba da takawa yana shiga cikin d'akin ba tareda ya warware d'aurin dayama fuskar shiba bayan ya gama k'are mata kallo, Koda ya isa kujerar dake daura da gadon ya jawo zuwa gaban gadon ya zauna, rik'e da Boy a hannun shi wanda har lokacin bai gama bashi labaran da yakeyi ba, yanda yake binta da kallo haka itama taci gaba da binsu shida Boy din da kallo batareda ta furta komai ba dan bata jin cewa akwai ranar da zata zagayo wanda zataji cewar ta gaji da kallon nasu domin su dai halittun maza biyun nan dake a gabanta sune abu biyu da take matuk'ar so da kauna a rayuwarta tana son d'anta son daya haura soyayyar da takeyi ma yaranta uku mata, haka shima uban take mushi wani irin mahaukacin son da take jin komai ya shiga gabanta tana iya kauda shi indai wanda zai shiga tsakanin ta da Sarkine,dan haka ba tareda k'osawa ba itama taci gaba da kallon su tana jin dad'i na k'ara lullub'eta, fatan ta a kullum shine Allah yasa shima wannan cikin na jikin ta Namiji ne ba mata ba, domin kullum likitan sai ya zaulayeta da cewa ko sojoji zata haifo musu ne wannan karan shi yasa ciwon laulayin su ya bambanta dana sauran, to itama dai addu'ar da takeyi kenan Allah yasa biyun zata haifo kuma yazama na duka maza, intayi yan biyu maza mai kuma ya rage mata yanzun da bata da kishiya ai shikenan kuma bata da sauran matsala. Can sarki ya bud'e baki cikin kakkarfan muryar shin nan da bata sarrafuwa ta dad'in rai yake tambayar ta "Ya jikin naki?" "Naji sauk'i Alhamdulillah yaushe kazo?" "Isowata kenan" "To wa ya fad'a maka banda lafiya Anty ne ta kira ka ko Daddy?" "Bako d'aya a cikin su, keda kike ciwon baki gayamin ba, sune kike saran su Kira su fad'amin?" "Kayi hak'uri" Shi kuma sai ya mata banza bai amsa ba, hakan da yayi kuma shike mata nuni da cewa ranshi a bace yake dan haka sai itama tayi shiru ta kama kanta, Bayan wani d'an lokaci sai kuma ya zaro wayar shi daga cikin aljihu sojan daya tuk'oshi ya kira sannan ya fad'a mishi inda zai shigo ya same shi, babu jimawa ko sai gashi, sai da sojan ya gaisheda uwar gidan su da mata ya jiki kafin ya rungume Boy da Sarki ya bashi dan tuni bacci ya kwashe Boy d'in, Umarni Sarki ya bashi akan ya kai Boy din can gidan Brigadier daga can kuma shima ya wuce gida zai kira shi da safe yazo nan d'in ya d'auke shi, "Basa bari ana kwana fa anan d'in !" Cewar Teemah. "Kai yi tafiyar ka sai da safe " Bayan sojan ya ficene ya fuskanceta da kyau, sai dai yana shirin yin magana ita kuma ta tari numfashin shi da tambayar shi, "Kaci abinci kuwa? Idan kanajin yunwa in kira a kawo maka me zakaci?" "Bana tareda yunwa na riga naci abinci", ya amsa mata a dake, dan haka ita ma sai ta gyara kwanciyar ta hannun ta a saman cikin ta da shine abunda Sarkin ya fara gani tun shigowar shi d'akin domin ba k'arya ta rame dan ma tana da mulmulallan jiki da farko kuma cikin nunuwa da hips ya k'ara mata yanzun daya k'ara kwari shine har ya bayyana, "Fateemah wai ke yaushe zakiyi hankalin sanin dai dai da kuma abinda yake ba dai dai bane iyeh?" Sai da ta turo baki gaba kafin ta iya furta "to ni mai nayi maka kuma yanzun? Kaga dai abunda ke gabana koh ka barni inji da lalurar dake jikina" "Eh Ai dama haka zakice tunda a kullum dama ke damuwar ki ce kadai taki, yanzun fisabilillahi inba ma kin d'aukeni wani mara daraja a wajen ki ba taya ma har zaki kwanta a asibiti tsayin lokaci ace nida nike matsayin mijin ki bani da masaniya akan hakan sai iyayen kine zasuyi dawainiyar da nine ya dace inyi? Fateemah mai yasa kike son ki zubar min da kima da darajar da nike da ita a idon iyayen ki ne? Ke a ganin ki abu mai kyau kenan kika aikata, kina da ciki baki sanar dani ba baki da lafiyan ma shima bazaki iya sanar dani ba karfa ki manta cewa ni d'in nan nine mijinki uban cikin dake jikin ki kuma, amma kika wofantar dani akan wani abunda bai taka kara ya karya ba, wai me yasa kikeyin hakane ke?" "Ai kaima tunda na dawo baka kirani ba, ai ya dace ka kira kaji kona iso lafiya ko a'ah amma da yike kana tareda wacce ta d'auke maka hankali ai bakayi hakan ba, alhalin ni kuma Allah ne yayi da sauran shan ruwana a gaba da har muka iso garin nan lafiya ban mutu a mota ko rasa d'an cikin da nima ban san cewa ina d'auke dashi ba, kuma da kake cewa ban kiraka ba nida nike ta kaina ne zan kira ka, bayan tunda na iso har yau ban k'ara samun cikakkiyar lafiyar jikina ba, kuma ai tunda ina da iyaye a raye kasan zasu kula dani" "Kinga ni koh? Wannan shine matsala ta dake, domin kwata kwata bakya son gaskiya ke kullum gani kikeyi cewa komai kika aikata akan dai dai kike, kuma ko mutum yaso ya miki gyara bazaki tsaya ki saurare shiba ma balle har ki gane inda ya dosa, ai nasan kina da iyayen tunda a gaban su na auroki amma ai hakkin kula dake yanzun a hannuna yake ba a wuyar suba, akan me zaki d'aura musu lalurar da kika san bazai gagareni d'auka ba, anyi magana kince ina can hankalina wajen wata saboda ita kika sa a cikin zuciyar ki yarinyar da ita sam naki damuwar baya gaban ta ita ta kanta kawai take, kuma in ban damu dake ba ai kin san bazan bar duka uzurorin dake gabana kawai dan inzo in ganki bayan kin b'ata min raiba" "To nidai ai na baka hakuri kuma ai namaji sauk'i dan Allah kayi musu magana su barni in koma gida wallahi bana son zaman asibitin nan kullum idan nace su sallameni sai suk'i" Tashi yayi daga kujerar da yaje zaune ya koma kan gadon sai da ya sanya hannayen shi ya dago ta daga kwancen ya zaunar bayan ya d'an jingina ta a jikin shi, wanda dama ita din abunda take buk'ata kenan wato ta rab'u da jikin nashi dan haka sai ta k'ara shigewa cikin jikin nashi da kyau, "I miss you nayi kewar ka sosai ina ta ciwo baka nan" "Bakiyi kewata ba da kinyi da kin nemoni da kanki" Ya fad'i hakan a yayinda ya k'ara tallafeta a cikin jikin shi, "Wata nawa ne cikin?" Ya tambaya bayan ya d'aura hannun shi kan cikin ta saman riga yana shafawa, Karo na farko data sakin mishi kayataccen murmushin ta da har saida sautin shi ya fito, hannun ta ta maida akan nashi hannun sukaci gaba da shafa cikin a tare, "Wata biyar, kuma nima ban san da cikin bafa tunda ina ganin period wai ashe ina da ciki sai yanzun daya girma ne nike mishi laulayi" "Sannu Allah ya rabaku lafiya" "Ameen, ya ka baro mutanen Zaria?" "Kowa yana lafiya" "Harda Amaryar ka?" "Ai kowa nace miki" Shiru sukayi dukan su babu wanda ya k'ara cewa komai har zuwa wani d'an lokaci, can ta fara laluban shi jin tana neman taso mishi da tarzoma ne hakan yasa ya fara kokarin zameta a cikin jikin shi, "What 😦? " Ta tambaya tana kwabe fuska, "Amma kinsan cewa a gadon asibiti kike koh?" "Amma ai nayi kewar ka" Ta fad'a tana k'ara kwanciya a cikin jikin shi, "Yes I know and I miss you too, amma koma miye ki bari har ki k'ara samun karfi ki koma gida tukun" Shesheshekan kuka ta fara kasa kasa, "Wai me nene kuma?" "Nidai wallahi ban yarda ba wata nawa?" "Oh bazaki hakura ba dai kenan?" "To ai ba dagani bane Baby ne ke son gaisawa da Daddy mana tab'ama kaji" ta kamo hannun shi ta daura a k'asan marar ta, kamar d'an cikin yasan hannun waye a wajen kuwa ya motsa, "Kaji koh?" Ta tambaya tana mai kallon shi, a marairaice, "Koma miye hak'uri zakiyi har zuwa gobe in aka sallame mu sai mu wuce gida kalli fa kiga dare yayi," Ya mata nuni da agogon dake cikin d'akin, "Ki kwanta kiyi bacci" ya fad'a bayan ya danna abunda ake kiran nurse din da ke kula da ita, "Zanyi fitsari tukun" Sai da ya kamata har zuwa cikin toilet din tayi fitsarin sannan ya bata umarnin cewa ta d'auro alwallah kafin ya kamota a jikin shi suka fito daga cikin bayin, Koda nurse din ta iso tayi mamakin ganin shi a cikin d'akin dan tunda aka kawo teemah asibitin itace ke kula da ita kuma bata tab'a ganin shi a cikin yan dubiya ba, sannan kuma tasan su yan uwan ta da wuri suke wucewa basa kai dare har haka, Dan haka bayan ta gaishe shi wanda ganin yanda yake ta lallab'a Teemah har ya kwantar da ita kamar wasu masu tsoron kada cikin ya fad'o daga jikin teemah din ne tace dasu, "Madam akwai abunda kike buk'ata ne?" Tayi tambayar cikin harshen turanci, Sarki ne ya amsa ba tareda ya kalleta ba da cewa, "Eh muna buk'atar k'arin bargo da pillow guda d'aya" Shima da yaren turancin ya amsa mata, "Amma sir anan d'in ba'a barin wani ya kwana da mara lafiya mune ke kula da komai da mara lafiya zai buk'ata, ina ga da kayi hak'uri ka tafi gidan in yaso sai ka dawo da safe" "Duk na san wannan tsarin naku sai dai kuma nima yau ina buk'atar in kula da matana da kaina kinga kema yau sai ki samu hutu tunda ni zan canje ki, kuma dai ai kamar babu wanda yasan ina cikin nan d'in sai ke kad'ai koh? Kinga in kikayi shiru har zuwa safe ma babu mai gane cewa wani ya kwana anan" Ganin yanda yake maganar a kame babu alamun wasa ne ya sata amsawa da to ta juya taje ta kawo mishi abunda ya buk'ata d'in, Tana fita ko ya maida kofar ya kulle ya dawo ya cire rigar jikin shi ya rage daga shi sai dogon wando da singilati wutar d'akin ya rage ya bar mara haske sannan ya k'ara komawa can gefen inda Teemah ke kwance ba wai dan tana bacci ba ya zauna, ita kuma sai ta rik'o tafukan hannuwan shi yasa a kan pillow sai ta maida kanta a kansu tayi pillow dasu, "Sarki" Ta kira sunan shi da k'aramar murya, "Ai dai nace kiyi bacci dare yayi koh," "Kana jin sona a cikin zuciyar ka irin son da kake cewa kana min kafin muyi aure da farkon auren mu?" Mai makon ya bata amsa sai ya zame hannun shi ya d'agota daga kwancen ya zaunar, pillows din ya gyara ma zama ya jingina su da fuskan gadon shi kuma sai ya haye saman gadon ya jingina da pillow din ya ware kafafuwan shi sai ya zamana ita ta koma tsakiyar cinyoyin shi, Sai da ya gyara mata zama a wajen da kyau ta yanda bazata takura ba sannan ya amsa mata da cewa, "Dama ni nace miki na fara sonki ne dan in dena son naki wata rana?, ke d'in dai Fateemah ke nike so tun kina da yarintar ki haka kuma zanci gaba da sonki har tsufan ki, a zaton ki dan kinyi haihuwa d'aya biyu hakan zai sa in canza miki ne? To ki sani ko duniyar zaki cikamin da yara indai kece uwar su zan rungume ku ke da su cike da farin ciki saboda kaunar da nike miki ba mai k'arewa bane, komai zaki min zanyi hakuri dashi inci gaba da kauda kai saboda son da nike miki ga darajar yara kuma dana iyayen mu," "To kana sona da yawa haka me yasa kayi min kishiya?" "Amma koma ya akayi ai kin san komai tunda a lokacin babu abunda na b'oye miki kuma kika bani goyon baya," "Kuma ai an kirani ance min ka saketa amma da kazo nan ai gashi baka fad'amin ba" Ajiyar zuciya ya sauke a bayyane, lallai ya tabbata kenan ashe komai dake faruwa a zaria akwai masu kaimata rahoto tana inda kike, "Fad'amin dad'i kikaji da akace miki na sake ta ko me?" "To ni na san abunda ya had'akune, kuma ai kaima kasan bazanji haushi ba" "Shi yasa nace kina da son kanki da yawa Teemah, miye abun farin ciki dan mijinki ya rabu da macen da yake aure, cewa fa akayi ciwon ya mace na ya mace ne" "Eh haka suke cewa amma ai kowa yasan in mutum na ciwo sai dai a tayashi zaman jinya wajen ce mishi sannu da kuma fatan samun sauk'i amma shi kad'ai yake jin azabar ciwon shi a jikin shi, ni dai bazanyi bak'in ci wai dan ka auri mata kun rabu ba, tunda ita ce ta auremin miji ba nice na aure mata miji ba" "In ita ta tafi wata ai zata shigo ne zuwa gaba" Ya bata amsa ba tareda ya damu da irin zaburar da tayi daga jikin shiba, "Wani auren zaka k'arayi kuma bayan wannan?" Ta tambaya kamar zata fashe mishi da kuka. *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/28, 12:04 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *BOOK 2* *PAGE 13* Da sallama Meenal ta shiga falon dawowarta kenan daga makaranta tun fitan da tayi tun safe ko kari batayi ba shi yasa duk ta galabaita tsabar gajiya da yunwar data kwaso, sai dai kuma Hajiya ko iya amsa sallamarta batayi ba ta fara sababin ta da bata gajiya akoda yaushe, "Wai ke ni nakan rasa mai yake damun kune yaran nan wallahi, ace tun kuna da sauran k'uruciyar ku ciwon mantuwa na neman cika muku kwalwa, kawai kin wani tafi kin bar waya a gida idan anyi magana kice mantawa kikayi da ita handset fa akace ba homeset ba amma sai ku dinga fita kuna barin waya a gida, kuma itama d'ayar wayar naki ba irin kiran da ban miki ta cikin taba har sai da cajin wayana ya k'are tass akan kiran ki amma a banza baki d'auka ba," Lallab'awa tayi ta nemi waje a d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna, ba tareda ta kula da sababin Hajiyar ba ta fara kiran "Aunty Larai dan Allah ki taimakeni da abinci ko wanne ne ki kawo min zanci wallahi yunwa nikeji" Daga cikin kitchen d'in Larai ta amsa mata da cewa "to Hajiya k'arama yanzun kuwa insha Allah" Shek'ek'e Hajiya taci gaba da binta da kallo, "Kujimin wani d'ibar albarka fisabilillahi ina magana da yarinya ta mai dani wata shashasha" "Hajiya sallama fa nayi amma ko amsawa bakiyi ba daga shigowa ta ko zama banyi ba kika fara min fad'a kuma ni ai bance miki na mance da wayar ba da sani na na barta a gida saboda bana son abunda zai rabamun hankali shi yasa koda naje makaranta itama k'aramar na sata a silent, yanzun ba gashi na dawo ba, saurin me kikeyi tunda kinsan cewa dai insha Allah duk inda naje nan dai zan dawo in kwana" "To Ameen Alaikum salam, sannu da dawowa uwata ya gajiyar makaranta, Larai mik'o mata abincin taci sai ta k'ara samun k'arfin ci gaba da maida min maganar kamar wata tsararta ce ni d'in tunda su sunfi k'arfin suyi ba dai dai ba a fad'a musu gaskiya" "Kiyi hakuri Hajiya kila dai bataga kiran naki bane shi yasa bata dau wayar ba" "Ke rabu dani wannan yarinyar da kikeji da gani itama tana da mugun hali irin na ubanta Almu inba haka ba miye laifina ana dan nayi fad'a akan taki d'aukar min waya?" Yunk'urawa meenal tayi ta amso abincin a hannun Larai ganin ta biye ma Hajiya ita kuma wallahi yunwa takeji, Bayan Larai ta koma kitchen shiru Hajiya tayi har saida Meenal din ta gama cin abincin, "Hajiya wai ya akayi ne hala kiran me kike min to wani abun ya faru ne bayan na fita?" "Ah ah komai bai faruba son jin muryar kine yasa na yi ta kira kamar wata shashasha ke kuma kika k'i dauka" "Yi hak'uri to ai kin san in lafiya lau ne bazan k'i d'aukar miki waya ba wallahi ban san kin kiraba" jakarta ta jawo ta fito da wayar daga ciki tana nuna ma Hajiya tarin miss call din da aka mata wanda ko bud'esu batayi ba balle taga ko su waye, "Kin gani koh Hajiya wallahi ban duba ko su waye suka kiraba kiyi hakuri" "To ki shiga ciki ki shirya tunda akwai sauran lokaci mu wuce kaduna, dan bayan fitan ki na samu kira daga wajen Jidda cewar Allah yayi ma mijin yar uwar ki Raheenat Rasuwa a safiyar yau kuma itama Raheenat din ta Haife cikin dake jikinta wanda sakamakon sak'on mutuwar daya iske sune yasa nakudar dole taso mata ta haihu an samu d'a namiji, shi yasa nike ta kiran ki nasan kuma suma mutanen can gidan naku sun neme ki a waya" "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un³" Shi meenal tayi ta maimaita wa tana hango irin tashin hankalin da Raheenat take ciki na rasuwar miji kwatsam babu jinya ba komai, kuka ta fashe dashi sosai dan Wallahi mutuwar ta dake ta, mutuwa farat daya irin haka kona wanda baka sani bane sai ya tab'aka balle kuma mijin yar uwarta. "Wai yayi rashin lafiya ne dama Hajiya ko hatsari yayi?"ta tambaya da muryar kuka "Babu ko d'aya kedai wallahi ajaline kawai ya riske shi dan sunce lafiya lau ya tashi har anyi sallan asuba dashi lafiya lau ma sukayi karin safe da iyalan shi kafin ya shige cikin dan yin sallan walha ita uwar gidan ne ta shiga ta iske shi kwance a kan daddumar da yayi Sallah ita a zaton ta ma ko bacci yake yi ashe tuni lokaci yayi ya tafi yabar musu duniyar daduk abunda ke cikin ta" Hajiya ta k'arasa fad'a da hawaye itama, zuwa wannan lokacin ko kuka shab'e shab'e Meenal keyi dan sosai mutuwar ta dake ta, "Ke ai ba kuka zakiyi ba tashi zakiyi ki shirya muzo mu kama hanya tun yamma batayi sosai ba" Wayar ta da ta lalubo number din Mommy Hauwa ta dannawa kira ta kara akunne tana kuma cigaba da kukan, koda mommy ta dauki wayar tambaya ta jefo mata da cewa, "Kun iso ne Meenal kuna ta ina ne? Mu muna Sashen uwar gidan bari inzo in same ku" Katseta Meenal tayi da cewa, "Mommy wai da gaske ne ya rasu?" "Ya rasu mana Meenal ana wasa da mutuwa ne?" Ta tambaya tana yanke wayan, wanda hakan ne kuma yasa Meenal din kara yawan kukan da takeyi, "Kai amma yarinyar nan ban san kallon mak'aryaciya kikemin ba tsayin zamana dake sai yau, ni ince miki mijin yar uwar ki ya rasu amma baki yarda ba shine sai da kika kira uwar ki kika tabbatar tukun, to yanzun da kika tabbatar da mutuwar dawo mishi da ran zakiyi ko k'ak'ah?" Ita dai Meenal kukan ta kawai takeyi, yanzun fisabilillahi shi kenan Raheenat ta rasa mijinta yaranta kuma sun zama marayu ciki harda wanda yazo duniya ayau shi ko damar sanin baban shi ma bai samu ba, Allah sarki Alhaji Saminu ubangiji Allah ya jikan ka" Suna cikin wannan jimamin ne biyu daga cikin masu gadin gidan sukayi sallama a kofar falon, Hajiya ce ta amsa musu, "Ya akayi ne Isah?" "Kayane zamu shigo dashi Hajiya" "Kaya kuma! To bismillah ku shigo," Rik'i rik'i suka shiga d'auke da buhun dankalin turawa, "Mai Jama'a ne ya dawo hala?" "Eh shine Hajiya shigowar shi kenan" "To ai da kun min bayani sai ince ku shiga da kayan tacan kofar kitchen din baya zaifi muku sauki,Larai zoki nuna musu inda zasu ajiye wannan d'in" Bayan sun shige dashi basu fito ta falon ba sai kawai suka fuce ta kofar bayan, tacan suka cigaba da shigewa da kayan har suka gama, Hajiya kuma ta haura sama tana k'ara jaddama ma Meenal cewa ta tashi taje ta shirya fa su kama hanya dan bata son tafiyar dare, Sai dai har Hajiyar ta k'ule bata motsa ba, Malam ta kira ta farayi ma gaisuwa cike da muryar kuka, "Mamana yanzun ne kikaji sakon rasuwar nashi hala? Shi yasa kike ta kuka bayan kin san mamaci ba kuka yake buk'ata ba" Sai da ta yi kokarin share hawayen dake ci gaba da biyo fuskanta kafin ta amsa da cewa, "Naje makaranta da wuri yau kuma banje da wancan wayar ba, wannan kuma ana ta kira a fad'amin sai dai itama na cire mata k'ara shi yasa duk banji kiran ba," Sai da taja majina sannan ta d'aura da cewa, "Yanzun ne dana dawo Hajiya take fad'amin rasuwar nashi, ubangiji Allah ya jikan shi Allah kuma ya raya abunda ya bari yaba iyalai hakurin rashi" "Ameen Ameen Mamana Allah yayi albarka, amma dai zaki bari har zuwa gobe ne sai ki tafi kije kima yar uwar naki gaisuwa koh? tunda kinga yamma tayi yanzun ana neman k'arfe biyar ne yanzun" "Aiba ni kadai zan tafi ba Hajiya ta shirya tun d'azun dawowana dama take jira nasan direban ta ne zai kaimu" "To masha Allah ubangiji Allah ya tsare suma iyayen naki suna can ai nidai na dawo gida tun bayan da aka gama jana'izah" Sallama sukayi ta yanke wayar, Tunda suke wayar hancin ta ke shak'o mata kamshin da ko bata tambaya ba tasan mallakin waye balle kuma shigowar su Isah ya k'ara tabbatar mata da cewa shid'in ne, A hankali yaci gaba da takowa bayan yayi sallama daga bakin kofar da yake tsaye, bata yarda ta d'agoba kanta a duke ta amsa sallamar tana laluben number din Meelat a wayar dake hannun ta kuma bawai kukan da takeyi ya dauke bane gaba d'aya ah ah har zuwa lokacin hawaye basu dauke a idonta ba ga kuma shashshek'an da takeyi kasa kasa, Gefen ta ya k'arasa ya zauna yana binta da mayen kallo hankalin shi a tashe sakamakon ganin hawaye shab'e² a fuskar da ya dawo da burin gani wanda kyanta ke karuwa aduk sanda ta k'awata fuskar nata da murmushi shine daga shigowa zai sameta tana kuka kuma, "Maiya sameki kike zaune anan ke kadai kina kuka? Kukan ne kikeyi?" Sai da ta tab'e bakin ta irin yanda yara keyi idan suna kuka sannan ta dago idanuwan ta wanda suka fara burkicewa kalan su ya canza daga farare zuwa jajaye ta zuba mishi, "Fad'amin mana meya same ki ko baki da lafiya ne? Kai ta girgiza mishi alamun ah ah, "Lafiyar ki kalau kenan?" "Eh" Ta bashi amsa, "To me ya faru?" Ya kara tambaya. "Rasuwa akayi" "Innalillahi wa'innah ilairir raju'un ubangiji Allah ya jikan musulmi" "Ameen" Ta amsa dashi, sai shi kuma ya kara tambayar ta cewa, "Waye ya rasu?" "Mijin k'anwata Raheenat dake aure a kaduna" "Allah ya jikan shi yasa mutuwa ta zama hutu a gareshi, ku kuma Allah ya k'ara muku hakuri" "Ameen" "To ki dena kukan hakan bakiga idon ki har sunyi jaba, kiyi mishi addu'a kinji" yana fad'in hakan ya kai tattausan hannun shi kan fuskar nata yana share mata hawayen da suke zubowa, "Ki dena kukan please fuskarki bata kyau da kuka tafi yin kyau idan kina murmushi, ita kuma mutuwa lokaci ne duk wanda nashi lokacin yayi zai tafine ko da bai shirya ma zuwan lokacin ba, ni da ke da kowama lokaci muke jira sai dai muyi fatan Allah yasa mu cika da kyau da imani yasa mu gama da duniyar lafiya mu tafi ana kewar mu masoyan mu kuma suci gaba da bin mu da addu'a, kiyi shiru kukan ya isa haka" 'To Nagode" ta amsa dashi harta mik'e da niyyar haurawa sama ya jefo mata tambaya da cewa "Hajiya fa?" "Tana d'aki tana shiryawa tace nima in shirya zamu tafi kadunan yanzun," "Ku dawa?" "Mu biyu" "Waye zaija motar nike nufi bawai ku nawa nike son sani ba" "Oho to ai nima ban sani ba amma in direbanta baya nan aini ke tuk'ata" "Eh amma ai baki tab'a tuk'a kanki zuwa Kaduna ba, jeki shirya ku fito sai mu wuce gaba d'aya dan dama nima gobe ne zan koma can din" "To basai ka zauna mu mu tafi ba, nifa da mota ta zanje" "Ai kindaiji abunda nace miki tunda niba mahaukaci bane da zan barki kiyi tuk'i a tsakankanin manyan motoci, kije ku shirya ku fito nace yamma nayi" Yana gama fad'in hakan ya juya ya barta nan tsaye tana cigaba da binshi da kallon mamaki, " Kuji min karfin hali fa mutum daga dawowar shi zai fara gindayawa mutane sharad'od'i ko waye ma ya gayyace shi zuwa gaisuwan", to in suka bishi zuwa can in fita ya kamata zuwa wani wajen da motar waye zata fita, Ganin ya juya ya fice abunshi itama sai ta haye saman jiki a sanyaye, Tubewa tayi ta fad'a toilet ta sakar ma jikin ta ruwa sabulu kawai ta goga ma jikinta ko soso bata saba tayi wankan ta fito, a gurguje ta shirya ko mai bata tsaya shafawa ba ta harhad'a yan kayanta kala uku a cikin karamin akwati ta d'auko wayarta data bari a gida ta kunna, "To in kin gama ki sauko mu tafi ni na riga na fito" Cewar Hajiya dake bakin kofa, "Gani nan fitowa nima na gama ai," Ta fad'a tana zura hijjabin ta dogo har kasa, koda ta fito hajiya bata saman a kasa ta sameta tana ba Larai sallahun ta kula da gida sai sun dawo, A can haraban gidan ko kafin su fito tuni AK ya kunna mota fitowar su kawai yake jira, "Ah ah kai kuma daga shigowar ka garin shine zaka k'ara kwasan mu kuma bazaka zauna ka huta ba ko ita ai tana iya tuk'amu zuwa can din ka shigo nasan ko abunci bakaci ba" Hajiya take fad'a ganin ya amshi kayan hannun Meenal yasa a cikin booth din motar shi harda ma nata kayan, "Bana tare da gajiya Hajiya dan bani na tuk'o kaina ba, ina wuni ya k'arin hakuri Allah ya jikan shi" "Lafiya lau ya hanya? hakuri da godiya, ameen ameen," Juyawa tayi ta kalli Larai ki shiga ciki ki d'ibo mishi kayan fulawan da kika had'a dazun koshi sai ya samu yaci a hanya ki dibo da dan dama kin san itama Meenal tana so" Da sauri Larai ta juya cikin bayan ta amsawa Hajiya sai gata ta dawo harda zungura zunguran gorunan exotic guda biyu ta mik'ama Meenal, Hajiya Jummai bata gidan ta tafi kano dan haka basuyi sallama da ita ba tun safen dai Hajiya ta fad'a mata rasuwar da cewa Meenal take jira idan ta dawo zasu kama hanyar Kadunan, hakan name yasa babu b'ata lokaci suka kama Hanya Meenal ce a gaba gefen mai zaman Banza hajiya kuma ta kame a baya shi kuma shi da kanshi yake tuk'in, Hajiya na zaune a baya take bashi labarin irin yanda rasuwar na mijin Raheenat din ya kasance babu ciwon fari bare na bak'i sai gawa iyalin shi ta tarar Allah kadai yasan yanda abun ya faru ko yana cikin sallan ne aka cire ran ko kuma sai da ya idarne allah masani, Koma dai menene ai shi kam Alhamdulillah ya tafi cike da nasara wallahi, muma dai allah yasa mu dace da kyakyawar karshe ameen, suna tafiya a motar ne kuma Meenal tayi kiran su Maryam a waya ta shaida musu batun rasuwar cewar yanzun haka sun kama hanyar wucewa can Kadunan sun mata gaisuwa da addu'ar Allah ya jikan musulmi suma kuma insha zasu yi kokari su shigo kadunan a gobe suma Raheenat gaisuwa, A gefen AK ko zai iya cewa wannan tafiyar tafiya ce mafi dad'i a wajen shi duk da dai bawai tafiya ce wacce aka shirya ta cikin dad'in raiba, Koba komai wannan shine karo na farko daya d'auki Meenal a cikin motar shi har zasuyi tafiya daga Zaria Zuwa Kaduna, dan haka zaiyi amfani da wannan damar ya cusa ma Hajiya ra'ayin zama a gidan nashi in yaso kullum shi yaji ya gani zai dunga kaisu can gidan gaisuwar yana d'auko su dan yasan in suka tare a gidan gaisuwar gani Meenal din zai mishi wahala, Sai da suka fice daga cikin zaria har sun d'an fara nisa tukun ya daga kanshi ta mirror din gaban motan yana kallon Hajiya, "Hajiya ina abincin da kika ce a dibo min yunwa fa nike ji wallahi" Ya fadi hakan yana satan kallon Meenal ta gefen ido, "To ai ga irinta nan shi yasa nace ka zauna a gida ka samu kaima ka huta, shikenan ayi rayuwar mutum ba hutu ba kanan ba kanan kamar kai kafi kowa son kud'i fisabilillahi wani kud'ine kake nema kuma bayan wanda ka tara iyee gashi nan duk ka fara zabgewa kana ramewa a tsaye tunda nasan ba wani cin abincin kake samun yi yanda ya kamata ba" "Nidai Hajiya yunwa dai nace miki ina ji" "Ke Meenal ina ce ke Larai ta damk'ama kayan fulawan ki bashi mana" "Hajiya gashi nan fa a gefen shi ai yana kallo," "Hajiya nida nike tuk'i to da wani hannun zan dunga d'auka ina kaiwa baki ina ci?" "To ni kake so in dawo gaban in dunga baka a baki kenan?" "Ah ah Hajiya ki dai mata magana ita ta dunga bani a bakin har in koshi kinga idan nace in tsaya sai na gama ci muci gaba da tafiya lokaci zamu b'ata kuma yamma na k'arayi" "To ai gata nan a gefen ta kunfi kusa" Hajiya na gama fad'in haka ta gyara zaman ta bayan ta ciro wani littafin addu'o'i shi taci gaba da karantawa bata k'ara bi takan suba, "To yane An mata a taimaka a bani abinci yunwa nike ji wallahi bakiga yanda cikina ya lafe ba" Ya k'arasa fad'a dayin k'asa da kwayar idon shi ya mai da kallon shi zuwa wajen cikin shi, Cikin nashi dake lafe cikin rigar dake sanye a jikin shi polo shirt fara tabi da kallo kafin ta kauda kai, "Please mana ko so kike ulcer ya kama ma future wife d'ina nine?" Yake tambaya k'asa kasa, Jawo roban da Larai ta zuba su samosa donut da meat pie din tayi sai taga harda Pepe chicken ta had'o musu, Mutuniyar ku dai kun san amanar dake tsakanin ta da nama balle kuma Hajiya kaza fa ake magana anan, dan haka tuni ta manta da batun shi ta d'auko wani d'an kwalelen cinya ta gyara zama ta fara ci, "Amma dai yarinyar nan kin iya d'aukar alhaki wallahi, abincin nan nawa nefa kuma yunwa nace miki inaji amma kin wani gyara zama kina ci ke kad'ai wato dad'i kawai hajiya da Larai suke baki shi yasa ashe naga sai k'ara kyau kikeyi abinki ni kuma bawan Allah sai faman rama nikeyi, to nidai a taimaka a sammun inci nima kar a ci da hakkina," *Ummiee Zaria*✍🏼 [8/28, 9:28 PM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *BOOK 2* *PAGE 14* Kadai jira ita future wife d'in taka tazo sai ta baka a bakin badai niba" ta fad'a hankali kwance tana ci gaba da cin naman ta, "Tunda gaki aiko kema kina iya zama wakiliyarta, Allah kuwa seriously ina jin yunwa,in kuma bazaki bani ba bari in faka a gefe ke sai ki amshi driving d'in ni kuma sai inci abincin tunda abun ya zama haka," "Allah ni ba wani tukin da zanyi ai tun farko saida nace kayi zaman ka mu tafi da mota na kak'i, tunda ko ka matsa haka nan zaka jamu ka kaimu" "To abincin fa?" "Ba gashi nan na ajiye maka a tsakanin mu ba hannu zaka dunga zirowa kana d'auka kana ci" Ta fad'a bayan ta ajiye abincin a gefen ta, Bai k'ara tanka mata ba har sai da suka shiga Zango sannan ya gangara gefe yana niyyar faka motar, "Me zakayi wai?" "Kina tambaya ne bayan ba makancewa idanuwan ki sukayi ba, to fakawa zanyi idan na gama cin abincin sai muci gaba da tafiyan" "Dan Allah karka tsaya wallahi yamma tayi" "Sai kince kin yarda zaki bani a baki" "Na yarda" yago naman tayi takai mishi baki, "Haaa" tace tana bud'e mishi nata bakin kamar wata wacce zataba yaro abinci, Cafka ya kaima naman data kawo kusa da bakin nashi ya had'a harda yatsarta ya d'an ciza kad'an yanda bazataji zafi ba, amma dan sharri irin na Meenal sai da ta tak'ark'are ta kwala ihu, "Ke miye haka?" Hajiya dake baya ta tambaya, "To bashi bane kawai ya cijeni a yatsa taba" "Cizo kuma kamar wasu k'ana nan yara, kaga nidai ka rufamin asiri ka lallab'a ka kaini ka sauke lafiya kafin kasa a sanya sunan mu a labaran dare cewa mun taso daga garin Zaria zamuje garin Kaduna gaisuwar mutuwa muma kuma munyi hatsari mun mutu, kar kaga na tara y'ay'a da jikoki kayi zaton kona shirya ma zuwan mutuwar ne duk da dai ita ba shiri ake mata ba amma dai zanso in k'ara mik'a takwarata d'akin mijinta a karo na biyu dan nidai ba takai nikeyi ba atoh yanzun idan tsautsayi ya gifta ai shi kenan sai ayi d'a kwance uwa kwance gara nima na bar baya ku kofa? " "Yi hak'uri Hajiya insha Allahu lafiya lau zamu isa, kuma aure ba namu ba har yaran mu sai kin aurar Allah dai ya k'ara miki lafiya Hajiya ta" Maida motar yayi kan titi sukaci gaba da tafiya, kin yarda ta k'ara bashi naman Meenal tayi har saida yayi mata alkawarin cewa bazai k'ara cizon taba, a hakan ma sai taci a kalla sau uku kafin ta bashi sau d'aya lemun da, da yike ta zura mishi stro a ciki shi da kanshi yake ja yana sha, A haka suna tafe suna hira har suka isa kawo, "Wani unguwa ne gidan nata yake?" "Unguwan Dosa ta can k'asa wajen yan majalisu" Ta bashi amsa, Juyawa yayi gefen Hajiya, "Hajiya nace a can gidan gaisuwar zaku sauka gaba d'aya ko in munyi gaisuwar zamu wuce can gida nane ku sauka a can in yaso gobe ko ban samu damar mai daku gidan gaisuwan ba ita sai in bata mota ta dunga kaiku da safe in dare yayi sai ku dawo, ina ganin kamar hakan zaifi duba da yanda gidan zai cika da mutane nasan zaku fi sakewa a gidana ko ya kuka gani?" "Eh to kuma kaima dai ka kawo shawara amma dai bazanyi saurin yanke hukunci ba sai mun isa tukun idan naga da takura anan din ai sai mu bika d'in" "Nidai Hajiya bazan je ko ina ba gaisuwar mutuwa fa mukazo shine kuma za'ace muje wani unguwan mu tare idan gidan nashi kuma yana da nisa fa sai dai inke ce zaki koma can gidan nashi ki tare ke kad'ai?" "In yana da nisa baga mota ba ko dama a k'afa nace ku taka ne?" Hajiya ce ta amshi maganar da cewa, "Nima shi yasa kikaje nace ya bari har muje mu gani in wajen yana da yalwa ai sai muyi zaman mu, nasan dai shima dan yasan bana son takura ne shi yasa yace mu sauka a gidan nashi amma inda nisa ai sai mu hak'ura" "Balle kuma ba wani nisa Sosai fa Hajiya ina unguwan dosa ina Malali? kedai bakauya ce kawai tunda ba wani sanin garin kikayi sosai ba kifin rijiya kawai baki san ko ina ba daga Zaria sai Zaria yaushe rabon daki k'etare zuwa wani wajen, yarinya kizo in bud'e miki ido kiga yanda ake wayayyar rayuwa ba irin wacce kika saba gani ba" "Eh d'in koma mai zakace" Suna kawo wa dai dai chawai na SMC akan titin unguwan dosan, Meenal ta fara cewa, "Stop! Stop!! Dan Allah ya'ya ka tsaya" "Ke meye wai kuma? Me zakiyi in mun tsaya anan?kefa kin cika fitina kamar sauro wallahi " Sai da ta karkata jikin ta tana waiga baya kafin ta amsa mishi da cewa, "Dan allah kad'an koma baya kad'an, kaji wallahi chips din wajen nan nike mutuwar so, shuuuu " Sai kuma taja iska tana bubbud'e kofofin hancin ta, "Dan Allah kai bakaji yanda kamshi ya cika maka ciki ba?" "Idan naji kamshin kuma sai mai ya faru? Naga dai yanzun yanzun kika gama ciye ciye balle kice min yunwa kikeji, in ma kin siya kafin ki samu lokacin da zaki zauna kice zakici aiya riga ya huce bazakiji dad'in cinshi ba zafiba kuma, in kina sone ki bari sai anjima ni zan dawo in siya miki harda kaza da kifi ma duka in kina so" Yayi maganar yana ci gaba da tafiya, "Kayi alkawari zaka siyamin d'in?" "Aike bakuwata ce dole in siya miki duk abunda kika gani kina so akwai wani waje ma a can Unguwar Sarki inda suke saida ice cream mai shegen dad'i wallahi, nasan zaki soshi sosai da zarar kika d'and'ana" "Waiyo Allah dan Allah Ya AK ka kaini, kasan yanda nake bala'in son ice cream kuwa balle wannan tunda naji ka yaba nasan zaiyi dad'i" "Ai yarinya dan ma ba'a gidana zaku sauka ba dana kaiki yawo kinga yanda cikin garin kaduna take da kayan dad'in da suke dashi naci wanda babu shi a kauyen ku" "To ai Hajiya tace in munga akwai takura can gidan naka zamu bika, kaga idan mukaje gidan gaisuwa da dare idan mun dawo sai ka Kaini yawon koh? , Kuma shine harda wani cema Zaria kauye koh? Allah ma yasa kaima can ka fito" Dariya yakeyi k'asa kasa, a zuciyar shi ko dad'ine ya rufe shi dan da alama hak'ar shi zata cin ma ruwa kamar yanda yake fata, "Dan Allah ya AK ka dunga dariya in kuma dariyar ke maka wahala ko murmushin ne ka dunga yi, Allah sosai yake maka kyau in kanayi" "Oh shi yasa bakya gajiya da kallona kenan?" "Nidai ai bance maka haka ba kawai dai na fad'a maka gaskiya ne cewa murmushi na maka kyau" "To tunda kina so zan dunga miki nawa murmushin amma da sharad'i idan na miki murmushin kema zaki min naki murmushin dan naki yafi nawa kyau" "Eh ai nima na fika kyau shi yasa nafika iya murmushi ma, Yaya kaga kana ta jana da surutu saura kad'an mu wuce layin koh! " "Ina ne layin nasu?" Ya tambaya ita kuma ta nuna mishi suka sulala cikin unguwan, A wannan lokacin zan iya cewa daga shi har ita sun manta da zaman Hajiya a cikin motar barin ma dai shi , domin labari kawai suka ci gaba dayi yana bata labarin yanda garin na Kaduna yake da wajajen hutawan da suke cikin cikin garin da alkawarin cewa duk zai kaita wajajen d'aya bayan d'aya kafin su koma, Su zauna a waje d'aya irin haka na tsayin awanni ace basu yi fad'a yanda suka saba ba sai ma hira mai dad'i dake gudana a tsakanin su, wannan shine na farko, Kila kuma hakan nada nasaba da kasancewar wannan d'in shine tafiya na farko da suka tab'ayi a cikin mota d'aya a tare, Tun bata ce mishi nan ne gidan ba ya gane gidan, saboda canopy da kujeru d'in dake kofar gidan ga kuma mutane nata d'aura alwallah dan tuni aketa ta kiran Sallah a masallatai, gefe ya nema shima ya faka nashi motar kamar yanda yaga motocin wasu a wajen, "Alhamdulillah "Hajiya ta ambata bayan ya faka, Kallon kallon aka fara tsakanin shi da Meenal, Meenal din ce tayi k'asa da muryar ta sosai tana d'an kwantowa ta inda yake, "Kai Yaya ashe fa tare muke da Hajiya a cikin motar nan wallahi na manta da ita sam" Fashewa yayi da dariya "Aiko sai na fad'a mata" shima ya fad'a murya can k'asa kamar yanda tayi. "Kana fad'a mata wallahi bazanje gidan kaba" ita kuma ta fad'a tana turo baki kafin ta janye jikin ta ta fita daga motan, shima fita yayi ya bud'ema Hajiya kofa, Ita dai Hajiya yau take ganin ikon Allah, Wato dai da kad'an da kad'an maganar da Yusuf ya fad'a matane yake k'ara rikediwa zuwa tantagaryar gaskiya ganin idon ta, To aiko ido zata zuba musu taga iya gudun ruwan mutum dan uban shi ai in yasan wata bai san wata ba, wato ita ya raina zai wani ce mata yarinyar fa k'arama ce bayan gashi a gaban idon ta ba kunya balle tsoron Allah ya tsare yar mutane har tana bashi abinci a baki, daga baya kuma ya b'ige da cewa ko zasu sauka a gidan shi, Aiko sai tayi maganin shi wallahi tunda yayi da maiyi, Baibi su zuwa cikin gidan ba anan wajen yayi alwallah ya shige masallacin dake kofar gidan shima dan ya samu jam'i, Su kuma cikin gidan suka wuce, tun daga harabar suke gaisawa da mutane, "Ina ne Sashen Raheenat d'in?" Hajiya ta tambayi Meenal ganin gidan ya kasu sashe sashe, "Gashi can wancan na ukun mai fenti mai ruwan toka" "To ai gara mu k'arasa koma samu mu gabatar da sallan muma akan lokaci kinga in mun idar sai mu d'aura da gaishe gaishen dan in muka tsaya gaisuwa da jama'a tofa har sai a kira ishsha'i bamu gama ba" A kofar falon nata sukayi kicibus da Innar yara wacce ke shirin fitowa, "Ah ah Hajiya kuna tafe ashe, barkan ku da zuwa hala takwarar kice ta matsa kuka taso da yamman nan?" "Ah ah wallahi Ameena ai da dan tani ne da tuni ma ina garin to sanda labarin ya iskeni ita kuma tana makaranta bata kuma dawo da wuri ba, ya mukaji da k'arin hakuri ya mai jegon kuma? Tana dai lafiya koh" "Hakuri sai mai aiki mai jego kuma Alhamdulillah suna lafiya su duka ita da Babyn ku shigo daga ciki" Bayan ta suka bi zuwa cikin Sashen dake cike shima da matan tun daga kan yan uwan Aunty Murja Maman Raheenat d'in zuwa kan sirikan gidan Malam din su Aunty Billy matar ya Sa'eed Matar Farooq Yayan Meenal d'in dama sauran Matan yayyen Meenal din da wasu daga cikin yaran Malam mata suma, A tsai-tsaye suka gaisa da mutanen falon hajiya bata yarda ta zauna ba sai fad'i take a nuna mata inda zatayi Sallah, D'aya daga cikin d'akuna ukun dake falon Innar yara taja Hajiya, dan lokacin Mommy Hauwa tana Sallah itama, D'aya bayan d'aya Meenal ta gaishe da yan uwanta mata dama matan yayyen nata suka ma juna gaisuwar rashin, "Mai jegon tana ina?" Meenal ke tambayar su, Farida matar Farouq ne ta amsa mata da cewa, "Tana cikin wancan d'akin"ta karashe da nuna mata d'akin da take nufi d'in, Mikewa Meenal tayi zuwa d'akin babu mutane sosai a ciki daga Mommy Hauwa sai Matar malam na biyu Dije dake rik'e da jariri ita kuma Mommy Sallah takeyi, Karasawa inda Dijen ke zaune tayi bayan tayi Sallama dijen ta amsa,sai da takai zaune a gefen gadon dijen ke tambayar ta " yanzun kuka iso", ita kuma ta amsa mata da, "Eh" tana amsar yaron, dan kyakyawa abunshi sai saiyi yakeyi kamar zai bud'e ido sai kuma ya koma ya rufe, Tausayin shine ya kamata har idon ta ya cika da kwalla, Gaisawa sukayi da Dijen tayi mata gaisuwa kafin ta tambayeta uwar yaron, "Tana cikin makewayi" cewar Dijen, Yaron na rik'e a hannun ta har Mommy ta shafa add'o'in da takeyi bayan ta idar da Sallah, Sabon gaisuwa sukayi itama Meenal d'in tayi mata gaisuwa, "Ina ita Hajiyar take na ganki ke d'aya?" Momy ta tambaya, "Tana tareda Innan mu a wancan d'akin dake kusa da wannan" Mik'ewa Mommy tayi ta fice daga d'akin bayan ta nad'e daddumar da tayi sallan ita kuma Meenal taci gaba da zama yaron rik'e a hannun ta tanaci gaba da kallon shi, Jin motsin bud'e kofar toilet din da Raheenat tayi ne yasata d'ago kanta da sauri sai kuma ta mik'e da sauri ta d'aura ma Dije yaron akan cinyanta ita kuma da hanzari ta k'arasa wajen Raheenat din suka rungume juna Raheenat din kuma sai ta fashe da kuka saboda ganin Meenal din, Mai makon Meenal din tayi aikin rarrashi ah'ah sai itama ta biye mata sukaci gaba dayin kukan, "Amma dai kun san wannan ba abun kwarai kukeyi ba koh, ke dama Meenal zuwa kikayi dan ki sata kuka ne kome, ke kuma Raheenat tun safe fa kike kukan nan amma ace mutum ko gajiya da kukan bayayi, ai ko dad'ewar da kikayi a cikin bayin nasan zuwa kikayi kikasha kukan shi kafin kika fito, fisabilillahi in kuka na dawo da matacce ai duban nin mutane ne zasu dawo duniya bayan sun mutu suci gaba da rayuwa kuma, ki saketa tazo ta zauna taba yaron nan Mama tun bai fara kuka ba, bawan Allah dan ma ta same shi mai hakuri tunda ya fad'o sau biyu kawai fa kika bashi abincin shi" Sababin da Dije keyi shi yasa Meenal ta sake Raheenat din bawai dan taso ba, tana share mata hawayen ta da sukak'i tsayawa, kafin ta kamo hannun ta ta zaunar da ita a gefen gadon itama ta zauna, "ya kikeji a jikin ki akwai inda yake miki ciwo ta ciki ko ta waje?" Meenal ta tambaya, Girgiza mata kai Raheenat din tayi alamun ah ah, "Babu inda yake miki ciwo?" "Babu kirjina ne kawai yake d'anyi min zafi kad'an kad'an" "Sannu kiyi hakuri kinji, amma kinci abinci?" "Meenal ban iyacin komai baki na ba dad'i ko yunwa ma banaji" "Kuma dai kin san bazai yuwu ki rayu da yunwa ba, Mama Dije ki had'o mata tea da abinci taci yanzun dan Allah inta gama sai tasha magani ta kwanta" To Dijen ta amsa dashi tana mik'ewa ta fice daga d'akin ita kuma Meenal ta zauna taci gaba daba Raheenat din baki wacce keba yaron Nono har ya koma bacci, Bata tashi ba sai da Dijen ta dawo da abincin kamar yanda Meenal ta buk'ata sannan ta amshi yaron ta kwantar, Sai da Raheenat ta shanye tea din ta faracin abincin kafin Meenal ta shiga toilet tayi fitsari kana kuma ta d'auro alwallah ta fito ta tada Sallah bayan ta idar bata tashi ba har saida ta gabatar da sallar ishsha'i Hajiya ma kuma ta shigo tayi ma Raheenat d'in gaisuwa, AK ma ya shigo har cikin Sashen na Raheenat din yayi gaisuwa tareda su ya Sa'eed da Farouq da suka had'u bayan sun fito daga masallaci. *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [8/29, 10:40 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 15* Tunda suka shiga cikin falon yake ware ido yaga ta inda zai gano Meenal ko Hajiya sai dai dukan su babu wacce ta fito falon ya daiyi ma mutanen falon gaisuwa Mommy Hauwa ma dake d'aya d'akin da Hajiya take ta fito sun gaisa itama ya mata gaisuwa Raheenat d'in ma ta fito sun gaisa, Bayan sun fito daga sashen na Raheenat gefe suka koma k'arkashin canopy d'in dake harabar gidan suna ci gaba da hira dan tunda aka idar da ishsha'i yan zaman gaisuwan suka watse sai ya zamana saura yan gidan kawai, D'aya bayan d'aya matan su Ya Sa'eed suka dunga fitowa sunayin sallama da mazajen su, sai yayi yunk'uri kamar yace su taimaka su kira mishi Meenal sai kuma ya k'asa suna zaune a harabar gidan har karfe 10 na dare ya gota su Ya Sa'eed suka fara haramar komawa masaukin su, dan haka tare suka fito daga cikin gidan dasu Ya Sa'eed d'in sai dai su suna fitowa sukayi Sallama dashi suka shiga motocin su suka wuce masaukin su duk da ya musu tayin zuwa can gidan shi amma suka nuna mishi a'ah karya damu, Bayan wucewar su shima cikin motar shi ya koma ya kwantar da kujerar motar ya kunna ac sannan ya sanya karatun qur'ani a radio din motar yana bi da sauti mara amo, Lokaci bayan lokaci yake duba wayar shi a zaton shi wai ko hajiya zata tab'o shi suyi haramar wucewa suma tunda dare ya farayi sai dai kuma shiru, Sai ya d'auki wayar da niyyar ya kirata kuma sai ya fasa, Can dai daya kasa sukuni ganin ana neman k'arfe 11 sai kawai ya maze ya lalubo number d'in nata ya doka mata kira, D'in din din wayar taci gaba da k'ara sai dai kuma harta yanke ba'a d'aga kiran ba, bai gajiya ba haka yaci gaba da danna mata kira ba k'ak'kautawa amma sai da ya mata kira 6 babu wanda ta d'auka, Ajiyar zuciya ya sauke mai zafi, To me ya samu Hajiya haka kardai ace hartayi bacci ne ta barshi a kofar gidan mutane ya dakon fitowar su, Yau rana ta farko da yayi abunda bai tab'ayi ba, Number d'in Meenal wacce ya dad'e da adanata a cikin wayar shi ya lalubo, ya dad'e yana k'arewa number d'in kallo wacce yayi saving dinta da emoji mai shape d'in 💞 heart, Ya dad'e yana jayayya tsakanin shi da zuciyar shi, wannan tana fad'i mishi cewa ya kirata kawai dan wannan shine damar da yake dashi na samun kusanci a tsakanin su, yayin da wata zuciyar kuma take ce mishi yayi hak'uri kawai ya wuce ya tafi tunda dare dai ya riga yayi in yaso ai gobe ma rana ce, sai yasan yanda duk zaiyi goben dan yaga sun koma can gidan nashi da kwana, Sai dai kuma a kokarin shi na fita daga kan number d'in nata kuma kawai sai yayi dialing number din ba tareda ya luraba har saida kara d'in d'in d'in da wayar take alamun cewa kiran yaje kan nata wayar ne ya ankarar dashi, Da azama har wayar na neman kub'ucewa daga hannun shi yayi saurin yanke wayar yana sauke ajiyar zuciya kamar wani wanda ya had'u da abun tsoro, bai gama dai daita kanshi ba wayar nashi ta fara k'ara, k'ur yama wayar domin kuwa Meenal d'ince ta biyo bayan nashi kiran, Kamar bazaiyi picking kiran ba sai kuma can dai kiran na gabda katsewa ya runtse idanuwan shi ya amsa kiran nata ba tareda yakai wayar kan kunnen shiba sai kawai ya sata a speaker, "Assalamu Alaikum" Tayi sallama daga gefen ta bayan ya d'auki wayar, "Ameen Alaikum Salam, baku gama bane wai dare yana yifa kice ma Hajiya ku nike jira ina waje a inda mukayi parking d'azun" Yana gama fada mata hakan yayi saurin yanke kiran ba tareda ya tsaya sauraren amsar da zata bashi ba, dan Allah ya sani bazaiso yaji cewar bazasu bishi zuwa nashi gidan daga bakin taba, Ita ko ata gefen ta bayan ta idar da Sallah Maryam da Meelat ta kira a waya ta had'asu da Raheenat sukayi mata gaisuwa, Ta dad'e zaune tare da Raheenat d'in a cikin d'akin dan ko lokacin dasu AK d'in suka shigo sashen tana jin shigowar su bata daiji fita zuwa falon bane shi yasa kawai tayi zaman ta bayan fitan su kuma cika d'akin da suken yayi da yayyin su mata nan kuma sabon hira ya b'arke akan mutuwar auren ta, da yike yawancin su tun bayan mutuwar auren nata basu had'u ba, Kun san mu mata ba gidan mutuwa ba yasin ko cikin mak'abarta ne sai dai in hirar bata zoba amma sai anyi, To hirar mutuwar auren Meenal d'in shi ya rage jimamin mutuwar da suke ciki aka cigaba da tattauna batun ko wacce a cikin su na tofa albarkacin bakinta daga masu ganin laifin Sarki sai masu ganin laifin Teemah, Itafa gaba d'aya ma wallahi ta manta da batun cewa wai zasuje gidan AK dan tunda suka iso ita da Hajiyan kowa nashi sabgar kawai yakeyi, Bata tashi tunawa ba sai da ta kira, koda ya kirata tana cikin yan uwanta suna hira ita kuma dama bata tab'a saving number din shiba shi yasa koda ya kirata bata san shi bane ganin dai cewa kiran ya katse shi yasa ta biyo bayan kiran dan taji ko waye kuma duk hirar da sukeyi ita bata san dare yayi sosai har haka ba, Koda ya gama rattafa mata abunda zai fad'a ya yanke wayar, bata wani damu ba sukaci gaba da hirar su ita da yan uwanta, dan rabon da su had'u a waje d'aya irin hakan gaskiya an dad'e tunda ko biki sukeyi a gida duk wacce tazo d'akin uwarta take sauka sai dai a had'u a tsakar gida amma yau gasu kusan su duka dan ma wasu basu samu isowa ba sai gobe wad'anda suke kusan ne dai yau suka samu isowa, Ita ko Hajiya a gefen ta tun bayan data idar da Sallah ta fito daga d'akin suka k'ara sabon gaisuwa da mutanen dake sashen har zuwa sanda Mommy Hauwa da Innar yara suka mata jagora suka shiga sashen sauran matan gidan suma suka musu gaisuwa bayan sun dawo kuma cikin d'akin da aka sauke tan ta koma aka gabatar mata da abinci taci, Duk abunda akeyi tana ta lura dan ta kirga d'akunan dake cikin sashen d'akuna ukune a kalla kuma mutanen dake cikin sashen mata wad'anda tasan kwana zasuyi kun kusa ashirin ko fin hakan ma banda yaran su, to idan dare yayi wani irin kwanciya za'ayi har aji dad'in bacci shi take ta lissafi, Sai dai bazatayi saurin bada kaiba tunda ita ba yarinya bace ta gane cewa shima daya gayyace sun zuwa gidan shi yana da nashi dalilin dan haka shiru zatayi tukun, duk zaman da takeyi lokaci lokaci take kallon agogo taga ko zai kirata, kuma itama koda ya biyo ayari suka shigo falon tsaf taji shigowar nashi kuma bayan Jidda ta shiga wajen tama ta k'ara jaddada mata cewa AK ya shigo ya musu gaisuwa dan ita Jiddan ma bata san cewa shine ya kawo suba tayi zaton ko da motar Meenal sukazo har sai da Hajiyar ta sheda mata cewa ai shine ya kawo su tukun, Ganin cewa Meenal bata neme ta shi yasa ta share batun duk da dai ta yanke cewa idan 11 tayi taga bai kiraba kuma Meenal bata tada maganar ba ita zata kira shi dan gaskiya tasan in tace ta kwana a gidan bazata sake ba, in yaso ita sai ta bishi Meenal din ta zauna tunda ita zata sake a cikin yan uwan ta, Sai gashi tun sha d'ayan bata buga ba da yaji shiru shi ya kirata, kuma duk kiran da yake mata tana kallo tsaf sai dai kuma itama sai ta wana shi kafin, Haka yaci gaba da zama a cikin motar yana duba lokaci daga kan minti d'aya sai gashi anci kusan mintuna 15 ba Hajiya ba Meenal, kamar ya tada motar yayi tafiyar shi dan yasan da gangan yarinyar nan ta shanya shi sai kuma dai ya daure ya k'ara ba zuciyar shi hak'uri ya danna ma number din nata kira a karo na biyu, Wayar bata dad'e tana k'ara ba ta d'auka, "Bakiga Hajiyan bane wai ko ya akayi ne kun shanyani a waje sai jira nikeyi duk mutane sun gama watsewa ko baku san dare yayi bane?" "Umm nifa bazan bika ba anan zan kwana sai dai ko ita Hajiyar ne zata bika," "Oh kenan ma d'an iska kika maida ni tun dazun dana kiraki ma baki fad'ama Hajiyan sakon ba," Mtwss yaja tsaki mai tsayi bayan ya yanke wayar dan ranshi fa ya fara baci yanzun kam, A bayyana ya furta, "Kunga abinda nike ta gudu tun tuni kenan koh, Soyayya da kana nan yara, to ita wannan ma tun ban furta mata cewa ina son ta d'in ba tasan ta shanya ni a waje kamar wani dan iska anya yarinyar nan duk ranar data gane ina sonta ba sai ta mai dani sakarai ba kuwa?, ina ma amfanin haka gaskiya soyayya bata min adalci ba miye haka mutum duk yabi ya susuce," Hannu shi ya d'aura a saman kai ya yamutsa gashin kan nashi yana fesar da huci mai zafi, "Wai yarinyar nan nufin ta duk zaman da nayi a wajen nan zai tashi a banza ne? Lallai ma naki wasa ne Wallahi baki isa ba, Allah yasa nima ina da gata a cikin gidan bari ma ki gani" Ya fad'a yana d'aukar wayar shi ya lalubo number din Mommy Hauwa, Babu b'ata lokaci ko ta dauki wayar da sallama, "Aunty nace dan Allah kiyi ma su Hajiya magana su fito haka nan mu wuce dare yayi, na kira number din Hajiyar bata d'auka ba ban sani ba ko tabar wayar nata a cikin jaka ne kin san halinta kilama ta manta dani ne" Ya d'aura da cewa bayan ya amsa Sallamar na Mommy Hauwa, "Ayya kayi hakuri bayi in mata magana zasu fito yanzun babu mamaki kam in akace maka Hajiya manta tayi" Ta fad'i hakan tana kallon Hajiyar, Shi kuma daga can gefen yanke wayar shi yayi hankali kwance dan yana da tabbacin cewa wannan aikin kuma ya kammala ba Hajiya ba har ita d'ayar mara kunyar saita fito, dan haka sai yama kawai ya tada kujerun motar daya kwantar ya gyara parking din motar zuwa dai dai bakin gate din gidan ta yanda suna fitowa shiga kawai zasuyi, Maida kallon ta wajen Hajiya Mommy Hauwa tayi bayan ta gama magana dashi, "Hajiya ina kika ajiye wayar ki hala?" "Me ya faru kike tambayar wayata?" Hajiya ma ta tambaya kamar bata san akan me zatayi magana ba bayan taji komai na kiran da AK din yama Jiddan, "Mai Jama'a ne ya kirani yanzun ashe tun tuni yana kofar gida yana jiran fitowar ku, ai dai ya kyauta wallahi da bai wuce ba, dan dama ina ta tunanin yanda za'ayi bacci a sashen nan yau, gashi har daren ma yayi, yace ya kiraki ba'a d'auka ba shine ya kirani ai gara kuje can d'in zakifi sakewa ma, ai dama kayan ku yana cikin motar koh naga baku shigo nan dashi ba?" "Ke barshi kawai ai dare kuma ya riga yayi kirashi kice nace yaje kawai saida safe zamuyi kwanan mu anan, ai dama ba munzo jin dadi bane" "Ah ah Hajiya dan Allah kuje kawai tunda har Allah yasa bai tafi ba koni ai dan dai kar aga mun kwasa duka mun tafine da nima binku zanyi can din, bari in kira Meenal itama tunda ta iso suna can sun kule d'aki sai hira suke kamar ba'a gidan mutuwa suke ba, " Jidda bata fito a d'akin ba sai da ta taso Hajiya a gaba suka fito a d'akin a falon suka had'u da Meenal wacce sai yanzun ne ta fito da niyyar zuwa ta isarma Hajiya sakon AK din, "Yauwa gara da kika fitoma muje Kunbar min d'a acan waje yana jiran ku ga dare yayi" Cewar Mommy Hauwa, "Mommy nifa anan zan kwana ai na fad'a mishi sai dai Hajiya ta bishi" "Ke dallah can ban son maganar banza, ita Hajiyar ce zata tafi can din ita d'aya ina ce tare kukazo dukan ku, wuce ki d'auko Jakar ki ki fito ku wuce dare na k'arayi" Badan Meenal taso ba haka ta koma d'akin ta d'auko jakarta ranta a b'ace, lek'awa d'akin itama Hajiya tayi dan yin Sallama da mutanen cikin, Sai da suka rakasu Hajiyar har bakin motar AK din dake kofar gidan, gidan baya Hajiya ta zauna kamar lokacin da sukazo, Meenal ma gidan bayan ta bud'e zata shiga Mommy Hauwa ce ta hanata da cewa, "Shi din driver din gidan ku ne da kema zaki koma baya ki kame ku barshi da tuk'aku? Dallah koma baya keda baki san abun arziki ba" Simi simi ta wuce ta bud'e gaban motan ta shiga ran nan nata a bace, sallama suka musu suka juya cikin gidan shi kuma yaja motar suka bar kofar gidan ranshi fess duk da yana ganin yanda Meenal d'in ke ta faman b'ata rai baibi ta kanta ba tuk'i kawai yaci gaba d'ayi, Kamar yanda yayi alqawari sai da ya koma ta chawai ya siya musu chips din da Meenal tace tana so da kazar sannan sukaci gaba da tafiya, shida zai d'auke hanya zuwa malali kawai sai ya mik'e zuwa unguwan Sarki koda ya isa inda suke siyar da ice cream din bai tayama Meenal shiga wajen ba fakawa yayi yaje ya siyo musu ya dawo motar ya k'ara bata wuta suka koma daga baya zuwa Malalin, Sai da yayi ta yawo dasu akan tituna kafin ya d'auke hanyar gidan shi, daga Hajiya har Meenal dai babu wacce ta tanka mishi a cikin su dan ita Hajiya dama tunda ta shigo wayar take amsa wayar Baba Usman dan haka bata damu da sanin ina yake kaisu ba sai dai in taga ya tsaya ta d'ago taga inda suke taci gaba da wayarta, Ita ko Meenal duk da cewa a cikin zuciyar ta taji dadin yanda ya cika mata alkawarin daya dauka taji dadi amma sai ta fuske abunta taci gaba da hura hanci duk da dai daurewa kawai take amma wallahi ta matsu su isa gidan nashi kafin ta bada kanta sakamakon kanshin chips dana kazar da suka mamaye cikin motar basar wa kawai takeyi amma da lafiya lau ne tabbas da tun a cikin motar zata fara aikasu zuwa masaukin su, "Bieeee" din daya danna ne ya dawo da hankalin ta kan kofar gidan da yake tsaye saboda tunda suka shigo cikin layin take faman bin gidajen layin da suka shigo din da kallo, gidaje a tsare lafiyayyu wanda kai bawa ko baka tambaya idanuwan ka ne zasu shaida maka cewa unguwan bana yaku bayi bane, dan gidajen sun jeru ne wannan yana wane wannan dan kyau, Waigawa tayi dan ganin ko Hajiya ta lura da abunda ita take kallo sai taga Hajiya ko a jikin ta hirar ta kawai takeyi, Sulalawa da motar yayi zuwa cikin gidan bayan an bud'e mishi gate d'in, Tun kafin ya faka take faman k'arewa gidan kallo, Hajiya dake bayan motar ita ta fara fita ba tareda ta jira ya bud'e mata kofa ba wannan karan, Mutuniyar ko sai da ta kwamuso ledar kaji dana chips din ta kafin ta fito daga cikin motar. [8/30, 3:18 PM] zainabusmanummiee584: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *BOOK 2* *PAGE 16.* Shiko AK bayan ya faka motar baya ya koma zuwa wajen mai gadin dake bakin gate ya na ta kokarin kullewa, "Assalamu Alaikum Malam Mansoor barkan mu dare fa ya gida?" Ya fad'a yana mai dafo kafad'ar Mansoor d'in bayan ya bashi hannu sunyi musabaha irinta maza, "Alhamdulillah Ranka ya dad'e barka da dawowa, ai ina ta zuba ido tun bayan da muka gama waya da kai sai kuma naji shiru, wallahi kaga yanzun hakan ina batun in kiraka a wayane inji ko dai ka fasa dawowa yau d'in ne sai kuma gaku, to barkan ku da isowa fa dafatan an baro mutanen gidan lafiya ya hanya kuma? " "Alhamdulillah ai mun ma shigo garin tun d'azun wallahi dan a cikin Unguwan Dosa ma muka gabatar da sallan Magriba da yike rasuwa akayi mana a can d'in, mu k'arasa ku gaisa da Hajiya tare muke dasu anan zasu dunga kwana kafin su tafi" Ba tareda ya saki hannun Mansoor din ba sukaci gaba da tafiya har suka isa bakin kofar dasu Hajiya ke tsaye suna jiran ya k'arasa ya bud'e musu kofar,ita dai Meenal tunda ta fito daga cikin motar take ci gaba da bin gidan da kallo, ba wani wargajeje bane wajen girma sai dai kuma gaskiya ya tsaru dan sosai ya d'auki hankalin ta sai faman kalle kalle take duk kuwa da cewa dare ne amma kana iya ganin komai da aka kawata gidan dashi a zahiri sakamakon kwayayen wutar lantarkin da suka haska gidan, Har k'asa Mansoor din ya duk'a ya gaishe da Hajiya ta kuwa amsa mishi cike da kulawa, Meenal dai bata jira ya gaisheta ba ita ta fara gaidashi dan ko babu komai ya girme mata nesa ba kusa ba, AK ne ya bud'e kofar suka shige ciki shi kuma mai gadin ya musu sai da safe ya koma, A falon gidan dukan su suka zauna, "Wash Allah na gaji wallahi" cewar Meenal a yayinda takai kwance, "Ai zaki gaji kam daga dawowa makaranta baki ko huta ba mun kamo hanya sannu ki samu kiyi wanka da ruwa masu dumi kafin kiyi bacci sai kiga kin warware koda gari zai waye bazakiji gajiyar a tare dake ba" Cewar Hajiya, "Hajiya d'an wannan tafiyar ne har kike cewa sai tayi wani wanka da ruwan zafi? Nida na d'auko hanya mai nisa na taho abinci ma a daddafe aka bani shi naci ga kuma shanyani da kukayi a kofar gidan mutane bayan na tuk'o ku daga Zaria zuwa Kaduna ko sannu baki min ba, ai dama na lura wallahi tunda yarinyar nan ta koma wajen ki kika dena tunawa ma kina dani, ni kuma na kasa zuciya in gyale ku keda itan nima in koma inda za'aji dani! " Ya k'arasa fad'a rannan a had'e shi a dole an mishi ba dai dai ba, Dariya Meenal ta fashe mishi dashi harda kyakyatawa tana nuna shi da yatsa, "Kai amma wallahi Allah taubashi kana da abun ban dariya, to wai dama kishi kakeyi dani ashe ban sani ba" Juyawa gefen da Hajiya take tayi tana ci gaba da dariyar nata take cewa, "Hajiya to ga autan kinan fa yana kishi dani dan Allah shima kice mishi inyaje bacci yayi wanka da ruwan zafi saboda kar gobe ya kasa zuwa masallaci sallan asuba saboda tsabar gajiya, kujimin fa Babban shi dashi wai yana kishi dani, to ma ce maka akayi dama kai kad'ai Hajiyar tafi sone?" Murmushi kawai Hajiya keyi tana binsu da kallo, Shiko cewa yayi, "Hajiya kina kallon ta koh a gaban ki fa take min rashin kunya amma bakice komai ba yanzun kuma idan nace zan tattaka ta kice na fiye cin zalin, to ai shi kenan Hajiya muje ki kwanta" Ya fad'a yana mikewa, "Toni me kuke so ince bayan d'azun ina kallon ku kuke ta hirar ku kun ma manta dani a cikin motar gaba d'aya sai yanzun ne zaku zo kuna wani yimin kurari, to wallahi ku kiyaye ni" Tsaye yayi cak shida Meenal suna kallon kallo, "Hajiya waye yace miki mancewa mukayi dake a cikin motar?" Meenal ta tambaya, "Ke dallah rabu dani nikam in dai kuna abunku ku dena sakoni cikin sirmen ku na fad'a muku, Shiko ledojin ya kwasa, "Hajiya muje kici abunci kinji kiyi wanka sai ki kwanta dare yayi fa kuma nasan gobe cewa zakiyi zaku wuce gidan gaisuwar da wuri" "Kai ni kyaleni da wani ciye ciye yanzun da daren nan ita dai data sakayin siyayyar sai tayi ta fama ni na riga naci tuwon dare na koshi kuci naku ku ajiyemin nawa in Allah yasa muna da rayuwa zan karya dashi da safe, ka koma ka ciro min kayana a bayan motar ka in canza wadannan na jikin nawa" "To muje in raka ki d'akin" Ya fad'a bayan ya ajiye ledojin, Gaba Hajiya tayi shi kuma yana take mata baya Meenal kuma na gefen shi suna jerawa sai wani uban d'age takeyi a dole wai so take ta jera tsayin ta da nashi, girgiza kawai yakeyi idan ya kalketa batareda yace da ita komai ba har ya isa d'akin dake gefen nashi ya bud'e musu kofar suka shiga, d'akine madaidaici wanda yake d'auke da set din gado 6 by 6, dukan su suka shiga cikin d'akin wanda ke gyare tsaf an lailaye gadon da zani mai kyau d'akin sai tashin kamshi yakeyi, gefen gadon Meenal ta zauna ita kuma Hajiya cikin makewayi ta shige kai tsaye, Juyawa yayi yabar d'akin bayan hajiya ta shige, ita kuma Meenal din sai ta biyo bayan shi tana cewa, "Matar gidan bata nan ne Autan Hajiya?" Kuji wani tambayan neman magana fa wajen yar gidan Malam fisabilillahi, Shiko ba tareda ya tsaya daga tafiyar da yake yiba ya ansa mata da cewa, "Dama akwai wata matar gidan ne bayan wacce tazo yanzun?" Shima ya tambaya, "Wacece tazo yanzun kuma? Oh Hajiya wai kake magana? " "Wacce take magana mana dai" "Tab badai niba kam" Kara sauri tayi ta cimmashi sukaci gaba da jerawa, Kafin tace "Allah taubashi gidan ka ya min kyau masha Allah, komai Cass wallahi Allah yasa a mora," "Duk kyan shi ai bai kai naki gidan da kika baro kyau ba koh?" "Aini wancan gidan ba nawa bane na maishi ne baga shi na baro can d'inba kuma wata ce zata maye gurbina, nifa kasan idan abu yamin kyau bana ma mutum hassada sai na fad'a wallahi shi yasama ban tab'a maka hassadar kyan da Allah ya maka ba sai dai ina danjin haushi kadan fa wani lokaci" Tsayawa yayi cak ya juyo yana kallon ta, Giraren ta duka biyun ta d'age mishi tana wani fari da idon ta, "ya akayi ne?" Ta tambaya tana ci gaba da kallon shi, "Yarinyar nan zata k'arar min da ruwan kai" ya fada kasa sosai ta yanda bazataji me yace ba, dan Wallahi yanda take dage gira da fari da idon nan ji yakeyi kamar ya wafto ta ya cusata a cikin jikin shi ko zai samu nutsuwa, "Muje mana ka tsaya kuma" ta furta ganin yayi tsaye sai faman binta da kallo yake shi baiyi gaba ba kuma baiyi baya ba, Maganar da tayi shi ya dawo dashi cikin hayyacin shi, Taku d'aya biyu yayi ya matso dab da ita kamar zai had'e jikin su waje guda sai kuma ya dakata ya d'an koma baya kadan duba da irin kallon da take mishi, "To me yasa kike jin haushi na dan ina da kyau? Bayan nima kyan tashi nayi na ganni dashi bani ne na zab'arma kaina kasancewa cikin maza masu kyauba?" Shiru tayi tana kifi kifi da ido dan yanda ya matse mata waje sai takejin faduwar gaba yana kamata, 'Uhummn fad'amin dalilin ki najin haushi na" "Aiko ban fadaba kaima ka sani, ai dan saboda kana da kyau din ne yasa yan mata ke binka, kuma ai nasha ganin ka in kana cikin majalisar ka sai kayi ta dariya da murmushi bayan akwai mata a wajen amma mu idan ka shigo cikin gida sai ka wani d'aure fuska" Dariya ma ta bashi sai dai baiyi dariyar ba sai yayi karamin murmushi kawai, "To yarinya ko dai kina kishi ne kinga yan mafa nata faman folawa?" Ya tambaya shima yana dage mata gira irin yanda ta mishi dazun, "Allah ya kyauta to wacece zanyi kishi da ita a cikin su bayan ba saurayina sukace suna soba, nidai dan Allah kayi aure kona samu in dunga zuwa maka gidan nan hutu" "Ke bafa gidana bane" "Gidan waye", ta tambaya tana b'ata fuska, "Haya nikeyi anan d'in kafin in k'arasa nawa ginin da nikeyi a marafa ki bari kafin ku tafi zan kaiki kiga gidan inda baiyi ba sai ki fad'a a gyara ko yar zuwa hutu" "Kai taubashi wai dan Allah duk kyan gidan nan na hayane? Ikon Allah amma dai gaskiya gidan yana da kyau nasan kuma hayar shi sai yayi tsada gaskiya gara ka gina naka kawai ka tare abunka wallahi, nifa abun baya burgeni ace mutum yana da halin da zai siya ma kanshi muhalli amma kaga yana yawon haya, wallahi kuma wani zakaga ga mata ga tarin yara duka a gidan hayan ana batun hidimar abincin da za'aci kudin makaranta kudin hayan dana hidimar yau da kullum amma a hakan sai kaga mijin sai yayi ta faman hawan manyan motoci yana yawo a gari alhalin ko fili taki d'aya bai mallaka ba sai ya mutu kaga ahali duk sun watse tunda babu muhallin zama. Suna wannan hirar har suka fita waje ya kwaso musu kayan nata dana Hajiyan ita kuma tana bin shi a baya, sai da yakai musu kayan har d'aki sannan ya dawo falon, ya samu tayi zaune tana cin chips din, "Ya'ya amma abincin nan yayi yawa fa Allah sai dai musa sauran a fridge gobe muyi breakfast dashi" "Shi yasa na siyo da tawa aI kici ki ture, kafin ki koma gida kina cewa kinzo kaduna ko ruwan sha ban siya miki ba" Ya k'arasa fad'a shima yana zama k'asa inda take zaune, cokali ya d'auka yasa a cikin chips din da take ci sukaci gaba da cin abincin tare suna hira, Kai shidai yau wallahi bazai ce komai ba sai dai yace Alhamdulillah wallahi me yafi wannan dad'i ace gaka ga abunda kake so kuna cin abinci da hora cike da soyayya, Ji yake kamar su dauwama a haka kar wani abu na sab'ani ya shigo tsakanin su, wallahi sai yakeji kawai kamar irin ai an riga an daura musu aure ita din matar shice take zaune a gaban shi, baiyi yunkurin bata abincin a baki ko sau daya ba sai dai kuma shi da kanshi ya dunga cire mishi tsokokin kajin yana tara mata a gefe d'aya ita kuma tana d'auka tana ci a haka har sai da ta koshi dam, sannan shima yaci wanda zai iyaci suka tattara sauran suka kai cikin fridge lodojin kuma suka sasu a cikin Bola, sai da ta raka shi har kitchen din ya wanke hannu sannan suka fito ya kulle kofar falon ya kashe wutar falon kuma, "Ina ne d'akin ka?" "Ya akayi?" "So nike in lek'a mana" "Kiyi me a cikin?" "Kalla fa kawai zanyi sai nima inje in kwanta!" "Ah ah kije dai ki kwanta dare yayi kya gani da safen in Allah ya kaimu" "Kai yaya lek'awa fa kawai zanyi" Daure fuska yayi ya koma mata AK din data sani a da can baya, "Ke wai ina wasa dake ne nace kije ki kwanta dare yayi koh bakiji me nace bane, kin san dai bana son inyi ta maimaita magana a lokaci guda koh?" Gaba tayi tana tura baki ta bud'e kofar d'akin da Hajiya ke ciki ta shiga tana tura baki, "Ku da ke kukeyi a falon tun d'azun?" Hajiya ta tambaya wacce ke zaune akan gadon hannun ta rike da littafin addu'a da alamun itama sai da tayi wankan dan ta canza kayan jikinta ma zuwa na bacci, "Mun tsaya cin abinci nefa Hajiya tunda ke kince kin koshi" Cewar Meenal shiko sai da safe kawai yayi ma Hajiyar daga bakin kofar daya coge ya koma da baya bayan ya rufe musu kofar ya shige d'akin shi. ******** Teemah amma dai tsayin shekarun zamana dake ina ganin kamar ai ban tab'ayi miki alkawari cewa zan zauna dake ke kad'aiba har zuwa karshen rayuwa na, Ya kamata ki gane cewa shi karin aure a wajen namiji kaddara ce idan Allah ya tsara cewa zan kara auro wasu matan bayan ke bai kamata kiyi mamaki ko jayayya ba, Miye ma wani abun damuwa ko tashin hankali bayan kinsan cewa ina son ki, duk wacce zan auro fa ke din dai ke zata tarar a matsayin uwar gidan ta, ya kamata ace kin shaideni kodan yanda nake kokarin wajen baki hakkin ki ba tareda na tauye kiba, Ni bance zanyi aure yanzun ba, amma ki sani niba nine nike da zab'in yanda kaddara zatayi da rayuwata ba idan Allah ya nufa cewa nan gaba zan k'arayin wani auren dole zakiyi hakuri ne kwatankwacin hakurin da kikayi a baya, Sannan ina mai maki ishara da ki kasance mace mai tsoron Allah aduk abunda zata aikata kiji tsoron Allah ki sani duk wani abun da zakiyi a sarari ko a fili koda ace ni da sauran jama'a bamu gani ba, tofa ubangijin daya halitto mu dan mu bauta masa yana daga sama yana kallon mu, sannan babu mara rabo a duniya irin wanda yake had'a Allah da wani masu biye biyen wajen boka ko malaman tsubbu dan suyi musu maganin damuwar su, ki sani in kika tauye wani kema Allah bazai barki ba sai ya saka ma wanda kika zalinta, Nidai ina son ki har gobe kuma ina kaunar ki a matsayina kuma na uban yaran ki bazan so inga kin tashi ranar lahira cikin mutanen da Allah yake fushi dasu ba dan haka nike son in k'ara jan hankalin ki ki sani ita mutuwa bata sanarwa a yayin zuwanta Allah yaga dama a yanzun da kike kwancen nan kike ganin cewa kin samu sauk'i akan a sallame ki gobe ki koma gidan ki, in Allah yaso sai ya aiko mala'ikun shi suzo su zare miki ran da kike takama dashi wanda ni ko mahaifan ki bamu isa mu dakatar da hakan ba, Teemah nasan ni duk abunda kika aikata kin yi shine saboda son da kike min, Amma kuma ni bazanyi akfahari da son ba alhalin son nawa ne yake ta neman jefa min ke a cikin wuta, Ki fadamin maina tauye miki a tsawon zamana dake mai kika nema wanda ni ban miki ba? Wacce kalar soyayya kike so wacce ban nuna miki ba? Mai ya rage a tsakanin mu iyeh, kefa matatace ni mijinki hakan bai wadatar ba, naga dai tun kafin ki aureni kin sani cewa ahalina ba masu zama da mace d'aya bane kuma a hakan kika aureni to miye kuma na tashin hankalin a yanzun, ko wani mutum yana samun dama na domin ya gyara kuskuren daya aikata a rayuwar shi ta baya dan haka kema zan baki wannan damar kamar yanda nima lokaci ya bani damar gyara kuskuren da nayi a baya tun ina raye, Ni bazan tab'a iya rabuwa dake ba saboda son da nike miki darajar yaran da kika haifamin da kuma na iyayen ki da kullum suke d'aukata a matsayin d'an su, Dan haka zan baki zab'i, indai har kina sona kamar yanda kike fad'a a kullum to zanso ki tattara komai da kike buk'ata ki bini mu koma Kaduna muci gaba da rayuwa ni kuma zan nema miki gida dai dai da ra'ayin ki wanda zaki zauna keda yaranki wadanda zan amso miki su ku zauna tare, Sannan maganar aikin ki bazan tab'a hanaki ba sai dai kuma dole ne ki nemi transfer daga nan zuwa can inya so kici gaba da aikin acan bayan mun koma can, maganar kasuwancin ki kuma dama ai bake ke gudanar dashi ba akwai masu kula mishi dashi dan haka kibar mu ni kuma na miki alkawarin cewa ko wani kasuwancin sabo kike buk'atar budewa a kadunan zan baki kudaden da zasu isheki wajen gudanar dashi, Sab'anin hakan kuma ina ga sai dai muyi hak'uri mu rungumi kaddarar rabuwa dan gaskiya bazan iya jele kullum ina raba hankali na bana kaduna bana Lagos bana zaria sannan bana sauran guraren da aiki ke Kaini ba, dan haka na baki zab'i ko ki bani mu koma can gaba daya ko kuma kiyi zaman ki kici gaba da al'amuranki amma bada igiyar aurena a kanki ba, sati d'aya zanyi anan dan haka kiyi tunani ki kuma yanke shawara cikin kwana kin da zanyi kafin in koma dan in san a wata matsayar muke," Yana gama karanta mata hakan ya sauka daga gadon ya d'auki pillow da bargon da nurse din nan ta kawo mishi ya koma kan kujera yayi kwance bai k'ara bi takan ta ba, Ita ko zaune take kawai amma idan tace hankalin ta baya tare da ita tabbas ba tayi karya ba, Bazatace bataji abunda ya fada mata ba, sai dai ta rasa tantancewa shin mafarki takeyi ne ko a farke take Sarki ya ajiyeta ya rattafo mata wadan nan kalaman masu kama da sukar mashi ko yankar takobi, Infa kunnen ta ya jiye mata abinda ya fad'a da kyau kamar maganar rabuwa taji yanayi a tsakanin su bayan ya shimfid'a mata sharadin da in batabi suba rabuwar ce zata biyo baya, To me yake shirin mafuwa ne ga mutumin da a yanzun yanzun ya gama maimaita mata kalaman tarin kaunar da yake mata, Daren yau daya kamata ta kwana cikin farin ciki na samun yanci cewa mijinta ya dawo mata shine kuma tun ba'a kwana ba yake neman rusa mata duk lissafin dako farawa batayi ba, Da kallo ta bishi tana rasa abin cewa harya kwanta mai kuma ya tuna sai taga ya tashi ya fad'a toilet alwallah ya d'auro bayan ya fito ya d'auko daddumar da yake gefen gadon nata ya shimfid'a ya tada Sallah ita dai bata k'irga ko raka'a nawa yayi ba tana kallo dai harya sallame yayi addu'a ya taso ya nad'e daddumar ya koma ya kwanta kuma baice mata k'alaba duk da yanda ta kafe shi da kallo kuwa, To itama dai jiki a sanyaye ta kwanta tana tariyo maganganun daya furta wadanda sukaci gaba da maimaituwa a cikin kunnen ta kamar yanzun yake furta mata su, To kenan hakan yana nufin cewa Sarki yasan abubuwan da take aikatawa a kanshi shi yasa ya mata wa'azi kenan ko kuma me ya faru? To amma ai inda bai sani ba da bazai tada maganar ba, Ta dade tana tufka da warwara itafa tana son mijinta dan son nashi ne ma yasata aikata komai da ake ganin ta aikata masu kyau da marasa kyau, to shine sai yanzun kuma da abubuwa suka dai dai ta zai bata zab'i, kenan idan harta sake ta zab'i cigaba da zama a Lagos da kuma aikin ta anan din duk yak'in da tayi a can baya saboda shi sun tashi a banza kenan, to ita da take fatan Allah yasa cikin yan biyun gareta me zai Hana bazata amince su koma can din ba ta rungumi sauran yaranta tunda komai yazo karshe su gina sabuwar rayuwar su abunsu, Sai da ta gama yanke shawara tsaf sannan ta sauko daga kan gadon ta nufi kujerar da yake kwance dan shi har bacci ya d'auke shi tuni, Dukawa tayi a dai dai fuskar shi tana shafa kanshi da hannun ta guda, Daya hannun kuma tana dan tsetstsefe gemun da baida wani tsayi sosai dashi tana kuma kiran sunan shi k'asa k'asa, Bud'e idon shi yayi a hankali yana kallon ta, "Mi kikeyi bakiyi bacci ba? Dare fa yayi jeki kwanta" "Sarki na yarda zan bika mu koma can Kadunar kamar yanda ka buk'ata amma dan Allah kar kace zaka rabu dani wallahi ina son ka, bazan iya yin rayuwa dako wani namiji bayan kaina a duniyar nan, kuma wallahi duk abunda na aikata nayi sune sakamakon kishi da kuma son ka da suka rufemin ido, amma insha Allah bazan k'ara ba" "Nifa bance kiyi saurin yanke hukunci kai tsaye ba shi yasama na baki dama saboda kiyi nazari sosai a tsayin kwanaki 7 din dana baki, saboda bana son in miki dole" "Na amince Sarki zan bika duk inda kake son Kaini bazan k'arayin maka musu ba dan Allah karka k'ara cewa zaka rabu dani wallahi zuciya ta zafi takemin" "Kin tabbata?" "Eh nayi alqawari" "To jeki kwanta zamu k'arasa maganar da safe bacci nikeji yanzun" Kwantowa take shirin yi a kujeran da yake kwance, "Ke miye haka bayan kin san nan wajen ba isar mu zaiyi ba so kike ki matse min baby ne?" "To ka tashi mu koma can sai mu kwanta yanda bazamu takura ba" "Kin san dai bana son musu koh" Ya fada yana rufe kanshi da bargo har saman kanshi, Dire dire ta fara tana kananan kuka cewa ita wallahi bata yarda ba sai dai ya tashi su koma can din su kwanta gaba d'aya, a babu yanda zaiyi haka ya tashi, yana mik'ewa ko ya mata d'aukar cak irin wanda akema jarirai bai direta a ko ina ba sai akan gadon, yana sauke ta ko ta sanya duka hannuwan ta guda biyu ta kamo fuskar shi a cikin tafin hannun ta, yana shirin yin magana ta had'e bakin su tana aikata mishi da kiss jikinta har rawa yake tsabar yanda jikin nata ke amsa kewar shi da tayi, To dai shima dama d'aurewa ce kawai yake bawai dan baya buk'atar matar tashi ba dan haka tuni ya sadaqar wajen biye mata suka raya daren suna farantawa juna rai, Asuba ta gari Sarki da Gimbiyar shi, Washe gari Sarki ya nema mata sallama, haka ko Dr din ya rubuta musu takardar sallama bayan sun gindaya mata sharad'od'i akan abubuwan da zata kiyaye har zuwa sanda cikin zai kai lokacin haihuwa ne suka kwasa suka koma gidan su, A cikin satin tattata batun zuwaga Moon Sarki yaci gaba da kulawa da Teemah wacce gaba d'aya ta canza mishi take binshi sau da k'afa tamkar ba Teemah da kowa ya sani ba wacce sai abunda take so takeyi, domin zagewa tayi wajen bashi kulawa kamar wasu sabbin ma'aurata ganin hakan shima sai ya sake mata a satin kuma yasa ta fara neman transfer shi kuma a gefen shi inda zata zauna a kaduna ya fara neman mata dan yasan cewa bata son zaman cikin bariki kuma shima ba muradin shi bane ajiye mata a cikin barikin, Satin shi na farko a Lagos duk wajen kula da matar shi ya cinye su sati na biyu ne ya fara kokarin ganin sun had'u da Moon domin ya duba takardun binciken da Joseph ya kawo mishi ranar da matar Joseph din zata haihu, Allah yayi itama matar Joseph din ta haihu lafiya a asibitin dan washe garin ranar ma kusan tare dukan su aka sallame su, A cikin binciken da Joseph din yayi akwai inda yaga ya sa sunan wajen shakatawar da Moon ke zuwa kusan kullum idan ta fito daga wajen aikin ta sai ta tsaya a wajen ta huta taci abunda take muradi wata rana kuma take away takeyi ta wuce dashi gida, kuma kullum tana isa wajen ne da misalin karfe 5 da mintoci na yamma wani lokaci ita d'aya wani lokacin ita da kawayen ta, Dan haka tun bayan daya dawo daga Sallan la'asar ya shirya cikin tsararriyar shigar data boye yawan shekarun shi da suka fara nunawa, wanda har sai da Teemah ta tanka a yayinda taga fitowar shi. "Abban Boy ina zuwa haka naga kaci gayu da yawa?" Ya danji wani irin domin dai babu halin da zai fito ya fad'a mata gaskiyar inda zashi dan haka sai kawai yace mata, "Muna da wani Meeting da karfe biyar shi nike son inyi attending kar inyi latti, sai na dawo ki kula da kanki" Sai da ya k'arasa inda take ya mata kiss a goshi sannan ya fice daga gidan yana jin wani iri, kamar dai bai kyauta ba haka yakeji, Tunda ya isa wajen ya nemi wajen zama ta inda zai iya kallon duk wani wanda zai shigo wajen dama duk wanda zai fita abinsha kawai yayi order ya zauna yana ci gaba da amsa kiran dake shigowa cikin wayar shi yana kuma jiran tsammani, Kamar yanda Joseph din yace kuwa hakane ya tabbata dan karfe 5 da mintoci Moon ta shigo wajen, Hadaddiyar yarinyar da tunda ta doso wajen ta kayar mishi da gaba saboda tsabar kwarjinin ta daya cika shi, tafiya take d'as d'as d'as abunta tasha wanka ta wanku kamar wacce bata fita cikin rana saboda tsabar hutu da gayun da suka bayyana kansu a tare da ita, Ita kad'ai ta shigo wajen babu d'an rakiya, allah da ikon shi kuma sai yaga kamar inda yake zaune ma take nufowa, koda wasa baiyi sakacin dauke idon shi a kanta ba har sanda tazo ta d'an gota shi ta wuce ta gaban shi ta zauna a kujerar da yake gaban shi kadan tana baza kamshi, yana ci gaba da kallon ta harta zauna waiter din wajen yazo ya tambayeta abunda take so ita kuma ta fad'a mishi shi kuma ya juya dan ya kawo mata, Gyara zama Sarki yayi yana k'ara gyara aye glass din dake sanye a fuskar shi, Sunyi zama na mintoci baiyi yunkurin zuwa inda take ba yana zaune a inda yaken yaga wani saurayi wanda shima tunda ta shigo ya lura da yanda ta d'auke mishi hankali, sai dai kuma ga mamakin shi saurayin yana zama a kujerar dake gefen ta ita kuma ta mik'e bai daiji abunda tace ma gayen ba, lura da yayi cewar fita zatayi sai shima yayi azamar ficewa daga cikin wajen dan ya jirayi fitowar ta, bayan ta fito motar ta ta shiga shima kuma ya take mata baya a cikin tashi motar ya bita har zuwa gidan su ba tareda ya bari ta ankare da cewa binta yakeyi ba, Sai da ya jera kwana 4 kullum zai rigata isa wajen kafin ta fita kuma shima zai rigata fita ya jirata a waje sai ya rakata har gida sannan ya juya, amma fa ya kasa mata magana saboda yanda yake ganin yanda take yarfa shi kullum, A kuma zuwan da yake wajen ne har ya samu damar yin magana da waiter din da take attending dinta kullum ya mishi yan tambayoyi a kanta kuma gayen ya tabbatar mishi da cewa kullum tana zuwa in kuma bata zoba takanyi order din abunda take so ne su aika mata dashi gida, kuma ko tazo bata kula ko wani saurayi a wajen abunda ya kawo ta shi kawai takeyi tayi tafiyar ta, to a kwana na biyar dai yaci alwashin cewa zai tun kareta ne kai tsaye kawai ko wacce wacce dan haka bayan sunbar wajen a hanya can inda babu yalwar motoci yasha gabanta da motar shi, Zama yayi kuma a cikin motar yak'i fitowa bayan ya tabbatar da cewa ya to she mata hanyar da zatabi ta wuce, Ita kuma ganin hakan sai ta fara danna mishi horn tana mishi ishara akan ya bata hanya ta wuce, amma fir ya nuna kamar ma bai san da shi takeyi ba, Wayarta ta ciro daga cikin jaka ta fito daga cikin nata motar ta fara d'aukar motar nashi hoto, ba tareda ta k'arasa inda tashi motar take ba, shima kuma hango fitowar ta daga mota shine yasa shi balle murfin nashi motar ya fito ya nufo inda take, bata sauke wayar ba haka taci gaba da d'aukar shi hotuna tana gamawa cikin sauri ta tura duka hotunan ma wata number, yana isowa inda take ta maida hannun da ke rik'e da wayar baya, "Malam lafiya maiya faru zaka zo ka rufemin hanya?"ta tambaya da harshen turanci Tsaye yayi suna kallon kallon shida ita batare da yace da ita k'ala ba, Ita dai kallon sani take mishi sai dai kuma gaba d'aya ta kasa tuna a ina tasan fuskar shi, "Magana nike son yi dake nasan kuma inba hakan nayi ba ba lallai bane ki tsaya ki saurareni duba da yanda bakya sauraron duk wanda zai tunkareki da niyyar gabatar da kanshi a gareki" Ya bata amsa da harshen hausa, mai makon turancin da tayi mishi magana dashi, "Bahaushe ne kai?😳" ta tambaya tana zare ido, "Ga tabbas kin gani," Shima ya bata amsa, shiru tayi tana k'are mishi kallo da kyau sai kuma can ta nuna shi da yatsa, "👉🏻 SARKI tsohon mijin Meenal 🤔?" Ta tambaya. Shi kuma ya amsa mata da cewa, "SUFYAN SULAIMAN LADAN nike Meenal din kuma da kika ambata eh ta tab'a amsa sunan mata ta a baya amma ita din har gobe matsayin k'anwa take a guna!" "Eh ai dole haka zakace mana tunda ka sakar min yar uwa bayan ka maida ta k'aramar bazawara, wai ma tsaya to ni miye had'ina da kai da kazo ka kulle min hanyar da zanbi in wuce, to bari kaji wallahi in wani abu ya sameni na riga na d'auki pic dinka dana motar ka da Address din inda nike na turama yan uwana in case in sunji shiru ban dawo ba su san wanda ya sace musu ni, dan haka gara ka bani hanya salin alin inyi tafiya ta dan bani da wata alaqa da kai". Kuyi hakuri yau ma dai babu editing kuma in bakuyi comment ba babu na dare, atoh🤷🏻‍♀️ #MEENAL #MAI JAMA'A #SHEIKH NASEER #SARKI #MOON #TEEMAH #MALAM #HAJIYA. [8/31, 10:25 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 17* Da gaske kike kuwa babu wata alaqa a tsakanin mu? Tuna dai ko k'ila kin manta ne!" Ya ambata a yayinda yake k'ara takowa zuwa inda take jingine da motar ta, "To wacce alaqar kuma ta rage a tsakanin mu bayan wacce ka yanke ta da kanka? Naga dai ai koda can ma kafin ka auri yar uwata ina maka kallon Ya'yan mune tunda koba komai ai ka girmeni kila ma ka haifeni, daga baya kuma bayan aure ya had'a ka da Meenal sai naci gaba da kallon ka a matsayin mijin yar uwata, yanzun kuma da komai ya k'are a tsakanin ku naga ai shi kenan koh, auren ai dama na dole ne yanzun kuma daka gaji da zama da ita ka saketa dan haka babu wata alaqa kuma a tsakanin mu!" Ta k'arasa fad'a tana wani jijjiga jiki da turo baki gaba kamar wacce irin dama can din nan tana da k'umin shi yau kuma sai Allah ya had'asu dan haka bari kawai ta sauke mishi duk abunda ta kunso ko zata huce, "Yanzun dai idan na fahimta dai dai kenan dai so kike kicemin kina fushine da fushin yar uwarki?" "Eh eh kwarai kuwa aiko baka tambaya ba kaima ka sani dole ne in tayata daka mayar k'aramar bazawara kishi bayan mu sa'o'inta ko auren bamuyi ba, haka zata dunga shiga cikin mu ana banbance tsakanin mu da ita ana nunata a matsayin bazawara !"ta fad'a amon sautin muryar ta na fitar da fushin da ke cikin zuciyar ta, "To naji kiyi hakuri koba komai ai dama aure da rabuwa kaddarori ne masu tafiya da lokacin su a tare, a shekarun baya Allah ya tsara cewa zan aureta har muyi zama na adadin wad'annan shekarun, shi yasa akayi auren ba tareda dukan mu muna soba yanzun kuma da lokacin rabuwa yayi sai allah ya raba kamar yanda ya had'a abun cikin kudurar shi, ni bazan ce ina farin cikin rabuwa da ita ko akasin haka ba kawai dai nasan cewa Allah shine yakeyin ikon shi a kan bayin sa shi ya had'a shi kuma ya raba dan haka ni bazanja da ikon shiba, sai dai Nagode allah da yasa bai bani ikon cutar da ita a zaman da mukayi k'arkashin inuwa d'aya tako wani fuska ba dama can Allah ya tsara cewa ita d'in ba matar da zan gudanar da rayuwar aurena da ita bane shi yasa ma rabuwar tamu tazo cikin sauk'i batareda an samu rarrabuwar kawuna ba duk da cewa a hakan ma nasan ita ce zata cutu dan in wani yasan gaskiyar cewar har yanzun tana tareda k'uruciyar ta wani bazai san da hakan ba, nidai ina mata fatan Allah ya bata wani mijin mafi alkhairi a gareta, wanda zaiyi alfahari da ita har karshen rayuwar shi. Ina fatan kuma keda sauran jama'ar da suke kallo na a matsayin mai laifi zakumin afuwa domin koba komai nid'in d'an adam ne ajizi kamar ko wane mutum, Dan haka ina rok'on arzikin a gafarta min kuskuren da ake ganin na aikata kaina bisa wuya na please 🙏 " Ya k'arasa fad'a yana mai d'an dukar da kanshi k'asa, Sanyi gabob'in Moon sukayi, dan ta yards abunda ya fad'a gaskiya ne d'an adam bai isa ya canza ma kamshi kaddarar da allah ya zana a rayuwar shi ba, dan haka itama sai tayi k'asa da kanta kamar yanda yayi tana wasa da da zoben ke sanye a yatsar ta na tsakiya, Ganin tayi shiru bata ce komai ba sai shi kuma ya d'aura da cewa, "amma ai ko babu komai ya kamata ace ko gaisuwa ne muyi koh? , ki duba ki gani fa saboda bazan iya ganin wacce nike ma kallon k'anwata in wuce ba tareda na tsaya mun gaisaba hakan ne yasa na biyo dan muyi gaisuwar yaushe gamo , Zanfi son ki cire batun wai na tab'a auren Meenal ki ajiye wannan batun a gefe ki d'auka cewar hakan bata tab'a faruwa ba dan nafi son kici gaba da kallona a matsayin wancan tsohon yayan naku na baya inda hali!" "Tab' lallai ma" ta ambata tana juya mishi kai irin fad'ama keya d'an kwali ya baka amsa d'in nan, "Maimoon!!! Ya kira sunan ta a dake bayan ya k'arema wajen kallo yaga babu wanda ya maida hankali akan tsayuwar nasu a wajen, Yanzun fa da a can wajen ya tunkareta haka zata mishi a cikin mutane koh? Ikon Allah da girman shi da komai wai ya tsaya da wannan yar abar amma wai sai da ya gama rattafa mata zance na hankali yayi zaton ko natsuwar da tayi dukan hankalin ta ta bashi tana fahimtar me yake cewa ashe ba hakan bane wai ya gama zuba zance shi yarinyar nan wai zata cema *lallai ma*, shi dariya ma ta bashi wallahi Allah, dan da Alama itama d'in dai in ba'ayi da gaske ba bazata biyu ta dad'iba dan daga ganin ta yar daru ce, , Juyowa ita kuma tayi ba tareda ta iya kallon fuskar shiba tace, "Ya Sarki dan Allah ka bani hanya in wuce gida lokacin komawa na gida yayi" "Ya kike zaton cewa zan barki ki tafi bayan ko arzikin gaisuwa ban samu daga gareki ba, a matsayina na yayanki bayan nasan ba kalar tarbiyar da aka baki a gida ba kenan," Har k'asa ta d'uka irin gaisuwar da Yaroba ko Nufawa kewa manyan su ta sauke gwuiwar ta d'aya a k'asa daya kuma ta dafe shi da tafukan hannun ta kanta a k'asa ta shiga gaishe shi, da cewa "Ina wuni ya Sufyaan? Ka wuni lafiya? Ya gida? Ya aiki? Ya ka baro mutanen Zaria? Ya ka samu mutanen nan d'in su kuma? To barka da zuwa fa, Allah ya maida ka gida lafiya nagode da zumunci Allah ya bada lada" Tana gama rattafo jerin gwanon gaisuwarta ta mik'e tsaye tana kakkab'e jikin ta bawai kuma dan ta kwaso kura ba, "Zan iya tafiya yanzun? A taimaka a bani hanya gida zanje" Allahu Akbar jama'a mutumin kufa ya Lula can nesa wallahi, Domin dai ita tayi mishi wannan gaisuwar ne cikin gatse amma kuma shi a wajen shi hakan ba k'aramin burgeshi da tafiya da hankalin shi tayi ba domin wallahi a tsayin rayuwar shi wannan shine karin farko da wata d'iya mace wacce ba daga cikin ahalin shi ta fito ba ta martaba shi da gaisuwar girma da mutun tawa irin wannan, Shifa dama can Allah yayi shi mutum ne mai son girma kuma sai Allah yasa ko a cikin family din shi sai ya zamto cikin manyan yaran da aka fara haihuwa dan haka yake samun girmamawa daga kannen shi haka kuma a wajen aikin shi sosai yake samun girmamawa bama a wajen na k'asa dashi kawai ba harda manyan shi sukan girmama shi duba da yanda shima komai kankantar ka yakan baka naka girman, Sai dai kuma yayi rashin sa'a na samun macen da zata girmama shi irin yanda yake so domin dai ita matar shi na gida inba wani abun take buk'ata a hannun shiba sau tari sai dai shine in sun kwana waje d'aya idan gari ya waye yake fara gaisheta, idan ko akayi rashin sa'a shi bai ce mata an tashi lafiya ko ina kwana ba tofa sai dai kowa a cikin su yaci gaba da gudanar da harkokin gaban shi ba tareda anyi wannan gaisuwar na safe ba, Amma sai gashi yau, k'aramar yarinyar da a haife ya haifeta tuni itace ta girmama shi da gaisuwa irin haka, to dan Allah tun yanzun ta fara daraja shi ina kuma ga ya maida ita mallakin shi ai shi kuma shi kenan sunan shi na Sarki ne zai k'ara tabbata wallahi, Ita fa a nata ganin ya tabbatar bata d'auki hakan da tayi da wani mahimmanci ba, amma shi a wajen shi hakan da tayi ba kad'an ba yasa fara shin sonta da kimarta ya k'ara hauhawa a wajen shi, dan a yanzun kam ji yake babu wani abu dai taso wanda zai rushe Soyayyar ta da yake jin tana dad'a ginuwa a cikin zuciyar shi dan haka ba zai tsaya Sanya ba dan koba komai ai dama yan magana cewa sukayi da zafi zafi ake dukan k'arfe, gara yayi da jiki ya aure ta ya adana, Allah dai yayi ma Meenal albarkha domin yarinyar nan shi kam a yanzun tsakanin shi da ita sai dai addu'ar fatan Alkhairi dan gashi dai ta silarta yana ta samun biyar buk'atar rayuwar shi d'aya bayan d'aya, A ranshi yana da burin ya samu mace mai waye wa, bawai iya bud'ewar ido ba *No* har da cikakken ilimi na boko dana islama kyakyawar mace wacce ko ranshine ya baci kallon ta kadai zaisa nutsuwar daya rasa ya dawo gareshi, mace mai tarbiyar da zata iya kula dashi da tarbiyar yaran shi, a yan kwanakin nan kuma a nazarin da yayi akan Meenal ya tabbatar da cewa itace sak irin matar auren da ya dad'e yana fatan k'are rayuwar shi da ita sai gashi yau kuma ta k'ara tabbatar mishi da hakan. "Ya Sarki fa!" Ta kira sunan da d'an karfi tana tafa tafukan hannayen ta a kusa da fuskar shi dan wannan shine kira na uku da ta mishi bai amsa ko d'aya ba bayan ita kuma a k'age take da son ganin tabar wajen ta koma gida dan dai ita bataga wani dalilin da zai sa ya wani tsareta ba atoh tsohon mijin Meenal nefa😒, Firgigit yayi yana sauke doguwar ajiyar zuciya, "Muje in raka ki gida! " Yana gama fad'in haka ya juya cike da takun shi irin na zaratan maza zuwa wajen motar shi, Itama motar nata ta koma bai bata daman da zata shiga gaban shiba, ita ma kuma bata matsan ta ba haka taci gaba da binshi a baya dan so take taga iya gudun ruwan shi, tunda dai ai ita tasan ba sanin gidan su yayi ba, sai kuma taga d'an bawan Allah yana shirin bata mamakin daya kusa sumar da ita domin dai a hankali a hankali sai gashi bai zarce da ita ko ina ba sai kofar gidan su, dan nesa da gidan kad'an ya faka, itama da mamakin daya Sanya ta a ciki ya k'asa b'oyuwa a kan fuskanta kusa da tashi motar ta faka sai ta sauke gilashin motan suka fara kallon kallo a tsakanin su, Ba tareda da fito daga cikin motar ba ta jefo mishi tambaya kamar haka, "Ya Sarki dama ka shirya yin kidnapped dina yau ne?" Ta tambaya muryar da tayi amfani wajen jefo tambayar da kuma yanayin fuskarta suna bayyanar da tsananin mamakin ta, "Kidnapped kuma wa zanyi kidnapped?" "Ni mana, to inba saceni ka shirya yiba ya akayi kasan gidan mu? Tsakani da Allah nidai nasan ba mak'iyiyar ka bace ni balle kace binciko maka ni kasa akayi, inba haka ba ya akayi kasan cewa nan ne gidan mu" "Wa tace miki iya mak'iyi kawai ake bincika ne? Ai masoyi ma abun bincike ne ki shiga daga ciki sai da safe ki gaishemin da mutanen gidan kafin in kawo musu nawa gaisuwar na musamman" Bai jira cewar ta ba ya fice a unguwar da gudu ta ribas sai da ya isa bakin babban titi sannan ya juya motar zuwa hanyar da zai mai dashi nashi gidan, Ita ko kasa gazgata abunda ya faru tayi, Ganin tana k'ara b'atama kanta lokaci a wajen sai kawai taja motar ta shige cikin gida tana watsar da tunanin abunda ya faru anan din, wata zuciyar ta na fada mata cewa kil'a dai yana lura da yanayin tuk'inta ne shi yasa ya gane gidan. *A CAN KADUNA KUWA* Washe gari tun da asubahin farko Hajiya ta farka, Al'adarta ne dama da zarar ta farka wanka take fara gabatarwa idan ta shiga cikin makewayi kafin ta d'auro alwallah, To yau din ma hakance ta kasance domin koda ta tashi saida ta gabatar da dukkanin uzurorin ta, bayan ta fito tayi zaman shafan mai sai da ta shirya tsaf kafin ta shimfid'a dadduma ta gabatar da raka'atainul fijir, bayan ta sallame ma zama taci gaba dayi akan daddumar tana jan carbi har sai da taji ana shirin tada Sallah a masallacin dake cikin unguwar, Yunk'urawa tayi da carbin ta a hannu ta k'arasa wajen gadon in da Meenal ke kudundune sai baccin ta take sha hankalin ta kwance, "Meenal ke! Ke Meenal wai bazaki tashi ba tun dazun sai faman k'ara gyara kwanciya kikeyi kamar ba Sallah ake kira a masallatai ba?, Kin san dai da wuri zamu bar gidan nan koh dan haka gara ki tashi kiyi abunda ke gaban ki atoh, "Hajiya yanzun zan tashi fa, kuma ma ai ba'a kira Sallah ba" Meenal din ta fad'a bayan taja bargon da Hajiya ta yaye daga jikin ta ta k'ara dukunkunewa a ciki, "Kin san ALLAH idan baki tashi kin wuce kin d'auro alwallah ba da carbin nan zan dake ki" Babu shiri Meenal ta mik'e zaune tana murza idanuwan ta bawai dan baccin ya saketa ba sai dan sanin da tayi cewa kadan daga cikin Hajiya kamar yanda ta furta tsaf tana iya zabga mata carbin nan wallahi, to ina dalili da asubahin nan baka karya da komai ba ka wani karya da duka, Mutum ya girma ma amma kullum abu kadan sai hajiya tace zata kai maka duka, Kafafuwan ta ta sauko kasa tana faman doka hamma da mik'a a tare, sai da ta lalubo hulanta wanda ya fita daga saman kanta tasa a kan nata sannan ta mike ta doshi hanyar makewayin, Tana rufo kofa shi kuma AK ya bud'e kofar d'akin da Sallama, koda ya leko kanshi cikin d'akin ganin Hajiya tsaye akan dadduma kuma ba kowa akan gadon kawai saiya juya shima ya fice daga gidan zuwa masallaci dan dama ya leko ne dan ya gani ko sun tashi, Bayan sun idar da Sallah gaisheda Hajiya Meenal tayi ita kuma bayan ta amsa sai ta d'aura da cewa, 'Ai sai ki tashi ki koma cikin makewayin kiyo wanka koh, tunda kinsan dai muna da wajen zuwa da safen nan da gangan kikak'i yo wankan tun d'azun ai duk dai salon mu b'ata lokaci ne na sani" "Hajiya dan Allah ki barni da batun wankan asuban nan sai kace wata wacce ta kwana cikin fitsari, naga dai ai duk sonki da sammako bazakice mu kama hanya tun yanzun zuwa can gidan ba, duk da dai gidan mutuwa ne amma na tabbata ko su yan gidan ba kowane ya tashi bacci a yanzun ba, Dan Allah ki koma ki kwanta ki hutama rayuwar ki ki bari har gari yayi haske idan muka karya anjima sai mu koma can d'in ni wallahi bacci ma nike ji" Jin hajiya na shirin fara jininin ta da bata gajiya sai kawai ta tashi tama fice daga d'akin ko hijabin jikin ta bata samu damar cirewa ba ta koma falon ta kunna TV tayi kwance a doguwar kujera tana kallo, Daga kallo har bacci ya d'auketa ba tareda ta ankara ba, ita kuma Hajiya jin shiru bata dawo cikin d'akin ba gashi ita kuma ta fara jin yunwa dan dama ita idan har tana gida to kari sau biyu ta keyi inta tashi da safe Zata nemi abinci in hantsi ya daga ma sai ta k'ara wani karin dan haka sai ta fito daga ciki tana tambayar Meenal, "Ke Meenal ina abincin da Abdul ya siyo mana ne jiya, tashi ki dindumo min shi in samu inci kafin juwa ya fara kamani, Ai matsalar Kaje bak'on waje kenan wallahi barin ma ace gidan babu macen aure, dan nasan gidan nan bai zama lallai ma a samu kayan abinci a cikin shiba tunda shidai gwanin nasan ko ruwan zafi k'ila sai an tsare shi da bakin bindiga kafin ya iya tafasa su asha tea dasu," Muryar Hajiyar shine ya tada ta daga baccin daya d'an fizgeta akan kujerar, "Oh wai ke ashe ma bacci kike duk wannan surutun da niketa yi ni d'aya?" "Me kike so Hajiya?" Meenal ta tambaya. "Me nike so kuwa banda abunda zan saka a bakin salati, tashi ki gani dan Allah ki shiga kitchen din nan ki had'omin abunda zanci kafin in farajin juwa na kamani" Mikewa tayi dan tasan halin Hajiya tunda har ta biyota zuwa falon to zaman lafiyan ta kawai tayi abunda tace d'in, Dan haka tana shiga kitchen din ta d'aura ruwan zafi tea ta fara h'adawa ta kaima Hajiyar sannan ta koma taci gaba da gyara sauran kaza kifi da chips din da suka saka a pridge jiya, Kayan fruit din data gani shake da fridge din duk sunyi k'ank'ara su da samu ta babballo ka karfin tsiya ta d'iba wadanda take muradi ta zuba su blander ta nika su ta zuba a cikin madaidaicin jug ta had'o da abincin ta fito daga kitchen din, Jera abincin tayi a kasan kafet din dake tsakiyar falon bayan ta matsar da center table din wajen can gefe, "Hajiya ki sauko ga abincin bari inyi wanko baki" "Ai ba iya baki zaki wanke ba ki had'o harda wanka ma na dai fad'a miki ina son mu fita da wuri shina wannan daga zuwa masallaci shiru har yanzun bai shigo ba nasan dai zuwa yanzun ai ko limamin masallacin tuni ya koma gida, in kina fitowa ki fitomin da wayata in kirashi, kafin yace min wani wajen ya wuce ya manta damu a cikin gidan" *Ummiee Zaria*✍🏼 [9/2, 10:06 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 18* Hajiya bata gama sauke maganar data d'auka ba AK ya fad'o cikin falon da d'an gudu gudu wanda alamu suka nuna cewa daga wajen gudun ya dawo, baiyi tsammanin ganin kowa zaune a falon ba dan haka ma ko sallamar da yayi k'asa sosai yayita wanda iya shi da yayi abunshi shi yasan yayin, Turus yayi a tsakiyar falon ya tsaya yana bin su da kallo, kamar wani wanda ya mance da wanzuwar su a gida, dan shi ya fad'o ne kawai abunshi baiyi zaton zai samu wani zaune a falon ba, ya manta shaf cewa Hajiya bata bak'unta duk inda taje sakewa takeyi ta bararraje abinta balle kuma gidan shi, ga al'adarta na yin karin kumallo sau biyu ko yanzun yasan fitowar nan nata baya rasa nasaba da neman abunda zata fara karin kumallon farkon dashi. "Ka tsaya daga can kana k'are mana kallo kamar wasu sabbin halittun da baka saba gani ba, k'araso ciki mana sai wani bin mutane kake da kallo kamar wanda yayo makuwa, ko ka manta cewa mutane sun kwana a gidan ne tunda ka saba kwana ka tashi kai kad'ai a cikin Sashen uwa wani Dangin mayu, wato dan haka shi yasa ka fad'o ko sallama babu to fisabilillahi mutum yana shiga waje ba sallama bama dole yayi ta rayuwa tareda shaidanun aljanu ba, Ke kuma ki fara shiga kitchen din nan ki dubamin duk wani abun da kika san babu na kayan abincin da zamu iya buk'atar amfani dashi kafin mu tafi kizo kimin list din su yanzun nan ki bashi kafin mu fita, dan nidai bazan dunga wayar gari zuru zuru ina tunanin dame zanyi karin safe ba" K'arasowa yayi ya samu waje daga gefen Hajiyar ya zauna, "Barka da safe Hajiya ya bak'unta?" "Barka ka dai, bak'unta kamar wata wacce taje wani bak'on wajen daban, gidan kafa nazo! " "Ina kwana Ya'ya" Cewar Meenal daga tsayen da take tana shirin zuwa kitchen duba abinda Hajiya ta Sanya ta, "Lafiya lau kin tashi lafiya, zoki zauna kiyi karin ki na riga nasa Mansoor yayi cefane tun jiya abubuwan da babu anjima idan na fita zan siyo" Canza hanya tayi ta wuce d'akin da suka sauka, bakin ta kawai ta wanke sai dogon hijjabin dake jikin data cire ta fito daga d'akin, Tare suka zauna dukan su Ukun suka gabatar da karin safen dan shima AK da wuri yake son fita daga gidan akwai inda zashi da safen, Duk jininin da Hajiya ta dungayi akan su samu su fita da wuri hakan bai samu ba, domin shiririta Meenal ta dunga yi kawai dan dai suja lokaci kafin su fitan, karfe 8 da kusan rabi suka fito harabar gidan, Mansoor ne ya k'araso ya gaisheda Hajiya itama Meenal ta gaishe shi, "Hajiya ai ban san fitan wuri zakuyi ba tun d'azun mai d'akina Hajara keson ta shigo ku gaisa ni kuma nace mata baku riga kun tashi bacci ba, dan Allah da kun d'an koma daga ciki bari in mata magana ta fito ku gaisa kafin ku fitan dan tun d'azun take kitchen tana had'a muku karin kumallo gashi kuma kun fito" "To haka akayi ai nayi zaton kai kad'ai ne a gidan ashe harda iyali gareka masha Allah gaskiya kayi kyan kai, ai aure daraja ne dashi wallahi, ina dalili mutum yayi ta rayuwa shi kad'ai kwallin kwal ba mace bawai kuma dan bashi da halin auren ba, ba damuwa kana iya mata magana sai ta fito mu gaisa tunda kaga mudai iya kwana ne kawai zai dunga maidomu gidan kuma nasan a sanda zamu shigo gidan ba mamaki tayi bacci, batun kari kuma ai da baka wahalshe taba wallahi dan yanzun muka gama karyawa a ciki dan dama tun jiyan da guzurin mu muka shigo gidan,kasan gidan da babu mace gara mutum yaje da guzuri koda ko garin kwaki ne atoh, wucewa yayi yana amsa ma Hajiya da cewa "to Hajiya bari dai in kiratan" Basu d'auki lokaci mai tsayi ba suka fito shida matar nashi daya kira da suna Hajara sai yaran su biyu mata Babban mai wayan duka bazata haura shekara hud'u ba sai k'aramar dake hannun uwar wacce ita ma dai batayi shekaru biyu ba, shi kuma Mansoor din hannun shi rik'e da basket mai murfi wanda cikin shi ke d'auke da wani madaidaicin jug mai had'e da kananun kofuna guda uku sai wasu madai daitan kuloli guda uku suma, Har k'asa matar nashi ta duk'a ta gaida Hajiya kafin ta maida gaisuwar kan Mai Jama'a cike da girmama wa suma suka amsa mata a mutunce, k'aramar yarinyar dake hannun matar meenal ta amsa tana murmushi bayan sun gaisa da Maman yaran, "Kuyi hakuri Hajiya ban san cewa da wurwuri haka zaku fita ba shi yasa ban lek'o tun d'azun mun gaisa ba dan Allah ku koma ku karya kafin ku fita tunda ga abun karin naku ya kammala" "Kaiya bayan na riga da na fadama me gidan ki cewa mun karya kuma shine sai da ya k'ara tattago kayan abincin ya fito dashi, ya za'ayi haka daga zuwan mu kuma zaku daura ma kanku dawainiya, Meenal amsa kayan kikai mota in mun isa can d'in maci dan bazataji dad'i ba idan bamu amsa ba, angode kunji Allah dai ya muku albarkha, Sai da suka raka su har bakin motar suka shiga sannan matar ta koma ciki ita da yaran, AK dake gefe yana amsa waya ne ya zagayo ta gefen da Meenal ke zaune, Key din motar dake rik'e a hannun shi ya mik'a mata ta window, "fito ki koma wancan motar ki biyoni a baya dan bai zama lallai anjima in iya zuwa d'auko kuba dan ina da uzurori masu yawa da zanyi" "To ni ai ba sani kan hanyoyin garin nan nayi ba" "Eh ai saboda sanin hakan shi yasa zan miki jagora a yanzun ta yanda bazaki sha wahalar gane hanyar dawowa nan d'in ba in dare yayi," Bud'e mata murfin motar yayi sai ya mata alamar ta fito da hannu, "To in ya zama haka kabar mana wannan d'in mana!" "Ah ah waccan d'in dai zaki hau ita tafi dacewa dake koba kin fison ki hau Babbar Mota ba?," ya tambaya yana nuna mata motar da yatsar shi, "To ai nidai in haka ne ai sai dai a barni in zab'a tunda ai da gangan mutum ya hanani zuwa da tawa motar" "Oh baki gode ba kenan da na miki tayin wannan d'in?" "Nidai bance ban gode ba kawai dai ni kayan aro ne bana so, so kake in dunga hawa wannan d'in sai na fara jin dadin hawan ta na kwana biyu sai in tafi in barta!" "Wa yace miki kayana ba naki bane?, bari in kin dawo sai ki duba duk motar da kike so anan d'in ki d'auka ni kuma na baki ita duniya da lahira" "Da gaske😳?" "Da gaske mana!, na saba yin wasa dake ne dama ko na tab'a miki k'arya ne?" "Ah ah amma nidai bana so mutum yamin kyautar koma d'aka kayi kukane, in kasan kana son motar ka kabar shi kawai wallahi tunda nidai ban rok'eka ba" Dariya ma ta bashi,wai shine dan yayi kyautar mota take cema karya mata kyautar koma d'aka kayi kuka, kai jam'a yarinyar nan ba'a tab'a iya mata wallahi Mansoor ya kira ya bashi key din motar da Hajiya ke ciki, "Kaja motar nan ka biyoni a baya" "To Yallabai" Da gudu ta k'arasa wajen motar tana zagayata, Motar fa ta had'u gaskiya dan motar kai da gani kasan ba kananan kud'ad'e aka salwantar kafin a mallaketa ba gata fara tass sab'anin wancan natan da Sarki ba bata da take bak'a wuluk ita kuma, "Kai gaskiya ni d'in nan fa mai sa'a ce wallahi na samu kyautar motoci har biyu a cikin watanni kad'an, kuma nadai fad'a maka Allah karma kazo zuwa gaba ka wani ce in dawo maka da motar ka, allah kuwa naci halak," Baya ta tayi da gudu ta koma wajen Hajiya bud'e kofar gefen da hajiyar ke zaune tayi cike da jin dad'i daya ke bayyane akan fuskarta take cewa, "Hajiya fito ki gani yauma na samu kyautar wata motar, taubashi ya bani kyautar mota shima, wuuuu ni yar gata mai yayye da yawa, oh Allah kaci gaba da lullub'e mu da arzikin da zamu amfana duniya da lahira Ameen" Fitowa Hajiya tayi tana cewa, "Ban gane ba wai anyi yamma da kare, Mota dai ta hawa irin wannan itace shi Abdul din ya baki kyautar ta da sanyin safen nan?" Hajiya ta fada tana jin jina wai kyautar motar manyan kudade Ak yayi da safen nan, Kamo hannun Hajiyar tayi tana dariyar jin dad'i tace, "eh mana Hajiya gata ma kina gani a gaban ki kuwa, wallahi gashi nan a gaban ki ai sai ki tambaye shi idan k'arya nike miki, Taubashi " sai kuma ta rufe baki🙊, "Au Ya AK dan Allah ba yanzun ka bani makulin motar kace kuma ka bani motar duka kyauta ba?, itafa Hajiya bata yarda ba ka fad'a mata da kanka" Kankance idanun ta Hajiya tayi tana kallon AK d'in dake gefe jingine da motar ya rungume hannayen shi a k'irji Meenal kawai yake bi da kallo shima yana murmushin ganin yanda take ta farin ciki dan kawai ya mata kyautar mota, Matsawa kusa dashi Hajiya tayi, sai da takai hannunta kan goshin shi ta tab'a, jin babu zafi a wajen sai ta cire ta maida hannun kan wuyan shi, "Kai Abdul zazzabin safe ne ke damun ka ko koh a ah iskokine suka bugeka ka kama kyautar mota da sanyin safen nan?" Meenal ce ta amsa da cewa "haba Hajiya iskoki kuma dan kawai ya bani kyautar mota, to shi ya Sarki daya bani wancan Motar kyauta mai yasa bakice shima iskokine suka buge shin ba? " Ta tambaya tana tura baki, "Yo shi wancan tsohon mijin naki ai toshiyar bakine yayi miki, wannan kuma babu kare bin damo in kyautar ce fisabilillahi aini ya dace ya bawa ita bake ba, tun yaushe nike cewa ya siyamin tikiti inje umara daga nan in kaima iyayen shi ziyara yana k'i kawai dan baya so idan naje in ma uban shi batun auren da yak'iyi, amma tsabar son kai nida kullum nike d'awainiya dashi bai canzamin motar hawa ba sai ke da yaushe yaushe ma kuka fara shiri a tsakanin ku,rabon ma da yamin kyautar zunzurutu tsabar kud'i harna manta, kullum sai dai ya kwaso kayan abinci yazo ya jibge min uwa wata sauran yunwa, In ma ba munafunci ba ina ce nan kullum da ke dashi d'in had'uwa goma rabuwa goma saina shiga tsakanin ku kullum sai kun raba hali kamar wasu kaji, amma daga jiya zuwa yau saboda bak'in munafurci kun wani had'e kai kun dunkule uwa wasu kashin awaki" Dariya ma Hajiya taba Meenal, "Hajiya kamar wasu kashin awaki fa kikace, to dan Allah wai dama kinfi so kiga muna fad'ane kullum, nidai wallahi na yafe mishi duka laifukan da yayi mun na baya harda na gaba ma, kuma dama can ai yarinta ne yasa muke fad'an yanzun kuma ni na girma, kuma tsakani da Allah ai kece kikace bana a can Saudiya din zamuyi azumi kuma ma ai bakice min kin mishi magana ya biya miki kudin jirgi yakiya ba," Juyawa gefen AK tayi, "To kai yaya me yasa baka biya mata kud'in jirgi ta tafi can d'inba?" "Oh so kike ta tafi ke kuma sai ki tsaya a gidan ke kad'ai?" "Eh kuma fa haka ne Hajiya ki bari kawai sai lokacin da kikace sai ya biya mana mu tafi taren koh Ya'ya" "Oh haka ka zama sai abunda tace maka shi zakayi kuma? To ai babu laifi mota koh Allah yasa alkhairi duniya dai Allah yasa nima na haifi yaran da suke tsaye cak wajen ganin sun sharemin hawaye na, yau idan nace motoci kaza nike so sai na zab'i wadanda za'a cikamin gida dasu, dan haka Allah ya Sanya alkhairi a kashe lafiya" "Ameen" meenal ta amsa dashi taja hannun Hajiyar ta maidata cikin motar AK din ta rufe mata motar sannan itama ta koma nata motar da tuni AK ya shige ciki ya zauna a gefen mai zaman banza, dan haka sai ta zaga gefen direba itama ta zauna taja motar, ita ta fara fita daga gidan kafin shima Mansoor yabi bayan su, sai da suka dakace shi ya rufe gate d'in gidan sannan suka kama hanya, suna tafe AK na nuna mata inda zata bi har suka isa gidan rasuwar, Ita ko Hajiya mamaki ne yake neman sumar da ita a bayan mota ita d'aya, dai ita dai rainin wayau kawai take gani sanka sanka daga jiya zuwa yau a wajen yaran na, oh wato shi nashi salon soyayyar kenan, yafi k'arfin ya fito ya furta wato siye zuciyar ta yake son da hidimar da yake mata ko miye nufin shi, "aiko ni nan nice maganin shi wallahi" "Magana kikeyi Hajiya?" Mansoor ya tambaya. "Ah ah Malam Mansoor cigaba da tuk'inka kawai" Yauma kamar jiya a kofar gidan dukan su suka nemi waje faka, "Nace to batun abincin sadaqa in akwai inda zan samu wadanda zanba aikin girkawa su kawo nan ina buk'ata" Cewar Hajiya a yayinda AK ya bude mata kofar mota ta fito "Abincin sadaqa kuma Hajiya?" "Kwarai kuwa ko shi kenan dan munzo gaisuwa sai mu share waje mu zauna ana dafawa ana bamu muna cinyewa?", "Ah ah Hajiya ba abunda nike nufi ba kenan, zan biya ta restaurant din da nike siyan abunci inyi magana dasu sai su kawo abincin ko zuwa da rana ne!" "To hakan ma yayi Allah ya bada lada, ke kuma zaki fito daga cikin motar mu wuce ciki ko har yanzun baki gama karema motar kallo bane tukun?" AK Bai bisu zuwa cikin gidan ba ya dai gaisa da mazan dake waje sai su Baba Adamu dake harabar gidan ya musu gaisuwa dan jiya da dare basu had'u da Baba Adamu da Baba Auta ba ya d'anyi zama na mintuna kad'an ya koma cikin motar shi Mansoor yaja suka juya. Suma su Hajiya sai da suka tsaya suka gaisa dasu Baba Adamu dake harabar gidan dasu Farouq sannan suka wuce sashen Raheenat a can ma wani sabon gaisuwar sukayi kafin suka fito, Mommy Hauwa ce tayi musu jagora yauma zuwa sauran sashen suma suka musu gaisuwa, anci gaba da zaman makoki yayinda yan uwa da abokan arziki sukaci gaba da bulbulowa tako ina suna zuwa domin yin nasu gaisuwar suma, da yawan wad'anda basu samu isowa tun jiyaba sune sukayi sammakon isowa yau d'in cikin su harda k'annen Malam biyu Mata wato Aisha da suke kira da (Momin Abuja) da kuma Fatima (Momi Zahra) wacce take aure a kano wato Maman su ya Abakar wanda yaso Raheenat a shekarun baya, Mutanen Zaria su suka fara isowa kafin na kano su, Meelat da Maryam sai misalin 12 na rana suka samu damar isowa su kuma Musty ne ya kawo su, Yau dai Raheenat tayi dauriya sosai wajen hana kanta kukan data wuni tanayi a jiya, ga kuma yan uwanta da suka cika sashen nata tako ina ta juya su take gani, motsi kad'an zatayi a fara tambayan ta "Me take so? Me yake mata ciwo, " Gaba daya basu bar mata fagen da zata samu nasa kanta a cikin damuwa ba, dan haka ganin yanda suke mata yasa itama ta sake a cikin su duk dadai bawai hirar take taya suba tana dai zaune ne da carbinta a hannu tana ja, Iso war mutanen Abuja ne yasa falon ya k'ara daukar harami domin kuwa duk da cewa ana cikin jimamin rashin da akayi hakan bai hana yan uwan baiyana farin cikin su na ganin juna ba, Babbar mota mutanen Abujan suka ciko mai d'auke da Momin Abujan ita da ahalin ta yara da manya, dan duk wanda yaji batun rasuwar shima sai yace zaije dan haka duk ta kwaso su suka taho tare, Misalin k'arfe 2 da wani mintuna ne kiran AK ya shigo cikin wayar Meenal inda yake shaida mata cewa ta fita kofar gidan abincin sadaqar da Hajiya ta buk'ata ya iso wato ta fita tayima matan iso su shiga da abincin cikin gidan, Hijjabin ta ta saka bayan tayi magana dasu Meelat akan su rakata kofar gida daga nan ta nuna musu kyautar data samu yau da sanyin safiyar Allah, suko basu musa ba suka rufa mata baya dan dama sun gaji da zaman waje d'ayan da sukeyi a cikin d'akin tun d'azun , Hajiya ta fara nema ta fad'a mata isowar masu abincin kafin ta fice tare dasu Maryam, da kuma wata yarinyar Momin abujan mai suna Amina itama amma suna kiranta da Sultana wacce tun isowar su ta mak'ale ma Meenal dan basu tab'a ganin juna ba domin ita Sultanan ba a hannun Momin Abujan ta tashi ba, rasuwar marik'iyar ta ce yasa ta dawo gida dan haka ba kowa ta sani a cikin mutanen Zaria ba wannan dalilin nema yasa suka kwaso suka taho dan daga nan kadunan Zaria zasu wuce suyi Zumunci kafin su koma ta yanda zasu san yan uwa sosai dan kaf a cikin ahalin yan Abuja ne kad'ai wad'anda ba kowa ya sani ba suma kuma hakance a wajen su . Suna shirin wuce inda su Baba Auta ke zaune Baba Adamu ya kira Meenal din da cewa, "Ke Meenal ku zonan" Karasawa wajen sukayi ita dasu Sultanan, "Sultana koh?" Baba Auta ya tambaya yana nuna Sultana d'in, "Eh Baba" ita kuma ta amsa, "Lallai ba shakka girman d'an mutum babu wuya, kin san wadan nan?" Ya tambaya yana mata nuni da su Ya Farouq dake zaune a wajen gefen su Baba Adamun, Girgiza kai tayi kafin ta amsa mishi da cewa, "Ah ah a iya hoto kawai na sansu, kuma suma ai nasan basu sanni ba" "Gaskiya ne kam ko kun santa?" Shima baba Adamu ya tambaya yana kallon su, wasu daga ciki sun amsa da cewa sun Santa lokacin tana k'arama wasun su kuma suka amsa da cewa basu Santa ba, "Ke kuma fa Uwata kin san wannan?" Baba Adamun ya tambaya yana nuna mata wani mutum dake zaune a gefen dasu Ya Farouq ke zaune tana lura dashi tun da sukazo wajen yake amsa waya ba kajin komai sai labarcin shi dake fita a tsaftace daga bakin shi kamar wani bak'on balarabe, Wanda shima jin ana tambaya akan ko an san shine ya sashi d'agowa, ido cikin ido suka kalli juna shida Meenal kafin ta kauda kanta ta amsa tambayar na Baba Adamu da cewa, "Ah ah ban san shiba, ban ma tab'a ganin shiba sai yau, wane ne shi d'in? " "Kunga irin ta ko ana zaune cikin k'asa d'aya illah banbancin gari kawai amma ace an wayi gari d'an uwa bai san d'an uwan shiba, tun yanzun da muke raye hakan yana kasancewa, anya in muka shud'e zaku iya rik'e zumuncin ku kamar yanda mu iyayen ku mukayi kuwa?, Koda yike ba laifin ku bane duka laifin Aisha ne da bata son turo Yayan ta in anyi hutu su zauna tare damu, su mutanen kano waye zaice bai san suba tunda lokaci zuwa lokaci ko babu sha'ani suna shigowa cikin yan uwa ayi zumunci dasu, to kin ganshi nan yayanki ne shima bayan shi akwai wasu ma Sunan shi Naseer shi kam duk da baya zama a k'asar duk yafi sauran yan uwan shi zumunci ga kanwar shi nan itama Sunan ku d'aya kinga itama sai yanzun data girma sannan ta nemo mu" "Ayya Baba aini Wallahi dan dai bana kusa daku ne da idan na fara muku jelen zuwa hutu sai kun gaji kunce in zauna a gidan mu, kuma ko yanzun tunda har Allah yasa na dawo to wajen ku zan tare kaga koh Baba shi yasa da zamu taho fa na kwaso kaya masu yawa saboda in zauna tare daku" Ta fad'a da sauri tana katse baba Adamu, "Ah to in ko hakane kin kyauta gaskiya" cewar Baba Auta shima, Su Fauxieyerh kanwar Meenal da suka shigo gidan yanzun ita da Sauran yan matan dake tasowa na gidan Malam din ne Meenal ta kira, su taba umarnin su koma wajen su duba motar wad'anda suka kawo abincin sai su shigo dasu, Komawar kuwa sukayi suka shigo dasu tace su musu jagora zuwa wajen Hajiya, Su d'an bata lokaci kad'an tare dasu Baba Adamun ana hirar zumunci kafin suka fito kofar gidan, Daya bayan daya ta bisu da kallo fuskarta cike da murmushin da yak'i daukewa a fuskar nata yau tace "ku duba cikin jerin gwanon motocin nan ku ganomin wacce tafi kyau a cikin su, " "Bebs wannan ai jan raine da d'aukar alhaki dallah ni bana son wulakanci in zaki nuna mana kawai ki nuna mana atoh" Maryam ce tace haka, Key d'in dake hannun ta ta latsa k'arar da motar tayi ne yasa suma saka saki k'ara harda tsallen murna a tare, "Wai Allah Qawata wane d'an aljannan ne ya baki kyautar wannan lafiyayyen motar? Kai gaskiya ko waye yaci a jinjina mishi Allah ni wannan ma har sai tafi min waccan da Sarki ya baki kyau ko Meelat?" "Ke dallah barni ni ina zan wani iya tantancewa wannan surprise duk ya rud'ani, gaskiya nayi miki murna sosai wallahi Qawata ubangiji Allah ya tsare ya kare,amma dan Allah waye da wannan k'atoton dawainiyar haka? Ko toshi aka fara mana tun yanzun ne bani da labari dan wannan motar ai tafi k'arfin ayi kyautar ta haka nan babu wani Babban dalili kawata fad'amin wani Babban kifin ne kika kamo mana kin san wallahi ke me sa'a ce duk inda kika shiga haka nan Allah ya yiki" Meelat ta tambaya tana dawowa da baya inda Meenal ke tsaye tana musu dariya, "To yanzun tambayar wanda ya siya motar zakuyi ko zaku shigane mu d'an zaga gari?" Ta tambaya tana d'age musu girarta guda d'aya ta wani kashe musu idon ta d'aya, "Kema ai kin sani dole ne ma mu d'ana ta wallahi, amma ni zan tuk'a" Cewar Sultana da itama ba'a barta a baya ba wajen tayasu murnar sabuwar motar, Key din Meenal ta mik'a mata ita tajasu suka bar unguwar, Maryam dake gaban motar ita ke nuna mata inda zasubi dan ita kam tasan kan garin na Kaduna sosai sab'anin su Meelat da Meenal daba wani zuwa garin sukeyi ba in ma sunzo abunda ya kawo su kawai sukeyi su juya, "Qawata wai bazaki fad'a mana waya miki kyautar motar nan ba?" Meelat ta tambaya tana marairaice wa, "Humm ki bari kawai my sister idan na fad'a miki ke kanki sai kinyi mamaki, ke Hajiya mafa sai da takai hannun ta jikin shi ta tabbatar da cewa lafiyan shi qalau yana a cikin hayyacin shi yayi kyautar sannan ta yarda," "Ke tsaya wai taubashin kine ya baki motar nan kyauta😳 kowa? " Maryam dake gaba ta juyo tana tambaya cike da mamaki, "Kin cinka dai dai An mata, shi din dai yau kam naci mota halak malak dan Wallahi bai isa kuma zuwa anjima yace wasa yake min ba Allah ma yaso ni a gaban Hajiya da wanda yake zaune a gidan nashi akayi komai" "Ke Meenal anya Yayan nan naki ba sonki yakeyi ba kuwa?