👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg1⃣ KATSINA Duk wanda ya san Jami'ar Umaru Musa Yaradua dake garin Katsina yasan wajen gari take, a k'alla ba a kasara ba tafiyar minti arba'in da biyar (45) ne zuwa cikin gari. Daliban aji d'aya, na (Department of MicroBiology) ne suka fito a gajiye daga aji misalin karfe shidda da minti biyar (6:05) na yamma kasancewar sunyi lectures 4-6. Mimi tayi wujiga-wujiga don tsabar gajiya, ta kalli kawayenta biyu tace "Wayyo Allah! da alamun zamu kwana a Hostel yau, ji yanda garin ya hade rai, ko dai ruwa zaayi?" Usheey cikin damuwa tace "kai! dole captain ya nema mana sauki gun lecturer nan, a yi rescheduling lectures din, ko wednessdays ne da safe, don bala'i 4-6 ran saturday?" Dayar me sanye da nikaf tace "Don Allah ku mu daga kafa, kar su cike bus din, kun dai san mazan nan ba hakuri zasu yi ba, balle yanda suka ga hadarin nan kowa so yake ya tafi gida." Miemee tace "nikam i dont have dat strength." Usheey tace "aikam tafiyarmu zamu yi mu bar ki, suka cigaba da tafiya. Mai sanye da nikaf din tace "laahhh! kun gani ko, school bus2 sun tafi." Miemee tace "wallahi kina da damuwa, mu kadai ki ka ga bus din ta bari?" Mai nikaf din ta dauke kai don tasan da ta sake bude baki tana iya fashewa da kuka. Usheey tace "Ai ke Mimi ko karfe nawa zamu kai na san ko a jikin ki." Daga nan ba wacce ta kara magana, ko da suka karasa Student center duhu ya fara yi, kuma matan da ke gurin daidaiku ne, wasu an basu lift. Miemee tace "ko mu zauna a kujerun SUG kafin bus ta dawo?"a Usheey tace "chap sabod gamu gantaIallu ko?" Dayar tace "to ya zamu yi? ko mu karasa gate kila mu samu ko commercial a chan?" Mimi tace "chap wallahi bazan iya tafiyar minti ashirin ba." Usheey tace "toh bari mu barki nan." Tafiya su ka fara yi miemee tace "bala'i wlh ba za ku barni nan ba, ta bi bayan su da sauri. Tafiya su ke yi suna fira jefi-jefi, dare kam har ya fara yi ga hadari ya kara haduwa, Agogon wayar ta karfe7 saura minti 15, Idon mai nikaf ya ciko da hawaye, tsiraran motoci suke wucewa, miemee tace "wlh a ruwa muke, dama mu samu lift. Usheey tace "eh wlh". Ba su rufe baki ba sai ga wata bakar mota mai bakin gilashi ta danno a guje, har ta dan gifta su, sai kuma motar ta fara dawo da baya da baya. Miemee tayi saurin gyara zaman rigarta, tace "yauwa ai nasan na annabi ba sa karewa, ga lift nan na zuwa" usheey tace "Barkan mu Allah ya takaita mana wahala ba sai mun je gate ba" me nikaf cike da mamakin kawayenta tace "yanzu motar nan mai tint zaku shiga? Kuna jin sauti na tashi kamar ba dare ba?" Usheey da miemee suka buga tsaki a tare, Usheey tace "kinga dai Besty idan muka bar motar nan ta tafi, ba mu san lokacin tafiyar mu gida ba, daga cikin makaranta ta fito balle mu ce sace mu za ayi, " Miemee cikeda takaici tace "Abu mai sauki, idan ba ta shiga sai mu yi tafiyar mu mu barta nan" kafin tace wani abu motar nan ta iso ta tsaya daidai su. Ido suka zuba ma bak'in windon motar, a hankali glass din ke sauka, idanuwan 'yan matan nan 3 tsam cikin halittun da ke zaune gaban sits din motar, Su biyu ne, daya na zaune sit din direba, dayan kuma na zaune a kujera me zaman banza, da alamu abokai ne, Mimi da fara'arta tace "sannun ku fa, please, cikin gari kukayi"? Me tuk'in motar ya dan yatsina fuska, a tak'aice yace "Eh" dayan ko kallon su beyi ba, ba tare da bata lokaci ba mimi ta sa hannu ta bude baya, zata shiga kenan me tukin motar yace "ba dai da Ninja din chann za a shigar min mota ba?" Mimi ta kalleshi da mamaki, tace "ninja kuma"? Yace ehmana wanchan me Nikab din, Ushee a hankali tace Seebi daga nikab dinki, wacce aka kira da Seebi ta kalli Ushee cike da takaici tace bazan daga ba, ba zan kuma cire ba, sai a sannan Abokin ya juyo don kallon mai nikab, itama ta dago kai kenan suka hada ido, sun dauki kusan seconds goma suna kallon-kallo, yayi saurin dauke kai, ya maida kallon shi ga Abokin shi, murya kasa-kasa kamar bai son magana"yace Maalesh donAllah mu tafi" wanda aka kira da Maalesh ya kalli miemee yace "Malama kulle min kofa ko?" Miemee za ta yi mar magiya kan yayi hakuri mai nikaf tayi saurin kulle kofar, Maalesh ya ja motar sa a sittin ya bar gurin. Mimi cike da fada tace "Haba SEEBI menene haka?" kin wargaza mana damar da mu.ka samu na tafia gida, Ushee tace aa fa mimi, shima ya sa wulakanci a alamarin shi, menene abun ce mata Ninja? kuma har sai ta cire nikab zai taimaka ya dauke mu? Mai nikab din tace "Dama chan basuyi niyyar daukar mu ba". Ushee tace Seebi kin lura da na gaban motar? Side view din shi kadai nagani, amma nagane Azababben guy ne ko kallo fa ba mu ishe shi ba, Uhm kadai Seebi tace a yayin da ta tuno kallon-kallon da suka yi da shi, Miemee cike da masifa tace tunda dai sun tafi ai shikenan, Seebi ta mana Bukulu, kila da ko numbern mu sun amsa, Usheey ta ce ke kuma matsalarki kenan sun amsa number? Harararta mimi tayi Seebi me nikab ta sa daria don ta saba ganin haka gun kawayen ta biyu, yanzu ba wannan ba burin ta a yanzu be wuce ta bude ido ta ganta a gida ba. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg2⃣ Haka suka cigaba da tafiya har suka fita gate, suka tsallaka titi, a lokacin kuwa dare yayi don bakwai ta gota. Zuciyoyin su ya fara karaya, tsoro da fargaba ya mamaye su, barin ma mai nikab din da ta fara hawaye a cikin nikabin ta. Sunyi nesa da gate Ushee tace "idan ba so kuke mu karasa cikin Gari a kafa ba ku tsaya mu samu mota ko daga cikin wadannan masu wucewa ne" Miemee please ki taran mana lift, Miemee ta tabe baki, tace "ba zan tsaida ba" donAllah mana miemee inji Mai nikab, in tsaida ki k'i shiga? Da sauri ta zame nikabin fuskarta, tace "kinga na cire gabaki daya" Miemee tayi murmushi tace "eh lallai dagaske kike" ta dan matsa bakin titi ta sa hannu, motoci goma suka wuce da karfi ba tare da sun tsaya ba, Mimi tace ba fa zasu tsaya ba, ni na gaji. Ushee tace "Dont give up" Miemee ta wurga mata harara tace malamai kuzo ku sa hannu kila mu samu wani ya tsaya. Ushee tayi daria ta matso kusa da mimi suka sa hannu. Daga nesa suka hango wata Jan Mota ya doso da full light dinsa, suka dage wurin daga hannu yanda za a gansu daga nesa, Motar ta cigaba da dosu har ta gifta su, Ushee da karfi tace "kaii yau mun shiga 3" Seebi da ke gefe hawaye kadai ke zuba daga idanuwanta. Horn suka ji ga baki dayan su ka kallo inda suka ji horn din,Miemee tace "lahh ga wata BMW na na zuwa da baya da baya, mai jan motar nan ne ya dawo, ushee tace muyi sauri mu karasa gunshi kafin ya chanza ra'ayinshi, sauri-sauri suka nufe me motar nan. Mimi ce gaba suna biye da ita a baya har suka iso inda mutumin yayi parking motarsa, ta window miemee tace Assalamu Alaikum, mutumin ya sauke glass din motar sa, hade da amsa sallamar Mimi, Waiyo Allah! Mimi bude baki tayi tana kallon mai motar, don ya hadu iya haduwa kamar shi yayi kanshi. Ganin kallon da Mimi ke mishi ne ya sa shi cewa "Cikin Gari zaku?" Ushee da ta lura kwatakwata hankalin kawarta mimi be jikinta ya sa ta matso kusa, itama kusan abun da ya faru da Mimi ya kusan faruwa da ita, amma ta dake tace ina wuni? Cikin gari zamuje, donAllah ko zaka rage mana hanya? Yace Bismillah, Ushee tace Mungode, tayi saurin zunguran Mimi, Mimi ta wayance tare da saurin shiga gaban motar, Ushee ta bude baya ta shiga tare da kallon kawarta da ke tsaye waje, tace "Seebi shigo mana" cikin sanyinta ta shigo da Sallama, ya dan waigo ya amsa sallamarta ya dauke kai, bayan ya kwashe takardun da ke bayan sit din. Gaishe shi sukayi duka ya amsa musu, yace Students ne ku, suka amsa mishi da eh, amma a hostel kuke ko? Ushee tace No day, cike da mamaki yace Day students kuma?ya akayi kukayi dare haka? Mimi cike da yanga ta bashi bayanin dalilin su na yin dare, ya jinjina kai, yace ya kamata a san nayi, in rescheduling lectures din za'ayi tok, idan kuma Buses za a karo don tabbatar da an kai kowa gida, is very risky a bar dalibi mara abun hawa a nan, balle ku mata. Allah shi kyauta suka amsa da Amin. Haka ya cigaba da tukin shi, Ba wanda ya sake magana, ba kajin komai sai karatun Qurani mai Girma kira'ar Sudais. Dif-dif sukaji, Alamun shigowar waya, mimi ta lek'a wayar kirar Iphone 6s da ke jone jikin radion mota (AUX) taga Meema jikin screen din, Mutumin yace ma mimi dan taimaka ki min swiping, da sauri mimee ta yi yanda yace. Ba tare da ya kanga wayan a kunnesa ba yace "Hello Assalam Ailaikum" wata Zazzakar murya su Ushee sukaji ta cikin speakers ba cewa "Hello Uncle Zaid kanajina?" Yayi murmushi yace "Ohh Meema, so nawa zan miki maganar amsa sallama? Oh sorry Waalaikum Salam, Uncle Zaid baka iso bane har yanzu? Meema ina cikin katsina, but sai naje masauki, idan na huta zuwa anjima ko da safe sai na zo gidan ko? A shagwabe tace "haba mana Uncle Zaid, You promised to come see us immediately you arrived" Ya sauke ajiyar zuciya, yace "toh bani 30mins zan karaso InshaAllah" tayi dariar murna, yay Uncle Zee Thanks, u d best" yace "erhm, Rafeek na gida?" tace "No be dawo ba ko" ya danyi shiru yace "toh sai na iso" kafin tace wani abu ya latse wayar. Ushee ta kalli Seebi, sukayi murmushi, matuk'a wanda aka kira da Uncle Zaid ya burgesu, daga jin wanda su kayi waya da ita sun san yar gata ce, don yanda take shagwaba da magana, a hankali ushee ta rada ma Seebi 'kila diyar yayar sa ce' seebi gyada kai tayi. Zaid ya dago wayarsa, ya dan rage gudu, ya shiga neman layin nephew dinshi, callertune din yazo karshe ba amsa, ya sake redialling, yanzun ma kamar ba za'a dauka ba, a ka dauka ba tare da ance komai ba, Zaid yayi gyaran murya, yace "Rafeek" chan kasa sukaji ance "Barka da yamma" Zaid yace "lafia lao, Kana ina?" kamar bazai tanka ba, yace "Gani nan Maalesh zai saukeni gida" yace"Okay toh, ku je ku min booking Liyafa hotel" Ok kadai yace ya kashe wayar, Zaid ya murmusa a baiyane yace "Rafeek ikon Allah".. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg3⃣ Zaid ya kallo Miemee yace"Ina kukayi?" mimi ta yi far da ido tace"dukkanin mu unguwanni daban muke, ka ajiye mu a National, sai mu hau keke napep" yace "Junction din bus? No, kubari na sauke ko wacce a unguwar su" mimi ta yi murmusi mai sauti tace "ji fa nayi ana jiranka" yace kar ku damu, ya kalli mudubi daidai saitin Seebi, yace Malama wani unguwa kuke? Seebi baki ya fara rawa ta kasa magana, da sauri ushee tace mu muna ta Wurin Gidan Masari, Miemee kuma na GRA wurin motel. Zaid ya jinjina kai yace wace Miemee? Miemee na murmushi tace "nice nan" ya sake kallon madubi yace kece wa? Ushee tace nice Ushee, wannan kuma Seebi, Zaid yayi murmushin da ke kara ma fuskar sa annuri, yace "inyee!, sunan yan gayu ne daku, Miemee, Ushee da Seebi" sukayi daria duka, yace toh bari mu fara sauke Miemee, ku ta unguwarku nayi. Da taimakon Miemee na nuna mai hanya Zaid ya iso har kofar Gidansu, yayi parking, miemee ta sadakar zaid zai tambayi numbern ta, sai wannan yanga takeyi, amma shiru takeji, a ranta tace kila zai tambayi su Ushee, ta bude murfin kofar tace "Thanks So much Uncle Zaid" ya yi murmushi yace bakomai, ta juya ta kalli kawayenta tace "toh kar dai a manta a fito da wuri gobe don muna da GSP karfe takwas (8:00)" Ushee tace "InshaAllah" Seebi tace "ki gaida Mummy" Miemee tace "Zataji, dayanku ya dawo gaba" Ushee ta bude murfin motar ta koma gaba. Mimi ta daga ma Zaid hannu, Ya ja motar ya bar layin ita kuma ta shige gida. Shiru ba wanda ke magana, sai da yazo unguwar yace ta wurin ina kuke? Ushee tace "ka ajiye mu a wurin Makarantar Salamah" ba wanda ya sake magana har suka zo daf da makarantar Salamah, yayi parking, Ushee tace mungode sosai, Seebi ta bude murfin motar, tace"Jazakallahu khair" Allah ya biyaka yanda ka taimake mu" da sauri ya waigo don yaji dadin adduar nan, duk da be samu ya ga fuskar yarinyar sosai ba yace "Amin Nagode" Suka rufe kofar ya ja motar sa yayi cikin unguwan, Ushee tace toh Seebi sai da safe, Allah ya kaimu Ushee, ko wa tayi hanyar Gidansu. Sai da tayi tafia sosai kafin ta iso gida, ta na ture kofar gidan ta ga Nenen ta tsaye, da sauri Nene ta rungumota tare da matse kwalla tace "Nasiba, ina kika tsaya haka? Duk kin tashi hankali na, ince dai lafiya ko?" Nasiba ta kalli kakarta cikin tausayawa, tace "Nene kiyi hakuri, darasi mukayi 4-6, ko da a ka tashi ba mu samu abun hawa da wuri ba, sai da ma mu ka tako har wajen gate kafin muka samu wani bawan Allah ya kawo mu har gidansu ushee" Nene tace bakiji yanda na tada hsnkali na ba, don naga baki taba kai wa haka a makaranta ba, na ci kuka na ni kadai, na fi minti 30 gaban gidan nan, ga shegen unguwar nan, ba wanda zaka aika. Da na hana babanki ya sai man waya, amma saboda irin haka, dole xai siyo min, Seebi tayi daria tace bari na shiga ciki in watsa, ko Laasar banyi ba wlh" Nene tace "yi maza, ga abincin ki chan a madafa" ta amsa tare da shigewa cikin gidan. Assalam Alaikum yayi sallama a kofar falon gidan, mamimakon a amsa mai, sai jin ihu yayi, yayyy!!! Ga Uncle Zee oyoyo, wasu yanmata biyu suka zo suka rungumeshi, takaici ya cika Zaid, be da yanda zaiyi sai dai k'irk'iro murmushin dole wanda hausawa ke cema Yak'e kafi kuka ciwo, Babbar ta ja hannunshi zuwa dinning area, tace "Uncle Zaid, i know u must be hungry" murmushi yayi yace "Aa meema, ciki na a koshe yake" ta marairaice tace "donAllah kaci, ni da kaina na girka maka, wallahi na dade ina yi, please" Ya mata murmushin da ke kashe ta yace "Meema i'm full wallahi, some other time ko?" be bari tace komai ba ya kalli dayar budurwar yace "Aneesa Yaya na nan? Tace "eh Uncle Zaid yana sama" mikewa yayi ya hau sama. Ya shiga da parlorn yayan sa da Sallama, Yayan ya amsa mishi cike da farin cikin ganin danuwansa, Barka da Yamma yaya, yayan ya amsa mishi da "Sannu da zuwa Engr. Zaid Ibrahim Lema, Zaid yayi daria, yace ka fara ko yaya? Nan suka fara fira irin ta wa da kani cike da aminci da kaunar juna, suna cikin firan ne Hajia Saude tayi Sallama ta shigo dauke ta tray, tana kwarkwasa kamar wata yarinya, "Ahh! Zaidu, ka iso kenan? Ya amsa mata ba yabo ba fallasa, ta dire tray din gabn mijinta ta na tsiyaya mai ruwan zafin shayi a dan karamin kofi, tace" Kaima a zuba maka Shayin ko Zaid? Ya mike da sauri yace "aa nagode, bari inje masauki nagaji" ya kalli yayanshi yace "Yaya bari na tafi zan shigo da safe in Allah ya yarda", Alhaji Habib Ibrahim Lema yace "Allah shi huta gajia Zaidu". A parlorn kasa ya iske meema da alamun jiran shi takeyi, tana ganinshi ta nufo shi da sauri, Uncle Zee har ka gama da daddy? Yace eh nagaji ne, zan tafi na kwanta, tace yanzu ba za kaci abun da na girka domin ka ba ko? Yace "sorry Meema" sai da na ci abinci kafin na karaso. Ba haka taso ba sai dai ba yanda zatayi da shi tace "toh munje in raka masaukin naka" yace wa zai dawo dake? Don ni bazan sake fitowa ba sai gobe, ta mai fari da ido tace"ba sai na kwana chan ba" ya zaro ido, yace ke bana son shiririta, ta wayance tace "haba, kasan wasa nakeyi" ya wuceta ta bi bayanshi "mai zan dafa maka da safe?" Yace "Nothing". Ta juyo a fusace tare da fashewa da kuka haye sama.. Daidai haraban gidan mai gadi ya wangale gate, wata bakar mota mai bakin gilashi ta shigo, Uncle Zaid ya tsaya kallon motar har tayi parking, bangaren kujeran direba a ka bude, na cikin ya karaso gun zaid da sauri yace "Uncle Zaid sannu da zuwa, ya Kaduna? Zaid ya amsa cikin sakin fuska lafiya lao Mahmud. Dayan ya fito cikin takun kasaita, kamar be son taka kasa, ya karaso gun da su Zaid ke tsaye, sai da ya zo daf da su, ya tsaya ya cire baki da kyar yace "ka zo lafiya?" Zaid yayi murmushi yace "lafiya kalau Rafeek, ya karatu? Maimakon ya amsa shi, hannu ya sa a aljihu ya zaro makulli ya bashi, yace " room 108, Allah huta gajia" ya maida duban sa ga abokinshi yace "Night Maalesh" ya juya ya bar Zaid da Maalesh a gurin. Zaid yayi murmushi ya tsaida shi ta hanyar kiran sunan shi "Rafeek Lema " Chak ya tsaya. _Bibilicious biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg4⃣ Uncle Zaid ya tako har gaban shi ya, yace "kana da matsalan wani abu? Do u need anything?" girgiza kai rafeek yayi, yace No, nothing, Zaid yace "nawa aka kama min daki? Rafeek yace "na riga na bada" kayan abincin ka fada kudi? Rafeek yace "akwai saura" karatu fa? A takiace yace "Lafiya " Zaid yayi daria yace "baka tambayi Mami ba" Rafeek ya dago jajjayen idon sa ya kalli kawun shi, Zaid ya fara daria don ya san ya kure hakurin shi, tunda har ya sa shi magana haka, yace to "ka tafi ko?" kamar jira yake ya fara tafia part dinshi, Zaid ya juya gun maalesh, Mahmud ya abokin na ka? Maalesh yace "Uncle Zaid, akwai improvement, don yanzu yana zuwa lectures, daga chan muke wai yayi lectures 4-6", Zaid ya kalleshi yace "good, kai yaushe kake gama service din? Maalesh yace"karshen wata" Zaid yace yayi "kyau copper, ka kawo min CV dinka kafin na bar katsina" Maalesh yace nagode Uncle Zaid. Kamar daga sama yaji muryan Rafeek nace wa "erhm, nace ba?" Zaid da Maalesh suka kallo shi, Zaid yace "naam, kace mene?" Rafeek ya danyi guntun tsaki yace " kace ma wannan yarinyar ta daina shiga harkata, ta daina kula ni" tsaf Zaid ya gane yarinyar da ya ke magana, amma sai yace "wace yarinya kenan?" Rafeek ya bata rai yace "Aneesa" Zaid ya dan murmusa, yace "haba Rafeek, ya zaayi ta daina kula ka? Ai ko ba komai zumunci ya hada ku, ba wani abu bane don ta kula ka, besides ai kanwar ka ce, duk da ba a saba ganin fuskar shi da murmushi ba, amma kallo daya zaka mishi yanzu kasan ranshi ya baci, ya daure fuskar nan tamau, zuciyar sa na tafarfa sa, da karfi yace " she's not my Sister, she's Nothing like my sister" Maalesh ya tsorata da yanayin abokin sa, don ya dade be ji ya daga murya haka ba, kuma uncle Zaid ya ke ma ihun nan? Kai Rafeek be cikin hayyacin sa" Rafeek ya runtse ido gam, Zaid ko sai daga baya yayi da na sanin cewa Aneesa kanwar Rafeek ce, tunda ya ga haka, ya san ran shi ya baci, kwata kwata be son ganin tillon dan yayan shi a damuwa.Rafeek ya bude ido a hankali ya sauke su fes kan Zaid, dan gajeren tsaki yayi yace "I am sorry" Zaid yayi murmushi yace "je ka kwanta Rafeek" Maalesh kai ma ka wuce gida Allah ya bamu Alheri" ya fada motarsa, Maalesh ya shiga motarshi ya tada, a ka bar rafeek tsaye yana kallonsu, maigadi ya bude gate Maalesh ya fara fita, daidai Rafeek uncle Zaid ya tsaya, yayi winning glass ya miko mishi takarddun Kilishi guda 2, yace a hanyar K'ank'ara na siya " Rafeek ya amsa yayi murmushi da gefen bakin sa, Zaid yace "Baka tambayi Ayman ba" Rafeek ya dan gajeren murmushi, yace "she's fine, she is always" Zaid ya jinjina kai yace "Good night Son" Rafeek ya daga mai hannu ya wuce. Nasiba, yau ba darasi ne zaki tashi ko sai kin makara? Nene, na gama makara wallahi, amm dai shiryawa nakeyi, na kusa gamawa, Nene tace" kin san nafi kowa son karatun nan, so nake naga kin zama dapta" Seebi tayi daria, tace"Nene Doctor ake cewa, kuma ai Nene ai ba karatun da nakeyi ba kenan" Nene tace "ke dalla rabani, duk daya ne, tunda ance zaki iya aikin asibiti da karatun,dama ni buri na in ga yar jikalle na aikin asibiti, idan naje ba ruwana da bin layi" Nasiba ta fito tana daria, tace "Oh Nene akwai abin daria, nikam bari in tafi don na san nayi latti." Nene tace "ga kalacin ki chan, yanzu na siyo miki kosai, ga koko na dama miki" tace Wallahi na tsaya kalaci latti zanyi, ushee na chan National ta na jirana, idan naje makaranta zan siya, Nene ba ta ji dadi ba, amma ba yanda zatayi, ta ciro #200 a hab'ar zaninta tace "gashi kin kara" Nasiba ta rungume kakarta, tace "nagode Nene sai nadawo" har waje ta rako Seebi ta na mata addua. Ya shigo gidan Cikin shiga k'ananun kaya, yayi kyau matuka, a parlo ya zauna yana neman layin Rafeek, ringing na 3 ya dauka "Barka da Safiyya" Zaid yace "Rafeek, ka tashi lafiya?" eh kawai yace, ka tafi school din ne? Rafeek yace "Eh, ina da lectures ne yanzu" Zaid yaji dadi sosai, yace "ni gani nan zan wuce Abuja, sai na dawo kaduna, ko na biyo ta makarantar muyi bankwana?, Rafeek ya girgiza kai yace ba sai kazo ba, Allah ya tsare hanya, ina gaida Ayman dina" Zaid yace "Ayman dinka zataji, amma ita kadai? Rafeek yayi saurin cewa "Safe journey" tare da latse wayan. Aneesa ce ta saukko taga Uncle Zaid zaune, bude murya tayi tace "Aunty Meema, ga Uncle Zaid" ta karasa gunshi "good Morning Uncle Zaid, Zaid yayi dan murmushi yace "Aneesa kin tashi lafia? Lafiya lao Uncle Zaid ba dai yau zaka tafi ba? Yace yanzu kuwa "yaya ya tashi ko?" Eh ya tashi, Uncle Zaid, ina da matsala" Ya dan kallota na me fa?, ta gyara Zama "Uncle Zaid, Yaya Rafeek ne, ba ya son in rabe shi, kullum da ya gannin kamar ya ga mutuwar shi, rannan har mari na yayi don na je dakin shi" ta karashe maganar ta tana kwalla, Zaid ya sauke numfashi, shi ma besan ta inda zai bullo ma lamarin Rafeek ba, kullum sai fadin rai, ya kasa manta abunda ya faru a baya, ya kasa cigaba da rayuwar sa kamar yanda wasu ke cigaba da rayuwar su idan wata k'addara ta fado musu. Ya daure yace " kiyi hakuri Anee, kinsan halin Rafeek, Miskili ne, ki daina shige mishi, kar wata rana ya illata ki, ki yi hakuri, ki taya shi da addua Allah ya shirya shi, da ina da ikon chanza shi da na chanza shi, amma Addua kadai yake bukata. Da sauri Aneesa tace Uncle Zaid wallahi zan iya chanza, ina son shi, zan iya zama da shi ta ko wanne hali, ku aura mishi ni, ni ce ALHERINSA. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg5⃣ Zaid ya yi mamakin maganar Aneesa, banda yarinta ya za'ayi tace a aura mata Rafeek? Uncle Zaid baka ce komai ba, Aneesa ta katse mishi tunanin. Yak'e yayi, yace "banda abunki Aneesa, wa zai ma Rafeek aure yanzu? Rafeek fa yaro ne, he is just 24" tace "Uncle zai- ya katseta ta hanyar daga mata hannu yace "please anee, no one is getting Rafeek married now" tayi raurau da fuska, tace"Wallahi ina son Rafeek, zan kuma jira shi, zan jure duk wani wulakancin da zai min. "Tunda maganan Soyayya akeyi, bari kuji labarin rai na" Meema ce ke fadin haka a yayin da ta ke sauko wa daga bene har ta karaso gaban su, sanye take da shara-sharar rigar baccin da ko guiwar ta bata rufe ba, Zaid ya dauke duban sa daa kanta, masauki tayi kan kujerar da yake zaune, fari take mai da ido tace "Uncle Zee, kasan irin son da nake maka? Ni bansan yanda akayi na fara sonka ba, kuma na sha mafarkin mun yi aure mun haifi kannen Ayman, Uncle Zaid ka aureni please. "Ya Salam!" Zaid ya furta a hankali tare da dafe kanshi, wasu irin mata ne wannan? Masu tallan kan su, Ya cije ya kalli meema da ke ta wurwulla idanuwa don ta burgeshi, wani takaici ya tokare mai wuya, ya san Meema na son shi, tun kafin yayi aure, amma ba zai iya auren ta a haka ba, sam rayuwar su basuyi kama ba. Alhaji Habib Lema da matarshi Hajiya Saude suka sauko kasa, da sauri Zaid ya tashi ya nufi gun yayan shi, yace "Barka da safiyya" Yayan yace "lafiya lao, Engr. Har anyi harramar tafiya?" Zaid yace InshaAllah "ya juya ya kalli matar yayan sa yace "Madam an tashi lafia?" fuska sake tace "lafiya lau Uncle" yayan yace "Zaid muje daga waje akwai wata maganar da nake so muyi, yace "toh yaya" Zaid ya musu Sallama da ga chan zai wuce, ba haka hajia saude ta so ba, ta so taji maganar da Alhaji zai gaya ma Zaid, ta so taji me zasu tautauna a kai. Meema ta kalli yayar ta rai a bace tace na "Nagaji Sauda, ya za'ayi na dinga mishi tallan kai na ya na ba dani? Nifa na fi karfin wulakanci da namiji" H.saude ta murmusa, tacd dadi na dake Maryam gajin hakuri, ai komai sai an bi a sannu a ke dacewa ko? Kiyi laakari da yanda ni na samu Alhaji, ki kara hakuri komai ya kusa zuwa karshe" Aneesa tace "Mummy ni kum-- Hajia saude tace " shhh, Matsalarki Rafeek ko? Nima shine kadai matsala ta, bana jin Zaid, Rafeek nakeji, amma kar ya damu idan ya sn wata be san wata ba, ku bar komai a hannuna kunji?" Meema da Aneesa suka chafe hannu cikin murna suna fadin "sai ke mata daya rak a gidan Habib Lema" ita ko dadi wannan kirarin ya mata dadi ta haye sama. A hankali yake tuk'insa, yana tunanin maganar da yayan sa ya gama mishi yanzu, a kan karatun Rafeek ne, inda yayan ke cewa "kaga Zaid, ni sai nayi wata da watanni ban daura Rafeek a idona ba, be yarda mu hada hanya, anya yaron nan be shaye shaye? Da sauri Zaid ya girgiza kanshi, yace " wallahi Rafeek be shan ko Sigari" Yayan yace "Zaid na kasa yarda da hakan shekara ta uku kenan Rafeek na Spill over a makaranta, last upper year spill over from nowhere, be gyara ta ba, last year ma be gyara ba, ina tsoron wannan shekarar abun da ya faru ya sake faruwa don da alamun abokan banxa yake bi suke bashi wasu k'wayoyin da ke taba mai kwakwalwa, shisa ya kasa kwantar da hankalinshi yayi karatu" da sauri Zaid ya katse shi, ta hanyar cewa "aa yaya, ka fadi Alkhairi ko kayi shiru, kowa ya san Rafeek mai k'okari ne da hazaka, kar ka manta tunda Rafeek ya shiga UMYU shine over roll dinsu, 4+pointer, komai ya dagule ne sakamakkon k'addara da ta riga fata, amma InshaAllah komai zai daidaita. Alh. Habib ya jinjina kai yace "haka ne Allah shi kyauta, amma kasan har yanzu ba ya min magana? Zaid ya tashi yana daria yace bari na tafi "Yaya sai na dawo karshen Sati" Alh. Habib yayi daria "wato ba ka son laifin shi ko?" Toh Allah ya kiyyaye. Wata tsohuwa ya gani da ga gefe ta na sa mai hannu, yayi mamaki don ba a titi yake ba, har yanzu be fita daga cikin Unguwar ba, ya dan gangara ya sauke gilashin motar shi, yace Lafiya Iya? Tsohuwar tace Yauwa bawon Allah taimaka ka zo ka ka duba min layin wutan chan, k'auri yake yi,nafi minti 30 tsaye ko zan ga wani namijin da zai duba mun, amma tun dazun shiru, Zaid yayi shiru ya na karantar tsohuwar nan. Can ya fito ya kulle kofar yace muje nagani, tsohuwar ta ja shi har cikin madaidaicin gidanta, daidai gurin, fuse din har ya fara spark , "SubhanAllah, kinga ya fara kamu da wuta" Zaid ya ga in dai ya bata wani lokaci wires din wurin za su fara ci, kuma baa san inda wutan zai tsaya ba, yayi jihadin sa hannun shi ya zaro fuse din ya cillar. Tsohuwar ta sa ihun murna har da tafin ta, tace "sannu dan Albarka, Allah ya sa ba abunda ya samu hannuka" Zaid ya dago hannun shi, Cikin ikon Allah ba abunda ya samu hannun. Zaid yace "ina zuwa, ya fita" tsohuwar ta bishi da ido, motarsa ya shige, bayan mintuna kadan sai gashi da mai gyaran wuta, Zaid ya kalli tsohuwar yace " Toh Iya, ga mai gyara nan, ni zan tafi" baki bude tsohuwar nan take kallon shi, bawan Allah tsaya, Zaid ya tsaya, tace Nagode kaji? Allah ya biyaka, Zaid yayi murmushi. "Amin Nagode Iyah, ni na wuce" tace "donAllah ka tsaya, na kwadanta maka zogale" yace "wallahi, sauri nake, kaduna zan tafi yanzu" tace toh dan jirani da sauri ta shige kitchen, sai ga ta da bakar leda ta mik'a mai, tace gashi ya amsa yana mamakin me ke ciki, tace kayan miya ne irin su daddawa, kuka, kanwa da su kanumfari" ya ce toh ni iyah-- ta katse shi ta hanyar cewa a kai wa Uwargida, idan babu kuma akai ma mahaifiya, Zaid ya sake wani murmushi, farat daya yaji son tsohuwar nan har ranshi, yace "toh nagode Iya" tace bakomai har ya juya tace "nidai, in kace min iyah, ji na ke kamar ka mayar dani wata tsohuwa, zaid yayi daria sosai, yace ai tsohuwar ce" tace "kai bawan Allah, ban wani tsufa ba" yace toh shekarun ki nawa? Tace goma-goma guda shiddada hudu Zaid(10*6+4) ya bude baki yace lalala 64 fa kenan? eh lallai baki tsufa ba" a tare sukayi daria. Yace "toh me zan dinga kiran ki dashi ? Tace "yanda jikoki na ke ce min, NENE" _Bibilicious biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg6⃣ Zaid ya murmusa yace "toh nene" tace "kai ya sunan ka"? "Sunana Zaid" tace "Zaidu Bawan Allah" yayu dariya yace "toh Nene bari dai in wuce kar nayi rana". tace "Gaskia ne, ince kaduna zaka ko? Ko ka san d'a na? Hafizu Mamman? Fari dan fulani" Daria sosai Zaid yayi yace "Nene kaduna babban gari ne, ba yanda zaa yi na san shi" tace "Allah ka bincika, duk kaduna shi kadai ne" Zaid da ya k'osa ya tafi yace "Toh Nene", Kudi ya ciro ya ba mai gyara suka kara Sallama. Har bakin motar shi ta rakashi, tana daga mai hannu tana mai addu'oin kariya. Ya tada motarshi yayi ribos,ya dau hanyar barin unguwar, Nene ba ta koma ciki ba har sai da ya kure ganinta kafin ta koma cikin gida, bini-bini sai ta saki murmushi tana tunanin Zaidu bawan Allah. Asalin Sunan Nene :Amina amma an fi saninta da Aminene, 'ya'yanta 6, dattijuwa ce me kimanin shekaru 65, Mijinta ya rasu shekaru 20 da suka wuce ya barta da 'ya'ya 5, a halin yanzu 2 suke da rai 3 sun rasu. Cikin wanda suke da rai akwai Fatiti, ita ce diyar Nene ta biyu, tana aure a Jihar Jigawa 'ya'yanta 3, Amina,Umar da Muhammad. Muhammad Bishir Sunan autan Nene, yana zaune da matarsa da 'ya'yansa biyu a Malali cikin jihar Kaduna. Nasiba ce ta farko sai kaninta Anan. Muhammad Yayi aiki a National Trust fund kafin a kulle kamfanin (Company). A hanlin yanzu ba ya aiki amma yana karban pension duk wata. Nasiba yar kimanin shekaru Sha tara a duniya(19), ba za a sa Nasiba a jerin farare ba, haka kuma ba za a sata a jerin bak'ake ba, wankar tarwada ce, me dara daran idanuwa, idan tayi murmushi kumatun ta sukan lotsa, bata fiye tsayi ba, kuma tana da dan jiki daidai ita, a takaice Nasiba ta kai macen da ake kira da masu kyau. Tayi karatun ta na Nursery, primary harda Secondary a Kaduna Capital School(KC). Bayan ta gama ne baban ta ya siya mata JAMB, da doki tace Abba ai Katsina zan sa ko? Ya harare ta cikin wasa yace "kina nan, don ko Rigachikun ba za ki wuce ba" ta turo baki tare da bubbuga kafa tace nidai wallahi Abba bana son KASU" tun nursery dina a nan nayi Abba, Shekaru 15 ina karatu a kd, ai change of environment na da dadi, ka ga sai in kular maka da Mamanka tunda tak'i yarda ta dawo gidan nan da zama" Umma tace "Eh kinyi gaskiya Nasiba, Nene na bukatar wani kusa da ita, tunda anyi anyi ta dawo kaduna ta ki yarda, ya kama ta kije chan kiyi karatun, Mutum ai rahama ne" Abba ya jinjina kai, yace "ko don Nene zan barki kije Katsina karatu" tayi ihun murna tace yauwa "Abban mu" Anan yace Adda Seebi yanzu kina murna zaki tafi ki barni ko? Sai ya fashe da kuka, da saurin ta rungume tillon kaninta ita ma kukan take yi tace yi shiru Anan, ai zan dingw dawowa hutu kaji?kuma ga Abban mu ga Ummin mu ai ka ga ba kai kadai bane ko? Da kalamai masu dadi ta lallashe shi har yayi bacci, ta dauki form din ta fita don zuwa dakin ta, ta cika 1st&2nd Choice UMYUK, Microbiology course don school din basu fara Medicine ba. Abba ya kalli matarsa yace Ummin yara, gidan nan na layout(Gidan gadon shi), ina ganin zan tada mutanen ciki Nene ta koma can, Gidan Kofa Uku ya tsufa,nan aka haifi marigayi Yaya Shehu fa, Umma ta kada kai tace lallai ya tsufa kam, kinga kuwa sai ta koma gidana na layout din, Ummi tace "toh Allah ya sa ta yarda, don yanda take son Unguwar nan, raba ta dashi sai Allah, saboda mutane da Abokan arzikkin ta ya sa ta hana a dauko mata wacce zasu dinga zama tare saboda kadaici," Abba yace ai Nene in ta kafe ba me tankwara ta, amma bakomi na san yanda zan bullo wa lamarin" Ummi tace Gidan fa? Yace "sai in gyara a zuba yan haya ciki" Cikin Ikon Allah, Watannin da basu rufe 10 ba, Nasiba ta samu Admission a Jami'ar Umaru Musa, course din da ta zaba suka bata, Gaba ki dayan su suka zo Katsina don rako Seebi, don daga Registeration ba za ta dawo Kaduna ba. Nene tayi murnan dawowan Seebi gunta, don ta na son jikokin ta sosai, bayan sun huta, Abba ya kebe da mahaifiyar shi, Nene tace "Ya akayi ne Mahammadu? Cikin ladabi yake maganan, yace " Nene, gidan nan ya tsufa, katangar kamar zata fado, shine nace ko zaki koma chan gidana na layout, tayi saurin katse shi "kai tsaya, ni da gidan nan mutu ka raba, shekaru sama da 30 ina zaune da yan unguwan nan lami lafia, kawai sai kace na tashi? Too don naki Garin Gwamna (Kaduna) shine kazo da wannan salon? Toh ba zan tashi ba, ina nan ni da gidan nan mutu ka raba, idan katangar ya tashi fadowa ya fado kaina, kaga nayi mutuwar shahada kenan". Abba ya ja numfashi ya san a rina. Ya sadda kansa kasa yace " Nene, ba wai gaba ki daya za ki koma chan ba, gyara zaayi, idan an gama daga katangar sai ki dawo, tace kai yaro ni zaka yi wa wayau? Ko da nake kauye ba a riga na zauna ba, ka fita idona. Abba ya girgiza kansa ya ciro waya ya kira yayar sa Fatiti, ringing biyu ta dauka, ya mata bayanin kudirinsa kan Nene, tayi na'am da maganar, ya mik'a mata wayar itama tayi tayi amma Nene tace aa. Ummi ma ta sa baki, Sai da aka kai ruwa rana kafin ta yarda, tace ni abunda ke batan rai shine unguwar nan shiru kamar ta mayyu baka ganin kowa awaje don bakin hali. Daga Abban har Ummin ba su tanka ba don kar ta chanza raayinta. A ranan Abba ya kira masu mota suka kwashe kayan Nene na bukata suka kai Gidan layout, A rannan Nene batayi kwanan Kofa Ukku ba". Abba ke raka Nasiba Registeration. A gurin reg. Ne ta hadu da Ushee da Miemee. Hussaina Umar(Ushee) Aisha Saliz (Miemee) kawayen juna ne, tun JS1 suke tare, Ushee da Miemee suna da kirki sosai, suna son junan su, Miemee ta fiye surutu da kaudi, Ushee kam akwai jan mutane a jiki. Wurin signing course form suka hadu, Inda Nasiba ta tambayi Miemee da ke bayanta a layi Biro, tace "donAllah ara min biro na rubuta mat.no dina nawa ya tsaya, Miemee da murmushin ta ta ciro ta bata, Miemee na son kyawawa, tace keme MCB kike? Tace "eh" Sunana Miemee, wannan kawata ce Ushee" Seebi tayi murmushi ta mika musu hannu sukayi musabaha tace"its nice meeting u all" nan suka dinke da labari har ya kai su da exchanging numbers, a nan ne suka gano gidan su Ushee be da nisa da gidan Nene. Haka Abotar su ta samo Asali. Wannan Kenan.. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg7⃣ "Kinsan jiya sai da nayi mafarkin Azababben Guy din nan?" Miemee ce ke maganar nan, Ushee da Seebi suka yi daria, Ushee tace ai ya hadu ne ba karya, Seebi tace ku ma kuka ga fuskar shi, ni jiyan nan ai a tsoroce nake, Miemee tayi tsaki, "ai wlh kina bada mu, kiyi ta wani nok'e nok'e kamar wacce tayi karya". Seebi tace banyi karya ba amma ai KUNYA ADON MACE (Na feedon biebee). Miemee ta kada idanuwa tace "story for the gods" Ushee tayi daria tace "ya isa, ku tashi muje Library mu fara Assignment din Wagini, Seebi tace "wallahi yunwa nakeji, daure wa kawai nayi aka gama first lecture" Ushee tace kinsan dai gobe za'ayi submitting, kuma gwara mu yi mu dawo before 12 kafin Mr Ola ya shigo, kin dai san rules dinshi ba a shiga idan ya shiga" Seebi tace "ba zaki gane yunwa Da nake ji bane, ku je ku mana Assignment din, Miemee tace "aa muje dai tare, sai mu fito mu ci abincin sha biyu saura minti talatin (11:30) Seebi tace "i can manage har time din muje". Tayi Sallama ta shiga Cafteria, tsirarrun mutane suka amsa ta dinga raba idanuwa, don yau kadai ta zo CAF ita kadai, dalilin hakan kuwa shine " ba su gama samun Assignments din ba gashi har sha biyu saura minti sha biyar(11:45), Miemee tace "tunda kin fi mu jin yunwa, kije ki yi sauri kici abincin, sai mu hade a class kiyi sauri fa, don muma duk ta kare tafiya zamu yi" Seebi tace Ok, muje ko Ushee? Miemee tace wlh ba za taje ba, ni kadai za a bari nan? Ki tafi kawai don you are waiting your time" Seebi ta harari Miemee tace "in kun ga dama kar kuyi sauri" Suka yi daria duka. Seebi ta wuce straight wurin reception desk, tace "Sannu ko" yaron ya amsa da mai "za'a kawo miki?" tace nikam bani koma meye sauri nikeyi aji zan shiga yanzu" yace" toh" ya shige ciki da sauri, don sauri ma ta kasa zuwa ta nema gurin zama. Jim kadan sai gashi ya fito da tray yace "hajia baki zauna ba?" tace "mik'o min kaji?" tray din ya bata, FriedRice ne da cowslow sai pure water. Nawa ne kudin? Yace "Dari Uku (#300)ne" ta ciro ta bashi ta amsa tray din Sai dai me? Juyawan ta ke da wuya ta ci karo da wani, ba ta san sadda ta sake tray din abincin ta ba, duk kayan ciki ya zube, ta dago idanuwan ta da suka kada suka yi ja ta kalli wanda ta buge, shi ko tunani yake wani me kasadan ne ya zubar mai da abinci a jiki? yana dagowa suka hada ido, tsaf ta gane shi, shine na gaban motar jiya, haushi ya turnike ta da ta tuna wulakancin da suka musu na k'in daukar su don tana sanye da nikab. Rafeek yayi dan guntun tsaki, da zai yi magana sai kuma ya fasa, ya juya don tafia, Nasiba tayi saurin shan gaban sa ta na huci tare da rik'e kugu, ranta a bace matuk'a, ga haushin ta zubar da abincinta, ga haushin yunwa, ga haushin missing lectures din da zata yi, ga haushin bata da wani kudin siyan abinci. Idonta ya kawo ruwa ba tare da saninta ba hawaye suka fara zuba daga idanuwan ta. Ido Rafeek ya kura mata, so yake ya tunkude ta yayi tafiar sa, ba halin shi bane tausayi, be damu da damuwar kowa ba, amma abin mamaki sai ya tsinci kanshi da ce mata "Me kike so?" _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg8⃣ Ta sa bayan hannun ta ta share hawayen ta, tace "ba kaine ka tsaya a baya na ba na kifar da abinci na, ka juya zaka yi tafian ka, ba ka ban hakuri ba, gashi yunwa nike ji, abun da ya fi ban haushi shine zanyi missing lectures dina." Kallon ta kawai yakeyi, ba wai ya fahimci bayyanan da take mishi bane, don shi ba ma'abocin sauraron korafe-korafen mutane bane, yana iya maka laifi ya fi ka zuciya, amma dai ya ji dai tace zatayi missing lectures. Mutane sai kallon R-lema sukeyi don da wuya kaga yana magana da namiji balle mace, in ka ganshi cikin CAF to takeaway yazo yi. Ya kalli mai bada abincin yace sake zubo abincin, ya samu wuri ya zauna, be kara bi ta kanta ba, tsaye tayi tana murza idanuwa, cleaner yazo don share gun, chan sai ga shi an kawo wani tray din, kallon ta yayi yace "zauna" ba musu ta zauna ya tura mata tray din gaban ta, ta kalli abincin ta kalle shi, tsaki yayi a ranshi, ya miqe ya fita, haka ta gyara zama taci abincin ta, wannan karon har da Orange juice. Tayi hamdala ta zaro wayarta, ta ma Ushee text "Lecturer ya fara? Jim kadan sai ga Ushee tayi reply da "eh ya shiga, kina ina?" ta mayar mata da "ina CAF, yana bari a shiga? Ushee tayi reply da " wlh bai bari, yanzu ya wulakanta su Chinyere, kuma ya kulle kofa" Nasiba ta hadiye kukan da ya so zuwa mata, ta ma Ushee reply da "ni na wuce gida, sai Allah ya kaimu Gobe" ta mike tare da daukar jakkarta tayi waje. Ba ta lura dashi ba har ta dan gifta yayi dan tsaki yace "erhm, nace ba? Ta dan juyo a firgice ganin shi ya sa ta sauke ajiyar zuciya tace "Wlh har na tsorata, kace mene?" kamar ba zai yi magana ba don yanda tayi maganar ta tuna mishi d wani abu, chan yace "Meyasa zakiyi missing lectures?" nan da nan idon ta ya kawo ruwa, tace "nayi latti, yana daga cikin ka'idojin malamin, na idan ya shiga aji ba wanda ya isa ya shiga, 12 yake shiga, gashi yanzu 12:19, kaga ko gwara na tafi gida akan naje ya hanani shiga karshe kuma ya wulakanta ni" Rafeek yace wani mallami ne wannan? Tace Mr Wagini ne. Yace ina kuke lectures din? Tace "Science Theatre" a takaice yace "biyo ni" be jira bin ta bakin ta ba yayi gaba. Babu yanda zatayi dashi da ya wuce ta bi bayanshi, tafia yake a nutse kamar be son taka kasa, fuskar nan tamke tamau duk inda suka wuce ji kake ana "R-Lema" mutane ba su damu da yanda yake basar da su ba idan sun kira sunan shi, ita ko Seebi ta kasa dauke idanuwan ta daga kallon shi, karantar shi take yi, komi nashi daban, ba kamar wasu mazan ba, ta tabbatar da wani ne suka jero haka sai ya isheta da magana, amma shi ko wannan ko kallo bata ishe shi ba, haka suka iso bakin Lecture hall din, Nasiba ta ja ta tsaya, tana kallon yan latti nan suna leke ta window, Rafeek ya taka har gaban kofar ajin da ke kulle ya sa hannu ya kwankwasa. Daga ciki Mr Wagini ne ke tunanin wani me kasadan ne ya ke kwankwasa mai, bayan shi da hannun shi ya kulle kofar, rai bace yace da na kusa da kofar"open the door" da sauri yaron ya je ya cire sakatar kofar ya bude, idon kowa a kan kofar, so suke su ga mai karfin halin kwankwasa ma Mr. Wagini. Shigo wa yayi yana tafian nan nashi,ya na bouncing a hankali, ba Matan ba harta mazan sai da su kaji ya burge su, kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa, da yawa za su so Mu'amala ko da ta gaisuwa ce ya hada su da Rafeek, Miemee tayi saurin tabo Ushee "OMG, ga wani Azababbe nan, ya tafi da imani na" Ushee tace "ni baki ji nayi shiru ba? Ai ya hadu ne over, mu dai kalli draman da zasuyi da Wagini". Har gaban Lecturern yaje, da alamun akwai sanayya tsakanin su, magana suka danyi kafin Rafeek ya juya ya bar Lecture hall din, Nasiba na tsaye inda ya barta, ta gaban ta ya wuce ta bishi da kallon mamaki, shi kuma wannan lafian shi kalau kuwa? Ko be gane ta bane ya wuce ta gaban ta ba tare da ya kalle ta ba? Ko kuma ya na nufin ta bishi ne? Duk a zuci take zancen nan, ba ta gama zancen zuci ba taji ana cewa "Mr Wagini yace duk na waje su shigo aji" da sauri suka fara tururuwar shiga ajin. Wuri ta samu ta zauna ta na tunanin Wannan Bawan Allah me tarin ban mamaki har a ka gama lectures ba ta fahimci komai ba. Kusan kowa zancen gayen da ya shigo aji dazun suke, wasu suce daga ganin shi dan zafin kai ne, wasu suce ya burgesu, Miemee ta kalli Seebi tace "kinyi missing, ba ki ga wani Azababben guy da ya shigo ji dazun ba" Ushee tace ni abun da ya daure min kai shine, yau Mr wagini yayi abun da be ta bayi ba shine barin late comers su shigo aji, Miemee tace "kuma fa immediately after fitan wannan ne yace ace su shigo" toh ko shi ya rok'i alfarmar abar su su shigo? Miemee tace wane shi? Be yi kama da lecturers ba, yaro ne student kamar mu, da kwai abun da ya kawo shi" kawai muce yau yan kirkin Mr Wagini suna kanshi" Ushee tace "gaskia kam" ta zunguro Seebi da kwata-kwata ba ta tare dasu, tafiya kadai takeyi, Seebi ta dan firgita ta k'akalo murmushi tace "Uhm" cikin zuciyarta kuma tunani take "Is it possible shi ya roke Mr Wagini akan a barsu su shiga?" Meyasa fuskar sa fa ba annuri? Meyasa da ya fito ko kallon ta beyi ba? Meyasa ko sunan ta ya kasa tambaya? Meyasa fuskar sa yake cikin yanayi na damuwa ko rashin walwala ne bata san ya za ta sa abun ba? Tambayoyi da yawa da take bukatar amsoshin su. Haka kurum taji tana son sanin Wanene wannan R-Lema? Nima biebee nace waye Rafeek Habib Lema?? _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg9⃣ ASALIN LABARIN: Anyi wani Attajirin mai kudi a garin Katsina mai suna Alhaji Ibrahim Lema, Matan aurensa 2, Karime da Hajjo. Karime ce Uwargida 'ya'yanta 4, Babba danta mai suna Habibullah, sai Aisha da Farida sai autan ta Zaid. Hajjo Amarya na da daya mai suna Hafiz. Alhaji Ibrahim yaso 'yan'yan shi su fi haka yawa amma da yake haka Allah ya tsara sai ya hakura. Zaman lafiya akeyi a gidan Alhaji Lema don yana bawa kowa hakkin sa. Habib shine babba a gidan, yana da kwazo don shine yayi gadon mahaifinshi don tsufa yazo mishi, a yanzu Zaid da Hafiz suna Secondary School matakin aji 5(SS2). Kasancewar Alhaji Ibrahim Lema sannane ne yasa abokan gaba ke kawo mai hari, hakan ta faru Yau Ranar Juma'a da misalin karfe 1 na dare yan fashi suka dira gidan Alhaji Iro Lema, Bacci yakeyi sai jin karar bindiga daga waje, da sauri ya diro ya fito waje, ganin diyarsa Aisha kwance shame-shame cikin jini hankalin shi yayi mummunar tashi, be ankara ba sai jin yayi an dora bindinga a kanshi ana fadin "if u make a move i will burst ur brain" "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" ya shiga maimaita wa, da kakausar murya aka ce ina kudin da kaddarorin ka gaba ki daya nake so ka tattaro min cikin mintuna da basu wuce 5 ba, kayi yunkurin wani abu yara na zasu fasa kwakwalawar matanka a gabanka kamar yanda aka ma diyarka. Hankalin Alhaji ya tashi, yace kar ku taba min iyali na, zan baku duk abunda kuke buk'ata, ba tare da bata lokaci ba ya tattaro musu kudadden da ke cikin gidan nan, da wasu k'adarori. Yan ta'adan nan suka kwashe komai suka fice, ashe sun dasa bomb cikin Gidan, cikin mintuna da basu fi 3 ba gidan ya tashi ya kone kurmus ba wanda ya tsira. Abunda yan taadan nan basu sani ba shine, fashin da suka ma Alhaji, basu taba kaso daya daga cikin goman dukiyar sa ba(1/10) Cikin daren nan makota suka fito don ceton su, amma ba suka komai ba, sun girgiza kwarai da mutuwan Alhaji Iro Lema da iyalansa, don mutum ne mai kirki da sanin darajar dan Adam. Bincike ya nuna banda yaransa maza cikin gidan lokacin da Bomb din ya tashi, Dama Habib na lagos yaje duba wani company din baban sa, Zaid da Hafiz na makaranta Ulul Albab. Sai dai aka turo musu saqon Rasuwar Mahaifan su da yayyin su, hankalin su ya tashi Matuka don sun san sunyi Rashi Babba. Bayan Sadakar Arbain Alhaji Tijjani Masanawa, (Aminin Marigayi Iro lema) ya kira su duka, yace "Allah yayi yau anyi kwana Arbain da Rasuwan Mahaifainka da yanuwanka mata. Shawara ta farko da zan baku shine kai Habib, kaine Babba, ya kamata kayi aure, burin marigayi kenan, Magana ta biyu kuwa shine ka rike kannen ka da amana, ka hada kansu ka musu duk abunda uba zai ma yayan sa don kaine ubansu kaine uwarsu, ba su da wanda ya fika a yanzu,Da Zaid da Hafiz duk daya suke, kar kace wannan dakin ku daya wannan ba dakin ku daya ba, aa, duk daya suke kaji? Ku kuma, ku mishi biyayya. Ku rike maraicin ku, Ku kwantar da hankulan ku kuyi karatu ku zama abun da zamuyi alfahari daku. Maganar karshe shine maganar Gado. Zaa tattara komai a hade, sai a raba Gadon kamar yadda Addini ya tsara, amma wani hanzari ba gudu ba, Hafiz da Zaid ba damka muku Gadon ku zaayi a hannu ba, aa Habibu za a ba ya ajiye muku har sai kun mallaki hankulan ku, kun gama jami'a sai a baku hakkinku, nan da shekaru 5 kenan ko 6. Ko akwai mai magana? Duk suka girgiza kai suka ce "aa babu" Alhaji tijjani yace "to Alhamdulilah Allah ya ji kansu ya gafarta musu". Duk suka amsa da "Amin" yace to ku sai ku shirya ku koma bakin karatun ku ko? Suka amsa da "to baba" yace to ku na sallame ku. Hafiz da Zaid suka tashi suka tafi. Alhaji Tijjani yace "Habibullah, wani nauyi Allah ya dora maka, ina fatan zaka rike amana? Yace "InshaAllah baba, mungode kwarai, Allah ya saka da Alheri Allah ya ja kwana" Alh. Yace "To Amin". Yauwa Baba karshen wata zan tafi Cairo, zanje magana kan Engines din nan wanda marigayi yayi order su, har yanzu ba su iso ba" Alhaji Tijjani yace "Toh Allah shi kaimu yayi jagora Amin, Habib mata fa? Habib yayi daria yace InshaAllah baba an kusa". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg🔟 CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT "Assalam Alaikum, that's my seat" ta dago fararren idanuwan ta ta kalleshi tace "oh sorry" tare da mik'ewa ta rabe ya shige ciki ya zauna itama ta zauna. Wayar shi ya ciro ya kira Alhaji Tijjani Salam Baba gani nan cikin jirgi yanzu zamu tashi" dsga bangaren Alh yace to ya an dace? Habibullah yace "Eh baba, zuwa karshen sati zasu iso" Alh yace toh MashaAllah, Allah ya kawo ku lafiya Amin" Sanarwa akayi jirgi zai tashi kowa ya sa seat belt dinsa, duk suka yi yanda aka umarta, cikin mintuna kalilan jirgi ya fara yunkurin tashi. Runste ido ta kusa dashi tayi, da yazo daidai tashi ta yi saurin dafa Habib tare da ririke mai hannu gam, ba yau ta fara hawan jirgi ba, amma Duk sanda jirgi yazo tashi haka take tsintar kanta cikin tsananin tsoro. Sai da Jirgi ya daidai ta a sararin samaniyya ta dawo hayyacin ta, da sauri ta kalli Habib baki bude, tace "donAllah kayi hakuri, i'm always like this duk sanda jirgi zai daga" Habib ya kalleta baki bude, yace "dama kinajin hausa" ta harareshi cikin sigar wasa tace "wai ma, ga zahiri ka gani" Habib dai kasa magana yayi, yana satar kallon ta. Kwata-kwata bata yi kama da bahausa ba, tafi kama da larabawa, a hankali ya karance ta; Fara ce sol, mai siririyar fuska, hancinta kamar fensir, tana da dan tsawo, sanye take da bakar Jallabiya ta nade kanta da bakin gyale, kai duk yadda akayi ta hada iri da Larabawa. Tana sane da irin satar kallon ta da yake yi, murmushi kadai tayi ba tace komai ba, ta ciro wani novel daga cikin handbag dinta. Habi dai ya kasa hakuri sai da ya tanka ta, yace " Erhm, amma ke ba bahaushiya bace ba ko?" ta dan daga kai sama tarw da murmushi tace "bahausa ce mana, bakaji hausa na radam ba amma meyasa kace haka?" yace "anya kuwa ke hausa ce?" kila zama da hausawa ya sa kika iya hausa, ko kadan bakiyi kama da hausa ba kinfi kama da balarabiya" dariya takeyi sosai, tace toh Baba na bahaushe ne gaba da baya mama tace yar kasar lebanon" Habib ya dan tafa hannayen shi biyu, yace "Ahap, ga magana nan ta fito, kin dai hada jini da Larabawan" dariya tayi, haka suka cigaba da fira har suka iso Aminu Kano Airport. Bayan sun gama Clearance ne suka fito wajen Airport din, Habibullah yace "nan garin kike?" tace "aa, katsina nake" Habib ya zare ido yace "Lah,ashe yar garin mu ce" yace toh zaa zo daukan ki ne? Tace noo ai bama su san yau zan dawo na, i want to make it a suprise" yace "that's nice, toh muje mu yi shatar motar chan" ya fada y na nuna motar kwamkwasiya da sukayi layi a chan gefe, tace "kar ka damu, i can take myself home" ya harareta ba tare da yace mata komai ba ya ja trollyn ta ya yi gaba, bata da zabin da ya wuce ta bishi a baya tana murmushi. Kafin ta isa har sun daidaita da da mai motar ya sa akwatin ta a booth, Habib ya bude mata baya yace "Bismillah", ba gardama ta shige baya, shi kuma ya bude kofar gaba ya shiga direba ya ja suka dau hanyar Katsinan Dikko dakin kara. Karfe 8 suka iso, Yace wani unguwa kikayi tace "GRA Bayan gidan Govenor", ya juyo da sauri yana fuskantar ta, yace ai unguwar mu ce, tace wai dagaske? Ya ce eh, to wani gida kike?" tace gidan Alhaji Tijjani Masanawa ai nan Habib ya hangame baki Yace u must be kidding me, Gidan Baba na kike? Itama da mamaki tace "nifa bana son zolaya" yace dagaske ba wasa ba" shine last person da nayi magana da shi a jirgi, Abokin baba na ne sosai, he's like a 2nd father to me and my siblings" tace "banyi mamaki ba, its a small world afterall, yace "haka ne but ya akayi ni ban sanki ba? Tace "da yake a Cairo nayi College zuwa Masters dina, so ban fiye zama a Nigeria ba, ko na zo banyin 1month nake koma wa" Habib yayi mamaki matuk'a yace wai ko kece Aisha?" Tayi murmushi tace ya akayi kasan sunana? Yace ai na kanji baba na waya dake, na taba tambayan shi wacece suke yawan waya?" Yace "kanwarka ce Aisha, tana Misra tana karatu" a haka suka iso Gidan Alhaji Tijjani, wani tangamemen Gida ne, har ciki direba ya shiga dasu. Habib ya fito ya bude mata ya ciro kayan ta yace" Shatu, Allah ya huta gajia ko?" sunan da ya kira ta dashi ya bata daria, tace "wato ba zaka shigo ba? Ko daman labari ne kawai ka keyi?" yayi darian shima yace mutum da gidansu sai an gayyace shi ciki?" karki damu inaso naje gida na huta, zuwa da safe zanzo ma gaida Baba " tace to shikenan, ta shige gida, shikuma ya koma mota suka fita daga gidan. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣1⃣ Washegari Habib yayi sallama parlon Alhaji Tijjani da Asuba, duk'a wa yayi har kada yace "Baba Barka da Safiya" Alhaji ya dago kai yace "lafiya lao Habibullah, ya gajiyar jiya? Habib yace "gajia ta bi jiki baba" Alhaji ya tambaye shi game da ayyukan da yajeyi a Cairo ya shaida masa komai na tafiya daidai. Yace "Jiya sai ku ka ga bak'uwa", Alhaji yace " Aisha ko? Sai da tace min tare kuke na gardama mata, amma daga baya na yarda da na tu a kaima fa jiya ka dawo, amma ya akayi ka shaida kanwar ka, don na san ba ku san juna ba?" Habib ya kwashe komai ya gaya mai, Alhaji ya jinjina kai yace "haka Allah ke abunshi". A kwana a tashi Habib da Aisha sun yi wata irin shak'uwa da junan su, har so ya shiga tsakanin su, soyayyah mai tsafta sukeyi, Alh. Na sane da su amma yayi shiru, a zahiri kuma yana farin cikin wannan abu don Habib mutumin kirki ne, irin shi yake so aura ma Tilon yarsa, amma tunda sun hada kansu tun wuri toh falillahil hamd. Wata rana Habib ya shigo gidan don zuwa kiran Baba tijjani, ya aika a kirashi, Bayan gaisuwa Alhj ya muskuta yace " Habib dalilin kiran ka shine in shaida maka yau za muje mu kai kayan sa bikin Aisha, tunda kai kadai ne yayan ta, ina so ka hallara wurin zuwa, idon Habib ya rufe, be san sanda yace "baba, wace Aishar? Ban gane ba? Yace " Aisha kanwarka ko? Aishan Misra" Habib ya zabura yace "what?, Baba kar ka min haka, wallahi nike son Aisha, kuma tana sona baba kar ka rabu mu don darajan Allah, cikin fushi yace kuma ai a aladance zuwa ake gidansu yarinya a daidaita tsakani, ba wai da ga gidansu yarinya zaaje gurin Namijin ba, hala dan sarki ne" ya fada a fusace. Sosai Alhaji Tijjani yayi daria, sai da ya tsagaita yace " Habib in banda abinka, ya zaayi dangi mata suje kai kayan biki? Ai ko a masarauta ba a haka, kwantar da hankalin ka d'a na, Kayan Biki zamu kwasa ni da kai muje chan gidan k'anena kuma waliyyin Aisha, in nema maka aurenta gun shi. Kunyar duniya ta lullube Habib, a take ya bar parlorn don kunyan baban da yakeji yana murmushi. Aisha tsallen murna takeyi da Habib ya gaya mata abunda ya faru tsakanin shi da baba dazun, tayi daria sosai tace "wato kai loverboy ko?, ka mance baba kana ta sakin layi" yayi daria shima yace "sanki ne ya jawo hakan" tace ni ba "ruwana". Yau bakin Habib har kunne don ko Baba Auwal kanin Baba Tijjanj yace wata daya kawai ya sa bikin 'yarsa. Baba Tijjani yace " ni da dana muna godia da wannan abu, Allah shi kaimu lokacin, na maka Alawarin dana zai kula da diyarka yanda ya kamata" duk sukayi daria. Baba Auwal yace "Yaya, ya maganar aikin Aisha a Wannan Oil and Gas Company din da Gwamnan Kaduna ya bata? Yace duk sanda taso yin aiki ta kai offer din nan, unlimited time ya bata, don yace ko ba shi ke mulki ba, ya riga yayi signing kuma dole a amince da offer" Alh ya tabe baki, yace " Kaduna fa? Toh gashi kuma kace aurar da diyar ka zakayi nan da wata, kaga ko aiki wani gari ma be tashi ba, in ma zatayi aiki, to wannan hakkin mijinta ne ya barta ko ya hanata, kuma dole sai inda zasu zauna" Habib ina kake so ku zauna? "Habib yace Baba nan gidan Marigayi da nake Gyara ginin nake so mu zauna, amma muna iya komawa Kadunan, sai na dinga zuwa katsina duk weekends, "sam ba zaayi a hakan ba, inda kayi niyyar zama nan zaka zauna, wato nan Katsina, sai ka zaba mata cikin ministries din nan, kaga wanne ya kamata tayi aiki a ciki, sai na kaima SSG CV dinta ya bata offer" sosai Habib yayi godia, yaji dadin adalcin Baba Tijjani, dama shi be da burin zama a gidan da aka haifesu, balle shi da ya ci gadon Gidan Ubansa. Yace Baba Nagode, Allah saka da Alheri, ina ga kuma tunda Public Admin ta karanta, zata iya aiki almost ko ina, ko za a duba BOA (Bank of Agriculture)? Baba Tj, yace "duk yadda kagani, ga baban ta nan kuyi shawara, ni idan ma zai yarda da kun barta da aikin nan, don na tabbata ba zata rasa komai ba da yardan Allah, kar taje ta wahalar da kanta gurin wani aiki" da sauri baba Auwal ya katse shi da harara yace"haba yaya, bari mana, diya ta fa Masters ne da ita, abar ta ta amfana da karatun ta mana" Baba Tijjani yayi daria, yace "daga bada shawara, yau Auwal harda harara na? Allah baka hakuri nima da karambani na na shiga maganar diyarka" ya kalli Habib yace "tashi muje kaji d'ana kafin a sake mana karnuka " Habib yayi dariya. "Oh boy! wai ya maganar Gadon ku ne? Tunda tsohon ku ya rasu shiru nakeji, kasan zaka ja kaya, ga ka da Gadon Uba ga ka daUwa, Oboi u rich oo" Abokin Hafiz ke wannan maganar, sun dawo hutun aji biyar, da sun koma zasu shiga SS3. Hafiz yayi murmushi, yace wai shi Anas meye damuwan ka da Gadon nan ne? Ince dai baka da gadon baba na? Wannan naci haka, tunda na dawo kake tambaya na, to ba a raba ba, ba ma bukkatar Gado yanzu, burin mu Allah ya gaffarta musu duka. Anas ya shek'e da daria yace "kai ni zaka ma bariki? Ni zaka ce ma ba ka da bukkatar Gadon ka? To bari kaji ina sane da an raba Gadonku, ka tashi da Miliyan 50 da Gidaje 3 da filaye. Hafiz yayi daria yace " Ohh, Anas, to ka sani me yasa kake tambaya na? Kai ni fa ba abunda zanyi da kudi" Anas ya sake shekewa da daria yace karya kake, kai ke ko da abunda zakayi da kudi, kai fa nan Millionaire ne, ga ka da kyau da kwarjin, zakayi abunda kaga dama ba me ce maka don me?, ka sa kallar kayan da kake so, ka hau motar da kake so, mata ma sai wacce ka zaba, kai kasan if you have money u have everything" Hafiz yace "na san da haka, amma yanzu karatu mukeyi, idan mun mallaki hankalin mu Yaya Habib zai bamu hakkin mu nida Zaid, for now mun amince ya dinga juya mana kudin" Anas yace "Ban taba sanin kai solobiyo mara tunani bane sai yau, dan Uba zaka sake ma ragamar dukiyar ka kace ya juya maka? Lallai a ruwa kake tsundum wallahi" Baki bude Hafiz ke kallon shi, ya daure yace "kai Anas, ka iya bakin ka, Yaya Habib matsayin Uba yake a gurina, kuma ba Gado na kadai ke hannun shi ba, harda na Zaid, kuma nasan zai rike Amana" Anad yace kai ni rabani da maganar nan, zaka yi nadamar barin Gadon ka wurin dan Kishiya, Aure zaiyi, Gida ya kera ma matarshi, daga Kasar Dubai ma ake Ginin, zai hada kayan aure, duk a dukiyar wa? Kana zaton a na shi? To kai wawa ne indai kayi tunanin haka, a cikin dukiyar ka zai yi duk wata hidima ta shi, da na ma kanin shi wanda suke Uwa daya, Saboda me? Sabida kai dan kishiya ne, kuma ba za su taba sonka ba" Idona hafiz yayi jaa sosai, da alamun zanttukan Anas sun shige shi matuka, Zuciyar sa ta fara zafi, shaidan na dada ingiza shi, yace Anas yanzu meye abun yi? Anas yayi dariya ganin ya samu nasara, yace "abu daya zakayi shine Ka karbi Hakkin ka". _Bibilicious Biebee_👧 🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣2⃣ Anas ya cigaba da cewa "Ka same su kace su baka hakkin ka kana da bukatar su, duk yanda zasu so shawo kanka ka fandare musu ka bada ma idon ka toka, duk inda suka bullo maka to ka bulle musu" Hafiz ya jinina kai, yace "toh, bari zan gwada bayan bikin Yayan sai na bijiro musu da bukata ta" Anas yace "bayan biki ai ya gama bushashar sa, yanzu ya kamata kaje ka sake sa" Haifz ya mike yace "bari inje" Anas yace Allah bada sa'a kar ka manta, sai ka nada ma idanuwan ka toka". "Yadai Hafiz?" naga kamar bakinka akwai magana? Ya akayi ne?" Habib ne ke tambayan Hafiz da tunda ya shigo dakin yake ta kame-kame. Hafiz yayi ta maza yace "Yaya, Gado na nake so a bani in rike a hannuna, a bani hakki na" Habib cike da mamaki yace "Lafiyar ka Hafiz? Bakaji me baba Tijjani yace ba? Sai kun gama Jamia za'a baku, Hafiz ya fandare ido yace "shidai a bashi yana da buk'ata" Habi yace "to shikenan Hafiz zan yi shawara da Baba Tijhani". Hafiz ya dan yi ysaki yace "Yaya, Gado na ne ko? To nace abani kayana ban son ajiyar, ina da hankalin da zan rike abu na, banga dalilin yin shawara ba, tunda dai shi da kanshi ya kira a ka raba Gadon nan, toh ni dai nace a bani kaso na" Yanda hafiz yake magana ya ba Habib Mamaki, zuciya taci Habib ya mike yace biyoni, ko kunya Hafiz be ji ba ya bishi, a waje suka ga Zaid, da sauri ya taro su yace "lafiya? Yana ga fuskar ku ba walwala? Habib yace "kaima biyo mu" ya fada motar sa ya bar gidan hanyar Bank yayi. Zaid da Hafiz mota daya suka shiga, a hanya ne Zaid ke tambayan Hafiz" Bros, wai ya naga yaya haka? Me ya faru? Hafiz ya dan tabe baki yace" ba fa abin da ya faru, kawai don nace yaban Gadona a hannuna ba sai ya ajiye min ba, ni zan aje abu na da kaina shine ka ganshi haka" Cike da mamaki da takaici Zaid ke kallon shi yace "Hafiz kasan me kake cewa kuwa? Me zaka yi da Gadon ka haka? Idan wani bukata ne dakai ka sanar dashi, shi me iya baka ne ba tare da ka taba Gadon ka ba, Haba danuwa na" da sauri Hafiz ya katse Zaid ta hanyar daga mai hannu yace "in kai yaro ne, ni ba yaro bane, ina da damar da zance a bani hakki na, idan kao ba za ka amsa naka ba, to ni zan amsa nawa, so please spare me the lecture" Kasa magana Zaid yayi har suka zo Safe din babansu, inda ya ke ajiye kadarrorin sa, Tuni Habib ya haye sama, suka bi bayanshi, Cikin Lokaci kalilan ya tattara duka Gadon su, da ma a kashe suke, ya kalle su yace "tunda, baba ya rasu ban taba daukar ko sisi ba nayi amfani dashi, duk kudin da kuka ga na taba to kudi na ne, hakkin gurin Aikina ba na Gado ba, to yanzu Hafiz ka bukaci Hakkin ka, ni Musulmi ne na san hukuncin wanda ya danne ma wani hakki, nikuma bana daga cikin masu dannewa mutane hakkinsu" ya tura mai wani dan safe box yace "Wannan Miliyan hamsin da hudu(54) ne, a ciki akwai filaye 3 da location dinsu, da gidaje 2 a garin Katsina" ya juya ya kalli Zaid yace kai kuma ga naka hakkin Miliyan hamsin da--" da sauri Zaid ya katse shi ta hanyar cewa "Haba Yaya? Me zanyi da kudin nan? Ni bank'i a sadakar da su Allah ya Jikkan su Baba, ba abunda zanyi da su, shi da ya ga zai iya ai Shikenan ka bashi hakkin sa" a fusace Zaid ya tilla ma Hafiz key din mota ya juya ya bar gurin rai a bace. Hafiz ya duka ya dauka key din motar da murmushi a fuskar sa yace "Nagode Yaya, hakika kai uba ne a gurin mu,tunda har ka san Hakkin dan Adam baka tauye ni ba, Nagode Allah ya bar Girma" mamaki ya hana Habib Magana. Hafiz ya dauke Safe din ya fita. Sai da ya kai Safe din Bankin da Baban su ya bude musu kafin ya kira Anas a waya, tunda suka hadu da Anas, Anas ke faman kuran ta shi" The multiple Millionaire, yanzu za a dama da kai, ina dukiyar? Hafiz ya dan bata rai yace ba ruwanka da inda suke" Anas yayi daria yace to shin kai filayen nan d gidaje me za kai dasu? Ai kawai kasa su a Kasuwa ka ci kudin su, in yaso in Ka tashi mallakar Gida sai ka gina Uban uban su". Da wannan huduba na Anas Hafiz ya sa gidajen shi da filayenshi kasuwa, a ka siyesu a wulakance ba tare da sanin kowa ba, Hafiz ya zama wani tauraro cikin abokan shi, yayi ta musu bushashar kudi. Baba Tijjani yayi fada sosai da yaji abunda Hafiz yayi, amma ya fi ba Habib laifi akan biye mishi da yayi, Habib yace "Baba ya zanyi dashi?, tutiya yakeyi Hakkin shi ne, ba wanda zai danne mishi, baba naga nima wannan nauyi ne ka sa mun, shiyasa na sauke nauyin, shi Zaid da na mika mai naahi kin amsa yayi yace ba abunda zai yi dasu, ina ga kar ka daga hankalin ka, kowa yayi da kyau zai gani. Baba ya jinjina kansa yace "Allah shi kyauta" Zaid "yace Amin". Bayan Sati daya Aka sha bikin Habib Iro Lema da Amaryar sa Aishatu Tijjani Masanawa bisa sadakin Naira Dubu Dari. Biki ne wanda ya amsa sunan biki, ba a tsawalla ba, ba ayi karya ba, ko lefe akwati 6 yayi a cewar Baba Tijjani Albarkar aure akeso. Ran da akayi dinner Hafiz ya taka rawar gani, don sai da masu Kida suka san da zaman shi, don dubu dubu ya dinga likawa, Suko sai kara kudashi suke suna cewa "kanin ango hafiz mai naira" shi ko kanshi sai kara girma yake yi ya cigaba da rawar sa yana ruwan liki. Da yawa cikin mata sun kyasa Hafiz don a cewar sa yaro da kudi sai a bashi ya sha. Habib zaune a high table yana kallon Hafiz na barin kudi. Hafiz ya koma wani abu daban, kamar ba kanin shi mai kunya ba, amma ji lokaci daya ya fandare ya zama mara ta ido, ya tuna satin da ya wuce inda hafiz ya sameshi a parlo yace "Yaya Ya shirye shiryen biki?" Ba yabo ba fallasa Habib yace "Alhamdulilah Hafiz muna tayi" Hafiz yace "Allah taimaka, yaya ga gudummuwa ta bikin ka" ya ciro wani da case, ya bude mishi, sarka da yan kunne ya mika mishi, Habib ya sa hannu ya amsa, Habib baki bude, yace Hafiz me zan gani haka kamar sarkar Zinari? Yayi daria yace Zinari ce yaya, a matsayina na kanin ka shine na ga ya dace na baka gudummuwa, ka hada a lefe" Habib ya bude baki da ya kara kallon Sarkar, ya tsorata da lamuran Hafiz, yace Hafiz wannan sarkar da kake gani Jiya da naje Siyayya a Shoprite a Kano na tayata, wallahi exact sarka, kasan nawa nagani? 