*⚠️ Ban yarda a canja min ko da harafi daya na littafin nan ba, balle kuma har a saffara shi a dora a Youtube ba tare da izinina ba, yin haka kan iya janyo wa mamallakin Channel din babbar matsala dan haka a kiyaye!* _Hasbunallahu Wa Nimal Wakeel_ *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy Free Page 1️⃣ *GUSAU ZAMFARA STATE NIGERIA.* *Gusau Rd/Sokoto Rd* *_Jifatu Shopping Mall_*   *_3:16pm_* Madara ta fi komai yawa a cikin abubuwan da na siya, ba dan komai ba sai dan sanin cewa mahaifina ya fi bukatar tea fiye da komai a yanzu. Gwando daya na cika da siyayyar kayan ciye-ciye da tande tande sannan na dauki wani kwando na cika shi da da wasu abubuwa na bukatun yau da kullum kamar sabulun wanka da wanki da turare sai kuma omo. Bakar abaya ce a jikina sai dan karamin mayafinta wanda hakan ya bani damar rika duka kwandunan na nufi gurin biya Amal na bayana rike da biscuit dinta. A saman dan teburin da suka tana dan lissafa kaya na dora kwandunan sannan na saka hannuna a jaka na ciro atm dina na rike a hannu ina jiran ya gama da wadanda suka gabana ya fara da ni sai na biya da pos din da yake gurin, domin na saba indai ban ciro albashi gaba daya idan na siye abu ina biya ne da atm. Sai da ya gama da mutum biyu sannan ya fara da nawa, sai da ya gama lissafa komai kamin na mika masa kudin ya fara dauko leda yana sakawa, ni kuma a iya sanina idan kai siyayya a jifatu sai ka biya suke saka maka a leda su sallameka. “Nawa ne?” “Hajiya an biya” Ya fada min yana ga aikin harhada min kayan a leda. A take gabana ya yanke ya fadi har sai da na dauki yan awanin sannan na sake tambayarsa. “Waya biya?” “Gashi can a waje” Juyawa nai na kallin wajen sai n hango Abdallah tsaye jikin motarsa idonsa akan wayar da yake dannawa. Dauke kai nai na cigaba da kallonsa har ya gama saka kayan a leda sannan na mika hannu na karba. “Thank you” “No mune da godiya Hajiya” Da duka hannayena na riko ledodin na nufo kofar fita Amal na rike da gefen rigata muka fito, ko da wasa ban kalli inda Abdallah yake tsaye ba balle har ya ga fuskata duk kuwa da na san hakan ba zai hana shi yi min magana ba idanya tashi. Bakin titin na nufo ina ta tafiya ina sai jin maganarsa nai bayana. “Ban biya kudin dan ki min godiya ba, kuma na san ba zaki min godiyar ba, amman ai ko kallona kya yi na dan ji sanyi ko?” Tsayawa nai cak na juyo na watsa masa wata banzar harara fuskata a hade kamar bakin hadari. Sai dai da alama harar tawa dadi take masa domin murmushi ne ya cika masa fuska har ya cire farin gilashin idonsa yana kallona. Dauke kai nai na cigaba da tafiya sai jin nai ya riko hannun Amal wanda hakan yasa na juyo da sauri sai ganinsa nai yana danka mata kudi a hannu. “Ku hau napep da wannan kin ji Amal nasan ko na ce na kai stubborn mother dinki a mota ba zata je ba” Amal bata ce masa komai ba ta karbi kudin daman haka take indai kudi ne da biscuit bata kin karba ko a hannun waye, jan hannunta nai muka cigaba da tafiya. “Yanzu na baro mijinki a can gurin damba area tare da abokansa da wasu mata” Sake juyowa nai karo na biyu na dubeshi da duba na bakincikin jin kalaminsa da kuma na tsanar ganin fuskarsa. “Miye ribar da zaka samu idan ka labarta min wannan? Kana tunanin zan yarda da kai? Mi zai saka mijina neman wasu matan banza a waje?” “To ni ma dai shi na gani, namijin da zai aje mace kamarki mi zai saka ya nemi wasu a waje?” “Baka tsoron Allah Abdallah saboda baka gudun taka dokarsa, kana isgili da ganganci ga dokokin aure da kumana Allah, shin zaka jidadi idan wani namijin ya kula matarka? Wani namijin ya iya furta wata mummunar kalma akanka gurin matarka? Kai baka kishin kanka? Daga yau karka sake yi min wata magana da ta shafi mijina ni mijina ba mazinaci ba ne, na lura kai baka san darajar aure ba kuma baka san kimar kanka ba balle har ka iya tsare mutuncin iyalanka” “Na san darajar Aure Halimatu, na san martabar aure, kuma ina mutunta aure da duk wani mai aure, kawai dai ina son ki ne, ina son ki san kamanni da hallita suna canjawa amman zuciya bata taba canjawa, alakar da ke tsakanina da ke ba zata taba yankewa ba, ko bayan so ai ni dan'uwanki ne ko?” “Ajinabi ba, kuma ina fatar ka san da hakan” Ya gyada min kai yana murmushi. Ni kuma na juya na cigaba da tafiyata. “Da ni nake da mace kamar ke ba zan bari ko tawaye na ya kalleta ba, balle kuma har wani namijin ya tsaya magana da ita, zan yi duk abunda zan yi na kare mutuncinta da martabarta” Ban sake kulashi ba balle har na tsaya sake ce masa wani abun, na yi sa'a ina kaiwa titin na samu napep a take na daga mata hannu ta tsaya na shiga. “Yan mangurora zaka kai ni” “Dari biyu” “Zan dai baka dari da hansi” “To muje” Sai da na fara saka ledodin hannuna na shigar da yana ta hudu wato Amal sannan shiga na zauna. “Momy ga kudin” Amal ta fada tana miko min kudin da Abdallah ya bata, karba nai na saka a jakata ina hade yawu, kamar hadin baki ina saka kudin karamar wayata tai ringing sai na fiddo hannuna tare da wayar ganin number surukata yasa ni saurin dauka. “Assalamu Alaikum Hajiya” “Na'am Halimatu kina lafiya?” “Lafiya kalau Hajiya ya jikin?” “Al-hamdulillah, na ce kin fadawa Aminu maganar kudin nan kuwa?” “Eh Hajiya na fada masa” “Idan ma baki fada masa ba ya kamata dai ki fada masa, har yanzu na ji shiru be ce komai ba ban sani ba ko baki fada masa ba, idan ma baki fada masa ba ya kamata dai ki fada masa yanzu, kuma izuwa yanzu ya kamata ace kina fahimtar cewar uwar miji ma kamar uwa ce, duk abunda ya shafe ni ya kamata ace kina daukarsa da muhimmanci” “Wallahi na fada masa Hajiya, amman zan sake masa magana” Bata ko bari mun yi sallama ba ta katse wayar, hakan kuma alamune da ke nuna cewar yau a fusace ta kirani. Haka na ke da yan'uwansa idan suna bukatar abu sai dai su kira su ce nai masa magana bayan ni kuma ba magana ta hake ji ba, mahaifiyarsa ma ta fi kusa da shi amman ita ma kanta sai dai tace na fada masa tana bukatar abu kaza da kaza, saboda gani suke komai na kame na mallake shi sai abunda na ce yake yi. Ko da yake shi ya nuna musu hakan domin a duk lokacin da suka bukaci abu ko da naira biyar ne sai yace balle nai magana da Halima, ganin hakan yasa suka dauki ido da baki suka dora min wai na mallake shi, ni kuwa nasan da zan samu mallakar kamar yadda suke zato da ba haka ba. Har kofar gida mai napep din ya kai mu na fita na ciro kudinsa na mika masa sannan Amal ta fito tana bata fuska wai rana sai kace a kafa muka zo. Ganin motar Abdulhamit wato tawayen Abdallah fake gefen icen da ke kofar gidanmu ya tabbatar min da zuwansa, daman can ya kan zo jifa jifa ya gaishe da su Mama. Ina gaba Amal na bayana tana kukan rana, gidanmu gidane mai yan mata da samari ina shiga yan matan gidanmu wato kanne waenda muke uwa daya uba daya da kuma waenda muke uba daya suka hau ihu da murna ganina. “Oyoyo Anty Halima” Da sauri kananna suka zo suka rika ledar hannuna, dayar kuma ta dauke Amal tai sama da ita tana dariya, daman haka gidan mu yake yana da wahala ka iya banbance yan dakin mu da waenda muke uba daya domin mu ba musan wani abu wai ubanci ba ko kuma yayan kishiya. Sai da na fara shiga dakin Inna na gaisheta sannan na nufi dakin mahaifiyata “Maraba da Sadiya” Cewar Mama da murmushi a fuskarta, ni kuma na zauna saman kujera ina mika mata gaisuwa tare da gaisawa da Abdulhamid. “Yau kuma nan aka zo?” “Eh Wallahi ya gida ya yaran?” “Lafiya kalau” “Yanzu ko na ke tambayarki aka ce kin kwana biyu ba ki zo ba” “Wallahi yanzu na rage fitar nan sosai saboda abubuwan sun yi yawa ga hidimar yara ga zuwa gurin aiki idan na dawo kuma nai aikin gida, ba ni da hutu ne Wallahi” “To Allah ya taimaka ni zan wuce” “Tun yanzu” “Tun dazu na zo fa, nan na ci abincin rana ma” “To a gaishe da su Hajiya” “Za su ji” Ya mike tsaye yana ciro makullinsa a aljihu, banbancinsa da Abdallah kadan ne ta wajen hakoransa na gaba dayan ya dan kare kadan sai kuma yanayinsa da ba na Abdallah ba, amman kama iri daya ni kaina ba dan banbanci tufafi ba da motar da na gani a waje idan har na shigo be bude baki ya min magana ba zan iya cewa Abdallah ne. Sai da Mama ta raka shi har gurin motarsa ta dawo, sannan take labarta min shinkafa ce ya kawo musu yar gobnati, daman haka familyn Baba suke suna da son zumuncin da son yi ma wanda ba shi da karfi a cikinsu, musamman ma Baba da suke ganin baya aikin komai kuma ga ciwon kafar da yake fama da shi, ga kuma iyali rututu mashallah, domin yan matan dakinmu kadai su hudu ne, idan aka cire ni da nake ta biyu da kuma yayana Maimunatu wace ke aure Kano da yaranta, ga kuma yayan Inna su ma su bakwai duka mata sa dai ita ta aurarda matanta hudu saura uku. “Kai shinkafar nan mai tsada, Allah ya saka musu da alheri” “Amin” Ta amsa tana tambayar ina na baro su Namra da Salim. “Suna gidan kanen babansu kin san yau weekend ne wai yace zai kaisu yawo tare da yaransa shine suka tafi Amal ce kawai ta ki zuwa” “Ita sarkin lakuwa daman kullum tana nan manne da ke, idan kika haifo wani sai na ga yadda za tai” Cewar kanwata Amina, ni kuma nai dariya na ce. “Aa yar auta ce ai” Kausar ta ce “Ba wani auta wata zaki haihu mu ga karshen lakuwa” Ban bi ta kansu ba na kalli Mama ina dariya na ce “Ga sabulu nan na kawo muku, sauran siyayyar ssai wani watan” “Babu komai Allah ya miki albarka” Daman haka nake wata siyayar da ban yi ba a wani watan na ke musu ita saboda ni ma kaina ina yi ma kaina wata lalurar domin ba komai namiji yake dauke ma ba, balle miji irin nawa, daman kuma can maza ba sa son ba ni ba ni wannan yasa na tsaya kai da fata akan aikina, a duk lokacin da an karbi albashina sai nai ma kaina da iyayena lalurar da bata gagareni ba. Bayan sallah la'asar na shiga dakin Baba na gaishe shi na bashi dubu biyar a cikin albashina kamar yadda na saba masa ko wane wata bayan siyayyar da na ke, yayi murna kuma ya min addu'a sannan na taso na fito harabar gidan inda kanenna suke zaune na zauna muna ta fira, a gurin Maryam na ga wani slim tea da kawarta ke saidawa na siye daya, ba dan ina da tabbacin yana yi ba sai dan neman rabuwa da kibar da na ke ko dan na huta da ci mun fuska da Abbah Adnan ke yi. “Wai Anty Halima kin gama karanta Littafin Zaki kuwa?” Jawahir ta tambaye ni. Ni ko na tabe baki ina murmushi. “Hmmm na karanta gaskiya ba laifi littafin yayi dadi, wannan iya gata da soyayya da Aliyu ke nuna ma Ataa” “Wallahi nima soyayyarsu ta tafi da ni, idan nai aure haka zan yi da mijina” Ta karasa tana rage murna dan kar Inna ko Mama su jiyota. Sai muka kwashe da dariya. “Ai auren yanzu ba wani soyayya a ciki Jawahir sai dai kawai hakuri da neman aljanna, amman duk wata soyayya ta littafi karki saka ran samunta a gaske, ban ce ba a samu ba ana samu amman kadan ba da yawa ba” Na fada ina tuna irin tsarin rayuwar da na shirya ma kaina da mijin da na aura kamin aure, sai dai ina yin aure sai na tarar da ba haka ba daga lokacin da na fara haihuwa kuma sai na ga canji a gurin mijina, har ta kai yanzu bana burge shi saboda na yi kiba na yi fadi litattana ta canja daga budurwa zuwa mai aure da yara hudu. Haka dai muka cigaba da firarmu gurin dariya mu yi har akai magariba, bayan na yi sallah na shiga dakin Mama na bata dubu biyar na bawa Inna budu biyu sannan na dauko Amal muka fito kannena biyu suka rakoni. Na samu napep nai min jinga daga unguwar zuwa igala quarters zai kawo ni dari biyu, a take na shiga su kuma suka kama hanya. Ko da muka isa na tarar Abban Adnan ya dawo domin na ga motarsa a harabar gidan tun kamin na shiga, da sallama na tura kofar falon na shiga, sai dai be amsa min ba kuma be dago ya kalli inda na ke ba, yana zaune saman cushion idonsa akan tv yana kallon hausa bakwai suna haska wani hausa film da ban tantance shi ba, jin muryar yara a upstairs ya tabbatar min da sun dawo kenan suna dakinsu domin shi kadai ne a falon. “Sannu da zuwa yanzu ka dawo?” Be amsa ni ba sai wani cin magani da yai ya kalleni. “Karki sake tura min yara gurin yawo, kin tura su kuma kema kin fita yawon ki” “Ba yawo naje ba gida naje kuma na fada maka kamin na tafi” “Na dai fada miki, bana son yarana suna zuwa gidan kowa, kuma na fada miki ki aje aikin nan bana so saboda aure na auro ki ba dan ki rika fita zuwa aiki ba” Bance masa uffan ba, idan sabo na saba da jin maganarsa ta na aje aiki, ni kuma na gagara ajewar kamar yadda yake bukata saboda be dauke min duka lalurorina ba, kuma ga iyayena suna da bukatar taimakona a yanzu, aikin ma da be fi shekara uku da farawa ba. Amal ta tafi kusa da shi ta zauna shi ko hankalinsa na kan tv sai yabon kyau Fati washe yake, na san yana yin hakan ne saboda na ji haushi kuma na ji, domin har yanzu na kasa sabawa da halinsa na yabon kyawun wasu matan a gabana. Ina jin ba dadi idan ya yabi wace bata da jiki ko ya nuna yana son mace marar jiki saboda na san ni din ba siririya ce ba, duk kuwa da kasancewar ba wata shahararriyar kiba ce da ni ta kaico ba, kuma na san matukar mutun be ce min kyakkyawa ba to ko ba zai kira ni da mummuna ba, domin ni ma ina da kyau na iya yadda Allah ya ga zai dace da ni, ina da haske sai dai ba can sosai ba. Upstairs na nufa dakin yarana na fara shiga na sai na samu Adnan da Aiman suna buga game a system dina, Namra kuma tana kwance saman gado ta rufe ido sai juyi take, cike da damuwa na zauna kusa da ita na kai hannu ina shafa bayanta. “Namra lafiya?” “Momy cikina ke ciwo sosai” “Me kika ci?” “Banci komai ba” Ta fada cikin kuka ba tare da ta bude idon ba. “Adnan me Namra ta ci? Ta ci yaji ko?” Sai a lokacin ya dago har ya lura da ba dawo, ya zo inda nake da murnarsa shi da Aiman suka dafa ni. “Momy kin dawo?” “Eh me Namra ta ci?” Adnan ya ce “Wallahi ban sani ba, Baba Sadi ya kai mu gurin wasa yara ita kuma ya fita da ita yace zata raka shi wani guri kila can ta taci wani abun, domin da suka dawo ta rika cewa cikina na ciwo” “Namra kin ci wani abu a can?” “Ya siya min nama na ci kuma da yaji a ciki amman kadan ne yajin na ci saboda kin ce na daina cin yaji” “To yajin ne ya saki ciwon ciki, bari na jika miki kanwa” Ya fada ina mikewa tsaye na nufi kofar fita, Aiman ta biyo ni a bayana yana fadin shi ma zai sha, daman haka yake duk abunda ya ga yar'uwarsa Namra ta sha shi ma sai ya sha komai dacin abun saboda tsabar rigima. *If you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660* 7/20/21, 8:28 AM - Buhainat: Ziyarci YouTube channel dina mai suna Taskar Khadeeja Candy domin samu duka littafaina a Kyauta https://youtu.be/P9GOP9cqP6Y karku manta ku danna min subscribe Comment & Share. *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 2️⃣ Sai da na jika mata kanwar ta sha na shiga dakina nai sallah isha'i, ina sallamewa nai saurin mikewa tsaye na nufi inda wayata take tana ringing na duba na yi zaton ko Abban Namra ne da farko sai dai ganin bakuwar number yasa ni aje wayar har sai na koma saman carpet har sai da na gama tasbihina nai addu'a ma mijina nai ma kaina da iyayena sannan na nemawa yara na shiriya. Daga bisani na mike tsaye na nufi inda wayar take aje na dauka na sake kiran layin da aka kirani da shi. “Assalamu Alaikum” Ni na fara mika sallamar kamin wanda na kiran ya fara min sallamar. “Wa'alaikissalam Halimatu” “Na'am Ranka ya dade” Na gane cewar ogana ne na gurin aiki wato oga Dahiru. “Ki yi kokarin hada document dinka kamin gobe ina da bukatarsu” “To ranka ya dade” “Kuma ki yi saving din wannan number ita ma number ta ce” “To ranka ya dade” Daga haka ya kashe wayar be sake ce min komai ba, ni ma kuma ban ce ba, daman kuma me zan ce masa, bayan kiran da yake min ma yana damuna balle kuma har nai wata magana da shi, zauna nai bakin gadon ina ta mamakin dalilin kiran da oga Dahiru yake yawan min a duk lokacin da yake bukatar wani abun, shin yana manta cewar ni ma ina da aure da iyali kamar shi, ban san miyasa yake son kira akan abunda be kai ya kawo ba, ba kira kadai ba har wasu abubuwna da yake min bana jindadinsu, domin duk abunda na ke ina kokarin kare mutuncin aure da kuma na yayana da mijina. “Momy ni dai gobe idan mun dawo daga scul gidan zan dawo ba zan je gidan Baba Sadi ba” Namra ce ta shigo tana wannan maganar tana wani bata fuska kamar zata fashe da kuka. “Saboda me?” “Bana son zawa can Momy dan Allah” “Ki yi hakuri Mamana, idan kun dawo nan gidan ba wani abun za ku yi ba, kuma kin ga ba girki balle ku ci, amman can Momy Hassana tana girkawa, za ku samu ku ci” “Momy to ki daina zuwa aikin nan pls ko kuma mu rika zama a gida a haka muna jiranki ki dawo” “Mamana akwai abunda ake miki a gidan ne da baki so?” Ta girgiza kai alamar aa sannan ta kwantar da kanta jikina. “Cikin ya daina ciwo?” “Eh amman yana min kadan-kadan ba sosai ba” “Zai daina In-Sha-Allah, na zubo miki abinci za ki ci?” “Za mu ci tare Momy zan wanke hannuna ba zan saka miki datti ba” Murmushi nai mata sannan na mike tsaye na fito daga dakin na sauko downstairs. Ban samun Abban Namra a falon ba, daman kuma ban saka rai ba domin ba kasafai yake dawowa da wuri ba, idan kuma har ya dawo to sai idan wani abun zai yi ko zai dauka amman dai ba haka nan kawai zai dawo gida da wuri ba ko kuma ya wuni ba. Tuwon da na girka dazun kamin na fita na zubo miyar kuka sannan na fito bakin kofar kitchen rike da abincin ina kiran Adnan domin bana son sai na zauna ya zo yace min zai ci abincin. “Adnan Aiman za ku ci abinci yanzu?” Babu wanda ya amsa ni a cikinsu balle kuma har su sauko kasan da sunan cin abincin, sai Amal da ban kora ba. “Ommy Ommy zan ci abinci” “To zo ki ci yar autana” Na fada ina karasa fitowa falon sannan na zauna kasan carpet din na zaunar da ita saman kafafuwana na soma bata. “Namra zo ga abincin” Da sauri ta sauko ta shiga kitchen ta wanke hannunta sannan ta saka min a plate, loma uku zuwa hudu kawai tai ta cire hannunta wai ta koshi. “Cikin ne har yanzu Namra?” “Eh ciwo yake min” Ya fada tana yamutsa fuska sannan ta kwanta a gurin ba tare da ta wanke hannunta ba, ni kuma ban matsa ba ganin gata jindadi har sai da na gama sannan na dauke plate din na kai kitchen na wanke hannuna da na Amal a can sannan na dawo na dauki Namra na shigar da ita dakinsu na cire mata tufafin jikinta na nai mata wankan dare kamar yadda na saba musu na saka mata kayan bachi sannan na kwantar da ita, Adnan nan kam sai da nai kamar ina yi sannan ya bar gabar system din ya tafi yai wanka nai ma Aiman suka kwanta, ni kuma na dauke system dina na fito na baro musu dakin. Dakina na dawo na kwanta gefen gadon Amal ta haye min kafafuwa tana kokarin fara kukanta na banza. Wayata na dauka na kunna data dama bana samun hawa online sai da dare idan yara sun yi bachi kuma na gama komai, grps din muna na Nothen Women's Advice na fara budewa na duba chat din sannan na shiga na Salma pre-order na duba abubuwan da ta turo cikin har da injimin wanki wanda na fi kowa bukatarsa a cikin gidan nan saboda wanki da nake na yaran nan gashi kwana biyu sun lalata. Ban bar online din ba sai kusan sha daya da rabi na dare, sannan na tashi Amal wacce a lokacin ta dade da fara bachi a take ta saka min kuka daman ta saba ko ba ai mata komai ba tana kuka balle kuma an yi da dalili. A haka nai mata wanka na saka mata tufafin bachinta na goyata saboda na samu ta daina min kukan. Dakin yaran na koma na ciro musu dayan set din uniform dinsu na dora musu a inda na saba aje musu sannan fito na shiga kitchen din n dauko abincin Abbah Namra na kai masa dakinsa duk kuwa da na san ba lallai ne ya ci ba domin ba ko da yaushe yake cin abinci a gida ba. A falo na fito da laptop dina na duba document din da oga Dahiru yace na shigo da su na fida su dabam a cikin wata folder sannan na rufe laptop din na koma dakin yara na kwantar da Amal. Na shiga nawa dakin nai wanka na saka kayan bachi na dawo dakin Abbah su na kwanta a take bachi yai gaba da ni abun ka da wanda ya gaji. Can cikin bachin nawa ina jin lokacin da Abbansu ya shigo duk yadda na so na dago nai masa sannu da dawowa sai na kasa saboda bachin da ya ci idona. Washe gari tun da asuba na tashi, sallah ce farkon abunda na fara yi sannan gabatar da addu'o'ina suma ba duka ba daman idan ba weekend ba bana samun tsayawa nai yi su gaba daya, ina saukowa kasa na shiga kitchen na shiga shirya musu abincin makaranta da kuma na karyawarmu, bayan na firaye dan na fasa kwai sannan na shiga dora ruwan zafin, Amal ce farkon tashi daman haka take tafi kowa rigima ko a dare idan ta motsa bata ji ba, indai yan rigimar suna nan sai ta saka kuka ta dawo dakinmu ta kwana. “Ommy Ommy” Ta fada tana murja ido cikin kuka. “Minene Amal?” “Bachi” “Je ki dauko zane” Sai kawai ta fashe da kuka, haka yasa dole na cire dankwalina na goyata da shi na cigaba da aikina. Ban tashi su Adnan ba sai da na tabbatar na shirya musu komai na makaranta sannan na tashe su nai musu wanka suka sauko kasa na hada musu tea kawai suka sha suka hau sama suka shirya cikin uniform dinsu kasancewar yau monday. Ni kuma na shiga cikin dakina na dauko kudin napep na saka hijab dina na fito na saka yarana a gaba muka fito har Amal muka nufi titi ina kokarin taron napep sai ga makocinmu kuma mijin kawata Hajara ya faka gefenmu tare da yaransa a cikin motar ya sauke gilashin motar yana miko min gaisuwa, sai da muka gaisa sannan ya ce da su Adnan su shigo motarsa suka shiga da saurin ganin yaransa daman can makarantarsu daya kuma yana yawan wucewa da su idan zai kai nasa yaran, wani lokacin ma har gida yake aikowa yace su fito zai kaisu makaranta. Sai da suka shiga motarsa sannan na juyo na dawo ni da Amal ina yanje da hannunta muka shigo cikin gida. Tea ta na dazun da bata karasa shanyewa ba na mika mata sannan na nufi dakin Abbansu, tufafin daya cire na jiya na fara dauka dan hade su da waendan kayan daudan nashi, al'adata ce duba aljihun rigarsa da wando kamin na saka su a kayan dauda saboda cire masa duk wani abu nasa da yake cikin aljihu. Rigar na fara dubawa sannan na saka hannuna a aljihun wandonsa, sai na ji abu kamar kwalin wani abu ina cirowa na ga kwalin kwandon sai dai ba cikakke ba da alama an yi amfani da shi. Ni a Kadai na san abunda na ji a wannan lokacin a take jikina na dauki rawa kamar dai yadda zuciyata ma take ta bugawa da karfi idanuwa na cika da hawaye. Juyawa nai ina rike da kwandon din a hannuna na kalli Abbah Namra da yake kwance saman gado yana ta sharar bachinsa hankalinsa kwance ni kuma nawa hankalin a tashe da kwandon a hannu. Dayan hannuna na saka na share hawayena da suka zubo na dauke kayan na fita da su, sai dai har nai aikin da nake na shirya Amal nai wanka nai shirin aikina hawayen ba su daina min zuba ba, ni kuma ban fasa sharewa da hannuna ba. Kamar yadda na saba yau ma na hada masa komai nasa na karyawa na shigar masa da shi dakinsa na kai masa, sai dai ban same shi a kwance ba sai na samu ya shiga bandaki da alama yana wanke baki ne, a can na baro Amal na fito na sauko kasa na nufi dinning na hadawa kaina tea amman sai na kasa sha saboda bacin rai da ke cikin raina, i decided na aje tea din na dawo saman cushion na zauna na dafe kaina. Wannan karon ba hawaye na ke ba wani abun ya ke jin ya tsaya min a zuciya marar misaltuwa daker na ke iya hadeye yawu da numfashi. Na kai minti talatin a haka sannan na tashi na koma dakina na dauko kwalin condom din na nufi dakinsa, kamin na kai hannu na tura kofar dakin na jiyo sautin dariyarsa hakan ya tabbatar min ko dai yana magana da Amal da take dakin ko kuma waya yake, ban yake dayan biyu ba na ji yana fadin. “Na samu hutu satin nan ina kike son muje?” Hakan yasa ni dauke hannuna daga jikin kofar daman can rikawa kawai nai ban tura ba. “Kaduna? To yayi ba matsala zan shirya mana komai, amman kamin na turo account dinki zan saka miki wani abu sai ki yi siyayyar da kanki kin san ni ba zan iya zuwa siyayya yanzu ba, kuma kin san idan ina fita da ke yau da gobe za a iya fara cewa wani abu” Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana ni ji ba, domin mutun ne mai daga murya idan yana magana da wani ko da kuwa kadan-kadan yake yi. Ji nai kamar ba zan iya sauraren firarsu suka ba hakan yasa na murda kofar dakin na shiga ina kokarin maida hawayen da suka cika min ido. “Oh Okay Faruk sai na shigo” Shine abunda ya fada sannan yai hanzarin kashe wayar, ya gyara zamansa yana kokarin fara cin abinci, ko da wasa ban bar wata alama da zata nuna cewar na fahimci da mace yake waya ba, duk kuwa da kasancewar bana iya sauya yanayi na rashin jindadi da walwala dake tare da ni a yanzu. Zaunawa nai gabansa. “Ina kwana” Na fada ba tare da na kalleshi ba. Shi ma bana tsammani ya kalleni kamin ya amsa min sai Amal kawai yake wasa da ita yana bata abincin shi ma yana ci. “Jiya Hajiya ta sake min maganar kudin ac” “Ai sai ki ce mata kin fada min magana, ni Wallahi na manta amman yau zanje na fada kudin In-Sha-Allah” “To Allah ya bada iko” Be amsa min da amin ba sai ya dago ya kalleni. “Ya akai kin san bana son ana tsare ni idan ina cin abinci akwai wani abun ne?” Har zan mishi maganar condom din sai kuma na hade yawu na gabatar masa da abunda na san ba lallai ne yai min ba. “Jiya ne naga wani injimin wanki da ake order daga waje shine na ce ko zaka saka min wani sai na hada da abunda yake hannuna sai na siya na huta da kai wanki” “Ba ni da kudi yanzu, ina albashinki? Ko aikin kawai kike ba a biyanki?” “Ana biyana mana kai ma ai ka sani domin da su na ke rage wasu abubuwan nawa” “To ki siya da shi ni ba ni da kudi yanzu, da kin ga mutun ya zauna kin fara masa maganar kudi kenan shiyasa ko zama gidan nan bana son yi kuma baki da lokacin magana sai lokacin da nake cin abinci” “Irin wannan lokacin kawai nake samun damar magana da kai Abban Namra, baka dawowa da rana sai idan wani abun zaka yi da dare kuma sai 12 ko 1 kake dawowa” “To ni dai ba ni da kudi yanzu” Ya fada yana wani kara hade fuska. Sai na aje masa condom din da ke hannuna murya a sanyaye na ce. “Ga wannan na gani a cikin kayan da ka cire jiya” “Oh jiya Bala ya bani ajiyarshi na manta na bashi abarsa” Ya fada kai tsaye kamar gaske ba tare da ya kalleni ba. Idanuwana cike da kwalla na ce “Ko dai na wanene Allah ya sani kuma yana jiran kowa a madakata” Ina fadar hakan na mike tsaye sai dai kamin na kai tsayen ya rigani yana daka min tsawa. “To me kike nufi? Zagin kike ko kuma Allah ya isa za ki min? Wai mi yake damunki ne Halima? Daman munanan mata kun fi komai bakin hali ku ba kyau ba sai sakawa mutum damuwa da bakin zargin tsiya” “Ba ni n hallici kaina ba Abban Namra, kuma saboda bana da siffar da kake so a jikin mace ba shi yake nufi ka bi wasu matan ba, kai kanka kasan ba haka ka aureni ba, auren shekara goma sha biyu bana kwana biyu ba ne, dole wani abu a jikina ya canja, na haihu har hudu dole jikina ya bude, ka dinga jin tsoron Allah Abban Namra....” Kamar jira yake na kare a take ya wanka min wani mahaukacin mare mai zafi kamar garwasun wuta, kamin nai ihu Amal ta fara fashewa da kuka ta rike masa kafa damn ta saba masa haka ida da su Namra da Adnan idan yana dukana, ni kuma ban tsaya komai ba ya juya da sauri na fice daga dakin ina kuka. “Dacan bana tsoron Allah aka ce miki? Wawuya kawai” Shine kadai abunda na ke iya jiyo yana fada bayan na baro dakin, da gudu na dawo dakina na zauna kasa na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya. 7/20/21, 8:28 AM - Buhainat: https://my.w.tt/kmm6u2LFKbb *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 3️⃣ Kuka nai mai isata sannan na tashi na shiga bandakin na wanke fuskarta na fito na nufi gaban madubin na dan shafa mai kadan da hoda sai dai hakan be boye kumburin da fuskata da kuma idanuwana sukai ba. Hijab din da yai yanayi da farar atamfar da nake saye na dauka na saka sannan na dauki wayata na saka a jakata na dauki laptop din na saka takalmi na fito daga dakina. Yau ban tsaya bin ta kan Amal ba balle har na kaita da kaina gidan kanensa daman wani lokacin shi yake kaita idan na fita na barta a gunsa wani lokacin kuma ni nake kai ta sai dai idan ni na kaita ta fi min kuka saboda takuwa irin nata. Na saba daman a duk lokacin da zanje aiki sai dai naje a napep ba dai ya kai ni ba, kusan tun da na fara aiki sau biyu ya taba rage min hanya ya kai ni da motarsa, babu kuma yadda ban yi ba da shi akan ya siya min mota amman ya ki ba dan bashi da hali ba, sai dan ya fi son nai ta wahalar zuwa aiki a napep ga kuma kai yara scul da nake duka a napep, ya bar ni da dawainiya kala kala kamin a dan bashi da halin dauka ba sai dan keta irin na shi. Har na shiga napep ban daina tunanin wayar da naji yanayi da wata ba, ciki har da zancen kudin da zai bata bayan ni na roki alfarmar ya cika min na samu na siye injimin wanki yace min ba shi da su, ga kuma zancen hutun daya samu har yana fadin wane gari take son suje, ada can kam na kasa yarda cewar Aminu yana neman matan banza duk kuwa da kasancewar ina ganin chat dinsa da wasu matan wani lokaci ko kuma na ji yana fira da su, sai dai a nawa tunanin irin chatting din nan ne na budurwa da saurayi da maza suke yi, wanda ba zaka iya raba maza da shi ba, sai dai ganin condom a aljihun wandonsa ya tabbatar min da abunda Abdallah yake yawan fada min, sukar auren da yake min na uban diyata yau na tabbatar da shi, no matter what Aminu zai fada min ba zan taba yarda ba, taya abokinsa zai bashi ajiyar condom miyasa shi ba zai aje da kansa ba sai ya bashi ajiya? Ban san lokacin da kuka ya kubuce min ba, ashe tun da na soma tunanin nake hawaye ban sani ba. “Hajiya Lafiya dai?” “Lafiya kalau dan Allah juya da ni inda ka dauko ni” Na fada ina jan majinar hancina,tare da saka hannuna na share hawayena. Kamar yadda na umarce shi haka ya juya ya koma, sai dai ban bari ya karasa ba na tsayar da shi na sauka na bashi kudin shi, daman ba gidan zan koma ba, gidan su kawata Hajara zan je na saba zuwa can a duk lokacin da abun duniya ya taru yai min yawa ita kanta da zarra ta ganni ta san akwai wata matsalar. Sallamar da nai cikin muryar kuka ce ta karantar da ita ina cikin wani hali. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u” Shi ta furta amaimakon ta amsa min sallamar, ta aje Affan da ke hannunta saman kujera ta taso ta nufo inda nake ta dafa ni ganin kamar ba zan iya karasowa saboda kukan da ya koma min sabo. “Halimatu” “Na'am” Na amsa daker, sannan na zauna a kujerar da ke kusa da ni ita ta zauna kusa da ni tana ta kallon kukan da nake cikin damuwa, har sai da nai wanda zan iya sannan na labarta mata abunda ya saka ni kuka a yau. “Wata kila da gaske ajiya aka bashi, ki rika kyautata masa zato dan Allah” Kaina na daga na kalleta. “Idan wacan ajiya aka bashi wayar da na ji yana yi fa?” Sai tai shiru domin a nan bata da amsar ba ni, ina da tabbacin babu wani abun da zata fada da zai kare shi a nan. “Ba zan ce kunne ki be ji daidai ba, amnan ina son ki sani yawancin mazan nan haka suke, suna nan kashewa matan waje kudi ko da kuwa ba su yi ma na gida ba, ki yi hakuri Halima” “Ko da yaushe idan na fada miki damuwa nai shiru kike cewa, ba ki tunanin hakurin nan zai iya zame min illa? Wallahi na gaji Haraja na gaji” “Karki gaji da bautar Allah, ki dauki aure a matsayin idaba kuma ibadar da ta fi ko wace wahala, dan'adam be tana yin hakuri ya kasa cin ribar hakurin ba, idan rashin kyautawa Aminu baya kyauta miki amman ki yi hakuri wata rana za ki ji dadi” “Yaushe zan jidadin? Tun da na haifi Adnan nake fuskantar wulakanci daga gurin Aminu har yau, haihuwa ta hudu kawai yake min wannan abun ime kike tunani a gaba? Ya GOBE NA zata kasance? Ina jin kamar babu wata matar auren da zata iya hakurin zaman auren da na ke da Aminu, shi ya min yan'uwansa su min ya zan ji?” Dafani tai tana min magana a hankali “Suna nan da yawa wadanda suka fi ki hakuri Halimatu, wasu ko abincin basa samu amman haka suke hakuri su zauna, ke ko har yana aje miki abinci ko da bashi da dadi ya dai baki lokacinsa ne kawai baya bashi da wasu hakokin, shin idan ba ki yi hakuri ba Halima so kike na ce ki kashe aurenki ki koma gidanku da zama cikin kannenki? Ya matan gidan ku a yanzu taskwas ne so kike a fara kirgawa da ke a zaurawan unguwarku? Ki tashi hankalin iyayenki da na yayanki? Kina da tabbacin shi wani mijin da zaki aura baya nema mata ko kuma zai baki lokacinsa? Ki bar yayanki su tashi a hannun wata wacce ba uwarsu ba? Adnan shekararsa goma sha daya kuma shine babba shi din ma kina da tabbacin zai iya yi ma kansa wata lalurar balle kuma sauran?” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u.” Shine abunda nake ta furtawa na dafe kaina. “Ki yi taka tsantsan da aurenki Halima saki daya ya rage a tsakaninku, wani abun ko dan yaranki ai kya yi hakuri ki zauna da mijinki a haka, kuma ki gode Allah da har mijinki yana amfani da Condom din, wasu mazan kamar tumaki suke babu ruwansu da kariyar kai, kuma wani lokacin mu kan mu mata muna da matsala, Halima ko yan gyare gyaren nan ba ki yi su kuma maza basa son haka, mace sai da gyra ko da ko baki haihuwa ba balle kin yi haihuwa har hudu” “Namijin da ba ya maka kallon sha'awa Hajara wani gyara zan tsaya yi akansa? Idan ma nace zan yi gyara zan bata kudina da lokaci na ne a banza” Na fada ina share hawayena. “Ba haka ba ne, ba jira za ki yi har sai shi ya kawo kansa gareki ba, ke ma zaki iya yin wasu abubuwan na wayewa da janyo hankalin mijinki izuwa gareki, su ma matan waje ai ai janyo hankalin mazanjenmu suke har su kao garesu” Kallonta nai ina sauke ajiyar zuciya. “Hajara yace na daina burge shi wai shi baya son mata masu kiba, kuma shi yanzu farar mace yake so ni kuma ba fara ce fes ba, kuma ina da ji ba siririya ba ce ni, bana ganin ina da wani sauran digon kyau da zan iya jan hankalin Aminu da shi a yanzu” “Bayan jan hankali, zamantakewar aure tana bukatar tattauna da fahimtar juna, kin rigani aure Halima amman kamar na riga ki karanta halin maza, ki zauna da mijin ki bashi hakurin abunda ya faru dazun ki nuna masa ke ce mai laifi ko da kuwa shi ne da laifi kuma ki fada masa zaki kiyaye, abu na biyu ki lura da abunda zaki iya canjawa sai ki yi kokarin yi, yar kwaliyar nan t tarbon miji ki rikayi mana haba Halima sai kace ba wayayya ba?” “Namijin da baya dawowa sai 12 ko 1 na dare shi zan yi ma kwaliya? Kuma ya riga ya furta cewar bana burgeshi a yanzu duk wani abun da zan yi aikin banza ne Hajara” “Ki gwada dai, akwai wasu kayan mata masu kyau anjima za a kawo min zan aika miki ki gwada amfani da su, ki maida komai ba komai ba Halima dan Allah ki yi hakuri ki zauna ko dan yayanki” “Da ma kin bar kayanki, rabon da Abban Namra yai mu'amala da ni tun daga lokacin daya fahimci ina da ciki, daman can ba bukatana yake ba balle kuma yanzu” “Ba daga nan take ba, ke dai ki yarda da ni ki gwada dan Allah, wanna kam ba mota ba ko jirgi kika ce kina so sai ya siya miki” Kai na gyada mata ina tabe baki gare da sake share hawayen da suke min zuba, jin motar mijinta yasa na mikewa tsaye, kamin mijinta ya shigo falon nai mata sallama na fita da sauri domin ba kasafai na ke son yana ganina a gidan ba, ba dan komai ba sai dan tsaron mutuncin aurena. Daga gidansu Hajara kai tsaye gurin aikinmu na nufi, sai dai ban shiga Office ba sai da na biya ta gurin masu printing na cikin company nai printing documents din sannan na shiga cikin office din. Na shiga a lokacin da wasu sun dade da shigowa ma'aikatar wasu kuma yanzu suke shigowa a yayinda wasu kuma sai anjima za su shigo kowa da yanayin aikinsa da kuma lokacin shigowarsa. A inda muke zaune mu uku ne a Office din daga ni sai wasu abokan aikina biyu duka maza, daga ni sai Kabeer sai kuma Emmanuel wanda yake ba bahaushe ba. As usual idan na shiga ina gaishe da duk wanda na tarar a office din, idan kuma su suka tarar da ni suna miko min gaisuwa cikin mutunci da girmamawa. Yau kam Kabeer kawai na tarar na office din hakan na nufi ya riga Emmanuel shigowa kenan. “Good morning Kabeer” “Morning Halimatu” Na mika masa gaisuwar a lokacin da nake kokarin zaunawa, shi kuma ya amsa min yana baro bangarensa zuwa inda nake zaune. “Kamar kina cikin damuwa yau kin karya kuwa?” Haka yake min a lokacin dana shigo office din yana kokarin kula da ni kamar matarsa duk kuwa da na san kular bata Allah da Annabi ce ba, na san yana da wata manufar akaina Hannu ya kai zai taba jikina sai nai saurin buge masa hannun na mike tsaye cikin bacin rai na ce. “Miye haka Kabeer taba ni za kai? Ka manta da ina da aure ko me? Wai miyasa kake min wasu abubuwan kamar baka cikin hayyacinka ne?” “Halima kenan, ni da ke mun zama daya a nan fa? Miye laifin dan na na taba jikinki?” “Idan a gurinka ba laifi ba ne ni a gurina laifi ne, ina da aure har da yara hudu abunda ban aijata shi da budurcina ba ba zan aikata shi da aurena ba” Ina fadar hakan na dauki documents din na wuce zuwa office din ogan mu, na yi zaton yana cikin musamman da na ga ya kirani jiya yace na shigo da takardun nan a zaton ko da saffafe zai duba su amman sai gashi ban same shi a office din ba. Hakan yasa na dawo nawa office din na zauna na soma aikina, gaba dayan ranar Oga Dahiru be shigo ba, haka ma wunin ranar Kabeer be ga wata sakewa a tare da ni kamar yadda ya saba gani ba. Har muka tashi daga aikin ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be yi kokarin yi min magana ba. Kamar yadda na saba bayan na taso daga aiki na wuce gidansu Baban Sadi wato kenen mahaifinsu domin dauko yarana daman yana daukarsu tare da yaransa ya kai su gidansa idan an tashi scul har sai idan na taso aiki na biya na dauko su a Napep mu dawo. A bakin kofar falon muka gaisa da matarsa sannan na kirasu suka fito banda Namra. “Ina Namra?” “Tana can part dinsa ai kin san indai yana nan to tana can part dinsa, ko fita zai yi da ita yake fita Allah ya hada jininsu” Cewar Safiya matarsa. Ni kuma nai murmushi ba tare da tunanin komai ba na kalli Aiman na ce yaje ya kirata na saka Amal da Adnan a gaba muka nufi gate da zimmar Namra da Aiman su cin mana. Kamin mu fice daga gate din gidan sai gasu sun ci mana Namra na ta sharar kwalla idonta ya yi ja sosai. “Ke lafiya?” “Cikina ke ciwo” “Oh wannan ciwon cikin ya matsa miki, bari yanzu idan muka muka je gida su Adnan suka wuce Islamiya sai na kai ki asibiti” “To Momy” Ta amsa min cikin kuka har sai da ta bani tausayi. Napep na tara na saka yarana sannan na shiga muka nufo gida. Indomie na fara dafa musu suka ci sukai shirin islamiya sannan na dora tuwo na shiga nai wanka nai ma Namra na shirya ta, sannan na fita na kira Kausar wata kanwar makociyata wacce budurwa ce daman na kan kirata ta rika min wasu abubuwa. Ita na barwa girkin sannan na ja Namra muka nufi Asibitin Yarima ganin likitan yara na maraice. Ba mu tararda jira kamar safe ba, daman da maraici ba a cika taruwa ba, a lokacin da muka shiga dakin likita ya tambaye ta komai ta fada masa yadda take jin cikin nata yana mata ciwo, sannan na rubuta mana hoto da awon fitsari sannan na rubuta mata magani. Sai da na kaita akai mata hoton fitsarin kuma suka ce a kawo na safe wanda zata fara yi kamin ta ci komai. Maganin ne kawai ban siya mata ba muka dawo. A saman kujera ta kwanta ni kuma na shiga kitchen na dora miya domin ko da muka dawo Kausar ta toke mana tuwon. Daf da magariba Adnan suka dawo daga makarantar islamiya, daker na tattara su sukai sallah sannan na kwashe miyar na zuba musu nasu na sako nawa ni da Amal muka ci Namra kan ko ruwa kasa sha tai, hakan yasa na dauki wayata na kira shi. Sai da ta dade tana ringing sannan na daga. “Ya akai?” Shine abunda ya far tambaya, ni kuma na mika masa gaisuwa “Ina wuni?” “Lafiya Kalau” “Namra ce bata da lafiya tun jiya cikina na ciwo shine na kaita asibiti dazun suka bamu awon fitsari da hoto kuma suka rubuto mata magani” “Wa kika tambaya kamin ki fita? Da izinin wa kika fita?” Sai na kasa amsa masa domin na san bana da gaskiya a nan, be kamata na fita ba tare da na tambaye shi ba, sai dai na san idan na tsaya tambayarsa ba lallai ne yace na tafi ba domin duk wani abu daya fito daga bangarena baya daukar sa da muhimmancin wata kila ma zai ce kashin kudin ne zan ja masa. “Ka yi hakuri dan Allah” Be amsa min ba yaja tsaki ya kashe wayar. Ji kuma na sauke ina jin raina ba dadi a take abincin ya fita raina daman da safe ban iya karyawa ba. “Adnan je ka kira min Kausar ta siyo ma Namra magani a chemist” Da sauri ya tashi daman dan son yawo ne shi da Amal a take ta rufa masa baya har da gudunta. I decided na aiki Kausar din na bata kudin da ke hannu ta siyo mata maganin kamin shi ya gama fushinsa ya siyo mata. Adnan na fita sai ga Afrah ta shigo wato yar Hajara da bakar leda a hannuna. “Wai ga shi Momy tace a kawo miki” Karba kawai nai na aje ba dan ina tunanin amfani da shi ba, domin na saba amfani da irin abubuwan nan ban taba ganin ribarsu ba, sai dai na ji wasu matan suna labarin abu kaza yana da kyau ko yana yi, ni dai nawa mijin bayan nuna min idan ma na sh wata kila kuma ni tawa hallintar bara karbar irin waennan abubuwan. Afrah na fita sai aka sake turo kofar falon aka shigo wannan karon Sa'adatu ce kawata. “A a maraba da manya” Na fada ina dariya. “Ah ai kune manya kuna cikin irin wannan gida haka ga uwar daula ai kukan ku kukai dacen auren mu mata kawai muka rako duniya” “Uhmm” Kawai na iya fada domin yawancin mutanen da suke zuwa gidana suka ganin kyakkyawan falona da gidan sai su tai min kallon kamar na fi kowa dacen aure. “Bari dai na kawo miki ruwa” Na fada ina nufar kitchen, ita kuma ta hau tambayar ina Amal da sauran yaran. __________________ Anya da gaske akwai mata irin Halimatu kuwa? 🤔 7/20/21, 8:28 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 4️⃣ “Sa'adatu kenan, kwana biyu ma kin daina dan lekowa, ko ya fara hana yawo ne?” Na fada bayan na mika mata ruwan sai ta wara ido. “Tab ya isa? Ai a hannuna yake sai yadda na ga dama na juya shi” “Too kaji manya a bamu sirrin” “Sirrin mai wuya ne Halima,amman Wallahi da ni nake da kyau ki da irin wannna jikin na ki sai na more” Kallon rashin fahimta nai mata. “Kamar ya ba?” “Ka more rayuwa mana, kai ta sha'aninka kana zuwa duk inda kake so” Ta fada tana janye mayafinta daga jikinta a take kirjinta ya bayyana, daman irin dinkin nan mai bayyana maman mace daga gaba. “Ai kin san halin wani namjin ba daya ne da wani ba, kin ga ke idan mijin ki mai sauki kai ne baban naki ba shi da dama” Na fada tare da kiran Aminu da babanta kamar yadda take kiransa kasancewar sunan mahaifinta ne. “Babu namijin da yake da dama Halima, ni kin ga mijina Wallahi zan iya tafiya wani garin na kwana iya kwanakin da naji sun min na dawo be isa ya ce min komai ba” “Too ku manya ne Sa'adatu” Na fada cike da sha'awa da kuma jinjina abunda ta fada, ko bata fada min da bakinta ba na san zata iya domin ta saba zuwa wani gari da sunan biki ko ganin yan'uwa ta bar masa yaransa sai ranar data ga dama ta dawo kuma ba zai yi komai ba. Abun har burgeni yake ni da wani lokacin ko makota sai Abban Namra ya hana ni zuwa. “Wai ya kika ba ni ruwa zalla a tsirara ba masu kala ne?” “Baban na ki ne be siyo masu kala ba” “Aa Babana fa komai kawowa yake karki cutar da shi, daman kin saba bakin sherinki ni bari ma na tashi daman bankwana na zo nai miki zanje Kaduna gobe In-Sha-Allah” “Kaduna kuma? Gurin me?” “Wallahi wani abun bikin ne ya taso mana zanje na kwana hudu ko sati ma a can” “Da yaran zaki je kenan” “Aa ni kadai zanje na shakatawata abuna yara su zauna gurin Babansu” “To indai baki yi hankali ba sai ya dauko miki wata” “Ai be isa ba Wallahi wa? Ni? Hmmmm ai na bashi wannan ya shanye” Ta fada tana wani turo dankwali tare da nuna min kasan kafarta. “Haka fa, na ji ance ana yi ko?” “Au tsayawa ji kikai? Ba ki ma aikata ba” “Ina ganin kamar akwai rashin dacewa a haka” “To yar sarkin Malamai” Dariya nai zan sake magana sai jin tsayawar motar Abban Namra mu ka ji, a take gabana ya fadi domin na san zai tambaye shi yaransa gashi tun da na aikasu basu dawo ba, kamin ya shigo falon hankalina ya tashi sosai saboda aiken da nai musu ga kuma fita kai Namra asibiti da nai ba tare da izininsa ba na san zai iya yi min fada a gaban kowa, ni kuwa abunda na tsana kenan ayi min fada a gaban wani musamman kawayena. Fuska a hade ya shigo falon ni kuma nai saurin mikewa tsaye na nufi inda yake ina masa sannu da zuwa tare da kai hannu na karbi jakarsa. Da kamar ba zai amsa min sannun da nai masa ba, sai dai yana gada ido da Sa'adatu sai ya sake fuskarsa. “Yauwa, a a diyata ce da kanta a gidan?” “Nice Babana ya garin ya gararin garin?” Ta amsa tana wani karkada ido, na yi zaton ko zata ja mayafinta ta rufe kirjinta ne kuma ta gyara ture kaga tsiyar da tai na dankwalinta amman ba ko daya, zama yai a kujerar da ke facing din tata yana murmushi. “Fatar kin zo lafiya?” “Lafiya kalau matarka ta bani ruwa masu sanyi amman ba masu kala na yi magana tace Babana be siyo ba” Sai juyo yai ya kalleni ina kokarin zama kusa da shi. “Ah ah drinks ya kare ne daman? Ai baki fada min ba” Kasa ce masa komai nai bayan kallon mamaki da nake masa rabon da ya siyo mana wani abu mai sunan lemu mu sha a gidan har na manta, amman yau saboda ya nuna yana siya har yake tambayar yaushe ya kare? Haka yake min idan ya ga mutane ni kuma bana iya karyata shi. “Jiya ya kare” Na fada ina hade yawun bakina. “Okay bari sai gobe a siyo ai ban sani ba, ina fatar kin ci abinci?” Ya karasa yana naida dubansa gurin Sa'adatu. “Aa ban ci ba” Sai ya juyo kaina. “Miyasa ba a bata abinci ba? Ko ba a gama ba? A kawo mata abincin mana” “Aa ni tafiya ma zanyi” Ta fada tana janyo mayafinta ta rufe jikinta tare da gyara dankwalinta. Sai shi ma ya mike tsaye da sauri yana ta kallonta. “Bari na rage miki hanya, ina takardar maganin take?” “Tana daki” “Je ki dauko sai na siyo daga can” Har na bude baki nai magana ganin da gaske yake zai wuce da ita sai kuma wata zuciyar tace nai kawaici na kyale shi. Dakina na shiga na dauko takardar maganin na kawo masa sai ya karba yana duba sannan ya kalleta ya ce. “Muje” “Matar Baba sai wani gamon kuma” “To Allah ya kiyaye hanya” Na fada ina binsu da kallon zuciyata na mugun tsoyuwa. Sai da suka fice daga falon na koma gurin windows din ina hangensu har suk shiga motar yaja sukai gaba, ajiyar zuciya na saki tare da sakin labulen falon sannan na dawo saman kujera ya zauna, na san Sa'adatu zata dauki hankalin Aminu saboda bata da jiki kamar ni kuma ita fara ce sosai kamar dai yadda yake yawan fada min yana son mace fara marar jiki ba irina ba. Tunanin yadda zan yi na rage kibar ne ya fara zuwa min a rai shi farin na san mai sauki ne zan iya siyen mayukan fari na shafa nai fari amman rage kibar ne zai ba ni wahala domin na gwada abubuwa da dama na rage kibar har yau ban dace ba, sai a yanzu na tuno da wani maganin rage kibar da na siye, tashi nai na nufi upstairs, ina shiga dakin na nufi gurin dana rataye jaka na dauka bude n dauko maganin na sauko kasa na shiga kitchen na zuba ruwan zafin da suke a filas na zuba maganin na kasa sugar kadan na fita shi, sannan na zauna ina sha a hankali, zuciyata cike da fatar ya karbe ni ni dai duk abunda zai shiryani da mijina mu yi zaman auren na jindadi da kaunar juna ina son shi, ina ji a raina inda har idan na kawarda kibar nan da ke jikina nai fari fes Aminu zai so ni to na shirya yi ko da kuwa zan kashe kudi da yawa. Ina cikin sha na jiyo Namra tana amai da sauri na aje kofin na fito da sauri na rikata, amai take babu kakkautawa, a take hankalina ya tashi daman abu kadan ya saka ni faduwar gaba ko kuka. A cikin falon tai aman har ta gama sannan na rika ta na kaita bandakinsu na wanke mata jikinta na saka mata wasu tufafin. “Momy sanyi na ke ji kum cikina ciwo yake” Ta fada cikin kuka jikinta na ta kyarma. Rigar sanyi na dauko na saka mata na kwantar da ita saman gadonsu na lullube ta sannan na fito na gyara falon. Sai da na gama gyaran sannan Adnan da Aiman suka dawo daga aiken da nai musu tare da Kausar din. “Ina kuke je kuka tsaya tun dazun?” Na fada cikin tsawa a take tsoro ya rufe Adnan. “Momy ko da muka je bata cikin gidan sai muka jira har ta dawo muka fada mata, ki yi hakuri dan Allah” Abunda sukai min be kai ya saka raina baci ba balle har na dake su, amman sai zuciyata ta rufe a take a gurin na mari Adnan kamar wani babba na ciro wayar caja na saka na zanesu tas suna da kuka da ihu Aiman na ni yake ta kira amman nai kunne uwar shegu da ihun na su kuma na tirsasu su yi shiru. “Kausar ki bar shi kawai daman magani za ki yo ma Namra kuma Babansu ya karbi takardar maganin” Da to ta amsa min ta fice da sauri ganin kamar raina a bace yake. Ni kuma na koma kitchen din na hada wa Namra tea wai ko zata iya sha amman ta kasa sha, sai kuka take hakan yasa hankalina ya tashi na sake gwada kiran Abbansu wayar tai ringing har ta gama be dauka ba. Be kuma shigo gidan ba sai sha biyu da mintuna kamar yadda ya saba, ni kuma har lokacin ban yi bachi ba ina rumgume da Namra ga Amal a bayana wacce ta cilasta ni goyonta saboda bakar rigima irin nata. “Sannu da zuwa” “yauwa” Ya amsa min fuskarsa ba yabo ba fallasa sannan na wulgo min ledar maganin ya nufi hanyar dakinsa, kwantar da Namra nai daga saman jikina zuwa jikin kujera na tashi na nufi inda ledar maganin take na dauka zuciyata nata soyuwa, na rasa gane wane irin zama na ke da Aminu, kamar waenda akai auren dole ko kuma basa kaunar junansu haka yake mu'amala da ni, ko za a yanka ni ba zan iya fadar abunda nai masa ba wanda ya saka yake min wannan wulakancin. Ta jikin kwalin maganin na duba yadda ake badawa na zuba na bata ta sha sannan na dauketa daga falon na sake maida ita dakinsu tare da yan'uwanta na kwantar da ita, kana na nufi gadon Amal na kwantar da ita ita ma nai mata addu'a na tofa mata sannan na janyo kofar dakin na fito. Dakina na koma na sauya tufafin jikina daga atamfa zuwa wani yadi mai kyau da kyalli na fesa turare na gyara fuska na shafa janbaki da dan man baki kadan dan yai kyali sannan na fito na nufi dakinsa. Da sallama na shiga ya amsa min yana cin abinci ba tare da ya kalleni ba. Sai na zauna gabansa ina ta kallon yanayinsa shi kuma hankalinsa na kan wayarsa. “Ya akai?” “Ba ni da hali na zauna da kai da sunan hira ko kallonka sai ka tambaye ni minene? Ban san abunda nai maka ba Abban Namra amman gaba daya ka canja min kamar ba kai ba, ni dai na san ba auren kiyayya mu kai ba amman irin zaman da muke da kai kamar na kiyayya” “Da bakamar yanzu ba ce Halima, auren soyayya mukai kuma ai zaman soyayya muke ko? Ko na kiyayya ne? Ke kanki kin san da bana son ki ba zan zauna da ke ba, kuma rayuwa tana sauyasa ke kanki ai ba kamar yadda kike ada kike a yanzu ba kin canja” Hawaye ne ya fara min zuba. “Canjin jikina kadai be isa ya saka ka wulakanta ni ba, ban sani ba ko na aikata maka wani laifi mai girma da ban sani ba, ko kuma a sani ni ina ganin kamar ba laifi ba ne, dan Allah ka yafe min Abban Namra, na kasa sabawa da zamankewar auren da muke, na kasa fahimtar juya min baya da kai ka yafe min idan wani abun nai maka dan girman Allah” Be ce min uffan ba har ya gama cin abincin ya sha ruwa sannan ya dago kansa ya kalleni ya ce. “Indai kina son mu shirya da ke, to ki aje aikin nan babu yadda za ayi kina aiki kina mu'amala da wasu maza a waje ni kuma kina zaune a gidana kawai a matsayin mata, gashi nan har idonki ya fara zarewa kina fita ba tare da kin tambaye ni ba abunda baki saba ba, Allah kadai yasan kalolin mazan da kike gamuwa da su” “Ka rika kyautata min zato, ko da yaushe kana yawan cewa ina mu'amala da wasu mazan a waje, kana yawan ganin kamar ina aikata fasikanci ne da aurena, ba zan iya aikata zina ba ba zan iya da hakki hudu ba, naka na iyeyena na yayana da kuma na Ubangijina, ina aikin nan ne saboda daukewa kaina wasu lalurorin kai ma ka sani, muna da hidima da yawa a gidanmu iyayena ma suna bukatar taimakona” “Dauke ma kanki wasu lalurorin? Miye bana miki ci ko sha?” “Ba ci da sha ne kadai abunda mace take bukata a gurin mijinta ba Abban Namra, akwai kulawa da wasu bukatun na yau da kullum da kuma ta yan'uwa da iyaye, amman indai har aje aikin nan zai saka ka shirya da ni mu koma muna zama da juna cikin amince da kauna, zan aje sai na kama sana'a” “Aa idan kin san idan kika aje aikin wata sana'ar zaki kama kar na ki aje aikinki daman ai ban isa da ke ba” Kasa cewa komai nai har kuma lokacin hawaye nake, Aminu wani irin murdadden mutum ne wanda baya fahimtar abu idan baya so ba. Taya zai hanani aiki kuma yace ba zan yi sana'a ba, kuma ba zai dauke min duka lalurorina ba? “Ga cikin nan na ce miki a zubar kin ki yarda, haba wane irin abu ne haihuwa hudu a shekara goma sha biyu, ai gashi nan duk kin bude kin wani tsufa, kuma yanxu ana ta abinci ai ba ta haihuwa ake ba ina zan iya da lalurar yara biyar a yanzu, idan kin yaye ki sake daukar wani kuma? Haba abu ai yayi yawa” Ya fada min kai tsaye, sai a yanzu na gane dalilin kauracewa shimfidata da Aminu yai. Mikewa nai tsaye na juyo da zimmar fitowa na baro masa dakin, sai na ji ya ce. “Zanje Kaduna gobe gurin wani aiki, wata kila nai kwana hudu ko sati” Ban juyo ba ban kuma ce masa komai ba, na baro masa dakin na dawo falo na zauna na rungume hannayena ina wani abun a zuciyata, idan nace zan kashe aurena hakika ban san wane hali yarana zasu fada ba, ban kuma san wane kalar mijin zan aura ba, idan kuma na cigaba da zama da shi zan saka kaina cikin damuwa ne kawai marar misaltuwa, domin ko a yanzu idan aka auna na san ba za a sara samuna da hawan jini ba, shekara goma sha daya ba yau ko jiya ba ne. “Idan kika cigaba da zama da mutumen nan, hawan jini ne zai kama ki, zaki kai wani mataki da baki iya komai daga lokacin kin tashi aiki, ba zaki iya tsinanawa kanki komai ba, ban ga dalilin da zai saka ki yi hakurin zama da mutunen nan ba wai wani zaman yayanki shi be san da yayan ba ne yake musguna miki? Ko ke kadai aka dorawa hakkin kula da su” Dafe kaina nai tunawa da maganar da Abdallah yai min akan Aminu, wani bangaren yana da gaskiya idan na ce nai hakurin zama ni ce zan cutu idan kuma na bar gidan still zan cutu da rashin yayana a kusa da ni. “Ko wane aure yana da kalubale Halimatu, ki yi hakuri ki ta addu'a ki karbi kaddararki da hannu biyu, idan kin bar Aminu kina da tabbacin shi mijin da za ki aura ba kamar Aminu ba ne? Idan ba ki hakurin zama da uban diyanki ba ba zaki iya hakurin zama da kowa ba, kuma daga haka za a fara kirga miki aure” Haka Mama take yawan fada min idan ina mata complain din Cewar na gaji da zaman auren nan. Yanzu kumaga sharadin Aminu na aje aiki idan har ina son ya shirya da ni, ba ni da tabbacin idan na aje aiki zai kula ni domin tun kamin aiki ya fara min wannan wulakancin, idan kuma na bar aikin wasu abubuwan da nake iya yi ma iyayena ba zan iya daukar dawainiyar ba, wasu abubuwan da nake iya yi ma kaina dole za su gagareni. Haka dai nai ta tunanina kala kala har kusan biyu na dare sannan na tashi na nufi dakina, wutar dakin na kashe sannan na hau saman gadon na kwanta na lumtse idona ba dan ina jin bachi zai dauke ni ba. Dilllll wayata tai kara alamar shigowar sako bude idona nai na ka hannuna saman aljihun gadon na dauki wayar ina dubawa. _Ki yafe min dan Allah, na kasa bachi saboda na san yau na bata miki rai, amman ban yi zimmar daba ki da wata manufa ba, ina ganin kamar ni da ke mun zama daya ne, kuma ni na dauke shi a matsayin wayewa ba wai dan wani abun ba, sai dai naga kamar ranki ya bace ki yi hakuri dan Allah ki shafa min kan yaran nan ki gaishe su_ _Kabeer_ Ina gama karant sakon hawaye ya wanke min fuska, wani wanda ba mijina ba shi yake damuwa da fushi da bacin raina har ya gaishe da yarana. Rumgume wayar nai a kirjina ina jin wani irin kyautata da ganin kimar Kabeer. __________________ Anya Halimtu zata aje aikin kuwa? Ko kuwa dai zata zabi zama da Aminu a haka? Wai mi yake damun Namra ne? 🤔 7/20/21, 8:29 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 5️⃣ Iyayena na gari abun alfahari idan kai dace da iyaye hakika ka yi babban dace, bayan su kuma sai miji shi ma idan kai dace da miji na gari ka samu ingantacciyar rayuwa idan Allah yai maka falala ka sake dace da yayana nagari ko kai an gama maka komai a rayuwarka. Al-hamdulillah ban san yanda tarbiyar yarana zata kasance ba bayan girmansu amman ina fatar su tashi akan tafarkin da na dora su akai, idan na samu haka ko da shi kadai zan iya gode Allah, duk kuwa da na san babbar jarabawar duniya ita ce ta rashin dacen miji. Ban taba jin kewar budurci ba irin yau, ji nake kamar ace yau ni din budurwa ce da na sake zaben wani mijin ba Aminu ba, na kwana rungume da sakon wani a kirjina saboda rashin kulawar mijina, da ace na san rayuwa zata sauya min haka bayan aure da na zabi zama a budurcin har na bar duniyar nan, bachi be dauke ni da wuri ba, haka kuma ban dade ina bachin ba na farka, kaina har wani nauyi nake jin yana min ga wani uban ciwon zuciya da nake jinsa har cikin kashin bayana. After sallah nai addu'o'in da na saba sannan na nufi kitchen domin hada ma yarana abincin zuwa makaranta, misalin bakwai saura na safe ya shigo kitchen din rike da jakarsa sai ya tsaya a jikin kofa, ni kuma nai kamar ba san da mutum a gurin ba har sai da yai gyaran murya sannan na juyo na kalleshi “Ina kwana?” “Lafiya kalau, ga wannan ki rike da wuri zan tafi saboda bana son rana yai min” Ya fada yana miko min dubu uku, kallon kudin nai na girgiza masa kai. “Ka kara akwai kudin da za su ishemu har ka dawo” Be ce min komai ba, ya aje kudin saman kitchen cabinet ya juya, a karon farko yau zai tafi wani gari amman na kasa ce masa Allah ya tsare sai binsa da nai da kallo. Juyowa yai ya kalleni. “Da ki min addu'a da karki min duka uwarsu daya ubansu daya, sai abunda Allah ya rubuto zai same ni, mugun nufinki ya koma kanki” Yana fadar hakan ya juya ya fice, ni kuma nai murmushi ina jin bakar maganar da ya fada min har cikin raina. Kaina na daga ina kallon kitchen din yadda tsarin gidanmu yake da siffar masu arziki ko kyautar rabin miliyan nai ba za ayi mamaki ba saboda ana ganin mai arzikin nake aure, amman yau zai yi tafiya saboda bakar keta irin nasa ya dauki dubu uku ya bani. Dauke kai nai domin na san idan na ce zan cigaba da tunani zan iya faduwa a gurin ko kuma wani abun ya same ni. Bakwai da rabi na shiga na tashi yarana nai musu wanka sukai alwala sukai sallah sannan na shirya su cikin uniform dinsu na makarantar boko ban da Namra da har yanzu bachi take jikinta kuma da dan zafi. Kasa suka sauko suka karya tare da Amal sannan na shiga dakina na saka hijab na fito na saka su gaba muka nufi gate. Sai dai mun yi sa'ar haduwa da mijin Hajara kamar jiya. “Ina Namra yau?” “Bata jindadi” “Subhanallahi Allah ya sauwake” “Amin” Sai ya saka yaran a motarsa har da Amal suka tafi, daman ta saba idan yan kwarai suna kanta tana yarda ta bisu su tafi idan ya dawo sai ya kaita gurin Hajara. Juyowa nai na dawo cikin gidan, sai na shiga dakina nai wanka ina cikin shiryawa wayarta tai ringing, dauka nai na duba sai ga number Abdulhamid hakan yasa ni picking na kara a kunne. “Hello” “Good morning Halima ya gida ya yaran?” “Lafiya kalau” “Na miki sako ta whatsapp wai baki hau ba so i decided na kira ki” “Lafiya dai?” “Account number dinki na k so dan Allah zan dan saka miki wani a ciki” Dauke wayar nai daga kunnena na duba dan kara tabbatarwa idab Abdulhamid din ne, ganin shi ne yasa na maida wayar a kunne na ce. “Abdallah yace ka saka min?” “Abdallah kuma?” Shiru nai na kasa cewa komai, na san tawayensa Abdallah shine mai yi min irin wannan dabi'un yana yawan fada min ba dadi Akan Aminu da aure daga daga cikin dalilin daya saka nai blocking dinsa ta ko'ina. “Halima Abdallah yace zai baki kudi ne?” “A a, eh yace amman an dade” “Rokonsa kikai?” “Eh” “Miyasa baki tambaye ni ba? Ba na fada miki ki rika fada min idan kina bukatar wani abun ba?” Na yi shiru ban ce komai ba. “Ki turo min account number dinki yanzu” “To na gode” Na sauke wayar daga kunnena ina tunanin dayan biyu, mi zai saka haka nan kawai Abdulhamid zai ce na turo account ya saka min kudi abunda be ta a ba, ko dai Abdallah ya saka shi yace yai kamar shi ne saboda na karba? Ban yanke dayan biyu ba na tura masa account din. Sannan na aje wayar na tashi na nufi dakin yara ina tuna rayuwar da mukai a baya, wata kila da shi na aura kamar yadda na tsarawa kaina da yanzu na yi dacen aure, sai dai lalurra da ke tare da shi ta sauya kaddararmu shi ya a zauna a haka har yanzu babu aure ni kuma nai auren na kasa dacewa da mijin. _Zan jira har zuwa lokacin da zaka samu lafiya Abdulhamid_ _Aa mace ce ke Halima be kamata ki zauna a haka na tsawon lokaci ba ba, idan na hana ki aure a yanzu zai zama na cutar da ke ne kawai_ _To zan aureka na zauna a gidanka har ka samu lafiya_ _Shi ma cutarwa ne Halima ba zan iya aurenki na danne miki hakki ba, ban san iya yaushe zan dauka kamin na samu lafiya ba, ke kuma wannan ce kadai damar da kike da ita ta zabar mijin aure, kuma iyayenki suna son ganin aurenki a yanzu kin kai matakin da ya kamata ace kina dakin mijinki_ _Yanzu rabuwa za mu yi kenan Abdulhamid?_ _Rabuwa ta zame mana dole shiyasa ban taba fadawa kowa ina kaunarki ba, kuma ban taba nunawa ba, ke ma kuma na nuna miki ne a zaton kamin ki gama karatunki wata kila na samu lafiya, ashe abun ba nan kusa ba ne wata kila ma ba zan warke ba_ Tunawa da wannan ya saka ni zubar hawaye, sai dai ina shiga dakin yara sai nai saurin sharewa na nufi inda Namra take kwance ya yaye blanket din na kai hannu na taba ta, sai ta bude ido. “Sannu Namra” “To Momy yau ba zan je scul ba” “Eh yau asbitin zan koma da ke ai su sake dubaki saboda ciwon cikinan” Jin na goya mata baya ba zata je scul ba sai ya saka ta sauko da kafafuwanta, na rika ta muka nufi bathroom. Mai na soma saka mata a brush ita kuma ta fara yin fitsari sai ta saka kuka. “Momy zafi” “Minene zafi?” “Fitsarin zafi sosai” Brush din n aje na zo na daga ta na saka ta a cikin tub din na ware kafafuwanta ina dubawa. Gurin ya mata ja sosai kamar an watsa mata yaji a ciki gashi har ya mata rame a ciki. “Namra me ya same ki a nan?” Sai kawai ta kara bare baki tana lekawa ta kasa ce min komai. “Ba komai” Na fada tana kuka, tsawa na daka mata har sai da ta zabura. “Fada min mi ya same mi a gurin” “Wayyo Allah na ba ni, Momy dan Allah ki yi hakuri” Ta fada cikin kuka tana yarfar da hannu. Mikewa nai tsaye fuska a hade na ce mata. “Kin san idan kika min laifi dukanki na ke ko? To yau yankaki zan yi kamar rago na soya namanki na zubar a bola” Ina fadar hakan na juya ya fice daga bandakin na sauko kasa gabana sai dukan shida-shida yake tsabanin uku-uku da na kowa ke yi. Kitchen na nufa na dauko wuka na hawo saman na shiga dakin sai an samu ta fito daga bandakin ta labe gefen gado tana ta rusa ihu. “Momy dan Allah ki yi hakuri karki kashe ni bana son na mutu dan Allah ki yi hakuri” “To fada min mi ya same ni a nan” “Idan na fada shi ma Baba Sadi yanka ni zai yi, wayyo na shiga uku Abbah..... ” Kasa magana nai jin abunda ta fada gaba daya sai jikina ya kara yin sanyi, ga wani uban kuka da take kamar zata shude. Aje wukar nai na mika mata hannuna. “Taso zo nan” Sai ta girgiza min kai. “Aa yanka ni za ki yi Momy ba zan zo ba” “Ba zan yanka ki ba ni mahaifiyarki ce ba zan iya yankaki ba, idan kin fada min abunda Baba Sadi yake miki ba zan miki komai ba” “Idan kuma na fada shi ma yanka ni zai yi wayyo Allah na” “Ba zan bari na yanka ki ba, kuma ba zan fada masa cewar kin fada min ba, wannan sirrin mu ne ai ba zan fadawa kowa ba” Na fada ina karasawa kusa da ita a hankali, sannan na kai hannu na rika ya dawo da ita saman jikina na rumgume har lokacin kuka take jikinta na ta rawa sosai. Kyale ta nai sai da ta ci kukan ta a jikina sannan na dago ta na share mata hawayenta ina mata murmushi ta yadda hankalinta zai kwanta ta yarda da ni. “Yata Namra fada min mi Baba Sadi yake miki?” “Ba zaki min komai ba?” “Eh kuma ba za su fada masa ba ai wannan sirrin mu ne mu kadai ko Abbah ba zan fadawa ba” “Yace idan na fada sai ya yanka ni kuma na kone gawata kuma yace idan an mutu can zan samu wuta tai ta kona ni ciki kasa” “Karya ne kawai yakr baki tsoro ne, fada min zan siya miki duk abunda kike so” Shiru tai na wani lokaci sannan ta sake daga kanta ta kalleni. “Momy ni bana son na mutu” “Ba zaki mutu ba idan kika fada min” “A nan yake saka min abu” Ta nuna gabanta tana kallon fuskata, sai nai mata murmushi ina nuna gurin. “A nan?” “Eh da kuma abaki yake saka min wannan abun” “Shine wani abun tsoro? Ai ba wani abun ba ne, da har zaki ji tsoro” “Amman shi yace karna fada” “Shikenan abunda yake miki?” Na tambaya ina jin kamar kuka sai kubuce min, su kan hawaye tuni na fara yinsu. “Eh da hannu yake saka min sai jiya da wacan monday ya sska min abun fitsarinsa a nan, kuma da zafi sosai idan nai kuka sai ya ce ba zai ba ni chocolate ba, kuma idan na fada zai ya ka ni?” “Da yaushe da yaushe yake miki haka?” “Idan muna part dinsa sai na kore su Adnan da su Safwan yace su tafi ni kadai na tsaya wai suna masa yahaniya ni ce kawai bana masa ihu sai su tafi idan suka tafi sai ya saka min hannu a nan ko kuma ya bani yace na sha, kuma ya ce idan ban hade wannan majinar ba sai doke ni, ko kuma ya saka bakinsa a nan ya yi min yadda nake masa, wata rana kuma idan mun tafi wani gurin sai ya fita da ni ya siya min abun dadi yai min haka nan ko yace nai masa, ko ranar da muka tafi yawo sai ya aje su Safwan da Aiman a gurin wasan yara ni ya tafi da ni a mota ya saka ni na sha masa tsanar sa, tsana haka yake cewa” Ban iya komai ba a lokacin bayan fashewa da kuka mai tsanani. Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen da ta taba kasancewa. Daga ni sai ire-irena mu ke iya bayyana yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni Halimatu aka keta ba na yata ba? “Namra miyasa baki fada min ba tuntuni?” “Ai yace idan na fada zai yanka ni kuma na fada miki bana son zuwa can ke kuma sai ki ce sai mun tafi kamin ki dawo daga aiki” Rasa nai abunda zan yi ko na ce mata sai kawai na sauke ta daga jikina na aje ta saman gadon na taso na baro mata dakin na dawo falo na zauna na safe kaina ina jin zuciyata kamar zata fashe. Kuka nai sosai ba na wasa ba ji nake kamar na hade zuciya na mutu na hutu gaba daya. Kamar wacce aka tsikara na tashi da sauri na koma sama na dauki Hijab dina na saka na dauki jakata da wayata na nufo dakinsu na dauke ta da kayan bachinta muka fito ko rufe gidan ban tsaya yi ba na nufi titi ina samun napep muka nufi asibiti. Har cikin asibitin hawaye nake ina sharewa gashi na yi rashin sa'a na tarar har an gama daukar suna, a karon na farko bayan na yi blocking din number Abdallah yau da kaina ba daga waya na kira shi. Bugu biyu ya dauka. “Ko dai kin kira ki min bakar magana ko kuma ki zage ni, domin na san ina da farinjinin da ba zaki kirani ki min magana kamar yar'uwa ba” Fashewa nai da kuka. “Dan Allah Abdallah ka taimaka min na zo an gama daukar suna na kawo Namra ne” “Kina ina?” “Ina bangaren yara bakin kofar shiga” “To zan zo na same ki a nan” Tsakanin kashe wayarsa da zuwansa be wuce minti biyar ba, da alama yana kusa da gurin kuma ya karasa inda na ke da sauri har yana hadawa da gudu. Ganin yadda hawaye ke min zuba yasa shi tsayawa yana kallona. “Halima lafiya?” Kasa magana nai sai yaja hannun Namra yana dubata. “Mi ya same ta wai? Lafiya kike?” Hankalinsa ya tashi sosai ganin ina kuka. “Lafiyarta nake son a abinci ka min” Na fada ina hawaye kamar ba gobe bakina na rawa. “Lafiyarta kuma?” Kasa amsa masa nai sai na juya da zimmar tafiya. “Halima?” Na juyo. “Lafiyar ki kuwa?” “Ban sani ba, ina jin kamar bana da damuwa kuma ina jin kamar akwai abunda yake damuna, gida nake son naje” “Wane gida?” “Gida gurin Mama da Baba na fada musu” Magana nake ni kaina ina jin kamar a mafarki nake maganar ba a zahiri ba. Tallabar Namra yai ya dorata a kafadarsa ni kuma ya rika hannuna. “Zo muje” Ya nufi hanyar da ya fito da ni, ni kuma ina ta binsa ba tare da nasan inda zai kai ni ba, mutumen da na ke ciwa mutunci ina zaginsa yau yana jaye da hannuna na kyaleshi. _______________________ Tsakanin Namra da Halima wa yafi zama abun tausayi? Namra da aka lalatawa rayuwa ko kuma Halima da take mahaifiyarta kuma take rayuwa da mugun miji? 😭 Allah kasa mu dace 🙏😪 7/20/21, 8:29 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 6️⃣ Office dinsa ya shiga da ni, sai ya saki hannuna ya sauke Namra daga saman kafadarsa ya zaunar da ita a saman kujerarsa sannan ya rufe kofar office din ya sake rika hannuna ya zaunar da ni a dayar kujerar dake kusa da kofar, sai ya zauna shi ma yana ta kallona ya kasa cewa komai, ni ma shi nake kallo amman ba kallo na ainahin kyausa ko wani abun daya shafi jikinsa ko fuskarsa ba, kallonsa nake a zahiri amman a badini zuciyata tana can gurin tunanin yau da kuma GOBENA, har yanzu na kasa yarda ba mafarki na ke ba, har yanzu hawayen ba su daina sauko min ba, har yanzu ban daina jin sautin muryar Namra na maimaita kanta a kwakwalwata ba, ji nake kamar yanzu take ba ni labarin nan, rumtse ido nai na kulle gam ina jin kamar idan na bude zan ga komai be faru ba, ji na ke kamar ace idan na bude idon zan farka daga mummunan mafarkin da nai yi ne. “Halima” Can cikin kaina na ji kiran Abdallah da sauri na bude idon ina kallonsa har nunfashina na rawa kamar wacce ta farka daga bachi, da gaske ji nake kamar ace mafarki ne ba gaske ba. “Miya samu Namra?” Ya tambaya fuskarsa na nuna tsantsar damuwa da ganin hawayen. Nuna masa Namra din nai na kasa cewa komai, bakina nai nauyi sosai kamar an saka min dutse a ciki, wata kila kalaman da zan furta a duniya sun kare ne, domin ina jin idan har bakina zai bude da sunan magana a yanzu to kuka ne kawai zai fito amman ba magana irin wacce ko wane lafiyayen mutum yake ba. Kai nake ta daga masa alamar ita din ce ita dince kamar wanda ya sake tambaya, shi kuma ya tattara hankalinsa ya maida akaina sai yawo yake da idonsa a fuskata. “Bana son zubar hawayen nan na ki Halima, ki bude baki yi min magana maybe i can help” Ya fada yana dauke kansa daga barin kallona ya dafe da hannunsa yana sauke numfashin da karfi, can kuma ya mike tsaye ya nufi gurin windows din ya tsaya yana kallon waje kamin ya buga hannunsa da karfi jikin ginin gurin. “Matsalarki duk ba zata wuce ta shegen mijin nan na ki ba, can you pls talk” Ya fada yana juyowa ya kalleni, yunkurin bude baki nai da zimmar magana da gaske sai na kasa maganar har kuma lokacin ban daina hawaye ba kamar an rubuto min ranar kawai domin kuka. Teburinsa ya nufa ya dauko takardarda biro ya aje min a gabana. “Rubuta idan ba zaki iya min magana ba” _So na ke a duba min Namra fyade akai mata_ Haka na rubuta a takardar na mika masa, yana karantawa ya zaro ido ya kalli Namra da sauri sannan ya kalle ni. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, garin ya?” Nan ma kasa magana nai sai dai na bude bakina ba kamar dazun ba da dantse har da hakorana. Barin gurin da nake yai ya nufi gurin Namra. “Namra wa yai miki haka? Fada min ya akai hakan ya faru?” Tana kallonsa sai ta fashe da kuka daman tun da muka shigo take alamar kukan ganin nima kukan na ke yi. Sauko tai daga kan kujera ta rugo a guje inda nake zaune ta rumgume ni tana wani irin kuka mai taba zuba zuciya, ni ma fashewa nai da kukan mai sauti na rumgume yata kankan a jikina ita kuka ni kuma, sai a lokacin na fara tambayar kaina ina tunanin abunda nai wa Sadi da zai yi ma yata haka? A kullum burina da mafarkina na tsare mutuncin kaina da na mijina da na yayana, amman yau wani a cikin familyn mijina ya keta yadda yata, ya rusa min komai. “Miyasa zai min haka? Mi masa a duniyar nan? Me zai ji a jikin karamar yarinya kamar Namra? Kuma yar dan'uwansa? Mi yasa zai saka mu a wannan halin ni da ita?” Magana na ke ina kallon Abdallah kamar shi zai ba ni amsar duka tambayoyina. Mikewa nai tsaye rumgume da Namra na fara zagaye dakin. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u” Haka nai ta maimaita ina jin zuciyata kamar zata rabe gida biyu, numfashina kuma yana ta kokuwa da jikina, sai na yi da gaske yake fita ya shiga. Abdallah ne ya miko hannu ya karbe ta. “Zan kula da ita zan yi mata duk abunda ya dace ke ki zauna a nan” Daga haka ya juya ya fice, ni kuma na nufi kujerar da sauri na zauna saboda kafafuwana da na ke jin kamar ba za su dauke ni ba, ga wani sanyi da nake jin na taso min har hakorana na son haduwa da juna. Babu wanda ya fado min a rai yanzu sai Abban Namra shi ya kamata ace yana tsaye a tare da ni muna wannan jimamin a tare ya kamata ace ya san halin da yarsa take ciki, da sauri na bude jakata na fiddo wayata na kira numbersa haka tai ringing har ta katse be daga ba, na sake gwadawa nan ma be daga ba, sai da na jira masa miss calls har hudu a na biyar ya daga a fusace. “Wai ya akai? Ina aiki kina ta damuna da kira” Kasa ce masa komai nai sai sauke numfashi nake, har ya gaji ya kashe wayar, wani irin abu marar misaltuwa na ji ya ratsa zuciyata ya tsaya min a makoshi, mutumen da ya fita be tambaya lafiyar yarsa ba bayan ya sa bata da lafiya yanzu kuma na kira shi yace min aiki yake ina damunsa, wane irin aiki ne wanda ya fi iyalinsa muhimmanci, wane aiki ma mutumen da yace min tafiya zai yi? A yanzu shi na ya kamata ace yana tsaye a bayana yana jimamin wannan lamarin tare da ni, shi ne ya kamata ace ya tsare min komai da ban nemi yin aiki ba da yanzu ina tare da yayana ba sai na kai su gidan wani ba, wata kila da be yi da yar wani ba da yanzu ba ayi da tasa ba. Jikina ne ya fara rawa har wayar da ke hannuna ta fadi ina ta jin wani abu na juya min a ciki kai kamar kwaro, ban san lokacin da Abdallah ya shigo ba sai muryarsa na ji. “Halima karki jawa kan ki depression” Kallonsa nai. “Kwanta” Ya fada sai na kwanta kamar daman can umarninsa nake jira. Sai ya cire rigar likitoci dake jikinsa ya rufa min. “Abunda na ke jiye miki kenan, shiyasa tun kamin ki haifi yaran nan nai ta nuna miki cewar ki rabu da mijinki, ki kashe aurenki amman kika ji, daman namijin da be iya komai ba sai neman mata ai dole shi ma a dana yarsa, yanzu ai sai yaji idan da dadi, wani abun bakinciki ma wai kanensa ne zai masa haka? Hakan na nufin familynsu gaba daya lalatacci ne kenan! Wai ya ma san abunda ya faru kuwa? Ko kuma yana can gurin bakin neme nemen matansa?” Haka yai ta magangunsa cikin bacin rai har yai ya gama ya fita bance masa uffan ba, daman can ba son aurena da Aminu yake ba, babu ranar da zan hadu da shi ba zai labarta min cewar ya ga Aminu tare da wata ba, kullum cikin bibiyar rayuwar Aminu yake saboda kawai ya ga aibunsa ya fada min, hakan yasa nai blocking dinsa a fb whatsapp da ma kiransa, shi kadai ne mutummen da bana jituwa da shi a cikin familynmu saboda sukar Aminu da yake min, a duk lokacin da ya fadi min cewar Aminu yana neman mata nakan karyata kuma na hana zuciyata aminta da hakan saboda kar na sakawa kaina rudani kar na saka shakku a zaman aurena da mijina. Na sha jin Aminu yana waya da mata ko na ga chat dinsu amman ina kokarin ganin ban zarge shi ba sai na dora abun akan ruwan dare da zamanin nan da wasu mazan aure suke na chat da mata a waje, duk kuwa da irin dadewar da yake a waje, sai dai kamashi da condom da jin zai yi tafiya wani garin da mace yafi komai karya min guiwa, ga kuma fyaden da akai wa Namra a yanzu, na san akwai kaddara wacce ki giftawa bawa, amman ina jin a jikina wata kila da Aminu be yi ba da ayi ma yarsa ba, domin ni dai na san ko zinar ido ban taba aikatawa ba, amman yau an yi ma yata. Tashi nai zaune na share hawayen idona, ina jin ba Baba Sadi ba, ko Aminu ne ya keta ma Namra haddi a yau ba zan kyale shi ba, rigar Abdallah da ke jikina na aje na mike tsaye na dauki jakata da wayata da ke kasa na nufi kofa kamin na kai hannu na bude sai Abdallah ya turo kofa ya shigo tsayawa yai kallona. “Ina zaki je?” “Gida, ina Namra?” “Zaki iya tafiya, idan na gama zan kawo ta” Tsayawa nai a gurin kamar an dasa ni, sai na ji kamar ba zan iya tafiya na bar shi da yata ba. “You can trust me, tana gurin blood test ma yanzu” “Thank you” Na fada sannan na ratsa ta gefensa zan wuce. “Ke kanki rayuwarki tana cikin hadari Halima, abunda zai fi miki kwanciyar hankali is ki raba kanki da wannan mutum, gashi yanzu dan'uwansa ya maida miki Namra babbar mace!” Wani banza kallo na watsa masa. “Kana tunanin akwai hikima abunda kake fada min a yanzu? Kana ji a ranka ya dace kai min wannan maganar a yanzu? Na kashe aurena na fito na bar yarana a can? Shine kwanciyar hankali da kake fada min? Ko kuma na zuba masa magani ya mutu shine zai nisanta ni da shi? Kullum burinka ka fada min wata bakar magana akan Aminu, kana tunanin dadi na ke ji? Ko kuma kana tunanin hakan zai saka na so ka ne? Hakan be kara min komai ba sai tsanarka Abdallah, ba yau na nake yiwa tanadi ba GOBENA, duk abunda nake ina yi ne saboda yayana da kuma GOBENA....” Cikin fushi na fada mishi hakan sannan na fice ba tare da sake ce min komai ba. Tun daga yanayin tafiyata za ka gane cewa ina cikin fusata, wannan karon ba kuka ne a zuciyata ba, kuzari ne irin na neman hakki ga wanda aka dannewa shi, ina jin a raina zan iya kwatarwa yata hakkinta, ko da hakan zai zama silar mutuwar aurena. Mai napep na tara na shiga be tsaya da ni ko ina ba sai kofar gida, dari biyu na ciro na bashi ban ko tsaya karbar canji ba na shiga cikin gidan. Yan matan gidan mu basa nan kasancewar ranar akwai scul masu zuwa aiki sun tafi masu makaranta ma sun tafi kuma a isa dawowo ba, Mama ta kawai na tarar tsakar gidan Inna na can dakinta tana bachi, tana ganin yanayi na ta san ba lafiya ba. “Halimatu?” Kusa da ita na zauna,sai na ji wani irin natsuwa da kauna ya shiga zuciyata irin na uwa da ƴa, ban shiga da kuka ba, kuma ban shiga dan nai musu kuka ba amman ganin mahaifiyata sai naji kamar ni ma din karamar yarinya ce a jikin uwarta a take na fara hawaye. “Lafiya? Lafiya? Miya same ki Halimatu” Wannan tambayar ce ta fito da Inna daga dakinta tana hamma. “Lafiya dai?” Wani irin abu na ji taya zan fada cewar kanen mahaifinta ya lalata? Sai da na ji na samu natsuwar ruhi da ta zuciya sannan na labarta musu komai. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u” Shine abunda dukansu suka fada, Inna ta dafe kai, Mama kuma ta daka kirjinta ido a waje tana ta maimaita Hasbiyallahu. “Wallahi Mama ba zan kyale wannan maganar ba, sai na kai shi kotu sai an kwatar mata hakkinta” Na fada cikin kuka, sai Mama ta nuna ni da yatsa. “Kul....! Karki so ma, ki kai kotu? Ki tonawa kanki asiri? So kike a yada ki a redio da tv ke da yarki a buga ku a jaridu? So kike idan yarki tai wayo ta koma ganin laifinki? So kike yarki ta rasa mijin aure? Halima karki yi wannan kuskuren Halima, karki alata rayuwar yarki da taki rayuwar” Inna ta karba mata. “Lallai kam duk yadda za a kwato mata hakkinta, zai zubar da mutuncinta ne kawai, wanda be san ayi ma ba yanzu ya sani, suma waenda ake yi ma wa kika taba jin an yankewa wani dogon hukunci? Balle wannan da zai iya tsayawa ya kwaci hakkinsa ya barki nan ke da yarki a cikin mummunar rayuwa, kuma ki jawa kanki da yayanki tsana a gurin dangin mahaifinsu, sannan ki kashe aurenki domin akan wannan abun kin san Aminu zai iya rabuwa da ke daman igiya daya ta rage” Mama ta gyada kai “Ko ma be sake ta ba, ai Mahaifiyarsa zata iya saka ya saketa tunda daman can ba sonta take ba” Hawaye ne suke min zuba irin zubar da bazan iya misaltawa ba, gaba daya kaina na kulle duk wani kuzari na kwatarwa yata hakkinta da nake da shi sai na neme shi na rasa, lankwafar da kai nai ina kallon Mama da abokiyar zamanta Inna hawaye na min zuba na ce “Mutuwar aurena kuke ji ba abunda akai wa yata ba?” Inna ce ta dawo gefena ta zauna ta juyo da ni. “Halimatu, duk wanda zai ce miki be ji zafin abunda akai wa Namra ba to makiyinki ne, sannan kuma duk wanda zai baki shawarar zama a gidan mijinki ki rike yayanki hakika masoyinki ne, Halimatu kanenki mata nawa ne a gidan nan suma neman rabuwa muke da su kai kuma sai ki ce zaki kashe aurenki ki dawo? Kuma kisan auren ma ya zama akan fyaden da akai wa yarki? Ki tonawa kanki asiri? Irin wannan maganar sasantawa ake sai a dauki matakin dan gaba, sirrinki ne wannan ki rike abunki ko yan'uwanki karki ba ri su ji, ki haka rame ki saka shi ciki ki rufe, ko a familyn mijinki karki ba ri kowa ya ji, ki yi hakuri karki ce za ki kai wannan maganar a waje, shi ma Abdallah da yaji ki yi magana da shi ki roke shi ki ce kar ya fadawa kowa kinji?” Na gyada mata kai ina share hawayena. “Na ji” “Na ji” Na sake maimaitawa ina gyada mata kai ido kuma suna ta yawo a tsakar gidan. “Na gane” Na fada ina cizon lisp dina, ni kadai na san abunda nake ji, ni kadai nake jin abunda yake min yawo a zuciya. “Aminu ya san da maganar?” “A a be sani ba” Na amsawa Inna kamar ba ni ba. “To a tsakaninku za ki yi wannan maganar karki nuna masa ma mun ji, kuma karki nuna masa kin kaita asibiti” “To” Na fada ina mikewa tsaye. “Ina za ki je?” Inna tace. “Ai da kin zauna har a jima tunda yace zai kawo miki ita” “Aa kara dai na je gida” Na fada ina tafiya. Mama ta mike tsaye ta biyo bayana tana fadin “Ki rike Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kinji? Dan Allah karki fitarta da maganar nan Halimatu” “To Mama” Na amsa mata ba tare da na jiyo ba, tafiya na fara yi a unguwarmu hawaye na sauko min ina saurin saka hannu na share, har na isa titi na tari napep mai mutum biyu na shiga nice ta uku, mai napep na tafiya ina hawaye har muka hau babban titi, ni aka fara saukewa sai na fito na saka hannu a jaka na dauko kudin mai Napep na mika masa sannan na tura kofar gidana zan shiga sai na jita a kunne, da alama mai gadin ya rufe daga can ciki har sai da na buga sannan ya bude min na shiga yana min sannu da zuwa. Yadda na bar gidan haka na same shi daman da zan fita ban rufe ba domin na fita hankalina baya jikina. Lokacin da n shigo falon sai na zauna a saman kujera kamar wata bakuwa na saka hannuna na dama cikin na hagu na fashe da wani irin kuka, zuciyata na ayyana min na sha wani abun na mutu kawai na huta. Hakika na ci kuma kuma kuka ya ci ni domin ya san da zamana a duniya a wannan yau, ina zaune a gurin ina aikin kuka har aka kira sallah azahar idona ya kumbura sosai har bana iya gani da shi sosai, tun ina kukan a zaune saman cushion har ta kai na fado kasa har na kwanta a gurin na mulmula na buga hannayena a kasa. Sai da na ji tsayawar mota sannan na tashi da sauri na leka ta window bata bakar motace da ban wayeta ba, sai dai hango mai kama da Abdallah ya fito cikin motar da shadda nai ruwan kwai yasa ni koma na dauki hijabina an saka na bude kofar falon na fita, ko da na fito ya doso kofar rumgume da Namra a kafadarsa. A bakin kofa na tsaya shi kuma ya karaso kusa da ni, tun daga yanayin tafiyar da kallon na fahimci ba Abdallah ne ba, domin mutun daya yake min irin wanna kallon wato Abdulhamid domin shi komai nashi a natse yake, saboda kara tantancewa na ce. “Abdallah....” “Abdulhamid” Da sunansa da ya fada yasa na kara tantance shi din ne ta hanyar kallon da nai wa bakinsa a lokacin da yake furta sunansa, domin shi haurensa na gaba ya dan kaure kadan. “Ya fada maka?” Ya gyada min kai. “Naje yin wani abun ne sai yace na biyo da ita zai shiga theater” Ya mika hannu na karbeta ina hade yawu. “Ki yi hakuri Halimatu, ko wane bawa da irin kaddararsa, kuma ko wane gidan aure da kalar nasa kalubale, duk wanda ya fada miki aurena da dadi 100% karya yake, akwai kalubale a cikin aure da rayuwa kala kala, dan haka ki yi hakuri, an rubuto haka zai samu Namra so no matter what you did ba zaki iya tare jaddararta ba, rayuwa ko da yaushe tana cike da kalubale so dukan abunda za ki yi karki yi shi dan yau ki yi dan Goben ki, ina rokon Allah ya zama a tare da ke kuma ya baki juriyar daukar wannan kaddarar” “Amin na gode” Na juya ina hawaye kamar ba wacce aka tsamo daga kogin kuka na shigo ciki jikina na bani kallona yake har na shigo. A saman kujera na aje ta tana ta bachinta da alama allurar bachi yai mata domin ko motsi bata yi. Wani sabon kuka ne ya zo min tausayinta da nawa ya rufe ni. “Al-hamdulillah Allah duk abunda kai dai-daine, idan ka ga dama sai ka akashe mu mu duka kuma daidai ne, da baka so ba, da komai be faru ba, kai ka kaddara min auren Aminu, kuma kai ka kaddarar abunda zai faru a yau, komai a cikin ikonsa da yardar ka ne Allah, ya ka zama gatana ka zama tare da ni Allah ya min mafita ka isar ka isar ma yata, Allah ka zaba min tsakanin kwato hakkin yata da igiyar aurena ya Rahamanin Rahim....” Na karasa cikin wani irin kuka da ban san da zamansa a cikina na sai yau.... ________________ Wane Halimatu zata zaba? Aurenta da Aminu wanda shine rufin asirinta da na yarta kamar yadda Mahaifiyarta ta fada? Ko kuwa kwato hakkin yarta wacce aka lalatawa rayuwa aka maida babban mace? #Abdallah #Abdulhamid #Aminu #Halimatu #ZawarcinHalimatu #Gobena #Freepage #Twinbrother *If you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660* 7/20/21, 8:29 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 7️⃣ Hawayena na share na tashi na shiga dakina nai alwala na soma gabatar da sallah azahar, ina Sallah shiedan na ta kawo min wasu abubuwan da be kamata nai tunaninsu a lokacin da nake a gaban Ubangijina ba, sai dai na yi nasarar fadawa Allah bukatata kuma na kai masa kuka. A lokacin da na sallame sai addu'a ta subuce bakina saboda tunanin da ya taru yai min yawa. Ida har na hakura na bar rayuwar Namra ta tafi a haka ni tawa rayuwar zata inganta kuwa? Taya zata inganta bayan yata zata kasance cikin kunci? Kyale Baba Sadi zai canja mishi hali ne daga abun yake? No sai dai ya kara masa kwarin guiwar yin hakan saboda an kyaleshi, hakan kuma ba zai saka Aminu sauya halinsa ba, miye ma amfanin zama da mutumen da ke mu'alama da wasu matan a waje, wanda har ya zama silar lalacewar ta wa yar? Shin yin shiru zai amfanin wani abu ne? Jin bugun kofar falo ne ya dawo a ni daga duniyar tunanin da na tafi. Tashi nai sanye da hijab da nai sallah na nufi kofar falon, ina budewa na ga Abdallah tsaye rike da hannun Adnan dayan hannunsa kuma rike da leda fara irin babbar nan ta pharmacy, Aiman kuma na gefensa, sam na manta da zancen dauko su daga makaranta sai yanzu. “Be kamata ace har yanzu kina barin kanen mijinki yana zuwa dauko yaranki daga makaranta ba, domin idan be samu mace ba mazan zai iya lalata su tun da duniyar ta canja ba maza ba mata” Shine abunda ya fada min kai tsaye, ni kuma na kwara bude kofar falon. “Adnan ku shigo ciki” Da sauri suka shiga falon ni kuma na fito na tsaya bakin kofar falon na janyo kofar na rufe. “Kin yi kuka da yawa Halima ga fuskarki nan ya nuna, kina tunanin kuka zan canja komai ne? Kina tunanin kukam zai saka Kanen mijinki nadamar abunda yai? Ko kuma mijinki zai fasa neman matan da yake ne yana gallaza miki? Haka zaki saka ranki a kunci kina ta damuwa?” Kasa nai da kaina ina jin wasu hawayen suna kokarin cika min ido. “Na je gida na kai miki yaran na yi tsammani kina gida, sai suka ce kin zo kin tafi, tun da na ji haka na san cewar sun karya miki kuiwa ko? Su baki shawarar rufe sirrin saboda kar wani yaji, Kanen mijinki ya ci bulus kenan? Bayan ya ci amanar dan'uwansa, rayuwar aure ba rayuwar kunci ce ba Halima, saboda kina neman lahirarki ko kuma kina son kyautata rayuwarki be kamata kullum ki yi zama da kunci kina tauye kanki ba, musulunci ma be yarda da irin wannan auren ba, yaushe rabon da ko kusantarki mijinki yai?” Hawaye ya fara sauko min, tabbas Abdallah yana da gaskiya akan dauki wata daya biyu wani lokacin har uku kamin Aminu ya zo min da bukatarsa. “Ba sai kin fada min ba na sani, namiji mai neman matar sosai kamar yadda Aminu yake baya iya kula matar gida, duk abunda zaki yi ba zaki burgeshi ba saboda idonsa sun bude akan wasu matan na waje kuma ya yarda sun fi ki komai, so baki da wata daraja da kima a idonsa, yana yawan fadar baya son mace mai irin siffarki halittarki bata burge shi, kuma kin tara masa yayana yana da kananan shekarunsa a lokacin da yake bukatar hutu ke kuma kika son hana shi jindadin rayuwa, shiyasa yake gallaza miki” Dagowa nai na kalleshia fusace na ce “Kana ta fadin karya da gaskiya akan mijinki, tsayawa a ina saurarenka ba shi yake nufin na yarda da kai ba, baka san komai akan mijina ba babu ruwanka da rayuwarsa” “Kwarai na san komai akansa, da yawa daga abokansa ina hulda da su kuma kin sani mazinata basa da sirri, har jinjirin cikin da kike dauke da shi na sani Halima, babu wanda be san irin zaman da Aminu yake da ke ba a cikin abokansa, saboda mijinki ba shi da sirri, ban san taya akai ma kika auri Aminu ba Halima sam ba mijin daya dace ki aura ba ne” “Baka isa ka shigo har cikin gidana ka ce zaka fada min wata maganar banza akan mijina ba, ka fice” Cikin wani irin tsawa na nuna masa gate raina na bace, daman ya saba a duk lokacin da muka hadu da shi sai ya fada min wata maganar marar dadi akan Aminu. Murmushi yai ya tabe baki ya miko min ledar hannunsa. “Maganin Namra ne, karki sake mata abunda zai tsoratata saboda kwakwalwarta a tsorace take a yanzu ya riga ya gama tsoratata so tsoron yana tare da ita har sai ta samu sakewa na wani lokacin kamin ta koma Normal, ki rika gasa mata da ruwan zafi. And idan kin ga dama ki dauketa ki kai ta riko gidan Kenan mijinki sai na yarda kin fi ganin kimar mijinki fiye da yarki, duk abunda kike idan saboda goben ki kike to goben ta fara lalacewa a yanzu tun da har zaki iya barin hakkin yarki akan aurenki......!” Yana fada min haka ya juya a fusace ya sauka daga dan gudun stairs din dake gurin ya nufi motarsa ya shiga yai ribas da karfi alamun da ke nuna ransa ya bace sosai kenan. Bude kofar falon nai na shigo ya maida kofar na rufe na jingina jikin kofar ina fashewa da kuka mai karfi. Na rasa abunda zan yi maganar mahaifiyata zan bi ko kuwa abunda nake ganin yafi? “Momy mi kike kuka?” Adnan ya tambaya daga shi har Aiman kallona suke. “Ba kuka na ke ba” “Gashi nan hawaye yana miki zuba” “Kaina ke ciwo” Na fada ina kirkiro murmushi tare da share hawayen. Hannu na mika musu sai duka suka zo na zaunar da su kusa da ni na shafa kansu sannan na daga kaina na kalli Namra da ke bachi saman cushion. Yayana na daya daga cikin babban kyautar da Allah kan yi ma bawa, wasu nema suke yi saboda Allah be basu ba, da ana siya da kudi da sun siya ko nawa ne, wasu kuma Allah ya basu mazan be basu matan ba, suna ta son mata ba su samu ba, wasu kuma matan Allah ya basu be basu maza ba, amman ni Allah ya hada min duka biyu ya bani maza biyu mata biyu a cikin shekara 11, sai dai ya bani su a inda ni kadai nake masa godiya da kyautar da ya ba ni, ni kadai na ke kallonsu na jidadi, mahaifinsu kan ganin yake na tara masa tsufa, har yana guduna saboda su saboda haihuwarsu ta canja min halitta na tashi daga buduwar zuwa mace mai yaya hudu da ciki na biyar, cikin da yake cewar na zubar baya bukatarsa. “Allah ya raya ku ya sakawa rayuwarka albarka ya tsare min ku” Na fada ina kara shafa kansu, sannan na mike tsaye na nufi kitchen na kunna gas na hada musu tea na gama musu da sauran biredin safe da yai saura na mika musu, ni kuma na shiga dora girkin rana duk kuwa da ina jin cewar ba zan iya ci ba amman dole na dora saboda yarana. Komai saboda su ne, zaman da nake da Aminu saboda su ne, idan na fita na barsu ban san wace irin rayuwa za su shiga ba, ban san wace macen ce zata raine su ba, fatar shiriyar da nake masa ko bana aurensa ina masa ita saboda na riga na haihu da shi. Ina cikin wanki shimkafa na ji yara suna murna. “Oyoyo Anty Hafiza” Kanwata ce wacce muke uba daya da ita, sai dai Allah ya hada jininmu kamar yan daki daya, bata boye min komai ni ma bana boye mata damuwata. “Yar aljanna... Da aka fada miki kuma sai kika ji kika dawo gida har kina girki, Allah mai ikon, da ya tashi sai yai mu uba daya amman hali kowa da na shi” Juyowa nai na kalleta da idona da suke kumbure, sai na ga hawaye na mata zuba mayafinta ma a hannu yake tare da jakarta. “Da ace ko wace mace zatai irin zaman auren da kike da mijinki, da maza sun huta da korafin matansu, kuma da ko wane yaro mai uwa da uba a raye be girma ya ga uwayensa a rabe ba, kina da hakuri Halima fiye da kima, sai dai hakurin idan yai yawa yana cutarwa, abun ya wuce kanki a yanzu rayuwar yaranki ake neman lalatawa, be kamata ki yi hakuri a nan gurin ba” Sai da na hade yawun bakina sannan na ce. “Inna ta fada miki abunda ya faru?” Sai ta matso kusa da ni tana kallon irin kallon nan na tsantsar tausayi. “Mama ce ta fada min, na rasa gane dalilin shirun da za ki yi, ban san mi yake damun iyayenmu ba, dukansu tsoron mutuwar aurenki suke ji, mu kuma da muke gida suna matsa mana akan lallai sai mun yi auren, suna matsa mana akan auren ko wane irin miji saboda mu bar gabansu mu kaucewa maganar mutane, ku kuma da kuke da aure suna son ku yi da zama auren ko da babu dadi saboda gudun magana, sun kasa gane aure rai ne da shi, idan lokacin mutuwarsa yai dole sai ya mutu, idan kuma lokacin yinsa yai sai anyi ammn sai su dauki damuwar duniya su sakawa kansu, yanzu so suke ki zauna da mutumen da be san darajarki ba kuma ki kyale kanensa ya ci bulus kenan? Idan ma bakinciki kashe ki zai yi sai dai ya kashe ki? No ban zan goyi bayan wannan abun ba, ba za ki kyale mutumen nan ba, ba ki fada min ba amman nasan Aminu yace miki yayi tafiya zuwa Kaduna to Wallahi ya tafi tare da kawarki Sa'adatu, Sa'adatu kin san ai kanwar Basira kawata ce ita Basira kawar Sa'adatu ce ita ta fada mata ita kuma Rahila ta fada min, yanzu irin wannan mijin har abun so ne? Irin wannan mijin ABOKIN RAYUWA ne?” Tsame hannu na yi daga cikin shimkafar da na ke wankewa na sake kallonta na ce. “Rayuwar da Aminu yake a yanzu bata dame ni ba, shawara nake da zuciyata na rasa abun dauka, maganar su Mama ko kuma kyato hakkin yata, ta wani bangaren gaskiya suke fada, idan na fita rayuwar yayana zata zama abar tausayi, idan kuma na cigaba da zama zan cutarta da kaina, dalili na farko da ya saka Aminu ya fara sakina saboda na yi fada da kanwarsa, na biyun kuma saboda aikina ne yace kar nai na ce sai na yi saboda be dauke min duka hakokina ba, akan hakan ya sake ni daga baya yace ya yarda na dawo na yi aikin, yanzu kuma saki daya ya rage idan ya sake ni babu zancen komawa saboda shika uku ne babu gyara, kuma bana jin zan tana iya auren wani mutun na fito saboda yayana na tsabawa mahallincina, idan har Aminu yai kuskuren rabuwa da ni a yanzu mun rabu kenan har abada ko da kuwa zan rasa duka yayana ne, amman a yanzu da nake cikin igiyar aurena ina kokarin zaba tsakanin auren, rayuwar yayana da kuma Gobena, duk idan auren da zanje duk more jindadi da soyayyar wani mutum da zan yi a gidan wani auren zuciyata tana gurin yayana, idan na bar gidan nan kamin Aminu ya auri wata matar gidan iyayensa zai sai su kuma idan har ya zama saboda fyaden da akai ma Namra na fita tabbas ba za su taba son yayana ba, idan kuma yai aure wace uwar zai auro musu?” “Amman kina da tabbacin wata rana Aminu zai iya sakinki ko baki masa komai ba? Saboda ya gaji da zama da ke? A lokacin ne sakin zai fi miki zafi fiye da yanzu, zancen ki zabi aurenki akan abunda akai wa namra be ko taso ba, Halima ya kamata ki sani ba Aminu ne kadai mikin aure ba, kuma akwa yara da yawa da suke tashi ba uwa ba uba balle ke da har kina da rai, kar maganar Mama da Inna ta karya miki guiwa” Kallona ta nake maganganunta na shiga jikina ta ko wace shiga, sai dai har yanzu idan na tuna maganar Mama sai na ji kamar ba zan iya komai ba. Ita ce ta karasa min girkin ni kuma na cigaba da gyaran gidan kaina a kulle, misalin biyar da yan mituna ta tafi gida ni kuma na dauki wayata na kira Hajara. Bugu daya ta dauka sai hayaniyar mutane nake ji sauti na tashi. “Halima muna gurin biki, ga yarki Amal ta dame ni da kuka wai ita Momy Momy” Na yi dariya kadan ba dan ina jin dariyar ba. “To ai ya kamata dai ta dawi gida haka nan tun safe ba bata gan ni ba” “Da na gama bikin za mu dawo ai In-Sha-Allah ya jikin Namra? Abban su Baby yace kin ce masa bata jindadi na so na shigo kuma dai sai na wuce sai idan na dawo dan nasan kina gurin aiki” “Eh to sai kun dawo a kula min da yata” Daga haka na kashe wayar, kamin na aje ta kiran Kabeer ya shigo wayata har na yi kamar ba zan daga ba sai kuma na daga a tunani wata maganar ce. “Allah yasa ba abunda ya faru tsakaninmu ne ya saka kika ki zuwa aiki ba” “Bana jindadi ne” “Subhanallahi kin sha magani?” “Allah ya sauwake ya baki lafiya, oga Dahiru ma ya tambaye ki dazun sai na ce masa kin ce za ki je ganin wata yau ba za ki samu shigowa ba, ita fatar ban yi laifi ba” “Ba kai ba na gode” Kamin ya sake cewa wani abu na kashe wayar, na bar jikin dinning din ina ta tunanin yadda zan fadawa Aminu abunda ya faru, na kyale shi har zuwa lokacin da Mama tace idan ya dawo, anya zan iya haka? Ba zan bar Sadi ya sake daukar min yara daga makaranta ya kai su gidansa, ba ma shi kadai ba ko mijin Hajara ba zan sake yarda ya kai yarana makaranta na ni zan kai su ni zan dauko su, Amal ma ba zata sake zuwa gidan ita kadai ba sai idan tare da ni ne, ba zan sake yarda da kowa akan yarana ba ko da kuwa mahaifinsu ne. Dole na fara fada masa a matsayinsa na ubansu kamin na dauki wani matakin, ko kuma yin gargadin kar Sadi ya sake dauko min yara daga makaranta, aikin nawa ma ina jin ajewa zan yi na tsaya na kula da yarana. Komawa nai dinning din na zauna na danna Number Abban Namra na aika masa kira, na yi sa'a bugu daya ya daga da far'arsa, ko da ma be daga ba na yanke shawarar aika masa sako. “Hello ya kai?” “Komai an yi Aminu, hankalinka kwance kana can tare da wasu matan ka tsare musu hakokinsu mu ka kasa tsare mana namu, mu da Allah ya dora maka, mu da idan ka mana zaka samu lada, tirrr da wannan kazamar rayuwar da kake zina har da matan aure? Duk karuwan garin nan ba su isheka sai ka nemi mai aure! Abunda kake aikatawa yau kaja an aikatawa yarta, ka yi da yar wani an yi da taka ka lalata rayuwar yar wani na lalata taka, ban tana zina ba kullum burina na kare mutuncin kaina da na yayana da na aurena da na iyayena da naka amman kai kullum burinka ka zubar mana da kima, yau saboda abunda ka ke Aminu wani ya yi ma yarka fyade” Tun da na fara jera masa zancen be ce uffan ba har na kai aya. “What! Me kike fada? Wa akai wa fyade, uban wa ya taba min ya? Kin je gurin bakin aikinki kin barta hannun wani an lalata ko? Waya sani ma ko can gun aikin kika tafi da ita kika sake ta? Saboda ba ki san zafin haihuwa ba sai son haihuwar kike baki iya zama ki kula da su, to Wallahi idan kin san wani ya taba min ya kamin na dawo ma gidan nan ma ki tattara kayanki ki koma gidanku” Duk fadan da yake a daukarsa Amal ce aka lalata ganin itace karamar su kuma ita ce marar wayo sosai. “Wanda ya lalata Namra a jininka yake, wanda kuka fito daki daya da shu uwa daya uba daya, Sadi Aminu Sadi dan'uwanka kanenka shi yai ma Namra fyade...!” Shiru yai na wasu yan dakiku kamin ya sake yin wata maganar kamar a rikice. “Kin san abunda kike fadawa kuwa? Sadi fa kika ce? Taya Sadi zai wa Namra fyade? Kuma idan ma an mata uban waye yaja mata? Da kin zauna kin kula da su wani abun zai same su ne? Karya ma kike Sadi ba zai yi ma Namra haka ba akwai dai abunda kike nufi me Sadi zai ji a jikin karamar yarinya? Kuma yata? Wallahi ki yi hankali da igiyar aurenki Halima.... Mace kamar riga take a wuyana” “Abunda kake ji a jikin wasu matan shi yake ji a jikin yarka, zaka gene ba ni da hankali idan kotu ta kwatar mata yancinta, tirrr da uba irin ka Aminu na yi nadamar aurenka a yau na tsare ka bana kaunarka Aminu, kuma idan ka haihu ga Zainab da Ibrahim ka sake ki a cikin wayar nan Aminu, abunda akai ma yarka be dame ka ba sai wasu maganganun banza! Tirrrr na yi nadamar haihuwar da nai da kai a yau, na gaji da auren yau ka baro garin Kaduna ka zo gusau ka sake saki dari ba daya ba....!” Na karasa fadar hakan ina buga hannuna da karfi a dinning table din, yarana gaba daya kallona suke har Namra da ke bachi sai da ta farka ta sakar min ido.. 7/20/21, 8:29 AM - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/EYNw36FV1ttAsmCUnTsXLH *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 8️⃣ Ina kallonta sai tausayinta da nawa ya rufe ni, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na dafe kaina. “Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u” Na fada cikin kuka, sai Adnan ya nufo ni yana fadin. “Yi hakuri Momy sannu” A zatonsa ciwon da nake masa ina na na dazun da ma fada masa ban sda lafiya ne yake damuna. A dole na share hawayena na kirkiro murmushi na mike tsaye na nufi inda Namra take. “Kin tashi?” “Ya jikin?” “Bana jin ciwon komai” Ta fada tana ta kallona da idonta da sukai ja saboda bachi, sai kuma ta kwanto da jikinta jikina. “Bari na kawo miki wani abun ki ci kinji yar kirki” Ta gyada min kai sai dai ina sauka mikewa tsaye daga kan kujerar sai ita ma ta sauko ta matsa kusa da ni kamar zata shige cikina. “Zauna bari na kawo miki” “A'a Uncle Abdallah yace ya daina bari kina yin nisa da ni duk inda kika je na biki ko da gurin aiki ne idan ba haka ba Baba Sadi zai iya zuwa ya yanke ni saboda na fada” Kamin nai wata magana Adnan ya nufo inda mike da sauri yan zaro ido. “Baba Sadi ne zai yanke ki? Mi kika fada” “Ba komai, zo muje” Hannunta naja ban bari ta sake cewa komai ba. Na nufi kitchen din da ita. “A cikin gidan nan wani be isa ya zo ya taba ki ba, ke ba a nan ba ko a wani wajen ne wani be isa ya taba ki ba, ki kwantar da hankalinki kinji yar kirki” Na fada mata ina kokarin zuba mata abincin, sai ta fara motsa ido. “Mama ina jin tsoro” “Ai Baba Sadi be san kin fadi wannan maganar ba, kuma ba fada masa zan yi ba dan haka ki kwantar da hankalinki kinji?” Ta gyada min kai, a plate na zuba mata abincin sannan na janyo hannunta muka fito falo, zaunar ita nai ina kokarin bata abincin sai ta ce. “Momy ban wanke baki ba” “To je ki wanke” Bata min musu ba ta tashi zuwa cikin dakinsu, daman can Namra ba yarinya ce mai kiriniya da jan magana ba, ko abu yake cinta yana da wahala ta iya fada ga ladabi da hankali kamar ita ce yayar Adnan, duk abunda na saka ta sai ta yi ba musu idan nace daina zata daina, ga jinkai duk abunda ta samu ita dai Momy dai Momy dai. Rashin ji da kiriniya sai Adnan shi da yake babba da Aiman dakr binta sai kuma wannan yar berar nan Amal ita kam fitinar ta tafi ta kowa ga barna komai ta dauka sai ta lalata.   Wayata ce dake kan dinning tai kara, sai na aje plate din a kasa na tashi na nufi inda wayar take, number Abdallah ce har na yi kamar ba zan dauka ba idan sai kuma wata zuciya tace min na dauka wata kila wata maganar ce aka Namra. “Assalamu Alaikum” Na masa sallama da sanyayyiyar muryar da ke fassara irin damuwar dake tare da ni, domin bana da wani sauran kuzari a yanzu. Sai da yai shiru for few seconds sannan na amsa min. “Wa'alaikissalam Halima ya jikin Namra na san ta farka yanzu ko?” Na gyada kain kamar yana gabana, shi kuma kamar ya san abunda nai sai ya ce. “Good ki yi hakuri na fada miki magana marar dadi dazun, rai na ne ya bace shiyasa, kuma dan Allah Halima karki saka damuwa a ranki, karki kamar ba zaki iya ba, kina da yan'uwan da zasu iya goya miki baya ki yi komai, karki bar Baba Sadi ya ci bulus” “Zan aje wayar” “Okay ki kula da kanki” Sauke wayar nai ina ta tunanin ranar da Abdallah zai canja, wannan wa'azin ma yana min shi ne saboda ya san idan har na ce zan kwace hakkin yata dole aurena zai mutu, shi kuma abunda ya dade yana jira kenan tun kamin na haifi Namra, ya kwallafa min rai kullum burinsa da addu'arsa aurena dai ya mutu shiyasa yake yawan fada min maganganu marasa dadin ji akan Aminu, ko da yaushe yana fada min be kamata na zauna da shi ba. Ni kuma ina daukar hakan da son zuciya da kuma son kai irin na bahaushen mutum, taya zaka kwallafawa ranka son matar aure matar wani? Saboda kawai kana da alaka da yan'uwantaka, wani lokacin har haukarsa nake gani domin mutun mai hankali da tunani ba zai yi abunda yake ba.   Ina cikin wannan tunanin na ji an buga kofar falon. “Shigo” Na fada domin na san kofar a bude take ban saka mata key ba. Hajara ce ta turo kofar falon ta shigo tana dauke da Amal sai dariya take bakina har kunne, rayuwarta na burni ne ita kan ta yi dacen aure ba kamar ni ba, abu mai wahala ka ganta a cikin damuwa duk wani abun da take bukata a take mijinta yake mata shi sai idan ba shi da hali. “Ga yarki nan ta ishe ni da kuka daga kawai na taimaka na je da ita biki, sai ka ce na sato ta” Na mika hannu na karbe ta sai ta ki zuwa sai ita fushi take tana turo baki. “Yi hakuri Amal kyale Mama Hajara mun bata da ita har da tufafin Afrah aka saka miki iyeee yarinyata ta yi gayu” Daker ta zo gareni shi ma da kuka, sai na rungume ta ina dariya. Sai dariyar da nake bata hana kawata kuma aminiyata fahimtar ina cikin damuwa ba. “Halima kamar akwai damuwa ko?” Dagowa nai na kalleta kamin na ce wani abun Namra ta fito daga dakinsu ta nufo inda nake. “Momy ina abinci Maman su Salma ina wuni” Hajara ta amsa mata ni kuma na fada mata inda tuwon yake. “Ina cikin damuwa Hajara, damuwar da ta fi ta ko da yaushe kuma damuwar da zata dauwama a zuciyata har abada, ko da kuwa yan hukunta Sadi, ban taba jin na tsani Aminu ba sa yanzu, ban taba dana sanin auren Aminu ba sai yanzu, ban taba jin natsani rayuwa ba sai yanzu, ban taba mafarkin ko jin ina son mutuwa a kusa da ni ba kamar yau, Wallahi Hajara ji nake kamar na sha wani abu na mutu na huta, ina ma Allah be hallice ni ba da duk wannan rayuwar ban ganta ba, ita ba bata gan ni ba, da Aminu be aureni ba” Da hawaye na ke maganar hawayen da ban yi zaton akwai sauransu ba. Cike da tashin hankali take kallona. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Halima me ya same ki haka?” Ban boye mata komai ba, tun daga zubin farko na fada mata komai ina kuka, ita ma fashewa tai ya kuka ta saka hannunta biyu ta dafe kanta. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Allah ka tsayar mana wannan abun a nan” Sannan ta dago ta kalleni. “Ban taba ji uba kamar Aminu ba, taya za ayi ma yarka fyade kuma ka tsaya karyatawa, ai ko ubanka aka ce yayi ma yarka fyade ba zaka karyata ba saboda duniyar yanzu ta lalace, ammn ke yake dorawa laifin? Da ya tsaya ya kula da iyalinsa yadda ya kamata kuma ya tsare mutuncin kansa hakan zai faru ne? Ban taba goyon bayan ki yi ma Aminu komai ba ban taba goyon bayan ki kashe aurenki ba, a kullum ina cikin addu'ar Allah ya karkato miki da mijinki gareki, amman yau kam ba zan goyi bayan ki bar wannan maganar ba, gobe zan je nai magana da Mama zan fahimtar da su abunda kika kasa fahimta, kuma zan tsayawa Namra sai inda karfina ya kare saki ne dai ko? Aminu ya sake ki Abban Afrah zai aureki In-Sha-Allah, ko kin yi lalacewar da kika rasa mijin aure ba zaki rasa nawa ba” Kallon yar'uwa nake mata ba kawa ko aminiya ba, na san a yadda Hajara ta dauke ni da kuma yadda yake jina zata iya min komai, ko da bana raye balle yanzu da take ganin idona. Sai dai na san abunda ta fada ta fada ne kawai a yanzu saboda ranta a bace yanke, domin ba wata macen da zata yarda mijinta ya auro mata kawarta da amincewarta. Hannuna na kai ya rika hannunta. “Na gode Hajara kin karfafa min guiwa sosai” “Wannan abun yayi yawa Halima Aminu yai miki yan'uwansa su rika ganin laifinki kina ganin kin maye komai na dan'uwansu sun dauki kiyayya sun dora miki, yanzu kuma abun ya wuce kanki ya koma har akan yaranki? Ace Kanen mijinki ya kai yana lalata da yaranki? Miyasa be yi da nasa ba sai na ki? Ko naki ne kawai yayan dan'uwansa, kai wannan tashin hankali da me nai kama? Kina cikin jarabawar aure kuma wani ya karo fado miki? Allah ya miki mafita Halima” “Ameen” Mun dade muna ta fira da ita tana ta kwantar min da hankali sannan ta tashi na rak har gurin gate ta wuce gidanta ni kuma na dawo cikin. Ina shigowa na shiga kitchen na debowa su Adnan na su tuwon na kawo musu sannan na dauko maganin Namra da ruwa na soma bata. Ina jin lokacin da mota ta tsaya da karfi har na daga labulen windows na leka waje sai na hango Hajiya tare da yayata mata uku wato mahaifiyar Aminu ce da kenensa. Ban ji komai a raina ba domin a yanzu zuciyata a dake kuma na san zuwan nata baya rasa nasaba da fadan da mukai da Aminu a waya dazun wata kila ya fada mata ne. Ashe kuwa na canka a dai dai domin ta shigo falon babu ko sallama tana shigowa cikin falon ta hau fadin. “Halima mi kika fadawa Aminu a waya?” Juyowa nai na kalleta na saba sauka na risina har masa na gaisheta idan ta zo gidan ko ni aje ko muka hadu da juna, sai dai yau bana jin zan iya yin haka. “Hajiya sannu da zuwa” “Ba sannu da zuwanki na ke so ba, wata magana na ji nake son ki sake maimaita min da bakinki” “Indai har Aminu ya fada miki, to ba bukatar na sake maimaita miki, iya kar abunda ya kamata ki gane shine ba zan yi ma Sadi kazafi ba haka nan kawai” “Kazafi ne mana, ai kin dade kina son raba kan gidan nan, kin rasa abunda za ki yi shine kika fake da wannan waya sani ko can gurin aikin naki kika kai yarinya aka lalata sai kuma ki zo ki fake da Sadi, wai ko baki san cewar ni na haifi Sadi ba? Kuma ni din mahaifiyar Aminu ce uba daya ya haife su nono daya suka sha” “Ko tagwaye ne su Hajiya be dame ni ba, yayanki kike tsaye a nan kina karewa ni kuma na san zafin haihuwa kuma na san zafin keta haddi saboda ni ma mace ce” Zakiya ta matso kusa da ni tana min tsawa. “Halima karki ce zaki ma Hajiya rashin kunya Wallahi na ci mutuncin ki” Ni kuma na mike tsaye ina nuna ga da yatsa a fusace. “Ke Zakiya iskanci ya tsaya a kanki, karki sake saka min baki a magana ke kanwar mijina ce ba yarsa ba, idan baki da tarbiya Wallahi zan gyara miki zama” Ta nuna kanta “Ni din? Ai kece marar tarbiya mai son hada yan'uwa bawan Allah yana can yana nema muku abunda za ku ci kina nan kina tada mishi hankali da yan'uwasa, ko da ya kira har kuka yake yace yana gurin aikin Kaduna amman kin daga masa hankali da maganar fyade” “Karya dan uwanki yake miki, ba aiki yaje yi ba hutu ya samu ya dauki karuwarsa suka je can gurin hutu, abunda yake ne yaja akai wa Namra kuma aka rasa wanda zai mata sai dan'uwansa” Hajiya ta nuna ni da yatsanta. “Ke marar kunya, fitsararki ta tsaya kanki karki ce zaki min iskanci, ni danaba mazina ce bane, daman can baki da aiki sai kawo kararsa kullum cikin kawo kararsa kike baki taba gode abunda yake miki ba, ke da kike aiki ba ace miki mazinaciya ba sai shi? Tirrr Wallahi mugun abun ki ya biki, kuma Wallahi ki hada kayanki ki bar gidanan ko ke kadai ce mace a duniya ya gama aurenki, ki koma can cikin agolayen gidanku,kuma Yaya sai an kaiwa Sadi shi zai rikasu sai dai ki mutu, wannan zumuncin baki isa ki raba shi ba” “Zan bar gidan nan Hajiya, amman idan Aminu ya damka min takardar sakina, ba zanje gidanmu na zauna da igiyar auren danki a kaina ba, kuma Wallahi ko ina za'aje sai na je sai na kwatowa yata hakkinta, ban san yayanki haka suke ba Hajiya da ban auri Aminu ba da Sadi be ganni ya ci zarafin yata ba, hakuri na ya kare indai aurena da Aminu na kare ko da kuwa hakan na nufin karshen rayuwata ne, tirr da ɗa irin na ki dan da za a cewa an yi ma yarsa fyade ya karyata ba tare da bincikar komai ba, ke kuma ki sako kafa ki zo ci mun mutunci ko? Kin zo ki shigarwa yayanki to Namra ma ƴa ce idan Aminu be san darajar ta da kimarta ba ni na sani kuma ba zan bar wannan maganar ba, kotu zata kwatar mana hakkinmu” Tun da na fara maganar babu wanda ya sake cewa uffan ba kanensa kadai ba har Hajiya tsaye tana kallona, ni kaina na san na yi mata abunda ban taba ba, ko kusanyar magana bana iyawa da ita balle kuma har nai sa'insa da ita. A yadda nakr jin kaina a yau ko marina tai zan iya ramawa, domin ina jin babu wata sauran alaka tsakanina da dangin Aminu yanzu. Har Laweeza ta bude baki zatai magana sai Hajiya ta hana ta ta hanyar daga mata hannu sannan ta saka su gaba suka fice daga falon. Faduwa nai zaune a gurin ina wani irin fuci kamar zakayan. “Momy ni ce naja fada ko?” Namra ta tambaya tana kallona tare da fashewa da kuka. Kallonta kawai nai sai na kasa cewa komai na mike tsaye tare da maganin da nake bata na nufi dakina, ina shiga na fada saman gadon a ruf da ciki, wani irin soya nake jin zuciyata na min bana jin kuma ba kuma za a kawo zancen dariya ko farinciki a tare da ni a yanzu ba, gaba daya bana jindadin komai ciki kuwa har da rayuwata. Ina yi awa daya a gurin sannan na mike tsaye na nufi bandaki amai nai bayan na gama na wanke bakina na fito ina shafa cikin da ke jikina, abunda be isa shigowa duniya ba na ke tausayawa wani abu na hade mai nauyi sannan na fito na nufo falo. Wani abun mamaki sai an samu Namra tana ta kuka har da shisshika kamar ranta zai fita, haka ne na nuna alamar ta ci kuka ta kenan sosai har ta gaji. Adnan da Aiman kuma suna zaune a guri daya kusa da ita sun rakube kasa kamar wasu marayu, Amal ce kawai ke ta sha'aninta da wayata da ke hannunta. “Adnan kuje ku kwanta kunsan gobe akwai scul” “To Momy” Suka tashi a tare suka nufi dakinsu a natse kamar ba su ba, yaran da sai na yi da gaske suke zuwa su kwanta ko kuma su yi bachi a duk inda ransu ya so sai na dauke su na kai dakinsu. Kusa da Namra na zauna ya dago ta idonta har yayi ja tsababen kuka. “Yar Kirki mi akai miki?” Bata ce min komai ba sai na kwantar da kanta jikina ina ta shafa kanta a hankali. Amal na gani ta rugo a guje tana kuka, daman haka take bata kaunar wani ya taba min jiki ko ya kwanta a jikina sai dai ita kadai. Dagata nai na ajeta a gefena na rumgume ta sannan na karbi wayata. Ganin sako a saman wayar yasa na shiga messages box sunan Abban Namra ne a saman kamar yadda nai saving number. Wani irin fargaba da tsoron bude sakon ne ya kamani a lokacin. Saurin sauke Namra da Amal dake jikina nai na mike tsaye na nufi gaban windows falon rike da wayar ba tare da na bude sakon ba. Na hade yawu ya fi a kirga numfashi na ma har gargada yake zuciyata na raya min saki na Aminu yai. Cikin karfin hali na kai hannu na bude sakon. _Ni Aminu Idrees na saki mata ta Halimatu Ibrahim saki daya a yau 4 ga watan 3, ya zama saki uku kenan babu gwara a tsakaninmu_ Ina gama karantawa na ji kamar ba a duniyar nan nake ba, ba dan bana bukatar sakin ba, sai dan saki abu ne mai kirma wanda ko baka kaunar mutum idan aka sake ka dole ne sai ka ji wani abun marar dadi ya ratsaka. _Karki kara minti daya a cikin gidana! Karki yarda na dawo gobe na same ki a cikin gidana, kuma karki daukar min yara_ Shine sako na biyu bayan na farkon, ban san ta inda hawaye suka taru a idona har suka zubo min ba, sai jika screen din wayata suke. “Zaki iya wannan Halimatu, wasu uwa da uba suka rasa balle ke da igiyar aure ce kawai kike rasa kuma auren mutumen da be san darajarki ba, akan yaranki ne right? Zaki iya yin komai akan yaranki, wannan be isa ya karya miki guiwa ba, be kamata ma hawaye ya ziyarci idonki ba saboda kin rabu da mugun mutum right?” Ni kadai nake magana da kaina kamar wata tabbabiya da sauri na share hawayena, na nufi Namra dake kallona. “Tashi muje gida” Na fada ina daukar Amal, dakin su Adnan na shiga har sun fara bachi na taso su na saka Hijab dina na dauki jakata domin bana jin iya tsayawa daukar komai a yanzu, waje muka fito gaba daya na rufe kofar falon sannan na saka yarana gaba muka fita gate din. Misalin tara da rabi muka isa unguwarmu wato family house dinmu, tun a waje na san Abdallah na cikin gidan sakamakon ganin motarsa da nai a waje, bayan an sallame mai Napep di na ji kamar ba zan iya shiga cikin gidan ba saboda Abdallah. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na saka kafata a cikin gidan, babu kwalla ko kadan a tare da ni a lokacin da na shiga cikin gidan sai dai ina shiga falon nai arba da Mama da kanena biyu da kuma Abdallah sai na ji kuka ya zo min marar misaltuwa. “Lafiya dai Halimatu” Mama ta tambaya tana kallona da yara hankalinta a tashe. “Mama Aminu ya sake ni.....” Na fada ina fashewa da kuka, kanwata Salma dake kwance kan kujera ta yi saurin tashi zaune tana zaro ido, Mama kuma ta dafe kai ita da Ummi. “Wow..... ” Shine abunda Abdallah ya fada yana mika dukan kallonsa a gareni fuskarsa da murmushi kamar ya manta a inda yake. ________________ Saki mace mai ƴaƴa huɗu saboda son zuciya 💔😪 Anya akwai imani a zuciyar Aminu kuwa? A matsayinki na mace ya kike auna abun nan ya kike ji a ranki?😪 Abdallah me yake yi ma murmushi? 🙄 Idan tawayensa Abdulhamid yaji ya zai yi 🤔 Anya Aminu zai barwa Halimatu yaranta kuwa? 7/20/21, 8:29 AM - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/Kd8IIfbBTC824Lw3DOeKra *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 9️⃣ “Wannan kaddararen aure yau Allah ya kawo karshensa, ni ban ga abun kuka ba ma balle wata damuwa” Shine abunda ya fito daga bakin Abdallah, Mama kam kasa cewa komai tai har lokacin tana dafe da kanta nima na kasa daina hawaye zuciyata tana min wani mugun zafi. “Ummi rikata ki shiga da ita daki mana” Cewar Abdallah yana kallona kamar ya taso da kansa din ya rikani. Salma ta taso ta zo ta rika daga tsayen da nake muka nufin dakin Mama tana rike da ni kamar yadda Abdallah ya bukata, muna shiga dakin na zauna bakin gado sai ta zauna kusa da ni tana kallona idonta taf da hawaye. “Ki yi hakuri Anty Halima haka Allah ya so, ki dauka wannan ma yana rubuce a cikin abunda Allah ya rubuto zai same ki” Na gyada mata kai ina ta kokarin taushe kukan da ke cina, Amal ce ta shigo ta zauna saman kafafuwana ya lafe kamar zatai kuka sai kace wacce ta san abunda ke faruwa. Salma kuma ta tashi ta fita ta barni a dakin daga ni sai Amal a nan na samu damar yin kukana iya yadda raina yake son, ina cikin kukan Mama ta shigo ta zauna bakin gado na yi zaton zata fara tambayar abunda ya faru ne ko kum ta tausaya min ko ta karfafa min kuiwa akan abunda ya faru, amman sai na ji wani abu dabam na fitowa daga bakin. “Ai ga irin ta nan kin kashe aure tun ba a aje ko'ina ba kin fara kuka, ina amfanin wannan abun? Kin saka kanki da yayanki a cikin matsala bayan kuma kin san saki daya ya rage ba wani gyara a tsakaninku? Halima rayuwa zatai yi? Yanzu duk maganar da muka miki muka ce ki rufe abun nan sai da kika tona shi?” Daga kaina nai na kalleta, ban san abunda take hango min ba na kokarin hanani yin komai akan abunda akaiwa Namra, na san tana gudun zaman gida a gurina kuma tana jin kwatankwacin zafin da nake ji na baro yayana a wani gidan, amman har yanzu na kasa gane dalilin na son boye maganar, indai na janyo ma yayana tsanena ina ganin kamar ba hujja ba ce. “Ko wace Uwa Mama tana goyon bayan abunda yayanta suke aikatawa ko da kuwa abun nan marar kyau ne, na kasa ganin kuskure abunda nake son aikatawa, na san kina min tunanin mutuwar aurena ne, amman tabbas aurena mutu ko da ta wannan dalilin ba, duk yadda kike jin zafi idan wani abun ya same ni haka nake jin zafi idan ya samu Namra, saboda nima uwa ce, kin taba fada mana cewar saboda mu kika zauna da Abbah a cikin lalurar da yake ciki ta rashin lafiya, mama ya dan Allah ki fahimta nima saboda Namra ne, kuma ba dan bana son aurena ba sai dan ganin kamar mutuwar auren a yanzu zata fi sauki sama da idan yayana suka girma, Mama Aminu ya sake ni akan be yarda da abunda na fada ba, ba wai ma ya roki na boye sirrin ba ko kuma ya roki kar na kai kotu ba, mahaifiyarsa har ikirarin cewa tai sai an kaiwa Sadi Namra ya rikata sai dai na mutu, Mama ina kuke son na saka kaina na ji sanyi? Me kuka son nai a duniyar nan?” Wannan karon hawayene yake zuba a idon Mahaifiyata, na sani kalamaina sun ratsata matuka kuma ta fahimci inda na dosa. “Kwatarwa yarki hakki abu ne mai kyau Halimatu, amman kwatar hakki a inda kwatar yafi rashin kwatar alheri to barin shi ya fi, idan kika kai maganar nan kotu kin sani Sadi da yan'uwansa ba yarda za su yi ba, kuma za su yi komai dan su wanke shi ciki har da mijinki tunda kin ce be yarda da abun ba, daga haka maganar zata tashi sama kanki ankaro an fara buga ku a jaridu ana fira da ku, kamin a kwato miki hakkin ki sai kin sha wahala, idab kikai nasa a hukunta na shekara daya ko watanin kadan me akai kenan? Idan kuma ba ki yi sa'a ba sai a kori kararku bayan na gama fadar kin batawa yarinya suna, irin wannan abun Halimatu rufewa ake saboda rayuwar yar ki a nan gaba wa zata aura? Wa zai aureta? Mi zata je ta tarar? Ina hango miki abunda zai zame miki matsala ne nan da wadansu shekaru masu zuwa wanda ke ba zaki gani ba a yanzu, zaki batawa yarki sunane kawai a cikin kawayenta yan'uwanta da kuma wandanda zata hadu da su nan gaba, ke da Hafiza da Doc Abdallah kun kasa fahimtar abunda nake nufi ne kawai wata kila sai nan gaba, shi ma abunda ya zo yana min magana akai kenan? Wa be kamata a kyale wannan maganar ba, ni kuma na fada masa indai da yawuna za aje kotu da wannan maganar a matsayina na mahaifiyarki ban yarda ba!” Kamar wacce aka saka da mashi haka magana Mama ta ratsa kirjina ta shiga har cikin kaina, tsakanin maganar fyaden da sakin da Aminu yai min da kuma maganar Mama sai na rasa wane yafi yi min zafi a kirji. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u” Na fada ina jin kirjina kamar zai fashe zuciyata ta fito waje, muna haka Baba ya shigo dakin yana turo wheelchair dinsa Inna na bayansa tana hawaye shu kuma fuskarsa na nuna tsantsar damuwar da ke tattare da shi. Ina kallonsu sai ya tuna min da wacan lokacin na baya lokacin da aka dura aurena da Aminu, lokacin da ko wace fuska take dauke da murmushi da annashuwa da jindadi. “Halimatu ya akai hakan ta faru?” Ban boye masa komai ba ciki har da ikirarin da Hajiya tai na kaiwa Sadi Namra ya rika. “Wannan maganar banza ce! Taya zai sake ki ba tare da sauraren gaskiya ba kuma be yi bincike ba sannan ya ce zai dauki yaya ya kai wa kanensa? Babu wanda ya isa ya rabaki da yayanki a nan za su zauna tare da ke idan kuma yayi musu kotu zata rabu mu da shi, domin yanzu babu sauran mutunci a tsakaninmu da shi, duk abunda yake takama da shi sai na gani!” Baba ya fada cikin fushi da daga murya kana kallonsa kasan ransa ya bace sosai, wanda ban yi zaton haka ba domin yana da wahala ka ji bakinsa maganar zamana da Aminu bayan ki yi hakuri aure sai da hakuri, na ji sanyi sosai kuma ina jin na samu kwarin guiwar rike yayana da kyau domin na samu mai goya min baya. Sun dade suna da maganar aurena da Aminu tun daga kan haihuwa ta ta fari har zuwa yau abubuwan da sukai ta faru da kuma abubuwan da suke gani ko ji, ni dai ban ce uffan ba domin har lokacin da kennana suka shigo suka saka baki ana yi da su ban ji ina furta ko da sunan Aminu ba a zance balle kuma har nai wata firar abunda ya shafeshi, sannan suna yi an saboda su nuna min kar na damu akan abunda ya faru. Sai kuma sha biyu sannan kowa ya nemi gurin kwanciya, a lokacin Amal ta dade da bachi a kirjina, sai da na kwantar da ita a kasa saboda fitsarin da take sannan na fito falon Mama neman su Adnan. “Ai tun dazun Abdallah ya tafi ta su gidansa, yace can za su kwana” Mama ta fada. “Har da Namra?” “Eh har da ita” “Akan me zai tafi da ita bana son tana rabar kowa a yanzu bari na kira shi...” Ina juyawa Hafiza ta kirani. “Anty Halima dan Allah karki kira shi yanzu, kin san dai indan kowa zai lalata miki yara ban da Yaya Abdallah, kuma saboda yana tausayin yaran yai so karki bashi kunya a yanzu” “Bana iya yarda da kowa akan yarana yanzu, indai har kannen mahaifinsu zai iya yin wani abu na lalata da Namra, to kowa ma zai iya lalata da ita, rayuwar ya mace a yanzu tafi ko yaushe bukatar tattali, idan na nesa be lalata maka ita ba, na kusa zai iya samu damar hakan, idon kowa ya rufe a yanzu Hafiza, ba zaki taba gane abunda nake nufi ba har sai kin yi aure kin haihu sannan za ki gane tarbiya da tsare yaya abu ne mai wahala, ban son na sake aikata kuskuren da na aikata na barin Sadi da yarana har ya samu damar yi min tabon da ba zai gogu ba har na koma ga mahallincina, da na san cewar zuwa na gurin aiki zai haifar da haka da ban yi aikin ba, da na zauna da yayana a ko wane irin hali, a ko da yaushe ina aina yadda Namra zata ji idan ta girma ta samu irin wannan labarin, ida na kuma na sake bari wani ya sake faruwa? Laifin akan wa zan dora shi?daman tun farko be kamata na yarda da kowa akan yayana ba” Na karasa tare da saka hannuna na share hawayen idona, sannan na kai dubana gurin mahaifiyata wacce ke kallona fuskarta da murmushi. “Kinji kwatankwacin abunda nake ji a lokacin da kike budurwa ke da yan'uwanki da kuma yadda nake ji a yanzu da nake tare da kanenki, a kullum ina cikin fargaba da tsoron kar wani abun ya same su kar wani ya lalata musu rayuwa, ko daga nan zuwa gidanki suka fita hankalina a tashe yake har sai sun dawo sannan na ke samun natsuwa, shiyasa a kullum bana da burin da ya wuce ko wacce na ganta a dakinta, Halimatu kina jin abunda na ke ji a matsayina na uwa, ke ma uwa ce” Dan murmushi nai kadan sannan na nufi dakinta na kwanta a kusa da Amal ina ta kallon fuskarta, kamin na sake tashi na nufi inda handbag dina take na dauko na danna number Abdallah sai na jita a rufe wata kila ya rufeta ne saboda ya san zan kira ko kuma ya saba rufe idan zai kwanta ne oho. A wani abun mamaki a daren sai na kasa runtsawa har safe, bachi ya kauracewa idona ba dan kuma ina tunanin komai ba, domin ban ji tunanin kowa ya zo min rai ba a wannan daren sai Allah ya saka min saukin abun har na ke jin kamar bana da damuwa a tare da ni. Misalin hudu saura na asuba na tashi na shiga bandakin domin yin alwala nai nafila kamin ayi assalatu, ina tsugunawa gurin fitsari sai jini ya fara min zuba a madadin fitsarin, sai da ya zubo min da dan yawa har da sare sannan nai fitsarin na wanke na tashi sai na ji abun be tsaya min ba. A dole na nufi dakin kanena na tashi Marwa ta bani pad na saka sannan na dawo na zauna na dauki carbi Mama ina ta ja, marata na dan murda min kadan-kadan. Haka nai ta dauri har kusan takwas da yan mintuna na safe, ina bawa Amal koko wayar Abdallah ta shigo. “Hello Assalamu Alaikum” “Wa'alaikissalam Momy ina kwana?” “Lafiya kalau Namra an tashi lafiya?” “Lafiya Kalau” Ta amsa min da muryarta radau har tana yar dariya. “Momy ga maman su Nabeela” Ta mikawa matar Abdallah wayar muka gaisa, sannan ta bawa su Adnan da Aiman, daga bisani ya karba ba tare da ya min magana ba ya kashe wayar. Number Hajara na kira na labarta mata abunda yake faruwa sai ta saka salati da sallami tana fadin sai ta zo. Bayan na gama da matsalar Amal na aika yaro aka siyo min pad da pants a shago na shiga nai wanka na fito na saka tufafin jiya, sannan a shiga dakin Baba na gaishe shi tare yi masa ya jiki. “Al-hamdulillah, na yi waya da Almu direba, zai zo anjima kadan sai aje kwaso miki kayanki, makulin gidan yana gurin Aminu ne?” “Eh dayan yana can daya yana gurina” “To za aje tare da ke saboda kar a hado da na shi, ki kwaso yana yaranki da na ki sai a kawo a nan,kamin na dawo ma ya tarar an kwashe komai na ki” “To Baba na gode” “Babu komai Allah ya bamu hakurin zama, kin san shi zaman gida sai da hakuri musamman ma gida nai kanne da yawa haka, sai kin yi hakuri d yan'uwanko kamin Allah ya kawo miki wani na gari” “In-Sha-Allah Baba” Na jidadin yadda ya nuna min kulawa sosai, tara da yan mintuna direban ya zo da babbar motarsa irin wannan ta kwasar kaya, tare da ni da kanena uku aka je muka kwaso komai sai da mu kai wa gidan tas da kayan sannan muka dawo, a unguwa kuwa kowa sai kallon yake ganin an kwaso kayan wanda be san da maganar ba ma yanzu ya sani. A dayan dakin da ake zuba kaya aka zuba gado na da kujeru da sauran tarkashe kayan sakawata kuma na kai su dakin su Marwa domin shi ne ke da girma sosai har ma na samu gurin shimfida katifa ta, na raba yan tsoman karana gefe. Tabbas na ji babu dadi a wannan lokacin domin bbu wanda zai so baro wadatacen gidansa ya dawo wani guri ya raba. Bayan mun gama na sanja wasu tufafin na bar Amal a gida na nufi gurin aikina. Kowa yayi mamakin ganina a wannan lokacin dmin ban saba zuwa da aiki a late ba ko ma naje late ba kamar haka ba, domin sha daya saura. Mun gaisa da Kabeer da Emanuel kamar yadda muka saba da halshen turanci kamin Kabir ya koma yana magana da ni da hausa daga can inda yake zaune ni kuma ina zaune a teburina. “Ya jikin na ki?” Shiru nai wata kila na fada masa bana jindadi ko? Oho na dai manta. “Al-hamdulillah” “Kin karya kuwa?” Nan ma shiru nai kamin na bashi amsa, na manta when last wani ya tambaye ni ko ya damu da na ci abinci. “Eh na karya” “Baki karya ba Haima na sani” Na fada yana dariya sannan ya mike tsaye yana fadin. “Bari na sauka kasa naje restaurant na siyo miki wani abun” “Aa Kabir na karya ban bukatar komai...” Be saurareni ba ya fice yana ciro wayarsa daga aljihu, dafe kaina nai kamin na dauki takadun da na tarar a gurin an shiga da su office din Oga Dahiru, da sallama na shiga na mika nasa gaisuwa sai ya amsa min yana kallona. “Kwana biyu ba ki zo office ba” “Bana jindadi” Na fada ina mika masa files din hannuna. “Kin ga likita?” “Eh malaria ce” Wani kallo yai min kamar be yarda ba, sai kuma ya karbi file din yana murmushi. “Halimatu kenan, Thank you you can go” Na juyo na fito daga office din ina ta mamakin kallon da yai min da kuma murmushin da ke fuskarsa. Ina kokarin zama a kujera ta gabana ya fadi na rashin dalili har sai da na kira Allah sannan na samu natsuwa, aikina na cigaba da yi har na tsawon minti talatin sannan Hafsat ya shigo office din mu hankalinta a tashe tana fadin. “Ku kuna nan zaune ba ku san an kade Kabir ba” Na riga Emanuel mikewa tsaye domin da hausa tai furucin kamin ta sake fada da turanci, sai naji abu kamar daga sama. “Taya?” Na tambaya hankalina a tashe. “Gashi can waje ban san yadda akai ba amman har kafarshi ta cire gashi can ana saka shi a mota za a kai shi asibiti... ” Ban san lokacin da na rufe bakina na watsa da gudu zuwa sakan ma'aikatar ba, tsakanin ni da Emanuel sai aka rasa wanda yafi wani saurin saka ya ganshi, sai dai dukan mu mun yi rashin sa'a domin tuni an saka shi a mota an nufi asibiti da shi, babu komai a tsakan titi sai shimkafa da ya siyo min da kuma jini, ban san lokacin da na fashe da kuka ba har sai da Raliya abokiyar aikina ta rikoni muka dawo cikin ma'aikata, a lokacin kasa yin komai nai kuma ban yi tunanin binsa zuwa asibitin ba a wannan lokacin sai sauraren marata dake murdawa na ke, kamin na dauki jakata na fito na tari napep na koma gida. Ina isa na tarar su ma sun gama na su fadan da Familyn Aminu akan yayana, wai sai an basu yara Baba kuma yace idan suna son yara su tafi kotu, sun labarta min abunda ya faru sai dai sun lura nawa hankalin ba a gurin nan yake ba a yanzu, gani sai wani duke duke nake saboda ciwon marar da nake ji. “Lafiya Halimatu” “Mama marata ke masifar ciwo” Ta yi saurin janyo kujera ta ba ni. “Zauna sannu” Na zauna ina jin kamar ba zan iya zaman ba, domin ko ciwon nakuda be kai wannan ciwon da nake ji a yanzu zafi ba. Wayata dake cikin jaka tai ringing sai dai ban kula wayar ba saboda ba ta wayar nake a yanzu ba. “Salma je ki taro Napep muje asibiti” Mama ta fada cikin tashin hankali ganin yadda nake cizon baki saboda azaba domin ta san ni da juriya. Kamin a taro napep din mu shiga zuwa asibiti sai na ji kamar zan mutu har da kuka hannuna akan marata sai murjawa nake. Mun yi sa'ar ganin likitar nai mata bayanin abunda nake ji a take ta saka a bani gado sannan ya rubuta min magani ta kuma fada min cewar abunda ke cikina ne yake kokarin zubewa za a min wanki mara. ___________ Kwana biyu nan ina busy shiyasa bana post kullum amman da zarar komai ya zama normal zan cigaba kamar yadda aka saba In-Sha-Allah. 7/20/21, 8:29 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 🔟 Ba mu dawo gida ba sai 6pm na yamma, domin bayan mace ta min wankin mara sai da likita ya bani damar hutawa na awa biyu da rabi zuwa uku sannan muka dawo gida.   Da dare Hajara ta kawo min ziyara ta nuna min damuwarta da kulawa sosai kamin addu'arta ta biyo baya, mun dade muna fira da ita sai goma na dare mijinta ya zo ya dauketa. Bayan tafiyarsu da kamar mintuna talatin Abdallah ya kirani a waya har na yi kamar ba zan daga ba sai dai tunawa da bana da aure a yanzu ya yake min hanzarin kin daukar da nake yi a baya, wata kila ma Namra ce take son magana da ni ko Aiman. Da nai picking ban ce masa komai ba, ko sallama da hello da ake idan an kira mutum ko kuma shi ya kira wannan karon bance ba, sai kawai nai shiruna ina jiran ya fara min magana. Shi kuma ya gagara cewa komai kamar wanda ya kira domin kawai yaji saukar numfashina, jin hakan yasa na kashe wayar na mike tsaye na nufi dakina ko kuma nace dakinmu ni da kannena. Tufafin jikina na canja na saka marar nauyi saboda yanayin garin da nake gani da kamar akwai hadari saboda zafin da yai yawa. Amal kuma na saka mata nata kayan bachi na kwantar da ita ina lallaba tai bachi sai ta fara min kukanta na banza daya saba yi wani lokacin idan za tai bachi. “Ai da an sani a bawa Ya Abdallah ya hada da ke ya tafi mu huta” Cewar Kanwata Haulat tana hararar Amal daman can basa shan inuwa daya da juna. Ni kuma nai murmushi na mika hannu na dago Amal na rumgumeta ina rarrashinta. “Ya Abdallah yazo dazun lokacin kina asibiti” “Ya kawo su Namra ne?” Na tambaya ina kallonta. “A a ba da su ya zo ba, shi kadai ya zo yana tambayarki sai Inna ta fada masa kina asibiti za a miki wanki mara” Tana rufe baki kiran wayarsa na shigowa a wayata, nan ma sai dai nai kamar kar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hana ni, picking nai na kara a kunne tare da sallama. Be amsa min ba kuma be ce min komai ba sai dai daga cikin wayar ina iya jiyo yadda yake ja da aje numfashi da karfi. Katse kiran nai na kwantar da Amal sannan nima na kwanta bayanta ina ta tunanin Kabir ko a wane hali yake ciki a yanzu inata auna zafin barin da na da kuma kafarsa da aka ce ta cire da gaske ma ta cire din ko kuwa dan karawa labarin magi dagishiri yasa tace haka? Number wayarsa na gwada kira da fari ta yi ringing har aka daga sai dai ina yin sallama sai aka kashe kiran na sake bugawa na ji wayar a rufe. Damuwa sosai ta shiga raina, ko ba komai ai mun yi zaman mutunci da Kabir idan na tsallake ko kuma na cire son tana jikin ko yi min maganar banza da Kabir yake kokarin yi ban san shi da wani hali na assha ba, tun ba jiya ba yana yawan damuwa na al'amurana, duk wani abun da ya dame ni zai nuna damuwarsa sosai a kaina, idan kuma akan wani laifin ne a gurin aiki to zai yi kokarin tare min ko ya wanke ki ko a gurin waye ne. Ko a kan wannan kadai ya kamata na damu da Kabir balle kuma saboda yaje siyo min abinci wannan abun ya same shi, ko da ciwon kai ne ya same shi ta dalilina dole na damu balle kuma hadari, abun sai ya hade min a guri daya har na rasa wanne zan fara tunani bayan damuwar da ke cina yanzu kuma wani abun ta samu Kabir ta dalilina. Har garin Allah ya waye Kabir na cikin raina ban jidadin rashin zuwa ganinsa da ban samu yi ba, kusan rabin mafarkin da nai na Kabir ne sai dai ba zan iya fahimtar sakon mafarkin ba, kuma na alakanta hakan da kwanta da nai ina tunaninsa. Duk da bana sallah haka ba be hana ni tashi da asuba da wuri ba kamar yadda na saba, ko bana sallah na kan yi addu'oina na safe idan ina lokacin period ne. ABDALLAH POV. Da gangan yake yai magana ya yi shiru yana ta sauraren yadda numfashinta ke fita fuskarsa na yalwantuwa da murmushin da shi kadai ya san sikarsa, bayan ta kashe wayar ya sake kira sallamar da tai masa ta saukar masa da natsuwa da kwnaciyar hankali daman can muryarta kawai yake son ji, domin ba shi da wani abun da zai ce mata, bayan son yai mata jajen ɓarin da tai ta waya, ɓarin kuma ba karamin dadi yai masa ba, domin ya kusanto masa da nesa kusa zuciyarsa na raya nasa a yanzu yana cikin ko wane mataki da zai iya nunawa Halimatu soyayyah, domin bata da auren a yanzu kuma ta cika idda indai har jinin ya tsaya mata. Kansa ya daga sama yana kallon tauraren da sukai ma sararin samaniya ado. Sannan ya maida wayar aljihunsa tare da zuba duk hanneyensa aljihun wandon, Halimatu ba zata so shi ba, ba zata taba amincewa da shi kai tsaye ba, domin yayi kuskuren nuna mata kauna a lokacin da take da igiya uku ta aure akanta har ta koma biyu har da zama daya, shi yake yawan fada mata mijinta yayi kaza ya yi kaza, yana yawan nuna mata Aminu ba irin mijin daya dace ta aura ba ne, ya dade yana jira zuwan wannan ranar ya dade yana addu'ar Allah ya raba auren Aminu da yar'uwarsa Halimatu saboda kawai shi ya aureta, yana ji a ransa kuma yana yawan rayawa a zuciyarsa cewar shi kadai ya dace ya zama mijin Halimatu, domin shi ne mutumen da zai iya nuna mata kauna zallarta ya kare mutuncinta ta martaba, and he know exactly how to lighten the candle of happiness in her life. Tun daga lokacin da ya dawo kasar nan tare da iyalinsa ya kyalle ido ya ga Halima sai Allah ya dauki sonta mai tsanani ya saka masa, har ya zama bashi da sukuni da walwala idan ban ganta ba ko be ji daga gareta ba, tun yana kokarin cire abun a zuciyarsa ya kawarda komai har ya gagareshi, har yake ji da ace ya san lokacin da take budurwa ko kuma yayi arba da ita tabbas da Halimatu bata da wani mijin bayan shi, domin tana da siffar da yake so a jikin mace komai na rayuwarta burge shi yake, the way she dressed, yadda take tafiyarda rayuwarta ga hakuri da kawaici ga magana ma so calmly, even simple makeup din da take burge shi yake. Daga lokacin da ya gano kalar mijin da take aure kuma sai tausayinta ya samu muhalli a zuciyarsa, kuma ya samu makamin yaki da igiyar aurenta. Ba abu ne mai sauki Halimatu ta karba tayinsa a yanzu ba, shi kansa ya sani domin haka ba zai yi kuskure nuna mata haka a yanzu ba ko kuma furta mata kalma so ko aure a yanzu ba, duk kuwa da kasancewar ta dade da jin daga gareshi saboda ya fada mata ba daya ba ba biyu ba cewar yana sonta yana kaunarta a lokacij da take da igiyar auren a akanta har take masa kallon mahaukaci ko kuma marar tunani, wannan dalili ya saka Halimatu tsanarsa fiye da kowa a familynsa. Ba irin wannan lokacin ya kamata ya nuna mata so ba, wata kila ma bata sha'awar auren a yanzu, sai dai ya shirya nuna mata kulawa da kwantar mata da hankali da kuma kaunar yaranta. “Daddy ba zaka shigo ba?” Juyowa yai yana kallon yarsa Suhaima fuskarsa dauke da murmushi, ya kai hannunsa ya daga sama. “Eyyyy ba ki kwanta ba Mamana?” “Yes mu na ta kallo da Aiman, amman kowa yayi bachi sai ni da kai da Aiman muka rage” “Okay je ciki ina zuwa” Ya fada yana sauketa kasa sai ta juya da gudunta ta koma ciki, shi kuma ya sake ciro wayarsa sai dai wannan karon ba Halimatu ya kira ba Hajiyarsa ya kira duk kuwa da bashi da tabbacin cewar zata dauka wata kila ma ta yi bachi. A mamakinsa sai tai picking call din da muryarta radau babu alamun bachi. “Hajiyata ba ki kwanta ba?” “Ban kwanta ba Husaini kai me kake a farke?” Jimmm yai na wani lokacin sannan ya ce. “To ni ma dai ba zan iya fada ba for now, amman dai na kira na fada miki cewar Halima ta yi miscarriage ya kamata ki dubata gobe inda hali, kin ga ko sakin da akai mata Hajiyata ba ki je kin mata jajaye ba” Daga dayan bangaren Hajiya tai murmushi mai sauti sannan ta dora da. “Zanje gobe In-Sha-Allah shikenan? Jikin nata dai da sauki ko?” “Ban sani ba, amman naje dazun ban tararda ita ba wai tana asibiti ni kuma bana son su fara zargin wani abun ne shiyasa ban je ba, amman ni ma gobe zanje ma dubata” “To sai ka biyo ka dauke mu mu tafi ai” “Aa Hajiyata zuwanki dabam na Abdallah dabam” Ya fada da murmushi a fuskarsa sannan yai mata sallama ya sauke wayar, fira da mahaifiyarsa ko yayansa na daya daga cikin abunda yake saka shi ciki nishadi da farinciki ko da kuwa yana cikin damuwa ne. Juyowa yai ya nufo balcony ya tura kofar falon ya shiga. To His surprise sai ya samu uwargidansa tsaye jikin window dakin tana kallon waje sai dai shigowarsa yasa ta juyo ta da dubanta gurinsa. Ya dan wara ido yana murmushi daya saba yi mata. “Suhaima ta ce kina bachi” Ta wani marairaice kamar karamar yarinya marar. “Taya zan iya bachi Doc be kusa da ni, na yi na dan guntun lokaci sai ya farka bachi ma ba dadi” Murmushi yai ya katsa kusa da ita yana mai jin son uwargidan har cikin ransa, ya kai hannunsa ya rumgumeta ta baya ya dora kansa saman wuyanta. “That's right Teema” Ta yi saurin juyowa ta kalleshi. “Teema kace fa?” “Eh ba sunanki ba ne?” “Amman ai ba haka kake kirana ba sai dai ka ce min Baby ko Madam ko Mom Suhaima” Dariya yai ya jiyarda ita ya sake rungumeta ta baya. “To Baby yau yan tsokarna sun motsa ne shiyasa” “Da wa kake waya?” “Da Hajiya” “Amman ka dade a waje fa” Ya sauke hannayensa daga rikon da yai mata ya saka hannayensa aljihu. “Ina ta tunanin mutuwa ne, mutuwa kawai ake a yanzu any how abun har tsoro yake ba ni, ina ta tunanin makomarmu ne” Ya fada yana hade yawun bakinsa domin shi ma yasan karya yai. A take Teema ta bata fuska damuwa ta bayyana a fuskarta jin furuncin daya fito daga bakin mijinta, hakika mutuwa abun tunawa a ko wane dare ko dakika sai dai ba kowa ne ke tunawa da ita ba sai masu imani da tunanin ya goben su zata kasance. “Allah dai ya saka mun cika da imani, nima abun na taba ni Wallahi” Ta fada bayan ta sauke ajiyar zuciya. Hannunsa ya kai ya riko hannunta ya nufi hanyar dakinsa da ita. “Ina Aiman? Suhaima tace sune kawai ba su yi bachi ba” “Na saka su bachin dole ai, kun zauna gaban tv kamar a gurin za su tabbata” Hannunta ya saki ya nufi dakin yaransa, a bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon Suhaima da Lubna sai kuma yayan Halimatu wato Namra da Aiman da Adnan, a ransa ya rika kwatatta yadda abun zai burge idan da ace shi Halimatu ta haifawa yaran nan gaba daya musamman Aiman da Adnan domin shi Allah be ba shi yaya maza ba, yan mata biyu matarsa ta haifa masa. Zuwa tai ta tsaya bayansa tana kallon yaran. “Minene?” “Ba komai” Ya kai hannu ya janyo kofar dakin sannan ya nufi dakinsa Teema na biye da shi a baya. HALIMATU POV. Karfe takwas na safe kofar shiga dakin da Kabir yake tai min, domin na kwana da shi a raina da na farka kuma sai na ji bana bukatar ganin kowa sai shi hakan yasa ban wani tsaya karyawa ba na nufo asibitin daman can abinci be dame ni balle kuma yanzu da damuwa ta zame min ci da sha, kuma ta zame min abokiyar fira. Ba ni kadai aka hana shiga ba, har da sauran masu ganin marasa lafiya da masu kawo abinci balle kuma ni da ban kawo komai ba. Muna tsaye a gurin har kusan tara da wani abu ba bar mu mum shiga ba sai dai an bar masu dauke da abinci sun shiga, ni kan sai na samu guri kusa da inda kofar take na zauna, na bawa kofar baya zaman jiran gawon shanu domin ban san lokacin da za a bada damar shigar ba, sai dai bana jin a yau zan wuni ban saka Kabir a ido ba ba dan komai ba sai dan damuwa da halin da yake ciki a yanzu wanda silata ne komai ya afko. Ji nai a dabani da wani hannu mai sanyi da alama mamallakin hannun ya taba ruwa mai sanyi ne ko kankara, ashe mamallakin hannu mace ce ba namiji ba ban fahimci hakan ba har sai da na juyo na kalleta na kuma tabbatar da macece ta hanyar sautin muryarta. “Kamar Haima?” Gabana ya fadi har na kasa amsa mata da eh ni din ce ko kuma a a ba ni ba ce, domin mutun biyu ne suke kirana da wannan sunan a duk fadin duniyar nan. Daga Abdulhamid sai Kabir, ba kuma zan ce a gurin Abdulhamid ta samu sunan ba, domin be taba kirana a gabab kowa da wannan lakanin ba, mutumen da be yarda na bayyana soyayyarsa ba taya zai fadawa wata ya taba kirana da wannan sunan a lokacin da na ke budurwa. “Har na wuce ki na dawo saboda kin min kama da Haima, kuma wannan shirun da kikai ya tabbatar min da cewar ke ce Haima! matar da Kabir ya cika wayarsa da hotunanta kuma matar da aka ce ita yaje siyo ma abinci wannan hadarin ya same shi, wani abun mamaki kuma jiya da kika kira wayarsa sunanki yai appearing da Spacial Haima” Wani dimmmm na ji kamar an dora min abu akao na kunya da nauyin kalamanta, hakika ni ma mace ce ba zan zo mijina ya kula wata mace ba kuma ba zan jidadi ba, sai a iya zamana da Kabir ban taba daukar hoto daga ni sai shi ba ko kuma ni kadai na tura masa to a ina ya samu hotona wata kila a media ko kuma a gurin wani wata kila kuma ya dauke ni ne a lokacin da nake aiki. “Shin baki taba sanin Kabir yana aure da yaya ba?” Ta jefo min tambayar da ban san ta ina zan tattara amsar da mika mata ba har ta gamsar da ita. “Ya kamata ace na damu da lafiyar mijina a yanzu ko dan saboda yayan mu, amman saboda ke idan na tuno sai na ce masa Allah ya kara, ke ya kamata ace kin fi ni damuwa da shi, ko ba komai kin fini samun lokacinsa kin fi ni samun soyayarsa da kularwarsa, kin fini muhimmanci a gurinsa” Tana fadar hakan ta fara takawa zata bar ni a gurin da dafin furucinta, cikin kuzari da hanzari na mika sautin muryarta dan isar da mata da abunda bata sani ba. “Babu wata alaka tsakanina da mijin, abokin aikina ne kawai kuma ni ma matar aure ce har da yaya be kamata ki zarge ni ba” Juyowa tai ta tsaya tana kallona kamar mai mamakin abunda ya fito daga bakina, a zatona zata yarda da kalamaina ne ko kuma ta dora su a ma'aunin tunani. “Matar aure? Kina nufin irin auren nan da be hana mai yinsa aikata komai ko? Kina nufin irin ijiyar auren da wasu kan take su aikata alfasha da wasu mazan ko?” Wani irin abu na ji ya taso min ina iya jure komai a cikin har da kazafin sata ko maita amman ba zan juri a kira mi karuwaba, domin na san illa da kazantar zina ban aikata ba dan haka ba zan yarda wasu su bata min suna ba. “Ke malama ban san ki ba bana da wata alaka da ke, ko ki iya halsheki ba zan jure irin wadannan kalaman daga bakin kowa ba...!” “Baki san ni ba ba ki da alaka da ni amman kina da ita da mijina ko? Banza marar sanin ciwon wawuya wacce igiyar aure bata hana ta aikata komai ba....” Cikin daga muryar take fada min haka, ban san lokacin da na karasa kusa da ita na wanke mata fuska da mari ba, abunda ya janyo hankalin wasu mutanen izuwa gare mu kenan daman tun da ta fara maganar aka fara tsayawa yana kallon mu... ___________ Tofaaaaaaaaa. Al-hamdulillah yanzu kan Al-hamdulillah na gama komai hankali ya dawo gurin typing.....