🤔" Meelat ta tambaya tana rike baki, Ita dai Sultana tunda ba sanin wanda suke magana akan shi tayi ba shi yasa ba tasa musu baki ba, "Umm umm baso ba aurena zaiyi, kawai shi kenan mutum bazai baka abu tsakani da Allah ba sai in akwai so a tsakanin ku, iskancin banza ina ce ni daku turaren shi muke fesawa me yasa tun da yake siyan turaren yana bani bai tab'a cewa yana sona ba, keni rabani me zai Kaini auren taubashi inba so nike hawan ruwa ya kamani ina zaman zamana ba" Meenal ta bata amsa tana harar ta. "Ameen ya rabbi Allah yasa ya aurekin, yo ai mu bazamu k'iba wallahi dan mu abun farin ciki ne ma a wajen mu ace yanda muke mu ukun nan muna auren Aminan juna, ba shike nan ba kuma zumunci sai illah masha Allah me yafi hakan dad'i, Nidai zan baki shawara da zuciya d'aya wallahi Qawata ko da wasa AK ya bud'e baki yace son ki yake ki rufa mana asiri kiyi saurin Amincewa da wur wuri kai in so samu nema sai a had'e bikin mu wallahi" "Ah ah ba biki ba suna" Ta fad'a tana kaima Meelat dake dariya duka. "My Sister Allah kuwa inhar abunda suka fad'a ya tabbata da gaske ki amsa kawai, dan Wallahi ina fad'a miki ba k'aramin mutum bane zai miki irin wannan kyautar" Cewar Sultana da sai yanzun tasa musu baki. "Rabu dasu kinji shima bazai wani fara cewa yana sona ba, dan ni mijin kaina nike so ba wanda zan dunga rabashi da yan mata ba, ai tunda kina nan zaki ganin ma idon ki ni inani ina auren mijin da idan ya fita gida zuciya ta zatayi ta hailala da salati har sai ya dawo". Sunyi yawo sosai gidajen kawayen su dake cikin gari basu suka koma unguwar dosa ba har sai bayan la'asar liss, Dare nayi kuma suka tattara ita dasu Maryam din da Hajiya suka wuce gidan AK dan yanda gidan ya k'ara cika yau abun harba masaka tsinke, D'ayan d'akin dake gefen wanda suka sauka ita da Hajiya suma su Maryam suka sauke nasu kayan, Hajiya dai da wuri tayi bacci sakamakon ciwon kan da tace yana damunta, wanda hakan ne ya basu damar shiryawa suka fice daga cikin gidan bisa jagorancin Maryam da kuma Meenal data Sanya musu kwad'ayin Ice cream din da AK ya siyo mata jiya, Yawo suka sha abunsu sukayo siyayyar abubuwan da suke so, basu suka dawo gidan ba sai wajen 11 da wani abu, Shiko AK yau da wuri ya dawo, sai dai ga mamakin shi Hajiya kawai ya samu a d'aki tana bacci, dan haka bai tashe taba ya fita daga sashen wajen Mansoor yaje ya tambaye shi "tun yaushe Meenal ta fita daga gidan nan" "Tun bayan da akayi sallan isha'i suka fita" "Suka fita ba ita kad'ai bace kenan?" "Eh su 4 ne ita da kawayen ta" Komawa ciki yayi ya kunna TV din dake falon yana kallo lokaci lokaci kuma yakan daga kai ya kalli agogo, Karfe 10 nayi ya d'auki wayar shi ya kira number d'inta, "Kuna ina ne har yanzun baku dawo gida ba kun san kuma dare yayi?" Ya tambaya bayan ta d'aga wayar daga can bangaren ta, "Mun d'an fita ne amma yanzun zamu dawo insha Allah" Daga karfe 10 zuwa 11n nan ya kirata a waya yafi k'arfin sau goma daga karshe ma tsoro ya faraji ko Sunje sun shiga wani unguwar da suka bace hanyar komowa gida ne, Dan iskanci kuma daga baya ma sai ta dena d'aukar wayar shi, sai yayi yunkurin fita ya nemo su sai kuma yayi tunanin ai baima san ainihin inda suke ba, Gagara zama a falon yayi ya fito tsakar gidan yana ta faman zuwa da dawowa, ba karamin salama ne ya ziyarci zuciyar shi a sa'ilin da yaji karar horn d'in motar su a kofar gate d'in gidan ba, Mansoor ne ya bud'e musu gidan domin shima yanda yaga AK ya damu sai ya kasa sukuni shima. *Kuyi hakuri uzurine mai k'arfi ya d'auke hankali na shi yasa bakuji niba* #MEENAL #MAI JAMA'A #NASEER #SARKI #MOON #TEEMAH *UMMIEE ZARIA*✍🏼 [9/3, 10:35 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 19* Gyara tsayuwar shi yayi fuskar nan tashi uwa ta shanun da Meenal take yawan fad'a yaci gaba da bin motarsu data shigo gidan da kallo har zuwa sanda Maryam da itace ta tuk'o motar zuwa gida ta gyara parking, "Kinga abinda kikaja mana ko Meenal shi yasa tun d'azun nike ce muku mu koma gida haka nan amma kuka k'i gashi nan duk kunsa hankalin bawan Allah ya tashi😌" cewar Meelat, wacce dama ita tun tuni ta damu akan suyi su dawo gidan amma su gwanayen sukak'i. "Ke dallah can kyaleni inace ke mu ke ma duk wannan gatan! Kwana nawa ya rage miki ki rasa yancin da kike dashi a matsayinki na budurwa zuwa matar auren da zamu kai gidan miji mu baro, daga nan kuma keda yawo sai dai na zuwa unguwa shima sai da izinin isasshe baki ba damar fita kai tsaye a duk sanda ta raya miki dan kin riga kin zama d'aurarra, ke inya so nuna isan shi a kanki ma sai ya bari kin shirya fitan ya murza kambum iko yace miki bai san wannan, dan haka yarinya wannan shine damar ki na k'arshe dan haka karki wani damu da fad'an da zaiyi, dan ko gobe ma sai mun fita wallahi ko yana so ko baya so, to haka kawai dan mutum ya fita bai gama abinda yakeyi ba za'a wani matsa mishi da kira, bari kigani yanzun muna fita zai rufemu da fad'a kalli fuskar shi ki ga yanda ya d'aureta Allah ni ban fiye son takura ba wallahi, shi kuma babu abunda yafi kwarewa irin yaga ya takura ma mutum" Maryam ce ta fara bud'e gaban motar ta fito sai Meelat dake gefen mai zaman banza kafin Sultana dake baya tare da Meenal itama ta sauko daga cikin motar ita ko oganniyar gyara zama ma tayi abunta bayan ta d'aga kiran da Salman ya mata dan dama tun da yamma da suka had'u a gidan gaisuwa yace mata zai kawo mata yawo inta koma masaukin ta, to d'azun daya kira ta fad'a mishi cewa bata gida sun fita dasu Sultana shine yanzun ya k'ara kira yaji ko sun koma gidan, inda haka banza ne ba lallai ta d'auki wayar nashi ba zatace dare yayi bata son damuwa dan ta lura dashi kwanan nan baya tashi kiranta sai dare yayi inta tambaye shi dalilin kiran kuma sai yace mata wai kawai ya kirane dan yaji ya take, Ita kuma bata tab'a daukar hakan a bakin komai ba, domin dai tun kafin ta auri Sarki dama shida ita suna shiri sosai, Bayan auren ta da Sarki kuma sai shirin nasu ya k'aru dan Sarki da kanshi ya bata damar komai take buk'ata tayi magana da Salman d'in kai tsaye, sai ya zamana duk cikin K'annin Sarki tafi shiri da Salman d'in. kowaccen su idan ta fito simi simi sai dai ta nemi waje ta rab'a a gefen yar uwarta ta tsaya haka nan suka jeru a gefe guda uwa wasu wad'anda ke tsayuwar assembly babu wacce ta iya cewa dashi komai a cikin su kamar yanda shima bai tanka musu ba, sai ma takawa da yayi gefen da ita oganniyar ke hakince tana amsa waya ko alamun damuwa babu a tare da ita, yana bud'e gefen da take zaunen abu na farko daya farayi shine zare wayar dake cikin hannun ta wanda ta k'ara a kunne tana maganar da tsabar munafunci koshi dake kusa da ita bayajin me take cewa, Latse kiran yayi ya kuma kashe wayar gaba d'aya, bai tsaya b'ata ma kanshi lokaci ba ya janyo hannunta ya fito da ita daga cikin motar itama ya jerata a kusa dasu Meelat wadanda suka wani duk'ar da kai k'asa, uwa wad'anda aka tsare a gaban alkali, k'asa k'asa suke satar kallon shi ko waccen su ta kasa d'ago kai ta kalleshi balle kuma su samu damar furta wani abun har zuwa lokacin saboda tsabar kwarjinin daya musu, K'ara daure fuskar shi yayi sosai kafin ya bud'e baki a kame sosai yace, "Daga ina kuke?" Bai tsaya jiran amsa daga kowaccen suba yaci gaba da jero wasu tambayoyin kamar haka, "Ina kuka je? Nace Kuma da izinin wa kuka fita gidan nan? Mai kuma ya hana ku dawowa dawuri tun tuni sai yanzun k'arfe 11 da wani abun, shin kun manta cewa ku matane da har zaku fita kukai irin wannan lokacin a waje? Ina kuka sani da har zaku fita, Ah ah ko dai salon ku fita wani abu ya sameku kusa mutane a shiga uku, idan da ace kun b'ace kuka kasa gane hanyar dawowa gida kuma fa? Ke kuma Jameela saboda kema ba hankalin kika fisu ba shi yasa kema da kike shirin zama macen aure kika biye musu kuka kai har wannan lokacin a waje, baki san cewa Amarya tsautsayi ne yake binta a duk inda ta taka k'afarta ba" Bai sarara ba yana nuna Meenal da yatsa yaci gaba da cewa, "Ke kuma saboda tsabar kin riga kin gama raina ni shine nake ta kiran wayar ki kika gagara d'auka saboda baki d'aukeni a bakin komai ba, shin kin san irin tashin hankalin da kika nemi jefa zuciya ta a ciki kuwa? In kuna son zaku fita mai yasa ba zaki nemi izini na ba? A ganin ki bazan iya barin duk uzurin dake gabana in dawo gida dan in kaiki inda kike buk'atar zuwa bane? Yanzun fisabilillahi ya kike zaton zanji inda ace wani abu ya sameku a fitar nan da kukayi, kun kama kun fice ni bana gida ita kuma Hajiya tana bacci hakan da kuka aikata dai daine kenan?" Ya k'arasa jero tarin tambayoyin shi a kansu yana mai kai hannuwan shi duka biyun ya yamutsa gashin kanshi, "Ya'ya! Ya'ya please dan Allah ka tsaya kaji, muma fa Allah bamu san zamu dad'e haka ba, kuma ai ba b'ata mukayi ba, Ba gashi mun dawo da kanmu gidan ba, kawai fa mun d'an fita zuwa wajen siyar da ice cream d'in daka siyo mana jiya ne, kuma ni ban san ranka zai b'aci ba amma kayi hak'uri kaji, abunda ma duka duka daga gobe dai shi kenan zamuyi komawar mu muma, kuma ai mun so dawowa gida da wuri a hanya nefa muka lura da wata mota dake ta bin mu a baya shine mukayi ta yawo da kyar fa muka samu muka b'acema mai motar" "Wata mota ta biyo ku a baya kuma?" Meelat ce ta amsa mishi da cewa "eh wallahi Ya'ya tun fa a wani shago da muka tsaya zan siya charger wayata dan na manta ban taho da nawa ba shine suka biyomu to mudai bamu kulasu ba, d'ayan yace wai yana son magana da Meenal ita kuma tak'i tsayawa ta saurare shi, kuma wallahi mu bamu hanata tsayawa dasu ba itace dai tak'i ko Sultana?" "Eh wallahi Yaya sai da mukace mata ta tsaya taji me zaice mata amma tak'i nasan shi kuma yana ta bin mu ne dan yaga inda zamu shi yasa ya biyo mu a baya" Cewar Sultana, "Oh wato ma so kukayi ta tsaya ta saurare shi! Ashe rashin wayan naku yakai har namiji ya tsare ku a titi ku tsaya dashi, ashe kenan data saurare shin kamar yanda kuka so da yanzun kuna can a titi su suna hira ku kuma kuna jiran su gama ku dawo gida, to ai ba laifi gobe ma in kun fita sai ku tsaya da duk wanda ya tare ku a titin tunda haka kuke so, ku shige kuje ku kwanta in kunga dama, in kuma baku tashi kwanciyar ba kuna iya kwana a nan ma in ya muku" Girgiza kanshi kawai yayi, sai kuma yayi gaba ya shige cikin falon ya barsu nan a tsaye, dan in yaci gaba da tsayuwa a wajen to dukan su sai sunji ba dad'. Kallon kallo suka farayi a tsakanin su bayan shigewar su ciki, Kafin Maryam ta d'aura hannun ta d'aya a kirji bayan ta sauke doguwar ajiyar zuciya ne tace "oh Allah mun sha da kyar, Allah nayi zaton zai d'an faffalla miki mari koda biyu ne a yanda naga ya d'aure fuskar nan, to dai anyi na farko anyi na k'arshe gobe kam ko ceton rai zakujeyi a wani wajen sai dai ince muku Allah ya bada sa'a a dawo lafiya" "Ke wai kin tsorata da fad'an da yayi ne? Tab ai wallahi ko gobe sai mun fita koh Bebs?" Ta fad'a tana mai da kallon ta kan Meelat, "Eh kekam zaki fita amma wallahi nidai babu ruwa na, dan nasan yanzun haka sai ya fad'ama mijina cewa munje yawo kina ganin saboda kar ya kira wayata yaji a alamar muna wani wajen ne ba gida ba shi yasa na kashe wayar gaba d'aya, to tsakani da Allah muna shiga ki k'ara bashi hakuri a toh" "Ai kuma sai kuyi" Cewar Meenal "Amma Sister mai yasa kikayi mishi k'aryar cewa wani ne ya biyo mu? kunga duk yanda ya damu kuwa😕?" Cewar Sultana, "Zauna a wajen to yasin da bamu ce mishi haka ba da har yanzun muna nan muna jero mishi dalilan da yasa mukayi daren, amma ba gashi yanzun harya gama fadar nashi ya wuce ciki ya barmu ba ku muje ciki please kafin mu k'arayin wani laifin kuma," "Tsaya Sister wai wannan d'in shima yayanki ne? Gaskiya dai yana da kulawa wallahi duba kuga duk ya damu kar wani abu ya same mu" Sultana ta k'ara tambaya. "Yayana kuma?😒" Itama Meenal ta tambaya, "To ba gashi naga kuna kama dashi ba, ai naga sauran Yayyinki da Baba Adamu ya nuna min d'azun bakya wani kama dasu sosai amma shi da ganin shi an san d'an uwan kine" "Ke bafa yayan ta wanda suka fito ciki d'aya bane taubashin tane! ba d'azun kinji muna maganar mota ba, to shine wanda yayi kyautar motar da muke magana ai" Maryam taba Sultana amsa tana dariya, "Miye *taubashi* kuma?" Sultana ta k'ara tambaya. "Cousin dinta ko ince miki abokin wasa kamar yanda kuke keda ita, kinga kamar yanda Maman ki take dasu Baba Auta haka shima baban shi yake da Mommy Hauwa shi yasa kikaga suna kama in kin lura ai zakiga dukan su fuskar kakar su Hajiya suka d'auko wacce muka dawo da ita d'azun kinga kuma ai ko ita Maman Meenal din da Hajiya take kama itama" "Wai dan Allah da gaske shine kuke hirar shi d'azun wanda ya bata wannan motar yau d'in nan?" "Shifa! Kin ganshi zazzafa koh,Mai Jama'a ake ce mishi saboda tsabar farin jinin da Allah ya mishi sai ma kinga yanda yan mata ke suma a kanshi kuma wai a hakan yar uwar ki ke kushe shi, kema da kikazo yau kika fara ganin dramar su tsakanin ki da Allah zaki cemin baki fahimci komai ba🤔 tsakani da Allah ko abun da ya aikata yanzun ai ya tona asirin abinda ke cikin zuciyar shi amma ita yar uwar ki babu abunda take ganewa sai karatun likitanci🤨" Meelat ta fad'a tana matsawa gefe, dan a kusa da Meenal take ta kuma san halin mutuniyar, "La'ilah ha'ilallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam yanzun nan Meenal wai dama duk zakalkalewar da kikayi d'azun wannan kyakyawan halittar kike kushewa? Kai amma dai da badun kar kiga zakewa taba da nace rashin rabo ne ke bibiyar ki, ina laifin wannan yace ma mace yana son ta ai da gudu zaki amsa shine ke kike wani jan aji! Zo Abuja kiga yanda yan mata ke neman irin su da kud'in su da kyau da ilimi ga kuma gata amma basa samu," Tunda Meelat ta fara soki burutsun zancen ta dama Meenal tayi gaba, bayan ta suka bi bayan su kwaso ledojin da suka bari a cikin Motar, Itace ta fara shiga falon, dan haka tana shiga sai ta nemi waje ta zauna a gefen kujerar da yake zaune, D'aya d'aya suka shigo duk wacce ta shigo kuma sai ta mishi gaisuwar da basu samu damar yi mishi ita a d'azun ba, Shiko a takaice yake amsa musu da cewa "lafiya lau," Sad'af sad'af suka sulale suka wuce ciki suka barta dashi a falon, Tunda ta zauna ko gefen da take zaune bai yarda ya kalla ba, hannu wanshi dai duka biyun suna saman kanshi wanda ya duk'ar yana kallon k'asa, "Ya'ya dan Allah kayi hakuri, kaga dai d'azun nace ma Hajiya mun dena fad'a yanzun kuma in taji ai dariya zata mana wallahi, nidai tunda kace baka son muna fitan ma to gobe zamu jira har sai ka dawo sai mu fita tare kaji?" Dago kanshi dake duk'e yayi yana binta da kallo idanuwan shi a k'an k'ance, "Oh kun ma shirya wani fitan a gobe kenan?" "Eh mana amma ai bazamu wani dad'e sosai ba zamu dawo da wuri I promise" "Meenal " Ya kira sunan ta, "Na'am" ta amsa dashi tana wasa da zoben dake yatsar ta, "Meenal kina jin tausayina kuwa?" "Eh wallahi sosai ma nikejin tausayin ka" "Karya kikeyi!" "Allah kuwa da gaske" "To me yasa kika fita bayan kin san dole zan dawo da wuri saboda ke?, amma kuka fita harma wani sakarai ke bin ku" "To aini ban san zaka dawo ba, kuma mu bamu san cewa dare yayi haka ba" "Meenal" "Uhumm" ta k'ara amsawa, "Meenal Zuciyata zafi take mun"ya fad'a bayan yakai hannun shi saitin da zuciyar take ya danneta da d'an karfi, "Baka da lafiya ne dama?" "Nima ban san ko wani irin ciwon ke damuna ba amma dai naji ba dad'i da naji cewa wani yaso tsaidake dan yayi magana dake, bai hak'ura ba kuma shine har saida ya k'ara bin bayan ku, to idan da mugune ya samu damar da zai cutar dake kuma fa ya kike tunanin zanji," Shek'ek'e take binshi da kallo dan ba wani gane abunda yake cewa takeyi ba, Rik'o hannun ta suna kallon juna ido cikin ido, kafin dakyar ya fizgo maganar dake cikin bakin shi, "Meenal ban san me yake faruwa dani ba, amma tabbas inajin babu dad'i aduk sanda na nesan ta kaina dake, Zuciyata takan kasance a kuntace idan na ganki a cikin damuwa komai k'ank'an tanta kuwa, Ina jin matsanan cin farin ciki aduk sanda naga murmushi kwance akan wannan kyakyawar fuskar taki, ki fad'amin me yake faruwa dani Meena. *Ummiee ce*✍🏼 [9/4, 6:16 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 20* Cigaba da kallon shi tayi ba tareda tace komai ba, "Tashi kije ki kwanta dare yayi!" Ya fad'a hakan a yayinda ya saki hannun ta daya rik'e tun d'azun, Mik'ewa yayi ya wuce wajen kofar falon ya rufe da makulli ya kuma kashe TV dake aiki dama sauran kayan wutan dake falon, Bai yarda ya kalli inda take ba ya wuce d'akin shi yana shiga ya kullo kofar, Ita ko da kallo kawai taci gaba da binshi tun tashin shi a wajen har saida ya k'ule ma ganin ta sannan ta d'age kafad'un ta, alamun ko a jikin ta itama ta tashi ta nufi d'akin dasu Meelat ke ciki, a zuciyar ta take cewa k'ila da gaske dai Hajiya keyi da tace yana da aljanu wallahi🤔. Suko iyayen gulma tun bayan barin su falon suna shiga cikin d'akin ledojin hannun su kawai suka ajiye suka dawo bakin k'ofar suke jeru uwa kujerar roba da ake d'aurawa d'aya dan d'aya domin duka ukun haka suka jera Maryam ce a k'asa ta lek'o kai sai Meelat sai Sultana a saman su sun kasa kunne da zuba idanuwa suna kallon abunda ke faruwa a cikin falon duk da ba wani jin abunda shi AK yake cewa sukeyi ba, Suna ganin shi ya shige itama kuma ta nufo d'akin sai sukayi hanzarin barin bakin k'ofar kowaccen su ta samu waje ta zauna suka kama bud'e ledojin da suka shigo dashi suka wani basar kamar basu ne suka gama lek'e yanzun ba, Da Sallama Meenal ta shigo itama ta nemi waje ta zauna, Maryam ce ta mik'a mata leda guda d'aya. "Ga nashi ki mik'a mishi waya sani ma ko k'ila baici komai ba tunda ya dawo yana gadin dawowar mu" Babu musu Meenal ta amshi ledar ta juya ta fice daga d'akin, Kofar d'akin shi ta tsaya sai da takai hannun ta tayi nocking kafin ta had'a da sallama tana jiran ya bata izinin shiga, "Bud'e ki shigo!" Ya fad'a bayan ya amsa Sallamar nata yana daga zaune a gefen gadon shi dan tun bayan shigowar shi d'akin bai iya tab'uka komai ba zama kawai yayi ya rasa ina zaisa kanshi, Shi baima san meya hau kanshi d'azun ya zaunar da yarinyar nan yana neman tona ma kanshi asiri a gabanta, Yanzun nan dan Allah daya fad'a mata gaskiyar abunda yajeki akanta kamar yanda kullum su Yusuf ke zugashi akan ya bayyana mata Soyayyar da yake mata ai yasan wani fassarar daban zata mashi, Wallahi tanama iya cewa dan ya mata kyautar mota ne ko kuma tace dama ba dan Allah ko da zuciya d'aya ya bata motar ba, dan haka zai jira lokacin daya dace sai ya fitar mata da abunda yake cikin zuciyar shi amma ba dai yauba. Sai da ta k'arayin wani sabon sallaman bayan ta shigo, "Ameen Alaikis Salam" Ya amsa kafin ya d'ago kai yana k'are mata kallo, "Ya akayi? Ba cewa nayi kije ki kwanta ba me kike nema anan kuma? Wato kin dai rantse sai kin shigo min d'aki sannan hankalin ki zai kwanta, to sai ki d'auki abinda kike buk'ata ki wuce ki bani waje bacci zanyi" "Ummh Ummh ba komai fa dama abinci na kawo maka dan Allah kaci kasha magani kuma kafin ka kwanta kaji!" "Kinga alamun yunwa a tareda nine? da zaki kawo min abinci ? Inda da gaske kin damu dani har haka ai da bazaki kwashi kawayen ki ku fice yawo ba, waye ma ya siya muku abincin?" "Allah kuwa babu wanda ya siya mana da kud'in mu muka siya, kuma kaga ai su bak'i nane kuma idan mutum yayi bak'i kamata yayi ya karrama su shi yasa nima na fita tare dasu muka d'anyo siyayya, kuma ai na duba kan dinning table banga alaman kaci komai ba, nidai kaci dan Allah kaji, ai dai na baka hak'uri nace maka bazan k'ara zuwa ko ina ba sai da izinin ka" Ajiye ledar tayi da sauri ta juya ta fice daga cikin d'akin kamar wacce tayi mantuwa, bai motsa daga inda yake ba harta k'ara dawowa d'akin hannun ta d'auke da wani wani faranti madai daici wanda ta d'auro kwalin 5alive sai gorar ruwa mara sanyi sosai da kofi guda d'aya akai, wani stool d'in data gani a gefen gadon shita jawo ta d'aura farantin akai sannan ta fidda abubuwan dake cikin ledan suma ta jera su a gefe, "Wai Ya'ya kai baka shan ko wani drink ne sai na yayan itatuwa? Babu coca cola ba fanta ko maltina babu a cikin pridge din gidan nan sai su 5 alive exotic da wadansu daban" shi dai da kallo kawai yaci gaba da binta ba tareda ya bata amsar tambayar taba, harta gama ta juya da niyyar barin d'akin ya ruk'o hannun ta, "Ni dawa zamuci wannan abincin da kika jera ne wai?" "Kai kadai zakaci shi mana nima zanje muci tareda su Meelat a d'akine" "Kwashe su ki wuce dasu ku k'ara a naku kuci ni ban saba cin abinci ni kad'aiba, ba kuma zan fara yau ba shi yasa ma jiya na zauna naci tare dake shine zaki kawo ki wani jeramin su a gabana kiyi tafiyar ki" Da mamaki take kallon shi, Dan Allah jama'a ina laifin wanda ya kula dakai ya kawo maka abunci kaci? Ita da tayi mishi abun arziki mai makon ya gode mata shine yake kok'arin kushewa! Ita fa duk tana mishi ne saboda ganin da tayi ranshi ya baci da fitar da sukayi inba haka ba fisabilillahi miye had'in ta dashi da zata wani biyoshi da abinci har d'aki tana lallab'a shi kamar wani yaron goye, Daurewa tayi tana cigaba da kallon shi take cewa. "To da kafin muzo nan kai dawa kake cin abincin ba kai kad'ai kake ciba?" Ta tambaya tana tura baki, dan itafa a k'age take tayi tabar d'akin ta koma wajen su Meelat dan fitan da tayi d'auko mishi ruwa sai da ta lek'a tace musu su jirata ta dawo sai suci abincin tare shine shi kuma yake wani son ya hanata komawa, "Da baki zoba a restaurant nike cin abincina ko kuma in siyo inzo muci da Mansoor in kuma d'aya daga cikin su Musty na nan tare muke ci yanzun kuma da kike nan jiya munci tare kinga kenan yau da gobe ma duk tare ya dace muci kafin ki koma koh? " Ya k'arasa fad'a yana d'age mata girar shi guda d'aya. "To amma Yaya nace masu Maryam fa su jirani har in dawo sai muci tare dasu😒" ta furta hakan a shagwabe, Jawota yayi ya zaunar a kasan carpet d'in dake d'akin bayan ya mik'e tsaye, sauke abincin data jera akan stool d'in yayi ya mai dasu kasa kan carpet , "Bismillah kici abincin nan inhar kina son barin d'akin nan in kuma ba haka ba tsareki zanyi wallahi" Ya furta yana kallon ta fuskar shi a daure babu alamun wasa, Badan taso ba haka tasa cokali da dunga diba tana cusama cikin ta,dan tasan tunda ya fad'a tofa tsaf zai aikata dan haka gara su rabu lafiya, gobe ma ai rana ne da bata d'auko abincin ta biyoshi dashi har cikin dakin ba ai da bazai samu damar yin mata wannan mulkin mallakan ba. shima gyara zama yayi yaci gaba dacin abincin da kyau yanajin nishad'in hakan a cikin zuciyar shi, ita ta fara tsame hannun ta daga abincin alamun ta k'oshi amma duk da haka bai bata damar tashi ba har saida ya kammala tsaf tukun, "Muje in rakaki kikai kayan kitchen sai kije ki kwanta" "Zan iya kaiwa ni d'aya fa!" "Ai nasan zaki iya din amma kuma na buk'aci yi miki rakiyar" Shi ya tattara inda sukaci abincin ya rik'o farantin a hannun shi duk da taso ta amsa ya hanata, bai damu da samun su Meelat da yayi zauna a falon sun kunna Tv suma suna cin abincin ba, illah ma d'auke kai da yayi sai da ya rakata har kitchen d'in suka wanko hannu, sannan ya fito ya barta a kitchen din ya koma d'akin shi, yana shiga wanka ya farayi yayi ya kuma d'auro alwallah yana fitowa ko mai bai shafama jikin shiba turare kawai ya d'an feffesa sai kuma ya Sanya kayan bacci ya gabatar da shafa'i da wuturi yana idarwa ya kashe wutar d'akin yabi lafiyar gado, Asuba ta gari jikar Hajjaju🥰. Ita ko kasa fitowa da wuri tayi daga kitchen din dan tasan wallahi badan Allah su Maryam suka dawo falon suka zauna ba, ganin tana b'atama kanta lokaci a cikin kitchen din ne yasata fito fuska d'aure bata kalli ko gefen da suka zaunen ba duk da kiran da suke mata na iya shege kin kulasu tayi tayi shigewar ta d'aki to itama dai kamar shi din tana shiga kayan jikin ta ta cire ta fad'a ban d'aki sai da ta gabatar da duk wani al'adar ta na kafin kwanciyar bacci sannan ta koma kan kujerar 3sitter guda d'aya wacce ke cikin d'akin ta kwanta ta rufe kafafuwan ta da dogon hijjabin ta, ganin ta kasa sakewa a kan kujerar dan bata saba kwana a kujera ba sai kawai ta mike ta fito daga d'akin zuwa wanda Hajiya ke ciki, Duk yanda su Meelat ke kiranta kin kulasu tayi ta shige d'akin ta kulle kofar da key ta k'arasa kan gadon gefen Hajiya ta kwanta, Ta dade a kwance tana hasaso kalaman AK sai dai kuma ta rasa irin fassarar da zata musu daga k'arshe dai ture tunanin tayi a gefe ta gabatar da addu'ar bacci ta shafe jikin ta dashi sannan ta rufe idon ta tana ci gaba da istigfarin da take gabatar wa aduk sanda tazo kwanciya bacci har zuwa sanda baccin yayi nasarar d'auketa, Suko su Meelat tun fitar da tayi zuwa kaima AK abinci tana fita Maryam ce ta fara cewa, "Bebs wallahi AK son Meenal yakeyi, amma kuga ita ko a jikin ta kamar ma bata gane halin da yake ciki ba,ko kuma ta gane tana basarwa ne kawai oho mata" Meelat ce ta gyara zaman ta kafin ta amsa ma Maryam din da cewa, "Tabbas hakan take kamar yanda kika hasaso dan ni (Love sunan da suke kiran juna ita da Musty)... Shi ya fad'a min hakan da kanshi kwana biyu bamu samu zama ni dakeba shi yasa ban miki bayani ba dan shima AK d'in tsabar zurfin ciki wallahi da kyar ya iya fad'ama Yusuf gaskiyar abinda yakeji akan Meenal d'in sannan kuma har yanzun bai iya fitowa fili ya fad'a mata cewa yana sonta ba sai faman kame kame yake ita kuma nasan bazata tab'a kawo zancen wani soyayya a tsakanin suba dan bashi bane a gaban ta, Love ya rok'i arzikina akan mu d'an janyo musu hankalin ita Meenal din dan shi Mai Jama'a har yanzun tsoron tunkaranta da batun yake, shi yasa kikaga d'azun na tabbar mishi da cewa wasu ne suka biyo mu dan ina son in k'ara tabbar wa, kuma gashi kema kin tabbatar, kedai shaida ce cewa mutumin nan bashi da wani mugun halin da mace zatak'i shi saboda su, kuma koba komai shi d'in d'an uwanta ne kuma wallahi da ace ba son nata yakeyi da gaske ba bazai yarda har su Abokan shi Susan da batun ba dan bai tab'a nuna shaukin shi akan ko wacce mace ba shi yasa suma suke girmama tarin kaunar da suka tabbatar yana mata kuma na mishi alkawarin cewa muma zamuyi bakin kokarin mu wajen ganin mun saita ta a hanya ta yanda cikin sauk'i zata gane son da AK yake mata kafin wani yazo ya mishi shigar sauri" "Aiko in haka ya tabbata ba k'aramin farin ciki zanyi ba, sai dai kuma ba anan gizo ke sakar ba dan ita dai kin kwana da salin halin ta, wallahi nasan koya fad'a mata cewa yana son ta d'in bai zama lallai ta d'auki abun da mahimmanci ba kina jin tana cewa wai ita ba yanzun zata k'ara aure ba karatu zataci gaba dayi, ban san uban miye zataci da karatun ba, kuma ni tsoro nikeji kar Baba Malam yazo ya maimaita mata wani auren irin wancan a karo na biyu dan kin san dai yanzun batun auren su Fauxieyerh akeyi Suda suka kammala Secondary to wallahi yana iya cewa zai had'a harda ita,inta tsaya wasa sai dai taji shelar d'aurin auren ta amma ita ko ka tsaya ka mata bayani ba lallai bane ta maka kyakyawan fahimta ba, Sai dai kuma abunda muke hasashe zai tabbata cikin sauk'i ne idan ya zamana shi din yayi gaggawar gabatar da kanshi saboda kinga a yanzun dai babu wani jajirtaccen da zan nuna ince shi take so kinga idan ya fada mata gaskiyar shi koba komai duk wanda zai kawo nashi kokon barar soyayyar to bayan shi zai biyo, dan kinga Ya Salman wallahi ina kula da takun shi muna zaune zakiji yazo yace son Meenal yakeyi, ke nifa hatta da Ya Sa'eed dan dai nasan yanayin kusancin dake tsakanin shi da Meenal tun zamanin yarinta ne amma da nace sonta yakeyi a yanzun saboda yanda naga yana shishshige mata, ke tsaya wai kin san ma cewa Dan Gidan Master ya dawo Kasar nan kuwa?🤔". "Wani d'an gidan master din badai Bash ba?" Meelat ta tambaya "Shi dai Bash tsohon saurayin Meenal din dai da kika sani, wallahi mun had'u ni dashi ranar alhamis d'in nan daya wuce a kofar doka na tsaya a asibitin Dr Meerah ina fitowa shi kuma yana Saukowa daga benen dake saman nan kin gane wannan plaza d'in nasu dai?" "Kwarai na gane cigaba da bayanin ki sai me ya faru?" "Ke Qawata kinga yanda ya dawo kamar wani bak'on balarabe kuwa kinsan dai ko dacan dama shid'in masha Allah balle kuma yanzun an k'ara girma kud'i da hutu sun kara bin jiki, Ina fad'a miki nidai ina ta sauri dan gida nike son isa da wuri sai naji ana kiran sunana daga baya, Koda na waiga na rantse miki da allah daga farko ban gane shiba, sai da yace min, (Baki ganeni bane 3ple M) kin san Allah koda ya kira sunan da yake kiran mu dashi a wancan lokacin k'ara jefani yayi a cikin rud'ani har sai da shi da kanshi yace min, (Suna na El Bashir Al Hassan Master). Allah naji kunya amma na maze dan ya riga ya gane cewa ban gane shiba, mun gaisa dai a tsai-tsaye kafin muyi sallama kuma ya tabbatar min da cewa zaimin har gida mu gaisa, kuma na tabbata cewa zaizo din tunda in baki manta ba Ada can ma bai tab'a cewa zai ma abu kuma ya kasa cikawa ba" "Turkashi lailai to akwai matsala inhar muka sake Bash ya bayyana kanshi a wajen Meenal ba tareda AK ya bayyana kanshi ba, duk da dai bani da tabbacin cewa har yanzun tana son shi amma dai abun bazaiyi dad'i ba sam idan ya dawo, kin san dai yasan gidan Hajiya kuma zuwa can d'in bazai mishi wahala ba" "To wai me yasa bazata so shi AK dinba bayan kuma naga alamar akwai fahimtar juna a tsakanin su?" Sultana ta tambaya. "Hummm kishi ne ke damun ta ba tareda ta sani ba, saboda shi dai mai makon ace idon shi akan mata, sai ya zamana su matan ne idon su yake kanshi ita kuma haushin hakan takeji, yanzun kina tambayar ta zatace miki ai yafiye kyaune shi yasa matan ke binshi ita kuma bazata iya auren mijin da yake da kyau ba bayan itama kullum cikin bibiyar ta mazan keyi cewa suna sonta, amma ah ah ita bata ganin nata kyan kullum nashi kadai ne ya tsole mata ido dan haka shi kad'ai take hangowa, Kin san tsohon mijinta a tsayin shekarun zaman da tayi gidan shi a matsayin matar shi ban tab'ajin ta yaba kyan shi ko sau d'aya ba duk da shima yana da kalan nashi kyan, sau tarima bata son muna sako shi koda hira mukeyi, amma da zarar ana hirar farin jini sunan mai jama'an shine na farko da zakuji ta ambata, dan allah ku fad'amin hakan da takeyi shi din ba soyayya bane? Amma ita shegen taurin kai gareta" "Ku tsaya kuji ni ina da shawara indai har zaku bani goyon baya to tabbas kwalliya zata biya kud'in sabulu komai zaizo cikin sauk'i" " Shawarar me kike dashi Sultana?" Suka tambaya a tare suna maida hankalin su a kanta, taso wa tayi daga inda take zaune ta koma tsakiyar su ta zauna, Kasa kasa sosai tace, "Kishi ko wanne namiji yana kishin abunda yake so kamar dai yanda shi din ya nuna, haka kuma itama duk da tana nuna batajin komai a kanshi amma dole ai kishin ta akan shi zai tona asirin zuciyar ta dan haka daga gobe wasan zai soma ni zanji da ita ta gefen shi, ku kuma sai kuji da ita ta nashi gefen sai dai kuma in har abunda nike fata ya tafi akan yanda muka tsara to dole zai zama nid'in zan kasance a inda take, ina nufin mai makon in zauna a family house dole zan zauna ne a gidan Hajiya inda shi da ita suke rayuwa ina fatan kun fahimci abinda nike nufi?" Mun gane mu kuma menene abunda zamuyi?, Dariya tayi kafin tace, "Hirar samarin da suke bibiyarta zaku dunga yi da gayya kuna ruruta abun aduk san yake kusa ina nufin kamar yanda kukayi d'azun dafatan dai kun fahimci me nike nufi?" Dariya suka fashe dashi suna tafa hannu a tare, "Oh Sultana gaskiya nagode Allah daya kawo mana ke a daidai sanda muke buk'atar ki, dan haka kamar yanda aikin mu ya fara daga yau haka zamu cigaba da d'aurashi a gobe ma har zuwa ranar da hak'ar mu zata cimma ruwa" Sun dad'e suna tufka da warwara akan yanda zasu tafiyar da Meenal dama shi kanshi gogan kafin suka tashi suma sukaje suka nemi wajen bacci. *washe gari* koda suka idar da Sallah komawa sukayi suka ci gaba da bacci, Hajiya dai mai karin Sassafe ita kad'aice ta fito falon ta k'arya da nata kayan dad'in da Meenal ta ware mata tun jiyan, To shima Dan mai karfi dai tun fitar da yayi masallaci bai dawo gidan ba, Hajiya kuma ganin su d'in basu da niyyar barin gidan sai kawai bayan ta shirya ta amshi key d'in Motar Meenal taba Mansoor shi ya kaita gidan gaisuwar ya dawo ma da Meenal d'in da key din, Suko basu suka tashi daga baccin ba sai wajen karfe 10, koda suka fito kuma raba aikin sukayi, Meenal ce ta tsaya gyaran d'akunan baccin su wanda suka kwana ita da Hajiya da kuma wanda su Meelat suka kwana a ciki batayi yunkurin lek'a d'akin mai jama'an ba duk da bawai tasan baya gidan bane, Meelat ce tayi gyaran falo su kuma Maryam da Sultana suka shiga kitchen, Nan da nan suka kammala aiyukan su kowaccen su taje tayi wanka kafin suka dawo falon suka fara shirin karin safe kafin subar gida, Suna zaune suna karyawa, Sadeeq ne ya fara shigowa falon da sallama kafin AK dake biyoshi a baya, Amsawa sukayi, kafin Meelat dake kallon Sadeeq tana dariya tace, "Anya kuwa ya Sadeeq in ka zarge wuyar Qawata da igiyoyin auren ka zaka dunga bari tana nisa dakai kuwa? Dubi fa jiya ne kawai amma har ka biyo bayan ta yau, Allah sarki ni nawa mijin ko yana ina oho, yau ko wayar safen ma bamuyi ba bawan Allah" Wuce wa ciki AK yayi tun bayan daya gama amsa gaisuwar su shiko Sadeeq gefen da Maryam ke zaune ya nema ya zauna, yana ma Meelat dariyar maganar ta, "Baby ko dai bakiyi murnar ganina bane in koma inda na fito naga sai wani k'ara duk'ar da kai kikeyi?" "Dama to kace min zakazo nan ne? Ina fa d'azun ma munyi waya kuma bakace min zakazo ba" Ta fad'a tana tura baki da kauda kanta gefe, Sai da ya mik'a hannu ya d'auko kofin shayin da take sha ya kurb'a kafin ya ajiye yana mai cewa, "Kiyi hakuri nima banyi zaton zan samu damar isowa nan d'inba Mai Jama'a ne ya tattago ni ko bakiyi murnar ganina ba? " " Nayi wallahi sosai ma," "To ki shirya mu wuce Zaria anjima!" "Ah ah wallahi ai bamuyi haka da kaiba mukam sai gobe zamu koma gida kai dai Allah ya kiyaye hanya," "Haka zamuyi Baby?" Ya tambaya yana marairaice mata, Fitowa AK yayi shima ya nemi waje ya zauna, a gefen Sadeeq sai ya zamana suna kallon juna shida Meenal, Ita ko Sultana dama tana ganin fitowar shi ta tashi tsam ta koma cikin d'akin da suka kwana Meelat ma ta rufa mata baya tana cemata bari tazo ta nuna mata wani abu,sai ya rage daga AK da Meenal sai Maryam da Sadeeq wadanda ke hirar su kamar ma sun manta da wanzuwar su AK a wajen, saida su Meelat suka share kusan minti goma sannan suka k'ara dawowa falon, Suna fitowa tun basu zauna ba Sultana ta fara cewa, "Sister Meenal wannan guy din naki wanda yace zaizo miki yawo jiya ya kira wayar ki na d'auka, nace mishi bakya kusa yadai tambayeni Address d'in gidan nan Meelat kuma ta mishi kwatance yace zaizo kafin mu wuce gidan rasuwar" "Waye yace ki tab'amin waya to?" "Kiyi hakuri nima dan naga tun jiya kuna ta waya dashi nasan saurayin kine shi yasa na d'auka, to miye tun yace zai zo dama batun jiya yaso zuwa ba" "Dallah can ni bani wayata, shegen karambani kawai meya kaiki tab'amin waya yanzun yana zuwa zai dameni da surutu" "Nifa ban fito da wayar ba tana can na saka miki a caji" Tunda Sultana ta fara maganar wai wani guy ya kira Meenal a waya, daga AK har Sadeeq suka bar abincin da suke ci, shi Sadeeq Sultana yake kallo kamar a cikin fuskarta ne zai hango fuskar saurayin daya kira Meenal din shiko AK meenal din ya kafe da kallo, "Waye shi kike shirin gayyato min shi gidan nan?" "Eh gaskiya kam waye shi?" shima Sadeeq ya tambaya fuska a daure, Maryam ce tayi saurin amsawa da cewa, "Kai Baby ba wani bane fa Ya Salman ne yake ta k'ok'arin ganen ya maye gurbin Yayan shi, Kaga muma muna ta tayashi yak'i amma ita Gimbiyar sai yanga take mana niko banga abunk'i a jikin shiba wallahi, in Babban yaya yaja baya shi k'arami basai ya shigo ciki ba sun mafi dacewa da Salman d'in wallahi" "Maryam kin san dai bana son haka koh! Ni da yau she mukayi dake cewa sona Ya Salman yakeyi harda zaki min sharri" "Oh bai fad'a miki ba wai dama? To nima ai ba fadamin yayi ba kawai alamun hakan na gani shi yasa ni kuma nike mishi kamun k'afa" "Ke Baby Salman SS Ladan kike magana k'anin Sarki? Kowa?" "Shifa Baby ashe ka gane shi, wallahi sonta yakeyi amma ita sai wani basar dashi takeyi bayan kuma auren ta dashi bai haramta ba ko a musulunce" "To ke tunda tace ba haka ba ai sai ki kyaleta koh, tunda ta nuna bata ra'ayi soyayya aiba dole bane, koh koh haka kawai dan su sukafi kowa gata ta auri yayan yanzun kuma sai ta k'ara auren k'anin to allah ya kyauta amma ai ana barin halak kodan kunya' "To Baby gani nayi gida bai koshi ba ai ba'aba dawa nama ba, tunda shi ya nuna ra'ayi ai gara ta bada kai kawai" "Meenal kina son shine?" Ya tambayi meenal din, AK da bashine wanda yayi tambayar ba har yafi Sadeeq din k'aguwan son jin amsar da zata bayar, "Allah ya kyauta min mai zanyi dashi" Ta bashi amsa tana cigaba da cin abincin ta, Wata k'atuwar ajiyar zuciya ce ta kwacewa AK Ba tareda ya d'auke idon shi akanta ba yace, "Ki kirashi ki dakatar dashi da zuwa min gida, kuma ko kin koma ban yarda inji ance yana zuwa wajen ki a gidan Hajiya ba kinji dai na fad'a miki" Suna gama karyawa suka kimtsa wajen suka fice daga gidan, Ita dai unin ranar rasa gane kan su Maryam tayi dan lokaci lokaci sai taga sun had'a kai suna k'us da Dariya a tsakanin su, ga kuma Sultana data isheta da shegen tambaya akan wai lallai sai ta bata Labarin waye AK, Wai ita dai wallahi yana burgeta, haka tasa ta a gaba sai uban kod'a shi take kamar shi kadai ne namijin daya rage a doron k'asa, duk yanda ake cika ciki yau yan matan nan uku sun cika ta, gidan mutuwa suke shi yasa ta d'aga musu kafa ita kuma sultana taga alaman sai ta ci mata uwa k'ila idan ta nuna mata true colors dinta zata kiyaye ta a lokacin, Allah ma dai yasa gobe za'ayi addu'ar uku kowa ya kama gaban shi masu zama sai anyi bakwai kuma su bada himma ita dai gobe kam Zaria zata kwana koda motar Haya zatabi ta koma gida kuwa, Yauma kamar jiya anayin Magrib suka koma gidan AK dan tunda yamma dama ya kira Maryam akan su dawo gida da wuri. *Ummiee ce*✍🏼[9/7, 9:27 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 21* Yau dai duk yanda Meenal taci burin su fita yawo hakan bai samu ba domin dai koda suka dawo gidan sun iske Mai Jama'a ya rigasu dawowa gida, ko bai fad'aba tasan da gayya yazo ya kafa ya tsare dan dai kawai karsu fitan tunda ya dawo daga sallan ishsha'i ko bakin gate bai k'ara lek'awa ba, harma da wani ba Mansoor Umarnin cewa ya kulle gate d'in kawai shima ya wuce ciki wajen nashi iyalan saboda babu mai k'ara fita a gidan. Da wuri ta mishi magana akan fitan da zasuyi, saboda kar yace yauma basu nemi izinin fitan ba amma sai wani cewa yayi ai dama abinci suke fita siya koh?, Dan haka in dai dan abinci ne su shiga kitchen su girka duk abunda suke son ci ya riga ya tanadar musu da komai, Duk yanda tasa shi a gaba da magiya k'iyawa yayi, sudai su Meelat tunda yace ba'a zuwa ko ina dama suka shafa ma kansu lafiya, Hajiya najin Meenal d'in na ta faman magiya amma bata sa baki ba har saida shi d'in yabar wajen ya shige d'akin shi saboda yanda ta dameshi, sannan hajiya tace, "Ina kuke batun zuwa yanzun da daren nan Meenal?" "Hajiya wani shago muka gani a fitar da mukayi da dare jiya shine muke so muje dasu Meelat ko zamu samo abubuwan da zamuyi amfani dashi na biki" "Shi shagon ba'a bud'e shi da rana ne?, lallai sai da darene zakuje siyayyar a garin da ba naku ba? Jiya mafa haka kuka fita kuma baku dawo da wuri ba, kunyi zaton ban sani bane tunda bakuji nace muku komai ba koh? Ai Abdul ya kyauta min da yasa Mansoor ya kulle kofar sai inga ta inda zakubi ku fita! In kuma ta katanga zaku ciccib'a ku fidda motar duk zan gani" Simi simi suka shige kowacce ta kama abinda zai fishsheta Maryam da Meelat sune suka fad'a kitchen ita kuma sultana ciki ta shige ta tsalo wanka, dan ita hakan ma ya mata dai dai ta yanda abunda ta tsarayi zai tafi mata batare shamaki ba zata jefi tsuntsu biyune da dutse guda d'aya. Wanka ta d'auka na d'aukar magana kamar wata mai shirin zuwa dinner riga da skirt na wani lafiyayyen bakin less d'in da aka mishi d'inkin daya zauna dai dai jikin ta ta sanya bayan ta fente fuskanta kuma saida ta b'ata lokaci wajen d'an d'asa d'auri kalar yan matan Abuja sannan ta rufe k'ofar wankan nata da turare mai d'ad'in shak'a kafin ta fito daga cikin d'akin da wayarta a hannu duk da kasancewar dare ne hakan bai hanata d'aukar kanta Selfie ba,tafa wanku tass wallahi Kamshin turaren ta da kuma k'arar da takun takalmin ta ke badawa ne ya maido hankalin Hajiya da Meenal wad'anda ke zaune a falon suna d'an hira jefi jefi wajen ta, cike da salon tafiyar ta mai d'aukar hankalin mai kallo ta k'araso inda suke kafin ta nemi waje a gefen Hajiya itama ta zauna, "Hajiyar mu barka da war haka!" ta ambata a yayinda takai zaune. Tun daga fitowar ta har zuwa sanda ta zauna da kallo kawai Hajiya ke binta, kasa shiru tayi har sai da ta mata tambaya cewa, "Bak'o zakiyi ne hala naga daga dawowar ki kin wani shiga kin shawo wanka kamar wata mai shirin zuwa turakar miji ranar kwanan ta?" K'aramin dariya Sultana tayi tana mai rufe idon ta da tafukan hannun ta alamun maganar na Hajiya ya bata kunya tace, "Kai Hajiya sai masu mazane suke kwalliyar dare? To su kuma matan da suke farautan wasu kuma fa? Nidai tarko nike d'anawa kuma ina fatan ganin ranar da tarkon nawa zai kama kurciya, Nagode allah iyamu ne anan da kin sani a kunya Hajiyata ashe shike nan mu yan mata bamu da damar yin kwalliyar domin d'aukar hankalin abokin farautar namu kenan ko ya abun yake?" Tab'e baki hajiya tayi kafin ta amsa mata da cewa, "Zance na dai ya fito kenan tunda dai wani ne akayi kwalliyar domin shi! To Allah yasa yana da rabo, amma ke ai in namiji zai soki ko bakiyi fente fente ba tsaf zaki kwaci zuciyar shi amma hakan ma ba laifin dama yan magana cewa sukayi ko kina da kyau ki k'ara da wanka, ai gara kiyi kiyi kekam ki bada himma wallahi kiyi auren ki, karki biye ma halin yar uwarki gatanan ita da anyi magana sai tace wai ita ba yanzun zatayi aure ba, ko zaman me take nufin zata zauna tamin a cikin gida ni ban sani ba" "Nidai Hajiya duk ba wannan ba, Nidai dan Allah kimin kamun k'afa dan kece kawai nasan zakimin tsaye har in samu muradin raina"Sultana ta k'ara fad'a a marairaice tana kwabe fuska, "To wani abun ne kuma yake faruwa hala?" "Ah ah Hajiya bai farun ba tukun ina dai fatan faruwar hakan shi yasa nace gara kawai in sanar dake tun da wuri dan Wallahi ke k'adaice nasan zaki samar min da mafita cikin sauk'i" "Ke nifa a rayuwa babu abunda ke b'atan rai irin mutum yayi ta kwane kwane bazaiyi magana dani kai tsaye ba, To in baki fad'amin ba taya kike zaton zan gano" K'asa sosai Sultana da duk'ar da kanta tana cigaba da murza yan yatsun ta data jerama zubuna guda uku, tace "Hajiya dan Allah karkice bani da kunya, wallahi ba rashin kunya bane kawai nidai inajin tsoron kar wata tazo tamin shigar sauri ne idan nayi nauyin baki, kuma naga aiba laifi bane dan mace taga namiji tace tana son shi mai makon Inbar abun a cikin zuciyata ya zamar mini wani k'atoton cutar da zai iya Kaini gushewata bayan nasan idan na furta ana iya samar min da mafita" Shiru tayi tana cigaba da mutsu mutsu dan gaba d'aya zuwa wannan lokacin tama kasa zaman da kyau kunyar k'aryar data aro ta d'aura ma kanta kuma ya hanata iya d'agowa ta kalli Hajiya duk da yanda takejin kallon da Hajiyar take mata, Itama kuma Hajiyar k'in cewa komai tayi har sai da ita Sultanan ta gaji da mutsu mutsun ta aro ma kanta jarumta kafin taci gaba da cewa, "Hajiya zaki taimaka min wajen samun abun da nike so?" Bata jira hajiyar ta amsa ba taci gaba da cewa. "Nidai ko bazan samu taimakon kowa ba zan fad'i abunda nike ji, Hajiya wallahi nidai ina son Ya Abdul Khareem Mai Jama'a dan Allah ki gabatar dani a wajen shi ko zan samu ya taimaka ya aureni! Wallahi ina son shi son da nike jin cewa bazan iya rayuwar aure dako wani mijiba inba shiba, dan Allah Hajiya kisa baki yanda zai saurareni su Meelat sun fad'amin duk yan matan dake nuna suna son shi basa sha ta dad'i amma ni kuma daga jiya zuwa yau son shi yamin kamun da bana jin zan iya jurewa ba tareda na bari ya gane ba shi yasa na fara tun karar ki dan ki tallafa min ko zan samu ya kulani" Ta k'ara fad'a harda matso wasu k'ananun hawaye na munafunci, Idan kunga yanda ta koma a gaban Hajiya dad'e duniya zakuyi zaton duk abubuwan da take fad'a gaskiyar su kenan bawai shirya su tayi ba, dan gaba d'aya ta juye ta koma kallar tausayi, Meenal da tun d'azun kallo d'aya tama Sultanan ta d'auke kanta ta maida kan wayanta da suke chat da Ya Sa'eed wanda yake tambayan ta akan goben zata koma zaria ko sai anyi bakwai ne, Jin wasu soki burutsun da tsinannun aljannun tsakar daren da suka hau kan sultanan suka sa ta hauka takeyi ne hakan ya sa Meenal d'in jan wani irin dogon tsakin daya fita da k'ara kamar zata cire harshenta,wani irin bak'in ciki mad'aukaki ne taji yana neman rufe ji da ganin ta, sai takeji kamar gizone maganganun na sultana ko kuma dai kila Sultanan ta shawo wasu kwayoyin da sukafi k'arfin kanta ne ko kuma dai aljannun gareta da gaske. Bata tsaya ba Ya Sa'eed amsar tambayar shiba ta mik'e tsam daga inda take zaune jin surutan yana neman wuce abunda kwalwarta zata iya d'auka, Zufa taji yana neman lullub'eta duk da ac da fankan da suke ta aiki a falon, d'aki ta shige kai tsaye dan tabbas tana buk'atar watsa ruwa masu sanyi a jikin ta k'ila ko zata dawo dai dai, Kai itafa sai takejin kamar ma dai aikin shedanu ne suka sa kunnuwan ta jiyo mata maganganun da ta tabbata k'ila ba haka Sultanan ta fad'e suba, inba haka ba taya ma sultanan da kwata kwata yaushe ma tasan Taubashin da har zata wani rikice da kukan cewa shi take so harda wani rok'on Hajiya akan ta taimaka mata, kai ina wannan ai sai dai aikin shed'anun wallahi, Dan haka sai kawai ta maida hankali wajen karanto addu'o'in neman tsari daga shaid'anu kafin ta tub'e ta shiga makewayin ta yi kunna shower ta tsaya a k'arkashin ruwan sanyi tana ta k'ok'arin ganin ta ture tunanin nukan dake neman rikita mata kwalwa, Ta dad'e a cikin bayin kafin tayi wanka ta fito, Sai da ta fara tsane gashin kanta da ruwa yama jagab da towel duk da bawai ruwan jikin gashin nata ya tsane duka bane bata damuba tana fitowa gaban Mirror ta k'arasa tayi zaman shafan mai saida ta gama shafa man kafin ta taje gashin kan nata sama sama ta d'aure shi da jan ribom k'arami sannan ta mik'e ta k'arasa inda akwatin ta yake ta ciro wasu riga da wando masu fad'i sosai na bacci ta zura a jikinta kafinta fesa turare k'aramin hula ta d'aura akan nata, Wayarta da tun shigowar ta cikin d'akin ta ajiye akan gadon ta d'auka dan yunwa takeji unin yau d'in bata wani saki jiki taci abinci a gidan rasuwa ba, tana ta tsumin sai sun fita sannan taci ma ranta abunda take so gashi shi wannan d'an iyan ya wani zo ya kejesu a cikin gida yasa an rufe mishi gate ta yanda bazasu samu damar fitan ba. tunda dai yau Sarkin isa iko da mallaka mulkin nashi ya motsa yace bazasu fita ba to gara ta gama komai da wuri ta kwanta ta hutama ranta shi kuma idan yaso sai yaci kanshi, Inyagan ta a arha yau ai gobe dai ba ganin ta zaiyi ba kuma daga ita har wancan mai shafar aljannun gidan zasu bari kowa yayi ta kanshi. Koda ta fita wannan karan ba iya Hajiya da Sultana kad'ai bane a falon ah ah harda ma shi kanshi gogan shima ko kunya baiji ba ya wani dawo falon ya zauna cikin k'annin shi mata, Tana fitowa falon bata kalli inda su Hajiya ke zaune ba kawai sai ta wani wuce su ta k'arasa inda shi gogan ke hakimce, Tana zuwa bata jira komai ba ta mik'a hannun ta kamo nashi hannun ta kama janshi, Ita nan a dole wai so take ta d'ago shi daga zaunen da yake ita nan ga yar mai k'arfi itama sai dai kuma duk yanda tasa k'arfin dan ta tadashi hakan ya gagara dan shima gogan zama yayi gingirim kamar wani gunki yana binta da kallo kuma baice mata komai ba, "Kai Ya'ya wai dan Allah bazaka tashi ba kana ganin k'arfina sai k'arewa yakeyi😣" ta fad'a tana b'ata fuska kamar mai shirin fashewa da kuka. "Me zan miki ne wai kike son damuna?" "Kai yaya ka taso ka gani mana, ai kasan dai haka kawai bazan zo ince ka taso ba" Mikewa yayi ita kuma taci gaba da jan hannun shi kamar wasu rak'umi da akala sai da suka gitta su Hajiya Sultana da magantu da cewa, "Sister ina zaki kaishi kuma? yanzun nan fa na kirashi ya fito saboda muci abinci ke kad'aifa muke jira dama yanzun kuma kin fita kin janye shi kuna shirin komawa" Sultana na saukewa Hajiya itama ta d'aura da cewa, "Ah lallai kam, to da kika fito kike neman k'ara mai dashi cikin d'akin mai zai miki a ciki ne wai?" "Uhmm nidai Hajiya ba ruwan ku ai takardun motana zamuje ya bani tunda gobe idan Allah ya kaimu idan muka fita da safe ba k'ara dawowa zamuyi ba, To idan na manta ban k'arbi takardun ba kuma fa? In ma abincin ne ku faraci kafin mu fito suma su Meelat ai naga basu gama ba balle su fito in kuma kunajin yunwa ne ai sai ku faraci ku biyun," Kamar da gayya haka tajashi fuuuu suka wuce ita ta bud'e kofar d'akin shi ta fara turashi ciki kafin tabi shi a baya, Suna shiga ta nemi gefen gadon shi ta zauna tana wani irin cika tana batsewa, Sai faman girgiza kafarta data d'aura d'aya kan d'aya takeyi, shiko tsayuwa yaci gaba dayi a gaban ta, shi bai zauna ba kuma bai tanka mata ba, dan bai sani ba ko laifin hanasu fitan ne yasa ta kawo shi d'aki take neman tsare shi saiya fad'a mata dalilin shi na hanasu fitan, "Kambala'i wallahi da gaske yarinyar nan bata da hankali lallai nema, wannan ma ai rashin sanin darajar kaine kawai daga ganin mutum.... " Kyacci tayi tama kasa k'arasa fad'ar me tayi niyyar cewa, "Wai me ya sameki ne kuma?" Ak ya tambaya ganin yanda take ta wani girgiza uwa wata mai shirin tada aljannu. "Eh aima dole ka tambayeni mai yake faruwa, Allah kuwa Taubashi ina fad'a maka inma asiri kake ma yan mata shi yasa da zarar sunyi ido biyu dakai suke kware maka gara ka ceci kanka ka karya asirin nan inba haka ba wallahi wata rana yan matan aljannu ne zasu fara bibiyar ka, haba dan Allah shikenan rayuwa kai da zarar kayi ido biyu da mace tun tafiya batayi nisa ba sai kaji zance yana neman canzawa" "Mai yake faruwa ne nace?" Ya k'ara tambaya a karo na biyu, "Ba kana kallo ba ita wancan bak'uwar dake kama da shafar aljannu to wallahi d'azun nan taje wajen Hajiya tana kuka take had'a Hajiyar da Allah da annabi akan tasa baki wai ita Sultanan ke son kafa, Kuma harda cewa ma tayi wai inba kai ta aura ba bazata iya rayuwa dako wani mijin ba, kaji fa, to tunda yanzun aka fara samun wacce ta iya tunkarar Hajiya gaba da gaba ba kunya bare tsoron Allah tace mata sonka take to tabbas zuwa gaba ma sai an samu wacce zatace kunyi auren sirri" Da kallo yake ta binta jama'a ga abun dariya amma kuma ba halin darawan, juyawa yayi ya maida kanshi gefe a yayinda dariyar ta nemi kubuce mishi karamin dariya mara sauti yayi yana rufe bakin shi da hannu kafin ya juyo inda take ya k'arasa ya zauna, "Wai ita wacece Sultanar?" "Yarinyar Yayan Baba Auta cefa, a abuja suke zaune nima ba wani sanin ta nayi ba sai wannan zuwan da sukayi, waya sani ma ko lafiyar kwalwa ne bai isheta ba" Ta fad'a tana tsatsare shi da ido tana jin me zaice kuma, Ga mamaki ta wai sai gani tayi fuskar nan tashi dake kwana ta uni a d'aure tamau amma sai ya wani saki fuskar yana murmushin shi mai narkar da zuciyar mai kallo, Giraren shi ya d'age kamar yanda ya saba indan zaiyi magana da ita yace, "Ashe ma yar uwarki ce, shi yasa tun jiya dana ganta nima na kasa nutsuwar kamar yanda naga itama ta rikice taga yaro d'an sawalwalin yan mata, To ashema abun zaizo da sauki tunda harta gani kuma ta yaba aini kuma babu wani zancen jan aji kawai kice mata na bada gari, ta turo manya kawai ayi batun sa rana dama nima na gaji da zaman tuzurancin nan haka, dama jira nike inji wata ta taya, bari ki gani inje in same su muyi magana baki da baki in a shirye take aini sharr wallahi kinga ko anan gidan saita fara zama kafin in kammala wancan koya kikace?" Ya k'arasa fad'a yana kureta da kallo ganin yanda tayi tsaye kawai tana bin bakin shi dake motsi da kallo kamar wacce bata gane me yake cewa ba, "Kaiii Wai kaima nan son nata kakeyi?😕" Ta tambaya a shekek'e tana jiran ya bata amsa, "To me zai hana bazan sota bayan ita dake mace ta kasa boye nata son da take min duk da irin kunyar da aka san mata dasu, gata da kyanta masha Allah aini ban san duk wancan zazzafan gayun data d'auka dan ni tayi ba da tuni na yaba, Amma kinga d'an bawan allah sai komawa gefe mayi Ina Satan kallon ta" Fuuuu ta mik'e bayan ta cika bakinta da iska tana shirin ficewa daga cikin d'akin ya rik'o kafadunta ya dawo da ita cikin d'akin, Baya ta juya mishi tana kunkuni take cewa, "Ni ka kyaleni inyi tafiya ta, badai Sultana kake soba kaje ai sai kuyi ta soyayyar ku can in kunga dama ma kuna iya konewa ni ba ruwa na" Juyo da ita yayi ita kuma sai kokarin kwacewa take ya hanata damar hakan, "Kishi Taubashiya? Fad'amin kishina kikeyi ne?" "Allah ya kyauta to akan me zanyi wani kishin ka, bayan kai ba mijina ba komai ba" "Kishina kikeyi Meenal ko ki yarda ko karki yarda" "Ni bana wani kishin ka kawai dai ina fad'a maka gaskiya ne" Ta fad'a tana murgud'a baki batareda ta dena jijjige jijjigen jikin da takeyi daga tsayen ba, "Kina son kiji gaskiyar abunda yake cikin zuciyata Meenal?" "Akwai wani gaskiyar ne bayan wanda ka furta yanzun cewar kana son Sultana?" Itama ta maida mishi da tambaya tana kauda kai gefe, "Akwai Meenal! Akwai gaskiyar dana dad'e ina shakkar fad'a miki ita, Gaskiyar da aduk sanda mayi yunk'urin furta miki sai zuciyata tayi nauyi sai kuma inga kin min kwarjini ta yanda nake rasa kwarin gwuiwata a gaban ki," Zagayawa yayi zuwa gefen data juya fuskarta yakai kafafuwar shi k'asa yana mai kamo tafukan hannayen ta cikin nashi, "Meenal ina son ki yarda da duk wata kalmar da zakiji ta fito daga bakina a yanzun zuwa cikin kunnen ki, Domin sakon dake d'auke cikin zuciyata ne nike son isar ma taki zuciyar, Ke ba k'aramar yarinyar da nayi ta ririta soyayyar ta a shekarun baya bane balle ince zaki kasa gane kalamai na," "Kara riko hannun ta yayi da kyau jin tana mutsu mutsu tana son zare hannun daga rikon daya mata, "Ina sonki Meenal, Ina matuk'ar kaunar, ina so ki sani cewa da kaunarki nike kwana a cikin k'irjina haka kuma da ita nike tashi, Ita wancan yarinyar cewa tayi bazata iya rayuwa da wani namijin ba sai nikoh? To ki sani cewa ni kuma bazan iya kasancewa a raye da cikakkiyar lafiya aduk sanda na k'ara rasaki a karo na biyu a cikin wannan duniyar ba," Sakin hannunta guda d'aya yayi sai ya d'aura duka hannayen nashi biyu akan hannun ta na dama, Sai da yakai hannun nata kan lab'b'anshi ya sakar mata wani kalar kiss mai tsotse jinin jiki ba tareda ya saki hannun ba duk da yanda yake ganin jikin ta na d'aukar karkarwa, yaci gaba da cewa, "Ina son ki Meenal wallahi ina son ki sona gaskiya da gaskiya bawai so na wasa ba, ki taimaka ki amshi tayin soyayya ta ki kuma bani dama ni kuma in gabatar da kaina a wajen iyayen mu su aura minke in tashi daga matakin tuzurun da kika dad'e kina kirana zuwa mijin auren ki. Misalin k'arfe 8 da mintoci Salman ya iso kofar gidan AK domin yau bai samu damar zama a can gidan rasuwar ba gashi kuma yana ta cema Meenal d'in zai zo Allah baiyi ba kuma yasan gobe idan har suka koma Zaria to wuyan gani zata mishi, Bai manta kwatancen da Meelat ta mishi ba dan haka koda zai taso bai kirata a waya ba har saida ya iso kofar gidan ya nemi waje yayi parking. Kiran wayanta da yayi, Hakan yayi dai dai da lokacin da AK yake durk'ushe a gaban ta yana koro mata kalaman da suke tsotse mata ruwan jiki, Da kyar ta samu ta sanya hannun ta guda da yake free ya zaro wayar daga aljuhun wandon jikin ta jikinta na karkarwa. No editing 🥳 *Ummiee ce*✍🏼 [9/8, 2:20 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 22* Batareda hannun ta ya dena rawa ba ta samu ta d'auki wayar ta dannata a speaker, shi kuma jin ta d'auka bayan yayi sallam dabai jira jin amsarta ba ya d'aura da cewa, "Ranki ya dade gani a kofar gidan fa, Allah yamin isowa, hello! Hello!! Hello Meenal kina jina kuwa?" Yayi ta maimaitawa jin tayi shiru bata amsa ba, Hannu AK ya mik'a ya zare wayar dake cikin hannun nata ya yanke kiran kafin ya kashe wayar gaba d'aya, Mikewa daga tsugunen da yake yayi sai ya kamo kafad'un ta da takufan hannayen shi ya k'arasa da ita gefen gadon shi ya zaunar, ita dai da ido kawai take bin shi kurrr ko kyaftawa bata son idon sunayi dan so take ta tantance shi d'in ne dai a gaban ta ko kuma wani shed'anin aljanine yayi suffa irin nashi dan taga alama yau gidan ruwan aljannu akeyi, A k'asa inda kafafuwan ta suke ya nemi waje shima ya zauna bai yarda kuma ya saki sannayen ta ba yanzun d'in ma tafin hannun ta yana cikin nashi yana mamma tsa matasu yaci gaba da cewa, "Karkiyi mamaki kokonto ko jin shakka akan dukan kalaman da zakiji daga gareni, I know that I am not perfect, niba kowa bane face d'an Adam wanda Allah kan iya jarabta a ko wani irin lokaci, Ni ba d'an soyayya bane dan haka ban kasance cikin sahun mazaje masu wasa da zuciyar mata ba, Na sani abu d'aya ke miki yawo akai shine yanda yan mata ke yawan bibiyata, Sai dai ina so ki sani yakice su da nikeyi daga jikina hakan bawai yana nufin ina wulakanta su bane kawai saboda sun nuna suna sona, Ah ah ita d'iya mace kaddara ce mai daraja, kasancewa ta namiji kuma bashine zai bani damar yin amfani da son da suke nuna min dan in wulakanta suba, Domin ko da nike namiji ai ina da yayye da kuma k'anni mata kuma bazanji dad'i idan naga wani yana wulakanta min suba, Wannan dalilin ne yasa duk mace da ta nuna min tana buk'atar kusanta kanta gareni ni kuma sai in nesanta kaina da ita, Tarayya na tsakanin namiji da mace sun kasune kamar haka, Kodai tarayya ta soyayya, ko kuma Abota na had'uwar jini ko kuma mummunar alaqar da addini ya haramta mana, Idan naso zanyi amfani da damar makin da nike dashi akan su wajen bin son zuciya in shiga cikin rayuwar su in kuma yi amfani da son da suke min in cimma manufata ko wacce irice akan su batareda nasha wahala ba, Amma kuma miye amfanin hakan wacce riba zanci idan na aikata hakan bayan a rubuce take cewa abunda kayi ma wani kaima shi za'a maka, ya zanji idan wani abu mara kyau ya faru da nawa ahalin? Wannan dalilin shine yasa a kullum nike k'ara rik'e kaina nike kuma k'ara nesanta kaina dako wacce mace sai dai kuma ku dama sauran jama'a gurguwar fahimta kukamin a ganin ku kawai Ina amfani da damar da nike dashi ne wajen wulakanta mata, Kun kasa hasaso cewa sufa matan ba nine nike gayyatar su zuwa duk inda nike ba, Kaini inda so samuna nane ace in rayu can wani wajen daban inda bazan dunga had'a ido da matan ba da hakan zaifi min saboda tsoron fad'awa halaka da nikeyi akoda yaushe, Kin san meya canza ra'ayina akan mata?" Ya tambaya a yayinda ya mik'a hannun shi ya gyara mata zaman gashinta daya zame daga cikin ribom d'in data d'aure shi ya maida mata shi ta gefen kunnenta, Kafin ya d'anja hannun rigar shi ya fara tsane mata sauran ruwan da yake gangarowa daga cikin gashin ta yana Saukowa kan wuyanta, Hannun ta ta mik'a ta rigo nashi saboda yanda takejin gab'obin jikin ta suna k'ara sanyayewa, Saida ya shafa gefen fuskanta da tafin hannun shi kafin ya k'ara komawa gaban ta d'in yayi zaman d'alibi a gaban malamin shi kana ya d'aura da cewa, "Kece macen da sonta ya fara narkamin dakakkiyar zuciyar da nike tak'amar cewa bata isa ta kamu da son kowata mace ba har sai wanda nid'in na duba naga ta cancanta, Yes nasan na raina ajin mata saboda yanda suke bibiyata kullum kamar naman da aka kasa a mayanka, Sai gashi kwatsam sonki yayi min shigar saurin ta yanda banyi zato ko tsammani ba, Nayi zaton soyayya kamar karatu ne mataki mataki wanda za'a farashi daga k'aramin mataki zuwa matakin sakandire wanda in ka kaican kaike da damar zab'arma kanka hanyar da kake ganin zata bulle da kai, Kodai ka d'auki fannin science ko kuma art, Kin san me? " Ya k'ara tambaya yana cigaba da binta da kallo ita d'ai ko motsin kwarai bata iyawa balle kuma ta samu kwarin gwuiwar amsa mishi, Shima dai ganin bazata amsa d'inba sai kawai yaci gaba da cewa, "Na dade ina hasaso kalar macen da zan nema aduk sanda na shirya fara gudanar da soyayya, ko sau daya ban tab'a hango kaina cewa wai ni ABDUL KHAREEM AHMAD MAI JAMA'A, zan k'are akan son k'aramar yarinya ba sai da zuciyata ta butulce min wajen nuna min isarta a kaina ta fad'a sonki da karfin tuwo, Na d'auka cewa soyayyar kamar wasan kwaikwayo ne yanda kaso haka zaka tsara ka shiryata kuma ka gabatar, Sai da na fara sonki na gane cewa ita soyyaya afkuwa kawai takeyi kai tsaye bawai mu ke k'irk'irarta ba, sai da nayi nisa a cikin soyayyar ki kafin na tabbatar da cewa zuciya tana da matsanan cin son kanta ita kawai ta samu wanda take so shi tafiso amma shi lokaci yafi adalci wanda ya cancanta shi yake bawa, kamar yanda abunda yake faruwa tsakanina dake, Kinga a shekarun baya inda na furta miki kalmar so bana da tabbacin cewa ko zaki aminta sai dai kuma koda baki amince ba nasan zan samu goyon bayan mutane da dama wanda kuma hakan yana iya tab'a zumunci dan duka gefen biyu kowa zaiso ya gwada ikon da yake dashi ne a kanki, Amma da yike shi lokaci yafi yima kowa adalci sai gashi lokacin yazo kuma komai ya warware batareda wani abu ya shiga tsakanin zumunci ba. Meenal ki sani ko ina numfashi ko banayi bazan tab'acin amanar soyyaya ta dake ba. Shin kinsan cewa duk yawan jama'ar mutanen danake mu'amalanta kad'an daga cikin sune suka samu kusanci da zuciyata? Misali iyayena saboda ina samun kariya daga garesu, kema haka naji akanki tun daga sanda na gano kishin ki a kaina, tundaga sannan kuma ban k'ara tunanin kowacce mace ba saike, Kawai a kullum burina shine na k'are rayuwata tareda ke a cikin shi, Ki sani ko ki soni ko kada ki soni har abada bazan tab'a dena sonki zan k'ara mai maita miki a karo mara adadi cewa, ni AKA Mai Jama'a *INA SONKI*³. Meenal bana so na sakeyin saken da zaki kufcemin ki amince dani na miki alkawarin cewa bazakiyi dana sanin bani amanar kankiba, Nayarda ko bakya sona wallahi zan zauna dake dan kaunar da nike miki kad'ai ta isa ta riqe auren mu, Nidai kawai ki amince min akan kaunar da nike miki dan yardar ki kad'ai nike nema. Ban tab'a sarewa ba dai dai dana sa'a guda tun ranar dana rasaki a kullum cikin addu'a nike idan har son da zuciyata ke miki alhairine a tsakanin mu allah ya tabbatar min dashi, Sai gashi yanzun bayan shekararun da har na sare nafara cire raina akanki Allah ya k'arbi addu'ata ya dawo min dake cikin rayuwata, Dan Allah karki sake jefa zuciyata a cikin quncin data rayu a ciki tsayin shekarun da kikayi nesa dani, Ban sani ba ko k'ila a cikin zuciyar ki akwai wanda kikejin soyayyar shi, amma ni a wajena hakan bai isa yasamin linzami ba domin ko son wani bashi ne ba a soka shine muradin ko wani mai so, bazanyi gaggawa wajen sonjin ra'ayin ki a kaina ba, Dole zan baki dama kije kiyi tunani akan hakan." "Mik'ewa yayi tsaye sannan ya wuce gaba zuwa wajen k'aramin pridge din dake cikin d'akin ya ciro mata ruwan gora mara sanyi sosai kamar yasan tana buk'atar jik'a makoshin ta da takejin ya bushe mata qamas, Sai da ya bud'e murfin goran sannan yakai hannushi guda daya ya tallafe kanta yakai mata ruwan a baki, Sai da tasha kusan rabin goran sannan ya cire goran daga bakin ta ya maida kan nashi bakin ya shanye sauran, jefar da goran yayi anan tsakiyar d'akin ya kamo hannun ta, "Muje kici abinci nasan mu suke jira tun d'azun" Ya fad'a a yayinda yake cigaba da mata jagora da niyyar barin d'akin, Abin takaici abin dariya da gudu yan gulman da suka lab'e daga bakin kofar d'akin suka bar wajen suka koma cikin falon ko wacce na neman wajen zama suka wani fuska suna kama wata hirar, *Abinda ya faru bayan Meenak taja Ak zuwa d'akin kuwa shine*....... Suna shigewa kusan a tare Maryam da Meelat suka fito Maryam daga kitchen ta kwaso sauran kayan abincin da bata gama kawowa kan dinning ba ita kuma Meelat sai yanzun ta gama shiri shi yasa ta fito, Suna ganin sun shige duk sai suka dawo tsakar falon sukayi tsai-tsaye gulma na cin su sai dai kuma ganin Hajiya sai suka so su fuske, "Ku kuma wannan tsayuwar zakarun damben da kukazo kuka min a tsakar kai na menene?" Hajiya ta tambaya a yayinda take bin fuskokin su da kallo, Dariya Sultana ta fashe dashi mara k'ara sosai tana nuna kofar d'akin na AK take cewa, "Kunga abunda na fad'a muku koh? Wallahi da gaske itama tana son shi, ai naso ace kuna kusa d'azun kuga a yanda ta iya kai kanta d'aki da kyar" "Ya akayi ne mutuniyar?" Meelat ta tambayi sultanan tana dafa kafad'arta, "Ke Beb dan Allah bamu musha wai ya akayi ne anci ancinye bamu da labari tun d'azun da naga kin d'au wanka naso inyi magana sai kuma dai na share" Waje dukan su suka nema suka zauna akan 3sitter din da Hajiya ke zaune duk da kujerar ta musu kad'an basu damuba, Tsaf Sultana ta shaida musu abunda ta fad'ama Hajiyan a gaban Meenal d'in tun kafin takai k'arshe suke dariya, Hajiya ko da mamaki take kallon su sai can ta bud'e baki tace, "Oh wai kuma kenan kun gane cewa shi Yayan naku son Meenal d'in yake?" "Haba Hajiya waye ma zai zauna dasu yace bai fahimci komai dake gudana a cikin zukatan su ba!"inji Meelat, Sultana kuma ta d'aura da cewa " Wallahi itama son shi take Hajiya ba gashi ba dai yanzun kinga komai daya faru a gaban idon ki, "To kenan ke da kikazo kina min kukan cewa kina son shi wannan d'in ma duk shirin kune a kansu ko ya abun yake?🤔" Hajiya ta tambaya cike da mamakin su ta yanda suka gudanar da komai gashi tun ba'aje ko ina ba su wad'anda aka ma gadar zaren sun fad'a, "To wai yayan nan kenan kuna nufin wayau kuka fini shi yasa tuntuni ni na kasa zarge su waje d'aya ko yayane?" "Ah Hajiya wane mu mu miki yawau kawai gani mukayi dukan su inba hakan aka musu ba bazasu fito fili su amayar da abunda ke cikin zukatan suba musamman ma dai shi da yakeyi kamar yana shakkarta wallahi, Sad'af sad'af Sultana ta cire takalmin kafarta ta k'arasa bakin kofar d'akin AK d'in da turawa kawai Meenal tayi kuma bai wani rufu da kyau ba ta kafa kunne tana jiyo hirar dake gudana tsakanin AK da Meenal d'in ganin hakan ne kuma suma Maryam da Meelat suka rufa mata baya, Basai ga Hajiya itama ta rashi tinkis tinkis tabi sahun suba, Kaf hirar daya gudana tsakanin su a cikin kunnuwan su babu abunda basuji ba, Hajiya ce ta fara komawa kan kujerar data dawo cike da Mamakin AK sai faman gyacci da gyad'a kai take saboda tsabar mamakin kalaman da kunnuwan ta sukajiyo mata sun fito daga bakin AK din, Intayi tayi sai ta tafa hannu ta rik'e hab'a tana sauke ajiyar zuciya, Har zuwa sanda motsin fitowar su yasa su Sultana baro bakin k'ofar, Su Ak na fitowa dama bai tsaya sauraran kowa ba ya wuce da Meenal d'in can wajen dinning yaja mata kujera kafin ya zaunar da ita, Ganin hakan ne kuma yasa suma su Maryam tasowa suka iso wajen, Sultana ce da rawar jiki ta fara saving d'insu sai da ta fara zuba ma Hajiya ta ajiye mata a gabanta kafin ta koma gefen AK da niyyar zuba mishi suma, filet din ta fara ajiyewa a gaban shi, "Ya'ya mai zakaci in zuba maka?" Ta tambaya da k'aramar murya tana kallon shi, Nashi kallon shi kuma ya maida kan Meenal dake zaune a gefen shi, Sultana bata jira jin ta bakin shiba ganin ya basar sai kawai ta mik'a hannu da niyyar d'auko kulan da yake gefe wanda ke d'auke da tuwon semo wanda aka tuk'ashi da kyau aka mulmula shi a cikin farar leda, Hannu itama Meenal takai ta fincike kulan mik'ewa tsaye tayi bata yarda ta kalli fuskar kowa a cikin suba har shi kanshi Ak d'in, tuwon guda biyu ta d'aura mishi a plate din data d'auko bayan ta d'auke Wanda Sultana ta ajiye ta maida gaban ta, Sai da ta had'a mishi komai da tasan yana buk'ata ta jera mishi a gaban shi kafin ta koma itama ta zauna, Faten dankalin turawa ta zuba a nata plate d'in itama ta faraci, Abu biyu suka zaunar da ita akan dinning din na farko yunwar cikin ta na biyu kuma gani takeyi kamar idan ta tashi sultana zata samu damar cusa kanta a wajen AK ne, A hankali take cin abincin su kuma su Maryam da ido suke gulmar su, Domin dai shi gogan nunawa yayi kamar bai san da zaman kowa a wajen ba daga shi sai gimbiyar shi kawai yake gani, dan lokaci lokaci zai juya wajen ta namomin data tara mishi a plate ma kusan kwashewa yayi ya maida mata cikin nata plate din, "Kici wannan kiji yanda yayi dad'i," Ya fad'a a sanda ya gutsuro leman tuwon samo din da yake ci ya dangwali miya ya had'a da namar kazar dake cikin miyan ya kai bakin ta, "Ci mana Allah kuwa yayi dad'i sosai" Ya k'ara furta hakan ganin tana kauda kai bata son ci daga hannun shi, Hannun shi d'aya yasa ya matse bakinta ya cusa mata tuwon yana dariya yake cewa, "Wallahi sai kinci shi gara in koya miki cin tuwo tun yanzun" Tafa hannuwa Hajiya ta fara tana salati da sallallami, "Kai Abdul Kahareemu! Oh ni Aminatu yau nikam nike ganin abunda yafi zare tsayi ganin idona, Nace wai ana cin tuwo dole ne yarinya tace kasan bason tuwo take ba amma harda wani matse mata baki ka d'ura mata uwa dai wanda akayi ma dole, Nace ana dole ne nikam, Ke wai tsaya ma, ina ce nan da kikaja shi zuwa cikin d'aki cewa kikayi zaki amso takardun mota, yanzun da kuka fito hannu na dukan cinya takardun suna ina? Ko koh ah ah dama tsabar gulma ne ya kaiku d'akin bayan kun gama gulmar ne kuka fito?" Daga shi har Meenal d'in babu wanda yayi gigin tankame Hajiya ke cewa, ita dai Allah take ta gama cin nata abincin ma ta bar musu falon, Dan haka ita ta fara gamawa ta mik'e shima kamar jiran tashinta yake sai ya rufa mata baya yana tambayan ta "Bacci zakiyi?" "Eh ta amsa dashi batareda ta tsaya ba, "Ok ga wayar ki,"ya zaro wayar daga aljihun shi yasa mata a cikin tafin hannun ta, "Karki kunna tafa sai da safe" Wucewa tayi zuwa d'aki shima ya shige bayan ya juyo yama hajiya sai da safe, Mamaki kusan sumar da Hajiya yayi daga zaunen da take tana kallon ikon Allah, "Jama'a wai dama haka maza ke komawa duk su makance idan suka fad'a soyayya?" Ta ke tambayar su Meelat da tashin su AK d'in ya basu damar fitar da nasu maganganun suma, "Ai hajiya yanzun dai sai dai mu baki irin shawarar da akeba sabuwar amarya, Kiji kik'i ji, Ki gani kiki gani, atoh" Cewar Sultana tana dariya. Sabon hirar gulman su Meenal din suka bud'e suna k'ara tabbatar ma da Hajiya irin alaqar soyayyar dake tsakanin jikokin nata wanda a kalaman sune itama ta dunga tuna wasu abubuwan da suka shud'e wanda tun wancan lokacin ya kamata ta gano komai amma bata maida hankali a wancan lokacin ba. Shiko Salman yana kokarin k'ara kiran wayar na Meenal ne shima kira ya shigo cikin wayar shi ana neman shi da gaggawa, Bayan sun gama magana da wanda ya kirashi sai da ya k'ara gwada kiran number din yaji wayar a kashe sai kawai ya juya, A zuciyar shi yake cewa shima dai bayan su zaibi gara aje can Zarian ayi duk wacce za'ayi dan shima fa a yanzun aure yake so ba kuma da kowa ba sai da Meenal dan haka in ita tak'i sauraron shi To cikin biyu ne zaiyi d'aya ko dai ya tunkari Baba Adamu ko kuma ya kai maganar wajen Malam kawai kai tsaye. No editing 😣 *Ummiee ce*✍🏼 [9/10, 9:21 AM] Ummiee Zaria: 🔱⚜️👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦⚜️🔱 *BOOK 2* *PAGE 23* Alaqa tsakanin Sarki da Moon zuwa yanzun zamu iya cewa abubuwa sun fara kan kama, Domin da fari yayi zaton abun na wasa ne, irin ai tunda k'aramar yarinya ce kwana nawa ne zai shawo kanta idan ya gabatar mata da abunda ke cikin zuciyar shi a kanta, Sai gashi kamar ita kuma tasan manufar shi a kanta domin dai tun ranar daya sha gaban ta da mota sai ta fara wasan buya tsakanin ta dashi, Wanda hakan ne kuma yasa dole badan yaso ba ya nemi hutu a wajen aikin shi ya zauna a Lagos d'in domin ya kuduri aniyar yad'a manufar shi da kyau bazaiyi wasa da damar shiba har sai ya samu abunda yake muradin mallaka, dan wani irin so da kaunar ta mai tsanani ne yake jin suna azalzalan shi. Acan Kaduna kuma tuni ya nemi muhallin da Teemah zata zauna a ciki in sun koma saboda ya faranta mata kamar yanda ya shaida mata kuma gidan irin wanda take da muradi ya shiya sai dai kuma abunda bata sani ba Sassa ukune a gidan wato dai d'aya nashi biyun kuma na matan shi, Salman ke kula da gyaran gidan dan yana son inya tashi tafiya su koma gaba d'aya kawai kafin nan kuma zaiyi k'ok'arin saito kan Moon kai shi in so samu ne ma baik'i a fara tsaida magana kafin ya koma ba, Sai dai ita gimbiyar da alama zai sha fama da ita, saboda yanda take nuna mishi bata son wata doguwar alaqa wacce ta wuce na gaisuwa ta shiga tsakanin su, Sai dai kuma duk yanda Moon d'in taso yakice shi hakan ya gagara dan sosai yake nuna nacin shi a kanta, Sai gashi a hankali a hankali Sarki ya dunga cusa kanshi wajen Moon d'in harta fara sake jiki dashi batareda ta ankara ba, Ya zamana tun tana basar dashi dan bataga dalilin kulawan da yake nuna mata da kuma yawan bibiyar al'amuranta da yake yiba har tazo dan dole ta fara sakin jikin dashi ganin ko sun had'u iya gaisuwa hirar wajen aiki dana karatu sune kad'ai hirar dake gudana a tsakanin su sai kuma wani lokacin yakan tuna mata kiriniyar da sukayi a shekarun baya lokacin daya fara sanin ta, A kance zuciya bata manta abunda take so koda ta manta shi na d'an lokaci ne, hakan ne yaso faruwa da Moon domin dai a wannan yawan had'uwar da yanda Sarki ke k'okarin cusa kanshi wajen ta dan ganin ta sake jikin ta aduk lokacin da suke tare, sai gashi bata ankara ba shi d'in ya fara zama wani b'arin farin cikin da zata iya cewa ta rasa a rayuwar ta, Bazata ce bata da farin jini ko kuma ta rasa masoya ba, Ah ah ita dai ra'ayin kanta ne yasa har zuwa lokacin bata wani sake ma maza fuska, ita d'in lauya ce mai kare hakkin mata dan haka a kullum suke had'uwa da cases kala kala na matsalolin da mata ke fuskanta a gidan aure su wanda zakuga wani baza'a samu dai daituwar kaiba har sai an kashe auren, Wannan dalilin shi yasa ta quduri aniyar bazata iya auren namijin da bata yarda dashi ba, tana son namiji wanda zai sota ya kuma zama mai tausayinta wanda zai kula da ita wanda zai tsare mutuncin ta dana iyayen ta ya kuma bata farin ciki ita da yaran da zata haifa mishi, Tana da k'ira irin na manyan mata masu cikakkiyar diri, hakan ne kuma yasa ko kad'an a tsarin ta babu auren Saurayin da baikai irin 38 zuwa 40 ba, tsayayyen namiji take son aure ba muna maza ba, sai gashi a yanzun da take jin cewa lokaci yayi daya kamata itama ta fidda mijin aure shi kuma Sarki ya fad'o cikin rayuwar ta yana neman yayi mata Kane Kane, To ina dalili fisabilillahi idan ana ganin ta tareda shi koda yaushe ai d'auka za'ayi ko saurayin ta ne, Kunga kenan duk masu shirin zuwa su gabatar da kansu a wajen ta ai sare musu guiwa zaiyi yasa su fasa fito mata da abunda ke cikin zuciyar su shi kenan ita kuma bawan bawan, Dan haka dole ta nemi matakin d'auka tunda wuri, Dafari matakin data fara d'auka shine d'auke k'afa ta hana kanta zuwa wajen da yasan tana zuwa kullum tunda anan yake samun ta, Sai ya zamana shi kuma daya fahimci cewa saboda shine ta d'auke k'afa da zuwa wajen kafin lokacin tashin ta aiki yayi yake zuwa wajen ya siya mata abubuwan da take buk'ata wanda yaron wajen ya shaida mishi sai ya aika mata dashi har office, Idan kuma akayi rashin sa'a bata office ta koma gida har gidan yake kaiwa yaba masu gadi su bata inji shi, Wannan abu da yakeyi ya k'ara jefa zuciyar ta cikin mamakin shi kwarai, Ya akayi yasan cewa tana yawan zuwa wajen? Ya akayi yasan gidan su? Ya kuma akayi yasan wajen aikin ta? Wadan nan amso shin duk tana buk'atar jinsu daga wajen shi, Domin dai inba wanda ya maka farin sani ba ko kuma yasa aka mishi bincike akan ka bai kamata ace mutum yasan yanda kake gudanar da rayuwar kaba. Duk yanda taso ta boye mishi kanta babu hali domin wani lokacin sai tana office dinta tana aiki zaije yasa a kira mishi ita, har ya zamana yan office d'insu sun sa musu ido da zarar yaje ake ce mata ga bak'onta ya iso, Ganin babu sarki sai Allah kawai sai itama ta share taci gaba da zuwa can d'in data dena zuwa saboda shi, Sai ya zamana tun tana d'ari² dashi har aka kai matakin da dan dole tazo ta sake dashi, Sai dai kuma koda ta tambaye shi yanda akayi yasan gidan su dama wajen aikin ta, bai wani tsaya ya bata amsa gamsasshiya ba, iya ka dai yace mata, "Aiba ku lauyoyi kad'ai bane kuka san kan yanda ake gudanar da bincike ba" Ita kuma tun daga ranar bata k'ara tada maganar ba, dan tasan dai bazai shigo rayuwarta dan ya cutar da ita ba duk da dai ita tana cutuwa da hakan, dan a kullum abubuwan da takeji a kanshi k'aruwa sukeyi daurewa kawai takeyi bata tab'a yarda ta nuna mishi ba shi yasa sau tari take gujema had'uwa dashi. Tunda ya fahimci cewa soyayyar ta ga wajen da take zuwa kullum sai ya zamana shima ya maida gun wajen zuwan shi, Can suke had'uwa zasuyi odan abunda suke so suci in lokacin tafiyar ta gida yayi zai rakata har kofar gida kafin ya juya ya koma, Daya fahimci cewa Teemah ta fara sa mishi ido akan yawan fitan da yake yi kusan kullum sai ya canza salo saboda dai a yanzun da take d'aukar al'amarin shi da mahimmanci shima kuma bazai so yayi wani abun na rashin kyautawa a gareta ba kodan saboda halin da ciki da take d'auke dashi ya ke jefata na yau lafiya gobe kuma babu tunda take haihuwa bata tab'a yin ciki mai tafe da zazzafar laulayi ba irin wannan dan haka shi kanshi ba k'aramin tausayinta yakeji ba, dan kullum addu'a takeyi Allah dai yasa yan biyune kuma maza🥰, Ganin tana damuwa da yawan fitan nashi, sai ya zamana wani lokacin ma tareda ita zasu fita sukan isa can d'in da wuri kafin Moon ta iso, duk ranar daya je wajen da Teemah baya tab'a bari Moon ta gansu domin kujerun dake can cikin lungu yake kama musu sai dai shi yakanyi zaman ne yana kallon kofar shigowa wajen, bazasu bar wajen ba kuma har sai ita Moon ta wuce tukun, Ita kuma idan bata ganshi ba wani lokacin takan d'an bata lokaci bata barin wajen da wuri, Bata da number din shi har yanzun balle tace ta kira wayar shi dan taji ko lafiya, Koda ma ace tana da number din bai zama lallai ta iya kiran ba dan har zuwa lokacin bata san matsayin da zata ajiye sabuwar alaqar daya ke kulluwa tsakanin ta da Sarkin ba, Sai dai ta sani tana matuk'ar tsintar kanta cikin farin ciki da jin dadi aduk lokacin daya nuna kulawar shi a kanta, kullum takan hana kanta zak'ewa a kan yawan tunanin shi, duk da dai har yanzun bai fito fili shima yace ga abunda ke cikin zuciyar shiba amma tana matuk'ar tsoron ranar da zai bayyana mata hakan, ita dai kawai tana tareda shine amma bazata ce tana son alaqar su ta yanke ko kuma alaqar tayi tsayi ba saboda idan har hakan ta faru to bata san da wani idon zata kalli yar uwarta Meenal ba ace ita Moon d'in tana soyayya da tsohon mijin yar uwarta, Dan haka sai kawai tayi waje na musamman ta ajiye shi a matsayin Ya'ya kuma abokin shawarar ta. *A can garin Kaduna kuwa, Washe gari* Koda asuba tayi duk yanda Hajiya takai ga iya sammakon tashi yau Meenal wacce tayi bacci rabi da rabi ta riga Hajiyar tashi tuni, domin dai Allah ya sani ta dad'e bataga daren da yayi mata tsayin da gari yak'i wayewa da sauri ba irin wannan dare, Domin dai gaba d'aya ji tayi kamar kanta na neman juyewa, akan tarin kalaman daya zazzage mata shi ko kananun shekarun ta bai duba ba zai ajiyeta ya dunga zaro mata kalaman da tunda Mommy ta haifota wani namijin bai tab'a furta mata suba, Tasan tayi soyyaya a shekarun baya, amma kuma babu soyayyar da yafi tsaya mata a rai kamar Soyyayarta da Bash, Allah Sarki ko yana wata duniyar yanzun Allah ne masani, Sai dai koshi iya kanshi da ita kalmar I love you Meenal su sukafi yawa a cikin kalaman shi, Bai tab'a zaunawa ya karanta mata kalaman soyayya mai tsumawa da tsotse ruwan jiki irin wanda AK ya zazzage mata har takejin kanta yana neman fashewa ba, Koda ace manya na zagewa idan sun samu waje su shek'a k'arya son ransu ta tabbatar da cewa AK bazai tab'a zaunar da ita dan ya k'aranta mata zantukan nan a matsayin k'arya ba dan ta hango tsantsar gaskiya a cikin idanuwan shi, sai dai ita kuma abun yazo mata a haguncen da har yanzun take ganin kamar bai kamata tayi saurin yarda ba, Ita wai wani tsautsayi nema ya kaita zuwa ta fad'a mishi abunda Sultana tace nema wai? Kenan da gaske ne kishin nashi takeyi? To in kishin ne mai yasa sai shine k'adai zatayi kishi ne wai? tun cikin daren da bacci ya gagari idon ta saboda tsabar firgicin data shiga sai kawai ta tashi ta had'a komatsanta tsaf ta killace su a waje d'aya kafin ta koma ta k'ara kwanciya ita da a kullum Hajiya ke fama da ita akan wankan wuri a yayinda ta tashi yin sallan asuba, sai gashi yau koda ta shiga da niyyyar alwallah kawai kamar yanda ta saba wannan ranar dai bata fito ba sai da ta sheqo wanka, Saida ta tashi Hajiya wacce ke baccinta a tsanake kafin ta koma gaban mirror tayi zaman shafan mai kafin Hajiya ta fito tuni ta shirya tsaf, Koda aka fara kiran Sallah ta tabbatar da cewa lokacin fitowar AK zuwa masallaci yayi kuma bazai fitaba har sai ya lek'o su sai itama ta haye kan dadduma ta kabbarta nata sallan, Bayan ta idar da raka'atainul fijjir ta tabbatar da cewa zuwa lokacin ya isa masallaci sai ta mik'e kayan Hajiya ta had'a suma tsaf sannan ta kwaso kayanta itama ta fito da akwatin ta dana Hajiyar takai cikin mota ta adana tana dawowa saida ta biya ta d'akin su Meelat dan tabbatar da cewa sun tashi, sama sama sukayi gaisuwa a tsakanin su kafin ta shaida musu cewa su shirya fa dan yau da wuri zasu wuce gidan rasuwar, "Me zamuje muyi da wuri kuma bayan ance sai zuwa karfe 10 za'ayi addu'a?, Gaskiya inaga dai sai dai in kece zakiyi gaba domin dai ni ina buk'atar ganawa da mai gidan nan ayau kafin mu tafi,ai laifin kine tunda kin san halin da nike ciki tun jiya naso in gabatar mishi da abunda ke cikin zuciyata akan shi amma kika janye shi, ke shikenan tunda baki shirya amsar soyayyar kowa ba nima bazaki bari in gwada sa'ata ko zan dace ba" Sai da ta matsa kusa da Meenal sosai kafin taci gaba da cewa, "Sister ki taimaka min kisa baki tunda naga kina da kusanci dashi sosai nidai ina son shi, amma in shi yace baya sona zan hak'ura, sai dai kafin in hak'uran sai na gwada sa'ata, Yanzun kuma idan na yarda nabar gidan ba tareda nasan matsayata ba ai kuma rashin nasara tace kawai zata tabbata" Cewar Sultana wacce fitowarta daga cikin bathroom kenan taji Meenal din na sheda musu batun fita gidan da wuri. "Wannan kuma damuwar kice ke d'aya babu ta inda ta shafeni, tunda dai kince kinji kin gani aiga fili ga mai doki, nidai karma kisani a cikin maganar nan kinji na fad'a miki" Tana gama fad'in hakan ta fice daga d'akin, koda ta koma d'akin data kwana makewayi ta shiga ta kuskure baki bayan ta fito ta koma kan daddumarta ta tayarda sallan asuba, Bayan sun idar Hajiya ce ta d'ago tana kallon ta bayan ta amsa gaisuwar da Meenal din ke mata, "Ya akayi ne wai naga sai faman shiri kike da sassafe, ko wani abu ya faru ne?" "Ah ah Hajiya so nike dai mu wuce da wuri muje ko akwai aikin da zamu iya kama musu tunda kinsan karfe 10 ne za'ayi addu'ar" "Oh Allah yau kuma keda kanki kike batun zuwa ki kama ma wasu aiki Meenal? Indai dan aikin ne ai gara ki nemi waje kiyi kwanciyar ki dan tun jiyan sun riga sun d'auko masu aiki ko munje yanzun sai dai mu zuba musu ido dan haka gara muyi zaman mu kinga zuwa k'arfe 8 haka sai mu fita," Duk yanda ta tasa Hajiya a gaba da magiya k'iyawa tayi dan dole tanaji tana gani taci gaba da zama a cikin d'akin ita d'aya, Gudun karma ta fita su had'e dashi dan bata san kalar kallon da zata mishi ba, dan Hajiya komawa falo tayi ita dasu Meelat sukaci gaba da gudanar da harkar gaban su, Zama taci gaba dayi a d'akin tana chatting da wayarta karfe 8 dai dai ta fito daga cikin d'akin rataye da hand bag d'inta a kafad'a ga mamakin ta sai taga wai a lokacin nema suke jera kayan kari akan dinning bayan kuma tun asuba take jin zuruntun su, "Wai dan Allah har yanzun baku gama ba dama?, miye kukeyi tun d'azun dana muku magana ne bayan nace muku ina so mu wuce da wuri, Hajiya kefa kikace zuwa karfe 8 sai mu fita yanzun kuma karfe 8 harda mintoci amma ko karyawa bakuyi ba" Ta k'arasa fad'a tana b'ata fuska. "Yauni nike ganin ikon Allah wajen yarinyar nan, Meenal wai ko akwai abunda kika manta dashi a gidan rasuwar can jiya ne? Inba haka ba nidai banga dalilin wannan azalzalawan da kikeyi mana tun da garin Allah ya waye ba, to in zamu takura kine ai gara kiyi gaba koh, mu in yaso mazo daga baya in kuma zaki jira harmu gama mu tafi taren to wannan kuma ya rage naki!" Hajiya ta fad'a tana cigaba da shan kunun gyad'a da kosan da Hajara matar Mansoor ta kawo mata shi d'azun nan. "Taimaka ki lek'a d'akin yayan ku ki tasomin shi yazo yasha kunun nan tun yana da zafin shi dan yana son kunun gyad'a sosai, Tunda ya dawo daga masallaci ya shige bai k'ara fitowa ba"Hajiya ta fad'a batareda ta kira sunan kowacce a cikin suba, "Hajiya bari in kira miki shi ita sai ta zauna ta karya d'in kafin ta wuce tunda sauri takeyi karmu b'ata mata lokaci nidai Hajiya kin san bazan yarda mubar gidan nan batareda kin gabatar dani a wajen shiba dan Allah kinji Hajiya," Juyawa tayi gefen da Meenal take tana tambayar ta "Sister me zaki sha kunun gyad'an ko Tea zan had'a miki?" Fuuu Meenal ta juya zuwa d'akin nashi a fusace bata ko kalli inda Sultana take ba, Tana wucewa su kuma suka fara mata dariya. "To wai ku nace dama haka akeyi shi kenan da zarar namiji yace yana son mace sai ta fara fushi kamar zata kaima mutane duka? Naga dai tun jiya sai wani faman kumbure² take ma mutane in bata son shi basai ta shaida mishi ba ko ana yin soyayya dole ne?" Hajiya ke tambayar su, "Kishin shi dai takeyi ba komai ba wallahi, ke kuma Sultana ya kamata kid'an sarara mata haka kafin ta kasa rik'e fushin ta akan ki" Cewar Meelat "Allah babu wani sararawar da zan mata har sai ta furta cewa da gaske itama tana son shi tukun dan nima ina taya shi kishi, amma muddin bata amsa cewa tana son shiba nima bazan barta ta huta ba, so nike inga hankalin ta ya tsayu a waje guda tukun" Ita kotanayin sallama a d'akin shi ta tura kofar ta shiga batare da ta jira mai dakin ya amsa ba, juyowa yayi daga tsayen da yake a gaban wardrobe din Shi yana binta da kallo, bata ci burki a ko inaba sai da ta k'araso inda yake tsaye yana binta da kallon, Manyan kayan daya tsiri sawa ne yauma a jikin shi, da alama dai shima shirin fitowa yakeyi dan wasu takardu ne a hannun shi yana dubawa, Babu gaisuwa ba komai ta fara kora mishi abunda ke cikin zuciyar ta, "Ya'ya ka fito ka fad'ama Hajiyan can su shirya subar maka gidan ka dan Allah" "Saboda me?" Ya tambaya a yayinda ya d'aura hannun shi d'aya daga kan goshin shi ya cusa yatsun nashi cikin gashin kanshi yayi baya dasu, Saida yakai hannun zuwa k'eyar shi kafin ya k'arayo gaba dashi ya wani yamutsa gashin kan nashi, "Oh Allah yayi dare gari ya waye, Yanzun kuma mai aka miki daga waye war gari fisabilillahi waye ya tab'amin Soul mate d'ina?" "To ba tunda na tashi da asuba nace ma Hajiya mu wuce gidan rasuwar can da wuri ba tunda yaune za'ayi addu'ar uku saboda mu kama musu aiki ita kuma sai tace wai bazamu tafi ba sai karfe 8, To yanzun kuma na fito mu tafi shine naga duk kan su ma babu wacce take da niyyar tafiya sai yanzun nema zasu karya fa" Ta k'arasa fada kamar zata fashe mishi da kuka, Oh ya rabbi, shi dai wallahi aiki ya ganshi, Wai dama haka yarinyar nan keda tab'ara kamar jinjirar goye ko kuma dai yanzun ne ta k'irkireta saboda ta k'arasa susuta shi?, "Ina kwana! Kin tashi lafiya! ina fatan kin samuyin bacci cike da nutsuwa a daren jiya?" Shiru tayi tana duk'ar da kai itafa batun gaisuwa ma gaba d'aya bai shigo mata cikin kaiba, bata san ma ya akayi idon ta ya rufe ta fad'o cikin d'akin ba alhalin tun d'azun saboda shi ta kunshe kanta a cikin d'akin tak'i fitowa, Ita dai gidan ne kawai takejin ya isheta so take ta fita waje ta shak'i iskar da babu numfashin Sultana da shi Taubashin a waje d'aya, A k'aqe take da son ganin sun bar gidan dan a yanda ta lura da cewa notikan kan Sultanan sun fice tofa tabbas tana iya tunkarar shi kai tsaye d'in ta fada mishi tana son shi, to kafin hakan ta fara gara ta d'auki matakin gaggawa, Ku sani itafa a nata ganin bawai tana hakan saboda kishin shi AK din bane, ah ah ita tana hakan ne saboda bata son ita Sultanan tayi abunda zata zubarma da kanta aji a gaban Namiji kuma koda ba AK sultanan keso ba ita a ganin ta kalar matakin da zata d'auke kenan na ganin ta hana Sultanar aikata abunda zata zo daga baya tana dana sani. Matsowa yayi kusa da ita ya tsaya shima, kafin yayi amfani da yatsar shi manuniya ya d'ago habarta yana ci gaba dabin fuskarta da kallo yace, "Bud'e idonki ki kalleni!" A hankali ta dunga bude idon nata data runtse har ta ware su gaba d'aya a saman fuskar shi, "Oya take a deep breath" Numfashin ta shak'a mai had'e da sassanyar kamshin turaren shi kamar yanda ya umarceta, "Ok breath out a hankali" A hankali ta sauke numfashin, Sai da yasata yi hakan sau uku kafin yace mata, "ya kikeji yanzun?" Ya tambaya da harshen turanci, "Ina kwana " Ta fad'a mai makon ta amsa tambayar shi, "Lafiya lau ya kika tashi?" "Alhamdulillah" "Waye ya b'ata miki rai kuma me yasa kike son ku tafi da wuri?" "Ba komai" "To muje ki karya kema kafin ku wuce d'in tunda tsoron zama anan d'in kikeji, zan gani zuwa gaba idan aka kawomin ke a matsayin mota ko ya zakiyi " Gaba yayi ta bishi a baya har suka fice daga d'akin, Sun iske su Hajiya nata k'aryawa hankali kwance kafin suma suka samu waje suka zauna, Su Maryam ne suka dunga mik'a mishi gaisuwa domin shi da Hajiya sun gaisa d'azun daya shigo gidan, kunun gyad'ar Hajiya ta gabatar mishi ya kuma sha kamar yanda Hajiya ta fad'a. "Hajiya nace ya kamata idan kun kammala muje kiga wancan gidan koh? Tunda yanzun dai idan kun koma ban san kuma sai yaushe zaki k'ara shigowa nan d'in ba," "Eh to kuma fa kaima kana da gaskiya tunda ya zama haka ai sai mu wuce yanzun daga can sai mu zarce gidan rasuwar basai mun dawo ta nan ba dan dama ita wannan a k'age take da mu wuce, amma dai kafin mu wuce ina buk'atar magana da kai" Meenal data rage ita d'aya sai shi da Hajiya akan dinning din dan su Maryam sun tashi ta yunk'ura da niyyar basu waje ya riko hannun ta, "Nima ina son magana dake Hajiya amma kafin nan ki yi hak'uri dai har ku koma gida idan na shigo sai muyi maganar a tsanake dan ina da abubuwan da zanyi masu mahimmanci yau d'in shine ma zai hana ni binku mu koma tare, Amma insha Allah zanyi kokarin shigowa cikin satin nan sai muyi maganar " Kauda kai hajiya tayi kamar bataga hannun Meenal daya rik'e cikin nashi ba tace, "Madallah ni ai dama kasan tatsuniyar gizo bata wuce kok'i, komai zan fad'a kaima kasan bazai wuce akan batun auren da nike so inga kayi ba, da fari dai zanso insan halin da kake ciki tsakanin ka da yarinyar da kacemin kana so kwanaki" Sai da yad'an waiga ya kalli Meenal ta gefen ido kafin ya amsa ma Hajiya da cewa, "Karki damu kanki da wannan maganar Hajiya dan na riga na gabatar da kaina a wajen yarinyar, Addu'an da zaki tayani dashi yanzun kawai shine, Allah yasa taji tausayina ta amsa min da wuri kafin ciwon sonta ya ya k'arasa firgita miki ni. *Ummiee ce*✍🏼 [9/10, 10:46 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *RUBUTAWA* *ZAINAB USMAN* *~{Ummiee Zaria}~* *Page 24* Yo Allah na tuba kai yanzun nan harma dan wata mace tace bata sonka har zaka wani d'aga hankali ka damu kanka bayan ba masoyan ka rasaba?... " "Hajiya bafa cewa tayi bata sona ba, kin san bai yuwuwa daga fad'a mata cewa ina sonta ta amsa min dai take a lokacin" "Koma dai yayane kawai ka fita sabgarta taje can ta k'arata da yawarta ita tayi ma kanta dan nidai banga abunda ka rasa daga cikin abunda ake buk'atar samun mijin aure dashi ba tunda ko kaga bata amsa maka ba son kane batayi gara ma haka wallahi dan Kaga ni dama gata naso in maka kana gani dai gashi nan abokan ka sai harama suke shi dama Yusufu tuni yayi muku fintinkau dan haka indai zakaji ta nawa gara kabar batun yarinyar nan kawai kazo ga wata matar Allah ya kawo na fidda maka ita ka aura, Gata kuma yar gida sannan na yaba da nutsuwa da hankalin ta kaga idan ka auri wannan d'in ita waccen yarinyar da kace kana so d'in ko zuwa gabane in Allah yasa ta amince sai kayi ta biyu da ita ko ya kagani?, Dan nidai dama bana maka sha'awar zama da mace d'aya wallahi," Yunk'urawa Meenal tayi da niyyar tashi tabar musu wajen, shi kuma yaja hannun ta dake rik'e cikin nashi ya maidata zaune ya kuma maida hannun nasu dake had'e kan cinyarta ya danne saboda ya hanata mik'ewar , "Ke kuma ina kike shirin zuwa? Ai gara ki zauna dan dama ina gamawa dashi kanki zan dawo atoh bawai na manta dake bane, Nace har yanzun duk wannan uwar wankan da fesa turaren da kikeyi a kullum kafin ki fita kar dai kice min asarar ruwan wanka da sabulu kikeyi kullum?, To ga dai lokaci yana ta tafiya amma har yanzun ban fara ganin manyan motoci suna jera min layi a kofar gidaba, Anya kuwa Yar wajen Jidda ba amanata kike ciba kuwa wajen k'in kula samarin da suke nuna ra'ayin su a kanki? Naga dai ko shekarun baya a lokacin da kike kwailar ki ma maza sun nuna maitar su a kanki yanzun kuma da kika koma tubarkhallah maka Allah sai inji shiru, to wai in baki basu damar zuwa gidanba ta ina zan iya tantance su wajen gano miki wanda ya cancanci auren ki a cikin su?" AK ya katse Hajiyar da cewa.. "Hajiya, amma dai na roki arzikin ki akan abar maganar nan koh? ba komai amma tunda kin matsa bari in fito miki a mutum!, Ita dai yarinyar da kike magana a kanta koma wacece bana buk'atar ta a cikin rayuwata, akwai maza da yawa a waje wad'anda suka fini quality da komai ma da kike ganin ina dashi, ni kuma ina mata fatan Allah ya had'ata da d'aya daga cikin su wanda zai sota har zuwa k'arshen numfashin su, Batun wai in fara auren ta ko wani zancen mata biyu da kike kawowa ina so ki soke shi in ma a mafarki kika gani ina tabbatar miki da cewa bazai tab'a tabbata ba domin bana da ra'ayin su, Naga dai kema naki mijin dake kad'ai ya rayu har zuwa karshen rayuwar shi, suma kuma yaran daya haifa har yanzun kaf cikin su banga wanda yayi mace sama da d'aya ba, oh sai nine kike ganin nafi kowa a cikin jikokin ki da kike kiran min auren mata biyu, Hajiya so kike ranar kiyama in tashi da shanyayyen gefen jiki ko ya? Kedai kin san cewa bazan tab'a iya adalci a tsakanin abunda na gani ina so da kuma wanda nayi alfarmar amsa saboda an cusa min ita ba, Aure dai ina kike so kiga nayi? To in hakan ne gata d'aya nike so kimin wajen tayani yak'in kwato abunda nike so d'in har zuwa sanda zai zama mallakina, Yar gida wanda kika san halinta kuma kika yaba da tarbiyar ta kike min sha'awar aura koh? To gata ayau a yanzun zan gabatar miki da ita batare da b'ata lokaci ba nidai na riga na gabatar da kaina a wajen ta, Ina son ta ina kuma fatan in mallaketa ta zame min matar rufin asiri, Gata nan zaune a gaban ki dan haka sai ki yanke hukuncin daya dace domin da ita dani dukan mu tarbiyar kine babu wanda baki san halin shiba a cikin mu," Mikewa yayi tsaye sannan ya d'ago meenal d'in tsaye itama, wacce zaune kawai take amma ji takeyi da da ace tana da wani layan zanan da zata latsa tayi b'atan dabo a wajen da tayi saboda tsaka mai wuyar da take ganin su biyun sun jefata a ciki, wannan ai ita akama turke wallahi. "Meenal meet my grandma Hajiya ta itace gatana tun ban san kaina ba, duk wani matakin nasarar da nataka a rayuwata zuwa yanzun da gudun mawarta na same shi, Ina fatan zaki kula min da ita fiye da yanda nike kula da duk abunda ya shafeta bayan auren mu?" Hijjabin dake sanye a jikin Meenal d'in taja da duk'unkune kanta gaba d'aya a cikin shi saboda tsabar kunyar daya lullub'eta, "Hajiya ga Ameenatu takwarar ki, zanyi amfani da wannan damar dana samu wajen gabatar miki da ita a matsayin macen da zuciyata ta zab'amin wacce nike fatan in k'arasa sauran rayuwata a tare da ita k'ark'ashin inuwar aure, Ina fatan zaki tayani yak'in neman amincewar ta akan maganar auren mu, Domin kamar yanda na shaida miki ne, na riga na gabatar da takardar barar soyayyata a gareta amsar ta kawai nike da buk'atar ji a yanzun wanda shine zai bani kwarin gwuiwar takawa zuwa mataki na gaba wato gabatar da kaina a wajen iyayen ta a matsayin mane min auren ta, Hajiya Ina sonta, so irin wanda ban tab'a zaton zanyi ma wata y'a mace shi ba," "Sadaqallahul Azeem! Allahu akbar ! Allahu akbar! Allahu akbar,,, Ashe ni Aminatu zanga wannan ranar a raye tun k'asa bai rufemin idon ganiba, Oh oh Allah Sarki duniya... " Batakai k'arshen surutan da takeyi ba ta fara sheshek'a tana shirin fashe mishi da kuka, Daga can cikin falon ko su Meelat da tun d'azun suka kashe kunne suna sauraron tattaunawar nasu, Sultana ce ta matso kusa saida ta k'arasa inda Hajiya take kafin ta tak'ark'are ta rangad'a gud'a uwa wacce ke taryar Amarya, "Ayyiriri yirie yiriii yirrrriiieee dukan su suka had'u suna yarawa, Hajiya dake sheshekar kuka basai gata itama ta biye musu suna rangad'a gud'ar atare dasu ba, Da baya ya koma ya shige d'akin shi ya barsu a falon dan shifa tsakani da Allah ya manta cewa ba iya su bane kawai a gidan akwai wasu ukun a gefe tare dasu, Sai dai ko kad'an baiji kunya ba shi a zuciyar shi ma dad'i yaji dan yasan suma zasu sa baki tunda a gaban su akai komai, Suko yana shigewa suka zagaye Meenal d'in data d'uke kanta dake duk'un kune cikin hijjabi akan table din dinning d'in tak'i d'agowa balle su samu damar ganin yanayin fuskarta, Basu damu da yanda tayin ba suka cigaba da tsokanarta da cewa, "Allah yabar mana jikar Hajjaju sirikar Hajjaju, zaman ki lafiya tashin ki lafiya yar gaban goshin Malam... Hajiya ce ta matso tana katsesu da cewa "ku matsa ku bama sirikata waje karku samin ita a gaba da tsokana, yoni ina nasan cewa kanshi yake ma kiwo ashe! Niko nike ta k'okarin yi mishi shishshigi, to ke Sultana kin daiji komai dan haka sai kija please ki rungumi sorry kiyi fatan Allah ya baki wanda ya fishi d'in kamar yanda shima ya rok'a miki, dan tunda ya iya kallon tsabar idona yace min ita yake so tofa bazai tab'a amsar naki soyayyar ba, To amma Takwara haka ake rayuwa ayi ta abubuwa bani da labari ko dai da gaske bakyason shi d'in ne shi yasa kika kasa amsawa? To bari kiji in baki shawara na gaskiya da gaske, dan ma karkice shid'in jikana ne shi yasa nike son taya shi yak'i ah ah wallahi ko d'aya dan kin sani duk wanda naga yana shirin yi miki dole akan auren wanda bakyaso sai inda k'arfina ya k'are, Amma shi dai tsakani da Allah zan fad'a miki idan har kikayi saken daya kucce miki tofa ba lallai bane ki samu mafiyin shi ko kuma wanda ya kaishi, Amma kinga in shine babu ta inda zanji fargaba dan na bashi auren ki domin dai dake dashi duka ina da iko daku kuma nasan bazai tab'a miki rik'on sakainar kashiba tunda yana sonki, Na tabbata cewa yana sonki naki so na hak'ika tunda har ya iya gabatar dake a gaba na yanzun, bazance ki amince mishi dole ba, Sai dai koda ace a yanzun bakya jin komai akan shi zan so ki bashi dama ko allah zaisa ki soshi d'in zuwa gaba, ni kuma na miki alkawarin inhar bakiji cewa kina son shi har cikin zuciyar kiba to bazan yarda kowa ya matsa miki cewa sai kin aure shi dole ba, wannan alkawarina ne kuma ku tayani sheda" Ta k'arasa fad'a tana kallon su Maryam, Insha Allahu kuwa zamuyi shedar ki Hajiyar mu, suka had'a baki wajen amsawa, "To amma Hajiya ai Sultana tana son shi!" Meenal ta fad'a batareda ta d'ago kanta ba, "Ke Sister ni wallahi ba dagaske nike yiba inma dan abunda kikaji na fad'ama Hajiya jiyane to kisa ranki a inuwa Ya AK naki ne ke kad'ai, ina tayaki murna ubangiji Allah ya sanya alkhairi sai dai dan Allah karkija mana aji ki bada gari kawai musha biki a wuce wajen" "Ni bazan auri mijin da tun baiyi auren farko ba kakar shi ke fad'in cewa tana mishi sha'awar auren mata biyu ba" Ta k'ara fad'a tana juya kanta da har yanzun bata d'ago shi daga kan table d'in ba, "Ah ah ha, Allah ya tsareni yi miki fatan zama da kishiya wallahi, To dai koni da nike matsayin kakarki mijina har ya kwanta dama bai tab'a ambata min sunan kishiya a cikin gida ba, Kuma dai har yanzun kina jin shima Yayan naki abinda yace dan suma dai nawa yaran babu mai kishiya a cikin su har yanzun, to wani mugun abun ne ni kuwa zaisa in so miki zama da kishiya yar nan! Kwantar da hankali indai wancan ne Allah ya nufa zai zama mijin auren ki ina tabbatar miki da cewa kishiya sai dai ki gani a mak'ota ko baki lura da d'abi'un shi bane kaf nasara sun gamayin tasiri akan shi... " Meelat dake dariya ne ta katse Hajiyar da cewa, "To Hajiya mai yasa wancan lokacin baki hana auren ta da Sarki ba bayan kun san yana da mata?" "Yanzun yar nan har kya tambayeni dalilin wannan aure? Yo shi wannan auren yana da dalilin da za'a danganta shi dashi ne bayan k'addara, ke dai ki bari kawai Allah dai yasa kaffara ne ya bata ladan zaman kuma, gashi dai tun ba'aje ko ina ba Allah ya mata canji na alkhairi ai ni wannan abu koshi uban gayyar bazai fini farin ciki ba allah dai ya kaimu lokaci," Da ameen dukan su suka amsa sunaci gaba dayi ma Meenal din tsiya, Daga nan gidan AK unguwan dosa suka wuce kai tsaye domin sun Riga sun gama cinye lokaci a gidan dan basu suka fitoba sai karfe 10 saura sakamakon hirar daya d'auke musu hankali, Hakan ne kuma ya shashantar da batun zuwa marafa dubo gidan AK da sukaso zuwa. An gabatar da addu'ar kwana uku ga mamacin lafiya, tun daga nan kuma bak'in da suka zo saboda a gudanar da addu'a dasu suka fara juyawa suna komawa gidajen su, wad'ansu yan garine wasu kuma bak'i, Yan zaria ma dai da yawan su sun koma Malam yayi magana akan komawar Raheenat gida idan yaso sai ta k'arasa wankan ta a can, amma kuma sai iyayen Mamacin wad'anda a gidan suke zaune suma suka rok'i alfarmar abarta a gidan har zuwa sanda zata gama wanka in yaso sai ta koma gidan tunda dai ita ba takabar mutuwar zatayi ba sakamakon haihuwar da tayi, A haka aka rabu sai dai anbar mata Innar yara da kuma wata mace yayar Aunty Murja sune zasu zauna da ita yaranta biyu kuma dama Babban da mai bi mashi tun kafin rasuwar mijin nasu rik'on su ya koma hannun kanin mijin da matar shi da suke zaune a Abuja wad'anda Allah bai basu haihuwa ba, A lokacin da duka ahalin suka fito da niyyar tafiya ne Meenal ta gabatar musu da sabuwar Motar ta da AK ya bata dan Farouq ne da yake ta ganin tana zirga zirga da motan a yayin zuwa gidan rasuwar yau ya gaji yake tambayar ta, ina ta samo d'anin mota, Hajiya ce ta ceceta ta bashi amsa da cewa, "Yayan ta ne ya bata ita tunda shi ya tara su da yawa baya hawa, sunyi mata Allah sanya alkhairi kafin suka kama hanyar komawa Zaria daga garin na Kaduna. *BAYAN WASU KWANAKI* Kamar yanda Sultana tace wajen Meenal zata sauka hakan ne ya faru domin sati d'aya kacal sukayi a unguwar Malamai family house shima dan kunyar da Meenal takeji na Hajiya ne yasa ta yanke hukuncin su sauka a can d'in ga kuma yan uwan su na kano da mutanen Abuja wad'anda suke gidan har yanzun basu koma ba, Matan auren ne kawai Malam ya kora gidajen su washe garin ranar da suka dawo daga kadunan, A kuma ranar da suka dawo Baba Adamu yayi amfani da wannan damar na had'uwar ahalin waje d'aya wajen had'a kan ahalin kwansu da kwarkwata ya k'ara ja musu kunne akan kulla da zumunci dan kar suga cewa basa gari d'aya suce zasu yarda zumuntan dake tsakanin su da sauran yan uwan su da suke zaune a wani wajen ya lalace, dukan su sunji dad'in wannan zaman domin anan suka k'ara sanin juna suka tantance wannan shine wane d'an wane yana zaune a waje kaza, sun kuma yanke hukuncin bud'e WhatsApp group wanda zasu cigaba da zumunci a ciki da tattauna abunda ya shafesu a cikin shi dan haka sai da sukayi exchanging numbers din junan su kowa ya ajiye number din dan uwan shi a wayar shi. A kuma wannan zaman na kwanaki da Meenal tayi a gidan ne suka fara yar tsama da Yayan su Naseer wato yayan Sultana wanda kowa ke kira da Sheikh, Abu na farko daya fara had'asu shine irin yanda tana malam yana nan nan dashi, Magana d'aya biyu zaice a kira mishi Sheikh, In dare yayi koda zataje cin abinci wajen Malam d'in kamar yanda suka saba a baya zata iske shi Sheikh din a hakimce a falon ko yana duba littafai ko kuma yana yin wani abun mai mahimmanci, Tun ba'aje ko ina ba ta fahimci cewa ba k'aramin kusanci ne tsakanin Malam dashi Sheikh din ba dan haka tuni kishin ta ya motsa da gayya wani lokacin idan ta shigo falon taban shi zaune kuma malam baya nan sai tak'i gaishe shi tayi komawar ta, dan a farko in tazo ta kan zauna ta jira malam shi kuma na bakin ta da iyayen shi a wannan zaman zaiyi ta jefo mata tarin tambayoyin shi da basa k'arewa, abun haushin kuma bazai tab'a zama da kai kuyi hira dashi na minti goma da yaren hausa ba, Ah ah magana d'aya biyu da kun fara dashi zai fara sako mata runkuma runkuman labarcin shi badan Allah yasa Malam yayi tsaye a kanta tun tana k'arama wajen ganin ta iya larabcin ba lallai da ba k'aramin kunya zata shaba, To fisabilillahi larabcin nan dai tunda ba yaren da aka haifi mutum dashi bane ai sai ya tsaya a iya nashi yaren koh? To shi da gaske so yake sai yakai k'arshen nata larabcin da take riritawa, to jama'a ita dake karatun likitanci yare nawa ake son ta rik'e ne? Kuma dan wulakanci ko turanci kake mishi shi bazai tab'a amsa maka ba sai ma yayi uwar shegu dakai kamar bai san me kake cewa ba, Da farko tayi zaton ko turancin ne bayaji sai daga baya data tambayi Sultana shine take ce mata wai ai Ya Sheikh yana jin yare sama da goma saboda k'asashen da yake karatu duk yanayin yaren su, Ita kuma tun ranar sai ta kuduri aniyar cewa sai ta rama wallahi, dan haka koya mata magana da larabci ita kuma sai ta maida mishi da yaren hausa, Daga baya sai ya tsiro musu da karatun safe dana dare, Da zarar an idar da sallan asuba dana ishsha'i duka yaran gidan zasu taru a falon Malam ayi karatun, Taso ta doje tak'i zuwa amma ba hali dan Mommy Hauwa da kanta take korata dan da ita ake karatun, Amma wai duk yawan yaran gidan nan d'an bawan Allahn nan idan ya tashi jefo tambayan shi bazai jefa akan kowa ba sai a kanta ita marainiya wayon shi salon in bata amsa dai daiba yasa yara su rainata, Dan haka dan dole ta zak'ulo littafan ta da suke karatun tare da baba malam a shekarun baya tana musu maraji'a gudun kar a samu bacin rana aji kunya, Abu dai kamar wanda ya asirce ahalin gaba d'aya domin kowa zancen shi shine ya sheikh, Ya sheikh kaza ya sheikh yayi kaza, dan haka kowa ma a gidan ya fara bata haushi, Wata rana sun shigo gidan ita da Sultana daga gidan su Meelat suke domin tunda suka dawo suke cigaba da gudanar da shirye shiryen bikin su babu kama hannun yaro, Har sun gota parking lot d'in gidan ta jawo Sultana suka dawo daga baya sakamakon Muryar Sheikh da taji cikin harshen turanci yana magana a waya, Sun dade tsaye a wajen tana k'ara sauraren yanda yake fitar da lafiyayyen turancin yana kuma had'awa da wani yaren da bata san ko na wani k'asa bane, Ita dai Sultana da taga tsayuwar bamai k'arewa bane gashi kuma ita fitsari ya matse ta kawai sai tayi wucewar ta ciki tabar Meenal d'in a wajen, Nauyin ido yanaji ya mishi yawa ne yasa shi kuma ya yanke wayar ya juyo dan yaga waye a wajen, "Me kikeyi anan?" Ya tambaya da harshen larabci kamar yanda ya saba, Ita kuma sai ta amsa mishi da turanci cewa, "Kallon ka nikeyi mana ina kuma sauraron ka kana turanci bayan kuma ni kullum idan nayi maka magana da yaren nuna min kakeyi kamar bakajin me nake cewa" Murmushi yayi kafin ya taso daga inda yake ya matso kusan ta sai da ya gota ta kafin yaci burki, bai juyoba ya amsa mata da cewa, "Yaren turanci ba shine yaren da zamu tashi dashi bayan mutuwar muba, shi yasa sam baya burgeni" "To amma kuma ai gashi nan naji ka iya sosai kanayi kamar a cikin su ka rayu!" "Ke da kika iya kikeyi a cikin su kika rayu ne?" "Ah ah ta bashi amsa tana girgiza kai, "Ok niko kinga a cikin larabawa na rayu shi yasa na iya yaren su, kuma ko ba komai ai yaren shugaban annabawa ne koh?" Yana gama fad'in hakan yayi gaba abinshi ya wuce ya barta a nan tsaye tana binshi da kallo cike da burgewa, Malam daya shigo tun d'azun tsayuwar Sheikh din ya hanga a kusa da Meenal k'arasowan shi inda suke hakan yasa yaji duk abunda suka tattauna sai shima yaji Sheikh din ya k'ara daraja da kima mai girma a idon shi koba komai dai gashi duk tarin ilimin bokon da yake dashi hakan bai sa ya yarda yaren addinin shiba. Wallahi babu editing kwana biyun nan rubutun kawai nikeyi, kuyi hakuri da mistakes *Ummiee ce*✍🏼 [9/11, 10:31 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA!*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *Page 25* Wani abu mai girma ne ya d'arsu a cikin zuciyar Malam a dai dai wannan lokacin, domin dama tunda Sheikh d'in ya iso garin na Zaria Allah yasa shakuwa da fahimtar juna a tsakanin shi da Malam domin Allah ya wadata Sheikh Naseer d'in da tarin ilimin addini sosai har gobe kuma yana kan neman ilimin ne bawai ya dena ba, dan haka da yazo sai ya sauke kanshi yake cigaba da d'aukar karatu a wajen Malam duk lokacin da Malam din yake gida,wani lokacin ma shine yake wakiltan Malam wajen karantar da dattawan dake d'aukar karatun bayan ishsha'i a wajen Malam d'in, Idan kuma Malam ya fita zai zauna yayi ta nazarin tarin littafan da suke falon na Malam, wannan halin nashi da Malam ya lura dashi na jajircewa wajen neman ilimin addini ne kuma yasa ya k'ara kusanci sosai a tsakanin su, Irin su Sheikh dole duk mutumin daya mu'amalance su yayi sha'awar had'a zuria dasu Domin dai babu ta gefen da yake da tawaya a rayuwar shi, matashin saurayi ne mai jini a jika dan duka duka bazai wuce shekaru 34 zuwa da 6 ba dan gatan da tun tashin shi bai san wahalar komai ba sai na neman ilimin da yasa a gaba, Wannan dalilin ne kuma yasa har yanzun ko tsayayyar budurwa baya da ita dan ko batun auren ma bai farayi ba tukun duk da cewa yanzun haka kannin shi maza biyu dake bi mishi duk sunyi aure sun barshi, iyayen shi kuma basu matsa mishi da zancen auren bane saboda sun san ko yayi auren tofa matar bazata samu kusancin dako wacce macce take samu tsakanin ta da mijin ta ba, saboda shi dai wani irin mutum ne mai matuk'ar son sirri a rayuwar shi kwata kwata baya son wani abu da zai had'ashi da jama'a balle kuma wani ya takura mishi, Yafi gane ya keb'e kanshi waje d'aya yayi ta karance karancen shi, Sai dai kuma shidin dan ka'idane dukan rayuwar shi yana gudanar da ita ne akan koyarwar addini d'an boko ne na gidi sai dai gaba d'aya baya mu'amalah irin tasu ko a sutura yafi ta'amali da kayan mu na hausawa in basu ba kuma to koda yaushe zaka same shine sanye cikin jallabiya inba a cikin d'akin shi ba bazaka tab'a samun shi cikin shiga ta k'ananun kaya ba, hakan ne kuma yasa duk wanda zai zauna dashi dole saiya zama mai kiyaye iyakoki domin abu k'ank'ani zaka aikata yanzun nan ya zaunar da kai ya fara karanto maka Allah yace annabi yace, Shifa tun tashin shi bai yarda yayi aboki ko d'aya ba, abokan shi sune kannin shi, Yana da fasali da k'ira mai kyau ga kuma cikar halitta kyakyawan namiji ne sosai sai dai bashi da hasken fata, Domin kaf yaran gidan su farare ne tass amma shi sai ya surka kalar tashi fatar batayi haske irin nasu ba amma kuma tashi sai tafi tasu d'aukar idon mai kallo shi ba bak'i bane ba kuma zamu sashi cikin sahun bak'ake ba ah ah yafi kama da bak'aken larabawa kamar yanda mutane da dama suke fasalta shi, Ganin farko idan ka mishi zaka hango tsabar hutu da tsaftar dake tare dashi dan shi saboda tsabar sanin ciwon kai ko d'an guje guje ko d'aga karfen da matasan zamani keyi bayayin su baya da kiba ko kadan ba kuma zamu kirashi da siriri ba komai nashi dai dai shi Allah ya mishi, Tun daga wannan ranar Malam yake ta neman hanyar da zai k'ir k'iri kusanci tsakanin Meenal da Sheikh domin shi dai yana ganin cewa Sheikh ne irin mijin da ya cancan ci auren Meenal dinshi, yasan idan har suka had'a kansu babu wanda bazaiyi farin ciki da hakan ba dan ya tabbatar da cewa idan Meenal ta auri Sheikh zataji dad'in zama dashi sosai ga soyayyar da zata samu daga dangin shi kuma domin ya tabbatar da cewa Momin Abuja zata kula da Meenal d'in kamar yanda zata kula da Sultana, sai dai bazaiyi gaggawa ba saboda baya son yayi wani abun dazai k'ara kawo nakasu a cikin rayuwar Meenal d'in a karo nabiyu zaifi kowa farin ciki idan ya kasance cewa sune suka had'a kansu bawai auren had'i ba. Dan haka sai ya zamana shima Sheikh din duk in suna tareda Malam sai malam yayi ta yabon kyawawan halayen Meenal d'in a gaban shi haka zaiyi ta bashi labaran daya shafi Meenal d'in harda irin yanda tayi nata yarintar da kalar rikicin da tayi tayi kafin auren ta, har rikicin da tayi lokacin auren ta da Sarki duk sai da ya bashi labari, Wannan dalilin ne kuma yasa shima Sheikh d'in yake kokarin nuna kulawar shi aka Meenal din dan ya tabbatar da kaunar da Malam yake mata kamar yanda ya dad'e yana jin ana fad'a, abunda shi kuma bai sani ba shine wannan kusancin dake tsakanin shi da Malam shine abu na farko daya fara jawo mishi bak'in jini a wajena Meenal dan gaba d'aya zaman shi a sashen malam din yasa gaba d'aya kota shiga wajen ita kuma bata sakewa. kullum idan Meenal taje wajen Malam sai yasan yanda yayi ya sako mata zancen Sheikh kullum Malam cikin yaba kyawawan halayen shi yakeyi a gaban ta, a kokarin shi na ganin ya cusa musu ra'ayin juna sai ya zamana duk wani abu daya shafi sheikh d'in Meenal yake sawa tun daga gyaran d'akin da Sheikh d'in yake kwana wanda yake anan cikin sashen na malam abincin da sheikh d'in zaici kai wani abun haushin ma ko aike malam zaiyi sai ya had'a meenal din da sheikh yace suje tare, Ita kuma gaba d'aya abun nan ya kai mata ko ina bata dai da yanda zatayi ne kawai, dan sosai fa sheikh yake shiga mata hanci da kudundine ba dama yaga ta zauna tana kallon films dannar waya ko wani abun zai wani fara mata wa'azi cewa da zaman da takeyi da qur'ani ko wasu littafan ta d'auko ta karanta, kai mutumin nan fa ya kai mata ko ina kamar akan shi aka saukar da ustazanci shi yak'i ya saki jikin shi yayi enjoying life din shi haka yake son duk wanda yake rayuwa a kusa dashi ya rayu kamar shi dai, haba dan jama'a a ina ake gudanar da rayuwa babu nishad'i naga dai ko abinci bashi ciyuwa sai an sarrafa shi da kayan d'and'ano. Wai saboda tsabar sa ido irin na ustazun nan wata rana sun shirya tsaf zasu fita ita da Sultana Tudun jukun suke son zuwa ita dasu Maryam a wannan ranar, har sun sallami Mommy Hauwa suna shirin fita sai Ya Sa'eed ya shigo sashen nasu, Bayan sun gaisa ne yake tambayar ta cewa, "Meenal yaushe zaki koma Tudun wada dan akwai sakon ki a hannu na amma nafi so sai kin koma sai inzo muyi magana ko kin dawo nan d'in kenan gaba d'aya?" "Ah ah wallahi nikam ban dauwa ma a gidan nan indai wancan sabon ustazun na cikin shi, komawa na kuma yana iya kamawa ako wani lokaci, duk Anbi an tara yan sa ido a cikin gidan ne zan zauna tab' In maganar tana da mahimmanci ka bari idan na dawo zanzo sashen ku sai kuyi maganar acan" "Ah ah sirri ne bana so kowa yaji shi yasa ki bari kawai idan kin koma can sai inzo, Ina zakuje yanzun? " "Tudun jukun zamuje daga nan zamu wuce G R A gidan Sa'adatu mukai mata anko kasan mu yanzun kuma ba zama, yauwa Yayana nace tunda dai kamin allah sanya alkhairi na mota har yanzun baka bani kud'in sa mai a motar ba!" "Oh yanzun kuma wajena za'a amshi kud'in man kenan?" "Ah ah nifa ba wai na rok'a bane amma dai idan ka bani bazan k'i amsa ba kasan ai nidai bana maida hannun kyauta baya" Hannu yasa a cikin aljihun shi ya zaro wallet din shi yan dubu dubu ya zaro bai k'irga ko nawa bane ya mik'a mata, "Gashi in kuma bazai isa ba in kun fita sai ki biya wajen Farouq ki amsa ko kuma a wajen shi sabon ustazun shima" "Ai da ina kusa bazaka b'ata kud'in nan bama, ke Meenal ina ce d'azun nan kika amshi kud'in mai a hannun Abban ku? Anya kina da tausayi kuwa? kin san bazaki iya cacar siya ma motar mai ba kika amshi kyautar ta nifa bana son wannan d'abiar naki na titsiye mutum kisa ya miki kyautar da baiyi niyya ba, ko kuma shi kenan tunda kin san suna baki komai kike so sai ki tun karesu kai tsaye, suma fa suna da nasu iyalan a k'ark'ashin su, ke baki da wani matsala sai dai a baki kud'i ki kashe" Cewar mommy Hauwa "To Mommy tsakani da Allah in ban amshi kud'i a hannun suba ai ko Allah ma sai ya tambayeni gani da yayye maza da yawa yarinya yar dangi to so ake inje in rok'a a wani wajen daban bayan gasu nan reras kin haifo musu ni, Ai hak'uri kawai zasuyi su dage da nema Allah kuma yaci gaba da bud'e musu k'ofofi na alkhairi suyi ta bani ina Tarawa a nawa asusun Allah Mommy kud'i nike son tarawa masu yawa in Siyama Babana gida yaje can gefe ya huta da hayaniyar jikokin da suka cika mishi gida. Da sauri Meenal din ta fice daga falon tana dariya, Tsaye a wajen motar ta ta iske Sultana, "Me kike jira kuma da baki tada motar ba?" Ta tambaya tana shirin zagayawa gefen mai zaman banza dan in zasu fita Sultanar ce ke jan motar dama tunda suka dawo, "Zonan kema!" Tajiyo muryar Sheikh yana bata umarni daga bayan ta, "Na'am nii ina kwana!" Ta fad'i nii d'in tana nuna kanta saboda ta tantance koda ita d'in yake yi, "Lafiya lau eh kefa ina zaku? Ina lura da yanda kullum sai kun fita daga gidan nan bakwa kuma dawowa da wuri ina kuke zuwa? " "Gidan Sa'adatu zamuje" Meenal ta bashi amsa, "A hakan kuma kike shirin fita babu mayafin kirki a jikin ki?" Shiru tayi tana binshi da ido kamar bata fahimta akan me yake magana ba, "Eh nace baki da Hajibi ne ke? tunda kika dawo ban k'ara ganin ki da Hijabi a jikin kiba kullum sai dai ki zura doguwar riga ki yane kanki da figaggen mayafi ki fita haka nan kina yawo a gari ko kunya bakyaji, ko dama su hijjaban dana dunga ganin kina sawa a can gidan rasuwar na aro ne?" Sim sim Sultana ta fara takawa sai da tayi d'an nisa dasu kad'an kafin ta tattaro rigarta ta kwasa da gudu ta koma sashen Mommy Hauwa dan tasan yana gamawa da Meenal din wallahi kanta zai dawo, Ita kanta Al'amarin na yayan su yana matuk'ar d'aure mata kai, tsananin shi yana neman yayi yawa wallahi shi fa ko a can Abuja kannin shi ba wani son zaman shi a kasar sukeyi ba domin dai daya dawo tofa dole kowa ya aro ustazanci ya yafa shima, shifa komai sanyi ko tsananin zafi bai kaunar yaga kannin shi mata da jiki a bud'e, ah ah in shiga zakiyi sai dai ki kin kima k'aton hijabi sannan kibi da safa hannu da k'afa ga kuma uban niqabi kamar wata ninja, Shi yasa tunda yazo gidan suke matuk'ar shiri da Fauxieyerh kanwar Meenal saboda ita dai haka nan Allah ya halicce ta duk wuya duk rintsi bazaka rasata da hijjab a jikin taba tana nan kullum jiki a kudundune uwa wata konanniya😒, Sab'anin Meenal da tun tasowar ta ita daman kowa yasan mafi yawar suturun ta dogayen rigunan abaya ne sai kuma ta lulllub'e jikin ta da mayafan su, koda tayi aure kuma bawai ta canza shiga bane, Yanzun kuma data samu cigaba sai ya zamana shigar nata ya canza mai makon dogayen rigunan da take ta'amali dasu a lokacin baya yanzun takan sirka dasu riga da zani ko riga da siket English were tafi amfani dasu ne ranar da take gida shima kuma tafi ta'amali da riga da Sket a gidan Hajiya ne kad'ai take sakewa tayi kalar shigar da tayi ra'ayi tunda can din babu tarin maza kamar nan gidan su, Mai da kallon ta tayi zuwa ga kayan jikin ta, Doguwar rigar abaya nefa navy blue a jikin ta sabuwa dal dan yau ta fara sakata yana cikin tsarabar da Momin Abuja ta kawo mata, kuma ko kad'an babu ta inda rigar ya kamata dan a sake sosai rigar take, kuma gyalen datayi rolling dashi ma yana da girma dan ya sauko sosai ya rufe mata har kasan k'irjin ta, "Ki koma ciki ki sanya hijjab in fitar ta zama dole!" "Iyye 😳" tace tana zaro idanuwa cike da mamaki, Jama'a yau nike ganin mulkin mallaka, to inba haka ba ina ma ruwan shi da itane da zai nemi matsa mata, Zaman shekaru 6 tayi da Sarki amma ko sau d'aya bai tab'a ce mata ta koma ta canza kaya wai dan zata fita ba, kafin auren ta ma ai tayi zama a gidan nan amma ko Malam bai tab'ayin mata magana akan shigar da takeyi ba, kuma ita a iya hasashen ta bataga ta inda shigar ta ya gaza ba, babu inda ta bari a bud'e komai a lullub'e yake daga kafarta tafin hannu sai fuskarta ne kad'ai fa a waje, "In kin gama nazarin kina iya komawa daga ciki, baki fita gidan nan har sai kin sa Hijjab na fad'a miki, dokar daya kamata ace kece kike kafama kannen ki sai gashi kema yi kikeyi kamar wata *Yarinyar goye* " Innalillahi jama'a wai ita Uwar malam ne ustazun nan ke cema tanayin abu kamar wata yarinyar goye, Aiko yasin ya shirya ganin aikin yara indai ita ne badai ya samu waje yazo gidan su ya zauna har shine yake ganin cewa yana da damar kafa mata wasu sharad'od'i ba. "Ni bani da Hijjab kuma wannan shigar ita na sabayi tun ban kai haka girma ba, kuma babu wanda ya tab'a cewa dole insa Hijjab dan zan fita dan babu ta inda suturar jikina ta kasa" "Sune basu ga inda ta kasa d'in ba amma aini gashi na gani, ki koma ciki ki tsaya a gaban mirror ki kalli kanki da kyau" "To ai dai nace maka bani da Hijjabai anan gidan kayana suna gidan Hajiya sai naje can zan kwaso tunda na aron da nike sawa na baro ma maisu kayanta" Tsalle daya yayi ya haye saman booth d'in motar dake kusa dashi ya d'auki kiran daya shigo wayar shi ya shareta, Haushi bak'in ciki da takaici sune suka nemi sata ta jawo kafar shi ya fad'o daga saman motar da yake zaunen, Kuma wallahi wallahi bai isa ya hanata fita daga gidan nan da shigar nan ba, Toma waye shi dazai wani ce zai kafa mata dokar da dole tabi, allah ma yasa ba iya wannan ne kofar fita daga gidan ba, dan haka fuuuu ta juya ta koma sashen nasu, tana shirin shiga Sultana ta sawo kai zata fito sanye da zumbulelen hijjabin ta har k'asa mai ruwan kwaiduwar kwai, "Ya koro ki kizo ki canza shiga kenan? " Sultanar ta tambaya tana dariya, "Wannan yayan naku sam bashi da halin kwarai wallahi to wai ma ni kad'aice mace a gidan nan dazai wani samin ido har haka? Ina ruwan shi da shigar jikina tunda dai bashine yake siyan min sutura ba, Kuma wallahi bazan canza kayan ko insa Hijjab dinba kuma sai na fita d'in sai dai idan na dawo ya dafani ya cinye" "Ke Sister karki wani b'ata ranki, akan abunda yace indai Ya Sheikh ne haka yake indai yana waje duk sai ya takura ma rayuwar mutane yake jin dadi" "Key din motar fa?" Meenal ta tambaya. "Gashi nan a cikin jaka ta" "Ok to jeki kawai zan same ki a kofar gidan su Meelat ko kuma mu had'e a kasar layi kawai dan ta k'ofar baya zan fita, idan ya tambayeki ni kice mishi nayi fushi na fasa fitan kinji" "Wai da gaske bazaki sa hijjab d'in mu tafi ba? Koni da kikaga nasa ai dan dai kawai a zauna lafiya ne amma muna fita zan cire shi sai zamu dawo zan mayar dashi a jikina" "Wallahi bazan saba in kuma ya tab'a siyamin kyalle da sunan sutura ne sai ki fad'amin, ke karfa kiga wai dan yana matsayin yayanki kiyi zaton zan d'aga mishi k'afane idan naga zai takura min tam" Tana gama fad'in hakan tabi ta baya ta fice daga gidan shiko Sheikh yana can yana zaman gadi koda Sultana tazo ta shiga motar harta mishi sallama cewa sai ta dawo bai tambayeta ina Meenal ba domin daga yanda tabar wajen yasan fushi tayi. Moon kwance take akan gadon d'akin ta misalin karfe 10 na dare, wayane a hannun ta tana chat dasu Meelat da suka bud'e group wanda suke tattaunawa akan bikin Meelat d'in, Sai dai lokaci lokaci takan fita da group d'in ta amsa sakon da Sarki yake turo mata, "Mai kikeyi har yanzun bakiyi bacci ba?" "Nothing important kawai muna hirane nida su Meelat kasan next week ne bikin ta so shirye shiryen bikin mukeyi muna tattaunawa ne" " oh kuna da biki shine ma babu gayyata?" Saida ta tura mishi da emoji mai murmushi kafin ta bashi amsa da cewa, "😊 wannan kuma tsakanin ka da k'anwar Meenal ne" "Oh kenan ke bazaki iya gayyata na a mai makon taba kenan? , to in haka ne ki shirya sai mu wuce tare gaba d'aya dan nima dama wani abune ya tsayar dani a garin ku da yasa nakai har yanzun ban koma ba kinga sai mu wuce kawai tare inba damuwa" "Ok to kana ganin har zaka gama naka uzurin kafin lokacin?" "insha Allah ina sa ran hakan addu'a dai nike tayi har yanzun da kuma neman zab'in Allah, Kin san me?" "Ah ah sai ka fad'a" "Aure nike so in k'ara Moon, kin san wanda ya d'and'ana zama da mata biyu da wahala ya iya rayuwa da mace guda 1 kuma sai in lalura ne ya gifta" Tun d'azun da suke hirar a kwance take, Amma tana gama karantar wadannan kalmomin ta mik'e zaune dangal gal gabanta na tsanan ta bugawa, Innalillahi wa'innah ilairir ta shiga karantowa kasa k'asa a yayinda take jin wani kalar tashin hankali yana yunk'uro mata, To kenan dama duk kusan ta kanshi da yakeyi da ita bawai dan yana sonta bane? To in har dama yana da wacce yake so a gefe mai yasa rana d'aya kwatsam ya dawo cikin rayuwarta har yasa zuciyar ta ta samu kusanci dashi, K'arar kiran daya shigo cikin wayarta ne ya katse mata dogon tunanin da takeyi, Number din shi da tayi saving da *King* ne ya fito b'aro b'aro a fuskar wayarta, Bata iya d'aukar wayar ba harta k'ara ci ringing d'in ta yanke, Sako ya k'ara tura mata ta WhatsApp din yanzun ma inda yake cewa, "Na kira baki d'auka ba! Koda yikema ba damuwa muyi hirar anan kawai" "Hummm" shine amsar data tura mishi, Bai damu ba ya k'ara tura mata da wani sak'on kamar haka, "Na samu macen da nike ganin zatayi dai dai da tsarina, saboda itane ma nabaro aikina na taho, sai dai har yanzun shakka da tsoron yanda zata amshe ni hakan yasa na kasa fitar mata da abunda yake cikin zuciyata, tsoro nikeji kar sai na tunkare ta ita kuma tace min na mata tsufa, I really don't know how to tell her I'm in love with her, ko zaki iya taimaka min?" Amsa ita kuma ta tura mishi da cewa, "Just let her know that you love her, tell her karka b'ata lokacin da wani zai so ya maka shigar sauri, kuma da kake maganar cewa ka mata tsufa indai tana sonka ai bazata tab'a ganin tsufan naka ba, kai dai kabar rai da abunda yake so kawai" Wani sak'on ya k'ara turo mata kamar haka, " You are right ok let me practice once on you first, *I LOVE YOU MAIMOON*" "I love you too, You can now go ka fad'amata gaskiyar abinda kake ji a kanta! Zan kashe wayana sai da safe, idan mun had'u zanji yanda kukayi da ita" Itama ta tura mishi "Wait please don't go, saboda na riga na fad'amata har ma ta bani reply ko" Ya aiko mata, "Wow na tayaka murna" "Bari in turo miki amsar da ta bani" Saman chat d'in su ya koma yayi tagging d'in amsar data tura mishi d'azun inda tace "I love you too" Sai ya rubuta mata "kinga amsar data bani" 😳 zaro idanuwan ta tayi waje cike da mamaki da sauri hannun ta ya typing ta tura mishi cewa, "Amma wannan ai chat d'in da mukeyi da kaine!" "Eh ai saboda kece yarinyar da nike so d'in shi yasa, Nagode kwarai da amsa tayin soyayya ta a gareki, a yau kinsa nima ina jin kaina kamar sabon saurayin da bai tab'a aure ba balle har ya haifi yara 4 insha Allah kuma zanyi k'ok'ari zuwa gobe in kawo ma Baba Usman gaisuwa da rok'on iri dan gaskiya ina buk'atar ki a kusa dani kwarai da gaske, ki kwanta kiyi bacci yanzun sai da safe, *I LOVE YOU TOO SWEATHEART*" Yana tura mata ya kashe data dan yasan dole zata nemi k'ara jin ta bakin shi. *Ummiee ce*✍🏼 [9/13, 4:11 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 26* Kusan raba dare tayi ba tareda ta iya rintsawa ba, kira ko ta kwatanta kiran shi sau adadin da bata iya lissafi ba, sai daga baya ta gane cewa da gangan nema ya kama tashi wayar ya kashe tunda dole yasan cewa zai sa zuciyar ta a shiga ukun da dole ta kirashin tunda ya sauka a online, Wai ita Sarki keso! Bai tsaya iya nan ba kuma har saida ya mata wayau yasa itama ta amayar da abunda ke cikin nata zuciyar duk da cewa ita koda ta rubuta mishi kalmar I LOVE YOU TOO,din ta tura tasan cewa kalmar daga k'asan zuciyar ta ta fito amma bawai da wani manufa ta tura hakan ba, Wato su maza idan basu nuna ma mace ban bancin yawan shekaru, wayau, da kuma hankali ba basa samun nutsuwa, Anya ma kuwa ba itace ta kwafsa ta yanda yayi saurin gane cewa itama son shi takeyi ba kuwa? Ita yanzun duk ba wadannan ne damuwar ta ba irin yanda yace wai gobe zaizo gida ya kawo gaisuwa, To idan Baba Usman ya tambayeta mai zata ce mishi? Kai gaskiya fa tana cikin chakwakiyar da bata san wanda zai fidda taba, waye ma wanda ya kamata ta tunkara da wannan maganar wanda zai bata shawarar daya dace? Meenal ce sai dai a yanzun kuma bata jin zata iya tunkarar Meenal din da wannan maganar dan har yanzun gani takeyi kamar taci amanar meenal din ne, to amma ai indai abun ya tabbata dole meenal din zata sani bai kamata kuma taji a bakin wani ba a dai yanda suke kamata yayi ace itace wacce zata sheda ma Meenal din komai dake faruwa to amma kuma ta yaya? Shin fitowa fili zatayi tace mata, Meenal tsohon mijinki wanda kuka rabu ya dawo wajena yana sona da aure ko da wani kalmar zatayi amfani wajen yi mata bayani, Wallahi Allah ita dai Allah ya sani tana cikin tsaka mai wuya sosai kuwa ga abun murna ya samu amma kuma babu halin yin murnan, Umman su da hawowarta saman kenan tazo d'aukar wani abunda ta manta bata d'auka a d'akin ta bane ta hango wutan d'akin Moon d'in a kunne, A gogon wayarta ta kalla wanda ya nuna kusan 1 saura na dare, mamaki ne ya kamata domin tasa Moon din mawuyaci ne ka sameta a farke zuwa wannan lokacin dan ita da wuri take bacci bata dogon hira duk ranar da batayi baccin da wuri ba kuma to tabbas sai dai in suna da wani case mai mahimmanci, dan haka mai makon ta wuce dakin ta kamar yanda tayi niyya sai ta juya akalarta zuwa d'akin Moon din dan ta kashe mata wutan. Da sallama ta shiga bayan ta tura kofar, tsayuwar cak tayi tana bin Moon d'in da kallo wacce ke kai kawo a cikin d'akin ta kasa zaune ta kasa tsaye mafita kawai take nema ta yanda koda maganar nan ya fita jama'a bazasu kalleta a matsayin maciyiya amanar da take son mijin daya saki yar uwarta ba, cikin yan awanin da basu kai uku ba duk ta firgice ta rasa nutsuwar ta, "Lafiya kike kuwa? Maiya sameki kike farke har yanzun? Wannan kai da kawowan kuma da kikeyi shima na menene?" Umman su ta jero mata tambayoyin bayan ta maida kofar d'akin ta kulle, Da hanzari Moon din ta k'araso inda take tana isowa bata jira komai ba ta rungume ta, Kukan tashin hankalin da take ta dannewa tun d'azun ne ya kwace mata ta fara rairashi ba kakkautawa, "Ke wai miye haka? Ya abunda na tambayeki daban baki bani amsa ba kinzo kin kankameni kina min kuka! So kike nima nawa hankalin ya tashi kamar yanda kika tada naki? Kiyi shiru kimin bayanin abunda yake faruwa da yasa kika kai har yanzun bakiyi bacci ba" "Umma ina cikin matsala ban san da wani idon zan kalli mutune ba idan abun nan ya tabbata, Mutane zasu dunga kallo na a matsayin maciyiya amanar da taso mijin yar uwarta" Kamata Umman nasu tayi suka k'arasa bakin gado suka zauna jin kalaman dake fita daga bakin Moon din wadanda ita bata gane musu ba sam, Sai da ta zaunar da ita kafin tasa hannun ta ta sharema Moon din hawayen ta kafin tace, "Kiyi shiru da kukan nan haka kimin bayanin abunda ke faruwa yanda zan gane" Wayarta Moon din ta d'auko ta shiga cikin chat dinta da Sarki hirar da suka gudanar a d'azun din ta nuna ma Umman nasu tun daga farko har karshe, "To menene abun damuwa ko tashin hankali anan Maimoon dan wani namiji ya nuna yana sonki? Yaune aka fara cewa ana sonki da zaki damu kanki ki d'aga hankalin ki nima ki d'aga min nawa hankalin, waneni shi d'in? " "Umma bazaki gane bane, domin ba kalmar son bane abin tashin hankali a wajena tunda ai ba akan shi na farajin kalmar ba, ah ah shida kalmar ta fito daga bakin shine tashin hankalin nawa a halin yanzun" "Shi yasa nima ai na tambayeki wane ne shi din?" Ummah ta k'ara tambaya a karo na biyu, Sauke ajiyar zuciya mai nauyi Moon tayi kafin ta iya kallon fuskar Umman nasu ta bata amsa da cewa, "Ya Sufyan Sarki Mijin da suka rabu da Meenal d'in Hajiya, Shine wanda ya furta yana sona kuma wai aurena zaiyi gobe kuma yake son yazo yaga baba dan ya nemi izini a wajen shi ni ban san ya zanyi ba tun d'azun nike kiran wayan shi ya kashe wayar ban san ya zanyi ba" Ta k'arasa fad'a da muryar koka kananan hawaye na Saukowa kan kumatun ta, "Turk'ashi! Shi mijin na Meenal ko ince tsohon mijin shine yace yana sonki? To ma a ina kuka had'u ya akayi yasan ki ko dama kun saba dashi ne? To shi bai san alak'ar dake tsakanin ki da ita Meenal din bane da zai wani zo yace son ki yakeyi ko koh dai salon ya b'ata zumuncin dake tsakanin ku, wannan ma ai ba maganar da ya kamata kunne ya saurara bane dan ana barin halas ko dan kunya inshi namiji ne bashi data ido aike mace ce duk da bawai hakan ya haramta bane amma kusancin yayi yawa, ke mema ya had'aki dashi?" Kaf abunda ya faru tun daga ranar daya sha gaban ta da mota har zuwa yau Moon ta kwashe tass ta sheda ma Umman su, "Maimoon kina son shine?" Shiru Moon tayi kafin ta amsa da cewa, "Nima ban san yanda zan kwatanta abun ba, amma nasan ina matuk'ar kokarin kame kaine akoda yaushe indai ina tareda shi," Riko hannun ta Umman tayi, "Moon bazance karki soshi ba domin ban san ya kikeji akan shi ba, sai dai zan miki tuni ne akan zumuncin dake tsakanin ki da yar uwarki Meenal ki d'auka cewa kece kika rabu dashi sai kuma kwatsam kikaji cewa ya koma sonta duk da kawancen dake tsakanin ki da ita ya zakiji, kibar batun cewar da akayi babu abunda ya hada su na auratayya koma dai yayane ita d'in tayi zama na shekaru a matsayin matar shi dan haka koda bata nuna a fuska ba tabbas ba lallai bane hakan ya mata dad'i a cikin zuciyar ta, ni dake dukan mu mata ne kuma ciwon ya mace na d'iya mace ne abinda bazan so ya faru dani ba indai zumuncin dake tsakanina da wata na gaskiya ne shima bazan so ya faru a kanta ba dan haka ina mai baki shawara da kisan yanda zakiyi ki cire son shi a cikin zuciyar ki in ma kin fara son nashi, In kuma babu soyayyar falillahil hamdu sannan karki yarda ki barshi yazo gidan nan a gobe kisan duk yanda zakiyi ki hana shi zuwa ganin abban ku dan su maza kusan tunanin su d'aya ne basu fiye damuwa da abun da ke iya zuwa ya dawo ba kinji dai na fad'a miki dan in hakan ya tabbata ban san da bakin da zan kare kaina wajen Hajiya ba dan haka babu ruwa na ki kuma kwanta kiyi bacci dare yayi" Tana gama fad'in hakan ta fice daga d'akin bayan ta kashe ma Moon din haske, Wannan dare dai sam baiyi ma Moon dadi ba domin sosai kalaman Umman su ya k'ara sanyaya mata jiki, kamar kuma yanda Umman nasu tace ta d'auki hakan a matsayin cewa a kanta ne abun ya faru itace ta rabu dashi sai ya koma yana neman yar uwarta ya ita zataji, Gaba daya sai takejin ai in itace hakan ya faru da ita tofa tabbas bazata iya d'auka ba, to waima miyasa tun farko tayi saken da har ta bar zuciyar ta ta kusantu dashi har haka? Lallai ita soyayya batayi mata adalci ba me yasa? Me yasa? Me yasa? Zuciyar ta zata kamu da son shi. Tsabar yanda tasa damuwa a ranta ne hakan yasa washe gari ta tashi da zazzafar zazzabin dako aiki bata iya fita ba dan sai da aka kira likita yazo har gida ya dubata, Fad'a sosai umman su ta mata sai dai duk abunda ke faruwa Umman bata nuna ma Baba Usman komai ba, Ita kuma Moon d'in duk da yanda take jin jiki haka tayi ta neman Sarki a waya amma bai kunna wayar shi ba gashi kuma ita ba sanin gidan shi tayi ba balle taje ta same shi, Wajen da suke had'uwa kuma tasan ko zaije wajen sai yamma yau kuma batama da tabbacin cewa zai yarda su had'u tunda gashi yak'i kunna wayar shima, tana ta addu'a ko baba Usman zai fita gida amma sai gashi yau tunda gari ya waye bak'i kawai yake tayi wad'an nan na fita wasu ke shigowa kuma duk in bak'in sun shigo sai ta aika kannnen ta su dubo mata, Daga ita har umman su babu wacce ta samu nutsuwar zuciya dukan su a tsorace suke. **** A gefen Sarki ko lafiya kalau yayi bacci a wannan rana cike da farin cikin kololuwar da zuciya ce kad'ai zata gane hakan, a yau daya fitar dake abunda ke cikin zuciyar shi akan Moon sai yakeji kamar ai har anyi angama dan haka kamar yanda ya kudurta dole a goben zai isa ga Baba Usman dan haka kwana yayi yana shawara da zuciyar shi akan shine zaije ko koh wani ya kamata ya wakilta yaje mishi ne? To wani wa zai wakilta? Brig, Gen, zuciyar shi ta bashi amsa, To amma idan yaje ma brig da maganar nan hakan bai zama cin fuska ba kuwa? Yaushe yaushe ya rabu da Meenal harda zai fara neman wani auren ga kuma Teemah ba wani lafiya take dashi ba kullum fama takeyi da kanta, kuma shi brig din fa uban matan shine, To amma idan bashi din ba ana ai bashi da wani shak'ik'in da zai tura, kuma koda Brig baiji maganar nan yanzun ba dole zaiji zuwa gaba dan haka gara ayi ta ta k'are kawai tun yanzun yasan cewa tunda brig namiji ne zai gane halin da yake ciki, Da wannan shawarar daya yanke ya samu bacci kai d'adi ya d'auke shi, Washe gari ko yana k'aryawa bayan ya gama abubuwan da zaiyi ya d'auki Boy yama Teemah sallama akan zasuje Barracks, Sun tattauna sosai tsakanin shi da Brigadier abunda bai tab'ayi ba shine yau yayi wato zauna wa ya labarta shima irin zaman da sukayi da Teemah dama abubuwan daya faru harma da dalilin rabuwar su da Meenal harda hukuncin daya yanke na k'ara aure dama yarinyar da yake son auren, Brigadier yayi fad'a sosai akan me yasa tsayin shekarun nan shi Sarki baizo ya shaida mishi irin rayuwar dake gudana a cikin gidan shiba, ranshi ya baci sosai dan haka bai b'ata lokaci ba shi da kanshi ya shirya bayan ya amshi adireshin gidan su Moon ya kira Aminan shi mutum biyu suka shirya suka tafi dad'i kamar ya sheqe Sarki dan baiyi zaton hakan zaizo mishi da sauk'i ba, Su brigadier sun isa gidan su Moon a wannan rana sun kuma samu damar ganawa da Baba Usman, Bayan gaisuwa sunsha hira sosai a tsakanin su domin ashe d'aya daga cikin abokan na Brigadier tsohon Abokin Baba Usman ne wanda suka dad'e basu had'u ba hasali ma dukan su basu san cewa gari d'aya suke zaune ba dan haka sai aka shiga hira da tuna baya irin na tsofaffin abokai kafin suka gangaro kan abunda ya kawo su gareshi, wato neman iri, anan ne shi brigadier ya gabatar da kanshi a matsayin uban Sarki a kudu kuma uban matan dashi Sarki d'in yake aure ya kuma k'ara dayi mishi fashin bak'i neman auren Moon din da suke so duk da kasancewar ta yar uwa wajen Meenal, Da yike kasancewar su maza hakan bai wani dame suba sai dai Baba Usman ya sheda musu cewa shi dai shine uban Maimoon kawai amma neman auren ta da bada shi yana hannun d'an uwan shi Ahmad ne wanda a halin yanzun kuma baya k'asar yana zaune a Saudiya ne tare da nashi iyalan, Jin hakan sai suka rok'e shi akan ko zai basu number din waliyin natan in yaso sai su neme shi suji ta bakin shi dan sufa da zafin su sukazo, Hakan ce ta faru domin a nan falon Baba Usman ya kira Abba Ahmad sukayi magana su brigadier suka kawo maganar neman auren da suka zo, Shi kuma ya shaida musu cewa suyi hakuri har ya shigo k'asar a sati mai zuwa dan neman auren yarshi yafi k'arfin ace ayi shi ta waya suyi hakuri har sai yazo sai ayi komai daya dace, A haka suka rabu kowa cikin farin ciki, Bayan brigadier ya koma ne ya kira Sarki ya sheda mishi yanda sukayi, shima dai yayi farin ciki da jin haka koba komai yana da hope akan samun Moon din tunda yanzun maganar taje gaban Manya dan shi dai zuwa yanzun yana jin cewa bazai iya b'ata wasu watan ni masu tsoho ba tareda ya mallaketa ba, A ranar da wuri Moon ta k'arfafa jikin ta bayan zazzabin ya d'an saketa ta fita zuwa inda suke had'uwa da Sarki sai dai kuma abun takaici haka tayi ta zama har gabannin magrib Sarki bai zoba kuma bai kunna wayar shi ba, gajiya tayi ganin dare ya kunno kai ta taso haka nan ta dawo gida jikinta a sanyaye, Da dare yayi koda Umma tama Baba Usman magana akan bak'in daya dungayi a yau d'in a zaton ta najin ko zaice mata Sarki yazo ko wani abun makamancin hakan sam bai d'auko mata hirar ba dan ce mata yayi abokanan kasuwancin shine kawai, Shi kuma yak'i fad'a mata gaskiya ne dan yasan a matsayin ta na mace bai zama lallai tama abun kyakyawar fahimta ba, dan haka ya yanke hukuncin gara yayi shiru har sai Abba Ahmad ya shigo k'asar zasu yanke hukuncin sannan su san ta yanda zasu shawo kan Hajiya akan maganar dan nata rikicin yasan yana gaba akan na kowa, Daga wayewar gari zuwa dare Moon ta aikama Sarki sako mara adadi tana rokon shi akan dan Allah karyace zaije ya samu Baba Usman akan maganar nan ita bazata iya auren mijin da suka rabu da yar uwarta ba, lokaci zuwa lokaci take dubawa ko ya dawo mata da amsar sakon nin ta amma babu wani motsi har aka kwana aka hantse, Bashi ya kunna wayar shiba sai da aka kwana biyu koda ta dana maganar kawai sai ya nuna mata ba komai bazai je wajen Baba Usman din ba har sai sanda ita da kanta ta bashi dama, Amma fa kullum safe rana dare baya gajiya da kiranta a waya kawai dan yaji muryar ta ya kuma tambayeta ya take, Ita kuma Umma ganin Moon din ta sake kuma shima Baba Usman baice mata komai ba sai tati zaton ko Moon ta shawo kan Sarki ne ya hakura dan haka itama sai tayi watsi da komai ta dukufa dama Moon din addu'ar Allah ya fito mata da miji na gari tati auren ta ta huta zaman gidan ya isa haka. A gefen AK ko tun bayan barin su Meenal Kaduna bai samu zama ba a kokarin shi na ganin ya kammala komai kafin ya wuce Zarian dan yanzun shirye shiryen bikin Musty shine abunda yake gaban su, Tunda Meenal tabar garin basu k'arayin waya ba koya kirata haka wayar zatayi k'ara harta gaji ta yanke bazata d'auka ba, Daya fahimci horashi take son yi ta nan gefen sai ya daina kira ya koma tura mata sakon ni, shi kanshi mamakin kanshi yakeyi ta yanda yake iya zama wajen tsara tausasan kalaman soyayya masu tsuma zuciya wadanda ke fitar da gaskiyar abin dake cikin zuciyar shi ya tura mata, Ko wani safe rana dare da kallar sakon da yake tura mata masu zafi kuma komai yakeyi in lokacin tura sak'on yayi zai ajiye ne ya rubuta sai ya tura mata ya tabbatar sakon ya tafi kafin zaici gaba da al'amuran shi, idan kuma yana son jin muryar Meenal d'in number d'in Sultana da yasa Musty ya amsa a hannun Meelat ya tura mishi yake kira, Ita kuma sai ta ajiye wayar a kusa da Meenal tayi ta janta da hira bayan ta d'auki wayar haka zaiyi ta saurare har sai ya gamsu zai yanke wayar, yawan jin muryar ta da yakeyi ta wayar Sultana ba kad'an ba yake rage mishi kewar ta duk da haka Allah Allah yakeyi ya iso Zaria tunda dai har yanzun bai san me nene gaskiyar abinda yake cikin zuciyar ta akan shiba, To itama dai Hajiyar taku a gefen ta tun tanajin wani iri a duk sanda zata ga sak'on shi har ya zamana yanzun Allah Allah take taga sak'on nashi ya shigo wayarta dan ta samu inda zata lab'e ta karanta, tsaf ta haddace lokutan da yake turo mata sakon sai dai duk rok'on da yake mata akan ta amsa mishi wato ta maida mishi amsar sak'on nashi tak'iyin hakan zata dai karanta tana murmushi amma babu amsa, Mutum biyu sune sukafi takura mata a rayuwarta yanzun na farko Salman wanda take ma kallon tabab'b'e tun daga ranar daya wanko k'afar shi yazo har gida ita ta d'auka wani abun arzikin zai fad'a mata amma wai gayen nan sai da ya karkace ya gyara tsayuwar shi kafin ya kalli tsabar idonta ya fad'a mata wai shi dai Salman shine yake sonta kuma ma abun bai tsaya nan ba harda wani ikirarin wai aurenta yake son yi abundai kamar a duniyar mahaukata wallahi, To dai ai ko daga dawanau ya kwato ya fito ai bai kamata ita tana matsayin matar da yayan shi ya aura ya sake ba shi kuma yazo ba kunya ba tsoron Allah yace wai shima sonta yakeyi zai aureta, Ita wallahi bata tab'a sanin cewa k'aton mahaukaci ta dad'e tana ma kallon mai hankali ba sai ranar dan rasa amsar da zata bashi ma tayi sai kawai ta juya ta shige cikin gida ta barshi a wajen yana kwala kiran sunan ta ko waigen shi batayi ba, Tasan in tace ta bud'e baki tayi magana a lokacin tofa tabbas tana iya lailayo k'atoton zagin da zata d'ura mishi ko kuma ta sheqe fuskar shi da mari ko ya dawo hayyacin shi, koda ta fad'a ma Sultana abunda ya faru tsakanin ta da Salman din dariya kawai tayi kafin tace mata, "Ai na fad'a miki dama cewa sonki yakeyi amma kikak'i yarda, wallahi in kikayi sake jan ajinki yasa kika k'i yarda ki amshi soyayyar AK tofa sai dai kiji ana shelar d'aurin auren ki a masallaci bayan an d'aura, Muko mik'aki zamuyi mu fito muna fatan Allah ya kawo yan hud'u" "Sultana kibar wannan maganar ki barni in fama mamakin abunda gayen nan yamin, Waini zai kalla yace yana so wato so sukeyi shida yayan shi su mai dani kwallon wasa wato yayan ya saki shi kuma bari ya kunno min kai, insha Allah ni kuma duk ranar daya k'ara shawo kayan mayen shi yazo ya k'aramin hauka sai nayi tsalle na tsatso karfi kafin in kakkafta mishi mari" Dariya sosai sultana take mata, "To ki yarda mana kawai tunda dai shi AK kince bakya son shi... " Yanke ta tayi da cewa uban wa yace miki bana son shi, Ko ban so da aure ba ai dai shi din dan uwana ne, kuma amsa soyayyar ne ban tashi ba tukun, kece baki san halin shiba na rantse miki da allah ina sakewa nace na yarda ina son shi tofa na shiga uku kenan bani ba k'ara shakar numfashi cikin kwanciyar hankali, Kinga wancan ustazun yayan naki da kike ganin yana matsa mana? To yasin nashi kad'an ne ni kuma yanzun bana buk'atar kowa ya takura min, kuma ai nace musu ni ba yanzun zan k'arayin wani auren ba" Wayarta data d'auki karar kira ne ya katse mata zancen bakin ta, "Sultana kin san wake kira?" "Waye"Sultana ta tambaya, "Mutumin mu na ranar nan wanda muka had'u dashi a kofar doka" Dariya sosai sultana ta fashe dashi tana cewa, "Sister kiji tsoron Allah kibar mutumin nan tunda ba auren shi dai zakiyi ba shima da shegen naci nayi zaton ya dena kira ai!" "Ki barshi kawai ai inya iya naci ni kuma nice maganin shi, kin san tun jiya yake nacin wai yana son zai gaishe da Mommy tunda na hana shi zuwa gida nace sai zuwa gaba tukun, To tun jiyan yake kirana wai in bata waya ni karan hauka ne ya cijeni dazai had'asu tab', Wai kin ma san me?" "Ah ah" "Wai tambaya na yake nawa nake buk'ata kudin da zanyi hidimar biki," Dariya sosai Meenal ta fashe dashi kafin ta d'aura da cewa,, "Kibar mugun wai ni zaima gatse harda wani cewa yaji shiru ban tura mishi da account number ba kona raina abunda zai bani ne, ni kuma tunani nike in tura ko in kyale shine to gashi dai kin gani sai faman kira yake tun d'azun" "Kawo wayar ki gani, da fari dai ki fara tura mishi account number din, idan ya tafi sai ki kira shi kice mishi Mommyn bata kusa ne amma gata ni kuma zan gyara muryata irin ta manya sai inyi magana dashi a matsayin Mommy muci kudin banza wallahi" "Allah dai yabar min ke My Namcy bari ki gani yanzun kuwa zamu gabatar da komai kamar yanda muka shirya" Amsar wayar tayi ta fara tura mishi account number d'in sai da ta tabbatar da cewa ya isa tashi wayar kafin ta danna mishi kira, Ita kuma Sultana tana gefe sai faman gyara murya take dan ko kad'an bata son su kwafsa, tsun tsune fa suka samu daga sama gasasshe dan haka ai suci rabon su kawai, Din din din karar da wayar keyi kenan alamun dake nuna wayar na ringing tacan gefen, Yanke wayar akayi cikin kankanin lokaci ya maido da kiran zuwa wayar Meenal d'in, "Ke gashi yana kira wallahi" cewar Meenal tana nuna ma Sultana, "To ki dauka mana kar kiran ya yanke kuma" " Assalamu Alaikum hello" ta ambata bayan ta daga kiran sai ta danna wayar a speaker, "Ameen Alaikis Salam Baby girl barka da war haka ya kike?" "Ina lafiya Yallabai, dama nace bari in kirane in had'aku da Mommyn kamar yanda ka buk'ata" "Ok ok aiko kin kyauta naji dad'i sosai ki bata wayar to" "Ok Mommy gashi zaku gaisa" Cewar Meenal tana tura ma Sultana wayar, Gyara muryar ta Sultana tayi sosai ta yanda ya koma kamar na Babban mace ba kuma na tsoffi ba ta rik'e wayar a hannun ta tana cewa, "Wanene kuma zaki had'ani dashi Yar Malam keda ko maganar samari bakya son ana miki a gidan nan wani kai sa'an ne wannan?" Ta tambaya kamar irin bata san shi na cikin wayar yana jin me take cewa ba, "Ni dai Mommy gaisawa kawai zakiyi dashi bance kice mishi komai ba atoh dan so nike sai mun k'ara shakuwa kafin in gabatar dashi kuma ke kad'aice ma yanzun zan had'aku" "Haba Meenal ko baki fito fili kin fad'aba ai nasan kina son shi Allah yasa dai ya rik'e min ke da amana kema kiyi auren nan dai" Sultana ta karasa fada kafin tace, "Assalamu Alaikum" "Ameen Alaikum Mama ina wuni" "Lafiya lau d'an nan ya gida ya aiki da wajen iyayen ka dafatan duk kuna lafiya?" "Lafiya lau Mama ya lafiyan jiki?" "Alhamdulillah d'an nan ya rayuwa? Sannu kaji naji dad'i sosai wallahi Allah dai ya maka albarka yasa ka gama da iyayen ka lafiya, Allah yayo jagora kaji, nagode kwarai da gaske" Shi kuma acan gefen shi amsa addu'ar nata yake tayi da "Ameen Ameen Mama nagode, ina dai ta rok'enta akan ta bani dama inzo gida in gabatar da kaina shi yasa nace ta baki wayar muyi magana ko zaki sa min baki ta amince" "Ayah ayyah indai wannan ne ai karka wani damu kanka, Tunda har ta had'ani da kai nasan ba k'aramin so take maka ba dan haka ka kwantar da hankalin ka abi komai a sannu dan nidai ka riga ka samu goyon baya daga gareni ban ganka ba amma sosai na yaba da hankalin ka" Hira sosai Sultana tayi da shi a matsayin itace uwar Meenal kuma tayi na'am da soyayyar da yake ma yarta kafin su kayi sallama sai da ya fad'a mata cewa zai tura ma Meenal din sak'o yanzun sai ta siya mata goro, Ita ko harda wani cewa "ayi haka d'an nan daga gaisuwa kuma sai ka fara dawainiya tun yanzun, to andai gode Allah ya k'ara bud'i" Sosai ta dunga kwarara add'u'a shiko sai dadi yakeji irin a dole ya samu k'arbuwa a wajen uwar budurwa, Bayan wayar ya koma hannun Meenal ne kuma ya k'ara tabbatar mata da cewa zai turo da sak'o dan Allah tayi k'ok'ari ta fita ta siyo ma Mommyn abunda tasan tana so wanda zai faranta mata rai, Shi baya gari yanzun haka amma yana fatan idan ya dawo zaici arzikin da zata bari yazo ya kawo gaisuwar shi na musamman a wajen Mommy, Lafiya lau sukayi sallama tana mishi godiya, suna yanke wayar ita da Sultana suka fara dariya kamar wasu tab'abb'u, "Ke tashi fa muje in tayaki ki had'a kayan ki dan Wallahi yau ban k'ara kwana a gidan nan kafin wancan mahaukacin Salman d'in anjima ya k'ara dawowa, "Ah zauna tukun muyi magana inji nawane nawa kason idan kud'in suka shigo mana" "Dallah can ai dai kya bari harya turo kafin muyi kasafi" Sultana ta bud'e baki zatayi magana kenan idonta ya hango mata Sheikh dake tsaye daga bakin kofa hankalin shi kachokam yana kansu, Fuskewa tayi kamar bata ganshi ba ta d'auki wayar Meenal ta shiga da sauri ta goge number din mutumin daga jerin kira ta shiga cikin message ma ta goge message din da suka tura mishi na account number sai zufa take had'awa dan tasan yau su kuma sai ta Allah fatan ta dai allah yasa Sheikh baiji hirar su ba Allah yasa yanzun ne ya iso wajen bawai tun d'azun ba, Ta yunkura zata bar wajen shi kuma ya k'araso fuskar nan kadaran kadahan bazaka iya tantance halin da yake ciki ba, "Koma ki zauna" Ya fad'a kai tsaye, Sai lokacin Meenal ta d'aga kai ta kalle shi, Zaman Sultana tayi kamar yanda ya buk'ata tana mik'a mishi gaisuwa bayan tayi kokarin boye tsoron dake cikin zuciyar ta, Gaishe shi itama Meenal ta mik'a hannu zata d'auki wayar ta da Sultana ta turo mata yakai nashi hannun ya d'auki wayar kafin ya samu waje ya zauna, Wayar bata da matakan tsaro dan haka kai tsaye call long ya fara dubawa sai dai ga mamaki babu wata number wanda akayi kira da ita yanzun dan number din dake wajen duka wad'anda aka amsa kira dasu ne tun na jiya ya gane hakan ne a sanda ya duba lokacin kiran, "Dawa kuka gama magana a waya yanzun?" Ya tambaya yana tsatstsare su da ido, Shiru sukayi kafin Meenal ta d'ago kanta suka had'a ido da Sultana kafin ta maida duban ta kanshi ita din shima yake kallo. "Uhumm ku nike saurara kuma karku sake kumin k'arya inba haka ba saina b'ata muku rai" Yana rufe baki ko numfashin kirki bata bari ya sauke ba ta amsa mishi da cewa, "Bazawari nane ya kira, ya buk'aci in had'ashi da Mommy ni kuma ban shirya gabatar dashi ma kowa ba shi yasa na had'ashi da sultana" Ta fad'a irin ko a jikin ta, tunda yace kartayi mishi karya ai dama ko baice ba gaskiyar zata fad'a tunda dai tasan bashi da wuta ko aljannar da zai saka ta, In ya iya takura ita tayi zama ma da wanda magana d'aya biyu zakiji yace "sai na zane miki jiki, saina mareki, sai na karya k'afarki" Kuma har yanzun ya kasa aikata ko d'aya balle kuma shi Sheikh d'in. Babu editing *UMMIEE CE*✍🏼 [9/13, 10:40 PM] zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 27* Yanzun ke tsakanin ki da Allah hakan da kikayi kina ganin kin kyauta kenan? Wannan ai tsabar yaudara ne da cin amana, idan bakya son shi mai yasa zaki yarda ki bashi number dinki, ina amfanin k'arya a cikin zaman takewa, ai gara ki fito ki shaida mishi cewa bakya ra'ayin shi a maimakon wannan k'aryar da yaudarar shi da kikeyi da girman ki da komai, baku kyauta ba gaskiya" Da yatsar shi manuniya yake nuna Sultana kafin yaci gaba da cewa, "Kema ashe haka kike? Wato k'ananan yara daku kunsan yanda zaku had'a kai ku cuci wani, ke kece mai gyara murya kika amshi waya kikayi magana dashi a maimakon Mahaifiyar ta daya buk'ata, kun manta ne da cewa koda shi baya ganin ku Ubangijin al'arshi yana ji da ganin duk abinda kuke aikatawa a sarari ko a cikin duhu?" Katse shi Meenal tayi da cewa, (Shehi ko kuma Ustaz)sune sunan da take kiran shi dashi mai makon ta kira shi da (Ya Sheikh ko Ya Naseer da wasu ke kiran shi dashi a gidan, "Shehi kaga dagani har Sultana fa duka ba laifin mu bane, Shi dai mutumin nan tun ranar farko na nuna mishi cewa yayi hak'uri bana ra'ayin tarayya a tsakanin mu amma ya nace ya tasani a gaba da rok'o Allah Annabi akan dai in bashi number na, Ni kuma girman Allah daya had'ani dashi shi yasa na bashi number d'in, To fisabilillahi tunda ni nasan ba son shi nikeyi ba ina zan yarda in had'ashi da uwata, kawai dan kar yaji ba dad'i a matsayin shi na Babban mutum shi yasa yau na had'ashi da Sultana kaga idan hankalin shi ya dawo jikin shi a hankali ni kuma zan san yanda zan fahimtar dashi ya gane bana ra'ayin shi amma kafin nan ai kasan sai nabi dashi a sannu tunda ban sani ba ko mugu ne kar inyi gaggawa in b'ata mishi rai ya kullaceni a banza dan Wallahi ance wasu mazan da asiri suke shawo kan mata" "Koma dai menene bai dace ku yaudare shiba, kuma ma kud'in minene naji yana batun zai tura?" Zaro idonta Meenal tayi wai mutumin nan lab'e ya musu ne da yazo ya titsiyeta a gaban shi yana musu wa'azi da tambayoyi ko ya abun yake ne? Wai dama suma maza sun iya lab'e ashe, to andai fad'i ba nauyi wallahi ustazu da sauraron hirar mata😒 "Kud'i kuma😳? Wani kud'in?" "Ke karki mai dani karamin yaro mana bayan duk abunda kuka tattauna naji ko kin manta a loud speaker kika sa wayar ne? To kud'in da kuke son yin kasafi akan shi nike magana ki kirashi yanzun nan ki fad'a mishi cewa bakya buk'ata, kinji na fad'a miki dan banga dalilin da zaisa ku amsar mishi kudi bayan kince bakya son shiba" "To amma shehi nifa ban rok'e shi kudin nan ba ra'ayin kanshi ne yasa yace zai tura kud'in, kaga kuma ai dai babu kyau maida hannun agogo baya koh? Wanda kuma yayi niyyar yin aikin alkhairi ai bai dace a dakushe mishi niyyar shiba sai yaga kamar ana mishi bak'in ciki da ladan dake ciki ne" Ta fada tana tura baki to waima akan me zai wani ce ta kira tace karya turo kud'in bayan ita harta fara kasafin abinda zatayi da su tun kafin su shigo, Akwai friends event da suke so su had'ama Meelat ita da Maryam da sauran friends dinsu a school, surprise suke so suma Meelat d'in shi suke ta yima shirye shirye ita dasu Moon kunga ko ai dole ta buk'aci kud'ad'e masu d'an tsoka to tana murna ta kamo jibgegen zakara kuma shine shi wannan ustazun zai wani zo ya nemi yi mata karan tsaye, Kara wayarta yayi alamun shigowar sak'o, Yana dubawa ko yaga daga bankin da take amfani dashi ne First Bank, Budewa yayi yaga Alert ne na zunzurutun kud'i har naira dubu d'ari biyu, Mamaki da tsoron Allah ne suka cika shi ya kasa cewa komai sai mik'a ma Meenal wayar da yayi yana cewa, "Duba kiga asarar dukiyar da kukaja mishi, Shin fashi kuka farayi ma maza ne babu wanda yake da labari ko a ina ma kuka samu fasahar aikata hakan? Kai shima dai duk yanda akayi b'arawo ne inba haka ba taya zaka d'auki kud'i zunzurutu har naira dubu dari biyu ka turama budurwar dako gidan su baka sani ba kawai daga kayi magana da Maman ta, Ki kiramin shi yanzun nan ya turo da account number din shi ku maida mishi da kud'in shi ki kuma fad'a mishi gaskiyar cewa ba son shi kikeyi ba dan haka gara ya dena wahalda kanshi" Kan kame wayar tayi tana tura baki, da ido tama Sultana signal akan ta tashi ta fita daga falon, Dan haka simi simi Sultanar ta tashi Allah yasa dama akwai Hijjabi a gefen ta dan tun d'azun sukaso zuwa gidan su Meelat sai zuwan Salman ya tsaidasu, Ficewa tayi daga falon tana fita batayi sallama da kowa ba ta shiga motar Meenal ta tuk'a ta fice daga gidan dan hakan shine matakin farko na tsira daga wa'azin Sheikh dan tasan shi kenan kuma sun shiga uku tunda har ya kamasu kirikiri wa'azine zasu sha har su gaji amma in bai gansu a gidan ba sai dai yayi jininin shi kada'i, "Yanzun nan shehi fisabilillahi da gaske kakeyi lallai sai na kira shi ya turo account number din na maida mishi kud'in? , kyauta fa ya bani ba tareda na rok'a ba taya zan maida kyauta bayan kaima kasan hakan babu kyau" "Kyauta daban Meenal wannan daban" "Babu ban banci tunda bamu rok'e shiba" "Ok kenan dai kina so kice bazaki kirashi ya turo account number din ki maida mishi ba? To in kinci kin san kudin me kika ci?" "Nidai koma dai menene kayi hakuri dan gaskiya ina jin kunyar yanda zan kirashi ai sai yaga kamar wulakanta shi kawai nake son yi" "Meenal!.... Bata barshi ya furta komai ba ta mik'e tsaye tana cewa, "Bari inje in tambayo idan Baba Malam yace in mayar mishi sai in maida" Tana kaiwa tsakiyar falon ta kwasa da gudu ta fice sai da ta tabbatar ta yi nisa da falon sannan ta tsaya ta waigo sai suka had'a ido yana kallon ta tana kallon shi kafin ta mishi gwalo harda kashe idon ta guda d'aya😜 ta kuma murgud'a mishi baki ta juya da gudu ta fice daga gidan, Tunda ya fara had'uwa da yarinyar nan abubuwan ta yake bashi matuk'ar mamaki ya lura da cewa kwata kwata Meenal bata da tsoro ko shayin da zata kasa aikata abunda tayi niyya a gaban shi, Duk yaran gidan ya lura idan yana waje suna kama kansu suna shayin aikata ba dai daiba amma ita, Ita kam kanta tsaye takeyin abubuwan ta ko a jikin ta kai shifa yama lura da cewa wani abun idan tanayi ganin idon shi yake sawa takeyin su, Amma yau dai abunda suka aikata ita da Sultana yasa ya fara jin tsoron mata, idan har su da ba wani hankalin kirki suke dashi ba suka iya aikata haka to sauran matan da suka fisu girma wayau da kuma shekaru su kuma ya suke tafiyar da maza kenan? Dama kenan haka mata suke tafiyar da namijin da basa so musamman idan suka had'u da sakaran namiji, kuga fa wannan shashashan daya tashi ya tura mata zunzurtun kudin daya isa ya cida marayu na tsayin wata d'aya a k'arance, "Allah ya yafe muku kuma ya shirye ku" Ya fad'a yana girgiza kai bayan Meenal din ta wuce, Shifa mamaki yakeyi ma da akace mishi wai likitanci Meenal din ke karantawa, dan shi a haka yanda yake kallon ta gani yake kamar rashin d'aukar abubuwa da mahimmanci da takeyi bazasu barta tayi karatu mai wahala kamar karatun likita ba. Suko tunda sun san abunda suka aikata kuma a yanda ta lura tsaf Shehin nan yana iya kai zancen nan gaban Malam dan haka kawai ya bud'e mata aiki, dan haka daga gidan su Meelat Tudun wada suka wuce a ranar babu wanda suka sallama sai da dare yayi nema da Mommy Hauwa taga shiru basu dawo ba ta kira Meenal din dan taji ko a gidan su Meelat zasu kwana shine Meenal din ke shaida mata cewa sun koma Tudun wada zatayi magana da Fauxieyerh ta had'o kayan Sultana gobe ta biyosu dashi can gidan, Hatta Malam a waya ta kirashi ta shaida mishi cewa suna Tudun wada, Baiyi fad'aba duk da cewa bai so hakan ba sai ma cewa da yayi ta gaishe mishi da Hajiya, Shiko Salman a ranar ma sai da ya k'ara komawa gidan Malam din da dare sai kuma ya samu labarin bata gida, Har gidan su Meelat yaje aka shaida mishi cewa basa nan, Kwana biyu ya jera yana jelan zuwa gida Hajiya amma Meenal bata bashi daman da zai gana da ita ba daga karshe ma masu gadin ta fad'ama cewa duk ranar da yazo karsu k'ara bud'e mishi gate suce mishi bata nan, Abun duniya duk yabi ya dame shi dan haka ya yanke hukuncin gara ya sami Uwar gida da maganar kawai, Baiyi k'asa a gwuiwa ba haka yaje mata da zance a wani zuwa da yayi gidan Hajiya masu gadin suka hana shi shiga, Dan haka bayan ya koma gida ne ya iske Uwar gida da malam Sulaiman a falon na Malam Sulaiman, Bayan sun gama gaisawa ne Malam Sulaiman din ke tambayan shi ya aikin gyaran gidan Sarki wanda ya siya a Kaduna yake tafiya, Shi kuma ya shaida musu da cewa komai ya kammala yanzun gida masu shi kawai yake jira su shiga cikin su, Ya dade a zaune ganin bashi da niyyar tafiya ne hakan yasa Baban nashi tambayan shi da cewa, "Salmanu lafiya kuwa ko akwai wani abu ne?" Kanshi a duk'e ya amsa da cewa, "Eh to dama dai wani magana ne nake so in fad'a muku" Yakai karshen zancen yana sosa keya irin yanda maza keyi in suna jin kunya, "To bismillah yi bayanin ka muna sauraron ka ai" "Uh uhm uhmm dama... Dama... dama ina so ince muku na samu matar da nike son, Umm nike son aure... Aure ne, to. To. Tooo shine dama.. Dama nace bari infad'a muku saboda ina son a shige gaba wajen yimin tambaya" Ya kai karshen zancen da kyar yana jin zufa yana d'an karyo mishi dan bai san yanda suma zasu kalli zancen ba, "Ah to masha Allah, shine tun d'azun ka kasa magana sai faman kame kame kakeyi" Cewar uwar gida cike da farin ciki mad'aukaki a fuskarta, "Bakiji d'an naki yau har da in ina ya fara ba" Shima Malam Sulaiman ya furta yana ma Salman din dariyar in inan daya dungayi akan maganar da batafi wasu yan takaitattun harafi ba, "A ina ka samo matar? Ina nufin yar wani gari ne kuma su waye iyayen ta?" Malam Sulaiman ya tambaya. Duk'ar da kanshi k'asa yayi sosai ba tareda ya iya kallon d'aya daga ciki su biyun ba ya amsa da cewa, "Ameenatu Meenal nike so, har cikin zuciyata nike son kasancewa da ita a matsayin matar aurena dan Allah kusa baki ku nema min auren ta" "Wai naji kamar ka kira sunan Meenal ko tsufane yasa banji sunan da kyau ba Baban su?" Uwar gida ta fad'i hakan tana kallon malam Sulaiman wanda shima Salman din yake kallo cike da mamaki mad'aukaki, "Ah ah ya kuma zaki maido tambayar ki kaina bayan ga wanda yayi maganar nan zaune a gaban ki, Nima dai ban fahimci mai yace ba, Kai wata Ameenatu Meenal din kake magana ne wai, Ina fatan dai ba matar da d'an uwan ka ya saka kake so bakoh? dan nidai nasan ita kad'aice Ameenatun da muke kira da Meenal kaf a cikin Dangi?" Malam Sulaiman ya tambaya yana jiran amsar da Salman d'in zai bashi, "Ana magana dakai kayi ma mutane banza, Ko bakaji tambayar da akayi maka bane?" Cewar uwar gida. Da kyar Salman din ya bude baki ya amsa musu da cewa "Eh ita nike nufi Aminatun Baba Malam kuma ai aurena da ita bai haramta ba tunda shi yaya bata mishi ba ni tayi min ina son ta zan aureta in zauna da ita" "Da kata Malam" Uwar gida ta fad'a a fusace tana d'aga mishi hannu alamun dakatarwa, "Kai baka da hankali dama ashe ban sani ba? Matar da d'an uwan ka ya aura ya sakice kake tunanin zamu sa baki a aura maka ita? Saboda ka mai damu mahaukata, To baka isa ba kayi kad'an dan haka karma ka sake in k'arajin maganar nan ta fito daga bakin ka koda wasa balle kuma har zancen ya fita ya zaga cikin dangi, Kajini da kyau na kashe zancen nan bakai ba auren Meenal in auren kake so ka duba a cikin Dangi ko a waje zamu aura maka ko wacece" Tana gama fad'in hakan ta mik'e fuuuu ta fice bata k'ara sauren mai zaice ba, Hannuwan shi ya hada alamun roko da jan gwuiwa ya k'ara gaban Malam Sulaiman, "Abba dan Allah kasa baki wallahi ina son ta please 🙏 " "Salman kana magana ne akan abunda kasan bazai yuwuba dan nidai bazan iya tunkarar kowa da maganar nan ba, zaifi kyau idan kaima kaji zance Mahaifiyar ka ka hakura ka nemo wata can daban ba Meenal ba mu kuma zamu tsaya muga mun aura maka ita" Shima tashi yayi ya shige ciki yabar din shi kad'ai a falon sai uwar zufan tashin hankali yake had'awa, akwai matsala fa gaskiya dan bayajin zaiyi saurin sarewa dole zaici gaba da gwada sa'an shi har su saurare shi in kuma basu saurare shiba shida kanshi zaije ya gabatar da kanshi a gaban Malam. Tunda Meenal da Sultana suka koma gidan Hajiya sai ya zamana zuwa unguwar Malamai ya musu wahala dan hankalin Meenal yana kan surprise din da suke son hadama Meelat dan haka ko a tudun wadan ma ba zama sukeyi sosai ba, Kuma tun dawowar su ko sau d'aya meenal tak'i yarda ta tsaya suyi magana da Hajiya akan AK dan da zarar Hajiya ta d'auko zancen ita kuma zata tsareta da cewa ai ita Hajiyar tayi alkawarin cewa wannan karan bazata yarda ayi mata aure irin wanda aka mata a baya ba dan haka su kyaleta ita ba yanzun zatayi aure ba, ko dan Hajiya taga AK jikan ta shi yasa take so ta matsa mata, To ai itama jikar Hajiyar ne bai kamata kuma ta nuna banbanci ba, Ita dai Hajiya ta kyaleta ne kawai amma tuni ta riga ta yanke hukunci suna gama hidimar bikin nan na Musty ita da kanta zata nemi Adamu akan maganar dan babu ruwan ta da Malam Almu. Misalin k'arfe 3 na rana ya iso garin na ZARIA, Yana mai d'aukin dawowa dan yayi tozali da muradin zuciyar shi, bai shaida ma kowa cewa yana hanya ba dan yasan idan tasan zaizo ba abun mamaki bane ta gudu ta koma Unguwar Malamai, Sai dai dole murnar shi ta koma ciki a sanda ya iso gidan Hajiya ke shaida mishi cewa ai basa gida sun daiyi mata sallama akan zasuje Makaranta, Sabon wanka yayi bayan da yaci abincin da Hajiya ta shirya mishi kananun kaya ya sanya, Kai jama'a wallahi AK bayaji indai wajen iya d'aukar wanka ne koba dan Allah ba idan yayi wani wankan dole ka tsaya ka kalle shi,wankan na yau k'ananun kaya ne bak'ak'e ya sanya dogon wandon crazy jeans sai vest daya sanya a ciki mai fad'i dan sam bata kama jikin shiba ya d'auko wata jacket itama bak'a crazy wacce duk akabi jikinta aka Yayyan ka ta saboda tsabar iya shege tun daga gangar jikin rigar har hannayen duka Anbi an yayyanka sai tsintsiyar hannun ne kawai wajen inda aka makala botura sune ba'a yanka wajen ba, Bandana bak'i ya d'aura akai haka ma a tsintsiyar hannun shi guda wanda ya nad'e hannun rigar zuwa sama suma sai ya sanya agogo da wasu yan hannu na gayu wanda maza ke sawa, Takalmin kafar shi ko irin 👢 boot din nan ne mai tarin igiyoyi shima baki, bak'in glass ya sanya ya toshe idanuwan shi dasu bayan ya gama yima jiki shi wankan turare ya fito daga Sashen, A farfajiyar gidan suka had'e da hajiya wacce ta fito itama wajen Dada Turai kakar billyn ya sa'eed take son zuwa, Harta gifta shi ta dawo daga baya tana tafa hannu wa, "Kai Abdul me nike shirin gani haka wannan shigar da kayi kuma irin ta d'iyan anna ina kake shirin zuwa ni Aminatu? Wannan ai kirama kai tsiya ne wallahi ka rasa suturar sawa sai wannan shegiyar riga ko ina a yayyage kamar wani sabon mahaukaci, fisabilillahi wa zai kalleka in bacin wannan tabon sallan dake goshin kaba ai sai ace k'atoton Anne ne kai wallahi, Ji takalmin da kasa ka tamke k'afa wannan kafin ka cire kace zakayi alwallah an liman ya idar da sallah tuni, Ni ko ina ce kwanaki naga duk ka zubar da wannan shigar naka na banza ka koma shigar hausawa sak, To yau kuma watan iya shege ne ya tsaya daga dawowan ka ka shiga ka cire suturar mutane kawai kayo shiga irin ta annan legos ka fito a haka zaka fita gari kana yawo a dunga nuna ka da baki ana cewa ai jikan prof ne," "Hajiya Birthday din friend dina zani fa taya zan je wajen da kananun kaya? Nidai kiyi hakuri sai na dawo" "Muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam yanzun a haka kake son in shige maka gaba a baka auren jikata kana Wannan shigar anya kuwa Abdul Khareem" Bai saurare ta ba ya shige motar shi yabarta a wajen tana faman surutai daga karshe fasa fita tayi ta wuce wajen jummai kai karan AK din. Shiko tun a hanya ya kira Sultana ya tambayeta suna ina ne ita kuma ta shaida mishi inda suke, Makarantar ba bak'on shi bane dan haka baisha wahalar gano inda suke ba, A can wani cafeteria suke ita da su Maryam da alamar sun gama tattauna wa ne suka isa wajen dan cin abinci, A kujerar da suke zaune ita da wani abokin su ne tana k'ara jaddada mishi abubuwan da take buk'ata, Sultana ce ta fara hango shi dan haka sai tayi ma su Maryam signal akan subar wajen, zare jikin su sukayi suka koma can gefe ita kuma tana duk'e ne sai faman list na abubuwa take rubutawa, Yana K'arasowa da Sallama yaja kujera guda d'aya a gefe ya ajiye a gefen ta ya zauna yana binta da mayen kallo, Muryar shi da kuma kamshin turaren shi data shaqa ne yasa ta d'ago kai babu shiri, Idanuwan sune suka fad'a cikin na juna sai ko ya wani d'age mata girar shi guda d'aya, K'asa sosai ta amsa sallamar ta maida kanta k'asa sai dai kuma ta gagara ci gaba da rubutun saboda yanda idanuwan shi ke yawo a jikin ta, Gayen dake zaune a gefe ne bayan ya amsa sallamar AK din yake tambayar shi da cewa, "Malam lafiya? Ko akwai wani abun da zamu taimaka maka dashi ne?" Wani irin kallo AK ya jefe mishi kafin a dake da jefa mishi tambaya da cewa, "Waye Kai?" "Ah ah ya zaka zo waje ka samu sannan ka kama tambaya na waye ni, ai sai dai ni in tambaye ka ko waye kai daka zo ka zauna a inda muke ba tareda izini ba" "Oh haka ne fa, na zauna ban tambayi izini ba koh? Koda yake ai babu buk'atar masoyi ya tambayi masoyiyar shi izinin zama a inda take, koba haka ba Soulmate?" Bata dago ba ta amsa da cewa, "Ina ganin ai mun kammala lissafin komai na buk'ata zaka iya tafiya yanzun dan muma wuce wa zamuyi" Ta fadi hakan tana mik'a ma gayen takardar data gama rubutu a ciki yanzun, Shima baija zancen da tsaho ba ya amshi paper din ya mik'e ya isa can inda su Maryam suke, ya rage daga ita sai AK a zaune a wajen. "Soulmate ba gaisuwa ko baki farin ciki da zuwana bane? Kinga niko tunda na iso na kasa jure rashin ganin ki shi yasa na biyoki nan. *UMMIEE ce*✍🏼 [9/15, 8:39 AM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 28* Ina yini" Ta fad'a a sanyaye tana d'an satar kallon gefen dasu Maryam suke, sai dai ga mamakin ta sai taga kusan gaba d'aya yan matan dake wajen hankalin su ya karkata ne akan kallon AK, Ita wallahi dama tasan za'ayi haka, wai mema ya sashi biyota har makaranta ne? "Lafiya lau Dr ya kike, ya school d'in naku?" "School Alhamdulillah barka da zuwa ya hanya?" "Alhamdulillah na iso lafiya, hanya kuma yana can mun baro musu, Me kuke shiryawa ne haka naga kina tayin dogon list?" "Surprise zamuyi ma amaryar ku, abubuwan da muke buk'ata na program din da muka shirya zamuyi anan cikin school ne nike rubutawa saboda karmu mance da wasu abubuwan, Me za'a kawo maka ?" "Ni bana buk'atar komai naci anan wajen balle kuma kafin in fito ma sai da Hajiya ta bani abinci naci, ke kawai nazo gani dan bazan iya jira har sai kin koma gida kafin in samu damar kallon wannan kyakyawar fuskar taki ba tashi muje wajen nan babu dad'in zama sam!" Ya fad'a a yayinda ya kai yatsar shi ya lakaci gefen kuma tun ta, "Ina zamu kuma?" "Kaiki zanyi in siyar dake" "To ni ai nazo cin abinci ne anan yunwa fa nike ji!" "Naga alaman hakan shi yasa nake son in kaiki inda zakici abincin a tsanake ba nan wajen da yake da hayaniyar mutane da yawa ba, Yama zaki zauna cin abinci anan bayan ga maza nan da yawa duk sai kallon ki sukeyi, Baki san hakan yana da had'ari ba ai baima dace ki zauna kina tauna abinci a bakin ki maza na kallon yanda bakin naki ke taunar abincin ba dan ba kowa bane yake da tsarkakakkiyar zuciya ba, kenan haka kike zuwa nan kullum da sunan cin abinci? " K'asa yayi da murya sosai ta yanda bai zama lallai taji mai zaiceba kafin ya k'arasa maganar shi da cewa, "Yarinya baki san wani jarababben daga kallon yanayin yanda bakin ki ke motsi ma kad'ai yana iya samun gamsuwa ba" "Na'am me kace?" "Cewa nayi kenan kullum anan kuke zuwa cin abinci?" "Ah ah ba kullum ba lokaci lokaci dai" "To na kashe zuwa wajen nan da sunan cin abinci daga yau, Bazan hanaki kizo kiyi take away ba amma dai ban yarda kizo ki zauna kici anan d'inba kinji na fad'a miki" "To saboda me zaka ce haka ai bani kad'ai nike zuwa ba, in ma kallo ne ba gashi nan ba kaima daga zuwan ka duk kabi ka d'auke hankalin yan matan wajen kalle su ka gani fa dukan su idanuwan su akanka yake ni ban san ma mi yasa ka biyoni nan ba" Ta fad'a tana juya idanuwan ta gefe da gefe harda wani tura baki, "Koma ke da waye ni dai ina rokon alfarma kiji tausayina ki rufamin asiri ki dena zaman cin abinci a wajen nan, Nifa inda hali ma gara ki dunga zuwa da abinci daga gida kinga nifa in abun ya zama haka zan ma Hajiya magana ta d'auki wata sabuwar mai aikin da zata dunga tashi da sassafe tana had'a miki abincin da zaki dunga zuwa dashi makaranta tunda naga aikin yana son yama Aunty Larai yawa amma bazan yarda kici gaba da zuwa irin wajen nan cin abinci ba nagode Allah ma kun kusa kammala karatun madai mutum ya huta " Yana karasa fad'in hakan ya mik'e ta bayan kujeran ta ya koma ya tsaya kafin ya sanya hannayen shi yaja kujerar da take kai din a zaune baya, Zabura tayi ta mik'e tsaye daga zaunen da take dan tasan dan k'ank'ani ne cikin aiyukan da zai iya aikata wa wato yace zai kama kafadar ta ya mik'ar da ita tsaye ko kuma dai wani abun makamancin hakan, "Ina zaka kaini to? Nidai ban zuwa ko ina gida kawai zan tafi😒" "Ni kuma nace ba gida ba wani waje zaki rakani" Jakarta ya mik'a hannu zai d'auka tayi saurin d'auke Jakar ta rataya a kafad'a, "Ok muje to tunda bazaki bari in rik'e miki Jakar ba" Karasawa inda su Maryam suke sukayi, Sultana ce ta fara gaishe shi da cewa, "barka da zuwa Brother ya hanya?" "Alhamdulillah Sultana ya kike?" "Ina lafiya! " Ganin haka yasa sauran yan matan dake wajen suma suka dunga tasowa suna mik'o gaisuwa bai damuba haka yaci gaba da amsa musu sai dai tsaf yake lura da yanda yanayin fuskar Meenal ya canza dan haka sai kawai ya waske da cema Sultana d'in idan ta gama abinda takeyi tazo su tafi, "Ah ah Brother kuje kawai nida Maryam zamu wuce unguwar Malamai ne daga nan zamuyi amfani da motar Meenal din kai sai ka wuce da ita" "Alright to ba damuwa sai kun dawo muje koh! "Nidai dan Allah ka tafi nima zan bisu muje can din tare kaji" "Ai kinji abinda Sultana tace dan haka kodai ki taka mu tafi ko kuma in nad'e hannun rigana in miki irin d'aukar da akema Jarirai, wai bana ce miki saboda ke na shigo cikin school din nan yauba, to wallahi in ma bakya so su kawayen naki su gane alaqar dake tsakanin mune gara tun wuri ki bini mu tafi salin alin sab'anin hakan kuma bazan bar nan ba har sai na tabbatar da nabar musu labari mai armashin da zasu dad'e suna tattaunawa akai kafin in tafi," Bata da wani zab'i wanda ya wuce ta bishi d'in, Dan haka badan taso ba haka su Sultana suka musu rakiya har zuwa inda yayi parking motar shi, shi da kanshi ya bud'e mata gidan gaba ta zauna kafin ya zagaya ta gefen driver yaja motar suka fice daga cikin school din. Maryam da Sultana dake tsaye a wajen har yanzun sun juya da niyyar komawa dan akwai sak'on da Maryam zata amsa kafin su wuce juyawar da Maryam tayi idonta ya sauka akan Bash jingine da motar dake gefen su kad'an hannuwan shi rungume a k'irji idanuwan shi kyar a kansu, Basarwa taso tayi ta nuna kamar bata ganshi ba sai dai kuma shi d'in duk da halin shock d'in da yake ciki na ganin Meenal hakan bai hana shi kiran sunan ta ba domin koba komai yana buk'atar tabbatar wa akan abunda idanuwan shi suka gano mishi, "Maryam" Ya kira sunan yana takowa da d'an sauran karfin daya rage mishi zuwa inda take, Bata iya amsawa ba har ya cin musu, "Maryam fad'amin dagaske Meenal ne idanuwa na suka gane min ko wata daban? Meenal na gani yanzun nan fa tare da wannan yayan nasu me nene ma sunan da ake kiran shi dashi? Uhmm uhmm mai jama'a, eh mai jama'a shifa, wallahi da idona na gansu yanzun nan ya bud'e mata murfin mota bayan ta shiga shi kuma ya shiga gefen direba yaja motar suka tafi, Mai yake faruwa ne? Dama shine mijin da aka aura mata ko ya abin yake shin ko dai gizo ne ko kuma mai Kama da ita na gani? Fadamin dan Allah kicemin ba ita bace mai kama da ita na gani ayau, inba haka ba mai zaisa inga Meenal anan bayan an tabbatar min da cewa wani d'an uwanta soja aka aura mata kuma ba anan zasu zauna ba?miye had'inta da mai jama'a kuma? " Juyawa tayi bayan ta damk'o hannun Sultana da niyyar subar wajen ganin yana shirin janyo hankalin mutane kan su, Da sauri yasha gaban su yana had'a hannuwan shi, "Please Maryam dan Allah ki tsaya kibani amsar tambayoyi na kaina ya d'aure da yawa, Meenal fa idanuwa na suka gane min bayan tsayin shekarun dana d'auka ban sata a cikin kwayar idona ba" Sultana ce ta katse shi da cewa, "Da kata dan Allah bawan Allah ya zaka zo ka taremu a hanya cikin mutane haka, duba kaga yanda kasa jama'a ke kallon mu in ma maganar da kake son yi da ita ya zama dole ai ba anan ya kamata ka tsareta da tambayoyin ka ba sai dai bari ni in sauk'ak'a mata wasu rud'anin da kake ciki a yanzun, Eh ita Meenal din dai ita ka gani sun fita tare da mijin da zata aura a yanzun duk yanda akayi alamu sun nuna cewa kana cikin samarin ta da aka kasa a shekarun baya, to ko yanzun din ma bana tunanin zaka samu galaba ko nasara a kanta domin kamar yanda wancan karan d'an uwanta ne yayi nasara a kanka wannan karan ma hakan ce zata k'ara faruwa dan haka gara ka shafama kanka lafiya Kaje kaci gaba da zama da yar matar ka ina ga hakan zaifi, Meenal ba rabon ka bace shi yasa take ta kucce maka, Maryam idan kin gama abinda kikeyi muna iya tafiya." Kusan sumewa yayi a tsaye bai iya motsawa ba har suka kule ya dena ganin su, "Ke wai waye wancan d'in?" Sultana ta tambaya, "Bash ne bash din da nace muku mun had'u dashi s kofar doka shine tsohon saurayin Meenal kafin auren ta da Sarki, Ban san meya shigo yi cikin makarantar nan yauba gashi duk addu'ar da mukeyi na kar Allah yasa ya bayyana to yau dai gashi ya ganta, na kuma tabbatar da cewa wallahi sai ya nemo ta" "Bash.... " Sultana ta maimaita sunan tana jin jina kai, "To ai ya riga ya makaro ko yanzun muke da nasara akan duk ma wanda zai bayyana bayan shi, Domin dai koda bata riga ta furta ma AK cewa itama tana son shiba ina tabbatar miki da cewa akwai son shi a cikin zuciyar ta dan haka kowa ya iya allon sa ya wanke🤷🏻‍♀️" Basu b'ata lokaci mai tsayi a makarantar ba suna amsan abunda Maryam zata amsa suka bar makarantar, kamar yanda shima Bash yabar makarantar ba tareda yayi abinda ya kawo shi ba, dan ganin daya ma Meenal yasa komai ya kwance mishi, Tsayin shekarun nan yayi hakuri da sonta ne kawai tun daga ranar da akace an d'aura mata aure da wanin shi, Ba k'aramin gwagwar maya yayi tsakanin shi da zuciyar shi kafin ya samu damar mai da son Meenal din can k'asar zuciyar shi ya nemi waje ya birne son nata a ciki ba, Yasa wuya yasha jinya yasha fama har sai da yayi jinya na watan ni saboda yanda batun auren ta ya mishi mugun bugun da dole ya kaishi k'asa war was, Yaci buri akan ta burin auren ta wanda a wancan lokacin shine buri mafi girman da yake kwana ya kuma tashi dashi a cikin zuciyar shi, sai gashi kwatsam wai bai tashi jin cewa ita d'in za'a d'aurama aure da wani ba har sai ranar d'aurin auren, Da badan yana da tabbacin cewa ita ma kanta bata da masaniya ba toda tabbas zaice babu namijin da aka ma mummunar yaudara irin shi, Saurayin daya riski labarin auren budurwar shi a yayinda ya shirya zuwa wajen d'aurin auren a matsayin zashi auren kannen ta, Kai shifa wallahi bai taba jin labarin soyayya irin nashi ba. Bayan fitar AK ba dadewa Ya Sa'eed ya isa gidan Hajiya, Bayan sun gaisa ne yake ce mata, "Hajiya akwai sak'on da Sarki ya wakilta ni in ba takwarar ki, Sai dai halinta dana sani shi yasa nace gara in fara zuwa wajen ki muyi shawara kafin in gabatar mata da sakon, nasan ke zakifi ni sanin yanda zan shawo kanta!" "Too sak'o kuma?" Gyara zama yayi kafin ya d'aura da cewa, "Hajiya nasan kin san burukan da Meenal take dasu a rayuwarta, Zuwa yanzun Alhamdulillah zamu iya cewa biyu daga ciki sun cika to cikon na ukun ne shi yake son cika mata, Gidan data tashi da burin ta ginama Baba Malam ne shi Sarki ya siya da sunan ta, Babu wanda yasan da batun siyan gidan daga shi saini daya damka ma amana saboda baya son kowa yasan cewa shi ne ya siya gidan, sai kuma ke da yanzun nike fad'amawa, Na fara zuwa wajen kine dan nasan ke zaki san dubarar da zamuyi wajen ganin Meenal ta amsa dan nasan halin ta tana iya cewa bazata amsa ba dan tuntuni take tarin kud'ad'e saboda ta siya filin da zata gina gidan. *UMMIEE* [9/15, 10:36 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 29* Babbar magana! Ashe dai yaron nan d'an kwarai ne kawai rik'on sakainar kashin da yayi ma auren su ne ya hanani gano kyawawan halayen she, to wai dama can haka yake da hannun kyauta amma ni ya wofantar dani ko kodai yanzun ne ya canza? Allahu akbar in ba d'an daya gaji arziki tsiya na kwance kwancin kwana ba wani mijin ne zai dunga bin macen daya saka da alkhairi kashi da kashi a jejjere irin haka? Kaga fa dank'areriyar k'atuwar motar daya bata a ranar daya kawo mata takardar freedom d'inta,wanda nasan wannan toshiyar baki ne bayan shi ga kuma wasu miliyoyi daga zuba mata a k'atuwar envelop su wad'annan dai tuni na canza su na tura can Saudiya wajen matar kawunta suka siya mata zinare suna can banki na kai ajiya, Shine kuma bai gaji ba yanzun ya biyota da wani alkhairin har gida, kai yasa wannan abu dai wallahi dan an riga anyi an gama ne amma da koni ina iya yin tsaye a maida mishi matar shi,kaga shi yasafa ake cewa gaggawa aikin shed'an, To aikin shed'an ne mana inba haka ba dubi kaga tsayin shekarun da sukayi da aure amma duk bai iya kyauta ta mata irin haka ba balle nima in gani in yaba, Inda hakan yakeyi tun farko ai da tuni kila sunyi haihuwa uku ko hudu kamar dai ku da kukayi auren tare dasu, ko yanzun ma kuma bazan mishi bak'in ciki ba wallahi tunda shima baiji bak'in ciki ba yake ta hidima da takwarata ubangiji Allah dai ya saka mishi da aljannah mafificiya Allah kuma ya bashi damar yin wani auren dan inbai k'ara aure ba tofa sam bai more rayuwa ba wallahi dan dai waccen shegiyar matar tashi Allah na tuba tooo Allah dai ya shirye ta in tana da rabo a aljannah kaga ko a ciki da falo ta zauna kasan ko ciki da falo a aljannah ai tayi girman Kaduna state da kewayen ta badan halin taba, Badai zan mishi baki ba amma dai zanje har gida inba ita uwar shi shawara ta k'ara dubawa tacan gefen ta ta nemo mishi wata matar tunda abun ya zama haka, ga dai ku da kanne mata a gida amma nasan ubanku bazai yarda ya k'ara bashi wata yar da sunan aure ba nikuma kaga duka jikokina basa kusa ai da na mishi had'i da wata ko za'a dace ko nima ba sai inyi ta dangwalan arziki ba! , Kai koh anyi kyautar gida da mota mai ya rage, next agenda kuma ai sai dai kaji anyi kyautar kujerar makka ina fad'a maka wallahi" Sosai fa Hajiya ta zage tana ta faman zugagama Sarki ruwan addu'a da sanya albarkha, duk ta mance komai da suka faru a baya alkhairin shi a yanzun duk ya goge komai. Shidai Sa'eed tunda Hajiya ta fara rattafo zantukan ta dariyar ta kawai yakeyi k'asa kasa, shi din ba bak'on ta bane yasan halin ta ciki da bai, "Hajiya to yanzun ya za'ayi?" "Ya za'ayi kuwa d'an nan wannan kyautar ai tunda har ta shigo gidan nan kuma ai bata fita wallahi, Dafari dai ka fara bani takardun in tabbatar na jimk'e su a hannu na tukun dan gara in jisu a tafin hannu na ta yanda ko addu'a na sun isa sama nasan bazasu dawo k'asa ba, Maganar Meenal kuma kadai ce amana shi Sarki ya baka baka son kowa ya sani koh?" "Kwarai Hajiya saboda ya yarda dani shi yasa ya damk'a min amanar komai a hannuna dan ko k'anin shi da suka fito ciki d'aya bai yarda yasan da batun siyan gidan ba saboda baya son maganar ta fita ta koma kunnuwan dangi" "Ya kyauta kuma nima ina mai tabbatar maka da cewa zancen nan zai tabbata ne a tsakanin ni da kai sai kuma ita mai gidan da zan shaida mata gaskiyar cewa Sarkin ne ya siya mata gidan daga baya, Yanzun abunda za'ayi kasan dama nace maka kayan d'akin ta da kud'in dashi Sarkin ya bata sune na siya mata gwala gwakai koh? To idan tazo zan damk'a mata takardun nan a matsayin cewa da wancan kudin ne nayi amfani aka siya mata gidan, Kaga daga baya idan ta gabatar ma da Malam gidan sai a fad'a mata gaskiya nasan zuwa lokacin in taji gaskiya ba zatayi bori sosai ba, amma yanzun in har aka ce mata Sarki ne ya siya gidan kachokan ba lallai nema ta amsa ba dan wani zubin itama tana tab'a bak'in hali na gado atoh" "Eh kuma fa Hajiya kema kina da gaskiya, in haka ne ai gara in yi saurin barin nan d'in kafin ta dawo da dai naso in jirata dan akwai maganar da nike son yi da ita?" Takardar ya mik'a mata ita kuma tasa hannu biyu ta amsa da bismillah, "Allahu Akbar kabiran Allah mai maida Sarki bawa, bafade kuma ya zamo sarki yau dai gani rik'e da takardar gidan takwara ta a hannu na, ko ya zatayi idan taga takardar nan, Amma fa Sa'eed wannan harkar naku akwai son kai a ciki, Banbanci zallah ake nuna min ganin idona, Wato yar nan dai tun tashin ta duka burin ta na duniya akan Malam almu ya k'are ni kuma ko oho, da alama dai mantawa takeyi cewa ni dai nice na haifi uwarta Yar banza kullum kuma nan take zuwa tana amshe min yan kud'ad'en da d'iyana suke bani na kashewa, zata zo ai yau dai duk tsiyar ta sai ta bani tukwuici wallahi kafin in bata takardar nan nima," "Kwarai ina bayan ki Hajiyar mu dan tabbas kin cancanci tukuici mai girma wannan karon, kinga idan ta baki nima sai ki fincino min kad'an kaga ciki insamu nasa mai a mota" "Kai tafi can wani rashin tsoron Allah ne zai sa in baka kud'ina kuda kud'i basa isan ku iyaye sun tara muku amma kuma kun kasa hak'ura kullum cikin neman su kuke in anyi magana kuce wai kogi baya k'in k'ari, To ai sai kuyi ta faman tara su a account sai kun mutu a kasa lissafi wasu kudin ma baza'a tab'a sanin inda kuka kai kuka boyeba, yanzun dai jirani in kawo maka sak'o ka kaima jikokina a toh," Da kanta ta ciccib'a ta mik'e ta nufi kitchen d'inta bata fito ba sai data shak'o k'atuwar leda taf da kayan kwalam da mak'ulashen da Meenal takeyi ta ajiye musu. "To gashi kuma ban yarda ka bud'e ba nima amana na baka atoh karma kace ban fad'a maka ba, Amma dai tunda kazo gara ka jira dawowar nata dan nasan ta kusa dawowa tunda kaga yamma tayi, Kaga na tuna kuwa, nace injin dai shi Baban naku bai riga ya fara amsa tayin mutane akan ta ba?" "Wa kike magana Hajiya?" Shima ya tambaya dan bai gane kan maganar nata ba, "Ina nufin manema auren ta mana!, dan kasan halin uban nan naku kar azo ni ina nan zaune da yarinya a gabana azo a k'ara mai maita min abunda ya faru sai aure ya rage kwana kad'an azo a shaida min" "Anya kuwa gaskiya da wuya dai, Na daiji ana maganar su Fauxieyerh da sauran yaran amma banji an ambaci sunan ta ba, Sai dai kuma koni ta nan gefe na akwai mutum biyu da suka min magana a kanta, yana daga cikin dalilin ma da yasa nike son yin zama da ita, saboda dukan su suna son gabatar da kansu a gaban Malam nine na dakatar dasu saboda nasan in sunje shi zai sasu a sahun mane ma ne, Amma in suka fara gabatar da kansu a wajen ta kinga ita zata tantance da kanta zata zab'arma kanta wanda ya cancanta," "Babbar magana wannan shine ake cewa ana wata ga wata! Kungani koh, ai dama nasan za'ayi hakan shi yasa nike ta son ganin ta mai da hankali ta tsayar da tsayayye dan nasan mai hali baya fasa halin shi, To ai ba iya gefen ka ni kaina nan ina da tsayayye gangariya anan gefe na sai dai ita kuma yar tutsun ne har yanzun ban gane ina ta dosa ba, Abinda za'ayi yanzun su biyun nan da kace, Nan dai zaka fara turosu suzo su gabatar da kansu a wajen ta, saboda wani dalili nawa, sannan karka yarda koda wasa ka bari zancen neman da suke mata ya isa kunnen Malam zanfi so zancen ya tsaya a iya nan," Hajiya sun dad'e suna tattaunawa da Sa'eed duka maganar kuma akan Meenal ne da samarin da suka fara kunno mata kai dan ta gefen Sa'eed din dai mutum biyun da yake magana dukan su yan uwanta ne, Aliyu yaron Maman kano ne shike bin Abubakar tsohon saurayin Raheenat a Yola yake aiki zuwa gaisuwar nan na mutuwar mijin Raheenat ne yaga Meenal d'in, Sai kuma Hashim shi kuma yaron yayan innar yara ne in baku manta ba a baya na fad'a muku cewa duka matan malam biyu auren zumunci ne dan haka suma Hashim da Aliyu dai dukan su yan uwan Meenal ne na kusa, Su kuma abinda yasa suka fara tunkarar Sa'eed da zancen son auren Meenal din saboda shiri da sukaga yana yi da Meenal din sosai shi yasa suke son suyi kamun k'afa, Hajiya ta dade zaune tana cigaba da nazarin yanda zata bullo ma al'amarin nan bayan fitar da Sa'eed yayi zuwa gidan su Billy, Duka dai wadanda Sa'eed ya gabatar mata yan uwan Meenal din ne na jini kuma dukan su biyun a cikin su babu na yarwa, To su biyu gashi sun fara bayyana tun yanzun a hakan ma iya su ta sani bata sani ba ko a gefen iyayen ta maza wasu ma sun kai nasu k'ok'on baran akan su ko yaran su, Idan fa tasa ido tabbas abubuwa zasu lalace ne zuwa gaba kad'an, kuma dai ai duk dad'in inuwar gemu bai kaiga mak'ogoro ba, Dan haka zatayi amfanin da wannan damar na zuwan da su Baba Usman zasuyi bikin Musty gara su tura su kawai suje su nemo ma AK auren Meenal din a wajen iyayen ta maza kafin abubuwan su cab'e dan tasan har wad'ancan suka gabatar da kansu tofa shi malam nashi yan uwan zai d'auka ita nata jikan ko oho🤷🏻‍♀️" A gefen AK ko duk yanda yaso yaga Meenal ta saki jiki dashi abun ya faskara, dan tunda ta shiga motar duk surutan da ya saki baki yanayi bata wani amsa shi daga umh sai umm umm sune amsar da take bashi, Dan itafa gaba d'aya a takure take saboda ita sam bata saba irin wannan rayuwar a tsakanin su ba, Ita dashi sun saba kullum ne da zarar sun had'u fad'ane abunda yafi yawa a cikin hirar su, yau kuma ya d'auko ta yana ta faman yawo da ita ta ina zata sake fisabilillahi ga wani Mayan kallo mai kashe jiki da yake binta dashi dan haka ba k'aramin takura tayi da zamar motar ba, "Ya'ya dan Allah nidai muje gida, Allah bana ma jin yunwar a yanzun idan munje gida zanci a can" Ta fad'a ganin yana shirin yin parking a kofar wani k'aton restaurant, "Karki damu ba shiga ciki zamuyi ba zanyo miki take away ne sai mu wuce gidan, ai na fasa zuwa sai dake d'in kuma dan haka ki kwantar da hankakin ki Dr zamu rayu a tare har tsufa insha Allah, Yanzun fad'amin mai kike son ci? Ko duk abinda na amso miki babu damuwa?" Ya tambaya yana kashe mata ido d'aya, Ita gaba d'aya ta rasa gane dalilin da indai suna tare bashi da halin da zaiyi magana da ita kai tsaye har sai ya had'a da d'age mata gira, Shi bai san hakan da yakeyi kunya yake bata ba gashi kuma a d'an lokacin itama ta koya ko magana sukeyi da su Sultana sai tayi ta wani d'age musu gira kamar wata yar iska, "Ka bari dan Allah! Kana sawa ina jin wani iri wallahi," Bayan shi ya maida kan kujerar motar yayi relax kafin ya bude baki murya can k'asa yana ci gaba da kallon ta yace, "Mai zan bari kuma?" Dage girar da kashe idon ta kwatanta mishi, kafin tace hakan da kakeyi, Tana k'ara d'age giraren ta, Ba kad'an ba hakan da tayi ya k'ara tsatso mata kyan daya k'ara tafiya da hankalin shi, Shidai wallahi komai tayi k'ara kyau take a idanun shi dan haka bayajin gajiya ko damuwa sam a duk sanda zai kasance tare da ita, "Kina da kyau 👌🏻" Ya fad'a yana kwatantawa da hannu, ita kuma sai tasa hannu ta rufe fuskarta saboda kunya ma ya bata wallahi, Dariya yayi kafin ya tashi ya zauna ya bud'e k'ofar motar, "Ki zauna a cikin motar karki fito fa, yanzun nan zan dawo" Da kallo ta bishi tana jin wani irin abu wanda a tsayin rayuwarta bata tab'a jin wani abu makamancin hakan idan tana tare da wani ba sai shi, Shi kad'aine namijin da idan tana tare dashi a cikin zuciyar ta takejin kamar an cire mata ko wani kalar damuwa, Nutsuwa takeji da salama a duk sanda suka kasance tare ba kuma zata iya cewa ga dalilin da yasa takejin hakan ba, amma tana jinta a yanayin da zuciyata ce kad'ai sheda akan yanda takejin bata sani ba ko hakan yana daga cikin alamun kamuwa da soyayya, in ko hakan ne sai tace akwai matsala dan itafa wallahi bata shirya ba, Sam sam sam bata shirya maida hankali akan soyayyar ko wani namiji ba, tana buk'atar isashshen lokaci kafin ta kamu da son wani, Ta sani cewa idan har tayi saken da AK yayi galaba da sauri haka a kanta tofa itace zata sha wahala, Natsuwa take fatan samu bayan aurenta bawai auren da zatayi ta gwabzawa da wasu matan akan mijin auren taba, "Ya dai tunanin me kikeyi haka ne?" Ya tambaya jin yayi mata sallama har sau uku bayan shigar shi cikin motar amma bata amsa ba, duk da idanuwan ta suna rufe yasan cewa bai isa ace daga shigar shi zuwa yanzun har tayi bacci ba, Jin shiru bata amsa bane yasa ya mik'a hannun shi duka guda biyun ya ware yatsun shi manuniya ya dannasu akan kuma tunta dai dai inda dimples dinta suka lotsa, "Auch" Ta fad'a tana ware idanuwan ta akan shi, "Ke dai raguwar likita ce wallahi kawai daga shigana shine kafin in fito har kinyi bacci, ko bakya da lafiya ne dan nasan yawon shirin bikin nan bazai barki ki zauna ki huta ma ranki ba" Sai da ta gyara zaman ta kafin ta amsa mishi a shagwab'e da cewa, "Ai tun d'azun sai da nace maka ka kaini gida kak'i" Waiyo Allah yarinyar nan wai me yasa bata neman zaman lafiya ne ita, Fisabilillahi sai ta sashi a gaba tayi ta mishi shagwaba tana kassara shi da salon ta, Wannan ma ai d'aukar alhaki ne wallahi, "Ki dena min wannan abun idan muna tare!" Ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya a jejjere, "Me nayi😳? " Ta tambaya tana zare ido, "Ba komai, zaki iya tuk'amu zuwa gida?" "Ni kuma? To ba kai ke tuk'in ba tun d'azun" "Eh nagaji ne yanzun bazan iya jan motar ba, ki daure ki mai damu gida" Bude k'ofar gefen ta tayi ta fita ta zaga zuwa driver seat shi kuma tsallakowa kawai tayi ya koma inda ta tashi ba tareda ya fita daga cikin motar ba, Ruwa mai sanyin daya shigo motar dashi ya bud'e ya kafa kai sai da yasha kusan rabi sannan ya zuba wani ruwan a cikin hannun shi ya dunga zuba su ta saman wuyan shi suna gangarewa cikin jikin shi ita ta tuk'a motar har gidan Hajiya a yayin tafiyar su ta komawa ko zaman shiru akayi a motar shi dai lafewa kawai yayi yana binta da mayun idanun shi, har sai da ta gaji ta mishi magana akan kallon yayi yawa kafin ya juya ya maida fuskar shi gefe yana kallon mutanen dake kai da kawo a titi. *Ummiee ce* [9/18, 2:40 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 30* Bayan ta faka motar a inda ya dace ta yunk'ura tana shirin bud'e k'ofar gefen ta dan ta fita a motar shi kuma yayi azamar rik'o hannun ta wanda hakan ne yasa dole ta dakata ta maida kallon ta kanshi, Girar ta d'aya ta d'age mishi tana juya yan yatsun ta alamun tambaya ba tareda bud'e bakin ta tayi ko wani furuci ba, "Saurin me kikeyi ne wai? Duk kin wani k'osa ki shige ciki ki barni ko! saboda kin gaji da ganina? " Ya fad'a batareda ya saki hannun ta daya rik'e ba, Kauda kanta gefe tayi tana basarwa, "Nace ba!" "Kace me?" Ta tambaya batareda ta kalleshi ba, "Ina son mu had'u anjima after sallan isha'i, Ok ok ina nufin zanzo hira anjima in kin bani dama please 🙏 karkice min No kinji Dr" "Hira...?"ta tambaya cike da mamaki, "Eh tad'i nike son zuwa mana ko kuma shikenan sai akace miki dan muna gida d'aya bani da daman zuwa hira wajen budurwa ta?" "Niba budurwar ka bace, ka bari har in amshi tayin soyayyar ka kafin ka kirani da suna budurwar ka"ta fad'a tana murgud'a mishi baki, "Nidai tunda har nace ina son ki ni a wajena tuni kika zama budurwar tawa dan haka idan an idar da Sallah zan nemo yaron da zan aiko ya kiramin ke ki fito muyi hira koba haka akeyi ba? Ke kuma in zaki fito sai kiyomin kwalliyar da zan yaba kafin fitowar naki koh?" "Uhumm uhmm " Sautin murmushin ta yafita a yayinda ta juyo fuskarta tana kallon shi, "Ba haka akeyi bane?" Ya k'ara tambaya yana kallonta shima fuskar shi da murmushi . "Ah ah mu a gidan mu ba haka akeyi ba," "To ai ba damuwa ki fad'amin yanda akeyi a gidan ku d'in nima sai inyi, mai nema ai baya fushi " "to mudai a gidan mu idan kaga yarinya kana sonta to iyayen ka zaka fara turawa wajen Baba Malam su tambayar maka izini daga wajen shi, Shi kuma idan yayi bincike a kanka yaga cewa ka cancanci ya baka yarshi ka aura a lokacin ne zai baka damar zuwa ku gana kaida yarinyar da kake so, bayan kun gana da ita ne za'ayi batun sa ranar aure dan mu gidan mu ba'a d'aukar lokaci ana jeka ka dawo kafin d'aurin aure! Kai kuma duk kabi wad'annan dokokin ka takesu ka wuce " "Oh my God ashe ma abun sauk'ine dashi har haka ban sani ba! To indai haka ne ni ai ta kwana min a gidan sauk'i tunda haka ne yau zan k'ara tuntub'ar Hajiya da maganar ta tura kawai a tambayo min d'in," ya fad'a yana bayyana jin dad'in shi dan baiyi zaton cewa abun zaizo mishi da sauk'i har haka ba, ashe daya tura manya shike nan sai dai ayi batun sa ranar d'aurin aure, "Nidai ban baka damar ka kai maganar nan gaban kowa ba, ai nace muku niba yanzun zanyi aure ba, indai kana son aurena dole sai dai ka jira har zuwa sanda zan kammala karatuna gaba d'aya, in kuma bazaka iya jira ba ka nemi wata" wai kina nufin cewa dole sai nabi wannan matakin kafin in gabatar da kaina a wajen iyayen ki? Ok na fahimta yanzun na gane kenan dai na riga na samu karb'uwa a wajen ki shi yasa kike son in gabatar da kaina a wajen su Baba Malam koh? Wow I really appreciate it Baby I really love you a lot " Ya fad'a a yayin da yakai bayan hannun ta kan bakin shi yayi kissing. Kwace hannun tayi tana yarfewa kamar wacce kiss din ya manne ma a hannun, "Nidai ka dena tab'ani bana so, kawai kai sai ka wani dunga rik'ema mutum hannu kuma ni karka k'ara gigin sumbatar hannuna daga yau bana so" Ta fad'a tana hararar shi, "Oh Baby its just a single kiss" ya fad'a batareda nuna damuwa ba shifa a wajen shi gani yake hakan ba wani abu bane duba da irin rayuwar da yake ganin wasu couple din sunayi idan suna 💏 dating shifa hannun ta kawai yayi kissing kuma bada wani manufa ba kawai dai so yake ya nuna mata son da yake mata, bai d'auka cewa hakan zai b'ata mata raiba, "Oh is just a kiss kake cewa ma? Amma dai ai kasan niba matar ka bace koh?" "But i wish ki zama matar nawa some day, Ok ok ok am sorry ban san hakan zai b'ata miki raiba,amma zan dunga kiyayewa daga yanzun" Bud'e murfin motar tayi ta fita ta wuce fuuu batareda ta k'ara kulashi ba duk da yanda takejin yana kiran sunan ta bata waigoba harta shige side d'in Hajiya Jummai wanda takejiyo hayaniyar yara a ciki tun d'azun da alama bak'i akayi a gidan tasan kuma bazai wuce Rukayya ce tazo gidan ba, "Ya rabb, badai wai har yarinyar nan tayi fushi ba? Kenan na kwafsa Tunda nayi kissing hannun ta?" Ya tambayi kanshi cike da jimami kafin yaci gaba da cewa "Oh Allah to wai ya yarinyar nan take so inyi ne? Ita bata san cewa ni ban saba da irin wannan rayuwar na tsayawa gaban mace inyi ta surutu kamar wani sakarai ba, duk k'okarin da nikeyi dan in faranta mata rai kawai nikeyi a kullum amma banga alaman hakan yana aiki a kanta ba, wai ya take so inyi ne? Neman izini wajen iyaye, Bada izinin ganawa da budurwa, Neman aure bayan sun gana tsakanin saurayi da budurwar," Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke kafin ya kwantar da kanshi a jikin kujerar motar "Kenan dai hakan yana nufin cewar ta yarda in gabatar da maganar aurena da ita a gaban iyayen ta?" Murmushin fuskar shi ya fad'ad'a, "Yarinya tunda haka kike so nima kuma hakan zan gabatar, zan tura iyayena su nemo min izinin kamar yanda kika buk'ata sai dai kuma hakan baya nufin cewa zan iya nesan ta kaina daga gareki, Bazan tab'a sararawa ba har sai kin zama mallakina," Ledojin ya kwasa ya shigar mata dasu sashen na Hajiya har sama ya haura ya bud'e d'akin ta ya ajiye mata nata kasancewar koda ya shigo bai samu kowa a falon ba shi yasa ya haura saman, dakin Hajiya ya lek'a itama bata ciki dan haka sai ya sauko da sauran ledojin a hannun shi, "Yanzun ka shigone hala? Dan muna cikin kitchen nida Larai shi yasa bamuji motsin shigowar naka ba, miye kuma wannan a cikin leda naji sai kamshi yakeyi wallahi," K'arasawa inda take yayi yana mai amsa mata da cewa, "Eh yanzun na shigo da ban ganki a faloba nayi zaton ko kina d'akine shi yasa na haura saman," Yana mik'a mata ledojin ya fice daga sashen ya k'ara shiga motar shi yabar gidan domin kamar yanda ya fad'ama Hajiya ne d'azun wajen birthday din wani Abokin shi yake son zuwa. Hira ke gudana tsakanin Meenal da Ya Sa'eed tun bayan baro warta sashen Hajiya Jummai ta shigo ta same shi a falon na Hajiya, sama ta haura a gurguje ta canza kayan jikin ta d'auko ledojin data tabbatar cewa AK ne ya ajiye mata su a d'akin ta fito itama, Baice mata komai akan maganar da yace mata yana son yi da itaba har sai da suka fito zai tafi bayan ya shiga cikin motar shi ya zauna ne kuma ya bata umarnin cewa ta shigo motar suyi magana, Bata musa ba ta shiga ta zauna, "Meenal "ya kira sunan ta yana maida hankalin shi gaba d'aya a kanta alamun dake mata nuni da cewa koma mene zai fito daga bakin shi yana da mahimmancin da yake buk'atar ta bashi hankalin ta yayin tattaunawar nasu, Babu abinda gabanta yakeyi sai fad'uwa dan bata saba ganin kamewar fuska daga wajen Yayan nasu ba domin dai shida ita kullum cikin wasa da dariya suke, yanda yaga tana ta faman binshi da kallo ta kasa amsa sunan nata daya kirane kuma hakan ya sashi k'ara kiran sunan a karo na biyu, "Meenal! " "Na'am ta amsa dashi gabanta yana ci gaba da fad'uwa, "Meenal kin san nayi miki magana akan cewa akwai maganar da nike so mu tattauna dake koh?" Baijira jin amsa daga gareta ba ya d'aura da cewa, "Wannan maganar ne yasa yau na baro duk abubuwan dake gabana nazo nan dan in samu damar yin magana dake" "To Ya'ya ina jinka allah yasa dai ba wani laifin nayi maka ba?" girgiza kanshi yayi kafin ya amsa da cewa, "Bakimin laifin komai ba zuwa nayi dai domin mu tattauna akan abunda ya shafi rayuwar ki, Meenal ke yanzun ba k'aramar yarinya bace kin riga kinyi girman da zuwa yanzun ya kamata ace kin san duk wani abunda yayi dai dai da tsarin rayuwar ki ba sai wani ya sanyaki a hanya ba domin duk wani hankalin da yakamata ace d'iya mace mai adadin shekarun ki ta mallaka kema kin mallake shi, Abunda nike so in miki nuni akan shi shine, Karkiyi tunanin cewa wai dan kinyi auren farko Allah bai had'a zuciyoyin ku keda mijin naki kun gudanar da zaman auren yanda ya dacr ba kiyi zaton cewa sauran maza suma haka suke nuna rashin kulawar su akan matan da suke aure! Ah ah ina sone ki gane cewa tun farko Allah ya nufa cewa zaman da zakuyi a matsayin miji da mata takaitaccen ne shi yasa duk abinda ya faru ya faru, Yanzun kuma da kuka rabu hakan bazai zama dalili a wajen ki ta yanda zaki tauye kanki ki hana wasu mazan tun karar ki da batun neman soyayya a wajen kiba , ko kuma ke ki k'untata kanki wajen hana taki zuciyar bata damar samun kusanci da wani a cikin su, A sanda kika bud'e zuciyar ki ma wani namijin ne kad'ai zaki gane abinda zuciyar ki take so dama wanda bata so, Karki yarda ki k'untata kanki ki kuma tauye masoyan ki wajen hanasu tunkaro ki,domin bazai yuwu ki cigaba da zama haka babu aure ba Kin sani koda ace iyayen mu basa raye mu yayyen ku maza zamuyi tsayuwar daka akan ku domin muga mun cigaba da kula da tarbiyar ku, abinda nike son ki gane anan shine bazai yuwu mucigaba da zuba miki ido kice zaki zauna haka babu aure ba domin hakan yana iya tab'a daraja dama mutuncin ki wanda ba iya kanki abun zai tsaya ba harmu makusan tanki abun zai shafa, Zuwana yau nazo ne saboda in baki shawara Meenal karki yarda kiyi sakaci ta yanda abinda ya faru dake a shekarun baya zai k'ara maimaita kanshi a yanzun, Domin dai yanzun haka maganar nan da mukeyi dake ina mai tabbatar miki da cewa akwai wad'anda suka fara kai maganar son auren ki wajen Baba Malam bayan su kuma nima haka akwai mutum biyu da suka gabatar min da kansu a matsayin suna son in shige musu gaba wajen kai maganar su wajen iyayen mu, a zahiri gaskiya kuma dukan su babu wanda bazanyi farin cikin ace ya zama mijin auren kiba, Sai dai kuma ko kad'an bana fatan a k'ara tauyeki wajen yi miki auren da baki shirya ma zuwan shiba ko kuma a zab'ar miki mijin da baiyi dai dai da zab'in zuciyar ki ba, Nasan a hakan kuma kema baza'a rasa masu tunkarar ki da batun soyayya ba, dan haka kece zakiyi ma kanki yak'i kiba zuciyar ki damar tantace mijin da kike son ki rayu dashi ni kuma zan shige miki gaba wajen gabatar dashi, Naba Aliyu da Ya Hashim number d'inki na kuma basu harda address din nan gidan domin su gabatar da kansu a gareki, Dukan su yan uwanki ne na jini sai dai kuma duk da kasancewar su dangin ki hakan baya nufin ki cusa ma zuciyar ki abunda bata muradi, zanso inji ra'ayin ki akan kowannen su bayan sun gabatar da kansu, in kuma kinsan cewa akwai wanda kika riga kikaba zuciyar ki zanso ki sanar dani tun yanzun ni kuma zan dakatar da zuwan su nan d'in nasan zasu fahimce ni, Karkiga har yanzun babu wanda ya tankamiki kiyi zaton ko an sa miki idone, ah ah na tabbatar da cewa shi kanshi Baba ya sa miki idone saboda ki sarara akan abinda ya faru, dan haka ina mai k'ara baki shawara gara tunda wuri ki gabatar da wanda kike so a gaban iyayen mu, ki bashi dama yaje ya gabatar da kanshi a wajen iyaye kamar yanda aka saba gudun abinda ka iya biyowa baya kin daiji na fad'a miki, ni zan wuce yanzun ki koma ciki ke kuma Na kuma ba Sultana sak'on sabbin kud'in da kikace kina buk'ata na lik'i ni zan wuce sai naji daga gareki" "Nagode Yaya insha Allah zanyi abinda kace d'in amma dan Allah ka dakatar da zuwan su Ya Aliyu da Ya Hashim gidan nan ni ban shirya ganawa da kowa a cikin suba" "Kiyi hakuri hakan bazai yuwuba dole ne suzo na riga na gama magana" "Amma Yaya.... " D'aga mata hannu yayi alamun dakatarwa, Ki wuce ciki nace tafiya zanyi aina baki dama idan basu miki ba kece zaki dakatar dasu daga kai maganar zuwa can gida bawai niba, ni shawarar da nike ganin itace zata fishsheki kawai na baki dan haka saida safe" Jiki a sanyaye ta bud'e k'ofar motar ta fita shi kuma yaja motar ya fice daga gidan, Sanyi kafafun ta sukayi dan dole ta nemi wajen zama ta zauna tana jin wani irin tashin hankali yana lullub'eta ta, Zufa kawai ke yanko mata tako ina uwa irin wacce aka tsare gaban Sarki tayi k'arya, Wani irin tashin hankali ne wannan yake shirin tunkarota kuma? Ita da take gudun masu mata shine saboda tsabar rashin mutunci su kuma wad'ancan dan suna ganin cewa su d'in suna da alaqa ta yan uwan taka da ita suke son yima rayuwarta kutse ba tareda ta shirya ba? Waiyo Allah ita, kenan da ace shi yaya sa'eed bai dakatar dasu akan tun karar malam da maganar ba kenan da tuni sun kai kansu wajen shi, Ita fisabilillahi ina ita ina k'ara wani auren zumunci kuma fisabilillahi, wai a hakan ma kuma dukan su masu mata shi Ya Aliyun fa matar shi ko haihuwar farko ma batayi ba dan duka duka auren su baifi shekara biyu da watanni ba shine tun yanzun yake batun k'arin aure, wato ya aureta ya had'a da wancan itama bayan dan lokaci yace wata kishiyar zai k'aro mata lallai ma, Shi kuma Ya Hashim da kyar mafa aka samu shawo kanshi yayi auren dan duk ya girmi su Ya Sa'eed yasin har Sarki ma ya girma matan shi biyu aka aura mishi rana d'aya amma da yike matan nashi gasar haihuwa sukeyi tuni suka suka cika mishi gidan da yara kusan 7 ita wani tsautsayi da rashin rabon ne zai sata aure shi, in ma ta aure shi da kishiyoyi zataji koda yaran su? Gidan da kusan kullum sai anyi damben bura uba a cikin shi aiko da maganar nan taje kunnen Malam da yaci amanarta ba kad'an ba, Waiyo Allah wai dama abunda mata ke fuskanta kenan aduk lokacin da auren su ko mazajen suke aure suka mutu? Shi kenan ko wani namiji sai yayi ta kawo musu hari ko wani mara ta ido ke dai zaice yana so, Tayi zaton cewa Salman ne kad'ai mara hankali shi yasa ya iya tunkarar ta kai tsaye, to ashe akwai manyan shi a gefe da ace sun kai maganar nan wajen malam ai da shi kenan sun shek'eta da ranta wallahi sai dai kuma wannan karan koma me zai faru ya dade bai faruba amma bazata zauna tanaji tana gani a k'ara mata wani auren dolen ba balle kuma har ace za'a aura mata mai mata. Koda akayi sallan isha'i ita fa gaba d'aya tama manta da cewar da AK yayi wai zaizo hira, To jama'a hira kamar dai wani saurayin arziki gida d'aya fa suke zaune, to in yazo hirar ma mai zaice mata? Ga kuma damuwar hirar da sukayi da Ya Sa'eed wannan damuwar duk sune sukayi mata katutu a cikin zuciya. Wani daga cikin yaran makotar sune ya shigo falon na Hajiya da Sallama, bayan ya gaishe sune Hajiya ke tambayar shi da cewa, "Ya akayi ne Khalid ko Maman kace ta aiko ka?" "Ah ah Ya Mai Jama'a ne ya aikoni wai yana kiran Aunty Meenal" Cewar yaron, "Mai jama'a dai na nan gidan nawa?" "Eh shi Hajiya" "Yana ina ne shi din daya aiko ka kiranta?" Hajiya ta k'ara tambaya, "Yana can a zaune wajen bakin gate" "To jeka kace mishi tana zuwa" "Ni babu inda zanje kai kace mishi nayi bacci" Cewar Meenal *Ummiee ce*✍🏼[9/18, 9:54 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 31* Khalid yi tafiyar ka gida kaji" Cewar Hajiya, bayan fitar yaron mik'ewa itama Hajiyar tayi ta wuce sama bata k'ara bi takan Meenal akan maganar ba dan ta k'uduri aniyar cewa bazata k'ara shiga maganar soyayyar su biyun ba, sai dai suga ta yanke hukunci kawai, Daga kan minutes ya fara lissafi sai gashi mintunan suna ta wuce wa shiru ba Meenal ba labari, wayar shi ya d'auka ya fara kiranta sai dai yarinyar nan dan wula walan walakanci haka tayi kunnen uwar shegu da kiran nashi duk da cewa yana da tabbacin taga kiran, Musty daya shigo gidan yanzun ne ya hango shi zaune sai faman latsa waya yakeyi, "Baa'ba yadai me kakeyi anan zaune kai kad'ai kuma?" Dogon tsaki AK yaja yana barbaza gashin kanshi, "Ya dai ko mutuniyar ce ta tab'o mana kai?" Musty ya k'ara tambaya, "Wai haka kuke fama da yaran nan dama? Da kyar fa na samu yaron dana aika cikin gidan nan akan ya kiramin ita amma wai sai cema yaron tayi ya fad'amin cewa tayi bacci alhalin kuma Hajiya tace ma yaron yace gata nan zuwa, kasan mintuna nawa na b'ata anan zaune ina jiran fitowar ta?" Bai jira Musty ya amsa mishi ba yaci gaba da cewa, "Kusan awana d'aya fa a wajen nan zaune na kira wayarta nasan kuma ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba cewa taga kiran nawa kin d'auka dai tayi saboda ta raina ni" "Calm down mana ya kake so ka b'ata ranka akan wannan d'an k'aramin damuwar, Menene ma na wani b'ata ma kai lokacin dahar sai ka wani nemi yaron aike cikin gidan a sanda kake buk'atar ganin ta? Gidan kune fa nan d'in kana kuma da damar da zaka iya shiga cikin shi a duk sanda kayi ra'ayi, oh wai nan dama kai kazo tad'ine kana jiran ta fito?" Musty ya fad'a yana nuna AK din yana kuma mishi dariya, "Zanci uban ka a wajen nan idan ka nemi matsamun kasani" "Miye laifina ni kuma daga baka shawara, kawai ka tashi ka bita cikin gidan tunda yau mulki takeji bazata yarda ta fito ba, kuma ai mai nema baya fushi kuma yasin ko nine ita ina da saurayi a gida bazan yarda in fito hira a harabar gida duk Sauro su gama cizona a banza ba" Gefen da AK d'in ke zaune shima Musty ya rab'a ya zauna,yana mai cigaba da cewa, "Baa'ba sai kayi hakuri fa indai yan matan nan ne duk haka suke da shegen jan aji amma na lokaci ne kaci gaba da tara ta kawai indai rabon kace duk zaka fanshe in kaso a rana d'aya" ya k'arasa fad'a yana dafa kafadar AK din ya jinjina alamun tabbaci. "Wai kai kasan cewa har yanzun yarinyar nan tak'i bani hankalin ta yanda ya dace, Idan nayi nan sai tayi nan na rasa me take nufi dani, wai har cemin fa tayi wai ita ba aure ne a gabanta ba yanzun, to wai so take ta maida ni d'an iska in zuba ido ina kallon maza na mata layi daga nan har zuwa sanda taga dama kafin muyi auren? Kana kallon dai yanda nike ta k'okarin canza kaina duka a kokarina na ganin na shawo kanta amma kasan me? Har yanzun banga wani canji mai girma a tareda ita ba har yanzun kallon taubashi abokin wasan ta take min" Ya k'arasa fad'a a dame sosai, "Bana so in tauye tane shi yasa nike tabi a sannu ba tareda na gabatar da kaina a gaban manya ba, amma tunda hakan ta zab'a ni kuma bani da wani zab'i sai na aikata hakan, idan Allah yasa su Baba Usman su iso lafiya zanyi magana dashi kawai suje su nemar min auren ta idan yaso daga baya ma daidaita tunda haka ta zab'a" "Hakan ma tunani ne mai kyau, nima naso inyi maka wannan maganar gara batun yaje gaban manya saboda idan hakan ya faru shine zata k'ara tabbatar da cewa da gaske kakeyi, Yanzun dai kar kayi fushi tashi kaje ka sameta a sashen Hajiyan kuma idan kaje koda wasa karka nuna mata b'acin ranka" "Musty yarinyar nan fa ta riga ta gama raina ni wallahi," "Ah ah ba raini bane su mata haka suke, hakan kuma da takeyi shike kara tabbatar da cewa tana da class dan haka karka damu kanka, Kasan yan magana sukace Mai ganin abu daga nesa da tantama yake sai mutum ya matso kusa zai gano abunda ya dace, Muje in taka maka" Jawo hannun AK din yayi ya mik'ar dashi tsaye, haka suka jera suna tafe suna k'ara tattauna wa sai da yakai shi har bakin k'ofar falon kafin ya juya ya koma da baya zuwa side d'in Hajiya Jummai shi kuma AK ya shiga falon da Sallama. Zaune a falon ya sameta wayarta ne rik'e a hannun ta wanda ta maida gaba d'aya hankalin ta akan wayar tana faman latsewa, da alama chatting takeyi kuma yasan baya wuce ace dasu Meelat take chat d'in, Kwarai kamar yanda ya hasaso dasu take chatting domin tun bayan tashin Hajiya ta maida hankalin ta akan wayan saboda yau su dukan su suna online suna magana ne akan isowar da Moon zatayi Zaria jibi, hankalin ta ya d'auku akan hirar nasu dan haka gaba d'aya sai bata k'ara tunawa da batun AK daya aiko yaro kiranta ba, Har ya isa inda take sam bataji motsin shigowar nashi ba gane hakan da yayi shi kuma sai ya koma ta bayan ta gefen kunnen ta yakai hannun shi ya tafa su da k'arfi "Faff" karar Sautin tafin hannun nashi suka shiga cikin kunnuwanta a bazata, sosai ta firgita wanda har hakan saida yayi sanadin data jefar da wayar dake hannun ta, tana shirin zurawa da gudu a cikin halin firgicin da take shi kuma ya rik'o kafad'un ta da hannun wanshi ya maida ta zaune, "Ke dallah can matsoraciya kawai, wai me yasa kin cika tsoro ne? daga d'an tafa hannuwa shi kenan duk kin wani bi kin firgice kamar wacce tayi karo da kura ko wani abun da zai iya cutar da ita! Nine fa ba kowa ba" Tureshi ta farayi tana kai mishi duka tako ina, Tsalle d'aya yayi ya tsallako daga bayan kujerar da take ya dawo ta gabanta yana dariya, "Nidai wallahi ka dauki alhakina, babu damar mutum ya zauna shiru indai kana gida sai ka sashi yayi surutu, waima Ina ruwan ka dani to?" "Niko keda ruwa dake Darling da fari dai wana kama?"ya tambaya yana tsats tsareta da ido, "To ni wani abu na maka da zaka kamani?" "Oh da gaske baki san abinda yasa zan kamaki ba? To waye na turo yaro ya kiramin tace ma yaron ya koma yace min tayi bacci? Shi baccin ai naga shi nazo na sameki kinayi, ba d'azun dama nace miki zanzo hira ba, mai yasa baki fitoba kika shanya ni a waje? wulakanci ne hakan da kikayi fa, amma dai ba komai na yafe miki karki k'arayin haka next time dan naji haushi sosai da kika shanya ni baki fito ba" Ya fad'a a fizge bayan ya d'an kame fuskar shi kad'an, Shiru tayi ba amsa, Shima kuma sai yayi shiru da bakin shi daga karshe ma sai ya jinginar da kanshi a jikin kujerar kawai yaci gaba da binta da kallo kamar ya samu tv shi dai wallahi Allah ya sani baya jin zai tab'a iya gajiya da kallon ta, dan shi kad'ai yasan yanda yake ji aduk yanda ta kasance kusa dashi irin haka Allah dai yakai damo ga harawa, ko baici ba ai zaiyi burgima son rai wallahi, Shifa bai iya kallo yana d'auke kaiba ah ah inzai kalleta kallon ga daga yake mata ita kuma sam ta kasa sabawa da hakan, da zarar ya fara kallon ta duk sai taji ta tsagu bazata samu kwanciyar hankali ba har sai ta dena jin nauyin idanun shi a jikin ta, dan haka ko yanzun bayan data d'auki wayarta kasa cigaba da chatting din tayi ko nasu chat din dake shigowa cikin wayarta kasa karanta su tayi a tsanake dan bata gane komai kuma, sunyi zaman a haka na tsayin lokaci baice mata komai ba sai kallo itama kuma ta kasa tanka mishi, gajiya tayi da zaman ta mik'e tana mikewa kuma shima ya mik'e tunda ta fara taka matakalan benen bata yarda ta juyoba domin tunda taji takun tafiyar shi a tare suke haurawa tasan bazai wuce yace zashi d'akin Hajiya ba, Sai dai abunda bata sani ba shine ita dashi a tare suka kai cikin d'akin da yake matsayin nata yanzun a gidan, bata lura dashi ba kwata kwata dan haka koda ta shiga sai tayi tsaye a tsakar d'akin dafe da k'irjin ta tana sauke a jiyar zuciya a jejjere dan tun dazun bata samu damar shaqa ko sauke numfashi da kyau ba har saida ta shigo cikin d'akin, Tunawa da tayi cewar bata kulle k'ofar d'akin bane hakan yasa ta juyawa da niyyar ta kulle k'ofar gudun karma idan ya fito daga d'akin Hajiyar yace zai lek'o nata, sai dai kuma tana juyawa taci karo dashi tsaye kik'am a gabanta hannayen shi goye ta baya yana binta da kallon nashi da yake mugun takurata, Bud'e baki tayi da niyyar kwarara ihu sai shi kuma yayi azamar daura hannun shi manuniya a saman lab'b'anta, "Shishshsh" yayi mata alamun tayi shiru da bakinta, Ganin hakan ita kuma sai ta fara matsawa baya saboda kusancin dake tsakanin su yayi yawa sosai ta yanda har tana iya ganin yanda numfashin shi yake sauka a k'irjin shi dan rigar dake jikin shi duk da cewar bata kama shiba sam amma wuyar rigar yana da fad'i sosai kuma yadin rigar irin mai kwanciya ne a jiki, ga kuma gashin dake kwance lufluf akan k'irjin nashi da suka nuna kansu ta inda wuyan rigar ya sauka, Kallo d'aya tama wajen a cikin kuskure tayi saurin d'auke kanta bata k'ara gigin kai idonta wajen ba ta ci gaba da matsawa baya, Ganin tana yin baya shi kuma sai yaci gaba da binta tana matsawa yana binta har takai jikin wardrobe din d'akin ta jingine dashi, K'ara matsowa yayi sai dai bai yarda ya matse mata waje da yawa ba sai yayi amfani da hannuwan shi ya dafe jikin wardrobe din ya zamana ya sanya ta a tsakiyar hannayen nashi, Kankame jikin ta dake rawa sosai tayi bayan ta runtse idonta da kyar ta samu ta iya fusgo magana da karyayyar murya tace, "Me.. Me... Me kakeyi, meee kakeyi haka dan Allah? Mai maa kazooyi anan too?" Murmushin mugunta yayi yana cigaba da kallon ta yace, "Oh baki ma san abinda nazo yiba bayan nazo tad'i kin shanya ni a waje saboda rashin tsoron Allah kika k'i fitowa, na shigo har ciki kuma haka bakiji tausayina ba kika k'ara shareni daga k'arshe ma sai guduwa kikayi, na biyoki kuma kina tambayar mai nazo yi, to hira nazo muyi a cikin d'akin tunda anan kike so muyi hirar koh?" Ya tambaya yana d'age mata girar shi, "To aini dama nace maka bazan zo ba" "To da bakizo ba bagashi ni dana matsu dason ganin naki nazo ba, ko bakiyi murna da zuwar nawa ba?" Tura baki tayi kafin ta bashi amsa da cewa, "To ai hira a k'ofar gida akeyi shine kai kuma ka Kama ka biyoni har cikin d'akin bacci na, anan ne zamuyi hirar ko koh so dai kakeyi Hajiya tazo ta ganka in shiga uku, Mai zance mata idan ta sameka anan? Nidai dan Allah ka rufamin asiri ka tafi ba dan halina ba" "Oh kunyan Hajiya kikeji bayan a gabanta na maimaita kalaman soyayya ta a gareki, Idan ta tambaya zance mata nazo hira ne mana tunda a gabanta na aiko yaro kika ce acemin kinyi bacci, Ni kuma bazan iya bacci ba tareda na ganki ba shi yasa na biyoki har nan" Ya furta hakan babu alamun damuwa ko d'ar a tareda shi, "To ai ka ganni tun a falo mai yasa baka tafi ba?" "Ok saboda ba iya ganin naki ne ya kawoni ba zuwa nayi ki bani amsar da nike jiran ji daga gareki, Shin kin amsa soyayyar tawa in aika nawa iyayen can gidan ku ko koh har yanzun baki gama nazarin da kikeyi a kaina ba?" "To aini na fad'a maka ba yanzun zanyi aure ba" "Ni kuma Ina mai tabbatar miki da cewa yanzun shine lokacin da nike buk'atar ki a cikin rayuwana dan haka rashin shirin ki bazai dakatar dani ba" "Nidai dan Allah ka tafi to naji na yarda gobe zan baka amsar eh ko ah ah din da kake son ji," "Gobeee" ya furta yana hura mata iskan bakin shi akan fuskarta, "Lallai bakya son in tafi indai har sai gobe ne bazan iya jira ba, kodai ki amsa ki furta min da bakin ki cewa kina sona ko kuma yau in kwana a cikin d'akin nan.... " Tun bai gama furta kalmar kwana a d'akin ba ta katse shi da cewa, "Meee 😳 "idanuwa a waje tana binshi da kallon tarin mamakin shi daya ke neman sa zuciyarta tsayawa daga aikin, "Wai anan d'akin zaka kwanan?" Ta tambaya saboda ta k'arajin tabbaci daga bakin shi, "Oh kina wasa dani koh kina ganin kamar bazan iya ba, Ok to bari ki gani" Kamo hannun ta yayi suka k'arasa k'ofar dakin dake bud'e har yanzun, da kafar shi yayi amfani wajen tura k'ofar ya rufe kafin ya murza key a jikin k'ofar, Kuka take shirin fashe mishi dashi ganin da tayi da gaske ya kulle k'ofar d'akin, K'arfi yasa ya juya ta kafin ya matsa gab da ita ya had'a bayan ta da k'irjin shi sai dai sam bai yarda ya matse taba, Duk'o da kanshi yayi saboda tazarar tsayin dake tsakanin su, ya cusa kanshi a gefen wuyanta ba tareda ya kwantar ba, rawa jikin ta ya d'auka dan take taji wani zazzabin tsoro yana neman kamata kankame jikinta tayi sosai, Bakin shi ya maida kusa da kunnen ta kafin murya can k'asa ya furta mata cewa, "To yane Dr kin shirya amsar Soyayyar nawa kuwa? Ko har yanzun kina da ja" Shiru tayi jikinta naci gaba da rawa, "Kinsan dai in baki amsa ba ana zan kwana koh?" Ya kara fad'a bayan yayi k'asa da muryar nashi sosai fiye da yanda yayi magana da ita a d'azun, "Eh na shirya yanzun indai na baka amsa ai zaka tafi koh?" Ta tambaya da muryar kuka dan Wallahi ita dai a tsorace take,kawai ya fice mata a cikin d'akin shi tafi muradi, "To kice kina sona sai in tafi, kuma da shauk'i nike so kalaman su fito daga cikin bakin ki" "To shikenan naji Ina sonka amma da sharad'in ba yanzun zamuyi aure ba" Ta fad'a da shakakkiyar murya, "Ban yarda dako wani sharad'i ba An mata, kuma ni ba haka nike son kalmomin su fito daga bakin kiba, haba ai ko kema kin san cewa sam baki furta kalaman naki da shauki yanda ya daceba, haka nike so inji kince, Abdul Khareem Ina sonka na kuma amince zan aureka mu rayu har k'arshen numfashi" Ya jero kalaman a natse kuma a tsare yana kwaikwayon muryar ta, "In kuma hakan bai miki ba bari in maimai ta miki nawa kalaman sai ke kuma ki bani amsa," A yanzun kam jingina ta yayi da jikin shi ya kuma ziro hannayen shi ya d'aura akan nata wanda suke cikin juna a dai dai cikin ta, "Ameenat Ina sonki irin son da zuciya da gangar jikine kawai suka san adadin shi, dan Allah ki tausaya ki amshi soyayya ta, ki bani dama in gabatar da kaina a gidan ku matsayin mai neman auren ki, ni kuma nayi miki alkawarin cewa zan kula dake fiye da yanda zan kula da kaina zanci gaba da sonki har zuwa gushewata" Yana maganan ne yana k'ara kan kameta a cikin jikin shi cike da shauk'i, hucin numfashin shi da kuma gashin gemun shi da yake gogar mata wuya sune abinda suka kassara ta ita kuma, sai dai duk yanda taso ta kwaci kanta hakan ya gagara saboda k'arfin su ba d'aya ba kuma ba rik'on wasa ya mata ba, "Ki dena wahal da kanki bazan sakeki ba har sai kin bani amsa, kinyi shiru ke nike saurare fa ko baki so in tafi in barki kiyi bacci ne?" "Ina so" ta fad'a da shakakkiyar muryar ta wacce tayi sanyi kalau, "Uhumm to ki fad'amin mana" "Ina, Iii... Inaa sonnn.. kaaaa" "Banji abinda kikace da kyau ba" "Ai nace Ina son ka nidai ka sakeni haka ka matseni fa kuma ai d'azun nan nace maka bana son kana tab'ani.... " Bata kai karshen zancen ba yasa karfi ya matse ta ya d'aga ta sama ya fara juyi da ita a cikin d'akin, Shi yana ihun murna ita kuma tana ihun kiran dan Allah ya sauketa tana ganin jiri, dan da gaske jirin take gani "Dukan k'ofar d'akin hajiya keyi ta waje tana faman kiran sunan Meenal, "Ke Meenal wani sabon shegen taka ne kuma zaki shiga d'aki ki rufe kina yima mutane iface iface, bazaki zo ki bud'e k'ofar nan ki gaya min ihun ubanme kikeyi ba" Jiyo bugun k'ofar da Hajiya keyi ba kakkautawa ne yasa shi sauke ta bai tsaya bi ta kanta ba duk da cewa yana kallon sanda jiri ya kwashe ta ya watsar a kan gadon ta dake gefe, Da sauri ya bud'e k'ofar d'akin yana budewa kuma ya janyo hannun Hajiya ya fara jujjuyata irin rawar nan da turawa keyi, ya farayi da ita sam bakin shi yak'i rufuwa tsabar farin cikin daya ke ciki, Bige hannun shi hajiya tayi da karfi ta kumayi amfani da k'afarta ta take nashi kafar da karfin da allah ya bata, Ta kuwa yi nasara dan Zafin bugun dana taka war su suka sanya shi cin burki na dole, a shagwabe ya kalleta, "Hajiya bakiga Ina cikin farin ciki bane shine kike so ki b'ata min mood din da nike ciki mai dad'i," Jawo Hajiyar yayi ya rungume tsan tsan cike da murna yake cewa, "Hajiya takwarar ki ta amsa tayin Soyayya na a yau, ta kuma yarda ta bani dama in tura iyayena a nemo min auren ta, shi yasa kikaga Ina ta murna Hajiya burin ki zai cika kwanan nan na ganin aure na" Daure fuska sosai Hajiya tayi tana binshi da kallo sheqeqe ta bud'e baki tace, "Shi soyayyar duk yafi k'arfin a bada amsar shi a ko Ina duk fad'in gidan nan har sai an shigo har cikin kuryar d'aki?, Kenan da tace ace maka tayi bacci wanko naka kafafuwan kayi ka biyota har cikin d'aki saboda gaka rasa kunya, to fita maza fita mata daga d'aki kuma kar in k'ara ganin ka a cikin d'akin nan koda wasa," "Hajiya bafa abunda kike tunani bane, kema ai kin san bazanyi haka ba, kawai dai na kasa hakuri akan jan ajin da take min ne shi yasa na biyota har nan d'in kiyi hakuri," Hannun ta yaja sai da suka kai bakin kofa yaci burki, kafin ya juya yana kallon Meenal data cukuikuye kanta a k'asa ta had'a kai da gwuiwa a gefen gadon tun bayan shigowar hajiya d'akin, "Dr good night " Ya fad'a yana aika mata da kiss din da yayi ma yatsun shi guda biyu ya nuna ta dashi, janye shi Hajiya tayi tana kai mishi bugu da mitan cewa bamashi da kunya a gaban idonta yake aikama jikarta kiss wato shi ga fitsararre sirikin zamani tana cigaba da mitan suka k'arasa fita daga d'akin tana cema Meenal , "Ki taso ki kulle k'ofar ki kuma dunga kulleta da key kina ji na fad'a miki karki yarda ki dunga kwanciya baki kulle kofa da makulli ba " Bata iya mik'ewa daga inda take ba har sai da ta tabbatar da cewa sun sauka k'asa kafin taje ta tura k'ofar d'akin ta rufe da key ta koma kan gado ta kwanta a rigingine tana kallon silin din dakin, murmushi ne ya kwace mata sai tayi saurin kai hannu ta rufe fuskarta tana mai jin kunyar kanta da kanta, Wai yau ita Meenal itace ta furta cewa tana son wani, harma ta bashi daman zuwa ya nemi a auren ta a wajen iyayen ta, Sam batayi zaton cewa hakan zaizo mata da wurwuri ba, lallai AK ya shammace ta da yawa, ita da taci buri mai girma nayin rayuwar da take so ta yanda zata biya bashin Yarintan ta da aka dakushe mata, sai gashi tun ba'aje ko Ina ba da alamu burin nata dai bamai cika bane. *UMMIEE CE*✍🏼 [9/20, 10:20 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 32* No editing 😒 Daga ABU kai tsaye Unguwar Malamai Bash ya wuce dan dole yana buk'atar yin bincike akan Meenal daya gani yau, da gaske auren nata ya mutune har take shirin yi wani auren ko ya abun yake? Idan yayi nazari akan maganar da yarinyar can mai kama da yar tsana ta fad'a mishi kenan hakan yana nufin auren Meenal ya mutu zawarci takeyi a yanzun haka! To amma in haka ne mai yasa bata neme shiba, Yayi zaton cewa a yanda komai ya kasance a tsakanin su suka rabu suna masu kewar juna ba tareda sun shirya rabuwa a lokacin ba ai bai dace ace yanzun auren ta ya mutu kuma harta kasa neman shi dan ta shaida mishi ba, yanzun ashe da ace baiyi katarin ganin ta a yau dinba da shikenan har saita k'arayin wani auren kafin in yana da rabon jin zance yaji daga baya? Anya Meenal tasan cewa rashinta ne ya hana shi yin wani auren har yanzun kuwa? Yaso Meenal irin son da bai tab'a tsammanin cewa zai iya hak'urin rashin ta ba, sai gashi a daidai lokacin daya gama tsara yanda zasu gudanar da rayuwar su a karkashin inuwar aure bak'in labari ya iske shi a ranar d'aurin auren ta, Sumewa yayi fa tsaf a sanda iyayen ta suke fad'a mishi cewa yau din shine za'a d'auren ta, *BARI MU D'AN KOMA BAYA KAD'AN* Idan baku manta ba a ranar d'aurin auren Meenal da Sarki wancan lokacin Aunty Hassana ta amshi Number din Bash a wajen Meenal da sunan cewa ita zata kira shi ta shaida mishi halin da ake ciki, In baku manta ba kuma a wannan lokacin shi Bash din yana ta fama da Meenal din ne akan ta amince mishi ya turo magabatan shi dan shima ya gabatar da kanshi a gaban Malam amma sam tak'i a cewar ta karatu zatayi. Abinda bata sani ba ita kuma shine tunda yabita² akan ta bashi dama tak'i shine kawai ya yanke hukuncin cewa a ranar d'aurin auren nasu Raheenat shima zai tura nashi iyayen, Dan haka koda kiran Aunty Hassana ya riske shi akan idan yana da hali yazo gidan Hajiya tana neman shi baiji wani d'arba dan koda ta kira dama shima yana tare da nashi iyayen ne da zasu tafi wajen d'aurin auren tare dan so suke idan an gama daura auren su kuma sai su nemi ganin malam dan su gabatar mishi da abinda ya kawosu wato neman auren Meenal, Ba karamin dadi yaji ba a sanda yaji cewa kiran daga yayan Maman Meenal ne, kawai sai tunanin shi yake bashi cewa k'ila Meenal din ce ta gabatar dashi a wajen su tunda inba haka ba ta ina Yayar mamanta zata san da zaman shi balle kuma harta samu number din shi ta kira shi kai tsaye haka, Dan haka daya tashi tafiya gidan sai bai tafi shi d'aya ba suka wuce tare da Kanin Maman shi d'aya da kuma wani Yayan Baban su wanda idan yaran mazan gidan su zasuyi aure shine yake shigewa gaba. Tarba na girma da mutunci akai musu duk da cewa ita Aunty Hassana batayi zaton cewa tare zaizo da iyayen shiba, sai bayan data fito ne taga bashi kad'ai bane dan dole suka koma sashen Hajiya domin dai bazai yuwu abar iyayen nashi a mota suna jira ba, Kuma koba komai tunda abun ba wanda za'a tsaya ana boyewa bane tasan dole zasuji dan haka sai tayi musu iso suka d'unguma zuwa Falon Hajiya gaba d'ayan su, Bayan sun gama gaishe gaishe ne Yayan Baban Bash din ya gabatar da kanshi a matsayin waliyin Bash da cewar dama a yau din sun shirya da sunan idan an gama d'aurin aure ne suma zasu gabatar da nasu neman auren sai kuma ga kira shi Bash din ya samu shine yasa suka d'unguma sukazo gaba d'aya tunda dai suma nan d'in ai iyayen Meenal ne tunda sun san da ace har wannan lokacin Prof Abdul Khareem yana raye dashi da kanshi yana iya bashi auren Meenal din, Jikin kowa yayi sanyi a wajen saboda jin abinda yake tafe dasu, Hajiya ko harda yar kwallanta dan ita wallahi da ace tasan da batun bash d'in nan da wuri da tabbas zatayi tsaye wajen ganin auren nan bai tabbata ba amma ina sai gashi ya bayyana mata a cikin kuraren lokacin da babu abunda zata iyayi dole saidai tayi hakuri, dukan su a wajen rasa kwarin gwuiwar shaida musu zancen auren Meenal din da za'ayi a ranar sukayi, Ita Anty Hassana dama tunda ta musu iso ta lallab'a tabar falon Abba Ahmad daya kasance shine Babba a yaran Hajiya shi Hajiya ta wakilta akan ya shaida musu halin da ake ciki, Saida yayi ma Bash doguwar nasihar data jefa Bash d'in cikin kokonto kafin ya shaida musu halin da ake ciki na auren ita Meenal din da Bash din keso, ya kuma fad'a musu gaskiyar cewa itama kanta yarinyar bata samu labarin d'aurin auren ba sai a jiya sannan aka shaida mata, tun jiyan kuma har yau bata cikin yanayi mai dad'i faruwan hakan ne kuma yasa ta shaida musu cewa bash d'in ne yake neman ta da kuma cewar ya dade yana son ta bashi damar gabatar da kanshi a wajen iyayen ta amma sai batayi hakan ba, Sun san cewa a yanda yake sonta dole zaiso ace ya kasance a wajen d'aurin auren kannin ta yau d'in sai dai kuma su bazasu so ace ya riski labarin a wajen daurin auren ba shi yasa suka kira shi dan su shaida mishi abunda yake faruwa, Tashin hankali irin wanda yake zuwa babu zato bare tsammani shine ya faru a wannan rana domin dai tuni fa Bash ya d'auke wuta, abu kamar wasa sai gashi ya zama gagarumi domin dai tunda suka fahimci ya suma suke faman sheqa mishi ruwa a k'okarin su na ganin ya farfad'o sai dai shiru, ya sheme kawai abinshi babu rai ba alamar shi, dan haka hankali tashe da iyayen nashi nasu Baba Usman suka rankaya asibiti, Hajiya ko a wannan rana tayi ma Malam Almu allah ya isa yafi cikin carbi dubu, a cewarta ga wani yana shirin sheqe nashi rayuwar akan jikanta amma mugun Yayan uba ya d'auki auren yar kanin shi da kullum yake ikirarin cewa yana sonta ya aura ma d'an d'an uwan shi wanda kowa yasan cewa ba lallai bane tayi daraja a wajen mijin ba tunda dai tuni tun Ana rade radi har kowa ya tabbatar da cewa matar Sarki ce Sarkin shi kuma bafade, Gaskiya Hajiya taji bak'in cikin wannan aure sosai sai dai kuma bata da yanda zatayi ta hana ko tasa a d'aura da Bash da yake can kwance s asibiti dan koda Allah yasa ya farfado rikicewa jikin shi yayi dole iyayen shi sai da sukayi jinyar shi mai tsayi, Bayan ya dawo hayyacin shi taso ganin Meenal kwarai sai dai kuma babu hali saboda dai tuni aka kaita d'akin Mijinta, gaskiya Bash yasha wahala sosai duk wanda ya ganshi a lokacin nan sai ya tausaya mishi domin sam ya kasa jure rashin Meenal, Wannan dalilin shi yasa Maman shi ta matsama Master akan gara Bash d'in ya tafi k'asar waje ko sa samu ya mance da Meenal badan yaso ba haka ya shirya suka bar k'asar, Shekara uku yayi a London ya matsa akan shi dai zai dawo Nigeria ganin da iyayen sukayi cewa zuwa lokacin ya cire batun Meenal sai suka yarje mishi dawowar, sai dai kuma tunda ya dawo Mahaifiyar shi ta fara matsa mishi akan maganar aure a cewar ta tunda Meenal tayi auren ta ai gara shima yayi, duk ta inda ta bullo mishi shi kuma sai ya kucce daga k'arshe daya gane cewa indai fa zaici gaba da zama a k'asar tofa bazata barshi ba ko auren dole ne sai ta mishi dan haka a sirrance ya had'a nashi ya nashi ya gudu yabar k'asa, Malesia ya koma wannan karan sai da yayi kusan shekara kafin iyayen shi suka gano inda yake, dan haka da suka tashi tafiya inda yake ita Maman tashi ita tayi tsaye saida aka d'aura auren shi da yarinyar yayan ta ikram sannan suka wuce mishi da amaryar shi can kasan, Wannan abubuwa da suka faru na doguwar jinyar da yayi da kuma yanda ya gudu yabar gida ba tareda sanin kowa ba sune dalilan da suka sa ita uwar shi ta tsani Meenal dan ita a ganin ta ai kawai Meenal din ce ta yaudareshi dan da ace tana son shi tun farko da bazata hana shi zuwa wajen iyayen ta ya gabatar da kanshi ba, Gashi yanzun ita tana gidan Mijinta hankali kwance ta manta dashi shi kuma har yanzun ya kasa cireta a ranshi balle ya maye gurbin ta da wata a cikin rayuwar shi, Todai a dole a babu yanda zanyi dole haka nan ya amshi auren iklima bayan iyayen ta sun kaita da sati d'aya suka tattaro suka dawo gida Nigeria, Zamane wani iri yake gudana a tsakanin ma'auratan domin dai shi tunda aka kai mishi ita gidan shi ko sau d'aya bai tab'a kallon ta a matsayin mata ba yanda ya saba gudanar da rayuwar shi tun farko haka yaci gaba babu abinda ya canja sai dai kuma yana dawowa gida da dare yake kulle k'ofar d'akin shi saboda yanda take ta faman kai mishi far maki abin ya isheshi, ace a kawo maka Amarya kuma wai budurwa amma tun baka nuna bukatar ka akanta ba ita ta fara kawo maka farmaki, dan haka sai ya d'auki matak'in k'in zaman gidan daya dawo kuma yake rufe k'ofa haka zatazo tayi ta bugu yayi mata banza, Ita ko baiwar allah dama tun tuni ta dad'e tana renon soyayyar shi sai dai kuma a sanda ta bayyana mishi lafiyayyen mari ya wanke mata fuska dashi da kuma gingimemen gargadi kan cewa koda wasa idan harta bari wani yaji zancen sai yaci mata uwa, Dan dole tayi hakuri ta kama kanta dashi badan taso ba sai gashi kwatsam daga baya suka samu labarin wai jaririyar yarinyar dashi bash din keso iyayen ta sun mata auren dole, ita Ikram ta girme ma Meenal nesa ba kusa ba sannan tana da waye da budewar ido dan kwata kwata bata da kunya, wannan halin nata shi yasa shi kuma Bash baya shiri da ita tun farko dan shi baya son auren macen da idanun ta suka riga suka bud'e irin haka yafi son karamar yarinyar da shine zai reneta da kanshi ya tafiyar da ita yanda yake so, Watanni aka share Ikram tana ta faman son ganin ta shawo kanshi kodan saboda bala'in dake cin jikin ta na kayan mata na bala'i da ta d'ud'dura ma cikin ta tunda aka fara zancen auren ta dashi sai gashi an kawota amma har lokacin ba'a samu cigaba ba, Ganin idan ta zauna a gida tofa wata rana sha'awa na iya sheqeta sai kawai ta dena zaman gidan, domin da zarar ya fice itama take yin nata shirin ta fice a binta, A haka sukaci gaba da rayuwa bai rageta da komai ba illah harqallah na kwanciyar aure, itama kuma tunda ta zama yar gari ta samu masu d'ebe mata kewa ga kuma kud'ad'en da yake tura mata na kula da komai na gidan duk wata sai kawai ta tattara shi da auren shi ta watsar, da auren ta idan taga dama zatabi saurayi suyi tafiyar kwanaki bata gida, har taje ta dawo kuma ba sani yakeyi ba kamar yanda shima har yabar k'asar yaje wani wajen ya dawo bata sani, sai dai in tayi katarin ji a bakin uwar shi ko kannin shi, Haka sukayi ta zama cikin wannan rayuwa har sai da suka shekara biyu da watanni da aure kafin ranar bacin rana ya risketa, domin dai tsautsayi ne yasa ranar ta gayyato d'aya daga cikin samarin ta har cikin gidan bata damu da cewa Bash yana nan ko baya nan ba tunda tasan ko yana gari idan ya riga ya fita gida da safe to sai tsakiyar dare zai dawo, Abinda bata sani ba shine a wannan satin shi gaba d'aya ma baya k'asar Nigeria yazo saboda rashin lafiyan daya kama Master dole ya ajiye komai ya wuce Nigerian bai saba sallaman ta idan zaiyi tafiya ba dan haka koda zai tafi bai shaida mata ba, sai dai kuma zuwan shi gida a wannan lokacin nasihan dashi Master ya mishi na cewa ya rik'e matar shi da kyau kar yace wai dan ya rasa Meenal hakan zaisa ya wulakanta Ikram domin koba komai ita din yar uwar shice, koda Master ya mishi wannan nasihar yana cikin Zafin ciwo shi kuma Bash ya ma Baban nashi alqawarin dai daitawa da itane saboda bazaiso ace ya kasa bin nasihar da mahaifin shi ya mishi a cikin halin rayuwa ko mutuwa ba domin sosai Master yake jin jiki babu wanda yayi zaton zai tashi a wannan ciwon hatta da iyalan shi sun cire rai, Sai dai kuma da yike ran bawa a hannun Allah yake sai gashi ya samu lafiya, a dawowar shi yaso ya fuskance ta su gyara zaman su dan ya shirya amsarta zai kuma gudanar da rayuwar auren su kamar na sauran ma'aurata sai gashi yana dawowa yayi mummunar gani, Domin dai ita Ikram tunda tasan cewa gidan ta bawai gidan da bak'i ke yawan zuwa bane dan haka bata wani damuwa da kulle kofa saboda unguwar da suke akwai tsaro sosai kuma su can ba kamar mu nan Nigeria bane da zakaji tsoron barin kofa a bude, Mummunar gani idanuwan shi sukayi mishi ganin da saida yayi silar yankewar numfashi daga k'irjin shi, a sanda ya farfado ko tuni kwarton daya tarar tare da matar auren shi ya cika ma wandon shi iska ya gudu ita k'adaice zaune a falon tana faman rusa mishi kukan munafunci da rokon shi akan ya taimaka ya rufa mata asiri shairin shed'an ne, Duk hakurin da take bashi bai iya ce mata komai ba yadai samu ya lallab'a duk da duhun da jirin da yake d'ibar shi haka yakai kanshi d'aki, Yayi kuka sosai domin yasan shima yana da laifi saboda da ace bai wofantar da itaba da babu yanda za'ayi tayi tunanin bin wasu mazan balle harta kawo mishi su gidan shi, shekaru kusan uku fa ake magana da auren su amma ko sau d'aya bai tab'a zama shida ita sukayi magana na fahimtar juna a tsakanin suba sosai yayi dana sanin irin rik'on sakainar kashin da yayi ma auren nasu lallai ya cutar da ita, Kwana biyu yayi a cikin d'akin ba tareda ya fito ba ita kuma tsoron shi da kuma abinda take tunanin zai aikata akanta sune suka sa ta tattara duk wani abunda ta mallaka tsayin zaman da tayi a k'asar ta tattaro komai tabi jirgi ta dawo Nigeria, sai dai kuma koda ta dawo bata fad'ama kowa ainihin dalilin dawowar nata ba, tadai ce musu shine yace tazo gida dan dama tun auren ko sau d'aya bataje gida ba sai sukayi zaton kawai ko ta kawo ziyara ne, Bayanda ya gama jinyar nashi ya fito domin yana son yin magana da ita ne ya tadda bata a gidan ganin babu kayanta a d'akin ta komai nata ta kwashe ne kuma hakan ya tabbatar mishi da cewa gida ta koma, Bai tab'a zaton cewa zata koma gidan ba dan yaso ne kawai tunda komai ya riga ya faru shi yaji ya gani zai rungumi kaddara abinda yaso suyi shine suje asibiti a fara duba mishi lafiyar ta, Idan har an tabbatar mishi da lafiyarta kalau to zai sa tayi istibra'i ne idan ta gama sai ya nemi wani Malamin da zai d'aura musu wani auren anan tunda bai san ko tun yaushe take mu'amala da wasu mazan ba, sai gashi kuma hauka da rashin hankalin ta yasa ta kwashi jiki ta koma gida, Ya kuduri aniyar bazai bita ba tukun zai zauna yasa mata Idone tukun har zuwa sanda zata dawo, idan kuma iyayen su sun neme shi to yasan cewa ta tona ma kanta asiri kenan, dan haka sai kawai yaci gaba da harkokin shi, Sai da tayi kusan wata biyu da tafiya kafin ya samu kira daga wajen Mahaifiyar shi akan cewa me ya hanashi zuwa bayan Ikram ta shaida musu cewa shine yace ta zauna har sai yazo sannan zasu koma tare, To bai zoba kuma yan gulma sun fara yad'a surutai akan zaman da takeyi har yanzun bata koma ba ko dai akwai wani abun a k'asa ne? Shiru yayi bai iya bata amsa ba data matsa sai kawai yace mata zaiyi kokari ya shigo k'asar zuwa karshen wata, karshen watan nayi ya shiryo ya dawo gida sai dai kuma abinda ya tarar bayan dawowar nashi har sai yafi na baya tashin hankali domin dai ashe ita Ikram tun dawowar ta mutane da yawa sun ankare da cikin data dawo dashi wasu da yawa sunyi zaton ko rainon cikin nema ya dawo da ita tunda acan k'asar basu da kowa sai su biyu, Sai dai duk wanda ya mata maganar cikin saita basar dan ta gaji dace musu bata da ciki ita a zaton ta hutun data samu a can kasar shi yasa mutane ke ganin kamar ko cikin take dashi, Ranar da yaje gidan su ikram d'in saboda kafin yayi magana da kowa zaiso ya farajin ta bakin ta idan babu wanda yasan abinda ya faru kenan komai zaizo mishi da sauk'i zai tambayeta ne idan tana ra'ayin zama dashi in kuma tace tafi son su rabu zai saketa ne kawai batareda ya tona mata asiri ba, Sai gashi daga zuwa uwarta ta tare da cewa ai tayi zaton ko sai watan haihuwar ikram din ya kama ne zai dawo, Da fari yayi zaton zolaya ne kawai sai da ta k'ara mai maita mishi cewa, "Ai tunda ta dawo nace to kunyi kyan kai dan dama rainon cikin fari ai sai gida, kodan saboda abubuwan kwadayi da ita zata buk'ata wadanda ba lallai ku same su a can k'asar ba," Yanke ta yayi a yayinda yake bin ikram din da kallo da cewa, "Ai bata d'auke da komai" Dariya tayi ita kuma a nata zaton tayi tsammanin ko kunya ne yasa shi fad'in hakan dan haka sai tace "to ai tunda gaka kazo sai ka d'auketa kuje asibiti dan a tabbatar mana da wata nawa ne cikin nata, dan gaskiya in cikin baiyi kwari ba bazan yarda ka d'auketa ku koma can wata k'asar ba dan ku yaran nan ba hakuri kuka cika ba kuna iya kuje can wajen rashin hakurin ku ku zunguro cikin ya fita" Bashi da yake cikin kwankwanto ba ita Ikram da ake zancen ciki a jikin ta itace take cikin tashin hankali mad'aukaki, Domin a iya sanin ta dai tasan cewa kafin ta fara yawace yawacen ta sai da tayi planing na shekaru uku saboda gudun b'acin rana, To ta ina kuma zatayi ciki, kenan planning din ne baiyi ba ko kuma dai wannan bala'in ne daban ake kira mata, zufa ke shatata tako ina a jikin ta, ciki fa ake magana bayan kowa yasan tana da aure amma ai babu wanda yasan cewa cikin bana aure bane, Yanzun idan shi kuma ya bud'e baki ya fad'ama duniya gaskiyar cewa bai tab'a kwanciya da ita ba da wani idon zata kalli iyayen ta bayan babu wanda yasan tana biye biye, Ita dai ta shiga ukun ta ta lalace da ace tasan da batun cikin nan da tun dawowar ta zata zubar da shege ko kuma tabi malamai a kulle mata bakin shi ruf ta yanda bai isa ya musa cewa cikin ba nashi bane, Ta ina ma zata yarda ta haifi cikin da uban nin shi suka kasu sama da biyar dan ita tsabar jarabarta bai barta ta rayu da namiji d'aya ba, indai kana da kud'i kana kuma sake mata su babu ruwan ta zata barka ne kayi ido iya iyawarka to yau ga ranar bacin rana, Dauriya sosai Bash ya aro ma ranshi koda Maman ikram din tace suje asibiti baiyi musu ba dan shima yana so a tantance din domin dai yanzun kam an yanka ta tashi, Allah ya gani yaso ya rufama ikram asiri kodan saboda kasancewar ta yar uwar shi amma hakan zai yuwune kawai in babu cikin a jikin ta idan kuma akwai to babu ubanda zaisa shi amsar cikin da bai san inda ta samo shiba wallahi, Uwar da kanta taja ikram din d'aki ta shirya badan taso ba haka ta fito ta same shi a mota suka wuce asibitin, Wani private hospital sukaje inda acan ne aka k'ara tabbatar musu da batun cikin, Tunda suka fito a asibitin ikram ke kuka shi dai bai kulata ba, to me zaice mata bayan inda yana da hali shima kamata yayi ya daura hannu akai yayi ta kwarara ihun har sai ya gamsu dan kanshi, Gajiya da kukan tayi dan kanta ta nemi ya faka dan tana son su nemi mafita tun yanzun, Bai musa ba haka ya faka motar a gefen titi yana binta da kallo da son jin abinda zatace, "Yaya ni dakai dukan mu munsan cikin nan ba naka bane, Kayi hakuri bansan da wani idon zan kalleka ba shi yasa na dawo gida, saboda in baka sararin da zaka yanke hukunci ba a cikin fushi ba, Wallahi tunda Nazo ban iya fadama kowa laifin dana aikata maka ba saboda bansan da wani idon zan kalli iyayena ba, Yaya ka yafe min nasan na cutar dakai wajen cin amanar auren ka gashi kuma tun ba'aje ko ina ba Allah ya saka maka nayo cikin daba na aure ba, nayi laifi kana da damar da zaka hukunta ni nasan ban cancanci cigaba da zama a matsayin matar kaba, sai dai kuma ina so in rok'eka alfarma d'aya dan Allah ka rufa min asiri kamar yanda baka fadama kowa dalilin dawowa na gida ba bana son iyayen mu su san abunda na aikata maka ka rufamin asiri dan Allah, ko baka fadaba nasan cewa ni yanzun ba matar auren ka bane sai dai kuma duk da haka zanso ka rubuta min takardar saki wanda zai zama shaidar dazan gabatar bayan ka koma a matsayin ka sakeni," Katseta yayi da cewa shi kuma cikin jikin naki ya zakiyi dashi? Zan zubar dashi saboda idan na haifeshi duk daren dadewa dole wata rana asirina zai tonu duniya zata gane cewa dan dana haifa da auren ka ba naka bane ni kuma bani da amsar da zan bashi idan ya tambayeni wanene uban shi, dan haka gara in zubar dashi tun cikin bai gama yin kwari ba," "Bakyajin tsoron wani abu ya sameki a yayin cire cikin? Ko baki san cewa har mutuwa anayi ba" "Na sani amma hakan shi yafi min," "Ok tunda hakan kika zab'a ni bazan tilasta kiba rayuwar kine sai dai ina fatan hakan daya faru ya zama silar da zaki canza rayuwar ki" A takaice dai a wannan ranar ikram bata yarda ta koma gida ba dan a hanya tasa ya sauketa bayan ya rubuta mata takardar saki d'aya ya damka mata ita kuma tayi cikin sabon gari ba ita ta koma gida ba saida aka kwalkwale cikin nan tsaf ta tabbatar da cewa ta rabu dashi koda ta koma gida kuma dauri ya ta aro sai ta sheda ma Mahaifiyar nata cewa ba ciki bane al'adarta ne yayi gardama amma an bata magani tayi amfani dashi har period din nata yazo, Shiko daya tashi komawa koda iyayen sukayi magana ce musu yayi ba can Malesia zai koma ba South Africa zashi ta zauna har sai ya koma kafin ta dawo, Sai da ya tafi da kusan wata biyu ita kuma lokacin tana da kusan wata HUDU kenan a gida kafin ta gabatar da takardar daya bar mata, Ganin abin yana shirin tab'a zumunci ne kuma yasa ta fadama iyayen nasu cewa suyi hakuri itace ta mishi laifi kuma itace ta nemi Sakin, Sunyi sunyi da ita ta fada musu maiya faru amma tak'i, shima kuma da aka tambaye shi sai cewa yayi su tambayeta, A haka dai maganar saki ya tabbata aure ya lalace ba tareda kowa yasan mai ya faru ba, Tun wancan lokacin kuma bai dawo k'asar ba sai wannan dawowar da yayi ya had'u da Maryam a k'ofar doka gashi kuma yau ya had'u da Meenal, Meenal din da rashin ta ne duk yayi sanadiyar fadawar halin daya tsinci kanshi a ciki tsayin shekarun nan, Taya kuma yanzun data dawo wata zatace mishi wai wani auren zata karayi, kenan suna nufin cewa zai kara rasata a karo na biyu? Koda ya isa unguwar malamai so yayi ya wuce gidan su meenal din kai tsaye sai kuma wata zuciyar ta hana shi dan haka sai yaci burki a k'ofar gidan su Meelat kasancewar shi zaka fara isa kafin gidan Malam, Cikin masu gadin gidan yayi magana da wani akan yayi mishi kiran Meelat d'in babu dadewa ko sai gata ta fito saboda basu dad'e da magana da musty ba yace mata zai bada sak'o a kawo mata amma sai gashi bayan fitar ta taci karo da bash, Bash dai tsohon saurayin Meenal wanda yayi d'awainiya dasu a shekarun baya, Lallai Maryam batayi karya ba da tace ya canza domin kuwa da gaske ne ya canza din ya k'ara girma da cikar kamala ga kuma arzikin da yaci uwar na baya, Fara'ar dole ta aro ta yafa ma fuskarta a sanda ta k'arasa inda yake, "Wa nake gani yau a k'ofar gidan mu kamar Bash din mu?" "Ni ne dai Bash din Meenal ba gizo idanuwan ki sukai miki ba, Jamila ya gida ya kwana da yawa?" "Ah ah aini bai kamata ma in tsaya ko gaisuwa muyi ba ace kana raye sai yau zaka nemeni tsayin shekarun nan ina ka shige Bash?" "Kiyi hakuri nayi laifi amma bana k'asar ne shi yasa ban neme kuba, nabar k'asar ba'a cikin hayyacina ba a sanda abubuwa suka dai daita kuma bani da kwarin zuciyar da zan iya zuwa unguwar nan shi yasa ban neme kiba sai yau ina fatan za'amin afuwa?" "Ah haba dai ba komai wallahi komai ya wuce ai, to ya bayan rabuwa ya rayuwa? Duk da dai Alhamdulillah yanda na ganka nasan an samu cigaba sosai, ya madam da yara to dan nasan kila baza'a rasa ba duba da shekarun da aka d'auka" Guntuwar murmushi yayi kafin ya amsa mata da cewa, "Alhamdulillah sai dai iyalin da kika tambaya ne har yanzun babu, sai dai muna fatan wannan karan a dace tunda shekarun baya dai an kasani" Ya karasa fad'a idanuwan shi a kanta, Murmushi itama tayi bata bashi amsa ba, Sai ya daura da cewa, "Dazun naga Meenal tareda wannan yayan nata na tudun wada, mun kuma hadu da maryam da wata kawarta dukan su a cikin ABU, Sai dai ita k'awar tayi wasu magan ganu wanda ban gane ba shi yasa nazo nan, Naso in wuce gidan su Meenal ne sai kuma naga ya dace in farajin ta bakin ki duk da ban sani ba ko kina gida ko allah yasa kinyi aure sai da na zo ne mai gadin ku yace min kina gida. *UMMIEE ce*✍🏼 [9/21, 8:22 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 33* To mu shiga daga ciki mana nasan bakasan ansa ranar aure na ba wannan satin mai kamawa zanyi aure kaga ba dad'i mutane su ganni tsaye da kai a nan dan haka bismillah mu shiga daga ciki ina ganin hakan zaifi " Cikin suka wuce suka nemi waje a farfajiyar gidan suka zauna, "Bari in shiga ciki in kawo maka ruwa," "Ba bukata ki barshi kawai nagode" "Ok tunda kace haka yanzun me kake son ji daga gareni?" Ta tambaya tana binshi da kallo, tunda har ya wanko kafafun shi yazo har nan tasan gaskiyar yake son ji daga bakin ta dan haka babu amfani ta boye mishi. "Ina son insan komai, idan nace komai Meelat ina nufin komai karki boyemin akan Meenal ," Gyara zama tayi da kyau kafin ta fara da cewa, "Kamar yanda ka sani a shekarun baya da suka wuce kaida Meenal duka mun shaida kuna son junan ku, nasan kayi bakin k'okarin ka wajen ganin ka shawo kanta akan ta baka daman gabatar da kanka a gaban iyayen ta amma hakan bai faru ba har zuwa sanda komai ya faru, tasha fad'ama na yanda kukayi da ita akan hakan,nasan a lokacin zakayi zaton ko bata sonka ne shi yasa amma kuma ita a gefen ta ba hakan bane, tak'i yarda ka gabatar da kanka din ne saboda tasan da zarar ka kai maganar ka gidan su to zancen aure za'ayi saboda kaima kasan yaran gidan su ba'a barin sukai har matakin da ita takai a lokacin ba tareda an aurar dasu ba, Wallahi³ Meenal bataci amanar kaba ta kuma soka da dukkan zuciyar ta a wancan lokacin, In baka sani ba bari in fad'a maka idan kuma ka sani hakan zai zama maimaici ne a gareka, ita kanta bata san cewa itama tana cikin wadanda za'a d'aurama aure a wannan lokacin ba har sai ana gobe daurin auren nata, tayi kuka tayi kuka babu kalar borin da batayi ba akan bata son auren amma kuma bata isa ta canza abinda Allah ya riga ya kaddara zai faru a lokacin ba sai dai kuma duk halin da take ciki bata manta da kaiba, ina da labarin kiran da Aunty Hassana tayi maka domin a wajen Meenal ta amshi number dinka, Kayi hakuri a lokacin nida Maryam mun kasa zuwa asibitin da aka kwantar da kai duba Kane saboda bamu sanda wani idon zamu kalle ka ba, munyi zaton cewa zuwan namu zai iya zama k'arin tsanani a gareka.... " Katseta yayi saboda shi ba wancan labarin daya riga ya sani yake son jiba, ah ah halin da Meenal take ciki a yanzun shine damuwar shi, "Yanzun Meenal tana ina?" "Tana Tudun wada gidan Hajiya, auren ta da Sarki ya mutu a watannin baya hakan ne yasa ta koma can da zama" "Me yasa bayan auren ya mutu daga ita har ku babu wanda yayi tunanin nema na?" "Saboda a iya sanin mu baka k'asar, kuma ko kana k'asar ma ai hakan bai dace ba tunda nidai nasan kayi aure, yanzun da allah yasa kayi katarin ganin ta ba gashi ka biyo sahu ba " "Eh bana k'asar kuma nayi auren kamar yanda kikaji, sai dai kuma nima mun rabu da matar" "Ayya to Allah yayi zab'i da mafi alkhairi" Cewar Meelat, "Ameen! Meelat meke tsakanin AK da Meenal domin a yanda na gansu yau jikina yana bani cewa akwai wani abu a tsakanin su kuma ita waccan yarinyar dana ganni tareda Maryam tace min wai shine mijin da Meenal din zata aura shi yasa Nazo nan dan ina son inji gaskiyar komai daga bakin ki dan nasan bazakiyi min karya ba" Ajiyar zuciya ta sauke tana kauda kanta gefe dan yanda ya tsareta da ido tasan gaskiyar maganar yake son sani, Kai Sultana dai bata ji sam wallahi,inba shegen surutun taba meye ya kaita wani ce mishi AK ne mijin da Meenal din zata aura bayan sun shaida mata komai dake tsakanin Bash din da Meenal, ai da tayi shiru da bakin ta ba lallai yasan cewa auren ya mutu ba, saida tayi gyaran murya kafin ta amsa mishi da cewa, "Itafa yarinyar nan daka gani shegen iyayine da ita, ko kuma dai kayi wani abunda ka b'ata mata rai shi yasa ta fad'a maka hakan, nidai nasan akwai kyakyawar alaqa a tsakanin su kamar yanda kaima kasan shi din d'an uwanta ne bayan hakan kuma ban san wani abun ba zaifi dacewa ka tun kare Meenal d'in kuyi magana kai tsaye ta yanda zakaji komai a bakinta" Sun danyi hira kad'an kafin ta rakoshi k'ofar gida sukayi Sallama shi ya shiga motar shi ya tafi ita kuma ta dawo gida, Tana shiga gidan Maryam ta fara kira ta fad'a mata cewa suzo ita da Sultana su sameta tana jiran su, a wannan ranar kuma Sultana bata dawo gidan Hajiya ba a Unguwar malamai tayi zaman ta saboda su sunyi zaton cewa tunda Bash yasan inda Meenal take zaije can ya neme ta. *washe gari* Hajiya, AK da Meenal ne zaune akan dinning suna karin kumallon safe, Wato dai Hajiya bata k'ara tabbatar da cewa soyayya yana sa mutum ya zama wani abun daban ba sai yanzun da so ya damk'e mata wuyan D'an mai k'arfi, gayen nan fa gaba d'aya ya fitsare kafafuwan shi yayi fatali da wani abu da akeji in ana gaban sirikai mai suna kunya, Dan dai Hajiya ko tana waje ko bata babu abinda ya dame shi zai aiwatar da abunda yayi niyya ne kawai abinshi, Domin dai tunda ya dawo masallaci yana komawa d'akin shi kayan shi ya tattaro shida su (Kabir wani yaron shine dake mishi aikace² idan yana gari) ya dawo dasu sashen Hajiya a cikin d'aya daga cikin d'akunan kasa ya zuba kayan, duk wani abu na bukata nashi sai da yasa su kabir din suka kwaso mishi, Tunda farar safiya masu aiki sukazo suka fara aikin yima gidan kwas kwarima, inda duk yake da buk'atar gyara an gyara sauran kuma ko ina aka bishi da sabon fenti gyara sosai akema gidan wanda badan komai ake yin shiba sai dan shirin bikin Musty, Hajiya tayi mamakin ganin AK ya kawo kayan shi sashen ta dan haka gaza yin shiru tayi saida ta magantu, "Kai wai nace wannan kayan naka da naga ka kwaso ka kawo nan badai kana nufin k'aura kayi daga can sashen ka ka dawo nan bako?" "Kema dai Hajiya kin san bana son kamshin sabon fenti kawai zan zauna anan ne na yan kwanaki kafin ranar bikin zan koma sashe na" "Ah ah Abdul wannan batu dai duk wanda yaji yasan gulma ne dajin baki, tsakani da Allah tun tuni kasan zakasa ayi aikin fentin gidan nan baka sa anyi tun kafin ka dawo ba sai yanzun daka dawo ne zaka wani tattaro min kayan ka kayo sashena wato dai shi kenan ni bani da sirri, duk wanda ya kwaso gyayyar shi wajena zai sauka, To ta ina ma zan yarda niko inyi rayuwa hankali kwance da kai sankacecen k'ato a sashe guda bayan nasan ina da budurwar daka ce kana so a cikin sashen," "Hajiya ban gane ba wani irin magana kenan kikeyi? Kenan dan Meenal tana zama anan tare dake shi kenan ni kuma bazan dawo in zauna anan d'inba, To miye laifin zaman nawa tunda dai ni ba dodo bane balle kice zanbi dare in cinye miki ita" Ya fad'a rai bace tsohuwar nan fa ya lura da cewa magana kawai take nema dashi, "Ah ah fa koma me zakace sai dai kace wallahi, amma ni bazaku mai dani sakarya ba bayan kasan yanda allah ya daura min saurin yin bacci, So kake ni ina can saman gado ina baccin asara kai kuma kaida ita kuna zaune falo kuna hira, kai din nan dai mai ido a tsaitsaye Allah kadai yasan abunda zaka iya aikatawa a bayan idona, Dan haka maganin kar ayi tofa kada a soma shi yafi" "Kenan dai Hajiya kina nufin so kikeyi kice baki yarda dani ba wato ga d'an iska ya dawo sasanki koh?" Saurin tarar numfashin shi tayi da cewa, "Ah wallahi karkayi min k'age kasa min magana a baki kasani fad'in abinda ba shine a cikin zuciyata ba, nidai gaskiya nike fada maka dan kar kayi zaton wai ko rashin yarda ne yasa bazanyi shedar kaba, Ah ah kulawa dai nike nunawa dan yanda naga kana nan nan da ita tofa ana iya samun matsala badai fata nikeyi ba Allah ma dai ya kiyaye dan ni ban haifi dan iska ko yar iskaba insha Allah kuma zuriata bazaku lalace ba, Duk ma abar maganar badai kace zaman kwanaki kawai zakayi ka koma naka sashen ba, to ga sharud'a, Na farko babu doguwar hirar da za'a raba dare ba'aje an kwanta ba, na biyu kuma baka ba haura sama ko magana kake so kayi dani sai dai ka jira idan na sauko ko kuma ka kirani a waya na uku kuma kowa ya zauna a inda yake atoh dan mu a zamanin mu ko hannun ki kika sake kikabar namiji ya rike sai dai ki wayi gari kiganki da ciki riki riki," Wai dan Allah jama'a mai Hajiya ta d'auki shi, bawan Allah dashi har shine za'a kafama wasu sharud'a dan kawai zaiyi zama na kwana biyu a sashen daba nashi ba, To yasin Hajiya bata san shi bane yanzun ne zai gwada mata cewa da gaske fa auren yake so, ko dai ta tashi tsaye ta tura a nemo mishi auren jikarta ko kuma shi yayi gaban kanshi. Hakan ne kuma yasa a wannan safen zaman da sukayi na karin ya tsiri nuna kulawar shi akan Meenal din da gangan a gaban Hajiyar, Tea Meenal din ta had'a da niyyar karyawa dashi kamar koda yaushe domin so takeyi ta gama da wuri ta wuce unguwar malamai dan rashin Sultana a gidan yasa tanajin gidan ba dad'i dan in Sultana tana waje ta iya d'aukema wanda take dashi kewa saboda barkwancin ta, Sai gashi ita data had'a tea ma kanta sunyi raba dai dai din shi da Ak domin idan ta d'aura ta kurb'a tana ajiyewa shima zai d'auki cup din ya daidaita dai dai bakin ta yasha, da suka shanye tea d'in kuma kunun gyad'ar da Hajiya ta zuba mishi shi ya koma yana bata a baki har ma in kunun da d'an dangwali gefen bakinta saboda tsabar iya hege yatsar shi yake kaiwa wajen ya goge kunun dashi sai ya lashe da hakorin shi, Duk wannan iskancin da yakeyi Hajiya kin kulashi tayi dan tasan wani abun ma yanayi ne saboda d'azun tayi magana to bazata biye mishi ya nemi maida ita sakara'u ba, shiko kunyar ta bayaji wai a gaban idon ta AK ya zauna yana cida Meenal abinci baki, Ita dai ido da baki kawai ta sake tana binsu da kallon ikon Allah saboda yanda shi uban gayyar ya nuna kamar ya manta da zaman ta a wajen, Abincin ya d'ibo a cikin spoon ya k'ara nufo bakin Meenal dashi, "Haaa nace Allah kuwa ina fad'a miki idan baki tsaya kinci abincin nan ba babu inda zakije yau a gidan nan" "To Yaya ai na fad'a maka na koshi, nifa tea kawai nike sha da safe amma Kali ka gani fa tun dazun kake duramin cous cous din nan bayan nasha tea nasha kunun gyad'a Allah idan ka matsamun amai zai sani" Ta karasa fada a marairaice dan Wallahi shi dai ke aikatawa amma ita kunyar ke kamawa, "Kalli ki ganifa saura kad'an ya rage daure kawai ki cinye sai kije ki kwanta abinki dan yau babu zuwa yawo ni dake a gidan nan zamu wuni muna d'ebema Hajiya kewa, Hajiya mai zaki dafa mana anjima " Banza dashi Hajiya tayi kamar bataji mai yake cewa ba, "Hajiya nidai dan allah kice mishi ya kyaleni haka wallahi na koshi" "To dan ubanka tace ta koshi ai sai ka gyaleta haka ko ana dole ne? Gaba d'aya kabi ka matsama yarinyar mutane saboda tsabar rashin kunya ma a gabana ka ajiyeta kana bata abinci a baki, wai yaushe ka zama haka bani da labari Abdul? Ke kuma dayar munafukan inace tun d'azun baki yake kina karb'a kamar bakisan da zamana a wajen ba sai yanzun ne zaki sakoni a shirmen ku, kai kuma Allah ina fada maka idan baka dena wannan b'are b'aren jikin ba tofa tattara ta zanyi ta koma gidan ubanta dan bazaku dunga abubuwan ku a gabana ba idan ku baku san kunya ba to ni ku barni da jin kunya" Haka dai suka gama karin safen Hajiya nata faman mita, A wannan ranar kasa wa AK yayi ya tsare ya hana Meenal zuwa ko ina kamar yanda yace, dan tunda ya tattaro ya tare a sashen Hajiyan idan kunga ya fita to masallaci zaije yana dawowa kuma zai koma dan harta baccin da yace Meenal tayi bai barta tayi ba dashi suka shiga kitchen da rana Larai nata mishi tsiyar cewa kar ya bada maza fa in dan in yace haka zaiyi to kafin aure zai zama mijin tace, tun Meenal na nokewa dan dole ta gaji ta sake jiki saboda yanda yake nuna damuwa da kulawar shi mad'aukaki akanta, motsi kad'an zatayi ya fara tambayar ta miya faru? Haka ya dunga riritata irin riritawar da bata tab'a tunanin samun kwatan kwacin shi a tareda shiba, duk da hakan ya matuk'ar faranta ran Hajiya amma sai bata nuna ba sai ma kushe su data dungayi akan in basu kama kansu ba dukan su zata kora subar mata gidan da dare yayi shida kanshi ya fita bayan ya tambaye su abinda suke son ci yaje ya siyo ya dawo suka zauna su ukun suka ci karfen 10 na dare Hajiya ta raka Meenal har d'aki saida ta tabbatar da cewa Meenal din ta rufe k'ofar ta da key kafin itama ta shige nata d'akin. washe gari ma bai fita ba yana manne da Meenal d'in har su Meelat Maryam Sultana da kuma Maimoon suka iso gidan domin koda Moon ta iso can gidan su Meelat ta sauka abunta acewar ta ko zata koma gidan Hajiya sai sun gama biki. "Hajiya nayi ma su kabir magana gobe zasu gyara sashen saukar bak'in gidan nan dan anan gidan nike son mu sauke bak'in mu tunda muna da isasshen masauki basai mun kaisu Hotel ba dan haka ki shiga ki duba abubuwan da ake buk'ata wanda babu a sashen sai a siyo a saka, Abincin da za'aci kuma har a gama taron bikin kowa ya watse munyi magana da Hajiya Yar ba'u itace zata dunga girkawa," "To kayi kyan kai kam dan dama nima naso inyi maka magana Allah yasa dai agama taron lafiya, kunyi magana da iyayen ka sun fada maka ranar da zasu iso kuwa?" "Ba muyi magana dasu ba" ya bata amsa, Tunda Meenal taji kukan motar ta tasan Sultana ce ta dawo gidan, dan ta fada musu cewa AK ya hanata fita ko ina gashi kuma gobe ne zasu gabatar da event din su wanda suka shirya gabatar dashi a makaranta dan haka tasan dole dama zasu biyo ta, Sai dai ga mamakin ta koda suka shigo sai taga harda Moon a cikin tawagar nasu, da gudu Sultana da Moon suka kwaso ita Sultanan Hajiya ta nufa tana fad'in tayi kewarta ita ko Moon wajen Meenal ta nufa Ak yana ganin hakan yayi saurin shiga tsakanin su ya maida Meenal din bayan shi yana d'aure fuska, "Ke miye haka kukeyi daga shigowar ki zaki kwaso gudu kice wani zaki rungume ta? Bakiga kin fita girman jiki bane ko salon dukan ku ku fad'i kujama mutane aiki?" Ak manya shifa ba komai yasa ya shiga tsakanin nasu ba sai kishi, tayama zai yarda yana zaune yana kallo ita moon din kawai ta wani kwaso gudu tace zata rungume mishi mata, ah ah fa sam ba wannan maganar kuma itama Meenal zaija mata layi ne da yanda yaga sunayi, Karma Sultana taji labari dan ya lura da yarinyar nan shegen son jiki gareta ko zama zatayi saita jingina ko ta kwanta a jikin Meenal din duk ta sakar mata nauyin ta shifa bazai yarda da hakan ba, abu indai nashi ne yafi so yaci gaba da zama a matsayin nashin kawai. "Kai Yaya dan Allah mun dade fa bamuga juna ba ai kaima kasan dole in so rungumar ta kodan inji dumin jikin bloody na a nawa jikin," "Aiko bazaki jishi ba, dallah can nemi wajen zama ki zauna ku kun girma amma har yanzun kun kasa dena behaving irin na yara," Tura baki tayi ta mik'a hannun ta ta kamo na Meenal wacce take mik'o mata, "Ke yar nan ke kuma daga ina kika fad'o nike ganin ki daga sama babu labari?" Hajiya ta tambaya tana bin Moon din da kallon mamaki, "Daga Lagos mana zuwa Zaria, kuma dan zanzo ai bai zama dole sai na kira na fad'a miki ba, kuma ni biki nazo shi yasa ma ban sauka anan ba na sauka acan" "Ikon allah ita uwar taki itace duk ta kitsa miki hakan kafin ki baro garin naku? Wato har ankai matakin da zaki shigo garin nan amma ki kasa sauka a gidan nan sai dai ki sauka acan wani gidan da baki had'a uwar komai dasu ba koh to ko kinki ko kinso nidai nice dolen ki dan ubanki, babu dangin iya balle na baba kinje gidan mutane kin tare to uwar me kikazo yimin anan d'in tunda nidai ai ban tura miki katin gayyata ba, yara iyayen ku sun barku a gaban su sunki su aurar daku nidai wallahi in ma bakin jini ke gareki ba a wajena kika d'auko ba sai dai can gefen uwar ki, kuma insha Allah su iyayen naki zasu iso su sameni basu barin garin nan sai sun tsaida zancen auren ki da koma waye inba haka ni dasu ne" "To wai Hajiya ni ce miki nayi na shirya auren a yanzun ne?" "Aikin banza dama waye zai tsaya biye miki? Wacece ke da kike zaton cewa dole sai abinda kike so za'a miki aure dai ko baki tashi ba ni na tashi aurar dake, inba ma rashin zuciya da rashin sanin ciwon kaiba ku kenan kullum kuna siyan ankon biki kuna zuwa bikin kawaye amma ko kishin ace kuyi auren kuma bakwayi, To gata nan dai ita naki yar uwar daga mutuwar auren ta harta samu wani mijin ke koh kina nan kullum sai k'ara girman jiki da yawan shekaru kikeyi amma shiru babu mashin shine kiji da kyau to bana na shirya tsaf babu yaro ko yarinyar da zan k'ara bari su shekara a gaban iyayen su indai sun isa aure kuma suna da halin yi sai sunyi, duk ku gama tsalle tsallen ku nice maganin ku. *UMMIEE CE*✍🏼 [9/25, 11:03 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 34* No editing 😒 *INA MAI BA MASU KARATU HAK'URI AKAN SHIRUN DA SUKAJI KWANA BIYU, HAKAN YA FARU NE SAKAMAKON MATSALAR RASHIN WUTA DA MUKA SAMU,* *~Ina kuke masoya kuma yan uwana makaranta?,~* ~shin kuna da labarin cewa gwanar ku kuma gwanata *JAMILA MUSA MARUBUCIYAR SHAHARAR REN LITTAFIN NAN MAI TAKEN KWARATA* tak'ara dawo muku da wani zazzafan labari mai cike da sark'ak'iyar hassada makirci munafunci bita da kulli kai harma da tsantsar SOYAYYAR da a dare d'aya ya juye ya koma wutar kiyayyar juna?~ *WUTAR K'IYAYYA* ~ce keci take kuma gudana a cikin rayuwar wani ahalin da suke jini d'aya ma'ana uwa d'aya uba d'aya?~ ~idan baku manta ba a baya itace dai wacce ta rubuta muku littafan nan masu d'auke da tsantsar fadakantar wa gami da nishad'in da har yanzun da yawa daga cikin mu nasan bama gajiya da karanta shi,~ ~ina magana ne akan littafan ta kad'an daga ciki irin su~ *KWARATA, BOYAYYAR SOYAYYA, ZAWARCI, SO MUGUN WASA Dama wasu wad'anda ban kira sunan suba* ~wadan nan littafan dana lissafo ko banyi k'ari bayani akan suba nasan kun san me suka k'unsa~ ~To wannan karan ma dai so nike ku shirya tsaf ban kuma ce kuyi garaje gurin karatu ba, ah ah karatun littafin Hajiyata nutsuwa yake buk'ata, littafin~*WUTAR K'IYAYYA* ~zai zo muku a kyauta ne kedai qawata daure ki loda ma wayar ki data da kuma isashshen caji domin ki samu damar karantu a natse na tabbata zakiji dadin shi domin ko namu ba irin nasu bane~ *karku manta littafin WUTAR K'IYAYYA kyauta ne ga masu buk'ata daga farko suyi magana dani kai tsaye ta wannan number din* 08061358462 *ni kuma zan an taya su cikin group din zaku same shi daga farko kuma batareda kunsha wahalar nema a wani wajen ba* ************Kunga kutashi muje ciki dan Allah," Meenal ta fad'a tana tarar numfashin Hajiya saboda jin da tayi Hajiyar tana neman mai da chapter din ya juya kanta shiko dama AK tunda ta fara surutun ya mik'e yabar musu falon dan Wallahi ya sani tsaf Hajiya tana iya kwafsa mishi a gaban yaran nan bai kuma bar falon ba sai da yakai bakin shi dai dai kunnen Meenal ya shaida mata cewa bai fa yarda da wani rungume rungume ba sannan ya fice abinshi jin Hajiya naci gaba da surutun ta na fama, inba haka ba dan Allah miye kuma nayi masu terere daga zuwan Moon din zata wani fara shelanta mata cewa ita Meenal ta samu miji? Itafa Hajiya matsalarta kenan duk maganar da yazo bakinta fad'in shi kawai take bata wani lura dako su waye ke wajen salon duk tasa kananun yara su gama raina mutum, Basar da kashe din da AK ya mata Meenal tayi dan tun bai bar falon ba ta fuske taje ta rungume Moon d'in irin rungumar da akema mutum na gefe tana mai cigaba da cewa, "Kema dai kamar wata wacce baki san halin Hajiya ba da zaki wani biye mata kina son b'ata ranki daga shigowar ki ko hutawa bakiyi ba ku wuce muje ciki kafin ta huce dan Hajiya kwana nan bata dako wani magana sai na aurar da mutum" "Eh lallai kam ai dama dole ki goyi bayan yar uwarki ni ki kwaye min nawa bayan! Kwana nawa ne dududu ita Maimunan zatayi ta tafi tabar ni dake a gidan nan? Batun aure kuma dan uban mutum ko yak'i ko yaso dole yayi shi in mutum baiyi ta arziki ba aiba abun kunya bane in kunji shela a masallaci ana sanarwa dan mu bayau farau a kan muba yima mace auren bazata, Oh wato ma ga azababbiyar tsohuwa koh shine har kike cewa ku wuce to karko ku sake kuce zaku hau min sama gara duk ku tattara kuzo ku fice min a sashe dan babu wacce na gayyato dama a cikin ku" Tsam suka mik'e ganin abun na hajiya bamai k'arewa bane suka fice daga sashen zuwa side d'in Hajiya Jummai acan suka baje hajar su ta firar yaushe gamo tunda dai ba laifi an dad'e ba'a had'uba kullum sai dai chat da kuma kiran waya, Suna cikin hirar nasu ne kuma Meelat ta kawo zancen zuwan da Bash yayi wajen ta da kuma labarin Meenal din daya tambayeta duk saida ta bata Meenal labari sannan kuma Meelat din ta tambayi Meenal ko bash din yazo wajen ta?dan allah ya sani ita dai bata so Bash din ya bayyana ba taso ace ko zai bayyana sai komai ya k'an kama tsakanin AK da Meenal din ba kuma wai dan bata son Bash d'in bane ah ah ita dai tafi son ace AK ne ya samu Meenal din akan duk sauran wadanda suka nuna ra'ayin su akan Meenal d'in. Sosai jikin Meenal yayi sanyi ba tareda ta iya ba Meelat dasu Maryam din da suka zubo mata ido suna jiran amsa daga gareta ba, Tayi matuk'ar mamaki dajin cewa har yanzun ashe Bash dinta Bash dai nata a shekarun baya d'an gidan master wai ashe har yanzun bai manta da ita ba tunda gashi har ya iya neman ta a ranar daya ganta, Allah Sarki rayuwa kenan a baya bata tab'a zaton cewa zasuyi rabuwa ta bazata irin rabuwar da sukayi dashi wanda ko sallama basuyi a yayin rabuwar ba, bayan auren ta kuma tunda ta tabbatar da cewa shi kenan ta rasa shi sai ta rungumi kaddarar ta duk da cewa a lokacin tana da number din wayar shi akai amma bata tab'a gwada kiran shi ko sau d'aya ba saboda bata san me zata ce mishi idan ta kira shi d'in ba, A wajen Aisha ta samu labarin halin daya samu kanshi a ciki yayin zuwan shi gidan Hajiya kuma bata tab'a tattauna maganar dasu Meelat ba suma kuma tun bayan auren ta babu wanda ya k'ara tada hirar wani daga cikin samarin ta a cikin su, sun tona k'asa sun burne komai saboda basa son hankalin ta ya tashi, daga bayane ma takejin cewa wai baya k'asar lokacin data samu labarin hakan ta bishi da fatan alkhairi saboda Bash mutum ne yana daga cikin mutanen da bazata iya mantawa dasu ba dan ya nuna mata kauna tun zamanin da take cikin k'uruciyar ta ta kuma yarda cewa Allah yayi cewa ba shine Mijinta ba shi yasa tun farko bata bashi damar zuwa gidan suba, Sai gashi kuma yanzun kwatsam yana son dawowa gareta a dai dai lokacin data amsa soyayyar wanin shi bayan kuma shi ta dad'e da mishi delete all a cikin memory d'in ta, Yanzun idan ya dawo ya k'ara gabatar da kanshi a karo na biyu ya zatayi?, da wani fuskar zata tarbeshi alhalin ita tuni ta dad'e da yima nashi soyayyar kabari ta birni a matsayin matacce. Shiru tayi domin gaba d'aya ta riga ta tayi b'acewar b'at a cikin tunanin halin da take ciki a yanzun yanda abubuwa suke neman jagula mata lissafi duk yanda take kamewa amma abun mamaki kamar wacce akayi shelar mutuwar auren ta domin dai kullum mazaje ne ke kawo mata hari ba'a makaranta ba ba kuma cikin gari ba kamar dai ita kad'aice bazawara a gari, Ga AK, ga Salman, ga Aliyu, ga kuma Ya Hashim sannan kuma yanzun ga bash ya dawo bata ma sa sauran samarin dake faman biyayyar ta wad'anda bata da alaqa dasu a lissafi ba dan har yanzun wasu ma basu san katamai man gidan suba balle su kawo mata hari, "Allah Sarki Bash nayi zaton ko ya manta dani tuntuni ai?" Ta furta kalmar a sanyaye, Tab'e baki Sultana tayi kafin tace, "Shidai kam alamu sun nuna cewa bai manta dake dinba har yanzun, gashi kuma ke tuni kin dad'e da mantawa dashi ni kam na gode Allah da yasa gayen nan ya dawo a makare, dan haka bari kiji duk ma ranar daya sake ya kawo kanshi wajen ki karki wani tsaya yin mishi muna muna ko munafunci ki fito fili ki fad'a mishi gaskiyar cewa tafiyar sa'ar ki da nashi basu jera hanya ba tunda gashi a wannan karon ma dai yana ji yana gani zai k'ara rasaki, zaifi mishi sauk'i idan ya tafi wani wajen ya k'ara lalube ko zai dace da samun abokiyar tafiya, kai ni ina rokon allah ma ya mantar dashi ke gaba d'aya wallahi Allah yasa kuma k'in tunkarar naki da yayi hakan ba yana nufin cewa zaiyi miki shigar k'arfi bane wannan karon , Dan yana iya komawa gefe yace zai tura iyayen shi kai tsaye wajen su Baba Malam kafin ya gabatar da kanshi gareki a karo na biyu, duba da abinda ya faru a shekarun baya sanadiyar rashin gabatar da kanshi da yayi a gaban iyayen ki" Ta k'arasa fad'a tana watsa hannuwa dan itafa tsakani da Allah duk wani wanda zai fito yanzun yace Meenal yake so to dole nema ta taya AK adawa dashi domin ba karamin dacewa take ganin Meenal tayi na samu AK ba, dan haka bazata yarda wani can yazo yace zaiyi takara da AK ba, Ba iya Meenal bace kad'ai taji saukar kalmar da Sultana ta fad'a a cikin k'irjin taba har su Moon sai da suka zazzaburo, "Kina nufin idan saurayi yaga kamar ke idan ya nemeki zaki bashi ciwon kai shine zaisa ya wuce wajen iyayen ki kai tsaye ya gabatar da kanshi a wajen su?" Moon ta tambayi hakan a k'age da son jin amsar da Sultana zata bata, "Eh kwarai kuwa kusan hakan ne amma shi ni a nawa tunanin ina ganin kamar tunda ai tun farko yasan dokar gidan su Meenal din shine yake so ya koma yabi tsarin duba da cewa rashin bin tsarin yana daga cikin dalilan da sukayi jagoran cin daya rasata a shekarun baya, Kuyi nazarin magana ta da kyau zaku fahimta, Meenal kinga dai ban san wani irin so kikama Bash din nan a baya ba, amma koma dai yayane ni zan fad'a miki gaskiya duk wanda zai soki a yanzun bana tunanin zai miki so irin wanda AK yake miki a yanzun kai ni banma ga uban meye ya hanaki kiba bawan Allan nan damar gabatar da kanshi a gidan kuba wai so kike sai an k'ara miki wani auren dolen ne kafin ki dawo cikin hayyacin ki?" Hummm suka dunga fad'a suna gyad'a kai cike da nazarin kalaman Sultanan dan dukan su sun san cewa gaskiya ta fad'a, Ita ko Moon a gefen ta ba k'aramin tashin hankali takeji a cikin k'irjin taba, kenan idan ta auna kalaman Sultanan hakan yana nufin cewa shima Sarki yana iya zagayewa yaje ya nemi aurenta ta baya batareda ya nemi jin nata ra'ayin ba? Duba da cewa tun sanda ya mata magana da farko ta nuna mishi ah ah bai k'ara tada zancen ba kuma ko a fuska bai nuna mata damuwa ba, ita kuma nauyin shi da takeji yasa har yau ta kasa k'ara tada maganar, to idan kuma tayi shiru har yaje ya zagaya ya nemi auren ta ta bayan gida maganar ta fito daga baya da wani idon zata d'aga ta kalli Meenal wani kalan bayani zata mata waiyo Allah ta shiga uku, zufa ta dunga had'awa ta ciki duk da sanyin fanka da ac din daya cika falon na Hajiya Jummai. Abinda ya faru a Lagos kafin ta taho, Tsakanin ta da Sarki lafiya lau sukaci gaba da ganin juna babu wani abunda ya canza a tsakanin su domin dai duk da cewa bai k'ara taso mata da maganar zuwa neman auren ta wajen Baba Usman ba hakan bai hana shi cigaba da nuna mata kauna da soyayyar da yake mata ba, Da farko had'uwar su iya waje biyu suke yin shi kodai a wajen aikin ta ko kuma da yamma a can inda suka saba had'uwa amma sai gashi daga baya kuma har gidan su yake binta, Ranar farko daya fara zuwa gidan tayi mamaki kwarai dan batayi zaton cewa shi d'in ne da gaske ba domin dai ko a ranar yaje can wajen aikin ta ya sameta sai dai bai dad'e sosai ba ya mata Sallama ya tafi a matsayin cewa sai sun had'u da yamma, da yamman tayi bai samu zuwa can wajen ba dan ya kirata ya sheda mata ta kirasu tayi order din abinda take buk'ata kawai sukai mata gida dan yayi busy bazai samu damar had'uwa da ita ba amma idan ya kammala abinda yakeyi d wuri zai neme ta, To itama jin hakan da yace sai bata damu kanta da cewa sai taje d'in ba sai tayi zaman ta kawai a gida, Daren ranar suna zaune a falo suna hira ita dasu Umma da sauran k'annin ta kiran shi ya shigo cikin wayar ta, Tashi tayi tsam bayan ta d'aga wayar ta koma d'aki saboda bata son tayi wani abunda zaisa Umman tayi zargin cewa har yanzun ashe suna tare ita da Sarkin duba da yanda ta fito k'iri² ta nuna mata rashin amincewar ta akan alaqar tasu dan ita dai tace bata yarda da auren cin amana ba, ta ina ma za'a fara ace wai mijin daya auri Meenal ya saka shine zai auri Moon a yanzun bayan dukan su kowa yasan bayan k'awance harda alaqa ta jini a tsakanin su, Tunda ta amsa sallamar daya mata bata yarda ta k'ara furta komai ba sai da ta tabbatar da cewa ta maida k'ofar dakin ta ta kulle shi da kyau, "Barka da dare dafatan ka wuni lafiya" "Alhamdulillah ya kike?" Ya tambaya "Ina lafiya" "Me kikeyi ne?" Ya k'ara tambaya, "Ba komai" "Ok to fito gani a farfajiyar gidan ku" "Na'am" ta amsa dashi bayan ta ciro wayar daga kunnen ta ta duba Number din domin tantancewa, "Eh ki fito nace ko insa ayi min iso ne in shigo ciki?" Ya fad'a ko a jikin shi, "Uhmm uhmm wai nan gidan kake magana" "Kuna da wani gidan bayan wannan ne anan Lagos dama?" "Ah ah amma ai baka cemin zaka zo ba, umm bawani nan nasan ma wasa kawai kakeyi min" Murmushi yayi daga can gefen shi, murmushin da harta cikin wayan sai da ta jiyo shi, kafin ya daura da cewa, "Yanzun dai koma wasa ne ko gaske duk idan kika fito zaki tabbatar in kuma kika b'ata min lokaci wallahi cikin gidan zan shigo kinji dai na rantse miki dan haka ki fito yanzun" yana gama fad'in hakan ya yanke wayar shi, Sororo tayi da wayar a kunne, Cike da mamaki to wai ma meyazo yi a gidan su da daddaren nan salon ya tona mata asiri a wajen Umman su, yanzun in Umman su tasan cewa Sarki na cikin gidan nan yazo hira wajen ta ya zatayi? Tunawa da rantsuwar da yayi cewa idan ta b'ata lokaci zai shigo cikin gidan ne hakan yasa dole ta fito daga cikin d'akin ko mayafi bata d'auka gudun karma Umman su taga fitan ta, ta k'ofar baya tabi a sace kamar b'arauniya sai da ta fice kafin ta tsaya ta warware dan kwalin rigar dake jikinta ya yafashi tana sauke ajiyar zuciya tun daga nesa ta hango shi zaune akan fararen kujerun dake farfajiyar gidan, gabanta naci gaba da fad'uwa haka dai ta daure taci gaba da taku harta isa inda yake wanda shima hango tahowar nata ne yasa shi mik'ewa dan ya tarota, "Shine kazo nan bayan kuma baka fad'amin cewa zaka zoba" shine kalmar data fara furtawa tun bata samu zarafin zama ba, "Bakiyi farin cikin ganina ba kenan? Niko kinga na kasa daurema zuwa gida in kwanta batareda nayi tozali da wad'annan fararen idanuwan naki ba shi yasa na biyo dare na taho kawai dan in ganki,nayi zato zakiyi farin ciki kema amma tunda bakiyi farin ciki ba kiyi hakuri kina iya komawa ciki tunda na ganki" Juyawa yayi da niyar tafiya tayi saurin shan gaban shi, "To ni ai bance ka tafi ba kawai dai nayi mamaki ne da kace min gaka tunda naga ko d'azun munyi waya kuma baka cemin zaka zo ba" "Ai nace miki kawai nazo ne dan in kalli fuskar ki a zahiri kuma na gani hankali ya kwanta kije ciki sai da safe"ya fad'i hakan yana zura hannayen shi a aljihun wandon jikin shi, Bata samu zarafin cewa komai ba Baba Usman ya bayyana a wajen daga cikin gidan ya fito da alama fita zaiyi, ba karamin tashin hankali ne ya risketa ba sai dai kuma ta danne hakan dan ba lallai bane a zatonta ya gane Sarki, kasa tayi da muryar ta, "Kagani kaja min ko ga Baba nan ya firo" Bai kulata ba saima wucewa da yayi ya k'arasa wajen baba Usman din sukayi gaisuwar da bataji me sukace ba dan Sarki bai tsaya ba sai da ya raka Baba Usman din har mota sannan ya koma inda take tsaye, "To yane yanzun dai bari in wuce kar in shiga lokacin ki da yawa" "Me kace ma Baba?" Ta tambaya tana bin shi da kallo a sanyaye, "Babu" kawai ya bata ansa dashi, "Babu me? " ita kuma ta tambaya, "Bance mishi komai ba, me kike tunanin zance mishi bayan gaisuwa, amma ke idan ya dawo ya tambaye ki cewa me nazoyi wajen ki wani amsar zaki bashi?" Ya tambaya yana tsareta da ido, Juyawa tayi sai da tayi taku d'aya biyu ba tareda yayi yunk'urin tsaidata ba kafin taci burki ta juyo ba tareda ta kalli idon shiba tace, "Sai da safe" Tana gama fad'in hakan ta juya tayi cikin gidan da sauri gabanta yana tsanan ta fad'uwa dan batasan me zai biyo baya ba kuma, Sarki bai gusa daga inda ta barshi tsaye ba harta shige cikin gidan, shi dariya ma ta bashi wallahi dan Allah kuga duk yanda tabi ta rud'e shifa gaba d'aya baiga abun tashin hankali a cikin al'amarin nan ba da take ta faman son ta hana ma kanta abinda zuciyar ta keso wanda kuma bawai hakan ya haramta a gareta bane, aiko mai kankat zai mata Allah dai yakai su Zaria lafiya, Cikin masu gadin su ya kira guda ya bashi sako yace ya mik'a mata cikin gidan, Ranar kwanan d'ar d'ar tayi domin motsi kad'an idan taji sai taga kamar Baba Usman ne zai aiko ayi mishi kiranta dan yaji ko waye yagan su tare, ko sakon da Sarki ya bayar aka biyota dashi bata bi ta kanshi ba k'annen tane sukayi didima a kanshi, Tun daga ranar Sarki ya tsiri yi mata zuwan bazata bazai tab'a fad'a mata cewa zaizo ba sai ya shigo cikin gidan sannan zai kirata cewa yana jiran ta, ita kuma ta kasa fitowa ta fad'a mishi cewar ya rufa mata asiri ya dena zuwa gidan, kuma bayan ganin farko da Baba Usman ya musu sau biyu ya k'ara ganin su tare bai kuma yi mata magana ba har sai ana gobe zata wuce Zaria a gaban Umman su ya kirata yake tambayar ta cewa, "Maimoon wanene wanda naga yana zuwa wajen ki hira a yan kwanakin nan?" Tsuru² tayi uwa an jijjiga bera a cikin buta, "Hira kuma Baban su ai a dai cikin kwanakin nan bana jin akwai wani saurayin dake zuwa hira wajen ta" cewar Ummah "Kece dai baki san ana zuwa hira wajen nata ba amma ai gata nan zaune a gaban ki kinji ta musa abinda nace ne? Ke Maimoon dake nake magana" "Abokin aikina ne"ta tsinci kanta da furtawa dan tasan yau ta shiga uku idan har Ummah tasan Sarki na zuwa hira gidan nan wajen ta, "Shi abokin aikin naki yake zuwa gidan nan har kike Rita ni ina gidan nan bani da labari" umman su ta fad'a cike da mamaki, "Kiyi hakuri" Moon tace kanta a k'asa, Shi kuma Baba Usman d'aurawa yayi da cewa, "Kin san me yasa na kiraki nan?" "Ah ah " ta furta tana girgiza kai, "Masha Allah to dama kiranki nayi dan in baki hakkin ki a matsayin ki na budurwa, shin akwai tsayayyen saurayin da kika tsayar a cikin samarin kine? Ina nufin wanda kike da burin aure?" "Baban su kaima dai kamar baka san hali ba, ina ma take kula samarin balle harta tsaida tsayayye nidai dama ai tun tuni nike ta maka magana akan Lukman d'an wajen Hajiya Hasiya ka sani sarai tun tuni yake bibiyarta take mishi wulakanci amma har yanzun yaron nan ya kasa hak'ura ya nemi wata ya aura, ita kuma da kullum take ikirarin cewa bata son shi ta fitar da wani mijin tayi aure tak'i tasa har yan uwana sun fara ganin kamar nice bana son in had'a zuria dasu to nidai tunda abin ya zama haka gara aba shi Lukman din komai koba komai dukan mu mun sheda yana son ta...." Saurin tarar numfashin ta Moon tayi da cewa, "Wallahi Umma nidai bana son shi, dan Allah karki matsa kice sena aure shi" "To Moon in baki auri Lukman ba wa kika tsayar ne bayan kullum nan ko mazan sun biyoki har gidan nan ma ba kulasu kikeyi ba, so kike mu zuba miki ido kici gaba da zama a gaban ki dan kawai muna zaune a kudu? Kina zaton inda a arewa ne har zamu yarda ki kawo uwar haka ba tareda mun aurar dake bane? Abban su nidai ina goyon bayan ka tunda tace bata son lukman d'in to kai ka duba a gefen ka kawai tunda ruwan ido yasa ta k'asa tsaida tsayayye" Kuka Moon din ta fashe musu dashi, cikin kukan take cewa "Dan Allah Baba karka min auren dole" "To Maimoon ya kike so muyi dake? So kike musa miki ido kiyi ta zama babu aure ne?" "Ah ah ai zan kawo mijin auren idan na samu" "To kiji ni da kyau, sati d'aya kacal na baki daga yau kije ki zauna kiyi nazari da kyau ki tantance a cikin samarin ki ki fidda gwani, koma waye shi ina so ki gabatar mana dashi idan mun isa Zaria yazo gida ayi magana saboda Abban ku Ahmad zai shigo k'asa ina buk'atar tabbatar da tabbatuwar zancen auren ki kafin sanda zai koma kinji na fad'a miki, tashi ki tafi" Jiki ba kwari ta mik'e tabar falon cike da tashin hankali, Dan Allah ita ta ina zata vara fidda miji a cikin sati d'aya kachal, sati d'aya fa kuma tasan kome zatayi bazai canza daga yanda yace sati d'ayan ba, Bayan fitan ta ne Baba Usman yake ba Umma labarin cewa akwai wad'anda sukazo neman auren Moon din a wajen shi baya son taga kamar ya mata dole ne shi yasa ya bata dama in akwai wanda take so to ta gabatar dashi dan babu fashi indai Allah ya kawo Abba Ahmad lafiya tofa bazai bar k'asa ba sai sun kammala zancen auren da yaran, Sai dai kuma kids Umma ta tambaye shi waye ke neman auren na Moon bai fad'a mata ko waye ba sai ma k'okarin d'auke hankalin ta da yayi da wani hirar a sanda ya shaida mata cewa yanzun hakan isar su Zaria Hajiya ke jira dan suje su nemar ma AK auren Meenal a wajen iyayen ta maza, Ita ko sosai tayi farin ciki dajin labarin cew AK ne keson auren Meenal wannan karon, Taso ta kawo mishi zancen Sarki da yake son Moon sai kuma ta hana kanta, Bayan Ummah tabar wajen Baba Usman wajen Moon ta wuce dan tana buk'atar magana da ita, "Maimoon kin daiji abinda Baban ku yace koh? Sanin kanki ne kuma sati d'ayan nan daya diba miki yana ciki babu wani sauran uzurin da zai miki, Maimoon nidai nayi miki sha'awar ki auri Lukman bama wai dan saboda kasancewar shi yaron yayata ba ah ah sai dan na yaba da tarbiyar shi da kuma soyayyar shi gareki, amma tunda kince bakya son shi bazan miki dole ba sai dai zan baki shawara duk mijin da zaki gabatar a gaban iyayen ki ina son ki fara natsuwa ki tabbar da cewa shin kina son shi har cikin zuciyar ki ko ah ah" Ta d'an bata shawarwari kafin ta fice tabar mata d'akin, Ita dai wallah tana cikin tsaka mai wuya domin dai tunda Sarki ya shigo cikin rayuwarta tayi fatali da duk sauran samarin da suke ta mata naci a baya, Sai yanzun data riga ta gama Koran kowa ne kuma za'ace a cikin sati d'aya ake buk'atar ta fidda mijin aure? A wannan ranar ma Sarki yazo wajen ta hira sai dai kuma tun zuwan shi ya gane akwai abunda ke damun ta amma juyin duniya yayi da ita akan ta fad'a mishi mike damunta tak'i, hirar ranar dai babu armashi haka suka rabu ya mata Sallama akan sai sun had'u a zaria. Shi kuma sarki tsakanin shi da Teemah yanzun kam komai zam zam dan bakin kokari Teemah tanayi wajen bashi kulawa abinda baiyi tsammanin cewa zata iya yinsu a shekarun baya ba shi takeyi mishi a yanzun, idan kaga yanda suke rayuwa bazakayi zaton cewa ba haka suka rayu tun farko ba, shi kanshi saboda kwanciyar hankalin daya samu harda wata yar k'iba yayi, batun gyaran gidan su na KD ko tuni Salman yayi tsaye komai ya kammala kayan su wanda teemah ke buk'ata tuni aka tura su zuwa KD duk wani shiri na tashi sun riga sun gamayi, kasuwancin Teemah din kuma ta mik'a shi a hannun Azizah ranar da Moon zata wuce Zaria suma shine ranar da zasu wuce KD, Ita Moon daga gidan su kanin ta imran ne ya kaita airports a wajen shiga jirgine kuma suka had'e da Sarki da nashi iyalan wato matar shi da kannin ta wad'anda zasu mata rakiya zuwa sabon gida, Sam Sarki bai shaida mata cewa shima wannan jirgin zaibi ba duk da cewa shine ya biya mata kudin jirgin, kai jama'a wallahi maza dai sun kware a wajen iya munafunci wai ita Moon itace Sarki zai nuna kamar bai Santa ba balle yasan daga inda ta fito a cikin jirgin nan tafa ganshi ya ganta amma sai ya wani d'auke kai sai wani iyayi yakeyi yana wani faman tarairayo tsohuwar matar shi zuwa jikin shi ita kuma sai wani k'ara langwabewa takeyi a jikin shi kamar dai a kanta aka vara d'aukan cikin haihuwa, zama na awan nine amma ji Moon tayi uwa kwana sukayi suna tafiya saboda tsabar kishi gashi kuma duk yanda taso d'auke kanta daga kallon shida matar nashi hakan ya gagara sai dai dasun had'a ido ita kuma take jifan shi da harara, Wallahi mutumin nan ma ya raina ma kanshi wayau dama yasan yana son matar shi har haka shine kuma zaizo yace yana son ta bai kuma ji kunyar idon taba yake kwantar da matar nashi a jikin shi wato hummm ba komai ai wallahi yayi da ya, Ba karamin Hamdala tayi ba a sanda jirgin su ya sauka, bayan saukan su dama so tayi ta d'auki drop kawai ya wuce da ita Zaria kai tsaye sai gashi wai dan munafunci suna sauka Sarki ya fad'a kiranta a waya, tana kallon kiran ita kuma tayi mishi banza, Ganin bata dauki wayar ba shi kuma sai ya tura mata messages yana shaida mata cewa ta jira akwai wanda zaizo ya kaita zaria, Tsaki tayi bayan ta karanta a bayyane ta furta cewa, Allah ya kyauta tahau motar shi ko jirgin nan inda tasan cewa dashi da matar shi a ciki da bata hauba, Duk abinda takeyi yana lura da ita hakan nema yasa bayan su Teemah sun shiga mota ita koma ya koma inda take tana shirin shiga motar da zai kaita zaria, mai da k'ofar data bude yayi ya rufe, "Ba nace miki akwai wanda zaizo ya kaiki ba me yasa bakyajin magana ne, Kwaro kai" Ya kira sunan kwaron bayan yaja hannun ta, "Ka d'auko kayanta kasa a mota ka kuma sallami shi wannan mutumin" Ya k'arasa fad'a yana cigaba da jan hannun ta zuwa motar da kwaro wanda bai dade da isowa wajen ba ya faka a kusa dasu, "Ok Sir" shi kuma kwaro ya furta sai da ya sallami mai motan da wasu yan kud'ad'e kafin mutumin da kanshi ya maida kayan nata zuwa motar kwaron, "Ni dai ka sake min hannu ina ruwanka dani ne wai,ina ce jirgi d'aya muka hawo tun daga Lagos zuwa nan amma ka fuske ka nuna kamar baka tab'a ganina ba sai yanzun ne idanuwan ka suka shaida maka ni?" Ta tambaya cikin fushi tana kwace hannun ta, "Too haka akayi?" Ya tambaya yana dafe gemu, "Ah ah ba haka akayi ba kuma ni bazan bi motar kaba tunda ba kai ka kawoni ba kasa ya maida min kayana cikin motar daya cirosu" Ta fad'a tana dafe kugu bayan ta b'ata fuska ta zunburo baki tana jijjige jijjige, Shi dai kwaro lallab'awa yayi ya shige gefen direba ya zauna cike da mamaki, Shifa yarinyar nan kallon idon sani yake mata sai dai kuma ya kasa gano a inda ya Santa amma kam tabbas ya Santa, To wai ma da Sarki yake ta wani lallab'ata kar dai ace Sarki wani auren zai k'ara, Kashe kunne yayi yana sauraren hirar su a yayinda Sarki yake cewa, "Moon please ki adana rikicin ki ba yanzun ba, naji nayi laifi kiyi hakuri kibi kwaro ya tafi dake idan nazo zan amshi hukuncina" "Moon "kwaro ya maimaita a bayyane, k'ara lekowa yayi, a bayyane ya k'ara cewa, "Wallahi itace, Moon dai k'awar Meenal, Meenal fa matar da Sarki ya saka tome ya had'ashi da Moon kuma?. *Ummiee ce* [9/28, 8:44 PM] zainabusmanummiee584: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 35* Tanaji tana gani haka Sarki ya juya zuwa wajen motar da matar shi take ciki ya shige ciki abinshi bayanda yasata a motar Kwaro ya kulle duk rikicin datakeyi na cewa ita bazata hau motar ba haka yayi kunnen uwar shegu da ita bai k'ara kulata ba tun bayan da yace mata ta adana rikicin ta har su had'u a Zaria , Kallo mai cike da madaukakin mamaki tabi bayan shi da shi har zuwa sanda mota biyun da akazo daukar su dashi suka fice daga cikin airports ɗin, Hummm Namiji dan baban shi, Bata san ya zata kwatanta abinda taji a cikin zuciyarta a dai dai wannan lokacin ba, abunda tasani kawai shine bataji dadin halin ko in kula ɗin daya nuna mata a cikin jirgin ba, to amma idan tace tayi fushi wani dalili take dashi nayin fushin alhalin iya kalmar I LOVE YOU ne kaɗai ya shiga tsakanin su, bayan shi kuma har yanzun ta kasa bashi damar da zai gabatar da kanshi a gidan su balle ya tantance matsayin shi, To ma wai me yasa zataji zafi dan ya nuna kulawan shi akan matar shi? zuciyarta ta tambayeta, ance kasowa dan uwanka abinda kake soma kanka ai itama bazataji dad'i ace mijinta ya kula wata budurwa a gaban idonta ba, Itafa laifin shi kawai take son gani ba kuma komai ya kawo hakan ba sai tsabar kishin shi, batayi zaton zataji kishi irin haka dan kawai ta ganshi tareda matar shiba, "To amma ai yasan ina son shi dan haka dole yasan zanji kishi", sai da ta tura baki gaba kafin murya ƙasa² cike da ƙunƙuni ta Kara cewa "kuma wallahi nima sai na rama" "Na'am kina magana ne?"kwaro dake tuƙi ya tambaya, "Ni ba dakai nakeyi ba"ta amsa mishi tana kauda kanta gefe, shima sai bai ƙara bi takan taba sukaci gaba da tafiya. Shiko Sarki a gefen shi dariya ma moon ɗin ta bashi, wai me yasa su mata basa son zaman lafiya ne wai? Ita yanzun tana fushi dashi cewa bai kulata ba duk da cewa ya ganta, to fisabilillah wani irin neman magana ne wannan? To so tayi shikenan kawai daya ganta d'in sai yabar matar shi da nata ahalin ya dawo gefen ta ya tare bayan kowa yana da mazaunin shi ko me take so yayi? To idan ma ya kulata me take so yayi matane? Ita da kullum take nuna cewa babu komai a tsakanin su tunda KO zuwan da yakeyi gidan su a sace take fitowa bata son asan cewa yana zuwa wajenta, Humm gaskiya rikicin mata sai su ita nata ma wasa ne bata san cewa inda ace matar shi tasan abinda yake tsakanin shi da itaba da Allah kad'ai yasan kalar tashin hankalin da zasuyi, shi bai shirya yin fitina dako wacce daga cikin suba in jarumta take son nunawa ta bari tukun har zancen auren su ya tabbata sai ya tabbatar da jarumace ita. Sak'o ya tura ma Moon d'in kamar haka "Kar kiyi fushi Baby zan kiraki idan Allah yasa kun sauka lafiya, ya kike" Koda saƙon shi ya isa cikin wayarta sai da ta karanta shi ta ƙara mai maita shi kusan sau uku, to mema yake nufi da cewa kar tayi fushi? To in tace tayi fushi ma ai bata da dalilin yin fushin wacece ita a wajen shi? menene matsayin ta? sune tambayoyin da take buƙatar amsar su daga gareshi, to dan Allah a yanda yake nunawa ne zata wani fito kai tsaye tace mishi iyayenta sun bata sati d'aya ta fidda mijin aure kuma ita shi zuciyarta ta zab'a, Tunda harta yarda ta kula mai mata ai dama tasan dole zata fuskanci abubuwa fiye ma da wanda yayi mata a yau, "Nace kiyi hakuri" ya kara tura mata, Ita kuma sai ta tura mishi amsa kamar haka, "don't Baby me, i am not your Baby😒" Bai ƙara tura mata ko wani saƙo ba tun bayan daya karanta amsar data tura mishi , dan yaga alaman rikici takeji da gaske, Acan gidan Sarki kuwa yan Zaria ne maƙil waɗanda sukazo domin tarewar tun daga kan iyalan gidan Malam yan gidan su da kuma yan uwan Uwar gida sun kammala gyaran gidan tsaf sai isowar masu gidan kadai sukeyi, dan haka koda suka isa babu ɓata lokaci akaci gaba da gabatar da walima yan Zaria basu bar gidan ba sai yamma sukabar masu gidan suna huta gajiyar tafiyar da sukayi kafin wucewar su kuma saida Malam Sulaiman suka zaunar dasu suka musu nasiha akan hak'uri da kuma zaman lafiya a tsakanin su especially its Teemah da bata da kowa a garin sai Mijinta da yaranta Uku wadanda Uwar gida ta dawo mata dasu hannun ta, to muma dai sai muce Allah ya zaunar dasu lafiya. Zaman shiru akayi a cikin mota tsakanin Kwaro da Moon babu wanda ya kula Wani har sai da suka isa jaji, fakawa yayi a kofar wani shagon da ake saida snacks a cikin motar ya barta ya shiga cikin shagon, bai jima ba ya dawo ya bud'e gefen shi ya shiga saida zauna kafin ya juya baya ta gefen da take ya mik'a mata ledar hannun shi, "Sarki yace bakici komai ba" Amsar ledar tayi bayan ta mishi godiya, shidai har yanzun bai dena mamaki ba, bai k'ara tabbatar da cewa lallai Moon din da yake hasashe bane har sai da bayan isar su Zaria ya tambayeta Ina suka nufa ita kuma ta shaida mishi da cewa unguwar malamai zai kaita, a gidan Baba Malam ta sauka wajen Mommy Hauwa saida taci abinci ta huta kafin ta kira Meelat ta tambayeta suna inane? Ita kuma taje ta same su. Wannan shine abinda ya faru, tunda ta sauka kuma taki d'aukar wayar da Sarki yake ta faman jera mata kira da tarin sak'onni, ***** "Yanzun Meenal idan Bash yazo wajen ki wani irin tarba zaki mishi? " Maryam ce ta k'ara jefo tambayar jin dukan su sunyi shiru, Ajiyar zuciya mai nauyi Meenal din ta sauke, "Zanyi murna da ganin shi mana, koba komai nasan ya damu dani sai dai ni kuma a yanzun bana jin komai a kanshi, ba kuma wai Ina kinshi bane ah ah Bebs please let's close this chapter I really don't want to think about it anymore, ke Moon wai ma uban me ya wani kaiki zuwa ki sauka a unguwar malamai bayan kin san cewa ni ina nan?" "Saboda bikina tazo shi yasa dole zata zauna kusa dani har a gama komai idan ta kaini gidan mijina saita dawo nan" Meelat taba Meenal amsa tana hararar ta. Washe garin ranar ne kuma suka gabatar da event din da suka shirya ma Meelat a school , kamar yanda suka shirya surprising dinta takoyi mamaki kwarai ta yanda har suka shirya komai na program din batareda sanin taba, hakan kuma bai hanata nuna dad'in taba sosai domin ba iya friends dinsu na cikin makaranta bane kawai suka samu damar halartar wajen harma da wasu daga cikin tsoffin k'awayen su na primary secondary dama yan uwa na kusa, sun shirya abun ya tsaru sosai kuma Meelart din ta samu tarin kyaututtuka daga abokanan arziki, anci ansha anyi raha haka kuma anyi ma Amarya fatan Allah ya basu zaman lafiya ita da mijinta a gidan auren su, daga school da aka watse taro dukan su unguwar malamai suka wuce, wanda hakan kuma yasa Meenal bata samu damar komawa gidaba dole a nan unguwar malaman suka kwana. Shiko AK a gefen shi tun rana yake faman jerama wayarta kira sai dai kuma ga mamakin shi wayar zatayi ta karane kawai har zuwa sanda zata gaji ta yanke batareda an d'auki kirar ba, Yasan cewa dole zatayi busy saboda program d'in dan haka sai ya mata uzuri da zaton ko idan tazo taga tarin missed call dinshi ita ma zata neme shi daga baya, Sai dai kuma abin haushi haka aka wuni zungur ko sau d'aya bata kira ba shima kuma daya gaji da jiran kiran nata ya k'ara kira bata dauka ba daga karshe ma sai aka dunga fada mishi cewa wayar tana kashe, Yaji fushi sosai dan ya shak'a domin dai ta fita gidane yau d'in da sassafe ko neman shi batayi ba balle suyi sallama, Messages din safe daya tura mata ma bata bashi reply ba koba komai ai yaci ace ta kira shi taji ya yake amma batayi hakan ba, shi kuma ya yarda girman ya kirata tak'i d'aukar wayar d'auriya ya aro ya d'aura ma kanshi dan so yake yaga iya gudun ruwan ta in har ba itace ta kira shiba to bazai nemeta ba wannan shine hukuncin ta. (Bari mu koma gefe mu gani zai iya k'in kiran🤷🏻‍♀️) Ita KO gaba d'aya yau d'in yanda abubuwan suka sha mata kaine yasa dole ta fita daga wani batun d'aukar wayarta ta duba ko ya kirata ba kuma wai dan ta manta da batun shi bane ah ah komai takeyi yana nan mak'ale a cikin zuciyar ta kawai dai bata son ta raba hankalin ta biyu ne dan shi idan ya kira waya bai san yayi magana na minti d'aya ko biyu ya yanke kira ba, ah ah ko bazaice komai ba haka zai ajiye wayar kuma yace dole sai ita ta mishi hira, yar karamar wayarta ce a tareda ita wayar da shi AK yaketa kira a cikin mota ta barta k'aramar kuma shi bashi da wannan number din, Bata waiwayi babbar wayar ba sai da dare, koda ta d'auko ta kuma ta dad'e da mutuwa dan haka sai bata damu da kunnawa ba kawai sai ta mak'alata a caji sukaci gaba da hirar yanda taron ya k'ayatar ita dasu Moon. Duk yanda ranshi ya b'aci na rashin kunna wayar nata haka ya daure da dare yayi kuma kasawa yayi ya tsare yana jiran ta dawo gidan ta fad'amishi dalilin ta na kama ta kashe amma har k'arfe 10 na