450,000. Tsadar ya hanani daukarta amma tayi kyau, naga dai akwai Zinari a lefen da na sa shisa na barshi, Hafiz meyasa ka kashe makudan kudi wurin siyan sarkar nan? Hafiz yayi dan daria yace "yaya kenan, toh kare da kudin sa sai ya sha lahaula" so nake nima na taka rawar gani a bikin yaya na mai sona, shisa na cire kudi har haka na siya maka, kuma ko da ya fi haka zan siya, don su san cewa ba Tsiya a dangi Lema, saboda haka yaya gashi" Habib yace shi sam ba zai amsa ba, Hafiz ya bata rai, yace don ba maman su daya ba shine ya ke nuna mai wariya, da Zaid ya kawo mishi abu amsa zaiyi, amanar da baban su ya bashi kenan? Nan da nan Habib ya rude yace"haba Hafiz ya kake magana irin wannan? kasan da kai da Zaid daya kuke a wurina" yace toh idan haka ne ka amsa, Habib ya amsa yace toh "Nagode" Habib ya kai kallonshi kan Zaid da ke zaune a gefe yana kallon mutane, shi ko dancing floor din be shiga ba, a ranshi yace Allah ya shirya Hafiz. Haka aka gama taron biki aka kai Amarya Gidan ta da ke Layout. (Amarya Aisha Allah bada Zaman Lafiya) _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣3⃣ BAYAN SHEKARA DAYA. Kama daga kayan maye, bin mata, chacha, ba wanda Hafiz beyi, barin ma Chacha da ya maida shi sanaa, wata rana har Lagos yake zuwa don yi Chachar, wata rana ya ci nasara, wata rana akasin hakan, da kyar ya samu 4credit a SSCE din su, makarantar ma da ya ya gama shi? Ko da suka koma aji 6 kullum yana cikin gari, shine scaling fence din school(diran katanga). Ba wanda ya san Hafiz da Halayen nan, don ko sigari ya sha sai ya siya alawa ya sa a baki kuma ya feshe jikin shi da turare. Tafiya takeyi da kyar, don tun wayewar garin yau take jin ta wani iri, ganin kafarta na gaza daukar ta ya sa ta zube kasa tana murkususu, kamar daga sama Habib da Hafiz sukayi sallama, da sauri Habib ya karasa gunta ya na cewa "Shaty na, lafiya? Ko haihuwar ce?" Kai kawai take girgiza mai tana hawaye ta na nuna mishi cikin ta, a rude yace da Hafiz dauko mota, Hafiz ya fita fa sauri, don ko Matar yayan su me kirki ce ya jawo mota har gabon Parlon kasa, Habib ya cicibeta yayi mota, Hafiz ya ja motar na sai Asibitin Turai Yaradua inda suke da File. Suna isa nurses suka karbeta, nan aka ce haihuwa ce, suka shiga da ita dakin haihuwa, sai da ta kusa Awa biyu kafin ta sauka, ta haifi santalelen saurayi. Sai da aka gyara su kafin aka sanar da su Habib, Habib yace muna iya ganin su? Nurse tace "why not? Da sauri suka yi dakin, murna gun su ba a magana, Zaid ya shigo da sallama don sunyi waya da Hafiz ya gaya mishi inda suke, Habib da Hafiz nayi ma Aisha Sannu, shi ko Zaid yana zuwa yayi inda jaririn ke kwance ya dauke shi ya rungume, ya dagi ya kalli yaron, a hankali yaron ya bude ido, wani ikon Allah sai Zaid ya ga kamar yaron yayi murmushi, Zaid yace "Uhhm Rafeeq(Gentle), murmushi kakeyi?" Hankalin Habib ya dawo kan Zaid da Jaririn, Habib yace "kai Zaid ya zaayi jariri ya maka murmushi?" Zaid yace "Wallahi Yaya baka ga wani soft gentle smile din da ya min ba" to naji zaka ara min na ganshi ko kuwa? Yayi dariya ya mika ma yayan shi jaririn ya matsa yana ma Aisha Sannu. Habib ya mishi Addua, ya kalli Aisha yace wani suna kike so a mai huduba da? Tayi murmushi tace RAFEEQ. Hafiz ya amsa yaron ya kura mai ido, ya kalli Aisha yace matas dangin larabawa menene kuma Rafeeq? Ta harare shi cikin wasa tace a koma islamiya a yi Arabiyya, Zaid da Habib suka fashe da daria, shi ko Hafiz ashe abun ya mai zafi amma sai ya dake ya share kamar ba komai, chan ya tsinkayi muryar ta, tana cewa Rafeeq na nufin(gentle friend/gentle ally). Uhmm kadai Hafiz yace. Bayan wata Shekara Aisha ta sake haifar diyar Mace, wacce taci suna Rafi'ah, Rafeek na da wata sha ukku,sai kace dan shekara 2 ne, don kato ne sosai gashi ja, ba inda be zuwa da kafar shi. A cikin shekaran nan Hafiz ya fara tsiyacewa, duk makudden Kudadden nan ya rasa inda suke tafia, da yake ance Kudin Gado bai da albarka don ba gumin ka bane ba, ba ka san zafin nemo su ba, gaskiar magana kudin hafiz sun kare ne a Chacha, Sai Anas da ke mishi wayau don yanzu ya san sirrin shi tas Hafiz dan kimanin shekaru 18 a duniya wanda Matasa ke ma lakabi da "Young Millionaire" ya wayi gari yau be da ko taro cikin safe dinshi, naira biyar ta gagare shi, duk kudadden sun kare a Chacha, hankalin shi ya tashi, ya shiga neman layin Anas be shiga, damuwa dari da sittin a kanshi, kwalbar syrup ya bude ya kwankwade tas kafin kace meye wannan ya bige da Bacci. Habibi ina ganin tunda Jamb din nan ya ki samuwa, me zai hana ka fidda Hafiz da Zaid Waje, suje suyi karatun su chan? Da suyi ta zaman banza" Habib ya kalli Matarshi Aisha da take shayar da baby Rafiyah yace " nima tunanin da nakeyi kenan, kawai na samo musu makaranta ko a Malaysia ne, amma sai nayi shawara da Baba" Aisha tayi murmushi ta na mai jin dadin Alakar Baban ta da Mijin ta. Ai ko Baba Tijjani ya amince dari bisa dari, nan da nan Habib ya shiga neman ma kannen sa makarantar a kasar Malaysia. "Kai Bahba akwai damuwa fa" Anas yace haba miloniya, wace irin damuwa? Me zai dameka Hafiz yce Wallahi kudin sigari na neman gagarata, gashi yarinyar nan Sofy na bina bashin eh yane har 250k, ni ban san yanda zanyi ba wallahi" Anas yace ba dai kudin nan sun kare ba? Hafiz yace "tas, komai ya ware" Anas yace "to kaii, ai gidanku da masu shi kawai ka tambaye su" Hafiz yace "kai tsaya Anas, nifa ina da kunya, ba a kai shekara 3 da naje gun yayana na mishi rashin kunya kan Gado na, ya dauko ya bani, Kawai yanzu saboda ta bare dani sai naje na tambaye su? Kasan bansan raini, ko a min wani gani gani, balle wurin kane na Zaid, kawai ka samo min mafita" Anas yayi daria yace bigboy no raini, to abun da nake gani kawai ka dan zaro kudin ba tare da sanin su ba, tunda kasan ma'ajiyar" Hafiz ya bude baki yace kaii, duk iyarshege na ba ruwana da sata, ba ma zan iya ba, kai ni ko barawo naga an kama ji nake kamar na harbe shi balle ni in dauka kai samo min wata mafitar, Anas yace "kai fa dan kauye ne, waya ce ma sata ne? ai ba sata bane, ai Baban ku daya, kar fa ka manta abun bros na bros ne" Hafiz ya sheke da wata mahaukaciyar dariya ya na nuna Anas da hannu yace bad boy, kuma haka ne ai, gaskia ka fada, Abun bros, na bros ne.. _Bibilicious Biebee_👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣4⃣ Hafiz ya yanke hukuncin ziyartar Save din da daddare, haka ko akayi, dare nayi wurin 8 ya san Yayan su na gida time din, ya wuce straight Gidan inda Save din yake, da yake an san Hafiz dan Gida ne, kuma ba wanda ya musu shamaki da shiga gidan ya sa mai Gadi ya wangale kofar Gate din, Hafiz ya shiga da motar shi, Staright office din ya wuce, ya bude lockcode (LEMA)din ya shiga hankalinsa kwance. Wardrobe din ya bude ya ga Save's biyu sai kuma inda aka cire nashi safe din, Irin Save dinshi mai kama da nashi ya jawo, aka sa enter password, Hafiz ya hau chanki-chankan(guessing) passwords, ya sa;Lema, be bude ba, wani tunani yazo mai, ai password din safe dinshi Hafiz Lema ne, kuma Yaya Habib ne yayi setting dinshi, which means toh wannan Save din can either be Zaid Lema or Habib Lema, bari ya fara da Zaid, cikin ikon Allah ya na typing Zaid Lema safe ya bude, wani ihun jin dadi Hafiz ya sake, baiyi wata wata ba ya kaushi kudin son ranshi, ya kulle yayi locking ya maida komai yanda yake ya fita. Bayan kwana 3 Hafiz ya dawo ya kara diban kudin nan, haka Hafiz ya maida Save din Zaid Bankin kudin shi, da yan bukattunshi ya tashi ko na abokan shi sai yaje Ma'ajiya(Save) din Zaid ya jida na jida, da abun yayi kamari sai dai Hafiz ya dauke Save din ya kai gida, cikin Save dinshi ya juye dukkan dukiyar da muhimmar takarddun daga Save din Zaid. Ya na tunanin ya zaiyi da Empty Save din Zaid? Ina zai wurgar inda ba zaa gani ba? Rafeeq da Rafee'ah sunyi bulbul da su, kowa na sonsu, maman su na ta zuwa Aiki, da su take tafia tunda tana da mai aiki, Soyayyahr su sai gaba takeyi da Habibinta. Hold up ne ya tsaida Zaid daidai titin Kofar kaura,kamar ance waiga gefe, Wani yake hangowa kamar Hafiz da wata babbar mata dake gaban mota, daga baya kuma Anas ne zaune, Zaid yayi mamaki, to ko dai Mamar Anas ce? Kai aa, in mamar Anas ce sai dai ta zauna bayan mota ko shi Anas din ya tuk'ata.Gani yayi matar ta sa hannu ta shafi kumatun Hafiz, cikin Zaid ya kada, Haka kurum zuciyar Zaid ya ki aminta da ganin da ya ma su Hafiz, ya bi Bayan su da aka basu hannu. Be bari sun lura dashi ba, don a hankali yake bin bayan su har suka zo wani Gida da Hafiz ya siya don holewa da yan matanshi ya shiga yayi parking, ganin wani mota a bayan su ya sa Maigadi barin gate din bude don a zaton sa tare suke. Tun da Hafiz yayi parking motar nan suka fara watsewa da wannan matar cikin mota, Anas kuma na kwankwadan Syrup duk sunyi nisa gun aikata Sa6o. Iya karfin shi ya shiga bubbuga gilashin mota, ji kake kwam kwam!! A firgice suka dago, Hafiz ya tsorata, da sauri ya fito, idanuwan Zaid suka kada sukayi jaa, da karfi yace "Haba Hafiz, me zan gani haka? Dama harkar mata kake yi? Ji wannan matar a haife ta haifeka wlh, amma kaji kunya". Hafiz dai ya kasa magana don kunya ya kama shi kamar kasa ya tsage ya shige ciki, Anas yayi ta maza yace "Ji mana Zaid" Zaid ya galla mai harara ya kalli matar da ke tsaye tana gyara tsayuwar rigar ta yace dallah wuce ki ba wa mutane guri, ko a jikin ta tace "Fizboy my balance" jiki na rawa ya ciro rafar dubu 1 ya bata ta sa a jiki ta mai blowing kiss, Zaid ya bita da harara" ya juya a fusace zai bar wurin, da saurin Hafiz ya rik'e hannunshi, yace "Zaid, i'm terribly sorry, Sharrin shaidan ne, yau na fara, kuma iyaka ta kenan wallahi, Zaid ka yarda dani" Zaid ya kalle shi shek'ek'e yace wannan kuma tsakanin ka da Ubangijin ka, shi zaka roka gafara bani ba" da sauro Hafiz yace" Wallahi na bari, da ma ba halina bane, kai ka sani, don Allah kar ka gayawa Yaya" Zaid ya kalli Hafiz, ya ga hawaye kwance cikin idanuwanshi, ya bashi tausayi matuk'a, yace Allah shi Kyauta ya shige motarshi ya tafi". Anas yace "Fizboy, Zaid ya ga gurin kwanan ka, yana kaninka amma ji yanda yake gasa maka magana kamar ka kashe wani, mtsww dole ka dauki mataki a kanshi" Hafiz yace "barni da dan shegiyar, zanyi maganin shi nan ba da jimawa ba".. SATIN DA BAI WUCE BIYU BA. Hankalin Habib yayi mummunar tashi da ya bude Wardrobe ya ga ba Save daya, ya duba ya ga Save din Zaid ne babu. Habib ya kwala wa Securities kira cikin rudewa, suka zo a gurgurje, yace "Akwai wani baren da ke shigo gidan nan ne?" Security yace "ai Oga Gidan nan ba me shigar shi daga kai sai kannenka biyu, a rude yace yaushe suka zo last? Yace " Oga Zaid yazo jiya, sai bayan Maghrib ya tafi, Oga Hafiz kuma ya kusa 3weeks rabon shi da nan arean" Habib ya fita da sauri ya shige motar shi, yayi gidan shi. Tsaye suke a parlo suna ball shi da Rafeeq, Aisha ta fito dauke da Warmers ta ajiye kan dinning ta kalle su cikin murmushi, tace Uncle Zaid da danshi, wallahi ku ka fasa min Showglass sai kun biya ni, in banda abunku wa ke kwallo cikin parlo? Zaid yace "haba Matas, don dai Showglass? In mun fasa ni da boy dina muna da kudin sayen miki wani ai--" be rufe baki ba Habib ya shigo kamar zai tashi sama. Aishatu ta tsorata, Zaid ya dauke Rafeeq da sauri don kiris ya rage Habib ya ta kashi. Aishatu ta matso da sauri, Daddyn Rafeeq me ya faru? Lafiya? Yace "ina lafiya shatu? Banga Save din Zaid ba. Kai zaid ka dauki Save din ka ne?" cikin rashin fahimtar abunda Yayan sa ke fadi yace "Yaya meye kuma Save?". Yaya har sai ka bata bakinka wurin tambayan inda Save din Zaid yake? Ai shi zai dauki abunshi? Idan ba shi ba wa zai dauka? Duk suka maida hankalin su ga Hafiz da yake shigowa parlorn, ya cigaba da cewa " bros, ashe baka gaya mai ka dauko ba?" Zaid baki ya sake galala yana kallon Hafiz, sai yanzu ya gane me suke nufi. Ran Habib in yayi dubu ya gama baci, da karfi yace "Zaidu, Ya za ka min haka? Idan kana da bukkatar Gadonka kamata yayi ka gaya min, ba wai kaje ka dauka kai tsaye ba, haka kurum ka sa hankali na ya tashi?" Zaid cikin rawar murya yace "Yaya, Wallahi ban dauka ba, hasalima ban san inda suke ba" Hafiz yace "Ka fara jokes dinka ko? Jiya jiyan nan kace man kana da bukatar Gadon ka na baka shawara ka sanar da Yaya" Zaid cikin bacin rai yace "Kaji tsoron Allah Hafiz, yaushe mukayi haka da kai? Wallahi ban san inda Save din yake ba Wallahi ban dauka ba" Habib yace "dallah rufe wa mutane baki, mutumin banza mutumin hofi, karya za a maka?, yace "Yaya wallahi-- tasss kakeji, Habib ya tsinke Zaid da Mari, ya shiga dukkan shi ba kaukauta wa, ni za ka tada ma hankali? After all i'm doing for u? Dukkan shi yake ko ta ina, Rafeeq na ta tsala Ihu, Aishatu ma kukan takeyi, da kyaur ta kwace Zaid hannun Habib ta turashi waje tace "Ruga daki Zaid". Habib ya zube kan kujera yana maida numfashi, yau yayi abun da be taba yi ba, bugun kanneshi,. Ran Aishatu bace, ta daga kai don neman Hafiz, tunani takeyi ina Hafiz yaje da Habib ya ke dukkan Zaid. Tsaye ta ganshi daga gefe, da alamun yana gun a lokacin da Habib ya ke ta jibgar Zaid, In dai idanuwanta ba yaudarar ta suke ba, to murmushi ne kwance kan fuskar Hafiz. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣5⃣ Tabbas Hafiz, murmushi yake yi don ko da suka hada ido da Aishatu gwalo yayi, a ranta tace me hakan yake nufi? Da kyar ta samu Habib ya sha ruwan sanyi ta tura shi toilet don yin wanka, ta shiga sintiri cikin daki tana tunanin abun da ya faru yau, tabbas akwai ayar tambaya akan lamarin. Ashe fitar shi, gidan Baba Tijjani yayi, ya gaya mai Karya da gaskia, hikimar yin hakan, kar Zaid ya zo ya fara samun shi ya wargaza mai lissafi shisa yazo ya fara gaya mishi, Cikin mamaki Baba Tijjani yace "kuma shi Zaid din ya ki amsa laifin sa? Hafiz yace "sai rantsuwar karya yake tayi" Ran baba Tj ya baci, yace tashi muje gidan. Tara su yayi duka a parlor, Zaid a kasa yana hawaye, Hafiz da Aisha kan kujera, Baba TJ yace "Habib Me ya faru?" yanda Habib ke magana zaka san ransa a bace yake, yace "Wai Baba, bayan munyi maganan Joint Ventures din nan, na tafi Warehouse don cire 2m daga Save din Zaid, na cire 5m daga Save dina kamr yanda ka shawarta kawai ina bude wardrobe naga saura Save daya babu daya, hankali na ya tashi a tunani na wasu yan ta'ada ne sukayi gaba da Dukiyar maraya, Ashe shi da kanshi ya dauke kayansa. Ran Baba Tj ya baci yace "kai Zaid meyasa ka dauke Ma'ajiyar ka ba tare da sanin wan ka ba? Zaid ya girgiza kai yace "Baba, banda masaniyyar abunda ya faru, ku yarda dani wallahi" Habib ya jefe shi da mukullin motar sa. Yace "ni kana bata min rai idan kana rantsuwa a kan karya, tsaya kaji Zaid, ni ba ka ban haushi ba don ka bukaci hakkin ka ba, da ka gaya min kana da bukata da da kaina zanje na dauko na damka maka komai kamar yanda na ma danuwan ka, amma kai kaje ka dauko, ka tada min hankali, yanzu kuma kana ta rantse rantse ka ki amsa wa." Zuciyya ta dau Zaid, yace Yaya shi kenan, na dauki Save dina, ina da bukkatun na shiya sa na dauka, ka yi hakuri idan na tada maka hankali. Yana kaiwa nan ya tashi ya bar musu parlon. Aishatu tace "anya Baba anyi ma Zaid adalci? Ai ya kamata ayi bincike, Habib yace wani bincike kuma? Bakiji ya amsa laifin sa ba? Tace ya amsa ne don bai da mafita, bayani yake muku amma ba ku son yarda, hasalima da ya fara bayani kuke katse shi, be da wata mafita in banda ya amsa laifin da bai aikata ba. Idan ana maganan irin wannan tarin dukiyar, be kamata ace an bar magana haka ba, what if Zaid bai dauka ba? Shikenan dukiyar ta salwan ta? Nidai ina ganin ayi bincike" Hafiz ya shiga hararrar ta a ranshi yana kiranta 'munafuka' Baba Tijjani yace kuma maganar ki Aisha abun dubawa ne, dole a yi bincike kam. Hafiz yace "toh a fara da dakin shi mana?" Zaid yace "wani gun zai kai ai ba zai aje a daki ba" Hafiz yace muje dai mu duba, dukkan su suka nufi waje don zuwa dakin Zaid, dakinshi ne na farko sai na Hafiz, Hafiz ne a gaba suna bin shi a baya har Aisha. Zaid na ciki yana kuka yana ganin su ya tashi ya matsa gefe, Hafiz ya shiga neme neme a wardrobe, Habib na daga katifar Gado sai ga Save na kallon su, gabaki daya suka sake sallati. Habib yace "Ahap, ai na gaya muku, ni na sani gashi nan dai, Habib ya ciro save din ya bude password din 'Zaid Lema' wayam ya ga save din, ko allura babu, Zaid ya hadiye wani irin mugun bakin miyau, ya san bai da wata mafita. Habib yace kagani ko Baba? Ba komai cikin Save din, ya salwantar da su. Baba Tijjani ya girgiza kai, yace "Zaid, ka bata wayonka" ya fita, Habib da Hafiz suka bi bayan shi. Aishatu ta kalle Zaid cikin ido, hawaye ne malale kan kumatun shi, fuskar nan tashi tayi Ja, tace "Zaid why?" girgiza kanshi yayi yace "Aunty wallahi i didnt do it" gyada kai tayi tace "i believe you". Bayan Sati 2. "Haba Habib, meyasa kake haka, don me zaka biya ma Hafiz kudin makaranta ka ce ba ruwanka da Zaid, ya biya ma kanshi? Naga dai da Hafiz da Zaid duk daya suke a gunka?" yace "Aisha, Ni Zaid ya sire min, ya bata wayon shi, ya ban kunya, shi yasa na zame hannu na kan lamarin Zaid, tunda yana da kudi sai ya biya ma kanshi duk makarantar da ya ga dama a fadin duniyan nan" tace "wai shin in ma haka ne, ai naga Hafiz shima an raba Gadon nan an bashi, shima yana da kudin nan, ai sai ka biya musu duka, ko ka k'i biya musu duka, duk su biya ma kansu, yace "hakan na ga daman yi" tace "kana raba daya biyu, na fa lura da kai, tun bayan da abun nan ya faru ka ke kyaran Zaid, ko gaisheka yayi baka amsa wa, ko yaranka ya dauka sai kayi ta mishi fada,kana hantarar sa, haka akeyi? Kar fa ka manta kaine uwarshi, kaine ubanshi. Habib yace "ke Aishaba abunda ya dameki, ko taro ba zan sake kashewa kan Zaid ba, and baki da hurumin yi min magana kan Zaid, duk randa kika sake cewa na ma Zaid kaza zaki fuskanci fushi na, this is my decision, and its final" ya tashi ya bar mata parlorn, Hafiz na jinsu, a ranshi yace wannan matar na shigar min hanci amma zan fyato ki... Tafiyar Hafiz ta kankama, yau suka tafi Abuja shi da Habib, inda Jirgin su zai tashi zuwa kasar Malaysia, Zai fara karatun shi fanni Computer Studies. Zaid ya ci kuka da ya ga Hafiz ya tafi, dagaske Yaya Habib yake kenan, dagaske ya zame hannun shi daga lamuran shi, toh shi ya zaiyi? Shi kenan ba zai yi karatu ba? Burin shi na zama Injiniya ba zai cika ba? Wa zai sponsoring dinshi? A yau ne yayi kuka sosai, a yau ne yake kukan Maraici. Ji yayi ana share mishi hawaye, ya dago kai da sauri, Rafeeq ya gani da sauri ya dauki yaron ya rungume shi yana hawaye. Aishatu tace Zaid tashi share hawayen ka. Ya dan zabura, ashe ba Rafeeq kadai ya shigo dakin ba, ya dan kwakulo murmushi yace Aunty tun yaushe kike nan? Tace "tunda ka fara sambatu" anan ne ya fuskan ci zancen zucin da yakeyi ya fito fili. Yace "Aunty yaya ya dauke Hafiz ya kaishi Malaysia, ni ina nan, ba sanaa ba karatu, ni ina ga zan fara aikin karfi kamar Welda ko Kanikanci, idan na tara sai na siya Jamb in cike ko ABU Zaria ne. Aishatu tace "kai Allah ya sawwake, Wallahi kafi karfin yin Welder ko Kanikanci. Aunty ba yanda zanyi, dole zan nema sana'a dole inyi karatu, ina son cin burin,tunda ba wanda zai dauki nauyin karatu na dole in tashi tsaye don neman yanda zan cigaba da karatu na. Aishatu ta mike tsaye, tace Zaid, ni Zan dauki nauyin ka, Zaid ka nemo duk makarantar da kake so a fadin kasar nan, in har be fi karfi na ba, Zaid zan tsaya maka da ga farkon karatun ka har karshen shi. "Zaid i will Sponsor you if let me". Zaid da mamakin furucinta yace "Aunty, kar ki damu, bana son daura miki wani nauyi, ba kuma na son ki samu matsala da Yaya" Aishatu tace "Kar ka damu, ba wani nauyin da zaka daura min, ko ban auri Habib ba ni me iya daukan nauyin ka ne, Babana ya gaya min irin Halaccin da Marigayi Lema ya mishi, kaga ko ban fadi ba duk abun da na maka. Kuma maganar Habib, ai ya amince kayi karatu, yace dai kwabon shi ne ba zai yi ciwo ba a kanka, to kar ya damu kwabon shi ba zai yi ciwo ba, kuma zakayi karatu a Turai. Muje muyi searching relevant Schools before its late" ba ta jira amsar shi ba tayi waje. Cikin farin ciki ya dauki Rafeeq yana wulla shi sama yana cewa "Rafeeq maman ka wace iri ce?" _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣6⃣ A parlor ya iske ta ta ciro Latop dinta ta shiga yanar gizo, tace "wacce Kasa kake da burin karatu, kumae kake so karanta?" Ya danyi jim alamun tunanin yace "USA, ina son karantar Engineering". Murmushi tayi ta fara searching Relevant Schools a USA; tace " zo ka gani Zaid, ga wani Havard University Cambridge nan" ya matso, details din School da komai ta duba, tayi naam da makarantar, shima haka ama ba laifi makarantar zaiyi tsada. Nan da nan ta fara ma Zaid processing, bayan Sati daya ta tura wani Yaron babansu da Zaid American Embassy dake Abuja don neman Visa. Komai ya kankama, don saura kwana 2 tafiyar Zaid Makaranta. A ranar Habib ya dawo gida Bayan ya sada Hafiz da makaranta, ya mai Wa'azin da ko kofar kunnen shi be shiga ba, Habib ya tabbatar mai da cewa duk wata zai dinga jin Alert na shigo mai, Hafiz yayi godia Sosai. Zaid ya zo mishi sannu da zuwa amma ko tanka shi baiyi ba, Aisha tace ya yan makaranta? Yace "Hafiz dan Malaysia ana chan bawan Allah, da zan taho harda kukan shi, ya ban tausayi". Aishatu tace "Allah Sarki, Allah ya bada Sa"ar karatu" yace Amin. Tace "Shima Zaid dai ya kusa tafiya" ya dan zaburo, ina zai tafi?" tace "yo karatu mana a USA, ko nan zai tsaya ya lallace?" Habib yayi tsaki, yace kinga abunda nake gaya miki ko? Shi ya dauke dukiyarsa,in ba haka ba, waye zai biya mishi karatu a Havard University? Aisha tace "nice nan,ni na dauki nauyin shi, zan tsaya mai har sai inda karfina ya kare" cikin mamaki Habib ya kalleta yace "Ke Aishatu, ina mai umartan ki da ki janye hannunki kan Zaid, tace ita sam, ita ta sa kanta Shin ba kai kace ba ruwanka da duk wanda zai taimaki Zaid ba? Kaine dai kwabon ka ba zaiyi ciiwo ba?Toh ni zanyi sponsoring dinshi, i'll endorse him, Deal with it Habibullah! Ta fice ta barshi zaune da mamaki. Kwana biyu ba zaman lafiya tsakanin Habib da Aishatu, Zaid yayi takaici, don a ganin shi shine sillar faruwan komai, har ya sameta yace "Aunty, tunda Yaya ya haneki da taimaka min, a bar maganan karatun nan kawai, Allah ya biyaki". Tace sam Zaid, karatu kamar ka tafi ka gama ne, i've spent alot on it, ba zan yi hasara ba, so make me proud, kaje kayi karatun ka, ta mishi yan nasihu da waazi. WasheGari Zaid ya je Gidan Baba Tijjani ya maj Sallama, Ya dawo gidan yayan shi ya durfana gaban sa ya na hawaye yace "Yaya ka yafe min, kar kayi fushi dani, kaine Ubana, kaine Uwata, fushinka kamar na Iyaye ne, Yaya kayi wa Allah ka samin Albarka a karatun nan da zanyi" Sosai ya ba Habib hakuri, shi yasan yana son kaninshi, amma fushi ya rinjaye shi, a ranshi ya sa ya yafe ma Zaid, yace "tashi ka tafi Zaid, Allah bada saa, a kula, know where you come from". Rannan tafiar Zaid da kyar aka banbare Rafeeq jikin shi, kuka yakeyi kamar ana zare mai rai, Ko Rafee'ah da bata san komai ba sai da tayi kuka, Aunty Aisha ma ta koka. 4Years Later(Bayan Shekaru 4) Abubuwa da yawa sun faru, cikin shekaru biyar nan, Ciki kuwa harda gama makarantar Hafiz da Zaid, ya kamata ace Hafiz ya gama ya dawo gida tun last 2years saboda Course duration dinshi 2and half year ne, amma shashanci da Iskanci ya hanashi dawowa, Hafiz ya kware a fannin Chacha da harkar cocaine (Gambling) duk Malaysian Gambling center sun san da zaman Hafiz, duk ya karar da kudin Zaid, kuma kullum shine tambayan Habib kudi, gashi duk bayan Wata 5 yake zuwa Nigeria, abun ya damu Habib amma bai yi magana ba. Hafiz shine drugs, duk wasu kayan maye Habib ba wanda be sha. Amma abun alajabi shine, hafiz beyi kama da mai shan ko da sigari bane. Yanzu dai Hafiz ya talauce, baida kudin Chacha, baida kudin Cocaine, ga Bashi ana binshi na wurin Gambling, wasu thugs ke barazanar daukan rayuwar shi, sunce ya biya su, yace Yayan shi zai turo, shiru sukeji don tunda ya ma Habib maganar kudi shiru kakeji, zaman shi Malaysia baida wani amfani, Returning ticket dinshi yaje yayi renewing don zuwa Nigeria, Ogan Yan Chacha ya had Hafiz da wani yaron shi don ya bishu Nigeria ya taho musu da kudin su. Hafiz beyi gardama ba, don shima yana da bukatar kudi, dole ko yazo Nigeria Alabasshi idan ya kara hada wasu kudadden ya dawo. Tunda Zaid ya tafi USA ya fara karatun shi cikin kwanciyar hankali, Kullum suna waya da Aishatu, Rafeeq da Zaid sun yi wani irin Shakuwa kamar yana Nigeria, da ya dawo school har ya san ya bude datan maman shi ya shiga Skype don suyi Video Call da Uncle Zaid, Rafee'ah tayi ta kuka kan Hamma Rafeeq ya bata wayar amma haka zaiyi banza da ita ta yita tsala ihu har sai Mami tazo ta amshe wayan ta bata ko shi Rafeeq din ya ga daman bata wayan. Duk wata Aishatu na raba Albashin ta ta tura ma Zaid rabi, Habib kan kira shi su gaisa, amma bai taba tura mai ko taro sisi ba itama Aisha bata taba tambayn shi ba. Wata sa'in idan ba a ma Aishatu Albashi ba, ba ta da sukuni, ta dinga zirga zirga kenan, ina zata samo kudi ta tura ma Zaid? Zaid ko yana fuskantar ta duk da ba ta fito fili ta gaya mishi damuwar ta ba ya kan fahimceta. Yace Aunty kar ki dinga damun kanki, zan sanu part time job a nan ko da Cafe ne, zanyi serving as Waiter. "Waiter? kar ka sake inji Zaid, kafi karfin nan, kar ka damu, i'll find a way to make money kaji?" yace "naji Allah rufa asiri" Jin ta kawai yayi, ba zaiyi kwance tana mishi komai ba, shima zai tashi don taimakon Kanshi. Tun tafiar Zaid Shekara Biyar kenan be taba dawowa gida ba, a ganin shi takura ne ga Aishatu ko kudin Jirgi matsala ne, shisa duk yanda taso yazo gida fir sai yaki yace har sai ya gama toh gashi dai ya gama sai shirin dawowa. BAYAN DAWOWAR HAFIZ. Tunda ya dawo ya ke sak'e sak'en inda zai samu kudi, yaje Warehouse be ga komai ba, da alamu Habib ya chanza ma'ajiya. Tunanin mafita yakeyi, gashi ba zai iya tambayan Habib kudi ba. Wani tunani ya fado mai, da sauri yayi murmushi. Karfe sha dayan dare(11pm), bayan Yara sunyi bacci, Aishatu ta dauke su ta kai dakin su, ta wuce dakinta ta tsala wankan ta, ta saka night gown ta fito ta jawo kofar tayi dakin Mijinta Habib, da sallama ta shiga, yace "Shatou na, har yaran sunyi bacci? Tace eh sunyi, Rafee'ah da rigima wai sai dai kar hamman ta ya Kwanta a cinyana, Habib yayi daria, yace "ina ruwan kishiyoyi, yauwa Shatou, dauko bargon dakin ki, jiya naji sanyi wallahi, tace kamar akwai bargo a nan, yace "eh yayi k'ura, gobe zan bada a wanke" tace "toh bari naje na dauko" ta juya ta fita a hanzarce. Hafiz na ganin Shigewar Aishatu dakin Habib yasan ita da fitowa sai gari ya waye, sadaf-sadaf ya shiga dakinta, drawern madubi ya je ya jawo be ga wani abun dauka ba, side drawer ya koma ya bude, dubu biyu da dari biyu ya gani (#2200) ya gani ya zare ya sa a aljihu yace ko sigari na sha. Yana jawo na kasan ya ga wayam, kamar ance ya ciro dirowar ga baki daya, yana cirowa sai ga wani dan case a kasa, ya ciro case din hannu na rawa, yana budewa ya ga wata dankareriyar Saitin Sarka da yankunne, da abun hannu da zobe, tsaf ya gane sarkar ce da ya siya ma yayan shi a matsayin gudummuwa lokacin bikin Aishatu, ihun murna ya sake harda yar hamdalan shi, yayi daria yace "wannan shi ake cema ja ya fado ja ya dauke" yayi sauri maida Drawern ya tura case din cikin rigar shi ya mik'e don fita. Juya wan da zaiyi wa zai gani? Aishatu ce tsaye kikam tana kallon ikon Allah hannayen ta kan kirjinta. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣7⃣ Iyakar tsorata Hafiz ya tsorata, ga case rike a hannun shi ba wurin boyo, amma da yake Hafiz namijin duniya ne sai yace "Aunty, ashe baki kwanta ba" kallon kai dakata ta mishi, tace "meye a hannunka?" yayi dan murmushi yace "Oh wai wannan? Sarka ne da yan kunne da na ba Yaya Ajiya kwanaki na dauki kayana" baki bude take kallon shi, tace "kai Hafiz kaji tsoron Allah, ajiya ka bashi ko kyauta? Ina cewa kayi ya sa a Lefen sa, shine gudumuwar ka?, kasan daukan abun wani ba tare da Izini ba Sata ne? Ya kalleta shek'ek'e, yace "Sata? Ta ina ya zama sata? I bought it da kudina, don na dauki abu na shine sata? Its mine anyways. Tace " its fine kai ka siya, i knw that, don ya gaya min, Hafiz Ka riga ka bashi, shi kuma ya bani, ko shi baida iko akan shi, its no longer yours". Yace "Madam, its mine, noone can get it from me, not even your husband, saboda haka sai da safen ki, idan kin isa ki gaya mishi ya zo ya amsar miki". Ya wuce ya barta tsaye. Aishatu da dafe kai, wai Hafiz ke gasa mata magana haka? Duk Habib ya ja mata, da be amsa ba tun farko, da wannan ranar ba tazo ba. Tabbas ta san duk cikin Sark'ok'in ta ba wanda ya kai na Hafiz? to ya za tayi tunda ya bukaci abin shi? A fili tace "Allah shi kyauta" Zuciyar ta ta ke waswasin gaya wa Habib? Toh tace mishi me?Ta haddasa fitina tsakanin su? Balle shi Habib dake matukar son Hafiz, ko Zaid be so haka. Kuma bata son wani abu ya kara shiga tsakanin ta Hafiz, don tsakaninta da Allah tsoron Hafiz takeji, yanayin sa na bata tsoro, a ranta ta kudiri cewa ba zata gaya ma kowa ba, idan yayi wari sa ji, ta dauki Blanket dinta ta datso kofar ta, tayi dakin mai gidan ta. Da Sassafe Hafiz ya je kasuwa don saida Sarkar nan, kasancewar ta tsaddadiyar sarka tun shekara biyar da suka wuce, da aka auna Kadan ne babu cikin Miliyan, Naira dubu dari tara da goma(910). Hafiz ya cire 650 ya ba yan Malaysia ya rike sauran da niyyar zai je Lagos Gambling kila ya ninka kudinshi so biyar (Allah ya shirya ka Hafiz.) Matashi dan kimannin shekaru 22 yayi sallama a kofar parlon Habib da ke zaune shi da iyalan sa, Habib ya dago kai tare da amsa Sallaman, kallon shi kawai yake yi yana son tuno fuskar, Aishatu ce ta mike tace "Zaid?" Rafeeq ya sake Ihu da karfi, da gudu ya nufe shi ya je ya rungume shi, shi ko Zaid ya daga shi sama yana "Oyoyo my boy" i've missed you so much, look at you" Rafeeq dan shekara 5 yace "welcome home Uncle Zaid" yace "Thanks son, ina baby Rafee'ah? Cikin hausan shi da be fita Rafeeq yace gata chan tana fushi wai ka daukeni" Zaid ya sauke shi yace "Ohh my baby come here" da gudu ita ma tazo ya dauketa, suka ida shiga parlorn, Sai da ya durkusa har K'asa ya gaida Aishatu da ke ta faman jera mishi sannu da zuwa, kafin ya kalli Yayan shi yace "Barka da Rana Yaya" Habib baki sake kamar soko yake kallon Zaid, kwata kwata ya chanza kama, kamar wanda aka ma wankan Engine yayi Jazir yayi kyau. Suka gaisa, kafin kace kwabo Aishatu ta cika shi da abinci. Kamar daga sama Hafiz ya fado Parlorn, da Zaid ya ci karo, kamar wanda yayi Gamo da Aljan yayi saurin juya wa, ashe Habib na kallon shi, yace "Hafiz ina zaka, baka lura da danuwan ka bane? Ba yanda zaiyi dole ya dawo. Wani murmushi ne kan fuskar Hafiz mai wuyar fassaruwa, yace " Hello brother, its good to see you again, welcome home" Zaid ya hadiye miyau, ya shiga tunanin baya, komai ya dawo mai sabo, ya sake hade wani bakin miyau, be san murmushin da Hafiz keyi na meye ba, a ranshi yace Allah ka min tsari daga Sharrin me sharri" a fili kuwa yace "Thanks, its good to see you too". A year Later(Bayan Shekara 1) Zaid ya gama bautar kasar shi a shekarar shi ta 23, Hafiz kuma a Shekara 24, Zaid Ya zama wani Azabbaben Guy, tun yanzu mata ke kawo mishi hari, Aishatu ta mishi maganan Masters yace, sai yayi settling. Rafeeq da Rafee'ah na ta zuwa school, da aji daya Rafeeq ya fi Rafee'ah, Dukkan su Allah yayi musu Baiwa na Kokari... "Kutumar Uban chan" Hafiz ya lailayo wata ashar, wa nake gani kamar Anas? Anas da ya koma wani Giant, Giya ta hura shi yayi daria yace "ni ne fa" Hafiz ya diro daga kan mota suka rungume juna, yace ashe "rai kan ga rai"? Rabo na da kai tun kafin in dawo Nigeria, kuma na yi ta kiran wayan ka baya shiga, gashi bansan gidan ku bare naje(wai duk abun nan, Hafiz bai san Gidan su Anas ba, What a fool😆). Anas yayi daria yace " wallahi na koma Porthacourt da zama" chan nake sana'a" Hafiz yayi shewa "da kyau maza, wannan wace irin sana'a ce da yayi transforming dinka lokaci guda? Duk ka koma wani Don? Anas yayi darian yan bariki, yace " abun sirri ne" Hafiz yace haba mutumen, kar ka min haka, ka fada mim hanyar samu nima in karu, Anas yace "Zaka iya?" Hafiz yace koma menene zan iya, indai har zan samu kudi" Anas yace "haka ne, kasan sai da kudi ake neman kudi, akwai kudi gurin ka? Hafiz yace "aa babu, kamar nawa ake bukata?" Anas "yace half million(#500,000). Hafiz yayi jim, sannan yace Ba matsala, i'll find a way, like always." Rana Dubu na Barawo.... Babu inda Yaya Zai ajiye Safe dinshi da wata kadarar sa, indai ba a bank ba, toh defintely a Office din kusa da dakin Baccin su ne, tunani Hafiz ke nan, ya zaiyi ya shiga ciki ba tare da kowa ya ganshi ba? Anas ya kira don shawara, Anas yace "kar ka damu, ina da master key din da zai iya bude ko wani kofa, kawai dai bari sai daren, sai na zo muyi operation din tare. Da daddare misalin 12:30 na dare, Anas da Hafiz basu sha wahalan shiga Personal Office din Yaya Habib ba. Suka shiga neme nemen, Hafiz ya jawo wata yar durowa, sai ga wata tamfatsetsiyar Agoggo Swatch ta fado, murna ya hau yi, Drawer na biyu kuwa wani Safe ne a jikin tare da kwado, Hafiz yace "Anas look what i've found, it got a small lock" Anas yayi daria yace "worry not, i gt a small key" ya sa dan karamin key, tsaf kwado ya bude. Wurin bude Safe suka ji gam, insert password ya nuna musu, Hafiz yayi murmushi, yayi typing, *Habib Lema* lock ya ki buduwa, ya yi typing *Habibullah* incorrect password, yayi tsaki ya yi typing *Habib* a nan warning alert ya fara, Anas yace "meye matsalar? Dama baka san password din ba?" Cikin barci yaji Alert mai karfi, a firgice ya tashi don ya jima da kwantawa, ya kunna bedside lamp, ya duba gefen shi ya ga Aishatu na barshi, still Karan na kara yawa, wayar shi ya shiga lalube, don a zaton shi Alarm ne, duk da beyi tunanin yayi setting Alarm ba, Ya duba ya ga ba wayar bace, ya dan fara bubbuga Aisha don Karan na kara yawa, ta tashi tana mutsitsika ido, "yadai Daddyn Rafeeq?" yace tashi"ki kashe Alarm din nan na wayar ki" cikin mamaki tace "Alarm dai"? Ta kalli Agogon dakin taga 12:40am, tace kai "Aa, ban sa wani Alarm ba". Habib ya Sauko daga kan Gadon, nan yaji karar ta wurin bedside drawer ne, ya dan matsa gurin. Zuciyar shi ta ayyana mishi *Brief case*Da sauri ya nufa Brief Case dinshi, don ba tantama *Warning Alert* din Safe din shi ne. Da sauri ya bude pincode din ya dauko wani dan karamin Machine kamar dan Ipad, Aishatu da dawo kusa dashi, Habib ina tunanin ba mu kadai ke gidan nan ba, ka hanzarta kiran Polisawa, yace Aishatu whoever this is, he's among us, in ba haka ba, wa ya san ina da office cikin Gida?. A Zuciyar shi, ya ce Zaid ne, aiko zai dauko mummunar mataki kan Zaid, yace "ba sai na kira police ba, i can handle this, idan nace miki Zaid na da Halin banza bazaki yarda ba, bari na nuna miki proof" wasu danne danne yayi a jikin machine din sai ga Fuskokin Hafiz da Anas sun bayyana, suna ta fama da saka incorrect Passwords. A hankali Habib ya furta "Hafiz? No it cant be" Aishatu ko batayi mamaki ba. "I dont know where the problem is, amma for sure Yaya sunayen mu yake sa as passwords, misali kaga zaiyi naming password after the owner, kamar ka ga da na dauki Safe din Zaid, karon farko na saka Zaid lema Safe ya bude, toh ban san mesa wannan yaki budewa ba, na saka Habib, na sa Habibullah duk sunki budewa, could it be possible ya sa Sunan First Son dinshi?" Rafeeq? Yes thats it! We are rich bro, password din is Rafeeq" Habib najin Haka ya zabura a guje yace Shikenan Aishatu ya gano Password din, Da Karfi Habib yace *Hafeeeeeeez*!! Sai da Gidan Ya amsa. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣8⃣ Ihun da Habib yayi ne ya tashi Zaid da Mdaga bacci, da sauri ya fito suka fito daga dakin baccin shi, yayi cikin Gidan don ya san tabbas ba lafiya. Hafiz a kidime yace " Akwai Matsala" Anas yace "mu ware kawai" Hafiz yace "aa its too late, lets just act smart" daidai nan Habib, Zaid, Aishatu suka shigo dakin. Zaid ya damke Anas, Habib kuwa bai yi sanya ba ya chakumo wuyar rigar Hafiz yace "What have you turned yourself to? A monster? A heartless, selfish person? Me ya sa ka dauke Safe din Zaid? Bayan kowa an bashi Kason shi? Ka k'ulla mai sharrin shi ya dauka, Wannan wani irin cin Zali ne?" Zaid ya kalle su cikin rashin fahimta, yace "whoa!, wani Safe aka dauke nawa? Hafeez cike da borin kunya yace " I dont know what You're talii about, let me go" Habib ya kai mai nushi a baki, ya ja wuyar Rigar shi har gaban TV din Office din ya kunna, ya kara jan shi har gaban Safe din ya saka Password din, Safe ya budu, dan karamin security camera da ke jone da Safe din Habib ya danna, sai ga fuskokin Hafiz nan da Anas tunda suka fito da Safe din, duk abubuwan da suka fada sai da suka gani kuma suka ji kamar a film, Zaid ya dinga maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Be son sanda ya sake Anas ba ya nufa Hafiz cikin zafin nama, Anas na gannin haka ya arta a guje. Zaid na zuwa ya daga hannu ya faska ma Hafiz mari har kala 2, yace "how dare you Hafiz?" dama kai ka dauki Akwatin nan kace nine? Ka sa Yaya ya tsane ni? Ka sa ni cikin Halin Kunci? Hafiz me na maka? Ni da kace ka na son kudin wallahi zan mallaka maka halak malak, amma sai ka bi ta bayan Gida, Hafiz i wont forgive you " Hafiz ya fashe da daria cikin borin kunya wacce aka ce da hauka ake nadeta, yace " *So what? Now that y'll know my deepest secret, what are you going to do? Ehh? Ya kalli Yayan shi what are u going to do Habib Lema? Hand me over to the police? Go on you never cared dama, ka kira min polisawa su tafi da ni, kaga ko ba wani Abu bane don dan kishiya ya tura kaninsa gidan kaso(jail)*." Zaid yace "Kar ka damu Hafiz, ai daga nan Police station kayi, naga you are so eager ka ganka behind bars(bayan kanta.) Hankalin Habib ya tashi ba zai taba tona asirin Gidansu ba, hada Hafiz da police kamar tona ma marigayi mahaifinsu asiri ne, Habib ya kalli Zaid yace "Zaid, so kake Hafiz ya biya ka kudi da kaddarar da ya satan maka?" Zaid yace "ni ba abunda zanyi dasu, Burina Allah ya ji kan mahaifa na, ya ji kan yanuwa na" Habib yace "Madallah, let him go" a tare Zaid da Aishatu sukace "what?" Habib yace Hafiz is our Family, kar mu tona asirin junan mu, mu taya shi da Adduan shiriya" Zaid be tanka ba ya bar office din, Aishatu ta bi bayan shi, Habib ya kalli Hafeez cikin sanyin murya yace"Jeka kwanta its late" Hafiz kunya da tausayi suka lullube shi, ya sa hannu cikin aljihun shi ya ciro Agogon Swatch din da ya sata, ya mika ma Habib yace "da a ce baba na da rai, he'll be very oroud of you Yaya" habib ya sa hannu ya amshi Agogon ba tare da yace komi ba, shi ko Hafiz ya sauka kasa zuwa dakin shi. Cikin dare Hafiz ya tattara kayan shi tas, ya ciro wayar shj ya kira Anas, Anas a tsorace ya dauka yace "hello, matsoraci kana ina,?" Anas yace kaii kaji yanda hanji na suka kada, na mugun tsorata?" Hafiz yayi dan tsaki yace "kai ni zo ka dauke ni ina nan ina jiran ka" Anas yace wa? Ba dai ni ba, bari ma turo maka Escaley kawai" cikin mintuna kadan Escaley ya kira Hafiz yace mishi yana waje, Hafiz ya kwashi kayan shi da kyar ya fita waje, Escaley ya taimaka mishi, Mai gadi na tsaye yana kallon ikon Allah, farar takarda Hafiz ya ciro ya ba mai gadi, yace ya ba Yayan shi ko Zaid da safe, me gadi yace "Oga Hafiz ina zakaje da daddaren nan, 2 ta kusa fa" be amsa shi ba ya shige mota Escaley ya ja motar. Tare suka dawo daga Sallahr Asuba, tun a hanya ba wanda ya kula wani, Zaid fushi yake da yayan shi kan abun da ya faru da daddare, Habib kuwa ya san dole ran shi ya baci, don ba a kyauta mai ba da be dauki wani hukunci kan Hafiz ba, Zaid ba zai gane ba, be san halin mutane ba, ana iya cewa don Uwar su ba daya da Hafiz bane ya tura shi prison, Amma zai mishi bayani idan ya sakko. Suna shiga Gidan mai gadi ya ciro takarda ya mik'a ma Ogan shi Habib yace "inji Hafiz, jiya karfe 2 ya bar gidan nan" hannu na rawa Habib ya warware takardar, Zaid har yayi gaba ya dawo don yana son jin me Hafiz ya rubuta a wannan wasikar. A bayyane Habib ya fara karantawa, ga abun da ya rubuta nan ; "*I know i'm a disgrace to this family, which is why i left you, na barku, zan shiga duniya, kar ku neme ni, ku mance kuna da wani danuwa me suna Hafiz, ba zan bari ku kara gani na ba, ku Shafe Hafiz Lema daga babin rayyuwan ku, saboda Hafiz Lema doesnt exist, Enjoy your lives without me brothers" Ba Habib ba harta Zaid sai da hankalin shi ya tashi, tsakanin danuwa da danuwa sai Allah, Jini ba wasa bane, nan da nan Zaid ya fara hawaye, da gudu ya shige daki Habib ya bishi a baya, Zaid ya dauko wayar shi ya shiga neman layin Hafiz sai da ya mishi missed calls nawa kafin ya dauka, A dake yace Ya akayi ne Zaid? Zaid na kuka yace DonAllah Hafiz ka dawo, kar ka barmu, Wallahi na yafe maka, ka dawo, nd i promise we'll be like Nothing wrong has ever happened, donAllah, i need You. Hafiz ya fashe da dariya, yace "You dont need me oo, idan na tsaya zan cigaba da yi muku barna ne, gwara nayi nesa daku, kar ku sha wahalan nema na, don ba za ku taba binciko ni ba" Zaid ya fashe da kuka, Habib yayi saurin karban wayan, ya kara a kunnen shi, yace "Hafiz ka saurareni" Hafiz ya katse shi, yace "Yaya kar ka bata bakin ka, i've decided, be Happy brother kafin yace wani abi Hafiz ya latse wayar. Habib ya shiga neman layin yaji swtiched off ashe Hafiz fito da Sim card din yayi ya tauna a bakin shi ya zubar. _Bayan Shekara Sha Biyar_ *(15 Years Later)* Gidan Alhaji Habib Lema cike makil da mutane , da Alamu Biki akeyi, Hajia Aishatu na hango zaune kan Gado cikin wata tanfatsetsiyar Leshi, kamar yarinya yar shekara 20, sam girma be nuna a jikinta ba, shigowa akeyi ana mata Barkan an daura aure lafiya, wasu mata suka shigo suna fadin "ina Uwar Ango take, taje ta fito mana da Amarya?" ta tashi tana daria, tana fadin "Ni da kaina?" suka ce " ke fa da kanki Maman Zaid tunda da bakin ki kikace Zaid ba kani bane, d'a ne" tayi daria ta nufi inda aka tanada domin Amarya da kawayen ta Amare, ta shiga da Sallama suka amsa tace ince dai kun gama kimtsa min Amarya ta? Duk sukayi daria, Amarya Safiyya ta sunkuyar da kanta, Aunty Aisha ta nufeta ta dago kanta, tace "MashaAllah, Safiyyah kinyi kyau, ku muje Filin Launcheon din, an tattaru Amarya kawai ake jira" Ango Engr Zaid Lema Suka shigo filin launcheon da Abokan shi, İnda aka tana da domin su suka zauna, Amarya ma aka rakota har gurin Angon ta, Bayan Aunty Aisha ta bude taro da Addua ta ma manyan Baki sannu da zuwa ta koma ta zauna kusa da Mijinta Alhaji Habib Lema. Dj ya kunna kida gida ya kaure da sauti, gudu yake yana bangaje mutane, babban burin shi ya ganshi a filin rawa, Maalesh na kwala mai kira kan ya bar gudu ya ki, har hularshi ta fadi, Maalesh yace "ka ga hular ka ta fadi, ka tsaya ka saka" ina samm bai ji ba. Sanye yake da kaya komai iri daya Da Ango Zaid wato farin Shadda Kaftan mai Malummalum, yana zuwa Filin rawan ya wani ci burki, ya fara kallon kowa one by one, ya juya ya kalli Mamin su ta girgiza mai kai alamun kar yayi, ya kashe mata ido daya(wink), Abban su kuwa murmushi ya mai, Ya kalli Uncle Zaid Ango, ya daga mishi gira alamun go ahead haba kamar wanda aka sa ma battery, ya fara takunshi daidai da sautin kidan, abun be mishi ba har sai da ya cire Malummalum dinshi ya wulla ma Maalesh ya cigaba da rawan shi yayi gaba yayi baya. Ango Zaid yace ma amaryar shi "kinga mutumin ki na cizgar rawa ko?" da yake ba kallo take yi ba kanta a kasa yake tace wanene? Zaid yace "waye in banda RAFEEQ?" _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg1⃣9⃣ Amarya ta dan daga kai taga tabbas Rafeeq ne ke wannan chashewar, wuri ya dauu sowa sabida Rafee'ah ta tashi cikin takun ta ta biyo Rafeeq filin rawa tana mishi like, shi ko sai rawa yakeyi iya karfin shi. Sai da Zaid ya mishi alamun ya isa kafin ya tsagaita. MC ya fara gabatar da shirin Biki, Hajia Aishatu ta bude taro da Addua, Rafeeq ya bada tarihin Ango, biki yayi biki, anci an sha, an gwangwaje, Rafeeq da Rafee'ah sun taka rawar gani, shima Ango ba a barshi a baya ba don sai da Rafeeq ya sashi rawan dole, akayi hotuna, sukayi Family Photo. Washegari aka daure aure, aka kai Amarya Gidan ta da ke Kaduna U/rimi, da yake chan Zaid yake aiki. Part daya aka ware ma Rafeeq a gidan Zaid don Zaid da Rafeeq kamar abokai suke, ba za ka gansu kace Kawu da dan shi bane. Rafeeq dan dangi ne,duk inda ya gifta sunan shi kawai zakaji ana kira, yanuwa da abokan azziki, manya da yara, kowa Rafeeq, tabbas Rafeeq yana da farinjini, ba don komai ba don shima he's a simple somebody, ba ruwan shi da zabe, yace ina yi da wannan ba nayi da wannan, aa kowa nashi ne, yana da son mutane, da son wasa, ya ja wannan tsokana, ya ja wannan tsokana, maza da mata, bashi da kyamar talaka. Rafeeq fari ne, bai ciki tsawo ba, bai cika gajerta ba, dan daidai, be da kauri sosai, kyakyawa ne ajin farko, har friends dinshi na mai kirari da ''all ladies eyes on Rafeeq'' duk budurwa mai ji da kanta ta na so a ce da ita budurwar R-Lema, saboda ya hadu, Arzikkin baban shi be sa shi girman kai ba ko kadan, haka fa yake a makaranta, kullum suna Cafteria shi da Abokin shi Mahmud Maalesh, Maalesh abokin Rafeeq ne tun Secondary School, Abotan Maalesh da Rafeeq ne ya sa Iyayensu ke zumunci, idan ka ga Mami da Mummyn Rafeeq zaka zata yanuwan juna ne, Maalesh is his partner in crime, idan sunyi laifi Uncle Zaid ke hukunta su, don ba sa jin magana, duk wani party sai sunje sun sha rawa, ba sa shaye-shaye, ba sa bin mata, amma yanmatan su sunfi 50, don shi Rafeeq kafin yace yana so to an riga cewa ana sonshi, Irin Matashin nan ne wanda be da wata matsala a rayuwa, kowa na shi ne, kar kuyi zaton Rafeeq be mayar da hankali a karatunshi, to ba haka bane, Duk Department din su na BioChemistry, ba kamar Rafeeq, Lecturers kance, "idan akwai abun da yafi 5point, to tabbas Rafeeq zai buge shi" irin su ne ake cewa "Always ahead of the Lecturers" saboda kokari, Allah ya ba Rafeeq k'wak'walwa, both ilimin Addini da na boko, a shekaran shi na 16 ya sauke AlQurani mai Girma ya kuma shiga Jami'a, Yanzu haka yana da shekaru 20 cifcif kuma bana zai gama Jami'a. Rafee'ah kuma tana karantar Sociology tana aji 2. Ba su fiye shiri da Rafeeq ba don ita shiru shiru ce, shi ko yayi ta tsokanan ta, Rafee'ah kyakyawa ce, bata fiye son magana ba, amma indai Rafeeq na gida dole sai ya sata magana da yawan surutun shi da tsokanam ta da yake yi, tun bata biye mishi har ta fara biye mishi, da ya mata take ramawa, idan kuma abun yafi karfinta, sai taje tana ma Mami kuka, mami kuma ta ma Rafeeq fada, hakan ba zaisa gobe ya kuma tsokanan ta ba. Gidan Habib Lema, gida ne da aka ginata cikin So, Aminci da yardan juna, suna matuqar son junan su, ba su da Matsalan komai, Mami(Hajia Aisha) ta tsaya tsayin daka wurin tarbiyantar da yaran ta bisa tafarkin Addinin musulun ci, tun suna yara Uncle Zaid ne Discipline Master, idan sunyi laifi shi ke hukunta su, Shiyasa Suka tashi da son junan su (Wannan Kenan). Daga sama Mami taji ana "Assalam Alaikum" ta bude idanunta a hankali don a gajiye take tun bayan biki, ta dan bude murya ta amsa sallaman tare da cewa "ku hawo saman please" Suka nufa sama, su biyu ne, kana ganin su kasan uwa ce da diyarta, diyar ba za wuce shekara 17 ba, a bakin kofa suka iske Hajia Aisha, tana ganin ta fadada murmushin ta, "Saude kece anan? Sai da muka gama bikin zakizo?" Saude tace "Ayyah madam, wallahi naje gida ne, shiyasa banzo biki ba" "bakomai ai, wannan diyar ki ce? Kafin kace wani abu yarinyar har ta zube kasa tana kwasar gaisuwa, Mami ta dago ta tana kallon ta, wani irin kama taga yarinyar nayi da Rafee'ah, tace what's ur name? Yarinya tayi murmushi tace "Sunana Aneesa" Wow nice name, sannun ku da zuwa, ku shigo" suka shiga ciki, kafin kace meye wannan Mami ta cika musu gaba da kayen ciye-ciye, suna ci suna fira jefi-jefi, Saude tace "bakowa a gidan sai ke?" tace "eh wallahi, ni kadai ce, duk suna kaduna, tunda aka kai Amarya basu dawo ba, Saude tace "Ayyah Allah basu zaman lafia" tace "Amin" Saude Secretary din Hajia Aisha Lema ne a Office, watan ta 6 kenan da fara aiki a office din Matar Habib Lema, tana da kwazo wurin aiki, shiyasa Hajia Aisha ke ji da ita. Six months back ne ta kawo CV dinta da qualification dinta na NCE, office din Madam Lema. Wurin interview ne suka bata tabbacin ba sa daukar masu NCE sai masu Degree, ta dinga kuka wai a taimake ta, mijin ta ya rasu, ya barta da diya daya, ba halin ciyar da ita suna cikin hali na kuncin rayuwa, yanda take kuka taba interviewer din tausayi, yaje ya sanar da madam din su, madam ta nemi ganawa da Saude, ta bata bayani, itama taji tausayin ta, tace "Madam ki taimake ni, kamar yanda Allah ya taimake ki, you are a mother, kinsan irin son da uwa ke ma diyarta, Miji na ya rasu ya barni da diya daya, dangin shi sun kwashe Gadon, ta tsaya a Secondary, ki taimake ni ki bani aiki da zan kula da diyata" Hajia Aisha ta ja numfashi, sosai Saude ta bata tausayi, tace "can you be my Secretary?" ai ko nan Saude ta zube ta na godia, tace tana so ta gode Sosai harda kukan murnan ta" washegari ta fara aiki as Madam's Secretary, Saude akwai kokarin aiki, da zasu tafi Hajia Aisha ta shiga Dakin Rafee'ah ta tsinto ma Aneesa kwancen kayan Rafee'ah, ta cika su da abun arziki. Bayan Wata Daya Gaba ki daya suke zaune a Babban parlorn Habib Lema, Uncle Zaid na fira da Uwar dakin shi Mami, Rafee'ah na kusa da Baban ta tana karanta mishi newspaper, daga gefe kuwa Rafeeq ne ke ba ma Aunty Seema(Matar Zaid Safiyya, sunzo ne) labarin yanmatan shi na makaranta da na Unguwa, tana ta daria, da kagan su kasan Happy Family ne wanda basu da damuwan komai da kowa. Wayan Alhaji Habib Lema yayi ringing, Rafee'ah ta tashi ta dauko mai kan sidestool, ta amsa ta sa ma babanta a kunne, "*Hello* *Yaya*? Dam gaban Alhaji Habib ya buga, ya mik'e tsaye cikin kidima, a hankali yace "Hafiz, kaine? Zaid da Mami suka mik'e tsaye suka nufo Alhaji da jikin shi ke rawa, ya kasa cewa komai, Zaid ya amsa wayan ya sa handsfree yace "Hello?" daga dayan bangaren aka ce "Hello Brother" Zaid yace "Hafeeez, is this you brother, where are you?" karbe wayan akayi daga hannun Hafiz akace "Hello This is Secret Service Agency Lagos, Hafiz Lema's been Jailed 10years ago, he's completed his Sentence, and is fined 500usd, come to the Agency for more details". Dif ya kashe wayan. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣0⃣ "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" duk suke fada, Alhaji Habib ya zauna ragajab kan kujera ya dafe kanshi da hannuwan shi, tunani yake me Hafiz yayi haka da aka kulle shi for 10years ba? Zaid yace yaya "meye abunyi?" Habib ya hadiye miyau yace "Zaid, a siyo ticket mu wuce Lagos din kawai, Zaid,yace "Yaya ka bari ni zanje Lagos din gobe da safe" Habib yace shi sam be San wannan ba, tare zasu tafi, nan da nan Zaid yayi waya Chanchangi Airlines ya siya tickets biyu. Shiru sukayi kamar anyi mutuwa, Rafee'ah ta yanke shirun tace "Abba wanene Hafiz?" Abba ya kasa magana sai Uncle Zaid yace "Yaya na ne, you were too little when he left, i dont think ko Feeq zai ganeshi" Rafeeq yace "na tunashi but i can't remember anything about him" Uncle Zaid yace yeah u were all young then" duk sukayi shiru, kowa da abun da yake sakawa a zuciyar sa, tunanin su daya, me hafix yayi a ka kulle shi har tsawon shekara 10?. Lagos Karfe 9 na safe Uncle Zaid da Alhaji Habib na Secret Service Agency (SSA), bayan long process aka sa da su da wani Oga, tambayoyi ya musu na Alakar su da Hafiz, Habib ya bashi amsa da "mu yanuwan sa ne, ni yayan shi, wannan kuma kanin shi" Ogan ya dauki wasu files guda biyu ya mika ma Alhaji Habib, ya amsa hannu biyu ya bude, hotuna ne na Hafiz da wasu 6, Zaid ya gane daya daga cikin su, abokin Hafiz nr wato Anas, a cikin hoton aka ga Boma-bomai,Bindigogi da wuk'ak'e, cikin su ya juya, Habib ya bude dayan file din, paper ce doguwa, ya shiga karantawa, Hafiz was an accomplice to Armed Robbers. Hankalin Habib ya tashi, ya fara hawaye, Zaid ya amsa ya karanta shima, kanshi ya girgiza cike da takaici. Oga yace "toh sati 2 da suka wuce ne ya cika Shekarun da aka diba mishi, an ki sakin shi ne sai ya bada 500usd, mun ta tamabyan shi wa zaizo bailing dinshi, yak'i magana, da ya ga bamu da niyyar sakin shi ne shine ya bada numbern ku, Zaid yace "yanzu 500usd za a baku sai ku sake shi?" Oga yace "eh" Zaid ya danyi guntun tsaki ya sa hannu cikin aljihun shi, ya ciro rafar dubu 3 ya dora ma Oga kan table, mutumin yayi murmushi yace "Sir we dont do it this way, u go to the bank and draft it to our Account" Zaid ya dan daga murya yace "you should have said that at first, u think we have time for this? Habib ya kalli Zaid yace "Calm down Engr" Mutumin yace "unless you'll pay here the change will be mine, you know 500usd is approximately to N250,000, and this is 300k" Zaid ya mai tsawa yace "shut the fuckup, take d goddam money and get us our Brother" Mutumin yayi daria ya mike tare da kallon Alhaji Habib, yace "i see your bro has guts, i'll get ur brother now" ya fita. Alhaji Habib yace "Zaid, kayi hakuri, muke nema gurin su, dole mu kwantar da kan mu" Zaid cikin fushi yace "yaya rabu dasu, iskanci ne, ji fa yanda yake magana, matsiyaci, kudi ne matsalan shi" Habib yace "ayi dai hakuri" duk sukayi shiru. Turo kofa akayi, Habib da Zaid suka mik'e tsaye, idon su kan kofar shigowa, Ogan ne ya fara shigowa Hafiz a bayan shi, Hafiz yayi bak'ih duk kyaun nan ya disashe, ga wata uwar k'asumba ya ajiye, duk yayi ba kyan gani, Rige rigen zuwa gunshi Zaid da yayan shi sukayi, Hafiz ya fashe da kuka, suko ba su damu da yananyin da yake ba suka rungume shi suna hawayen suma. Da kyar hafiz yace "ku gafarce ni yanuwa na, na san ban kyauta muku ba" Alhaji Habib yace "shhh, Hafiz not now, lets get outta here" Suka nufa hanyar fita, Zaid ya watsa ma Oga harara, shi ko dariya ya bashi don yaga Zaid ya dauki abun da Zafi, yace ga Kayan shi da aka amsa kafin a kulle shi, Zaid yace "ka jika ka sha an bar maka" sosai Officern yayi daria, yace "till we meet again ko" Zaid yace "ganinka ba Alheri ba, ba Amin ba" ya fita shima. Drivern Office din Lema textile Company Zaid ya kira, within some minutes ya hallara Agency din, ba jira suka shiga, Golden Hotels suka nufa, Hafiz ya shiga dakin shi, yafi 1hour yana wanka, yana fitowa ya ga Wasu riga da Wando da Zaid ya siyi mishi, ya dauka ya saka yaci abinci yayi Sallah. Bayan sun huta Driver ya sake zuwa ya dauke su, yayi Airport dasu, don yau suke son wuce wa. Bayan mintuna kalilan jirgin su ya tashi, Cikin Awa daya suka iso Kano ta dabo. Kafin suje masauki sai da suka biya Barbers Corner don a ma Hafiz Aski, Tsaf hafiz ya fito da kyau, don yini dayan da yayi ya fara kyau. Washegari driver ya dauke su sai Katsina ta dikko dakin kara. Tana tsaye tsakar Gida tana jiran isowar su, don tun da suka shigo KT Alhaji ya kirata yace sun iso, ga su nan karasowa. Rafeeq da Rafee'ah na school, Mota na shigowa Haraban Gidan gaban Hafiz ya bada Hinqim, komai ya dawo mai sabo, a ranshi yace "it all started here" Sannu da zuwa Aisha take ta faman yi ma Hafiz, harda hawayenta, Hafiz duk ya koma wani sukuku, be sakin jikin shi, ta gabatar musu da abinci, kadan Hafiz yaci, yanda kuka san bak'o sai rab'e rab'e yake tayi. Alhaji Habib ya lura dashi yace "ka sake jikinka Hafiz dis is your home" Hafiz yayi murmushin takaici, yace "Yaya, nasan duk kuna da miliyoyin tambayoyin da kuke so ku min, kuna so kuji yanda na tsinci kaina a kurkuku" Habib ya katseshi yace " Aa Hafiz, abunda ya wuce ya riga ya wuce, kar a maida hannun Agogo baya, muyi addua Allah ya tsayar nan kawai" Hafix ya girgiza kai yace "Aa yaya, dole ku san me ya faru, dole kusan irin rayuwan da nayi bayan bari na Gida" Zaid yace "Gaskia ne, muna sauraronka" Hafiz ya fara labarinshi kamar haka: Shekaru Goma da suka gaba ta(Last 10years) Muna barin Katsina, Straight dauki hanyar Porthacourt, ni da Abokaina 2, Anas da Eskaley, mun kwana mun yini a hanya, har muka isa wani gida, Gidan Thug Gang (Sunfi kama da kauraye )din su Anas ne Amstrong da Willy, Kwanan mu 2 a PH Anas suka nuna min wuraren bude idanuwa, kamar Night Club, Gambling Center, Da Gidajen giya, duk na kware a harkokin nan. Ba mu rufe Sati 2 ba naji Armstrong na gaya ma Anas su shirya akwai Operation yau da daddare gidan Commisioner, yace "okay we'll prepare" nace da Anas wani irin operation ne wannan? Anas yayi daria yace "my guy, ba zaka gane bane, share kawai" Nace "haba Anas, kar ka mun haka, ka fada min mana" yace "kagane, Amstrong ce min kawai yayi zamuje iperation, amma be gaya min takamaimin me zamuyi ba" Nace "then i will go with u" Anas yayi dariya yace "no u cant, yi shiru kar ma Armstrong ya jika" ashe Armstrng na jin mu, yace "he's right you cannot come with us boy" boy ne sunan da Armstrong ke cemin kenan tun zuwan su PH, a ganinshi ni karamin dan iska ne, cikin fusata nace "i am not a boy" Armstrong yayi murmushi yace "show me, today get ready and be prepared" Anas yace "Oga i dont think this is a good idea" Armstrong yace "its time we train him". 