✍️ 7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 1️⃣1️⃣ “Ko yar iska ce ni na fi karfin iskanci da Kabir, mutumen da ke daukar the same salary da na ke dauka, mi ya samu mi ya bani na fi karfin abunda kike tunani na fi karfin aikata alfasha da aurena da yayana” Na fada mata cikin zafin nama bayan na wanke mata fuska da mari, wata matar da ce da ban wayance wacece ita ba ta zo da sauri ta rike matar Kabir din tana kiranta da sunanta. “Haba Maryam wannan abun da kike ba mutunci ba ne, ai ko da gaske mijinki yana aikata alfahari be kamata ki tsare mace a hanya kina mata wannan maganar ba, ballanta baki da tabbaci akan hakan kamata yai ki fara damuwa da damuwar mijinki a yanzu Kabir yana a halin tausayin a yanzu abunda likito suke fada jinin ya kai har cikin kansa zai rayu ba zai rayu ba haukacewa zai yi ko ya manta komai duk be dame ki ba sai wani abun da ba zaki iya canjawa ba! Haba Maryam” “Wallahi Anty karuwarsa ce kuma saboda ita wannan hadrin ya same shi, yanzu kuma dan rashin kunya har ta sako kafarta ta zo ganinsa? Haba Anty da wanne zan ji da ciwonsa ko da ganinta” Ta fada cikin kuka ni kan tuni jikina yai sanyi jin abunda ya same Kabir jinin ya taba kwakwalwarsa, abun ya tsorani sosai kuma ya jefani a cikin wata duniyar tunanin da fargabar yadda gobensa zata kasance. Takawa na fara yi ina tafiya na nufo gate din fita daga asibitin gaba daya ba tare da na sake cewa komai ba, kallo daya za ka min ka fahimci akwai damuwa a tare da kamar yadda tunani ya kawo min ziyara a yanzu. Kar dai ace saboda ya rabe ni hakan ya same shi? Kaddararta ta fara wuce iya ni kawai har ta fara taba yayana da mutanen da suke kusa da ni? Tambayar da na yi ma kaina kenan tambayar da ban san wanda zai amsa min ita ba. Guri na samu kusa da gate din na zauna a saman wani guntun dakali idona cike da kwalla, ban samu kaina a cikin tausayin wani mutum wanda ba jinina kamar yadda tausayin Kabir ya dirar min a zuciya yai min kawaya a ruhi, ya nemi jijiyoyin jinina da jiki ya rike. “Halimatu” Muryar Abdallah ce ta hankalto ni har na dago kaina na kalleshi hawaye na min zuba. “Zama kikai a guri kamar wannan har kina kuka a public? Mutane fa suna ta kallonki” Cikin wani irin sanyin muryar da natsuwa yai min maganar da sautin da ni kadai zan iya ji da kuma fahimtar kalmomin da yake furta min. Sauke kaina nai daga kallonsa zuwa kallon titi ina ta yawo da ido. “Abdallah ina tunanin Gobena ne, ya zata kasance? Miyasa abubuwan nan za su faru ta dalilina? Na farko yata? Na biyu kuma abokin aikina? Abunda ya faru da Namra kamar jiya ne, ban sammaci wani abun da zai taba zuciyata kamar haka zai sake faruwa ba, idan wani abun nai nauyi ya sake faruwa da ni ina jin kamar ba zan iya jure ba” Risinowa yai gabana yana kallon fuskata. “Share hawayenki zo muje a mota ki min bayani maybe zan sama miki mafita” Sai na sake dago kai na kalleshi a karo na biyu, a yau Abdallah yai magana ta hankali da nuna kulawarsa a kaina, ko da yake a can baya ma ai yana nunawa sai dai wacan karon ina ganin rashin dacewar hakan saboda akwai igiyar aure a kaina, kuma a baya duk wata magana da zai min ta Aminu ce da abunda ya shafe shi. “Abdallah zan iya rikon ka kamar dan'uwan? Abokin shawara? Wanda zan labartawa damuwata ya nema min mafita? Dan Allah?” Sai ya kasa ce min komai, ba dan komai ba dan sai dan ya san inda manufata ta dosa, daga lokacin da zai rike ni a matsayin yar'uwa to babu zancen soyayya ko aure a tsakaninmu, ni kuwa abunda na fi so kenan, domin ban tana yi ma Abdallah kallon so ko kauna ba balle har ta ga kai ga aure! Mikewa yai tsaye ya nufi inda motarsa take, sai a lokacin na lura da inda ya faka ta, tashi nai na bi bayansa ba tare da na share hawayena ba. Na bude front seat ma shiga shi kuma ya tashi motar ya koma da ni cikin asibitin, a daya daga cikin guraren da aka tanada domin likitoci su faka motocinsu ya faka motarsa sannan ya juyo ya kalleni. “Idan har hakan zai faranta miki rai Halima zan yi, amman ki sani zan cutu domin ba abunda nake so kenan ba, sai dai zan jira har lokacin da zaki fahimci da gaske na ke, fada min minene damuwarki?” “Abokin aikina yayi hadari saboda ni, kuma yanzu na ji cewar akwai yiyuwar jimin ya tana kansa wata kila ya haukace ko ya manta komai ko ya mutu” Na fada kai tsaye ina share hawayena. Sosai ya nuna min damuwarsa. “Subhanallahi miya same shi haka?” A take na labarta masa komai har zuwa fadan da mukai da matarsa. Na yi zaton ko zai tausaya masa ne sai na ga murmushi a fuskarsa. “Kin kasa yarda cewar kina da kyau da kan iya jan hankali wasu mazan izuwa gareki saboda Aminu yana yawan fada miki cewar baki da kyau ko? Kina da kyau Halima seriously kina da jikin da ko wane namiji zai so ki kasance a tare da shi, ina tunanin abunda ya ja hankali abokin aikinki kenan har ya kai ga mallakar hotunanki da sakawa sunanki spacial saboda ke din ta musamman ce” Na yi kasa da kaina ina tuna lokacin da Aminu yake fada min cewar kibar jikina ta masa yawa shi yar siririyar mace yake so wacce ke kamar zata kare, mace da zai nuna mata soyayya ta nuna masa yai zaman jindadi da ita ba zaman tara masa yaya ba. “Bana son ki saboda kawai wadannan abubuwan da na lissafa miki, no ina fada miki hakan ne saboda ki yarda cewar ke din kyakkyawa ce kuma Allah be rage ki da komai ba” Maganar da yai ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na fara zuwa, hakan yasa nai kokarin kawarta maganar. “Taya zan fahimtar da matarsa cewar ni ba karuwarsa ba ce” Sai da ya danna horn din motarsa kamar wani ne a gaban mu alhalin babu komai a gabanmu sai fulawoyi. “Ki sakawa ranki sallama for now Halimatu, ki cire zancen cewar saboda ke wannan abun ya samu abokin aikinki, kuma ki manta da zancen fahimtar da matarsa, ki daga musu kafa na wani lokacin idan ya samu lafiya kamin lokacin sai ki je ki ganshi kuma ki fada masa ya fahimtar matarsa sannan kuma ki gargade shi daya cire kansa akan duk wani abun daya shafe ki, Halima kin san abunda nake so da ke?” Na girgiza masa kai alamar ban sani ba. “So na ke ki manta da komai da kowa a gabanki ki maida hankalinki gurin aikinki kuma ki kula da yaranki sai kuma zancen Namra shi ma ki jajirce wajen ganin kin kwato mata hakkinta barin wannan maganar zai bawa kanen mahaifinta damar yi ma wata yar ne” “Amman Mama tace na bar maganar saboda kar na jawa Namra abun kunya idan ta girma” “Halima ya kamata ki gane wani abu, ke fa uwa ce idan ba ki yi abunda zai kwantar miki da hankali akan yayanki ba to be kamata ki bar damuwa a ranki ba, duk wanda zai nuna miki yadda za ki kula da yaranki a bayanki yake, duk wanda zai damu da abunda ya damu danki ko yarki a bayanki yake, ke fa mutunce ya kamata ki san da wannan, ki yi wani abun da zai zame miki kwanciyar hankali kuma ya zamo abun koyi a gurin wasu matan, bari kashi a ciki baya maganin yunwa hankalinki ba zai taba kwanciya ba har sai kin hukunta wannan mutumen right?” Na gyada masa kai gaskiya ya fada, ni kaina ina son yin hakan sai dai yadda Mama ta nuna bata so yasa na fara cire rai daga yin abun. “Zan tsaya miki Halimatu, zan goya miki baya zan miki duk wani abu da kike bukata kuma zan baki kariya i promise you this” “Zan tattauna da Mama har sai na ji ta bakinta yardar Allah na tare da yardar iyaye, bana son na yi wani abun da zai zamewa mahaifiyata ciwo” “Yes hakan na kyau, sai dai wani lokacin iyayena suna nuna mana abunda suke gani a kamar zai cutar da mu alhalin ba cutarwa ba ne Allah ya taimake mu” “Amin ya Rabb na gode Abdallah” Na fada ina dubansa sai shi ma ya dubuni ido cikin ido wani tsan na ji na rashin jindadi for the first time yau na ji nauyi da kunyar Abdallah ya dira saman kaina. “Ya jikinki?” Ya tambaya still idonsa a kaina. “Al-hamdulillah” “Ina fatar kin ji sauki sosai” “Na ji sauki” “Mashallah. mama tace min kin tafi tafi aiki ashe ganin wani kika zo” “Na fada mata da ga ganin Kabir zan wuce gurin aiki ne maybe ta dauka na wuce ne, ka biyo da gida ne?” “Yes na zo na duba jikinki ne kuma ina son nai maganar karatun su Adnan da ke as her mother” Kallonsa nai ba tare na ce komai ba sai ya cigaba da maganar still idonsa na kaina. “Ina son canja musu makaranta ne zuwa wacce su Suhaima suke yi idan kin ba ni dama amman kuma kin aminta” “Aa Abdallah na gode da kulawa ka dawo da su gida, ni zan duba musu wata makarantar dabam” Ina kokarin kai hannu na bude ganbun motar na fita sai ya danna lock motar ta rufe hakan yasa na juyo ya kalleshi shi ma ni yake kallo da kyau. “Na fadi wani abun ne daya bata miki rai? Ko na yi wani abun ne marar dadi?” “Ba ko daya, yayana ne babu ruwanka da su” “Amman yanzu kika gama fadar cewar zan zama miki dam'uwa? To miye laifi dan na saka su Namra a scul” “Bana so, yarana ne dan Allah ka kyale su, zan iya kula da abuna zan iya musu komai” “Ba zan cutar da su Halima kamar ba ki san ni ba” “Ka kyale ni dan Allah Abdallah bana bukata” Na fada ina hade hannayena tare da fashewa da kuka. “Miye abun kuka daga wannan maganar?” Ya karasa yana unlock din motar, ni kaina ban ga wani abun kuka a cikin lamarin ba, sai dai ina jin a yanzu kamar bana da wata garkuwar shiyasa kukan ya fi kusa da ni. Bude motar nai na fita ina share hawayena. Na isa gurin aikina cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, yanayin da ba zan iya fadarsa ba, hakika inacikin damuwa bayan ta yarana da tawa yanzu kuma ta Kabir ta hau kaina. Wunin ranar ban iya tabuka komai ba saboda yawan kallon mazaunin Kabir da neka sai na rika ganin kamar yana nan ko kamar zai shigo irin yadda ya saba. Sai dai idan na tuna cewar yana can kwance asibiti sai na ji babu dadi. Ko dan saboda sabo idan abokin aikinka baya kusa da kai kanki babu dadi balle irin wannan mai dalili. Tun da na fara aikin shekara hudu ban tana jin aiki ya gundure ni ba, ban taba jin na tsani aikina kamar yau ba, idan na kalli inda Kabir yake zaune sai na ji babu dadi ba ni kadai ba har Emanuel ya damu da hakan saboda yanayinsa da na gani, ban tana jin damuwa da lamarin Kabir kamar wannan karon ba, tausayinsa ya hanani sukuni kamin lokacin tashi aikina yai har na tsalwala. Biyu da mintuna na tashi daga aiki daman wani lokacin nakan tashi haka wani lokacin har uku saura ko uku da wani abun. Tafiya nakecikin kamfanin ina tunanin abunda zai sake samu na, domin ina jin a jikina kamar kullum wani abun zai yi ta samuna ko wani na kusa da ni marar dadi. 7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 1️⃣2️⃣ “Hajiya barka da tashi ya kafafuwan?” A natse yake mata magana kamar yadda ya saba, ita kuma ta dago ta kalleshi da kyau tana tauna ragowar goron da ke bakinta. “Hassan kwana nawa rabon ka da gidan nan?” Shiru be amsa mata ba. Hakan ya bata damar cigaba da yi masa fadan a zuciyarta kuma tausayinsa ne fal a ciki. “Ana rayuwa haka? Ko wane bawa ai da kalar kaddararsa, amman sai ka rika saka kanka a damuwa ba kai ka dorawa kanka abun nan ba” Kunya ce ta lullube shi, duk kuwa da ya san gaskiya Hajiya take fada masa and he know rashin lafiyarsa na daga cikin abunda ya fi ko wane daga masa hankali, tun abun baya damunsa yanzu har ya kai matsayin da idan aka auna jininsa za a iya cewa ya hau, babu inda be nemi magani ba a duniyar nan amman babu alamun sauki balle ma saukin, babu abunda be yi ba tun daga na hausa har zuwa na gargajiya amman shiru kamar an shuka dusa. Shi yanzu abun tsoro ma yake ba shi domin yana ayyana a ransa kuma yana jin kamar ba zai taba warkewa ba, burin da ko wane mai rai yake da shi na son yai aure shi kan na shi yana nesa da shi, tun ana kiran yaushe zai yi aure a family da friends har ta kai yanzu dai su tsarge shi suna kiransa da tazuru wasu kuma su ce masa mijin aljana wanda hakan ba karamin ciwo yake masa ba. “Karka yanke kauna daga rahamar Hassan, daman ita rayuwar duniya tana cike da jarrabawa, kuma kowa da irin tasa, karka fasa neman magani kar kuma na ce ba zaka nemi aurenba, ka kwada neman auren kamar yadda kake a da, wata kila a dace wata kila kuma kamin lokacin auren yai sai Allah ya baka mafita” Ya gyada mata. “Zan cigaba Hajiya, duk dai ina jin kamar ni haka Allah yai ni” “Babu wata cuta da bata da magani a duniyar, idan ka cire tsufa da mutuwa shine kawai basa da magani, a kullum ina cikin yi maka addu'a kuma In-Sha-Allah za a karba mana ko ma an karba, kowa da irin jarabarwarsa Hassan ga yar'uwarku nan aure ya mutu ai duk cikin jarabawa ne bayan ta fito kuma ciki ya zube wata kila ma kuma ta zubar da cikin ne ta huta da wahalar duniyar” Kallon rashin fahimta yai Hajiya, idan tace yar'uwasa zai fara kawo sisters dinsa da suke daki daya kamin ya hango na wani gurin, a cikin familynsu ma sisters dinsa ma ai suna da yawa abunka da mai yawan yan'uwa. “Wace Hajiya?” “Halimatu...... ” Haka ya ji sautin sunan sahibarsa kamar daga wata duniyar, Halimatuu... Ya maimaita cikin mamaki da bakinciki jin abunda ya faru. “Taya? Garin ya?” “Ai kasan abunda ya faru da Namra ko to shine sanadi yau kusan kwana uku ma da faruwar abun ko hudu kuma cikin da ta fito da shi ya zube har sai da akai mata wankin mara anjima na ke son zuwa na ganta” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, ai kamar saki daya ne ya rage ko?” “Saki daya ne kuma ya karasa kai wannan mutumen ba shi da imani sam ” Wani irin na rashin jindadi ne ya ziuarci Abdulhamid, sai yaji kamar kanwarsa da suka fito ciki daya aka saka, a take ya fara ayyana irin yadda Halimatu zata ji halin da zata kasance duk kuwa da ya san dama can ya san ba dadin zaman auren take ji ba. Wanda yake yawan alakanta hakan da kansa domin yana ji a ransa da ace yadda yai soyayyarsa da Halimatu a boye da ya samu cikar burinsa da yanzu shi take aure da yanzu duka yaran na shi ne,ya dade yana fargabar zuwan wannan ranar yau ga ranar ta zo da ba zai iya yi mata komai ba. _Bana da tabbacin wanda zan aura zai rike ni amana Abdulhamid, amman ina da tabbacin kai idan ka aure ba zaka wulakanta ni ba, bana jin idan ka aureni zaka iya rabuwa da ni har sai idan mutuwa ce ta dauke daya daga cikin mu_ Cikin kuka take masa maganar muryarta har rawa take. _Ki yi hakuri Haima, ba zan iya cutar da ke ba, ba zan iya aurenki na zaunar da ke a gidana ba bayan na san bana iya yin komai da mace, idan nai hakan na cutar da ke kuma duk abunda zai biyo baya laifina ne ba na ki ba_ _Wallahi zan jira ka zan zauna da kai har zuwa lokacin da zaka samu lafiya, ko wane masoyi yana da burin yin wani abun na faranta rai na sadaukarwar ga masoyinsa, Abdulhamid ka ba ni dama dan Allah zan aureka a haka kuma zan jira har zuwa lokacin da zaka samu lafiya_ _No ba zaki gane abunda na ke nufi ba, ban tsammaci cewar zai kan wannan lokacin ban samu lafiya ba_ _Ka hanani bayyana soyayyarka, daman saboda ka san ba zaka aure ni ba ko? Yanzu kuma ka hanani aurenka_ _na hana ki bayyana soyayyata saboda na san wannan ranar zata so wata kila na samu sauko ko akasin haka, kin ga yanzu da ban samu sauki ba babu wanda ya san mun yi soyayya da ke, da ace na samu sauki kuma da yanzu ne zan bayyana soyayyata, ki fahimce ni mana Haima Wallahi ina kaunar ki amman ba zan iya hana ki auren lafiyayyen miji ni na aureki, ba kuma zan hana ki auren kowa ki jira ni ba domin ban san lokacin samun lafiyata ba, kuma iyayenki a yanzu ma sun damu su aurar da ke, Allah ya riga ya rubuto ba zan aureki ba...._ Duk wani magana da Hajiya ke yi be ji ko daya ba saboda ya lula a duniyar tunanin abunda ya faru tsakaninsa da tsohuwar soyayyiyarsa yana murza zoben da ta saka saka mata da kansa a wani lokaci can baya. “Hassan....” Da sauri ya dago ya kalli Hajiya domin ya ji kiran kamar daga wata duniyar. “Na'am Hajiya?” “Ba ka ji abunda na ce ba ne?” “Na ji.... Na ji.. Na ce eh ba ki ji ba ne?” “Saboda me?” “Haka nan kawai” “Haka nan kawai sai ka ki zuwa aiki? Abun ya fara taba har da aikinka ne?” Sai a lokacin ya fahimci abunda Hajiya take magana akai domin a dazun amsa mata kawai yake ba tare da yaji abunda take fada ba. Mikewa yai tsaye yana murmushi. “Zan je aiki mana Hajiya, ban fahimta ba ne sai yanzu” “To Allah ya tsare yai muku albarka” “Amin Hajiya sai na dawo” Ya fito yana jin cewar a yanzu ne ya dace ya nemi magani ko dan Halimatu, idan ma bar warke ba zai aureta a hakan matukar a yanzun zata aminta domin yana jin cewar shi kadai mutumen da zai iya yarda ya aureta da yaya a yanzu kuma ya mantar da ita komai. HALIMATU POV. Wani abunda ya bani mamaki rashin samun abun hawa tun daga kan babura har napep duk wanda na tara ba ya tsayawa. Abun har mamaki ya bani na rika shafa kaina ina lalabawa wai ko basa ganin nane amman sai na jini a mutum kuma ai ina ganin mutane an kallona sai dai tsayawa su dauke ni ne basa yi. Tun ina tsaye ina taro har ta kai ga na fara takawa ina bin gefen titi, da na gaji da tafiyar sai na samu guri na hutu, na sake cigaba da tafiya sai yamma lis na isa gida ban taba jin gajiya irin ta yau ba damin ban taba shan wahalar tafiya kamar yau ba. Na tararda kowa da kowa na tsakar gida kamar yadda aka saba yin shimfida a harabar gidan a zauna ana ta fira da dare dare. Suna ta min sannu da zuwa ni dai ban bi ta kansu ba na wuce zuwa falon Mama sai na samu Abdallah a zaune yana game da wayarsa Namra na gefensa tare da Aiman da Adnan sun zagaye shi Amal kuma na saman cinyarsa tana kallon wayar, tsayawa nai ina kallonsa shi ma ya dago ya kalleni fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Sannu da tafiya” Sannan ya mike tsaye yana gyara rigar shaddar da ke jikinsa. “Kin ce na dawo miki da yaranki ko? To ga su nan sai ki saka su makarantar ai” Yana fadar hakan ya raba gefena ya wuce ni kuma na bishi da kallon takaici da mamakin karfi hali irin nasa, yara dai nawa ne kuma na zabi na saka su da kaina to ina ruwansa, tun ba yau ba Abdallah na da son shiga rayuwata tun igiyoyin aure suna kaina ina yawan nuna masa bana so amman baya fasawa. Ba wai bana son ya saka su karantar ba ne canja musu makaranta abu ne mai kyau wanda ni ma nai tunanin hakan sai dai bana son yadda yake son shige min ne da yawa, har ga Allah bana jin zan iya karbar wani tayi daga gurin Abdallah na so, taya zan so mutunen da na kaunace dan'uwansa kamar na mutu, mutumen da be san darajar aure ba kuma mutumen da be taba martaba ni saboda ina da igiyar aure ba, mutumen da a kullum fatar mutuwar aure yake min.   Adnan na aika a shago ya siyo min suga da madara da biredi na hada tea mai sanyi na sha, domin yau ban saka komai a cikina ba sai ruwa, a lokacin da zan fita ban ci komai ba ga shi na ci tafiya a kafa kamar marar galihu. Na yi sa'a bana sallah hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin yau ko ta kan Amal ban bi na hau kafita na fara sheka bachi kamar wacce ta shekara batai bachi ba. Ban farka ba sai 11pm a lokacin wasu sisters nawa sun yi bachi su kan yara ba a maganarsu daman can abu ne mai wahala su wuce 10 ba su yu bachi ba ko lokacin da muke gida suna ganin game balle nan da babu. Wani irin ciwon kafafuwa ne ya taso min kamar wata tsohuwa da kaina na zauna ina matsa abu saboda azaba. Na yi minti talatin a haka sannan na tashi na shiga bandaki na tsaftace kaina na canja pad na fito na nufi dakin Mama.    Na same ta tana hamma kamar dai ni da bachin be wadatar da ni ba, kusa da ita na zauna ina amsa mata cewar lafiya kalau gajiya ce kawai ta saka ni bachi. “Ya jikin abokin aikin na ki?” “Jiki ba dadi Mama ance ma wai jini zai iya taba kansa ni abun ya bani tsoro sosai, amman matarsa sai ci min mutunci take” “Akan me? Miye hadinki da matarsa?” Na jera mata komai kamar a gabanta ya faru, sosa abun ya bata mata rai har take yabon matar da rashin kunya da kuma tunani, mun dan dauki lokaci muna tattaunawa maganar kamin na soma mata shimfida da zancen Sadi. “Wai Halimatu ba zaki share maganar nan ba? Yanzu fa aurenki ne ya mutu kin dawo cikin kenanki kin zauna su ma muna fatar rabuwa da su ke kin dawo maimakon ki fara tunanin yadda Goben ki zata kasance ki samu mijin aure shine kike neman batawa yarki da kanki suna? Ke yanzu kina ganin wani ma idan ya ji kina da yara hudu zai aure ki ne? Ai ba kowa ke son mace mai yaya ba ma, sannan wani ko ya so ki ba zai yarda ke je masa da yaya ba” Kallo mamaki nai mata. “Mama yaushe aurena ya mutu ma balle har ace wani ya zo nemana? Kuma ni yanzu ai ban shirya ma aure ba” “Baki shirya ma aure ba? Kika magana kamar ba yar musulmi ba? Ke yanzu ko dan ki bawa Aminu haushi ai kyayi aure da wuri, sannan ga kanenki nan suma neman rabuwa na ke su ke kuma kin dawo har ki fara tunanin zama? Halimatu kina da tunani kuwa?” Babu juyin duniyar nan da ban yi ba dan na fahimtar da ita irin matsalar da na fuskanta a gidan Aminu wanda ya saka aure ya fita a raina amman ta kasa fahimta, idan na dauko zancen kotu kuma sai ta tare ta nuna min ba haka har na gaji na taso na baro mata dakin. As usual na farka raina babu dadi babu walwalah daman na saba tashi a haka tun ina gida Aminu balle kuma yanzu da abubuwan suka kara min yawa. Kudina na saka na siyo ma yarana koko da kosai na basu suka sha suka koshi, na san ba za su iya jiran na gida ba domin sun saba da cin abinci da wuri, balle kuma abincin gida na taru ba ba lallai ayi musu yadda zai wadatar da su ba. Bayan na gama da su na aika aka siyo min madara da biredi na hada tea ina sha. Wayata da ke gefena ce tai kara alamar sako tun daga saman screen din wayar na karanta da sakon tare da sunan mallakin sakin. “Good Morning.” Dauke kai nai ganin Abdallah na dauka ma ko zai yi zuciya ya kyaleni ashe ba shi da zuciyar ma, ina jin lokacin da wayar ta koma ringing na ki kulawa saboda bana bukatar kallon mai kiran ba, abunda ban sani ba ashe kawata ce Hajara take kirana ba Abdallah ba, ankarowa da hakan yasa nai saurin picking. “Hello Hajara” “Na'am Halimatu ya gida ya aiki? Ko baki kusa da wayar ne?” “Eh ina breakfast ne ya yaran?” “Lafiya kalau ga ni kofar gidanku ki fito mu gaisa” Mamaki ne ya kamani. “Kofar gida kuma? Miyasa ba za ki shigo ba?” “Ke dai ki fito kawai” Mamaki ne ya kamani ba dan kankane ba, taya Hajara zata so har gidanmu bata shigo ba tace wai na fito mu gaisa? Wata kila wata maganar ce mai muhimmanci ita ce amsar da zuciyata ta bani a take na bar cin abincin da na ke na dauka hijabina na saka Amal ta biyo bayan muka fita tare. A bakin kofar gidan mu na yi arba da motar Isma'il sai dai ban kawo komai a raina ba a zatona ko tana cikin motar ne, haka ne yasa na karasa ya buga kofar gilashin motarta. Saukar gilashin motar sai yai min almara mijin Hajara ne kadai a motar ba tare da ita ba, mamaki ya hanani cewa komai sai sakar masa ido yai, shi kuma yana ta faman zuba min murmushi kamar auduga, bude motar yai ya fito yana ta kara min murmushi da haurensa na makka fari. “Hajara tace min na fito tana kofar gida” “Eh haka ne, amman dai ya kamata mu kamin a dora da bayani ko” “Ba da kai ba da ita” Na maimaita masa saboda ya fahimta amman sai ya kara dilmiyar da ni. “Da ni zaki gaisa ba da ita ba” Ya fada Yan mikawa Amal hannu ta zo sai tai bayana ta boya kamar wacce bata san shi ba. “Ina fatar kina lafiya” Nauyi baki na yi na kasa ce masa komai har ya sake jefo min wata tambayar. “Ya gida ya yaran?” “Lafiya Kalau” Na juya da sauri sai ya kira ni. “Halimatu... ” Har na yi kamar ba zan juyo ba sai kuma na juyo na kalleshi. Bude motarsa yai ya dauko wata ledar ya miko min. “Ga wannan inji kawarki tace a gaishe ki” “Ka maida maita ka fada mata bana son gaisuwarta kuma ka fada mata karta sake aiko ka a kofar gidanmu da sunan gaisuwa” Dariya yai yana gyara tsayuwar agogon hannunsa. “Halimatu kenan, ba zuwa Hajara ne kawai ba, ni kana na ga akwai bukatar na kawo gaisuwa kuma na jajanta miki akan abunda ya faru” “Da alama baka fahimci da wane yare nake maka magana ba, amman idan ita idan ka isar mata zata fassara maka” Ina fada masa hakan ta juya na koma cikin cike da mamakin karfin hali irin na Hajara, shi ma kansa Isma'il din mamaki ya bani domin na lura ba shi da kunya irin yadda na ke da Hajara ai ko ni na tallata masa kaina a tunani be kamata ya amsa min ba. Bayan na koma cikin gidan na shirya, na fito da zimmar zuwa gurin aikina ba, abun mamaki sai na kasa samun abun hawa kamar dai wacan karon, ganin haka yasa na canja shawara daga zuwa gurin aiki na nufi Hauwa International School, wato makarantar su Namra kamar da wasa na tari wani mai napep ya tsaya hakan ba karamin dadi yai min ba ban ko tsaya fada masa inda zanje ba na shiga ciki da murna yadda kasa wance bata saba shiga Napep ba, ina cikin fada masa inda zai kai ni wayata tai ringing, sai da Hajara ta jera min kira hudu sannan na daga rai a bace. “Minene?” “Haba Halimatu ai ko dan ya kamata ki mutunta Mijina” “Naga alamar ke da mijin na ki kamar ba ku da hankali Hajara, na gargade shi ke ma kuma na gargade ki karki sake yi min wannan wasa” “Ni dai van kora dan wani gargadin ki ba, na kira ne kawai na fada miki ban fada masa abunda ya fito dake daga gidan mijinki ba, kuma ban fada masa abunda ya samu Namra ba, kuma ni mijina ba zuwa yai ya fada miki cewar yana son ki ba, cewa ina son ki abu ne mai tsada a gurin mijina ya fara gadaki ne ya ga ruwanki...” Ta karasa tana dariya sannan ta kashe wayar ba tare da jiran irin amsar da zan bata ba. Kadan ya rage mamaki ya kashe ni anya Hajara na cikin hankalinta kuwa kuma ta san abunda take kokarin aikatawa? Wai daman da gaske take da take zancen mijinta ya aureni? Ko kuwa dai gwadani take? Idan gaskoya ne ko karya ni ba zan iya auren mijin kawata ba, yar'uwata ma zance domin Hajara ta fi karfin kawa a gurina. Har na isa makarantar nai abunda zan yi na gama na kama hanyar aikina ban daina mamaki ba da kuma jinjina karfi hali irin yana anya irin matan nan suna nan kuwa? Ni sam na kasa yarda da gaske take ma. *BAYAN WATA DAYA.* Babu makarantar da ban leka ba nai yawo da takardun transfer su Adnan ba amman aka ki karbarsu a ko'ina, daga private school har na gobnati abun har tsoro ya soma ba ni, a duk makarantar da na kai su sai su kamar za su karba sai kuma su bullo da wani abun, wata makaranta ma ko kallona ba sa yi yadda kasan wacce akai wa wani magani haka nai ta shimlalo a gari neman makarantar da zata dauki su Adnan da Namra amman ina! Hakan yasa n watsar da zancen karatunsu na maida hankalina gurin aikina duk kuwa da kasancewar bana jindadin aiki a yanzu saboda rashin Kabir ba kuma dan na shaku da shi ba sai dan tuna abunda ya same ni yana ni walwala a cikin office din, musamman da aka kawo wani da zai maye gurbinsa, ko da wasa ban sake gwada zuwa duba shi asibiti ba, sai dai na kan gwada kiran wayarsa kuma bana samu, ta hanyar wani abokinsa da ke aiki a inda nake na samu labarin cewar an kai shi kano a asibitin kwakwalwa saboda abun ya taba hankalinsa, na tauyasa masa ba kadan ba na kuma tausayawa matarsa da duka danginsa musamman da na samu labarin cewar iyayensa duka biyu basa raye, ta wani bangaren kuma ina tausayin kaina domin ban san me gobena ta tanadar min ba ban san abunda zan tarar nan gaba ba. *Lahadi* Kasancewar yau ranar hutu ce kamar dai jiya sa ta kasance asabar, dukan mu muna zaune gida har kanena ana ta zancen duniya, yawancin firar da muke ta rashin tsaro da ke addabar al'ummar mu ne da kuma tsadar rayuwa da muke ciki, ina zaune Abdallah ya shigo ya gaishe da Mama da Inna kanena kuma suka gaishe shi ya amsa musu amman bakina be hadu da na shi ba, ba baki kadai ba idona ma ban daga na kalleshi ba balle har na mika masa gaisuwa. Tashi nai ya nufi daki yana rike da hannu Namra waccena lura tana sakewa da shi sosai a duk lokacin da ya leko mu, Mama ta tashi ta bi bayansa suka shiga falon tare, ina nan waje zaune amman hankalina yana can inda suke duk na bi na tsargu sai kace wacce tai wani abun gulma. Bayan yan mintuna Namra ta fito hannunta rike da chocolate. “Momy wai ki zo inji Mama” Na tashi cikin kuzari na bi bayanta, ina shigowa idonsa na kaina kamar daman can rayuwarsa ta takaita akan kallona ne kawai. “Miya hanaki saka su makaranta” “Na kai su ba a karba ne” Na fada ina dan turo baki a shagwabe abunda ban saba ba, kuma ban san dalilin zuwansa a yanzu ba. “Daman ai ba za akarbe su ba tunda kika bata min rai” Ya fada yaa ta kallona da idonsa kamar maye, sai a yanzu na fahimci inda zance ya dosa, kar dai kwahi yai min aka ki karbar su a makaranta saboda shi twins ne shi da Abdulhamid. “Kwahi kai min kenan? Ai ni kwahin ka ba zai kama ni ba” “Kwarai shiyasa ranar ai kika samu Napep ta kawo ki har gida” Har yanzu kallona yake yi irin kallon nan kamar ni din tv sa ce. “To wani abun kika masa kenan?” Cewar Mama tana murmushi, ni kuma na maida hankali gurin kiran wayata da ke shigowa. Abdulhamid ne rubuce a screen din wayar, hakan ya saka gabana faduwa ba dan komai na sai dan Abdallah na zaune a falon, kusan tun lokacin da na fito nai bari Abdulhamid be taba kirana da sunan yi min jaye ko sannu ba, ba zan ce dan be ji ba, domin ko last time da Hajiya ta zo ta fada min cewar Abdulhamid ya kawo ta amman be shigo cikin gida ba. “Hello....” “Haima” Gabana ne ya yanke ya fadi jin ya kira ni da sunan da na manta when last ya kirani da sunan. “Na'am... ” Na amsa kamar mai koyon magana. “Kina lafiya?” “Lafiya Kalau” “Ina fatar kina gida, gani nan zuwa amman ba zan shigo cikin gida ba magana kawai zan yi da ke na koma” “To... ” Ina amsawa ya kashe wayar, idon Abdallah na kaina tana ta min kallon tuhuma, ni kuma na gagara tsayuwa na gagara zama sai yawo na ke da ido kamar marar gaskiya, ba dan komai ba sai dan bana son Abdulhamid ya zo ya tarar da Abdallah, duk kuwa da ban san abunda zai kawo shi ba na san dole daya daga cikinsu ya zargi wani abu. Musamman Abdallah da ya fiye shiga hanci da saka min ido. #TeamAbdulhamind #TeamAbdallah #TeamAminu 😜 #TeamHalimatu 7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 1️⃣3️⃣ “Kamar baki da gaskiya Halimatu...” Sai da na kalli Mama sannan na kalleshi. “Bana da gaskiya kamar ya? Wannan wace irin magana ce Abdallah?” Ya dan tabe baki yana ta wasa da hannun Amal kamar ba shi yai maganar ba. Kamar an daki hannuna sai na yi yai min majiyar, ban san lokacin da na saki wayar hannuna ta subuce ta fadi kasa, a take ta watse a saman tedar da ke falon kamar abar da aka taka da mota ko aka sakawa dutse aka daddaka. Subhanallahi Mama ta furta ni kuma na risina a gurin ina kallon wayar ina jin kamar na fasa kuka tuni idona suka cika da kwalla, har ga Allah na tsani na rasa wani abun da na ke matukar so ko yake da muhimmancin sosai a rayuwata, na san phone ce amman ina jin babu dadi domin samun irinta a yanzu ba abu mai sauki a gareni a lokacin da na ke gidanmu dawainiya ta zata min yawa yanzu fiye da, ga kuma zuwan da Abdulhamid zai yi ban san abunda zai kawo shi ba wata kila ma baya son kowa ya san da zuwansa. “Ya akai wayar ta fadi?” Mama ta tambaya sai an amsa mata muryata na gargada alamar ina daf da fashe da kuka. “Ban sani ba Mama a hannu ta zame ta fadi” “Laa shikenan wayar Momy ta fashe bamu da wayar game” Namra ta fada tana wani bude baki, Abdallah kam ko dago kai be yi ya kalleni ba sai wasa yake da yatsun Amal kamar be san abunda ya faru ba. “Momy yanzu da wace wayar za mu rika game...?” Wani bakin haushi na ji ban san lokacin da na dakawa Namra wacce tai maganar tsawa ba. “Da wayar ubanki... ” Sai a lokaci Abdallah ya dago ya kalleni sai kuma ya kalli inda wayar take ba ce min komai ba sai dai fuskarsa ta nuna alamar bachin rai, mikewa yai tsaye yana saa dayan hannunsa a aljihu. “Mama ni zan tafi, kuma yaran nan a yi kokarin saka su makaranta domin barin su hakan nan ba zai yiyu ba ya kamata a san abun yi lokaci na ta tafiya” Wata uwar harara na watsa masa saboda haushinsa da na ke ji, wacce be san ma ina yi ba domin be kalli inda na ke ba da Mama yake ta maganarsa, ita kuma tana nanata masa cewar za a saka su makarantar, hannu ya saka aljihu ya ciro kudin da ban san ko nawa ne ba ya aje mata a hannun kujerar da take zaune sannan ya karaso inda na ke duke ina ta kallin wayar da na gagara tattarawa na kwashe ya ce. “Halimatuuu mu kwana lafiya” Har na yi kamar na bude baki na aika masa da bakar magana sai kuma wata zuciyar ta hanani ganin a gaban Mama ne da kuma yara. Tare ya fita da Amal da Namra Aiman ma ya bi bayansa. “Halimatu kina jin yana miki sai da safe amman kika gagara karba mishi miye haka?” Mama ta fada cikin yanayin damuwa da rashin amsa masa da ban yi ba. “Mama ba ki kohi yai min wayar ta fadi ta fashe ba” “Kohin zai saka waya ta fadi har ta fashe? Ai naga ko kallon ki be yi ba kuma ba wata maganar ta bacin rai kika masa ba balle ace, abu ne dai da Allah ya kawo” Ban sake cewa komai ba na tattara wayar na mike tsaye na nufi dakin Mama na zauna bakin gadonta kamar wacce aka kwashewa tunani a kwakwalwa, babu komai a raina sai bacin ran faduwar wayata, ina zaune a gurin yara suka shigo da yan dari biyar biyar a hannu wai Uncle Abdallah ya basu, ni dai ko kallonsu ban yi ba balle har na karbi kudin na adana musu saboda bakin haushin Abdallah da na ke ji. Ban yi dabarar na karbi wayar daya daga cikin yan matan gidanmu na kira Abdulhamid ba sai da aka sallame sallar isha'i, a lokacin kuma yan zaman majalisar kofar gida sun soma shimfida tabarsu su zauna. Idan ma nace zan yi magana da shi sai dai na koma ta kofar gidan makotan mu wanda hakan ba zai min dadi ba domin a hanya ne. Ban yi kasa a guiwa ba na karbi wayar Hafiza na lalabo number Abdulhamid a wayarta na aika masa da kira, kamar jira yake a take tai picking din call din yana rangadamin sallama, bayan na amsa na koro masa da bayanin wayata ta fadi har ta fashe. “Oh ni na dauka ko kashe wayar ki kai, domin nata kira ban samu ba” “Wallahi faduwa tai ta fashe screen din ma ya watse gaba daya” “Subhanallahi garin ya?” “Ba zan iya fada ba, ni dai kawai tana hannuna ta subuce ta fadi kasa, ka zo ne?” “Na zo, sai dai ban karaso kofar gida ba saboda bana son kowa ya san da zuwana, dan ki kawai na zo” “Ka tafi ko kana nan?” “Na tafi amman na fi karfin one hour a gurin kamin na tafi” “Ayyah ban jidadi ba” “Karki damu zan shigo gobe In-Sha-Allah” “To Allah ya kai mu” “Amin mu kwana lafiya” Ba bari na sake cewa komai ba ya katse kiran, ni kuma na sauke wayar ina ta tunanin abunda zai kawo shi gurina ni kadai, wata kila kum zai yi min jajen abunda ya faru ne ko kuma ya bani wata shawarar, ban raba dayan biyu ba Hafiza ta shigo dakin na mika mata wayarta bayan n goge call din domin Bana son ta san da wanda nai wayar. Sai kuma na nufi inda jakata take na bude na dauko dubu biyu saboda ina son siyo man goge baki da Vaseline din mu daya kare. Hijabina na saka ina Kwalawa Namra kira ta zo ta raka domin ta fi sauran natsuwa da abun hankali, sai dai duk yadda nai ta noke noken na fita ni kadai ban samu sa'a ba har sai da Amal ta gan ni ta biyo da gudu tana kuka, a dole na tsaya na rika hannunta sannan na nufi dakin Mama na shaida mata cewar zan je shagon titi na siyo man shafawa da kuma na wanke baki. “Ba zaki aika kanenki si siyo miki ba?” “Ina son fitar ne Mama” “To Allah ya tsare” Na amsa da amin sannan na kama hanya ina rike da hannu Amal Namra kuma na gefena na hagu dukansu suna sanye da riga da wando ne yan kanti. Cikin tsananin kunya na ratsa kofar gidanmu na wuce saboda taron da maza yan zaman majalis sukai yi. Wanda na san a nan ma ba zan rasa wanda zai yi gulma ta ba, koma na ce gulmarmu yan gidan gaba daya domin mun tara yan mata Masha-Allah, wanenda aka dade ana zancen wai mai kudi suke jira wasu kuma tuni suka fara yi kanena zargin masu nemansu duk na neman auren suke zuwa ba iskanci ne kawai ke kawo su, ni kuma na dade da yin zurfi wajen sanin cewar aure da haihuwa da mutuwa da rayuwa duka na Ubangijin Annabi Adamuna, wato Allah S W T wanda ke rubutowa bawa abunda zai same shi tun gaban bawa ya zo duniya. Lokuta da dama kan jarabi bawa da abu ba dan Allah baya son bawan ba sai dan gwada karfin imaninsa da kuma aikinsa. Idan na tuna mahaifina da mahaifiyata ina samun kaina a cikin wani kogo mai cike da tausayinsu musamman ubana wanda na san shi mutane za su zaga, kuma shi zai fi kowa shiga damuwa, domin bayan yan dakin Mama akwai na dakin Inna waenda sukansu yan mata ne da suka kasance a karkashin inuwarsa. Gashi lafiyar kafafuwa ma bata wadace shi ba. “Momy a nan za mu yi ta zama? Daddyn ba zai zo ba?” Maganar da Namra tai ka katse min zancen zuci da na dade da yin zurfi a cikinsa, gabana ya fadi ba faduwa ta tsoro ko fargaba ba, ba faduwa ta irin amsar da zan bata ba, ko kuma abunda zan mata ta fahimta ba, faduwa dai irin ta ko wace uwa mai yayana yana daya daga cikin dalilin daya hana ni fitowa a gidan Aminu gudun irin rayuwar da yayana za su yi idan bana gidan, sai dai kuma yanzu da suke hanuna kuma ya rufe idonsa daga kallonsu balle waiwayarsu ya rayuwarsu zata kasance? Mama tana yawan fada min ba ko wane namiji ne zai auri da yayana ba, idan ma ya aure ni ba zai yarda na zauna da su ba, anya idan na bar su a gida za su samu kulawar da nake musu fatan samu? Ya makomarsu zata kasance lallai juma'ar da za tai kyau tun daga laraba ake gane ta, indai har yau ba tai musu kyau ba ya gobensu kenan? “Momy ga fa shagon can, ko ba shagon Takur ba?” Namra ta fada tana girgiza hijab dina, wani irin numfashi naja na sauke hawayen kam tuni suke wanke min fuska sai dai ban fahimci hakan ba sai da Namra tai min magana ganin ina kokarin wuce shagon da ban san mun kawo ba sai yanzu. “Eh shi” Na fada ina share hawayena sannan na karasa gurin shago, sai da ya sallami duka mutanen da suke gabana sannan na mika nawa kudin na fada masa abunda za a bani ya mikon na siya ma Amal da Namra biscuit na rike biyu domin na san indai Adnan da Aiman sun gani sai sun tambaya ina na su? Bayan na karbi canji na juyo tare da yarana muka kamo hanyar dawowa gida. Tunanin dai na dazun ya sake fado min a rai, har na kasa fahimtar shi Aminu ya yafe min su ne gaba daya hakan ya saka ya kwashe har wata daya ba kira ba aike ko kuwa yana jira sai su kara girma ne ya karbe su? Karar qaraurawar keke na ji kamin na yi kokarin kauchewa tuni keken ta bugeni ni kuma na gibi Namra ni da wadanda suke kan keken muna fadi kasa, saurin tashi nai cike da kunya Allah ma ya tsare ba mutane sosai a gurin da na ji kunya kam. Mutumen da ke rike da keken yayi saurin karaso inda na ke ya daga Namra yana kabe mata jikinta tare da rika fuskarta. “Cutest ba ki ji ciwo ba?” Ta gyada masa kai, Amal kam da gudu taje ta dauke chocolate din da ya fadi a gurin dawo inda nake da gudu ta boya. “Daddy wacan yar yarinyar ta dauke min chocolate dina wanda ban fasa ba” Wata yar karamar yarinya ce maganar wacce bata wuce sa'ar Adnan ba, kananan kayana a jikina sai dan kwalin atamfa da aka daura mata, a kusa da ita wata matashiyar mace ce tana sanye da abaya wacce na ke kyautata zaton budurwa ce ganin jikinta babu mayafi sai hula mai kyau sai kyalli take kamar an watsa mata kananan taurari a jiki. “Sannu....” Ta fada tana dan kawarda fuska kamar tana jin kunya ta. “Muna ta miki horn amman baki ji ba, har Daddy ya kade ki” Yarinyar ta fada ita tana kallona. “Ko kuma ku baku lura ba? A hanyar nan ba dan keke kawai akai ta, at least tun da kun gan ni agefen hanya ai sai ku koma tsakiyar hanyar ku wuce” Na fada da dan fusata domin har ga Allah na ji haushi kuma ba da yarinyar na ke ba da mahaifinta nake. “Hey cutest hold this for your Mom” Da murmushi ya mikawa Namra ledar da ta subuce daga hannuna ta fadi bayan ya kwashe kayan ciki ya saka a ledar. Ni kan ko kallona be yi ba ya nufi inda kekensa take irin kenan nan ce mai tsada sosai ya tashi keken, dogon jeans ne a jikinsa sai yar vest fara ya daure jacket dinsa a kunkurunsa, kana ganinsa ka san irin mazan nan ne marasa kunya domin namiji mai kunya ba zai biyo hanya da vest ba duk dai ban san inda suka fito ba, sai da ya hau keken sannan na daga yarinyar da ke kiransa da Daddy ya dora ta daga gaban keken. “Kin ga yarinyar ta dauke min chocolate kuma mug dina ya fadi? Sai ya kenan?” Yarinyar ta fada yana nuna inda Mug din yake sai a lokacin na lura da mug din, da alama yarinyar irin yaran nan masu shegen kodin tsiya da tsiwa, domin har wani juya ido take tana motsa baki kamar wata babba. Babbar kuma wacce ta fi tsananin kama da shi ta hau baya tana dago min hannu. “Bye..... ” Ikon Allah su kuma haka suke? Sun buge ni ko sannu babu? Ko ma miya tsayar da ni kallonsu oho, daman can da ganinsu ai ba gidan mutunci suka fito ba. Ni kadai nake ta mita ta a cikin raina har muka iso gida, sannan na karbe chocolate din da Amal ta dauka na yarinyar na jefar, babu irin kukan da ba tai ba na ki na kulata har ta gaji tai bachi. Washe gari bayan mun gama karyawa na fara shirin zuwa aikina, kanwata Husna ta shigo wai na zo falon Mama ana kirana, ta gwarin guiwata na nufi falon Mama ance karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da ka aikata, na shiga falon da rabon ido dan ganin mai kirana sai naga Mama ce kadai a falon hannunta rike da farar leda mai rubutu da zanen wayoyi a jiki. “Mama ke kike kirana?” “Aa Abdulhamid ne yana waje saka hijabinki ki masa godiya waya ya kawo yace a baki” Ta amsa min cikin rashin jindadi da walwala. Dakinta na shiga na dauko hijabi na nufi kofar gidan. Sai na same shi cikin farar motarsa zaune yana danna wayarsa, farin gilashin motar na kwankwasa da zimmar ya bude min na gaishe shi kuma nai masa godiya sai na ga ya miko hannunsa daga can cikin motar ya bude min motar da alama so yake na shiga ciki na zauna. Haka kuwa akai na shiga uncomfortable na zauna sannan na mika masa gaisuwa be amsa min ba kuma be kalleshi ba har lokacin taba wayarsa yake. “Yau ba zaki je aiki ba ne?” “Zanje ina cikin ne aka ce kana kirana” Sai a lokacin ya dago ya kalleshi a natse. To je ki karasa shirinki sai na kai ki. Kallonsa nai har na bude baki na ce masa a a sai kuma na tuna da abunda ya faru da ni a lokacin da nai gardama da Abdallah ban sani ba shi ma ko yana da kohin kar ya min na kasa samun abun hawa. “To by the way na ga waya na gode sosai” “No no no never mind je ki shirya kawai” Ya fada yana dauke idonsa daga barin kallona, ni kuma na fita daga motar na shiga cikin gidan na karasa shirina sannan na shiga falon Mama dan mata sallama kuma n karbi wayar da har yanzu bana jin murnar siya min ita da yai. Wani kallo tuhuma Mama tai min sai duk na ji babu dadi a take shikan shikan rashin natsuwa suka bayyana a jikina da kuma fuskata. “Ina kyautata zaton Abdulhamid be san Abdallah na zuwa gidan nan ba, kamar yadda yau din ma nake kyautata zaton Abdallah be san Abdulhamid ya zo ba, sai dai ke kin sani kuma ina tunanin kin san daidai da rashinsa, na dade da fahimtar cewar Abdallah yana son ki ko dan saboda kulawar da yake nunawa yaran nan, sai dai abunda ban sani ba kuma nake son sani a yanzu shi ma Abdulhamid son ki yake yi?” I find it so difficult na amsa mata, ni kaina a yanzu ban sani ba iyakar abunda na sani Abdallah na so ko be fada min ba ya nuna min balle kuma ya fada min tun a lokacin da igiyar auren Aminu take kaina, ba zan iya shaidar abunda ya kawo Abdulhamid a yau ba, domin bana da tabbaci yana so na har yanzu kamar yadda zuciyata ya kasa goge shi a raina, ko kuwa dai tausayine kawai a tsakaninmu. “Dukansu yan'uwna junane Halimatu kin sani, bayan yan'uwanta ta jini ma su tagwaye ni a ciki daya suka fito a rana daya kuma a mahaifa daya, mace daya ta raine su uba daya ya haife su, karki aikata abunda zai zame mana matsala ni da mahaifinki domin uwar data haifi mahaifinki ita ce ta haifi mahaifin Abdallah, mahaifin Abdallah da mahaifinki uwa daya uba daya suke karki lalata alaka Halimatu” “Ban kira Abdallah na ce ya zo nan, zuwan Abdulhamid a yau ma bana da masaniya sai da na ganshi” “Ba shi nake kokarin fahimtar da ke ba, ki sallami daya daga cikinsu saboda gudun abunda zai iya faruwa a gobenki, idan kuma dukansu ba ki ra'ayinsu to ki sallame su duka shi ya fi alheri Allah ya tsare a dawo lafiya” Ya miko min ledar sannan ta mike tsaye ta fice ta bar a falon tsaye, ji nai kamar a san saka gatari an sare duk wata gaba ta kuzari da ke jikina. Kamar wata marar lakka haka na fito daga cikin gidan na nufi inda motarsa take na bude na shiga shi kuma ya tashi motar muka hau hanya. “Ban jajanta miki kan abunda ya faru ba, na yi hakan ne saboda na baki lokaci ki huce bacin ranki, kuma bana son wata magana ta shiga tsakanina da ke a lokacin da kike idda, ko da ko gaisuwa ce, amman yanzu ina jin I'm free to name what ever i want daga gareki saboda kina da yanci” Ban ce masa komai ba ina ta kokarin maida hankalina gurin titi amman na kasa, magaganun Mama sun tsaya min a kai. “Ban jidadin abunda ya faru ba, Aminu kuma be yi miki hallaci ba amman mai hakuri yana tare da nasara, kuma kansa yai ma na san wata rana zai yi nadama ya gane cewar yayi kuskure a lokacin da ke din kin masa nisa” Still ban ce masa kuma ba, hakan kuma be hana shi cigaba da magana ba. “Jarabawa ce ta rayuwa, you know wani lokacin Allah yana jarraba bayinsa da abubuwa daban dabam, kamar yadda ya jarrabe ki da miji kamar Aminu ni kuma ya jarabe ni da cutar da na kasa samun maganinta har yanzu, wanda hakan yasa har bana son kawo tunanin aure a rayuwata....” Juyowa nai na kalleshi a take zuciyata ta cika da tausayinsa. “A da na sadakar na cire rai daga samun lafiya, kuma na aje duk wani abu na neman magani, amman daga lokacin da na ji cewar Aminu ya sake ki sai na nemi duk wannan abun na rasa, na ji cewar a yanzu ya dace na nemi magani kuma na nemi aurenki ko da ba za ki so ni ba, ba dan komai ba sai dan na faranta miki kuma na cika burina a kanki, ban sani ba ko akwai soyayyar Abdulhamid a zuciyar Halimatu ko a a, idan ma babu zan yi kokarin samawa idan kuma akwai sai na kafafata na ingantata” Ya karasa daidai lokacin da ya faka motarsa a ma'aikatarmu sai ya zauna daidai yana dubana da fuskarsa ta tausayi. “Na san za ki mamaki jin irin wannan maganar daga bakina kai tsaye kuma a karon farko da na ziyarce ki, daman abunda na ke son mu tattauna kenan a jiya, saboda ina son nai mata sha daya ne idan ma hadiye zuciya zan yi na mutu na san makomata idan kuma dama za ki ba ni nan ma na san makomata, ni dai har gobe ina son ki Halimatu kuma ina alakanta abunda Aminu yai miki da rashin aurenki da nai ta hanyar kin yarda da shawararki ta cewar na aureki na cigaba da neman magani za ki yi hakuri da ni a haka, ko kuma ki jira ni na nemi magani amman duka na ki yarda, na san da cewar Allah ta rubuto hakan zai faru amman komai yana da sila....” Jimmm nai na dan wasu mintuna sannan na ya cigaba. “Wata kila zuciyarki ta raya miki cewar na cika son kai a yanzu ko? Kina da gaskiya ba ko wace mace ce zata auri namiji irina ba, shiyasa ban gwada neman kowa ba sai ke ban taba saka son wata mace a raina ba sai ke kuma har gobe ke ce a raina Halimatu, zan iya baki damar yin shawara matukar kika ji za ki iya aurena a haka, ko kuma ki jira har na samu lafiya zan fi kowa farinciki, idan kuma kika ji ba za ki iya ba nan ma ba zan zarge ki ba.... ” “Zan shiga office na gode” Shine kawai abunda na fada na share hawayen da suka fara min zuba tun a lokacin daya fara maganar....... Anya Halimatu zata iya zabe tsakanin dan'uwa da dan'uwa? Anya zata iya zaba tsakanin mutuwa da rayuwa? Domin auren namiji irin Abdulhamid mutuwa da rayuwa ne. A ganinku waya dace ta zaba? Ina labarin Aminu ne? Ko ya Kabir yake? Shi kuma Abdallah haka yake da an bata masa rai sai kohi 🤣🤔 #TeamAminu #TeamAbdulhami #TeamAbdallah #TeamHalimatu #ZawarcinHalimatu #Gobena 7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 1️⃣4️⃣ A bakin gate din gidan ya tsaya da kekan Namra da ke gaban keken ta sauka, sannan Barra ta sauka suka nufi yar karamar kofar gate din sukai knocked mai gadin ya bude musu suka shiga sannan ya budewa Ahmad gate din gaba daya ya shiga da keken ciki. Katon gida ne plate mai dauke da shuke shuke gaban gidan kamar bayansa yake domin za kai tai kallon fuskar gidan amman ka gagara gane kofar shiga har sai idan an nuna kama ka, daga fentin kofar har fentin gidan har mayan motocin da ke harabar gidan duka farare ne tasss, irin farincikin nan mai burgewa da dare da rana kuma ya kawata maka ido idan kuma ya hadu da hasken rana sai ka dauka ba a Nigeria kake ba. Bangaren da aka faka motocin ya nufa ya sauka daga kan keken ya kai hannunsa ya bude gareji ya saka keken ciki sannan ya maida garejin ya rufe, sannan ya soma tafiya cikin wani irin taku da ba na sarauta ba kuma bana kasaita ko ci da kai ba, sai dai duk wanda zai kalli yadda yake dora kafarsa a kasa zai yi tsammanin tausayin kasar yake ko kyamarta, wata kila ma a iya fassarashi da mai nuna isa da dagawa. Zagayawa yai can baya inda ya sama kamar dabam da gidan kofarsa ma a can baya take, tun kan ya karasa ya saka hannunsa ya kwance daurin jacket din dake kugunsa, sannan ya kai hannunsa ya tura kofar ya shiga. Sanyin ac ne da hasken garin gulub tare da dadadden kamshi suka fara masa lale marhabun, katuwar plasma kuma na ta aikinta, remote ne farkon abunda ya fara dauka ya canja channel din daga Al Jazeera zuwa Tvc news. Sannan ya nufi hanyar dakinsayana shiga ya rana jikinsa da tufafin da ke jikin nasa ya daura tawul, a take farin fatar jikinsa da siffarsa ta zati ta bayyana, cikin wani irin ya na saka su a washing machine sannan ya shiga ya bawa jikinsa hakkinsa sai da ya tabbatar komai na jikinsaya wanku sannan ya fito ya shirya cikin wata farar shadda mai kyau da haske zanen jikin shaddar ma abun kallo ne balle kuma aikin da ke jikinta. Wani tsadden turare ya dauko ya saka bayan ya saka wani a cikin jikinsa da vest din da zai saka. Murmushi yai yana kallon kansa a madubi, shi kansa ya san yayi kyau balle kuma da ya dora hular da ta dace da shaddar. Sajen fuskarsa ya kwanta gwanin sha'awa har wani shining yake. Wallet dinsa ta fara ziyartar aljihunsa kamin makulin mota da sababin kudade su biyo baya, sannan ya dauki agogon hannunsa ya saka, for the second time ya sake duba kansa agaban katon madubin da ke dakin madubi da mutun zai iya ganin har kasansa da takalminsa. Cike da annshuwa ya fito daga dakin zuwa falonsa sai ya duba agogon hannunsa sannan ya zauna a saman manyan cushion din ya kalli labarai na yan mutuna kamar mai jiran ciron lokaci domin tsadadden agogon hannunsa na nuna 9pm ya mike tsaye ba tare da ya kashe tv ba ya fice daga falon. Bangaren mahaifiyarsa ya nufa wacce ta zame masa dole a duk lokacin da zai fita ko da zuwa nan da kofar gida ne sai ya sanar mata, hakan ya saka cousins dinsa da yan'uwansa and friends suke kiransa da Mommy's Boy domin har time take ba shi na fita da dawowa matukar ba aiki zaije ba ko wani lalurar na dabam wanda ita ma kanta ta san mai muhimmanci ne, duk da kasancewarsa ya girma har ya haifi ya mace yar shekara tara bata daina masa haka ba, shi kansa ya saba abun ya bi masa jiki idan ya fita be sanar da ita ba sai ya ji kamar ya aikata wani babban zunubi, ita ce abokiyar shawararsa kuma abokiyarsa domin komai zai yi sai ya sanar mata ko da ko abun be taka kara ya karya ba, hakan yasa take sanin ko wane sirrin na zamantakewar aurensu, domin a cikin dabi'un daya sabunta da su a gurinta ko dankwali ya siyawa matarsa sai ya siya mata kuma sai ya fada mata tun kamin ya siya din, idan kuma ya siyo zai kawo mata ta fara gani ta zaba ko ta canja masa tukuna ya kaiwa matarsa. Ya shiga falon da fuskarsa da annuri kamar sabon ango, daman can yana da irin fuskar nan ta samarin aljanna wadanda zaka gansu kullum fuskarsu kamar suna murmushi ko da kuwa ba murmushin sukai ba ga haske fuska da haiba, ga natsuwa da kwarji kamar wani Zaki. Hakimce take saman kujera sanye da wata holland yar ubansu wuyanta ya ji zinari kamar yadda hannunta ke amsa amo a ko wane motsi da tai, kallo daya za kai mata ka karanci sifofin da ke fuskar mahaifiyar sune a fuskar dan, kamanni na hanci baki da kuma ido a siffa da sura da hallita irin ta da'namiji kuma Ahmad Gwarzo kamar yadda mahaifiyarsa take kiransa. “Momy barka da dare.... ” Ta juyo cike da isa tana kallonsa, irin kallon nan na farinciki da kaunar uwa ta ga danta. “Barka da Gwarzo irin wannan shiri haka ina zuwa?” “Zance zanje mana Mom” A yayinda kalmar zancen ta dira a dodon kunnenta sai ta za me mata kamar wata mummunar kalamar marar dadin jin, annushuwa da ke fuskarta ta sai ta gushe murmushin kamar na dole. Dauke kai tai kamar ba ita ya bawa amsar ba ta maida dubanta gurin plasma. “Bari na je kai na saba alkawari tace na zo 9” Ya fada yana shirin juya daman can tun da ya shigo be zauna ba. “Karka wuce 10pm” Ta fada bayan ta kalli agogon zinarin da ke jikinta fuskarta babu alamun wasa. Juyowa yai kamar zai ce wani abu sai kuma yai murmushi ya juya ya fice. Ita kuma ta bishi da kallo tana jin kamar ta hana shi tafiya zancen, Hajiya Uwani irin iyayen nan ne da ke kishin matan yayansu musamman Gwarzo da bata hada shi da kowa ba a duniya, ba tun ba ta saba kashe masa aure ta kan saka shi ya saki matarsa idan zamanta a gidan be mata ba ko ma ta sake ta da kanta wani lokaci, wasu matan ma da kansu suke neman fita idan suka ga matsuwar ta musu yawa, ba dan kuma babu arzikin ki akwai shi har na zubarwa amman haka take bi ta takurwa matan da Ahmad Garba Gwarzo yake aurowa har sai ta fitar da su a gidan, Hajiya Uwani na da wani irin hali da ba san mutanen Kano da shi ko ma na ce mutanen Gwarzo domin daga ida har mijinta yan asalin karamar hukumar Gwarzo ne, wannan dalilin ya saka daga abokan Ahmad har ita kanta Momy da duka familynsu suke kiran dan nata da Gwarzo. Juwuriyya ce mace ta tara da Ahmad ya aura kuma ita ce mace da ta jajirce a wajen zama da shi har tai nasarar haifa masa ya mace wato Namra, duk kuwa da irin kin son haihuwar da Hajiya Uwani take yi, ta jure duk wani cin zarafi da muguwa daga uwar mijinta saboda kawai ta zauna da Ahmad, kuma ta zauna da shi ra rayu da shi na tsawon shekara biyar kamin tai hadarin mota ta rasu. Hajiya uwa bata yarda danta ya cire kudi mai yawa da sunan yi ma mace hidima idan ma yayi ta kan rage tace ta yi yawa, haka ta ke juya duk matan da Ahmad take aure kamar waina tana kishin matan Ahmad sosai. Latest Benz ya shiga White color daman duk motocin da suke gidan farare ne, sai dai kawai sunanyensu da kudinsu su banbanta, tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate ya fisge motar kamar domin shi kawai akai titin GRA ring road. in time ya isa kofar gidan Alhaji Yunusa Dan-Gaske, kamin ya danna horn ya ka kai hannunsa ya dauki iPhone dinsa da ke cikin motar ya kira Zainab. “Hello Ina kofar gidan” Ya fada kamar wani dan sarki sannan ya danna horn aka bude masa gate din ya kunna kai a harabar gidan.. HALIMATU POV. *Bayan sati biyu...* Sati daya nai ina raya ko wane dare da sallah da salatin Annabi, na mikawa Allah zabina a tsakanin zama a gida nan ba tare da aure ba da kuma yin auren, domin ni ba dan Abdulhamid ba da ban kawo maganar aure a kusa ba, a da na yi planning akan na cigaba da aikina na rike yayana har zuwa wani lokacin domin ban shirya fuskantar wani kalulen zaman aure ba a yanzu saboda wahalar da na sha a gidan Aminu, sai dai yadda Mama da Inna suka tsaya kai ta fata wajen ganin na cire wannan burin a raina yasa na sassautawa kaina, ga kuma rokon Allah da nai sai ya saka min son auren a raina fiye da lokacin da nakr budurwa ma. Na roki Allah ya zaba min a tsakanin yin auren a yanzu da kuma hakura da auren har na wani lokaci, amman ban roki Allah ya zaba min a tsakanin yan uwa guda biyu ba wato Abdallah da Abdulhamid, a iya ganina da fahimta Abdulhamid ya fi Abdallah cancantar aure a yanzu domin shi be taba auren ba gaba daya a rayuwarsa, kuma ni ya so tun a lokacin da nake budurwa yanzu kuma da auren ya mutu ya dawo min. Ko ba komai ya hade kwadayinsa na furta min kalmar so ko cancantar zama da Aminu be taba fadin wata mummanar kalma akan Aminu ba, duk kuwa da irin sanin da yai na irin zamantakewar auren da muke da halayensa, be taba daga waya ya kira ya fada min wani abun marar dadin ji ba, idan har ya kirani sai idan wani babbab dalilin ne ko kuma idan mun gadu da shi a gida. Tsabanin Abdallah da yake yawan fada min abubuwan da Aminu yake aikatawa a waje bayan yabon surata da yake da nuna yana sona tun daga lokacin da ya dawo daga kasarsa ya saka ni a idonsa. Wani lokacin har mamakin yadda Abdallah yake min wasu abubuwan na ke domin an tabbatar da ace shi ne a matsayin Abdulhamid da ya so ni tun ina budurwa da Allah kadai ya san irin chabar da za ayi. Na fi jin natsuwa da Abdulhamid fiye da Abdallah, wata kila saboda zuciyata ta taba son sa ne, ko kuwa dan ina tausayinsa ne oho, ga shi ya dage sai kai kawo yake, domin idan be zo yau ba, to zai zo gobe tun ina fargabar kar wata rana Abdallah ya tarar da shi har na daina, ko da yake Abdallah ma tun daga wacan ranar da ya min koho wayata ta fashe be sake dawowa gidan ba, kuma be sake gwada kiran sabuwar wayar da Abdulhamid ya siya min ba, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin ya bani damar sakewa da kula Abdulhamid a duk lokacin da yai min sallama. Ta wani bangaren kuma ina yabon Abdallah sama da Abdulhamid, domin shi mutum ne mai son yara ko na ce mutum ne mai son yayana tsabanin Abdulhamid da ko fuska baya sake musu daman can kowa ya sani Abdulhamid ba a mutum ne mai son yara ba, sai dai ban dauka har da nawa ba ganin kamar ni din ta dabam ce a gurinsa. Yes yana nuna min so da kulawa irin wadanda na rasa a gidan Aminu, shi tun a yanzu ya fara nuna min su sai dai a duk lokacin da muke waya be taba cewa ya yarana ko ya gaishesu balle kuma har ya riko musu wani abun taba. Ba kamar Abdallah ba da har saman jikinsa suke hawa su karbi wayarsa su yi game, rashin sakewa da yarana yana daya daga cikin abunda yake daga min hankalin bayan maganar daina aikina da yai min idan har na amince zan aurenshi. Ya nuna min cewar shi yana da kishin da ba zai iya barina nai aiki ba, kuma yana da halin da zai iya dauke min komai, daga lokacin da yai maganar daina aikina zuwa yau na kasa yanke hukunci kuma na kasa zaba na kasa shawara da kowa, ba dan komai ba sai dan na san duk wanda zai shawarce ni zai ce na daina aikin na yi zaman aure. Na san dole ne Abdulhamid ya ji tsoron naje nai aiki saboda kar na hadu da wani namijin ya burge shi bayan shi baya iya komai, wai da gasken ne baya iya komai din ko kuwa dai gwadani yake ya ga idan zan iya zama da shi? Ko kuma karfin soyayyar da nake masa? Ni dai na san ba dan soyayya kawai zan aure shi ba har da tausayin halin da ya samu kansa wanda na so yin wannan jihadin tun a baya. Yana yawa fada min sai na ji na ki ji, saboda za ayi ta kananna maganganun akan mu, ganin ni bazarawa ce har da yaya hudu shi kuma saurayi, ko da yake ba irin yaran samarin nan ba ne irin tazuran nan ne da suka dade ba su yi aure ba, amman duk da hakan na san sai yi magana, ban kawo zancen rashin lafiyarsa ba saboda na san ba kowa da ya san da matsalar ba. *** *** *** Yau dai na yanke shawara ba zan je aiki ba sai na sake gwada nemawa yarana wata makarantar ko Allah zai saka a dace idan kohin Abdallah ya janye daga jikinsu ko kuma jikina zance tun da ni ce mahaifiyarsu kuma ni ce sila. A Napep na saka su muka kama hanyar Gwarzo International School, babbar makaranta ce da babu irinta a garin Gusau makaranta ce da ta amsa sunan makaranta kamar yadda na ke jin ana fada babu kamar dalibansu, sai dai makaranta ce mai tsada sosai ba kowa ke iya saka yaransa a makaranta ba saboda kudin da ake kashewa. Ni kaina na san ba lallai na iya jurar biya musu kudin ba, zan dai gwada ne kawai idan an karbe su sun fara karatun sai na canja musu ni dai burina kohin da Abdallah yai mana ya karye kawai. A lokacin da mai napep din ya faka bakin gate din makarantar na ji wani iri ganin irin manyan motocin da ke kawo yaran makarantar. Sai dai ban yi kasa a guiwa na biya mai Napep din kudinsa na kama hannun yarana muka nufi cikin makarantar, wani abun da zai kara burgeka da makarantar yadda aka tsaurara tsaro domin sai da aka gama bincikamu sannan aka bar mu muka wuce a nan na soma ganin malaman makarantar har da turawa. Da tambaya na isa office din principal din dake can hawa na biyu, office ne da aka kawata shi da kayan alatu kamar ba a cikin scul ba, guri na samu na zauna daman tun kan na shigo office din sun fada min cewar yana gurin Assembly. Su Namra suka zauna a a doguwar kujerar da ke kusa da kofa ni kuma na zauna a kujerar da ke kallon teburin principal din. Bayan kamar minti goma zuwa shabiyar aka turo kofar office din aka shigo. Mutumen nan ne da ya kade ni da kekensa yana rike da hannun yarinyar da wacce ta sha kitso mai kyau kuma take tsananin kama da shi, shadda ce a jikinsa ita kuma tana sanye da uniform din makaranta dan guntun skirt ne blue da farar riga sai takalmin makaranta da Scul bag a bayanta mahaifinta, sai wani babbata fuska take da alama wani abun akai mata shi kuma yana ta sham kamshi sai kace wani hege😏 Ni dai kallo daya nai musu daga shi yar sagartacciyar yar tasa na dauke kai shi ko kallon inda muke ma be yi ba. “Ke tashi ta zauna...” Fuskata na gabas na jiyo munafukar muryarsa yana yi ma Namra magana wai ta sauka ta bawa yarsa guri ta zauna, juyo nai ina masa kallo uku saura kwata na dakartar da Namra da ke kokarin tashi ta bar yar tasa guri... “Ke karki tashi, ai da be fi da ba yadda ka kawo yarka a makaranta haka na kawo tawa, dan haka ba zata sauka daga kujera ba tun da kujerar makaranta ce ba da gidan kowa ba” Yadda kasan ina fada da mutum mutume haka yai min, yana ta lasa wayarsa kamar ba da shi na ke magana ba, ni ma haushi na ji na bawa banza ajiyarsa ina gyara gyalen abayata dake kaina. Muna haka principal din ya shigo, wani abun da zai baka haushi yana ganin mutumen ya fara rawar jiki da shi har da janyo masa kujerarsa ya zauna. “Ai na san abunda ya kawo ka ranka ya dade daman na san sai Karamar Hajiya ta tsokano mana kai” Principal din ya fada yana ta washe hauro, da alama dai wannan mutumen yana dan ba shi lashi ne shiyasa ya ke ta masa far'a yana yin kamar be gam mu ba. “Karamar Hajiya tace kun dake ta” “Wallahi ranka ya dade bulala biyu ne kawai akai mata ita da yarinyar da sukai fadan” “Amman kasab ka'idar makarantar nan ba a duka? Then why za ku dake su daga ita har wacan yarinyar?” “A yi hakuri ranka ya dade dan horo ne kawai ba wai wani abun ba” “To wannan dai ya zama na karshe” “In-Sha-Allah ranka ya dade In-Sha-Allah” “Hajiyata wuce class kinji” Yarinyar ta dan bata fuska. “Daddy baka ba ni komai ba” “Kin san ai bana baki kudi” “Daddy pls” Sai kawai ta saka kuka, tsawa ya daka da alama kuma tana tsoron fushinsa ba shiri ta ranta a cikin na kare ta fice daga office din. Sai ta fice sannan principal din ya kalleni. “Hajiya lafiya dai?” “Yarana na kawo ina son na saka su a makarantar nan” “Su duka? Ina mahaifinsu yake?” Na dan yi shiru na dakiku kamin na amsa masa. “Baya kusa shi ya ce na kawo su” “A ka'idar makarantar nan maza suke kawo yara ba mata ba, sannan ba ma karbar yara a irin wannan lokacin saboda an yi nisa da karatu ko wane aji akwai adadin dalibin da ake bukata” “Dan Allah ku taimaka min zan biya kudin makarantar ko nawa ne In-Sha-Allah” “Zancen biyan kudin makaranta ai wajibi ne, taimakon ne dai ba zai yi yu ba yanzu” Rasa nai abunda zan sake ce masa sai na bata fuska kamar mai shirin yin kuka. “Miya hana su karatu da wuri?” Mutumen ya tsomo min baki a magana yana kallon yarana. “Canja musu za ayi” Na bashi amsa kamar an min dole. “Saboda mi za a canja musu scul din? Kuma kika kawo su a wannan makarantar” “Ra'ayi” Na fada ina mikewa tsaye cike da fusata sai a lokacin ya kalleni domin duk maganar da yake su yake kallo ba ni ba. “Ya ana magana za ki tashi kuma kika sani ko a taimaka miki... ” “Bayan ka ce babu a taimakon da zaka iya yi mana? Sai ka ce mu ba kudin za mu biya ba ai kyauta na roka ba, kuma ba wannan ce kawai makaranta ba” Principal din ya fada, ni kuma na bashi amsa a fusace domin har ga Allah na ji haushi wato saboda ya ga alamar mu ba masu arziki ne kamar wannan ba shine zai wani ce a tainaka mana tun da ya saka ba ki bayan farko ya fada mana ba wani taimako, irin wannan makarantar ma ko yaran ka sun yi karatu aciki wulakanta ka za ayi da yaran. Har principal din ya bude baki yai magana sai mutumen ya daga masa hannu yana lasa wayar da ta zame masa dole. Ni kuma na sako yarana a gaba muka baro makarantar cike da dana sanin zuwan da nai. 7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 1️⃣5️⃣ Sai da na sauke su gida sannan na wuce gurin aikina cikin damuwa, damuwar rashin karatunsu da kuma na abunda ya faru a makarantar yau. Na yi mamakin ganin wani a kujerarta mamakin ba dan kankane ba sai kuma tsoro ya biyo na soma rayawa a zuciyata ko sun kore ni ne kuma? Ko kuma wani abun ne? Ban cewa Emanuel komai ba balle kuma bakon mutumen kai tsaye na nufi office din oga Dahiru. Sai na fara knocked bayan ya ba ni izinin shiga na tura na shiga. Gaisuwa na fara mika masa a maimakon ya amsa min sai ya kai hannu ya dauki wayarsa ya shiga waya da wanda na ke zaton abokinsa ne domin yanayin firar da yake ya nuna haka, ina tsaye a gurin har yai wayar ya gama sannan ya kalleni da murmushi a fuskarsa kamar zai ce wani abu sai kuma ya mike tsaye ya zago inda na ke ua miko min hannu. “Congratulations kin hau matsayin Kabeer a yanzu kin samu karin mukami....” A tsakanin miko min hannunsa da yai da kuma sanarwar karin girman sai na rasa wanne yafi ba ni mamaki, miyasa za a kara min girma kai tsaye bayan akwai waenda suka fini cancantar hawa kujerar Kabir? Da wata manufa yai ko kuwa dai rabo ne ya koka kamar yadda na kowa yake kokawa? Ban ankaro ba na ji na rika hannun nawa yana shaking. “Congrats Dear” “Kabir fa?” Na tambaya bayan na yi saurin cire hannuna daga na shi, ina ta fargabar kar ace min ya mutu. Sai ya juya ya koma kujerarsa ya zauna ni kuma na bi shi da kallo. “Kabir ya samu tabin hankali, abun nan ya taba shi har cikin kwakwalwarsa, a yadda suka rubuto mana ma an tafi tashi lagos yanzu haka, bayan an bar Kaduna da shi” Tausayinsa ya kamani ni a lokacin da yake can yana rashin lafiya yana fama da kanshi a lokacin aka dauki position dinsa na aiki a aka ba ni, da ace ba ni ba ce da murna zan hau shi yayinda shi yake can hana fama da kansa. “Ku kuka cire shi daga aikin?” “Dole ne wannan ai Halimatu saboda kamfani ne ba aikin gobnati ba, ba za mu iya jiransa har ranar da ya warke ba, ko da ma ya warke ba za mu iya sake daukarsa aiki ba” Babu tantana idan na sake bude bakina kuka ne zai fito, hakan yasa ban sake ce masa komai ba na juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fito daga office din. “Halimatu....” Na ji kiransa bayan an fito daga office din, juyawa nai na koma cikin office din ba tare da na amsa ba, sai ya miko miko min wata takardar da ke tabbatar da zamana a position din, karasa nai cikin rashin kwarin guiwa na karba na fito. Na sake dawowa office din mu cike da damuwa ina zaunawa a kujerar da Kabir yake sai hawaye suka ce min sallamu alaikum, babu wani dan 'adam da za ayi ma bushara da karin girma a duniyar ya ji babu dadi sai ni da tawa kaddarar ta zo a haka, ba san abunda ya hanani sukuni da farinciki ba, na kasa samun jindadi da annashuwa, tun ina hawaye kadai har na koma yin kuka mai sauti, Emanuel ne yai ta ba ni hakuri amman sai na ji kamar yana horara min wutar kukan a zuciyata, bayan ko wace dakika biyar fuskar Kabir ce take min gizo, rayuwar da mukai a baya idan zai miko min wata takardar ko ya karba ko ya min wata maganar a cikin har da yawan murmushin da yake min, ina ta jin sautin muryarsa. Bar bar gurin aikin ba sai da na rubuta takardar resigned ba tare da neman shawarar kowa ba, a lokacin da na aje takadar a office din oga Dahiru baya ciki hakan ya bani damar ficewa ba tare da shan kai ba. Na isa gida da kumburarrin idanuwa saboda kukan da na yi a office, duk wanda ya kalleni ya san bana cikin walwala da nishadi, daga Babana har Mama ba su farinciki da aje aikin da nai ba, ba su fada min ba amman na gani a fuskarsu da kuma yanayin maganarsu. Allah yasa hakan shi ya fi alheri shine abunda suka fada min, ni kuma na amsa da min kamin na taso na baro musu dakin na dawo dakin da nake kwana cikin damuwa. Kwana biyu da faruwar hakan Abdulhamid ya turo magabatansa aka tsayar da magana, Baba be yi komai ba sai da amincewata kamar yadda shari'a ta shar'anta. An saka lokacin auren saba ga watan Rajab wato watan azumin tsofi. A daren ranar na kasa ganin walwala a fuskar Namra, tun kan nai maganar kanenna suka fara cewa kishi take ni kuwa na san ba kishi ba ne domin har yau Namra bata san cewa mahaifinta ya sake ni ba ita dai tana ta ga ya daina zuwa kuma ba mu koma gidansa ba, tun daga wacan lokacin da ta min maganarsa bata sake min ba, Namra ma ina ta san wani saki   balle ta kawo wani abu a ranta ko da yake yaran yanzu wayo ne da su ba kamar mu ba.   Ina daki ina fidda musu kayan bachi ta shigo ta kwanta saman katifar tana ta kallona kamar wata bakuwarta, ni kai na sai da kallon nata ya saka na tsargu duk kuwa da kasancewar karamar yarinya ce. “Namra minene?” Na tambaya ina dan murmushi da ban san ma ta ina ya samu hanyar fito min ba. “Momy aure za ki yi?” Na gyada mata kai ina karfafa ma kaina guiwa. “Daddy fa?” Na dan yi jimm kamin na amsa mata. “Namra mun rabu da Daddynki shiyasa na dawo nan gidan na zauna, shiyasa Daddynku ya zo ranar yana fada yana cewa sai an ba shi ku” “Ba za ki sake komawa gidan ba?” Na gyada mata kai. “Shi ma ba zai zo nan ba?” Nan ma na gyada mata kai, sai ta ɓata fuska kan ka ce kwabo hawaye sun fara mata zuba, janyota nai a jikina na rumgumeta ina rarrashinta. “Namra ai ba daina ganin Daddy za ku yi ba, za ku ganshi lokaci zuwa lokaci, ni kuma kuna nan tare da ni babu wata damuwa” Kuka tai sosai kamar wacce akai wa bushara da mutuwar ubanta ko tawa mutuwar har wani shidewa take numfashinta na yin sama, ni kaina ban san lokacin da na fara hawayen ba. Daga ni har ita muka kwana kamar marasa lafiya, na kasa farinciki da auren Abdulhamid da zan yi kuma na rasa na rasa dalilin hakan.    Washe garin ranar Abdallah ya sallamo gidanmu, a yawance ya shigo falon ya gaisa da Mama ya shiga ya gaishe da Baba sannan ya shigo dakin da na ke ya tsaya a bakin kofa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa. Ni kuma na kasa kallon inda yake ma balle har na bude baki nai masa magana. “Am... Yaran nan ya maganar karatunsu?” Sai a lokacin na dago na kalleshi kwarjininsa ya cika idona sai dai hakan be saka ni dauke kai ko janye idanuwa daga nasa ba. “Na je Gwarzo ba su karbe su ba, wai sai da ubansu” “To miyasa ba ki fada min ba? Yanzu idan ban yi magana ba haka za ki zuba musu ido karatunsu ya lalace?” Sai na ji wani iri kamar ba ni ba, magana yake da ni kamar wanda be taba furta kalma so a gareni ba. “Kin amince a akai su?” Na dan kawar da idona daga kallonsa ina girgiza kai alamar ban amince ba. “Haba Halimatu idan ba ki amince ba ya za ki yi? Ko Aminu za ki maidawa su ki ce ya saka su? Ya kamata ace idan za ki yi abu kina tunani gaskiya, ko da yake har yanzu akwai kurciya a take tare ke yaran ma ai mabiyi da mabiyi ne ba wani dogon tazara” Sai na ji kamar magana ya fada min a cikin magana, ban yi aune ba na ji yana wata maganar da dariya a sautin muryarsa. “Idan baki amince ba zan kai karar ki gurin Baba na ce kin hana asaka yara a makaranta” “Abdallah zan saka su” Na yi maganar a cikin muryar da ke karantar da mai saurarenta damuwata, sai yai min wani kallon tausayi yai min magana a hankali. “Zan saka su Halimatu karki damu, karki min musu pls” Ya roka kuma ya samu domin ban iya masa musun ba sai gyada masa kai da nai alamar na amince. “Thank you” Ya furta sannan ya fice daga dakin ni kuma na hade wani abu marar dadi da ban san ko minene ba na rumtse ido. ***     ***   *** A satin suka fara zuwa makaranta, daga uniform har Littafai da school bus da ke zuwa daukarsu da komai Abdallah yai, aikina kawai wanke musu uniform shi ma ba kullum ba domi kanena ne suke wankewa su goge musu, bangaren abinci na samu sauki sosai domin a makarantar ake ba su na safe da kuma na karfe sha biyu daya da rabi kuma a kawo su gida. Tun daga lokacin ban sake saka Abdallah a ido ba da na kira wayarsa nai masa godiya ma kin dauka yai. Wata rana muna cikin fira da Abdulhamid na ke masa zancen yarana akan tafiyar da zan yi na bar su a gidan. “Amman za su rika zuwa suna ganina a gidanka” Na fada ina karantar yanayinsa. “Haka ne” Ya fada yana hade yawu, ni kuma na ji wani iri, be karfafa min guiwa ba kuma ba ce zai hana su zuwa ba, a ranar har muka karkare ba mu tattauna wani abun arziki ba. Misalin goma na dare na shigo gida, dakinmu na wuce kai tsaye sai na samu dukansu sun kwanta a saman katifa sun yi bachi har Amal da bata bachi da wuri. Ido na kura musu ina ta kallonsu kamin na zauna na kai hannuna na safa su, ina ta jin su kamar wasu marayu zan auri wanda baya farinciki da zuwansu a gidansa ga mahaifinsu har yau be leko ko ya turo a duba lafiyarsu ba, gaba daya ma sai na ji kamar na fasa auren kuma babu dama. Shinfida nai musu na kwantar da su a inda nasaba kwantar da su Amal kuma na rumgumeta mu kai bachi rumgume da juna. Tun daga lokacin wata irin shakuwa da kauna ta kara shiga tsakanina da yayana ba ma kamar Amal da take karama, har ta kai ko laifinsu bana son a gani dana ji kukan daya daga cikinsu sai na ji babu dadi. Ban sanarda kowa zancen auren ba sai ana sauran sati biyu ciki kuwa har da aminiyata Hajara, a ranar da ta sallamo gidanmu ta nuna min bachin ranta sosai har take labarta min wai mijinta ya fara gina gida mai part biyu saboda ni da ita. “Hajara ba ki da hankali” “Babu wani rashin hankali Halimatu, abokiyar zama tana da dadi ko da dan yau da gobe, kuma ko Abban Afra be aure ki ba zai karo aure saboda akwai son karin auren a ransa, ba ki san kudirinmu ba, ba ki san iya abunda muka shirya akanki ba” “Wai ba ki ma kishin mijinki?” “Wallahi ban taba jin kishi akan ki auren mijina ba, na san waye mijina za sama miki rayuwa mai kyau irin wacce kika rasa a gidan Aminu, kuma zai rike yaran nan da muhimmanci ko ba komai ai hakan zai bawa Aminu haushi tunda abokinsa ne” “Wallahi ni ba zan iya ba Hajara, taya zan yi kishi da yar'uwata?” “Ba zaman kishi za mu yi ba, zaman yan'uwa za mu yi” Duk yadda tai ta kokarin convince dina na yarda da ita sai na kasa, ni kallon marar tunani ma na koma yi mata, a ranar dai mun sha fira sai da yamma ta tafi. Washe gari sai ga kawata Sa'adatu na yi mamakin ganinta ba ni kadai ba har da kanwata Hafiza domin ni dai na san ban fada mata cewar zan yi aure ba, rabona da ita ma tun a lokacin da ta fada min cewar za tai tafiya tafiyar da Hafiza ke labarta min cewar da Aminu tai yi ta. A al'adar ko ma na kira shi da dabi'a bana iya cin fuskarka mutum a kusa da shi kamar yadda na ke saurin yarda da mutane, komai mutum yai min zan shanye na mai da komai ba komai ba. Haka muka zauna muka sha fira da ita daman a gidan babu wanda ya san akwai wata alaka tsakaninta da Aminu daga ni sai Hafiza, hakan yasa Inna da Mama suka sakar mata fuska kamar yadda suka basa tun ina budurwa. Sosai ta nuna min rashin jindadin mutuwar aurena da Aminu da kuma tambayar wai da su Namra zanje gidan sabon mijin nawa ko a'a. “Ya ce na je da su, ni kuma na ga kara dai na bar su a gida tun da sun fara sabawa da nan din” “Eh kuma kin yi tunani, tun da na ji ance saurayi ne wanda za ki aura” Na kalleta da mamaki. “A ina kika ji?” “Hmmm Halimatu kenan, ai abun duniya baya boyuwa ballantana ma kin san wannan babban sakamako ne Allah yai miki Allah yasa dai kyakkyawa ne kamar yadda kike kyakkyawa kin san ke fa matar manya ce” Murmushi nai tare da canja mata fuska, hakan yasa ta hade duk wani zancen da ke kunce a bakinta tai min sallama ta wuce har da mikawa su Amal 2k ni dai ko rakiya ban mata ba. Duk yadda kawaye da yan'uwa suke ba ni kayan gyara da tsima jiki kin sha nai sanin mijin da zan aura, dan haka ba zan sha abun da zai zo ya dame ni ba ko ya zame min matsala. Sai dai bana nunawa kowa sanin cewar babu wanda yasan da matsalar Abdulhamid sai ni. Daga ni har shi ba mu tsara yin wani event ba, dama ni ba budurwa ce shi ne dai ya kamata yai hakn kuma be yi ba, wata kila saboda shi ma din kansa ya san be cika cikakakken ango ba ko kuma dan baya da son hayaniya ne oho.   Ranar da aka daura aurena da Abdulhamid sai na kasa farinciki kamar wacce akai ma auren dole, wata kila saboda na san irin mijin da na aura ko saboda zan tafi na bar yayana ko kuwa saboda dan'uwan Abdallah na aura wanda ya saka ce min komai akan hakan har yanzu. Duk wata murna ta iya fuska ce da hakora amman bata kai zuci ba, gaba daya ma neman son Abdulhamid nai da ke zuciyata na rasa, da na tuna cewar baya son yarana sai ji kamar bana bukatar zama shi, duk kuwa da kasancewar be fito kai tsaye ya fada min ba amman alamu ya nuna haka. A wunin ranar da akai wunin biki Amal na biye da ni duk inda zanje, ba Amal kadai ba har da Namra Aiman da Adnan ne kawai ke ta sha'aninsu su kan fito basu kula ba, Amal har wani sabon kuka ta tsira ba tare da am mata komai ba. Tun da magariba kanena Zayyanu ya karbe ta ya fita da ita da Namra saboda ya dauke musu hankali kar su ga tafiyata. Inna da Mama sun min huduba kamar yadda su kai min a farkon daren da za a kai ni gidan Aminu, sai abun ya dawo min sabo ina ta hawaye kamar bakuwar aure. Baba ma ya min tasa bayan wacce yake ywan min tun daga lokacin da aka saka ranar auren. Ban san abunda ya hana jin bana son tarewa a ranar ba sai naji kamar ace sai nan da kwana biyu zan tare. Motoci da Abdulhamid ya turo na daukar amarya motoci ne amsu kyau da tsada, ba mota daya ko biyu aka kawo ba, motoci da yawa aka kawo na daukar amarya da kawayenta ni kaina abun har mamaki ya ba ni sai ka ce wata budurwa, ko da yake a gurinsa auren fari ne dole abokai da yan'uwa su yi masa kara. “Hafiza ga yayanki dan Allah ki kula min da su, na san kowa yana kula da su yadda ya dace amman zan kara tunatar da ke ne saboda na san halin yara da cin rai, ta bangaren makarantar su a kula min da su dan Allah” Haka na fadawa Hafiza kanwata wacce muka fi shakuwa, ina jin wani abu ba dadi kamar ina bar mata wasiya. Dafa ni tai tana karfafa min kuiwa. “Karki damu Yaya Halimatu za'a kula da su In-Sha-Allah, Allah dai ya baku zama lafiya da hakuri, idan kika cire komai a ranki sai ki ga kin saba kamar can baya” “Na gode Hafiza” Misalin tara da yan mintuna aka kai ni gidan Abdulhamid da ke can bayan science, har muka isa kafata ta taka cikin katon gidan mai kyau ban daina jin kewar yayana a raina ba, ba ma kamar Amal sarkin takuwa yau ko a jikin wa zata kwana oho... AMINU POV.........✍️ ___________________________ To fa Halimatu za a fara sabuwar rayuwa, Allah bada zaman lafiya. Anya dai ta kyautawa Abdallah kuwa? 🙄😏 7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...* _My Tomorrow_ By Khadeeja Candy 1️⃣6️⃣ Milk shadda ce a jikinsa sai farar hula, fuskarsa na ta sheki kamar shi ne angon ga wani kamshin tutare da yake mai sanarda zuwansa tun kamin ya iso. Abu biyu ne babu a tare da shi walwala da sai kuma yar ramar da yai kadan. Da sallama ya shigo falon Hajiyarsa sannan ya zauna da bismillah, kamin ya mika mata gaisuwa daga inda yake zaune. Sai ta amsa masa tana ta kallon yanayinsa yanayin da ya sauya masa tun sati biyu da suka gabata. “Hajiya ta sai yanzu ake karyawa?” Ya fada yana kallon kofin tea da ke hannunta. “Aa yau da dumamen tuwo na karya sai yanzu na ke shan tea” Be sake cewa komai ba ya maida hankalinsa a gurin tv da ke kunne. “Ba kaje aiki ba yau ko kuma ba a aikin ne yau?” “Zan je yanzu, Suwaiba na kai gidan Abdulhamid, daman ta matsa min tun kwanaki baya tana son zuwa na hana ta sai yau dai na kai ta” Har lokacin da yake maganar be kalli gefenta ba. Yana shirin mikewa tsaye ta ce. “Jiya Mal Dalhatu ya zo nan” Da sauri Abdallah ya juyo ya kalleta jin ta ambaci mahaifin Halimatu. “Mi ya kawo shi?” “Yace yana ta son ya zo yai mana godiya be samu dama sai yau saboda yanayin jikinsa” Dan murmushi yai ya kawardar fuskarsa. “Baba Karami akwai karfin hali, miye abun godiya a ciki ai yi wa kai ne” “Yi wa kai ko kashe kai? Akan me za ka dauki nauyin irin wannan dawainiyar haka? Ya fada ko ruwan da aka sha a gurin wunin nan kai ka kawo su” Cikin muryar da ke bayyana rashin jindadinta tai masa maganar hakan kuma ba karamin mamaki ya ba Abdallah ba, domin be taba ji ko ganin ta hana su yin wani aikin alheri ba musamman abunda ya shafi yan'uwa. “Akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka dauki nauyin hidimarta? Har da wani daukar yara ka saka su makarantar kudi ina ruwanka ba su da uba ne?” A karon farko ta yi masa maganar a tsawace tana dire kofin tea da ke hannunta da karfi. “Ban yi dan wani abun ba Hajiya, a gaban ki Alhaji ya bar mana wasiyar taimakon yan'uwa da mabukata, kuma tun ba yau ba idan za ayi biki a gidan Baba Karami mu na yi masa abu mai nauyi saboda mun tashi mun ga Alhaji na yin haka kuma ya mana wannan wasiyar, ba hidimar aure kawai ba har abincin da za su yi ke da kanki kin sha daukar abu daga nan ki aika musu balle kuma mu da muke jininsa” “Ba alheri na ke hana ka yi ba, wannan karon ka yi alherin ne a gurbin da be kamata ka yi shi ba, akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka nuna mata kula har da duniyarka” “Hajiya idan Halimatu ta auri Abdulhamid kamar ni ta aura, ni da Abdulhamid duka daya ne kuma.... ” Hannu ta daga masa. “Na fika sanin wannan kai da shi duka ni na haife ku, ina magana ne kawai akan abunda yake bayyane ni na san Abdulhamid ba son Halimatu yake ba, ita ta janyo ra'ayinsa ba kuma saboda kowa ba sai dan kai” “Haka ya fada miki?” “Ba sai ya fada min ba, ni na san waye ďana, be taba zo min da maganar wata mace ko son yin aure a wannan yanayin da yake ciki ba sai a wannan lokacin, mutumen ma da neman lafiyarsa ya saka a gabansa? Rana tsaka ya zo min da zancen auren nan idan ba ita ta nuna masa ba taya za ayi ya kawo wannan tunanin a ransa? Kuma ya rasa mace aure sai Halimatu bazawara? Mai yaya hudu yana saurayinsa bayan kuma ba iya komai yake ba Allah yasa dai tsakani da Allah zata zauna da shi” Murmushi Abdallah yai ganin yadda Hajiyarsa take ta bude wuta. “Ban da abinki Hajiya Abdulhamid ai ba yaro ba ne da zata nuna masa hakan ya yarda idan har ya san baya son ta ko kuma zai cutu” “Ko dai minene Husaini be dace Halimatu ta auri Hassan ba bayan ta san kana sonta ban goyi bayan Abdulhamid ya auri Bazawara ba a aurinsa na fari na kyale shi ne kawai saboda na lura da ra'ayinsa na son yin haka kuma bana son na karya masa guiwa saboda ya dade yana mafarkin aure be samu ba, kuma na tabbatar shi kansa be san kana son ta ba Wallahi ba zai aure ta ba, amman ita ai ba yarinya ba ce ya kamata tai tunani indan har ba zata aure ka ba to be kamata ta auri dan'uwanka ba, ko da kuwa shi ya nuna mata son da gaske sai da ta fasa aurenku duka, Hassan ya ji da wanne yayanta guda hudu ko kuma lalurar da take gabansa? Da gangan tai wannan saboda ta bata zumunci kuma ya batu” Abdallah ya shafa kansa tare da hade yawu sannan ya kalli Hajiya a raunana ya fara magana muryarsa kasa kasa. “Jikina yana yawan ba ni haka, ina yawan jin cewar kamar Halimatu ta jayo soyayyar Abdulhamid ne ba shi ya kai kansa ba, sai dai zuciyata ta kasa yardar da hakan, tun daga lokacin da kika fada min Abdulhamid ya zo miki da maganar auren, ko wane dare sai na lalubo na ga ko zan hango wani abu da zai saka na zargi Halimatu amman Wallahi Hajiya na kasa ganin laifinta, a maimakon haka sai tausayinta ya kara kamani saboda na san Abdulhamid ba kamar ni ba ne baya son yara a rayuwarsa, ko da ma yana son yara ba zai kaunace su a lokacin da yake saurayinsa ba ita kuma take a bazawara ta zo masa da yara, ga mahaifinsu be kula da su ba, and yan gidansu gaba daya mata ne mazan uku duka kanane da ba su yi wani wayo da za su iya kula da tattalin kanensu ba, balle ma yayan yayyu, abu ne mai wahala ta samu mai kula mata da yaranta yadda ya dace” “Can ta matse mata ina ruwan wani? Ita yarinya ce da ba zata yi tunani ba kamin ta aikata abu? Ni Wallahi da tausayi take ba ni amman yanzu na natse ko ganinta bana son yi, ba dan kuma komai ba sai dan wannan wawanci da ta aikata, ni Wallahi bana son Abdulhamid ya auri bazawara kuma bazawarar ma wacce dan uwansa yake so kuma ita ta san hakan amman ta yarda” Wannan karon wani dogon numfashi yaja ya sauke. “Hajiya akwai wani kuskure da na aikata a can baya, wanda na ke tunanin wata kila saboda shi Halimatu take son hukunta ni kuma na cancanci haka” “Haba Husaini wani irin laifine da zai saka ta auri dan'uwanka saboda kai? Ni ban ga cancanta aurenta da Abdulhamid ba Wallahi na san waye ďana” “Hajiya na yi kuskuren furtawa Halimtu cewar ina sonta a lokacin da take da aure, tun da na dawo kasar nan na ganta sai ta ga ta canja min kamar ba ita ba sai Allah ya dauki son ta ya saka min a rai, a lokacin na yi ta kokarin ganin na haka zuciyata abunda take son cusa min amman na gagara, Wallahi Hajiya har ta kai idan zan kwanta ko ina wani abun sai tunaninta ya fado min a rai, musamman da na samu labarin yadda mijinta yake da kuma irin yadda take hakurin zama da shi, a lokacin shaidan ya yaudare ni kuma yayi galaba a kaina zuciyata tai ta nuna min cewar Halimatu bata dace da auren Aminu ba, ni ta dace ta aura a lokacin akwai good understanding tsakanina da ita, hakan yasa na fara nuna mata irin halayen mijinta da abubuwan da yake marar kyau, daga lokacin muka fara samun matsala da ita, a lokacin ne na fada mata kai tsaye cewar ina son ta.... ” Shiru yai for few seconds ya shafa fuskarsa sannan ya sake sauke numfashin a karo na biyu. “Na fada mata zan iya aurenta idan har zata iya kashe aurenta ta fito, kuma na yi ta aikata abubuwan da nake sa ran za su iya zama silar mutuwar aurenta, Astagafurullah ....Abubuwa da yawa Hajiya har ta fara fada min bakar magana tana min kallon wani shaidani yes ni kaina a ynzu ina jin na aikata ba daidai ba, amman a wacan lokacin sai na kasa gane hakan duk da na san bata dace da auren Aminu ba amman ai he dace na yi sanadin mutuwar aure ba ko?” Hajiya ta gyada masa kai. Sai ya maida kansa kasa yana taba agogon hannunsa “Yes i know... Kuma na san shi ya janyo min wannan matsalar a yanzu, so ko da ma ita ta janyo soyayyar Abdulhamid batai laifi ba inda dai ta hukunta ni tai i deserve it, and Abdulhamid ya fi ni bukatar aure a yanzu saboda yana a situation din ba ko wace mace zata iya aurensa a yadda yake ba sai mai hakuri da jajircewa kamar Halimatu” “Babu wanda ya san da wannan matsalar sai mu, sai kuma ita a yanzu waya sani ko ta gagara zaman ta fita ta tona mana asiri kuma ta bayyana ma duniya halin da Hassan yake ciki bayan a da yana cikin rufin asirin Allah? Na fi tausayin Hassan fiye da kai na dade ina jiran zuwan ranar da zan ga Hassana yayi auri yana rayuwa ta farinciki kamar kai kamar kowa, amman na bana farinciki da auren nan, saboda yayi auren a lokacin da be dace ba kuma da wacce ba ta dace ba” Mikewa tsaye Abdallah yai yana jin wani abu na rashin jindadi yana kawo masa ziyara. “Haka Allah ya kaddara” “Haka Allah ya kaddara kuma da son ranta ba, idan ma wannan hukunci ne take tunanin ta yi to kuskure ne babba” “Zan je gurin aikin Hajiyarmu ba wani abun ko?” “Babu” Sai da ya kalli yanayinta sannan ya sa kai ya fice ransa ya susuwa zuciyarta na konuwa. HALIMATU POV. Al-hamdulillah shine abunda na ke yawan maimaitawa tun daga lokacin da na saka kafata a gidan Abdulhamid, duk wani abun na jindadi rayuwa da mace zata nema a gidan miji Abdulhamid ya tanadar min shi, tun daga na ci har na sakawa a jikin har na kallo, kamar wata kwai haka yake tarairaiya ta a yadda yake nuna min kulawa da soyayya ban tsamanci samunta a gurinsa kamar haka ba. Yana yawan nanata min cewar ina da wani irin girma da daraja a idonsa saboda aurensa da nai alokacin da yake dauke da lulurar da ba ko wace mace ce za ta yarda ta aure shi a haka ba, wannan dalilin yasa yake da kara gwarjini a idonsa. Ya kara maida hankalinsa gurin neman magani fiye da da, ni ma kuma ina kokarin yi masa abubuwan da zasu taimaka duk dai bana ganin wani alamu na warkewar sai ban taba gajiyawa ba ko na fitar da rai domin na san babu cutar da bata da magani. Ina samun kwanciyar hankali a aurena da Abdulhamid fiye da wanda nai a baya da Aminu, ko ba komai zai nuna min kulawa zan kwanta a kirjinsa na farka a gefensa mu ci abinci tare mu yi fira mu yi hara mu yi nishadi, ba kamar a gidan Aminu ba da ba shi da lokaci na. Bana da wani fargaba ko tunani a gidan aurena bayan ta mutum biyu yayana da kuma Hajiya wato mahaifiyarsa domin na lura a duk zuwan da muke gaishewa kamar bata na'am da ni, bayan a baya kuma ba haka na santa ba, duk dai ba wani zuwa muke sosai ba amman a duk lokacin da muka je gaisheta ko kuma muka fito daga wani gurin muka biya sai ta yi min tarba ba a baya da kai ba, ko kuma ta bar a nan a falon ba ita kadai ba har yayanta mata biyu na lura haka suke min basa son fira da ni balle kuma irin wasar nan ta matar yaya, namijin ne kawai babu ruwansa shi kan idan muka tarar da shi a gida mu yi ta fira abun kamar ba kanen mijina ba, amman bayan wannan bana da wata matsala da Abdulhamid idan ka cire na kyamar yayana da yake yi, domin na lura ko zancensu baya son ina yi idan aka kira waya da sunan za mu gaisa da su a lokacin da yake kusa da ni da a take yanayinsa zai canja, be taba siye ko da biscuit din maira goma ya mika min ko ya bawa wani yace a kai musu balle kuma har ya tambayi lafiyarsu ko karatunsu, sai dai ina masa uzuri da wannan ganin cewar shi din be taba aure ba sai yanzu kuma daman can ba mutum ne mai son yara ba, ballanta na san yadda wasu mazan suke basa son yayan wasu a kusa da su, musamman Abdulhamid da na lura da alamar yana ďan da kishi ba kamar wasu ba, tun daga lokacin da yai kokarin hana ni aikina na lura da hakan ga kuma ya hana yin ko. Wane irin social media saboda kar na hadu da maza, yana yawan fada min cewar na rike masa kaina na tsare masa kaina kar na bar shaidan ya rinjaye ni, wani lokacin na kan amsa masa da to ko nai masa alkawarin haka ba wani lokacin kuma sai dai na yi dariya, domin a tunani babu abunda zai kai ni na aikata wani alfama ko da bana da aure balle ina da shi, ba wai na fi karfin shaidan ba ne, kawai dai ina tuna baya ne a lokacin da Aminu zai iya shafe wata da watannani ba neme ni ba kuma babu kulawa da magana mai dadi ga shi ina zuwa aikin ina ganin mazan amman ban aikata ba, balle yanzu da nake auren mutumen da ya san darajar aure kuma bana ganin mazan ma, to mi kam Allah na tuba wace tsiyar ce zata saka ni aikata hakan. A zaman aure da Abdulhamid wani abun da zai baka mamaki shine rashin iya girki, wanda ni kaina yake bani mamaki kuma ya ba ni tsoro, tun da na zo gida ban taba dora girki ko da ruwan zafi ne ya tafasa ba, idan na dora miya yadda na hada ta haka zan zo na tararda ita haka tuwo ma, shiyasa ban taba yin jalof ba lalle shimkafa da wake, indai har za mu sha tea sai dai Abdulhamid ya dora mana, indai har ni na dora ba zai tafasa ba ko da kuwa a gas ne ko electric kettle. Sai dai be taba sakawa Abdulhamid ya min fada ko nuna bacin ransa a hakan hakan ba, kullum safe shi zai dora mana ruwan da za mu amfani da su da rana kuma yai mana take away haka ma da dare, na kuma rasa gane dalilin haka bayan a can baya na iya girki na kamar ko wace mace, amman tun da na tsinci kaina a gidan Abdulhamid sai komai ya lalace. Ranar wata labara da misalin sha daya da yan mintuna na ji an buga kofar falona, na yi tsamammi ko daya daga cikin yan matan gidan mu ne hakan yasa na tashi da kuzari na bude, abun mamaki sai nai arba da Suwaiba matar Abdallah kuma uwar yayansa mata guda biyu, na yi mamakin maganinta domin ta dade tana min waken zuwa amman bata zo ba sai yau, mun sha fira a ranar daman can Suwaiba mace ce mai son fira da far'a da haba haba da jama'a, ban yi zaton Abdallah ya kawo ta ba har da ta labarta min cewar shi ya kawo ta amman ya aje ta gurin gate wai yana sauri jaye gurin aiki. Ta labarta min abubuwa da yawa a ciki har da na rashin son yara da Abdulhamid yake da shi, sannan ta dora min da cewar yawanci maza basa son yayan da ba na su ba, balle kuma Abdulhamid da yake saurayi, tana ta nanata min cewar sai na yi hakurin haka kamar ta san abunda ya fi damu na kenan, duk kuwa da kasancewar ban taba fadawa kowa ba. Ganin na dauki waya na kira Abdulhamid na ce yai mana takeaway sai abun yai ta bata mamaki. “Kar dai ace har yanzu baki fara girkin ba, ko kuwa amarcin ne ya motsa kike jin ba za ki iya dafawa ba?” Dariya nai kamin na bata masa. “Wallahi ba haka ba ne, idan na dora girkin baya dahuwa yadda na saka shi haka zan tararda shi kuma ga wuta ga komai amman ba ya yi” “Too kar dai ace Abdulhamid ma yana da kohi kamar Abban Suhaima, ni ma idan nai masa wani laifin ko kuma na bata masa rai haka zan dafa abinci a ranar ba zai dafu ba sai na bashi hakuri” Ta fada tana dariya... Ni ma dariyar nai sai dai ba irin ta ta domin ni wani tunanin ne ya zo min, kar dai ace Abdallah ne yai min kohi nake ta samun wannan matsalar? “Ko da yake shi ma a tawaye ne dole za a samu dukansu suna yi, wata kila wani abun kika masa sai kin ba shi hakuri sannan za ki daidaita, amman fa ni kin san da na dauka ko Abdulhamid ba shi da kohi” Zancenta ne ya dawo da ni daga duniyar tunani sai na sake yin murmushi a karo na biyu. “Haka ne ai wani ba a iya ganewa sai idan wani abun ya faru” “Haka ne” Sai guraren karfi biyu ya kirata a waya yace ta fito bakin gate yana jiranta, a lokacin Abdulhamid be dawo ba, sai na saka Hijabina na rakata har gurin motarsa bayan na deba mata wasu abubuwan daga turaruka na da kayan kwaliya, gilashin motarsa a sauke yake amman ko da wasa Abdallah be dago ya kalleni ba da na gaishe ma sai ya amsa min a gajarce kamar be san ni ba, bayan sun wuce na dawo ciki gidan ina ta nazarin kalamanta. Daga karshe na yanke shawarar kiran Abdallah nai masa magana, haka kuwa akai bayan Abdulhamid ya dawo mun ci abinci mun yi fira ya fita sallah la'asar ni kuma na nemo number Abdallah ya aika masa kira, ringing tai kamar zata katse sannan ya daga, ban tsaya yi masa sallama ba balle gaisuwa kai tsaye na ce. “Abdallah magana na ke son mu yi” Sai na yi shiru bayan na fada masa hakan ina jiran na ji amsar da zai ba ni kamin na dora amman be ce min komai ba har sai da nai zaton ko wayar ta katse ne. “Idan ka kullace ni da wani abun dan Allah ka kwance, tun da na zo gidan nan kullum nai girki ba ya yi” “Babu hannuna a ciki” Ya amsa da muryar da na jita kamar ba ta shi ba. “Wata kila kana jin haushina ne, ko kuma kana jin bacin rai a kaina ne” “Ban taba jin haushinki ba, kuma ba ki bata min rai ba, abunda kika aikata ne kawai idan na tuna ina jin babu dadi ne” “To ka daina jin babu dadin, shiyasa bana iya girkin idan na yi ba yayi, dan Allah ka kwance Kohin da kai min” Ina iya jiyo saukar numfashinsa kamin ya ce. “Ban kullace ki da komai ba Halimatu, ke yanzu yar'uwata ce kawai kuma matar dan'uwana, yan'uwanta ta fi gaban wasa ko babu Abdulhamid babu abunda zai shiga tsakanin mu” Yana fada min hakan ya kashe wayar, a take wani abun marar dadi ya kawo ma zuciyata ziyara. Har na gabatar da sallah la'asar ban daina jinsa ba, bayan sallah isha'i ina kwance saman kujera falo Abdulhamid ya fito daga bedroom ya nufo inda nake kwance, sumbatar kaina yai kamin ya daga ni na tashi zaune sai ya zauna sannan ya kwantar da kaina saman kijinsa yana shafa fuskata. “Gobe fa ina tunanin zanje Abuja” Dagowa nai na kalleshi sai na ga murmushi a fuskarsa. “I know za ki yi mamaki ai, ni ma zuwan dole ya zame min kuma i think idan na samu yadda na ke so zan dawo ranar da na tafi” A take na marairaice fuska kamar zan masa kuka. “Mi zaka je yi Abuja?” “Wallahi wasu takardu ne na ma'aikatar mu da ake son su jibi kuma dole sai an kai su Abuja an saka hannu shiyasa zan je, idan an saka hannu za a ba mu kudi masu dan dama sai mu juya su” “Tare za mu je?” “Na so haka amman be samu ba dole mi kadai zan je, amman a promise you idan ban dawo ranar ba washe gari zan dawo” Har cikin raina na ji babu dadi sai na ji kamar tafiyar shekara zai yi, a ranar na kwanta a jikinsa sosai yadda kasan wata jaririya haka na zama. Washe gari daga ni har shi mun tashi da wuri, shi ya hada mana abun karyawa ni kuma na shirya masa komai na tafiya, a tare muka karya ina ta narke masa a jiki tun yana daujar abun wasa har shi ma ya so ma jin babu dadi. Na masa complaining din rashin mai gadin mu sai ya ba ni hakuri ya ce za a samu idan ya dawo bayan yayi min izinin zuwa gida na gaishesu ganin duk na bata rai ya san idan naje zan dan sake sosai, har gurin mota na rako shi nai masa addu'a sosai ta neman tsari da kuma alherin hanya, saboda na san yanayin kasar ana cikin halin fargaba balle tafiyar a mota zai je ba a jirgi ba. Bayan tafiyarsa da awa daya na shirya na nufi gidanmu, yan gidan mu sun yi murnar ganina sai zolayata suke wai ina ta shining. A yanayin dana tararda Amal be min dadi ba, wai zawo take da amai yau kwana uku amman basu fada min ba ganin ba su gaza mata a komai ba, na san suna bata kulawa sosai ammn dai ai ya kamata ace sun sanar da ni a matsayinta na yata kuma karama, ko da yake na lura sukansu yanzu yaran idan suka gan ni sai su yi kamar ba su gan ni b babu ruwansu da nuna son zuwa ganina in banda Amal da ta kasa sabawa da kowa har yanzu. Wata kila Mama ta ki ta fada min ne ganin kamar zan iya daga hankalina ga shi kuma Abdulhamid ba son yara yake ba kamar yadda kowa ya lura da hakan. A ranar Amal a jikina ta wuni lokaci zuwa lokaci sai ta kalleni ta sauke ajiyar zuciya abun har ya soma ba ni tsoro, na so na kaita asibiti duk kuwa da Mama ta fada min sun kai ta ga kuma da aka rubuto mata na gani amman hankalina zai fi kwanciya idan na kaita da kaina. A ranar nai deciding na dauko ta na dawo da ita gidan aurena tare da ni ba in yado washe gari sai na kira Abdulhamid na fada masa cewar na zo da ita saboda bata da jindadi kuma na nemi izininsa na kaita asibiti. Bayan magariba na baron gidan da ita na debo wasu daga cikin tufafinta, har na iso gida babu komai a zuciyata sai tausayinsa, wata kila har da kewata ta sakata wannan ciwon saboda yadda ta saba da ni sosai. A gaskiya ranar na ji babu dadi marar misaltuwa, wani abun mamaki da muka dawo gida tare sai ta dan sake Allah ya kawo mata sauki har ta labari take ba ni wai Adnan ya dake ta ya zageta, sai dai idan an taba jikinta ina jin zafi a can gidan bata cin komai amman a nan da na bata abaya sai ta ci ta kwanta a jikinta ta tafe sosai kamar wata kyanwa. Misalin tara da rabi na shiga kitchen na gwada dora indomie, wani abun Allah sai gashi ta dahu kamar yadda na saba dafata, ban san lokacin da na daka tsalle na dibe ba dan murna. Ta window kitchen na hango dorowar mutum ta gate, ta hanyar hasken fitulun da ke cikin gidan ne na iya gane wanda ya diron yana sanye da bakaken kaya fuskarsa ma a rufe da bakin fuska. A furgice n rugo da gudu na yo falo sai an samu Amal har ta yi bachi da sauri n rufi kofar falon na rufe zuciyata na bugawa kamar zata fado, abunda ban sani ba ashe na rufe falon da daya daga cikinsu ba, ban lura da hakan ba sai bayan an rufe kofar na yi baya sai na hango mutum ya fito bayan labule rufe da fuska kamar wacan yana nuna ni da bindigar da ke hannunsa. *Khadija Abubakar Alkali* 7/20/21, 8:32 AM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 1️⃣7️⃣ Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u. Shine abunda nake ta maimaita a raina ina kallon bindigar da ake nuna ni da ita, zuciyata na wani irin zillo kamar zata tuma ta fado kasa. Ban ankaro da a filin na ke neman ceton Ubangijina ba har sai da mamalakin bindigar ya dora hannunsa a bakin da bana iya tantance saboda mask din da tai wa fuskarsa kawaya. “Shiiiiiiiiiiiii, kwanta” Kamar umarni nake jira a take na kwanta a guri kamar gawa, ina iya jiyo karar bude gate din gidan da akai kamin daga bisani a bude kofar falon sai shigowar mutane na ji ina kyautata zaton wanda ya diro ta gate ne ya bude musu suka shigo shi kuma na falon ya bude musu kofar. “Ina mai gidan?” Sautin muryarsa ba jina kadai ya razana ba har da ilahirin jikina da kwakwalwata, ban tana sanin haka tashin hankalin haduwa da mai makami yake ba sai yau, kamar wacce aka cewa ga mutuwa ta nan a gaba na haka na ke ji. “Ina mai gidan yake...!” Ya sake daka min tsawar da na ji ta kamar a mafarki, bana jin zan iya amsa musu domin numfashina ma rawa yake balle kuma muryar da na ke jin kamar ta kare a lokacin. “Ke tashi zaune” Ya sake daka min tsawa a karo na uku, sai na tashi ta sauri cikina har wani kuka yake saboda tsoro. Da dai-daya na bisu da kallo kamar zan ga wanda na sani ko ya san ni amman ban ga fuskar kowa ba a cikinsu sakamakon mask din da suka saka. Wanda ke kusa da ni ya saita bakin bingarsa a gafen kaina. “Ina mijinki?” “Baya nan....” Na amsa idanuwa a rufe gam ina jimke hannayena, tashin hankalin da ke cikin kaina yana ta kara hauhauwa. “Karya kike... Idan ba ki fada mana inda yake ba za mu kashe ki” Wannan karon na tabbatar ba jikina kawai yake rawa ba har da kayan cikin da ke cikin cikina da kuma kaina. “Wallahi baya nan ya tafi Abuja” “Ina kudin da ya shigo da su jiya?” “Be shigo da kudi ba takardar ce ya je ya kai Abuja a saka masa hannu” “Idan baki ba mu kudi ba za mu kashe yarki” Sai a lokacin na bude ido a take na nemi tsoro da gudun kar su kashe ni da na ke na rasa. “Wallahi Wallahi babu kudi a cikin gidan nan, idan ba ku yarda ba ku duba ko'ina” “Idan muka duba muka ga kudi za mu kashe ki” Na gyada kai duk kuwa da kasancewar bana iya tantance mai maganar a cikinsu. A take ya bada umarnin a shiga a duba masa ko'ina na gidan, ba dakina kadai ba har falo sai da suka hankade komai sannan suka yarda da babu kudi a cikin gidan. “To dauko mana zinari” “Ba ni da zinari ba ni da komai” Ina rufe baki na ji saukar mari gafen fuskata. “Ki dauko mana zinari na ce” “Ko kashe ni za ku yi, ku sake min wani rai ku sake kashe ni ba ni da abunda zan ba ku bana da azurfa ma balle zinari Wallahi bana da komai” “Okay Anas dauko mana yarinyar can idan ubanta ya dawo ya ba mu kudi sai ya karbo ta” Ban san lokacin da na girgiza musu kai ba. “Aa Wallahi ba yarsa ba ce, ba babanta ba ne kuma bata da lafiya dan Allah ku rufa min asiri karku dauke ta” Ina ganin ya nufi gurin da Amal take na nufi gurin da rarrafe ina kuka majina na min zuba, fisgota yai da hannu daya ta mikar da ita tsaye sai ta lauye kafafuwanta ta fara kuka irin kukan na yaran da aka tayar daga bachin da be ishe su ba ballantana ita da lafiya bata ishe ta, kafafuwanta na rike na fashe da wani irin kuka marar sauti. “Anas sake ta” Kamar umarni mutumen da aka kira da Anas yake jira sai ya sake Amal da sauri ni kuma na rumgumeta, ita kuka ni kuka. “Kin ce ba ki da abunda za ki ba mu ko? To ni ina da abunda zan ba ki ta so nan zan bar ma mijinki sako, idan ya dawo ki fada masa ya aje mana kudi kamin mu sake dawowa...” Yana fadar hakan ya mikr tsaye ya nufo inda na ke, da wani irin karfi na rashin imani ya fisge Amal daga jikina ya wulgarda ita kasa ya ja bayan rigar atamfar da ke jikina kamar wata baiwa ya nufi bayan kujerar da sauran suke zaune da ni. A gurin ya yaga mutuncina, a gurin ya karya martabata, a gurin yai min bakin digon da ban taba mafarkin yi ma kaina ba, a gurin ya tarwatsa rayuwata, a gurin ya gussar da ragegen farincikina, a gurin ya saka min tsoro da fargaba da bakincikin GOBENA. a gurin ya biya bukatarsa ina kuka da  gurnani kamar wance bata taba sanin da'namiji ba a rayuwarta. Ba badurwa wa ce ni ba balle nai kukan karbar budurcina da yai dai dai nai kukan karbe martabata da farincikina. Har ya daga daga jikina ya gyara wandonsa ban daina kallon fuskarsa ba, so nake ko yayana na ga wanda ya keta min haddi, ji nake kamar ace ina da ikon cire a lokaci na raba shi da rayuwarsa, hawayen da suke sauko min a lokacin ne suka tabbatar min da kukana be kare ba, bakincikina be gushe ba. Risinowa yai kamar zai sumbanci bakina ya dauki zobensa da ya fadi mai alphabet din A ya saka a saman hannunsa sannan ya bar jikin kujerar ya koma gurin da sauran yan'uwansa suke. Ina jin lokacin da suka fita daga falon da kuma tashin motarsa, wasu hawaye masu zafi suka sauko min daga inda nake zaune, ban taba jin wulakanci da kaskanci kamar na wannan ranar ba, ban tana jin na tsani rayuwata kamar yau, ban tana jin kyamar kaina kamar yau ba, na dade ina kare mutunci da martaba da aurena ko babu amman a yau wani wulakantacce marar daraja ya kawar da duk wannan.   Komawa nai a gurin na kwanta kamar gawa, numfashin da ke fita daga hancina ne yake tabbatar da rayuwata,  zuciyata na zafi da ciwo kamar an saka takobi mai kaifi an yanka ta gida biyu. Sannu a hankali na fara jin numfashin kamar baya wadatar da hancina hakan yasa na bude bakina ina fitar da numfashina a hankali. Ina jin kukan Amal amman na kasa dagawa na je gurin da take, jikina ya mutu kamar wacce akai wa allura, wayata ma dake kitchen ringing take sai dai yau ba ta Amal na ke  ba balle wayar. Kukan Amal da ringing din wayata suka ba ni wani yanayi na dabam, yanayin da ya saka ni tausayawa kaina da kuma yata Namra, ina ta auna irin halin da ta tsinci kanta ko kuma wanda zata tsinci kanta a ciki nan gaba...   Ina kwance a gurin har dare ya raba, a lokacin Amal ta ci kukanta ta gaji ta tayi bachin wahala, sai a lokacin Allah ya kawo min kuzari har na iya rarrafawa na shiga dakina da rarrafe na iss bandaki, ba karfin jiki na kawai abunda na rasa ba har da na zuciya wanda shine silar rasa na jikin gaba daya. Duk yadda nai unkurin mikewa tsaye sai na kasa kamar wacce bata da fafuwa haka na zama, ba ciwo ko nauyinsu na ke ji ba, jin su nake kamar babu su a jikina raunin da ke zuciyata yana sauka har cikin jikina, ba jimin yai ba, amman a yau ina jina kamar cikkakkiyar budurwar da aka fasawa budurcinta. Allah nai ta ambata a zuciyata, bakina kuma yana da rawa alamar kuka be kara min ba ko ma nace ban fara shi ba, jin jikina nake kamar ba nawa, daker na iya mikewa tsaye ban san abunda ya same ni ba sai zamewa nai na fadi kasa, ban sake unkurin tashi ba, a gurin na kwanta ruf da ciki hawaye na ce min sallamu alaikum har aka fara kiran farko na sallah asuba. A lokacin ne na samu kuzari har na gwada tashi tsaye bayan an zauna na yan mintuna. Allah kuma ya amincin min na iya kunna hitar da ke bandakin na zauna a cikin tub din na rafka wani uban tagumi, ina ta neman inda hawaye za su fito min na rasa. Sai da na hada ruwan nai wanka na tsaftace kaina sannan na fito na dawo bakin madubin gadon ana zauna ina ta kallon kaina. A zahiri kaina na ke kallo amman a badini GOBENA na ke hangowa ya zata kasance? Miyasa abubuwa mabanbanta suke ta faruwa da ni? Idan na fita daga wannan sai na fadawa wannan? Mijina ne ya fado min a rai! Idan Abdulhamid ya ji zai zauna da ni? Zai cigaba da so kamar yadda yake? Zai kaunace mi mu cigaba da zama kamar mata da miji? Wata kila kuma ya juya min baya waye zai so wani namijin ya kusanci matarsa balle irin wannan da kika fashi? Ban san lokacin da na dauki Vaseline din dake gaban madubi ba na jefi gaban madubi da shi a take ruwan madubi ya tarwatse wani irin kuka mai taba zuciya ya ziyarce ni, sai ga ni a kasa ina kuka da hargagi kamar mahaukaciya, kamar wacce aka tsakala sai na yi saurin tashi zaune ina girgiza. “A a ba zan fada masa ba, wannan sirina ne ni kadai ni kadai ya dace na rufe abuna babu wanda zai sani, ba zan taba fada masa ba, ba zan iya rusa farincikin aurena da kaina ba, ban shirya fuskantar wani kalubalen na rayuwar aure ba a yanzu, ba zan fadi abunda zai saka Abdulhamid ya tsane ni ba, ba zan fada masa abunda zai saka ya kyamace ni ba, ko wannan bakincikin zai kashe ni ba zan fadasa kowa ba, wannan kaddarar Halimatu ce ita kadai” Wannan karon a fili nai maganar ina ta karfafawa kaina guiwa, duk kuwa da ina jin wani bangaren na jiki da zuciyar ya son sauya min tunani daga boyewar zuwa fadawa Abdulhamid gaskiya. Wani irin kuzari da karfin hali ya zo min a take nemi rashin karfin na rasa, tawul din jikina na cire na saka doguwar riga na fito falo da zimmar duba Amal sai na samu kaina da duba bayan kujerar na kasa dauke idona daga barin kallon gurin ina ta aina abunda ya faru hawaye na min zuba. Ba tare da tsoro ko fargabar komai ba na fito harabar gidan ina ta kalle-kalle kamar bakuwa, dubun asuba be hanani ganin ko'ina a gidan ba, ba su fasa mana komai ba bayan gate din da suka bar mana bude. Ba tare da tsoron komai ba na nufi gate din na da kaina  na rufe, ba tsoro ba, a yanzu ina jin ko mutuwa na shirya mata balle kuma tsoro. Falo na dawo na zauna na zubawa Amal ido kamar ance min ita ce maganin damuwata, wayar da ke kitchen din ce ta fara ringing cikin sauri na tashi na shiga kitchen din sai na tararda wayar kife a kasa hannu na kai na dauko wayar sai screen din wayar na gani a tsage sai dai hakan be hana ni ganin kiran Abdulhamid ba da sunan da nai saving din numbersa ✨🔐Final choice❤😍 tare da aljanun da nai yi ma sunan kwaliya da su. Samun kaina nai da kasa daukar kiran har ya katse wani ya sake shigowa ya katse sannan sako ya biyo baya. “Baby na kira tun jiya ba ki daga ba ina son jin muryarki na isa lafiya. Pls ki kula min da kanki” Ina gama karanta sakon na narke cikin wani sabon kuka na rumgume wayar a kirjina, ina ta jin kamar ba zan iya boyewa Abdulhamid, idan na boye masa ban masa adalci ba. “Amman kuma idan na fada masa zai yarda? Zai gasgata ni bayan ba su dauki komi ba? Ba su fasa mana gate ba balle kofa, ba su harba bindiga ba balle na ce makota su ne shaida ta?” A fili na ke ta aiko tambayoyin ina mai jin kamar akwai wani a kusa da ni ya amsa min su. Waya turo su? Da gaske kudin suka zo karba ko kuma daman can mutunci suka zo yagawa? Turo su aka ko su suka turo kansu? Ina suka ji ko suka san cewa Abdulhamid ya samu kudi ko zai samu kudi? Ban ankara ba na ji an tayarda ssallah Asuba hakan yasa nai hanzarin baro kitchen din na dawo dakina, alwala na fara yi sannan na gabatar da sallah asuba, na sani sarai ba kyau kukan da ba na tsoron Allah ba a sallah amman na kasa tsayarda da hawayena har nai sallah na gama, babu komai a addu'a ta sai tarin Allah ya isa da neman tsarin Allah daga shiga wata damuwar. Misalin bakwai na fito falo jikina na min nauyi kamar ba nawa, gurin Amal na nufa na dubata har lokacin bachi take sai dai jikinta da zafi kamar jiya, hannu na saka na dauke ta na nufo daki da ita kamin na shiga dakin ta farka da kuka tana kiran sunana, amman na kasa amsa mata sai kokarin rabata da tufafin jikinta nake. Wayata ce ta sake ringing haka yasa na aje Amal na nufi inda wayar take, Final choice ne rubuce akan wayar har na yi kamar kar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hanani hakan yasa na danna picking na kara wayar a kunne ina hawaye. “A ka'ida idan kika daga wayata sallama kike fara min cikin nishadi da walwala, sannan gaisuwa ta biyo baya amman yau babu ko daya” Ya fada bayan ya dauki lokaci yana sauraren numfashina, lumshe ido nai na bude hawaye na sauko min har lokacin ban samu kwarin guiwar fada masa damuwata, idan na fada masa ban san iya halin da zai shiga ba ban san ya zamantakewar aure zata kasance ba! Ban san ya zamu rika kallon juna ni da shi ba. “Tabbas akwai damuwa a tare da ke matata, sai dai bana da tabbacin damuwar ta rashina ne a kusa da ke ko kuwa wani abun ne dabam, na ji ba dadi gaskiya domin har ga Allah bana son abunda zai bata miki rai a yanzu Haima, bana son wani abu ta zai taba zuciyarki saboda ina matukar kaunarki.....” Wasu zafafan hawaye ne suka sauko min ban san lokacin da naja dogon numfashi na sauke ba. “Fada min waya taba ki?” Ya sake tambaya, sai na girgiza masa kai kamar yana gabana, sannan nai saurin share hawayena. “Babu komai babu komai I'm fine” “No you're not pls....” “Trust me babu abunda ya faru kawai dai ya farka ne jikina babu dadi kuma i miss you so much” Daga can cikin wayar ina iyo jiyo sautin murmushinsa tare da aje numfashin jindadi a lokaci daya. “Karki damu yau zan dawo ai ni kaina i miss you alot, fada min me kika ci?” “Yanzu zan karya ban farka da wuri ba” “Haima bana son kina zama da yunwa fa, ace har yanzu ba ki karya ba? Pls ki daina haka bana so okay” “Yes ba zan sake ba” “Je ki karya zan sake kiranki, i love you” Kai kawai na iya gyadawa na sauke wayar daga kunne na hawaye na min zuba kamar ba gobe, a hankali na zauna a gurin ina jin wani abun marar dadi yana ratsa zuciyata. “Wani ya taba ni Abdulhamid wani ta taba maka mata, wani ya keta haddin matarka wani ne ya rusa raguwar farincikina, wani ne ya saka ni a dakin da ake dandana dakin fyade da ke da ke tarbar ko wace mace mai aure ko budurwa wacce namiji ya keta mata haddi, an yi ma yata jiya kuma ni akai yi wa? Right.... ” “Yes kuma wannan sirrina ne ni kadai babu wanda zai sani be kamata kowa ya sani ba, ko da Mama ce ba zan fadawa kowa ba, ni kadai na sani kuma ni kadai ya kamata na dandana dacin abun daman” Magana nake da kaina ina ta kokarin karfafawa kaina guiwa. Hawayena na share na mike tsaye sai wasu suka sake zubo min, saurin runtse ido na nai gam na dantse bakina tareda hannuna na hagu. “Za ki iya, za ki iya Halima.... ” Shine abunda na ke ta fadawa kaina kamin na ji muryar Amal tana kwala min kira. *Khadija Abubakar Alkali* 7/20/21, 8:32 AM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 1️⃣8️⃣ Sai da na gyara Amal na gasa mata jikinta sosai da ruwan dumi wanda hakan yasa ta dan kara sakewa har na hada mata tea ta sha ta rike yankan biredin a hannu sannan na shiga gyara ko'ina na gidan. Duk kuwa da kasancewar barayin ba su mana barna ba ko barin wata alama da zata saka a gane cewar sun shigo cikin gidan ba, ba su balla mana gate ba balle kofa ba su yi harbi ba balle su tafi da wani abun, babu ma wanda zai shigo cikin gidan ya yarda wani ya shigo da sunan sata. Sanin cewar Abdulhamid na son sakwara yasa na dafa da miyar agusi, bayan na gama na shiga nai wanka na dawo palo na zauna rumgume da Amal jikinta da dan zafi sai dai ba kamar jiya, ni kuma zuciyata cike da zafi fiye da ko yaushe har bana iya controlling hawayena. Sai daf da magariba Abdulhamid ya dawo sai da na wanke fuskata sannan na fita na bude masa gate, iya kar kokarin da zan iya yi na boye damuwa na yi amman hakan sai ya ci tura saboda damuwar da ke raina a yanzu mai girma ce.   Tun daga muryata da kin son hada ido da nake da shi ya fara karantar damuwata. “Kin fada sosai Haima idonki kuma ya kumbura gaba daya ba ki cikin natsuwarki, na fada miki zan taso daga Abuja zuwa nan amman ba ki kira kin tambayi lafiyata ba bayan ba ki saba haka ba” Cikin rashin natsuwar da kirkirar irin karyar da zan masa na kalleshi ina hade yawu, sai a lokacin na tuna cewar yunin ranar ban saka komai a cikina ba sai ruwa shi ma ba da yawa ba, a rayuwar yau na manta da an taba halittar yunwa a cikin duniyar nan. “Hankalina ba kwance ba Amal ba lafiya” “Subhanallahi miya same ta?” Ya fada yana rufe motarsa ya matsa kusa da ni ya kama hannuna yana murza yatsuna a hankali. Dagowa nai ya kalleshi a maimakon na amsa masa sai hawaye suka sauko min. “Je ki dauko mayafi na kai ki ki ganta yi sauri” Ya fada cike da kulawa a zatonsa Amal tana gida ne ba a gidansa ba. “Tana nan a falo jiya na dauko ta... ” Saurin sakin hannuna yai ya nufi kofar falo, wanda hakan ya ba ni damar share hawayena na bi bayansa, ina shiga na same shi kusa da Amal zaune yana taba jikinta fuskarsa dauke da murmushi, a hannun kujerar na zauna ina ta kallon bayansa, a zahiri bayansa na ke kallo a badini kuma makomar aurenmu na ke hangowa a tsakanin fada masa gaskiya da kuma boyewa, idan na fada masa zai jure? Zai zauna da ni a haka? Idan ma na boye mi ye amfanin boyewar? Wace iri zan ci? “Ashe ma da sauki kike ta kuka haka har kin tada min da hankali” Ya fada yana juyowa ya kalleni ba karamin jihadi nai ba na aron murmushin da ban san da zaman sa a duniyata ba na yafa a fuskata. “Al-hamdulillah amman dazun jikinta kam akwai zafi sosai, kuma ina ta fargabar rashin fada maka da ban yi ba na dauko ta ka yi hakuri” “Karki damu ai lalura ce” Ya ba ni amsar yana maida hankalinsa gurin Amal. Ni kuma na tashi na shiga bedroom cikin rashin kuzari na hada masa ruwan wanka ina mikewa tsaye na ji an rungume ni ta baya. “I love you so much Haima, kuma na zo miki da albishir In-Sha-Allah ina daf da samu lafiya ko yau kamin na baro Abuja sai da na ga wani likita kuma kwarare ne, ki cigaba da hakuri very soon za ki zama kamar ko wace matar aure” A hankali na sauke ajiyar zuciya sannan na share hawayena na juyo ina fuskantarsa wasu hawayen na sauko min fuskata kuma da murmushi har na bude baki nai masa magana sai ya rumgume ni a zatonsa hawayen murna ne. Mun dauki lokaci mai tsawo a haka kamin ya sake ni ya shiga wanka ni kuma na fita na hado masa abinci na kawo masa dakinsa.   Bayan sallah isha'i na fara shirye shiryen mai da Amal gida gurin Mama saboda nasan Amal idan har tana ganina ba zata iya kwana ita kadai ba ko kuma ita da wani ba, kamar yadda nake zaton Abdulhamid ba zai min lamanin kwana shi kadai ba ni na kwana da yata, na yi zaton zai ce na barta ta har na wani lokaci ko kuma gobe amman be ce min komai ba be hanani ba kuma be ce min na kai ta ba.   Bayan na gama shiryata nai masa magana cewar ya kai ni a motarsa na maida ita gida, ga mamakina sai ya saka hallabiyarsa ya dauko makullinsa ya bude mana mota muka shiga ni da ita, abun ka da yaro sai ta kara lafewa a jikina har da saka hannayenta ta rumgume ni ta bata fuska sosai kamar zata fasa kuka. Ban ce masa komai ba har muka isa gida duk kuwa da kasancewar shi din yana ta min fira sama sama. Wani abun mamaki tun da na shiga gidan Namra ba ta yi na'am da ganina ba, kallo na ma sau daya tai ta dauke kanta bata sake kallon inda na ke ba, Aiman dai na tarar yayi bachi Adnan ne kawai ke kwance tsakar gida rike da karamar wayar Haulat yana kallo. A lokacin da na aje Amal sai ta fara kuka alamar bata son rabuwa da ni da sauri Namra ta zo ta dauke ta ta nufi dakin Inna da ita ba tare da tace min komai ba. Raina ya sosu ba kadan ba, kar dai ace yayana sun fara tunani ko na zabi wani ne na bar su? Babu ubansu a kusa da su kuma ni na na tafi na bar su. Har muka dawo gidan ban sake na yi walwala yadda ya kamata ba, sai dai ko kadan hakan be damu Abdulhamid ba saboda a tunaninsa ina son saka damuwar yara a raina ne. A haka muka kwashe wata uku na saka sakewa da shi kamar yadda muke a da, har ya fara zargi yana tambayar ko dai na fara kosawa da zama da shi ne haka ne saboda baya iya komai, na fada masa ba haka ba ne amman be yarda ba har ta kai ya fara kokarin gamsar da ni da hannunsa, hakan kuma be kara min komai ba sai damuwa na fada masa bana jindadin yadda nake zaune dabam da yayana ne. “Ai aure ya gaji haka, yaran ba daya ba ne Halimatu balle a ce a dauko su mu zauna da su, kuma tsakani da Allah ba zan biye miki ba idan har aka dauko yaranta zan takura kuma zan cutu ba dan bana son su ba sai dan irin tsarina kuma na ra'ayina bana son yanayi kin san ni, kuma any how ina iya rumgumarki ko nai kissing dinki idan akwai yara ba zan iya ba” Ban ce masa komai ba, iya kar kokarin da nai na fahimtarsa ne da kuma yi masa uzuri sai na danna nawa damuwar da kyautata masa zato tun da shi be taba yin yayan ba kuma be saba da su ba na sani shi ba kamar Abdallah ne ba. “Na san kina hakuri Halimatu na zama da namiji irina mai kamar fanko, shiyasa matsayinki yake da girma azuciya saboda kin yi jihadin da ba ko wace mace ce zata iya ba, ko da kuma kin bukaci rabuwa da ni a yanzu ba zan ga laifinki ba....” “Na aureka ne saboda ina son ka Abdulhamid, ba aureka dan saboda nai sadaukarwar kawai ba, sai dai son ka ne ya fara gina zuciyata tun farkon fari da soyayyarka ka fara sanin miye so” Na fada ina kallon cikin idonsa da dukan gaskiyata, murmushi yai ya kai hannu ya shafa fuskata. “Ina ta saurare ina ta jira.... ina ta tsammani yaushe zan samu lafiya na nuna miki irin son da nake miki? Wata kila nan kusa ne wata kila kuma nesa ne, ban sani ba, ba a sanar min ba, fata kawai na ke yi, sai dai ba zan gushe ina neman taimakonki na addu'a ba da kuma rokon ki kara hakuri da ni har zuwa lokacin da zan samu lafiya, idan kuma lafiyar ta gagara samuwa zan sawwake miki kije ki auri mai lafiya saboda kar na tauye miki hakki, ba burina ne nai ta kallonki a haka ba Halima” Tausayinsa ne ya nemi gurbi a zuciyata yai kwance, kalamansa suka rasa ni kaunarsa ta kara samu muhallin a zuciyata, murmushin na sakar masa sai ya kama hannuna ya kai saitin zuciyarsa. “Ina jinki sosai a zuciyata, ina jin kaunarki fiye da yadda kike tunani, dan Allah ki tsare min mutunci, kuma ki rika kula min da kanki ba fata na ke ba amman ina fargabar ranar da wani abu zai faru ace za ki bar ni” “Ba zan taba barinka ba ban aureka dan na rabu da kai ba” “Thank you” Ya fada yana kissing din hannuna. Ni kaina na san Abdulhamid na so na, na san mijina yana kaunarta kuma ina kaunarsa amman na rasa dalilin rashin sakewa da samun farinciki da bana yi a yanzu wanda hakan ke saka shi cikin damuwa. “Gobe zamu je mu gaishe da Hajiya,ya kamata muje cikin daren nan mu siya abunda za mu rika mata domin da safe zan aje ki can idan zan wuce gurin aiki kuma ba lallai ace lokacin masu super market sun bude ba” Tashi nai na shiga dakina na canja tufafi jikina a tsakanin shiryawa da na shi be wuce minti ashiri ba ya yan kai sannan mu ka fito, da kansa ya bude min motar na shiga sannan ya shiga mazauninsa ya tashi motar, da mu kai bakin gate sai ya fita ya bude mana gate din ya fita da motar sai kuma ya rufe ta muka kama hanyar jifatu. Har muka isa zuciyata raya min take na fada masa gaskiya, ko ba komai ai shi mijina ne be kamata na boye masa ba, abunda ban sani ba ashe shi fira yake ta min ban lura ba sai da ya kira sunana. “Na'am” Na amsa da sauri a daidai lokacin da kiransa ya dawo da ni hayyacina. “Me kike tunani?” “Komai bana na tunanin komai” Da hannu ya nuna min alamar na bude motar na fita yana ta kallon yanayi kamar mai tuhumar wani abu, a hankali na bude motar na fito kamar wata marar lafiya, a tare muka jera muna tafiya daf da za mu shiga cikin gurin wani mutume mai kama da mahaukaci ya miko mana hannu alamar mu ba shi, da na kalleshi da kyau sai na nemi damuwata ta da tunani na rasa, hankalina ya tashi har na kusan rikicewa. Kabir ne Kabir abokin aikina Kabir din da ya kamu da lalurar saboda ni ashe da gaske abun ya taba kwakwalwarsa, da gaske ya haukace. Ni yake mikowa hannuna yana ta kallona sai kuma ya juya yana kallon Abdulhamid ya mika masa hannu, Abdulhamid ya saka hannunsa aljihu ya ciro dari biyu ya mika masa, sai ya juya ya fara tafiya yana dingishi alamar kafar tasa akwai ciwo ko rauni a gurin. “Haima kuka kike yi?” A rikice na kalli Abdulhamid ba dan na san abunda ya fada ba sai dan sunana da na ji ya ambata. “Kabirr...... ” Na ambaci sunansa ina maida numfashi. “Kin san shi ne?” Wannan karo na ji abunda ya fada hakan yasa nai saurin gyada masa kai na juya da sauri fuskanci kofar shiga Jifatu din. “Kuka fa kike” Da na taba fuskata sai na ji hawaye masu zafi suna sauko min, da sauri na share hawayena na karasa ciki sai ya biyo bayana, har na yi zaben abunda za mu siyawa Hajiya ban daina hawaye ba, babu yadda ban yi ba dan na tsaida hawayena amman abu ya ci tura. Na riga shi dawowa cikin motar na zauna kamin ya biya kudin siyayyar, a front na zauna ina ta kallon Kabir da ke mikawa masu zuwa gurin hannu idan aka ba shi sai ya koma ya zauna, idan ya hango wani ya sake tasowa, kallonsa be haifa min da komai ba sai bakinciki da kuka mai tsanani? Rayuwarsa da baya ta dawo min, ina ta ganin murmushinsa da kulawarsa a kaina. Mutumen da ke da son kwaliya ga tsafta yau shine a wannan halin? Ina matarsa? Ina mahaifiyarsa? Ina danginsa? Miyasa suka bar shi haka babu kulawa? Hango Abdulhamid tafe yasa na share hawayena na yi saurin gyara fuskata, gidan baya ya bude ya saka ledar sannan ya dawo mazauninsa ya tashi motar, har muka isa gida be ce min komai ba yana farkin na bude motar na fita ina shiga falo wani sabon kuka yai min lale marhabun hakan yasa na nufi kitchen da sauri na wanke fuskata. “Ba zan hana zuciyarki tausayin wani ba, amman yana da kyau idan za ki ji tausayinsa ki yi a bayan idona ba gaban idona ba, na ji zafi sosai Halima ace hawayen nan saboda wani namijin kike zubar da su ba ni ba, abunda ba ki taba sani ba shine ina da tsananin kishi, ina kishin ace matata ta kula wani ba ni ba, I'm sorry to say yaran nan ma idan na tuna ba da ni kika haife su ba ina jin babu dadi, saboda ina tsananin sonki kuma ina kishinki, na san idan nai shiru zan cutu ne kuma na kwari kaina ke kuma kin kasa gane haka....” Magana yake min a yayinda yake tsaye a kofar kitchen din yana kallon bayana ni kuma ina kallon windows din kitchen wasu sabbin hawayena na sauko min. Ban yarda na jiyo ba har sai da na ji motsi ficewarsa daga kitchen din, sannan na dawo dakina na shiga bandaki nai kuka mai isa har sai da na ji amai ya taso min sannan na sassautawa kaina, sai dai ban samu salama ba har sai da nai aman sannan na hada ruwan nai wanka na shirya cikin kayan bachi na hau gadona na kwanta, a yanayin yadda ya nuna min bacin ransa ban yi zaton zai zo dakina ba, domin haka Aminu yake min a duk lokacin da muka samu tsabani, sai dai a mamakina sai ga Abdulhamid ya shigo dakina ya kwanta bayana yana sumbatata ya saka ni a kirjinsa ya rumgume ni sosai. “I Love you” Shine abunda na san ya rada min a kunne kamin bachi yai gaba da shi, ni kan har kusan biyu saura na dare ban yi bachi ba, babu komai a duniyata sai tunani da damuwa. Kiran sallah farko muka farka shi ya tafi masallaci ni kuma na nai sallah a gida, Misalin takwas muka karya sannan na shiga nai wanka shi ma ya shirya muka fito da zimmar zai aje ni gidan Hajiya ya wuce gurin aiki, ya lura da yadda na saka sakewa tun jiya damuwa karara a fuskata sai dai be min magana ba har muka isa. Tare muka shiga cikin falon sai muka same Hajiya zaune a kujera daya ita da Abdallah, tun da na kalleshi sau daya ban sake kallon inda yake ba har na zauna sai dai jikina yana ta ba ni cewar idonsa na kaina, ni kam na manta when last na saka Abdallah a idona ma dan ni har na manta da shi a duniyata. “Hajiya ina kwana” Ya mika mata gaisuwa ina dan risinawa, sai tai kamar bata ji ba ta maida hankalinta gurin Abdulhamid da ke magana da Abdallah. “Lafiya kake karyawa a nan” “As you know ko Madam tana nan ina karyawa a nan ai balle yanzu da tai tafiya” Yadda Abdallah ya amsawa dan'uwansa sai da abun ya ban mamaki domin babu alamar shauki ko wani far'a a tare da shi. “Matarsa bata nan taje Kaduna gurin biki” Hajiya ta amsawa Abdulhamid, sannan ta kalli inda nake ta dauke kai kamar ta ga wata makiyiyarta. “Hajiya ina kwana” Na sake miki mata gaisuwa,wannan karon ta amsa amman sai da ta dauki lokaci, ban damu ba daman tun da na auri Abdulhamid na lura da Hajiya kamar bata na'am da ni, ledar siyayyar da muka mata na tura mata gabanta sai kawai ta kalli ledar ta mike tsaye ta nufi dakinta tana fadin. “Kai ma ka karya ko na kawo maka abun kari” “A a ni kam sai da muka ci abinci muka fito gida” Ya fada yana kallona da murmushi a fuskarsa, ni ma murmushi nai masa kamin na maida dubana gurin roben da ke saman glass table din da Abdallah ya aje mug din hannunsa. Farin zobe ne mai kamar na silver da alphabet din A a ciki, alphabet din baka kamar na wacan zoben da na gani a daren bakinciki. “Kin ji sai na dawo zan zo na dauke ki” Abdulhamid ya fada min haka bayan ya mike tsaye, kai na gyada masa sai ya shiga dakin Hajiya yai mata sallama ya fice, kamar fitarsa na ke jira nai saurin kai hannu na dauki zoben da ke aje, da sauri Abdallah ya miko hannunsa fuska a hade ya rike hannuna. “Ba ni zobena” “A ina ka same shi?” Nima na tambaya rai a hade cike da tsananin mamaki, a maimakon ya amsa min sai kawai ya watsa min wani kallo da ban san ma'anarsa ba, tunani be tunatar da ni cewar a falon Hajiya muke ba, ban kawo a raina cewar Abdulhamid zai iya dawowa ba, ban damuwa da rikon hannu da karfi da Abdallah yai ba saboda hankalina ya dauku akan zoben da son sanin dalilinsa, daman ya san za mu zo da har yasa ya cire zoben ya aje a inda zan gani ko dai na yi gamda da katar din ganin ne? Motsi muka ji daga bakin kofar shigowa falon alamar za a shigo hakan yasa yai saurin sakin hannuna ya sake miko min dayan hannunsa. “Ba ni na ce” Ya fada a tsawace wanda hakan yai daidai da shigowar Abdulhamid a falon. “Minene?” Ya fada yana kallon yanayi da nasa. Da sauri na saki zoben ya fadi kasa shi kuma ya mike tsaye ya kai hannu ya dauka ya fice zuwa dakin Hajiya, a sannan Abdulhamid ya karasa kusa da ni ya miko min wayata yana kallon fuskata. “Ga wayarki” Ya miko min yana aje mumfashi a hankali sannan ya juya ba tare da ya sake ce min komai ba ya fice, dafe kaina nai gabana na mugun faduwa, faduwar da ba ban san ta Minenen ta fargabar kar ya zargi wani abu ko kuwa ta fargabar ganinmu ko kuma ta fargabar zoben da na gani a hannun Abdallah? AHMAD POV. Kansa a kasa yake sauraren Momy, idonsa sun rikide gaba daya saboda bacin rai, ta ya yanzu Momy za ta zo masa da wannan maganar? Wani irin magana ce wannan wacce hankali ba zai dauka ba, taya zata hana shi auren wannan saboda kawai ita Shuwa ce? “Wallahi ance mallake miji suke ni sam ban yarda ka aureta ba ka nemo mata” Dagowa yai ya kalleta cikin tsananin bacin rai da damuwa. “Amman tun farko da na fada miki family yarinyar na fada miki wacece ita ya kamata ki hana ni ba sai yanzu da yar mutane ya kamu da so na ba, har na gaisa da mahaifita sun yi magana sun ce na turo magabata sannan ki kawo wannan maganar haba Momy wannan na reason ba ne.... ” Zare masa ido tai ta wurgarda remote din tv a kujera. “Idan a gurinka ba komai ba ne, ni a gurina komai ne, ba zan bari ka auri yarinyar da zata mallake min Kai ba, ka juya min baya ni da Baby Namra ba zai yiyu ba” Tana kai wa nan ta mike tsaye ta nufi upstairs tana fadin. “Ai dole ne idan za ayi aure ayi bincike ba zan yarda ka auro min yarinyar da zata canja ka ba, ko wacce zata zo ta kashe ka ta kwashe dukiyarka ba, mata ba abun yarda ba ne musamman na yanzu.... ” Tana shigewa dakinta, kanwarsa ta taso ta dawo kusa da shi ta zauna tana masa rada. “Wallahi ka kai je ka kaita gurin wani boka ayi mata asiri ta yarda ka auri wannan yarinyar... ” Duk yadda yake cikin bacin rai sai da ta saka shi murmushin dole saboda wautarta, sannan ya mike tsaye yasa hannuns aljihu ya fice daga falon harabar gidan ya fito ya jingina da motar yana cikawa bakinss iska ya san halin mahaifiyarsa idan ta ce bata yarda da abu ba, babu yadda za ayi ta yarda da shi har abada, idan kuma bata son abu babu mai cilasta ta so shi, shi yanzu ya zai yi da matsalarsa a duk lokacin da ya taso da maganar aure sai ta nuna bata so, ya kasa fahimta wace irin uwa ce ita? Miyasa ko da yaushe take kishin ganin yayi aure? Ko take kishin duk matar da ya aura? Forget about the past shi yanzu ya zai yi da yar mutane idan ya barta za a ce ya yaudareta daman can ba auren yai niya ba, after that idan ya nemo wata ita ba Momy zata iya cewa tana da wata matsalar. Kansa ya daga yana kallon katon gidan mai cike da kayan alatu, mi mahaifiyarsa ta nema ta rasa? Then miyasa shi ba zata bar shi ya samu nasa farincikin ba? Miyasa ba zata bar shi ya gina rayuwarsa ba? Kara wayar da ke hannunsa tai alamar sako number Momy ce. _Ka dawo karfe 8pm_ Yana karanta sakon ya shafa kansa yana busar da iskar bakinsa. “Ohhh Momy ni fa ba yaro ba ne why all these rules?” Bude motarsa yai shiga ransa babu dadi yai ma motar key ya danna horn aka bude masa gate ya hau titi ba tare da sani inda zai je ba, gari yake ta zagawa a titi, maganganun Hajiya ne suke ta masa yawo a kai shi ya rasa gane abunda yake damun mahaifiyarsa. Har ya daga wayarsa ya kira abokinsa wanda ya saba labarta masa damuwarsa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, he decided ya faka motarsa gefen titi yai relaxing cikin motar for a while sannan ya koma gida, after ya faka motarsa gefen titi ya sauke gilashin motar ya kwantar da kujerar motar tare da cire hular kansa. Wata yarinya ya hango gefen titi tana kuka, sai da ya kalli ko'ina yaga babu kowa a tare da ita sannan ya bude motar ya fita ya nufi inda take. “Ke lafiya? Me kike yi ma kuka?” “Bacewa nai” Ta amsa masa cikin kuka. “Garin ya?” “Muna tare da Mama Hafiza mun zo biki shine kuma yanzu ban ganta ba, tace na zo bakin titi na same ta mu wuce na zo ban ganta ba kuma na koma ban gane gidan da na fito ba” “Ina Mamanki?” “Tana can gidanta” “Babanki fa” “Ban san inda yake ba” “Rasuwa yai?” “Aa tunda ya saki Momy mu ban sake ganinsa ba, ita kuma Momy mu ta auri wani...” The way da tai masa maganar sai ta bashi tausayi, ya san da ace tare take da mahaifiyarta ko mahaifinta ba zai su tafi su barta ba ko kuma su yi saken da zata bata, risinawa yai yana kallon fuskarsa. “Miye sunanki” “Namra” “Wow cute you sunan yata, yanzu za ki iya gane gidan ku?” Ta girgiza kai alamar no. “Wace unguwa kike zaune?” “Yan magurora” “Gurin wa?” “Karkar mu” “Ita ke rikonku?” Ta gyada masa kai. “To yanzu kin san yadda za mu yi? Zan saka ki a motata na kai ki gidanmu da safe sai na kai cigiyarki, ko kuma naje unguwarku na nemi nai unguwar na damka masa ke kin yarda” A take ta gyada kai sai ya rika hannuta ya nufo motarsa da ita ya saka ta shi ma ya zagaya ya shiga. “Ita Mamanki wane unguwa take?” “Ban san sunan unguwar ba” “Ba ki taba zuwa ba?” “Na taba zuwa sau daya” “Sau daya?” Ya tambaya yana kallonta da mamaki sai ta gyada masa kai. “Miyasa sau daya kawai?” “Kaka tace mana wanda ta aura baya son yara shiyasa bata tafi da mu ba” Tabe baki yai yana yi ma motar key. “Ji wani irin selfishness dan Allah mutum be son yara kuma ka yi aure ka tafi ya bar su, yanzu nan idan ni bana kwarai ba ne shikenan kin fada mugun hannu mtsszzzzzzzzzzzzzzzzz” Yaja wani dogon tsaki yana jin kamar ace shine uban yarinyar ya ci mutunci uwar, ko da yake shi miyasa uban ma ya bar su hannunta. “Imagine ayi ta haihuwa bana iya kula da yara ko ba a son dawainiya da su, shi uban baya so ita ma bata so” Ya fada yana mai jin haushi iyayen duka biyu. ‘Ba ma gidan uban da zan kai ki cigiya, idan suna son ki su nemi ki da kansu’ Wannan karon a zuciyarsa yai maganar. Sannan ya cigaba da tuka motar, abun da yaro ta man ta sha kuka ta koshi kamin ya isa gida har ta yi bachi. After yayi farkin ya zagayo ya bude motar yana kokarin daukarta ya dora a kafadarsa ta farka, sai dai hakan be hana shi daukarta ba ya nufi cikin gidan da ita, kamin ya karasa Baby Namra ta fito daga falon tana masa oyoyo. “Daddy sannu da zuwa” “Yauwa Baby” Ya fada yana shafa kansa da dayan hannunsa tare da murmushi. “Daddy wacece wannan?” Ta tambaya tana kallonsa be amsa mata ba sai da ya shiga falon Hajiya ya sauke Namra saman kujera. “Je ki kawo mata ruwa ta sha, kawa na samo miki” Sai ta bata fuska. “Ni Allah ya tsare ni ba kawata ce ba” Ta fada tana nufar hanyar kitchen, shi kuma yai murmushi yana kallon Namra wacce ta takure guri daya kamar mai jin tsoro, shi sai yanzu yake ganin kamar ma ya taba ganinta. “Ina ka samo ya?” Hajiya da ke tsaye upstairs tana latsa waya ta tambaya daga can inda take tsaye tana kallonsa. “Wasu mahaukatan iyaye ne da ba su san darajar yaya ba suka jefar da ita” “Jefarwa kuma?” Hajiya ta tambaya tana saukowa daga stairs din. “Yes” Ya amsa mata yana maida dubansa gurin Baby Namra wacce ta fito kitchen rike da kofin ruwan. *Khadija Abubakar Alkali* 7/20/21, 8:33 AM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 1️⃣9️⃣ Labarin GOBE NA ba labari irin wanda na saba yi ba, shiyasa tun kamin na fara sakinsa na fada muku cewar rayuwar aure ce mai cike da kalubale, idan ba ku manta ba inkiyar labarin ZAWARCIN HALIMATU, labari ne na rayuwar kala kala ta gidan aure da zawarci, da kuma rikon yara da kula da tarbiyarsu, zancen dan Allah Candy kar ayi kaza ko ki canja kaza be taso ba, matukar ana son labarin ya tafi a yadda aka tsara kuma a isar da sakon da ake son isarwa. GOBE NA ba labarine na zallar soyayya ba, yana tafe ne da kalubalen na rayuwa, duk irin halin da Halimatu take ciki ko zata kasance a ciki akwai mata da yawa da suka dade da shiga cikin wannan halin, ko suka fita shiga matsala ma. Wallahi a three weeks ago akwai wacce ta kirani tana kuka tana fada min abunda akai wa Namra a labarin haka akai wa yarta kuma har yau babu wanda ya sani mijinta ya hanata magana, secondly mijinta kamar Aminu yake, a lokacin da ta ba ni labarin mijinta sai da kaina ya daure Wallahi. So akwai mata da yawa da suke fuskantar rayuwar gida aure kala kala, ko da ba mu tabo duka ba ya kamata ace muna taba wani bangaren na rayuwarmu ta yau da kullum ai. Labarin zai tafi a yadda na tsara shi ga wanda yaji zai iya bi fine. *** *** *** “Aa Gwarzo wace uwar ce zata jefar da yarta haka nan kawai? Ka taba ganin bolar yaya?” Momy ta fada bayan ta zauna tana kallon Namra. “Oh Momy ba ki ji inda na samo ta ba, uwarta na son ta zata jefar da ita” “Idan ma haka ne ai ba laifi uwar ba ne, na uban ne akan me zaka bar yarinya na tsawon lokaci ba ka neme su ba? Taya ma zaka bar ma mace dawainiyar yara bayan ba da su ta zo ba?” “Ita na fa uwar da laifinta” “Baka san abunda ya fito da ita daga gidan mijin ba, ba duk mace ce bata son yaranta ba ni ban yarda akwai mace da bata son yaranta ba, wata kila ma hankalinta yana can tashe” “Ko dai zan maida ita sai gobe sai jikinsu ya fada musu, ko goben ma sai da maraice” Ya fada yana shafa kan Namra. “Yarinya kyakkyawa suna son wufintar da ita” Momy ta yi murmushi. “Ya sunanki?” “Namra” Ta amsa hankalinta kwance kamar ta san su. “Allah sarki Baby Namra kin samu takwara” Baby Namra dai bata komai ba sai wani shigewa take jikin Momy. “Sai gobe zan bada cigiyarta a radio idan sun ga dama su zo nan su dauke ta” Ya fada yana mikewa tsaye. Sai ita Namra ta mike tsaye zata bi shi. “Zauna nan Momy zata kula da ke” Momy ta mika mata hannu tana murmushi. “Zo nan jikata yar albarka” Ba musu taje ta zauna saman kujerar sai Momy ta dorata a kafafuwanta. “Ajikin nawa?” “Uku” “Wace makaranta kike?” “Gwarzo International school” Momy ta yi dariya, Ahmad ma da ke kokarin fita juyowa yai ya kalleta. “Wow i feel it tun farko na ji kamar ina da alaka da ita, ashe yarinya yar makarantar mu ce shiyasa take da natsuwa” Ya fada yana wani miskilin murmushi. Momy dai ta girgiza kai tana kwantar da Namra a ciyarta. “Idan kuma iyayenki sun ba mu ke sai mu rike abar mu mun kara samun wata daman ina son yara” “Da gaske?” Namra ta tambaya Momy ta gyada mata kai. HALIMATU POV. Ban samu wani sakewa da ya kamata ko wace matar da ta yi a gidan uwar mijinta ba, saboda ban ga fuskar Hajiya ba, kamar wata bakuwa haka na zama a cikin gidan. Har aka kira azahar babu komai a zuciyata sai tunanin dalilin tsanar da Hajiya tai min daga auren dan ta zuwa yanzu amman ban samu dalili ba, a iya tunani wanda ya ce yana son naka ya gama da kai ko da kuwa Abdulhamid yana da lafiya kamar kowa ballanta ta san yadda lalurar danta take amman na amince a haka na ce zan zauna da shi a kalla na cancanci girmamawa da ganin mutuncin da kauna daga gareta. Amman ban samu haka ba sai wulakanci da tsana da suka boyo baya bayan a baya kuma ba haka take min ba. Wata kila kuma jinina ne a haka domin Hajiya ma mahaifiyar Aminu da kanensa basa kaunata saboda gani suke na tare komai na mallake musu dan'uwa wata kila ita ma tana min wannan kallon ne. Bayan na shiga bandakin tsakar gidan nai alwala na yi sallah a saman dankwalina, ban jira ta ce min na shigo ciki ba,kamar na san ba zata ce na shigo din ba domin ko ruwa bata ba ni ba, abincin rana ma da aka gama kanen Abdulhamid ne suka kawo min. Ina zaune ina lazimi da hannuna Abdulhamid ya kira cikin sauri na daga kiran domin duk na tsawwala da zaman gidan na yi zaton zai fada min na fito mu tafi ne kamar yadda yace zai dawo ya dauke ni. “Aiki ya min yawa Haima, sai da la'asar zan zo daukarki” Bana son na kara zama gidan ko da na minti talati ne a yanzu hakan yasa nai saurin yi masa requesting. “Ko na tafi gidan su Hajara kamin ka zo? Ba nisa sosai daga nan zuwa can daman tana ta min complain wai ban je gidanta tun da nai aure” “Bana son ki hau achaba” “Napep zan hau” “Okay sai kin dawo” “Na gode” Har dakin Hajiya na shiga nai mata sallama ta amsa min ciki ciki, na fito raina babu dadi na nufi gidansu aminiyata Hajara, har ga Allah ban jidadin yadda mahaifiyar mijina take min ba, domin ni mace ce mai son dace da uwar miji yadda yake ganin wasu iyayen mijin suna nunawa surukansu kulawa abun har burgeni yake amman ni na kasa samu a aurena na farin a wannan ma ban dace ba. Na isa gidan a Napep kamar yadda na fadawa Abdulhamid, sai dai ban jidadin samun mijinta a gidan ba, domin kunyarsa na ke ji tun daga lokacin da ya nuna yana son ya aure. Da sallama na shiga shi ya fara mika min gaisuwa sannan na zauna saman cushion dinta shi kuma ya tashi ya fita. “Amarya ba kya laifi yau an tuna da mu” “Kullum ai kina cikin raina” “Ni ai fushi na ke da ke ni da nai miki kyautar miji sukutun kika gujemu kika kama dan'uwanki” Ta fada bayan ta dire min kofin ruwa, murmushi nai sai na maida kaina kasa ina kallon carpet dinta. “Kawata kamar kina cikin damuwa” Dagowa nai na kalleta ina ta tunani ta ina za ki fara dora mata bayani. “Ina ciki ba daya ba ma, amman naga kamar Abban Afrah na nan....” Rufe bakina ke da wuya muka ji tashin motarsa, sai ta tashi ta sakawa kofar key sannan ta dawo kusa da ni ta zauna tana kallona cike da damuwa. “Ban san wane zan fara fada miki ba, tsanar da mahaifiyar Abdulhamid tai min ko kuma ganin Kabir da nai a titi yana yawo a haukace? Ko fyaden da akai min, ko kuma son yayana da Abdulhamid ba yayi?” Ina maganar hawaye na sauko min, rikicewa tasa ka ta kasa ce min komai, har na wadansu dakiku. “Halimatu akai miki fyade ko kuma wanda akai wa Namra kike magana?” “Ni dai akaiwa” “How, when? Waya miki fyade?” “Ban sani ba Hajara shi nake kokarin sani yanzu, kaina gaba daya ya kulle” “Fada min yaushe abun ya faru?” Ban boye mata komai ba tun daga a to z ganin ita din ta zama kamar yar'uwata, kuma daman can ina bukatar abokin tattaunawa. “Amman miyasa kika boye masa Halima? Miye ribar boyewar? Mijinki ne kuma shi aka zo nema da ba a tararda shi ba akai miki haka ai ya kamata ya sani” “Hajara kina ganin idan na fada masa zai zauna da ni? Ba zai iya zama da ni ba, na ji kuma na gani da yawa akwai matan da suke fansar ran mazajensu a yi mu su fyade saboda kar a kashe mazanjensu daga karshe mazanjen su rabu da su su kasa zama da su, babu namijin da zai ji anyi ma mace fyade tana a gidansa kuma ya cigaba da zama da ita, ballanta Abdulhamid da baya iya komai da mace” A firgice ta kalleni. “Kamar ya baya iya komai?” Tun daga farko nai mata shimfidar labarin har zuwa auren mu. “Amman Halimatu kin yi wauta, akan mi za ki auri miji kamar wannan? Ba ki san za ki iya jefa rayuwarki cikin hatsari ba?” “Na riga na raba tun a gidan Aminu yana da lafiya amman sai mu kwashe wata hudu uku har biyar be neme ni ba, shi ma da yake da lafiya na daure balle wannan?” “Ba daga nan take ba, a can baki da kwanciyar hankali, a nan kuma hankali a kwance yake za ki ci ki koshi dole wata rana ki ji kina bukatar mijinki a kusa da ke, bayan rashin lafiyar na Halimatu mutumen baya son yara kuma kika aureshi a haka, and kin san dan'uwansa yana son ki kuma kika take hakan kika aure shi? Fada min taya mahaifiyarsa zata so ki wata kila ita din ta san dan'uwansa yana son ki amman kika zabi ki auri daya ki bar daya, wanda be dace ki yi haka ba tun daga farko” Hannu na saka na rufe fuskata ina kuka a hankali. “Ki fada masa gaskiya na san ba zai gujeki ba, duk namijin da za ayi ma wannan Sadaukarwar ba zai taba gudunki saboda wannan ba, musamman idan yaji cewar shi aka zo nema” “Idan kuma ba shi aka zo nema ba fa Halima? Idan wanda yai min fyade ya zo ne saboda kawai yai min fyade fa?” “Akwai wanda kike zargi?” “Dan'uwansa?” Ta yi saurin rufe baki tana kallona. “Ya taba miki maganar banza ne?” “Be taba ba, amman zoben da na gani a hannun mutumen da ya min fyade yau na ganshi a gurin Abdullah har na kai hannu na dauka ya ce na bashi” “Amman daman can yana da dabi'ar neman mata ne? Kuma jiya kawai kika gan shi da zobe?” “Ban san shi da wannan dabi'ar ba, ko a lokacin da yake ta son na kashe aure be taba min maganar banza ba, ni ban taba lura da hannubsa ba balle har na tantace kalar zobensa, amman ba a shaidun mutum kuma yanzu yana ganin na auri dan'uwansa babu yadda zai yi” Hannu ta kai ta dafa kafadata. “Ki kyautata masa zato Halimatu ganin zobe kawai ba zai tabbatar da cewar shi din ne ba, ba ayi ma mutum daya zobe kuma idan har shi din ne mi zai saka ya aje zobe a inda za ki gani? Mi ma zai saka ya nemi yi ma matar dan'uwansa fyade? Dan'uwan ma twin brother? Haba Halimatu” “Zai iya mana ko kin manta abunda Sadi yai ma Namra?” “Saboda Sadi ya lalata diyar yayansa ba shi yake nufin Abdallah yai ma matar yayansa fyade ba, duk yadda duniya ta lalace akwai na gari, duk kuma yadda duniya take ciki da mutane kirki dole akwai bata gari, karki saka ranki a rudu ki sake janyo wata matsalar a tsakanin yan'uwa, ni yanzu abunda na ke so da ke ki shirya gobe zan zo na rakaki kije asibiti a duba lafiyarki domin irin waennan mutane wani lokacin baka san ko suna dauke da ciwo ba, kuma baki sani ba ko ciki ya shige ki tun da abun ya faru ya kamata kije ayi miki wankin mara” A take hankalina ya tashi da Hajara ta kawo min maganar ciki, dacan ban kawo hakan a raina ba hankalina ya karkata ne a gurin fyaden kawai ba dan kuma na san bana iya daukar cikin ba, lallai na zama doluwa wani lokacin haka nake abu kamar marar kwakwalwa kuma marar ilmi, tabbas idan nai ciki na shiga uku kuwa. “Yaushe rabon da ki ga al'adarki? Idan ma akwai cikin ai za ki gane” “Bana iya ganewa saboda ina wata shida ban yi al'ada ba wani lokacin biyar, idan ina al'ada akai akai sai idan ina shayarwa, shiyasa na ke saurin daukar ciki idan ina shayarwa, amman bana jin wata alama da ke nuna ina da ciki bana jin komai a yanzu” “Duk da haka muna bukatar zuwa asibiti saboda cire kwankwanta, ai wani cikin sai ya fara girma yake wahalarwa kin manta cikin Adnan? Shi da ma yake cikin farin amman ba ki sha wahala kamar sauran ba?” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u” Shine abunda nai ta maimaitawa na dafe kaina ina kuka. “Ki kwantar da hankalinki Halimatu, akwai mata da yawa da aka ketawa haddi ba ke kadai ba, wasu ta dalilin wani abu kalilan, ba ke kadai ce a cikin wannan halin ba, amman shawarar da zan baki ki fadawa mijinki gaskiya idan ma ya zabi rayuwa da ke ai ba akanki farau ba” “idan na bar wannan gidan auren Hajara ban san ina zan sake shiga ba, ban san wa zan fadawa ba, a can mi zan tarar, idan kuma na zauna zaman gaban iyaye ba dadi da shi ba ko ga budurwa balle a gurin mai yara kamar ni, bana son a fara kirga min aure Aminu ma idab ya samu labari ai zai ce gashi nan har aurena ya mutu tun ba a je ko'ina ba, zaman zawarci ba shi da dadi Hajara dan zaman da nai na iya sakin da Aminu yai min zuwa auren Abdulhamid ban jidadin ba ga natsatsin iyaye, ga lalurar yara tun da mahaifinsu babu ruwansa da su, bana son na fadawa Abdulhamid wannan abun ya sake ni saboda haka, idan ma har na samu cikin zubarwa zan yi a sirrance na cigaba da zama da mijina, ina jindadin Abdulhamid kuma ina son sa bana son shiga wata matsalar a yanzu, idan na fada masa ba lallai ne ya yarda ba, saboda ba ni da wata shaidar, wata kila ma ya zargi cewar na kasa tsare kaina ne na kasa hakuri shiyasa na aikata hakan yanzu kuma nai masa wannan karyar, tun da Allah ya rufe min asiri kara na rufewa kaina ko na samu salama” Kai ta gyada min tana share hawayenta. “Hakan yayi idan ma kin samu cikin ki zubar kawai mu rufe wannan sirrin, Allah ya dafa miki ya rufe mana asiri” Jinginawa nai da kujerarta ina jin zuciyata na wani irin kona marar misaltuwa. Hajara ta yi ta saka min maganganun na kwantar da hankali da karfafa guiwa a gareni har zuwa lokacin da Abdulhamid ya zo daukarta, ba ni kadai ba shi kansa na lura kamar baya cikin walwala sosai, ni da shi mukai shiru cikin motar kamar wasu kurame ni da abunda nake ta sakawa a zuciyata shi kuma yana ta tukinsa yana kallon titi. Daf da za mu isa kiran Mama ya shigo wayata, ba tare da tunanin komai ba na danna picking na soma magana cikin muryar da ke karantar damuwarta ga mai saurarenta. “Hello Mama” “Halimatu Namra na gurin?” “Aa tace aka kawo ta ne?” “Aa mun dauka ko taba nan ne, Teema taje gidanki bata tararda kowa ba” “Eh mun fita ne tun safe lafiya” “Namra ce ba a gani ba tun jiya” Kamar saukar aradu haka na ji maganar ban san lokacin da na ambaci sunan Ubangijina da karfi ba, wanda hakan yasa Abdulhamid kallona da sauri. “Kamar ya ba a ganta ba? Ina ta shiga? Waya fita da ita?” “Tare da Hafiza suka je biki wai Hafiza tace ta same ta bakin titi bata zo ba, kuma taje gidan bikin ta duba bata can sun jiya muke ta nemanta har makarantar anje bata can” “Amman tun jiya Mama ba a fada min ba?” Na tambaya idanuwa na kawo ruwa. “Wallahi saboda tsoron kar hankalinki ya tashi ne yasa ba a fada ba” Sauke wayar nai ina kuka ina jin wani irin tashin hankali na ratsa ni marar misaltuwa har gumi karyo min yake. “Lafiya?” “Namra ta bata” “Subhanallahi garin ya?” Ban iya ba shi amsa ba saboda kukan da ya ci karfina. “Yi hakuri za a ganta In-Sha-Allah bari na sauke ki gida yanzu” Ya fada yana miko min tissue. 7/21/21, 10:43 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣0️⃣ DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤ son so Fisabilillahi💞😍 *** *** *** Kamin mu isa gidan har wani jiri nake jin yana dibana, zuciyata kam kamar ta fashe ga wani uban zafi da kirjina ke yi, kaina sai sarawa yake.    Ko parking din kirki be yi ba na bude motar na fita na shiga cikin gidan cikin tashin hankali kamar yadda su ma na tararda su cikin tashin hankali, gaba daya ban tarardar yan mata gidan mu ba da samarin biyun duk sun fita neman Namra Baba na tsakar gida rike da sandar damuwa kara a fuskarsa. A bakin balcony na zauna na dafe kaina. Inna na min bayanin yadda abun ya faru da guraren da aka je nemanta bata can. Mahaifinta ne ya fado min a rai. “Ko Aminu ya dauke ta ba a sani ba?” Na fada ina kallon Mama, a yayinda Abdulhamid ya shigo yana gaisawa da su. “Mi zai saka Aminu ya dauke ta, mutumen da tun da ya bata baya be sake dawo ko tambayar lafiyarsu ba” Cewar Inna sai Mama ta karba mata. “Nima dai shi na gani, kuma a ina ma zai ganta?” “Ko tana gidan Abdallah?” Na fada ciki ina hawaye. “A a bata can tun dazun da shi ake ta nemanta, shi ma yace kar a fada miki saboda kar hankalinki ya tashi, yanzu yanzu ma suka fita da Samira har.... ” Baba ne ya tari numfashin Inna da ke maganar yana fadin. “Ku ba Allah cigiya In-Sha-Allah za a ganta, idan ba dan sake irin na Hafiza ba taya zaka fita da yaro ka ce ya same ka titi bayan yaron be san gurin ba” Komawa nai na zauna a gurin na fara rare musu kuka, idan ba kukan ba ban san abunda zan yi a yanzu ba. “Bari naje na duba makarantarsu...” Cewar Abdulhamid yana kokarin juyawa sai Inna tai karaf tace. “Ai har can Abdallah ya tafi....” Baba ya sake saurin tarar numfashinta. “A a be je can ba, islamiyarsu dai yaje, zaka iya zuwa can ka duba” Sai da Abdulhamid ya fice sannan Baba ya hau yi ma Inna fada wai ta cika tsoma baki a maganar da babu ruwanta. Ni kam sam ban ga illar maganarta ba kamar yadda ita ma kanta da Mama ba su ga haka ba, wata kila kuma akwai abunda Baba ya hango. “Mama zan je gidansu Aminu na duba ko tana can” “To da Abdulhamid din be wuce ba ai sai ya karaki” “A a shi yaje can din ni zan duba gidansu Aminu” Na bawa Mama amsar ina mikewa tsaye. “Mi zai kaita can ma” “Nema ne ai Mama” Ban tsaya na jira su kara kashe min jiki ba na zari jakata na fito cikin gidan kamar wata mahaukaciya. Kamin mai napep din na kai ni gidan su iyayen Aminu har na matsu abunka da wanda je cikin tashin hankali. A bakin gate ya tsaya ni kuma na shiga cikin gidan da sallama. Kana gani na kasan hankalina ba a kwance yake, ba Hajiyar Aminu ba ko kanensa sun yi mamakin ganina a cikin gidan, ban musu magana ba kamar yadda suma suka saki ido suna kallona kamar wata bakuwarsu. Har cikin falon na shiga na gaishe ta ita ta amsa min da dan mamaki sannan na tambaya ko Namra tana nan. “Namra da kuka kekashe kasa ke da yan'uwanki kuka ce ba za ku bayar ba, bayan kun gama ikirarin an bata ta mi za mu dauko ta tai mana? Ai mun yafe miki ita ki dafa ki ci ko ki saida babu abunda za mu da ita” Mikewa nai tsaye cikin bacin rai na ce. “Ke kika fi kowa abun yi da ita saboda jininki ce, kuma tambaya kawai na zo saboda idan tana nan na tafi da ita saboda kula da tarbiyar” Mikewa tai tsaye ta nuna ni da yatsa. “Ke Halima ki shiga hankalinki karki ce za ki so har cikin gidan nan ki min rashin kunya, ki bar ganin an kyale ki Wallahi kika min iskanci sai an karbe yaran nan daga hannunki” “Da kuwa kin bude abunda yake rufe, da kin tona asirin danki dan sai duniya ta ji abunda ya aikatawa yar dan'uwansa” Na bata amsa a fusace sannan na juya na fice na barta tana ta surutanta, inda na bar mai Napep din a nan na same shi. “Kai ni igala quarters” Na fada bayan an shiga Napep din, yana tafiya ina nuna masa inda za abi har ya sauke ni a kofar gidan Aminu, bayan Hajiya ban san ko tana gidan ba neman be ba a cire tsammani wata kila ma ya ganta a wani gurin ko kuma ita ta fadi can a kai ta ba tare da mun sani ba.   Mai gadin yai na'am da ganina yana ta washe min hakora da tambayar yaushe gamo. “Dan Allah Malam Garba tambaya nake ko kaga Namra a gidan nan?” “Namra dai ta wajenki?” “Ita, ta bata tun jiya” “Subhanallahi Wallahi ban ganta ba, amman ki tambayi Alhaji ai yana ciki, Hajiyar ma tana ciki” Fadar Hajiya ma tana nan ciki ya tabbatar da cewar Aminu yayi sabon aure kenan. “Aa bana bukata na gode” “Allah ya tsananta rabo” “Amin” Na amsa ina hawaye, ina shiga cikin napep din kuka ya kwace min. “Hajiya Lafiya?” “Yata ta bata tun jiya kuma ba a ganta ba... ” “Subhanallahi a ina?” “A gurin biki taje ita da kanwata” “Aiko na ji ana cigiyar wata yarinya a fm dazun, amman ban sani ba ko ita ce” Da sauri na kalleshi. “Yaushe? A ina? Ya sunanta?” “Wallahi ban rike sunanta ba amman dai dazun ina sauraren fm a napep na ji ana cigiyarta” Ya karasa yana kunna fm din. “Dan Allah ka taimaka ka kai ni can mu binka kasan inda fm din take?” “Eh na sani Allah yasa ita ce” Kamar nai tsuntsuwa na tashi na isa fm din haka naji, abun ka da guri mai nisa daga igala quarters zuwa Damba sai tafiyar ta zame min kamar ta wani gari, muna isa na fita na shiga ciki na fara tambayar mutane hankalina a tashe, sai wani ya shiga ciki ya duba takardun cigiyar ya rubuto mana number wayar da aka bada sannan ya fada min sunanta. Ina jin ya ambaci Namra wani dadi marar misaltuwa ya lullube ni. “Sai kinje Samaru ki tambaya gidan Alhaji Muhamad Gwarzo” “Na gode” Tun kan ya gama magana na juya da sauri na fito na shiga napep din na fada masa unguwar da zai kai ni, a hanyar mu ta tafiya kiran Aminu ya shigo wayata, na gane ne numbersa ne saboda na haddace ba dan number tana da suna ba. Har na yi kamar ba zan dauka ba sai kuma wata zuciyar ta hana ni na danna picking na kara a kunne na. “An ga Namra?” “Ashe kana iya damuwa da ganinta ai na dauka ka manta da kana da yaya” “Halima bari kiji na fada miki wallahi duk yata ta bata ko wani abun ya sameta sai na wulakanta ki, sai na sa kin yi nadamar haihuwarki da akai a duniyar nan Wallahi Wallahi dan haka ki nemo min yata tun wuri” Be jira abunda zance ba ya katse kiran, wani uban haushi ne ya cika ni har na ji ina ma dai ace ban dauki wayar ba.   Da tambaya muka gane gidan, domin number da aka bamu mun yi ta kira ba a dauka ba, daga baya ma sai aka kashe wayar. Wani irin katon gidane mai katon gate irin na manyan mutanen nan da suka ci arziki har sukai kashinsa, kai idam ma baka sani ba za kai zaton gidan fillar kai ne saboda girmansa da tsaruwarsa, ko ina na gidan an kawatashi da fulawoyi da kuma irin dagayen itacen nan masu haska gida. “Sannu Malam dan Allah yata na ke nema kuma ance tana nan” Na fadawa mai gadin bayan nai kwankwasa kofar gidan ya bude min na shiga ciki. “Ina aka ce miki?” “Ce min akai gidan Alhaji Muhammad Gwarzo” “Eh nan ne shiga ciki” Kai tsaye na doshi cikin gidan, a maimakon na shiga part din farko sai na nufi dayan part din da shi nake hango kofarsa tsabanin babban part din da na kasa ganin kofar shigarsa, wata kila kuma ta karamin ake shiga.   Kofar falon na hango a bude tun ka na karasa, na yi iya yadda shari'a tace wato yin sallama da na ji ba amsa min ba na kunna kai cikin katon falon mai cike da sanyin ac da daddadan kamshi sai dai ban fasa sallamar duk kuwa da ban ga kowa ba. Ina kokarin juyawa na fita wani mutun ya fito daga wani bangare na falon yana rike da plate da ke dauke da soyayyen kwai sai kofin tea. Wani shegen short ne a jikinsa kirjinsa kuma a tsirara dan babu riga a jikinsa. Da gila ya tambayi abunda ya kawo ni falon. “Yata ta bata aka ce tana nan gidan Alhaji Muhammad Gwarzo... ” Wani kallo na watsa min daga sama zuwa kasa sannan ya zauna ya aje plate din hannunsa a saman center table din dake kusa da shi yana cigaba da kallo, zuwa can kuma ya dauke kai ba tare da ya ce da ni komai ba. “Yata nake nema na fada maka” Banza yai min kamar ba zai amsani ba, sannan ya ce. “Idan kin ganta ai sai ki dauka” “Idan bata nan ka fada min bata nan ba sai ka wulakanta ni ba domin ba bara na zo yi ba” Na fada a fusace, ina tuna inda na taba ganinsa. Uffan be ce min ba ya dauki tea gabansa yana sha tare da maida hankalinsa gurin katuwar plasma dake manne a wallpaper falon. Juyowa nai a hasale na fito daga falon marasa na murdawa, kamin na isa dayan part din sai da na rike cikina kusan sau uku. Ina isa na zauna a gurin na runtse ido ina sauraren radadin da take min. Daker na iya tsada hankalina har na lura da kofar falon, cike da karfin hali na unkura na mike tsaye na isa bakin kofar ina kokarin kai hannu na nai knocked aka bude kofar daga can ciki. Fuskar Mutumen dazun din nan ne da ke wacan part din da na baro, sai dai wannan karon akwai jallabiya a jikinsa, mamaki ya kama ni shi din ko kuwa su ma twins ne kamar Abdallah da Abdulhamid? Ko kuma wata hanyar ya biyo ta can ciki ya isa wannan part din? Sai da nai kamar ba zan masa magana ba, sai kuma wata zuciyar ta hana ni abunka da nama. “Dan Allah yata nake nema aka ce min tana nan” Be ce min komai ba ya fito daga falon ya sauko stairs din ya nufi gurin wata mota dake fake kusa da inda nake zaune. “Tana nan ciki” Ya fada bayan ya bude motar. Unkurawa nai na tashi na nufi kofar falon na shiga ina takawa a hankali saboda abu nake jin kamar zai zubo min. Na yi mamakin karamci da sakin fuskar da na tarar a fuskar Hajiyar gidan ina yin sallama ta amsa min tana min sannu da zuwa kamar ta san ni, Namra na ganina ta taso da sauri ta nufo inda nake tana dariya. “Momy” Rumgumeta nai na lumshe ido. AHMAD POV. Da gangan yake son ya shiga motarsa ya yi tafiyarsa saboda kar ma mahaifiyar yarinyar ta ga fuskar yi masa godiya ko yi masa wata maganar. Ji yake kamar ya fada mata bakar magana son ransa aka my wufintar da yar da tai amman ba shi da damar wannan tun da shi ba uban yar ba ne kuma ba shi da alaka da ita. Ko ba komai dai ya san hankalinta ya tashi tun da ga shi har tana zubar jini.   Tun kamin ya karasa gate aka bude masa gate din, ganin wani tsaye da mota a bakin gate din gidan yasa ya tsaya ya sauke gilashin motar yana kallon Abdulhamid da na shi gilashin yake sauke. “Malam lafiya?” “Wata yarinya muke nema aka ce tana nan gidan mun kira number da aka ba da a sanarwa muka jita a kashe shiyasa na zo” “Kai ne mahaifinta?” “No ni ne dai nake auren mahaifiyarta” Abdulhamid ya amsa kai tsaye, sai Ahmad ya kalleshi da kyau sannan ya dauke kai. “To ka tsaya nan za a fito maka da matarka” Ya karasa yana kallon wayarsa. Number sis dinsa ya lalubo ya aika mata kira, in few seconds tai picking. “Sis ki fadawa matarta mijinta yana jiranta a waje” “Okay Ammn bro bleeding ta ke, ya dan jira ta shiga bandaki” “Ki fada mata na ce” Yana fadar haka ya kashe wayar ya karawa motarsa wuta ya hau titi, Abdulhamid na zaune cikin wata mai kama da Ahmad din ta budo karamar kofar gate din ta leko shi daga can cikin motar da yake zaune tace. “Kai ne mijinta?” Abdulhamid ya gyada mata kai. “To ka dan jira ta fito tana bleeding amman ta dan shiga toilet ne” “Ta ji ciwo ne?” “No i think ta samu miscarriage ne... ” Ta fada tana dan zare. “Miscarriage...?” Ya maimaita. “Yes ban dai tabbatar ba, amman kasan idan am samu tashin hankali yana iya causing wannan matsalar, amman ba lallai ne ya zube duka ba, amman dai shawara ka kaita asibiti yanzu dan tabbatarwa” Tun da ta fara yake kallon yadda take ta zuba masa zance har ta gama, daman daga ganinta irin yan matan nan ne masu surutun fadi baa tambaye ka ba. “Okay” Ya amsa mata zuciyarsa cike da mamaki, kai ta gyada masa sannan ta juya ta koma ciki, kamin ta isa falon wayar da ke hannunta tai ringing alamar kira. Soul mate ne rubuce a saman screen din, murmushi ne ya bayyana a fuskarta jikinta har rawa yake ta kara wayar a kunnenta sannan ta nufi wani bangare na gida cike da shauki tana amsa wayar. HALIMATU POV. Ban lura da jini dake zubo min ba har sai da na zauna a saman manyan cushion din dake falo, shi ma saboda Hajiyar ta yi magana ne. “Subhanallahi kin ji ciwo ne?” A lokacin da na duba sai na lura da jinin ya bata duk sawun kafata yake jini ya bata gurin. A iya sanina dai ban ji ciwo ba ban fadi ba balle na ce na ji ciwo ne, jini ba ta kafa yake min zuba ba ta cikina ne duk da kuwa da bana da tabbacin hakan domin ban ji zubowar komai ba sai jin alamar zubowar da na ji dazun ashe har ya zubo ban sani ba. “A a ban ji ciwo ba” Na amsa mata gabana na faduwa wani sabon tashin hankali na kusantata. “Allah ya tsare idan ba miscarriage kika samu ba” Hajiyar na rufe baki wata budurwar da ke zaune a dinning ta ta amsa da. “Shi ne ma, kin san tashin hankali yana saka haka ko da ciki ya yi kwari ba re kuma ace yana sabo kuma.... ” Bata karasa Hajiyar ta daka mata tsawa. “Haba idan kin fara zubawa ba ki san ki tsaya ba? Shiyasa kike samu matsala da Yayanki kina da yawan magana” Da hannu tai zip up din bakinta. “Taso muje ciki ki gyara jikinki” Naga karamci sosai a gurin matar nan babu kyama ta shiga da ni har cikin dakinta ta kai ni bandakin ta bani duk wani abu da nake bukata tun daga pad da pant da doguwar rigar da zan canja. Kamar kazar da kwai ya fashewa haka na fito daga bandaki jikina babu kwari na dawo falon a maimakon na zauna sai na yi tsaye kamar an dasa ni wasu sabbin hawayen na cika min ido. “Baiwar Allah ki zauna mana yau masu aikin na mu basa nan balle akwai miki ruwa” “Aa na gode sosai Hajiya, gida zan tafi yan uwana suna can suna ta neman Namra, na gode sosai da karamci na ji dadi da yata ta fada hannun mace mai karamci da son mutane kamar ki Allah ya saka da alheri” “Babu komai Gwarzo za ki m godiya ai, muna zaune ya zo da ita sai fada yake wai kun wofintar da ita, dan Allah a rika kula” “In-Sha-Allah” Bayan na amsa mata, ta dauki wayarta dake gefen cushion din ta kira number da na ke zaton ta wacan mutumen ce. “Za ta tafi da yarinyar nan” Shine abunda na ji ta fada ban ji abunda ya fada mata ba, murmushi kawai na ga ta yi sannan ta aje wayar tana kallona. “A kula dan Allah ina zuwa” Tsakanin shigarta dakinta da fitowarta be wuce minti biyar ba ta mikowa Namra dake rike da hannuna abu a leda sannan ta shafa kanta. “To bye bye jikata” Murmushi Namra tai ta yi mata bye bye sannan nai mata godiya muka fito, har mu ka bar gidan ban saje ganin yarinyar nan mai shegen surutu kaar suda ba. Na yi mamakin ganin mai napep din a gafen gidan fake da napep dinsa, ni har na manta da shi lallai ba karamin hakurin yai ba na tsayawa jirana har na fito. Ya nuna min jindadin ganin yata kamar ya san ni har yake tsokar Namra wai ta tashu hankalin Mamanta. Ni dai na san na fada masa unguwar da zai kai ni wato family house dinmu sai dai tafiyar da isa cikin unguwar ban san an yi ba har sai da Namra ta girgiza ne, ashe hawaye na ke ban sani ba tashin hankalin da ke cikin kaina ya mantar da ni duniyata na dan kankanen lokaci, tsoro nake idan ba cikin ba ne kamar yadda Hajara tai min hasashe, sai dai taya bayan ban tana jin wata alama ta cikin ba? Hasalima ni sai na gama al'ada na ke saurin daukar ciki? Wata jarrabar ce ta sake hawa kaina? Ko kuma dai wani ciwon ne dabam ba ciki ba? No ciki ne! Ita ce amsar da nabawa kaina saboda azabar ciwon mararda neke ji ba irin wanda na saba ji ba ne,hakan ya tabbatar min da cewar cikin ne yake zubewa ko ma ya zube duk da ban tana yin bari ba ban san yadda abun yake ba. Muna fita daga Napep din yan gidan mu suka fito waje da sauri ganin Namra suka saka ihu, sai a lokacin na lura da motar Abdallah da ke fake kofar gidan. Jakata na bude na dauko dubu biyu na mikawa mai napep din ya amsa da murna yana min godiya, sannan na shiga cikin gidan kamar bana cikin hayyacina. “Al-hamdulillah” Shine abunda Abdallah ya fada ganin an shigo da Namra, sai dai ko da wasa be kalli inda na ke ba. A lokacin ne na ji suna fadar su ma sun ji sanarwa a gidan radio kanen maza biyu ma sun nufi can tare da Hafiza. Ko minti biyar Abdallah be kara cikin gidan ba ya ce zai tafi Mama da Inna da Baba suna ta masa addu'ar Allah ya raya mana zuri'a ya saka masa da alheri. “Kuma Allah ya ba ni da namiji Mama ina son namiji sosai” Ya fada yana saka hannayensa aljihu. “To Allah ya baka namijin mai albarka, ko ya baka tagwaye maza irinku” Cewar Inna tana dariya shi kuma ya amsa da amin shi da Baba da Mama. Daf da zai fice na yi juyo ina kallon bayansa zuciyarta na raya min abubuwa da dama, sai wani zafi take min kamar a dora tasa a saman garwasu a yanka zuciyata an saka ciki ana soyawa. 7/21/21, 10:43 PM - Buhainat: https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=sQG%2BQrKDPbZSTHpyCfMXShnbvN2tI%2BsZNLVYrdA6bjlL2NTuuf5lSa3ifr1FPIjSdteY9%2F%2Bh1LOSQGVUFd3maZGuVfSixkfHR3I18rApWQw%2FvycatsVhITYmzS2o1SD6 *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣1️⃣ ABDALLAH POV. Yayi parking daidai da lokacin da yake sauke wayarsa daga kunne. A natse ya bude motar ya fita ya nufi kofar shiga falon. Da sallama ya shiga falon kamar yadda ya saba, Suwaiba ta amsa masa murya kasa kasa ba tare da ta kalle inda yake ba sai aikin latsa waya take. Kusa da ita ya zauna yana sauke gajiya idonsa na kan matarsa. “Kawo min ruwa” Ya fada bayan ya kai hannu ya fisge wayar daga hannunta, facebook take kan wani page na Real Life Diaries, sannen shafi ne da yake wallafa matsalolin mata da mazan ma aurata domin samun mafita ta addu'a ko shawara ko taimako idan ta kama.   Sama sama ya duba labarin page din wani gurin yai dariya wani abun kuma yai tsaki musamman idan ya leka comment section. “Gashi” Ta mika masa ruwan fuakarta ba yabo ba fallasa bayan ta bata yan mintuna kamin ta kawo masa. “Ni na manta when last na leka page din nan, wani lokacin post din mutane bata min rai yake wallahi” “Wani lokacin kuma ana samun mafita ai, shiyasa ake yin posting din” Ta fada tana kokarin zama kusa da shi wato a inda ta tashi dazun. Kallonta yai kamin ya kai ruwan a bakinsa ya shaye gaba daya sannan ya aje kofin ya kai hannunsa ya janyota ta kwanto jikinsa. “Ya akai Subee? Fada min matsalar ki” “Babu komai” Ya fada still fuskarta na nuna akwai damuwa. “Ba mu saba boyewa juna damuwa ba, fada min matsalarki” “Ba komai” Ta sake maimaitawa. Wayarta ya mika mata yana fadin. “Ba ki tambaya ko anga Namra ba?” “Ai na san an ganta, da ba a ganta ba da ba zaka dawo gidan nan ba” Kallonta yai for few seconds sai kuma yai murmushi as usual. “Shine abunda ya bata miki rai?” “Tun safe ka fita gidanan baka dawo ba sai yanzu, ko rantsuwa nai ba zan yi kaffara ba wata kila ko aiki baka je ba, ka tashi hankalinka gurin neman yarinyar nan wanda na san ko Inteesar ta bata ba zaka tashi hankalinka kamar haka ba” Wannan karon raba jikinsa yai da nata ya juyo da kyau ya kalleta yana karantar yanayinta. “Yar yar'uwata ce ta bata fa, ita ma din kamar yata ce” “Ta ma fi yarka ai, gatan da kake musu baka ma yayanka wannan gatan, makarantar da ka saka su Inteesar 60,000 ake biya duk bayan wata uku amman Namra makarantar da aka saka su dubu 130,000 ake biya duk term” “And...?” “And ba su da wanda zai dauki dawainiyarsu ne sai kai Abdallah? Why kai why?” “Amman ai kin san mahaifinsu ya rabu da Halimatu ko? Kuma yaran nan a yanzu abun tausayi ne suna bukatar tallafi a rayuwarsu, kuma Halimatu yar'uwata ce kin fi kowa sanin haka” “Dan ya rabu da ita sai dawainiyarsu ta dawo kanka? Miyasa Abdulhamid b dauki dawainiyarsu ba? Be fika kusanci da mahaifiyarsu ba?” “Abdulhamid babu ruwansa da yara kin sani, ba sai an fada miki ba” “Amman ita kadai ce mai yaya a familynku? Miyasa ba kai wa wasu ba sai ita? Komai daga ita sai familynta? Lokacin da Hafiza ta zo nan ta fada maka Namra ta bata kuka fita tare ko magana ba ka min ba” “What are you try say?” “Dawaniyar ta maka yawa Abdallah, kai mata kai wa iyayenta kai wai yayanta kai wa yan'uwanta why?” “Pls just stop.....” Ya fada yana daga mata hannu fuskarsa na nuna tsananin bacin ransa. “Dukan abunda zan yi ma wani a familyna ki kawarda idonki, babu nairar ki a ciki, kuma familyna ne ba naki ba so babu ruwanki da abunda ya shafi family na, dukiyata ce yan'uwana ne” Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya nufi hanyar dakinsa cikin bacin rai. A take ranta ya kara baci, iyakar abunda zuciyarta take raya Abdallah yana son daya daga cikin kannenta Especially Hafiza ganin kamar jininsu ya fi haduwa a cikin kanenta, daman can tana raya ma zuciyarta haka sai dai bata dauki abun da gaske ba kamar yau ganin yadda hankalin mijinta ya tashi akan bata Namra. Yana shiga dakin ya cire kayan jikinsa ya daura tawul, yana kokarin shiga wanka wayarsa tai ringing, dawowa yai ya dauki wayar Doc Auwal ne rubuce a wayarsa. “Hello Doc Auwal” “Doc Abdallah ya kake?” “Lafiya kalau” “baka shigo ba yau gashi Abdulhamid ya ce na baka sakonsa” “Sakon me?” “Ban san na minene ba daga kano dai jiya Doc Faruk ya kawo min yace na baka kai kuma ka bada Abdulhamid” “Ba zan shigo yau ba sai gobe, wallahi wata yata ta bata ba mu ganta ba sai yanzu” “Okay bari na biya na kai masa kawai” “Okay” Wulga wayar yai a saman bed dinsa yama fadin. “Abdulhamid kana ta wahalar da kanka, tun asirinka na rufe har kowa ya ji sirrinka, after you already know za ka samu lafiya ne kawai only if na haifi da namiji....” Bathroom ya shiga ya sakarwa kansa ruwa, har yai wankan ya fito ransa a bace yake da maganar da matarsa tai masa. HALIMATU POV. sai da hankali ya kwanta sannan na kira Abdulhamid na fada masa cewar an ga Namra tana tare da ni ma, godiya yai ma Allah ta cikin wayar nake ina jiyo shaukin muryarsa kamin mu yi sallama. A lokacin ne Husna take min zancen wai ta kira Abdulhamid tace yaje gidan radio saboda an yi sanarwa wata yarinyar kamar yadda suka ji daga bakin jama'a. “Ayya ma zai je ai ba wani son motsa jiki yake ba ni har mamaki nake idan yai nasa yayan ko ya zai yi” Kallonta nai ina murmushi yayinda na ke gyarawa Namra zama a cinyata. “Kin san kowa da rayuwarsa, na fi kyautata zaton Abdulhamid yana kishin rika yaran wasu ne, kuma kin ga daman can Abdulhamid babu ruwansa da yara” “Ai ba yara kadai ba har manya ba wani so yake ba, shiyasa be taba burgeni ba ni Wallahi da ma Abdallah kika aura tun farko  ya.....” Hafiza bata karasa ba Mama ta tari numfashinta, wanda hakan yai min daidai. “Wannan wace irin magana ce Hafiza? Mace ta taba auren wanda ba mijinta ba? Kuma wanda mace take so ai shi zata aura, kar na sake jin irin wannan maganar a bakinki” Bata sake cewa komai ba ta dauki wayarta da dan guntun gyalenta ta da saba yafawa ta fice daga falon na Mama zuwa dakin Inna wato dakin Mahaifiyarta. A gidan an wuni sai bayan sallah isha'i Abdulhamid ya zo daukata ya shiga cikin gida ya gaisa da su Mama sannan ya fito muka kama hanyar gida.    Ba mu yi wata fira a motar ba saboda ciwon marar da ya kasa sakina, pad ma sau hudu ina canjawa, shi kuma na lura kamar baya cikin walwala. A haka muka kwana ko wanne da abunda take sakawa a zuciyarsa, nawa tunanin dabam shi ma nashi dabam duk kuwa da kasancewar ban san damuwarsa ba.   A rungume da juna muka kwana kamar yadda muka saba, sai dai na riga shi tashi saboda na gyara kaina, sannan na shiga dora mana abun karyawa cikin kankane lokacin na gama komai saboda ina son zuwa asibiti.   Sai da nai wanka na shirya sannan na shiga na tashe shi ya fito muka soma karyawan. “Ban maka magana tun jiya ba, ina son naje asibiti marata tana min ciwo tun jiya na yi zaton ko zan ji sauki kamin yau amman ban ji alamun haka ba” Na masa maganar a yayinda muke cikin karyawa. Dagowa yai ya kalleni sai kuma ya kai fork dinsa ya dauki dankali ya ci. “Kina Menstruation ne?” “Yes” Mikewa yai tsaye kamar ya nufi dakinsa ya dauko wayarsa kamin ya karaso kusa da ni ya kira Abdallah. “Kana asibiti ko gida?” Ban san mi yace masa ba na ji dai ya sake cewa. “Okay ga mu nan zuwa, Halima ce bata jindadi zan kawo ta yanzu” A take na ji gabana ya yanke ya fadi, gashi bana son ya zargi wani abun balle na ce masa bana son Abdallah ya duba ni. “Bari nai wanka sai n kai ki gidan Abdallah ya dubaki” Kai kawai na iya gyada masa ya juya ya koma ciki, har yai wankan ya shirya ya fito ban samawa kaina mafita akan abunda zan yi ko na ce da zai hana zuwan gurin dan'uwansa ba. A dole tasa na saka hijab dina na na dauki jakata da wayata na fice ina gaba yana baya har muka fito daga falon, a gaban motarsa naje na tsaya ina jiran ya karaso ya cire key din na bude sai ji nai an rumgumeni ta bayana. “I love you so much” A hankali ya fada min haka sannan ya sake ni ya danna keys din hannunsa motar ta fita daga lock. Front seat na zauna shi kuma ya shiga driver seat a usual, sai dai har muka isa gidan Abdallah be kalli inda nake ba be ce min uffan ba kuma ban ga wata walwala a fuskarsa ba, hakan yasa na fi kyautata zaton wata kila rashin lafiyarsa ce ya saka a rai ta hana ni sukuni a take tausayinsa ya rufe har idanuwa suka soma cika da kwalla. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na bude motar na fita, wannan karon shi ne a gaba ni ina baya. Mun dan jima tsaye a gurin kofar kamin Suwaiba ta bude mana. Na yi kokarin kirkirar far'a na yaɓa a fuskata duk kuwa da irin halin da nake ciki, sai dai yau na same ta akasin yadda na saba samunta ko kuma na ce nake ganinta, domin tun da na auri Abdulhamid ban taba zuwa gidan da sunan kawo mata wuni ba sai yau shi ma kuma wannan da daliline. Cikin falon muka shiga na zauna a saman cushion Abdulhamid kuma ya zauna kusa da ni yana ta kallona kamar ba shi ba. Bayan kamar minti biyar Abdallah ya fito a daya daga cikin bedroom din da suke falon. Shi ma dai fuskarsa babu walwala kamar ta matarsa, sai da ya mikawa Abdulhamid hannu suka gaisa sannan ya zauna ba tare da ya kalli inda nake zaune ba. “Ina kwana?” Na mika masa gaisuwa ina ta kallon zoben hannunsa, zoben da ba kasa samun natsuwa da shi har yanzu. “Ina kwana” Sai ya dawo min da gaisuwar still be kalleni ba sai Abdulhamid yake tambaya abunda yake damuna. “Mararta ke ciwo” “Tun yaushe?” “Tun jiya, magani nake son ka rubuta mata” “Ya kike jin abun?” Wannan karon ya kalleni a yayinda yake tambayar tawa. “Ina dan jin tana min ciwo ne” “Sosai ko kadan and tun yaushe?” “Jiya” Tashi yai ya shiga daki, be dade ba ya fito rike da takardar magani ya mikawa Abdulhamid. “Dan Allah daga yau idan matarka bata da lafiya ka kai ta asibiti direct ba sai sai nan ba, ko ba komai zata fi sakewa idan tana ganin mace yar'uwarta” Ba Abdulhamid kadai ba, ni kaina da nake matar Abdulhamid na yi mamakin jin furuncinsa, wanda na tabbatar hakan be yi ma Abdulhamid min dadi ba ko kadan. Uffan be ce masa ba bayan kallonsa da yai ya karbi takardar tare da ce min na tashi mu tafi. Daga gidan Abdallah kai tsaye gidan Hajiya ya wuce da ni, ban so haka ba amman ban isa na nuna masa ba kasancewar mahaifiyarsa ce. Ita kanta ta lura da yanayinsa na rashin jindadi daman can yana fama da shi balle kuma yanzu da Abdallah ya kara masa da wata maganar. A gaban idona take tambayarsa abunda yake damunsa sai ya amsa mata da cewar babu komai, daga bisani ya kalleni ya ce. “Ki zauna a nan idan an dawo aiki zan biyo miki da maganin sai mu wuce gida, Hajiya ba ta jindadi shiyasa na kawo ta nan ta huta kamin na tashi aiki” Ya karasa yana fadawa Hajiyar. “Allah ya saukewa” Ta fada tana dauke kai irin abun be dame ta ba. Shi kuma yai mana sallama ya tashi ya fice. Da kallo Hajiya ta bishi har ya fice sannan ta kalleni. “Ke me ke damun mijinki?” “Kwana biyu nan haka yake, kuma yanzu muka fito gidan Abdullahi ya kai ni ya dubani shine ya ce karya sake kawo ni to ban san ko shi ya bata masa rai ba” “Husaini ne ya ce masa haka?” A take ta daga wayarta a gurin ta jira Abdallah ta fada masa tana son ganinsa, abun ka da mai jiran kiran uwa a ko da yaushe, sai gashi ya zo cikin kankanen lokaci dama can babu tazara sosai tsakanin unguwarsu Hajiya da ta Abdallah. Fuska a sake ya shigo kamar ba shi ne na tarar a can ya hade rai ba, ko dan wannan mahaifiyarsa ce oho. Bayan ya zauka Hajiya ta sallame ni ta hanyar cewa na tashi na ba su guri. Ba musu n tashi na fita daga falon sai an samu guri kusa da kofar falon na zauna ina ta sake sake a raina, ta wani bangare raina fes yake da zubar jinin da nake domin na san indai ciki na zube a yanzu, ta dayan bangaren kuma ina jin tausayin mijina. Ban san abunda Hajiya tace masa ba sai dai na ga ya fito ransa a bace har ya wuce ni sai kuma ya juya ya nuna ni da yatsa kamar ba Abdallah ba. “Ina ta kokarin ganin na fita daga hanyarki, ya kamata ke gane ke matar dan'uwana na ce a yanzu, duk wani abu daya shafe ni ko kika san zai saka dan'uwana kusantar da ke a gareni ki yi kokarin kauce masa, idan ba haka ba ran mijinki zai yi ta baci fiye da yadda kike zato kuma za ki jawa mijinki shiga damuwa fiye da wacce yake ciki...” Idanuwa ne suka fara yawo a fuskarsa. “Baka da tausayi Abdallah ba ka da kirki, ba ka san damuwar kowa ba sai ta ka, kai baka tausayin dan'uwanka ma? Bayan halin da yake ciki na damuwa kake neman kara saka shi wani? Kamar ba uwa daya ta haife ku ba? Abun da ya kamata ace ka taya shi tausayin kansa da neman lafiyarsa amman sai neman kara jefa shi a damuwa kake?” “Babu ruwana da matsalar mijinki, ba tausaya min ba, dan haka babu tausayi a tsakaninmu samun lafiyarsa ko zamansa haka har a bada be dame ni ba saboda shi ma be bar ni na samu farinciki na ba” Kallon mamaki nai masa. “Ya kake kokarin aron wadansu dabi'u da halaye marar kyau ka yafawa kanka Abdallah, kana abu kamar ba kai ba? Dan'uwanka jininka? Wallahi Abdulhamid ba zai taba yi maka abunda zai hana ka samun farinciki ba, ba ka da kirki da halin kwarai shiyasa baka taba burge ni ba, kana da son kanka da yawa shiyasa ban tana jin son ka a zuciyata ba....!” Fadada fuskarsa yai da murmushi kamar ba shi ba. “Wani lokacin Wallahi mata ba ku da hankali” Yana fadar hakan ya juya ya nufi gurin motarsa. AHMAD POV. Tura kofar falon yai ya shiga da sallama, Momy ta amsa masa tana rike da wayarta. “Dan halak, yanzu nake kokarin kiranka fa, tun da ka fita baka dawo ba” “Ban dade da fita ba ai” Ya fada yana kokarin zama. “Eh na sani, bana son kana yawon nan idan ba aiki ba ko wani uzurin” “Haba Momy sai kace wani karamin yaro” “Ba zaka gane ba ne ai, yan mata yanzu shegen wayo ne da su a take za su ci maka kudi su gudu, kuma na sna indai ka bar gidan nan ba iya kula kake da kanka ba” “Yanzu ni kamata yan mata za su yi wa wayo?” Ya nuna kansa. “Hmmm Baka san mace ba, har yanzu kai yaro ne, ka ci abinci?” “Eh na ci abinci” “Ka koshi?” Murmushi yai yana ta mamakin yadda Momy take ta maida shi karamin yaro, sam ta ki yarda shi din namiji ne kamar kowa, sometimes har mamaki yake shi dai yasan ba girma ne be da shi ba balle ace tana ganinsa da karamin jiki, shiyasa wani lokacin ko yana bukatar baya nunawa saboda kar ta samu damar yi masa haka. Baby Namra ce ta fito daga bedroom dinta tana masa oyoyo. “Daddy sannu da zuwa” Ya mika hannunsa ya rikota. “Yauwa darling y scul?” “Fine Daddy wannan Name sake din tawa ta tafi” “Yeah Momy ta zo ta dauketa did you miss her” “Yes Daddy” “Ke da kika ce ba ki sonta?” “Yanzu kuma na ji ina sonta, daddy za ka kai ni gidansu?” “Ban san gidansu ba” “Pls daddy” “I'm serious” Ya fada yana kara gyara mata zama a jikinsa, har cikin ransa yake jin son yarsa fiye da komai a rayuwarsa, musamman idan ya tuna cewar bata da mahaifiya a raye. “Idan kin je makaranta ki tambaye unguwarsu sai a kai ki” Wannan karon Momy ce take maganar. “Wane class take Momy?” “4 tace min kamar 4 kamar 3 na manta dai ki bincika” Da sauri ta gyada kai tana murmushi. 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy *Gaba daya littafin nan Sadaukarwar ne ga Zainab A Baba💖* 2️⃣2️⃣ AHMAD POV. Wayarsa ce tai ringing, da gangan ya ki duba wayar ya ga mai kiran balle yai deciding idan zai dauka ko ba zai yi picking ba. Babu kira mai muhimman a gurinsa kamar na Hajiyarsa sai kuma na kanwarsa da yarsa su ne kadai mutanen da suke da muhimmanci fiye da komai a rayuwarsa, yana girmama kiransu yana mutunta bukatunsu, kamar yadda yake martaba su. As long as yana tare da Hajiya ko yana cikin gida, duk wanda ya kira shi sai idan yaga dama zai daga kiransa kowa shi a duniyar nan kuwa. “Ba wayarka ce ke ringing ba?” Cewar Hajiya ganin be daga ba duk kuwa da ta san halinsa na kin son call, ya fi son sako fiye da kira. “Ita ce wata kila wane ni bana son amsawa yanzu” “Ko dai yan matan ne ke kira?” Kallonta yai da murmushi a fuskarsa. “Kowa da bukin zuciyarsa, Allah na tuba wace mace ce zata wahalar da kanta yanzu na son dan Hajiya?” “Hmmm ai yan matan yanzu shegen wayo ne da su, yanzu sai su tatse ka tass baka sani ba” “Hajiyata, kin kasa gane cewar ni ba yaro ba ne, ka ci abinci? Me ka ci? Yaushe zaka dawo, karka wuce minti talatin a waje, da sauransu na yara ne, Hajiya ni babban mutum ne a yanzu tun da har Daddy ya kirani nai min wasiyar kula da ku, kuma cikin ikon Allah da iyawarsa na iya rike gidan nan da kula da ku da tafiyar da komai na kamfani yadda ya dace ya kamata ace kin fahimci cewar dan ki ba yaro ba ne a yanzu” Murmushi tai Murmushi mai sautin irin na su na manya. “Har gobe kai yaro ne Gwarzo, maza ai ba wayo ne da ku ba, ba komai kuke ganewa ba sai na nuna muku” Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya kalli Baby Namra. “My Love je ki dakinki bari mu yi magana da Hajiyarki ko?” “Okay Daddy” Sai da ta sumbanci kumatunsa sannan ta haye sama, shi kuma ya bita kallo kamin ya ciro wayar tasa da ke ringing yai picking. “Yusuf ya akai?” “Lafiya kalau, oga ya gida ya family?”     “Fine go straight to the point” “Oga maganar vip ne” “No ya dai kusa ka san kace baka son sai abu yai gab a fada maka, shiyasa na tuna maka” “I think kudin shekara ya kamata mu fara biya na wata wata nan yana confusing dina, ka lissafa na shekara nawa ya kama zan turawa abokina number ka sai ku yi magana” Be jira Yusuf din da ya kira wayar ya kashe ba, balle har ya saurare abunda zai fada ya kashe wayar, yana kallon Hajiyarsa zai yi magana ta tari numfashinsa. “Har yanzu ba a daina biya Vip din nan ba? Shekara nawa Gwarzo? A yanzu ka gama maganar cewar ka girma, ni nasan abunda na ke ai na san waye kai” “Ba haka ba ne Hajiya, abunda kika kasa ganewa freedom din danki,  Hajiya kin kasa bari na yi komai kamar ko wane namiji, kin ki aminta na zauna a gidan kaina, kin hana auren duk yarinyar na kawo, ko fita nai idan na wuce ka'idar da kika ba ni sai kin nuna bacin ranki ko kuma ki nuna min hankalinki ya tashi ba ki san inda na ke ba, duk yadda nake son na fita na fira a waje na wuce 9 ko na kai 10pm sai ki ce min ba haka ba. Exclusive City, a nan na hadu da Halima, a kujerar da nake biya a yanzu a gurin na same ta zauna, kin sani Hajiya every week muna zuwa gurin mu sha iska, and ta taba fada min ita take biyan gurin ko da bata zo ba, and after mun yi aure ita ta cigaba da biyan gurin, duk yadda na so na cigaba da biya sai ta hana ni, she once told me na bari sai idan bata da rayuwa sannan na cigaba da biya, and nai mata alkawari daga lokacin da na auri wata macen ba zan sake biya ba, alkawarinta nake kokarin cikawa Hajiya gurin nan yana da muhimmanci a gareni saboda mahaifiyar Namra, ko rai aka bata mata a gurin take zuwa tai kuka, idan kika mata wani abun a gurin take zuwa ta zauna tai bacin ranta ta gama sannan ta kira tace idan na taso daga office na biyo ta nan na dauke ta, wani lokacin kuma da kaina nake zuwa nemanta a gurin, ni kaina a yanzu ko anjima ko wani lokaci na kan je can na zauna kuma na samu natsuwa kamar tana raye... ” Ya yi shiru idonsa tab da kwalla, uffan Hajiya ba ta ce ba har ya mike tsaye ya saka wayar aljihun shaddarsa da ya zuba hannayensa aljihu ya nufi upstairs. Wani irin abun na rashin jindadi ke masa yawo a zuciya, haka yake samun kansa a duk lokacin da ya tuna da matarsa Halima, wacce yake yawan fada mata cewar daga ita ya gama so, mace da yake ganin babu mai hakurinta da kirkinta a duniyar nan. Ajiyar zuciya ya sauke sau uku zuwa hudu sannan yaja wani dogon numfashi ya busar a bakinsa. Ya kai hannunsa ya murda kofar dakin Baby Namra ya tura ya shiga ciki. Agaban plasma take zaune rike da drawing book da pencil a hannunta tana drawing wani bird da ake nuna a kids channel. Daga bakin kofar ya tsaya yana kallonta zuciyarsa fal da kaunar yarsa, sannan ya karaso kusa da ita yana ayyana abubuwa da dama akan rayuwarsa da nata. ‘Ko da na ayi aure zan yi ne kawai saboda ke, saboda ni da ke mu samu kulawa amman ba dan zan taba son ko wace mace a duniyar nan ba’ Kanta ya shafa yana murmushi kamar yadda ita ma ta dago ta kalleshi tana murmushin. “Daddy what” “Ba komai” Ya fada yana cigaba da kallonta, ita kuma ta maida hankalinta gurin tv ta cigaba da abunda yake. Wayarsa ya ciro ya nemo number Rayyan. “Rayyan” “Ranka ya dade” “Yusuf ya kira ni wai kudin wata sun kare, na ce masa za ku yi magana akan na year sai ka bashi zai fi” “Okay amman ban gane Yusuf din ba” “Wanda yake Exclusive City, kudin Vip nake nufi” “Okay ina da number shi ai bari na kira shi yanzu” “Okay ya fada maka ko nawa ne na shekara sai na bashi” “Consider it done” Daga haka ya yanke wayar ya cigaba da kallon abunda yarsa take zanawa. HALIMATU POV. daga karshe na yanke shawarar fadawa Abdulhamid gaskiya, na san duk yadda zai ji zafi da tashin hankali ba zai kai kamar lokacin da abun ya faru ba, kwana biyun nan na lura yana cikin damuwa wata kila saboda abunda Abdallah yai masa ne a kwana baya duk da be fada min ba amman ni kaina na lura da hakan, abunda zuciyata take yawan fada min idan ban fada masa gaskiya ba, idan ya ji a wani gurin ba zai ji dadi ba ba kuma zai fahimce ni ba. Amman kuma ta ina zai ji? Wa zai fada masa bayan babu wanda ya san wannan sirri daga ni sai Allah sai kuma kawata Hajara? Doyar da nake ferayewa na aje na rike wukar kamar ita ce zata sama min mafita. “Zan fada masa gaskiya, ina jin kamar ba zan samu peace of mind ba idan ban fada masa ba, ina jin kamar na ci amanarsa ne” Ni kadai nake magana da kaina a kitchen kamin na aje wukar na wanke hannuna saboda wayata da na ji tana ringing. Cikin hanzari na nufi inda wayar take, a lokacin da na kai hannu na dauki wayar sai na kasa picking din call din ganin number mai kiran duk kuwa da ba suna, Aminu ne na san ba wata magana mai dadi zai fada min ba, wata kila haukansa zai min ko kuma ya min gargadinsa na iska da ya saba, sai da ya jera min four miss calls sannan na daga, nai masa shiru tare da hade rai kamar yana a gabana. “Hello Halima” “Ya akai?” Na tambaya ina kara hade fuska kamar ance yana ganina. “Sai an yi wani abun zan kira? Alaka fa har yanzu bata yanke a tsakaninmu ba saboda yara” “Babu wata alaka a tsakanina da kai Aminu, kuma bana fatar wata alakar ta sake kulluwa a tsakaninmu, wacan da mu kai a baya ma ka dauka cewar labari ne” “Ta wuce labari Halimatu tun da har kika haifa min yara hudu, maza biyu mata biyu Al-hamdulillah, yanzu ma kira nai na tambaye lafiyarsu, kuma na ji idan akwai abunda suke bukata idan zan taho musu da kaya sai na siyo musu” Duba wayar nai dan tabbatarwa idan har number Aminu ce da gaske ko kuma a a. Kamin na maida wayar a kunne na ya kira sunana ya kai sau uku cikin tausasshiyar murya kamar ba shi ba. “Lokacin da nake gidanka ma baka damu da tambayar lafiyar yayanka ba, sai yau? Ko kunya baka ji ba? Yarana ba sa bukatar komai daga uba irinka Aminu, mahaifiyarsu ta ishesu kuma zata iya yi musu komai, karka sake kirana domin ni matar wani ce a yanzu” Ban jira abunda zai ce ba na yanke wayar, mamaki fal a zuciyata wanda ya kasa boyuwa har ya bayyana a fuskata, sake duba wayar nai a karo na biyu, neman dalilin kiran Aminu na ke a wannan lokacin na rasa? Me yake so? Ko kuma na ce mi yake kokarin aikatawa? Me zai saka ya tambayi yaransa? Gaba kaina sai ya kulle har na girkin na gama ban raba dayan biyu ba, ko dai Aminu yana da wata manufar akan yaransa ko kuma yana shirin lalata min aure ne. Abdulhamid be shigo ba sai bayan sallah magariba, na masa sannu da zuwa kamar yadda na saba na raka shi har daki na hada masa ruwan wanka domin na san wanka ne abunda mijina yafi bukata a duk lokacin da ya dawo daga gurin aiki. Kamin ya fito na jera masa abinci da ruwa mai sanyi sannan na fiddo masa da jallabiyarsa, da kaina na karbi karamin tawul din na natse masa jiki sannan na shafa masa mai sannan ya saka gajeren wando ya dora Jallabiyar sama. Zaunawa yai ni kuma na soma zuba masa abincin  ina ta kallon yanayinsa kamar yadda na lura da kwana biyun nan ya fiye kallona. A tare muka soma cin abincin kamar yadda muka saba sai da na tabbatar ya kusa koshi sannan na fara bijiro masa da maganar. “Hubby Akwai wata magana da nake son mu yi mai muhimmanci....” Tarar numfashina yai. “Ya jikinki....? Na manta dazun da muka tashi ban tambaye ki ciwon marar ba” Wani dif na ji numfashina yai dogon zango, kamar wacce zata suma sannan ya dawo min kamar an jefo shi. “Na ji sauki, akan hakan ne nake son mu yi magana” “Uhm ina jinki” Yadda yai maganar da yadda ya fuskance ni sai ya saka ni tsoro da fargaba kwarjinisa duk sai ya cika ni, har na kasa furta komai. “Ina jinki” Spoon din hannuna na aje na kama hannunsa na rike na saka idona cikin nasa. “Ban san yadda zaka dauki abunda zan fada maka ba, ban san ya za ka ji a zuciyarka ba, ban san wani irin kallo za kamin ba, za ka iya cigaba da zama da ni akan kaddarar da ta same ni ko a'a, ban sani ba iyakar abunda na sani shine bana da kwanciyar hankali idan ban fada maka.....” Idona ne ya cika da hawaye sai nai saurin kawar da fuskata daga barin kallonsa. “Me kika aikata?” Yawun bakina na hade na sake kallonsa a karo na biyu sannan na ce “Ban aikata komai ba, darajata aka taba....!” “Ban gane ba” Shiru nai na kasa cewa komai sai hawaye na ke shar kamar ba gobe, shi kuma bayan kallona babu abunda yake. “Zaka iya tuna lokacin da ka tafi Abuja karbar wasu takardu? Ka bar ni ni kadai?.....” Cikin natsuwa irin ta masu gaskiya na zayyana masa komai, ba natsuwa irinta ta masu kwanciyar hankali ba, kallon kallo muka ko yi ma junanmu akuya kallom kura, idona na hawaye ina kallonsa, yayinda shi ma yake min kallon da ban san na minene ba, yarda ko akasin hakan ko kuma tausayi? Sosai nake Kallona na kasa dauke idona daga kansa, so nake ya fada min cewar ya aminta da ni tausayi da kulawa da kauna nake son gani a fuskata, so nake na ga idonsa sun cika da hawaye saboda mu yi kukan a tare mu yi jumamin a tare. Be ce min komai ba, be kuma daina kallona ba, be nuna min wata alama ta yarda ko akasin hakan ba, ban tsinka jimami a idonsa ba balle har na iya hararo tausayi a zuciyarsa. Ni din ce da kaina na tsargu na mike tsaye na bar masa gurin, ina jin zuciyata na min wani irin zafi kamar zata fashe, idonuwana kuma suna ta min yaji saboda hawaye daya hana ni gani daidai. Dakina na dawo na kwanta saman gadona na mika hannuna na janyo fillo ya dora kaina dayan hannun kuma na rika shafa gadon da shi kamar ban san abunda nake ba, kwancin ya gagareni sai na sauko na zauna a kasa na dora kaina a saman gadon. Uwa ce ni, amman a yau ji nake kamar ace akwai wata uwar a kusa da ni ta rarrashen ta fada min komai zai wuce, ina son naji wata kalma mai dadi ina son na ji an fada min cewar wata rana zan yi dariya wata rana zan yi farinciki, ina ma a ce Mama ta san da maganar nan da ita kadai zata iya ba ni hakuri ita ce kadai zata taya ni mu yi kuka tare kamar yadda nai da Namra. “Kaicon ki Halimatu? Wace ƴa ce za a yi mata fyade kuma ayi ma uwarta? Nai kukan yata kuma nai nawa? Yau kenan ya gobena zata kasance?” Mikewa nai tsaye ina kara magana da kaina kamar wata tabbabiya. “Ya isa shikenan komai ya wuce, abunda ya faru ya riga ya faru ba zan iya canja shi ba, ba kuma zan iya goge shi ba, shikenan ai kaddarata ce wannan” Ina kaina nan na fadi kasa zaune na fashe da wani irin kuka da ban san ta ina hawayen ke fito min ba. Na kan yi kuka har na samuwa natsuwa ko kuma na samu sukuni amman a yau sai na nemi natsuwa da sukunin na rasa, kukan ya ko ya tsaya min kamar yadda hawayen ma ce min sallamu alaikum. Wani kalar sara na ji kaina na yi idonawa har rufewa suke saboda ciwo, har kuma lokacin hawayen ba su daina min zuba ba. Karfin hali nai na tashi na shiga kitchen na dauko flask din na hadawa kaina tea da cup nai ta feta har ya sha iska sannan na kurba kadan, wani abun mamaki sai na kas hadewa kamar wacce tasha wani abun mutuwa, kuka ya subuce min. ‘Ke fa uwace Halimatu, idan Namra ko Amal ko Adnan ko Amir suka shiga damuwa gurinki za su zo, ke za ki sama musu mafita, so be a strong woman....’ Shine abunda zuciyata yake fada min, kai na gyada ina karfafawa kaina kuiwa sannan na shiga bandaki nai wanka har kan nawa da ke ciwo sai da wanke dan kaiwa na samu salama. Daure da tawul na fito na nufi gaban madubi na zauna ina ta kallon kaina, hawayen idona be daina zuba ba kamar yadda ruwan kaina suke zuba. Ina jin motsin shigowar Abdulhamid gabana ya yanke ya fadi, daga jikin kofar dakin ya tsaya yana kallona. “Amman Halima ba su bar wata alama da za a gane cewar yan fashi sun shigo gidan nan ba? Ba su fasa komai ba? Ba su dauki komai ba? Ba su harbi kowa ba? Kuma duk a unguwar nan ba su shiga ko'ina ba sai nan? Kuma ba su zo ba sai ranar da bana nan?” Ta cikin madubin na aika masa da kallo sai murmushi ya bayyana a fuskata, still hawaye na sauko min. “Wacce zan fara amsawa a cikin tambayoyinka?” “Halima babu yadda za ayi 6arawo mai makami ya shigo gidan nan be bar wata alama da zata nuna cewar ya shigo ba, and if gaskiya ne miyasa ba ki fada min tun farko ba sai yanzu, and miyasa kika yi kokarin zubar da cikin? Ba ki fada min ba sai da kika fara gano cewar na gane halin da ake ciki shiyasa kika kirkiri wannan? Na kasa yarda cewar ke ce Halima!” Wannan karon juyowa nai na fuskance shi. “Ni din ce dai Abdulhamid, ka yi tunani iya yadda zuciyarka ta kawo maka, Halimatu ce! Karka damu wannan din ma yana cikin kaddararta, na yarda wani sabwar kaddarar ce ta fuskance ni kuma ta bude min sabon shafi, na shirya karbar ta da hannu biyu, na sani bakinciki baya taba dawwama, kamar yadda jindadi ba ya dawwama, ko dai bakincikin ya tafi ya bar ni, ko kuma ni na mutu na bar shi, kuma gaskiya a duk inda take gaskiya ce zata bayyana ko da bayan raina...” Takowa yai ya karaso kusa da ni ya dafa ni ya tayarda ni tsaye ya kalle ni da idonsa da ke zubar da kwalla. “Saboda ina kaunarki na aureki, har ga Allah na yarda da ke..... amman zuciyata ta kasa natsuwa da wannan, duk wani kuduri da nake da shi akanki ne, duk wani buri da nake da shi akan ki ne, na san kin yi jihadin aurena bayan kin san bana iya komai, wannan kadai ya isa ya nuna cewar kina kaunata, amman be isa ya wadatar da cewar za ki iya tsare kanki ba, wannan abun da ya faru laifina ne na cutar da ke, taya son rai yasa na cilasta miki aurena bayan na san ba zan iya sauke hakokinki ba, komai kika aikata ba ki yi laifi ba Halima saboda ni ne ba mutum ba, da ace ni din namiji ne kamar kowa da duk hakan be faru ba da baki rasa komai ba” Hannayensa ya kai ya riko fuskata ya matso da tasa fuskar daf da tawa yana hawaye kamar yadda ni ma nake. “Wannan sirrinmu ne, babu wanda zai ji? Karki fadawa kowa mu bar wannan a tsakaninmu, na miki alkawari ba zan ta a fadawa kowa ba, babu wanda zai ji wannan abun daga gareni, kuma zan cigaba da zama da ke kamar yadda muka saba, na sani ni ma wannan jarabawata ce, and i think this is the only way da zan iya repay na aurena da kika a yadda na ke marar lafiya, saboda Allah ya kaddaro min haka a rayuwata, na yafe miki har Allah na yafe miki kuma ina fatar Allah ya yafe miki....!” Yana kaiwa nan ya hade yawun bakinsa ya dauke hannayensa daga fuskata ya juya yana cigaba da hawaye ya fice. Ban yi zaton akwai wani sauran karfi a jikina ba, a take kafafuwana suka fara rawa sai gani a kasa zaune jikina na ta rawa kamar wacce ta fito daga cikin kankara.! ABDALLAH POV. Cikin wani irin bachin rai ya shigo gidan, tun daga yanayin parking dinsa ma ya isa a gane hakan balle kuma idan a kai arba da fuskarsa, zuciyarsa har wani bugawa take da karfi kamar zata fito. Dukan yaransa suna falo kasancewar yau Thursday babu islamiya school, suna masa sannu da zuwa amman be amsa musu ba kai tsaye ya nufi dakin Mahaifiyarsu. Tana zaune saman gado tana waya ganinsa da kuma yanayinsa yasa ta katse wayar tana kallonsa. “Me yake damunki Suwaiba?” Da karfi ya aika mata da tambaya sai da hantar cikinta ta kada. “Me na aikata?” “Ba ki san abunda kika aikata ba? Ba a nan muka gama maganar Halimatu ba? Akan me za ki dauki wannan maganar ki kaita social media a page irin wannan?” “Ba ni bace ni ban kai komai a page ba.. ” “Ba ke bace wacece? Taya za asan da labarin idan ba ki fada ba? Har da sunan Namra? Da maganar School fees? Haka kawai ki dauki maganar da an riga an yi ta ki saka a media? Wace irin shawara kike nema? Kin san mutane sai zagina suke, a ina za su sama miki mafitar? Kina tunanin idan Halima ko Abdulhamid suka ga wannan ya za su ji? And look at the way da kika fadi labarin is like zargina kike ma? Kin ja ana ta tsina mana alrbaka ni da ita” “Maganar kenan Halima Halima....” Ya kara matsowa kusa da ita yana nuna mata wayarsa da ke hannunsa. “Yes Halima Halima, Halima yar uwata ce, kuma ni ba mazina ce ba ne, ban nemai matan waje ba ma babu yadda za ayi na nemi yar'uwata yar'uwar ma matar dan'uwana, ko a lokacin da Halima take gidan Aminu ban neme ta ba balle yanzu da take auren dan'uwana, ni ba mahaukaci ba ne kuma na jahili ba ne ba zan taba neman aikata Zina da Halima ba har abada! no matter how much I love her, ki shiga hankalinki karna sake jin sirrin gidan nan a media” Yana fadar hakan ya juyawa ya fice daga dakin cikin bacin rai. Second to last sentence na sa ya fi komai rudata ya yanke mata hanzari kuma ya jefata a duniyar tunani. ‘No matter how much I love her....’ Those that means Abdallah yana son Halimatu? Zargin da yan comments suke ya zama gaskiya kenan? Cewar da suke yana son ta ne wasu kuma na fadar cewar yana tarayya da ita ne ya zama gaskiya kenan? Ada kam sam ita bata kawo ma kanta wannan tunanin ba, ta fi zargin ko Abdallah yana son kanenta ne, amman yanzu kam gaskiyarta fito. Da sauri ta kunna data ta shiga page din da ta tura neman shawara ta shiga kara duba Comments din followers. _Al-hamdulillah, mun dawo fatar dai Yan Team Halimatu da Abdullah da Abdulhamid da Ahmad har ma da Aminu ba su yi fushi ba 😊_ 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/C40KoSeXq9l35nIiFXS1Rz *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣3️⃣ Na kan dora komai a mizanin kaddara, na yarda dukan abunda ya same ni ko zai same ni rubuttacen al'amari ne daga gurin mahaliccina, wani be isa ya goge min ba kamat yadda ban iya na yayewa kaina ba. Wannan ma yana cikin kaddararki Halimatu, haka zuciyata take yawan fada min kuma ina samun natsuwa sosai idan na tuna cewa ko wane abu da izinin Ubangijina yake samu na. Iyakar kokarin da nai na danne zuciyata ne daga kokarin aikata wani abu marar kyau wanda wani bangare nata yake hararo na ke ganin kamar mafita a gareni. Tun daga lokacin ba mu sake hada shimfida da Abdulhamid zai ba, ma'ana dai be sake leko dakina ba kamar yadda ni ma ban sake taka kafata dakinsa ba matukar yana a cikin gidan, ban fasa masa girki ba be fasa ci ba, ban kasa mika masa ko wace irin gaisuwa ba, sannu da dawowa, Allah ya tsare daman halina ne. Sai dai ban sake ganin walwalar fuskarsa ba kamar yadda walwalarsa ta hana tawa walwalar. Idan ina zaune a falo baya zama, idan kuma yana zaune na zauna sai yai kamar ya tsargu a take zai tashi ya shige dakinsa. Ban taba ganin laifin Abdulhamid min akan wannan ba, idan na saka kaina a matsayinsa ni kaina na san kwatankwacin abunda zan yi kenan, ba lallai ne ya gasgata ni ba, kamar yadda ba kowa zan fada haka ya yarda ba, sai dai abunda yafi min ciwo kallon da yake min na cewar na ci amanarsa. Ina ji ina gani zaman gidan yaki yai min dadi, na kasa sakewa, kwanciyar hankali yai min kwara walwala ta yi min bankwana, kuka da damuwa suka kwankwaso min kofa. Har ta kai bana iya bachi idan lokacin bachin yai, sai dai na raya dare da sallah ko kuma na zauna nai ta kallon sillin ko da kuwa bana tunanin komai bachin ba zai dauke ni, da rana kuma sai na tsargu ina ganin kamar ni ce kadai nake cikin matsala. Da kaina na fita chemist din dake unguwar na siyo maganin mura na ruwa a duk lokacin da na ji ina bukatar bachi sai na sha, wani abun mamaki a take bachi zai dauke ni kuma sai na manta da duk wata damuwa dake tare da ni. Da dare kawai ba, da rana ma idan na ji damuwar ta matsa min na dan kan sha sai kuma na samu salama da natsuwa, na sani akwai illa abunda nakr sha, kuma na san ba abu ne mai kyau ba, mace kamar ni mai yaya hudu ace na buge da shan kayan maye domin na samu bachi, wannan ma yana saka ni damuwa sai dai babu yadda na iya idan ban yi hakan ba ban san abunda rashin bachin zai janyo min ba. Gaba daya yanayi na ya canja ni kaina na sani, bana sakewa kamar da ga ciwon ido ya saka ni a gaba har ta kai bana iya daga idon sosai. Tun lokacin da abun ya faru ban sake fita da sunan zuwa unguwa ba ko wani gurin, Hajara ma ban sake labarta mata komai ba, a ganina duk wanda zan fadawa ba zai sama min mafita ba dan haka babu amfanin fallasa sirrin nawa. Yau ma kamar jiya ta kama weekend sai dai yau Sunday ba Saturday ba, Abdulhamid tun safe ya fita kamar yadda ya sabawar kansa yanzu da fita ranar weekend ya wuni a wani gurin sai dare zai dawo, bayan da can ba haka ya saba ba. Lamarinsa na ya bani tausayi ta wani bangaren kuma sai ya bani tsoro na kan yi tunani anya ko wace mace zata iya sadaukarwar da nai? Auren mutum kamar Abdulhamid a lokacin da tawa kaddarar ta same ni sai ya juya min baya? No be kamata nai wannan tunanin ba, shi ai ba shi da lafiya rashin lafiyarsa babbar damuwarsa ce sai kuma ni na kara masa wata, ya fa kamata na gane wani abu a duk lokacin da wani ya rabe ni sai wani abu marar kyau ko kuma na bakinciki ya same shi, misali kamar Kabir ko yana ina ma yanzu? Ni kadai nake zaune a falona ina ta sake sake da tunani kala kala wasu masu amfani wasu kuma marar amfanin. A tsorace na kalli kofar falon saboda knocked din da akai, haka nake yawan tsorata ko iska ya kada sai gabana ya yanke ya fadi. Sai da na sake jin an kwankwasa kuma na ji kamar hayani a waje sannan na tashi na nufi kofar na bude. Kanwata ce Hafiza tare da Namra da Aiman da Adnan da Amal da kuma wata yarinyar da ban waye ta sosai ba. Da gudu suka rumgume ni su dukansu wani kalar farinciki na ji wanda na dade ban ji irinsa ba, lallai ya'ya rahama ne, a take idona ya cika da kwalla ni kaina na san na yi kewar ya'yana, dukawa nai na dauki Amal muka shigo falon tare da su. Bayan sun huta na dauko musu abincinmu, sannan na shiga dora wani domin ban san da zuwansu ba kuma nasan wanda za su cin ma ba isarsu zai yi ba, ina cikin kitchen din Hafiza ta same ni da zancen siyayyar da Aminu yake ta musu Namra a kwanakin nan, daman kuma Mama ta fada min a waya a duk lokacin da ya zo sai ta fada min domin ita ma mamaki abun yake bata kamar ni. Daga ni har sun mun rasa dalilinsa na nunawa yarana kulawa a yanzu, bayan siyayya ma duk bayan kwana biyu sai ya zo ya fita da su ko kuma ya duba lafiyarsu. “Ni kaina Hafiza na rasa ganene dalilin Aminu na yin haka, mutumen da can ma be kula da yaran ba, har cewa yake na tara masa yara har hudu da kurciyarsa, yanzu kuma shine yake nuna musu kulawa abun yana bani tsoro” “Ko ma minene nufinsa ba zai samu nasara ba, matukar dan ya cutar ke ko su zai yi” “In-Sha-Allah, ba zai samu wata dama ta yin wani abu ba” “Amman Anty miyasa kika daina zuwa gida? Baba ma kwana biyu ciwon kafafuwansa sai tashi suke?” A take gabana ya fadi hankali kuma ya tashi abunka y'a da uba. “Subhanallahi amman shine ba a fada min ko a waya ba?” “Ba ke kadai ba ko su Anty Murja da suke nesa ya hana a fada musu wai za a daga musu hankali kawai, kin san ciwon nasa idan ya tashi yau ciwo gobe lafiya haka yake masa shiyasa” “Allah ya bashi lafiya” “Amin, Mama da Inna sai zancen ki suke su suka ce na zo da su Namra ma mu duba ki lafiya kike? Kuma gaskiya na ga alamar ba lafiya ba” “Kamar ya?” Na tambaya ina kokarin kirkiro murmushi. “Haba Anty kalle ki fa, duk kin rame kin koma kamar ba ke ba, ke da kika da jikinki mulmul ma sha Allah amman yanzu ko ki na fi ki ki ba, duk kin yi baki kin lalace Gaskiya akwai abunda yake damunki” “Babu abunda yake damuna Hafiza” Ina fadar hakan na juyo na fito daga kitchen din domin bana son ta cika ni da tambayoyi. Ina fitowa Namra ta fara bani labarin Daddynsu yana zuwa gurinsu yanzu har ma siyayyar da yai musu, tana cikin lissafa abubuwan da ya siyo musu sai Adnan ya karbe daga nan sai Aiman har da Amal ma labarta min take abubuwan da Daddy yake musu, wani irin farinciki da annushuwa nake ganin a fuskar yayana, da alama hakan da yake musu a yanzu yana musu dadi, ko ni da nake babban na so mahaifina a kusa da ni balle su da suke kanana kuma babu ni a kusa da su. A nan Namra take nuna min new friend dinta mai irin sunanta. “Momi kin tuna lokacin dana bata a gidansu aka kai ni, kin suna ita ce yarinyar gidan” Sai a lokacin na tuna har na wayi fuskarka. “Momi Daddynta yana sonta sosai komai siya mata yake, kuma har shi yake zuwa daukarta idan zata koma gida” “A ina kika hadu da ita?” “A school din mu take ita ce tana so na friend tace ita bata da friends kuma Momi ita ma sunan Mominta Halima, amman ta rasu.... ” Hannu na mika mata alamar ta zo, sai ta taso daga inda take zaune a kan Center tebur ta nufo inda nake sanye da English Wears dinta kanta babu dankwali balle ayi maganar hijabi. “Kin ganeni?” Na tambaya bayan na rike hannunta, sai ta gyada min kai tana murmushi irin murmushin nan na yara masu kiriniya. “Momi na fada mata yau za mu zo gidanki shine tace tana son ta ganki, tace daddynta ya kawota kuma ya kawo ta” Namra ta fada da mamaki a fuskarta, domin ita bata tashi cikin irin wannan gatan ba, da mahaifinta zai mata abu ko kuma ya nuna mata kula balle har ya dauketa ya fita da ita. “Daddynta yana sonta sosai Momi har da waya ya siya mata, yana bata chocolate komai siya mata yake, kuma gidansu har da motar wasan yara ya siya mata da lilo irin an scul dinmu” Ta sake fada, ni kuma sai nai murmushi na shafa kanta domin na san abunda yata take ji, kwatankwacin abunda nake ji idan na ga wata mace ta yi dacen mijin aure. “Kin yi dacen uba, Allah yai miki albarka ya jikan mahaifiyarki” Da kanta ta amsa min da Ameen kamin ta saki hannuna ta nufi gurin su Adnan, da alama dai ta sake sosai da su kamar wasu yan'uwanta. A gidan suka wuni tare da Hafiza sai dare suka tafi, duk yadda ta so na labarta mata damuwa ban yarda na bude mata cikina ba. Tafiyarsu da minti ashirin Abdulhamid ya dawo a lokacin ina zaune falo, bai yi knocked ba daman yanzu ya gane sai dai ya saka key ya bude kofar falon ya shigo. Na masa sannu da zuwa ya amsa min irin amsawar nan kamar an masa dole, a yadda na lura Abdulhamid yana zaune da ni ne irin zaman nan kamar na dole domin ba zaka ga zamantakewar aurenmu ka ce zaman ne na masoya ba. Na so na gabatar masa da zancen zuwa gida duba Abbah a wannan lokacin sai kuma wata zuciyar ta hana ni, na yanke shawarar da safe zan fada masa idan ya gama karyawa. Ashe abunda ban sani ba Abdulhamid tafiya zai yi a garin da ban san ina ba ne, sai da safiyar ta waye bayan na gama hada masa abun karyawar na yi ta jiran ya fito shiru be fito ba, har tara da rabi ganin be saba kai wa hakan ba yasa na shiga dakinsa sai na samu dakin wayam babu kowa a ciki sai wata farar takardar a saman gadonsa, karasa nai na dauki takardar wacce ke saman kudin da ban san na minene ba har sai dana karanta takardar. “Tafiya ta kamani zuwa Kaduna, zan dawo on Tuesday ko Wednesday ga kudi nan ki yi amfani da su.....” Ina gama karanta takardar hawaye ya wanke min fuska, a yanzu bana da martabar da Abdulhamid zai kalli ya fada min cewar zai yi tafiya? Zauna nai bakin gadon ina tuna irin rayuwar da nai a gidan Aminu, a da na yi tunanin komai ya wuce, ashe abubuwan da zan fuskatanta suna da yawa, ko wace mace da irin jarrabawar da take tsintar kanta a cikin a gidan mijinta, wata mijinta neman mata yake, wata ya hana ta ci da sha, wata ya hana ta lokacinsa, wata ya hana ta kudin kashewa. ni kuma irin tawa kaddarar kenan. “Al-hamdulillah” Na furta sannan na share hawayena na taso na fito daga dakin, dakina na dawo na bude drawer ta na dauko maganin bachi na kurba kadan na kwanta, da niyar nai bachin kadan sai ga shi na zarce da dogon bachi ban farka ba sai la'asar. Azahar ma sai da na ramata sannan na dora da la'asar din, haka kuma be min dadi ba domin ban saba ramuwar sallah ba, idan ba da wani dalili mai karfi ba. Ganin ni kadai ce a gidan yasa ban wahalar da kaina wajen girka komai ba, daman can ba ci nake ba saboda shi nake girkawa kuma yanzu baya ma garin. Wayarta na dauko na kira layin Baba, ringing biyu ya dauka na gaishe shi cikin girmama da kauna ya amsa min da kuzarinsa. “Baba ya jikin?” “Al-hamdulillah jiki da sauki sosai sai da suka fada miki ko?” “Hafiza ta zo jiya ta fada min, Baba ciwo ba abun boyu ba ne, musamman irin naka da idan kafafuwan suka tashi baka iya takasu, ya kamata aje asibiti a sake dubawa” “Kafafuwan da sauki fa, yanzu nan ma Abdullahi ya dawo da ni gurin gashi, shi ke kaini aka gasa kafafuwan kullum, da sauki sosai ki kwantar da hankalinki” “To Baba na so na shigo sai Abdulhamid yai tafiya, amman idan ya dawo ko kuma na yi waya da shi na nemi izininsa zan zo na dubaka” “Allah ya miki albarka Halimatu, karki zoba da izininsa ba, ayi ta hakuri” “To Baba Allah ya kara maka lafiya” Da amin ya amsa na sauke wayar ina hawaye, duk yadda na so na daga waya na kira Abdulhamid na tambayi izininsa na zuwa gida sai na kasa, daga karshe na yanke shawarar tura masa sako. Ko minti biyu ba ayi ba ya dawo min da reply har da kalmar da nake zaton zolayace kawai ko kuma ya rubutu min ne saboda ya saba rubuto haka a karshen ko wane irin text da zai min. “Subhanallahi Allah ba shi lafiya, ki je gobe, kuma idan na dawo zamu je mu duba shi, zan kira shi na masa ya jiki. Ki kula da kanki i love you.....” Daker na iya hadeye yawun bakina tare da wani abu da na ji ya tsaya min a makoshi. Sannan na tashi na shiga gyara gidan domin yau ban yi gyaran safe ba tunda wuni nai ina bachi. Sai na kimtsa ko'ina na gyara komai sannan na shiga nai wanka, sai kuma na dawo gaban madubi na zauna ina ta kallon kaina, ni kaina ban lura da na yi rama sosai haka ba sai yau, ban ɗaga daga gurin ba sai da na ji wayata na ringing, number mama ce cikin sauri na dauka tare da sallama, bayan mun gaisa na sake mata ya jikin Baba ta amsa min da sauki tare da kara fada min Abdallah yana ta hidima da shi. “Allah ya saka masa da alheri ya biyaki” “Amin. Halimatu me ke damunki?” “Me ya faru mama?” “Kin daina zuwa gida, kuma Hafiza ta fada min kina cikin damuwa amman kin ki ki fada mata” “Babu komai Mama kawai dai bana jindadi ne kwana biyu” “Halimatu, ni fa mahaifiyarki ce, ko ms ke damunki ni ya kamata na fara sani kamin kowa, kuma idan ba ki fada min damuwarki ba wa kike da shi da za ki fada masa?” Hawayen na ji ya cika min ido, tabbas ina bukatar mahaifiyata a kusa da ni kamar ko wace ƴa. “Mama idan na zo gobe zan fada miki komai, maganar ba zata yiyu ta waya ba” “To Allah ya kawo ki lafiya” “Amin” Na sauke wayar sannan na tashi na nufi wardrobe na dauko kayan bachina wando da riga na saka. Da kaina na tafi na rufe gate din gidan saboda yau ni ce kadai a gidan daman Abdulhamid ya saba rufewa yau kuma ba ya nan, bayan na rufe gate a dawo na rufe kofar falo na kashe kayan kallo da wutar falon sannan na shiga dakina na kwanta ba dan bachi ba domin na san bachi ba zai dauke ni haka nan kawai ba sai idan wani abun na sha. Data ta na kunna na shiga media rabon da na yi chat ma har na manta, na samu sakkwanin da yawa musamman ta whatsapp, na groups da na private har na gaji da bibiyar grps din na kashe datar. Misalin daya da yan mintuna da na ji kamar ana taba kofar falonmu, da farko tsoro ya kamani a tunanina ko aljanuna, sai da na jai motsin yayi yawa har da saka abu aka dukan kofar ana kokarin ballanta sannan na taso na fito daga dakin cikin karfin hali. Isowa falon tai daidai da balla kofar da akai domin kadan ya rage ba su cireta ba har ginin gurin sai da suka taba gurin balle kofar. Wadancan mutanen ne dai wadanda suka zo wacan karon, masu sanye da mask da kuma bingogi. A take a nemi tsoron da ke cikina na rasa, ashe akwai ranar da ko mutuwa za kai arba da ita baka tsoronta. “Waye ku? Me kuke nema agurina? Waya turo k? Shi wanda ya turo ku me na tare masa?, miyasa ba ku zuwa sai a lokacin da mijina baya nan? Fyade kuka sake zuwa min? Ku sake sakawa mijina ya ki yarda da ni kamar wancen karon? Ku saka bindiga ku harbe ni zai fi min jindadi da kwanciyar hankali sama da ku same min wani cikin, ko waye kai ka san ni kuma ka san cewa mijin ba shi da lafiyar da zai iya kusantata shiyasa kake min haka saboda ka tarwatsa rayuwata, to Allah ba zai barku ba sai ya saka min.... ” Ina rufe bakina daya daga cikinsu ya karaso kusa da ni ya buga min kan karamar bindigar da ke hannunsa abaki, wani azababben zafi na ji kamar babu bakin ma, ko kuma wacce aka cirewa hakora, a take jini ya samu hanya. Uku suka zauna a kujera yayinda sauran suke a tsaye. Ban iya sake cewa komai ba, dan ban yi zaton bakina yana ajikina ba har lokacin, faduwa nai zaune na tara hannuna jinin dake zuba daga bakina yana ta tsiyayomin. “Yau ba gurin mijinki muka zo ba, kuma ba mu san cewar mijinki baya gari ba, ba turo mu akai ba zuwan kanmu ne, kuma baki san daya daga cikinmu ba, sai dai na lura zuciyarki tana da tauri a yanzu” Wanda ya buga min bindigar ne ya fada min haka yana tsaye akaina, muryarsa gargada take kamar wani boss kuma kamar yana taunar wani abu a baki, da alama ya boye ainahim muryarsa ne dan kar na gane shi, domin zuciyata bata yarda cewar wani ne dabam wanda ban sani ba. Risinowa yai ya kai hannunsa da cikin bakar safar hannu ya taba cikina. “Amman da gaske kin yi ciki? Da gaske a akwai ciki a jikinki?” Ya tambaya yana matsa cikin nawa da karfi kamin ya daga bindigarsa sama har sau uku, ban tana sani haka bindiga take da kara da kuma firgirtawarta ba sai yau, wani abu na ji cikin kaina daga nan ban sake sanin inda nake ba.! 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣4️⃣ A yanzun ma ina bukatar wani ya tsaya min? Har a yanzun ma akwai wata hujja da nakr bukata kamin na gamsar da Abdulhamid ko wani da yake kusa da ni cewar an shigo gidanmu? Bayan fasa min baki da sukai ga kuma halbi da balle kofar falo, ashe har da gate din gidan suka fasa mana, sai dai maganin bachin da na sha bachin da na sha be bar ni na ji bude gate din ba sai na kofar falo.   Sama sama nake jin maganar da su Mama da sauran kanena mata na yi, ban bude idona ba balle na iya tantance dare ne ko safiya ko kuma rana, sai dai a haniyar da nake ji kusa da ni har da Abdallah da wata macen da nake jin suna ta kira da Doc Safiyya.   “Halimatu....” Macen ta kira sunana, sai dai ban iya amsawa ba saboda ban yi zaton akwai sauran magana a bakin da nake jin kamar babu shi a sauran halittar jikina, saboda zugin da na ke ji. Kamar a mafarki na ji ta taba bakin ba shi na bude ido na zabura na tashi zaune da sauri. “Sannu...” Shine abunda ya fito daga bakin Abdallah yana kallona da mugun tausayi. Ban san yadda bakin nawa yai ba amman ina jinsa kamar ya min nauyi ga wani uban zugin da yake min kamar an cireshi. Fita yai ya bar mana dakin likitar ce ta gyara min bakinta ta saka min bandeji sannan suka canja min daki zuwa wani.   A lokacin da aka shiga da ni a na kiran sallah asuba, tun da na lumshe idona ban bude ba har Abdallah ya shigo yana miki min waya. “Mijinki yana son waya da ke” Ban bude idona ba ban kuma yi wata alama ta zan bude din ba, har ya gaji ya maida wayar a kunnesa ina jin yana fada masa cewar bachi na ke. Yana fita Mama ta shigo da shesshekar kukanta ta zauna a kujerar da ke kusa da gadona, a lokacin ne na bude idona na kalleta idonta sun yi ja sosai alamar kuka tai da yawa. “Sannu Halimatu...” Daker na gyada mata kai sannan na sake maida idon n lumshe, ban sake budewa ba sai da rana ta soma haskowa cikin dakin. A wannan karon ba Mama na gani ba Inna ce zaune a mazaunin Mama. “Sannu” Nan ma kan na gyada mata ina jin ya min nauyi kamar ba nawa ba. Da kanta ta je ta kira wani likita namiji ya zo ya duba ni ban samu matsala ta ko'ina ba sai ta bakina shi ma kuma gindin bindigar da suka buga min ne, kamar wata karamar yarinya haka na zama duk yadda aka so na ci abu sai na kasa saboda zafin da bakin ke min. Ruwa kawai na sha shi ma kadan, sannan na tashi na shiga bandakin da ke cikin asibitin nai alwala na gabatar da sallah asuba. Ina sallame sallar abunda ya faru ya dawo min, a wannan karon ban samu wata shaida kmar wacan karon da na samu zoben mutumen ba wanda na ganshi a hannun Abdallah, a yanzu abunda nake ta kokarin shine siffanta surar mutumen ko zan iya gano waye ne yake min haka, idan an siffanta shi da Abdallah sai idanuwa su nuna min kamar Abdallah ya fi shi jiki, wata kila kuma dimaucewa ce ta sa ba zan iya tantancewa yadda ya kamata ba. Idan ba Abdallah ba waye? Wana tarewa wani abu? Amman miyasa zan yi ta zargin Abdallah? Saboda shi ya saka ki a gaba ya hana ki rawar gaban hantsi, ita ce amsar da zuciyata ta ba ni.   “Ba mu san cewar mijinki baya nan ba, wannan karon ba gurin mijinki muka zo ba, da gaske akwai ciki a jikinki?” Su ne kalmomin da ke ta maimaita kanta a cikin kwalkwalwata, dalilinsu na ke bukata, da gaske ba su san cewar mijina baya gari ba? And idan ba a gurin Abdulhamid suka zo ba, me za su zo su yi gurina? Fyaden suka sake zuwa su min ko kuma wani abun dabam? Ban raba dayan biyu ba Hajiya tai sallama ta shigo tare da yar autarta wato kanwar su Abdallah, Inna ce ta amsa mata, ni kuma na juyo daga saman carpet din da nake zaune na kalleta. Ba shakka na ga tausayi a fuskarta tana ta min sannu ina gyada mata kai domin har lokacin ban yarda wata kalmar ta fito daga bakina. “Ta ci abincin?” “A a ruwa kawai ta sha shi ma kadan” Inna ta bata sai ta sake cewa. “Allah dai yasa ba su mata komai ba” “Aa bakinta dai ne suka fasa, ina jin ko sun buga mata abu ne” “Ayyah, Allah dai yasa ba su taba ta” Wannan karon sarai na fahimci gun da tambayar Hajiya da dosa, ba lafiyata take nufin an taba ba, martaba take magana, da farko na ji ba dadi wata zuciyar na fada min cewar danta take tayawa kishi ko kuma take yi ma fargaba, ta wani gurin kuma tana da gaskiya domin mai kaunar ka ne kawai zai iya kulawa da wannan. Ba ita kadai ba na san mutane da yawa ma za su kawo wannan tunanin a zuciyarsu wata kila har da Abdulhamid din. “Aa ba su mata komai ba, bakin ne dai suka taba” Inna ta bata amsa sai Hajiya ta dora da bayanin yadda aka kawo ni asibiti. “Ni ai ina kwance sai ga kiran Hassan, tsoro duk ya kama ni domin be saba kirana irin wannan lokacin ba, gashi kuma yace min zai yi tafiya har ya kira ni ya ce min su isa, cikin tsoro na dauka sai na ji shi ma hankalinsa a tashe muryarsa har rawa take wai na kira Husaini na fada masa yaje asibiti,na ce wace asibitin lafiya, a nan ya fada min wai makocinsa ya fada masa yan fashi sun shiga gidansa har sun yi harbe harbe” A nan Inna ta tari numfashinta da cewar. “To ya akai ya san sun shiga?” “Ai makoncin nasa ma sun shiga gidansa suka karbe zinari, kuma suka shiga gidan da ke kallon na su Halimatu shi mai gidan ma sun kashe shi, to shi wannan wanda ya kira Hassan din shi ya kira yan sanda kin san shi ma dpo ne, ko da suka zo har sun gudu sai ganin gate din gidan Hassan akai a bude, shi ma na makocinsu a bude iyalai sai kuka suke” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, to wai turo su akai ko me?” Inna ta tambaya sai Hajiya ta tabe baki “To waya sani, shi dai wannan Alhaji ance ba su karbi komai ba kashe shi kawai sukai wai sun ce ransa kawai suke so, shi kuma na wannan Alhaji Munir din sun karbi gulagulai da kudi, shi ma Alhaji Munir din sun fasa masa kai ai, ko da suka kawo Halimatu Asibitin nan kansa na jini shi ma an bashi gado aka ce” “Subhanallahi, ko shine na ji Anty na cewa na leka na ganshi? Allah sarki Allah ya tona asirin ko su waye” A zuciyata na amsa da amin, ina ta tsarguwa da kallon da Hajiya ke min. “Amman ke ba su dauki komai a gidan ba ai ko?” Na girgiwa Hajiya kai alamar a'a “Ikon Allah sai suka fasa miki baki kawai dan zalumci, kai mutum.....” Ta karasa da fuskar tausayi, ni kam tuni hawaye sun cika min ido har sun fara wanke min fuska. Ban sake maida hankali akan duk wata fira da suke da Inna ba, domin tunani ya rabu biyu, makomata na ke hangowa da kuma kokarin wanke Abdallah da zuciyata ke yi. Anya zai iya aikata kisa? Taya mutum mai aikin kamarsa ma zai iya shiga fashi da makami? Me zai kai shi shiga? Yes wata kila ba shiga yai ba gaba daya ba, what if labawa yai a cikinsu saboda ya samu biyan bukatarsa? Can kuma wani bangare na zuciyata ya jefo min wata tambayar? Miyasa sai Abdallah na ke zargi? Mi zai saka dan'uwa yai ma matar dan'uwansa haka? Miyasa be min a lokacin da nake gidan Aminu ba sai a nan? Saboda a can yana ganin zan iya fitowa wata rana kamar haka na aureshi amman a yanzu babu wannan damar? Na riga na auri dan'uwansa dan uwan ma twins brother dinsa.... Na kasa yarda cewar shi kadai din ne, zuciyata kuma ta kasa natsuwa cewar ba shi din ne ba, na kasa zargin kowa sai shi. Sai da Hajiya ta fice sannan na samu natsuwa da sukunin mikewa tsaye na nufi gurin windows domin ba Hajiya kadai ba, Inna bata cikin dakin a wannan lokacin, tsakanin kalaman Hajiya da zargin Abdallah da kuma tambayayin da mutumen yai min da kalaman Hajiya sai na rasa wanne zan fara tunani? Wasu abubuwa na ji suna min yawo a cikin kai ga wani uban nauyi da zuciyata tai. Kaina na jingina jikin window ya lumshe ido ina jin kamar zan samu mafita a nan. Ajiyar zuciya na sauke ya fi a kirga sannan bude idon da ke cike da hawaye ina ta kallon mutane da ke kai kawo harabar asibitin, duk wanda na hango burge ni yake domin na san damuwarsa ba ta kai kamar tawa ba, murmushi nake hangowa a fuskar wasu wasu kuma dariya na ke gani a fuskarsu abunda ni na gagara samu. Wani na soma hangowa kamar Kabir kamar ba shi ba, sai da na kara maida hankalina sosai gurin kallonsa da yanayinsa na hauka da yake ciki ya tabbatar min da Kabir din ne, har yanzu tsingiltar take yana tafiya ya nufo cikin asibitin, sai ga securities din da sauri su ka zo suka rika shi suka fitar da shi daga asibitin. Neman natsuwata da damuwata nai na rasa, gaba daya sai hankalina na koma gurin Kabir din. Ban san kuka nake mai sauti ba, har dai da yarana suka shogo na ji muryar Adnan yana min magana. “Momy kuke kike yi?” Juyowa nai na kallesu na gyada masa kai alamar eh kukan nake, domin a bayyana hake kuma ba zan iya boye shi ba a wannan lokacin, gaba dayansu suka fashe da kuka har Amal da take karama ganin nima ina kuka, risinawa nai a gurin na zauna a kasa sai suka zo kusa da ni suka zauna. Ni da su aka mai rarrashin wani, wani bangare na rayuwata ta baya ya fara fado min a rai, a lokacin da na samu cikina na farko cikin Adnan, ina farinciki ina jindadi saboda ina son ya'ya, amman Aminu ya nuna min ba haka ba sai dai a zubar shi be shirya haihuwa yanzu ba, rana za su tsufar da shi, za su hana shi shakatawa yadda ya kamata, daga lokacin komai ya sauya min na fara fuskantar kalubalen na rayuwa kala kala har na haifi Amal. Babu sunan da be kira ni da shi ba, yace min ina ta haihuwa kamar kaza, ina ta tara masa yaya saboda idan ya mutu na co gadonsa. Daga lokacin da na baro gidansa na yi zaton damuwar ta wuce na yi tsammani dadi zanji a gidan Abdulhamid ashe ba haka ne ba, wahalar bata kare ba damuwar ba ta wuce ba. “Haba Halimatu ya za ki saka yaya a gaba kina kuka suna kuka? Miye haka?” Maganar Inna ce ta saka na dawo hayyacina har na goge hawayena na mike tsaye na hau saman gadon na kwanta. ABDALLAH POV. Yana fitowa daga dakin theater ya nufi wani dakin dan tsabbace jikinsa da kuma cire tufafin da ya fito da su daga tiyatar, sai da ya cire komai ya wanke hannunsa sannan ya nufo office dinsa. Zaunawa a saman kujerarsa sai ya ji kamar be zauna ba, sai da ya gyara zamansa sai yaji ba zaman ne abunda yake bukata ba. Tsaye yai dafe da kansa yana motsawa a hankali sai hawaye suka sauko masa. “Why....?” Jinginawa yai da ginar office din yana hawaye, he can't remember when last yai hawaye ko ya shiga damuwa irin haka, ko a lokacin da Halimatu ta auri dan'uwansa be samu kansa cikin damuwa kamar haka ba. “I'm such a stupid.... Me yake damuna wai? What is wrong with me?” Ya daga kansa sama hana hawaye tare da kuka marar sauti. “Miyasa jabawata za ta zo a nan? Mi nai? Oh my God Allah kai kadai kasan dalilin da ya saka ka dora min son Halimatu....” Juyawa yai yana kallon wayarsa da ke ringing. “Kuskure ne abunda na ke yi, be kamata na bar Abdulhamid ya gano komai ba” Ya busar da iskar bakinsa sannan ya nufi gaban teburin ya dauki tissue paper ya goge fuskarsa. Kiran na sake shigowa yai picking. “Hello Hajiya” “Na'am ya aikin?” “Al-hamdulillah” “Husaini na ce ka saka a yi ma Halimatu gwajin ciki da na hiv” Mamaki ne ya cika fuskarsa. “Why?” “Why? Kamar ba ka san abunda ya faru ba?” “Amman Hajiya kin ce ita da kanta ta ce ba su mata komai ba” “Ai to fada za tai? Ai ba zata fada ba” “Hajiya be kamata ki yi wannan maganar a yanzu ba, za ki kara sakata cikin damuwa ne, kar ma ki kawo ma Abdulhamid wannan tunanin dan Allah, ki aje wannan maganar na gafe” “Wallahi ba zan aje ba, dan ba zan yarda ta cutar min da ɗa ba” Tana fada hakan ta kashe wayar. Zaunawa yai a kujerar ya dafe kansa. HALIMATU POV. Da yamma Abdulhamid ya shigo asibitin, shi ma na ga damuwa da tausayi a fuskarsa da kuma kulawa a mu'amalarsa. Ni kuma na kasa sakewa da shi ko da na minti daya, irin kallon da nake ma Aminu na ke masa a yanzu. Bayan magariba polices suka zo suka suna min bincike sai a lokacin na yi dauriyar da na bude bakina na rika amsa musu tambayoyinsu, sun tambaya ko zan iya gane mutane na amsa musu da a a domin fuskokinsu a rufe suke kuma muryarsu ma a boye take, sun dauki duk bayanin da ya kamata su dauka sannan suka tafi. Kwana na biyu a asibiti suka sallame ni ganin na samun sauki, sai dai a cikin magunguna da suka ba ni har da na hawan jini kamar yadda suka fada min cewar ina da shi, a ranar da zan koma gidan mijina sai na ji kamar zan koma a cikin wata duniyar ta dabam, domin a asibitin ina ganin mutane familyna abokaina da kuma yayana suna cire min kewa ba kamar a yanzu ba da zan koma ni kadai. An gyara komai a gidan kamar babu wanda ya shigo, kofar ma an canja ta kamar yadda aka canja gate din, har na shiga dakina Abdulhamid be ce min komai ba, ni ma kuma ban ce masa ba, daman kuma ni me zan fada masa? Ce masa zan yi ka yarda da ni? Ko na tausaya min? Ko kuma ya zo mu yi kuka tare? A daren ranar ji nai kamar ba zan iya bachi ba dan haka na tashi nemam maganina da ke saka ni bachi amman ban samu ba. Na tsorota sosai rashin ganin maganin da nai domin na san akwai wanda ya ga maganin har ya saka hannu ya dauka. Wanin kuma ba zai wuce Abdulhamid ba domin shi kadai nake da tabbacin zai iya bincika duk abunda yake so a gidan nan. A haka na kwana bachi ba bachi ba, minti daya biyu uku na farka, kamin ya sake daukata kuma sai an dade, da safe shi ya shirya mana abun karyawa da kansa ya shigo ya tashe ni na fito falo, amman sai na kasa cin komai, shi kan ya ci biredi ya sha tea sannan ya tambaye ni akwai wata matsala? Ko abunda na ke bukata na girgiza masa kai. “Okay zan aiko miki da takeway da rana, da dare ma idan za a dawo zan siyo mana wani abu, me kika so ki ci?” “Bana bukatar komai” Kallo kawai yai ya dauke kai ya shiga dakinsa ya shirya ya fita. Daga lokacin sai zanantakewar mu ta sake sauya sabon salo baya bari nai girki sai dai ya siyo mana abinci, na sa yana min hakan ne domin ya nuna min ya damu da ni bayan kuma ya kasa kwanta a gadon da nake kwana kamar da, ya kasa sakewa da ni kamar da, sai yawan kallona da yake kamar mai tunani, zuciyata na raya min be natsu da ni ba, wani lokacin ina jin kamar barin gidan shine mafita a agare ni da kuma shi, Har nai sati da sallamowa Hajiyarsa bata sake daga waya ta kira da sunan ta tambaya ya jikina ba balle har ta zo ko ta aiko a dubani, Abdallah ma tun a lokacin da ya miko min waya a asibiti ban sake jin duriyarsa ba, ba ma wacce ta fi ba ni mamaki kamar Suwaiba matarsa wacce bata zo ba kuma bata kirani ta tambayi lafiyata ba balle tai min jaje, abun har ya daure min kai wata kila kuma ita ta fara bin bayan Hajiya ne wajen tsanata duk da ban san na musu komai ba, ni kam bana dacewa da iyyen miji, haka uwar Aminu da kanensa suka tsane ni, ko da yake bana da sa'a da dacen rayuwa shiyasa saka hakan yake faruwa da ni. Bayan mun gama cin abincin dare ya fada min cewar na shirya gobe za mu je asibiti, be fada min dalilin zuwan ba ni kuma ban cire tsammanin wani ko wata za mu je gani ba, ashe abunda ban sani ba gurin gwaji zai kai ni gwaji zai kai ni, mamaki ya cika ni, har na kasa boye damuwata da kuka a lokacin, sai dai ban ce masa komai ba duk kuwa da kasancewar a yanzu na kara katsewa da lamarinsa. Mijina be yarda da ni ba kenan. “Zanje office na dawo kamin a gama, saboda akwai layi sosai” Kai kawai na iya gyada masa na bishi da kallo har na daina hangoshi. Miyasa ba zai fada min naje nai gwajin ba? Mi yasa ba zai fada inda za mu je ba tun jiya? Idan ma aka samu ina dauke da hiv ko wata cutar Abdulhamid rabuwa zai yi da mi kenan? Lallai na sake sarewa da lamarin maza! Ina zaune a gurin ina bin layi hawaye na min zuba har aka kawo kaina, duk wanda ya gan ni a cikin wannan yanayin zai yi tunanin ko ina tsoron kar ace ina dauke da cutar ne. Bayan an dibi jinin nawa na fito na baro asibitin ba tare da tsayawa sauraren komai ba, ba fargaba nake kar ace ina dauke da cutar ba, na kasa raba dayan biyu a tsakanin neman Abdulhamid ya sake ni ko kuma na cigaba da hakurin zama da shi? Da kafa nake tafiya ina ta kallon ababen hawa da mutanen da ke kai kawo ba dan bana da kudin napep ba sai dan ina jin kamar tafiyar kasa zata sama min sassauci, ban san inda zanje ba tafiyar kawai nake duniyata na juya min. Wayata na ji tana ringing alamar kira ban tsaya komai ba na saka hannuna a jaka na fiddo wayar ba tare da na duba sunan mai kiran ba nai picking. “Kin fito daga asibitin ne?” Muryar mai kiran ta karantar da ni ko waye ne. “Na fito ina bakin titi” “Bakin titi gurin me?” “Ban sani ba....” Na amsa ina jin kuka kamar zai kubuce min. “Daidai ina kike tsaye?” Waigawa nai na duba hagu da damana sannan na soma masa kwantanci. “Ina kusa da Exclusive City” “Okay shiga ciki ki zauna ga ni nan zuwa” Kai na gyada masa kamar ance yana kallona sannan sauke wayar na share hawayen da suk zubo min na nufi Exclusive City din, babba guri ne na manyan mutane yan kasaita, gurina da masoya suka fi zuwa saboda tsarinsa da kuma abubuwan kawa da aka tanadar a gurin ga abinci kala kala, haka na ke jin ana yawa fada duk da ban taba zuwa ba sai yau. Duk sai na ji dabam abun ka da wanda be saba ba, duk kuwa da kasancewar gurin kowa be kula da kowa ba, akwai guraren zama da yawa amman sai na ji na tsawwala kamar ba zan iya zama a gurin ba. “Akwai wanda kike jira ne?” Daya daga cikin ma'aikatan gurin ne yai min tambayar yana sanye da rigar aikinsa. “Aa ina son na zauna a gurin da babu mutane sosai” “Okay ga vip 1 can ga kuma vip 2 can, za ki iya zama a daya daga ciki” Ya fada yana nuna min vip 1 da ke kasa da kuma 2 din da ke sama, zuciyata ta fi natsuwa da 2 din ganin shi a sama yake kuma bana iya hango komai daga inda tsaye hakan na nufi na cikin ne zai iya hango na waje, tsabanin na waje da ba zai iya hango wainar da ake toya a cikin ba. Kai tsaye na nufi hanyar da zata kai ni VIP 2 din, ina shiga na samu gurin fiye da yadda nake tsammaninsa domin tsakanin wani teburin da wani a akwa doguwar tazara ga kamshi da iska mai dadi na kadawa, komai na gurin ja ne gwanin sha'awa sai wani dan sauti da ke tashi mai dadi ta taba zuciya mai kuma daidai da kowane irin yanayi. Ko wane tebur kujera uku ce zagaye da shi amman ban da tebur daya mai kujera biyu masu fuskantar juna. Zuciyata ta fi natsuwa da shi fiye da sauran hakan yasa na nufi gurin na ja kujera daya na zauna. Wata irin natsuwa ta sauko min ba natsuwa irin ta masu kwanciyar hankali ba, natsuwa da samun damar yin kuka issasshe ta samu damar tausayawa, ta samu damar yin tunani da kuma nemawa kai mafita....! 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣5️⃣ “Abun nan fa ya wuce iya abunda kike tunani, Wallahi mutanen nan ba za du yi karya ba, kuma ga zahiri kina gani, abubuwa sai kara kwabewa suke” Aminu ne yake wannan maganar yana shafa kansa cikin tsananin damuwa, hannunsa na dama rike da takardar transfer. “Iko sai Allah, ni wani abun yana bani mamaki Wallahi, taya za ka biye maganar bokaye? Tun farkon fari ma mi ya kai ka gurin ya saka tsinbo? Da har za su fada maka karya da gaskiya ka yarda” “Hajiya ai dubiya yanzu babu wanda yake zaune, ba maza ba mata ba kowa kuma yadda lamurran nan suka fara lalacewa ai dole na saka a bincika min, ba ni kadai ba ko Alfa da ya kai ni sai da abun ya daure mata kai” “Allah kadai ya san gaskiyar wannan lamarin wata kila ma gurin malaminta ka fada, ko kuma shi alfan yana goyon bayanta ne, shiyasa suka hada kai ai maka haka” “Babu wani zancen goyon baya Hajiya fa a zahiri kike ganin komai sai lalacewa yake” “Kai fa baka iya tashin hankali ba, kai yanzu dan Allah Aminu har ka kawo maganar dawowa da Halimatu a gidanka? Mace da bata kaunar uwarka bata son yan'uwanka? Ka duba ja ga har kazafi tai wa Sadi fa? Wallahi har a bada ba zan taba son Halimatu ba” “Hajiya abunda ba ki sani ba, ko wane dan'adam yana da good side of him kuma bad side, Wallahi Hajiya ba dan ina son dawowo da Halimatu ba, acire zancen arziki, Hajiya Halimatu ta fi Murja hakurin zama da ni, Halima ko bata son abu bata nuna, sannan ko fada nai mata ko na ci zarafinta sai dai tai kuka ta ba ni hakuri, and tana kokarin ganin ta gujewa bachin raina, zan iya tafiya inda nake so nai iya adadin kwanakin da nake so na dawo bata ce min komai, amman ban isa nai ma Murja haka ba Wallahi Hajiya, idan na dawo tara na dare Wallahi sai Murja ta yi min fada, amman a lokacin da Halima take nan zai iya kai wa 1 na dare a waje kuma ba zata ce min komai ba, Murja ta bi ta saka min ido akan komai nawa, ba ni d sukunin daukar waya na latsa a cikin gidana idonta na kai” Hajiya ta saki baki. “Ban gane idan kai dare tai maka fada ba? Uwarka ce ita? Ita ta aje ka ko kai ka aje ta da zata maka fada? Ita ba mata ba ce da ba zaka mata magana ba” “Hajiya ba za ki gane ba ne, idan ranta ya bace, jikina har rawa yake Wallahi” “To acan gurin malaman da kaje ba su fada maka komai akanta ba?” “Me za su fada min? Ni yanzu ba ta nata nake ba, ta Halimatu na ke domin sun fada min matukar ban mayar da ita ba, ba zan taba ganin komai daidai ba, kuma ga alama nan kina ganin bayan rage min mukami da akai yanzu an min transfer zuwa enugu, duka duka yaushe ne rabuwar mu? Idan aka kara dadewa kila ma bara zan koma, tun da sun ce ita ke da kashin arzikin duk abunda na samu saboda ina tare da ita ne, ni da farko ma na dauka ko sammu ne kai mi shiyasa ma har na biye ta Alfa ya kai ni gurin ashe ba asiri ba ne rabuwar da mu kai ce, Hajiya ki duba fa ki ga abun hawa ma neman gagara ta yake, motata na mata gyara uku abunda ban taba ba, yanzu na siye sabuwa ita ma engine dinta ya tsaya, sabuwar mota fa Hajiya Motar miliyan biyar ace engine dinta ya tsaya” “Wai kana nufin ba da motar ka zo ba?” “Wallahi Alfa ne ya sauke ni bakin gate, tun jiya motar ta tsaya tana can gurin ma su gyara” “To abun nan fa d daure kai ni na fi zargin sammu gaskiya, asiri ne akai maka, ko ita ai zata iya maka asirin na ka lalace tun da ta ga ka sake ta, ko kuma abokan aiki ko makota” “Hajiya Malami hudu msgana daya suke, babu wanda yace asiri ne, ni dai ki taimaka min ta dawo dan Allah” “To ai ban ga ta inda zan iya taimaka maka ba, matar nan fa ma aure tai gidan wani take” Dafe kansa yai. “Kai Hajiya, ko wane da idan yana cikin matsala gurin uwarsa yake zuwa ta sama masa mafita, amman ke sai kokarin kin yarda kike da ni” “Ba yarda ne ban yi da kai ba, nawa binciken zan yi akai” “To ki kara bincika mu ji idan za a samu results daya, ni yanzu yarana nake son na fara dawowa da su hannuna, na san ina dauko yaran nan hankali zai dawo kaina dan bata hada su da kowa ba” “Tana son su za tai aure ta bar su?” Cewar Hajiya tana tabe baki. “Wannan ai na dabam ne, idan naja yaran a jikina na nuna musu su janyo uwarsu ai dole hankalinta ya dawo nan, Wallahi shegen son ya'ya ne da ita Allah kadai ya san yadda akai ma tai aure ta bar su” “Kudi ta bi, shi wanda ta auran ba ance dan uwanta ba ne kuma mahaifinsu ya bar musu dukiya, ai kudi babu abunda basa sakawa, ni ganin na ke komai kai ba zata bar wacan mijin ta dawo maka ba” “Zata dawo ai kin dan yadda take so na, kuma daman first love shine so ai, kuma ni na san Halima na so sosai Wallahi, zata dawo da gudu ma” “Uhm... ” Mikewa yai tsaye. “Motarki na nan Hajiya?” “Wallahi na aiki Musa direba da ita Mafara sako zai karbo min, ka kira Sadi ya kawo maka motarsa daya mana ai mota biyu ne da shi” Ba musu ya koma ya zauna ya ciro wayarsa ya kira kanensa Sadi. Ringing biyu zuwa na uku ya daga. “Sadi kana ina?” “Gani kusa da gidan Hajiya” “To ina gidan karaso ka sauke ni gida” “Okay” Bayan na sauke wayar, Hajiya ta cigaba da yi masa maganar so take ta karkarto hankalinsa da barin zancen maido Halimatu domin ita a ganinta ba mafita ba ce, zuciyarta ta fi natsuwa da sammu akai masa ko dai Halimatun tai masa ko kuma wani dabam, ba a wuce minti ashirin ba Sadi ya shigo gidan cikin sabuwar shadda light yellow da hula kubu sai kamshin turare yake. S tsaye ya gaisa da Hajiya domin shi ma a hanya yake akwai inda yake son zuwa. “Gida zaka sauke shi” “Ina motarka ne?” Sadi ya tambaya yana barin kallon Hajiya wacce tai masa maganar. “Wallahi ta samu matsala wai engine dinta ta buga” Aminu ya fada cike da damuwa a fuskarsa. “What, motar da ka siyo satin nan ko dai wacan tsohuwar” “Tsohuwar ai siyar da ita nai, wannan dai sabuwar” “Garin ya?” “To ni ina ma zan iya cewa ga dalili, abubuwan ne dai sai hamdala” “Allah ya kyauta, tashi muje” Sai da Aminu da Hajiya suka amsa da Amin sannan ya mike tsaye suka fice tare. Har gida Sadi ya kawo Aminu, bayan ya bude motar ya fita Sadi ma ya bude ya fito wai bari ya gaisa da Madam. Aminu na shiga cikin falon Murja da taso da sauri ta rumgume shi tana masa oyoyo sai shagwaba take zubawa kamar wata karamar yarinya. “Ina tare da shi fa Hajiya” “Dan kana tare da shi sai ya hanani nunawa mijina soyayya?” Murmushi Sadi yai ya dauke idonsa ya nufi kitchen. “Bari na sha ruwa” Kitchen din ya shiga da kansa ya dauko cup ya bude freezer ya dauko robar ruwa ya bude ya soma bulbulawa. Kamar daga sama ya ji am rumgume shi ba shiri ya dire ruwan da yake sha ya juyo da sauri yana kallon kofar kitchen din. “Kai dan Allah sarkin tsiro, ya shiga dakinsa” “Amman ai zai iya saukowa yanzu kuma ya shigo nan” Ya fada da rada hankalinsa a tashe yana kallon kofar kitchen din dan ya san the worst thing da zai aikata shine ya bar dan'uwansa ya san alakar da ke tsakaninsu. “Ka daina zuwa kwana biyu, i miss you” Ta fada tana dora hannunta a saman lips dinsa sai lumshe ido take da fake eyelashes dinta. “Murja alakar mu ta da ba kamar ta yanzu ba ce fa, saboda dan'uwana kike aure dole nai tsaka tsantsan” “Auren dan'uwanka ya hana alakar mu cigaba ne? Tun farko ba kai kaja ba, da aka aurena zan auri yayanka ne, sai wani kwana kwana kake min jikina kawai kake so” Saurin turarenta yai daga jikinss ya fito daga cikin kitchen din jin kamar motsin fitowar Aminu a falo, kai tsaye ya nufi kofa ya fice daga falon gaba daya. Dariya murja tai ta nufi dakin mijinta, da taimakonta yai wanka ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan ta gabatar masa da abincin rana. Cin abincin suke yana ta sake2 yadda zai bullo mata, so yake ya fada mata cewar yana son ya dawo da yaransa a gidansa amman yana jin tsoronta, baya son bacin ranta idan ranta ya bace ji yake kamar zai mutu, ko motsi dai sai ya rasa natsuwarsa saboda tsoron abunda zai fito daga bakinta, haka Allah ya saka masa tsoronta kamar mutuwarsa, idan ranta ya bace har kuka yake mata gurin bata hakuri abunda be taba yi ma wata mace ba, ko Hajiyarsa baya tsoro yadda yake tsoron Murja. AHMAD POV. “Na dauko Baby Namra daga gidan Hajiya, ka dawo gida da wuri karka wuce 8” Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya amsa mata ta okay. “Yayi Mommy's Boy” Rahim ya fada yana dariya. “Ba fa abun dariya ba ne seriously bana jindadin abunda kake min” “Okay sorry but abun nan yana ba ni dariya” “Ba abun dariya ba ne, abun nan gaba yake kara yi ba baya ba, na rasa yadda zan bullowa lamarin nan, yanzu fa ta kai har wayata Hajiya ta ke karba ta duba, irin ita bata yarda da ni ba,kullum ganin take kamar yan mata wayo za su min” Rahim ya kara matsowa kusa da shi ya da fashi. “Magani kawai kai aure Gwarzo, matukar ba aure kai ba zai Hajiya ba zata daina ganinki a yaro ba” “Auren ba mafita ba ne, yaure uku nai kamin na auri Halima amman ko wace ta kasa zama da ni sai Halima ita ma kuma saboda ta yi hakuri ne, bayan rasuwarta mace biyu na aura Hajiya bata barin na zauna da mata, tun da idan bata ga dama ba sai ta hana ni cin abincin mace ta ce bata yarda da shi ba, kuma ko yarinyar na nemo idan bata gamsu da ita ba ba zata bar ni na aureta ba” “Wata mace zaka aura ba yarinya ba, mace mai hakuri da sanin ya kamata, kuma kamin ka aureta ka fara gabatar mata da Hajiya ka fada mata komai na ka karka boye mata, kai idan ta kama ma kai auren a boye kai yi dan samawa kanka mafita, dan Hajiya har yanzu bata daina ganinka a yaro ba, bata yarda ka girma ba” “Wallahi abunda take min ko Baby Namra albarka, dan yau idan Baby Namra ta ga dama zata iya zuwa wani guri a cikin familymu tace can zata kwana kuma Hajiya ta barta amman ni ban isa ba, abun da Hajiya take min har dauren min kai yake wani lokacin har daure min kai yake” “Ka samu wata ka aura, irin macen nan da ta saba shan wahalar gidan aure, ka aureta kuma ka fada mata komai karka bi soyayya ka auri yarinya ta zo tai ma Hajiyarka hauka ko ta kasa hakuri da kai, iirin dai mace mai yaya biyu uku aha” “Kai ba zan iya auren macen da wani ya aura ba, you know ina da kishi sosai, ba zan iya zama macen da wani ya aura ba balle ma wacce tai aure har fiye da daya” “To ai kaji matsalar ka fi son ka auro yan matan nan na zamani kansu na hayaki dole su ce ba za su zauna da Hajiya ba, ba wai dan kana sonta zata aureta ba, kai ko auren kwangila ne kai kawai da zarar ka samu yancinka gurin Hajiya sai ka rabu da ita ta auro wacce kake so, ya kamata ka amsa sunanka na Gwarzo fa, na san baka daukar rainin kowa a kamfani, idan ka bawa mutum umarni jikinsa har rawa yake ya cika maka aikinka, to ko a gida ya kamata kana motsawa” “Da Halima na nan da yanzu na amsa, Ba zan taba son wata ba Rahim, ni mijin matacciya ne, na riga na auri Halima kuma na auru, duk mace da zan aura zan aureta ne kawai dan samun mafita amman ba dan kauna ba” Yayi maganar cikin sanyayyiyar murya, yana sotsa lips din, zuciyarsa na sosuwa da kauna Halimatunsa Uwar Baby Namra. “Halima ta yi min abunda wata macen bata taba min ba, ta haifa min Baby Namra, ta yi hakurin zama da Hajiya har na tsawon shekara biyu...” Rahim ya soma lura da yanayin abokinsa, daman ya saba shiga a irin wannan yanayin a duk lokacin da aoa dauko maganar Halimatu, a kokarinsa na kawar da maganar ya dauko masa maganar kamfani. “Yauwa na manta ban fada maka ba, sun fa turo takardun nan ta mail din kamfani amman sai mun yi printing out....” Mikewa Ahmad yai tsaye cikin damuwa. “Dan Allah ka daina maganar wani kamfani a yanzu, lemme go and rest...” Fita yai daga gurin ya nufi motarsa, yana shiga ya dauki hanyar Exclusive City. HALIMATU POV. Na yi kuka iya wanda zan iya, na yi na gaji na rarrashi kaina domin ba ni da mai rarrashina a wannan lokacin. Daya daga cikin waitress din dake gurin ne ya zo yana tambaya idan ina bukatar wani abu? “Bana bukatar komai, akwai wanda na ke jira ne” Juyawa yai ya koma gurin da yake tsaye, ya cigaba da danna wayarsa, binsa nai da kallo kamin na ji wata murya mai cike da bacin rai tana min magana. “Waya aje wannan matar a nan?” Juyowa nai na kalleshi da kumburarrin idanuwana, mutunen nan ne daya taba ture ni a keke, kuma shi ne wanda na gani a lokacin da naje kai Namra School, kuma shi ne mutumen da ya tsinci Namra. Da saurin waiter din dazun ya zo yana tambayar ba'asi. “Taya za a bar wata ta zauna a seat din nan? Me ke damunku? Da alama kai bako ne, kuma laifin ba na ku ba ne laifin shugabanku ne, for more than ten years ina biyan kudin gurin nan saboda tsabar rainin hankali yau za ku bar wani ya zauna? Oh haka kuke idan bana nan daman you're very stupid” Sauran waitress din suka zo suns bashi hakuri, wanda ni ban ga dalilin hakan ba, ko da yake na ji ya ambaci sama da shekara goma yana biyan seat din da alama baya son kowa ya zauna ne. “Ke dalla malama tashi ki rasa kujerar da za ki zauna sai wannan” Ko kadan maganarsa bata 6ata min rai ba, da alama macen da yake biyawa kudin kujerar tana da muhimmanci a gareshi, ba kamar ni ba. Mikewa nai tsaye na kalli kujerar sannan na kalleshi na ce. “Ka yi hakuri ban san cewa kujerar ta ka bace, ban san alakarka da mai seat din ba, mata, yar'uwa, uwa, ko ya ko kanwa, amman ka bata hakuri a madadina, domin ko wacece duniyarta kyakkyawa ce, kuma mai fadi ce shiyasa tai dace da mai kare martabar gurin zamanta ba ma ita din ba” Hannu na kai na dauki jakata na yi gaba abuna ina jin zuciyata kamar zata fito, na taki sa'a ina kawowa bakin gate din gurin Motar Abdulhamid na kunno kai a harabar gurin, sai da ya faka motar yana kokarin fita na nufi gurin motar na bude na shiga. Ba tare da yace da ni komai ba yai ma motar key muka kama hanyar gida. __________________ Wai ni kadai na ke hango wani abu?🤔 Bari mu ga masu brain me kuke hangowa? 🤔 Tafdijam 😲 fatar dai kun shirya tafiyar domin yanzu aka fara..... 😊 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣6️⃣ Na yi mamakin ganin kawata Sa'adatu tana jirana a farkon shiga falona, ko wa nuna mata gidana ma oho ni har na manta da ita a cikin duniyar nan. Tun kam Abdulhamid ya faka motarsa ta mike tsaye tana ta kallon motarmu. Har ya faka motar ya bude ya fita be ce mim komai ba kamar yadda nima ban ce masa ba tun bayan shigowa a motar.   Irin kallon nan da ta saba na yan bariki ta fara yi min kamin ta mikawa Abdulhamid shi tare da gaisuwa. Shi kuma ya amsa mata da fuskarsa ta rashin sakewa da mutane, ma'ana ba yabo ba fallasa ba kamar Aminu ba da idan ya ganta bakinsa har rawa yake wajen amsa mata gaisuwa. “Wa nake ganin kamar Sa'adatu?” “Ba kamar ba ce ni dince, tun da kin yadani ni ai na nemo ki” Na yi dariya kamar yadda ita ma tai tana bin Abdulhamid da kallo har ya shige falon sannan ta kalleni. “Shine angon na mu?” “Eh shine” Sai ta tabe baki har da wani lumshe ido ta bude. “No wonder ake mana rowarsa, ashe kyakkyawa ne mai naira, gaskiya Halima kina dacen auren maza masu kyau da kudi, ko da yake kina da kyau ne shiyasa, da ni ke da kyaunki da yanzu na ci kudi” ‘Yes ina dacen aure a gidan hutun amman ba dan na hutu ba, sai dan na fuskanci wani kabulen’ Na fada a raina a fili kuma sai nai dariya na ce. “A takaice dai mijina ya burge ki, gashi kuma shi ba kamar Aminu ba ne balle ku kulla” Kallon rashin fahimta tai min tana yar dariya kamar ta ji kunya. “Ban gane ba?” “To ya za'ayi ki gane kuwa? Ke dai zo muje ciki” Ina gaba tana biye da ni a baya har muka shiga falo. A kujerar da ke kusada kofar ta zauna ta zubawa Abdulhamid ido ni kuma na nufi two seater da yake zaune yana lasa waya na zauna a kusa shi, kamar wanda wani abun ki ya zauna kusa da shi haka yai saurin tashi ya nufi dakinsa, iyakar kokarin da nai na danne damuwar da na ji ne dan kar Sa'adatu ta zargi wani abu. Na tashi na shiga kitchen na dauko mata ruwa da lemun mu na hausa na kawo mata. Sai gashi ya sauko ko inda nake be kalla ba ya nufi kofa ya fice a uzurce. “Halimatu wane irin zama kike da mijinki?” Kamar daga sama na ji tambayar Sa'adatu tana mire baki. “Kamar ya?” “Ato kin san ni bakina baya shiru, na ga kamar akwai yar matsala a tsakaninku ko kuma shi haka rayuwarsa take?” “Wai Sa'adatu sakin fuska yasa raini ya shiga tsakaninmu har ta kai kike iya fada min duk abunda ya zo bakin kina mu'amulantata yadda kika ga dama” Sakin baki tai ganin kamar na taso mata da fada. “Haba Hajiya ta, makano ne kawai zai shigo gidan nan yace be fahimci akwai rashin jituwa tsakaninki da mijinki ba, kuma wanda ya damu da kai ne ya damu da matsalar ne kawai yake nuna maka damuwarsa, kalle ki Halima Wallahi har kin fi auki a gidan Aminu dama da nan” “Zuciyarki bata raya miki ko bana da lafiya ba? Babu abunda ya zo kanki sai rashin Jituwa?” “Hmm yanzu dai Allah ya baki hakuri, mu bar wannan maganar, ya yaranmu ya su Amal?” “Suna lafiya” Na amsa mata ina kara hade fuska tare da dauke kai. Shiru ya shiga tsakaninmu kamin ta sake dauko wata maganar. “Amman wai Halimatu ba kya kewar yayanki? Na ga Aminu ma da ke damu da yaya ba, yanzu yana ta shiga damuwar rashinku balle ke da kike tare da su kullum” “Ke da kike iya barin Salim da Yusura kina zuwa wani gurin, ba tare da sanin irin kulawar da za a basu ba kika tafi hankalinki kwance har wani gari, balle ni da a gari daya ne kuma bautar Allah zan yi?” “Ba ki gane ba ne, ni ai tafiyar kwana biyu ce ko uku, idan na dade na yi sati ke kuma aure ne fa, kin san wani lokacin baka sanin darajar abu sai idan baya kusa da kai kamar yadda Aminu yake a yanzu karki so ganin yadda ya koma abun tausayi duk inda ya zauna sai zancenki yake da na yaransa” “Idan abu yana da muhimmanci a gurinka baka taba yarda ka rasa shi, tattalinsa kake, kana Ala ala kar ya subuce maka, domin duk ranar da ka rasa abun nan ka rasa shi kenan har abada, be kamata ki kawo min zancen wani namijin ba a gidan mijina, na dade da mantawa da Aminu ko wani abun daya shafe shi, ko da wasa karki sake min maganar Aminu” “Ai na san Aminu ya kuntata miki amman Wallahi Halimatu yana cikin damuwar rashinki a yanzu, matar da ya aura ma ta rasa gane kansa” “Wai Aminun ne ya turo ki yace ki zo ki fada min yana cikin matsala?” Ta dan wara ido. “Ahhh ni ina na ga Aminu da har zai ce min haka” “Za ki gansa mana ke ai falkalsa ce, za ki iya sanin halin da yake ciki ko ma ya fada miki da kansa” “Subhanallahi Haba Halimatu wannan bawa irin magana ce, na san dai ina raba wasu mazan, amman taya za ayi na raba mijinki Fisabilillahi, ni ba zan iya wannan cin amanar ba” “Shiyasa a kike biyarsa kuna zuwa har wani garin kuna kwana, ke fa san komai da ke tsakaninki da Aminu, na samu ido ne kawai saboda na bar ku da Allah, shiyasa na tattara lamarinku na aje gefe, ba Aminu ba ko mai sunansa bana son ji yanzu balle shi din da kansa daga ke har shi na tsaneku tashi ki bar min gida” Da sauri ta mike tsaye jikinta har bari yake. “Kamar ba Halimar da na sani ba, da alama dai wani ya shiga tsakaninmu” “Za ki fita ko sai na wulakanta ki” Daukar jakarta tai ta juya da sauri ta fice tana waigena. Har bakin kofar gate na bita na tsaya sai da na tabbatar ta fice daga gidan sannan na rufe gate din na dawo cike da bacin rai.   A lokacin dana zauna falo sai bacin ran abunda Abdulhamid yai min a gaban Sa'adatu ya tsaya min a rai, yanzu har ta kai Abdulhamid na kyamar zama a kusa da ni kuma ba zai iya boyewa a gaban mutane ba sai ya nuna? To ko dai ina dauke da cutar ne?ko kuma kiyayyar ce tai zurfi har haka a zuciyarsa. Ba yau kadai ba tun daga lokacin da abun nan ya faru na fahimci irin zaman da nake da Abdulhamid sai dai na yau yafi na ko yaushe. Ba zan iya wannan zaman ba, sai kace an masa dole da ni ko kuma auren kiyayya mu ka yi? Idan har ya zai iya rabu da ni kai tsaye ba to ni zan iya neman rabuwa da shi domin rabuwar ce mafi a'ala a yanzu, zai fi samun natsuwa idan bana kusa da shi kamar yadda ni ma zan fi samun natsuwa idan na san bana tare da shi. Ba Abdulhamid kadai ba ni inajin idan ma na rabu da shi ba zan sake auren wani namijin ba, domin na fahimcin gaba daya maza basa da kirki kansu kawai suka sani, ina ji a raina da ace ni ce ba zan iya yi ma Abdulhamid haka ba bazan iya rabuwa da shi ko nuna masa damuwa ba. “Gaba daya mazan duniyar nan ba su da karki, gaba daya kansu kawai suka sani, su auri mace suna wulakantata suna yi mata yadda suka ga dama” Na furta da karfi ina fashewa da kuka tare da dafe kai. “Zan nemi saki, dole ne Abdulhamid ya sakeni, kuma ba zan sake aure ba, zan samu wani aikin zan rike yayana na cigaba da kula da su, ba zan sake yarda ciwon da namiji ya kashe ni ba, na gahi hakan nan wahalar ta isa haka...... ” Wani abu na ji ya taso min ya tsaya min a kahon zuciya ya danne min numfashi, a guje naje na bude freezer na dauko ruwa mai sanyi na sha sannan na samu relief. Ji nai bana bukatar komai sai shan maganina shi kadai na ke sha ya lulani wata duniyar da nake mantawa da komai, gashi kwana biyun da nai ba sha ba har wani abu nake ji a cikin kaina kamar hayaki. Falon na dawo na bude jakata na dauko 2k na saka Hijab din da n cire na shiga bedroom na dauko keys na rufe gidan na nufi chemist din unguwar inda na saba siyen maganin. AHMAD POV. “Maganar gaskiya ba ka kyauta ba Gwarzo....” Yayi saurin taron numfashinsa yana shafa kansa. “Na sani.... Ni kaina bayan na mata fadan na ji cewar ban yi daidai ba, musamman da bata min tsawa ba kamar yadda nai mata, you know i hate mutum yai min tsawa” “Ita ai ba laifinta ba ne laifin ma'aikantan gurin ne kuma.... ” “Kuma What Rahim...? Sai son nanata maganar nan kake yi, i feel like na yi abunda be dace ba hakan be wadatar ba?” Da mamaki Rahim yake kallon abokin na sa, daman can haka yake wani irin murdaden mutum ne mai wuyar sha'ani, shi ya kawo maganar abunda yai ma Halima, kuma ya fadawa masa be ji dadin yadda yai mata ba and now yana kokarin bleme Rahim akan ya bashi laifinsa. “Muna magana ka ce you need to rest ka bar nan baka ce min ga gun da zaka je ba, ashe Exclusive City ka nufa, yanzu kuma ina zaune ne ka dawo ka bani labarin abunda ya faru, and now kana son ganin laifina, shiyasa kake samun rashin jituwa da mutanen ka, mutum ko naman jikinsa zai yanka ya baka sai ka ce da biyu yai, Hajiya ce kawai maganinka Wallahi, ba Hajiya ce kadai take saka matanka na guduwa ba Gwarzo Kai kanka matsala ne” Tsaki yaja ya dauki hularsa ya saka ya fice daga falon yana ciro keys din motarsa a aljihu. @360 isa gidan Hajiyarsa, as usual sai da ya fara shiga falonsa kamin ya wuce dakinsa, sai dai wannan karon be shiga da yanayin da ya saba ba, idan har bw shiga da sallama ba to zai shiga da far'a fuskarsa a sake sai dai yau babu ko daya. Be ma ankaro da ba kuwar da ke falon ba har sai da ta gaishe shi. “Ina wuni” “Lafiya kalau” Ya amsa mata sannan ya zarce dakin Hajiya kasancewar be same ta a falon ba. A daki ya same ta tana aikin fesa ma jikinta turare da alama wanka tai ko kuma ta saka sabon kaya kamar yadda ya ga kwaliya a fuskarta. “Gwarzo yanzu nake kokarin kiranka fa?” Ta fada far'a fal tana aje turaren da ke hannunta. “Amman dai a lokacin dawowa ta bwyi ba ko?” “Ba wannan ba ne, ba ka ga bakuwa a falo ba?” “Na ganta” “Je ku gaisa” “Mun gaisa ai” “Je ku gaisa dai, ai ba irin wacan gaisuwar ba ka kalleta da kyau” “Eh sai in ji me?” “Ka ji kana sonta mana” Kwantawa yai a kan kujerar da ke dakin yana girgiza kai. “No no no no Hajiya, yanzu kuma ai bata mata na ke ba, ina ni ina mace yanzu” Wani kallo Hajiya take masa shi kan be ma kula ba sai zuba zance yake. “Da ma namiji ne sai naje na zauna mu sha fira amman mace a yanzu ni... No lalalalala, na dai namiji ne” “Mace ta daina baka sha'awa a yanzu” “Eh mana da ma namiji ne” “Mazan ke burge ka kenan?” Dagowa yai ya kalleta ganin ta zuba masa ido yasa ya tashi zaune. “A'uzubillahi bafa can nake nufi ba, i mean da namiji ne dan'uwan sai mu yi fira” Ya mike tsaye tare da zuba hannayensa aljihu ya fice daga dakin, dan yasan halin Hajiyarsa yanzu sai ta sauya ma zancensa ma'ana shi ko ba dagon zance yake so ba. Part dinsa ya nufo har lokacin hannayensa a aljihu yana takawa a hankali kamar mai jin wuyar cira kafar. Be yi  mamakin ganin kofar falonsa a bude ba tun da ya san mai masa haka a duk lokacin da aljanun nata suka tashi. Yana shiga ta zo da gudu ta rumgume shi tana dariya. “Yes Daddy Oyoyo, Daddy na gyara maka dakinka na goge komai na sa turare” Kanta ya shafa cike da kaunarta, yana murmushi. “Good girl Allah yai miki albarka” “Ameen Daddy za ka kai ni gidansu kawata Namra ko?” Iskar bakinsa ya busar ya rika hannunta suka nufi kujera ya zauna, ya zaunar da ita saman cinyarsa sannan ya soma mata magana a hankali. “Baby ke kullum kina zuwa gidansu kawarki nan amman ita ba kasafai take zuwa nan ba” “Daddy ai su gidansu ba su da mota, shiyasa bata yawan zuwa, ni dai ina son zuwa gidan Daddy pls... ” “And Baby na yi m maman kawarki fada” Ya fada yana shafa kanta har yanzu jin yake be kyauta ba. Ta zaro ido tana rufe baki. “No Daddy how?” “Laifin tai min nai mata fada, so ko kinje gidansu ba zata miki yar fuska” “Daddy tana aiki a karkashinka ne?” “No” “Then why kai mata fada?” “Wani abun tai min wanda ya bani haushi” Baby Namra ta yi masa wani kallo. “Daddy waye be da gaskiya tsakanin kai da ita?” “Ni ne” Ya amsa kai tsaye sai ta sauka daga saman kafafuwansa. “You should apologize to her” Sakin baki yai be ce mata komai ba. “For the sake of me Daddy bana son na bata da kawata Namra ina sonta, idan muje gidan ina jindadi akwai mutane da yawa a gidan kuma duka suna suna kuma Daddy scul din mu daya, Mommynta ta shafa kaina tace Allah ya min albarka Daddy why za ka yi fada da ita?” Kokarin fashewa da kuka take, domin har cikin zuciyarta take son zuwa gidan su kawarta Namra and tana jindadin yadda yan gidan suke mu'amalantarta. Hannayenta ya kama “Zan kaiki gidan amman ba zan bata hakuri ba, ni nake da gaskiya ai” “Amman yanzu ka ce kai ne da laifi fa” “I mean na yi fadan da yawa amman dai ni ne mai gaskiya” “Daddy.... ” “Baby.... ” Shi ma ya marairaice fuska kamar yadda tai yana kokarin rarrashinta Hajiya ta shigo falon. “Gwarzo” “Na'am Hajiya” “Taso ka kaita gida” “Bata wuce ba?” “Eh kai zaka kaita gida, kuma ka tsaya ka kalleta da kyau” “Tooo....” Ya fada da dan mamaki, sannan ya saki hannun Baby Namra. “Baby zan je na dawo sai na kaiki gidan ki bata hakuri a madadina kinji?” Ta gyada masa kai tana share kwalla, Hajiya na gani hankalinta ya tashi. “Baby ya akai? Me kike yi ma kuka?” “Daddy ne ya tsokani momyn kawata Namra” “Garin ya? Shi ne kika kuka kuma?” Ta gyadawa Hajiya kai, shi kuma ya fice yana ta sake sake a ransa. Falon Hajiya ya shigo sai ya samu yarinyar a zaune ta natsu sosai guri daya tana wasa da yatsun hannunta. “Hajiya ta ce zan kai ki gida” “Okay tau” Ta mike tsaye tana daukar katuwar ledar da Hajiya ta bata tana unkurin tafiya sai ga Hajiyar ta shigo rike da hannun Baby Namra tana fadin. “Ka biya da ita asibiti kanta ke ciwo, na bata magani ta sha tace min be daina ba” Da okay ya amsa can kasan zuciyarsa kuma ya raya cewar lallai da gani hajiya na ji da bakuwar nan. Har gurin mota ta rakosu sai da ta shiga sannan tace.. “Ikilima ki ce ina gaishe da Hajiya na gode sosai sai na zo” “In-Sha-Allah zan fada mata na gode Hajiya Allah ya saka da alheri” “Ba komai Wallahi a sauka lafiya” Sai da ya tashi motar aka bude musu gate sannan ta koma ciki. Tafiya kadan sukai Ahmad ya rage gudun da yake ba tare da ya kalleta ba ya ce. “Ke ni ban san asibitin da zan kaiki ba, duk asibitin da zamu je yanzu sai mun bata lokaci kuma company mu yau basa aiki balle na kai ki chemist din dake ce, ku ba ku da likita ne da yake duba ku ko kika saba zuwa gurinsa?” “Akwai wani likita da ke dubani, amman yanzu na sa ya tashi asibiti yana chemist dinsa” “Ina chemist din take?” “Tana can gurin tudun wada locos” “Za ki gane gurin?” “Eh na san gurin” Be sake ce mata komai ya canja hanyar tafiyarsa zuwa gurin da ta fada masa, ita tai ta fada masa gurin har suka iso. “Ki shiga ki ganshi zan jiraki a mota, duk yadda akai sai ki fada min zan ji da komai” Ba musu ta bude motar ta fita shi kuma ya ciro wayarsa ya soma latsawa tare da kwantar da kujerar motar. Kamar hadin baki sai ga sakon karta kwana ta line Hajiya ya shigo. _Ka samu wani abu ka bata, ko ka siya mata wani abun_ “To duk dai” Ya furta yana murmushi, kamar wanda aka cewa dago, yana dago kansa yana hago Halima ta fito daga chemist din rike da leda baka. Bude motar yai ya fito, sai ya fito sai ya fara tambayar kansa me zai ce mata sorry? No ai ya girmi wannan yana jin idan yace mata haka ya kayardar girmansa. Amman ai ya kamata ya bata hakuri ko dan Namra, kuma tabbasa ya san be kyauta mata ba. zagaya yai ta inda take tafiyar dayan hannunsa a aljihu dayan kuma rike da waya ya sunkuyar da kansa kamar da gaske hankalinsa yana kan wayar ne. “Ya akai lafiya? ” Ta tambaya ganin kamar zai tare mata hanya. Dagowa yai ya kalleta sai kuma yaji nauyi bude baki yai mata magana. “Ko nan din ma hanyarta ne? Ko kuma tsabar rainon wayo ne kawai da wulakanci irin na ka, ko na maka kama da yar tasha ne, domin yanzu na fahimci babu komai a tare da kai sai wulakanci kawai, a duk lokacin da na hadu da kai sai ka wulankanta ni ko kasa a wulakanta ni, kai na fahimci sam ba mutumen kirki ba ne, sai wani jijji da kai, kana jin kai wani ne kuma kai ba kowan kowa ba, abun kai min dazun na kyale ka ne kawai saboda ina ganin kamar ni ce bana da gaskiya but then i realized na fi ka gaskiya, kai sam baka da kirki sai wani son nuna isa kamar mai garin Gusau, to bari na fada maka karka sake cewa zaka min wani rainon wayo Wallahi zan mugun wulakantaka, dan na gane ku mazan nan ba ku da mutumci, by the way ina da miji ina da aure ina da yaya karka sake ka ce zaka min magana Mtscheeeessss.....” tun da ta fara maganar yake kallonta har ta gama taja masa tsaki ta kara gaba ta bar shi a gurin da mamaki. “I just....” Ya fada yana daga hannunsa tare da bin bayanta da kallo, sai kuma ya ksa cewa komai ya jimke hannun. “Am... Baya nan wai be shigo ba yau” Ikilima ta fada shi kam har ya manta tare da wata suka zo, sai a lokacin ya soma lura da ba su kadai ba ne a gurin. Kasa kasa yake satar kallon mutane be taba jin tozarci irin wannan ba. Matsawa yai kusa da Ikilima. “Mutane suna ganinmu lokacin da take min fada?” “Yes da karfi fa take yi dole kowa ya kalleku ai” Wani abu na ji kamar ya netse a kasa, saboda ya san people would think ko ya mata wani maganar banza ne. And she's right be kamata yai magana da matar aure ba, dan idan shi ne wani nai magana da matarsa zai iya masa komai ma, but shi ya manta da maganar aurenta ma. Oh does she think sonta yake yi? Ko kuma ta maida shi wani banza ne take fada masa haka, har ya shiga motar be daina sake sake ba. “She got lucky bana fada da mata, amman wallahi da namiji ne yai min haka sai an dauki gawarsa a nan i hate nonsense” Ya fada yana fisgar motar kamar zai tashi sama, after few minutes ya bugu sitiyarin motar da karfi. “Matar nan ba tai ba, i hate her so much, da ganinta mahaukaciya ce” Ikilima dai bata ce masa komai ba bayan kallonsa da tai, tsoro dai ya gama kamata dan ta lura ransa ya bace sosai. “Ai duk laifinki ne da kika kawo ni gurin nan, da ta isa tai min kallon banza ma, amman ji irin maganar da ta fada min son ranta, sai yanzu ai na gane bakar magana ta fada min” Nan da nan jikin Ikilima ya fara rawa domin ta lura har fuskarsa ta canja sa gumi yake kamar marar gaskiya duk kuwa da irin ac da ke cikin motar. “Har da wani wai kana jin kai wani ne, ai ni wani din ne ke ba kowa ba.... Mtchhhh” Yaja tsaki yana jin kamar a gabanta ne ya rama, domin a duniyar nan yafi tsanar tsaki fiye da komai, da ka yi masa tsaki ko ka tofar masa da yawu kara ka mare shi ko ka zage shi..... 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣7️⃣ Na isa gida cikin bacin rai, ban taba jin na tsane wata halitta kamar yadda na tsani wannan mutumen ba, a yadda na fahimci rayuwata ina ta faduwa da mazaje marasa mutunci, maso sun su taka ni yadda ransu yake so, wanda ni kuma nake ganin ba zan dauki hakan a yanzu ba, na gama indai kuka ne akan wani namiji ko shiga damuwa akan wani namijin ba zan sake bari wani ya saka ni damuwa ba. I can live without aure indai har zan iya tsare kaina da mutumcin na tarbiyantar da yayana, zan iya shiga aljanna, haka zuciyata ke raya min i feel like idan har Abdulhamid ya sake ni ba zan sake wani auren ba, zan cigaba da aikina ina kula da yayana, zan nemi ya sake ni bana bukatar sake zama da shi ji nai na tsani duk wani namiji a duniyar har na rika jin na matsu ya dawo gidan, kamar ance min da ya dawo zai rubuta takardarta ya ba ni.   Maganin da na siyo dan na sha na samu bachi ne ammn sai bachin rai ya hana ni sha. Wani irin kuzari da karfin hali nake jin yana ratsa ni, i feel like ko da duniyar nan za su taru su tsane ni i can live, even for the sake of my children right? Yes this is right time da zan nunawa duniya wacece ni, wannan lokacin ne ya kamata na amsa suna, i don't know what the future bring ban ce ba zan sake facing wani challenge ba, but zan iya jurewa zan iya daurewa daga lokacin na fara rayawa kaina cewar gobena mai kyau ce. Na yi kuka a lokacin da na ke fuskantar wulakanci a gidan Aminu, na yi kuka a lokacin da akai ma Namra fyade, na yi kuka a lokacin da Aminu ya sake ni, na yi kuka a lokacin da akai min fyade, amman hakan yana nufi sai na zauna nai ta kuka akan komai akai min na bar damuwa a raina? No be kamata na karaya ba, be kamata na lauyewa kaina hakkina dan ina mace ba! I have to say it out loud, i have to fight for my right. Kamin dare yai Abdulhamid ya shigo duk na matsu sosai, saboda irin abunda na kudirewa zuciyata, ban girka komai ba har dare, can bayan sallah isha'i sai gashi ya shigo gida kamar yadda ya saba, da ada ne ko be yi sallama ba ya shigo zan masa sannu da zuwa amman a yau sai na ji ba zan iya yi masa hakan ba. Ga duka alamu yau da yunwa ya dawo, domin yana dawowa ko dankinsa be shiga ba ya nufi dinning rike da wasu takardu a hannunsa. Ganin babu abincin a dinning din yasa ya juyo ya kalleni. “Ina abinci?” “Ban girka ba” Daga inda nake zaune saman kujerana bashi amsa kai tsaye. Be sake cewa komai ba ya tashi ya nufi hanyar dakinsa yana shiga na rufe masa baya, sai na same shi yana kokarin cire rigar shaddar da ke jikinsa, hango shigowata ta madubi da yai ne yasa ya tsayar da cire rigar ya juyo ya kalleni “Kina son wani abu ne?” “Ina son sanin result din gwajin da nai nake son sani” Juyowa yai da kyau yana kallona for like ten seconds sai kuma ha dauke idonsa daga kallon da yake min ya kalli wani gurin dabam. “Positive....” “Al-hamdulillah.... Abu na biyu kuma ina son ka san cewar komai yana da lokaci kuma yana da iyaka, a lokacin da na aureka babu wanda ya cilasta ni ra'ayin kaina ne, and now mun gaji we need some space” Sake kallona yai a karo na biyu kamar wanda be fahimci yarena ba, wata kila kuma yana mamakin furucina ne. “Saki na ke bukata...!” I say it.. “Are you sure? Ba ki bukatar sake shawara ko tunani” Shine abunda ya fito daga bakinsa, sai kuma ya matsa kusa da ni ya kai hannunsa biyu zai dafa kafadata, ni kuma nai saurin matsawa. “Bana bukatar ko daya” Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya furta. “Shikenan zan ga abunda zan iya yi akai” Yana fadar hakan ya juya ya cigaba da cire rigarsa ni kuma na fice na bar masa dakin. Ko kadan ban ji kuka a tare da ni ba kamar yadda na saba yin kukan a duk lokacin da wani abun bacin rai ya same ni, but i feel bad ina jin na yi abunda be dace ba, miyasa ba zan jira har zuwa lokacin da shi din zai bukaci sakina ba? Why? Bana da wata hanyar ne sai wannan idan har zan jira to zan cigaba da kashe kaina ne da rai na. Can bayan na yi sallah isha'i ina kokarin kwanciya ya shigo dakina ya aje min takeway ya fice. AHMAD POV. Hajiya na kallonsa ta san danta yana cikin bacin rai, sai dai ta yi shiru ne saboda ta saba masa haka a duk lokacin da yake cikin damuwa idan har taji bata ji yace mata komai ba sai ta tambaya. “Hajiya yau ko?... No first of all ita wannan yarinyar da kika saka na kai gida wacece ita?” “Sai ka fara fada min damuwar” “Wallahi wata bad luck na hadu da ita yau, ban taba jin na tsani mace kamar yadda na tsani matar nan ba, i hate her... ” “Me tai?” Kadan ya gutsurawa Hajiya labarinta yana ta tsaki. “Kai ma ai be kamata kai haka ba, ko dan yarta na abota da yarka, sannan matar aure ce akan me zaka tare ta a hanya da sunan ba ta hakuri? Kai yanzu yadda kake da kishin tsiyar nan wani ya isa ko kallon matar ka yai?” Kallon Hajiya yake da mamaki he thought zata bashi gaskiya ta bawa wacan rashin gaskiya ne. “Okay....” Sai yai shiru, kamin ya sake tambayarta. “Ita wannan yarinyar fa?” “Yarinyar nan da ka gani bazawara ce” “What....?” Ya tambaya da mugun mamaki domin a tunaninsa budurwa ce, a yadda ya ganta yarinya karama. “Yes ta yi aure bata dace ba mijinta har dukanta yake kuma ta hakura ta zauna har sai da yan uwanta suka kashe aure, sannan gidansu mahaifiyarta ita ce ta hudu, so ta san  halin rayuwa tun da ta taso a gidan yawa kuma duk mace da zata yi hakurin zama da miji mai duka zata iya hakurin zaman aure a ko'ina, shiyasa na ke son idan ta maka ka aureta” “Aure yanzu Hajiya? Hajiya ba tai min ba, abu kamar ta tsinke ni bana son mace ramanmiya irin wannan, and kin san abunda ba zai taba yiyuwa ba ne na auri matar wani Allah ya sauwake, ba zan taba auren bazawara ba, ba zan iya auren matar da wani namijin ya aureta ya sake ta ba, ko kuma mijinta ya mutu har a bada, Hajiya ke ma kin san wannan” “To wai miye a zaurawan nan ne? Haba Gwarzo, na aje wannan akidar dan Allah ni fa yan matan nan na yanzu ba yarda zan yi da su ba, kara wacce tai aure ta dandana dacin auren zata fi iya zaman aure a gidan nan” “Ba dai bazawara ba Hajiya” Ya sake nanatawa sannan ya tashi ya fice daga falon, part dinsa ya nufo har yanzu zuciyarsa cike da take da bacin rai abunda ya faru. “Imagine wai ni matar nan ta tsaya ta fada wa maganar banza wai... Wani ni Ahmad hmmm” Yayi kwafa sannan ya tura kofar falonsa ya shiga gumi na karyo masa, daman can haka yake da ransa ya bace sai ya fara gumi jikinsa yai zafi sosai kamar marar lafiya, idonsa ma a take suke canja, zuciyarsa kuma tai ta wani zillo kamar ta fito, shi kansa idan ransa ya bace baya iya controlling kansa, that's why yake taka tsantsan yana gujewa duk wani abu da zai kawo masa bacin rai. AMINU POV. Hajiya ba ta yarda ba har sai da ta saka aka yi mata na ta bincike, a gurin malamanta da kuma malaman kawayenta, sai dai duk inda take abu daya ake fada mata cewar arzikin danta hana tare da matar da ya rabu da ita, wasu ma har kara rura wutar abun suke ana fada mata cewar da ace be sake ta ba da yana daf da samun wani abun. Sai dai hakan be gamsar da ita ba har sai da ta sake saka kawarta Hajiya Mairo a gaba suka tafi gurin wani malamin. Ba su tsaya bin layi ba abun ka da masu kudi, sai aka bi da su ta wata hanyar suka shiga cikin dakin malamin. After sun gaisa ya dauko kasa ya fara bincike domin shi haka yake ba ya bari mutum ya fada masa dalilin zuwansa, sai dai shi ya fada maka abunda ya kawo ka. Yayi kusan minti ashirin yana duba kasar sannan ya dago ya kalli Hajiya Mairo. “Waye Aminu? Gashi nan yau sun nuna min da Maganarsa kuka zo” “Tabbas hakika maganar Aminu ta kawo mu, yaron abokiyata ne kuma aminiyata” Ya gyada kai sannan ya kalli Hajiyar Zuwaira wato mahaifiyar Aminu ya ce. “Sun fada min komai, dan ki na fama da gurguncewar cigaban rayuwa haka ne?” Tai saurin gyada kai. “Haka ne” “To ai danki ya baro kyau tun ranar haihuwa, ga shi dauke da kwaryar alheri sai kuma ya bari ta fadi ta fashe” Hajiya Zuwaira ta yi masa kallon rashin fahimta. Sai yai yar dariya ya gyara zamansa. “Na san baki fahimta ba, wato tauraruwar danki sakaina'u ce, irin wannan tauraruwar bata iya haske har sai ta hadu da yar'uwarta mai iya daukar nauyinta, ma'ana mai taimaka mata ta haskaka, da danki zai hadu da taurari dubu idan be hadu da wannan tauraruwar ba gasri to abu ne mai wahala ya iya haskaka ya daukaka yadda yake so, daman ko wane dan'adam yana da tauraruwarsa to ita ta danki haka take” “To amman Malam.... ” Sai ya daga mata hannu. “Wacece Halima?” “Matar da ya saki ce ita ce uwargidansa” “To ita ce mai wannan tauraruwar gasri, tauraruwa ce mai tsananin haske da kaifi gaske, tana haska ko wane irin tauraruwa, ban ce dan ki ba zai arziki ba, amman da ace yana tare da ita ina mai tabbatar miki ko matar gobna bata ita ta nuna miki yatsa ba” “Amman Malam ai can baya tare da ita kuma yana al'amuranshi” “Amman ya kai kamar haka?” Ta girgiza kai alamar a'a. “To kin gani, zai iya samun mai irin tauraruwar amman abun ne mai wahalar gaske” Hajiya Mairo ta ce. “To amman Malam dole sai Aminu ne kawai idan ya aureta zai yi arziki ko kuwa idan wani ya aureta shi ma zai iya yin arzikin?” “Sosai kuwa ai kowa ta raba zai yi arziki, ita daman haka tauraruwar take” Cikin damuwa Hajiya Zuwaira ta ce “Yanzu babu yadda za'ayi tauraruwar tasa tai haske? Kenan dole sai da ita?” “Akwai mana, amman aiki ne mai wahalar gaske kuma za a ci kudi” “Karka damu indai har za a samu biyan bukata ba matsala” “Za ki siye sa daya, da fararen balbelu uku sai fafaren kaji bakwai, sannan za a biya masu aiki 30k” Murmushi Hajiya tai. “Wannan ai ba wata matsala ba ce, sai dai ba zan iya siyowa ba zan dai bada kudin sai ka siyo komai da kanka, sai dai ba ka fada mana nawa za a biya ka” “Ni sai bukata ta biya sannan za a biyani” A take a gurin ya lissafa mata kusan dubu dari biyu da za a bada na kayan aiki, sai ta karbi account dinsa da zimmar idan ta koma gida zata turo masa, bata bar gurin ba sai da ta aje masa 10k na shan ruwa. Har suka dawo ita da Hajiya Mairo ba su daina mamaki da jinjina lamarin ba. Ba ma kamar Hajiya Mairo domin ita nata tunanin dabam. ABDALLAH POV. Tun daga lokacin da suka samu matsala da Suwaiba ta canja masa, ya lura da hakan a dabi'unta da halayyarta da kuma yadda take mu'amalantarsa a yanzu.   Shi kau iya kokarin da yake na ya fahimtar da ita ne ta daina ganin laifinsa ko kishin Halimatu, a iya ganinsa shi be ga dalilin wannan kishin da take ba, be san abunda zai saka ta ji haushi dan yayi ma yar'uwarsa alheri ba, tun da ita ma babu abunda ya rageta duk wani abu da take bukata yana yi ma kuma yai ma yan'uwanta, sai dai duk bata ga na kowa ba sai na Halimatu. Duk yadda take kokarin avoiding dinsa shi kuma kara shige mata yake yana nuna kamar wani abu na bacin rai be taba shiga tsakaninsu, daman can haka yake idan yai fada da ita kokarin mantawa yake saboda kullum auna tunaninta yake yana ganin be kai na shi ba, a ganinsa mace mai rauni ce kuma ba komai suke iya tsayawa su yi tunani ba, duk yadda abu ya zo musu haka suke karbarsa shiyasa shaidan yake yin galaba akansu. Idan har ya ce zai rike ta a ransa zata iya shiga matsala, matukar ya rike bacin ran mutun a zuciyarsa sai wani abun ya faru da mutun domin yana da kofi, idan har ka bata masa rai za ka ga daidai ba, shi kansa har mamakin kansa yake wani lokacin abu yake kamar wani maye. sai da yai shirin office saf sannan ya nufi dakin matarsa yana kamshi turare mai dadi. Yana shigowa ta wani dauke kai be damu ba ya karasa kusa da ita ya kama hannunta ya sumbata. “Zan tafi office sai na dawo” Bata ce masa koma ba, shi ma kuma be jira ya ji wani abu daga gurinta ba, daman be yi tsammanin ta fada masa wani abun ba ko da Allah ya tsare ne ba tun da fushi take da shi, ba kamar da ba da har bakin mota take rakoshi. Daga gidanshi gidan Hajiya ya nufa as usual daman sai ya biya ya gaisheta yake wucewa office, ko a dawowa ma idam time be kure masa ba sai yayi mata sallama yake dawowa gida. Ya dauki Hajiya kamar wata abokiyasa yana jindadin fira da ita sosai duk wano sirri na shi ko shawara ita ce, kamar yadda ita ma ta fi shakuwa da shi fiye da Abdulhamid.   