dare ya wuce basu ba alamar su, gaza hak'uri yayi yana ciccjiwa haka dai ya daure ya kira wayar Sultana, bayan ta amsa kiran ko gaisuwar da take mishi bai amsa ba ya jefo mata tambaya kamar haka, "Ina Dr take?" koda bai kira suna ba tasan Meenal yake nufi, dan haka sai ta amsa mishi da cewa "tana falon Baba Malam in kai mata wayar ne?" "Me takeyi acan d'in ne? Ita Ina takai wayarta Nike ta kira a kashe? " "Wayarta ya mutu babu caji bari in kai mata wayar" "OK kuma idan kin shiga bance ki bata wayar ba, kawai dai ki zauna kusa da itane yanda zanji muryarta" Amsawa tayi da cewa to kafin ta tashi ta wuce falon Malam d'in, Ya Sa'eed, Ya Sheikh, Ya Naseer sai Meenal cikon na 4 sune zaune a falon suna hira a tsakanin su Meenal da Ya Sa'eed su nasu hirar suna tattaunawa ne inda yake tambayar ta cewa ya suke ciki tsakanin ta dasu Aliyu, wayarta dake caji a gefenta ta d'auko saida ta kunna wayar kafin ta shiga cikin WhatsApp ta nuna mishi chat d'inta da Ya Hashim inda yake fad'amata cewar yana son ta bashi ranar da zaizo gida ya sameta yana son su tattauna wani magana a tsakanin su, ita kuma ta dai bud'e sak'on ne kawai ta karanta amma bata bashi amsa ba saboda bata riga ta yanke inda zasu had'uba, Bata son ya sameta a gidan hajiya ne saboda tana tsoron AK, Eh mana dole tace tana tsoron shi tunda tasan idan yaga Hashim din kai tsaye cewa zaiyi saurayin tane ita bata son ma yaga Hashim din dan tsakani da Allah Hashim dai ya mata tsufa wallahi tasan idan AK ya ganshi ma dariya zai mata, shifa yanzun saboda tsabar samun waje wai har itane zai kafama masu gadin gidan dokar cewa duk wanda yazo gidan su fara tambayan shi wajen wa yazo inhar mutum yace wajen ta yazo to karsu barshi ya shiga su fad'ama kowa waye cewa bata nan, dan Allah jama'a kuji wani k'arfin halifa irin na AK FISABILILLAH haka ake rayuwa gaskiya saurayi a cikin gida baiyi ba wallahi, "To me yasa baki bashi amsa ba, Meenal Ina jiye miki abinda zaije ya dawo fa," ya fad'a murya k'asa² kamar yanda suke magana shida ita d'in tun d'azun babu maijin abinda suke tattauna wa, "Zanyi kokari gobe idan na koma gida ince mishi yazo" "Ah ah kawo wayarki dai ki tura mishi sak'on yanzun" Badan taso ba haka tayi typing ta tura ma Hashim din cewa yazo tudun wada gobe ya sameta da rana dan tasan da rana AK bai cika zama gida ba, "Shi kuma Aliyu fa?" Ya k'ara tambaya, "to ai shi cewa kawai yayi insa rana zaizo mu gaisa,"ta fad'a tana tura baki, "OK tunda abin ya zama haka shima ki tura mishi sak'on yazo gidan gobe ya sameki" "To kai Ya'ya idan dukan su sukazo a lokaci d'aya kuma fa?" "Uhumm Meenal kenan to ke zaki bari suzo duka a lokaci d'ayan ne? Ai kowa lokaci zaki bashi, na tabbatar da cewa dukan su zasu kiraki a goben dan ki basu lokacin da zasu zo su sameki ke kuma saiki basu lokacin daya dace" Suko Ya Sheikh da Ya Naseer suna hira ne akan walimar da aka gabatar a gidan Sarki domin shi Ya Sheikh shi Malam ya wakilta zuwa walimar a maimakon shi sabida daga Sarki har Ya Sheikh din basu wani san juna sosaiba, yanda Sarki ya nunajin dad'in shi da zuwan su gidan nashi da kuma yanda ya dunga nan nan dasu shine abinda ya burge Sheikh d'in har hakan yasa yanzun ya d'auko hirar suke tattaunawa, Koda Sultana ta shiga falon bayan gaisuwa gefen da Meenal take itama ta rab'a ta zauna, a kunne ta rad'ama Meenal cewa "ko dai shima Yayan mu ya shiga sahun zawarawane"tana nufin ya Sa'eed ko shima son Meenal din yake, "Dallah can matsa OK kibani waje yar rainin wayau kawai kuma sai Allah ya saka min" "Allah ya baki hak'uri"cewar sultana tana gyara rik'on wayar dake hannun ta, Sun dade a falon suna hira har zuwa sanda Malam ya shigo kafin sultana ta janye Meenal din daga falon suka koma wajen Moon wacce ke falon Mommy Hauwa rik'e da waya tana dakon jiran kira daga Sarki, Wallahi Sarki yayi mugun bata mamaki wai ita maimoon itace Sarki ya banzatar tun rabuwar su a airport daya tura mata massage lokacin suna hanya har yanzun bai Kara bi takanta ba domin ko message d'in daya saba tura mata unin yau gaba ko sau d'aya bai tura mata message ba kuma bai kirata ba, Tayi tayi ta danne ta nuna irin bata damuba d'in nan amma wallahi maganar gaskiya ta kasa danne hakan, idan ita kuma ta d'auki waya da niyyar ta kirashi sai taji kai inah, ai in ta kirashi to ta fad'i ba nauyi wallahi, dan shirun da yayi ita ta d'auke shi ne a matsayin cewa wato tunda ya koma sabon gida ya tare cikin iyalinshi shi yasa ya manta da ita to ai ba komai domin a sanda zaiyi lokacin ta itama kuma zata rama ne. Washe gari Meenal ta koma gida a daren jiya kuma sam koda wayar ta tayi caji bata damu da cewa bari ta kira AK ba tak'i kiran shine saboda tasan yana iya cewa ta koma gida a wannan daren, Koda ta isa ta tarar da motar shi a cikin gidan ta kuma ji dad'in hakan dan ko babu komai itama tayi kewa, gaza shigewa sashen Hajiya tayi har saida ta juya akalar tafiyar ta zuwa side d'in shi, hannu takai ta bud'e k'ofar amma sai tajita a kulle ta nocking ta farayi wai ko Allah zai sa ya jiyota daga ciki yazo ya bud'e mata, sai dai kuma har ta gaji da dukan k'ofar baizo ya bud'e mata ba, jikinta yayi sanyi sosai harta fara tunanin to kodai yayi fushine tunda tun jiya data fita babu kiran waya ba sak'o, to amma ai koma menene bai kamata yace zaiyi fushi da ita har haka ba koba komai ai yasan dole zatayi busy a jiyan ba gashi yanzun yau ta dawo ba, shine dan wulakanci har ita zata zo tana buga mishi k'ofa amma yak'i zuwa ya bud'e mata dan kawai ya samu tazo ganin shi, aiko yayi da y'a wallahi, juyawa tayi jiki a sanyaye ta wuce sashen Hajiya, Shiko AK dama sunyi da Sultana cewa idan Meenal ta baro unguwar malamai ta kirashi, dan haka tana wucewa Sultanar ta kira shi ta shaida mishi cewa Dr fa tana hanyar komowa zuwa gida, sai da ya duba agogo ya auna dai dai lokacin isowar ta kafin ya taso daga cikin bedroom din shi ya fito falon ya murzama k'ofar falon key, sannan ya koma ya nemi waje ya zauna wayar shi a gefen shi yana jiran isowar ta. Kamar yanda ya kiyasta bata wuce adadin lokacin daya d'iba mata ba ta iso gidan yana kuma jin shigowar motar ta ya mik'e zumbur zuwa bakin window ya yaye labulen wajen yaci gaba da tsayuwa yana kallon ta harta fito daga cikin motar, yalwataccen murmushi ne ya kawata fuskar shi a yayinda yaga ta nufo sashen nashi dan haka sai kawai ya saki labulen ya koma kan kujera ya d'aura kafa d'aya kan d'aya kuma duk bugun da takema k'ofar yanajin ta dan daga karshema tasowa yayi ya lab'e a wajen window yana lekota har zuwa sanda ta gaji da dukan k'ofar ta juya, yayi mamaki da yaga ta k'ara dawowa bakin k'ofar kuma yayi zaton ko zataci gaba da nocking ne sai kuma yaga ta fara danne danne a wayarta babu b'ata lokaci kiran ya shiga, tabbas da ace bai sanya wayar shi a silent ba da asirin shi ya tonu a lokacin dan yasan tabbas zata iyajin k'arar wayar nashi, kira uku tayi bai d'auka ba dan haka dole tabar wajen a fusace. Kamar yanda ya sa'eed yayi hasashe hakan ne ya faru domin da Aliyu da Hashim dukan su sun kirata da safen dan suji lokacin da zasu zo gidan su sameta, Ta shaida ma Ya Hashim cewa zuwa 12 shi kuma Aliyu zuwa k'arfe 2, Dan haka 12 dai dai kamar mai auna lokaci domin ko 12 nayi Isah ya sallama falon na Hajiya cewa Meenal d'in tayi bak'o, bata wani damu ba tunda ai ta riga tasan da zuwan shi dan haka sai kawai tacema Isah ya shigo dashi ita kuma ta haura sama wajen Hajiya dake d'aki ta shaida mata cewa ga ya Hashim yazo gidan zasu gaisa, Hajiya bata wani nuna damuwa ba sai ma cewa da tayi tana mishi barka da zuwa taci gaba da abinda takeyi, Fitowa Meenal din tayi ta sauko k'asa shiko Hashim tun daga kan benen yake binta da kallo dan shifa dama Allah ya sani batun yauba ya dad'e yana kwad'ayin yarinyar nan abinda ya hana shi motsin k'arfi a shekarun baya yasan ko ya nema Malam bazai bashi ita ba, Amma yanzun da take matsayin bazawara yasan bazai sha wahala wajen shawo kan dangiba wajen ganin sun goya mishi baya, Da fara'a ta sauko, "Barka da zuwa ya Hashim ya aiyuka, kayi hak'uri na barka kana jira koh?" "Ah haba dai babu damuwa ai dafatan kina lafiya ya likita ya gidan ya karatu kuma?" Alhamdulillah wallahi ba kasha ruwa ba" ta fad'a tana nuna center table d'in gaban shi wanda aka jera kayan motsa baki, Ruwa kad'ai yakai hannu ya d'auka ya bud'e murfin ya tsiyaya ma daidaici a cikin kofi kafin yakai kofin bakin shi yasha ruwan, "Alhamdulillah" ya fad'a bayan ya gama shan ruwan sai ya maida kofin ya ajiye, "Ina fatan dai zuwan nan nawa bazai zama takurawa a gareki ba"ya furta hakan yana mai kureta da idanu, "Ah haba dai ko d'aya ai saboda nasan bazan takura ba shi yasa nace kazo yau dan yau ne nike da damar zama a gida cikin satin nan ina da bikin Aminiyata" Gyara zaman Babbar rigar dake jikinshi yayi yana k'ara gyara zama da kyau ya fuskance ta, "Wato ainihin abinda yasa kikaji na nemi son ganin ki domin mu dai daita Meenal ba komai bane sai dan in shaida miki sirrin dake cikin zuciyata" Da kallo ta cigaba da binshi tana jin abun wani iri, abun ya mata bambara kwai dan Wallahi shifa Hashim din ba yaro bane amma jibi yanda yazo yasata a gaba ko kunya wai shi a dole yaxo fad'a mata cewa yana sonta, "Kina jina koh Meenal? Kinga dai ni ba bak'on ki bane kin san ni kin san waye ni kin san iyayena, gidana, matana, yara na dama komai nawa duk kina da masaniya akan su, to abinda nike so in shaida miki shine nidai na ganki kuma kinyi min dan haka ina son ki da aure, kar kiyi zaton ko yanzun ne na fara sonki ah ah tun kafin Malam ya badaki ga wancan wanda ya kasa rik'ekin nike son ki ina tabbatar miki da cewa da ace nasan cewa rik'on sakainar kashi zai miki da tun lokacin na fito mun kara mai rabo ya d'auka a tsakanin mu, amma da yike Allah yace ked'in rabona ce shi yasa ya sako min ke salin alin, dan haka nidai yanzun kin san cewa niba yaro bane dan haka bazan juri zuwa hira ba na dai fara sanar miki ne kafin inkai maganar gaban Baba Malam dan bana son abin ya d'auki lokaci" Ku nemo ruwa ku an taya ma yar gidan malam dan zantukan bak'onta dai sun sumar da ita🤣. *Ummiee ce* [9/28, 10:54 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 36* No editing 😒. Lallai ma mutumin nan, Dan Allah kuga yanda yake magana wani isa² kamar ba wanda yazo neman yardarta ba, ah ah magana kawai yakeyi kanshi tsaye abinshi kamar mai bata umarni wai yazo ya fad'a mata ne kafin yakai maganar gaban Baba Malam, to me yake nufi? Kenan so yake yace shi bai damu dajin ko tana son shi ko akasin hakan ba kawai shi gaban kanshi yake son yi, aiko bai isa ba gara ta taka mushi burki tun yanzun wallahi, Dan haka sai kawai itama ta gyara zaman ta tad'an yo gaba kad'an akan kujerar da take kai a zaune, "Ya Hashim ban fahimci zancen kaba, ko kuma dai ince ban gane inda ka dosa ba, naji kana maganar kai zance gaban Baba Malam?" Ta k'arasa kai zancen nata da alamun tambaya itama tana kallon shi, "Eh hakan nike so Meenal tunda har nazo na gabatar da kaina kuma to me za'a jira ai sai akai maganar gaban manya kawai su shiga ciki a tsaida ranar d'aurin aure kinga a kallah ko sati biyu ko uku aka sanya aiba laifi tunda dai ba auren budurwa bace balle ace za'ayi wani dogon shirye shiryen biki"ya k'arasa fad'a yana wani washe baki uwa kwarton daya hango wawan zama, Kai innalillahi wa innah ilaihir raju'un wallahi yau dai da badin tun a gida ba'ayi musu tarbiyar zagin na gaba dasu ba da sai ta duba kafin ta zak'ulo gingimemen k'aton zagin da zata sauke ma bawan Allahn nan, tsabar takaici da bakin ciki ne suka rufe mata ido har bata san lokacin data d'ago kanta tana kallon shi ido cikin ido ta furta mishi cewa, "Nagode kwarai Ya Hashim da yanda ka nuna kana sona tunda gashi har ka iya biyoni inda nike ka shaida min hakan baka b'ata lokaci ba, sai dai ka sani nima bazan b'ata maka naka lokacin kafin in baka amsar kaba, dafari dai kayi hakuri kace ka soni tun kafin aurena da tsohon mijina sai dai kafin kayi wani yunk'uri na subuce maka, a lokacin allah yayi kai ba mijina bane shi yasa ka rasani, To a yanzun ma ina mai bakin cikin sanar dakai cewa hak'urin da kayi a karon farko shi zaka k'arayi a karo na biyu domin tuni wanin ka ya riga ya gabatar da kanshi kuma harma na amsa mishi dan haka kayi hakuri domin dai yanzun d'in ma ka rasani a karo na biyu, dan haka basai kayi wahalar kai maganar gaban iyayen muba na riga na baka amsar da kake buk'ata" tana kaiwa dai dai wajen tayi shiru tana shaqar turaren AK wanda ta tabbatar da cewa duk yanda akayi yana kusa dasu tunda har kamshin turaren shi ya iso hancin ta, Sam bataji dad'in dawowar nashi gidan a dai dai wannan lokacin ba dan ko kusa bata so yazo ya sameta da bak'o a dai dai wannan lokacin ba dan haka duk da yanda idanuwan ta ke kwad'ayin son kallon shi zuciyar ta kuma ke bata umarnin ta d'aga kai ta kalle shi d'in k'iyawa tayi, Yayinda shi kuma Hashim da jikin shi yayi sanyi kalau sakamakon jin kalaman ta ya bud'e nashi bakin ya fara mata magiya da cewa, "Meenal karkice zakiyi saurin yanke hukunci domin kuwa ita mace allura ce a cikin ruwa mai rabo ka d'auka, wata kila shi wanda kike so d'in kila ba alkhairi bane a gareki kuma koma yayane duk yanda wani bare zai soki ba zai soki kamar mu yan uwan kiba, nidai ina sonki shi yasa harna taso na fad'a miki duk da sanin da nayi cewa acan gida kafin Namiji ya tunkari mace dole saiya gabatar da kanshi a gaban iyaye sun amince mishi, koda kikaga nazo nazone saboda in baki naki hakkin a matsayin ki na bazawara wacce ta tab'a aure" A fusace ta yanke shi da cewa, "Eh naji, naji ni bazawara ce basai kayi ta mai maita min ba Ya Hashim amma ka sani kai kaine kake min kallon bazawara su sauran masu nuna son aurena basu tab'a kallona a matsayin zawara ba, soyayyar ka kuma nace bana buk'atar ta domin dai na riga na tsayar da zuciyata waje d'aya ni mace ce ba namiji ba balle ace ina da damar zama da miji sama da d'aya, ina kuma tabbatar maka da cewa koda ace Allah da kanshi ya halatta wa mata auren miji sama da d'aya su zauna dasu a lokaci d'aya to kai dai baka cikin jerin mazajen da zanyi ma kaina fatan yin tarayya dasu, Kai d'an uwana ne dan haka dole in baka girman ka, kayi hakuri ka tafi amma kafin nan ka tabbatar ka cireni a cikin jadawalin matan da kake burin mallaka kana da matan ka har biyu da tarin yara idan k'arin auren ya zama dole babu laifi ka nema a wani wajen amma nidai na yafe dan haka ka gaida gida,"tana gama fad'in hakan ta mik'e ta haye sama abinta ta barshi anan zaune mamakin kalamanta yasa ya gaza tsayar da ita, Shiko AK tunda Meenal ta shaida ma Hajiya zuwan Hisham din ita Hajiya itace tayi kiran shi akan yazo tana son magana dashi, Dalilin Hajiya na kiran shi kuma tayi hakan ne dan yazo ya ganema idon shi Hisham din saboda ma girman kai yasa yayi zaton cewa shi shikad'ai ne yake da burin mallakar Meenal d'in, sauran dalilan ta na aikata hakan kuma ita tasan kayan ta, idan taso muji zuwa gaba zata fad'a da bakin ta kamar yanda har yanzun bata shaida mana yan da sukayi da Yusuf a lokacin da ya kai mata labarin son da AK yakeyi ma Meenal ba, Shiko AK shi yayi kyakyawan ji da gani domin dai Allah ne yaso shi dan saura kad'an jinin shi yayi hawan da babu shiri a sanda ya kunno kai cikin falon ya iske Meenal d'in shi zaune wani garjejen k'ato na koro mata bayanan soyayya, jinginewa a bango yayi ya samu yayi tsayuwar d'aukar posta dan haka duk abunda suka tattauna kaf a cikin kunnen shi, Tana shigewa ya juya ya fita a falon shima can bakin gate ya koma yana jiran fitowar Hashim d'in, Shiko Hashim ciccibawa yayi ya mik'e bayan ya fito motar shi ya bud'e ya d'auki ledar kayan siyayyar daya mata ya k'ara komawa cikin falon Larai data fito daga kitchen dan kwashe kayan motsa bakin da aka ajiye mishi yaba ledan yace ta kaima Meenal shi kuma ya fice daga falon ya koma motar shi ya kunna yabar gidan, "Tun yaushe mutumin nan ya fara zuwa gidan nan bani da labari?" AK ne yake tambayan masu gadin gidan, "Wallahi yallabai mudai yau muka fara ganin shi bai tab'a zuwa ba sai yau" "To daga yau sai yau so nike wannan ya zama zuwan shi gidan nan na farko kuma na k'arshe, kuna jina koh" ya fad'a yana rike kunnen shi guda d'aya, "Sorry Sir" suka had'a baki wajen fad'a, "Bana so in k'ara ganin shi yazo gidan nan ko yazo karku bud'e mishi gate duk kuma wanda ya yarda ya taka dokar nan to ya shirya barin gidan nan domin daga ranar ya gama aiki a gidan nan kunji na fad'a muku" Fuuuu ya juya ya wuce sasan shi duk da hakurin da suke ta faman jera mishi, Koda ya shiga d'akin shi kasa samun nutsuwa yayi sai faman jeka dawo yakeyi, Wai dama haka masoyi yakeji idan ya tarar da wani a tareda masoyiyar shi, domin dai shi d'azun ji yayi kamar numfashin ne yake son barin cikin k'irjin shi, "Kai ina wallahi bazai yuwuba bazai tab'a yuwuwa in cigaba da zuba ido maza suna kaima Abinda Nike so farmaki ba," ya fad'a a fusace yana shurin kujerar dake kusa dashi da kafar shi da karfi har sai da kujerar ta matsa daga mazaunin ta, Ruwan sanyi ya d'auko ya kafa gorar a baki sai da yaji ruwan ya k'are sannan ya yarda gorar, shi bai san me yasa da zarar ranshi ya baci sai mak'oshin shi ya k'afe ba har sai ya nemi ruwa yasa kafin yake jin dama², Yaso ya fita yaje ya doka mata warning itama sai kuma yaga to ai a cikin abunda ya faru babu laifin ta tunda gashi da kunnen shi yaji sanda ta fad'ama mutumin cewa ta fidda miji, tashi yayi ya fice daga gidan gara ya shiga cikin mutane k'ila hakan zaisa zuciyar shi ta sarara, Ita ko Meenal koda ta shiga d'aki Allah ya sani kalaman Hashim sun b'ata mata rai dan har kuka saida tayi, babu kalmar daya b'ata mata rai irin yanda ya dunga maimaita kalmar bazawara a kanta, Eh taji ita zawara ce amma aiko zawarar tana da yancin da namiji zai bita da lalama wajen neman soyayyar ta bawai ta karfin tsiya ba,ita dai wannan aure ya zame mata auren bacin suna da ace ba'ayi mata shiba da har yanzun tana nan da cikakken darajarta matsayin cikakkiyar budurwa, sab'anin yanzun da dole sai an danganta da sunan bazawara, shiru tayi tana tuna irin yanda AK ya dunga tafiyar da ita cike da tsantsar kulawa kafin ya furta mata kalmar soyayya haka ma yanzun yanda baya iya boye adadin son da yake mata dan ma dai ita da take dan kakkaucewa shima da yake matsayin matashin saurayi, Amma kuga Hashim please tsofai tsofai dashi shine zaizo ya fad'a mata magana son ranshi yana kaskantar da ita a gaban idonta, wallahi wannan ta tabbatar da cewa koda kaddara ta aure ta gifta a tsakanin su ba lallai ne ya iya riketa da kyau ba, AK yazo kuma ta tabbatar da cewa yagan su shi yasa bai shigo falon ba ya koma, Wama yasani ko ita yazo dubawa yaga kota dawo tunda jiya basu had'uba d'azun kuma dataje side din shi tayi ta nocking baya nan, gashi ya dawo da farin ciki yazo ya cimma bacin rai ta sani cewa dole zaiji ba dad'i, Kafin ta ankara a zaman da tayi cikin d'aki sai kiran sallan k'arfe biyu ta jiyo daga masallaci dake k'ofar gidan, Gabanta ne ya fad'i yanzun kuma saura Aliyu shi kuma yaxo taji shima me yake tafe dashi, Lallabawa tayi ta shige ban d'aki tayi tsarki kafin ta d'aura alwallah ta fito ta tada sallah, Mintoci kad'an da idar da sallanta Hajiya da kanta ta leko cikin d'akin nata, "Idan kin idar ki sauko k'asa kina da bak'o" Yankewa gaban Meenal din yayi ya fad'i har saida taji marar ta ta cika da fitsarin tsoro, bata san tsoron ko na minene ba, shin tana jin tsoro ne kar AK ya k'ara zuwa ya ganta da wani? Ko kuma abunda shi Aliyun zai gabatar mata take tsoro? Ya riga dai yazo babu kuma yanda za'ayi ta doje tace bazataje ba dan haka dole ta mik'e sai da ta koma tayi wani fitsarin dan mitsil kafin ta fito gaba d'aya jikin ta babu wani karsashi a tareda ita, Ya Sa'eed ne yama Aliyun rakiya dan haka su biyun ta samu zaune suna hira a tsakanin su, bayan gaisuwa ta buk'aci data kawo musu ruwa shi Aliyun ne ya dakatar da ita da cewa ta barshi kawai, Fita Ya Sa'eed yayi daga falon yana amsa waya wanda kuma yayi hakan ne dan yabasu daman tattaunawa a tsakanin su, "Hajiya Meenal likita bokan turai, yau dai gani a gaban ki dafatan dai kinyi farin ciki da zuwan nawa?" Murmushin yak'e tayi mishi, "Ba dole inyi farin ciki ba tunda bawa zai kawo gaisuwa wajen uwar gijiyar shi, ko ka manta cewa nice dai Gimbiya Aminatu uwar d'akin ku kanawa?" "Wane ke yarinya yita kanki maza ne a gaban ki" "To yayi yanzun dai me matar ka ta bayar ka kawomin, kuma shine baka taho min da yarona ba" Dariya yayi kasancewar shi mutum mai yawan fara'a, "Saurin me kikeyi haka, indai yaronki kike son gani ai kamar yaune in kinso kina iya rik'eshi ma ya zauna a wajen ki nasan uwar shi bazata hanaki shiba niko dai dama kin san bani da tacewa kune iyayen d'anku" Shiru tayi bata amsa ba tana d'an murmushi, hakan ne kuma ya bashi damar kiran sunan ta, "Meenal gani nazo duk da cewa ni na nemi ki bani damar zuwan nasan zakiji mamakin dalilin zuwan nawa" "Ah haba dai wani mamaki kuma dan kawai za'a sada zumunci, ai naji dadi sosai wallahi kaga tunda na dawo nan yanzun bana sanin wad'anda sukazo, Kamar dai kai kaga da ace baka fad'amin ka shigo garin ba da har sai kayi kwana kinka ka koma bani da labari k'ila da sai dai daga baya ko zanji amma daka nemeni bagashi kazo mun sada zumunci ba" "Eh kinyi gaskiya kam to Allah ya bamu ladan dake cikin sadar da zumuncin" Ameen suka amsa baki d'aya, "Meenal wannan zuwan da nayi wajenki zuwane na musamman domin ina so mu tattauna ne in gabatar miki da wani abunda nike ganin cewa ya shafi nidake, yarda da kuma amincewar ki nazo nema domin dai duk da kasancewar ki yar uwata bazan so hakan yasa a miki dole a kaina ba, ni ba kowa bane kamar dai yanda kika sani ne suna na ALiyu Jibril kuma ni d'in ma'aikacin banki ne ina zaune a garin yola nida matata da yarona d'aya, yau kuma nazo wajen kine dan in gabatar da kaina a matsayin saurayin da yake fatan samun amincewar ki kafin ya shiga cikin sahun manema auren ki, Nidai na ganki ne zuciyata kuma ta gamsu da tarbiyya da tsarin ki, babu wanda yamin tallah ah ah nidai naga Abinda nike so shi yasa na biyo Meenal ina sonki ina kuma fatan idan akwai alhairi a tsakanin mu Allah ya shige mana gaba wajen tabbatuwar aure a tsakanin mu, ina fatan Allah yasa wani bai rigani ba, kamar kuma yanda na fad'a miki ne bazan miki dole ba inhar kinji bakya ra'ayina ki fad'amin duk da hakan bawai yana nufin zanyi saurin sarewa in jaye kai tsaye bane ah ah zanyi ta gwada sa'ata dan ban sani ba ko kila rabon samun naki yana nesa bane" Shiru tayi yayinda a cikin zuciyar ta kuma take cewa, "Shi wannan dan saukin kaine ba irin d'ayan ba amma duk da haka hakuri kaima zakayi dan gara inyima tufka hanci tun yanzun idan nayi sake zuwa anjima zaku iya zamar min kadangarun bakin tulu" A fili ko sai ta amsa da cewa, "Ya Aliyu naji dadi matuk'a ubangiji Allah yabar kauna, nagode da yanda ka nuna kulawar ka a kaina ta yanda har ka iya cireni a cikin jerin yan mata da zawarawan dake yawo a gari ka zab'eni in zamo maka matar ka ta biyu" Washe baki yayi tun bata gama kai karshen kalaman taba ya fara furta, kalmar "masha Allah ³, nima nagode sosai a yanda kika tarbeni" "Ya Aliyu kayi hakuri nasan da gaske kake sona tunda har ka iya baro tarin aiyukan dake gabanka dan kawai kazo ka furtamin cewa kana sona, ka sani nima ina sonka sai dai kuma ni bawai so irin na aure nike maka ba, ah ah ina maka so ne irin na d'an uwa shak'ik'i wanda zai iya tsayawa ya goyama kanwar shi baya wajen ganin ta samu Abinda take so duk rintsi, kayi hakuri da ace kai ka fara zuwa ka gabatar da soyayyar ka kafin wanda zuciyata ta ansaw tabbas da taka soyayyar zan d'auka inbar nashi, dan haka nike mai baka hakuri domin zuciya ta tuni ta zab'i wanin ka Ina fatan hakan bazai tab'a zumuncin muba" Tana kaiwa nan tayi shiru tana binshi da kallo k'asa k'asa, "Amma Meenal ya kamata kije ki fara yin tunani kafin ki yanke hukunci ina ganin hakan zaifi" "Kayi hakuri ya Aliyu gaskiyar kenan na fad'a maka," "Ah ah ni bazan takura kiba zan baki isashen lokaci kiyi tunani zan k'ara tuntuban ka zuwa gaba, na kuma gode da kika tarbeni baki kuma boyemin Abinda yake cikin zuciyar kiba, ni zan tafi" Mikewa yayi sai da ta raka shi har k'ofar gida inda suka faka motar su hango AK da tayi zaune a majalisar shine wanda tsautsayi yakai idonta wajen har suka had'a ido shi kuma ya jefeta da wata k'atuwar hararar datasa hantar cikinta kadawa ne kuma yasata juyawa ta koma gidan babu shiri, yau kam sai ta Allah, Biyo bayan ta yayi tun kafin ta isa sashen Hajiya yasha gaban ta, "Waye wancan kuma? Oh wato na d'azun yazo ya wuce bance miki komai ba shine yanzun ma Kika k'ara gayyato wani har cikin gidan nan dan ki wulakantani?, Meenal idan baki sone basai kinyi hakan ne zaki tabbatar min da rashin son ba, idan kinayin haka kina wasa da lafiya ta ne ko so kike kiga bayana in yaso sai ki kawo wani ko kuma su a cikin su ki zab'i wanda zaki rayu dashi!" Ya fad'a cikin d'aga murya, bai saurara ba ya d'aura da cewa, "Dan kawai nace ina sonki shine kike ta faman wasa da zuciyata, minene laifina dan naso ki? Duba fa ki gani unin jiya gaba d'aya kin hanani ganin ki na kiraki waya baki d'auka ba na tura sako baki bani amsa ba, kin san yanda na damu kuwa? Zuciya ta ciwo take min aduk sanda kikayi nisa dani amma haka nan na danne na miki uzuri tunda nasan kina cikin hidima, dazun na shigo gidan da burin inyi tozali dake haka nazo na iskeki da wani tsohon dake ko kunyar zaman yin zance dashi bakiji ba, kinsan halin dana kasance a ciki lokacin? Wai anya Meenal kina jin tausayina kuwa?" "Ina jin tausayin ka mana kuma dukan su su biyun daka gani ai ba samarina bane dukan su yan uwana ne" "Ki rike jawaban ki domin dai ni ba yaro bane kuma shi wanda yaxo da farkon in baki sani ba duk tattaunawar ku a cikin kunnena naji komai, na kuma tabbatar kema kinji tsayuwata a kanku, Meenal fisabilillahi in so kike ki kasheni ai bakyaso inyi mutuwar kwaf d'aya ba" "Nice zan kashe ka kuma?" Ta tambaya da karamar murya, "To inba so kike kiga bayana ba fisabilillahi awa nawane da wancan ya wuce shine har wani yazo, Badai ni kike so kiga bayana ba? To shikenan ni kuma insha Allah zan kauda kaina daga kanki zan baki dama kiyi iya abunda zuciyar ki keso kafin in waiwaye ki" Yana gama fad'a mata hakan ya juya fuuu ya wuce kafin ta ankara harya shiga motar shi an bud'e mishi gate ya fice daga gidan. *Ummiee ce*✍🏼 [9/29, 6:38 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 37* Abun dai sai gashi kamar wasa amma kuma sai ya juye ya zama gaske domin dai tundaga ranar da AK yafice gidan a gaban ta bai k'ara yarda tayi tozali dashi ba domin gidan ya bari gaba d'aya yayi komawar shi Kaduna abinshi, Ya zab'i yayi nesa da itane dan dukan su su sarara basai yana kusa da ita bane idan tayi wani abun zai gani har ranshi ya baci? To ya tafi ai sai taci Karen ta babu babbaka yanace itace a lokacin baya take tashin hankalin ta akan yan matan dake nuna cewa suna ra'ayin shi, wato ita harma ta samu damar kula wasu samarin harda basu damar zuwa har cikin gida su sameta alhalin shi ko ya nuna yana buk'atar keb'ewa da ita ta fito suyi hira a waje bata yarda shine zata zauna da wasu gardawa daga ita sai su a cikin falo wai sunan sunzo hira wajen ta, gaskiya dai yaji kishi matuk'a. Dan haka tunda har ta b'ata mishi rai yayi rantsuwar bazai kulata ba har sai tayi biko dan yaji mai zafi ya daka domin ai ba mata kad'ai keyin yaji ba zai gani kwana nawa zai d'auketa ta sauke shegen girman kanta ta neme shi. Bai k'ara kiran wayarta ba haka kuma ya soke aika mata sakon nin soyayyar daya saba tura mata sau uku a rana ma'ana safe rana dare, Ku gane horon iyafa iya ita yake son horawa dan kuwa shidai yana da Sultana a gefe ita ke sanar dashi duk wani halin da Meenal din take ciki tun daga ranar daya d'auke mata wuta, idan yaso jin muryarta zai kira wayar Sultana idan kuma yana son ganin ta zai kira Sultana video call ita kuma sai tayi amfani da back camera ta hasko mishi sahibar nashi, Ita ko Meenal Allah kad'ai yasan halin da take ciki domin dai duk yanda takai ga dannewa tana ta boyewa saida abin ya nuna a jikinta karsashin ta da walwalanta duk sai ya ragu laifin kanta kawai take gani da ace bata basu daman zuwa gidan ba da bazai gansu ba balle yayi fushi, gashi a banza ta b'ata mishi rai ta dalilin su alhalin shi kullum burin shi shine yaga ya faranta mata saboda dai kar tayi fushi, a d'an lokacin nan ba k'aramin sanya shi tayi a cikin ranta ba matsayi mafi kololuwa ta kaishi ta yanda batajin zata iya had'ashi da kowa gashi tun tafiya batayi nisa ba ita ta fara b'ata mishi rai dan haka duk sai tabi ta tsanagwami kanta, So take ta kira shi taji yana ina wani hali yake ciki? Yana lafiya ko a'ah duk bata sani ba ashe ji da ganin shi da takeyi a kusa da itama rahma ne? Yanzun da yayi nesa sai takejin kamar bata da lafiya duk ta rasa kuzari da kwanciyar hankalin ta, To wai shi me yasa ma zaiyi fushi har haka ne?, inhar da gaske ya saurari hirar ta da ya Hashim kamar yanda yace ai ya kamata ya fahimci cewa su d'in dukan su basa gaban ta shi dai shi ta zab'a, wato shine yama tattara yabar mata gidan to ai shi kenan tunda haka ya zab'a yama dad'e bai tafi ba yafi ruwa gudu in yaso badai dan yaga tana son shine yasa yake son ya jata a k'asa ba? To soyayyar taci uwata kuma kewa ai bata kisa dan haka can da yawar shi, A wannan halin da take ciki haka ta dunga daurewa tana cigaba da nuna bata damuba suka cigaba da gudanar da sha'anin bikin su a unguwar malamai take uni saboda gyaran jikin da suma sukeyi dan yanzun basa zuwa yawo,su kuma su Maryam ganin shirun ta yayi yawa ne kuma basa ganin tana yawan amsa kira daga wajen AK kamar yanda suka saba sai ranar maryam ta gaji take tambayar ta ko sun samu matsala ne ita da mutumin nata? Bata boye musu komai ba kaf abunda ya faru ta kwashe ta fad'a musu, Ajiyar zuciya Maryam ta sauke bayan ta gama jin jawabin Meenal din, "Bebs me yasa to baki kirashi kin bashi hak'uri tun ranar ba? Kema dai kinsan cewa ko waye dole zaiji babu dad'i" "To me zance mishi idan na kira shi?" Ta tambaya da karyayyar murya dan Wallahi a dame take kwarai, "In ma kina jin shakkun karki bashi hakuri ajin ki ya zube ne to ki kirashi idan ya d'auka sai ki basar kawai kice kin kirane kiji ya yake" Meelat ce tayi magana wannan karan dan tasan tsabar jin kaine ya hana Meenal d'in kiran shi tun tuni, "Sister don't call him just send him a short text message,"cewar Sultana, "Me yasa bazata kira shiba bayan kuma tsakani da Allah ita ce bata kyauta mishi ba ai kamata yayi ta kira ta bashi hak'uri tun sanda Abinda ya faru shine zakice ta tura mishi sak'o" Maryam ta fad'a tana jiran jin dalilin da yasa ita Sultanan tace kar Meenal ta kira shi, "Will You please let me explain my self ko in barku da iyawar ku?" Sultanan ta fad'a tana wani shan kamshi, irin ita a dole tana nemar musu mafita, "Ok muna jinki"suka fad'a a tare harda Moon wacce tunda suka fara hirar bata sa baki ba saboda ita damuwar da take ciki yaci uwar na Meenal ya shanye domin ita meenal ai tasan matsayin ta a wajen nata masoyin ko yau taso gabatar dashi a gaban iyayen ta kuma tasan da gudu zasu amince amma ita fa??? Gaba d'aya tun zuwanta komai yake shirin zama tarihi a tsakanin ta da Sarki, alaqar da taso ya yanke a tsakanin su tun tuni shine bai yanke ba sai yanzun da yasan cewa ya riga ya mata dashen son shi a cikin nata zuciyar! Me yasa wai maza basa da adalci ne? Wannan abun shita gudarma kanta tun farko shine kuma yasa tun farko tak'i sakin jiki dashi tayi ta d'ari² tana kakkaucewa dan dai ya rabu da ita amma yak'iya, Bai barta ta huta ba har saida ya riga ya gama siye zuciyar ta, bikin Meelat yau saura kwana biyu sannan ita kuma kwana 7 din da Baba Usman ya bata tuni ta cinye shi, jiya da dare kuma shida kanshi ya d'auki waya ya kirata yana k'arayi mata tuni akan maganar su cewa karta manta dai ta fad'ama duk wanda ta tsayar cewa ya shirya turo iyayen shi cikin satin nan suzo su gabatar da kansu, Ta tabbatar da cewa duk wani bak'on da zaizo ma Hajiya biki tabbas jibi idan Allah ya kaimu kowa zai halarto nan Zaria to wani amsa zata ba iyayen ta a sa'ilin da suka zaunar da ita danjin wata tsayar a matsayin mijin auren ta? Wallahi tana son Sarki bata tabbatar da cewa ta kamu da mugun son shiba sai bayan zuwan ta garin nan da shi kuma yayi dif ya d'auke mata wuta ba kira ba sak'o, To wanda ya wofantar da ita irin haka taya zata gabatar dashi ma iyayen ta? Idan suka kirashi shi kuma yanuna musu cewa baya ra'ayin ta ya zatayi kenan, Me yasa rayuwarta ya juye upside down cikin kankanin lokaci haka?, Tayi shiru tana sauraron shawarar su Sultana zuwa ga Meenal ne dan tasan ba iya Meenal dince kad'ai zata amfanu ba itama tana buk'atar shawarar sai dai kuma ta yanda zata bud'e baki ta shaida ma Aminan nata halin da take cikina ta gagara yin hakan duk da cewa ita Meenal din bata boye mata komai na alaqar ta da AK ba ta kuma tayata murna domin duk wanda yaga masoyan biyu yasan sun dace da juna kwarai, sai dai ita kuma ga abin yana matukar damunta a cikin zuciya amma ta kasa sharing din shi ma kowa a cikin su, to mema zatace musu bayan shi dayace yana son nata yanzun kuma ya juya mata baya, *** Daurawa Sultana tayi da cewa, "Tsaya kiji sister kin san dai ba kece budurwa ta farko da ta fara muna mishi soyayya ba, dan haka na tabbata yasha jin kalaman ban hakuri a wajen yan mata daban daban tunda ya saba kullum suke neman shi dan haka komai yayi gani zaiyi akan dai dai yayi shi, Idan kika sake kema kika shiga sahun su kika ce a duk sanda kuka samu sab'ani haka kema zaki dunga jera mishi kira dan ki shawo kanshi tofa gani zaiyi baki da banbanci dasu, Ki saurareni da kyau, bawai ina nufin cewa koda ace kece kikayi laifi kiyi mursisi ba, ah ah in kinyi laifi dole ki bayar da hakuri amma bada rawar jiki ba, ke macece kina da naki darajar dole kuma ki rik'e darajar ki, dan haka dole salon ban hakurin ki ya banbanta, akwai banbanci wajen ban hakuri tsakanin saurayi da budurwa da kuma mata da miji, ke yanzun bakuyi aure ba dan haka salon saurayi da budurwa zamu d'auka, kamar yanda nace d'azun sak'on text zaki tura yanzun ki d'auki wayar ki, ba rubutu mai tsayi zakiyi ba ki rubuta mishi cewa (kana lafiya) sai ki tura mishi, Idan ya maido amsa hakan yana nufin cewa fushin nashi bamai nisan zango bane, idan kuma mukaji shiru sai muje mataki na gaba ina fatan kun gane🤷🏻‍♀️" Ta k'arasa fad'a tana kai gorar fanta bakin ta ta kurb'a, A yayinda Meenal ta d'auki wayar ta tana rubutu itama Moon nata wayar ta d'auka ta rubuta same abinda Sultana tace ta tura ma Sarki itama kamar yanda Meenal ta tura ma AK, Ita ko Meelat tasowa tayi tsam ta zauna a inda Sultana take zaune tana jiran Meenal ta cika umarni ta k'ara d'aura mata wani karatun, Dafa kad'unta Meelat tayi "Sultana a ina duk kika san wad'an nan abubuwan? Abubuwan da kikeyi suna bani mamaki da kuma d'aure min kai manyan cen ki yayi yawa" Hannun Meelat din sultana ta kama ta sauke shi daga kan kafad'arta, tana yatsina fuska tace "ku dai da kuke son mai da kanku baya sai kuyi ta zama waye yace muku iya ilimin boko da islamiya kad'ai mace take buk'ata dan ta rayu cikin salama ne? Baku san dole mutum yana bukatar ilimin zama da mutane ba, to ilimin zama da mutane ne wannan domin yana da kyau kasan dawa kake zaune ko dawa zaka zauna dan kaci maganin zama dashi, AK bai tab'a soyayyar gaskiya da gaskiya ba sai a yanzun Meenal itace first love d'in shi amma sai wasa takeyi da damarta ta kasa gane cewa abubuwan da takeyi shi Sabon abune a wajen shi domin dai tsayin rayuwar shi ya saba mata ke kod'ashi suna kware mishi, Sai gashi yanzun da take da damar d'aurashi akan nata tarbiyar ya kuma biyu mata yanda take so shegen wauta yasa tun tafiyar batayi nisa ba tana ta faman kwafsawa, wallahi ina jiye miki kar abubuwan da kike mishi susa yayi dana sanin fad'awa soyayyar ki.... " Katseta Meenal din tayi cikin fushi da cewa, "To ni uban me nayi mishi kedai dama tuntuni na gane kinfi son shi dani" wayarta da yayi k'arar shigowar message ne ya katseta itama har rige rige sukeyi wajen d'aukar wayar su duba ko sakon shine ya shigo, Maryam ce tayi nasarar d'aukar wayar, "Wallahi shine" ta fad'a har hannun ta yana rawa a yayin bud'e sakon, "Did you miss me?" Shine abunda ya tura, dan haka a fili Maryam ta karanta dukan su suna sauraren ta, "Kinyi kewar shi? " itama Sultana ta maimata da k'aramar dariya a muryar ta, "Wallahi AK yana sonki sosai Meenal karki yarda kiyi sakacin da zaki rasa shi kinga nifa tsayin lokacin nan tsumayin kira ko sak'on ki kawai yakeyi gashi dai kin gani sakon ki na isa gareki ya dawo miki da martani alamun da ke nuna shima yana cikin kewar ki" Rufe fuska Meenal tayi da tafukan hannayen ta tana dariyar jin dad'i, koba komai tunda har ya dawo mata da amsa tasan cewa yana lafiya dama damuwarta tasan ya yake, Daga gefen Moon itama nata amsan Sarki ya dawo mata dashi ga abunda nashi sakon ya kunsa shi kuma, "I miss you soo much My Moon please allow me to come and see you, can i call to hear your voice now please" Yalwataccen murmushi ne ya bayyana a fuskarta itama, sai dai bata bashi amsa ba tana jiran jin tabakin sultana tukun na, D'aurawa Sultanan tayi da cewa yanzun dai tunda mun tabbatar yayi kewa shima to ki gyale shi karki maida mishi ko wani amsa mu bashi mintoci mu gani ko zai k'ara turo wani sak'on" "Kuma😳 to idan kuma ya k'arayin fushi fa?" Meenal din ta fad'a tana kallon Sultana a marairaice, "Bazaiyi fushi ba ina mai tabbatar miki da cewa kodai ya kiraki ko kuma ya turo wani sak'on" Kamar yanda Meenal ta natsu tana jiran tsammani haka ita ma Moon dukan su tsammanin suke jira, maryam ce ta yanke shirun da cewa "Sultana kina gani har hanji ne?" Dariya sosai Sultanan ta fashe dashi, "ni kuna bani mamaki wallahi" "Ah ah kedai kike bamu mamaki abin mamaki kuma wai a hakan baki da tsayayyen saurayi to me kike jira" Moon ta tambaya, "I am waiting for Mr right, nima mijina nike son in aura kamar ku dai wanda bazaiji nauyin ko kunyar nuna kaunar da yake min a ko ina ba kun gane ai dan nidai bana son ustazu wayayyen namiji nike so shi yasa har yanzun ban gama tantancewa ba, kunsan kwanaki wani abokin Ya Sheikh ne yaxo wai shi nan ala dole ni yake so" fashewa tayi da dariya tana dukan cinya tace "wai wai wai wayaga Sultana matar ustazu ninja kenan Allah dai ya raba bawa da wahala" dariyar suma suka tayata, Moon ce ta amsa da cewa "kai gaskiya sultana kuna fama da wancan yayan naku, wai Sheikh fa in fad'a muku tunda na sauka a gidan nan wallahi ko sau d'aya bai yarda mun tab'a had'a ido ba, ke ko a hanya muka had'ufa duk'ar da kanshi yake shekaran jiyama wai harda Fauxieyerh yayi wai me yasa ni bana sa hijjab idan zan fita kuma wallahi yanzun ya dena zuwa sashen mommy Hauwa wai saboda ni bak'uwa ce, gaskiya dai yayan nan naku sufofin yan aljannah sak gareshi Allah dai ya bashi mata dai dai shi" Hirar Sheikh din suka d'auko sukaci gaba da caccakan shi sultana tana basu labarin abokin shi da idan zaizo hira wajen ta saiya kwaso littafan addini wai da hirar banzan da zasuyi gara ya d'aura mata karatu abudai kamar a zamanin annabawa, Suna cikin hirar ne wayar Meenal ya k'arayin k'ara sak'on AK ne ya k'ara shigowa wannan karon ma, "Tun ba'ayi auren ba har kin fara yaji daga tudun wada zuwa unguwar malamai, to karki kiyi dare da yawa yau ki dawo da wuri I love you too" ya rubuta daga k'arshe, "Hohoho dan Allah kuzo kuga yanda ake gudanar da wata sassanyar soyayya anan to wallahi yau nikam gidan Hajiya nika kwana yo ina dalili zan tare anan ga inda ake shan madarar love jama'a karfe nawa yanzun?"cewar Sultana Shiko Sarki cewa yayi, "ki shirya tarbata ayau idan na iso zan kiraki see you soon" Hohoho dad'i kamar ya sumar da Moon haka ta dunga ji murmushin fuskarta kwata kwata yak'i d'aukewa, "Kai ku tsaya! Waiku dan Allah baku lura da Moon ba wallahi akwai abunda take boye mana bata so mu sani tunda tazo na lura da hakan yanzun kuma ku kalli yanda take murmushi barrister me kike b'oyewa ne ko kema kin rufta cikin kogin ne?" Maryam ta tambaya tana kada kai da nuna Moon din da yatsa, "Yarsa ido kawai ke dai kika sani ni babu wani abunda yake damuna" Meenal ce ta amsa da cewa "dan allah kyaleta ai kallonta kawai nake ki barta idan tayi wari ai zamuji yarinya in ma fargaban aure kike gara ki bari dan tunda Hajiya ta matsa kema kin san ba fashi gara ma ki zayyano mana naki samarin mu bajesu a teburin shawara mu tayaki zab'e atoh in kuma babu ni zan miki mijin" Ita dai Moon shiru ta musu bata kulasu ba lallai yau idan Allah yasa Sarki ya iso lafiya ga da ga zasuyi shida ita tagaji da boye boye matsayin ta kawai take son sani a yau basai gobe ba, Anayin Sallan Magrib Sultana da Meenal suka wuce tudun wada, ita kuma Moon cigaba da zama a gidan su Meelat tayi saboda idan ta koma gidan Malam bata san yanda zatayi ta fito su had'u da Sarki ba dan ko babu komai itama bazata yarda wani yagan su tare ba, ta kuma tura mishi sak'on Allah ya kawo shi lafiya, A gidan Hajiya ko su Meenal suna isa Sultana tayi mata jagora suka shiga kitchen shinkafa suka samu an girka a gidan dan haka sai ta d'aura mishi tuwo raba hannu sukayi sultana ta dafa tuwon na masara ita kuma ta mishi miyar kub'ewa d'anye bayan sun kammala komai sama suka haura ita dai Hajiya kallon su kawai takeyi bata tambayesu dalilin shigar su kitchen ba balle suce ta fiye gulma gyara zaman ta dai tayi da kyau a falon ta dan tasan dai in ma bak'o zasuyi dole gidan zaizo dan tunda taga Meenal ta dawo gidan da wuri tasan ba'a banza ba, Kwalliya na musamman yau Sultana tasa Meenal tayi itace kuma ta zab'ar mata kayan da zata sanya atamfa d'inkin riga da siketa ta kuma gyara mata fuska da kwalliya duk da kwalliyar bamai yawa bane daga hoda mascara sai jan baki Sultana tayi tayi ta sanya kwalli ita kuma tace a'ah wai bata son ta zaqe da yawa ya raina ta, k'in Saukowa k'asan sukayi sukaci gaba da zaman su a d'aki Sultana tana k'ara ba Meenal d'in shawarwari, Karfe 9 saura sak'o daga AK ya shigo wayarta, "Ki fito ki sameni nan da minti biyu a haraba" Sultana ta mik'ama wayar bayan ta gama karantawa jiki na rawa ta tashi ta isa gaban mirror soson shafa hoda ta d'auka tad'an k'ara gyarawa ta d'auki turaren ta shima ta kara feffesawa ta zura takalmi, jiki na rawa ta fice daga cikin d'akin dan gani takeyi kamar idan ta tsaya b'ata lokaci minti biyun suka cika komawa zaiyi batareda ta ganshi ba, dariya sosai Sultana take mata, wai ba saban ba an fad'a soyayya. Da gudu ta sauko ta fice daga falon ko Hajiya dake tambayar ta lafiya ta sauko da gudu gidan uban wa zataje da daren nan take shirin ficewa bata saurari Hajiyar ba ta fice dan itama tasan tana tsayawa lokaci kawai zata b'ata mata, A harabar gidan taci burki tana gyara zaman rigarta ta kuma yafa gyalen nata a gefen kafad'un ta ta rife k'irjin ta, tana waige waige taga ta inda zai bullo, Shiko dama tunda ya iso gidan shida kanshi ya karkashe wutan tsakar gidan ya kuma ce kar wanda ya sake ya kunna, ita ta fito daga cikin haske ne shi yasa koda ta fito duhun wajen yasa bata ganshi ba yayin da shi kuma yake can gefe yana k'are mata kallo daga cikin d'an kankanin hasken daya rage a tsakar gidan a hankali ya dunga takowa harya k'araso inda take yayinda ita kuma ta hango kawai sai kunyar kanta ya kamata dan tasan da zarar yaga kwalliyarta yasan cewa dan shi tayi dan haka sai ta juya baya taja gyalenta ta rufe fuskarta tana murmushin da bata san dalilin yin shi a wannan lokacin ba, shin najin dadin ganin shi ne ko koh dai, Shiko yana isowa babu b'ata lokaci ya tsaya a bayan ta hannayen shi ya d'aura akan kunkumin ta ya rik'ota ya matso da ita zuwa jikin shi sai dai bai bari bayan ta ya tabi jikin shiba ya kwantar da kanshi a kad'arta daidai kunnen ta ya rad'a mata cewa, "Likita did you missed me?" Ya tambaya da wata irin murya kwantacciya kamar baya son yin maganar, Yummm haka ta dunga jin jinin jikin ta yana gudu daga wannan jijiyar zuwa wata, Wallahi ji tayi kamar ta juyo ta rungume shi tace mishi nayi kewar ka AK, sai dai kuma ita d'in kunya ce ta haifeta dan haka bazata iya aikata hakan gareshi ba, "Ki amsa min mana kewar nawa ne yasa kika gaza hakuri sai da kika nemo ni?" Da sauri ta amsa mishi da cewa "ah ah kamannin fuskar kane dai ya fara bacemin shi yasa nace bari in tab'oka gashi kuma yanzun kazo naga fuskar naka" "Da alama soyayyata ta rikita miki tunani shi yasa kika kira inzo ki ganni ko zaki dawo hayyacin ki kenan" Juyo da ita yayi suna kallon juna ido cikin ido bayan ta d'an sauke gyalenta da tayi amfani dashi ta rufe fuska saiya zamana iya idanuwan ta yake gani, da kad'an² ya dunga matsar da fuskar shi har ya zamana goshin su ya had'e dogon hancin shi ya goga akan nata hancin yana cigaba da kallon tsakaiyar idanun ta, K'asa ya k'arayi da uryar shi, "toya yanzun kin d'auki hoton fuskar nawa dan so nike ki adana shi da kyau a cikin memoryn ki ta yanda bazaki k'ara mantawa ba" Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana kankame jikin ta dan Wallahi ba k'aramin jarumta take gwadawa wajen hana kanta bashi kyakyawan runguma ba, wani iri take ji sosai a jikin ta natsuwar data rasa ne takejin yana dawo mata har bata san ya zata kwatanta yanda takeji ba, Baya ya matsa yana mata dariya kafin yace "to likita na gane wato bazaki iya rikewa ba koh? Nima daurewa nikeyi muje daga ciki kafin a sab'a lamba" ya k'arasa fad'a yana kashe idon shi d'aya da d'age mata giraren shi, Kai jama'a wallahi AK bayaji, dan ba karamin kunya ya bata ba har sai da taji kamar ta nutse a wajen. *Ummiee Zaria* [9/29, 10:49 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 38* A daidai k'ofar falon Hajiyan yaja ya coge hab'ar shi ya dafe kamar mai tunani kafin yana wani fusgewa cike da basarwa yace, "Ni anyama zan shiga nifa da nace sai nayi sati ban shiga falon nan ba kuma adadin kwanakin satin basu cika ba har yanzun dan haka kije kawai saida safe, damuwar ki ai dama na rashin ganina ne koh to gani kin ganni hankali ya kwanta" Juyawa yayi da niyar barin wajen ita kuma da azama ta tari gaban shi, boyayyar murmushin da bata bayyana a fuskar shiba yayi dan dama yayi hakan ne dan yaga shin zata hana shi tafiya ko zata tsaida shin? Da gaske dai itama ta kamu ashe? Yake tambayar zuciyar shi, a fili kuma sai ya fuske yake tambayar ta da cewa, "Yane akwai wani abun ne kuma?" duk'ar da kanta tayi tana wasa da yan yatsunta batareda ta d'ago sun had'a idoba tace, "To bakai bane kawai daga zuwan ka ko zama bamuyi ba zaka wani ce zaka tafi, kuma fa ku lafiyata baka tambaya ba bayan kayi kusan sati ban ganka ba Allah kuwa har ciwo saida na kusayi" Subhanallah ta furta tana rufe baki dan Wallahi subutar bakine ba abunda taso cewa kenan ba, wai miye haka yake faruwa da ita ne duk tabi ta wani rikice a gaban shi kamar wata sabon shigar soyayya salon duk ya gama raina ta, Daure fuska tayi ta kauda kai gefe dan karma ya raina ta ehe, Takowa yayi zuwa inda take ya rik'o hannayen ta duk da yanda take k'okarin kwace wa ya hanata, "Fad'amin meya sameki da baki ganni ba? Baki da lafiya shine bazaki kirani ba? Meke miki ciwo yanzun ko kin warke? Idan baki da lafiya ki dunga kirana kina fad'amin kinji ni kuma komai nikeyi zan barshine in dawo inzo in dubaki lafiyar ki tafiye min komai karki k'ara yarda kiyimin wasa da lafiyar ki" hannun shi d'aya yakai kan wuyanta wai shi nan a dole so yake yaji ko jikin ta akwai zafi, Baya ta matsa kad'an shi mai yasa ya kasa gane cewa ita bata son yana garajen kai hannun shi jikin ta ne? Duk sanda ya tab'a ta jikinta sanyi kalau yakeyi kamar an cirota daga cikin k'ankara, "Nifa na warke kuma nace ka dena tab'ani bana son," "Kin warke?"ya tambaya yana binta da kallo bayan ya cire hannun shi a wuyan nata, "Na warke fa," "To sannu Allah ya k'ara sauk'i yanzun kije ki kwanta saida safe" Ita da take cewa bata son yana tab'ata sai gashi ta rik'o hannun shi a shagwabe, "to zaka wuce kuma baka shiga cikin ba, nayi maka girki fa ko bazakaci abincin dana b'ata lokaci na girka maka ba?" ta tambaya a marairaice, Da mamaki yake kallon ta kafin yace "ni kikayi ma girki wai?" Shiru tayi ba amsa, "Me kika girka min koda yike koma menene ci zanyi tunda ke kikayi, ashe dai ana sona har haka amma da sharad'i bazan shiga inciba har sai kinyi alqawarin cewa zaki bani abincin a baki in kuma ba haka ba ink'i shiga wallahi" ya karasa fad'a yana d'aure fuska, "Kai dan Allah" ta fad'a tana bubbuga kafa a kasa, Shi kuma saiya kauda kanshi gefe kamar bai ganiba, "Nidai dan Allah muje gaskiya in bakaci ba zanji babu dad'i kuma zanyi fushi, indai zakaci naji zan baka a bakin" "Kinyi alqawari? Kuma kar ganin idon Hajiya yasa kice bazaki bani ba idan mun shiga" ya fad'a yana kamo hannun ta suka shiga falon da sallama a tare, Gilashin dake taimaka ma Hajiya wajen ganin kananun rubutun dake cikin littafin addu'oin dake hannun ta tana dubawa tasa yar tsarta ta sauke zuwa kan hancin ta, ta saman gilashin taci gaba da kallon su bayan ta amsa sallamar da sukayi girgiza kai tayi tana tab'e baki kafin ta gyara zaman gilashin taci gaba da karatun ta, AK bai saki hannun Meenal ba har suka k'araso inda Hajiya take kafin ita Meenal din ta zame hannun ta a cikin nashi ta wuce kitchen ta fara kwaso abincin data shirya mishi ta barshi suna gaisawa da Hajiya, fira suke a tsakanin su akan isowar su Abba Ahmad da su Baba Usman dama sauran ahalin gidan da zasu iso gobe, Sai da ta gama shirya abincin akan dinning kafin ta dawo yake, "na gama shirya maka abincin fa" "Ikon Allah wato yan magana dai duk abunda zasu fad'a akan dai dai yake, cewa fa sukayi inda ranka kasha kallo, yau ko nice na tabbatar da haka yanzun nan dama ke takara hana kanki sukunin da kikayi daga dawowar ki d'azun kika shige cikin kitchen kika fara girke girke dan munafunci shi kike dafama abinci? Ina fa zaune a falon nan kika kammala amma ko tayi bakiyi min ba alhalin naga dai kayan abincin ba ubanki malam bane ya aiko min dashi, aini tunda naga kin dawo gidan nan da wuri yau dama nasan a rina wai an saci zanin mahaukaciya ashe d'an gudun hijira ne yake tafe, to duk dai ku gama munafuncin ku insha Allah gobe iyayen ku suna isowa zan iza keyar ku gara su tafi can su amso auren ko tarewa ne ayi daga baya dan nidai bazaku jawomin sabon zance da karkata kaiba ina zaman zamana ku maisheni tsohuwar kawai wallahi, Kai kuma ina fad'amaka su kud'ad'en nan da kake ta faman boyon su a cikin asusun bankin ka gara ka fiddasu kayi k'okarin kammala ginin can da kaketa shiririta har yanzun ka kasa kammala shi in kuma wancan gidan hayan zamu kai maka matar duk salmakal, nidai bazan iya gani ba bazaku jamin makantar da ban shirya ma zuwan ta ba, kuma nima ki dibo min tuwon ki kawo min shi zanci" Sim sim Meenal ta wuce ta d'ibo ma Hajiya tuwon ta kawo mata, "Kin daiji kunya meenal nan inda nice nace ina son kimin tuwon nan na tabbata k'ememe zakiyi amma shi kin iya zagewa kika shiga kitchen kika girka mishi" Ita dai Meenal bata kulata ba ta juya ta koma kan dinning d'in surutun Hajiyar ne yasa Sultana saukowa, "Hajiya keda waye kike fad'a da daren nan?" "Nida wa kuwa banda wadan nan su biyun, koda yike kema ai duk jirgi guda ya kwaso ku kwashi kafafuwan ki kiyi gaba ki bani waje" "Allah ya baki hakuri Hajiyar mu, barka da zuwa yayan mu ya kwana biyu" "Lafiya lau sultana ya kike ya shirye shiryen bikin?" "Alhamdulillah ya naku kuma?" "Mun gode Allah zo in aikeki d'akina please" Karasawa kusa dashi tayi shi kuma ya cire key din d'akin ya bata, "Sorry akwai kaya a falo kiyi ma cikin su Kabir magana wani ya tayaki kwaso kayan ku shigo dasu" Amsar key d'in tayi ta fice shi kuma ya gyara zama ya fuskanci Meenal "Bismillah na shirya"ya fad'a yana bude bakin shi alamun ita yake jira, Sai da ta saci kallon Hajiya ta tabbatar da cewa hankalin ta baya kansu kafin ta dawo da hankalin ta kanshi ta fara bashi tuwon a baki, Yana cikin cin abincin Sultana ta dawo ita da Isah ne suka kwaso kayan dan Kabir baya gidan, "Ku ajiye kayan anan" ya fad'a daga inda yake, Bayan ya gama cin abincin falon ya koma ita kuma Meenal ta kwashe kayan takai kitchen ta gyara wajen, ware kayan yayi ya tura ma Hajiya nata gabanta "Hajiya ga naki kayan cin biki ne kuma ga naku nan" "Ah dad'ina dakai wani lokacin akwai iya kamantawa Allah dai yasa ba'a nuna min banbanci ba, da dai ni kad'ai kake ma abu amma yanzun tunda ta kwara ta dawo gidan nan muke zaman kishiyoyi sai ka mata abu sai goma da kudin ka ni banci nera biyar taka ba, Ke sultana matso min da kayan nan kusa dan idan na duba naga naku yafi nawa tsada canzawa zanyi atoh" Bude kayan sukayi kayane tun daga kan atamfa leshi shadda ga kuma takalma da jakunkuna a cikin kayan su Meenal ko harda su d'an kune da sauran kayan kwalliya na mata godiya duka sukayi Hajiya kuma na addu'ar allah ya kara arziki nata kayan ta fara kwashewa tayi ciki dasu kafin Sultana itama ta kwashi nasu ta haye sama ta ba masoyan waje dan su samu damar tattaunawa da kyau, Suna cikin hirar ne kuma wayarta tayi k'ara wanda bata yi tsammanin kiran shi a dai dai wannan lokacin bane ya kirata, ba kowa bane kuma face Sarki, Tayi kamar bazata d'auka ba kasancewar AK dake wajen sai kuma ta hasaso rashin d'aukar wayar kuma yana iya sawa ya zargi wani abun dan haka sai kawai ta dake ta d'auki wayar bayan tama AK "Ya'ya bari in amsa wannan kiran" "Ki gama wayar ki fad'amin dalilin da yasa har yanzun kike kirana da suna Ya'ya bayan ga sunaye nan masu dad'i da masoya ke kiran junan su amma ni sai dai ki wani ce Ya'ya ko dad'in ji babu" "Assalamu Alaikum" ta fad'a a yayinda ta d'auki wayar gaisuwa suka fara gabatar wa, kafin sarki yace, "Nayi laifi shi yasa kike fushi dani koh?" Da sauri ta amsa da cewa "ah ah wallahi Ya'ya ba haka bane abubuwa ne dai suka d'an shamin kai shi yasa ban kira ba amma dama ina da niyyar kira inyi maka fatan alkhairi na tarewa a sabon gida" "Kina gida ne?" Ya tambaya yana katseta, "Eh ina gida" ta fad'a tana Satan kallon AK wanda shima jin tace tana gidane yasa ya kalleta, "Ok to zamu iso gidan anjima kad'an nida kyautar da kikaimin Allah yasa dai Hajiya batayi bacci ba dan ina son mu gaisa" "Da gaske kakeyi Ya'ya? Kai amma ko wallahi naji dad'i sosai ba damuwa sai kun iso ai Hajiya ko tayi bacci ma ina iya taso maka ita balle kuma idonta biyu ma yanzun haka" Yanke wayar sukayi duka su biyun ita ko dad'i kawai takeji, Kenan hakan yana nufin Sarki ya amshi Moon a matsayin yana son ta, "Keda waye a waya?" "Nida Ya Sarki ne" ta fad'a kanta tsaye, Daure fuskar shi yayi shi kuma, "wani Sarkin?" Kallon shi tayi da mamaki wani irin tambaya ne wannan kuma, shine zaice mata wani Sarki, aiko ita ta fishi zama yarta kife dan haka cikin idon shi ta kalla ta kuma bashi amsa da cewa, "Ya Sarki dai daka sani tsohon mijina shine zaizo" ta fuske abinta, "Me zai kawo shi gidan nan da daren nan ne naga sai wani rawar kai kikeyi?" "Matar dana zab'a mishi ya aura zai kawo min mu gaisa kuma daga nan zai nemi iri a wajen Hajiya bakaji yace yana son su gaisa ba? " "Ni ban gane me kike nufi ba" "Ok ok to bari in maka gwari gwari, kana Jina?" "Eh ina jinki" "Yauwa kagani ko tun shekarun baya can kafin ma insan cewa za'a had'ani aure da shi a cikin k'awayena akwai wacce ta nuna tana son shi dan yana burgeta tun a lokacin, da farko nayi zaton wasa takeyi amma yau da gobe yanda take yawan tambayar shi da kuma sako min labarin shi idan muna hira da ita a waya duk da cewa ba gari d'aya muke ba a hankali saina fahimci cewa ta kamu da son shi amma azatona bata gane hakan ba ko kuma dai tana boye min, kai daga karshe dai na gane da gaske son shi takeyi duk da cewa tasan yana da mata harda yara amma bata damuba tace zata zauna dashi a hakan sai gashi kwatsam rana d'aya mafarkin ta ya ruguje daga sanda aurena dashi ya tabbata, Kasan me?" "Me zan sani kuwa kici gaba da bani labari kawai" "A lokacin na tausaya mata duk da cewa nima din abin tausayin ce lokacin, kaga dai tanaji tana gani ta rasa masoyin da take so tun bata riga ta gabatar da kanta a wajen shiba, ni kuma sai aka k'ak'aba min shi duk da nasan kawata na son shi amma babu yanda na iya, kasan har hakuri saida ta bani akan cewa da tasan cewa shine zai zama mijina da bazata tab'a yarda ta furta tana son shiba, kuma lokacin da nike gidan shi bata tab'a zuwa gidan sai baya nan saboda bata son su had'u shi yasa ni kuma da muka rabu ya rok'eni in fad'a mishi abunda nike so sai na bashi hoton ta da address dinta harma da number ta akan cewa idan yaji yana sonta ya neme ta to kaga ashe ya nemeta har sun sasanta kansu shine zai kawo ta in warware mata dan nasan dole ko ba komai zataji wani iri kar ace tana soyayya da mijin daya rabu da kawarta" "Amma dake da ita duk yarinta ke damun ku" AK ya fad'a yana tab'e baki, "Kai ya'ya yarinta kuma? Halacci dai nayi mata dan bashi da mugun halin da za'akishi" "Wacece ita hala?" Kauda kanta gefe tayi, "ai idan na fad'a maka fad'a zakayi tunda gashi yanzun ma kace wai yarinta ke damun mu" "Waye yace miki zanyi fad'a nid'in? Ai nima nasan zafin soyayya yanzun dan haka bazanga laifin kuba dukan ku, ke abunda kikayi kin kyauta shi kuma Allah yasa yasota da gaskiya har cikin zuciyar shi kar yayi mata kallon macen da aka cusa mishi kamar dai yanda ya miki" "Ah ah bazaiyi haka ba insha Allah," "Wacece nace ko bazaki fad'amin nima in goya muku baya ba?" "Moon" "Kina nufin Maimoon dai na Baba Usman?" "Eh" girgiza kai yayi kafin yace "allah ya shirye ku yaran nan ashe kun dad'e da k'onewa an kara ne kawai babu wanda yayi a cikin mu" "Kai dan Allah waima konewa, nidai dan Allah kasa baki a maganar nan nasan idan Hajiya ta amince dole kowa ya yarda kaji?" "Ke wai mutumin da ba'a tabbatar da lafiyan shi bane zaki had'ashi aure da yar uwar ki?" "Lafiyan shi kalau mana waye yace maka bashi da lafiya ne?" "Oh lafiyar ce kenen yasa yayi ta kallon ki uwa hoto..... "Katse maganar yayi bai k'arasa ba itama kuma sai kawai ta basar, Sukaci gaba da hira tana mishi magiya akan dan Allah yasa baki Hajiya ta amince, *** A unguwar malamai ko Sarki yana isowa Zaria ya kira Moon a waya cewa ya shigo tana ina ne? Yanke wayar tayi sai ta tura mishi text cewa tana gidan su Meelat amma yanzun zata ajiye Maryam a gida dan motar meenal wanda shi Sarkin ya bata tana hannun Moon d'in da ita suketa zirga zirga ita da Sultana, idan ta ajiye Maryam zata kira shi sai ya fad'a mata inda zata same shi dan gaskiya a tsorace take bata son wani ya gansu a tare, Bayan ta sauke maryam a gida ta juyo a k'ofar gidan shi ta sameshi shima a cikin nashi motar kamar yanda yace mata zai jirata a wajen, bata fito daga motar ba ya kunna nashi motar yayi gaba ita kuma ta dunga binshi a baya har suka fita daga cikin unguwar suka kama hanyar tudun wada, horn ta dunga danna mishi tana son ya tsaya dan tana son taji ina zai kaita badai gidan Hajiya ba amma ya shareta ta kira shi a waya yana d'auka sai cewa yayi ta kwantar da hankalin ta tabiyo shi suje kawai, Ita dai a babu yanda zatayi ne ta dunga binshi kila ya lura da tana cikin furgici shi yasa ya canza hanya ba wanda ita ta sani yabi ba kafin ta ankara dai kawai tagan su a bakin gate d'in gidan Hajiya ne bai tsaya a waje ba horn yayi aka bude mishi gate ganin motar Meenal a bayan nashi ne kuma yasa su Isah basu tambaye shi wajen wa yazo ba tunda tare yake da yar gida, A harabar gidan dukan su suka nemi waje suka faka shine ya fara kashe tashi motar ya fito ya koma motar da Moon ke ciki dan ta kasa kashe motar balle ta fito, Sak'e² kawai takeyi, me Sarki yakeyi haka da zai jawota suzo gidan nan bayan yasan Meenal tana nan, gefen mai zaman banza ya bud'e ya shiga ya zauna, "Hajiyata idonki kenan, to barka da dare ya gajiyar hidin dimu ai da nace to Sarki kuma laifin me yayi tunda gimbiyar shi ta baro kudu zuwa arewa babu kira ba sak'o? Ashe dai ina da sauran gata ba'a manta dani ba, Karki damu kanki cewa zakiyi wani dogon tunani akan dalilin zuwan mu nan, dafarko dai nazo gaisheda Hajiya ne ina kuma son gabatar da kaina a gaban ta kafin Allah yayi ma su Baba Usman isowa gobe, na biyu kuma nazo ganin kanwata ce ina son kuma tasa baki ko zaki yarda da batun neman aurena a wajen ki ki yarda cewa ba yaudaran ki zanyi ba nasan duk wannan nuku²n da kikeyi saboda Meenal kikeyi abunda baki sani ba shine da yardar Meenal na kawo kaina gaban ki, sai da na fara rokon alfarma a wajen ta akan tamin hanyar yanda zan sameki tunda nidai ina sonki kuma addini bai haramta aure a tsakanin muba ita tabani number address dama sauran bayanai a kanki dan haka kima dena damun kanki da zaton ko kinci amana ko wani abun makamancin haka nine nan na ganki ina so ba cusa min ke akayi ba" (Ku gane Sarki ya boye mata gaskiya ne saboda kartaji ba dad'i, bawai da wani nufin daban ya juya labarin ba) "Ina fatan cewa yanzun da kikaji gaskiyar komai bazaki k'ara hanani gabatar da kaina ko kuma kici gaba da boye soyayyar muba?" D'ago kanta tayi ta kalle shi, "dama Meenal tasan komai?" "Eh ta sani" "To amma bata nuna min tasani ba" "Saboda bata son kiji babu dad'i shi yasa" "To ya akayi kasan su Baba zasu iso gobe?" "Saboda na riga na gabatar da kaina tun a Lagos yanzun haka Abban ku na Saudia ake jira yana isowa komai zai kammala ina fatan kinyi farin ciki dajin hakan?" Kafafuwan ta ta cusa a tsakanin cinyoyin ta tana boyewa murmushi kwance a fuskarta, "Oh kunyana kike ji yanzun kuma, to bari kiji nidai gaskiya bazan yarda aja lokaci mai tsayi ba dan ina bukatar matata, sannan kuma zakiyi hak'uri dan idan Allah ya nufa an d'aura auren bazaki zauna a Lagos ba Kaduna zaki zauna tare da uwar gidan ki da yaranta bazan hanaki aiki ba sai dai ina fatan aikin ki bazai sa ki gaza samun lokacin da zaki bani kulawar daya dace ba?" Shiru tayi bata amsa mishi ba, Wayar shi ya ciro ya kara kiran Meenal ya shaida mata cewa suna harabar gidan, "Ya'ya sun iso" take fad'ama AK, "Ai naji isowar su tun d'azun kuma nace miki ki dena kirana ya'ya koh" "To da wani sunan zan kiraka?" "Jeki shigo dashi zamu zab'i sunan daga baya" "To muje tare" Tare suka fita tunda suka fito kuma AK ya kama hannun Meenal din ya runtse cikin nashi tayi tayi ya sake mata hannu yak'i, "Oh ke bakya son shima ya gane cewa kema kin samu mijin aure ne?" Koda suka isa hannu AK da Sarki suka ba juna sukayi musabaha ko wannen su fuska kadaran kadahan babu fushi kuma babu sakewa, a can gefe Moon ta lab'e dan daga AK har Meenal din kunyar su takeji wallahi, AK ne ya musu jagora har falon na Hajiya suna shiga kuma Moon ta gudu sama Meenal kuma ta take mata baya tana tsokanarta da cewa ai dama ta fad'a mata cewa koma miye take boyewa idan tayi wari zasuji, "Da gaske dai ashe kaine sirikin nawa?" AK ya fad'a bayan sun zauna, Karamin dariya shima Sarki yayi kafin ya maida mishi martani da cewa, "Kamar yanda kaima gashi da gaske naga alaman kana shirin zama sirikina, ko ka manta ita Meenal din kanwata ce, kaga kenan komai yazo da sauk'i sai muyi bani mandaqo in baka Manda kai anan kaine zaka jagoranci zamowana siriki a gidan ni kuma sai in maka jagoranci nima a gidan mu kaga komai ya tafi dai dai kenan" Dariya AK yayi kafin yace "ina fatan dai ka shirya fuskantar Hajiya gaba da gaba koh? Dan kasan itace boss gaka kuma jami'in tsaro balle ince ka bata cin hanci dan ina fad'a maka matar nan yar rashawa ce" Dariya Sarki "karkaji komai na riga na shirya fuskantar kowa dama qalubalen daga kanwar kace itama nasan yanzun kam na gama da gefen ta," "To ai ba laifi indai ka shirya to nidai na baka dan koni ina iya aurar maka da ita"'cewar AK, "Allah ko mutumina? To in haka ne nima na baka uwar Malam a matsayina na Babban yayan ta ka fito kawai idan ka shirya" Sarki ya fad'a yana bashi hannu suka kashe, Sultana ce ta sauko kasan ita nan a dole wai kitchen zataje alhalin kuma tsabar gulma ne ya fiddo ta Sarki take son gani dan labarin shi kawai takeji yau kuma gashi yazo har gida ina zata yarda wannan damar ta wuce ta bata sauko sun gaisa ba, "Yauwa Sultana koma saman nan dan Allah kice ma Hajiya tayi bak'o" "To" ta amsa dashi kafin ta mik'ama Sarki gaisuwa bayan ta k'are mishi kallo, juyawa tayi zuwa d'akin na Hajiya da Sallama ta bud'e k'ofar ta shiga, "Me kuma ya faru na dawo d'akin ma bazaku barni in huta ba sai kun biyoni" "Allah dai ya baki hakuri Hajiya dama Mai Jama'a ne yace in kiraki kinyi bak'o yana falo yana jiran ki, kamar dai saurayin Moon ne yazo gaishe ki dan tare da ita suke" tana gama fad'a mata ta fice daga d'akin, Ita kuma Hajiya jin cewa saurayin Moon shi yasa bata b'ata lokaci ba ta ziro hijabi ta fito ita dai Allah ya sani tana matukar so taga ta aurar da jikokin nan nata, shi wannan din da yazo in dagaske ne ai dama kawai zata bashi ya turo iyayen shi ayi a wuce wajen dan dama ita Batama Moon din sha'awar auren Lagos, Batayi saurin gane ko waye a falon ba har saida ta sauko ta nemi wajen zama ta zauna shi kuma sarki tana zama sai ya zamo daga kan kujerar shi ya fara gaishe ta, Lafiya lau suka gaisa sai da ya koma ya zauna ta kare mishi kallo da kyau kafin ta maida kallonta kan AK " kai Abdul nace wannan kamar d'an gidan uwar gida ko? Ina nufin tsohon mijin Meenal koba shi bane? To me kuma ya kawo shi nan? Nidai Sultana cemin tayi Saurayin Maimunatu ne yazo gaishe ni koshi wancan d'in ya wuce ne?. *Ummiee ce* [9/30, 10:51 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 39* D'aure fuska AK yayi dan karma Hajiya taga fuskar shi sakwa² ta d'auki maganar su shiririta dan yasan halinta tsaf tana iya daga shi har Sarkin ta musu fatattakar kare, amsa mata yayi da cewa, "Eh shi d'in ne dai wanda kika hasaso kuma babu wani wanda ya wuce shine dai, tareda Moon d'in suka zo nan koma menene tsakanin su ai zakiji daga bakin shi tunda dai gashi yazo," "Kai d'an nan kar kayi fushi kaji, karkaji nace mai ya kawo ka nan kayi zaton ko da wani nufi na fad'i hakan, ah ah wallahi kai kam ai ka zama d'an gida zuwan daren nedai ya bani mamaki, dan nasan ba sabon ka bane, to Barka da zuwa fa ya wajen iyalin naka da ita uwar gidan kuna dai lafiya koh? ance ma kayi sabon gida dan haka, ka dawo nan Kaduna gaba d'aya kaida iyalin taka to Allah ya sanya alkhairi yasa anyiwa wayan raine, allah kuma ya k'ara arziki a kuma cigaba da kiyaye addu'a sai kaga kofofin arziki suna ta budewa wallahi" "Ameen ya rabbi Nagode kwarai Hajiya kowa lafiya lafiya Allah kuma ya k'ara miki lafiya kema" Sarki ya amsa dashi kanshi a k'asa, "To ameen dai madallah ina fatan dai lafiya dan nayi mamakin ganin ka?" Hannun shi yakai bayan k'eya yana gyara zaman hular dake kanshi kafin ya d'an k'ara sassauta murya duk da muryar tashi bata rik'uwa yace, "dama Hajiya nazo gaisheki ne" "Kai madallah aiko ka kyauta nagode da gaisuwa Allah dai yayi albarka kaji, Gashi kuma kayi min zuwan dare amma dai nagode wanda ya biyoka har gida ya gaisheka ko bai kawo maka komai ba ai ya kula da kai, toni zan shige daga ciki ka gaisheda gida" Ta yunk'ura da niyyar tashi AK ya tsaida ita inda yake cewa, "Hajiya zuwan nan da yayi fa wajen ki yazo dan iri ya gani a gidan ki ya biyo, kuma ni a matsayina na yaron gidan babba munyi magana dashi harma na bashi sa Albarkan ki dai muke nema yanzun Hajjaju" Komawa tayi ta zauna tana maida kallonta kan AK dake magana, "Kasan nifa idan mutum zaiyi magana dani nafi gane ya fito kai tsaye ya fayyace min komai bana gane nuku² da kananun munafunci, yo fadama gareni a cikin gidan balle ace ina noman rani da za'azo neman iri a wajena?... " Katseta ya k'arayi da cewa "amma Hajiya aikema kince Sultana ta fad'a miki cewa saurayin Moon ne yazo koh" "Kai dakata min dan Allah,ina ce koda na fito ku biyu na cimma zaune anan d'in shifa wannan d'in da kakeji da gani shine dai tsohon mijin Aminatu ko baka ganeshi da kyau bane ko kuma dai kallon tsoro ka mishi? Ina had'in tsohon mijin Aminatu kuma da Moon wacce ke can kudu?ina ga dai a hanya suka had'u shi kuma ya rage mata hanya zuwa nan gidan kasan kuma ita Sultanan ba sanin shi tayi ba shi yasa tace haka inba hakaba Wannan ma ai ba zancen da kai zai d'auka bane abu dai kamar muna garin da ba'a sallah" K'ara d'aure fuska AK yayi jin Hajiya tana neman jagwalgwala maganar, da hausa fa yayi magana da ita bada wani yaren ba balle tace bata gane me yake cewa ba, shi kuma Sarki sai wani k'ara nok'e kai yake, "Hajiya koma dai garin suwa muke shi dai d'in da kike gani yau yazo gidan nan ne dan ya gaishe da kakar budurwar da yake nema ya kuma gabatar miki da kanshi a matsayin mai neman auren jikar ki, Kai kuma ka wani zauna kayi shiru ni kad'ai zan maka yak'in neman auren ne?" Dif ruwan kan Hajiya ya d'auke dan Wallahi ita dai a cikin kalaman da AK yayi babu guda d'aya wanda zata iya cewa ta fahimci abunda yake nufi, Kuji wani hauka fa wai cewa yake shi Sarkin ne wai saurayin moon to wannan batu ai sai dai a garin mahaukata wallahi, "Tuf tuf tuf" ta tofar da miyau daga bakin ta, "Kai dai kana da bak'ar d'abia wallahi Abdul, wacce magana ce kake fad'a haka irin ta masu shaye shaye?, Shi Sarkin shine yace maka son Moon yake ko koh ah ah kaine da iya tsara zance ka tsara jawaban ka dan kawai ka mai dani wata abokiyar wasar ka, to wallahi ka fita idona tun wuri in rufe, ya mutum zaizo har gida dan ya gaishe ni da girman ka da komai sai kawai ka wani tak'ark'are ka dunga sheqa mishi k'arya, Kai kuma wallahi ka daiji kunya dirkeken soja dakai ka zauna kana jin yana sheko k'arya akan ka baka zage kwanji ka wauwanke mishi fuska da mari ba aikin banza kawai" Gyara zama Sarki yayi duk da yanda yaga Hajiya tana kumfar baki hakan bai sare mishi gwuiwa ba, domin dai tunda har ya iya kawo kanshi ba wani can da ban bane ya kawo mata zancen to gara ayi wacce za'ayi kawai, dan haka sai ya zamo daga kan kujerar da yake zaune bayan ya zame hular kanshi ya ajiyeta a gefe, bai yarda ya kalli fuskar hajiya ba ya fara magana, "Hajiya kiyi hakuri ban sani ba ko har yanzun a mai laifin daya aurar miki jika ya saka kike kallona, bazanga laifin kiba in kin kalleni a matsayin mai lefin sai dai ina mai k'ara baki hakuri abunda ya faru tsakanina da Meenal ya riga ya faru ya wuce, aure ne Allah ya kaddara a tsakanin mu a cikin zaman mu kuma sai Allah yasanya hijabi a tsakanin mu, tun kafin in san zan auri Meenal nakejin soyayyar yar uwarta a cikin zuciya ta, ban bayyana bane a wancan lokacin saboda nayi duba da k'aracin shekarun su ko secondary school basu gama ba, Allah ya sani ban tab'a kallon Meenal da fuskar soyayya ba a tsayin zamana da ita, rashin sonta kuma bai sa na cutar da ita ba, nasan zaki fassara abin ta fuskar cewa kusancin yayi yawa na auri Meenal yanzun kuma ince ina son Moon saboda dangar takar iyayen su da suke uwa d'aya uba d'aya amma Hajiya a addinan ce hakan ba haramun bane....." Hannu Hajiya ta d'aga mishi alamun dakatar wa, "Eh kawai haka mutane ke cewa ba haramun bane amma mu hausawa cewa mukayi ana barin halas kodan kunya kuma wata kusar tafi wata, dab haka in ma dai wannan shirmen ne yasa ka kwaso jiki da tsakar daren nan uwa mafatauci ka duro min gida tattara maza maza ka koma inda ka fito, idan a dangin ku kun saba kwamacala ni anan gidan baza'ayi min ba, yo ita Moon din hauka takeyi ma da zata yarda harta kulaka kana matsayin tsohon mijin yar uwarta sune fa sukayi ma Meenal din yan matanci a matsayin kawayen amarya, yo wannan abi idan ya tabbata kuma ai sai a buga mu a jarida wallahi ace ka auri yar mace ka saki ka koma kan yar namiji," K'ara gyara zama yayi ko gezau bai nuna alamun mikewa ba balle tasa ran zai bar mata falon, Sultana wacce tun d'azun take zaune akan dinning domin bayan ta kira Hajiyar data sauko kitchen ta shiga ta zubo abinci ta zauna tanaci, biyu ta raba hankalinta d'aya akan abincin da take ci d'aya kuma tana k'arewa Sarki kallo tana kuma sauraren hirar dake gudana a falon, Ko ita fa maganar yayi mata wani iri, taya ma zaka auri k'awa ka saki sannan kuma kace zaka auri aminiyar ta wannan abun baiyi ba sam koda ko ace babu dangan taka na jini a tsakanin su balle kuma tsakanin Moon da Meenal kai gaskiya kusancin yayi yawa ko ita bazata goyi baya ba dan hakan yana iya shafar zumunci, tututura abincin tayi ta maida plate din kitchen ta wuto da niyyar haurawa sama ne Hajiya ta tsaida ta, "Ke Sultana haura maza kiyi min kiran Moon ta sauko yanzun ina son magana da ita dan bazasu mai dani wata sakarya ba ita Moon din har idonta yayi budewar da zata zagaye taje tana soyayya da tsohon mijin yar uwarta" "Hajiya me yasa kike so dole dai sai kin tadama kanki hankali ne wai? Miye na damuwa a cikin maganar nan naga dai AUREN nan ba wai ya haramta bane, amma sai tada jijiyoyin wuya kikeyi idan ita yarinyar tana son shi zaki hanata abunda take so ne?" "Kwarai zan hanata dan ko ban isa da itaba na isa da ubanta" ta amsa dashi tana huci, "Hajiya dan Allah kiyi hakuri wallahi ba yanda kike tsammani bane, da zuciya d'aya nike son Maimoon kuma nayi alkawarin zan kula da ita zan riketa amana idan kuka bani auren ta dan ina sonta" "Ita waccan da aka aura maka da farko meya hanaka kulawa da ita ka riketa amanan? Ita data kasance maka zab'in uwama kayi fatali da ita ka kai gida ka jirgeta uwa majigi shine zaka k'ara sad'ad'owa ido babu kunya kace wata jikar nawa kake so, wato ni gani Hajiyar mahaukata ni kuma sai in goya maka baya to baka isa ba har yanzun rass nike lissafina bai goceba," Su ukun suka sauko Maimoon Meenal sai Sultana a bayan su, kuka mara sauti moon takeyi Meenal ke bata hakuri da cewa tabar kukan tana kuma share mata hawaye har suka sauko k'asan, Tun kafin su nemi waje zama hajiya ta kaida tambayoyin ta kan Moon d'in, "Ke bar kukan munafuncin naki dan bazai fishsheki ba kizo ki fad'amin uban meye tsakanin ki da tsohon mijin yar uwar ki, Maimoon ashe har zaki iya zagayewa dan cin amana kije kina soyayya da mijin daya maida miki yar uwa k'aramar bazawara sai yau da tsakar daren nan saboda tsabar kun shahara wato kun riga kun gama kulla tuggun ku shine ya wani kwaso min ke kukazo min gida zai wani ce wai yazo gaisheni da kuma rok'on iri, to ba iri ba yabanya ma taci buhun ubanta, ido ba kunya kika kwaso shi kuka yimin saukar dare alhalin ko sanda yana auren yar uwarki gata nan nidai ba zuwa min gida yakeyi ba, Ke kuma da kika wani kwakumeta a jikin ki wani irin rashin sanin ciwon kaine wannan amanar ki taci fa ta koma tana tarayya da tsohon mijin ki duk bamu da labari... " "Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki dena fad'ar nan haka dare nefa, amma sai faman fad'a kikeyi kuma ai ban ce miki bani da masaniya akan abunda yake faruwa ba, nasan kuma kuma nice ma na bashi number waya da adireshin gidan su moon d'in acan Lagos yaje ya sameta" "La'ilaha illallahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam³" hajiya ta dunga maimaita tana tafa hannuwa cike da jimami da mamaki duka a lokaci d'aya, "Yanzun nan ke yar gidan Jidda Ashe rashin sanin ciwon kan naki har yakai can, ace miji ya sake ki wai kuma harya dawo ya miki dadin bakin cewa yar uwarki yake so ke kuma saboda rashin sanin ciwon kai kika d'auki number da adireshin ta kika bashi, To ke Moon dama can son nashi kema kikeyi koh shi yasa koda yaje kika amshe shi hannu bibbiyu?" "Ah ah Hajiya wallahi gashi nan koshi zai fad'a miki gaskiya tun sanda yazo wajena ni ban bashi fuska ba shine dai ya nace kuma koda na fad'ama Umma itama cewa tayi in rabu dashi bata bani goyon baya ba, shi yasama koda yace zai tura ni kuma na hanashi turawa saboda ban san da wani idon zan kalli mutane ba wallahi Allah Hajiya ko yanzun ban san cewa nan gidan zai kawo muba da bazan biye mishi muzo tare ba dan Allah kiyi hakuri Hajiya"ta k'arasa fad'a a yayinda ta durkushe a wajen tana kuka, "Maimoon" AK ya kira sunan ta a dake, Bata iya amsawa ba saboda tsoron daya rufeta dan tasan kila shima kallon yar cin amana zaiyi mata, "Waiba sunan ki na kira bane da bazaki iya amsawa ba, taso ki dawo nan kusa dani tambayar ki zanyi" ya fad'a a tsawace, Da rarrafe ta k'ara inda yake hawaye dama² a fuskarta, "Kina son Sarki?" Dan dago kanta tayi kad'an ta saci kallon hajiya wacce ba ita kad'ai ba dukan su Moon d'in suke kallo sai dai ita kuma mai makon ta bashi amsa ah ah sai kawai ta maida kanta k'asa ta fashe da kuka mai k'aramin sauti irin mai fitowa daga cikin zuciyar nan, Ita taya zata iya amsa cewa eh tana son shi bayan ga Hajiya nan ta kafa ta tsare akan bata yarda da zancen auren ba, Batajin ta Meenal domin a zaman da sukayi ita da Meenal a cikin d'akin zancen da suka tattauna kenan dan Meenal din ta fito ta fad'a mata gaskiyar cewa itace taba Sarki number da Address din ta kuma inhar Moon din tana son Sarki har yanzun ita zata tsaya ta jajirce wajen fahimtar da iyayen su bayan ita kuma suna da goyon bayan AK dan haka shawo kan Hajiya bazai zama aiki ba, amma yanda taga Hajiya na tada jijiyoyin wuya ne ya karya mata kwarin gwuiwa dan Wallahi idan har Hajiya tace ah ah to ah ah din ne zai tabbata ita da Sarki sai gani sai hange. "Moon karkiji tsoron kowa anan ki fad'amin in har kina son Sarki ni kuma na miki alkawari wallahi zan tsaya miki har sai na tabbatar da d'aurin auren ki, kin san dai koni ina da ikon aurar dake koh amma bazan ce mishi na bashi ya turo ba har sai naji ta bakin shi dan haka ki bud'e baki ki amsa min karkiji tsoron kowa kina dani ninan zan tsaya miki, kina son Sarki zaki aure shi" Gyad'a kanta tayi alamun eh, Shi kuma sai yace "ah ah bana son maganar kurame da baki na tambayeki dan haka bud'e murya ki bani amsa kina son shi" "Ina son shi amma Hajiya ai tace bata yarda ba" "Fad'i ki k'ara ban fa yarda ba shima da yake neman d'aure miki gindin naga uban shima a karkashin ikona yake bare kuma shi, shida bai aurar da kanshi bane yake batun aurar dake," "Hajiya yarinyar nan dai gashi a gaban ki tace tana son shi dan haka dan Allah kiyi hakuri kisa albarka ki barsu suyi auren su dan baki san abunda Allah subhanallah wata alah ya b'oye a cikin tarayyar suba idan akwai rabon aure da haihuwa a tsakanin su ina mai tabbatar miki da cewa idan fa har kika d'age akan cewa baza'ayi auren ba Allah yana iya nuna ikon shi akan ki, sai ya d'auke ki daga duniyar gaba daya bayan kin gushe su kuma suyi auren har su hayayyafa.... " "Kaine zaka mutu Abdul Khareemu badai niba dan uban ka, harni zaka fad'ama cewa idan na d'age zan mutu, to insha Allah zanci gaba da zama cikin koshin lafiya har zuwa sanda zan gama aurar da jikokina tass dan hasken fuskar annabi, wato so kakeyi kace ni bani da taqawa bani da tawalu'u to ni bazan ja da ikon Allah ba tunda shi ya had'asu ita kuma tace taji ta gani sai shi to ai sai suje suyi ta fama dama ni surutun mutane ne bana so ato yanzun duniya abin surutu sam bashi da kad'an wacece nima dazan zakalkale inyi ta tada jijiyoyin wuya bayan ita Meenal din ma naga ta nuna ko a jikinta, Kai kuma kaji da kyau karkaga na saduda kayi zaton ko zansanya maka idone bayan auren sai yanda kayi min da rayuwar jika ah ah gara in fad'a maka ka shirya wannan karan koni ko kai in kuma kasan cewa har yanzun baka isa da gidan kaba to kar In k'ara ganin kafar ka a wajen jikata, idan kuma ka isa da gidan ka ka kai namiji gobe iyayen ta maza zasu iso dan haka kayi hanzarin turo naka iyayen garesu dan a gabatar da neman aure ba kuma lokaci mai tsayi za'aja ba dan sabon gida kayi gara itama ta tare a cikin shi tun yana da sabun tan shi" "Nagode Hajiya Allah ya k'ara girma dama kuma tun a can Lagos din na tura manya sunyi magana dashi Baban namu shine ma yace ayi hakuri a jira har Abban saudia ya iso k'asar sai a gabatar da komai idan sun iso nan, na dai yanke hukuncin zuwa in gabatar miki da kaina ne shi yasa nazo yau kiyi hakuri dan Allah" "Ikon Allah kace min sai da kuka riga kuka shirya komai kaida iyayen ta kafin ka iso nan, to ai yayi, ai koba komai da ta fad'a wani hannun gara kai d'in koba komai na gida ne kuma kowa ya maka shaidar arziki inaga dama can Moon itace allah ya kaddara zata zama matar ka shi yasa auren ka da yar uwarta yazo a yanda yazo to Allah ya sanya alkhairi ya kuma kad'e fitina karkaji komai kaji tunda shi wannan uban nata ya yanke cewa ya baka nasan koda ace iyayen su basu sani ba shi zaiyi bakin gwagwadon shawo kansu balle kuma ashe suma suna sane toni awa ince zanyi jayayya da ikon ubangiji" AK ne ya fara tashi ya shige d'akin daya zuba kayan shi wanda yake nan k'asan sanadiyar kirar wayar shi da akayi, "Ku tashi ku bamu waje zanyi magana dashi," cewar Hajiya tana kallon su Moon, Mikewa sukayi dukan su suka haura saman sai da ta tabbatar sun shige ta kuma kalli k'ofar d'akin AK taga a rufe yake sannan tayi k'asa da murya ta fara cewa, "Tashi ka koma kan kujera" sai da ya koma kan kujerar sannan ta daura da cewa, "Sannu fa da kokari d'annan wallahi nidai tunda uwata ta haifoni duniyar nan ban tab'a ganin mijin da bayan ya rabu da mace yake binta da alkhairi ba irinka, sannu kaji Allah dai ya k'ara arziki amma kam kayi hidima ga mota ga kud'ad'e ga kuma kyautar gida sukutun, nace to kardai kace kaji shiru ita Meenal din bata kira tayi maka godiya ba wallahi ba laifin ta bane laifina ne domin nice har yanzun ban gabatar mata da gidan a matsayin kyauta daga gareka ba, Kasan halin Meenal sarai yar tutsuce tana sanin cewa daga wajen Kane kyautar gidan tana iya murje ido tace bata buk'ata shi yasa kawai na yanke hukuncin cewa zan bata ne a matsayin cewa kayan d'akin ta dana siyar ne na had'a da kudin daka bata nayi mata ciko na siya mata gidan nasan zatafi yin farin ciki da haka, Daga baya idan ta gabatar ma da uban nata idan komai ya lafa sai in bud'e mata gaskiyar zancen, Sa'eed kuma ya fad'amin cewa baka son asan cewa kaine ka siya gidan da sunan ta dan haka ka kwantar da hankalin ka wannan sirrin babu maijin shi daga nan wajena kuma shima nasan bazai tona ba, Sai batun Moon kuma nidai na baka goyon baya dari bisa dari sai dai bazan gaji dayi maka tuni ba nasan dai zuwa yanzun kasan kalar matar da kake aure atoh dan haka a daure a cigaba da kiyaye azkar sadaqa da kyauta a kuma dunga shan tsarin jiki duk da allah ke tsarewa amma kula da kaya dai yafi ban cigiya, ban kuma ce wai dan zaka auri jikata ita na gidan ka wulakanta taba koba komai ka dunga duba matsayin ta na uwar yaranta idan tayi ba dai daiba ka tsawatar mata kaine sama da ita, ita kuma Allah ya shirye ta tabar duk wasu abubuwan da basu dace ba Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakanin ku, Na fad'a maka dai da wuri nike son ayi komai dan had'awa nike so ayi dana shi wannan yayan nasu daya gama zazzageni a gaban ka, dan shike neman auren Kanwarka Aminatu shin ko wajen ka zamuzo neman auren nema kai Babban yaya?" Hajiya ta tambaya da dariya a muryar ta, "Ai hajiya indai shine na bashi Meenal ko gobe ya shirya yazo da goro kawai ni kuma zan d'aura musu aure," "Oh kace kaima gaban kanka zakayi kamar yanda shima ya daki k'irji wai shi mai k'anwa zai aura mata wanda take so, to ai shi nashi maganar bata shiga gida ba tukun amma da iyayen shi sun iso zasu kai zancen can gidan su, ai ka gane ita waccen da suka haura sama tare dasu Meenal din ko?" "Ah ah ban ganeta ba gaskiya" "Ash sha to kanwar kace itama d'iyar mamarku ta Abuja ce tunda sukazo da rasuwar mijin Raheenat ita bata koma ba ta tare a wajen takwarar ta Aminatu, idan kaje gidan Malam ma zakaga d'an uwan ta yana nan wani ustazu suna ce mishi Sheikh Naseer yaro mai hankali dashi ni burgeni yake da farko har nayi sha'awar had'ashi da Moon fa ashe ba rabon shi bace" Dan murmushi Sarki "eh nasan shi Sheikh d'in ita ce dai ban wayeta ba, Hirar ne sosai ya b'arke tsakanin Hajiya da Sarki suna zaune a falon har karfe 11 na dare ya gota, sai da Ak ya fito daga d'aki yake ce mishi, "Sarki idan ka biyema Hajiya fa zaku kwana kuna hira ne idan kuma ka shirya kwanan gidan sirikai ga d'akina nan idan kun gama hirar sai ka shigo mu kwana tare," Agoge Sarki ya kalla yana mik'ewa tsaye, "kasan kwata kwata banyi zaton lokaci yaja haka ba ashe dare ya farayi ban sani ba kuma ko gida ban shiba, Hajiya bari in wuce nagode kwarai Allah ya k'ara girma da jinkiri mai albarkha" "Ameen ta amsa dashi tana mai cewa ka gaishe min da uwar gida kwana biyu bamu had'u ba, Ficewa sukayi shida AK daga falon sai da AK ya raka shi har wajen motar shi sukayi sallama ya tada motar ya fice daga gidan duk da cewa AK yace mishi ko ya kira mishi Moon suyi sallama ne shi kuma Sarkin yace ah ah ya barta kawai tagama hutun kukan son shi da tayi d'azun, Falon ya koma bayan wucewar Sarki sai da ya kulle kofa kafin shima ya shige ciki kamar ya haura sama ga k'ara gano Meenal sai kuma ya hana kanshi ya wuce nashi d'akin shima ya rufe k'ofa. *Ummiee ce* [10/2, 10:46 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 40* No editing 😒 A wannan daren su Moon sun dad'e basuyi bacci ba domin Sarki yana barin gidan ya kira wayarta yana mata tsiyar cewa "ashe har haka yayi nisa a cikin zuciyar ta bai sani ba tunda gashi harta kasa rik'ewa ko kunya batajiba taje tana kukan tana son shi a gaban Hajiya, ai shi bai san cewa shi d'in d'an baiwa bane sai yau dan haka ta bar kuka tunda dai ta nuna tana so to jira kad'an kawai zatayi kafin ya canza mata suna daga Maimoon Usman Abdul Khareem, Zuwa Maimoon Usman Sufyaan, Tun yana hanya suke magana da ita bai yanke wayar ba har saida yakai gidan shi kafin ya mata sallama kuma sai da yasa ta had'ashi da Meenal, "Kanwata nace wato da yike kin samu wani Yayan makwafina shi yasa ko tunawa dani ma bakyayi yanzun koh?" "Ah ah wallahi Ya Sarki ba haka bane, kaga ga hidimar karatu da kuma shirye shiryen bikin besty Meelat da muke tayi shi ya d'auke min hankali yasa ban kira kaba amma kayi hakuri na manta kuma ban tayaka murnar sabon gidaba Allah yasa alkhairi ina kuma tayaka murnar samun soyayyar yar uwata allah dai ya nuna mana ranar " "Ameen ya rabbi nagode da addu'a ai nasan dama bai wuce kice inyi hakurin ba bayan kin ware ni a gefe kuna biki babu sanarwa balle insa rai da goron gayyata, bana ma ko kud'in ankon ba'a nema a hannu naba nace too abun har yakai haka? anya ba'a canza min matsayi ba kuwa uwar malam?" Dariya tayi kafin tace "ah ah wallahi ba haka bane yayan mu karkayi fushi ai ba'a gama bikin ba bama a fara ba tunda gaka ka iso aini kuma nasan daga daren yau na tashi daga Meenal na koma Hajiya Ameena mai uwa a gindin murhu ai bayacin tuwon shi gaya allah dai ya k'ara arziki Ya maimartaba angon Maimunatu" "Wannan irin kod'awa da kikamin Meenal ai dole a baki kyauta yanzun fad'amin cash kike so ko kuma transfer dan gudun mawar da kika bayar yau dama kin cancanci tukuici mai tsokama kuwa, dan haka ko nawa kike buk'ata ki nemi Salman gobe ya baki kamar yanda aka saba... " "Wai Salman Yayan mu? Ah ah nidai karka had'ani da Salman fad'a mukeyi dashi gobe dai idan na shigo unguwar zan aiko ko kuma in amsa sakon ta hannun mutuniyar ka" sallama sukayi ta maida ma moon wayar, ikon Allah wato dai kusancin da basu samu a baya tsakanin shida itaba shine yake son wanzuwa a yanzun a sanda take gidan shifa ita zata iya rantsuwa da Allah cewa basu tab'a zaman hira a tsakanin suba koda ya kirata a waya kawai zai tambayeta lafiyar tane sannan kuma yaji ko akwai wani abunda take buk'ata, itama kuma bata neman shi sai in tana da wani buk'ata na kud'i ko kuma idan fita zuwa wani wajen ya kama zata kira ta nemi izini amma kun gani tun bayan rabuwar su komai ya canza yanda yake mata wallahi kamar dai ba Yayan su Sufyaan mai karnukan nan data sani a shekarun baya ba wanda ko muryar shi kaji dole ka kama kanka, haka Sultana tasa Meenal a gaba da tarin tambayoyi dan itafa tayi mamaki bata tab'a zaton cewa haka zataga Sarki ba dan haka ta gaza hakuri sai da ta tanka, "Wai dama wannan shine Ya Sarkin?" Saboda ita dai ba sanin shi tayi ba kuma a yanda take jin su Maryam na bada labarin shi tayi zaton cewa zatagan shi wani dattijo ne irin kamar dai wanda yake nemar shekaru 40 da wasu hayaniya a sama haka, amma sab'anin hakan sai ta ganshi wani wankakken d'an gayu dashi wanda kai a kallo d'aya ma wallahi bazaka ce yana da yara har 4 har sun fara zama yan mata ba sai dai kace saurayi ne irin wanda baiyi aure da wuri ba d'in nan dan sam jikin shi bai nuna adadin shekarun shiba, Koda tayi tambayar Meenal shareta tayi dan haka taci gaba da cewa "Ke Meenal wai wani irin zama ne kukayi kukoh harna tsayin shekaru har 6 amma aka kasa samun cigaba? Daga ke harshi kukayi ma kanku bak'in ciki wato yanda yasa miki na mujiya kema haka kika sa mishi saboda tsabar rashin sanin ciwon kai, Ni wallahi in fad'a miki gaskiya babu ta yanda za'ayi in rayu da irin wannan mijin irin rayuwar da kukayi gida d'aya kuma kuna ganin juna ace in sa mishi ido inyi ta kallo ban kai mishi cafka ba yo dan Allah kwace goruba a hannun kuturu har wani abunda za'a tsaya ana ba kai wahala ne, na rantse da Allah shida kanshi ma zai kawo kan shi har inda nike koda dad'in rai ko babu batareda ya tsaya shawara da kowa ba, koda yike bari dai inyi shiru tunda mai afkuwa ta riga ta afku harta wuce inaga dai Allah yasan abunda ya shirya shi yasa ban bayyana a zaria ba a wancan lokacin su kuma wadanda ke tare dake suka kasa baki mafitar daya dace, ke kuma Moon bari kiji in fad'a miki wallahi idan har kika sake kikace kema irin wutar da yar uwarki tayi a baya zakiyi to ki sani koni nan sai na miki Allah ya isa idan ita rashin rabone ya rabasu to ke ki d'auka cewa dama can kece mai rabon ba ita ba, zan kuma baki shawara daga yau daga ita harshi karki k'ara musu kallo a matsayin wadanda suka tab'a rayuwa karkashin inuwar aure ki d'auka cewa ita d'in dai kawai k'anwa take a gareshi kamar yanda nidake dama kowa ya shaida hakan, Sarki dai yana sonki kema kuma kina son shi dan haka nemo zanin goyo kiyi d'amara ki goye abinki tsaf wallahi, karki sake koda wasa kice zaki dunga tunawa cewa yana da wata matar bayan ke a duk sanda kuka kasance tare, nuna mishi cewa shi shikadan shi shi kika sani shi kika waya kike kuma gani a gaban ki da bayanki dan shi din dai shine duniyar ki , Ki nuna mishi kauna ta hanyar nuna kulawar ki akan dukan abunda ya nuna miki yana da mahimmanci a wajen shi, ki tayashi son iyayen shi, yan uwan shi da yaran da ya haifa, bance ki nuna soyayyar ki ga matar shiba dan ba dolen ki bace ita, sai dai kiyi kokari ki dunga danne kishin ta a gaban shi karki yarda in kina hira dashi kice zaki dunga sakota a cikin hirar ku haka kuma shima karki yarda ya dunga kawo miki hirar ta kowacce ta tsaya matsayin ta ki kuma dunga kiyayewa karki yarda kice zaki shiga hakkin ta wato misali kiran waya a sanda kika san yana gida, In fad'a miki gaskiya wannan had'i naku yamin dad'i dan tsakanina da Allah dama tunanin wacce zata shige cikin gidan nan tayi luff a matsayin matar gidan madadin Meenal kullum shike cimin tuwo a kwarya ke gidan nan fa Yasin duk wacce ta shige shi matsayin mata to ta kwantar da kai tayi luf taci arzikin ta hankali kwance abinta kinga ni dama ban tab'a shiga ba kullum dai idan nazo wuce shi sai na yaba a cikin zuciyata yanzun kuma ga dama ta samu kina shigewa gidan nan ai mu shar abunmu wallahi , bari in baki wata shawara ban sani ba ko zaki d'auka kinga zama gida d'aya keda kishiya na rantse miki da Allah sai kin kai zuciyar ki kololuwar nesa dan yau da gobe duk yanda zata takale ki ku raba hali sai tayi ke wani abun ma da gayya zatayi dan dai kawai taga ta b'ata miki rai balle kuma kishiya irin matar shi da naji labarin nata kishin yake a sarari dan haka nidai a nawa hangen gara ki lallab'o shi ya ajiye ki a wannan gidan nashi na garin nan ita kuma taci gaba da zama a Kaduna, Falalane mai girma raba gari da kishiya domin idan dai tana inda take kema kina naki wajen wata rana ma mantawa zaki dungayi cewa bake kad'ai bane domin idan yana wajen ta gani zakiyi kamar tafiya yayi ya dawo gareki, tana da masaukin ta anan cikin gidan iyayen shi dan haka baki da fargaba cewa idan tazo zata sauka a gidan ki, zuwa Kaduna ki tare ba dole bane a gareki in kinso dai kina iya zuwa can din lokaci bayan lokaci amma dai ya zamana cewa nan dai kece mai iko dashi, wallahi nayi miki murna kwarai kekam Allah dai ya sanya alkhairi yasa ace gara da akayi barkan ki da shigowa cikin ahalin mu duk da dai naji babu dad'i kad'an a sanda naji Hajiya tace da taso ne ta badaki ga d'an uwana ya Sheikh amma ba komai na hakura dan bazan miki bakin ciki ba". Hira sosai suka sha a wannan dare kafi bacci ya nuna musu fin k'arfi wajen yi gaba da kowacce a cikin su, yau dai rana na farko da Moon ta samu damar yin bacci cikin salama sab'anin sauran ranakun da suka wuce wad'anda ta dunga lissafin yanda abubuwa zasu kasance sai gashi Allah da ikon shi komai ya tafi a saukake ba tareda an samu rarrabuwar kawuna ba. *WASHE GARI* Gidan Hajiya mak'il ya cika da bak'i na nesa dana kusa kowa ya hallara sai faman hada² kawai akeyi, cikar gidan kuma ya k'aru ne kasancewar ba iya ahalin gidan ne kad'ai suka samu damar isowa a wannan rana ba harda abokanan su Musty kamar yanda AK yace anan zasu sauka anan d'in suka sauka,abokan sune wasu tun na yarinta wasu kuma anyi makaranta tare sai dai kuma kai mai kallo da zarar ka gansu ko baka tambaya ba kasan babu sakarai a cikin su domin duk kan su kowa yana da abun hannun shi duk wanda ka kalla dole sai kaji kamar karka dena kallon shi dan sun san hannun su gashi ko wannen su sunsha wanka sun gaji kamshin ko har baka tantance na wani ga kuma giyar kud'i dake d'ibar su sai suka zama abun sha'awa a wajen sauran matasa sai dai sunji babi dad'i bayan isowar su da suka samu labarin cewa babu wani shagalin da aka shirya na cashewa a bikin na abokin su domin fa sunzo da niyyar su warwasa biki dai na rana d'aya dan haka suka tada balli cewa basu yarda ba ko ba'ayi komai ba su zasu shirya ma amarya da ango dinner, da kyar suka samu Mai Jama'a yasa baki aka tsaida batun dinner d'in dan shi da Musty cewa yayi baya buk'atar bidi'a su bisu da addu'a kawai. A gefen su Meenal ko suma dai tun wayewar gari suka fice daga gidan domin agenda dinsu na yau shine kunshi da gyaran gashi da yamma kuma zasu gabatar da bridal shower wanda iyasu mata ne zasu halarta gobe kuma shine zasu gabatar da kwarya kwaryar walimar da suka shirya wanda maza da matan dukan su zasu halarta, kud'i masu nauyi AK ya sauke ma sultana kafin fitar su a matsayin kudin kunshi dana gyaran kai nasu dana amaryar su, su kuma sauran abokan sosai suka nuna nasu bajintar wajen saukema k'awayen na amarya komai zasu buk'ata dan haka suma kawayen babu tausayi haka suka dunga lissafo musu abubuwan da suke buk'ata harda wad'anda basu zama dole ba, Safiyya matar Yusuf wase itama a ranar ta iso dan haka itama gidan Hajiya ta ajiye su Affan ta shige cikin su Moon aka cigaba da gudanar da abubuwa da ita, kuma shima Sarki kamar yanda yayi alkawari ya sauke ma Meenal d'in Alert mai nauyi a cikin wayarta wanda har saida Sultana ta dunga mamaki wai sudai mazan zaria idan zasuyi kyauta a dunkule sukeyin shi kamar basu san zafin nema ba, ita ma dai Allah ya had'ata da wanda zata shak'o wuyar shi tayi ta goge mishi hadda. **** A jiya kasancewar koda Sarki ya isa unguwar na malamai dare ya riga yayi sai kawai ya wuce gidan shi ya nemi wajen bacci, Bayan gari ya waye kuma yana dawowa daga sallan asuba yayi wanka ya shirya ya wuce gidan su, kowa yayi mamakin irin sammakon daya bugo daga Kaduna dan haka sai uwar gida ta fara tambayar shi da cewa "lafiya kuwa wannan irin tafiya na sassafe" Kai ya maida k'asa cike da rashin gaskiya yana non nokewa ya amsa mata da cewa, "lafiya lau" "Ko wani abu ya farune?" Ta k'ara tambaya, "Ah ah babu abunda ya faru, da yike nayi shigowar dare ne a jiyan shi yasa ban shigo nan din ba," sai da ya k'ara duk'ar dakai kafin yace, "Ina son zan k'ara aure!" Shiru yayi yana jiran jin amsar da zata bashi, Ita ko sai tayi shiru abinta kamar ma bataji mai yace d'in ba, D'aurawa yayi da cewa, "Na tura can gidan su yarinyar wajen iyayen ta a Lagos sai dai kuma a lokacin shi mahaifin ta bayan sunyi magana da wanda na tura yace a dakace su saboda waliyin dazai bada auren ta baya k'asar idan ya dawo sai su koma ayi magana, to jiya dana iso naje na gaisheda kakarta ita kuma ta shaida min cewa indai na shirya to suma a shirye suke dan basa son abin ya d'auki lokaci, tana dai nufin idan za'aje a tafi da komai na neman aure kawai dan a cewarta bata son a wuce nan da wata d'aya yau iyayen yarinyar zasu shigo gari shi yasa nace bari in zo in muku bayani" "To ubana mai kake nema a gunmu kuma tunda ka riga ka shirya harka riga ka tura magabatan ka mu nan bamu da labari daka kawo min zancen yanzun mi kake so ni kuma ince ne? Ai ni kuma bani data cewa sai dai in muku fatan Alkhairi tunda kai dai ka zama d'an kanka har kayi girman da zaka tura wasu can daban nema maka aure bayan mu iyayen ka muna raye to ai ba laifi idan ansa ranar sai a shaida mana mu sanar da yan uwa,dama ka dad'e kana neman auren ne abunka mu bamu da labari, kai yanzun inba rashin ta ido irin naka ba yaushe ka rabu da ita wancan shine yanzun da matar ka ke fama da jikinta yau lafiya gobe ciwo shine zaka tattago wani sabon aure, koda yike ai in bakayi ba baka gaji iyayen ka ba" "Kiyi Hakuri Hajiya ita yarinyar dama nidai na dade ina ra'ayin ta ban samu damar gabatar da kaina bane sai yanzun" "Ai Allah 🤔 to sannu aikuwa na maka murna to wasu iyayen ka tura can gidan su tunda su dai iyayen ka na nan banji suna labarin ba?" Duk'ar da kai yayi kafin yace "Brigadier ne ya nemo min auren ta" "Brigadier dai uban matar ka?" Ta tambaya tana mai jinjina abun, "Kai amma dai kam kam sam baka da kawaici baka da ta ido, yanzun ka rasa wanda zaka aika nema maka aure sai uban matar da kake aure Sarki wannan wani irin rayuwa ce, wai ma tukun na ita yarinyar da kake neman wacece ita?" "sunan ta Maimuna iyayen ta dukan su yan nan ne amma mazauna Lagos ne" "Su waye iyayen nata anan d'in nike son sani?" Allah ne ya taimake shi wayar shi tayi k'ara a daidai lokacin da take jiran amsa daga gareshi dan haka sai yayi amfani da wannan damar ya sulale ya fice daga gidan, Gidan Malam ya wuce suka had'e da ya Sheikh a sashen Malam din sukayi ta hira. Da dare Hajiya ta tara su Baba Usman a falon ta maganar zuwa neman auren AK da take son suje a gobe ta fara gabatar musu, Dukan su daga iyaye mazan har matan kowa ya nuna farin ciki da jin dadin shi na had'in auren a bayyane, bayan an gama tattauna akan auren su AK maganar Moon shima Abba Ahmad ya sako hajiya bata katse mishi hanzari ba har sai da yakai karshen zancen shi da cewa maneman auren Moon d'in zasu iso gidan a gobe dan ya kirasu cewa ya iso k'asar dan haka gara suzo a tsaida komai daya kamata, "Suwa ke neman aure Maimunan?" Hajiya ta tambaya, Gyara zama yayi dan yasan anzo inda yake tsoro azo din, "Hajiya dama munk'i shaida miki ne mukace sai munzo sai a gabatar da komai a gaban ki, Wannan yaron d'an gidan Malam Sulaiman na unguwar malamai d'an yayan su Mukhtar mijin Jiddan ki shine yaje har can Lagos da zancen yana neman auren Maimunatun Brigadier uban matar shi ne kuma yaje mishi neman auran shida abokan shi mutum biyu cikin su harda tsohon abokina, To dai tun lokacin nace musu su d'an dakata har in iso k'asar saboda in gabatar miki da zancen kafin isowar su" "Masha Allah sai dai kuma ban gane dogon kwatancen naka ba naji kace d'an yayan Mukhtar, wai mijin Jidda na kake magana ko wani daban?" "Eh shi dai Hajiya" "Ikon Allah to waye yayan nashi ni ban gane shiba" Shiru yayi yana kallon gefen da Baba Usman yake zaune wanda ya fuske abinshi kamar bai san akan me suke magana ba, "Hajiya shifa yaron shine mijin da Allah yasa ya auri Meenal a shekarun baya" "Ohh wai kana so kace min Sufyaan dai Sarki wanda aka aura ma Meenal ya saki shine ya dawo neman auren Moon yar uwarta kuma?" Cacaca falon ya haura da surutan mata har baka gane abunda suke cewa, dan a karkace zancen ya shiga kunnuwan su, Gyara zama Hajiya tati dan taba kowa damar tofa albarkacin bakin shi, Abba Ahmad shi dai da yaga surutan yak'i karewa shi ya tsawata musu da cewa, "Dan Allah kuyi ma mutane shiru ku barmu mu tattauna abunda ya taramu anan" Shirun sukayi suka koma jimami k'asa² inba rainin wayau ba taya ma ya auri Meenal yanzun kuma ya dawo yace Moon yake so ai wannan sam ba maganar da hankali zai d'auka bane, Sufa matan sun natsu ne dan sun san cewa babu ma ta yanda za'ayi Hajiya ta goyi bayan al'amarin amma wai sai suka jiyo muryar Hajiya tana cewa, "Aiko dai indai Sarki ne Maimunatu kam ta more miji dan Wallahi samun miji irin shi dai yanzun sai an tona, dan haka suna isowa babu b'ata lokaci su gabatar da komai kawai ayi batun sa rana dan haka sai ka kirasu ka sheda musu suzo da shirin su" Duka jama'ar falon da kallo irin na mad'aukakin mamaki suka dunga binta, Anya wannan Hajiyar da suka sani ne kuwa? Umma ce ta gaza shiru tayi magana cewa, "Hajiya tsohon mijin Aminatu fa ake magana taya kuma za'ace Maimoon ta aure shi, in auren za'a mata ai gara a bata dama ta fad'i wanda take so sai a aura mata in ma babu ga d'an yar uwata nan Lukman tun bata kai haka ba yake kwakwa a kanta" Sai da Hajiya ta k'are mata kallo tsaf kafin tace, "Shi auren Sarki da Moon d'in akwai ta inda Allah ya haramta shi a musulunce ne?" Shiru falon yayi wannan Karon ma Umman ce dai ta amsa da cewa, "Amma Hajiya kusancin yayi yawa kuma Ana barin halak kodan kunya" "To nidai na riga na gama magana Moon dai Sarki ta zab'a a matsayin miji in baki sani ba ni na fad'a miki yanzun dan haka shi zata aura, shi dan yar uwarki tace bata son shi dan haka babu mai mata dole, ku kuma jini da kyau maganar nan ta tsaya iya nan bana son in dunga jin wasu k'ananun magana suna tasowa a bayan fage, dama can Allah yayi cewa Moon ce matar shi tun farko wanda kuma duk yace zaiyi jayayya da hukuncin Allah to ya shirya shida Ubangijin shi, ba kuma Moon ba duk wata yar data isa aure ina bukatar ganin magabatan wad'anda ke neman su kafin kubar garin nan". Tana gama kora musu nata jawaban ta haye sama abinta ta barsu suna k'ara cakalkala zancen, A daren Abba Ahmad ya kira Brigadier sukayi magana shi kuma ya tabbatar mishi da cewa insha Allah zasuyi k'okarin isowa Zaria a gobe, wannan kenan, A daren Meenal Sultana da Safiyya matar Yusuf suka dawo gidan na Hajiya dan AK ya shaida ma Meenal cewa karsu sake suce zasu kwana a unguwar malamai su dawo gida su kwana, Bayan dawowar su har sunyi wanka sun kwanta suna hira tsakanin su ya kira wayarta akan ta fito ta same shi yana jiran ta, tana tura baki tana komai haka nan tasa hijab ta fita badan taso ba dan Wallahi yau ba karamin gajiya tayi ba, Bashi a falo dan haka sai ta bude kofar falon ta fito dan har yanzun akwai hayaniyar a gidan tasan kila yana farfajiyar gidan, Koda ta fito bata lura dashi ba sai ji tayi kawai ya jata zuwa bayan wata k'aramar bishiya dake kofar falon, "Waiyo Allah na wanene kai miye haka" take fad'a tana son kwacewa, Juyo da ita yayi yana dariya, "Kedai matsoraciya ce wallahi, yanzun nan ke fisabilillahi da ban kira ki ba haka zaki kwanta kuma har ki iya yin bacci abinki bayan kin san yau uni nayi da yunwar son ganin fuskar ki, da ace Sultana bata d'auki hoton kwalliyar ki ta turamin bafa da shike nan kin sha dani,ai dai kema kin san hakan bai dace ba nina fa" fa d'a yana lankwashe kanshi a gefen kafad'ar shi, "To kaima ba kana cikin naka abokan ba! Shi yasa ai ban kira ka ba saboda kar in dame ka" "Waye yace miki zaki dameni ne?" "Ba kowa" "To fad'amin kinyi kewa na yau" Murmushi tayi tana d'an rausayar da kai gefe, "Allah nidai gani nikeyi sam kamar baki wani damu dani ba" "Na damu dakai mana" "Tsaya kiga hotunan da Sultana ta tura min" ya fad'a yana nuna mata hotunan a cikin wayar shi, "Kinyi kyau amma dai gaskiya ni bana son kina goga wannan abun a bakin ki in zaki fita koda ko inda zaki shiga babu mata" "Me?" Ta tambaya tana d'ago kanta ta kalle shi, Shi kuma sai yakai yatsar shi dai dai bakinta a jikin hoton, "wannan jan abun da kika goga a bakin ki nike magana" "Wai jambaki? Baiyi min kyau bane? To amma ai yau kowa yace nayi kyau" Ta fad'a a shagwabe, "Eh ai nima saboda kyan da kikayi yayi