3:00am Gidan Commisioner of Youths suka kai ma farmaki, duk suka hade kan mutanen gidan cikin babban parlor harda shi Commisioner din. Hafiz aka bari a Cikin mota, da bindigar Katako, bayan Armstrong ya buge mai warning, kar ya bar bakin mota, no matter what, don zasu iya fitowa at anytime, Anas, Eskaley, da armstrong suka shiga ciki, duk a zaton shi sauran ma bindigar katakon ne, duk a zaton shi kudi kawai zasu amsa suyi gaba, sai labari ya sha bambam da yaji karar bindiga, sosai ya tsorata, Be ankara ba yaji Siren din motocin police, Hafiz ya kidime ya fito daga motan da gudu, charap police suka kamashi da yake Ajebo ne be iya gudu ba. Su Eskaley kuwa sai fafatawa suke da jamian tsaro, suna harbin junan su, nan take a ka harbe su 3, ko shurawa basuyi ba suka mutu, Iyalan Commisioner kuwa ba wanda ya mutu, sai dan shi da Anas ya harba a kafada, an garzaya dashi Ambulance. Abun da ya faru shine, Ashe Akwai diyar Commisioner da take wayan dare(NightCall) ta bayan dakin ta taji ana cewa "Idan ya kawo gaddama kawai mu harbesu mu shiga mu nemi golds a dakun nan su, yanzu kawai mu nemi hanyar shiga cikin gidan" da gudu ta diro a kan gado ta fita da gudu, straight dakin babanta tayi ta gaya mai Abun da taji, da sauri ya danna waya ya kira Jami'an tsaro ya sanar da su, suka bashi tabbacin gasu nan zuwa, da sauri ya nufa dakin matar shi da babban danshi don sanar da su, kafin kace meye wannan yaji an dora mai bindiga a kai, Anas ne yace "idan ka motsa sai na tarwatsa kanka" Commisioner ya sandare, Eskaley da Amstrong suka shiga sauran dakuna suka fito da duka mutanen gidan, suna tambayan kud'adde ne Police sukayi surrounding dinsu duka har suka kashe su Anas. Hafiz ya cigaba da cewa" ko bincike ba a tsayayi ba aka maka ni kotu, kasancewar ni kadai suka kama jikina yayi sanyi, na fada musu gaskia, na amsa laifi na, Kotu me adalci ta ya yanke min hukuncin 10years a Jail+ hardships da 500usd Fine, to kunji abunda ya faru dani bayan bari na Gida. Allah sarki danuwa mai dadi, daga Alhaji Habib da Zaid kuka suke barin ma Aisha da tun farkon Labarin Hafiz take kuka. Sai da sukayi me isar su duka kafin Hafiz ya duk'a har k'asa ya nemi gafarar su duka, Habib yace bakomai Hafiz Allah shi kyauta gaba, Allah ya sa kuma ka koyi darasi, duk wanda ya bar gida gida ya barshi. Hafiz yace "InshaAllah Yaya, ba za ku sake kamani da wani laifin ba", yace "toh Allah yasa" ya juya ya kalli Aunty Aisha yace "Aunty kiyi hakuri da duk abunda na miki, da sauri ta katse shi tace baka min komai ba, Allah ya yafe mana" Hafiz ya kalli Zaid zai yi magana, Zaid ya tareshi da murmushi yace "Welcome home Brother". (Muma munce Welcome Hafiz Lema, Lubie maitafsir tace "Dont cause any trouble" Aisha Yau kuma tace "Allah ya sa ba tuban muzuru kayi ba😐", nidai Biebee nace ku biyoni kuji rayuwan Gidan Lema bayan dawowar Hafiz Lema) _Bibilicious Biebee 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣1⃣ Rafee'ah ta shigo parlorn da gudu ta na kukan Shagwaba ta fada kan baban ta, Abba yace "Rafee'ah baby me ya sameki?" ta turo baki tace "Abba ba Hamma bane kece min Jaki head" Zaid ya fashe da daria, yace "kema ki dinga k'ok'ari kamar Feeq dina, kin tsaya kan makeup" Abba ya harareshi yace Zaid mind your own bussiness" Zaid ya sa wani darian, Rafee'ah ta kara tunzura, ta sake saka wani kukan, Mami tace "Yi shiru babyna, ki barni da Rafeeq da Uncle Zaid dinku, zanyi maganin su, ta mak'e kafada, nidai ba Uncle Zaid dina bane, na Hamma ne" "Shikenan baki gaida Uncle Hafiz ba, ko ba ki ganshi bane" Zumbur Rafee'ah ta tashi, ta nufa Uncle Hafiz da ya kura mata ido, yana murumushi, fadawa kanshi tayi, tace "Welcome Home Uncle Hafiz, we missed you" ya shafa kanta yace my preety princess, nayi missing dinku duka, na dawo, ba zan sake nesa da ku ba" ta rungume shi, yace "ina Hamman naki?" ta turo baki, sai yaje dropping Ya Mahmud a gida, ke waya dawo dake? Tace shi ne fa, chan baki layi ya sauke ni, harda cemin Jaki head" Zaid zaiyi daria Rafee'ah tace "ntoorrrh, ai dai Uncle Hafiz dina ya fika kyau". Duk sukayi daria. Hafiz yace "wani level kike yanzu?" tace level 2 Sociology" "uhm nice, meye CGPA dinki? Da murna tace 3.70, tafi Hafiz ya fara, yce "thats my girl, so smart,keep it up kinji?" Zaid yayi gyaran Murya yace "talking about Smart, kun tuna min da wani matashi, wanda ko shekaru 20 be cika ba, wanda idan ka ganshi da malamai zaka zata lecturer ne, hwanda lecturers suke using dinshi to shine, CGPA dinshi 4.98(is it possible?) wanda ake ma lakabi da 'Face of Science department' wannan ba kowa bane illa: Rafeeq Habib Lema" Rafeeq da ya shigo parlorn yanzu yayi bowing yana daria, thanks Uncle, Zaid yace "dont mention son" Rafee'ah ta tabe baki, Rafeeq yaje ya rungume Hafiz ya mishi sannu da zuwa, Hafiz yace "me Princess ta maka ka sata kuka?" Rafeeq yace "pri mene? Princess din daddawa?ai wannan she's no princess, she's Jaki head, tayi scoring 10/15 a Assingnment" Hafiz ya harareshi, yace "Wallahi ka fita idona, tayi kokari sosai, dont mind him primcess, kinyi k'okari kinji" Rafeeq yace Uncle Zaid, gaya musu if an Assignment is to be marked over 15, what would be R-lema's Score? Zaid ya gyara murya yace 19/15. Daria suka fashe da, har Hafiz, banda Rafee'ah da tabe baki tace "whatever ", tasan idan ta biye ma Uncle Zaid, da Hamman ta kuka zatayi, haka suke ganging up a kanta kullum ko Mami ba ta isa ta sa su su daina ba, ta mik'e ta shiga ciki. Abba da Mami sai daria suke tayi suna kallon draman team Feeq da team Fee'ah. Rayuwan jin dadi, So da kaunar Juna akeyi a Gidan Habib Lema, Zaid ya koma bakin aikin shi, Rafeeq da Rafee'ah suna ta zuwa makaranta, Hafiz kuwa Mami ta mishi processing aiki a office dinta, yau ta shaida mishi da Monday zaifara zuwa aiki. Sallam tayi, Rafeeq da ke zaune a parlorn ya dago ya amsa, da murmushi a fuskan shi, Sannu da zuwa, Aneesa ta ma kanta mazauni akan kujera, ta gaida shi tana wulla idanuwa, Rafeeq yace "Ammata ya kike? Feeyah kike nema? Aneesa tayi fari da ido, "noo Mami nazo gaidawa" yace "Ayyah, Mami kuwa na Office" tace bakomai ai" nan suka shiga fira, abunku da masu surutu biyu, sai labari sukeyi ba sa gajia, ya tambayeta wani school take? tace "zata sake WAEC da JAMB ne, this year" har indomie suka dafa a kitchen, cikin lokaci kalilan Aneesa ta kamu da son Rafeeq, ni dai nace indai Rafeeq ne, zaiyi pieces da zuciyanki. Aneesa na nan har Maalesh yayi dropping Rafee'ah daga School, Kallon rashin Sani Rafee'ah ta ma Aneesa. Aneesa na ganinta tace sannu da zuwa sis" Rafee'ah tace "yauwa sannu" tana kallon ta, don somehow taga suna kama da Aneesa, Rafeeq yace Aneelurv, bari na miki introducing wannan, She's Jaki head, Diyar House Help din gidan mu ce" Rafee'ah ta bata rai tace "Hamma mana, wallahi sai na gaya ka da Uncle Hafiz" Rafeeq ya dinga daria, Aneesa tace share Yaya Rafeeq, kowa ya san kin fi karfin diyar house help, muje ciki ki rage kaya" Rafee'ah ta harari Rafeeq suka yi ciki ita da Aneesa, sai da ya bisu ciki, don idan Rafee'ah na gida baya barinta, yana son tsokanan ta. Tun daga rannan, Aneesa ta maida Gidan su Rafeeq gidan zuwanta, tana shishige musu, don Aneesa akwai ta da son 'yayan masu kudi, ga shi son Rafeeq ya kamata, yana hankalce da ita, bata san Rafeeq ba irinta yake so ba, a cewar shi son yara yan Secondary School ChildAbuse ne, kuji dan rainin wayau, ko shi din nawa yake?. Tazo shiga parlorn, shi kuma ya fito hannun shi dauke da Plate din abinci, suka ci karo, Shinkafar da ke plate din ta zube, Aneesa tayi saurin durkusawa tana tattarawa, yace "Oh Sorry, wallahi ban gani ba" Hafiz ya dago kai don ganin wacece da muryan nan, defintely ba Rafee'ah bace, Haka kurum sukaji gaban su ya fadi dukkan su, suka kura wa juna ido, k'okari Hafiz yakeyi ya tuno inda ya san fuskar nan, don defintely ya san wannan fuskar, amma da yayi la'akari da wannan ba zata wuce shekarun Rafee'ah ba, yace a ranshi kila kama ne, to da wa? Oho!. Yace "karki damu, zan sa a share", tace "thanks" yace ke kawar Rafee'ah ce? tace "noo yaruwata ce" a ranshi yace no wonder suke kama, dama ina tunanin inda na san fuskar ashe don kamar da sukeyi ne da Rafee'ah nake ganin kamar na santa, kila dangin Mami Aisha ne. Da haka ya wuce part dinshi ita kuma ta shige cikin Gidan. "Attention Everyone, this Is Hafiz Lema, yau zai fara aiki a wannan Company din,zaiyi Serving as General Manager, ina fatan zaku bashi hadin kai da goyon baya kamar yanda kuke bani" Director kenan Aisha Lema ke sanar da Co-workers dinta kan sabon Manager da aka samu, ta nuna ma Hafiz Office dinshi, ta shige nata. Waya ta kira reception, take tambaya har yanzu Secretary ba ta zo ba?" aka ce "eh bata zo ba" tace ina ne manta immediately ta na zuwa" yes madam. Da sauri ta shigo Office din Madam, tace "Madam kiyi hakuri, Wallahi-" Hajia Aisha Lema ta katseta ta hanyar daga hannu, tace "Issokay, dama ince miki anyi sabon GM, kije kiyi filing credentials dinshi, and kiyi documenting Account dinshi, and ki bashi Constitution of his Office" Cikin ladabi Secretary tace "yes Ma" ta amsa files din daga hannun Madam, ta karanta Sunan da ke jiki 'Hafiz Ibrahim Lema' a tsorace ta dago kai ta kalli Madam dinta, hajia Aisha na lura da ita tace "yadai, Secretary?" ta k'irk'iro murmushi tace "bakomai", ko kina mamakin Sunan ne? Ba abun mamaki bane, Hafiz kanin mijina ne, Yayan Zaid ne, yayi dan tafia ne sai yanzu ya dawo. Murmushin da be kai zuci Secretary tayi, tace "i'll go ahead" ta fita, tayi kan desk dinta. Hannu bibiyu ta dafe kanta, tunani ya cika mata k'wanya, Hafiz lema ya dawo? Hafiz lema zai bata mata shiri, Hafiz lema zai wargaza mata duk wani Plan din da zatayi kan Lema Family, kaii ba zata yarda ba, tana da advantage kan shi, she'll use it against him, zumbur ta mik'e ta harhada files, tayi Office din GM. Sai da ta k'wankwas kafin ta shiga da Sallama, a yayin da Hafiz ke waya da Zaid, be dago yaga ko wacece ba. Wuri ta samu ta zauna tana karantar Hafiz, Ya Chanza, yayi kyau ya kara haske da sanin da mishi a da. Hafiz ya katse wayar ya juyo da kujerar sa, da murmushi ta kalleshi tace "Good Morning Sir" zumbur Hafiz ya mike cikin firgici ya nuna ta da yatsa yace "Saudah" tayi murmushi ta mik'e tana fari da ido tace "Don Hafiz Lema feezoboy, its good to see you again" Hafiz ya dan sausauta murya yace "Sauda what are you doing here?" ta daga kafada tace "i work here" yace "Sauda what are you upto?" tace "nothing much, i just want to give our daughter a proper life?" a rude Hafiz yace "What?, me kike cewa? Tayi darian 'yan duniya tace " Our love bore fruit, da ka tafi ka barni, ka barni da cikin diyarka, yanzu kuwa ta zama 'yar budurwa cos she's 18 now" Darian takaici Hafiz yayi, yace ke Saudah, na sanki da duniyanci, i wont let you blackmail me, ko kina so kice min ko a lokacin da nikadai kike tarayyah, kar kiyi tunanin na manta ko ke wacece, ina sane dake" tace "nasan zakayi tunanin hakan, amma ina da proof Aneesa diyarka ce" ta ciro wayarta fa lalubo hoton Aneesa ta mika mai, tace "gashi duba kagani, duk wanda yaga wannan ya san Jinin Lema ce, don ba ta da maraba da Rafee'ah Lema. Hafiz cikin rudani ya amsa ya kura wa Hoton Aneesa ido, ya gane ta, itace ya gani a gidansu kwanakin baya, tabbas wannan gudan jinin shi ce. Ya dago kai yace "tasani?" tace "aa bata sani ba, she believes you are dead" yace "Sauda, gaya min gaskia, what are u upto? me kike shirin yi?" tace "its simple, So nake Habib Lema ya aureni, and you going to help me da taimakon ka zan shiga Gidan shi matsayin matar shi" _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣2⃣ Daria Sosai Hafiz yayi, yace "i know you are stupid, but bansan stupidity dinki ya shahara har haka ba, kina son Habib Lema ya aure ki? A mafarki ko? To bari kiji, ko a mafarkin, Habib Lema ya fi karfin ki, Habib Lema ya miki fintikau, Tsakanin ki da shi nesa nesa" tayi daria ta mik'e tace "Hafiz, Sai na Auri Habib Lema, i am asking u now nicely to help me, u know what i am capable of right? Bani da kyau, kuma dole ayi abu yanda nake so". Zuciya taci Hafiz ya zo ya makure mata wuya ya buga ta da bango, k'akarin amai ta fara, tace "Feezo, ka sakeni DonAllah, you are hurting me" Yace Saudah " listen to me close, wannan shine warning dina na farko kuma na karshe, Stay away from my family, Habib be miki komai ba, idan akwai wanda ya miki wani abu, to nine, ni zaki hukunta, dont let my Family into this, they didnt do anything wrong, ina rok'on ki Saudah" ya karashe magana yana mai sausata murya, tare da sakinta. Ta gyara tsayuwar rigarta, tace "nifa ba wani mugun abu nace zanyi ba, Allah ne ya jarabbeni da son shi, kamar yanda ya taba jarabbata da sonka, amma son da na maka, ko rabin wannan be kai ba, ina son Habib Lema, Ina ganin zan rasa raina idan be aure ni ba, so ka kwantar da hankalin ka, Aurena kawai nake so yayi, ba wai ina so na tarwatsa muku Family bane, zaka taimaka min, ko don Diyarka" ta na kai wa nan ta yi hanyar fita, Hafiz ya dinga kiranta amma bata tsaya ba.ta fice. Har aka kusa tashi office Hafiz be samu sukuni ba, tunanin maganganun su da Sauda yayi tayi, Wai yanzu shi ke da diya? Shegiya? Wacce aka haifa ba ta hanyar aure ba? Ya akayi haka?. Shekaru 16 da suka wuce (16 Years Back). Food is Ready Restaurant Sabon Gari Kano. A lokutta da dama idan Hafiz da Anas sunzo yawon banzan su a Kano, wannan Gidan suke zuwa don cika Cikin su, da rabon kudin da suka ciyo wurin Gambling(ChaCha). Wuri ne 'wanda yan iska da yan tasha ke cin Abinci, Shagon Maman Sauda ne, Sauda da kanwarta Maryam suke serving abinci, idon su bude yake don suna hulda da yan tasha, har Sauda na ba da Jikinta don Kudi, Tun randa Allah ya fara kawo Hafiz Shagon maman Sauda, Sauda ta kamu da son shi bilhakki, ta fada ma mamanta, maman ta tace "ke kinga Saude, wannan yaro akwai kudi jikin shi, ki tatso mana shi kawai, ki bar wani batun soyayyah kinji? Ta turo baki, tace ni gaskia mama son shi nake, har ina so na aure shi, Maman tace "aure? Babban magana" a haka Saudah ta kudurta a ranta ko ta halin k'ak'a sai ta auri Hafiz Lema, don gayen ya hadu ta kowane fanni. Anas ya Kalli Hafiz yace "Kaga Saudah sai signal take maka ko? DonAllah ka bata chance, kullum muka zo Kano, bata da wani sukuni, sai neman attention dinka, kalleta fa She's not bad, da kyanta, da dirin ta, ta hadu ko ta ina" Hafiz ya buga tsaki yace "na sani mutumin, nifa da zata zo in huta da ita in biyata da na fi kowa jin dadi, amma ita sam wannan be gaban ta, wai aure take so muyi, kai har wani abu take so muyi wai shi Soyayyah" Anas ya tuntsire da daria yace "duk a zatona Sauda ta waye ashe da sauran ta, wake Soyayyah yanzu? Ai kawai mata yan hutu ne, a huta dasu a biyasu kowa ya ware, banda jakkan ci har ta na so ta aure ka" "bar banzar" inji Hafiz. Karaf kan kunnen Saudah, tazo ta zauna kusa da kujerar Hafiz, tace "Anything for u" mikewa tayi ta ja hannun shi, shi ko sai binta yake, wani daki ta ja shi. Anas ko sai babbake wa yakeyi da daria. Bayana Wata 3 Kai ya banga gilmawar mutuniyar taka ba, Hafiz yace ga Maryam chan bari in kirata, "Maryam" tazo tace "sannu, baka ga Aunty Sauda ba ko?tana Gida Mummy ta rufeta, wai tayi Ciki kuma kaine ka mata cikin" wani irin Ashar Hafiz ya lailayo, yace "na ma uwar ta ciki? A gidan uban wa? Da ke da saudan da Uwarku food is ready kun kwashi kan--- Anas yayi saurin taran numfashin shi, yace "Haba my man, kaga ka fara janyo hankalin mutanen nan, yanzu za suyi mana caaaa, nan ne Maman Sauda tazo, ta sassauta murya don bata son mutane su ji su, tace "Hafiz, zo mu shiga daga ciki, akwai magana" da kyar Anas ya ja Hafiz cikin dakin. Maman Sauda ta fara magana, tace "Hafiz, dama jira nake kazo kano, don na san zakazo, Sauda na dauke da ciki wata 3, tace cikin kuma naka ne, Hafiz ya zaburo yace "bangane ciki na bane? Ni kadai nayi hulda da ita, ni so daya na taba hurda da ita, so taje ta nemo uban cikin ta ba ni ba" Maman sauda tace "aa Hafiz, kar kace haka, Allah ya jarabci sauda da son ka, tunda ta fara ganin ka ta kilace kanta don kai, kuma ta tabbatar min da cewa cikin ka ne" Hafiz yace ba fa zam yarda ba, yarinya taje tayi ciki zaa ce ni na mata?" Mamar Sauda tace "to ko zaa bari ta haihun ne, sai aje a gwada jini?" Anas yace Sam hakan ba zai faru ba, ai abun be kai ga haka ba, kudi kawai zaa baku ku cire, kai feezo ciro kudi kawai, ka bata ta murje shege, idan aka bari ta haife cikin Yawah go dey, kasala go burst" Hafiz ya danyi wani tunani yace nawa zai isa a cire ciki? Mamar Sauda taji maganar kudi, tace 250,000. Hafiz ba ji komai ba ya rubuta mata Cheque din dubu dari uku. Suka bar gurin, tunda daga ranar be sake waiwayan Food is Ready Restaraunt ba. Abunda ya faru bayan nan; Maman Sauda tayi tayi sauda suje a zubda cikin nan, sauda ta yi k'ememe tace wallahi ba zaa zubar ba, tana son babyn ta, a cewar ta, da an zubar da cikin nan duk wani burin ta na auren Hafiz zai ruguje, Abun da zata haifa kadai ne zai sa Hafiz ya aure ta. Bayan kankanin Lokaci Maman Sauda ta rasu sakamakon ciwon cikin da tayi rana daya, ko kwana bakwai baayi ba Sauda ta saida gidan Abinci suka hada kayan su ita da kanwar ta suka bar garin, suka nufa Wudil wurin dangin baban su, da suka ganta da ciki sai tace ai tayi aure mijin ya rasu, dangin sunyi mamakin auren Sauda ba da sanin su ba, amma ba suyi mamaki sosai ba don sun san cewa uwar su Saudan ba kirki ne da ita ba. Lokacin haihuwar Sauda nayi ta haifi diyar ta mace, Ba su ko kara ganin Hafiz ba ko abokin sa Anas, diya dai taci suna Aneesa, haka Aneesa ta tashi gata nan dai, Sauda ko ba binciken da batayi akan Hafiz ba amma ta kasa gane komai game dashi, ta sa ba dan Kano bane zuwa yake, amma ta kasa gane takamaiman garin da yake, haka ta hakura da binciken shi, har ta manta dashi. Bayan 15 years Aneesa na da shekara16 ta gama Secondary Sch din GGS wudil, don ma mamarta na mata jumping, don Aneesa na da Girman Jiki sosai, idan kaganta zaka zata irin yan matan Jamian nan ne. Aneesa shagwababiyar yarinya ce, ta samu daurin gindin Mamarta da Auntyn ta maryam, acce take kira da Aunty Meemah, sai ahunda takeso akeyi, ta taka duk wanda ya so kawo mata cikas. Sauda na kitchen taji ana kiran "Habib Ibrahim Lema" a TV da sauri ta fito ta k'ura ma Tv ido tana kallon wanda aka kira da COO (Chief Operating Officer) of Lema's Machinery Company. Tsaf ta karance shi, tabbas wannan jinin Hafiz ne Baban Aneesa, Habib na kama da Hafiz Sosai, amma yafi Hafiz komai, ta fada a ranta, ta aiyana ma ranta, ta kudurta a ranta, ta ma kanta alkawarin Auren Habib Ibrahim Lema, ko ta halin k'ak'a don yanzu tafi karfin Hafiz Lema. Asuban Fari ta ma Gidan bokan ta na kan tudu Sammako, ta zaiyane mai bukatun ta, boka yayi daria yace Saude kin debo mai Zafi. Tayi daria tace "ina sane, shiya sa na zo don ka gaya min koma don Abun ya zo min da sauki"yace gaskia ne, nan boka ya zaiyane mata komai game da Habib Lema, da Iyalan sa, Har Hafiz dake lagos kulle sai da aka shaida mata, komai bokan kan tudu ya gaya mata game da Family din Habib Iro Lema. Tayi daria tace lokaci yayi da zan tarwatsa Happy Family din nan, tana dawowa Gida ta shirya yanda zata yi komai tun daga farkon zuwan ta Katsina, ita da diyarta don Meema na makaranta a nan Wudil, Tana zuwa Katsina ta nufi wurin Aikin Aisha Lema, ta samu karbuwa gunta kuwa, toh gashi abu zaizo mata da sauki tunda Hafiz ya dawo, ita da bata sashi cikin list dinta ba, amma tinda har ya dawo, komai zai zo mata a sauk'ak'e zatayi amfani dashi ta cimma burinta. Wannan shine Labarin Hafiz da Saudah, da kuma Musababbin zuwan Sauda Katsina, to ko Allah na bata ikon auren Habib Lema baban Rafeeq? Nidai nace wane ita tayi kishi da Mameen mu Aisha? Ku biyoni don jin yadda za'a kaya. ​Bibilicious Biebee​ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣3⃣ Hafiz ya Sauke Numfashi me nauyi, tunda yazo Office ya kasa tab'uka komai, yana tunanin Zancen su da Sauda na jiya, ya na tsoron ta fito masa ta bayan fage,ya na gudun ta ma 'yan uwan shi wani mugun abun, har ranshi yana shakkun Sauda, be gama tunanin shi ba ta turo k'ofa, da Sallama, firgigit ya amsa, zama tayi a kujerar da ke fuskantan shi, tace "Good Morning Baban Aneesa, da fatan kayi baccin da ka dade bakayi ba" Hafiz yace "Sauda, ki bar wannan maganan, i'll pay u ko nawa kike so, just disappear from our lives" tace "sam, hakan ba zai faru ba, Dole ka dau responsibilityn diyar ka, dole ka bata rayuwan farin ciki, dole ka inganta mata rayuwar ta, idan ba haka ba, wallahi ba zaka ji da dadi ba" a dan tsorace yace "me zakiyi" ta yi daria tace "zan kaita gaban Yayan ka, ince ga diyar Hafiz lema, shekaru 16 da suka wuce kayi min fyade, ka ga ko zaka koma gidan jiya, yanuwan ka za su kara tsanan ka, su tsangwame diyar ka, niko ina iya hallaka duk wanda zai tsangwami diyata ko yayi gigin kiranta da Shegiya". Zufa ya shiga keto ma Hafiz, ba zai so Sauda ta tona mai asiri ba, yana tsoron Sauda ta ma Yanuwan shi wani mugun abu, jikin shi duk yayi sanyi, ya karaya sosai. Hafiz ya ja goron numfashi, yace "Sauda, ni zan aure ki, muyi rayuwar mu da diyar mu tare ba tare da kowa ya san diyata bace, Muyu aure Sauda please" ta fashe da wani mugun daria tace "Hafiz, na fi karfin ka, Wallahi ni ba tsarar ka bace yanzu, yayin ka ya riga da ya wuce, ni Habib Lema nake son aure" Hafiz yace "wai Sauda mesa kike haka ne? Bawan Allahn nan be miki komai ba" ta mik'e tace shikenan, tunda kaki yarda da deal din da na maka offering, bari inje in sanar da su gaskian lamarin, barin fara da uwar dakinku Aisha Lema, tana cikin Office ma yanzu haka" Cikin zafin nama ya damk'ota yace "aa dan Allah Sauda, kar ki min haka" cikin daga murya tace "ka sake ni" a hankali yace "OK, i will do what you want" tayi murmushin cin nasara tace yauwa ko kai fa, zama tayi tana mai duban shi cikin yanayi na yaudara, ta ciro wani kullin takkarda daga cikin jakkarta ta mik'a mishi, tace "ka sama yayan ka a abinci ko abun sha, make sure ya ci ko ya sha" ya kalleta cikin rashin fahimta, tace Amsa mana ko kana tunanin zan yi poisoning din shi ne? Son shi fa nakeyi, idan ya mutu ya zai aureni? Ba zan taba kashe shi ba coz ina sonshi, so cire wannan tunanin a kanka" ya amsa yace "Sauda, i dont want anyone to get hurt" ta mike ta dauki jakarta tayi hanyar fita, har ta kai bakin k'ofa ta tsaya ta dan kallo shi, tace "noone is getting hurt, i promise". Haka Hafiz ya dinga juya maganin nan, ya na sak'e sak'e a ranshi. Daily Tea din da Alhaji Habib ke sha da daddare Mami ta kawo mai, yana karatun Jarida, yace "thank u Shatu na, u ar d best" tayi daria, tace "kafin a min amarya ko?" yayi daria yace "ke kinsan ba wata bayan ke" tace "ahhh bansani ba" ta mik'e tace bari inje in dafa ma Rafeeq ko indomie ce, nasan Rafee'ah ba zata dafa mai ba" "Indomie kuma? Ba abinci ne? tace "kasan yau Taliya akayi" "Assha, ni wannan abu na Rafeeq bangane mai ba, zai ci indomie amma ba zai ci Taliya ba? Toh meye maraban Dambe da Fada?" tayi daria tace ai kai ka shagwaba shi haka" yayi daria yace barin min first Son dina" tayi daria ta shige kicin". Hafiz ya shigo da Sallama, ya zauna tare da gaida Yayan shi, Yaya Habib yace "Oga Hafiz, ya aikin yau?" yace "Alhamdulilah yaya, Tea zaka sha? Yace eh, as usual, ai nafi 20years ina shan tea duk dare" Hafiz yace "haka ne, nima barin dauko cup inzo mu sha" ya mik'e don zuwa kitchen, ya samu Opportunity ba zai yi watsi da hakan ba, a kitchen ya iske Aishatu, yace ahh Mami Abinci kikeyi?" tace Hafiz an shigo? Wallahi dan rigimar nan nake dafa ma indomie kafin ya shigo gidan" Hafiz yayi daria yace "dan Zaid dan rigima, ina baby na?" tace "tana daki, tana sanaar ta, kasan in ta dauki wayar ta" yace na ma kusa chanza mata waya, Iphone6s, tayi chatting din da kyau" tayi daria yace "ina mugs dinnan nima yau zan bi yaya in sha Shayi?" tace Shayin Ibada,tare da miko mai Kofin tangaran". Ya faki idanun yayan shi da yake ta duba jarida ya juye maganin nan tas, ya tsiyaya ruwan zafi cikin kofin, yace yaya "bismillah" wai Hafiz kai ka zuba min tea din? Ai da ka bari Maminsu ta zo ta zuba min" yace "no yaya bakomai", shima ya tsiyaya ya zauna suna shan shayi suna Fira. Asuban ci ta ma Garin Jigawa gun bokan na kan tudu, kasancewar yau Weekend: Bayan ta gama ma boka kirarin da ta saba mishi, tace " na kan tudu aure zanyi" ya kalleta yayi daria yace "naga hakan saude" tace "ai ni nasan akwai nasara, abunda nake so da kai na kan tudu, bana son a samu mishkila, kar ko ya tambayi dalilin ko ba'asin auren nan, kar kowa yace don me, inshort a rufe ma kowa baki kan Auren nan" daria ya tuntsure da, yace "an gama" yayi yan tsubbace tsubbacen shi yace komai daidai ne" ta ciro kudi masu yawa ta dire mishi tare da yin godia. Hankalin Hafiz ya dan kwanta don yaga kwana biyu har sun wuce ba abunda ya samu Yaya Habib, tabbas kam Sauda ba wani mugun abun zata ma yaya ba. Ji Yayi kawai ya na son zuwa Office din da matar shi ke aiki, Zuciyar shi na tunzura shi, yace da Driver "mu tafi Office din Madam" Direba Yayi mamakin Umarnin Alhaji, amma be tanka ba yayi Ofishin Madam for the first time da Alhaji. Alhaji Habib ya fita ya nufi cikin Office din ba tare da yasan me zaiyi a ciki ba, yayi knocking bakin k'ofar Secretary, Sauda da ke ciki tace "yes come in" Alhaji Habib ya tura kofa tare da Sallama. Zurum Sauda ta mik'e tsaye, gabanta ya yanke ya fadi, Duk yanda take zaton Alhaji Habib lema, ya wuce tunannin ta, yayi ne ta ko wani fanni, Kwarjinin shi ya cika mata fuska, shima kallonta yake yi da murmushi a kan fuskar shi, lokaci guda ya ji ya kamu da son ta, Sai da ta daidaita natsuwan ta da yaudarariyan murya tace "Welcom sir, i'll tell the Director You are here" cikin sark'ewar Murya Alhaji Habib yace "no i'm here for you" murmushi tayi ta gefen kumatu don ta san tunda ya sha maganin nan dole zai zo neman ta. Tace sit please, ba tare da jin komai ba ya zauna suka dan fara magana, har ya mata maganan aure, ba da bata lokaci ba ta amince mai. "Sauda ga wannan files din ki shigar da shi cikin documents din-- bata rufe baki ba idon ta ya kai kan mijinta dake zaune yana ta kyalkyale daria shida Secretary. Shima ya dago ya kalleta da murmushi "Shatou nah" tace "Habibi what a suprise, what are u doing here? Yace "gani nan dai, har nayi gamo" tayi daria tace gamo kuma? Da mene? Ba tare da yaji dar ba yace "da matar aure" dammm gaban Mami Aisha ya buga, firgici da tsoro suka baiyana a fuskar ta, ta zaro idanuwa tare da dafe kirji tace "a ina?" yace "a nan, Secretary dinki Sauda" take firgici da tsoron fuskan ta ya koma murmushi tace "ai sauda na da kirki, Allah ya tabbatar da Alheri" Wani shuumin murmushi Sauda ta saki. Bayan Wata Daya Abu kamar wasa, Yau ake daura Auren Alhaji Habib Lema da Amaryar sa Sauda Ahmad. Zaid da Matarsa sunzo tun shekaran jiya,Manyan mutane daga wurare daban daban sun hallara, har yau ba wanda ya daga kai ya ce don me Habib zaiyi aure? Ba abun da ya damu kowa da bikin nan, Rafeeq ko har Dinner ya hada ma Baban shi. Muje zuwa ​Bibilicious Biebee​ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣4⃣ Zaman Lafiya akeyi a gidan Alhaji Habib Lema, Har yau Amarya Sauda na nan a matsayin Secretary na Mami Aisha, da Mami tayi maganan a chanza mata wurin aiki tace "aa, ita dai a barta nan don ta saba, haka mijin su ya barsu don yana jin dadin yanda matan shi suka hade kansu. Hafiz ma girma yake basu duka, ba za ka ta bacewa sun san juna shi da Sauda ba, don da ga gaisuwa ba abunda ke hada su, Aneesa kuwa in kaga tayi wani abu sai ka rantse da Allah ita ce diyar Habib Lema ba Rafee'ah ba. Rafeeq kuwa be da matsala, idan ya shigo gidan be da aikin yi sai tsokanan Rafee'ah da Aneesa fada.. Bayan Wata 2 (Bakin Rana) Gidan Shiru kamar ba kowa a ciki, Rafee'ah na Kaduna Gidan Uncle Zaid, taje taya Aunty Safiyya zama don ta na da juna biyu, kasancewar hutu, Aneesa na BUK wurin Aunty Maryam, Rafeeq na chan suna flexing da su Maalesh, Hafiz da Alhaji Habib sunje wani Bussiness trip . Sauda ta kirashi a waya tace " Alhaji ya Lagos? Yace "Ohh, banso kika kira ba, coz suprise nake so na muku, sai dai kawai ku ganmu, yanzu ma in less than 2hrs zamu shigo katsina" daria tayi cikin salon yaudara tace "kace yau da mun sha Suprise" yace "ina Shatou na?" ranta ya sosu, ta tsani taji yace "Shatou din shi" gashi shi be jin komai gaban kowa haka yake ce mata, zai sani, itama zata sani, don kawai ta barsu suyi enjoying time dinsu ne for the main time kafin ta fara operation dinta, ta daure dai tace "ni dai duk yau ban ganta ba, k'ila ta fita ko kuma tana daki" yace "to ki dai sanar mata da zuwan mu" ta murguda baki kamar yana ganinta tace toh sai kun kar'iso." Dakin Mami Aisha ta shiga da Sallama, tana zaune kan gado tana latse laptop dinta, ta amsa mata cikin sakin fuska, tace "Sauda kin tashi lafiya?" "lafiya lao Yaya Aisha" suka yi shiru, har saudah zata gaya mata dawowan Alhaji sai wata zuciyar tace kar ki gaya mata, sak'esak'en da ta jima ta nayi ya fado ranta, ta tambayi zuciyar ta "to ko damar ce ta samu yanzu? Bari inyi amfani da damar nan" ta mik'e da sauri tace "bari in dan hada mana Sobo" Mami Aisha tace kamar kin san ina marudin shan Zobon ki. tace "karki damu i wont take long". Ta shiga dakinta da sauri, tana sak'esak'en abun yi, ta yanke hukuncin kiran Mak'ale, ringing daya biyu ya daga, cikin muryan yan iska yace " Hello Matar lema ya akayi ne?" tace "mak'ale kana ina ne?" yace gani wurin Goruba road" tace "donAllah yi sauri kazo akwai aiki" yace "to gani nan karisowa" "yauwa idan kazo ka kirani" Ta gama hada tsobonta tsaf, ta ciro wani k'ulli daga habar zaninta, ta ware, magani ne na gari ta zube shi a cikin cup din ta karkada, sai kuma ta ciro wasu k'wayoyin magani ta zuba a ciki, ta karkada sosai ta dauka ta nufi dakin Mami Aisha. "Lahh har kinyi me?" tayi daria tace "har na hada, ai ba wuya" ta dire mata jug da cup din, Mami tace "nagode sosai" tace "haba ai bakomi bari inje in daura sanwan rana" ba jira ta tsiyaya sobon a kofi ta sha, ta kara tsiyaya wa ta shanye, ya cigaba da aikin ta a kan computer. Saude da ke Labe bakin k'ofa ta daka tsalle ta na murnan ta sha, da sauri ta koma dakin ta ta kira Mak'ale tace "wai ya? Kana ina? Yace wallahi gani nan bakin gate dinku yanzu nake shirin kiran ki" tace "toh bari in fito in shigo da kai" ta yafa mayafi ta fita da kudi a hannu. "Baba ina kwana?" Sauda ta gaida baba mai gadi, Cike da faraa da rawan jiki ya amsa da "Mun tashi Lafiya Hajia?" tace "Alhamdulilah, dama dan Ganyen Latas (lettuce) ke so ka siyo min" yace "toh toh ba matsala, barin samo yaro ya siyo don ba a bar gate din haka ba ba kowa" "aa baba kai zaka je ka siyo, sauri nakeyi" tace a dan fusace, ya danyi shiru sai yace "to, barin in yi sauri in je" nan ta tsaya har sai data ga ficewan shi, ta lek'a taga yayi nisa. Ta hango motar mak'ale daga nesa ta kira shi a waya yace "hello baby?" tace ka shigo mak'ale" yace "toh gani nan". Tare suka shiga cikin gidan, parlo ta tsayar dashi tace ina zuwa, lek'awa dakin Aishatu tayi taga tayi daidai kan Gado tana sharar bacci. Murmushi Sauda tayi, ta janyo laptop din tayi shut down, ta maida cikin jakkar ta ajiye kan side drawer, ta kwashi sobon ta da cup ta fita dashi, ta dawo ta dinga bubbuga Mami Aisha, amma ko shurawa batayi ba, kamar matatta haka take kwance. Saude ta danyi ihu taga ko zai tada Aishatu, amma ko ta motsa, Sauda ta saki murmushi tace things will go as planned. Bayan Minti Talatin(30 mins Later) Bakin Gate Hafiz ya dinga Horn, ba alamun Baba mai gadi, to ko ina yaje? inji Alh Habib, daidai nan Rafeeq ya danno motar shi kwanar Gidan, ya k'araso, Ganin Motar Uncle Hafiz tsaye ya sa shi fitowa daga nashi motar, zuwa yayi ya k'wank'was kofar side din Uncle Hafiz, yayi winning "Sannun ku da zuwa Uncle Hafiz, Daddy Sannu ya hanya? Bamu san yau zaku dawo ba" Suka amsa mishi gaisuwan su, Uncle Hafiz yace "mu kam Rafeeq bude man gate dinnan, Bansan inda Baba yaje ba" Rafeeq ya kalli Gate din yace "to ko ina yaje? Its unlike him" ya karasa tare da shiga gidan don bude Gate, Uncle Hafiz ya shigo da motar sa, Rafeeq ma yaje ya shigo da tasa. Sauda na jin dirin motar su ta fara tsalle, ta gyara zaman kan kujera tarw da rafka Uban tagumi hannu bibbiyu. A tare su 3 suka shigo parlorn, Alhaji Habib na ba Rafeeq labarin Bussiness trip din su, suka shiga da Sallama, Ta dago ta amsa a sanyaye, Sannun ku da zuwa Alhaji, Hafiz sannu" "sannu ya gidan? Rafeeq yace "Auntyn mu lafia naganki haka?, u look disturbed" tace "Rafeeq, wallahi Mami ce naji ta shiru, tana daki tun da na tashi, na kwankwasa na kwankwasa shiru, na zata ma ta fita ne amma baba maigadi ya bani tabbacin kai kadai ka fita yau" Rafeeq yace "toufa, its unlike her baccin Safe, This is just 12:30" Sauda tace "nima dai haka nagani" Hafiz maybe she needed the sleep, shes just sleeping" Alhaji Habib da yaji Hankalin shi ya ki kwanciya, yace "kaii Rafeeq, je ka tado ta, Azahar ma ta kusa" Rafeeq ya haye sama, Sauda ta cigaba da cewa "tun dazun da mukayi waya da kai na lek'a don in gaya mata dawowan kuamma shiru na jita wallahi". K'wank'wan "Mami kina ciki?", ya murda k'ofan sai dai damk'e ya jita, yace "mammy, ki bude Rafeeq ne, ko duk baccin ne haka? "Mammy mana, ki bude Daddy ya dawo" nan ma shiru, duk ya rude ya shiga k'wankwasa kofar iya karfin shi. Alhaji Habib ya dan daga murya yace "Rafeeq Har yanzu ba ta bude ba?" daga sama Rafeeq yace "Daddy ba ma ta magana, kuma kofar is Jammed" da Sauri Alhaji Habib ya mik'e ya hau Saman, su Hafiz suka rufa mai baya. Shima knocking ya fara yana cewa "Shatou na, kina ciki? Are you okay" Shatou taso ki bude mana k'ofa" Sama sama sukaji a na magana, da suka kasa kunne sukaji muryan namiji ne na cewa, "Mun shiga 3, Aisha ki tashi, tashi maigidan ki ya dawo, Haba Aisha duk gajiyan ne, ai ya kamata ki tashi daga baccin nan haka, ki tashi ki nemo min hanyar fita" Rudani da firgici ya ziyarci zuciyar Alhaji Habib, kirjin shi kamar ya tsago daga rigar shi ya fado don tsoro, hannu ya sa ya toshe bakin shi don wani kuka da yaji ya zo mai, yana k'okarin lalibo adduar "Innalillahi wai inna illaihir raji'un" "Allahumma arjirni fi museebati wa akhlifni khairin minha. Hafiz kuwa take Ran shi ya bashi wannan makircin Sauda ne, ya kai duban shi ga Sauda yana mata kallon tuhuma, da ta lura da kallon da Hafiz ke mata, ta girgiza kanta alamun ba ruwan ta, tayi saurin kawar da kanta daga duban shi. Rafeeq ko da be fahimci komai ba ya cigaba da k'wank'wasa kofar, "Mami na Open up please, you are making us worried" ji yayi an taba k'ofar, ya matsa baya yana murmushi ya kalli Daddyn shi, yace "Dad, she's opening up, she's fine". Bawan da yace da shi komai, sai k'ofar da suka tsura wa ido. Mak'ale na cire key ya murda kofar ya danna a guje har yana buge Alhaji Habib da ke kan hanyar shi, duk suka bishi da ido, Hafiz yayi yunkurin binshi da gudu Alhaji Habib yayi karfin halin rik'o Hafiz, ya girgiza mai kai alamun rabu da shi, Rafeeq cike da alamun tambaya yace "Daddy waye shi?" Alhaji Habib be ce komai ba face hawayen da ke zuba daga idanun shi, ya matsar da Rafeeq gefe yaym shiga dakin Aishatu, burin shi ya ga Aisha ta ce mishi "mafarki yake, this is not true" don so yake ya tashi daga wannan mummunan baccin da yake, Hafiz ma ya bi bayan shi, sauda ma ta rufa musu baya suka kutsa dakin Mami Aisha. Rafeeq da shifa kwatakwata k'wak'walrshi ta dode, be gane komai ya bi su a baya. Hafiz yayi saurin dauke kanshi daga duban Aisha, Sauda kuwa daura hanayenta tayi guda biyu a kai, Alhaji Habib ya zame k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai, Rafeeq da ke tsaye kamar mutum-mutumi (Robot) don duk wasu daurar da ke aiki a k'wak'walwar shi ta dauke dif, sakamakon abun da ya gani. Mahaifiyar shi ce Kwance Zindir ba kaya haihuwar Uwarta. Rafeeq da karfi yace "Mammmmmmmiiiiiiiiiiiiiiiyy" firgigigit Mamy Aisha ta tashi. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣5⃣ Da karfi Mami Aisha tace "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, ne zan gani haka?" ta fada tare da neman abun da zata kare jikinta dashi, da sauri Sauda ta bude Closet dinta ta ciro mata zani da hijab ta bata, ta amsa da sauri ta suturta jikin ta. Ta bisu da kallo daya bayan daya, ta fashe da kuka, me ya faru dani? Aljannu suka shige ni ko? Suka min tunbur? Kumin magana" Sauda ta fara kukan munafurci tace haba "yaya, ya zaki ce haka? Kwarto fa kika kawo cikin daki, amma yanzu kina neman cema na ba kisan me kikayi ba? Zurum ta zube a kasa, don kafafuwan ta sun gaza daukar ta, a ranta tace kwarto? Ta dago taga yanda Alhaji Habib ke zubar da hawaye da sauri ta rarrafa gurin shi, ta rik'o hannun shi, Kamar wanda shocking ya taba, yayi saurin janye hannu shi tare da mik'ewa, ya nuna ta da yatsa yana kuka, "Aisha, kin cuceni, kin haince ni, kin ci amana ta, was it hard for you to wait for me?" kuka take yi sosai, ta kasa cewa komai sai girgiza kanta da takeyi, da kyar tace "kayi hakuri Habibullah" wannan magana da tayi ne ya sa shi tabbatar da zance, shikenan Aisha ta ci amanar shi, ta kawo kwarto har cikin dakin ta da tsakar rana, ba tsoron Allah. Da kyar yace "Aisha na sake ki saki daya" ya fice daga dakin, Sauda ta hau kururuwa ta bishi a baya "haba Alhaji be kamata kayi haka ba, be kamata ka yanke hukunci kana bacci ba, Alhaji ka maidota yanzu pls" tsawa ya daka mata yace "Saudat, kina so ki bita kenan? Da sauri tayi shiru kar daga neman kiba ta nemo rama. Ba ta ji dadin saki dayan da Alhaji ya mata ba, duk a zaton ta saki 3 zai mata, amna dayan ma ba laifi, zata tabbatar Aisha ba ta dawo gidan ba har abada. Hafiz ya kalleta cike da tausayi tabbas wannan aikin Sauda ne ya rasa me zaice shima ya fita ya rage daga Rafeeq sai Mami, har yanzu tana nan duk'e inda Habib ya barta, Rafeeq ko na nan tsaye, ya kasa motsi, abubuwan ke dawo mishi kai, ya kasa yarda da Abun da idon shi yagani, da ya runtse ido Mami yake gani zindir, Mami ta dago kai a hankali ta sauke su kan Rafeeq, da jijiyoyin kanshi sun mimike, fuskar nan tayi Ja, idanuwan sa ma sun kada sunyi jazir, Mami bata damu da halin da take ciki ba ta mike ta nufo Rafeeq, yanayin da ta ganshi ya firgita ta matuk'a, ba ta taba ganin Rafeeq a haka ba. Hannu ta cire zata riko shi don ta zaunar da shi kan gado, da sauri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu, yace "dont touch me, Kar ki taba ni" cike da mamaki ta kalle shi, tsana da kiyayya taga ni kwance kan fuskar Rafeeq, yace "bana so in sake ganinki" baki na rawa tace "Rafeeee--q" yace "Wallahi na tsane ki" kafin ya sake wani magana yaji wani lafiyayyen mari tassss a fuska, hannu ya sa ya dafe kuncin sa, ya na dagowa ya sake ji a kara sakar mishi da wani marin da ya fi na dazu, duk a zaton shi mamin sa ce ke marin shi, dagowa yayi don sake yab'a mata wasu bak'aken maganganu, sai ya ga akasin haka, Hannun Mami ya gani rik'e da hannun Uncle Zaid da ke niyyar sake marin Rafeeq karo na 3, ta tare shi ta hanyar rike hannun. Huci Zaid keyi, ya nuna Rafeeq da hannu "How dare you Rafeeq?" kasan da wanda kake magana? Rafeeq be bi takan Zaid ba ya kalli mami ido cikin ido, yace " i wish i had a different mother" ya juya ya fice. Cikin zafin rai Zaid yace" Rafeeq Habib Lema, come back here" Mami tayi saurin cewa "Zaid, laifi na ne, na mishi babban laifi, na ma kowa babban laifi, i dont know what exactly happened but i know i didnt do what they are accusing me of'' Zaid yace " Mami wai meke faruwa ne? Na rasa ganewa, tun kafin in shigo katsina na dinga neman layin ki, be shiga, na shigo gida na ga alamun ba lafiya, don Hafiz na k'asa na kuka, na tambaye shi me ya faru ya kasa magana, ban bi takan kowa ba na hayo sama gunki, na iske wannan mugun kalamai da Rafeeq ke fada miki, ina zargin Rafeeq koya fara Shaye shaye" Mami na kuka sosai tace "ko daya Zaid, Rafeeq na da hujjan yin hakan, kaji kaji abunda na sani" "inalillahi wa ina ilaihir rajiun" inji Zaid, Mami har tayi nadaman gaya ma zaid, a zatonta shima yarda zaiyi da zargin da ake mata na kawo kwarto cikin gida. Tace Zaid "Wallahi ban san komai game da hakan ba, ni dai kaji yanda na tashi na tsinci kaina" Zaid yace "yi shiru mami kar kiyi zunubi, na san halinki,Wallahi akwai wata k'ulalla, akwai wata a kasa, tabbas wannan wani irin tuggu ne aka shirya miki, to wa??" Mami tace "Allahu Aalam, Zaid ka saurareni da kyau, wannan boyayyen alamari ne da ba wanda yasani sai Allah, Habib ya sake ni, i wont be there to protect my children, whoever came for me is coming for my kids, is defintely coming to hunt my Childeren down, sunci nasara a kaina, Zaid kar su ci nasara a kan 'ya'ya na, Zaid i want u to protect them" Zaid na kuka yace "Mami yaya ya yi saurin yanke hukunci, baya cikin hayyacin shi ne sanda ya sakeki, mu bari ya sauko, sai ayi magana nasan gaskia zata fito, ya maido ki dakin ki. Murmushin takaici tayi, tace " Zaid kenan, yanzu dai bawanan ba, Rafeeq yayi fushi sosai, fushin da be taba yin irin shi ba, ina tsoron kar zuciyya ta kai shi yin aikin da na sani, ina tsoron zuciyar Rafeeq, Zaid ka bishi donAllah, Ka kula min da d'a na" kamar wanda aka tsunkula ya tashi zumbur, don ya mance halin da ya ga Rafeeq dazun. Yace "Mami ki jirani i'll be back and everything is going to be Alright" a hankali tace "Go Zaid, Go" be sake magana ba ya fice da Sauri. Matakala bibbiyu, uku uku Zaid ya dinga hadawa ya sauka k'asa, sai dai ga mamakin shi Wangale yaga gate, ya duba gefe ya ga ba motar Rafeeq da yagani Parke a gefe hankalin shi ya daga, daidai nan sai ga Baba Maigadi ya shigo gidan da Cefane da Lettuce din da Sauda ta aike shi a hannu, Zaid yace "baba ina Rafeeq" Baba yace " Zaid yanzun nan na ga motar shi ta wuce fiyauu, na tsorata da yanda naga yana tuk'i, da alamu sauri yake" Hankalin Zaid ya tashi, ya na tafiya ya na magana yace "akwai matsala a gidan nan baba, matsala babba" Zaid ya fada motar sa ya bi bayan Rafeeq baba Maigadi ya mishi Allah ya kiyaye. Zaid na fita itama ta hada kayan ta, kana ganinta kasan hankalin ta a tashe yake, duk ta dauki abubuwan buk'ata, ta sauko k'asa ta bude motar ta da ta siya da kudinta ta tura Akwatin ta, da sauri Baba Maigadi ya nufo gunta, "Hajia Lafia? Tafia zakiyi? Ince dai lafiya fuskar ki tayi Jaa, kuka kikeyi ne?" da kyar tace mishi "Baba, Habib ya sake ni" Salati maigadi ya saki, yau mun shiga uku, shi habibun ya sake ki?" me yayi zafi haka?" Murmushi tayi tace baba barin tafi, don Allah a kula da su Rafeeq, akwai wata Musiba da ta shigo gidan nan" Baba da ya fara kwallah yace InshaAllah, Allah shi yaye ya sa ku daidai ta da Alhaji ya maidoki dakin ki, don Wallahi ba shi kadai yayi rashi ba muma munyi". Tace nagode ta bude motar ta ta shige ta bar Haraban Gidan Habib Lema. Gudun da Rafeeq keyi na tashin hankali ne, kamar zai buge mutane, Allah dai ya cigaba da kare shi, don be ganin gabanshi shi dai yasan tuk'i yake, ba tare da yasan inda ya dosa ba, Kiran Zaid ya shigo wayar sa, amma yanda sauran kiran suka shigo suka yanke haka wannan ma ya katse, Zaid ya damu matuk'a da kyar ya kira Maalesh ya ji in gidan su Rafeeq ya nufo Maalesh ya bashi tabbacin tun wurin 11 suka rabu. Zaid gudu yake yana duba hagu ko dama inda zai ga Rafeeq, kawai dai ya yanke hukuncin bin Hanyar Jamia ta wurin Ring road, speed ya k'ara, ba jimawa kadan Zaid ya hango motar Rafeeq daga chan nesa, gudu yake kamar dan tseran mota, hamdala Zaid yayi ya k'ara gudun motar shi, horn yake ta mai amma yak'i tsayawa, ta mudubin motar Rafeeq ya gane motar Uncle Z, shima ya kara gudun motar shi, Shima Zaid ya kara na shi, Gudun da sukeyi yafi kama da na masu race, ba me niyyan tsayawa, Burin Zaid ya tarar da Rafeeq, shi ko be da wani burin da ya wuce ya ta tafia har sai ya manta da wani damuwar shi. Zaid ya taka motar nan da karfi, har Allah ya bashi ikon shan gaban motar Rafeeq, Ran Rafeeq ya baci, niyyan shi ya cigaba da tuk'in har ya buge motar Zaid, amma zuciyar shi ba zai bari ba, Uncle Zaid ne fa a motar, mutumin da yake so sosai, ba zai so ya buge shi ba, be da wani zabin da ya wuce ya tsaya da motar sa. "Aishatu lafiya? Kinzo kin tasamu gaba kina ta kuka, wani abun ne ya faru?" Baba Tijjani ne mahaifin Mamin su Rafeeq ne ke mata tambayar nan, duk ya tsufa sosai, mamar tace "haba mama na, idan wani abu ya faru ki gaya mana, ba wai ki tasamu da kuka ba" da k'yar ta tsagaita kukan ta ta labarta musu iyakar abun da tasani, Sallalami da Salati suka fara, mamarta harda kuka, Baba Tijjani yayi shiru yana nazari, chan yace Aishatu, na san wa na haifa, na yarda dake, ban haife ki don ki zama ma zinaciya ba, da mijin ki da 'yaranki, tabbas idan aka duba wannan lamari zaa ga shiri ne a dunkule sai mai hankali zai gane" Mamar Mami tace "amma shi kuma habib harda Saki? Baba Tj yace "sharri ne dai don a hadata da mijinta, ni ban ga laifin Habib ba, don ko ya samu duk wani evidence da ya ke bukata, ko wani namiji haka zaiyi, amma ina da tabbacin da Habib ya kwantar da hankalin shi ya duba lamarin nan zai gano gaskia, tashi ki shiga daki Allah shi zai saka miki" tace baba ina so in bar gidan nan, don na san Zaid ba zai taba bari na a nan ba, duk yanda zaiyi sai ya maida ni gidan Yayan shi, bana son hakan ya faru na fiso Habib ya gano gaskia da kanshi kuma ina bukatar lokaci da zan huta in yi idda na, ina neman izinin ka na barin garin" "Aa Aishatu, ba zan bari kiyi zaman kanki ba" Mama tace "ta je Malumfashi gurin Inna mana" Baba Tijjani yace "kina iya zama malumfashi gun kanwara mamarki?" tace "Eh Baba, idan ka min izini yanzun zan tafi" yayi shiru yace "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare ki kula da kanki". Ganin Rafeew be da niyyar fitowa daga motar shi ne ya sa Zaid fita da sauri ya nufe shi, har ya tako gaban motar Rafeeq, ya bude gaban motar, ya sa hannu ya fito da Rafeeq, ya kalle shi, shima ya tsorata da yanayin Rafeeq, fuskar nan ta yi ja, idanuwan nan sun kada sunyi jazir, ga digon hawaye ko k'wallah, jijiyoyin kanshi sun mik'e. Zaid ya tausaya ma Rafeeq sosai yace "Rafeeq" Ko kallon shi Rafeeq beyi ba, Zaid ya kara cewa "Rafeeq kayi hakuri, kayi kuka, cry it all out, kar ka barshi a ranka, pour your heart out, i know this is hard for you, let it flow Rafeeq, let it flow" Da sauri ya rungume Zaid sosai, sai a sannan ya samu Hawaye suka fito daga idanuwan shi, sai a sannan ya fara kuka a hankali yace "Uncle Zaid, Help me" _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇?‍ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) *Assalamu Alaikum* _Da farko zan fara da nuna godiata da jin dadin yadda kuke biye dani a cikin_ _littafina na *KE ALHERI CE*_ _Nagode sosai Allah ya saka maku da alkhairi yabarmu tare._ _Kamar yarda korefe korefe sukayi yawa akan page 23 na littafina masu yi a grps da masu biyoni prvt duk ina son inyi clearing mind dinku daga abinda kuke ganin na aikata da wasunku suka daukeshi daidai da kuma wadanda suka dauke shi ba daidai ba. (Yin daidai sai ubangijinmu cos_ _dukkanmu tara muke bamu cika goma ba_) _Kamar yadda kuka sani duk wadda tabi littafina daga page one zuwa yanzu tasan inda littafina ya dosa.. Kamar yarda kuka karanta kuka gani there is darkness in *Rafeeq's* life wanda yake saka shi yin duk wani abu da wasu dabiu da ba halinshi bane a da, wanda har na gangaro zuwa page 24 inda kowa ya gane dalilin shigar *Rafeeq* wannan yanayin da yake na yanzu._ _Kaidi irin na mata( *Wanda ko shaidan tsoronsu yake*) ya kuma hadu da kaidi na kishiya mara imani babu abinda baya janyowa.. abinda ya faru da Mami is well planned by Saude so ko sirikinta ne zai iya ganinta a yanayin data samu kanta_ _balle kuma dan cikinta sbd dama burinta ta kafa shaida mai kyau ta ido sbd idan dunia zata taru tana gaya ma *Rafeeq* abinda_ _mahaifiyarshi tayi bazai taba yarda ba kamar yarda uncle Zaid da iyayenta basu yarda ba..Saude tayi hakan ne dama don su gani da idonsu su zama shaidar kansu,wanda hakan ya tabi zuciyar Rafeeq har ya_ _haddasa mai duhu da bakin cikin da yake kwana yana tashi dashi kullu yaumun.._ _haka kuma rayuwarshi ta watse ta tarwatse sbd abinda ya gani da idonshi._ *_Kowacce tayi addua Allah ya rabata da muguwar kishiya sbd babu abinda basu iya aikatawa tunda babu Allah a cikin al ammuransu._* _Allah yasa muna fahimta da amfana da darussan rayuwa dake ciki_ *Biebie* luv u loads💖❣💕 Pg2⃣6⃣ Kuka yakeyi kamar karamin yaro harda majina, Uncle Zaid beyi yunkurin hanashi ba, sai da yayi ma ishi kafin ya tsagaita da kukan. Uncle Zaid ya kira Maalesh yace yazo ya iske shi ring road yana jiran shi, kar yazo da mota, baa fi 15mins ba sai gashi, a rude Maalesh ya fito don be san meke faruwa ba yace "guy howfa? Kallo isasshe Rafeeq be ma Maalesh ba, Zaid ya mai alama da yayi shiru. Key din motar shi ya ba Maalesh, ba tare da ya tambayi me zaiyi da key din ba ya shige motar Uncle Zaid, shikuma zaid ya tura Rafeeq cikin motar sa, Zaid ya zauna a mazaunin driver ya ja motar ba me cema danuwan sa k'ala, jefi jefi Rafeeq yake sauke ajiyar zuciya, hanyar gida suka dauka, a hankali Rafeeq yace "please dont take me home" ba musu Zaid ya chanza hanya ya nufa gidan su Maalesh, daidai gidan su Maalesh Zaid ya tsaya yin horn, Rafeeq be jira maigadi yazo ya bude gidan ba ya fita daga motar ya shige Gidansu Maalesh ya nufi side dinshi. Zaid ya girgiza kai ya fito, Maalesh ma ya fito, yace Uncle Zaid me ya faru da Rafeeq ne? Ban taba ganninshi haka ba, da kyar Zaid yace "he is broken" ya sake bashi key din motar shi, yace "je ka kai motar Rafeeq gida ka dawo yanzu" Akwai mutane cikin gidan?" Maalesh yace "aa Mummy taje kaduna, ba kowa" yace key din dakin ka fa? Maalesh yace "akwai daya gun Rafeeq, amma ga wannan incase ya barshi gida" Zaid ya amsa ya nufa cikin Tangamemen Gidan su Maalesh. Be ga Rafeeq ba a kofar dakin, hakan ne ya bashi tabbacin Rafeeq na ciki, ya murda kofa yaji ta rufe, key din da Maalesh ya bashi ya zaro ya bude kofar, tare da shiga da Sallama, chan kusurwa ya ga Rafeeq kwance, be kula shi ba ya shiga toilet yayi Alwala kasancewar lokacin Sallah yayi. Bayan ya idar da Sallah ya zauna kusa da Rafeeq ya janyo hannun shi ya hade da nashi, yace Rafeeq ka saurareni, "Mamin ka ba tayi- da sauri yace kar kayi shaidar zir Uncle Zaid, ni nasan abin da nagani, naga zahiri ba labari aka ban ba" Zaid yace najih Rafeeq, kaga zahiri ba labari aka baka ba, amma shin kagan su suna aikata Zina? Mahaifiyar ka ba ta chanchanci haka daga gareka ba, kar ka mance irin So da K'auna da take maka, Rafe--" Uncle Zaid ya isheni, Wallahi zan bar maka gidan nan, idan kana min maganar ta kana sawa ina k'ara tsanar ta" jimm Zaid yayi, sai ya yi shiru don baiwa Rafeeq Lokaci, ya mik'e yace "bari inje in dawo". Isketa yayi kitchen tana kokarin dafa ma Alhaji Habib Ruwan Zafi, Hafiz yace " Sauda, na san kina da hannu akan abun da ya faru da Aishatu, komai shirin kine ke ki ka k'ulla mata wannan sharrin." tayi wulwul da ido, tace haba Hafiz, me kake cewa? Rashin imani na be kai nan ba, muna zaman lafia da ita me zai sa in neme ta da sharri, ni bansan me ka mayar dani ba, yace "Sauda na san halinki sosai, wallahi nayi bincike nagano gaskia, to zan tona miki asiri wallahi" Sauda tayi daria tace "Hafiz kenan, to barin fito maka da real color dina, idan nice me zakayi? Uban me kake iya yi? Kasan dai halina ko? Ka ka shiga gona ta, idan ka min shishigi zakayi kuka da kanka, kar ka manta Rayuwarka a tafin hannuna yake. I own u, so watchit" ta fice ta barshi tsaye. Bakin gate ya hadu da Maalesh, yace ka kai Motar? "Eh Uncle Zaid" ok ban key dina ni, Maalesh ya nika mishi, yace "Uncle Zaid" Zaid yace ina sane da kai Maalesh, nasan there are millions of questions da kake so kayi, ka jirani ina zuwa, and Rafeeq give him space" Maalesh yace "Sai Ka dawo". Ya shiga ciki Zaid kuma ya fito. Da Zaid ya koma gida be ga Mami ba, hankalin shi ya tashi, ya sauka kasa ya tambayi baba mai gadi yace ko ya ga wucewar ta? Ya bashi tabbacin ya ga ta fita da kaya, da alamu tafia zatayi, da sauri ya shige mota ya nufa gidan Baba Tijjani. A sukwane ya shiga Parlorn, Baba Tj na zaune yana Azkhar, yace Zaid "lafia ka shigo a haka?" yace "baba ina Mami?" cikin mamaki yace wace "mamin? "Ina Aunty Aisha mamar Rafeeq?" Zaid ya dan fada a fusace, Baba Tijjani yace tana gidan ta mana, ce maka tayi zata zo nan? Baba dagaske ba ta nan? Yace "dama Ina maka karya?"Zaid yace "aa baba ba haka nake nufi ba, tabar gida ne na zata nan tayo, kuma wayarta a kashe" yace "aa ba mu ganta ba" Zaid be jira ba ya fita ba tare da ya basu labarin abun da ya faru ba, a ganin shi abun kunya ne suji Yayan shi ya sakar musu diya bayan hallacin da Baba Tijjani ya musu. Mama tace "Alhaji ya ba ka gaya mishi gaskia ba? Yace kinsan halin Zaid, ba zai barta ba, duk inda take sai yaje ya daukota, abar ta ta gama iddan ta, she needs time" tace "Hakane" Hankalin Zaid a tashe Matuk'a, duk inda yasan zai bincike Mami Aisha yaje be ganta ba, ya kira wayarta yafi a irga a kashe, Zafi biyu, ga rashin sanin inda take, ga matsalar Rafeeq, a bayyane yace "Allah kayi mana Agaji" yayi niyyar zuwa gidansu Maalesh don ganin Rafeeq, sai ya fasa don yasan Rafeeq na bukatar lokaci sai kawai ya wuce gida. Hafiz ya sake labarta mai abunda ya faru, Zaid yace "wallahi Hafiz Shiri ne, ban yarda ba, akwai wata manakisa, kuma i promise i wont rest har sai na gano who is behind this na sada shi da hukuma" Hafiz ya danyi jim, so yake ya gaya ma Zaid wacce yake zargi, amma sai ya tuna gargadin da ta mishi dazun, inda take cewa "Hafiz, dont try to bring me down, if i go down, i'll drag you down with me" miyau ya hadiye yace "gaskian ka Zaid, its hard to believe, Allah ya baiyanar da Gaskia cikin sauki" Zaid be ce komai ba saboda yanda Zuciyar sa ke tafasa. Wurin Yayan shi ya hau a sama, ya ci saa shi kadai ke Parlorn, ya shiga da Sallama, har yanzu be bar kukan ba, Zaid ya kalli yayan shi cike da Tausayi, yace "Yaya kaima kuka kakeyi?" Habib Yayi murmushin takaici yace Zaid " kaga abun da uwar dakin ka ta yi min ko?" Zaid cikin bacin rai yace "yaya kaima ka yarda? Haba yaya, wai ba ka san wacece Aisha ba? Shekarun ku nawa da ita? Tun kuruciyart bata kawo gardi gida ba sai yanzu da ta fara tsufa har da diyanta? Haba Yaya kai haka kake baka bincike? Haka fa kamin a baya, dai daga baya kazo kana da nasani, you should have give her a time to explain, am sorry but ka dinga amfani da hankali." Habib yayi shiru yana nazari, magananganun Zaid sun shige shi, daga kallo daya zaka san cewa jikin shi yayi sanyi, amma ya kasa cewa komai, Sauda da ke labe a bakin k'ofa ta ja tsaki, tace wannan Zaid din yana neman bata min shiri, amma da sannu zanyi maganin shi" Tana shiga daki ta kira Boka na kan tudu, ta nemi da ya janye tunanin Aishatu daga kan Habib, Boka yace ba matsala, anyi an gama, tace "yauwa, saura Maganan k'anin nan nashi, Zaid, Boka yace "uhm uhm Sauda, kar ki b'allo ma kanki ruwa, ki rabu da wannan, amma shi kina iya hadawa da kissan ku na mata" tace "to shikenan yanzu dai ka janye min hankalin Alhajin". "Rafeeq be kamata ace kana fadan mugun kalamai kan mahaifiyar ka ba" Maalesh ne ke zancen nan cikin bacin rai, Rafeeq ya kalleshi galala yace "Maalesh, ka min shiru, idan kuma so kake ka nuna min nan Gidan ku ne, sai na tafi na bar maka gidanku yanzu, ba wai ce maka akayi na rasa wurin zuwa bane" Maalesh ya buga tsaki tare da fita ya bar mai dakin don idan ya biye ma Rafeeq zasuyi ba dadi cikin daren nan. Bayan Kwana 3 Gari yayi ma Zaid Zafi, ba inda zai saka ranshi yaji dadi, Gashi ba inda be nemi uwar dakin shi ba labarin ta, Gashi Idan ya ma yayan shi maganar ta sai ya hau masifa don jiya saura kiris Ya mareshi don yace mishi ya kamata ya yi bincike don gano gaskia(Bokan kan tudu yayi aiki kenan) Gashi idan yaje gun Rafeeq don su tautauna kan Mahaifiyar shi sai ya birkice yak'i ko tari, don Zaid ya fara magana har ya gaji Rafeeq ko k'ala ba zai cemar ba haka zai bar Gidansu Maalesh ya koma Gun Yayan shi, nan ma ba wani sauki, sannan kuma ya zagaya duk inda ya san zai ga Mami Aisha amma shiru ba wani dace. Bayan kwana Uku Yau Sunday aka kira Zaid a Office, aka ce ya dawo Kaduna saboda akwai aikin da zaa tura shi Lagos, be da wani zabi da ya wuce ya koma Kaduna, kafin ya bar Katsina sai da yaje Gidan Baba Tj, ya roke shi da ya gaya mai gidajen Yanuwan su da ya ke ganin Mami zataje amma fir yak'i gaya mishi, haka ya bar gidan cikin rashin jin dadi, Gidan su Maalesh ya nufa. Maalesh ya gani tsakar gida yana Basketball, Maalesh ya karaso ya gaida shi, Zaid ya amsa mai cikin sakin fuska ya tambaye shi "Mahmud, ya abokin naka?" Maalesh yace Uncle Zee wlh ba sauki, abun Rafeeq gaba yake kara yi, tun gaisuwan da naji ya maka jiya da Safe, Wallahi har yau ban sake jin yace ko a ba, haka zan gama surutai na ko kallo ban ishe shi ba" Zaid ya jinjina kai, yace Abun Rafeeq sai Addua bari in ganshi". Zaid ya Iske Rafeeq Zaune, kallo daya ya mai ya ga rama da Baki'n da Rafeeq yayi, Zaid ya cire baki ya kira sunan shi cike da tausayawa, Be amsa ba ya juyo ya kalleshi, idon nan har wayau jajir, Ya tsura ma Zaid ido, Zaid yace Rafeeq zan tafi Kaduna yanzu, akwai abun daya da nake so kamin please ba don na isa ba" da Sauri Rafeeq ya tashi yayi hanyar toilet, don baya son zancen da Uncle Zaid ke son mishi, da sauri Zaid ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Rafeeq ka saurareni, Wallahi ba maganar Mami zan maka ba" Rafeeq ya dan dakata don shi a zaton shi maganar Mahaifiyar shi zaa mishi. Zaid ya umurce shi da ya zauna, kamar ba zai zauna ba ya zauna, Zaid yace "Son, Ina so ka koma Gida, zaman ka a gidan aboki ba zaiyuwu ba, kar ka manta ba zaman kanka kake ba, kana da mafada, na baka lokaci don ka dawo daidai, amma abun naka girmama yake, dole ka koma Gida, kaji ko?" Shiru Rafeeq ya mishi, Zaid yace "Rafeeq Habib Lema, kajih ai?" kamar ba zai tanka ba ya gyada mai kai alamun yaji, Zaid yayi murmushi yace "thank you, Rafeeq, zan koma Kaduna yau, there are somethings i need to attend to" Shiru dai Rafeeq ya mishi be ce komai ba, Zaid ya gaji da zaman shi ya tashi yace "to Rafeeq ni na wuce" nan ma be ce mai komai ba, Har Zaid ya kai bakin kofa a hankali Rafeeq yace "Uncle Zaid" da sauri ya juyo yace "naam Rafeeq, me kake so? You need something?" Rafeeq dai yayi shiru kamar bashi ya yi magana yanzu ba, ya rasa me zai ce mai, Zaid dai yayi tsaye yana jiran me zaice mai, amma yaji shiru, da Rafeeq ya rasa me zai ce ma kawun nashi sai ya taka har gaban sa ya rungume shi, Zaid ko ya rungume shi shima, daidai da saukan hawayen Rafeeq, Zaid ya dinga lallashin shi, a hankali Rafeeq yace da Zaid "Please dont tell Rafee'ah.. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣7⃣ Zaid ya dago yace "kar ka damu Rafeeq, Rafee'ah ba za ta sani ba" gyada kai kawai Rafeeq yayi, Zaid yace "akwai wani abun kuma? ya sake girgiza kai Alamun Aa, Zaid yace "toh, na tafi" Rafeeq ya koma kan Gado ya zauna. Zaid ya fice, gun Maalesh ya isa, yace "Mahmud, ni na wuce Kaduna, sai weekends kuma, Nagode sosai, Yau zai koma gida, ka cigaba da kula mun da Rafeeq, zan dinga kiranka ina jin yanda yake" Maalesh yace "Bakomai Uncle Zee, mudai fatan mu Allah ya sa gaskia ta baiyana, Rafeeq ya dawo normal self dinshi, don nafi kowa Affected da yanda Rafeeq yake yanzu" Zaid ya jinjina kai ya chanza zancen yace "In bada na shan Mai?" Maalesh ya sosa kai yana daria, Zaid ya ciro Bandir din dari 200(20000) a Aljihu ya ba Maalesh. Maalesh yayi Godia sosai ya raka Uncle Zaid har mota kafin ya dawo gun Rafeeq. Rafeeq ya kalle shi zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mik'e ya zira takalman shi, ya je gaban Tv inda Maalesh ya ajiye Key din mota ya dauka ya zo ya ba Maalesh, cikin wasa Maalesh yace "kai ni fa ban san iskanci, kurma ka koma ne?" Rafeeq uban Zuciya ya galla mai wata muguwar harara ya wurgar da Key din ya fice daga dakin, Maalesh yace "ikon Allah har yayi fushi? Duk da muke wasa fiye da wannan be ta fushi ba sai yau?" binshi yayi a guje har ya taddo shi, yace haba "R-Lema, wasa ne fa, Gida zakaje ko? Muje" Rafeeq dai be ce komai ba ya zagaya ya shige mota. Gidan su Rafeeq kamar ba mutane, shiru kake ji, Rafeeq ya fito daga motar Maalesh ya bi Haraban Gidan da kallo, komai ya dawo mai sabo, yaji ranshi ya kara jagulewa, part dinshi kawai ya nufa ko cikin gidan be kalla ba, Maalesh yace "R motar Daddy na nan, ba zaka je ka gaida shi ba?" ko kallo Maalesh be ishe Rafeeq ba ya bude dakin shi ya shige, Maalesh ne ya shiga cikin gidan, ya iske Daddy da Saude a parlor suna fira, da alamun ba su da damuwar komai, ya karisa da Sallama, Alhaji Habib ya dago yace "Mahmud ne?" "eh daddy nine ina kwana?" ya amsa mai cikin sakin fuska, "Maalesh ya su maman ka?" inji Sauda yace "suna lafia sunce a gaidaku aunty" A. Habib yace "Mahmud ina abokin ka? Maalesh ya fara sosa kai, yace "yana daki be dan jin dadi ne" Zumbur ya mik'e yace "SubhanAllah barin je inga dan Zaid" ya fita Sauda ta rufa mai baya, duk ranta ba dadi ganin yanda mijinta ya rude don yaji ance Rafeeq be lafia. Sunfi minti uku suna Sallama ba amsa, a zaton su bacvi yakr yi, Maalesh ne ya tura kofar suka shige ciki, ga mamakin su zaune yake idon shi biyu, kallo daya ya musu ya dauke kai, ganin da ya ma Daddyn shi cikin koshin lafia, be da wata damuwa abun ya bashi haushi, wato be damu da abunda matar shi tayi ba kenan? Kwafa yayi a ranshi". Sauda ta dan matso kusa dashi cike da kissa tace "Rafeeq my boy, are u Alright?" Rafeeq ya kawar da kanshi kamar be san da wata halitta tsaye a gun ba, muryar ta ya tuna lokacin da take cewa "Yanzu yaya kwarto kika kawo cikin dakin auren ki?" haka kurum yaji ya tsane ta, be son ganin su duka har Daddyn shi. Alhaji ya matso yace "Rafeeq ka min magana, wani abu ke maka ciwo?" da kyar bakin shi ya motsa yace "donAllah ku fita" don kwata kwata be son ganin su. Ba Gardama Alhaji Habib yace "muje Sauda he wants to be alone " Suka fita suka bar mishi dakin har Maalesh. Wayar shi ya jawo har zai danna kiran Uncle Zaid ya fasa, sai ya tura mishi sakon message "I'm home" kadai ya tura mai, lokacin da sak'on ya isa ga Zaid tuk'i yakeyi, ya bude sak'on yayi murmushi yasan Rafeeq ba zai k'i yin abunda yake so ba, sai ya maida mai Reply da "Nagode". Haka Rayuwar Rafeeq ta kasance cikin k'una da dacin rai, duk ya koma wani iri, ga wata uwar K'asumba ya fara ajiyewa, ba ruwan shi da kowa da komai, har mahaifinshi don ya zame mishi dole ne yake amsa mai magana shima maganar bata wuce "a" ko "aa", Alhaji Habib be jin dadin yanda danshi ke yin dari dari dashi, ya kira kaninshi Zaid ya kaimai kara, Zaid ko saidai ya bada hak'uri yace a tayashi da addua. Hakan ba zai hanashi gobe ya koma dakin Rafeeq din ba, tunda shi ba shiga yakeyi ba, sai a kwana a yini Rafeeq be ce "a" ba, tun Maalesh na damuwa har ya daina damuwa. Hankalin Maalesh ya tashi da ya tuna Jibi zasu koma Makaranta, 2nd Semester Level 400 final Semester dinsu kenan a Jami'ah, ga project ga defence ga wacece, taya Rafeeq zai wuce idan yana haka? Da sauri ya dialing number Uncle Zaid ringing biyu Zaid ya dauka "Hello Mahmud?" bayan gaisuwa Maalesh yace "Uncle Zaid Jibi fa muke komawa School, ga shi shine final semestern mu a makaranta, Dole sai Rafeeq ya kwantar da hankalin shi yayi focusing kan Semestern nan, shi ke topping din Department dinmu, Uncle Zaid Wallahi duk Sciences bs kamar Rafeew Lema, lecturers naji da shi, idan ya sa wasa zaiyi k'asa sosai don abun nashi k'ara girmama yakeyi wallahi, yanzu da idan nazo tayashi fira ya kan dan kulani, amma yanzu wallahi har inzo in gama surutu na, in gama zama na in tafi in ya tanka ni, kai da ba ka gurin ka tanka, Uncle am afraid for him" hankalin Zaid yayi kololuwa gun tashi, burin da ya jima yana ci kan Rafeeq na son rugujewa, tunda Rafeeq ya shiga nursery yake adduan Allah ya nuna mai randa zai gama Jami'ah, to ga lokacin yazo daidai da k'addarar sa, ya zaiyi? Dole Rafeeq ya maida hankali, dole Rafeeq ya dawo normal self dinshi, Zaid yace "Mahmud kar ka damu, gobe InshaAllah muna nan dawowa da Rafee'ah tunda hutu ya kare, komai zai daidai ta." Sun Iso Katsina Lafia, tunda suka shigo Haraban Gidan taji Gabanta ya fadi, ta kalli Uncle Zaid tace "Uncle Zaid gaba na ke faduwa, kamar wani abu na shirin faruwa" Zaid yace "kin fara superstitious beliefs din nan naki ko, ba abunda zai faru kinji Rafee'ah?" tace "Allah ya sa, i cant wait to see my Mami and my troublesome Hamma Rafeeq" Damm gabanshi ya fadi, ana wata ga wata sai yanzu ya tuna Rafee'ah bata san wainar da ake toyawa ba, ba ta san me ya wakana ba tun bayan Zuwan ta kaduna, ko da ta ishe shi Kan tana kiran wayan Mamin ta a kashe sai yace taje India Medical Checkup, kuma Dr ya bata rest so ko waya bata amfani da shi, ta yarda dashi don ta san be mata karya, kafin yace wani abu tuni ta fita daga motar, ta na kiran "Hamma Rafeeq i'm home" da karfi ta ke maganan, Gaban Rafeeq ya fadi jin muryar Rafee'ah, be san lokacin da ya shige toilet ba ya wanke fuskar sa don kar ta ga damuwa itama ta tada nata hankalin. Cikin gida ta shige ta na fadin wai ya na ji Gidan shiru ne? Ba kowa ne? Alhaji Habib ya fito yana Oyoyo Baby, hajia Sauda tana biye dashi a baya, da sauri Rafee'ah taje ta rungume Daddyn ta tana "Daddyna i've missed u" daga ta yayi sama yana juyi da ita kamar wata baby ita ko tana ta daria. Ya direta yana "i missed u more my angel" taje ta rungume Sauda, Sauda na ta murmushin munafurci tana "haba ai gwara da Zaid ya dawo da ke, tunda ya dauke mana ke gidan ba dadi" ita ko Rafee'ah sai k'yalk'yala daria take yi, tace ina Aneesa? Sauda tace tana chan BUK wurin kanwata, zuwa k'arshen wata zasu dawo" Daddy yace ya Safiyya(Matar Zaid)? Rafee'ah tace "Daddy ta na nan lafia, ta kusa haihuwa ma" Allah ya raba lafia. "Daddy wai ina Uncle Hafiz da Hamma Rafeeq?" Daddy yace Uncle dinki na Yobe na aike shi, Rafeeq kuma na Dakin shi. Tace "Ohh yana jina yayi shiru ya kyale ni ko? Barin je in iske shi" ta sauka k'asa tayi hanyar dakin Rafeeq. Tunda daga waje take kiran "Bigbro Rafeeq, wai ba zaka fito ka ganni ba? ta kutsa kai cikin dakin, turus ta tsaya ganin Rafeeq zaune kan kujera sanye da Bak'in Gilashi, mamaki ya baiyana fuskarta, da sauri ta je ta rungume shi, ganin yanda ya mata ne yasa ta dagowa da sauri, "Hamma na, baka ganni ba? A hankali yace "naganki, Rafee'ah" baka yi murnan gani na bane? Shiru ya mata, ta dinga mishi tambayoyi be bata amsa ba, Ga mamakin ta sai ganin hawaye tayi ya gangaro kan kumatun sa, cikin rudewa tayi saurin zare Gilashin idonshi, tace "mai ke faruwa ne? Baka da Lafia ne?" Daidai nan Zaid ya fito daga toilet din dakin yace "Rafee'ah, ki rabu dashi, be da lafia ne, kuka ta fashe da tace be da lafia? Wani irin rashin lafia ne wannan? Uncle Zaid ko kallona fa beyi ba, Hamma da kullum ya ganni burinshi ya takura min, ya nemi tsokana na, tunda na tafi Kd be kirani ba, idan na kirashi beya dauka, and yanzu kuma na dawo irin welcome din da zai min kenan? Ko kallo ban ishe shi ba? Ina mai magana ko tanka ni beyi ba? Uncle Zaid ko wani abu yace "na mishi?" da sauri Rafeeq ya rungume kanwarshi ya na kuka itama tana kuka ama ya kasa ce mata komai, sun ba Zaid tausayi, da sauri ya rabasu yace "fee'ah tashi ki shiga ciki" ba musu ta fita daga dakin tayi sama, Zaid ya kalli Rafeeq, yace "if you really dont want her to find out, then be yourself" yana kaiwa nan ya kabbara Sallah don ya san bazai samu amsa daga bakin shi ba. Yana idar da Sallah ya kalli Rafeeq yace "muje cikin Gida" Rafeeq ya dago ido ya kalleshi zaiyi Complain amma maganar ta mai nauyi, Zaid yace "ina jiranka" yayi gaba ya bar shi Zaune be da niyyar motsawa". Aunty Yaushe Mami Zata dawo? Kafin Sauda tayi magana Zaid dake shigowa Parlorn yace "nace miki sai taji Sauki, Dr ya bata bed rest, soon zata dawo" ya karashe maganar yana me kallon Sauda yana mata inkiya da ta goyi bayanshi, sai a yanzu ta gane dalilin da yasa dazun Rafee'ah ba tace ima mamar ta ba, wato sun boye bata, aiko ba zai sabu ba, sai ta samu hanyar fallasa mata. Zaid yace "Aunty ina Yaya?" tace "yana nan Office in kusa da dakin shi" Zaid yace da Rafee'ah "ki shiga ciki ki kwanta ki huta" ta mik'e ta nufa daki. Sauda tayi Parlorn Alhaji Habib, Zaid ya rufa mata baya. Yana zaune, Zaid ya gaishe shi, Alhaji Habib yace "Engineer har an iso? Ya hanya? Ina aka tsaya ne sai dai na ga shigowar yar gidanka? Zaid yace "Alhamdulilah, Ina Dakin Rafeeq ina Sallah" Alhaji yace "hmm lamarin Rafeeq sai gaba yake k'arayi, bansan me na mishi ba" Zaid yace "ba ka mishi komai ba, lokaci kawai yake buk'ata maganar shi ce ma nake so muyi" kamar an jefo shi ya shigo parlorn, yayi Sallama amma Zaid kadai ne ya fuskancin Sallama yayi, ya samu wuri ya zauna kusa da Zaid, Zaid ya tsura mai ido yana mai nuni da ya gaida Mahaifin shi da Auntyn su, fuska yayi yaki kallon side dinsu. Zaid dai ya san bazai tanka ba ya juya ga yayan shi yace "Rafeeq dama na kiraka ne nan gaban Ubanka mahaifi, shawara zamu baka, ba mu da gatan da zamu maka da ya wuce Addua da Shawara, kai Baligi ne kasan ciwom kanka, kasan abun da yake daidai kasan wanda ba daidai ba, kasan fari kasan bak'i, Rafeeq Abun da ya faru ina so Ka dauke shi a matsayin kuskure, Kaddara, ka rungume kaddararka, Kai musulmi ne, ba wai nace ka yafe ma mahaifiyar ka bane, so nake ka gano gaskia ka gane kurenka dukda ba laifinka bane, shisa kaga na daina takura maka da maganar ta. Alhaji Habib da matarshi dai ba su ce komai ba Zaid ya cigaba da cewa " Well this is not about your mom. Its about you, ina so ka maida hankali ka fara last semester din nan naka da kyau, yanda kowa ke Alfahari da kai kar ka bamu kunya, kamar yanda kake yi da, make us proud like always, ka fita da first class dinka that you truly deserve kajih?" Rafeeq kallon window kawai yakeyi, be tanka Zaid ba. Don dai ya sa Rafeeq Farin ciki Zaid yace "kuma zan siya maka mota son ranka, ka fadi wanda kake so Gobe ka ganshi a gidan nan" nan ma be ce komai ba, Hakan yasa Alhaji Habib yace "toh nima Uncle din Yara baza a barni a baya ba, nima ina da kyautar da nakeso in ma Rafeeq" ya mik'e ya fita duk suka bishi da ido gaban Sauda ya fadi tana ta tunanin meye kyautar da Alhaji zai ma Rafeeq, Jim kadan sai gashi ya dawo da wasu files ya zauna, yace "Sauda da Zaid kuyi shaida, Kafin a samo Shaidu, Companyn Tie and Dye na Sokoto, da Hide and Skin na Keffi na Mallaka ma Rafeeq, ko na mutu ba su a cikin Gado, kuma da ka gama Service, komai na other Companies dina zasu dawo k'arkashin ku kai da Rafee'ah, Zaid ya washe Bakih yace kai MashaAllah, Angode Allah ya k'ara girma" Sauda kuwa Ba tasan duniyar bakin cikin da ta lula ba, kiris ya rage ta fashe don ta kumbura, ta kasa boye bakin cikinta da hassadar ta. Amsa Rafeeq, Alhaji ya miko mishi Files din, Zaid ya mai Alama da ya amsa, kamar ba zai karba ba ya sa hannu ya amsa a hankali yace "nagode" Daddy yace tashi kaje ka adana. Kamar jira yake ace yatashi ya tafi ya mik'e da sauri, Files din ya mik'a ma Zaid, Zaid ya sa hannu ya amsa, yana bashi ya fita daga Parlorn. Zaid ko Farinciki yake tayi. Sauda kuwa ta na hada hanya don ta daina gani saboda bakin ciki ta fita. Daki ta fada ta fashe da wani irin ihun takaici, ta daura hannu a kai, na shiga uku, Alhaji har ya fara rarraban kamfanonin ka? Be sakani cikin lissafi, wato daya gama Sabis zai maida komai karkashin sa shi da kanwar shi, ni kuma da tawa diyar oho, wallahi ba zai sabu ba, sai inga ta inda zai gama makarantar balle yaje service din har ya zama wani tsiya , ita kuma Rafee'ah sai ta tsani kanta, don boka na kan tudu zan sa ya Sa Rafeeq ya mata Fyade, ko kuma ta zama karuwar Yayanta, sai in ga ta inda zasu zama abun Alfahari ga mutane. Sai kowa ya tsanesu, shima Alhaji ya tsine musu ya koresu daga gidan shi, su shiga duniya, sai ya rage daga ni Sai diyata sai muci karenmu ba babbaka ta sa shewa kamar wata zararriya da sauri ta ciro wayarta ta latso number Boka na kan tudu ta labarta mishi plan dinta. Yace "Saude wannan magana ba ya waya bace ki zo Gobe kawai sai a duba" tace "to na kan tudu, ka tsumayi zuwa na gobe, da Asubar fari zan taho". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣8⃣ As promised, This page is for you Aunty Baraka❤❤❤ Washegari Alhaji Habib yace da Sauda zata raka shi Kano, haushi kamar ya kasheta don tayi niyyan zuwa gun boka na kan tudu yau, haka suka tafi Kano ba don taso ba. Rafee'ah ta rada ta inda zata bullo ma Rafeeq, don har yanzu bata san damuwar shi ba, da ta matsa ma Zaid sai ya gaya mata, sai yace mata "zaifi kyau ki taya shi da addua, Shi kadai yake bukata, kar ki tsananta Bincike you might end up hurting yourself" haka Rafee'ah ta cigaba da shishige ma Yayan ta ko zata samu ya dawo yanda yake a da, amma shiru ba cigaba, haka zata karashe surutun ta ta barshi, duk yanda yake so ya dan dinga kula Kanwar tasa hakan ya faskara, abun ya zame mishi jiki, Yanzu magana ya zame mishi wani gagarumin Aiki, da Zaid kadai zakaji yana magana, shima be wuce ya bishi da kalma biyu ko uku ba, abun Rafeeq ya wuce Miskilanci, don abun yayi k'amari har ace be iya shiga cikin Gidansu ya ci Abincin da Matar Uban shi ta dafa, kai ko daki aka biyo shi dashi be ci haka zai bar musu shi inda suka aje mishi shi, Be cin abincin Gidan su kwata kwata, sai dai yaje gun me indomie ya sha shayi, da Zaid ya lura da hakan sai ya siyo mishi Cupcakes,Biscuits Shortbread da Drinks kalakala ya ajiye mai a daki tunda yana ganin asaran cin Abincin Gidan su.. Da kyar Maalesh ya sa shi shirin Makaranta, ba don yaso ba, sai dai kawai baya so su tsaya gardama da Maalesh, ya shirya suka wuce School, tunda suka isa Sciences aka zagaye motar Maalesh, Maza da Mata kasancewar R-Lema na kowa ne, Maalesh yace "Guy, dole ka fa sake fuska, mutanen ka na jiran fitowar ka" be kula Maalesh ba sai ma dauko wani Bakin Gilashi irin no respect din nan ya k'wama a fuskar shi, ya bude Kofa ya fita, ji kake ana R-Lema, ko kallo basu ishe shi ba, tafian shi kawai yakeyi, burin shi ya ganshi a Class, duk suka bishi da kallo suna mamakin wanna Shariya na R-Lema, sai duk suka maida kallo ga Maalesh, Maalesh ya shiga raba idanu kamar yayi K'arya, da k'yar yace "kuyi hakuri, R-Lema na da dan damuwa ne, ky tayashi da Addua". Mutanen kam suka jinjina kai, da alamu kam, don ba haka suka saba ganin shi ba, shi mutum ne mai son jamaa, da da ne, da ya fito zai dinga ba mutanen nan hannu suna gaisawa, ya dinga jan tsokanan yan matan nan, ana wasa ana daria, lallai dole suke tayashi da addua Allah ya yaye mishi damuwar shi. Ai ba Daliban ba, harta Mallamai sun san da Chanjawan R-Lema, yanda kasan hoto haka yake zaune a aji, ba motsi, ba kamar da ba, kafin Lecturer ya gama tambaya har ya bada amsa, amma yanzu ko sun tambaye shi shiru zakaji yayi, bawai be gane abun da ake koyar dashi bane, tsaf yake fahimta kamar kullum, abunda yake ganin asara shine ya bude baki yayi magana ko ya bada amsa, yana jin kuiwar magana, kwanaki da ya ba wani Lecturer haushi koran shi yayi a aji, don ya dinga mishi magana jo tak Rafeeq be ce mar ba, abun ya ba mutumin haushi ya kore shi, sai da Maalesh ya je ya sanar da Level Coordinator dinsu, kasancewar Coordinator abokin Zaid ne, Yazo ya bada hakuri, yace yayi hakuri Rafeeq is Mentally Sick, yayi considering dinshi tunda kowa yasan ba haka yake a da ba. Da haka aka rufe bakin lecturers, ko sunzo ba sa tambayan Rafeeq don sun san ba tanka su zaiyi ba. Duk nacin da Yanmatan Rafeeq keyi don ya kulasu haka suka gaji suka hakura, don ko sun fi k'uda k'wak'wa iskar da ya debo su Rafeeq be kallo, Cafteria da da ya maida shi Gidan Uba, a rana sai yaje so nawa, yaje ya siya ma yanmata abinci, yanzu kuwa ko kallon hanyan beyi, in ka ganshi cikin Makaranta yana aji, da sun gama lectures be kara ko minti zai bar ajin don be son surutu, Chan bayan Labs inda ba ka ganin kowa yake zuwa ya zauna shi kadai. Haka Rayuwar shi ta cigaba da tafia.. Duk Yanda taso ta kebe ya je gun bokan ta Alhaji Habib ya toshe, be bata damar zuwa ko nan da chan ba, ko ina zaije da ita yake zuwa, be barin ta ita kadai, ta rasa yanda zatayi, haka dai ta hakura har suka karaci kwanakin su a garin Kano. Bayan Sati Uku Sauda ta kalli Boka cikin kunan rai tace "ya zaka ce min hakan ba zaiyiwu ba? Meye ba zaiyiwu ba? Kaine fa kake share min hawaye na, kai ke biya min buk'atu na"(Waiyazubillah, ya mu Mata, mu kula, mu lura, aikin Boka na tasiri ne da Yardar Ubangiji, Boka be Isa Ya biya mana Bukattun mu ba. Allah sa mu dace). Ta yaya zan ce maka ga abun da nake so kace min ba zaiyuwu ba? Kasan taya na bar Katsina na zo nan? Ni yanda nake so haka zaayi, Kawai Rafeeq nake so ya fyade kanwarsa". Boka yace "Saude kar fa ki manta, duk aikin da kike samu muna miki shi yanda kika buk'ace shi, tunda kikaji nace wannan bazaiyuwu ba toh ki hakura da wannan, amma na riga na biya miki dayan bukatar hana Yaron Gama Makaranta" Sauda ta katse shi ta hanyar cewa "yo ni raba ni da wata makaranta, yo ya gama ina ruwana, ni buk'ata ta shine Alhaji ya tsine musu duka, kai ni ban k'i su mutu ba" Boka yace "Ke Saude saurareni kiji, jijsan aiki na kamar yankan wuk'a yake, ba wanda ya kaini aiki me kyau, na hango miki gaba ne, duk wanda zai ce miki ki bashi kudi ya miki Aiki kan Mijinki akan 'ya'yansa, to nayi imani kudinki kawai zasu ci, ba wani mugu a doren k'asar nan da zai iya hada Mijinki da Yaransa ba, wai shin baki san so da ke tsakanin d'a da mahaifi ba? Kar ki ga kinci nasara kan Matar shi, kice suma zaki ci nasara, Saude shawara zan baki, idan kika matsa kan hakan, to Asirin ki na Gaf da tonuwa.. Sauda ta k'ule matuka, ta mik'e cike da Masifa, tace" kai na kan tudu, kar ka cika ni da wannan soki burutsun, ai baka gaya min Imani ya fara shigan ka ba, idan ka tsufa baka iya biya min buk'ata ta sai ka sanar dani, bawai ka dinga ce min hakan bazaiyiu ba? Ba ka k'ara gani na nan, zanje in samo wanda zai iya min abun da nake so" ba ta jira amsar shi ba ta fice daga Bukkar. Cikin Kwanaki 20 Saude ta zabure sosai, duk inda ta san zata samu bokaye ta bi, burinta Rafeeq ya lalata ma Rafee'ah Rayuwa, sun san aikin da ta ke so a mata ba me yiwuwa bane amma sunk'i gaya mata sai dai su ce mata taje Gida zata ga aiki da cikawa, haka zata dawo gida tayi ta jiran tsammani, shiru takeji, sai ma wani Gatan da Alhaji yake k'ara ma yaran sa, haka zata chanxa wani boka, Bokaye kuwa sai cin kudinta suke yi, da ta gano su dai tayi watsi da dukkan su ta zauna gaban Madubi ta na kallon kanta tace "Haba Saude, sai kace ba mace ba, idan Plan A yak'i ci, sai a gwada Plan B, Wato K'issa" ba Bokan da zai k'ara cin kudina, cikin ruwan Sanyi zanyi maganin ku Rafeeq da Rafee'ah.. Bayan Wata Daya Karatu suke kain da nain, Rafeeq ya dage da Project dinshi, be kula kowa yake abubuwan shi, kwanaki kadan ya rage su fara Final Exams, Rafee'ah har ta saba da Shariyar Rafeeq, itama tana ta karatun ta cikin kwanciyar Hankali, Babban Tashin hankalin ta Mamin ta, ta fara gano akwai wata makarkashiya, duk wanda ta tara da maganar mahaifiyar ta sai yayi shiru, har takanas taje gidan Kakanin ta don tambayo idan Mahaifiyar ta take, amma bata samu amsa daya k'wak'wara ba, sai hanya hanya suke mata. Yau tace InshaAllah dole sai ta gano gaskiar inda Mahaifiyar ta take, Bayan ta dawo School ta nufa dakin Aunty Saude, ta tura kofar da Sallama, Sauda daga ciki tana waya da Meema da Aneesa tayi saurin latse wayar tana addua Allah ya sa Rafee'ah bata ji me take fada ba. Ta amsa mata sallamarta, "Rafee'ah sannu da zuwa kin dawo?" "eh Aunty ya Gida?, kina da lokaci? Akwai maganan da nake so muyi" Sauda tace ohh Rafee'ah, barin yi Sallah sai inzo muyi magana ko? Rafee'ah tace toh, nima barin shiga in watsa ruwa". Sai da tayi wanka tayi Sallah ta fita parlorn k'asa, Saude ta sauko itama, tace "Rafee'ah, har kin fito? Tace "eh Aunty i'm just eager to talk to you", Saude tace "tohfa, what's it about?" Rafee'ah ta rik'o hannayen Saude guda biyu ta zaunar da ita, tace "Aunty, donAllah ina so ki gaya min gaskia, duk wanda na tambaya baya bani gamsashiyar Amsa, ki taimaka ki gaya min, ina Mami na take? Na kusa wata 3 daga dawowa na da kaduna, ba labarinta, kar kuna 6oye mun wani abu, please ki gaya min". Cike da makirci Sauda ta fashe da kuka, nan da nan Rafee'ah ta rikice "Aunty me ya sameki? Ko dai Mami na mutuwa tayi?" Saude cikin kukan munafurci tace" ko daya Rafee'ah, zan gaya miki abunda na sani game da Mamin ku, amma kar ki ce ma kowa ni na gaya miki don ba sa so ki sani" Rafee'ah ta gyara zama tace "InshaAllah" Sauda ta kara sautin kukan ta, tace "Rafee'ah, ashe maminku yar iska ce? Ashe Magajiya ce uwar karuwai? Kwarto ta kawo cikin dakin auren ta, Kwartu--" bata k'arashe zancenta ba taji an sauke mata wasu kyakyawan mari biyu, a zabure ta dafe kuncinta, ta daga idanuwan ta taga Rafee'ah tsaye tana huci kamar Zakanya, Sauda ta dago a fusace, tace "Rafee'ah, ni zaki mara? Don na gaya miki gaskia? Don ma ban gaya miki gaskian lamarin ba? To kwance a ka ganta haihuwar uwarta da gardi" Wasu Mari ta sake ji an sake mata wasu na bin wasu, Mamaki ya rufe ta, tabbas ba Rafee'ah ce tayi marin nan ba, kafin ta ankara taji muryan mijinta Alhaji Habib cikin daga murya yana cewa "Rafeeq, dont, kar ka sake taba ta" Rafeeq beji ba illa ma dunk'ule hannun da yayi zai kai mata nushi, da murya karkausa Uncle Zaid ya kira sunan shi "Rafeeeeq". _Bibilicious biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg2⃣9⃣ Fasa nushin ta Rafeeq yayi, ya sauar da hannu yana ajiyar zuciya, Zaid ranshi a bace, be ji dadin abun da Sauda tace game da Mami ba, k'ila da shi ke kusa da ita da ya karairayata, Alhaji ne yace cikin fada"ke ma dai me yasa kika gaya mata? Tun farko Zaid ya nema Alfarma gun mu yace kar a gaya mata, do u want to break her? Bakiga yanda abun yayi affecting Rafeeq ba? kinsan zai yi affecting dinta, maybe worse than Rafeeq, u shouldnt have told her" Sauda ran ta ya gama baci, amma ganin Mijinta da Zaid tsaye ya sa ta fara kukan munafurci, tace "Haba Alhaji kasan ba zan taba yin wani abun da zai cutar da su ba, ina son su kamar ni na haife su, Rafee'ah ce ta titsitsiyeni da tamabayoyi. Rafee'ah ta sake ihu dakata " Daddy, Uncle Zaid, Hamma, wai me ke faruwa? Bana fahimtar komai, tell me this is not true, ku fahintar dani, ku ce mun Sharri aka mami na" kuka takeyi sosai, kamar ranta zai fita, Rafeeq ya rikota, yace "kiyi hakuri Rafeeah, shiyasa tun farko ban so a sansr dake, coz nasan cewa u'll be broken" ta dan zabura kadan, ta ma rafeeq wani kallon da be taba ganin ta mai ba, tace "Me kake so kace? Ka yarda da sharrin da aka ma mami? Ashe wayon banza ne dakai?" Da sauri ya kalleta don be tabajin irin maganar nan daga bakinta ba, sam be ji haushin ta ba, yace "Rafee'ah, i saw Mami with my eyes" da sauri tace "you must be stupid Rafeeq, da ka manta who ur Mother really is, ka manta the type of woman she is, ka bari anger yayi controlling dinka, look at you now, you are miserable" Alhaji yace "Rafee'ah, ki kula da yanda kike ma Yayanki magana, beyi k'arya ba, tabbas abunda sauda ta fada miki gaskia ne, Zaid ne ya nemi Alfarman a boye miki saboda kina iya shiga wani hali a matsayin ki na mace, amma tabbas Mamin ku Kwarto ta kawo dakin aurenta, Mamin ku ta dade tana cin amana ta" tsananin bacin rai Rafee'ah ta shiga, tace "whoever believe this is a stupid idiot, wallahi sharria aka mata, makiri ba ta inda be yin makircin shi, ta daga hannayen ta sama ta cigaba *amma Wallahi Tallahi Billahi*, _da yardan Allah da izinin Allah_, _Whoever did this to my mum is going to pay for it_, _ba zan taba hutawa ba har sai na bi mata hakkinta_ *Ya Allah ko yau na fadi na mutu Allah ka bani hanyar saka wa Uwata*, *Ya Allah ka amshi addua ta ka bani iko Ameen* Wani irin dumm Sukaji a jikin su gaba ki daya, gaba ki dayan su suka ji a jikin su wanna addua ta Rafee'ah karb'abba ce, Sauda hankalin ta ya tashi matuk'a, Zaid da Alhaji Habib bakin su ya mutu murus, Rafee'ah ta juya da gudu ta haye sama tana kuka, Rafeeq kuwa hankalin shi ya gama tashi, abun da yake gudu ne ya faru. Zaid yayi saurin bin bayan Rafee'ah. Sauda ta dafe kanta takaici goma da ashirin, Yaran Mijinta sun mammareta a gaban mijinta amma ya kasa cewa komai? Nan gaba k'ila belt zasu sa mata su mata mugun bugu, wai har Rafeeah ta daga hannu ta mareta, Rafeeq ma haka. Tabdijam aiko sun tsokalo wa kansu tsuliyar dodo, ita kadai tasan abun da zata musu, ba shegen bokan da zai ci kudinta wanna karon da kanta zatayi maganin su once and for all, ita kadai ke ta maganar ta. A.Habib ya shigo dakin matar shi, tana ganin shi ta fara murmushi, Alhaji ka shigo, yace eh "Saude, hakuri nazo baki kan abunda yaran su ka miki, basu kyauta ba" sauda a ranta tace "jar uba, wato ba zai ban hakuri a gabansu ba don kar suce ya musu ba daidai ba shine ya biyota daki ko? A fili kuwa tace "haba Alhaji, ni ko daya ban rik'e su a rai na ba, ai da na kowa ne, na mata uzuri, tana cikin tsoro da rudani, amma wlh Alhaji bakomai" Alhaji har ranshi yaji dadi, yace "shiyasa nake son ki, nagode Saude." Bayan Maghrib Uncle Zaid ya shiga dakin Rafee'ah da Sallama, ciki ciki ta amsa don tana ji haushin kowa a gidan, Kan side drawer ya zauna yayi yace "Rafee'ah" ta dan yi shiru kafin tace "kaima ka yarda da k'azafin da akayi ma Mamin mu?" Zaid yace "ban tab'a yarda ba Rafee'ah, Mami ba haka take ba" farinciki ya lullube ta, da sauri ta juyo inda Uncle Zaid yake zaune, ta riko hannuwan shi biyu tace "Uncle Zaid, ka taimake ni mu gano inda Mami take, Uncle Zaid so nake a wanke ta daga zargin da suke mata duka, har Daddy ya maidota dakin ta, Uncle Zaid so nake duk wanda yake bayan wannan manakisar ya wahala, ya wulakanta, Uncle Zaid ka taimake ni" Zaid ya sauke gwaron numfashi yace" Rafee'ah its not easy as u think, Wallahi ba inda ban neme Mamin ku ba, a wani zuciyata ta bani she's safe, only if i know where i can find her, zan fi kowa jin dadi" Rafee'ah tace "Uncle Zaid, dole mu nemo Mami, Zaid yace "toh Rafee'ah ta yaya?" tace muje mu ga Baba Alhaji (Baba Tj) na fi zaton yasan inda take" Zaid yace "wallahi nafi sawu nawa yace shima nemanta yake" Rafee'ah ta mik'e ta zura Hijab dinta tace "Uncle Zaid, i dont believe baba Alhaji, i have a feeling he's hiding something". Zaid yace "lets go findout" a tare suka bar Dakin don zuwa gidan Kakan su Rafeeq. Rafee'ah ta durkusa gaban Kakanta, tana kuka kamar ranta zai fita, tace "Baba Alhaji, mesa ba zaka gaya mana inda Mamin mu take ba? Haka kake so mu cigaba da rayuwar mu ba Uwa? Kua da ranta? Baka ga yanda Rayuwar Rafeeq ya koma ba? Hankalin Baba Tj ya tashi, cikin in ina yace " wai waya gaya muku na san inda take?" Rafee'ah tace kaji tausayin mu ka gaya mana, watanni 4 kenan rabon mu da mahaifiya, please ka fada mana" Baba Alhaji yayi shiru, yace "nifa ba zan maida ma Habib Aisha ba, har sai gaskia ta baiyana da kanshi, sai Habib ya bambance. Sai a sannan Zaid yayi magana yace " Baba ba mu na nemanta bane don ta koma gidan Yaya ba, ina so na tafi da ita gida na ne, na san duk inda take kadaici ya ishe ta, amma idan ta zauna gidana time to time zata dinga ganin su Rafee'ah" Baba Tj yace Aa Zaid, zan dai gaya muku inda take amma bazai yiwu ka kaita gidan ka ta zauna ba, ai akwai matsi da takura ga ka da iyali" Zaid yayi saurin cewa "Haba Baba,kar fa ka manta ko bata auri Yaya Habib na ni me kula da ita ne, ma tsare mutuncin ta, donAllah baba kar ka hanani" Mama tace "gaskia ne Alhaji, ni na amince ma Zaid, ka fada musu" Baba Tj yace "Hakane, Aisha na gidan Goggon ta dake Malumfashi tsawon watannin nan, kuma har ta gama Iddanta" Rafee'ah tayi saurin rugume kakan ta don murna yace "tafi chan kar ki karya ni". *KUYI HAKURI, ABUNDA YA SAMU KENAN YAU, BA KUMA NAN NA SO TSAYAWA BA,WANNAN YA FARU NE SABDA WASU DALILAI. INSHAALLAH GOBE DA SAFE ZAKU GA CIGABAN 29 ATTACHED TO THIS PAGE, DA NA SO BARI SAI DA SAFE, AMMA DA YAKE NAYI ALKAWARI SHISA, PLEA[truncated by WhatsApp] 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg3⃣0⃣ Saude ce ta nufa gun Rafeew ta na kururuwa, tana fadin yau mun bonu "Shima ya mutu" Zaid dake tsaye tun dazun ya kasa motsi sai hawayen da ke bin kumatunshi, ya tuna inda Rafee'ah ke rok'on shi ya barta ta bishi Malumfashi, da ya hanata binshi da duk sai yaji ya tsani kanshi, ya share hawayen shi, ya taka har toilet din Rafee'ah ya dibo ruwa a cup, yazo ya yayyafa mai, Zumbur Rafeeq ya tashi, Saude mamaki ya lullubeta, ya akayi Rafeeq ya tashi? Daman be mutu ba?, Rafeeq ya fashe da kuka, tare da Rungume Zaid, "Uncle Zaid, Rafee'ah ta tafi ta barni, Rafee'ah ta mutu, she was in my room yesterday, telling me she loves me, Uncle Zaid why didnt i tell her i love her back? Ina sonta wlh Sosai, ta dawo, i so much hate myself right now" duka dakin suka fashe da wani irin kuka mai tsumma Rai. Hafiz ne yayi karfin halin cewa sai ayi Gaggawar kaita makwancin ta, barin je in sanar a gidan Radio, karfe Goma Za'ayi jana'iza, Alhaji Habib kamar mace kai kadai ya daga. Zaid yace da Hafiz "donAllah ayi prolonging dinshi zuwa Azahar" Hafiz yace saboda me? "Ai gwara a kaita gidanta na gaskia" Zaid yace "ina zuwa" ya fita da Sauri, be tsaya ko ina ba sai gidan Baba Tj, nan ya shaida musu Mutuwar, yace "Allahu Akbar" Zaid yace "Baba, so nake ka kira Mami ka gaya mata, Iliyasu ya dauko ta ita da Safiyya, ba zaa kai Rafee'ah ba sai Mami tazo ta mata addu'a, Ba musu ya lallubo ta a waya, ta dauka da Sallama, Baba "ina kwana?" ya amsa, yanda taji muryan shi ta tabbatar ba lafia, gaban ta ya tsanan ta faduwa don tun ran da Rafee'ah ta tafi taji jikinta yayi sanyi kalau. Yace "ki shirya ke da Matar Zaid direbanshi zai dauko ku ya kawo ku Katsina" cikin daburcewa tace Lafiya Baba? Waye be lafia? Mama ce?" yace aa Mamarki na chan daki kalau take" to baba Gaya min na san tabbas ba lafia" Yan nasihohi Baba ya fara mata kan daukar K'addara, nan ta dago mutuwa akayi, cikin rawar murya tace "Baba, Rafeeq ya rasu ko?" yace "aa, ba Rafeeq bane, Yaruwar sa ce" wasu zafaffen hawaye na tashin hankali suka soma kwaronyowa daga idaniyarta, a hankali tace "Rafee'ah" Baba yace "itace, Aishatu" _Inalillahi wa ina ilaihirrajiun, Allahumma Ajirni fi Musibati wa akhlifni khairin minha_ jikinta ya fara rawa. Ta zube kan kujera, "hakuri zakiyi Aishatu, yau da safe ta tashi da Amai" da kyar tace "Baba yanzu Safiyya zata taho, ni ba zan zo ba, ayi gaggawar kai ta makwancinta, _Ubangiji Allah ya yafe ma Rafee'ah, Allah ya gafarta mata, Allah ya sa chan ya fiye mata nan, Allah ya sa Aljanna firdaus ce Makomarta_ *Ameen* dif ta datse wayar. Zaid yace " Baba, ya tace? Tace a kai Rafee'ah a rufe ta, ba za tazo ba" Zaid yace "aa Baba, ta zo donAllah, barin sake kiranta" Baba ya dakatar da shi "Aa Zaid, ka barta, chan din zai fiye mata kwanciyar Hankali a bata Space, shes a mother". Ba dan Zaid ya so ba ya rabu da ita. Suka tashi suka tafi Gidan Lema. Mami ta iske Safiyya a Daki, tace "Safiyya sai ki shirya ko? Tafiya ta kama ki katsina" yanda Matar Zaid ta ga Mami ta san ba lafiya duk da ba kuka take yi ba" tace "Mami Lafiya?" tace "Rafee'ah ce ta Rasu" Inalillahi wa ina ilaohir rajiun tace ta pashe da kuka" Mami tayi saurin fita daga dakin. Sai da ta ci kukanta ta gode Allah kafin ta kira Mijinta Zaid, ya tabbatar mata da Mutuwar yace yanzu ma Wanka zaa mata, karfe Goma zaa yi Janaizar ta. Ya tambaya "ya Mami?" tace "gata nan dai, Allah ya dora mata Tauhidi, tayi tawakkali" yace "Allah sarki Mami, to ke ki lallaba ki shirya, Iliyasu ya kawo ki Allah ya kiyaye hanya tace "Amin". Bayan tafiyar Matar Zaid Mami ta fito Parlor, ta zauna ta shiga tunani, Allahu Akbar daidai nan Suka rabu Shekaran Jiya, ta tuna Yanda Rafee'ah ke ta nannukarta tun zuwan su Kaduna, yanda bata yarda tayi nesa da jikinta, ta rungume ta ta kwanta kan cinyarta, ko toilet zata shiga sai ta rike hannun Mami ta jata har bakin toilet din ashe duk na bankwana ne? Ta tuna lokacin tafiar ta har ta fita ta dawo da gudu tace Mami kice Allah ya min Albarka, " tayi daria tace Allah miki Albarka Rafeeah, Allah baki miji Nagari, wanda zai kula min dake" tayi daria tace "Ina sonki Sosai Mamina" "nima ina sonki Sosai Rafeeah ta" muje in rakaki Uncle Zaid dinku na waje yana jira. Nan mami ta fashe da kuka mai tsumma zuciya. Allah ya gafarta miki Rafee'ah, na yafe miki duniya wa lahira, Allah ya hada fuskokin mu a Aljannah firdaus.. 11:00am. Rafeeq kwance kan Gadon Asibiti, don a Mak'abarta ya sume yayin da aka Birne Rafee'ah, daga Gidansu zuwa Makabarta yayi suma kusan kala 5, da ance a maida shi gida sai yace shi be yarda ba dashi zaayi Janaizar Kanwar shi, kafin a rufeta ya suma, bayan an rufeta ma haka, Maalesh ne yace da Hafiz, Uncle Hafiz barin kaishi asibiti, ya samu hutu a chan, Hafix yace "kayi dabara Mahmud". Haka Rafeeq yayi ta zaman Asibiti har sai da aka gana Zaman makoki, da ya tashi ya fara sambatu zaa mishi Alluran bacci. Bayan Kwana 3 Rafeeq zaune cikin dakin shi, Maalesh na gefen shi, dawowan su kenan daga Asibiti, Maalesh ya k'ura wa Rafeeq ido, kallo daya zaka mai kaji ya baka tausayi, Mutuwar Rafeeah ya mugun girgiza shi, idan an lek'o yi mishi gaisuwa har mutum ya zauna ya gama maganar shi Kallo be ishi Rafeeq ba, Maalesh ne ma dai ke amsa gaisuwar, Bayan an watse Maalesh ke cewa "kai Rafeeq abun ka fa k'ara gaba yakeyi, muma fa duk mun girgiza da mutuwar Fee'ah, barin ma gaya maka abunda baka tab'a sani ba, Ina mutuwar Son Rafee'ah, na sota kamar raina jira nayi lokaci yayi in baiyanar mata da son da nake mata, nayi dakkon sonta da dadewa, amma ta tafi ta barmu, nayi Alhinin mutuwart amma Sai naga ba abunda ta fi buk'ata da ya wucei Addua, sai na dau k'addara ya kasance ko da yaushe ina mata addua, toh idan addua take buk'ata, har mutane suzo don taya ka Addua ka gaza ce musu Amin? Haka akeyi?" kamar Rafeeq zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mik'e don fita daga dakin, ganin haka Maalesh yayi saurin mik'ewa yace ba sai ka bar min dakin ba, dakin ka ne, nine zan fita" ya fice ya bar Rafeeq tsaye, yana so yace mai ya dawo amma ya kasa. Meema da Aneesa kanwar Sauda zaune cikin Parlor, tun randa akayi rasuwar sukazo, Zaid ya shigo ciki, Aneesa ta mik'e da sauri, tace "Uncle Xaid ina wuni?" ya amsa da murmushi lafia lao Aneesa, kinsha hutu ya kano?" tace Alhamdulilah, ya k'arin hakuri? Allah ya jikanta, ya Amsa da "Amin" Aneesa sai zungurin Auntyn ta Meema take tayi, tun shigowar Zaid parlo ta sandare daga zaune, don farat daya taji Son Zaid ya mamaye mata Zuciya, Sai da Aneesa ta takata da karfi kafin ta dawo hayyacin ta, da sauri ta gaida Zaid tare da mai gaisuwa, ya amsa ta tare da cewa "barin hau sama gun Yaya". Ya haye Sama. Meema ta kalli Niece dinta tace "Omg, Wallahi naga mijin aure, ina sonshi, kuma sai na same shi ta halin k'ak'a waye shi? Aneesa tayi daria tace " Kanin Daddyn su Rafee'ah ne, kuma yana da mata" tace "ba mata ba ko Matan sa hudu sai ya aureni". Aneesa tace "muje dai ki gaya ma mommy". Sama Suka hau dakin Sauda, Meema tace da yayarta "Sis, nayi new catch cikin gidan nan, kuma ance K'anin Mijinki ne, nidai na samu mijin Aure" Sauda ta zaro ido a ranta tana Allah ya sa ba Hafiz bane, karaf Aneesa tace "Uncle Zaid ne" Sauda ta sake Ajiyar zuciya tace "Ke wannan ya miki nisa, yana da mata" Meema tace nidai na samu miji, sai ki min hanyar samun shi" Saude tace "sai ki ja hankalin shi ta hanyar Kissa" tace "Ahap sis har sai kince, kar fa ki manta wacece ni" sukayi shewa tare da chafe wa, Aneesa tace Kinga ni in auri Rafeeq, ke ki auri Uncle Zaid, mummy na auren Daddy, kinga shikenan duniya zata sanmu as Rightful Heirs to the Lema's property. Duk sukayi daria, Meema tace "shi kuma Rafeeq din wayei? Aneesa tace "haba Aunty Meema, so nawa zan gaya miki Rafeeq dan Mijin mommy ne, kuma love of my life, don shi zan aura " Saude ta kalli Diyarta Aneesa, ta san yanda take son Rafeeq, kuma ba za taso yin magana gaban ta ba tace "Aneesa je ki duba yanda Rafeeq yake, m sure he needs someone to talk to" tace "eh wallahi bari inje" ta fita da sauri.. Fitowar Hafiz kenan daga Parlorn Alhaji Habib lema, ganin Zaid ya sa shi fitowa, ya dan basu guri ne don su tamu tataunawa da Zaid, yazo wuce wa, daidai kofar dakin Sauda yaji tana cewa; Saude ta kalli kanwarta tace "Meema, shi wannan Rafeeq din da kikaji Aneesa na magana dan Alhaji ne fa, wani irin banza yaro ne me baudaden zuciya, wai shi Aneesa ke so, kinsan kuwa yaron nan har Marina suka tabayi shi da wanda ta mutu?" Meema ta zaro ido tace "ke haba?, to ke me kika musu,kar kice min baki masu komi ba? Tace "trust me, ban musu komai ba time din, illa kara jan su jiki da nayi, sai Mak'ale ya kawo mun poison, na zuba musu Abinci, poison din ba me kashewa nan take bane, slowly ya ke cin yan hanji, a karshe sai mutum ya mutu don gudun zargi, to too bad Rafee'ah din ce kadai ta mutu da alamu shi be ci abincin ba, amma bakomai shima ba dadewa Zai bi yaruwar sa". Sowa Meema ta sake tace " shisa nake sonki, nobody dare mess with us" tashin hankali ya rufe Hafiz, Ya bugo kofar dakin da karfi. Sauda da Meema suka tashi a firgice. Suna rok'on Allah yasa Hafiz be ji su ba, wani irin kallon tsana ya bi Saude da Meema, Yau duk me zai faru sai dai ya faru wallahi, don he wont let this pass, dole ya tona asirin Sauda, Meema tayi saurin cewa "Uncle Hafiz ina wuni kwana da yawa" wani irin mugun kallo ya wurgeta dashi, cikin dacin murya ya fara magana "Sauda ashe rashin imanin ki yakai haka? Wani irin zuciya ne dake? Shin baki tsoron Allah? Ba kiji komai ba kika kashe innocent soul kamar Rafee'ah? Kisa fa Sauda? Toh wallahi asirinki ya gama tonuwa, yau din nan xaki fuskanci hukuma, Duk duniyancin Sauda yau ta rude, ta shiga rok'on hafiz da ya tsaya suyi magana, ba abunda yake zato bane, yace "baki da hankali, kina nufin banji me kuka ce bane? Ko ban fahimci abunda kuka ce bane? Ai duk abunda kuka fada is straight, ba sai na nema wani bayani ba, abu daya kadai zance miki, dole a zartar da hukunci kanki. "I wont let you keep hurting innocent souls, i wont let you keep hurting the people i love" ko ina na jikin Sauda rawa yake, tace "Hafiz Is not that you are saint or perfect, kar ka manta kai ka kawo ni matsayin da na ke a yanzu, da taimakon ka na shigo gidan nan, kuma kar ka manta da diyarka Aneesa, think wisely, tona ni barazana ce ga ruining reputation dinka, kuma if i go down, you go down with me as well". Hafiz yayi wani murmushi, yace "Sauda kenan, i dont care, ko me zai faru ya faru, ni nakawo ki gidan nan right? Kuma nine silan barin ki, its time i do good thing to the people who did alot for me, i dont care about the consequences, I am Ready, you cannot use me again". Yana kaiwa nan ya juya don barin dakin, Sauda da Meema a rude suka bishi a baya suna mai magiya amma fir ya k'i kula su, Parlorn Alhaji Habib ya shiga, Wayam ya gani, ya lek'a dakin nan ma baya nan, Sauda ta sauke numfashi, Hafiz ya wurga mata harara ya ciro wayar shi ya danna ma A.Habib Kira ringing daya ya dauka "Hello Hafiz" "naam Yaya, kuna ina, ni da na barku parlo kai da Zaid" yace "Eh wallahi, dama Zaid ne ya buk'aci muje Makarantan su Marigayi mu sanar dasu Rasuwarta" Hafiz yace "Okay, gani nan zan biyoku Umaru Musa din" Alhaji Habib yace "lafiya Hafiz?" Hafiz yace "sai dai nazo, yau ranar tonon Silili ne, there are things you need to know, yau ZAN FASA KWAI" dif ya kashe wayan, Sauda ta rude matuka, tana ma Hafiz magiya, we can fix this, feez-boy na tuba kar ka min haka" ai ko kallo bata ishe shi ba ya fice ya bar dakin. Hannu ta daura a kai ta saka ihu, "Shikenan tawa ta sameni, karya ta ta kare asiri na ya tonu" Meema cikin tashin hankali, don gani take idan asirin Yayarta ya tonu, bata ba auren Zaid gashi ita kuma har ga Allah ta sama ranta auren shi, cikin bacin rai tace "Haba sis, dont easily give up, akwai hanyar hana tsaida Hafiz, tunda yanzu fita zaiyi, kawai ki kira bad boys dinki kice su tareshi su gama mai aiki" Sauda cikin doki tace "kutt har na manta da wannan hanyar, hankalina ne baya jikina, bari nayi hanzarin kiran Mak'ale" da gudu ta fita tayi dakinta ta dailo numbern Mak'ale. Ringing biyu ya dauka "Hajjaju mutanen makka" ba ta tsaya sanya ba, tace "Mak'ale kana ina?" yace "gani ta wurin Fatima Shema Housing Estate" Hamdala tayi tace yauwa, wani aiki nake so ka min, ga Hafiz nan zuwa Umaru Musa University, so nake ka tareshi, ka kashe shi, i dont want him to make it to Umyuk" mak'ale yayi shiru yace "haba hajia, wannan aiki da safiyyan nan? Ba kya tsoron aka mamu? Gashi mu uku kadai ne, ba sauran mu" tace Mak'ale ka taimakeni, akwai matsala idan Hafiz ya isa Jamiar nan, zan baka Miliyan Guda" Shewa Mak'ale yayi yace angama "Hafiz Lema ya zama gawa" tace "yauwa Mak'ale, zaka gane shi ko?" yayi daria yace "baki da matsala, har kalar motar shi na sani" ya datse wayar Sauda ta sake Ajiyar Zuciya tana labarta Meema yanda sukayi da mak'ale. Tuk'i yakeyi gaban shi na faduwa, ya sha round din Alkalem University ya dauki hanyar Institutions Road, ya na duba side mirror daidai FCE yaga kamar ana binshi, ko da ya duba mirror din sosai ya gane fuskan Mak'ale, shine ya fito daga dakin Maman su Rafeeq a ranar da suka ganta zindir. Nan jikin shi yayi sanyi, tabbas Sauda ce ta turo shi ya mishi wani mugun abu, gaban shi ya tsananta faduwa, ya taka giya ya k'ara gudun motar shi, suma su makale suka kara gudu, Hafiz ya tsorata matuk'a ya zaro wayar shi yayi dialing numbern Zaid "Hello Hafiz ka taho?" Hafiz yace "Zaid kazo ka taimake ni, akwai wasu masu bina" SubhanAllah a ina? Gamu nan mun kusa Batagarawa, sai fafatawa mukeyi, a guje Zaid ya fito daga office din da suke zaune shi da Alhaji Habib be tsaya mishi bayani ba ya fita, Alhaji Habib ya mik'e, yana kwalawa Zaid kira, Zaid be tsaya amsa shi ba. "Hafiz kana jina? "Eh zaid ina jinka" "yauwa i'm on my way" Zaid incase i dont make it-- Zaid yayi saurin katse shi Hafiz stop, i wont let anyone hurt you gani nan zuwa" "Zaid listen to me, ina so ku yafe min, And you cannot trust Sauda" kafin Zaid ya ce wani abu ji yake kiiiiiiii Alamun cin birkin mota, da karfi Zaid yace "Hafizzzzzz" sai ji yayi ance "kai fito daga motar nan" Zaid ya kara gudun da yakeyi har ya kai inda yayi parking motar shi. Mak'ale suka ma Hafiz mugun bugu kafin suka tura shi motar su suka bar gurin. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg3⃣1⃣ A cikin mota suka lumama Hafiz Wuk'a, bude k'ofa sukayi suka wurgar dashi suka wuce, nan da nan mutane Suka taru kan Hafiz, Zaid ya fito daga Jamiar ya dinga kiran layin Hafiz har ya katse ba a dauka, nan ya ga taron jamaa daga gefe, kamar ya wuce sai Zuciyar shi ta kwadaita mai da ya tsaya, yayi parking motar yq kutsa cikin mutanen nan, ganin Hafiz yashe a k'asa jini ya sa shi karasawa da sauri, Yana kwala mai kira, Ya rungume Hafiz a jiki, sai tari yake tayi, murmushin Karfin Hali Hafiz ya sake da k'yar yace "Zaid, brother, ina neman yafiyar ku kai da Yaya akan duk wasu abubuwan da na muku, ku yafe min, ka ce ma Aunty Aisha ta yafe min itama, na san na mata laifi" Zaid kuka yakyi sosai, yana cewa "Stay Still Hafiz, i'll bring you to a hospital" Jamaa ku taimaka mana donAllah, Aiko bayin Allahn gurin Suka ciccibi Hafiz, suka kaishi motar Zaid, Zaid ya rokesu idan da wanda ya iya tuki ya jasu, wani dan makaranta ya ansa key din, shi da wani gaba, Zaid rungume da Hafix a Bayan mota, tarin Hafiz ya tsananta, kafin a kaishi asibiti ya amsa kiran Allah, Zaid ya fashe da wani irin Kuka, Gida ya bukaci su wuce, Alh Habib yai ta kiran Zaid a waya, da kyar Zaid ya dauka ya gaya mai halin da ake ciki, nan gaban Alhaji ya yanke ya fadi kasa Sumamme, don har Ranshi yake son Hafiz, DVC din UMYUK ya shiga rudani, da sauri ya dauko bottle water ya shafa ma Alhaji Habib, Attishawa yayi da k'arfi ya farfado, Sallalami ya farayi, yana kuka kamar mace. Gida DVC ya kawo shi, a tsakar gida ya ga an shinfide gawar Hafiz, duk yan gidan na nan tsaye, ya tako har gaban gawan ya bude fuskar Hafiz, gashi nan fuskar tayi fayau, Waiyo Allah, zo ku ga kuka gun Alhaji Habib, Rafeeq na tsaye yana hawaye, mutuwar Rafeeah ta dawo mai sabo, ga Uncle Hafiz ya rasu, kwana Goma Tsakaninsu da Rafeeah, Zaid a zaune kusa da gawan yana kuka, Sauda da ke gefe sai ihu take tayi, Aneesa da ba wani sabawa sukayi dashi ba taji jikinta yayi sanyi, kuka take kamar ranta (Mahaifi ba wasa bane) Liman yace "ai sai a gaggauta a mishi sutura akai shi Makwancinsa" da taimakon Baba Tj da Yan Unguwa aka yi ma Hafiz wanka a Parlon Gidan, cikin Mintuna da basu wuce 50 ,ba aka kai Hafiz gidan shi na gaskia. Alhaji Habib fa ya zare, ko Rasuwan Rafeeah be firgita shi kamar yanda na Hafiz ya gigita shi ba, duk ya bi ya fita daga hayyacin shi, Ya fara tambayan kanshi? Why are these happening to him? Da sauri yayi Istighfari da zuciyar shi ta tunasar dashi kar kayi sabo, kai musulmi ne. Bayan Sati 1 Anyi Sadakar Bakwai din Hafiz, Zaid zaune da Habib da DPO din Police suna bincike, don ankai report cewa Kashe Hafiz akayi, Maganganun da sukayi da Hafiz ranar da ya rasu Suka dawo ma Alhaji Habib, Alhaji Habib da har yanzu be dawo normal ba yace "nifa da ya kirani, cemin yayi zai biyo Makarantar su Rafeeq, akwai Maganar da yake so ya gaya mana, har yana ikirarin Yau zai fasa kwai" Zaid yace "Jim kadan kuma ya kirani a tsorace yana neman taimako gurina wasu na binshi a baya, wasu da be san ko su waye ba, ina jinsu lokacin da suka umarce shi da ya fito daga motar" Officer yayi rubutu ya dago yace ko kun san shi da abokan gaba ko da wanda kuke zargi? Alhaji Habib yace "babu" Zaid ya tsaiya tunani, Hafiz yace mai he should'nt trust Sauda, to me tayi? Based on what? He's not sure, so ba zai zargeta ba, amma mesa Hafiz zaiyi warning dinshi? He has no clue". Officer ya musu Sallama ya tafi don fara gudanar da bincike. Zaid kuwa ya kudurta a zai fara binciken shi shi kadai, zai kuma fara da Sauda. Bayan Sati 2 Zaid ya kalli nephew dinshi yace "Rafeeq, saura kwanaki biyar ku fara final exams dinku, Shin Rafeeq ba zaka ma kanka fada ba? Shi ba zaka fara karatu ba, ina da labarin ko lectures baka zuwa, duk tests din da akayi bakayi ko daya ba,ina so kayi karatu ka fita da first class, for how long do u want to live in the past? Its time you move on, please start studying" shiru ya mai be tanka shi ba, Zaid yace "Feeq, kana fa jina" kamar ba zai tanka ba yace "I dont want to, i am not ready" Zaid ya dan sassauta murya yace "Haba Feeq, ka kwantar da hankalin ka ka koma makaranta, kana da hope, kana da what it takes to acheive your dreams in life, please Rafeeq buckle up" Zaid fa ya kai Rafeeq bango, cikin daga murya Rafeeq yace" bana son acheiving komai, my life is already ruined long time ago, i dont have any hope, i dont want to live anymore, Rafeeah should be here, i supposed to die, i dont wanna live, i want to die, meyasa da ta sake ziyartar Family din nan ta dauki uncle Hafiz? Mesa ba ta daukeni ba, ni ke son mutuwa, mesa da Thugs suka zo kisa suka kashe uncle Hafiz? Ni ya kamata su kashe ba shi ba, i wish Akwai wanda zai kasheni, or i wish i could end my life" Zaid ya kashe Rafeeq da Mari, ya nuna shi da yatsa "I didnt raise you as my child to be a non-believer, Kai Musulmi ne, You act like one, not one who fight with his Destiny, you are Rafeeq Habib Lema, kuma Dole ka rungumi kaddararka, Makaranta kuwa sai kayi shi, i've waited for this for so long" Rafeeq ya k'ek'eshe ido yace "Wallahi bazan yi karatu ba, i dont want to study, i dont want to, idan kuma ka matsa mun Zan shiga duniya, you will never ever see me again" Zaid ya tsorata, yayi saurin Rungume shi, yana kuka, "aa, Rafeeq be kai ga haka ba, na bar maganan ba zan matsa maka ba, please dont leave me i cant live without you" Jikin Rafeeq yayi sanyi ganin Uncle Zaid na hawaye a kanshi, wani irin so Uncle Zaid ke mishi, ya dan dago ya share mai hawaye. Washegari Zaid ya je Umaru Musa Yaradua University, Maalesh ya mai jagora gurin HOD dinsu, Zaid ya gaya musu matsalar Rafeeq, yana so a bashi shawara, Level Coordinator na su Rafeeq yace "Inaga yayi deferring semester din, har sai ya dawo normal, so that it wont affect his CGPA" HOD yace "Gaskia, ne, Yayi Deferring Semester din wato zai Jiginar da Semester din, ba wai yayi spilling bane, only disadvantage din shine, Mates dinshi zasuyi Graduating shikuma zai dawo" Zaid yace is better ai hakan, InshaAllah zuwa next year din zai dawo normal self dinshi sai ya zo ya cigaba daga inda ya tsaya" nan suka tsaida Magana. Zaid ya samu Yayan shi ya mai bayanin komai, Yayan yayi naam da hakan, yace to kai Zaid meye plans dinka kan danka? Ina tsoron Zuciyar Rafeeq tunda har ya iya ikirarin shiga dunia, kar abokanan shi suyi influencing dinshi, su koya mai wasu halayar" Zaid yace " nayi tunanin haka, shisa nace za mu danje hutu da shi, zan dauke shi muje Embassy muyi purchasing Visa" Alhaji Habib yace "hakan yayi, K'ila ya dan washe ya dawo daidai". Zaid ya sanar da Rafeeq zasuje dan hutu a kasar waje, ya fadi any country of his choice, Rafeeq beyi wani murna ba don shi a ganinshi be kamata ace yana jin dadi ba, be ce komai ba, Zaid yace ko muje Dubai, ko London, ko Saudi? Rafeeq dai be ce komai ba. Zaid dai ya yanke hukuncin zuwa Paris Bayan sunje sunyi Umra, ya gama musu komai, ya dauko Hutun Wata 3 a Gurin Aiki, suka wuce Saudi Arabia da, sai da sukayi kwana 7 kafin suka wuce Paris. Watan su Biyu a Paris daga shi sai Zaid a daki daya a Gado daya, Yanzu Ba yabo ba Fallasa, kadaran-kadahan dai, da kyar ya ke bin Zaid gurin bude ido, Zaid be da wani burin da ya wuce ya ga ya kyautata ma Rafeeq,hakan ya sa Rafeeq ya sa Zaid a zuciyar shi sosai, yaji duk duniya be da wanda yake so sama da Zaid, ya sama mishi gurbi a ranshi, shima ya kudurta a ranshi InshaAllah zaiyi k'okarin kyautata ma Rafeeq.Haka suka dawo Nigeria. Nigeria ta na nan yanda suka barta, ba wani cigaba game da binciken Hafiz, ba wani leads, Alhaji Habib yace a barsu Allah e Zai isar musu, Mayya kuwa Wato Meema, son Zaid kamar ya kasheta, ba gun bokan da bataje ba ya karkato da hankalin Zaid gareta amma a banza, da taga ba sarki sai Allah sai ta fara chusa kanta gunshi, tana nuna maitar ta fili, tuni Zaid ya dagota, amma shi ya datse ma kanshi, shi Mijin Mace daya ce wato Safiyya. Zaid ya kasance mai taka tsantsan da Sauda, duk da be ga wani alamun Sauda na da wani hali ba, amma be cin abincinta be kwana gidan, dadin shi daya ba ruwan Rafeeq da cikin Gidan, shisa yake siyo mishi abubuwan bukata na kayan kwali da gwangwani. Zaid ya koma bakin aikinshi, Mami ta rok'i Zaid da ya nema mata dan karamin Gida, ba zaiyiwu ta cigaba da Zama a cikin shi ba, da iyalan shi, wata rana zaa gaji da ita, duk yanda Zaid yaso tankwara ta ya kasa, be da wani choice da ya wuce nema mata Gida a Malali, tayi Parking ta koma chan, tana me kewan Safiyya da ta sha kuka ranar rabuwar su. Bayan wata 1 Su Maalesh sunyi Graduating, suna ma jiran ayi posting dinsu Service (Bautar kasa). Rafeeq ya kira Zaid a waya, Zaid yayi mamakin ganin kiran wayan shi, da sauri ya amsa, kamar ba zaiyi magana ba Rafeeq yace "an fara registeration, nayi, idan anzo 2nd Semester zan koma Makaranta" dadi kamar ya kashe Zaid, ya dinga shima Rafeeq Albarka, yasan yayi hakan ne don shi, don ya sa shi jin dadi, kuma ya sa shi din". A yau Asabar Safiyya Matar Zaid ta haifi diyarta Mace kyakyawa Kamar Rafee'ah, Jini ba wasa ba, Murna gun Zaid kamar ya rungume Iska, Ranar Suna aka radawa diya Suna Rafee'ah, yan Katsina sunzo suna, Sanin zasu zo ya sa Mami tak'i Zuwa sunar tayi zaman ta Gidanta, Rafeeq ma ya zo, ya dauki diya ya rungume yaji sinta har cikin jinin jikinshi, dadi biyu, Ga ta jinin mafi soyuwar Halitta Uncle Zaid, ga ta da Sunar Rafee'ah. Bayan Yan suna sun watse Safiyya jini ya barke wa Safiyya, ta fara tsinkau tsinkau,Zaid ya tsorata matuka ya danna kiran Aunty Aisha, suka dunguma suka kaita Asibiti, Nan dai Safiyya tace ga garin ku nan. Inalillahi wa ina ilaihir rajiun. Bayyana Rudun da Zaid ya shiga bata baki ne, kowa ya ji mutuwar Matar Zaid Safiyya, sai dai mu roki Allah ya sa Aljanna ce makomarta. Zaid ya Zare kamar zautattace, don yana kaunar Matarshi fiye da tunani, yana tausayin su shi da diyar shi Rafee'ah-Ayman, Rafeeq da Baban shi da Maalesh sunzo janaizar, sun sauka masauki, Meema ji take yau Sallah a gunta don ba karamin farinciki mutuwar matar Zaid tayi ba. Kwana 3suka tafi, banda Rafeeq da yace shi zai tsaya da Zaid don yasan yana bukatar shi, kamar Lokacin suna, Mami bata bari sun ganta ba, sai Bayan da suka tafi ta dawo gidan Zaid tana kula da diyar shi. Rafeeq ya fito daga mota ya shiga gidan Uncle Zaid, Kai tsaye yayi Parlor, Tsaye ya ga Fuskar da ba zai taba mancewa ba, Fuskar Mahaifiyar shi, tsaye take rungume da jaririya, Jikin Rafeeq ya hau kyarma, idon shi ya rufe da sauri ya je ya fizge Rafeeah-Ayman, daga hannun ta, ya rungume ta, Zaid ya mik'e da sauri yace "Rafeeq" yace "me wannan Matar takeyi a gidan nan? Har ta ke taba min k'anwa? Zaid ya sausauta murya yace "Shes been here for a while" Rafeeq cikin bacin rai yace "and you never bothered to tell me? Zaid yace" coz u never asked, u never wanted to talk about her" Idan har kana so ka kara ganin kafana a gidan ka, This woman has to leave, bana so in sake ganinta, kar kuma ki sake daukar min kanwa don kar ta koyi baki da mugun halinta" Zaid ya kaura mai Mari, ya nuna shi da yatsa" I wont let you disrespect your mother" Baby ta fashe da kuka, Rafeeq ya rungumeta, be damu da marin da ya sha ba yace "yi shiru kinji fee'ah, zan samo miki me raino, mace mai mutunci ba kamar wasu matan ba" Zaid yayi saurin kwace diyar shi daga hannun Rafeeq, yace "bata da wata mai raino da ya wuce Mami, ba ta da Uwa da ta wuce Mami, itace Uwarta, duk me zakayi kayi" Rafeeq ya kalli Mami da fuskarta yayi jazir saboda kuka yace "Ba zaka sake gani na a gidan ka ba" ya fita a fusace, Mami ta bishi da gudu tana "Rafeeq, ko kallonta beyi ba" Zaid ka bishi kar ya dauki hanyar Katsina yanzu, kar wani abu ya same shi" haka Zaid ya bishi a hanya, ya dinga lallashi, da yake Rafeeq din be iya fushi da Zaid, nan da nan ya sauko amma dole ya bar Kaduna a ranar ya wuce Katsina a ganin shi zaman shi be da amfani. Bayan Shekara Daya (A gurguje) Abubuwa da dama sun faru a shekarar da ta gabata, Kamar yanda Sauda ta sha k'okarin Kashe Rafeeq ta hanya da dama bata samu nasara ba, har ta hakura ta barshi na wani lokaci, kila yayi amfani, Daga abubuwan da suka faru, ciki kuwa har da Spilling din da Rafeeq yayi a Makaranta, an rasa gane dalilin spilling dinshi, don an binciko takardun shi an ga Yayi passing, an rasa ta ina aka samu tangardan(Ni dai nace Boka na kan tudu), Rafeeq kuwa ko a jikin shi, dama da Uncle Zaid ya koma karatu last year, amma yanzu ko sama zata hade da kasa ba me sashi komawa School, Su Maalesh sun fata bautar kasa.Zaid yayi Mamaki matuka, dole kenan sai ya sake dawowa? Matsalar shi daya yanda zaiyi convincing Rafeeq ya sake wasting shekara daya, Sai da Zaid ya hada da kuka kafin Rafeeq ya amince da zai sake dawowa, da sharadin idan ya sake failing ba shi ba boko har abada, Zaid yayi saurin Amincewa da hakan, a ganin shi Wannan karon akwai nasara. A wannan karon ne Seebin Nene suka Shiga Jamiar Umaru Musa Yaradua. *Wacece Alheri?* Ta yaya ta zama Alheri? *Shin Sauda zata cigaba da Samun Nasara a duk abunda ta sa gaba?* *Rafeeq na tava dawowa daidai kuwa?