Ba kasafai Abdulhamid yake zuwa da safe gaishe da Hajiya ba, wani lokacin sai da rana ko dare, wani lokacin ma sai ya wuni be shigo ba sai dai yai mata waya. A kujerar da mahaifiyarsa take zaune ya zauna yana mika mata gaisuwa. “Lafiya Kalau ya aka tashi ya yaran” Ta amsa masa fuskarta da alamun magana. “Abdulhamid” Daman haka yake masa he can't say Abdulhamid ina kwana saboda yana jin age mate dinsa ne, tun da yake a rayuwarsa be taba bude baki yace wa Abdulhamid ina kwana ko ina wuni ba, sai dai ya kira sunansa. “Likita ykk” “Lafiya kalau” Ya amsa yana kallon yanayin Hajiya da kuma shi kansa Abdulhamid din. “Lafiya wai?” “Lafiya kalau wai Halimatu ce tace ta gaji da zama da shi saki take so.... ” Ji yai kamar an zuba masa ruwan sayi a kai a take tsigar jikinsa ta tashi. “Saki?” “Eh” Hajiya ta amsa masa. “Why?” Abdulhamid ya daga kafadunsa alamar be san dalili ba. “No dole akwai wani abu, akwa abunda kai wa yarinyar nan Abdulhamid haka nan kawai Halimatu ba zata ce ka sake ta ba, i know who's her” Hajiya ta tabe baki tana fadin. “Ni nace dai ko ta gaji da zama da kai haka nan ne ba” “No bana tunanin haka duk dai na san matsalar ce tai haifar da komai, amman wata kila tana jin kunyar kan ta ne akan abunda ya faru” Cewar Abdulhamid, a take Abdallah ya gyara zamansa yana girgiza masa kai. “idan har akan matsalar ne be kamata ta saka kanta cikin damuwa ba, matar da zata bar yayanta ta bar aikinta ta yarda ta aureka bayan kuma ta san irin lalurar da kake tare da ita, be kamata dan wani abun ya same ta ka barta ta shiga damuwa ba, and she told you ba su yi raped dinta ba, miyasa ba za ku yarda da ita ba?, Abdulhamid Halimatu kamar amanace a gurinka kuma matarka ce ka zaunar da ita ta nuna mata baka da matsala da hakan kuma ta kwantar da hankalinta, Abdulhamid yarinyar nan.... ” Be karasa ba Abdulhamid ya tari numfashinsa. “Halima ba yarinya ba ce, yaranta hudu ta san me take yi. She told me babu wanda yai forcing dinta ta aure ni and now she want divorce” “Ai sakin ma shi ya fi alheri” Abdallah ya juyo ya kalleta cike da damuwa. “No Hajiya ke kika haifar da wannan matsalar kika saka Abdulhamid ya rika ji a ransa kamar an yi raped matarsa, and now kina kokarin ki karfafa nasa guiwa ya sake ta haba Hajiya be.... ” “No tun kamin ayi wannan abun i suspect something, and yes na kai ta an mata hiv test and the result din positive, maybe dai tana jin kunyar kanta ne.... ” Da mugun mamaki Abdallah yake kallon dan'uwansa. “Don't tell me you don't trust your wife...? Why all the insult bro? Taya za kai ta ayi mata hiv test? Kasan halin da za ta shiga?” “Ba zaka fahimta ba ne Abdallah, ni na san abunda yake nan, and matar nan yanzu har shaye-shaye take fa, na ga kwalaben maye a dakinta, and wani lokacin zan tarar tana ta bachi kamar wacce ta mutu, idan ta farka idonta har canjawa yake” Kamar an saka scissors an yanke jiyojin jikinsa haka ya ji, be taba jin tausayinta irin yanzu ba, yana jin da ace shi ne Halimatu ta fada masa cewar ba'ayi mata fyade ba babu abunda zai hana shi yarda da ita, even if an yi mata fyaden ma zai iya zama da ita a haka. “Akwai abunda yake faruwa a tsakaninku Abdulhamid, wanda ba ka son mu ji kuma ba lallai ne sai mun ji ba, amman ka dubi girman Allah ka ji tausayin yarinyar nan, ace har ta fara shaye-shaye amman kake maganar sakinta? Abunda ya same ta kaddara ne miyasa ba zaka nuna mata hakan ba? Rashin lafiyarka ma ka nuna mata zaka nemo magani, i promise you zaka samu sauki soon...” shiru Abdulhamid yai for a while kamin ya sake bude bakinsa ya ce. “I think rabuwar shi ya fi alheri a tsakaninmu dukan mu za mu samu kwanciyar hankali” Wani irin kallon Abdallah yai masa. “Ta auri mutunen da be cancanta ya zama mijinta ba, Abdulhamid ban yi tsammani haka daga gareka ba... ” “Ba ka fahimta ba ne Abdallah tun kamin wannan abun ya faru Halima tai ciki, kuma ta zubar da shi ba tare da na sani ba....” “Ciki? pregnant.... Ciki?” Ya maimaita har sau uku, sai kuma yai saurin mikewa tsaye ya nufi window falon ya tsaya a gurin yana shafa kansa, gaba daya zuciyarsa ta gama narkewa da tausayin Halimatu yanzu kam. A hankali ya busar da iskar bakinsa yana sauraren yadda Abdulhamid yake labarta abunda ta fada masa da kuma kin yardar da yai da ita. Lumshe ido yai ya bude, so yake yacewa dan'uwansa Halimatu tana da gaskiya amman taya? Shi kansa ba shi da hujja, iyakar abunda yai imani da shi, shi kam ya yarda da Halimatu ko da bata kafa hujja da komai ba, and ya san idan har Halimatu za ta aikata zina to zata aikata ne tun a lokacin da take gidan Aminu. Juyowa yai ya kalli dan'uwansa. “Amman ka yi magana da ita? Abdulhamid ko da da gaske Halima ta aikata haka ta cancanci ka zauna da ita, macen da zata bar yayanta, ya bar duk wani abu mai muhimmancin a gareta ta yarda ta aureka da matsalarka ta gama maka komai, kama yai ka tambaye ta ka bincike ta wata kila ta iya gane wanda yai mata wannan abun sai a bincike shi amman duka ba ka yi wannan ba sai kawai ka juya mata baya? And now kana maganar ka sake ta? Ka yi convince dinta ka nuna mata sakin ba mafita ba ne a gareta, ta shiga damuwa da yawa, Abdulhamid, Halima deserve a happiness” “Ya isa haka Husaini wuce ka je gurin aikinka” Hajiya ta fada a tsawace tana daga masa hannu. Ya gyada mata kai yana hade wani irin abu daya tsaya masa a kahon zuciya. Ko minti biyu be kara cikin falon ba ya fito ya shiga motarsa, Halimatun dai ce ta tsaya masa a rai ya kasa rika ko da sitiyarin motar har na tsawon lokaci ba yi wata halitta da yake tausayi a duniya kamar Halimatu ba. How he wish shi ne a step din Abdulhamid da ya nuna mata soyayya da kauna ya rumgumeta har sai ta manta da duk wani bacin rai a duniyar nan. Ya dade a gurin kamin ya tashi motarsa ya danna horn a bude nasa gate ya fita da motar, titi ya hau yana tunanin inda zai je direct asibiti gurin aikinsa ko kuma gurin Halimatu? He need to talk to her, sai kuma wata zuciyar ta ce nasa no, kuskure ne yai magana da ita a yanzu, ba zata fahimta ba, son da yake mata ma yana jin a ransa cewar ya aikata baban zunubi kuma yana jin kamar ya ci amanar dan'uwa, wannan kadai ya saka shi a damuwa. And maybe idan yai magana da ita ta fahimta ta daina zancen sakin, he can talk to her as her brother wata kila ta fahimta. Haka yake ta sake sake a ransa, daga karshe ya yanke shawarar kiranta a waya, sai dai kuma idan ya kirata a waya dan'uwansa ya ji he may think something else... But yes he can talk to her as Abdulhamid brother as his best friend, as her husband best friend. Har cikin ransa baya son ta rabu da Abdulhamid saboda ba mafita ba ne a gareta, and idan ta rabu da shi yanzu zuciyarsa kan iya bijiro masa abunda ba mai yiyuwa ba ne akanta. Wayarsa ya ciro ya aikawa Abdulhamid sms. “Can i talk to her? As your brother” Immediately yai masa reply. “Yes i trust you” The truth word break his heart sai yaji ina ma be tambaya ba. But yes mace ta bukaci saki a gurin miji ai ya kamata yan'uwansa su ji daga gareta su ji dalilinta. Sai da ya saita natsuwarsa sannan ya dauki hanyar gidan Abdulhamid yana ta tunanin a irin halin da zai samu Halimatu. Zuciyarsa sai raya masa take kar yaje, ya faka motarsa a bakin gate sannan ya fito ya tura kofar gate din ya shiga cikin gidan. Ya dade tsaye a kofar falon sannan yai knocked. For like five minutes ta bude kofar suna hada ido, idonsa ya cika da kwalla wani irin tausayinta yake ji yake kamar ya dauke ta ya hade ta manta da komai. “Abdulhamid ba ya nan” “Gurinki na zo” Sai ta saki kofar falon shi kuma ya turo ya shigo cikin falon ya zauna a kujerar da ke kusa da kofar falon. Daga inda take tsaye fuska babu annuri ta ce “Ina jinka” Sai ya nuna mata kujera alamar ta zauna, ba musu ta zauna a kujerar da ke nesa da shi sosai, after ta zauna ya soma magana a natse. “zan yi magana da ke as Abdulhamid brother, Abdulhamid ya zo mana da magana marar dadin ji daga gareki, b zan iya nanata maganar ba amman ina fatar ba haka zan ji daga bakinki ba.... ” Bata ko jira ya karasa ba ta dora da nata. “Haka yake ko ba zancen saki ba?” “Amman Halimatu wannan ba mafita ba ce a gareki and... ” “And what? Idan ya sake ni mutuwa zan yi?” Kasa ce masa komai yai, gaba daya ta canja a tsaye take kamar ba ita ba. “Be kamata ki canja rayuwarki ba akan abunda ya same ki, kowa ya san kaddara ce, ki tattara komai ki aje a gafe ki barwa Allah labarinsa, dabi'un da kika dauka yanzu ba za su kai ki ko'ina ba and mijinki yana son ki yana cikin damuwar abunda ya same ki....” “Babu abunda zaka fada min da zai saka na canja kudirina Abdallah, bana son jin wata magana daga gareka ko wace iri ce, let it go can't hold me back anymore, duk abunda ya faru ai kai ka janyo you try to act innocent, da ba ka aikata min abunda ka aikata ba, da yanzu komai be faru ba, na rasa gane wane irin mutum ne kai Abdallah na kwarai mai son taimakona da yarana, ko kuma mai son ruguza rayuwata?” Still now be iya ce mata komai ba, gaba daya jikinsa ya gama sanyi, be fahimci inda zancen ta ya dosa ba. Ita kuma bata fasa fayyace masa komai ba. “Mutumen da yai min fyade be rage komai a zoben hannunka ba, na danna na cige ina ta boye abu saboda na samu natsuwa a zaman aurena, amman Abdulhamid ya masa yarda da ni, ba zubar da cikin nai ba zubewa yai saboda tashin hankalin batan Namra, amman yana ganin kamar na aikata alfasha da wani ne na zubar da cikin, shin idan na fada masa dan'uwansa ne ya aikata ya kake tunanin zai ji?” Rumtse idonsa yai da mugun karfi ya fisgi kansa kamar ba shi ba. Be taba jin magana daci ba irin wannan, ba a taba munana masa zato ba irin wannan, amman a maimakon ya ga laifinta sai tausayinta ya kara rufe shi, tausayin da be san daga ina yake ba, gani yake yanzu kanta a chushe yake, bata fahimtar komai da kyau kuma tana da raunin tunani. A lokacin da ya bude ido sai ya ji kamar ba a duniyar nan yake ba, maganganunta na ta maimaita kansu a cikin kunnuwansa. Zoben hannunsa ya kurawa ido, kokarin tuna inda ya tsiya zoben yake a office right! Wani mai kawo musu kaya ya kawo rings even though shi ba masoyin zobe ba ne ya tsiya daya ya saka saboda zoben ya masa kyau. Yes he remembers at first ma mai alphabet H ya dauka sai kuma ya ga rashin dacewar hakan then ya canja to A mai sunansa. Magana ya fara yi tana rabe masa hawaye na sauko masa. “Na san kin san ina son ki... Na fada miki... Kuma... Kin san haka.... Amman soyayyarki.... Bata taba saka min sha'awarki ba.... Ban tana jin sha'awar na rika hannunki ba daidai da minti daya Halimatu..... Indai har dan jikinki ne.... Zan bukace ko a lokacin da kike gidan.... Aminu.... Ko a lokacin da kike zawarci.... Ba yanzu da kika auren dan'uwana ba.... Wallahi ban tana aikata zina ba.... Zuciyata bata taba raya min akanki ba..... Kullum burina da fata na aurenki ne.... Saboda ki huta ki samu kwanciyar hankali.... Tausayi kike ba ni Halimatu... Yana daya daga cikin dalilin da ya saka nake daukar dawainiyar yaranki..... Da ke kanki... Na ke damuwa da damuwarki..... Yes i love you.... I do love you..... I love more i did before... Amman yanzu duk wannan ya wuce saboda kin riga kin auri dan'uwana twins brother na..... And yes na so na aure ki saboda na samu da namiji ko ba komai hakan zai kara min kaunarki.... Amman yanzu duk wannan ya wuce.... ” Lumshe ido yai ya bude har lokacin yana hawaye. “Idan har zan miki fyade, ba zan bar wata alama da za a gane ni ba, bazan shigavgidan makotanku har a kashe wani da ni ba saboda kawai na biya bukatar da zan tashi a gaban Allah ina tsoron amsata ba, a lokacin da akai wa Namra fyade ji nai kamar yar cikina aka taba, da acce Mama bata saka baki ta hana abun ba, da sai inda karfin ya kare, then mi zai saka ke nai miki? Robe kadai ya isa ya bada hujja Halimatu? Ni kadai ne sunana yake tashi da A ko kuwa ni na fi kowa arzikin da za a kero min irin wannan zoben? Ni da na ke fargabar ki shiga tashin hankali kuma ni zan saka ki ciki? Siffar mutumen da muryarsa irin tawa ce? Komai na sa irin nawa ne? Miyasa za ki nunana min zato? Saboda na ce ina son ki....! Wallahi ko ke kadai kika rage a cikin mata Halimatu na zan bi dare nai ma matar dan'uwana fyade ba.... ” Mikewa yai tsaye ya cire zoben hannunsa ya nufi center table din da ke tsakiyar falon ya dora zoben sannan ya tada kai ya kalli Halimatu. “Karki kashe aurenki saboda ni, karki fadawa Abdulhamid wannan maganar, domin na san dan'uwana ya fi so na akanki, kuma karki fadawa Hajiya wannan maganar, itama na san ta fi so na akanki, ki yi tunani Halimatu karki jefa kanki cikin matsala lastly ki daina shaye-shayen da kike for the sake of your children...” Yana kaiwa nan ya juya ya fice yana share hawayensa da handkerchief. Amman hawaye suka ki tsaya masa har ya shiga motarsa, key yai mata sai da yai nisa da unguwar sannan ya faka motarsa gefe ya jingina kansa jikin kujerar motar ya Lumashe ido. “Allah kai kadai kasan dalilin da ya sa saka min kaunar Halimatu, Wallahi na kasa ganin laifinta.....” A fili ya furta zuciyarsa cike da tausayinsa, gani yake kanta ba daidai yake ba damuwar da take ciki bata iya barinta tai tunani da kyau, tabbas ta jefeshi da mummunan zato kuma ya ji zafin hakan yai bakinciki sai dai ya kasa ganin laifinta uzuri yake ta mata! *5K WORDS 😲* 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣8️⃣ ABDALLAH POV. Be iya zuwa gurin aikin ba kamar yadda ya tsara zuwa tun farko, gaba daya ji yake kamar ba shi da lafiya, ji yai baya bukatar ko'ina sai gidansa. A take ya dauki hanyar gidan, a ka'idan zai shiga gidansa yana shiga da sallama kuma fuska a sake ko da kau yana cikin damuwa yana kokarin yin hakan saboda yaransa, duk damuwarsa ko wata matsala nasa baya son tana shafar iyalinsa musamman yaransa Abdallah mutum ne mai tsananin son yara ko da ba na shi ba balle kuma na shi, wannan yasa duk irin matsalar da suka samu da Suwaiba matarsa baya taba bari yaransa su gane.   Babu kowa falon at that time, daman yara suna scul Suwaiba kuma tana dakinta, kai tsaye dakinsa ya wuce yana jin wani irin zazzabi na rufe shi, kwantawa yai saman gadonsa yai ruf da ciki ya rumtse idonsa sosai. Yana jin wayarsa na ringing ya ki ya duba mai kira ma balle yai deciding zai dauko ko a'a, ya kusan awa daya a haka sannan ya bude idonsa ya tashi zaune yana duba wayar, Abdulhamid ne ke kiransa. Sai da ya busar da iskar bakinsa sannan ya danna picking. “Abdallah” “Na'am” Ya amsa yana gyaran muryar. “Ya kuka yi da ita?” Shiru yai for few seconds sannan ya ce. “Tace ta fi bukatar sakin ko dan cutar da take dauke da ita” Daga dayan bangaren Abdulhamid yai shiru kamar mai nazari har Abdallah ya dauka ko ya kashe wayar sannan yai magana. “Idan kuma na ce bata dauke da cutar fa? Zata zauna?” “Amman miye gaskiyar lamarin ne?” “Maganar gaskiya bata dauke da cutar” “Then miyasa ka ce tana dauke da ita?” “Ina son na gane wani abu ne, kuma ina tunanin idan na ce mata haka zan ji wani abu daga gareta, amman na ga hankalinta sam be tashi ba, even i thought zata yarda ta zauna saboda tunanin idan ta fita za a kyamace ta, but then i realized idan har na cigaba da zama da ita, zan iya cutar da ita kuma ni ma zan cutu, domin har ga Allah zuciyata ta kasa natsuwa da ita, ta wani bangaren ina ganin kamar rabuwar shi ya fi alheri” “Amman Abdulhamid miyasa za ka ce tana dauke da cutar, na kasa yarda da kai, wani lokacin sai kai ta abu kamar marar tunani” “Idan taje wani gurin ta yi gwajin ai za a tabbatar mata idan tana dauke da cutar ko akasin haka” “Ina fatar rabuwar ta zame muku alheri kai da ita” Shine kawai abunda Abdallah ya fada ya kashe wayar ya kaita a goshinsa, babu abunda ke ransa sai irin halin da Halimatu zata shiga. “What if Abdulhamid yana da lafiya? Da duk wannan zai faru? Da ko kin yi cikin ba zai gane cewar ba na shi ba ne, ni na jefaki a wannan matsalar, saboda ni ne silar wannan matsalar....” Ya furta yana kara rumtse idonsa, kokarin da yake na kawarda damuwar abunda Halimatu ta fada masa ne, gudun kar wani abun ya same ta, and the most of all zai wanke Abdulhamid daga rikon da yai masa a zuciyarsa. Bude idonsa ya sake yi ya lalubo number Halimatu ya aika mata sako. “Na zurfafa a son ki na sani, na nuna miki son kaina na sani, na kaurara da yawa na sani, kina da gaskiyar ki yi yarda da duk wani abu da zuciyarki ta fada miki, amman ina dada jadadda miki karki kuskura fadawa Abdulhamid wannan maganar” After the sms ya kwanta saman gadon yana jin kamar ba shi da wani kuzari. Abubuwan da ta fada masa is painful suna ta kona masa zuciya, after like two hours ya kira wani a asibitin ya fada masa cewar ba zai sami damar zuwa ba a yau. Tun da ya kwanta babu fuskar da yake ganin sai ta Halimatu old memories yake tunawa daga lokacin da take yan mata ba tai aure ba, a lokacin duk be fara son ta ba har tai aure shi kuma ya bar kasar duk be fara son ta har ya dawo yai aure ya haifi yarsa ta fari be fara sonta ba, sai da suka hadu a family meeting a lokacin tana da aurenta har ta haifi yara uku, tun daga ranar Allah ya dora masa sonta, yanayin jikinta mu'amalarta kyauta da komai nata sai ya rike burge shi, musamman da ya samu labarin waye mijinta da irin kalubalen da take fuskanta a gidan aure sai ya fara tausayinta yana ganin kamar shi ya dace ta aura ta samu jindadi, kamar yadda yake jin cewar idan ya aureta zai iya haifar ɗa namiji tunda ita duk tana haihuwar maza da mata, and bugu da gari ga sonta da yake. But why he fell in love with her? Sai yanzu yake ta ganin laifin kansa, he know maybe da be so duniyarta da tunaninta be bata haka ba ta bata munana masa zato ba. Har scul bus ta kawo yaransa daga makaranta yana a dakinsa kwance, yana jin hayaniyarsu amman damuwar da ke ransa ta hana shi tashi ko da zaune balle har ya fito falo.   After yayi sallah azahar a cikin dakin Suwaiba ta shigo ta zauna kusa da sallayar tana karantar damuwar mijinta. “Lafiya dai? Na ji ka dawo tun dazun kuma baka fito ba” Kallonta yai yana kirkirar murmushin da yaki ya fito a kumatunsa balle har ya tsaga bakinsa, a kokarinsa na boye mata damuwarsa ya kirkiro mata wasa. “Ba fushi kike da ni ba” “Wannan dabam, kana cikin damuwa ga idonka nan ya nuna” “Bana jindadi ne, dazun da na fita sai da nai amai shiyasa na dawo” “Ka sha magani?” Hannunta ya kama. “Ina likita har ake tambayar na sha magani?” “Na kawo maka abinci?” “No ba yanzu ba” Kamin ta sake cewa wani abun su Inteesar suka shigo dakin ita da kanwat suka fado jikinsa. Sai Suwaiba ta rika kokarin daga su. “Kyale su tafiyarki” Ya fada yana shafa kansu, tashi tai ta fice tana musu fada wai kar su dami Daddynsu ba shi da lafiya duk kuwa rashin gamsuwar da tai na cewa ba shi da lafiya din da gaske.    Sama sama ya tambaye scul sannan ya ciro wayarsa ya cire mata key ya mika musu su game so that su kyale shi ya samu natsuwa, a gurin ya kwanta su kuma suka tashi suka bar dakin suna murya Daddy ya ba su iPhone dinsa su yi game.   Har yanzu jikinsa ya kasa sakewa yana ta jin kansa kamar marar lafiya irin wanda ya dade kwance yana jinya, tsakanin fitar su Inteesar da kwantarwarsa be wuce 40 minutes ba Suwaiba shigo dakin rike da wayarsa fuskarta a jagule. “Abdallah miye haka?” Saurin bude ido yai jin muryarta kamar mai shirin yin kuka, sakon da ya aikawa Halimatu ne dazun take nuna masa, tuni kwalla sun cika idonta. Tashi yai zaune yana kallon fuskarta, gaba daya sai abun ya kara jagule masa shi ya manta ba be goge ba, and ko da ma be goge ba why zata karbi wayarsa a hannun yara ta masa bincike? “A lokacin da nai zargi cewa kai ban yi daidai ba, yanzu miye haka? Yar'uwarka kuma matar dan'uwanka Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....” Hannu ya kai ya rikota ya zaunar da ita bakin gadon sannan shi ma ya tashi daga kan tile din da yake ya zauna bakin gado ya rike hannayenta. “Babu alakar komai a tsakaninmu” “To wannan wane irin sako ne? Miye ma'anarsa? Na kasa gane wace irin alaka ce a tsakaninku? Idan nai zargi ka ce min ba haka ba, Abdallah da me na rage ka?” “Ba ki rage ni da komai ba, idan ina wani abun da be kamata ba zaki fi kowa sani” Fashewa tai da kuka ta runtse ido, kamar yadda shi ma ya rufe idon ya hada kansa da nata yana hawayen da be yi zaton za su sake zubo masa ba. “Ashe ba za ki iya shaidun mijinki ba? Ba kisan abunda mijinki zai iya yi da wanda ba zai iya ba? Wani ba zai zo yace miki ga mijinki can a dakin wata karuwa ba ki karyata shi? Har yanzu ba ki san waye Abdallah ba Suwaiba?” Bude idonsa yai yana kallon idanuwanta da ke rufe suna zubar da hawaye still goshinsa da nata suna hade guri daya. “Me kika son nai miki ki yarda da ni? Rantsuwa kike son nai miki? Ko qur'ane kike son na dafa miki? Ko kuma Halimatun kike son na dauko miki da kanta ta fada miki?” Kai ta girgiza ta jimke hannunsa sosai a cikin nata alamar ta yarda da shi, sai dai har yanzu kukan take mai sauti. Kansa ya daga ya janta jikinsa ya rumgume yana hade yawun bakinsa tare da saka dayan hannunsa ya share hawayensa. “Wani lokacin wani abun yana faruwa da mu saboda yana daga cikin kaddararmu, wani na dan lokaci ne kawai na jarabawa, wani kuma har a abada zai zauna da kai” A fili yai furucin yana sauke ajiyar zuciya, kamin ya koma zancen zuci. ‘Da ace na san zan hadu da ke Halima da ban dawo kasar nan ba, ko da na dawo da ban zauna garin nan, hakika duk wanda aka jarrabe shi da son wani an fi kowa yi masa babbar jarabawa, Allah kadai yasan abunda yake nufi da ni’ Ya kara rumgume matarsa yai ya kai bakinsa saitin kunnenta. “Babu komai a zuciyata yanzu sai tausayin Halimatu, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwar kanki da matsalar nan dan Allah” “Dama kaunarta kake yi Abdallah wata kila da zan fi samu natsuwa fiye da ka fada min cewar tausayinta kake, tausayi ya fi so tsatsa a zuciya Abdallah” “Ki daina saka kanki a cikin damuwa, Halimatu ta riga ta auri dan'uwana, ba zan taba iya aurenta ba a yanzu ko da ko Abdulhamid ya rabu da ita, duk wani abun da zan mata ko nai ma yayanta zan yi mata ne kawai dan kyautata da kuma tausayinta da na ke, Halimatu yar'uwata ce ko ba komai dole na taimaka mata ballantana akwai yan'uwanta, kuma duka familynsu babu wani mai karfi da Halimatu zata iya jingina da shi yai mata irin abunda na ke mata” Ta gamsu da bayanansa abunda bata gamsu da shi ba, shine zancen cewa ba zai auri Halimatu ba ko da Abdulhamid ya sake ta, ko da dai hausawa suna cewa ana barin halak dan kunya, amman a yadda Abdallah yake damuwa da lamarin Halimatu abu yana daure mata kai, ta sani abun kunya a gurinsa ace dan'uwansa ya saki mata shi ya aura, dan uwan ma twins brother dinsa, amman ta kasa yarda tausayin Halimatu kawai yake ta san ba tausayi ne kawa ba har da so, wannan abun ya tsaya mata a zuciya, abun da ciwo ace kana tare da mijinka zuciyarsa tana begen wata. HALIMATU POV. I thought ba zan sake zubar da kwalla ba, i promise my own self ba zan sake shiga damuwar wani namiji ba, but i feel like ban kyautawa Abdallah ba, i feel like na yi kuskure na fada masa haka, miyasa ba zan bari har sai asiri ya tonu ba? Amman da na bar maganar a cikina da har yanzu zargin Abdallah yana a cikinta. And now da ba Abdallah ba ne wanene? Babu wanda zan iya zargi a iya hangena da tunanina, wata kila yan fashin ne da gaske! Amman miyasa ya shafa cikina har ya tambaya da gaske ina dauke da ciki, miyasa yace wannan karon ba gurin mijina suka zo ba? A gaban madubi nake zaune ina kallon kaina hawaye na sauko min, nazarina ya ki ya kare, tunanina ya ki ya gano komai. Ban matsa daga inda na ke ba har sai da na ji motsin motar Abdulhamid. Bandaki na shiga na wanke fuskata na fito bakin gado na zauna. Sai ga shi ya shigo ya zauna kusa da ni, ban kalleshi ba amman jikina ya ba ni cewar kallona yake. “Abdallah ya fada min kin ce kin fi son sakin, ni kuma ba zan ki yi miki abunda kike so....” Yana fadar hakan ya saka hannunsa aljihu ya dauko takardu guda biyu ya miko min. “Ina miki albishir din cewar ba ki dauke da cutar hiv na fada miki haka ne kawai saboda na ga reaction dinki” Hannu na saka na karba at first na yi zaton ko takardar gwajince sai nai arba da abunda ya kusan raba zuciyata gida biyu. _Ni Abdulhamid na saki matata Halimatu saki daya a yau_ Bayan rubutun saki sai kuma na kwanan wata a kasa, Wallahi na yi zaton kukan a lokacin amman sai na nemi shi na rasa babu ko alamunsa a tare da ni, a dayar takadar kuma cheque din kudi ne dubu dari biyar. “Wannan na minene?” “In case of....” Ya amsa min muryarsa na rawa. Sai na girgiza masa kai ya dora cheque din a saman gadon. “Bana da bukata” Ina furta hakan na nufi wardrobe dina na bude na dauko akwaiti na fara zuba kayana, abubuwan da ya kamata ace na zuba a ciki ba su na zuba sai tarkace jikina na ta rawa kamar wata marar gaskiya. Ina kokarin rufe akwatin ya zo ya rike akwatin sai na daga kai na kalleshi, hawaye fal a fuskarsa a maimakon ni da aka saka na yi kuka ban yi ba, sai shi da yai sakin yake kuka. “Zan kula da komai, idan kina bukata za ki iya yin iddarki a nan” “Bana da bukata” Sai ya kada min kai kamar wani yaro da mai bashi umarni, mikewa nai tsaye na dauko hijbina sai ya rike. “Ba za ki bari sai da dare ba?” “Gida na ke son zuwa” Nan ma kan ya gyada min. “Bari na kai ki, zan saka a kwashe komai na ki a kai miki” Ya fada yana ficewa daga dakin, ni kuma na bi bayansa rike da jakar hannuna, da kuma takardar sakin, har lokacin ban ji kuka ko wani abu makamancin kukan a tare da ni ba, sai dai zuciyata ta yi wani irin nauyi kamar dutse. Ko da na fito har ya tashi motar ya bude min front seat, ni kuma na bude back seat of a shiga na zauna, sai ya fito ya rufe front seat din ya bude gate ya fita da motar sannan ya koma ya rufe ya dawo cikin motar. Sai da yai nisa da tukun ya faka motarsa gefen titi ya jinginar da kansa jikin sitiriyarin motar ya fashe da kuka kamar karamin yaro. Kamar hadin baki sai nawa idanuwan suka cika da kwalla. “Why? Why all this?” Ya furta cikin sautin kuka, sai ya dago kansa ya jingina da kujerar motar, ina iya jiyo lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannu ya share hawayensa ya cigaba da tukin, sai da muka iso kofar gidan mu sannan ya juyo ya kalleni. “Zan iya maida auren idan kina so” Kai kawai na iya girgiza masa alamar a'a ma bude motar na fita, sai da na taka har bakin kofar gidan na saka kafata, sai na ji babu abunda na ke bukata sai kallon Abdulhamid. Juyowa nai na kalleshi, lokacin da ya turo da motoci aka dauke ni aka kai gidansa nake tunawa yau kuma gashi ya dawo da ni da kansa, zancen mahaifiyata na bata son a fara kirga min aure ya fado min a rai, da na san zan haka GOBENA zata kasance a gidan Abdulhamid da ban aureshi ba, ban ji ina tsanarsa ba, sai dai na nemi soyayyarsa da ke zuciya na rasa, hawaye yake kamar yadda ni ma nake yi. Hannu na saka na share hawayena duk kuwa da na san fuskata ba zata iya boye kukana ba, sannan na shiga ciki gidan, iyakar kokari na yi dan na tsayar da hawayena amman abun ya faskara haka na shiga gida ina hawaye. Inna da Mama da Baba da Hafiza duka suna tsakar gidan zaune ko wane fuskarsa dauke da far'a da alama nishadi suke. Baba na kishingide saman tabarma Inna na tsaye jikin kofar kitchen din dake tsakar gidan, Mama kuma na zauna a saman kujerar mata kusa da Baba Hafiza ce zaune a kofar dakin Mama tana shan rake, suna ganina da yanayi sai duk jikinsu yai sanyi. Gaban Baba naje na gurfana rike da takardar a hannuna ina hawaye na kasa daga kai na kalleshi. “Shi aure yana da rayuwa da mutuwa kamar mutum da rayuwa, idan lokacin mutuwarsa yai babu mahani, kuma abu kalilin kan iya sakawa ya afku ko ya mutu, ko da dalili ko babu, dan haka ki sawa rayuwarki sallama ki dauka cewar ajalin aurenki a gidan Abdulhamid ne yai” Da sauri na dago na kalleshi, jin magana mai dadi da kwantar da zuciya da samar da natsuwa daga bakinsa, tun kan na furta ya fahimci cewar aurena ya mutu. A take na share hawayena ina gyada masa kai alamar na gamsu. “Saki nawa yai miki?” “Daya ne Baba daya yai min” Na furta muryata na rawa, sai Mama tai karaf ta ce. “Amman me kika masa mi ya hada ku?” Kamin na ce komai ba Baba ya daga mata hannu. “Ba yanzu ba, tashi ki je ciki ki huta, Allah yai miki albarka” Ban san lokacin da murmushi ya kubuce min ba, kaunar mahaifina ta kara cika min zuciya, ya famshe ni daga tambayar da ban san mi zan fada a matsayin amsa ba. “Madallah da kai Baba, ina ma ko wane uba kamar kai yake? Madallah da uba irinka, madalla daka zama jigo ga Halimatu....” Na fada ina hawaye cike da shaukin sonsa, Hafiza ce ta taso daga bakin kofar da take zaune ta zo da gudu ta rumgume Baba tana kuka tana fadin. “Ina kaunarka Baba Allah kara maka lafiya” Dariya yai ya tashi tureta daga jikinsa ya tashi zaune. Ni kuma na dago na shiga dakin Mama. A dare Mama bata iya hakura ba har sai da ta ji dalilin mutuwar auren, ni kuma ban boye mata komai ba cikin har da fyade da kai min da abubuwan da suka faru, sai dai ban yarda na fada mata cewar Abdallah na ke zargi ba. Na ga rashin jindadin mutuwar auren a fuskarta, daman wace uwa ce zata zo auren yarta ya mutu? Balle Mama da take daukar abu ta saka a rai, su Salma da Hafiza ma da suke yan mata ba su yi aure ba abun ya dame ta balle kuma ji ace aure na biyu ya mutu. Sai dai duk da hakan ta nuna min zama da Abdulhamid din ba mafita ba ne sakin ya fi tunda har yana zargina. Da yamma Su Adnan suka dawo daga islamiya, ganina suka hau murna kamar wacce suka shekara ba su gani ba, ganin na kai har bayan i'shai yasa Namra ta fara tambaya wai nan zan kwana. “ A nan zan kwana, yanzu na dawo kenan sai illla ma shaa Allahu” Wani irin tsalle ta daka ta dire tana murna ta kama hannuna ta rike. “Momy da gaske?” Na gyada mata sai ta kara rumgume ni tana ta murna. “Yeee mun huta Momy ta dawo” Iya murnar da yata take na ganina a kusa da ita ya isa da tabbatar da cewar yarana sun yi marmarina duk kuwa da suna zuwa su ganni ko na gansu idan bukatar hakan ta kama, sai dai ko wane d'a yana bukatar mahaifiyarsa a kusa da shi, amman ni na bar su na auri Abdulhamid, a yau ya saka min da haka! Da tunanin abun na kwana a zuciyata har safe. Washe gari Baba ya kira ni a dakinsa ya tambaye ni abunda ya faru, a nan na tsige masa tun daga biri har wutsiya, a ganina shi mahaifina ne be kamata na boye masa komai ba. Shi ya ba ni shawarar zuwa asibiti na sake yin gwajin hiv dan tabbatarwa. Ban yi wata wata ba na shirya na tafi gurin gwajin. Ban dawo ba sai yamma domin daga asibitin na wuce gidansu kawata Hajara, a lokacin da na labarta mata mutuwar auren sai ta fashe da kuka kamar an mata mutuwa. “Wannan wane irin abu ne yake ta bibiyarki Halimatu? Tun farko sai da na ce ki auri Abban Ikram da yanzu duk wannan abun be faru ba kika ki” Kai na girgiza mata. “Wallahi sai ya faru, abunda Allah ya rubuta ya samu bawa babu mahani, na yarda da wannan” “Allah sarki Halimatu, ga ki da tauhidi ga yarda da kaddara, Allah ya yaye miki wannan abu da yake bibiyarki” Ta fada cikin kuka ni kuma na amsa da amin. Bayan sallah magariba na koma gida, sai na tararda tsakar gidamu cike da kayana na daki, alamar Abdulhamid ya aiko min da su kenan kamar yadda yai alkawari, mama ce take labarta min cewar a gurin kawo kayan har da mahaifiyarsa wai tai ma baba bayanin komai, wata kila shi ya turo ta dan ta wanke shi kar a ga laifinsa, wata kila kum ita ta saka kanta a tunanin ba zan fada musu gaskiyar lamarin ba, mama ta fada min har da cheque din kudi ta bawa baba ya ki ya karba, hakan kuma ba karamin dadi yai min, domin bana bukatar komai na Abdulhamid a yanzu. Da kaina na shiga na fadawa Baba result dina cewar ban daukr da shi, yayi murna matuka dai kuma ya sake ba ni shawarar zuwa wata asibitin na sake yin gwaji. Ban watsar da shawararsa ba, na tafi kusa asibiti uku ana min gwaji result na fada cewar bana dauke da cutar, daman can ni hankali na be taba tashi akan hakan ba, ko da Abdulhamid ya fada min ban ji komai a raina kuma ban san dalilin hakan ba. A dakin da na bari cikina na koma da kaya na jera komai kamar wacan karon, a nan kam gaskiya na ji babu dadi sosai domin a takure na ke duk kuwa da kasancewar gidan ubana ne amman gidan yawa ne, ba irin gidan nan ne na masu kudi ba da za a ce kowa da dakinsa. Ranar da na cika kwana uku da dawowa sai ga Aminu ya zo kofar gidan ya aiko da siyayya wai a bawa yaransa kuma yana kiransu, an fada min haka yake musu a yanzu duk bayan kwana biyu ko uku, ni kau na rasa dalilinsa na yin hakan bayan dacan ba haka ya saba ba. Be san ina cikin gidan ba na sani tun da ba kowa ya san aurena ya mutu ba, na san yana cikin mutunen da za su yi murna da mutuwar aurena domin ya sha fada min a lokacin da nake gidabsa cewar babu namijin da zai iya zama da ni sai shi saboda bakin halina. Fita yai da da su yai musu waya siyayyar ya hado musu da kudi sannan ya dawo da su suka shigo gida suna ta murna. A daren mun dade muna tattaunar maganar yadda a yanzu hankalinsa ya dawo gurin yaransa, abunda ya bawa kowa mamaki a gidan mu, Mama ta karkarta min hankali da wata maganar wai ko shine mutumen da yai min fyade. “A a mama ba Aminu ba ne, na san siffar Aminu ciki da waje, yadda yake idan ya saka tufafi kanana kaya ko manya kuma yadda yake mu'amalarsa, da shi ne da tuni zan gane, ko kadan wannan mutumen be yi min yanayi da Aminu ba, idan har shine dole zan gane, kuma me ma zai saka Aminu yai min haka, mutumen da baya kaunata, wanda ya kasa hakuri har ya dawo ya saki ni ta waya ya sake ni fa, mutumen ya wulakanta ni Mama Wallahi ko sunansa bana son ji” “Ai saboda kiyayyar da yake miki na ke zaton haka, saboda ya jefa ki a matsala ki kasa zaman auren” “Ko ma wanene ina rokon Allah ya bayyana min shi” Na furta ina hawaye zuciyata cike da kuna, Mama ta amsa da amin. Mun dade muna fira a dakinta, cikin har da zancen Abdallah tana cewa da ma shi na aura ita tun farko shi ta so na aura amman na ki ni dai ban ce mata komai, saboda ban taba fada mata cewar Abdallah yayi ta neman na kashe aurena na aure shi ba.... AHMAD POV. Tarin takardu ne a gabansa da laptop yana ta aikin cika wannan cire wannan saka wannan, aikin daya taru masa ne na satin daya shige wanda be be yi ba yake yi yau ganin yau assabar ce babu karatu. Mug din coffee na gefensa lokaci zuwa lokaci ya ke dauka ya sha. Be tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah azahar sannan na fito daga garden din ya shiga part dinsa yai alwala ya nufi masallacin dake unguwar, after sun yi sallah ya shigo gida, as usual ya nufi part din Hajiya, yar aikinta kawai ya samu a falo hakan yasa ya nufi dakinta tun kan ya karasa ya jiyo muryarta ita da abokiyarta suna fira, har ya juyo da zimmar ya fasa shiga sai kuma ya juya ya shiga da zimmar ya tambaya iya Baby Namra. Sai da ya gaishe da abokiyar Hajiyar sannan ya kalli Hajiya ya ce. “Hajiya ina Baby?” “Bata nan, wannan mahaifiyar Ikilima ce, Hajiya ga danki nan ko da yake ai kin san shi” “Na san Gwarzo ai tun ba yau ba” Cewar matar tana dariya, shi kuma ya saci kallonsa ya sake kallon Hajiya ya ce. “Ina taje Hajiya?” “Gidansu kawarta Namra” Kansa ya daga sama ya saka hannunsa ya dafe. “Oh Hajiya kin san na ce miki kar a kaita can, matar nan ba mutunci ne da ita ba wata kila ma kallon banza zata mata, shiyasa duk bibiyar da take min ban yarda na kai ta ba” “To ina ruwan yara da lamarinku, ta sha mun kai tana son zuwa can sai a hana ta? Su fa yarane babu ruwansu da wannan, kuma dazu ta fada min cewar Momyn kawarta ba a gidan take ba” “Hajiya dan Allah ki aika a dauko ta, ni dai bana son abotar nan, bana son yawan fitar nan da take Wallahi” “Zan aika amman sai da yamma, abincin ka yana part dinka” Be sake ce mata komai ba ya juyo ya baro jikin kofar, sai a yanzu yake mamaki no wonder yau weekend kuma bata zo ta dame shi ba, da yanzu tana nan ta saka shi gaba da hana shi aikin nan tace sai su yi game ko ya fita da ita kamar yadda ya saba mata every weekend. A dayan bangaren kuma yana ta ganin karfin halin Hajiya na zon hada shi aure da bazawara dan shi dai kam ya raya a ransa ba zai taba auren bazawara ba. “Allah kadai ya sani wata kila ma yarta bata da miji, miye na wani zuwa gidan iyayen mai son yarki a yi maganar auren da ke” Ya fada yana kokarin zama sai jin haushi yake kamar ance masa zancen aurensu ya kawo ta. HALIMATU POV. Washe gari ya kama Saturday babu scul sai islamiya, dan haka na tashi da wuri na gyarawa yarana suka tafi makaranta, har Amal a yanzu tana son zuwa islamiya duk wani kuiya da son jiki yanzu ta daina shi ganin babu ni a kusa da ita. Around 12 suka dawo daga islamiyar suka cire uniform suka saka kayan gida na zuba musu shinkafa da wake da akai a gidan, sai Amal ta murje ido ta kanne kafadarta ita sam ba zata ci wake ba, daman can na san Amal is not fan of wake da shimkafa amman na dauka ta canja ganin bana nan, a dole na tashi na dora mata indomie da kwai. Ina cikin kitchen din ta zo ta same ni ta rike rigata tana tabe baki. “Momy za ki goyani” Dariya yai ina mata kallon Mamaki. “Wato kin ga Momy a banza ko? Amal kin fa girma yanzu ya kamata ki daina wani abun, yanzu ba kamar da kike ba” Bata fuska tai tana kokarin kuka. Kanwata Salima tai dariya ta ce. “Kin ganta nan wallahi dole sai an goyata a cikin gidan nan, ko dai Namra ta goyata ko wani a cikin gidan nan idan ba haka ba sai ta shige cikin daki tai ta kuka tana kiranki, yanzu kuma kin dawo dan haka ki yi ta goyon abarki daman can ke kika saba mata” Dariya nai na kai hannu na dauke na dorata a bayana, ina kokarin kwance dankalin kaina na goyata da shi na ji Sallamar Baby Namra wato kawar Namra yar mutumen nan marar mutunci, da kuzarinta ta shigo da far'a har da yar ledarta a hannu. Gaba daya yan matan gidan mu suka hau yi mata oyoyo suna ta murna da zuwanta da alama dai sun saba da ita ba kamar yadda na ke tunani ba. Ita ma da far'a take ta gaishe su daya bayan daya sannan ta nufi dakin Mama inda ta san su Namra suna can. Ni dai ina goye da Amal ina dahuwar indomie sa gata ta shigo tare da Namra, Namra na nuna min ledar hannunta. “Momy kalla turare da chocolate Hajiyarta ta ce ta kawo mana” “Eyeee lallai kun gode” “Laaaa Momy Good afternoon” Ta fada tana mamakin ganina “Ykk ya makaranta?” “Fine” Sosai yarinyar take kama da mahaifinta, sai dai ita tana da far'a da son mutane ba kamar shi ba. Kana ganin fuskarta ita da Namra ka san suna murna da ganin junansu, daman kwana biyu nan suna da damuna da maganar zuwa gidan ni kuma na banzantar da maganar sai ga ta a yau ta zo. Amal ma sauka tai daga bayana ta bi bayansu. Ina sallame sallar la'asar Adnan da Namra suka shigo tambaya wai za su je waje su yi wasa, har ta bukaci na bata kudi ta biya kudin lilon da ake kusa da mu su biya su hau, ban musa musu ba na dauko jakata na ciro naira hansin na mika mata suka fita da gudu har suna rigengen. Wani irin faduwar gaba ne ya same ni sai na ji kamar na kira su na ce su dawo, gaba daya na ji babu dadi, ban kuma san dalilin hakan ba, zuciyata tai ta bugawa da karfi kamar zata fito tsabar faduwar gaban da nake, a take na soma ambaton Allah, sai dai ban wani damu ba ganin yamma ce na san shaidanun aljanu ma suna saka haka. Bayan na gama azkar na dauko wayata na shiga YouTube in duba wasu videos har biyar da rabi tai sannan na fito tsakar gidan kamar yadda muka saba zama na zauna cikin ya'uwana. Sallama akai mana muka amsa sai yaro ya shigo yace wai ana kiran Baby Namra direban ta ne ya zo daukarta. Kamin mu ba shi amsa Adnan ya shigo gidan da gudu har ya faduwa wasu yara na biye da shi jikinsa duk kasa ya fado kaina. “Momy Namra Namra....ta fada rijiya..... ” Ban san lokacin da na ture shi ba na mike tsaye na daki kirji idanuwana a waje. “Wace Namra?” *Jiya na yi 5k words yau kuma na yi 5k+ words 🤔 wace addu'a kuka min ne?🙄 Pls ku ba ni ita nai ma Halimatu ta koma gidan Abdulhamid 💔😪* 7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 2️⃣9️⃣ “Baby Namra....” Jin maganar tasa nai kamar daga sama, ban san lokacin da na doshi kofar fita da gudu ba, har sai da Inna ta riko ni. “Tsaya ki saka hijab dinki” Sai na koma cikin gidan da gudu na shiga dakin Mama ban tsaya neman hijab na janyo zanen da nai arba da shi a saman gadonta na lufe kaina kamar wata tsohuwa na fito hankali a tashe. Yan mata gidan mu na biye da ni, rijiyar da na sani a unguwar mu na nufa sai Adnan yace min ba ita ba. “Momy ba ita ba, rijiyar malam ya'u” Tsayawa nai cak jin ya ambaci rijiyar da na manta when last a dibi ruwa a cikinta, rijiyar da ake cewa har ma sha ruwa akwai a ciki. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, miya kaiku gurin rijiyar malam ya'u” Sai na maida dubana gurin Salma wacce tai maganar. “Namra ce ta ce muje can mu yi wasa” A nan ma kallon Adnan nake, kamar wacce bata da makoma haka na zama, jikina yai sanyi ga uban sara da kaina ya soma yi. Tafiya nake ina jin kamar ana mayarda ni baya ina tafiyar ina jin kamar ba kasa nake takawa, sam ban lura da babu talkami a kafafuwana ba sai da na isa bakin rijiyar kafafuwana suka taka sanyin ruwan da ke gurin. Leka rijiyar da nai ma sai da wani jiri ya kama ni saboda hudunta da kuma dadewarda tai ba a bude ta ba. Wasu mazan unguwar mu ne suka shiga ciki suka daukota a yanayin da na ganta na sam abu ne mai wahala ta rayu, ta ji ciwo a kai a fafafuwanta ma ta samu rauni hannunta har zubar da jini yake. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Shine abunda kawai na iya furta na saka hannu biyu na dauke, abun ka da marar karfi ga kuma rashin kuzari na tashin hankali sai na fadi a gurin tare da ita, har sai da kanena suka zo suka dauketa ni kuma na bi bayansu hankali tashe, har na isa gida kuka nake ina jin mutane na tambayar ko mi ya kai su can, garin ya suka fada a wannan tsohuwar rijiyar, sam ni kam ba tambayar ce a gabana yanzu ba ceto ran yar mutane ne a gabana. Muna shiga gida na dauko hijabi da jakar kudina na saka takalmi na muka nufi titi ni da kanena kusan rabin unguwar suna biye da mu wasu na fadi bata da rai wasu na tambayar yadda abun ya afku. Napep muka shiga kai tsaye muka nufi asibitin fmc, mun tararda mutane da yawa a emergency kuma sai mu ka yi rashin sa'a babu likitoci da yawa kasancewar yau Saturday. Sun karbe ta domin duk wanda ya ganta a dole ya tausaya mata, sai dai duk da sun karbe ta din hankalina be kwanta ba na kasa zaune na kasa tsaye, zuciyata ta na ta raya min cewar bata da rai ganin tun da aka cirota daga rijiyar bata motsi bata numfashi ga raunukan da ta ji. “Anty ki zauna” Salma ce ta dafa ni tana fadin haka, sai na girgiza mata kai ina kuka domin ba zan iya ba. “Ko ki kira yaya Abdallah...” Salma na fadin haka zuciyata ta raya min yes na kira shi maybe he can help, jaka na lalaba ban ji wayata ba sam ban lura da jakar kudi ce kawai a hannuna ba har sai da Salma ta miko min ta ta wayar. “Gashi ki yi magana” Da na karbi wayar sai na rike na rasa yadda zan yi da ita. “Ya dauka fa” Sai nai saurin karawa a kunne. “Hello....” “Wake magana” Muryar Suwaiba ce da alama wayar tana hannunta ne. “Ni ce Halima ce Ina Abdallah” Ta dade bata ce min komai ba har sai da nai zaton wayar ta tsinke. “Hello” “Bachi yake” “Ki taimaka min dan Allah ki tashe shi, ina cikin matsala yarinyar da..... ” Ban gama fadar abunda zan fada ba ta tari numfashina da masifa. “Haba Halima ya kamata ki gane Abdallah fa kanen mijinki ne, duk da ya rabu da ke be kamata wata alaka na shiga tsakaninku ba, ki shafa matsa lafiya dan Allah” “Yanzu ma in cikin matsala ne shiyasa na kira shi...” Na fada domin kawai ta fahimci akwai dalilin kiran ba hakan nan kawai nake kiransa ba. “To bachi yake” Ta tsinke wayar. Kwallar idona ta hanani ganin komai, hayaniyar mutanen da suke emergency sai na ji kamar ina wata duniyar, tabbas ina jin bakina yana motsi amman ban san me nake fada ba, Salma ta karbi wayarta ko na bata ko jefarwa nai duk ban sani ba, sai kuma na ji wani na tambayar ina yayen yarinyar nan, wata kila da mu yake wata kila kuma ba da mu yake ba duk ba zan iya ganewa a yanzu wani hudu ne ya rufe min ido ga idon a bude amman na kasa ganin komai. “Anty.....” Can cikin a na ji muryar Salma ta kirani kamar tana wata uwa duniyar. Tassssss na ji saukar wani azababben mari a gefen kumatuna, marin da ba a taba min irinsa ba tun da uwata ta haife ni a duniya, wani zafi na ji ya mamaye min ilahirin fuskata kamar wuta, a take kafafuwana suka kasa daukata. “Ku rike ta....” Shine abunda na iya jiyowa shi ma kamar daga can wata uwa duniyar, ji jai na buga hannuna a wani abun mai kamar karfi sai dai ko kadan ban ji zafin ba har numfashin da ke jikina yai gaba abunsa... 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣0️⃣ AHMAD POV. Aikin yake ta yi zuciyarsa na gurin yarsa, hakan nan kawai yake jin cewar baby Namra is not safe, yana ta ganin kamar matar nan zata mata kallon banza ko ta fada mata magana marar dadi saboda shi, and he can't take it anymore ko akansa balle akan yarsa da yake ji da ita, zuciyarsa na ta raya masa abubuwa, he feels like ba zai sake barinta taje gidan ba zai dauke mata hankali da wani abun. “Daga ganin matar nan bata da mutumci ko na five naira” Ya furta zuciyarsa na kara raya masa cewar macen auren mai mutumci ba zata iya tsayawa ta fada masa magana marar dadi kamar yadda Halimatu tai ba. Sai yanzu ma yake jin shi be yarda fa tarbiyar gidansu ba kar su lalata masa ya. Mikewa yai tsaye yana kallon agogo hannunsa da ya nuna masa karfe biyar da yan mintuna. Takardunsa ya kwashe ya dauko laptop dinsa ya nufi part dinsa ya aje su a can sannan ya fito harabar gidan ya kira almu direba, Almu ya zo da gudunsa. “Kaje ka dauko Baby inda ka kaita dazun” “To Alhaji” Direct bangaren Hajiya ya nufa, sai ya same ta a falonta mai mata mopping na matsa mata kafafuwanta. A one seater ya zauna yana kallon fuskar Hajiya da ke cike da far'a, wanda yake kyautata zaton nasabar farincikinta da zuwan matar nan ta dazun. “Ka ci abinci kuwa?” “No kin san ai idan ina aikin nan bana iya tsayawa cin komai” “Larai tashi ki dauko kulolin na zuba masa” “No zan ci after magrib” Ya fada zuciyarsa na ta yi masa sake sake akan farincikin Hajiya, baya son ya tambaya tai masa maganar Ikilima ko abunda ya shafeta so he decided ya kyaleta kawai idan ma maganar da ya kamata ace ta ji ce yana zaunesa za tai masa maganar. Hannu Hajiya ta kai ta dauko wayarta ta kira direban Baby Namra bugu daya ya dauka. “Hello Almu kaje ka dauko Baby Namra” “Ga ni a hanya Hajiya Alhaji ya fada min ai” “Okay” Ta aje wayar sannan ta kalli Ahmad tana murmushi. “Ko dan Baby ai ya kamata ka auri yarinyar nan, dan nasan yadda Baby take da rigima kamar kai ita kadai zata iya zama da ku, Wallahi dazun da mahaifiyarta na ba ni labarin irin hakurin zaman auren da tai sai ta kara burge ni” Shiru yai kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya kalli Larai ya ce. “Za ki iya ba mu guri Larai” Da sauri Larai ta mike tsaye sai Hajiya ta ce. “Why?” “We need privacy Hajiya, idan muka maganar Family be kamata wani ya ji ba” “Aiko dai ina jindadin matsa min kafafuwan nan da take” Tashi yai ya tare a gaban Hajiya kasan carpet yaja kafarta daya ya soma matsawa. “Hajiya ki ce matar nan ta zo miki tallar yarta kawai, ai kamata yai ace ta bari wasu su fada, kuma ni babu abunda za ku fada min da zai saka na aureta, na fada miki bana son auren matar wani Hajiya you know it” “Wallahi wannan yar albarka ce, irin wannan mai hakuri ba har tausa sai ta min ba” Kansa ya daga ya kalli Hajiya, ya san suna da arzikin da za su iya yin duk yadda suke so, after masu mata girki da shara da wanke wanke da gyara harabar gida da mai bawa fulawa ruwa everyday, now sukukarta take son ta rika matsa mata kafafuwanta, he just don't know why Hajiya take son mulkar sukukanta da hana su yancinsu, be isa ya siyawa matarsa abu ba ba da sanin Hajiya ba ko da ko anko ne, balle kayan sallah komai sai ta zaba ake musu. “Hajiya.....” Sai kuma yai shiru ya busar da iskar bakinsa, ya san mahaifiyarsa so tana da right ta yi duk yadda take so da shi ko da iyalinsa, but this time around maganin kar ayi kar a fara ba zai yarda yai auren a yanzu ba, idan ma zai yi ba bazawara ba kamar yadda take so, domin shi dai a rayuwarsa yana kyamar ragin wani, ya fi son shi ya rage maka as long as mace ta auri wani ta fito ba zai iya aurenta ba ko wacece ita a duniyar nan and no matter how much he loves her. “Ka amince kenan?” Da sauri ya amsa. “No Hajiya ba zan iya auren yarinyar nan ba, I Wallahi ko hannun macen da wani namijin ya aura bana jin zan iya rikewa balle kuma har na aureta” “Wai wannan wace irin bakar akida ce?” Hajiya ta fada a fusace tana janye kafarta. “Wallahi Haka Allah yai ni Hajiya, ina da masifar kishi ina da kishin bala'i ni kadai na san abunda na ke ji” “To Allah ya raba mu da bala'i.... ” Kamin ya amsa da Amin Almu ya shigo jikinsa na rawa cikin falon har yana kokarin faduwa, ko sallama be yi ba abunda be taba tun da yazo gidan ba Hajiya ba ko Ahmad sai da ya firgita da yanayinsa. “Alhaji....Hajiya... An jefa Baby...Na ji ana fadin Baby ta fada rigiya” “Na shiga uku ban lalace ba” Hajiya ta fada Ahmad kuma ya mike tsaye da sauri yana kallon Almu. “Wace Baby?” “Baby Namra Wallahi yanzu na ji ana fadar hakan ina tsaye kofar gidan na aika yaro ya kirata sai yaron ya shigo gida da gudu yan..... ” “Almu Enough...!” Be gama ba Ahmad ya daka matsa wata mahaukaciyar tsawar da ko Hajiya sai ta ta ji zuciyarta kamar zata fado, balle shi Almu da Ahmad yake kallo kamar idonsa zai ciro. Hannunsa ya saka aljihu ya ji babu keys juyawa yai da wani irin gudu da ya manta when last yai irinsa ya shiga part dinsa ga keys din a inda ya saba aje su amman ya kasa ganinsu sai da ya rumtse idonsa. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ya furta gabansa na kara faduwa, bude idon yai ya kai hannunsa ya dauki keys din ya fito da sauri ya nufi gurin motarsa, a yanayin yadda ya bar gidan da yadda ya hau titi duk wanda ya kalleshi ya san ba tukin hankali yake ba, ko dai ace yayi shaye-shaye ko kuma ba shi da hankali ko so yake ya kashe kansa. Cikin kankanen lokaci ya isa unguwarsu Halimatu, sau biyu kawai ya taba zuwa kawo Namra da kuma daukarta, ya san inda kofar gidan take amman be taba takawa ba sai yau, haka ya fita be ko kashe motar ba ya shiga cikin gidan su Halimatu kamar ba gidan matan aure ba. “Ina yata take?” Ita ce sallamarsa, sai aka rasa mai bashi amsa kowa yai cirkocirko. “Ta fada rigiya Momy taje da ita Asibiti” Adnan ya amsa masa. “Wace asibitin?” “Na ji tace fmc a napep suka je” A nan ma Adnan ne ya bashi amsa, juyawa yai da sauri ya koma cikin motar, da wani irin karfi ya fizgeta sai da kura ta mamaye gurin. Yana shiga fmc ka tsaye ya wuce emergency ko'ina dubawa yake har ya hango Halimatu tsaye tare da kanenta biyu. Tun ka ya karasa ya rika ganinta kamar wani bakin maciji, yana isa gurin tana juyowa a take ya kifa mata mari, tangal-tangal tai tana kokarin faduwa sai mutane suka fara fadin a riketa Salma ta riko ta amman ina tuni ta kai kasa, hannunta ya daki wheelchair dake gurin. Haba malam, haba bawan Allah Subhanallahi, sune abubuwan da suke fitowa a bakunan mutanen da ke gurin. “Ina yata” Ya tambayi likitan. “Mahaifinta ne kai?” Runtse ido yai kamar ba zai amsa masa ba, sai kuma ya gyada masa gudun bata lokaci. “Muna bukatar jini” “Ina take?” Ya tambaya numfashinsa na fita kamar wanda yai wani aiki ya gaji. Da hannun likitan ya nuna masa kofar dakin. “Tana ciki” Da sauri ya shiga gurin, katon guri ne da ake aje mutane wasu kasa wasu saman gado ana shiga da su wani dakin likita na dubasu. Tsaye yai yana kallon yarsa kama da matacciya take masa domin bata motsi kuma babu alamar rai a tare da ita. “Baby.... ” Ya furta cikin tashin hankali. “Tana da rai jini likitan ya ce a kawo sai a duba ta, sun tafi su dauko gado... ” Be ko tsaya kallon mai matsa bayanin ba ya nufi yarsa yasa hannu biyu ya dauke ta cike da kuzari jin cewar tana da rai. Kamar wani mahaukaci haka ya fito da ita mutane sai kallonsa suke, ya sakata a mota sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa da gudun tsiya ya bar cikin asibitin SJT hospital ya nufa da ita kasancewar ita ce asibitinsu kuma asibitin masu kudi wacce za a baka kulawa a take. Kamin ya karasa ya saka hannunsa aljihu ya lalaba wayarsa sai ya ji wayam babu komai sam ya manta da cewar a gida ya bar wayar sai yanzu da yake bukatar kiran family Doctor su. Yana isa suka karbata a take suka fara bata kulawa, jini ne abunda suka bukata bayan sun shiga da ita ICU, kamin ya kai gurin da za a dibi jinin nasa jikinsa har rawa yake. A ana cikin dibar jinin sai ga family Doc su ya shigo gurin hankalinsa a tashe. “Subhanallahi Gwarzo, yanzu ta kira tace na duba mata ko ka zo nan, na shiga emergency Doc Nura ke fada min an shiga da Baby ICU kai kuma kana nan, garin ya hakan ya faru...?” Kai kawai Ahmad ya daga ya kalleshi, shi da kansa ya karancin irin tashin hankalin da Gwarzo yake ciki ya fi gaban kwatance. After an gama dibar jinin Ahmad ya riko rigar Doc Nura da idanuwansa da suka gama rikedewa ya ce. “Dan Allah ka yi duk yadda za ka yi ka ceto rayuwar Baby, dan girman Allah” Ba Doc Nura kadai ba duk mutanen da ke gurin sai da ta ji tausayin Ahmad, gashi dai ba kuka yake ba amman idanuwansa da jikinsa da fuskarsa sun nuna damuwarsa karara, even the way da yake numfashin kasan yana cikin tashin hankali. Doc Nura ya gyada masa kai. “Karka damu In-Sha-Allah zata tashi” Sai a lokacin ya sake shi, ya dafe kansa ji yake kamar ace yana da wani abun da zai yi yarsa ta dawo normal. Mikewa yai tsaye ya bi bayansa a bakin kofar dakin da aka shiga da ita ya tsaya ya jingina jikin bangon dakin ya Runtse ido, yana jin muryar Hajiya amman ja kasa daga kansa sai kokuwa yake da numfashinsa. ABDALLAH POV. Daure da tawul ya fito daga bathroom dan karamin tawul a kafadarsa yana goge ruwan da ke kansa. “Waya kara ni” Ya tambayi Suwaiba da ke zaune bakin gadonsa. “Babu kowa” “Amman na ji wayata ta yi ringing kuma na ji kin yi picking sai kuma kika fita” “Ni ce na gwada kiran ina son na gane idan wayata tana aiki ne” The way da tai masa magana sai ya ji be gamsu da abunda ta fada ba, if gaskiya ne then why da tai picking ya bar dakin? Be sake ce mata komai ba, ya zauna gaban madubi ya soma shafa mai, jin bata zo ta taya shi ba yasa ya juyo ya kalleta. “Ba za ki taya ni ba?” Bata bashi amsa ba, sai dai irin kallon kunar zuciya da take masa ya karantar da shi damuwarta. “It seems like kamar akwai abunda yake damunki” “Yes alakarka da Halimatun nan ne ya ishe ni” Juyowa yai gaba daya ya fuskance ta. “I thought we talk about this issue kuma kin fahimce ni” “No i didn't,and i won't” Kai tsaye ta amsa masa da kamar fada, mikewa yai tsaye ya dauki wayarsa ya cire password din ya shiga call list ya duba mai kiran, bakuwar number ya gani a take ya aikawa Number kira, sai da tai ringing har ta katse ba a dauka sannan ya sake kiran layin aka daga cikin muryar kuka Salma take magana. “Hello.. Ya Abdallah” “Miya faru?” Ya tambaya ba dan ya san mai maganar ba, sai dai ita Salma tana da number sa. “Anty Halima ce sume” Gabansa ya fadi. “Ta suma kamar ya?” “Dazun ba Anty Halima ta kira ka ba? daman muna asibiti wannan Namra ce ta fada rijiya shine babanta yanzu ya mari Anty Halima ta suma” “Kuna ina?” “Muna asibitin Fmc” Be saka cewa komai ba ya katse kiran, zuciyarsa bata bashi kowa ba sai Namra ta ya akai ta fada rijiya ita tambayar da ta fado masa a rai, and why Aminu zai saka hannu ya daki Halimatu bayan ita take dawainiya da yarta, saboda kawai ya mayarda ita wata banza shine yake ta yi mata yadda ya ga dama. “Miyasa bata kira wani ba a family sai kai? Bata fi kusa da Abdulhamid ba shi da ya aureta ya saketa cikin mutunci? Ji yadda kake zanzana kamar.... ” Kan ta karasa ya daga mata hannu. “Please....” Sai kuma ya juyo daga jikin wardrobe da yake tsaye ya kalleta yana gyara hannun rigarsa. “Alaka ta da Halimatu ba ta yankewa matukar ina da rai, saboda haka ki sakawa zuciyarki salama, idan za ki iya yarda da mijikin fine, idan kuma aka samu akasin haka za ki wahalar da rayuwarki ne kawai, na fada miki kuma a yanzu zan sake maimaita miki hakan, for now on ba saboda na auri Halimatu nake wannan abun ba i just want to make her happy....” Yana kawai nan ya nufi gurin da kananan abubuwansa suke ya dauka ya saka aljihu ya fice daga dakin cikin sauri. Kamin ya isa asibitin zuciyarsa ta cika, ransa ya bace sosai from now on zai rika defending Halimatu as her brother, taya wani can wai shi tsohon mijinta zai saka hannu ya daketa saboda kawai yarta ta fada rijiya. “Ji wani irin zalimci” Ya furta yana jin wani irin bacin rai an taba masa Halimatu, a take wani bangare na zuciyarsa ya aika masa tambayar da ya rasa amsar ta. “Miyasa na damu har haka? What if mutane suka zargi wani abu? Miyasa nake ta zurfafa lamarinta a raina har yanzu....?” Yayi farkin motarsa gurin da kowa yake fakin sannan ya fito ya nufi cikin asibitin yana kokarin sake kiran Salma dan sanin inda suke a cikin asibitin. HALIMATU POV. Ashe suma na tana da dadi kamar dai shan maganin bachi, ta kan mantar da kai duniyar da kake ciki da kuma duniyar kuncinka balle kuma wata damuwa da fargaba ko kuka da tsoro. Indai har haka itama mutuwar take to ni kam ina maraba da ita daga yanzu har zuwa lokacin da zata sallamomin. Sannu sannu Halimatu. Muryoyi biyu na ji wadanda ba zan iya tantancewa ba kamar na Inna da Mama kuma kamar ba na su ba, iyakar unkurin da nai na bude idanuwa ne sai na ji sun min nauyi sosai, a cikin kaina kuma kamar babu komai ina jinsa kamar fanko. Ban ankaro ba na ji numfashina yai nauyi gurin fita daga kirjina haka ma gurin shiga sai na yi da karfi yake wucewa. Da wani irin karfi na umkuro na tashi zaune tare da bude idanuwa har sai da Inna da rike ni. Tabbas Inna ce ga fuskarta nan ina gani kamar a mafarki bakina na motsi amman ban san mi nake cewa ba, kai na daga sama gaba daya komai kamar ba gaske ba nake ganinsa. Kamar a min shokin sai na ji na farko daga mafarkin da nake. A zahirin ma ga Inna nan rike da ni Sai Salma da Aisha da Fati tsaye a kaina, Salma ta rufe bakina tana kuka tana kallona kamar yadda Inna ma take kuka ita da Fati. “Anty Halima...” Aisha ta kira sunana tana kallona kamar a firgice. “Na'am” Na amsa mata ina kokarin tuna abunda yasa aka kawo ni a nan. Na tuna Namra ta fada rijiya muka kawota ko? Sai aka mare ni? Amman waya mareni? Miyasa aka mareni? “Ina Namra take?” “Babanta ya dauke ta” Salma ta amsa tana share hawayenta. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba, sai na ji kamar wata tsotsa tana min yawo akai. A lokacin da hankalina ya dawo sai na ga Abdallah da wasu likitocin uku tsaye a kaina suna kallona. Wannan karon Salma hannu ta dora saman kai tana hawaye, Aisha ma kuka take. “Wai miya faru? Namra ta mutu ne?” “Bata mutu ba... ” Abdallah ne ya amsa min yana saka hannunsa a aljihu. “Ina son na ganta” Ina kokarin sauka daga kan gadon ya ce. “Akwai drip hannunki ki zauna sai ya kare” “A a ba zan iya ba ina son na ganta” “Ba mu san inda ya kaita ba” Ya amsa min fuskarsa ba yabo ba fallasa. Hakan yasa na koma na kwanta sai kuma na ji yana maganar hoto. “Idan drip din ya kare Mama za ta kaita ayi mata hoto” “Ba ni da lafiya ne?” Na tambaya sai yai saurin ba ni amsa. “Lafiyarki kalau” Bayan ya amsa min ya cigaba da kallona kamar mai tunani. “Ina son ganin yarinyar nan ina son ganinta ta mutu bata mutu ba ban sani ba i need to see her!” Na fada a tsawace kamar ba a hayyacina ba. “Idan ka san inda take a kaita ta ganta” “Ban sani ba amman zan bincika” Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin sai sauran likotocin suka bi bayansa. Ni kuma na lumshe idona ban bude ba har sai da na ji motsin shigowar mutum, Hafiza ce ta shigo hankalinta a tashe tana sharar kwalla. “Sannu Halimatu” Haka take kirana yana da wahala ta ce min Anty indai ba mutane sai arzikin ke saman kanta ba. “Yauwa, yarinyar ta rayu” “Ance tana da rai, mahaifinta ya kaita wata asibitin aka ce” Ban sake ce mata komai ba, har sai da Abdallah ya shigo da kansa ya karaso ya cire min drip sannan ya ciro wayarsa ya kira wani likita da ban san wanene ba ya ce. “Zan dauketa na kaita ta ga yarinyar yanzu idan mun dawo i will call you” Daga haka ya maida wayar aljihu ni kuma na sauko daga saman gadon na biyo bayansa, a harabar kofar shiga Ward din inda mutane suke shinfida tabarma suna zaunawa na hango Inna sai ta taso ta tare ni. “Halimatu kin taso” “eh zan kaita ta dubo Namra ne idan mun dawo sai a je da ita gurin hoton” Abdallah ne ya bata amsa a madadina sannan tai mana Allah ya tsare ta bimu da kallo, yana gaba ina biye har gurin motarsa, da kaina na saka hannu na bude motar na shiga na zauna daga lokacin kuma ban sake sanin inda nake ba. Sai can na farka na ga yana kallona. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Shine abunda ya furta, kallonsa nai kamin na kalli titin sai a lokacin na lura da motarsa fake take a gefen titi kuma ba a cikin asibitin muke ba, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi motar muka hau titi, SJT hospital muka shiga, babbar asibiti mai zaman kanta a zamfara, asibitin masu kudi domin ko katin ganin likita kawai ya isa siyen wani maganin a yadda nake jin ana fada domin ban taba zuwa ba. Agurin da aka tanada domin faka motoci ya faka motarsa sannan ya bude ya fita, ni ma na bude na fita sai wani irin sanyi baibaye ni sanyi ba na wasa ba, a take hakorana suka fara haduwa da juna. “Koma cikin motar ki zauna” Ya fada min sannan ya ciro wayarsa ya kira Hafiza yai mata kwatancen inda muke, tun da ya soma wayar na ke kallonsa har ya gama ya cigaba da latsa wayarsa, sak Abdulhamid nake gani a sura da hallitarsu sai dai shi ya dan fi Abdulhamid kwauri kadan, a hallaya kuma sun banbanta, tunawa da Abdulhamid sai ya haifar min da wata kalar damuwa a cikin raina. “Abdallah” Ni dai na san na kira sunansa har ya dago ya kalleni ban kuma san dalilin kiran nasa da nai ba, bayan ga wannan ban sake sani ko jin abunda ya fito daga bakina ba, kamar an min shocking dai na ji na dawo normal, amman a kasa nake zaune fuskarta har da hawaye da ban san yadda akai suka zubo ba, saurin tashi nai zaune na saka hannu na share hawayena a lokacin da na kalli Abdallah sai na ga idonsa cike da kwalla yana ta min kallon tausayi. “Miyasa nai hawaye? Mi yake faruwa da ni...?” Na tambaya ina kokarin fashewa da kuka, sai ya busar da iskar bakinsa “Ba komai” Da kansa ya kai hannunsa ya bude min motar. “Shiga ciki ki zauna na ce” “Ina son ganin yarinyar” “Idan Hafiza ta zo zamu shiga ciki ki ganta” Zaunawa nai cikin motar sai a lokacin na tuna da yata. “Ko ina Namra take? Ko har da ita ta fada rijiyar? Kamar bata fada ba ko?” Na tambayi kamar ya san amsar. “Tana nan lafiya kalau” Ban sake cewa komai ba, har Hafiza ta isa sannan na fito daga motar daman kafafuwa na waje suke, shi kuma ya rufe motar yai gaba muka bishi, mun yar tafiya mai dan ni sa sai dai ba sosai ba har muka isa bakin wasu dakuna, daki na hudu ya tura kofar ta bude sai ya tsaya be shiga ba yai min alama da na wuce. Ni na fara shiga sannan Hafiza sai kuma shi. Baby Namra ce kwance saman gado tana bachi jini na ta shiga a jikinta. An saka mata wani abu a wuya an daure kafarta da hannu a gefen idonta ma bandeji ne. Mutum hudu muka tarar a dakin ciki har da mahaifinta, kamar wanda ya ga bakin maciji haka yake kallona fuskarsa babu annuri, ban taba hada ido da wani naji firgita kamar yadda na ji a lokacin da na kalli Abban Baby Namra ba, a take na nemi natsuwata da karfin halina na rasa, na rasa sai fargaba da razana suka lullube ni, kamar wata karamar yarinya haka na zama na rasa sukuni har sai da na koma bayan Abdallah na tsaya. “Kina da wani irin karfin hali, how dare you” Babu wanda yace uffan daga mutane da suke dakin har Abdallah da Hafiza. “And let me tell you Wallahi idan yata ta mutu i will make your life miserable, you will die in jail kina ji kina gani zan tarwatsa rayuwarki, you will pay for this, ba kin zabi kashe min ya ba?” The word jail ta saka ni jin wani iri, is like kamar ban taba jin kalmar ba, kuma kamar ance min gunduwa gunduwa za ayi da ni. Ba tsoron gidan yari nake ko police ba amman ban san abunda ya saka ni tsoro ba har jikina ya fara rawa kamar wata bakuwar kalma haka na rika jinta a kaina, a take garin ya fara sauya min zuwa wani yanayin dabam, can na tsinkayo Abdallah nayi masa magana. “Taya mace da ta haifa ta san zafin haihuwa zata dauki yar wani ta jefa rijiya? Ya kake magana kamar ba namiji ba” Wani banzan kallon yai masa irin na sai a yanzu na lura da kai din nan. “And who are you? Her husband?” “No I'm her brother” “Just?” Ya tambaya da irin sigar rainin wayo. “Just ne?” Abdallah ya tambaya a fusace. “Who do you fucking think you're? After all the slap da maganar da ka fada mata yanzu and you want to deal with me? Daga ganinka ba ka yarda da kaddara ba” Sai ya daga wa Abdallah gira. “Yes ban santa ba, saboda ban hada hanya da ita ba, akan yata?..... Hummmm” Wata budurwa ce ta taso ma Abdallah budurwar da na tana gani a gidansu lokacin da naje. “Excuse me man, yar mu aka taba kasan darajar ranta?” “Hey young lady control yourself, and ban sani ba kuma ba na son na sani” Juyowa yai ya kalleni. “Muje Hafiza riko hannu” Yana fadar hakan ya fice, a maimakon ya ta kama hannun nawa kamar yadda ya fada sai ta tsaya yi musu bayani. “Ku fahimce mu, Halima ba zata kama yar wani ta jefa a rijiya ba, ko da kau bata santa ba balle ta santa, yanzu haka ba a hayyacinta take ba amman ta damu sai an kawo ta ta ganta, tun daga lokacin da ka mareta bata sake zama mutum kamar kowa ba, daga ni har ita ba mu san yadda akai yarka ta fada rijiya ba.... ” “Aljanune da ita kenan? Shiyasa ta dauki Baby ta jefa rijiya, daman ai ba tai kama da masu hankali ba, ita aljannu take takama da su ni a kaina rauhanai ne, na fita hauka” “Ba haka nake nufi ba...” “Idan baki min shiru ab har da ke zan daure fita ki ba ni guri” Ita yake ma masifar ni ce da jin tsoro sai hawaye nake kamar domin hawayen kawai aka hallaci ni. Hannu ta rika muka fice daga dakin ita hawaye ni hawaye har muka isa gurin motar Abdallah. Gidan baya muka zauna ni da ita, kamar uwa da ya haka kanwata ta rumgume ni a jikinta sai na fashe da kuka mai tsanani. “Gida nake so dan Allah ka kai ji gida... ” Na furta cikin kuka, shi dai be ce min uffan ba har muka bar asibitin. 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣1️⃣ ABDALLAH POV. Tukin motar kawai yake zuciyarsa na sosuwa da kukan da Halimatu take yi, on the other part kuma maganar da Ahmad yai ta tsaya masa a rai. A iya tunaninsa duk mai kokarin cin mutunci Halima yana yi ne saboda yana ganin bata da mai tsaya mata kuma ana ganinta a mace mai rauni. “Wata kaddarar, ta kan zabi wasu mutanen ta tare musu ko wane irin fada, ta tsaya musu ta hana ni ganin abun ki ko damuwa. Wata kaddarar kuma jefa wasu take a damuwa da bakinciki ta saka har duniya ta juya musu baya, mi yake damuna ne? Miyasa komai ni ce komai ni ce? Na gagara samun farinciki ko dan kankane dan kannen kamar haka...” Ta nunawa Hafiza yatsanta tana hawaye. “Komai ni ce, komai ni ni din dai Halimatu na fi kowa shiga cikin matsala, mutane gasu nan ina ganinsu suna farinciki amman ban da, kin gansu?” Hafiza ta kasa ce mata komai sai kuka take yana rike mata hannu. “Ga su nan fa ina kallo ke ba ki gansu ba?” Ta fada tana nuna gilashin motar, da gaske mutane take gani kwakwalwarta na kawo mata abubuwa da yawa, ciki har da rayuwarda tai a baya duk abunda ya zo daga bakinta fada take, abubuwan da take fada ba komai ba ne sai damuwarta. Kuka take tai dariya a lokaci daya kamar wata tabbabiya. Ta kalli Hafiza dake mata kallon tausayi tana hawaye. “Wacece ke? Na baki labarina? Ni wata mace ce mai haduwa da abubuwa kala kala” Sai kuma tai shiru ta sake kallon Hafiza ta kalli kanta. “Wacece ni?” Abdallah na jin hakan ya busar da iskar bakinsa ya faka motarsa gefen titi ya fita be dade ba sai gashi ya dawo rike da gorar ruwa ya bude motar ta gafen da Halima take ya cire murfin gorar ya kai mata ruwan a baki, a Hankali yake bata ruwan tana sha sannan ya cire gorar daga bakinta ya kai bakinsa ya kumda ruwan a bakinsa ya fesa mata a fuska, runtse ido tai na yan dakiku sannan ta bude kyakkawan idanuwanta sukai arba da na fuskar Abdallah. “A ina muke miya faru?” “Babu abunda ya faru” Mikewa yai tsaye ya bayan ya bata amsa ya rufe motar ya zagaya ya shiga side dinsa ya tashi motar. “Miya faru miyasa na jike ina zamu je?” “Asibiti” “Ka kai ni gida” Ta fada kai tsaye. “Kina da bukatar ganin likita” “Bana bukata Abdallah bana bukatar kowa ya rabe ni a yanzu balle har ni na rabi wasu, duk wanda ya rabe ni sai wani abu ya faru da shi....” Bata gama fadar abunda take fada ba ya daka mata tsawa. “Ya isa haka kike sakawa kanki tunani kala kala har abun yana taba kwakwalwarki, I'm sure idan level din gushewar hankalinki ya wuce iya nan ko yayanki ba za su zauna da ke ba....” Ta dago kanta ta kalli Abdallah ta madubin gaban mota idonta cike da kwalla. “Ba ni da hankali kenan? Shiyasa na ke jin kamar ina bachi kamar na suma, ashe gushewar hankali ne? Kenan haukace ta kama ni?” Ta lumshe ido ta a hawayen da Abdallah yake jin zubarsu har cikin zuciyarsa, har yaji ina ma be fada komai ba ina ma furta komai ba! Har ya kai ta kofar gidan ta bude mota ta fita ta shiga gida be daina kallonta ba, sai ta shige gida sannan Hafiza ta bude motar ta fita sai ya kirata. “Hafiza dan Allah a kula da ita, bana son nai mata cilas a zuwa asibitin ne yanzu, amman zuwa gobe zan turo direba ya maida ita kin ga ai ba su bata sallama ba kuma tana bukatar kulawar likitoci, and karki barta ita kadai pls shi ke kawo yawan tunani ku rika yi mata abunda zai sauke mata hankali” “In-Sha-Allah, mun gode Ya Abdallah” Be ce mata komai ba yai ribas ya dauki hanyar gidan Hajiyarsa zuciyarsa cike da tunani kala kala. Sai da ya faka motarsa harabar gidan maganar Halimatu ta fado masa a rai. Tabbas sukan kaddarar kyakkyawa ta musu rumfa ta tare musu ko wane fada, ta musu gata, bayan kuma ba zabin su ne ba hukunci na Allah. Idan auna yadda rayuwa ta shimfida musu kyakkyawar rayuwa da kuma rayuwar Halima sai ya ji imani da tsoron Allah ya kara kama shi, lallai ba yin kansa ba ne, domin yana da tabbaci da bawa ne yake zabawa kansa irin rayuwar da yake so da Halimatu bata zabi rayuwar da take a ciki ba a yanzu. A duk takunsa sunan Halimatu ke yawo a kansa, ko ina zai motsa tausayi ya mamaye shi, ya kasa ganin laifinta ya kasa samun hanyar rabuwa da ita a kullum kaddara kara kusanto masa da ita take. Ko da ya shiga falon idonsa ya canja kala saboda damuwa. He got lucky Hajiya ce kadai a falon tana kallon wayarta. Sai da ya tsaya ya cire takalmin kafarsa sannan yai sallama ya shiga cikin falon, a kujerar da ke fuskantar ta Hajiya ya zauna yana gaisheta. Ta amsa masa tana aje wayar a gafenta domin ta hango damuwa a fuskar danta kamar yadda ko wace uwa mai kula take gane idan danta yana cikin bacin walwala ko kishiyar hakan. “Husaini lafiyar ka yau kuwa?” Dagowa yai ya kalleta a hankali. “Ban san yadda za ki ji idan na tambaye ki ba, ban san ya zaki dauki tambayar ba, amman Hajiya kin taba tambayar kanki ko ki yi tunani miyasa Allah yai mu masu rufin asiri kamar haka?” Sakin baki tai tana kallonsa kamin ta amsa. “Ah Ah daman can Allah ya kaddara mu din masu arziki ne” Ya gyada kai. “Haka ne da yai mana arzikin kuma sai ya hada mana da farinciki, wasu kuma ya ba su arzikin ya hana su farinciki, wasu kuma ya ba su farincikin ya hana su arzikin, wasu kuma ya hana su arzikin ya hana su farinciki yadda ya so haka yake haka yake kasancewa, duk a cikin ikonsa ne” “Wai miya faru ne, ban gane wannan maganar ba?” “Halima Hajiya” Yana fadar sunanta sai yai shiru kamar ba zai cigaba ba, Hajiya kuma ta gyada kai. “Zancen kenan Halimatu Halimatu, ka kasa cire matar nan a ranka” “Hajiya ta ya zan cire abunda ba ni na sakawa kaina shi ba? Da ina da iko da dama da ban bar zuciyata ta kamu da son Halimatu ba tun farko” “Dan Allah na hada ka da girman Allah ka bar yarinyar nan, ka daina shiga zabgarta ka manta da ita a rayuwarka” “Idan umarni ne zan bi, idan kuma shawara to zan amsa miki da cewar Wallahi ba zan iya ba Hajiya, Soyayyar Halimatu a zuciyata kaddara ce, Hajiya na san Halimatu tun kamin tai aure, amman Allah be dora min kaunarta sai da tai aure ta haifi yara biyu, da igiyar aurenta na kamu da sonta Hajiya, shim ba ki yi mamaki ba? A yanzu na tabbatar ba son ne kawai a kaddarar da ke tsakanina da ita ba, har da taimakon rayuwarta da tsaya mata a wasu abubuwa, kamar yadda Allah yake bawa wani bawa abinci a karkashin wani bawa, ko yai maka kyauta da hannun wani bawan” Taso yai ya baro kujerarsa ya zauna kasa yana kallon mahaifiyarsa da duba irin na yaro mai neman dauki a gurin mahaifiyarsa. “Dan Allah karki hana ni yi mata ko wane irin taimako Hajiya, yarinyar tana cikin damuwa tana bukatar mutane a kusa da ita” “Halima ba yarinya ba ce, ka daina mata kallon yarinya, duk mace da zata haifi yara hudu ta san me take” Hajiya ta fada tana kallon wani gurin fuskarta a hade. “Yarinya ce Hajiya haihuwar da taima ta sauri ce, har yanzu Halimatu bata haura 26 ba, tana da rauni da yasa Hajiya, damuwa ta mata yawa yanzu har rasa tunaninta take, damuwarta kawai take iya karantowa idan tai losing memory ta” “Ba damuwa bace matsalar Hassan ya fada ai, tana shaye-shaye kuma duk mai shaye-shaye dole ya hadu da irin wannan matsalar gasu nan muna gani sai haukacewa suke, ni ina mamakin wace irin damuwa ce da ba za abar wa Allah ba, damuwar me ma? Idan bayan cin amanar da tai Hassan ya sake ta... ” Bata karasa Abdallah ya tafi numfashinta. “Hajiya da gaske kin yarda Halimatu ta aikata abunda Abdulhamid yake zargi? Na rasa gane dalilin tsanar Halima da kike a yanzu, mace da za tai aure ba ta dace ba, ayi ma yarta fyade mijinta ya saketa saboda haka, ta dawo ta bar yayanta da aikinta ta auri d'anki da bashi da lafiya wata kaddarar ta fada mata a keta mata haddi da aurenta, kuma d'anki yai mata sakamako da saki a lokacin da take bukatarsa ki kasa ganin tausayinta? Wallahi na tabbatar da Abbah yana da da Abdulhamid be isa ya saki Halimatu ba, domin yana yawan fada yayansa ba su isasu taba masa yan'uwa ba, yan'uwan ma Baba Dahiru mutunen da be a shi da amini irinsa, duk inda Abbah ya saka kafa kafarsa tana nan, ina tuna lokacin da Abbah yake mana wasiya da son zumunci da taimakon masara shi, musamman Baba Dahiru, babu irin neman arzikin da ba su yi tare da Abbah ba, amman shi Allah be bashi ba, daga karshe ya koma ciwon kafafuwa ya tare a gida, sannan Allah be ba shi yaya maza ba sai a lokacin da tsufa ya kama shi balle su taimake shi, matan kuma babu wata mai tsiyayar sana'ar da zata iya taimaka masa sai Halimatu da take aiki kamin ta rasa aikin nata, yanzu macen da ta taso a irin wannan rayuwar bata baki tausayi ba?” Tsawa Hajiya ta daka masa. “Bata ba ni ba...! Bana kaunar yarinyar nan Husaini, ita kadai tasan bakin nufin da ke zuciyarta shiyasa take haduwa da abubuwa, da gangan ta taki soyayyarka ta auri dan'uwaka, ta barka kana ta wakenta, shi kuma yana can zuciya cike da kuncinta, ai ko dan hallacin da kake mata be kamata tai maka haka ba, ta san kana son ta kuma yar ta yarda ta auri dan'uwanka bayab kuma ta san ba da zuciya daya zata zauna da shi ba, ko da ma zaman ya yiyu da wane ido zata kalleka? Ina da tabbacin Halimatu taja Hassan a jikinta ne ta nuna masa zata aureshi saboda ta musguna maka, ashe ba kai kadai tai niyar ciwa mutunci ba duka ku biyun ne, ina da tabbacin Hassan ba zai taba yafe maka ba idan har ya gano ka taba sonta kuma ka bari ya aureta, taya zan so yarinyar Husaini ka fada min, ku yan biyu ne a mahaifa daya kuka rayu, ciki daya kuka fito a rana daya ta sani kuma ta aikata wannan abun? Ba yanzu ba, gaba na ke hange tsabanin da mahaifinku yake gudun kar ku samu kuna daf da rusgawa a wannan ramen matukar baka cire kanka daga dramar wannan matar ba” Ya girgiza mata kai. “A'a Hajiya, kaddarar ce a haka, ina da tabbacin da ni ta aura da ta samu jindadin da ta rasa har ma da doriya, amman wahala da bakinciki be kare mata ba shiyasa ta auri Abdulhamid sai waenan abubuwa suka faru da ita” Wannan karon kallon tsoro Hajiya tai masa. “Na bonu wannan wane irin abu ne Husaini? Wani irin so kake mata haka?” Hajiya na masa tambayar ya lumshe ido ya dora kansa saman kafarta ta dama yana sauke ajiyar zuciya. ‘Wani irin so ne, wanda hannu be isa ya rubuta ba, ba ki ba zai iya furtawa ba, zuciya ta cika da kaunar Halimatu, rai na ta aikin begenta ta mamaye illahirin jiki da tausayinta, babu gurbin ganin laifinta, balle kiyayya ta samu muhalli...’ A zuciyarsa yake wannan maganar a fili kuma sai ya bude idon ya dago kansa ya kalli Hajiya ya ce. “Tausayinta kawai na ke” “Ka fara bani tsoro, duk yadda na ke tunanin abun nan ya wuce nan, sai dai ina gargadinka kar ka kuskura ka bar dan'uwanka ya san cewar wata alaka ta taba shiga tsakaninku” Shiru yai na few minutes. “Hajiya kin san miyasa na zo yanzu? So nake ki saka Abdulhamid ya maida aurensa da Halimatu” Kallonsa Hajiya ta tsaya yi kamin ta mike tsaye. “ Ada dai ina maka kallon mai hankali da tunani, to yanzu na gano baka da shi, Halimatu ta dauke ta tafi da shi, ai zamanta a gidan dan'uwanka ma hatsari gareku sai yanzu na gano, kuma Al-hamdulillah da ya saketa Allah ya hada kowa da rabonsa” “Wallahi Hajiya tana bukatar Abdulhamid a kusa da ita, dazun ma da ya rasa tunaninta maganarsa take min, hannunwanta ta nuna min ce min take na kalla na ga yadda Abdulhamid ya rabu da ita, ya kasa yadda da ita ya kasa riketa....” Tabe baki Hajiya tai. “Wani makircin sai mata, kai miya kai ka gurinta?” Be boye mata komai ba, ciki har da marin da Ahmad yai mata. “To Allah ya kyauta yai mafita” Shine abunda Hajiya ta fada ta shige dakinta, ta kasa samun muhallin da zata sake kaunar Halimatu a ranta, ada kam tana kaunarta sosai amman ban da yanzu da take ganin kamar Halimatu na son tarwatsa mata kan yaya ne. Sai 10 ya bar gidan bayan ya yanke shawarar tunkarar Abdulhamid kai tsaye da maganar. AHMAD POV. Ya kasa barin kowa yai jinyar yarsa ciki kuwa har da mahaifiyarsa, zuciyarsa ta cika da rauni har yake ganin idan ya daga kusa da Baby Namra zai iya rasata, mutuwar mahafiyarta yake tunawa and think he's not ready to bear the pain. After yayi losing mahaifiyarta ace yanzu ita ma ya rasa ta? The pain was almost more than he could bear. Tun da aka shigo da ita ICU bata motsa ba, yana ganin numfashinta yana tafiya yasan yarsa tana da rai, amman ba shi da tabbacin za ta tashi. Iskar bakinsa ya busar yana neman ta inda iska zai shiga hancinsa ya huda zuciyarsa ya zauna ko ya samu sassauci. Be taba jin ya tsani wata hallita ba kamar yadda ruhinsa ya cika da tsanar Halimatu. Abubuwa mabanbanta zuciya take raya masa, wata kila wulakanta masa Y'a akai har ta kai ta je waje ta fada rijiya, wata kila ma tsawa tai mata shiyasa ta ji haushi ta fada rijiya, ko kuma ta koreta daga gidan ita kuma taje gurin rijiyar, what if yarta ce ta jefata? Ya mai akai ta fada rijiya? “Ki yi addu'a kawai yata ta rayu, ya rabb pls save me” Ya furta yana maida numfashi da karfi, sannan ya kalli tafin hannunsa, wanda tun a lokacin da ya mare Halimatu hannunsa yai sanyi har yanzu, maybe because be taba marin mace ba sai yanzu kusan shi a rayuwarsa ma be taba dukan kowa ba sai ita. Ji yake ya zama wani irin mugun mutum idan ya tuna ta, yadda zai sarrafa rayuwarta idan yarsa ta mutu kawai yake tunani, kamin ya kai hannun nasa ya rike hannun yarsa.......... Runtse ido yai be bude ba sai da Hajiya ta shigo tare da likitan da suka fita dazun. “Gwarzo ya kamata kaje gida ka huta fa, 12 ta yi” “Hajiya ina son na maida ita Abuja a akwai wata asibiti a can wata kila za ta fi samun kula fiye da nan” Likitan ya matsa kusa da Namra da sauri ya taba ta, babu alamun numfashi a tare da ita, a take hankalinsa ya tashi ya fara bata taimakon gaggawa amman mai kira yayi kira wanda ya bada aro ya karbi kayansa, fita yai ya shigo da wasu likiton abunda ya kara tadawa Ahmad hankalin kenan, ta yadda ya ga fuskar ko wannensu da yadda suka ja zanen asibitin suka rufe ita sai ya zuba hannayensa aljihu ya daga kansa sama ya rumtse ido. “Na yi imani da kai Allah, kai kake kashewa ka raya, La'ilaha illallahu..... ” Ya furta yana jin kamar babu komai a zuciyarsa, duk kuwa da ya kasa gasgata yarsa ta tafi ta bar shi da gaske. hajiya kam fashewa tai da kuka tana ta salati har ta kasa tsayi sai da aka fito da ita daga dakin. Dafa shi da Doc Nura yai ne yasa shi bude ido ya kalleshi. “I'm sorry Gwarzo take heart” “Da gaske ta rasu?” Ya gyada masa kai sai ya runtse ido, ya bude yana murmushi. “Subhanallah” Ya juya ya kalli gawar Baby Namra, sannan ya sake kallon Doc Nura. “Dan Allah ka taimaka ka kaini gida i don't think zan iya driving” Har zuwa lokacin da ya fadawa Doc Nura haka, be ji komai a ransa game da mutuwar yarsa ba, ya yarda ta mutu amman be ji zafi ko jin kewa ko tausayi a ransa ba, be kuma san da dalilin hakan ba. Wani yanayi yake jin kansa ba damuwa ba bakinciki. A motar asibiti aka saka baby Namra, shi kuma ya shiga Motar Doc Nura Hajiya da darebanta kuma suka shiga nasu motar, aka baro motar Ahmad asibiti har sai da direban ya dawo ya dauka. Hajiya ce da kanwarsa suka kira familynsu suka sanar musu mutuwar Baby Namra. Hajiya na aikin hawaye yarta na rusa kuka wato kanwar Ahmad wacce ta shaku da Baby kamar wata kawarta, Ahmad kam part dinsa ya shiga ya kwanta saman gadonsa rairaim ya lumshe idonsa yana maida numfashi a hankali. Wayoyinsa na ta ringing amman ya kasa ko da motsawa balle ya dauka.... AMINU POV. Zaune yake Sa'adatu na kwance saman jikinsa hannunsa a cikin rigarta yana ta wasa da kirjinta, sam baya jin komai ba ya jin cewar abunda yake aikata akwai zunubi duk kuwa da kasancewar yasan sakamakon mu'amala da matan banza balle mace mai aure kuma kawar matarsa. Haka yake a bangarenta bata jin cewar cin amanar mijinta take, ta dauki alhakin Allah da na mijinta ga kuma na yayanta hakan be taba damunta ba, taba taba jin ko ras a ranta zuciyarta tana nishadantuwa da alfasha kamar yadda shi ma yake ji. “Wallahi na rasa kwarin guiwar da zan fada mata cewar zan dauko yayana” “Wai kai wani irin tsoro kake mata ne? Tana matarka amman ko magana zaka mata sai ka rikice” “Wallahi nima ban sani mugun tsoronta nake kamar mutuwa” Ta tabe baki sannan ta tashi zaune. “Ni dai dan Allah ka yi duk yadda za ka yi ka dawo da Halimatu, ta zauna cikin yayanta, daman can ban jidadin rabuwarku ba domin bana son naga ana raba mace da yayanta, dan tsabani kadan daga tambaya fita unguwa sai ka saketa” Iskar bakinsa ya bursar domin yasan shi ya fada mata haka cewar ya saketa saboda ta fita unguwa ba da izininsa ba. Amman yanzu yana son ya dawo da ita ko dan arzikinsa ba yana jin kamar yafo samun natsuwa yayi yadda yake so a lokacin da yake auren Halimatu ba kamar yanzu ba, uwa uba kuma ga arzikinsa ance yana tare da ita. Wayarsa ya dauka ya soma lasawa yana fadin. “Zan dawo da ita dole ma ne na dawo da ita, amman yaran zan fara karbewa tukuna yadda take da shegen son yara dole ta biyo su” Bayan ya fadi haka ya kara wayar a kunne. “Babyna ya kike” “Lafiya kalau Baby kana ina?” “Ina gurin aiki amman yanzu zan iso gida” “Sai ka iso love you” “Love you too” Ya aje wayar yana tuna lokacin da yake auren Halimatu, at any time zai iya shiga gidansa kuma sai a time din da ya so dawowa zai dawo ba kamar yanzu ba, da wannan ta saka masa ka'idar indai zai dawo gida ya rika kiranta yana sanar mata, and be isa ya dawo pass 9 ba, a yanzu gida yake sallah isha'i wani lokacin har da magariba ma, be isa ya shirya tafiyar karya ba, balle har ya dauki wata macw su je tare, shi yake batawa Halimatu rai amman tai ta bashi hakuri, ba kamar wannan ba da ita zata bata masa ran kuma ya bata hakuri wani lokacin har da kukansa, gaba daya rayuwa ta masa juyin masa jindadi yai masa upside down. Shi kansa yanzu ya kasa gane kansa ga tsoronta ya cika masa zuciya ko magana zai mata fargaba yake. Mikewa yai tsaye yana sauke ajiyar zuciya. “Ya kamata na je gida yanzu, idan kin gama ki rufe dakin ki basu makullinsu” “Okay” Ta fada yana gyara rigarta. **** Murja na aje wayar ta kalli Sadi tai saurin sauka ka gado. “Gashi nan dawowa” Shi ma zabura yai ya sauka daga kan gadon ya dauki rigar shaddarsa ya saka. “Abunda muke fa nake tunanin wata rana asirinmu zai tonu, shiyasa na ce miki mu rika haduwa wani gurin kar wata be kira ba ya riske mu” “Ni fa ba zan iya yawo boye boye ba sai a fara cewa ana ganina ina yawo, amman kai idan ka zo wa ya san abunda ya kawo ka gidan yayanka? Kai dai ko ka gaji da ni ne?” Bakinsa ya kai yai mata kiss “Ina zan gaji da ke Murja, tun kina waje ban gaji da ke ba balle yanzu da kike gidan yayana” “To ka tafi dai kar ya tararda kai sai mun yi waya” Ta fada tana turashi, ba musu ya dauki keys dinsa da wayarsa da ya saka a silent ya fice da sauri ita kuma ya nufi wardrobe ta dauko zane ta daura sannan ta bude karamar jakarta ta dauko kullin wani abu ta nufo kitchen da shi, kular miyar taushe ta bude ta kwance abun ta zuba kadan sannan ta saka spoon ta garwaye miyar ta fito da sauri ta maida maganin a muhallinsa ta shiga bandaki. HALIMATU POV. Me yake faruwa da ni? Da gaske hauka na ke a yanzu? Tsantsar damuwa ce ko kuma shaye-shaye da na fara ne ko kuma gamu nai? Har na shigo cikin gidan mu bana raba dayan biyu ba. Dare ne a lokacin amman a gidanky kamar rana, domin kowa yana farkewa cikin da har da yayana. Sannu kowa ke min suna ta min kallon tausayi, ni kuma na amsa na zauna q tabarmar da aka shimfida tsakar gidan. “Momy...” Muryar Namra ce da na kalleta sai ta kara boya bayan Aisha tana hawaye, can kuma ta leko. “Momy dan Allah ki yi hakuri karki da ke ni, Wallahi ba ni na jefata rijiya ba, ita ce ta hau taba dirowa tana hawa shine murfin ya balle ta fada ciki Wallahi ba ni ba ce” Ta fada cikin kuka kamin Inna ta karba mata. “Dan Allah karki mata komai Halimatu, tun dazun take dakonki, ta kasa zaune ta kasa tsaye ta ce idan kika dawo yanka ta za ki yi, ki dauki abun nan a matsayin kaddara” Idona ya cika da hawaye tausayin yata ya kama ni, sai na mika mata hannu alamar ta zo. “Ba za ki min komai ba” Na gyada mata kai sai ta tako ta zo gurin ta kama hannuna nawa ni kuma na jata jikina na rumgume, ni da ita muka fashe da kuka a tare. Ashe ba mu kadai ba, har sauran kanena da Inna sai da sukai hawaye ban lura sai da na tashi zan je dakin Mama. Wani abum hamdallah a lokacin da na shiga dakin Mama sai na tararda ita a kwance magani a gafenta da ruwan zafi, daman can na san tana da hawan jini sai dai ba kasafai yake tashi ba sai idan wani abun ya faru ko ranta ya bace sosai, wannan karon na san tashin hawan jinin nata baya rasa nasaba da abunda ya faru. A gafen gadonta na na zauna kasa na dora kaina a saman gadon ina bachi ina kuka, Adnan ya shigo ya dora kansa saman cinyata sai kai hannu na dafa kansa. “Bana da sa'ar komai a rayuwata, ko a lokacin da na haife ku mahaifinku ce min yai na tara masa yaya, zan tsofar da shi....” Tuna ba ni kadai na ke ba yasa na yi saurin yin shiru sai dai hakan be hana Adnan fahimtar yarena ba. “Kamar yaya Momy” Hannu na kai na rufe bakina na hade yawu. Sai ya dago ya kalleni. “Momy dan Allah ki daina kuka” Ya fada yana kokarin fashewa da kukan. Hannu na kai na kama fuskarsa na rike. “Adnan kai na fara haihuwa Allah ya raya min kai, ya inganta rayuwarka yai maka albarka ba baka ikon kula da kanenka ko bana raye” “Ameen” Mama ta amsa daga kwance da take tana kallona. Saurin share hasayena nai. “Ashe kin farka ya jiki?” “Ya na ki jikin?” Shiru nai na wani lokacin ina kallonta kamin na amsa. “Na ji sauki” Sai ta tashi zaune cikin rashin kwarin jiki ta shiga bandakin da ke cikin dakin.a zaune nai bachi duk yadda Mama ta so na kwanta sai na kasa ko na kwanta ma bachi baya daukata hakan yasa na tashi nai alwala na raya daren da nafila. Misalin hudu da rabi nai sallamar karshe a lokacin da na daga hannuna na yi kirari ga Ubangijina nai salati ga annabi na sai na rasa mi zan fara roko, lafiyata ko ta Baby Namra ko farinciki ko gushewar damuwa? “Allah ka min mafita ka tsaya min, ka isar min a komai da komai ka zama gatana, ka yafe min laifukana, ka sadani da rahamarka” Bayan na gama na sake rufewa da salatin Annabi, ban tashi daga gurin ba har aka kira sallah asuba, bayan na gama sallah na dauko qur'ane na soma karantawa har bakwai da yan mintuna sannan na tashi, ina jin kaina na juya kafafuwana kuma sun yi nauyi kamar yadda idanuwa sukai. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Baby Namra ta rasu gashi ana sanarwa a Zamfara redio” Shine abunda ya dira a kunne na da muryar Salma. Sai ni ma na karba mata a Hankali daga cikin dakin da nake tsaye. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Sai nai bayabaya har na kai jikin ginin dakin na jingina, hawaye suka ce min salamu alaiki...... 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣2️⃣ Barka da Sallah Allah ya maimaita mana 🙏❤ Hannu na kai na rufe bakina, wannan karon ba kuka ido da baki kawai nake ba har da zuciya da kwakwalwa da jikina amsa amo yake. Kuka nake ta ko'ina irin kukan da ban taba yi ba, irin kukan da ban taba sani yana tare da ni ba karkawar nake kamar wacce ta shekara a cikin kankara hakorana na hadewa da juna suna wata kara, wani kalar hayaki nake ji a cikin kaina. “Ashe har yanzun kukan be kare ba Halimatu” Mama ce tai maganar sai na dago na kalleta tsaye take jikin kofar dakin da nake ita ma kuka take kamar ni. Kai na gyada mata kamar wani abun arziki sai kuma na ji ana fisgata kafafuwana suka kasa daukata, wani farin haske ya baibaiye idona tashin hankali da nake ji a yanzu bana jin cewar ko daya daga cikin yayana ne ya mutu zan samu kaina a yadda na samu kaina a yanzu. “Ki ce Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Mama ce take fada min abunda zan fada, ba dan ina ganin fuskarta ba, ba fuskarta kadai ba komai bana iya gani a yanzu sai dai ina jin hannunta a jikina tana rike da ni. Unkuri nai da zimmar na bude bakin na furta abunda ta umarce ni sai bakin yai min nauyi kamar ban taba magana da shi ba. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba sama nake kasa nake duniya nake ko a lahira ban sake sani ba, sai duniyar ta duburce min hankalin ya tafi numfashin ma yai min dogon zango.... AHMAD POV. Tun bayan da aka kai Baby Namra a gidanta na gaskiya be sake zama a aje ba, duk wanda ya kira wayarsa ko ya zo gidan da sunan masa gaisuwa ba zai dauka ba ba kuma zai fito ba. Wani abu yake ji a tare da shi shi ba tsoro ba ba kuma fargaba ba, baya son ayi masa gaisuwar mutuwar yarsa, har yanzu kuma ya kasa saka komai a bakinsa bayan ruwa, ya kuma kasa jin komai a game da mutuwarta. Ita kanta Hajiya a yanzu tafi shiga tashin hankalin da gwarzo yake ciki fiye da jimamin mutuwar Baby Namra, ta fi kowa sanin danta yana da hakuri da juriya, sai dai wannan karon ta kasa banbance hakurin ne ko kuma damuwa? Ta san yadda yake son mahaifiyar yarsa balle kuma ita yartasa. Yana tsaye gaban madubin dakinsa Hajiya tai sallama ta shigo jiki a sanyeye damuwa da bakinciki karara a fuskar uwa mai damuwa da ciwon danta. A bakin gadonsa ta zauna tana kallonsa har ta bude baki tai magana sai ya tari numfashinta. “Hajiya Allah kadai yasan irin ihun da Baby tai kamin ta mutu, ita kadai ta san irin ciwon da ta ji” Idonta ya cika da hawaye tana masa kallon tausayi. “Ka fara jin zafin mutuwarta kenan” Juyowa yai ya kalleta. “Har yanzu dai, kawai na rasa dalilin da zai saka a kashe min ƴa ne” Kallonsa Hajiya take da uwar ramarsa da rashin kuzari da yake fama da shi. “Na kasa yarda cewar matar nan zata iya tura yarka a rijiya ta mutu bayan kai ka ceto ta ta yar, kullum mahaifinta da yan gidansu sai sun zo gaisuwa a gidan nan, babu yadda mahaifinta bw yi ba akan ya ganka amman saboda kace baka bukatar ayi maka gaisuwa na hana, ita kanta matar da kake zargi sun fada min cewar tana asibiti bata san inda kanta yake ba sanadin wannan abun” Dan murmushi yai kadan na takaici. “Hakan yana nuna da ganganta ta aikata, saboda ta ji nace zan daureta ne  shiyasa ta shirya ciwon karya” Zuwa yai ya zauna kasa kusa da Hajiya ya dora kansa a saman cinyarta sai wasu hawaye masu zafi suka soma sauko masa. “Hajiya kina iya tuna lokacin da take cewa bata son ta mutu ita kadai? Idan zata mutu zata tafi tare da ni da ke?...” “Tana yawan fadar cewar bata son ta sha wahala idan zata mutu” Hajiya ta karasa masa. “Ta yi mutuwa mafi kaskanci Hajiya, ta samu rauniya ka dama, Allah kadai yasan wahalar da tasha kamin ta mutu” Ya fada yana shafewa da kuka, for the first time bayan mutuwarta yau ya ji wani abu marar misaltuwa yana ratsa zuciyarsa, kewar yarsa yake ji a yanzu ji yake kamar ya rumtse ido ya bude ya ganta a kusa da shi, wani irin bakinciki ne ya soma rufe shi ta koina. “Hajiya ina ma ace ba da gaske ba ne, mahaifiyar yarinyar nan ta tafi yanzu kuma..... ” Sai ya kasa karasawa saboda kukan da ya ci karfinsa. Daga shi har Hajiya aka rasa mai rarrashin wani. Kanwarsa ce Siyama ta zo bakin kofar dakin ta tsaya tana kallonsu itama kukan take kamar su. “Be kamata a kyale matar nan ba, ta raba mu da farincikinmu, ta dasa mana bakincikin da ba zai tana goguwa a zuciyarmu ba” “Ba zan kyaleta ba, ba zan bar wannan abun ba Siyama” Ya furta cikin mueyar kuka still kansa na kan cinyar hajiya kamar wani karamin yaro, ita kuma ta dora hannunta a saman kan nasa tana ta rarrashinsa. “Ka dake ka daure ka shiga jama'a kuma ka amsa kiran wayarka, duk wanda akaiwa mutuwa yana jin babu dadi amman a haka yake daurewa, yau ake sadakan uku ya kamata ka fito cikin mutane ka zauna irin wannan kebancewar da kake kana kara bayyana rashin tawakalinka ga Allah ne, ya kamata mu yi imani da kaddara dukanmu” Kuka yake ba dan kadan ba, kuka yake ba na wasa ba, kukan da be tana irinsa ba, kukan da be taba saka ran yinsa ba. Kukan da tun da Namra ta mutu be ji irinsa na kusanta shi ba, ko mutuwar matarsa be yi kuka haka kamar na Namra ba, tun Hajiya na taya shi kukan har ta share hawayenta ta koma bashi hakuri tana karfafa masa. Daga karshe dukan maganganun Hajiya sun shiga jikinsa ya ji karfin hali da karfin zuciyar da yake jin zai iya fita ayi addu'a ukun yarsa da shi. Haka kuwa akai ya fita ya shiga mutane ana ta masa gaisuwa yana amsawa cikin karfin hali, sai dai a duk lokacin da akai masa gaisuwar sai yaji wani abu ya tsaya masa a zuciyarsa daker yake iya hada yawun bakinaa ya hade abun, tun yana iya hadewa da yawun har ta kai sai ya kurba ruwa yake jin abun ya wuce masa, wasa wasa ya fara jin numshinsa na yin kasa har sai da ya koma ambaton mahallincinsa. Babu wanda be tausaya masa ba, duba da irin shakuwar da ke tsakaninsa kuma sanin cewar ba shi da mata a yanzu, gashi mahaifiyar yarinyar itama ta rasu, ga wata uwar ramar da yai cikin kwana biyu kawai ya koma kamar wanda ya shekara kwance yana ciwo. Bayan sallah la'asar akai addu'a sai mutane suka fara watsewa, wasu kan so su sake masa gaisuwa sannan su wuce musamman wadanda ba su samu ganinsa ba sai a yau. A cikin mutanen har da mahaifin Halimatu wanda tun da akai mutuwar kullum da shi ake karbar gaisuwar. Da hannunsa ya turo wheelchair dinsa ya karasa kusa da Ahmad ya mika masa hannu Ahmad ya mika masa nasa hannun yana amsa gaisuwar da yake masa. “Ni ne kakan abokiyar yarka Namra...” Baba na rufe baki Ahmad ya tsaya cak yana kallonsa kamin yai saurin janye hannunsa. “Me ka zo yi nan?” Baba yai shiru kamar mai tunanin ta inda zai fara. “Ka fada min cewar yarka bata da laifi? Ko kuma ka bani hakuri akan abunda tai? Ko kuma saboda ka yi min gaisuwa sai na ce na yafe mata...?” “Da dai ka saurareni d’a na” Baba ya fada cikin sanyayyiyar murya, a take Ahmad ya daga masa hannu yana mai jin baya ma bukatar saurarensa. “Bana son jin komai daga bakinka, ka fadawa yarka ta jira kiran kotu, domin ba zan kyale wannan maganar ba, yarka kake kokarin karewa ni ma kuma kadin yata zan bi” “Haba dai d'ana arzikin ba hauka ba ne ka saurareni mana” “Ni ba danka ba ne da danka ne ni da yarka bata kashe min ya ba....” Yana kawai nan ya juya a fucewa ya bar harabar gidan. Part dinsa ya shiga ya ya dauki wayarsa dake ringing sai ta ya fara amsa kiran amsu masa gaisuwa sannan ya samu damar kiran lauyansa. *** *** *** Cikin tsananin damuwa Baba ya tura kekenasa ya fita daga gidan, daman haka yake idan zai tafiya mai nisa saboda baya iya taka kafa sai ya hau kekensa a maimaikon yai tafiyar da sanda, baya damuwa yace dole sai yaje da yayansa sun turashi ko su rika shi, ganin duk yayan nasa mata ne sa maza biyu da basu gama tasowa ba. Da kansa ya tari Napep bayan ta tsaya ya mike tsaye ya taka kafar a hankali ya shiga bayan ya fada masa inda zai kai shi, mai nepep din da kansa ya fito ya kama keken Baba ya nade ta ya saka ta a ciki sannan ya koma mazauninsa ya kunna napep din. Har suka isa gida Baba be daina tunanin maganar da Gwarzo ya fada masa ba, idan har da gaske yace zai daure Halimatu to dukansu suna cikin matsala domin za a kara mata wata damuwar ne bayan wacce take fama da ita a yanzu, ga kuma mahaifiyarta wacce ta koma sai an kwantar idan zata tashi ma sai an rikata saboda ciwonta na hawan jinin da ya saka ta a gaba. Cikin rashin kuzari ya isa gida sai da mai napep din ya fito masa da kekensa sannan ya ciro 200 naira ya mika masa bayan ya shi canja ya kwalawa dansa karami kiran. “Abbah....” Sai gashi ya fito da gudu. “Shiga da wannan kujerar koma ciki ka dauko min sandata” A nan ma da gudun ya shiga ya da keken ya dauko sandar ya kawowa mahaifinsa sannan suka shiga cikin gidan tare, a kishingide ya samu Mama saman tabarma Aisha na mata fita kofin fura a gefenta an saka kankara a ciki domin ita kada take iya sha a yanzu sai kuma maganin da aka rubuto mata asibiti. Daga inda take ta daga kanta ta kalli Baba tana ganin yanayinsa ta san ba zai bada labari mai dadi ba, sai ta maida kanta ya rufe ido. “Sannu... ” Baba ya fada sai ta daga masa kai a hankali, tana cizon baki tare da sauke ajiyar zuciya a hankali. Baba ya dubi Aisha “Aisha kin dawo?” “Eh Anty Hafiza da Husna da Inna suna can” “Ya jikin Halimatu?” “Wallahi Baba har yanzu bata magana, bata san wanda yazo kanta ba, ko motsi bata yi idan ba su likitocin suka juya ta ba sai dai tai ta kallon mutane ko kuma tai ta bachi” “Al-hamdulillah Allah mun gode maka, a nan din ma ba wani sauki, ina ganin mutanen ba za su bar maganar nan ba, ya tabbatar min da bakinsa cewar sai ya kaita kotu” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Mama ta fada a hankali sannan ta bude idonta. “Ka yi magana da shi?” “Baya son saurarena” “Ka yi magana da mahaifiyarsa?” “Shi mai karar be saurareni ba taya kike tunanin mahaifiyarsa zata saurare ni?” “Ita ai uwa ce zata fi shi hankali da tunani” “Bana tunanin ba da sanin mahaifiyarsa ko izininta yake wannan abun ba” “Idan ka yi min izini ni zanje nai magana da ita” “Ba za su saurareki ba” “Ba zan iya ganewa ba har sai na yi magana da ita, idan bata saurareni ba sai mu kai kararsu a gurin Allah” “Taya za ki iya zuwa ki yi magana da ita Mama ke da baki da lafiya ma” Aisha ta tambaya. Sai Mama ta unkura ta tashin zaune. “Zan iya Aisha ciwon Halimatu ya fi ciwona damu na” “Tashi ki taro napep mu tafi” “Da dai za ki ji magana ta da kin zauna domin ba za su saurareki ba” “Da dai ka bar ni na tafi hankalina zai fi kwanciya” “To Allah ya sa'a a dace” Shine abunda Baba ya fita da shi, sannan Aisha ta fita da kanta ta taro mai napep din ta dawo ita da Teema suka rika Mama suka saka ta a napep din. Kamin su isa har ta gaji saboda ciwon zuciya da ba jiki, ba a hana su shiga ba kusan gate din gidan ma a bude saboda masu zuwa gaisuwa da kuma wadanda ba su gama ficewa ba. Mama bata taba zuwa gidan ba sai yau saboda rashin lafiyar da ya same ta tun daga lokacin da aka kwantar da Halimatu asibiti, daga ita har Aisha da Teema daman Inna ce da su Hafiza suke jigilar zuwa gaisuwa kuma suje asibiti gurin Halimatu. Da taimakon mutane dake fitowa cikin gidan aka nuna musu kofar falon Hajiya har suka isa. Sun tararda falon a cike da mutane hakan yasa Mama ta fara gaisuwar ta kansu kamin ta kalli wacce take zaton matar gidance ta ce. “Ke ce Hajiya” “Aa ni yayarta ce Hajiya tana cikin bari a kira miki ita” Wata budurwa dake kusa da ita zaune aka aika ta kira Hajiya, sai gata ta sauko babu dadewa waya makkale a kunnenta har ta zauna, sai da ta gama wayar sannan Mama ta mika mata gaisuwa tare da ta'aziya. Hajiya ta amsa tana mata kallon rashin sani. “Hajiya zan iya kebancewa da ke? Magana nake son yi da ke” Jimm Hajiya tai tana kallonta kamin ta mike tsaye ta nufi dakin baki da ke kasa. “To sai ki biyo ni” Hajiya na gaba Mama na biye da ita tare da Aisha wacce ta rikota har suka shiga dakin. Madaidacin daki ne mai dauke da gado da katifar kasa sai kuma wardrobe da yan kayan kwaliya kadan. A saman gadon Hajiya ta zauna mama kuma ta zauna a kasa sannan ta kalli Aisha tace. “Je can waje ki jira ni” “To Mama” Amsa mata sannan ta juya ta fice sai ya rage daga Hajiya sai Mama ne kawai a dakin. “Na san baki san ni ba Hajiya baki taba ganina ba, ba kisan inda na fito ba” “Haka ne ban gane ki ba gaskiya” Hajiya ta fada tana aje wayarta a gafen gadon tare da tattara dukan hankali ta fuskanci Mama. “Ni mahaifiyar Halimatu wacce kuke zargin ta kashe muku jika....” Shiru tai na dan wani lokaci tana shawaye kamin ta cigaba. “Alfarma na zo nema gurinki Hajiya, kuma ba dan yata ta aikata abunda kuke zarginta ba, Wallahi yata mutuniyar kirkice ba, ba dab tana nawa ba sai dan zan iya shaidar halinta ko da ba yata ba ce, sannan na san ke uwa ce za ki iya jin abunda wata uwar take ji idan aka lakawa yarta sheri alhalin tana da gaskiya, kuna da arzikin da za ku iya hadawa da ni da ubanta duka ku daure amman ba shi nake son ki duba ba, adalci nake son ki yi danki kuma ki yi wa yata” “Wane irin adalci? Dazun Gwarzo ya fada min cewar mahaifinta ya zo yana rokonsa ke kuma kin zo yanzu idan har da gaske bata aikata ba miyasa kuke ta magiya? Anya mai gaskiya zai yi haka?” Mama ta daga kai ta kalli Hajiya hawaye na sauko mata. “Za ki iya ba ni kur'ane na rantse Hajiya? Wallahi ina zaune tare da ita a lokacin da jakarki ta fada rijiya, yara suka shigo da gudu suka fada mana cewar Namra ta fada rijiya, Wata kaddara ce take bibiyar Halimatu wacce ban san yadda zan kwatanta miki ita ba, ina tausayi Halimatu fiye da duka yayan da na haifa ni kadai na san halin da yata take ciki, bani da tabbacin rayuwa wata kila zan iya mutuwa yanzu ko anjima ko gobe amman ina son kamin na mutu na tabbatar yata ba zata je gidan yari da laifin da bata aikata ba” “Idan har da gaske bata aikata ba to kotu zata bata gaskiya mu ta bamu rashin gaskiyar” Kai Mama ta girgiza ta sake duban Hajiya tace. “Bari na baki wani labari Hajiya, kin taba haduwa da macen da akai mata fyade akai wa yarta kuma mijinta ya rabu da ita saboda tana kokarin kwatowa yarta hakkinta?” A take fuskar Hajiya ta canja. “Wa aka yi wa haka?” “Halimatu Hajiya..... ” Babu abunda Mama ta rage daga labarin Halimatu sai da ta fayyacewa Hajiya komai tun daga aurenta da irin kalubalen da ta fuskanta har zuwa yau da wannan kaddarar ta mutuwar Namra ta fada mata, ba mama kadai ke kuka ba, wannan karon har da Hajiya da ake ba labarin sai da tai hawaye. “Amman kuma ita yarinyar kuka kasa kwato mata hakkinta?” “Taya? Taya Hajiya? Taya za a kwato hakkin macen da mijinta ya karyatata ya gasgasta dan'uwansa akan yarsa? Mutun yarinyar kawai za a zubar a bata mata suna ita da mahaifiyarta” Hajiya ta share hawayennta. “Wannan ba hujja ba ce be kamata ku bar wannan maganar ba, kuka kokarin boyewa ne saboda gudun kunya, na tabbatar abunda kike kokarin boyewa na hana a bi wa yarinya hakkin kina kokarin daba wuka ne a ciwo, abun nan yana kasan zuciyarku ke da mahaifiyarta, miyasa za ku boye idan har za ayi wa mata da kananan yara fyade ana boyewa babu ranar da za a daina” “Maganar ta dade da wucewa Hajiya, yanzu alfamar ki nake nema kar Halimatu ta sake shiga wani kunci” “Zan yi mishi magana, za a samu mafita In-Sha-Allah” “Na gode Allah ya kara sutura, Allah ya saka da alheri” “Ita Halimatun tana can asibitin?” “Tana can amman bata cikin hayyacinta” “Gaskiya be kamata ku bar maganar nan ba, taya? Za a ketawa uwa haddi ayi ma ya kuma ku danne wannan bakincikin ku hade saboda gudun kunya?” Mama ta unkura cike da karfin hali ta mike tsaye. “Na gode Hajiya na gode Allah yasa ki rike min wannan sirrin” Cikin karfin hali ta fara takawa zuciyarta na mata mugun nauyi ta fice daga dakin. 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣3️⃣ Sai da suka gama tsara komai da lauyansa, sannan ya taso tare da shi suka shigo falon Hajiya, a lokacin 8 har da yan mintuna na dare. Da kansa ya tura kofar falon ya shiga Barrister na biye da shi a baya. Hajiya na zaune kasan center carpet Siyama ta dora kanta saman cinyar Hajiya ta lumshe ido kamar mai bachi, alhalin ba bachin take ba tsabagen ciwo kaina ya saka ta a gaba da damuwar rashin Baby Namra.   Barrister ne yai sallama Hajiya ta amsa mi shi tana kallon danta, ramarsa ta yanzu har ta fi ta dazun da jiya ga wani rashin kuzari da yake fama da shi, ko be fada mata ba ta san abunda ya kawo lauyansa a gidan, ta saurari duk wani abun da Gwarzo da Barrister suka fada mata da kuma yadda suka tsara shigar da karar, bata katsi hanzanrinsu ba har suka yi suka gama, bayan barrister yai mata sallama ta kalli Gwarzo tace. “Idan ka raka shi ka zo ina son magana da kai” Ta okay ya amsa mata sannan ya mike tsaye suka fice tare da barrister. A harabar gidan ma sun kusan awa daya suna tattaunawa kamin yai masa sallama ya sake dawowa falon Hajiya ya zauna. Shiru shiru Hajiya bata ce masa komai ba tana da kallon plasma dake falon, har sai da ya kagara da kansa yai magana. “Hajiya kin ce akwai maganar da kike son yi da ni?” Juyowa tai a hankali ta kalli gefen da danta yake zaune a saman cushion. “Zaka iya tuna lokacin da mahaifinku ya rasu?” “Eh” “Kana iya tuna silar mutuwarsa?” “Ciwon suga ne” “Matarka fa?” “Hadarin mota ne” “Miyasa ba kai karar likitan da ya duba mahaifinku ba a lokacin da ya rasu? Miyasa ba jai karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarka ba?” Kallon rashin fahimta yai mata, why Hajiya zata bijiro masa da wannan maganar? Taya zai yi karar wanda ya kirkiro motar da tai silar mutuwar matarsa? Taya zai yi karar likitan da ba shi ya kashe mahaifinsa ba? “Fada min? Ko kuma ka fi son Baby Namra ne akan mahaifinka? Ko kuma ran Baby ya fi na Matarka daraja?” “Ba... Ko... Daya...” Ya amsa kamar ana matso maganar daga bakinsa. “Then why zaka yi karar matar nan Gwarzo? Miyasa kake son dora mata laifi? Kana da wata hujja da ke nuna cewar ita ta kashe Baby Namra?” Wani dogon numfashi ya ja ya sauke, sai a yanzu ya fahimci inda zancen Hajiya ya dosa. “Saboda matar bata da mutunci ko kadan, kuma a yadda take da zafin zuciya zata iya aikatawa, kuma idan har bata aikata ba miyasa suke jin tsoro ita da iyayen?” “Da zaka ji labarin matar nan da ka tausaya mata, kaddara ce ta fada mata kuma mahaifiyarta tai min rantsuwa....” Saurin saukowa yai daga saman kujerar yana hade wani bakin abu daya tsaya masa a makoshi. “Hajiya dan Allah? Bana son na ji duk wani abu da ya shafe ta, ba ina kokarin kai kararta ba ne saboda na danne mata hakki no hakki yata nake kokarin kwatowa?” “Wace hujja kake da ita wacce ta nuna maka cewar matar nan ita ce ta kashe Baby? Haba Gwarzo ya kake neman zautuwa akan mutuwar da ba yau ta saba bakuntarka ba?” Sakin baki yai da mamaki yana kallon Hajiya miyasa tai saurin canja har take kokarin hana shi bayan ita ma a da tana goyon bayan karar? Siyama ce ta tashi zaune ta tana kallon Hajiya da mamaki. “Hajiya be kamata a kyale wannan maganar ba, taya zata kashe Baby kuma a barta?” Hajiya ta daka mata matsawa. “Kar na sake jin bakinki ba ki san komai akan rayuwa ba, kuma idan manya suna magana karki sake tsoma bakinki” “Amman gaskiya ta fada Hajiya indai suna da gaskiya kotu zata ba su gaskiyarsu mu kuma ta ba mu rashin gaskiyar” Kallonsa Hajiya tai da kyau “Mutuwar nan ta dauke mahaifinka ta dauke matarka, yanzu kuma ta dauke yarka, wata rana ni zata dauke kuma ta dauke kanwarka kamin ta dauke ka, wata rana zata zo da zaka rasa wanda zai hana ka aikata ba daidai ba balle ya fada maka kuskurenka....” “Bana tunanin idan wannan ranar ta zo zan iya rayuwa Hajiya, na rasa babana na rayu na rasa matata yes na rayu yanzu kuma na rasa yata still zan rayu amman bana tunanin idan na rasa ki zan rayu, ku kadai kuka rage min a yanzu daga ke sai Siyama ku kadai nake da ku a yanzu, Allah ya min kyautar mata ya karbe, ya ba ni ya ya karbe, mahaifina ma ya karbi abunsa, ba ni da kowa a yanzu daga ke sai yar'uwata sai dangi” Ya fada hawaye na sauko masa, sannan ya taso daga inda yake zaune ya nufa inda take ya rumgumeta. “Na bar maganar nan har bada Hajiya, Wallahi na barta” Hajiya ta lumshe idonuwanta dake cike da hawaye zuciyarta cike da tausayin danta. “We're three mu kadai muka rage, babu Baby babu Daddy” Cewar Siyama tana fashewa da kuka tare da rumgume Hajiya. “Allah ya musu albarka” Hajiya ta fada da muryar kuka, hakan yasa Gwarzo tashi ya bar falon yana share hawaye wasu na sauko masa. HALIMATU POV. Na ga abubuwa daya a cikin dogon bachi na, abubuwa mabanbanta, masu rikitarwa wadanda ba zan iya fassawaba, tabbas bachi da na dade ina yi a yau yana daure da mafarka kalakala. Ina ji a jikina kamar ban taba bachi mai nauyi irin wannan ba, domin ba jikina kadai ya mutu ba har fatar idona ji nake kamar ba zan iya budewa ba, numfashin ma idan ya fita daker ya ke dawowa, a duk lokacin daya dawo sai na ji wani bari da ban gama tantancewa daga ina yake fitowa ba, sai dai na sa tabbas ba na muhallina ba ne. A zuciyarta nake ta amboton mahallincina hakan ba karamin taimaka min yai har na samu karfin buden idon ba, sai kuma nai saurin maidawa na rufe sakamakon hasken da na ji yai min yawa idon har wani yaji na ji suna min. Cikin karfin hali na kai hannuna na murza idon sannan na sake budewa ina karewa dakin kallo sai a yanzu nake gane ko warin asibiti ne nake ji, amman miya kawo ni asibiti? Shi nake kokarin tunawa, a take kaina ya tsara na nemi duka tunani na rasa sai na sake rufe idon ina jin bakina da daci. Tuna abunda ya faru yasa ni saurin bude idon a nan abun neman ya samu hawaye suka fara aikinsu, unkurin tashi nai zaune amman na kasa saboda rashin kuzari. Hakan na cilasta min cigaba da karewa dakin kallo, ina haka aka turo kofar dakin wani ya leko ni sai kuma ya rufe dakin, da alama wani yake nema domin haka wasu suke idan suna neman wani sai su rika bibiyar daki suna lekawa. Har na lumshe idona sai kuma na sake jin an bude kofar a karo na biyu sai dai wannan karon na ji alamar shigowa duk kuwa da kasancewar idon nawa a rufe suke. Wani irin fitinannane kamshi turare na ji ya maye gurbin warin asibitin da nake ji hakan yasa ni saurin bude idon karaf nai arba da wani kyakkyawan farin mutum wanda ba zan iya kiransa da saurayin ba ba kuma zan ce masa mai aure ba tunda ban san gaibu ba, yana da manyan idanuwa ga dogon hanci, bakar rigar dake jikinsa ta haska fuskarsa gwanin daukar hankali. Matsowa yake ta yi kusa da ni yana kallon fuska kamar mai son tantance wani abu, van yarda a zahiri nake kallonsa ba har sai da na runtse ido na sake budewa, sai a yanzu na fahimci mutumen dazun ne da ya leko ni ya sake shigowa. “Sannu.... ” Ya furta min yana cigaba da kallona. “Yauwa” Na amsa daker, sai ya kalli kofa ya sake kallona. “Ya jikin?” “Al-hamdulillah kai likita ne?” Jimm yai kamin ya bani amsa, hakan yasa ni tsaye na kare masa kallo da kyau, kusan a kuskure nai arba da sarkar cross din dake wuyansa wacce nake kyautata zaton ta zinari ce, kamar yadda hannunsa yake dauke da agogo da awarwaro na zinari haka ma zoben hannunsa, ba rigar jikinsa kadai ba har jean da ke jikinsa kana kallonsa kasan mai tsada ne. “Yes ni Doctor ne how are you feeling now?” Yana fadar hakan ya nufi gurin files dina ya bude yana dubawa sai dai babu alamar natsuwa a tare da shi in each seconds sai ya kalli kofa kamar mai tsoron shigowar wani. Ba zan iya karyata cewar shi din ba likita ba ne domin ban san a wace asibitin nakr ba, ba kuma zan iya gasgata cewar shi din likita ne ba domin ban ga alamun hakan a shigarsa da natsuwarsa ba, ko da yake likitoci ma sun fi saka kananan kaya. “Ina mijinki?” Ya tambaya yana kai hannunsa ya taba jikina. “Miya faru?” “Akwai maganar da nake son yi da shi” Ya fada babu alamar wasa a tare da shi. “Idan wani abun ne ka fada min likita ba ni da aure a yanzu zaman kaina ke” Shiru yai yana kallon na dan wani lokaci kamin ya kai duka hannayensa ya rika ni ya tashe ni zaune, sai dai har lokacin ba shi da natsuwa. “Haihuwarki nawa?” “Hudu na samu miscarriage daya” “When last kika samu miscarriage?” “Ba a dade ba be wuce wata biyu zuwa uku ba” “Mi kikai aka kawo ki asibiti mi yasa kike kuka?” Hannu na kai na taba fuskata sai na ji sanyin hawayen dazun da ba su bushe ba. “Wata yarinya ta fada rijiya kuma ta mutu shine abun ya firgita ni” “Shiyasa kika samu kanki unconscious?” Kallon rashin fahimta nai masa. “Miyasa kake ta min wadannan tambayoyin?” “Sun shafi lafiyarki ne, na duba files dinki na ga komai after that kina fama da cutar damuwa, kin sha maganinki yau?” “Ban san an kawo ni asibitin ba sai yau” Saurin tashi yai tsaye sai ya kai hannunsa a karo na uku ya taba fuska, sai kuma ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayar da ban taba irinta ba ya miko min. “Saka min Number ki a nan zan, akwai bayanin da zan miki akan ciwonki yanzu sauri nake yi” Tsakanin wayar da fuskarsa sai idanuwa suka kasa tsayawa kallon abu daya, fuskarsa ko kuma wayar ko tambayar da ta cika min zuciya? Mi zai saka likita ya tambayi number wayata? Wane irin bayani ne da ba zai iya yi min ba? “Wane irin likita ne kai? Wane bayani ne da ba zaka iya yi min ba? Ni ban gane ba? Waye kai? Ka bar ni na ji da abunda yake damuna dan Allah” “I'm sorry” Ya fada sannan ya nufi kofar fita kamin ya fice ya sake waigo ya kalleni. “i'm sorry” Sannan ya fice, ni kuma na lumshe idona ina maida numfashi a hankali, tsakanin fitar Mutumen da ban san wanene da sake turo kofar dakin a shigo be wuce minti biyar da yan dakiku ba. Da sauri na sake bude idon a zato na shine ya sake dawowa sai ni arba da Abdallah ido cikin ido wani irin faduwar gaba na ji wanda ban taba jin irinsa ba, sai na ji yayi min wani irin kwarjini kimarsa ta cika ido, hakan yasa ni kawarda kaina daga barin kallonsa har ya karaso kusa da ni, yawo ya rika min da hannunsa a fuskata kamin ya kai hannunsa ya taba ni. “Halimatu....” “Na'am” Na amsa ba tare da na kalleshi ba, ina iya jiyo sautin fitar iskar bakinsa kamin ya kai hannunsa ya daga idona. “Sannu yaushe kika tashi?” “Ban dade sosai ba” “Okay” Da kanshi ya shiga ba ni kulawa kamin ya fita ya hado min tea ya dawo. Ya mika min tea na saka hannu na karba idonaa na kaina, yana ta kallona kamar be taba ganina ba, har na gama shan tea na aje kofin be dauke idonsa daga gareni ba. Dagowa nai na kalleshi a zatona zai kawarda idonsa ne amman kamar jiran yake mu hada sai ya cigaba da kallona ido cikin ido, hakan yasa sai duk na ji na tsargu. “Yan gidan mu basa nan?” Sai ya gyada min kai still idonshi na kaina. “Kwananki tara a nan sai yau kika farka” Kwana tara? Kenan ba bachi nayi ba kamar yadda nake tunani suma nai? Na tambayi kaina kamin na sake kallonsa na ce. “Da gaske Baby Namra ta rasu?” Nan ma kan ya gyada min yana cigaba da yi min kallon da ban san na minene ba, shigowar wani likitan ne yasa shi saurin mikewa tsaye ya saka hannayensa aljihu yana yi Doc maraba. “Ya jikin nata?” “Da sauki.... ” Haka Abdallah yai ta ba ni kulawa fiye da yadda na cancanta, sai dai hakan ba karamin taba ni yai ba, miyasa Abdallah zai yi ta bani kulawa bayan na zabi auren dan'uwansa sama da shi? Bayan na yi masa zargin shi yai fyade? Anya na cancanci girmamawa da kulawa daga gareshi? Duka yan gidansu yan'uwa na kusa da kawaye na sun zo ganina ciki kuwa har da mahaifiyar Aminu, ban da mahaifiyata, ko baba da bashi da wadacacciyar lafiya sai da ya zo ganina amman ban ga mahaifiyata ba, idan na tambaya sai ace min tana gida tana miko min gaisuwa hankalina be kwanta ba sai da nai waya da ita muka gaisa sai dai a yanayin da na jita kamar ba lafiya ba. Aisha da Hafiza ne suka labarta min yadda Mama da Baba sukai da mahaifin Baby Namra da kuma zirga zirgar gaisuwar da suka rika zuwa yi. Kwana na biyu asibitin aka ba ni takardar sallama, a ranar da aka sallame ni a ranar Aminu ya kawo min ziyara, ba karamin mamaki ya kamani ba da nai arba da fuskarsa, domin a yanzu bayan Mahaifin Baby Namra babu wanda na tsana kamar shi, su biyun nan bana kaunarsu a rayuwata. Be zo min hannu biyu ba yayi min siyayya mai yawa, bayan mun gaisa be sake ce min komai ba kamar mai kunyata sai wani sunsun da kai yake baya son kallona. Nima ta bangarena ban da kallon tsana babu abunda nake masa, ko ya jikin da ya ce min kasa amsawa nai sai Husna ce ta amsa masa shi kuma ya rike hannun Adnan yana ta wasa da shi gwanin kunya. Muna haka Abdallah ya shigo wani tsaya yai cak ya kalleni ya kalli Aminu. “Waye wannan?” “Mahaifinsu Namra ne?” Aisha ta amsa masa. “Daman Namra tana da uba? Miya kawo shi nan? Naga dai ba Namra ce bata da lafiya ba mi ka zo yi?” Dagowa Aminu yai ya kalleshi. “Na zo duba jikinta?” “Sai yanzu kake damuwa da jikinta? Lokacin da take gidanka ka kula da ita ne? Dan Allah mana tashi ka fice ko na saka a wulakantaka yanzu nan” “Akwai alaka a tsakanin mu ba ka isa ka raba wannan ba, so ko ka so ko ka ki dole ne alaka ta cigaba da tafiya har a bada saboda akwai yaya a tsakaninmu” Aminu ya fada yana mikewa tsaye “Yayan da baka damu da su ba? Yaran da kanenka ya lalata yarka ka kasa yin komai? Malam zo ka wuce” A fusace Aminu ya fice daga dakin, aiko Abdallah kamar jira yake sai yai kaina da masifa kamar zai cinye ni. “Tsakanin ke da shi ban san waya fi wani hauka ba, taya mutumen daya aureki ya raba ki da danginki ya kuma can ya wulakanta ki ya ci zafinki ke da yar ki  yanzu zai zo dubaki har ki saurareshi? Wace irin mahaukaciya ce ke? Ko sonshi kike ne? Son shi kike?” Yana ta maimaita min tambayar son sa na ke yafi a kirga be yi shiru ba har sai da na amsa masa a fusace hawaye na sauko min zuciyarta cike da wani irin bacin rai da bakinciki marar misaltuwa. “Eh son shi nake shikenan?” Yawo yake da idonsa a fuskata kamin ya gyada min kai. “Yes shikenan....!” Ya fice ya bar a ni a dakin ni da Aisha ban san lokacin dana fashe da kuka ba. ABDULHAMID POV. A natse ya shigo ya falon ya zauna bayan sun gaisa da Hajiyarsa sai shiru ya biyo baya alamar akwai damuwa a tare da shi, sai dai Hajiya bata lura da hakan sai aikin motsa furarta take. “Hajiya mi yasa baki taba fada min cewar Abdallah yana son Halimatu ba?” Da sauri Hajiya ta juyo ta kalleshi. “Wace irin magana ce wannan? Taya Hussein zai so matarka? Wacce ka rabu da ita” “Wallahi Hajiya zan iya dafa miki al'qurane cewar Abdallah yana son Halimatu, sai dai abunda ban gane ba kamin na aure ta yake son ta ko kuma bayan na aureta? Ko kuma bayan rabuwarmu?” Hajiya ta aje kofin furar tana dan murmushi tace. “Ba haka ba ne Husaini yana tausayinta ne kuma.... ” “Abunda yake mata ya wuce tausayi Hajiya, ni ba mahaukaci ba ne na fahimci komai yanzu, kuma na san ke ma kin sani” “Ni ban san komai ba kuma Husaini ba son Halimatu yake ba, hasalima duk wani taimako ita ce take neman yai mata” Hajiya na rufe baki Abdallah na shigowa dakin fuska babu annuri ya kwaso fushinsa na asibiti ya shigo gidanta da shi. Har ya zauna be cewa kowa uffan ba, kamar ya san zancen a ake, sai dai a badini kalaman Halimatu ne suka taba masa zuciya. Hajiya ta watsa mata wata uwar harara kamin ta rufe shi da fada. “Daga ina kake?” “Asibiti” Ya fada yana dan sakin fuskarsa shi sai yanzu ma ya ankara da ya shigo babu sallama kuma be gaishe da Hajiya ba. “Abunda kake yi wa Halimatu yayi yawa Husaini gashi nan har dan'uwanka ya fara zarginka.... ” Abdulhamid yai saurin tarar numfashinnta. “Ba zargi nake ba Hajiya zahiri na gani, kawai abunda na masa ganewa, shin kamin na aureta ne yake sonta ko kuma bayan na aureta ne?” Abdallah ya kalli Abdulhamid with confused. “Saboda kawai ina taimakonta sai ya zama ina sonta?” A take Abdulhamid ya daka matsa tsawa abunda be taba ba. “Sonta kake Abdallah, ni ba mahaukaci ba ne abunda kake mata ya wuce taimako, kuma abun kunya ne ace na saki mata ka koma kana bibiyarta” Tabe baki Abdallah yai. “Daga kai har Aminu ba ku dace da zama mata kamar Halimatu ba gaba daya ba ku da hali ba ku da tunani... Kuma ba ku da tausayi... ” “Eh sai kai gwani, je kai yi campaign ta aure ka” Abdallah ya mike tsaye a fusace. “Wai miye damuwarka da taimakon da nake yi ma mata ne? Ka riga ka ji baka bukatar zama da ita ka sake ta, to miye damuwarka da ni ko ita? Baka san cewa ina taimakon Halimatu tun kamin ka aureta ba?” Abdulhamid ma ta mike tsaye. “That's mean kana sonta tun kamin na aureta kenan? Miyasa ka bari na aureta bayan ka san kana sonta?” “Wai minene matsalar ka Abdulhamid? Abdulhamid?” “Kai ne matsala Abdallah? Taya taya taya zan saki mata twins brother naya rika bibiyarta?” Abdulhamid ya fada cikin daga murya. “Haram nai ko kuma taimakon da nake mata ne ba dace ba?” “Ana barin halak ko dan kunya, kuma ko dan gudun zagin mutane, kuma ni cin fuska ne a gareni kuma abun kunya a gareka” “Bana gudun zagin mutane, kuma wata halak din take baruwa Abdulhamid, wata halak din...!” “Husaini......! ” Tsawar da Hajiya dakawa Abdallah ne yasa Abdulhamid ficewa daga falon a fusace. “Enough is enough, so ba hauka ba ne kana ta wahala akan yarinyar da ta kasa daga kai ta kalli soyayyarta a idonka, da gangan ta take soyayyarka ta auri dan'uwaka, ba ka da hankali ne kai? Yanzu hakan da ran dan'uwanka ya bace ya maka dadi kenan? Baka da magana sai ta Halimatu baka da time sai na Halimatu, baku taba fada da junanku ba sai akan yarinyar, to ya isa haka an kai karshe” Ta karasa hawaye na sauko mata, Abdallah dai be ce komai ba all what he try to do ya saukar da fushinsa ya samu natsuwa. “Daga yau sai yau, ban yafe ka sake shiga safgar Halimatu ba, ban yafe ka sake taimakonta da komai ba” A rikice ya girgiza mata kai da sauri sai ta daga masa hannu. “Fita ka ba ni guri” Hannunsa ya saka ya dafe kansa kamin ya juya da sauri ya fice daga gidan gaba daya.... 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣4️⃣ “Kai ma wani irin ka zama ne Aminu? Kamar ba kai ba? Har ka tsaya wani katon banza ya ci maka mutunci akan matarka ka kasa ramawa sai yanzu zaka zo nan kana wani huce haushi kana fada min? Haka yarinyar ta saka gaba wai ba zaka maida yaranka a gidanka ba kuma ka saka mata ido ya biye mata sai kace ba kai kake aurenta duk ka bi ka zama wani irin mutun” Uffan be ce ba har Hajiya ta gama yi masa fadan, shi kansa a yanzu ya san ba kamar da ba ne, duk wani kuzari da kazarkazar irin nasa yanzu babu shi a tare da shi, tun da ya auri murja komai nasa ya sauya ga tsoronta da yake kamar mutuwarsa, abubuwa sai fada masa suke. “To idan ba zaka iya zuwa kai wa matar taka fada ba, ni zanje da kaina nai mata fadan kuma dole na yayanka su zauna a gidanka kamin uwarsu ta dawo, dan yara ba za su zauna suna ta gararanba a gari ba ba kamar marasa gata” Da sauri ya dago kansa jin Hajiya tace zata je tai wa Murja fada. “A'a Hajiya zan sake mata magana zan lalaba har ta yarda” “Har da yarda? Ka lallabata? Uwarka ce ita? To ba zan lamunta ba, ba zan dauka ba, ko tana so ko bata so dole ne yara su dawo gidan ubansu, da har zance zan rika maka su amman yanzu na fasa ko zaku mutu sai sun zauna a gidan nan” Cikin rashin jindadin ya kalli Hajiya. “Hajiya komai dai a bi a hankali kin san ba ko wace mace ke son rikon yaran wata ba, kuma kin ga bata haihu ba so duk wani responsibility na yara bata san shi ba” “Idan suka zauna gidan ka daukar musu mai kula da su, yaran ma ai da wayonsu kuma ba fata muke a wani dade ba mahaifiyarsu zata dawo, duk yadda za ayi sai ta dawo duk inda zan fita na shiga sai na yi amman Halimatu sai ta dawo maka, ko dan arzikinka ya dawo” “Shine kawai abunda nake fata yanzu ni har abunda nake ganin yafi a bar yaran a hannunta idan zata dawo sai ta dawo tare da su gaba daya, sai na kama mata wani gidan ita da yara su zauna” “Idan ba a karbe yaran ba taya za ayi? Ta dawo? Ai sai an karbe yaran shaukin sonsu da kaunarsu ya shiga zuciyarta sannan ta san muhimmancinsu ta dawo maka” “To Hajiya idan Murja bata yarda da zamansu ba ai dole na hakura har ta dawo gaba daya..... ” Ya karasa yana ciro wayarsa dake ringing daga cikin aljihun gaban rigarsa, ganin daga gurin aikinsu ne yasa shi hanzarin daukar wayar. After sun gaisa mutumen yake sanar masa ya zo yanzu ana nemansa. “Okay gani nan zuwa, amman lafiya dai?” “Ka zo dai” Ya sake amsawa da okay sannan ya kashe wayar gabansa na mugun faduwa kamar yadda jikinsa yake fada masa ba lafiya ba. “Wato yanzu sai ta aminta sannan yara za su zauna gidan lallai Aminu, kamar ba kai ba kamar an sauya ka Wallahi” “Rayuwa dole ai tana sauyawa Hajiya, yanzu dai bari naje gurin aiki ana nemana” Ya fada yana mikewa tsaye, Hajiya kam da kallon mamaki ta bishi har ya fice. Direban Hajiya yai ma magana ya sauke shi a gurin aikin na su da zimmar idan ya gama abunda yake sai ya samu wani cikin abokan aikinsa su sauke shi gida, tunda abun ya zame masa haka mota bata kaunarsa sabuwar da ya siya ya kashe mata kudi har ya gaji bata gyaru ba, idan ma ta tashi cikin kwana biyu zata sake samun wata matsalar. Cikin tsoro da tunani kala kala ya shiga ofishin shugaban na su, ya tararda wasu mutane a ciki hakan yasa shi neman guri ya zauna har sai da ya sallami bakin nasa sannan ya karasa gurin teburin ogan yaja kujera a daya daga cikin kujerun da mutanen suka tashi ya zauna yana mika masa gaisuwa. “Makullin office dinka nake son ka ba ni da duk wasu takadar da suka shafi ma'aikatar da wadanda suke hannunka...!” Tas tas tas gabansa yai mugun bugawa. “Ranka ya dade lafiya dai?” Wanda ya kira da ranka ya dade ya dauko wata takardar ya mika masa, sanyi jiki Aminu yai gurin karba kamar yasan abunda ke ciki ba alheri ba ne. “Ranka ya dade takardar me ce?” “Ka karanta ai ka yi boko” Ya hade yawu yafi a kirga sannan ya bude zungureriyar takadar wacce ya kasa fahimta abunda aka rubuta a ciki ba dan kuma be iya karanta turancin ba sai dan baya cikin natsuwarsa. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ranka ya dade me nai aka kore ni? Kamar kora na ke gani ko?” Ya tambaya jikinsa na bari bayan ya karanta takardar a galabaice ga wata uwar gumi daya tara a goshi. “A gaskiya ni kai na ba zan fadar dalili ba abu ne daya taso daga sama” “Amman ana sallamar mutum ba tare da yayi laifin komai ba ranka ya dade? Idan wani laifi nai a fada min sai na gyara, aikin nan shine rayuwata” “To ina ganin abunda yafi ka koma gida sai ka rubuta apology letter sai ya aiko min ni kuma zan tura ta sama In-Sha-Allah, amman dai sun fi zarginka da wasa da aikin ga kuma rashin zuwa aikin akan lokacin” “Allah yasa hakan shi yafi alheri, na gode” Ya fada yana mikewa tsaye jiki a sanyaye zuciyarsa a daure. Office din nasa ya nufa a lokacin daya shiga sai ya rasa abunda zai yi a ciki sai kawai ya nemi gurina zauna ya rumtse ido, tunani yake son yayi ya kasa tunanin me zai yi? Kayansa da suke office din ya kwashe ko kuma tunanin gobensa? Ko tunanin laifin da ake tumarsa da shi? Anya wannan kawai ya isa ya saka a koreshi daga aikin da ya shafe shekaru yana yi? Ko dai akwai wani wanda yake masa makarkashiya yake bibiyarsa da sheri? Shigowar abokinsa ne yasa shi dago kai ya kalli kofar da idanuwansa da suka gama sauya kala. “Tahir kaga abunda mutanen nan suka min?” Ya fada yana nuna masa takardar kamar ya fasa kuka. “Aminu sai hakuri idan mahassada suka saka mutun a gaba sai addu'a tun jiya aka bada takardar nan amman kowa ya kasa kawo maka shine yau bayan ka bar office yace a kira ka shi zai baka” Ya busar da iskar bakinsa. “Yace na rubuta takardar bada hakuri” “Kai share banza ai duk da shi akai maka wannan sherin budurwarsa yake son dorawa a kujerarsa” “Wacece Habiba?” “No Jalila dai ba tare yake da ita ba” Duk wata magana da yake yana yinta ne kawai cikin karfin hali amman ba dan yana da kuzari da karfin zuciya ba. Da taimakon Tahir ya hada duk wani abu daya san na shi ne ya kwashe a office din ya saka a kwali Tahir ya saka masa a motarsa, sannan ya koma office din shugaban na su ya mika masa keys din da wasu abubuwan da suja shafi ma'aikatar yai masa sallama ya fito. Tun da suka kamo hanyar gida Tahir ke ta ba shi magana yana nuna masa hanyar da zai bi a maida shi aikin da kuma manyan mutane da ya kamata yai ma magana. A cikin motar Tahir ya bar komai nasa ya fita daga motar ya shiga gidansa cikin damuwa da tunani kala kala, he wasn't surprised ganin motar Sadi a harabar gidan daman can ya saba zuwa gidan idan an kwana biyu wani lokacin kuma yana shigowa tare da shi, suna da kyakkyawar fahimta tsakaninsa da Murja ba kamar Halimatu da daman can tun a farkon fari basa samun jutuwa wanda ya samu asali daga Hajiya wacce bata son Halimatu. Tafiya yake yana jin kamar ba kasa yake takawa ba saboda damuwar data cika masa ruhi, a yau kam ba tare da ya kira murja ya sanar mata da zuwansa ba zai shiga gidansa duk kuwa da kasancewar tai masa gargdin cewar karya dawo gida babu notice, sai dai tashin hankalin dake tare da shi a yau ya mantar da shi dokarta, shi yanzu ma tsoronsa daya kar ya fada mata gaskiya ta guje masa, ko kuma ta juya masa baya, anya ma zai iya fada mata cewar an koreshi daga aiki bayan ko amarci bata gama ci ba? Duka duka ko shekara batai ba tana tunanin jindadi zai bijiro mata da wannan maganar? Har ya tura kofar falon ya shiga be yanke shawarar fada mata gaskiya ba ko kuma boye mata idan ma ya boye mata me boyewar zai haifar tunda dole ne wata rana sai ta san gaskiya. Ganin babu kowa a falo sai tv dake aikin watso labarai yasa shi mamaki, sai dai be kawo komai a zuciyarsa ba ya leka kitchen din dake bude nan ma wayan babu kowa kai tsaye ya nufi dakin Murja yana tabawa ya ji shi a kulle an saka masa key daga can ciki. Hakan yai mugun daga masa hankali har ya kai hannu yai knocked sai kuma wata zuciyarta hana shi, to ko dai Murja bata nan ne? Ta rufe dakin ta manta bata rufe falon ba? Idan kuma bata nan mi ya kawo motar Sadi a cikin gidan? Kuma ina Sadin yake? Juyawa yai da sauri ya fice daga falon ya zagaya ta can gurin windows dakin Murja da zimmar ya leka dakin sai ya samu windows din suma a rufe. Dawowa yai falon ya zauna ya zubawa kofar dakin ido, yana ta kokarin hana zuciyarsa zargi yana ta kokarin kyautatawa matarsa da dan'uwansa zato! Sai me? Sai ya kasa natsuwa ya kasa sukuni gaba daya sai ya manta da zancen sallama hankalinsa gaba daya ya dawo a nan. Wata dabarar ce ta zo masa sai ya fita harabar gidan daga can inda ba za a jiyo muryarsa ya kira line ta da sunan da yai saving number ta sweetheart ringing tai har sai da ta kusan yankewa sannan tai picking. “Hello Baby” “Na'am ykk zan dawo gida yanzu” “Okay sai ka iso i love you” “I love you too” Ya amsa mata yana maida numfashi. Sannan ya maida wayar aljihu ya nufo falon, har lokacin ba a bude dakin ba kuma be ji motsi ko alamar za a bude din ba hakan yasa shi jin sanyi a ransa sai hankalinsa ya fi karkarta da yarda cewar wata kila ta fita wani wajen ne? But wait idan ta fita ina Sadi? And me ya kawo motarsa a nan? Ganin ba shi da amsar tambayar yasa shi sake nufar kofar dakin da zimmar knocked sai dai kamin ya karasa aka bude kofar daga can ciki ga mamaki Sadi ya fito daga dakin sanye da shadda yellow hullarsa a hannu yana gyarata. Kamar hoto haka Sadi yai tsaye a gurin ganin Amnu, kamar yadda Aminu ma yai tsaye kamar an dasa shi a gurin sai dai hakan be hana shi murmushin mamaki ba. “I...na.. Mu...rja...” Ya tambaya maganar na fitowa daga bakinsa daker. A rikice Sadi ya nuna masa dakin daya fito a take gumi ya karyo masa. “Tana..... Ta... Na... Ci... Ki.... Al.... Al... Aljannunta.... Ne suka... Taso.. So... So... So” Murja kamar jira take tana jin haka ta buga wani mahaukacin ihu ta fadi kasa ta soma murje murje.... HALIMATU POV. Ban jidadin yadda na amsawa Abdallah cewar yes kaunar Aminu nake ba, bayan kuma ni kaina na san karya na fada na fada ne kawai cikin bacin rai sanadiyar maimaita min tambayar da yake ta yi, sai dai a yanzu ina jin cewar ko kallon banza be kamata ace ina yi ma Abdullah ba balle har na fada masa wata maganar marar dadi, na ji babu dadi sosai haka yasa na yanke shawarar kiransa idan na natsu na bashi hakuri, sai dai kuma ya cancanci na kira na bashi hakurin? Hakan ba janyo min wani abun ba? Idan kuma ban bashi hakurin ba zai iya daukar da gaske son Aminu nake, halin a yanzu ko sunansa bana son ji balle har a alakanta kalmar so da shi, no ba sai na kira shi ba indai Abdallah ne da zarar ya gama fushinsa ya sauka zai koma kamar komai be faru ba. Haka dai muka isa gida a napep da sake sake kala kala a raina, na kulla wannan na kwance wacan har na fita daga napep din. “Mai motar can fa tun dazun yake biye da mu” Mai nepep din ya fada yana fito mana da kayan mu, da na daga kaina sai na hango wata kafirar bakar mota mai bakin gilashi wacce ban taba ganin irinta a fili ba sai a fina finai, mai motar kamar ni yake jiran na dago na kalleshi sai ya sauke gilashin motar a hankali, me zan gani? Mutumen nan ne wanda na taba gani a lokacin da na farka a asibiti kafirin nan, wani irin faduwa gabana yai a take na nemi natsuwata na rasa. “Hasbiyallahu wani'imal wakeel” Na furta ina cigaba da kallonsa kamar yadda shi ma yake kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Na sake furtawa daga Aisha har Husna kallona suke kamin su kalleshi sai yai sauri daga gilashin motar yai ribas ya juya inda ya fito. “Kin san shi ne?” Mai Napep din ya tambaya. “No” “To Allah ya sawwake yanzu mutane abun tsoro ne, garkuwa ake da mutane ta ko'ina” Na dan tabe baki. “Allah na tuba to ni idan an yi garkuwa da ni me za a tsinta?” “Ai ba shi mutane suke dubawa ba, kuma ai akwai matsafa masu dauke mutane, sai dai kuma idan sonki yake” Na sake duban mai napep din da kyau kamin nai murmushi na girgiza masa kai. “Ni kan yanzu ai na girmi so” “Ta ina? Ga ki kyakkyawa da jini a jika? ” Daga ni har shi har kannen da muke tare dariya mukai, Maganarsa sai ta tuna min da wata maganar marar dadi da Aminu ya taba fada min. “Look at you duk kin yi wani muni kin tsufa..... ” Ajiyar zuciya na sauke na dauki wasu kayan na shiga da su cikin gida ni da Husna Aisha kuma ta tsaya sallamar mai napep din sarkin bargwanci. Na jidadin ganin Mama da nai duk kuwa da kasancewar na ganta jikin nata sai a hankali amman hakan be hanani jindadin ganin farincikina ba, ba ita kadai ba kowa a gidan ya jidadin dawowata musamman ma yarana wadanda suka rika tsalle kamar na shekara bana gidan, Amal ta zo jikina ta zauna tana ta zuba min shagwaba. ABDALLAH POV. Luma biyu yai ya ji kamar ba zai iya cin abinci ba sai ya aje spoon din ya kurba ruwan dake gabansa. “Lafiya kake yau?” Ya dago a hankali ya kalli Suwaiba sai ya amsa mata a hankali tare da tashi ya bar mata dinning. “Bana jin dadi ne” Da kallo ta bishi ta tabe baki. “Ai shine daidai da kai na san da ba haka nai maka ba ba zaka fita safgar wannan shegiyar Halimatun ba, amman yanzu da Abdulhamid ya san gaskiya ai dole ka kama kanka dan na san zai taka maka burki da wuri, tun da ku maza ba kunya ce da ku ba yanzu nan sai kace zaka aureta, idan anyi magana kace tausayinta kake to sannu sahabi.... ” Ta cigaba da cin abincinta ranta fes duk kuwa da kasancewar bata san makasudin bacin ran mijin nata ba, sai dai ta san baya rasa nasaba da abunda ta fadawa Abdulhamid domin a yadda ta ga ransa ya bace ta san ba zai bar maganar ba! Dakinsa ya shiga ya kwanta ya rasa abunda ke masa dadi, a duk lokacin da ya tuna maganar Hajiya ta gatangar da ta gina tsakanina da Halimatu sai yaji wani abu ya tokare masa zuciya, be tabbatar yana sonta da gaske ba sai a yanzu da yake jin kamar Hajiya na kokarin rabashi da ruhinsa ne. Ya rasa dalilin Hajiya na kin masa uzuri ya rasa dalilin hajiya na tsanar Halimatu tun daga lokacin da ta auri Abdulhamid, yes yasan tayi kuskure na auren Abdulhamid bayan kuma ta san yana sonta, amman ai itama mutun ce kamar kowa ko? Zata iya daidai zata iya akasin haka, then miyasa Hajiya ba zata kalli wannan tai mata uzuri ba? Ko da yake yanzu ba laifi Hajiya ba ne laifin Abdulhamid na yi mata maganar da nuna bacin ransa. Bayan kuma ba shi da wata hujja a yanzu domin da yana sonta kuma ta damu da ita da be sake ta da be juna mata baya ba. Hannunsa ya kai ya dafa zuciyarsa yana kara fadawa wani kogin tunanin. Wai yanzu duk wani abu da yake yi ma Halimatu janye zai yi? Ba zai sake mata komai ba kenan? Babu wata alaka da zata sake shiga tsakaninsu? Ya tambaya kansa yana jin wani irin shauki da son ganin fuskarta. ______________________ Anya Abdullahi zai iya jurewa? Da gaske Aljanun murja ne suka taso? Waye yake bibiyar Halimatu kuma a yanzu? 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣5️⃣ Kasa cewa komai yai  ya tsaya a gurin kamar an dasashi, Sadi kan sai gumi yake hadawa abun ka da marar gaskiya, Murja kuma na can dakinta tana aikin ihu kamar da gaske Aljanun ne suka ziyarce ta har da wani yare take shi ba yarbanci ba, ba kuma iyamuranci ba. “A kaita asibiti, no gurin malamai” Fadi ya fada wiki wiki da ido, sai Aminu yai masa murmushi tare da gyada masa kai alamar gamsuwa. “Za a kaita” Ya amsa masa sannan ya nufi dakinsa jikinsa babu kwari, saman gadonsa ya zauna sai ya rasa abunda zai fara tunani, korarsa da akai a gurin aiki ko kuma tararda dan'uwansa tare da matarsa? Kwantawa yai saman gadon yana ta kallon silin. “Aminu ka ji tsoro Allah abunda kake mana baka kyautawa, ka rika tunawa kana da yara kana da mata, ace magidanci kamar idan ya bar gida ba zai dawo ba sai karfe daya ko biyu na dare...?” “Ke Halima a nan gidana ne ina da yancin shigowa a lokacin da nake so na fita na lokacin da na ke so, ba ki isa ki saka min doka a gidana ba” “Ba doka nake son saka maka ba, abunda kake yi nake kokarin nuna maka illarsa, duk abunda kai wa matar wani sai an yi ma taka, kuma duk abunda kai wa yar wani sai an yi wa yarka....” “Idan iskancin kike so ni ban hana ki yi ba, ga ki ga guri har kya fada min wani wai sai an yi ma yar wani matar wani dan baki da hankali” “Allah ya tsare ni, ban aikata zina ina budurwa ba ba zan aikata da aurena ba, ga hakkin yayana ga na iyayena ga na mijina ga na ubangijina? Wallahi ba zan iya ba” Ya fada tana share hawayenta sannan ta tashi ta bar masa dakin. Tuna wannan yasa shi share hawayensa ya rumgume hannayensa a kirjinsa. A yau na mallakawa murja komai, ita ke saka masa duk dokar da tai mata, be isa ya kai 9 a waje ba, be isa ya dawo gidan ba tare da saninta ba, amman hakan be hana ta cin amanarsa ba. Abunda be taba mafarki ba, domin a lokacin da zai aureta sai da yai bincike mai karfi aka tabbatar masa da tarbiyarta sannan ya aureta, sannan ya yaba da shigarta da hankalinta shiyasa ya aureta ashe be tsira daga abunda yake gudu ba, kuma ta rasa wanda zata aikata da shi sai dan'uwansa uwa daya uba daya! Wani irin abu yaji ya tsaya masa a kirji ya danne masa numfashi har sai da yai saurin kifewa a saman gadon ya runtse ido sannan ya samu  sassauci. “Allah yasa ka gane kuskuren da kake aikatawa da wuri, ko dan yaranka..... ” Maganar Halimatu ta sake dawo masa. “Na gane Halimatu na gane......” Ya fada yana fashewa da kuka wasu hawaye masu zafi suna sauko masa. Kamar an tsikare shi sai ya zabura tai saurin tashi zaune. So da gaske Halimatu take da fada masa cewar Sadi yai ma Namra fyade? Sadi ya daka masa wuka har sau biyu kenan? Yayi saurin tashi zaune, ji yai babu wanda yake bukatar gani a yanzu kamar Halimatu da yayanta. Tashi yai ya fice daga gidan gaba daya, a bakin gate ya samu abun hawa ya fada masa unguwar su Halimatu, kamin su isa duk sai ya tsawalla kamar wanda ya shekara ba ga yaranba. Sai kuma yai rashin sa'a ya tarar bata gidan wai ta tafi dauko yaran daga School. Kai tsaye Scul din ya wuce a can ya sameta ta tana kokarin taron napep tana rike da hannun yaranta. Sai a lokacin yake jin rashin kyautawa ta ya zai barta ita kadai tana daukar responsibility ba yaransa bayan yana raye? Gaba daya sai jikinsa yai sanyi, karasa yai kusa da su, kallo daya tai masa ta dauke kai sai ya koma gaba Namra ya risina ya kai hannu ya shafa fuskarta yana murmushi. “Daddy ina wuni?” Kasa amsawa yai sai ya rumgume ta hawaye na sauko masa. Tun yana yi a hankali har ta kai mutane na kallonsa. “Miye haka? A cikin jama'a muke fa, ka sake ta gida zamu je” Sakinta yai ya dago kai yana kallon Halimatu wacce ke watsa masa wata uwar harara, kamin ya kai hannu ya shafa kan duka yayansa sannan ya mike tsaye ya share hawayensa, ita kuma taja yaranta sukai gaba, yana tsaye a bakin titin yana kallonsu har suka samu Napep suka shiga suka bar shi a gurin. Shi ma achaba ya hau ya dauki hanyar family house dinsu. Ko da be fada ba kana ganinsa kasan yana cikin tsakanin damuwa, kamar yadda mahaifiyarsa ta karanta a fuskarsa. Gashi ya shigo mata har dakin bachinta babu sallama balle gaisuwa. “Aminu lafiya kake?” A lokacin daya dago kansa sai hawaye ta gani a fuskarsa. “GOBENA Hajiya tunani nake yadda zata kara kasancewa....” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, miya faru kuma?” “Hajiya yanzu na gane, ba dan na rabu da Halimatu na rabu da arzikina ba, saboda na cutar da ita ne, hakkinta ba zai bar ni ba, samun irinta a duniyar nan sai an tona, kullum nasiha take min bata tana nuna min gazawarta, da gangan Hajiya da gangan nake kauracewa Halimatu sai nai wata uku hudu ban neme ta ba kuma a haka take hakuri da ni......” Ya fada yana fashewa da kuka kamar mace har zaman kujerar ya gagare shi sai da ya sauko kasa. Sai a yanzu yake jin wani irin zafi da bakincikin abunda Sadi yai ma yarsa da kuma matarsa ashe akwai zafi wani ya kusanci matarka, sai yanzu yasan zafin da uba yake ji idan aka lalata masa Y'a. “Aminu ka fada min abunda yake faruwa mana, ka gada min hankali” “Hajiya yau an kore ni gurin aiki... Amman bashi ya fi bata min rai kamar kama Sadi da nai da Matata Murja.... ” Idan akwai abunda yafi sakin baki da mamaki sai da Hajiya ta yi shi. “Kasan me kake fada kuwa Aminu?....” A nan labarta mata komai idonsa ko gani basa yi daidai saboda hawaye. A take Hajiya ta saka kuka. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yanzu Sadi da matarsa da yaransa zai yi matar dan'uwansa haka?” “Hajiya kin tuna lokacin da na saki Halimatu saboda ta fada min Sadi yai ma Namra fyade? Daga ni har ke ba mu tsaya mun yi tunani ba....” Hajiya ta dafe zuciyarta tana hawaye. “Indai har haka ne Sadi ba zai gama lafiya ba, wane irin da na haifa?” A wunin ranar daga Hajiya har Aminu wuni sukai cikin jimami da damuwa, sai da Dare Sadi ya shigo gidan shi ma dan Hajiya ta kira shi ne, har lokacin ba shi da natsuwa da kwanciyar hankali, Hajiya ta rufe da fada tana kuka, amman sai kokarin kare kansa yake. “Hajiya Wallahi Aljanunta ne suka gaso kuma tana fisge fisge shiyasa na kaita daki na kwantar da ita” “Kaji tsiron Allah Sadi idan babu duniya akwai kiyamar Allah, wace irin lalacewa ace kana tare da matar aure mai auren ma matar yayanka? Bayan kai ma kanka kana da aure da yara? Ko ka amsa ka aikata ko kar amsa wannan maganar zata tsaya a tsakaninmu daga ni sai kai sai Aminu, ba zamu fitar da wannan sirrin ba” Duk wani abu da Hajiya ke fada, Aminu dai be ce uffan ba, kansa n kasa har sai da Sadi zai tashi sannan ya dago ya kalleshi. “Tun yaushe kuke tare?” Jimmmmm yai kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya ce. “Tun kamin ka aureta, class mate dita ce” “Allah yai maka yadda kai min” Ya fada masa sannan ya mike ya fice daga dakin ya bar su daga Sadi sai Hajiya. HALIMATU POV. Tsawon wata uku kenan ban sake saka Abdallah a ido na ba, hakan kuma ba karamin saka ni yai a damuwa ba, na rubuta masa sakon karta kwana na bashi hakuri amman be maido min da amsa ba, na kira wayarsa several times be yi picking ba. Ba zan iya zuwa gidansa saboda na bashi hakurin abunda ya faru ba, sai dai ban abunda zan masa da zai saka ya sauko daga fushin da yake da ni ba, a iya zamana da Abdallah be taba fushi da ni na tsawon lokaci haka ba, ko da ban bashi hakuri ba yana saukowa da kansa balle har na bashi hakuri. Da kaina na zauna ina ta tunani da tariyo abunda ya faru so nake na gane idan maganar da na fada masa mai zafi ce sosai da har zata saka ya gujeni haka. Amman kuma ai na huta da shi, ni da nake neman maraba ma? Dan ya nesance ni a yanzu ai na huta ko? Wata zuciyar ta aika min da tambaya, a maimakon na jidadi sai na ji akasin hakan, wata kila saboda na dan saba da shi ne shiyasa na ji babu dadi a yanzu, wata kila kuma saboda abunda na fada masa ne yasa nake jin babu dadi, haka dai nake ta sake sake na ni kadai na kulla wannan na wance wacan.    Yau ma after na shiryawa yarana sun tafi school na shirya na fito da zimmar leka gidan kawata Hajara wacce na dade ban ziyarce ba, a yau can nake son zuwa yau so nake ba bude nata cikina ina son na ji irin shawarar da zata ba ni ina son na ji yadda zata kalli abun. Na yi kyau matuka ni kaina na san na yi kyau domin bakar abaya ce a jikina wacce take yi ma ko wace mace kyau, gashi na tsirka da jan mayafi, sam ba zaka gan ni kace Halimatu bace domin na rame sosai ni kaina ina ji a jikina domin yanzu bana jin nauyin jikin kamar da kusan dukan tufafina sun min yawa. Napep na tara na shiga na fada masa inda zai kaini ina cikin napep din ina tunani ban san mun isa unguwar ba har sai da mai napep din ya tambayi inda zai sauke ni. “Idan ka dan kara gaba kadan ya isa” Na fada masa ina kallon wata motar da nake kyautata zaton mu take bibiya, ko na nace ni domin tun daga lokacin da nai arba da wannan mutumen ba kasafai bake fita ban ga mota tana bibiyata ba, kuma ba kalar mota daya ba, wani lokacin zai sauke gilashin motar ya kalleni amman ba zai ce min uffan ba, wani lokacin kuma ta cikin motar yake bibiyata, tun abun na bani tsoro har na fara sabawa, ban san mi yake nema a gareni ba, a iya sanina ban yi ma kowa komai ba balle ace wani ya saka ni a gaba dan ya cutar da ni. Bayan na biya nai napep din na tura gate din gidan na shiga sai da muka gaisa da mai gadin sannan na nufi cikin gidan.   Na jidadin tararda ita ba tare da kowa ba, domin ko mijinta ya fita aiki balle kuma yara da sun tafi school. Tana ganina ta washe hakora “Yau garinmu inji maki baki” Da dariya na zauna saman cushion muka gaisa sai ta tashi ta hado min abun karyawa, ban musa ba na karba daman da safen nan koko kawai na sha, sai da na ji na koshi sannan muka dauko labaran duniya har take min zancen komawa makaranta na cigaba da karatuna. “Ni yanzu ba wani karatu dake gabana, karatun da nai ya isheni aikin nake son samu, na dogara da kaina iyeyena ma suna bukatar taimako na ga yara a gabana ga kanena ga ni ni kaina, kuma kin san karatu dole sai da wanda ya tsaya maka...” Ya janyo fillon kujera ta rumgume tana kallona. “Zan tsaya miki ki yi karatu Halimatu, ko nawa ake kashewa zan kashe miki so nake ki yi karatu ki kai matakin da ko aiki zaki samu ba karami zaki samu ba sai babba wanda zai zama na har wasu ma'aikatan a karkashinki suke, ya zamana kina iya daukar nauyin yan'uwanki da ke kanki da iyayenki da kuma yaranki” “Thanks for the opportunity amman har ga Allah a yanzu bana sha'awar karatu bana jin ma kwakwalwata zata iya daukar wani abu a yanzu” “To aure kike so?” “Bana da kudirin aure a yanzu Hajara, kin fi kowa sanin irin kalubalen da nake fuskanta a rayuwar aure, kwata kwata Yanzu aure baya burgeni, aiki dai nake son samu saboda na dogara da kaina domin bana da mai taimaka min a yanzu, Abdallah da nakr ganin yana dauke min wani nauyi shima ya fara guduna” Fuskar mamaki tai “Kamar ya?” Ban rage ba ban kara ba daga abunda ya faru tsakanina da shi wanda nake ganin shine silar fushin da yake da ni. “A gaskiya baki kyauta ba, amman shi kuma ya dauka da zafi” “Na san ban kyauta ba, tun daga lokacin abun ke ta damuna har yanzu na ta masa sako na ta kiranshi amman be daga ba be kuma maido min da amsa ba, Wallahi abun yana da damuna” Na fada idanuwa na taf da hawaye. “Kina son Abdallah Halimatu....” Wani kallo na watsa mata a kaikaice. “Ko ki yarda ko karki yarda son Abdallah kike Halimatu kuma kin yi kuskure tun farko da kika auri Abdulhamid bayan kin san Abdallah yana sonki ga kuma tarin kyautatawar da yai ta miki, yanzu gashi zaki cutar da kanki” “No ba ki gane ba ne, ba son Abdallah nake ba” “To miyasa kike kuka saboda ya kaurace miki?” Na kai hannu na share hawayen da suka zubo min. “Ai ya kyautata min da yawa ko? So ya kamata na ji babu dadi idan ya kwaurace min ko?” “Hakan be isa ya saki a damuwa ba, akwai son Abdallah a rayuwarki wata kila ba ki sani ba, wata kila kuma kina boyewa ne kawai, so abunda nake ganin yafi kije kai tsaye ki same ni a gidansa ai ba zai kyale ki a can ba, ki bashi hakuri idan ki kai hakan kin wanke kanki” “Kina ganin idan naje matarsa ba zata zargi wani abu ba?” “Ke fa jininsa ce Halimatu, taya matarsa zata yanke alakarku? Ke wai ni yar a manta ma ban fada miki ba kinji Aminu ya saki matarsa?” “Haka Asma'u makociyata take fada min a chat, ko me hada su kuma?” Hajara ta tabe baki. “Me zai hada su kuwa ban da bakin halinsa, wace macen ce zata dauki abunda kike dauka? Ai babu macen da zata iya zama da Aminu” Na yi murmushi ina tuna lokacin da yake ce min wai babu namijin da zai iya zama da ni sai shi saboda bakin halina da sa'idon da nake masa. “Wata kila shiyasa ya fara munafurci, kin ga yadda yake kula da yaran nan a yanzu kamar ya lashe su? Wallahi idan ya gan ni har wani sunsun da kai yake kamar mazuru” “To ko so yake ya dawo dai.... ” Na tofar da yawun bakin. “Allah ya kiyaye haba Hajara ai dai kya min fatar kwarai ko? Wallahi ni yanzu ko a kafa aka daura min Aminu ba zam iya jansa ba, ke idan na ganshi har wani tashin zuciya nake ji” Na fada ina yatsina fuska sai Hajara ta saka dariya. “Balle ya ga kin yi slim kin yi kyau abunki Ma-sha-Allah” Mun dade muna fira da ita kamin na bijiro mata da zancen mutumen nan da ke bibiyata, ita ma kanta ga tsorata da lamarin har ta ce mai reporting ma yan sanda saboda gudun abunda zaije ya dawo, kuma ban ki ta taba domin dan'adam abun tsoro ne a yanzu. Na dauki shawararta na zuwa bawa Abdallah hakuri dan haka daga gidanta sai na wuce gidansa kai tsaye da kwarin guiwa na. Na dade ina knocked din kofar falon kamin matarsa Suwaiba ta bude min, muna hada ido sai yanayinta ya sauya. “Ah ah ahhh Abun kuma yanzu har cikin gida Haba Halimatu?” Ina ta tunin abunda zan fada mata sai na ji muryar Abdallah yana amsa mata. “Ni nace ta zo....” Sakin kofar tai wanda hakan ya bani damar shigowa cikin falon, sai na hango shi zaune saman sofa sanye da Jallabiya laptop a jikinsa da alama wani aikin yake. Daga inda nake nai tsaye na kasa cewa komai sai ya aje laptop din ya nufo ya ratsa gefena ya fito daga falon, sai nima na juya na fice a harabar gidan muka tsaya ni da shi, yana ta kallona kamar zai cinye ni, ni kuma na gagara ce masa komai na gagara daga ido na kalleshi kwarjinsa da kimarsa ta cika min ido ga wani uban faduwar gaba da nake ji kamar mai jin tsoro. “Kin lalata komai Halimatu, kin aikata kuskure, taya zaki auri Abdulhamid bayan kin san ina sonki? Why? Saboda ki musguna min? Haka Hajiyata ta fada min, kin san me? Da Hajiya ta fi kowa son ki saboda ina sonki kuma gana ganin kamar kina so na, daga lokacin da kika ja ra'ayi Abdulhamid a kanki sai ta lamarin ya lalace, gashi yanzu aurensa be haifa miki da mai ido ba, kuma ya haifar mana da matsala gaba dayan mu, baki tunani idan za ki yi abu Halimatu baki tunani.... ” Ya fada yana hada duka hannayensa ya daki kaina. Dagowa nai na kalleshi idona taf da hawaye zan yi magana ya tari numfashina. “Sai kuka da an miki abu sai kuka.. ” Yayi saurin juyawa sai kuma ya juyo. “Ya akai? Miyasa kika zo nan?” Na fara matsar yatsuna ina hawaye. “Zuwa nai na baka hakuri akan abunda na fada maka a asibiti wanda ya saka kake fushi da ni....” “Yanzu kin fara jin son na a cikin ranki? Shiyasa har kika damu da fushin da nake da ke? Bayan komai ya lalace?” Ya juya ya fara tafiya. “Ka yi hakuri dan Allah Wallahi ba abunda ke raina kenan ba” Juyowa yai ya kalleni “Ni bana fushi da ke ba zan iya fushi da ke ba....” Haka kawai ya fada min ya cigaba da tafiyarsa har ya shige cikin falon. Ni kuma na juyo hawaye wasu na bin wasu na fito daga cikin gidan, ina tafiya ina jin ana bina a baya a lokacin sa na waiga sai sake arba da fuskar mutumen nan da ya saba bibiyata. Faka motarsa yai ya fito ya miko min handkerchief. “Pls...” “Waye kai? Me kake nema a gurina? Idan ma sace ni za kai ni bani da wanda zai karbo ni, idan kuma yarana zaka sace ban da kudin karbo su” Murmushi na gani a kyakkyawar fuskarsa. “Zaki iya shiga motana na kai ki gida, sai ki aminta da ni” “Ba zan shiga ba, miye hadi n dake kai rista ni musulma” “Soyayya ai babu ruwanta da addini, haka dai aka fada min mai irin addinin suna da kirki da karanci ba kamar yadda na same ki ba” “Wani yayi amfani da hakuri na ya cutar da ni, wani yayi amfani da soyayyata ya cutar da ni, kai kuma kana son kai amfani da addinina ka cutar da ni, to ba zan yarda ba ban yi kowa komai ba ba zan yarda ayi ta cutar da ni ba” Ina fada masa haka na cigaba da tafiyata. “Idan cutar da ke na zo yi kar Allah ya bar ni da raina a yau” Tsayawa nai cak kamin ya juyo na kalleshi da mamaki. “Kai kuma daga ina?” Matsowa yai kusa da ni ya miko min hannunsa. “Sunana Abraham akwapo” Tsayawa nai kallon hannunsa sake sanye da manyan zobuna sai dai ba irin wadanda can ba ne na zinari wasu kala ne na dabam sai dai duka alphabet dinsu A ne. Sai kuma na kalli fuskarsa. “Ni musulma ce miyasa kake bibiyata? Zan kai report dinka a gurin police yau” “Okay” Ya juya ya shiga motarsa na yi zaton tafiya zai yi amman sai ya fito rike da wani kamin littafi yai rubutu akai ya mika min. “Sunana Abraham ga number motata nan da number wayata da address din gidana ko da sun bukaci gani na” Ni kan a tsaye da nake mamaki ya kusan kashe ni. “Waye kai....?” Sai yai murmushi ya saka hannayensa aljihu. “Za ki ba ni damar kasancewa abokinki?” Shiru da nai ban bashi amsa ba ban kuma daina masa kallon mamaki ba yasa shi sake sakar min murmushi. “Ina mika kyakkyawar gaisuwata a gurin yaranki” Sannan ya shiga motarsa yai mata key ya bar ni a gurin tsaye da mamaki.... _____________ Wake irin tunanin da na ke 🤔 7/21/21, 10:45 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣6️⃣ Na kasa jefarda takardar kuma na kasa fadawa kowa cewar ya bani takardar kamar yadda na kasa fadawa yan sanda. Shi kuma be fasa chusa kansa a cikina ba, har kara ma da bibiyata kawai yake amman a yanzu har yarana yake yi ma siyayya ta kudi mai yawa ya kai musu a scul a gida kuma ya aiko min da ita, a kullum ina fargabar idan Mama ta tambayi wanene shi wa zan fada mata ba? Bayan karyar da nai mata cewar wani ne dana hadu da shi yake min haka yai ma su Namra, amman idan aka samu akasi yarana ko kuma Mama da kanta ta ganshi fa? Duk wanda ya gan ni da kafiri zai yi mamaki abunda ya hada ni da shi ina diyar musulmai. Sai dai a yadda na fahimta kamar shima yana gudun mutane domin baya min magana a inda yakr ganin jama'a da yawa, sai idan ina a kebance kamar idan zan hau napep ko na sauka ko zanje wani gurin sai kuma da dare zai aika yace ana min sallama. Duk kuwa da ban tana fitowa da sunan amsa sallamar da yake min ba, hakan be hana shi aiko min lokaci zuwa lokaci ba, kamar yadda yake yawan bibiyata yana rokon na saurareshi. Ni kuma na kasa saurarensa saboda bana jin aminci a tare da shi wata kila saboda ba addinin mu daya da shi ba oho, sai dai a yadda na lura yana da kamun kai da taka tsantsan da kuma natsuwa wacce ba ko a musulman mu ba kowa kake samu da wannan ba.   Ba ni da wata fargaba a yanzu sai ta abubuwa uku,wannan Abraham din sai kuma Aminu wanda shi ma ya saka ni a gaba da yawan bugo min waya da sunan zai gaisa da yayansa tun yana kira ina dagawa na bawa yaransa har ta kai yanzu idan ma ya kirani sai dai na mika musu wayar su su yi magana da shi, hakan kuma be hana idan ya kare magana da su yace su ba ni wayar idan ni kadai ce ko kuma da kanen sai na yanke kiran idan a gaban Mama ne kuma na kan dauka saboda ta gargade ni cewar na daina kin karbar wayarsa ko dan darajar yarana, ina yi mamata biyaya ne kawai saboda ina gudun bacin ranta gudun kar tace ban dauki shawararta ba, amman har ga Allah bana kaunar jin sunan Aminu ma balle jin muryarsa, shi kuma yanzu har wani zillon rashin kunya yake domin wani sa'in har cikin gida yake shigowa ya gaishe da Mama da Baba sannan ya fita, ga wata bakar al'ada da ya tsiro ta daukar yaran yana tafiya da su gidansa ko wani gurin daban su wuni can sai dare zai kawo su gida. Idan na nuna zan hana sai Mama tace min ba haka ba. Wani lokacin sai dai nai ta jin haushin a zuciyata kawai amman ban isa na nuna a fili ba saboda kar mama tace saboda ita nake yi.   Na tattara komai a yanzu na aje a gafe, babu da bukakata da damuwa kamar abu na ukun nan wato neman aiki, duk inda naji wata ma'aikata ko wani kamfani sai na mika takarduna, sannan na saka addu'a a gaba nai ta yi ko Allah zai saka a dace.! Bayan na gama sallah isha'i ina rike da wayata ina latse latsena kamshin turaren Abdallah yai min sallama kamin muryarsa ta daki dodon kunnena, a take na nemi natsuwata na rasa sai na ji duk na kwadaitu da son ganinsa fuskarsa a take na aje wayar na unkura ina gyara Hijab dina na mike tsaye ina juyowa sai nai arba da mutum, faduwar gaba ta same ni a lokacin wacce take yayin yin haka a duk lokacin da nai arba da Abdallah, abun ka da wacce ta rude sai na kasa komawa na zauna daman dakin babu kowa sai ni kadai da aljanuna idan ma ina da su, ratsawa nai gefensa na da zimmar na fita domin a bakin kofar yake tsaye ya zuba min idonsa kamar ya cinye ni, ban san yadda akai ba na kasa lura da kyau har na buga kaina da garun kofar a take goshina ya fara zogi ni kuma na saka hannu ina murzawa jikina na ta rawa kamar marar gaskiya, har lokacin be dauke idonsa daga kaina ba kuma be kauce daga kofar ba. A dole na koma na zauna saman kujerar da ke kusa da inda nai sallah, amman me sai na gagara samun natsuwa domin jikina na bani cewar idonsa na kaina. Sai da ya ji muryar Inna ta doso dakin tana masa lale marhabun sannan ya karaso cikin dakin ya zauna a saman carpet din da na tashi wanda nai sallah, idonsa ya koma gurin kafafauwa ya sakar musu ido kamar mai son tantance abu, ni kau na daga abuna sama na dora saman kujera na lullube su da hijab, sai kallon ya koma gurin hannayena, su ma na nade abu cikin hijab din sannan ya kalli Inna wacce ta shigo ta zauna. “Abdallah yaushe rabonka da gidan nan” “Bana samun zama ne sosai yanzu shiyasa aikin yana min yawa, ya gida ya kwana biyu?” “Lafiya kalau ya gurin su Hajiya?” “Tana lafiya tana gaishe ku” “Muna amsawa mun kwana biyu ba muje ba itama bata zo ba, ina Suwaiba da su Inteesar?” “Duka suna lafiya, na ga Baba a waje ai mun gaisa ina Mama?” “Ta dan zagaya makota jikin ne idan yai mata nauyi sai ta zagaya saboda asibiti ma ance ta rika dan takawa tana shiga mutane” “Allah sarki gidan yau ku ne akwai a ciki? Duk ina yan matan Baba?” “Wallahi duk sun tafi wankin Amaryar da ake nan makota, kawarsu ce take aure kuma ta zama kamar yar gidan nan har yaran duk suna can shiyasa ka ga gidan babu kowa” “Okay” Ya amsa yana maida dubansa gurin wayata wacce ke kusa da shi, kamar na kai hannu na dauka sai ganin nai ya dauki wayar yana ta shafa screen din domin tana da password ba zai iya bude ta ba, ganin shiru yayi yawa yasa Inna ta tashi ta bar mana dakin daga ni sai shi sai fankar sama da ke ta aiki ba mu iska kasancewar akwai nepa. “Zan nemawa su Namra transfer zuwa government schools” Ya fada ba tare da ya kalleni ba, kamar yasan zan tambayi dalili sai ya ce. “Saboda na san ba za ki iya cigaba da biya musu school fees a wannan private school ba” Har ga Allah na ji babu dadi amman ban nuna masa ba, domin ban san dalilinsa na yin hakan ba, wata kila ya gaji da taimakon da yake ba ni ne a yanzu ganin kamar ba zan taba aurensa ba. “Allah yasa hakan shi ya fi alheri” Na fada da muryata da ke nuna lamarin be min dadi ba. Sai ya kalle ni kamar yana mamakin jin haka daga bakina. “Ba zaki tambayi miyasa nai haka ba? Ba ki damu ki san dalili ba?” “A lokaci da ka shige musu gaba har suka samu karatu a wannan makarantar ban tambayi dalili ba saia yanzu da zaka canja musu? Ka yi min alheri da yawa Abdallah wanda ni na san har na mutu ba zan taba iya biyanka shi ba.... Ba zan zarge ka da komai ba” Mikewa yai tsaye ya jefo min wayata tare da jan tsaki. “Ba ki hadu ba Halima....” Yana fadar hakan ya fice, ban ce masa komai ba na fiddo hannuna dake cikin hijab na dauki wayata, ko da na kunna sai ganin screen din nai ya tsaga. Hakan da Abdallah yai be karamin komai ba sai kuzarin neman na kaina, kamin aikin ya samu ina son mai amfani da kudin hannuna na fara sa'a domin zaman banza ba nawa ba ne a yanzu. Kwana uku da faruwar hakan ya kawo min takardar transfer dinsu har gida, a ranar Mama take tambayata dalilinsa na yin hakan nima na ce mata ban sani ba, sai da na labarta abunda ya faru asibiti. “A duk yadda akai ba a iya yanke alakarki da Aminu saboda yaya sun shiga tsakaninku yaran har hudu ba ko daya ba” “Za a iya yankewa mana Mama, Aminu ai be damu da yaran nan ba tun suna gidansa balle yanzu da ba sa tare da su” “Ai yanzu ne yake sanin darajarsu Halimatu, ba ki lura da yadda Aminu ya canja ba? Ba ki lura da irin kulawar da yake bawa yaransa ba?” Hafiza ta tsire baki. “Ni fa ina ganin kamar so yake yace Halimatu ta koma masa...” Ni ko nai karaf na ce. “Allah ya kiyeye gatari da saran shuka, ni da Aminu a lahira idan na shiga aljanna wata kila na hango shi a bakin kofar wuta, dan yana da wahala idan Allaj ba kona shi ba akan zalincin da yai min” “Halimatu kenan kina kara girma amman har yanzu hankali ya ki zuwa miki, kin kasa duban yaran dake gabanki ko dan su ai kya kyautata wasu kalaman akan mahaifinsu” “Mama har yanzu ban gama warkewa daga tabun Aminu ba, saboda shi na samu kaina a duk wani hali da nake ciki a yanzu, mutumen da zai dube ni ya kira ni da mummuna yace ina ta haifa masa yara saboda na tsufar da shi, ya sake ni saboda na fada masa cewar dan'uwansa yana neman lalata yarsa? Sannan yai taraiya da kawata? Haba mama wace irin mutunci kike tunani zai shiga tsakani na da Aminu? Ni kadai na san irin kalubane da na fuskanta a gidansa” Na karasa idananuwana na cika da kwalla, sannan na unkura na tashi na nufi inda jakata take na dauka daman da shirina na fito. “Mama idan ko Hafiza idan su Namra sun dawo daga scul ki fada musu ba za su sake zuwa ba daga yau, saboda kar su saka rai, zan bawa Aisha kudin Napep ta je ta dauko su dan nasan kamin na dawo lokacin dawowarsu daga school yayi” “To Allah ya bada sa'a ya tsare” Cewar Mama. Hafiza kuma ta kalleni daga sama har kasa tace “Allah yasa mai kamfanin yana kallonki yace ya samu mata” Ni kuma nai dariya. “Ai na girmi aure yanzu, ko nawa za a bani ba zan iya aure a yanzu ba, mun dai yi kuma gama da yarda Allah” “Kara dai da kika ce da yardar Allah, aure ai shine martabar mace, kuma kin san ba ido zan saka miki kina zama a gida ba ko? Mutanen unguwa ma sai su yi ta yi da ke, musamman idan kika fara aikin nan wani ba tunanin alheri zai miki ba, yanzu sai ki ji an fara tsegumi, daman can ana lissafa mu na yan mata wai mun ki aurarda su.... ” Mama ta tari numfashina tana ta kora bayani, ni dai kan uffan ban sake cewa ba, nai musu sallama na fice, har nai addu'a fita daga gida, ban daina mamaki da sake sake a raina ba, na kin ganin laifin da Aminu da Mama take da kokarin wankeshi a idanuwana, ga kuma zancen aure da take kokarin bijiro min da shi, anya ya gama da warke daga radadin azabar kunar da Abdulhamid da Aminu suka min da har zan yi tunanin aure? Ko da ma ace yana gabana ballantana yanzu da bana sha'awarsa.   Na isa gurin da zanje cikin lokaci domin na tsarawa kaina isa gurin da misalin tara na safe sai ga ni na isa takwas da rabi da yan dakiku a kai, duk kuwa da kasancewar babu wanda ya san da zuwana a kamfanin hasalima ni kaina ban san mai kamfanin ba ban san tsari da dokokin kamfanin ba amman ina kyautata zaton a lokacin ne za a samu duk wani wanda ake tsammani samu a kamfani. Kamar dai ko wane kamfani shi ma wannan yana da masu gadi dake sanye da uniform mai sunan kamfanin wato Crown Company Limited. Sai dai ba su kadai ba har da Sojoji a gurin.              Sai da suka auna jikina idan bana dauke da bom sannan suka ba ni damar shiga ciki, ba ni kadai suke yi wa haka ba, har masu mota sai sun bude musu bayan mota sun duba sannan su basu damar wuce ciki. A iya zamana garin gusau ban taba shiga cikin kamfanin ba, to me ma zai kaini tun da ba siye ko siyarwa zan yi ba, a yanzu ma dan ina neman aiki ne kamar yadda nake cewar kamfanin yana neman ma'aikata yan boko wadanda za su iya communicating da wasu mutanen amman da yalshen nasara wato turanci. Sai dai ban san inda ake bi a shiga kamfanin ba, domin na lura da kofar kamfanin ta kasu gida uku wasu na fita da shiga a ta farkon wasu a ta biyu wasu a ta uku, tsaye nai a gurin ina ta tunanin wacce zan shiga, ta farko haka zuciyata ta raya min dan haka na nufi kofar gadan gadan, a nan ma wasu matsaran ne rike da abun awonsu kamar dai na bakin gate. Sai dai da alama su basa barin mutum ya shiga sai idan ya nuna musu wata yar takardar wacce nake ganin kowa yana ba su su duba kamin su barshi ya shiga ciki. Hakan yasa ban karasa a gurin ba sai na juyo na nufi kofar tsakiya wacce mutane suka fi fitowa a cikin, wani abun burgewa ma kofar ita take bude kanta sai jujjuyawa take gwanin sha'awa, ina kokarin kutsa kai na shiga cikin kamfanin na Abban Baby Namra ya fito daga ciki yana sanye da shadda mai ruwan madara, ba laifi na dan saki fuskata domin har ga Allah na yi nufin gaisheshi sai kawai na ga ya hade fuska kamar bakin hadari daman can fuskar tashi ba a washe take ba, balle yanzu da ganina yasa ya kara hade ta kamar yaga mala'ikan mutuwa. Hakan kuma be hana na mika masa gaisuwa ba, amman sai yai min banza ya wuce abun shi, a take na ji duk na muzanta domin akwai mutane a kofar kuma na san wasu sun ji gaisuwar da na mika masa. Sai kuma duk na ji haushin kaina, miyasa na gaishe shi tun da farko ma? Miyasa ban kyale shi ba na yi tafiyata? Why na nuna na sanshi ma? “Miya kawo ki nan?” Kamar daga sama na ji tambayarsa da wata bakar murya tashi, har daka min tsawa yake kamar wata yarshi. “Ban sani ba” Na fada cikin tsiwa ba tare da na kalleshi ba na cigaba da tafiyata ina jin haushin kaina, na gaishe shi ne saboda ina ganin kamar akwai mutunci a tsakani ko dan abokatar da ke tsakanin Baby Namra da Namra, ko da yake daman daga ganinsa ba zai yi mutunci ba sai wani jijji da kai sai kace shi yafi kowa arziki a gari, Allah kadai ya san abunda ya kawo shi kamfani ma wata kila shi ma wata alfamar ya zo nema amman sai son nuna isa. “Wai miya kawo ki nan” Na fada a fili ina tsire baki har wani namijin da ke reception din ya dago ya kalleni. “Na'am....” Sai na dan saki fuskata nai masa murmushi. “Sannu dai Malam daman na ji kamar ance kamfanin ku yana neman ma'aikata” “Eh amman ba zuwa ake ba, ta email ake turo mana sako” “Minene mail dinku?” Ya fada min sannan na sake ce masa. “Sai dai matsalar ban taba zuwa kamfanin ba, ban kuma san tsare tsaren kamfanin ba ban san mi kamfanin yake ba” “Kamfanin mu yana siye da siyar da zinari tare da narkawar da kuma saffarashi ta hanyar yin abun wuya dan kulleni ko kuma wani abun na kayan ado na jiki ko na riguna” “Na gode sosai, ta mail din zan tura cv na?” “Yes idan sun duba suka ga kin cancanta za a kira sai ki zo” “Na gode” Na fada masa ina dariya. “Your welcome.” Tare da murmushi as respond. Ni kuma na jiyo na fito daga kamfanin, abun ka damai salo sai da nai ma security guard din sallama sannan na kama hanya, ban yi wata tafiya mai nisa ba na hango Kabir zaune a gafen hanya tufafin jikinsa sun yi datti ga surar kansa ta taru gaba daya ya soma canjawa ga wani abun datti da jikinsa yai. Karasa gurinsa nai da sauri ina kiran sunansa sai ya dago kansa da sauri ya kalleni ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Hannu na saka a jakata na dauko dubu biyu na mika masa, be karba ba ba kuma yi min alamar zai karba ba, hakan yasa na risina na aje masa kudin na soma tafiya ina hawaye ina waigensa, har na tari napep na shiga be daina kallona ba kuma be kai hannu ya dauki kudin ba. Gaba daya rayuwarsa ta baya sai ta dawo min sabuwa, Kabir mutum ne mai tsafta ga far'a da son mutane, musamman ni yana kula da ni yana nuna min kauna, duk kuwa da yake haramtacciyar kauna na nemana bayan yasan ina da aure. Na fi alakanta ganin da nai a haka da rashin mahaifiya a raye domin na tabbatar da ace mahaifiyarsa tana raye ba zata bar danta a haka ba, domin ba duka yake ba balle ace ana gudunsa ba zagi yake ba, kusan sun ta haukar nan ta same shi ko magana baya yi. Wallahi har na isa gida hawaye ba su daina zubar min ba, sai da zan fitaa napep din sannan na share hawayena na sallame shi na shiga gida, ashe wani kukan zan tarar a gidan mu, na shiga n samu hankalin kowa a tashe, ka rasa wanda zai fada min cewar Amal ta samu hatsari. “Wai miya faru ne?” Na tambaya ganin kowa yana ta bina da kallo. “Amal ta samu hatsari” Inna ta fada min muryarta a hankali. “Ko dai ta mutu? Ku fada min?” “Ba mutuwa tai ba tana asibiti ma” Hafiza ta amsa min. “Garin ya ta samu hatsarin?” “Aisha taje daukarsu daga school sai ta tarar wai Aminu ya dauke su, sai ga kanwarsa ta zo yanzu ta fada mana wai Amal ta samu Hatsari, so yake ya kashe miki yayan” “Wace asibiti?” “Wai Yarima bakura yanzu yanzu ta bar gidan” Ko jakata ban aje ba na ja kanwata Husna muka nufi asibitin domin an fada min Mama da Aisha suna can sun tafi, haka muka shiga cikin asibitin mukai yawon duniya muka gama ba mu gane inda aka kwantar da Amal ba, daga karshe n yanke shawarar kiran Aminu a kan dole na tambaye shi, shi ma nai ta kiran wayarsa ya ki ya daga har yamma. Ga shi daga Mama har Aisha babu mai waya balle na kira su, hankali yai mugun tashi, wata zuciyar na ce min naje gidansu Hajiyarsa na tambaya sai kuma na ji kamar ba zan iya zuwa ba, ba hatsarin Amal ne kawai ya daga min hankali ba har da rashin ganin Adnan Aiman Namra da ban yi ba domin ance suna can tare da shi. “To ko kuma din sun samu hatsarin ne?” “Waya sanar mishi? Mu dai kar ya kai mana uwa ya halaka” “Wai ina ka kai min yara ne Aminu.....” Kamar hadin baki ina rufe baki sai ga kiransa ya shigo a wayata. Da sauri na daga jikin har ba ri yake. “Ina Amal din ina yarana...” “Muna nan Royal Hospital tare da su” Tsakanin akatse kiran wayar da mikewa ta tsaye bana jin ya ci dakika daya ma, cikin sauri na fita cikin gidan na isa titi na hau achaba na nufi asibiti. Sai da na sake kiransa na tambaye shi gurin sannan na karasa, a waje na samu Mama da Hajiyarsa suna zaune kamar abun arziki, Hajiyarsa na ganina ta taso ta tare ni da yar far'arta ni kam ko kula ta ban yi ba na tura dakin na shiga. Daga Aiman har Adnan da Namra da Aminu da kuma Aisha suna cikin dakin, Amal na kwance an saka mata bandeji akai sannan an saka mata wani karfe a baki an kware bakin ga halshenta da dinki. “Miya same ta me kai mata?” Na tambaya a tsawace ina kallonsa. Sai ya kalleni a sanyaye ya kasa ce min komai. Sai mahaifiyarsa ce ta amsa min. “Ya dauko su daga Scul ne yana kokarin tsallaka titi da su sai wani mai Napep ya hade Amal” “Momi kuma halshenta ya cire yanzu aka dinke mata shi..... ” Aiman ya karasa mata, ban san lokacin da na kalli Amal ba na sake kallon Aminu ya ce. “Kaga abunda ka ja min a gurin ya ko? Miya kaika daukar min yara?” “Mhaifinsu ne ni Halima ki rika tunawa da wannan... ” Ya fada ido raurau kamar zai fashe da kuka. “Sai yanzu ka san kai mahaifinsu ne? Sai yanxu kasan su din yayanka ne?....” “Haba Halimatu” Mahaifiyarsa ta tari numfashinta sai yai saurin daga mata hannu. “Barta ta fadi duk abunda take son fada Hajiya...” Wannan karon nuna shi nai da yatsa. “Ba fada kawai zan yi ba, gargadin ka zan yi akan yarana? Karka sake kula su ko kallonsu karka sake yi balle har ka dauke zuwa wani gurin karka sake nuna hada jini da ni...” “Ba zan yi abunda zai jefasu a matsala ba, abunda ya faru kaddara ce wacce ko wane dan'adam be isa ya wuce ta ba, kuma ina son ki rika tunawa cewar har gobe ni mijinki ne domin akwai yaya a tsakanin mu kuma ba a san abunda gaba zata haifar ba..... ” Taba sanin cewar kiyayya Aminu a zuciya ta kai min makura ba sai a wannan lokacin, tasss na wanke masa fuska da mari, mari daya be min ba har sai da na kara masa na biyu ina kokarin yin na uku Namra ta rike min hannu tana kuka sai ta rumgume Babanta. kasa cewa komai nai na fice daga dakin ina hawayen da ban san na minene ba. Ko da na fito ana ta kiraye kirayen sallah mutane waje kowa harama yake hakan yasa na nufi gurin da aka tanada dan aje motoci na zauna saman wani tebur da wasu maza suka tashi, a lokacin da na zauna sai na saka kaina cikin kafafuwan na rushe da sabon kuka, ji nai an zauna a saman tebur din da nake zaune da sauri na dago kaina na kalli gefena. Abraham ne sanye da blue T-shirt da facing cap black kamar yadda wandonsa yake, ko da wasa be kalli inda nake ba sai raba ido yake yana kallon harabar asibitin, Bluetooth din dake gefen kunnensa na ta balli da jar wuta. “Mi kike yiwa kuka?” Kawar dai nai wasu hawayen na sauko min. “Abubuwa da yawa da yawa da yawa... ” Na kasa daina fadin da yawa din har sai da ya kalleni. “Kamar me da me?” “Ba za su lissafu ba, idan na fita daga wannan na shiga wannan na gaji da rayuwar nan, na rasa yadda zan yi.... ” Ji nai ya rika hannuna... “I will be safe in this hand of mine, fada min matsalarki kuma ki fada min wanda ya saka ki a damuwa yanzu nan... I can give you another life..... ” Kamar an min shocking haka nai saurin fisge hannuna na mikewa tsaye ina kallonsa. Kamar yadda shi ma yake kallona. “I will take the pain,.... take it away....” Hannu na saka na share hawayena na nufi inda na fito da sauri na barshi a gurin zaune. #Team Gwarzo #Team Aminu #Team Abdallah #Team Abdulhamid #Team Kabir #Khadeeja Candy #GOBENA 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣7️⃣ ABDALLAH POV. After ya bar gidansu Halimatu ya koma office, sai dai ya kasa natsuwa da abunda Hajiya ta saka shi ya aikata kuma yana ganin be kyautawa Halimatu ba, yanzu dawainiya za tai mata yawa. Haka dai yai aikin da tunaninta a ransa kamar kullum bayan ya tashi office yai sallah masallacin asibitin sannan ya nufi gidan Hajiyarsa.   A yau harabar gidan ya tararda ita ta shinfida katuwar tabarma ita da yar aikinta suna ta fira. Kusa da inda suke zaune yai parking sannan ya fito daga cikin motar fuskarsa na nuna alamar akwai damuwa a tare da shi, tun kan ya karaso mai aiki ta miko masa gaisuwa sannan ta tashi ta koma cikin gidan. “Hajiya sannu da hutawa” “Yauwa” Ta amsawa tana kokarin kawarda fuskarta daga damuwarsa, shi kuma ya zauna kusa da ita sosai ya soma mata magana a hankali. “Hajiya da dai zaki duba maganar” “Maganar Halimatu ko? Ko gaisawa ba mu gama yi ba za ka dauko min zancenta” “Wallahi Hajiya tun daga lokacin da kika shaya mana katanga a tsakani sai na shiga cikin damuwa, ba aurenta zan yi ai Hajiya, bayan soyayya akwai tausayinta a zuciyata wanda shine makasodin karuwar soyayyarta a raina, hanani taimakonta da kika yi sai ya jefani cikin damuwa” “Indai kana neman albarka ka bi umarnina ka huta” “Amman Hajiya harda yaranta?” “Har da su....” Ta amsa masa da karfi alamar ta fusata sosai. Sai yai kasa da kansa, na wani lokacin kamin ya tashi ya saka takalminsa. “Hajiya zanje gida na huta, a tashi lafiya” Shine last word dinsa da ita sannan ya nufi motarsa ya shiga, a maimakon ya nufi gidan kamar yadda ya fada sai ya juyarda motarsa zuwa gidan iyayen Halimatu, hakuri yake son ya bata akan abunda ya faru dazun, if ba zai iya taimakonta a yanzu then ba shi da yancin fada mata bakar ji yake kamar yai mata wani aibi, daya bayan daya yake ta tunanin maganganun da yai da ita dazun a lokacin da yaje kai mata takardar transfer dinsu Namra, even if be fada mata bakar magana ya kamata yai mata wata maganar da hankalinta zai kwanta ba wai ya barta a cikin duhu ba za tai ta zarge zarge akansa hakan kuma ba karamin jefata zai yi magana damuwa ba.   Yana isa ya fita daga motar cike da gwarin guiwa ya nufi cikin gidan, sai da gaisa da kanenta sannan ya nufi dakin Mama. “Mama bata nan Halimatu ma bata nan sun tafi asibiti” Ya juyo yana kallon Ramla wacce ke masa maganar. “Waye ba lafiya?” “Amal ce aka ce ta samu accident on their way back to school” “Subhanallahi suna wace asibitin?” “Royal” Da sauri ya fice daga gidan be ko tsaya gaisawa da Inna ba, hankalinsa ya tashi sosai a take tausayin Halimatu ya kara kamashi. “Oh Allah.... ” Ya furta yana hannunsa na hagu saman kai. Tunanin halin da Halimatu take ciki yake gashi ba shi da halin taimaka mata a yanzu. Ya busar da iskar bakinsa yana girgiza kai.   Sai ya shiga cikin asibitin sannan ya ciro wayarsa ya kira Halimatu domin sanin a inda suke, a maimakon ya ji muryar Halimatu sai muryar Aisha ta daki dodon kunnensa, itace ta kwantanta masa inda suke ya karasa gurin da kuzarinsa, sai dai yana bude kofar dakin ya shiga idonsa sukai arba da Aminu sai wani rashin jindadi da walwala ya mamaye masa zuciya. Da Mama kawai ya gaisa sai Aisha da ta miko masa da gaisu, ko da wasa be kalli inda Aminu yake ba balle mahaifiyar Aminu da ke binsa da kallo. “Mama garin haka ya faru?” “Wallahi suna kokarin tsallaka titi ne wani mai achaba ya kade ta” “Subhanallahi” Ya karasa kusa da Amal yana dubata, sai Aiman ya zo ya kama hannunsa yana kiran Uncle. Dan murmushi kadan Abdallah yai masa domin yau babu walwala da far'a a tare da shi, hannu ya kai zai shafa kansa sai Aminu ya kai nasa hannun ya fisgo Aiman yana jin wani irin kishi da kiyayyar Abdallah na taso masa. Da gangan Abdallah yai masa wani shegen kallo na uku saura kwata, kamar zai yi masa dariyar abunda yai sai kuma ya dauke kai ya kalli Mama. “Allah ya saukewa Mama, ya kamata a saka ido sosai akan yaran nan, a samu wanda zai rika kaisu ya dauko su zai fi....” “Ba sai ka fada mana ba, can baya da ake kula da su kai kake kula da su ne? Ba yara ba ne mu da zaka fada mana abunda za mu yi” Aminu ya fada cikin fusata da daga murya. Ko da wasa Abdallah be kalli inda yake ba sai yai kamar be ji abunda yake fada ba, har sai da ya duba agogon hannunsa sannan yai masa wani kallon wulakanci, cikin wata irin isa da jin kai ya zuba hannayensa aljihu yana fadin. “Magana kake Malam Aminu... Ai ban lura da kai bane Aminu... Ashe kana gurin...” Maganar Abdallah bata karawa Aminu komai ba sai fusata da kawo zuci kusa har launin idonsa ya canja. “Ya za ayi ka lura da ni ka shigo hankalinka sama” Dariya Abdallah yai kamar ba komai sai kuma ya juya ya kalli Hajiya. “Ikon Allah ashe har da mahaifiyarka ma, Na shigo hankalina yana gurin Amal ne, ka san ni Allah ya saka min son yaya musamnan na Halimatu, to sannu Hajiya” Ya karasa yana da risinawa kamar da gatse, sannan ya kalli Mama still with murmushi a fuskarsa ya ce. “Mama zan fita sai na sake dawowo” Har Aminu ya bude baki ya sake fadar wani abun sai Hajiya tai masa hani da ido, hakan yasa shi hade maganar tare da bacin ransa. Abdallah ya nufi kofar fita yana kallon Aminu fuskarsa da murmushi mugunta. HALIMATU POV. Har na yi nisa sai kuma ya juyo na dawo gurin da yake da sauri, ban same shi a gurin ba hakan yasa na daga kaina na fara waige waige a gurin, kamar yasan shi nake nema sai ya dago min hannu daga can inda yake tsaye jikin wata kotuwar mota mai ruwan toka, kamar kar na karasa a inda yake, sai dai kuma akwai tarin tambayoyin da shi kadai zai amsa min ba, akwai abubuwan da nake son a banbance min, ina son ko wane launi da zanen kaddarata ya fito min a kalarsa, fari yai fari fes bakin yai baki wulik ta yadda zai fuskanci alkibila ta, ina son sanin wanene shi, a yau ina son nai ninkaya a duniyar tarihinsa, ina son na bazama a duniyar mafarkinsa a kaina na wanzu da burinsa da dalilin bibiyata da yake. “For the last time waye kai?” Ita ce tambayar da na fara aika masa tun kamim na isa daf da shi, ina ta yawo da idanuwa a fuskarsa. “Kina da bukatar hutu, ya kamata ki huta daga baya sai mu yi maganar” “Hutu? Hutu a duniyar macen da ta zo bauta? Hutu a rayuwar matar da manta da jindadi a rayuwarta? Fada min waye kai...!” Na fada da iyakar karfina har sai da ya soma tsorata ta yanayi na. “Sunana Abraham zauna a ciki sai mu yi magana” Ya fada yana bude min motarsa. “Sunanka baya min dadi ka daina maimaita min abunda na riga na haddace, kasan me nake nufi ka bani amsa kawai” “Idan na baki amsa ba zaki guje ni ba? Idan na fada miki waye ni ba zaki kyamace ni ba? Ki min alkawari cewar fada miki waye ni ba zai kawo kiyayya a tsakaninmu ba” Kallon mamaki nake masa. “No wait.... Why all this?” “Saboda na taba cutar da ke.... ” Har lokacin da yake maganar ban kawo komai a raina har sai da ya fadi kalmarsa ta karshe, zuciyarta ta fara raya min wani abun da ban taba mafarkin faruwarsa, lalabe na fara yi a duniyar tunani na, sautin wacan muryar nake hada da wannan, ina ta kokarin siffanta surar wacan da wannan, farat daya na nemi duniyar tunanin nawa na rasa, abubuwan da nake kokarin hadawa duk suka watse, sai na ji kan nawa kamar babu komai a ciki. Tafiya nai bayabaya kamar zan fadi sai yai saurin kai hannunsa zai kamani. “Dan.... Allah... Kar.. Ka... Taba... Ni... ” Na fada a wahale, wasu zafafan hawaye na sauko min, kamar yadda shi ma idanuwansa suka fara fitar da hawayen. “I can't hide it anymore yanzu, ba zan iya cewa ba da gangan na aikata ba, i rape you amman ban tsammanci zan dawo gareki ba, and on that very night da kika fada min kin samu cikina ban iya bachi ba a ranar saboda tunani da farinciki jin haka, daga lokacin na samu kaina da kaunar ki da kuma son rayuwa da ke, because my only hope and pray is na samu haihu kamin na mutu, na san zan iya mutu at any moment, but i want to make my parents proud, and ina son ko na mutu na bar carbon copy na....” Ya karasa muryarsa a dakishe saboda kuka. Risinawa nai gabansa na hade hannayena kamar neman gafara. “Why do you rape me? Mi mai maka?” Sai shi ma ya risino saitin fuskata yana share hawayensa. “I don't know why, na san dai mijinki na je nema a wannan daren.... ” Be gama maganar ba na mike tsaye na juyo tafiya na fara yi kamar mai ciwon kafafuwa, ko wace dagawa da takawa tana min nauyi, ga nauyin zuciya da ya danne min kirji har yana neman numfashina, ina tafe wasu hawaye masu zafi suna sauko min yawun bakin gaba daya ya canja gumi na ta karyo min har kasan marata murdawa yake, ina ta girgiza kai alamar a'a a'a ban daina ba har sai da na hango Abdallah ya fito daga cikin emergency sanye da shadda hannayensa duka biyu zube a aljihu... Tsayawa nai cak ina kallonsa, a yau ji nai kamar an halittoni ne kawai domin kallonsa, kaunarsa da tausayin kazafin da nai masa wanda har ya kai ni ga furta masa. Babu kamar kai Abdallah Wallahi babu irinka, mutumen da ya kasa nuna min kyama balle yayana, mutumen da ke bani taimako da kowace hanya, mutumen da idan nai gudu naje gunsa da bukatuna da damuwata zai tara hannayensa biyu ya karbe ni, na yi kuskure tabbas na aikata kuskure na barin mutune da ya dace da zama abokin rayuwata.... “Kullum cikin kuka kike please smile....” Maganarsa ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da nake, ashe ya karaso kusa da ni ya ban sani ba, fuskarsa da murmushi yana min alama da nai murmushi da yatsan hannunsa biyu kamar yadda murmushin yake a fuskarsa. Ban tana jin kaunarsa Abdallah sai yau ban taba jin kimar Abdallah ba sai yau ba, ban taba jinjina abunda yake min ba sai yau. Murmushin nai ina hawaye. “That's my girl....” Ya furta sannan ya maida hannun aljihu yai gaba abunsa, kamshin turarensa ya daki hancina har sai da ma lumshe idanuwana.... Na samu dakika biyar a haka kamin na juya ina kallon tafiyarsa cike da kaunarsa, wata kila jikinsa ne ya bashi cewa ina kallonsa sai ya juyo ya kalleni tare da aiko min da kyakkyawan murmushin wanda ya sanyaya min zuciya ji nai kamar na ruga na rumgume shi na fada masa cewar yau Ni Halimatu ina kaunarsa..... ___________ Ana wata ga wata, ina masu team Abraham ashe abun na ku.....🤐😥 Team Abdallah Team Gwarzo Za mu ga team din da yafi yawa 💃💃 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣8️⃣ Ban koma cikin dakin ba, a harabar da amsu jinya suke zama na samu butar wata matar nai alwala ta bani carpet nai sallah nai addu'a sannan na tashi na nufi wani bangare na asibiti gurin da aka kawata da furanni da kuma hasken fitulun kasancewar hudu ya fara. Tsaye nai a gurin ina ta kallon sama wata iska mai dadi na kadawa hawayen idona na ta aikinsu, babu abunda nake tunani sai Abdallah babu wanda nake hangowa a tare da ni sai a yanzu nake ganin dacewar tarairaya ta da Abdallah. “Uhmm na san na bata miki akan maganar da nai dazun amman iya gaskiyata nake fada, kina da damar da za ki ji haushi na ki tsaneni kuma zan jira har zuwa lokacin da zaki warke daga raunin da nai miki.... ” Juyowa nai a hankali na kalli Aminu wanda ke min maganar, sai a yanzu nake kallonsa da kyau ya rame sosai ya dan yi duhu. Dan murmushi nai na nufi wata karamar balcony na zauna sai shi ma ya tako ya zo ya zauna kusa da ni. Magana na fara yi ba tare da na kalle shi ba “A lokacin da nake budurwa idan mai ma mahaifiyata ko mahaifina wani aiki ko abunda ya faranta musu rai, sukan ce min Allah yai miki albarka ya baki miji na gari, ni kaina ina yawan addu'ar a sallah ta, a lokacin da ka zo kace kana so na ka aureni sai na ji cewar Allah ya amsa addu'o'inmu, bayan na yi haihuwar farko ka juya min baya, sai na fara addu'a ina ta fata da ganin kamar wata rana zaka daina, da nai haihuwa ta biyu sai na fara karaya, daga lokacin ne na dauka cewar aurenka yana cikin mummunar kaddarata, domin zama da mazinacin namiji ba abu ne mai sauki ba, kullum ina cikin fargaba, kullum ina cikin addu'a, kamin wani lokaci sai alakar auratayyarmu ta canja, na kuma maka kamar bakin maciji, idan nai kwaliya ina jiran ka dawo ka yaba min, ba zaka dawo ba sai tsakiyar dare, a maimakon idan ka kalleni kace na yi kyau sai ka fada min cewar siraran mata suna can suna can waje suna jiranka, a gabana kake yabon wasu mata a wayarka ko a tv saboda kawai na ji zafi, bayan ka san a lokacin da ka aureni ba haka nake ba, kyau jikina na daya daga cikin abunda ya dauki hankalinka har ka zo gurina ka nuna kana son aurena, a gidanka halitta ta canja Aminu saboda yayan da na haifa maka yasa jikina ya bude, halitta ta tashi daga budurwa zuwa matar aure, na bar iyayena na bar yan'uwa da kowa nawa na koma gidanka cikin yan'uwana da zama, amaimakon ka tausaya min ka mutunta ni sai na zama abar wulakantawa, kai ka yi min mahaifiyarka tai min yan'uwanka su yi min, ka dinga fada kana cewa na haifa maka yara da yawa zan tsofar da kai, hakan yasa na fara tunanin planning, kace na ciki kiba kai ba haka kake son mace ba ka fi son siririya, babu irin kudin da ban kashe ba akan nai slimming amman ban samu sa'a ba duka ka san saboda me? Saboda na faranta maka saboda na gyara rayuwar aurena, wani lokacin idan na unkura sai na ji kamar ba zan iya fita na bar yayana ba, hakan yasa na yarda aurenka yana cikin kaddarata, wasu akan jarabesu da kiyayyar uwar miji, ko yan'uwansa, wasu kishiya wasu mijin wasu yaya wasu rashin abinci wasu rashin lafiya, to sai aka jarrabe ni da abubuwada yawa, da gangan kake kin siyo mana abu mai dadi ko na marmari wanda za mu ci mu jidadi saboda kawai ka musgun min, ka dauki karan tsana ka dora min saboda kawai na aureka na haifa maka a yaya, a ranar da na tambaye ka 2k ka hana ni a ranar na ga alert dinka na turawa wata 30k+ ka tuna....?” Tun da na fara naganar yake hawaye har na kai aya, be iya bani amsar tambayar ba ko kallona sai ya kasa yi. Hannu na saka na share hawayena ba tare da sun bar zuba ba. “A kowa ce rayuwar aure akwai kalubale, na sani shiyasa na jure zama da kai a wacan lokacin. Amman wani abun mamaki a lokacin da kake ki na kaka nuna min kiyayya a lokacin ne Abdallah ya nuna yana so na, bashi kadai ba a duk inda na shiga maza basa dauke ido a kaina amman nawa mijin....” Kasa karawa nai saboda kukan da ya ci karfina. “Na yi miki abubuwa da yawa Halimatu, a lokacin ina jin kamar ke din matsala ce a rayuwata, ban gane muhimmancin ki ba sai bayan na rasu da ke, duk abunda zan fada miki a yanzu na san ba yarda za ki yi ba, amman Wallahi zuciyata babu wanda take mamari take kauna sai ke, na aikata babban kuskure na rabu da nai da ke, amman ko a wacan lokacin ina son ki Halima, kawai dai sherin zuciya ne da na shaidan. Amman a yanzu na canja Wallahi duk wani hali marar kyau nawa yanzu babu shi..... ” Sai a lokacin ya kalleni ya sauko daga zaunen da yake ya risina gabana. “Ki dubi girman Allah ki yafe min, ki duba yayanmu ko dan su ki yafe min, ni da Hajiya duka mun yi nadama, Wallahi babu daren da bana kukan rashinki Halima....” “Kana son na yafe maka?” Yayi saurin gyada min kai jikinsa har rawa yake kamar ba shi ba. “To ka maka dan'uwanka a kotu, ka tsaya da kafafuwanka har sai ka kwatowa yarka yancinta......” Ina fadar hakan na mike tsaye ina share hawaye na kauce daga gabansa na fara tafiya.... “Idan nai hakan zaki yafe min ki dawo ki zauna da ni da yayana?” Juyowa nai na kalleshi. “Wata kila dai zan iya yafe maka na goge sunanka daga bakar takardar da na rubuta shi, amman zancen zama aure a tsakanin ni da kai wannan har abada ne, sai dai wata mai sunana amman ba ni ba....” Ban tsaya jiran abunda zai fito daga bakinsa ba na nufi dakin da su Amal suke, har a lokacin Mama da Hajiyarsa suna dakin a zaune, kusa da Amal na karasa na zauna ina tambayar Aisha wayata. “Yaya Abdallah ya zo nan” “Eh mun gaisa da shi” Na fada ina yin kasa da idona saboda jan da sukai. “Halimatu ayi hakuri da rayuwa, mun san mun yi kuskure mun laifi amman a dubi girman Allah a yafe mana wallahi yanzu Aminu yayi nadama ......” Kaina na daga na kalli Hajiyar Aminu wacce ke maganar murya kasa kasa kamar za tai kuka, sai na kalli Mama nace. “A nan za ki kwana? Ko ni zan tsaya na kula da ita?” Sai Hajiyar Aminu tai karaf tace. “A a ni zan kwana nan kuje ku hutarwarku” Jin hakan yasa na mike tsaye nai musu sallama na fice. A daren ranar kasa bachi nai saboda tunanin rayuwar da nai a gidan Aminu, tabbas na fuskanci kalubale wanda ba ko wace mace ce zata iya jurewa ba. Da asuba bayan na yi sallah na dora da karatun qur'ane, misalin shida da yan mintuna na sha ruwa na koma bachi, bayan begen Abdallah da zuciyata ta kwanta da shi har da mafarkinsa sai da nai a bachin nan nawa na safe. Kiran waya ne ya farkar da ni duk kuwa da kasancewar bakuwar number ce hakan be hana ni dauka ba. Tun da sallamar matar ta daki dodon kunnena na gane mahaifiyar Aminu ce, ita ta fara miko min gaisuwa ni kuma na amsa mata da ina gajiya. Ta fada min wai kar a dafa komai tasa an kawo musu daga gida, ni dai da to kawai na amsa mata na aje wayar. Misalin tara na shirya na cikin bakar abaya kamar yadda na fi son sakata a duk tufafina na fita da zimmar idan na bar gidan Abdallah na je asibiti, so nake na tafi na bawa Abdallah hakuri kuma na fada masa labarin mutumen nan, and i got lucky na tarar ya shirya cikin kananan kaya na shirin zuwa office. And wani karin farincikin kuma shi ya bude min kofar da kansa yana rike da mug. “Ina kwana?” Na gaishe shi ina murmushi sai ya amsa min fuskarsa ba yaboba fallasa. “Ya kai?” “Zan iya shigowa magana nake son yin da kai.....” Daga can bayansa na jiyo muryar Suwaiba tana da fada. “To wannan abun ya wuce gona da iri, ya zama iskanci da cin fuska, kuma Wallahi ba zan dauka ba ke bakya ma jin munya bibiyar kanen tsohon mijinki... Kai tirr Halima kin yi abun kunya.... ” Da muryar da na san zata iya jiiyoni na ke fada masa cewar. “Ka ce tai hakuri na san babu dadi, amman babu abunda zai yanke alaka a tsakaninmu...” “Muje waje mu yi maganar” Shine abunda ya fito bakinsa, bakin nasa nake ta kallo kamin nai backwards na fita daga falon, wanda hakan ya bashi damar fitowa ya janyo kofar ya rufe. “Ya kai....” Yan yatsuna na fara murzawa sai hawaye. “Daman na zo ne na baka hakuri akan abunda ya faru..... ” “Ai na ce miki ya wuce ko? Ni ban rike ki da komai ba tun wacan karon na ce na yafe miki” “Ba shi ba, akan duka abubuwa da nai maka” “Na yafe miki Halimatu....” Na kalleshi cike da kaunarsa wacce ta mamaye qalbina take taraiya da numfashina a yanzu, kai na gyada masa alamar gamzu. “Kuma ina son ma fada maka wani abu....” Sai yai hanzarin katseni. “Bana son jin komai a yanzu pls” Na sake gyada kan a karo na biyu ina hade yawuna. “Amman magana ce mai muhimmanci akan maganar fyaden..... ” “Oh Please haba dai bana son jin komai a yanzu” “Shikenan, zan jira har zuwa lokacin da kake son ji, zan tafi amman dan Allah ka rika daukar wayata idan na kiraka kuma ka rika min reply idan ka ga sakona pls dan Allah” Be ce min uffan ba har na juyo na fara tafiya, sai jin mutum nai a gafena yana takawa tare da ni. “Dan Allah Halimatu ki cire komai a ranki, ki nemi aiki ko wata sana'a zaki iya tallafawa kanki ki rage damuwa kin ji? Ki cire kowa a ranki” Tsayawa nai na kalleshi. “Babu kowa a raina a yanzu, na cire komai na fahimci komai, babu wanda yake cikin raina Abdallah sai kai....” Kallon mamaki yake min is like kamar be yarda da ni ba, juyawa yai ya kalli bayansa kamin ya nuna kansa. Ni kuwa na gyada masa kai cike da kuzari, can ya busar da iskar bakinsa. “Ya rabb, wato baki daina shayeshayen nan da na ce ki daina ba ko?” Na matso kusa da shi ina girgiza masa kai. “Ban sha komai ba Wallahi a hayyacina nake” “No Halima ba zata fadi haka a hayyacinta ba, ko dai damuwar nan ta dawo miki ko kuma kin koma ma shaye shayen” “Wallahi ban sha komai ba” Na fada ina masa magiya kamar zan fasa kuka. “Shikenan ki tafi gida” “Zan tafi duk abunda ka ce zan yi Abdallah” Kamar umarninsa nake jira sai na juya da sauri na fice daga gidan. AHMAD POV. Glass cup ne a hannunsa yana kurba lemun a hankali, while idanuwansa suna watching plasma but his heart is one where else. Yana jin tsananin damuwa da kadaici a rashin Baby Namra da Matarsa da kuma mahaifinsa a rayuwarsa, sai dai his try be strong for him mother and his sister Siyama, domin su kadai suka rage masa a yanzu, he feels like da ace mahaifinsa yana raye da abubuwan sun masa sauki, kamar yadda da ace Baby Namra tana nan wata kila da be shiga damuwa haka ba damuwar da ke taba lafiyarsa ta taba rayuwarsa, he missed his wife his father his daughter. Be dawo daga duniyar tunanin Gobensa ba har sai da Hajiya ta soma magana da shi ayayinda take zaune saman sofa Siyama na kasa tana matsa mata kafafuwanta. “Dazun Laraba ta kirani tace wai dan Allah a taimaka mata a dauki danta aiki a kamfaninku...” A hankali ya juyo ya kalleta. “Ai ba irin su muke dauka ba, yan boko, kuma kin san Attahiru ba wani boko yai mai zurfi ba, idan ma yayi ba zai wuce secondary school ba” “To a duba masa dai haka nan tunda har ta roka sai a samu inda aka laba shi” “Hajiya ki dai fada mata masu ilmi muke dauka saboda kamfanin a yanzu yana bukatar gogaggun.....” Be marasa ba ya fara tari da sauri ya aje lemun hannunsa ya ciro handkerchief dinsa ya tari jinin da ya fito daga bakinsa. The white handkerchief din ya bawa Hajiya da Siyama damar ganin jinin da kyau, daga Hajiya har Siyama sai ka rasa wanene hankalinsa ya fi tashi... “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Mi zan gani haka?...” Cewar Hajiya. Sai yai murmushi yana nuna mata cewar ba komai ba ne. “Habo na ke yi, daji ne ya kamani da mura ba wani abu ba” “Brother yaushe ka fara haka?” Siyama ta tambaya hawaye na sauko mata, kallonta yai he know he can't hide anything from her domin karatun likita take kuma ta fi kowa sanin waye dan'uwanta. “Can we talk private?” Hajiya tai saurin amsawa tana girgiza kai tana kuka. “No I'm your mother be kamata ka boye min komai ba, how do you expect your own mother to live after you death? How? Ku kadai kuka rage min daga kai sai wannan” Ta nuna Siyama hannunta na rawa tana fashewa da kuka. Da sauri tashi yai ya koma gabata. “Wallahi Hajiya ina shan magani kuma i believe zan ji sauki, duka duka ban hi sati da fara wannan tarin jinin ba, kuma na ga different doctors sun bani magani ina kan sha” Siyama ce ta taso ta zo bayansa ta rumgume shi ta fashe da kuka. “Please Brother we love you..... ” He feel so hopeless, so emotional but a haka yake kokarin ganin ya zama very strong for them. 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 3️⃣9️⃣ Tun daga lokacin da Hajiya ta lura da halin da danta yake ciki bata sake yarda ta barshi ya zauna shi kadai ba indai yana gidan to yana falo tare da ita ko kuma yana harabar gidan suna fira, a ganinta sakewarsa zai taimaka masa fiye da kadaicewar da zai yi shi kadai yana tunani da saka kansa a damuwa.   Kamar yadda ta saba masa after dinner suna zaune dinning ta dauko masa zancen aure domin shi ne abunda ta fi son taga yayi a yanzu ko zai rage masa damuwa har ma ya kawo masa farincikin samun wata haihuwar. “Tun kwanan baya na maka magana akan aure kace zaka yi tunani ba ka ce min komai ba” Ya kurba ruwan da ke gabansa kadan yana dan murmushi. “Hajiya bana son zancen aure a yanzu” “Saboda me? If saboda ni ne zaka iya zama a wajen gidan nan da matarka, and ba zan cilasta maka auren Ikilima ba, sai ka dauko budurwa da kake so ka aura” “No ba wai Budurwa ko bazarawa ba, a halin yanzu mace bata gabana, ni ban ki na mutu a haka ba” “Saboda me? Ni bana son ganin jikanka ne? Ku kadai Allah ya bani ai zan so ku yi aure ku yi juri'a da yawa ba kamar ni ba” “Kawai ina ganin kamar idan na sake haihuwa rasata zan yi, ni kuma bana son abunda zai sake kasani a damuwa yanzu” Hajiya ta yi murmushi. “Baka da karfi zuciya sai kace ba namiji ba” “Hajiya ba zaki san abunda nake ji ba, babu wanda zai shiga a irin halin da nake ciki a yanzu ace be samu kansa a damuwa ba” “Yes dole na ka damu an sani ai, amman ka rika sassautawa rayuwarka, ita daman rayuwa tana tafe da kalubale kala kala, wani mai sauki wani mai wahala, sai dai duk halin da zaka shiha ka rika tunawa akwai wadanda suka fika shigarsa, idan arziki ne akwai wadanda suka fika, idan talauci ne da damuwa akwai wadanda suka wankeka suka shanye, kai mata kawai ka rasa sai ya kuma uba, akwai wata macen da na gani na ita tana da uwar a raye uba a raye dukan ya'yanta suna nan, amman kalubalen rayuwar da ta shiga ko kan akaifarta baka shiga ba, tun daga lokacin da na ji labarin matar nan abun ya tsaya min a rai” “Indai har tana da kowa a raye mi zai saka ta a damuwa” Har Hajiya ta bude baki ta fara labarta masa labarin Halimatu sai ga Siyama ta dauko fuskarta dauke da damuwa taja kujera ta zauna tana fadin. “Ni kam i don't think zanje gaskiya” Ahmad ya kalleta. “Why? Saboda Baby bata nan? Mu da Hajiya za mu je kamar yadda muka saba a kowace shekara” Yana fadar hakan ya mike tsaye ya bar dinning table din ya nufi hanyar da zata fitar da shi daga falon zuwa part dinsa. Hajiya ta kalli yarta cikin kwarin guiwa tace. “Idan ba mu karfafa masa ya manta da komai ba, taya za mu taimaka masa wajen tunawa da abunda zai tsaya masa arai, a kowa ce shekara shi yake bada kaso 50 a cikin dari na wannan wasa da ake na children day, 25% daga kamfaninsa ne, 25% daga makarantarsa ne, sauran al'umma da kamfanonu su dauki 50%, taya mutun zai yi wannan aiki kuma ya kasa halarta taron da yake talarta duk shekara, saboda kawai yarsa ta rasu sai yace ba zai je ba” “Nifa ban ce kar yaje ba” “Shi kike nuna masa mana saboda babu Baby Namra sai ya kasa jurewa ya nunawa duniya yana cikin damuwar rashinta har yanzu, ya kamata ki karfafi dan'uwanki shiga irin abubuwan nan zai rage masa damuwa, ko a lokacin dq Baby take raye wannan children game din yana cikin abunda tafi so fiye da komai a rayuwarta,to yanzu dan bata da rai kike tunanin mahaifinta ba zai je ba?” “No Hajiya ina jin ba dadi ne, kusan every year tana cikin mutanen da suke bada award wa wadanda sukai nasara, kuma tana zaune tare da shi....” Ta karasa tana fashewa da kuka, Hajiya ta tashi daga kujerar da Siyama take zaune tana rarrashinta. “Haka Allah yake ikonsa, haka na rasa mahaifinku a lokacin da nafi tsananin bukatarsa, amman da nai hakuri sai komai ya wuce, na koma ina farinciki kamar ba ni ba, idan muka yi hakuri sai ki ga Allah ya sauya mana da wani abun na daban” Siyama ta rike hannun Hajiya tana ta kuka, haka take a duk lokacin data suna Baby, domin ta zame mata kamar kawa kusan abubuwa da yawa a tare suke duk kuwa da kasancewar ta girma sosai amman ta dauke ta kamar kawarta. Magani ne first abunda ya fara sha a lokacin da ya shiga part dinsa sannan ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya sakarwa kansa ruwa, ya fi karfin 30m ruwan na dukan kansa sannan yai wanka ya fito daure da towel, zuwa yai gaban madubi ya tsaya yana kallon kansa. Ba rama kadai ba har bakin rai mutuwar Baby Namra ta kara masa daman can dariya ba babinsa bace balle yanzu da yake jin abune mai wahala wani abun dariya ya kusance shi balle har yai ta, a nan ma ya dade yana kallon kansa kamin ya saka kayan bachi ya kwanta. Da wuri ya farka saboda akwai abunda yake son yi a office, ko da ya fito part dinsa cikin shirin zuwa office ya fito ya shiga part din Hajiyarsa 7:13am. A kitchen ya sameta tana hada musu breakfast, tana da mai aikin amman ta fi ra'ayin girka musu da kanta musamman shi da tasan ba ko wane abincin yake ci ba, gashi da kyama komai tsaftar mace idan hankalinsa ba kwanta ba sai yace ba zai ci abunda ta dafa ba. “Yau da wuri ka tashi gashi ban gama hadawa ba” “Akwai abunda nake son yin a office fin ne shiyasa” Ya fada yana daukar cup ya hadawa kansa tea. “Zan tafi yanzu idan komai ya zama Ready a fada min na aiko direba ko kuma na dawo na ci” “Okay Allah ya maka albarka” “Amin” Ya amsa da dan murmushi kadan a fuskarsa sannan ya fito cire da kofin tea ya nufi motarsa ya bude ya shiga, yana mata key mai gadin ya bude masa gate ya fice, da hannu daya yake driving dayan hannun kuma na rike da cup din yana kurbawa a hankali. Yana kusan isa kamfaninsa ya rage gudun da yake yana ta kallon Halimatu ta cikin bakin gilashin motarsa, shi be san abunda take a nan ba kusan kullum indai yayi sammako sai ya ganta idan kuma zai tashi ma yana ganinta tana bawa mahaukacin nan abinci, ko miye alakarsu oho! Ko da yake ita din ma ai kallon mahaukaciya yake mata, shi ganinta da yake kusa da kamfaninsa ma bata masa rai yake domin bayan mutuwarsa babu wacce ya tsana irinta, sai dai duk haka idan ya ganta a gurin sai ya tsaya ya kalleta sai dai idan ya ganta ya rika jin haushinta yana jin haushin kansa, duk ranar da be ganta ba har jira yake ga ko zata zo ta bawa mahaukacin abinci. To ko shine uban yayanta? Wata zuciyar ta tambaye shi. Oho mata ma ko wanene can ita ta sani Allah yasa ma wata rana ya makureta.... Ayyana a ransa sannan ya karasa kamfanin da kansa ya shiga cikin ana ta miko masa gaisuwa amman ko kallonsu be yi ba balle ya amsa sai wani sham kamshi yake. HALIMATU POV. 6 MONTHS LATER..... Al-hamdulillah Al-hamdulillah Al-hamdulillah, da sannu rayuwa ta soma sauya min ta inda ban zata ba, domin ko a mafarkina ban kawo cewar zan samu aiki a kamfanin nan ba, duba da irin mutanen da sukai applying sai dai komai na Allah ne cikin ikon da yarda ya amince aka dauke ni aiki a kamfani, aiki a gurin yamin dadi ba dan komai ba sai dan Kabir kusan ko wace Safiya ta Allah nakan siye abinci a hanya ko kuma na siyo na dafa naje masa da shi idan zanje aikin, haka ma idan na dawo indai akwai canji a jikina zan siya masa abinci na tsare shi sai an tabbatar ya ci ya koshi sannan na dawo gida, hakan kuma na karamin faranta min rai yake ba, har ta kai a yanzu idan ya gama cin abinci na tashi sai ya tashi ya bi har bakin gate din kamfanin sai idan security din sun hana shi shiga sannan ya zauna a gurin ko kuma ya koma can a inda ya saba zama ya zauna har sai na gama aikin ya fito na bashi abincin. Wani irin dadi nake ji, a taimakon abincin da nake bashi a yanzu, ina jin cewar na bawa wani mai bukatar taimako taimako na, a kamfanin ma kowa yana mutunta ni kamar yadda nima nake bawa kowa girmansa, bana da matsala da kowa ga wasa da dariya sai kace daman can mun dade tare a aikin, bana fuskantar wata matsala a aikina sai dai fargabar abu daya, wato Mahaifin Baby Namra, tun daga lokacin da na fara aiki a kamfanin aka bani takardu da da magazine din kamfanin sai na gane cewar shine mai kamfani kamar yadda na lura da cewar shine mai makarantar da can da Abdallah ya cire su Namra domin a can mna ganshi kamar yadda na taba ganinsa a wannan kamfanin aau daya, domin hotonshi ne a jiki an rubuta masa shugaban kamfanin Ahmad Muhammad Gwarzo, sai dai ba kowa ya san haka ba kasancewar ba a saka hotonsa a kamfanin ba balle sunansa, kusan tun da na zo ban taba ganinsa ba, sai wacan ganin da nai masa a farkon zuwana kamfanin neman aiki. A yanzu kam kullum a cikin fargaba nake ina karanta masa hasbunallahu da rokon kar Allah yasa ya ganni har na samu wani aikin na bar masa kamfaninsa, domin ina ji a jikina cewar duk ranar da ya gano ina aiki a karkashinsa sai ya wulakanta ni ya ci min mutumci kamin ya koreni. Bayan shi ba ni da wata fargaba kuma ina jindadin aikina, ko ba komai kamfanin yana kusa da inda Abdallah yake aiki, hakan yasa na daukarwa kaina kullum da misalin karfe biyu na rana sai saka order an kaiwa Abdallah abincin rana a office dinsa, tun ina zuwa kullum na kai kudin har na fara biyan na wata wata, sai dai duk da haka Abdallah be taba kira wayata da sunan ya min godiya ko ya nuna min ya jidadin abunda nake masa ba, ko kuma ya gargade ni akan na daina ba, sai dai mai kai abinci ya fada min be taba cewa a daina kawo masa ba, tun daga lokacin da na fara aiki a kamfanin kusan kullum sai na turawa Abdallah sakon Barka da Safiya abun har ya xame min kamar ibada sai dai shi be taba maido min da amsa ba, idan na masa magana a whaspp ko fb sai ya karanta amman ba zai ce min komai ba, tun ina jin babu dadi har na soma sabawa da wannan sabon halin nashi. Haka zai shigo gaishe da su Mama da Baba gida, ba zai ko kalle inda nake ba haka ba kuma ba zai hana na yi masa magana ba, wani lokacin ya kan amsa min sai dai idan na matsa da magana sai yai mana sallama ya tafiyarsa. Gaba daya ya canja min taimakon da yake ba ni ya daina, sai dai ba shi ya dame ni ba kamar rashi sakin fuskarsa da kula ni da yake a yanzu, ga shi Allah ya dauki soyayyarsa da kaunarsa da tausayinsa ya cika min zuciya da su. A yanzu ta kai idan ba zancen Abdallah ba bana son labarin ko wane namiji, duk wata soyayya da nai wa Aminu da Abdulhamid a baya ashe ta karya ce a yanzu nake soyayyar da gaske, haka zan raya dare da begensa a zuciyata da tunanin abubuwan alherin da yai, da girma da yaraba hudu amman tunanin soyayyar wani ta hanani sukuni, idan na ga wani da sunansa sai na ji ya burgeni saboda kawai Abdallah. Sai a yanzu na gane cewar na aikata kuskure babba na zabar Abdulhamid na bar Abdallah, a yanzu kam ina ganin laifin Abdallah kadan na cewa yana so a lokacin da igiyar aure take saman kaina, da farko ina daukar cewar fushi yake da ni daga baya kuma sai na fahimcin cewar kamar kokarin cireni yake a ransa ya nesanta kansa da ni, wanda hakan ba mai yiyuwa ba ni a tsakanin ni da shi, har ga Allah na tabbatar Abdallah yana so na, kamar yadda nake jin a yanzu da a raba ni da soyayyarsa kara a raba ni da raina. Ko da Abdallah ba zai aureni ba ina son na saka masa da soyayyar da ya nuna min ni da yayana. “Wai da gaske kike za ki shiga gasar nan?” Kaina na dago na kalli Hafiza wacce tai min maganar ina murmushi domin na lura kamar bata yarda da zancen da nai na cewar zan shiga tare da yara a wasar da za'ayi Next Week ta children day ba. “Why not? Ko dan farincikin yarana ai zan shiga, bani da matsala da kowa yanzu ba aure ke kaina ba balle na ce” “Amman gaskiya matan hausawa ba sh cika shiga irin wannan ba” “Ai dai mata suna shiga ko? To nima zan shiga idan na saka wando zan dora abaya a sama na saka karamin hijab dina” Na fada ina jin cewar har a raina zan yi domin farincikin yarana kawai, domin a yanzu bani da damuwa sai ta yarana da iyayena sai kuma tawa, na tattara komai na aje a gefe, Aminu ma da ya matsa min na fada masa kotu zan kai shi idan be daga min kafa ba, sannan na jadadda masa matukar be saka Sadi a kotu an kwatarwa Namra hakkinta ba ba zan taba yafe masa ba, wanda nake tunanin abu nai wahala yai hakan ko dan Hajiyarsa na san ba zata bari ba. “Yes Momy kuma mu za mu cinye....” Aiman ya fada yana daga hannu tare da dariya, sai na gyada masa kai. “In-Sha-Allah kuma idan mun yi ta daya, zan yi amfani da kudin na saka ku a wata makaranta private school so that ku samu karatu mai kyau, sauran kudin na rika juyawa ga aikina kamin lokacin biyan wasu yai na san zan samu na biya” Namra ta yi karaf tace. “Momy pls ki siya mana kayan wasa kuma pls” “Zan iya muku, ki yi addu'a Allah yasa mu yi na daya” “Amin kullum zan yi addu'a idan na yi sallah” “Da alama dai wanda ya siya miki ticket din nan ke da yaranki yana ji da ke sosai, ko mother letter din nan fa kusan 20k ake bada ita” Hafiza ta fada tana dago min wata farar takardar mai zagen kamar abun zinari. “Kuma kin ga ticket ma na shiga gurin kawai 10k ne na shiga game kuma 30 domin ko baka ci ba za su baka wani abu wanda kuma yai na daya million daya da award da kallon azurfa, haka dai na biyu har zuwa na biyar, muma na ga alamar shi wannan bawan Allah da yake ta wahala da ke kamar ba ma sonshi kike ba, oh maza akwai daukarwa kai wahala” Ta sake fada tana tabe baki “Baki san waye shi ba, kin taba ganinsa?” “No kawai dai naga yana ta kashe miki kudi ne hakan nan, ko jiya sai da Mama tai magana har tace zata same ki ku yi magana indai a aurenshi za ko yi ba, to ki sallame shi kar dawo daga baya yace sai an biyashi” Shiru nai na dan wani lokacin, idan har Mama ta same ni da zancen ban san me zan fada mata ba, idan har taji cewar kafiri ne zata tsorota ta kuma nemi hanani kulawa wanda na daina tuntuni amman shi ya kasa janye kansa daga jikin kullum sai neman kara shiga jikina yake, na rasa yadda zan yi da shi babu bakar maganar daban fada masa ba babu irin gargadin da ban masa ba amman babu abunda ya canja. “Yana da kyau Momy amma yana saka sarkar cross kuma yana sawan cin chewing gum....” Na yi saurin rufewa Namra baki. “Kar naji maganar nan gurin wani, duk wanda ya fadeta a cikinku sai na dokeshi, tashi ku shiga ciki... ” A tsawa na yi musu maganar fuskarta babu alamar wasa hakan yasa duk suka tsorata har Amal suka tashi suka shige daki suka bar mu a waje ni da Hafiza, a kokarin dauke hankalinta daga zance na dauko mother letter din na rike ina tambayarta. “Me ake da wannan hala?” “Uwa ce zata rubuta tahirin rayuwarta da kuma yadda take kula da yayanta daga karshe sai ta rubuta daga uwar su wane da wane, sai ta saka a cikin dan box din wasika, idan mc ya zo shi zai karanta sai ya fada cewar daga uwar su wane idan anji an san ko su waye ake nufi” “Wow abun ya kayatar” Na fada ina jin cewar ni ma zan rubuta komai na rayuwarta a cikin wasikar da kuma yadda nake kula da yarana sai dai na zan fadi sunan da suna yara ba ba, ba so nake a san ni ba kawai dai ina son nao sharing tarihin rayuwata ga wadansu iyayene musamman abunda ya shafi Namra domin kawai ya zame musu darasi su kula da yaransa da kyau, ba kamar yadda ni nai sake har haka ta faru da yata ba, zan rubuta komai nawa a cikin har da rayuwar aurena a gidan Aminu da auren Abdulhamid da soyayyata da Abdallah, haukacewar da Kabir yai da kuma mutuwar Baby Namra fyaden da akai min akaiwa yata, sai dai ba zan fadi sunan kowa a ciki ba. “Ke fada min ina kike hadu da shi?” Ta tanbayeni daman na san za a rina, a banza ma Hafiza tai gulma balle wannan mai dalili. Abunka da yar'uwa duk kuwa da kasancewar ba uwar ma daya ba uba ne kawai amman bama boyewa juna abu idan ma ba wanda ya sani ba ba zai taba sanin cewar ni da Hafiza yan uba ne ba, domin a gidan m ba zaka taba sanin yan dakin Mama da kuma yan dakin Inna ba, kowa uwarmu ce idan Mama bata nan bama da matsala ko damuwa mun san Inna zata mana kamai, kusan Hafiza ma a dakin Mama take komai nata a can take yi wani lokacin ita da Mama har sirri suke babu wanda ya sani sai idan sun fada. Kamin na gama bata labarin har mararta ta cika da fitsari, tsoro duk ya bayyana a idonta da jikinta. “Bari nai fitsari na dawo” Da gudu ta nufi bandakin da ke tsakar gidamu tai fitsari sannan ta dawo ta zauna tana zaro ido. “Dan Allah ki ce kin yafe masa mana, Wallahi zai iya fusata ya zo ya halbemu, kin ga dai ni ko dan karatun ban gama ba, balle na ci moriyarsa, ga yaranki kanana, Baba Lafiya ma bata isheshi ba, dan Allah ki yafe masa kar ya zo ya halbe mu dan Allah kema zai iya halbeki Wallahi...” Da farko dai na dauki maganarta serious daga karshe kuma sai ta bani dariya domin na lura tsoro ya gama cika mata ciki, ina cikin dariya Baba ya shigo bakinsa a haushe yana da far'a. “Kun ji abun Allah yanzu fa sallamar da kai min ina fita wani ya bani 100k kyauta” Ni da Hafiza muka hada ido kamin su Inna da Mama su fito daga dakin da murnarsu, gaba dayan gidan sai ya kaure da murna abunka da talaka mai neman na yau da gobe ya samu kyautar 100k a rana daya ina bakin yan gidanmu zai rufu, ni kaina na nuna murna kuma na jidadi ganin yadda Mama da Baba da Inna suke ta murna suna masa addu'a, sai dai ni na san mutum daya zai iya wannan abun wato Abraham. “Amman Baba kai kadai ya bawa kyautar?” “Gaskiya bani kadai ba ina tsaye da Malam Isuhu ya min sallama ya miko min 100k shi kuma Isuhu ya ba shi 5k” “Baba yaro ne?” “Aa dattijo ne amman ba zai kaini tsufa ba gaskiya, yana cikin wata bakar mota mai kyau kana ganinta ka san mai kudi ne sosai, shi dai mai ja masa motar ne matashi” “Uhmm” Na fada ina rafka uban tagumi tare da kallon Inna da ke fadi. “Allah mai iko sai ka ji wani yayi kyautar abu kamar banza yanzu har dubu dari ka bayar kyauta, wasu Allah yai musu arziki” Mama ta taya ta. “Ina jin dai zakka ce, ko kuma irin masu kudin nan da ke bin gidajem talakawa suna ba su kudi” “Ko dai minene mun gode Allah shi kuma Allah ya saka masa da alheri, daman an kwana biyu ba mu girki da nama ba gobe da safe idan Allah ya kai mu sai a samu mana nama mu ci” Cewar Baba, sai duk suka dariya ban da ni da ke ta wani tunanin na dabam. Har aka isha'i babu abunda nake sai tunanin yadda zan bullowa lamarin nan, wata zuciyar na fada min cewar na sanar da police kawai n huta ko kuma na sanar dasu Mama idan kuma nai hakan hankalinsu zai tashi, idan kuma na kyale shi abun nan kara gaba zai yi. Misalin takwas da rabi yaro ya shigo wai an sallama da ni ba waje, da farko na dauka Aminu ne domin shi ma yana min hakan ganin bana daukar wayarsa sai kawai ya aiko kirana kai tsaye sai idan na fita na ganshi, sai dai mafi akari Abraham ya fi min haka, domin shi be tana kirana a waya ba ma, be tana ce min na bashi number ta ba. Aiko kamar jira nake na zari hijabi na saka na bi bayan yaron da ya aiko kirana, ko da n fita yana can nesa da gidanmu kamar yadda ya saba tsayawa, hango ni yasa shi fitowa daga motar ya rike gambun motar yana ta kallona har n karaso. “Me kake so? Kana ta bibiyar rayuwata, na fada ka fita daga hanyata, bana kaunar ganinka Abraham kai ne silar lalacewar aurena ba baka aikata abunda ka aikata min ba da har yanzu in zaune tare da mijina... To me kake nema a yanzu?” “Yafiyarki mana, na rasa gane wace irin mace ce Halimatu, me zan yi ki yafe min? Fyaden da nai miki kuskure ne, na yarda na lalata miki rayuwar aure, amman haka ba ya kara fito da kalar mijinki ne kawai, na nuna miki cewar ba zai iya zama da ke idan wani abun ya same ki ba, and I'm here for you, na ji na aikata laifi amman yafiyarki nake nema, and i promise you zan dauki nauyin yaranki da iyayenki da kanenki, zan inganta rayuwarki” “Da kudin haram? Kudin da kuke tare mutane masu hakki ku karbe musu abu? To bana so kuma karka sake bawa mahaifin kudinka na haram” “Su waye muke tarewa muna kwace musu hakki? Halima har addinina n ce zan bari na shiga na ki saboda kawai ina kaunarki amman kin ki aminta why? Daman haka musulmai kuke?” “Karka kuskura ka kasa zancen addinina a ciki maganarka, kuma tirr da kai ni ba zan auri dan fashi ba dan fashin ma wanda ya keta min haddi” Ya gyara tsayuwarsa yana kallon. “Waya ce miki ni dan fashi ne?” “Miya hada ka da bindiga a wacan daren?” “Saboda kawai n rike bindiga sai ya nuna ni dan fashi ne, a yanzu ma ina da ita a mota, ke dai ba kisan komai a game da ni ba, ba ki san waye ni ba, iyakar abunda kika sani na miki fyade sai sunana sai kuma bibiyarki da neman yafiyarki da nake” “Idan na yafe maka zaka daina kula ni zaka daina bibiyata zaka daina zuwa kofar gidan nan zaka daina bibiyar yarana?” “No ai yafen min da za ki yi shine ki aure ni, ki haifa min yara.....” Da sauri na rumtse idona ji nai kamar ace akwai wani makami a kusa da ni na daba masa a kirji ya mutu a gurin, saboda zafin da maganarsa tai min, taya mutun zai keta min haddi da aurena kuma yana kafiri ina yar musulma sannan yanzu ya dawo yana min maganar aure har da haifar masa yara, saboda kawai ni Halimatu ai komai nawa dabam ne.... Ji nai an haska fuskata hakan yasa na bude ido ashe wayarsa ce ya haska min a fuska ganin ina hawaye yasa shi ce min. “I'm sorry ban zo nan dan na saka ki kuka ba, zan tafi see you at Children's Day” Yana fadar hakan ya koma cikin motarsa yai mata key ya bar ni a gurin tsaye ina hawaye. “Ba zan je ba, saboda kai ka siyo min ticket din” Na furta a fili ina ayyanawa a raina cewar ba zanje din ba.... _____________ Wai ashe Abraham yana da team 🤐 Who can guess what will happen next? 🤗 Ni dai ina Team Aminu 😝😝😝 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣0️⃣ Hakan nan yau yake sha'awar zuwa gurin aiki da wuri, daman kuma ya tashi ya ji jikinsa sai a hankali so yana bukatar yai aiki da wuri ya dawo gida if possible. And he like to wear a suit today like always sai dai wani lokacin yana saka shadda dan yafi jinsa more comfortable fiye da suit.   Bayan ya gama shiryawa ya shigo bangaren Hajiyarsa still ya same ta tana aikin hada masa breakfast sai dai yau ba ita kadai ba har da Siyama. As he already knows siyama bata tashi da wuri sai idan makaranta zata je, amman ga a kitchen tare da Hajiyarsa da mai aikinsu har ma da cousin dinsa Khadija wacce kwararriyar banker baker ce.  “Yau me kuka hadawa haka ne?” Da sauri dukansu suka juya suka kalleshi domin ba su san da zuwansa ba sai ganinsa da kai a kofar kitchen yana ta kamshin turare. “Amman Bro you wake early” Cewar Siyama tana nufo inda yake. Agogon hannunsa ya duba wanda ya nuna masa bakwai da yan mintuna. “Yeah ina son naje aiki da wuri ne” “Oh bro i wanted to surprise you.....” Ta fada tana bata fuska, sai Khadija ta tari numfashinta tana murmushi. “We can still surprised him dear... ” Ya kalli Khadija da fuskar rashin fahimta. Sai ta jango masa kujerar kitchen din ta aje bayansa. “Dan zauna” Be zauna ba be kuma nuna alamar zai zauna din ba balle har ya furta wani abu. Siyama know him well, he is no nonsense at all, hakan yasa ta hade hannayenta. “Pls” Sai da ya kalli Hajiyarsa wace ita ma tai masa alama da ya zauna din sannan ya zauna yana binsu da kallo. Da gudu Khadija da Siyama suka fita daga kitchen din, like 6 minutes suka dawo sai Hajiya ya fita. “Close your eyes pls” Be musa ba tunda Siyama ce tai masa maganar, a take ya rufe idon sai ta kama hannunsa yana masa jagora a hankali har suka fita daga kitchen din, gaban dinning area ta nufa shi sannan ta saki hannunsa. “Now open your eyes....” A hankali ya bude idon, by surprise yai arba da katon birthday cake mai hotonsa. “Wow” Ya furta yana kallon mahaifiyarsa da ke Murmushi kamin ya rumgumi Siyama wacce ke ce masa happy birthday. “Thank you Blood, Thank you Mom, thanks Sis” Ya fadawa Siyama Hajiya and Khadija wacce tai masa respond da murmushi. “So duk kun san yau birthday na kenan, ni na manta sam” “Taya za ayi na manta ranar da na maifi Ahmad Gwarzo...” Cewar Hajiya tana murmushi, sai yai murmushi ya kai hannunsa ya debi cake din ya kaiwa Hajiya a baki. “I love you Hajiya ta” One after the other ya bisu ya saka musu cake din a baki har Khadija, sannan suma suka ba shi, daga bisani Siyama ta ciko hannunta da cake din zata shafa masa sai yai saurin rike mata hannu ya murda har sai da ta kai kasa tana ihu. “Wayyo Hajiya....” “Gwarzo karka kare min ya” “Hajiya ba zan bari ta bata min tufafi ba today is special day for me...” Sai duk suka saka dariya har ita Siyamar sannan ya sake ta ya dauki tissue ya goge hannunsa. “Yau din nan ko? I very very special day for us, i call your friend on phone and i told him ya saka kowa yai surprise dinka da wani abu each and every person a kamfaninka, so karkaje ka dinga musu fada ni na saka su” “Kina da hankali Siyama?” “No sam sam Hankali wala gare ni a yau, la la la and in the laila akwai celebration... ” Ta fada tana rawa. “Hajiya yau yarki bata da hankali” Ya fada sound so serious domin gani yake yau Siyana hauka take ji how zata kira company su tace kowa yai surprising dinsa, and now tana gaya mishi akwai celebration, shi rabon da yai celebration din birthday sa tun matarsa Halima na da rai. “Tana da hankali she's just celebrating her brother birthday” Khadija ta fada tana murmushi Siyama tace. “Louder pls” “No ina ganinki da hankali Khadija karki biye wannan” Daga haka ya juya ya fice yana murmushi, sai kuma ya juyo yana kallon Hajiyarsa. “A saka min cake dina a fridge pls” “Okay Breakfast fa” “Zanje office din na san kamin na dawo kun hada sai na ci, akwai wanda nake son meeting da shi a 8” “Okay Allah ya tsare” Sai da ya amsa da min sannan ya fice daga falon ya nufa haravar gidan gurin da ake aje motoci. He choose ya black kalar suit dinsa sannan ya shiga.    Sai ya kusa isa kamfanin sannan ya rage gudun da yake, like always dan kawai ya gani idan ma din ma Halimatu zata bawa mahaukacin nan da be san alakarsu ba abinci, to his surprise yau be ganta ba sai dai mahaukacin na nan a zaune, haka nan kawai ya faka motarsa gefen titi yana ta kallon mahaukacin he just wanted to see idan zata ba shi abinci yau, ko ma bata ba shi ba shi miye nasa a ciki? Yaja tsaki a maimakon yaja motarsa yai gaba sai ya dauko wayarsa ya shiga whatsapp yana duba status din Siyama wacce ta sika status din da hotonsa tana masa kalamaina na kauna irin na yar'uwa da dan'uwanta, sai da ya dora hotonsa a status dinsa ya rubuta happy birthday to me sannan ya shiga duba na sauran yan'uwansa da abokansa, daga lokacin ne n banks dinsa suka shigo sai kuma fb da sukai masa happy birthday. Ya fi karfin minti talatin a gurin sannan yai ma motarsa key ya karasa office din, hakan nan yaji baya son fita daga motar ma and he don't know why sai kawai ya ciro wayarsa amininsa kuma abokin aikinsa. “Happy birthday Boss” “Thank you, Salim ya ganar Inuwa? Kana ganin zai samu zuwa yau kuwa” “Yes ai ba zai tsaba alkawari ba amman na san yau rana ce mai muhimmanci a gareka, zan masa jagoran komai kai sai ka huta” “Thank you zan fito amman sai anjima” “Okay” Daga haka ya aje wayar yai reverse ya koma hanyar gida, still sai ya sake tsayawa yana kallon mahaukacin na tsawon five minutes sannan ya cigaba da tukinsa. HALIMATU POV. Bayan tafiyar Abraham wani tunanin ya fado min a rai, a iya tunani be kamata na kyale shi a haka nan yana ta bibiyar rayuwata ba, ya kamata na kai shi gurin yan sanda su mana tsakani ko ba komai zan samu salama kuma zan fada musu cewar dan fashi ne ko zai kashe ni sai dai ya kashe ni. Ban sanarwa kowa ba sai dai na kudirci abun a zuciyata, a daren ban yi bachi ba sai pass 12, ina ta tunanin irin matakin da ya dace na dauk domin na san nan gaba kadan iyayena za su bukaci saninsa to sai na ce musu me?   Da wuri na shiryawa yarana sannan na karya bayan su ma sun karya suka kama hanyar makarantar wacce ta kasance nesa da unguwarmu kadan, yau ban basu kudin tara ba saboda ina son dafa musu indomie tare da Kabir, da kaina na nufi shagon unguwarmu na siyo indomin sai ya rage naira goma ce kawai canji dan haka na bukaci ya bani chewing gum da ita idan ma na karbar na san rigima kawai zata zama tsakamin Namra da Aiman da Amal kara Adnan yana dan daga kafa wani lokacin baya biyesu.   Sai da na dafa indomie na zuba musu a cularsu sannan na dauko leda na kwashe ragowar indomin na zuba ciki, a gaggauwace na nufi bandaki nai wanka na shirya sai dai hakan be hana ni shafa janbaki da hoda ba har da kwalli kamar yadda na saba,  riga da zane na atamfa na dauko na saka sannan na saka hijab dina ya saka wayata da a jaka na fito ina yi ma su Mama da Inna sallama. Sai da na karanta addu'ar fita daga gida sannan na fita, ina karasa titi nai sa'a da mai adaidaita babu kowa a ciki bayan na tare na fada masa ya kai ni police station da ke can unguwar kwaza, wata zuciyar na fada min kar ka kai maganar gurin yan sanda saboda gudun abunda zata zame min, amman kuma idan ban kai ba me zan yi? Haka zan zuba masa ido yana ta bibiyata? Bayan na fada min ko na yafe masa idan ban aureshi ba ba zai daina bibiyata ba. Nesa da station din aka sauke ni domin masu napep ko abu hawa basa karasa har gaban gurin, bayan na bashi kudin na shiga ciki, gabana sai faduwa yake kamar marar gaskiya, abunka da wacce bata saba zuwa gurin yan sanda ba. Kai tsaye na shiga ciki har da yar sallama ta suka amsa min wanda na ganin da yar fuska far'a na nufa na fada masa abunda ya kawo ni a gurin, ba shi kadai ba ko su sauran da suke sauraren labarin nawa sai da sukai mamaki. “Amman kuma ba ki san shi ba?” “Ban san shi ba ba ni da alaka da shi, kawai dai yace yana so na ni kuma na nuna masa bana sonsa hakan kuma be saka shi ya daina bibiyata ba, and jiya ma sai ga kudi an aikowa mahaifina ina zaton shi ya bada yace a bashi amman shi mahaifin nawa be sani ba, kuma ni ina tsoro kar abun yai nisa ya zame min fitina” “Kin ce kin taba ganinsa da bindiga?” “Eh a motarsa ba, ina tunanin dan bashi ne” “Ko dan kidnapped ba, wannan babban case ne gaskiya, ina ganin abunda ya kamata a fadawa PRo sai ta shiga tai masa bayani” “No kai ta gurin oga direct zai fi, idan ya hannatawa Pro shikenan, mu sai mu rubuta statement” Atsakaninsu su uku suke wannan shawarar, kamin dayan ya shiga ciki be dade b ya fito ya ce akwai case din da yake idan ya gama sai na shiga, haka na samu guri a gurin na zauna ina ta kallon wasu mutane da ke shigarda kara da wadanda ake saurarensu suna kare kansu. Bayan kamar minti talati ya sake lekawa ya fito yace min na shiga, shi yai min jagora ciki har da bude min kofar na shiga sannan ya janyota ya rufe, mutumen da na tarar yana zaune a irin kujerar nan ta office mai lilo, ya bani baya wanda hakan ya bani damar daga kaina saman ina kallon office din, kamin ya kare wayar ya juyo ya kalleni arba nai da abunda ban tana tunani ba abunda ban taba tsammani ba, a take jakar hannuna ta subuce ta fadi, nai baya da sauri kirjina na mugun bugawa kamar zai fito. “Ya akai?” Ya tambaya ni fuskarsa ba yabo ba fallasa. “Ni ban gane ba, tagwaye ne ku, kama ce, ko kuma kai din ne dai?” Murmushi yai. “Ni din ne dai, wa kika kawo kara? Ni ko wani?” “Daman kai dan sanda ne kuma kake fashi da makami?....” “Shiiiiiiiiiiiiiiiiiii” Ya furta tare da saurin mikewa tsaye ya nufo inda nake, kan ya karaso har na kai hannu na bude kofar na fita da sauri jikina sai rawa yake, ina fitowa na nufi gurin kular abincin yarana zan dauka sai dayan yace. “Kin masa bayani” “No waya yake, yace naje na dawo, bari na kaiwa yarana abincinsu a makaranta na dawo” “Okay ba matsala” Daga haka na samu na fita daga station din, mamaki ya saka ni mike hanya ina ta tafiya ba tare da na tari abun hawa ba, sam hankalina be bani a gafen titi nake ba har sai da nake tsallakawa ba tare da na saurari horn din da motocin ke min ba. Ban ankara ba na ji abu ya buge bugu bana wasa ba, har sai da nai bayabaya na fadi kan kwalbatin da ke gefen titi. “Ba ki da hankali ana miki horn amman sai kokari tsallaka titi kike kurma ce ke?” Iyakar kokarin da nai na fita daga kwalbatin ne kamin na dago na kalli mai motar wanda ya rufe da fada babu ko tausayi. Muna hada ido yaja wani bugun tsaki ya koma cikin motarsa da ke bude ko inda nake be sake kallo ba. “Wawa kai ne mahaukaci tun da baka iya tsayawa ka duba mutane ba, ko tokin be iya ba sai jin kai kamar wani Governor, ko titi na gidanku ne....!” Be sake ce min uffan ba har yaja motarsa ya bar gurin. Wani mai acahaba ne ya tsaya yana tambayar idan ban ji ciwo ba. “Ban jimu ba faduwar kawai nai” Na fada domin bana jin ciwo komai a jikina. “Dan Allah ki rika kula idan za ki tsallaka titi irin wadannan ba imani garesu ba” “Na gode” Na fada idona na cika da kwalla, lallai a yau na tabbatar Ahmad gwarzo be da imani kuma be da mutunci, taya zaka buge mutum ka wuce ba tare da ka duba lafiyarsa ba, ko da yake ni mai laifi da nai kokarin tsallaka titi ba tare da na duba ba, amman duk da hakan da ace mutum ne mai imani da zai tsaya ya duba idan be jimi ciwo ba, wata kila saboda yaga ni ce yasa yai min haka ko kuwa daman can halinsa haka yake? Ban bar gurin ba sai da na tari mai napep na fada masa makarantar da zai kaini ta su Namra, wacce ya kamata ace can na fara zuwa kamin na je station din amman saboda gudun kar nai latti yasa na fara zuwa can zuwa da be amfani da komai ba. Tsayar da mai napep din nai na nufi shagon da ke kusa da makaranta na siye musu pure water shiga har cikin makarantar na kai musu abincinsu tare da ruwan sannan na fito, na sake karbar wani ruwan na Kabir na fadawa Mai napep din inda zai kaini. Daidai kusa da Kabir ya aje ni na biyashi kudinshi sannan na fita na nufi gurin Kabir din na ciro indomie da ke jakata na bashi sai da na tabbatar ya saka hannunsa ya ci ya koshi sannan na bashi ruwa ya sha, ni kuma na mike na fara takawa da kafar da sai a yanzu nake jin tana min wani irin mugun ciwo, kaina sai sarawa yake ina dan jin jiri kadan-kadan. Cike da karfin hali na karasa kamfanin, ba laifi na gaisa da masu gadin gurin kamar yadda muka saba sannan na karasa cikin kamfanin ina tsinginta saboda zafin da kafar take min idan na taka. Duk wanda ke magana da ni idan ya gan ni sai ya tambaya me ya samu kafar sai na ce fadawa nai kwalbati. Haka na nufi bangaren mu na tura kofar na shiga sai na samu Yunus yana musu wani bayani da ban fahimci me yake nufi ba, har sai da ya gama musu sannan ya juyo yana min bayani. “Yau dai kin zo late, daman ina musu bayani ne akan yau birthday shugabanku, so yana da kanwa Siyama ta kira ni ta ce tana bukatar kowa da kowa yai masa kyau komai kankantarta, na san ba abu mai yiyuwa ba, domin yawa ma'aikatan kamfanin bata sunansu ba ne shiyasa tace haka, so ni kuma na zabi ku da kuke sabbin dauka ku yi masa haka” Bance komai ba har yai gama fadar abunda zai fada, ina jin a rain kamar ba zan iya ba, taya zan bawa wanda baya kaunar ganina kyauta, amman kuma ai be san wanda ya shi ba, sai dai ni kuma hankali ba zai kaunata ba matukar nai masa kyautar, ho me ma zan bashi me nake da shi da zan bashi. “Kamar me za mu bada...?” Abokin aikina ya tambaya. “Komai kake da shi zaka iya ba shi, ko biro ne idan kuma akwai mai kudi a cikinku sai ku siyo wani abu a nan waje ku bashi, mu na dai son kamin ya shigo mu yi masa kyautar” Dukanmu muka amsa da to ni dai ba dan raina ya so ba, wasu suka rika fita suna siyo masa abun da ya samu ban da ni da na rasa abunda zan bashi kuma bana jin zan saka kudi na siya masa komai. Kusan duk a tare muna doshi office din nasa, wanda ban taba zuwa ba sai yau, tun daga muka doshi inda office dinsa yake sai na zama bakauya yadda kaban taba ganin kamfanin ba haka na zama, wata kalar wallpaper ce aka kawata gurin da ita mai wani irin daukar ido da kyau, ga wani uban sanyi ac mai ratsa jiki, sai da muk shiga office biyu ko wane da ma'aikaci a ciki sannan muka isa office dinsa, wanda kanshin air freshener mai dadi ya fara yi mana marhabun, ya kawata office din da hotunansa wani gurin yana tare da mahaifiyarsa wani gurin da Baby Namra sai kuma wanda sukai wani a gurin meeting wani da turawa, tebur biyu ke cikin katon office din daya a yana fuskantar kofar shigowa wanda shine babba, sai kuma karami dayake gefe mai dauke da desktop computer har guda biyu bayan laptop din dake saman babban tebur din, sai kuma wata doguwar durowa mai cike da littafan da kuma numbobin karammawa. A kasa gaban teburin aka umarce mu da aje duk abunda muka kawo masa kusan mu goma sha daya, wasu suka aje biron kamar yadda ha fada wasu littafi wasu kuma sun rufe kyautarsu da irin ledar nan mai kyali. “Ku yi hakuri is like kamar na yi force dinku, tun jiya ya kamata na fada muku amman ba samu dama ba yau din ma sai da na dub status dinta sannan na tuna” Duk muka shiga nuna masa cewar babu komai ai kyautatawa, duk wanda ya aje juyawa yake ya fita, har ya zama ni ce ta karshe, hannu na saka na cire agogon hannun duk kuwa da kasancewar na mata ne na aje a saka tare da chewing gum daya sannan na juya na fita ina aynnawa a raina cewar wata kila zubdasu zai yi. Har na dawo na fara aikina ban daina jin kafata da kaina suna min ciwo ba, hakan yasa na nemi izini na fita daga ward din mu da zimnar na kai kaina titi gurin mai chemist din nan na siyo magani. Ina kawowa reception nai arba da Ahmad ana nuna masa abu a katuwar plasma dake gurin, wani irin mugu faduwa gabana yai domin na san yadda ya tsane ni balle ace yau ya gano ina aiki karkashinsa. Da kallo ya bini har na kusan ficewa sai na ji an daga min tsawa da wani irin karfi. “Keeeeeeeeeeee!” Ba ni kadai ce mace a gurin ba, amman ina jin muryarsa na san da ni yake, hakan yasa na juyo na kalleshi. “Me kike anan?” Shiru nai na kasa cewa komai har sai da mutumen da ke kusa da shi ya amsa da. “A nan take aiki tana cikin sabobin ma'aikatan da aka dauka, zo nan” Mutanen ya karasa yana min alama dana karaso gurin da hannu. Ba musu na karaso gurin. “Ku sallameta” Da sauri na daga kai na kalleshi idona cike da hawaye, tabbas yau da ace Ahmad shi ke da kamfanin nan da sai na yi masa wankin babban bargo, amman ba wannan damar. “Ka taimaka min dan Allah ina da bukatar aikin nan....” Na roka ba dan komai b sai dan na san idan har wannan aikin ya subuce min kamin na sake samun wani aiki ne a gareni. “Ranka ya dade tana da takardunta fa, duka ma'aikatan da aka dauka suna da takardu” “Ku aje ta reception....” Shine kawai abunda ya fada har ya juya sai kuma ya juyo yana kallona “Karki shigo min kamfani da kwaliya, ba dandali ba ne nan” Kai na gyada masa alamar okay ina share hawayena sannan ya juya ya wuce ya bar a gurin tsaye mutanen da ke gurin na ta kallona. Ji nai ba zan iya zuwa siyen maganin ba saboda kunya da kukan da ya rufe ni na wulakancin da Ahmad yai min a yau. Sai na koma ward din aikinmu na zauna, tsakanin shigowata da zamana be kai minti goma ba wani ya shigo ya canja min gurin aiki zuwa reception. AHMAD POV. A hanyarsa ta karasawa gida ne ya kade Halimatu at first ya fito da fada a cikin motar sai dai ganin ita dince yasa shi jan tsaki ya koma cikin motarsa duk kuwa da irin bakaken maganganun da take fada masa, ya kyaleta ne kawai saboda ita din macece baya fada mata yana daukar namiji mai fada da mata ragon namiji, balle kuma ita da ba shi da lokacinta. Gida ya koma ya karya sannan ya dawo kamfanin, a reception ya tararda ma'aikatansa a gaban katon plasma dake gurin suna kallon harin da aka kai barno, sai dai ganinsa ya saka kowa ya kama gabansa, ban da Rilwal dake labarta masa abunda ke faruwa. Uffan be cewa Rirwal ba, yana kokarin kama hanyar office dinsa sai ga Halimatu ta fito daga wani bangare na kamfani abunda ya bashi mugun mamaki, kararsa ta kawo? Ko kuma wani nata ne a ciki? Ko wani abun ta zo yi? Da kallo mamaki ya bita har sai da ta kusa ficewa daga gurin sannan ya daka mata tsawa, ta juyo jikin a sanyaye. “Mi kike a nan?” Ya tambaya co's idan ma zuwa take kamar yadda ya ganta a wacan karon yai mata warning kar ta sake zuwa masa kamfani yo his surprise sai rirwal yai masa bayanin aiki take a gurin, a take ya bada umarnin a koreta. Sai dai yadda ta marairaice fuska tana hawaye tana rokonshi, yasa shi canja mata position a maimaikon korar gaba daya. Kai tsaye ya nufi office dinsa ya bar a gurin tsaye tana hawaye da suka saka shi jin babu dadi, yana tura kofar office din farko mutane da ke office din ya mike tsaye yana gaisheshi, haka ma na biyu sannan ya shiga office dinsa. Sam ya manta da zancen da Siyama tai masa cewar tasa ayi kowa ya bashi gift sai da yaga taren abubuwan da ba zai iya tsayawa ya tantace ko kiye da miye ne a gurin ba. Gaban teburisa ya karasa ya zauna, hannu ta kai ya danna telephone dinsa. “Zo” Shine kawai abunda ya fada ya sannan ya mike tsaye ya cire rigar dake jikinsa ya dorata a bayan kujera. Mutane da ke office na biyu ne ya shigo da sauri sai Ahmad ya nuna masa kayan dake kasan tebur din. “Kwashen abun nan ka san inda zaka kai su... ” Ya fada yana masa nuna da baki idonsa na kaiwa akan wani agogo da chewing gum kwara daya dake gefe agogon. He don't know why he find it so intereste to touch. “Mi komin wannan agogon” Mutumen ya dauko ya miko masa, sai ya karba yana dubawa agogo chewing gum diary na daya daga cikin abubuwan da his late wife Halima take bashi as a gift a idan yai birthday, tun kamin ta aureshi har bayan aurensu. Ji yai ba dadi tunawa da matarsa da yai, da kansa ya duka ya dauko cingon da wani karamin diary dake can gefe ya nufi kujera ya zauna. “Kasan wa ya min kyautar agogon nan da diary nan da chewing gum din nan?” “Wallahi ban sani ba ranka ya dade, su da yawa suka shigo kuma ban san waye ba cikinsu dan ba gabana suka aje ba” “Okay take the rest” Dorowarsa ya bude ya saka diary da agogon a ciki sannan ya bude chewing gum ya kai bakinsa. He can't remember when last na ci chewing gum sai yau hakan yasa ya ji ya masa tauri, or maybe saboda wannan karami ne ba irin mai tsada da ya saba ci ba. Haka nan kawai Halima ta fado masa a rai, did she deserved to work a kamfaninsa? Bayan dazu dazun nan ma ta gama zaginsa, ashe kuma ta san a kamfaninsa take aiko amman ta ci masa mutunci? Ko da yake shi ya kadeta kuma be tsaya ya dubata ba yai tafiyarsa, amman duk da haka ai be kamata tai masa rashin mutumci ba. Laptop dinsa ya janyo ya bude ya fara duba wasu abubuwan. After like 40 minutes Yunus ya shigo masa da wasu takardu, after ya gama masa bayani yake tambayarsa. “So ka biye shiriritar Siyama kasa am bata min office da gift ko?” Yunus yayi dariya. At least ai an saka ka farinciki, tunda birthday ka ne, ban saka kowa yayi ba amman dai na saka sabbin ma'aikatan mu ne su baka abunda ya samu” “Nope ka san ba komai ke burge ni ba” Har ya dauke kai sai kuma ya juyo da sauri. “Sabbin ma'aikata? Har da wannan farar mata tana nan ciki....” “Wace farar mata?” “Wacce na saka aka canjawa position dazun baka nan?” “Yeah amman na samu labari, har da ita dukansu na saka ai ita ta aje maka chewing gum da agogo” Jimmm Ahmad yai. “O.... Okay....” Ta fada yana daina tauna chewing gum tare da yatsuna fuska... I feel like na karo wani page anjima da dare 😝😝😝 amman ga masu comments kadai 🙄🙌 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣1️⃣ HALIMATU POV. Ba laifi sai na ji kamar inda aka dawo da ni a yanzu ya fi na farkon dadin zama, domin a can rubuce rubuce ne, a nan kuwa kula da masu shigowa ne kawai gashi sai fira muke tare da sauran ma'aikatan, daya mace ce wacce ta kasance kabila ce sai ni ta biyi sai maza uku, ni kadai ce ba ni da uniform a cikinsu, domin ni tufafin gida ne a jikina.    Ban yi awa daya a gurin ba aka kawo min wando da riga na kamfanin, irin na sauran ma'aikatan da suke gurin mai dauke da sunan kamfanin, tare da wani dan abu da ake sakawa a wuya wanda ke dauke da sunana sai kuma gurin saka hoto, har ga Allah bana son saka kananan kaya abu ga mai dan jiki balle ni da Allah ya horewa abun duk yadda zan so boyewaba boyuwa zai yi ba, na saka skirt ma suka bayyana balle kuma wando, na dade rike da tufafin ina da tunaninsa sakawa ko akasin hakan, sai dai na san idan har na ce ba zan saka ba zasu iya korata. Ba ni da wani zabi da ya wuce na saka din ai idan ina a reception din babu mai ganina tunda katon tebur din ya tare ni sai dai idan zan tashi kuma idan zan tashi zan iya canja tufafi ko kuma na saka mayafi. Bandakin kamfani na nufa na canja tufafi sannan na saka hijab dina na fito reception din a lokacin da na tsaya a inda ba a ganina sai na cire Hijab din na cigaba da aikina hankalina a kwance. Wani abun burgewa ashe na wadanda suke reception din har da abincin ake kawo musu da ruwa tsabanin da da sai dai yunwa da kashe ni.    Mu uku muka je cin abincin tare da blessed da Walid, muna cikin cin abincin yake dauko mana labarin sabon kamfanin da za ake tunanin budewa a wata jihar sai dai suna tantamar garin da za a bude, mun dade muna tattaunawar har nake bayarda shawarar da ace za su yarda da sun bude a Kano domin can ne cijiyar Kasuwanci, ko kuma Jos duba da yanayin garin Walid kuma yace Abuja, a haka dai muka gama cin abincin muka tashi muka koma gurin aikinmu su biyun da basu ci ba suka koma ciki dan cin abincin.   Ina tsaye a gurin sai ga wasu fararen mutune sun shigo, da fari dai na dauka turawa ne, a take hankalina ya koma gurinsu tun kan su karaso nake ta kallonsu cike da burge domin kusan sai nace ban taba ganin turawa a zahiri ba sai yau, sai dai na lura sauran abokan aikina ba kamar ni suke ba, wata kila sun saba ganin turawa ba kamar ni ba da na zama bakwaya har murmushi nake musu kamin su karaso.   Ko miye abun burge a farar fatar ma oho sai kace ni din ba fara bace ko da yke nawa farin mai kyau ne, domin na su ba shi da kyau kallo farin yayi yawa har wani kashe ido yake.   Suna isowa sa abokin aikinki ya tarebe su da yaren turanci su kuma suka masa magana da faransanci hakan yasa na fahimci cewar faransawa ne ba turawa ba kamar yadda nake zato. Hakan yasa na yi kaudin yin musu harbun da tambayar abunda suke bukata a dan abunda na iya na yaren faransanci. A take suka mayarda min da amsa, aiko nan dade ya kusa kashe ni wai ni na magana da wanda ba yare ba kuma ba yan kasa ta ba. Da suka fada min wanda suke bukatar gani wato shugaban kamfanin sai na fadawa Walid shi kuma ya nuna min yadda zan yi na kira na sanar idan bukatar irin haka ta taso, kamin na danna number wanda yace min shi ake fara kira a sanarwa, sai ga Yunus din ya fito daga cikin kamfanin ya tare su da far'arsa har ya basu hannu suka gaisa, sai dai shima na lura be iya faransanci ba kamar dai sauran abokan aikina. Godiya suka min da yarensu na mayar musu da godiyar nima sannan suka bi Yunus zuwa ciki. After like 15 minutes ya fito yana tambayar wai na iya faransanci ne sosai. “Gaskiya ba sosai ba gaisuwa kawai na iya sai dan abunda ba a rasa ba, ban iya sosai ba” “Amman za ki iya kula da su kamin mai fassara mana ya iso?” “Yes” “Good zo muje” Sai da na dauki gyalena na yafa sannan na bi bayanshi, sai dai a yanayin yadda yake tafiya ne yasa nai saurin cin masa duk kuwa da kasancewar ina tafe ina dingishi ne sai muka jera a tare muna tafiya a tare, ba laifi yana da sakin fuska da son magana ba kamar mugun gogan ba, a nan yake tambayar inda na iya yaren faransanci, na fada masa tun a secondary school na yaren yaren sosai lokacin da muna can sai dai shiga FUG yasa na manta da wani abu, ga kuma abubuwa na rayuwa sai na watsar da abun. Sai a lokacin da zamu shiga cikin office din ya bukaci na cire mayafin nawa, hakan yasa ni jin babu dadi wanda har ya bayyana a fuskata. “No ba wani dadewa za ki yi ba, za ki yi tambaye abunda suke bukata ne kawai sai kuma fara gabatar musu da abunda zan nuna miki kamin mai aikinmu ya iso” “Ba fa komai na iya a faransanci ba, ba zan iya wani dogon bayani sosai ba” “I know saboda kar mu barsu shiru ne, tun mun zama kurame mu da su” Ban musa ba na cire Hijab din kamar yadda ya bukata, daman can dankwalin atamfa ne a kai, ga farar riga da bakin wando na kamfani sai ya bada wani kala na dabam, na yi zaton su kadai ne a dakin taron, sai na tarar har da Angry Bird din ya wani shakimce a saman kujera yana ganina ya wani hade rai. Ni kuma na tsaya bakin kofa har sai da Yunus din yai min iso. Na shiga ciki na tambaye su abunda suke bukata na sha suka bukaci ruwa kawai, shi ma kuma da aka kawo ba su sha ba, abunka da marar yarda, haka nan dai cikin rashin iyawa na rika dan nuna musu abubuwan da Yunus ya nuna min, wanda suke a katon wani abu mai kamar tv kuma shi ba tv ba, da removed din hannuna na rika nuna musu kalolin zinarin da suke a ciki, domin ya fada min abun nan ja na jikin remote din kawai zan taba su za su rika canjawa da kansu. Muna haka sai ga mai fassarar ya shigo, na yi zaton idan ya shigo umarni za a bani na fice sai gashi ya saka ni cigaba da danna remote din shi kuma yana musu bayani da halshen faransancin, ina jin wani abu wani abun kuma bana gane komai, wani abun zai fada ma Ahmad da Yunus abunda suka ce ne sannan ya cigaba da yi musu bayanin, har akai aka gama Ahmad be ce komai ba, sai aikin tsutsar minti yake, ni kuma ban ma sake kallon inda yake ba. Sai da suka gaisa da shi sannan suka fice tare da mai fassarar, hakan yasa na aje remote din ina jiran a bani umarnin ficewa, amman Yunus din sai karin bayani yake ma Ahmad din. Ni kuwa hankali gaba daya yana gida ga garin ya hada bakin hadari kamar yadda nake hange ta cikin gilashin da ke gafenmu. “Ranka ya dade zan iya tafiya” Na fada ina kallon Yunus din a tare suka kalleni daga Ahmad din har Yunus ne. “Sorry yau mun baki aiki da ba naki ba” “Babu komai” Har na aje remote din ina kokarin juyawa sai yace. “Ta ina za ki bi? Na sauke ki” Kamin na bashi amsa Ahmad din ya tari numfashinsa sound so serious fuskarsa babu alamun wasa. “Shi kuma wacan aikin wa zai yi?” Nikam daman ba shiga motar zan yi ba, hakan yasa kamin ma Yunus din ya bashi amsa na ce wa Yunus din. “Na gode ranka ya dade zan fi sakewa idan na hau napep” Daga haka na juyo na fito daga office din ina mamakin irin kiyayyar da Ahmad ke min akan abunda har a gurin Allah bana da laifi domin ban aikata ba, wato yaji haushin da Yunus din yace zai rage min hanya ko waya fada masa ma shiga zan yi oho. Da tunanin hadarin na fito hakan yasa ban wani tsaya canja tufafi ba yafa mayafina na dauki kayan na saka riga a handbag dina domin ita kadai zata iya shiga sauran kuma na rike a hannu na bi hanya domin tuni abokan aikina sun wuce har wasu sun karbi duty. Ina tafiya aka fara yayyafi ban yi zaton zai yi karfi ba, hakan yasa na kara harama da zimmar kamin ruwan yai karfi na samu abun hawa, da ganin hadarin ba irin wanda idan an fara ruwan nan ba ne a daina, wata kila za a dade a na ruwan. Ko da na fita gate babu masu Napep sai achaba su ma kuma kowa da goyonsa, sai gudu suke ni kuma na maida himma sai tafiya nake ina waige waige ko zan samu abun hawan, ban nisa sosai da kamfanin ba aka sako da wani ruwa mai mugun karfi, hakan yasa ni cira kafa har da dan guduna na nufi inda wata yar rufar kwano wacce ke kusa da inda Kabir yake. Babu kowa a gurin hakan yasa na shige rumfar da sauri na fake, domin tuni ruwan ya fara jikani. Sai dai wani abun mamaki duk ruwan nan da ake Kabir na zaune a inda ya saba zama ruwan na duka kansa, ban san lokacin da tausayinsa ya rufe ni, da sauri na aje kayana da jakar hannu a gurin na fita a ciki a rumfar na nufi inda yake cike da karfin hali domin a yanzu kafar ta fi min zafi fiye da dazun. Da fari magana na fara masa akan ya taso ya bar gurin sai na ga yana ta kallona kamar be gane ni ba, hakan yasa na kai hannnu zan riko shi, aiko kamar jira yake sai ya hayayyako min yayi cikina yana zare ido abun be taba, ina baya baya yana cikina har samu sa'ar riko mayafina ya fisge shi gani a gafen titi hakan yasa nai unkurin gudu sai yai nasarar kai mun duka mai shegen zafi, ya kuma rikoni yana kokarin makureni. “Ni ce ni ce Kabir.....” Shine kawai abunda nake iya fada cikin ihu da daga muryar, tare da kokarin kwatar kaina amman ina karfin mace da namiji ba daya ba tuni ya samu sa'ar fara makurata, ga ruwan sama ana yi balle a kawo min agaji, ko ma ba a ruwan ba kowa ke shiga lamarin mahaukaci ba ballantana ma gurin babu jama'a sosai. Kamar daga sama na ji ana kokarin taimaka, sai duka ake kaiwa Kabir ta ko'ina ban san ko waye ba har sai da na samu sa'ar kubucewa daga hannunsa, ruwan dake sauka da kuma makurar da na sha bata hanani gane cewar Ahmad bane, abunda ban tana zato ba, ban tana tunani ba balle har nai mafarki yau yake faruwa a zahiri. Nikam ban tsaya komai ba ganin fadan ya koma tsakaninsu yasa na dauki mayafina da sauri na nufi inda jakata take na dauka tare da kayana na fara tafiya kamar an koroni ko waige inda suke ban sake ba. Sai da nai tafiya mai nisa sannan na soma tafiya a hankali ina cigaba ta taron Napep, cikin sa'a motar Abdallah ta wuce ni sai kuma ta dawo baya daidai ta tsaya daga can cikin motar ya bude min front seat. Da sauri na shiga jikina har rawa yake. “Ina kika fito?” Ni dai ban iya bashi amsa ba domin har yanzu ban gama dawowa daidai ba. “Ina kika fito...?” “Aiki” “Aiki da wadannan kayan? Wando ne fa a jikinki da riga..” Na dan kalli jikin nawa, ruwan da ya jikani yasa tufafin sun dan kama jikina. “Karki sake saka su daga yau, idan ba barki ki saka tufafinki na hausawa ba, ki daina aikin” “Am.... ” “Ba shawara nake ba ki ba, umarni ne” Ya fada yana daga min hannu fuskar nan tasa a hade kamar dai ba shi ba. AHMAD POV. Hannunsa ya kai ya ciro chewing gum din daga bakinsa sannan ya mike tsaye ya nufi window ya jefar da cingan din yana cigaba da yatsinar fuska.   Ai tun farko be kamata ya ci cingan din ba ko da ba ita ta aje masa ba balle kuma a hannunta ya fito macen da babu ta biyunta a gurinsa gurin tsana. Yawun bakinsa ya tofar a window Yunus dai be ce masa komai ba bayan kallon da ya bishi da shi sannan ya fice.   Haka ya wuni yana tofar da yawu kamar wani mai sabon ciki, yaba ta jin haushin tauna cingan din da yai, daga bisani ya koma jin haushin Siyama wacce ta bukaci ayi masa abun, kamin jin haushin ya koma gurin Yunus wanda yake ganin shi ya biye mata.   After sallah azahar Yunus ya shigo office din yana sanar masa cewar bakinsu sun iso. “Amman Dahir ya zo” “No yana kan hanya dai” “To ya za'ayi communication da su” “Karka damu da wannan, yanzu dai kaje ka gaisa da su” After haka ya fice, Ahmad ya bata minti biyar a zaune sannan ya nufi freezer dake office din ya bude ya dauko sweet ya bude ya saka a bakinsa, dan yasan ba zai je can yana tofe tofen yawu ba sai kace mai sabon ciki, idan ma be sha sweet din ba tashin zuciyar da yake ji ba ba zai bar shi ba. Sai da ya dauki rigarsa ya saka sannan ya nufi dakin taro, yana shigowa suka mike tsaye tare da bashi hannu ya gaisa da su da halshen nasara ya fara yi musu barka da zuwa duk kuwa da yasan ba lallai ace suna jin wani abu bayan welcome da kuma gaisuwa ba. A gurin daya saba zama ya nufa ya zauna, yana kokarin ciro wayarsa daga aljihu aka turo kofar dakin Yunus ne ya shigo, Halimatu na bayanshi ta tsaya daga jikin kofar har sai dai Yunus din yai mata iso, wani irin bugawa zuciyarsa tai, duk sai yaji ransa ya bace sai dai ba damar ya nuna a gaban mutanen a dole ta sa ya shanye, sai dai yana mamakin abunda ya kawo ta dakin taron. Takawa ta fara yi tana juya yai arba da mazaunanta sai yai saurin runtse idonsa duka biyu, can kuma ya bude dayar yayinda dayar take a makkale ya rufeta, sai kuma yai saurin rufewa yana jan tsaki a ransa. Be bude ba har sai da yaji ta fara magana da su alamar ta juyo kenan sannan ya bude ido, kallo daya yai mata yaga yadda kayan suka karbe ta sai kuma ya dauke kai. Har akai meeting din aka gama be bari ta san yana kallonta ba, ba ma ita ba ko Yunus da ke kusa da shi ba zai iya gano ya kalleta ba ko a'a domin ta kasa kasa yake kallonsa irin na munafukai. After sun gama ta bukaci fita sa Yunus ya nemi rage mata hanya a take Ahmad yai karaf ya hana shi, yana ta mamakin shisshigi irin nasa, after ta fice ya tabe baki ya tashi tsaye ya face daga kamfanin, office dinsa ya nufa yana kara jin bachin rai na kama shi, zaunawa yai saman kujerarsa ya rufe laptop dinsa sannan ya fito daga office din ya nufi gurin motarsa da sauri, so yake ko da za a sako da ruwan yana gida ko banza yau ai ranar birthday sa ne. A hankali yake tukinsa, sai dai kamar yadda ya kusan zame masa ibada kallon gurin da mahaukacin nan yake zama a kullum saboda abincin da Halimatu take ba shi yasa shi kallo a yau, yana tunani a yau kam ba zata tsaya ba tun da ta fita tana sauri kuma gashi garin har ruwa ya fara sauka, to his surprise sai ya hangota a gurin tare da shi, at first ya dauka ko wani abu ne mai kama da wasa daga baya ya fahimci kokuwa ce suke wanda be san dalilinta ba. “Ashe dai itama bata da hankali, daman can ba tai kama da masu hankalin ba” Ya furta sannan dan karawa motarsa wuta, kamin ya sake kallonsu da kyau ya fahimci dai fada suke, sai kawai ya faka yana ta kallon yadda mahaukacin ya kai mata duka kamin ya hango mahaukacin ya makureta har tana neman taimako. Cigaba yai da kallonsu, har sai da ya fahimci da gaske mahaukacin kasheta zai yi sannan yai unkurin bude motar, a take wata zuciyar ta hana shi, then ya fara tunani ai shi human being ne not like her, ba zai iya kallo ayi kissan kai ba. Cikin sauri ya fita daga motar ya nufi i da suke ya fara dukan mahaukacin ta baya har Halimatu ta samu sa'ar kubuce a hannunsa ta ranta a na kare sai fadan ya dawo tsakaninsu da mahaukacin shi da mahaukacin aka rasa mai hankali kowane kai wa wani duka yake, a cikin rashin sa'a mahaukacin ya naushi idon Ahmad ai take ya ji kalar garin ta canja, be san lokacin da wani karfin ya zo masa ba ya saka kafafuwansa ya buge Kafafuwan mahaukacin ya fadi kasa, a take Ahmad ya ranta a ciki na kare yana dafe da ido daya ya nufi motarsa a rikice ya bude motarsa ya shiga saboda wani azababben zugi da idon ke masa, @360 ya fisgi motar da ido daya da yake gani da shi. 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣2️⃣ Da hannu daya yake tuka motar yayinda dayan hannunsa yake dafe da idonsa, wani zafin bala'i idon yake masa ga ruwan da ake kama da bakin kwarya, har baya iya gani da kyau saboda karfinsu. A dole ya faka motarsa gafen titi, slowly ya dauke hannunsa daga idon da ke masa wani mugun zugi, ji yai idaniyar ta cika da abu mai kauri shi ba hawaye ba kuma ba ya san jini ne har sai da ya duba hannunsa. Jini a ciki kuma shine yake cika masa idon har baya gani da idon daya.   Lumshe idanuwan yai duka biyu yana sauraren yadda zugin yake shigar masa har cikin kansa, a rufe da idon ya saka hannun aljihu ya dauko wayarsa sai a lokacin yai kokarin bude idon daya yana duba iPhone dinsa wacce ta gama daukewa dip, sakamakon ruwan da ta sha, ba wayar kadai ba tufafin jikinsa ma sun gama jika seat dinsa balle kuma wayarsa. Iskar bakinsa ya bushar yanzu be san yadda zai yi ya kira Doc Nura ba balle yaji idan ma yana gari ko yana asibitin ko gida, daman can a tsarinsa be yarda wani likitan ya duba shi ba sai family doc su, domin ya yarda da aikinsa hundred percent. “Ba ma ita ce mahaukaciyar ba ni ne mahaukacin, taya zan shigar mata fada? Fadan ma da mahaukaci dan'uwanta? Matar da ta kashe min yarinyar? What's is wrong with me?” Ya fada yana jin haushin abunda ya aika.. “Bata ma tsaya ta dubani ba fa sai kawai ta gudu, idan ma kashe ni zai yi ita dai ta tsira, mahaukaciyar banza i hate her” Ya sake fada cikin fusata yana cizon bakinsa. A gurin ya tsaya har sai da ruwan suka dauke gaba daya sannan ya karasa tukin zuwa gida kamin ya isa har wani jiri yake ji cikin kansa. “Ai I'm human being be kamata ina gani ayi kisan kai ba, shiyasa na taimake ta, amman yanzu na gano matar nan bakincikina take so take ta illatani bayan ta kashe min ya, be m kamata na barta tana aiki a kamfani na ba ai” Shi kadai yake ta magana da kansa har ya faka motarsa a harabar gidan, yana kokarin bude motar ya fita ya tambayi kansa. “Ko ma miya kai ni fada da mahaukaci? Da mahaukaci da mahaukaciya suna fada ni mai hankali miya kai ni ciki?” After ya fito daga motar ya bawa kansa amsa. “Kaddara.... ” Part dinsa ya wuce, yana shiga ya fara ziyartar bandakin ya wanke fuskarsa, ya saka tissue yana tare jinin a hankali sannan ya dawo dakinsa ya dauko dayar wayarsa da ke gida yana kokarin kiran Doc Nura. “Hasara nawa ga saka ni a yau? Ta saka na jika tufafina ga idona daya ga phone dina.....” Wani irin haushinta ne ya kara cika msa zuciya. Sai da ya tabbatar Doc Nura na aibitin sannan ya canj tufafin jikinsa ya dauko key din wata motar ya fice ba tare da ya leka part din Hajiya ba, domin baya son ya tashi hankalinta. A asibiti babu kalar dariyar da Doc Nura be msa ba. “To kai yanzu miya kaika raba fada da mahaukaci? Ai gashi an bak tukuici” “You make me hate her more” “Wai wacece wannan?” “Wata mahaukaciya ce mai ruwan masu hankali” Ya hada fuska babu annuri can kuma yai murmushi. “Ita ma fa taji wuya, ba da wasa ya moreta ba” Dadi yaji tun da ita ma ta ji wuya, but maganar Allah shi yafi kowa shan wuya tunda shi be shi yaja mahaukacin ba. Bayan Doc ya duba idon ya bashi maganin na sha da shafawa a idon ya kuma fada msa yadda zai kula da ido. After ya dawo gida ya kira shiga part dinsa ya kiran Yunus. “Yu akwai wani mahaukaci da ke kusa da kamfanin mu, daga hannun dama gurin wani shagon kwano, za ka iya gane shi?” Sai da Yunus yai tunani sosai sannan ya amsa masa da. “Yes na gane shi kullum nn yke zama” “Ka sa a dauke shi a kai shi gidan mahaukata” “Why?” “Why? Ya zan baka umarni ka tambayeni why?” Ya amsa a fusace, kamar Yunus din ba abokinsa ba ne, saboda yau yana cikin zafin kai. Bayan ya kashe wayar yaje gaban madubi yan duba idon, idonsa daya yayi kwancin jini a ciki gaba daya gefen idon ya kumbura, abunka da farin mutun har wani ja gurin yai.   “Ina zaman zamana ta ja min masifa.....” Ya karasa maganar ta tari sai jini ya biyo baya, daman haka yake yanzu da ransa ya bace sai ya fada tarin jinin sai ciwon kirji.   Toilet ya nufa aman jini yai ba kadan ba, shi kanshi sai da abun ya dan tsorata shi, har yana zargin wata kila saboda ya sha ruwan sama ne abun ya kara hade masa, wanka yai sannan ya dawo dakinsa ya sha maganinsa ha kwanta. Sai 4:21 ya farka, sallah ce abunda ya fara gabatarwa sannan ya duba idon nasa kamin ya nufi part din Hajiya. Tana ganinsa hankalinta yai mugun tashin musamman idon nasa wanda ta hango jan jini a ciki. “Miya same ka Gwarzo?” “Hadarin nan ne da ya taso ina kokarin shiga, mota sai kasa ya shigar min ido” “Wannan ba kasa ba ne, hannu ne ga kwancin shi nan a idonka, kaga ni ko shiyasa bana son kana zuwa kana dadewa a waje, na sha fada maka da kun gama aiki ka rika dawowa gida, na san halinka da zuciya wata kila kaje ka bugu wani ya rama” Hannu ya kama yana kokarin zaunawa da murmushi a fuskarsa. “Haba Hajiya ai na girmi wannan, Wallahi kaddara ce kawai amman In-Sha-Allah ba zai sake faruwa ba” “Bari na kira Doc Nura” “Naje gurinsa ya bani magani ya duba idon” Sam bata yarda ba har sai da ta kira shi da kanta tai magana da shi ya tabbtar mata da cewar ya dubashi sannan hankalinta ya kwanta. “And daga yau ba zaka je aiki ba sai nan da one week” Da sauri ya kalli Hajiyarsa yana sakin baki. “Amman Hajiya kin san idan ba da ni ba wani abun ba zai yiyu ba” “Doka ta ce wannan” Ta fada fuskarta babu alamun wasa. “Yaro ba san ciwon kansa ba, sai idan ana nuna maka abu kace kai ba yaro ba ne” Rasa yai abunda zai ce mata, ba zai iya karya dokarta ba, kuma ba zai so fashin zuwa aiki ba, zai iya amfani da bakin gilashi ya rufe idonsa. “Idan an yi magariba ka kwanta karka tashi sai an yi isha'i, zan dafa maka carrot da allayau da wake yanzu suma suna gyara ido” A dolen dolensa ya amsa mata da okay, ta tashi ta shiga kitchen da zimmar dora masa girkin, shi kuma ya bita da kallo yana ta tunanin randa Hajiya zata yarda da cewar ya girma san ciwon kanshi. HALIMATU POV. A hankali na kalleshi, fuskarsa a hade take sam babu alamar wasa a umarninsa. Na sani ba lallai ne su yarda su canja min aiki ba, balle kuma har su yarda na rika saka wasu tufafin na dabam, Ahmad ba zai min wannan lamanin ba, ko a da balle a yanzu da ba san yadda na baro shi da karfi ba, ba laifi ya nuna kulawarsa tun da har ya taimaka min ba dan shi ba wata kila da yanzu na zama gawa, domin ba kadan Kabir ya makure ni ba. Tunanin nake ta yi ni kadai ina shafa wuyana da har yanzu ciwon yake min. “Amman za su iya cewa ba za su yarda na daina saka kayan ba” “Sai ki daina aikin” “Idan na daina aikin da me zan kula da kaina? Kamin na samu wani aikin abu mai wahala, kuma ka san bana da mai taimakona a yanzu sai Allah” “To sai ki samu miji ki yi aure, ki rike Namra da Amal Aiman da Adnan kuma ki maidasu gurin Babansu.....” Kai tsaye ya fada min maganar nan ba tare da ya kalleni ba. Wani irin kallon mamaki nai masa, ban yarda daga bakinsa kalaman nan suke fitowa ba, sam ban yarda Abdallah na ne ba, taya zai min wannan maganar me yake nufi da ni? To sai ki fitar da miji ki yi aure...... Kalmarsa na ta maimaita min kanta a cikin kaina. “Kalmar ka ta min nauyi Abdallah, tana kokarin rikecewa, ban gane komai ba” Ajiyar zuciya ya sauke ba tareda ya kalleni ba ya ce. “Har gobe ina sonki, har gobe ina kishinki, har gobe ina tausayinki ki saka wannan a zuciyarki, kuma wannan kaddara ta ce zan mutu da sonki.... Na sani kuskure ne na so matar yayana bayan ya rabu da ita, sai dai sonki ya dade a zuciyata tun kamin ki auri dan uwana, kin riga kin lalata komai Halima, Hajiya ta min katanga tsakanina da ke....” “Har da aurena....?” Na tambaya murya na rawa, idanuwana kuma suka soma aikinsu. “Taya kike tunanin samun farinciki a auren da uwa bata so? Dan'uwa baya so? Da wane irin ido za mu kalli al'ummarmu? Zan mutu da kaunarki Halimatu wannan ita ce kaddarata.....” Ban taba jin abu marar dadi irin na yau ba, Abdallah be taba fada min wata bakar magana ba irin yau, gaba daya sai na nemi farincikina da kuzarina na rasa, wani irin bakinciki ya cika min zuciya. “Sauke ni a nan” Na fada ina kawarda fuskata, ba musu ya faka motarsa gefen titi ni kuma na bude na fita, ina jikin babu kwari kamar na fadi. Key yai ma motarsa ya kara gaba ya bar ni a gurin tsaye ina hawaye. “Shiyasa ya daina kula ni? Miyasa na auri Abdulhamid tun farko? Miyasa tunani be bani Abdallah ba sai a yanzu? Miyasa kaddara take min haka? A lokacin da ya kamata ba jidadi sai wata matsalar ta saka ni a gaban? Gaba daya ban san jindadi a rayuwata ba....” Na fada ina fashewa da kuka, ruwa na ta dukan kaina. Kasa na fara tafiya daman tazarar dake tsakanin inda ya sauke ni da gidanmu babu nisa sosai, tun ina tafiya ruwan na sauka da karfi har suka rage, ban daina tunani da kuka ba. Ruwan da ke saukowa ya taimaka min da ya hana a gane ina hawaye saboda yana dukan kaina. A lokacin da na shiga gida kowa yana daki ya fake, kai tsaye na nufi dakin Mama, ban saba shiga ba sallama ba amma a yau haka na shiga babu sallama mana ma iya kallon wake falon waye baya ciki. Dakin Mama na shiga na cire tufafin jikina na dauki zanenta na daura, tana ta kallona da yadda nake motsa jiki babu kuzari. “Lafiya kike yau kuwa?” “Nima ban sani ba, ko lafiya nake ko ba lafiya nake ba” Na amsa mata ina hawaye. “Miya faru” Juyowa nai na kalleta. “Mama ni ce babba a cikin yayanki, ya kamata na zama mai hankali da tunani ko? Da hangen nesa amman duk ban zama ba” Zaunawa nai kusa da ita na kai jikina a cinyarta na kwanta ina kuka. “Fada min matsalarki miya faru” “Mama Abdallah..... Ya fada min a yau ba zai aureni ba” Murmushi tai. “Halimatu kenan, daman taya za'ayi Abdallah ya aure ki? Bayan dan'uwansa ya aure ki? Kuma dan'uwan nasa yana nan a raye? Mu ma ai ba zamu bari ki aikata wannan kuskuren ba, domin na san kiyayya da gaba ce zata shiga tsakaninsu wanda mahaifiyarsu ba zata so hakan ba” “Amman.... Ba.... Haramun...ba ne... ” “Ke kika san wannan, abubuwa da yawa yanxu al'adarmu ta mayarda su haram saboda kunya da gudun samun tsabani, kin yi kuskure Halimatu da dai tun farko ne kina da damar zabar Abdallah ki bar Abdulhamid amman ba ki yi ba, tun farko Abdallah ya kamata ki aura na ta nuna miki amman kika kasa ganewa, mutum da be taba kyamar yayanki ba, be taba nuna gajiyawa a taimakonki ba, shine mutumen da ya kamata ya zama abokin rayuwarki tun farko” Dagowa nai na kalleta. “Amman wani abu be taba shiga tsakanina da Abdulhamid ba....” “Mutane ba su san da wannan ba”   Tashi nai daga dakin gaba daya, na nufi dakina, na zauna saman katifata ban ji ina bukatar komai ba sai kuka da nadama. A ranar ban rumtsa ba har sai da na rubuce labarin kaddarar rayuwata tas a jikin takardar da Abraham ya karbo min.   Da akam ban yi niyar zuwa ba, amman yanzu zanje saboda yara wadanda ke ta daukin zuwan.   Misalin takwas da rabi na dare aka aiko ana kirana, na san be wuce Abraham ba, wannan karon ban musa ba na saka Hijabina na fita, a inda ya saba tsayuwa na nufa yana tsaye a gurin jimgine da motarsa yana kallona har na karaso. “Ya kike?” “Ina lafiya” Na amsa ba tare da na kalleshi ba. Sai kuma yai shiru yana kallona. “Kamar kina cikin damuwa” Sai a lokacin na kalleshi. “Kaine karin damuwata, da zaka daina bibiyata da na samu salama, ka tafi na yafe maka, kaima kana cikin kaddara ta ne” “Za ki aureni kenan?” “Ba zan aureka ba” Na amsa masa ina kuka. “Ko da zan musulunta?” “Ko da zaka aikata abunda ya fi musulunta, idan zaka musulunta ka musulunta saboda Allah kawai, saboda gudun azabarsa, saboda tsoronsa saboda kaunar Annbinsa, karka musulunta dan ni domin ni bana tabbata amman Allah tabbatacce ne, wanzanje wadatacce, tsarkaken, tsabtatacen, ka musulunta saboda tsoron wuta da kwadayin aljanna, zaka iya musulunta a yau saboda ni gobe Allah ya karbi rayuwata, shi zaka ci gaba da musuluncin ne ko zaka daina? Amman idan ka yi saboda Allah shi Allah tabbatacce ne, imaninka zai tabbata har Aljanna, kada kai komai saboda ni a yanzu ba aurene a gaba na ba, bana jin zan sake soyayya ma balle aure” “Saboda me....?” “Saboda mutumen da nke so, ba zai taba aurena ba, ya fada min zai mutu da so na a ransa, ni kuma zan rayu da kaunarsa har izuwa ranar da ajalina zai riske ni... ” Na karasa cikin kuka. “Wane mai sa'a ne wannan?” “Wani ne wanda ya so ni a lokacin da duniya ta guje ni, ya taimaka a lokacin da bana da mai tsaya min, ya so yayana a lokacin da ubansu ya guje su” “Then miyasa yanzu ba zai aureki ba?” “Saboda na auri dan'uwansa, mutumen da ka keta min haddi a gidansa, dan Allah wannan zuwan ya zama na karshe a gurina, ka barni na ji da damuwata” Na karasa ina hade hannayena ina rokonsa. “Ke ba ki yarda haduwar mu kaddara ba ce? Taya za ka yi mace fyade a dare a lokacin da kake boyon kanka, sai kuma ka dawo da rana ka kawo kanka ba tare da fargabar komai ba? Da zaki buda zuciya babu abunda za ki gani sai kaunarki, son ki yasa na ke sha'awar barin addinina na dawo na ki, zan iya hakurin zama da ke a haka da soyayyar wani a ranki, da sannu zan koya miki so na har ki aminta....” “Babu namijin da zai koya min so a yanzu, sai da safe.... ” Ina fadar hakan na juyo na nufo gida ina jinsa yana kirana na kina amsa har na shigo gida. Tun daga ranar babu ranar da bana bachi da bakinciki, sai a yanzu na gane cewar na yi kuskure a lokacin da babu hanyar gyara kuskuren. Daga lokacin ban sake zuwa aiki ba, umarnin Abdallah ya hau kaina na cewar na bar aikin idan ba za su canja min tufafi ba, ban tafi na fada musu ba sai dai na san mawuyacin abu ne su yarda su canja min, balle kuma na jawa mai kamfanin fada da mahaukaci ko ya ma suka kare oho.   A ana gobe children day, Aminu ya sallamo min, ban fita ba hakan yasa ya nemi izinin shigowa cikin gidan ya shigo ya same a falo ina gyara tufafin su Aiman. Da sallama ya shigo na amsa masa kaina babu dankwalina ga gashin kaina ya sha tsiro kanana gwanin sha'awa.   Tashi nai naje na dauko Hijabina na saka sannan na dawo na zauna. “Yanzu Halima kin fi son rayuwar yaran nan ta tagayyara? Ba sa nan basa can? Haba Halima ko ba dan ni ba ko dan yara ai kamata ki duba...” “Kamin ka sake ni ya kamata kai wannan tunanin ba a yanxu ba, a iya tunani baka shaye shaye Aminu sai neman mata miyasa kwakwalwarka take ta nuna maka cewar zan dawo gareka?” “Shi ma Wallahi na daina, na riga na gane kuskurena Halima, kuma na yarda abunda ka aikatawa yar wani za a aikatawa, kuma zaka dandani dacin abunda ka aikatawa matar wani a gurin matarka” “Shiyasa ka rabu da ita kenan? A lokacin ne ka gane cewar ina da matsayi a rayuwarka, shiyasa na dawo gareni, na jidadi idan har ka shiryu da gaske, domin har gobe kai ubansu Namra ne” “Ban taba ganin mace mai hakuri da kawaici ba irinki Halimatu, wata mace bata taba so na kamar yadda kika so ni ba, ban gane hakan ba sai byan na rabu da ke, da farko arzikina ya fara karaya, sai aka fada min saboda na rabu da ke ne, arzikin yana tare da ke, amman kin san me? A yanzu na gane mutanen nan karya suke fada, ba saboda na rabu da ke na sara wasu abubuwan ba, saboda na ci amanarki ne kuma a maimakon na zauna da ke a haka sai na sake ki, na kuma kyale ki da hidimar yara, wanda hakkina ne, shiyasa Allah ya nuna min sakamakona tun a nan duniya” “Hakan yana da kyau ko ba komai ai yasa ka shiryu, ina maka murna” “Ba murna kadai nake son ki taya ni ba, ina son ki dubeni da idon rahama ki tausaya min dan Allah” “Idan ma ka zo nn ne saboda ka fada min ka shiryu to ka yi kuskure, ka daina dogon mafarki a kaina, ni a yanzu na maka nesa, tun daga lokacin da na baro gidanka ban sake sha'awar zama da kai ba” “Yaran mu hudu fa Halima, kin fison ki auri wani ki bar uban diyanki? Wa zai kula da su kamar yadda ke za ki yi?” “Ka auro musu wata uwar mana, idan baka da wacce kake so ni zan iya nemo maka” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Ya fada yana dafe kansa, ni kuma na dauke kayan na fice daga falon na bar shi ciki. A ranar da zamu je gurin da ake bikin na ranar yara da duniya, na shiryawa yarana cikin kananan kaya sannan ni kuma na saka bakar abaya, tun takwas da rabi mu ka bar gidan gudun kar mu yi latti kuwa da kasancewar akwai mintuna talatin kamin a fara. Ba a bar mu mun shiga ba sai da na nuna musu dan karamin katin hannuna, sannan suka bude mana kofa, wani irin katon filine mai kamar stadium an jera kujera sai kuma wata yar rumfa da akai daga sama wacce na kyautata zaton ta manyan bakine, ko da muka shiga har an fara gabartawa ana yi wa mutane maraba, a inda aka nuna min na zauna gurin na musamman inda yaran manya da iyayensu suke zama, tsabanin dayan bangaren da yake na talakawa irina, akwai taron mutane sosai ba Lalla ne ka iya ganewa kowa ba.   