yawa shi yasa nayi magana dan bana son inga kin shiga waje idanu sunyi miki yawa inba haka ba kuma lallai zaki fara yawo da facemask" Dariya ma ya bata dan haka ta dara "Waima facemask ana zaune kalau kaima ai kana da kyau me yasa baka sawa idan zaka fita?" "Ina sawa mana kece dai baki gani ba" "To nidai zanje in kwanta kaga dare yayi" "Ke yanzun nan fa kika fito" ya fad'a yana riko hannun ta, "To ai na gaji da yawa ne yau" "Ok tunda kin gaji saiki zauna a gida gobe basai kinje ko ina ba" "Tab lallai ma bikin Meelat nefa" "Eh bikin nata fa so kike insa miki ido kiyi ta ba kanki wahala shike nan bazaki huta ba, kinga nima duk yau haka nike ta jina kamar banda lafiya kuma nan d'ina sai k'aikayi yakeyi" Ya fad'i hakan a yayin da yakai hannun ta d'aya gefen fuskar shi dai dai wajen dimple din shi, "Me yake damun ka to? In sosa maka?" Ta tambaya ta kallon shi da tausayi a fuskar ta, "Ai ba sosawa akeyi ba" "Me akeyi?" Jawota yayi zuwa gaban shi kafin ta ankara taji Sautin muah a gefen nata fuskar, Kwacewa tayi tana kai mishi duka, "Allah nidai ban yarda ba ai nace maka bana son haka amma baka ji," "Ok ok sorry to zoki rama to shi kenan" Daga bayan su sukaji tafi na tashi RAF RAF RAF, "Kai amma AK kaf shekarar nan banga mara kirki kamar ka ba, Yanzun nan dama ashe tsabar munafunci har budurwa gareka shine mu bamu da labari, wacece ita? To yau dai Allah ya tona maka asiri anyi walkiya mun ganka, Wallahi Musty baka kyauta min ba daka kasa kirana tun tuni ka bani labari ni kuma in tattaro kayana in dawo nan in tare ayi komai a gaba na" "Kai dallah ai da ace a lokacin na fad'a muku karyatani zakuyi amma yanzun da Allah yasa kaji kuma ka gani kaga kaima sai kaba wasu labari, yanzun dai muje ciki dan Allah ka wani zo duk ka tsorata min Ya"cewar Musty, "Kan uba wallahi ban wucewa sai naga ko wacece" wayar Shi ya ciro ya fara musu hotuna duk da cewa wajen babu haske sosai, Shi kuma AK ganin haka sai yaja Meenal din ya maidata bayan Shi ya boye, "Faisal zanci uban ka in baka dena d'aukar mu hoto ba, Matar tawace kake son d'auka ka watsa kowa yagani?" Yan hannun Meenal din yayi sai da suka kai bakin kofar falon ya bud'e ya tura ta, "Wuce ciki sai da safe" Shi kuma Faisal cewa yayi "haba AK wannan ai wulakanci ne bazaka bar yarinya ta gaisheni ba haka akeyi duk kabi ka wani boyeta to yanzun ya za'ayi idan na ganta gobe in ganeta? Kai dai d'an iskane wallahi kuma wallahi kowa sai yaji zancen nan haba ashe Shi yasa ka barmu a waje ka shigo ciki wato kazo duba lafiyar fulawar ka". Juyawa yayi da gudu zuwa inda sauran abokan su suke yana basu labari su kuma kamar masu jira haka suka taso AK gaba akan cewa lallai fa ya kira musu ita ta fito ta gaishe su su ganta, Shi kuma yace musu uban kuturu yayi kad'an, Ya dai sha sharri ba kad'an ba kowa da abunda yake cewa wasu na fad'in wai Allah yayi ya samu aljanar data aureshi ta rabu dashi da kyar wasu kuma na cewa, wai hala dai bashi ita akayi dan sun san da wuya ace shine ya ganta yace yana so, Sanda Yusuf ya zauna ya fara basu labarin badakalar da aka sha kafin ya furta mata yana son ta koh kasa zama a cikin su Ak yayi dan haka suka hauro kamar zasu cinye namar Shi d'anye. *Ummiee ce*[10/3, 3:49 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 41* Washe gari kasawa AK yayi ya tsare tun asuba yake jiran saukowar Meenal k'asa, dan haka tana saukowa koh gaisuwa bai tsaya sun yi ba yake ce mata, "Amma da wuri zaku fita daga gidan nan yau koh?" "Eh ina kwana!"ta bashi amsa, "Lafiya lau ya gajiyar ki" "alhamdulillah" "Idan zaki fita yau ki d'auki abubuwan da kika san zaki buk'ata dan bana son yawon nan tsakanin nan da can unguwar ki zauna a can d'in kawai idan an gama bikin kya dawo ni kuma in ina son ganin ki zan biyoki can d'in kindai ga yanda gidan nan ya cika da maza ni kuma bazan yarda kiyi ta faman shige da fice a gaban su ba," Allah mai iko dafa itace tace mishi zata je can d'in ta tare ta tabbata sai yayi tsalle ya dire kafin ya kafta mata kashedin cewa Shi sam bai yarda da hakan ba, amma gashi yanzun a sauk'ake ya sallama ta ai ita hakan ma gaba ta kaita, dan haka bata tsaya jayayya ba sai kawai ta amsa mishi da cewa "to" "Zo muje ki gaishe dasu Abba" ya fad'a yana jan hannun ta suka fice daga falon na Hajiya zuwa sashen su Abba Ahmad, kai jama'a AK dai sam ya manta da wani abu wai Shi kunya domin dai can yaje gaban iyayen shi wai yana gabatar musu da Meenal din a matsayin sirikar su, Shi bai san da batun zaman da akayi a gidan jiya ba dan lokacin baya gidan dan haka saiya kama rokon Abba Ahmad din cewa dama su yake jira suje su nemo mishi auren ta. Da wurin suka wuce kamar yanda ya buk'ata ba tareda tarin abokan shi wadanda sukaci burin son ganin ko wacece Yarinyar da shi d'in wa kwarema ba, wannan rana dai ko ina ya zama busy gidan Hajiya suna ta shirin zuwa d'aurin auren Musty da neman auren AK kuma da zasu gabatar a gidan Malam bayan an gama d'aurin auren ga kuma shirin tarbar bak'in su wad'anda zasu taho neman auren Maimoon da sukeyi, A gefen Sarki koh koda ya shiga gidan Malam yaso ne dama ya same Shi yayi mishi bayanin Neman auren da za'aje mishi ayau sannan kuma yaso ace batun neman auren nashi ya fitane ta bakin Malam d'in ta yanda basai anyi ta surutai akan hakan ba sai dai kuma koda ya shiga bai iske Malam ba wai yayi sammakon zuwa kano wajen wani d'aurin auren shida Ya Sa'eed amma Baba Adamu da Baba Auta su suna gida, Abune da bazai yuwuba wato yace zai kai batun ga Baba Auta duk da cewa yasan bazaik'i zuwa ba amma shi dai yana jin kunya gaskiya, dan haka bayan sun d'an tab'a hira shida Sheikh sai ya wuce sashen na Baba Adamu bayan gaisuwa sun d'an tab'a hira dashi dan gane da aikin Sarkin dama fannin kasuwancin su kafin Sarkin ya gyara zama ya fara korama Baba Adamun abunda ke tafe dashi, "Baba wato dama aure nike so in k'ara!" "Ah ah masha Allah kaga jarumi to yanzun fa ya ake ciki?" Adamun ya tambaya yana taya shi murna "Eh to da yike ita Yarinyar ita da iyayen ta dukan su a Lagos suke zama, ni kuma ganin idan na kawo maganar nan wajen ku kamar zan baku aiki na tashin da zakuyi kuje har can sai kawai naje ma Baba Brigadier da maganan shine shi kuma ya d'auki abokan shi suka je can gidan su Yarinyar suka samu mahaifin ta domin neman izini,to baban dai tun lokacin ya sheda musu cewa yayan shine waliyin ita Yarinyar kuma shi ba anan Nigeria yake zaune ba, dan haka sai ya had'asu da yayan nashi sukayi magana akan idan ya shigo sai suzo nan agabatar da komai daya dace, to jiya dana shigo gari naje can family house din su munyi magana da kakarta ta kuma shaida min cewa in za'aje atafi da komai na neman aure dan so take asa rana gaba d'aya," "Masha Allah kace yar Babbar gida ka nemo mana to ai bashi da komai mu ai hakan ya mana badai kai ka riga ka shirya ba?" "A shirye nake duk yanda suka yanke yamin," "Ina ne family house din nasu?" "Iyalan gidan Prof Abdul Khareem ne wanda ke tudun wada" "Prof mahaifin Mommyn ku tanan gidan kake nufi?" "Eh shi nake nufi" Jin jina kai Baba Adamu yayi kafin ya kara jefo mishi tambaya cewa, "Kuma su can d'in sunsan cewa kaine ke neman auren yarsu?" "Eh sun sani dan dafarko ma ita Yarinyar taki saurarena amma da mukaje can gidan wajen Baban ta shi ya fahimce mu kakar suma kuma ta bada goyon baya" "Wai kana so kace min Hajiya tasan da cewa kaine ke neman auren jikarta a karo na biyu kuma harta amince?" Baba Adamu ya fad'a cike da mamaki "Eh ta sani, itama Meenal ta sani dan itace ma tayi min jagora wajen yar uwar nata" "Ah to masha Allah dama ai amincewar nasu shi mukafi buk'ata, tashi kaje insha Allah za'a gabatar da komai yau basai gobe ba karka damu dasu iyayen ka na nan kuma ni zan musu bayanin komai da kaina," Su Brigadier sun iso shida abokan shi su biyu sai, kuma shida kanshi ya zauna da Malam Sulaiman ya mishi bayani akan dalilin su na zuwa garin, ba k'aramin kunyar abinda Sarki ya aikata Malam Sulaiman yaji ba, ta ina ake haka fisabilillahi ka taso Baban matar ka tundaga wata uwa duniya ya taho har Zaria nema maka aure, shi dai yace babu inda zashi dan haka sai ya wakilta kanin shi Lawal da kuma Baba Adamu suka kwashi juna su biyar zuwa gidan Hajiya, Sun samu tarba na girma da mutuntawa a wajen su Abba Ahmad babu b'ata lokaci kuma suka gabatar da komai daya dace na neman aure tun daga kan kud'in gaisuwar uwa da uba goro da cingum komai da ake buk'atar shi a wajen sun gabatar dan haka aka tsaida rana nan da wata uku idan Allah ya kaimu da rayuwa, Sai bayan da komai ya kammala kafin shima Baba Usman ya bijiro ma da Baba Adamu zancen son zuwan da sukayi can wajen su ayau dan su nema ma AK auren Aminatu suma, Sun d'anyi maganganu dan ya shaida musu cewa Malam baya nan amma tunda har Allah yasa su sunzo nan ai basai sun basu wani wahala ba kuma tunda dai har su yaran sun dai daita a tsakanin su zaiyi ma Malam bayani idan sun tashi zuwa sai suzo suma kamar dai haka da duk wani abun buk'ata na sanya rana shi dai ya basu Meenal duk da cewa dama Meenal din tasu ce. To an dai watse taro cike da tarin farin ciki na murnar arzikin da ake shirin kullawa, tare dukan su suka wuce wajen d'aurin auren ana gama wa kuma su brigadier suka juya basu kwana ba duk da cewa Sarki yayi musu tayin kwanan, A gurguje..... Gefen Amarya da k'awayen ta lafiya lau sukaci gaba da gudanar da shagulgulan bikin su an d'aura auren Jamila da Angonta Mustapha da rana bayan an sauko daga masallacin juma'a da yamma aka gudanar da kayatacciyar walima wanda ango da amarya suka halarta tareda abokan su, anayin sallan magrib kuma angwaye suka kawo mota suka kwashi Amarya da kawayen ta zuwa GRA gidan amarya anayin sallan ishsha'i kuma suka k'ara kwasan su bayan an k'ara shirya amaryar zuwa wajen dinner, sai da aka kwashe yan uwa kaf kafin Amarya da kawayen ta suka fita daga k'arshe gaskiyar yan magana da suke cewa ko wacce mace ranar auren ta ana k'ara mata kyau domin dai wani irin kyau mai d'aukar hankali Meelat ta tsatso a wannan ranar, a cikin wad'anda suka zo d'aukar amarya har da AK sai dai shi ya shaida musu cewa ba d'aukar Amaryar Musty yazo ba ah ah shi yaxo d'aukar nashi amaryar ne tunda har ubanta yace ya bashi ta riga ta zama nashi kuma yanda kuraye sukayi yawa a wajen gara ya kula da kayan shi, Sultana da Maryam ne suka rik'o Meelat tareda wata yar uwar su Meelat din suka fito da ita Musty dake cikin motar da zasu saka amaryar da kanshi ya fito ya tari abinshi ya janye ta zuwa cikin motar, AK dake cikin nashi motar ne shima ya fito a sanda ya hango Faisal na k'okarin sa Sultana da Meenal su shiga cikin motar shi, Gaban Meenal din yasha fuska a d'aure yake cewa "ina kike shirin zuwa da wannan kwalliyar na fuskar ki" "Me kwalliya na yayi yanzun kuma?" "Amma ai nace miki bana son kina goga wannan abun a bakin ki a sanda zaki shiga cikin mutane koh?" Hankacin shi ya ciro daga cikin aljihun rigar shi, "Nidai dan Allah karka goge min ina son abuna a haka" ta fad'a tana tura baki, "Aminatu" wata daga cikin kawayen su dake tareda Maryam a wajen motar Sadeeq ta kirata, dan haka saita juya da sauri tabar wajen tana mishi gwalo, shi kuma sai ya k'arasa wajen Faisal suna magana, K'awar nata ce ke tambayan ta bayan ta k'arasa inda suke, "Friend amma dai wannan yayan ki ne koh?" Ta tambaya tana nuna mata AK, "Eh Yayana ne" meenal ta bata amsa, "Yana da mata?" Ta k'ara tambaya, "Ah ah" "Oh saurayi ne kenan bashi da mata?"ta k'ara tambaya tana gyad'a kai, "Eh saurayine" meenal ta k'ara amsa mata, "To dan Allah friend kid'an gabatar dani a gunshi mana wallahi nidai ina son shi yamin shine dai dai kalar mijin da nike son aure" ta k'asa fad'a tana karye wuya alamun rok'o, Fuuuu Meenal ta wuce tabar wajen a fusace zuwa wajen da motar AK yake tana isa ta bud'e bayan motar ta shiga ta kullo k'ofar motar da k'arfi a fusace, Sultana ce ta k'arasa inda Yarinyar take tana dariya ta dafa kafadarta take cewa, "Ke baki san shine mijin da zata aura ba shine zaki wani kirata kice kina son mijinta, gaskiya dai baki kyauta ba"tana gama fad'ar hakan ta wuce abinta ta shige motar Faisal, Shiko AK ganin da yayi ta wuce su a fusace da kuma yanda ta bud'e bayan motar ta shiga hakan ne yasa ya juya zuwa wajen motar shima ya bud'e bayan ya shiga ya sameta tana ta faman cika tana batsewa, "Ya akayi ne? Meya sameki?" Sai da ta watsa mishi harara mai lafiya tana turo baki tace "duk ba kai bane," "Ni kuma mai nayi?" "Eh ai haka zakace da ace baka fito daga cikin motar ka shiga cikin yan mata ba ai da bazata ganka ba balle harta wani cemin wai tana sonka" ta fad'a tana kauda kai gefe, Murmushi yayi ita kuma Sautin murmushin nashi ne yasa ta juyo taci gaba da masifa, Shidai bai kulata ba hartayi ta gaji ashe wai shirun da yayi mata kuma yayi laifi dan haka sai kawai ta kama murfin kofar da niyyar bud'ewa ta fice, Fincikota yayi ta fad'o cikin jikin shi kuma yasa hannu ya kulleta gam a jikin nashi, "Yi hakuri to naji nayi laifi in ma kince karmuje can d'in ai sai muyi zaman mu basai munje ba" "Tab duk wannan kwalliyar da nayi ne zan wani zauna a mota bikin Meelat dina akeyi fa" "Oh dama kwalliyar badan ni akayi ba kenan anyi ne dan wasu su gani, ai kin tunanin ma d'azun nace a goge jan bakin nan kika k'i" Mutsu mutsu ta fara a jikin nashi tana son kwacewa, "Nidai kabar min kwalliya ta kuma kana ganin duk sun wuce fa" Sakin ta yayi da sauri ya fice daga motar ya zagaya gefen direba ya zauna bayan ya gyara rigar shi data fara yamutse wa sakamakon mutstsukan data sha a wajen Meenal, "Anan zaki zauna ko zaki dawo nan ne?" Ya tambaya batareda ya waigoba ya kunna motar, tsallakowa ita kuma tayi batareda ta fita ba ta dawo gaban motar, Tissue ta yago bayan ta zauna ta goge jan bakin dake bakinta sai da ya fita tass kafin ta maye gurbin shi da lips glows ta d'an k'ara goga hoda kad'an ta kuma gyara zaman d'aurin kanta, da gefen ido yake kallon ta harta gama basu yi tafiya mai nisa ba suka isa inda ake gabatar da Dinner d'in koda suka isa amarya da ango sun shige babu wasu mutane sosai a waje, Bude kofar shi yayi yafita kafin ya zagaya ya bud'e mata nata side din ya mik'a mata hannun shi ta kama ya fito da ita, gefe ya maidata ta jingina da jikin motar shi kuma yasa kanshi cikin motar wani chain ya ciro a cikin dashboard ya fito dashi a hannun shi sai da ya maida kofar motar ya rufe kafin ya riko hannun ta na hagu ya mak'ala mata chain din da aka k'awata shi da wasu irin duwatsu masu gyalgyali, d'ayan chain din dake tare dana hannun ta makala a nashi hannun shima sai kuma ya cire wani d'an karfe k'arami dake matsayin mabud'in chain din ya saka a cikin aljihun shi, "Menene wannan d'in?" Ta tambaya, "Idon ma tambayi kin d'auka zan barki hannu sake ne in mun shiga kiyi ta yawo idon kowa a kanki?" "Wai shi yasa kasamin ankwa a hannu? Kai dan Allah yaya to haka zamu shiga ciki mutane suna kallon mu kuma fa harda yan gidan mu a ciki" "Eh haka na yanke kinga idan muka shiga a hakan duk wanda yagan ki yasan cewa matata ce a tareda ni" Kamar ta bude baki tayi ta kurma ihu haka taji sai dai kuma idan tayi mishi kuka ai ta bada kanta dan haka kawai ta bud'e yar k'aramar Purse din dake rik'e a hannun ta ta ciro face mask guda biyu, ta mik'a mishi guda d'aya itama tasa d'aya, "Me kikeyi da facemask a cikin purse kuma?" "Shi nasa d'azun da zamuje wajen walima dan ni bani da niqab," "Kuma sai kikafi yin kyau ma a hakan" Sun gudanar da Dinner lafiya har zuwa kusan 12 dare kafin taron ya tashi masu komawa gidan Amarya aka wuce dasu tare da amaryar sauran jama'a kuma suka koma unguwar malamai, andai yi biki lafiya an kuma watse yan nesa dana kusa kowa ya koma inda ya fito, *Muje a gurguje* Bayan kwana biyu su Baba Usman suna ta jiran kira daga Baba Adamu dan suji yaushe ne zasu je tunda dai Malam ya dawo, Shi kuma a gefen Baba Adamu abubuwan ne suka d'an sha mishi kai dalilin hakan ko zama bai samu sunyi da Malam ba balle kuma ya shaida mishi yanda sukayi a yayin zuwan su tudun wada neman auren Moon dan ko labarin neman auren ma a bakin Baba Lawal jama'ar gidan sukaji haka ko suka dunga kucin cina zancen da cewa ba'a kyauta ma Aminatu ba taya Sarki kuma zai koma yace yar uwarta yake nema da aure kuma, Sun daiyi maganganu wanda hatta da uwar gida bata so hakan ba sai dai kuma tunda an riga an gabatar da komai har an tsaida ranar biki sai kawai ta bisu da addu'a allah yasa ita Moon d'in ta zama cikon farin cikin da Sarki ya rasa tsayin shekaru, A gefen Salman ko ya riga ya gama yanke hukuncin tun karar Malam tunda gashi daga uwa har uban shi babu wanda ya d'auki maganar shi nason auren Meenal da mahimmanci balle wanin su ya shige mishi gaba amma gashi shi ai Sarki yaga yar uwar Meenal din yana so har an bashi, Gafen Aliyu daya Hashim suma duk sun shirya tsaf dan zuwa gabatar da kai a gaban Malam domin suma sun bincika anan gida sun gane cewa har yanzun ba'a fara zancen auren Aminatu a cikin gidan ba dan haka kowa ya yanke hukuncin gabatar da kanshi kawai wata kila shine mai rabo, A gefen Sheikh Naseer da Meenal kam Alhamdulillah yanzun abubuwa sun d'anyi sauk'i ba kamar kwanan baya dako zaman inuwa d'aya bata son yi dashi ba, Tun dawowar ta gidan lokacin bikin Meelat bata yarda ta koma gidan Hajiya ba har yanzun dan yanzun ya zama gidan sirikan ta, kullum safe da yamma da ita ake karatu a falon Baba Malam kuma Sheikh ne Malamin, sosai malam yasa ido yake lura da yanayin kusancin dake tsakanin ta da sheikh d'in yanda suke mu'amala ya matuk'ar kwantar mishi da hankali dan haka yanzun ne dai dai lokacin daya dace ya agabatar da nashi tsarin a kansu, Dan haka ba tareda ya nemi shawara da kowa ba kawai wata rana bayan sun kammala karatun su da maza keyi da dare kamar kullum idan an idar da karatun wanda Sheikh ke gabatar wa shi kuma Malam sai ya rufe da addu'a, To yauma dai bayan sun kammala karatun anyi addu'a har mazan sun fara shirin fita malam ya dakatar dasu, dan haka duk suka dawo cikin masallacin suka zazzauna suna jiran jin me zai gabatar musu, Gyarar murya yayi kamar yanda ya saba aduk sanda zaiyi magana kafin ya daura a yayinda ya maida kallon shi kan Sheikh yake cewa, "Nasan zakuyi mamakin yanda na dakatar daku daga tafiya kuyi hakuri wani d'an sanarwa nike son yi" Ba komai Malam duk sukace suna cigaba da sauraren shi, Shi kuma yaci gaba da cewa, "Alhamdulillah nasan dukan ku nan dai kun wayi wannan bawan Allahn da a yanzun shine mai gabatar mana da karatun tukan da mukeyi, to masha Allah ga wadanda basu san ko waye shi d'in ba shi d'in dai yarona ne domin ko d'an da kanwata ta haifane a can k'asar larabawa ya gabatar da karatun tukan shi, dan haka nike son yau a yau a gaban dukan ku ku shaida ni Malam Al mustapha na bashi auren d'aya daga cikin yayana mata dan bazan yarda yaci gaba da zama a matsayin gwauro ko kuma yabar garin nan batareda mata ba" Kabbara gaba d'aya masallacin ya d'auka jama'a na fatan alkhairi da cewa kwarai hakan ne ya dace dama bai kamata abar Babban mutum babu mata ba, wani dattijo ne shima ya mik'e yake k'ara sanarwa cema shima yana da yan mata a gidan shi yana kuma rokon alfarma ko sheikh zaizo gidan shi ya duba cikin yaran shi shima, tunda koba komai ai Babban mutum kamar Sheikh mace d'aya bazata wadace shiba, Duk fa yanda sheikh yaso ya zame sun hana shi damar hakan dan wani ma daya tashi cewa yayi shi kuma ya bashi gidan da zai zauna da matan anan cikin garin Zaria, kai kyaututtuka dai kala da kala Sheikh yasha shi a wannan rana data zame mishi tsaka mai wuya dan shi dai bai san ko wacce yar malam yake nufi ba tunda bai kira suna ba, Wai shi da yake batun tattarawa ya koma Abuja shine ake batun yi mishi tarko a Zaria shi ina shi ina auren mata har biyu fisabilillahi. Haka aka watse karatun ranar kowa na farin ciki shi kuma aka barshi cikin jimami, a wannan daren kaf unguwar ya d'auka cewa ai Malam yaba Sheikh mata kowa idan ya tambaya cewa wacece a cikin yaran gidan aka ba sheikh din sai kowa yace bai sani ba, Kafin gari ya waye labari ya isa kunnen Salman Aliyu harda Hashim, Dan haka gari na wayewa Salman ne ya fara isa falon Malam ya gabatar da kanshi matsayin mai neman auren Aminatu, Shigar shi d'akin da gabatar da kanshi babu jimawa sai ga Hashim koda ya shiga ya samu Salman kuma hakan bai hanashi gabatar da kanshi ba shima a gaban Malam matsayin mai neman auren Aminatu shima, Babu wanda Malam yaba amsa a cikin su har Aliyu shima ya iso shima dai yanda suka gabatar da kansu hakan shima yayi, Sai da gama jin ta bakin su dukan su kafin yace musu duk suyi hakuri su koma zai nemi ganin Aminatun zai neme su daga baya, Ana cikin wannan al ajabi ahalin gidan master suma suka iso gidan da rana tsaka, Bash ne da iyayen shi hudu maza, Sun gabatar da kansu a matsayin masu neman auren Aminatu suma sun kuma k'ara daba Malam din labarin abinda ya faru a baya wato lokacin da shi Bash ya rasata da irin jinyar da yayi ta sanadin rashin ta, Sannan suka shaida mishi cewa su dai a shirye suke suna fatan kuma wannan karan za'aba d'an su. *Ummiee ce* [10/3, 10:34 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 42* To suma dai daga bash d'in har iyayen nashi bayan malam ya gama sauraren bayanan su hak'uri ya basu akan zai nemi jin ta bakin Meenal din dan haka zai neme su daga baya, Jin hakan sai su kuma suka rok'e shi akan ko Bash din zai iya fara zuwa wajen Meenal d'in?, Malam yasan ko yace musu ah ah indai yaran yanzun ne yasan sai shi Bash din ya nemi hanyar da zai samu ganawa da Meenal din dan haka sai kawai yace musu babu damuwa yaba Bash din damar zuwa ya gana da ita, To sudai sun tafi da hope d'in cewa za'a dace dan haka suka tafi cikin farin ciki. A cikin gidan Malam d'in ko dama tun cikin dare har zuwa wayewar gari kowa hasashe kawai yakeyi akan wacece Malam zai had'a aure da Sheikh domin dai yanzun haka a cikin gidan Malam kawai yanzun haka suna da yan mata guda d'ai d'ai har 5 wadanda dukan su sun isa aure, duk da a cikin su akwai wad'anda aka fara zancen auren su amma sun sam tsaf Malam yana iya canza ra'ayin shi, Tun cikin daren har gari ya waye musu kawai akeyi wannan idan yace wacce malam zai ba sheikh sai wani kuma yace ah ah wacce kaza dai sukafi dacewa ita da Sheikh sudai iyayen su mata babu wacce tace ko kanzil su yaran gidan da sirikan gidan ne kawai keta faman yin hasashen su,duk wannan hasashen babu wanda ya kawo zancen had'in Meenal da Sheikh dan a ganin su tunda akwai yan mata a gidan bai zama lallai malam ya kawo ta a lissafi ba, Sai gashi basu gama hasashen nasu ba suka fara ganin jerin gwanon da akema falon na Malam yau, Duk abinda ya faru a gaban Farouq da Sa'eed ya faru saboda zuwan Salman yayi dai dai da suma suna cikin falon na Malam kuma har sai da Malam ya sallami su Salman din suma suka bar falon dan haka su biyun su suka shiga da labarin cikin gidan, Koda suka shiga falon Mommy Hauwa musu kawai akeyi dan tun safe Sultana ta tasa Fauxieyerh a gaba da tsokana akan cewa tasan had'in da malam yayi ita yaba yayan ta, suma kuma sauran yan falon duk sai suka yarda da maganar Sultana duba da cewa kowa yasan cewa akwai shiri sosai a tsakanin Sheikh da Fauxieyerh dan haka sai suka sata a gaba da tsokana cikin masu tsokanarta kuma harda Meenal da Moon ita dai Moon cewa tayi wannan had'i yayi dai dai dan dama mace inba irin Fauxieyerh ba babu wacce zata iya zama da Ya Sheikh ta dadin rai haba shikenan mutum ya maida kanshi ina zaka masallaci ina ka fito islamiya, dan haka sun san Fauxieyerh cema ba kowa ba duk da cewa A sashen Baba Auta akwai Fauxieyerh da Fatima, sashen Baba Adamu kuma Rayhan, sai can sashen Malam kuma Akwai Aisha da Asma'u, amma duk sauran dai basuga dacewar su da Sheikh ba sai Fauxieyerh, Suna cikin hirar ne su ya Sa'eed suka shigo ko zama basuyi ba Sa'eed ya fara kiran sunan Meenal, "Kai yayan mu tun baka zauna ba daga shigowa ka faramin kiran mafarauta gani nan fa ko ka fara makanta ne dan na lura idan Maman twins tana kusa baka gane mutane" Ta fad'a daga inda take zaune akan kujera Sultana na tsaye ta bayan ta tana mata kitson kalaba a kanta, Karasawa shi kuma yayi ya zauna bayan ya amsa gaisuwar da yan falon suka mishi ne yake cewa, "Ke ya kukayi keda su Ya Hashim?" Sai da ta wulwulga idonta cikin falon tana mishi alamu da idanu, "Ni ba wannan ne a gabana ba dukan su yan falon dai imu imune babu bare, Amma Meenal ai ce miki nayi idan baki ra'ayin ko d'aya daga cikin su to ki dakatar dasu daga zuwa kai maganar nan gaban Baba, wato ashe duk shawarar dana baki babu wacce kika d'auka to tunda haka kika zab'arma kanki yanzun ai sai ki shirya dan dukan su gasu can sunzo sun gabatar ma da Baba kansu a matsayin masu son auren ki ciki harda wancan mara kunyar Salman" Natsuwa sauran yan cikin falon sukayi suna sauraron shi kamar su yake ba labarin ba Meenal ba, yana kai k'arshe suka had'a baki masu cewa "what" da zare ido nayi masu cewa "me" da zare ido suma sunayi ita dai Meenal kusan sumar zaune tayi, "Shi Salman din ne yanzun haka yaje ma Baba da batun cewa ita Meenal din yake son aure?" Aunty Murja wacce harda ita ake zaune a falon ta tambaya, "Kwarai kuwa Anty bayan shima harda Aliyun Yola da kuma Ya Hashim, dukan su haka suka jera sahu a gaban Baba dukan su wai auren Meenal suke son yi dan sunji jiya yayi sanarwar cewa ya bama Sheikh mata a cikin yaran shi mata, Gata a zaune Aunty nan na tashi na tafi har gidan Hajiya na sameta na bata shawara saboda su biyun ni suka fara sama akan maganar ta ni kuma na dakatar dasu daga zuwa wajen Baba nace su fara samun ta da maganar tukun, ban ma san cewa wai ashe harda Salman shima son ta yakeyi ba" Kallon shi ya maida kan Meenal din yana mai cigaba da cewa. "To ai gashi nan baki dakatar dasu ba sun taho sun aikata abinda na gudar miki kuma shi baba yace musu suje tukun sai yaji ta bakin ki kin san ko cikin ukun nan dole ki d'auki d'aya" Daga bayan su Mommy Hauwa ta amsa da cewa, "Babu wanda ya zamar mata dole a cikin su, domin nidai kaf din su banga mijin dazan iya aurama Meenal d'ina ba, in suna ganin dan sun kai maganar gaban Baban ku shine zaisa a tilasta mata ta zab'i d'aya daga cikin su to sunyi tumbur ai na fad'a tun a baya cewa Meenal ta gama yin aure a cikin ahalin nan kuma ta gama d'in kenan, wallahi koda ace akwai wanda take so a cikin su bazata aure shiba balle kuma nasan tunda ba nonon mahaukaciya tasha ba bazata ma fara ba," K'arasowa falon tayi fuska d'aure ta nemi kujera ta zauna, Aunty Murja itama ta amsa da cewa "gaskiya kam kaf din su babu mijin auren Meenal anan yanzun shi Salman baiji kunyar Baban naku ba harya iya zuwa yace mishi yana son yabashi auren ita Meenal din? Oh wato harya manta da abinda yayan shi yayi koh wato shi rasa kunya, ko koh dan yaga a lokacin babu abinda ya faru, shi kuma wancan Babban banzan Hashim haka ya wanko nashi kafafuwan tsofai tsofai shima ya taho da kanshi ba aike ba, to dai kaf cikin su garama Aliyun shima kuma duka duka yaushe yayi auren dahar yake neman k'ari, ko ko ita Meenal din ita k'adaice mace da duk zasu daka mata wawaso haka, To wannan yak'in dai naki ne ke Meenal dan haka tun kafin tafiya tayi nisa gara ki shaida ma Baban naku cewa bakiga mijin aure a cikin suba," Cacaca haka falon ya k'ara rudewa gaba d'aya aka ture zancen Sheikh da Fauxieyerh da akeyi aka cigaba da caccakar zancen su Hashim barin ma da ita Meenal din ta basu labarin yanda tayi dasu duka ukun tun sanda suka tunkare ta da maganar, Hashim dai yafi kowa shan caccaka sai ko Salman duk da wasu suna ganin cewa shi Salman ai da ace ba Yayan shine ta aura da farko ba tofa da kosu sai su taya shi yak'i, ita kuma Mommy Hauwa dai ta tsaya akan bakanta kan cewa babu Meenal ba k'arayin wani aure a cikin wannan ahalin, Duk da tasan batun neman auren Meenal da AK takeyi bata kawo zancen ba dan karma suce saboda d'an yayan ta yana son Meenal din ne yasa tace haka, Magana dai koya akayi ta a gidan yawa sai ta fita, dan haka cikin lokaci k'ank'ani maganar ta bazu a cikin gidan dama mak'ota, Mommy da kanta tace Meenal din su koma can gidan Hajiya dan tasan tunda akayi haka tofa dole Malam zai nemi jin ta bakin Meenal din, Ita dama Sultana abinda take so kenan dan tun d'azun take faman kiran wayar Hajiya amma abun haushi layin ta a kashe koya akayi Hajiya tabar wayarta ta mutu oho domin ita dai ko 98 percent gareta zatace a sa mata caji tafiso taga wayarta da 100 percent koda yaushe, ta kunsa gulma iya gulma jira kawai takeyi su isa ta fesa mata, Itafa Sultana da Moon yanda suka damu ita uwar gayyar ko a jikinta wannan karon tunda ta samu goyon bayan Mommy Hauwa tasan bazata yarda a k'ara mata wani auren dole ba koda ko ace bata da tsayayyen saurayi balle kuma ita da take da AK, Suma da suka d'aga hankali suna dai tausaya mata ne kawai amma ita jikinta yana bata cewa sam Baban ta Malam bazai k'ara maimaita kuskeren baya a karo na biyu ba, badai yace musu duk suje sai yaji ta bakinta bane? To ita kuma abu mai sauk'i kalmar eh ne ko ah ah fa, ya rabata dasu dukan su, Abinda kamar wanda dama can an riga an tsara shine domin ganin ahalin Bash sai ya k'ara ba kowa mamaki ace mace d'aya maza hudu sun gabatar da kansu a matsayin masu neman auren ta kuma duka a rana d'aya! Yau dai yan gidan Malam na ganin ikon Allah. Yaro Malam ya aika sashen Baba Auta dan ya kira mishi Meenal tazo su gana da bash kafin su wuce, Sai gashi yaron ya dawo mishi da amsar cewa ance Aunty Meenal tana tudun wada gidan Hajiya kaka, Hakuri Malam yaba su akan cewa Ashe Meenal d'in bata gidan, dan haka dole suka wuce inda shi kuma Bash a ranshi ya yanke hukuncin cewa can gidan Hajiya zai bita tunda dai yanzun ya samu lasisin dazai tun kareta, Nasan masu karatu zasuce to meya hana bash zuwa gareta tun kwanan baya? Abinda ya faru shine a sanda yabar gidan su Meelat gidan su ya koma, Yana isa kuma da murnar shi da komai ya isa d'akin hajiyar su wacce ita kuma ganin shi cikin farin cikine yasa ta tambaya ya akayi ne tagan shi yana ta washe baki? , Babu b'ata lokaci shi kuma ya zauna ya zayyane mata ganin da yayi ma Meenal harma da bayanan daya samu akan ta na mutuwar auren ta, Ta tausaya mishi kuma ta tayashi murna daga baya domin ita duk tsayin lokacin nan tayi zaton cewa shi bash din tuni ya dade da cire Meenal din a cikin zuciyar shi, Amma irin farin cikin data ganshi a ciki yau saita gane cewa soyayyar Meenal din ashe ba mutuwa tayi ba dogon bacci dai tayi yanzun kuma ta taso, Tana son d'anta dan haka take son farin cikin shi, ita bazataja da hukuncin Allah ba tunda tasan irin wahalan da Bash din yayi a shekarun baya wata kila yanzun dawowarta gareshi ya zama alkhairi a garesu baki d'aya, Dan haka sai ta tuntube shi cewa to yaushe zaije ya k'ara gabatar da kanshi a wajen Meenal din karo na biyu? Shi kuma sai yace mata baya son ya k'ara maimaita kuskuren da yayi a baya dan haka bazai tunkari Meenal d'inba har sai an nemo mishi izini a wajen iyayen ta, An fara maganar cewa za'a tura can gidan Malam neman izini ne kuma a lokacin jikin Master ya motsa dan jinya yakeyi har yanzun ciwon nashi yakan d'an motsa mishi lokaci bayan lokaci, Motsawar ciwon ne kuma yasa aka ajiye maganar zuwa gidan malam da sunan sai sun dawo daga ganin likita wanda harda Bash d'in suka tattara suka tafi, sunyi zaton tafiyar bazai jasu tsayin kwanaki ba sai dai kuma suna barin k'asa jikin ya k'ara rikece wa basu dai suka dawo k'asar ba sai jiya kuma suna dawowa a jiyan aka wakilta wadanda zasu taho tambaya gidan malam kuma yau suka iso yanzun zasu saurari kira daga malam ne kamar yanda yace musu. Koda su sultana suka isa tudun wada Hajiya bata gida tana can gidan Dadah Turai, amma Sultana bata huta ba sai da tabi ta har can gidan, A kofar gidan suka had'u ita Hajiya tana dawowa ita kuma Sultana tana k'ok'arin shiga, "Ke kuma lafiya wato kin shigo gidan baki sameni ba shine bari ki biyo sahuna, to juya mu koma gani nan nima na fito in ma gulma kika gintso mu koma can muyi ta" "Hajiya ai tunda kikaga na kasa zama na biyoki kema kin san cewa da walakin wai goro a cikin miya labari ne da d'umi d'umin shi yake tafe dani nayi ta kiran wayar ki tun ina unguwar malamai amma a kashe," "Ba dole kiji wayata a kashe ba yar nan, Allah ya had'ani da jikoki masu bak'ar barna, ina zaman zamana fa a cikin sashena d'an nan na wajen Hasana inda kika san an aiko shi haka ya biyo ni ban san uban me yakai wayata hannun shiba sai k'arar fad'uwarta kawai naji taratsatsa ya rotse kayan kwalbar a ties to dai haka na kwashe shi shida wayar bayan na zane mishi jiki tsaf da zabori nakai shi wajen uwar shi kuma na fad'a mata wallahi sabuwar waya fil nike bukata kafin nan da faduwar rana inba haka ba ran uban kowa saiya ba'ci dan nidai bazan d'auki Asara ba tunda bance ta saki d'anta ya biyoni har sashena ya nakashe min wayata yar shafa ba" Suna tafe suna hira hat suka isa falon Hajiya, sai da Hajiya ta zauna sannan tace to ya akayi kinje kin taso keyata kuma bakice dani komai ba, "Hajiya Ina aka kwana batun neman auren Meenal ne?" Sultana ta tambaya, "Ke aini kin tuna min, Nidai Allah ya had'ani da mashiriritan yara wallahi, kigafa tun ranar da akasa ranar auren Moon dasu Usman sukayi magana da Adamu a falon nan yace musu zai kai maganar gaban Malam idan ya basu lokaci sai suje agabatar da komai to nidai tun ranar banji wani ya k'ara tada maganar ba a cikin su, Ke tsaya wani abu ya farune da kike tambaya ta?" "Humm Hajiya ke kina nan kin saki baki to abubuwa suna can suna faruwa a gidan Malam" "Me kuma ya faru yar nan?" "Kinga Hajiya jiya da dare Malam yayi sanarwar cewa yaba Yayana Sheikh auren d'aya daga cikin yayan shi, To wallahi tun daren jiyan muke canki canka, mun kaso gano wacce malam yake son had'asu da Ya Sheikh sai kuma kawai yau da safen nan sai ga jerin gwanon maza har uku sunje sun gabatar da kansu wajen Malam din da sunan wai suna son auren Meenal" Katseta Hajiya tayi da cewa, "Mazaje uku kuma daga ina aka samo su?" "Kinga kanin Sarki Salman shiya fara zuwa dan dama tuntuni yake bibiyar Meenal din ita kuma ta taka mishi burki, todai tun baibar falon Malam ba saiga wani shi kuma wai Ya Hashim sai kuma Ya Aliyu shima" "Uhumm sai shi kuma malam d'in yace dasu me?" "Ce musu fa yayi wai suje duk zai neme su idan yaji ta bakin Meenal din, mu bamu san meke faruwa ba muna zaune suya Farouq ne suka shigo da labarin shine ita kuma Mommy Hauwa tace mu dawo nan" "Ah lallai ma, to ai ba laifi su ai sunje tambaya ne koh?" "Eh " Sultana ta amsa, "Toni kuma auren zan tura a nemo min shi a yau basai gobe ba bari ki gani ai da zafi zafi akan daki k'arfe allah ma yasa akwai sauran lokaci har yanzun tunda yanzun nema ake idar da sallan azahar" Tana gama fad'in hakan ta fice daga falon, Ita ko Sultana tsallen murna ta kamayi dan ita dama abinda take so kenan, Ita dai haka nan kawai taji tana matuk'ar sha'awar ganin AK ya auri Meenal, dan haka sai ta nemi waje ta zauna ta lalubo wayarta ta danna ma number din AK kira, Yanke kiran nata yayi kamar yanda ya saba sai shi kuma ya kirata daga baya, Babu b'ata lokaci ta d'auka sukaci gaba da gaisawa, "Nace ne dama bari in tambaya inji yaushe zaka shigo gari?" "Wani abu ya faru ne Sultana?" "Eh to gaskiya dai abubuwa na shirin faruwa zaifi kyau ace dai kana kusa" "Bani labari maiya faru kuma karki boye min komai" Gyara zama tayi ta kora mishi labarin abubuwan da suka faru tsakanin jiya da yau bata boye mishi komai ba, Godiya yayi mata shi kuma akan cewa zai kamo hanya yanzun amma karta shaida ma Meenal din cewa sunyi waya, Fatan Allah ya kiyaye hanya tayi mishi kafin suka sauka akan layi, Hajiya ko tana fita sashen Abba Ahmad ta wuce kai tsaye, ta same shi yana cin abincin rana dan haka itama saita nemi waje ta zauna, "Kai Ahmad nace ya kuke ciki ne akan maganar zuwa neman nan ne wai?" "Hajiya ai kinsan shi Adamun cewa yayi yanda sukayi da Malam zai tuntub'e mu shi muke jira dai har yanzun" "Toni na gaji da jira malam dai yana nan a gari dan haka yanzun nike so ku shirya k'afata kafarku muje a nemo auren nan insan a wata matsayar muke, Haba jama'a wai inace da kune masu naci kullum kuna magana akan cewa yaron nan yak'i fadda matar aure yanzun kuma ya fidda amma magana sai tafiyar hawainiya take, Ni inda ace tun farko nasan haka zaku b'atamin lokaci wallahi dako kusa bazan tsaya ina jiran isowar kuba tunda dai allah yasa ina da mutanen arzikin da zasu shigemin gaba wajen ganin abun nan ya tabbata dan haka yanzun ka d'aga waya ka kiramin Usman yazo idan ma kud'in da zakuyi hidimar kuke bakin cikin fitarwa a aljihun ku ni allah yasa na nemi kud'i kuma na tara tun baku da wayau, Dan haka yazo yamin lissafi daga naira 1 zuwa adadin dazai isa a siya abun bukata na zuwa neman aure dan yau gidan nan ba'a bacci sai nasan ina muka kwana" "Hajiya toki bari in tuntubi shi Adamun muji ta bakin shi tukun!" "Ba Adamu ba Adumo kaji koh nace ba Adamu ba Adumo to bari kaji wallahi a yau d'in nan zaku ai watar da abinda nasa ku k'afata kuma kafarku dan karma ku dawo kuzo kuna sheqa min k'aryar abinda ba'ayi ba," Tana gama fad'in hakan ta fice daga sashen ta wuce sashen baba Usman cigewa tayi a falon ta fara kiran sunan shi, Tare shida Umma suka fito falon, "Biyoni muje" ta fad'a tana wucewa gaba dan haka sai ya take mata baya sashen Abba Ahmad suka k'ara komawa abinda ta fad'ama Abban shi ta k'ara maimaitawa a gaban Baba Usman ta kuma sashi ya kira samarin gidan akayi list na komai da ake buk'ata ya basu kud'i sukaje siyowa goro da cingum dama duk abinda ta lissafa akwai shi a kasuwar tudun wada dan haka yan aiken basu jimaba suka dawo da kaya nik'i niki, kafin dawowar su kuma ta shiga can gidan su Dadah ta taso keyar mazan gidan mutum biyu ta kuma sa Sultana ta kira mata Musty a waya tayi magana dashi akan cewa koma ina yake ko me yakeyi ya sake yazo gida ya sameta, Gangami sosai Hajiya ta had'a bayan ta tabbatar da cewa komai ya kammala yanda take bukata ne kuma tasa suka shiga cikin mota suka bar gidan zuwa Unguwar Malamai. To gadai Hajiya can tayi gangami, kuyi addu'a Allah yasa karta dawo sai ta amso auren jikokin ta Ameen please 🙏. *Ummiee ce*✍🏼 [10/5, 3:33 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 43* Bayan fitan su Hajiya kitchen Sultana ta shiga ta d'ibo dambun nama a cikin bowl ta kuma had'o da lemun exotic mai sanyi kafin ta dawo falo ta zauna ko takan su Meenal da Moon bata biba wad'anda suka kunshe kansu a cikin d'aki ko hirar uban me sukeyi bata da masaniya tun bayan shigowar su gidan, Kuma har hajiya ta had'a gangamin gayyarta suka bar gidan su biyun basu da labarin abinda yake faruwa a cikin gidan, Wayarta tayi connecting da speakers d'in dake girke a falon tayi playing wak'a kafin ta koma ta nemi waje takame bayan ta zauna ta d'auki k'afa ta d'aura d'aya kan d'aya ranta fess abunta itafa matakin da Hajiya ta d'auka ba k'aramin dadi ya mata ba wallahi, Itafa dan dai kawai karta koma gidan a yanzun ace ta fiye shegen gulmane amma wallahi da sai tabi bayan su itama ayi komai a gaban idon ta, Allah dai yasa Hajiya ta jajirce akai k'arshen komai a yau dan Wallahi ita fata take Allah yasa wannan zuwan kawai Hajiya ta fitittike tace bata barin gidan Malam sai an d'aura aure, muga k'arshen mayu, Inba maita ba Meenal dai kamar ita kad'aice kwallin kwal mace a cikin dangi da za'ace a rana d'aya maza uku sun jeru jerin gwanon neman auren ta, Cigaba dacin dambun ta tayi tanayi tana gyad'a kai dan wak'ar gwanja take saurare tana kuma bin wak'ar mai taken "Asha rawa rawa mata kusha rawa rawa kusha sha'anin ku duniyace... Sama mataaa" Kai da kaga yanayinta kasan bata d'auke da ko wani damuwa, Tayi nisa wajen cin dambun ta kirar daya shigo wayar shine ya katse mata wak'ar da take bi, "Wani d'an anacen ne yake son takura wa rayuwata ne?" Badan tasoba haka nan dai ta mike taje ta d'auki Number din Ya Sa'eed ne mai kiran dan haka bata tsaya yanga ba ta amsa kiran da sallama, "Kuna tudun wadan ne?" Ya jefo mata tambaya, "Eh "ita kuma ta amsa mishi, "ina Meenal?" Ya tambaya, "Suna sama ita da Moon ni kuma ina falo, kai kana ina ne Ya'ya?" "Ina gida ki..." Saurin yanke tayi da cewa, "Yauwa dan Allah karkaje ko ina dan Hajiya tana hanya ita da iyalan gidan nan ta had'o gangamin sun zasu zo nan gidan neman ma Mai Jama'a auren Meenal" "Ban gane ba! Me kike cewa ne?" "Allah kuwa da gaske nike fad'a maka Mai Jama'a shike son Meenal da auri nan gidan dai babu wanda bai sani ba kuma tun ranar da akasa ranar su Sarki su Baba Usman sukayi ma Baba Adamu magana shi kuma yace musu zaiyi magana da Baba Malam idan kun dawo daga kano duk yanda ake ciki zai kira ya musu bayani sai suje gidan ayi magana...." Katseta shima yayi da cewa, "Shine ke kuma kina zuwa gidan yanzun kika ba Hajiya labarin abinda ya faru na zuwan su Salman wajen Baba yau koh?" "To shiru kake so inyi ne bayan kuma nasan itama Meenal din AK take so, ni bawai bana son ta da sauran bane ah ah amma dai zanso ace wannan karan ta samu wanda take so" "Turk'ashi lallai yau akeyin ta" Ya Sa'eed ya fad'a daga can gefen, "Me ya faru kuma Ya'ya?" Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yace, "Kin san bayan fitan ku wani Bash sunzo gidan nan shida iyayen shi kuma suma neman auren ta sukazo sannan sun shaida ma Baba cewa wai shi din tsohon saurayin ta ne har labarin abinda ya same shi a lokacin auren ta da Sarki saida suka labarta ma Malam yanzun haka shi ya nemi izinin ganawa da ita kuma Malam ya yarje mishi yanzun haka na tabbatar da cewa yana hanyar zuwa nan gidan wajen ta," "Wai kana nufin shima mayen nan yau yaje gida?" "Kin san shine?" "Eh na san shi naji labarin shi dama tun a KD da muka dawo kuma kafin biki mun had'u dashi a makarantar su Meenal din kuma wallahi ni dakai na nace mishi AK zata aura bashi ba, wato ashe da bai tunkare ta ba can gida ya tafi kai tsaye kamar yanda nayi hasashe tun farko lallai ma gayen nan to Allah ya kawo shi lafiya, kuma wallahi bazan fad'a mata zaizo ba nan zan zauna in jira zuwan shi" "Sultana mai kike shirin aikatawa? Kardai kice zaki mishi rashin kunya dan baki sani ba ko har yanzun ita tana son shi" "Ah ah wallahi bata wani son shi, idan da ace tana son shi ai bazata amsa ma AK ba tunda Maryam ta bata labarin cewa ya dawo k'asar har sun ga juna ita dashi tun lokacin, Nidai Yaya duk ba wannan ba dan wannan mai sauk'i ne yanzun dai so nike ka taimaka ka wuce falon Malam kayi mana jiran isowar su Hajiya inda hali dan Allah kayi min video d'in komai da zai gudana ko kuma kayi min audio in komai ya kammala ka turo min dan Wallahi ji nake uwa inyi tsuntsuwa in dawo ayi komai a gabana, da ace nasan hakan zai faru da bazan bar gidan ba har Sai sunzo wallahi" "Oh yanzun kuma ni kike so ki maida ji da ganin ki koh, wato gulma kike so in kwaso in labarta miki" Saida tayi k'asa da murya kafin tace, "Gulma na nawa kuma bayan yanzun ka gama bani labarin zuwan wancan mayen," Daga murya tayi tana cewa, "nidai ai da Allah na had'aka" Yanke wayar yayi daga can gefen shi batareda ya bata amsa ba, ita kuma sai cire wayar a kunnen ta tana dariya, "Kujishi da karfin hali fa dan Allah shima ba gulman ya kirani ya fadamin ba yanzun?" Wuce wa tayi ta maida wayar a speaker ta dawo taci gaba dacin dambun ta, sama sama ta farajin sallama mai had'e da nocking da akeyi daga kofar falon a hankali, Dan tsam tayi a zaton ta ko Larai zatajiyo sallaman ta fito ta duba ko waye sai kuma taji shiru Larai bata fito ba, d'age bowl din dambun tayi daga kan cinyarta ta maida shi a gefe ta ajiye kafin ta mik'e kwalin exotic din a hannun ta tana kurb'a, "Ameen Alaikum salam wanene ana zuwa"take fad'a a yayinda take takawa zuwa kofar falon "Kaiii.... 😳 da gaske Ya Sa'eed yake wallahi! Kai kuma me kazoyi a gidan nan kuma?" Ta tambaya tana fita daga falon tayi gaba ta lek'a bayan shi dan taga shi kadaine ko nan d'in ma tareda waliyan nashi ya taho, Maimakon ya amsa mata sai kawai ya kewayeta ya wuce ta gefen ta ya shige cikin falon,kallon mamaki tabi shi dashi kafin da sauri ta dawo da baya tasha gaban shi tana wani ware hannayen ta tare mishi hanya irin a dole ita ta tare mishi hanya karya wuce d'in nan bayan already fa ya riga ya shiga cikin falon, "Ina tambayar ka me kazoyi shine kake k'ara shigewa gidan mutane ba tareda izinin masu gidan ba? To dai koma wa kake nema bazaka samu ganin shiba dan mutanen gidan basa nan ni kad'aice a gidan kuma ni bana maraba da bak'o irin ka dan haka ka juya ka koma inda ka fito an gode da ziyara idan Hajiya ta dawo zan fad'a mata tayi bak'o, Meye ma sunan ka? Koda yike babu ma buk'atar jin sunan naka" Wannan karan ma bai amsa taba ya k'ara zagayeta ya isa kan kujera ya zauna ya barta a tsaye ta rike kwonkwoso tana wani jijjiga jiki kamar wata wacce take shirin yin dambe dashi, "Nace maka fa masu gidan basa nan shine kuma har da neman wajen zama ka zauna?" "Can you please do me a favor?" Ya tambaya batareda ya kalleta ba, Karasawa inda yake tayi tana wani tab'e baki, "Favor? Me kake buk'ata?" "So nike ki shiga daga ciki ki kira min Meenal saboda ita nazo nan bawai saboda keba, idan kuma bata nan ina son zanyi magana da Hajiya" "Tab sannu wato ma nice zan zama yar aiken ka, kuma ai nace maka babu kowa a gidan!"ta fad'a a yayinda tayi wucewar ta takoma kan kujerar data tashi ta d'auki dambun ta taci gaba daci, Bai k'ara kulata ba shima sai kawai ya cire wayar shi daga aljihu yaci gaba da latsawa, Harara kawai take ta faman aika mishi daga inda take zaune, saboda tsabar iya hege irin na Sultana duk k'arar speaker din data kunna wanda har a harabar gidan ana iya jiyo shi amma saida ta k'ara volume dan kawai ta takura ma bawan Allah , Shiko bawan Allah ko gezau bai nuna hakan ya dameshi ba, Yarinyar nan fa alamu sun nuna cewa idan bai biyo mata ta bayan gida ba to tabbas bazasu shirya ba, Dan haka sai kawai ya soka wayar shi a cikin aljihu ya mik'e, Ita kuma da gefen ido take binshi da kallo a zaton ta ko har ya gaji da zaman ne ya nema ma kanshi sauk'i zai tafi, sai dai ga mamakin ta maimakon ya nufi hanyar k'ofa domin fita daga cikin falon sai taga ya wuce wajen kayan kallon dake falon, bata gama tunanin abinda zaiyi a wajen ba taji falon yayi tsit wato wakar da take sauraro na gwanja mai taken (kuyi ta kanku muma muyi ta kan mu dariya bafa soba) ya d'auke sakama kon zare socket da Bash yayi daga jikin wuta gaba d'aya, Zabura tayi ta mik'e tana binshi da kallon mamaki, "Kai 😳 ina ruwan ka dani to da zaka zo ka kashe min? Nan fa ba gidan ku bane da zaka zo ka takura min," Ta kowa yayi yazo ya zauna a inda ya tashi ko kallo bata isheshi ba, fuuu ta kwashi jiki zataje ta k'ara kunnawa, A tsawace yace mata "karki sake kice zaki k'ara kunna min wak'a a wajen nan" "To ai nan ba gidan ku bane Malam" Larai ne ta fito daga cikin kitchen, "Sultana bak'o kikayi ne? shine ko ruwan sha baki kawo mishi ba?" "Allah ya kyauta niba bak'ona bane" "Ina wuni" Bash ya gaisheda Larai "Lafiya lau bawan Allah Barka da zuwa gashi kazo kuma Hajiya bata gida bana tunanin ko zata dawo yanzun kuma!" "Ah ah ba wajen Hajiya nazo ba wajen Meenal nazo ko zaki taimaka ki kiramin ita?" "Ke Sultana me yasa to baki kira mishi ita d'in ba" "Tab tab' ai wallahi bazan kirata ba, taya ma zan kirata bayan nasan shi din neman takara yazoyi" ta fad'a tana kauda kai gefe, Wucewa sama Larai tayi dan ta kira mishi Meenal din sai da yaga ta haura kafin ya maida duban shi kan sultana, "Abokin takarar wa kike cewa?" Saida ta harare shi kafin ta bashi amsa da cewa, "ai tun ranar da muka had'u sai da na shaida maka cewa ka d'auki na annaba dan ita d'in dai ta riga ta k'arayin maka nisa a karo na biyu amma bakaji ba dan maita sai da ka k'ara biyota, to dai duk ka gama zarya da rawar jikin ka baka samun ta yanzun din ma wallahi" Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau kafin yace, "Me yasa kika tsaneni har haka? Na tab'ayi miki wani abinda ya b'ata miki raine? A iya sanina dai tsayin shekarun rayuwata babu a inda na tab'a ganin ki balle wani abu ya had'ani dake amma ban san me yasa tun had'uwar mu na farko kike jefoni da bak'ak'en magan ganu ba ko k'awayen ki sun fad'a miki wani maganar ne a kaina ina son sani?" "Ni mai sa in tsane ka? Allah ma ya tsareni kawai dai ni gaskiya nije fad'a maka dan bana son inga mutum yana cusa kanshi a inda bashi da kwarjini," "A zaton ki idan Meenal ta nuna bata ra'ayina a yanzun zan gaza cigaba da rayuwa ne? Ina son Ameena da zuciya d'aya dan haka zan taya ta son duk kan abinda take so koda ace hakan yana nufin cewa ni zata ajiye a gefe ta d'auki wani na, zata bata kwarin gwuiwa saboda duk yanda nake sonta bazan tauyeta akan dole saita zauna dani ba alhalin nasan cewa soyayyar ta wanina takeyi wa bani ba, amma a yanzun bazanyi saurin yanke hukunci ba har sai naji ta bakin ta daga sanda kuma ta tabbatar da zancen ki cewa ta riga ta fidda ma kanta mijin da take ganin cewa shine zab'in zuciyar ta ni kuma zan bita da fatan alkhairi ne dan ba kaina farau rasa abin so ba kuma baza'a k'areshi a kaina ba ina fatan kin fahimta" Mak'alewa Meenal tayi a tsaye, dan tunda Larai ta shiga ta sheda mata cewa tayi bak'o ita da Moon suka biyo bayan Laran suka fito dan ita Meenal tayi zaton ko cikin su Ya Hashim ne wani ya biyota nan gidan idan sune koh Wallahi rashin mutunci zata shuka ma ko waye a cikin su tunda su basu san lala ma ba ta tsiya zata tafi dasu, Sai dai tun kafin ta sauko idanuwan ta suka hasko mata fuskar Bash tsaf, Bash d'inta dai a shekarun baya shine yau zaune a falon Hajiya da sunan yazo wajen ta, itafa harta cire rai da cewa zai nemata tunda taji shiru tun sanda Meelat tace yaje gidan su take sa ran zuwan shi shine sai yau ne zai bayyana a gareta, Tsayuwar tane kuma yasa itama Moon taci burki sukaci gaba da sauraron hira tsakanin Bash din da Sultana, Larai ko tana saukowa ko lura da ita Bash din baiyi ba ta wuce falo ta had'o mishi kayan motsa baki ta kawo ta ajiye mishi, Kamo hannun Meenal Moon tayi suka sauko kasan a hankali, Da sauri Bash ya mik'e yana jin kamar yaje ya tattaro ta ya cusa ta a cikin jikin shi saboda tsabar farin cikin daya lullub'eshi a yayin ganin nata, "Bash " Moon ta kira sunan shi fara'a kwance a fuskarta, "Ashe rai kanga rai yau sai gaka a gidan mu" Da fara'a shima ya amsa ta da cewa, "Moon d'in Meenal long time... " "No see... "Ta k'arasa fad'a tana dariya, "Barka da zuwa gaskiya nayi murnar ganin ka banyi zaton cewa zamu k'ara had'uwa ba, ya bayan rabuwa da iyali" "Alhamdulillah Moon kefa ya kike ya naki iyalin? Ko kema gwauruwa ce kamar dai ni?" Kujerar da Sultana ke kai ta isa ta zauna dan ita Sultana tun maganar Bash din kafin saukowar su Moon bakin ta ya mace murus, "Meenal bismillah k'araso ki zauna mana ko bakiyi murna da ganina bane"ya fad'a yana kallon Meenal, Kwalkwal idanuwan ta suka kawo kwalla tana shirin yin kuka, "waye yace maka banyi murnar ganin kaba?" Ta fad'a da muryar kuka hawayen idonta suna gangarowa zuwa kan kumatun ta, Zama tayi a kujerar kusa dashi tana goge fuskarta da tafin hannun, "Me yasa tun tuni bakazo ba bayan kuma Meelat tace min kaje can gidan su kuma kasan ni bani da number dinka balle in kira ka?" Sanyi jikin shi yayi dan haka baiyi magana ba har sai da shima ya koma ya zauna, "Kiyi hakuri banyi hakan da niyyar ba tun lokacin naso inzo in ganki sai dai kuma a ranar jikin Dady ya motsa dole washe gari muka wuce dashi asibiti amma tsayin lokacin nan kullum cikin tunanin ki nake shi yasa muna dawowa na matsa akan dole aje a nema min izinin ganin ki a can wajen Baba Malam yanzun haka daga can nike," D'ago kanta tayi bayan ta k'ara share hawayen ta, "Bash baka manta dani ba?" "Me zaisa in manta dake Meenal? Bayan na riga nayi ma kaina alkawari cewa koda ace kena rasaki insha Allah zanyi ma kaina makwafin ki a duk sanda Allah yamin arzikin haihuwar ya mace a cikin yaran da zai azurta ni dasu" Tana murmushi hawaye na cigaba da fita daga cikin idon ta tace, "Takwara zakayi min?" "Insha Allah kuwa" "Nagode" ta fad'a tana goge hawaye, "baka sha ruwa ba, Sultana zuba mishi ruwa yasha" "Ah ah bazan sha ruwa daga hannun wannan yar tsanar ba" ya fad'a yana cushe fuska, "Eh kuma nima bazan baka ruwan da zaka shaba" cewar Sultanar tana murgud'a baki, Dan haka sai Meenal din ta mike ta zuba mishi ruwan ta mik'a mishi ya kuwa amsa ya kafa kai sai da ya shanye kafin ya ajiye kofin, "Tashi muje daga waje in baki wani labari"inji Moon, "Ke nima ina da labarin badawa amma dai yanzun babu inda zani dan bazan bar falon nan aci amanar Yayana ba, Ke sister ki fad'a mishi gaskiya fa karki cutar dashi wajen kin fad'a mishi gaskiyar cewa wani daban ne a cikin zuciyar ki yanzun ba shiba, kai kuma ai yanzun kace min zaka tayata son abinda take so koh? To ga dama ka samu" Janyeta Moon tayi suka fice a cikin falon harabar gidan suka zauna anan ne kuma ita Sultanan take ba Moon labarin cewa su Hajiya fa sun tafi unguwar malamai nemo auren Meenal, dan haka sai suka fara kiran waya dan suji ko su Hajiya sun samu isa can d'in ya ake ciki kuma, A falon ko bayan fitar su kafe Meenal bash yayi da kallo kafin ya bud'e baki yace, "Kin kara kyau sosai Dr" Duk'ar da kai tayi tana murmushi, kaima ai ka k'ara kyau sosai bani labari ya bayan rabuwa?" "Abubuwa da yawa sun faru dani marasa dad'i Meenal sai dai yanzun Alhamdulillah komai ya wuce ya zama labari gashi kuma kema ina fatan wannan karan Allah yasa in dace" "Iyali fa?" Ta tambaya, Dan haka saiya gyara zama ya labarta mata abubuwan da suka faru tun daga ranar daya samu labarin d'aurin auren ta a wannan falon da suke zaune, halin daya shiga dama auren da akayi mishi bayan ya koma zama a malesia rabuwar su ikiliman sai dai bai fad'a mata gaskiyar silar rabuwar nasu ba dan wannan sirrine mai girma da yayi alkawarin cewa babu maiji daga wajen shi, Ta tausaya mishi dan har saida tayi mishi hawaye, Kafin ta gyara zama itama ta bashi nata labarin a takaice, sun jajanta ma juna kafin ya k'ara jefo mata kalmar d'azun, "Meenal Baba Malam ya bani damar cigaba da zuwa ganin ki sai dai kuma jikina yayi sanyi dajin maganganun Yarinyar can.. " "Sunan ta Amina inkiyar ta kuma Sultana ita d'in yar uwata ce da Maman ta da Babana uwa d'aya uba d'aya suke" "Bataci sunan taba sai na maketa wata rana idan taci gaba dayi min rashin kunya"ya fad'a yana tab'e baki, "Sultanar zaka make?"ta tambaya tana dariya, Basar da zancen yayi, "Fadamin suwaye suke kan layi a yanzun dan ina son sanin abokan takara na, Tunda naji Yarinyar can nata maimaita magana d'aya nasan da gaske takeyi dan batayi kama da makaryata ba" "Me yasa kake son sani tun yanzun?" "Kina mamakin me yasa koh? Ki dena mamaki ina son sani ne dan in baki goyon baya, idan ni zuciyar ki ta zab'a miki zanyi farin ciki matuk'ar gaske, a kasin hakan kuma bazan takura kiba sai dai in Baki k'arfin gwuiwa tsayawa akan ra'ayin ki ko baki san cewa yanzun an dena yayin auren dole ba? Idan na matsa saina aureki nasan ban miki adalci ba" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke, Dambun da Larai ta debo mishi ta mika hannu ta d'auko sai da ta d'ibo takai bakin ta kafin ta mik'a mishi bowl din, "Kaci yayi dad'i" Amsa yayi ya faraci batareda ya kusa mata ba, Gyara zama tayi kafin taci gaba da magana kamar haka, "Bash" "uhumm" ya amsa mata sakamakon abin dake cikin bakin shi, "Nayi farin cikin matuk'a ayau da Allah ya k'ara hadamu, ka nemi jin abinda yake cikin zuciyata game da kai a yanzun, sai dai zan fad'a maka gaskiyar cewa Meenal din daka sani a yanzun ba wacce ka sani a shekarun baya bane, Meenal budurwa kasani wacce ke magana dakai kuma bazawara ce wacce tayi aure shekuru masu dan tsayi wacce da ace tana da rabon ciki da haihuwa da tuni an sakata cikin matan da ake kira iyaye, Alaqa ta ganin girma da mutunci ne ta had'ani da kai a baya kafin alaqar tamu ta rikid'e ta koma soyayya, Na soka sosai a wancan lokacin ban kuma tab'a kawo rabuwa a tsakanin mu ba sai dai kuma ba haka Allah ya tsara ba, bayan aurena kuma ban tab'a tunanin rabuwa da Yayana na duk kuwa da irin zaman da mukeyi na kalar na sauran ma'aurata bane, ina so ka sani nayi yak'i da zuciyata sosai a kanka ban sarara ba har saida nayi iyayina wajen ganin na cire soyayyar ka dama duk wata damuwar da zata hanani karatu domin shi kad'ai nasa a gabana ba komai ba, banyi tunanin ajiye sauran sanka a zuciyata ba dan ban tab'a hango ranar mutuwar aurena zaizo ba, komai ya afku da sauri ta yanda auren ya mutu har na zamana ya dawo nan, Nasan zakaji babu dad'i idan nace maka koda aurena ya mutu ban kawo ka a raina balle in neme ka, Ka sani na riga nayi rami tuni na riga na burne komai dan haka sabon babin rayuwa na gina ma kaina, a hakan ne kuma d'an uwana ya gabatar da soyayyar shi gareni, abinda banyi zato ko tsammani ba" Shiru tayi shi kuma sai ya mik'a hannu a sanyaye ya mika mata ruwa, sai da ta amsa tasha kafin taci gaba, "Bash ina matuk'ar son Mai Jama'a, son da ban tab'a zaton cewa zanyi ma wani namiji ha irin son nike mishi, ina farin ciki idan nagan shi cikin farin ciki ina kuma jin rashin dadi idan ni ko wani ya b'ata mishi rai, ina son shi bawai dan yana matsayin d'an uwana ba, ah ah ina son shine kawai saboda shi zuciyata ta zab'a kayi hakuri³" Sai da ta maimata mishi kalmar kayi hakuri har sau uku kafin taci gaba dacewa, "Bazan iya raba zuciyata da son shi in zab'e kaba, hakan kuma bawai yana nufin ina k'in ka bane ah ah har yanzun kallon ka nike a matsayin makusanci na domin ma baka matsayi na musamman a zuciyata batun soyayya nedai nike so mu barta komai ya faru akwai dalilin faruwar shi ni dakai Allah bai k'addara zamu zamo mata da mijiba" Tunda taci gaba da bayani ya maida kanshi k'asa harta gama, "Ba komai Meenal hakan ma nagode, kuma ina ma Dan mai k'arfin murna" Murmushin yak'e, "Baka manta sunan da muke kiran shi dashi ha ashe?" "Taya zan manta kuwa? Yanzun dai muje ki takamin in wuce, yauwa kuma Hajiya tace tana gaisheki, muje ki takamin in wuce" "Nagode Bash nima ina gaisheda Hajiya, amma kasan bani da number dinka kuma kake batun tafiya baka bani ba? " "Kina buk'atar number na?" "Eh mana ka sani ko a cikin yan Matan gidan mu in baka d'aya! Kuma koba ma haka ba aidai kasan na dad'e ban tambaye ka kudin anko da kaza ba, Wai kasan me?" Yana dariyar maganar ta yace ina zan sani yar Malam, ko yanzun ma kud'in kazar za'a amsa ne?" "Ah ah wallahi badai kud'in kaza ba aini nafiso a siyo min kazar a gashen ta, dama zance maka ne yanzun fa nima k'atotuwar Hajiya ce wallahi motocina dai dai har uku" Ta fad'a tana kad'a kai cike da kurari, Fashewa yayi da dariya sosai, Ita kuma sai ta d'aure fuska, "Auw dariya ma kake min mai makon ka tayani murna duk masu tsada nefa yan yayi" "Sorry sorry nifa dariyar murna nike miki tunda Allah yasa burin ki na mallakan manyan motoci ya cika saura wanne kuma, uhumm dama burin uku ne ai zama likita, matoci manya, sai ginama malam gida koh?" "Baka manta ko d'aya ba yanzun biyu sun cika saura d'aya insha Allah shima saura kiris" "To Allah ya sanya alkhairi kawo wayar ki in sa miki number din" Mika wayar tayi ya amsa ya zuba nashi number din yayi saving da sunan shi kafin ya kira, saida kirar ya shiga ya yanke sannan ya mika mata wayar, Fitowa harabar gidan sukayi fuskar su d'auke da murmushi Sultana wacce duk hirar da suke da Moon hankalin ta yana kan kofar falon ne ta taso, "Kai murmushi fa naga kanayi?" Ta tambaya tana zagaye shi, "Karki k'ara kulani ina ruwan ki dani?" "Ke Meenal baki fad'a mishi gaskiya bane duk shawarar dana baki" "Na fad'a mishi" "Kuma shine naga ya fito yana murmushi?" "Moon zoki janye yar tsanar nan a gaba na kafin inyi ball da ita"cewar bash, "Wai nice zakayi ball dani kawai dan nayi tambaya, To wai kai bakaji kishi bane ai kamata yayi inga ka fito fuska a d'aure kana cin magani" "Amma kamar kina da ciwon mantuwa koh? Ina ce d'azun nan nace miki zan tayata son abinda take so? To abinda nike yi a yanzun kenan" "Wai dama da gaske kakeyi? 😳 ashe dai kana da kirki har haka, sannu to Allah ya k'ara hakuri" "Ka dena biyema Sultana inba haka ba ko kwana zakuyi bazata dena saka kanayin surutu ba, Nidai muje in nuna maka motocina karma kayi zaton labarin kanzon kurege na baka" Can parking space suka wuce ta nuna mishi motocin sai da ya zagaye su duka ya kuma yaba, kafin yayi sallama dasu ya shiga motar shi yabar gidan su koma suka koma harabar gidan suka dasa sabon hira anan ne kuma takejin cewa wai ashe Hajiya ta kwashi bataliyan ta sun wuce gidan Malam, Ita dai ranar yau bata san ko wacce kalar rana zata kirata ta, allah dai ya isa tsakanin ta da mutum uku, Salman Hashim da Aliyu duk su suka jawo mata koma menene suna dai zaune suna jiran jin sabon update daga gidan Malam. A gidan Malam ko fitowar su Bash da iyayen shi yayi dai dai da dawowar Baba Adamu gida a wannan lokacin dan haka lafiya lau sukayi gaisuwa a tsakanin su, yana tareda gajiya shi yasa bai tsaya ba kawai ya wuce nashi sashen sai bayan da yayi wanka yaci abinci ne Aunty Murja take shaida mishi abubuwan da suka faru yau a cikin gidan na zuwa neman auren dasu Salman sukayi wajen Malam har zuwa kan su Bash da suka bar gidan a yanzun, Dafe kai yayi cike da jimami, "Akwai matsala ne?" Ta tambaya tana jiran jin amsar shi, "Hajiya da su Usman sun nemi auren Meenal a wajena suna nema ma Mai Jama'a nasu tun ranar da mukaje nema ma Sarki auren yarsu ni kuma na shaida musu cewa zan yi ma Malam bayani sai yasa ranar da zasu zo ayi magana, Wallahi abubuwa ne suka shamin kai banyi zaton cewa hakan zai iya tasowa a yanzun ba kuma, yanzun me zance ma Hajiya idan taji zancen nan bayan kuma su suna da yak'ini akai na shi yasa nasan basu taso sun taho wajen Malam ba tun lokacin" Mikewa yayi ya fice daga falon dan gara yaje ma malam da batun tun yanzun kafin abubuwa su tab'arb'are Allah yasa dai sanarwar da Malam yaba Sheikh mata ba Meenal din yake nufi ba! Dan in har ita yake nufi tofa akwai matsala gaskiya dan koshi bazai goyi bayan abunba indai yarinyar ta nuna bata so koda ko babu zancen AK a hannun shi balle kuma su yasan dashi suka dogara, Malam kad'ai ya tarar a falon nashi saida suka gaisa kafin Malam din ya kora mishi bayani akan zuwan iyalan gidan Master wadanda ya gani, kafin ya koma baya kuma ya bashi labarin zuwan su Salman kamar dai yanda yasamu labari daga wajen matar shi, sai da malam ya gama nashi jawabin duk da ajawabin na Malam ya gane cewa su Salman maganar su bai d'ad'a Malam da k'asa ba, Bayani shima ya gyara zama ya kora ma Malam din na auren dasu Baba Usman suka nema a wajen shi. *UMMIEE* [10/5, 11:23 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 44* Ya'ya ina ganin dai wannan karan ya dace muba Yarinyar nan dama ta zabi mijin aurenta da kanta! basai munyi mata zab'i kamar yanda aka saba yiba, Duba da cewa dukan su wad'anda suka nuna muradin auren nata a yanzun yan uwa ne idan ka cire shi wannan da sukazo daga baya, wad'ancan ukun tun daga kan Salman har Aliyu duk wanda akaba ita d'an uwan shi zaiga cewa shi ba'ayi mishi adalci ba, amma kaga idan muka bata zab'i ta fidda wanda take so a cikin su da kanta dole sauran zasuyi hak'uri kuma baza'ayi kananun magan ganu akan hakan ba!, Maganar shi d'ayan d'an uwan nata d'an gidan Ahmad kuma shima kaga ba abune wanda za'a ture ba tunda iyayen shine da kansu suka tareni da maganar saboda sun san cewa ina da damar dazan iya aurar da Meenal d'in, Sannan kuma a bayanin su sun nuna min cewa su Yaran sun riga sun dai daita kansu dan haka kaga zancen mu muce zamuyi mata shishshigi wajen zab'ar mata miji wannan k'aran bai taso ba," Sai da Malam ya k'ank'ance idanuwan shi kafin ya jefoma Baba Adamu tambaya kamar haka, "Wato Adamu dai so kake kace ni bazan zab'ar mata mijin daya dace da ita ba kenan?" "Subhanallah haba Yaya yaza kace haka, wallahi ko kusa ko alama ba abinda nike nufi ba kenan taya zan kalli idon ka ince haka bayan duk yaran gidan nan tun daga kan yayyen ta mata har zuwa yan k'asa da ita kaine ka zab'ar musu mijin kuma suke zaune lafiya lau a gidajen auren su, Itama abinda yasa nace haka saboda a yanda nata neman auren a yanzun ya kasance ne al'amarin ya dangana da duka ahalin ta biyu mu nan gefen uba da kuma can gefen uwa, kaga dai kai yanzun tsakani da Allah idan kace kaine zaka mata zab'i kamar yanda ka saba na sani Ya'ya bazaka ce zaka bata shi d'an gidan Ahmad ba, Idan kayi haka kuma su yan uwan Jidda bazasuji dad'i ba zasu kalleka a matsayin mai son kanka wato kak'i su kaba naka kuma idan aka duba kusancin duk abu d'aya ne,... " Kara yanke shi Malam yayi wannan karon ma yana mai cewa, "Dama ce maka akayi akwai wanda nike shakka ko tsoro a cikin su idan na tashi yin hukunci ga abinda nike da iko akan shine?, ai ba tsoron surutun mutane nikeyi ba abinda ya dace nike aiwatar wa koba komai kafin in yanke hukuncin sai nayi hangen yaya goben su yaran zai kasance kuma Alhamdulillah ina alfahari da hakan domin kaf yaran dana aurar babu wacce take da matsala da mijinta suna can zaune a d'akunan su babu rashin ci balle nasha kaga auren miji mai ilimin addini ko tanan ya musu rana dan ni ban damu da aura ma yata wayayyen mutumin daku kuke hange ba mutum mai tsoron Allah nike buk'ata wanda zai riketa amana " "Na sani Yaya kuma nima bawai na k'alubalance ka bane akan hakan sai dai su jama'a kallon da zasuyi ma hakan da ban, arziki dai nike roko dan Allah wannan karon ka bata damar zab'e a cikin su saboda ayi ma kowa adalci nidai bana son ayi abinda za'azo ana ganin laifin juna ko kuma zumunci ya tab'u" "Adamu wai wakakeyi ma kamfe a cikin su? Shin a tsagina kake? ko koh tsagin dangin matar kanin ka masu tak'ama da dukiyar da Allah ya basu?" "Ko d'aya ina dai ganin laifin kainane sakama kon jin kirin da nayi ban samu damar gabatar maka da nasu batun atun sanda suka buk'aci hakan ba, dan na tabbatar da ace tun lokacin na Kawo maganar gaban ka da hakan bata faru ba, koba komai kuma ai ido da kunya ace su nema mu kasa basu duba da cewa kwanan nan suma sukaba namu d'an auren yarsu duk da sunfi kowa sanin kusancin dake tsakanin ya'yan, ka dai duba al amarin nan kafin kace zakayi hukunci Ya'ya idan kuma ba haka ba ni zanyi tunanin ko har yanzun baka son had'a zuria dasu ne kamar dai yanda ka nuna shekarun baya kafin auren Jidda da auta da kuma yanda ka dunga mu'amalantar ta bayan auren wanda kowa yasan baka sake mata ba sai bayan data haifo mana Meenal a cikin gidan nan, idan kuma abun nan ya tabbata nasan da yawan mutane suma irin hasashen da nayi zasuyi itama kuma kanta uwar Meenal d'in da ahalin ta zasu hasaso hakan dan haka nike rokon ka tsaya ka duba magana ta da kyau kafin ka yanke hukunci, kayi hakuri kuma dan naji zancen sanarwar da kayi naba Shehi auren d'aya daga cikin yaran nan ina fatan dai ba ita Mama ka bashi ba?" "Adamu³" Sai da Malam ya kira sunan shi sau uku yana amsawa kafin Malam din yaci gaba da cewa, "Ka dai fad'amin abinda ya Kawo ka nan koh?" "Eh yaya, amma ai baka bani amsa ba dan yanzun haka dai ban san me zance dasu Ahmad ba, shin in basu damar zuwa gareka ne ko koh dai wannan k'aran ka bani damar gabatar da abinda ya dace? Kar suji shirun yayi yawa su suce zasu zo nan dan bana son labarin nan yaje musu batareda sunji daga gareni ba" "Adamu akwai wani abunda zaku iyayi ne a yanzun idan nace na riga na yanke hukuncin bada auren Meenal ga wani?" Malam ya tambaya fuskar nan tashi a d'aure kamar tasowar hadarin kaka, Shiko Baba Adamu d'an murmushi yayi shima yana gyad'a kai, "Eh to idan ita Yarinyar tace taji ta gani tana son shi zab'in naka falillahil hamdu bani da abin cewa dan dama abinda take so shi nike mata fatan samu wannan karon, Akasin hakan kuma inaga sai dai kayi hakuri a duba cikin k'annen ta sai abashi in baya muradi kuma sai ya hak'ura, indai kuma Shehin ne kamar yanda nike hasashe ai duk d'aya ne nasan koshi bazai so ayi mata dole ta zauna dashi kamar yanda akayi mata dole ta zauna da Sarki a baya ba, ni dama tunda naji zancen nasan bazaka goyi bayan aura ma d'aya daga cikin su Salman Aliyu ko Hashim ita ba, Shehin dai shine zab'in ka gareta kamar zuciyata ta bani, dan haka kafin ni dakai mu yanke hukuncin zan kirata in zauna da ita ta fad'a min gaskiyar wanda take so a cikin su biyu shehin ne ko shi Mai Jama'a dan ni nacire zancen wadannan bak'in da sukazo nan wurin ka d'azun tuni basu a lissafina" Kallon mamaki Malam kebin Adamu dashi, Wai shine yau Adamu keson ya k'alubalance shi akan auren Meenal? Meenal fa ake magana ba sauran yaran gidan ba, to harshi zai fad'a mishi abinda ya dace da Meenal dama wanda bai dace da ita ba? Shida ko uwar data haifi Meenal din bazata nuna mishi son Meenal din ba, Minene aibun Sheikh da har shi Adamun yake tunanin cewa Meenal zata k'ishi bayan tarin nasabar da yake dashi, ai shi abun alfahari ne a wajen shi had'a zuri'a da Shehi kuma lissafin shi bai hango kowa ba sai Meenal yasan kuma itama zatayi alfahari dashi wannan karon, "Yaya bari inje duk yanda ake ciki zuwa dare zan dawo in labarta maka" (Nasan wasu zasuce Baba Adamu yayi tsaurin ido, sai dai in baku manta ba tun a farkon littafin na shaida muku cewa Malam da Adamu sak'o da sak'o ne sannan tun farko yanda Baba Auta yake tsoron Malam shi Baba Adamu baya tsoron shi haka, kuma kaf cikin ahalin babu wanda yake iya tsayawa a gaban Malam ya tsage mishi gaskiya irin shi Adamun, duk irin mulkin mallaka da Malam yakeyi akan kowa Adamun baya magana dan yasan cewa Malam ya isa dasu balle kuma yaran da suka haifa, Amma abinda ya faru na mutuwar auren Meenal da kuma mutuwar mijin Raheenat hakan yasa yake ganin ya dace afara ba yaran gidan damar zab'arma kansu abokan rayuwa domin dai tun farko inda ace ita Meenal an barta tayi ma kanta zab'i da ba haka ba, itama kuma Raheenat da aka d'auki tsoho mai tarin shekaru aka had'ata aure dashi ko sakandire bata gama ba da ace an jira ta gama aka bata dama da yanzun ba cikin taka ba take ba, duk da cewa yasan komai daya samu bawa Allah ne yakeyin shi amma lokaci yayi da za'a kawo canji a gidan kuma zaiyi amfani da kaunar da malam yake ma Meenal ne wajen cin nasara akan Malam d'in, bawai baya son ta da Sheikh bane ah ah in ta zab'i sheikh zaiyi murna da hakan kodan samu k'aruwar d'ankon zumunci a tsakanin su da yar uwar su, amma fa ya shirya tsaf wajen bata goyon baya a yayinda zata nuna bata ra'ayin shi Shehin. A can harabar gidan ko motocin su Abba Ahmad ne ya shigo gidan a jere bayan an bud'e musu gate, Dan haka suka layu a harabar gidan mota 3 ne sai Hilux cikon ta 4 wacce ke d'auke da tarin kaya mak'are a bayan ta, Kasancewar yau gidan ya uni idanuwa da kunnen yan gidan a bude rass wajen ji da ganin kayan ban mamakin dake ta gudana a cikin gidan yau dan haka tsayuwar motocin babu d'ad'ewa yaran gidan suka fara fitowa dan suga waye yazo gidan yanzun kuma, Suma sirikan gidan mata ba'a barsu a baya ba wajen yin dogon lek'e daga nasu sashen, ba duka yaran gidan ne suka san su Baba Usman ba dan haka su da suka fara fitowa daga cikin mota sai yaran basu wani waye su ba, har sai da Hajiya ta fito tukun suka baibayeta suna mata oyoyo, Aka bar matan gidan cikin mamakin mai kuma ya kawo Hajiyar gidan ita da wad'annan mutanen ga kuma kayan da suke hange anata saukowa daga bayan mota sun kasa tantance ko kayan miye daga farko har sai da aka sauke kayan tass aka loda su a gefe, ganin idan su su dai kayan da ake gabatar wa a yayin sa rana suka hango domin harda su tabarma da kafet ga kuma setin akwati mai guda uku da kit tarin kwalayen dake wajen da drinks ko kasa kirgawa sukayi suna da yawa, kus kus suka farayi a tsakanin su babu dai damar fitowa a ganar ma ido dan Baba Malam yana gida, Sai da aka sauke komai kafin Baba Usman yake cema Hajiya, "Zamu sa ayi mana iso ne ko zamu shiga ciki ne dan naga k'ofar falon na Malam a bud'e?" "Wani iso kuma Usmanu? bayan mun riga mun kawo kan mu ai munyi mai wuyar" Juyawa tayi inda yaran ta basu umarnin kwasar kayan zuwa falon Malam suko dama umarni suke jira dan haka tuni suka fara aiki, Yaran gidan manya maza dake zaune a falon Mommy Hauwa wato su Sa'eed dasu Farouq ne suka fito daga falon suna ma su Baba Usman Barka da zuwa, ita dai Hajiya bata bi takan kowa ba tayi gaba tabi sahun yaran da suka kwashi kaya zuwa sashen Malam, Da sallama yaran gidan suka d'uru cikin falon na Malam ko wannen su d'auke yake da abinda yake iya d'auka na daga kayan da hajiya tasa su kwasowa zuwa nan d'in, Wasu huhun goro suka kwaso, wasu kwalayen biscuits wasu kuma na sweet kaya ne dai gashi nan kamar masu shirin bud'e shago, "Kai daga ina wannan kayan kuma? Waye yace muku ku shigo dashi nan?" Malam ya tambaya a tsawace, Alhassan yaron ya sa'eed ne ya amsa ma malam da cewa, "Hajiyar tudun wada ne sukazo ita da wasu bak'i kuma ma itace tace mu shigo da kayan nan falon ka" Yaron yana rufe baki hajiya ta shigo falon da sallama ayarin ta suna biye da ita a baya suma sallama d'auke a bakunan su, Gyara zama Baba Adamu yayi daga inda yake zaune yana amsa sallamar masu shigowar, a cikin zuciyar shi ko cewa yake aiki ga maiyin ka, wato Hajiya taji shiru shine tayo mai gaba d'aya, satan kallon Malam yayi sai yaga fuskar nashi da d'an sauk'i yanzun sab'anin d'azun daya d'aureta yasan kuma sakewar fuskar dan zuwan bak'in da baiyi zato ko tsammani bane a yanzun, lallai ranar yau Allah ne kad'ai yasan abinda ya boye a cikin ta sai fatan Allah ya mana mafi alkhairi kawai. "Barkan da zuwa" daga Baba Adamu har Malam suka dungayi ma su Abba Ahmad su kuma suna amsawa, "Bismillah ku zazzauna ga wajen zama" cewar Baba Adamu a sanda ya mik'e tsaye daga inda yake zaune yana taron su, Zazzaunawan sukayi dan akwai isashen kujerun zama a falon su Ya Farouq da suka kwaso sauran kayan suka shigo dashi suma suka jera a tsakiyar falon inda yaran suka zuba nasu, gaisuwar su suka gabatar ga bak'in kafin suka mik'e, "Kai Abdul shiga cikin gida wajen iyayen ka su baka ruwa ka kawo masu kawun nan ka" Cewar Baba Adamu, Ficewa Abdul din tayi, su kuma su Ya Sa'eed sai suka koma gefe can ta wajen kofar falon sukayi zazzaune, Saida aka gama jerin gwanon gaishe gaishen da za'ayi kafin Hajiya ta jefo nata zancen cike da barkwanci take mai cewa da Baba Adamu, "Haba Malam Adamu kai kuma hakayi daga cewa idan ka dawo zaka samu Yayan ka da zancen shi kenan kuma sai muji shiru kamar dai an aiki bawa garin su," "Ayimin aikin gafara Hajiya abubuwa ne suka d'an shamin kai amma yanzun haka maganar da muka gama tattaunawa da Yaya kenan dan dama yau nike son zuwa can gida akan maganar" "To ai nidai gajiya nayi da jira nace gara dai in tuso keyar su mu taho ayi mai yiwuwa shi yasa ka ganni da rana fatse fatse kasan yan hausa na cewa zuwa dakai yafi sak'o yau dai nace da kaina zanyo jagora inzo ayi komai a gaban idona dan su kullum idan na tambaye su ya ake ciki saidai suce min kai suke saurare baka tab'osu akan maganar ba, Niko naga ai mai nema da zafin nema akan sanshi to dai ka ganmu da shirin tsaff muka taho wallahi dan nidai sam banga abinda zamu tsaya muna jeka ka dawo akan shiba kai koh abune ya zama duk na gida zan aura ma takwarata miji dole inyi da jiki, Yanzun dai ya ake ciki ? Injin dai riga ka gabatar ma dashi Malam zancen neman? dan nidai ka gani ganin idon ka da shirina tsaf na taho dan in koma gida da daddad'an labarin bayarwa" Faffad'ar murmushi ya k'awata fuskar shi dashi, "Hajiya karkiji komai tun farko ma da nasan kuna hanya dani zance kiyi zaman kine basai kin wani wahalar da kanki zuwa nan d'inba abinda yar nan dai kuma takuce ko kufa kuna da hurumin da zaku iya aurar da ita ba lallai sai mu ba" Wannan karon Baba Usman ne ya amshi zancen da cewa, "Ah ah Malam Adamu ai hakkin kune muzo mu nemi auren ta a wajen ku, kaga koh ai komin nisa dole mu taso zuwa inda kuke dan neman izini da yardar ku balle kuma nan da nan dai ga baki ga hanci," "Kwarai kuwa ko ga gida ga gida ne dole muzo mu nema ma d'an mu balle kuma nan sha'anin neman aure ai ba abin wasa bane" Wannan k'aran Alhaji Musa ne ya amsa wato Mahaifin Billyn Ya Sa'eed ina fatan kun gane shima dai sirikin Malam ne tunda Yarshi tana aure a gidan. Su dai su Farouq dake tare da Musty da wani abokin su AK Kamal ata wajen kofa k'asa² su Farouq d'in ke tambaya akan wa akazo nemar ma aure kuma wace Yarinyar ake son auren? Musty ne ke musu bayani k'asa k'asa nan kuma jikin su yayi sanyi ta wani gefen sunyi ma Meenal murna ta wani gefen kuma suna jimamin abinda zai faru ne, yau dai su basu da abinda zasu iya cewa domin Allah ne kad'ai yasan abinda ya b'oye yasa abubuwan sukazo a haka, Gyaran murya Alhaji Sani yayi wato Yayan Alhaji Hamza, kafin yaci gaba da magana a yayinda yaga kowa ya natsu ana sauraron abinda zaice, Taron ya bud'e da addu'a kamar yanda addini ya koyar sai bayan da kowa ya shafa sannan ya k'ara gyara zama ya fara magana kamar haka, "To Alhamdulillah anan dai koda ace bamuyi wani dogon bayani ba alamomin da kuma suffar da muka shigo da ita kad'ai ta isa bayyana ma kowa abinda yake tafe damu gareku, Amma duk da haka mu masu nema Bazamuyi shiru ba, Masha Allah kamar dai yanda aka saba tunda dai wannan ba shine alaqar farko da zamu kulla a tsakanin mu ba domin alaqa ta dade da kulluwa a tsakanin mu tun daga lokacin da kukaje kuka nemi auren Hauwa'u Jidda a wajen mu kuma muka baku" "Kwarai kuwa wannan hakan yake" jam'ar wajen suka amsa banda su Ya Sa'eed dake can gefe, Sai da akayi shiru shi kuma yaci gaba da cewa, "Bayan Auren Jidda a cikin ahalin nan alaqa tsakanin mu daku taci gaba da habbaka ne daga sanda ta samu k'aruwar ta na farko, Tana ci gaba da samun k'aruwar arziki alaqa na dad'a hab'aka, koba haka ba?" Ya tambaya, "Haka ne" suka amsa dashi suna gyad'a kai alamun tabbatar wa a gareshi, "Alhamdulillah Allah yayi cewar silar shigowarta gidan nan shine silar kulluwar alaqa mai k'arfi a tsakanin mu domin yanda kuka rik'e mana ita da amana shi ya bamu kwarin gwuiwa wajen baku wata Y'ar namu a sanda kukaje nema ma d'anku auren ta koba haka ba? Dan da ace baku rike Jidda da mutunci ba bazamu baku auren Bilkisu ba" "Wannan haka yake" suka k'ara maimaita wa, a cikin masu amsawar kuma harda Malam wanda yake amsawa cike da alfaharin an yabe su, Cigaba yayi da cewa, "baku tsaya anan ba bayan Bilkisu kuka k'ara d'aukar yarmu kuka ba naku yaron, eh saboda ai itama Meenal din da kuke tak'amar takuce muma tamu ce kamar yanda kai Malam Adamu ka fad'a a d'azun" Yar k'aramar dariyar raha akayi, Baba Adamu kuma ya amsa da cewa "kwarai Meenal taku ce Alhaji" "To kaji gaskiya dai gashi kuma bayan ita yanzun kuma kun k'ara biyomu kun nemawa d'an gatan d'anku auren Yar mu Maimunatu wanda muna sa ran insha Allah nan da yan watanni ne za'a gabatar da nasu bikin koba haka ba kunga ko ai alaqa tsakanin mu daku takai kololuwar da ko yaro ya d'aga kai bai iya hango wa, dan haka ne yanzun bamuyi shayin zuwa nan d'in tafe da kayan mu ba dan mun san wuyarta dai mu nema ne a wajen ku mun san bazaku hana ba" "Wannan haka yake" Baba Adamu ya amsa dashi shida Alhaji Kamal shiko Malam kauda kanshi yayi gefe, "To yau dai zuwa mukayi dan mu nemarwa takwarar marigayi Abdul Khareem auren Yarku mai Babban suna munzo gareku da yak'ini muna kuma fatan Allah yasa wani bayyi mana shigar sauri ba?" Tsit falon yayi shi Baba Adamu yayi shiru ne dan a ganin shi an kai gab'ar daya kamata ace Malam yayi magana yanzun kam, Su kuma sauran yan falon sunyi shirune suna jiran jin amsa daga bakin mutum biyu ko dai Malam ya amsa musu ko kuma Baba Adamu, Kafe Malam Baba Adamu yayi da ido dan haka dole badan Malam yaso ba ya fara magana kamar haka bayan yayi gyarar muryar daya saba, "Alhamdulillah muna yi muku Barka da zuwa kuma duk munji bayanan da aka gabatar, Kafin ku shigo mun zauna mun d'an tattauna da shi Adamu domin shi da kuka ba Sallahu shine ya d'anyi nauyin baki wajen isar min da sak'on ni kuma rashin sanin abinda yake faruwa yasa a jiya bayan mun gama karatun da muke gabatar wa a masallaci na gabatar da sanarwar bada auren ita Mamana ga Sheikh Naseer malamin dake mana karatu wanda ya kasance d'ane a wajen k'anwata Zahra wacce uwa d'aya uba d'aya suka haifemu kamar dai yanda kuka san bamu da yan uba," K'ananun maganganu ne suka fara tashi daga can bakin k'ofa inda su Sa'eed ke zaune, inda suke tabbatar ma juna da zargin su dan su dama tun jiya sun zargi cewa Meenal ce Malam yaba Shehi ba kowa ba, lallai ko akwai gwarama yau, Gyaran murya Malam ya k'arayi, kafin ya d'aura da cewa, "Sannan kuma bayan sanar war da nayi daren jiya safen yau ma na samu bakuntar mutum uku wadanda dukan su sunzo min har nan cikin falon nawa sun kuma gabatar da kansu a matsayin masu son neman auren Meenal din wadanda dukan su dangin tane na kusa, mutum na farko da yaxo akan maganar Yayan tane domin dai k'anin mijin da muka aura mata da farko ne shima yaxo yana rokon mu aura mishi ita yana son ta ya kuma yi alkawarin riketa da amana, Mutum na biyu kuma shima yaro yayan tane domin da uban shi damu yaran wa da Kane muke, Na ukun su kuma shima d'ana ne domin yaron k'anwar muce wacce ita kebin Adamu wato kunga ko dukan su ukun makusanta ne na kusa wanda in akace abi cancan ta dukan su sun cancanci a aura musu Meenal" Dan shiru yayi sai dai kuma babu wanda ya amsa harya gama sauke ajiyar zuciyar shi yaci gaba da cewa, "Bayan su ukun can kuma d'azun nan da azahar kafin isowar ku na k'ara samun bukuncin wasu manema auren nata inda suke shaida min cewa d'ansu yaso ita Meenal din tun kafin wancan auren nata amma itace a lokacin batayi saurin bashi dama ba acewar ta sai ta gama makaranta zatayi aure, suma dai fitaccin ahaline wadanda koba niba kowa zaiso had'a zuria dasu, To gaku kuma kunzo kuma duka dai buk'atar d'aya ce daku da sauran duka dai auren uwata kuke nema...." Katse shi Hajiya tayi saurin yi tun kafin ya gama feso maganar dake cikin bakin shi, "Duk wannan lissafe lissafen da kayo ni basu ne damuwata ba domin duk cikin su ban cire mijin da zan iya sadaukar wa ita ba, Shi Salman d'in in yana da kunya ai ko hanyar falon nan bazai biyo ka da zancen son auren matar da d'an uwan shi uwa d'aya uba d'aya ya saka ba, ko ya manta irin rikon sakainar kashin da d'an uwan shi yayi mata ne? Da badun jajircewa naba da kila har yanzun tana gidan shi a girke tana cigaba dayi mishi shara da wanke wanke, Anji ba haramun bane amma dai ko babu komai ana barin halas dan kunya dan haka cire shi a lissafi wannan ba mijin Aminatu bane, Mu gangara kan shi Hashimu yake kowa? Oho koma da miye sunan shi shima bai cancanci auren Meenal ba dan bazan yarda daga hannun mai mata d'aya ta fad'a hannun mai mata biyu da tarin yara ba sannan kuma ba wani darajar ta yake gani ba barin in baka labarin yanda hirar su ta kasance a gidana kafin yazo maka da zancen" A gurguje ta labarta musu hirar Hashim da Meenal na ranar da yaje tudun wada kafin ta gangaro kan Aliyu, "Shi kuma Aliyun in ba neman fitina da shegen kwad'ayi irin na maza ba ina shi ina batun k'ara aure? Auren ma ya rasa wacce zaice yana so sai Meenal dan Allah kun tab'a ganin inda aka had'a gudun jirgin sama dana mota? Ina ai bama zai yuwuba dan haka shima na cire shi a lissafi, Allah sarki bawan Allah Sheikh shikam wannan dai da ace bada jikana ya had'a nema ba wallah dako ni ina iya yi mishi tsaye wajen ganin an bashi mata! Kuma ko yanzun ma karkuyi zaton cewa son kaine zai sa in zabi nawa jikan in barshi, ah ah wallahi ita dai Yarinyar ne na tabbatar da cewa jikana take so bashi wanda babanta ya k'ara zab'ar mata a karo na biyu matsayin mijin da zata aura ba, amma idan ana musu ana iya kiran ta dan aji nata ra'ayin aka su biyu, Yauwa batun shi wancan yaron Bashar ne ko Bashir shi dai d'an gidan Master Wanda ake cewa suma sunzo d'azun to ku nasan kune baku san shiba tun a wancan lokacin amma ni nasan shi dan har suma yayi a falona ranar da aka d'aura mata aure shakarun baya, Shima na cire shi a jerin masu neman aure dan koba komai wannan sha'anin na cikin gida ne bazamu kawo bare ba, Yauwa ina magana akan Shehi da kuma Jikana Abdul, Wannan dai ni kaf banga abunda za'a tsaya ba kai wahala ba, shi dai jikana shi yaga yar uwar shi saboda ra'ayin kanshi bawai dan wani ya tallata ko kuma a cusa mishi ita bisa dole ba, ah ah shi yaji ya gani cewa kaf fad'in garin nan k'asa dama duniyar gaba d'aya ita dai yaji ya gani yake so, Duk kunyar dana san yaron nan dashi haka ya murtsiketa tass ya tareni za zancen cewa yana son yar uwar shi, wanda ni kuma dama tun kafin ma ya furta alamomin da yake nunawa sun tona mishi asiri a wajena kafin kuma ya furta mata abokan shi ya fara fesama su kuma suka sameni har cikin d'akina aminin shi ya shaida min halin da shi Abdul din yake ciki, Inda ace naso to da tun lokacin zansa a shige gaba a nemar mishi auren ta a lokacin tunda bayan mutuwar auren ta ni daku duk munsan cewa bata tareda idda a kanta amma banyi Hakan ba, Kunsan me yasa?" "Ah ah Hajiya" da yawa daga cikin su da suka natsu suna sauraron ta suka amsa, Ita kuma sai taci gaba da cewa, "Saboda so nike ya tantance abinda yake ji akan ta, ni kuma so nike in gane zurfin da Soyayyar ta yayi a cikin nashi zuciyar, Bana son inyi saurin shigewa gaba akan maganar ne saboda koda yake jikana bazan so ya sameta salin alin ba dan so nike yasan zafin ta yanda ko bayan auren zai riketa da kyau ba rikon sakainar kashin da wasu mazan sukeyi ma mata ba" Dan dago kanshi malam yayi yana kallon hajiyar dan yasan dai maganar ta na k'arshe da biyu tayi shi, Ita ko bata damu ba taci gaba da cewa, "Dan haka sai nakau dakai ban nuna na gane komai ba har zuwa sanda ya gaji da nuk'u nuk'u dan yakeyi ya furta mata, Tun lokacin daya furta kullum bashi da magana saina shidai in tura a nemo mishi auren ta surutun shi kuma bai sa nayi hakan ba duk da cewa duk da iyayen shi basa gari ina da damar dazan wakilta wasu su nemo mishi auren kuma a bashi amma banyi hakan ba, saboda so nike ya d'and'ana zafin da akeji a yayinda zakaga wasu mazan suna kaima abinda kai kake farauta cafka, hakan zai sa kaima ka jajirce, to Alhamdulillah duk wasu abubuwan da nike buk'atar tantancewa a tsakanin su na kammala ina kuma da tabbacin cewa ko yanzun aka d'aura auren su zasu rike junan su su kuma rayu cike da soyyaya shi yasa na had'o kan duk wad'anda suka dace a gabatar da komai a gaban su muka taho, Mun taho da komai daya kamata tun daga kan kud'in gaisuwar uwa da uba har zuwa komai da ake buk'ata wajen gabatar da neman aure, domin a sanya mana rana, to amma yanzun zuwa na da kuma jawaban da naji daga bakin ku hakan yasa na canza ra'ayi bayan gabatar wa Ina so Uban shi ya biya kud'in sadaki kawai a wannan taron a d'aura aure gaba d'aya domin hakan ne kad'ai zai sa hankalina ya kwanta, jikana dai ba d'an iska bane baya shaye shaye baya sata, haka kuma baya caca balle yabi Matan banza duk inda aka shiga ko ina nasan jam'a zasu shede shi dan ba abanza yaci sunan da kakan shi yasa miba Mai Jama'a, Kai Usmanu kun fito da kud'i a jikin ku ko nice zan biya mishi sadakin?" Daga can bakin k'ofa kusan mutum hudu suka had'a baki wajen cewa "nine zan biya mishi" Musty Farouq da abokin Musty da kuma Ya Sarki wanda basu ma san da tsayuwar shi a wajen tun d'azun ba sune suka fad'i haka, "Kai masha Allah kunji yan albarka to kai Adamu ai sai ka yanke mana sadakin auren yarka kaga masu jiran a fad'a su biya ma suna da yawa ashe, kaga dai alamun kowa nason wannan had'in kenan, oho wanda baiso bama dai In allah yaso sai anyi balle kuma rabon ciki da haihuwa basu bar kowa ba. *Ummiee ce*✍🏼 [10/7, 10:40 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜ *BOOK 2* *Page 45* Bud'ama Sarki hanya sukayi ya shigo cikin falon shima tareda Ya Sheikh wanda shima dawowar shi gidan kenan dan tun safe ya fita a gidan zuwa gwargwaje inda yakai ma wani abokin shi ziyara dawowar shi gidan yayi dai dai da shima Sarki zai shigo dan haka sai kawai suka shigo gidan a tare, koda suka iso kofar falon Sarki yaso ya juya ya koma shi Sheikh ne ya hanashi akan gara su isa suji me yake faruwa dan daga ganin taron ga kuma motocin da suka gani a farfajiyar gidan sun kasan abune mai mahimmanci ake tattaunawa a falon wanda ya had'a kan ahalin gidan, suma kuma ai ahalin gidan ne dan haka su k'arasa kawai ayi dasu suma. basu san abubuwan da aka tattauna akai daga farko ba jawaban da Hajiya ta gabatar daga k'arshe kawai sukaji dan haka sai shi Sarkin baiyi k'asa a gwuiwa ba dan dama yayi niyyar cewa in batun auren ya tashi shine zai shige ma AK gaba duk da cewa yar gida za'ayi , yanzun kuma da yaji bayanan Hajiya dole ya bata goyon baya kodan a kawo k'arshen rarrabuwa da kawunan ahalin yake son yi akan zancen auren Meenal d'in daya tashi a yau kamar tashin Bomb yake shirin tarwatsa kan ahali wanda babu wani yayi zaton haka, Shifa bawai yana ma Salman bakin ciki bane danshi Salman d'in yana son matar dashi ya saka ba, ah ah shi dai kawai cancanta yake dubawa kuma koba komai ita Meenal AK take so bai kamata a k'ara tauyeta akaro na biyu ba dan in akayi hakan itace zata cutu tunda su mazan dukan su koda ace sun aureta hakan bazai hana su k'ara wani auren baya itaba kenan dai duk wanda aka aurawa a tsakanin su Salman din ba'a mata adalci ba, yama gode Allah da Allah yasa ya shigo gidan a dai dai dan shigowar shi dama yazo ne dan yaba Malam hak'uri akan abinda Salman yayi shi kuma yayi amfani da damar ya kawo zancen AK ga Malam to ashe ma Mai gayya mai aiki ta gaji da jiran gawon shanu ko kuma dai itama labarin jerin gwanon neman auren ne yaje kunnen ta shi yasa ta kwaso nata iyalan ta taho? Komai dai ya akayi shi hakan ya mishi dai dai yau yana bayan Hajiya tuk'uicin kyautar datayi mishi ne shima zai maida mata. Shifa Sarki dalilin aika²r da Salman ya aikata da safen na zuwa wajen Malam kai tsaye bayan tun farko saida iyayen shi suka tsawatar mishi amma yayi kunnin uwar shegu dasu yayi gaban kanshine yasa shi barin komai dake gaban shi a yau d'in ya taho Zarian bayan Uwar gida ta kirashi ta labarta mishi abinda ake ciki, Domin bayan da Salman ya bar wajen Malam gida ya koma dan ya riga ya k'una baya tsoron wuta dan haka yana zuwa kafin ma labarin ya koma kunnin su Uwar gida shi da kanshi yakai musu labarin ya kuma kafa musu hujja da cewa inhar mutanen tudun wada da suma suke matsayin iyayen Meenal ta gefen Mahaifiyar ta zasu iya ture komai daya faru a baya suba Sarki auren yarsu a karo na biyu, to shima baiga dalilin da zai sa anan suce zasu hana shi auren Meenal ba tunda dai shi yace yaji ya gani yana sonta, dan haka tunda su sun kasa tambayo mishi shi yakai kanshi kuma su sani babu abinda zai hana shi auren Meenal inhar ta amsa tana son shi yasan Malam zai aura mata shine dan koba komai yafi su Aliyu da Hashim kwarin gwuiwa koba komai a cikin su shine Saurayi yasan Malam bazai bata mai mata ba, Fad'a sosai Malam Sulaiman da Uwar gida suka rufe shi dashi akan me zai aikata haka amma bai saurare suba sai ma ficewa da yayi yabar gidan kuma a yau basai gobe ba zai k'ara komawa wajen Meenal su daddale kafin Malam ya nemeta domin jin ta bakin ta, K'ananan surutan da gidan Malam Sulaiman din ya d'auka ne yasa ita Uwar gida ta kira Sarki a waya dan gara yazo ya tsawata ma Salman d'in dan ita dai bata san da wanne zataji ba da surutun kishiyoyi da facalolin ta keyi akan maganar ko kuma da iskancin da Salman din ya tsiro musu dashi na k'in jin maganar su, Itama fa bawai tana k'in auren bane, ah ah tadai san cewa ko kowa zaiso auren tofa bai zama lallai malam yayi murna da had'in auren ba kilama laifinta zai k'ara gani ko kuma yace itace ma ta tura mishi Salman d'in, tunda itace dai tayi tsaye aka ba Sarki Meenal ga kuma abinda ya biyo baya yanzun kuma ace Salman wannan ai laifinta kawai Salman din yake son Malam ya cigaba da gani wallahi. Sarki bai zauna ba sai da ya k'arasa har gaban kujerar da Hajiya take bayan sun mik'a gaisuwar su ga mutanen da suka tarar a cikin falon shi Sheikh a bakin k'ofa su Sa'eed suka gyara mishi ya zauna anan ne kuma yake tambayar su "me yake faruwa ne? " su kuma suka d'an labarta mishi komai a gajarce, Sarki ko hannu yasa a cikin aljihu duk wata takardar Naira dake jikin shi sai da ya zubeta a gaban Hajiya tundaga kan yan dubu zuwa k'ananan canjin dako shi bai san nawa ne a dadin kud'in ba, Yana gama zube mata su ya koma da baya shima can dai gefen da su yaran gida suke Abdul ne ya tashi a inda yake yaba Sarki wajen ya zauna, Tun sarki bai kai ga zama ba Musty da Kamal suma suka mik'e yanda Sarki yayi ma aljihunan shi kwal haka suma sukaje suka zazzage nasu nauyin aljihun a gaban Hajiya wacce take ta faman washe baki ranta fess sai albarkha take sanya musu, Malam ko a lokacin idan ka mishi kallo d'aya bazakayi marmarin k'arawa ba saboda ya d'aure fuska sam babu alamun fara'a ido kawai yasa yana kallon ikon Allah, Dan wallahi yasani sarai cewa da biyu Hajiya tayo mishi gangami saboda yace wani abunda bai dace ba a gaban sirikai girman shi ya zube, wai shi za'a biyo har cikin d'akin shi a nuna mishi isa akan Yar da ubanta ma a k'ark'ashin ikon shi yake, wallahi da yasan haka ne zai faru a yau da ba sanarwar bada auren Meenal d'in ga Sheikh zaiyi a daren jiya ba auren kawai zai d'aura in yaso sai yaga uban da zai kashe auren. Abun mamaki sai gashi harda ya Sheikh shima yabi ayari cikin masu juye tattalin arzikin aljihun su a gaban Hajiya kafin ka an kara kud'i sun taru domin kaf d'in yara mazan dake falon sai da suka juye aljifan su bayan sun gama kuma haka suma iyayen Maza sukabi ayari, shi dai Malam kallon ikon Allah kawai yakeyi, Alhaji hamza ne ya fara fidda nashi kudad'en sai Alhaji Musa, Shidai Baba Adamu cewa yayi yaga alamun yaron nasu d'an gatane dan haka bazai sa musu ko sisi ba dan kud'in shi tattalawa zaiyi ya Siyama Meenal din gadon bacci, Farantin da aka d'aura ruwan da Abdul ya kawo musu Hajiya ta juye kayan cikin farantin a k'asa, Sai da tasa gyalen ta ta goge farantin kafin ta kwashe kud'ad'en nan kaf ta zuba a farantin ta k'arasa gaban Malam ta ajiye, "To Malam Almu ga sadakin takwarata nan yan uwan ta sun biya, Nasan dai ko kud'in zaku yanke bazaku yanke wanda zaikai adadin wannan ba dan haka gashi nan shima in bai wadatar ba zamu k'aro ninkin adadin su saboda ta cancanta" Mai da kallon ta ga sauran jama'ar falon tayi saida ta k'arewa kowa kallon tsaf kafin ta tsaida duban ta akan Sheikh, "Malam Naseer" Ta kira sunan shi a sanyaye, "Na'am Hajiya" shi kuma ya amsa mata fuskar shi a sake, "Kai kuma bawan Allah daga zuwa kaima sai kabi ayarin masu tarbace? Tun baka san ko sadakin wa ake had'awa ba, to da fari dai hakuri zan baka kayi hak'uri nazo nayi maka shigar sauri ina fatan bazaka kullace ni a cikin ranka ba?" "Ah ah Hajiya me yayi zafi da harni zan k'ullace ki kuma?" "To dai batun in tsaya yi maka kwana² ma duk bata taso ba, Zanyi magana ne akan sanarwar da Malam ya bada jiya cewa ya baka mata shin kai kasan wacece aka baka ne?" Sai da yakai duban shi kan Malam kafin ya amsa mata da cewa "ah ah Hajiya ban sani ba sai dai koma wacece ina farin ciki zan kumayi maraba da shigowar ta cikin ruyuwata tunda har kyautar ta hannun Baba Malam ya fito yasan na cancanta shi yasa ya bani na kuma gode ubangiji Allah ya k'ara girma yasa a gama lafiya" "Ameen..... " D'aukakin jam'ar dake cikin falon suka amsa gaba d'aya, Ita kuma Hajiya sai taci gaba da magana bayan ta amsa da Ameen din itama, "Masha Allah lallai ka cancanci a baka mata ako ina ne kuwa Naseer, To a jiya dai shi Baban naku ya sanarda cewa ya baka Meenal sai dai sunan tane bai k'ira acan d'in ba dalilin rashin kiran sunan nata a jiyan kuma wannan shiya barma kanshi sani, Amma mu dai ya fad'a mana cewa itace ya baka a wannan zaman da mukeyi, Ba bayarda ita din da yayi gareka ne damuwar ba, ah ah damuwar shine daya k'ara d'aukar ta ya bayar a karo na biyu ba tareda yayi shawara da kowa ba bayan ita din ai kowa yasan cewa tana da uwa a raye koba komai in ba'aji ra'ayin ita Yarinyar ba tunda ana ganin cewa an isa da ita to ita kuma uwarta fa?, ko har yanzun dai ita uwa nata alaqar kawai na haihuwa ne amma in anzo batun hukunci akan abinda ta haifan shikenan sai kuma a nuna mata cewa bata da ikon ko isar da za'a iya jin ta bakin ta?, Humm koda yike ba wannan maganar nike son fad'a maka ba kana jina koh?" Ta tambaya tana kallon Sheikh d'in, Baba Usman ne yayi saurin tarar numfashin Hajiyar jin da yayi ta fara sauka akan layi dan shidai bazai so ta raba halin ta a falon kafin subar gidan ba dan haka sai yayi saurin d'aurama Sheikh da cewa, "Kayi Hakuri Naseer shi Baban ku bai san da batun neman da d'an uwan ku yakema ita Meenal din ba nasan shi yasa yayi kwad'ayin baka ita saboda cancantar ka, sai dai mu kuma tun kwanaki muka gabatar ma Baban ku Adamu da batun neman shi kuma sai Allah bai bashi ikon kawo ma Malam zancen ba sai yau. zuwar mune kuma Malam yake sheda mana cewa kai yaba Meenal duk da cewa daga safen yau zuwa yanzun bayan kai daya ba a jiya mu mune mutane na biyar da mukazo neman auren ta a yau, Bamu san abinda ke cikin zuciyar ka akan ita Yarinyar ba barin ma kuma daya zamana Malam bai kira suna ba tun jiyan sai dai mu muna da tabbacin cewa ita da d'an uwan ta suna son junan su shi yasa suka had'a kansu k'arewa ma itace ta buk'aci shi d'an uwan nata ya kawo zancen nan gaban iyayen ta shi kuma ya wakilta mu a matsayin mu na iyayen shi maza, muna fatan koda ma ace kana son ta to zaka iya sadaukar da son da kake mata dan ganin ta samu abinda take so a wannan karon?" Tunda Baba Usman ya fara magana kan Sheikh yake k'asa domin idanuwar kowa a kanshi yake kowa so yake yaji mai zaice kuma, Shiko a zuciyar shi mamaki kawai yakeyi, shifa wallahi koda Malam ya bada sanarwar tun jiya bai kawo kowa a cikin zuciyar shiba sai Fauxieyerh saboda kaf gidan kowa yasan da cewa yafi shakuwa da kuma sakewa da ita, dan haka shi yasa koda suka dawo gida a jiyan bai nemi jin ta bakin Malam din ba dan shi bai tab'a kawo zancen Meenal a cikin kanshi ba, Jama'a shi wani tsautsayi ne zai sa shi auren wancan Yarinyar data iya cinye maza da kalaman bakin ta? Yarinyar dazai ce ta koma tasa hijab ita kuma tabi ta wani k'ofar ta fice daga gidan ba tareda ta sanya hijab din ba, Ah ah wallahi shikam Meenal tafi k'arfin shi garama da akayi walkiya inba haka ba da haka zai saki baki shi a ranshi yana tsammanin Fauxieyerh a gefe kuma ana shirin aura mishi Meenal, Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke kafin ya d'ago kanshi yana kallon Malam yace "Baba dama ba Fauxieyerh bace Yarinyar daka bada sanarwar zaka bani auren ta a jiya?" Dagowa shima Malam yayi fuska d'aure yace " Meenal ce Yarinyar dana sanar da cewa na baka a jiya kuma har yanzun ban canza ra'ayi ba Naseer kuma nasan daga kai har ita babu wanda zaiyi yunkurin bijire min a cikin ku, idan ma baka son ta a yanzun ina mai tabbatar maka da cewa tana da kyawawan halayen da idan ka zauna da ita zaka sota saboda su, kamar yanda nake da yakini kan cewa itama bazata k'ika ba, ina fatan kuma ko yanzun bazaka watsa min k'asa a ido ba dan na riga nayi niyyar baka ita tuntuni k'arewa ma har nayi sanarwa jama'a sunji dan haka babu wanda zai sa in sauya magana a cikin ku" Shiru falon ya d'auka kowa yana jimami da mamakin kalaman malam Wannan karfin hali har ina! , Hajiya ko wani irin kallon wasa ma kake yi Almu take aika ma Malam din, Ganin haka sai shima Sheikh d'in yaci gaba da cewa "Amma Baba Meenal ita d'in tana da wanda take so kuma nima Fauxieyerh nike so in har za'a canza min da ita zanfi yin farin ciki da hakan ayi hak'uri a duba al'amarin nan wallahi ban tab'ajin soyayyar Meenal soyyaya irin ta aure a cikin zuciyata ba balle har inyi kwad'ayin auren ta....." "Yi shiru abin ka d'an nan aika gama magana, Fauxieyerh dai kace kana so koh?" hajiya ta tambaya, Bata jira amsar shiba taci gaba da cewa, "Ni nan dai nice na haifi Jidda ita Uwar su Meenal da Fauxieyerh dama sauran yayyen su dake zaune a gefen ka dan haka na baka Fauxieyerh, tunda ko nace na baka nasan ko uban Fauxieyerh Mukhtar bazai kalli idona yace zai k'alubalance niba," Harar gefen ido ta aikama Malam tana fatan Allah yasa ya kulata, wallahi silleshi zatayi tass dan ta gaji da halin shi haka nan, Sai dai shima yau kamar yasan abinda ta shiryo sai ya kama kanshi, Ita kuma sai taci gaba da magana "Adamu ka shirya amsar ma d'anku auren Jikata Fauxieyerh ayau kamar yanda zaku bamu auren Yarku Meenal ayau ko baku shirya ba? In kun shirya ga uban Fauxieyerh nan a gefen ka nasan ko Mukhtar yana yana raye koya mutu tsaf zai iya wakilta yayyen matar shi wajen aurar da yaran shi mata dan haka ni a matsayina na uwa na wakilceshi na wakilta Usman ya amshi auren Fauxieyerh" Yanda Hajiya tasha kunu take faman bada umarni zakayi zaton ko gidanta a kaxo bawai itace taje gidan sirikai ba, ko mantawa tayi ne oho🤔 Kai jama'a Hajiya yar bala'ice wallahi, inba karfin hali ba kizo cikin gidan iyayen yarinya kuma kice wai zaki basu auren ta😠, "Na shirya Hajiya indai za'a bamu ai bazamu k'i amsa ba" Baba Adamu ya amsa mata, Malam fa bai tab'a sanin cewa da ranshi da lafiyar shi har za'a iya had'a kai da ADamu aci mishi amana ba sai yau, to cin amana mana tunda gashi dai yau shi Adamu ya juyama baya ya koma tsagin dangin matar kanin shi, Domin dai abin mamaki yana zaune Hajiya tace wai a raba kayan da suka kawo kashi biyu ta sadaukar da kaso d'aya ga Adamu tukuicin kyautar da zai basu na auren takwarar ta sannan ta nad'a Abba Ahmad a matsayin mai bada auren Fauxieyerh kuma kaf falon nan aka rasa wanda zai iya takama Hajiya burki, haka aka rabe kayan biyu kud'in sadak'in da aka had'a ma tasa aka k'irga aka raba biyu, sai da komai ya kammala kafin tace to kowa ya kira yan uwan shi wad'anda suke kusa idan suna da halin da zasu iso a gabatar da d'aurin auren a gaban idanun su dan sallan da za'a gabatar na la'asar a masallacin su Baba Malam d'in take so ana idar da sallah a gabatar da d'aurin auren, Auren kawai take so a d'aura yau daga baya sai ayi duk sauran tsare tsaren da za'ayi na tarewa da kuma taron biki, Malam dai ganin babu wanda ya k'arabi ta kanshi sai kawai ya tashi ya shige cikin d'akin shi yabar musu falon suci kansu , Suko nan fa suka yunkura aka fara kiraye kirayen waya ana sanarda zancen d'aurin auren, dan sai a lokacin ne kuma Baba Adamu ya kira mutanen abuja wato can gidan su Sheikh din ya shaida musu halin da ake ciki suma kuma sun bada goyon baya akan cewa gobe zasu shigo garin dan k sun taso yau bazasu iso akan lokaci ba, shima kuma Abban su Sheikh din ya kira mutanen shi dake nan Zaria ya sanar dasu zancen auren dan su wakilce shi, Abba Ahmad da Baba Usman sunyi² da Hajiya akan tayi hakuri abar batun d'aurin auren ko nan da zuwa ranar juma'a ne amma matar nan ta coge tace bata san zancen ba, yau dai take bukatar a d'aura auren duk wanda zai mace shiya dad'e bai sha fiya fiya ya mutuba tunda har aka iya nuna mata bak'in ciki zallah ai ba iko da isa aka fita iyawaba, Dama can da take bin abubuwan da sauk'i ba tsoro ne yasa take hakan ba, Suna fitowa daga cikin falon Musty ya fara kiran wayar AK sai dai kira 4 ya mishi amma bai amsa ba dan haka saiya juya akalar kiran zuwa k'an Yusuf wase, bai tsaya jira su gaisa ba ya fara kora mishi bayani akan abinda ke faruwa, "Hajiya ce tace dole sai dai a d'aura auren a yau?" Wase ya tambaya, "Eh wallahi kuma anyi anyi da ita ta bari ma ko zuwa gobe ne wallahi tak'i yarda"Musty ya bashi amsa "Turkashi to yanzun fa ya za'ayi kenan nidai kasan ko nace in taso daga Abuja yanzun indai ba layar b'ata zanyi ba bazan samu d'aurin auren ba, ga kuma Sadeeq shima yana nan, amma bari in kira sauran friend nasan baza'a rasa wadanda suke cikin gari ba kaima kayi kira ko za'a samu,zanyi maka transfer yanzun sai ku k'ara kud'in sadaki kasan tuntuni dama Ina fad'a muku cewa ni zan biya sadakin auren AK toga ranar tazo,insha Allah zan shigo ko zuwa dare ne dan yau dole ma in kwana a Zaria shi angon ka kira shi ka fad'a mishi halin da ake ciki ne? " "Na kira shi Ina ganin baya tare da wayar kasan dai ko baya kusa zan gabatar da abinda ya dace balle kuma anan ma muna tare dasu Abba ga Kamal kuma a tareda ni" Cikin mintunan da basu fi talatin ba sai ga kofar gidan Malam ya cika da jama'a wai a hakan