* Da tambayoyi da dama da kuke son amsoshin su, ku biyoni sannu a hankali. *********** CIGABAN LABARIN. 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg3⃣2⃣ *UMYU Katsina*. "Nasiba Muhammad, maabociyan sa nikab, yanzu da hukumar Makaranta tayi hani da sa nikab sabo da matsalolin tsaro ya zakiyi?" Miemee ce ke maganar nan, ta na yi tana daria, Ushee tayi saurin shafewa tace "Ahh, k'ila zata daina zuwa Makaranta, yajin aiki zasuyi ita da yanuwanta Ustazai masu sa Nikab" suka sake fashewa da daria. Nasiba ta dan harare su, tace ba abun daria bane "Dollah ku bar dariya, its not like its funny, ni ban ga amfanin hana mu sa Nikabi ba, idan yan Boko Haram din sun tashi shigowa Makaranta Nikabi zasu saka?" Miemee ta sake fashewa da wani dariyan tana cewa "Seebi dangin Shekau" Ushee ta tuntsire da daria, duk suka k'ular da ita, ta san cewa idan ta biye musu zata iya fashewa da kuka, sai ta tashi ta bar musu Ajin, su kuma daria taci k'arfin su, sun kasa bin ta. Tafiya takeyi tana mita, R-Classes ta nufa, hanyan da tasan ba kowa ta bi, tana ta tafiyar ta ta na tunanin yanda zata cigaba da zuwa Makaranta ba Nikab taji kamar K'andagare ya hau ta, wani irin tsalle ta daka sai ta ji ta buge wani abu, a firgice ta dago, tsoro ya kamata da ta ga R-Lema, yana lulaya goshin shi don anan ta kaimai karo, ta tattaro nutsuwar ta tace "donAllah kayi hakuri, K'andagaru suka biyo ni, ban ganka a gabana ba, sannu kaji? rabawa yayi ta gefenta ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, Mamaki ya turnike Nasiba, a baiyane tace "shi kuma wannan wane iri ne?". *Malali, Kaduna*. "Ayman, ga Daddyn ki" dugul dugul ta tako tana ta washe baki, Zaid ya daga ta ya wulla ta sama ya chafe, ya rungume ta yana juyi da ita, ita ko sai dariya take tayi. Mami da ke kallon su tace "ka ga, kar ka sake min d'iya ta fadi" Zaid yayi daria, yace wane ni in kada diyar Mami?dariar tayi tace "ashe kana tafe? Ya hanya? Ya yan katsina? Yace "Alhamdulilah suna ta gaishe ku" tayi dai murmushi don ta san in banda iyayenta ba wanda zaice a gaida ta, tace "barin dora ma ka abinci, nasan ka gaji" yace "Wallahi kuwa Mami, Yunwa nikeji banyi breakfast ba na taho" me kake so kaci? Yace "tuwo miyan kuka" tace "ahh ba yunwar kakeji ba, tuwo ai zai dauki lokaci" yace "Wallahi ina jin yunwa, amma ina iya tsayawa har ayi tuwon" tace "sai dai daddawata ta k'are" ya mike tsaye yace "kar ki damu na miki tsarabar daddawa da kuka, duk sun bide min mota da wari, Wallahi kiris ya rage na wurgar dasu, ashe zasu min rana" be jira ta cewarta ba ya fita, Ayman a hannun shi, har ya bude mota ya dauko ledar k'ullin ya dawo, ya mik'a mata, ta bubbude tace "Zaid wadannan kayan daga ina? Yace " Wallahi wata tsohuwa ta bani" Tsohuwa kuma a ina? Yace "a Katsina" tace Zaid ka santa ne ka amshi wadannan abubuwan? What if shes upto something, number 1 lesson, u cant trust people?" Yace "Relax, i trust this one, i trust Nene, yanzu dai ki sa daddawan da yawa, miya ya fi dadi" Mami ta kwashi ledar ta na mita, tace "yanda na ga dama haka zanyi, in kayi fushi kayi aure and stop ordering me around" Daria yayi sosai yace "yi hakuri Mamin mu". Haka Mami ta gama tuwo miyan Kuka da ya ji busasshen kifi, Zaid ya ci sosai, yaji dadin Miyar nan, ita ma Mami taji dadin Kukar, daga jinta sabuwar kuka ce, sai santi suke tayi, Mami ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen shi kuna Zaid yac cigaba da ma Ayman wasa, Yarinya kyakyawa sosai, yar shekara 1 da yan watanni, idan ka ganta za kayi zaton tayi 3years din nan, sabida yanda take yar b'ulb'ul da ita, kuma ba wai Nono ta sha ba, bayan Rasuwar Safiyya Madara ta ke ta sha, NAN kuma aka ci saa ya karbeta, Dangin Mahaifiyar ta sunso su amshe ta amma Zaid ya hana, yace shima Mamar shi(Mami) zata riketa, haka suka hakura, Little Rafeeah na zaune tare da Mami a unguwar Malali, kullum Zaid sai yazo ya duba lafiyar su kafin ya tafi Gidan shi, yana tausayin Ayman, amma idan ya tuna tana tare da Mami sai hankalin shi ya kwanta don ya san Ayman ba za tayi maraicin Uwa ba. *KATSINA* "Me ya samu Nasiban Nene na ga ranta a bace haka? ko shi lapturo(lecturer) din ku ne ya bata miki rai gobe in mishi asubanci inji dalili?" ba ta san lokacin da ta fashe da daria ba, tace "Nene, Wallahi Hukumar Makaranta ce wai mu daina sa Nikabi saboda k'asa ba lafia, ana iya yin Basaja a shiga Makaranta ayi barna" Nene tace "kai sun kyauta, ba ki san yanda na k'ijinin in ganki da nikabi ba, kamar wacce tayi k'arya, ke da ba tsiraicin kika fiddo ba, amma duk ki rufe fuskar ki ruf" Nasiba ta shagwabe fuska tace "Kai Nene, so kike ranar Makaranta ta kodar dani? Kuma mutane suyi ta kallo na?" Nene tace "ke tafi chan, yo ai sai ki shafe fuskar ki da hoda, kuma in ta kallo ne ai kin kai a kalleki, yar jikalle ta jikan Yan Sudan, donAllah ki dinga gyara fuskar ki kamar wannan yar gayun, Meemo take ko wa?" Nasiba ta fashe da dariya, ta tashi ta yi hanyar daki tana cewa "Miemee ake cewa ba Meemo ba" Nene tace "ni rabani da sunan Aljannu, yarinya da sunan ta me dadi Maryam ta koma wata Meemai ko wace tsiya" ita dai Nasiba daga cikin daki take ta daria, Nene ta cigaba da Mitar da idan ta fara bata san tsa tsaya ba, "kema Baban ki ya bata miki suna wai ba a iya kiranki da sunan Yankan ki sai Seebi har ya koya min nima" a hankali tace "Amma fa sunan fa da dadi, na yan gayu, Seebi, Seebin Nene" me Nasiba zatayi in ba daria ba. Nene ma ta sa daria ashe ta na jinta, ta mik'e tana fadin "Uban me ake ma daria cikin k'urya?". Maalesh ya fito daga Motarshi da ya parka ta a haraban Gidan su Rafeeq, Aneesa na ganin shi ta k'araso da sauri tana yauk'i tana karairaya, Maalesh ya fara mata murmushin da be kai zuciyar sa ba, " Yaya Maalesh, howfa" yace "Anee baby ya kike?" Lafiya fa, dama ina so in kara maka tuni kan Yaya Rafeeq, Wallahi son shi na cinye min yan Hanjina, na rasa me na mishi da ko ganina ba ya son yi, idan na je gurin shi yanda kasan yaga bak'ar Jab'a, kallon arzik'i baya min, gashi zuciya ta ta kasa hakura dashi, ya zanyi?" Maalesh da ya k'osa ta gama maganar ta don warin gashin dokin ta ya cika mai hanci, yace "karki damu zan mai magana" dadi ya rufeta, kafin tace wani abu Maalesh yayi gaba. "Guy Yane?" Rafeeq ya dago kai ya kalli Maalesh da ya shigo yanzu, da k'yar yace "Normal" Maalesh yace "ba ka kirani nazo nayi picking dinka yau ba?" kamar ba zai ce komai ba yace "Da mota naje" "Ohh, is that so?" nan Maalesh ya shiga bashi labarai, abubuwan da suka faru da friends din su, har zuwa inda Aneesa ta tare shi, Rafeeq dai be ce komai ba ya cigaba da latsa wayan shi, Maalesh be damu da shariyan Rafeeq ba don inda sabo ya saba, wasu lokuttan Maalesh na bashi labarai ne ba don yaji ta bakin Rafeeq ba, kawai don dai Yayi keeping dinshi Company, kasancewar he's alone, Ba wai Rafeeq be gane Labaran da Maalesh ke badawa bane, tsaf ya ke fahintar shi, don wasu lokaci idan Maalesh ya bashi daria ya na dan murmusawa abu kadai ke mai wuya, Magana. Ya na jin k'yuwan Magana, yana ganin Asaran Yin magana. "Sis nikam Nagaji, ya zanyi wai da son Zaid?" Sauda ta kalli kanwar tace "Meema, dont give up so easily, kafin ki samu abun da kikeso dole ki wahala, kar ki manta wahalar da na sha kafin na samu kaina a Gidan nan, kar ki damu, ke dai kawai ki cigaba da jawo hankalin shi" wani Jawo hankali? So nawa kuma? Ai ni ina ganin idan har na yi Zindir gaban Zaid ba zai ji na burge shi ba" Sauda tace kar ki damu in ya san wata, be san wata ba". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) 3⃣3⃣ Wannan Pagen Naki ne *Aunty Sady Yar Mutanen Jegal*, Nagode Da Kaunar da kike nuna min, Allah ya bar Zumunci Amin😘😘. *UMYU Katsina* Kallon wurin da ta ci karo da R-Lema take tayi da suka zo wucewa ita da su Miemee, kamar ance ta waiga ta ganshi Zaune kan dakali, ba Waya, ba littafi ba komai da ke taya shi hira, shi kadai tal, Miemee tace "Lahh, ku kalli Azababben gayen nan na rannan, Usheey ta kallo shi, Seebi dama shi take kallon, Miemee tace " Wallahi sai naje mun gaisa" Nasiba tace "Uhm uhm Miemee ina jiye miki Wulak'anci" Miemee tace "haba Seebi ba kalar mu bane a ke Wulakanta wa, just watch me" ta gyara zaman rigar ta tana karairaya ta nufi R-Lema. Kusa dashi ta zauna tana cewa "Sannu fah" kallo daya ya mata ya dauke kai, Miemee bata damu ba tace na ga kai kadai ke zaune, its seems you are lonely, shiyasa nace barin zo in taya ka fira. Rafeeq ya tashi tsaye ya bar mata gurin a ranshi kuwa cewa yayi "wannan ta cika hayaniya" Me Nasiba da Usheey zasuyi? In banda Daria. Miemee ta k'ulle iyakar k'ullewa, tace to meye abun daria, cewa yayi yana da lecturers, Nasiba tace "kaii Miemee, muna fa kallonku, ko A be ce miki ba" Usheey ta kara tuntsirewa da daria, Miemee da haushi ya kamata ta harare su tace "to sai me?" tayi gaba, suna daria suna binta a baya don abun ya basu laugh. *Malali Kaduna* "Waalaikum Salam" Ummi ta amsa Sallamar da taji daga waje tare da fitowa, "Ahhh Mamin Ayman ce da Ayman? Sannun ku da zuwa" da sauri ta koma ciki ta ciro tabarma. Mami dake dauke da Ayman a hannu kuwa tana ta murmushi, Ummi ta fito ta Shimfida tabarma tare da umurtan Mami ta zauna, suka gaisa. Mami tace "wato Ummin Anan, na ganeki, bakya son shiga gurina ko? Gashi Allah ya riga da ya hadamu, ko Anan ba kya turomin yazo tayamu fira, ko ba ki san Hak'k'in Mak'otaka bane? Ummi tayi Murmushi tace " Wallahi ba haka bane, abubuwan ne sai a hankali, kiyi hakuri zamu dinga shigowa" kafin su k'ara magana Wayar Ummi dake kan window tayi ringing, Ummi ta mik'e ta dauko wayar, Seebin Nene ta gani a jikin Screen din, ta dauka da Sallama, daga chan aka amsa, Ummi ina wuni? Ya gida da kowa da kowa? Lafiya Alhamdulilah, ya karatun ki? Muna tayi Alhamdulilah, toh Allah ya bada sa'a, ina Anan?yaje Islamia, ina Nenen? gata nan, Nene ta amsa wayar da cewa "Halo, Dije, ince dai kuna lafiya? "Lafiya lau Nene" Ina Mahammadu? tace "ya fita" Nene tace "to kice mai jiya kiris ya rage muyi gobara, wannan abun chanza layi yayi ta k'auri, ni kadai cikin Gida kamar Mayya, lokacin Nasiba na Makaranta, ina ta bacci kawai naji abu na k'auri, da kunji sak'on mutuwa ta, ko da ka fito wajei neman taimako sai da na share kusan minti 30 waje banga ko akuya yazo wucewa ba, sai ga Zaidu bawan Allah har da mai gyara ya kawon, Na dade ina gaya ma Mahamadu bani son unguwar nan, ba mutane, wai sai yace "Haka Unguwan yan gayu suke" yo ni ina ruwana da wata Unguwan Gayu? Yanzu da ba dan Zaidu bawan Allah ba, da gidan nan ya kone kurmus" Ummi tace "SubhanAllah, Allah shi kyauta gaba ya kuma kare" Nene ta cigaba da mitar ta "daidai da burodi idan zaka saya sai ka taka har bakin titi, k'osai kuwa sai kin ci uwar tafia zaki ga mai k'osai, ni na saba Unguwar mu ta da, duk lungu da sako akwai mai k'osai, ko tari nayi zaa jini a Mak'ota, nidai gaskia ba zan iya ba, a maidani cikin Mutane, ba na son Unguwar nan na masu k'arya". Ummi ta karai da murya tace Nene kiyi hak'uri zan sanar dashi InshaAllah, za'a samu Mafita". Nene cikin tsegumi tace "Ai gwara a samu Mafitan, kuma kice--" Nasiba tayi saurin kwace wayar tace "Laahh, Katin sun K'are" tayi hakan ne don ta san Nenen ta da mita, idan ta kama zance bata san ta tsaya ba, ko bari batayi sun gaisa da Umminta ba da kyau, aiko zata sake kiranta da ta k'ebe. Ummi ta kalli Mami tace " hakuri Mamin Ayman, ina magana da surukuwa tace, Mami da ta gama jin Zancen Ummi na waya, kasancewar Wayar China Phone ce. Mami tace " Bakomai, najita akwai barkwanci, wani gari take ne? Ummi tace tana Katsina, diyata na chan tare da ita, tana karatu a Jamiar Garin. Mami taji faduwar Gaba don duk yanda taji an ambaci Katsina sai ta jita wani iri, balle wannan da taji wani bak'on almari na ziyarta tace "Allahu, Ayman zo mu tafi Gida" Ayman da ke ta wasa ta gunguro gun Maminta Ummi ta musu Rakiya har bakin kofa. Bayan Wau 'yan kwanaki. *Katsina* Zaid ya shigo Unguwar su Alhaji Habib Lema da misalin k'arfe 3:30pm, yana tuk'in shi cikin kwanciyar hankali Daidai Gidan Nene ya tsaya ya parka Motar shi, bari ya shiga ya gaida Nene, ya fita ya shiga Soron Gidan da Sallama a bakin sa, "Assalam Alaikum" Wata siririyar murya yaji ta amsa mai Sallamar shi, Hijabi ta jawo kan igiyar shanya, tana me mamakin yau waye a gidan su? Lek'awa tayi ganin Zaid tayi tsaye ya, shima kallon ta yakeyi, ji takeyi kamar ta sanshi wani gurin, shikuma kallo daya ya mata ya gane ta, itace ya taba lift ita da kawayenta kwanaki, Sansayar Murmushi ya mata yace Seebi? Da sauri tace Ina wuni? Ya amsa mata, cikin wasa yace "Me kikeyi a gidan Kakata?" ta zaro ido cikin sanyinta tace "Nenen ce Kakar ka?" Dariya yayi yace "ehmana" daga ciki Nene ta fito, Nasiba ke da waye ke ta dumi a waje? Cikin murna tace "Lahhh, ga Zaidu bawan Allah" da sauri ta rik'o hannun shi har cikin Gida, tace da Nasiba "ke dauko Tabarma ko darduma" da sauri ta dauko ta shimfida mai, "Zaidu Sannu da Zuwa, kazo lafiya?" Nasiba dai ta bisu da kallo, tana ta kallon ikon Allah yanda Zaid da Nene suke ta labartawa, "Nasiba baki san shi ba ko?" ai Shine Zaidu bawan Allahn da bakina ya kasa daina ambaton shi, wanda ya taimaka mana randa muka kusa Gobara, Nasiba tayi murmushi tace "Allah Sarki, Nene ta bani labarin abun da ya faru, Mungode da taimakon da ka mana, Allah ya saka maka da Alheri" har ranshi yaji dadin adduarta gareshi, yace ai Seebi mun taba haduwa kece dai ba ki gane ni ba" tace "ni? A ina?" yace wata rana ba a wuce Sati 2 ba, na dauko daga wajen Umaru Musa, na a je kawarku wurin Motel, ku biyu kuma kukace in sauke ku a Salamah, kin tuna? Nasiba ta zaro ido, Tabbas kaine, na tuna, dama nima ina ta tunanin inda na sanka, nan fira ya barke, idan kaga Nasiba, Zaid, da Nene na fira sai ka rantse sun dade da sanin juna, Nasibar da ta ke da wuyar sabo, bata da saurin sabo, sai gashi nan da nan taji ta sake da Zaid, haka kurum taji Zaid ya samu gurbi babba a zuciyar ta. Sai da Zaid yaci Burabiskon Da Nene tayi kafin ya musu Sallama ya wuce Gidan Yayan shi. "Assalam Alaikum" bakin shi kadai ya kalla ya san ya amsa Sallamar, da ka kalleshi ka san yaji dadin ganin Zaid, amma ya kasa nunawa, Zaid dai ya Zauna, yace "R-Lema" da k'yar Rafeeq yace "Sannu da Zuwa?"" yauwa Rafeeq ya kake? Ya skul? Sai da ya dauke shi Seconds kafin yace "Alhamdulilah" "Kaci abinci?" kai kawai ya daga mai tare da nuna mai Ledan take away din da yayi a Crispy. Zaid ya jinjina kai yace "akwai wata matsala? Ko akwai abunda kake so?" Rafeeq ya girgiza kai alamun aa, Zaid ya mik'e tare da dafa Rafeeq yace "Good" bari in k'arasa cikin Gidan isowa ta kenan, Rafeeq bece komai ba, har sai da Zaid ya kusa barin dakin ya cire baki yace "Ya Rafeeah-Ayman? Zaid ya juyo da murmushi yace "Shes fine, tana Gaida Yayan ta" Murmushin gefen kumatu Rafeeq yayi, ya dauke duban shi daga Zaid don kar ya mishi wata magana da zai bata mai rai (kun dai san Maganar ko? Maganar Mami). Meema na ganin Zaid da zuro a guje zata rungume shi, da sauri Zaid ya ja gefe yace lafia? Cikin kissa tace "Uncle Zee, naji dadin ganin ka ne, nayi ta kiranka ba ka dauka ba, na Kuma kace mana zaka zo ba, da kyar yace "i was driving" ya yi saurin hayewa Sama don ya k'i jinin Meema, wani irin warin Man bleaching da gashin doki takey tayi. Meema taje ta barbade jikin ta da turaren da boka ya bata, wanda yace "idan har Zaid ya shak'i kamshin, to sai yanda tayi da shi, Zaid juwa ya shiga ya gauda Yayan shi, Sauda na zaune tace " a kawo maka abinci?" ya danyi murmushin yak'e yace "aa Nagode" ta kalli Mijinya cikin Kissa tace "ka ganshi nan Alhaji, ni bansan me na mishi ba be cin abincina, be taba ci ba, haka zai kamo hanya tunda daga Kaduna, amma ko ruwan Gidanka be sha" Zaid ya dan wayance yace "Wallahi sai na cika ciki na kafin nake k'arasowa nan" Alhaji Habib dai ya murmusa yace "kun fi kusa" yauwa Zaid, ya karatun Rafeeq? Kasan idan be ci Exams din nan ba Spilling na 3kenan zaiyi ko?Mates dinshi daga masu Service sai masu Aiki" Zaid yace " Yaya, Rafeeq zaici Exams dinnan da yardan Ubangiji, this is his last year a School, just have faith" Alhaji Habib yace "Allah shi yarda" Sauda a ranta tace "sai mu gani" Zaid ya musu Sallama ya sauko k'asa. Meema na ganinshi ta k'araso, Da sauri Zaid ya toshe hancin shi saboda wani irin warin tashina hankali da ya ziyarcin hancin shi, Meema meye ke wari haka kamar Jab'a?" tace "Jaba kuma?" Zaid yace "sai anjima idan na tsaya a nan Kaina zai min ciwo" da sauri ya bar gurin takaici ya hana Meema bincshi, wai ita ke warin Jab'ar ko turaren? Ta fashe da wani kuka mai tsuma rai. *UMYU KATSINA* Jugum jugum sukayi suna neman mafita, Awan su 3 a Library, suna neman yanda zasu yi Solving wannan Assignment dinsu na Calculus, gashi 5 ta wuce, gashi da Sassafe karfe 8 zaayi Individual Submission a Office din Course tutor, kuma yace idan suka kwafa na juna zai gane, Ana tsoron Malamin da Course dinshi kasancewar dangin Maths ne, ana samun Carry Over da yawa, hankalin daliban da keyi a tashe, ko wannen su ya dage yana iyakar k'ok'arin shi, gashi 5 har ta wuce, ba yanda Miemee Usheey da Seebi zasuyi illa su wuce Gida don Maghrib ta k'arato, Miemee tace zata ba lesson teacher din k'annenta ya mata Solving, Usheey kuma tace " Zata duba cikin Note book din brother dinta shima yayi Course din lastyear, idan Allah ya sota ta samu, Nasiba da idon ta ya ciko ruwa ta kasa magana, don bata da wata mafita, ta tsani CarryOver amma ta sadakas ta fadi course dinnan, dole sai ya dawo mata Next Year. haka suka wuce Gida. K'arfe 7 Zaid ya Shigo Gidan, tunda ta gaishe shi bata sake magana ba ta cigaba da Kallon Takardanta kamar ansa zai fito, Zaid ya zauna kusa da Nene, yace "yau Seebi boko ake ta sha? Yau ba a ma Nene Fira?" Nene tace rabu da ita 'yar nema, ka ganta nan tun dazun nake ta magana ta min banza, tunda ta dawo take ta rubuce rubuce tana yaga takarda, ko abincin kirki ta kasa ci, shine kagan mu zugum zugum kamar kurma, ina ta Addua Allah ya kawo mun kai. Yayu daria, yace "Seebi Assignment ne halan?" tace "Wallahi Uncle Zaid, part of our CA test ne, kuma ban iya ba, tun dazun nake ta solving amma na kasa, yace "mugani" da sauri ta mik'a mai ya bude baki "lalala, Calculus, tabdi, ai ko lokacin da mukayi Calculus da k'yar nayi passing course din yanzu ko ko kasheni zaayi ba zan iya cewa ga yanda akeyi ba" hawayen da take makalewa suka gangaro, Zaid kadai ne hope dinta, gashi shima be iya ba, Zaid ya lura da yanayin da ta shiga yace "yaushe zaayi Submitting? ta fashe da kuka, Zaid ya rude yace " Calm down ki kin magana" tace "Gobe da Sassafe before 8, kuma individualy yace don zai gane idan mun kwafa daga junan mu". Zaid yayi shiru for sometime, wani tunani yazo mai, amma yana gudun abunda zai faru, amma kuma dole ya taimaki Nasiba don tana bukatar taimako shikuma yana da halin taimaka mata, ba tare da tunanin me zai faru ba ya ciro wayar shi ya latso Numbern Rafeeq. Kamar ba zai daga wayan ba ya dauka ba tare da cewa komai ba, Zaid yace " Hello Son" chan k'asa Rafeeq yace "Yeah" yace "kana Ina?" da kyar yace "gani nan zanje gidan su Maalesh" "donAllah i need your help" Rafeeq yayi saurin cewa "Menene are you ok?"don yaji Uncle sounds so serious, Zaid yace "i'm fine, i need you to come back, daidai kwanar Gida kafin kaje Salamah, Please" be bari yace komai ba ya kashe wayar shi ya na rok'on Allah ya sa yazo" Nasiba ta tsare shi da idanuwa, yace "Nephew dina ne, ina ganin Zai iya miki Solving problem dinki" Dadi ya lullube Nasiba, Mintuna 45 suka shude, ba Rafeeq ba alamun shi, Nasiba ta damu kwarai, Zaid kuwa ya cire rai da zuwan Rafeeq, don har yace ta miko mai ya gani yayi trying solving din. Kirrrrrr Wayar Zaid tayi Ringing, da sauri ya dauka ganin Rafeeq, "Hello" Chan k'asa yace "Nazo kwatacen" da sauri Zaid ya zura takalma yace gani nan fitowa. Daga nesa ya ga Rafeeq, da sauri ya k'arasa gunshi, "Rafeeq thanks for coming" Rafeeq be ce mai komai ba illa binshi da yayi da ido, alamun ka min bayani, Zaid kuwa yak'i cewa komai don ya san Halin Rafeeq, yana iya ce mai wata zaiyiwa Assignment yace ba zaiyi ba ko kuma yace be iya ba k'arshe ya tafi ya barshi, shiyasa Zaid be ce komai anan ba, k'ila idan a chan ne yaji kunyar Nene da Nasiba ya mata, duk da ya san ranshi sai ya baci, yace "please ka biyoni, ganin asarar cewa ina zamu?ko me zanyi? Yasa Rafeeq bin Zaid a baya ba tare da ya ce uffan ba, har Soron Gidan Nene, Zaid yayi Sallama, cikiciki Rafeeq yayi Sallaman shima Nene ta amsa, Zaid na gaba Rafeeq na biye dashi kan shi a k'asa, Nasiba na ganin R-Lema tayi Zumbur ta tashi tsaye, Nene tace "Lahh Zaidu Bawan Allah, wanene wannan me kama da kai?" kallo ba ta ishe Rafeeq ba, Zaid yace "Rafeeq ba ka gaida Nene ba" ba tare da ya kalleta ba yace "ina wuni"ciki ciki Nene ta amsa tana mai wasa, dauke kai yayi ya sauke shi kan Nasiba, kallo daya ya mata ya dauke kamar be taba ganin me irin halittar ta ba, Rafeeq da ya k'osa yaji me ye amfanin zuwan shi gidan nan ya kalli Zaid cikin tuhuma, Zaid ya k'i yarda su hada ido, don yasan shi yake kallo, ba tare da ya kalli Rafeeq ba yace "Son, Assignment ne ya gaggari Seebi, nima na gwada tawa fasahar na kasa, nasan you are in good in Calculus, shine nace bari in kiraka ka taimaka mata DonAllah" Waiyo Allah kuzo ku ga bakinciki kwance kan fuskar Rafeeq ji yake kamar ya dora hannu a kai ya sa ihu saboda takaici, wai me ya sa Uncle Zaid ke mishi hakane? Zaid kuwa har yanzun ya ki kallon Rafeeq din balle ya san halin da yake ciki, "I am sorry" ya furta a hankali don ya san Rafeeq din shi yake kallo. (Readers me kuke ganin Rafeeq zaiyi? K'ila tafiar shi zai yi ba tare da yace musu komai ba, don da Alamu Uncle Zaid ya gama kashe Rafeeq) _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg3⃣4⃣ Kusan Mintinu Biyu Rafeeq na tsaye, shi be ce komai ba shi be tafi ba, Nasiba ba tayi mamaki ba, don ta san halin Rafeeq na shariya da k'yaliya, Nene kuwa ido ta sa ma Rafeeq ta kasa gane me ke shirin faruwa, har Yanzu idon Zaid na kallon Gefe, Rafeeq da takaici ya gama rufe shi ya hau tunani, tabbas da wani ya mai abunda Uncle Zaid ya mishi da ba abun da zai hanashi barin gurin, Amma Uncle Zaid ne, ya fi K'arfin Wulakanci a gunshi, ajiyar zuciya yayi ya mik'a ma Nasiba hannu kamar me rok'o, Nasiba tace me zan baka? Rafeeq ya dan yi guntun tsaki, Zaid yayi saurin kallon su yace da Nasiba "bashi question Paper din, da sauri ya dauko ta bashi, ya amsa ya karanta, a ranshi ya yi tsaki yace Question din is straight forward, i dont knw why some people are dumb, ba su san komai ba, ji wannan simple Question din,(ni bibi nace ba kowa bane kamar ka ba dan rainin wayau) wata zuciyar tace harda Uncle Zaid fa, a ranshi yayi dariya, amma a baiyane fuskar nan tamk'e tamau. Kan tabarman ya hau, ya ciro biro cikin wandon shi, ya duk'a ya fara solving question din, tunda ya fara rubutu be dago ba sai da ya gama, yana gamawa kuma ya mik'e ya zira takalman shi ya bar Gidan. Zaid ya bishi da sauri, Nene da Nasiba suka bishi da ido, ita Nene Mamakin Wannan yaron Zaidu BawanAllah take, a ranta tace ko kurma ne? Nasiba kuwa Mamakin da takeyi yanda tafi Awa 5 tana kokarin yin wannan Assignment din ta kasa, amma shi cikin mintinan da basu wuce 7 ya gama komai, lallai ta jinjina mai, shiru-shirun shi ba a banza ba tunda ya san abunda yakeyi, haka kurum taji Rafeeq ya burgeta, ta durkusa ta dauki Papern, rubutunshi ta bi fa ido, neatly kamar irin rubutun Computer, tabi steps din da yabi, taga abun very clear, kawai sai ta tsinci kanta da Murmushi a hankali ta furta R-Lema. Nene da ta zuba mata ido, tace "Toooooooh, ke kuma gamo kikayi? Nasiba ta fashe da daria. Ko da ya fito har Rafeeq ya kai bakin motar shi, Zaid yace "Rafeeq" chak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, Zaid ya iso har gabanshi yace "ka saurareni, nasan na maka laifi, na maka karambani, kayi hak'uri" dan guntun tsaki Rafeeq yayi ba dan komai ba don Zaid zai sa shi magana yace "ka isa da ni ne, bakomai, stop apologising" ya shige mota ya ja ya bar Zaid tsaye, Zaid kuwa dadi ne ya lullube shi, lallai Rafeeq is improving, shi a zaton shi fushi zaiyi dashi, amma Rafeeq ya bashi mamaki kuma yaji dadi, a ranshi yace"Allah ka kawo ma Rafeeq Sauyi" ya juya ya koma gidan Nene. Ya na shiga Nene ta tare shi da maganar Rafeeq, "Nace Zaidu Bawan Allah, shi wannan fa?" Zaid yace "Dan Yaya na ne" Nene tace baya magana ne? Ko kurma ne? Zaid yayi murmushi yace "yana Magana" Nene tace "to ya na ganshi haka kamar wani Zararre, ji uban gashin da ya ajiye, ko ni Mace ya fini, shi ko bai da lafiya ne?" Nasiba ta kasa kunne don jin me Zaid zaice don ta na san sanni meyasa Rafeeq yake haka, Zaid yace "haka yake, miskili ne" Nene ta jinjina kai tace "Lallai kam naga Alama, Shekaru na 68 ban taba ganin Miskili kamar shi ba, ya ci a bashi Sarkin Miskilai" Daria sukayi duka, Nene tace "Bari in tashi in zubo maka Tuwon Masara miyan kuka da na dafa maka" Zaid yayi murmushi yace "yauwa Nenen mu ni da seebi kadai". _Bayan kwanaki Biyar_. *UMYU Katsina* "Nasiba Muhammad, MCB 1220" Gabanta ya buga ya fadi a lokacin da Course Tutor ya sake kiran sunanta a karo na biyu, a hankali Miemee tace "Seebi ke fa ya ke kira" jikinta ya hau rawa sosai, idonta ya ciciko da hawaye, ai ba inda zataje, kuce bata zo ba tunda ba sani na yayi ba, cikin karaji lecturer yace "Where is Nasiba1220?" bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba saboda ya firgita ta sosai, yace "are you Nasiba?" kai ta daga alamun eh, yace come down here, gabanta ya tsananta faduwa, bata san me tayi ba, k'ila batayi assignment din ta da kyau ba, jiki na rawa take tafia, all eyes on her, haka ta daure ta karada gaban stage, karo na farko da ta fara missing Nikabin ta, ta tsaya gabanshi, ya mika mata Marker bayan Yayi copying Question din da ya basu, yace "solve this"Nasiba tayi Adduoin ta ta fara rubutu kan Board, dama tayi mastering Solution din da Rafeeq ya mata, har sai da ta gama komai, Lecturer ya ciro scripts dinta ya mik'a mata, ta amsa ido ta zaro, *20/20* tagani murna ya ziyarce ta, yace "give her a round of applause" Aji ya kaure da tafi raf raf raf. Yace shes the only one that scored 20/20 apart frm her none of you made it to 15/20, am proud of you" A hankali tace "thank you sir" ya zaro 2000 a aljihu yace "have this" da sauri tace "no sir, you dont have to This" ya tsare ta da idanuwa ta amsa tayi godia, aji suka tafa mata, kamar ance ta lek'a window, tana lekawa ta ga Rafeeq ya zo wucewa, ta kalli Lecturerr tace "excuse me please sir" da murmushi yace Goon my dear, da sauri ta fita daga Ajin, sauri sauri, gudu gudu ta cimma shi don ta san ko kiranshi tayi ba zai juyo ba ga idon mutane a gurin, sai da tazo gab dashi ta mai Sallama, kamar ba zai tsaya ba ya tsaya tarw da juyowa, suna hada ido cikin in ina tace "Erhm, dama ina son yi maka Godia ne, anyi Marking scripts kuma nikadai naci 20/20" ta karasa tare da mika mai takardan hannun ta, ido ya tsareta da shi, ba tare da ya kalli papern ba ya juya zaiyi tafian shi, da sauri tace "Nagode Allah ya saka da Alheri, Allah ya kara basira" Chak ya tsaya, ita kuma ta juya ta ta fi, da sauri ya juyo amma har tayi gaba, ya dade rabon da yaji shi cikin Wannan yanayin, a hankali ya furta *"Me ke faruwa*?" *MAFARKI* "Baiwar Allah", taji wata zazzakar murya tayi kiranta, Nasiba ta juyo ta kalleta,sanye take da fararan kaya masu alfarma, fuskarta sai kyalli, tace "donAllah taimako nake so ki min, idan kika taimaka min Allah zai taimake ki, Nasiba tace wani irin taimako kike so in miki? Tace "wallah, bashi naci a wani Shago, wata rana na je siyan lemo lacasera, na bada dubu aka ce ba chanji, in tafi idan na samu na kawo, toh har yau Allah beyi na kai ba, yanzu kuma nayi nisan da ba zan iya dawowa in ba mai shago hakkinshi ba, ki taimake ni ki kai mai Nera 120, kinsan Allah na yafe hakkin komai banda hakkin mutim, Nasiba tace " bakomai, a wani shago ne?" tace " Masanawa Supermarket,Umaru Musa" toh InshaAllah zan biya miki, to ya sunanki? Don yanda zanma mai shago bayani" tace karki damu, kedai kawai ki bada da niyyar ni ki ka biya ma wa, hakan ya wadatas" Nasiba tace "Zanyi hakan InshaAllah " tace nagode". Nasiba ta muskuta daga baccin da tayi, don ta jima batayi mafarki ba, ta koma bacci. Washegari Tunda tayi Sallahn Asuba ta dinga tunanin Mafarkinta na jiya, Neneta lura da ita tace "lafiya Seebi?" Nene nayi mafarki da wata jiya, tana rokona in biya mata bashin lemun da ta siya, ina so in yi yanda tace" Nene tace "Sannu Sharifiya, wa yace miki Mafarki Gaskia ne?" nan Nasiba ta shashantar da maganar. Tun daga ranar Nasiba ta dinga wasu Mafarkai masu tsoro, sai in dai bata kwanta bacci ba, da ta kwanta sai mafarkai masu ban tsoro, Yau dai ta tsaya tunanin dalilin mafarkanta, zuciyarta tace k'ila wannan mafarki na da nasaba da k'in biya ma wannan matar bashinta, tunda rana daya ta fara wannan mafarke mafarken, dole zata je ta biya mata bashin, ko ta samu kwanciyar hankali ta daina Mafarki. Yau ta na zuwa Makaranta ta wuce Masanawa Super Market, ta ciro dari biyu ta mik'a ma me shago, yace "me zaa baki?" tace bakomai, wata rana kawata ta zo siyan Lacsera da dubu kace ba chanji, shine ta aiko ni in kawo maka, me shago ya amsa ya mika mata chanji, tazo juyawa taji ta taka kafar wani, a tsorace ta dago, ganin Rafeeq ya sa zuciyanta halbawa, be tsaya bin ta kanta ba ya wuce fridge ya ciro Soy milk, yazo gun biya ya ciro dari 5 ya bashi, be tsaya karban chanjin shi ba ya bar Shagon. Me shago yayi Murmushi yace "R-Lema kenan" Nasiba tace "mallam ka san shi ne?" yace ai ba wanda be san Rafeeq ba" Nasiba ta matso gunshi tace donAllah kasan dalilin da yasa yake haka? Yace "da Rafeeq na kowa ne, da da ya shigo zai dinga ja na da surutu, rana daya ya chanza, ba wanda yasan dalilin chanjin shi, gashi da k'okarin shi, duk Sciences shine over roll, amma Shekarar shi 6 a jamian nan, mates dinshi duk sun gana services dinsu, ba wai be da k'okari bane, aa ba wanda yasan dalilin Spilling din da yake tayi" Nasiba ta jinina kai tace "abun akwai ban mamaki, amma me ya maida shi hakan? Yace "ba wanda ya sani, iyakar abunda na sani kenan". Nasiba a ranta taji tana son sanin me ya maida R-Lema haka. *MAFARKI* "Ina Godia da Biyan bashin da kika min, Nagode, don yanzu na samu kwanciyar hankali" Nasiba tace toh "Alhamdulilah, bakomai" Yauwa kinyi abu na farko cikin Uku da na keso ki min, abu na biyu da nake so kimin shine; ina So ki binciki wani Makwabcin ku mai suna Rafeeq Habib Lema, ina so ki san ko shi waye, sannan kuma ina so ki shiga rayuwar shi" a razane Nasiba tace what? Kinsan me kike fada ne? Saboda mene zaki ce inyi haka, baiwar Allah don na taimaka miki dazun ba shi zai saki ki dinga sani abubuwa ba, ba zanyi ba, ba zan yi ba, mutumin da ko kallon arziki ban ishe shiba, toh ba zanyi yanda kike so ba, Musulmi na kwarai shine wanda be shiga hakkin da ba nashi ba" Yarinyar ta kama hannun Nasiba, kamar zatayi kuka, donAllah ki taimakeni, ki yarda dani" Cikin masifa Nasiba tace "Sabida mene zan yarda dake? Bansanki ba, bansan komai game dake ba, kinzo kina sani abubuwa? Toh wannan karon ba zan tainaka miki ba, kizo kiyi abunda kike sani da kanki, duk nisan da kike kizo ki yi aikin ki da kanki, idan kinso daga yau ki di ga zuwa min da mummunar siffa, ki hanani bacci, ba zanyi yanda kike si ba" . Yarinyar tayi dan murmushi, tace "da zan iya da nayi" Nasiba tace" zaki iya mana tunda kina tunanin ni zan iya" tace ke zaki iya don kina nan duniya, ni kuma ba zan iya ba, don bana duniya" cikin firgici Nasiba tace "me kike nufi da hakan?" Yarinyar tace " *My Name was Rafee'ah Habib Lema, na Rasu Shekara daya da Rabi da suka wuce*". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) *Allah Sarki Yanuwa da Abokan Arzikki, da Masoya❤ duk na ga sak'onnin Ta'aziyoyin da kuka min, nagode Allah shi karb'a, ya biya ku, shikuma mamaci Allah ya ji k'anshi (Baba Hashimu) Allah ya gafarta mishi, Allah kasa ya huta. Da duk Musulman da suka riga mu Gidan Gaskia, mukuma in tamu tazo, Allah ya sa mucika da kyau da Imani Amin, Nagode Nagode Nagode, Allah ya barmu tare.👏🏽👏🏽👏🏽.* Pg3⃣5⃣ Firgici da tsoro suka ziyarci zuciyar Nasiba, ta fara karkarwa, ta na ja da baya, baki na rawa tace "Fa+ta-talwa" Rafee'ah ta yi saurin cewa "DonAllah kar ki ji tsoro, banda niyyar cutar dake, ke musulma ce, kuma kinyi Imani da hakan, karda ki sa ma ranki ni Fatalwa ce, ni ba Fatalwa bace, da iko da k'uddirar Allah nazo miki a Mafarki, Mafarki kike yi dani, DonAllah ki kwantar da hankalin ki, banda niyyar cutar da ke .(Mu sani Ba Fatalwa a musulunci, Wanda ya mutu ya mutu, ba yanda matacce zaizo cutar da kai, in ka ga Mattace a ido, to gizo yake maka, ko kuma kayi mai mugun abu kafin ya mutu, ka sa ma ranka ne,shine kake ganin kamar zaizo maka, amma Tabbas ana mafarki da Matattu, _to Nasiba dai Mafarki takeyi da Rafee'ah_.) Nasiba ta sauke numfashi, hankalin ta ya dan kwanta, Sai da Rafee'ah ta ga Nasiba ta samu natsuwa sai tace "Kamar yanda nace, ina so kin dan wanene Rafeeq, ina so ki shiga Rayuwar Rafeeq, ina so ki sauya duk wani abu da ya danganci Rafeeq, ina so ki warware zare da abawan cikin gidan Lema, akwai abubuwa da yawa da zaki fuskanta, akwai hadari a cikin wannan aikin, amma ki sa Allah a gabanki, ba zai barki ke kadai ba, sai kin jure kin daure". "Bazan iya ba, ni ala musuru ce? Da zan miki duk wadannan abubuwan? Saboda mene zaki dinga bibiyata cikin mafarki kina sani abubuwa?" inji Nasiba, Rafee'ah ta nuna ta da yatsa, tace saboda *"KE ALHERI CE"* cikin rashin fahimta Nasiba tace *"NI ALHERI CE?"* Rafee'ah ta gyada kai tace *"Eh, KE ALHERI CE"* ba za ki gane ba yanzu, amma a sannu zaki fahimci dalilina na ce miki haka, ta dan sasautar da murya tace "Nasiba, Rafeeq yaya na ne ina sonshi sosai, Rayuwar shi na cikin 6ata, ki taimake ni ki min wannan aikin, Allah kadai zai biya ki" Nasiba tayi shiru tana tunani, tabbas ita shaida ce kan halin Rafeeq na Shariya, da k'yaliya, itana tana kwadayin jin labarin shi, kuma tasan tabbas yana cikin damuwa, chan tace "Shikenan, Allah ya mana jagora" dadi ya lullube Rafee'ah, tace "Nagode Sosai, but one more thing, you must not tell anyone about your Dreams and your Mission, kar ki gaya ma kowa, komai kusancin ki da mutum, ki min Alkawari kinji?" Nasiba tace "InshaAllah ba wanda zai sani" Nagode sosai, ki fara binciken ki da wuri, ba mu da lokaci" Rafee'ah tace "InshaAllah". Rafee'ah ta mata sallama ta tafi, daidai nan Nasiba ta sauke ajiyar zuciya me nauyi cikin bacci, gyara kwanciyarta tayi. _7:50am_ "Nene yi zaman ki, barin je in siyo k'osan", aa Seebi budurwa dake sai a ga kin tsaya bakin titi siyan k'osai? Yo meye? Wa ke bina bashi?" ni zanje, ba me bina bashi" Nene tace "kawai sai a ga yar budurwa kamar ki na bin layin k'osai?" Nasiba tace "ni kuma gani mara tausayi, kina fama da Masassara don kar ace gani budurwa, sai in barki kije siyan k'osai, to ba dani ba, kinga tafiya ta" Nenen tace "ai sai kiyi, tun yaushe zazzabin ya sauka?" Nasiba ba ta tsaya tanka ta ba ta fita daga dakin, Nene kuwa ta dan kishingida, ko minti daya baayi ba wayar Nasiba ta hau ruri, Nene ta buga tsoki " wani dan anacen ne ke kiran waya da fara saffiyan nan? Sun maida waya Kamar wata Ramadana, haka ta dinga mita har wayar ta tsinke, chan ta hau ruri, Nene ta mik'e ta zaro wayar k'ark'ashin pillown Nasiba ta latsa tare da cewa "Hello" "Assalam Alaikum Seebin mu ni da Nene" Nene tace "Laaah, Zaidu bawan Allah, Kai ne?" yayi murmushi kamar yana gavanta, yace "Eh Nene, nine, kamar kinsan kiran nan naki ne" tace "Allah ko? In ka ji kira Samu ne" yayi daria, yace "Addua nake buk'ata, an tura ni Ingila wani Aiki, kuma zanyi sati 3zuwa wata 1 a chan, shine muke barar addua" tace ai addua kullum cikin yinta muke, Allah ya kareka daga masu jan Kunne" yace "su waye masu jan kunne?" "Tabdijam! Turawa mana" Dariya Zaid yayi sosai, tace "Af! Daria na baka ko? Ai turawa muggai ne, sai an hadasu da *Li'ilafi kuraysh*" Sosai Zaid ke dariya, yasan idsn ya biye ma Nene, haka zata dinga sa shi daria har yayi missing flight dinshi, yace "nikam ina Seebin mu?" Taje siyo K'osai da burodi" Zaid tayi dan jim, Nene ta fuskanci shirun Xaid, Ehtace "kai ma kagani ai, gardama tsiya gareta sai da nace mata ta bari in siyo, tace wai aa, wai ban lafiya ita zata ta siyo" Zaid yace "baki Lafiya Nene? "Zazzabi ne ya lullube ni jiya da daddare, amma yanzu ta sauka, na ji sauki" "Nene ko zakije asibiti? "Kai ni rabani, komi Asibiti, to naji sauki" yace "to shikenan Nene, ni zan tafi, kice da Seebi zan kirata idan na sauka" Nenen tayi Murmushi tace "to Zaidun Seebi, Allah ya tsare ya kare ya bada saa" kiris ya rage dadi ya kashe Zaid, yaji dadin wannan kalami na Nene, yace "Amin Nenen mu". *Kaskon Mai K'osai* Lubbatu mai k'osai (Sorry Lubie😂) ta shahara gun soyen k'osai, ga dadi, ga tsafta, gaban kaskonta mutane ne sosai suna jira a soya a basu, Nasiba na daga cikin masu jira, tayi tagumi daga gefe tana tunanin Mafarkin ta na daren jiya, tana tunannin yanda zata bullo wa lamarin, taya zata shiga Rayuwan R-Lema ba tare da taimakon kowa ba? Ta ya zata san ko shi waye ba tare da ta tambayi Zaid ba? Allah ka kaow min Mafita" sama-sama ta ji firan Lubbatu mai K'osai, da wani dan datijjo, da alamun Customern ta ne inda datijjon ke cewa "Ni banga k'awar fada ta yau ba, da ta na nan ba zan gaji da jiran layin nan ba" lubbatu tayi daria, tace " nima bangan ta ba yau, da ta na nan da ta dinga mitar har yanzu ba a soya min nau ba?, ko kuma tace ta rigaka zuwa nan" daria yayi yace "aiko idan zan wuce gida zan biya gidan ta inji ko lafiya yau ba ta fito siyen k'osai ba" lubbatu mai k'osai tace "anya Maigadin Gidan Lema ba da Aminene za'ayi ba?" ya fashe da darian jin dadi yace "ai na fi k'arfinta" Nasiba da ta yi k'ask'e tana jin su, a ranta ta maimaita "Maigadin Gidan Lema? Isit possible gidan su R-Lema yake Gadi?" Don tana da tabbacin wuraren nan gidan su R-Lema yake, kuma tabbas maganar Nenen ta suke yi, Allah sa haka ma, Don ta fara aiwatar da aikinta tun wuri. Ba jimawa a aka sa ma Baba Maigadi Gidan Lema k'osan shi, cikin saa a ka zuba ma Nasiba nata, Baba Maigadi yayi Gaba Nasiba tabi bayan shi, tace "ina kwana baba?" da faraa yace "lafiya lao Jikata" haka suka cigaba da tafia har Nasiba tazo gida, zata shige kenan yace "Jikata dan tsaya?" cikin gidan nan zaki shiga?" tayi murmushi tace "eh, Baba" yace "ko Aminene na ciki? Na jita shiru yau bata zo siyan k'osai ba" tace "eh ta na nan, bata ji dadi bane jiya da daddare " yace "Assha! DonAllah kice da ita, Maigadin Lema na Sallama" bawai don tana da tabbas ba tace "Baba kai Maigadin su Rafeeq ne?" ya washe baki yace " Yo eh, ai nine Maigadin su, tun lokacin Iro Kakan Rafeeq kenan" Murmushin Nasara Nasiba tayi, tace "Baba, barin maka Sallama da Nenen" ta shige gida. "Nene ana Sallama da ke?" Nene tace Sallama kuma? Wanene? Seebi cikin sigar zolaya tace "bazawarin ki" ke zan saba miki, badai Zaidu bane don yanzu ya kira yace an turashi Ingila aiki zaiyi wata Guda" Haka kurum Nasiba taji ba dadi, zata yi kewan Zaid, tace "wani Maigadin gidan Lema" murmushi Nene tayi tace "Danrainin wayau, nasan zuwa yayi jaje na yau be ganin ba a gurin siyan K'osai" Nasiba tace "Toufa, har kun saba da Shi, ko dai ko dai?" harara Nene ta jefeta da shi, tace barin je mu gaisa" Nasiba tayi saurin cewa aa, barin dai ce ya shigo sai ma in shek'a mana koko, Nene ba ta ce komai ba Nasiba taje ta shigo da Baba Maigadi. Bayan sun gama kalaci ya musu Sallama, Nasiba tace "barin raka ka baba" yace to Jikata, ya kalli Nene yace to "Aminene, Allah ya kara sauk'i, sai na sake zagayowa" cikin wasa tace " Idan zaa dawo a dawo da karin ciwo, bawai azo a isheni da dimin surutu ba" Gabaki daya suka sa daria.. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) Pg3⃣6⃣ A hanya, Nasiba ta dinga jan shi da fira, da yake Baba Mai gadi saurin sabo ne dashi, nan da nan yake bata amsar tambayoyin da ta ke mai, Nasiba a ranta tace "Hanya Mafi saukake da zan san ko kai waye Rafeeq" Baba mai gadi yace "ke Nasiba, kinga har kin rakoni Gida, na jaki da yawa" tace "lahh har mun iso? Ya nuna gidan da yatsa, yace "ga gidan nan" gabanta ya yanke ya fadi, wani irin Tamfatsetsen gida ta gani, gidan ya hadu, a ranta tace "So this is where you live R-Lema" Baba yace to ki koma gida Nasiba, sai nazo gobe, ta dan marairaice fuska tace "Baba nasan Nene ta koma bacci, idan ba damuwa in zauna nan in tayaka fira" bench ya dauko ya ajiye gaban Gidan, ta Zauna, yayi daria yace wani irin fira zamuyi? tace "labari zaka ban" "wani iri kenan" a ranta tace "Astagfurullah Zanyi karya" ta sausauta murya tace "Baba labarin Rafeeq zaka bani, Makarantar mu daya, da ni budurwar shi ce, yana sona sosai, amma rana daya ya sauya min, ina son shi kamar me, amma sai naga ya daina kulani, yanzu ko gani na yayi kallo ban ishe shi ba, shine nake tunanin ko yaudarata dama chan yakeyi?" da sauri ya girgiza kai yace " kar kice haka, Rana daya Rafeeq ya sauya ma kowa, Rana daya K'addara ta gifta ma Rafeeq" Nasiba tace Baba ka ban labari *Wanene Rafeeq* Ajiyar Zuciya yayi, yace Rafeeq D'a ne kamar kowa, mai fara'a da son Jama'a, kinji kinji................ Tsaf Baba maigadi ya kwashe ya bata labarin duk abunda ya sani game da Gidan Habib Lema har zuwa zaman da sukayi yau. Sosai Nasiba ke kuka har da Majina, lokaci daya tausayin Rafeeq ya lullube ta, Sam bata ga laifin Rafeeq ba, lallai Rafeeq abun tausayi ne, Lallai Rafeeq na buk'atar taimako. Baba Maigadi yace "Nasiba mun dade zaune a nan, ki tashi ki tafi Gida" ajiyar zuciya ta sauke tace "Baba, Labarin Rafeeq na cike da Abubuwan ban Alajabi da Mamaki, da tausayi, baba yanda kasan a fim" Baba maigadi yace a takaice ma kenan, "zato zunubi amma ina Zargin Matar Ubanshi Saude ga duk wani abun da ke faruwa cikin gidan nan, ban taba dai ce ma kowa komai ba" da sauri tace "Saboda me kace haka Baba?" "Saboda randa aka ce an kama Mahaifiyar Rafeeq da kwarto cikin daki, Saude ta fito ta aikeni siyan Gayen lataz, kafin na dawo har an saketa, tun daga rannan komai ya sauya, Alhaji be kara maganar da kowa ba, kinga kuwa beyiwu haka, ko yaya ne sai an maida magana, amma ko maganar ka mishi zai nuna be ma san wacece Aisha ba, kinga ko anan akwai ayar tambaya, sai maganar Karatun Rafeeq, makarantan ku daya, ke kinsan irin kokari da fasahar da Allah ya bashi, amma har yau ya kasa gamawa, abokin shi Maalesh har ya gama bautar k'asa, nan ma akwai ayar tambaya, sai maganan Rasuwar Rafee'ah, mutuwa dole ce ta na kan kowa, Ana gobe Rafee'ah zata rasu, ta fito da Cooler abinci ta fito nan tana zolaya ta, tace dani "Baba, yau da Hammana zan ci abinci" nace kice sanwa kika ma yayanki tace "Aa, antu saude ta dafa mana" ta shiga ciki, chan sai ta fito, nace har kun cinye? Tace "be ci ba ya riga da ya siyo nashi, ni kadai naci, ko na juye maka sauran a plate? Nace "aa Rafee'ah nagode" washe gari Rafee'ah tace ga garinku nan. Tunda Aisha ta bar Gidan nan, ban kara cin komai na Gidan ba, don ba bani ake ba, ruwa Saude bata taba miko min ba, Alhaji be taba cewa don me baa bani abinci ba, shi da ke ganin girma na da darajata, Zaid kadai ke min ihsani, da idan kinga yanda muke wasa da daria da Rafeeq, abun ba aa magana, amma yanzu komai ya jagule, ni Wallahi ina Zargin Saude, hanalina be kwanta da ita ba". Nasiba ta nutsu ta na jin Zancen baba Maigadi tace "Allah shi saka ma wanda aka zalunta" yace "Amin" horn akayi da k'arfi, jiki na rawa yace ina zuwa ya shiga gidan da sauri ya wangale Gate din, Meema ce da Aneesa cikin wata katuwar Mota, Meema ta harari megadi tace uban me ya hanaka bude gate da wuri? Yace "kiyi hakuri" tsaki ta buga ta figi motar da Sauri Nasiba ta ja baya don kiris ya rage su bi ta kanta. Saida ya kulle gate din ya dawo gun Nasiba tace baba su waye wannan? Yace "Kanwar Saude ce, da diyarta, in sukayi wani abun sai ki rantse su 'yayan alhaji ne, ita Aneesar naji labari har ta koma Aneesa Habib Lema a Makaranta" Nasiba ta jinjina kai tace "baba barin wuce" nan sukayi Sallama. Tun kan hanya Nasiba ta hau tunanin yanda zata fara wannan Mission dinta har ta je gida tana sak'a da warwara, ta rasa yanda zata yi, amma abun da ta kudirta a ranta, Zata taimaki Rafeeq, zatayi yanda Rafee'ah ta bukace ta da tayi, nan Allah ya cire mata duk wani tsoron abun da zai je ya dawo, ta san its not an easy thing, amma haka kurum zuciyar ta ta amince da duk halin da zata shiga, zata yi sacrificing kanta, she's willing to take the risk, bayan jin ta bakin Baba Maigadi, da hujjojinshi na Zargin Matar Baban su Rafeeq,komai zai zo mata da sauk'i, nan ta gane ba Rayuwar Rafeeq kadai zata shiga ba, Rayuwar Gidan Lema gaba ki daya zata shiga "So help me God". To tambayan shine "Ta yaya zan shiga Rayuwar su Gaba ki daya?" zuciyarta tace "barin jira Rafee'ah a mafarki". Da daddare sai juyi take don tayi Mafarki, amma Shiru ba Rafee'ah, washegari ma kwatakwata batahi mafarkin komai ba, kwana 3 ta jera tana jira tayi Mafarki da Rafee'ah amma shiru, tace ma kanta " it seems like i am on my own, Allah ka taimake ni." *5:50pm* "Sannu Nene" Nasiba tace cikin damuwa, tun kwana 2 da suka wuce Nene ke kwance, ta rasa me ke damunta, ta k'i yarda suje Chemist, kuma ta k'i yarda Nasiba ta gaya ma Abban ta, Nasiba duk ta shiga wani yanayi, a iya wayon ta, ba ta taba ganin Nene tayi ko da ciwon Kai ba, cikin rashin kuzari Nene tace "Wai uban meye zaki tasani gaba ki zabga uban tagumi kina kuka iyi? Ko kinga na mutu ne? Nasiba tace "Nene nifa ban taba ganin kiyi ciwo ba" Nene tace da yake ni Waliyya ce sai in k'i ciwo, ko kullum in banda lafiya sai inzo inyi kwance kamar wata ke a gurin, to Nasiba ko ciwon Ajali ne me zuwa ma mutu farat daya, to barin bar miki wasiyya" da sauri Nasiba ta tashi ta shiga daki ta bar Nene kwance tsakar gida, don ta san Nenen k'arfin hali kawai takeyi tana maganar nan, kuma idan ta biye mata sai ta sa ta kuka don Bakin Nene ba ya shiru. Nasiba ta rasa yanda zatayi, ba ta san kiran Abban ta don ta san shi da damuwa, yana iya kamo hanyar Katsina da Marecen nan, ya zatayi? Bata gama tunanin ba Wayar ta ta hau ruri da sauri ta dauka + ta gani wato lambar waje ne, ta dauka da Sallama, a dayan bangaren "Waalaikum Salam Seebin mu ni da Nene, ya kike ya karatu? Tace " Uncle Zaid, Alhamdulilah, ya Aikin? Yace "Alhamdulilah, ina Nenen?" kamar jira take ta fashe da kuka, lokaci guda Zaid ya rude, "me ya faru? Me ya same Nene? Wani abin yake faruwa a katsinar? Ki min magana Nasiba" daga jin muryar shi kasan hankalin shi a tashe yake" ta dan tsagaita tace "Uncle Zaid, Nene ba ta da Lafiya, tun kwana 5 da suka wuce, ina tsoron wani abu ya same ta, ban taba ganin ta haka ba, amma ta k'i yarda muje Asibiti ko nagaya wa baba na" Zaid yayi dan shiru yace "no wonder, randa na kira naji muryar ta wani iri, ashe ba lafia, kuma bata gaya min ba" "ai ba zata gaya maka ba, don Nene wata irin mata ce me Zurfin ciki, nima don ta kai kuri na san cewa bata jin dadi, har yanzu bakin ta ya ki mutuwa" Zaid yace "ki kwantar da hankalin ki, ki tashi kuyi shirin Asibiti aje a dibo ta" Nasiba tace Uncle Zaid " ba zataje ba, Nene is so stubborn" yace "trust me on this ki kai mata wayan". Haka ta mik'e ta kaima Nene Wayar, Nene ta amsa da Sallama, Zaid ya gaida ta, "lahh, Zaidu bawan Allah, kaine Ya Ingilar?" yace "Alhamdulilah, ashe ba kiji dadi ba?" saida Nene ta wurga ma Nasiba harara kafin tace "Kai kalau nake" "Aa Nenen mu, ga muryar ki nan, ni dai ki tashi ki kimtsa gashi na turo a zo a kaiki Asibiti, donAllah kar kice Aa" ba yanda zatayi tace "Toh Zaidun Seebi, tunda yanzu maganar ta kadai kake ji" duk sukayi daria, ta mik'e da k'yar ta shiga bandaki, yace "Nasiba, ku shirya za a zo a kaiku Asibiti" tace "Uncle Zaid ina iya kaita, ba sai an zo ba" yace "don't be silly, zan sake kira inji ya jikinta" dif ya katse wayar. Nasiba tayi murna, tace "Allah Sarkin Uncle Zaid, Our Guardian Angel." A karo na 3 Ya shiga lalluben layin Rafeeq, sai ya kusa shiga sai ya datse kiran, don yana fargaban abun da zai ce mai, Rafeeq be son irin haka, amma ya zaiyi? He is his only choice, chan dai yayi shahada ya sake kiran wayar Rafeeq, ringing biyu Rafeeq ya dauka ya kafa a kunne ba tare da yace komai ba, Zaid yace "hello son, ya kake?" kamar ba zai yi magana ba yace " Barka da Yamma" Zaid yace "Kaci abinci?" "Uhm" kadai yace, Zaid yace "Rafeeq ka tuna Nene? Wacce kama granddaughtern ta Assignment last week? Kamar ba zai tanka ba yace "yeah" " she's sick wallahi, she's been sick for days" a ranshi yace to why are u telling me? Allah ya sa ba cewa zaiyi inje in gaishe ta ba don ba zuwa zanyi ba, shiru be ce komai ba Zaid yace "Kaji ai?" da kyar yace "Allah ya bata lafia" "Amin, Rafeeq i want you to do something for me, DonAllah ka dauke ta ka kaisu Asibiti" cike da mamaki yace "What??" Zaid yayi saurin kwantar da kai, donAllah they need help, kaisu Asibiti kawai zakayi, this is all i'm asking for, Please" dif Rafeeq ya kashe wayan, takaici uwa ya kashe shi, shi be san meyasa Uncle Zaid ke sa shi yawan magana ba, in banda neman Magana shi zai kaisu Asibiti? Why they need help, shi First Aid box ne? Kai akwai Sakel, shi be kai kanshi Asibiti ba zai kai wasu? Ga Maalesh baya nan, to ko dai ya kira musu Ambulance? Amma Uncle Zaid ya fi k'arfin ya sashi abu ya k'i yi, be da wani Zabin da ya wuce mik'ewa ya shiga mota. Daga gidan su zuwa gidan su Nasiba yayi tsaki yafi dubu, gashi yanzu fi Minti 5 yana tunanin yanda zai shiga gidan, Kamar yayi kuka, Ya ciro wayar shi ya tura ma Zaid text, "i'm there" don be son mishi magana a halin yanzu, Zaid yayi saurin kiran Nasiba, yace "ku fito yana waje" ta shaida mai da yanzu zasu fita. Ya tura ma Rafeeq da cewa "there are coming now, kindly greet the sick person please, Please Rafeeq, for me" tsaki ya buga Wannan Uncle Zaid din yana sani abun da ban yi niyya ba, takaici ya hana shi tsayuwa, ya koma motar shi ya Zauna" ba ayi minti Daya ba Nasiba ta fito rik'e da Nene, ta waiga ta waiga bata ga kowa ba, daga chan taga wata jan mota mai bakin Gilashi, da alamu ba kowa ciki, "to ina wanda Zaidun ya aiko?" "inaga bai karaso ba, mu koma daga ciki" duk wannan lek'e lek'en da sukeyi Rafeeq na kallon su, ganin zasu koma ciki ya sa shi yin horn, Nasiba ta juya inda taji horn, ta ga haske a ta cikin motar nan zuciyar ta ya bata, R-Lema ke cikin motar chan, ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai zata samu ta shiga rayuwar shi, tace "Nene, ga motar chan" "wanchan mota kalar jini, ga bak'in windo shi kike nufin mu shiga?" cike da takaici tace "toh, ko Uncle Zaid din ne zai sa a cutar da mu?" da sauri tace "ni ba haka nace ba muje muje kar ki kaini gaba" su ka karasa har inda yayi parking, har yanzu be fito ba, Hannu ta sa ta bude k'ofar baya, Nene ta shiga da Sallama ita ma ta bita ta shiga ta rufo kofar, Nasiba ta kalleshi tace "ina wuni?" be amsa ba, shi dai ya tsinci kanshi da cewa "Ya jiki? Sannu da jiki" Nene ce da fara'arta tace "Naji sauki sosai" be sake magana ba ya ja motar, cikin nutuswa yake tuk'in shi, Nasiba na karantar duk wani abu da yakeyi, tausayin shi take ji sosai, ba tasan lokacin da hawaye suka soma zubo mata ba, tayi saurin sharewa don kar Nene ta gani ta tara mata mutane, be zarce ko ina ba sai Asibitin K-Dara, ya shiga yayi parking, shiru shiru be ce musu komai ba, Nasiba tace "Nene anzo fito mu shiga"suka fito, ga mamakin ta shima ya fito yayi gaba hanyar entrance din, suka bishi a baya, Nene na mata mitar "shi kuma wannan haka yake dunkum?" Seebi dai bata ce komai ba, Rafeeq ya tsaya ya yanki kati, ba layi, ya kira Dr Daran, yace "Baba gamu gaban Office dinka" yace to Rafeeq ku shigo, hannu kawai ya nuna ma Nasiba Office din ya samu guri ya zauna, Nasiba kuwa ta gane me yake nufi, ta sake rik'e Nene suka shiga cikin office din, yace kune Patient din Zaid? Nasiba tace "eh" ai ya kirani ya sanar dani zuwanku" ya shiga yi ma Nene tambayoyi, da gwajegwaje, kusan Minti 45, kafin yace " Inna Zamu baki daki, Hawan jinin ki ya tashi" Nasiba ta zaro ido tace "hawan jini Dr?" meyasa ta samu hawan jini? Yace "Ke kuwa ta tsufa, ai tsufa ce, don ma jikinta me kyau ne kuma tana regulating din shi,amma still zamu bata gado don kar ta kamu da Diabetes, don na fara ganin Symptoms din a tare da ita, kar ki daga hankalin ki, yanzu barin na muku processing gado, Suka fita waje da Dr din, Nasiba ta leleka bata ga Rafeeq ba, a ranta tace "ya ma yi kokari da ya kawo mu" Dr ya rubuta aka basu Gado, A ka kaisu har dakin, Nasiba na tunanin yanda zataje Gida kwaso kaya. Rafeeq ya shiga Office din Dr, ashe Sallan Maghrib ya je yayi, ya ga basa nan, Dr yace "nayi admitting din su ne,suna room 12, HBP ne da ita, and a minor Diabetes, shine muke so ta samu rest, zan kira Zaid in sanar dashi don yace duk me ake ciki in kira shi, Rafeeq ya danyi gajeren tsaki yace " Me ake so?" Dr yace wannan taje ta dauko musu kayan bukatar su, don zasu kai 3-5days, payment kuma zan tura ma Zaid, Rafeeq yace "a ina zaayi?" yace a gun Cashier, Rafeeq be sake cewa komai ba ya fita, sai da yaje yayi payment kafin ya fita daga Asibitin, Jifatu yaje, ya siyo kayan Amfani, Su kayan Tea ne, fruits, karton din Ruwa, Bargo, Sallaya, da duk wani abun da yasan zasu buk'ata, Rafeeq shine da tsaywa siyan Kaza, ya koma Asibiti, Irin leburori yasa suka kwasan mai kayan, yayi gaba suna binshi a baya, har gaban dakin room 12, umarni ya musu da su shiga da kayan, shi kuma ya juya, daidai nan Nasiba tace Nene barin je in dauko kayan bukatar mu, don ba musan har yaushe zamu tsaya anan ba, Nene tace "toh akwai kudin Nape hannun ki?" eh akwai. Tana bude k'ofa ta gansu tsaitsaye da kaya nik'i nik'i, ta bude baki, sukayi sallama tace wannan kayan kuma fa daga ina? Suka ce wanchan ne yace mu shigo da su nan, Nasiba ta lek'a don tava wasu ke nufi, ga mamakin ta Rafeeq ne yana tafia da sauri, da sauri ta bi bayanshi, gudu gudu amma ta kasa cimma shi, daga nesa take ta kwada mai kira tana "R-Lema, R-Lema dan tsaya don Allah" shi kuwa yaji wannan kiran da ake mai, amma be tsaya juyowa balle ya ga ko waye, a tunanin shi irin mutanen nan ne da suke binshi a school, be juyo ba balle ya tsaya ya cigaba da tafian shi, ita kuwa bata fasa binshi ba, ba ta fasa kiran shi ba, bata damu da yanda ake kallon ta ba, "Rafeeq Please tsaya" wani tunani ya zo mata ta dan daga murya tace *"Hamma Rafeeq"* Chak ya tsaya, gaban shi ya yanke ya fadi, Muryan K'anwar shi yaji, a hankali ya furta "Rafee'ah?"... _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) *Sometimes, its hard for you to figure out what to write when you want to tell someone how much you Appreciate them, but it does'nt matter, i'll say it and write it anyhow. She's more of a Mentor, A Role Model, a Teacher, A Guide, A Respected, Loving and Caring Person, She's one who always wants to share, she's Determined and Confident, Her Support and Advice has helped lotta people, she has touched lives, ofcourse she's touched Mine and lotta people i know, She's Simply Amazing coz She's her, She's AUNTY SIS.* *This page is for you Aunty Sis* Pg3⃣7⃣ A hankali ya juyo, suna hada ido da Nasiba, yayi saurin dauke ido yana waige waige, kamar me neman wani abu, a hankali ta sake furta *"Hamma Rafeeq"* Mamaki ya lullube Rafeeq, tabbas ya san shi muryar Rafee'ah yaji, duniya ita kadai ke ce mishi Hamma, a ranshi yace *"to wannan kuma fa? Why is she sounding like my sister?"* a hankali Nasiba ta fara magana *"Mungode Sosai da wannan hidima da kayi damu, Allah shi saka da Alheri, Allah ya biya ka"* ta na kaiwa nan ta juya ta koma cikin Asibitin, shikuma yayi tsaye kamar an dasa shi, ya kasa motsi, shi beyi gaba ba, shi beyi baya ba, mamaki da tsoro ya kama shi, ya shiga tambayan kanshi, *"Meyasa wannan take magana kamar Rafee'ah, there's something about her, i just dont know how to describe it"* da kyar ya shiga mota ya bar Asibitin Jiki a Sanyaye. Tunanin wannan dawainiyan da Rafeeq ya musu take tayi, komai ya tanadar musu, ashe yana da kirki? ashe Zuciyar shi bata ida macewa ba? Ashe yana da sauran kirki tattare dashi? Toh in ko haka ne, ba zai wuyar tankwaruwa ba, Allah ya bata saa Amin, ta kalli Nene tace *"Zaki ci Kaza?"* Nene ta kalle ta da mamaki tace *"bangane zanci kaza ba, naga dai don ni a ka kawo shi"* Seebi ta girgiza kai tace *"naga dai marasa lafia ba su fiye cin abinci ba, nama ma bai dame su ba"* harararta tayi tace *"ni ya dameni zubo min"* dariya sukayi gaba ki daya. *Rafeeq* zaune yayi tagumi hannu bibiyu, ya lula duniyar tunani, shi fa be fiye tunani ba, amma tun da ya dawo daga Asibiti ya ke tunanin wannan yarinyar, mamaki yake mesa take abubuwa kamar Rafee'ah? Mesa take kiran shi da sunan da kanwarsa kadai ke kiransa da shi? Ko ta san fee'ah ne? Maganar ta komi na yana mai kama da na Fee'ah, haka kurum yaji a ransa yana son sake ganin ta. *WasheGari* Rafeeq ya shirya don yana da Morning lectures, ya fita daga dakin shi, a tsakar Gida ya ci karo da dukka 'yan gidan, dauke kai yayi kamar be gansu ba ya chanza hanya ya nufa motar sa, Alhaji Habib ya ciri baki yace *"Rafeeq"* kamar ba zai juyo ba ya juyo yana kallon su one by one, Daddy, Saude Meema sai Aneesa ne a tsaye, wani gololon bakin ciki yaji da ya hada ido dasu duka, dadi kamar ya kashe Aneesa yau tayi tozali dashi, kwana biyu ta lek'a dakinshi sai taji a kulle, a hankali ya tako gaban su kallo daya ya ma Baban shi, da kyar yace *"Daddy Barka da Saffiya"* Alhaji Habib da murmushi a fuskar shi yace *"Ibn Zaid ka tashi lafiya?"* kai kawai ya gyada mai, yace *"Zanyi tafia, zanje Abuja , zanyi kwana biyu"* yace "Sai ka dawo" "yaushe Baban ka zai dawo?" a k'agare yace *"Upperweek"* *"baka gaida Auntyn ka ba"* da sauri Rafeeq yace *" na makara, na tafi"* ya wuce ya bar su tsaye a nan, Saude ta bude baki cike da mamakin Rafeeq, Alhaji ya wayance *"Rafeeq kenan, an samu yau zai je school"* Aneesa tayi saurin bin shi a baya, "Ya Rafeeq jira ni nima makarantar nayi, sai ka ajiye ni" be tanka ba, burinshi ya fada motar sa, *"Ya Rafeeq mana"* tayi saurin shan gaban shi haushi ya kama shi, shi dai ya tsani Aneesa,cikin hargowa yace *"zaki matsa min ko sai naci Ubanki"* Duk diramar da akeyi akan idon Saude,Meema da Alhaji akeyi , ita kuwa Aneesa dadi ya kama ta, yau wace rana Rafeeq ya mata magana, ita ba ta k'i ya dinga lailaya mata Ashar kullum ba, indai shine hanyar maganar shi gareta, Rafeeq ya lura kwata kwata hankalin Aneesa be gun shi, ta tsura mai ido tana zabga murmushi, tsaki yayi ya raba ta gaban ta ya wuce, ta an kara da hakan da sauri ta rik'o hannun shi, yana waigowa a fusace ya haska ta da wata irin hadaddiyar mari, ji kake tass, Ya nuna ta da yatsa, *"kar ki k'ara gigin tab'ani, idan ke maiyace to ki ci kanki, banza dangi Mayyu"* ya idasa motar sa, ya fada ya danna wani uban horn Baba Maigadi ya bude gate, a sittin Rafeeq ya bar gidan. Zo ku gane min Fuskar Saude, yanda ku kasan Zakkanya, sai huci take tayi, Meema kuwa zaro ido tayi sosai tana Mamakin Rafeeq, wato sune dangin Mayyu? Alhaji kuwa dafe kanshi yayi don kunya, Aneesa kuwa tana ganin fitar Rafeeq ta fashe da wani irin kuka, A gudu Saude ta karisa ta rungumo ta, ta ma kasa cewa komai don Rafeeq ya gama kashe ta, Alhaji ya matso yace *"Anee Baby kiyi hakuri, kema tunda kinsan halin Rafeeq, ki daina kulashi"* Waiyo Allah zo ku ga takaici kwance kan fuskar Uwar Aneesa, wato ba zai yi fada ba ko? Gaskian hausawa da suka ce Naka Naka ne, Hajia Saude ni barin wuce, da kyar tace *"Allah ya tsare Hanya"* be tsaya wata wata ba ya fada mota direba Ya ja motar suka bar gidan, kamar jira suke ya fita Meema tace *"JarUban chan, Sis kina kallo? Ya zaayi ya mare Aneesa?"