Bayan na zauna na kalli wata macen yar sanda dake tsaye kusa da ni na tambaya gurin da ake aje takadar ta nuna min wani dan karamin daki da zan shiga, a gurin na bar su Namra na shiga ni kaina sai na samu wani kwando na gefe ta tarin wasiku a ciki, a gefen kusuwar kwandon na jefa wasikar sannan na fito. Bayan na dawo na zauna ina rabon ido na hango Ahmad zaune gaban teburin manyan baki, wani irin faduwa gabana yai sai nai kokarin kawardar fuskarta ima satar kallonsa, sanye yake da shadda ash color sai da hula kalar shaddarsa, idonsa kuma anye da bakin gilashi wanda ya kara masa kyau da kwarjini. Fuskarnan a hade sai sham kamshi yake, yana kallon mutane one after the other. Sai a lokacin kunya ta kamani ya kamata naje nai masa godiya abunda yai min, ban je ba ban ma sake komawa kamfanin ba, ko ya suka kwashe da Kabir din ma oho, sai dai ina da tabbacin a ranar Kabir be gane ni bane saboda ina sanye da tufafin da ban taba sakawa ba, kuma gashi ana ruwa. Duk wani abunda ake idonsa na kai, kamar yadda nawa ma yake kai, garin kalle kalle na na hango Abraham zaune a daya daga kujerun da aka tanadarwa yan kallo, muna hada ido ya dago min hannu yana min murmushi ni kuma nai saurin kawar da fuskata. Muna zaune a gurin har akai abubuwan da za ayi sannan aka fara gabatar da wasar numbobi jikin katin aka fara kira har aka kira number mu 17. Fita muka yi tare da yarana muka shiga filin da aka tanadar mana, sai a lokacin na lura da cewa ba ni kadai ce uwa bahaushiya ba a gurin, akwai wasu uwayen hausawa biyu bayan ni. An raba an sawa gida uku uku ne, wanda hakan yasa hankalin kowa ya dawo kanmu ciki kuwa har da Ahmad. Da farko daukar kwai ne akan spoon daga gurin wani dogon tebur zuwa inda ko wace uwar take, yaranta za su dauko da gudu su kawo mata sai ta karba ta saka a gidansa, idan aka girga ko daya be fashe ba to ka ci wannan gasar, na biyu kuma debo ruwa ne murfi bottle zuwa inda anke har a cika wani karamin bokiti, na ukun kuma ko wane yaro sai saka safa a kafarsa ta dama sai yai tafiya da ta hagun har ya isa gurin mahaifiyarsa idan be taka kasa da safar ba su ma sun cinye. A hudu kuma wanda shi ne na karshe za abawa ko wane yaro damar rubuta dalilinsa na son cin wasar da kuma wanda zai sadaukarwa. Yara uku kawai suka bari na shiga da su duk kuwa da kasancewar dukansu Abraham ya siya musu tickets din, sai dai sun yi hakan duba da wanda za a hada ni da su, daga mai yara biyu sai uku. Sai da suka fara bawa ko wane yaro takardar da biro suka ware kowa dabam yai rubutunsa sannan suka karba,sannan aka soma wasan. Ba zan yabi yarana kadai ba, domin a na ga wasu yaran da suma suka maida himma suna ta kokarin ganin sun ci kamar yadda nawa yaran ma suke har abun ya soma bani tsoro, na sani idan ban ci ba yarana ba za su ci dadi ba, kamar yadda nima ba zan jidadin ba ko dan kwallafa rai a kudin ba, akwai ciwo ace ka shiga gasa kuma baka ci ba. Sai da muka fara karawa da mutane farko mu kai nasara a na biyun ma muka yi nasara haka a hana hudu har na karshe ma Allah ya ba mu nasara duk kuwa da kasancewar a lokacin jikinsu Namra da Adnan da Aiman yayi sanyi domin sun gaji sosai. After mun gama aka saka muka koma saman muka tsaya tare da magabatarwa, sannan suka karbi account number kowa, a lokacin da muka shiga garsar mun fi mu ashirin da daya amman da aka gama mu shi kawai aka tsayar a gaban gurin. Sai da aka fara karanta abunda yan ko wane team suka rubuta a takadar, idan an gama sai a fadi number team din sannan a fadi sunan wanda ya rubuta, sai kuma yan team din su daga hannu. A lokacin da aka kawo gurin na mu, abunda Aiman ya rubuta shi Adnan ya rubuta haka ma Namra. ‘Momy ta mana alkawari idan mun ci zata biya maka kudin makaranta da su, kuma zata siya mana kayan wasa’ A gaskiya na ji kunya na ji kunya sosai a lokacin da aka karanta cewar wai idan na ci zan biya musu kudin makaranta, duk sai na ji kamar na muzanta, a gurin fadin abun wasan ne ya sha babban ita Namra ta ce teddy, Aiman yace keke, Adman kuma yace mashin din nan na yara. A gurin sadaukarwa kuma kowa yace idan ya ci zai sadaukarwa Momy wato ni kenan, ban da Namra wacce tace idan ta ci zata sadaukar wa kawarta wace ta rasu wato Baby Namra. Ba kadan abun ya taba min zuciya ba, wato har yanzu Namra bata manta da kawarta ba. 3rd position aka fara sanarwa, wato team 13, a take gurin ya garwaye da ihu ana ta taba musu a lokacin ne bugun gabana ya soma karuwa, ina cikin masu tabawa ammn hakan be hana ni tsorata ba, ni da sauran masu jiran sakamakonsu. A na biyun ma an yi ihu, an taba musu wato team 6. Mai sanarwarwa wacce yar jarida ce a gidan redio sai da ta dauki lokaci tana jan rai har sai da tsoro ya kama duk wani wanda ke cikin wasan hakan tasa na runtse ido ina ta addu'a, Namra kuma ta rike min rike da duka karfinta ta rumtse ido. “The winner is....... Is..... Is....... ” Haka tai ta jan abun kamin ta fadi. “Team 17........” Wani irin mahaukacin tsalle Namra ta daka ta dire tana ihu tare ta rumgume Aiman suka fashe da kuka. ba ita kadai ba, ni kaina hawaye na ke abu ga mai shawaye kusa, Adnan ma rawa ya fara har su jujuyawa, kowa taba mana yake ciki har da Ahmad da ke kallonmu da Murmushi a fuskarsa. Sauran ba su ci ba suka sauka daga stairs din sai muka rage team uku kawai, sam ban lura da mahaifiyar Ahmad ba har sai aka kirata ta bada award ga mutanen na uku, a lokacin ne nake jin suna kiranta da tsohuwar shugabar ma'aikata, a na biyun aka kira wani kwamishina ya ba su award. A lokacin da aka zo gun mu sai aka gayyato Ahmad Muhammad Gwarzo, sai da ya fara ba ni cak din kudin sannan sannan ya gaisa da Adnan da Aiman, kana ya risina ya shafa kan Namra ya sumbanci goshinta. “How are you my dear” “I'm fine” “Congratulations” “Thank you Sir” Ita ta mikawa Award din sannan ya tsaya aka dauke mu hoto kamar yadda akewa kowa. Idanuwa ba su sauka a gurin kowa ba sai Abraham wanda ke a tsaye yana taba mana tare da yin well done da hannunsa yana murmushi. Sai da aka gama komai sannan muka koma gurin mu muka zauna tare da sauran mutane na kusa da mu suna ta tayamu murya, kasa hakura nai har sai da na kira waya na sanar a gida sannan na maida hankali gurin shiri na gaba wato karanta wasikun uwa. Duk wacce aka karanta wasikarta akan ce daga uwar wane da wane matar wace, sai ta taba mata mai gabatarwa ta yi maganganu akanta sannan a cigaba. AHMAD POV. Ba kasafai ya cika son irin wadanna taron ba, saboda dadewar da ake ga kuma tahaniyar mutane da speakers wandanda suke takura masa. Amman a haka ya daure tun da kusan shine babban bako a gurin kuma abunda aka saba yi a ko wace shekara ya zame masa dole a bana ma ya tsaya ayi da shi. Babu abunda ya burge shi kamar kalaman Namra na cewar idan ta ci zata sadaukarwa yarsa Baby Namra abunda be yi tunani ba, ko ba komai hakan da tai ya saka masa sonta kuma ya saka ransa yayi fes a taron, duk kuwa da kasancewar a farkon ganinsu be yi murna ba, babu abunda be ayyana aransa ba na ganin har da ita a gasar. Yana kallon agogon hannunsa ake karanta wasiku wanda yake sa ran ba za a gama karantasu da shi ba, be natsu sosai ba har sai yaji mai gabatarwar tana maranta labarin wata kalar murdaddiyar rayuwa, wata kalar rayuwa ce mai wuyar fassarawa, mai wahalar gaske, ga tarin tausayi da taba zuciya duk wanda labarin ya samu masauki a kunnensa, ga shi kadai ba kusan duk wanda ke gurin sai da zuciyarsa ta sosu da labarin msu saurin kuka a take suka fara hawaye. “Daga wata uwa mai kaunar yayanta.... ” Mai gabatarwar ta karasa cikin muryar kuka tana daga takadar sama. “Wace uwa ce wannan dan Allah? Wacece ita? Dan Allah ko wacece ke ina son ganinki ina son na ganki kawai, hakika ke jaruma ce jajirtacciya, kuma tsayayyiya mai karfi zuciya you deserve an award....” Taja mashina sannan ta cigaba. “and... Dan fashin da yake bibiyarki zai iya cutar da rayuwarki ki san da wannan, ni ko ba zan iya ba ki kariya ba na san jami'an tsaro za su ba ki, kuma In-Sha-Allah zan tsaya miki har ki samu salama, ba bayyana ki zan yi ba, ba nunawa kowa fuskarki zan yi ba balle har na fadi sunanki, taimakonki zan yi, and i promise you a cikin albashi na na wannan watan kina da 20,000 dan Allah ki same ni ko a ina ina son ganinki, ko wace irin uwa ce ke ina son ganinki dan Allah....” Cikin kuka Ummulkhar take fadin hakan hannunta rike da loudspeaker dayan kuma rike da takardar yayinda idanuwanta suke zubar da hawaye. Babu wanda zuciyarsa ta raya masa sai matar nan, sosai ya maida hankali yana kallon gurin da take zaune tare da yaranta, the way ta take sharar hawaye ya kara karafafa zatonsa a kanta, labarin yarsa ya shigo ciki duk kuwa da bata fadi sunansa ba ko sunan yarsa sai dai ta fadi cewar mahaifin yarta ya zargeta da kisan yarsa saboda kaddarar mutuwarta ya fada mata, kamar yadda kadarar gushewar hankalin abokin aikinta ya fada a kanta, an keta mata haddi an ketawa yarta, mijinta ya ci zarafinta, a kokarin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa, ga labarin samun aikin kamfanin da tai ya shigo ciki sai dai shi ma bata fadi sunan kamfanin ba..... Wani irin kallonta yake, har ya ji kamar gilashin dake idon sa ya tare ganinsa sai ta ya cireshi yana cigaba da kallonta, ita kuma ta soke kai kasa yana ta latsa waya tana sharar kwalla, wa akai wa fyade? Wacen karamar ko babbar? No wait mutunen da take bawa abincin a kusa da kamfaninsu abokin aikinta ne? Is that why take kokarin kula da shi? Waye mijin na ta? Waya ke bibiyarta? A lokaci daya ya jerowa kansa wadannan tambayoyin, da bashi da amsar su, and he can't take his eyes on her kamar his life defend on her, tun bata lura da kallon da yake mata ba har ta lura ta soma rasa natsuwarta, sai a sannan ya saka gilashin idonsa ya cigaba da kallonta ta yadda ba zata fahimta ba, zuciyarsa cike take da tambayoyin da ita kadai zata iya amsa mashi su, ita kadai duk wannan abun akanta? Be tana jin labarin da ya shiga zuciyarsa ta tsuma zuciyarsa ba irin na yau, bw tana jin labari mai tausayi da tashin hankali ba irin yau, kuma a haka she's still alive tana ta farincikinta ita da yaranta, har akai abunda za ayi a gurin aka tashi be kawarda hankalinsa daga kanta ba..... ______________________________ Yau na yi 5,176k words na biya bashi 🙌😍 #Team Aminu #Team Abdallah #Team Ahmad #GN #KhadeejaCandy 7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2 *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣3️⃣ ABDALLAH POV. He's walking slowly tun daga inda ya aje motarsa har zuwa cikin falon Hajiya, gidan sai kamshin sabon fenti da aka yi jiya yake. A gajiye ya shigo falon sai ya tarar babu kowa sai sanyin ac. Zaunawa yai a saman sabin kujeru da Hajiya ta sake ya ciro wayarsa yana latsawa, ya kusan minti talatin a haka sannan Hajiya ta fito rike da wuka da katon mangoro a plate. “Husani kai ne ka shigo” Ya dago a hankali ya kalleta. “Eh Hajiya barka da yamma” “Yauwa sannu dai, ya aikin? Yau baka shigo da safe ba” “Na fita aikin ne da wuri saboda tiyati za ayi, shiyasa” “Okay abincin fa akawo?” “A a gida zanje yanzu” Daga haka bata sake ce masa komai ba, shi ma kuma be ce mata ba, daman kusan kullum idan ya shigo gidan shiru yake ko wata maganar ake sai daiya bisu da ido. “Ana ta shirye shiryen biki har yanzu baka ce komai ba” “Allah ya sanya alheri” Ya fada a takaice, sai kuma yai shiru kamin ya sake kallonta. “Hajiya na yi wani laifi” A take ta dago kai ta kalleshi da sauri. “Mi kai?” “Kin min tsakani da Halima, tun daga lokacin ban sake kula ta ba, sai kwana goma sa suka wuce, na ganta a hanya tana tafiya da tufafin da be dace ba, hakan yasa na tsaya na dauke a motata saboda kare mutuncinta, ki yafe min dan Allah” “In ban da kai da abun ka, miye amfanin kare mutuncin macen da bata san mutuncin kanta ba, da wata ce ai ba zata yi shigar banza ta fita ba, talla take yi kenan Allah ya kyauta” Yawu ya hade da karfi da ba Hajiya ba ce da be lamuncin jin wani kalami marar dadi daga bakin kowa ba akan Halimatu idan ba zai iya cewa komai ba to ba zai saurara ba. “Wato dai na gane ba zaka iya fita daga tsafgar yarinyar nan ba, saboda ka samu salama kuma ku samu fahimta da dan'uwanka yasa na yi muku tsakani amman hakan be wadatar ba, tun da ga shi nan har yanzu ba ku jutuwa da juna, kuma ka kasa daina kulata, har yanzu dai tana nan cikin ranka, yarinyar da ta haifarda rashin jituwa tsakaninku? Yanzu shirye shiyen auren dan'uwanka ake amman babu ruwanka komai sai dai ka bishi da ido haka ake? Ku uku kawai Allah ya bani idan ba ku hada kai ba ya kuke son zama?” “Ba daga ni ba ne Hajiya, Abdulhamid yana ta ganin laifina ne har yanzu, ko magana nai masa sai idan yaga dama zai amsa ni” “To ai dole ya rika maka haka, taya zaka rika bibiyar matar da ya saka? Wacce ta zama makiyiyarmu? Ta ruguza rayuwarku?” Kallon mahaifiyar tasa yai ya dauke kai, wani lokacin idan tana yin abu kamar wacce bata taba karatu ba, ne san abunda yasa son zuciya yake rinjiyarta ba. Be ce sake ce mata uffan ba har tai fadan ta gama, sannan yai mata sallama ya fice zuwa gidansa. Da dan kuzarinsa ya shiga gidan yaransa na harabar gidan suna wasa kasancewar yau Thursday after school babu islamiya a yau. Da gudu suka zo suka masa oyoyo ya daga su sama yana dariya ya sauke sannan ya rika hannunsu suka shiga cikin falon, a falon ya sake musu hannu ya nufi kitchen gurin da yake jiyo motsin Suwaiba. Daga baya ya rumgumeta yana sumbatar gefen kumatunta. “Madam me kike girka mana” “Me nake girkawa dai ni da yarana kai da bazawarar ka ta dauke maka nauyin cin abincin gidana” Ta fada tana yatsina fuska. Sai yai murmushi rabon da Halima ta aiko masa da abinci tun ranar da ya dauko ta a mota, ya juyo da ita tare da saita idanuwansa cikin nata. “Kin ga abunda ke hada ni da ke mita, da rashin yarda, wanda ya baki labarin tana aiko min abincin be baki labarin ta daina ba?” “Kana kareta ne kawai, amman yq za ayi ta daima bayan ta fara kuma silar hakan ka daina cin abincin rana a gidanka? Daman can ai irin yan barikin zaurawan nan sun fi kowa iya karuwanci” “Abunda take min kyautatawa ce kawai a matsayina na dan'uwanta kuma kin fi kowa sani Halima na tsattsiya ce” Yana fadar hakan ya sake ya juya ya fice daga kitchen din fuskarsa na nuna rashin jindadin kalaman Suwaiba, tabe baki tai ta bishi da kallo haushi, ita kadai ta san abunda take ji ta rasa gane wani irin so yake ma Halima? Ko da yake ba laifinsa ba ne laifin Halimar ne daman shi namiji ai kamar yaro ne, duk inda aka bi da shi can yake, ta dade tana masa maganar abincin da Halima take aika masa a office duk kuwa da kasancewar ya sha nuna mata cewar baya son maganar, ta hanyar Yayanta da ke aiki Asibiti a matsayin nurse ta samu labarin. “Sai na ci miki mutunci Wlh, sai na bayyana halinki a gaban kowa, daga lokacin zan gani idan za ki sake bibiyar Abdallah banza ballagaza kawai, in banda jahilci taya zaka auri yaya kuma ka koma bibiyar kane, kaji iskanci, sai an tozarta ki Wallahi” Ta fada tana kwafa sannan ta juya ta cigaba da aikinta... AHMAD POV. tukin motar kawai yake amman hankalinsa yana can ya tafi gurin labarin da ya ji, sai a yanzu ya fahimci a kashi 100 na kaddarar rayuwa shi ko kashi daya be dauka ba, domin shi ya da mata sai mahaifi kawai ya rasa, amman ita ta rasa abubuwa da yawa a ciki akwai farinciki akwai gata akwai mutunci, a haka kuma har tana filin sake daukar wani kalar bacin rai a zuciyarta, tunawa yai da yadda take yawan masifa wata kila saboda tana cikin damuwa ne, ta yi kokari ta jajirce da har bata haukace ba ko kuma wani ciwon ya hana ta tashi kamar yadda shi a yanzu ciwon zuciya yake neman kai shi kasa. Tunawa da yai da irin abunda yai mata a wacan lokacin da kuma kadeta da yai yasa jin wani iri, anya mai irin wannan rayuwar ya cancanci a sake shimfida masa wata bakar magana ma balle har a aikata masa wani abu marar dadi? An keta mata an keta haddin yarta shi ya fi komai tsaya masa a rai, see yadda yake kyamar auren matar da ta auri wani auren sunna ma, to ita faya zata ji an yi mata da karfi? And ayi wayarta yar da bata san komai ba? And a lokacin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa bayan kuma kanensa ne ya ketawa yar haddi, wani irin mugun miji ne wannan? Baya son ta aureta ne? Ko dole akai mata? Aunata yake a matsayin Siyama, ya zai ji idan wani ya taba masa kanwa kamar haka? And the most saddest thing bata da mai tsaya mata tun a wacan lokacin, she's the first born ya tuna a cikin wasikarta ta fadi hakan, and the other sad part is ya kara mata damuwa da zarginta da mutuwar Namra, sai a yanzu yake gode Allah da Hajiya ta hana shi daukar mataki a kai da ya cutar da innocent soul. “Gwarzo... Ba gida za mu je ba?” Sai a lokacin ya tuna ba shi kadai yake a motar ba, Hajiya tana baya tare da shi. “Gida za mu je” “Na ga ka dauki wata hanyar ne” Sai a lokacin ya lura, bakinsa ya cikawa iska ya busar sannan yace. “Zagoyo zan yi” “Okay, bikin nan ya kayatar sosai fiye da yadda aka saba yinsa a shekara, wai ka gane wacce ta ci gasar nan kuwa?” Hajiya na yin maganar zancen yaranta ya fado masa, na cewar idan ta ci zata biya musu kudin makaranta. “Wow....” Ya furta a fili yana jinjina irin jarumtarta da karfi zuciya. Hajiya kuma sai ta dauka da ita yake sai kawai ta cigaba da shimfida masa labarin. “Wannan ce fa mahaifinyar su Namra yarimyar da ke tare da Baby Namra, ashe har yanzu bata manta da ita ba, tace idan ta ci sadaukarwar ta Baby Namra ce” Be ce komai ba sai tukin yake a hankali yana jin wani abu na masa yawo a zuciya na rashin jindadi har suka isa gida. “Labarin ma da aka karanta ina kyautata zaton na mahaifiyar yarinyar nan ne Halima.... ” “Halima...... ” Ya maimaita sunan yana kokarin juyowa ya kalli Hajiya, be taba sanin sunanta ba sai yau, duk kuwa da aikin da take a kamfaninsa, sunan da ya fi ko wane suna yi masa dadi a duniya, har yanzu yana ganin yadda ya wulakanta a kamfaninsa a lokacin da ya bukaci a canja mata position sai a yanzu yake ganin hawayen da take da irin rokon da ta soma masa tana kuka tana fadar dan Allah kar ya koreta tana bukatar aikin nan, and in the restaurant a vip 1 a lokacin da ta zauna a saman kujerar sa matarsa take zama, he remember wadansu kalamai da ta fada, wacce take nan ta yi sa'ar ba kamar ita ba, daman duk wannan take nufi? “Oh ya rabb” Ya furta a fili gaba daya zuciyarsa ta daure ta yi nauyi da tausayin Halima. Can ya tsinkayo Hajiya na kokarin fita motar tana fadin. “Domin labarin da mahaifiyarta ta ba ni, yayi daidai da abunda aka fada a gurin nan kuma ga shi taje tare da yaran, ina jin labarin na gane ita ce, cikin ma uwar bata fada min duka ba, tun da wani abun sai a yanzu na ji, amman matar nan ta ga rayuwa Wallahi ban san lokacin da nai kuka ba” Fitowa yai daga motar yana kallo mahaifiyarsa wacce ke sanye da tsadadden lace. “Amman Hajiya ba ki taba fada min ba” Hajiya ya kalleshi da kyau. “Ina zan fada maka labarin makiyiyarka? Matar da kace baka son jin komai nata” “Da kin fada min ko da a tsawace ne, ko kuma ki cilasta min saurare ai dole zan ji, wani mai imani ne zai ji labarin matar nan be ji tausayinta ba?” Ya fada yana hade yatsunsa fuskarsa dauke ta tausayi. “Duk lokacin da nai unkurin fada maka sai kace ba zaka saurara ba, tausayinta ne yasa na hana ka kaita kotu ai, ko lokacin da aka fada maka bata cikin hayyacinta ba cewa kai karya ne ba, saboda kawai ta kashe maka ya ne? Ni ko na san mai imani ba zai kashe rai ba sai idan wata kaddara ta fada masa, sai a yanzu da Allah ya kaddara ya bude maka zuciya ka ji komai” Yes he remember an fada masa she's unconscious ya ki yarda, and he remember how her father beg him akan case din amman be saurareshi ba, and the slap a lokacin da ta kawo Baby Namra asibiti ya mareta har sai da ta fadi..... Ji yai wani irin abu na rashin jindadi da kyautatawa ya mamaye shi, be taba jin tausayin wani abu mai rai kamar a yadda ya ji tausayin Halima ba a yau, a waje daya kuma yana ta jinjina karfin hali da dakiyar zuciya. Part dinsa ya nufa yana ta tunani kala kala yes hak rayuwa take zaka ga mutum kawai sometimes a cikin farinciki amman ba san abunda yake zuciyarsa ba, ba zaka iya fassara damuwarsa ko nasararsa ba, da ace be ji labarin Halimatu ba da har yanzu be daina mata kallon makiyiyarsa ba, wata kila da Allah kadai ya san irin abubuwan da zai mata.... A dare kwana yai da tunanin abun a ransa, duk kuwa da yasan condition dinsa rage yawan tunani yana ciki. HALIMATU POV. Labarina ya taba zuciyar mutane da yawa a guri kuma nima ya taba ni a karan kaina, domin sai rayuwar da tunanin gobena ya dawo min sabo. Iyakar kokarin da nai kar nai kuka a bainar jama'a ne, sai dai na zubar da hawayen da ban san adadinsu ba, an rayuwata ta lalace kuma an bata ta yata, amman na yarda da wani abu daya, ko dan yayana zan rayu, zan kara jajircewa zan tsaya tsayin daka na amsa sunan da Ummulkhar ta kira ni da shi wato Jaruma. Rai na ya kwadaitu da zancen kudin da ta ware min a cikin albashin kamar yadda ta fada, sai dai ina tunanin karbarsu abu ne mai wahala a gurina domin zai iya zama silar da zata saka a gane ko wacece ni wanda hakan zai hanani sakewa cikin mutane. Ba mu tashi daga taron ba na ji alert a wayata, na naira miliyan daya, aiko a take na nemi damuwata na rasa farincikin ganin kudin ya maye gurbinta. Cikin murna muka fita daga taron wani abun burgewa sai muka zama abun kallo har da masu dauka hoto a tare da mu da award din da aka ba mu, ina yin gaba kadan na hadu da blessing abokiyar aikina, sam ban san ta zo taron ba sai da tai min magana mun gaisa da ita ta tayani murna sannan ta gaisa da su Namra tana fadin ashe ina da yara. Sai nai murmushi. “Ke ma ai kin san ina da yaya” “Eh amman ban dauka har hudu ba, kuma kyawawa da su har sun fiki kyau” Dariya nai sai ta soma tambayar dalilin rashin zuwana aiki kwana biyu. Ban boye mata komai ba na fada mata cewar wani dan'uwana ya hana ni aikin ne saboda uniform din be dace da ni ba. Dariya ta fara min tana ta mamakin wautata, wai ya zan daina aikin ban je ma fada musu dalilina ba idan ba su aminta su canja min kayan ba ko kuma gurin aikin ba sai na daina amman a haka ai ba ni da hujja kuma na bar damata ne. Ta yi tamin magiyar na je gobe na fada musu haka idan basu yarda ba sai n aje aikin, ni kuma na amsa mata da to duk da nasan ba za su yarda su canja min ba, amman yanzu na samu kudina zan iya yin sana'a ta kamin na samu wani aiki, tare muka jera muka fita tana fada min wata mata da ke yawan zuwa nemana tun da na daina zuwa aikin har number wayarta ta bari tace idan na zo a kirata. Ni kam mamaki ya cika kuma tsoro ya kama ni wacece kuma? Allah yasa ba wani karin damuwar ba ne, can kuma matar Kabir ta fado min a rai wata kila ita ce, dan nasan wannan mugun Ahmad din ba zai kyale shi ba, domin ko a yanzu na lura da kallon bakincikin da yake min, na ja masa fada da mahaukaci kuma ga shi na ci gasa na san hakan ba karamin zafi yai masa ba. Idan na naje aikin Yunus din zan yi ma magana ko Tahir wanda shi ne shugaban sashen mu, shi kam na san ko kallo ban ishe shi ba kuma ba zai saurare ni sai dai ma ya fada min wata bakar maganar. A ranar gidanmu ya cika da murna ba mu kadai ba har da makotan da suka samu barin sai da suka zo taya mu murna, Inna da Mama duk tsoro ya kama su wai kar a biyo dare ace sai an bada miliyan din, har ta hana a fadawa. Ba su kadai ba ni kaina na kwana da tsoro a ranar saboda halin tsoro da kasar nan take ciki abu kadan zai tsonewa wani ido. Washe garin na tashi raina fes zuciyata kal babu damuwa ko kadan sai farinciki da annushuwa rabon da na samu kaina a haka har namanta, domin a yanzu bayan damuwata har da ta Abdallah tana damuna, tun daga wacan lokacin da yai min magana ban sake sakewa ba, su namra ma baki har kunne suna ta far'a, ban barsu sun je makaranta ba sai da nai kusu kashedi akan kar suje suna fadin abunda muka samo a school din, kuma su fadi gaskiya cewar kudin yana cikin account ba a hannu ba. Bayan sun tafi nima na shirya cikin riga da zane na atamfa na saka hijabina, sannan na shiga dakin Mama na fada mata cewar zan tafi kamfanin na nemi alfamar canjin tufafi ko gurin aiki kamar yadda blessed ta bani shawara, daman tun da dare na labartawa Mama abunda ya faru da kuma matar da ke nema, har ta farara min kuiwa yin haka daman tana da complain cewar na daina aiki ba tare da na yi magana ba ban san ko za su aminta su canja min aikin ba. A yau ban fita ba komai ba a hannuna da sunan kawai Kabir ba duk kuwa da kasancewar zuciyata na raya min na rika masa wani abu kamar yadda na saba, domin tun a lokacin da na daina zuwa aiki na daina kai masa abincin, haka ma take away da nake sakawa a kaiwa Abdallah na daina kasacewar hanya daya ce da gurin aikina a ko yaushe ina bada kudi na ce a kai masa idan 1pm ta yi ko 12,30pm. Napep din da na tara akwai mutane biyu a ciki ni ce ta uku, a dole sai da ak saukesu inda za su je sannan aka kai no kamfanin wannan karon har bakin gate din kamfanin aka sauke ni, tsabanin da da ake sauke ni kusa da Kabir sai na bashi abincin sannan na wuce, babu irin dubawan da ban yi ba amman ban ga Kabir ba hakan kuma ba karamin haifar min da tsoro da zullumi yai ba, ina ta rokon Allah yasa ba mugun can yai masa wani abun ba. As usual sai da na gaisa da masu gadin sannan na shiga ciki, kai tsaye reception na nufa fuskarta dauke da murmushi da sauri blessed ta zo ta rumgume ni. “Oyoyo we miss you” Ta fada sai kace wani dade muka yi muna aikin tare, ko da yake komai gamon jini ne. A nan fira ta kaure tsakanin na da su suna ta tambayar dalilin rashin zuwana aiki na fada musu sannan suka rika taya ni murna wai blessed ta basu labarin na ci gasa, a lokacin ne nake tambayarsu macen da take zuwa nema sai Rilwal ya ce “Ai zata zo kullum sai ta zo nemanki a nan” Na bukaci number wayar da suka ce ta bari tace a kirata idan na zo, sai Rilwal ya nuna min ita a wayarsa, na yi ta karanta number ban gane mai ita ba, sai kawai na zuba numbobin a wayata, ga mamaki sai sunan Suwaiba ya fito, miyasa take nema anan? Ba tasan gidan mu? Kuma tana number wayata idan har son ganina take? Wata matsalar ce? Ko wani abu ya faru da Abdallah? Haka zuciyata tai ra raya min abubuwa kamin na basu amsar cewar na gane mi number, nan suke fada min cewar babu wanda ya shigo a cikinsu daga sarkin girman kan har Yunus din da Tahir, hakan yasa na nemi guri na zauna dan na jirasu, ni kaina na san na yi sammako sai dai na zo da wuri ne saboda gudun na na zo suna tsaka da aiki a hana ni ganinsu tun da komai an kamfanin a tsare yake. Ban yi minti goma da zama ba naji ana nuna domin sam ban lura da mutane da suke shigowa ba hankalina yana ka ce wayata, ina dago kaina nai yi arba da Suwaiba ta nufo inda nake rai a bace tana tafiya kamar ta fadi abun ka da siririyar mace. “Kashedi na zo nai miki, ki fita hanyar mijina” Ta fada cike da masifa tana daga murya iya karfinta, hakan yasa hankalin kowa ya dawo kaina. “Ki fita hanyar mijina, yafi karfinki” “Ba ki isa da mijin na ki ba ne shiyasa har kika zo baina jama'a kike min ihu, da ni nake auren Abdallah Wallahi idan na hana shi kallon wata macen ya hanu.... ” “Ina zan isa da shi kin masa magani kin malleke shi bakar bazawara.... Yar duniya mai bibiyar mazan mutane, aure biyu kika kashe kina bibiyar mijina, marar mutunci kin zubar da yara hudu kin bar ubansu kina bibiyar nawa mijin, dan kawai ba ki san darajarsu ba...... Wani irin karuwanci ne da zaki rika aika masa abinci kullum..... Mijinki ne ko danki?” Kalmar bazawara bata taba min zafi ba irin yau, ashe akwai ciwo idan aka maka gorin zawarci, a take na ji muzanci ya kamani tace na kashe aure ina bibiyar mijinta ko da karya ta fada wasu zasu gasgatata, na ci mutunci na a bainar jama'a ta gama da ni. Duk yadda na so na ki yin kuka sai na kasa hawaye suka fara min zuba bakina ya kulle gam na rasa me zan ce mata jikina sai rawa yake ina jin kamar na dake ta. “Securities arrest her...” Kamar saukar aradu haka muryar Ahmad ta dira a kunnena, da juyo idonw da hawaye na kalleshi yana tafe cikin kamfanin tare da Yunus, a lokacin da Security kamfanin suka nufo inda muke tsaye na yi zaton ni za su rike, sai na ga su kama Suwaiba macen cikinsu ta fisgeta da karfi. “Ku rufe min ita a kamfanin nan sai ga uban waye mijin naki da za ki zo cikin kamfanin mu kina mana hankali how dare you” Ya sake fada, a rikice na kalleshi ina hawaye. Sai ya karaso cikin kamfanin yana kallon amsu kallon fadan mu fuska a hade. “Ku kuma me kuka tsaya yi kuna kallo ana insulting dinta instead of ku yi wani abu kowa ya saki ido fools” Yana fadar hakan sai kowa yai saurin kama gabansa, shi kuma ya wuce ta gabana ba tare da ya kalleni ba ya bi hanyar da zata sada shi da office dinsa. 7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2 *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣4️⃣ Rasa nai abunda zan yi, na bishi nai masa magana ko kuma na zauna ko na tafi gida? Ya Abdallah zai ji idan aka ce wani ya tsare masa mata saboda kuma a kamfaninmu, no ba saboda ni ba ne saboda ta yi hayaniya ne dan haka babu ruwana a ciki.    Akai akai mutane suke ta kallona, har na soma tsarguwa, tashi nai koma can wani gefe da ba a ganina sosai na zauna, wata zuciyar na fada min cewar naje nai maganar aikina sai dai kuma idan na yi maganar aikin aka koreni ba tare da an gama maganar Suwaiba fa?   Na kusan awa daya a gurin ina ta tunanin abun ne naje nai masa maganar Suwaiba ko ta aikina, amman ina ruwana da matar da ta ci min mutunci a bainar jama'a, ai kara a kira Abdallah din domin na san ba da saninsa ta zo nan ba. Ban raba daya biyu ba, aka aiko wata mai sanye da suit kirana, haka ta saka ni a gaba ina baya har muka isa office din Ahmad. A one of visitors chair na tarar da Abdallah zaune, ni kuma sai na tsaya daga bayansa tun da ba a bani izinin zama ba, juyowa Abdallah yai ya kalleni sai kuma ya kawardar fuskarsa ba tare da yace komai ba. “Look man aiki bake fa zaka tsayar da ni anan for more than 20 minutes, ba kallo office dinka na zo yi ba” Abdallah ya fada a fusace, hakan yana nuna alamar Abdallah ya dade da zuwa kenan. Da hannu Ahmad yai min alama dana zauna ba tare da ya kalleni ba. Ba musu na zauna a kujerar da ke kusa da Abdallah ina ta kallonsa shi kuma sai yai kamar be san da ni a gurin. After like 5 minutes Ahmad ya kalleshi yace. “Aiki nake yi ko baka gani ba? So kake na aje aikin na kula ka? Kai da ka zo ganina ba appointment? And you got lucky na barka ka shigo har office dina ka zauna tare da ni, ban barka visitors room ba?” “Ba kai na zo gani ba, Matata na zo na ji dalilin riketa da kuka a nan” “Bata fada maka abunda tai ba? Ko a hanya kawai za mu ga mace a hanya mu dauko ta?” Babu wasa a fuskar Ahmad a yayinda yake wannan maganar, kamar yadda Abdallah ma nake ganin abun ya masa zafi. “Matarka ta zo nan tana mana ihu na rashin tarbiya tana fada akanka, tana fada da ma'aikaciyarmu ba za mu dauki wannan ba” “Kai kuma ka rufe ta, saboda gaka hukuma” Ahmad ya kwanta jikin kujerar yana masawa Abdallah cikin zafin rai. “Yes ko akwai abunda za ka yi? Kana ta son nuna isa, bayan you are nothing wanda be isa da iyalinsa ba har ya isa yace zai fito waje yai yi takama? It's a shame” “Family issues ne wannan babu ruwanka a ciki” Abdallah ya fada yana kokarin danne fushinsa. “Family in my company? Public place?....” Ganin abun kamar zai zame musu fada yasa nai hanzarin cewa. “Na yafe ni tai wa cin mutunci na yafe mata, dan Allah ka barta ta tafi” Ina fadar hakan Abdallah ya daga min yatsansa alamar babu ruwana a ciki, Ahmad kuma ya tari numfashina “To ni ban yafe ba...” Ya fada kai tsaye yana kallona. A lokacin ne Abdallah ya mike tsaye cikin bacin rai ya daka masa tsawa. “And who are you? Mi kake takama da shi” Wani shegen kallo Ahmad yai ma Abdallah, mamaki ya kama shi wato a maimakon ya bada hakuri ya karbi laifin matarsa amman sai neman kareta yake, hakan ya kara tabbatar masa da cewar Halima bata da gata domin da tana fa shi da yau ba shi zai yi fadan nan ba wani wanda ya tsaya mata ne zai yi shi. “Kudi Alhaji......... ko baka gani ba, na isa ne isar ta isa ma matuka, kawai dan kun ga mace bata da gata sai ku yi ta taka ta any how, idan yar wani mai kudi ce ko kuma tana da wanda ya tsaya mata shashanshar matarka bata isa ta taka kofar gidansu ta fada mata bakar maganar magana ba balle har ta shigo gurin aikinta tana kiranta da suna kala kala tana cin mutuncin, so warn your wife for the last time, bilahil'azee idan ta one bad word daga bakin matarka zuwa ga Halima sai a rufeta a cell ba acikin kamfanin nan ba” Abdallah yayi murmushi yana duba agogon hannunsa, sannan ya kalleni ya sake kallonsa. “Ba kai ne mutumen da yace idan yarsa ta mutu zaka rufe Halima ba? Ba kai ne mutunen da baka yarda da kaddara ba? Ba kai ka mareta har sai da ta suma ba? Kai duk abunda kai mata ai saboda kana ganin bata da gata ne, yanzu har kana da bakin da zaka fadi haka? Mi ka sani a akan Halima? Baka san komai ba akan rayuwarta fadi tashin da tai ba ka sani ba, sai a yanzu? Tsohon dan iska shiyasa ka bata wando da riga ta saka so that ka rika kallon siraicinta? So kake ka burgeta a yanzu? Shiyasa zaka fara acting kamar wani mutumen arziki... ” Su suke fadan ni nake kuka, Ahmad be sake cewa komai ba, ya danna dan wani maballi da ke gefen teburinsa, ba a dauki lokaci ba sai ga security kamfanin sun shigo. “Ku fitar min da shi bana son hayaniya.... ” Da sauri suka nufi gurin da Abdallah yake saye sai kuma suka saka rika shi sai kokarin masa magana suke. “Karku taba shi zai fita da kanshi.... Abdallah dan Allah” Ya fada ina masa magiya, kallo yai ya dauke kai ya juya ya fice daga office din rai a bace, sai security din suka bishi a baya. Karasa matsawa nai kusa da teburin na hade hannayena ina kuka. “Ka saka a saki matarsa dan Allah, na san ka tsaneni, duk abunda zaka yi Saboda ka musguna min ne ko kuma wani na kusa da ni, idan har ya zama dole sai ka dauki mataki akan abun dan Allah ka hukunta ni ba matarsa, saboda ni komai ya faru...” Ba tare da ya kalleni ba ya nuna min wata kujera dake can kusa da kofa. “Je can ki zauna” Abun ka da mai jiran umarni sai na nufi kujerar na zauna ina kuka a hankali domin har ga Allah ban jidadin da ran Abdallah ya bace ba, kuma ban jidadin abunda Ahmad yai masa ba. “Idan kin gama kuka ga tissue box kusa da ke ki goge fuskarki, akwai ruwa a fridge” Yana fadar hakan ya dauki laptop din da yake aiki da ita ya fice ya bar ni a katon office din, ni ko ban fasa aikin kuka ba har sai da nai wanda ya ishe ni na dauki tissue na goge hancina da idona sannan na bude fridge din na dauko gorar ruwa na sha, domin makoshina ya gama bushewa. Bayan na sha ruwa na koma a inda na tashi na zauna. Kalamansa na dazun ne wuka rika dawo min a rai kamar yadda na Abdallah ma suka tsaya min, na rasa ganewa Ahmad ya fara saukowa daga fushin da yake da ni ne? Da har zai ce idan Suwaiba ta sake fada min bakar magana sai ya rufe? Ya bar ni na shigo har office dinsa ya fada min idan na gama kuka na goge fuskata na sha ruwa... Ina tsaka da tunanin sai gashi ya shigo tare da Yunus yana ta murza wani karamin turare a hannunsa, kallona kawai Yunus din yai be ce komai ba ya cigaba da maganar da yake da Ahmad bayan ya gama ya fice wata matar ta shigo da kofin tea guda biyu ta aje a saman teburinsa sannan ta fice. Daukar dayan kofin yai ya nufo inda nake zaune ya miko min, mamaki ne ya hana ni karbar cup din har sai da ya kalleni. Sai nai saurin girgiza masa kai na mike tsaye. “A a na gode” Kallo yai for few seconds sannan ya furta. “I'm sorry....” Ya juya yana kurba tea ya nufi teburinsa. “Be kamata ka bani hakuri ba, duk abunda ya faru laifina ne, ni na ja komai sanadina komai ya faru kuma kamfaninka ne kana damar ka yi duk irin hukuncin da kake so....” “Akan dora miki laifin kisan Baby Namra da na yi” Ta tari numfashina, wannan karon mutuwar tsaye nai, da gaske hakuri yake ba ni? Ahmad din ne ko wani dai dabam, na dan juya na kalli bayana na sake kallona. “Ki yi hakuri dan Allah” Ya maimaita min da yaren da na fi ji. Har lokacin kallonsa na ke gaba daya kaina ya gama kwancewa, mi ke faruwa ne? haka na tsura masa ido ina ta masa kallon da ban san na minene ba, mamaki kadai ko kuma har da tuannin maganar Abdallah? Da gaske hakuri yake bani ko kuma wani abun yake shirya min saboda na kashe masa ya? Kamar yadda yake zargina? “I say sorry” Na hade yawun bakina. “Ba komai ba, wannan ma yana cikin kaddarata ne” Ina fadar hakan na juya zan fice daga office din. “Ina za ki je?” “Gida” Na fada ba tare da na juyo ba, idona na cika da hawaye. “Aikin fa?” “Na aje” “Saboda me?” “Tufafin da nake sakawa be dace da ni ba” Na amsa cikin muryar kuka, har yanzu na kasa yadda Ahmad ya bani hakuri akan yarsa, har zuciyarsa yake bani hakurin? Miyasa? Taya yanzu ya yarda ba ni na kasheta ba? A take wasikar da na rubuta a jiya ta fado min a rai, ya fahimci ni ce kenan, kuma zuciyarsa ta bude har ya iya yarda a yanzu ban aikata ba, Al-hamdulillah akalla wani abun ya ragu daga bakincikin da yake raina, a yanzu yana kallona a matsayin marar laifi tun da har ya iya ba ni hakurin. Shigowar Yunus ne yasa nai saurin share hawayena sai dai hakan be hana shi fahimtar kuka nake ba. “Lafiya?” Ya tambaya yana kallo da mamaki a fuskarsa. Ban saurari abunda Ahmad ya fadawa Yunus din ba domin har lokacin kokarin tsayarda kukan farincikina nake. “Biyo ni muje” Yunus din ta fada ni kuma na juya ina rokon Ahmad amman ko kallona be yi ba. “Dan Allah ka saki matar can dan Allah” Ganin Yunus din ya fice yasa nima na bi bayansa, yana gaba ina bayansa har muka isa wani guri, hannunsa ya kai ya tura kofar sai ya bude ya shiga ni kuma na tsaya a waje har sai da ya yi min izinin shiga. Dan madaidaicin office ne mai dauke da desktops har biyu a teburi daya, sai dan karamin fridge da ac makale a dakin daga gefen ac window ne mai kofa biyu wanda yake bawa mutum damar hango windows din office din Ahmad kamar yadda shi ma zai iya hango na cikin office din idan an bude. “Kin iya typing ai ko?” Na gyada kai. “Yauwa to duk emails din da za a turowa kamfanin nan anan zai shigo wanda kika ga ya dace oga ya gani sai ki masa forward kai tsaye zuwa email dinsa, idan kuma za a aika wani abu to all ma'aikatan mu ke za a bawa ki yi typing sai ki tura, sai dai daga yanzu lokacin tashi aikinki ya canja daga 3 zuwa 5pm, amman ba kamar wacan ba ne nan ana bada abinci saboda zaman da kike” “Ban gane ba....” Na fada a hankali cikin sanyayyiyar murya. “Yanzu nan ne office dinki congratulations” “Da gaske?” “Ga zahiri kina gani” A take idanuwa suka kara cika da kwalla. “Na gode” “Oga ya kamata ki yiwa godiya” “Dan Allah ina rokon alfarma” “Na san kai ma oganka ne, amman kuna da kyakkyawar fahimta wata kila za ka iya yi masa magana ya ji, dan Allah ka saka ba ki ya saki matar da ya saka a ka kulle” “Ya sake ta ai, tun dazun mijinta ya tafi da ita” “Da gaske? Amman cewa yai ba zai barta ta tafi ba” “Gaskiya tun dazun aka wuce da ita” Dan murmushi nai na juya ina kallon office din. Shi kuma ya juya fice ya bar a gurin tsaye n rasa abunda zan yi murna ko kuka ko mamaki? Kasa komai nai a cikin office din sai kawai nai zaune ina ta kallon office din, misalin daya da mintuna wata ta shigo da abinci ta ba aje min, takeway ne na jalof da naman kaza a ciki. Nikam ban ci ba duk kuwa da kasancewar ni kadai ce a dakin sai na saka abina a jaka. Biyu na yi na shiga bandakin da ke office din nai alwala na fito nai sallah sannan na dauki wayata na kira gida na fadawa Hafiza ta fadawa Mama an canja min aiki dan haka yau sai 5pm zan dawo. Har karfe uku ban duba email din ba ban kuma tura komai ba, har sai da Yunus din ya sake dawowa ya nuna min yadda ake da kuma wandanda ya kamata a turawa Ahmad din. Karfe biyar na yi na dauki jakata na fito daga office din, ko da na fito Rilwal da Blessed basa gurin sun gama aikinsu sun tafi. A lokacin da na isa gida na labartawa Mama da dukan yan gidan abunda ya faru tsakanina da Ahmd da kuma abunda Suwaiba tai, a nan Hafiza take fadar wai Suwaiba ta kirata kwanan baya tana tambayar inda nake aiki ita kuma ta fada mata ba ta yi tunanin wani abun ba ashe dan ta samu zuwa ta ci min mutunci ne. Su namra na bawa abincin office din, suna ta murna sun ga har da nama a cikin gurin rabon abun har ya so zame musu fada sai da Husna ta shiga tsakani. Bayan na huta na ci abincin da aka girka gida, na watsa ruwa na sake shiryawa cikin wasu tufafin na nufi bankin da ke kusa da mu, kudin gasar da na ci nake son cirowa na samma kowa wani abu a ciki sannan nai sauran lalurorin da suke gabana. 200,000 na ciro na saka a jaka ta cikin tsoro domin a lokacin an fara kiran sallah sai nake ganin kamar akwai wasu a biye da ni duk kuwa da ba ni kadai na ciri kudi a atm din ba. Ina yin gaba kadan sai wata farar mota mai bakin gilashi ta faka a gabana, na san ba zai wuce Abraham ba amman hakan be saka ni jin tsoro ba har sai da ya bude motar ya fito. “Ki daina cirar kudi a atm idan yamma yayi, wani zai iya sa miki ido wasu ma ba diban kudin suka je yi ba kallon masu cire kudin suka je yi” Ban ce masa komai ba nai gaba kamar zan wuce sai ya saka ya cin min. “Kin gani jin labarin ki ya kara min kaunarki, kuma ya kara kafafa min guiwar aurenki, ni kadai zan rayu dake ba wata kyama ba wani tunani, ina da kudi zan sakar miki su ki jidadin rayuwarki” “Ba kudi ne jindadin rayuwa ba, da su ne da masu kudin ba su shiga kunci ba, ni farinciki nake nema da kwanciyar hankali” “Na sani shiyasa zan baki ai” “Baka isa ka bani farinciki ba, baka isa ka keta min haddi da aurena ba har nai ciki yanzu kuma ka biyo ni kace zaka aureni, addininmu dabam al'adarmu dabam, baka san zafin da nake ji a raina ba, baka san yadda mace take ji idan an keta haddinta ba, saboda kai namiji ne, mace tana jin matukar bakinciki ko hannunta a rike balle a keta haddinta, kasan saboda me? Saboda martabarta kimarta mutuncinta jindadinta farincikinta yana a nan ne, to kai ka zubar min da duka wannan ka saka uwar mijina da mijin da ya sake ni suna min kallon karuwa wacce ta zubar da mutuncinta tai fasikanci da wani namijin har ta samu ciki, wannan tabon ba zai taba gogewa ba, idan kuma ka zo ne saboda ka kashe ni da bakincikin kallonka da nake kana da dama” Na karasa cikin kuka. “Idan nisanta kaina da ke zai saka ki farinciki, i will do that, amman bana da niyar saka ki bakinciki, sai dai sama miki farinciki ada bakincikin fyaden da nai miki kawai yake damuna, amman a yanzu har da rayuwar kuncin da kike ciki, kina da zuciya mai kyau kuma kina da hakuri” Bayan ya fadi haka ya bude motarsa ya shiga yai mata key ya bar ni a gurin tsaye. Sai da na daina hango motarsa sannan tari napep na shiga. Ko da na isa gida har an gama magariba, bayan na sallame mai napep na lura da motar Abdallah, na yi zaton yana cikin gidan ne sai ji nai ya kirani, ina juyowa na hango shi ya fito hanyar masallacin unguwar sai ya nufi gurin motarsa ya tsaya, hakan yasa nima na karasa kusa da shi na tsaya. “Ki yi hakuri da abunda Suwaiba tai miki, ban san yadda akai taje gurin ba kuma ban fada mata cewar kina kawo min abinci ba, kin san zuciya kowa da irin tasa ba tai tunani ba a lokacin da ta aikata abunda ta aikata dazun kuma ban jidadi ba” “Tana da gaskiya Abdallah, tana tsoron wata ta karbe nata miji mai karamci da sanin ya kamata, mai kula, mai tausayi, mai taka tsantsan akan komai, kai kadai ka yarda da ni Abdallah baka taba yarda cewar na aikata laifi ba, kai kadai ka yarda cewar ban aikata zina, kai ne kadai ka yarda fyade ka min har na samu ciki, amman Hajiyarka da Abdulhamid ba su yarda da ni ba, kai na zarga a lokacin da aka min fyaden kuma na fada maka, amman gujeni ba baka kyamace ni ba, baka fasa so na ba, baka kasa taimaka min ba, so na be taba sa ka nemi aikata alfasha da ni ba, baka taba kyamar yayana ba, Wallahi ina son ka Abdallah ina son ka har kasan raina” Na karasa cikin kuka mai tsanani. Har ga Allah ban taba jin son wani da namijin a raina kamar yadda nake jin Abdallah a raina ba, sai bayan komai ya lalace na gano shine mutumen da ya dace da ni. “Ke dai ba kya gajiya da kuka, shiga ciki Suwaiba tana jiranki” “Ina son na fada maka wani abu, mutumen da yai min fyade, ya dawo yan so na” “Wooo What....!” Ya furta da karfi muryarsa na amayar da mamakin da ke cikinsa. “Waye? A ina ya ganki?” “Labari mai tsawo ba zai yiyu a yanzu ba” “Waye shi kin san shi ne?” Na girgiza kai. “Ban san shi ba, sunansa Abraham, dan sanda ne, yana aiki a unguwar gwaza, kuma shi ba musulmi ba ne” Na daga kaina sama ina shanye kuka. “Abraham.....” Ya maimaita sunan sannan ya jinjina kansa. “Shiga ciki za ku yi magana da Suwaiba” Na gyada kai alamar gamsuwa sannan na saka hannuna na share hawayena sannan na juya na nufi gidanmu. Ko da na shiga na samu Suwaiba zaune falon mama tana ta rutsar kuka kamar ba ita ba, tana ganina ta soma bani hakuri tana fadin na yafe mata, a iya sanina Abdallah baya duka balle nace dukanta yai ya cilasta mata zuwa ta ba ni hakuri sai dai idan wani abun ya fada mata ko kuma cilastata yai. 7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2 *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣5️⃣ ABDALLAH POV. Zuciyarsa cike take da tunanin abunda Halima ta fada masa, ba sau daya ba ya sha jin sunan Abraham a gurin Abdulhamid, sai dai da kamar wuya ya iya fada mta kai tsaye idan har shi din ne? Mi zai saka ya tonawa kansa asiri? Mi mai zai saka yayi mata fyaden tun farko? Miyasa yai shigar yan fashi? Sai dai ya yarda Halima ba zata masa karya ba, tun da ita din bata san Abraham ba, kuma bata san cewa shi din ba musulmi ne ba, idan har ba shi ya fada mata ba. Yana tsaye jikin motar Suwaiba ta fito daga cikin gidansu Halimatu ta nufo i da yake da hijabinta har kasa, be tsaya jiran ta karaso ba ya bude side dinsa ya zauna yai ma motar key tana shiga ya tashi motar. Ta yi zaton hanyar gida zai nufa sai ta ga ya dauki hanyar family house dinsu. “Doc baka hakura ba?” Ta tambaya cikin kuka, ko kallon inda take be yi ba har ya shiga titin unguwarsu. “Na ba ka hakuri kace ita zan bawa hakuri ita ma na bata, amman be isa ya saka ka yafe min dan abunda nai ba” Sai a lokacin ya kalleta. “Dan abunda kika yi? Da ne ma? Kin san irin kuncin da Halima take fuskata kike neman kara mata wani? Ko ba u so a tsakanina da ita ai ita din yar'uwata ce kuma kin sani, ko dan yan'uwantakan da ke tsakaninmu be isa ya saka ki raga mata ba ko da ma ace ita ce ta nemi fada da ke? Ko karuwata ce ai ya cancanci ki kyaleta saboda mutuncina, amman wai dan shashanci da aurena akanki ki shiga public place kamar nn kina magana any how, idan auren zan yi kin isa ki hana ni ne ko fadan ki sai ya saka na fasa?” Tun da ya fara fadan take kuka har ya faka bakin kofar gidansu. “Da gaske sakina din za ka yi?” “Ko dai ban sake ki ba, dole na samawa su Inteesar wata uwar mai tarbiya da sanin ya kamata” Da sauri ta hade hannayenta. “Dan Allah kai hakuri, ka sake ni idan sakin zai saka ka huce haushi daga baya sai ka maida ni amman karka kara aure dan Allah, wallahi na bari ba zan sake ba” “Yanzu kuma na gano har da hankali baki da shi, idan aure zan yi kin isa ki hana ne? Ba a aure na aureki? fitar min a mota” Ya fada a tsawace fuskarsa babu alamar wasa. “Dan Allah ka yi hakuri...” “Nace ki fita....” “To yaushe zaka dawo ka dauke ni?” “Ban sani ba” Yadda ya daka mata tsawa ne yasa ta saurin bude motar ta fita. Sam bata taba ganin Abdallah a cikin irin wannan yanayin ba, su kan samu sabani wani lokacin ko da shine da gaskiya sai tai fushi da shi a haka kuma zai bita ya bata hakuri su shirya, amman be tana yunkurin fada mata bakar magana ba, yau kam ta kai ya saka hannunsa ya mari fuskata hakan be masa ba sai da ya cilastata ta je ta bawa Halimatu hakuri abunda yafi kona mata rai kenan, bayan yai mata baraza da saki yanzu kuma ya cilasta mata zama gidansu har yana zancen kara aure. Lallai sai yanzu ta tabbatar ba kadan yake son Halimatu ba, saboda kawai ta taba yau duk yai mata wannan har yana fadar wai ta taba mutuncinsa, bata kara jin ta tsani Halimatu ba sai da yai reverse da motarsa ya barta bakin gate din tsaye tana kallonsa. Kai tsaye gidan Hajiyarsa ya nufa, har lokacin tunanin abunda Halima ta fada masa yake, yana ta neman dalilin da zai saka mutumen yi mata fyade, yana bukatar fadada bincike, kamar yadda yake bukatar jin komai daga bakinta. Sai da yai parking sannan fita daga motarsa ya nufa kofar falon Hajiya wacce ke bude, hango ana mopping yasa shi tsaya bakin kofar yana kallon Hajiyar wacce ta nufo inda yake rike da filo. Fitowa tai waje harabar kofar da aje fillon saman wani center carpet da aka shinfida mata gafen kofar ta zauna, tana tsastsagar hakora hakoranta biyu na makka suna bayyana. A gabanta yaje ya zauna, yana mika mata gaisuwa. “Lafiya Kalau, Husaini ya gida? Wani gurin ka fito ne hala?” “Eh Suwaiba na kai gidansu” “To wani abu suke a gidan ne?” “Kai ta nai ta kwana biyu dai” Hajiya ta tashi daga kishingiden da take tana kallonsa abunda bata taba ji ba. “Ban gane ta kwana biyu ba? Miya faru? Tsabani kuka samu ne” Be boye mata komai ba daga abunda ya faru har hakurin da ya saka ta bawa Halimatu, a maimakon Hajiya ta bata laifin sai ta koma ganin laifin Abdallah. “Wato sai yanzu na gano ba karamin so kake ma matar nan ba, nima dan ina mahaifiyarka ne na hana ka kuma ka hanu, miyasa za ka ga laifin Suwaiba? abunda Halima take ni kaina ina jin haushi balle kuma ita da take matarka” “Matata Hajiya na sani, amman ba zan lamunci matata ta ci mutuncin yan'uwana ba, ko akwai so ko babu Halima jinina ce, yadda mahaifinmu be yarda mu raina yan'uwansa ba haka ba zan yarda ni matata wacce na auro take karkashin kulawata ta raina min yan'uwa ba, ta tsaya a matsayinta na matata, Halima kuma tana nan a yar'uwata” “Uhm Allah dai ya kyauta idan baka mutu ba komai gani kake, ita ma dai ban da iskanci ya zata rika aika maka da abinci guri aiki neman suna? Bayan tasan kai kanen mijinta ne? Wallahi yarinyar nan bata da kunya sam na raina tarbiyarta” “Hajiya kin dai tsani Halima kuma bata miki komai ba, matsalarta daya ta auri Abdulhamid kuma Abdulhamid din nan danki ne, ina laifi ta taimaka masa ta aure a halin da yake ciki? Amman kin dauki tsana kin dora mata bata miki komai ba Hajiya, yanzu ai zaki ga ranar ta, zaki gane ta yi jihadin auren danki, ba aure zai yi ba? Yanzu ba budurwa zai auro ba? Duk wanda be san ba shi da lafiya ba yanzu zai sani, ke da shi yanzu za ku gane idan Halima tana da hakuri ko babu” Tun da ya fara maganar ta zuba mishi ido, ta rasa gane wani irin so yake ma Halima nan, da baya ganin laifinta kuma baya son a ga laifinta. “Ta dai rubuce ka ta shanye Huisani ina tunanin ko ni da nake mahaifiyarka ba ka so na kamar yadda kake son matar nan, bata samu kan dan'uwanta ba kai ta samu kanka shiyasa kullum ciki mata bauta kake ita da yayanta” Murmushi yai. “Hajiya miye laifin Halima dan ta auri Abdulhamid kuma bata aureni ba? Kuma ba cewa tai dole sai ta aureni ba” “A lokacin da ka ce min kana son ka aureta, wallahi na yi murna sosai, kuma na jidadi domin na fi kowa son hada zumunci da iyala Malam Usman saboda alakarsa da mahaifinku, kuma ita wannan Suwaibar ba kiba take ba zaka auro mai dan kubakuba Wallahi naji dadi tunda ita Halima jikinta luwailuwai yake, aa wai kawai sai na ji zance ya canja ban san yadda akai ta ja hankalin Hassana ba ko dan tana ganin kamar ya fika arziki oho, shi da ba ruwansa da zancen aure ma taja hankalinsa har ya zo da maganarta, kuma bayan tasan kana sonta, yanzu da auren ya dora da sai ka rika kallonta a gidan dan'uwanka kuma kana sonta? Wani abun haushi ma har da aurenta take neman maza waje ko shiyasa ta aureshi dan ta samu damar hakan Allah masani, yanxu kuma aure ya mutu kana nuna alamar sonta taya zamu shirya da dan'uwanka? Kuma jama'a ku ce musu me? A family ayi ta mana kallon tumakai” Kamar yace wani abu sai wata zuciyar ta hana, ya san dai duk yadda zai yi ma Hajiya bayani ba fahimta za tai ba, ba kuma zata daina ganin laifin Halima ba, shi kanshi be jidadin abunda tai ba a wacan lokacin sai dai ya dauki abunda ta aikata da rashin tunani da kuma kaddarar da ke binta. Agogon wayarsa ya kalla. “Hajiya zan wuce gida sai da safe” “Allah ba mu alheri, na manta ban fada maka ba, surukan Hassan sun kira sun roki alfarmar a daga auren har nan da December” “Sun kara wata hudu kenan” “Allah ya kaimu ya sanya alheri” “Amin” Daga haka ya juya ya fice daga gidan. HALIMATU POV. A daren na rabawa kowa abunda zan bashi, babu wanda be yi murna ba. Washe gari aka tashi da hadari a garin sai dai hakan ba hana ni saurin shiryawa yarana suka wuce makaranta ba, ni kuma na shirya na nufi gurin aiki ina ta Allah Allah kar a sako da ruwa. Na yi sa'ar samun napep na shiga ina fada masa inda zai kai ni, mu tsaka da tafiya ya soma nuna min wata mota da ke binmu mai motar na mana hannu da mu tsaya. A lokacin da na leka sai na gane Abraham ne na rasa yadda zan yi da shi, me zan masa ya fahimci bana son ganinsa ma balle saurarensa. Ban bar mai napep din ya tsaya ba sai da muka kusan isa kamfanin sannan na bukaci mai napep din ya sauke ni, mai napep din na yin parking Abraham ya faka gaba da mu kadan ko kudin shi ban bashi na nufi gurin da Abraham din yake rai a bace. Ko da na isa ya sauke gilashin motarsa aiko take na nufeshi da masifa. “Me kake da bukata ne? Miyasa zaka rika bibiyarta? Bana son ganinka bana son wata alaka ta shiga tsakanina da kai, dan girman Allah ka kyale rayuwata na huta” “Ihu fa kike yi? Ba ki tsaya kin saurare abunda zan fada miki ba, na san ba kya son ana ganina a gidanmu shiyasa na biyo napep din da kika hau” Har na bude baki nai magan sai na ji tsayuwar mota a bayana, juyowar da zan yi na yi arba da Ahmad yana sauke gilashin motarsa. “Lafiya?” Sai na kalleshi na kalli Abraham sannan na sake kallonsa na ce. “Lafiya kalau” Ban san dalilinsa na tsare Abraham da ido ba, sannan ya sake kallon yace. “Shine mutumen da yake bibiyarki?” Na kalli Abraham wanda yai saurin tada gilashin motarsa yana mata key. “A a makocin mu ne” Be sake ce min komai ba ganin Abraham din ya bar wajen, sai shima yai ma motarsa key ya karasa cikin kamfanin, sai a lokacin na sallami mai napep din na karasa cikin kamfanin da kafa, ina shiga abokan aikina suk fara min murn wai an canja min aiki an bani wanda ba shi da wahala kuma mai albashi da mai tsoka, na yi murna kamar yadda su ma suke tayani murnar sannan na wuce office dina ina sanye da tufafin da na fi so kuma suka fi karbata wato abaya. Ganin Ahmad da nai a cikin office din tsaye jikin window ya bawa kofar baya hannayensa duka biyu zube a aljihu, gaba daya office din kamshin turarensa yake. A zatona ko na yi latti ne ko kuma wani abun na aikata ba daidai ba. “Ina kwana ranka ya dade” Be amsa min ba be kuma juyo ba, sai yai kamar be san da n shigo office din ba, wata kila kuma be san na shigo din ba, tun da ban yi knocked ba, hakan yasa na juya na fita daga office sai na tsaya daga bakin kofa nai knocked, ima ta jira ace na shigo amman shiru be ce min ba, ni ko na dage ina ta kwankwasa kofar a hankali. Can dai na gaji da tsayuwa sai na dan tura kofar a hankali da zimmar lekawa na ga ko ya nufo kofar ko kuma zama yai ko wani abun yake, kamar munafuka haka na leka office din kamar hadin baki sai muka yi ido hudu da shi ya juyo daga jikin window yana kallona da mamaki, saurin komawa nai na rufe kofar duk sai kunya ta kamani, amman hakan be saka na fasa knocked din ba, har lokacin kuma be ce min na shigo ba ko na tafi, lallai wannan mutum akwai girman kai tsinya, a gurin nai ta tsayuwa da na gaji na nemi guri na zauna, zan iya shiga yace na shigo ba tare da ya bani izini ba, tunda kamfaninsa ba, ko da yake na ga alamar kamar ya sauko daga yadda yake ba kamar da ba. Ina jikin kofar ya bude ta da dayan hannunsa yayinda dayan kuma yake cikin aljihu. Tsaye yai yana kallona ni kuma na tashi tsaye ina sadda kaina kasa. “Office din nawa ne ko naki?” “Amman ai kamfanin na ka ne, kai ke da ikon office din” “Office din nawa ne ko naki?” Ya sake tambaya. “Nawa ne” “Idan wani abu ya bata a office din nan ke za a tuhuma, ba a farin office bude kamar yadda kikai, ki rika kula da wanda zai shigo ko ya fita a office din” Ya karasa yana nuna min security camera dake bakin kofar office din, sai a lokacin na lura da ita. “Ke zaki bawa mutum izinin shiga office dinki ba wai ki tsaya jiran ya baki izini ba” “To idan na shiga kace na maka ba daidai ba fa” Barin jikin kofar yai ya karasa gaban teburin aikina yana duba wasu takardu dake wajen. Hakan yasa na shiga office din naja kujerata na zauna. “Me kake nema?” Be amsa ni ba sai duba takardun yake har ya dauko wata takardar ya nuna min ita saitin fuska. “Wannan.....” Juyawa yai ya nufi kofa har zai fice sai kuma ya juyo ya kalleni da manyan idanuwansa masu daukar hankali. “Miyasa ba ki yi reporting mutumen nan gurin police ba?” “Shi ma ai dan sanda ne, kuma yace min ya tuba ya ba ni hakuri, kuma yace zai musulunta ya aureni” “Dan sanda? Ya akai kika sani?” “Ranar da naje kai kara a office din akan shi sai n same shi a office din kuma kamar shi ma yana da mukamin a cikinsu m dan oga ake kiransa” Dawowa yai gaban teburin ya tsaya yana kallona. “Fada min one good reason daya saka shi yi miki fyaden a wannan ranar byan kin ce dan sanda ne, da kakin ya tafi” Kallonsa kawai nai na ki na amsa masa, shi kuma ya tsare da ido irin na babba da yaro, fuskarsa na nuna alamar ya fusata. “Ok fine...” Ya furta yana dauke idonsa daga kaina zuwa ga takadar da ke hannunsa. “Fuska a rufe da bindiga mijina suka je nema a lokacin baya nan shine suka ce za su bar masa sako” “So yanzu kin yafe mishi kenan? And you believe zai musulunta, kina ganin da gaske yayi nadamar da zai saka ya iya bayyana knsa a matsayin wanda yai miki fyade? Kina ganin zai yrda ya bar aikinsa da sana'ar saboda ke? Domin bayyana kansa a matsayin wanda yai miki fyade yana nufi rasa komai nasa ne, and what makes you think musulunci da gaske zai yi shi? Baki tunanin idan ya samu sa'arki zai iya aurenki ya dauke ki ya maidaki wani gurin inda baki isa ko harrarsa ki yi ba, addinin kuma sai yaga dama zai yi?” Na yi shiru ina ta nazarin kalamansa. “Fada min miyasa ya dawo gurinki?” “Yace yana bukatar haihuwa, saboda zai iya mutuwa a ko yaushe” “Hakan yana nufin yana neman haihuwa kenan be samu ba, sai da yai min miki fyade that's why ya kawo kansa, ina yar'uwar takardar nan?” Ya karasa yana nuna min takardar, a take na shiga dubawa zuciyata cike da tunani, duk wani duba takardun da nake idonsa na kaina. “Kin san wani abu? Kina da saurin yarda da mutane, kina da tsoron fushin wasu, kina iya shanye bakinciki dan wani yai farinciki, sune abubuwan da suke kara saka ki a damuwa, rayuwarki abar tausayi ce Wallahi, a yanzu ma za ki iya fadawa a wani tarkon” Ya fada yana kallona kamar ba shi yai maganar ba, domin bubu alamun hakan a tare da shi. “Ban ga takardar ba” “Kije reception ki tambaya inda suka tura takardar ki karbo” Yana fadar hakan na nemi guri ya zauna, ni kuma na saka kai na fice har an isa reception din suk fada min office din da zanje, wani bangare na kamfanin office din yake a lokacin da na isa tsayawa nai jikin kofar na kwankwasa har sai aka bani damar shiga sannan na shiga na gaisa da matar na fada mata abunda nake bukata sai ta dauko wasu files ya duba ta miko min takardar. “Ke ce sabowar ma'aikaciyarmu ko?” “Eh” Na amsa mata, tare da mika mata hannuna kamar yadda take miko min nata. “Yayi kyau sunana Zainab” “Halima” Sannan na jiyo na fito daga office din na nufo office dina, wannan karon ma sai da nai knocked sannan na shiga, jakata na tarar a bude hannunsa kuma rike da wayar da nake kyautata zaton tawa ce to me kuma ya kai shi a gurin jakata da har zai saka hannu ya dauko wayata, da sauri na kai hannu na fisge wayar ina bata fuska alamar ban jidadin abunda yai min ba. Uffan be ce min ba sai kallona yake, kamar ance min na duba a saman tebur din sai na kyalla ido na hango wayata kusa da jakar, hakan na nufi wayar da na karba ba ta wa ba ce kenan tashi ce. Aiko ba shiri dora tashi wayar a saman tebur din na dauki tawa ina jin kamar kasa ta bude na shige ciki. “Takardar...?” Ya tambaya fuskarsa babu alamar dariya, sai a lokacin na tuna da abunda naje neman, mika masa takardar nai ya karba ya mike tsaye. “Miye aikin shi da har yan fashi za su nemansa?” Da gangan nai kamar ban ji shi ba badan komai ba sai dan ya fita ya bar min office din. Ban bashi amsa ba har ya kai hannu ya dauki wayarsa yana ta kallona ya fice. Sai a lokacin na samu natsuwa har na cire wayar tawa a password na, kamin na taba komai sako ya shigo min da wata bakuwar number. “Fatar kina cikin koshin lafiya, na yi ta kira baki daga ba kina rejecting calls din, ko ba komai Halima ko dan yyanmu ai kya raga min ba kisan maganar da zan miki ba, izuwa yanzu idan ba rain kike son ya bar jikina ba ya kamata ace kin tausaya min, Wallahi kullum abunda na aikata yana damuna, na rasa samun sukuni idan har baki dawo gareni ba Halima ban san halin da zan kasance a gaba ba, tabbas Gobena zata zama mai rauni kuma abar tausayi” Ina gama karanta sakon na goge, sai yanzu na gano dalilin dauko wayata ta Ahmad yai wata kila kiran yai yawa ne shiyasa ya dauko yana mim rejecting kamar na saka shi. Na yi aikina kamar jiya yau ma ban ci abincin sai dai na sha ruwan lemun da aka kawo min tare da takeaway. Misalin biyar na tashi ban bar office din ba sai da nai sallah la'asar, daga office din na wuce gidan kawata Hajara, mun dade muna fira na labarta mata abubuwan da suka faru tun bayan rabuwarmu wato bayan zuwan da nai na karshen a gidanta. Sai magariba na baro gidan, kamar koyaushe napep yar gidana na hau na doshi hanyar gida. Ina fitowa daga napep din nai arba da Abraham dake tsaye jikin kofar gidanmu, sanye da riga da wando na shadda har da hula guluf din dake bakin kofarmu na haska fuskarsa tufafin sun masa kyau kamar ba shi ba, waiga nai ko'ina ban ga motarsa ba, ban ga alamunta ba, bayan na sallami kai napep din na nufi inda yake tsaye yana kallona na ce. “Minene kuma?” “Tambayarki na zo yi, bayan mutumen dazun? Wa kika fadawa na miki fyade kuma ina bibiyarki?” Shine abunda ya fito daga bakinsa yana ta kallona fuskarsa babu alamar wasa. “Babu shi ma kuma fada masa nai ba” “To ya akai ya sani?” Na masa shiru sai kallon mamaki nake masa. “Waye kai Abraham ina son sanin tarihinka, waye kai?” A maimakon ya bani amsa sai kawai ya amsa min da. “Sirrina nawa ne ni kadai, sai ke ya kamata ki san da wannan” Yana fadar hakan ya daga jikin kofar gidanmu ya nufi hanyar titi da kallo na bishi har na daina hangoshi, sannan na juya ina kokarin shiga gida Namra ta fito da saurinta ganina yasa ta tsaya. “Momy yi sauri ga Daddy nan ya zo, ya mana siyayya har da ke” “Kai Kai Kai..... Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Na furta da karfi ina dora hannu saman kai..... 7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2 *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣6️⃣ Bayan tafiyar Aminu, Abdallah ya kira ni a waya sai na tashi na bar dakin na shiga dakin inna inda babu kowa ina amsa masa wayar, tambaya yake akan Abraham din ina fada masa abunda na sani da kuma farkon haduwarmu har abunda ya kawo isuwa yau. “Bayan ni akwai wanda ya san da wannan maganar” “Eh ogan mu na gurin aiki” “Halima kin amince masa da yawa, kin manta waye shi ne?” “A a babu wani aminci a tsakaninmu, ya nemi yafiyata ne, kuma na rubuta labari ne a ranar children day a gurin ya gane cewar ni ce saboda labarin yarsa ya shigo ciki da kuma na kamfaninsa” “Ban gane ba zuwa kikai kika fallasa kanka abayyanar jama'a” “Aa....” Daya bayan daya na bayyana masa yadda abun ya faru har da zancen siyen tikitin da Abraham yai, hakan kuma ba karamin bata masa rai yayi ba. “Wayuya kawai taya shi Abraham din zai siya miki ticket kuma ki karba ki je” “To ba gashi na ci gasar ba” “Dalla can Sakarya kawai” Ya kashe wayarsa, a iya tunanina nikam ban ga illar zuwa bukin da nai ba, to ina ruwana da shi ai ba san shi na je ba, dan yarana. Ko da na fito dakin dukansu suna zaune a tsakar gida har Mama sai zancen Aminu suke, kusa da Inna na zauna ina sauraren Mama da ke fadin. “Namiji dai ba shi da kunya, yanzu duk abubuwan nan da Aminu yai miki har yana iya murje ido yai miki siyayya ya kawo miki yana rokon ki koma masa?ya manta irin cin mutuncin da yai miki ne ko kuwa ya runtse ido ne ya zo?” “Hmmm Mama ke ma dai kya fada, ni wallahi yanzu ko mai sunansa bana son ji sai na rika ganin kamar ma halinsu daya” Na Fada ina tabe baki,Sai Inna tai dariya tace. “Kuma kin ga fa inda rabon shiryarwa sai a shirya tun da akwai yaya har hudu, ai ko aure kika yi a wani wajen hankalinki yana kansu, nikam da za ki bi ta tawa da kin koma masa tun dai ya gyara halinsa kuma mahaifiyarsa ma yanzu tana sonki” Mama ta tari numfashin Inna tana girgiza kai. “A a wahalar da ta sha ta isa haka nan, ai ba ayi rai dan wani rai ba, wani lokacin mai hali baya fasa halinsa, Allah dai ya baki wani na kwarai wanda zai so ki tsakani da Allah, wanda zai kaunace ki har karshen rayuwarki, ya zame miki gata hawayen da kika zubar ya share miki su, kuma ya so yayanki kamar nasa, wanda zai rika jin tausayinki yana tsoron cutar da ke” Dan murmushi nai. “Samun irin wannan namiji yana da wahala Mama, mutum daya na san zai iya min haka, shi kuma babu wannan damar a yanzu, nikam na yanke kauna daga yin aure a yanzu” “Haba dai fata na gari lamiri, idan ba ki yi aure ba ki yi me? Aure ya haife ki kuma ya haifa miki yaya, ina kan fatana na ganki a dakin mijinki” Aisha da Hafiza da Husna kamar jira suke suka hau yi mata yaya, ba ma kamar Hafiza sarkin Baki. “Mu da ba a kauna ai sai a kai ku kofar gida a aje, wai har wani fata ake mata ga ku zaune, ita ba kara ita ba tayi auren har ta haifi amsu yi mata addu'a, mu da ko mashinshinin ba mu da fa?” Duk dariya muka saka har ita, sannan su ma tai musu addu'ar. Sai a lokacin na dauko siyayar da Aminu yai min na bude ina dubawa, Atamfa ce har biyu da turare da sabulun wanka da wanki sai yan kayan tande tande, komai ban dauka a gurin na rabawa Mama da Inna atamfar salubun wanka da wanki kuma na bawa kanena turaren na bawa Baba, sauran kayan tande tande kuma a nan na bar su a tsakaninsu suka raba suka cinye. Ina zaune a gurin amman ko chocolate din ban ci ba, sai aikin danna wayata nake. “Gobe idan Allah ya kaimu ina son zuwa gidan Gwaggo Ramatu” Mama ta fada. “Gaskiya kam kin kwana biyu ba ki leka ta ga, gata ita kadai ta rage muku cikin Gwaggonin” Na fada still idona yana kan wayata. “Shiyasa ai nake son zuwa, sai na siya mata salubu na kai mata” Da gangan na kalli Hafiza na ce “Ga sabulun Hafiza nan ta baki ki kai mata” Wata uwar harara ta watsa min. “Eh ni da ba kya kauna, to ba zan bayar ba, kuma Mama dakinki zan aje shi idan ma ban ganshi ba ba ruwana ni” Ta fada tana tashi ta bar mana gurin. “To idan ba ruwanki ai ba ruwan kowa” Na fada ina dariya Inna ma dariya take, haka ma Mama daman sun san Hafiza bata da na biyu a cikin gidan indai babin fada ne da matsifa, sai dai fa akwai son yan'uwanta kamar ranta, hakan yasa baka iya banbanta ni da ita kace kowa da uwarsa, mu zama kamar uwa daya daman kuma uban ne ya hada. Washe gari ta kama friday farar rana kuma kuraren lokaci, hakan yasa na gama shiryawa su Amal da wuri suka wuce makaranta ni kuma na shirya a yau ma abayar na saka sai dai wannan maroon color ce, sai da nai musu sallama sannan na nufi gurin aikina. Tun daga lokacin dana fito gida nake saka ran haduwa da Abraham saboda sabon da yai min na bibiya a baya wani lokaci amman har na isa ban ganshi ba, a yau ma ban ga Kabir ba, hankali ya dan tashi daman na san Ahmad ba zai kyale shi ba bayan abunda ya faru, to amman ina ya kai shi? A wane hali yake? Har na shiga cikin kamfanin ban daina yiwa kaina tambayoyi a game da Kabir ba. Can zuciyata ta kawo min cewar na taimaka masa da kudin na da samu ko zai samu lafiya, ba karamin dadi na ji ba da wannan idea ta fado min a rai. Ina isa office dina na tura kofar na shiga, kamar dai jiya yau ma na tarar an goge ko'ina an saka air freshener mai kamshi, jaka ta na fara dorawa a saman tebur din na kunna desktop din sannan na nufi window ma bude, tsaye na hango shi jikin windows din office dinsa hannunsa daya a aljihu dayan kuma rike da cup. Maida window nai na rufe na dawo na zauna na bude na fara duba abubuwan da suke kan teburin. Misalin 12pm Yunus yai knocked ya turo kofar ya shigo. “Halima ko?” “Yeah” “Kuna da meeting yau, ba ki duba takardun ba” “Na duba amman ban gane ba, ni? Kasan ni bana zuwa meeting” “Idan general ne dole da ke saboda mail din kamfanin na is under your control” “A ina ake meeting din?” “Karma hotel, ku kadai ake jira tuni sun fara taronsu ma” Na mike tsaye da sauri. “To ni da wa zan je?” “Ki dauki Laptop dinki ki samu Oga a waje, yana mota yana jiranki” Na dan ji wani iri, da shi kuma? “Ba ni da Laptop” “Shi zai baki” “Okay” Na fada ina daukar jakata na rataya sannan na nufi kofar fita ina gaba yana baya sai duk na ji na tsawwala ba dadi namiji ya saka ka a gaba ban san mi yake kallo a bayana ba duk kuwa da kasancewar na san abayar jikina bata matse ni ba sai dai hakan be saka na natsu ba har sai na na saka shi gaba ni na koma bayansa ina tafiya. A harabar kamfanin na samu motar Ahmad fake ina fitowa sai direban dake gaban motar ya fito ya bude min motar, abunda ba a tana min ba, kuma ban tana ganin Ahmad wani yana jan shi a mota ba sai dai shi yaja amman yau hakimce yake gidan baya ya saka suit dark blue, kallo daya na masa na dauke kaina a yau kam kyaunsa har wani tsoro ya bani ko dan ban taba ganinsa hakimce kamar haka bane? Ko kuwa dan ban tana ganinsa da kalar tufafin bane oho, sai kamshin turare yake. “Ina kwana...” Ya furta min so calmly kamar ba shi ba, ganin cewar ni ban gaishe shi ba, wata kalar kunya naji sai kaina yai girma kamar dutsen dala. “Ina kwana...” Na mayar masa, be amsa ni ba ya maida hankalinsa gefen titi, har muka isa be kalli inda nake ba, nima kuma ban sake kallonsa ba har muka isa. Direban ya zagaya ya bude masa nikan ban jira a bude min na bude na fito daga motar mai sanyin ac wacce har ta fara saukar min da mura. Wata yar karamar laptop direban ya miko min da pen sai wani littafi mai kamar diary, sannan dauko wata jaka wacce nake kyautata zaton ta Ahmad ce yai gaba ni da Ahmad din muka rufa masa baya, kana ganin kofar shiga dakin taron kasan taro ne na manyan mutane, domin an zuba securities a gurin gwanin sha'awa. Na yi zato ko sai mun yi musu wata magana ko nuna wani abun sannan su bar mu shiga ga mamaki ne sai kawai na ga an bude mana kofa, daf da zamu shiga cikin gurin Ahmad ya risuno saitin kunnena ya rada min. “Ki kashe wayarki” Yana fadar hakan yai gaba abunsa ya shiga cikin gurin, ya bar a bakin kofar tsaye da mamaki, to miye wani abun mamaki? Wata kila baya son aji muryarsa ne shiyasa yai haka. Umarninsa na bi na dauko wayar na kashe sannan na maida ta a jaka na shiga cikin gurin. Ina shiga na fara rabon ido, babu mutane sosai amman kusan rabin taron duk turawa ne, wasu a taeburin manyan baki wasu a teburin masu daukar darasi irinmu, ga wani katon majigi da ke saman gurin wanda da shi suke ta nunawa mutane abubuwansu. A zagayayyen tebur muka zauna ni da shi, sai dai kujerar tawa tana fuskantar tashi ne kamar yadda shi ma yake fuskanta ta, amman idonsa yana gurin abunda ake nunawa a majigin. Nikam sam hankali baya gurin abunda ake fada yana gurin mutanen dake gurin ne, idan na kalli wannan na kalli wacan har na kallo Ahmad, da idon yai min alama da na maida hankalina gurin abunda ake, ba musu na tattara hankalina na maida gurin mutanen, muna zaune a gurin har kusan karfe daya. Direban dazun ne wanda ya kawo mu ya sake shigowa gurin ya nufo inda muke zaune ya kai bakinsa saitin kunnen Ahmad ya fada masa wani abu. A take na ga yanayinsa ya sauya, sai ya tashi tare da diraban suka fita, ni dai ina zaune a gurin har ya dawo a yanzu kuma baya kallon kowa sai ni, just me and me alone, har aka tashi daga taron 1,30pm bayan an bi ko wane tebur an dora takeaway da ruwa da lemu. An yi mana hoto da turawan da kuma sauran wadanda suka zo taron, sannan mutane suka fara watsewa, nima na tashi ganin ogan ya tashi shi be dauki komai ba daga abunda aka kawo masa na sha da ci sai direbansa ne ya dauka ni kam na kai hannu na dauki abuna, ko ruwan ban bari ba, balle kuma yar karamar takadar da aka dora mana sama wacce nake kyautata zaton kudi ne. A kofar fitowa suke bawa mutane memo da magazine da kuma calender. Sai da muka shiga motar sannan ya kalleni ya kalli kayan hannuna har na ji yar kunya. “Ina wayarki?” “Tana cikin jaka” “Mu gani” Ya zuro min farin hannunsa. “Na kashe ta fa” Ganin be janye hannun ba kuma be dauke idonsa daga kaina ba yasa na saka hannu a jakar na dauko wayar na mika masa, a zato na dubawa kawai zai yi ya bani sai na ga ya zura ta aljihu, kamar nai magana sai kuma wata zuciyar ta hana ni. Ba mu yi nisa sosai da hotel din na ga direban ya faka motar gafe ya fita ya zaga bayan motar ya dauki abubuwan da ya dauko a gurin taron sannan ya rufe, Ahmad kuma ya fita daga motar ya shiga mazaunin direba yaja motar, ni kam ina zaune baya abuna sai dai sanyin ac yayi min yawa har na fara jin kamar ciwon kai na son kamani. A nesa da masallacin gada biyu ya faka motarsa ya bude ya fita sannan ya zagayo inda nake ya bude min. “Zanje nai sallah ki dawo gaba” “Ban iya tukin mota ba” “Ban ce ki tuka ba, a front seat zaki zauna” Na fito na bar kayan a baya sannan na rufe motar na bude gidan gaba na zauna ina ta mamakin karbe min waya da yai, can kuma na tuna da abunda yai min jiya, wata kila dan kar ayi ta kirana ne muna tare kuma baya son hayaniyar kiran, amman ai sai ya bar min wayata yace kar na kunna. Ni dai ina zaune a motar har aka sauko daga sallah juma'a mutane suna ta wuce, sannan ya bude motar ya shigo yai mata key muka hau titi, a hankali yake tukun kusan ko wace mota ta zo sai ta wuce mu, kusan da mu da masu tafiya kasa duk daya idan ma akwai tazara kadan ne. “Kin na rasa yata ko?” Na juyo na kalleshi sai na ga ba ni yake kallo ba, amman tabbas na san da ni yake domin daga ni sai shi ne a motar. “Eh” “Na rasa mahaifina ma, na rasa Matata mahaifiyar Baby” Ya sake fada still be kalleni ba. “Allah ya musu rahama” Be amsa da amin ba, sai yai wata maganar ta dabam. “You got lucky baki tana rasa kowa ba, the pain of losing someone is unforgettable, mahaifina na fara rasawa, mahaifina yana da ciwon suga, a lokacin da abun ya taso masa an fitar da shi waje, a cairo ya rasu a lokacin na shiga tashin hankali sosai, kin san saboda me?” Na girgiza kai. “Saboda Hajiyata, ya mace zata ji idan ta rasa mijinta? Ya da zai ji idan ya rasa mahaifinsa? Ya yar'uwa zata ji idan ta rasa mahaifinta? A lokacin nauyin Hajiya da Siyama da nawa ni kaina sai taro duk a kaina, tausayin kaina tausayin Hajiya tausayin Siyama, mu biyu kawai Allah ya bashi, daga ni sai Siyama, Hajiya tana son yayana sosai, sai dai duk haihuwarta yaranta rasuwa suke daga ni sai Siyama muka tsaya, shiyasa take son Siyama sosai wani lokacin tana kiranta da autarta, kamar yadda nima take so na sosai har take kishina, tana ganin kamar wata macen zata karbe mata ni, lokacin da muka rasa mahaifi komai na mu ya tsaya cak, ciki har da rayuwarmu domin mahaifinmu shine komai na mu, kullum Hajiya tana cikin damuwa Siyama ma haka” Yayi shiru ya kai hannunsa ya dauki gorar ruwan da ke cikin motar ya bude ya kurba sannan ya aje. “Daga lokacin na fara tunanin gina rayuwata, da ta mahaifiyata da kuma ta kanwata, a lokacin ne na fara neman aure har akai nasara na auri wata yarinya, she's my first wife but not my first love, domin na aureta ne ba wai dan na san miye soyayya ba a lokacin, a gida daban muka tare, daga lokacin da nai aure sai rayuwa ta ta canja daga matashi wanda yake zaune a gidan mahaifinsa zuwa mai mata da yake zaune a gidansa, na aje aikin da nake na soja a lokacin na cigaba da kula da kamfanin mahaifina na zinari, a cikin na bude makaranta wa Hajiyata duk wani abu na makaranta a hannun Hajiya yake zuwa, a da kullun tare da Hajiya muke karyawa komai kusan tare muke amman da nai aure sai abubuwa suka sauya, daga lokacin sai Hajiya ta fara ganin kamar matar da na aura tana kokarin mallake ni ne, sai ta cilasta min dole sai na dawo a cikin gidan mahaifina na kama part daya na zauna da ita, ita kuma tace ba zata zauna da Hajiya ba, daker na samu kanta ta amince muka zauna tare, sai kuma ta hanani cin abincinta tana cewa zata saka min magani a ciki, ta fara takura mata ta saka abubuwan da ya kamata ace mai aiki ce zatai, da ta kasa jurewa sai ta nemi fita Hajiya tace na sake ta, a haka nai aure har uku yana mutuwa saboda takurar Hajiya, ban zamu wacce ta dade ba sai mai sunanki, mace mai hakuri kamar ke, mai kawaici da sanin ya kamata, ita ta haifa min Baby Namra, a cikinta na biyu ne ta rasu, a ranar da ya rasu ni kaina bana iya gane kaina, domin rasa abokin rayuwa yana nufin rasa wani bangare na jikinka...” Ya karasa muryarsa na rawa, hannuna na kai na dauki daya daga cikin tissue da ke cikin tissue ibox na mika masa sai ya karba. “Thank you” Ya tare gefen idonsa sannan ya sake kurba ruwan, ya bude gilashin motar iska ya shigo wata kila sanyin ac baya wadatar da shi. “Sai ta bar ni da Baby, after that na sake aure biyu ya mutu, dayan saboda Hajiya dayan kuma saboda matar bata son Baby sai ta rika kishin yata tana ganin kamar ina nuna mata so da yawa ne, daga lokacin sai an gimgine maganar aure a gafe, na cigaba da rayuwata da yau da kullum, sai gashi na samu kaina cikin farinciki a haka muke rayuwa da kanwata da mahaifiyata da yata sai kuma sauran dangi na yan'uwa, amman dai a familyn mu mu kadai muka rage yayan Abbah, so the day I lost Baby, ba zan iya fada miki abunda naji ba, at first ban ji komai ba sai daga baya, kuma na kasa blaming kowa sai ke saboda a gurinta ta rasu, and she always talking about her friend i mean your daughter, tace na baki hakuri be kamata nai fada da mahaifiyar abokiyarta ba, so the day that i decided zan baki hakuri....” A nan din m shiru yai sai hawaye ya gangaro ta gefen idonsa. “Ina son yata sosai....” Ya fada yana rumtse idonsa na wani lokaci kamin ya bude. “Tana da sakewa, tana da kyauta duk da kasancewar ta karama, ga ta da wayo, ga son mutane bata da abokin shawara sai ni bata da abokin wasa daga ni sai Siyama wacce ta zame mata kamar kawa, sai kuma Hajiya wacce ta zame mata mahaifiya, Baby bata da kawa ko daya sai yarki da ta samu daga baya, that's why take yawan damun kanta kullum sai ta ganta.... ” Ya lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya da karfi. “Abubuwa da yawa suna faruwa saboda ni, kai ma idan kana tare da ni wani abun zai iya samunka Dan Allah ka sauke ni a nan” Na fada ina kawarda fuskata wasu hawaye masu zafi da radadi suna sauko min, a yau kan na manta da damuwata labarin Ahmad ya ban tausayi, domin rasa uba, ya, mata, abubuwa ne da basa fassaruwa da ko wane kalar yare. Murmushi yai ya miko min tissue da na bashi “Take your tissue back” Na karba na share hawayen, sannan ya miko min ruwa na karba na kurba sai na rike gorar, ina jin kamar wani hawayen zai sauko min. “Can I imagine your life without your parents?” Dam dam dam na ji gabana ya yanke ya fadi, kallonsa nai kamin na kalli gorar ruwan dake hannuna. “Uba wani jigone na rayuwa, bayan Allah da manzosa, iyaye ne suke da muhalli na biyu a rayuwar ko wane dan'adam, daga lokacin da ka rasa uba za a fara kiranka maraya, saboda uba gangone na gingina, shi zai nemo ya kawo a ci, shi zai tufatar ya ciyar ya shayar ya ilmantar, uba wani jigone na rayuwa, gata ne, uwa kuma ita ce gaba daya rayuwar, idan babu uwa duk farincikin da zaka samu a duniyar nan ragaggene no matter what it's, uwa abokiyar tafiyar rayuwa ce, abokiyar shawara abokiyar kuka abokiyar dariya abokiyar farinciki abokiyar bakinciki, idan da yai kuka ka ji ba a rarrashe shi ba, to babu mahaifiyarsa a kusa ne, macen da zata dauki cikinka tun yana da second daya har yai wata tara ta haife ka ta jure kashi da fitsarinka ta rayu da kai a ciwo da ba ciwo, har ka mallaki hankalin kanka? Uwa ita ce gaba daya duniyar. No never... I can't imagine my life without one of them they are my super supporter's my everything” Na karasa cikin kuka, ina jin wani irin shauki da kaunar iyayena ya kara kamami, iskar bakinsa ya busar ya jingina da kansa jikin kujerar motar yana kallona kamar bashi ba. “Zan kai ki gida gurin Hajiya ki yi sallah” Na share hawayena ina kallonsa. “Mun tashi daga aikin ne?” Na gyada min kai yana kokarin parking motar still idonsa na kaina. “Idan haka ne ai kara na wuce gida kawai” “No gurin Hajiya za ki yi sallah” Bance masa komai ba sai na maida dubana gurin yan yatsun hannuna, ina jin faduwar gabana yana karuwa ga wani uban ciwon kai da ya saka ni a gaba, ban san miyasa yau Ahmad ya zame min wani dabam ba shi ba. Key yai ma motar muka hau titi wannan karon ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa gidan, horn daya ya danna aka bude masa gate, ya kunna kai a cikin gidan, be yi farkin a ko'ina ba sai bakin kofar falonsu, fita yai shi kadai yace na jira shi a motar ya shiga cikin, be jima ba ya fito ya bude min motar yace na fito, haka na fito ina jin jikina ba kwari na shiga ciki, kamar dai wacan karon wannan karon ma Hajiyar da far'a ta tarbe mu sai dai yanayin yadda take kallon fuskata tana nuna alamar tausayi. Bayan mun gaisa, tai ma Kanwarsa magana tace ta kai ni ciki nai sallah, da sauri yarinyar da aka kira da Siyama ta tashi tai min jagora har dakin Hajiyar, a bathroom dinta nai alwala ko da na fito an shimfida min carpet an dora Hijabi sama, sai kawai na dauka na saka na fara sallah azahar a lokacin uku ta kusa. Ina sallah shaidan ya fara yayo min tunani kala kala, kamin na gama sallah jikina har rawa yake, ina gamawa na cire hijabin na dauki veil din abayata na yafa na fito falon inda Hajiyar take na zauna, Ahmad ma yana zaune a falon ina son nai masa magana na kasa. “Siyama kawo mata abincin” Ya fada yana kallon yanayi gaba daya idona ya fito fuskata ta sauya. “Wayata ina son magana da.... ” Tun kan na karasa ya tari numfashina. “Zan baki anjima” Wannan karon kallonsa nai da kyau. “Wa na rasa Ahmad? Uwa ko Uba, ko yaya? Ko kane? Fada min” Mikewa tai tsaye yana kallona sai nima na mike tsaye. Can kasa kasa na jiyo Siyama na fadin. “Ku fada mata gaskiya mana, dole ne ta sani” “Siyama fita ki bar falon nan” Ahmad ya fada mata a tsawace, kamar tana jira ta juya ta fice cikin fushi. “Ka fada min wanda na rasa, ba zan iya dawo musu da rai ba, iyakar abunda zan yi hakuri ne” “Muje na kai ki gida” “Ka bani wayata” Na daka matsa tsawa da wata irin murya daban taba sanin ina da ita ba, gaba daya jikina rawa yake. “Ina da kanen, idan an rasa Uba sun zama marayu wa zai kula da su, idan na rasa Uwa wa zai maye musu gurbinta shikenan sun rasa gata” Na fada ina rufe ido kamar mai nazari. “Allah baya barin wani dan wani duk a can muka fito iyayenmu sun tafi sun bar mu, kuma a can zamu koma gaba daya” Mahaifiyarsa ta fada idonta cike da hawaye, takawa na fara yi sai na ji kafar ta malgwade ina neman faduwa har sai da tai saurin rike ni, a hakan na sake unguri takawa kafafuwan suka fara rawa sai ta na tsaya cak, da nai unkuri na uku sai na tafi zan fadi har sai da Ahmad ya rike ni da kanshi ya zaunar akan kujerar. “Ki natsu sai na kai ki gida” “Ka kaini yanzu” Na fada kai tsaye tare da mikewa tsaye na fara tafiya cikin karfin hali, ba shiri na ji numfashina yai sama wani hudu ya baibaye idona, jikina kuma yai arba da kasa..... __________________________ Allah ka jikan mahaifina kai masa Rahama ka saka aljanna ta zama makomarsa, Mahaifiyata kuma ka karasa mata lafiya da kwanciyar hankali da natsuwa ka yafe mata kurakuranta kasa ta cika da imani 🙏 da duka sauran iyayenmu musulmai 😭🙏 Rashin iyaye wani ciwo ne da ba a manta shi 💔💔💔 may Allah see us though. 🙏 7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣7️⃣ A yau kam kamar an halittoshi ne kawai domin kallon Halimatu, ya kasa zama kamar yadda a tsayin ma ya kasa yin nesa da ita sai daf da gadon da take kwance, fuskarta yake kallo, be taba tsaya ya kalleta kamar haka ba, daman can ahali shi ba mutum ne mai tsaya ya kwankwace mace ba. Amman a yau yana jin kwanciyar hankali da natsuwa a kallon Halimatu, dogon hancin ya fara kurawa ido kamin idanuwansa su sauka akan karamin bakinta, fuskarta circir bata da rama kuma bata kumbura sosai ba ta cike abunta gwanin sha'awa, farin fuskarta dana jikinta har wani shining yake, ga jikinta Ma-sha-Allah irin wanda ake so a mata, tana da jiki sai dai ba can sosai ba, akwai kurciya sosai da yarinta a siffarta da surarta amman ba irin ta under 20 ba, irin wacce zaka kalleta kai zaton Amal ce yarta ta farko ba Adnan ba, babu abunda ta rasa a siffar ya mace sai na tsuwa da kwanciyar hankali. Ta saman idonta yake hango damuwarta, labarin abunda ya same ta ta kuma yadda yake tunanin Gobenta zata kasance, be san miyasa yake tausayinta da yawa ba, yes be taba jin labarin daya taba masa zuciya ya hana hankalinsa kwanciya ba kamar nata, sai dai be taba tunanin hakan zai saka wani kusanci a tsakaninsu ba, the way da ya daukota ya kawo gurin Hajiyarsa, yadda yake ta kokarin boye mata mutuwar mahaifinta and ya bata tahirin rayuwarsa a free, ko da yake yayi hakan ne saboda kawai ya nuna mata ko da ta rasa ba ita kadai ce a cikin jarrabawa ba. Kansa ya daga sama ya sauke numfashi a hankali, hannayensa duka biyu na zube cikin aljihu, can kuma ya sauke kan yana cigaba da kallonta, wani sinadarin tausayinsa ke fita daga cikinta yana shiga zuciyarsa, tausayinta ta cika zuciyarsa makil, a yadda take ya mace ace tana cikin irin wannan kalubalen na rayuwa ita din abar tausayi ce matuka. Hannunsa ya saka aljihu ya fiddo wayarta, hakan nan kawai yaji yana sha'awar kunnata, and he press the power button ya kunna wayar. Hoton yaranta hudu a screen din wayar, he found himself smile yana shafa screen din wayar. “Beautiful kids” Ya furta yana maida hankalinsa sosai gurin kallon Amal, a zatonsa ita akai wa fyaden tunda ita ce karama marar wayo. He was just imagine if ace shine mahaifinta, ya zai yi wa mutum yana jin aransa zai iya kashe wanda yai wa yarsa haka, but look at them a maimakon ma ya yarda da mahaifiyarsa sai ya karyata ya saketa akan hakan, tunawa yai da lokacin da Namra ta bata har ya tsinceta, yanzu ya gane duka responsibility na yaran akan mahaifiyarsu, shi uban babu ruwansa, zuciyarsa ta cika da tsananin mamaki ashe ana samun useless father like her husband? Wayarta ce tai ringing sunan Abdallah ne rubuce a saman wayar, haka yai ta kallon wayar har tai ringing ta katse be dauka ba, at the end yai deciding ya sake kashe wayar ganin wata Number ma ta sake kira mai sunan Hajara. Yana kokarin mayardar wayar aljihunsa aka turo kofar dakin aka shigo, wata dattijitowa ce da ba zata gasa 50+ ba, ko tantama babu yasan yar'uwar Halima ce tun da ya aika direba a can gidansu a fada musu ta suma ya kawo ta asibitin kuma wani nata ya zo ya zauna da ita. “Sallamu alaikum” Matar ta fada da katon Hijabinta, sai ya amsa mata yana binta da kallo. “Ke ce?” “Yayar mahaifiyar Halimatu” “Alright, ga wayarta aje mata Allah ya sauwake” Ya fada yana mika mata wayar, ita kuma ta karba tana masa godiya. “An gode Allah ya saka da alheri ya kara sutura” “Amin, an kai shi ne?” “Eh an kai shi gidansa na gaskiya tun dazun” “Ok” Juyawa yai ya fice, sai da ya biya ya samu Doc Nura a Office dinsa yana duba wasu marar lafiya, tsaye yai har sai da ya gama. “Doc zata kai yaushe kamin ta farka?” “Zata dauki lokaci, tun har bata farka na da aka kawo ta nan, kuma a gida ma kace ai kun saka mata ruwa ko” “Yes a can din ma bata farka ba” “Hakan na nufi zuciyarta ba kamar tawa take ba, gaskiya akwai damuwa sosai a zuciyata, irin wannan bugawan zuciyan wani lokacin ya kan so da ajali, kara ma naka idan rai ya bace yana nunawa duk da shi ma mai hadarin ne, amman irin nata yafi naka hadari domin irinta za a cigaba da bata mata ran ne, ba tare da an san tana da wannan ba, idan kuma zuciyarta ta cigaba da buga kamar haka zata iya mutuwa a take, kuma ina tunanin bata shan magani ko?” “Ban sani ba gaskiya” Ya amsa zuciyarsa na kara cika da tausayinta. “To ya kamata a tambaye ta, ko kuma a ga likitanta, yanzu dole sai ta farka zamu iya yin wasu gwaje gwajen, amman jinin zuciyarta yana gudu da karfi fiye da kima wanda hakan matsala ne babba gaskiya, har yanzu da take sume zuciyarta na bugawa fiye da yadda ake son tana bugawa” “Babu wani abu da zaka iya yi mata Doc i trust you” “Yeah dole ne sai mun san irin gwaje gwajen da akai mata, kuma tana karkashin shan magani ko a a? Kamin yanzu ya zuciyarta so dole sai ta farka ko kuma idan kasan likitan da ke dubata zaka iya hada ni da shi” “Ban sani ba, ban san komai akan hakan ba, dole sai ta farka ko kuma wani daga danginta ya fada” “Yanzu dai best medicine shine a daina bata mata rai ko barinta da damuwa, duk maganin da za a bata zai taimaka mata ne kawai abun yai kasa, amman ba zai iya wakar da ita ba, matukar ba ta daina damuwa ko kuma a daina bata mata rai ba” “Thank you” Shine abunda ya fada ya juya zuciyarsa cike da tunani kala kala ya fice daga office din. Harabar asibitin ya fito ya nufi gurin da ya aje motarsa ya shiga yai mata key, ba gida ya jufa kai tsaye ba, family house din su Halimatu ya nufa a gurin yai musu gaisuwa ya kuma shiga har cikin gidan yai ma mahaifiyarta da yan'uwanta gaisuwa. Ko da ya fito unguwar ana Sallah magariba a hanya ya tsaya yai sallah sannan ya karasa gidan Hajiyarsa jikinsa duk a sanyaye, mutuwar mahaifin Halimatu ya tuna masa da mutuwar nasa mahaifin da kuma matarsa da yarsa, kuma ta tuna masa cewar Hajiya da Siyama ne kawai suka rage masa. A falon Hajiya ya zauna tasa aka kawo masa abincin amman ya kasa kallon abincin ma balle ya ci. Ita kanta mutuwar mahaifin Halimatu ya tuna mata da mutuwar mijinta mutum mai dattako da taimako. Haka yai zaune ya zubawa katon tv ido duk da hankalinsa ba a can yake ba. “Allah yai muka albarka Ahmad kai da Siyama, ya yalwantar zuri'ar Muhammadu ta karkashinku” “Amin Hajiya” Ya fada yana dauke kansa daga kallon tv ya kalleta. “Ina tunanin aika abincin a gidansu What do you think?” “Hakan na da kyau, a yanzu mai taimaka musu suke nema, Allah dai yai masa rahama” “Amin, dazun da safe nake ta tunani a raina cewar ya kamata na samu mahaifinta da maganar mutumen nan mai bibiyarta, domin ina tunanin iyayenta ba su sani ba, a gidansu ma bana tunanin akwai wanda ya sani, a tare muka je meeting dazun ina son nai mata maganar ganin mahaifinta, amman duk sai naji ina jin nauyi na kasa yi mata magana, ashe duk lokacin ma ya rasu” “Allah be kaddarar ganawarku bane, amman wannan yarinyar tana cikin taskon rayuwa, a halin da take ciki kuma wani ya fada mata, Wallahi ta bani tausayi sosai, tana bukatar farinciki ko yaya ne a yanzu” Be yi kasa a guiwa ba ya labartawa Hajiya abunda Doc Nura ya fada masa. “Irin wannan mahaifiyar da ace tana da kudi sai ta dauke ta ta kai ta can wata kasar ta huta ta wannan kunci har sai ta samu sauki ta dawo, Allah sarki rayuwa kenan Allah ya yaye mata” “Amin” Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya. HALIMATU POV. Ba zan iya fadar awannin da na dauka a sume ba, dan dai ba a mutuwa a dawo na nace mutuwa nai na dawo, domin komai na dakin ganinsa nake fari tas, ina jin yawun bakina ya kafe, hayaniyar mutanen uku da ke tsaye kaina ma jinta nake kamar wani yare, ina jin suna taba jikin suna soka min abu suna danna zuciyata can kuma suka daga idona, na kusan minti goma shabiyar a haka sannan idanuwana suka fara gani daidai, sai dai jikin babu kuzari ko kadan yawun bakin ma har a yanzu babu su, numfashin ma ina jin kamar baya isata. “Sannu” Likitan ya fada, sai na gyada masa kai, ina kallonsa ya sake yi min wata allurar a cikin ruwan dake shiga cikin jikina. Bayan fitar likitocin na fara kokarin tuna abunda ya kawo ni dakin, a take kaina ya saka hawaye suka samu haya, a hankali na juya kaina sai nai arba da inna Lami, hakan ya tabbatar min da mahaifi na rasa kenan, domin da Mama na rasa da Inna Lami ba zata iya zuwa nan ba saboda kukan rashin yar'uwarta uwa daya uba daya. “Sannu Halimatu Allah ya baki lafiya” Unkura nai na tashi amman na kasa sai hawaye nake jikin nawa har lokacin babu kuzari. “Lafiya kalau na fita na bar Baba, miya same shi?” “Ai baya bata da kadan Halimatu, ciwon ciki ne ya taso masa sai amai ko kamin ayi wani abu yace garinku” “Da gaske Uba na rasa” Na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi. Ban tana jin irin abunda na ji a yau ba, kamar nai hauka nake ji, kamar nai ihu na dawo da shi, ashe haka yaran da suka rasa iyayensu suke ji? Ashe haka mairaici yake da ciwo, ga ni kenan da nai aure har na haifi yara, ina ga kanena da basu yi auren ba, a take tausayinsu ya kara rufe min zuciya. Na dade ina kukan duk yadda Inna rai rarashina sai na ji kamar tana kara kura wutar kukan ne, misalin karfe daya aka bani tea na sha sai lemun hausa da aka yanka min, a daren ban sake runtsawa ba har safe. Duk yadda likitan ya so na sauna har nan da kwana biyu ban nuna masa amincewa ta ba, a dole ya sallame ni bayan ya bani shawarar na sake dawowa nan da kwana biyu domin a duba lafiyata. Ya fada min halin da zuciyata take ciki da kuma irin treatment din nake bukata. Misalin goma muka baro asibiti tare da Inna, da wasu yan'uwanmu da suka zo dubamu, kamin mu isa gida Mama ta fado min rai, sai duk tsoro ya kamani kar na zo na rasa ta ita tun da tana da hawan jini, tun a napep din nai ta kokarin tsayar da hawayena amman abun ya gagara ashe hawayen mutuwa su suke yin kansu, ina ta ganin kamar idan na isa gida zan yi arba da Baba ne a inda ya saba zama, sautin muryarsa yana ta dawo min a kunne, yadda yake dariya da duk wani hali nasa na kirki zuciyata tana ta janyo min shi. Ban kara tsinkewa ba sai da nai arba da yan karbar gaisuwar a kofar gidanmu, lallai mutuwa babu wanda ba shi da tambonki, a lokacin dana shiga cikin gidan sai kukan kowa ya koma sabo, saboda yadda nake ta nawa kukan, idan na kalli kanena da mahaifiyata da abokiyar zamanta sai na rasa wa zan tausayawa. Hakika mutuwa bata da dadi, duk wanda ya zo mana gaisuwa sai yai mana nasiha akan hadin kai da son junanmu, an yi ta zuwa mana gaisuwa mutane da yawa wasu har bana ganesu, abunda Abdallah yai min ya kara min son sa sosai a raina, ya nuna min na zama mai karfin zuciya da dakiya, ni ce babba idan kanena sukai ba daidai ba na musu fada kamar yadda zan yi ma yayana, ya kawo abinci mai yawa da kudi. Abdulhamid ma ya saka an kira masa ni yai min gaisuwa, Aminu kam da shi akai zaman uku har aka gama, ranar da akai sadakan ukun mama take fadin cewar Ahmad ya aiko muna da abinci da kudi mai dama kuma ya shigo har cikin gidan yai musu gaisuwa. A daren ranar Abraham ya ziyarce ni, irin ziyarar da ya saba kawo min a duk lokacin da ya so ganina. At first fuskata ya fara haskawa da wayarsa. “Ki yi hakuri, rashin wani ba dadi duk da dai ban rasa kowa ba, amman na san babu dadi can I hug you” “Na gode” Na fada ban jira cewarsa ba na jiya na bar masa wajen, a daren ranar sai gidam ya zame mana kamar wani kango, muna ta firar Baba muna kuka, Aisha take cewa kara ni na yi aure na haihu har yaga yayana su ko auren ba su ba, sai naji duk tausayinta ya kara kamani. Wasa wasa aka dauki sati daya babu Baba Mama da Inna suka shiga takaba, a lokacin ne na kara tabbatar da mutuwarsa, a kowace rana sai na tuna yadda nake zuwa gaishe shi da yadda yake shigowa cikin gida. Haka na kwashe sati biyu ban leka gurin aikina ba, kowa kuma be leko ni daga can ba, sai dai wata na karewa na ga albashin 67000, maimakon na jidadi sai na ji rashinsa domin na saba a lokacin da nake aiki nakan cire wani abu nai ma Baba da Mama da Inna siyaya. Washe garin ranar da na ga albashin na shirya na tafi gurin aikina, ban ji kowa ya min gaisuwa ba hakan yana nufin babu wanda ya san da zancen mutuwar kenan, na nufi office dina cikin rashin walwala, sai na samu matar can a ciki wato Zainab, mun gaisa da ita cikin mutuntawa sannan tai min bayani wai oga ne yace ta zauna na wucin gadi har zuwa lokacin da zan dawo. “Okay” “Amman ki fara zuwa ki fada masa kin dawo tukuna” Ba musu na juya na fita daga office din na nufi hanyar da zata sadani da office dinsa, sai na shiga office na farko na shiga na biyu sannan na isa nasa. Ko da na shiga yana zaune jikin kujera yana waya, ganina ya saka ya yanke wayar ya taso da far'ar shi ta wayayin mutane kamar ba Ahmad ba ya tare ni. “Wow my friend na dauka zaki yi wata fa” Na yi kasa da kaina. “Ina kwana ranka ya dade” “Lfy kalau ya hakuri” “Al-hamdulillah, na zo office na tararda wata” “Yeah kin san gurin ba a barinsa hakanan ba kowa, shiyasa muka sakata kamin ki dawo, ina fatar ba mu yi laifi ba” “Kamfaninka ne kana da dama da yancin da zaka yi duk abunda kake so, ciki har da korata ko canja min gurin” Na fada muryata na fita so slow. “Hajiya tace kar na koreki, yanzu ko kin min laifi bana da halin korarki tun da Hajiya ta shiga tsakani, kin shiga ranta sosai kusan kullum zancen ki muke.....” Na yi murmushi ina murza yatsun hannuna, yatsun nawa ya kalla sannan ya kalli fuskata kamin ya juya zuwa gurin teburinsa. “Na gode” Daga can inda yake tsaye ya dago ya kai ya kalleni. “Da me?” “Da komai da komai, na gode Allah ya saka da alheri” “Amin Allah ya bamu hakuri we almost sharing the same journey, yanzu kin fahimci yadda rashin mahaifi yake kamar ni, gashi kece babba duk wanda zai miki magana zai ce ki yi kokarin hada kan yan'uwanki right” Ya karasa yana murmushi kamin ya cigaba. “Haka akai ta min sai nake jin kamar an dora min wani nauyi akai, na rika ganin kamar ba gaske ba ne, ina ta ganin kamar idan na shiga gida zan ga Abbah, idan na kalli Hajiya ta bani tausayi haka ma Siyama, yanzu da nai hakuri na dauki nauyin sai abun ya zo kin da sauki, amman fa har yanzu Hajiyata bata yarda na girma ba, idan zan fita zata bani time din dawowa idan na dade zata kirani tace na dawo dare yayi ko rana, babban mutum kamar ni” Daga ni har shi murmushi muke sai ya tako ya karaso kusa da ni ya miko min tissue, ashe ya lura da hawayen da suka taru a idona. “Miyasa ba ki koma gurin Doc ba?” Na yi shiru ban ce komai ba, be kuma be fasa kallona ba, can kuma ya karasa ya dauki wayarsa ya taba sannan ya kalleni. “Zaki iya zuwa office dinki” “Na gode” Na fada sannan na juya na fito daga office dinsa na nufi nawa office din, ko da na shiga matar bata nan, sai na suke jakata na zauna a kujerar ina ta tunanin mahaifina. Ban yi aikin kamar yadda na saba ba, domin rashin kowa a kusa da ni sai ya kara saka ni cikin damuwa da tunani kala kala ciki har da na rayuwata da kuma Kabir ko yana ina ma yanzu Allah masani. Misalin biyu da rabi Ahmad ya shigo office dina ganinsa yasa na tashi tsaye. “Wata takardar nake nema, ta green light company” A take na fara duba takardun da suke gaban teburin sai kuma nai arba da ita. “Takardun da kika san zan yi amfani da su ki rika kai min ko kuma ki bawa sakatarena” “Okay In-Sha-Allah zan kiyaye” Har na mika masa takardar ya juya nace. “Ranka ya dade ina son tambaya” Juyowa yai yana kallona. “Dan Allah Kabir nake tambaya, wani mahaukaci wanda ya makure ni ka” Murmushi yai. “Mutumen da kika ja min ya naushe ni ido kenan” Nima murmushin nai. “Kina son ganinsa ne?” “Eh tun ranar ban sake ganinsa ba” “Na saka a dauke ke shi ne akai shi gidan mahaukata” Na ji ba dadi har hakan ya kasa boyu a a fuskata, sai kallonsa nake na rasa abunda zan ce masa. Dawowa yai gaban teburin nawa ya tsaya yana kallona. “Karki damu, ina son ki samu natsuwa ne sai mu fara processing din nema masa lafiya, tun da naga ciwonsw ya dame ki” Da sauri na mike tsaye baki sake ina zaro ido. “Da gaske?” “Da karya” Ita ce amsar daya bani ya juya ya fice daga office din yana murmushi. __________________ Assalamu Alaikum. Ban yi niyar cewa komai akan littafin nan ba, duk kuwa da irin comments din da nake gani musamman whatsapp, wasu na complain abunda nake ma Halima yayi yawa so so this and that, akwai ma wacce tace min tana kwankwanton imani akan irin halin da nake saka Halima, na ji zafin maganar amman nai mata uzuri saboda ina daukar tana cikin irin mutanen da ke karatu basa daukar darasi burinsu kawai a samu nishadi. Ina son ku sani idan ma baku sanin ba, idan kuma kun manta na tuna muku tun farkon fara labarin nan sai da na fada cewar ban sani ba ko zai muku dadi ba labari ne na soyayya ba kamar yadda aka saba, labari ne na fadi tashin rayuwa, kalubalen rayuwar da na aure wanda zai tabo wani bangare na rayuwarmu ta yau da kullum. Duk yadda kike jin dadi Wallahi baki kamo wata ko a farce da jindadi ba, haka duk yadda kika a cikin tsanani baki kai kan akaifar wata shiga kunci rayuwa ba, labarin nan kirkiren labari ne amman ni nasan ba za a rasa wandanda suke rayuwa irin ta Halima ba, domin na ci karo da wasu a lokacin da nake rubutun nan, wani jarabarwarsa kadan ne wani da yawa, kuma kowa da inda Allah yake jarrabarsa. Idan baki cikin matsala wata na ciki, kuma ban cilastawa kowa karantawa ba sai wanda yaji yana ra'ayi, dan haka dan Allah kar wacce ta sake yi min wata magana marar dadi akan rayuwar Halimatu, duk wanda ya sake fada min rashin arziki goma billahil azeem zan fada masa ashiri, ba dole sai rai na so. And wandanda suka tuna mahaifansu jiya, wasu har da kuka, ina addu'ar Allah ya jikansu, mu kuma ya sa mu cika da imani. Ameen thumma Ameen. 7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣8️⃣ Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi marar misaltuwa,  na fito daga cikin gidan na nufo inda motar Ahmad take fake ya sauke gilashin motar yana kallona har na karaso, da kansa ya miko hannunsa ya bude min motar, na shiga ciki na zauna ina gyara jakata. Sai yai motar key muka hau titi sannan ya kalleni. “Happy?” Na gyada masa kai idanuwana suna kokarin cika da hawayen jindadi. “Yes” Sai yai kyakkyawan murmushin daya karawa fuskarsa kyau. “Thank You” “No thank you da kika amince, hop dai kin fada musu ke za ki yi ba ni ba” Na yi shiru ina kallon gorar ruwan daya dauka zai sha. “Sun jidadi sosai, kuma sun yi supporting” Murmushi kawai yai ya kalle ya karasa kurbe ragowar ruwan, ba mu yi wata tafiya mai nisa ba ya faka gefen titi yana kallona. “Bari na karbo ruwa shagon can, bana iya zama ba ruwa a mota” Bude motar yai ya fita, da wani irin kallo na bishi na jindadin daukar nauyin duba lafiyar Kabir da yai, haka Allah yake lamarinsa idan ya zo taimaka maka sai ya maka hanyar samun abun ko ta ta silar wani ne, and farincikin dana gani a fuskar yan'uwan Kabir a yau da naje musu da labarin ya kara faranta min rai fiye da kima. Wata farar mota ce ta faka gaban ta Ahmad sam ban kawo komai a raina ba, har sai da na hango Aminu ya fito daga cikin motar a fusace ya nufo inda nake, ganin hakan yasa na bude motar na fito na rufe tun kan ya karaso. “Halima me kike a cikin motar nan?” Haka ya aiko min da tambaya kamar wani ubana. “Ban gane mi nake a ciki ba?” “Abunda kike be dace ba, tun dazun na hango ki a cikin motar nan ina biye da ku har kika shiga wani gida kika fito, ya kamata ki san abunda kike fa wannan ba muharramin ki bane, kuma ki rika tunawa cewa kina da yara” “Wace irin magana kake yi haka Aminu?” “Kin san me nake nufi” Ya fada yana kara hade fuska, sai wani huci yake kamar ba shi ba. “Ya akai?” Ahmad ya tambaya yana kallona hannunsa rike da gorar ruwa biyu. “Ba komai” Na fada ina dauke idona daga barin kallon Aminu. “Oh ba komai za ki ce masa? Malam akwai komai wannan mata ta ce, miye hadin ka da ita?” “Who's this?” Ahmad ya tambaya yana kallona. Sai Aminun ya amsa masa da kansa cikin fusata. “Mijinta ne uban yayanta” Wani kallon uku saura kwata Ahmad yai masa. “Sannu Uban yaya, da alama dai kana shaye shaye, domin mai hankali ba zai yi abunda kake yi ba” “Ba shaye-shaye nake ba, ciye ciye nake, ka fita hanyar tun kamin dare yai ma, domin matata ce” “Babu wani abu a tsakanina da shi Aminu, boss dina ne a gurin aiki, kuma kai baka isa ka hanani magana da wani namijin ba, domin babu igiyar aurenka a kaina” “Amman akwai yaya a tsakaninmu ko?” Ya fada cikin daga murya mutane har sun fara mana taro, Ahmad ya bude min front seat. “Shiga ki zauna” Ina kokarin zaunawa Aminu ya fisgo Hijabina har sai da fuskata ta daki ganbun motar. A take Ahmad ya wulgar da gorar ruwan dake hannunsa ya zabgawa Aminu mari cikin zafin nama. “You're very very stupid” Aminu ya zaburo zai rama Ahmad ya rike masa hannu ya wulgar. “Ni ka mara? Ni ka mara? Na san ko ni wanene? Akan matata?” Shine abunda yake ta fada yana nufi gurin motarsa ya dauko wayarsa daga can gurin motar ya tsaya yana wayar, kamar yadda Ahmad din ma yake waya a kusa da ni. Faruk naji ya kira sunan mutumen sannan ya fada masa abunda yake bukata tare da bashi addireshin inda mike. Sannan ya juyo ya kalli gefen goshina dake zubar da jini. Zagayawa yai ya bude motar ya dauko tissue ya mika min. “Sannu” Ya fada cike da nuna danuwarsa. Sannan ya kalli Aminu dake kokarin shiga motarsa yace. “Indai ka cika kai dan iska ne ka tsaya nan” A take Aminu ya rufe motar ya sake nufo inda muke. “Me kake nufi? Tsoronka ake ji? Uban waye kai a cikin garin nan? I warning you Wallahi Wallahi idan na sake ganinka da matata sai na halaka ka, dan iska kawai marar mutunci mai neman matar mutane” Uffan Ahmad be sake ce masa ba, sai danna wayarsa yake. Aminu kam duk maganar daya yago sa ya yabawa Ahmad, ban tana ganin bacin ran Aminu irin na yau ba, tun da be tana fada a kaina ba, be tana nuna damuwarsa dan wani ya kula ni ba sai yanzu, jikinsa har wani rawa yake, kana kallonsa ka san kishi ne ke dawainiya da shi, kuma na banza domin a yanzu kam na masa nisa. “Ina kokarina ashe kai ke dauke mata hankali, wawa kawai” Ya karasa yana kai kafarsa ya shuri motar Ahmad, har lokacin Ahmad be kula shi ba, sai da motar soja ta iso, da hannu Ahmad ya nuna musu Aminu. “Ku masa shegen duka sai ya dawo hayyacinsa” Ba ni kadai ba duk wanda ke a titi kallon motar sojojin yake, a yadda naga yana wayar na dauka police zai dauko ashe uban police ne, kamar sun samu nama haka suka ka kama Aminu, suka ci kwalarsa amman be daina bala'in ba. “Ni zaka saka a ciwa mutunci? Sai na wulakanta ka wallahi, ka shirya haduwa da ni...” Ko da suka saka shi motar har sun fara dukanshi. Mutane sai bin motar sojojin da kallo suke kamin su juyo kan mu kallo ya dawo gurinmu. Ba mu bar gurin ba sai da Ahmad ya kira direbansa ya tafi motar Aminu sannan ya shiga tashi motar yai mata key.   “Kin yi kokari haka kika zauna da mahaukacin nan? Be cancanci mata irinki ba, tun farko ya kamata ayi bincike kamin a aura masa ke, how will you face the world ki ce wannan uban yayanki ne? Wani irin hauka yake haka?” Ni dai bance uffan ba bayan hawayen da nake. “Shiyasa yake cin zalinki, komai akai miki sai kuka da abun dariya dana bakinciki ko wane kuka dai i wonder how your next husband will handle you” Ya fada da kamar fada, sannan ya faka motarsa gefen titi ya fita, ya bar ni a cikin motar ni kadai. Tun ina hawayen da gaske har ya daina zuwa sai da ya leko ta gilashin motar ya kalleni sannan ya bude ya shigo muka cigaba da tafiya. Asibitin da aka taba kwantar da ni a lokacin da Baba ya rasu ya nufa da ni, sai da ya faka motar sannan ya zagayo side dina ya bude min motar ba tare da yace min komai ba, ni kuma na saka kafafuwana waje na fito sannan ya rufe motar yana gaba ina biye da shi har muka shiga cikin asibitin, har office din likitan muke da kansa yaja min kujera ya zauna sannan ya zauna a dayar kujerar ya risino yana kallona. “Bari likitan ya zo yanzu kin ji? Sannu” Ya kasa dauke idonsa a kaina ni kuma na gagara daga nawa idon na kalleshi. “Ji yadda ya gusar da farincikin da kika ji dazun, cikin kankanen lokaci, ina mamakin yadda akai kika auri mutunen nan tun farko....” Ya fada yana kallon likitan daya shigo office din, wacan likitan ne dai wanda ya duba ni a wacan karon. Sai ya daga fuskata ya duba goshin nawa sannan ya tambayi abunda ya faru. “Buguwa tai ta murfin mota” “Ayyah sannu” Ya fada sannan ya juya ya fita, ba dade ba ya dawo dauke da wani karamin akwaiti sai ya hanyo dayar kujerar ya zauna. “Cire Hijabinki” “Ba sai ta cire ba” Ahmad amsa masa tun kamin nai wani unkuri. “Indai gyaran kake so a mata dole sai hijabin ya matsa daga goshinta” Doc Nura ya fada yana kallonsa, sai ya taso ya karaso kusa da ni, ya daga fuskata sama ya saka hannunsa ya janyo hijabin nawa ya raba shi da fuskata kamar zai cire sai kuma naji ya yagashi, sannan ya maida min shi a jikina ya zamana kaina na iya wucewa hijabin ya sauko saman wuyana. Murmushi kawai likitan yai ya dauko safar hannu ya saka sannan ya soma gyara min goshin, idan naji zafi sai ya rumtse ido and Ahmad na kusa da ni yana min sannu. Bayan likitan ya gama ya saka min bandeji sannan ya rubuta mana magani. “Zaki iya jirana a mota” Ya fada yana mikomin key din motar, ba musu na karba na juya na fito daga office din, ina tafe ina tunanin haukar Aminu har na isa gurin motar, amaimakon na bude na shiga ciki na zauna sai kawai na zabi tsayawa har ya fito, ya dauki lokaci a ciki kamin ya fito ya nufo inda nake tsaye jikin motar, hannu ya miko min na bashi key din ya bude ya shiga sannan nima na shiga. “Kika yi ta tsayuwa waje? Ko baki iya budewa ba ne” “Na iya” Kallona yai kamar zai yi magana sai kuma ya dauke kai yai ma motar key muka kama hanya, ba kai ni gida ba sai da ya biya ta wani shopping yai min siyaya sannan ya shiga da ni cikin unguwarmu. “Ban san ko kina son na kai ki har kofar gida ba ko kuma na aje ki a nan” “Nan din ma yayi na gode sosai, dan Allah kai hakuri da abunda Aminu yai maka....” “No karki damu, ni be min komai ba” Ya mika hannunsa baya ya dauko ledodin ya miko min. “Ki rikawa yara wannan, and ina son na yi miki maganar karatunsu?” Na masa kallon rashin fahimta. “I mean idan kin amince i will take them back to Gwarzo International school” “A a suna makaranta a yanzu, da na yi deciding na canja musu sai kuma na yanke shawarar kara na bari har su kai Secondary school sai na nema musu private” “Baki son makarantarmu ne? Then i will pay su shiga wata private school din” “Ba haka ba ne...” “Ba haka bane minene?” A yadda na lura Ahmad yana daya daga cikin irin mazan nan masu saurin fushi, kuma abun kankane kan iya bata masa rai, domin tun kamin na karasa ya tari numfashina cikin muryar dake nuna fusatarsa a fili, jin na yi shiru ina kallonsa sai yai sauke ajiyar zuciya ya fara magana slowly. “Kin dai ga mahaifinki ba wani kula zai yi da su ba, ke kuma a yanzu kina neman mai taimaka kiki ne, to miye a ciki dan na dauki nauyin karatunsu? Uba kamar wannan? Zai tsaya ya damu da rayuwarsu ne ma balle karatu? Idan mutum ne mai hankali da natsuwa zai same mu a titi ne yana ihu and called you his wife? Imagine?,  i said idan makarantar ne baki gamsu da ita ba zan iya biya su yi wata makarantar, idan kuma taimako na ne bakya so then get out of my car” Ya karasa fuskarsa babu alamun wasa, ni kan kallonsa kawai nake mamaki cika ni, to ana taimako dole ne? Idan ya maida su a makarantar wani abu ya faru sai kuma a sake ciresu? Bana son yawo da karatunsu a yanzu domin shine rayuwarsu. Bude motar nai nai fita. “Okay fita kika yi? Fine...” Jin ya fadi hakan yasa na dawo cikin motar na zauna cikin damuwa. “Nace ki fitar min daga mota” Yawun bakina na hade na na kalleshi a natse nace. “Ba wai bana son karatun nasu ta dalilinka ba ne, bana abunda ya faru da su a baya ya sake faruwa yanzu, ko a da na dawo gida a lokacin da aurena ya mutu Abdallah ne yake kula da su ya saka su a makarantarku, daga baya kuma sai ya cire su wanda hakan be min dadi ba, a dole tasa na dawo da su makarantar gwannati” “Sai kuma aka fada miki kowa kamar Abdallah ne idan na saka sun cire su zan yi” “Shi ma ba da son ransa ya cire su ba, mahaifiyarsa ce ta cilasta shi saboda bata son alakar da ke tsakaninmu, bana son hakan ya sake faruwa” “Babu abunda zai sake faruwa, Hajiya bata da matsala da ke, kusan ita ta fara min magana tun kamin na yi tunanin yin haka, so if you want zan aiko direba gobe ya dauke su, idan kin yi shawara pls let me know” Ya karasa yana miko min katinsa. Na kalli kattin kamin na kalleshi na ce. “Na amince” Murmushin yai har lokacin be janye katin daga miko min da yake ba, wata kila son yake na kira so that ya samu Number na, domin tun da nake a rayuwata be tana kirana ba bamu tana waya ba. Ganin na ki karba yasa ya maida katin ya aje, ni kuma na rufe masa motarsa, na kama hanyar gidanmu na barshi a gurin tsaye ni dai har na shige gida ban ga motar ta bar gurin ba.   Ina shiga gida hankalin kowa ya tashi ganin goshina da bandeji. A falon Inna na zauna ina labarta musu a abunda ya faru. “Kai amman wannan mutunen ya burge ni, ai daman Aminu daidai ne ya samu mai cin ubansa....” Hafiza da fada cikin jindadi, kamar daga sama muka ji Namra dake sanye da uniform ta fashe da kuka. Husna ta nuna da hannu tana fadin. “Kin ga wacan kin ga wacan munafukace, ke yanzu duk abunda ubanki nai muku har son shi kike?” Mama ta tari numfashinta tana fadin. “Karki ga laifinta a duk yadda uba ya lalace ko uwa ta lalace ko da ya lalace akwai kauna a tsakani kuma baka son wani abu ya same shi, amman dai yakamata ki masa magana kar ya saka su masa mugun duka fa su ji masa ciwo ko su kashe shi ma” Sai a lokacin wannan tunanin ya zo min, kar su masa dukan mutuwa laifi ya dawo kaina, daman kuma ga halin da nake ciki, ko kuma shi Ahmad din na ja masa matsala. Haka na wuni da tunanin abun, sai a lokacin na ji haushin rashin karbar number sa da ban yi ba. Bayan an sallame sallah magariba Mama take min wata magana wacce ban taba kawo ma kaina ba. “Halimatu, ya kamata ki daina shiga motar maza haka nan, ba mutuncin ki ba ne, yanzu ne sai ki ji mutanen unguwa sun fara magana, ni kaina ba zan so ace yau kina cikin motar wannan gobe kina wannan ba inda ba ta kama dole ba” Gaskiya ta fada min wacce babu mai fada min ita sai mai kaunata, be kamata ina shiga ko wace irin mota ba, na sani yanxu ne sai a fara magana a unguwa ana cewa na lalace ko kuma ina jaye jayen maza barka, wasu ma kan iya dogara da cewar ganin mahaifina baya raye ne. “In-Sha-Allah zan kiyaye Mama, amman yana da wahala na shiga motar wani idan ba da wani dalilin ba, amman duk da haka zan kara kiyayewa” “Hakan yayi, Allah ya fito miki da mijinki na gari ki yi aure” “Amin” Na amsa tare da amsa sallamar yaron dake ta doko sallama tun daga kofar gida. “Wai ance ana sallama da Halima” “Je kace waye” Yaron ya fita be dade ba ya dawo yace. “Yace wai Abraham ne” “Je kace gani nan zuwa Bayan yaron ya wuce Mama ta kalleni tace. “Abraham kuma? Wane irin sunana ne wannan?” “Mama bari na dawo dai” Na tashi already ina sanye da Hijab dina na nufi kofar waje, a inda ya saba tsayuwa ya tsaya, ni kuma na karasa gurin ina tunanin da me kuma zo wannan karon. “Gani” Na fada ina kallonsa. Sai ya fito daga cikin motar da yake zaune ya kalleni. “Na taba fada miki ina son ki” “Ka sha fada min” Sai yai murmushi mai sauti. “Ina son ki Halima, ko da ba zaki so ni ba ni dai ina sonki, na kwanta da mata da yawa, ba su yi ciki ba sai ke da nai ma fyade, likito ma sun fada min ba zan iya haihuwa ba saboda kwayoyin halittata ba su da karfin da zasu ba mace ciki, na sha magani har na gaji, amman ji just one mistake kikai ciki, mi zai saka ba zan so ki ba? Na fada miki rayuwata tana cikin hadari zan iya mutuwa a ko yaushe, domin a duk lokacin da asirina ya tonu wow....” Sai yai shiru yana sotsa bakinsa. “Na kamu da mugun son ki, ba zan iya cutar da ke ba, idan ma tsoro kike ji ki daina, ki kwantar da hankalinki ki daina sakawa ana bincike akaina, domin idan asirina ya tonu bomb....” Ya fada yana cikawa bakinsa iska, ni kam mamaki ya gama cika ni, sakawa ana bincike akansa kuma? “Ni ban saka kowa yai bincike ka ba” “To wa ya saka? Mutumen nan ko? Why kika fada masa sirrina” “Ni ban fada masa ba” “Ya za'ayi ya sani idan ba ki fada masa ba” “A wasikar da na rubuta ranar children day ya ji” “Ko mutum yaji idan be san ki ba ba zai gane waye ba just tell me the truth” “Ban maka karya ba, labarin yarsa da kamfaninsa ya shigo ciki shiyasa ya gane cewar nice, a ranar da ya gan ni da kai kuma sai ya gane cewar kai ne mutumen da ke bibiyata” “Okay.....” Ya furta kamar mai nazari. “Saurayinki ne?” “Why” “Nothing” Ya amsa ni fuska ba yabo ba fallasa. “Miya ssmu goshinki?” “Na ji ciwo ne” “Garin ya?” Na yi shiru ban amsa shi ba, be sake ce min komai ba, ya bude motarsa ya shiga, ta gilashin motar ya miko min bandir din yan 1000. “Zaki iya yin wani abu” “Na gode” Na fada ba tare da na karbi kudin ba na juya. “Halima magana ta karshe ina rokonki dan Allah ki amince ki aure ni, i promise you zan kula da ke ba zan taba barin ki samu damuwa ba, ban ce ki so ni auren kawai nake bukata dan Allah” Juyowa nai na kalleshi hannayensa biyu a hade suke alamar rokona yake yi. “Dan alfarmar Annabinki, dan Alfarmar Addininki, dan darajar mahaifinki, i promise you zan kula da yayanki zan taimaki familynki zan saka ki cikin farinciki marar misaltuwa” Kasa ce masa komai nai jiki a sanyaye naa juya na dawo gida, zuciyata na kyautata zaton Ahmad ne ko Abdallah yake bincike akansa. AHMAD POV. Zaune yake a dakin Hajiya hannunsa rike da karamin plate wanda aka zubawa kwadon zogale da yaji kayan hadi ga tumatir da albasa a ciki.   “Kasan Khadija ai ta gama karantarta” “Wace Khadija?” “Khadija dai, yar Hajiya Hanne” “Okay na gane” “Shekarar nan zata fara service” “Okay congrats to her” “Shine shekaranjiya na ke yi ma mahaifiyarta maganarka nace me zai hana a hada ku?” “What?” Ya tsaya da cin zogalen da yake yana kallon Hajiya. “Ni. Did i say ina son ta?” “Tana da kyau ai” “Ban ce bata da kyau ba Hajiya, ni ma ai ina da kyau, ammn ban ce miki ina sonta ba Hajiya” “To ai naga ita din budurwa ce, kuma na san budurwa kake so shiyasa” Kasa cewa komai yai kuma ya kasa hade zogalen da ke bakinsa, ya san Khadija tana da tarbiya ga kyau ga ilmin ga wayeye kuma gata budurwa amman shi har ga Allah be ji ta kwanta masa a rai ba, and taya zai yi facing mahaifintar kanwar mahaifiyarsa yace mata be amince ba? Why Hajiya zata masa haka? Siyama ce ta shigo dakin rike da waya tana latsawa. “Yaya mutanen nan fa suna ta jiranka a falo” “Oh ni wallahi har na manta da su, wai me suke so ne” Hajiya ta fada tana kallon Ahmad, daker ya hade zogalen da ke bakinsa ya aje plate din yana kallon kanwarsa. “Je ki fada musu, ba ni za su bawa hakuri ba, su je su roki Halima idan ta yafe musu then their son will be free” Siyama ta yi wani fari da ido. “Wace Halima kuma?” “Just go and tell them” Ba musu ta juya ta fice daga dakin. “Wace Halima Gwarzo?” “Halima dai matar nan mahaifiyarsu Namra, ex-husband dinta ne ya fasa mata goshi da motata” “Garin ya” Mikewa yai tsaye yana fadin. “Ina zuwa” Ya fice daga dakin Hajiya na binsa da kallo. __________________ Halimatu & Aminu Halimatu & Ahmad Halimatu & Abdallah Halimatu & Abraham Bari muga Team da suka fi yawa. 7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 4️⃣9️⃣ A lokacin daya fito falon ya samu Mahaifiyar Aminu da wata yar'uwarta da dan'uwan mahaifinsa.   Ganin Ahmad yasa suka kara marairaice fuska, shi kuma ya mikawa namijin hannu suka gaisa. Sannan ya amsa gaisuwar da mahaifiyar Aminu ke musu. “Case din ba a hannuna yake ba, kuma ba ni aka jiwa ciwon ba, so if ita Halima tace ta yafe then ur son is free” “To yanzu ita zamu je mu roka kenan?” “Definitely” Hajiyar Aminu ta marairaice fuska. “Dan Allah dan Annabi ka taimaka mana, a saki Aminu hankalinmu duk a tashe yake” “Haba Hajiya me kike so nace miki dan Allah? Idan Halima ta hafe masa Wallahi ba ni da matsala ni” “Idan kai baka san ni ba ai ita Hajiya ta san ni, dan Allah kira min ita Yarinyar” Ta karasa tana kallon Siyama, ba musu Siyama ta tashi ta nufi sama, bata dade ba ta sauko tana latsar waya. “Gata nan zuwa” Ba a bata lokaci ba Hajiya ta sauko ta zauna saman kujera, tana yi ma Hajiyar Aminu kallon rashin fahimta. “Hajiya ina wuni?” “Lafiya kalau ya gida?” “Alhamdulillah Hajiya ba ki waye ni ba?” “Wallahi ban gane ba, kila an kwana biyu” “Be ke kika yi Shugabar lamurran mata ba, a lokacin Gwanna Garba Doru?” “Eh Haka ne” “Ni kuma ai na yi bawa matar Gwanna shawara a wacan lokacin” “Allah sarki kin san abun da yawa, ya kwana biyu” “Alhamdulillah, dan Allah Hajiya alfarma nake nema ki saka baki dan ki ya sako min da na Aminu, ance yana hannun sojoji dazun sun kira ta wayarshi suka sanar mana suka ce wai ya samu matsala da dan wajenki, shi kan shi Aminun na san be san Gwarzo ba da ba zai yi fada da shi ba Wallahi” Hajiya ta kalli Ahmad. “Wani abun ya hada ku ne?” “No ba komai, kawai dai ina tare da Halima ne dazun mun je yin wani abu, sai ya fito a titi yana mana ihu kamar mahaukaci, kamin nai wani abu ya buga ta da mota, that's why na kira Faruk yasa a aka dauke min shi” “Subhanallahi, to ita Halima ta san shi ne daman?” Hajiyar Aminu ce ta amsa mata. “Eh shine baban yayanta, tsohon mijinta ne da kaddara ta raba” “Allah sarki, Gwarzo ka kyale shi dan Allah” Ta karasa tana kallon Ahmad, shi ma kallonta yai. “Ba ni da matsala Hajiya, kawai taje ta bawa Halima hakuri ita akai wa laifi idan ta hakura, shikenan ai ba matsala ba ce” Hajiya ta sake kallonsu. “To kuje ku ji ta bakinta idan ta amince a sake shi, ba matsala ba ne, tunda ita a kaiwa laifin yana da kyau aji ta bakinta” “To Hajiya, bara muje indai Halima ce ai bata da matsala” Cikin rashin jindadi Hajiya ta tashi tare da yan'uwanta suka fice. Siyama kamar jiran take su fita sai ta kalli Ahmad da sauri. “Yaya ina kuka je hala?” Kallonta yai yasan ba komai ke cinta ba sai gulma, ashe duk abunda ake hankalinta na gurin amman ta fake da latsar waya. “Wani guri” “Wani guri ina? Ya ganku a inda be dace ba ne?” Tambayar da Hajiya tai masa tana kallonsa cike da son jin irin amsar da zai bata. Dan murmushi yai ya shafa kansa. “No akan wani marar lafiya ne da nace zan dauki nauyin maganinsa, kuma ita ta san mutunen shiyasa muka je tare tai ma familynsa magana shine kawai” Dariya Siyama tai. “Oh kishi yake dan ya ga kana sonta” “She's just my friend” Ya amsa ba tare da ya kalleta ba. “Yeah i mean friend, like friend....” Ta maimaita tana yi ma Hajiya kallon gulma. “Gwarzo ai baya son bazarawa, shiyasa na nema masa auren Khadija ai, budurwa ce kuma mai tarbiya” Kallon Hajiya kawao yai ya dauke kai be ce uffan ba. HALIMATU POV. Da tunanin Abraham na shiga gida, rokon da yai min ya karya min zuciya, indai har mutum zai hada ka da Annabi ya roki abunda kasan zaka iya masa anya ya dace na tsallake? Ko da musulunci da yace zai yi? Ko dan ya tuba da gaske? Sai dai me? Har gobe bana son jin wani kalami daga bakinsa bana kaunar ganinsa kuma bana tunanin zan koyi soyayyarsa balle har na iya kamar yadda yake tunani. To me zanyi? Na yafe masa be bar ni ba, na san idan ma na daina kulashi hakan ba zai wadatar domin kuwa ba kyaleni zai yi ba, to ko dai na kai kararsa a wani gurin ne na fallasa sirrinsa? A hankali na sauke ajiyar zuciya ina ta tunanin mafita, hakika ina neman abokin shawara wata zuciyar na nace min na fadawa Mama ta wani bangaren kuma ina jin tsoron yadda hankalinta zai tashi, gashi daman ba lafiya ta isheta ba ga kuma rashin mijinta ina ganin kamar idan na labarta mata hakan zai iya janyo mata matsala, amman ai bani da abokiyar shawara sai ita bana da wanda ya fita, ko ba komai na san dole zata tambayi waye Abraham kamar yadda ta bukata dazun. Har na unkura zan tashi da zimmar shiga har uwar daka na labarta mata komai sai muk ji sallamar mata biyu tun kan na ga mahaifiyar Aminu na gane cewar ita ce saboda yanayin maganarta.   Bayan Inna ta amsa musu suka nufo falon Mama suna ta doka sallama, ni da Mama dake can cikin daki muka hada baki gurin amsa musu, komawa nai na zauna Mama kuma ta fito daga dakin sanye da Hijabinta. Kallo daya zaka yi ma Hajiya ka fahimce cewar tana cikin tashin hankali, daman can haka take Allah ya zuba mata son yaya musammn Aminu bata kaunar abunda ya same shi, yana daya daga cikin dalilin daya saka ko fada mukai ko na kai kararsa sai ni ta ba ni laifi. Sama sama suka gaisa da Mama har take mata ya karin hakuri, amman idonta na kaina tana min wani kallo kamar na mamaki. “Halima gurinki muka zo” “To Hajiya Allah yasa ba laifi nai ba” Na fada ina kallonta sai ta dan tabe baki tana murmushin da ni kaina na san be kai zuci ba. “Akan maganar Aminu ne da kika sa aka kama, yanzu abunda kika yi kin yi daidai kenan? Ko ba komai ai uban yayanki ne komai Aminu ya lalace sai kin fi kowa jin ciwo, haka komai Aminu yai arziki sai kin fi kowa jindadi, saboda yayan da ke tsakani, yanzu daidai ne ki saka sojoji su kama shi bayan kin san ba za su masa da sauki ba?” Da fari murmushi nai kamin mamaki ya biyo baya ya na jin kalamanta na rainon waya da take akai. “Aminu ba ni yai fada ba, kuma ba ni na saka a kama shi ba” “To bakinku dai daya kenan? Shi yace ba da shi yai fada ba da ke yai, ke ma kin ce haka, yanzu ina gaskiyar magana a nan...” Mama ta tari numfashinta tana kallona. “Ba haka zaki ce ba Halimatu, ki fada gaskiyar abunda ya faru, kuna hanya ne na ganku ya fara fada yana kiranta matarsa yana masifa da shi wanda suke taren, sai kuma gashi ya buga kanta da murfi mota a kokarinsa na ya jnyota daga jikin motar mutumen sandiyar haka ya fasa mata goshi dai kina gani a goshinsa, shi kuma wanda suke tare yaji haushi ya saka soja suka kama shi” “Ah to ya isa ya raba tsakaninsu ne, tun da akwai yaya ai dole ne yai magana da ita, waya san gobe ban da Allah, aka san abunda gaba zata haifar? Ko aurenki yai ya isa ya yanke alakarku ne ai alaka Allah ya riga ya hada Wallahi” Ba mama kadai ba ni kaina kallonta nake da mamaki, sai masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba sai fada take da Ahmad din da baya nan a zatonta so na yake, a raina na ce idan kin isa ki je a gansa ki yi. Matar da suke tare wacce ita mahaifiya ce a gurin Aminu ta dakatar da ita. “Yanzu dai ba ta wannan muke ba Hajiya, shi bazarawarin naki yace sai kin amince sannan zai saki Aminu, dan haka yanzu ki tashi muje ki fada masa cewar kin yafe” Kallonta nai wani irin dadi ya lullube ni ko ba komai Ahmad ya mutuntani kuma ya nuna musu cewar ina da muhimmanci ba kamar yadda danta yake wulakanta ni ba. “Kuje ku fada masa na yafe” “A a tare zamu tafi ki fada masa, tunda idan munje zai iya cewa sai ya ji ta bakinki ko kuma ki kira wayarsa a yanzu nan ki masa magana” Hajiyar Aminu ta fada. Bana son na fada musu bana da number su kamar yadda bana son zuwa gidan domin kawai fada masa cewar na amince, ina kokarin yin magana Mama ta tari numfashina “Halima tashi kuje ki fada masa da bakinki kim yafe” “To Mama” Na tashi na shiga ciki, Hijabin dake jikin na canza daga fari zuwa brown dogo har kasa mai gyale sannan na bisu muka fita, ashe har da namiji suke ya tsaya a waje, wanda kanen mahaifin Aminu ne. A motarsa muka shiga ya dauki hanyar gidansu Ahmad, tun da muka shiga motar babu wanda yace uffan har muka isa.    Harabar gidan tana nan da kyauta kamar kullum, ga haske ta ko'ina gwanin sha'awa, musamman bangaren da aka zagaye da fulawoyi an saka wasu kananan gulub sun haska su gwanin sha'awa.   Fita mukai daga motar muka nufi kofar shiga falon Hajiya ta fara knocked, ganin an dade ba a bude kofar ba ta sake yi, nan ma shiru har muka soma gajiya da tsayuwa. Hakan yasa na nufi kofar da zimmar na kwankwasa da karfi ta yadda za su ji wata kila bugawan da Hajiya take basa ji ne, tun da gidan masu kudi komai na su dabam ne. Ina kai hannuna Ahmad ya bude kofar fuska a hade alamar ransa a bacen yake kenan, sai dai muna hada ido sai ya saka min murmushi ko da wasa ba kalli mutanen da muke tare ba sai yai kamar be gansu ba idonsa na kaina ya kara wangale kofar falon. “Shigo” Ni na fara shiga sannan suma suka biyo baya, da kansa ya nuna min wata one seater ya ce na zauna, ba musu na zauna ina kallon kanwarsa wacce ke kallona tana dan murmushi. “Sannunki” “Yauwa Sannu Halima ko?” Na gyada mata kai. “Ya goshin naki?” Ya tambaya yana kallona. “Alhamdulillah” “Siyama kawo mata lemu” “No ba sai an kawo ba, daman mun zo ne akan maganar Aminu, mahaifiyarsa tace ka ce sai na amince za a sake shi” “Yes sun miki cilas ne? ” Mahaifiyar Aminu ta saki baki. “Ikon Allah wane irin cilas kuma? Akwai fa yara a tsakaninsu yara hudu ai ko ba komai a hakura tun da ba a san abunda gaba zata haifar ba, yara hudu yau a ba wasa bane komai abu ya lalace dole akwai alaka akwai wannan son a tsakani, tun da idan babu shi ba zaki rike masa yaya a hannunki ba” A iya tunanina mahaifiyar Aminu tana fadar hakan ne saboda Ahmad ya ji cewar ina da yara hudu idan ma be sani ba ya sani, saboda ya fasa aurena ko so na kamar yadda take tunanin so na yake, ta yi hakan ne kawai dan ta muzanta ni idan ma baya son yara sai ya fasa aurena tun da ta san ba duk namiji ke son yaran da ba na shi ba. Kallon nai zan yi magana Ahmad ya girgiza kai alamar kar na ce komai. “Kin amince?” Sai naji kamar bace a a ko dan Hajiyar amman rahamar zuciyata ta hana ni. “Eh na yafe” Wayarsa ya dauka ya kira wnda nake kyautata zaton direbansa ne. “Ga iyayen mutumen nan zasu fito yanzu, kuje tare kamfani ka dauko motarsa then ku wuce AP barack ku karbo shi gurin Faruk” Yana sauke wayar ya kallesu yace. “Za ku iya fita direba na jiranku” A dolen dolen sukai masa godiya har da addu'ar Allah ya saka da alheri. Suna mikewa tsaye nima na mike sai yai alamar na zauna da hannu, haka kuwa akai sai na zauna din su kuma suka fita. “Siyama je ki kira Hajiya su gaisa” “Ow... Owk... Owk.... ” Ta tashi ta nufi upstairs tana wasa da wayar hannunta. “Na gode” Na fada ina kallonsa, sai ya juyo dubansa daga kallon Siyama izuwa gare ni. Kasa nai da kaina ina wasa da yan yatsun hannuna sosai nake son nai masa maganar Abraham domin ina kyautata zaton tsakanin shi da Abdallah ne suke bincike akansa, wanda nake ganin hakan kamar hatsari ne ga rayuwarsu. Ina zaune a gurin Siyama ta sauko tace wai na shigo dakin in ji Hajiya, kamar mai jira na tashi na nufi upstairs din Siyama na shiga dakin nima na shiga sai na zauna a saman kujerar dake gefen windows ina gaisawa da ita tana min sannu da ciwon da na ji, ta tambayi Mama sannan ta dora da ya karin hakuri.   Ban wani dade ba ganin dare na na yi mata sallama na taso na fito daga dakin, Ahmad na tsaye jikin stairs din yana kallon kafafuwana har na sauko. “Muje na sauke ki” “No zan hau Napep” Tabe baki yai. “Kin fi son Napap kenan da motata okay muje na taka miki” Tare muka jeru da shi muna kusan isa gate Siyama ta kwala min kira, a gurin muka tsaya har ta iso, ta miko min ledar hannunta. “Gashi in ji Hajiya” “Wannan ba tarbiya bace ya zaki kwala mata kira kamar wacce tai sata?” “To Yaya idan ban daga murya ba kuka fita ita Hajiya ai fada zata min tace ban ba wa Halima, yanzu kuma na bata ka fara min masifa wai ina murya da yawa” “To ai sai ki kira wayata ko nata ki ce mu jiraki” “Ina na ga Number ta?” “Bata number ki” Ya fada yana kallona sai ta miko min tsadaddiyar wayar. “Sa min number ki” Ba musu na karba na saka mata, sai da na mika mata wayar sannan ya ce. “And ta girme ki ko ba komai she deserve some respect” “Yeah Yeah Anty Halima....” “Lim's” Ya furta sannan ya juya muka cigaba da tafiya. Siyama har ta juya ta juyo tana kallonmu. “Wowwwwwwww” Juyowa nai na kalleta sai yace min. “Share ta kanwar nan tawa da kike gani bata da hankali” Murmushi kawai nai muka fice daga cikin gidan, mike titi mukai izuwa babban titi inda ababen hawa suka fi yawa. “Akwai maganar da kike son min ne?” Na kalleshi ban ce komai ba. “Na lura da yanayinki, kin san yanzu na karance ki ina iya gane yanayin damuwarki ko far'a ko makamancin haka just say it” Na yi murmushi ina saka duka hannayena na rike ledar da nake kyautata zaton turareka ne a ciki saboda irin kamshin da suke, sai na ji duk wata kimarsa da mutunsa sun kara karuwa a idona. “Akan maganar Abraham ne?” “Abraham dai? Why kike son magana akansa? Bakinsan bana son jin sunansa ba? Idan na tuna ya miki fyade sai na ji kamar na kashe shi na datsa namansa na soya shi sannan na watsa shi a cikin wuta ta kona shi” Tsayawa nai ina kallonsa hasken dake unguwar yana haska min fuskarsa. “It pain me” Ya maimaita yana yamutsa fuska. Kasa nai da kaina. “Saboda karka saka kanka a hatsari ne, and dazun ya zo min da wata magana ne wacce ta sanyaya min jiki, and ba zan jidadi ba idan wani abun ya same ka sanadina, yawancin mutanen da suka kusantata kaddarata ta kan shafe su” Ban boye komai daga abunda ya faru tsakanina da Abraham ba na fada masa, sai kawai na ga yana dariya yana kallona dariya sosai fa kamar yana kallon wata yar wasan Comedy. “Pls how old are you? Har yanzu akwai kurciya a tare da ke. And dan kawai an fada miki magana sai ki yarda? Kina saurin yarda gaskiya, and who told you idan Abraham ya aure ba ki haihu ba zai zauna da ke? How sure are you zai bayyana kansa ya daina duk abunda yake saboda ke?” “Ba wai ina nufin na aure shi ba...?” “Then me kike nufi? Pls karki sake min maganarsa ki bar masu bincike su bincika abunda suke so akansa, so that ki samu salama ni ma kuma hankalina na kwanta” Na gyada masa kai. Sannan muka cigaba da tafiyar ya zuba hannayensa aljihu, da kansa ya tara min napep na shiga ya fada masa inda zai kai ni, sannan ya ciro kudin da nake kyautata zaton sun kai 3k ya bawa mai napep din. “Na tabbatar ta shiga gida sannan ka dawo” “To ranka ya dade na gode sosai” Ya amsa cike da far'a sannan yaja Napep din muka nufo gida. AHMAD POV. tsaye yai a gurin har sai da ya daina hango napep dinsu sannan ya juyo ya dawo gida, duk abunda yai a gaban mahaifiyar Aminu yayi ne just to make her feel special, wani irin tausayi take ba shi ko kallonta yai sai yaji kamar zai zubar mata da hawaye.   Part dinsa ya nufa a ranar kwana yai da tunani kala kala, sai sake sake yake a ransa. Misalin tara da wani abu ya shiga part din mahaifiyarsa, sai ya same ta a kitchen kamar kullum mai aikinsu kuma na jera abinci a dinning. “Ina kwana Hajiya” “An tashi lafiya?” Ta amsa tana murmushi jinginawa yai jikin kofar kitchen din yana murmushi. “Al-hamdulillah, Hajiya ba zaki daina wahalar da kanki akan girkin nan ba” “Na san baka son abincin mai aiki shiyasa nake girka maka da kaina, amman idan kai aure zan huta” Murmushi yai ya kai hannunsa a kirjinsa yana shafa farar shaddar dake jikinsa. “Soon In-Sha-Allah” Da sauri Hajiya ta juyo ta kalleshi. “Da gaske?” Ya gyada mata kai. “Khadija dai?” Sai ya bar jikin kofar ya nufo inda take yana murmushi. “Wata ce dai wacce ta cancanci rayuwa mai kyau, wacce ta yanke kauna daga samun jindadi, wacce take bukatar tallafi ita da yayanta da yan'uwanta, wacce zuciyata ta cika da tausayinta” “Halima ce?” Hajiya ta tambaya tana murmushin jindadi. Sai ya rumgume ta ta baya ya dora kansa saman wuyanta. “Hakan nan kawai nake jin kamar idan ba ni na aureta ba, zata iya auren wani ya ci amanarta kuma ta sha wahala, and idan ta auri wani ba ni ba, zai so yayanta? Zai iya taimakonta? Zai jin tausayinta kamar ni? Kin san me take fada min jiya? Wai tana tsoron kar kaddararta ta shafe ni, tsoro rabar mutane take, ina son na cire mata wannan tsoron i want to make her feel special, and duk wani kalami da mahaifiyar mutumen tai jiya da ni take, a tunaninta ina son Halima ne, Idan har ta amince min na aureta, zan aureta ne kawai saboda in tausayinta amman ba dan ina sonta ba” Ya sake ta ya juyo gabanta ya tsaya. “And ina son mace mai hakuri kamar ta, the way she talk, yadda take gudanar da rayuwarta da yadda take taka tsantsan everything is perfect i like her, and her name, ke ma kuma naga kamar ta ku zata zo daya” “Duk macce da ta auri dana ta yi babban dace, and i believe matar na deserve a better life, ban kawo maka zancen ta bane saboda na san baka son bazawara, sai dai na lura jininku ya hadu hankalinku da tunaninku yana kokarin zama daya, zan fi kowa farinciki idan hakan ya tabbata saboda tana burgeni, daga ganinta kasan macece mai hakuri mai tarbiya mai hankali mai natsuwa da yadda da ko wace irin kaddara, irin matar nan duk namijin da ya aureta yayi sa'ar aure, abunda kake kudiri idan alheri a tsakaninku ina rokon Allah ya tabbatar” “Amin Hajiya” Ya amsa yana murmushi, har ga Allah shi dai kam ba son Halima yake ba, domin tuna tayi aure har biyu ga fyade yana bata masa rai, dukan wani abu da zai mata na tausayi ne kawai da kuma gudun halin da zata fada nan gaba, and the way ta Hajiya take son yai aure zai sake cika mata burinta na auren, sai dai yana jin inda har zai yi auren so Halima ce macen da tafi cancanta ya aura, ko ba komai ita kadai zata iya hakurin zaman da Hajiya, kuma a yadda ya lura da Hajiya tana son ta tan tausayinta ba zata cutar da ita kamar sauran matan ba. AMINU POV. Ko da suka isa har an fito da shi, sun zuba shi nan jikin wani siminti fuskarsa duk ta kumbura jikinsa ma kana gani kasan ya sha duka, da ido daya yake iya dagawa ya kalli mutane, jin muryar Hajiyarsa yasa shi jin sanyi, dacan kam ya dauka ko kashe shi za su yi. Hajiya da kuka da komai suka dauke shi suka saka shi a motarsa da direban Ahmad ya biyo su da ita, daga barak din suka wuce da shi asibiti, sai da suka kusa isa asibitin sannan Hajiya ta fara Allah ya isa dan can kan kasa daga ido tai ma ta kalli tarin sojijin, domin ba a bar su sun shiga ba sai da Direban ya kira Faruk din ya sanar masa sannan Faruk din ya bada umarnin a zo a tafi da da su ciki.   “Wannan ai zalunci ne, to shi Bazawarin nata soja ne daman” Kanen mahaifinsa wanda shima sai a yanzu ya samu baki ya fada, babu dai wanda ya amsa shi duk jimamin abun kawai suke. Bama kamar Hajiya da take jin kamar ita aka daka. “Wallahi duk inda zan shiga sai na shiga sai na ga inda za ayi auren nan, bakar azzalumar mata, da shegen bazawarin nata daman can ba son shi take da alheri ba, wannan bakin zalincin wallahi Allah ya saka muna” Riri Hajiya take kuka tana jin kamar ace sun fi Ahmad arziki da iko da sai ta saka an wulakanta shi fiye da yadda yai ma danta amman ba dama, tun da sun fisu arziki da komai ma ciki har da sanin darajar dan'adam. 7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣0️⃣ TWO MONTHS LATER..... Alhamdulillah Thumma Al-hamdulillah.   Godiya ce abunda ta cancanci fita daga bakina na yanzu, izuwa ga mahallincina ko da kuwa ina cikin tsananin rayuwa ballantana yanzu da rayuwar ta fara sauya min. Abubuwa da yawa da ban zata ba daga Ahmad suna ta samu na, ni da shi a yanzu kusan mun zama abokai, yana sake min sosai yana fada min abubuwan da za su kwantar min da hankali, yana dora ni a kowace hanya ta jagoranci. Ban tana sani haka yake da sakewa da son jama'a ba sai yanzu, a cikin abubuwan da yai minba kamar yadda ya dukufa a nemawa Kabir Lafiya, wanda farinciki ba ni kadai ya saka ba har da yan'uwansa domin na ga hakan a fuskarsu, asibiti aka maida shi suka masa duk wani gwaje gwaje daya kamata, sannan suka dora shi akan magani, duk wani abu da za a kashe masa ko aka kashe masa ta aljihun Ahmad yake fita.    da abun ya ki yi a nan ne suka tura asibitin sokoto wato uduth, tare da yan'uwansa biyu aka je, da kuma matarsa.   Bayan nemawa Kabir lafiya kuma yarana ya saka su a makarantarsa, school bus ke kaisu tana daukosu.   Wani lokacin ina da na kalleshi sai na ji kamar na bude masa zuciyata yaga irin farincikin daya saka ni, idan kuma na tuna abubuwan da suka faru tsakaninmu sai nai dariya, farkon haduwarmu da kuma abubuwan da yai min na cin fuska kamin yanzu, da kuma yadda muke a yanzu sai wani abun ya bani dariya wani kuma ya bani mamaki. Kamar ko yaushe yau ma na shirya shirin zuwa aikina, cikin bakar abaya kusan abaya tafi yawa a cikin tufafi domin ina jin sakewa sosai idan na saka ta gashi babu ruwanka da wani rike hijab ko gyara gyale.   Ban yi kwalliya ba, hoda ce kawai na shafa bayan mai sai dan turaren da na saka, sannan na shafa dan mai a bakina na dauki bakar jakata na rayata na nufi dakin Mama nai mata sallama, a tsakar gida na samu Inna ita mai mata sai na dawo na kama hanyar zuwa office din rai na fes.   Na samu napep daf da kofar gidanmu ya sauke wasu sai kawai na tsayar da shi na fada masa inda zai kai ni sannan na shiga.    Misalin tara da yan mintuna na isa office din, ko da na shiga na samu komai tsaf kamar kullum, wato masu gyara office din sun gyara shi sai kamshi yake. Jaka na aje a inda na saba ajewa na nufi window ya bude abun mamaki yau Ahmad ya shigo da wuri na hango shi jikin windows sa tsaye hannunsa daya rike da mug dayan kuma a aljihunsa har yana dago min mai kofin alamar gaisuwa. Ni kuma na daga masa hannu ina murmushi sannan na juyo na zauna a kujera na fara aikina. Knocked akai kamin na ce komai Yunus ya turo kofar office din ya shigo. “Good morning” “Morning how are you sir” “Fine, hope dai baki gaji da ni ba” Ya fada yana murmushi kamar yadda nima nake mayar masa da murmushin. “No haba dai Bismillah” Na fada ina nuna masa gurin da system din take. Yau kusan kwana biyu kenan a office dina yake aikinsa saboda system din da ke office dinsa ta samu matsala kamar yadda ya fada min.   “Yau ma dai kin yi kyau kamar jiya, wai kiye sirrin” Ya fada yana nufar gurin da System din take yana aje kayan dake hannunsa. Ni kuma sai nai dariya mai sauti. “Na gode, sirrin aikin kamfaninku ne ka san yana karawa ma'aikatanku kyau da natsuwa” He was laughing so hard kamar na fadi masa wani abun dariya sosai. “Oh wow okay zan fadawa mutanen kamfaninku haka kuwa, so that kowa ya rike aikinsa da kyau kar yai laifin da zai saka a koreshi” Nima dariyar nai. “Gaskiya ya kamata kam, ko ma an koresu ku makale kar su je” “Hahaha Haima kenan” Ya fada yana cigaba da dariyar, wani abu na ji marar dadi ya ratsa zuciyata sakamakon kirana da yai da sunan da Abdulhamid ke kirana da shi. ban sake cewa komai ba na cigaba da aikina, sai jin nai wayata ta yi kara alamar sako, a zato na mtn ne hakan yasa na share wayar ban duba. “I think this week zan je Abuja In-Sha-Allah” Na kalleshi. “Gurin me?” “Wani aiki ne, kin san can din ma muna da branch, so idan mai gida be je ba dole ni zan je” “Okay kace zaka leka garin manya kenan” Dariya yai. “Kin tana zuwa Abuja?” “No ni ai ban taba wuce Gusau ba” “Oh duk wayewar nan taki? Ya kamata ace kin zagaya manyan birane ai” “To ai ban san kowa ba, kaga ko ai ba zan tashi naje garin da ba dangi ba na zauna” “Ba dole sai kana da dangi zaka ziyarci gari ba, idan kina da friends ko ma a karan kanki zaki iya zuwa ki huta” “Hm da dai ace ni namiji ce zanje amman ina mace ai be kamata ba” “Believe me akwai matan da suke zuwa garin da ba su san kowa ba, wasu idan za su yi birthday haka ko suje bikin friends dinsu” “Tab ni kam ba zan iya ba, na je garin da ban san kowa ba? Amman masu zuwa birthday a wani garin basa celebration ko? Dan na san ba za su samu masu binsu ba” “Irin yaran manya haka, ko manyan mata wasu ma ba su tsayawa kansu ba, so suna zuwa da friends dinsu sai a hadu can ayi ta abubuwa wasu har kasar suke bari fa, kuma kin san ba kowa ke celebration din birthday ba, like me ni ma bana bikin birthday amman a ranar zan ci na sha na yi duk abunda na so” “Nima haka nake yi gaskiya, ban tana bikin birthday ba, ko cake ban tana ci a ranar birthday na ba sai dai na gode Allah nai saka a status shikenan” “Ni ina ciye ciye gaskiya, kuma zan iya ma mutane abu albarka birthday na, my is 22 December” “Mine is 4 October” Ya kalleni. “O really? That's mean gobe kike birthday kenan?” Na yi dariya ina gyada masa kai. “Wow ki ce ke princess ce kenan” Dariya na sake yi, a raina ina fadin princess sai kace wata yarinya. Wayata ce tai ringing sai da na dauke kaina daga computer sannan na kai hannuna na dauko wayar ganin bakuwar ce yasa ban damu na dauka ba sai kawai na aje wayar a saman tana ringing. “Ah gaskiya ya kamata ki yi mana celebration” “Haba wannan kuma ai sai yara” Na fada ina kallon number kiranta ya sake shigowa. Hannuna kai na dauka na danna picking nakara a kunne. “Hello Sallamu alaikum” “Zo office dina yanzu nan” Yana fadar hakan ya kashe wayar, ko ba a fada min ba na san mai murya, kuma na san duk a kamfanin nan shi kadai ne zai kira haka kai tsaye ya bani umarni, duk da be taba ba, be ma taba kiran wayata ba, and the way da yai maganar kamar yana cikin fushi. Hakan yasa na dan tsorata, a take na fara tunanin abunda nai wanda ba daidai tsakanin jiya zuwa yau, domin hausawa na cewa karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da kai, but if i can remember ai dazun da na shigo mun gaisa da shi idan fushi yake da ni ba zai daga min hannu ba, oh maybe wani abun nai ba daidai ba, a take na fara duba sakkwanin mail din wai ko akwai wanda ya kamata na aika masa kuma ban aika ba. “Ko a kamfanin nan ne ya kamata ki yi mana celebration” Yunus ya fada yana danna computer dake gabansa yana murmushi, nima murmushin nai na mike tsaye rike da wayata da sai a lokacin na ke ganin sakon da ya turo min. “Same ni office yanzu” Oh ashe ba mtn ba ne kenan dazun, na fada a raina sannan na nufi kofar fita ina fadin. “Ina zuwa Sir” “Okay” Ya amsa hankalinsa na gurin abunda yake, cikin faduwar gaba da fargaba na nufi office din kuwa da nasan ban yi wani abun ba, kuma a yadda nake da shi a yanzu bana tunanin akwai wata matsala a tsakaninku, sai muryarsa ta tabbatar min da ba lafiya ba.   Na tura office din na farko na shiga har na gaisa da mutumen dake ciki, haka a na biyu har na kai a nasa office din na tura na shiga bayan na yi knocked. Ina shiga ya watsa min wata uwar harara, har sai da gabana ya fadi. “Sai yanzu kika ga damar zuwa?” “Ban ga sakon ba ne sai yanzu, ina zaki gan shi hankalinki yana can wani guri, me Yunus yake yi a office dinki?” “Aiki” “Shi office dinsa kwantarsa ake a ciki?” “System dinsa ce ta lalace” “Kuma ba zai iya magana a gyara ba, sai dai ya zo office dinki ya zauna shi tsohon dan iska, ke kuma kin saki jiki sai dariya kike kin kebe da shi kamar wani muharraminki” The way da yai maganar sai naga kamar ba shi ba, to miye laifi dan Yunus ya zauna a a office dina? Naga dai idan wani abu zamu aikata ai ba za mu bar windows a bude ba, kuma yana maganar Yunus din ba muharramina ba ne shi din muharramina ne da na kebe da shi a nan? I was so so confused. “Zauna nan” Ya nuna min kujera, na yi zaton wani abun zan masa dan haka na nufi kujerar na zauna. “Look at you kuna da exchanging words, mi kuke cewa” Kallon mamaki nai masa. “Magana kawai muke” “Mi yace miki?” Na yi shiru ina ta tunanin ta inda zan fara, ni kam yaushe rabon da ayi min haka wai a tsareni ana son na fadi wani abu da na fada ko kuma wani ya fada min. “Maganar zuwa Abuja ne da yai min, sai maganar Birthday, sai.... At first dai cewa yai na yi kyau sai..... Maganganu dai haka... ” Sama sama na tsakuro abunda zan iya fada na fada masa, domin na lura ba da wasa yake tambaya ba. “Ji dan Allah kin saki baki kina ta magana da shi har da zancen zuwa Abuja, cewa yai ki bishi ku tafi?” Na zaro ido ina bude baki. “A a Wallahi ya za ayi yace haka? Na fada masa ban taba zuwa ba ne, shine muke zancen” Kamar hadin baki sai ga Yunus din yayi knocked. “Yes” Ahmad na bada umarni ya shigo rike da wasu files a hannu, kallo yai ya sakar min murmushi kamin ya karasa gurin Ahmad din yana fadin. “Tace gobe ne birthday ta shine nace ya kamata tai mana celebration, kuma tace bata taba zuwa Abuja ba, gaskiya ya kamata a turata ko ta hanyar aiki ne taje ta gano Abuja” It's normal for a friend like Yunus yai magana da friend dinsa like that kamar Ahmad, kuma ban ga wani illa a ciki ba, amman sai Ahmad yai masa banza ya karbi files din kawai ya aje. “Miya samu System dinka?” “Wallahi ta tsaya ne gaba daya, ban san abunda ya same ta” “Kuma ba kai magana ba” “No na yi magana da Tukur yace min baya gari shiyasa” “Kuma Tukur ne kawai yake mana gyara a kamfanin nan?” “No na dai fi yarda da aikinsa” “Ka dauko wata ka kai office dinka” “Okay” Ya amsa sannan ya juya ya fice, yadda Ahmad yake masa maganar kai ka rantse da Allah be san Yunus din ba aiki ne kawai ya hada su, domin yana masa magana ne ta sigar yaro da ubangidansa babu alamar murmushi ko wasa a duka Maganarsa, bayan kuma shi Yunus din ya fada min cewar Ahmad din childhood friend dinsa ne kuma kaf a kamfanin ba shi da aboki irinsa, saboda ya yarda da shi 100% Haka Ahmad ya zaunar da ni a office din for more than 3 hours, ba dan na masa aikin komai ba, after every 30 minutes sai yaje gurin windows dinsa ya leko sannan ya dawo ya zauna wata kila Yunus din yana can yana aikin ne tun da ya riga ya fara.   Ban san abunda ya zo masa a rai ba sai ganin nai yana kallona yana murmushi. “I know zaki ce ni din ai ba muharraminki ba ne ko? Yes amman ni ina da karfin jini the way da zan iya controlling kaina akan wasu maganganu ko aikata wani abun ba, ba kowa zai iya haka ba, and ita mace komai shekarunta komai girmanta sai ana controlling dinta saboda karamar kwakwalwa ne da su, more especially Lims” Ya fada still smile, ni dai ban da idon da na sakar masa babu abunda na ce, har na fara tunanin to ko dai Yunus din dan iska ne? “Dauko lemu ki sha” Ya fada yana dora duka kafafuwansa saman katon tebur din, tare da kai yatsansa jikin dogon hancinsa. “No Na gode” Sai ya dan tabe baki. “Kamar kin ji haushi ko? Ke ana tausayinki kin gagara ganewa, by the way likitocin da suke uduth sun bada shawarar a fitar da Kabir india saboda a can ne za a iya masa aiki mai kyau a kwashe jinin daya kwanta a cikin kwakwalwarsa, sun ce bashi magani zai dauki lokaci mai tsawo kamin ya samu lafiya kuma za a kashe kudi sosai, amman idan an masa aikin kuma aka yi a sa'a zai iya samun sauki cikin kankanen lokaci” “Ba za a iya yi masa a nan ba? Zuwa india ai za a kashe kudi da yawa” “To ke zaki kashe kudin ne? Ko kudin a aljihunki za su fito? Ko kuma kudin na ki ne? Are you the money or the money is yours? Ke kin fiye son shiga uku” Ya fada yana mikewa tsaye ya nufi fridge din ya bude ya dauko lemun ya nufo inda nake. “Already na fada musu su shirya komai daya kamata, kawai dai na fada miki ne just to let you know” Ya miko min lemun, karba nai da mamaki a fuskata haka yake wani lokacin, daga abun arziki ina tausayin kudin da zai kashe sai ya ce min wai ba ni ce kudin ba, and look at him now kamar ba shi ne ya gama hade fuska dazun ba, sometimes yana abu kamar wani mai aljanu. “Kamar mai aljannu ko?” Jin ya fadi haka yana murmushi yasa nai saurin mikewa tsaye ina girgiza kai, a zatona a fili nai maganar har ya ji. “No mai Al.... Jifai nake nufi....” Na fada da sauri sai yai dariyar da ta bayyana hakoransa. “Ashe na canka daidai yadda naga kin rike lemun daman na san gulma kike a zuciyarki ki ce wannan mutume kamar mai aljanu” Nima dariyar nai sosai har idona ya cika da kwala ashe ma ba a fili nai maganar ba, canka yai ni kuma garin kare kaina sai na fallasa kaina. Murmushi yake yana kallon yadda nake dariya kamar ba ni ba. “Cute you, dariya na miki kyau” Daidaita natsuwata nai, na koma na zauna na rike lemun. “Tashi muje mu ci abinci” “No ana kawo min abinci a office everyday” “Ba zaki koma office din nan ba sai gobe that's final” Hannunsa ya kai ya dauki keys din dake saman tebur din. “Amman handbag dina tana office din” Sai ya miko min keys din. “Je ki jirani a mota” Ba musu na karba keys din na juya na fice daga office din, na san inda yake aje motarsa dan haka na nufi gurin kai tsaye na tsaya a gurin ina jiransa, be jima ba ya fito tare da wata mata wacce rike da jakata ta kawo min jakar shi kuma ya karbi keys din ya bude motar ni ma na bude na shiga front seat. Tun da ya kama hanyar restaurant din be ce min uffan ba sai dai lokaci zuwa lokaci yana kallon inda nake, ni ma kuma ban ce masa komai ba, zuciyata nata raya min abubuwa da dama har muka isa gurin.   