ma ba kowa yasan da batun d'aurin auren ba domin da lasifikar masallaci akayi amfani wajen shelanta d'aurin auren wanda hakan yaba kowa mamaki matuk'a, Manyan restaurant uku Musty ya kira yayi odar d'in abinci ya kuma ba su Hafees kud'i suka je suka sissiyo drinks din da za'a raba da abincin bayan an gama d'aurin aure. An maida d'aurin auren karfe 5 na yamma wanda hakan ne kuma ya sa suka samu k'arin lokacin gabatar da abubuwa a tsanake, Baba Adamu yasa yaran gidan sun sharo cikin masallacin kuma suka gyara harabar gidan saboda amsar bak'i, Cikin gida ko ya rud'e da surutai domin su dai basu san me yake faruwa ba har saida taron falon Malam ya watse Hajiya ta shiga cikin gida suma sauran mazan gidan suka shiga acan ne labari ya isa kunnuwan mata, Shi kuma Sheikh bayan fitar mutane a falon shida Baba Adamu ne sukabi Malam har cikin d'akin shi suka dunga bashi baki, akan cewa dama Allah ya nufa cewa Meenal ba matar Sheikh bace kuma Alhamdulillah tunda ashe shima Fauxieyerh yake so, inda kuma ace hakan bai faruba haka za'ayi auren koda ita tayi biyayya ta amshe shi zatayi zaman auren ne ba cikin dadin raiba shima kuma zai rasa abinda yakeso kunga dai kenan babu biyan buk'ata, To dai Malam a babu yanda zaiyi haka ya hakura shima ya shiga cikin sahu wajen kiran nashi mutanen yana sheda musu d'aurin auren daza ayi karfe 5 tunda dai ita magajiyar hakan ta yanke, A can falon mommy Hauwa ko Hajiya cike da farin ciki ta shiga tana zuwa bata zauna ba tace a bata ruwa a buta dan farin cikin da take ciki dole nema ta gabatar da nafila kafin ta sauke farilla na nuna godiyar ta a wajen Allah Subhanahu wata'alah daya nuna mata wannan ranar da zata aurar da Meenal ga AK Ina ma ace Prof yana raye tasan dasai yafi kowa yin farin ciki da wanzuwar hakan, Kafin ta idar da Sallah su Farouq suka shaida ma Jidda abinda yake faruwa, to ya zatayi tunda har Malam ya zubda makaman aiki ai kuma ita ba'a bakin komai take ba, Yadai tabbata cewa daga ita har Baba Auta basu data cewa akan al'amarin yaran da suka haifa tunda gashi yau ma dai isa aka k'ara nuna mata akan yaran nata har biyu bama d'aya ba, Itafa kwata² bata san cewa alaqar soyayyar da ake ambatawa a tsakanin AK da Meenal yakai matakin da har za'ayi zancen aure ba, to na Fauxieyerh da Sheikh ma bata tab'a lura ba inba yau da ake batun cewa kila ita Fauxieyerh ce malam yaba Sheikh d'inba, *Mu tafi a gurguje* Karfe 5 dai dai tarin jama'ar da suka taru a kofar gidan Malam suka shaida d'aurin auren Abdul Khareem Ahmad Mai Jama'a tareda Amaryar shi Aminatu Al Mustapha Umar Farouq, akan sadaqi mai daraja, Haka kuma aka d'aura nasu sheikh da Fauxieyerh shima, an rarraba ma bak'i abincin dasu Musty sukayi order dasu drinks sai snacks da sauran su, Ango AK dai bai samu damar halartar wajen d'aurin auren ba dan har akaci aka sid'e bashi da labari su musty ne keta amsa fatan alkhairin da mutane keyi a madadin shi, Salman dai yayi kuka kamar zai tsiyaye kwayar idon shi, bai tabbatar da cewa ya rasa Meenal ba sai da aka gama sanar da d'aurin aure yaga ana ta taya su Abba Ahmad murna wai harda Sarki fa a wajen d'aurin aure yana taya mutane murna wato dai shine ba'a so, Fauxieyerh dai koda ta samu labari bata wani damu kanta ba, dan dama dai itama tad'an fola ma Sheikh d'in bata dai bayyana bane kawai yanzun kuma daya tabbata cewa shima d'in yana son ta mai zai dameta. Bayan gama d'aurin aure Hajiya tabi ayarin ta sun koma tudun wada bayan ta k'ira waya ta sheda ma Dada abida ya faru ta kuma bada umarnin cewa a d'aura abinci saboda masu zuwa yi musu fatan alkhairi, Alhamdulillah aure dai ya tabbata yan ciki bak'i kuma sai su mace atoh, mudai bari mu koma tudun wada mu gani ko AK ya iso in kuma bai iso ba mu bishi hanya mu taro kayan mu😜. Koda kirar wayar Sultana ya isa ga AK lokacin yana marafa can gidan shi dan yanzun ne ya tada aikin gyaran gidan tuk'uru dan yana tsammanin bikin dai ko za'a sashi bazai wuce ace a had'a ayi gaba d'aya tareda nasu Sarki ba, dan Allah yasa ma dama tuni anci k'arfin aikin abubuwan da ba'a k'arasa bane akeyin su a yanzun, Dan haka bayan gama wayar shi da sultana motar shi ya shiga kawai ya juya zuwa Malali can gidan shi koda ya isa a k'ofar gida yayi parking ya sauka da k'afa ya karasa cikin gidan bai tsaya bata lokaci ba ya cire wandon 3quiter din dake jikin shi ya canza shi da wani farin wandon jeans crazy ya cire polo din dake jikin shi ya d'auko waya rigar bak'a mai kamar na sanyi ya d'aurata akan farar vest din dake jikinshi ko zip din rigar bai rufe ba ya juya ya fice daga falon garin sauri yabar gidan ne kuma ya manta da wayar shi wanda yake cikin aljuhun wandon daya cire yana fitowa ya mik'ama Mansoor key din sashen shi dan bai sani ba ko kila ya kwana ko kuma ya dawo ko zuwa dare, Normal dama idan yana tuk'i baya tafiyar nawa yau kuma da yake cikin hanzari sai gudun motar nashi ya k'aru Allah allah kawai yake yaga Allah ya kaishi Zaria lafiya yaje ya amayar da abinda ke cikin zuciyar shi, To Allah dai ya tsare taubashi, Tunda su Sultana suka k'ara komawa suka zauna zaman hira a tsakar gidan bayan wucewar Bash basu tashi ba har saida rana ya kawo inda suke kafin suka tattara suka koma cikin falon na Hajiya ita dai Sultana labari take jira na abinda yake faruwa acan unguwar malamai ita kuma Moon ta samu kira daga Sarki akan cewa ya shigo gari dan haka zai shigo nan gidan ya ganta zuwa anjima, Ita kuma Meenal duk da halin faduwar gaban da take ciki haka ta matse ta d'auki wayar Meelat wacce ta kira take rok'on ta akan dan Allah ta taimaka taje gidan ta Meelat d'in tana neman ta ita kuma tace mata wallahi bata zuwa, "Bani da lafiya fa Besty" cewar Meelat, Ita kuma Meenal ta bata amsa da cewa, "Kisha magani in kuma yaji miki ciwo ne ai kinsan yanda zaki gyara kanki dan nidai bazan zo inyi gyaran b'arnar da mai sunan Malam yayi ba wallahi garama ki kama jikin ki" K'asa kasa suke maganar amma tsabar gulma sai da Sultana ta jiyo bata iya yin shiru ba kuma sai da tasa baki, "Wai Meenal badai kuna nufin sai yanzun Meelat ta sauke gammon dake kanta ba🤔? Ni ai nayi zaton tuni ta wuce babbak'u ta shiga mai wasali" "Ina ruwan ki da gammon data d'auka! Kuma ba mai wasali ba mai tafiya ta shiga😕" "Ke tsakani da allah mamaki nikeyi ke koh kwana nawa dakai mishi ita shiko bawan Allah yakawai sai yasa mata ido kawai yaci gaba da kallo duk da cewa rai naso amma yayi ta had'iye yawu gaskiya Musty waliyyine ko a cikin maza abudai kamar rainon tsoffi bawan Allah abunshi, Tana gidane ko asibiti?" Sultana ta k'arasa maganar da tambaya, Moon ce ta amshi zancen da cewa, "Haba ke kuwa me zaikaita asibiti ana zaune k'alau?" "Ai wai kina ganin hakan bazai iya faruwa bane? Na rantse miki tunda har kikaga tayi kiran Meenal tofa tabbas ta had'u da hatsarin maza allah dai ya bata lafiya oh Allah Yasin ta bani tausayi" Hirar Meelat sultana da moon suka cigaba da kacal calawa ita kuma Meenal ganin iskancin su bana karau bane kawai saita tashi daga kusa dasu ta koma can gefe a cewar ta wai bazasu lalace d'iyar malam ba tunda su sun zama fanko ki iska kawai suke busawa, Number din AK ta kira dan tun asuba basu k'ara yin waya ba, tasan yayi busy shi yasa bai kirataba dan haka ita kuma ta kira dan taji ya yake, sai dai harta gama ringing ta katse ba'a d'auka ba tasan da ace yana kusa da zai yanke kiran nata ne shi sai ya biyo bayan kiran dan haka sai ta shiga cikin message tayi typing kamar haka, "Heart kana can kana aiki nasan k'ila ko abinci baka nema kaci ba, Call me back if you are less busy I miss you 😍" Ta tura mishi, "Sister shirya muje gidan Meelat please" inji Sultana, "Wallahi bazanje ba shi da yayi barnar shi zai gyara kuma babu inda zakuje" "To idan kuma tana buk'atar taimako fa?" Moon ta tambaya tana dariya, "Inma uban taimako take buk'ata dai babu inda zaku dan dukan ku dai babu likita balle ta dubata kuma ita ai nasan kafin ma ta naimi taimakon sai ta fara taimaka ma kanta dan haka baku zuwa" Fad'owa cikin falon yayi kosu dake zaune basuji sallamar shiba dan iyashi da yayi kayan shi shi yasan yayi abinshi, Babu wacce ya Kala tsakanin Sultana da Moon balle susa ran zai amsa gaisuwar su, ita kuma tun kallon farko datayi ma fuskar shi tasan cewa akwai matsala yanda taga fuskar nashi a d'aure irinta shanu har fiyema da yanda yake daure musu ita a dah, Hannun ta ya kamo batayi musu ba ta mik'e ta bishi a sanda ya jata zuwa cikin d'akin daya maida nashi anan kasan dan itama tana buk'atar keb'ewa dashi dan taji abunda ya same shi ya koma haka, Maida kofar d'akin yayi ya rufe sai faman huci mai zafi yake fesarwa, Kallon shi takeyi hankali a tashe jin baice mata komai ba bayan shigar su d'akin, "Ya'ya maiya sameka? Baka da lafiya ne? ko wani ne ya b'ata maka rai? Meya faru?" Sai da yasa hannu ya yamutsa gashin kanshi kafin yayi taku biyu ya matso inda take, "Meenal Ina sonki"ya fad'a da karamar murya "Nima Ina sonka" "Kullum fatana da burina akan ki shine ki zama mallaki na" "Nima Ina burin ganin hakan ya kasance a tsakanin mu" "Ke k'adaice a cikin zuciyata tunda kika shiga cikin ta kuma na rufeta ruf ta yanda babu wata macen da zata k'ara shiga ciki bare tayi kwadayin samun gurbin zama kin san da haka?" "Nima kai kad'ai nake so dakai kuma Nike fatan in rayu har gaban abada" "Idan nayi addu'a zaki amsa min?" "Eh mai zai hana!" "Allah ya miki Albarka Hajiyata," "Ameen" ta amsa "Allah ya cika miki duka burin ki na alkhairi ciki harda zamowa matata," "Ameen"ta k'ara amsawa tana rufe fuska da tafin hannun ta "Ina addu'a allah ya tsone idon mak'iyan mu ya kuma toshe idon duk wata macen da zata ganni tace tana so balle kuma ta kawo mana wata tangard'a a tarayyar mu" "Ameen" ta k'ara amsawa cike da shauk'i tana jin ta acan saman gajimaren soyayya, "Kema kuma Ina addu'a da fatan Allah ya nakasa duk wani namijin da idan ya ganki zaiji yana sonki ko kuma yayi burin mallakar ki balle kuma har yace zai gabatar da kanshi a gaban iyayen ki da sunan yana son auren ki, Ina kuma rok'on Allah duk wanda zai kawo ma aurena dake tangarda allah ya kashe shi ya mutu ya huta muma mu huta" "Ameen" ta amsa dashi sai kuma can kamar wacce aka zabga ma mari ta zaro ido, "Heart wannan wace irin addu'a ce haka, babu kyau fa musulmi yayi ma d'an uwan shi musulmi mugun baki balle kuma fatan mutuwa" Ta fad'a a shagwabe, "Amma ai dani nace allah ya to she idon duk macen da zata ganni tace tana so kin amsa da ameen" "To ai wannan daban" "Ok in wancan daban kenan wannan ma d'aya ne da wancan insha Allah duk wanda zai kawo min matsala a maganar aurena dake sai ya mutu idan bai janye ba dan inaji a jikina kedin rabona ce " "Gaskiya nidai ba amin ba, oh dama saboda kazo kayi ma yan uwana muguwar addu'a shi yasa ka taso tun daga kaduna kazo nan Ina ta kiran ka baka iya d'aukar wayata ba, wani munafukin ne ya kiraka ya baka labarin abinda yake faruwa ne ma?" "Oh ashe dai akwai masu yin bakin cikin aurena dake d'in kenan tunda har kin ma sansu?" "Aiba laifi bane idan d'an uwa yaso yar uwar shi, da kai dasu dukan ku *DANGINA* ne yanda kake takamar kana da alaqa dani haka suma dan haka banga dalilin da zai sa kabi su da muguwar addu'a ba, idan addu'a ne ai nice ya dace inyita akan ka tunda nasan yanda kake da farin jini a wajen mata amma na rintse ido nace bana ganin kowa sai kai bayan nasan ko auren ka nayi ban isa in hana wasu Matan son ka ba" A matuk'ar fusace kamar dai wanda ta kalli girman shi ta zaga cike da hayagaga ya fara maida mata martani da cewa, "Wallahi³, Sai da ya maimaita rantsuwar wallahi sau uku kafin ya d'aura da cewa, "Kinji rantsuwar musulmi, to wallahi ki bud'e kunne kiji da kyau ko sun k'i ko sun so saina aure ki, bawan shi wancan Yayan baban naki da yake nuna ikon shi a kanki kullum ba kinaji koda ace duka *DANGINA* da naki dangin ne a yanzun sukace zasu k'alubalance zancen aurena dake kuma su juya min baya ni nan AK sai na aure ki sai dai duk wanda bazai iya gani ba yasha poison ya mutu, Dan haka kodai kije ki fad'ama wancan yayan Baban naki cewa ni dai ni kike so kika kuma fitar a matsayin mijin aure ba wad'ancan lusaran da suka gabatar da kan su a wajen shi ba, ya aura miki ni kowa ya samu kwanciyar hankali ko kuma wallahi in saceki in d'aukeki daga k'asar gaba d'aya babu mai k'ara ganin mu ko jin labarin mu har sai ranar dani naga dama na dawo dake, Shawara nike baki kodai kije ki fad'a mishi gaskiyar cewa ni kike ra'ayi kike kuma burin aure, Ko kuma ni in d'auke ki ta yanda bazai k'ara ganin ki ko jin labarin inda kike ba balle yayi tunanin k'ara had'aki aure da wani sakaran, shawara ya rage ga mai shiga rijiya, nayi sake a shekarun baya wanda saken nawa ne kuma yasa na rasaki a wancan lokacin, A zaton ki mahaukaci neni dazan sa ido Ina kallo shi Yayan baban naki ya k'ara ba wani can da bai cancanta ba auren ki kamar dai ke kad'aice Ya mace a cikin ahalin ku? Wallahi tunda har kika sake na sauke girman kaina na iya fitowa na shaida ma duniya cewa Ina sonki to a yanzun dai banga uban da zai fito yace zaiyi takara dani wajen neman auren ki ba, ki d'auka cewa wancan auren da aka miki a baya a mafarki kawai ya faru kamar yanda nima na d'auke shi matsayin mummunar mafarki, yanzu ne zakiyi aure kuma ni d'in nan nine mijin ki" Hannu ta d'aga mishi "Dakata Malam idan zakayi maganar ka kayi shi iya tsakanina ni dakai amma kar ka sake kayi zaton cewa dan kace kana sona hakan zaisa in zuba ido ka raina min ahali balle kuma har rainin wayau yasa ka tab'o shi wanda kake kallo a matsayin yayan babana, To bari kaji shi din ni ban tab'a mishi kallo a matsayin yayan ubaba tunda nayi wayau a ubana nike kallon shi har yau da gobe da jibina zuwa karshen numfashi haka zanci gaba da kallon shi, Shi dai da kake son aibatawa shine ni domin shi yayi tsaye wajen samar min da gatan da har kai dama wasu kuka gani kukayi sha'awa dan haka ina son in tabbatar maka da cewa shi din dai akalar rayuwata duka na damk'a mishi ita a hannun shi yanda duk ya juyani haka zanbi shi ba tareda tambayar dalili ba dan duk wanda zai nuna min so ko kauna harma da kulawan dakai kake ganin kana bani to a bayan nashi ka biyo, Wallahi da ace an halatta wa mace kin yin aure taci gaba da zama gaban iyayen ta da gaban shi zan koma in k'arasa rayuwata a tareda shi kamar yanda na faro ta, Matsayin shi a wajena yafi k'arfin in tsaya a gaban wani namijin harya bud'e baki ya nemi ai banta shi ban dun kule hannu na naushi bakin ko waye ba koda ko ace shi d'in mai maganar yafi ni tsayi zanyi tsalle ko in nemo abinda zan cimma tsayin bakin shi in nausa kafin mu cigaba da bala'i, balle kuma kai, Ka sani da kazo kace kana sona harna amince bawai dan Ina tsoron ka bane ko kuma wani dalilin na da ban, Ah ah na amshi sonka ne a zatona matsayin ka na d'an uwana zakaci gaba da tayani yin biyayya ga ubana ciki harda girmama sauran *DANGINA* shine tun ba'aje ko Ina ba kake ganin kamar har kana da zarrar da zaka tsaya a gabana ka nemi ai bata uban da bani da kamar shi, a haka kake so incigaba da sonka har in aure ka bayan nasan bai zama dole ka girmama ubana wanda shine gatana ba," "Please Meenal karkice zaki min gurguwar fahimta, ki sani cewa wallahi ko waye ya fad'a miki cewa zai soki fiye da son da nike miki karya yake miki babu wanda zai had'a son shi da kaunar dani nike miki, Ina sonki meenal shi yasa bazan so inga an k'ara rabani dake a wannan lokacin ba" "Oh soyayyar ce tasa ka fara tunanin tsame ni a cikin *DANGINA* zuwa wata duniyar ta daban? Kasan abinda yasa naji zan soka harma in rayu tareda kai a wancan lokacin? Saboda tsubin nutsuwar da Allah ya maka na kuma yaba da kyawun halayyan ka, Amma a yanzun daka fara fitomin da ainihin ka hakan yasa na gano rashin dacewar mu, Abdul bazan aureka ba zan koma gida wajen Yayan babana wannan karon ma zan bashi dama ya k'ara zab'ar min miji a karo na biyu" Tana gama fad'a mishi hakan ita kuma ta juya mishi baya ta fashe da kuka, Allah ma ya sani kalaman AK sun bata haushi sun kuma kona mata rai, Domin ko bai fito fili ya furta ba a cikin zancen shi ta shinshino rashin son da yake ma wanda ta d'auka a matsayin gatan ta, taya zata yarda so ya rufe mata ido harta tsaya a gaban shi yana neman zagin uban ta bata d'auki mata ki ba indai har itace so zaici amana irin haka to taci uwar son tasha ruwan kanwa maganin kwarnafin ciki, Sanyi jikin shi yayi sosai shi kuma, Shifa duk abinda ya fad'a bada mugun nufi ya furta suba yadai fad'ane kawai saboda ranshi da yake b'ace, Ya ita kuma take neman juya zancen haka daga d'an magana kuma shine zatace wai ta dena son shi ta fasa auren shi, Da sanyin jiki ya koma inda ta juya, "Meenal " ya kira sunan ta a sanyaye ita kuma sai ta k'ara juya mishi baya tana cigaba dayin kuka, "Meenal Ina son ki karkice zaki juyamin baya a daidai lokacin da nike sa ran na kusa mallakar ki" "Ni kuma nace bana sonka kuma ban auren ka tunda ka raina min uban da bani da kamar shi" ta karasa fad'a tana kara sautin kukan ta, Wallahi jiri yaji yana neman maka shi da kansa, "Ki rufa min asiri meenal bazan iya rasaki a wannan lokacin ba Ina sonki, Kuma ni bada wata manufa nayi magana ba tsoro dai nikeji kar a maimaita abinda ya faru a baya kiyi hakuri ki fahimta" Kara juyawa tayi ganin ya k'ara binta inda ta juya, Haka sukaci gaba dayi duk inda ta juya shi kuma zai bita yana faman son ya fahimtar da ita cewa shifa bawai ya raina baban ta bane, kawai dai tsoro yakeji, "Bana son..... " bai bari takai k'arsher kalmar ba da karfin tsiya ya jawota zuwa cikin k'irjin shi ya rungume a cikin jikin shi tsamtsam ya ta bude baki zataciga da masifa karaf ya had'e bakin ta da nashi ya fara aika mata da wasu irin mahaukatan zafafan kissing masu juya kwakwalen mata irinta wadanda basu saba keb'ewa da namiji ba, Duka da yakushi ta dunga kai mishi a k'okarin ta na ganin ta kwace amma ko gezau baiyi ba, Baya tayi da jikinta da karfi shi kuma ya biyota suka fad'a kan gadon dake kusa dasu yako k'ara danneta gaba d'aya batareda ya sarara daga aikin daya sa kanshi ba, Astagfirullah astagfirullah Astagfirullah yau dai duk yanda AK yake kai zuciyar shi nesa sai da bakin Yarinyar nan tasa hege shed'an ya kusa cin galaba akan shi domin dai rufe ido yayi ya tumurmushe ta saida ya murtsuke bakin rashin kunyar nan tsaf, itama dai tun tana ciccijewa tana tureshi har dan dole ta hakura ta nemi biye mishi dan jiki da jini atoh kuma itama dai a shekarun ta ai takai matakin da idan namiji yace mata kule zata maida mishi Cass ai wacce za'ayi wallahi, 😒 To dai ansha baki an kuma tsotsi kunne an lashe wuya kafin dai ayi batun kaima yan biyu da sauran sassan jiki hari Allah ya kwato mana gogan a hannun shed'an kila dai ya tuna cewa har yanzun ba'a d'aura auren bane dan haka a sanda jikinta ya amsa ta fara neman kai naushi itama shi kuma sai ya murgina gefe ya sauka a jikin ta yana faman maida numfashin dake neman d'auke mishi tun d'azun hakan ne kuma yabata damar jin kunyar kanta dan haka sai kawai ta dunkule itama taja bargo ta kudun dune a ciki dan bata da bakin magana, To me zatace jama'a bayan saura kad'an ta mance kanta, sai da yaji numfashin shi ya koma mishi dai dai kafin ya yunkura ya sauka a gadon, "Tashi ki fita min a cikin d'aki tunda kin samu abida kike so, ban hanaki ba kuma in kinga dama anjima idan muka k'ara had'uwa shima ki k'ara fad'amin cewa bakya sona ni kuma bazan gaji da kawo ki nan inci gaba da ladafta bakin rashin kunya ba badai ni kika ce bakya soba?" Yaye bargon tayi ta mik'e zaune, "Ka daiji kunya wallahi mugu mai shan bakin mata kawai kuma nidai ban yafe tab'amin jiki da shan bakina da kayi ba" "Ai saboda a iya bakin na tsaya shi yasa kika samu damar magana, duk ranar da hauka yasa kika kara cewa zaki rabu dani ko kuma bakya sona gonar ki zan shiga inyi b'arna wallahi an dad'e ba'a kaini kotun musulunci ba k'aramar yarinya kawai har nine ma zaki kalli idona kice bakya so dan kawai na fad'a miki gaskiya" Kuka ta fashe dashi, "eh din ba'a sonka kuma bana yin auren na fasa ko ko a k'afa aka daura min kai saina kwance na gudu inda bazaka k'ara ganina ba mai farin jinin mata kawai" "Oh kice min dama kullum ashe target dina kikeyi shi yasa da nace idan kika k'ara cewa baki sona zanyi noma yanzun kika furta, To bismillah inkin shirya nima na shirya k'aryar rashin kunya kikeyi" Juyowa yayi ya nufo inda take, da wani irin zafin nama ita kuma tayi kifiya ta sauka a gadon kafin ya ankara harta bud'e kofa ta fice da shegen gudu ko d'an kwalin ta bata tsaya d'auka ba, "Ke dawo ki d'auki d'an kwalin ki karkisa a fara yimin kallon d'an iska dan duk wanda ya ganki a haka ko nace ban tab'a kiba bazasu yarda ba mara kunyar karya dake kawai" Ina itafa tuni ta haye sama abinta shi yasa ko jiyo shi batayi ba, Su kuma su Sultana tun d'azun suka wuce sashen su Moon wajen Umma dan ita da kanta ta leko tayi kiran su Bayan da Hajiya ta bada sallahun a d'aura abinci kafin su dawo gidan acan ne kuma sukaji labarin d'aurin auren AK da Meenal din da akayi, dan haka Sultana ta sato jiki ta dawo falon dan ta fesa ma AK labari sai dai kuma tana shigowa ta hango Meenal ta haye sama da gudu bata gama tunanin dalilin gudun da Meenal keyi ba sai kuma ta hango AK kuma duk maganganun da yayi taji su rass dan haka sai zuciyar ta ya bata ko shima ya samu labarin d'aurin auren ne, shi yasa ya fara celebrating D'aga murya tayi ta kira sunan shi "Ya AK" Bai amsa ba sai dai ya juyo yana kallon ta har ta isa gareshi, "Congrats angon Meenal Ubangiji Allah yasa ace gara da akayi, muma yan baya Allah ya aurar damu" ta fad'a da fara'a sosai a murya da fuskar ta, "Wai Yaya dama ashe ana d'aura aure ko ango baije wajen ba? Ni wallahi ban tab'a jin daga zuwa tambaya ace an d'aura aure ba sai yau, dan Allah kaje kayi wanka kasa manya kaya kaima kafin su Hajiya su dawo inba haka ba ai baza'a wani gane cewa kaine angon ba" "Me kike cewa ne Sultana auren wa aka d'aura ne?" "Lah wai basu kiraka sunce maka an d'aura ba? Tsaya ka gani" Shifa shirme ya d'auki zancen ta ko kuma dai kila tana mishi wasa ne, dan haka sai kawai ya tsaya yana kallon ta harta d'aga wayarta ta d'anna kira, Number din ya Sheikh ta kira yana d'auka ko bayan tayi sallama ya amsa ta jefa mishi tambaya kamar haka, "Ya Sheikh da gaskene wai an an d'aura auren ka da Fauxieyerh ita kuma Meenal da Mai Jama'a?" "Ke kina Ina ne da kike kirana a yanzun? Bakya gida kenan" "Nidai dan Allah ka amsa min tabbaci nike son samu kuma nasan kai baka k'arya" "Eh Sultana Allah yayi a yau nasamu k'aruwar aure nima na zama ma gidanci" Kit ta yanke wayar, "Kaji koh Wallahi da gaske an d'aura dan ya Sheikh baya k'arya" Kofar d'akin AK ya bud'e ya fito a tsakiyar falon ya yi sujudur shakur bayan ya d'ago sai da ya d'aga hannuwa sama yayi addu'o'i harda hawaye yana shafawa kuma baibi takan Sultana ba ya fice da gudu Sashen Abba Ahmad ya shiga, Akwai mata a falon amma bai damu daya tsaya gaishe su ba ya wuce da sauri yana kwala kiran Ummi, "Kai lafiyar ka zaka fad'omin cikin gida kana wani kwala kiran sunana uwa dai sabon makaho" Maman su Bilkisu daya wuce su a falon ne tace "bashshi Amina ke koh ango nefa" "Da gaske ne an d'aura aurena da mai sunan ki ummi?" "Da gaske ne mana ba abinda kake buri kenan ba dama?" Rungume ta yayi yana dariya, Dan haka sai itama ta rungume shi tana cewa "na tayaka murna Ina fatan kuma zaka riketa amana, Allah ya baku zaman lafiya da zuria masu albarka" "Ameen Matan falon suka amsa shi kuma sai ya saketa daga rungumar daya mata ya juya ya fice daga sashen gaba d'aya tsabar farin cikin da yake cikine yasa bai tuna da wayar shiba tun d'azun sai yanzun, aljihunan shi ya fara lalube sai dai kuma baiji wayar ba, kenan dai a kaduna ya barta, komawa cikin sashen Ummi ya karayi da gud'a, Wayarta ya amso ya k'ara fitowa number din musty ya fara kira, "Kana ina? "Ya tambaya bayan musty ya d'auka, "Kai kana Ina yanzun haka?" Shima musty ya tambaya, "Ina gidan Hajiya kazo yanzun please" "Fito kofar gida ka jirani" Yanke wayar yayi shi kuma AK mai makon ya fita wajen sai ya koma sashen Hajiya gaskiya fa Sultana ta fad'a mishi gara yaje yayi sabon wanka yasa manyan kaya shima ya fito a matsayin ango sak, Kafin ya shiga d'akin shi har ya fara tunanin haurawa sama yaje yama Yarinyar nan albishir amma sai ya fasa, Zaiyi lokacin tane anjima badai shi tayi ma rashin kunya ba hummm, Bayan ya fito daga wanka cikin sabbin manyan kayan daya d'in ka da bikin Musty ya zab'o wata lafiyayyar farar shadda mai had'e da malum malum wacce akayi ma aiki blue din zare ya sanya, tsaf ya shirya ya fito a angon kafin ya fito daga d'akin hula a hannu sai zabgaga kamshin turaren dayayi ma jikin shi wanka yakeyi, Kawayen Hajiya data kira ta shaida ma batun auren ya tarar a zaune a falon cikin su kuma harda Dadah turai, Su kuma kamar masu jiran fitowar shi haka suka lullubeshi suna gud'a, Gidan hajiya fa ya cika da makota mata suna cikin gida suna aikin abinci suna kuma jiran dawowar yan d'aurin aure, Tunda su Musty suka dawo tudun wada suke wasa da motoci a majalisar su dan haka wajen ya cika dam da mata sa harda wad'anda basu samu zuwa can wajen d'aurin auren ba shagali kawai sukeyi abin su, dan haka sai shi kuma ya janye jikin shi yayi cikin gida, Sasan AK din ya fara zuwa ganin kofar ya kulle yasan baya wajen dan haka sai ya wuce sashen Hajiya kai tsaye, a falon nata ya sameshi mata sun dabaibaye shi suna mishi gud'a yana Karasawa shi kuma ya ciro kud'i daga cikin aljihun shi ya farayima Ak manni dasu dariya. *Ummiee ce* [10/10, 8:51 AM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA *👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 46* *My Aleesah where are you? Ki sani tundaga kan wannan page din har zuw karshen labarin na sadaukar dashi a gareki domin kin cancanta na yaba kwarai da kokorin ki*😍.... Da kyal suka samu suka fice daga cikin falon suna dariyar Dadah wacce ta d'age akan cewa sam bata yarda da shigo shigo ba zurfin da aka mata kishiya da yamma sakaliya ba, Haka kawai tana zaune daga zuwa tambaya sai taji tashin zancen wai an rangad'a mata kishiya ba notice, Su kuma k'awayen Hajiya suna taya ta da cewa tabbas suma suna tayata kishi, A harabar gidan sukaci burki bayan fitowar s daga falon suka nufi inda su Baba Usman suke, domin su Musty sun rigasu barin can gidan Malam shi yasa su sai yanzun suke isowa tareda uwar garken wato Hajiya. "Kai ku matsa ku bani hanya in isaga mijin Aminatu Abdul Khareem d'ina haba jama'a haka akeyi duk kunbi dai kun yanyame min jika kamar wani naman kasuwa bazaku barshi ya iso gareni mu taya juna murna bayan kowa yasan cewa nice kashin bayan arzikin daya samu na auren jikata, Nice nan fa k'ashin bayan nasarar shi wai a hakan ma dan auren yazo ne babu zato amma ji yanda aka cika min gidan dama unguwar kamar dai wad'anda akayo ma shela, Zonan kaji mai Babban suna zo wajena kaji yau dai Alhamdulillah alkawarin Allah ya cika masu murna suyi akasin haka kuma mutum sai ya rufe kanshi a daki inyaso karya fito sai ranar kiyama" Janye jikin shi yayi daga cikin abokan shi da suka baibaye shi suna mishi mishi murna da fatan alkhairi ya k'arasa wajen Hajiya da iyayen shi yana isa baiyi wata wataba yabata kyakyawan runguma, "Hajiyata da gaske kun amso min auren ta? " ya tambaya cike da mad'aukakin fara'a a fuska da muryar shi, Itama da fara'a sosai ta amsa da cewa.. "Da gaske ne mana Abdul ana wasa da igiyoyin aure ne dama? Kai dai yau Allah ya nufa cewa rana bazata fito harta fad'i batareda igiyar auren ka ya hau kan mai suna naba, Ka daiga ikon Allah koh! Inda ace ayau din nan wani zai tareni yace min ke Amina ki shirya yau za'a daura auren jikokin ki tofa ina fad'a maka da sai na kalli kwayar idon mutum kafin in kirashi da suna mugun makaryaci, Eh mana kaikoh tunda mudai nan mun saba komai sai an bishi daki daki kafin a kaiga batun daurin aure, kaga dai ayi tambaya na angani Ana so, Idan an amince aba saurayi dama ayi zancen baiko dasa rana amma mu babu d'aya da muka gabatar tun bayan dai da iyayen ka suka ma wancan d'ayan uban nata batun shi kuma da yafi kowa iya shiririta yaje yayi ta sha'anin gaban shi bai tada zancen ba, ai dole kowa yayi mamaki dajin batun auren nan tunda dukan mufa saida muka sallaci sallan azahar kafin mu fita zuwa can gidan, To da Allah dai ya kaddara cewa yaune ranar kamar yanda yan magana ke cewa mutuwa, Aure da haihuwa dukan su lokaci garesu to kaima dai yau naka ranar yazo amma kaga kai da yike Allah yana sonka shi yasama ya baka ni a matsayin kakarka gashi munje da batun sa rana amma mai makon hakan mun amso maka auren gaba d'aya" Kara rungume ta yayi tsam tsam hawayen farin ciki na cika mishi idanu dan kamar yanda Hajiya tace ne koshi yau kam ya jinjina ma girmar kudurar ubangiji lallai Allah ne kad'ai keyi inyaso kuma babu mai hanawa tunda gashi yau allah ya mallaka mishi Meenal a dai dai sanda take cikin tutsu, dazun nan fa ta gama mishi rikicin cewa bata auren shi ashe daga shi har ita basu san cewa aure ya tabbata akan su a daidai lokacin ba, to kodai shaukin auren nema ya kwashe shi yau yakusa sab'a lamba?, murmushi mai fad'i yayi hawaye na zirarowa daga cikin idon shi, "Nagode Hajiya, Nagode kwarai ubangiji Allah ya bada lada, Allah ya kara miki lafiya ya kuma raya manake kiyi jinkiri mai amfani da albarka ameen nagode kwarai kuma nayi miki alkawari insha Allah zan rike mai sunan ki da amana bazan taba yin abunda zaisa tayi kuka dani ba zan cigaba da sonta har zuwa sanda zanja numfashina na karshe a doron k'asa " *Ameen! Ameen Ameen Abdul Khareem ubangiji Allah yasa albarka a cikin auren ku Allah ya zaunar daku lafiya Allah kuma ya baku ikon sauke hakkin juna hakika nafi kowa murna da faruwar wannan al'amari, Allah ya baka ikon rike Amina kamar yanda mai sunan ka ya rikeni har zuwa sanda mutuwa ce ta rabamu" Ta k'arasa fad'a da muryar kuka idanuwan ta na zubda hawayen itama kamar dai shi, Ameen jama'ar dake wajen suka amsa, Bayan ya raba jikin shi dana Hajiya wajen su Baba Usman ya koma suma kuma saida ya bisu d'aya bayan d'aya ya rungume su yana musu godiya akan jajircewar su na ganin sun samar mishi abinda yake so Hajiya dai sashen ta tawuce bayan itama ta gama amsa gaisuwar jama'ar dake harabar gidan, Shi kuma Musty da sauran abokan su sai suka janye AK zuwa kofar gidan cikin sauran matasan da suka cika unguwar suna taya shi murna, Taro ne ya had'u na ban mamaki a wajen nan domin shi kanshi AK yayi mamaki da ganin yawan mutanen dake wajen, koda ya shigo gidan fa a d'azun dai dai kun mutane ne a wajen amma yanzun duk inda ka kalla jama'a ne tako ina, lallai AK ya tabbata mai jama'an na gasken gaske wai a hakan ma ba kowa yaji labarin zancen auren ba, Matasa sunyi kara gaskiya dan duk wanda labarin yaje kunnen shi baya zama sai yazo dan k'ara samun tabbaci dan da farko da yawa wasu sun karyata zancen auren, Dan haka kafin ka ankara unguwar ta cika mak'il dan ko abincin da Hajiya tasa aka dafa a cikin gidan kafin a fito dashi waje har ya k'are dan ma shi Musty tun dawowar su daga wajen d'aurin auren ya k'ara bada order a wad'ansu gidajen abincin banda na restaurant din dake nan kofar gidan nasu, Ko kafin ace karfe 8 na dare tuni Yusuf da iyalan shi harma da Sadeeq sun hallara a gidan Hajiya suma kuma tareda nasu mutanen suka taho domin dai duk wanda akace ma an d'aura auren burin shi kawai yazo ya tabbatar ne dan kowa mamaki yakeyi wai AK aka d'aura ma aure babu gayyata to dan uban shi inma sune bai son gani wajen bikin shi sai sunje shagali sosai fa aka gabatar a kofar gidan Hajiya rana suma kuma matan suna ciki suna nasu, A can gidan Malam ko bayan an gama d'aurin aure Hajiya da gayyarta sun wuce suma dai haka sukaci gaba da k'arbar bak'i yan zuwa Allah sanya alkhairi yan uwa nakusa suma dai tuni suka hallara duk da kuwa yanda abin yazo musu a girshe, Baba Auta bai samu shigowa gidan ba sai gab magrib dan Baba Adamu ne ya kirashi ya shaida mishi abinda ake ciki, Bayan an idar da sallah suna shiga gida Malam ya had'a kan Baba Adamu dashi Baba Auta a falon shi, "Auta nasan ka samu labarin abinda Hajiya tazo tayi min a falon nan koh! To Alhamdulillah ta gama nata nima zanyi nawa ikon, domin mu dai gidan nan tunda mukayi wayau bamu tab'a ganin inda aka gudanar da neman aure irin wanda ita ta jogoranta a yau ba, Inda kuma nace zan tsawata a dazun din nasan kowa laifina zai gani to Alhamdulillah na bata dama itama kuma ta dama sai dai kuma tunda suka sa aka d'aura auren a yau tofa bazasu jingine min yarinya taci gaba da zama tana yawo da auren d'an su ba, Kai Adamu kai da kayi jagora kaine zaka kira su ka shaida musu cewa yau labara ni kuma na tsaida ranar juma'an nan mai zuwa a matsayin ranar yinin biki da tariya dan haka su fad'i inda d'ansu zai zauna da ita gobe za'aje ayi mata jere, shi kuma Sheikh ka tambaye shi idan bashi da inda zai ajiye Raheenat d'in to akwai takardar gidan da Alhaji Mai Kud'i ya bashi jiya ya kawo min takardun tun a daren jiyan sai aje gidan aduba in akwai gyara kunga sai ya hak'ura da tarewa acan su zauna a wancan sashen dake gefen nasu Sa'eed tunda a gyare wajen yake kafin lokacin dazai koma Abuja,yauwa kuma karka manta kasa mai d'akin ka tayi list na duk abubuwan da basu had'o dashi ba na auren budurwa ciki harda lefe dan kar suga an d'aura aure suyi zaton ko sun sha, a kuma je a d'auko min ita Meenal din a can gidan ta dawo nan, sai abu na k'arshe karku manta ku kira sauran mutanen da basuji auren ba dan ranar juma'an dai za'ayi yinin biki dakai amare d'akin su, kuna iya tafiya na gama magana" Yana gama fad'in hakan ya mike ya shige cikin bedroom din shi ya barsu da binshi da ido, Baba Adamu ne ya fara mikewa kafin yace "muje koh auta dan kasan dai dole yanda yace din shi za'ayi muje in zauna da maman nin su inji yanda za'ayi batun kayan d'akin su in yaso sai muyi magana da Hajiyar kano tunda ga yanda abun yazo" A daren Baba Auta yaja Mommy Hauwa zuwa sashen Baba Adamu basu tashi a zaman nasuba sai da suka kira Hajiyar kano suka gama magana akan kayan d'akin su Meenal din akan duk yanda ake ciki batun wajen zaman su Meenal din zasu kirata a yayin zaman nasu ne kuma suka kira itama Momin Abuja dan suji ko akwai inda Fauziya zata zauna acan din an kuma samu dan ashe tuni shima Sheikh ya tanaji gidan da zai zauna da nashi iyalin batun auren ne dai yaki maida hankali, Baba Usman suka kira akan batun wajen zaman Meenal shi kuma daya tambayi Hajiya sai tace mishi a sashen marigayi zasu zauna kafin ya k'arasa ginin shi su koma Kaduna, a cikin daren komai na shirin biki ya kammala a gidan Malam Sa'eed aka tura can gidan Hajiya ya taho da Meenal da Sultana, a gefen Meenal tun bayan data haura sama bata k'ara marmarin saukowa ba, a sanda kuma ta fara jiyo hayaniya a cikin gidan ta dauki hakan kawai a matsayin gayyar hajiya ne dan haka sai bata wani damu kanta cewa sai ta sauko ta duba abinda akeyi ba, su kuma daga Moon har Sultana babu wacce ta neme ta har saida Meelat ta iso gidan sune kuma suka kira Maryam suka bata labari saidai koda suka haura saman sunyi bugun kofar d'akin da meenal ke ciki har sun gaji amma haka tayi kunnen uwar shegu dasu tak'i bude musu kofar har suka gaji suka juya, Bayan anyi sallan ishsha'i har d'akin Hajiya tabi Meenal d'auke da takardar gidan da Sarki ya siya da sunan Aminatun, tana zama Larai ta shigo da abincin da Hajiya tasa ta d'iboma Meenal din tana ajiye mata ta fice ta barsu, Ita kuma Meenal tun shigar Hajiya d'akin dama ta wani d'aure fuska dan karma Hajiya tace zata wani bata labarin yanda sukayi acan gidan su, "Kina nan kin kulle kai a d'aki uwa dai wata matar mamaci kinaji ana hayaniya kin kasa fitowa Sarauniya Aminatu to ni dana matsu ai gani na biyo sahu, d'auki takardar nan ki dubamin ko takardar menene?" Hajiya ta fad'a tana mika mata takardar, amsa tayi ta fara dubawa tun bata kammala ba ta d'ago kanta tana maida kallonta kan Hajiya, "Hajiya... Tarar numfasjin ta Hajiya tayi da cewa, "Eh abindai da kika karanta a rubuce haka yake, ba kullum burin ki shine ki siyama Baban ki Malam gida ba? To ga gida nan yau kin mallaka dan haka sai kije ki mallaka mishi sai me kuma kike da muradi yanzun? Iye uwar malam" "Hajiya gida na?" "Kwarai kuwa gidan ki yanzun nidai tukuici kawai ya rage ki bani tunda na isar da nawa sak'on" Rungume takardar Meenal tayi tana dariya sosai cike da jin dadi tace, "Hajiya kece kika siyamin gidan?" "To da dai nace bazan fad'a miki gaskiyar wanda ya siya gidan ba saboda shi dai dan Allah yayi kuma yana son hakan ya zama sirri ba tareda kowa ya sani ba amma dai yanzun naga babu amfanin boyewa" "Waye ya siyamin gidan to?" Ta kara tambaya, ita kuma Hajiya ta amsa mata da cewa Sarki ne ya siya gidan kuma yace kar a fad'a miki amma ni nasan zaki rik'e wannan sirrin dan ko Moon bana so taji labari haka ma sauran mutanen gidan ku idan iyayen ki sun tambaya ki fad'a musu cewa kudin kayan ki dana siyar ne muka hada aka siya gidan dashi " Duk da bayanin da Hajiyar tayi mata amma haka taso ta botse kan cewa ita ai tana da kudin ta kuma dasu zata siyama Malam din gidan, sai da suka hau sama suka sauko kafin Hajiya tace, "Ki shirya Sa'eed zaizo ya maidake gida" "Gida kuma Hajiya saboda me?" "Saboda kin zama matar aure in kuma zakiyi zaman kine kawai basai munyi wahalar zuwa d'auko ki mu dawo dake nan din ba ai shike nan" "Waima matar aure"ta fad'a tana tab'e baki dan bata d'auki maganar da mahimmanci ba, Ficewa Hajiya tayi kuma itace da kanta taja kunnen Sultana akan koda wasa karta ta yarda zancen auren a gaban Meenal kuma koda Sa'eed din ya iso Hajiya da kanta tama Meenal din jagora suka fita ta kofar kitchen har suka bar gidan babu wanda ya lura da Meenal din, *muje a gurguje* Washe gari komai da Malam ya buk'ata tun daga kan lefe zuwa duk wani abun buk'ata haka su Hajiya suka shiryo suka kawo gidan Malam kaya bani da kaya ba abin ma dai kamar da gayya sukayi shi dan su nuna ma Malam cewa basu gaji tsiya ba na bakin hajiya, Suma kuma gidan Malam din a ranar sukaje suka shirya ma Meenal sashen da aka ware mata a gidan Hajiyan matsayin inda zata zauna harka dai na arzik'i rab'a rab'a haka yake gudana tsakanin gidajen dan kowa baya son aga gazawar shi, A ranar da Meenal ta koma gida ba k'aramin bori tayi ba, Kenan dai ya tabbata ita kenan bata da gatan da za'aji ta bakinta aduk sanda zancen aurenta ya tashi, dan Allah yanzun hakan da suka aikata mata shi basai yayi zaton ko dama can an gaji da ita bane shi yasa kawai daga zuwa tambaya za'a wani ce an d'aura mata aure, Haka dai tayi borin ta gaji babu wanda yabi ta kanta sai Fauxieyerh ce ta koma ban baki dan ita Sultana cewa tayi wai karyar iskanci Meenal din keyi, Baki fa duk sun hallara yan nesa dana kusa sai harkar arziki kawai akeyi kai in kaga nima bazakace wai bikin da yazo babu shiri akeyi badan kowa ya saki jiki ana harkoki amma banda Meenal wacce ta d'auke ma kowa wuta ciki harda kawayen ta, suko basu wani damu ba dan sun san fushin ta bazai sauya komai ba, *Ranar juma'a* murmushin gefen baki yayi yana mai cigaba da kirar wayar sai dai har yanzun daga can gefen ita da yake aikama kiran bata dauki wayar ba, Da alamun damuwa akan fuskar shi ya bude kofar motar da yake ciki ya zuro kafar shi daya waje daya tana ciki, fita yayi daga gefen kira zuwa gefen tura sakonni yaci gaba da rubutu...... Abokan shi dake daura da motar da yake ciki a zaune ne suka karaso dukan su cikin shiga na Alfarma sunsha wanka har ba'a tantance kalolin turarukansu,daya daga cikin sune ya bude murfin motan ta gefen mai zaman banza sai dai duk da yaji sanda suka karaso da kuma surutun da suke mishi akai hakan baisa ya dago kai ya kalle suba har saida ya kammala rubuta sakon ya kuma turashi zuwa inda yake so in bata dauki kiraba ai dole zataga sako, Fuskarshi cike da murmushin da yaki rabuwa da fuskar tashi tun daga ranar laraba zuwa yau daya kasance juma'a duk da cewa dama yakan dan saki fuskar ta shi sai dai sam baza'a sashi cikin mutane masu yawan fara'a ba, amma yau kam kowa ya shaida yawan fara'ar tashi tana da nasaba da samun cikar burin zuciyar shi da yayi a wacce yake da tabbacin tarewar ta a d'akin shi yau dan hakan ne zai kara tabbatar da kasancewar su ma'aurata. "Abakar ya akayi kun sallame sune?"ya tambayi wani abokin shi bayan ya gama shan kamshi, "Eh kusan hakan Dan su abba sun wuce tun dazun nasa su hafees suyima sauran jagora gamai bukatar zuwa" "ok" kawai ya iya fada yana mai kara duban wayan shi a zaton shi ko zai samu amsar sakon daya tura mata sai dai har yanzun dai ba wani sako daga wannan lambar, "Da kyau Dr" ya fada a bayyane yana mai fita daga cikin motan mika mishi hannu sauran abokan sukayi suna masu tayashi murna dafatan dorewar zaman lafiya da fatan samun zuria masu albarkha! shi kuma yana amsa musu da "ameen nagode" Abakar ne ya matso gefen shi hannu ya mika mishi "congratulations once again my brother". . Thanks abuu nagode sannu da kokari allah yabar zumunci, ya fada yana mai runguman abakar din ta gefe. (jar uba) aka fada daga gefe " lallai kullu yaci amanar koko, wai gayun nan tun ban mutuba zasu fara wareni" karasowa yayi ya hada su duka biyun ya rungume haka suma sauran abokan su Yusuf Musty Sadeeq Faisal kamar da sauran su suka karaso suma suka rungume su abun dai gwanin burgewa. "Kai! Kai!! Kai!!! Kai Dan allah ku cikani duk kun wani dakune ni kamar sabon jariri a hannun juya kar ku taramin gajiya tun daren baiyi ba ku cikani dallah" Fashewa abokan sukayi da dariya baki daya, " Ah to eh mana gaskiya kunsha dani nida ya dace in rungumi yar amaryata kawai wasu gaddawa daku kunzo kuna dakunata,gaskiya duk wanda ya k'ara rungume ni sai nayi mishi Allah ya isa" sadeeq ne yakai mashi duka shi kuma saiya goce "Eh lallai Mai Jama'a amma ba komai ai munyi mai wuyar tunda munyi tsayin daka har an daura amma zakaci ubanka wallahi ai daurawa akayi bata tareba. idan banje na zugata ba kacanza min suna, kai imba banda Allah yana sonka ba taya har zaka rigani yin aure nema?" ya karashe fada yana rike haba irin abun ya kai mishi ko ina din nan,ba tareda yadamu da abun da sadeeq din yace ba ya kalli Abuu yana me cewa,. "Wai kunsan yarinyar nan tunda gari ya waye nike kiran ta taki daukar min waya?kuma fa tun ranar laraba da tayi min rashin kunya bamu k'ara had'uwa ba ta gudu gidan su" ya karashe maganar yana mai girgiza kanshi dan abinda ta mishi fa ya bashi haushi, Murmushi abakar yayi musty ne kuma yace " kai haba mai jama'a karka wani bata ranka shareta kawai ai duk wayon amarya ko taki ko taso dole dai sai ansha manta balle wannan amaryar da tazo a lokacin da ake cikin halin rabbana atinaa.....kai da kake cike da yunwanta, share kawai AK yau dai insha allah bamu ba baccin dare har sai mun kai amarya dakinta" "ko a kafadane kuwa", wani daga cikin su ya karasa mish, wani kuma daga cikin su yace "kaga koh zance wasan buya, kin daukar waya, dama duk wata dojewa ya kare yau dole kuturu yasha ladan aski" Haka dai sukaci gaba da sakin layi suma, kun san mazama sun iya sakin layi wani lokacin kamar dai mu mata 😅. Basu bar harabar masallacin ba sai da yawancin jama'a suka watse sannan suma suka shiga cikin nasu motocin suka dauki hanya a tsanake kuma a jere suke tafe gwanin burgewa ba tareda wani ya wuce wani ba, tun daga tudun wada har zuwa GRA gidan Sadeeq . """""" """"Meenal kuma a gefeta gaba daya ta kasa masalta yanayin da zatace ta tsinci kaita a ciki yau juma'a da take da tabbacin cewa yau za'a mik'ata d'akin ta dan yanda taga ana ta shirye alamun sun nuna mata hakan, a kasan zuciyarta ta sani bata bakin ciki ko kadan amma a gefe guda kuma cike take da fargaban auren nan da yazo babu shiri dan haka tun safe take gujema idanuwan mutane badan komai ba sai dan yanda abokan wasan su suke neman saki ta gaba da tsokana dan haka ta gudu can gefen Baba Malam dan nan ne bashi da cin koso bata baro can d'inba sai da aka taso daga masallacin juma'a saboda bak'in da tasan zasu cika sashen dan haka sai ta fice ta lallab'a ta dawo sashen su ta shige d'akin Baba Auta. Kwance take a kan gado tunani ne kawai ya cika mata kai sai faman mulmula take daga farkon gado zuwa karashen shi kamar mai nakuda ko kuma ciwon mara, a dai dai lokacin da hayaniyar mutane ya karu saboda walimar da ake gudanar wa na mata anan cikin gidan haka itama zuciyarta taci gaba da gudu bata kara sarewa ba har sai sanda kunnuwanta suka jiyomata shelan da malaman keyi cewa a fito da Amare Bata karasa jin karshen zancen ba tafashe da matsanan cin kuka tana mai ambatar innalillahi wa'ainnah ilaihir'raju'un........ Haka naci gaba da maimaitawa tun ina kukan da karfi harya zamana hawaye ne ke fita ba muryar ihu, Ita Allah ya sani ba'a yanda ta tsara abubuwa suke zuwa mata ba, ita shikenan bata da halin da zata more nata rayuwar shi kenan kullum sai aureta yayi ta zuwa mata a hagun ce babu wanda yake damuwa da ra'ayi ko abinda take muradi, "Allah sarki su Meelat sudai sunji dadi wallahi komai nasu a tsare ba irin naga da yake zuwa da arangizo ba". Ta fada tana mai cigaba da zubda hawaye "me yasa komai nawa baya zuwa a yanda nike son shi? alhamdulillah allah nagode maka daka tsaramin kalar tawa rayuwar a haka,ya allah ka sanyama wannan aure albarkha kasa ya zamto aure na karshe da zanyi a doron kasa, Allah ka bani ikon yima mijina biyayya a zaman da zamuyi ameen ya rabbi" ta fada tana goge hawayen idonta. Pillow din dake gefenta ta rungume hakika ranar yau tamata zuwan bazatan da batayi tsammani ba haba dan Allah an daura aure babu shiri ai ya dace ace ita kuma a bata damar shiryawa da kyau kafin asa ranar tarewa, Amma kowa ya azalzala kamar dai dama duk sun gaji da ita, in kayi magana ace kayi hakuri kayi biyayya, "wato ni Abdul zai munafunta bayan na nuna mishi a'ah shine ya zagaye yaje ya koma ta sama ya nemi aurena ba tareda sanina ba a matsayina na bazawarar dake da yancin zabarma kanta miji shine harda zuwa gabana yana ma yan uwana mugayen addu'a wato tunda shi yasan abinda ya taka wato,hakika kullu yaci amanar koko" ta fada ina tura baki "nidai kamar mara gata duk lokacin aurena ba wanda yake damuwa dason jin ra'ayi na,duk yanda suka yanka hakan zanbi. anyi na farko ba'a bani zabina ba duk da na nuna bana so,shine na biyun ma gashi a haka akayi shi,e mana to bashi gashi ba yanzun din ma bata canza zani ba,shi kenan nidai a kullum bani da zabi kenan? Amma ai ba laifin kowa bane laifin Mai Jama'a ne tunda yaje kai tsaye ya nemi aurena bayan na sanar dashi cewa ban shiryama wani aure yanzun ba,wato ma ni aka hade ma kai a gidan nan aka mai dani kamar wata bare wai daurin aurena ne akayi da yamma kawai dan sun mai dani zawarar da gaske,wai ace harda Sultana duk shegen gulma da tsegumin ta wannan karon ta kasa kwaso gulmar ni ta fad'amin saima aka hada baki aka karamin auren dole! Ita da take kawata ta amana da ita aka shirya aka kara gabatar da komai suka rufe ". Kalmar auren dolen data furta ne yakara dawo mata yama tsaye a zuciya, "Shin da gaske auren dole akamin? Ko auren gata? " Ta tambayi kanta, a matsayita na bazawarar da tayi zaman aure na tsayin shekara 6 iyayenta suka kara wanke saurayi dal suka auramata, saurayin daya kasance saurayin da bashi da tamka a fadar zuciyarta a wannan lokacin,taya zata kira hakan auren dole murmushine ya subuce mata "lallai ni mai sa'ace,to wai ma kukan me nike????? Ba amsa ............. Tana cikin wannan hirar tsakaninta da zuciyarta ta jiyo karar wayarta dake ajiye a gefenta, mika hannunta tayi ta dauko wayar saidai kallo guda ta ma number din dake yawo akan wayar ne ya kayar mata da gaba, " shike nan ni Aminatu ta faru ta kare iko da nuna isa kuma tsakanina da mutumin nan ai sai ta Allah maye kawai ka kira har ka gaji baza'a d'auki wayar ba" number din ba suna domin ban ajeta akan wayar ba har yanzun amma ko ciwon mutuwa takeyi kallo guda zata mata ta shaidata, " Abdul Khareem" ta fada a bayyane tna mai murguda baki "baza'a dauki wayar ba wato burinka ya cika bari ka kirani" ta fada tana mai kife wayar,ganin ba gajiya zaiyi da kiraba hakan yasa ta cire karar wayar gaba daya yanda koya kira bazata dame ta da karaba,inya gaji ai dole ya hakura da kira shima dauko wayar tayi da niyar in kasheta gaba daya sai gashi kamar mai hasashe tna daukar wayar sako na shigowa cikinta,ko bata budeba tasan dan anacen ne dan babu number din kowa akan wayar sai tashi, dan tun jiya da Sultana ta amshi nata wayar da sunan zata kira bash tayi mishi albishir har yanzun bata dawo mata dashi ba data matsa da tambaya ma cewa Sultanar tayi wai ita dai ta manta inda ta ajiye wayar wallahi, sai da safen yau ne ta kawo mata wannan sabuwa ce kuma babu komai a kanta. Tun kiran farko daya shigo wayar taga number din shi yasin tasan shine yasa aka dauke mashi nata wayan, Ba tareda ta karanta sakon ba na kashe wayar baki daya ta koma taci gaba da kwanciya,. "Hummmm dan samari duk ka gama rawar jikin ka ai bazakusan nasara ya shuka tsiya ba sai zashi ganin gida,ba kana murnar kai angoba aiko ban tarewa yau boyewa zanyi inda babu mai ganina" murmushin mugunta tayi a bayyane tace "shawara mai kyau" harda tsallen jin dadi saida tayi daga kwancen da take "yo ni hauka nike in tare yau lallai idan na tare yau tabbas gobe a gadon asibity za'azo aci gaba da ganin amarya😢 mugu kawai mai shan bakin Mata" Ita kadai a daki Yayin da acan cikin gida mata ke cigaba da gudanar da biki babu kama hannun yaro domin dai ita d'ayar amaryar wato Fauxieyerh babu abinda yasha mata kai ta sake abinta tana walwala bata takura rayuwarta ba, bayan an gama walimar da aka nemi Meenal aka rasa can ta kofar baya wajen sashen su ya sa'eed masu kidin kwarya sukaja da'ira suma dai sai faman ihun kiran amarya meenal suke amma babu amarya meenal taki fitowa sai iyayen amaryar ne da su Sultana suketa kara'i domin ranar yau ba bakin ciki domin ko bakama Meenal kara kataka ba kayi Fauxieyerh ustaziyar gidan malam wacce da kyar ta yarda ta fito filin sai dai kamar soja haka ta zamar musu ko dan rausayar nan babu. A can gidan Hajiya ko shiri sukeyi sosai na tarbar amarya gida ya cika dam da gayyar yan uwa da abokanan arziki bakin Hajiya yau dai yak'i rufuwa, gefe guda kuma yan mata da samarin gidan ne suka shirya nasu shagalin suma sun rantse cewa baza'a barsu a baya ba dan haka suka ware gefe guda a harabar gidan suka kira masu decorations suka shirya musu shi ganin burgewa a cewar su tunda ya Abdul yace babu casu to sun san bazai hana na cikin gida ba,suma dai sun shirya sun kuma dau wanka duk wanda ka gani sai dai kace masha allah sai zabgaga kamshi sukeyi sunfa wanku,. ~~~~, Su kuma angwaye bayan sun baro gidan Sadeeq sun dawo tudun wada tun daga junction din gidan Hajiya zuwa fadar mai jama'a tarin motocin da suka gani faffake ya shaida musu cewa lallai jama'ar mai jama'a sun taru dan ko ina Abubuwan hawane fake Kama daga mashin keke napep mota da kuma wasu mutanen a waje,musty dayafi sauran bakine ya gaza shiru saida ya tanka "kai AK anya kakanka bai jika maka hatimi kasha a lokacin da yake raye ba kuwa?" Ya fada tana mai kara bin motocin dake fake da kallo "lallai halin mutum jarinsa my brother please say Alhamdulillah".. dariya sauran sukayi suna masu mai maita kalmar alhamdulillah di gangarewa yayi ta wani gefen daban ya fito ta saitin masallacin,duk da cewa an kammala liyafar cin abincin amma har yanzun dai akwai jama'a sosai a gidan bai shiga masallacin ba saida ya nufi gefen da motocin shi ke fake sannan yayi amfani da key ya bude motar ya zuba wayoyin shi hula da babbar rigar shi,kulle motar yayi suka karasa cikin masallacin shida su sadeeq da suka idar da alwallah yanzun,. Bayan an idar da sallah da yawa daga cikin abokan shi motocin su suka shige domin komawa unguwan unguwar malamai gaisuwar sirikai daga can kuma idan sun d'auko amarya wajen dinner za'a rànkaya dan gogan yace ba uban da zaisa matar shi tayi dare a wajen wata uwa dinner dan ma maita ne yasa suka dage cewa sai anyi badan shi yaso ba, sai da yaga da yawa daga cikin su sun wuce tukun shima dasu sadeeq suka shiga cikin nasu motocin suka takema sauran baya,tarin messages din dake wayar ya fara bi bayan ya bude data domin bama sauran sakonnin social media damar sauka suma, da yawa daga cikin sakonnin na fatan alkhairi ne da taya murnar samun karuwar aure wasu daga ciki kuma na ban hakuri ne daga wadanda basu samu zuwa ba duba da yanda bikin yazo babu shiri, *******"******* A gefen hafees kuma bayan sun isa saida suka gabatar da sallah la'asar sannan suka shiga cikin gidan kamar yanda suka tsammata dam gidan yake da jama'a a hakan yaci gaba da kukku tsawa cikin mutanen duk inda yake tunani zaiga Aminatu ya dubafa bai gantaba,dan har maryam ya gani da sauran kawayen su amma wai suma basu san ina ta shigeba tun kafin daurin aure,dakyar ya samu ya gano Aunty Hassana maman Abiey can cikin filin rawa suna cashewa acewar su ko amaryar bata fitoba bazasu fasa abunda suka shirya ba. *Ummiee ce* [10/10, 11:24 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 47* Mom Abiey dan Allah ina Meenal take? Nasan bazaki rasa sanin inda take ba, wallahi ina zaman zamana ya AK ya tasoni wai in kawo mata waya zaiyi magana da ita kinsan kuma ban isa ince mishi ban ganta ba raina ya b'aci a banza kuma nima yau bazan so in b'ata mishi raiba", Dariya tayi "kai koh Hafees ai yau dai duk fadan mai jama'a dole ya daga kafa ko ka manta yau din babbar rana ce a gareshi?" "Nidai taimaka ki kaini wajen ta in sauke wannan nauyin in huta," "Muje" tace dashi a yayin da tayi gaba shi kuma ya take mata baya, Can sashen baba Auta suka wuce domin nan ne kad'ai inda yake da k'arancin cikowar mutane cikin falon suka shiga babu kowa a ciki domin tun bayan da su Baban suka dawo daga sallar juma'a suka shigo cikin gidan abinci kawai sukaci anan falon sai suka koma harabar gidan inda aka kafa rumfuna sukaci gaba da zama suna ganawa da nasu bak'in, Dan haka sai nan din ya kasance shiru cikin jerin dakunan dake jere na k'arshe Mom Abiey ta kwan kwasa kafin ta bude kofar ta shiga da sallama shi kuma Hafees yana tsaye ta bakin kofa bai shiga cikin d'akin ba, zaune ta iske ta a bakin gado dan tun bayan data fito daga wanka ta shafa mai take zaune a wajen tana tunanin yanda zatasa kaya ta shiga cikin gidan dan tasan da zarar ta shiga tofa ta shigesu a hannun abokan wasa dan tun jiya basu barta ta sarara ba dalilin sune ma yasa ta dawo nan d'in ta b'oyema ganin su, ace warsu wai sun bada gari dan sunga alamar karfin jinin su itda Mai Jama'a duk wanda ya tsaya masu a hanya tofa kiyama zai zarce kobabu shiri dan haka sukam sun bada gari dan sunga alamar gara subi yarima susha kid'a dan wanda ya iya zuwa d'aya ya watsar da mazaje har 4 a rana d'aya tofa duk wanda yace zai shiga gaban shi yasan aradu ya tara, kai gaskiya dai babu irin sharrin da basu mata ba wai ashe tsohon tuzurun dama duk wannan lokacin ita ya tsaya jira shi yasa yaki aure waya sani ma ko dama rabon a jikin shi yake dan haka nema auren ta da Sarki yazo a haka, Ita kuma data gaji da iya shegen da suke mata sai tace musu "ai mazama ana musu auren dole mai yasa shima basu duba ko a dangi sun hadashi da wata ba? ko tsoron shi sukeji ne?" kuma ta fada musu sudaiyi a hankali dan ita mutum ko shishshigi yafiye yima abinda take so bazai taba ci gaba ba balle kuma har yace zai so abinta take so sai dai kwabar shi tayi ta ruwa, shi yasa wasu ma da suka kai hajar su kasuwa ko kallo basu samu ba balle a fara tunanin ta ina ciniki zai fada,hakan da tace musu kuma da wata karamar mara kunya takeyi a wajen dan wata yar balaja'u ce cikin yan uwan Maman AK da sukazo daga maiduguri inba gulma ba kinzo ma uwar ango biki ai sai ki tsaya a inda take koh? Maye na wani kwaso jiki ki taho gidan su Amarya to ashe wai ita Ramlat din son AK takeyi shi kuma gogan kun dai san hali dan saboda itama gaba d'aya ya dauke kafa zuwa wajen kakan nin shi na gefen uwa, To da labarin auren yaje musu dai ance wai harda suma tayi shine fa tun zuwan su ta kwaso jiki wai ita wajen Amarya zata sauka a cikin zuciyar ta kuma to take ta zauna da Meenal din dan taga uban miye ta fita da har shi AK ya zab'i Meenal din ya barta, ita kuma Aisha wacce suka zo gidan Malam din tareda Ramlat din itace taba Meenal labarin son da Yarinyar kema AK ita kuma dai dama tun kallon farko datama Ramlat din ta gama raina mata da wayau shi yasa ma ta kasa sake mata fuska, tunda ta fada musu haka ta shige ta basu waje babu wanda ya k'ara ganin ta, Kayan da anty fati ta kawomata ta daga doguwar rigane na wani tsadadden material fari tass itafa har yanzun abubuwa basu dena bata mamaki ba wai daga ranar laraba zuwa juma'a mutanen gidan su ashe harda anko sukayi dan munafunci harda su Sultana ayin anko ko wani telan nema ya tsaya ya musu d'inkin ankon oho nata kayan ma da aka gabatar mata bata san daga ina suka fito ba,zura rigar kawai tayi batayi wani kwalliya ba dan haka koda Maman abiey ta shigo zaune ta taddata saman gado kamar wata mai danyen jego inda ta ajiye abincin data kawomata dazun ta nufa tana bubbudewa. "Ammi me yasa bakici kazar nan da yawa ba bayan nasan yanda kike son naman kaza shi yasa fa ni da kaina na b'ata lokaci na had'a miki ita yanda zata miki dad'in ci?" Ta juya ta tambaya fuskarta na nuna alamun bataji dadin yanda Meenal din tayi ba, " Naci ! kuma wallahi ko dadi babu nina gaji da ciyeciyen nan" ta karasa fada tana tura baki, "oho yarinya ko kici ko karkici ki sani kanki kika mawa bani ba dan haka ruwanki, insha allah wata rana sai kin kirani kina rokon in taimaka miki nayi miki wannan hadin a lokacin ni kuma zanci miki uwa ranar," "Ni din wai? allah ya kyauta wallahi me zanyi da ita?" "Lokaci na zuwa da zaki san amfanin ta kuma na rantse miki da Allah sai kinci ta, ga kuma hafees nan tsaye a bakin kofa nasan kinyi halin tsiyar naki shi yasa ya'yan ya turoshi ya kawo miki waya kedai Allah ya shirye ki wallahi Allah ya miki gata kina ma mutane iskanci" "toni Mai zaice min?" Ta tambaya tana tura baki, "shigo hafees" Maman abiey tace tana mai zama a gefen Meenal din kiran maryam tayi akan suzo su same ta a sashin baba sannan ta yanke Wayar, tunda Hafees ya shigo ita kuma saita daure fuska, dariya yayi "amarya kiyi kawai ai lokacin kine nidai bazaki wani layance min ai nasan komai anaso ana kaiwa kasuwa yarinya in gaskiyane mai yasa bakice bakya yiba ko kuma da akace an daura sai ki tada aljannu amma sai mukaji lukus an fad'a miki dan kin hana kanki sukuni za'a fasa wani abune? Kice bakya so wallahi kiga yanda ake buga wawuso wasuma bazasu samu ba sai dai suyi hakuri" da farko kin kulashi tayi kamar batasan dawa yikeyi ba. saida ya isheta da surutu sannan tace mishi "ai kasancewar ko yanzun taimaka muku nayi domin idan lokacin baya ya iya hakurin rashina ka sani a yanzun tabbas idan ya rasani kuma zaku rasa shine a wannan lokacin, wannan dalilin ne yasa naji zan iyayin jihadi in zauna da shi in ba haka ba ai kai kanka kasan nafi karfin yaro, inba kaddara ba mema zanyi da tuzuru ni aminatu," "Karya kikeyi wallahi! kema kinsan mai jama'a yafi karfin kice mishi yaro ko kice mai zakiyi dashi,dan yafi karfin nan dan batun yau ba kema kinsan yanda mata ke gwagwar maya suna gwabzawa a kanshi kuma har gobe bata canza zanin ba, bakiga Ramlart bace yarinya mai zubin hurul ain har suma tayi da taji ya aure ki kinsan ko yanzun yace yana sonta da gudu zata yarda ta aure shi" "toni ina ruwa na tama kashe kanta saboda son da take mishi in taso ai duk wanda rai yayi ma dadi ba wallahi bai kaiya maishi ba, aikin burrr inji tusa ai duk haukan da suke a banza tunda ya tsallake su ya dawomin duk da na nuna bana bukata,kuma sun fadi kasa ba nauyi domin ni dinnan na musu fintin kau domin koba komai ai ni ina ciki su kuma suna waje kuma kamar yanda ada ya musu nisa haka nisar zatayi ta karuwa kamar tazarar sama da kasa mijina baya kamuwa garesu kai ka taba ganin an kama inuwa?" ka sani cewa mai jama'a ya musu nisa sai gani sai hange ai sun Riga sun bar shiri tun rani, sun kumayi wasa da damar su dan haka daukar dangana dole", ta karasa fada tana murguda baki cike da tsiwa, " oh yanzun kika san da hakan? wato tunda anyi mai wuyar an d'aura koh, Naga kema ai baki duba hakan ba tunda ai ba ko tausayi haka kika dunga Jan mana shi a kasa ko ce miki akayi bamu da labari saboda cin zalin an d'aura auren ma tuni amma bazaki bar mana shi ya huta ba amma ai karashen tuka tuki tik, yanzun kam komu ma zamu samu mu sarara tunda ya kauce a layi muma sai mu yunkuro allah yayi aure da mara kwabo," "Munafuki kace aure kake so shi yasa kake ta kame²" Bai kulata ba dialing din number din Ya Abdul din yayi sai ya mika mata Wayar , karba tayi ganin kallon da anty fati ta ke mata ne yasa ta kai wayar kunne "Assalamu Alaikum" ya fada daga can gefen shi cikin sassanyar lafazi da kwantaciyar muryar shi da saida ya tsirga mata har cikin cikinta. batayi tsammanin cewa tayi kewar muryar dama mai muryar kanshi ba sai yanzun dan a kalla yanzun kwana 2 kenan data toshe duk wata kafa da zai ganta ko yaji muryata gaskiya dai AK ya gama da ita wallahi, fita su Hafees sukayi daga dakin suna hira shida Mom Abiey tasan kuma sunyi hakan ne saboda ta samu sakewar yin magana da Abdul din amsa sallamar tayi kamar yanda yayi itama din cike da kasalar data gaza boyuwa a cikin murya ta, "Ammina" Ya kira sunan ta "uhmmm" ta amsa " ina yini," ta gaidashi sai ya amsa da cewa " lafiya lau ya akaji da jama'a?" shiru tayi bata amsa mishi ba, "Wife me yasa kike min haka ne? Yanzun fisabilillah abunda kikeyi kina kyautawa kenan? , Allah ne kadai yasan irin matsanan cin farin cikin dana shiga daga ranar laraba zuwa yau bayan tabbatuwar dauruwar igiyar aure a tsakanina da ke, naso matuka ace na raba wannan farin cikin tare dake amma a dai dai lokacin ke kuma nike ta kiran wayar ki amma ko tausayi na bakiji ba kikaki daukar min waya bayan haka na tura miki text message shima ba amsa, Wai dan allah me yasa kika daina sona ne yanzun? fushi dani kiyeyi akan maganar ranar nan? to miye laifina dan na jajirce wajen ganin na mallake ki dan ki zamo uwar yayana? Ke din nan sheda ce akan ban taba soba sai akanki a kanki na san so idan dadi naji ko akasin hakan kinfi kowa sani, amma abun mamaki wai saida aski yazo gaban goshi sannan kike kokarin juyamin baya me yasa? Shin ban cancanci in mallake ki bane kome? wallahi ina sonki³" Saida ya maimaita cewa yana sonta sau uku kafin ya d'aura da cewa "karki manta cewa karfin son da nike miki shi ya rikeni tsayin shekaru ba tareda na iya kallon wata diya a matsayin mace ba balle har inyi sha'awar kai kaina gareta, akan hakan har wasu sun faramin kallon ko bani da lafiyar alkalami ne babu irin mummunar fassarar da ba'a munba duba da yanda su Musty ke mu'amala da yan mata amma ni duk yanda matan ke bina sam basa gabana, Amma ko sau daya ban tabajin bacin raiba, to taya kike ganin yanzun zanyi wasa da damata in bari ki kara kubuce min a karo na uku kamar wanda akama baki inaa haba yarinya kema kinsan rashin ki a gareni yanzun sai dai a kirashi da ganganci". gaskiya itama tasan tadan so ta tsaurara to amma ai mu mata dama dajan aji aka sanmu, amma kalaman shi sunyi tasiri kwarai a zuciyarta har sunsa taji ban kyauta ba a yanda ta wofantar dashi na kwana biyu,. "Yanzun fisabilillah da bance a kawo miki wayaba shi kenan koh? Niko Ammi?nidai kikeyi ma wasa da zuciya koh?" " Kayi hakuri" tace, shi kuma sai yace "da kyau nidai koh," "kayi hakuri" ta kara cewa, "bazan karaba" Shi kuma sai yace "ya wuce kinci abinci? "Ya tambaya gyada kai tayi kamar yana kallonta, "ba kai nace ki dagamin ba ki bani amsa da baki" "eh naci maman Abiey ta kawo min naci" " kina inane haka?" " Sashen baba," "to muma gamu a hanya zamu zo gidan yanzun," to tace, " ki shirya kafin mu iso" to ta kara amsawa dashi, "Ke yarinya ya nike jinki kasa² ne ko har kin firgitane? Haba yarinya tun kafin su kawo ki su baroki ai gara ki a dana tsoron zuwa dare kinji", tura baki tayi kafin tace "tsoron me kuma ni zanji? kuma ni mutum ya dena cemin yarinya tam, kuma albishirin ka ai aure dai aka daura tarewa sai nasa lokaci ba nace maka ni ban shirya yin wani aure yanzun ba", "keeee" ya fada cikin daga murya "wasa kikeyi yarinya ni zaki maida dan iska a daura auren kice wai zakici gaba da zama a gida!, wasa kenan to wallahi karkija ma kanki yanzun muna isowa ince a wuce dake wato ga Abdul din banza duk uban jama'ar dana tara kawai sai su watse basu kaimin mata gida ba,kai aiko da anji kunya wallahi ke kimayi istigfari dan wannan k'aton sab'one wai kice tarewa ba yanzun ba ashe ma ba auren aka daura ba", kunkuni ta fara "Dawa kike?"ya tambaya a dake, " Bada kowa ba". "da kyau" shi kuka ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya, yanke Wayar tayi kai wallahi Abdul Khareem dan bala'ine. Shiko mugun a gefen shi dariya yayi kafin a bayyane yace "Kai wallahi yarinyar nan tafa rainani Dan ma ta daukeni sakarai nine zata latsa kujimin wani bankada wai ba zata tareba, amma ba damuwa very soon duk zan tsitstsige miki gashin rashin kunyar da naga sun tsiro miki zaki shigo hannuna," Tana yanke Wayar su Maryam suna shigo d'akin su hudu ne Maryam, Maimoon Meelat sai Aisha,maryam ce ta zauna a gefenta "Amma wallahi amaryar AK kinci uwar rainin wayau ashe dama kina cikin gidan nan muke ta faman neman ki duk wanda ya tambaya sai dai muyi karyar kin dan fita dan iskanci kuma kika kama waya kika kashe" Inji Maryam Moon kuma tace "Dallah shareta gudowa tayi saboda taji dadin yin celebrating din samun cikar burin ta da kyau ba tareda an takura ta ba ku baku ganewa ne wai? nidai bama wannan ba kinsan dai muna binki bashin kazar amarcii....idan mun yafe na baya wannan kam k'arya da ciwo muce mun yafe" ta fadi kalmar amarciii a iskance, fashewa duka sukayi da dariya harda ita Meenal din da ta daure fuska da farko, "koba kazaba ki bari har inci naki tukun kafin in biya" tace cikin dariya. "Yasin saiko kin biyashi" cewar Meelat batare data dena dariya ba tace "ban taba sanin ana biyar bashin kazar amarciii ba sai yau,ai shi kenan sai in bada kudi a siyo kazar muci" ta fada tana musu kallon kasan ido, "aiko wallahi baki isa ba,"suka hada baki wajen fada, Aisha ce ta d'aura da cewa "wanda dai ango zai kawo miki muma shi din zamuci ai wallahi ba wacece aka kwara irina nawa kazar da ko dandana ta banyi ba kukazo kuka dauketa," "kika bamu dai" Meenal ta fada tana dariya ta kuma ci gaba da cewa "aikin banza kuma rashin cin kazar baisa ta canza zani ba dan haka muka isko amarya an mata cin koshi " ta fada suna kara fashewa da dariya, kai jama'a wallahi tunda aka fara hidimar bikin nan batayi dariya irinta yau ba, shi yasa take mutuwar kaunar an matan nan nata dan indai muka hadu sai sunyi nishadi, "gara ma kusa ranku a inuwa dan yanda bakuci waccan kazar ba wannan ma bata ciyuwa muku dan nidai ban sa ranar tarewa ba," kallon juna sukayi suna fashewa da dariya "lafiya"Meenal ta tambaya tana binsu da kallon dariyar me kukeyi? Maryam ce tace "haba kawata ke dan rashin imani har tunanin rashin tarewa ma kukeyi? To aiko indai tarewa ne anyi angama allah ya kaimu dare ki gani," marairaicewa tayi ta koma tsakiyar su ta zauna jingina kainta tayi a kafadar Maryam sannan ta dago fuskarta ta fuskance su saida ga kare musu kallo su duka 4 sannan ta kara shagwabe fuskarta Tace " yanzun dan allah duk dasa hannun ku kuna goyon bayan wannan auren dolen da aka k'ara yimin?......" Kallon juna sukayi kafi sukaja tsaki kamar hadin baki tureta maryam tayi daga jikinta ita kuma Meenal saita kara rungume ta, "Meenal auren dole ko auren gata? Ke yanzun nan har kina da bakin cewa an miki auren dole bayan duk duniya ta shaida bakida masoyin daya kama kafar Abdul acikin zuciyar ki,duk yanda kika kai ga boye matsayin da yake dashi a cikin zuciyar ki duk wanda ya zauna dake sai ya gane haka, ke yanzun a tunanin ki akwai wani d'a namijin dazai miki kalar soyayyar da mai jama'a yake miki ne?bance baza'a samu ba amma dai da kamar wuya gaskiya kar kuma kiga dan kina da tarin samari, ah ah tarin samari bashi bane wanda zai soki tsakani da allah ya kamata ki hanga" Aisha ce ta dafa kafadarta "Amina mu masoyan kine na gaskiya dan haka dole musu duk wani abunda zai kawo cigaba a rayuwar ki kuma dole mu fada miki gaskiya,koda ace ya Abdul ba dan uwana bane dole ne in jinjina mishi irin jajircewar da yayi akanki, Wallahi³ inda kin rasa mai jama'a to ko wanda ya kama kafar shi ba zaki samu ba bari in tuna miki wani abunda nike ganin kamar kin manta Amina kefa bazawara ce auren ki kuma ba zama na wata 6 kikayi a gidan mijin ba shekarun 6 ake lissafi sannan ke yanzun baza'a kiraki yarinya ba domin ko akallah koba komai kinba kin dad'e daba 20 baya, amma duk wadannan basu hana mai jama'a zage damtse wajen ganin ya zame miki mijin aure a karo na biyu ba duk da shi din saurayi ne matashi ga kuma arziki ke kanki sheda ce akan yanda mata ke binshi tun tale² balle kuma yanzun dako ba'a fad'iba kema kin san cewa arzikin bana ya zarce na bara, amma a hakan duk ba wacce ya kallah a cikin su ke din dai da zuciyar shi keso ke dince dai ba canji, sannan karamin misali ki duba yanda ya gabatar da Neman aurenki,duk da zumuncin dake tsakanin ku wanda yasan da ace ana bada kyautar mace to ko kyauta ya cancanci a dauke ki a bashi,amma duba ki gani duk wani abu da ake gabatar wa wajen Neman aurenki bai ban²ta dana budurwa ba.." "wallahi yan matan da yawa ma basu samu hakan ba" cewar Sultana dake shigowa cikin d'akin yanzun, "kawata kiji tsoron allah ki rike mijin ki da kyau,dan wallahi in kikayi wasa kece da kuka danko yanzun kinsan akwai yan hassada a gefe" " Ai yan hassada nasu wasa ne ina kika baro kurayen dake ta faman dana mishi tarko basa ko gajiyawa?" Meelat ta amsa ma Sultana Tura baki Meelat tayi "to me yasa tun wancan lokacin basu aura mishi niba sai yanzun?" "Saboda yanzun ne lokacin da Allah ya tsara muku yayi shi yasa Allah ya tabbatar ba tareda kinyi tsammani ba kuma lokacin kanki na hayaki nasan tsoro kikaba shi shiyasa bai iya bari an gane yana sonki ba" cewar Maimoon Maryam ce ta riko hannu ta "kawata kinsan a duniya dukan mu muna taya juna son abunda wanin mu keso,kinsan babu ta inda zamu zuba ido muna gani ki kara subucewa ya Abdul a wanna karan aurenki na farko dana ki dauka kaddarar kuce tazo a hakan amma a yanzun idan kika guji Abdul Khareem hakika kin zalince shi dama ke kanki nasan yanda aka gabatar da komai a gaggauce ne yasa kike neman hanama zuciyar ki abunda take muradi amma ai shima baya da masaniya akan komai kuma meye burin masoyi wanda ya wuce ya mallaki abinda yake so, amma ki sani mai jama'a fa ba kwallon mangwaro bane balle kice gara kiyar ki huta da kuda wallahi Abdul Khareem bai taba fita a zuciyar ki koda ace Sheikh aka aura miki mu mun shaida hakan, to akan me zaki nemi ki zalinci zuciyar ki? kimana alfarma ki ajiye komai a gefe tunda dai har shi da yake matsayin saurayi yace yaji ya gani aimu abun tunkaho ne a wajen mu ki dena ganin cewa wai ai har yanzun baki da banbanci da budurwa tunda baki san Namiji ba ki sani sunan mace yana canzawa ne daga ranar da aka tabbatar da igiyoyi uku akanta na auren wani koba haka ba?" Takai karshen zancen tana tambayar su Meelat "kwarai kuwa "suka amsa ta,. " Allah kawata ni mamaki ma kike bani wacce macene zata samu hadadden saurayin da mata kala² suke binshi gida da office tace wai bata so?"cewar Meelat " To ai kinji matsala ta farko wadannan tsinannun matan da suke binshi a kullum Kamar kuda ta ina zan fara fisabilillah" ta fada tna kallon su, "ke dallah matsa inda ace suna gaban shi kema kin san da baiyi zaman tuzurancin da yayi zuwa yanzun ba, Gaskiya kin bani mamaki to wai shi dan uban tsuntsun soyayyar ina ya tashi yaje harda kike neman juyama Abdul baya ki nuna bakya yayin shi bayan munsan duk karya ne to dan haka in ma laifin wani zaki gani ki fara ganin nawa nida nakai ma Hajiya labari dan naga kina Neman ki mai damu mutanen banza, kuma alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu ke nan kin saki jiki cewa haka zaisa miki ido bazai nemi aurenki ba har sai kin gama boko, toke wai gidan ubanwa ma zaki kai bokon da idan yau kika fad'i kika mace shi kenan ya tashi a banza? Mtwss" taja tsaki "gaskiya saura kadan ince ban yafe ba dan kin gwara mana kai" ta fada tana kai mata duk zabura tayi ta goce, "to ni da kaina na bud'ema Bash gaskiyar cewa AK kike so bashi ba duk da nasan shima yana sonki amma banga amfanin boye mishi komai dake tsakanin ki da Mai Jama'a ba kuma ni na rokeshi akan yayi hakuri ya janye dan idan yayi kuskuren auren ki to tabbas gangan jikin ki ya aura amma zuciyar ki tana tareda mai jama'a,kuma alhamdulillahi kwalliya ta biya kudin sabulu dan shima baija zaren da tsayi ba ya saki, hakan nema yasa kikaga harmu mun fita sabgar ki dan munsan cewa gata aka miki, haba yarinya tayama zamu yarda ki mana bakin ciki ai insha allah yau sai kwanan dakin mai jama'a" ta karashe fada tana ran gwada guda ayyiririiiii haka dukan su suka dauka, " wallahi sai mun kaiki" Ita dai zuwa yanzun bata da ta cewa fa bada gari. atoh dama itama kin auren da takeyi bawai har zuci bane, irin dai a tauna tsakuwa dan aya taji tsoro ne,. Sultana ce ta fara waka,. "Ranar muke jira yau gashi tazo muma da tamburan mu gashi munzo ango mukeyima shida amarya.......haka suka dunga wakoki suna rawa, gaskiya taji dadin kasancewar su tareda ita a wannan lokacin har saida taji haushin kanta yanda tazo ta wani zauna a dakin ita kadai da farko, Saida maimoon ta fente mata fuska ta tsatsomata duk wani boyayyen kyauwunta sannan Sultana tamata d'aurin d'ankwali yar yayi basu hutaba saida suka tabbata ta fito a amaryar sak, Masha Allah kunsan Yan magana sunce amarya kota buzuzuce.............. To itma dai yau ko hasidin iza hasada dole ya bata hanya idan ta doso! Saida sukayi hotuna dasu videos na tarihi injisu sannan Aunty fati ta iso tana cewa su fito angwaye sun iso tun d'azun, Basu fita daga dakin ba saida suka kara fesheta da kalolin turare masu dadin shaka sannan suka mata jagora bayan sun lulluba mata gyale a saman kai, tun kafin su fita daga sashen kamshin turaren su ya gayama sauran jama'ar dake kusa dasu cewa gamai gayya mai aiki nan wato amarya da kanta, Bakajin kalmar komai daga bakin mutane a dai dai wannan lokacin sai dai masha Allah!!!! Gogan nata tafara hangowa domin kunsan zuciya da zarar ta iso waje Wanda ke cikinta take fara ganewa, balle kuma gogan nata dama ya lafiyar giwa ko banza dama shidin gayun ne da kanshi balle kuma yau ranar tashi ce, Yafa hadu yasha wanka ya gaji wallahi ita dai allah ya sani bata gajiya da kallon mai jama'a batun yauba, "Tubarkhallah" Ta furta kasa², tana cigaba da kallon shi ta cikin gyalen ta kuma ta tabbata shima din ita yake kallo dan taji nauyin idanuwan shi a jikinta. Lallai alkawarin Allah baya tashi, ta sani taso Abdul son da bata tab'a kwatanta shi akan kowa ba, amma allah ya sani bata tab'a kawo auren su a kusa irin haka ba, Amma gashi ta zama matar AK alhmadulillahi...... Koda Abdul ya gama waya da Meenal suna kofar gidan, bayan sun gama gaishe²n iyayen da sukazo yi wasu daga cikin abokan shi mota suka shiga suka wuce wajen da za'a gudanar da dinner domin karasa shiri dinner din zai gudana ne bayan magrib, daga wajen dinner ne kuma za'a sada amarya da dakin ta. Sunyi sunyi da Abdul akan su shirya wani program din bayan dinner Amma sam yaki, yace shi bazai tara bidi'a da yawa ba in suna so su burgeshi To suyi ta sama auren albarkha kawai shine Abunda yake so. To suma dai a gefen su basuja zaren da tsayiba Dan haka suka hada gaggarumar dinner acewar su baza'ayi bikin "Mai Jama'ai " lami ba mahadi ba, Gaskiyar yan magana dake cewa masu layya nacin nama, wallahi abokan shi gaba daya Kamar basu san zafin neman kudiba, Tunda suka shiga gidan nan suke rabon kudade sun raba a cikin gidan wajen iyaye mata sannan bayan sun fito kai tsaye filin wasan da matasan gidan suka hada nasu casun Suka karasa nan ma dai haka suka dunga masu yayyafin nerori. kowa yayi mamakin yanda mai jama'a da kanshi ya shige cikin su duk da ba wani rawa yayi ba, Amma ya musu liki abokan shi dai kam su sukace in bakuyi bamu waje Dan sun warwasa abunsu, acewar su bikin daya rana in basu mishi karaba Ai sunci amanar zama. Gaskiya dai sun burge dan sun bada Kala wallahi , Ana ta casu Amma shi dai Ango burin shi yaga ta ina gimbiyar shi zata fito, Yasan dai duk inda take dole ta fito su gaisa da abokan shi, sauyin bugun da yaji zuciyar shi tayi shiya tabbatar mishi da cewa duk inda take tabbas tana kusa dashi. ***Dan haka tun kafin su karaso tsakiyar wajen ya kafe hanyar da mayatattun idanuwanshi, yana mai jiran yin tozali da muradin zuciyar shi. Kam ya rike ta da kwayar idon shi ko son kiftawa bayayi, a wannan lokacin shi kadai yasan yanayin daya riski kanshi a ciki, wallahi badan su baba suna cikin harabar wajen ba, Babu ubanda ya isa ya hanashi zuwa ya rungume matar shi a wannan lokacin da yakeji Kamar ya dauketa kawai su bace bat abinsu. Shi wallahi da za'a kyauta mishi kawai a bashi matar shi yayi gaba da abunshi, Dan allah in bama daukar alhakiba Ai kamata yayi daga daura aure kawai a mika amarya dakin ta. Hummm ya sauke ajiyar zuciya a bayyane, dai² lokacin da suke karasowa cikin filin, "Lallaima yarinyar nan, wato bama zata matso inda nike ba".ya fad'a kasa² A wayen ce ya lelleka gefe da gefe saida ya tabbatar babu wani idon kunya daga cikin mutanen dake wajen zagaye dasu, sannan ya juya ya hango inda su baba suke Allah da ikonsa zuwa wannan lokacin babu su baban a wajen sai dai wasu daga cikin abokan su. "Alhmadulillahi "ya fada yana mai karasawa wajen da Ameena take tsaye suna gaisawa da abokan shi sun sata tsakiya sun dage wai sai tayi rawa tunda Mai Jama'a shi Yakiya, duk wannan wainar da ake toyawa har lokacin fuskanta rufe yake cikin gyale Kamar yanda ta fito, jawo hannun ta yayi daga cikin su zuwa ainihin tsakiyar filin. Wallahi tunda taga ya dososu gudun zuciyarta ya karu, "ya allah kar kasa gayen nan ya bani kunya a wajen nan" kawai take fada a zuciyarta. Taushin hannun shi dagaji a cikin nata hannun shi yasa sakar zucinta yankewa taso t doje a sanda ya jata amma ba hali karfin ba daya ba, baiyi magana ba da idon shi yaci gaba da kallonta kuma bawai murmushi yake ba, Ita dai bata gane yanayin da yake cikiba, Dan dago kaita tayi dan ta saci kallon shi kawai idota ya fada cikin nashi. "Na miki kyaune? "Ya tambaya yana kashe mata ido, Murmushi tayi ba tareda ta amsa ba, "kinyi kyau" yace kasa². Bata san ko dama can sun shirya hakan bane da abokan shi domin kamar hadin baki haka suka zagayesu suna musu likin fafare bugun fct Abuja kudaden nan kamshin su daban ne kun daisan yanda sabon kudin kamshi shi yake da dad'in shak'a balle kuma ya fito daga tsaftace cen aljihu, wato sabon Abu baka gajiya da kallon shi yasin sabon kudi akwai daukar hankali, Allah dai ya tsine tsiya ya mana katangar karfe tsakanin mu. Wani abokin su mai suna Wazir ne yace wai sunyi likin ganin fuskan Amarya. Dan haka Ango ya taimaka inba rowar ta yake ba ya bude musu fuskarta, To shima dai dama a kagare yake Dan haka bai tsaya yanga ba ya fara kokarin dage lullubin fuskan. Dukan su haka suka fidda wayoyin su masu daukar hoto nayi masu video suma haka, Ita dai wallahi gaba daya kunyar da bata san yaushe ta fara jinta ba ita ta kamata gashi ba wajen buya dan su Maryam ma gefe suka koma suna kallon ikon mai sama. Da sauri ta runtse idonta a sanda ya maida gyalen zuwa kan kafadunta, shiko kyar haka yake binta da wani mayataccen kallon shi mai kara sata tanaji gabban jikinta suna macewa, "Bude idon!" Ya fada a hankali yana sauko da tashi fuskar dai dai tata bayan yadan rankwafa ya dai²ta tsayinta da nashi, Kara nokewa tayi tana neman hanyan guduwa kafin ta ankara saijinta tayi gaba dayanta ta shige cikin jikin shi tayi kane², shiko Dama Abunda yake muradi Kenan dan haka baiyi kasa a gwuiwa ba wajen riketa gam a cikin jikin shi baifa tsaya a iya rungumar ba itadai taji abokan shi suna fadin "YOU MAY KISS THE BRIDE, halal kiss and hug" kujimin wani salon rashin dajara wani irin kissing kuma Ana zaune kalau Kamar wasu masu auren coci gidan Malam nefa .... Zaro ido tayi "Dan allah kar kayi! Karkayi kissing dina a cikin mutanen nan please 🙏 kagafa wallahi duk kallon mu akeyi kuma su Baba suna nan, Kai Dan allah wani irin kissing kuma a gaban jama'a muke fa" Take fada tana kokarin kwace jikinta kara kankameta mugun yayi yana dariya, "Kunyar su kikejine bayan sun riga sun aura min ke?" "Eh mana kannen mune fa a wajen kuma kaima ai dai baka yarda kayi faduwar bak'ar tasa a gidan sirikai ba" Wallahi AK mugune, kugafa tun dazun ko murmushin shi bai bari ta gani ba, Amma yanzun daya shirya bata kunya a cikin mutane shine da dariya harda kyakyatawa. Kasa yayo da bakin shi duk wasu alamu sun nuna sumbatata zaiyi amma ga mamaki na sai naji saukar bakin shi a goshina, Kai wallahi ta tsorata allah kadai yasan dalilin da yasa ya fasa abunda yayi niyya, Waiyo Allah kuzo kuga ruwan flashers na masu daukar hoto, kafin ta ankara shi uban gayyar da kanshi wannan karan ya fara mata liki, Aifa Kamar jira saiga matan cikin gida suna bulbulowa suma dai gaskiya sunyi kara kwarai, sunyi rawa a cewar su wanda bai takaba da bakin ciki zai mace, gaskiya dangi da dadi suke wallahi duk wanda ya rasa ahali tabbas yaci a tayashi kuka dan ban san waye ya kira yayyenta maza su Ya Farouq ba haka suka zo suka shiga cikin mu akayi ta hotuna dasu kuma suma sunyi liki, kallon mutanen da suka cika wajen ta dungayi a cikin zuciyata kuma tana kiyasta yanzun duk yawan su badan kowa suka hallara ba sai sabida su, Dan da yawa daga cikin su batagan su a lokacin aurenta na farko ba Amma wannan karan duk da yanda auren yazo dangi na nesa dana kusa kowa ya hallara, lallai Yan magana sunyi gaskiya da sukace (dakan d'aka, shik'an d'aka, tankaden bakin gado) wallahi hakan nan sai taji wani farin ciki ya kamata yanda Yan uwa takowani gefen suka sasu a tsakiya duk dakewar mai jama'a saida suka sashi rawa gaskiya dai wajen nan duk wanda ka gani fuskar shi cike take da farin ciki idan ma akwai masu bakin ciki to sunyi kokari kwarai wajen adana hakan a cikin zukatan su, gaskiya anyi nishadi kwarai a wajen Dan musamman ma yayen mu maza masu forming cewa su ustazai ne su kansu yau saida suka Dan tattaka kuma naji dadi Dan nasan Dan ni sukayi iyayen mu mata ma sun nuna nasu farin cikin Dan sun shigo filin suma anyi dasu Amma dai Mommy taki fitowa tace bada ita ba a shiga ruwa lafiya, a takaice dai anyi buduri sosai a wajen ana ta abubuwa banga Fauxieyerh ba Sultana ke cemin ai an wuce da ita Abuja tuni kuma shima Ya Sheikh ya bisu , sai anan na gane cewa wato yan gidan saboda babu Shehi shi yasa suka rak'ashe abinsu, Duk likin da akayi a wajen kuma su firdausi kannena sune kwamitin kwashe kudi ban san ya zasuyi da shiba,dan haka na jawo ta na rad'a mata a kunne cewa 50/50 zamuyi idan sun gama k'irga su kawo min kasona wallahi. *UMMIEE CE* [10/11, 9:19 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 48* Karku manta fa duk wannan budurin da ake uban gayyar fa yana gefen ta dan koda yace ya gaji da rawar da aka sashi na dole bai yarda yaje ya zauna shi d'aya ba saida ya jata zuwa kujerar da aka tanada dan Ango da amarya saboda tsabar kishin ganin ta tsamo² cikin yayyen ta da kannin ta maza da yaji yana neman tafiyar mishi da numfashi, Haba suma dai abu babu kara ba komai a gaban shi matsayin shi na mijinta zasu wani dunga kakkama mishi mata suna sata rawar dole kawai dan dai suna takamar cewa su yayyen ta, ya take kan yayyen yawuce😠 koda suka zauna kuma koda wasa yaki ya raba hannu ta da nashi a hakan kuma su Sa'eed din basu hak'ura ba haka suka dunga biyo su ana musu hotuna Baba Adamu da Baba Auta suma sunzo har wajen anyi hotunan dasu amma Malam baizo ba dan baya cikin gidan a lokacin. "Wana Kama?"Yake tambayar ta bayan sun zauna, "waka kama kuwa?" Ta bashi amsa, "Ok ba laifi, yarinya kina duba lokaci kuwa?"Ya fad'a yana kara yin kasa da muryar shi, " saura dan k'ank'anin lokaci kibar gidan nan keda shi kuma sai dai ziyara," matse hannu ta dake cikin nashi yayi, "da zafi fa!" Tace mishi, shi kuma sai ya amsa mata "Eh Ai nasan zakiji zafin shi yasa na matse," "Ai dama kai muguntar ka bata sauka akan kowa saini marainiyar wayon ka," " eh to ya zakiyi dani? Amma ga shawara, mai zai hana anjima in an kaimin ke gida ki rufe kofa dani a ciki kinga saiki hukunta ni ba wanda yaji koya gani, koya kikace? Shawara ce kyauta ki hukunta ni kawai ki huce haushi dan nasan kina da fushina dama" Gyara zama tayi ta fuskance shi, "Wai wa za'a kai maka yau? " Bata tsaya saurarar amsa daga gareshi ba ta daura da cewa, "kamanta abunda na fada maka dazun ne? Ni ban shirya tarewa yanzun ba, Kamar yanda ban shirya aure yanzun ba kukamin dole to sai ku Bari in shirya tarewa da kaina.........." Hannun shi guda dayan dake free yayi amfani dashi wajen tab'a mata gefen wuyarta, da ido ta bishi da kallo. "Baki da lafiya koh? Amma kuma jikin ki ba zafi," "Ni lafiya ta kalau,"ta amsa tuna tura baki, "Masha allah to albishirin ki! Wallahi yau kam insha Allah ko suma kike kina farfadowa bazaki kara kwana a gidan nan ba kinjima na rantse mai kankat Kenan kuma ke Kin san halina" ya fada yana d'age mata kafadun shi, Shi Kenan ta faru ta kare dan wallahi tasan tunda har ya rantse to magana ta zaunu. Basu tashi daga wajen ba sai gabanin magrib abokan shine sukama jama'a magana akan su shirya idan an idar da sallah ne za'a wuce wajen dinner, Su kuma mazan fita sukayi zuwa masallaci matan kuma suka shige ciki dan ita dama tun kafin su an kara aka shige da ita cikin gida bayan dawowar Malam. Takardar gidan da Hajiya ta bata ta d'auko ta wuce d'akin Baba Auta, da sallama ta shiga Mommy ce da Baba Autan zaune da alama wani abun suke tattaunawa, "Amarya Meenal taho nan kusa dani ki zauna" cewar Baba Auta yana yafito ta da hannu, "Me kike nema anan kuma keda ya dace ace kina can ana shirya ki ko baki san ana idar da sallah za'a wuce dake bane?" Inji Mommy Tura baki Meenal din taci cikin kunkuni take cewa, "Ai dama ni tuntuni nasan bakya wani sona kuma nima ai ba wajen ki nazo ba wajen Babana nazo" "Ina fa zan soki tunda Allah yasa bake kad'ai na haifa ba, keda hankalin dukan dangi yake kanki ne zan wani damu kaina saboda ke, Idan nasoki ke kad'ai su sauran yaran nawa wazai so mun su tunda a fili ake wareki a barmin su, ke mai uba komai aka rarumo sai a juye kanki dan haka kije can ki k'arata" "Ah ah Jidda me yasa zakice haka, Taho nan kinji uwar masu gida ki fad'amin abinda kike so" Karasowa tayi ta zauna a gefen shi, bata ce komai ba illah takardar data mik'a mishi, Amsa yayi saida ya gama duba takardar kafin ya mik'ama Jidda itama, "Takardar minene?" Ta tambaya, "Ki duba mana"maida kanshi yayi kan Meenal "Nayi miki murna kwarai uwata ubangiji Allah ya sanya alkhairi" Ameen Meenal ta amsa ita kuma Mommy cewa tayi, "Ina kika samu gida kuma Meenal mu bamu da labari?" "Gidan Babana Malam ne ba nawa ba na fara nuna muku ne kusa albarka kafin in kai mishi takardar kuma kudin kayan dakina da Hajiya ta siyar ne na had'a da nawa kudin ita kuma tayi min ciko aka siya gidan" "Masha Allah lallai ina alfahari da uwata allah ya miki albarka yasa ki gama lafiya kinji, maza jeki yanzun ki kai mishi nasan zaiyi farin ciki matuk'a Allah yayi miki albarka ya baku zuria d'ayyaba" "Allah yayi albarka"itama Jidda tace a yayinda take maida mata da takardar, Tana amsa ta fice daga cikin d'akin a harabar gidan suka had'e da ya Farouq da Ya Abdul, "Ina zaki kuma?" Suka tambaya, "Ya dan Allah muje ku rakani wajen Baba Malam" "Ke fad'an ne bazaki bari akai ki ya miki ba shine ke zaki kai kanki saboda kin k'osa kibar gidan?" Cewar Abdul yana dariya, "Allah ya kyauta"tace kafin ta wuce a fusace su kuma suka rufa mata baya, "Ke ki tsaya mu jera mana ko bakyason rakiyar ne kuma?" "Eh bana so" A natse ta shiga falon babu wasu mutane a ciki Innar yara ce kawai sai Maman kano da kuma shi Malam d'in, Sai da ta gaishe su kafin ta k'arasa ta zauna a k'asa dai dai k'afar Malam wanda yake ta washe baki yana binta da kallo cike da so, "Kinci abinci yau kuwa Mamana? Ameena zuba mata abinci taci" "Ai bana jin yunwa Baba" "Ba'ayi haka ba uwata gara dai kici ko babu yawa ne babu kyau zama da yunwa kuma kin fini sanin hakan a matsayin ki na likita" Koda su Ya Abdul suka shigo suma waje suka nema suka zauna bayan sun gaishe dasu, "Ya akayi ne?" Maman kano ta tambaya Farouq ne ya amsa mata da cewa rakiya mukayo ma Amarya, Takardar Meenal ta mika ma Malam, "Takardar micece kuma wannan uwata bayan kin san nidai banyi boko ba balle in gane me aka rubuta, Kai Baba zoka dubamin takardar nan" Tasowa Farouq yayi ya amshi takardar a ladafce ya duka anan kusa da Meenal saida ya gama duba takardar kafin ya dago yana kallon Meenal fuskar shi cike da fara'a yace, "Baba takardar gida ce, kuma sunan Meenal aka rubuta a jikin takardar" "Gida kuma uwata waya baki kyautar gida sukutum haka?" Malam ya tambaya yana tsare Meenal da ido, "Gidan kane ba nawa ba, Gidan kane na siya maka ina so ka koma can da zama nan gidan hayaniya yayi yawa dan Allah baba karkace min bazaka amsa ba ko kuma kace bazaka koma ba dan gidan bashi da nisa nan k'asan layi ne" Ta fad'a a marairaice, "Mamana wayace miki ni ina da burin barin gidan nan inje inyi rayuwa a wani wajen ne?" "Nasan baka da burin barin nan Baba amma nidai ina son ka koma can ka zauna Baba shi yasa na nemi gidan dake kusa da nan kaga ko a k'afa ne kullum zaka tako kazo nan" To dai bayan jani inja din da akayi tsakanin Malam da Meenal mutanen gidan suma sun sa baki dan haka Malam ya amshi gida kuma kowa sai albarka yake sama Meenal din, Yayin da wasu suke ganin cewa kamar ita tafi kowacce mace sa'a a cikin dangi kiran Sallan ne ya watse zaman falon na Malam, Bayan sun shige kowa haramar sallah yayi ana saukowa daga sallah kuwa aka fara kwasar mutane ana wucewa dasu wajen dinner wadanda sukace bazasuje dinner ba kuma gidan Hajiya aka dunga wucewa dasu ganin d'akin Meenal din, bayan masu wucewa sun wuce su Aunty fati da Aunty Sas da wasu daga cikin Yaran Malam mata su kadai suka rage a gidan domin harsu Maimoon suma sun wuce Maryam ce kawai a tareda ita sabon wanka suka sata tayi suka mata sabon shiri, nan suka sata a tsakiya sukaci gaba da mata nasiha akan hakurin zaman gidan aure duk da sun san cewa zaman gidan miji ba sabon abu bane a wajen ta amma ai akwai banbanci sosai tsakanin wannan auren da zaman da tayi da Sarki, ita abun ma wallahi dariya yake bata wai ita akema nasiha ko mantawa sukeyi cewa wannan shine aurenta na biyu oho itafa ji takeyi irin a dole tasan komai ko ba'a mata nasiha ba zata kula da komai yanda ya dace, Sai dai bata da yanda zatayi haka ta Bude kunnuwa taci gaba da sauraran su, koda suka kira Mommy akan tazo ta mata nata nasihar wannan karon ma k'iyawa tayi saima cewa da tayi meya rage wanda basu fadamata ba kuma ita yanzun aiba karamar yarinya bane, itadai ban biye mataba dan haka har inda take taje ta isketa ta rungumeta tana kuka dan wallahi jikinta yayi sanyi, zata k'ara barin gidan zuwa gidan miji a karo na biyu. "Allah ya muku albarkha, ya kuma baku zuri'a masu albarkha ki rik'e mijinki da auren ki da kyau Meenal kowa dai ya miki shedan hakuri dan haka kije kici gaba da hak'urin banda yawan k'orafi ko kuma kai k'arar shi wajen Hajiya dan kingan ki a kusa da ita duk da dai ba a gidan zaku dauwa maba ki kuma kula da yawan ibadan ki Allah ya baku zaman lafiya" Ameen sauran jama'a suka amsa dashi sannan suka banbareta daga jikinta, duk wani nasihar daya kamata iyaye maza suma sun mata shi tun d'azun a falon Malam. Sai da suka k'ara shiryata suka Kara fesheta da turatuka masu sanyi marasa hayaniya Sannan Aunty hassana ta nad'a mata lafaya ta yane mata jikinta, sannan suka rikota suka fito harabar gidan wajen yayi tsit kamar ba acikin shi aka tara mutanen d'azun ba, wasu sun wuce wajen shagali wasu kuma gidajen su suka koma, Mota 4ne kadai a wajen 3n dai Yay yenta maza ne ta tsakiyar da take nan fara tass sabanin sauran da suka kasance bakake aka bude mata, Bayar motar suka sata Meelat ce a gaba gefen mai zaman banza yayin da Musty ke zaune a kujerar driver, Tun sanda aka bud'e murfin motar kamshin turaren shi da baya buya shi ya tabbatar mata da wanzuwar shi a cikin motar dan haka tasha jinin jikinta, duk da darene hakan bai boye kyau da tsaruwar motar ba allah kadai yasan nawa aka dandake kafin a mallaketa, bata tab'a ganin AK da farar mota ba tun bayan waccan daya bata kyauta dan duk motocin shi masu duhuwar kala sunfi yawa sai yau duk da kowa yasan favorite color din shi sune black and white, Dama yasha fadar cewa a farar mota za'a dauko mashi mata gashi ko ya tabbatar shi dai wallahi haka nan allah yayi shi mota da sutura bayajin kyashin kashe kudade masu nauyi wajen mallakar su, tun sanin da tayi mashi a baya shi mutum ne mai son gayu Kamar mace, haka kuma yake da son kyale² domin kowa yasan komai nashi mai kyau da tsadane tun daga kan sutura takalmi hula agoge zobe komai nashi abun sone gwanin burgewa kamar yanda yake mai kyau shima, bata manta zamanin yarinta sanda take zuwa satan turare a dakin shiba, murmushi tayi kuma wai dan rashin wayau tun daga can take feffesawa a jikinta kafin ta iso waje asirin ta ke tonuwa dan kanshin ke rigata isa waje, satar turare ko tonon sililiii...... Sauran motacin suma suka shiga aka d'auki hanyan zuwa wajen shagali, tun basu fita a cikin layin suba yake fad'ama Musty "Dan allah ka rufamin asiri kayi tafiya a hankali dan batun yauba naji tsoffi na fadin amarya tsautsayi gareta balle kuma yanzun da take tareda angonta a gefen ta koba haka ba wife?" Ya fada yana matsowa gefen da take ita dai bata amsa shiba dan tasan magana yake nema, Shima kuma Musty din bai tanka mishi ba shima, hannuwan ta ya riko yana wasa da dogayen yatsunta da suka sha xanen lalle ga kuma kwalliyar zobbunan da suka kara k'awata su, Saitin bakin shi yakai hannun ya bashi sumba muah yaja tumbar mai sauti, kokarin janyota zuwa cikin jikin shi yake ita kuma tana cijewa da hannu take mishi nuni dasu Meelat dake gaban motar suna nasu hirar, " miye haka wai?" Ya fad'a kasa², " To Ai bamu kadai bane a cikin motar" ta fada tana kokarin turashi baya, "to ke ina ruwan ki dasu? bakiga suma nasu soyayyar sukeyi bane?" "Kai bakajin kunyan sune?" "Kunyan wa zanji a cikin su Ita koshi? Baki ga su nasu rashin kunyar harda result sun samuba ko bakiga yanda yake neman kwakwume ta bane shima? To shida ya iyama matar shi nine bazan rungume mata taba nima? Dan haka Banajin kunyar su " ya bata amsa kai tsaye "To ni inaji gaskiya" "kin san allah in baki kiyayeni ba zansa Musty ya juyamin motar nan zuwa Tudun wada" ya fada cikin dakakkiyar murya, shiru tayi tana mishi hararar kasar ido babu bakin magana, "kice tak kiga yanda akeyi yarinya! Marowaciya ma dake ko dan kissing din ma kin hanani, kina abu sam ba wayewa kamar ba budurwar ABU ba, da watane tun a cikin motar nan zata fara tattalina kafin mu isa duk sai ta yamutse min kayana ta yanda kowa zai shaida cewa lallai ango nike a yau, Amma ke mutum yana rungume kima kina tureshi kuma in ance dake yarinya kiji haushi" Itadai tunda ta samu ya dena tattab'a tan da yake tayi tsit da bakinta jawota yayi ya rungume yana maida ajiyar zuciya, *** A hankali Musty yaci gaba da jan motar kamar yanda AK ya umarta a hankali sukaci gaba da tafiya har zuwa wajen taron, gaskiya sunyi kokari matuka wajen kawata wajen duk da darene amma ko ina cike yake da haske,kallo d'aya zakama d'akin taron kasan cewa bana talaka bane koda suka iso su kadai ake jira dan haka ba wani b'ata lokaci Yayyen ta maza suka fito kwansu da kwarkwa duk da yanda AK yake wani nan nan da ita shi a dole ga mai mata haka suka sa su Musty suka mishi jagora zuwa cikin d'akin taron sai da suka tabbatar da cewa ya zauna kafin su kuma suka sa Meenal d'in a tsakiyar su wasu na gaba wasu kuma sun jeru a bayan ta haka suka mata jagora har cikin hall d'in suna tafe suna mata liqi wasu daga cikin su kuma suna feshe ta da turaruka masu k'amshi abin gwanin burgewa wallahi, Saida suka kaita har inda AK yake kafin Ya Sa'eed ya rik'o hannun AK ya had'a dana Meenal din, "Ga amanar kanwar mu nan mun baka" "Allah ya taya rik'o yan cikin hall din suka amsa dashi, shi kuma bayan ya rik'e hannun ta tasowa yayi daga kan kujerar yana rik'e da hannunta saida zagaya suka gaggaisa da mutanen da suka zo wajen domin su musamman iyayen su mata da maza sannan abokan ango da kawayen ta suka musu jagora zuwa kujerar da aka tanada domin su, lallai bikin Mai Jama'a ake dole kaga taron jama'a gaskiya tayi farin ciki sabida ganin mutanen da ke wajen da yawa daga cikin su wasu sunyi shekaru basuga juna ba wasu mate dinta ne na school wasu kuma childhood friends dinta ne da suka dade basuga juna ba sauran jama'ar kuma kunsan dan wa sukazo ita har mamaki take yanda akayi mutane sukaji labari har suka hallara haka, gaskiya dai tayi farin cikin ganin yanda mutane suka taru saboda su musamman yanda yayyen ta maza suka nuna ma kowa yanda suke ji da ita duk da lura da uban gayyar yanda yake wani jajjanye ta daga cikin su. Sai fatan allah ya maida kowa gidan shi lafiya ameen. Bayan Bude taro da addu'ane kuma aka ba iyaye dama wajen tofa albarkhacin bakin su, kuma alhmadulillahi sunyi jan kunne sosai kuma sun fadakar unyi bayani sosai akan aure, hakkin miji akan mata, da kuma hakkin itama matar akan mijinta wanda baba Adamu ne yayi wannan jan kunnen sannan kuma yakara jan hankali akan mahimmancin hakuri da abokin zama daga nan akaci gaba da shagali, kai gaskiya dai taron dinner din ya kayatar anci ansha kuma anyi rabon abubuwa kala²a wajen bayan an rufe taro da addu'a ne kuma aka fara watsewa dan karfe 10 dai dai aka tashi, masu wayau dai basu yarda sun bar wajen ba saida sukayi sallan ishsha'i, Da yawa daga cikin abokanshi da bata san suba ya gabatar mata dasu wasun su sun mata kyauta a wajen yayin da wasu sukace sai sunzo gida, Sun daiyi sallama da wadanda zasu koma garuruwan su wadanda sukazo daga nesa, Sai dai tana kasa tana dabo domin tun zuwan su wajen take an kare da tawagar wasu mata wanda ko shakka babu gasan suna cikin gayyar mai Jama'a kuma ko yanzun haka da mutane ke watsewa su suna ciki, tun dazun taso ta tanka amma dai ta danne to yasin bata barin wajen nan ta bar mijinta cikin kuraye duk da tasan halin kayanta Amma kula da kaya yafi ban cigiya, Ba tawagar kowa bane face tawagar Hafsat ita din kuma tsohuwar budurwar AK ce tun zamanin yarinta nasan baku manta da ita ba mijin data aure mutuwa yayi tun bayan data gama takaba kuma take ta faman bikon AK din sai dai kun san mai hali, kafin ta ankara kuma kawai sai labarin d'aurin aure taji har yanzun kuma bawai ta dena son AK din bane a wautar ta wai ko a mata ta biyu ne sai ta shiga gidan Mai Jama'a inba batar basira ba shidin dabai aureta tun tuntuni ba wai yanzun ne zai aureta, " Lallai dani suke wasan to wallahi sai naci musu uwa kana inbi da ruwan kanwa maganin kwarnafin ciki, kuma shima Zai fadamin dalilin da yasa yayomin gayyar karuwai," Tunda suka fito take cika tana batsewa, tayi² ta danne kishin dake yunkuro mata amma abun yana neman ya faskara......... Matsowa kusa da ita yayi, "meya sameki?"ya tambaya ganin yanda take ta wani kunbure kunbure, " Ai dole kace meya sameni tunda kayomin gayya harda na karuwai wajen tarona," "Ke waye ya miki gayyar karuwan?" Tura baki tayi bata amsa mishi ba "To bari kiji ni ban gayyace suba kuma ita Hafsan da kike magana a kanta in baki manta ba tun baki da wayau nike tare da ita kin san da ina ra'ayin ta daba wannan maganar akeyi yanzun ba," "To da baka ra'ayin ta basai ka fada mata ta fita a sabgar kaba, Shine kuma dan maita duk inda kake haka zata dunga binka Kamar karya to wallahi nikam a kiyayeni idan da nayi shiru yanzun ba abunda zai gagareni," haka nan ta dunga warwarewa tana yab'a maganganu gaba daya kishi yabi ya rufemata ido, kai jama'a gaskiya kishi jidaline shi dai daga karshe ido ya zubamata dan ba amfanin yin kace nace da ita a yanzun saida ta gaji dan kainta tayi shiru, ruwa yasa aka miko mashi shi kuma ya budemata ya kafamata ruwan a baki wai tasha, Kuma da tasha taji saukin tukukin da zuciyarta ke mata, "Nagode" Tace dashi bayan ya cire gorar a bakinta, Aunty hassana ce ta karaso inda suke ta cire hannunta a cikin nashi tana mishi tsiyar kodai su wucene shi zai wuce da amaryar shi da kanshi? AK fa ba kunyace ta wadace shiba Dan haka da sauri ya amsa mata "Eh aunty kuje kawai tunda dama ai da yawa sunje sunga daki kinga gobe sai suzo suma amaryar sallama kafin su wuce" " Kai 😳" ta fada tana zaro ido fincike hannunta dake cikin nashi tayi da gudu ta koma bayanta ta b'uya daga bayan Aunty Hassanan ta leko kanta tana fadin "wallahi ban yarda ba," Dariya jama'ar dake wajen sukayi shiko yasin ko a jikin shi sai ma kara matsowa da yayi yana neman kamota "Dan Allah kizo idan na sallami bak'i sai mu wuce tare" wata katuwar harara ta watsa mishi tana mak'e kafada alamar bata yarda ba, " Fine " shima ya fada yana dage kafadun shi wani shegen kallon kasar ido ya bita dashi alamar zaki shigo hannu yarinya, Ita kuma ta mishi gwalo tana murmushi, hannun shi manuniya ya nuna zuwa kirjin shi alamun "ni koh?" Had'e hannu tayi alamun ban hakuri 🙏. Motar da Musty ya d'auko su a ciki ita ta mai dasu sabanin d'azun da suka taho su hudu a cikin motar yanzun kam sun kara yawa, ita da Aunty hassana da Maimoon a baya sai Maryam da Sultana ne a gaban motar bata san ko miye sultanar take nunama Maryam din a waya ba kuma Faisal ne kejan motar, A haka suka jera tare da sauran motocin suna tafe suna hira har zuwa gidan Hajiya wanda yake matsayin gidan auren Meenal din a yanzun... Koda suka isa sun samu da yawa daga cikin motocin da suka kawo mutane sun wuce sai tsiraru wadanda suka tsaya tarbar amarya, Bayan sun faka a harabar gidan Hajiya ce da kanta ta fito ta tarbe su da sabuwar butan ta wanda ta ciko shi da ruwa ta fito dan haka saida ta umarce Meenal din da tayi alwallah da ruwan cikin butan, bayan ta idar Hajiyar ce ta k'ara rike hannunta sai da ta zaga da ita kaf sashen gidan iyayen ta su Baba Usman suka sa ma auren albarka kafin suka nufi sashen Meenal din, Sai da Hajiyar tayi mata umarni da ta shiga da kafar dama bayan sun gabatar da addu'o'in a kofar shiga sashen, haka suka rakata da addu'ar zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma zuria masu albarkha, sun kumayi addu'ar yanda suka kawota cikin aminci ubangiji yasa mutuwa ce kadai zata fiddata daga gidan aure ta, Basu zauna a falon ba kai tsaye sama suka haura da ita zuwa dakinta suka mata masauki akan gadonta, Itadai fuskarta tana lullube dan haka bata samu damar karema gidan kallo ba, a bakunan mutane takejin yanda suke zuzuta kyawu da tsaruwar da gidan yayi, kun san dai yanda akeyi in ankai amarya dan haka itama mutane sukaci gaba da shigowa kallon ta duk da kasancewar fuskarta na rufe wasu sukan mata sallama akan sai sun dawo suna, wasu kuma sukance sai sun shigo gobe, a haka dai yawancin mutanen suka watse, Dan baba Malam yace bamai kwana ita dai taso ace sun kwana amma ba yanda zatayi tunda babane ya yanke hukunci itada tace bazata tare yanzun ba karshen magana dai to gashi har sun kawota sun barta na bakin AK, Hafees ne ya shigo dakin da sallama karasowa kusa da ita yayi "matar Ina wayata?" Da hannu ta mishi nuni da Sultana ba tareda tayi magana ba, shima baija maganar da tsayi ba ya juya inda Sultana din take mikewa tayi tace "muje waje wayar tana cikin jakata a mota," Oh ni y'asu wai ita zasu maida karamar yarinya da zata fita shine tama Maryam signal itama ta rufa mata baya kujifa Dan sun raina ta wai a tunanin su wayau sukama Meenal irin bari su gudu sai dai inji shiru din nan ni wallahi dariya ma suka bani, bayan sun fice ne Maimoon ta rufe kofar gyalenta ta cire sannan ta matso kusa da Meenal din, "kawata" ta fada tana mai mikar da ita tsaye daga zaunen da Meenal din take, lafayar dake jikinta ta warware ninkeshi tayi ta sashi cikin wardrobe, "tashi kiyi wanka na hada miki ruwa a ciki,"ta fada yayinda taci gaba da kakkabe² tana kara kimtsa dakin ta kara feffesa room freshener dan sun kunna turaren wuta dama tun kafin su Meenal su shigo, Mikewa tayi tana mita "Nidai gaskiya gaba daya yau kun takuramin kun mai dani Kamar wata agwagwa, haba bini² kadan kuce inyi wanka, dazun nan fa nayi wanka!" Barin abunda takeyi tayi ta juyo tana kallon Meenal din, "To wallahi sai kinyi shi kinjima na rantse kin maci uwar rainin wayau wato mun miki mai wuyar ai Bari kimin iskanci......." " Eh din to me yasa baku barni a gida ba" rike baki tayi tana kallonta da mamaki, Kayan baccin da Moon ta ciro ta ajiyemata akan gadon ta mika hannu na kwasa, Juyawa fayi cikin bayin tana tafe tana murguda mata mazaunai, "Yar rainin wayau in zakiyi murgud'e² ki sai ki jira har shi ya shigo dan nidai in kin min kinyi ne a banza" wanka sosai tayi da ruwa mai dumi dan wallahi gajiya takeji sosai a jikinta dan baccine taf cike da idonta, bata fito ba saida ga dauro alwallah, Koda ta fito ta samu Moon ta canza zanin gadon ta sanya wani kayan data fito dasu a hannunta Moon ta amsa sai da ta feshesu da turare sannan ta ninke ta adana, Gaban mirrow ita kuma Meenal din ta karasa ta mutstsuka mai sannan tadan bi fuskarta da hoda yar kadan dan ta kashe maskin man, "Baza kiyi kwalliya ba?" Ta tambaya " ke dan allah rabani da wani kwalliya da daren nan gado fa zan hau bacci nikeji" bataja da tsayi ba ta mika hannu wajen turarukan da suke laye akan mirror din taci gaba da fesa ma Meenal bayan ta tabbatar komai ya kammala gyalenta ta yafa, "Sister bari mu wuce dare yayi yau a unguwar malamai zamu kwana" shiru tayi ba amsa tana binta da ido, dariya tayi "Bari in kara miki tuni wallahi kazar mu! kazar mu!! Kazar mu!!! Kinji sau uku na maimata koh to wallahi ki adana mana ita da kyau, Dan ba yafiya tsakanin mu da wannan kazar tunda allah yasa muna da rabon ganin ranar biyan bashi to a biya a huta, Yauwa kuma kiji tsoron allah banda rowa, kin daiji wa'azin da malamai sukayi akan hakkin miji akan mata Dan haka yasa kikaga na canza zanin gado dan wancan yan ganin amarya sun dakuna shi, Ubangiji Allah kasa nan da wata Tara mu dawo taron suna Ameen ya rabbi " ta k'arasa addu'ar tana shafawa a fuska, "Asha amarci lafiya kidai tausaya ki daga mishi kafa kin san dai saurayine ba sabawa da buga wasan yayi ba sai kin bishi ahankali," "Kutmelesi amma wallahi gaba d'aya kin gama dani dan wulakanci nine ma zan d'aga mishi kafa? Gaskiya allah saiya sakamin wannan katon sharrin da kikamin, ke wuce ma ki tafi nagode allah ya huce gajiya, kuma sai Allah ma ya saka min, Kai gaskiya kin kwareni wainice zanbi tsohon tuzuru a hankali to yasin kofar dakin ma zan rufe inba hakaba nasan tabbas gobe a asibiti za'aci gaba da zuwa ganin amarya muguwa dake kawai" Dariya ta fashe dashi bata kara kulata ba ta bude kofar ta fita Hijab Meenal ta zira ta take mata baya domin gidan yanzun tsit yake ba jama'a a side din amma tanajin hayaniya a farfajiya kilan angwayen ne suka dawo, Saida ta taka mata har zuwa bakin kofar falon kasa, ta bude kofar kenan najiyo muryar Mai Jama'a, Ai da gudun besfa wallahi bibbiyu ta dunga tsallake benen Allah dai ya tsare batasha kasa ba, Tana shiga daki ta maida kofar ta rufe tana numfarfashi, ta baya ta fada gado tana ma Kanta dariya, itadai bata san abunda ya sameta ba tunda aka yi auren nan gaba daya wani irin shakka da tsoron Mai Jama'a takeji, Yana daga cikin manyan dalilan da suka sa ta tsiri wasar buya dashi, wallahi ita kadai gasan kalar jidalin da take hangowa a cikin kwayar idonshi, Nima dai mai rubutun na tausaya mata shi din tun fil azal dama ya lafiyar kura bare kuma yanzun! "Lallai dole in zage damtse dan dazarar ya gane abunda nike ma tsoro na kade har ganye na" Tashi tayi ta koma cikin makewayi ta kurkuro baki sannan ta koma gefen da aka ware domin ganawa da ubangijin al'arshi, Bayan ta idar ta dade akan dadduman tana gabatar da addu'o'in samun zaman lafiya tsakaninta da mijinta sannan nltayima iyayen su addu'a dama sauran musulmai baki daya. Hijab dinta ta cire ta ninke shi sannan ta karasa ta kashe hasken wutar daya cika dakin gabar wanda yake a gefen gadon, saida tayi addu'ar bacci ta shafema jikinta sannan ta kashe sauran hasken data bari tabi lafiyar gado, A gefen mai Jama'a kuwa.... Bayan su Amina sun wuce sadeeq yama magana akan ya sallami duk wata mace da take wajen baya bukatar ganin su, sai da ha tabbatar da sun wuce din sannan ya fito daga mota cikin hall din suka koma da sauran abokainshi, Abunda ya dauremai kai a lokacin shine ganin wajen dund'um wato babu haske a cikin hall din duk da kasancewar ga haske ko ina a waje, "mutane sun gama watsewa ne? " ya tambaya sai dai bai samu amsa daga wajen kowa ba kutsa kanshi yayi cikin hall din dan haka nan hikejin kamar wani abu suke shiryawa, yana shiga yaji fashewar Abu a saman Kanshj a dai² sanda wasu kana nan abubuwa masu kyalkyali suka fara zuba a jikinshi wutar wajen ya dawo. Happy married to you! Happy married to you!! Happy married, happy married, happy married to youuu........... Haka suka hada baki dukan su wajen fada, Bude idonshi yayi baki sake yna kallon su, dan yayi zaton koda zan iske mutane to zasu kasance tsiraru ne a wajen Amma ga mamakin shi sai yaga wajen cike yake dam da mutane kuma mazane zallah ba jinsin mata, wasu daga cikima bai gansu wajen ba sai yanzun, Lallai gayun nan sun shammace shi wai dan fitan nan da sukayi shine har sun canza docoration d'in dake wajen sun kara gyara wajen ga kuma kayan kida a gefe ba wanda akayi amfani dasu dazun ba, gaskiya dai yayi farin ciki matuka domin abun yazomai unexpected Ashe sun san Abunda suka shirya shi yasa da yace musu ba wani event basuja zancen da tsayi ba, Ganin yayi tsaye cak ne yasa suka jawoshi zuwa cikin fili bayan sun umarci DJ daya basu sauti, gaskiya sunyi kokari domin wai wankan ango suka shirya ba tareda sani shiba sun kuma wanke shi da turaruka da tarin kudade, Duk wani turaren da suka san AK na so saida suka yayyafa mishi duk son shi da kamshi saida yaji yana hawa mai kai a yau, ( gaskiya dai anci amanar turare haka akayi ta feshe turarukan makudan kudade a iska, yo suba kudiba balle in kwaso mu raba damasu karatu) Gaskiya kamshi abun sone daure ko turaren durine ki siya ki dunga shafawa kawata, karki yarda ki dunga shiga mutane kina tsami please!!! Sunyi k'ok'ari kuma yaji dad'i ya kuma yaba musu basu bata lokaci sosai a wajen ba sukayi sallama da dayawa daga cikin su suka kuma raka wasu masauki, sannan Yusuf da Sadeeq suka daukoshi zuwa gida, bayan sun iso nan din ma dai bamu samu mutane ba domin dare ya farayi a lokacin, " Yane anan zaku kwana ne ko wucewa zakuyi?" Dariya musty yayi "kai malam me kake nufi? Muda muka rako ango ai kasan bama tafiya sai mun damka ka a hannun Amarya Dan haka muje ciki mutumina ya fada yana kallon Sadeeq," "Wa zaku raka dakin amarya kamar wani yaro?" "Sabon shiga zamu mik'a" cewar Yusuf Gyara zama hayi akan kujerar motan haci gaba da latsa wayarshi yana kallon hotunan Meenal da yasa Hafees ya dauko mishi ita dazun ba tareda sanin taba, Har sun fita sun fara tafiya yana ganin dai sun lura ban biyo bayan su bane shi yasa Sadeeq juyowa Amma ga mamakin shi koda ya dawo bayan motar ya bude ya fiddo ledoji daga ciki, su kuma sauran motar daya hango su hafees a ciki suka k'arasa, motar Maryam kenan Maryam dince ta tambaye su "Ina angon" nuni suka mata da motar da suka iso a ciki, fitowa tayi ta iso inda yike nocking din side din da yake zaune Maryam tayi bayan ya sauke glass din gefen gaishe shi tafarayi "Mai Jama'a Barka da dare ya akaji da taron jama'a? " "Alhmadulillahi "ya amsa dashi "ya naku gajiyan mun godefa ubangiji Allah yabar zumunci ya kuma saka muku da gidan aljannah," Murmushi tayi "zamu wuce ne dama nace sai na jira isowar ka dan allah Ya Abdul duk da nasan ko ban baka amanar kawata ba zaka riketa da amana, sai dai ince kayi hakurin zama da ita sannan ka kula mana da ita ubangiji Allah ya baku zaman lafiya yasa ace gara da akayi" "Ameen ya rabbi" ya amsa dashi yana mata godiya fitowa yayi suka jera har zuwa inda motarta sannan yama sauran godiya suma Musty yama magana akan ya sallami kawayen Amarya a yayin da Maimoon ke fitowa daga cikin gidan, in baku mantaba jin muryar shine yasa Aminatu komawa cikin gidan da gudun besfa. Bayan wucewar su Maryam ne Sadeeq cikin dariya Yake cewa "kai ai da munyi katuwar mantuwa fa a shiga dakin amarya ba tareda kazar amarci ba aiko dai da anji kunya wallahi," Yusuf na dariya yace "Aiko dai yau da amarya ta kullema ango kofa kuma wallahi tafiyar mu zamuyi mubar ango yayi kwanan keso", Shafa kai Mai Jama'a yayi bayan sun kai bakin kofar falon yana murmushi kasa² yake cewa " wai yaushe kukayi wannan cefanen?" Yayi tambayar yana mai tsaresu da idanuwanshi, musty ne yace "Dan Allah Mai Jama'a kadena tsareni da wadannan idanuwan naka to gudun mawar na Faisal ne dan nima na shafa'a shine ya aiki su Ahmad dazun suka siyo kafin mu taso daga wajen can," " nagode" yace yana mai rungume su gaba dayan su, sadeeq ne cikin shashsheka yake cewa "wallahi ji nike Kamar a mafarki wai yau Abokina yayi aure da burin zuciyar shi har gamu munyo rakiya zamu damka ango ga amaryar shi ya fada yana share hawaye, lallai rabon kwado baya hawa sama ko yahau saiya sauko. Congratulations once again friend ubangiji ya dauwamar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auren ku," ameen suka amsa dashi baki daya, Shiko Yusuf daurawa yayi da cewa "nasan mai Jama'a yana matukar kaunar Amina Amma tun aurenta na farko sai nayi zaton tunda ya rasata a lokacin shikenan zai kulle babin ta duk da gaskiya na bashi laifi sosai a lokacin domin shi yayi nauyin baki harta subuce mishi, Ashe tukun na dai Wasa farin girki ban kara tabbatar da kaunar da yake mata ba sai yanzun Alhmadulillahi gashi yau komai yazo karshe, shi dama mahakurci akace mawadaci yau Kam ba burin mai Jama'a ne kawai ya cikaba burin mune gaba daya ganin abokin mu cikin farin ciki dauwa mamme," Oh! Oh!! Wadannan abokai sunsa sassan jikina yayi sanyi, nasan masu karatu ma sun yaba! "Kai! Kai!! Kai!!! Dan allah ku cikani kun wani bi kun dukunkune ni Kamar sabon kwabo a hannun kuturu, bayan kun san amaryata na jiran shigowa ta" Dariya suka fashe dashi dukansu sannan suka karasa cikin falon matakala suka hau zuwa sama, falon dake saman sukayi ma kansu masauki sadeeq ne yace ma mai Jama'a Dan allah kirata mu samu mu wuce dare yayi. Ok yace yana mikewa "wallahi nasan tayi bacci yanzun Amma bari in d'auko muku ita" ya karasa fada yana mai shigewa cikin corridor din da dakunan bacci ke jere kofar dakin da yake a matsayin nata ya karasa handle din kofar ya murda da niyyar bude kofar baiyi mamakin jin kofar a kulle ba domin yasan dama za'ayi hakan, murmushi yayi "lallai ma yarinyar nan waima ni ta rufema kofa kai! " Juyawa yayi zuwa nashi dakin Bude kofar yayi da key sannan ya shiga da sallama a bakin shi kofar closet din dake dakin nashi ya bude ya shiga sannan ya danna wani madanni ga mamakina kofa naga tana budewa, shiga yayi sai gashi a cikin wani daki duhun daya rufe dakin ne yasa banyi saurin gane ko inane wajen ba, Da wayar hannun shi yayi amfani wajen haska dakin harya isa inda gadon dakin yake, gefen side drawer yaje ya kunna lamp sannan haske ya haska dakin duk da hasken bamai yawa bane bai hanashi hango kyakyawar fuskar masoyiyar nashi ba dake baccin ta hankali kwance. Gefen gadon ya karasa ya zauna sannan ya mika hannun shi ya sauke bargon data rufe jikinta dashi zuwa kasan cikin ta ya maida bargon sannan yayi amfani da hannun shi guda wajen gyara mata gashinta da suka fita a cikin hulan dake kanta daya zame duk da bawai hulan ya cire bane Amma gashin tadai kusan rabi yana waje, Cigaba da shafa fuskarta yayi a hankali har zuwa kan kananun lips dinta da suke nan fresh, dukawa yayi a saman kanta saida ya manna mata kiss a goshi sannan ya sauko da bakin shi kasa zuwa dai² bakinta yana daura bakin shi a nata ita kuma ta bude idanuwanta suka fada cikin nashi ya kuwa riketa gam da idanuwan shi yana cigaba da kissing dinta a yunwace, motsawa ta farayi alaman tana son tashi, dagowa yayi daga jikinta yana marai²ce fuskar shi, "Yanzun fisabilillah kissing din ma bazanyi shi hankali kwance ba, to tashi muje falo su musty da sadeeq suna jiran ki in mun dawo sai mu daura a inda muka tsaya dan yau No gyangyadi! No bacci! Yarinya zatayi kwanan bautan Aure..........." Gyara kwanciyar ta tayi "Allah ni bacci nikeji" ta fada tana Kara jan bargon rike bargon yayi, "wai ta ina ka shigo?" Ta tambaya tana tashi zaune, " ke to miye nufin ki? Ai wai Kenan nufin ki kin rufemin kofa ne in kwana a dakina ko me? Kedai a jiki gashi kin girma amma har yanzun yarinta ne cike da kanki ai dai na fada miki ba bacci koh? Wallahi in baki sauko ba daukarki zanyi Dan allah sai kinje" ya fada yana dauko mata hijab din da tayi sallah dazun, haka nan dai ta sauko tana tura baki rikota yayi yadan rungumota ta gefen kafadar shi, Kallonta yayi da gafen idon shi "waike nima zaki rufema kofa Dan kin gama raina nikoh?" Tura baki tayi ba tareda ta bashi amsa ba, "Da kyau"ya fada shima yana kauda kai, "to kayi hakuri" ita kuma tace, shareta yayi bai amsa taba, "Kayi hakuri Dan allah," ta k'ara fada "ki rike hakurin ki dan ke zanba hakurin anjima kad'an dan kinsan dai yau dagani saike koh ?"ya fada yana dage mata giraren shi biyu da wani munafukin murmushi a fuskar shi, "ko bazaki sha sweet ba? halshen shi ya fidda daga cikin bakin shi yana dan karkada shi, "zaki sha koh?" Ya kara tambaya yana tsareta da idanuwan shi da suka fara kankancewa, Kauda kai tayi tana murmushi " Yauwa yar kanwata ai nasan bazaki ki shaba koh? " Ya kara fada yana mai k'ara rungumota sosai zuwa cikin jikin shi ya sunbace ta a goshi "ina fa sonki da yawa yarinyar nan kinga yau ko bugun da zuciyata keyi in kina kusa dani ya ragu," ya fada yana mata hararar wasa, Kara langwabewa tayi a jikin shi domin wallahi duk wata gaba dake jikinta saida ta mace a wannan lokacin. "Yarinya Ai kema kin san nayi shekaru ina taraki dan haka yauce ranar kwasan adashe ki gode Allah yau din babbar ranace a gareni dan haka zan dan sassauta miki kad'an nasan kema zakiyi farin ciki ko Matataa... ? Itadai bata k'ara samun zarafin magana ba domin ko idan dai har mai Jama'a yace zaiyi Abu tofa ko za'a mutu sai yayi, Dan haka yau dai ta sadakar sai yanda allah yayi da ita kuma........ Karku manta tuzuru nefa,,,,, Koda suka k'arasa falon mikewa tsaye su sadeeq sukayi, Barka da fitowa amaryar mu suka fada a tare, rufe fuskata tayi da tafukan hannunta tana k'ok'arin janyewa daga jikin AK Amma gayen nan sai ma kara chachume ta yayi da gayya, ina ruwan ba saban ba ko kuma ince Dan kauye yayi agogo, Kujeran dake daura dasu 2 sitter ya masu masauki akak, Yusuf ne ya bude taron da addu'a, Sannan suka masu yan nasihohi bayan doguwar addu'ar da ko wannen su ya masu sannan suka kuma gabatar mata da wata jakar briefcase a matsayin kyauta daga abokanan su a gurguje dai sukayi masu sallama suka wuce, " Ki jirani anan " yace yana maiyi musu rakiya, gyara kwanciya tayi a kujeran dan wallahi har yanzun baccine cike da idonta baiji maba ya dawo bayan ya kulle kofa ya kashe fitulun dake kasan sannan ya hauro sama bai kulata ba ya jawo ledojin nan ya bubbudesu, kayan ciye² ne a cikin su sai kayan sha a wata ledar daban " tashi ki zauna muci abinci yunwa nikeji" ya fada yana zama a kasa saman kafet din dake malale a wajen, saukowa itama tayi ledar da kaji ke ciki ya tura mata gabanta, Waiyo Allah hajiya kaza tun kan ta sauko kamshin su ya tadomata da duk wata tsohuwar yunwar dake boye cikin hanjinta, Kajin nan fa sunsha hadi sannan sun samu lafiyayyar gashi gasu luka² ko ina tsokace kwance sai kyalli suke, mukut fa hadiye miyau, itadai allah ya sani tana matukar so da kaunar Aunty kaza soyayya mai danko ne a tsakaninta da kaza Dan haka batajin zata iya wuce tayin ta. Amma dai duk da haka batayi saurin bada kai ba saida ta latsa shi, Duk wannan sakar zucin da take shi hankalin shi yana kan cin chips din shi da yikeyi, mika hannu tayi zan diba chips din ya janye " haba Amarya ai yau ranar cin kazace Bari ki gani" ya fada yana janyo ledar kajin gaban shi, "gashi ko kamar sun sanki da maitar kaza suka kwaso miki kici ki gaji," bata rai tayi "ni bazanci kazar ba," " Iyeee" yace da dan karfi yana kallon ta "me naji kince? " " Cewa nayi bancin kazar" dariya ya fashe dashi " karya kikeyi wallahi haba An mata ni zaki layance mawa nine fa! ko kin manta bayane da kike hadani Allah annabi in siya miki kaza? "To ai baya kace yanzun kuma na girma,kuma ni ban tab'a cewa ka siya min kaza ba" " Allah wasa kikeyi ke tsaya ko kema kawayen ki sun zugeki karkici kazar ne? " Wallahi dariya sosai ya bata "kai Ya Abdul" tace tana dariya " Eh mana ba haka kukeyi ba to garama kici dan ko bakici ba ni inajin yunwa kuma sai nacii... " ya fada sai naciiiiin a iskance, Hararar shi tayi "to ai kasan wannan kajin na kawayen Amarya ne" ta fada cikin subutar baki, "zakumayi bayani to ci ki rage musu nasan ai bazai ciwu miki dukaba ni kuma kinga kifi zanci," " to "tace ciccire mata tsokokin yayi yana ajiye kasusuwan a gefe, "Yau wata rana wai kaza bata ciyuwa a wajen wata, kawai yarinya kice biyan bashi zakiyi kinci nasu suma suci wannan kai wallahi yaran nan sai a barku" ya fada yana dariya, "To ashe da nayi gangancin zuwa ba kaza da batun Musty ya tabbata da amarya ta rufema ango kofa, kai ai dole ma in ma gayun nan godiya sun cetoni daga kwana ni daya, kinsan nifa nama manta ana shiga dakin amarya da kaza kiji wani ganganci dukan mace da magariba," A baki yayita bata saida ya tabbatar cewa ta koshi sannan ya kyaleta tissue ya jawo ya goge mata baki "to zoki kwanta anan kafin in gama sai mu shiga daga ciki " ya fada yana kwantar da ita a cinyar shi, Wallahi duk baccin da takeji neman shi tayi ta rasa ya gudu ya barta sai faduwar gaba data dungajin yana kamata, shiko bai karabi ta Kanta ba maida hankali yayi ga abincin shi bayan ya gama, zame kanta yayi ya maida mata pillow din kujera a makwafin cinyar shi sannan ya tashi tattara ledojin abuncin yayi ya shige dasu cikin madaidaicin kitchen din dake saman saida ya ajiye ko wanne a inda ya dace sannan ya wanko hannun shi ya fito daga kitchen din, tanajin motsin fitowar shi ta tashi zaune tana mutsitsika ido, hannun shi ya miko mata ita kuma ta Kama ya dagota daga zaunen da take, wayoyin shi ya zuba cikin aljihu sannan yayi amfani da dayan hannun wajen daukar briefcase din nan, bata ankara ba taji yamata daukar cak, "Kai😳" tace tana zaro ido cike da mamaki "nidai ka sauke ni karka yarda ni," " ke yarinya irin ku guda goma in aka dauramin ku sai in zagaye gari ba tareda na gajiyaba," " to sannu iliya Dan mai karfi" Kai tsaye dakin shi ya masu masauki bai sauketa a ko ina ba sai kan gadon shi, kunna fitilun dakin yayi "masha allah" ta fada dan gaskiya ba hassada dakin yayi kyau, Dakin mai Jama'a nefa Ai dole asha kallo....... Kurukus kuje kuyi bacci🤣 *UMMIEE CE*✍🏼[10/14, 10:53 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 49* Wayoyin shi ya kashe ya sasu a caji waiwaya wa gefeta yayi giran shi guda ya dag " ke yarinya tashi muje muyi wanka nima bacci nikeji" " Nayi wanka" ta fad'a tana turo baki a shagwab'e, "Eh aina gani amma wannan nina bukata," "to" tace dan tasan musu dashi bashi da wani amfani zaman lafiya kawai idan yace ayi to ayin, akasin hakan kuma asan me zai biyo baya, ita hauka takeyi ma da zata tsaya tana musu dashi bayan tasan daga ita sai shine a cikin sashen gaba d'aya! Ah ah wallahi zaman lafiya ai yafi zama sarki ma balle ita d'iyar Malam. Miko hannun shi yayi ya Kama nata hannun ya mikar da ita tsaye, kyakyawar runguma yamata tsam² a jikin shi yana mai sauke wadansu irin ajiyar zuciya masu kashe gabban jikin mace, Oh Allah wata dai aure rahamar shi daban ne, adacan idan ya matse mata waje har karkarwa takejin hanjin cikin ta suna mata saboda tsabar tsoro, amma yau daya rumgumeta sai takejin wani irin sanyin dad'i da nutsuwa na lullub'eta, Dan Allah inba aure ba wane mutum yasa mace a cikin d'aki daga shi sai ita su kulle kofa gida cike da mutane ciki harda iyayen shi dama wasu idon kunya, dan haka itama dai a wannan lokacin Bushe fitilar idonta tayi tak'ara rungumeshi tsam ta yanda takejin kamar ya bude mata cikin jikin shi ta shige dan wani kalar nutsuwar zuciya data gangar jiki takejin yana ratsata, Hijab din dake jikinta ya yaye yayi jifa dashi, Kwantar da kanshi yayi a saman kafadarta yana hura mata iska mai zafi dake fita daga cikin bakin shi zuwa cikin kunnen ta da wuyan ta a yayinda yake amfani da halshen shi yana d'an lasar bayan kunne da gefen wuyan ta, hakan da yake yi ita kuma shike k'ara kashe mata jiki dan haka sai ta k'ara kankame shi a cikin jikin ta saboda yanda tsigar jikin ta suke ta tashi tana jin yanda jinin jikinta ya k'ara gudu, Yanda ita kuma takeyin ne yasa shi kuma notikan shi suka fara warwara dan haka da zafi² ya dunga sakin mata numfashin shi mai kama da sheshekar kuka akan fatar wuyanta sai da ya taabbatar sakon da yake aikawa ya kai madakatar da yake bukata sannan yabi fatar wuyar nata da kisses din shi masu zafi tun daga cikin kunne kan wuya kafin ya dawo kan bakinta, Wallahi ita dai a lokacin nan allah ne kadai yasan yanayin data shiga dan wasu tsutsotsi taji sunamata yawo a gabobin jikinta sai dai cike da k'arfin hali ta fara k'ok'arin raba jikinta da nashi jin abun yana neman wuce waje kuma, Shi kuma ganin tana neman kwacewa saiya cusa duka tafin hannuna shi a bayanta ta cikin riga ya fara shafa gadon bayan nata kamar dai yana mata susar bayan, bata fara jin saukin kaikayin ba har saida yaci gaba amfani da hannuwan shi wajen shafo wasu daga cikin sassan jikin nata, domin daga susar baya sai taji yana neman juyar da ita dan haka dam ta kara rungume shi zuwa wannan lokacin itama kanta hannuwanta kaikayi sukemara dan haka bata kwaresu ba da gwarin gwuiwar ta itama na fara aikin lada, irin abubuwan da yakemata itama ta fara kwatan tawa ita dai bata san ya akayi ba kafin ta ankara ta sama rigar jikinta ta fita ko ta kasa oho dan bata san ya akayi da rigar ba domin jin saukar hannun shi kan nipple's dinta ne ya ankarar da ita cewar an fara shiga sabon babi, Karfi tasa wajen kwace jikinta daga gareshi tana waro idanuwa waje cike da mamaki kai wallahi maza dai bata ido fisabilillah da Wannan hasken tar a cikin d'akin ne ya wani kama ya cire mata riga, yaufa aka kawota shiko duk saurin da yakeyi ai dai in yana tsoron Allah kamata yayi ya d'aga mata k'afa har bak'in dake gidan su gama watsewa zuwa nasu garuruwan amma shine yake wani tab'ata. fisabilillah yanzun ya gama cin abinci fa bare tace yunwa yikeji, to in ma yunwar ne ai taga dai ita sunan ta Meenal ne ba tuwon daya saba narka kullum ba, Waiyo Allah ta fada a bayyane yayinda taji ya k'ara fusgota zuwa cikin jikin sha kai tsaye kuma ya k'ara maida hannuwan shi yama dukiyar nata wani irin matsa kamar mangwaro a hannun yaro, "Ya Abdul da zafi wallahi dan Allah ka bari"ta fad'a muryar ta na k'aryewa alamun dake nuna gab take da fashe mishi da kuka,shiko ina ma yasan tana magana mugun.... Abun nema ya samu ai nasan dama yau ba kanta, " Ya akayine yarinya?" ya tambaya da shakakkiyar murya ba tareda ya cire hannun a wajen ba, "Kaya nane fa in ban fara sauke hakki da wuri ba aiko Allah bazaiyi farin ciki da hakan ba karma Brothers din da suka had'a kudi suka biya min sadaki suji labari ai kema kin san idan na kyaleki naci amanar su, dan allah ki rufamin asiri karki hadani da Allah ki cuceni kar kuma kimin rowa ki kwareni, Baby idan kika hanani hakkina ayau zan hanu Amma ki sani kinci zalina kuma kin dauki alhakina kin san dai niba yaro bane sannan da lafiya ta ba karamar wahaltuwa nayiba tsayin shekarun nan, nasan allah ne yamin gata ya tsareni ban fada zinace² ba, Dan haka ina mai baki hakuri kiyi hakuri ki daure ki jajirce wajen kula dani ata ko wani fanni ina sonki da yawa shi yasa na kasa ba ko wacce mace matsayin ki a cikin zuciyata domin ko sau daya tsayin shekarun nan sonki bai tab'a barina na huta ba, Alhmadulillahi yanzun dai komai ya zama labari tunda kin zama tawa". ya fada a yayin da ya dagata sama yana jujjuyawa da ita kamar yanda akema yara, dukan su dariya sukeyi cike da nishadi, "Ni ina hauka ne zan yarda ink'i sauke hakkin ki in kwana cikin tsinuwar mala'iku ai hakan ma zunubin gangancine,ke baki san cewa gari na wayewa sunturin nan da akeyi na zuwa ganin amarya wasu da yawa gulma ne kawai yake kawo su dan suzo su gani ko ango yaci nasarar doke yan wasa a filin dambe ba, amma in bakya son ladan daren farkon ai sai inyi hakuri kuma har gafara ma sai na tayaki nema a wajen Allah dan nasan k'ila dai tsoro kikeji koh?" Ya k'arasa kalaman shi da tambaya yana d'age mata giraren shi kai mai Jama'a da shegen wayau yake wai ita yakema hannunka mai sanda, Saukota yayi k'asa ita kuma ta kara rungume shi tana rufe kirjinta da jikin shi, yana dariya yace "ya akayi ne? tubewa zanyi muje wankan ai saurin me kikeyi Baby?" Kunya sosai maganar shi ta bata dan haka sai ta saki jikin shi ta juya baya da hannuwan ta tayi amfani wajen kare kirjinta duk da sunfi hannun nata girma amma dai yafi ta sake su a haka tsirara, Baiji kunyar taba haka ya kama kayan jikin shi ya cire ya rage daga shi sai gajeren wandon shi na ciki, ta baya ya lallab'o ya rungumenta bayanta daba komai ya mannu da faffadar kirjin shi da ba komai sai kwantaccen gashi, da hannun shi yayi amfani wajen zagaye cikinta, kwanto da kanshi yayi dai² kunne ta ya furta mata, 'yane kin shirya"ya k'arasa fada yana huramata iskan bakin shi cikin kunne "nidai sanyi nikeji bazanyi wanka da daren nan ba," Ta amsa dashi tana lak'e kafad'a, "Haba Baby karki damu sai muyi amfani da ruwan zafi" " A'ah nidai bacci nikeji kaje kayi wankan ka fito zan jiraka anan" "Bashi yuwuwa yarinya kafata kafarki" ya fada a yayin da yake juyo da ita gaban shi baiyi wata² ba wajen hade bakin shi da nata bakin shi na cikin nata yaci gaba da magana " kin san bana son musu koh?" kadan² ya cigaba da shan bakinta tun yanayi a hankali har ya fara warwarewa yana kara kaimi, wallahi kasa bujirewa tayi duk da yanda taso ta kame kanta abun da takeji yak'i rik'uwa dan haka bata san ya akayi ta biye mishi sukaci gaba da murza totur ba, bai sassauta ba saida yaga alamar tafiyar tana so tayi tsayi dan gab yake da idasa warwarewa sannan yamata daukar cak zuwa cikin makewayin, Itadai bata gama dawowa daga sararin samaniya ba sai da taji zubar ruwan sanyi a jikinta dan a k'arkashin shower ya tsaidasu dan haka sanyin yana ratsa ta ita kuma saita kankameshi tana b'ata fuska "Ya akwai sanyi fa" "na sani"ya fada yana mai taran ruwan a tafukan hannun shi ya watsamata a kirji, Dukewa tayi shi kuma ya kama dariya, atakaice dai badan taso ba haka Mai Jama'a ya wanke mu tas itadai mai sauran kunya bata yarda ta bud'e idoba har akaci aka sid'e, towel ya jawo ya daura mata bayan shima yasa rigar wanka a jikin shi sannan yamata nuni da tayi alwallah, bayan sun fito shi ya jasu sallar nan mai falala ta ma'aurata kamar yanda sunnah ta koyar to yau suma munbi sahu kuma yayi masu doguwar addu'ar samun zaman lafiya da zuria masu albarkha, bayan sun idar itadai bata tsaya wani iyayin shafe²n mai ba turare kawai ta feffesa sai Vaseline data murza a baki dan bata son lebenta suna bushewa, Da towel din jikinta ta haye gado ta lume cikin bargo tana mai addu'ar Allah ya kawo bacci ya yi gaba da ita kafin lokacin da zai hawo gadon, Shiko dan gayun sai da yayi zama na musamman a gaban mirror yayi shafe² bayan ya gama yabi sassan jikin shi da turaruka masu dadin shaka saida ya gamsu cewa komai yaji sannan ya iso kai tsaye zuwa gadon ya haye da bismillah yana neman sa'a wajen ubangiji, cikin bargon ya shige ba tareda jiran iso ba, Wallahi AK tantagaryar mara kunya ne a tuben shi yake fa tuf bata san hakan ba sai da ya hada jikin shi da nata, Itadai tsit tayi kamar mai baccin gaske taso taci gaba da pretending amma ina jikinta yak'i bata had'in kai dan haka nan jikinta ya Kama rawa to fisabilillahi ai dole jikin mace ya kwashi rawa kukoh abunda baka saba dashi ba kwana fa da k'ato a gado d'aya kuma dan tsabar son ya nuna ma duniya cewa shi din digirgirarren tuzuru ne kawai ya wani shige mata bargo a tub'e🤔 to dai Allah ya shirya mutum kawai mu dai zamuce..... Da wayau ta samu tad'an k'ara jan jikinta gefe kamar irin a magagin bacci, Sai da ya bud'e idon shi ya k'are mata kallo da kyau dan har lokacin jikinta bai daina rawa ba duk yanda ta dunkule kuwa, Bai damu ba sai ma jan nashi jikin shima da yayi yabita ya k'ara matse tazarar data bayar tsakanin su, Kafar d'aya ya d'aura a saman cinyarta hannun shi d'aya akan konkoson ta sannan yakai fuskar shi wajen gashinta da hak'orin shi yayi amfani wajen janye ribom din data d'aure gashin dashi kafin ya maida hancin shi cikin gashin yana shakar kamshin da gashin keyi, "Muah"ya sauke mata kiss mai k'ara a saman kai yana k'ara matseta a cikin jikin shi gefen kunne ta yakai bakin shi yana huramata iskan bakina shi a cikin kunne yayinda k'afar shi da hannu basu iya tsayawa waje d'aya ba dan haka tuni jikinta yaci gaba da rawa ba kak kautawa kamar wacce zazzabi ke shirin rufewa, Da karfi ya juyo da ita jin tana son yi mishi gardama dan ta wani kama towel din ta cukuikuye shi a jikin ta to shi har itace ma zata wani gwada mishi k'arfi, dan haka yana juyo da ita baiyi wata² ba ya haye saman jikinta dan tsabar mugunta kuma haka nan ya sakemata nauyin shi kafafuwan shi yasa ya raba nata kafafun da karfin tsiya, dan hadesu tayi gam, hannuwan shi kuma basu tsaya waje daya ba duk inda hannun shi ka iya zuwa saida ya sadashi dashi da wayau ya dunga murza jikin shi a nata har yayi nasarar zame towel din tana daura towel din ya koma gefe shi kuma yana ganin hakan ya fincike shi ya watsar a k'asa, Ita kuma hakan ne yasa ta kwalla k'ara, "Waiyo Allah dan Allah kayi hakuri wallahi ni bacci nikeji kuma ma bani da lafiya yasin kuwa" Sai da kifa kanshi a tsakiyar k'irjin ta yana murzawa kafin yakai hannun shi kan cikinta yana shafawa a hankali sannan ya iya amsa mata da wata iriyar murya wacce bata fita da kyau yace, "Nima bana da lafiya kuma ke k'adaice maganin damuwa ta ki d'aure ki tsaya in samu nutsuwar da nike nema a tareda ke nayi alkawarin bazan baki wahalar da kike guduba, nima ai bazan yarda gari ya waye azo aga amarya ta kasa tafiya dai dai a tafi dani a baki ba d'an kad'an kawai zaki sammin," Yana gama surutan shi ya maida bakin shi akan abubuwan da suke ta zagin mishi k'aniya tun d'azun, Hannunta duka biyun ta d'aura a kanshi a kokarin ta na ganin ta tureshi daga aikin da yake sai dai kamar mayen k'arfe haka ya kafe kanshi a wajen ko gezau, Daga tana neman rage mishi lagwada ma sai ya had'e hannayen nata duka biyu bayan ya mai dasu ta saman kanta ya rikesu da hannun shi d'aya Dagowa yayi yana bin fuskarta da kallo kafin yakai bakin shi kan nata bakin ya lasa ita dai runtse idonta gam tayi dan bazata iya kallon shi a wannan yanayin da yike ciki ba, "Ammina ina rokon allah yanda ya cikamin burina na mallakeki ayau daya kara cikamin wani burin nawa ya bani ikon yin ajiya anan" ya fada dai² sanda ya maida hannun shi kan mararta yana shafa marar a hankali wanda ita kuma yasata yin wani irin bank'ara babu shiri dan sosai shafar ya shigeta, "Ameen ya Allah"ya amsa ma kanshi muryar shi cike da farin ciki, nima dai na tayashi da Ameen a cikin zuciyata. Cigaba da wasa da hannun shi yayi daga kan mararta zuwa saman yen tagwayenta yana kuma bi yana lasar wuyarta, Ajiyar zuciya mai nauyi ya dunga saukewa a bayyane sanda ya maida duka hannayen shi akan su, "kin san batun yau ba nike da fushin su! Ina son su sosai kici gaba da kulamin dasu kinji? Kuma banajin dadi ina magana kina min shiru ki dunga bani amsa da baki," Shirun tayi yanzun ma bata amsa ba, Dan haka sai k'ara matse ta da k'arfi a jikin shi "to zan gyara" ta amsa a wahale jin numfashin ta na shirin guduwa ya barta, "Yauwa yar kanwata" bakin shi ya daura akan guda yana mai tsotsa cikin sigar tsokano zance bawai ya turbutsa shi a bakin bane a'a yayi amfani da hannun shine wajen tumbulo su sannan yakai bakin shi kan nipple's din yana wasa da halshen shi akai sannan sai ya dan rike su da labban shi yana massaging kansu. Tayi zaton ko abin na wasa ne dan tun d'azun take rik'e kanta dan kar yaga lagonta ya rainata amma yanzun kam tabbas tasan ta fad'a rijiya dan bata san wani tsautsayin yakai hannu ta saman kanshi ba , Itafa burita ta tureshi ne dan taji yana neman ballo mata ruwa dan sosai gab'obinta suka bud'e suna amsar sak'on nin shi Ashe takai Kainta makasa ne, To kafin dai ta ankara gaba daya ya riga ya fice a saiti kamar ba mai jama'an data sani ba, Dan da gudu ya saki abin duniyar ya dawo kan bakinta dake mishi magiya akan yayi hakuri ita bacci takeji, Hannu ya mik'a gefe ya kashe hasken d'akin yayi duhu gaba d'aya a hankali ya karanto addu'a kafin a tsanake ya fara neman hanyar shi bada garaje ba dan baya son yayi abinda zai tona ma kanshi asiri, Kan kameshi tayi a sanda yake goga jikin shi a nata halittar wani irin abu daga shi har ita suka ringa jin yana ratsa su wanda baki bai iya furta ya yanayin yake, A haka yaso ya shammace ta yayi wuf sai dai Yarinyar nan fire ta hana shi dan yana yin dogon motsi take matsewa tana mishi rakin ita dai bata yarda ba wallahi ciwo zaiji mata, sunyi wannan ragabzan na kusan mintuna goma ganin tana son b'ata mishi lokaci sai kawai ya zame zuwa kasanta yayi tsugun ni a gabanta kafin ta ankara ya d'age kafafuwan ta sama ya kuma had'e su da hannun ta ya rik'esu dam shi kuma ya sauke kanshi a inda yake da fushi yaci gaba da aiki, Sai daya tabbatar da cewa yayi fata² da duk wata nutsuwar da take tare dashi yasan cewa yakai ta mak'urar da dole ita da kanta zata nemi sulhu dan dole badan taso sannan ya mirgine ya koma ya kwanta akan pillow ya juya mata baya yana sauke numfashi,sai da ya d'an dawo hayyacin shi kad'an kafin ya juya gefen ta yaga yanda ta dunkule jikinta sai mazarin tashin hankalin daya taso mata yakeyi, tadan bashi dariya fa amma hakan nan ya maze dan shima a wahalen yake jawota yayi zuwa gefen shi sai dai bai bari sun matse waje d'aya ba yake cewa.. "kai ai mantawa nayi ma tashi ki zauna ki maimaita abunda kika fadamin ranar nan, uhmm mema kikace?" Kokarin kamoshi zuwa jikinta take shi kuma yana zuk"ewa, "Ba cewa kikayi ke kinfi karfin yaro ba? Koba haka kikace ba? " Ya tambaya bayan ya juyo da fuskar data juyar gefe suna kallon juna, "Dan allah kayi hakuri" ta fad'a a marairaice dan wallahi ita ba wannan surutan take son ji daga bakin shiba bayan yana kallon halin daya jefata jikinta babu inda baya mata k'aik'ayi, "Haba yarinya ai ba Wannan maganar yanzun dai bari in maida abun rubutu na cikin wando har zuwa sanda zai girman da zai zane minke tas, daga nan zuwa sanda zaki gama karatu hakan ya miki koh? ko kuma kimin adalci daga yau har zuwa ranar da zaki tare a wancan gidan kinga sai muci amarcin mu a can mu k'adai babu batun jin kunyar had'uwa da sirikai idan gari ya waye" "Dan Allah kayi hakuri wallahi subutan bakine" Ta fada dan allah ya sani irin bala'in daya tasomata tasan tabbas bazata iya runtsawa ba tareda ya kwanta ba dan abunfa ba sauki wai ciwon arne, "Oh yanzun ne da kike bukata na kika san niba yaro bane? Kuma fa har cewa ma kikayi baki sona, Wai nine ma baki kauna koh? To ai ni nine raba gardama dan tuni na tanadi poison dama nace idan kin tarene zan damka miki ki bani insha in mutu kinga kin huta sai kici duniyar ki da tsinke," Yunkurawa yayi zai sauka da sauri ta zabura tana mai rungume shi a jikinta cikin kuka take cewa, "Wallahi ina sonka, ina son ka, ina sonka, ina sonka to wai tayama zance bana sanka alhalin kowa yasan kai kadaine a cikin zuciyata, kuma ai kaima kasan ina kaunar ka tayama zan dena sonka?" Jan majina tayi sannan ta daura da, "kuma aini duk Abunda nayi nayine saboda kar ajina ya zube haba dan Allah kaf a cikin Dangi fa babu wacce aka tab'ayima irin auren dani akayi min, kuma ai naga wadancan shegun Yan matan da kullum suke bibiyar ka har yanzun basu dena binka ba sune suke bani haushi kullum nike kara tunzura, kuma wallahi ko yanzun sai naci musu uwa tunda har sukazo min wajen biki ba gayyata" yi yiyiyiii taci gaba da kuka kukan kishi da kuma jidalin dake dawainiya da ita a cikin jikinta, Jawota yayi ya zaunar akan cinyoyin shi, "ke yarinya wai dama kishine yasa gaba daya kikabi kika kwarkwance kika nemi sa zuciyata bugawa? Amma dai kin dauki alhakina har karamar jinya fa saida nayi mata ta juyama miji baya," "To ai nima ramawa nayi ai kaine ka basu fuskar da suke binka" ta fada ina tura baki da wayau ta cusa kanta a cikin jikin shi sosai ta kuma d'aura hannun ta a k'irjin shi tana shafawa kadan², Dariya yayi "gaskiya yarinya bakyajin magana hankalin nan dai da sauran shi har yanzun, to ai shike nan ni ai bazan iya miki rowa ba amma da sharadi, indai kina so sai kin min alkawarin nima zakimin duk abunda nike so kuma bazaki min kukan shagwaba ba kin yarda? In baki yarda ba sai in sauke ki a gadona in saita miki hanya zuwa dakin ki... Bata bari ya gama maganaba ta rufe mishi baki da nata bakin Dan haka tuni ya bada kai suka koma ruwa akaci gaba da fafatawa, Yayi² a tunanin shi ko network dinta bashi da karfi sosai sai dai kuma ina itama din ma dai jarwuya ce a wannan fannin duk da kasancewar ta sabon shiga kuwa, kara warwarewa kawai takeyi tana kokarin maida naushi duk da dai har yanzun bata barshi ya wuce inda yake kaima hari ba a hakan dai duk yanda take ganin cewa wayan ta yakai ta hanashi isa bakin boda sai da ya nuna mata cewa ya riga ta shak'ar iska dan bugun kifa d'aya kwala ya mata ta nemi tsaga ihun daya nemi toshe mishi kunne duk da ba sosai shima yakeji da gani a lokacin ba, Yadai tausaya kamar yanda yace dan bai yarda ya kwace da yawa ba zuwa d'aya yayi ya ya kankameta bakin shi na kwararo mata ruwan addu'a ita kuma ba baka sai kunne, dan tun ba'aje ko ina ba dama ta raina kanta, 🤣🤣🤣anci in cinye dan haka mu tafi a gurguje, Bayan wani d'an lokaci shine ya fara fitowa daga cikin makewayin ya barta dan k'iyawa tayi duk da yanda shi yaso ya tsaya ya dubata wai ko yaji mata ciwo, Babu wani ciwon dayaji mata dan bata bari in dambatu da kyau ba, ruwan zafin daya mata amfani dasu sau biyu ne ya rage mata rad'adin da takeji dan haka koda ta d'auro alwallah ta fito a bakin kofar bayin ta same shi tsaye yana ganin fitowarta ko ya k'araso, "Sannu ai dai banji miki ciwo bakoh?" Bata kulashi ba taci gaba da tafiya a hankali, D'aukar cak ya mata yakai kan kujerar dake gaban mirror ya zaunar da ita a hankali kamar wanda ya d'auko kwai, Magungunan da bata san ina ya samo suba ya ballo ya bata had'e da ruwa tasa, duk yanda take nokewa haka ya shafa mata mai sama² ya d'auko wata doguwar rigar bacci ya zura mata, D'aukar ta ya k'arayi sukabi ta kofar daya shigo cikin d'akin zuwa nashi d'akin a saman gadon shi ya mata masauki ya kwantar da ita shima ya kwanta a gefen ta sai da yayi addu'ar bacci ya shafe su dashi kafin ya rufe su da bargo ya jawota cikin jikin shi ya mak'alkale, To asuba na gari jikokin innah, *WASHE GARI* Tunda Hajiya ta farka da asuba take tambayar mutanen da suka kwana a sashen ta ko AK ya shigo sashen da dare, Sai dai kowa zaice mata baiga shigowar shiba, Jimami ne ya hanata komawa cikin d'akin ta sai ma waje data nema ta zauna a falon ta wai ita nan zaman jiran shigowar shi takeyi kamar yanda ya saba kullum idan ya fito daga masallacin sai ya shigo ya gaisheta indai yana gari kafin ya wuce nashi sashen, Itafa mamaki ma takeyi dan Wallahi jiya dai inba an had'a baki da wani ko wata bane suka bata maganin bacci tasha cikin wani abun a rashin sani to bata san ya akayi ba dan har shirin zuwa wajen dinner tayi bayan da jama'ar gidan suka watse sai gashi wai bata farka ba sai wajen karfe ukun dare ita da tun daren taso taja kunnen AK akan jikan ta tasan yaran yanzun da shegen wutan ciki karfa yaje yace zai sa k'arfin nan da Allah ya bashi ya afkama jikarta tun yan biki basu gama wayewa ba, Jama'a fisabilillahi dududu nawa ma Meenal din take da zaije mata tun yanzun ita da take nan tana ta shirye shirye nefa akan tayi ma Meenal din shiri na tashin hankali yanda ko yaje mata bazai mata lahani ba, Ita dai Allah rufa mata asiri yasa ba'ayi aika aika a cikin gidan taba, Shiru shiru ba AK ba labarin shi har misalin karfe 8 na safe dan haka ta mik'e, "Larai kin had'a kayan karin amaren nan?" "Eh Hajiya na had'a yanzun dama nike tunanin wanda zan ba ya mik'a musu" "To d'auko kizo muje" "Hajiya da kanki? Ai da kin bari an ba yara sun kai" "Ke bar wannan batu gara dai inje in gano ma idona ko suna bukatar taimako na kedai kin san in tuzuru ya samu mace" Daukowa larai tayi tabi Hajiya tinkis² suna tafe Hajiyar na amsa gaisuwar mutanen dake harabar gidan har zuwa sashen su AK, Nocking kofar ta dungayi ba kakkautawa, "Anya lafiya suke kuwa Larai, kinga har yanzun fa banji motsin suba balle su bud'e kofar ko zamu je bakin gate in tambayi su Isah ko ya fito yaje masallaci yau" "Hajiya dan Allah ki dena damun kanki Amare nefa" "To aike Larai abinda ke bani tsoro kenan, idan akace ya kamata ya mata fashin kwakwa ai ba kanta. *UMMIEE CE* [10/16, 9:42 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *PAGE 50* Ke Larai kina ganin wannan abu na lafiya kuwa? To indai lafiya lau ne ai dai yaci ace an jiyo mu azo a bud'e mana kofa, to kina gani dai babu su babu alamun su wayasan me yafaru ko yake faruwa a cikin" "Hajiya shi yasa dai nace da mun koma in yaso ko zuwa anjima idan sun tashi sai aba yara su kawo musu abincin" "Ke barni fa Larai tunda kikaga na gaza zama na taso aike kinsan da walakin, Wallahi ina fad'a miki duk a tsorace nake yanzun idan na juya muka koma waye zai tsaya ya taimaka mata idan tana neman taimakon? Wannan aikin ai sain..... " Bata gama kai k'arshen kalmar ba aka bud'e kofar falon daga ciki, AK ne tsaye a bakin kofar yayi bake² jikin shi sanye da jallabiya fara tass fuskar shi cike da annuri kai mai kallo daga gani basai ka tambaya ba kasan ango ne sharr a gaban ka, Basarwa yayi kamar baiji abinda Hajiya tace ba, kuma ba tareda ya janye daga bakin kofar ba sai ma gaisuwar daya fara aika musu dashi, "Hajiyata da Hajiyar kitchen barkan ku da safe dafatan kun tashi lafiya?" "Alhamdulillah Babban Mutum ya kwanan Amarya da gajiyar taron biki?"cewar Larai, "Alhamdulillah"shima ya amsa dashi, ita ko Hajiya ba gaisuwar shi take buk'ata ba dan haka sai ta taka zuwa cikin talon "shin zaka bamu hanya mu shiga mu gano halin da yar mutane ke ciki ko mai kake nufine da kayi mana bake² a bakin kofar" Ta k'arasa fad'a tana ture shi gefe ta shige ciki, A baya ya bita yana cewa "Hajiya karki d'aga murya mana bacci fa takeyi kin kuma san hayaniya yana tada mai bacci, indai abinci ne ai dai ko baki biyomu dashi ba idan muka tashi zamu nema" "Ubanka nedai yake hayaniya bani ba, mara mutunci kawai wa yasan kalar azabar daka gana mata a daren jiya?kuma kai kayi zaton kai na biyo da abincin? To Allah ya tsareni ni takwarata nazo dubawa shi yasa na taho mata da abin kari, Nasan kunyar abinda ka aikata ne yasa tana jin muryana yanzun haka ta kasa fitowa Allah dai yasa bakayi mata mugunta ba" Sama Hajiya ke shirin haurawa tanaci gaba da sababi shi kuma yayi saurin shan gaban ta, "Haba Hajiya ai in kina son ganin ta magana zakiyi ni kuma sai in haura saman in sauko miki da ita, amma a ina ake kice zaki haura wajenta da kanki d'akin mijifa kololuwar sirri gareshi ai gara kid'an tsaya daga nan" Kallon banza ma Hajiya ta bishi dashi batason b'ata lokacin ta a k'asan dan haka bata saurare zantukan shi ba ta k'ara zagaye shi ta haura saman tana kwala kiran sunan Meenal, "Takwara wai kina ta ina ne ko jikin ne ya hanaki fitowa?" D'akin dake matsayin na Meenal din ta bud'e tana sa kai da niyyar shiga ciki idanuwan ta basu sauka ako ina ba sai kan gadon da akasha dambe akan shi daren jiya, pillows din dake gadon duk gasu nan anyi watsi dasu a k'asa, bargon ko rabi a kan gadon rabi a k'asa shiko zanin gadon duk yabi ya cukuikuye wani wajen ma ya zame ana ganin katifar dake kan gadon, "Eh lallai zargina ya tabbata"ta fad'a tana juyowa baya ta maida kofar ta rufe, Koda ta juyo babu AK a wajen, amma wai matar nan mai makon ta rufa ma kanta asiri ta kwashi tsufanta ta juya ta koma inda ta fito ah ah tsabar dai cewa ta rantse sai taga kwal uwar daka sai kawai ta juya zuwa nashi d'akin babu neman izini ba komai ko tsoron yin gamo da katar batayi ba domin tanayin sallama ta murd'a hannun kofar ta bud'e ta shige ciki kawai abinta, "Hajiya" Meenal ta ambata cike da mamakin ganin Hajiyar, Shima AK da mamaki yake binta da kallo, "Yanzun nan fisabilillahi da gaske dai Hajiya sai da kika biyomu har nan?" K'arasawa bakin gadon da suke kai tayi itama ta nemi gefen ta zauna tana ture AK da hannuwanta, " kai dallah matsa can ka bani waje uban meye a cikin d'akin da zan gagara shigowa cikin shi bayan ka riga kayi b'arnar ka tun jiya sannu Meenal sannu kinji, injin dai baiji miki ciwo ba? Kai kuma je k'asa ka kiramin Larai" "Hajiya amma dai kin san babu kyau yima gidan Amarya sammako koh? Nidai kawai cikin hakkina kike son shiga" ya fad'a rai bace dan Wallahi shi kam baiga dalilin ta na zuwa mishi sashe da sassafen nan da tayi ba haba dan Allah ai kamata yayi ace koda za'a lek'o su sai a bari sai zuwa irin nan da k'arfe 12 na rana haka lokacin sunyi biyan bashin baccin da ake binsu amma dan Allah da sanyin safen nan Hajiya tayo musu sammako, Badan yaso ba haka ya saki hannun Meenal ya mik'e ya fice daga cikin d'akin, Waiwayawa Meenal tayi ta maida kallon ta kan AK dake ficewa a cikin d'akin tana jin kamar tace mishi ya dawo karya fita a d'akin dan tasan Hajiya ta korashine kawai saboda ta samu damar yi mata tambayoyin k'ak'a uwar ka ta haife ka, Taji dadin zuwan Hajiyar ta wani fanni domin dai da ace Hajiyar bata zoba to da yanzun haka tasan yana nan yana daka ta kamar sakwara dan ta lura AK ya cire kunyarta ya jefa a rijiya ya kulle inba haka ba taya daga wani dawowar shi daga masallaci zai wani zo yace mata gashi yazo, To yazo d'in mai zata mishi? tunda asuba ya tashe ta yin sallah shi kuma bayan yayi alwallan ya fice zuwa masallacin shima kafin ya dawo saida tayi wanka kafin ta fito ta gabatar da nata sallan harda azkar duk da cewa tanayi ne bacci na neman cin k'arfin ta, bai jima sosai a masallacin kamar yanda ya saba koda yaushe ba sai dai koda ya shigo sai ya cimma ta kwance akan dadduma bacci ya k'ara d'auketa batareda ta shirya ba, duk'awa shi kuma yayi yasa hannu ya cire mata hijjab a hankali kafin ya maida tafin hannun shi d'aya ta wajen k'ark'ashin k'eyarta ya tallabo d'ayan hannun kuma ya cusa shi ta k'ark'ashin cinyarta ya d'agota cak sama zuwa cikin jikin shi kafin ya juya ya sauketa akan gado bayan ya janye bargon dake kai gefe, yana ajiyeta ita kuma ta juya ta wani gyara kwanciyar ta abunta shi kuma juyawa yayi zuwa gefen da d'an k'aramin pridge din dake cikin d'akin yake saida ya ciro ruwan gora mara sanyi sosai ya bud'e yasha kafin ya maida sauran ruwan cikin fridge din ya rufe sannan ya cire jallabiyar jikin shi ya jefata akan kurar dake gefen fridge din ya wuce kai tsaye zuwa cikin bathroom yayi wanka a gurguje ya fito yana tsane ruwan jikin shi ko mai bai tsaya shafawa ba ya haura kan gadon, Bacci ta kawai takeyi abinta hankali kwance sai da ya k'are mata kallo daga sama zuwa k'asa kafin ya haura kan gadon yasa hannun shi ya ware kafafuwan ta ya shiga tsakanin su, Bude idon ta tayi a yayinda yasa k'arfi ya janyo hannunta guda d'aya ya d'agota daga kwancen da take ya maidata zaune, "Waiyo Allah nidai dan Allah ka kyaleni inyi bacci" "Haba Baby tun cikin dare fa kike bacci yanzun kuma kice bazakiji dani ba aiko yayane dai ya kamata kid'an gatanta ni" Janyota yayi zuwa cikin jikin shi ya maida kafafuwan ta ya nad'e su a bayan shi ita kuma ya shiga bata sumba tako ina ba kakkautawa, Duk yanda taso ya barta ta koma bacci k'iyawa yayi ita kuma ta hanashi rawar gaban hantsi dan tasan cewa idan har tace ta barshi yayi yanda yake muradi tofa matsala za'a samu d'an sauk'in da take jin ta samune zai k'ara rura mata shi ta yanda duk wanda ya kalleta saiya san ta kwanta da miji, Tofa anata wannan budurin ne shi ya dage akan cewa kad'an kawai zaiyi bada yawa ba ita kuma tana bashi hakurin cewa ya rufa mata asiri ya bari har zuwa dare tukun shine suka farajin dukan k'ofar da Hajiya keyi, Badan yaso ba dole ya d'agata ya shiga cikin bayi yayi tsarki ya kuma wanke fuska yana fitowa ya maida jallabiyar jikin shi ya fice daga d'akin yana mitan waye yazo musu gida da sanyin safe. Mik'ar da Meenal din tsaye Hajiya tayi jujjuyata ta dungayi tana bin jikin ta da kallo kamar dai tana neman wani abunda babu a jikin Meenal d'in, "Taka zuwa bakin kofar can inga yanayin tafiyar ki" cewar Hajiya tana ma meenal nuni da kofar bathroom din dake cikin d'akin, "Hajiya ni lafiyata kalau fa"ta fad'a tana turo baki, waiya Hajiya takeyin hakane ita wallahi duk sai takejin kunyar Hajiyar yana kamata, "Karma ki wani raina ma kanki wayau ance miki ban gane mijinki ya kwanta dake bane a daren jiya" "Innalillahi kai Hajiya dan Allah ki dena maganar nan"ta fad'a tana rufe fuska kunya duk ya rufeta, "Inba keba ai wallahi banyi zaton cewa akwai macen da Abdul zai kwanta da ita washe gari ta iya mik'ewa gadagal haka yanda na ganki ba, sannu jaruma" Juyawa Meenal tayi fuu ta fice daga d'akin dan taga alaman yau Hajiya sai an ma bakinta farsa da ruwan zafi, "Ai tafiya zakiyi ki barni daga na fad'i gaskiya? To kunyan uban me kuwa ya miki saura nawa da zakiji bayan daga ke har shi babu wanda baiyi ma wanka a cikin ku ba, kinga ko ai nasan komai" A bakin kofar Meenal ta had'u da Larai wacce ke tsaye tana dariyar rikicin Hajiya da Meenal d'in, "Ina kwana" "Lafiya lau Amarya ya gajiyar biki?" "Wani gajiya kike tambaya Larai bayan gashi nan kingan ta ta mik'e gadagal kamar dai ba amaryar data kwana da miji ba, Muje d'akin ta ki tayani gyaran shi kafin bak'i su fara sallama dan haka suka bar d'akin a yamutse wallahi abudai ba kintsi" "Nidai wallahi bance kowa ya biyoni d'akina ba zan gyara abuna da kaina , wama yace ana shiga ma mutum cikin daki idan baya nan ne?" Ta waiwayo tana tambayar Hajiyan, "Ke dallah yi takanki baki ma gode allah da yasa kina dani ba, Inba ni din ba wa kikaga ya nemi inda kike? Kuma kibar shiga d'akin nan ki sauka k'asa ki karya ki dawo nan ina jiran ki kizo ki shirya mu koma can sashe na" "Sashen ki kuma Hajiya Amaryar da aka kawo jiya?"Larai ta tambaya, "Oh so kike Inbar mishi ita ya idasa aikata nufin shi a kanta tun bak'i basu watse ba? Ah ah wallahi kafata kafarta tunda dai Allah yasa ta samu ta tsallake rijiya da baya ai tayi barka," "To in haka ne ai ina ganin sai ki bari zuwa dare haka dai Hajiya bawai tun yanzun da safen nan ba" Kasa Meenal ta sauka ita kuma Larai ta shiga cikin d'akin Meenal din ta fara kimtsa shi Hajiya kuma na ware kayan da Meenal din zata sa, *a gurguje* Misalin k'arfe 11 na safe su Sultana suka iso sashen Meenal zuwa wannan lokacin kuma tuni Amarya ta shirya tsaf harma ta fara amsar bak'i bisa jagorancin Hajiya da tayi tsaye sai da taga komai ya kammala kafin ta tusa k'eyar AK suka bar sashen, "Amarya ta Ango"Maryam tace, Ita kuma Sultana ta amsa mata wakar da cewa "Ango na Amarya ya allah ka barsu suyi zaman so da kauna" "Nidai dafari kafin ince komai a fara fito min da kazata tukun dan ita ta kawoni" Maryam ce ta fad'i hakan tana dafa kafadar Meenal wacce ke zaune a kan kujerar gaban mirror, "Ke Sister bar batun kaza ni da nazo in ma Amarya gashi shine dan bakin ciki na ganta rass abunta, Wannan wani irin rayuwa ne yanzun Meenal haka kika zab'i ki kwana da fushin Allah a kanki mala'iku na kwashe miki albarka saboda wulakanci, kenan dai hanashi kanki kikayi duk wa'aza da jan kunnen da iyaye suka miki" Moon takai karshen zancen cike da jimami dan kafin su iso gidan babu kalar musun da basuyi ba a tsakanin a zaton su zasu zone su isketa a kwance tana jinya taji maza, Banza dasu Meenal tayi bata kulasu ba dan tasan so suke ta kulasu su samu abunyi ita ko bazasuji mutuwar Sarki a bakin ta ba, "Wai Madam ina kajin suke?"Maryam ta k'ara tambaya, "Suna cikin kitchen"ta ansa mata, "Wanne daga ciki na k'asa kona nan sama?" Maryam ta k'ara tambaya, "Wannan na saman"tana rufe baki Maryam da Sultana suka fice zuwa kitchen ita kuma Moon sai ta matsa inda Meenal, "Kina lafiya dai koh?" "Lafiya ta kalau mana me kika gani?" "Ah ai aiko banga komai ba dole in tambaya, ya kamata kuma ki koma k'asa saboda bak'i masu zuwa ganin d'aki nan d'in sirrin kine bai kamata kowa yayi ta shige da fice anan ba, ki d'auki abubuwan da zaki buk'ata ki koma cikin d'akin dake k'asa zuwa dare sai ki dawo nan" Meenal din batayi musu ba ta d'auki kayan da zata buk'ata suka koma k'asan ko su Maryam da suka gama dindimen kajin su d'akin kasan suka dawo suka samesu tare kuma suka baje sukaci kajin har da ita Meenal din Meelat ma tace su jirata ta iso aci kazar da ita amma sukace bazasu iya jira ba sun dai ware mata nata a gefe, Sosai Meenal ta sake a cikin su sukaci gaba da hira tana kuma k'arbar bak'i ciki harda yan gidan su yayyen ta mata da suka biyota da sauran kayan ta wanda ba'a kawo gidan ba, Da yamma bayan jama'a sun ragu dan hatta da bak'in da suka cika gidan yawanci duk sun koma inda suka fito, Zaune suke sun zagaye farantin jolof rice suna ci, "Meenal kin shirya inyi miki wata gulma?" Maryam ce ta tambaya, Su kuma sauran suka amsa da cewa "Aiba Meenal ce kad'ai keson jin kanun labarai ba harda mu muma!" "Gulmar wa kika samo mana kuma?" Meenal ta tambaya tanaci gaba da cin abincin ta, Sai da Maryam din tayi dariya son ranta tana kallon Sultana wacce ta kakkafe Maryam din da ido tana mata alamun dan Allah tayi shiru, "Kan uba lallai nema Sultana wato idan gulmar wani ne kece chairlady amma yau da abun ya juyo kanki shine baki son a sani to wallahi baki isa ba sai na fad'a kuji min yar tsanar nan fa" Maryam ta fad'a tana hararar Sultanan, "Ai ko baki ba kanki wahala ba ni daga ke har ita kallon tsaf nike muku wato ita Sultanan tunda ta cokalo zuciyar d'an mutane shine take neman tayi mishi wulakanci, To duk ku gama munafuncin ku aini ko jiya da muka had'u dashi a wajen dinner na fad'a mishi cewa wallahi indai ya shirya k'arya wani saurareta ya wuce kawai kanshi tsaye ya koma wajen Baba Malam tunda ga yanda abubuwa suka kasance ya rasa Meenal to sai suyi mishi madadi da Sultanan," cewar Moon tana hararar Sultana, Hayayyak'owa Sultanan tayi tana mai cewa, "Allah ya tsareni wallahi nikam nafi k'arfin ayi madadi dani, Shid'in wani tsamiyar biri dashi ne zai waniyi madadi dani, Aini wallahi nafi k'arfin shi me ma zanyi dashi yana ji da isa kamar wani d'an Sarki, ke ni kaf Zaria ma fa banga mijin aure ba, ku barni kawai in koma Abuja ko Allah zaisa inyi gamo da katar da wani b'arkeken Alhajin dazai gina min gidan sama in shige abuna sai nayi sati masu aikina dake k'asa basuga kalar fuskata ba" ta k'arasa kalaman nata da k'arkato d'aurin kanta zuwa gaban goshi, "Aiko dai wallahi an mata kinyi karya kice Bash bai burge ba, sai dai kawai kice kina so kina kaiwa kasuwa" Meelat ce ta amsa musu yanzun, "Wai bash ne yace yana son Sultanan?" Meenal ta tambaya, "Kwarai kuwa ke koh ai Sultanar mu bata wasa bace dole in namiji ya kalleta gaban shi ya fad'i bari kiji in baki labarin abinda ya faru ranar da aka d'aura auren ki da yamman yarinyar nan bata huta ba sai da ta cire number din shi a cikin wayar ki, Video d'in zaman da akayi a falon Malam dana d'aurin auren ku duk ta kwasa ta tura ma Bash din bayan ya Sa'eed ya turo mata video din kamar yanda ta buk'ata, Dan allah kuce yarinyar nan ba kashe d'an mutane taso yiba?" "Ke Sultana meya kaiki inda ace da kika tura mishi bayan ya bud'e wani abu ya same shifa?" Cacaca sukaci gaba da surutu kowa dai cewa yake Sultanar bata kyauta ba ita kuma ta had'e fuska tasha kunu abinta, Meenal ce kad'ai bata tofa komai ba tana dai bin su da kallo ne kawai, "Sai me ya faru kuma daga nan?" Moon ta tambaya, "Yauwa to bayan ya gama kallon video din shine ya k'irata dan yaji ko waye ya turo mishi video din tunda ai shi dai bashi da number din ta, duk da yace min ya kwada number din a true caller Sunan Amina ne yayi appear a wajen amma bai tabbatar da cewa ita bace sai da ya k'ira, Ita kuma bayan ta gama jan ajinta kafin ta d'auki wayar data d'auka sai tambayar shi tayi cewa congratulations kaga sakon dana turo maka?, Ai dama nace maka an kasa ka toga tabbas nan ka gani basai na tsaya maka dogon zance ba, Shi kuma sai yace mata oh kece Amina Sultana koh?, Kwarai nice dai ashe ka gane ni, Na taya yar uwar ki murna sosai ina kuma fatan Allah ya basu zaman lafiya ita da mijin ta, ke kuma ina miki albishir kamar yanda kika min dan kema ki shirya nan da kwana kad'an zaki zama Amarya mallakin wani kamar dai yanda itama a yau ta zama mallakin mijinta, yana gama fad'a mata haka sai kawai ya yanke wayar shi abinshi, Ita kuma bata wani damu ba sai kawai taci gaba da harkokin ta, daga nan shi kuma sai ya taso rayuwarta a gaba da yawan kira da sak'o dan a daren da sakon ta na auren Meenal ya riske shi shi kuma ya yanke shawarar yin ma Meenal madadi da ita dan haka washe gari ya kirata, ya fad'a mata cewa sonta yake yi fa kuma daya ce ta shirya ma nata auren bada kowa yake nufi ba sai dashi, Haka ta rufe ido ita kuma ta tsitsigale shi kamar dai yanda ta saba hakan kuma baisa ya gajiya ba haka yaci gaba da bibiyarta kuma ko jiya yaje wajen dinner ita Sultanar ce ta hanashi shiga nima acan na ganshi kuma duk shi ya bani labarin komai ni kuma nace mishi ya tura wajen Malam kawai karya b'ata lokaci," "Munasira wato shine take ta nokewa dan karmu sani mu tayata murna to wallahi nidai na bashi, ko ku baku goyi baya ba kuwa" Meenal ta fad'a tana kaima Sultana duka, Haka suka tasa Sultanar dayau bakin ta ya mutu murus gaba suna tsokana. Da dare Hajiya na idar da sallan ishsha'i ko hijab bata cireba ta kama hanyar sashen su Meenal bata jira komai ba ta taso k'eyarta suka koma sashen Hajiyar, AK ko tun barin shi sashen nasu da safe bai k'ara komawa ba dan ko abokan shi da zasuyi sallama da Meenal Sadeeq ne ya musu Jagora, Da dare yayi koda ya shigo rashin ganin ta a falon k'asa bai d'aga mishi hankali ba sai dai ga mamakin shi a saman ma dai shiru ne duka d'akunan ya duba bata nan, hakan kuma bai sa ya wani damu kanshi ba sai ma bathroom daya shige yayi wanka yana fitowa yayi shirin bacci lokacin karfe 11 harta gota, Dakin ta ya koma dan yasan zuwa yanzun duk inda ta shiga ya isa ace ta dawo ta nemi makwanci amma koda ya duba bata babu alamarta, To ina take? shida yayi tambayar shi ya ba kanshi amsa da cewa sashen Hajiya, dan haka can ya nufa amma koda ya isa wai har sun rufe k'ofa ta baya yabi Allah ya taimake shi basu kulle kofar kitchen ba dan yana turawa yaga ya bud'e, Da kwarin gwuiwa ya shige ciki dan so yake ya ritsa yarinyar nan ta fad'a mishi dalilin ta na dawowa nan ta tare, To data dawo nan tana nufin shi kad'ai zaici gaba da rayuwa acan ne? Falon dund'um yake da duhu dan haka sai yayi amfani da torch light din wayar shi ya haska ya haura zuwa saman, Kamar wani b'arawo haka ya dunga sand'a d'akin hajiya ya fara lek'awa ya hango ta nannad'e cikin bargo sai kwasar baccinta takeyi abunta, Maida kofar yayi ya rufe ya k'arasa d'akin Meenal k'asa² yayi sallama a yayin shigar shi cikin d'akin yana binta da kallon mamaki, yayi zaton zai sameta tana bacci ne amma wai sai gata zaune a tsakiyar gado dangalgal sai wasu d'irka²n littafai irin nasu na likitanci dake gefen ta d'aya kuma yana rik'e a hannun ta tana karantawa rigar shimi singilat ne a jikinta da wani burmemen siket ne ko wando bai dai tantance ba, Daure fuskar shi yayi tam a yayinda yake k'arasawa inda take karma taga damar shi tace zata raina shi, Itama din kuma da kallo kawai take bin shi tun shigowar shi dan dama ita jikinta ya fad'a mata cewa wallahi sai ya biyota nan d'in musu ne kawai bata so tanayi da Hajiya shi yasa ta biyota suka taho tare, Tun bai kai zaune ba ya jefo mata tambayar dake cikin bakin shi, "Me kikeyi anan har k'arfe 11 na dare ya wuce baki koma sashen kiba?" "To ba Hajiya bace taje ta taho dani" "Ban gane cewa ta taho dake ba, ta taho dake kamar ya?" "Oho nima ban sani ba ta dai ce anan zan zauna" "Ke dallah ban son rainin wayau tashi ki wuce mu tafi" "Ai dai kana gani karatu nikeyi kuma yanzun kawai sai in bika mu tafi Hajiya bata sani ba," "Kambala'i! Eh lallai bakya neman zaman lafiya yarinyar nan shin to wai ma waye mijin ni ko hajiya?" Shiru tayi bata amsa shiba shi kuma sai yasa hannu yahau tattara takardun data jibge akan gadon yana mai dasu mazaunin su, "Tunda anan kike son mu kwana yau ai shi kenan"ya fad'a a yayin da yakai zaune a gefen ta ita kuma sai ta matsa, "Nidai ka tashi ka fita in ma anan sashen zaka kwana ai naga dai kana da naka d'akin a kasa ka sauka ka koma can nidai kar Hajiya taji motsin ka" "Ke wai ya kike korona ne, miye in Hajiya taji motsina bafa kwartanci nazo yi ba wajen matata nazo, Inma dai bacin an raina ni taya daga kaimin Matar jiya yau za'a wani d'aukota a dawo da ita nan,tunda kin zab'i zaman nan ai gani nima nazo" "Wai anan kaima zaka kwana?" "Kwarai kuwa tsorona kike jine? Naga dai tsakanina dake kuma ai babu wani abu da yayi saura me ya rage kuma bayan jiya babu abinda ya rage ban gani kuma na tab'a shi da hannun nan nawa ba"ya fad'a yana d'aga hannayen nashi, "Nidai dan Allah ka tafi ai gobe da kaina zan koma can d'in" "Ah ah ai kuma na fasa nima na shirya yin mak'otaka da Hajiya kinga ita tana can tana bacci mu kuma gamu anan zamuyi gabatar da bauta"matse mata waje yayi bayan ya sak'ala hannun shi ya rike kugunta ta gefe, "To yane kin shirya?" Muryar ta na karkarwa ta amsa mishi da cewa, "nidai gaskiya indai anan din zaka kwana to tsaya kaji, babu runguma kuma ba kiss bacci kazo yi ka kwanta ga waje nan kaga dai aini karatu nikeyi koh?" "Ke wai ni zaki kafama wasu sharud'anki na banza? To bari in gani waye mai taurin kai a tsakanin mu biyun," K'arfi yasa ya maida ta zuwa baya shi kuma ya haye saman ruwan cikin ta yana kissing sassan jikinta yana kuma mata cakulkuli a lokaci d'aya, Duk yanda taso ta rik'e dariyar ta gudun kar Hajiya ta jiyo su hakan ya gagara, babu shiri ta dunga kyalkyala dariya shima yana tayata, "Waiyo Allah Yaya dan Allah ka bari kar kasa dariya na ya k'are" "Oh Yaya ma kike cewa ko? Wato dai har yanzun ban kai matsayin da zaki sauya min suna zuwa mai dadi ba, to bazan bari ba yau sai kin kirani da daddad'an suna" "To Kayi hakuri ka zab'a da kanka ni kuma zan kira ka dashi" "Naki wayan kedai zaki zab'a da kanki" ya fad'a yana cigaba da aikata aikin daya sa kanshi, "Honey" "Ah ah ba dai honey ba" "Sugar to" "Sugar kuma ana zaune kalau tea zaki sha?" "To sweetie" "Shima bai min ba" haka yasa ta ta dunga jero mishi sunaye amma duk wanda ta kira sai yace bai mishi ba ta canza wani, "To dan Allah kai kana tayin abu kamar dai Baby" "Wow what a nice name, kinga kenan daga yau na zama Babyn ki nidai hakan ya min" "Ah ah nidai ban yarda ba gaskiya taya kawai k'aton ka dakai sai in wani kiraka baby kuma ka amsa" Ihun dariyar sune ya tashi Hajiya daga bacci bayan ta farka ta d'an jima a kwance tana son ta tantance daga ina dariyar yake fitowa ko dai cikin bak'in da akayi ne wani ya kawo mata tsarabar aljanu masu dariya, Jin dariyar yaki d'aukewa ne ta mik'e ta sauko daga gadonta tana karanta ayatul kursiyu a bayyane ta bud'e kofar d'akin ta fito, Hasken wuta ta hango daga cikin d'akin meenal kuma daga nan takejin dariya dama k'ananan surutai, "Wai yaron nan biyo yarinyar nan yayi ita kuma munafukan ta bud'e mishi kofa ya shigo suke min iya shege a cikin sashe?" Kofar d'akin ta fara bugawa, "Kai Abdul tattaro Matar ka kuzo ku barmin sashe bazaku hanani baccin dare ba wallahi, Ke kuma badai ni zaki juya ma baya ina tausaya miki ke kuma bakyajin tausayin kanki ba? Da kaina fa na kulle kofar falon nan saboda dama nasan tabbas zai biyo sahu wato shine ya kiraki kikaje kika bud'e mishi kofar ya shigo, to ku tattaro ku wuce can ku k'arata" Shi dama ai da gayya ya aikata abunda yayi dan haka babu b'ata lokaci yama yar Matar shi d'aukar chak ya sauketa akan gadon, "Ka gani ko shi yasa ai nace ka koma, ka koma kai kuma kak'i tafiya gashi nan ai kaja ta ritsa mu" Bai kulata ba sai da ya ciro Hijab yasa mata kafin ya k'ara mata daukar cak tana wutsul² da kai mishi duka akan ya sauketa yak'i sai ma gyara rikon ta da yayi ya bude kofar ita kuma sai ta cusa fuskarta a k'irjin shi saboda kunyar Hajiyar daya rufeta, Duk surutan da hajiya keyi bai tanka taba har suka sauka k'asa ya bude kofar falon sai da ya fita kafin yace da Hajiya " Hajiya sai da safe kuma dan Allah goben nan dai in Allah ya kaimu a raye kar ayi saurin zuwa kawo mana breakfast da sassafe idan mun tashi zamu zo mu amsa" Yana gama fadar hakan ya wuce abinshi yabar Hajiya naci gaba da sababi, "Wani shegen ka ajiye dazai muku girki? Ai kuma kunyi da y'a wallahi bacci kuma idan k'unso ku yini goma kunayi jarababbu kawai". *UMMIEE CE*✍🏼 [10/18, 3:06 PM] Ummiee Zaria: ⚜️🔱👨‍👩‍👧‍👦 *DANGINA*👨‍👩‍👧‍👦🔱⚜️ *BOOK 2* *INA MAI CIKE DA FARIN CIKI A YAU DA ALLAH YA BANI IKO NA GANIN NAKAI K'ARSHEN WANNAN LABARIN MAI SUNA A SAMA* *NAGODA KWARAI GA MASOYA WAD'ANDA SUKAYI JIMIRIN BIBIYAR LABARIN TUN DAGA LITTAFI NA D'AYA HAR ZUWA YAU, KU SANI CEWA UMMIEE ZARIA NA KAUNAR KU KUMA NA YABA DAN HAKA NIKE MA KOWA FATAN ALKHAIRI,INA SONKU³ SAU A DADIN DA BAKI YA GAZA FURTAWA YAN GROUPS DINA FAMILY HOUSE DA DANGINA COMMENT SECTION DAMA SAURAN GROUPS NAGODE KWARAI INA FATAN ALLAH YA HAD'AMU A GABA CIKIN AMINCIN SA* *BAYAN WASU KWANAKI* Amarci sosai ake gurza tsakanin AK da Amaryar shi wanda tun Hajiya na yawan surutu in taga sunyi wani abun har dai yakai dan dole ita da kanta ta gaji ta shafama kanta lafiya ta kawo ido ta zuba musu, kuma dan wulakanci basu tashi barbad'a ruwan rashin kunyar su ako ina sai sunzo sashen ta, tayi kora harta gaji amma sunk'i suyi zuciya su dena zuwa mata sashe, dan haka ta taso AK d'in a gaba da mita cewa yayi da jiki ya kammala gyaran gidan shi na Kaduna ya kwashi matar shi subar mata gida ita bazata iya gani ba dan kar suja mata makantar wuri, shi kuma yace mata barin Zaria ba yanzun ba har sai sun bar mata d'an raino dan in suka bar gidan tun yanzun ciwon kewar su yana iya kamata. Acan unguwar malamai ko maganar gidan Malam da Meenal ta bashi ko ana watse bikin Meenal d'in yaran gidan mazan su da mata kowa ya bada nashi gudun mawar wajen sanyama gidan kayan furniture da sauran su ana kammala gyaran gidan kuwa suka shirya walima gangariya Malam yanaji yana gani dai haka shida iyalan shi suka koma sabon gida aka bar Baba Adamu da Baba Auta a family house suda sauran ahalin, Soyayya tsakanin Bash sa Sultana kuwa abu dai kamar wasa tun tana basar dashi tana nuna ita batayi har dai da taimakon su Meelat, Maryam, Moon da ita kanta Meenal din wanda suka tayashi yak'in neman zab'e a fadar Sultanar daga k'arshe dai sunci nasara ta amsa sai gashi a hankali abubuwa sun kankama dan koda Bash ya k'ara tura iyayen shi wajen Malam a karo na biyu Malam bai b'ata musu lokaci ba a gaban iyayen nashi ya kira Sultanan ya zaunar ya kuma tambaye ta shin ko tana son Bash d'in? kuma da yardar ta ya turo a nema mishi auren ta?" Bata tsaya ba sharia wahala ba itama ta amsa da cewa eh, bayan ya sallameta tabar falon mahaifin ta ya kira ya mishi bayanin halin da ake ciki kuma yarinya ta amsa cewa eh tana so dan haka yana so a basu dama suje can Abuja su nemo auren ta, Alhaji Mahmoud yaso ace Malam ya zartar da komai amma sai Malam din ya zame akan gara dai ya basu ranar da zasu je shi sai yayi ma iyayen bash din jagora, To dai da yike magana ne na manya babu wani kolo² ya basu ranar da zasuje dan haka iyayen Bash suka bar gidan Malam cike da farin ciki *wannan kenan*, Itama Maryam a gefen ta ana gama bikin su AK Sadeeq ya sata a gaba da cewa shima fa a yanzun ya fasa wani jira har saita kammala karatun, Tunda dai yan watan ni ne suka rage musu kawai tayi hak'uri ta k'arasa a cikin d'akin ta itama kamar dai sauran kawayen ta, Taso ta bujire sai dai da wuri ya taka mata burki wajen kai maganar gaban manya babu b'ata lokaci kuma aka sa bikinsu sati d'aya tsakanin su da nasu Moon ita kuma Sultana bayan zuwan su Malam Abuja wata d'aya kachal akasa nata bikin dan haka nasu Sultanan za'a farayi kafin nasu Moon da Maryam d'in, AK tuni ya koma KD yaci gaba da gudanar da abubuwan shi sai dai yanzun a maimakon weak ends da yake dawowa zaria sai ya mai dashi duk bayan kwana d'aya ko biyu, wani lokacin ma bazai fad'a mata cewa yana hanyar zuwa ba sai dai kawai ta ganshi kwatsam duk da bako yaushe yake tareda ita ba hakan bai rage komai na daga kauna da kulawar da suke ba junan suba. *** Bayan wani lokaci da bikin su Meenal hutun yan makaranta ya k'are dan haka bak'in gidan Hajiya suka fara haramar komawa gidajen su akan sai bikin Moon kuma idan Allah yakai rai zasu dawo, Dan haka ana gobe zasu tafi suna zaune a falon Hajiya suna hirar dare Hajiya ta kawo nata batun da cewa, "To dai gashi naga sai shirin barin gari gobe kukeyi amma kaf cikin ku har yanzun banga wanda ya dunk'ulo yan kud'ad'en shi yace min Hajiya ga wannan gudunmawa naba," "Gudun mawar me kuma Hajiya? Akwai wani sha'anin da za'ayi ne bamu da labari?" Baba Usman ya tambaya Amsa mishi tayi da cewa, "Sha'ani kai ! inace nan har akaci aka sid'e bikin d'anku babu wanda a cikin ku hankalin shi ya bashi cewa bari ya bani gudun mawa zan aurar da jikata ah ah ko koh dan kuma kuna aurar da d'a, shi kenan ni kuma bazaku bani nawa gudun mawar na auren jikata ba, In takamar ku shine kun ba uwarta gudun mawa naga dai uwarta daban ni kaka marigiya daban, Kuna ganin dai yanda suka bugi k'irji suka gyarama yarinyar nan takwarata sashenta komai acan acan wallahi babu ne kawai basu siyo sun kawo ba, To yanzun kuma dashi naku d'an ya kammala ginin gidan shi so kuke in saka ido su iyayen nata ne zasu k'ara zuba mata kaya a cikin wancan gidan shima?" "Hajiya nifa na riga nayi oder d'in komai da za'asa a cikin gidan ban fad'a miki bane dama naso sai komai ya kammala sai in kaiki ki duba abubuwan da babu sai a k'arasa kafin mu tare acan..... "Cewar Ak Katseshi Hajiya tayi da cewa, "Kai dallah can matsa bani waje ina magana da iyayen ka kana samun baki ko kaji na kira sunan ka a zance nane?, In kayi hakuri ai dana gama dasu kanka zan dawo ko ce maka akayi na manta da kaine? Da kake zancen sa kaya a gida kuma Allah ya kyauta jikata ta dogara da kayan da miji ya siya salon wata rana kai ko yan uwanka kuyi mata gori ah ah wallahi," "Haba Hajiya waye zai mata gori kuma?"AK ya tambaya yana b'ata rai, "To bari kaji in ma siya zakayi sai dai ka tabbatar da cewa da sunan ta ka siya, kayan nata ne halak malak ta yanda ko yau ka fad'i ka mutu babu mai sanya su cikin sahun kayan gado atoh namiji kuma da gadara ko koh salon in yan uwanka suka san cewa kaine ka siya su dunga zuwa gidan suna mata abubuwa isa²? halin dangin miji kuma ni wanne ne za'a layance min ni Aminatu" Umma ne ta amshi zancen da cewa, "Hajiya ai ba laifi bane idan yace zaisa kayan daya siya a gidan tunda ai koda ace aure bai had'asu ba shid'in ai yana da halin da zai d'auke ma iyayen shi kayan d'akin k'annen shi mata kuma ita Meenal din ai bata da banbanci da kannen shi tunda dai Jidda ce ta haifeta kamar dai sauran jikokin gidan" Katseta Hajiya tayi da cewa, "Shi yasa ma nima yanzun a gaban ku na shaida mishi cewa zai zuba kayan ne da sharad'in cewa kayan mallakar meenal ne ba nashi ba, Yo nawa akayi da zarar k'addarar da ba'a fata ta gifta tsakanin miji da mata sai gori ya tashi, ko kuma in mijin ya mutu yan uwa sai suzo suyi bake² suna kurin cewa ai nasu ne ya siya kayan ba daga gidan su ita matar ta kawo ba, Kuma ni koma dai menene bazai hanani amsar kudin gudun mawa a hannun kuba garama ku had'a ku bani tun yanzun basai zuwa gaba idan wasu hidimomin sun taso ku fara min kame² ba ni ban yanke ko nawa nike buk'ata ba balle kuce na tsanan ta kar kuma mutum ya fara nufo ni da wasu yan kud'ad'en da basu fi k'arfin in dunkula inyi kyautar su tashi d'aya ba" Yanda Hajiya ta kafe dole sai da kowa ya sauke mata nashi gudun mawar mai nauyi in ma baka da cash zatace kayi mata transfer, Wadanda kuma sukace sai sun koma zasu tura mata tasa an rubuta mata sunan su a cikin yan bashi, Bayan tafiyar mutanen gidan kuma tabi AK har can Kadunan inda suka tafi tareda Hassana suka duba sauran abubuwan da gidan ke buk'ata aka siyo akasa, sai dai koda AK ya tambayeta akan yaushe Meenal zata tare anan din sai cewa tayi wani tarewa kuma ai hak'uri kawai zaiyi daga nan har zuwa lokacin bikin Moon zuwa lokacin itama Meenal ta gama jigilar zuwa makarantar da takeyi in yaso sai ta dawo gaba d'aya. Haka rayuwa yaci gaba da gudu babu k'ak'kautawa, Raheenat ta gama wanka tuni dan haka Malam yace ta dawo gida tunda dai ai ba zaman takaba zatayi ba, dan haka ya tura aka d'aukota ita da kayanta tana kuka mutanen gidan nayi haka suka rabu tunda mai rabawa ya raba, Bayan komawar ta Zaria a lokacin ne shi kuma kanin mijin ta ya bijiro da batun cewa yana son Malam ya bashi auren ta saboda ta koma taci gaba da kula da d'an data Haifa dama sauran da suke wajen shi a Abuja, Malam baik'i ba sai dai ya nemi jin ta bakin Raheenat d'in a zaton kowa sun d'auka zatayi murna da hakan kodan saboda rik'on yaranta sai dai ita kuma ta buga k'asa akan cewa bata auren shi, Kuma yarama da ake magana ai tun kafin uban su ya mutu ya kwashe su ya basu shida matar shi tana musu fatan Allah ya tayasu rik'o, Dan kowa yaga yaran yasan basu rasa komai a wajen suba dan dashi da matar shi sun rik'esu kamar sune asalin iyayen su ba Raheenat da marigayi ba, sai yanzun dan k'asa ya rufe idon mijin ta shine shi k'anin shi zai lallab'o yace wani wai zai maye mata gurbin yayan shi saboda yaran ta, To inda ace kuma itace ta mutun ba mijin bafa?dole dai ai a gefen uba yaran zasu rayu Haka dai akayi ta cakalkala zance dan dole dai kowa ya shafama kanshi lafiya bayan abubuwan sun lafa ne kuma Ya Abakar tsohon saurayin Raheenat d'in ya yunk'uro ya fara nuna kulawan shi a kanta da d'an da take goyo duk da cewa bawai ya fito mata fili akan yana son maida Soyayyar su na baya ne sai dai duk mai hankali in ya kalli abun yasan me ake nufi, shima dai tun bayan daya rabu da Raheenat din a wancan shekarun k'asar ya bari yaje yana cigaba da k'aratu bai dad'e sosai da dawowa ba kuma tunda ya dawo ake mishi zancen aure amma bai maida hankali ba can Abuja yake zaune a yanzun haka yana aikine da central bank, To dai zamu iya cewa tsohuwar soyayyar da aka binne ce ake kokarin tono ta domin shi dai bayan da yaga cewa boye boye bayayi dole ya fito tsaya tsayin daka cewa yaji ya gani Raheenat dai yake so bai damu da cewa ai tayi aure harda rabon yara uku ga kuma wani tana shayarwa yanzun ba, Shifa a yanda yaso so yayi a d'aura auren su ta tare a gidan shi taje can taci gaba da rainon Umar sunan yaronta wanda sukai ma lakabi da Khalifa itace tak'i akan ya daiyi hakuri ba yanzun ba har sai ta yaye, Sultana ma ta koma Abuja inda ake ta shirye shiryen gabatar da bikin ta dan acan Abujan za'ayi komai kuma acan zasu zauna ita da Bash d'inta, *Bari mu lek'a gefen Teemah matar Sarki* Tun bayan tarewar ta a sabon gida babu wani abu wanda yake d'aga mata hankali domin dai ko babu komai gata tare da yayan ta wadanda a yanzun ne take k'okarin nuna musu kulawa dan ta gyara kuskuren da tayi a baya,dan bayan dawowar su hannunta sam haka sukak'i sakin jikin su da ita kamar dai ba uwar data haife suba, babu shiri ta fara kokarin jansu a jiki ta hanyar daukan su su fita shopping a tare ko wajen wasannin yara, wani lokacin ma tare dasu take kwana a d'akin su, Da Alama dai kamar yanda tace ta tuba to tuban na gaskiya tayi bawai tuban muzuru ba dan wallahi sosai ta canza halayyanta da kuma yanda take mu'amala da mutane a yanzun, Bata da damuwar komai dan babu abinda Sarki ya rageta dashi na daga soyayya da kulawar da yake bata sai dai lafiyan jikin ta ne kawai da yayi k'aranci yau lafiya gobe ciwo laulayi dai irin na masu ciki a haka dai take jurewa tana kula da iyalan ta iya iyawarta, A sanda zancen neman auren Sarki ya bayyana a cikin dangi kowa ya sani yan gulma sun so sukai mata labarin kamar yanda suka saba labarta mata abubuwan dake gudana a cikin ahalin tun ma tana zama a Lagos, Sai dai abinda basu sani ba shine tun a ranar da brigadier ya sauka a kadunan kafin su isa Zaria gidan ta ya fara biyawa ya sauka shida abokan shi, Ya kumayi amfani da wannan damar wajen yima ita Teemah din nasiha a matsayin shi na mahaifin ta, Ya lissafo mata tarin damar makin data samu a baya amma tayi fatali dasu saboda kawai tana tak'amar cewa mijin ta yana sonta yana fatan cewa a yanzu zata an kare wajen ganin ta gara kurakuren ta dan samun nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali, dan yana sane da yanda tayi amfani da son mijin ta gareta ta taka mishi darajar Dangi ciki harda iyayen shi, Ya kuma bud'e mata gaskiyar zancen cewa kar tayi zaton ko jama'a basu san abinda ta aikata na ganin ta tarwatsa auren da mijinta yayi a baya ba, Ah ah kowa ya sani an dai juyama zancen baya ne saboda darajar su iyayen ta da kuma yayan data haifa, Amma kar tayi zaton ko dan ta aikata hakan shine zai hanashi k'ara neman wani auren tama gode Allah da yasa har yanzun mijin nata bai canza daga matsayin daya bata a baya ba sai dai ta sani yanzun hakan ma zancen auren mijin nata ne ya kawo shi garin shine kuma wanda zai jagoranci auren, Ya kumayi mata nuni da cewa taji tsoron Allah wannan karan kartace zata k'ara jefa kanta ga aikata shirka domin dama ne Allah ya bata nata gyara kuskuren data dad'e tana aikatawa, yanzun ne lokacin da zatayi yak'i da tsohon halinta na mugunta da kuma son kai, kar tace zatayi mugunta domin dai in muguntar da tayi bai dawo kanta ba tofa yana iya afkawa kan yayan data haifa dan gasu nan dai har sun fara zama yan mata, sannan babu laifi mai girma irin shirka ta duba ta gani cewa da tana da cikakkiyar lafiyar da take gudanar da rayuwar ta yanda take so amma sai gashi a yanzu dududu wata nawa ne data nemi lafiyar nata ta rasa? Aiko wannan ya isa taji tsoron Allah tasan cewa shine ke tsarama bawa kaddara ta faru kuma a yanda shi Allah yaso tunda gashi rabuwar Sarki da Meenal hakan bai hanashi yace zai k'ara neman wani auren ba kuma tayi hankali idan har tace zata matsa ko kuma ta tada hankali k'aramin aikin ubangiji ne ya kauda ita a cikin duniyar kuma mutuwar ta bazai sa a fasa komai ba iya kacin bayan an haka k'asa an burneta ayi zaman makoki na kwanaki kadan bayan hakan kuma shi dai mijin bazai fasa auren ba sai ma hujja na k'arin auren daya samu tunda dai ko babu komai dole zai auro wacce zata kula dashi da yaran shi, ta rufa mishi asiri domin yanzun idan tace zata d'aga hankalin da wani abun zai sameta bayan hawan jinin da take fama dashi na masu ciki tofa su iyayen ta da y'ay'anta su zasufi kowa kokawa dan su sukayi rashi mafi girma sab'anin sauran al'umah, Sun mata nasiha da jan hankali sosai shida abokan shi akan tayi hak'uri karta d'aga hankali, ta sha kuka sosai harta gode Allah dan Allah ya sani bata tab'a hasaso cewa wai Sarki zai k'ara batun wani auren a yanzun ba, ta d'auka cewa shi kenan ita da kishiya sunyi hannun riga ashe akwai sauran rina a kaba to haka dai itama Mahaifiyar ta ta kira tayi ta bata baki har suka samu ta sarara dan duk tambayoyin da uwar ta mata akan ko taga wani canji daga wajen Sarki ita dai bataga wani canjin daya mata ba yana nan kullum a matsayin Sarkin ta mai sonta ako wani yanayi tayi alkawari cewa insha Allah zata daure zuciyar ta wannan karon bazata yarda tace zata koma bin ko wani boka ko Malam akan wannan auren ba tana kuma fatan Allah ya yafe mata tarin laifukan ta na baya, Zata dai shirya ma zuwar koma wacece zatazo su zuba wacce duk ta iya allon ta ta wanke ai bata da fargaba tunda tasan cewa mijinta yana sonta dan haka bazata d'aga hankalin taba , kodan saboda abinda ke cikin ta wanda aka tabbatar mata da cewa biyu ne take d'auke dasu inko wani abun ya same su ai itace tayi asara ba kowa ba, Dan haka duk kiran da yan gulma suka dunga mata bata bi takan ko d'aya ba daga karshe ma duk watsa number din su tayi a blacklist tayi blocked shegu, Da Sarki ya dawo ma tayi zaton ko zai boye mata sai gashi shi da kanshi ya zauna ya warware mata komai harda alaqar Moon da Meenal na zamowar su yayan wa da kanwa bai boye mata komai ba ya kumayi mata alkawarin cewa insha Allah baza taga ko wani canji a gareshi ba sai dai na alkhairi dan kamar yanda bai wulakanta ta a wancan auren nashi ba wannan karon ma bazai tab'a bari ta wulakanta ba dan shi dai har gobe yana sonta kuma yana alfahari da ita, Koda wasa kartayi zaton ko gazawarta ne yasa yayi sha'awar k'ara aure ah ah dukan su yana son su shi yasa zai zauna dasu yana fatan kuma zata bashi had'in kai wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin su a matsayin ta na babba wato uwar gida sarautar mata. Da lokacin bikin Sultana yazo tun ana sauran kwana uku Meenal taso tafiya can Abuja saboda yan zaria da suka kwasa tunda wuri suka wuce amma sam AK ya murza nashi kambun yace mata bai san wannan zancen ba, Kuma fa shi bawai yana Zarian bane dan a wannan satin yana yana kano ma amma saboda wulakanci ya hanata tafiya wai sai dai ta jira har sai ana gobe biki sai Kabir ya kaisu Abujan ita da Hajiya, tayi naci tayi magiya akan ya barta tabi Maryam su tafi tare amma yak'i dan haka tayi fushi sosai dashi suka koma share juna shi kuma da yaga idan ya kirata bata d'auka sai yazo ya dena kiran nata gaba d'aya, Hakan da yayi kuma sai ya k'ara kuleta wato ma ya nuna mata cewa bai damu da fushin ta ba irin taje tayi tayi din nan ko fushi ta d'auka dashi sosai kamar ta ciji kanta, sai ana jibi biki kafin ya k'ira Hajiya akan su shirya gobe Kabir ya wuce dasu Abuja, Ita kuma Meenal tayi fushi dan haka koda Hajiya ta shaida mata yanda sukayi da AK sai tace bata zuwa bikin ta fasa ai dama ko bataje ba babu abinda za'a fasa taso taje da wuri ne dai saboda koba komai dai ai zancen auren Sultana akeyi ance kuma wanda yayi maka kaima sai ka kamanta, Yanda Hajiya taga ta kafe akan bata zuwa ne yasa ta ja jikin ta tabi gayyar yan unguwar malamai wanda suka rage basu tafiba sai a ranar sukayi tafiyar su ta kuma shaida ma AK cewa Meenal din tayi fushi ita kuma bazata iya tsayawa lallasa mishi mata ba tunda dai ba itace takar zomon ba, Ita ko Meenal tun bayan data tabbatar da cewa Hajiya ta wuce Abuja ta koma sashen ta ta k'ule a d'aki tana kukan bak'in ciki da takaici wai ita AK zaima haka dan kawai yaga an bashi ita a arha, Mai yafi wannan haushi dan Allah dan kawai ana auren ka shi kenan sai ayi tayi maka iko da isa, In ma zaiyi mata iko akan komai ai bai kamata ya mata iko akan wannan ba, Sultana fa Sultanar da itace silar auren ta a ranar da bata shirya ba wato da abinda AK zai saka mata kenan dan kawai ya mata magana akan tarewar ta a KD ita kuma tace mishi bata shirya ba yayi hak'uri har su k'ark'are komai na makaranta inta kallama komai sai ta bishi su koma saboda yanzun zirga zirga zai mata yawa mata shine fa kawai ya wani d'auki fushi da ita, ai yasan tana karatu tun kafin a d'aura auren su ah ah sai yanzun ne yake son tsiro mata da wani tsirfa na daban, To dan Allah nata karatun da shima yasan shine burin ta na karshe da yayi saura take k'ok'arin ganin karshen shine zata tattara ta watsar ta bishi bayan aski ya riga yazo gaban goshi, Wannan ma ai kowa yasan fushin rashin gaskiya yakeyi to yaje can yayi tayi ta hak'ura da zuwa bikin kuma bazata tare a kadunan ba, Sosai tasha kuka ita kad'ai a cikin d'akin k'arin bak'in cikin ma sai da su Meelat suka dunga kiranta a waya dan suji yaya dan tuni ita Meelat tabi Musty Abujan wai har Moon dake Lagos ta isa Abuja tun jiya sai ita shak'ik'iyar Sultanar ce shiru har yanzun gata a cikin garin Zaria hummm Inba aure ba jama'a waya isa, Zazzabi mai zafi ne yayi mata dirar mikiya inda ta dunga kwarara amai tun tana iya mikewa zuwa makewayi tayi har k'arfin jikinta ya k'are takoma yin shi daga kwance anan k'asan tiles din da take mulmula babu komai da yayi mata saura a cikin dan kwana biyun nan sam bata da nutsuwar zaman cin abinci saboda halin da AK ya sanya su na d'auke mata wuta da yayi akan abunda bai kai ya kawo ba, Da kyar ta samu ta iya jan jikinta ta mik'a hannu ta d'auko wayarta, Larai ta fara kira dan tasan Hajiya Jummai bata isa dawowa daga wajen aiki ba yau alhamis Hajiya kuma bata nan Laran ce kad'ai zata iya taimaka mata a yanzun, Da kyar ta samu ta iya lalubo number din ta danna mata kira wayar bata dad'e tana ringing ba ta d'auka, "Aunty Larai dan Allah kizo sashena yanzun bana da lafiya" Ta samu ta iya fad'a da kyar kafin ta yanke wayar, Daga can gefen Larai ko bata jira komai ba ta saki abinda takeyi ta garzayo zuwa sashen Meenal d'in, tun daga k'asa take kiran sunan Meenal din tana tambayar d'akin da take ciki, Ita ko tsabar wahala ne yasa sam bata iya bud'e murya ta amsa ma Laran dan haka sai kawai Larai taci gaba da bud'e kofofin dakunan saman tana dubawa ganin bata a d'akin ta, d'akin dake gefen na AK ta sameta a ciki kwance a kasa babu yanda take, dan haka da gudu ta k'arasa shiga cikin falon, "Ke Meenal meya sameki haka? dama baki da lafiya ne kuma kila dawo kika zauna anan ke kadai? Sannu lallaba ki taso muje ban daki ki gyara jikin ki ai bakyayi ta zama cikin kazanta ba" Kamo Meenal d'in tayi a hankali suka k'asara cikin bayi ta wanke mata fuska tasa mata ruwa a baki ta kuskure ta gyara mata jikin ta inda aman ya tab'a ita dai sai rawar sanyi takeyi har suka fito, Lallab'awa tayi ta kwantar da ita a gadon kafin ta fice d'akin taje ta d'auko tsintsiya da parker ta kuma had'o da tsumma ta gyara wajen daya b'aci tsaf kafin ta fitar da komai ta dawo da burner ta jona shi a soket tasa turaren wuta, Yana fara aiki Meenal ta zabura tana to she hanci, "Waiyo Allah me yasa kika sa turaren nan wallahi wari yakeyi shi yasa na gudo daga wad'ancan dakunan fa na dawo nan dan jiri da ciwon kai yake sani " tun bata k'arasa ba ta fara yunkurin amai a haka jikinta ba k'arfi ta sauko daga gadon bayan ta rufe hancinta da bargon data yaye ta rufama jikin ta saboda sanyin da takeji ta kama hanyar fita daga cikin d'akin, Da kallon kurullah Larai ta bita bayan ta zare socket d'in tana son tabbatar da zarginta akan Meenal din, "Kamar fa ciki ke jikin yarinyar nan? Allah mai iko lallai ko in cikine sai muce rabo ya rantse, to ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi" Bayan Meenal d'in ta biyo, "To ina zakije yanzun kuma? " Larai ta tambaya ganin Meenal na sauka daga bene zuwa k'asa, "Sashen Hajiya zan koma nan wari yakeyi wallahi ke bakiji ba?" Ta juyo tana tambayar Larai, "Ah wallahi nikam kamshi naji, kece dai hancin ki ya shak'o miki warin" "Oho nidai bazan zauna anan ba" K'arasowa Larai tayi ta rik'e ta suka k'arasa sauka a benen suka fice daga sashen Meenal din zuwa na Hajiya kamar yanda Meenal ta buk'ata, "To me zakici yanzun in kawo miki kici sai kisha magani ki kwanta?" Larai ta tambaya, "Ni bana jin yunwa bacci kawai zanyi dazarar na tashi zanji na warware" "Ki daure dai ko tea in kawo miki kisha" "Ah ah sai dai in zaki dama min kunun tsamiya kuma ina son yayi tsami sosai kula kar asa sugar a cikin kunun" "To yanda kike so haka zan miki shi" Kitchen Larai ta koma bayan ta raka Meenal din tsohon d'akin ta, da yike suna da komai na had'in kunun nan da nan sai gashi ta dama dan haka ta zuba a kofi takai ma Meenal din wacce har bacci ya fara figarta, "Tashi ga kunun kisha" Yunk'urawa tayi ta tashi zaune sai Larai tasa mata pillow a bayan ta ta jingina, Amsar kofin kunun tayi ta k'afa kai tana sha tana hutawa har saida ta shanye shi tass kafin ta mik'ama Larai kofin, "Nagode Aunty Larai anjima shi zaki k'ara damamun dan Allah kinji" "Mai zai hana in dama miki tunda kina so, yanzun dai koma ki kwanta Allah ya baki lafiya kinji" Bayan fitan Larai kowama tayi ta k'ara kwanciya can cikin bacci take jin kamar Hannu a saman fuskar ta yana shafa ta dan haka a hankali ya dunga bud'e idon ta tun tana gani dishi² har dai ta ware idon tass akan shi, Bata san daga ina kuka ya taso mata ba kawai dai ta tsinci kanta da mashe mishi da kokane sosai ta kuma murgina ta juya mishi baya, "Subhanallah My Baby what's wrong with you? Meya sameki" Ya tambaya yana k'ok'arin tattarota zuwa cikin jikin shi, "Don't you dare touch me ina ruwan ka da abinda ya sameni ko yake damuna?" Ta fad'a tana kai mishi duka tako ina kamar wata mai shirin tada bori, Daga hannuwan shi sama yayi alamun yayi surrender a sanda ya saketa, "Allah ya huci zuciyar ki ya baki hak'uri" Ficewa daga d'akin yayi ya sauka k'asa zuwa kitchen, "Ah ah Babban mutum yanzun ka iso?" "Shigowata kenan dafatan na sameku lafiya?" "Alhamdulillah ya hanya? Ka shiga daga ciki Meenal din tana nan a kwance bata jin dad'i d'azun ma amai tayi tayi shi yasa ta dawo nan wai can sashenta yana mata wari," "Tun yaushe ne bata da lafiyan?"ya tambaya "Ah ah gaskiya ban sani ba sai dai ko zaka tambayeta dan nasan da ace Hajiya ma tasan bata lafiya da bazata wuce Abuja ta barta ba" "Taci abinci ne?" "Eh to d'azun dai kunun tsamiya tace tana so dan haka shina dama mata tasha ban san me zatace tana so yanzun ba kuma" "To dan Allah ki taimaka min kije can d'akin ta kid'an had'amin wasu daga cikin kayan ta wucewa da ita zanyi" "To ai baida damuwa Allah dai ya inganta" Wucewa yayi ya koma d'akin Meenal d'in kuma har yanzun bata dena kukan ba sai ma k'arfi da kukan nata ya k'ara bayan daya bar d'akin a ganin ta mai yasa yana ganin tana kuka ya tsallake ya fice bai tsaya ya saurareta ba, Koda ya shiga duk yanda Sautin kukan nata ke yakusar mishi zuciya daurewa yayi yana zuwa ya yaye bargon jikin nata ya cusata a k'irjin shi ya matse, duk yanda taso ta kwace hakan ya gagara sai ma hannun shi da yayi amfani dashi ya zage zif din rigarta ta baya ya rabata da rigar shima ya cire rigar jikin shi ya k'ara kankame ta a jikin shi zafin jikin ta yana ratsa shi, "Shishshsh yi shiru kukan ya isa haka nan ba gani nan a gaban kiba me yayi saura kuma? Bakiga har kofa sai da na rufe ba saboda kar a jiyo ihuna a yayinda kike hukunta ni, Am sorry nasan nayi laifi amma kiyi hakuri" Tsakanin mata da miji sai Allah dai haka AK ya sata a gaba da lallashi saida ya tabbatar da cewa ya goge duk wani fushi nashi data d'iba kafin ya shammace ta suka buga wasa zagaye d'aya badan ya koshi ba haka ya kwashe ta sukaje sukayi wanka tuni zazzabin jikinta ya kama gaban shi suna fitowa ya shirya ta shima ya maida nashi kayan ya rik'o hannun ta suka sauko k'asa, Kunun da Abincin da Larai ta dafa duk a kula ta zuba musu sukayi guzuri kafin suka mata sallama suka bar gidan tabi su da fatan Allah ya kiyaye hanya. Sun sauka Abuja lafiya tuni kuma Meenal ta shige cikin yan uwa da kawayen ta akaci gaba da shagalin biki da ita, anyi biki lafiya Amarya ma ta tare a gidan mijinta cikin aminci kwana uku Meenal tayi a Abuja AK ya tattaro ta suka zarce KD abinsu anan suka k'arasa cinye satin sai ranar juma'a kwana 7 da barin su Zaria sannan Meenal ta shawo kanshi da kyar ya maidata gida, Tun shigar su kina Hajiya kebin Meenal din da kallon k'ak'a uwar ka ta haifeka dan bayan dawowar ta Larai ta bata labarin ciwon da Meenal din tayi harda amaye²n data dunga yi, Sai da ta gama mata kallon tsaf kafin hannun ta rike da baki tace, "Larai fito daga kitchen din nan dan Allah ki tayani gani wallahi ciki nike hangowa a jikin takwarata" "Waima ciki ana zaman lafiya, yaushe nayi auren da har zaki wani fara kiramin ciki dan Allah" Meenal tace tana tura baki, shiko AK da kallo shima yabi Meenal din yana son ya gano cikin, "Allah Hajiya nima dai cikin nike hasashe" Larai data fito ta amsa ma Hajiya, "Ke taho nan inji ina da ina ke miki ciwo? Koda yike aike wani cikin fa baya nuna alamu har sai ya fito, amma kedai kam nasan cewa shine a jikin ki" Shashantar da zancen Meenal tayi akan itafa bata da komai, A kwanakin ko sosai AK yasa mata ido yana lura da ita dan akwai wasu abubuwa wadanda batayi a baya yanzun kuma ta tsiro dasu ciki harda abincin da bataci ada yanzun ta fara cin su sai dai tun ranar datayi amai din nan bata k'arayi ba bata kuma yawan laulayi sai dai cikin kankanin lokaci jikinta ya bud'e ta cika tayi dam kamar ba ita ba sai shegen kwad'ayi da cikin yasa mata tsakanin ta da miji ko yanzun ne ake zuba tsantsar love dan tunda ya lura da yanda ta amshi ragamar filin wasa ya tattaro ya dawo Zaria sai yanda tayi dashi, Ga alamun ciki tako ina sun bayyana amma har yanzun ita tak'i yarda cewa cikin gareta kuma ko ance ta auna sai tace ba wani awon da zatayi bayan ita tasan bata da komai, A haka Allah yakai lokaci aka shiga cikin hidimar auren Moon da Sarki inda akayi hidima sosai a lokacin ne kuma cikin jikin Meenal ya tona kanshi kowa yasan da zaman shi murna ko a wajen dangi har baka tantance wa yafi wani murna karma uban cikin yaji labari sai kuri yake ma Musty cewa sunan dai ya riga shi aure ne kawai amma gashi nan shi zai riga shi haihuwa ko iya haka aka tsaya sun san shine gaba dasu, Malam ma yayi murna sosai dan har gidan Hajiya sai da ya tako ya duba jikin Meenal Hajiya kuma sai da ta yad'a mishi magana a ranar cewa, "Ai wannan aure ita dai babu abinda zatace ma Allah sai godiya, domin gashi dai Allah ya nuna musu cewa wani baya auren matar daba tashi ba haka kuma rabon wani baya zama a gidan wani, dan hakan nema yasa ba'aso mutum yayi jayayya akan zancen aure dan bai san me Allah ya boye a cikin al'amarin ba, ita dai ta gode Allah da yasa rabon dake jikin su ya zamo silar gaggautuwar auren su" Duk da cewa Malam yasan dashi take bai kulata ba har taci ta sud'e, Tun bayan da aka kammala bikin Moon Amarya ta tare a gidan ta shi kenan ciwo kuma ya taso ma Teemah ganga² wanda dole likitoci suka basu shawara akan ayi aiki a cire yaran dake cikin ta gudun kar a rasa ita ko yaran, Hakan ko akayi anyi aikin cikin nasara an ciro mata yara biyu duka yan maza sai dai gaskiya itakam uwar sosai take jin jiki duk da cewa bawa baya cire rai da rahamar ubangiji amma ita dai ta fara sarewa dan haka ta roki alfarmar a kira mata iyayen ta dasu Uwar gida dan ta rok'i gafarar su, Hankalin Sarki daduk na wani wanda yake kusa dasu sosai ya tashi dan jinin Teeman ya haye sosai ga kuma zubar jini da takeyi, Washe gari Brigadier da ahalin shi suka sauka a garin Kaduna kamar yanda yan Zaria suma sukayi sammako ciki harda Moon suka taho dan duba jikin nata, Wallahi duk wanda yaga yanda Teemah ta koma a lokacin take sai ya zubda mata hawaye dan kallo d'aya zaka mata ka tabbatar da cewa tana jin jiki dan ta d'ashe tass kamar babu d'igon jini a jikinta, Ta rok'i gafara mijinta dana iyayen shi kafin nata iyayen da yayan ta, Ta kuma tambaya cewa ko Meenal tazo dan itama tana son ta rok'i gafarar ta dan itama ta cutar da ita sai dai kuma Meenal bata samu halin zuwa ba dan haka sai ta rok'i Sarki ya kira mata Meenal din a waya ya had'asu ta roki Meenal din gafara, Meenal kuma tace ita dama bata rik'e ta a raiba dan haka karta wani damu kanta allah dai ya yafe mana baki d'aya, Waje ta nemi a basu tana so zatayi magana da Sarki da Moon dan haka yan d'akin suka fita aka barsu su uku, Kamo hannun Moon d'in tayi ta had'a dana Sarki ta runtse su a cikin nata, "Maimoon nauyi nike so in d'aura miki, Nauyin kula da mijina da kuma tarbiyar yara na, tun daga sanda likitoci suka tabbatar min da cewa ina d'auke da ciki nike fata da addu'ar cewa Allah yasa cikin namiji Allah ya bani wannan karon, Kinsan saboda me nike ta wannan addu'an?" Girgiza kai Moon tayi ba tareda ta iya bude baki ta amsa ma Teeman ba, Ita kuma saita d'aura da cewa, "Saboda tun haihuwa na na farko nike ta fatan Allah ya bani Namiji dan a nawa zaton haihuwar namiji shine zai bani damar mallake mijina dama duk wani abunda ya mallaka, Amma Allah da ya duba zuciya ta yaga ba niyyar alkhairi ne dani ba sai ya nuna min ikon shi wajen bani haihuwar akai ² sai da na jera yan mata har uku amma duk ban nuna godiya ta wajen Allah ba alhalin wasu nacan da arzikin su lafiyar su suna yawon neman haihuwar amma har yanzun Allah bai nufa sun samu ba, Haka na haifi yan matana amma kaf cikin su babu wacce naja a jikina na nuna mata kauna har zuwa sanda uban su ya gaji da gani ya kwashe su ya dawo dasu gidan kakan su, Wallahi ko damuwar dana nuna a lokacin bawai har ciki zuciya ta bane dan ni dadi ma naji dan dama gani nike kamar suna takura min, bayan haka kuma Allah ya bani cikin Boy, ina son yarona sama da yanda nike son kaina domin a duniyar nan daga shi sai uban shine Allah ya jarrabe ni daso idan aka cire iyayena," Tana shashshaka taci gaba da cewa, "Ki duba ki ga yanda rayuwar ta juyamin a sanda buri na ya cika yau ni Fateemah nice na zama uwar yara maza har biyu a lokaci d'aya, Sai dai kash damar haihuwar kawai Allah ya bani domin bani da tabbacin cewa zanyi rayuwa dasu balle har in tarbiyar tar dasu daga nan har zuwa girman su, Jikina yana bani cewa tafiya zanyi in barsu ba tareda sun san dadina na uwa a wajen suba, dan haka zanyi amfani da wannan damar in damk'a amanar su a hannun ku keda uban su ina fatan zaku kulamin dasu bayan ba raina, Dan Allah ki rik'e min yarana kamar yanda zaki rik'e naki karki duba cewa su din yayan kishiya ne kice zaki kuntata musu, Ina fatan zaki kula dasu ki kuma tarbiyar tar dasu fiye da yanda nima zanyi idan ina tare dasu... " Bata kai k'arshen bayanin taba numfashin ta ya fara sauka dan haka da gudu Sarki ya fita waje ya kira likita suka shigo suka cigaba da dubata, Babu wanda yayi zaton cewa Teemah zata k'ara kwana a raye amma da yike Allah ne mai kashewa da rayawa a hakan tayi kwana biyu a asibitin ganin jikin yak'i sauk'i ne kuma yasa Brigadier ya rok'i alfarma wajen Sarki akan cewa zasu wuce da ita Lagos washe gari shima baik'i ba dan ko ina sukace zasu kaita indai zata samu lafiya bazai hanaba, Sai dai kafin dare kuma jikin yaran duka biyu ya rikice aka rasa mi yake damun su dan kowa dai yasan lafiya lau aka haife su sai gashi kafin ace a gama bincike a gano abinda ya same su dukan su biyun Allah ya k'arbi abinshi, Mutuwar da babu wanda bata sa kuka ba a wajen, Ba'a yarda uwar ta sani ba dan tuni dama ta fice a hayyacin ta akaje akayi jana'izar su zuwa gidan gaskiya, ita kuma washe gari iyayen ta suka wuce da ita Lagos kuma harda Sarki da Moon suka bisu yan Zaria kuma suka koma sukaci gaba da amsar gaisuwa acan, Anyi bikin Maryam lafiya kuma itama a zaria zata fara zama kafin in sun kammala karatun su ta tare a Abuja, Bayan wani lokaci jikin Teemah yayi sauki sosai dan har an sallameta daga asibiti ta dawo gida, Koda ta samu labarin rasuwar yaranta kuma sai Allah ya daura mata wani irin dakiya da dangana, A yanzun kuma da suke zaune gida d'aya ita da Moon lafiya kalau suke zaune babu maijin kansu dan idan ka shiga gidan ma bazaka gane ko wacece keda girki ranar ba a cikin su, had'uwar kansu kuma ba k'aramin kwanciyar hankali ya saukarwa Sarki ba dan yanzun haka yana shawarar ajiye aikin shine ya dawo gida kawai yaci gaba da kasuwancin shi ya zauna cikin iyalan shi ya basu cikakkiyar kulawa yanda ya dace. Alhamdulillah su Meenal karatu ya kammala a yau dai ta amshi kwalin karatun ta na zama likita ita da su Maryam dan haka bayan an kammala shagalin makaranta suka dawo gida suka d'aura sabon celebrating na kammaluwar cikar burin ta guda uku, Ta kuma amshi kyaututtuka masu yawa daga hannun mijinta da *danginta* tako ina kauna kawai ake nuna mata ita da d'an cikin ta a satin ne kuma akayi masu rakiya zuwa kaduna sabon gidan ta kuma Hajiya ma tattarawa tayi ta bisu dan tace bata zama a Zaria ta zauna su kuma suje can jarabar su yasa su k'arkad'o mata tattab'a kunne, An sanya ranar auren Salman tareda kanwar Raheenat wato yarinyar Baba Adamu kuma shi Salman din ne yagan ta yace yana so dan haka Malam ya bashi dama suka dai daita kansu, A lokacin dai kusan biki takwas aka had'a akayi a lokaci d'aya harda na Raheenat da Ya Abakar Alhamdulillah *dangi* sai kara fad'ad'a yake tako ina, *Bayan shekara uku,* Nagode Allah daya kawo ku, to wallahi ku shirya k'afarku kafar yaran ku in kun ta shi wucewa ku wuce da abunku na gaji da hutun haka zaman da sukayi min na kwanaki ma Allah ya bani ladan surutun da sukayi ta sani, yo jama'a ina dalili ku da haihuwar yara ni kuma dayi muku wahala dasu? Kun san zasu dameku kukayi tayin cikin su kuna haihuwa? In gaskiya ne ai sai ku tura ma iyayenku can su tayaku raino bawai ni tsofai tsofai dani ba nayi dawainiyar iyayen ku nayi naku yanzun kuma ga yaran ku" Hajiya ce ke wannan surutun a yayinda AK ya rik'o hannun Meenal suka shigo cikin falon da k'aton cikin ta a gaba, "Amma dai Hajiya kece ki kace a kawo miki su fa," AK ya fad'a a yayinda ya zaunar da Meenal saman kujera, "Ai boyemin gaskiya kukayi tun farko da sai kuce min haka yaran ku keda shegiyar b'arna harda na mugunta, Wallahi tunda sukazo na dena samun damar yin baccin rana in kaga na huta a gidan nan to saifa in nasa Kabiru yakai can gidan Malam shine nike hutawa kafin su dawo" Da gudu yaran suka fito daga cikin kitchen ko wanne da filet din abinci a hannun shi, Oyoyo daddy suke ta fad'i a sanda suke k'okarin k'arasa wa inda AK da Meenal suke shi kuma AK sai ya bud'e hannu ya taresu dan yasan suna iya isa su afkama Meenal din dake fama da kanta, "Baku ganin abinda ke gaban Mommy ne kuke kokarin danneta?" "Daddy Hajiya tace mana Mommy zata haifo mana wani mommy irin na khairat" Ahmad wanda suke ma lakabi da Ayman yaron Meenal na farko ya fad'a, "Eh dady na ai kaima kana son k'anin koh?"AK ya maida tambayar nashi kan Usman yaron su na biyu wanda suke kira Akram, "Mommy babies da yawa zaki aifo mana muma koh?"Akram din ya tambaya da hausar shi da bata fita sosai, "Eh ai gara ta haifo da yawan ko itama ta samu ta huta da haihuwar da takeyi duk bayan shekara d'aya, Ni Inba a kan kuba kaf dangin ma babu wacce ta tab'ayin gwarne wallahi amma ku tsabar jaraba kafin yaro yayi kwari kin kwaso wani" "Hajiya ba gara mutum yayi haihuwar ya gama da wuri ya huta ba" cewar Meenal tana b'ata fuska, "Eh aifa shi yasa kike ta sauri to allah yasa a gama lafiya" Sultana da Bash tuni suka bar k'asa suka koma Malesia can inda ya baro, itama kuma ta haihu yarinyar ta guda d'aya wacce bash din yama Aminatu takwara, kuma har gobe zumuncin su yana nan babu abinda ya girgiza, Moon ma a shekarar farko da auren ta Allah ya bata k'aruwar yan biyu duka maza, biyun da suka koma ne suka dawo ta jikinta kuma itama har yanzun lafiya lau suke zaune ita da teemah da yaran su ga kuma Salman da matsar shi da suke tare dasu a gida d'aya, Maryam da Meelat mutanen abuja suma dukan su Allah ya basu Meelat yaranta biyu mace da namiji maryam kuma tana da yaro d'aya. *ALHAMDULILLAH ANAN ZAN DASA AYA, ABINDA NA RUBUTA DAI DAI UBANGIJI ALLAH YASA MISHI ALBARKA, AKASIN HAKAN KUMA INA FATAN ALLAH YA YAFE MINI* *YAN UWA MARUBUTA DA MAKARANTA WADANDA SUKA TAYANI TURA LITTAFIN ZUWA SAURAN GROUPS INA FATAN ALLAH YA SAKA MUKU DA MAFIFICIN ALKHAIRIN SA NAGODE KWARAI DAN NA YABA, KUNA DA YAWA SHI YASA BAZAN RUBUTA SUNAN KU BA,* *XIEYERH NAGODE KWARAI DA KAUNA🥰* *Ni ZAINAB USMAN UMMIEE ZARIA dana shirya labarin na tsara na kuma rubuta ina yima d'aukakin makaranta littafin DANGINA fatan alkhairi, allah ya bamu ikon yin koyi da abinda littafin ya kunsa mai kyau mu kuma watsar da marar amfani. *UMMIEE CE*