* Saude da haushi ya mata katutu tace *"Bari dai Meema, ina mamakin wannan karfin halin Rafeeq, Ko ni uwarta ban mareta ba, sai shi lallai Ya Tafka babban kuskure, this is the last time you will hurt my daughter Rafeeq, i know What to do with him"* sai a sannan Aneesar ta dago, tace *"No Mom, you are so not doing anything to him, if anything should happen to him, i'll hate you for the of my Life"* ta ruga a guje ta koma cikin gida. Yanda kuka san an shuka Saude haka ta tsaya, saboda Rafeeq Aneesa ke cewa zata tsaneta? Lallai kam dole ta dauki mataki kan Rafeeq, Meema sai tunzurata take tayi, ita kuma sai hawa take, ta cika tayi Pam. Tuk'i takeyi cikin kwanceiyar hankali, kamar ba abunda ya faru, ko kadan beyi tunanin abunda ya faru gidansu yanzu ba, ko a kwalar rigar shi Burin shi kawai ya sake ganin ta, tsintar kanshi yayi da zuwa Crispy, yayi ordering breakfast leda 3, Chips egg and Plantain, aka mai packaging, ya biya ya koma mota, ya kunna yana tunanin yaje ko kar yaje, zuciyar sa me tunzura shi ga mai yanayi da Rafee'ah tace yaje, haka kuwa akayi, don Rafeew Asibiti K Dara ya nufa, cikin minti k'alilan ya isa, ya kwaso leda 2, ya fita yana tafian nan na shi, sai gashi gaban Dakin da aka kwantar da Nene, ta window ya lek'a su, inda Nene ke cewa *"Kinga dai ki shirya ki wuce Makaranta ko? nace miki zan iya zama har ki dawo, ba abunda ke man ciwo "* Nasiba tace *" ni fa na gaya miki ba inda zanje, ni da Makaranta kuma sai kinji sauki kinyi garau abunki"* Nene ta sausauta murya tace *"kiyi hakuri Jikata, ki tafi DonAllah, bana so ki samu matsala da Makaranta"* Seebi tace *"Wallahi ba zanje ba"* Nene ta buga tsoki da k'arfi tace *" Nifa bana son mutum me shegen taurin kai da kafiyyar tsiya"* Seebi tayi daria tace *"Ai fah, ni barin je in siyo mana Kalaci"* Rafeeq na jin haka yayi saurin Aje ledojin gaban k'ofar dakin, da sauri ya bar gurin. Ta na bude k'ofa ta ci karo da wadannan ledoji ta tsugguna ta dauka, tace wannan kuma fa? Wani Kamshi da tayi amanna na Rafeeq ne taji, da sauri ta juya ko zata hango shi,amma wayam ba ta ga kowa ba, tabbas wannan ledojin Rafeeq ya aje su, ta hau tambayan kanta, to meyasa be shigo ba? Ohh na manta he is R-Lema, he cannot come in, ta saki wani Murmushi, tace *"R-Lema i'm Coming for you"*. A kan Sitiyarin Mota ya kifa kanshi Ya shiga magana a zuciyar shi shi kadai, *"She cannot start skipping School"* guntun tsaki yayi ya tada Mota, ya bar Asibitin, me makon ya wuce Makaranta, sai ya wuce Gidansu Maalesh, yana shiga gidan ya wuce Cikin Gidan straight, kai tsaye ya shige ciki, Mom din Maalesh ya gani zaune kan 3 sitter, ta hade kafa daya kan daya tana kurban Koko a cup, Hajia Maryam kenan{Om Eman} kallo daya zaka mata zaka san cewa Yar boko ce, zatyi tsarar Mamin su Rafeeq, k'awarta ce sosai, da k'yar taji sallaman Rafeeq, ta dago ta kalleshi, ta amsa da fara'a tare da mik'a mai hannu ta mai nuni da yazo ya zauna kusa da ita, tana son dan Aniniyarta sosai, Zama ya zo yayi kusa da ita a hankali yace "Mom barka da Safiyya" tace "Son Ka tashi Lafia?"* kai kawai ya daga mata, Murmushi tayi a ranta tace oh ni Rafeeq when will you ever change? Shiru ya dan gifta, tace zaka sha Koko? Girgiza kai yayi alamun Aa, tace "to me kakeso in hada maka?" da kyar yace *"bakomi"* chan ya kamo hannun ta yace *"Mom, Hajjo zaki bani"* (Hajjo Mai aikin su Maalesh ce, tsohuwa ce, tun Maalesh na jariri take gidan) ta kalleshi da alamun tambaya, yace *"Jinya zatayi a Asibiti"* Mom tace Jinyar wa? Waye be Lafiya? To anzo gurin, idan akwai abunda Rafeeq ya tsana be wuce ya bude baki yayi bayani ba, baya son dogon surutu, be san ta inda zai fara bata bayanin nan ba, kawai sai ya mik'e zai fita tayi saurin kamo hanun shi, *"haba Rafeeq, ya zaayi ka fara magana kuma sai ka tashi ka fita?, jinya wa Hajjo zatayi?* Tsaki mara sauti yayi yace *"ki bari kawai, na fasa"* Girgiza kanta tayi tace "Rafeeq you are very Stubborn" ta harare shi ta mai umarni da ya zauna, ta shiga ciki ta iske Hajjo na kakaci, tace da ita Hajjo, idan ba matsala Rafeeq ke so kije Asibiti kiyi jinya, kinsan hali na tambaye shi waye be lafia,da ya min bayani ya gwammace a barshi, Hajjo tayi dari tace kna ruwan dan gidana, ba komai Wallahi, zanje, kinsan akwai ladan masu Jinya, ina kwadayin shi, Barin tashi in shirya, Mom ta mata Godia, ta koma parlor inda ta bar Rafeeq, ta daure fuska tana hararar shi, shi ko sai Murmushi yake tayi, dan yana jinsu ita da Hajjo, ba jimawa Hajjo ta fito da ledar kayanta, ta ma Mom Sallama, Rafeeq ya kamo hannun Mom tayi saurin fizgewa, a hankali yace *"Mom, Nene ce bata da lafia, Kakar erhm ya ma sunanta? ya tsaya yana son tuno sunan da yaji ana kiran yarinyan, yace toh na manta sunan, i've said enough mun tafi"* be jira cewar ta ba ya fita, ita kuma Murmushi tayi, tana me tausayin Yaron Aminiyyarta. Hajjo Ta ishe shi da surutu cikin mota, idan ya tanka to wanda ba sa wurin sun tanka, yayi shiru ya maida hankalin shi kan tuk'in sa, har suka iso Asibitin, ya ciro paper da biro yayi rubutu, ya mik'a ma Hajjo, yace *"ki basu, Daki na Goma Sha Biyu"* Hajjo ta san halin shi sai kawai ta kwashi kayanta ta shiga cikin Asibitn, da tambaya aka nuna mata dakin su Nene, ta shiga da Sallama Seebi ta amsa mata tare da gaida ta, ta amsa mata, Nene ta dago tana Kallonta, ta mata ya jiki, da ta lura suna mata kallon rashin sani sai ta ciro takardar da Rafeeq ya bata ta mik'a ma Seebi, ta amsa kallo daya ta ma rubutun ta san nashi ne, don ta yi mastering rubutun shi, duk inda ta gani zata gane, ta fara karantawa *"She'll be staying with Nene Until she's discharged, and you,,,, you are so not skipping classes, Come out now"* ta karanta letter ya fi a kirga, wannan wani irin Letter ne? Ba gabas ba yamma, sai orders din da yake badawa, to ko wannan matar yake nufi da zata zauna da su har sai an sallame ta? Ita kuma ba zata yi missing School ba kuma ta fito waje ta sameshi? Haka yake nufi? Indai haka ne, to it means ya ji me suke cewa da Nene dazun, hakan na nufin ya damu da lamarin su? He cares for them this much? Lallai he's doing more than enough for them, its time ta fara cika Alkawarin da ta daukar ma Rafee'ah, Allah ka taimakeni, nan taji wani kwarin guiwa, tayi saurin fita, Nene tace "ke kuma ina zakije?" ina seebi tayi gaba, Hajjo ta riko hannun Nene tace "Ni zan yi jiyar ki kawata" Nene tayi murmushi kawai. Inda yayi parking Jiya ta nufa, sai ko gashi zaune kan mota, ya cire rai da zuwan ta, shi kuma ya ki tafiya, sansayar muryar ta yaji tayi Sallama tare da cewa *"Hamma Rafeeq"*da sauri ya diro daga kan motar, yana me kallon ta, Murmushi ta mishi tace "Hamma na ina kwana?" kawai sai ya ga ta chanza ta koma Rafee'ah, da sauri ya lumshe ido ya, chan ya lula duniyar tunani, *"Kai Rafeeq wannan ba Rafee'ah bace, Rafee'ah ta rasu, She's never coming back, dont let this girl mess with your head, you cant let her play with your mind "* ya bude ido tare da yin guntun tsaki, ta gaban ta ya wuce ba tare da ya kalle ta ba yace *" Get In The Car"* ya shige ya barta tsaye, na take wasu tunanin suka zo mata, Anya zata iya? Zata iya da Zafin kan Rafeeq? Anya zata iya da halin shi? anya zata iya jure komai? Ji tayi wani abu ya k'arfafa mata zuciya, taji wani irin Kwarin Guiwa, A baiyane tace *"I Can and I will, I musnt give up, not now not ever, Rafeeq Lema da yardan Allah sai ka dawo daidai"* tana kaiwa nan ta fada motar. (Please Lovers❤ Ignore all the Typos and Errors👏🏽👏🏽👏🏽) _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) This Page is for you Hauwa Nayaya❤. Pg3⃣8⃣ Yana jin shigowar ta amma be dago kai ya kalleta ba, illa tada motar da yayi ya ja motar suka bar Asibiti, ba wanda ke cewa danuwan sa k'ala, gaban Seebi sai faduwa yake tayi, shi kuwa jefi jefi sai taji ya buga tsaki, ko tsakin me yakeyi? oho! Ga mamakin ta sai gani tayi ya sha kwanar Unguwar su, tayi saurin kallon shi, sam be san iskar da ya dauko ta ba, don ko ta gefen ido be kalleta ba kuma yasan Shi take kallo, daidai gidan su Seebi yayi parking, be ce da ita komai ba, har kusan minti 3, ganin ba zai mata magana bane yasa ta fita daga motar, tana fita kuwa yaja motar ya tafi, baki hangame ta bi k'urar motar da ido, shi kuma haka yake? Yanzu da bata dauko jakkar da ta ajiye makullan gida ba ya zatayi? duk yanda take zaton Rafeeq ashe ya wuce nan, ya wuce tunanin ta, a baiyane tace *"R-Lema, you are full of wonders"* zata bude gidan kenan ta hango Baba Maigadi, da sauri ta k'arasa gun shi, da faraa suka gaisa, yace *"Nasiba, Aminene shiru, dazun da naje siyan k'osai na biyo tanan na ga k'aton kwaddo, shin lafiya?"* Nasiba cikin damuwa tace *"to da sauk'i dai, jikin ne, amma tana asibiti"* *"Allah sarki wani Asibiti kenan?"* *"Asibitin Dr Dara"* ya tabbatar mata da zaizo, sukayi Sallama ta bude gidan ta shiga, sai da ta share gidan kafin ta shiga tayi wanka, tana fitowa ta shirya, ta dauki litattafai ta sa cikin jakka, ta ciro waya ta kira Ushee, ringing daya ta ծauka, bayan gaisuwa Seebi tace *"Ya Karfe nawa zaa fara lectures?"* *"11 ne"* *"Okay to gani nan zuwa, Allah sa in samu Mota a National"*(School Bus Stop). Ta fito ta rufe gidan, ta fara tafia, tsaki tayi don tasan ba zata samu Napep din da zai kaita National ba sai ta kai bakin Titi, na Nene tace Unguwa kamar Mak'abarta. Tafia take da sauri, sai ji tayi mota na mata horn, k'in tsayawa tayi sai ma saurin da ta k'ara, daga cikin motar yayi tsaki ya k'ara gudun motar har ya sha gaban ta, kallo daya ta ma motar ta shaida me ita, ta tsura ma Bak'in gilashin windon motar ido kamar tana ganinshi, shima anan ya samu ya k'are mata kallo, abunda ya kasa ganewa shine, meyasa take rinewa ta koma mai Rafee'ah? Mesa idan suna tare yake ji kamar yana tare da Rafee'ah? Ya lumshe idonsa a hankali ya bude, chan kuma ya buga guntun tsaki. Nasiba da ta gaji da tsayuwa a gun, Har yanzu dai be fito daga motar ba, be sauke windown shi ba, gashi kuma ya tare mata hanya, to me ya ke nufi ne? Ko yana nufin ta shiga motar? ta yanke hukuncin shiga motar, ta yi jihadin bude motar ta shiga, dama abunda yake jira kenan, ya yi ribos ya dau hanya ba tare da yace mata k'ala ba. Ya duba agogon hannun shi, yayi guntun tsaki, k'arfe 10 da minti 10, Lectures dinshi 8-10 ne, ya tabbatar an gama yanzu, ya maida hankalin shi ga tuk'in sa, Nasiba tace a ranta *"barin ja shi da labari yanda zai sake da ni"* jikin ta na rawa a hankali tace *"Hamma Rafeeq wani Course Kake?"* shiru kakeji ba amsa, a zatonta be ji me tace ba ta bude murya ta sake mai tambayar, guntun tsaki taji yayi irin kin dameni nan, yayi mata banza ya manna mata hauka, Waiyo Allah, Nasiba duk tabi ta tsani kanta, tana dana sanin mai magana, ji take kamar tayu kuka, Allah yaso ta ba gaban mutane take ba, da ta gama jin kunya don wannan ya kai Dizgi, hawayen ds take mak'alewa suka soma gangarowa, da sauri ta juya tare da share hawayen tana kallon window inda suke k'etara wurare don Makarantar da nisa haka suka cigaba da tafiya ba me cena danuwansa komai, a hankali taji yace *"ina BioChemistry"* da sauri ta juyo ta kalleshi, kamar ba shi yayi magana yanzu ba, ita har ga Allah ta manta da ta tambaye shi, wato sai da ya ga dama ya bata amsa ko? Muje zuwa indai zaka dinga amsa min da sauki, a ranta take waddannan maganganun, tace *"BioChemistry naso a bani,suka ban MicroBiology, na so yin change of course don course din akwai wahala"* shiru yayi na wasu mintuna, chan ciki yace *"You are so lazy, ke komai wahala, i wonder how you passed your WAEC"* ta juyo ta kalleshi da mamaki, fuskar nan tamk'e, kamar ba shi yayi magana yanzu ba, ta murmusa a shagwabance tace *"Allah Hamma Rafeeq i'm not lazy, ka tambayi Nene"* da sauri ya waigo ya kalle ta, har sitiyari na k'okari kubce mai, tabbas da da mota ko machine a gefensu da ya buge su, Muryar Rafee'ah sak yaji, ya tsura mata ido, murmushin ta mai kayatarwa take mai, zaiyi magana kuma ta fasa ya maida hankalin shi kan tuk'i, ta lura da yanayin da ya shiga, itama ta tsorata hajan yasa ta ja bakin ta tayi shiru, har suka iso Makarantar be sake cewa 'a' ba, har gaban department dinsu ya kawo ta, yayi parking, a hankali yace "MicroBiology Is a very good course, dont worry you will enjoy it with time" da k'yar take magana kamar ance dole sai yayi, da bata kasa kunnenta sosai ba da bataji me yace ba, don ciki ciki yayi maganar, murmushi tayi tace *"Nagode Hamma Rafeeq, Allah ya saka da Alheri"* dif kamar ruwa ya shanye shi duk sanda yaji ta kira sunan shi ya kan shiga yanayin da besan yanda zai fassara shi ba, ta bude murfin mota tace *"Hamma Rafeeq na tafi thanks once again"* Waiyo Allah ji yayi kamar yayi ihu har ta kusa barin motar yace *"nace ba?"* ta gyara zama tace *"ya kace Hamma Rafeeq?"* dan guntun tsaji yayi yaba takaicin tsaidara da yayi, amma dole ya kawo karshen abun tunda shike cutuwa ya sake wani tsakin yace *"Sunana Rafeeq"* murmushi tayi tace *"ai nasani Hamma Rafeeq"* an kuma, runtse ido yayi ya bude yace *" you dont have to cal my name, in kuma ya zama dole si kin kira sunana ki kirani da Rafeeq ko R-Lema not Ham-whatever"* tace *"aa Hamma Rafeeq, ba zaayi haka ba, kasan dai ka girmeni, kuma ni Ummi ta tace in dinga girmama nagaba da ni, i cant just call your name without showing some respect, So I chose to Call You _Hamma Rafeeq_ wato _YayaRafeeq_ kagane?"* Waiyo Allah, ta gama kashe Rafeeq, ya ma kasa ce mata komai, sai k'ura mata ido da yayi, gabata dayata rikide t koma Rafee'ah, yanayin maganar ta irin na Rafee'ah, har yanda Rafee'ah ke turo baki idan tana so ya mata abu wannan ma nayi, kanshi ya dau Zafi, Nasiba kuwa tsaf ta gano shi, *Hamman* ne beso tace mai, ba yanda zaayi ta daina kiranshi da hakan don ta gano wannan ne Weakness(Weakpoint) dinshi, da haka zata sa shi a hanya, bude murfin motar tayi ta wuce ce Department dinsu, tana mamakin k'arfin halin da tayi, yanda ta cire kunya ta fara mission dinta a yau, ta sara ma kanta don ta yi namijin k'ok'ari wurin sa Rafeeq magana da yawa haka. Rafeeq kuwa kasa motsi yayi ya bita da ido har ta k'ulle ma ganinshi, mamakin kansa yake yi, wai yau shine da magana da wata mace haka, yau yayi sentence din da ya fi biyar? Kuma ba da Uncle Zaid ba ko Maalesh? Lallai abun mamaki tsaki yayi yace ma kansa "I wont let this girl affect me, shes not Rafee'ah, stop getting into my head" Jiki a sanyaye ya kunna mota ya bar gurin. *"Allah sarki ashe Nene bata ji dadi ba? dole kam muje mu dubo ta after School"* Miemee gayu ke maganar nan, Usheey tace "gaskia kam da mun gama lectures sai muje mu tari Bus" hankali Seebi be gunsu, tunanin diramar da sukayi dazun da R-Lema takeyi, lallai ta yi k'ok'ari. Miemee ta zungure ta, kina jin mu kuwa? Firgigit ta gyada kai, suna mamakin sabon haliayar Seebi, amma dai ba su ce komai ba, haka suka cigaba da lectures har karfe 2. Da sauri suke tafia amma sun makaro, Buses sun tafi, sai sun jira dawowar su, Usheey, tace da muyi ta Wannan jiran, gwara mu taka bakin gate mu tare su a chan, kafin suzo nan duk mazan nan su shige su bar mu, kunga anyi ba'ayi ba" haka suka dauki hanyar gate suna fira jefijefi, banda Nasiba da ta lula duniyar tunani, kamar daga sama ta ji horn din motar shi, waswasi take anya kuwa shine? Miemee kuwa tuni ta fara gyara zaman rigarta, tana fadin "kunga wata Azababben mota na mana horn?" a tare suka juya ga motar, gaban Nasiba ya fadi ganin motar Rafeeq, bata son su Miemee su san halin da suke ciki, a dabar ce tace "kun ga dai kuzo mu wuce" Miemee tsce wlh idan ba ku shiga ni sai na shiga" Usheey tace "muje Seebi, ba mu san lokacin da za mu bar Makarantar nan ba, muje kawai" Miemee tace daga ganin wannan gayen Ya Azabtu, don ba kowa zaki ga an bar shi ya shigo da Tint makaranta ba, Allah kasa yace ya na sona" Seebi kawai sai taji daria ya zo mata, a ranta tace "Lallai Miemee, indai Rafeeq ne zaice yana sonki to zaki bushe". Usheey tace kun ga dai kuzo mu shige kafin ya chanza raayin shi, Miemee ce tayi gaba suna binta a baya, ta bude k'ofar gaba ta shiga, Seebi tayi murna da hakan fatan ta daya kar ya nuna ya santa, ita da Usheey suka shiga Baya, Waiyo Allah Miemee na ganinshi taji wani irin dadi, tana fari tace "Ina wuni" Usheey ma ta gaida shi, bece komai ba ya kunna motar shi ya bar wurin, suka bar makarantar suna tafia, Miemee ta sake cewa "sannu fa? Ya School?" nan ma ba amsa, daga baya Seebi ta rada ma Usheey a kunne kar ki sake magana, ta dinga zungurar Miemee ta baya don tayi shiru, amma Miemee Zak'al taki yin shiru, wai kai baka magana ne? K'iiii ya taka burkii, ya gangara k'asan titi yayi parking, tsaf Seebi ta gane me yake nufi, yana nufin su fitar mai a mota don Miemee ta dame shi, idan ya bar su a dajin nan ai be kyauta musu ba, Miemee da fi'ili tace "yadai motar ce ta lalace? A hankali yace "Get Out" da mamaki Miemee da Usheey sukace "What?" cikin dan daga murya yace "ku fita nace" a tsorace suka kalle shi, Usheey tace DonAllah BawanAllah kar ka aje mu nan, kaga nan ba inda zamu samu abun hawa, ka taimaka ka kai mu ciki gari, be ce komai ba, be kuma tada motar ba. Ba tayi niyyar magana ba amma tasan hali nai, ba zai tafi ba har sai sun bar mai motan shi, daidai yanda zai jita tace "kayi hak'uri Hamma" ta mirror ya kalle ta, yayi dan guntun tsaki, ya kalli Miemee yace "kina da hayaniya" da sauri tace "yi hakuri, ba zan sake magana ba" ta bude murfin motar ta fita ta zagaya gun da Seebu ke zaune ta bude, "inshort Seebi koma gaba donAllah ke baki da hayaniya" Daria suka bata su duka, ta bude murfin motar ta fita ta koma gaba, ta na rufe wa kuwa ya ja motar shi ya bar gun, ba wanda ya sake magana har suka shigo cikin gari, a Royal Reataurant yayi parking ya fita, suka tsaya kallon kallo, ko cewa zaiyi su fito, yayi shigewar sa abin shi, Usheey ta tuntsire da daria Seebi ta taya ta, dariar da suke rik'ewa tun Batagarawa, Miemee ta hade girar sama da ta k'asa, sai da sukayi mai isar su, Usheey ta kalli Miemee tace "kina da hayaniya" Seebi ta sa daria, Miemee ta harare su tace its not funny wallahi, Wannan wani irin Guy ne? Kullum cikin k'unci, kun ga fuskar shi murtuk'e?amma fa hakan be hana kyawunshi fitowa fili ba" Seebi ta girgiza kai tace "kina da damuwa" duk suka fashe da daria, suna ganin ta fito duk suka yi shiru kamar sunga wani dodo, dauke yake da ledoji a hannu, ya bude motar ya ajiye wurin kafar Seebi, ya ja mota ya tafi, tafia sukeyi, shi be tambaye su inda zai aje su ba, Miemee ta rada ma Usheey ince mishi ya aje mu nan? Usheey tace baki daddara ba ko? To ba ruwana, duk suka ja baki sukayi shiru, mamaki ya cika Usheey da Miemee da suka gansu a Asibiti, to ko da ma ya san nan zasu zo? To waya gaya mai? Seebi ce ta fara bude motar kafin su Miemee, duk suka mai Godia, be ce komai ba, sauri sauri Seebi ta bar gun suna binta a baya, ya juya ya kalli ledar da ta bar mai a mota ya buga tsaki da k'arfi, ni ta bar ma Abinci?ni me zanyi dashi? Tsaki ya sake bugawa ya kwashi ledojin zai shiga Asibitin kenan ya ga Baba Maigadi, yayi mamaki amma be nuna mamakin sa ba, illa dauke kai da yayi dob be san tambayoyi, da sauri Baba maigadi ya karaso yace "Ahh Rafeeq me kazo yi a Asibiti? Nuna mai ledojin hannun shi kawai yayi, Au abinci ka kawo wa wasu? Ya gyada kai, yace "Nima wata makwabciyar mu nazo duba wa" da sauri Rafeeq yace "Nene?" da mamaki yace "eh ita" ko da yake ba abun mamaki bane tunda Nasiba ta san shi, amma dai Aminene ta ciri tuta tunda har Rafeeq zai zo dubata harda karin ciwo, Rafeeq yace "Baba ka kai musu wannan inji Uncle Zaid" "ya dawo ne?" tsaki Rafeeq yayi yace "baba ka amsa" da sauri ya amsa Rafeeq yace "daki na sha2" don kar ma ya sake sa shi magana ya juya ya tafi, shi ko Baba maigadi ya wuce cikin Asibitin. Miemee da Usheey suka ma Nene Sallama, Seebi ta fito rakasu, a bakin k'ofa suka hadu da Baba Maigadi, ta gaida shi, tace "baba barin raka k'awaye na, yauwa 'yar baba je ki dawo ina nan" sai da ta rakasu bakin gate din Asibitin ta dawo, yana nan inda ta barshi, yace "ya jikin Aminene? tace "da sauk'i" yace "gashi inji mutumin ki Rafeeq, wai inji Zaid" ya mik'a mata ledar, ta bi ledojin da ido, ohh dama na su ne? Lallai Rafeeq a gaishe shi, tace "Yanzu muka rabu, be ce min namu bane" ai na mayi mamakin ganin shi anan, bayan abun da ya faru yau da safe a gida" da sauri tace "Baba Me ya faru yau?" Ya kwashe komai da ya faru tsakanin Rafeeq da Baban shi da su Aneesa, harda abunda Saude tace da martanin da Aneesa ta mayar, Nasiba ta tsorata, tace *"Baba kar suyi mishi wani mugun abu, Dole Rafeeq ya dage da Adduo'i, zan tambayi baba na ya rubuto min adduoin tsari"* Baba Maigadi yayi murmushi yace "lallai Nasiba, baki san waye Rafeeq ba, Yo Allah na tuba Sallah kadai Rafeeq keyi don ya zama dole yayi shi, to tsaya kiji, Rafeeq be Sallah a Massalaci baya jam'i, sai a daki, kuma da ya idar yake tashi, baya addua a ganin shi be da bukatar wani abu da zai rok'a, be da saurin jin dadi, shifa yanzu be k'i ace ya mutu ba, a takaice dai Rafeeq baya Addua" Nasiba ta fashe da wani irin kukan da bata san lokacin da ta fara shi ba, cikin kuka tace *"Waiyazubillahi, wani irin Masifa ce wannan? Wane irin mugun hali yake son jefa kanshi ? In banda abun shi wa ke cire rai daga rahamar Allah? Waye baya da bukkata gun Ubagijin shi?"* cikin Masifa da dacin rai kamar tana gaban shi tace *"R-Lema kana cikin 6ata Wallahi, kuma ko ka k'i ko ka so sai ka dawo hanya"* _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) This is for you *Maryam AD Bappa(Umm Eeman)* Thanks for Everything ILY❤❤❤ Pg3⃣9⃣ Nasiba ci kukan ta ita kadai, ta share hawayenta, ta kimtsa fuskarta gudun kar nene ta ishe ta da tambayoyi, suka dunguma zuwa dakin tare da Baba mai gadi. Kowa da abun da yake sak'awa a ransa. Shigar su dakin yayi daidai da fitowar nene daga bandaki, inda ta dauro alwala zatayi sallah, Hajjo kuma na zaune kan darduma tana lazumi. Nene ta washe baki ganin Baba maigadi suka hau gaisawa, yai mata ya jiki, Seebi kuwa duk yadda taso ta boye damuwarta ta kasa, Nene ta dan gane yar jikallenta na cikin damuwa, ta tambaye ta "ko lafiya?" Seebi tace "Nene ba komai, gajiya ce kawai amma nasan in na dan huta zan ware" Nene ta amsa da to Allah huta gajia. Bayan tafiyar Baba ne suka zauna suka ci abinci su ukun duka, suna kammalawa Seebi taja gefe ta rusuna tana tunanin ta inda zata fitowa *R-LEMA* don tabbas rayuwarsa na cikin gagarumin hadari. Kuma He is proving so difficult to deal with. Haka ta dinga 'yan tunane tunanen ta, ta sak'a wannan ta kunce wancan har bacci ya dauketa ba tare da ta samu mafita ba. Yau Alhamis kwanan su hudu kenan a Asibiti. Seebi ta idar da sallar Asubah ta kammala adduoin ta, littafanta ta janyo ta dan dudduba don tana da lectures 9am kuma Malamin ya iya test din bazata. Bayan ta gama revising ne ta rufe ta maida komai cikin jakarta, ta saka Hijabi kan kayan baccin dake jikinta tare da gyara fuskar ta sama sama don batayi wanka ba, tayi wa nene da hajjo sallama ta wuce gida don shirin Makaranta saboda sauran kayan da ta da ke Asibitin sun yi Datti. 6:50 ta isa gida, sai da ta share gidan ta ta gyara ko ina kafin ta fada toilet tayi wanka ta shirya ta, ta fito Gida 7.55am. Sauri take ta isa bakin titi don ta samu abun hawan da zai kaita National don kar tayi missing Bus. Kamar kullum, Tuk'in shi yake cikin qasaita, daga nesa ya hangota, kamar ita kamar ba ita ba, kai itace, wannan yarinyar ce, a ransa yace "Wannan kuma me takeyi a nan? (kuji se kace be san nan gidansu yake ba) guntun tsaki yayi yace "Da naje daukan ta a Asibiti da nayi zuwan banza kenan" ya sake wani tsakin kamar yana gabanta. Horn taji da karfi, da sauri ta dode kunnenta tare da juyawa a k'ufule don ganin me neman kashe mata dodon kunne, ita da ba kan hanya take ba, Idonta ya kai ga Motar Rafeeq, haka kurum taji dadin ganin shi duk da ta san ba wai kulata zeyi ba, ko ba komai, ba zatayi latti ba, kuma zata samu daman mishi magana. Bude motar tayi ta shiga don tasan ba ce mata zaiyi ta shiga motar ba, cikin wata muryar da bata san tana da shi ba tace "Ina Kwana Hamma Rafeeq" Jan motar shi yayi, ya dau hanyar school yayi kamar be jita ba, har ta cire rai da zai amsata, don sunyi tafiyar kusan 4mins kafin taji yace *"lafiya"* da mamaki ta kalleshi, ta ma manta da ta gaishe shi, a ranta tayi dariya tace *"bakasan waye jikar nene ba sai ka dawo hanya da Yardan Allah"* wani kwarin guiwa taji, ta gyada kao tace "i can do it" Cikin sigar shagwaba tace *"Hamma na please..."* sai kuma tayi shiru tare da duban sa. Wani uban tsaki ya buga da sai da taji tsoro, ya maida hankalin shi ga tukin sa, don duk yanda ta kirashi da *"Hamma Rafeeq"* sai numfashin sa ya dauke, balle yanzu da ta zak'e wai *"Hamman ta"* "wannan yarinyar ta fara koyon surutu, ta fara zak'ewa" Kamar ba zai ce komai ba yace " what?" ta ji dadi tare da samun karfin guiwa, tace dama zance ko in munje wancan shagon zaka dan tsaya na sai Ziza Milk, don banci komai ba ina sauri kar nayi latti. Besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba, cikin sakwan da be wuce 2 ba ya daure fuska, a ransa yace "what is funny?" ji yadda take sunne kai kamar mara gaskia, lazy girl she cant even skip breakfast. Be dai ce da ita komai ba Daidai wani shago ya tsaya, tayi murmushi tace "yawwa Hamma na Nagode" Ta dauki jakarta, tana k'okarin bude kofar taji ya bude tasa kofar ya fita tare da rufowa. Gyada kai tayi cike da tausaya wa, don shi duk abunda yakeyi bata jin haushin, illa ma tausayin da yake bata. Be dauki lokaci ba ya dawo da leda kunshe da soft drink da kuma date bars ya aje mata kan cinya, ta masa godia suka dau hanya. Ta bude jakarta don saka ledar a sama ta tsinci muryar sa *"EAT NOW"* tace " *to Hamma na*. Ta bude tana ci har suka iso School, har bakin Department dinsu ya kaita, kimtsa bakin ta tayi masa godia ta fice. Shikuma ya ja motarsa ya k'ara gaba. Yana wucewa ta sauqe wani gauron numfashi tace "Wai Allah nagode maka da ka sa min dauriya, Allah ka kara shige min gaba Ameen" Zaune take gefen nene tana waya da Uncle Zaid, inda take sanar dashi cewa Nene ta warke, likita yace zuwa magriba zai Sallamesu. Uncle zaid yace "Alhamdulillah, Nene ta ji sauk'i, idan anyi sallamar ki sanar dani" tace "toh" Ta masa godiya suka yi sallama. Ta miqe ta shirya tace "Nene zan shiga makaranta bani da lecture, amma ina da Assignment din da zanyi submitting kafin lokacin sallahr Juma'a, da an gama sallahr Jumaa'h zan dawo wuraren k'arfe biyu, sai a hada kayan kafin likitan ya zo ya bamu Sallama". Murna gun Nene kamar me, tace "wlh dama na gaji da Asibitin nan, Mutum da lafiyarsa amma an kawo Asibiti an ajiye, amma fa zanyi kewar 'yar gasasshen Kazar da dunkum ke kawowa" (Dunkum ne sunan da Nene ta sa ma Rafeeq) ba Seebi ba harta Hajjo dake gefe sai da ta dara tace" Kai k'awalliya, jika na ne Dunkum?" Nene tace "yo ehmana, ayi mutum shi he daria, be murmushi be magana? Hajjo tace "lamarin Rafeeq sai du'ai, haka yake" Nene tace "Shiyasa na rik'e furfurata, ba ruwana dashi, don in na mai magana ya share ni, ina iya kulle shi daki karfe ukun dare inci Ubanshi, dan uban mutum" me Hajjo da Nasiba zasuyi in ba daria ba, Nasiba har da kwallah, Hajjo tace "Lallai Nene Lafiya ta samu" Nene tace "dama garas nike, uwayen fiili suka daura man zaman dole a Asibiti, wato Seebi da Zaidu bawanAllah" Nasiba dai ba ta tanka ba. Dan zaman da sukayi na kwanaki biyar Hajjo da Nene suka Saba don Nene akwai surutu da saurin shiga rai, hajjo kuwa akwai barkwanci.. Ku daga daga k'afa mu isa on time kunga yau Friday, Buses cika zasuyi da wuri. Seebi ce mai maganar nan, Usheey tace "in ba haka ba sai mun ci uwar trekking kafin mu samu naAllahn da zai bamu Lift. Kamar Baki, ga Buses har uku amma duk a cike mak'il har bakin K'ofa, Seebi ji take kamar tayi kuka don haushi. Tasan Nene na chan na zuba idon ganin ta, ita da ce mata 2 zata dawo, gashi har uku. Miemee ta bada shawarar su fara takawa Ko Allah zaisa su samu lift ko kuma rage hanya kan Buses su jiyo atleast yafi tsayuwar. Usheey tace "Miemee don Allah in za a bamu lift yau kar ki yi over sabi please" Seebi na gimtse daria tana fuska, Miemee ta daure fuska tace "Munafuka, say your mind" Seebi tace "Kina da Hayaniya" Miemee tace "Kuna da damuwaaa" ai kuwa duk suka fashe da daria, Miemee tace Wallahi gayen nan ya mugun raina ni" sukayi daria suka fara tafia. Tafia suke tayi, sun danyi nisa sai ganin motar R-lema sukayi a gaban su, basu tsaya wata wata ba suka nufe motar, Seebi zata bude kofar baya ta shiga Usheey ta buge hannun tace "donAllah shiga gaba kar ya chanza raayin shi" Miemee ta harare su tace dama ce muku akayi zan shiga gaba? Seebi ta shiga gaba duk suka koma baya, a tare suka gaida shi, kai kawai ya daga musu, ya ja motar shi ya tafi, ko da suka iso cikin gari ya kalli Ushee ta mirror kamar zai yi magana sai fasa, tsaf Seebi ta dago shi, so yake yace dasu Usheey ina zai sauke su amma ya kasa, Seebi tace "DonAllah ta wurin Asibitin Dr Dara kayi?ni nan zan sauka" Shiru yayi kamar be ji ba, ganin be da niyyar tsaiyawa ya sa tace "Kana iya ajiye mu anan" kamar jira yake kiiii yaci burki, yayi parking, Usheey da Miemee suka mai godia ko uffan be ce musu ba, suka bude suka fita, Seebi zata bude k'ofar kenan ta fita ya sa lock, su Miemee na kullewa ya ja motar shi yayi gaba" Su Miemee suka bi motar da Ido baki a hangame. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg4⃣0⃣ A tsorace ta dan kalleshi, ko bi ta kanta beyi ba ya hau titi kanshi a tsaye, Maimakon suyi hanyar Asibiti, sai bani tayi ya dauki hanyar *Sally's Cuisine* ba tace da shi komai ba har ya iso yayi parking, fita yayi ya shiga, nan ta samu damar amsa Wayar Usheey da tun da suja aje su take ta faman kiran ta, "Hello Seebi ina zai kaiki?" tayi daria tace "Asibiti" "haba har hankalin mu ya kwanta" tana ganin ya fito tayi saurin katse wayar, Hannun shu dauke da ledoji 4 ya aje mata 3, dayan kuma ya aje a seat din baya yaja mota sukayi Asibiti. Ko da suka isa Asibtin, har ta bude murfin mota zata fita, Zuciyar ta ta bata shawara, ko bazai amsa ba, ki masa godiar dawainiyar da yake tayi daku, Abinci lunch da dinner baya fashin kawo muku, ga kai ki makaranta da dawo dake duk da ba kullum ba. Ta juyo ta gyara zama yanda tana fuskantar sa tace *"Hamma Rafeeq, Yau Dr ke sa ran Sallamar mu, mun gode kwarai da dawainiyar da kakeyi da mu, Allah ya biya ka, Allah ya saka da Alheri ya, Allah ya ji kan Magabata, Albarkaci Rayuwar ka, Allah ya kuma Saka maka duk Zalincin da aka taba maka, wanda ba za ka iya yafe su ba"* tana kaiwa nan ta fice daga motar, bata tsaya sauraren abun da zai ce ba, Yanda kuka san Hoto, haka Rafeeq ke zaune a gun, ko yatsar shi ya kasa dagawa, be san lokacin da ya furta *"Ameen*" ba. Haka kurum yaji dadin Adduointa, Shi be san meyasa ba, amma yana jinta a jikin shi, kawai yaji ya bata babban matsayi a ran shi, jinta kamar FEE'AH. Da k'yar ya kunna mota, saboda jikin sa ya mace gabaki daya, ji yayi ya kasa tafiya, guntun tsaki ya sake ya duba Aljihun motar shi ya ciro paper da biro, rubutu yayi sannan ya fita ya shiga Asibitin, daidai Dakin ya chokara a jikin kofar yadda in an bude zaa gani, yayi tafiayar sa. Seebi na idar da Sallah ta dauki Abincinta, Su Nene har sun gama da Abincin da Nasiba ta shigo dashi,nan zaman jiran Sallama sukeyi, Nasiba tace "bari inje in ga Dr, k'ila ma ya mance da yace yau zai sallame mu" Nene tace "E danAllah, na k'agara inga nayi juyi kan Gadon K'arfe na" sukayi daria duka. Tana murda kofa wata kaaramar Takarda ta fado, duk'awa tayi ta dauka, ta na budewa tabi rubutun da ido, Murmushi tayi a hankali tace "R-Lema" a nutse ta fita daga dakin ta fara karantawa ga abun da yace _"Ameen to your Duas. Idan an sallame ku, ga number na ki min text you DONT have to Call just TEXT"_. Seebi tayi murmushi ta sake karantawa, tace *"R-LEMA kenan Allah ka bani ikon taimaka ma beautiful soul dinnan"*. Tasa kai ta wuce office din Dr. A hanya suka hadu da Dr da Nurse Sai suka juya suka koma dakin. Nurse ta gwada Bp da Temperaturen Nene, komai daidai, Likita yace "Mama, kin ji sauki sosai, zan sallame ku, Amma donAllah ki rage cin Jan Nama" Nene ta bishi da kallon kai gaja, tace *"yaro wani Nama ne Ja?"* yace "Naman Sa, ko na Awaki" Nene ta tuntsire da daria, tace "Su balangu da tsiren da nake ci kake son hanani ci ko? Yace " Mama saboda Lafiyar ki ne, bawai ina son hanaki bane" ta tabe baki tace "toh dai bari kaji Ubana *Mamman* Shanun shi 31, duk bayan wata ake kashe mana daya, ba saidawa ake ba ci mukeyi, kuma ban taba jin ance wani naman Shanu yasa shi ciwo ko wani abun Allah sauwak'a ba, toh nidai _Aminene Mamman_ da bakin ciki ya kashe ni gwara Dadi ya kasheni Ehe" Nasiba tayi saurin cewa "I'm so sorry, She's always like this, InshaAllah she'll regulte it" Dr yace "Dont worry i have someone exactly like her at home" Nene ta cika tayi fam tace "Oho dai, Sai ka sallame mu yau, Ke kuma ni zaki chanzawa ko? To in ma zagina kukai da Ubanki Mahammadu kuke" Dr ya fashe da Daria yace "yi hakuri Mama ga takardar sallamar ki" yafi maka don yau ko baka sallameni ba gida zan kwan" Nasiba ta girgiza kai cike da takaici, Hajjo kuwa sai daria take tayi. Dr na fita Nene tace " _kinga latso min Zaidu bawan Allah a waya, ba gardama Seebi tayi yadda nene tace, Yana ganin kiranta ya yanke ya sake k'ira Zaid yayi Murna kwarai da jin Sallamar su Nene, kuma ya bata shawaran bin yanda Likita yace, jin shi kawai Nene tayi don ba ta da Mak'iyi kamar me son rabata da Nama, nan dai ta hau yi mishi Godia da Adduoi, Ya tsaidata ta hanyar cewa Haba Nene, Kun wuce nan, babu godia a tsakanin mu. Sukayi Sallama. Bayan Seebi ta karba wayar ne yace mata zai turo a maida su gida, tace ai "Hamma Rafeeq yace in gaya mai idan an sallame mu" da Mamaki Zaid yace "Rafeeq dai?" tace "eh shi" shi da kanshi yace haka?" tace "eh" "Rafeeq yana zuwa ne?" tace "Duk da ba shigowa yake ba, amma yana kawo mana Abinci Rana da Dare, sometimes ya na aje ni makaranta" Allahu Akbar zo ku ga jin dadi gun Zaid, Ashe Rafeeq na da sauran Mutunci da tausayi a tattare dashi? Be taba ganin Rafeeq ya damu da lamuran wasu ba kamar su Seebi lallai akwai Improvement, yace da Seebi "to sai kun koma gida mayi waya" sukayi Sallama. Duk zaton Nasiba da Nene Zaid ne ya sa Rafeeq dawainiya dasu, duk abunda yake yi saboda Zaid ne, nan suka gane cewa ashe Rafeeq ne ya sa Kanshi, ba kowa ba. Nan Nasiba ta k'ara samun wani k'warin guiwar Aiwatar da Kuddirinta. Seebi ta kwafi numbern da Rafeeq ya bata, ta masa text din as he demanded. Ga abun da tace; _"Assalamu alaikum Hamma Rafeeq anyi discharging din mu, mun shirya, we are good to go"_ Yana wanka yaji wayarsa alamar shigowar sak'o, bayan yayi Sallah, ne ya daga wayar ya ga message daga new number, ya bude ya karanta, dan guntun tsaki ya ja (Ikon Allah! sak kace bashi yace ta mai ba). Key kawai ya dauka ya fice daga gidan sai Asibiti, yana isa ya mata text "Ku fito". Seebi na jin shigowar text ta duba taga Shine, ba su wani dau lokaci ba suka fito harabar Asibitin da kayan su. Inda yake aje Motar shi sukayi, ta na zuwa ta iske Booth a bude, be fito ba haka Seebi ta shiga saka a kayan boot sai da ta gama, sannan ta bude gaba ta shiga ta zauna su nene kuma sun shiga baya. Sai da suka bar Asibitin, da kyar yace " Ya Jikin?" Nene ta murmusa a ranta tace Uban Kasaita, a fili kuma tace "Alhamdulilah, na watsake" kamar ba zai ce wani abu ba yace "Sannu Fah" tace "yauwa" a hankali tace kamar dangin Maguzawa wai sannu" Hajjo da Nasiba kadai suka jita, Murmushi kawai sukayi, tun daga nan ba wamda ya sake magana har sai da suka iso gida, ya juya ya dan kalli Hajjo yace "Hajjo Mom tace ki k'ara Sati daya sai ki koma gida" tayi murmushi tace "ba damuwa" Tare da taimakon Hajjo suka shiga da kayan su ciki, sai da ya tabbatar sun gama kwashe wa ya danna horn, ta lek'o ta window, ya mik'a mata manyan ledojin Abinci, yaja motar sa yayi gidan su Maalesh. *England* Zaid ne kwance kan tafkeken Gadonsa yana waya da Mami, inda aka bashi Ayman ta dinga mai gwaran cin ta, har sukayi Sallama sannan ya kira Nasiba, Suk gaisa ya tambayeta ya jikin Nene ta amsa masa da sauk'i. Suka danyi hira sannan ya gaisa da Nenen itama ya musu Sallama. Nan ya hau tunanin wanda zai sa ya musu Grocery shopping, don ya tabbatar suna da Buk'ata, baya son takura wa Rafeeq, Saboda abunda ya fahinta, Rafeeq has done more than Enough, kuma baya so ya k'ure shi . Maalaesh ya fado ransa, Take ya kira wayansa, Ringing biyu ya dauka "Hello Mahmud" nan take ya gane Uncle Zaid ne, don shi yasan shi kadai ke kiran shi da sunan shi na Asali, "UncleZee ina wuni" suka gaisa, yace "Mahmud ina so donAllah ka min Shopping na kayan Abinci, da kayan buk'ata na Gida, ina so ka kai wani Gida na nan ku sa da gidanku na Layout(Gidansu Rafeeq yake nufi) Nan ya mishi kwatancen gidan. Malaesh yace "Angama, anything for you uncle Z" barin je yanzu ma, "barin maka transferring kudin" da sauri yace "Noo akwai kudi hanuna Uncle Z" "dont be Silly Son, i'm sending now" Murmushi Maalesh yayi yace "Nagode" suka yi Sallama, Nan take Zaid ya mai Transfer din 100k. 2:47pm Seebi na zaune bisa kujera yar tsugune, tana yi wa Nene tsifa, i Nene da Hajjo na kan tabarmar k'asa, Sallama suka ji, da sauri Seebi ta zaro Mayafin ta kan Igiyar Shanya, Nene ta daura dankwali tare da Amsa Sallama, Maaleah yace "donAllah nan ne Gidan Nene?" da sauri tace Eh Yaro Shigo, nice nan Aminene, yace toh ina zuwa, Yara ya samu ya sa su kwasan kayan ya ce suka shiga gidan nan, Mamaki ya rufe su Nene, ana haka ne Maalesh ya bi bayan su ya shigo, yana ganin Hajjo ya bude baki "Laaaah Hajjo, kece nan?" tace "Maalesh yaushe a gari?" yace "jiya na shigo, na tambayi Mom kina ina tace ba kya nan" tace aiko dai gani anan, ya durkusa ya gaida Nene, ta amsa mai cikin Fara'a, yace "kece Nene daga gani" ta nuna kanta da Yatsa tace "Nice nan Aminene Yar Mamman, duk duniya ba wata Nene sai ni" ta nuna Nasiba da hannu tace "Nenen Seebi kake ji" ya juya ga wacce aka cema Seebi, ya ga shi take kallo, tsaf tagano shi, shine wanda kwanaki da zai basu Lift yace sai ta cire Nikab, kuma Shine Abokin R-Lema, ta dai maske ta gaishe shi, "Lord have Mercy" inji Maalesh, tuni Nasiba tayi gaba da Imanin shi, da kyar ya amsa mata fuskar shi cike da Annashuwa. "Hajjo tace Maalesh wannan kayan fa?" yace "Uncle Zaid yace a kawo" Nene ta chafe "Allah Sarki Zaidu Bawan Allah, Allah shi biyaka ya saka da Alheri, Malush kaima Nagode maka" Yayi daria yace Nene "Maalesh nake ba Maalush ba" duk sukayi daria, na da nan Maalesh suka dinke da Nene, k'wank'waman su iri daya na surutu, sai yi suke tayi yanda kasan sun dade da sanin juna, dama shi Maalesh saurin Sabo ne dashi, nan Hajjo ta zubo mai Burabusko ya kwasa kamar ba gobe, sai kallon Nasiba yake tayi, ita kuwa sai smilling take tayi tana jin diramar su da Nene, har kusan Laasar be da niyyar tafiya. Wayar sa tayi k'ara, ya ciro daga Aljihu ya duba, ya kalli Hajjo yace dan gidan ki ne, tayi murmushi tace "Rafeeq Ho" ya dauka "my guy howfa?" kusan sakwan 3 beyi magana ba chan yace "kana ina? Nazo gida baka nan" Maalesh yace "Wallahi gani ta wurin gida Uncle Zaid ya aikoni" tsaki Rafeeq yayi yace "ina jiranka" ya kashe wayar, Nasiba ta tsura wa wayar Maalesh ido, kamar tana jiran Rafeeq ya fito daga ciki, Nene tace "Wannan uban Yan k'asaitan ne ko?" Maalesh yayi daria yace "Nene kinsan Rafeeq ne?" ta ta6e baki tace "ai wannan sai kun hada mai da tofi" yayi daria yace barin je, sai na dawo ya musu Sallama ya kalli Nasiba yace "Bye Beautiful" ita kunya ma ya bata ta rufe fuskar ta da tafin hannayen ta. Yana shiga Dakin shi ya ga Rafeeq kwance kan Gado, ya bubbuga mai k'afa, kamar ba zai tashi ba, ya mike sukayi side hug, Maalesh cike da doki yace "I met her, Wallahi naganta yau" da k'yar Rafeeq yace "Who?" Maalesh yace "The love of my life, Seebi, Uncle Zaid ya aike ni Gidan su yanzu in kai ma Nene sak'o" a dan tsorace Rafeeq ya kalleshi, kamar zaice wani abu sai ya fasa, be damu da Rashin Ansashi da Rafeeq yayi ba, Maalesh ya cigaba "Shes beautiful, ai kasanta, ta hadu ko? Zamu dace? Haka ya ishe Rafeeq da maganar Nasiba, yace " Guy do you think she'll like me? Wallahi ina sonta, kawai ganinta nayi gefe na kamar an jefo ta, ina ganin ta naji She's the one, wannan shi ake kira "LOVE AT FIRST SIGHT" cikin kufula da daga murya Rafeeq yace "Will you Shut the f**k up? _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg4⃣1⃣ Maalesh ya kalleshi da mamaki yace "Guy, Calm down" Rafeeq yayi guntun tsaki cikin yanayin shi yace "ban ga dalilin da zai sa ka dinga min maganar wata yarinya ba, duk ka bi ka ishe ni" Maalesh cikin doki yace "Feeq ba zaka gane ba, Wallahi ina sonta, sosai fa" kamar ba zai ce komai ba yace "She's Innocent, dont hurt her" da sauri Maalesh yace "Wallahi i wont, shes not like the rest of the girls i'm with, Wannan ta dabance, guy bani shawara ya zanyi?" chan cikin mak'ogaro yace "Tell her" "bansan mesa ba i lost the courage, ai da tun dazun na gaya mata" Rafeeq yayi shiru ya cigaba da latsa wayar shi be ce komai ba, Maalesh ya yi rigingine kan Gado, Rafeeq ya dora wayar shi kan cikin Maalesh, Maalesh ya tashi da sauri ya dauki wayar Rafeeq ya duba, kan Screen din ya ga Message ya karanta, ya kalli Rafeeq don neman k'arin bayani, guntun tsaki Rafeeq yayi yace "The girl's Number" wani irin super Maalesh yayi ya duro, ya rungume Rafeeq, donAllah numbern ta ne? Kai Nagode Breh, naji dadi Wallahi" Shi dai be ce dashi komai ba, Maalesh yayi copying number din yayi saving a wayanshi. Tana tsakiyar su Nene suna fira, wayar ta yayi ringing, ko da ta duba New number ne, ta dauka da Sallama, Muryarta yafi komai dadi inji Maalesh, ya amsa yace "Hello, Beautiful" wani ajiyar zuciya ta sake ta amsa da Ina wuni don ta san me muryar, yace "kingane me magana ne? Cikin jin kunya tace "eh" to waye? ta yi Murmushi tace "Ya Maalesh ne" Waiyo dadi, Ya Maalesh, karo na farko bayan Rasuwar Rafee'ah yaji an kirashi ta wannan sigar, yace "Seebin Nene, you are a Blessing, kinji Voice dinki kuwa?" kunya ya bata sai bata amsa shi ba, yace "are u there? Kinyi shiru?" a hankali tace "i'm here" "Seebi will you be my friend?" Daria kawai tayi, ya kike daria? "Ba kya so in zama Abokin ki? A hankali tace "Aa" yace "Aa mene? Kina so? Will you be my friend? A hankali tace "yes" Darian jin dadi yayi yace "let me warn you, my friends usually say i'm a Sweet Soul, abun nufi shine Wata rana Abokantakar mu na iya rikidewa ya koma Soyayya" Daria kawai tayi, nan suka sha fira don Maalesh akwai Zance, sun dade suna waya inda ya shaida mata zaizo Gobe don Jibi zai wuce Kano inda yake Service. *Washe Gari* K'wank'wasa k'ofar yayi, sai da ya kusa minti 3 kafin yazo ya bude mai, hararar shi Maalesh yayi ya ra6a ta gefen shi, ya shige cikin Dakin, Da k'yar Rafeeq yace "Sorry i missed your call" Maalesh yace "and you cant call back?" Guntun tsaki Rafeeq yayi yace "I said i'm sorry didnt i?" Maalesh ya k'ulu ya mik'e zai fita da sauri Rafeeq ya rik'o shi, kasa magana yayi ya girgiza kanshi, Maalesh ya dawo ya zauna, Rafeeq yace "Look, wannan Aneesar banzan ce take takura min, shisa na kulle k'ofana, coz duk abunda zan mata bazata yi zuciya ba, so da ka kirani i thought itace shisa ban dauka ba" Maalesh ya girgiza kai cikin takaici, ya akayi sunana da na ta yayi kama, har da ka zata itace?" a takaice yace "ban duba wayar ba" "Oh lord have Mercy" Inji Maalesh da sauri Rafeeq yace "Kayi kyau Sosai, ina zakaje ne haka?" Don dai ya 6atar da zancen don yasan Maalesh da mita kamar Nenen Seebi. Murmushi Maalesh ya sake yace zanje Gidan Nene ne, zanje musu bankwana, Tsaki Rafeeq ya sake "Do you really have to go there?" Maalesh ya amsa da sauri "Yes My other Half is there" wani Mugun tsaki Rafeeq ya sake tare da kwanciya kan Gado, Maalesh ya mik'e yace "Feeq, barin je sai na dawo" da sauri Rafeeq yace "Wait" da Mamaki Maalesh ya kalleshi, Rafeeq ya dauke ido be so su hada Ido da Maalesh yace "I'm Bored, i'm coming with you" be jira cewar Maalesh ba ya fice daga dakin, Maalesh da mamaki ya maimaita "He's Bored?" Sabon Salo, gemu a kafada, yau Rafeeq yake cewa he's bored, shida be k'i ya kulle kanshi a daki ba, be komai, lallai kam, toh K'ila ya fara Chanza halinshi, Allah ya sa don sai nafi kowa Farinciki, ya fita tare da kulle dakin da Mukulli ya bi bayan Rafeeq. Bakin Zauren Gidan Maalesh ya doka Sallama "Assalam Alaikum" daga Ciki Nene ta Amsa, tare da cewa "Bismillan ku" Maalesh a gaba Rafeeq na bin shi a baya sai shan k'amshi yake tayi, kamar an ce dole sai ya shiga, ta Window Nene ta hango su, da sauri ta fito tana tafa hannayen ta, tana fadin "Ga Maalush ga Maalush" wani Murmushi Rafeeq ya saki ba tare da ya sani ba, suna hada ido da Nene yayi saurin daure fuska tare da dauke kai, ko meyasa be so taga Murmushin shi oho,a fili Nene tace "Chan ta Matse maka a matsatsen wandon ka"Maalesh ya fashe da daria, yace Nene ke dawa?" ya juya ya kalli Rafeeq da ya hade girar sama da ta kasa, Nene tace ni rabani da wannan Mara fara'a, Sannun ku da zuwa dai" ta bude baki tace "Seebi, fito da tabarma, ga Malush da Dunkum" Maalesh dai sai daria yake tayi, Hajjo ta fito, suka gaisa da Maalesh, tace "Rafeeq" Murmushi kadai ya mata, ya dauke kai, Nene sai ikon Allah take kallo, a ranta tace "Lallai yaro, kazo gidana ka dinga sha min kunu? To uban tauri ma yaci ubanshi" ta gyada kai ta shiga cikin kichin don ita kadai tasan me zata ma Rafeeq, Nasiba taji dadin zuwan su, ta dauko Tabarma ta fito kanta a k'asa ta shinfida musu, Maalesh ya fara zama sai Rafeeq, Maalesh ya bita da ido, ta dukursa ta gefen da Rafeeq ke Zaune tace "Ya Maalesh, Ina Wuni?" Maalesh yace "Lafiya lao Beautiful, ya Jikin Nene?" "Nene ta ji sauk'i Alhamdulilah" Kafin yace komi wayar shi ta fara ringing, ya dauka, Nasiba ta kalli Rafeeq, duk da ba ita yake kallo ba yasan shi take kallo, kamar ance ya kalleta, Idanuwan su suka hadu, ido cikin ido suke kallon Juna, a sanyayye Nasiba tace "Hamma na Ina wuni?" tsaki yayi ya dauke kansa, ko a jikinta ta tashi ta koma ciki, da sauri ya bi bayanta da ido, duk ya ji haushin da be amsa ta ba, tsaki yayi ya juya ga Maalesh, ashe tuni ya gama wayar, kallon juna sukayi, Nene ta katse musu hanzari, gaban Maalesh ta ajiye kwano, tace "Maalush dan Albarka, ga Zogale na kwandon ta maka kaci kai kadai kar ka ba kowa" ta karasa fadin haka tana kallon Rafeeq ta gefe ido, sosai ta ba Rafeeq daria, kallon Gefen shi yayi ya dinga Murmushin mara sauti a ranshi yace "Chill Tsohuwa, i cant eat this Sh*t" Maalesh yace "Kai Nenen mu kina ji dani fa, duk wannan ni kadai?" Ehmana dole nake ji da kai, wasu ko kallo basu isheni ba ai" Rafeeq ya kawar da kanshi gefe don yana gudun kar daria ta kubuce mai, wai don shi tsohuwar nan ke habaice habaice, lallai tana da damuwa, ta shekara tanayi ko a jikin shi, haka Maalesh ya zage sai cin Zogale yakeyi, da yake shi yana son abubuwan gargajia, Nene ta dauko kujerar tsakar gida ta zauna, don ta na ta Rok'on Allah sa Rafeeq ya nuna yana son ci ta k'are mai tanadi. Ga Mamakin ta har Maalush ya gama Rafeeq be dago kanshi ba, Rafeeq ya zunguro Maalesh, ya k'agara su tafi, Maalesh yace "Nene, bari mu tafi, gobe zan koma kano InshaAllah" Nene ta hau suburbuda mai Adduo'i kala kala, ta kwalawa Seebi kira tace kuzo kuyi bankwana Gobe zai tafi, ta fito ta raka su har Waje. "Ya Maalesh a kano kake aiki? Yace aa, Service nakeyi, befi wata 2 in gama ba, sai in samu aiki sai in fito a sa bikin mu ko? Dariya tayi sosai tace "you are funny" yace "you think so ko?" ya kalli Rafeeq yace "Guy, tell her ba wasa nakeyi" tsaki Rafeeq ya buga tare da bude mota ya shiga, duk ba su damu ba don sun san saran Rafeeq na tsaki, sai da sukayi Sallama kafin ya Shiga mota suka wuce. *MAFARKI* "Assalam Alaikum Nasiba" Murmushi tayi tace "Sai yau Ko Yaruwa ta Rafee'ah?" "Afuwan Ukhti, Ya Hakuri da Hidima?" Nasiba tace "Toh mungode Allah" Rafee'ah ta fara magana cike da natsuwa "Da farko zan fara da gode miki, kin aiwatar da Aikin Farko da na saka ki, ina me miki albishir da kin riga da kin shiga Rayuwar Rafeeq, kinyi Namijin k'ok'ari, ina jinjina miki, abu na gaba shine, kinsan ance duk yanda mutum keso ya ci Nasara, ya kuma samu Albarka da Ribar Rayuwa, to ya bi Mahaifanshi, Musamman Mahaifiya, duk yanda kake son samun Nasarar Rayuwa, Idan baka bi Mahaifiyar ka ba, to ba zaka taba ganin daidai ba, duk me ka taba zai ruguje, kai ko da ka samu to bazaiyi Albarka ba" Nasiba ta jinjina kai tace "Haka ne" Rafee'ah ta cigaba "Toh abu na gaba shine, ki daidaita tsakanin Rafeeq da Mahaifiyar shi, indai kina so Rafeeq ya gama Makaranta wannan Zangon, to dole sai ya samu Albarkar Uwa, ba wannan ba dai, Duk da yana cikin Duhu, ya nemi gafarar Uwarsa, don ko yau ya fadi ya mutu sai Allah ya tambaye shi, don be nema samun Haske ba, ki Daidaita tsakanin su, Nasiba" Nasiba cikin Firgici tace "Ta ya zanyi haka? Kinfi kowa sannin kafiyar Rafeeq, ina zan nema Mahaifiyar ku? Ina zan ganta? Ta ina zan fara?" *Ke Alheri Ce* *Ke Alheri Ce* *Ke Alheri Ce Nasiba Muhammad* bat ta Rafee'ah ta bace, a firgice Nasiba ta farka daga Baccinta, "ki taimake ni Rafee'ah, atleast give me hint ya zanyi? duk ta bi ta jike da zufa, Minsharin Hajjo ya tunasar da ita Mafarki ne tayi, da sauri ta sauka kan Gado ta fita daga Dakin, ta dauro Alwala tazo ta kabbara Sallah, sai da tayi Raka'ah Shidda kafin ta dukufa da Adduoi, Alkah ya shige mata gaba, ya kawo mata komai a Sauk'ak'e. *9:45am* "Ki tsaya kiyi Kallaci Seebi" "Aa Nene zanyi a Makaranta, sauri nake kar bus ta tashi" "to Allah ya taimaka, a gaida miemo gayu" "Zataji sai na dawo" da sauri ta bar Gidan ta na ciro yar Tecno dinta a jakka ta latso number Usheey, "Usheey, kin isa National? Akwai Bus? Usheey tace " Eh Seebi, biyu sun tashi saura daya, kiyi sauri kar ta cika mu tafi" Seebi kamar tayi kuka, tace Gani nan na kusa bakin Titi, zan samu Napep" "Okay to sai kinzo" Ji take kamar tayi gudu, don in Last bus ta wuce bata san yadda zatayi ba. Kamar a sama ta ga Motar Rafeeq a gabanta, bata san lokacin da ta sake Murmushin da ke kara ma fuskar ta kyau ba, ba watawata ta zagaya ta bude K'ofar ta shiga, k'amshin sa ya sa ta lumshe ido, ta bude baki zata gaishe shi, sai kuma ta tuna wani abu sai ta fasa, har ya ja motar shi shiru shiru bata gaida shi ba, ya saurara yana jiran ta gaishe shi amma bata ce ko 'a' ba, a ranshi yace ko lpy? Ta gefen ido ya kalleta sai hura hanci take yi, tana girgiza kaf'a tana kallon window, yau kuwa meye Haka? Guntun tsaki yayi yace ma kanshi "why do i even care?" ya dauki hanyar Makaranta, kusan minti 10 ba wanda yace da danuwan sa k'ala, Nasiba tayi wani shu'umin Murmushi, sun kusa Makaranta daidai Daji-dajin hanyar, Nasiba ta daddage ta buga tsaki da k'arfi, har cikin kunnen Rafeeq, da sauri ya dafe kunnensa da hannu daya, be yi magana ba, Tsut ta k'ara jan wani tsakin da ya fi na farkon k'ara, Haushi ya cika Rafeeq, kamar yayi me, be dai tanka ta ba, ya tsani Tsaki (kuji mun Rafeeq, wai ya tsani Tsaki) Nasiba na lura dashi, ta k'ara jan wani dogon tsaki daidai ta taka burkin Motar da Rafeeq yayi ji kake k'iiiiiiii, Nasiba ta tsorata sosai, ta kalleshi cike da tsoro, ba tare da ya kalleta ba yace "Get Out" Nasiba ta juya ta kalli dajin nan ga sanyi, gashi bata tunanin zata samu na Allahn da zai karasar da ita Makaranta, har zata bashi hak'uri, sai kuma ta fasa, bude k'ofar tayi ta fita, kamar jira yake ya ja motar shi ya wuce, ya barta nan tsaye, hawaye suka soma kwaranyowa, tayi dana sani, meyasa take son k'ureshi? Ita dake son fiddo shi daga yanayin da yake ciki, Meyasa ta k'osa, to gashi ya direta kan hanya, kuma ba zata iya takawa ba, don tafiar da saura, ta rasa yanda zatayi ta zauna gefen Titi ta na me rokan Allah ya kawo Bus ta tsaida su ko a tsaye sai ta tsaya. "Mtswwww" tsakin da Rafeeq yayi kenan Karo Na 8 bayan ya dire Nasiba, meyasa zai ajiye ta bakin hanya? Yanzu if shes not careful Mota ya bugeta fa? Tsaki ya sake yi tare da kallon Mirror dinshi, chan ya hango ta zaune gefen Titi kamar Almajira, Tsaki ya sake yi yasa trafficator yayi U Turn ya koma Baya, horn ya mata da sauri ta dago ta sake Murmushi, a ranta tace "Ba zai iya bari na anan ba" kawar da kanta tayi gefe kamar bata ganshi ba, tsaki yayi da k'arfi, ya danna mata horn, ko dagowa batayi ba, takaici kamar me, wai shi yau ake ma haka? Allah Allah take kar yayi zuciya ya barta nan, amma wani zuciyar ta bata karfin guiwa, Matso da motar yayi kusa da ita ganin zai take mata k'afa yasa ta tashi ta hau kan dakali, da k'yar yace "Get In the Car" A takaice tace "No thanks" tsaki yayi yace " Nace ki shigo ko? So kike kiyi Missing Lectures?" a tsiwance ta murguda baki tace" What do you care idan nayi missing lectures? Werent you the one that dropped me here? Ba zan shiga ba" ta sake murguda bakinta, kamar Tv ya ke kallonta, mamakin ta yake, yaushe ta koyi Rashin kunya? Yaushe ta samu guts din mai magana haka? Yau Shi R-Lema ake ma haka? Lallai Yarinyar nan bata sanshi ba, be san me ta taka ba. Abun Mamaki be daddara ba yace "ki shigo motar nan" ta juya tace "ba fa zan shiga ba nace" kamar zaiyi kuka, besan lokacin da yace "Will you Please get in the Car now? Please". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) *This is for y'lls Members of Miemee Bee 👄Novels, You guys are Simply the best, I see lotta _™Nasi-Feeq_ , lotta _™Nasi-Zaid_, too bad no ~™Nasi_Lesh~ , lols😂 ILY'lls❤❤❤ Together we keep it moving💋 *#1love* Pg4⃣2⃣ "Oh shit" ya fada da ya tuna abunda yace, yau shine da cewa please? Kuma ba amfanin shi ba, sai na wanda ya ce ma wa? Lallai in har bata shiga motar nan ba zai tafi kuwa ya barta, a 6angaren Seebi kuwa, kalmar 'Please' ta maimiata cike da mamaki, Yau Shi R-,Lema ke cewa please, aah akwai cigaba, akwai nasara, amma me tasan in ta tsaya jan aji tafia zaiyi ya barta, kuma ba lallai bane ya dawo a wannan karon, a sakwan da be wuce iku ba Rafeeq yayi shawaran tafia, sakwan da be wuce biyu Nasiba ta fada motar, be tsaya jira ba ya hau kan titi, ko kallon shi batayi ba, shima bai kalleta ba, har suka zo Makaranta, ya kawo ta bakin Department dinsu, ya na parking ta fita tayi banging door shi kanshi ya firgita, ya bi ta da ido yana mamakin Wannan bak'uwar Halin da shi be san da ita ba, to ko dai tana da damuwa ne? Saboda ya san ta kullum ta shigo Motar shi sai ta gaida shi, in ko yayi dropping dinta sai ta zabgo mai addua tana mai Godia, amma yau ba Sannu bare Nagode. Tsaki ya ja yana fadin "Matsalar ta, i dont need her thanks, greetings whatsoever" ya ja motarshi yayi gaba. Zaune take kan lallausan Rug dake kusurwar dakin ta, jingina tayi kan luntsuma luntsuman throw pillows da aka wa bangaren ado, Grapes take ci a k'asaita ce, Meema ta shigo ta zauna kusa da 'yaruwarta, ta daga kai sama tana kallon POP din dakin, da Walpaper, da wakeken gadon ta, ga madubi shak'e da turarruka masu yawa. Ta dafata tace "Meema, ji yanda kike kallon dakin kamar yau kika fara shigowa" Meena tace "Hmm Sis, ina mamaki ne, rayuwa na gudu, a wani lokaci, ko gidan kanmu ba mu da, ba mu da Sanaar da ta wuce saida Abinci, amma in one time, God has buttered our Bread" Sauda tayi saurin cewa "You mean My Bread?" daria sukayi gabaki daya, tace " Tabbas ke mai sa'a ce, don kuwa duk abunda kika sa a gaba, ba makawa sai kin cimma sa, ga ki da hangen nesa da kuma hikimar magance Nesa tun kan tazo kusa" Saude tayi wani shu'umin murmushi, tana jin dadin yadda kanwar ta ke k'oda ta. Meema ta cigaba da cewa "saidai wannan karon na rigaki hango nesan da zata iya kawo miki cikas, da sauri ta gyara zamanta tace "yi magana Meema" Meema ta gyara zama tace " kin taba tunanin yadda Rayuwa zata kasance miki idan Alhaji Habib yau ya fadi ya Mutu? Tace "Da sauri tace "bangane ba Meema, yi min bayani dalla dalla" Ina nufin yau in Alhaji ya mutu, in banda tumunin takaba ba abun da zaki tsira dashi? Kina da labarin Yau Alhaji ya mutu tsinke ba za a ba Aneesa ba? Don bata da Gadon shi? Komai zaa tarkata a ba Rafeeq, be fi a baki kaso daya cikin takwas ba, sauran kuwa na Rafeeq ne, shi zaa ba komai" tace Meema ina son Habib, ba na ma tunanin mutuwar sa, kuma ni bazan kashe shi ba sabida Gadon sa be dameni ba" Meema tace "ai ba ina nufin ki kashe shi bane, ina nufin in ta Allah ta kasance ya mutu yau, da me zaki tsira, ai bana tunanin zaki tashi da abun azziki, gashi diyarki bata da gadon sa balle a sa rai zaiyi yawa" Saude tayi zuruuu tana nazarin Maganganun Meema, tabbas tayi Magana kuma abun a duba ne "toh Meema yanzu, meye abun yi?" Meema tace kawai sawa zakiyi ya Mallaka ma Aneesa wasu k'adarorin sa, da dukiya" Saude tayi Murmushi tace "i know what to do, bari ya dawo daga tafiar nan". Kwanci ta shi ba wuya gun Allah, su Seebi Semester ta ha, don yau suka fara hutun Mid-Semester break, haka kurum taji ita ta na son Zuwa Gida gun Iyayenta. Dama Safiyyar Yau Hajjo ta koma gida, don Nene tace ta koma bakin aikinta ta ji sauki, Nasiba ta shiga gun Nene, "Nene barka da hutawa" Tace "yauwa Seebin Nene" tace "mun dan samu hutun kwana 7, shine nace mu shirya mu tafi Kaduna mu dan chanza guri" Nene ta yi Kamar bata ji ta ba, Seebi ta sake maimaita mata, tace" KE nasiba ki fita ido na, shin ni tsarar kice? Nasiba ta kalli Nene da mamaki, tace me nayi? Nace wani abu da ba daidai ba? Nene tace ki kalle ni ki ce man in zo muje Kaduna hutu, ni yar firamare ce? Sai inje in ma Uwaki zaune cikinem gida, yan unguwa su tacewa Uwar miji ta tare Gidan D'a to ba haka nake ba, in ma Mahammadun ya aiko ki to shima zan gamu dashi" Nasiba ta kalli ta Nene cike da mamaki, shin me yayi zafi haka? Girgiza kai tayi tace "Wallahi you are always out of point" Nene tace "Eh baturen ma yaci kutumar ubanshi, nan gani nan bari" Nasiba ta shige daki tana mamakin Nene, ita in anyi gabas to yamma zatayi, ta gurgiza kai ta hau hada kayanta. WasheGari Tun da farar Safiyya Nene ta shiga kasuwar 'yar kutungu, tayo ma su Ummi Siyayya, su garin Alkama, Sansamin yaji, Kuka, busasshan kubewa, daddawa da dai sauran su. Sauri take ta dawo gida, tana shigowa taga Nasiba na kalaci, ta sauke ajiyar zuciya, tace lafiya Nene? Nene tace "Allah Allah nake kar ki tafi, don nasan ki da d'oki, tace "ya zanyi in tafi ba muyi Sallama ba?" Nene tace "yo nasani? Da kin tafi da sai kin raina kanki wallahi" tayi daria, "Me zai faru da na tafi" tace "Wallahi mota zan shiga in biki har kadunan, in lakada miki na jaki, sannan in juyo in dawowa ta Katsina" me Nasiba zatayi in banda daria, daria har da hawaye, Nenen ma Dariya tayi. Tayi shirin tafiya, Nasiba tace da Nene "kinga ki shirya mu tafi, ya zaayi ki zauna ke kadai a nan, hajjo ba ta nan, DonAllah Nene nah" Nene tace "Shin in tambayeki, Shekaru 21 da daya da nayi nikadai cikin gida me ya cinye ni? Me ya kama ni? Eyi? Nasiba tace " Wanchan Unguwar akwai mutane, kina jin motsin mutane, wannan fa? Tace "Ke ni rabani, ba fa inda zani, Ina nan kinji Nenen Seebi? Allah ya kaiki lafiya ya dawo mun dake lafiya" Amin Nene na, tace to Nene ga wayata nan zan bar miki, sai mu dinga gaisawa muna jin lafiyar Juna, ba musu ta amsa, sukayi Sallama har tasha Nene ta raka Nasiba gaban ta suka tashi. Ta musu fatan Allah sauke su Lafiya. Ba ta bar tasha ba sai da ta ma wani Conduster tatas don yace mata "Hajiya tafia ne?" tace "aa uwarka ce". Tunda ta fara masifa bata yi shiru ba, wai ya mata rashin kunya yana mata maganar Yan tasha, Da k'yar wani mutumi ya lallabata ya Ya fidda ta waje ya sama mata Napep ta wuce Gida. *Malali Kaduna* Karfe Hudu saura minti 10 (3:50pm)Nasiba ta shigo Unguwar su,m, a Lokacin ana ta kiraye kirayen Sallahr Laasar, da ta hangi Gate din Gidan su taji wani sanyi ya ratsa ta, ta biya mai Napep kudin shi ta fada gidan, tun daga Gate take kwada Sallama. Ummin da ta yi Rakiyya tace "Muryar wa na keji haka kamar Seebin Nene? Bata ankara ba taji an fado mata a jiki "laah itace ashe", ta rungume diyarta suna Daria, daga Katsinar? Ina Nenen? " tana chan ta k'i yarda ta biyo ni" tayi daria tace "ba ki gaida Mamin Ayman ba" tayi daria tace "sorry ban lura ba" Seebi ta juya ga inda matan da Ummi ta rako ke tsaye, ga Mamakin ta, matar ita take kallo, ta shagala da kallon ta, Nasiba ta tsurawa matar ido tana son tuno inda ta san fuskar, ta dai daure tace " Ina wuni? Shiru, Ummi ta dan dafa Mami tace "Mamin Ayman wannan diya tacw na ce miki tana karatu a Jamiar Katsina" Firgigi tayi kamar wanda aka tada daga bacci, tace "Allah Sarki" ta juya ga Seebi tace "Lafiya lau, kin dawo Lafiya?" "Alhamdulilah" ba ta jira sunce wani abu ba tace "barin koma gida kafin Ayman ta tashi" to a gaidata inji Ummi, suka juya cikin Gida, Mami ta tsaya bakin gate ta juyo tana kallon bayan Seebi, a ranta tace "Allah mai iko, meyasa nake ganinta kanar Rafee'ah?". Murna gun Abbi da Anan ba a magana, kamar sun yi shekara basu ga juba ba, nan Nasiba ta dauki wayar Ummi ta kira Nene, har tayi Ringing ta gama bata dauka ba. *WasheGari* Tun da Safe Nasiba ta shirya Anan, ta raka shi har Makaranta, ta dawo gida ta ciro Garin Alkaman da Nene ta siyo musu ta tankade shi, Abbi ya fito daga daki, ya ganta sai aiki tankade takeyi, yayi Murmushi yace "Sarkin aiki, kin fa dawo kenan, to me za a mana yau?" tayi daria tace "Barka da fitowa Abbi, Alkubus zan mana" yace "Ahh kice yau zamu kwashi Gara" tayi daria, ta cigaba da aikinta, ko da Ummi ta fito tace zata sa mata hannu cewa tayi "Ummi ki bari, aiki na ne" haka ta zage ta kwaba Alkamar nan, ta yi hadin Alkubus, da kanta ta fita tayo cefane, tazo ta gyara kayan miya da kabewa ta yanka Alaiyahu, ta hada da kifin gwangwani, sai da Kwabin Alkamar ya tashi kafin ta zuba a madanbacci, nan da nan gida ya kaure da k'amshi, bayan ta gama ne ta zuzzuba a Cooler, Ummi tace "Ki saka ma Mamin Ayman, na san zataji dadin shi" Wannan matar da kika rako jiya? Tace "eh ita, tana da kirki, ba su dade da dawowa nan Unguwar ba, ta girmeni amma tana mutuntani" Allah sarki inji "Nasiba" Ummi tace "kiyi wanka ki mik'a mata, tunda Anan ya tafi Makaranta" Nasiba tace "toh". Kwanan shi biyar be ganta ba, so da dama zai zo bakin k'ofar gidan yaga ko zai ga fitowar ta amma shiru, ya mata text kala 2 ba reply, wayarta in ya kira har ta gama ringing baya dauka, a rana sai ya jera tsaki fiye da dari, haka kawai yake jin kanshi wani wani iri, gashi Maalesh ba ya nan, haka kurum yaji he wants to see her, zumbur ya tashi daga kan gado, ya zura takalman shi, fita yayi daga gidan be dauki Mota ba, ya taka har k'ofar gidan Nene, mintin shi sha biyar tsaye gaban gidan, ya rasa yanda zaiyi, to wai ma ya ganta yace mata me? Tsaki yayi ya juya, zuciyar shi tace to ko lafia dai? Ko ciwon Nene ya tashi ne shisa ya daina ganin gilmawarta, ko a Unguwa sometimes ya kan ga wucewarta zuwa shago, dawowa yayi, ya tura k'ofar gidan, ya shiga Chan k'asan Mak'ogaro yayi Sallama, Nene na zaune tsakar gida tana gyaran wake ta amsa Sallamar tare da cewa Bismillah, kamar ya juya da ya ji muryar Nene, amma be san me ke tunzura shi ya shiga ba, cikin tafiar shi ya ida shiga gidan, Idon Nene a kan shi, a ranta tace "Yau su Dunkum ne a gidanmu" ba yabo ba fallasa tace k'araso ga wuri ka zauna, kan kujera ya zauna, chan taji yace "Sannu fa" kallon shi tayi tace "Ahh! Ai kai ke da Sannu me ciwon baki" be tanka ta ba, suka zauna jugum ita kuwa ta cigaba da tsintar waken ta, shi ko waige yake ta inda zai ga ta bullo, amma shiru, ko duniya zata nad'e ba zai iya tambayar Nene inda take ba" sun kusa minti 30 ba wanda yace ko 'kala, Nene ta yi Kamar bata san da kowa gun ba, sai 'yan wakokin ta takeyi masu kama da habaici (kuji min Nene kamar wata yarinya)haka ya k'araci zaman shi ya mike sai da yayi dan guntun tsaki kana yace "sai anjima" kamar jira take tace "mu jima da yawa" ya juya ya fita, ta bi bayanshi da gyatsine tace "Dunkum dangin Tsaka". "Assalam Alaikum" ta fada cikin Siririyar muryar ta, Mami na zaune ta yi firgigit ta tashi don Nasiba ta gani tsaye gabanta da kwano a hannu wasu lokuttan tana rikidewa ta koma Rafee'ah, da Sauri ta amsa Kwanon Hannunta, ta rungumo tana shafa fuskar ta tana hawaye, Sandadar Nasiba tayi, ta kasa tabuka komai, chan Mami ta dawo hayyacin ta, da sauri ta ja baya tare da fadin "I'm so sorry, kina min kama da diyata, kiyi hakuri" Nasiba ta girgiza kai tace "lahh bakomai" ta jawo hannun ta ta zaunar da ita, suka gaisa, tace "Ummi ce tace ako miki" ta bude Coolern tana fadin me muka samu? Ahh Alkubus? Aikam Nagode sosai" ta dan ballo tasa a baki" gashi kuwa yayi dadi" Murmushi kawai Nasiba keyi, Ayman ta shigo parlon dauke da Doll babyn ta a hannu tana tafia dagwas dagwas, da alama tafiar batayi kwari ba, Nasiba ta tsura wa 'yar diyar ido, har Ayman ta tako kusa da Mami, Mami ta dagata sama, "Ayman baby na kin tashi? wa ya sauko dake daga kan gado? Yarinyar dai lafe wa tayi jikin Mami, Nasiba tace "Ayman sunan ta? tace "eh" Nasiba ta mik'a hannu tace "Zo nan Ayman" ga Mamakin Mami Ayman ta nufa gun Nasiba, Mami tace lahh kin ciri tuta, k'uiywa ne da ita, amma tazo gunki, ba ta yarda da kowa, ko gidanku mukaje bata yarda ta sauka k'asa zata mak'ale a jiki, daga ni sai Baban ta je daukan ta" Nasiba tayi murmushi tace "haka yara suke ai" Mami tace "to ya karatu? Wane Course kike?" tace "MicroBiology" "Allah sarki ajinki nawa?" tace "Aji na Daya" idon Mami ya kawo ruwa, Nasiba ta lura tace "Mamin Ayman lafiya?" Mami tace "you see, Diyata bata samu ta gama Makaranta ba, da ajinta biyu zata uku" Nasiba tace "Allah Sarki, Aure tayi ne?" Mami tayi murmushi ne ciwo, tace ta koma ga Mahalici, shekarar ta daya da rabi da Rasuwa" Nasiba ta rausayar da kai cike da tausayawa, tace "Allah Sarki Ubangiji Allah ya mata gafara, ya sa ta huta Amin" "Amin Nagode, shekarar ki nawa?" tace "19" tace "ita kuwa tana da Shekaru 20 ta riga mu gidan Gaskia, Shes just like you, ba wai kuna kama bane, aa, kawai ina ganinta a cikin ki, i see alot of her in you, shiyasa lokacin dana ganki i was so emotional, ki dinga sata a adduar ki kinji? Murmushi Nasiba tayi tace " InshaAllah, Ya Sunanta?" Murmushi Mami tayk tace "Sunanta Rafee'ah" zabura tayi ta zaro ido tace "Rafee'ah Habib Lema?" da sauri Mami ta gyada kai hadi da cewa "Eh itace, kinsan ta ne?". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) *Wannan Page din nakune Masoya _Nene Mamman(Nenen Seebi)_ Nene loves you all❤* Pg4⃣3⃣ Nasiba ta fara sheshek'ar kuka ta nuna Mami da yatsa tace "kece Mamin Rafeeq?" da Sauri Mami tace "eh nice Nasiba, kin san Rafeeq ne?" Allahi Akbar da sauri Nasiba ta rungume Mami tana kukan farin ciki, Mami tarasa gane me Nasiba ke nufi da kukan da takeyi ne, daga bisani ta tsagaita kukan da takeyi, ta share hawayen ta, Mami ta tsura mata ido, tace "Nasiba me yasa ki kuka? Shin dama kinsan Rafeeq da Rafee'ah? Ki min magana ծiyata. Wani guntun tunani tayi ta girgiza kanta da sauri tace "aa ban sansu ba" ta mik'e da sauri tace "barin je gida Umminmu na Jirana" ba ta jira cewar Mami ba ta juya zata bar gun, da azama Mami ta rik'o hannun ta tace "Nasiba kar ki min haka, na san kina b'oye min wani abu, daga yanayin da kike a yanzu nasan kin san su, dukkansu, sanin da kika musu Sosai ne, ki fada min, Ya Rafeeq yake? Ba ta bari sun hada ido ba, murya na rawa tace " ni bansan su ba" haka kurum taji bata yarda da ita ba, akwai abin da ta ke 'boyo, ya zaayi da farko ta nuna ta sansu har ta na fada mata sunayensu yanzu kuma tace bata san su ba, ba zaiyiwu ba, yanda Nasiba takeyi ya nuna cewa tasan wani abu game da Rafeeq. Ta kamo hannunta tace "Nasiba ke da Anan kadai ne gun Mahaifanku ko? Toh haka Rafeeq da Rafee'ah, na rasa Rafee'ah, K'addara ta rabani da Rafeeq, Ina sonsa sosai, ina so in san Halin da yake ciki, tun bayan tafian Uncle dinshi, bana samun Details yanda ya kamata, Misali Ummin ku ke cikin situation dina, zaki so ki ganta cikin matsanancin hali?" ta nuna zuciyar ta da hannu ta cigaba da cewa "You see dis heart of mine? Its Empty, you have no idea what i've been through, i mean what i am going through, i've Swallowed alot, ki taimakeni, Help a Helpless Mother please". Nasiba ta isa gareta ta rungume ta, kuka takeyi sosai, ta dago ta share hawayen Mami, tace " Mami ki bar kuka, i will tell you everything i know about Rafeeq, da yanda na sanshi, Komai" jan Mami tayi har kan kujera, ta dauki Ayman ta sata a baya, da hijabin jikin ta ta goya ta, ta fara rirriga ta har ta koma bacci, ta kalli Mami tace "ina zaa kaita? Da hannu Mami ta nuna mata cikin daki, Nasiba ta kai Ayman daki, ta dawo ta zauna kusa da Mami. "A Makaranta na fara ganinshi, shi da abokin shi Maalesh, ina tare da k'awayena muna neman abun hawan da zai maida mu Cikin Gari.............................................." tsaf ta kwashe komai da ya wakana tsakanin ta da Uncle Zaid da Rafeeq ta gaya mata daga ranar da ta fara ganin su har zuwa rana irin ta yau. Abu daya ta boye mata, Mafarkan da takeyi da Rafee'ah, bata gaya mata tana mafarki da Rafee'ah ba. Mami tayi Murmushi tace "Its a Small World afterall, So kakar kice Nenen da Zaid ke ban labari? Wacce ta bashi kuka da daddawa?" kai Seebi ta daga, ta riko hannunta tana murzawa tace "Labarin da Maigadin Lema ya baki, dukda ba ki gaya min me yace miki ba, kin yarda zan iya aikata abun da ake zargina dashi?" Murmushi Nasiba tayi tace " Bansani ba, and i wont Judge you, but i know a responsible Mother wont do that at her Matrimonial Home" Murmushi Mami tayi tana jin son Nasiba har ranta, irin son da take ma Rafee'ah tace "kinsan lokacin da na fara ganinki, naji ina sonki, like i told you I see Rafee'ah in you, Nasiba shin zaki zama diyata? We'll you make me feel like a Mother again? Kuka Nasiba ta fashe dashi, ta rungume Mami ta na daga mata kai, tace "Mami nah, you are my Second Mom" kukan farin ciki Mami ta fara yi "Seebi na, ina sonki kinji?" nima ina sonki Mamina". Daria sukayi duka. Nasiba tace "Ayman fa? Kin sake aure ne? Mami tayi murmushi tace "anya zan sake Aure kuwa? Bana tunanin zan so wani ծa namiji baya ga Daddyn su Rafee'ah" da sauri tace "Aa Mamina kar kice haka, ba me cire rai daga rahamar Allah, kar kiyi Mamaki zaki koma dakin ki, abu ne fa na Allah, bana so kina cewa haka kinji Mami na" Murmushi Mami tayi ta k'ara jin son Nasiba a ranta, tace "Rafee'ah-Aymana taci sunan Marigayiya Rafee'ah, Ayman diyar Zaid ce, be taba gaya miki yana da ծiya ba? tace "aa be fada min ba" Mami tace "Matar shi ta rasu Shekarar da ta wuce, bayan suna ta Rasu" cike da tausayawa tace "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata, ya sa taci Albarkar Haihuwa, ita kuma Allah ya rayata" "Ameen Ameen" Mami tace "to kodai Yak'i gaya miki yana da d'iya ne don kar kice ya miki tsufa, ba kya son tsoho? Cike da kunya da jin nauyi tace "Lahhh Mami" tayi saurin boye fuskarta jikin Mami don taji maganar wani iri, ita kuwa Mami sai dariya take mata. *Katsina* "Shin Sallama ake ko fito? (whistle) inji Nene, daga bangaren shi ya buga tsaki da yaji muryan Nene, ji yayi kamar ya koma, don dai zuciyar shi na tunzura shi yazo ya ga Seebi da ya juya wlh, don Wulakanci ya daddage yayi Sallama amma sai tace yana whisir? Wannan tsohuwar na da damuwa, be bi ta kanta ba ya sake Sallama cikiciki, tace "Shin, an amsa maka ka shigo mana" tsaki yayi ya nufa cikin gidan, sanye yake da 3quarter, Nene na ganinshi ta chanza fuska tace "Touuu, nidai ince, nasan za'a rina naji sallama kamar fito, ashe su dunkum ne dangin tsaka" Ya kalleta sosai yayi kamar be jita ba, tace "ka tsareni da ido, to ai sai ka zauna ga tayani gulma nan" ya tsaya yana mata kallon rashin fahimta ta nuna mai kujera tace cewa nayi ga kujera ka zauna, guntun tsaki yayi ya zauna, yana kallon saitin dakin su, yana jiran yaga fitowar Seebi, Nene ta zauna kan tabarma kusan minti 15 be ce komai ba, da taga shirun yayi yawa ta daure tace "ina Malush?" shiru be amsata ba, a ranta tace ko dai be ji ni bane? Ta bude murya ta sake cewa "Nace ina Malush?" shiru ya mata, Nene ta bude baki cike da mamaki tana kallon shi, chan k'asa taji yace "Yana Kano" Lallai kawai tace tana jinjina kai. Shiru ya sake giftawa har fiye da na dazun, kusan minti 20. A karo na uku (3) ya sake jin K'arar waya, tun dazun wayar ke ringing tana katsewa, k'arar wayar na damunshi, kuma shi yak'i tashi ya tafi, dan guntun tsaki yayi ya kalle ta yace " Wai ba karar Waya nakeji ba?" Nene ta hau salati, tace "kai don Manzon Allah? Wai wayace? Yo tun Shekaran jiya nake jin irin k'arar nan banyi zaton waya bace, wai ashe wayar Nasiba ce" be dai ce da ita komai ba har wayar ta sake ruri, cigaba da surutu tayi tana bashi labarin yanda takejin k'arar wayar kullum, ta ma mance rashin jituwar su, yace "ai sai kije ki dauko ga wayar chan an sake kira" da gudu ta ruga daki, amma kafin taje ya katse, kan Wardrobe ta ciro wayar, tun randa Nasiba ta bata wayan ta aje a sama ba ta sake bi ta kan shi ba, ta fito da wayar a hannu ta mika ma Rafeeq "kaga dunkum, duba min kagani waye? Kamar bazai amsa ba, sai da ya gama kallon wayar a hannunta kafin ya amsa, ya jujjuya wayar a hannun shi, a ranshi yace "Tecno, sai k'arar tsiya" ya bude wayar, 34 Missed Calls ya gani, accordingly ya duba Missed Calls din, Abbina Uncle Zaid, Ummina, Ya-Maalesh Miemee, Usheey, Hamma na, a ranshi yace Hamman ta? Messages ya duba, Daga na Uncle Zaid, sai na Maalesh sai wanda ya mata, a sama yaji muryan Nene, inda take cewa "Shin zaka gaya min wanda ya kira ko sai ka gama latse latsen wayan, ko no engilish? Guntun tsaki yayi, da kyar yace "wai Abbi" tace "Mahammadu ne, baban Nasiba latso min shi" a ranshi yace wa ya tambaye ki? Ya mata dialing numbern, ringing daya suka dauka, cike da doki tace "Halo, Mahammadu ya kuke? Yanda Nene ke waya zar takaici, kamar bakauyiya, hakan yasa shi mikewa don tafia, ya kalleta yanda take daria, a hankali yace "kina da matsala" karaf kan kunnen Nene, tace "da wa kake? Ni ke da matsala? Matsalar ubanka?" be tsaya bi ta kanta ba ya fice daga gidan, ta bi bayanshi har zaure, "tsaya mana, rasa kunya beran kitchen, da ba don ina kunyar Zaidu bawan Allah ba yau da sai na maka mugun duka, in maka lagalaga, in kuma kai ka Asibiti, yanda kayi jiyyata nima inyi jiyarka dan banten uba" kwatakwata ta manta da wayar da takeyi. Su har sun gaji da Magana sun kashe. Ta dawo ciki tana mita, ta kafa waya a kunne, Hello, daidai nan Seebi ta sake kira da wayar Abbi, a firgice Nene ta cire wayar daga kunne don k'arar ya cika mata kunne, ta latsa wayar ta kafa a kunne, tace "hallo Mahammadu" Seebi tace "Nene na nice" cikin masifa Nene tace "to dan kece sai ki dod'en kunne da kira?" Nasiba ba ta damu ba tace "ke da wa kike fada, naji kina ma wani masifa?" nene tayi tsaki tace "ni da wannan dunkum dangin tsakan mana, wai ni zai kalla yace ina da matsala" Seebi ta gane da Rafeeq take, da Sauri tace "shi yazo?" tace "tun tafiar ki kullum sai yazo, ya tasani gaba yayi ta kallo kamar Tb, shine zai ceman wai ina da matsala, ai wallahi da ya tsaya da sai na bubbuge shi" Nasiba ta shiga tunani a ranta tace "Allah sarki Hamma, ni yake nema, i made a mistake da ban sanar dashi zanzo Kd ba" Nene tace sai ki man shiru? Dallah bani Uwar taki mu gaisa" da sauri tace "Ahh Nene ga Ummin ba sai kin zaga man Uwa ba". Daria Ummi keyi ta amsa wayar suka gaisa da Nene. Seebi kuwa ta tashi ta fada gidan Mami. _Malali Kaduna_ Haka Nasiba zata zauna tayi ta ba Mami labarin Rafeeq, wani zubin taji tausayin shi wani zubin tayi daria, kamar yanzu Nasiba ta bata labarin Dramar Nene da Rafeeq, Mami tayi dariya harda k'walla, tace "ai Nene ce daidai shi" tana burgeni, Seebi tace "ai haka mutane ke cewa, wai Nene na na burge su, don dai basu zauna da ita bane, da tuni ta gudire su, Nene is very Annoying Wallahi, don dai kawai tana da ban daria, amma kwana daya zaki yi da ita duk zakiji ta isheki" Mami tace "ba wani nan, ni dai ba zata ishe ni ba" Seebi tace "hmm, wallahi Mami ba zaki gane ba" wayar Mami tayi ringing, Nasiba ta je ta dauko mata kan dining, Zaid England ne ya fito a Screen, Nasiba tace "Mami ga Uncle Zaid" Mami tace dauka mu rudar dashi" Seebi ta dauka wayan "Assalam Alaikum Uncle Zaid" da sauri Zaid ya duba Screen din wayan ya ga dai Mami ya kira, to ya yake jin muryan Seebin Nene? To ko kiran ya yi roaming ne ya koma numbern Seebi? Tambayoyi da dama, da k'yar ya Amsa Sallama, yace "Seebin mu nida Nene" tace "lahh ya akayi ka gane?" "your voice is always on my head, ba zan taba manta da voice dinki ba" taji kunyar maganar shi amma sai tace "arent you suprised? Ba number na ka kira ba fa? Zaid ya tashi zaune yace "Noo way" tace "Yes Way, bari ma ka gani" ta mik'a ma Mami wayan ta mata alama da bara taje gida ta dawo, Mami ta amsa tana Daria, yace "Mami how is this possible? You met Nasiba?" tace "Ehmana, what makes you think i wont find my Sister Inlaw? Or ince daughter na, don diyata ce, kai ne siriki na" yace "shhh Mami kar ta jiki" tace "kar ka damu ta je gida, mak'otan mu ne, Yayan Anan" da mamaki yace "dama Nasiba yayan Anan ce?" tace "iko na Allah" yace to Mami ya akai kuka saba da juna haka? Mami ta kwashe labarin da Nasiba ta bata duk da briefly ta bashi, labarin da shi kanshi Zaid be sani ba, ya jinjina kai, Mami tace "Wallahi Zaid baka ga yanda take son Ayman ba, yanzu haka tana bayanta ta goya ta" Dadi ya lullube Zaid, duk me son shi, to ya so Diyar shi, nan ya ba Nasiba wani matsayi a zuciyar shi, Mami tace "Allah ya sa yanda take son Ayman ta so babanta, ko da yake dan k'anina haծaծծe ne, ba macen da zata k'i shi" daria Zaid yayi yace "easy dai, sai na dawo zan sanar da ita _sirrin dake raina_" tace "sai ka dawo, yanzu sai yaushe?" yace "don sun raina mu sun k'ara mana additional 2weeks, sai next month in Allah ya yarda" toh Allah ya yarda, nan sukayi fira sukayi Sallama. *Katsina* Nene ina kika shige ana ta kira? tace kai dai bari, gani ina ta Soya Farar da Anan yace a soya mai in ka dawo da Seebi in baka ka kaimai" Abbi yace "kema dai Nene, sai ki biye ma Anan don yace yana son Fara, shi yanzu haka ya mance" tace "Tiya biyu na siyo mai, baka ga bak'ar wahalar da naci a kasuwa ba, kuma ina dawowa na gyara ta, yanzu har na soya tiya daya, gani ina soya gudan tiyar" Abbi yace "Taya b'era b'ari". Yau be jira amsan Sallamar ta ba ya shigo ciki, sakamakon wani k'amshin da yaji, ya na tunanin k'amshin meye wannan? Wannan dai ya fi karfin suyan kaza, tana waya ta ganshi tsaye, tace " yau kuma Sallamar da akeyi k'asa k'asa baa samu damar yi ba? Ko muryar ce ta ida daukewa? Ni tashi min akai ga kujera chan" Abii yace "Nene ke da waye?" tace "ni da Dunkum" "wanene kuma Dunkum?" tace "ka tambayi Seebi waye Dunkum dangin Tsaka" Inaaaa Sam Rafeeq be san tana yi ba, hankalin shi na kan Soyayar Farar da ke cikin gwagwa, ya hadiye wani mugun miyau kamar tsohon maye, rabonshi da Fara shekari sun fi 10, tun suna zuwa Islamiyya, nan Rafee'ah zata siyo musu, suyi taci, har Farar dari 2 suke siya, haka kurum yaji yana son cin Farar nan, ko don tuna baya, yana son cin farar nan for times sake, kuma dai yana so. Nene ta sauke kaskon ta hadeshi da na gwagwan, tana dagowa taga idon Rafeeq tsam kan gwagwar Fara wani shu'umin Murmushi tayi, a ranta tace"Yau ranar Nene ce" Ta dauki soyayyar cinyar farar nan ta sa a baki, ta wani lumshe ido tace "kaii wannan fara zad dadi, kamar kunne na ya tsinke" Rafeeq ya sake hadiye miyau, suna hada ido da Nene yayi saurin shan mur ya dauke kai, a ranta tace "yaro da ni kake zance" ta shige daki ta zauna tana kallon shi ta windo, a ranshi yace "na san wannan tsohuwar ba bani Faran nan zatayi ba, kuma gashi raina ya biya, i want, i will just take it" be tsaya wata wata ba ya durkusa ya dibi guda biyu ya sa a baki, waiyo dadi, yana kara sa hannu yaji an damk'o bayan rigar sa tace "Yihuhu Na chafko shi, na chafko b'arawon fara ta" a hankali yace "Akwai matsala Lord Have Mercy". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg4⃣4⃣ Ya dago fuska a daure kamar bai taba dariya ba, ya bi hannunta da ido, yanda ta rik'e mishi bayan riga, a hankali yace da ita "Sakeni" tace "nak'i na sake ka din, nace nak'i" yace "me na miki da zaki rike min riga?" "tambaya kakeyi? To Sata kai man, ka satar min Fara" ya sake tamk'e fuska, wai wani irin Sata?" wanda ka min mana, ai daukan abun da ba naka ba Sata ne, ni kuma ban baka Fara ta ba ka dauka" ya nuna farar da yatsa yace "wanchan abun zanci, Allah ya kiyaye in ci k'waro" tace "Kai Dunkum, ka fita idona, ni da na ganka durkushe, in ba ci min Fara kakeyi ba meyasa zaka durk'usa a gun? Ruku'u kakeyi?" da k'yar yace "da ki ka ganni Durkushe k'andagare na ga zai hau, shine na kore shi, dana sani da na barshi ya hau" tace "Ayiriri nanaye, kai Dunkum ka raina ma kanka wayau ba ni ba, Shekaru na Goma so Shidda da dori (60+) kasan ko ba kalar barikin da ban gani ba, tunda ka ci min Fara ta, ina so ka amsa laifin ka, ka bani hak'uri a wuce wurin" guntun tsaki yayi ya juya zai bar gidan, da sauri ta jawo rigar shi, tace "Sai fa ka ban hakuri" a k'agauce yace"Goodness, Wallahi kina da Damuwa, ga ki da Hayaniya" tace "zaka ga damuwa idan kaji ka a *Jakar Magori*" kallon Rashin Fahimta ya mata, tace "Too, ba ka san Jakar Magori ba ko? No radio a gida? To wurin da zan kai Labarin ka ne, k'arfe 11 dare in ka kunna Radio zakaji ance "Jakaaaar Magori, Dunkum ya Saci Farar Nene a garin Katsina" a ranshi yace "this Woman is Unbelievable, zata aika" ganin idan ya biye mata zasu ta Fafatawa ne, gashi kuma yau ta sashi magana fiye da Sentence 10, kanshi har ya fara ciwo, juyawa yayi zai fita, Nene ta sake Chafko Rigar shi, Tsoki ya buga da k'arfi yana cewa "wai ke wace iri ce?" "sai fa ka bada hakuri" Daidai nan Maalesh ya shigo da Sallama, Nene na ganin shi tace "Yauwa Maalush, zo kayi Shaida, Dunkum ya min satar Fara" Maalesh da Murmushi kwance kan fuskar shi yace "Nene, ban gane ba?" tace ka tambayi "Dunkum ya maka bayani" ya juya ga Rafeeq ya ga irin rik'on da ta mai kamar wanda ya saci Mota, daria ya kubce mai, yace "Guy howfa? Looks like you've fall into the Old Woman's trap, what did you do?" Rafeeq cikin k'uluwa, yace "Tell her to let go" dak'yar Maaldsh ya sa Nene ta sake Rafeeq, tace " yo Maalush, ci min Fara yayi, kuma ni ban bashi ba, kuma ya k'i yarda ya ban hakuri, ni ko na kamashi kamar na kama Aradu" Maalesh ya fashe da Daria, ya juya ya kalli abun da aka kira da Fara, ya yamutse fuska kamar ya ga kashi, ga kalli Rafeeq da mamakin ta ya ya ci wanchan abun me kama da kyankyaso, yace "you ate that? Rafeeq yace "You are crazier than she is, i cant eat that" kamar ta san abunda yake cewa tayi saurin cewa "Karya yake, a shinshina hannun shi" Maalesh ya shashantar da maganar ta hanyar tambayar Nasiba tace "ai Nasiba kwananta 4 Kaduna Jibi zata dawo" "Lord of Mercy" inji Rafeeq, so All this While Nasiba na Kaduna? Yake bata lokacin shi on this Woman? Yazo ya sha zaman banza amma bata ce mishi Nasiba ba ta nan ba? (Ka tambayeta ne?) dogon tsaki yayi ya fincike mukullin hannun Maalesh ya fita, Nene ta bishi tana dariya tana fadin "Dunkum tsaya kaci Fara, tsaya a k'ulle maka Leda" daria takeyi sosai, don ta san yau tayi maganin Dunkum, Maalesh yayi Dariya, yace "ranshi ya baci, barin je" tace ranshi ne ya baci? To ya sa omo ko kilin ya wanke shi" Maalesh yayi dariya, yace barin je Nene zan dawo Anjima nima iso wata kenan" tace "Allah huta gajiya" ya fita amma be ga komai ba sai k'urar Motar shi, Murmushi yayi ya taka zuwa Gidan Lema a k'afa. Yana shigowa dakin ya fada Toilet dinsa, Shower ya sakar ma kanshi, tunani kala kala, wai me ke kaishi gidan Nene ne? Zuciyar shi ta bashi amsa da "Kana kewar wannan Yarinyar ne" da sauri yace "Noo, ba ita nake missing ba, i only miss seeing my Sister in her" tsaki yayi yace "stop getting to my head i dont want" haka ya cigaba da magana shi kadai kamar zararre. *5:00pm* Zaman kadaici ya ishi Nene, ta rasa yanda zatayi, gashi ita ba gwanar shiga Makota ba, don gidajen makwabtan akwai Karnuka, kuma ai ta k'wank'wasa wa ba a amsa, Wayar Nasiba ta dauko ta kura wa wayar ido tana jira a kirata, shiru, ta na ta 'yan latse latsen ta, bata san ma dai abun da takeyi ba, tsaki ta buga "ina dalilin zaman mutum shi kadai" (Nene ke kika jawo) ta jawo Gyalenta ta fita waje,tana kallon Unguwar, Mugun tsaki ta buga da ta ga Unguwar Wayam ba ko dabban da ke wucewa, Kamar a sama taga wata Mota Me kalar bula(blue) ta doso ta, ai da murna ta fara sa ma Motar Hannu. Birki na cikin motar su ka ja k'ii, don ba su lura da ita ba, a fusace Meema ta fito, Aneesa ma ta fito, Nene da Murmushin ta tace "Sannunku 'yan jikokina, kuyi hak'uri na tsaida ku, DonAllah ku dan latso min Zaidu bawan Allah a wayar nan" ta na me mik'a musu wayar Nasiba, Meema ta kalli wayar cike da tsana tace "Ke Almajira, in banda jahilci, ba ki sanmu ba zaki tsaida mu kice mu kira miki wani? Har kina daura k'azamin hannun ki kan mota ta?" Aneesa tace "Aunty Mee mu tafi don Allah, irin wannan da su ake conspiring a maka wani mugun abun, its all a ploy" Ta ja hannun Auntyn ta, suka koma Mota, Meema ta ja motar tare da bad'e Nene da k'ura, yanda kuka san Hoto haka Nene ta tsaya, wai yau ita a ka ci ma fuska kuma ba tace komai ba, haushinta daya da ba ta ci uwar babbar su ba, amma a fili tace "Ubangiji Allah ka sake hadani da su" ta koma Cikin Gida tana jin haushin kanta. *Malali Kaduna* "Nasiba, kin taba ganin uwar da tayi fushi da danta? ko tayi fushi dashi na wasu lokaci ne, ko me ya ke mata ba za ta tab'a fadin Mummuna kalami a kanshi ba, tsakanin d'a da Mahaifi sai Allah, balle ni da ban taba ganin Laifin Rafeeq ba illa Laifina, nice na sakashi a halin da yake ciki yanzu". Nasiba ta kamo hannun Mami tace "karkiyi Blaming kanki, k'addara ce ta riga Fata, nidai DonAllah kice kawai ki yafe mishi duk da kince be miki komai ba" Mami tayi Murmushi tace "Toh Nasiba, na Yafe ma Rafeeq Duniya da Lahira, na yafe mishi, Ubangiji Allah ya sa ya gama da Duniya lafiya, Allah ya bashi saar karatu, Allah ya ma Rayuwar shi Albarka" da sauri ta Rungume Mami dadi kamar ya kasheta, ita a ganinta zataji Saukin komai tunda Rafeeq na tare da Adduar Mahaifiya, tace "Ameen Mami, ki Cigaba da mishi addua kullum, InshaAllah ba zai tab'a tab'ewa ba" Mami ta tsura wa Nasiba ido cike da k'auna tace "Bless you Daughter, you have an Amazing Heart, Ke Alheri Ce" Murmushi kawai Nasiba tayi, don bata son tayi magana Mami ta cigaba da kukan da takeyi, tace "Mami yaushe zakizo Katsina? Katsina na missing dinki" Murmushi tayi tace "i have no Bussiness left in katsina, Duk Wata Baba na da Mama na su na zuwa duba ni" Nasiba ta sigar zolaya tace " are you sure you have no Bussiness in Katsina? Mahaifarki ce fa, besides, your One and Only Love is there, nasan he still inside that pure heart of yours" Mami ta daburce tana unconditional Murmushi, tace "ke Nasiba maganar me kikeyi haka? Shuttup ni ba kowa a zuciya na, na tsufa" Nasiba tayi dariya tace "Is that so? Then why are you blushing?" Murmushi Mami tayi tace "How i wish zan sake ganin Habibullah" "Awwwn Mami ta tuna da tsohuwar Zuma" tace "Kinsan ana cewa Zaid me kyau ne, Hafiz Me kyau ne, amma Wallahi duk Habib ya fi su kyau, harta Rafeeq da ke kama dashi be kamo k'afar shi ba" Sosai Nasiba tayi daria tace "zai k'ara kyau idan kika koma dakin ki" Mami tace "Hmm nagaji da tsammanin Ranar nan" Nasiba tace "Dont worry Mami,Akwai Allah, gaskiya zata baiyana, zai gano gaskia da na rashin bincike ne ya sa shi daukar mataki take yanke, amma kar ki damu, Have faith" Mami tace "dadi na dake you give me Hope" Sukayi Murmushi, kuma chan sai Mami ta fara matsar k'wallah, Nasiba tace bari in kira miki Nene ki sha dariya. *Washegari* Ina Nasibar ne? Sai mun rasa Motar K'arfe 10? Ummi tace "wai ta shiga yi ma Mamin Ayman Sallama yanzu zaka ga ta taho" Abii yace ai gwara tazo mu ta tafiya. Mami tace "Yanzu ba zaki k'ara mana hutun ba? Kin bari mun saba sosai sai kice zaki wani koma?" tace "Ayyah Mami, nima na saba dake Sosai, idan mun tafi ba zamu dade ba zamu dawo, trust me zan dawo" Mami tace "to shikenan, ga wannan kiyi using as Pocket Money" "Nooo Mami i cant accept your Money" Mami ta tsura mata ido, tace "ni na dauke ki ne a matsayin Rafee'ah, and i can do anything for you, don break my heart" "Mami kudin sunyi yawa ne ki raba biyu" " Haba Nasiba dubu Goma ne fa, ba yawa, inshort why dont you be like Rafee'ah? Be like Mami kudin sun min kadan, i need more" daria Nasiba tayi tace "Okay, I'll accept this Nagode" "Yauwa diyata" tace "One more thing" ta zaro dan karamin Zoben da ke k'aramin yatsar ta ta sa ma Nasiba a yatsa tace "this is my love for you" Nasiba ta bi zoben da kallo, tana so ta tuno inda ta san Zoben, Zoben me kyau ne sosai, kuma Azurfa. Mami tace "kinsan waya bani Zoben Nan?" ta girgiza kai, Mami tace "Rafeeq ya bani shi on my 40th Birthday, Daga Dubai ya sa akayi su Guda 2, ran Birthday na ya sa min a yatsa yace "Mamina, this is my love for you" ya bani gudan yace in sa mishi a, yace "this is the twin of your ring, even if we are far from eachother, this Ring is linked to Our hearts" daria kawai nayi nace dashi"he's Crazy" amna Nasiba yanzu Rafeeq ya tsane ni, nasan Ya dade da wurgar da Zoben shi" Nasiba tace "Aa Mami, wallahi be wurgar dashi ba, yana nan a yatsar shi, ni na san na san Zoben nan a wani wuri, a Yatsar Rafeeq na sanshi" Mami tayi dariya tace"Nasiba kenan, you want me to feel better, shikenan naji, its yours now" Nasiba tace "Aa Mami, wannan naki ne, ki ansa" Mami tace "bansan gardama tashi muje, ni ma zan kai ku tasha, kar ku rasa motan hawa" suka fita tare, a ranta tace "with this Ring Rafeeq, you'll be your Mother's Son Again". Da sauka shiga gida ne ta nuna ma Ummi kudin da Mami ta bata, Ummi ta mata fadan meyasa ta amsa, Mami tace don na ba diyyata kudi shine nayi laifi? Ko iko zaki nuna min kanta ki nuna min diyarki ce, tace "laaaah Mamin Ayman be kai nan ba, ai an fi so diyarki taji tausayinki" Mami tace kya dai ji dashi, gabaki daya sukayi daria. *4:00pm* *Layout, Katsina* "Sannun ku da zuwa, kun sha hanya" Ya mutan Kaduna? Duk suna lafia, Nene ta gabatar musu da Danwaken da ta musu, tana basu labarin zaman kadaicin da tayi, Nasiba tace "Oho dai, ke kika jawo, sai da na ce miki ki taho mu tafi kaduna, ki ka k'i" tace "ke ni ban son mita ba gashi kin dawo ba? Ko wani abun ya kamani?" tace"kin daiyi kewa ta" Nene tace ko kadan, ban k'i ki koma ba, ko a habar zane na" Abbi dai na jin su sai dariya yake musu. Suna cikin cin danwake sai ga Maalesh da Rafeeq sunyi Sallama, da Sauri Nasiba ta kalli kofar zaure don jin muryar shi, sanin kanta ne tayi missing din Hamman ta, shima karaf idonshi kanta wani naunauyar Ajiyar Zuciya yayi, "Finally! shes back" Maalesh kuwa Murmushi ya bita dashi, Maalesh ya matso ya ba Abbi hannu, ko be sani ba yasan Baban Nasiba ne, Abbi ya bashi bayan hannu don yana cin danwake da hannun, Maalesh a ladabce ya gaida shi, Nene kuwa cewa takeyi Sannu da Zuwa Malush, Nasiba ta tashi da sauri tayi kamar zata shiga kichin, daidai yanda zaijita tace "He's my Dad, show some Respect" harara ya bi bayanta dashi, yayi dan guntun gajeren tsaki ya da zata ji shi ita kadai, ya dan matsa kusa da Abii da k'yar yace dashi "Barka da Yamma" Abii yace "Muna lafiya?" Ido Cikin Ido suka kalli juna, nan da nan yaga baban Nasiba ya mai kwarjini, haka kurum ya kasa shiru ya amsa da "Lafiya k'alau, anzo lafiya?" Abbi yace "Alhamdulilah" Nene tace "Ahh su Dunkum yau anyi Wayau" Hararar ta yayi ya dauke kai, Abbi na kallon shi, akwai wani Hikima tattare da yaron, akwai wani abun da ya hango game da yaron, daga gani Yaron dan Baiwa ne, yanda yake abubuwan shi, yana kallon yanda Maalesh ke bin Nasiba da ido, amma shi wannan kallo bata ishe shi ba, haka kurum yaji yana son sanin game da Yaron, bude baki yayi yace "Seebin Nene, zubo ma bak'i danwake" Maalesh Yace "Aa Baba mungode bana cin danwake" "Abokin ka fa?" da sauri Nene tace "Ya k'oshi da dai Fara ne, wannan ko ba a bashi ba zai dauka" duk suka bita da ido cikin rashin Fahimta, dauke kai Rafeeq yayi, Abii ya k'ara cewa "a zubo maka Danwaken?"Kamar jira Rafeeq yake yayi saurin hadiye wani miyau, tun da ya shigo gidan ya ke bin Danwaken plate din Abbi da ido, ya sha Mai, da kayan hadi, yana iya cewa Danwake ne best food dinshi, rabon shi da ci tun Mami na nan, kuma gani yake wannan tsohuwar da gayya take abubuwa don ya nuna ya na son ci ta samu damar Wulakanta shi, girgiza kai kawai yayi alamun aa, in har yace baya son cin danwaken nan to yayi k'arya, har ranshi ya biya, kuma besan dalilin da ya sa Nene keyin duk wani abun da yake son ci ba, shi da abinci be damai ba, tsaki kawai yayi, Duk abunda yakeyi a idon Abbii, ya kalli Maalesh yace "ya sunanka?" Maalesh cikin ladabi yace "Sunana Mahmud" Nene tace "laah gaka da suna me dadi amma ka yarda ake ce maka Malush" daria kawai yayi, Abii ya maida hankalin shi kan Rafeeq da kwatakwata ya dauke kai, yace "Kai fa ya Sunan ka?" Rafeeq yayi kamar be ji ba, shi kuma Abii be sake tambayan shi ba, Nasiba kuwa jikin ta ya fara rawa, bata so Rafeeq yayi banza da mahaifinta, bata so mahaifinta ya tsani Rafeeq kan halaiyar shi, da Rafeeq yaji shiru, ba a sake tambayan shi ba, ya dago kai a hankali ya kalli Abii, shima shi din yake kallo, gajeren tsaki yayi a hankali yace "Sunana Rafeeq" Abii ya jishi sarai, yace "Banji ba" kamar ba zai tanka ba, amma Abii ya mai girman da ba zai iya share shi ba, ya dan bude murya yace "Sunana Rafeeq". Abii ya jinjina kai, Rafeeq yayi Zumbur ya mik'e sabida yana jinshi wani iri gaban Abii, ganin haka Maalesh yace "to Nene mun gaida ku, bari mu wuce" tace "Toh Malush mungode, su Dunkum a gaida gida" tuni ya kusa Zaure, Abi ya bude murya yace "Rafeeq" k'yam ya tsaya ya kasa tafia, da k'yar ya juyo, Abii ya kalli Nasiba yace "Je ki zubo mishi Danwaken" a hankali Rafeew yace "Nak'oshi" Abbi yace "Ka tafi dashi anjima sai kaci" dama tuni Nasiba ta cika Umurnin Mahaifinta, ta kawo ma Rafeeq Coolern, dauke kai kawai yayi, ganin haka yasa ta ba Maalesh Coolern, Maalesh ya amsa yayi Godia, ya ja Rafeeq suka bar Gidan. Nene tace "Yau kam me ke damun Dunkum?" Abii ya zauna yace "Seebin Nene, Wanene wannan? Me kika sani game dashi?" Gaban Nasiba ya yanke ya fadi, Nene tace " ai wannan shin d'an Zaidu Bawan Allah da na jima ina baka labari, shi haka yake, wani Dunkum, ba fara'a, ba ilhamar fuska, yanda kasan takashin shanu, haka fuskar shi take murtuk'e kullum" Abbi ya jinjina kai, yace "Seebi, bakin ki akwai Magana, me kikasani game dashi? Ni na hango bak'in duhu tattare dashi" Nene tayi karaf tace "bawani bak'in duhu, Fadin Rai ne kawai ya mai yawa" Seebi tace "aa Nene, akwai wani Labarin da ban sanar dake game da Rafeeq ba, kunji kunji••••••••••. Tsaf ta kwashe labarin Gidan Lema ta basu, kamar yanda Baba Maigadi ya sanar da ita, kamar Yanda ta gaya ma Mami, Ta dai b'oye Mafarkin da take da Rafee'ah. Allahu Akbar inji Nene "Allah Sarki Dunkum, ashe ba yin ka bane, Lallai akwai B'oyayyen Alamari a tattare da Gidan nan, ni gaskia ina zargin matar Baban su" "aa Nene kar kiyi saurin zargi" "tace dole iz zargeta mana Mahamman, ita kadaice zata yi hakan" Abbii yace "kamar yanda shi da kawun shi suka taimaka miki lokacin da baki da lafiya, InshaAllah zan taimaka mishi da wasu Adduoi, kuma kafin in bar Katsina zanje gun Abokina Me *Arriyadh Islamic Medicine* a taimaka mishi da magunguna, har shi mahaifin shi, in ma akwai Kaidin Mace da yardar Ubangiji komai zai warware cikin iko na Allah" Nene cikin jin dadi tace "Yauwa dan Mallam Jikan Mallam, da ba ka shashanatar da kanka kan boko ba, da yanzu ni nasan kai babban Malami ne da ake tak'ama dashi a k'asa baki daya, yanzu ma na san zakayi k'okarin ka" Nasiba kuwa bata san kalar Farincikin da zata yi ba, hak'k'un ta yarda da Mahaifinta, kuma ta na murnan zai taimaka ma Rafeeq, sai dai su Rok'i Allah ya basu nasara. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Assalam Alaikum, ina muku fatan Alheri, ina godia da yanda kuke biye dani a wannan labarin, ina me baku hak'urin rashin ji na da kukeyi kullum, hakan na faruwa ne saboda wasu 'yan dalillai, kuyi min uzuri don zan dinga tsallake kwana daya banyi typing ba, in kuma an samu yanda nikeso, zaku dinga jina kullum kullum, Nagode Allah bar zumunci. Pg4⃣5⃣ Abbii da Nasiba gaban Mallamin *Arriyadh Islamic Medicine* bayan Abbii ya karanto ma Mallam Matsalolin Gidan Lema. Mallam Usman ya jinjina kai, yace "Alhamdulilah, wannan labari da kuka bani akwai 'kulalliya, ko ba sihiri zamu taimaka da adduoi, balle wannan ma daga ji an san akwai Sihiri, ta iya yiwuwa Shi Alhajin an sa shi ya mance Uwargidansa, tunda kunce be sake waiwayarta ba, sai kuma shi Rafeeq baa so ya gama Makaranta tunda ance shekarar sa ta biyu kenan yana maimaita aji, kuma ba wai don ba ya ganewa ba, kuma ba ya k'aunar uwarsa, alhalin duk yanda Uwarka take to akwai wannan So da K'auna dake tsakanin su, toh tabbas akwai Mak'arkashiya a ciki kuma InshaAllah zaa warware komai da yardan Ubangiji. Abu na farko; Ina so su sa a ransu cewa duk abunda ya samu bawa to da yarda da ikon Allah ya same shi. Su kasance masu Adduoi da Tauhid, Zaa musu magani duka, Shi Alhaji zaa bashi maganin da zai taimake shi ya tuno abubuwan da suka faru a baya, shi kuma Rafeeq zaa bashi Maganin da zai sa mai dangana a ranshi, yanda zai yafe ma Mahaifiyar shi, wani Jarka Mallan ya dauko, yace "Wannan Ruwan Karatun Kurani mai girma da Addu'oin Shifa, Lallai Rafeeq da Habib su maida shi ruwan Sha din su, in so samu ne ko abinci a dinga dafa musu da shi, shi zai tsare su daga Sharrin mai Sharri" ya ciro wani robar swan, yace wannan kuma Man itattuwa ne, Man Habbatussauda, Man Ridi, Man Hulba, Man Zaitun, Man tafarnuwa, Garin Luban, da Adduoi kama daga AmanarRasulu, Ayatul kursiyu, da zikirin Safe da Maraice, Wannan na Rafeeq ne, shi ne zai saka mishi Salama da dangana a rai har yaji cewa yana son sanin abun da ya faru a wannan bak'in rana. Sai Kuma Saukar Alkurani da zaa musu sai ayi tawassali da Karatun sai a rok'i Allah ya baiyanar da Gaskia. Amma dole sai sun yarda da hakan, maana sai sunyi Imani da Allah shi zai firda su daga Abun da ya shige musu duhu". Abbii yayi Godia Sosai, yace "InshaAllah zaayi yanda kace Mallam Usman, Nasiba kina ji ko?" Nasiba da zufa ya gama keto mata, tana tunanin yanda zaa sa Rafeeq shan wadannan Magungunan. Da sauri ta gyada kai, tace "Eh Abii, zaayi yanda yace" yace to Madallah. Magungunan Dubu Sha biyar ne, amma saboda Sanayyar da ke tsakanin Mallam da Abii yace su bada dubu 10, kafin Abii yace wani abu Nasiba ta zaro kudin da Mami ta bata ta mika ma Mallam, Abii ya bita da ido, ta shaida mishi "ai kudin da Mamian Ayman ta bata ne" haka suka dawo gida cikin Keke Napep. "Tabdijam, ai yanda ka bashi Magungunan nan haka zai dire maka su don ba sha zaiyi ba Wallahi" cewar Nene bayyan sun bata labarin abunda ya faru a Islamic center, Nasiba tace "Abii ka kirashi ka mai Magana k'ilan idan yaji daga bakinka, ya dinga sha" Abbii ya jinjina kai, yace "Kira min shi a waya" da sauri Nasiba ta amsa wayar Abii ta sa mai Number Rafeeq tayi dialing, Wayar ta dade tana ringing, har ta gaji da ringing ta mutu, kallon Abbi tayi tace "be dauka ba" Nene tace "ina zai dauka yasan zaku sa shi magana, Abii yace "sake kiran Shi" Nasiba ta sake kira, sai da ya kusan tsinkewa ya daga, dama yana ganin kiran farkon, ganin be san number ba yaki dagawa sai yanzu, Karawa kawai yayi a kunne ba tare da yace komai ba "Assalam Alaikum" muryan Abbi ya ratsa mai kunni, zumbur yayi ya mik'e, sai dai ya kasa amsa Sallamar, Abii yace "Rafeeq, in ka samu lokaci, kazo gidan Nene yau ina jiranka" Abbii be jira amsar Rafeeq ba ya kashe wayar, Rafeeq ya tsura wa Wayan Ido kamar zai ga Abii a hankali yace "Why is he Bossing around?" guntun tsaki ya koma ya kwanta. Da kyar ya iya cewa "Assalam Alaikum" Abbii ya amsa tare da umurtan shi ya shigo, ya shiga ya zauna kan tabarma, Nene da Nasiba na ciki, basu san shigowar shi ba, Abbii ya tsura ma Rafeeq ido, guntun tsaki yayi yace "Barka da Yamma" Abbii yace "lafia lao Rafeeq, ka ci Abinci?" samun kanshi yayi da girgiza kai alamun "aa" Abbi ya ciri baki ya kira Nasiba "Seebin Nene, zubo ma Rafeeq Abinci" Nene ta kalleta tace "Dunkum yazo ne?" Seebi tace "ya zaayi in sani ni da muke nan zaune dake" Nene ta kai mata duka tace "Tambayar ki nayi ba ce miki nayi ki gayan magana ba". Rafeeq ya kalli Abii, yana so yace mishi kar a zubo mai abinci amma ji yayi bakin shi yayi nauyi, ya kasa Magana, shi besan dalilin da yasa yake jin shi wani iri gaban Baban Yarinyan nan. In ma dai girma ne Daddyn shi ya girme Abbii Nesa ba kusa ba, guntun tsakin mts yayi, Nene ta zubo mai Shinkafa da Miya, da lettuce a gefe, tazo ta ajiye mai, karaf idon shi ya kai ga Zoben yatsan ta, kafin ya samu damar sake ma Zoben kallo ta tashi, tace "Hamma Ina wuni" bata sa ran ya amsa ta ba ta koma cikin daki, Abbii yace "Bismillah" ba musu ya ja plate din gaban shi ya fara ci a hankali, be ci da wani yawa ba ya ture, Abbi bece komai ba yace "Rafeeq" Kasa amsawa yayi ya dago kai ya kalleshi, Abbii Wani makaranta kake? A k'agauce yace "Umyu" wani Course? "BioChem" Abbii yace shekarar ka nawa a School din? Da sauri Rafeeq ya kalleshi, Abbi ya mishi alamun ina sauraren ka, guntun tsaki yayi yace "6years" Abbii yace "Spilling kake tayi?" "Uhm" kawai yace don baban Nasiba ya fara k'ureshi, "Let me help you" a dan tsawace yace "I dont need your help" Shiru Abbii yayi ya kawar da kai gefe, ganin be kyautu a ce ya daga ma Babban Mutum murya haka ba yasa shi cewa "Look i'm sorry, but i dont need your help". Ya mik'e zai tafi, Abbii beyi yunkurin hanashi ba don yasan dole Rafeeq zaiyi wuyan Sha'ani, amma zai lallaba shi har ya yarda. "Dunkum Yazo daki ya gaida ni, k'afana na ciwo" chak Rafeeq ya tsaya shi beyi gaba ba shi beyi baya ba. Me wannan tsohuwar ke nufi da shi ne, kamar yayi gaba kuma sai ya tuna She's Uncle Zaid's Favourite, in har ta kirashi ta gaya mai bata da Lafiya, to tabbas zai maido shi yace yazo ya dubata ko kuma ya kaita Asibiti, kuma dole ya buge mata warning, ta daina ce mai Dunkum" Dogon tsaki yayi ya dawo ya wuce Abbi, ya cire Takalma gaban daki ya shiga ko Sallama, Nasiba na ganinshi ta mik'e tsaye, bata yi tsammanin zai dawo ba, ko kallo bata ishe shi ba, ya kalli Nene cikin b'acin rai yace" ki daina ce min Dunkum, ba sunana kenan ba" Nene tayi daria tace "Au haba? Ashe ba sunanka kenan ba, ai ni bansani ba, duk zato na sunan ka Dunkum, ya sunanka? Cikin daga murya yace *"I am Rafeeq Freaking Lema* "get that into your Oldie Skull" Nasiba cikin rudu tace "Heyy, Watch It" ya juyo ga Nasiba a fusace yace "Warn your GrandMother She should Stay the Hell away from me, you all should" ya bar Wurin a fusace be ma lura da Abbii baya nan ba ya fice, Nene ta bude Murya, "Sunanka Kenan Dunkum dangin tsaka, har sai randa ka koyi Magana kuma ka bar tsaki, rannan zaka koma sunan yanka ka, amma yanzu dai muje a Dunkum din" yana jinta amma be tsaya tankata ba, don ya san ya sake bude baki yana iya fashewa da kuka. "Nene meyasa kike ce mai Dunkum? Ki bari donAllah, kinsa shi ya tunzura har yana gaya miki magana, Gudumuwar da zaki bada wurin ganin Ya warke kenan?" cewar Nasiba, "Ke dallah rufen baki, kinzo kina min fada kamar Inna Ladingo(Maman Nene) ni ko zan bada Gudummuwa babba wurin saito Rayuwar Dunkum, Gundunmuwata daya shine zan taimaka in dinga sa shi yana magana ko ya k'i ko ya so, tun beyi har yazo ya saba ya dinga magana, kuma wannan shegiyar tsakin, dole sai ya bari, in yayi tsaki har k'walkwata wallahi, amma dai yanzu ya daina ban haushi tunda na fahimci cewa ba yin kanshi bane, be 6atan rai, tun asali ma be 6atan rai, shirun shi da miskilancin shi ne bana so, kuma dole sai ya koyi magana" Seebi ta kalli Nene ta girgiza kai "to wa ya ce miki ana so ya dinga magana, miye matsalarki da rashin magana?" "ke tafi chan, ke me kika sani? Sai ya koyi surutu ko yana so ko be so, wata rana kuma sai ya gode mun dana bada guddumuwa gun sa shi magana" Daria kawai Nasiba tayi tace " ta ina bayan kin korashi, bana tunanin ko gidan nan zai sake zuwa" Nenen tace "Lallai yarinya baki sanni ba, ai ni ba wanda ya isa ya shareni, ko ka shareni kan ka ka mawa, shiyasa lokacin ina kamar ki banjin komai don saurayi yace ya fasa, don ba a kwana zai dawo, kar ki damu da sannu Dunkum zai kawo kanshi" daria Nasiba tayi tace "yo ai ko halinki ya isa ya kori saurayi, nasan lokacin ki an sha gwagwarmaya da ke" Nene tayi shewa tace "Kamar kinsani, duk samarina sun sha masifata, Kakan ki kadai ne ya kasa ya tsare yace sai Aminene" ta girgiza kai tace "Allah ya ji k'anka Mallam, ka cika masoyi na hak'ik'a" Nasiba tayi daria, Nene ta cigaba da bata Labarin kalan Soyayyar da sukayi da Kakan Nasiba. Ashe yana binshi a baya har ya isa gida, yana jin duk abunda ya faru tsakanin Rafeeq da Nene, yanda ya fito daga gidan rai a bace ya sa shi binshi a baya har ya banka gate din gidan su ya shiga a fusace, Baba maigadi ya mik'e yana cewa Rafeeq Lafiya? Banza yayi da shi yayi hanyar dakin shi, Sallama Abbii ya ma Baba Maigadi, suka gaisa a mutunce, yace "gun Rafeeq nazo" Baba Maigadi ya kalleshi yace "Anya zaka so gannin Rafeeq a halin da yakr yanzu? Yanzu ya shigo gida rai a bace" Abbii yace "ba damuwa, ka min izinin ganinshi" Baba maigadi yace "Indai nine bakomai, yaro kana min kama da wata Aminiyata Aminene" Abbii yayi Daria yace "Ni ne Autan ta" Baba Maigadi yace "Haba biri yayi kama da mutum, kaind Mahaifin Nasiba ko? Ga kama nan wallah" daria yayi yace "barin ga Rafeeq" ya nuna mishi dakin Rafeeq da yatsa, kai tsaye Abii ya nufa dakin. "Assalam Alaikum" be jira amsar shi ba ya shiga ciki, kwance ya ganshi yayi ruf da ciki, kafar shi ya dan ja, Zumbur Rafeeq ya tashi tsaye, yana mamakin Abbii, a ranshi yace wai "me mutumin nan ke nufi da shi?" Abbii ya kalli Rafeeq yace "Kasan cewa Nene Mahaifiya ta ce? Ita ta haifeni?, ko ya take i cannot replace her, She's my Mom ba zan lamunce wani ya mata rashin kirki ba, i cant watch anyone disrespect her, the words you used on her were harsh" shiru yayi, yana nazarin maganganun Abbii, tabbas be kyauta ba, the woman is soo annoying, sai dai ya dubi Girman Abbii yace "Kayi hakuri" Abbii yayi Murmushi yace "Bakomai" na maka Uzuri ai. Rafeeq ya kalleshi, Abbii ya cigaba da cewa "Kana jin zuciyar ka na maka nauyi, kana jin ka tsani duniya, wata sa'in ka kan so da ma ka mutu, kana gajia da rayuwa, kana cikin wani Bak'in duhu, Bacin rai da rashin Dangana ya hanaka neman Haske, abu yayi k'amari da har Addua baka iya yi don a ganinka baka da wata buk'ata da ya wuce a ce ka mutu, baka da wata ragowan Jin dadi a Duniya" be bari yace komai ba ya cigaba da cewa "Rafee'ah, mafi Soyuwar k'anwa a gareka, ka san wani hali take ciki a yanzu? Ba kasan tana bukatar adduar ka ba? Baka san ba abun da mamaci ya fi buk'ata da ya wuce addua ba? k'anwarka na bukatar Adduarka, in dai hakane, to for her sake, you have every reaaon to stay alive, you have to survive, you have to achieve your Goal in Life, you have to go back to your normal self, and one day get Married and your kids will pray for your Late Sister, You have to Fight that Demon in you for your sister" wasu manyan jijiyoyi suka ma Rafeeq tsaye a kai, so yake yayi kuka amma ya kasa, kukan yak'i fitowa, shi kanshi yasan cewa yayi sakaci, a hankali yace *"Help Me"* Alhamdulilah inji Abbii, yace "Help yourself first, How? ina so ka fara Sallah cikin Jami'i, kai Bawa ne dole ka rok'i Allah haka zaka yi da hannu ka gaya mishi bukantunka, Akwai wani ruwan adduoi da zaka mai dashi ruwan sha dinka, ba daci ba bauri ba komai, ruwa ne Kawai ka maidashi ruwan ka, sai abu na k'arshe akwai Wani Magani da zaka dinga Zuwa Gidan Nene Kana sha Yamma ko Dare, InshaAllah wannan zasu taimake ka" Rafeeq ya ja gwaron Numfashi, yace " I will do everything you said, amma i dont have to go to her Place, zan iya shan Maganin a nan ba sai naje gidan ta ba" Abbii yace "Ina so ka yarda dani, kayi yanda nace" dan guntun tsaki yayi yace "Najih" Abbii yace Your Medication Starts today, muje kasha maganin, sai ka taho da Jarkan Ruwan" be kulashi ba ya tashi ya fita, Abbii ya rufa mai baya. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀      NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) This Page is for you Mrs Ruff Baby Aisha(Maman Irfaan) ILY❤ Pg4⃣6⃣ Abbii ya shiga gidan, Rafeeq na biye dashi a baya, Nene ta kallesu zatayi magana Abii ya mata nuni da tayi shiru. Ya kalli Nasiba yace "Seebi kina iya dauko Jarkan ruwan nan? Ta daga kai, ba ta jira cewar Abii ba ta shige daki ta kinkinmo jarkan Ruwan, da kanshi ya dauko Kofi ya bulbulo ya Mik'a ma Rafeeq Cup din, yamutse fuska yayi ya kurba, jin da yayi ba taste, ya sashi kafa kofin ya shanye ruwan ciki tass. Ya shiga cikin Dakin, ya dawo da Robar magani na hadin mai da zuma, Ya nuna ma Rafeeq yace wannan shine dayan Maganin, shine wanda nake gaya maka za ka dinga sha so daya a rana, kuma shine zaka dinga zuwa wurin Nene ka dinga sha, Cokali daya ne, ba zaka ji dadin shi ba, amma daurewa zakayi ka sha" kai kawai Rafeeq ya daga, Spoon Nasiba ta mik'o ma Abbi, ya tsiyaya maganin cike yayi bakin Rafeeq dashi, Rafeeq ya bude baki Abbii ya juye mai, wani iri taste mara dadi yaji, tuni yayi yunkurin zubdo shi, amma Abbii ya sa shi dole ya hadiye, ya sake bulbulo mai ruwa Rafeeq ya shashe bakinshi, Abbi yace "Sannu, daurewa zaka dinga yi, kasan magani ba dadi, Allah dai yasa a dace "Zan tafi" inji Rafeeq, Abbii yace "To ka tafi da jarkan ruwan" Rafeeq ya kalli Jarkan ya ga bazai iya dauka ba har gida, yace "Zan dawo in dauka" Abbi yace ai ba da duka zaka tafi ba, diba maka zaayi, idan ka shanye sai ka ka'ara kawowa a dura maka, ko robobin da kake shan Ruwa, dazun naga kusan guda nawa a Dakinka, yanzu ke Nasiba ki samo roba ki zuba mai, gobe sai ya kawo Robobin da za a dura mishi a ciki, sai ma ya sa a fridge in yana bukatar mai sanyi", "sai kuma chan gida ka basu su dinga maka abinci da ruwan" ganin yanda ya chanza fuska ne yasa Abbi fahimtar be cin abincin gidan, kuma ya tuna Nasiba tace siyan abinci yakeyi, sai yace "ko su nan zasu dinga dafa maka abinci? In dai ka samu lokaci ka dinga lek'owa kaji ko?" kai kawai ya daga. Nasiba ta dura mai, kamar jira yake tana bashi ya juya, har ya kusa fita ya juyi ya kalli Nenen da tsura mai ido, ya danyi guntun tsaki yace ma Abbi "kace mata ba ruwan ta da ni, magani kawai zata dinga bani" Murmushi kawai Abbi ya mai alamun Yaji, Nene zata yi magana Nasiba tayi saurin toshe mata baki, duk sukayi daria. "Nene nasan ba zai jure shan maganin nan ba in yana wurinshi, shiyasa nace zan bar maganin a gunki, yanda zai dinga zuwa yana sha a gabanki ya hadiye, amma DonAllah kar ki biye mishi kuyi ta sa'in sa" Nene ya ta6e baki tace "najih" Abbii yace "Nikam Seebi Rafeeq baya miki kama da wata?" Murmushi Nasiba tayi tace "Mamin Ayman" Abbi ya gyara zama yace "ya akayi kikasan ita ke raina?" tace "saboda da ita su ke kama, Mamin shi ce" Abbi yace "bangane ba" tace "Maman shi ce Mahaifiya" "Allahu Akbar biri yayi kama da mutum" inji Abbi nan Nasiba ta shiga basu labarin yanda sukayi da Mami, duk suka tausaya mata. ***************** Yau ne tafiyar Abbi, ya shirya kayanshi sun fito domin rakashi tasha, sai ga Rafeeq ya fito daga motarshi da Robobi cikr da Leda, ya kalle su one by one, kafin yace "Barka da Safiyya" amsa wa sukayi, binsu yayi da ido kafin yace "Ruwan zaa bani" Abbii yace "to ke Nasiba kije ki dura mai ruwan, Nene kuma kiyi zamanki ba sai kinyi wani rakiya ba" tace "ai wallahi sai na raka ka" Seebi tayi fuskar tausayi tace "Hamma Rafeeq bari mu raka Abbii tasha, idan mun dawo sai in dura maka" Rafeew be ce komai ba Abbi yace "Aa, je ki dura mai, muna jiranki" nan Rafeeq ya gane cewa yau Abbi zai koma Kaduna, ya kalli Abbi cike da nutsuwa, dan zaman da sukayi tsakanin Jiya da Yau yaji zuciarshi ta kwanta da shi, be son ya tafi, ina ma ace ya k'ara kwanaki, yanzu da be zo ba tafiya zaiyi without saying goodbye? a hankali ya kalli Rafeeah da ke jiran ya miko mata ledar robobin, yace "Wait, we'll all go" Abbii yace "aa Rafeeq, ka tsaya kayi uzurin ka" Rafeeq be jira cewar Abbi ba ya taka har gabanshi ya amshi jakkar hannun shi, ya wuce motar shi ya bude ya saka a booth, hakan ne yasa Abbii Murmushi ya nufa motar ya zauna gaban mota, su Nene da Nasiba cikin murna suka shiga bayan mota, Rafeeq ya ja motar yayi Tashar KTSA. Ba me maganar har suka iso Tashar, har cikin tsar Rafeeq ya shiga da motar sa, bayan da Abbi beyi ba da a sauke shi nan su juya, amma yak'i, jin ana Fadin Kaduna Kaduna ya sa Rafeeq parking ya nufa Motar, da Sauri Abbi ya fita ya bi bayanshi, Rafeeq gaban kwandaster (conductor) yace mai "Nawa?" karen mota yace "1500" Cikin Aljihu Ya sa Hannun shi, ya zaro 2k Abbii yayi saurin rik'e hannun Rafeeq, Rafeeq ya kar6e hannun shi cikin nutsuwa tare da girgixa ma Abbi kai ya mik'a ma Kwanduster din, kamar jiran zuwan Abbi ake, Motar su ta tashi, bayan sun bishi da adduoin sauka Lafiya, suka koma Mota. Rafeeq ya ja ya bar tasha. *********** Da dare ya nufa Gidan Nene amsan Magani, Sallama yayi ya shiga, Nene ke zaune tana jin radio, Nasiba na gefe tana duba Wani Littafi, tace "Hamma na sannu da zuwa" Kallon Nene yayi instead ya amsa gaisuwar Seebi yace "Sannu Fa" Nene da yak'en da ya fi kama da kuka tace "Ahh kai ke da Sannu" be kulata ba ta tashi dauko Magani don ta zan silar zuwan kenan, Ganin haka Nasiba ta matsa kusa dashi tace "Hamma ka ci abinci?" kamar ba zai amsa ba yace "i am not hungry" ta marairaice tace "DonAllah in dafa maka ko Indomie ce?" shiru yayi kamar be ji ta ba, har ta cire rai zai amsata ta mike don komawa mazaunin ta, cikiciki taji yace "Ki dafa min" Da sauri ta juyi da murmushi dauke kan fuskar ta, daure wa yayi kamar ba shi yayi maganar ba, da sauri ta zura Hijab ta bude jakkar School dinta, yana kallonta, sai da tayi hanyaf fita ta tsinkayi muryar shi yace "Ina zaki" tace "Shagon Ummu Sudais zanje in siyo Indomie din" (GWS Ummu Sudais ILY). Guntun tsaki yayi ya mik'e ya zura takalman shi ya fita daidai ita yace "Ki barshi" tace "Hamma-" katse ta yayi ta hanyar daga hannu yace nace "ki barshi ko? Koma ciki" ba musu ta dawo ciki amma ranta ya baci, to meye abun daga murya? Nene ta fito da Goran Maganin a hannunta tace "Ina Dunkum din?" Seebi ta ta6e baki tace "ya tafi" Nene ta daga murya tace "Kika barshi ya fita?" Seebi cike da takaici tace "rike shi zanyi ince ya dawo? Nene tace "ke tamabyar ki nayi bace miki nayi ki zagar min uwa ba" Seebi dai ba ta sake magana ba ta shige Daki. Chan sai ga Rafeeq ya shigo da Carton din Indomie da crates din k'wai guda biyu, Nasiba na ganin shi tayi saurin tashi ta tarye shi don ta ga yanda yake tafia kamar zai kife, tace "Hamma you dont have to do that" hararar ta yayi yace "jeki dafa min, i am hungry" wani dadi taji ya lullube ta da sauri ta aje kwalin gaban Nene, Nene ta kalli Rafeeq tace "Sannu fa" wani murmushi ya kubce mai, wai shi take koyo, wannan tsohuwar is full of wonders. _Bayan Minti 15_ Gaban shi ta dire Indomie din da aka dafa da ruwan Magani da fried Egg, kamshin ya cika mai hanci, tuni ya fara Salivating, Ba wasa ya hau cin indomie din yana jin dadi, Nene ta ta6e baki tace "kadifiri, a gama jin dadi a zo a kur6i magani" ai ko yana gama sha, ta zuba magani a cikin spoon tace "Kar6i" warin maganin ya daki hancin shi, ga shi ya ci k'wai haka kurum yaji amai ya taso mai, ya fara k'ak'arin amai, ganin yamutse yamutsen fuskan da yakeyi sai tayi zaton iyarshege ne, da sauri ta toshe hancin shi, kafin ya ankara ta mai dure, ta juye maganin a bakinshi, ta sa gudan hannubta ta damk'e bakin Rafeeq, gashi be nunfashi, be da zabin da ya wuce ya hadiye maganin, sai da yayi sakwan 15 kafin Nene ta sake shi, Nasiba ta kasa ce ma Nene komai don tasan yau akwai dirama, da gudu ta bulbulo mai ruwan Maganin shi ta mik'a ma Rafeeq, ba sanya ya kafa kai ya shanye ruwan, ya juyo ya na ma Nene wani irin kallo. Kunnenta ta kama da hannu biyu tace "Sori Gaye" Sosai ta bashi daria, kauda kai yayi lokaci daya ya murtuk'e fuska, chan kuma yace "kina da hayaniya, ki dinga yin abu a hankali" Nasiba ta bude baki, a zatonta Nene zata balbale shi da masifa, sai ta bata mamaki da cewa "Naji Dan gaye na, ga Farar ka tun rannan na ajiye maka" ta ciro Farar a gefen Tabarma da yake dare ne ba wanda ya lura dashi. Murmushi Rafeeq yayi wanda ya sa fuskar shi kyau Sosai ya sa hannu ya amsa tare da kallon Nene, Nene ta san me zai ce, a tare sukace "Sannu Fa" Nene da Nasiba suka sa daria, shi dai Murmushi kawai yayi. Nasiba tace a ranta "Finally these two are getting along. Lallai magani ya fara aiki so soon" *********** Bayan Kwanaki Goma(10days later) (Kuyi hakuri da page din nan, girman Alkawari ya sa nayi typing page din, Zan dasa daga nan gobe InshaAllah👻) 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀      NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) This page is for you my Everlasting Babe Miemee 👄Bee❣and My Coach Lubie Maitafsir❣ Aunty Sis and I love you two to the moon and back #1love. Pg4⃣7⃣ "Oh shit! sorry Angel i didnt mean to shout at you" duk yayi wani iri kamar me shirin kuka, 6are baki ta sake yi, kamar