Motar na tsayawa na bude na fito shi ma ya fito yai gaba ina binsa a baya, restaurant din da Abdulhamid ya taba cewa na tsaya a ciki na jira shi ce, wacce na shiga ciki na zauna a kujerar da Ahmad din ya rufeni da masifa saboda na zaunarna kujerar da ban san ta wacece ba a gurinsa. A yau ciki muka shiga har vip din inda set din yake, da kansa yaja min kujerar, sai na kasa zama kuma na gagara cewa komai and na kasa dauke idona akansa, gabana sai bugawa yake da sauri kamar zai fito. “Zauna mana” Ya fada so calmly yana min wani irin kallo da na kasa natsuwa. Na zauna kamar yadda ya umarce ni amman kamar wata karago haka na zama, idan zan juya gaba daya zan juya idan zan juyo gaba daya zan juyo, kana kallo kasan bana cikin natsuwa ba kuma natsuwa irin ta wanda yake cikin tashin hankali ko zullumi ba ko fargaba ba, no natsuwa dai irin ta Wanda yake ganin wani abu kamar a mafarki. “Me za a kawo miki?” “Just water” Na fada ina kallon waiter din. “Kawo mana Jalof plate biyu da lemu” Ya fada masa sannan ya kalli. “Is hardly na ci abinci a public place like this, bana cin abinci a awaje yawanci Hajiya ta ke girka min, sai dai ina yawan zuwa gurin nan tare da mahaifiyar Baby lokacin da take raye just to make her happy, saboda ta saba zuwa gurin tun tana budurwa, a yau ma na san sai Hajiya tace min miyasa ban ci abinci a gida ba, kuma saboda ke ne, na zamu so nan ace me zaki ci ki ce ruwa ba, you must eat with me” Magana yake min a hankali kamar mai kokarin fahimtar da ni. Wani abu nake hangowa a idonsa wanda nake kokarin karyata kaina kansa. Ba shiri na mike tsaye ya dauki jakata na rataya. “I don't think i deserve this, ya kamata ka cigaba da mutunta kujerar matarka” Ina fadar hakan ban tsaya komai na na nufi hanyar sauka daga gurin har ina sauri kamar zan fadi. Ina fitowa gurin na tari napep na shiga, hawaye suka fara sauko min, tsoro nake ji kamar Ahmad ya bijiro min da abunda Aminu, Abdulhamid, Abdallah, Abraham suka bijiro min da shi, idan ya tambayi so a gurina na amsa masa da a a ban kyauta ba, sai dai ni ban shirya ba, na gaji da halin maza, ba zan sake aikata kurskuren auren mutunen da zan yi kuka a karkashin igiyar aurensa ba. Idan na tuna Aminu da Abdulhamid duk haka suka min kamin daga baya su saka ni dakin kuka su juya min baya, babu muhallin kowa a zuciyata a yanzu, idan har akwai wanda ya cancance ni a yanzu Abdallah ne, ba kowa ba, ba zan yarda Ahmad ya yaudare ni na fada soyayyarsa, a yanayin gidansu da irin girman da suke da shi, ba lallai ne idan ya aure ni ya ga kima ta ba, domin mu talakawa ne masu rufin asiri ba masu arziki ba, idan har mahaifiyar Aminu zata raina talaucin mu ya zama silar da ya saka ta kara wulakanta ni tana cewa ina kwashe arzikin danta ina kaiwa gidanmu ina ga mahaifiyar Ahmad? Secondly idan Abdulhamid be iya hakuri da ni ya zauna da ni a gidansa da aka min fyade ba taya wani zan ji labarina da rana tsaya kuma yace zai hadiye ƙashi ya zauna da ni babu kyama? Shin idan ma na yarda wata kadarar ta sake samun a gidansa zai iya zama da ni ko kuwa shi ma juya min baya zai yi? No I'm not just ready. Mai napep na isa kofar gidanmu sakon kar ta kwana na shigowa wayata daga number Ahmad. “Miyasa kika ce baki cancanci haka ba? Miyasa kika tafi kika barni? Why kike jin tsoro? Mi zuciyarki ta raya miki a kaina?” “Nothing, you're just my friend” Ita ce amsa da na bashi bayan na karanta sakon, sannan na share hawayena na fita daga napep din. “No I'm not just your friend” “I'm not” Ita ce amsar da ya maido min a take. Sai kawai na goge sakon, na sallame mai napep na shige gida, kallo daya Mama tai min ta fahimci damuwa, tai ta min tambayoyi a gurin aikinki ne ko a Abraham din ne domin na dade da labarta mata komai akansa, sai kawai na ce mata babu komai. Misalin tara da wani abu na dare, Aminu ya kira wayata, rabon da na ga kiransa a wayata har na manta, kusan tun da Ahmad ya saka aka mai masa duka be sake zuwa ba ko kirana ko da da sunan duba yaransa ne. Ba tare da tunanin komai ba na dauki kiran, sai ya sanar min yana kofar gida dan Allah na fito magana zai yi da ni. Tashi nai na jari hijabina na saka na fadawa Inna wacce nake zaune a dakinta sannan na fita wajen, kusa da kofar gida na same shi zaune a cikin motarsa da ke fake. Tsaye nai jikin motar na ce. “Gani” “Ki shigo ciki dan Allah” “Duk abunda zaka fada ka fada a nan” “Maganar da zan yi tana da muhimmanci dan Allah ki taimaka ki shigo” Jin haka yasa na bude motar na shiga, ina kallonsa sai na ga idonsa sun kumbura sun yi ja sosai alamar ya ci kuka ba kadan ba har ya sauya masa kala. Mun dauki lokaci mai tsawo zaune a cikin motar be ce min komai ba kuma ya kasa kallon inda nake, ni kuma mamaki ya cika ni ina tunani yau kuma da wacce ya zo. “Yau ce rana ta karshe Halima, da zan daina rokon ki dawo gareni, a yau kan na yarda na rasa ki har abada, a yau na yarda na yi kuskuren da ba zai taba gyaruwa ba, a yau ina rokon Allah ya baki miji na gari wanda zai taimaki rayuwarki, wanda zai baki soyayyar da kika rasa a gidana, wanda zai nuna miki kulawa, ya fifita ki ya tausaya miki, wanda ba zai wulakanta ki ba kamar yadda nai yi.....” Yai shiru sai kuma ya kai hannunsa ya kama hijabi ya jimkeshi sosai a hannunsa. “Wallahi ji nake kamar na bude bakina na dauke ki na saka a ciki na hadeye ki zauna a cikina har a bada amman babu wannan damar, na riga na rasa ki har abada, ina son ki Halima ina son ki san da wannan ko bana raye, duk abunda nake miki a baya ina yi ne kawai ba dan bana son ki ba, ina yi nw kawai saboda sharin zuciya da kuma ajizanci na dan'adam, dan Allah ki yafe min” Wasu irin hawaye yake yana kallona numfashi na fitar masa daker, a take jikina yai sanyi. “A lokacin da kike fada min illar abunda nake yi, da cutar dake na ke yi ban ga hakan ba sai yanzu da lokaci ya kure min, na tuba tuba na gaskiya, amman ba ni da tabbacin idan Allah zai yafe min abunda nai, kuma ina jin tsoron haduwa da shi, shin a yanzu idan nai jinya na mutu jinyar zata zama silar kankarewar zunubaina ko kari? Saboda ni na jawa kaina” “Ban gane wannan maganar ba...” Na fada muryata na rawa, dayan hannunsa ya kai ya dauko farar takardar ya miko min. “Ba kawarki kadai nai mu'alama da ita ba, amman ina da kyautata zaton ita ta laka min ciwon, domin na naji labarin kawarki Sa'adatu tana dauke da cutar bayan na tuba na daina mu'alama da ita, ban yi tunanin komai ba ban kawowa raina komai ba, har sai da wannan abun ya faru dukan da sojoji suka min da aka kai ni asibiti, sai suka min gwaje gwaje, a ciki na samu wannan, bayan na warke na koma gida na sake zuwa asibiti biyu ina samu result daya, and do you know what? Da aka saka Sadi yai gwajin sai aka samu shi ma yana dauke da ita, haka ma Murja kuma ina kyautata zaton dukansu ta dalilina suka samu..... ” Tuni hawayena ya jika takadar da ya kunna min wutar cikin motar ina karantawa. “Hiv Aminu?” Ya gyada min kai yana kara jinke hijabi hawaye ma sauko masa. Ban tana jin tausayin Aminu ba tun bayan rabuwar mu sai yau. “Zina ba tai ba Halima, bata haifar min da komai ba sai bakinciki da talauci, na yi wa yar wani an yi ma yata, na yi da matar wani kanena yayi da matata, yanzu kuma ta jefani a ramen da babu mai ceto ni, daga ni har Sadi har Hajiya ba mu da kwanciyar hankali da natsuwa tun daga lokacin da abun nan ya faru har yau ko abincin kirki Hajiya bata iya ci......” Ya karasa yana jingina kansa jikin sitiriyarin motar ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya. _______________________ Wayyo Aminu ya bani tausayi 😢😭 To ita kuma Halima me take nufi da Ahmad? 🤔 ko da yake tana da gaske ance duk hadarin daya baka kashi..... 🤥 Har Gobe ina Team Abdallah 😘😘😘 7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy Ina godiya sosai Maman Sayyed,  sakonki ya riske ni, Allah ya bar kauna kuma ya ba ni ikon yi kullum 🥰 Gaisuwa ga duk makarantan labarin Gobena, a duk inda suke Allah bar kauna 🥰🌸❤️ 5️⃣1️⃣ Wani lokacin Allah yana mana talala mu yi ta aikata zunubi har sai idan ya tashi kama mu sannan yai mana damkar da zata saka mana nadama da dana sani, a duniya kenan da Aminu ya fara haduwa da sakamakonsu, to ina kuma a lahira? Sai dai ina kyautata masa zato kasancewarsa musulmi kuma ya gane kuskurensa ya tuba, Allah yana son bayinsa masu tuba. Na shiga gida da tunanin Aminu a raina, ba ma ni ba a halin yanzu Aminu be isa ya tunkari wata mace yace yana sonta ba, sai idan mai dauke da irin lalurarsa ce ko kuma idan boyewa zai yi, wata kila ma yayan da yake aibantawa yana cewa na haifa masa yara da yawa zam tsofar da shi sune kadai yaran da Allah zai ba shi. A ranar na kudirta a raina cewar ba zan fada musu cewar mahaifinsu yana dauke da cuta ba, fada musu ba zai haifar musu da komai ba sai tashin hankali duk kuwa da kasancewar akwai kurciya a tare da su, ba lallai ne su fahimci komai ba.   Har ga Allah na jidadin da cutar ta kama Sadi da Sa'adatu ko ba komai dukansu sun ci amanar aure kuma sun ci amanata, Sa'adatu kawata ce ta zabi tai mu'amala da mijina bayan kuma ita ma din tana da aure da yara, sadi kuma ya ci amanar dan'uwansa yai ma yar dan'uwansa fyade, ko da yake har da sakacina a wasan lokaci na barinsu da nake suna kebewa a tare yawan shige masa da take ban taba hanawa ba, saboda ban kawowa zuciyata komai a kansa ba, ko da yana zina ban tana ayyanawa a raina cewar zai iya lalata yar dan'uwansa ba, ashe duniyar ta dade da canjawa daga sanin da nai mata, a yanzu babu yarda a tsakanin yaranka da kowa, domin bayan Namra na yi ta ganin labarai masu sosa zuciya wasu uncles dinsu zasu lalata su wasu kuma ubansu na ciki ko makota, kai har malaman makarantar boko da islamiya ba a bari ba, hakan yasa na kara saka ido akan duk wani motsi na yayana ba mata kadai ba har mazan domin suma ba a yanzu ana lalata su, mun kai wani zamani da babu aminci a zukatan mutane kowa kokarin cutar da kai yake. A washe garin ranar sai na tashi kamar wata marar lafiya, ba labarin Aminu kadai daya saka jikina sanyi ba har da tunanin Ahmad abunda ban tana ba, ko da dai rana ban tana kwantawa ko tashi da tunaninsa ba. Sai dai jiya na raba dare da tunanin abunda yai min da wasu alamomi da sai a yanzu nake fahimtar inda ya dosa. “Hello Lims fatar kin tashi lafiya Happy birthday” Shine farkon abunda ya fara shigo min a waya, kamin na bank dina su turo min. Ni kan har na manta da wani zancen birthday sai yanzu.   Aje wayar nai na fito tsakar gida na debi ruwa na shiga daki na juna a electric kettle, haka na bi yarana na zuba musu ruwa sukai wanka sannan suka karya suka saka uniform. Zuwa nai na gabansu na risina ina kallonsu wani irin farincikin marar misaltuwa ya lullube ni lallai yara rahama ne, no matter how suke rashin ji ko suke cutar da junansu. “Allah yai muku albarka ya shirya ku da duk yaran musulmi, ya tsare ku.” Duka suka amsa da amin, daya bayan daya na busu da addu'a ina dafa kansu ina karantawa har na gama sannan school bus dinsu ta iso, da gudu suka fita daga gidan kowa yana kokarin ya riga dan uwansa gwanin sha'awa. Da kallon kauna na bisu zuciyata cike da shauki ina murmushin jindadi da yi ma Allah hamdalla. Ina juyawa sai ga Namra ta dawo tare da Adnan suna rike da wani katon kwali wanda daker ma suke iya daukarsa, an nade kwalin da fata jar leda mai kyale. “Momy Momy gashi inji direban Bus yace wai a baki” Jin hakan yasa nai saurin tashi na karasa na karbi kwalin. “To Momy bude ki sam mana abunda ke ciki” Namra ta fada jikinta har rawa yake. “Kin san abunda ke ciki?” “No” “To kuje makaranta idan kun dawo zan ba ku nima ban san miye a ciki ba” “Momy to waya baki?” “Namra... Ba yanzu kika karbo sakon ba? Ni ina zan san wanda ya bani to?” “Momy ai shi mai bus din mu ba son ki yake ba ko?” Ta tambaya tana sako min ido, sai a lokacin na daka mata tsawa domin na fara gundira da tambayoyinta. “Ban sani ba, wuce kuje sarkin gulma” Dariya tai ta nufa kofar fita da gudu daman tuni mai bus din ya danna musu horn alamar yana jiransu. “Daddy na yace idan wani ya zo son ki na fada masa, kuma sai na fada masa wannan” Hafiza wacce ta nufo dakin da nake ta tari numfashinta. “Tsohuwar munafuka ki ce tace masa i love you” “Mama Hafiza i hate you” Ta karasa fada sannan ta fice daman shi Adnan tun da ya aje kwalin ya koma ita ce dai ta tsaya gulma. Aje kwalin nai a tsakiyar falon Mama na gagara budewa, ko ba a fada min ba na san Ahmad ne yai domin shi yasan yau nake birthday gashi kuma direban motar scul dinsu ce. Hafiza ce ta bude kwalin sauran yan'uwana duk suka zagaye kwalin kowa yana son ya ga abunda ke ciki, katuwar kwalbar strawberry guda biyu ta fara fitarwa sai cake dan madaidaici wanda aka rubutawa happy birthday, a kasan cake din wani madaidaicin kwali ne, da kanta ta bude kwalin sai ta ciro wata farar takardar sannan ta ciro turare man shafawa da wata sarka wacce nake kyautata zaton zinari ne. “Oh my god oh my god see love abeg duk Babban Baby Namra ne ya aiko ko?” Ta tambaya tana kallona, sai na rasa me zan ce mata idan nace a a na yi karya tun da fa gaskiyar a bayyane, ban gama tunanin irin amsar da zan bata ba na ji ta fara karantawa wasikar dake tare da kayan. “On your birthday, I want to remind you that you are special, not only to me but to all those who are privileged enough to know you for the amazing person you are. People like you are hard to come by, but getting to have a woman like you is indeed a gift, People tell me that the best years are still to come. I have to agree with that because my upcoming years will be spent with the world’s most amazing woman. Happy birthday to someone who improves every life she enters. You always know how to make an impact, but none so strong as the one you made on my heart. I will turn your black and white world into full-blown technicolor. Happy birthday to the leading actress of my life, If anyone is deserving of all the happiness in the world, it’s you, you are a wonderful mom, a loving woman, and a fantastic human being. Happy birthday Lims❤️” Kamar sautin waka haka nake jin ko wane kalami da Hafiza take karantawa a bayyane, wani irin shauki da jindadi naji ya kama ni, ba na kalaman da Ahmad yai min kadai ba har na kyautar da yai min a yau da kuma nuna min ranar haihuwata tana da muhimmanci abunda wani be tana min ba, jin ziciyata tana kokarin alakantuwa da wani abu yasa nai saurin kawarda abun a zuciyata, domin idan har na nace zan sake biyewa kalamai ko wasu abubuwan na koma dakin so to lallai ban dauki darasi akan abunda ya faru da ni ba, domin Aminu ma yana nuna son kamar ba gobe a lokacin da yake nemana, Abdulhamid ma mun yi soyayya da shi a boye kamin daga baya ya dawo min, kuma dukansu ban tsammaci haka daga garesu ba sai gashi sun juya min ba, miyasa shi ma Ahmad din ba zai juya min ba, shi ma ai namiji ne kamar su, ba a gane na gari a fuska ko a aiki har sai an zauna da mutum musamman maza. “Ke me kike tunani? Ni daman na san wannan rawar kafar da yake son ki yake, ya ga ruwan da ke masa wanka.... Oh wayyo ni inama ace Aminu zai ga wasikar nan yau” Dan murmushi nai. “A cikin wasikar kin ji yace yana so? ku rika fahimtar abu mana” “Ohhh se dis woman, sai ya fito ya furta miki ne? Ai su manyan mutane basa fada maka suna sonka, ke bari ma na fada miki ko zancen basa zuwa sai dai a kai musu mata, yanzu idan ya fara zance da ke sai dai ya aiko mata a dauke ki akai masa ke” “Oh really?” “Yes Lims” Sai duk suka kwashe da dariya, a gurin suka gutsitsira cake din aka cirewa su Namra na su na debi kadan na ci na sha lemun sannan na tashi na shirya na nufi gurin aikina.   As usual ina shiga na nufi office dina kai tsaye, ina shiga office din gabana yai mugun faduwa, zuciyata ta soma bugawa da karfi kamar zata fito sakamakon arba da nai da Ahmad tsaye jikin tebur dina yana sanye da farar shadda kansa da hula sai kamshin turare yake, rikewa nai na kasa sake daga ido na kalleshi kuma na kasa juya na fita daga office din kamar yadda na kasa karasa ciki. “Lims shigo mana” Kamar mai koyon tafiya haka na fara takawa na karasa cikin office din. Har na kai gurin kujerata na zauna ban iya daga ido na kalleshi ba. Wani dan karamin abu mai kamar akwati ya aje min yan zagaye shi da wani jan zare. “Happy birthday, kin san on my birthday kin bani kyautar agogon da me ma?” Ya tambaya yana yatsina fuska kamar da gaske ya manta. Muna hada ido sai ya kanne min ido daya ya sakar min kyakkyawan murmushi, sannan ya juya ya fice yana kokari saka hannayensa aljihu. Murmushi nai haka nan kawai sai na ji farinciki ya cika min zuciyata ya wanzarda nishadi da cikinta. Zaren na fara budewa sannan na bude box din mai kama da box din agogo, domin shi na fi kyautata zaton gani a ciki. To my surprise sai nai arba da chewing gum, irin wanda na bashi a ranar birthday sa, ban san lokacin da murmushinsa mai sauti ya subuce min ba. *** **** ***** Kana kallon fuskar Abdallah kasan yana cikin tashin hankali kamar yadda Hajiyarsa ma take ciki, kusan na nashi tashin hankalin ne ke saka shi a damuwa ba kamar na Hajiya wacce ta bi ta gigice saboda batan Abdulhamid, wanda yau kwana uku kenan ba san inda yake ba kuma ba a ji duriyarsa ba, idan kuma aka kira wayarsa bata shiga shi kuma be kira ba, yawancin mutane sun fi kyautata zaton an garkuwa ne suka dauke shi duba da halin da ake ciki a kasar. Hajiya kuma tana ganin kamar yan yankan kaine suka sace shi, domin idan yan garkuwa ne ba zai kwana har uku a gurinsuba, ba tare da sun kira waya sun fadi abunda suke bukata ba, yayinda dan'uwansa Abdallah kuma yake wani tunanin na dabam. “Ya dade a nan zaune, yana ta latsa waya can kuma sai ya kalleni yai shiru kamar mai tunani, ashe yana ji a jikinsa” Hajiya ta fada cikin kuka. “Yana zaune aka kira sallah isha'i, a gida yai ta be je massallaci ba, har na yi mamaki dan be saba sallah a gida ba ko ta asuba balle isha'i tun tashinsu shi da Husaini ba su saba sallah gida ba saboda Alhaji ya koya musu sallah masallaci, na ce masa ga abinci yace min a a ya koshi na bashi ruwa shayi ya sha, na sa Furera ta hada masa ruwan shayi ya sha, be bar gidan nan ba sai kusan 11pm sannan yai min sai da safe ya tafi, ita ake har yau be dawo ba, kuma ya saba zuwa da safe ya gaishe ni haka da dare kamin ya wuce gida kusan ma nan yake wuni saboda ba shi da mata a yanzu, kuma dan shirye shiryen bikin nan da ake kusan kullum yana nan da shi ake duk wasu shawarwari tun da lokaci ya kusa” “Allah dai ya bayyana shi a duk inda yake” Wata dattijiwa dake kusa da Hajiya ta fada fuskarta dauke da damuwa. “Amin” Abdallah ya amsa tare da sauran mutanen da suke falon, gaba daya idonsa da hankalinsa yana gurin Mahaifiyarsa. “An kai report gurin police amman har yanzu shiru” “Ai wannan abun bana police bane kawai, ya kamata a shiga malamai ayi sadaka Allah ya bayyana shi a duk inda yake, massada babu abunda basa yi gashi ana kusan biki saura wata daya ace babu ango ina lafiya?” “Amaryar ita ma ai tana can hankalinta tashe ance sai kuka take, ko abinci bata iya ci” Cewar Hajiya. Hajiya Rukaiya wacce kanwace ga Hajiya ta rausayar da kai cike da tausayawa. “Wayyo Allah, ai dole Allah dai ya bayyana shi” A nan ma Abdallah ya sake amsawa da Amin sannan ya mike tsaye. “Hajiya bari na leka office na dawo” “To Allah ya tsare ka kai ma” “Amin, In-Sha-Allahu za a ganshi ki kwatarda hankalinki dan Allah” Kai kawai ta gyada masa ta Lumshe idonta dake cike da damuwa. Shi kuma ya fice daga falon jiki ba kwari. __________ Ayi hakuri da wannan 🙏 7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣2️⃣ Garin daukar cingan din naji na taba wani abu mai kamar karfe, da na ciro cingan din na duba da kyau sai nai arba da makullin mota.   Ba shiri na mike tsaye ina dubawa duk da bani da motar ina kallon wannan makullin na san cewa na mota ne, wani irin faduwa gabana yai sai an rasa abunda zan yi kuma na kasa yarda cewar makulin motar ne, yana sane ya saka min shi ko? Ko dai ba da gangan yai ba. Maida makullin nai na dauki box din na nufi office dinsa.   Tsaye na tararda shi jikin fridge ya kafa gorar ruwa a bakinsa yana sha, ganina yasa ya sauke ruwan ya juyo yana kallona. “Ina....ina tunanin ka yi mantuwa a box din na ga wannan” Na fada ina budewa na dauko makullin na nuna masa. Sake cika bakinsa yai da ruwan sannan ya aje ruwan ya rufe fridge din. “No ina sane na saka, na yi ta tunanin abunda zan ba ki as birthday gift, sai na ga babu abunda ya dace a yanzu nai miki kyauta da shi kamar mota, saboda zuwa aikin da kike sai ki huta da hawan napep” “No i can't accept this” Na fada ina nufar teburinsa na aje makullin. “Lims why” “A'a Halima dan Allah, ranka ya dade kana min abunda ba a cikin dokikin kamfanin nan yake ba, ko da kana taimako ina tunanin kana taimako na ne saboda Allah, ba zan iya karba kyauta mai girma irin wannan ba, bana son alakar mu da wuce haka” “Why? Kina tsoron an sake shiga rayuwarki? Saboda Aminu ya cuce ki? Abdulhamid ya juya miki baya? Abraham ya yaga rigar mutuncinki? Dukansu maza ne ko ba haka ba? Kina tsoron ki sake komawa wani hali ko? Kina tsoron kar wani yace yana son ki wata rana ya juya miki ba right? Kina da gaskiya kuma kina da hujja kuma dole ayi miki uzuri....” Ya matsa kusa da ni sosai yana kallon cikin idona. “Duk abunda nake miki, ina yi ne saboda na ga na faranta miki rai, ba ke kadai kika cancanci farinciki ba, nima na cancanci farincikin, amman na danne nawa na manta da nawa, na danne duk wani bakin rai da damuwa da suke raina, saboda ke na sama miki farinciki, daga lokacin da samu labarinki sai nai kokarin mantawa danawa kin san saboda me? Saboda tausayinki ya cika min zuciya” Ya kara matsowa daf da ni. “Dukan abunda nake miki ina yi ne saboda zan iya kuma saboda na fi karfin abun, ba zan taba yi miki wani abu dan kawai ya tambayi so daga gareki ba, zuciyata bata taba raya min na siye soyayya kowa ba, balle kuma ke, ban taba jin cewar nai miki wata kyauta ko wani abun jidadi dan na tambayi soyayyarki da shi ba, Lims ina son shiga rayuwarki na taimake ki na taimaki yayanki da yan'uwanki” Na yi saurin kaucewa ina aje numfashi. “Ni ban shiryawa aure ko soyayya a yanzu ba, duka mazan nan da suka yaudare ni babu wanda be nuna min so na gaskiya ba, amman daga baya komai ya canja, kai mai gidanane be kamata alakar mu da wuce haka ba, indan har da gaske taimako na zaka yi to ka taimake ni saboda Allah kawai” Dayan hannunsa ya saka aljihu, ya juyo yana kallona. “Ni ma ba zan bari kiyi yanka akan danye ciwo ba, ai baki gama warkewa daga ciwon ba, ke kike kokarin saka kanki a so ba ni ba, na kai ki a restaurant din da nake cin abinci ne har na zaunar da ke a kujerar da kike zargin wani abu ne saboda na yarda da ke, na daukeki yar'uwa ne shiyasa na tura miki sakon cewa I'm not just your friend, na aika miki da sakon birthday ne a gidanku saboda kina daga cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata, dukan abunda nake miki saboda kawai ina tausayinki ne kuma ina son ki samu farinciki, idan zan siye soyayyarki ba ta wannan sigar zan biyo ba, shim fada min na taba furta cewar ina son ki? Ko na taba zuwa gidanku da sunan zance? Idan zan nemi aureki a gurin iyayenki zan tafi ba a gurinki ba, domin ni kallon budurwa nake miki yar 18, ba zan yi magana da ke ba har sai da izinin iyayenki, amman abubuwan nan da nake yasa kin fara tunanin son ki nake? Ashe son ki yana da arha da yawa” Na kasa cewa komai sai hawaye nake, wani irin abu na rashin jindadi da kunya ya baibaye ni, tabbas be furta yana so na ba, amman ya nuna yana kokarin boyewa a yanzu saboda yana ganin kamar ba zan ba shi hadin kai ba, wata kila kuma na yi kuskuren fahimta taya babban mutum mai rufin asiri kamar Ahmad zai ce yana so na? Taya mutumen da ya san wani ya min fyade zai yarda ya zauna da ni? Taya mutumen da samu komai na jindadin rayuwar duniya zai ce yana so na?       Matsowa ya sake yi kusa da ni ya mikomin tissue. “Share hawayenki, babu kalmar da na fada dan na bata miki rai, babu kalmar da na fada dan na muzanta ki, ba zan ga wanda zai fada miki wata magana marar dadi ba na saurara masa, ba zan cilasta karbar abunda ba ki da ra'ayi ba, lokaci yayi da ya kamata ace kin samu jindadi rayuwa kin daina kuka, ko akan yara ko akan komai ma, shi nake kokarin nuna miki, ki kwantar da hankalinki ki sake jikinki” Ya fada cike da nuna damuwar hawayen da nake zubarwa, da kansa ya janyo min kujera ya aje bayana. “Zauna” A take na zauna daman jikina ya dade da yin sanyi. Sai ya risina gabana yana kallon fuskata, fuskarsa na dauke da murmushi. “Fada min gaskiya ko dai ke kike so? Dan kin ga ni kyakkyawa ne?” Yanayin da kuma sigar da yai min maganar na san ya fada ne kawai dan ya saka ni murmushi, kuma na yi murmushi ina share hawayena. “A yafe min hawayen nan da na saka kika zubar, seriously bana son naga kina kuka, bana son na ganki cikin damuwa, idan har ba zan iya cireki a ciki ba to be kamata na saka ki a ciki ba” Ya karasa yana kama kunnesa kamar wani karamin yaro. Sannan ya mike tsaye ya nufi gurin kujerar. “Idan kina son motar zaki iya dauka, idan kuma ba kya ra'ayi” Na karasa yana daga kafadunsa alamar hakan be dame shi ba. “A a na gode” Na fada sannan na tashi na nufi office dina ina jin nauyi, zuciyata kuma babu dadi, kamar be dace nayi masa maganar ba, idan ma zan maida kyauta ba sai na nuna dan wani abu ya ba ni ba, sai a lokacin ne na ji wata kunyar ta kara baibaiyeni. Cikin rashin kuzari na zauna na fara aikina ina jin jikina sai a hankali, haka ma rai, juyawa nai na kalli windows dakina dake rufe sai na mike tsaye na karasa gurin ya bude windows din, hangoshi nai tsaye yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa, kamar kullum hannayensa na zube aljihu. Juyowa nai na dawo na zauna amman na kasa samun natsuwa lokaci zuwa lokaci sai na waiga na kalli windows a duk lokacin da zan kalli windows sai na ganshi tsaye yana kallona. Tashi nayi naje na rufe windows din sannan na samu natsuwa, bugun zuciyata ya daidaita har na samu damar fitar da numfashi a natse. Na cigaba da aikina amman sai na nemi natsuwata na rasa gaba daya na kasa tsayarda hankalina guri daya, kuma na rasa dalilin haka, after every two minutes sai na ji gabana ya fadi, ba faduwar gaba irin na tsoro ko fargabar faruwar wani abu ba, faduwar gaba ne irin wanda ban saba jin irinsa ba.   Misalin sha biyu saura wayata tai ringing, sai na saka hannu a jakata na dauko wayar. Abun mamaki yau Abdullah ne yake kirana, abun ka da mai nema jiki na rawa na dauka ina doka sallama kamar yana gabana, da fari na yi zaton ko zai min murnar birthday na ne tunda na dora a status kuma na san zai gani, amman bayan mun gaisa sai ya bijiro min da wani batun na dabam. “Abdulhamid ya bata yau kwana uku” Da mamaki na ce. “Abdulhamid ya bata kamar ya? Sai kace karamin yaro?” “Nima ban sani ba, an nemi an rasa wayarsa kuma bata shiga, so na fada miki ne saboda ki kula saboda ina tunanin batansa baya rasa nasaba da Abraham” “Abraham kuma?” “Eh Abokinsa ne, so be careful” Yana fadar hakan be tsaya komai ba ya kashe wayar, mamaki da al'ajab suka rufe ni, daman Abdulhamid yana da alaka da Abraham ne? Amman a cikin babu wanda ya taba nuna min cewar ya san wani, shi kansa Abdallah be tana nuna min haka ba duk kuwa da kasancewar na fada masa komai a game da Abraham din.   To idan ma Abraham ya saci Abdulhamid me zai masa? Me zai saka ya sace shi? Hakan na nufi Abraham yana da alaka da Abdulhamid kenan shiyasa yai min fyade ko kuma me? Ko kuma shi Abdulhamid din ya san Abraham din ya min fyade? Amman kuma Abraham din ai shi police ne, sai dai a sigar da suka shigo gidan zuwan farko da kuma na biyu duka ta sigar fashi suka shigo, a zuwansa na farko ma ya bukaci kudi kuma ya tambayi ina Abdulhamid yake, ba kowa na sani a abokaninsa ba, amman be taba min labarinsa ba, ko da yake Abdulhamid ba mutum ne mai yawan magana ba dan baya son hayaniya. Wani tunanin ne ya fado min a rai, ba ni ce kadai a cikin hadari ba har da Ahmad, domin kuwa Abraham yasan da cewar Ahmad ya san sirrinsa, idan har zai iya sace Abdulhamid to ba zai bar Ahmad ba, jiki na rawa na tashi da sauri na nufi office dinsa, domin gaba daya tsoro ya gama kamani, ko da na shiga na tarar yana waya, sai dai ganina yasa yayi saurin yanke wayar ya ta so ya nufo inda nake tsaye. “Lafiya ya naga hankalinki tashe?” “Yanzu Abdallah ya kira ni ya fada min wai Abdulhamid ya bata, kuma yana zargin da sa hannun Abraham” Kansa ya daga kasa ya lumshe ido ya busar da iskar bakinsa sannan ya bude ya kalleni. “Kin tada min hankali sosai na dauka wani abu ya same ki, to miye naki a batan Abdulhamid din ko Abraham” “Zai iya cutar da kai, tun da ya san kasan sirrinsa, ko da yana da sanda, a lokacin da suka shigo min ta siffar yan fashi suka shigo min, zai yi maka komai, zai iya kokarin cutar da kai, idan wani abu ya same ka ta dalilina, ba zan jidadi ba, ban san inda zan saka kaina ba, ban yafewa kaina ba” Na karasa cikin muryar kuka, kara matsowa yai kusa da ni ya kai hannunsa kamar zai taba ni sai kuma ya fasa ya juya bayansa, yana maida numfashi, can kuma ya juyo ya kalleni. “Za ki iya zuwa gurin motata ki jira ni?” Na gyada masa kai da sauri daman tuni hawaye sun wanke min fuska jikina rawa kawai yake kamar mazari. “Good girl je ki yanzu” Na juya ina share hawayen na fita na koma office dina na dauki jakata da wayata na nufi inda motarsa take. Kamin ya iso duk na matsu, sai dai na lura da mutane sun fara saka mana ido cikin har da blessed wacce idan ta gan ni na fito ba a lokacin tashi ba take ce min wai zan fita da oga ne ko? Tun kan ya karasa ya matsa remote din motar ta fita key ni kuma na bude na shiga na zauna, yana shigowa ya tashi motar muka bar kamfanin. Ganin muna ta tafiya ba tare da ya min magana ba yasa na ce. “Ba ka ce min komai ba” Kallon idona yai da ke cike da hawaye. “Lims sarkin kuka, ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ki” “Ba ni ba kai” “Ni kuma ke ce damuwata” “Haba ranka ya dade...” Ya katseni “Ahmad” “Ahmad....” Na maimaita cikin sautin kuka sannan na cigaba. “Wannan ba abun wasa ba ne, Wallahi zai iya cutar da kai, duk mutunen da zai iya keta haddin aure ya lalata rayuwar wata to zai iya komai, ban san adadin abunda ya aikata ba, ban san iya abunda yai ma wasu ba, wata kila ya tana kisa, ban sani ba, zai iya cutar da kai, kana tunanin idan wani abun ya same ka ni zan jidadi? Zan iya walwala?” “Duk wannan hawayen saboda ni? Mi kake nai?” Ya tambaya yana faka motarsa gefen titi. “Ka kwarara tsaro a gidan da kamfani, kuma ka fadawa police halin da kake ciki” “Police ba za su iya ba ni tsaro ba, kuma ki kwantar da hankalinki babu abunda zai same ni” Ya miko min ruwa. “How ta yaya zaka ce babu abunda zai same ka bayan Abdulhamid ya bata kuma....” “Abdulhamid yana hannun DSS” “What....?” Na masa wani irin kallo na mamaki. “Yes su suka kama shi yana Abuja” “Ho.. How.... Do you know kai kasa aka kama shi?” Na nuna shi da yatsana. “No bincike yasa aka kama shi, har Abraham din suna can tare” “Miya faru? Fada min?” “Nima ban sani ba” “Then taya ka san an kama su?” “Mataimakin DSS na jihar nan he's my friend, shi ya fada min” “Miyasa aka kama su? Kai ka saka aka kamasu?” “Saboda me? Idan ma zan saka a kama wani ai Abraham zan saka a kama ba Abdulhamid ba, na fada masa matsalar Abraham ne kawai ana cikin bibiyar sa ana bincike ta masa, sai ga wannan ya faru da Abdulhamid din, shi ya fadi Abraham aka kama su” “Amman miyasa aka kama su din?” “Kin san sana'ar da Abdulhamid din yake yi?” “Yana saida mota kuma yana aiki” “Ya taba baki labarin Abraham, ko kuma shi Abraham din ya taba baki labarin Abdulhamid” “A'a” “Shiyasana fada miki, Abraham din ba son gaskiya yake miki ba, ba zai bar abunda yake saboda ke ba, ba kuma zai fallasa miki sirrinsa ba, da dawo gareki ne kawai saboda yana son haihuwa, kamar yadda ya fada miki zai iya mutuwa a ko yaushe idan asirinsa ya tonu, ya taba fada miki cewar yana da mata?” Na girgiza kai da sauri. “A a” “To yana da mata tana can garinsu enugu, dukansu su biyu suna wani business, kuma babu mai sanin alakarsu sai su i think basa yawan ziyarta juna ne saboda gudun kar a zarge su” Bude motar nai na fita ina shakar iskar waje. Sai shi ma ya bude gefensa ya fito ya zagayo inda nake. “Hakan na nufi Abdulhamid ya san cewa shi yai min fyade kenan?” “Be zama lallai ya sani ba, domin ba kowa zai yarda abokinsa ya keta haddin matarsa ba, zai kuma iya yiyuwa ma shi ya saka shi, ko ma dai minene gaskiya zata bayyana” Dana lumshe idona sai hawaye suka sauko min. Ina jin lokacin da Ahmad yaja dogon numfashi ya sauke. “Sometimes, Allah yana jarrabar bawanaa ba dan baya son bawan ba, daga baya kuma sai ya kawo masa sauki, a yanzu ne zaki gane ba karamin taimakinki Allah yai ba da ya raba ki da Abdulhamid, shi kan shi uban yayanki da za ki bibiya tahirinsa wata kila za ki samu wani abun ya same shi, ko kuma zai same shi a gaba, shi kansa Abraham din da kin yi kuskuren aminta da shi kin aureshi da kin jefa kanki a cikin wata matsalar, trust me Allah yana son ki, and i think lokacin kukanki ya kare, wani jindadin nesa, wani za ki ga sai ya tsufa ta hanyar yaya zai samu, wani kuma sai ya sha wahala, wani kuma ya jidadin farko daga baya wahalar ta zo, ki gode Allah Allah ya kawo miki sauki tun a yanzu” Bude idona nai na kalleshi, sai na ji ya kara kwanta min a rai, yana da gaskiya wani jindadin nesa yake, wani kuma ba za a taba jindadin ba har abada. “Bana son ki saka kanki a damuwa, bana da tashin hankali a yanzu kamar damuwarki, Doc Nura ya fada min cewar idan zuciyarki ta sake bugawa zan a iya rasa ki, so bana tafar haka, kina bukatar ki rayu ko dan saboda yayanki da ni, ina ji a raina cewar ni kadai ne namijin da zan juya duniyarki ki jidadi, na baki abubuwan da kika rasa, na ranta ran mahaifiyarki da yan'uwanki, ba alfahari nake ba, ba kuma ina fada da wata manufa ba, dukan abunda zan yi a yanzu dan na saka ki cikin farinciki ne na mantar da ke damuwarki, a yanzu kam bana jin zan iya bari ko kuda ya cutar da ke lims, wahalarki ta yanke da izinin Allah” Ji nai kamar ya daure ni, indai jin kalamai ne na sha jinsu daga bakin maza, amman baka gane gaskiyar kowa sai ka zauna da shi, sai dai idan na kalli Ahmad sai na ga kamar be yi kama da mutanen da za su iya wannan ba. Sai dai idan har kalamansa suna nufin soyayya ko aure to ban shirya ba a yanzu, bana jin akwai namijin da ya cancance ni a yanzu sama da Abdallah. “Zamu iya komawa Gurin Aikin?” “No na fito da ke nan waje ne saboda ki samu natsuwa and fresh air, yanzu kuma ki zan kai ki gida ki huta just for today daman yau birthday ki ne you're princess” Na juya na shiga motar, shi ma ya zagaya ya shiga yai mata key. “Kamin na hadu da ke, idan na tuna babu matata babu Baby Namra babu Mahaifina sai na ji duniya ta ta koma upside down, ammn daga lokacin kaddarar rayuwarki ta same ni sai komai ya canja, na zama jarumi na ji cewar nima zan sake samun farinciki, a duk lokacin da na tuna da yata sai na tuna ki sai na ji bakincikin rashinta ya tafi” Kallonsa nai sai ya sakar min irin murmushin nan da ake cewa ya fi kuka ciwo. “Ya isa a nan zan sauka sai na hau napep” “Ba ki son a gan ki da ni ne ko? Fine” “No bana son ina shiga motar mutane ne, yanzu sai ka ji ana magana” “That's why na baki mota ai dan na dauke miki wahalar hawan napep, kuma tsakani da Allah ina jin bakincikin hawan Napep da kike saboda namiji ne zai tuka ki” “Idan ka bani motar ka bude hanyar da za su kara zargina, a fara magana akai” “To shikenan zan aje miki har lokacin da za ki bukata” Har na bude motar da zimmar fita sai kuma na kalleshi. “Baka fada min wani irin business suke ba?” “Nima ban sani ba, amman ko minane idan sun gama bincike ai kowa zai ji” Na fita daga motar sannan na rufe mishi motar sai ganin nai ya sauke gilashin motar. “Ki kula min da kanki” Ya fada sannan yai ma motar key ya hau titi, ba ni da abunda ya wuce na bi motarsa da kallo har sai da na daina hangota. 7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣3️⃣ ABDALLAH POV. Misalin tara da yan mintuna ya shigo gurin Hajiyarsa kana kallonsa kasan yana cikin damuwa. Yayyen Hajiya ya tarar a falon wato Hajiya Altine da Hajiya Rukaiya, sai da ya gaishe su sannan ya wuce dakin mahaifiyarsa, yadda ya same ta zaune saman carpet rike da carbe fuskarta da damuwa sai ya kara jefashi a cikin nasa damuwar. Kusa da ita ya zauna bakin gado yana kallonta da Fuskarsa da ke bayyana damuwarsa karara. “Hajiya barka da dare” Ta dago ta kalleshi kana ganin idonta ka san ta sha kuka. “Barka dai Husaini, ya aikin” “Alhamdulillah, Hajiya ki rage saka kanki a damuwa, In-Sha-Allah za a ga Abdulhamid” “To Allah yasa ni abun yanzu har tsoro yake ba ni, jikina yayi sanyi sosai, idan na duba sai na rasa abunda Abdulhamid zai yi wa wani da zai cutar da shi mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, Allah yasa ba yan fillar kai ya hadu da su ba, domin na san masu neman kudi fansa da su suka kama shi da yanzu sun kira sun fadi abunda suke bukata” Jimmmm Abdallah yai kamin ya kalleta a natse ya ce. “Hajiya zaki iya tuna lokacin da akai yi Halima fyade?” “Na sani” “Mutumen da yai mata fyade wani kirista ne, kuma abokin Abdulhamid ne, ban san miya kai shi gidan ba har yai ma Halima fyade, a yanzu kuma ina kyautata zaton kamar da sa hannunsa gurin dauke Abdulhamid” Cikin tashin hankali Hajiya ta kalleshi. “Kamar kai ya akai ka sani?” “Halima ta fada min mutumen ya dawo yana sonta, saboda cikin da tai shi kuma haihuwa yake nema, bata aminta da shi ba amman ya dage yana son ta aure shi, shiyasa na fada mata gaskiyar cewar shi yai mata fyade, sai dai ita bata san yana da alaka da Abdulhamid ba, ni kai dai na sani nima kuma saboda na taba ganinsu tare har hotuna sun yi tare, shi mutumen police” “To me zai saka ya dauke Hassan?” “Saboda ni na fadawa Abdulhamid gaskiyar daya kasa yarda da Halima a lokacin da abun ya same ta, ke da shi kuna ganin kamar ta aikata zina ne, yayi ta bakinciki yana fadar cewar shi Abraham zai ciwa amana, wata kila yai masa magana ko yai masa wata barazana shi kuma Abraham din ya dauke shi” “Amman miyasa baka fadi wannan ba? Sai yan sanda su bincike shi mutunen?” “Hajiya idan baka iya kama barawo ba, sai barawo ya kama ka, shi Abraham din police ne kuma da na bincika sai na samu labarin cewar baya cikin garin nan a office dinsa ma har an saka wani, amman mu saurara na kwana biyu tukuna tun da mun kai report din gurin Police kuma ana Addu'a, ko minene zai bayyana In-Sha-Allah” “Amman irin wannan ai kama shi za ayi a bincike shi ko kuma ita Halimar, waya sani ko ma ita ta saka shi ya sace shi saboda ta dauki fansa balle ta ji zai yi aure, kuma ta ga shi Abraham din yan sonta” “Haba Hajiya wane irin Halima kuma?” “Zata iya yin komai wannan yarinyar da kake gani, ni sam ban yarda da ita ba ma” “Babu hannunta a cikin nan, kuma na fada miki ki bari nan da kwana biyu idan ba mu ga wani abun ba, sai mu fada musu wanda muke zargi” “To ko ma dai minene Allah ya bayyana shi” “Amin” Yayi kusan awa daya a dakin sannan yai mata sallama ya fice. Aiko kamar fitarsa take jira ta fito falo ta labartawa yan'uwanta abunda ya faru dukansu sun cika da mamaki. “Wannan maganar ai ba abar a kyale ba ce” Cewar Hajiya Altine, sai Hajiya ta amsa ta tana ware hannu. “Ni ma shi na gani ban zafafa abun ba ne saboda a gabansa ne, na san zai iya shiga cikin lamarin tun da uwarsa ta shigo ciki, yadda kika san ta wanke gaba ta zuba masa ya shanye haka yake da ita, ko sunanta baya son a ambata a wani abu” Hajiya Rukaiyah ta dora da. “To waya sani, ko wani abun tai masa, amman duk yadda akai ta san inda Abdulhamid yake” “Nima shi nake tunani, saboda bakinciki zai yi aure gashi ita ba tai ba zai iya sawa tace shi mutunen ya sace shi, ko kashe shi ma zasu iya yi, ko kuma su masa wani illar, kuma Allah kadai yasan gaskiyar lamarin nan wata kila ma daman can ta san abokinsa nw ta aure shi dan su kashe shi su ci dukiya Allah ba basu sa'a ba, Allah ya gani ko da akai auren nan ba zan ce miki yaron nan yana son Halimatu ba, be taba nuna min ba, kuma a lokacin ma ta neman lafiyarsa yake amman sai ya zo min da maganar aure daga sama, ban san yadda akai ta janyo hankalinsa ba ma, kamar abun magani, cikin kankanen lokaci akai komai” “Kin san abunda za ayi? Ko yanzu ita ya kamata a kama, idan ta ji wuya dole ta fadi inda shi Abraham din yake da Abdulhamid din, wannan ai ba maganar bari ba ce” Cewar Hajiya Altine tana tabe baki alamun mamaki ya gama cikata. “To yanzu a kira Yusuf a fada masa, gobe tun da farar safiya a doka masu sammako a kamo yar iskar, yarinya ta same mana fitina a cikin dangi” Hajiya ta fada tana kara yamutsa fuska. Hajiya Altine ta ce. “Haka za ayi, daman Yusuf din ya fada min ai akwai inda suke saka mutum su saka masa wata hula duk iskancinsa sai ya fadi abunda yake gaskiya, bari na kira shi....” Ta karasa tana danna number dan nata rai a bace, Hajiya kuma ta zauna saman cushion tana ta rawa da kafa tana kara kashe ido, babu komai a zuciyarta sai tsanar Halimatu. HALIMATU POV. Na iso gida cikin wani yanayi da ban taba samu kaina ba, ni dai ba zan ce ina son Ahmad ba, haka kuma bana kin shi, sai dai a yau kalamansa sun kashe min jiki sosai. Mama ta yi mamakin ganin na dawo gida da wuri bayan a a lokacin na saba dawowa ba sai yamma, karya nai mata na ce mata yau babu aiki da yawa shiyasa aka tashemu. Har na yi kamar na labarta mata abunda ya faru da Abdulhamid sai kuma wata zuciyar ta hana ni, domin na san ita ma din zata zargi Ahmad da saka a ka masu kamar yadda nima zuciyata take zargi, kuma zata iya cewa zatai wa Hajiya jaje gudun kar ace bata ji ba idan taje kuma dole zata bada labarin abunda na fada mata ne, idan kuwa Hajiya ta ji haka zata zarge ni, so rufin asirina kawai nai shiru da bakina na bar abun a cikina, har sai ya bayyana. Babu irin tunanin da ban yi ba a ranar har cikin daya ina abu daya, dan son gano abunda Abdulhamid da Abraham suke aikata marar kyau, idan na saka wannan na kwance wacan na kulla wannan, sata yake? Tare da Abraham din suke fashi? Ko kuma wata sana'ar ce dabam? Duk wani mugun aiki da zan kwatanta Abdulhamid da shi sai na ga kamar ba zai iya aikatawa ba, wata kila ma dai Abraham din shari yai masa saboda kar ya cutu shi kadai, domin ko a lokacin da na ke aurensa ban ga wata alama da ta nuna rashin gaskiya a tare da shi ba, duk da yake baka iya gane gaskiyar mutum mai boyo, Abdulhamid kuma yana daga ciki irin mutanen nan da suke boye abu, soyayyar da muka da shi ma a lokacin da nake budurwa a boye muka yi saboda baya son kowa ya sani. Haka dai nai ta sakesake na har dare raba ban yi bachi ba, domin tun ina jin alamar bachi bachin a idona har ya fitar min gaba daya, tashi nai na fito bakin balcony na zauna ima ta kallon taurari kamar mai kidayarsu, babu komai a tare da ni sai tunani kala kala. Can ciki ciki na ji wayata dake kan drawer tana vibration alamar kira yana shigowa wayata. Sai na tashi na koma dakin, hannu na kai na cire carjin sannan na dauki wayar sai nai arba da number Ahmad, gabana ne ya fadi kamin mamaki ya rufe ni, miyasa ya kira ni yanzu? Abunda be tana ba, ko kirana a gida balle a wannan lokacin da agogon wayata ya nuna karfe biyu saura, to ko dai fada min zai yi an sako Abdulhamid? Ko kuma wani abun zai fada min dabam, kiran na daf da tsinkewa nai picking na kara a kunne sai dai ban yi magana ba sai da na fito balcony. Ina ta jiran yai magana be ce min komai ba, idan na duba wayar sai na ga kiran na tafiya har sai da na gaji da kaina na ce “Hello” “Lims, kema kin kasa bachi kamar ni kenan?” “Eh” “Kin san me? Dakina yai min ba dadi sai na fito na zauna harabar gida sai kidayar taurari nake, yanzu kuma haka nan kawai na ji ina bukatar jin muryarki, duk ban yi zaton za ki dauka ba” Ya fada da murmushin da zan iya jiyowa, kana jin muryarsa ka san ransa kal yake fa farinciki. Na yi shiru ban ce masa komai ba. “Fada min miya hanaki bachi?” “Ni ma ban sani ba, na samu kaina da kasa bachin ne” Murmushinsa mai sauti ne ya daki dodon kunnena. “To je ki kwanta, so that's ki tashi da wuri i need to see early in the morning” “Okay” “Sweet dreams Lims, ki rufe idonki ki tuna duk wani beautiful memories we share together za ki yi bachi, kuma ina rokon ki yi mafarkina take good care of yourself for me pls” Be jira abunda zan ce ba ya yanke wayar, for the first time na samu kaina da shiga calls list na kurawa number ido for no reason, before murmushi ya biyo fuskata, sai da na sake kallon taurarin sannan na tashi na koma daki na kwanta. Lumshe ido nai thinking all the good memories we share together kamar yadda ya fada, babu abunda na fi tunawa kamar tears din da muka share with one tissue, and location da yai maganar wai ko dai ina son sa ne? Samun kaina nai da murmushi, kamin wani lokacin bachi yai gaba da ni. Na farka raina Fresh har wani shauki nake ji, domin ina aiki ina yan wake wake na, ina cikin shiryarwa su Namra su tafi makaranta muka ji muryar wata mace wacce hausa bata isheta sosai ba. “Dan Allah wacece Halima” Zumut nai na fito ance son kira kamar bazarawa, na amsa da cewar ga ni ina kallon matan ashe ba daya bace sai dai dukansu su biyun suna sanye ne da uniform din yan sanda. Kamar jira suke na amsa suka nufo inda nake suna fadin. “Zamu je da ke office din mu ki amsa wasu tambayoyi” “Me nai?...” Ban gama rufe baki ba suka rika ni muka fara ja in ja da su, da gudu Hafiza ta zo ta buge hannu police din ta hau ta da masifa. “Mi tai muku? Haka kawai za ku shigo cikin gida mu kamata? Wace duka ta baku izinin shiga gidan mutane anyhow” Police din ta nuna ta a fusace. “Ke mahaukaci ki san abunda kike yi, karki ce zaki taba police zan ci mutuncinki, marar kunya kawai” “Yes louder pls mu nan gidan sai mu kashe mutum ba komai ba ne a gurin mu, dan haka mun fiki tantiranci” Cewar Hafiza tana zare mata ido kamar ba da police take fada ba. Sai da Mama ta daka mata tsawa sannan ta umarce da ta dauko min Hijabina. “Amman Mama...” Hafiza bata gama fadar abunda zata fada ba Mama ta tari numfashinta. “Dauko mata Hijabinta na ce, duk inda za a je indai tana da gaskiya gaskiyarta zai fito da ita, Allah yana tare da mai gaskiya” Ranta be so ba taje ta dauko min Hijabi na karba na saka, sai da muka fara tafiya sannan yarana suka fashe da kuka, ba ma kamar Amal wacce ta biyoni har kofar gida tana kiran sunana. “Momy.....” Ban san lokacin da hawaye ya wanke min fuska ba, ko ba komai sun tozarta ni, sun saka ni a motar police patrol, duk wanda zai gan ni a ciki dole na zargi wani laifin na aikata, duk kuwa da kasancewar ban san abunda nai ba, ga kuma mutane da suka tara mana a kofar gida, domin motar har da maza sai suka tsaya daga waje. Ina jin lokacin da Inna take tambayatar wane station ne za a kai ni sai mai tukin motar ya amsa mata da. “State CID” Har muka isa gurin ban daina tunanin abunda na aikata wanda zai saka ayi min wannan kamun ba ban san na yi fada da kowa ba, ban san na yi wa wani kazafi ko kage ba, ban san mi na tarewa wani ba. Abun da kamar wulakanci domin muna isa suka saka ni a cell suka rufe, ko minti biyar ban yafe ba ba na hango Inna tare da Aisha da Mama da, like ten minutes wani kanen mahaifin mu ya iso gurin tare da yayansa. Na yi minti talatin a ciki sannan aka fiddo ni aka nufi wani office da ni, ina shiga na samu Hajiya a zaune tare da yan'uwanta, kallo daya na yi mata na gane dalilin kamoni da akai. Mutumen da ke zaune a gabamu yana karanta min abunda ake zagina da shi dan Hajiya Altine wato yayar Hajiya, na san shi ya san ni amman a yau sai kamar be taba ganina ba. “Ni ban san inda Abdulhamid yake ba, kuma ban san inda Abraham yake ba, nan fa cid ce babba kuma kai police ne Yusuf kai baka sani ba ni ya za ayi na sani?” “Karki fada min maganar banza karki sake kiran sunana ki dauka ba ki taba ganina ba a rayuwarki” Shine abunda ya fada min a tsawace, sai na kalli Hajiya na ce. “Ba kiyayya ta shiga tsakanina da Abdulhamid ba, soyayyah ce kuma shi ya ji ba zai iya zama da ni ba ya rabu da ni, me zai saka ki yi min wannan zargin? Me nai miki Hajiya wannan maganar wace irin kiyayya ce?” “Au baki sani ba? Munafuka, ai auren da kika masa ba na Allah bane, kin janyo hankalinsa saboda ki ci dukiyarsa tun da kin ga shi yafi dan'uwansa kudi, to shi aiki yake yana sai da motoci, dan uwansa kuma likita ne kawai, ko cikin nan Allah kadai yasan gaskiyarsa kin dauka ba zai yarda ta magana tun da kin shanye shi kamar yadda kika yi ma Abdallah, duk yadda akai da hadin bakinki aka sace min d'a, tun da kin ga zai yi aure kin ji bakinciki, wai dan har baki da kunya kike soyayya da kanensa? Kin taba ganin inda aka auri yaya kuma yana da rai a auri kane? Wato gaki autar mata ko, ban cin kin raba kansu kuma ki shiga ki mulke mu son ranki ga bayi, kin ma ci uban rainin wayo Wallahi” Haka tai ta jera min bakaken maganganu sai abunda ta mance, jikinta har rawa yake kamar zata dake ni. Ban taba jin nadamar aikata wani abu ba kamar auren Abdulhamid a wannan lokacin, sai dai bawa be isa ya wuce kaddararsa ba. “Za ki fada mana da arziki ko kuma sai cilasta ki?” “Ban san komai a kai ba” Na fada ina hawaye, bana son fadar komai saboda kar na jefa Ahmad a matsala, kuma idan Hajiya ta san ta dalilina ne zata kara zargina ne. Haka aka raya aka kada aka juya aka na tsaya kai da fata ina fadar ni ban san komai akai ba. Daker aka bawa kanen mahaifina damar shigowa cikin office din wanda shi ma kanene ga mahaifinsu Abdallah, babu irin maganar da be yi da Hajiya ba amman ta ki saurarawa ita ala dole sai na fadi inda danta yake. “Hajiya zumunci kike kokarin lalatawa, abunda kike yi be kamata, da uban yarinyar da mijinki uwarsu daya ubansu daya, akan me za ki yi wannan abu? Idan Alhaji yana da rai ke kin isa ko hararar zuri'arsa ki yi? Wallahi na tabbatar da ace Alhaji yana da rai yau ba za ki kwana a gidansa ba” “To sai kaje ka taso da shi a yanzu ka saka ya sake ni, ni ba ku ga abunda tai min ba ta raba kan yayana, da gangan ta kulla soyayyah da Husaini yanzu kuma ta zo ta auri Hassan, yaro ya bata ga ayoyi tambaya akanta sai ku ce na kyaleta saboda ni ban san zafin haihuwa ba? Wallahi ko Alhaji ne a raye ba zai yarda a taba masa yayaba” Kamar wacce take fada a ciki unguwa haka ta rika daga muryarta tana fadi abunda ranta yake so, Baba Buhari sai yai shiru kawai yana mata kallon takaici. Muna office din har la'asar, ganin na ki amsa laifina na ki na fadi komai yasa Yusuf din yace a shiga da ni wani daki, sai ya hada ni da wasu mata police suka tafi da ni wani bangare na gurin, suka shiga da ni cikin wani daki mai hudu, a yadda na fahimta abun kamar hadin baki ko ma nace cuta ce zallarta domin a iya sanina ko maza sai idan an dokesu kuma an kwana biyu ba su fadi kowa ba sannan ake saka a gurin, amman ni kamar daman can suna jira na ne. A rayuwata ban taba ganin inda aure ya zama kiyayya ba kamar nawa da ya zame min haka da Hajiya. “Ba zaki fada ba?” Dayar ta fada min cikin tsawa. “Ni ban san komai ba” Na amsa ta har lokacin zuciyata bata ayyana min na fadi komai ba. Wata hula suka saka min a saman hijabin da ke kaina, sai kuma suka cire min Hijabi suka saka min hular, wani namiji dake gafena na ga ya kunna wani abu sannan na daki hular kan nawa, a maimakon na fara bayani kamar yadda aka ce min mutane suna yi sai na nemi hankalina na rasa. AHMAD POV. Murmushi yake yana kurba tea dake hannunsa, ya nade kafafauwansa yana zaune gaban Hajiya, ita ma murmushin take tana fadin. “Haka nake son mace tana da tsantsaye da rayuwa, kasan da wata ce kana bata motar nan zata hau murna ta karba jiki na rawa” “Sosai ma Hajiya, kuma Wallahi wannan abun ya kara min kirmarta sosai a idona, sai na ji ta kara shiga raina sosai Wallahi” “Amman ka mata magana kuwa?” “Har ynzu dai, ki taya ni da addu'a, tana da dan taurin kai dan kadan kuma tana da wuyar sha'ani shi ma kadan, saboda tana tsoron rayuwa” “Allah ya tabbatar da alheri yasa kuma ya karba maka” “Amin Hajiya Amin” Ya amsa cike da jindadi addu'ar mahaifiyarsa, sannan na aje mug din ya mike tsaye. “Bari naje office” “To Allah ya tsare, ka dai kusa zama babban mutum kamar da” Murmushi yai ya fice yan shafa kansa. Driving yake zuwa office cikin nishadi da annashuwa, haka nan kawai idan ya tuna yayi waya da Lims da daren nan sai yaji wani dadi ya lullubeshi. He arrived in time just to see her face yana son yadda yake tsawa jikin windows yana hangota musamman idan zata bude windows din office dinta. Haka yai ta tsaye a gurin tun yana duba agogon ya ga nine saura har ya koma ya zauna can kuma ya taso ya tsaya ya koma ya zauna har kusan 11am abunda bata taba ba, domin duk dadewarta bata wuce 9 ko 9:30. A take ya ji duk ya damu, wayarsa ya dauka ya kira wayarta sai ya jita kashe, a lokacin ne ya fara tunanin ko dan abunda ya faru jiya yasa yau ta ki zuwa aiki kuma ta kashe wayarta? Sai duk yaji ya shiga damuwa, har kusan 3pm ba wani labari, line ta ya sake gwadawa, sai yai sa'a wannan karon ya shiga, kamin a dauka duk ya matsu. “Hello Lims” “Ba Halima ba ce kanwarta ce Hafiza, Halima tana gurin yan sanda” “What? Miya faru?” “Dazun suka zo suka kamata da safe, ba irin wulakanci da ba su mana ba nan gurin wai suna zarginta da hannu a batan tsohon mijinta, tana can hannunsu sun kulleta” “What? Wane station din ne?” “State cid office” Kashe wayar yai ya mike tsaye cikin zafin rai da rashin natsuwa na kira lauyansa, sai da yai masa bayanin komai sannan ya fada masa cewar su hadu a can din. @360 na isa gurin, ko motarsa kadai ka kalla kasan babban mutum ma'ana mai ji da naira balle kuma shigarsa ta suit da yai, yana shiga cikin gurin lauyansa ya iso, duk wani shiga da fita da ake ciki lauyansa ne yake magana bashi ba, suna shiga office din aka kira Hajiya ta iso tare da Hajiya Rukaiya, ba su zauna ba Abdallah ya shigo office din shima. Ahmad na kallonsa ya watsa masa wani mugun kallo. “Kai kasa aka kamata kenan?” Abdallah yai kamar be ganshi ba ko inda yake zaune be kalla ba balle har ya amsa shi. Hajiya ta kalli Ahmad da kyau tace. “Waye kai? Ko kai ne Abraham din? Ni na saka aka kamata ba shi ba” “To kina nan zaune za a fito da ita, kuma idan akan Abdulhamid ne ni zaki saka a kama ba ita ba, nine silar kama shi da akai yi ba ita ba” “Kai Malam karka fada mana maganar banza, idan baka san darajar iyayenka ba ni san nawa, karka ce zaka yi ma mahaifiyara rashin kunya” Abdallah ya fada a fusace. Sai Ahmad ta tabe baki yana kallonsa. “Kasan darajarta ka bari ta ci mutuncin wacce bata da laifi?” “Hey my friend don't tell me rubbish” “An fada maka who are you?” “Ai kai za a tambaya, ka so nan kana wani nuna isa wa kake a gurin Halima? Wallahi idan na so ko kallonka Halima ba zata sake yi ba stupid human being” “Oh really? Ni ko zan nuna maka wani abu ne a gurinta, ka jira nan da one month sai na nuna maka waye ni a gurin Halima, sai ka gane darajata ta fi taka a gurinta” Yana fadar haka ya mike tsaye da zimmar zai fita sai ga lauyansa ya shigo yana fadin su tafi gata can an saka a mota. Ba shiri Hajiya ta mike tsaye. “Ina Yusuf din yake? Ya za a saki yarinya bata fadi komai ba? Ni ina dana yake” Juyowa Ahmad yai ya kalleta. “Dan ki yana Abuja hannun DSS kije ki yi fada da su idan kin isa, and idan wani abu ya samu Halima dukanku ba zan kyale ku ba har kai” Ya karasa yana nuna Abdallah. Abdallah ya masa wani mugun kallo. “Look at you fool sai na nuna maka baka isa da Halima ba trust me.... ” Ahmad be sake ce masa komai ba ya fice. Abdallah kuma ya hau rarrashin zuciyarsa domin ji yake kamar ya hau Ahmad da duka, Hajiya kan jikinta gaba daya ya gama sanyi jin Abdulhamid yana hannun DSS. _________________ Guess what will happen next. 7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣4️⃣ Yadda kafarsa take taka kasa da karfi ya isa ya isar maka da cewar ransa a mugun bace yake, balle kuma kai arba da kyakkyawar fuskar nan tasa wacce ta koma kamar bakin hadari idanuwansa gaba daya sun gama canja kala daga fari zuwa ja. Wani irin nishi yake irin wanda bacin rai ya dannewa numfashi, gumi kawai ke karyo masa daman can haka yake idan ransa ya bace sai gumi da dannewar numfashi. Tare da barrister suka isa gurin motar, sai ya kai hannunsa ya bude gidan baya inda aka saka Halima, hannunsa ya kai ya taba fuskarta zuwa hancinta dan tabbatarwa idan tana raye, tabbas yaji tana numfashi sai dai kana kallonta kasan bata cikin hayyacinta. “Wai hula suka saka mata” Barrister Nuhu ya fada yana tsaye bayan Ahmad, dagowa Ahmad yai ya kalleshi da wata irin murya marar dadi saurari yace. “Barrister ka shigar da karar matar nan da dan sandan da yai mata wannan abun, zan kaita asibiti yau yau nake son ka fara komai, ba zan iya yafewa ba, ba zan iya kyale wannan abun ba” Yana fadar hakan ya zagaya zai shiga motarsa sai ga Inna da Husna sun iso. “Mun gode Allah ya saka da alheri” Be iya amsa su ba sai kawai yace. “Asibiti zan kaita yanzu, asibitin Dr Nura za ku iya samun mu a can” Yana fadar hakan ya bude motar ya shiga, yai mata key, kamin ya isa asibitin ya sake kiran wayar Halima duk da yasan bata hannunta amman yana son magana da Hafiza ne, akai sa'a wayar na hannunta domin ringing daya ta dauka. “Hello, ke ce kanwar Lims ko?” “Eh” “A gabanki abun ya faru?” “Eh komai a gabana akai, Mama ta hanani binsu ne can station din, baka ga wulakancin da sukai mata ba har waje suka fita da ita ba Hijab sai da na bita na saka mata mutane sai kallonta suke kamar ta yi sata, tun cikin gida ma yar sandar guda ta fara marinta” Juyawa yai ya kalleshi Halima wacce idonta ke rufe sannan ya ce. “Zan tura miki number wani barrister amman ki kira shi da line ki ba line Lims ba ki fada masa duk abunda ya faru zai shigar da kara akan case din” “To ina ita Halima take?” “Gata nan zan kaita asibiti” Yana fadar hakan ya kashe wayar, ya sake waigawa ya kalli Halima, sai duk yaji tausayinta ya kara kamashi, da wani irin karfi ya daki sitiyarin motar, yana wani irin nishi kamar zai ciro zuciyarsa daga kirjinsa. Yana kunna kai cikin asibitin wayarsa tai ringing kamar jiran kiran yake yai picking da sauri. “Barrister” “Na'am Ranka yadade ina son na san cewar shin abunda ake zarginta da shi, bata aikata ba din gaske? Kuma bata da hannu a batan mutumen?” “Bata da alaka da shi mutumen yana hannun DSS, bata da hannu a batan sa ko wata mu'amala da shi” “To ya akalarka take da ita?” Juyawa yai ya kalli Halima sannan ya amsa ma Barrister. “Matata ce....!” “Za a shigar da karar a madadinta ne ita kanta ko kuma....!” Shiru yai for a moment, yasan dai kotu ba a mata wasa, kuma shi din be riga ya auri Halima ba, idan aka shigar da sunan shi din mijinta ne kotu ta gano babu auri a tsakaninsu zai iya kawo musu matsala, how he wish ace ya aureta, ya tabbatar da yau Hajiya ko Abdallah basu yarda ko yatsa sun daga sun nuna mata ba balle har su saka a kamata. “A madadinta zaka shigar, mutanen nan sun wulakanta ta Barrister i want them to regret, su nemi yafiyarta da kansu kuma kotu ta yanke musu hukunci so that's su san ita ma din mai matarba ce, har marinta sai da yar sandar tai kanwarta ta fada min komai, zan tura mata number ka zata kiraka ta maka bayanin komai, an ji hular da suka saka mata ko criminal sai wanda ya kai kololuwa ake yi ma haka, it's just like plan sun tsara kasheta ne kawai Allah be basu sa'a ba” “Karka damu za ayi duk abunda ya dace” Ya sauke wayar daga kunnensa daidai lokacin da ya isa harabar asibitin, sai da yai parking a emergency sannan ya fito yana kiran wayar Dr Nura, sai kuma yai rashin sa'a Dr baya cikin asibitin a lokacin sai dai ya saka ayi mata duk wani abu daya dace kamin ya iso. Gurin Ahmad ya samu ya zauna ya jimke hannunsa ya dora a saman bakinsa yana wani irin kashe ido zuciyarsa sai tafarfasa take. “Sokon banza wawa” Ya furta tunawa da kalaman Abdallah da yai. “Daga ganin matar nan yayanta duk ba na albarka ba ne” Ya mike tsaye yana jin wani irin tsanar Hajiya da Abdallah, daman can ya tsani Abdallah tun abunda ya faru a kamfaninsa wanda matar Abdallah tai yi ma Halima wulakanci. “Saboda suna ganin bata da gata kowa ya kwaso hararsa sai ya zuba akanta” Ya fada yana safa da marwa a gurin. Dr nura be dauki dogon lokaci ba ya iso gurin ya shiga bata taimako da kansa.   Inna na isowa Mama ma ta iso tare da kanen mahaifin Halima, kana ganin fuskarsu kasan hankalinsu a tashe yake. Dukan yadda Ahmad yajin zafin zuciya sai ya dannen shi yana kokarin kwantar musu da hankali. “Ku kwantar da hankalinku, zata samu sauki likita yana ciki yana dubata” Mama ta gyada kai hawaye na sauko mata. “Dukanta su kai?” Inna ta tambaya. “Ban sani ba tukuna sai likitoci sun gama bincike su” After like 40 minutes Dr Nura ya fito daga dakin ya nufo inda suke. Ahmad sai kallonsa yake ya kasa tambayar komai. “Ba wata matsala a yanzu nan da awa uku zata farka” A hankali Ahmad ya cikawa bakinsa iska ya busar, ya Lumshe ido ya bude sannan ya mike tsaye ya bi bayan Doc Nura. Mama da Inna da Husna kuma suka nufi dakin da aka wuce da Halima. “Ka tabbatar babu wata matsala Doc” Bayan sun shiga office din Ahmad yake tambayarsa domin gani yake kamar ya boye ne ganin iyayenta. Sai da Doc Nura ya zauna sannan ya amsa masa. “Babu wata matsala, abunda aka buga mata akan ne ya mata nauyi shiyasa hankalinta gushewa, amman babu wani matsala” Ba zai iya zuwa dakin ya zauna ba bayan Mama da Inna ya san suna ciki kuma zuciyarsa ta ki aminta ya tafi ya barta cikin asibitin sai kace bata da kowa ko kuma bata san kowa ba, so he decided ya zauna a office din Doc Nura yai jiran awanin da Doc yace zata farka, da kansa ya kira Hajiya sanin cewar zata kirashi idan an yi magariba be dawo gida ba. “Hajiya yau ba zan dawo gida da wuri ba” “Why?” “Lims ta samu matsala ne” “Wacece lims?” Runtse ido yai ya bude sai a lokacin ya tuna da Hajiya fa yake waya, duk da ba kunyarta yake ba domin ta zama kamar friend dinsa amman duk haka ita bata san yana kiran Halima da Lims ba duk kuwa da irin yadda sunan da yai mata ya bi bakinsa, duk da haka be kamata ya fadi haka a gaban Hajiya ba. “Halima i mean” “Subhanallahi matsalar me ta samu?” “Kanta ya bugu da wani karfe muna asibiti yanzu haka, so ba zan bar asibitin ba sai ta farka” “Allah sarki, babu matsala Allah ya bata lafiya” “Amin thank You Mom” “Se ka dawo” Ya sauke wayar yana murmushin jindadim yadda Hajiyarsa ta amince a take ba kamar yadda take masa ba a da, ko kuma dai dan yana Halima ne oho. HALIMATU POV. Ba zan iya kiran bachin da nai da suma ba, ba kuma zan iya cewa ban suma ba, sai dai abunda na sani hankalina ya bace na dan lokaci a lokacin da aka saka min abun da, sai dai ina jin hayaniyar da suke kamar cikin mafarki kuma kamar a wata duniyar, har dauko ni da akai aka saka ni a mota zuwa asibiti har shigowa asibiti duk ina ji sai dai ba ji irin na mai rai ba kuma bana iya bude idona balle nai motsi, hakan ne ya tabbatar min da ba suma nai ba domin wanda ya suma baya sanin abunda ke kansa, sai dai daga lokacin aka suka min allura sai hankalin nawa ya tafi ban farka ba sai da aka sauko daga sallah magariba. Na farka cikin rashin kuzari yawun bakina ma ba dadi kamar wata mai ciki, ba na wahala ne kawai ba wata kila har da yunwa domin ko karin safe ban yi ba. “Sannu Halimatu” A hankali na daga kai na kalleta wacce ita kadai ce a dakin, sai ya gyada mata kai alamar gamsuwa, sannan na maida idona gurin kofar da aka turo. Ahmad ne ya shigo hannunsa rike da ledodi tun da muka hada ido yake sakar min murmushi har ya aje ledar yana fadin. “Ga kayan marmari na gani a gate na riko muku” “Allah ya saka maka da alheri” “Amin, ya jikin nata?” “Al-hamdulillah yanzu ta bude ido” “Okay, Baba babu ruwan shayi ko?” “A a babu su yanzu kam, ga dai tuwo nan da aka kawo” “Shayin dai zai fi, ko zaki kira gida ki ce a kawo mana ruwan zafin in yaso sai na karbo kayan tea nan waje, Doc yace idan ta farka a bata tea” Da to Inna ta amsa sannan ta tashi ta fita daga dakin, kamar jira yake ta fice sai ya nufo gadon da nake kwance ya kwanto da fuskarsa daf da tawa. “Na ji tsoron sosai da na ganki a galabaice dazun, na dauka ba za ki yi saurin farkawa haka ba, ya jikin naki” Kamar mai rada yake min magana sai kallon cikin idona yake kamar zai cinye ni, kai na gyada masa alamar na ji sauki. “Wani gurin na miki ciwo?” Na girgiza kai. “Can you talk?” Nan ma dai kan na gyada. “Then say my name” “Ahmad... ” Na fada cike da nauyin baki, murmushi ya sakar min. “That's my girl” Ya fada yana kara kashe murya sannan ya mike tsaye ya nufi inda nake zaton bandaki ne ya bude ya shiga sai gashi ya fito rike da karamin bokoti ya nufo inda nake, sannan ya dauko daya daga cikin ruwan gorar da suke saman drawer wadanda nake kyautata zaton shi ya siyo su ya bude daya. “Za ki iya tashi ki wanke bakinki?” Haka nan na unkura ba dan ina jin karfi ba na tashi na zaune na tara hannuna yana zuba min ruwa ina kaiwa a baki n kuskure na zubar, sannan na soma wanke fuskata. “Ji yadda suka saka pretty face din nan na ki ya rame” Ni dai ban ce komai ba, ko ban duba madubi na san na rame domin na ji fuskar tawa ta zurma. Yana aje ruwan ya dauki bokitin ya maida sannan ya nufi kofar fita yana. “Bari na fara yin magana da Doc kar na baki wani abun ya saba doka” Da kallo na bishi har ya fice kofar bata rufe ba aka sake turo ta Mama ta shigo tare da Mama Ramatu. “Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode maka” Shine abunda take fada har ta iso inda nake ta zauna bakin gadon tana kallona fuskarta da murmushi. “Ya karfin jikin Halimatu?” Cewar Mama Rahamatu sai na amsa mata da Al-hamdulillah. “Kina jin wani ciwon a yanzu?” “A a” Na fada ina kallonta babu komai a cikin idanuwa sai son mahaifiyata da kaunarta. Likitan nan ne ya shigo tare da Ahmad ya tambaye ni jiki na fada masa bana jin komai sannan yace a bani abinci na ci sannan a bani magani. Ahmad da kansa ya dauko ayaba ya mikawa Mama yace ta ba ni, ita kuma ta rika barewa tana saka min a baki ina taunawa a hankali har na koshi. “A saka miki tuwo?” “A a cikina ya cika” A nan ma shi ya ballo maganin ya mikawa Mama ta bani na sha. “Mama rumgume ta, idan mutum ba shi da lafiya yana jindadi a rumgume shi” Ya fada yana kallona, Mama ta amsa da to tana dan kallonsa kamar yadda nima nake mamakin maganarsa sai kace wata karamar yarinya zai ce a rumgume ni, Mama ta kara haurowa kan gadon taja ni jikinta ta rumgume, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba sai na ji natsuwa ta sauko min har na Lumshe ido. “Am Baba daman ina son na fada muku wani abu, na yi magana da lauyana zai saka kara akan abunda akai wa Halima so i think ya kamata ku sani” Ba shiri na bude ido na dago na kalleshi kamar yadda Mama ma take kallonsa. “A a idan su idonsu ya rufe sun aikata abunda suka aikata, mu be kamata mu yi haka ba, ba a taruwa a zama daya, akwai zumunci mai karfi a tsakani, da mahaifin Abdallah da mahaifin Halimatu” “Amman su basu san da zumuncin ba ne suka aikata abunda suka aikata?” “Hankali da tunani ba daya ba, kuma ba a biye son zuciya kamar yadda tai” “Ba ki ga yadda sukai mata ba? Zata iya rasa ranta fa sanadin haka” “Tun da Allah yasa ba a rasa ran ba hakuri shi ya fi, amman shiga kotu a yanzu zai kara lalata zumunci ne kuma ka jawa Halimatu bacin suna a cikin dangi” Wayarsa ce tai ringing kamar yana nema sai kawai yai picking call din ya fice daga dakin, a lokacin ne Mama ta dube ni cikin yanayin damuwa tace. “Karki ba ri a kai matar yayan mahaifinki kotu, ita ma uwa ce a gareki, na sani da margayi yana da rai wata kila da yanzu kina can gidansa zaune yana kula da ke, inda yana raye da duk abubuwan nan ba su faru ba, idan kika bari aka saka Hajiya kotu saboda abunda tai miki Abdallah ba zai taba ganin farinki ba, ko dan shi kadai be kamata ki bari akai Hajiya kotu ba, domin zai kara lalata zumuncin ne, idan hankali ya gushe hankali ne yake dawo da shi, ki masa magana kar ya kai abun nan kotu dan Allah” “In-Sha-Allah zan yi magana da shi Mama” “To Allah ya miki albarka” “Amin” Tun da Ahmad ya fita ban sake saka shi idona ba sai washe gari da safe, misalin bakwai da wani abu. A lokacin ina zaune a dakin ni kadai domin ba sa barin kowa ya shigo da safe sai yamma ta yi. Ya shigo hannunsa rike da kwandon dake dauke da kulolin har kala uku dayan hannunsa kuma rike da filas din ruwan zafi. “Ina kwana....” Na mika masa gaisuwa sun kamin ya karaso, be amsa ni ba kuma be min murmushin daya saba ba har ya aje kayan. “Ga breakfast in ji Hajiya” “Ina kwana?” Na sake mika masa gaisuwa a nan ma be amsa ni ba. “Ya jikinkin na ki?” “Al-hamdulillah” Daga haka be sake ce min komai ba sai ya ciro wayarsa ya shiga dannawa. Kallonsa nai yanayinsa da yadda yai min sai ya sa na ji babu dadi. “Kai hakuri na ja maka ba.....” Kamin na karasa ya tari numfashinta. “Ba ki ja min komai ba, ni na ja miki duk wannan abun daya same ki, ba ina fushi ne saboda abunda ya faru ba, kawai ina mamakin hali irin ba ku ne, taya za a ci zarafin mutum kuma ya hana a bi masa hakkinsa? Su ba su san da zumunci ba ne suka wulakanta ki? Har marinki fa aka ce yar sanda ta yi aka fito dake waje babu mayafi babu wulakancin da ba su muku ba, kin san abunda nake ji a zuciyata?” Kai na girgiza masa. “Babu wanda ya mare ni, kuma ba mu fito cikin gidan ba sai da mayafi, duk wanda ya fada maka tsabanin haka karya yake” “Kanwarki ta fada min kuma baza tai karya ba, kina boyewa ne kawai” Shiru nai ina tunani a cikin duka kanena babu wacce zata iya fadar haka sai Hafiza. “A ina ka ganta” “Na kira wayarki ta dauka, ita ta fada min komai” Na yi shiru domin bana son karyata kanwata a gabansa, ko ba komai gobe ba zai sake ganin girmanta ba, balle har ya yarda da ita. “Idan hankali ya gaushe hankaline yake dawo da shi, ita ita ta aikata kuskure mu be kamata mu aikata ba, ta aikata abunda ta aikata ne saboda tana tunanin ni ce silar batar danta” “Amman miyasa ke kadai zata zarga? Ya akai ta san da maganar ma? After na fada miki wa kika fadawa?” “Saboda bata so na, kuma ta fada tana tunanin na dauke Abdulhamid ne ko kuma na saka an dauke shi saboda zai yi aure, kuma saboda ya ki zama da ni, tana tunanin ni an saka Abraham ya dauke shi saboda na dauki fansa” “Amman ba ita kadai ba har wannan Abdallah.... ” “Abdallah ba zai taba min haka ba, i trust him, ba da sa bakinsa Hajiya tai min haka ba, ba zai taba bari ba, balle har shi yai min, kiyayyar da Hajiya take min a yanzu ta samo asali ne ta dalilin soyayyar da Abdallah yake min” “Miya hana ki aurenshi?” Ya aiko min da tambayar kai tsaye, kallonsa nai ina kokarin kawarda da hawayen da suke son zubo min. “ A wacan lokacin Abdallah ya nuna min soyayya ne ta hanyar da be dace ba, shi yake yawan kawo min labarin abunda Aminu yake, yana son na kashe aure na na aure, wanda a musulunce haramun ne, domin Annabi yace baya tare da wanda ya so matar wani, ko ya zuga matar wani dan ta kashe aure ta ko da kuwa shi din zai aureta, a lokacin da aurena ya mutu, sai Abdulhamid ya fito so na bayan kuma Abdallah yana so na, amman shi Abdulhamid be san Abdallah yana so na ba, Abdallah kuma be taba sanin cewa na yi soyayya da Abdulhamid a lokacin da ina budurwa ba. A lokacin ina jin tsoron abunda ya kashe min aure kar na sake fada mishi, da kuma ganin da nai Abdallah yana so na tun ina a gidan wani sai nake ganin kamar idan na aure shi, aure ba zai dade ba hakan yasa na take aurensa na auri dan'uwansa, daga lokacin sai mahaifiyarsa ta fara kina, ashe Abdallah ya fada mata yana so na, sai take ganin kamar ni na ja hankali Abdulhamid ne na aureshi saboda na batawa Abdallah, saboda babu wanda ya san mun yi soyayya da Abdulhamid saboda a boye mu kai a wacan lokacin ya hana na bayyana soyayyar, wanda ban san dalilin hakan ba wata kila saboda ba shi da lafiya ne yana tsoron soyyayyar mu ta bayyana sirrinsa, a jiya ina jin tana fadar cewar na lalata zumuncin da yake tsakanin Abdallah da Abdulhamid, ban san iya abunda ya shiga tsakaninsu ba, kuma na san saboda ni ne, komai bana yinsa daidai, yanzu ma idan aka kai Hajiya kotu saboda ni Abdallah ba zai jidadi ba” Dan murmushi yai ya tabe baki “Kamar dai Abdallah nan yana da muhimmanci a gurinki” “Yes, ya taimake ni a lokacin da nake bukatar taimakon, ya rike yayana kamar nasa a lokacin da ubansu ya guje su, kuma mijin dana aura wato Abdulhamid ya nuna min baya bukatarsu, duk son da Abdulllah yake min be tana neman yin lalata da ni ko sau daya ba, mi zai saka ba zai zama mai muhimmanci a gurina na” “Duk da haka dai abunda mahaifiyarsa tai miki ba ki cancanci yayanta ba, kuma ya nuna karara bata kaunarki, domin abunda tai miki makiyi ne kadai zai iya yinsa, zai iya zama silar ajalinki da baki farka ba a yanzu yaya kenan? And tell me taya za ki auri yaya uwa daya uba daya twins ya sake ki, yanzu kuma ki yi tunanin auren kane? A addinance ba haramun ba ne, amman a al'adance haramun ne, so pls ki manta da zancen auren Abdallah for now” Da kanshi ya tashi yaje ya hada min tea ya miko min, har na karba zan kai baki sai yai saurin dakatar da ni. “Tsaya tsaya muji” Ya karba ya kurba kadan. “Yana da zafi ba ri ya sha iska” Ya fada yana kura min ido. “Ji nake kamar ace da aurena abunda nan ya faru, zan kyale Hajiyar for now, amman shi dan sanda da yar sandar da ta mareki sai na hukunta su” Kallonsa nai na dauke kaina. “Akwai damuwa karara a fuskarki” “Idan na ce babu damuwa a tare da ni a yanzu na yi karya” “Don't be afraid i will by your side, you will be safe” Kallonsa nai sai ya sakar min murmushi. “I will surprise you idan kika ji sauki kika koma aiki, a gaban kowa da kowa and i hope you won't disappoint me” Ya fada sound so serious. ABDALLAH POV. A yanzu Abdallah yana jin ba shi da babban makiyi kamar Ahmad, daman can Allah be hada jininsu ba balle kuma yanzu da ya zama sanadin tashin ciwon Hajiya sakamakom fada mata da yai Abdulhamid yana gurin Dss, ya san duk wanda dss ta kama yana aikata wani mugun abun ne, be tana zargin dam'uwansa da aikata wani mugun abu ba, a yanzu ma ba zai iya zarginsa ba domin ba a fadi abunda yai ba, be zama lallai dan yana abota da Abraham ace aikinsu daya ba, sai dai kalamar da Ahmad ya fada cewar shi ne sanadin zuwansa dss din ya fi komai tsaya masa a rai. Lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya yana kallon mahaifiyarsa wacce ke kwance an daura mata mata drip a hannu sai sharar bachi take. Mikewa tai tsaye yana kallon dakin kamar wani bakonsa sai ka ce ba dakin Hajiya ba. Sam be jidadin abunda Hajiya tai ma Halima ba da ya san haka za tai da be fada mata komai ba, a dayan bangaren kuma yana tunanin ko a wane hali yanzu Halima take ciki? Har ya dauko wayarsa kamar ya kirata sai kuma wata zuciyar ta hana shi, ajiyar zuciya ya sauke a hankali zuciyarsa na sosuwa da kalaman da Ahmad yai masa, yana mamakin wai a yau har wani zai nuna masa isa da Halimatu,shi ko zai nuna masa cewar be isa ga Halimatu ba, dan murmushin takaici yai. “Mahaukaci, marar tunani, mayaudari” Ya furta murya kasa kasa, yana jin a ransa ko da shi ba zai auri Halimatu ba tun da Hajiya tai musu shamaki to ko Halimatu bata dace da auren banza mutum kamar Ahmad ba, mutumen daya gama wulakanta ta yai mata kazafin kisa, yanzu kuma ya dawo yace son ta yake dan bashi da kunya. He know shi kadai zai aureta ga rike tsakani da Allah babu wata kyama, babu tunanin komai a ransa, ba dan Hajiya ta shiga tsakaninsu ba wata kila da yanzu ya aureta ta haifa masa da namijin da yake ta mamari, yake ganin kuma zai iya samu idan ya aureta domin ita ta haifi both maza da mata ba kamar matarsa Suwaiba ba da ke haihuwar mata. *** *** *** Wasa wasa aka kwashe sati daya kullum sai an sakawa Hajiya drip duk da bi ta rame kamar ba ita ba. A ranar hankalin Abdallah ya tashi sosai ganin halin da mahafiyarsu take ciki, kusa kullum a gidan yake wuni domin shi yake kuka da ita, a yau ma sai da ya tabbatar bachin Hajiyarsa yayi nisa sannan ya kama hanyar gidansa da tunani kala kala. Yana isa harabar gidan su Inteesar suka zo da gudu suka tare shi kamar yadda suka saba, sai ya fito daga motar yana murmushin karfin hali ya rika hannunsu suka nufi cikin falon. Ko da ya shiga Suwaiba na zauna a falon, ta kashe dauri sai kamshin turare take. “Sannu da zuwa” “Yauwa” Ya amsa mata cikin yanayin da ke nuna damuwarsa karara. “Ya jikin Hajiya?” “Al-hamdulillah” Ya kalli Plasma da take kallo kamin ya sake kallonta yace. “I think ya kamata ki koma can gaba daya, saboda kula da Hajiya” Ta dan wara ido. “Ah Doctor Idan na koma can to yara fa?” “Za ku koma can har su in yaso driver ya rika kaisu school daga can, idan ta samu sauki sosai sai ki dawo” Juyar da Fuska tai gefe ta bata rai alamar ita akam fa baza tai ba. *** *** *** Duk wani shiga da fita babu irin wanda Abdallah ko yan'uwansa ba su yi ba amman shiru labarin Abdulhamid har suka fara zargin ko dai an kashe shi ne. A week later in the evening aka dawo da su Gusau bayan hukumar ta bada umarnin rufe duk wani guri da Abdulhamid da aikinsa Abraham suke saida motoci, sakamakon kamasu dan akai da safarar makamai, ga kuma fashi da makaminda Abraham ke yi ta karkashin kasa bayan aikin police din da yake, da bakinsa ya fadi mutane da suka yi wa ciki har da makocin su Abdulhamid wanda babban dan siyasa ne, suka kashe a lokacin da suka je unguwar a ranar da ya so ya kashe Abdulhamid, ba a dawo da su gida ba sai da suka fadi komai ciki har da yadda suke shigo da makaman da kuma wandanda suke kaiwa da inda suke karbowa. ______________________ It's 4200k words today 🙌😊 7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣5️⃣ Idan na ce zan iya fadar kulawar da na samu a gurin Ahmad da mahaifiyarsa na yi karya, domin a kwanan da nai asibiti kullum sai na yi bachi yake tafiya gida, mahaifinyarsa kuma sai tavaiko mana da abinci safe, rana da na dare, sau uku tana zuwa duba ni asibiti, a duk lokacin da ta zo tana yi min kalaman da suke kara min kimarta a idona kuma su kara kwantar min da hankali. Tana yawan fada min cewar nai hakuri, kuma na cigaba da yarda da kaddara kamar yadda nake, kar nai tsammanin Allah ba zai sake jarabata ba, kuma kar na tsammaci sake samun wata kadarar a gaba, na kyautata zaton kuma nai ta addu'ar, haka zata zauna tai ta fira da Mama ko Inna kamar ba matar babban mutum ba ko kuma na ce uwar babban mutum, da aka salleme mu a asibitin ma sai da ta kira ta ji muryata. Yau kam na kara yarda da maganar mutane da suke cewa duk abunda ya baka tsoro wata rana zai baka tausayi, duk kuma abunda ya baka tausayi wata rana zai baka mamaki. Idan nai na hada kalubalen rayuwar da na fuskanta da na Aminu da Abdulhamid, sai na gane cewar ni din ban ga komai ba, domin a halin yanzu Allah ya min mafita kuma ya wanke ni, wani kalubalen a farkon rayuwa yake wani a karshe, wani a tsakiyar rayuwarsa, ba duka arziki ne na halal ba, na kuma ko wane arziki ne na haram ba, ba duka talauci ne kunci ba, ba kuma duka kunci ne takauci ba, saboda ina cikin takauci ba shi yake nufin ba zan jidadi rayuwa ba, idan kuma ina da arziki baya nufin aki jarabbatata.   Ta wani bangaren na kanyi mamakin abunda ya kai Abdulhamid aikata wannan mummunan abu, ko da yake ko wane bawa be isa ya wuce kaddararsa ba. Kamar yadda ban wuce komai ba sai da ya same ni. Ba ni kadai nake cika da mamaki ba har da Mama da Inna, da duk wani wanda ya san waye Abdulhamid, mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, dole kowa yayi mamakin wannan abun, wata kila Abraham ne yaja zuwa ga mummunar rayuwa, wata kila kuma shi yaja Abraham din, gaskiyar abun yana a tsakaninsu sai kuma bincike idan ya tabbatar. Dago kaina nai daga kallon wayar Hafiza da nake wacce ke dauke da hotunan su Abdulhamid, da Abraham da wani wanda ban wayance shi ba, an saka musu handcuffs, police na tsaye a bayansu an jarida kuma nata aikinsu. Na mika mata wayar ina fadin. “Abdulhamid ya ban tausayi” “Tausayi? Tausayi fa kika ce Halima? Haba mutumen daya sakeki har wani tausayinsa zaki ji, ke dai Wallahi kina da matsala” Na yi shiru domin na san ba zata taba fahimta ba, sai dai abunda ya fi tsaya min a rai shine shin Abdulhamid ya san cewar Abraham ne yai min fyade? Da saninsa akai? I need to know, na fada ina sauke ajiyar zuciya a hankali. Na unkura zan tashi kenan sai ga su Namra sun shigo da gudu kowanensu rike da leda a ko wane hannu, ledan kuma ba karama ba irin babbar ledar nan ta super market. “Momy Guess what...?” Aiman ya fada yana wani irin murmushin jindadi. “What it's?” Na tambaya da mamaki a fuskarta. “Wannan Boss din naki, baban su Baby Namra ne ya dauke mu daga school ya je da mu wani katon shago yace mu dauka duk abunda muke so” Wannan karon Adnan ne yake magana, sai Namra ya kyalkyale da dariya. “He say we should called him Daddy, wai yana jiranki a waje yana can cikin mota” Kana kallonsu kasan suna cikin farinciki, jin cewar yana waje yasa na dauki Hijabina na saka na leka kofar gidan, sai ko na ganshi daf fa kofar ya faka motarsa. Ganina yasa ya sauke gilashin motar yana miko min murmushi. “Lims how far” Dan murmushi nai nima “Mun gode Allah ya saka da alheri, kana ta dawainiya da yara” “Bude back seat din nan akwai na ki” Ya fada yana dauke fuskarsa kamar baya son nai masa godiyar. Na yi kamar yadda ya umarta na bude gidan baya na dauko katuwar leda na fito da ita. “Na siyo miki turare duk da ban san choice dinki, amman ni nafi son irin wannan wanda na siyo miki, na mata ina son na ji mace ta saka shi” “Na gode Allah ya saka da alheri” “Ki dai shirya komawa aiki on Monday, tun da lafiya ta samu sosai” Na gyada masa kai sannan na ce. “In-Sha-Allah, amman dan Allah ina neman wata alfarma” Kashe motar yai gaba daya, ya fito daga ciki ya zagayo inda nake ya saka hannayensa duka biyu aljihu yana min wani irin kallo wanda da ace akwai wani kusa da ni da sai na ji kunya, domin idonsa ya sako min sosai kamar zai cinye ni. “Name it” Ya fada kamar mai rada. Kasa nai da kaina ina wasa da ledar da ke hannuna. “Lims..... ” Ya kira sunana cikin wata irin siga wacce ta saka sigar jikina tashi, da na kalleshi kuma sai na kasa jure irin kallon da yake min. “Okay Babe mu shiga mota sai ki fada min idan ba zaki iya fadi in public ba....” Idan ban yi kuskuren fahimta ba kamar yace Babe right? Mistake yai ko kuma da gangan ne? “You know bani da wannan hurumin da zan rumgume ki na kallashe ki na tambaye ki abunda kike so, so please just tell me idan ba so kike ki wahalar da zuciyata ba” The way da yai maganar kamar yana rokona ta shigar lallashi akan na fada masa abunda ni nake da bukata. “Daman ina son na tambaya ne ko ana barin mutum ya ga Abdulhamid” Na fada cikin tsoro da fargaba, runtse ido yai ya bude ya sake kallona. “Abdulhamid....” Ya maimaita sunan. “Why?” “Akwai tambayar da nake son masa, ina son naji amsar daga bakinsa ne kawai” “It's necessary?” Na yi kasa da kaina, sai yai saurin matsawo kusa da ni. “Okay Okay Okay... Kin san irin criminals din nan ba kowa ake barin yana shiga ganinsu ba, saboda gudun abunda zai faru, tun da suna tare da miyagun mutane ne, but idan kina son ganinshi i can talk to my friend sai yai mana hanya ki ganshi, idan ya bada date zan fada miki sai ki shirya na kai ki” “Thank you so much” “No Lims dadi nake ji idan kika bukaci wani abu nai miki, so thank you so much for the offer” Ya fada sound so serious, sannan ya zagaya zuwa side dinsa yana kallona tare da fadin. “But make sure ba wani kalma mai dadi za ki fada masa ba, ba zan jidadi ba idan kika furta wata kalma mai dadi ga wanin Ahmad, saboda Ahmad yana da kishi sosai idan yana da da dama ma, ko a unguwarku ba kowa za ki yi wa magana ba i swear” Ya bude motar yana min murmushi. “Take care of yourself” Sannan ya shige motarsa yai mata key ya bar ni tsaye a gurin ina mamakin kalamansa. Yace Baby at first, and second to the last sentence ya fadi wasu abubuwa da ban gane ma kansa ba, i thought ba soyayya muke ba, but why yake irin wannan behaviors din? Na san ko bw fada min ba abunda yake min da kuma kulawarsa akaina tana nuna damuwarsa ne, kuma akan damune ne da abunda ake so, ko kuma ya zama muhimmin a rayuwa. Sai dai ni din a yanzu ban shirya ba ban kuma san ranar da zan shirya din ba.   Ko da na koma cikin gidan an tarar sun bude abubuwan da ya siyo musu suna ci, sai labarin abubuwan da suka gani suke badawa, ni kuma an zauna saman tabarma na bude ledar, kananan cakes a ciki sai wata kyakyawar sarka mai ruwan zaiba, turare ya fi yawa sai man shafi cream and lotion, da shower gel, kana ganinsu kasan masu tsada ne.   Ina jin yadda kannen suke kamgama shi ni dai bance komai ba, har suka ci suka shude sannan na dauki kayan bayan na basu cake din na nufi daki na aje. Kamar wasa da dare Ahmad ya kira ni a waya ya fada min crwarna shirya gobe misalin ten zai zo ya dauke ni ya kai ni can abokinsa yace zai bar ni na shiga nai magana da shi, a lokacin kuma dai na ji kamar bana son zuwan wata zuciyar tai ta raya min cewar miyasa na bukaci haka? Ban kwanta ba sai da na fadawa Mama abunda nake da kudiri akai. “Amman dole ne sai kin yi magana da shi? A iya tunani na Halima, ya kamata ki nisanta kanki da yayan Hajiya, ba nuna nufin ki yanke alaka ba, a a ki yi nesa nesa daga duk wani abu da zai iya sakawa a zarge ki, iyakar cin mutuncin da nuna kiyaya Hajiya ta yi miki shi” “Na sani Mama kawai ina son na masa wata tambaya ce, wacce nake son amsar ta daga bakinsa” “To Allah ya tsare, tare za ku tafi da Ahmad din?” “Eh In-Sha-Allah” “To yayi kyau” Shiru ne ya biyo baya kamin ta kalleni tace. “Ba zan matsa miki ki yi aure ba, kamar yadda ba zan hana ki sauraren kowa ba, sai dai duk wanda kika san ba aurenshi za ki yi ba, to ki sallame shi da wuri ba sai yayi ta wahala a kanki ba” Ko bata fito fili ta fada min ba, na san Mama tana magana ne akan Ahmad kuma tana da gaskiya, ya kamata na dakatar da shi daga abubuwan da yake min ko ya fara min, kar abun yai nisa ya zame min wata sabuwar matsala.   Kamar yadda ya fada min zai zo da ten ya dauke ni, sai nai gaggawar yin duk wani abu da nake kamin lokacin na sallami yarana suka tafi Islamiyarsu kasacewar yau Sunday suna zuwa makarantar safe ne, sannan ni kuma na shiga nai wanka na shirya cikin bakar abaya, na yafa farin veils karama wanda ya tsaya min iya wuya, ban shafa komai a fuskata ba bayan powder sai dan man baki dana goga, na feshe jikina da turaren da Ahmad ya akwa min jiya, turare ne mai dadin kamshi ina jinsa a gurin manya mata idan na shiga buki ko office. Sako ya turo a waya cewar yana waje yana jirana. “Hey Beb ina jiranki a waje idan kin shirya” Bayan na karanta sakon na samu kaina da faduwar gaba, ina ta jin tsoro zuwa bayan kuma ni na bukaci haka, sai da na sanarwa Mama sannan na fita ina addu'ar fita daga gida. Ina fito daga cikin gidan ya sauke gilashin motarsa yana kallona har na karaso, da kansa ya fito ya bude min motar ni kuma ban shiga ba sai da na fakaici idon mutane, bayan na zauna ya maida motar ya rufe sannan ya zagayo side dinsa ya rufe gilashin motar yana kallon. “Kin san Allah? Da kika fito daga gida na hango ki ji nai kamar naje na rumgume ki? And the way you're walking wow Ma-sha-Allah” Na yi murmushi ina kallon yadda black suit din da ke jikinsa yai masa kyau sai mu ka yi anko kamar na fada masa nima bakin kaya zan saka. Ya bata minti goma a gurin baya aikin komai sai kallona can kuma ya shaki kamshin turaren da ke jikina ya lumshe ido, kamin yai ma motar key mu kama hanya. Kamar wacce tai masa maganin kallo haka ya saka min ido yana ta kallona yana murmushi kamar ba driving yake ba, har tsoro na rika ji kar ya mu yi accident. Mun yi tafiya mai nisa sosai sannan muka isa gurin daga ba a bar mun shiga cikin ba sai da abokin nasa ya fito, the way da abokin ya rika min magana sai na fahimci cewar Ahmad ya fada masa cewar ni matarsa ce wata kila, domin a cikin kalamansa har da zancen wai mijina yana so na sosai duk yabi ya dame shi shi dai matarsa matarsa. Kallona kawai Ahmad din yai ya kashe min ido yana murmushi, can kuma muna sake hada idon sai ya sake kanne min ido daya ya leko da halshensa kadan yai min gwalo still yana murmushi. “Gaskiya Ma-sha-Allah ka yi dace mata, Allah....” “Na sani, zamu iya shiga ciki?” Tun kamin mutunen ya karasa Ahmad ya katse shi yana hade rai kamar ba shi ba. Dariya mutumen yai ya juya muka nufi cikin gurin, nesa da ni Ahmad ya tsaya dan bani damar yin sirri, ni kuma na karasa ciki na zauna a gurin da aka tanada, ta ko'ina akwai security amman hakan be hana ni jin tsoro ba, gabana sai faduwa yake, duk bayan minti daya sai ya juya na kalli Ahmad sai ya dago min hannu ya aiko min da sakon murmushi. After like 14 minutes aka fito da Abdulhamid daga shi sai vest da gajeren wando, gaba daya ya canja, daman can ba jikin ne da shi sosai ba sai ya kara ramewa fuskarsa tai kamar wanda ya shekara be ci abinci ba. Har ya zauna a kujerar dake facing dina be kalleni ba.   Yana ta murza wuyan hannunsa, tsakanin ni da shi sai aka rasa wanda zai fara yi ma wani magana, sai da na sake juyawa na kalli Ahmad ya dago min hannu yai min murmushi sannan na ji karfin guiwa fara ambatar sunansa. “Abdulhamid....” “Miyasa kika zo nan?” Na tari numfashina ba tare da ya kalleni ba. “Kin jidadin abunda ya same ni ko?” A lokacin ne idona ya soma cika da hawaye. “Mi zai saka na jidadi? Ko da ban san ka ba, ballantana kai din dan'uwana ne jinina” Sai a lokacin ya dago ya kalleni. “Ina son nai maka wata tambaya wacce nake son jin amsarta daga bakinka” Na hade yawun bakina sannan na ce. “Miya hadinka da Abraham?” “Abokina ne more than 11 years, na hadu da shi a Lagos, a lokacin da naje gurin hutu, a hotel din da na sauka daki daya muka zauna a lokacin, kasancewar babu dakuna da yawa a hotel din, kasancewar ana bikin nada sabon sarki a garin, and hotel din da muka sauka kusan duka an kama dakunan ciki kasancewar ta babbar hotel, we share the same room and he is the one da ya biya komai, ya sake min sosai we exchange our numbers, lokaci zuwa lokaci mu kan hadu, some time kuma a waya, saboda shi police ne yana yawo gari gari, shakuwarmu tasa muka fahimcin juna sosai duk kuwa da kasancewar ba Addininmu daya ba, shi ya fara dorani akan sana'ar siyar da motoci, shi ya nada min jari duk da a lokacin ba wai bana da kudin ba ne, kawai dai bana ra'ayin abun ne, bayan mun fara sai ya sake nuna min wannan hayar, ban dubi hadarin da ke ciki ba sai na kalli yawan abunda zan samu, sannu sannu na fara tun ina yi ina jin tsoro har na daina, sai duk irin alakar da ke tsakanina da shi, ba kowa ya san muna abota ba, saboda abu ne da ke bukatar sirri idan aka ga alakar ta yi aminci sosai za a fara zarginmu, that's why idan zamu hadu sai dai mu hadu a sirrice, har Allah yasa ya dawo garin nan da aiki” Yayi shiru tare da kawardar da fuskarsa. “Amman ka san cewar  Abraham ne mutumen da yai min fyade?” “Na Sani, ko da Abdallah ya fada min na sani” Ya amsa ba tare da ya kalleni ba. “After na rabu da ke, na gano cewar shine saboda ya fada min yasan wandanda suka kashe Alhaji Sama'ila na yaddo, and you told me on that very night suka keta miki haddi, and guess what a wannan daren ya shirya kashe ni ne, saboda babu amana a tsakani, wanda ni ba zan iya hakan ba, shi yana ganin kamar na karbe masa jama'a na fishi samun kudi, domin shi wasu mutanen suna tsoron mu'alama da shi ganin cewar Jam'in tsaro ne, kai tsaye na tuhume sa da cewar shi ya keta miki haddi kuma ya amsa min da cewar yes shine, and now yana neman inda zai same ki ne, saboda kin ci ciki bayan shi be taba kwantawa da mace tai ciki ba, and he already know ni bana da lafiya” “Amman baka taba fada min ka gano shi yai min fyade ba, baka nemi afuwar kazafin da kai min ba, ba ka wanke ni a idon mahaifiyarka ba” “Komai ya riga ya lalace Haima, a lokacin na gano cewar Abdallah yana son ki, Hajiya tana kin ki, kuma na san ba zaki tana dawowa a gareni ba, saboda ni ba zan iya komai da mace ba, shiyasa na bukaci boye soyayyarmu tun farko bana son wannan sirrin ya bayyana, gano cewar Abdallah yana son ki shi yafi komai bata min rai, kuma lokaci ya kure Haima komai ya lalace, na kasa yarda da ke na rabu da ke, and silata abokina ya keta miki haddi” Hawaye ya fito daga idonsa. “A lokacin ne na gano cewar na rabu da matar da ba zan taba samun irinta ba har na mutu, na rasa komai ba ni da mata ba ni da yaya, babu irin neman maganin da ban yi ba amman na kasa samun lafiya saboda Abdallah” Ya karasa yana murmushin bakinciki wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, sai ya kalleni. “You got lucky za ki auri mutunen da zai ba ki abunda ni da aminu muka kasa ba ki.... And the way da ya dage da neman tona sirrinmu i know yana son ki sosai” Waiga nai da zimmar na kalli Ahmad amman sai ban ganshi a gurin ba. “Ba so na yake, abunda kai min kai da Aminu ya tsorata ni daga son wani ko aure a yanzu, murum data na yarda da shi a rayuwata Abdallah shi kadai nake da tabbacin na zai cutar da ni ba....” “And you can't marry him....” Ya fada kai tsaye yana kallona da murmushi a fuskarsa hawaye na sauko masa. “Ba zai yiyu ki aure ni ba, kuma ki auri twina brother dina, bayan kuma ina raye, Hajiya ba zata yarda ba, hakan kuma na zai kara min komai ba sai tsanar Abdallah, and i know duk yadda za ki so shi ba zaki so shi kamar yadda ni kika so ni ba, I'm your first love i know ko yayana wata rana sai kin ji so a zuciyarki kamar yadda ni ma ba zan iya cire soyayyarki a raina ba, so you can't marry my brother kuma ki rayu da so a zuciyarki, no matter what Abdallah zai baki Hajiya ba zata tana son ki ba, saboda tana ganin kin shiga tsakanin yayanta” Mikewa nai tsaye sai shima ya mike. “Ban sani ba ko zan sake ganinki ko a a, ban sani ba ko za su yanke kin hukuncin dauri rai da rai ne ko kuma za su halbemu ne i don't know, but i wish you all the best in your entire life, and I'm sorry for what I did” A lokacin ne hawaye ya fara sauko min kamar ba gobe, tausayinsa ya rufe ni ya sadakar ya san cewar kashe shi za ayi kenan, maganganunsa suka rika min yawo a cikin kai, cewar ba shi da mata ba shi da yafi komai tsaya min a rai, kasa tafiya nai sai kallonsa nake ina hawaye kamar yadda shi ma ya rika waigena yana kuka kamar ba shi ba. Har na nufo inda motar Ahmad take na bude na shiga ban daina hawaye ba, yana kallona hankalinsa ya tashi. “Me ya faru? Mi yai miki?” Kasa magana nai sai kokarin saida hawayen nake, hakan yasa shi fusata ya bude motar sai fita nai saurin riko rigarsa ina girgiza masa kai. “Be min komai ba” “Then why are you crying?” Na yi saurin share hawaye. “Ba komai” Kallona yai for a moment sannan ya rufe motar muka kama hanya, sai da muka hau titi ya dauko ruwa ya miko min, na karba na bude ya sha ruwan sosai sannan na rufe na aje. Har muka isa gida ban ce masa komai ba shi kuma be fasa kallona ba, bayan yayi farkin na fita cikin motar. “Thank you” Na furta ba tare da na jira abunda zai ce ba na shige cikin gidan, a wunin ranar sai na kasa sukuni cikin abunda nake tunani har da zancen samun lafiyarsa wanda yace Abdallah ne, kamar ya? Shi ya masa wata allurar ne ta zame masa haka? Amman Abdallah ya san da da wannan kuwa? Mi zai saka yayi masa haka? Kamar ya san ina tunaninsa sai akai sara ka gaba, kiransa ya shigo wayata, sai dai wannan karon kasa daukar wayar nai har tai ringing ta katse sai ya sake kira sannan na dauka. After mun gaisa yace min. “Abdulhamid yace kin je gurinsa yau” “Eh” Na amsa masa a takaice duk da na san ya kira ne saboda ya san dalilin zuwana. “Okay” Har zai aje wayar na ce. “Abdallah zan iya tambayarka wani abu?” Shiru nai na wani lokaci har sai da yace. “Ina jin ki” “Da gaske kai ne silar ciwon Abdulhamid?” Shiru yai daga can cikin wayar sannan kamin ya aiko min da tambaya. “Kamar ya?” “Ya fada min kai ne sila, taya?” “Magana ce mai tsawo Halima zan na same ki gida daman akwai maganar da nake son yi da ke” “Ka fada min dan Allah, zuciyata ta kasa yarda kuma na kasa natsuwa” Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace. “Abun ya dade tun muna samari ne, na tashi da son yara musamman maza, and Abdulhamid ya san da haka, kamar wasa wata rana muna magana nace masa zan riga shi aure, shi kuma yace ko na riga shi aure ba zan haifi namijin da nake da buri ba, ni kuma na ce masa shi kuma ba zai ma taba haihuwar ba har sai na haifi namijin, and na gano haka ne after Suwaiba ta fara haihuwar Mata, and last barin da tai ma macece, yayi min kofi ne and after that Hajiya ta ba mu maganin kare kofi saboda abubuwan da suke faruwa, na shi ya kare nawa kuma ya rage kaifi that's what i know” *** ( Wannan abun ya faru a gaske, Hasana da Husaina, Husaina tai ma Hassana kofi cewar ba zata taba aure ba, ita kuma Husaina tace mata ko tayi auren ba zata taba haihuwa ba, har yau kuma suna nan da rai sun fara manyanta Hassana ba tai aure ba Husaina kuma bata haihu ba) *** Ajiyar zuciya na sauke ina mamakin yadda sukai wa junansu illa. “Zan zo gobe akwai maganar da nake son yi da ke” Ban sake ce masa komai ba na kashe wayar, a ranar na kwana da mamakin abun a zuciyata. Sai mafarka da safe kamar wata marar lafiya, haka dai na shiryawa su Amal suka tafi makaranta sannan ni kuma na shirya, yau ma abayar na saka sai dai wannan ash color ce tsabanin jiya da na saka black, sai da nai ma Inna da Mama sallama sannan na nufi gurin aikina kamar yadda Ahmad ya bukaci na dawo aiki bayan hutu daya ba ni wai sai na samu lafiya.   Napep na hau bata sauke ni ko'ina ba sai kofar gate din kamfanin, na gaisa da masu gadin kamar yadda na saba sannan na nufi ciki, a reception ma sai da na tsaya na gaisa da Blessed mace mai kirki da son mutane, sai da ta tambayi abunda ya hanani zuwa aiki kwana biyu na fada mata cewar bana jindadi ne, sannan na wuce na nufi office dina. Ina kai hannu na tura kofar office din gaba daya sai naga kamar ba nawa ba, hakan yasa na dawo waje da sauri na sake kallon kofar sannan na sake shiga, gaba daya an kawata office din da abubuwan kawa kamar gurin taron biki, idanuwana sama na shiga cikin ina ta kallon kyale kyalin da ke saman sai wani kamshin rose ke tashi an kuma jera fulawar rose har saman kujerar da nake zama. Ji nai kamar na taka wani abu mai tsantsi hakan yasa na kalli kasa da sauri sai nai arbar da fulawar rose an yi rubutu da ita cikin mayan haruffa. *WILL YOU MARRY ME...* Wani irin faduwa gabana yai, da ni ake ko da wata abunda nake gani a fina fine nake karantawa a litattafai yau shi ne a gabana, motsin da na ji a bayana yasa na juyo da sauri kamar a rikice nai arba da mutum duke a gabana...... ______________ I can advertise your business with some of my pages and status just chat me. 08036126660😊🙌 7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣6️⃣ Red suit ne jikinsa babu abunda ke fita daga jikinsa sai kamshin turare, kallona kawai yake sai dai ba irin kallon da ya saba min kamar zai cinye ni ba, wannan karon ido a lumshe yake kallona kamar mai jin bachi. Nikam gaba daya jikina rawa yake ban tana ganin a fili ba ba a taba min irin haka ba ban kuma saka ran wani zai min ba, juyawa nai na karewa office din kallo na sake kallonsa daga ni sai shi ne a office din amman na kasa yarda cewar da ni nake, na kasa yarda ba mafarki nake ba har sai da na runtse ido ya bude na sake runtsewa na bude sannan na yarda ba mafarki nake ba, daman shine mamakin da yace zai ba ni? Na nuna kaina sai ya gyada min kai. “Will you be my wife for the rest of my life?” Ya fada da bakinsa still yana duke a gabana, hannunsa rike da dan karamin box da zobe ciki. Rasa nai abunda zan yi idan na ce masa no ransa ba zai masa dadi ba, sai dai be kamata yai min haka ba at least i need to think ina bukatar nai shawara, but what else i can say more YES. “YES.....YES....YES...” Na maimaita har sau uku ina gyada masa kai idanuwana na cika da kwalla da ban san na minene ba, rashin ba ni damar yin tunani ko shawara ko kuma mamakin abun ko kuma amsawar babu shiri? Ko kuma na bakuntar sabon al'amari? Ba zan ce na murna ba dai domin a yanzu ban zan iya tantance a halin na ke ba farinciki ko akasin haka? “Oh Yes Babe my search is done”      Ya furta, gaba daya hannayensa ya hada ya matse sosai ya runtse idonsa yana wani irin murmushi da ba zan ina fassarasa ba, sannan ya mike tsaye ya kama hannuna for the first time ya yana kokarin saka min zoben da nake mamakin yadda akai ya san size din yatsuna, after ya saka min zoben mai haske da kyalli kamar na gold sai dai wannan zaiba ne, kallona yai ya dora hannunsa saitin zuciyarsa. “You're here in my heart, you're my destiny, you mean to be mine, so let's give love another life....” Faduwa yai gabana kamar mai neman gafara ya jimke hannayensa ya lumshe ido. “Duk yadda zan fada miki irin farincikin da nake ciki a yanzu, to zan yi karya ne kawai, but i can promise you one thing nothing can keep us apart, all i want is to live with you, i will be someone that you can always turn to, i will be everything you want, you mean the way to me, i will fix what it broken, Lims i need you” Sai kuma ya mike tsaye yana kallona da murmushin da zan iya kiransa da dariya, ya zagaya bayana ya zagayo ya sake haka kusan sau hudu sannan ya sake tsawa a gabana yana sauke numfashi, har lokacin ina tsaye a gurin ina murza zoben da ya saka min, har lokacin bana jin murna farinciki, bakinciki damuwa ko akasin haka, I'm not happy kuma i'm not sad. The way da yake fadi wasu maganganu sai na ji kamar ba shi ba, domin a yadda yake a da zaka iya rantsewa Ahmad ba zai iya furtawa wata kalar so ba, watan kuma ni Halima, dana dago sai idanuwa suka sarke cikin nasa na saka kawarda nawa, shi kam daman kamar hakan yake so sai Murmushi yake sakar min, hawaye ne suka sauko min, sai ya matsa kusa da ni sosai. “You should know this love i share was never mean to die, co's i don't wanna see you cry, i will never treat you bad, ban tana yarda so nake ba sai Lims kin san yadda nake ji a raina? Kamar na dauke ki na hade you're the queen of my heart, wani irin farinciki nake ji marar misaltuwa” Ya shafa kansa tare da daga kan sama yana busar da iskar bakinsa, ya nufi gurin windows office dina ya tsaya sai kuma ya juyo ya kalleni. “Ba zan iya tuna ranar da wani farinciki ya same ni kamar haka ba....” Maballin gaban suit din ya bude ya nufo inda nake ya kama hannuna ya dora saitin zuciyarsa. “This where you belong, i hold you close to me” Da gaske zuciyarsa bugawa take da mugun karfi kamar zata fado kasa, duk yadda nake jin bugun zuciyata nashi ya ninka nawa sau dari, janye hannun nawa nai har lokacin na kasa cewa komai, bakina yayi nauyi sosai a kaina kuma ina jin kamar babu wasu kalmomi ciki, a hankali na ji ana busa min iska a idona sai na lumshe ido ina shakar iskar bakinsa mai kamshin strawberry, har na daina jin iskar ban bude idon ba sai da na ji an bude kofa an fita sannan na bude idon a hankali, ban ganshi a gabana hakan ya tabbatar min da cewar ya fita daga dakin kenan. Kujera na nufa na dauke fulawar rose din ya zauna na rumgume ta a hannuna ina ta kallonta kamar ance min makomata tana ciki, na hade yawun bakina yafi a kirga kamin ya sake duba daya zauna a hannun kamar dan ni akai shi, kamar ance na juya na kalli windows sai na hango shi tsaye yana kallona. A wunin ranar kasa aikin komai nai sai jikina yai kamar wacce akai wa allurar rashin kuzari ga kuma magana da na kasa cewa komai, gaba daya sai m afka duniyar tunani, i think kuma ia say i will never fall in love, amman me kenan? Ko da yake ba zan ce ina son Ahmad ba kuma ba zance na tsane shi ba, amman makomar yarana fa? Shi ma zau dauke su kamar yayansa? Ko kuma zai yi min irin na Abdulhamid ne? Mahaifiyarsa za tai maraba da ni ko kuma dai ita ma kamar Hajiyar Aminu da ta Abdulhamid take? Da gaske zai iya rike ni tsakani da Allah ko kuma a a, ba zan iya gano haka a yanzu ba all what i have to do is nai Istihara na sanarwa Allah matsalata na kuka masa damuwata sannan na nemi mafita a gurinsa, na nemi zabinsa a tsakanin auren Ahmad ko akasin haka.   Na sani duk yadda zan tsorata da auri ko na guji aure, shine dai matarba da cikar kamala ta, shine zai kare mutumcina yai min katanga daga duk wani abu da zai iya samuna a kafin igiyar aure, so ba ni da wani zabi da ya wuce na kaunaci sunnar manzo na nai bibiyaya ga Ubangijina, kuma na yarda da wannan kaddarar ko da kuwa ita ma kamar wadancan take domin shine cikar imanina.   Kamar ance daga ki gani sai ganin mutum nai jikin kofar office din ya rumgume hannayensa yana kallona, sai murmushi yake kamar wanda be taba shiga damuwa ba, kamar jira yake na dago sai ya karaso ciki ya tsaya gaban teburina yana min kallo daya saba. “Za ki yi magana da Hajiya ta yanzu nan, tace tana son magana da ke, bata yarda da ni ba” Ya fada min a hankali kamar mai magana da yaro karami yana son ya fahimta. Be jira cewata ba kamar yasan ba abunda zan fada din ya ciro wayarsa ya kira number ta ya saka a hands-free sannan ya kwanto jikin teburin yana cigaba da kallona, kamar wanda kallon nawa yake kara masa karfin ido. Ina jin lokacin data dauka sai yace. “Hajiya ga ta” Ya miko min wayar ni kuma na mika hannu na karba ina kallonsa kamar mai tunanin abunda zan yi da ita. “Yata.... Da gaske ne abunda Gwarzo ya fada min? Wai kin amince za ki aure shi.....?” “Eh haka ne...” Kamar an matsi bakina haka maganar ta zo min subul da baka. Shi kuma sai ya turo bakinsa ya aiko min da kiss marar sauti daga inda yake tsaye. “Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah ya tabbatar da alheri a tsakaninku, ya kawardar fitina da sharin sheidan da na zuciya, ya kawar da idon makiya” “Amin” Wannan karon shi ya amsa yana wani lumshe ido. “Yanzu kin yarda?” “Na yarda kuma na fi kowa farinciki zan yi ma Siyama wannan albishir din, Allah ya maka albarka, kai da kanka ka nemo matar ka I'm very happy” murmushi yai ya yanke wayar, ni kuma na mike tsaye na fara shirin tafiya. “Daga yau idan na fito daga gida zan biyo na dauke ki, idan kin tashi aiki kuma ni zan kai ki” “Amman....... ” “Shiiiiiiiiii” Ya dora hannunsa saman bakinsa yana min alama da nai shiru. “Kuma idan kin je gida ki bar mahaifiyarki ta san abunda yake faruwa, nima zan yi magana da Hajiya zata sanarwa wadanda ya kamata ina son dai cikin satin nan na tabbatar da gaske kin zama tawa, idan an daura aure ban ki ba amman ba zan yarda sati ya shige ban biya sadakin wannan kyakkyawar Babyn ba” The way da yake magana ban ga alamun da wasa yake ba, amman ya yake min haka kamar mai ba ni aiki? Ko dai ya manta ni bazawara ce? Wani irin biyan sadaki a yanzu kamar wanda ya matsu ko kuma nace wace aka gaji da ita? Anya yau Ahmad lafiya yake kuwa? Daga zancen saki aure sai kuma maganar manya su shiga lamarin kamar wani abunda ba gaske ba? Daman a cikin surprise dinsa har da wannan ko kuma yanzu idea ta zo masa? Kamar wacce yai ma wani magani sai na kasa ce masa komai sai kallonsa nake ina mamakin al'amarinsa, kamar wanda aka ce masa zan gudu, a take ni tsaro ma ya kamani. _________________ Finally Halima tace Yes to a bani goro 🙄 7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣7️⃣ “Ban san abunda Hassan yake nema a duniyar nan ba, ban san wani abu da ya rasa ba, ban san kadarar da ta kai shi fadawa wannan mummunar sana'ar ba, na jama kansa masifa... Wata kila a kashe su wata kila a barsu su kasara rayuwar gidan kaso, amman ko da an sake su an kunyata su tun da an bayyana fuskokinsu kowa ya gansu, a lokacin da ya kamata ace ya samu farinciki sai kuma wannan kaddarar ta fado masa...” Hajiya ce take wannan maganar hawaye na fitowa daga idonta, wani irin abu ta ji ya tsaya mata a zuciya tun daga lokacin da gaskiya ta bayyana har yau yana nan tsaye ya tokare mata kirji. Abdallah ya sauke ajiyar zuciya, shi kanshi shi jidadin halin da dan'uwansa da mahaifiyarsa suke ciki ba, no matter how bad your blood is, jininka jininka ne, and idan akwai wanda zai yi blame me a yanzu Ahmad ne domin shine silar faruwar hakan, duk kuwa da yasan abunda Abdulhamid yake ba abun kwarai ba ne, amman yana tunanin ya tona masa asirine saboda ya saka Halima ta so shi kuma ta guje Abdallah, miyasa da ya gano haka ne be fadawa Halima a sirrance ba sai a san yadda za a bullowa lamarin, amman ya zabi ya tozarta shi haka wanda silar hakan ga mahaifiyarsa a kwance tana fama da jinya. Idan har Ahmad zai iya kitsa cuta a zuciyarsa kamar haka then be yi deserve ya aure Halimatu ba, domin shi ma ba a san iya abunda yake sakawa a zuciyarsa ba kuma ba a san abunda yake a karkashin kasa ba, ya fada masa sai ya nuna masa shi din ba kowa ba ne a gurin Halima that's for sure sai yayi, duk abunda yai ko zai yi zai tashi a tutar babu ne, ko mazan duniyar nan sun kare he don't think zai bar Halima ta auri Ahmad, rayuwarsa tana nuna masa babu wanda ya cancanci Halima sai shi, duk da ya san Hajiya ba zata bari ba a yanzu wata rana zata bari, so zai jira har zuwa lokacin da zata yarda but right now all what he want is yai magana da Halima. Tun da har Ahmad ya saka bakinciki a zuciyar mahaifiyarsa shi ma sai ya saka a tasa zuciyar, sai ya nuna nasa kudinsa da wata isarsa ba su isa su siya masa soyayyar Halima ba. “Duk yarinyar nan ce taja komai nasadinta komai ya faru, sam babu alheri a tare da ita, bata nufar mu da khairan ai sheran” Hajiya ta fada tana kokarin dora laifin akan Halima a ganinta sanadinta ne asirin Abdulhamid ya tonu har haka ya same shi, domin shi mutumen daya shige gaba akai bincike aka tona asiri saboda Halima yai dan haka komai ma ya faru ita ce sanadi. Abdallah dai be ce komai ba sai saurare kukan mahaifiyarsa yake. “Da na san haka zai Faru Wallahi da tun farko ban bar shi ya aureta ba, Halima ta zame mana fitina a cikin iyali, ta lalata mana komai na rayuwa Allah ya isa tsakanina da ita, ban san me nai mata ba ta tattara duka farincikin nawa ta dauke, ta tarwatsa mana komai har ta kai yau ga ni kwance saboda bakincikinta” Sai a wannan karon Abdallah yace. “Laifin wannan dan iskan ne, shine yai komai ai” “Amman ai sanadin ne ko? Waya sani ko ita ta saka shi ma” “Amman ai ba ita ta saka Abdulhamid a wannan harkar ba” “Ko ba ita ta saka shi ba, asirinsa saboda wa ya tonu? Allah yana son mai rufawa dan uwansa asiri, idan ba dan su kunyata mu ba taya za su nemi yi masa wannan cin mutuncin” Shiru yai yana jin tsanar Ahmad tana kara hauhauwa a zuciyarsa. AHMAD POV. Be taba yarda da gaske yana son Halima ba sai yau, domin farinciki da yake ji a tare da shi ya wuce misali. Taya zai kwatanta yadda yake jinta a zuciyarsa na amincewarta kawai ashe daman tuni ba tausayinta kawai yake ba har da son ta, driving yake amman gaba daya hankalinsa yana gunta after every one minute sai ya kalleta with smile on his face. Wani irin abu yake jin yana masa zillo a zuciya babu abunda yake ayyana aransa sai idan ya kai kasance a mijinta ya zai tsinci kansa? A hankali ya busar da iskar bakinsa ya kalleta wannan karon idanuwansa sun samu masauki a cikin idonta, sai tai saurin kawardar idonta shi kuma yai murmushi ya cigaba da tukinsa har suka iso cikin unguwar. “Ya isa” “Why?” “Ba sai ka kai ni kofar gida ba, zan sauka a nan” “Okay Lims komai kike so shi zan miki” A gafen hanyar ya faka motarsa yana kokarin fita ta bude mata tai saurin budewa ta fita, sai da ta rufe motar sai ya sauke gilashin motar ya kira sunanta. “Lims...” Jimm tai kamar ba zata juyo ba sai kuma ta waigo ta kalleshi a tsorace. “I love you...... I love you so much.... And i know i love you.....” Kasa cewa komai tai kuma ta kasa matsawa daga inda take, kamar yadda ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa, kallonta yai for few seconds sannan yai reverse ya juya ya koma inda ya fito, sai da ya fita daga unguwar sannan ya dauki hanyar gidansu cikin wani irin farinciki marar misaltuwa, abunda be taba saka ran samu ba. After yayi parking habarbar gidan ya fito yana wasa da makullin hannunsa ya nufi part din Hajiya. Kamar ya san shi suke jira yana shiga Siyama ta taso ta sauri ya rumgume shi. “Congratulations” “Thank you Sis” Ya saketa ya nufi gurin mahaifiyarsa kamin tace komai ya rumgume ta. “Na gode Hajiya, you're such a wonderful Mom, thanks for everything” Ya saketa ya zauna kusa da ita yana kallonta. “Na fi kowa farinciki a yau, kasan saboda me? Ka nemo matarka da kanka, kuma wacce kake jin ta kwanta maka a rai, duk a baya ma ma san kana nemo amman sai matsala ta shiga ciki, to wannan karon bana fatar sake faruwar wani abu, a duk macen da zaka aura na kan jin kamar zata malleka ka ta kwace ka ne, amman wannan yarinyar ina jin natsuwa sosai a tare da ita, na dade ina maka fatar auren bazawara musamman irin wannan mai hakuri, domin wasu zaurawa wahala ce take fito da su daga gidanjen mazajensu wasu kuma kishiyoyine suke fito da su, duk mace da zata taba aure ta fito tai zaman zawarci ba tare da ta zubar da mutuncinta ba, hakika wannan matar abar girmamawace domin zawarci abu ne mai tsada kuma mai wuyar sha'ani, duk mace da tai zaman aure ta fito tai zaman zawarci to tayi rayuwa ne guda biyu mabanbanta, akwa challenges da yawa a rayuwarta, tun daga kan uwaye yan uwa masu neman aurenta yayanta mijin da ta fito gunss ko ya rasu, zaka tarar ta fuskanci kalubale, wanda a gaba idan za tai aure zata jure hakuri domin samun ribar auren, akwai fa'ida sosai a auren bazawara Gwarzo sai a yanzu zaka sani” Ya hade yawun bakinta sannan ta sake kallonsa tana murmushi. “Abu na biyu kuma ina tunanin lokaci yayi daya kamata ace na bar ku kun tafi duk inda kake so kai da matarka kui rayuwarku yadda kuke so” Yayi saurin girgiza mata kai. “Nonono Hajiya, Wallahi ba zan iya ba a yanzu ne kika fi bukatar na zauna a tare da ke, ko ba komai Siyama mace ce zata tai aure, gidan wani zata je ni kuma aurowa zan yi na kawo, akwai abubuwa da zaki bukata wanda dole ni ko matata ne za mu yi miki, ba ki da wani zabi daya wuce ki bar mu mu zauna a tare da ke” “Idan kuma ita bata so fa? Wasu matan basa son zama da iyayen miji na sani, musamman ma irina” “Me zai hana ta so? Halima tana da hankali, zata so zama da ke Hajiya, kuma ai kowa da part dinsa ba part daya ba ne, to me zai saka dukanku ku takura?” Murmushi tai. “Allah yai maka albarka ya hada kanku ya sa wannan auren alheri a tsakaninku” Shi da Siyama suka amsa da amin. “Na fada mata yai magana da mahaifiyarta domin sanarwa duk wanda ya dace, saboda ina son a cikin satin nan na san an tsayardar maganar” “Ouhhhhh Yaya da sauri haka? Cewar Siyama sai ya kalleta yana murmushi yace. “I swear to Allah ji nake kamar da na yi sake kadan kamar haka zan iya rasata, idan son samu ne ma idan anje tambaya a daura auren a can, idan ya so duk wani shirye shiyen sai ya biyo daga baya, idan ma tace ba zata tare ba sai da da shekara ba ni da matsala” Siyama ta tsire baki. “Wannan Lims din dai ana ji da ita” Hajiya ta yi murmushi tana kallonsa. “Kana da abokin takata ne hala?” “Yes Hajiya kin san mace ko bata da kyau ai bata rasa masoyi, balle ita kuma akwai wani cousin dinta da nake tsoron sherinsa kuma kin san cousins ba su da kyau” Gaba dayansu sukai dariya har shi. HALIMATU POV. Na manta rabon da wani ya furta min kalmar so haka kai tsaye, gaba daya sai na ji kamar ya sare ko wace gaba ta jikina, kalmar tai min nauyi a zuciya har ta sauko min a kirji. Gaba daya rayuwar yau ta zame min kamar mafarki at first na tafi office na tararda abunda ban yi zato ba kuma na amince ba akan cilas ba kuma ba dan zuciya tana ki ko tana so ba. Da kafa na karasa gida sai dai ban labarta wa kowa komai ba ciki kuwa har da mahaifiyata, to idan ma zan fada mata ta ina zan fara? Me zan fada mata? Yarana ya zan ce musu? Zai karbe su kamar ubansu? Ko kuma zai musu na Abdulhamid ne? Miyasa ban tambaye shi duk wannan ba na amince masa zan aure shi? I don't think na shirya yin wani auren na bar yarana.   Har akai sallah isha'i ina ta tunani daya, bayan Mama ta sallame sallah na tashi na koma kusa da ita na zauna sai kuma na kasa cewa komai. “Wata maganar kike son yi?” Kasa nai da kaina gabana na faduwa sosai na ce. “Mama yanzu idan nace zan yi aure be yi kusa?” “Kin taba ganin mace tai kusa da aure ko ta makara?” “Ba haka ba ne, ina tunanin rayuwar na da fito ne” “Idan kina kallon rayuwarki ta baya, to har a bada gobenki ba zata taba yin kyau ba, ki yi fatar samun gobe mai kyau, ke a yanzu kamar kan titi kike idan kika ce za ki tsaya waiga bayanaki to mota zata zo ta gabanki ne ta kade ki ta takaki tai miki illa, amman idan kika fuskanci gaba sai rayuwarki tai kyau fiye da yadda kike tsammani, shi bawa ba a son yana yanke kauna daga rahamar Allah” “Mama na yi wani abun da nake jin kamar ban yi daidai ba, Ahmad ya nemi aurena kuma na fada masa cewar na amince zan aure shi sai dai a yanzu ina ta jin damuwar amincewar da nai, saboda yarana...” Ina kai aya na ga Mama na murmushi. “Bayan kin amince kuma shaidan yake son raya miki wani abu a zuciya? Ko yanzu ai lokaci be wuce ba za ku iya yin magana, amman dai duk mutunen da zai rika yayana ai kana gane shi ne tun gida, bana tunanin Abdulhamid ya taba daukar yaranki ko sau daya ne a mota? Amman Abdallah da shi wannan har makaranta suka saka su, kina tunanin mutumen da zai san abunda ya faru da ke da halin rayuwar da kika tsinci kanki a ciki zai yi tunani saka ki cikin wani kunci?” Kallonta nai a raunace na ce. “Mama wasu maza suna da son kansu ne, kuma idonsu kan rufe har sai sun samu abunda suke so” “Haka ne, amman shi aure fahimtar juna ake so a ciki, za ki iya samunsa ku tattauna, idan ya aminta falillahil hamdu idan kuma ya nuna miki ba haka ba zai ki sake wata shawarar” Mama tana da gaskiya matsalar yara mai sauki ce domin zan iya magana da shi akan. Har na bude baki an sake wata maganar sai muka ji sallamar Abdallah, daga uwar dakan da muke muka amsa masa yanayin yadda Mama ta kalleni kana gani kasan mamakin ganinsa take, ni kam na san da zuwansa. Tun da ya shigo idonsa na kaina har ya gaisa da Mama be daina kallona ba, idan sabo kuma na saba da irin wannan kallon daga gurin Abdallah. Bayan sun gaisa Mama ta tashi ta fice daga dakin sai ya rage daga ni sai shi ne a ciki. Shiru ne ya biyo baya be ce min komai ba ban ce masa ba, can ya ciro wayarsa ya soma latsawa. “Me ke tsakaninki da Ahmad Gwarzo?” Kamar daga sama na ji tambayar, ba zan yi mamaki ba idan Abdallah yai kishi daman ya saba kishina tun da yana so na. “Babu komai” “Yaushe muka fara haka da ke?” Ya fada yana kallon irin kallon nan dake nuna da gaske yake. “Ba karya nake ba, babu komai tsakanina da shi” “To idan ke baki da wata manufa akan shi shi yana da ita akan ki” “Kamar yaya” “Son ki yake mana ko be taba fada miki ba?” Na yi shiru kamar na ce masa ya fada min a yau har ya nemi amincewar aure na kuma na amince sai kuma wata zuciyar ta hana ni domin na san abun ba zai yi ma Abdallah dadi ba. “Be kamata ki karbi soyayyar wani ba a yanzu Halima, wanin ma kuma Ahmad Mutunen daya dora miki laifin kisa sanadin hakan kwakwalwarki ta tabu, a iya tunani yanzu kin yi hankali kina da tunanin ya kamata ki gane mai miki so ya gaskiya ki aure shi” “Kai kake min so n gaskiya Abdallah na sani, amman kuma aurenka abu ne da ba zai yiyu ba” Gyara zamansa yai yana kallona. “Kamar dai ba ke ba Halima yau ke da kanki kike fadar aurena ba zai yiyu ba” “Saboda Hajiya da Abdulhamid” “Hajiya idan zamu iya bata lokaci zata fahimta” “Ba zata taba so na ba Abdallah har kasa ta nade ba zan taba zama fara a gurin Hajiya ba, bana son na sake aikata wani kuskuren idan na aureka a yanzu mutane za su zage mu Abdulhamid kuma zai ga cewar bamu kyauta masa ba” “Gaba daya ya canja miki tunani Halima, ya dauke miki hankali, ya chusa miki wasu abubuwan da babusu akan ki, amman ya kamata ki yi tunani ko da ba zaki aure ni ba be kamata ki auri Ahmad ba, bakinsan komai akansa ba, Halima bana son alaka tana shiga tsakaninku, idan har zan roki wani abu ku yi a yanzu to zan roki ki aje aikin nan a kamfaninsa” Ya fada da kamar fada har yana nuna ni, Yanzu kam bana jin Abdallah ya tsani Ahmad saboda ni kawai wata kila har da abunda yai ma dan'uwansa, sai dai duk kusanci ni na Ahmad be kai da Abdallah ba duk irin taimakon da zai min yana bayan na Abdallah, idan har Abdallah zai ce kar na auri Ahmad Wallahi zan iya ko dan na faranta masa ne balle kuma aje aiki wanda shi ya fi komai sauki a gurina tun da har ya bukaci haka, bana jin akwai wani abu da Abdallah zai bukata a duniyar nan na kasa masa ko da kuwa raina ne, balle abunda ran ya mallaka. “Zan aje aikin gobe In-Sha-Allah” Na fada ina kallonsa, ina kallon lokacin daya ja dogon numfashi ya sauke sannan ya busar da iskar bakinsa ya mike tsaye ba tare da ya ce min komai ba ya nufi kofa, sai kuma ya juyo ya kalleni ido cikin ido. “Wallahi ina son ki Halima” Wani tausayinsa ne ya kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya. “Ba wai kaddarar mu ce kawai a haka ba, rayuwarmu ce, wata kila idan mu kai hakuri za mu iya cin ma nasara....” Shine abunda ya fada sannan ya fice daga dakin, ni kuma sai na nemi jindadi na rasa, taya zan kalleshi na fada masa cewar zan auri Ahmad? Ya zai ji? Ya zai kalli abun? Zuciyarsa zata iya dauka? Ashe da na ce zan rayu da kaunarsa ba zan iya ba? Kar idona ya rufe na sake aikata abunda be dace ba, da gaske Ahmad ya cancanci zama abokin rayuwata ko kuma wata kaddarar ce take bibiyata? Gaba daya sai na kasa ganewa, kamin na ankaro hawaye ya fara wanke min fuska.   Ban kwanta ba sai da nw labartawa Mama abunda Abdallah yake bukatar nai na aje aikin. “Kuma za ki aje?” “Mama kina tunanin akwai abunda Abdallah zai nema a gurina da ba zan masa ba?” “Halima karki yarda ki sake aikata wani kuskuren, wannan karon bana jin kaddarar ce sai dai son zuciya, domin komai a bayyana yake auren Abdallah a gareki ba zai yiyu ba, ni kaina ba zan bari ba, ba zan hana ki aje aiki ba amman kar alakar Abdallah ta shafi alakar da ke tsakaninki da Ahmad, kar kuma ki bari alakar da ke tsakaninki da Ahmad ta shiga tsakaninki da Abdallah” Shine abunda ta fada min sannan tai shirin kwanciya. Ni kuma na tashi na koma dakina na kwanta cikin yarana, ina ganin kiran Ahmad na shigowa wayata amman ba kasa dauka. Washe gari ko su Namra ba su riga ni fita daga gidan ba ba dan zan aje aiki kadai ba sai dan na gujewa shiga motarsa kamar yadda ya fada zai rika kai ni yana dauko ni kullum wanda hakan na san ba karamar matsala zai ja min ba, ko da takwas tai ina cikin office dina sai dai yau an kwashe komai kamar ba gurin da aka jera rose ba a jiya. Na zauna saman kujera ina ta tunanin yadda zan fada ma Ahmad cewar zan aje aiki na san dole zai tambaye dalili. Ina jin wayata ta yi ringing na dauko ya duba number shi cikin sauri nai picking. “Morning Lims” “Morning too” “Ga ni kofar gida fito muje” “Ina office” “Amman ba na fada miki ni zan rika kai ki ba?” “Akwai maganar da nake son nai da kai mai muhimmanci” “Okay Babe gani nan zuwa” Ya yanke kiran ni kuma na aje wayar ina ta kallon hoton yarana da ke screen din wayar. Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai ga shi ya turo kofar office din fuskarsa da annuri. “Karki sake min irin wannan game din seriously bana son kina hawa Napep” Uffan ban ce masa ba, duk kuwa da na san ba zan iya dauka ba taya za a ace kullum ya kawo ni aiki ya maida ni, ko da yake aje aikin ma zan yi na huta. Zaunawa yai a kujerar da ke fuskantar tawa yana kallon yanayina. “Akwai damuwa a tare da ke, fada min minene” “Ina son na aje aikina” Na fada kai tsaye sai yai min kallon rashin fahimta mamaki karara a fuskarsa. “As how...?” “I want to resign” “No i mean why?” Na yi shiru kamar ba zan amsa shi ba. “Saboda na ce zan rika kai ki kullum na dauko ki? Idan ba kya ra'ayi that's normal we can talk, kin san bana son bacin ran ki i won't force you” “Ba Saboda shi ba ne, Abdallah ya bukaci haka.....” Mikewa yai tsaye yana murmushin da zan iya kiransa da dariya. “That stupid guy ko?....” “He's not stupid, Abdallah yana da muhimmanci a rayuwata...” “How dare you.......!” Ban karasa ba ya daka min wata mahaukaciyar tsawa ya ture desktop din dake saman teburina ta fadi kasa har wani zaro ido yake kamar mai aljanu yana maida numfashi da karfi. Tsorata nai garin na mike tsaye kujerar da ke kai ta kade ni na fadi ni da ita, kamar yana jira sai ya zagayo inda nake ya risino kusa da ni ya nuna da yatsa. “Ba a maganar wani namijin a gabana matukar ina son mace, ina da kishi ki kiyaye wannan, bana lamuntar ki kira wani namijin da muhimanci a rayuwarki idan ba mahaifinki ko dan ki ba” Sai da ya fada min hakan sannan ya mike tsaye ya fice daga office din a fusace, nikam daman jira nake yana fita na tashi tsaye na dauke wayata da jakata na fito daga kamfanin gaba daya na dawo gida. Da daren ranar sai ga shi ya kira ni yana ta bani hakuri akan abunda yai min, na yi zaton ko zai yi magana akan aje aikin da nace zan yi ko kuma Abdallah amman be min ko daya ba sai da zamu yi sallama sannan yace min. “Ki yi ma Mama magana, ta fadawa wadanda ya kamata sai su saka mana rana da za su zo” “To” Shine abunda na ce sannan ya aje wayar, na fada mata kamar yadda ya bukata sai dai maganar yarana na kasa masa ita kuma abun ya tsaya min a rai.  Da aka fadawa kanen mahaifina sai suka nuna jindadinsu suka tambaye waye shi miye sana'ar shi a ina iyayensa suke duk na fadawa Mama ta fada musu, the following day suka saka musu rana assabar wato jibi kenan. Kamin ranar Ahmad ya zo shi da abokansa biyu suka gaishe da Mama da Inna suka kawo musu alheri mai yawa da kudi. Tun daga ranar a kowa wane karshen dare wato misalin hudu da rabi ko hudu na kan tashi nai alwala nai sallah nafila raka biyu raka ta farko zan karanta fatiha da kulya'ayu sau goma, a raka ta biyu kuma na karanta fatiha da kulhuwallahu sau goma sha daya, bayan na sallame sai na sake sujada na yi salati sau goma, nai Subhanallahi walhamdulillahi har zuwa karshe sau goma, sai rabbana attina fidduniya hasana wafil'ahherati har zuwa karshe sau goma sannan na fadawa Allah bukatata na auren Ahmad idan akwai alheri a cikin Allah ya tabbatar ya bani ikon amincewa kuma ya saka min natsuwa, idan kuma babu alherin Allah ya kawo min mafi alherin shi ma ya zaba masa wata. Haka na jera rana ku nan kullum sai na yi sallah nan na roki Allah. A iya tunani idan sun je za su gaishe da iyayene kawai wato kanen mahaifina da yayyensa, da kuma neman izinin zuwa fira kamar yadda ya fada min ashe ba haka ba ne. Da goma suka ce masu za su hadu misalin sha daya saura sai ga kiran kanen mahaifina ya shigo wayar Mama, be ce mata komai ba kawai yace ta ba ni wayar. Na karba na kara a kunne ina masa sallama sai ya amsa min yai na mika masa gaisuwa ita kan be karba min ba yace. “Ba ki fada mana idan sun zo za ayi daurin aure ba? Haka nan ake abu ba a fadawa sauran yan'uwa ba ba ayi komai ba? Gasu nan sun zo da mota kusan biyar da mutane da goron daurin aure da alawa da dabino” Kasa magana nai, sai na ji abun wani iri wai daurin aure haka nan kawai daga zuwa tambaya sai kace na fado daga sama, to me ni ma zan ce? Nace a a karya yake ban ce a daura auren ba? Ko kuma na ce ban amince da hakan ba? Ban gama tunanin abunda zan fada ba na ji muryarsa yana fadin. “Ke nake saurare Halimatu” “Baba duk yadda kuka yi daidai ne” “A a ke muke saurare, ke kika turo shi ai idan kin amince sai a daura ni ba mu da matsala idan kuma ba ki amince ba sai ya nemi sasanci a gurinki” Gaba daya sai na zama kamar wata kurma, na kasa cewa na amince ko kuma a a ban amince ba, zuciyata tai wani irin nauyi kamar wacce bata tana aure ba. “Na amince Baba” Na fada hawaye na sauko min ina numfashi daker. “To Ma-sha-Allah, Allah yasa alheri sadakin fa nawa za a yanka masa?” “Baba duk yadda kikai daidai ne” “To Allah yai miki albarka” “Amin....” Na amsa ina fashewa da kuka, ji nake kamar ban taba auren ba gaba daya abun ya zame min bakon al'amari, da gaske kuka nake sosai kamar wata karamar yarinyar da akai wa auren dole, Mama tai yi ta tambayar dalilin kukan nawa na kasa fada mata saboda kukan da nake ji nake zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito waje, idan aka tambaye ni dalilin kukana ba zan iya fada ba domin nima ban san abunda ya saka ni kukan ba. Abu kamar wasa bayan minti talatin Kanen mahaifina ya kira ya fadawa Mama cewar an daura aure ne, ijiyar auren Ahmad uku ta hau kaina, a lokacin ne kuka yace dazun ban ci komai ba yanzu zan yi shi, kowa ya cika da tsananin mamaki a gidan sai dai dukansu suna murna sanin cewar alheri ne wannan karon yai musu bazata ba sheri ba, duk wanda ya tambayi mi nake yi ma kuka sai na ce ban sani ba domin har ga Allah ni kaina bansan dalilin hawayen ba. Bayan kamar awa daya kanen mahaifina suka kawo goro da alawa da dabinon dauren aure sannan ya ciro dakina a aljihunsa ya rika hannuna ya danka min. “Ga sadakin nan Halimatu, mun ce su bada 30k sai suka ce one million za su biya, babu yadda ba mu yi ba akan su rage amman suka ki, ina addu'a wannan aure yasa ya sanya nasa albarka ya saka alheri yasa gidan zamanki ne” Da gaske miliyan daya nake gani a matsayin sadakina, ni Halimatu abunda ban tana gani ba ban kuma tana ji ba an biya sadakin bazawara har haka kuma bazawarar ma mai aure biyu da yaya hudu. Dana karba sai na bawa Mama na ce ta aje min, ita kuma ta kulla goron da alawa da dabino ta bada aka kai makota wai a fada musu an daura auren Halimatu yau.   A lokacin da su Namra suka dawo daga islamiya sai ta dame ni da tambaya. “Momy aure kika yi?” Na gyada mata kai. “Momy da wa? Da wa? Da wa?” Sai na kasa masa nata ita kuma ta kasa daina tambaya har sai da Aisha ta daka mata tsawa. “Haba Namra wannan tambaya haka?” “Momy Daddy kika aura?” Na girgiza mata kai alamar a'a sai ta fashe da kuka sosai. “Momy tafiya za ki sake yi?” A gurin ta fadi da uniform dinta na islamiya tana ta kuka. Babu wanda ya rarrashe ta sai Hafiza ita ta fada mata wanda na aura kuma ta fada mata wannan karon ba zan tafi na bar su ba ne tare za mu tafi.   Har akai sallah la'asar ban daina ganin kamar mafarki nake ba, kuma ban daina hawayen ba, ina zaune saman carpet din dana kare sallah ina yi ma Allah godiya kuma ina kara rokon ya tabbatar da alheri a tsakaninmu, sai ga kiran Abdallah ya shigo, rawa jikina ya fara yi na fara kallon wayar kamar na ga wani dodo, na kasa daukar kiran har ya katse, lokaci daya na fashe da kuka marar sauti, na san duk inda yake a yanzu ya samu labarin daurin aurena wanda hakan ba zai masa dadi ba.   Bayan sallah magariba aka daf da sallah isha'i wani gurin ma har an fara yaron ya doko sallama ya shigo gidanmu da manyan ledodi. “Wai gashi in ji Ahmad kuma yace yana sallama da Halima a waje” Wani irin faduwa gabana yai sai naji kamar ban taba arba da shi ba, kamar wani bako na ji shi, har nai kamar ba zan je ba sai dai yadda Mama ta matsa min yasa dole na zari Hijab dina na saka na nufi kofar fita jikina ba kwari gabana sai faduwa yake. Can nesa da gidanmu na hango motarsa a fake sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na doshi gurin, kamin na karasa na ji an rumgume ni ta baya ya dora kansa saman wuyana. “Al-hamdulillah...... Lims you're finally mine....” “Mutane za su iya ganinmu” Na fada ina hango daidaikun mutanen da ke can nesa da mu suna sha'aninsu wasu kuma na alwala. Sai ya sake ni ya juyo da ni yai kissing goshina kana ya hade goshinsa da nawa yana goga min hancinsa a hankali sai kallon cikin idona yake. “Why are you crying?” Ban ma san da hawayen sun zubo min ba sai da yai maganar, shiru nai ban amsa shi ba. “Lims do you love me....?” “Ban sani ba...” Na fada da iyakar gaskiyata, wasu hawayen na sauko min, halshensa na ji a saman kunci na yana lasar hawayena. “Wannan hawayen mai sanyi ne, ni na san kina so na Lims....” Ya fada bakinsa na taba nawa murya can kasa kasa kamar mai rada, saurin lumshe idona nai muna ta shakar numashin juna.... ___________________ Ayi hakuri two days mun yi biki shiyasa ban samu damar typing ba 🙏 Gashi nan na yi muku 5k words na biya bashi 🏃🏻🏃🏻🏃🏻 *Where are are the classy ladies 🤔 mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼 da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lambobin 09137294470 08034236800* 7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣8️⃣ Raba jikina nai da nasa. “Mutane za su iya ganinmu” Be ce min komai ba yaja hannuna ya karasa gurin motar da ni ya bude gidan baya na shiga sannan shima ya zagayo ya shigo ya rufe sannan ya rika hannayena ya soma murzawa yana kallon fuskata. “Ban miyasa nake jin ki a zuciyata fiye da kima ba, ina jin cewar na fi kowa dace a duniyar nan, a yanzu bani da wani buri sai na aurenki kuma ya cika ina son sosai, irin son da bana jin wani namiji ya taba miki shi, bana tunanin akwai namijin da ya fi ni son ki” Ya sumbanci hannun nawa. “Kamin na aureki, idan wani ya fada min zan aureki zan karyata shi kuma na fusata, amman a yau da Yayan mahaifin yai min albishir da cewar an daura aurena da ke sai na rasa inda zan saka kaina dan murna, na rasa abunda zan bashi na kyautata masa na goron abunda ya fada min, na gode da kika amince min na gode da kika ba ni damar shiga rayuwarki, na gode da kika karbe ni a duniyarki” Ya karasa tare da kai hannunsa yana shafa fuskata, sai kuma ya jani jikinsa ya kwantar da ni ya rumgume ni sosai kamar ba gobe. “I love you so much Lims” Ya fada calmly kissing my forehead, dayan hannunsa kuma yana mutsa yan yatsun hannuna. Mu kai shiru kamar babu mu a cikin motar baka jin komai sai saukar numfashinmu, can ya saka hannunsa ya dago kaina ya dora bakinsa a saman nawa kamar zai tsosa sai kuma ya bar shi a haka yana ta kallon idona da na rufe, ji nai an busa min iska a saman idon hakan yasa na bude muna hada ido sai ya hade bakinsa da nawa, a hankali yake kissing din lisp dina sai kuma ya cire bakinsa a nawa ya kai gurin tsinin hancina ya tsosa sannan yai kissing forehead dina ya sake rumgume ni a kirjinsa tsantsa yana sauke ajiyar zuciya. “What else i can say more than Al-hamdulillah, you're finally mine” Muna haka na hango mota ta faka a kofar gidanmu, ina ganin motar na san cewa Abdallah ne, Ahmad kam be gane shi ba har sai da ya fito daga cikin motar ya jingina yana lasa. Wayar da ke hannuna tai ringing kiransa ya shigo, kallon wayar nai na kalli Ahmad sai na kasa daga kiran. “Me ya zo yi?” “Wata kila yana son magana da ni ne” Bude motar yai yace min na fito muje, abunda ban so ba ke nan domin nasan ganin mu a tare da Ahmad ba karamin bata ran Abdallah zai yi ba, ba zan iya musa ma Ahmad ba kamar yadda ba zan so Ahmad yai abunda zai kara batawa Abdallah rai ba. Ya rufe motar sannan ya rika hannuna muka nufi gurin da Abdallah yake tsaye, daga inda yake tsayen ya dago idonsa yana kallon mu har muka iso, na kasa ce masa komai shi ma be ce min ba Ahmad ma be masa magana ba, sai kallon juna suke kana ganinsu kasan da akwai abunda kowa ya aje kasan zuciyarsa, Ahmad murmushi yake yana ta lilo da hannuna duk yadda na so na kwace hannun sai ya ki saki, na yi tunanin Abdallah zai yi wani abun ne ko kuma ya fada masa bakar magana amman ga mamakina sai ya sakar wa Ahmad murmushi ya mika masa hannunsa. “Congratulations, that's good daman ka ce zaka nuna min ko waye kai a gurin Halimatu ko? Na gani yanzu ina taya ka murna” Sai da Ahmad ya kalli hannunsa nasa sannan shima ya mika masa nasa. “Thank you” A lokacin ne Abdallah ya kalleni da murmushin a fuskarsa yace min. “Ina taya ki murna” Ni kam kasa amsawa nai sai Ahmad ne ya sake ce masa “mun gode” Sai ya bude motarsa ya shiga yai ribas ya juya ya bar mu a gurin tsaye ina bin motarsa da kallo. “Kun taba yin wata magana ne da shi?” “Eh lokacin da mahaifiyarsa ta saka aka kamaki ba, yace min wai ni waye ne a gurinki da har zan nuna masa isa, sai na ce masa zan nuna masa ko ni wanenen nan da dan lokaci” Na yi shiru bance komai ba, hakan yana nufin shi da Abdallah sun yi sa'insa kenan, wata kila shiya saka Abdallah ya nemi na bar aikin a kamfanin dan ya nuna masa ya isa da ni. Ji nai ya saki hannuna ya juyo gabana yana kallona. “Bari na barki ki huta, ki yi list din duk abunda kike so kin san yanzu hakkinki da na yaranki yana kaina, da safe zan zo na karba” Ya fada sannan ya shafa fuskata, har ya juya sai kuma ya juyo. “Ba ni line wayarki” “Why....” “Just” Ban musa masa ba na ciro line ya mika masa. “Amman akwai numbers din yan'uwa da kawaye na a ciki” “Okay idan na dawo gobe zan zo da sabon line sai ki dauki numbers din a ciki” Kai na gyada masa sai ya juya can kuma ya sake juyowa a karo na biyu yai min alama da na zo, sai na karasa kusa da shi kamar yadda ya bukata, saitin kunnena ya kai bakinsa ya rada min “Muje ki min sallama” Ko be fada kai tsaye ba na san abunda yake nufi maybe he want to kiss me or hug, ko something like that, ni kuma bana son mutane su fara saka mana ido ace mun fara yin abunda be dace ba a bainar jama'a. “Akwai mutane fa” “To muje zauren gidanku” “Nan ma za a iya saka mana ido, ka bari har ka dawo” “Ba zan bari ba....” Ya fada yana wuce ni ya nufi cikin zauren gidan a dole na bishi a baya, ko da na shiga har ya jingina da bangon gurin yana jiran shigowata, hannunsa ya kai ya kama kwankwaso na ya rike ya hade fuskarsa da tawa. “So this woman here is mine” Ya fada da sigar da babu wanda zai ji sai ni, ni dai hankali yana kan kofar gida kar wani ya fito daga cikin gida ya gan mu. Bakinsa ya saka cikin nawa ya tsosa iya yadda yake jin ya samu natsuwa sannan ya sake ni, kamar an masa shocking haka ya zabura da karfi ya bankare sai kuma ya runtse ido, kamin ya bude su a hankali ya kalleni. “Good night Sweetheart” Ya fada yana kissing kumatuna sannan ya juya ya fita daga zauren, hakan kawai na samu kaina da son kallonsa, haka n leko a zaune ina ta kallonsa har ya karasa gurin motarsa ya bude ya shiga yai mata key ya fice. Wata irin natsuwa da sakewar zuciyata da nishadi ne suka ziyarce, rumgumar da yai min sai na ji kamar mu kasance a haka har a bada, gaba daya jikina kamshin turarensa yake murmushi ya maye gurbin hawayen da nake, ina jin a raina kamar na yi dace duk da ban tabbatar din ba, sai a yanzu nake jin wata irin natsuwa da farincikin amincewa da nai, wata kila dazun ba kukan bakinciki nake ba, kukan farinciki nake ban gane ba, da kuma yadda abun ya zo min a bazata. “I love you so much Lims” Na yi murmushi ina jindadin tuna kalmar daya fada min a dazun, har yanzu bana jin ina son sa kamar yadda bana jin tsanarsa ko kasan a raina, amman am happy I'm now officially Mrs hakan ma wata martaba ce babba, na juyo na nufo cikin gida, sai da na gama sallah isha'i sannan na bude ledodin da ya kawo min, kaza ce babba har guda biyu da lemu sai kayan tea da katon burodi da kuma ku a cikin farar takarda 20k. Washe garin ranar na tashi cikin walwala ba laifi ina ta jin nishadi a raina, bayan su Namra sun tafi Islamiya sai ga Aminu ya sallamo ya shigo cikin gidan, kamin ya karaso falon Mama nai saurin dauko Hijabinta na saka ya rufe jikina sannan na dawo falon na zauna. Ya shigo da sallama na amsa masa ina murmushi kamar ba ni ba. Shi ma murmushin ne kwance a fuskarsa sai dai ba irin murmushin nan na jindadi ba irin murmushin nan mai kamar na dole. “Ina kwana” “Lfy kalau” Ya amsa yana ta kallona kamar be taba ganina ba, a raina na raya cewar da ace Ahmad nan Aminu yake min kallon nan da yanzu wani abun ya faru, ban san lokacin da wani murmushin ya subuce min ba har sai da na ji Aminu na tambayar. “Me kike yi wa murmushi?” “Ba komai” “Na ga alamar dai kina cikin farinciki” Na yi kasa da kaina ban ce masa komai ba. “Daman na zo ne na taya murna, na ji abunda ya faru ance kin yi aure jiya, shine nace abun babu gayyata” “Nima abun ya zo min bazata ne shiyasa” “To congratulations Allah yasa alheri Allah yasa wanda zai rike ki amana ne” Yanayin yadda maganar ta fito daga bakinsa kana ji kasan ba dadi ya fade ta ba. Ni dai na amsa da Amin. “Nima na zo na fada miki ne zan maida Murja” Kallon Mamaki nai masa. “Murja da wacce ta ci amanarka?” “To ya za'ayi? Nima ba amanar wasu na ci ba? Kin mutum mai irin matsala ba ko wace mace yake aure ba, kuma idan nace zan nemi mace mai irin ciwona na aura, ban fallasa sirrina ne kawai, kara dai mu rufawa juna asiri ni da ita mu yi zama na tsakani da Allah” “Allah yasa hakan shi ya fi alheri” Na fada cike da tausayawa. “Amin ina fatar dai yarana ba su san da maganar nan ba” “Ban fada musu ba, kuma ba zan taba fada musu ba In-Sha-Allah” “Na gode” Ya ciro kudin da za su kai 30k ya miko min. “Ga wannan kwai siye wani abu” “A a muna da komai” “Haba dai hakkina ne ai” Na kai hannuna na karba sai ya sakar min murmushi. “Ina taya wanda ya aureki murna, hakika ya samu mata mai kawaici, mai hakuri, kuma kyakkyawa” A yau Aminu da kansa ne yake fadar ina da kawaice abunda be taba fada ba a lokacin da nake gidansa, a yau shi da kansa yake kina da kyakkyawa kyau da ya kasa gani a lokacin da nake kusa da shi. “Ina fatar mutumen da kika aura zai rike miki yaranki” “Ka yafe mushi su ne?” “A irin wannan condition din dole nai nesa nesa da su, kuma kin san masu irin matsalar mu musamman maza ba wani dadewa suke a duniya ba, bana son na mutu na barki da dawainiya, ina son ko da zan mutu at least ace kina samun wanda zai taimaka miki wajen kula da su, maybe ma su ne kadai yayan da Allah zai ba ni a duniya i don't know” Ya karasa hawaye na cika idonsa. “Cuta ba mutuwa ba ce Aminu...” “Tawa ta mutuwa ce Halima, kawai dai ki yi ta saka musu albarka” Ya mike tsaye. “I wish you all the best” “Na gode” Murmushi yai min as respond sannan ya saka kai ya fice, ni kuma na tashi na nufi dakina na saka kudin a cikin jakata, sannan na fito na fara gyare gyare dakina da dakin Mama daman Aisha ta share dakin Inna. Da azahar aminiyata Hajara ta shigo gidanmu da murnarta kamar zata cinye ni, wai ita babu abunda yai mata dadi kamar yadda Ahmad yafi dukan mazanjen da na aura rufin asiri, domin da ce wani makaskanci na aura da yanzu makiya sun saka min dariya amman duk wanda yaji ga wanda na aura sai yace hakurin da nai ne Allah yai min wannan sakamakon, ni kan har ta ci ta shude ban ji komai araina ba wai dan Ahmad yana da arziki, wata kila saboda dukiyar tasa bata gabana ne, ni yi mamakin inda ta ji domin ban fada mata ba gashi line ma yana hannun Ahmad balle nace ko kiranta nai, ashe abun har ya fita da goron da aka raba a makota da kuma can family mu wannan ya fada wancan jin babban mutum ne nn da nan maganar ta yadu ita ma gurin wata kawarta tace wacce ita kuma yar'uwarmu ce. Sai yamma ta tafi gida, bayan Abban Afrah ya zo daukarta da kansa har da shi yake min murna wai ya ji na yi aure Allah ya sa alheri, a wunin ranar na damu matuka da ban ji daga Ahmad ba, duk be wani saba min sosai da kira ba amman a yanzu ai ni matarsa ce ya kamata ace ya kira ya ji tashina, ko da yake line yana can hannunsa kuma ban san uzurinsa ba. Can da la'asar sai ga Siyama ta shigo gidanmu, sai da ta gaisa da kowa sannan ta bukaci ganina aka fada mata ina dakin Inna, ina zaune a dakin ta shigo sanye da atamfa mayafinta a hannunta tare da jakarta, da sauri ta zo ta rumgume ni. “Matar Yaya” Na yi dariya ina dan jin kunyarta sai ta zauna kusa da ni muka gaisa cikin far'a. “Hajiya tace tana gaishe ki” “Ina amsawa” “Yaya yace ya zo na karbi takardar idan kin rubuta” Sam ni na ma manta da zancen wani rubuta abubuwan da muke bukata sai a yanzu. “Wallahi ban rubuta na manta” “Ayyah za ki iya rubutawa a yanzu?” “Ko kuma mu bari har gobe ko jini saboda ko na rubuta wani abun zan iya mantawa da wani a yanzu” “Okay to ba matsala” Ta saka hannunta a jaka ta dauko sabon line ta miko min. “Ga line yace ki saka zai kira ki” “Okay lafiya yake” Na tambaya bayan na karba. “Lafiya kalau” Sai ta mike tsaye “Ni zan tafi in-law Allah ya baki ikon rike min brother na da gaskiya, because yayana yana son ki sosai, Hajiya da ni duka muna son ki Allah yasa kar ki ba mu kunya” “Allah ya bani ikon kula da ku duka” Na fada ina murmushi sai ta amsa da amin ta fice rike da makullin motarta. Ban tashi daga inda nake ba na kira Aiman ya dauko min wayata na saka line ciki, ina kunnawa kiransa na shigowata sai nai picking na kara a kunne tare da sallama. “Tun dazun nake ta kiran line ne ina son ki saka na ji muryarki, ya kike?” “Ina lafiya, Siyama ta kawo min shi yanzu nan” “Na sani kin bata list din” Yanayin yadda yake amsa min kamar a wahale, ni kuma na amsa masa cikin sanyi jikina. “Aa na manta ban rubuta ba sai gobe” “Ba ki da matsala Queen, za mu yi waya anjima” Daga haka ya kashe wayar. ABDALLAH POV. Har a yanzu bana ganin laifin Halima a iya abunda yake gani Ahmad kamar ya mata cilas ne tun da gashi abun daga sama suka ji daurin auren. Zai iya rasa komai ya hakura ban da Halima, in his own life ya san Halima ba son Ahmad take ba, kuma yana ganin Ahmad kamar ba zai iya rike Halima da gaskiya. Duk kuwa da irin kirarin da mahaifiyarsa take na cewar wai daman can Halima haka take so ta bata alakar da ke tsakaninsa da dan'uwansa yanzu kuma ta hana dan'uwansa aure kuma ita ta yi aurenta, a yanzu babu abunda Hajiya bata sani ba na abunda Abdulhamid ya aikata da alakarsu da Ahmad amman saboda bakar kiyayay ta kasa daina ganin laifin Halima, a ganinta ai saboda ita asirin Abdulhamid din ya tonu gashi ta kassarasa masa rayuwa ita ta gyara nata. Abdulhamid ma da Hajiya ta kai masa labarin auren Halima kam yayi farinciki da ba Abdallah da aura ba duk kuwa da ya san Hajiya ba zata bari ba amman auren Abdallah zai fi komai tsaya masa a rai idan har ace haka din ta kasance. Babu abunda yafi yi ma Hajiya ciwo kamar sanin cewa mutunen da Halima ta aura a yanzu yafi yayanta rufi asiri, babu abunda take fata take kuma son ganin kamar lalacewar auren ko kuma Halima ta shiga wani hali. A ranar da za a fara shiga kotu da Abdulhamid da Abraham da wasu mutane hudu babu irin kukan da Hajiya ba tai ba sai ta ji kamar ta hade zuciyata ta mutu dan bakinciki. AHMAD POV. A ranar da ya bar gidansu Halima be iya kai kansa gida ba, saboda wani irin azababben ciwo da ya rika jin yana masa yawo a jiki, a dole ya faka motarsa gefen titi ya kira driver din gidansi yace ya zo ya tuka shi. Da suka isa gida sai ya wuce part dinsa ya kwanta yana ta jin abun na masa yawo a cikin jiki sai dai hannunsa ya fi ko'ina yi masa zafi domin yai masa nauyi kuma ya masa kamar an dora shi akan garwashin wuta. Duk yadda yake da juriya da iya dakewa a daren kasa hakuri yai idan yai tsaye ya zauna ya tashi haka yai ta yi har garin Allah ya waye. Da asuba ma kasa sallah asuba yai saboda bala'in ciwon da hannun yake masa, gumi sai ke to masa yake ta ko'ina kamar wanda maciji ya tsara, kamin haske ya dan shigo Hajiya ta shigo part dinsa ganin shi be fito ba har jin yai kamar ba zai rayu ba. Tana ganin halin da danta yake hankalinta yai mugun tashi da taimakon mutanen gidan suka saka shi mota aka nufi asibiti da shi, wani abun mamaki da aka yi kwaje kwaje aka duba hannu ba a same shi da komai ba, amman Ahmad azabar ciwo yake masa sosai idan ya samu sauki sai idan an masa allurar kashe ciwo sannan zai ji abun ya kwanta masa amman ko allurar bachi aka masa baya jin sauki domin ciwon baya bashirin bachi. Sai dai likitocin sun fada masa yawan yi masa allurar matsala tun da ba aiki za ayi masa ba, hakan yasa shi da kansa ya shirya fita waje ganin likita, ko da wasa be fadawa Hajiya cewar tun daga lokacin daya gaisa da Abdallah abun ya sameshi ba domin baya son tai blamed Lims dinsa, secondly kuma ya hana kowa ya fadawa Halima halin da yake ciki saboda kar hankalinta ya tashe kuma kar canfin da take na cewar duk wanda ya kusance ta sai wani abu ya same shi ya tabbata, yana son ganinta amman ba dama sai dai ya kirata a waya, ko video call be son yi da ita saboda kar ta fahimci halin da yake ciki. HALIMATU POV. Wasawasa aka kwashe kwana takwas ban saka Ahmad a ido ba hakan kuma ba karamin damuwata yai ba, domin sai na ji kamar na saba da shi a kullum ne, zai kira ni a waya da safe da rana haka ma da dare amman hakan be wadatar ta da ni ba. Ya aiko an karbi list din duk abunda na rubuta an siyo har ma da wanda ban rubuta ba duk an siyo kuma ba kadan ba da yawa aka siyo wanda zai dauke mu tsawon lokaci muma amfani da shi. A iya sanina yadda Ahmad yake nuna min kauna kamar ba zai iya kwana biyu be saka ni a ido ba balle kuma yanzu da nake matarsa, amman miyasa ya dauke min kafa tun daga wacan ranar? Ko dai shi ma mahaifiyarsa bata so? Ko kuma wani abun ne? Ina tsaka da tunanin nan wayata tai ringing ganin kiransa ne yasa nai hanzarin dauka. “Hey Babe na ykk” “Ina lafiya” “How are my kids?” “Suna lafiya” “Na kira na ji muryarki, kuma na miki albishir cewar Kabir yana ta samun sauki ana tunanin end of this month ma su sallame shi, domin an masa tiyata an kwashe jinin daya taba kwakwalwarsa yanzu sun dora shi akan magani ne” “Ma-sha-Allah Allah ya saka da alheri” Na fada cikin rashin far'a kamar ba labarin nake son ji ba, ban san abunda ya hana ni jindadi ko murnar samun lafiyar Kabir ba bayan kuma na dade ina fatar samun haka. “And... I think gobe ko jibi zan je United Kingdom wato London for some works” Na y shiru ban ce komai ba, domin ban san abunda zan ce ba gaba daya jikina sai ya ba ni kamar ba lafiya ba. “Idan akwai abunda kike bukata ki fada min” “Kai nake bukatar gani Ahmad i need to see you” Daga can cikin wayar ya jiyo sautin murmushinsa mai kama da dariya. “Wow i got lucky Matata tana so na da yawa haka nan, idan na dawo zan zo In-Sha-Allah” “Ba zaka zo mu yi sallama ba?” “Ba zai yiyu ba ne yanzu haka ina Abuja, daga can zan wuce i'm ban fada miki ba, but karki damu next time tare za mu tafi In-Sha-Allah” Jin na yi shiru yasa shi cewa. “Kin ji Baby na? Are you there” “Allah ya tsare” “Amin i love you” Na aje wayar ina ta kallon screen din, idan har da gaske wani aikin ne zai kai shi da sai yaje da ni, ko dai shi ma mahaifiyarsa ta masa katanga da ni ne? Ko ba da amincewarta ya aure ni ba? Tun da akai auren ba ban taba gaisawa da ita ba, ni kam dai ina rashin dace da in-laws, but wait miyasa zan zargi mahaifiyarsa? What if ba shi da lafiya? Domin a duk lokacin da nake waya da shi ina jin muryarsa ba a yadda na saba jinta ba. A take gabana ya fadi hankalina yai mugun tashin da sauri na dauki wayar na aika masa da kira amman haka tai ringing har ta katse be dauka ba..... __________________ Ina yan Team Kabir kun ji ya fara jin sauki 💃 Jiya wata yar Team din Abdallah tana ta min rankwashi a kai 😢😪 To ai ba san maci tuwo ba sai miya ta kare 😥🙄 *Where are are the classy ladies 🤔 mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼 da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lqmbobin 09137294470 08034236800* 7/21/21, 11:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 5️⃣9️⃣ Kwance take a dakinta tana kallon windows din dakinta da suke bude, pillow na rumgume a kirjinta babu abunda ke fita daga idonta sai hawaye masu zafi.   Mai aikinsu ce Hindatu ta turo kofar dakin ta shigo da sallama. “Assalamu Alaikum, Siyama Hajiya na nemanki” “Ki ce zan zo” Ta amsa ta ba tare da ta juyo ta kalleta ba. After like one hour Hajiya ta turo kofar dakin ta shigo. “Siyama....” Sai a lokacin ta fara kokarin yin kamar bachi take, hakan yasa Hajiya ta karasa kusa da gadon ta zauna leken fuskarta da hawaye ya gama yi mata kwalliya. “Miye abun kuka kuma? Me yake damunki?” Juyowa tai da kyau ta kalli Hajiya wasu hawayen na cika mata ido. “Hajiya...” Sai kuma tai shiru ta tashi zaune tana matsar yatsun hannunta. “Ba ki fito kin ci abinci ba, ko yau ba kya zuwa makarantar ne?” “Hajiya bana son na sake rasa kowa” Ta fada cikin hawaye. “To wa za ku rasa?” “Ban sani ba, amman yanzu idan ciwo ya kama wani a cikinmu sai na rika ganin kamar zan rasa shi ne, i don't want to be alone....” Ta fashe da kuka, tana kwantawa jikin Hajiya. “Babu abunda zai samu yayanki zai samu sauki In-Sha-Allah, ki daina tada hankalinki kin ga nima kina daga min nawa, da kuzari da karfin zuciya da nake da shi sai ki sa ya karye” “Hajiya ina jin tsoro” “Ki daina kawai ki yi masa addu'a, ki tashi ki wanke bakinki ki fito ki yi breakfast” Ta gyada kai tana share hawayenta Hajiya ma ta yi saurin tashi tana tare hawayen da ke son zubo mata, cikin rashin kuzari ta fita daga dakin ba Siyama kadai ba ita kanta abun ya bata tsoro jin cewar ba a ga komai ba kuma gashi yace yana jin ciwo, tun daga lokacin da ciwon ya same shi baya iya komai daga zaune sai tsaye sai kwance wani lokacin kuma ya kan dan zagaya cikin asibitin amman fa sai idan am masa allurar kashe ciwo, ga shi baya wani iya cin abu mai nauyi daga lemu sai ruwa sai tea shi ma can ba a rasa ba, sai dai tana addu'a kuma tana fatar idan an je check up din nan a gano matsalarsa. A dinning din take zaune amman ta kasa taba komai balle ta ci kamar ba ita ta dafa abun karyawar ba, yadda yake fito daga part dinsa ya zo part dinta su karya ko kuma idan ba shi da lokaci sai ya dauki breakfast din ya tafi da shi ko mug ne abunda yafi tsaya mata a rai, yau kusan 7 days yana asibiti mutumen da bata bari yai nisa da ita, and the most saddest part is aurensa aka daura yana cikin farinciki wannan abun ya same shi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta dora hannayenta saman dinning din ta dafe kanta kamin ta kike tsaye ta nufi upstairs dan jin tai bata bukatar cin komai. HALIMATU POV. Ba karamin tsoro ne ya kama ni ba, na san ban tana kiran Ahmad ba tun da nake a rayuwata, amman mi zai saka yanzu na kira shi yaki dagawa? Amman ya kamata nai masa uzuri, after like seven minutes a sake gwadawa still be daga ba na sake gwadawa be daga ba haka nai ta yi har kusan 20 miss calls amman be yi picking ba, a lokacin ne fargabana ya karu tsoro ya auri zuciyata na fara sake sake kala kala, ji nai bana da natsuwa kwata kwata a rayuwata jikina ya bani cewar akwai abunda Ahmad yake boye min. Tashin nai na shiga dakina na canja tufafin jikina na saka wata rigar yadi na dauki medium veil na yafa na saka talkamina na dauki yar purse dita cikin dabara na fice na bar gidan domin na san idan nace zan fadawa Mama zata iya cewa ba zan fita ba tare da izinin mijina ba, tun da ba fada mata zan yi gurinsa zan je ba, ina tafe ina waige waige kar wani dan gidan mu ya gan ni kamar wata marar gaskiya, Allah ko ya bani sa'a har na tari napep na hau ban hadu da kowa ba, zuciyata bata raya min na je ko'ina ba sai gidansu Ahmad, duk kuwa na san hakan be dace ba amman ba ni da wata mafita wacce ta fi wannan ko dan samun natsuwar zuciya dole naje na ga halin da yake ciki, tun da yanzu yamma ta yi ba na san baya kamfaninsa.   Sai da mai napep din ya kai ni har kofar gidan na sallame shi sannan nai knocked din gate din gidan cikin sa'a kuwa mai gadin ya bude min, sai da muka gaisa da shi sannan na tambaye shi ko masu gidan suna ciki, ya amsa min da suna ciki har ma da bude min kofar, sai da na doshi harabar gidan sannan na soma tambayar kaina to idan na shiga ciki me zan fada musu? Idan ma mahaifiyarsa ce tai masa katanga da ni fa? Kuma gashi na shigo har cikin gidan anya shi ma kansa zai jidadi? No wait idan ma babu duk wannan anya ban yi rashin kunya ba na tukari idansu kai tsaye? A take duk na ji wani iri hakan yasa ban karasa ba na juyo na dawo gurin mai gadin. “Dan Allah Malam ko zaka shiga ciki kace ana sallama da Ahmad?” “Wai Alhaji... Alhaji ai.... ” Sai kuma yai shiru ya kalleni. “To bari a fada musu” Ya nufi cikin gidan ni kuma na bude gate din daker saboda shegen nauyinsa na fita daga waje na tsaya, kamin ya fito har na matsu bugun zuciyata ya karu ga tsoro ga fargaba da tunanin rashin dacewar zuwana sai suka taru suka tsaya min a rai. A tsammanina Ahmad din zai fito ko mai gadin amman ga mamakina sai kanwarsa ta fito waton Siyama, tana ganina ta saki far'a ta karaso ta rike hannuna. “Laaaaa In-law shine kika tsaya a waje" Nima nai mata murmushin daya kasa boye damuwata cike da kunya na ce. “Bana son shiga ciki ne” Sai taja hannuna tana fadin. “Dan Allah shigo ciki magana, sai ku gaisa da Hajiya” “A a dan Allah ki bari, ba sai na shiga ciki ba amman Ahmad na zo....” Sai kuma kunya tasa na kasa karasawa, sai tai murmushi. “Ai baya nan ya tafi jos.....” Da sauri na kalleta domin ni ba jos yace min ba. “Jos kuma?” “Amman ba can yace min ya tafi ba” Wani abu tai da ido tana yar dariya kamar marar gaskiya. “Eh na tuna daga jos zai wuce can garin da yace miki zai tafi...” “Wane gari?” Na sake tambaya ina ta kokarin gano gaskiyarta, sai ta fara kame kame wanda hakan yasa hankalina ya kara tashi. “Can inda yace miki, Kadu.... Na....” “Ni Abuja yace min” “Eh eh daga Jos din zai je Kaduna da Abuja, daman Abujar ya kamata nace tun dazun sai na fadi wani gari” Ta karasa tana murmushin rashin gaskiya. Hannayenta na kama biyu na rike cikin wata irin siga ta magiya na shiga rokonta. “Dan Siyama idan akwai wata matsala ki fada min” A iya abunda zuciyata ta raya min Ahmad na cikin gidan yace ace baya nan, hakan na nufin Hajiyarsa ta hana shi ganina kenan ko kuma wata matsalar ce ta dabam daga sashenta. Sakin hannayen nawa tai tace. “Ina zuwa” Juyawa tai ta koma cikin gidan, ni kuma na tsaya a gurin zuciyata kamar zata fito, hawaye sai wanke min fuska yake ina sharewa, a yanzu kam idan har ta tabbata Hajiyarsa ta shiga tsakanina da Ahmad ban san ya zan yi ba, wata kila akwai matar da take son ya aura ba ni ba shi kuma ya aure ni ba d amincewarta ba, indan sabon da tsanar uwar miji na saba sai dai bana jin cewar zan iya jure wannan idan har ya tabbata abunda nake zargi ne.   “In-law Hajiya tace ki shigo” Dagowa nai na kalleta idona da hawaye na girgiza mata kai. “A a zan tafi dai, ki ce ina gaishe da Ahmad din” “Ba zata jidadi ba idan kika tafi ba ki shigo ba, bayan kuma ita da kanta ta bukaci haka” “Ina tsoro kuma ina jin kunya” “Akwai maganar da Hajiya take son fada miki dan Allah ki shigo ko kuma naje na kirata” Na yi saurin dakatarta ita. “A a dan Allah” “To muje” A dole na bita a baya bayan na share hawayena, babu abunda zuciyata take raya min sai irin cin mutuncin da Hajiya zata min ko kuma gargadi, a lokacin ne naji ina ma ace ban zo ba, kamar wata marar gaskiya haka na shiga falon sai na tsaya daga bakin kofar na zauna jikin wata karanar kujera mai kamar ta kwalliya dake jikin kofar, ita kuma Siyama ta nufi dakin Hajiyar, ni kam gabana sai faduwa yake har yawun bakina daker nake hade su, ina jin motsin saukowar Hajiyar gabana ya kara faduwa. “Ahhhh Haba dai Siyama ya zaki barta a bakin kofa? Yanzu idan Yayan ki yana nan Wallahi kin san sai yace mun wulakanta masa mata” “A a Hajiya ita ta zauna a can daker ma fa ta shigo cikin falon nan” Siyamar ta fada tana rigan Hajiya zaunawa. Hakan yasa na dan dago kadan na kalli Hajiya tare da mika mata gaisuwa sai ta amsa min da murmushi. “Lafiya kalau taso dawo nan Yata” Ta fada tana taba kujerar da take zaune wacce ta zaman mutum uku ce, ban iya musa mata ba na tashi na koma a inda ta bukata wato kusa da ita na zauna a kasa wata irin kunya na kara rufe ni, ai kam da kunya ace na so neman miji har gidansu!   “Kawo mata abinci da lemu Siyama” Umarnin Hajiya Siyama ta bi a gabana ta jera min kula biyu wacce nake kyautata zaton tuwo da miya ne ko shinkafa da miya, sannan ta kawo min lemu da ruwa da kofuna ita da kanta ta bude lemun ta zuba min a kofi sannan ta koma ta zauna. Kunya ta hanani ko da kallon nemun balle na dauka na sha. “Hajiya zan tafi” Na fada ina mikewa tsaye cike da kunya. “A a ko abincin ba ki ci ba?” “A a koshe nake” “Ba Ahmad kika zo nema ba? Zauna mana” Hakan da tace sai yasa kunya ta kara rufe ni. “A a daman... ” “Zauna Yata ke ma kina da hakkin sani” Cewar kina da hakkin sani yasa na koma na zauna cike da son jin ko minene. “Yata... Mijinki ba shi da lafiya Siyama ta fada min cewar yace miki ya tafi Abuja, be je ko'ina ba yana asibiti, yace miki haka ne saboda baya son a tashi hankalinki, ni da Siyama duk ya roki kar mu fada miki halin da yake ciki, sai dai na fada miki ne saboda ke matarsa ce kuma kina da hakkin sani, na san ya mace na da kunya da kawaici tun da har kika iya zuwa nan dan jin lafiyarsa aiko kin nuna mana kauna, ya kamata ke ma ki san halin da yake ciki” Tun da ta fara maganar na ji zazzabi ya rufe ni, a razane na kalleta. “Hajiya me ya same shi? Dan Allah ku fada min” Na juya gurin Siyama ina hawaye. “Rashin lafiya ce ki kwantar da hankalinki da sauki ai sosai, yanzu haka na gama shirin fitar da shi waje jibi zamu tafi” A take jikina yai sanyi gaba daya sai na nemi kunyar da nake ji na rasa na kama kafafuwan Hajiyar na rike. “Dan Allah ku kai ni na gan shi, ina bukatar ganinsa dan Allah” “Siyama tashi ki kaita” Hajiya ta fada ita ma hawaye na sauko mata kamar yadda Siyamar ma take balle kuma ni da kuka ya zame min abinci. Da sauri Siyama ta tashi ta nufi dakin da nake kyautata zaton nata ne bata dade ba ta fito rike da dan mayafi da makullin mota, ni kam jiki na rawa na tashi na bi bayanta, kusan a tare muka shiga motar domin zuciyata sa ya soma raya min abubuwa marasa dadi. Wayarsa na soma kira wannan karon ma sai da tai ringing ta katse ba a daga ba. “Idan yana cikin azabar ciwon baya iya daukar kira” Siyama ta fada tana tuka motar tana kallon sunan yayanta dake gaban wayata, ji nai kamar ba zan iya hakura ba sai na sake kiran na ci sa'a ya daga. “Hello Lims...” Sai na kasa magana saboda bana son yaji kukana. “Lims.... Lims.... Lims....” Haka yai ta kirana amman na kasa amsawa daga karshe na kashe wayar gaba daya, sannan na kalli Siyama na ce. “Tun yaushe ne ba shi da lafiya” “Wacan asabar din da ta wuce, yace ya ji abun yana driving be ma iya kawo kansa gida ba sai da ya kira driver ya tuka shi ya kawo shi gida saboda hannun da ke masa ciwo, yace mana be yi kwana ba saboda azabar ciwo kuma da aka je asibiti aka auna sai aka ce ba a ga komai ba” “Mi yake damunsa?” “Ciwon Hannuna ne, wani lokacin har cikin jikinsa yace yana jin abu, idan ya taso masa sai an daure ko kuma an masa allura sannan yake samun sauki” “Hannun ya bugu da wani abu ne?” “Mu dai be fada mana ba gaskiya, yace cikin dare ya soma jin abun” A gurin da aka tanada dan aje motoci ta aje motarta muka fita kusan har na fita sauri ma duk da ban san inda yake ba har sai da ta shiga dakin da kanta ina binta a baya. A zaune muka same shi an daure hannunsa na dama da belt dayan hannunsa kuma rike da waya. Yana ganina ya watsawa Siyama wata muguwar harara wacce ta saka ta kasa karasa cikin dakin. “Zuwa kikayi kika dauko ta ko?” “A a Wallahi ita ta zo...” “Shut up.... Ban fada miki kar a fada mata ba? Ko ban fada miki tana da hawan jinin ba?” “Yes amman..... ” “Fita ki ba ni waje.... And if wani abu ya samu matata i swear sai kin yabawa aya zakinta” Cikin tsawa sosai yake mata fadan ya ma kasa tsayawa ya saurareta, da sauri ta juya ta fice tana kuka. Nima da nake tsaye bakin kofar kuka nake ina kallonsa yayi wani irin mugun rama sosai kuma kana ganinsa kasan ba shi da wani kuzari. “Kin gani ko? Saboda kukan nan yasa nace kar a fada miki yanzu sai ki tashi hankalinki....” “Amman ina da hakkin sani, ni matarka ce, a iya tunanina babu wani boye boye a tsakaninmu, be kamata ka boye min wannan ba.... ” Na fada cikin kuka, sai ya aje wayar ya miko min hannunsa na hagu, ni kuma na taka na karasa kusa da shi na kama hannun na rike. “Can you please hug your husband” Na rumgume shi kamar yadda ya bukata ina fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya. Da dayan hannun ya rika shafa bayana yana min magana a hankali kamar yadda ya saba. “Babe please kukan kin nan yana taba min zuciya, bana son wata damuwa ta same ki shiyasa na ce kar a fada miki” “Daman na sani.... Shiyasa nake tsoron rabar mutane ko kuma mutane su rabe ni... Saboda wani.... ” Ban karasa ba yasa hannunsa na hagu ya dago fuskata ya hade bakina da nashi, we spend more than 5 minutes muna abu daya kamin ya cire bakinsa ya hade goshinsa da nasa. “I miss you....” Ya fada cikin rada. “Daman can ina fama da ciwon kirji kuma kin sani, to shine yanzu ya sauko min har a hannu, so ki daina canfa kanki idan kina haka haka ne zai ta sakancewa da ke, Allah yasa dai baki fadawa Hajiya wannan maganar ba? Kar ki sa ta fara zargi ta tsorata ta dauka da gaske ne” Na girgiza kai a hankali hawaye na sauko min. “Ban fada ba... Amman....” “Amman.... ” Yaja hancina sannan ya saka hannun ya share min shawaye. “Karki sake irin wannan maganar, tun before na aure ki nake jin wannan ciwon yafi min tsanani a yanzu kawai pls smile” Ya fada yana jan kumatuna, all what i try to do is na tsayardar zubar hawayena. Tashi nai na zauna saman gadon kusa da shi, a yau kam ni nake masa irin kallon da yake min wani irin jinsa nake a raina gaba daya tausayinsa ya gama mamaye min zuciya. Kissing forehead dina yai sannan ya saka hannunsa na hagu ya kama hannuna ya rike gam. “Sarkin kuka i love you” Kwantar da kaina nai kafadarsa ta hagu ina jin wani sabon kukan na son fito min. A hankali na fara jin yana motsi da na kalleshi sai na ga ya rufe ido yana cizon baki, a take hankali yai mugun tashi cikin sauri na mike tsaye ina tunanin abunda zan yi, dayan hannunsa yasa ya rike hannunsa na dama yana wani irin nishi yana ambaton Allah. “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Shine abunda na furta ina fashewa da kuka, a yanayin yadda nake ganin fuskarsa da kuma yadda ya rike hannun ya isa ya sanar min da irin azabar da yake ji, wacce nake jin kamar ace akwai abunda zan iya a dauke masa ciwo gaba daya, da sauri na fito daga dakin da zimmar zuwa dakin da Doc Nura yake domin na san asibiti tun da ba yau na fara shigowa ba, a kujerar dake kusa da dakin na yi arba da Siyama zaune tana latsa wayarta tana ganina ta mike tsaye. “Ciwon ya tashi kenan?” Ban ko kula ta ba na nufi hanyar da zata sadani da dakin likita ina kuka, kamin na karasa mutumen da ke gadin kofar office din ya tare ni. “Likita nake nema ciwon Ahmad ya tashi” “Baya office dinsa tun dazun ya fita” Juyawa nai da gudu na koma dakin sai na samu likitan da wasu likitoci biyu suna tsaye a kansa, Siyama kuma tana gefe tsaye tana kuka, belt din suka kwance suka sake saka masa wani sannan sukai masa allura. “Dan Allah ku je waje..... ” Ni da ita muka fito daga dakin muka tsaya a waje, ita kuka ni hawaye. “Ki yi hakuri zai samu lafiya in Allah ya yarda” Na fada ina dafata domin a yadda ita take kuka dole ne ni tasa ni na hade nawa kukan na zama jaruma na lallashe ta. “Ina fatar hakan, baya son muna zuwa kusa da shi saboda kar mu ga halin da yake ciki, tsoro na ke ji ina jin kamar.... kamar.... Yaya mutuwa zai yi.....” Na yi saurin rufe mata baki. “Haba dai cuta ai ba mutuwa ba ce, zai samu sauki In-Sha-Allah” A lokacin ne wani kukan ya zo min, tana da gaskiya ni da ita za mu iya rasa shi, saboda haka suka rasa yarsa, idan har ya kasance ni ce sila fa? What if ya kamu da wannan ciwon ne saboda ya aure ni? Ban raba dayan biyu ba Doc Nura ya fito daga dakin, ya nufo inda nake tsaye ni da Siyama yai mana maganar da zata kwantar mana da hankali cewar Ahmad zai samu sauki. Sai da ya wuce zuwa wani gurin sannan Siyama ta bude dakin ta shiga, ni kuma na bi bayan likita na cika kafa kamin ya shige na cin masa. “Doc dan Allah ina son magana da kai” Juyowa yai ya kalleni. “Ina jin” “Dan Allah miye abunda yake damun Ahmad?” Shiru yai kamar mai nazari. “Hajiya bata fada miki ba?” “Ta fada min tace ba a san ko minene ba amman ina son kara ji daga bakinka” Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. “Gaskiya ne, an yi duk wani hoto daya kamata amman ba a ga komai ba, kuma shi yace yana jin ciwo yana masa yawo a hannun” “Amman tun yaushe abun ya fara?” “Yace min ranar assabar da dare, ya fito daga gurin abokinsa da dare, wai be iya kai kansa gida ba sai da ya kira direbansu ya kawo shi, na tambaye shi ko ya ci wani abu ne ko kuma hannun ya bugu da wani abu? Yace min a a yanzu jibi za a fita da shi, asibitin da za a kai shi tana da kyau tana daya daga cikin asibitoci masu kyau da iya aiki a duniya, ina sa ran ko minene za su gano In-Sha-Allah ki kwantar da hankalinki” Na gyada masa kai sannan na juyo na fara tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa, babu komai a zuciyata sai tausayin Ahmad da kuma zargin kaina domin a wannan assabar din guri ya fito, ban san ko ya biya ta wani gurin ba, amman tabbas na san ranar ce abun ya same shi. Jinginawa nai jikin wani gini ina hawaye, wayata tai ringing da na duba sai na ga number Hafiza, share hawayen nai na dauki kiran. “Hello” “Halima kina ina?” “Dan Allah kina kusa da Mama?” “Eh ita tace a kira ki ai ta duba bata gan ki ba” “Bata wayar” Ina jin sallamar ta a kunnena sai na fashe da kuka. “Mama na fita na zo nan asibiti Ahmad ba shi da lafiya” “Subhanallahi miya same shi?” “Hannun shi ke ciwo, kuma likitan yace ba a gano matsalar shi ba an yi hoto ba aga komai ba, Mama tun ranar assabar din daya bar gurin be sake lafiya ba har yau” “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, kina asibitin ne?” “Eh Mama tsoro nake ji” Na fada ina kuka domin har ga Allah tsoron nake ji. “Ikon Allah abu kamar na iska? Ki kwantar da hankalinki za ku zo yanzu In-Sha-Allah” “To” Na kashe wayar ina share hawayena, sannan na nufi dakin da yake na tura na shiga, ban samu Siyama a dakin ba shi kadai na samu a zaune kamar dazun, a take hawaye suka fara wanke min fuska amman shi murmushi yake min wanda zai kwantar min da hankali, karasa nai kusa da shi na saka hananyena duka biyu na rika fuskarsa ina ta kallonsa har ga Allah ban tana jin son sa da tausayinsa a raina ba irin yau. “Tun ranar da ka bar gurina baka sake lafiya ba, ba a gano dalilin ciwon nan naka ba, Ahmad ba zan daina zargin kaina ba, idan wannan ciwon be barka ba zan yafewa kaina ba, na dade ina jin tsoro bana son mutane suna samu matsala saboda ni, kuma ina ji a jikina cewar ni ce sila....” “Shiiiiiiiiiiiiiiiiii” Ya dora hannunsa saman bakina. “Ke baki dogara da Allah ba ne? Kin gani saboda gudun hakan yasa nace kar a fada miki, zaki saka damuwa a ranki har ciwonki ya taso, sannan za ki so ki fara magana marar kyau har ki sa a fara zargin wani abu, musamman ma Hajiya ta ko Siyama, dan Allah Lims ki bar wannan a matsayin sirrin mu, bana son wani yace zai ga laifinki ko ya tsane ki a yanzu, kina bukatar farinciki ko bana raye, and I'm sure idan ba ki samu a gurina ba Hajiya da Siyama za su ba ki, saboda sun san ina son matata sosai...” Ya karasa yana sumbatar hannuna. Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rumgume shi ina jin kamar akwai abunda Ahmad ya boye min, har ga Allah ba zan daina zargin kaina a kan ciwon Ahmad ba domin a lokacin da be aure ni ba abun ba haka yake ba, why sai yanzu? Ko dai ni din ba alheri ba ce a gurin jama'a? Sanadina ya rasa yarsa, yanzu kuma ace ya zama mijina kuma ta kamu da ciwo?  Ina kokarin tsayar da kukana zancen Siyama da na Doc Nura ya fado min a rai, cewar a daren assabar din data gabata abun ya same shi and a wannan assabar din yana tare da ni ai kuma daga ita ne be dawo ba, hakan na nufin a ranar ne ya kasa kai kansa gida? Kuma a wannan ranar he hold my hand wata kila daga nan abun ya same shi. “Abu kamar na iska” Maganar Mama ta dawo min, no wait a daren ma ai ya gaisa da Abdallah, kuma Abdallah zai iya masa wani kofi, indai har ransa ya bace, i can remember ni ma ya taba min a lokacin da ya bukaci na shiga motarsa na ki sai an rasa mai napep din da zai dauke ni, and i lokacin da na auri Abdulhamid ma ya taba min na kasa girki, ya taba min wayata tsage ba tare da ta fadi ba, and yayi ma Abdulhamid ma, tabbas zai iya yi ma Ahmad inda har za a duba ace ba a ga komai ba tabbas Abdallah ne.   Shine abunda zuciyata ta raya min kai tsaye, domin a wannan ranar Ahmad ya rike hannuna har gaban Abdallah kuma na san hakan ba dadi zai masa ba, secondly the way da ya ba Ahmad hannu su gaisa ba dan Allah bane, how Abdallah zai yi wani murna ya aure ni? Wanin ma wanda ya bukaci na daina aiki a kamfaninsa saboda baya son taraiya mu... Ban san lokacin da na mike tsaye da sauri ba hankalina yai mugun tashi. “What...?” “Ya kamata naje gida ba su san na zo nan ba gashi yamma ta yi” Kallona yai from head to toe. “Ji veil din da kika fito da shi Lims, nasa doguwar riga ce amman ina bukatar ki rika rufe min jikina” “Zan saka next time, zan dawo anjima kadan...” Na fada ina nufar kofa da sauri sai ya kira ni. “Hey Lims are you okay?” “I'm fine” Na fada ina kokarin kwantar da hankali. “Okay come here and kiss me” Dawowa nai na yi kissing dinsa sai ya rumgume ni da dayan hannun nasa. “I love you” Ya rada min sannan na sake shi na mike tsaye na dauki purse dita na fice daga dakin. A phone list dina na shiga na nemo numbersa da ke kan gmail nawa na danna masa kira da sabon line na, ringing rai sai da ta kusa katsewa sannan ya daga da muryar da ke nuna be san mai magana. “Abdallah kana ina?” Yana jin muryarta ya gane ni ce mai magana. “Halima.....” Yayi shiru sai kuma ya amsa. “Ina gida” “Wane gidan?” “Gurin Hajiya” Kashe wayar nai na nufi hanyar fita daga ward din ina ta sauri kar na hadu da su Mama. *Where are are the classy ladies 🤔 mata yan kwalissa ga awwaba scent tazo maku da hadadun turarukan wuta humra body oil turaren jiki na tsuguno da kayan gyaran jiki kaman dilka scrub organic soap 🧼 da sauransu akan farashi daidai aljihu say no karnin da warin damshi na lokacin damina zaaiya samunmu a wannan lqmbobin 09137294470 08034236800* 7/21/21, 11:11 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 6️⃣0️⃣ For the first time a yau zan tunkari Abdallah da maganganu a cikin gidan Hajiya babu tsoro ko fargaba a tare da ni, sai dai ga dukan alamu shi din ya kasa natsuwa sai kiran wayata yake ni kuma na ki na dauka domin face to face nake son ganinsa ba ta waya ba, kamin mai napep din ya isa har na matsu, yana saukeni na biyashi kudinshi na buga gate din sai na ji shi a bude, hakan yasa na tura kofar na shiga babu kowa a harabar gidan sai motoci ina ganin motarsa na tabbatar da lallai yana gida kamar yadda ya fada min. Kai tsaye na nufi kofar falon nai knocked sai na ja na tsaya, after some seconds ma sake kwankwasawa. A hankali aka bude kofar Abdallah ne ya fito daga cikin falon ya janyo kofar ya rufe yana kallona da mamaki a fuskarsa. “Halima lafiya?” Ya tambaya a hankali kamar mai rarrashin yarinya. A yau da na kalleshi sai na ganshi kamar ba Abdallah ba, duk wata kima da matarta da mutunci da nake ganinsa da ita a yau sai na nemeta na rasa. “Ina mamakin yadda zaka fada min abunda ba shine a ranka ba, ina mamakin yadda ka tozarta yardar da nai da kai ka watsar da amincin da nai maka” Karara mamaki da al'ajab suka bayyana a fuskarsa. “Halima are you okay?” “No I'm not, me yasa zaka fada min abunda ba shine a ranka ba, akan me zaka ce kana son farincikina bayan ba haka ba ne a ranka?” Matsowa yai kusa da ni ganin yadda nake daga murya, idanuwana kuma na nuna tsantsar bakin raina. “Wace irin magana ce wannan? Me yake damunki?” Ya fada murya kasakasa. “Kaine damuwata Abdallah, kai ne matsalata” “What happen?” “Ka rantse min baka san abunda yake faruwa ba....!” Murmushi yai ya lumshe ido ya bude. “Wai wannan banza... Ai...” “Shi ba banza ba ne mijina ne na sunna!” Na fada cikin wani irin zafin rai da ban taba sanin ina da shi ba. Sai ya sake yin murmushi. “Na sani ne ai, har na taya shi murna remember?” “Yes a ranar ka cije shi a hannu” “Maye ni ne ko aljani da zan masa wani abun?” “No amman kai kana da kofi, kai ka yi wa Abdulhamid ya kasa aure, ka taba min ba sau daya ba ba sau biyu ba, Abdallah na sani zaka iya kullatar Ahmad a rai” “Yes...” Ya amsa min kai tsaye yana hade fuska kamar ba shi ba. “Ya fada min zai nuna min matsayinsa a gurinki, kuma ya fada ya cika na sani yayi forcing din ki ya aure ki, he deceive you ba ki san waye shi ba, how could he? Ya aure ki by force and ya holding hannunki a gabana bayan ya san na fi kowa son ki? How dare he?” “No how dare you....! Ahmad be aure ni ba sai da amincewa ta, abunda kai masa ya nuna baka son farincikina, domin yan'uwansa da danginsa ni zarsu zarga idan hakan ta faru ya kake tunanin zan kasance?” “Amman Halima ba son shi kike ba, ta ya za ki auri mutumen da ya laka miki laifin kisan kai? Ko kin manta ne? Mutumen daya tashi sakawa a rufe ki gidan yari? Babu kalar maganar da be fada miki ba, Ina son ki Halima kin sani ina da kudurora akanki, i just want you to get a better life, kuma idan mu kai jira na wani lokaci wata kila Allah zai cika mana burinmu” “Jiran shekara dubu nawa? Jiran ranar da Hajiya za ta so ni har ta amince na aure ka? Ko jiran ranar da Abdulhamid da bakinsa zai roki na aure ka? Ko jiran ranar da mutane za su ga dacewar haka su ba mu shawara aikatawa? Ba so na kake ba Abdallah kana son ka ne, a lokacin da na ke auren Aminu ka sani mijine uban yayana amman kullum sai ka fada min aibinsa, kullum sai ka fada min abunda zai bata min rai saboda na rabu da shi na aure ka, ka sani neman auren matar aure haramun ne Annabi ya hana amman ka nace kana ta min campaign kanka, babu abunda baka min dan na kashe aurena na aureka, wannan dalili ya hana ni auren shiyasa na zabi na aure dan'uwanka domin shi be taba min haka ba, duk kuwa da kasancewar shi ya fara so na kamin kowa, yana sane nai aure amman be taba ce min Halima ki kashe aurenki ki aure ni, Abdulhamid ya fika zuciya mai kyau, domin shi be taba cutar da ni ba, kawai ya kasa aminta da ni ne a lokacin da kaddara ta fada min, and now na sake auren wani ba kai ba, so kake na kashe auren na fito aure ka? Saboda ka cika son kanka kuma ka kasa yarda da kaddara, miye laifin Ahmad idan na aure shi kuma zan samu farinciki a gidansa? Ashe ba farinciki kake min fatar samu ba?” Na karasa a tsawace hawaye na sauko min. “Halima kamar ba ke ba” “Ni ce dai, na zo na gargade ka ne, idan wani abu ya samu mijina...! Ba zan taba yafe maka ba, kuma hakan ba zai saka ya sake ni ba ba zan taba rabuwa da shi ba har a abada...! Domin ni na yarda da abunda ka kasa yarda da shi KADDDARA” Na kare ina nuna shi da yatsa, sai ya girgiza min kai ya kara matsowa kusa da ni “Haba Halima kina da raunin tunani, ta yadda idan wani ya kisa miki wata maganar sai ki hau ki zauna akanta, ki rika kokarin samawa wasu farinciki ba kanki ba, yanzu duniya ta wuce wannan kowa kansa ya sani, kamar kin manta waye Ahmad? Miya zai kitsa miki abubuwa a kaina kuma yardar da mutumen da kika gani a jiya sama da ni?” “So kake GOBE NA ta lalace, so kake mutane su fara guduna suna ganina kamar wata annoba? So kullum nai ta dauwama a bakinciki da damuwa? Na gaji i deserve happiness” “Shi nake kokarin ba ki, i promise you za ki samu farinciki a tare da ni, dukannin mafarkina da burina akanki ne, Halima ina miki son da wani da'namiji be taba miki shi ba....” Yana karasa Hajiya ta bude kofar falon ta fito, a yanayin yadda na ganta da kuma yadda fuskarta ya nuna ta ji komai. A gabansa ta tsaya yana kallonsa shi ma kallonta yai sai yai kasa da idonsa. “Da gaske kai ne silar ciwon Hassan?” Ta masa tambayar tana masa wani irin mugun kallo, sai yai shiru ya kasa amsawa kuma ya kasa daga ido ya kalleta. “Ka amsa min? Eh ko a a?” Ta daka matsa tsawa jikinta har bari yake. “Eh....” Tasss ta wanke masa fuska da mari kamar daman jiran take ya amsa mata da eh din, hakan kuma be wadatar da ita ba har sai da ta sake marin dayan baren fuskar. “Amman baka da tausayi baka da imani Husaini.... Allah ya wadaranka....” Cikin kuka take mishi wannan maganar, shi kuma har lokacin be motsa daga inda yake ba. Sai kuma ta juyo ta kalleni tana hawaye. “Fita ki bar min gida, ba ke ba yaya har abada, ko bana raye ka auri Halima ban yafe maka ba.....!” Ta karasa tana nuna shi da yatsa, a rikice Abdallah ya kalleta ya kalleni sai ya fadi kasa ya rike kafafuwanta ya fashe da kuka kamar ba shi ba. “Noooooooo Hajiya dan Allah..... Hajiya dan Allah, Hajiya dan Allah.... Hajiya dan Allah.... Hajiya dan Allah...” Ya maimaita hakan ya fi a kirga yana rike da kafafuwanta yana kallona kuka yake sosai kamar ba namiji ba, sai kuma ya mike tsaye ya rike hannayenta. “Hajiya ina son Halima Wallahi baki san kudurina ba dan Allah karki shiga tsakaninmu haka....” A take ta fisge hannunta ta sake wanka masa kyakkyawan mari. A lokacin ne yai shiru ya runtse ido. “Ka gani ko? Dan Allah ka kyale min mijina.... Ina son abuna” Na fada ina hade hannayena nima hawaye nake kamar shi, sai ya bude ido ya kalleni kamin ya juya yana kallon mutanen da suka fito daga falon suna tambayar ba'asi, Hajiyar kuma ya koma cikin falon tana kuka. Ni kuma na juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fara tafiya ina jin wani abu marar dadi. Sai da na kai gate din sannan na juyo na kalleshi har lokacin yana tsaye a inda yake yana kallona, juyawa nai na bude gate din na fita. Sai da nai tafiya mai nisa sannan na samu napep na shiga ta mayardar da ni asibitin ko da na isa ana kiran sallah magariba, kai tsaye na nufi ward din da Ahmad yake ina isa na tura kofar dakin na shiga, sai na samu Mama da Inna zaune a dakin ga Hajiyarsa da Kanwarsa Siyama da wata wasu mata hudu da ban wayance su ba, sai dai ina kyautata zaton yan'uwan Ahmad din ne, shi kuma yana zaune saman gadon wani kallo kawai yake aiko min wanda ke nuna ba lafiya ba. A sanyaye na shiga muka gaisa da mahaifiyarsa sai ta gabatar da ni a gurin matan, sannan tace min. “Kin gwangwanin Gwarzo nan” Hakan yasa na sake mika musu gaisuwa sannan na tsaya a kusa da Inna sai dai a duk lokacin da na kalli Ahmad sai ya dan harare ni kasa kasa, sannan ya sauko saman gadon ya shiga bandaki yai alwala ya fito, Hajiyarsa ta umarce ni da na shimfida masa carpet su kuma suka tashi suka fita tare da bakin. Inna da Mama suka mike tsaye Inna na ce min. “To mu kan mun tafi Halimatu sai kin dawo Allah ya kara sauki” “Amin inna sai na zo” Sai da suka juya sannan ya kawo kunnensa kusa da nawa ya rada min. “Ki ce musu nan za ki kwana” Na lake kafada alamar ba zan fada ba, shi kuma ya kware min ido kamar mai yi da karamar yarinya. Sai da suka fice sannan na shiga bandakin nai alwala na fito na zauna bakin gado har sai da ya gama sannan ya tashi ya dawo saman gadon ni kuma na hau carpet din nai sallah, babu komai a addu'a ta sai nemawa Ahmad lafiya da rokon Allah ya tsare min shi. Sai da na shafa addu'ar sai ya miko min hannunsa na hagu, na rika na tashi tsaye sai ya dawo da ni kusa da shi na zauna, sai ya saka hannunsa saitin kwankwaso na yana ta wasa da shi, ya dora gemunsa saman wuyana sai yasa ta bakinsa ya janye mayafin kaina ya sauko kasa, bakinsa saitin kunnena. “Na fadawa Hajiya ta sa a shirya miki ticket mu tafi tare” “Amman Ahmad tun da ance ba a ga komai ba why not a yi addu'a kasan wani lokacin iska da kandu suna yin haka fa” “Ba laifi ya zama iska ba, kin san Nigeria ba mu da irin wannan cigaban yanzu za a iya zuwa a can su yi gwaje gwajensu kuma a gano matsalar” “No ba na asibiti ba ne” “How do u know?” Kamar mai rada haka yake min magana in each word sai ya tsotsi kunnena sannan yake fadarta wani sa'in kuma sai ya busa min iska a kunnen. A kalleshi a natse na ce. “Baka fada min tun daga lokacin da ka gaisa da Abdallah ne abun ya same ka ba” Sakina yai yasa hannun nasa ya rike fuskata. “Ina kika je dazun?” Na yi shiru. “Ba gida kika je ba, na sani dominbda suka zo sun tambaye ki kuma Mama tace kin buga mata waya kina kuka, i suspect something fada min ina kika je? Don't lie to me” “Magana nai da Abdallah....” A take fuskarsa ta canja. “As how?” “Akan ciwon ka ne” “Oh ya Allah, taya za ki je ki yi magana da shi? Kin san ko tunawa nai akwai son ki a zuciyarsa sai naji kamar na kone, akan me za ki je ki yi magana da shi? Lims why? Is not allowed ya ji muryarki ma ji drees dinki ma, gown ce fa sai mayafi Babe why?” Ya karasa kamar yai kuka, hakan kadai ya isa ya karantar da ni irin zafin kishin da Ahmad yake da shi, so idan har zan zauna da shi dole nai tsaka tsantsan da rayuwarsa. “Saboda na san shi yai maka kofi, kuma da na masa maganar ya amsa min da cewar shi din ne, tun da yana jin haushinka na san dole zai maka, shiyasa na ce maka ba na asibiti ba ne, ya yi ma dan'uwansa kuma ni ma ya sha min” “Ba kofin ya dame ni ba, maganar da kika yi da shi ta dame ni, Allah kadai ya san abunda ya ce miki kila ma yace Halima ina son ki” Na dan zaro ido. “Aa be ce ba fada fa mukai da shi” “Fada did he touch you” “Oh oh No ba irin wacan fadan ba, fada na baki” Ture ni yai daga jikinsa. “Daga ni dan Allah” “I'm sorry, amman na damu da halin da kake ciki ne” Ya fada ina kada kafata domin tafiyar abu nake ji kamar ƙuda, ina jijjiga kafar na ji abu ya fado mai nauyi, saurin mikewa nai tsaye sai ganin kunamu nai har uku a inda kafafuwana suke, ban san lokacin da na daka tsalle na dale saman gadon ba ina ihu. “Ka gani ko? Ya fusata da ni shine yai min kunamu nan” “Shiiiiiiiiiiii karki bari Hajiya ta ji maganar nan” Ya fada yana rufe min baki. “Shiyasa na fada maka cewar ciwon hannunka nan ba na asibiti ba ne, ayi maka addu'a zai fi sai ka mu sauki” Na fada kamar zan fashe da kuka, jana yai jikinsa ya rumgume. “Amman kin san yanzu an riga an gama shirya komai Hajiya ba zata yarda a fasa ba, kuma zuwan ma yana da amfani ko ba kuma hakan zai kara tabbatar da maganarki kuma Hajiya ba zata zargi komai ba” “Amman taya za a samu maganin kofi a asibiti? Ahmad kai tunani mana” “Okay fine zan yi magana da Hajiya sai nace mata a hada da addu'a hakan ya miki?” “Eh ni ma kuma za ki rika maka fatiha kafa bakwai kullum da safe a ruwa kana sha idan zaka iya shan yawuna” “Hmmmm har abunda ya fi yawunki ma zan iya sha, kin san minene” Ya fada yana shinshinata tare da dora hannunsa saman cinyata. “A a bana son sani” Sai yai murmushi ya sauka saman gadon ya dauki takalminsa da hannunsa na hagu ya kashe kumamun dake ta yawo a cikin dakin sannan ya dawo ya zauna a inda nake yana kokarin kai hannunsa kirjina aka tana kofar da sauri na dauki mayafina na rufe kaina shi kuma ya dauke hannunsa daga jikina. Yunus ne ya shigo rike da ledodi a hannunsa, after sun gaisa da Ahmad ya gaisa da ni sai kuma ya soma zolayata. “Amarya ashe ashe ba mu sani ba....” Wani kallo Ahmad yai min hakan yasa ban biyewa wasan da yake min ba. “Yunus ka fa san ni bana son wasa da iyalina please take note” The way da yai masa maganar babu wasa ko kadan a tare da shi, sai dai hakan be hana Yunus din yin dariya ba. “Daman na zo ne na dauke ta ayi mata hoto Hajiya tace a shirya mata komai da ita za a je” “Ban gane ka dauke ta ayi mata hoto ba? Ta dai baka hotonka karami ko?” “Ba shi kadai ba ka san za a mata passport” “Okay kuma kai zaka kaita ayi mata” “Alhaji bana da matsala idan kai zaka shige gaba ayi mata komai, yanzu dai ya jikin naka?” “Al-hamdulillah zan mata komai” Ya fada yana kallona. Sun dan dade suna fira kamin yai mana sallama ya tafi. A lokacin ne na zuba mana abincin a plate daya ni da shi, be wani ci sosai ba hakan yasa nima na ji ba zan iya ci ba, ya bukaci na hada masa tea. “Shiyasa ka rame baka cin abinci” “Sai na samu lafiya zan ci abinci na koshi na more” “Ba gashi na zuba maka yanzu ba ka ci ba” “Ba wannan abincin ba, wacan abincin wanda aka dade ba a hadu ba, kuma na yi marmari da yawa” Murmushi nai ba tare da na kalleshi ba na cigaba da hada masa tea, da na kawo masa masa be karba ba sai yace na bashi da kaina, haka na rika ba shi tea kamar wani karamin yaro. “Sha mana” Na kurba kadan na bashi ya sha, bayan ya gama mukai sallah isha'i. Ban tashi daga saman carpet din ba sai ga Hajiyarsa ta shigo tana tambayar ko akwai abunda muke bukata. “Sai dai ko shi ni ai gidan zan tafi” “A a nan za ki kwana, wannan kuka da kuka min dazun idan kika je gida ai sai ki yi mafarkin kukan kuma” Ta fada tana murmushi ni kuma nai kasa da kaina kunya ta rufe ni, Ahmad kan dariya yasa kamar ba shi ba. “Ashe dai ana so na” Kasakasa na wasa masa harara. Sai Hajiya tai murmushi. “Allah dai yai muku albarka kuma ya ba ka lafiya ka koma gida cikin iyalinka” Daga ni har shi muka amsa da amin, sannan tai mana sallama ta fice. Duk yadda na so ya kwanta saman gadon ni na kwanta kasa sai yaki, ala dole sai dai mu kwanta saman gadon a tare ko kuma shi ya sauko kasa mu kwanta. “Gadon ai ba zai dauke mu ba” “Ai ba dole sai mun wadata ba, ko kuma mu kwanta kasa” “Ya za'ayi kana rashin lafiya ka dawo kasa ka kwanta?” “Kin san dai ba zai yiyu mu kwana daki daya kuma a daban daban ma wannan ai haramun ne ma” “Inji wa?” “Inji ni” Ya nuna kansa, ban san lokacin da na saka dariya ba. A dolen dole muka kwanta kasa ni da shi, muka lulluba da Bedsheet daya yadda ya rumgume ni a jikinsa yana shafa ni kai ka rantse da Allah ba ciwo yake ba. Da asuba sai da na dumama masa ruwa yai wanka ni kuma na shiga nai alwala ko da ya fito na gama sallah na gaishe shi na shimfida masa carpet din yai sallah bayan ya gama na karanta masa fatihar ya sha sannan na hada masa tea. Misalin bakwai da wani abu direbansu ya kawo mana breakfast ba laifi nan ma da na zuba mana ya ci wata kila saboda mun ci tare ne ko kuma dan na yi magane jiya yasa yau ya ci oho. Sai tara da wani abu mahaifiyarsa ta shigo, ni kuma na fita na basu waje. Ina tafiya wayata tai kara alamar shigowar sako, number Abdallah ce. “Ina fatar mijin da kika aura ya rike ki amana Halima, i wish you all the best ....” Shine abunda ke rubuce a cikin sakon, ban miya sa ba sai duk na ji wani iri. Har na koma dakin jikina a sanyaye yake. “Na yi magana da Hajiya akan ko a daga tafiyar nan har gaba sai ce ba zai yiyu ba, amman dai ta aminta za a saka da addu'a din” Ban ce masa komai ba na hau saman gadon na zauna na dora kaina sama wuyansa. “Babe are you okay?” Na kalleshi. “I'm fine, Allah ya baka ikon rike ni amana” “Amin” Ya sumbaci goshina. “Ba zako taba kuka da ni ba In-Sha-Allah i love you so so so much” Ya fada try to hug me with both hands. “Baka jin ciwo ne?” “Da sauki dai gaskiya” Murmushi nai na rumgume shi. Ban dauka da gaske yake ba har sai da muka je tare da shi aka min komai na tafiyarmu a yadda nake ganinsa na jidadi domin baya nuna alamar ciwon ko da akwai ma yana boye min, domin ya fada min duk bayan awa uku sai hannun ya taso masa da ciwo amman yanzu kam Al-hamdulillah. Tare da shi da direban da ke jan mu ya sauke ni kofar gida, sannan shi kuma ya wuce. Da na shiga gida sai Hafiza ta rika zolayata kamar ba kanwata ba iskanci kala kala ko kunyar Mama da Inna bata ji, ko da yake daman can Hafiza ba wata doguwar kunya ce da ita ba. After na yi wanka na canja tufafin jikina ina gyarawa su Amal kayansu Inna ta shigo tana tambayar wai da gaske ne taji a gurin mama cewar da ni za a tafi. “A a aiko hakan yayi Allah ya bashi lafiya” “Amin” “Inna” “Na'am” Har ta juya na kirata ta juyo. “Dan zauna dan Allah” Ba musu ta zauna saman katifar da muke bachi, a nan labarta mata abunda nake zargi a ciwon Ahmad da kuma a abunda ya faru tsakanina da Abdallah a maimakon ta yaba min sai ta rufe ni da fada. “Sakaryar banza sha sha ba, marar tunani, komai Abdallah yai miki kar karki manta dan'uwanki ne kuma saboda yana son ki yai, ai ko a munafurce mutum ya nuna maka kauna ya fi wanda ya fito kirkiri yace baya son ka” “Amman Inna shine fa yai masa wannan kofin” “Idan shi din ne ai sai ki bishi da lalama ba da hauka ba, Abdallah ya gama miki komai a rayuwarki Halimatu be cancanta ki saka masa da wannan ba, ke dai kan baki da tunani sam sakarya kawai” A fusace ta fice ta bar dakin ni kuma sai duk na ji babu dadi, na rasa abunda zan yi na ji sanyi a raina na rasa tunanin da zai nuna min na yi daidai ko akasin hakan. ABDALLAH POV. Tun da Hajiya tai furucin nan sai ya ji kamar an zare masa rai a cikin jiki, har lokacin kuma ya kasa ganin laifin Halima, iya abunda yake tunani Ahmad ya kira mata abubuwa ne akansa ita kuma ta yarda shiyasa ta zo har cikin gidan Hajiya tai masa kalamai marasa dadi. Sai dai daga lokacin da Hajiya tai masa furucin cewar ko bayan ranka ya auri Halima bata yafe masa ma ya cire zancen aurenta ya aje a gafe, hakan kuma ba zai saka kaunarta ta goge a zuciyarsa ba, sai dai yana da yakinin idan ba Halima ya aura ba ba zai taba samun cikar burinsa ba na haihuwar da namiji, a iya kwallafa rai ya kallafa mata rai da zato da kuma tunanin idan ya aureta burinsa zai cika na haihuwa da namiji kuma zai samu damar kusanci da abar son sa. “Yanzu na gane ba laifinta ba ne, har da naka kana da son ka Abdallah taya zaka runtse ido ka tsaya kai da fata akan cewar sai ka aureta? Matar da dan'uwanka ya saka? Kuma dan'uwan naka ma twins brother dinka? Kuma yana raye? Bayan kasan bana son yarinyar nan, hakika na tsorota da lamarinka, idan har zaka ita cutar da dan'uwanka to ni ma zaka iya cutar da ni” “Subhanallahi Hajiya wace irin magana ce wannan? Abdulhamid shi ya fara cutar da ni, domin yayi min kofin ba zan taba haihuwar da namiji ba, kuma Hajiya kin san yadda nake son namiji, yana daya daga cikin dalilin da yasa nake son na auri Halima” “Kum illata kanku kun cutar da kanku, amman kai kafi cutar da dan'uwanka, ko da baka haifi namiji ba ai kai ka yi auren har ka haihuwa? Shi fa? Dubi inda ya kare yanzu da yana ko ya ce da ban kalli yar na ji sanyi ba? Amman damuwarsa bata dame ba ka, kai neman da namiji kawai kake? Babu ruwanka da matsalarsa, kana kallon yadda yake ta fafutukar neman magani amman baka taba tausaya masa ba Allah ya wadaranka Abdallah, ka so matar aure, kuma matar dan'uwanka saboda selfishness reasons, Halima ce kawai mata a duniya? No saboda ka musguna ma dan'uwanka ne kuma kana ganin idan ka aure ta zata iya haifa maka namiji tun da last child dinta mace ce kuma tana haihuwar maza da mata ne, Wallahi karya kake kai baka isa kai abunda Allah be yi ba, komai kofin ka ba zaka iya yi wa kowa abunda Allah be masa ba, ashe ba laifin Halima ne kawai ba har da kai, ta yi tunani a lokacin da ki aurenka ta auri dan'uwanka ko ni ce haka zan aikata domin kai abun tsoro na, ka maida kanka wani kalar mutum dukanku kun zamar min wasu iri” Ta karasa tana fashewa da kuka, sai yai sauri sauka daga saman kujerar da yake zaune ya matsa kusa da ita ya kama hannayenta yana hawaye. “Hajiya dan Allah ki yi hakuri, Wallahi na bar zancen Halima har abada, kuma In-Sha-Allah zan nemi maganin kofin zan karya shi, dan Allah karki kuka saboda ni” Kawarda fuskarta tai tana share hawayenta. “Da bakincikinka zan ji ko da na dan'uwanka? Tun jiya na kasa bachi saboda abunda na ji, na rasa wane kai din wane iri ne?” “Zan canja Hajiya i promise you this” Ya fada yana kokarin kwantar mata da hankali. 7/22/21, 9:15 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 6️⃣1️⃣ Ta waya nake labartawa Hajara abubuwan da suka faru, ba laifi ita kam yaba min tai akan abunda nai wa Abdallah. “Daman can ni dai hankalina be kwanta da wannan mutumen ba, kuma taya zaki auri yaya ki auri kane dukansu suna raye, yanzu wannan abun da kika yi har Mahaifiyarsa ta kara shiga tsakani ai dole ya kyale ki ki samu kwanciyar hankali, ko ba komai kuma ta ji abunda Abdallah yai ma dan'uwansa ko dan haka ai dole ta daina kin ki” Na tabe baki kamar tana gabana na ce. “Haka dai kike gani, amman a iya tunanina abu ne mai wahala Hajiya ta iya so na, kiyayya ta riga ta shiga” “To can ta matse musu mu ai ba mu da case da su a yanzu, za mu je mu ci amarcin ma a waje ma ba a kasar nan ba” Ta fada tana keto wata shegiyar dariyar jindadi. “Wani irin amarci kuma Hajara? Jinya dai ko?” “Ke kar ki maida ni yar iska mana, idan kun je jinyar sai ya saka miki ido yana hadiyar yawu? Mazan yanzu? Ko kana gidanku ma ya ka kare balle ana tare? Make sure dai kim gyara kamin ku tafi” “Jinya fa zamu je hajara, kuma gobe zamu wuce ina wani zancen gyara” “Ko yanzu dai lokaci be kure ba, ai ba dole sai kin yi wani shegen shaye-shaye nan ba, bari Abban Afrah ya dawo idan ya amince min zan je gurin Hajiya Bilki na karbo miki wani set da take badawa na amare, sha daya ake amman aikin shekara yake, kuma idan kika sha baki bukatar kara shan komai da sunan gyara, kuma ba wani da yawa bane ba sai kin wahala ba, amman fa ki shiryawa aiki dan ni kaina wallahi sai da na ci kwakwa balle kuma ke da kika kwana biyu ba a hadu ba” Daga ni har ita dariya muka saka, daman can Hajara ta san irin wadannan abubuwan shiyasa kullum gidanta baya rabo da su har mamaki take a lokacin da ina auren Aminu amman bana sha kamar ita. “Amman fa gaskiya kusan 32k take bada shi, kuma kudin da ke hannuna ba zai wuce 14k ba idan ma yayi, kin ga bikin nan naki ma ya fado min gaf amman dai kamin a tare na san na shirya In-Sha-Allah kuma na san ba zata yarda ta bada shi a akan bashi ba domim bata da yarda sam duk sabonka da ita” “Karki damu turo min account dinki zan miki transfer yanzu” “Shegiya amarya ki ce har kin ji dala? Ehhen” Dariya nai na watsa da carbin da ke hannuna. “Ba na shi ba ne, wannan kudin ya dade ban baki komai ma a ciki ba kin ga sai na hada na turo miki” “A a lalai ba ni da case matar Amadu ki ce abun akas yake... ” Sai da tai ta wasa da zolayarta ta da saba sannan mukai sallama ta turo min account din na tura mata kudin da kuma dan ihisanin da nai iyar yi mata. Sannan na aje wayar na janyo akwatina ina hada kayan da nake son zuwa da su, sai da na gama sannan na tashi na shiga na yi wanka na saka atamfa na shafa yar hoda kadan na saka hijabi na nufo dakin Mama.   Fada na samu tana yi ma Aisha sai na samu guri na zauna har ta gama sannan na ce. “Mama zan koma asibitin” “To jikin na shi dai da sauki ko?” “Gaskiya da sauki sosai, domin ya daina jin zugin tun jiya, yanzu nauyi ne kawai yake masa, tafiyar ma dan mahaifiyarsa ta ki yarda ne shiyasa da an fasa” “Ai kara a aje din ko ba komai hankalinta zai kwanta, za ta fi samun natsuwa, Allah ya kara masa lafiya” “Amin Mama kin kara yarda aikin Abdallah ne ko?” “To akanki Halima waya isa ya taba dan gidan Hajiya?” Da karashe da murmushi ni kuma nai dariya ina mikewa tsaye, sai da nai mata sallama na shiga nai ma Inna sannan na fita, direban da ya dawo da ni dazun dan nai wanka ne na samu a waje. “Ah daman baka wuce ba?” “Cewa yai na jiraki har ko yaushe ne na dawo da ke” Murmushi nai na bude mazaunin baya na shiga na zauna ina tuna gargadinsa na dazun cewar na rika saka niqab. Muna isa cikin asibitin na kiran sallah azahar, ko da na shiga dakinsa na samu Siyama zaune saman kujera rike da wayarta sanye da rigar likitoci. “Matar Yaya sannu da zuwa” Na amsa ina murmushi. “Yauwa sannu kanwar yaya ya kike?” “Ba kalau ba tun dazun nake jiran driver ya kai ni gida wai sai ya dawo da ke sannan za akai ni Hajiya Siyama guda gida” Ta fada tana hararar bandakin, daga can cikin bathroom din ya amsa mata da. “Ba a dauko Hajiya matar Alhaji ba ke Hajiya kanwar Alhaji sai a dauko ki? Waya ce ki bari saurayin na ki ya barki, ko wani ya hanaki fitowa da motarki?” Ta matsa kusa da ni tana min rada. “Haka fa yake idan ya samu lafiya ba ma zaman lafiya ni da shi...” Nikam kasa cewa komai nai sai dariya nake. “Lims gulma ta take ko?” “A a” Ina amsa masa ya fito daga bandakin fuskarsa na ta haske irin ta sabon ango. A take ta dauki jakarta ta mike tsaye tana fadin. “Ni dai na tafi Allah ya bada sauki” Na amsa da amin ina binta da kallo shi kuma ya kabbatar sallah, hakan na bani damar tashi na shiga bandakin nai alwala na fito na jirashi har ya gama sannan na gabatar da tawa. Da kansa ya zuba mana abincin a plate daya spoon ma daya ya saka ya dora abincin gafena nikan sai kallonsa nake domin na lura tun jiya yana kokarin aikin da hannun. “Hannun ba ya maka nauyi sosai ne?” “Ba sosai yake min ba ina sai jin kamar jijiya ta rike ne” Ya debo abincin da kansa ya kai mu a baki sannan shi ma ya ci. Shi yai feeding dina har na koshi sannan na karbi plate din na aje, sai kuma yaja ni jikinsa ya rumgume. “Mata da miji idan suna zaune ba a zama nesa da juna ki koyi wannan yana kara soyayyar da shakuwa ko wani gurin muka je za mu rika tunani da kewar junanmu” Yana gama fadar hakan ya saka hannunsa cikin hijabina yana kokarin kaiwa kirjina. “Ba bari muji da akai wanka sun wanku” Ya fada cikin rada sai nai saurin raba jikina da nashi. “Baka da lafiya amman sai rashin ji kake....” “Ahen ahen ahen please nahhhh” Yayi maganar ta sigar shagwaba kamar wani dan 3 years sai marairaice min yake yana tabe baki irin yadda yara suke idan suna son abu. Nikam abun dariya ma ya bani wannan kuma ai ya zama ba jinya ba, duk yadda nai kokarin nisa da shi sai ya ce min ba haka ba. Sai da mutane suka fara shigowa sannan ya shafa min lafiya. A yau kam na ga yan'uwan Ahmad sosai a asibitin wata kila saboda gobe zai bar kasar ne yasa suke ta zuwa kamar ana turowa idan wannan ya fita wata ko wani ne zai shigo, duk basa shigowa hannu sake masu kawo abinci ko siyayya wasu kuma idan za su fita sai su ba ni kudi, mun gaisa da wasu da yawa daga cikinsu ya gabatar da mu kuma ya gabatar ni a gurinsa kowa sa cewa yake sun ji abu daga sama wai ba sanarwa. “Amaryar ce sai da haka shiyasa, sai da dabara” “Ato ko dai kwace kai wa wani ne?” Cewar wata tabashiyarsa tana dariya. “To wannan tsaleliyar matar zan samu a banza, ai kinsan sai na yi da gaske, duk masu neman wasa suka tsaya ni kuma nai muku na shirwa” Duk suka saka dariya har ni. Bayan sallah magariba na fara shirye shirye zuwa gida sai ya fara kallona kamar mai mamaki, nikam yau na rantse gida zan kwana ko da karbar sakon da Hajara tace min zata kawo idan an gama sallah isha'i. “Ba dai gida za ki je ba ko” “Gida mana, tun da gobe za mu tafi ai kara na ce gida tun yanzu sai na kwana can nai musu sallama” “A a ni ba zan iya kwana babu ke ba” “Can da da kake kwanan fa?” “Can da ai ban rabi jikinki ba, yanzu kuma na saba kwana biyu nan ba zan iya ba gaskiya, haramun ne ma” Ya fada yana riko hannuna. “A a Mama tace na dawo gida na kwana so that nai sallama da su Namra” Marairaice min yai. “Tsoro nake ji, kuma ciwon zai iya tashi idan baki nan” Yanayin yadda yai maganar yasa ban san lokacin da dariya ta subuce min ba. Shi kanshi dariya yai ya rumgume. “i love you Babe, gaskiya ba zan jidadi ba idan baki kwana a nan ba, amman babu yadda na iya, dole nai hakuri” “Yauwa na debi kala biyar na tafiya yayi? Kar na deba da yawa ya sama kauna” Na fada daman ina son nai masa tambayar tun jiya. “Ki kara” “Za mu dade ne?” “Ba sani ba tukuna, wata kila za mu dade wata kila ba za mu dade ba ya dangata daga yadda suka ba mu, amman kin san ko na ji sauki sai dai Hajiya ta dawo ta bar ku can ko?” “Saboda me? Ba kai aka kai ba?” “Kin san idan mutum ya dade yana jin kishin ruwa idan ya samu ruwan ba ya musu shan hankali” Kallonsa nai da kyau ina mamakinsa a dacan idan aka ce min Ahmad zai yi haka wallahi zan karyata. “Anya dai kai ne?” “Ni ne fa, ai dan iskan cikin gida ne ni, Allah dai ya bani lafiya” “Lafiya ai ta samu marar lafiya ba zai yi abunda kake ba” “Ina ma kika sani hmmmm Allah dai ya kai damo ga harawa, ya nuna mana mu dan yi nisa da Hajiya akwai kara'i” Ya karasa yana kwafa yana kokarin kyalkyalata, dariya nai sai yai kissing kumatuna yana shafa bayana, sai kuma ya dago fuskata ya soma tsosar bakina try to remove my Hijab, sai da nai da gaske sannan na raba jikina da shi. “Komai abunki dai dole ki jira driver ya zo or else ki kwana nan dan ba zan bari ki hau Napep ba ana kalle min kaya” A nan ma dariya nai ina ta jin kunyarsa sai dai na lura sam ya sauya kamar ba shi ba kunyar ma bata gabansa, hannunsa kuma baya zama kurum matukar muna zaune dakin daga ni sai shi. A dole nai jiran ya kira driver a waya ya iso, kamin na bar asibitin sai ya nemi na dora masa ruwa. “Kin ja min wanka matar nan duk kin lalata ni” Juyowa nai na kalleshi da mamaki ina kokarin fita, sai ya kanne min ido daya ya aiko kin da sakon kiss. Ni kam dariya nai na fice daga dakin. Ko da na isa gida na tararda Hajara na jira na, tana ganina taja hannuna muka nufi dakina na kori su Namra da ke ciki muka zauna saman katifa ta, sai ta bude jakarta ta dauko abun ta bude tana mika min daya bayan daya. “Wannan idan zaki kwanta bachi zaki shafa shi a kasan mararki, za ki ji sanyi kamar kankara, wannan kuma a kasa za ki tona ki zuba garshi a kasa sai ki saka wannan karamin a gabanki wannan kuma ki zuba a garwashin sai ki yi tsuguno za ki ji na cikin ya nairke kamar mai kuli karki taba ki barshi haka ya kwana a jikinki sai da safe ki wanke da ruwan dumi, wannan garin kuma da madara za ki sha, shi kuma wannan na kwayun ki hade shi duka da ruwa hmmmmmm to kwanta ki yi bachinki ba kya bukatar komai Hajiyata shi wannan hadin ma ba a bawa mai kishiya saboda gudun hada fada ko haddasa saki, sai dai idan kun dawo ki yi dilke da sauran gyaran jiki” Rumgume ta nai ina murna idan ba kawar amana kawar arziki ba wa zai maka wannan? “Na gode sosai Hajara” “Babu komai Allah dai ya baku zaman lafiya” “Amin ya rabbi” Na rakata har gurin motar mijinta mu kai sallama na dawo cikin gida, shi da na sha tun cikin dare na sha da wanda tace na yi tsuguna duk nai. Ni kaina sai da na soma tabbatarda lallai akwai alamun maganin mai kyau ne, domin tun a jikina na ga canji fitsari da nake ma ina yi ina jin zafi abunda ko da ina budurwa ban ji ba. Tun da farar safiya ya kirani muka gaisa yace na bawa Mama wayar ya gaisa da ita yai mata bakwana sannan na kaiwa Inna ita ma sukai bankwana sannan ya aje wayar bayan ya fada su Namra ba za su je ba yau wai zasu mana rakiya airport. Misalin tara ya aiko da mota, gaba daya sai naji wani iri kamar kar na tafi saboda kewa ko zuwa wata area ma ina jin kewa balle kuma tafiya ce ta kasa da kasa, kamin na shiga motar sai da nai ta kuka ina jin kamar idan na tafi ba zan dawo ba, ba su Namra kadai suka raka mu ba har da Aisha da Hafiza. Kai tsaye gidansu Ahmad din aka wuce da mu mun ga tarba ta musamman Hajiya kamar ta hade ni ita da sauran mutanen da suka zo musu bankwan, ban saka Ahmad a ido ba sai da zamu bar gida sannan ya shigo dakin Hajiya domin ni a dakinta ta aje ni su Namra suka tsaya falo. Ya shigo cikin shiga ta alfarma kamar ba shi ba ko kunyar Hajiya be ji ba ya zauna kusa da ni yana karbar rubutun data miko masa, sai da ya shaye tass sannan ta bashi wani ya shanye ta dauko masa ruwan addu'a a nan kam yai fir wai ba zai sha yawun wani ba, rubutun ma dan kar ya mata gardama ne. “Ni naga ma abun da sauki sosai Allah ya kara lafiya” Ta fada cike da jindadi sannan ta fice, shi kam kamar yana jira ya mika hannu ya riko ni. “I miss you” “Dakin Hajiya muke fa” Na fada ina kallon kofa domin na san ba karamin kunya zan ji ba idan ta gan mu. Dariya yai ya saki hannuna nawa. Ba mu wani dade sosai ba muka fito daga cikin gidan har na nufi motar da muka shigo sai Siyama tace. “A a ba ita zaki shiga ba ga motarmu can” Ta nuna min wata bakar mota wacce Ahmad da Hajiya suka shiga, a tare muka nufi motar sai ga Amal ta fito daga wacan motar da gudu tana fadin wacce na shiga zata shiga. Ina kokarin yi mata fada Ahmad ya bude front seat ya ce ta zo, a tare da shi ta zauna gidan gaba, ni da Hajiya da Siyama kuma muka zauna a baya, ina ta jin kunya sai dai na lura Hajiya bata kula wannan ba sai ma kokarin fira take da ni idan an kai wani gurin tace min ga kaza nan. Sai da muka isa sakkwato muka huta a wata hotel sannan muka wuce airport, ko da muka isa ya rage sauran minti talatin jirgin ya tashi zuwa Abuja, a nan mukai duk abunda ya kamata sannan mukai sallama da su, Siyama har da hawaye ta rumgume dan'uwanta tana masa addu'ar samun lafiya sannan ta rungume Hajiya nima ta rumgume ni. “Matar yaya ki kula min da yayana kin ji” “In-Sha-Allah” Daga haka mu kai sallama da su tare da yarana sannan muka shiga cikin jirgin ina ta jin kewar gida, kujerar da ke kusa da window ce tawa sannan ta Ahmad sai kuma ta Hajiya a baya kuma ta wani ce da nai zaton direba ne domin shi ya tuko mu duk kuwa da shigarsa bata nuna hakan ba. A lokacin da jirgin zai tashi duk muka saka belt sai jin dagawarsa nai hakan kuma ba karamin tsoro ya saka min ba abunka da wanda be taba shiga ba. Ina ta addu'a domin gani nake na yi kusa da mutuwa tun da jirgin ya daga sama. Ba zan iya sanin awanin da muka dauka ba kamin mu isa Abuja wata kila ma yan mintuna ne tun da ance jirgi sauri ne da shi, sai dai naji Hajiya na fadin mun yi sauri. Sallah akwai na san mun yi a wani gida da nake kyautata zaton na yan'uwansu Ahmad ne, ko awa daya ba mu yi ba a gidan muka koma airport din abinci ma sai a can muka ci, gaskiya garin Abuja na da kyau mayan gidaje ta ko'ina ga tituna gwanin burgewa ga yanayin garin da sanyi ba kamar Sokoto ko Zamfara ba. Manyan shuke shukensu ma abun kallo ne, airport din ma gwanin burge wa kowa ka gani tsab da shi sai hada hada ake ba ruwan kowa da kowa. Wani jirgin muka shiga ya daga da mu zuwa kasar nasara.... Na sha bachi kam sosai a cikin jirgin a duk lokacin da zan farka sai na gan ni a kafadar Ahmad, can kuma ya tashe ni ya bani tea a wani karamin kofi da biscuit shi ma ba wani mai yawa ba, bayan na gama sha wata mace mai sanye da uniform ta zo ta karba. Mun dade sosai muna tafiya kamin mu isa, a iya sanina mun baro Nigerian da yamma lis amman da muka sauka nan sai na ga safiya ce fal, ga wani uban sanyi mai ratsa kashi. Cikin airport din Ahmad ya fiddo rigar sanyi ya saka min a saman abayar da ke jikina ya bani safa na saka na a hannuna a kafa ma ya bani na saka sannan na cire talkamina ya bani wasu talkamin masu rufe na saka shi ma ya saka kamar yadda Hajiya ma ta saka sannan muka nufi gurin tex. Kusan tun da muka bar airport din sai na ce ban hadu da bakin mutum ba har muka isa hotel din da aka kama mana bana aikin komai sai kalle kalle, ashe a Abuja ance min baki ga komai ba yanzu ne kallo yake. Komai na su a cikin tsari yake gwanin ban sha'awa ga bin doka da oda, tun da muka sauka cikin jirgin Ahmad ke rike da hannuna har muka isa dakinmu da aka bare mana. Ina zaunawa bachi yace sallamu alaiku, sai jin nai yana tashina. “Lims ta so mu yi wanka sai ki yi bachin mu kuma za mu karasa asibitin” “No nima zan bi ku” “A a Hajiya tace na barki ki huta” “Da gaske” “Ai ba zan miki karya ba” “Yaushe tace ban ji ba kuma ai tare muka shigo nan” “A waya ta kira ni” Ya nuna min wayarsa. Yana kokarin rika hannuna. “Taso muje mu yi wanka mu yi sallah jirana take” “To ka shiga ka fara yi sai....” “A a nan ai babu wanda zai sa mana ido ki saki jikinki” “Aa wallahi ba zan iya ba a yanzu” Na fada ina girgiza masa kai, sai ya dafa kaina. “Why da rantsuwa? Wata rana ke zaki bukaci haka ma” A gabana na cire tufafin jikinsa sai da na kawarda fuskata ya daura tawul ya wuce bandakin ba tare da jin komai ba, ni kam gaba duk naji wani iri ji nake kamar wacce bata mu'amala da wani ba haka na ji, gaba daya komai sai na koma kin sabo musamman Ahmad da na lura lamarinsa azimun ne. _________________ Na so na karasa pages din kamin sallah amman Allah be nufa ba, dan haka zamu tafi hutu sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya amince mana In-Sha-Allah. 7/25/21, 4:10 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 6️⃣2️⃣ Sai da ya fito daga wankan sannan na shaga, da sabulu kawai nai wankan domin babu soso a ciki sabulun ma ba irin na mu na Nigeria ba ne, bayan na gama na daura karamij tawul din har na nufo kofa na fito sai kuma wata zuciyar tace min kara dai na maida tufafim jikina kar na fita da wannan guntun tawul ai da kunya.   Ina kokarin daukar kayan na saka sai jin nai an yaye labulen bandakin daman ba kofa ba ce bandakin na glass ne sai lalulen da aka saka dan kare wanda yake wankan. “Ba ki gama ba ne” Ya fada yana kallona tun daga saman kaina har kasan kafafuwana. Tsaye nai da kayan ka kasa sakawa na kasa ajewa na kasa fitowa wata irin kunya mai tsanani ta rufe ni. Sai da ya hade yawu sannan yai murmushi ya juya yana fadin. “Fito ki saka tufafin ki, ni ba wani abu zan miki ba” Kallon jikina nai tawul din karami ne sosai ta yadda idan na duka za a iya ganina idan kuma ban rike shi da kyau ba zai iya subuce min ya fadi. A haka na daure na fito ganin babu wata mafita na nufi gurin akwaitina da zimmar na fito da doguwar riga na saka, sai jin mutum nai a bayana ya dora hannayensa saman kafadata yana sharce min ruwan da ke kai bakinsa saitin kunnena ya rada min. “Ki daina jin kunyata, ni mijinki ne kuma zaki wahalar da kanki ne kawai, ni kaina ina da kunyar amman akan halila gaskiya babu wannan ina sakewa nai yadda nake so, ni da ke abu daya ne a yanzu” Ya karasa tare da tsosa kunnena, wani yarrrr na ji rabon da na ji irin haka har na manta, kamar wacce aka daurewa baki haka na zama da kansa yaja hannuna zuwa gaban akwatinsa ya bude ya dauko wani mai mai kamshi ya zuba a hannunsa ya fara shafa min kamar nai magana sai kuma a kasa, haka ya ji ko'ina na jikina ya shafa min man har a cikin yatsun kafata, sannan ya fara kokarin kwantar da ni saman gadon a nan kam Allah ya bani ikon magana “Ban yi sallah ba” Bakin da nai magana da shi ya kurawa ido gaba daya idanuwansa sun canja kana kallonsa kasan natsuwarsa ta dade da barin jikinsa, can kuma ya kalli cikin idona sai kuma ya sake kallon bakina tare da kai hannunsa ya taba lisp din a hankali sannan ya sake ni ya juya ya nufi bandaki, ni kuma na mike tsaye daidai ina gyara tawul din dake kokarim subucewa gaba daya, kamar an koroshi haka ya dawo da gudu ya rika ni ya fara kissing din bakina yana wani irin haki yana shafani kamar wanda aka ce za a raba da ransa idan be sumbance ni ba. Ban san iya lokacin da mu ka dauka a haka ba, tun muna tsaye har tsayin ya gagara muka kwanta saman gadon, wanda hakan ya bashi damar kai hannunsa a kirjina yai wasa da shi yadda ransa yake so. Sai da aka soma kwankwasa kofar sannan ya daga ni da sauri ya nufi kofar sai dai be bude ba sai ya tsaya daga jikin kofar. “Waye?” Ya fada yana cizon lisp dinsa tare da aje numfashi a hankali. “Kai fa nake jira tun dazun” “Hajiya gani nan zuwa yanzu please I'm sorry” Ya fada yana maida numfashi sai da ya tabbatar ta tafi sannan sake nufo ni yana murmushi. “Na manta Hajiya na jirana idan na fita zance ke kika tsayar da ni a nan” Bance masa komai ba nai kasa da idona, wannan karon kafafuwansa biyu ya raba ya kai bakinsa gurin hancina sai da ya tsotse shi tasss sannan ya dagani ya fara kokarin cire tufafin jikinsa. Juyaawa nai na bashi baya tare da yan Bedsheet din na rufe jikina, ina jin sautin dariyarsa da kuma maganganun da yake fada na rashin kunya har ya shige bandanki, nima dan murmushin nai ina lumshe ido, ni kaina a yau wani shauki ya ziyarce ni wanda na manta rabon da na ji irinsa, wata irin natsuwa da annashuwa suka sauko min, na kasa daina murmushi har ya gama wankan ya fito, ya sake shiryawa cikin wasu riga da wandon ya fesa turare sannan ya kwanto bayana yai kissing din gefen wuyana yasa hannunsa ya kama hannuna yatsunsa cikin nawa. “Ki yi bachi ki more” Juyowa nai da sauri da zimmar nai masa magana sai bakina ya gogi nasa numfashina ya gauraya da nasa, babu abunda yake kallo sai bakin nawa. “Talk” Ya fada bakinsa na gugar nawa, a dole nima a haka nai masa magana bakina da nasa na gogar juna. “Ina son naje nima ai” “So kike mu je can mu taru mu lalace? No za ki tsaya a nan ki huta kamar yadda Hajiya tace idan sun ba ni gado bayan kin huta zan aiko a dauke ki, kuma zan siyo miki sabon line da zaki rika amfani da shi a nan so that ki kira Mama ki sanar mata mun iso” Ya karasa tare da kissing dina sannan ya daga ni ya nufi akwatinsa ya rufe ya dauki abubuwan bukata ya saka aljihu,sai kuma ya sake nufo ni da kansa ya dago ni ya rumgume ni ya sake kissing dina sannan ya fita tana dago min hannu. Da kallo na bishi har ya fice ina mamakin hali da dabi'unsa idan aka fada maka Ahmad zai iya zanzarewa yai haka saka rantse da Allah karya ne kace ba zai aikata ba, ni a rayuwata ma ban taba auren namiji marar kunya kamar Ahmad ba, shi komai nasa kirkiri yake kuma da gasken gaskiya to wa ma zai ganshi yace shi aka kawo jinya? Fitarsa da kamar minti bakwai aka kwankwasa kofar dakin Tashi nai jikina nata kamshin turarensa na dauki rigata na saka sannan naje na bude, wata farar mace na gani dauke da tray din abinci ta miko min, sai na rufe dakin na juyo na dawo, burger burger and snacks sai drink da safafen kwai, ban kula abinba na nufi bandaki da murmushin daya kasa bari kumatuna, wanka nai sannan nai alwala na fito har lokacin murmushi nake ina jin wani irin shaukin kaunarsa a raina. Haka na bi na rama ko wace sallah sannan bude abunda aka kawo na ci wanda zan iya ci na bi lafiyar gado na kwanta bachi son raina nai ta bachi kamar dan ni kadai akai bachin. Ban farka ba sai kusan la'asar shima kuma bugun kofar dakin ne ya tashe ni wannan karon wata makar mace ce mai zubin yarbawa ta kawo min tuwo da miyar taushe ga namomi a ciki na yi mamaki sosai ashe a acan ma ana samun irin abincin mu, sai da muka gaisa da ita na karba tana tambayar daga wani garin na zo nan. “Gasau Zamfara” Sai ta amsa min da ta san garin sannan tai min sallama ta tafi, duk da ban ji kiran sallah ba dana duba agogona ya nuna min hudu har da wani abu a lokacin, hanzarin shiga bandakin nai na yi alwala ya fito nai sallah sannan na ci abincin na koshi na sha ruwa na sake bin lafiyar gado na kwanta na cigaba da bachina. Dana auna lokacin magariba yayi sai na tashi nai sallah sannan na jira isha'i itama nai, ina ta jiran Ahmad ya aiko a dauke ni be aiko ba har dare ya soma misalin tara matar nan ta sake kwamkwaso dakina ta kawo min doya da miya, ina ci ina lumshe ido domin doyar ta yi laushi sosai ga dan zaki zaki kana aji kadan wata kila sun saka madara ne dan alamu ya nuna haka yadda doyar tai fari.   ‘To fa komai a nan banza ne, ko a nigeria da rayuwa take da tsada ai wasu na kan yi doya da madara da miya balle a nan da komai yake banza’ Na fada a raina ina ta kara auna doyar da miyar kifi, bayan na gama cin abincin ina kokarin kwantawa sai na ji an buga kofar, da kuzarina na nufi kofar ya bude, sai nai arba da Hajiya tana sanye da riga da wando sai karuwar rigar sanyin data dora sama kamar ba ita da dankwalin da tai rolling kanta da shi har da su gilas, kasa nai da kaina na gaisheta ta amsa min tana cire madubin idon sannan na bata hanya ta shigo ciki. “Za mu je da ke can gurin Gwarzo ne” “Jikin nasa da sauki ko?” “Da sauki sosai ba su dai ba su dai babu wani result ba amman kana ganinsa ai kasan da sauki kan dan yace ya daina jin komai yanxu, ina jin dai har da addu'ar nan da muka hada masa da rubutu, kin san wani lokacin iska ma suna haka fa” “Haka ne Hajiya Allah ya kara lafiya” “Amin ki saka rigar sanyinki mu tafi” Na mike na dauko rigar sanyin da Ahmad ya saka min na dora saman doguwar rigata sannan na dauki mayafin abayar na rufe kaina muka fita tare da Hajiya. Taxi muka shiga amman kamar wandanda suke a cikin motar gida haka muke a cikin taxin, ni kam bana aikim komai sai kallo ashe garin ya fi kyau da dare ko'ina haske ne ga mayan allunan talla kala kala har da na jaruman india. “Halimatu?” Hajiya ta kirani sai ya amsa a hankali na juyo na kalleta. “Zan tunatar da ke wani abu ban sani ba ko kin sani ko kuma kina kan hanyar sani ne, mijinki yana da kishi sosai, dole sai kin yi hakuri da shi ta wani bangaren kuma ki yi kokarin kare masa mutuncinsa, mijinki yana son girmamawa, ya fada min cewar yana kaunarki kuma yana matukar tausayinki, ki yi kokari ki kare martabarki karki bari kaunarki da tausayinki da ke zuciyarsa ya gushe, sannan kuma mijinki yana da fushi sosai ba duk abu ne yake bata masa rai ba, amman idan ransa ya bace baya sauraren kowa har sai ya sauko, amman kuma baya riko daga fushin nasa ya sauka shikenan za ki ga komai ya wuce, ki yi ta hakuri da shi wani lokacin yana da wuyar mu'amala duk da na lura yana sonki sosai, sai dai kasancewar ki bazawara zai saka ki ga ya miki wasu abubuwan da za ki ga kamar yana kyamarki ko baya son ki, sai dai na san idan kika yi hakuri komai zai wuce, kanwarsa ma na nan Siyama, duk da tana da girma amman bata da hankali da natsuwa na magana da mu'alama wani lokacin, ita ma sai kin yi hakuri da ita, ni kaina da nake mahaifiyarsa sai kin yi hakuri da ni, nima wani lokacin ina da tawa matsalar kin san kuma duk wanda yace zo mu zauna to yace zo mu saba ne dole wata rana sai an samu rashin jituwa a zamantakewa, ina fada miki wannan ne sabod bana fatar wani abu ya hada da Mijinki har ya kai ga kun rabu Allah ya tsare, ina fatar ki zama matarsa ta har abada, matar da mutuwa ce kawai zata raba ku, ina matukar jindadin yadda nake ganinki ke da mijinki, sai nake jin kamar be tana aure ba sai a yanzu ne zan yi suruka” Na natsu sosai na saurari each and every word da ya fito daga bakinta, a lokacin daya na ji hawaye na cika idona, a yau Hajiya ta yi min abunda wata uwar mijin bata taba min ba, ta nuna min lallai ƴa ta dauke ni. “Kada Allah ya nuna min ranar da zan yi miki wani abu na bacin rai Hajiya” “Amin” Ya miko min line. “Gashi yace a baki, na sa ne ki yi amfani da shi kamin a samo miki na ki” Na karbi line ina dubawa sannan na ciro wayata na bude na cire dayan line na saka nasa. Katuwar asibiti ce mai kama da ma'aikata da dare ne amman ko'ina na gurin kamar rana, gata fes an gyara ko'ina kamar ka kwanta. Ni dai bana aikin komai sai rabon ido ina bin Hajiya sai jin nai an kamo hannuna ta baya a hankali da sauri na waigo sai na ganshi cikin rigar asibitin mai blue yai min alama da nai shiru sannan ya saki hannun nawa yai hanzari ya cin ma Hajiyarsa ya sha gabanta. “Hajiya ga ni nan fa” Tsaya tai tana masa kallon mamaki. “Miye haka zaka fito daga dakinka kana a matsayin marar lafiya?” “To ai na ji sauki Hajiya zaman daki ni kadai ba dadi” “Allah ya kyauta ni zan koma na kwanta na gaji sosai” Har ya juya sai ya rumgume ta yana mata godiya. “Ya kamata kam tunda kika zo baki runtsa ba Allah ya biyaki” “Amin Allah ya maka albarka ya baka lafiya” Ya fada tana murmushi sannan nima tai min sallama ta juya daga ni har shi binta mu kai da kallo sai ta fice gaba daya sannan ya sake kamo hannuna ni ko na kalli jama'ar dake kai da kawo a wajen ina jin kunya. “Ke nan ba ruwan kowa da kowa” Ya fada yana nuna min wani dake rike da hannun matarsa, sai na dan matsa kusa da shi ina kallonsa uniform din sun masa kyau ya saje a cikinsu kamar wani bature cike da kulawa na ce “Ya jikin ka?” “Na ji sauki” “Amman likitocin ba su fitar da result din ba haka Hajiya tace” “Sun fito da result mana” Na kara kallonsa da sauri. “Da gaske?” “Eh” “Me suka ce?” Sai ya kawo kunnensa kusa da nawa ya rada min. “Sun ce wai ina da ciki ........” Ban san lokacin da dariya ta subuce min ba haka na bude baki kamar mahaukaciya na fara dariya babu kakkautawa kowa sai kallona yake, shi ma dariyar yai ya rumgume cike da farinciki ya saka kaina a kirjinsa ya rungume ni tsantsan. “I love you” Daga dariya na koma hawayen da ban san na me bane jindadi ko akasin haka? Ban sani ba ko abunda Ahmad yake min zai daure ban sani ba ko rayuwarmu zata cigaba da tafiya a haka ko kuma na dan lokaci ne, amman tabbas shine kalar mijin da na dade ina mafarki, mai sani dariya da nishadi a kowane lokaci, mijin da zan kallo na yi farinciki na jidadin ina aurensa mijin da zan kalla ya burge ni wanda iya yai kwalliya zan ji nishadi a raina, mai kula da ni mai damuwa da matsalata mai tausayina kuma mijin da yan'uwansa za su kaunarce ni mahaifiyarsa ta dauke ni kamar yarta ashe wannan ranar zata zo? Allah kasa wannan farincikin nawa mai daurewa ne. A zuci nai maganar a fili kuma sai na sauke numfashi a hankali ma dago muka gada ido naja hancinsa ina murmushi, sai wani abu yai min da fuska kamar da gaske ya ji zafi. Yana rumgume da ni muka shiga dakinsa da aka tanadar masa, gadon asibitin ba daya ba ne da iirin namu na naija kirarsa da fadinsa ba daya ba ne, komai an tanada a adakin sai wani dumi kake ji gwanin dadi kamar ba a asibiti ba, da kansa ya zaunar da ni saman gadon sannan ya zauna yaja ni zuwa jikinsa ya rumgume can kuma ya ji kamar rumgumar bata masa ba sai ya kai hannu ya cire rigar sanyin da ke jikina. “Tun dazun kina nan cikin raina sai mamarinki nake” Ya fada yana sauke min numshinsa a fuska, ni kuma na lumshe ido ina sauraren sakwannin da yake aika min, da na ji abun na kokarin wuce gona da iri ne yasa na tashi tsaye. “Ina ganin ya kamata ka kwanta saboda na huta” Kallona yai da wasu rikitaccin idonsa sai nai saurim kawarda fuskarta na zauna saman kujerar da ke kusa da gadon. “Ke yanzu na miki kama da wanda zai kwanta yai bachi? Taso mu kwanta” Ya taso ya janyo hannuna, duk yadda na so na ki kwana a saman gadon hakan be samu ba, domin ba aminta ba ni da shi muka kwanta saman gadon a tare, aiko bachin da be yi ba kenan sai kusan daya na dare, ni kam tun ina jin hannunsa na kai sako a jikina har bachi yai gaba da ni. Ko da na farka sai ganina nai ni kadai a akan gadon ya lullube ni da Bedsheet shi kuma yana saman kujerar zaune yana tasbihi da yar carbin nan da ake makalawa a hannu. Saurin zabura nai mike zaune sai ya sakar min murmushi. “Good morning” Sauka nai saman gadon ya nuna min bandaki na shiga, na juya kan fanfon ya na ji zafi dayan bangaren kuma sanyi, sai da na kira shi ya zo da kansa ya hada min sanyi da zafi sannan nai wanka na fito na sallah a kan carpet din dana gani a gurin, ban maida under Wears dina ba domin sun lalace sai na saka abayar kawai nai sallah. “Me kike son ki ci?” “Duk abunda zaka ci” “Ni ke kin ishe ni ai ba sai na ci wani abu ba” Na yi kasa da kaina sai yai murmushi ya miko min hannunsa. “Fada min mana sai na saka miki order” “Zan samu irin abincin jiya?” “Uhmmmm amman ba ki tunanin cin wani abun dabam, ai kin ga nigeria kika baro, ya kamata ace kin dandana abincin su na nan, da safe ma rasa nai mi zance a baki shiyasa nace su kawo miki burger da snacks, da rana kuma nai miki order irin naki” Na zauna saman kafafuwansa kamar yadda ya bukata sannan yasa hannayensa na zagaye wuyansa da su. “Ashe ana samun abincin nigeria a nan” “Eh amman akwai tsada sosai” “Zo muje wani restaurant din mu ci abinci a can” Ya fada yana wasa da yatsun hannuna. “Za su bari ka fita?” “Eh mana kayan gida zan saka sai mu tafi” Haka kuwa akai ya saka tufafinsa wando da riga ya dora rigar sanyi sama nima ya saka min tawa sannan ya rika hannuna muka fita tare, taxi muka shiga shi ya fadi inda zamu je mai taxin na sauke mu ya ciro kudin kasar ya mika masa sannan ya maida wallet dinsa muka nufi wata hotel wacce ba tai girman wacce muka sauka da farko ba. Sai da ya biya komai ya nuna id dinsa sannan suka ba mu makullin daki, wannan dakin be yi girma da haduwar wacan dakin ba, a nan ya kira wata number da hausa ma naji yana magana da matar sannan ya fada mata ta kawo mana tuwo da miyar taushe zai aiko mata da address din inda yake ta waya sannan ya bukaci ta sake kaiwa a inda ta kai jiya, number dakin daya fada ne yasa na gane Hajiya za a kaiwa. Sai da ya gama tashi wayar sannan na saka number Mama na kirata muka gaisa har take shaida min a can yanzu karfe uku da rabi ne na asuba sabanin nan da yanzu tafiyar ta waye ma. Hakan yasa nace karta tashi kowa ta bari idan rana ta yi sai na kira ta mu gaisa da su Namra, da kansa ya bukaci na bashi ya gaisa da Mama tai masa ya jiki sannan sukai sallama. Sai da muka ci abincin muka koshi sai labari ya canja, ashe a cin abincin kadai muka zo har da daukar wani sabon karatu mai darasi mabanbanta, tun yana yi ina hanawa har na gano da gaske yake a dole kyale shi da abunda yake halalinsa, ko wace kusurwa ta jikina sai da Ahmad ya isar mata da sako, ko wane bangare na jiki inda jini da jijiya ke aiki sai da yasan da zaman Ahmad a wannan safiyar, ba ma kamar bakina da kirji domin numshina har wani nisan zango yake ya dawo, at first nima na mori abun kuma na taimaka masa yadda ya dace domin ni kaina nayi marmarin rayuwar, kamin mai aiko sakon ya iso da kansa. Waya aike ki? Miyasa kika yi? Waya ce ki aminta tun yanzu? Shine abunda nai ta mamaitawa akaina, kusan ko a lokacin da nake budurwa ba ji azabar da naji a yau ba, wata kila saboda abunda na sha ne ko kuma saboda na hadu da Gwarzo namiji ne, wanda ya dade be hadu da abunda ko wane lafiyayen namiji yake muradi ba kamar yadda ya fada min a cikin abunda ba zan iya jiransa da yana maye ba ko kuma bachi balle na ce mafarki, a zahirin yai ta sakarmin wasu kalaman da sun fi karfin hankalina da tunani balle har na haddace su, da gasken gasken hawaye na ke da idanuwa na azaba, kamar an saka wuka an yanke gurin haka naji, wani zugi na tashin hankali ke fitar min har kasan kafafuwana, jinin da ya zubar min har tsoro na ji a zatona wani abu na gurin ne ya samu matsala babu abunda na tuno sai maganar Hajara cewar na shirya dan sai na fadi wanda ya aike ni lallai kuwa yau zan fada. Unkura nai na tashi amman na kasa sai naji kamar an zare min lakka a jiki. “Sannu” Ya fada yana shafa fuskata kamin ya sumbace ni, sai kuma yanjo ni jikinsa ya rumgume, saukar hawayensa na ji a cikin gashin kaina hakan yasa na dago da sauri na kalleshi sai ga fuskarsa da murmushi idonsa a lumshe sai wani abu yake da baki kamar wanda ya ci yaji. Maida kaina nai jikinsa na kwantarda kaina. “Da gaske ke bazarawa ce Lims? Da gaske ke kika haifi su Namra? Ko cs akai miki aka cire su? No wait da gaske kamin ni akwai namijin da yai mu'alama da ke?” Na yi shiru na lafe a kirjinsa kamar ba ni. Sai ya soma shafa bayana. “You're beyond my expectations, ban san abunda zan fada miki ba ban san kalmomin da zan hada na furta miki ki gansu ba, amman lims when i say kin hadu ina nufin haduwa makura iyakar kurewa, i just can't believe kin taba aure Wallahi balle ace kin haihu, ke din ta musamman ce” Ya fada kissing my hand, sannan ya dago ni daga kirjinsa ya kurawa fuskata ido sai kuma ya sake rumgume ni sosai yana sauke ajiyar zuciya. “Idan zan yi ma Allah godiya sai na rasa da wace kalmar zan yi amfani, ta ina zan fara gode masa? Al-hamdulillah thumma Al-hamdulillah” Ya furta yana kara lullube min jikina da Bedsheet din da muke rufe ni da shi. “Ya kamata mu koma asibiti kar Hajiya ta zo bata same mu ba” “A a sai mun gaji tukuna” Ya fada yana kara rumgume sai kokarin komawa ruwa yake da sauri na bar jikina ina jin kamar zan fashe da kuka. “Mum gaji da Wallahi” “Kin gaji dai ke” Ya fada with smile on his face, sannan ya sauka saman gadon ya nufi bandaki. “Bari na ga kan toilet din na hada miki ruwa” Ba mu bar hotel din ba sai kusan la'asar a nan mu kai azahar da la'asar sannan muka koma asibiti, babu kalar albarka da be saka min ba babu irin godiyar da be min ba, each and every 30 minutes sai ya tambaye ni wai daman haka zauwara su ke? Shi ko yan matan da yake aure be taba arba da wacce ya samu abunda yake so a gurinta ba kamar yadda ya samu a gurina, har fada yake wai lallai mata suna suka tara. Da muka dawo cikin asibitin tafiya kawai nake ina daure ina nuna kamar babu komai amman ni na san akwai komai ba irin na safiyar wacan daren amarci nawa dana kasa tafiya daidai ba ne, wannan kam ina tafiya sai dai ina jin azaba sosai da sosai. Tun da Ahmad ya girma a nan sai yai wayo kusan kowace safiya sai mun tafi hotel din da sunan karyawa a can kuma bama dawowa sai dare, tun ina jin nauyin kar Hajiya ta gane har na barwa Allah domin na lura ko sau daya bata taba tambayar ko a waya yana ina ba? Ko kuma tace daga ina muka dawo idan mum tararda ita a asibiti, sai dai shi ne ma zai ce yau guri kaza mukaje na ga gari, alhalin ba gaskiya ba ne, idan na kalleshi sai ya kanne min ido daya ko ya daga min gira. Satin mu daya a asibitin sannan suka sallame shi bayan sun yi bincike iya binciken su ba su gano komai ba, sai dai hakan be hana su dora shi akan magani ba, tare da wasu shawarwari ciki har da motsa jiki wanda suka ce yana da kyau ga lafiya. Washe garin ranar da suka sallameshi ne muka kamo hanyar Nigerian cikin farinciki da kaunar juna, Hajiya kam tun kam mu dawo ta sanarwa kowa cewar danta ya samu lafiya, a raina nace ni kam ai na fi kowa sanin ya samu lafiya kam, ba mu bar kasar ba sai da Ahmad ya dauke mu ni da ita muka shiga wani shagon siyerda kayan sakawa da na ado muka siyo sannan muka shiga na yara na siyoma su Namra da Amal teddy Adnan da Aiman kuma mashin din wasar yara da wani madubi mai canja kala, Inna muka na siyo mata turare ita da Mama. Sai a lokacin na gane ashe kayan mu na nan sun fi nasu na can arha domin duk abunda muka siya idan Ahmad ya fada min kudinsa a kudin Nigeria sai na jinjina abun. Karfe 2:00pm daidai jirginmu ya sauka a Abuja babban birnin taraiyar kasa FCT. _____________ Fatar kun yi sallah lafiya Allah ya maimaita mana 😍🙏 7/26/21, 1:29 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 6️⃣3️⃣ Mun iso Zamfara cikin aminci da farinciki, tun airport yan su Ahmad suka tarbo mu da muka iso sai muka tararda gidan kamar ana wani karamin ba a gaskiya na yaba da yadda yan'uwan Ahmad suke nuna kulawa da son zumunci. Mun tarar an mana girki ga lemu kala kala gwanin sha'awa, a nan na kara sanin wadanda ban sani ba daga familynsa su ma muka suka san ni. Sai da na huta na ci abincin sannan Siyama ta shigo tace min Hajiya tace idan na kintse za a sauke ni gida, aiko da sauri na tashi daman tun dazun babu abunda nake sai tunanin gida da mamarin ganin nawa Familyn. Direbansu aka saka ya kai ni har gida a nan wata murnar ta barka duk da kasancewar mun dawo Tuesday ne yara suna makaranta amman su ma manyan hakan be hana su murna da ihun ganina ba. Ban tabbatar da na yi missing gida ba sai da na ganni tsundun a ciki, wai har na yi tafiya na dawo sai abun ya koma min kamar a mafarki lallai rayuwa tana da ban tsoro kuma lallai duk abunda yai farko dole yana da karshe. A nan ma an shirya min wani abincin irin namu na daidai gwargwadon hali bancin Kifin data saka a shimkafar jalof har da nama ta siyo ta soya min ta siyo min lemun Coke, a yadda naga tana ta murna da ganina ni kaina na san ta yi marmarina. Gidan be kara haukacewa ba sai da su Namra suka dawo daga makaranta a nan wani sabon murna ya tashi suka dinga hawa suna sauka kowa Momy Oyoyo, wani irin farinciki naji ya baibaiyeni at least nima dai abun alfahari ce ga iyalaina duk da ban yi musu wani abun na gwaninta ba ko na azo a gani. Ana gama sallah magari sai ga kiran Ahmad ya shigo wayata, bayan mun gaisa yake tambayar yaushe na tafi wai ban nemi izininsa ba ni kam dariya ma abun yaban. “Ban fa tare ba” “To miya raba dambe da fada? Ko baki tare ba ai igiyar aurena tana kanki, kuma tarewan zai wuce kwana biyu ne ko uku” Na zaro ido. “Wane irin kwana uku sai kace yar roba? Haba dai ina laifin wata uku hudu” “What......! Ai ba zan iya barinki ko wata daya ki yi ba, kin san fa ina bukatar kusa da ni kuma ga wannan dan uwan naki zai iya zuwa fa” “Haba dai ai mahaifiyarsa ta riga ta shiga tsakani, dazun Mama ke fada min wai karshen watan nan za a sake shiga kotu, ga Hajiyar ma lafiya bata isheta ba, yanzu ai ba ta nawa yake ba, ai na yi aure dole zai daga min kafa” “Baki san halin Namiji bane Lims maza suna da wani irin hali, idan suna son abu ko?hmmmm ni dai gaskiya ba zan iya bari ki yi wata uku ba a cikin watannin nan Allah kadai ya san wanda zai ganki ko bayan shi Abdallah wata sani ko wani dabam na nan yana dakonki” Dariya nai sai ya fara rantsuwa. “Wallahi Allah kuwa ba zaki gane ba ne, ni kuma bana son ana ganinki kuma idan kina gidanku ba natsuwa zan yi ba kara dai na san kina dakina na rufeki abuna” Na sake dariya, mun dade muna fira dashi kamin ya bijiro da fitinarsa nai masa sallama na tashi nai sallah isha'i... Akwai wani irin natsuwa da kwanciyar hankalin da farinciki a cikin aure musamman idan ka dace, akwai akasin hakan kuma ga wanda be yi dace ba kamar yadda nayi da farko, ko da yake ko a yanzu ina kyautata zaton dacewar ne kawai da alamun da na gani a gurin Ahmad wanda ban gani ba a gurin wani namijin. Sati biyu da dawowata amman duk wanda ya gan ni a yanzu sai yayi magana cewar na canja jikina yayi kyau fuskata har wani sheki take, ramar da nai na cike ta a yanzu ni kaina na san na canja ban tare ba amman abinci da na sha sai wanda na zaba ni da yarana, ko wace safiya ka'ida ne sai ya kira ni ya tambayi yana tashi da rana haka kin ci abinci? Kina da wata damuwa haka yake min a kullum da dare kuma ko wace rana sai ya zo. Tun satin daya shige Hajara ta kawo min kayan gyara jiki na kirji da wanda zai saka jikim tai ta sheki ga dilken da nake zuwa gidan Zil-touch tana min a duk bayan kwana biyu, na maida hankalina sosai gurin siyen wasu abubuwan da na ssn bana da su a gidansa dan aure ko kuma wandanda suka lalace cikin har da siyer da kayan dakina da zimmar yin sabbi. Ranar wata lahadi ina zaune sai ga Siyama ta shigo bayan mun gaiss da gaisa da mutanen gida sannan na shiga na dauko mayafina domin ya fada min zata zo ta dauke ni muje gidan saboda na duba wallpaper da aka saka min idan ta yi, na nuna masa ba sai naje ba sai ya ta kura akan lallai sai naje a dole na amince. Tare muka fita da ita bayan mun isa kofar gate din tai horn aka bude mata, mu na shiga cikin gidan na tarar an sabunta sabon fentin bangaren Hajiya gwanin sha'awa. Na yi zaton part din Hajiya za mu fara zuwa kamin mu shiga part din Ahmad din wato part din da zan zauna, amman sai Siyama ta fara shiga da ni part din Ahmad, an kawata gurin da sabon fenti sai kamshi yake, ina shiga falon nai arba da sabon cushion da curtains duka maroon color, dinning din na sabo, an zuba komai sabo a kitchen da bedroom din ma sabon furniture ne mai kyau, sauran dakunan ma duka sabin furniture ne. Gaba daya sai na ji kamar an sare min gabobin jiki na rasa abunda zance, sai a lokacin na gane abunda Ahmad yake nufi da cewar kar na wahalar da kaina shi baya bukatar komai ni yake so ba wani abu nawa ba. “Komai ya miki? Idan akwai abunda be miki ba ki fada sai a canja ko a kawo kamin lokaci ta kure” Siyama ce take maganar tana janyo kofar kitchen din. Tsaye nai a gurin kamar an dasani na rasa abunda zance wani guntun hawaye ya tsaya min a ido. Sai ta sa dariya “Daman Wallahi Ya yace yanzu ana nuna miki sai kin yi kuka, har muka dinga dariya ashe da gaske yake” Murmushi mai na share hawayen. “Idan ban yi kukan farincikin ba Siyama na me kike son nai?” “Kawai ki gode Allah” “Al-hamdulillah” Na furta fili da badini, sannan muka fito daga part din ina ta tunanin yadda zan labartawa su Inna abun, cikin tsananin kunya na shiga part din Hajiya, ko zaman ban yi ba Siyama ta labarta masa cewar na yi kuka sai yai murmushi yana kallona. “Ni ai na san halin kayata” Bayan mun gaisa da Hajiya ta sa aka kawo min lemu sannan ta fada min. “Nasa Ril_kamshi ta hada miki turare kayanta suna da kyau” Wallahi ni nai kamar na saka kuka a gurin, da wanne zan ji da abunda Hajiya tai min ko da na Ahmad? Ko kuma da kaunar da suke nuna min ni da yayana? Sai na rasa da wane baki zan yi mata godiya na rasa kalmomin da zan hada su isar da sakon godiyata yadda ya kamata. Ban wani dade sosai ba Ahmad yace na taso ya maida ni gida, Hajiya bata bar ni a fito haka nan ba, sai da ta hada min yan turaruka da man shafawa kamar yadda ta saba ta bawa Siyama ta kawo min. Tun da muka bar gidan na kasa dauke idona akan Ahmad, wani irin kaunarsa da kimarsa suka cika min ido, farincikin da nake ji a raina ma shine sila, ina ta tunanin kalar da zan siye yanzu ya dauke min wannan nauyin. “What” Ya tambaya yana murmushi ganin irin kallon da nake masa. Sai ya kai hannunsa ya kamo hannuna ya saka yatsunsa cikin nawa kana ya sumbacin hannun nawa. “Na san zaki ce zaki wahalarda kanki gurin siyen kaya wata kila dan abunda ke gareki ma ya kare, so tun da ina da hali da dama me zai sa na bari ki yi? I just wanted you to know that ke nake so, kuma ina son farincikinki” “Thank you, i mean Thank you” “You shouldn't” Ya fada yana kara kissing din hannuna, da hannu daya yake tuki dayan hannun kuma yana rike na nawa hannun har muka isa wani shagon dinki. “Zauna a nan ina zuwa” Na fada min sannan ya bude motar ya fita, ya shiga shagon sai gashi ya fito tare da wata mace kabila, sai da ya shiga ya zauna sannan ta leko ta gilashin motar ta gaishe da da far'arta. “Ya aikin ya gidan?” “Lfy kalau Alhamdulillah, ki fada min address dinki zan zo na auna ki” Na fada mata kamar yadda ta bukata sannan ya tashi motar muka bar wajen, mun dan yawata cikin gari kamin ya dawo da ni gida sai zolayata yake wai yana da kanwar hannu a dube ni ban tare ba amman har na yi fresh skin dina sai shinning har wani jan kumatuna yake. “Allah kin ma fini fari fa, ji hancin har tsawo ya kara” “To ai ba kai ya kamata ka fada ba mutane ya kamata ace sun fada” Kallo tai baki sake. “Su waye mutane? Baki san ni bane lims a kalleki ace kin yi kyau? Hmmmm” “To ai mata ba maza ba” “Har matan mana baki san yanzu akwai mata yan iska masu kwacewa miji mata ba? Maganar Allah ni ko mace ba zan yarda ta tsare ki da ido ba ba yarda zan yi ba” Bude motar nai na fita ina dariya sai ya sauke gilashin motarsa ya kira ni jiyowa nai na dawo. “Ina son na fada miki for the very last time bana son wata mu'amala na shiga tsakaninki da Aminu, na san akwai yayansa amman na dauke masa komai idan ba abunda ya zama dole ne a matsayin na uba ya gabatar da shi ba, idan zai yi magana da ke akan komai ya kira wayata da ni zai yi magana ni kuma sai nai magana da ke” Babu alamun wasa a maganarsa kamar yadda fuskarsa ta nuna. “In-Sha-Allah” Ya gyada min kai ya bi ni da kallo har na shige cikin gida sannan na ji tashin motarsa. Bayan kamar thirty minutes da dawowata mai dinki ta isko ni har gida ta auna ni. ABDALLAH POV. A cikin ko wane shafin rayuwar dan'adam akwai kaddarar rayuwarsa mai kyau ko marar kyau, wani ta so masa da sauki wani da wahala wani daga karshe ya samu cikar buri wani kuma ya koma a gurin mahallincinsa ba tare da rai ya samu abunda yake so ba. Sai dai yarda da ko wace irin kaddara yana cikin cikar imanin bawa, yarda samu da rashi na Allah ne yana karawa bawa kwanciyar hankali da wadatar zuci, a iya yarda yanzu kam Abdallah ya yarda akwai son Halimatu a cikin kaddararsa, akwai rashin aurenta a tarihin rayuwarsa. Iyakar hijadin da yai ne shine na rufe babin tahirin sonta a zuciyarsa wanda a da ya kasa haka sai a yanzu da ya yarda da kaddararsa kuma ya yarda ya rasa Halimatu har abada! Domin ko bayan Ahmad da yake da tabbacin ba zai sake ta ba, idan ma ta Allah ta kasance ace ya mutu ita tana raye aurenta ba zai taba yuyuwa ba domin Hajiya tace ko bayan ranta bata yafe nasa ya auri Halimatu ba, a dayan bangaren kuma idan ya zauna yai tunani a yanzu da son kai ya fitar masa a zuciyata, ya kan tausayawa dan'uwansa na rayuwar da yai da kuma wacce sai fuskanta a gaba, sai a yanzu ne yake ganin rashin dacewar auren Halimatu bayan kuma dan'uwansa yana raye, a yanzu yana jin cewar Halima ta cancani farinciki ko da ba a gurinsa ba ne idan har zata samu farinciki da kwanciyar hankali ya kamata ya kyaleta tun da ba zai taba aurenta ba, sai a yanzu yake nadamar neman aurenta da yai da auren wani akanta sai a yanzu gane girman laifin daya aikata a wacan lokacin idonsa ya rufe baya iya ganin laifin kansa baya iya ganin laifin Halima saboda so ya rufe masa ido da kuma neman haihuwar namiji. Sai dai har zuciyarsa na dauke da kaunar da kuma muradin son haihuwar namiji domin maradinsa ne tun kamin yai aure, har yanzu ya kasa sauke burin da yake da yakinin ba zai taba tabbatuwa ba domin dan'uwansa ya riga ya soke shi da mashi. Abubuwa uku suka fi tsaya masa a rai, haihuwar Namiji, matsalar dan'uwansa sai kuma damuwar da Mahaifiyarsa ta dauka ta saka a ranta na matsalar Abdulhamid. HALIMATU POV. Na yi zaton kamin na tare za a kawo min kayan duk kuwa da kasancewar ban masa maganar lefe ba, amman shiru ana ta shirye shiryen tarewar amman be aiko min da komai daga cikin sutura ba, hakan yasa na cire kudina na siye tufafina masu kyau lace da Atamfa da shadda lace yar ubansu a gurin Khadeeja Candy, na kaiwa tela ya dinka min tun kamin ranar da za a tare din. Ba wani shirye shirye zan yi ba, bayan wunin biki wanda ya zama al'ada a ko wane biki na budurwa ko bazawara, ana sauran kwana uku wunin alert ya shigo watana mai nauyi har sai da na zare ido, ina ganin sunan wanda ya turo min nai murmushi na shiga contact list da zimmar kiransa sai ga kirashi ya shigo wayata. Cikin shauki da kauna na dauki kiran ina murmushi kamar ance yana gabana. “Na ga Alert” “Eh abububuwan da za ku yi na mothers day din, za su iya dai ko?” “Haba dai wannan kudin ai yayi yawa” “Da gaske?” “Haba dai” Na fada a shagwabe sai shi ma ya rama yadda nai masa. “Haba dai Babe” Daga ni har shi sai muka saka dariya kamin ya dauko min zancen yadda su a nasu gidan za su yi masu wunin da irin abubuwan da za su tsara nima na fada masa abubuwan da nake son yi da rabawa mutane. Wanda yake cewa ba zai barni nai sati biyu a gida ba sai gani na yi wata har yan kwana biyu sama domin shi ma kansa da babu ishesshen lokaci ba zai samu damar aiwatarda komai na gidansa ba, Hajiya ma ba zata samu wadataccen lokacin yin wani abun ba, balle kuma ni uwar bikin gaba daya. Na yi gayyata sosai har wandanda ba su san na yi aure ba sai da suka sani, an dafa abincin kusan kala hudu domin Ahmad ya wani wadataccen kudin da zan yi duk abunda nake so har na rage, lemu ma kala kala a siya, bayan yan abubuwan dande dande da lashe lashe da ake sakawa a takeway da kaskon turare da turaren wutar da kofi ko plate a bawa mutum idan zai je gida. Nina makeupover (I like you girl 😘) ce ta gyara min fuskata na fito kamar wata yar sha biyar kowa sai yaba ni yake, ga dinkina dan ubansu na farin lace da farin mayafi kana ganina a cikin jama'a kasan ni ce amarya domin na haska kowa, duk wanda ya ganni sai yace na yi kyau. Na jidadin da Ahmad ya aiko mana da mai daukar hoto duk kuwa da kasancewar ya san akwai waya amman hakan be hana shi turo kwararen mai daukar hoto ba. Cikin farinciki da jindadi akai yinin biki kowa sai sambarka yake, bayan sallah isha'i manyan motocin na alfarma suka faka kofar gidanmu kowa sai kallo yake wadanda ba su san wa zai aura ba a unguwar sai kallo ake ana mamaki masu neman salsala kuma suka fara. Mama da Inna sun min nasiha sosai akan hakuri da biyaya kamar yadda suka saba min a kowane aure nawa da nake na dawo, sai dai wannan bana fatar dawowar fatana ba rubuwa da Ahmad har sai ta Allah ta kasance. Yan'uwan mahaifina ma sun min nasiha suka min fatan alheri tare da addu'ar Allah yasa gidan zamana ne. Ana kokarin fita da ni Hafiza ta zo ta rada min a kunne. “Lims din Amadu dan Allah idan kin yi sallah ki saka da mu a addu'arki Allah ya kawo na mu na gari, wadannan yan iskan samarin masu zuwa zance kawai ba neman aure sai bakin rowa Allah ya bamu da su” Dariya nai na kalleta sai tace. “Wallahi fa ki duba aure na uku kika yi, mu nuna nan ko daya ba mu yi ba, kuma ba farin jinin ne babu ba, masu son auren da gaske ne basa zuwa” “Komai ai yana da lokaci Hafiza, ni din da na riga ku aure baki ga yadda auren ya kasance min ba? Kowa ai da jarrabawarsa, wani abun nesa yake wani a kusa, idan akai hakuri za a cin ma komai” “Na sani ni dai ki saka mu a addu'a, kin ga Inna da Mama da yan unguwa ai ba su san wannan ba, yan mata hudu a gida, Yaya nata aure tana barinsu ina lafiya, yan kanennan na mu ma sai taso suke za su cin mana a tsawo” Ban yi mamaki na san indai Hafiza ce zata fadi fiye da haka ma, da dai ace Aisha ce ko Husna take maganar da ce ina kunyarsu amman Hafiza sai gyaran Allah ba kunya ba tsoro kuma bata jiran sai an mata. Ko ba a fada na ni an san wasu dan gulma da neman ganin gidan da za a kaini yasa sun bin motocin daukar amarya tun da a budurwa nake ba balle ace dole sai kowa yaje, amman Al-hamdulillah shi ma farinciki ne kuma na san ba za su je su tarardar wani abin tsegumi ba, sai dai kowa ya bawa idonsa abinci. Ni kaina da na already na ga gidan kamin a kawo ni amman hakan be hana ni zama bakauya ba a birnin, wata kila kuma dan yana dare ne sai ko'ina da gidan ya dauki haske ga shuke shuken da suka kara kawata gidan gwanin sha'awa. Bangaren mahaifiyarsa aka fara shiga da ni Gwaggota na rike da hannuna kaina na cikin gyale jikina sanye da shadda lace mai ruwa kwai, sai kamshin turare nake kamar yadda muka shiga muka tarardar falon Hajiya ma yana kamshin turaren wuta. Muna shiga matan dake cikin falon suka fara guda kamar an aurowa dansu burduwa, sai saka min albarka suke yan matan na daukata hoto, har cikin dakin Hajiya aka shiga da ni tai min nasiha sannan na taso tare da mutanen da muke tare aka nufi bangare na da ni. Mutane da yawa sun yaba da yadda aka samu part dina so Ma-sha-Allah, ciki har da masu fadin mai hakuri mawadaci, basu dade ba suka fita har su Hafiza aka bar ni kadai a dakin ta cikin a nan na yaye gyalena ina kara kallon yadda kalle da aka min ja yake ta haiba. Few people ne suka raso Ahnad zuwa dakina, a yadda suke zolayarsa yai musu shiru yana murmushi sai ka rantse da Allah ba shi ba ne, sai wani sun sun yake da kai kamar mai kunyar gaske. Suma sun mana nasiha irin tasu sannan sukai mana addu'a, sai da ya raka su ya dawo, sai ya zauna kusa da ni ya cire min mayafin yana murmushi kamar yadda nima nake tsakanin fuskata da tasa sai na rasa wacce ta fi wata annuri, hannuna ya kama ta sumbata sannan yaja ni jikinsa ya rumgume. “Al-hamdulillah, a yau Allah ya tabbatar mana da abunda ba mu taba mafarki ba, abunda ba mu taba kawowa a rai cewar zai faru ba a tsarim rayuwarmu, nesa ta zame mana kusa kunci da bakinciki ya zame mana farinciki da nishadi, ina rokon Allah yasa mutuwa ce zata raba mu kuma ya bamu zuri'ar mai kyau mai albarka, kuma ya bamu ikon kula da su da dauke sauke nauyinsu da yake kan mu” “Amin” Na fada ina wasa da zanen shaddar dake jikinsa, ji yai kamar rumgumar da yai min ba tai ba sai ya kara matseni sosai ya kirjinsa. “Wallahi gani nake kamar ba gaske ne ba, Al-hamdulillah Allah” Ya sake fada cike da nishadin, sallah godiya ga Ubangijince farkon abunda muka fara gabatarwa sannan neman tsarin Allah da kuma ni'imarsa ya biyo baya, muka ci daga abunda ya shigo min da shi, kana ya zuba min madara na sha sannan muka sake dabbaka wata sunnar. Washe gari tun kamin mu tashi bachi Siyama da kwankwaso mana kofa, ina jin lokacin da ya daga ni a hankali saman kirjinsa ya kwantar da ni, ya gyara min duvet din sannan ya sumbace ni ya tashi ya fita. Be dade ba ya dawo ya sake jana kirjinsa ya rungume ba mu tashi ba sai kusan tara har da wani abu, shi ma dan Hafiza ta kira ni ta fada min cewar akwai yan'uwan Inna da za su zo yanzu. A lokacin ne na tashi nai wanka na fito na tafi gaban madubi na shirya ina kokarin mikewa tsaye na hango shi ta cikin madubin yana kallon jikinsa ba riga sai tawul din daya daura shima iya kwankwasonsa. Murmushi nai na juyo ina kallonsa. “Kawai gani nake kamar ba gaske ba ne” Na sake yin murmushin sannan na nufi wardrobe a zatona kayan da nace Hafiza ta dauko min yana ciki sai nai arba da wasu tufafin dabam a ciki juyowa nai na kalleshi. “Nawa ne?” “Eh mana, daman ai ba zan kai miki gida ki yi kwalliya wani ya gani ba, ni da na siya ni za ayi wa kwalliya da su” Bayan ya fadi haka ya karaso kusa da ni ya dafa ni yana min inda aka jera takalmin, akwai kayan da ba a dinke ba sai dai dikaken yafi yawa kuma kowane kaya da kalar hijabinsa babu gyale ko daya, gyale kan sai na abayar da aka saka a ciki amman bayan shi ban san wani mayafi mai suna veil a cikin kayan ba. Ko ba a fada min ba ni kaina a fahimci Ahmad mutum ne mai kishi hijabin kuma zai taimaka min na kara kare martabata da kuma mutuncin aure da kuma abunda Ahmad yake cewa na boye masa wai na sa shi kadai. Sati daya Hajiya ta dauka tana mana girki na safe na rana na dare bata taba gajiyawa ba, sai da akai satin daya sannan ta sa aka kirani ita da kanta ta zaunar da ni falonta ta fada min cewar daga gobe zan fara girkawa mijina abinci da kaina. “A ka'ida kwana uku ake, amman saboda ki huta yasa na dauki sati daya ina miki, yawancin duk abunda kika ga ina girka muku shine favorite din mijinki, dan haka sai ki haddace wani abun kuma za ki iya karawa dan kanki ko kuma ki saffara masa wani abun irin naku na yan zamani” “In-Sha-Allah Hajiya na gode sosai Allah ya saka da alheri ya kara miki lafiya” “Amin Allah ya muku albarka ku ma” A nan na amsa da Amin, sannan na tashi na dawo part dina raina fes. Zaunawa nai saman kujerar da yake zaune sai ya dago ya kalleni sannan yasa hannunsa ya zagaye mazaunena. “Hajiya tace zan fara maka girki daga gobe” Na fada ina jan hancinsa dayan hannuna kuma a kunnensa ina wasa da shi. Lumshe ido yai ya bude yana tsutsar lips dinsa. “Kin iya?” Na dan yi fuskar shagwaba. “Haba shi girkin?” “Eh mana wasu yara irinki ba a koya musu girki a gida saboda son jiki” Dariya nai sai ya kamo kaina ya hade goshinsa da nawa, ya sumbanci hancina yana isar min da numfashinsa. “Idan baka kiya ba zan iya saka ki catering school ki koya mana” “No ni din eh to ban hana ko dan koyan wadansu abubuwan ba na zamani amman indan girki ne irin na mu na hausa ai na saba yi na iya daidai gwargwado” Mikewa tai tsaye ya ja hannuna muka nufi kitchen, gaban gas ya fara tsayar da ni sai ya koma bayana ya rumgume ni, da dayan hannuna ya rika nuna min yadda zan yi amfani da gas din. “Na fa iya” Bakinsa ya kai saitin kunnen yana cizona a hankali yace. “Ki dauka baki taba aure ba sai yanzu, ki dauka wannan auren shi ne aurenki na fari, ki dauka komai sai a yanzu ne za ki koya sai a yanzu zaki iya, ki dauka Ahmad ne mijinki na farko kuma na karshe har abada” Na gyada kai a hankali ina dan matse fuska domin maganar yake yana cizon kunne a hankali kamshin turarensa duk ya cika ni sai tayar min da zuciya yake. “Okay” “That's my Lims” A dolen dole na biye masa ya rika nuna komai na kitchen din da yadda ake amfani da shi, wani abu kan ban san shi ba sai da ya fada min sauran kam duk na sansu kuma na saba amfani da su, domin ko a gidan Aminu da gas nake aiki balle kuma Abdulhamid. Bayan mun gama muka fito daga kitchen din sai ya sake ni ya shiga ciki yai alwala, ina zaune ya fito yana sake hannayen rigarsa dake nade. “Tashi ki yi alwala zanje masallaci” Ya fada yana kissing dina, a kokarin yi masa addu'ar Allah ya tsare na ji lemun da na sha dazun ya dawo min a baki, saurin mikewa nai tsaye sai ya rike ni. “Lafiya?” Karnin turarensa yasa na fara sheka amai a gurin kamar wacce ta fi wani abu, sakina yai sai yai baya baya yana kallona baki sake kamar mai mamaki sai kuma ya rugo a guje yazo ya rumgume yana murmushi sai kuma ya sake ni. “No wait....” Sai kuma ya sake rumgume ni ya sake sakin ya sake rumgume ni yayi min haka yafi a kirga sai dariya yake. Can ya cire hular kansa ya jefar ya fara zagaya falon yana kallona kamar mai mafarki, sai kuma ya nufo ni ya daga fuskata yana kallona “I can't believe this” Ya fada kamin ya sake ni ya fadi a gurin yana ma Allah Sujada. Ni kan a raina nace daga ganin na yi amai idan kuma ya kasance malaria ce fa? Domin ni ban saba ciki da amai tun yana yaro ba sai ya fara girma hasalima ko irin laulayin nan na masu yaron ciki ban saba yi a ba sai ya fara fitowa na ke cin wuya har sai na raina kaina. 7/28/21, 8:33 PM - Buhainat: *GOBE NA...* By Khadeeja Candy 6️⃣4️⃣ Iyakar kokarin da nai na danne dariya ta ne domin har ga Allah ya bani dariya matuka, daga ganin amai sai ya sa rai da ciki, ko da yake idan ance ina da cikin ba mamaki tunda mahaifa a bude take kamar yadda Aminu ya fada wai ina ta haihuwa zan tsufar da shi, yau kuma gashi Allah ya kawo ni inda ake kaunar yaya ake son haihuwa. Ganin abun nasa ba mai karewa ba ne yasa na nufi gurin da nake aje tsintsiya na dauka na dawo gurin da zimmar gyara gurin sai ya kai hannu ya rike hannuna. “That's my condition idan mace tana da ciki bata aikin komai sai cikin ya tsufa” Kallon mamaki nai masa. “Wani irin ciki dan Allah what if malaria ce?” Dan murmushi yai murmushin dake nuna alamar be jidadin kalmar ba, ya karbe tsintsiyar ya aje ya matsa kusa da ni ya rike hannayensa yana min kyakkyawan murmushinsa cikin sanyi murya yace. “Kin fatar ciki ne mana, da ko ya ko kuma duka biyun Allah ya hada ban ki ba, ina son haihuwa lims ina son yaya, yaya rahama ne sanyin idaniya ne i need my own family too, Hajiya ma tana son na haihu Siyama ni kaina ina son naga yayana na ciki, ko yayana nawa zaki haifa min ina so ni dai fatana su zama masu albarka kuma masu tausayinmu” Sai kuma ya zaunar da ni ya kara jimke hannuna yana kallona cikin idona da idanuwansa da suka koma kalar tausayi. “Ba zan iya fada miki yadda na ji a lokacin dana rasa Baby, idan har wannan aman da kikai ya tabbata ciki ne zan fi kowa farinciki Lims, and idan kika duba rayuwar nan bata da wani tsayo wata kila zamu dade wata kila ba zamu dade ba akalla ya kamata ace kamin mu bar duniya mu yi sadakatul jariya, sannan mu haifi yayan da zasu rika mana addu'a bakya fatar ki ga jinina za su yi kyau idan sun biyo ki look at your nose” Ya fada yana jan hancina yana murmushi, nima hancin nasa naja. “Ko kuma idan sun biyoka ba, Allah ya bamu masu albarka” Kiss ya mannna min a goshi ya tashi yana fadin. “Shiga ciki ki gyara jikinki zanje nai sallah na dawo sai na gyara gurin” Ba musu na tashi na nufi hanyar dakin, bina yai da kallo sai da shiga sannan na ji ya bude kofar falon na fita. Da na shiga bandakin sai na tsaya haban madubi ina kallon kaina. “Ba dai wani cikin ba ne? Ke dai Mahaifarki a bude take da anyi abu kadan sai ciki, da gangan dai kike yi so kike ki tara min yaya na rasa yadda zan yi nai saurin tsufa, ki hana ni jindadin rayuwa, yaushe kika haye Aiman da har za a ce kin dauki wani cikin? Mtchssss” Abun dariya wai abunda Aminu yai min a lokacin dana samun cikin Amal ne ya rika dawo min, lallai na yarda bayan wuya sai dadi kuma komai yai farko dole ne yai karshe gashi a yau na aurin wanda jiran haihuwar ma yake ba kyama ba. Tufafina gaba daya na cire tufafi na sake wanka nai alwala na fito daure tawul a kirjina sai na same shi gefen gadona a zauna yana ta kallon kofar bandakin kamar mai jiran fitowata. Gaban madubi naje na tsaya sai ya mike tsaye ya tsaya a bayana yana kallona ta cikin madubi wani irin kallon ne da a zan iya fadar ma'anarsa ba. “Da sannu ina ta maye gurbin abubuwan da na rasa” Na yi murmushi sai ya rumgume ta baya yana sumbantar kafadata dayan hannunsa kuma a kaina yana shafa kananan tsorayen da ke kaina. Juyowa nai ina kallonsa, sai ya sa hannunsa ya lakaci kumatuna. “Ya akai?” Kasa ce masa komai nai sai kallonsa nake ina murmushi a raina ina ayyana irin kyau da Allah ya hore masa ga sura da cikar zati irin na da'namiji. “Kin yi sallah?” Ya tambaya yana had goshina da nashi, hakan yasa nai saurin sakinsa na nufi wardrobe na dauko wasu tufafin na saka ya shimfida min pray mat na saka Hijabi, har na yi sallah na gama banda kallona babu abunda Ahmad yake. “Zan samo wacce zata rika dan share share da mopping girki kuma sai na karbo gurin Hajiya” “Zan iya komai bama bukatar mai aiki, salon wata ta zo ta karbe min kai” Na fada da iyakar gaskiyata. Ya dan wara ido ya dawo kusa da ni ya zauna. “Kina tunani akwai wacce zata kwace place dinki? No one i mean no one” “To idan kuma tai creating nata place din fa” “Ai ba dadin zama za ta ji ba, kin riga kin karbe Hajiya Siyama ni da duk Family na” “Ni dai ban yarda ba” “Dole ma ki yarda wannan ka'idata ce indai macce nada ciki zan barta ta ji da dawainiyar cikin ne kawai sai na dauke mata na gida amman banda kaina” Ya fada da murmushin. “To yanzu shikenan sai ka cewa Hajiya ina da ciki Fisabilillahi sati daya da kawo ni?” “A a ba fada mata zan yi ba, sai sai tace ba mu da hakuri mun yi ciki tun a waje, abun ai da kunya, amman kuma idan kika yi wata 8 kika haihuwa ganewa za yi fa?” Magana yake da ni yana zaro ido kamar mai magana da wata karamar yarinya har da bude baki. Ni ban sansan lokacin da na fashe da dariyar ba na buge masa bakin sai ya rumgume ni yana kissing dina. Kamar wasa, abu ya zama na gaske ko kofina Ahmad baya barin na dauke, idan ya bar ni na yi wani aikin sai idan baya nan, wata tsohuwa aka dauko tana mana aiki wanke wanke da shara sai mopping da karbo mana abincin gurin Hajiya, ban san abunda ya fadawa Hajiyarsa ba kullum sai ta kawo min abincin rana da dare wani lokacin kuma idan bana sha'awar abincin sai ya siyo min. Sai dai tun wacan aman da nai ban sake yin wani ba, kuma a kullum sai Ahmad ya tambaye ni me kike ji me kike so ina ke maki ciwo idan kin ji wani abu ki fada, haka yake kula da ni kamar wacce mai cikin fari, idan ya fita kuma ya ga wani abun kwadayi sai ya siyo min wai be sani ba ko ina so. Be barni naje gida ba sai da nai wata uku da kuwa da irin kewar da nayi da ganin su Inna da Mama, suna Namra kam ko wane weekend sai ya dauko su sun zo mana hutu. Kowa fadi yake na canja wai fuskata ta kara cika fari na ya fito kamar ba ni ba, ni kaina na san na canja domin ina jin nauyin jikina a yanzu sabanin da. A gidan na wuni sai dare yaje da kansa ya dauko ni bayan ya shiga ya gaisa da su Mama yai musu alheri sannan muka kamo hanya. “Zaki ci tsire?” Yana tambaya na hade yawu dan na hango mai tsiren yana gasawa gefen hanya. Sai ya faka motarsa ya fita ya siyo min ya dawo. “Sauran ice cream” “A a ba ki san sanyi yana effecting abunda ke ciki ba? Na lura da ke kullun sai kin sha ruwan sanyi fa sai ma na cire makulin fridge din nan ai” “Ai kadan nake sha” Be ce min komai ba ya faka gefen titi ya sake fita ya siyo min ice cream sannan ya dawo motar a lokacin ni kam har na yi nisa da fara cin tsiren. Ko da muka isa gida na cinye rabi sai dai ba ni kadai ba har da shi dake tukin miko min bakinsa yake na saka masa. A part dinsa yai bakin motar ya zagayo ya bude min kamar yadda ya saba na fito rike da kedar sai ya rufe motar sannan ya karba ledar hannuna. “Jira ni a nan na fito Hajiya na da bako zaki je ki gaishe shi” A gurin na tsaya har ya shiga ciki ya fito, sannan ya bude motarsa ya dauko tissue ya gyara min bakina kamar wata karamar yarinya ya jefar sannan ya rika hannuna muka nufi part din Hajiya. Sai muna daf da shiga sannan ya saki hannun nawa ya bude min kofar falon na shiga bakin kumshe da sallama Hajiya ce kadai a falon sai mai aikinta sam ban lura da su Kabir ba da wata mai zaman mahaifiyarsa wace suka tafi waje tare da ita da matarsa da wasu mutanen da suke tare da su ba sai da naje zan zauna. Aiko ba shiri na gwalo ido baki saki ina kallonshi shi ko sai dariya yake min. “Kabir.....?” “Na'am..... ” Kara zaro ido nai jin muryarsa ce da gaske kuma gashi har ya amsa min ga shigarsa tsaftsaf cikin kamala, aiko na nufi cikin wani irin mamaki da bazata sai jin nai an rike ni an dawo da ni baya. “Ke” Sai na juyo na kalli Ahmad baki saki farinciki har cikin raina. “Ba ka fada min ya dawo ba” “Ba gashi kin gani ba” Ya fada yana kokarin zama har lokacin be saki hannuna ba, aiko dan murya ban san lokacin dana rumgume Ahmad din ba sam na ma manta da zancen wata Hajiya tana gurin, har ga Allah ya jidadin samun lafiyar Kabir hakan ya wanke raina fes. Godiya suka rika yi ma Ahmad da Hajiya kamin su shiga yi mana addu'a kala kala suna saka mana albarka. “Ka yi sa'ar mata Halima tana da kirki tana da mutunci kuma ta san kanta” Kabir ya fadawa Ahmad yana kallona, a nan Ahmad ya wani dauke kai yana murmushin yake kamin ya kalleni murya kasa kasa yace. “Tashi kije part din mu ki jira ni” “Wayyo ina son na ga lafiyarsu” Yar hararata yai ya hade rai, sun sun na tashi ba dan rai ya so ba nai musu sallama har lokacin Kabir kallona yake yana murmushi na fice. Part dina nadawo na zauna na karasa cinye tsiren na sha ice cream nai nas raina kuma fes, sannan na dauki waya na kira Hajara da kuma yan gidanmu na labarta musu samun lafiyar Kabir Mama ta ji dadi sosai sai yabawa Ahmad yake tana mana addu'ar karin zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai da ya shigo sannan na aje wayar ya zauna kusa da ni yana fadin. “Sun wuce daman dogiya suka zo yi” “Na so naga tafiyarsu, Wallahi kamar mafarki nake gani wai Kabir ya samu lafiya” “A a ba zan bari ba, naga mutum sai kallonki yake yana fadin na yi dacen mata, kin san zafin da na ji kuwa?” Na yi dariya. “To ai shi bada wata manufa ya fada ba” “Ya za'ayi na sani namiji ne fa hmmm” Dariya na cigaba da yi, nikam kishin Ahmad har mamaki yake ba, ashe da shi ne ba zai yarda nai aiki da aurensa ba a kullum idan zan fita Hijab nake sakawa amman haka be hana yace min yaga ana kallona indai muna tare ne ya rika kallon maza kenan ya ga wanda ya kalle ni da wanda be kalleni ba, sai yawan nanata min cewar na dinga kiyayewa shi fa yana da kishi. Al-hamdulillah, bayan godiya babu abunda zan yi ma mahallincina, a can baya da nake cikin wuyar ma nai masa godiya balle yanzu da nake cikin ni'imar Allah da Rahamarsa har na shiga wata na biyar da cikina ban san wani abu ciwo ba, iyakar abunda nake yawan yi kwadayin sai amai shi ma kuma ko da yaushe ba, sai dai na lura wannan cikin ba kamar sauran ba ne, domin wannan yana min girma sosai idan kuma ya tashi min motsi ba guri daya ko biyu nake jin motsin ba. Ranar da na koma asibiti na fadawa likitar wacce ta kasance mace ce yar'uwata, wacce Ahmad ya sama min kuma ya fada min ita kadai zata rika duba ni, duk da irin amincin da ke tsakaninss da Dr Nura kin yarda yai ace shine ke duba ni. Sai da ta gama abunda take ta tabbatar da lafiya ta tambaye ni ko ina jin wani abu nace mata a a sai dai motsin kawai ina jinsa ba daya ba. “Eh daman ai dole zaki ji wannan, Allah dai ya raba lafiya” Maganarta ta ban mamaki kamar na tambaya sai kuma nai shiru na, wata kila ba daya ba ne shiyasa nake jin haka domin har nauyi yake min, sai a lokacin na tuna Ahmad be bani takadar gwajin da akai ba da hoto ya fadar fada min edd na is 21 on May wata kila ya sani shiyasa yaki fada min. Bayan na fito na kira shi a waya na sanar masa na fito, be dade ba ya kira ni yace na fito muje, fanken da nake ci n aje na dauki haka na rike a hannu na fita zuwa inda yake. A mota nake masa zancen abunda likitan ta fada sai fara dariya yace cewa “Jinina mai karfi ne ba daya na saka miki ba biyu ne” “Da gaske?” Dariya ya sake yi yana kallona. “Wannan tashin hankalin nake gudu shiyasa ban fada miki ba” Bance masa komai ba har muka isa gida, dayan ma ya ka haife shi balle biyu Allah na tuba duk da haihuwa idan Allah ya kawo maka saukinta sai ka samu sa'ida. A lokacin ne na fara laulayi mai wahala irin wanda ban taba yi ba, ga amai da na ci abinci sai amai ga ciwon jiki, komai nake son abu idan aka kawo min shi sai kuma na ji ya fita raina haka dai Ahmad yai ta hakuri da ni sai masifa kala kala, ko be min komai ba na zauna nai ta masa kuka duk yabi ya rude, idan aka samu sa'ida sai fa idan na yi bachi yadda kasan wata yarinyar goye haka na koma sai son jiki da shagwaba kala kala, wanka ma wani lokacin sai na ki nace ba zan iya ba sai dai shi ya min. Kulawa kam ina samunta sosai a gurin Hajiya da kuma danta, domin ko nishi nai da karfi sai Ahmad ya tambayi lafiyata. “Lafiya....” “Zogale nake son ci” Ya kalli agogon falon wanda ya nuna karfe goma sha daya. “Ina za a samu zogale yanzun” “Ni dai ita nake son ci” Na fada a shagwabe kamar zan fashe da kuka, kuma har ga Allah na kusan kuka dan nauyin cikin ya fara isata ga bachi ina son yi amman ba hali ko na kwanta ba zan yi bachin ba. Tashi yai ya nufi dakinsa sai gashi ya fito sanye da shadda amaimakon kayan bachin dake jikinsa dazun. Sai kusan 12 ya shigo hannunsa rike da bowl da murfi a kai, dayan hannunsa kuma rike da bakar leda kusa da ni ya zauna ya aje yana fadin. “Gashi an samo” Tashi nai zaune da mamaki domin har ga Allah ban yi zaton za a samo ba, domin har da neman fitina yasa na ce masa ina son zogale. “Ina ka samu” “Hajiya nai ma magana sai tai magana a gurin Hajiya Binta su wai suma siye da yawa su aje ne har kullin ma ta debo min” Ya fada yana bude min zogale ce a cikin har da kankararta ta kame sosai. Hannu na kai na dauki kuli daya na fara taunawa sai ya tashi ya dauki zogalen ya zuba mata ruwan zafi sannan ya dawo falo ya cire rigarsa ya koma kitchen din, ina jin lokacin da yake daka kullin a turmi. Sai da ya hada komai sannan ya dauko ya kawo min a falon, kamin ya kwada min yawona kamar za su zuba tsabar kwadayi, ya san halina da son yaji dan haka ya zuba nasa dabam ni kuma ya kara min yajin, ci nai gaba daya na cinye ban raga ba har da sude kwano ba dan kuma na koshi ba daman tun da cikin ya fara girma ba abu kadan ke isata ba sai nai ta ci kamar zubawa ake a wani gurin ba a cikina, hakan kuma be hana na amaye shi. Shi ya kwashe komai ya kashe kayan kallo sannan ya taimaka min na mike tsaye daker muka nufi daki. Sai da nai wanka sannan na dauki wata katuwar ridar yadi na saka domin ita kadai nake sakawa na jidadin kwanciya. Saman gadon na hau na kwanta, sai ya tashi zaune ya fara min addu'a yana tofa min saman cikin sannan ya kwanta bayana ya rumgume ni ya dora hannunsa saman ciki. Ga shi ina jin bachi amman idona suka ce fir ba dai bachi ba, can a ji kamar ana saran kashin bayana hakan yasa a tashi zaune ina hawaye a hankali nikam duk wahalar da nake sha a cikin ban taba shan irin wannan ba. Tashi yai shima zaune dan san na kasa bachin ne kamar yadda nake wani lokacin, sai ya matsa baya ya jingina da gadon ni kuma na matsa jikinsa ya rumgume ma kwanta a kirjinsa yana dan matsa min jikin a hankali har bachi yai gaba da ni. Cikina na cikin wata a bakwai akai shigar kotun karshe akan case din su Abdulhamid, shekara ashiri aka yanke masa hukunci zaman gidan kaso, Abraham kuma da sauran mutanen aka yanke musu hukunci daurin rai da rai domin bayan safarar makama an same su da laifi fashe da makami da cikin har da kisa wani babban dan siyasa. A rana na wuni rai babu dadi sakamakon labarin da na ji ko da ban san shi ba a matsayinsa na musulmi dole na tausaya masa balle kuma akwai yan'uwanta ta jini a tsakani, bayan kuma rayuwar Abdulhamid abar tausayi ce sosai domin be mori komai daga cikinta ba, abun ka da mai neman kuka an fada masa mutuwa sai na zauna nai ta rusa kuka tun Ahmad na ban hakuri har ransa ya bace ya fita ya bar min gidan. Sai bayan sallah isha'i ya dawo fuskar nan babu annuri ni ko a lokacin na waye kamar ba ni ba sai faman yawo da katon ciki nake tsakar falo. Ina masa sannu da zuwa ya amsa min ya dauke kai ya shige dakinsa ko kula ni be yi ba, hakan yasa na nufi dakin nasa na same shi yana kokarin cire tufafin jikinsa sai na zauna akan stool din madubin, sai da ya cire rigarsa sannan ya dafa ni. “Tashi nan” Ya zaunar da ni saman gadon ni dai sai kallonsa nake. “Me aka maka kake bata rai” “Akan me zaki zauna ki yi ta rusar kuka akan an yankewa wani hukuncin laifin daya aikata” “Daman ina neman kukan ne” “To from now on bana son na sake jin sunan Abdulhamid a gidan nan ko abunda ya shafe shi” Yana fadar hakan ya shige bandaki, haka da yace min sai na ji kamar yace min je ki mutu, aiko a gurin na fara kuka na rashin dalili, daman can sai na yi kukan nake samun natsuwa, ga ciwon jiki ga nauyin ciki ga shi gato duk inda zanje ina nishi kamar na dauko duniya, ga rashin bachi ga shi komai na ci abinci sai na amaye shi tass sannan nake zama lafiya to da wanne zan ji. Har gama wanka ya fito ban daina kukan ba, kusa da ni ya zauna yana dariya. “Wannan ciki dai Allah ya taimake ni ki haife min shi lafiya, na lura har ni haushina kike ji” Kamar fa ya sani dan zuciyata cike take da haushinsa na rashin dalili tun da ba wani abu yake min ba, ga shi kadai ba har Hajiya da duk masu aikin gidan haushinsu nake ji haka nan dai nake daurewa ina gaisheta kullum, har ta dauke min zuwa sasshenta ganin cikin nawa zama daker tashi daker idan zan zauna tace zauna sannu haka ma idan zan tashi, idan nace ina bukatar abu kuma in ya kai wata duniyar sai ta nemo min shi. “Mai ciki..... Mai ciki.... ” Ina kokarin zama yake ce min haka yana min gwalo kamar wani karamin yaro, fillon kujerar na dauka na jefa masa ina dariya sai ya shi ma yasa dariya yana zolayata. “Yar Babyta idan fa zaki haihu ni zan miki nakuda” “A ina a taba ganin namiji yayi nakuda” “Ni dai sai na yi” Ya fada yana daga min gira daya sai kace wani tsoron dan iska. “Ni dai dan Allah Ya Omri ka daina jana ka bar ni na ji da yayanka” Na fada ina nishi daker daman haka nake idan suka motsa sai su haye min zuciya daker nake numfashi, taso yai ya dawo inda nake zaune ya duka gabana ya bude cikin yana kallon yadda yake motsi sai kuma ya dora kansa sama ya lumshe ido yana murmushi, kamin ya ciro wayarsa ya fara daukata hoto. Ko da na shiga watan haihuwa ta na zama wata abar tausayi, domin idan zan kwanta sai na nade wani zane sannan na dora cikin akai, dayan fillon kuma na dora kafafuwana sannan nai matashin kai da Ya Omri. Ana sauran sati Edd na ya cika na je asibiti sai suka rike ni bayan sun min hoto sun dubani abunda suka fada min wai ba zan iya haihuwa da kaina ba, a lokacin na samu kaina a cikin tashin hankali marar misaltuwa, ba ni kadai ba har da yan gidanmu da kuma Hajiya da Ya Omri, sai a lokacin ne na san cewa abunda ke cikina hudu ne ba biyu ba kamar yadda Ya Omri ya boye min. Sosai ya so fitar da ni waje domin amin aikin acan amman naki domin ganin nake ko mutuwarce kara dai na mutu a kusa da mahaifiyata. Be ki amince min ba sai dai kuma be min yadda nake son din ba domin a cikin kwanakin ya sa aka shirya min komai muka tafi Abuja wata private hospital mai shegen tsada da kyau ga kula kamar za su cinye mutum, yawancin ma turawa ne suke duba matane sai kwararun likitoci. Duk kwana daya a dakin 170k ake biya bayan sauran responsibility na asibiti. A ranar Likitan aka min theater kamin a shiga da ni babu wanda ban nemi yafiyarsa ba babu wanda ban yi ma kuka ba, har da amanar yarana na bada hakan yasa hankalin kowa ya tashi, ba ma kamar Ya Omri da har wani rama yai, ni kam har ga Allah na dauka mutuwa zan yi domin duk haihuwa ni nake yi da kaina na tiyata ba, kuma ban tana shan wahala irin na wannan ba. Sai dai cikin ikon Allah da iyawarsa da yardarsa sai aka min theater ban san ma anyi ba domin hankalina baya jikina a lokacin, sun dade suna kira sunana kamin na amsa musu domin numfashina yayi nisan zango ga jikin ina jinsa kamar ba nawa ba. Al-hamdulillah likitar da fada tare da sauran nurses da kuma wata likitar ita ma mace Nurses din ma dukansu mata ne. Sun dade a kaina kamin dauko baby dora min a kirji. “Duba ki gani me kika haifa” Cikin lumsasun idanuwana na duba na ce “Mace” Suka sake dora min dayan “Namiji” Suka sake dora min wani. “Namiji” Na fada idona na cika da kwalla, sai musulmar cikinsu tai hamdalla suka canja min gado suka dora ni akan wani sannan suka rufe min jiki suka turo ni akan gadon aka fito da ni. Mama da Hajiya da Ya Omri ne rike da yaran uku babu komai a fuskarsu sai farinciki. Wani dakin dabam aka kai ni suka jona min gorar jini suka saka min iskar da zata taimaka min gurin numfashi sannan suka min Sannu suka fita. Sai ga Ya Omri na ya shigo rie da Baby fari sol cikin kayan sanye masu kyau da tsada. Gefena na aje baby sannan ya doko ya sumbanci goshina ya rumgume ni hawaye na sauko masa. “Thank you so much, Allah ya miki albarka” “Ya Omri nawa na haifa?” “Four amman guda ya koma” Yana rufe baki sai ga Nurse ta shigo da daya Hajiya kuma rike da daya, wani karamin gado dake kusa da ni na asibiti aka jera su, Hajiya ta matso kusa da ni tana min sannu da jiki. Naga kulawa na ga gata ba a gurin mijina ba, ba a gurin Hajiya ba duk wani abun da ya take bukata a gurin uwa Hajiya tana min shi, Ya Omri na kam Wallahi yadda yake dawainiya da ni da damuwa har tausayi yake ba ni. Sati na daya suka sallameni muka dawo gida, a nan aka ce min ban ga komai ba indai gata ne da kulawa, daga gurin yan'uwan Ya Omri kamar wandanda basu taba samun haihuwa ba a dangi sai a a kaina haka suka rika kula ni kamar zasu dafa ni su cinye. Madara aka siyo ana hada musu da ita domin nonon baya isarsu bama kamar mazan da ba su iya sha kadan ba. Kayan barkar da Ya Omri yai min sai kace hauka ne ko kuma be san zafin kudi ba, ban cin wadanda nai ta samu gurin yan uwansa da kuma nawa dangin domin kowa ya ji na haifi yan uku sai yayi mamaki kuma ya zo ganinsu. Har abokansa ba a bari a baya na gurin bawa yaran kyauta da zuwa ganinsu ga su farare sol gwanin sha'awa ni kaina burgeni suke balle kuma ubansu da ya rasa inda zai dauka ya aje su wanda hakan shi yafi komai yi min dadi, at least na haifa wa wanda yasan darajar yaya kuma ya san kimata domin kullum a cikin tausayina yake da nuna min kauna. Ranar wata Monday akai suna wanda ya kama sati biyu kenan, dayan aka saka masa sunan mahaifin Ahmad wato Muhammad wanda akai wa lakabi da Sudais dayan kuma aka saka masa sunan mahaifin Hajiya Abubakar aka masa lakani da Shuraim, mace kuma aka maida sunan Namra, sai dai ita ana kiranta da Little Namra. An yi shagali iya shagali har abunda ban taba mafarkin za a raba ba anyi, a ranar daga ni har su mum sha bachin gajiya daman tun da suka zo dubiya ba su da aiki sai bachi sai kuma shan nono. Kusan rabin rainon su a hannun Ya Omri na yake indai yana gida to babu ruwana da su sai idan nono za su sha ko madara, idan kuma baya gida ga Baba mai kula min da su ba ni da matsalar daukarsu dan wani lokacin shi da kansa zai musu wanka ko ya wanke musu kashi ko tsarki. Sai da su kai shekara biyu da wata biyar sannan Ahmad yasa aka maido da su Namra da Amal da Aiman da Adnan a gidan, sai dai matan dakinsu dabam mazan ma haka, hakan kuma ba karamin faranta min rai yai ba, hakan ne ya kara tabbatar min da cewar lallai Ahmad ya rike yayana kamar nasa, lokaci lokaci Aminu kan kira shi ya tambayi lafiyarsu wani lokacin kuma sai ya aiko da mota a dauke su ya tafi da su yai musu shopping ya dawo da su, shi kansa rayuwarsa abar tausayi ce a yanzu domin matarsa bata haihuwa ba har yanzu wata kila ma su Namra da yak wulakantawa a baya su ne kadai ya'yansa tun da ita wacce yake aure ta riga ta lalata mahaifarta. Ga dan'uwansa wato Sadi ya zama aban tausayi domin ciwo ya kai shi kasa babu kyau gani, sam ba zaka ganshi kace shine ba, nikam hakan dadi yai min domin kuwa Allah ne ya nuna masa iyakarsa tun a yanzu kamin ayi wani hisabin a lahira.... Kiri da muzu Ya Omri ya hana ni zuwa barkar haihuwar da Suwaiba ta sake yi na macen da Abdallah baya so, duk kuwa da kasancewar ita din ta zo a lokacin dana haifi yan uku, sai dai mijinta be zo ba kuma be aiko ba be kuma kira ba. Sai na rasa yadda zanyi taya zata haihu na ki zuwa bayan kuma na sani, ai sai ga rashin kyautawa ta, da na san zai hana ni tun farko da ban tambaya ba sai na masa wata karyar na tafi. “Idan ban je ba ba zata jidadi ba ko Mama ba zata jidadi ba kuma Wallahi ban kyauta ba, komai fa ta wuce abunda ya faru duk a baya ne” Banza yai min yana ta wasa da yaransa sai kyalkyalar dariya yake shi da su kamar ma be san ina zaune a dakin ba. Can ya dago ya kalle ni. “Magana kike?” “Barkar Suwaiba” “Idan ba bacin raina kike son gani ba ki daina min maganar nan, haka kawai ki taka ki tafi gidansa yai ta kallonki” “Ba zanje lokacin da yake nan ba” “Na ce ba za a je din ba, ko a munafunce ban amince aje ba” Ya fada fuskarsa babu alamun wasa, har yanzu yaki yarda Abdallah ya daina so na ya kasa manta abunda ya faru na rasa wane irin kishi ne Ya Omri yake fama da shi ko mai sunan Abdallah baya so, Aminu ma dan ya zame masa dole ne. Duk yadda na so nai convincing dinsa ya amince fir ya ki a dole na hakura sai dai na siye abubuwa na bada nace a kai mata wanda na san hakan ba zai mata dadi ba. Ranar wata Lahadi ina zaune dakina rike da waya ina chat ya shigo rike da wasu takardu ya zauna kusa da ni yana fadin. “Ina tunanin bana da mu za a yi hajji” Ban san lokacin dana jefar da wayar hannuna ba na tashi na fuskance shi baki sake ido har gurin gira. “Da gaske?” “Yes tun da yara sun yi kwari ai ya kamata ke ma ki kai ziyara, sai mu koma tare, idan Allah kuma ya amince mana kuma sai mu yi ummara idan lokcin yayi” Rumgume shi nai cikin wata irin murna marar misaltuwa sai ya fara dariya yana fadin. “Idan mun dawo zaki karo min yan uku” “Har yan goma zan karo maka” Ya fara dariya yana rumgume ni. “Kamar gaske, salon kukan ya dawo ta fitina ko” Murmushi nai sai ya rike fuskata yana kallon cikin idona kamar ba gobe. “I love you so much” Ya fada da rada sai ya sumbanci goshinsa na mayar masa. “I love you more” Abunda ban sani ba, ba ni kadai Ahmad ya biyawa ba har da har da Mahaifiyarta da Inna, bayan gyaran gidan da yai musu ga dawainiyar kai abinci duk wata kusan hidimarsu ta dawo kansa, tsanannin dadi da farinciki har na rasa inda zan saka kaina. A tare mu kai hajjin da su wanda su kansu ba su taba saka ran wata rana za su tafi ba balle kuma ni, sai gashi komai ya canja mana kamar ba mu ba, bayan wuya sai dade kuma mai hakuri kan dafa dutse, abunda ban taba zato da tsammani ba shi yake ta zuwa min ba ni da matsala da Hajiya sai dan abun da ba a rasa ba, kusan ma yanzu tafi son jikokin fiye da da domin a yanzu Siyama tai aure tana dakinta ta bar Hajiya sai idan ta kawo ziyara, kamar dai su Hafiza da Husna da Aisha hankalina a kwance yake a yanzu ga yara a gabana gwanin sha'awa muna rayuwa cikin daula kamar gidan ubansu. Gobena tai kyau, Gobena ta zo min ta inda ban zata ba, Gobena ta same min mai Annuri da haske. ***** ******* ******* ***** AFTER SOME YEARS... Da gudu Amal ta fito dakinsu Adnan ta ho kaina kamar zata fada kan tsohon cikin da ke jikina sai kuma ta dawo bayana ta boya, Adnan din sai kokarin kamota yake. “Ya akai?” “Momy wai ina operating system tazo ta karbe” “Momy ba tashi bace ta Anty Namra ce kuma tace kar na bari ya dauka” “To ina ruwanki ki bani karatu nake” Sai a lokacin na daga kai na kalleshi. “Kai ina taka?” “Ya ki tashi Sudais ne ya saka mata ruwa” “Amal ba shi idan ya gama sai ya baki ki aje masa” “A a Momy tace kar na bashi” “Zan barshi ya doke ki fa” “Ni dai ba zan bada ba gaskiya” Ta fada tana make kafada. “Je ka dauko ta Aiman kyale ta yar neman fitina” Da huci ya nufi dakinsu yana fadin duk da shiga hannunsa sai ya doketa, daga inda take tsaye ta rika masa gwalo tana cewa. “Ai dai na hana, kuma idan ka dake ni idan Daddy ya dawo na fada masa, ai yace ka daina dukanmu” “Bana son hayaniyar nan sauka saman kaina” Na daka mata tsawa sannan ta sauka saman kujerar ta nufi gurin Lil Namra, tashi nai na nufi bedroom dina ina tafiya daker...... *TAMMAT BI HAMDILLAH* Godiya ga Allah mai kowa mai komai wanda ya bani ikon fara rubuta labarin nan 8 months ago har na kawo yau. Darasin da ke cike Allah ya bamu ikon amfani da shi ya yafe mana kuraruranmu. Godiya ga makaranta labarin Gobena a duk inda suke, da yawa mun fara rubutun nan da wasu amman ba mu karasa tare ba, sakamakon yanayin labarin, wasu sun fada min basa son labarin da babu soyayya wasu su ce min wahalar Halima ta yi yawa sun daina karantawa so so kaza kaza, a haka dai na daure na cigaba da rubutawa, Na fada tun farko cewar ban sani ba ko labarin zai muku dadi ko akasin haka domin ba zallar soyayya ba ne, rayuwace ta kalubalen da fadi tashin na rai da kaddara, ni na san akwai wadanda suka fi Halima shiga gararin rayuwa a zahiri, kuma bayan wuya sai dadi, sai gashi ina tsaka da rubuta nai ta haduwa da mutane masu kwatanta rayuwarta da ta Halima wata ma idan ta fada min halin rayuwarta wallahi har ta fi Halima shiga matsala, ban da wace akwai tace min sak yadda Aminu yake haka mijinta yake, akwai wacce tace min yadda Sadi ya lalata yar dan'uwansa Namra, haka kanen mijinta ya lalata yarta, wasu kuma matsin lamba ce daga iyayen miji kamar yadda Halima take sha. Ina matukar godiya kuma ina jinjina gurin wandanda suka jure karanta wannan littafi har muka kawo yanzu Allah yasa mu amfana da darasin dake ciki. Godiya gare ku yan wattpad, da yan Whatsapp, da facebook i love you All Fisabilillah ina godiya sosai Allah ya bar ran so. 1 ina ya fi burge ki a cikin littafin nan? 2 Mi ya fi baki tausayi? 3 ina ya fi baki haushi? 4 ina ya fi saki dariya? 5Wane darasi kika koya a cikin littafin nan? 6 Any kuma zaku iya yarda da kaddararku kamar Halimatu? Ance bayan wuya.......☺ *** *** *** Sai kuma idan mai kowa mai komai ya amince min mun hadu a littafi na gaba. Best regards 💚💛💜💙❤ Khadeeja Candy 🌺😍😘