ana k'wak'ule mata idanuwa, kuka Rafeeq ya fashe dashi sosai, be son kukan Ayman, yana waigawa ya ga Uncle Zaid ya idar da Sallah ya tsaya yana kallon su kamar TV, ganin Rafeeq na kuka ya sa Zaid daria, da sauri Rafeeq yayo kan Zaid kamar zai kife shi da duka don takaici, yana kallon su amma ya k'i cewa komai, "Uncle please make her keep quite" a tak'aice Zaid yace "No, i didnt make her cry, you make her calm" Cikin marairaicewa Rafeeq yace "pleaseee" Zaid ya ksrbeta, tana ganin shi tayi lamo tana ajiyar zuciya, Zaid yace "ka duba bayan Seat akwai Basket dinta ka kawo min, she must be hungry" da gudu Rafeeq ya fita waje duk ya bi ya rude, Zaid ya bishi da ido ya na Murmushi, chan sai gashi ya dawo da Basket din Abincin Ayman-Rafee'ah, Zaid ya ce bude flask din ka zuba ruwan zafi a bowl din ciki, Sai da ya dauraye Dan kwanon kafin ya bude flask din, Zafi rau kamar yanzu aka zuba a ciki, tun Ruwan Zafin da Mami ta sa musu a flask ne da safe, har yanzu be huce ba, nan Zaid yayi guiding Rafeeq ya dama mata Baby food din, Zaid ya lasa yaji yayi daidai ya shiga bata a baki kamar yanda ya ga Mami nayi, ta dinga sha har tayi gyatsa, Zaid yace "kwaso kayan booth din gaba ki daya, banda Trollys din, akwai dan kit daga gefe kayan wankan ta na ciki" haka Rafeeq yaje ya dauko, suka tu6eta a tare, tayi kashi a pampers dinta, Rafeeq ya rintse ido tare da kawar da kai gefe ya mata tsarki, hannun kamar zai yaddashi, Zaid ya dinga musu daria, a tare suka mata wanka da ta juya ta hada ido da Rafeeq sai tayi kamar zatayi kuka(😩) Da sauri Zaid "zaice yi shiru babyn hammanta" sai tayi shiru ta fasa kukan, haka suka gama mata wanka duk sun jik'e kayansu kamar sunyi wasan ruwa, kusan Minti 30 suna shiryata kafin Zaid ya hadata da chocholate daTeddy bear, Daga Rafeeq har Zaid suka zube kan Gado yaraf a gajiye, suna maida numfashi kamar wanda suka shekara suna aiki, Rafeeq cikin gajiya yace "You should get married, only to someone who will take good care of her" Zaid shima yana maida numfashi, be ta6a wahalan Ayman ba kamar haka, lallai Mami na k'ok'ari, shima a gajiyen yace "Yes, you are right, i'll get married soon" suka kalli juna suka sa dariya. Jin horn din Motar Alhaji Habib yasa Zaid mik'ewa, yace "Yaya ya dawo" Rafeeq be ce komai ba, Zaid ya mai nuni da Wata Leda yace "ga tsaraban ka chan" murmushi kawai yayi ya bude ya ciro kwalin Turare, da agogo, da links na kaya, da pack din Vest, sai takalmi. Murmushi Rafeeq yayi yace "You are the best". "Babyn hamman ta zo muje mu gaida Yaya" Zaid ya kalli Rafeeq yace "ko kuka takeyi akace yi shiru babyn hammanta zakaji tayi shiru, she has no idea who the hamma is, yau ta ganshi tana mai RM" murmushi kawai yayi yace "A sannu zata san waye Hamman ta" Rafeeq ya mike ya nufeta yace" zo muje gun Hamma" ga mamakin shi ta mika mai hannu shi kuwa ya sa6e ta, suka fita, Zaid ya dauki ledar Tsaraban da ya ma 'yan cikin gida. Shekara kusan daya da wani abu rabon da ya taka koda k'ofar parlorn cikin gidan, tana hannunshi ya dinga bin parlorn da ido, yana nan yanda yake, a hankali ya shiga tunano bak'in abun da ya faru, tun daga Randa yaga Mamin shi da wani a daki zuwa ranar rasuwar Rafee'ah, dalilan da ya ke hanashi tunkarar dakin kenan, ya juya zai koma, Zaid yayi saurin girgiza kai yace "mu shiga" ba musu ya bi bayanshi suka hau Sama har Parlorn Daddy. Daddy na ganin su ya mik'e tsaye, bawai mamakin dawowan Uncle Zaid yakeyi ba, aa Mamakin ganin Rafeeq yakeyi a cikin gidan a Saman shi, hawaye suke shirin bullo wa yayi saurin tare su, ya wayance da amsar Ayman hannun Rafeeq, Zaid ya durk'usa yace "Barka da Dare Yaya" Daddy yace "Engineer, saukar yaushe?" "Jiya na dawo" sai ga Saude ta shigo tana takun ta, wai ita tazo taryar Miji, aiko ganin Zaid ya sa ta 6are baki "Meema ga Uncle Zee" "inalillahi" zaid ya furta a ranshi, kafin ya ankar sun rugo da gudu ita da Aneesa wai su zasu mai Oyoyo, da azama ya mik'e yayi saurin mik'a musu ledar Tsarabar su don ya san dukkan su ba mai hankali ciki suna iya fado mai, Meema da ta shagala da kallon Zaid, bata taba ganin hallita me kyaun Zaid ba, Zaid ya gama tafiya da ita, wannan karon ko ta halin k'ak'a sai ta samu cikar burin ta, Dole Sai ya aureta, like hell look at him, ya hadu ne, balle ya sha madarar England, duk ya k'ara cika, ya kusa 40 amma dubeshi kamar dan 25, ita kadai take tunaninta. Aneesa da dadi ya gama kasheta, yau Rafeeq ya zo Sama, ta matsa kusa dashi "Yaya Rafeeq, wata sabon ganin" dogon tsaki ya ja ya mik'e tsaye, tunda Shigowar Sauda ya fara ganin duhu, ya kalli Zaid yace "Uncle I'll be downstairs" be jira cewar kowa ba ya fita ya sauka k'asa. Aneesa tace "kagani Uncle Zaid? Yaya Rafeeq ya tsaneni, ba yason ko magana in dinga mishi, duba fa yanzu yana ganina kamar ya ga kashi, shine ya fita" "Ki cigaba da hakuri" kawai yace da ita. Saude tayi k'wafa ta juya taga Alhaji Habib Dauke da wata kyakywan diya tace "Alhaji ina ka samo yarinyar nan? Yayi danyi yak'en takaici yace " 'yar gurin Zaid ce" ai ko Meema tayi saurin cewa "Laaah Ayman ce yau a gidan mu, daddy kawota, Aneesa ma ta yi hanzarin cewa ni za a ba ita, saude ma tace " ku bari in fara daukarta, ai tana nan gidan, ganin su uku sunyo kanta gadangadan, hakan kuwa ya ba Ayman tsoro ta fashe da wani irin kuka, Zaid ya dafe kai ya girgiza kai, Alhaji Habib yace "kunga kun bata tsoro, Karbeta Injiniya" Zaid yace "k'uiya gareta bata yarda da kowa" ya sa hannu ya amsheta. Saude tace "baka taho da nanny dinta ba?" a ranshi Zaid yace "Nanny dai? Dama Ayman na da Nanny?" Meema ce cikin kissa tace "kema Sis banda abunki wace Nanny zai zo da? Bayan ya kawo Ayman wurina ai ba sai yazo da wata ba, i know how to take care of kids more especially my Daughter" Saude da Aneesa suka sa Shewa, wannan gaskia ne, shidai Zaid wani yak'e kawai yakeyi, wanda da shi gwara yayi kuka, har yanzu Ayman ba ta daina Tsala kuka ba. "Ka san kuwa tana yarda da Nasiba? Duk k'uiwan Ayman bata yi ma Nasiba, don har goyata takeyi taje gidansu da ita idan tayi bacci ta maido min ita, so nasan ba zaa sanu matsala ba ko kwana nawa zatayi gun Nasiba da kakarta" Muryan Mami ya ji a kanshi a lokacin da ya tuna labarin da ta bashi kan shak'uwar Nasiba da Ayman. da sauri ya sauka k'asa Meema zata bishi Daddy yayi saurin cewa "da kin barshi ya lallasheta, sai ya maido miki ita tunda a gurinki zata kwana". Dadi ya kamata don duk zaton ta, ita aka kawo ma Ayman. A k'asa ya ga Rafeeq a dafe kai, duk yanda yake jin kukan Ayman a ranshi, ya fi tsanar ya ga Aneesa da Uwarta shiyasa ya kasa komawa sama da yaji kukan Ayman, Zaid ya kalleshi yace " Start the Car" ba gardama ya fita da sauri ya fada motar shi, ya kunna Zaid na zuwa ya shige, suka fita daga gidan, a hankali Rafeeq yace "Ina Zamu?" a wahalce Zaid yace "Gidan Nene" don har yanzu Ayman bata abr kuka ba, cike da mamaki yace "What? Gidan Nene? Are you kidding me? Sabida me? Why there of all places" Zaid ya kalleshi yace "Sabida chan tazo hutu, akwai matsala ne?" da sauri Rafeew yace "yes big one, matsala babba" "that woman is very noisy, and annoying tana da Hayaniya" Zaid yace "Thank you, but She's living with them for as long as my stay in KT" sai da Rafeeq yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya murtuk'e fuskan nan da ta samu sassauci kwana biyu, sai ya koma dunkum din shi yayi focusing kan tukin shi har k'ofar gidan Nene. Har Cikin Gidan Baba Maigadi yai mata Iso, da Aneesa ta ci karo, wani kallon da ta watsa mata yasa hanjin cikinta kadawa, "ke wa kike nema?" baki na rawa Nasiba tace "Alhaji na ke nema" "burauba, daddy na kike nema? Uban me zai maki? Shegia karuwa har gida" hayanniyar da Aneesa keyi ne ya sa Hajia Sauda saukowa tace "Anee ke da waye? Ta bi Nasiba da ido, haka kurum taji gaban ta ya fadi, nan ta ji ta tsani Nasiba, ke me kikeyi a gidana karfe 7 din dare? Nasiba tayi shiru, karaf Aneesa tace " Wai Daddy take nema" Meema tace " ke ko turo ki akayi ki kashe shi? Ko ki fadi me kika zoyi ko miyi miki Zindir Wallahi" jikin Nasiba ya fara rawa, da ta sani da ta yarda sunzo da Nene, don sai da ta buk'aci ta rakota saboda dare amma tace "aa ta bari zata iya, ai dare be gama yi ba, kuma yanzu za ta dawo. Nadamar rashin barin Nene ta biyo ta. Sauda tace "kai ku amso min ledar nan, k'ila kayan Asiri ne a ciki, ana so a juye hankalin Mijina" Meema da Aneesa su kayo kan Nasiba, matuk'a ta gama tsorata, Meema ta damk'o ledar, *kar ki bari kowa ya ga magungunan na sai Alhaji, don kiga yan gidan na cikin Zargi, ba mu san waye mugun a ciki ba* maganar Mallam Usman ya fado mata, da sauri ta fizge ledar daga hannun Meema, Meema kuwa ta kamtse Nasiba da Mari, marin da bata taba gani anyi ma wani ko da a film ba, wani ihu ta saka, ihun da ya fargar da Alhaji Habib da ke sama, yana jin hayaniya k'asak'asa, ya sauko da sauri ganin yarinyar nan me kama da Rafee'ah durkushe rungume da wani abu Aneesa da Meema suna ta jibgarta kamar Allah ya aikosu, ya sa shi karasawa gurin ta da gudu, ya dagota, Saude ta sake "Salati, shikenan Karuwar sa ce, dube yanda ya dagota, Alhaji wannan 'yar cikin ka ka ke bi?" ya dago jajjayen idonshi ya kalleta, amma sai ya kasa magana, yace "Nasiba, tashi mu tafi" tana kuka ta mik'e, Sauda tace "Alhaji kar ka fita" chak ya tsaya, amma ga mamakinta sai yace "Kiyi hakuri yanzu zan dawo" ya ja Nasiba har gun Motarshi, ya mata umurni sa ta shiga, Saude kuwa kamar wacce aka dasa a gurin idonta ya koma bula(lols i cant even imagine) "wata sabuwa inji yan chacha" yau Alhaji ne da mata gardama? "Meema tace Lahhh sis ya fita, ya fara miki gardama" Sauda ta yi wani ihun takaici ta bar gurin kamar zata tashi sama. ******** Sai da ya fita bakin Gate ya danyi parking, yace "Diyata, ban san ta inda zan fara baki hakuri ba, ni na ja miki, kiyi hakuri donAllah, ta tsagaita kukan tace bakomai Daddy, ta ciro ledar da mik'a mai tace " gashi inji Mallam, yace zaka dinga sha Safe, Rana Dare, kuma ka dage da Addua, ka dinga tsayuwar Dare, InshaAllah zaka fita daga sharrin me sharri" yanda take mai bayani sai yaji ta burgeshi, ya ji ya na sonta, irin son da yake ma Rafee'ah, yake ji dama diyar shi, ya nisa yace "Nagode kinji? Allah ya miki Albarka", ya sa hannu ya ciro kudi masu yawa ya bata, ta girgiza kai tace " Aa ba zan amsa ba, DonAllah nayi" yace "nasani ni na baki ki karba" ta ki tace "zan je Gida" yace "barin fara kaiki Asibiti a duba ki" tace "haba ba komai" yace "Kinga fuskar ki ya kumbura, dole a duba ki" tace "Allah bakomai zanje gida kafin Nene ta shiga damuwa" yace "dama zan biki in ba su hakuri kan abun da ya faru a sanadiyata" tace "daddy thats not necessary please" ya nuna ta da yatsa yace "bana son musu, ki nuna min hanyar Gidan ku" tace "to a sanyaye" ta shiga nuna mai hanayar Gidan "Ahhh muryar wa nikeji kamar muryar Zaidu bawan Allah?" Murmushi yayi yace "nine dai Nenen mu ni da Seebi" tace wacece wannan take ta tsala kuka haka? Ya mik'a mata yace "Jikar ki ce" ta amsheta ta tillata sama ta chafe, ta fara yi mata tawai har sai da tayi shiru, kafin ta shiga daki ta goyeta tsaf da zani, kafin ta fito, ta kalli Rafeeq da ya sha mur tun bayan Sallamar da yayi lokacin da suka shigo be sake magana ba da murmushi tace "Ah ah, gaye ya akayi ne? Naga fuskar ka yau kamar lokacin da kake Dun... Sai kuma tayi shiru tare da sa hannunta kan baki tana daria" guntun tsaki ya ja ya kawar da kai gefe, gyatsine tayi irin i dont care dinnan, tace kaji dashi "dunkum dangi tsaka" ya kalleta da sauri, tace "kaji ai cewa nayi dunkum, ko ba tsaki yayi ba? Magani sai ya fara aiki, sai abu ya rikice, to yau obados (over dose) zan baka.Tsakin ya kuma yi, shi dai Zaid daria yake tayi, yace " Nenen mu mun same ku lafiya?" ta janyo kujera ta zauna tace "Lafiya lao mutan Ingila, haka ka koma? Kaga yanda kayi kyau kuwa? Kamar da Amurka(America) daria kawai yayi, Daria kawai yayi, tace "Wannan fa?" ta nuna bayanta, yayi murmushi yace " 'yar guna ce" tace "Ahh wannan ba jika bace, wannan diyata ce, ni diya zanyi da ita, ina Mamar ta ta? Tsaki Rafeeq yayi yace " she asks to many questions, tana da damuwa gata da hayaniya" shifa a ranshi yayi maganar be san maganar ta fito fili ba, Nene ta mik'e ta shiga daki sai gata ta dawo da igiyar chargy na radio ko fitila, cikin daga murya tace "Zaidu bawanAllah, yau ko ni ko Dunkum, ta hau k'okarin kwance Ayman da ke bayanta, wai zata ma Rafeeq dukkan tsiya, Zaid yayi saurin tashi, don shi a zaton shi wasa takeyi, amma yanda ya ga ta dage ya sa shi bata hakuri, shi kuwa Rafeew yana nan ko gezau beyi ba tace " Haba Zaidu Bawan Allah, na dade ina hakuri da Dunkum, sai yayi ta gaya min Maganganu yana min turanci, rannan har bangaje ni yayi ya bi ta kaina ya wuce, Nagaji, yau ko ni ko shi" Zaid ya shiga bata hakuri, yana ma Rafeeq ido da ya bata hakuri, shi kam ya dauke kai kamar be san ta nayi ba, ana Cikin haka ne Nasiba tayi Sallama. Daga muryarta Nene a san cewa ba lafiya, duk suka zuba ma Soro ido, Nene tayi saurin karasawa gunta tace " Seebin Nene, me ya samu fuskar ki?" Nasiba tace "bakomai" tayi gaba ta tsaya kusa da Uncle Zaid tace "Ina wuni? An dawo Lafiya" ba ta jira amsarshi ba tayi gaba zuwa daki, don idan ta tsaya dogon magana ta na iya fashewa da kuka. Zaid duk ya bi ya damu yana so ya ji matsalar ta, "Ke Seebi" inji Nene, chak Nasiba ta tsaya da ta ji yanda Nene tayi kiranta in a serious tone, Nene ta matso kusa da ita tace " ni nasan ke baki da abokan fada, baki da neman tsokana, kina da gaskia ana iya dukkan ki ki kasa magana, ki gaya man, wani dan abun uban ne ya bugeki har ya kumburan maki da fuska? Kamar jira takeyi ta fashe da kuka, Nene ta sake hawa sama tace "a gidansu Dunkum din ne a ka bugeki? Eyi? Ki gaya min" ita dai bata fasa kukan ba, Rafeeq yayi guntun tsaki ya matso kusa da ita yace "kinje gidan mu ne?" yo eh daga gidanku take "Me kika je yi a gidanmu? Eh?" Nene cikin fada tace "kai dallah dakata min, go gefe, zaka tasata a gaba kana mata fada, sak'o takai ma babanka, shine aka samu watsatssu da suka mata hakan? To wallahi ba zan yarda ba ko uban waye ya taba man 'yar jikata sai ya yaba aya zak'inta" Sai yanzu Zaid yayi magana duk da be gane me suke nufi ba duka ya kalli Rafeeq yace "Calm down Feeq, Nene fada ba zai maganace komai ba, bari ayi abun a tsanake, Seebi, su waye suka buge ki?" cikin sheshekar kuka tace "wasu mata ne su biyu, don sunce in basu ledar hannuna nak'iya shine mamansu ta sa su suka dinga duka na, sai da babansu yazo ya k'wace ni tare muke yana waje" a hankali Rafeeq yace "Aneesa da Meema" Nene tace "Babbar Balaeen chan, wallahi da Aneesar, da uwarta da wace tsiya sun tsokalo tsuliyar dodo, ba su san da su ta6a Seebi gwara sun kamu da farar masassara, yau sai na gwada musu wacece Aminene Mamman" ta figi hijabinta da ke kan igiya, ai ko duk suka yo kanta, Zaid yayi saurin rik'e mata Hijab, ai ko ta daddage ta buge hannun Zaid, daidai Soro ta ci karo da wani Mutum ta kalleshi galala tace "kai kuma fa?" _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) _Nagode da Adduoin ku, masu kirana da masu min message a Whatsapp da Sms Ina godia, ina muku Albishir da naji Sauk'i sosai, kuma zaa cigaba da yanda akeyi InshaAllah. Allah ya bar Zumunci. Pg4⃣8⃣ Duk suka bi bayan Nene, Rafeeq na gannin baban shi a ranshi yace "Interesting! Daddy a gidan Nene" shi kuwa Zaid cewa "yayi Yaya me kakeyi anan?" nan Nene ta gano bakin Zaren tace "touu Alhaji Habib Lema ne, gaya min, da saninka ne Matarka da 'yayanta suka ma jika ta mugun bugu?" Alhaji Habibi duk ya daburce, be taba ganin tsohuwa me masifa haka ba, yace "kiyi hakuri Wallahi ba da sani na bane, ni ne na kar6eta" Nene tace yo abun azziki kayi? Dalilin wa aka bugeta? Nace dalilin wa? A hankali yace "kiyi hakuri a dalilina ne, hakan bazai sake faruwa ba" tace "k'warai kuwa, hakan ba zai taba sake faruwa don yau watna cin ubansu ya tashi, har matarka" tayi hanyar fita da sauri Seebi ta rik'ota, duk suka shiga bata hak'uri tana cicijewa banda Rafeeq da ya koma gefe yana Murmushi, ya tabbatar Nene yar daru ce, da k'yar suka shawo kanta don tana ganin kimar Zaidu dan Albarka, ta dawo ta zauna kan kujera, Nasiba tace ma Daddy kayi hak'uri, shez always like this" murmushi ya mata yace "karki damu" ya zauna kusa da Zaid dake kan tabarma, cikin gunguni Rafeeq yace "ai da kun kyaleta taya zata je gidan mutane ta buge su?" ashe ta ji shi cikin fada tace "Ai da kun bari naje sai ka ga ta yaya naje har na musu dukkan tsiya, sai ka tantance, kaima bawai k'yaleka nayi ba" Uncle Zaid yace "Feeq quiet!". Zaid yace "Yaya wai ne ya faru? Wani Sak'o Nasiba ta kai maka? Ajiyar Zuciya Alhaji Habib yayi, ya fayyace musu komai tun haduwar su a Gun mallam, har zuwa yanzu da ta kawo mai magani, Zaid ya jinjina kai yace "Ashe ba nikadai nake ganin Nasiba kamar marigayiya Rafee'ah ba" Nene tace "kama sukeyi ne wai?" Alhaji Habib ya bata amsa "basa kama anma yanayinsu iri daya komai" Rafeeq dai be je komai ba, sai kallont yakeyi, ita kuma hankalinta baya nan yana gun Aymana da ke rik'e a hannunta, hayaniyar Nene ya hanata bacci, Zaid yace "Yaya to maganin dai ka sha su yanda ya kamata, don ka daina jin Yanda kakeji Allah ya sa a dace" yace "Amin" Zaid yace "Feeq ka je gida ka kwaso kayan Ayman, dare na k'ara yi" a zucciye yace "Seriously shes sleeping here? Cikin daga murya Zaid " Yes Rafeeq, shes sleeping here" kamar zaiyi magana ya fasa ya wuce fuuu kamar zai tashi sama, Nasiba ta bishi ido a ranta tace"why? Yana da matsala ne don zata kwana nan?" ta ta6e baki. "Engr. nace baza ka kai Rafeeq gun Malamin nan me magani ba, yana maganin Sihiri ko asiri, ko aljannu, da masu taurin kai, abunda ya sa na yarda Mallamin, ba dan tsubbu bane, kuma be aiki da Aljannu, da kalmar Allah da Adduoi da suek a cikin Kurani da Hadisi ya ake amfani, ba a san inda zaa dace ba, wannan zucciya ta Rafeeq na bani tsoro" Zaid yace "Duk da akwai Chanji a halaiyar Rafeeq zan kai shi a duba shi, Nasiba kin san wurin ai? Idan kim dawo school gobe sai ki rakamu, Nasiba tayi gyaran murya tace "da akwai abunda baku sani ba Uncle, Rafeeq Yana na magani already, ko yau da Daddy ya ganni a gun Mallam Ruwan maganin shi na koma an so mai don wanda aka bashi da farko ya k'are, Ruwan Adduoi ne, ya maida shi ruwan sha, in kuma a gidannan zai ci Abinci, to da ruwan maganin ake mishi dahuwar, sai kuma Wani maganin hadin magunguna, shigen naka ne Daddy, shi maganin zai sa mai hakuri da dangana a zuciyar shi, to Alhamdulilah an fara samun Nasara". "Allahu Akbar" inji Daddy, "Engr. Ka lura da wani abu game da Rafeeq bayan dawowan ka?" Zaid yayi murmushi idonshi kan Seebi, duk ta gama tafiya da imanin shi tsaf, maganarta yanayinta, komanta y bureshi, yace "eh Yaya, Rafeeq is somehow changed, naga chanji wallahi, ashe akwai silar chanjin shi" Nene tayi magana, tace "ai da Mahammadu yazo ne ya mishi wuriwuri har ya amso mai magani ya kuma tilasta mai sai ya sha, yanzu ms zai dawo in bashi na yau" Daddy yace "abunda bangane ba, shine Zaid dama kun san su Nasiba? Ya abun yake?" Nene ce taba Daddy labarin daga farkon haduwan su Zaid har zuwa yau, Daddy ya jinjina kai dama akwai irin mutanen nan? Masu maida damuwar wasu nasu? Kuma tsakanin su da Allah? Ba don wani abu ba? Kai su Nene ba abun yadawa bane, mutanen Arziki ne, ashe sune Silar saukowan da Rafeeq keyi yanzu, Allah ya musu Albarka, Lallai su Nene *ALHERI NE* a rayuwar su. Daddy yace "Inna Mungode k'warai da wannan karamci naku, ba abunda zan iya biyanku dashi, amma ina so in dauki Nauyin karatun Nasiba, wallahi a sanda na fara ganinta na fara Sonta, irin So din da na ke ma diyata Rafee'ah, donAllah ku bani wannan damar" Nene tayi darian murna tace "Ai jahili ke maida kyauta, an baka dama,Allah ya bar zumunci" duk suka amsa da "Amin" ya cigaba da cewa, "My daughter, ke kuma daga yau if you ever need anything, come straight ahead and tell me, dont hesitate to tell me, zan baki number na, you can easily reach me" tayi godia Sosai. Nan Rafeew ya shigo da Sallama, suka amsa mai, Akwatin Ayman ne sai kayan wankan ta, sai kwandon Abincin ta, Seebi ta taimakeshi ta shiga da kayan cikin dakin Nene, tana jerawa bayan ta kwantar da Ayman kan Gado ta sakar mata Net don kar soro su cijeta. Nene ta kalli Rafeeq ta tuburne fuska tace "ai sai kaje ka dauko maganin ko?" bakin shi ya turo ya mik'e yana gunguni, dakin ya shiga saman wardrobe inda ake ajiyewa ya dauko ya kalli Nasiba da take ta ririita Ayman tana bacci ya ta6e baki ya fita da robar maganin, kitchen ya shiga ya zaro chokali, Daddy da Uncle Zee suka bishi da ido, yanda yakeyi kamar yaron da ke tsoron magani, duk sai ya basu daria suka gumtse. Kawar da kai yayi ya mik'a mata, ita ma ta kawar da kanta ta amsa, su a dole basa shiri, ta bude ta tsiyaya mai, kamar kullum ta toshe hancin shi ta dura mai, tare da gumtse bakinshi har sai da ya hadiye, guntn tsaki yayi yace "kina da matsala" ai ko igiyar chajin radion kusa da ita ta wawuro ta shauda mai a baya "Ouuuuchhhh!" ya fada yana sosa baya, da Daddy da Uncle Zaid suka tuntsire da daria, ya kallesu yace "Its not funny it hurts" Nene ta mik'e tace kana so in k'ara ma ne? Ba na hanaka turanci a gabana ba? Tsaki yayi ya kalle su duka yace "I'm outta here" ya juye ya fita, tana daria tace "ai da ka tsaya mana, kai karatun ka iya Najiriya, da ka tsaya nasa Zaidu bawan Allah shi da yaje Ingila ya turance min kai, ya kafirce min kai da turanci" ai kam Daddy dariya harda rik'on ciki, Zaid ya kalli Nasiba da ke daria k'asa k'asa, yace "are they always like this?" tace "Yesss, they are always like this like all the time" Nene tace "Au kuma turancin ne?" duk suka sa Daria, Daddy ya mik'e yana daria yace "Nene da jikokinta baza ku kasheni ba, nayi Gida" Sukayi Daria har Gate suka rakashi, suka mai Sallama, a waje suka ga Rafeeq zaune kan mota au ashe be tafi Ba inji Nene "kema dai ki barshi donAllah" Daddy yace "R-Lema, mu tafi kaji kar Nene ta sake dukkanmu kai" Rafeeq ya lura duk daria suke mai, to meye abun daria, guntun tsaki yayi ya murtuk'e fuska, ya sauko daga kan motar, ya mik'a ma Zaid mukullin motar shi ya bi bayan Daddynshi, Nene tace "Guznight gaye" kallonta yayi ya buga tsaki tace "Auu, Dunkum dangin Tsaka". Duk suak fashe da daria. "Seebin mu, zo ki tayani kwasan kaya" tayi murmushi ta biyo shin gun booth, Nene kuwa tayi shigewar ta ciki tana murmushi, Manyan Ledoji guda 3 ya kwaso a booth din, yace "muje ko?" tace "Uncle Zaid cewa fa kayi inzo in tayaka" yace "kuma nagode muje" sukayi daria suka shiga ciki, Nene na nan kan tabarma, ya dire ledojin gabanta yace "Nenenmu ga tsarabarki ta Ingila ga kuma na Seebi" Nene ta bude ta na murna, Seebi kuwa kasa taba ledar tayi, tace "Allah ya saka da Alheri, Nene ta ciro Dogayen riguna marasa nauyi, tana murna, tace kamar kasan ina son dogayen riguna, sai dai kawai na zumbula su, kai madallah madallah da Zaidu dan Albarka, kai ALHERI NE, Allah ya biyaka ya raya Zuri'a, ta dinga shatato mai Adduoi, yaji dadin adduoin ta yace " Amin Ameen" Nene tace ke baki bude taki ledar ba, sadda kai tayi k'asa Nene tace "ke tafi chan shashasha, mik'o min ni in bude" kwalin waya ta fara cirowa, Iphone 6s, sai doguwar Riga mai wando, da dan jacket dinshi me kama da boyfriend jacket, sai takalma, sai kuma kwalin turare, sai kuma chocholates. Nene tace "Anya Zaidu BawanAllah kayan nan basuyi yawa ba?" Nasiba ta kalli kayan ta wutsiyar ido da sauri ta zabura ganin kwalin Apple, tace Uncle Zaid, i cant accept these, they are too much wallahi" ce mata yayi "Shhhh, they are not, they are all yours, and you are accepting all" Nasiba ta girgiza kai tace "Nene kingani ko, ki ce mai sunyi yawa, bazan iya amsa ba donAllah" Nene tace "gaskia ne kayan sunyi yawa, daga gani zasuyi tsada, amma ya zaayi aikin gama ya gama, Ingila ne balle a ce zaa maida su, ya zakiyi dole ki karba, amma nesitym(next time) kar ka k'ara irin wannan kaji? Zaid na daria yace " toh Nene ba zaa k'ara ba" Yauwa danAlbarka, ke kwashe kayan ki kai daka zamuyi hiran yaushe gamo da Zaidu dan Albarka. ***** "Zaidu gaya min kana Son Seebi ne ko? Don wannan kayan sun fi kama da na toshi" cewar Nene ta na me daga mai Gira, Zaid ya daburce ya fara in ina, Nene da ta dago jirgin shi tace "kai kar ka wani damu, naji ka harda su in-ina, ai tuni na dago Jirginka, Son Seebi kakeyi" Zaid yayi murmushin jin kunya ya shafe k'eya yace "Nene taya kika sani?" tace "kai Zaidu na fa kwan biyu, ko kallon da kake binta dashi ai ya isa in gane, balle ni nan da saurin dago zance nikeyi, kaga ko Maalush sonta yakeyi" Zaid ya dan kallo ta yace "Mahmud dai? Tace shifa, shima kallon da yake binta dashi ne yasa na gano shi, kaga kar ka damu, kar kace baza kayi takara da Maalesh ba, bana zato ya ma sanar da ita, hikima ta ce ta dago min shi, Kayi saurin isar da sak'on zuciyarka gareta, don bana tunanin tana kula wani da namiji" Zaid ya share gumi yace "Nene kina ganin zata soni? Ba za tace na mata tsufa ba?" "Kai dallah tafi chan, kai tsoho ne? Duk tsufan ka ka kai Aminene Mamman? Ko ni zaka aura eyi? Ka manta kai Hadadden mutum da duk mace zata so samun ka? Kai ka kai da ba macen da zata guje ka, ko tace ka mata tsufa, ko da ka kai tsufa na, kaga Zaid, irin Ka nike ma Seebi adduar fatan samu, kaga mu ba makwadaita bane, Mu muna da rufin Asirin Allah, munfiso ayi Aure cikin rufinAsiri da so da k'aunar juna, kagane? Gwara ta aurei wanda ya san darajarta da kimarta, kuma ni Wallahi kai nikeso da Jikata, shawara daya zan baka, ka nemi So gurin Seebi" ya jinjina kai yace "InshaAllah Nene, zan nemi So Gurinta, in kuma Allah ya yarda, Zan auri Nasiba" Nene ta tafa hannayenta, tace yo Seebi zata zama sirikata don ni fannin Ango nike" yayi daria. A bangaren Nasiba ta gama jin komai don Nene ba a yi sirri da ita, ta rasa ganewa murna zatayi ne ko kuwa? Tabbas Uncle Zaid ya kai a So shi, don bai da makusa ko kadan, bata damu da tsufan shi ba, amma ta kasa yarda, Namiji kamar Uncle Zaid yace zai aureta, ai kam ta dace, ta nuna kanta da Yatsa, Wai ni Uncle Zaid keso?. Ba ta ankara ba taji yana kiranta, yace ta dauko mai wayarta zai saka mata Sim a sabon wayarta, duk ta kasa fita, Nauyi da k'imar shi suka k'aru a idonta, da k'yar ta fita tana susuna kai, Nene ta shige ciki bayan sunyi bakwana da Zaid, yanda takeyi ne ya bashi tabbacin taji su, hakan ma daidai ne, ya samu saukin wani abun, ya lura ta kasa daina murmushi, da kyar ta mik'a mai wayar, cikin muryar shi me sanyi yace "Seebin mu ni da Nene yadai? ta dago a hankali ta kasa hada ido dashi don kunya, yace " so you've been eavesdropping? Kinji tace gobe zaa daura auren mu ko? Shine kike ta kunya" da sauri tace "laaahh ba haka tace ba fa, cewa tayi ka nemi So a gurina" da sauri ta toshe bakinta, shi kuwa yayi daria yace "ashe dai kinji komai, so tell me, Zaki iya Auren Tsoho kama na? Ta rufe fuskarta da hannunta biyu ta tura kanta cikin cinya, yace " Magana fa zakiyi 'yanmata na, I love you Seebi, right from the first Day, i want you to give me chance and experience 'the Old School' love" da sauri ta tashi ta shiga daki ta barshi zaune don ya cika ta da kunya, kalaman shi sun mata nauyi, Zaid yayi murmushi, yace "i take that as a Yes" ya kwashi wayoyin duka ya fita dasu, saboda zai kai a yanka Sim din ta window take lek'en shi, ta na Murmushi, muryan Nene ta ji a sama "Hegiya ana so ana kaiwa Kasuwa" da sauri ta murtuke fuska ta fita zuwa kitchen. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg4⃣9⃣ 7:45am "Ayman Zauna kici Indomie kinji?" Ayman ta k'ura ma Nasiba ido kamar me son gane Wani abu chan kuma sai ta fashe da kuka, Nasiba tayi saurin Rungume ta tana cewa "yi shiru kinji babyna in kaiki gurin Mami?" gyada kai tayi, tace ''to kici sai muje gun Mami a Motar Daddy ko?" nan ta shiga bata Indomie din tana ci har ta fara fiddoshi idan ta bata alamun ta k'oshi, Nasiba ta fita da plate Ayman a binta a baya duk inda taje, Nasiba ta sata a baya ta juye ruwan Zafi cikin bokiti ta tu6eta ta mata wanka, ta zo ta mata shafa ta sa mata wasu riga da dogon wando, sai ta sa mata Sweater sabida sanyi, tana cikin haka ne sai ga Zaid yayi Sallama, ai ko Ayman na hango babanta ta ruga a guje gunshi, ya dagata ya chafe, yace "Baby Good Morning" ita ko sai daria takeyi, Nasiba ta fito tana dari-dari ba tare da ta kalleshi ba tace "Ina kwana" cike da k'auna ya amsa mata gaisuwar, yace "Ya Bak'uwa, halan ta hana ku bacci?" Nasiba ta girgiza kai tace "Ai tunda ta kwanta bata tashi ba sai yanzu" a ranta tace "zai so ya san me taci" tace "yauwa taci Indomie kawai, ko akwai abunda zaa k'ara bata? Ya ta6e baki yace " Oho, ku kuka san in ta k'oshi, but ai nasanta bata da juriyar yunwa, da ta ji yunwa za tace miki "Friso" duk sukayi daria, yace "ina Nene?" tace "Nene taje siyan K'osai tun dazun, k'ila akwai layi ko suna chan suna Gardama da Maigadin gidan Lema" dariya yayi yace "wai kullum sai taci k'osai?" tace ai kuwa harda koko da ta dawo zata dama koko, wai idan bata ci K'osai ba ji takeyi kamar mara lafia" Zaid yayi daria yace "Nene Ikon Allah", ya sa hannu cikin Aljihu ya ciro wayarta ya mik'a mata, yace "gashi an yanko sim din" cike da kunya ta amsa tayi Godia. Suka yi dan shiru na wani lokaci sai chan yace "yau ba Lectures ne?" tace "Akwai" yace "to ya? Banga an shirya ba?" tace "ai bazan je ba" ya kalleta yace "saboda me?" tace "Ayman mana" yace "No No No, bamu yarda ba ko Ayman? Jeki ce ma Mummy ba mu yarda ba ta shirya yanzu mu kaita mu jirata ta gama lectures ko baby? Mummy ta maimaita a ranta, tirkashi, yace " Oya Madam, je ki shirya, hubbynki da babynki zasu raka ki Makaranta. Mun baki 30mins to dressup, Oya make it fast" ta tashi cikin jin kunya, bata so ta mishi gardama, haka ta shige dakinta" Daidai nan Nene ta shigo gidan da Sallama hannunta dauke da bakar Leda. Ahh Zaidu BawanAllah har ka iso kenan, yayi daria suka gaisa, ta shiga kitchen ta juyo K'osai din a plate ta shek'a Koko, ta fito inda su Zaid suke dauke da Jug da kwanon ta dire gaban Zaid da ke ta wasa da Ayman, ta koma ta dauko Kofi da teaspoon, ta dauki k'osai daya ta ba Ayman a hannu, Zaid yace "anya kuwa zata ci?" Nene tace bari ka ga ku yaranku sai indonie ko? To bari ka ga" Cikin saa yarinya ta hau cin k'osai, Nene ta fashe da daria tace "Yarinya is know K'osai" Sosai Zaid yake daria, harda k'warewa, tace "maza muci na san bakayi kalaci ba, ka zuba kokkon" ba musu ya sa hannu cikin plate din yana mai kara son Nene har ranshi bata da matsala wallahi (Anya Zaid? Tambayi Rafeew ka sha labari) chan yace "Nene ina na Seebi?" tace ce maka tayi zataci? To bata ci nai" ita sai Tea da biredi, ko indomie. "Dallah ki saka sabin kayan da yayi maki tsaraba mana jiya, kinga harda mayafi, ai gwara ki sa yaji dadi" Cewar Nene, "Anya Nene?" "mtssw, in za ki sa ki saka, in ba zaki sa ba ke kika sani" Seebi tace "zan saka" nan ta sa Doguwar riga da ya kusa zuwan mata idon sahu, da dogo. wandon kayan, ta dauko mayafin gyalen ta yafa, yiriri inji Nene, Wallahi jikata son kowa kin wanda ya rasa, wanga kyau haka, wanda be sanki ba yace kamar kin sa A cuci maza, ni ko da na sanki nace Gashi ne, takawar ki lafia Jikar Aminene Mamman, daria ta bata Sosai, ji take kamar ta sa Hijab, anma Nene ta rantse ba za ta sa ba wai ita da tsiya yau sai Seebi tayi shigar Miemee Yar gayu. Maza ki fita Zaidu na jiranki a mota yace, ta dauki Jakkar Makarantar ta, Nene ta ciro dari 2 ta bata sukayi Sallama ta fita. Wasa yake ma Ayman cikin Mota, ji yayi kamar ana kallon shi, waigawan da zaiyi ya Nasiba cikin shiga ta Alfarma, Sosai tayi kyau, ya fito ya zagayo gunta, ita kunya ma ya hanata shiga motar shisa ta choge tana kallonsu cikin k'auna, muryar Zaid ta dawo da ita duniyar da suke inda yake cewa "You look beautiful Seebi nah, Ayman tell mummy she looks Beautiful" kunya ya sa ta rufe ido, ya bude mata k'ofar gaba ta shiga, duk ta bi ta tsargu, haka suka kama hanya, ta amsa Ayman suna tafiya kamar wasu Maaurata, yana kallonta jefi jefi yana mata magana irin ta masoya ita kuwa Allah Allah take a iso School, coz taji maganganun Bambarakwai, har gaban Faculty ya kawo ta yace zasu jirata tace "Aa Uncle Zaid, donAllah ka tafi, ina nan har 2 a School ka tafi please, yace to in kun kusa tashi ki kirani kinji?" tace "to shikenan" ta shafa kan Ayman ta juya ya kira ta "Seebi" ta juyo tace "Naam" yace "I love you" ai kuwa duk ta daburce ta rasa me zatayi, daria yayi kawai ya ja Motar shi yayi gaba ya barta tsaye, Ji tayi an dafata, a firgice ta waigo ganin Miemee ya sata sauke ajiyar Zuciya, tace "Seebi waye wannan ya sauke ki? In ina ta farayi, tace "Uncle Zaid ne" Miemee tace "Uncle dinki ne?" kai kawai ta daga ta wofintar da maganar da tambayar Ushee, ta shaida mata cewa bata k'araso ba amma tana hanya. 12:45pm (Hikma Restaurant) Miemee ta kallesu a karo na biyu, ta lura da maganar da sukeyi k'asak'asa tun a aji, yanzu ma sunzo CAF sun cigaba, da alamu Seebi bata so inji labarin da take ba Usheey, don sunfi kusa, ganin hakan ne ya sa Miemee ta tashi ta basu wuri tace bari taje tayi musu ordering abinci don gudun zuciya, suka cigaba da labarinsu harda kashewa a tafa. Miemee na hangensu, ranta a 6ace it hurt Sosai, yanda ta dauke su ba haka suka dauke ta ba, amma bakomai tunda haka ne she will keep her distance tunda clearly sun nuna mata they dont want her among them. "Anee Lema, kamar wata nike gani da irin kayan ki" Aneesa da ke cin Dankali ta kalli k'awarta Meesha tace " na lura Kayan nan nawa sun tsole miki ido, to kina ganin su Nikadai ke dashi duk fadin Katsina, jiya Uncle dina ya kawo min Tsarabar, daga England so idon ki ne" Meesha ta girgiza kai tace "Wallhi wanchan da ke zaune tare da me Red veil irin kayanki ta sa, komai harda gyalen" da sauri Aneesa ta juya idonta ya hango mata Nasiba, ta bi jikinta da kallo taga irin kayan ne, Meesha tace "Ko 'yaruwarku ce, Uncle dinku ya siyo muku komai iri daya don kuyi Anko?" Cikin masifa tace "No, wallahi ba 'yaruwata bace, Allah ya sauwake wanchan middleclass girl din? Ko jiya Mum dina sai da ta tambayi dad dina idan suna da Relation, ya kuma tabbatar mata da cewa ba 'yanuwa bane, Aneesa tace " Yariska ce, jiya har gidan mu tazo neman Dad dina" Tabdijam k'ila ma tayi seducing Uncle din naki ya muku siyayya iri daya" Anee tace "Lallai kuwa zan koya maya hankali" ta mik'e tsaye ta nufi Seebi da Ushee da ke zaune. Tun daga nesa Seebi ta hango Aneesa hanjin cikinta suka kada, ta mik'e tsaye, ai kuwa Aneesa na zuwa ta kamtse Seebi da Mari lafiyayyu har kala biyu, tare da nuna ta da yatsa "stay away from my Family" Seebi dafe da kuncinta, tana hawaye, Ushee tace "haba baiwarAllah me ta miki ne zaki ci zarafinta?" Aneesa tace "ko zaki rama mata ne?" Usheey tayi shiru don ta fi Seebi tsoro, Aneesa yarinya ce ko shekara 18 bata rufe ba, amma girman jiki ne da ita, girmanta zai sa ayi zaton Babba ce shiyasa ake jin tsoron ta, "kuma Wallahi kije ki cire kayan nan, duk randa na sake ganinki da su sai na wulakanta ki" hankalin mutane ya dawo kansu, sunsan Aneesa Lema da Masifa, wani yace "kema kije kiyi yanda tace mana" da sauri Seebi zata juya ta tafi taji an rik'o hannunta tana dagowa taga Miemee tsaye, tace "Ba inda zaki, in Uban wani yace ta sa irin kayan da kika sa sai taje ta cire tunda tafi k'arfin a ga ta sa irin kayan ki" "Ke kuma wacece yar shiga sharo ba shanu?" inji Meesha, kallon Ke gara Miemee tayi mata, tace "Rama marinki" Seebi ta girgiza kai, Miemee cikin daga murya tace ki rama Marinki Nasiba Muhammad" Aneesa da mamaki ya gama kashe ta tace ke banza ke wacece? Ba zata rama ba ko zaki rama mata ne?" kafin ta sake wani magana taji an kaure da mari kala 2, Miemee ce da k'arfin halin nan, Usheey da Seebi da kowa na gun na mamakin Miemee, Miemee ta nuna ta da yatsa tace "She's my Friend, f**k her up, and i'll f**k u down" Aneesa cikin borinkunya tace "We'll meet again, this is not the end of this, Meesha get my bag" tafita ,Meesha taje ta dauko jakkar ta bi bayan Aneesa. ********* Usheey tace "Seebi me ya hadaku da ita ne?" Seebi na kuka Miemee ta tashi zata bar gurin, Usheey tace "ahh Miemee ina zaki?" tace "i'm giving you two space, ai naga kamar maganan Sirri zakuyi" Seebi ta dago kai idonta sunyi Jaaa tace "wace irin magana kikeyi wannan? Miemee tace " Seriously? Ai naga sirri kuke tayi tun dazun, kuna magana K'asa k'asa, ba kwa so in ji maganar da kukeyi, to tell you the truth it really hurts me, yanda na dauke ku ba haka kuka dauke ni ba, nice me bakin Reza, da idan abu ya sameni na Sharri ko na Alheri ku nake fara sanarmawa, because i love you two like my sisters, Amma ku kwatakwata ba haka kuka daukeni ba, a ganin ku ni ballagaza ce, da naji zanje fesa ma mutane, i'm not worth sharing your secrets, kuna wareni a cikin ku, ai gwara in fidda kaina" zata wuce Seebi da Usheey sukayi saurin kamota, Usheey tace "haba Miemee is not like that wallahi, ba abun da kike tunani bane, kin tsargu ne kawai, dazun cikin aji nine ma ke bata labarin Usman(Saurayin Usheey) kuma kinsan da labarin, kuma abunda ya sa muke magana a hankali kar Mallam ya fitar da mu yace mun isheshi da surutu, yanzu kuma a CAF ne ta fara bani labarin, tace a bari sai kinzo nice na matsa mata coz i'm eager to hear, nace idan kin dawo sai ta sake baki labarin" Seebi tace " I am sorry Miemee Wallahi ba haka bane, abunda Usheey ta fada gaskia ne, Wallahi i love you both equally, kiyi hakuri please don't think otherwise" Miemee ta kalli bestfriends dinta, ta amince ba k'arya suke mata ba, don ta yarda dasu tayi murmushi tace "Group Hug" suka rungune juna su 3. Nasiba ta sa hannu cikin jakkarta ta ciro wayarta Iphone Ta daga musu sama a tare sukace "Nooo way" tace "Yes wayy" Miemee ta amsa tana Omg, this is real Wallahi Iphone dince" suka ta Daria, Seebi tace " da kayan jikina da wayar nan, Uncle Zaid ya bani su" Miemee tace "Uncle Zaid?" Seebi tayi daria tace "wannan da kika ma lak'abi da Azababbe, shine wannan da kika zauna gaban motarshi randa mukayi lectures 4-6, randa mukayi trekking har bakin gate, wanda kikace ya hadu Sosai, wanda ya fara kaiki gida Kafin ya kaimu namu gidan" Miemee ta katse da murna tace "ya isa Seebi, na ganeshi wallahi ko ba me waya ta AUX ba? Kuma shine ya kawo ki School? Babe whata are you hiding? Ki fada mana Please" tayi daria tace "to kunji kunji......" ta gaya musu komai tsakaninta da Lema Family Amma banda Mafarkanta. Sun tausaya ma Rafeeq matuk'a amma Miemee ta ta6e baki, tace "Poor R-Lema, He's lost, but thats no reason da zai dinga treating mutane asif they are trash or something" Seebi ta Usheey suka hada baki sukace "kina da Damuwaaaaa" daria sukayi duka, Usheey tace "Seebi, gaya min kinason Uncle Zaid ko?" tace "Wallahi i dont know nidai nasan kawai ina ganin girman shi" Miemee tace "Shegs kina so,lemme lecture you on how to keep a boyfriend" Seebi tayi daria ta dauki jikarta tace ku tashi mu tafi gida, kunsa munyi missing lectures ba gaira ba dalili, saura 15mins a gama kun ga kuwa zuwan mu be da amfani" Usheey tace "ba Sallah ba salati, labarin ne kamar kar ya k'are kamar a film, saukin ma dai munci Abinci" Miemee tace mu biya Central Mosque muyi Sallah, in munci Sa'a mu samu bus muna fitowa" haka Miemee ta biya musu Plate dinsu 600duka don cikin su 3, ta fi su hali, suka bar CAF. ******** "Lahh ga motar R-Lema da alamu yana cikin Massalacin nan" Miemee tace sai me? Ga bus nan kuzo mu shiga kafin a ciketa, Seebi tace "Aa, mu jira ya fito, kinsan ko ganin mu yayi anan bazai barmu ba, gwara mu jirashi" Usheey, tace "Ni wallahi nagaji kafin mu isa Bus ta jigata mu" Miemee tace banson raini wallahi, duk me ya mana yau kuka ja mana, Nasiba tayi daria tace naji na yarda, wurin motar suka tsaya, sai ko gashi kamar an jefo shi yana tafiar nan nashi cikin isa, kallo daya ya musu ya dauke kai, a ranshi yace "Wannan ta kile yau ita ne da Veil, tayi kyau" chan kuma yayi tsaki yace "sha its none of my Bussiness" ya bude motarshi ya zauna, shi be tafi ba shi be basu damar shiga ba, Seebi tayi Jihadi tace mu shiga, suka bude suka shiga, tace "Hamma ina wuni" kamar ba zai amsa ba yace "lafiya" Usheey tace Ina wuni yace "Sannu fah" Miemee kuwa ta dauke kai duk abun Miemee bata san Raini da wulakanci, bata fiye hakuri ba(waya ga Diyar Aminene Mamman) Shi be ma lura da ita ba ya ja motarshi ya bar School, duk suka kasa magana sai gudu yake tayi dasu, ya bi ta Ringroad, kamar ya rufe bakin su duk sukayi shiru, sai gasu sun bullo ta Salamah, har ya wuce k'ofar Gidan Nene zai yi kwanar Gidan Lema Nasiba tayi saurin cewa "Hamma zamu sauka a nan" "Oops na manta" ta k'irkiro murmushi tace "bakomai" yayi parking suka fita, Miemee ta cika tayi pam, tace "Wallahi Gayen nan dan rainin hankali ne, abun nashi wallahi harda Iskanci" Usheey tayi daria tace mu ai munzo gida, muje ki samu Napep, Seebi tace "ai tunda tazo nan sai ta shiga ta gaida Nene, kuma taga Daughter na" suka sa Shewa, suka nufa Gidan Nene. Nene na ta dirka ma Ayman Kokon da rage dazun da safe, tana ganin Seebi ta mik'e ta mata Oyoyo, duk sai ta burgesu, Seebi ta daga ta sama Oyoyo my baby" Ahh su Miemee 'yar gayu, da Usheshe, sannun ku, shigo ku zauna, A'ah Nene mu gaisa wucewa ma dai zamuyi, nan suka gaisa, sukayi Ayman tazo gunsu ta mak'e ta lafe gun Seebi, Seebi tace Nene bari in rakasu, sai da suka tsaida ma Miemee Napep, sannan ta raka Usheey gida kafin ta gangaro gida. **** Daga Nesa Aneesa ta hango Nasiba rungume da baby, tace "Ohh dama nan Unguwar kike? Matsiyaciya aiko zaki ci Ubanki, ta dinga bin bayanta a hankali a motar ta, har taga Nasiba ta shiga wani gida, Aneesa tace a ranta ban minti 10 yanzu zan dawo gareki" kuma in dai idonta be gaya mata k'arya ba, to tabbas diyar Zaid ce a hannun Seebi, tace "Bala'in chan" Nasiba na shiga ta zauna kusa da Nene, ta na tambayarta abunda Ayman taci, Nene tace "Baban ta be dade da maido ta ba, yanzu taga ina shan kwakwo naga ta na kallo na, ko da na bata sha take tayi, mik'ota ta shanye kingin" Kafin Nasiba tace wani abu taji Sallamar shi, da Mamaki ta dago ta kalle shi, tace "Hamma" be kula ta ba ya kalli Nene da ke dirka ma Ayman Koko yayi cukun cukun da fuska, ya danyi tsaki yace "Neh-neh, meye wannan take sha?" ta kalleshi tace "Ahh Neh-neh Naji kace? Wai kai in tambayeka komai sai ka fade shi da turanci ne? Nenen ma sai ka fade Shi da boko? To nidai ba sunana NehNeh ba, in ka koyi kiran sunana Sai kazo in baka Amsa" yayi dan guntun tsaki tace "Tsukakke" ya kalli Nasiba yace "Meye take bata?" tayi murmushi tace "Kokko Ne" "shine ya bata mata baki haka?" ya sake dan guntun tsakin yace "Zanci Indomie and Egg" jiki na rawa tace "Bari in dafa maka" tayi saurin shiga kicin ya zauna kan kujera yana mik'a ma Ayman hannu yana cewa "Come here Angel, hamma is here" Ayman ta mak'e kafada alamun Aa, aiko Nene ta fashe da daria, tana ma R-Lema gwalo, daria ta bashi, gudun kar yayi daria gaban Nene ya sa shi dauke kai. ****** Ta dibar ma Ayman a dan bowl ta zuba ma Rafeeq a plate ta tsiyayo mai Ruwanshi ta kawo mai, "Thanks" yace yace "Nene in zubo miki? nene tace ni rabani da Indonie dinnan, zan shi waina na nan anjima, Nasiba ta zauna tana ci tana ba Ayman A baki, Bam Sukaji an bugo k'ofa da k'arfi, Nene tace "oh Allah, Iska ne haka? Allah na tuba nidai kar k'ofata ta 6alle Kafin wani ya sake magana sai ga Saude ta shigo gidan tana ma gidan kallon wulakanci, ta chakare dankwali gaban goshi, hannunta kan k'ugu, Meema da Aneesa na bin bayanta, ashe Aneesa taje ta gaya musu k'arya da gaskia, Nene tayi saurin mik'ewa shi ko Rafeeq tunda ya musu kallo daya ya dauke kai ya cigaba da cin Abincin shi, Nasiba tuni ta fara kyarma, Aneesa tace "Ya Rafeeq me kakeyi a nan?" kallo bata ishe shi ba, Saude ta kalli Nene galala tace ke tsohuwa, nazo in ja ma wannan kilakin kunne, amma tunda gaki to gwara in miki sai ki ja mata kunnen da kyau, Wannan karamar kilakin na bibiyar Mijina, tana bibiyar k'anin mijina, Kuma tana bibiyar dan mijina don ga zahiri nan, ta nuna Rafeeq, har ta isa ta daga hannu ta mari diyata? Ta sa k'awayenta su mata duka? Wannan 'yar iskar har ta isa? Meema ta chafe "ni ai kamar na so in gane wannan tsohuwar, Anee ba ita bace ta taba tsaida mu a hanya ta bamu waya ko mu kira mata Uban wa? Matsiyaciya, Asiri suke ma mutane dube Rafeeq da be ko kallon pampon gida ya zage ya bude ciki yana cin Abinci, dubi kayan jikin ta komi irin na Anee, Asiri suka ma UncleZee ya siyo mata irin shi, banzaye matsafa kawai. Har yanzu jikin Seebi be bar rawa ba, Nene ko sai dai ta bi wannan da kallo ta bi wannan da ido, sai da ta gama karance su tsaf. "Ke Aneesa dauko Ayman mu ta fi gida, idan na k'ara minti 1 anan zan iya sik'ewa don nan ko gidan Karena Albarka" Aneesa ta dauki Ayman, Ayman ta 6are baki, sai a sannan Rafeeq ya dago, da rinannun Idanunshi yace "Let her Go" be san meyasa ya kasa tanka su Saude da suke cin Zarafin su Nene ba, "Saboda mene Rafeeq?, mune fa dolen ku, baku da kowa, mune yanuwanku ba su ba, You are not related by any chance" cikin tsawa yace "I said let her go" da sauri Aneesa ta direta, ta tattaka ta nufa Nasiba ita kuwa ta kasa daukarta, don gudun abunda zai dawo, Rafeeq yace "duk abunda zakuyi ko zakuce kuce, but dont you dare touch this Soul" Saude ta kalle su ta watsar tace "ku taho mu tafi, tsayuwan mu nan is useless, ke dai Na gaya miki ki jama jikar ki ne ko diyarki kunne, in ko ba haka ba to sai zaman Katsina ya gagareki" Nene tayi murmushi tace "nidai tambaya daya zan muku, donAllah kune kuka taran ma Nasiba jiya da daddare?" Aneesa cike da Rashin kunya tace "Eh mune, yanzu ma ba ita ba har ke sai mu taran mawa" Nene tayi daria tace "Alhamdulilah MashaAllah dama amsar da nike son ji kenan" ta kwance dankwalin kanta ta daura a kai, ta kalli Nasiba tace ke dauki Aymana ku shige daki kar ki sake ki fito, Nasiba ta san Nene ba Alkhairi zatyi ba tace "Nene DonAllah--" Nene tayi saurin katse ta da cewa "dan Ubanki ku shige daki nace ko, zaki dauketa ko sai na fara da ke? Jiki na rawa ta dauki Ayman ta shige daki, Meema tace " What is she trying to do" Aneesa tace 3 against 1" sukayi daria duka.Nene ta k'ulu ga turanci sun yi, sun k'ara da6awa ta kalli Saude tace " Uwarki ce Ogan kilakai, cikin dakin kwarto ta mutu, ke kuma randa na baki waya nace ki kira min, ai baki tsaya kinji wanda nace ki kiramin ba, Ubanki nake so ki kiramin a lokacin, cikin ku wa ya fara taba fatar Seebi? Saude da ta gama harzuk'a da zagin da tsohuwar nan ke musu tace "Nice nan" bata ankara ba taji Nene ta buggan mata Baki, bata ankara ba taji Alamun gishiri gishiri a baki Aneesa tace "Laaaah Jini? Kika fidar ma Mom dina Jini? Tayo kan Nene gadan gadan, nene ta kwashe ta da Mari, Marin da ta ga Stars na walkiya, tace "ga Marin Da kika ma Nasiba,Yo ni Allah na tuba Ai Ba Uban da ya isa ya sa Zaman Katsina ta gagareni, naci uwarki in baki hana zaman katsina gagarata ba" Rafeeq yayi murmushi yace "Interesting! Thats what i'm talking about" ya kwashe plate da cup dinshi ya kai kitchen, ya fito yana daria yace dasu "You all can leave while you still can, this the only opportunity you have, is now or never" Saude ta dago ta kalleshi cikin masifa tace "I never back down from a fight, this woman will regret doing this to us" Rafeeq yayi murmushin mugunta yace "in that case, i'll sit back and Watch" Nene tace "Uban me kake ce musu? Yayi Daria yace "ce musu nayi su fita shine tace wai ba zasu fita ba sai sun koya miki hankali, wani abu ma da tace ba zan iya fada miki ba saboda yayi nauyi da yawa" Nene tace "kayi wa Allah ka gaya min? Girgiza kai yayi, Nasiba daga ciki take cewa "Hamma stop, its not funny" Nene kuwa cewa tayi ''in kika fito sai kinci ubanki Nasiba" ta damk'o wuyan Saude ta chusa ta a hammata, ta matse, Meema tayo kanta,Nene ta wurga Saude kamar kayan wanki Saude ta buge da bango, Nene ta ci nasarar damk'o gashin dokin Meema ta dinga ja, Meema sai ihu takeyi, Nene ba ta bar Meema ba sai da tsinka kitso daya, kan Meema sai jini itama ta yadata k'asa, ta cicibo Aneesa da har yanzu bata gama kukan marin da ta sha ba, Nene ta buge bakinta tace ke me bakin rashin kunya ko? Ni kikeyi wa turanci? ta waiga ta hangotayizar da ta dauko jiya don dukkan Rafeeq, ta waiga taga Rafeeq na darian mugunta harda rik'e ciki, tace "kai dunkum mik'on Chazar chan" da sauri ya dauko ya mik'o mata, ta dinga shauda ma Aneesa, Aneesa na ta ihu, Saude ta taso don cetar diyarta ita ma bata tsira ba, Nene ta hau shauda mata itama, Meema kuwa lafe wa tayi chan baya, dafe da kanta, Saude Ihu, Aneesa Ihu, Rafeeq Daria harda Hawaye, jin Alamun zaa shigo yasa tace "kai dunkum maza kaje ka rufo gidan nan" Rafeeq harda tuntube gun fita don tsabar dariya, nan suka ci Karo da Zaid, cikin tashin hankali yace "Feeq ihun me nakeji haka?" Rafeeq daria ya hana shi magana sai nuna baya yake tayi, Zaid ya shiga da sauri, ganin Nene na laftar Saude, Aneesa da Meema kamar Allah ya aikota ya sa shi cewa "SubhanAllah, Nene me zan gani haka?" ba ta fasa laftar su ba tace "Wallahi Zaidu bawan Allah ka matso gurin nan sai na Lafta maka kaima". (Toufa Readers, shin Hankalin Nene Daya?) _Bibilicious Biebee,_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀      NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg5⃣0⃣ Zaid ya daga hannun shi alamun ban hak'uri, yace "Nenen mu DonAllah kiyi hak'uri" Inaaa sam Nene Hankalin ta yayi nisa ta ba ta jin abun da Zaid ke cewa, haka ta cigaba da kilar su, Zaid yayi saurin cewa "Nene kin ta6a cewa idan ina son wani abu a gunki, kar inya shakkan sanar dake, ko menene zakiyi min shi, in har befi karfin ki ba, Nene wannan ne abu na farko da na fara tambayanki Nene DonAllah, ki bar su haka, kiyi hakuri, sun ladabtu, na tabbatar ko me suka miki sun gane kurensu" Kallon Zaid tayi tana nazarin shi, chan kuma sai ta yada Chazar tace "Wallahi, sunci darajar ka, kai kadai ka isa ka hanani wlh, don ko Mamman ya dawo duniya yanzu sai mun kai ruwa rana kafin zan hakura wallahi" Zaid yayi murmushi yace "Nagode Sosai" Saude ta tashi tana kakkabe jikinta, Aneesa da Meema ba su bar gurnanin kuka ba Saude ta tuna cewa ba abunda Tsofin mutane ke tsoro kamar Yan sanda, tace "Wallahi Yan sanda zan kawo miki, sai kinyi nadamar ta6a Lafiyar jikin mu" aiko Nene ta tunzura tace "YanSanda? Naciii uwar Yan sanda, naci uwar hukumar jami'an tsaro dukkansu, Kinci uwarki idan baki dauko mun 'yan sanda ba, ke bari ma in k'ara laftar ku yanda zaki dauko mun su da hujja" ai ko Nene ta wawuro chazar ta, haba zo kuga relay tsakanin Miemee Saude da Aneesa, har suna tura junansu ko wannen su na rigerigen fita daga gidan Nene, a wannan karon ba Rafeeq ba hatta Zaid sai da ya dara. Nene tace "kina iya fitowa me tsoro kamar farar kura" Simi simi Seebi ta fito daga dakin rungume da Ayman da ta ci kuka ya gaji, Rafeeq yayi k'okarin amsarta Ayman tak'i yarda sai dai Babanta ya amsheta ya sakata kan kafada, don yau taga tashin hankalin da bata taba ganin irinshi ba. Zaid ya nisa yace "Wai me ya faru ne? Me ya kawo su Meema gidan nan?" Nene tayi charap kamar jira take ta shiga karanto ma Zaid abubuwan da suka faru tun bayan shigowar su Aneesa, ran Zaid ya 6aci matuk'a sai ya fi ganin laifin Rafeeq cikin 6acin rai yace da Rafeeq "why didnt you stop them da suka fara zagin Nene? Meyasa baka hana su ba? Kamar bazai amsa shi ba, sai dai ya daure yace "Saboda i know she'd handle them in her ways, which she did" ran Zaid ya 6aci zai sake magana Rafeeq yayi saurin cewa "Look Uncle i tried to warn them, i even told them to leave, but they didnt want to listen so i let them be, ko ba haka ba Neh-neh?" kamar ta san me ake cewa tace "Hakane Zaidu Bawan Allah" nan Zaid ya dai bata hak'uri ya ba Nasiba Hakuri, ya kalli Rafeeq ya galla mai harara shi kuwa ya dauke ido yayi kamar be ganshi ba, Nene tace "ka bar hararan shi, ai ni yau Dunkum ya burgeni, kasan shi ya mik'o min Chazar, kuma ya fassara min abunda suka ce" Rafeeq yayi dan guntun tsaki kamar ba shi ya gama daria dazun ba, Nene tace "Su dunkum ashe ana ganin hak'oran ka? Wato kai mugun abu ne abokinka ko? Sai kaga abun mugunta kake daria, ai da nasani da na shafda maka a gadon baya sai kayi darian da kyau" Zaid da Seebi sukayi daria shi kuma ya daure fuska. Saude ta ja Majina tace "Sai na koya ma tsohuwar nan hankali, sai tayi nadamar abun da ta mana, sai zaman katsina ya gagareta, Wallahi sai ta yaba ma Aya zakinta" Meema na matsar k'walla tace "Wallahi Sis, in ke ba kiyi maganinsu ba ni sai nayi, wallahi zan iya kashe su da hannuna, duk tsanar da na ma tsohuwar nan, nafi tsanar Jikarta, na tsanesu, tsanar da ban ta6a ma kowa ba" Aneesa cikin kuka tace "Mommy, make them Suffer" Saude tayi darian mugunta tace "Ku zuba min ido" ta zaro wayarta ta lalubo Numbern tsohon Amininta *Mak'ale*. ************* K'arfe 9:30am ta fito don zuwa makaranta, lectures take dashi karfe 11:00am zata fita da wuri ne don ta samu Abun hawa ta isa da wuri, don tafiar kusan minti 45 ne, sauri takeyi bayan ta gama shirya Ayman tana bacci tace da Nene "Uncle Zaid zai zo ya dauke Ayman, zai kaita gidan Kakanin su Rafeeq (Baba TJ) ta musu yini, in kuma ta yarda ta kwana toh, Nene tace "to shikenan sai yazo kema Allah ya dawo dake Lafiya" har sunyi Sallama Nene tace ba zaki tsaya kici wani abun ba? tace "da naje Makaranta zan siya Panke, na fiso in isa da wuri" ta mata adduar tsari ta fita daga gidan. Kamar daga sama taji horn dinshi ta waigo da sauri ta sakar mai murmushinta, shi kuma kamar ya ga wani kashi ya wani tubune fuska tare ds kawar da kai, bude k'ofa tayi ta shiga, "Hamma Rafeeq Good Morning" tsaki yayi yace "Fine" ya dauke kai, tunda suka hau hanya ba me ma danuwanshi magana, har suka iso makaranta, anan ne tace ya kaita ta bayan Science Theatre, kamar ba zai yi kwanan ba ya sha kwanar da k'arfi har tana bugewa da window, daidai Theatre suka tsaya, ba mutane a gurin, sai jefi jefi ake ganin tsiraran mutane. A ranta tace "Ya Illahi! Gani gareka" me makon ta fita sai ta gyara zamanta ta sa hannu cikin jakkarta ta ciro zoben da Mami ta bata, ta sa a yatsar ta na kusa da k'arami, ta gefen ido ya ke kallon duk abunda takeyi, ta wutsiyar ido ya k'are ma Zoben kallo, wani abu ya ji game da zoben, da sauri ya juyo gareta inda take wasa da yatsunta tana juya zoben a yatsar ta, Mukut! Ya hadiye miyau, ya kalli yatsan hannun shi yaga Irin Zoben ne, ya sake kallon na hannunta, sai da ta lura da ya tantance kafin ta bude k'ofar tace "Hamma sai anjima nagode" har ta sa kai zata fita ta tsinkayi muryanshi inda yayi guntun tsaki yace "Nace ba?" murmushi tayi kafin ta dakata tace "ya kace?" Sai kuma yayi nadamar tsaidata to me zai ce mata? Zuciyar shi ta tunzura shi yace "Ina kika samo zoben hannunki? Anzo gurin tace " Auu wannan Zoben yatsa ta? A wonderful woman, with a beautiful heart gave it to me, kasan mene? Ta bani tarihin Zoben, wai her Beloved Son gave it to her ranar Zagayowan haihuwarta randa ta shiga shekaru 40, wai ashe musamman ya je Dubai ya sa akayi mishi Zobe guda biyu, ya kawo mata as her birthday gift, ya sa nashi ya sa mata nata yace da ita '"Mamina, this is my love for you, ya nuna mata na hannun shi yace this is the twin of your ring, even if we are far from eachother, this ring is linked to our Hearts"' Hamma na DonAllah basu burgeka ba? Ya dago ya kalleta, ta kasa gane yanayin da yake ciki, idanun nan sun kada sunyi Jazurrrr, ta firgita har ranta amma sai ta dake ta na karfafa ma kanta guiwa tace "Laaaahhh Hamma kalli Zoben hannunka, kamar nawa, duba ka gani, iri daya ne Wallahi, How is that even possible? A lokacin kuma a ranshi yace "She met Mami" tsigar jijiyoyin jikin shi suka tashi saboda tashin hankali" bata fasa magana ba tace kaima Zoben ka na da dan biyu? Akwai wanda ka ba Zoben ka? K'ila kaima Maminka ka ba" da k'arfi yace "Shutup" a tsorace ta kalleshi tace "Hamma na, are you okay? Did i said something wrong?" cike da nutsuwa yace "Get Out" Tsoro ya gama cikata, ba ta taba ganin ya fusata haka ba, muryar shi ta sae ji cikin karaji ido rufe "I said get out" jiki na rawa ta dauki jakkanta ta bude k'ofa Zata fita sai kuma ta fasa, ta dawo ta kulle k'ofar, jin an kulle kofa ya sa shi bude ido a hankali, ganin ta zaune ya bashi Mamaki daure fuska yayi sosai yace "are you deaf? Dont you understand English again? Okay nace ki fita, ki fita ki Barmin Mota na Kai tsaye tace "bazan fita ba, you have to listen to what i am about to say to you, idan ka ga dama kayi aiki dashi idan ka ga dama ka watsar yabi ta bayan kunne, Rayuwa daya ce, you only get to live once, idan yau ka fadi ka mutu ka san makomar ka? Ni bansan kusancin ka da Ubangijin ka ba, amma yau ka mutu ina kyautata zaton kai dan wuta ne, saboda Me? Saboda kana Fushi da Mahaifiyar ka, baka neman Albarkar ta, kar ka manta akwai hakkinta akan ka, Fushi, duhu, emptiness, loneliness sun cika Zuciyar ka, kai kana tunanin kai ke da kanka, you can get to do whatever you like whenever you please with No Apology, kai komai kayi daidai ne 6acin rai ya hanaka facing reality, abu is very clear amma Zuciyarka ta mutu, ko ince ka kashe Zuciyar ka da kanka, alhali you are a good person with a beautiful heart, amma baka so ka ga hakan, you are forcing yourself to be mean, amma kasan Zuciyarka kai mutumin kirki ne, ga ka da tausayi, da kula, please realize that side of you, da tsawa ya katse ta cikin daga murya yace "Nooo, you think you know me? You know Nothing about me, nkw get out of the Damn Car" itama cikin muryar kuka take cewa "Nace maka ba inda zani, i am not done talking to you, if you dont want to realise your good side, then i'll make you realise them, lokacin da aka kai Nene Asibiti, mesa ka ke kula damu? Abinci safe rana da dare? Me sa kake kaini makaranta? Zuciyar ka me kyau ce amma ka danneta kai a dole ba ka damu da kowa ba, ko kuma ba wannan ba, ka tuna randa kace in fitar maka daga mota, randa zaka kawo ni Makaranta? Randa nake ta maka tsaki? Ka direni a tsakiyar daji? Na san ka tuna, ka tafi me ya dawo da kai? You could'nt leave me there because you care" da sauri yace "No i dont, i was only saving you from your Stupidity, kin tsaya tsakiyar titi kar mota ta bigeki, people would get hurt people like my Uncle Zaid and Maalesh" tace "koma dai meye you care about the people you love, ba dole sai ni ba, dama ai ni ba kowa bace, amma su ka damu da damuwar su, ka kasa barina sabida su, ka ga kuwa wannan shine abunda nake so ka fahimta, you have a beautiful heart" "ke i dont care about anyone, Uncle Zaid is all i care about and maybe Maalesh,i can sacrifice anything for them" ta mai wani kallo tace "really? To tell me, har yanzu me kakeyi da Zoben hannunka? Me kakeyi da danuwa Zoben da ka ba Maminka? Saboda kana sonta, akwai 6angaren zuciyarka da ke sonta, akwai 6angaren zuciyarka da ke son sake ganinta, fushi da bak'ar zucciya suke hanaka, Rafeeq na girgiza kai yace " Ki min Shiruuu please, Ya isheni Nasiba" da sauri ta kallo shi, a iya saninta da shi ko Seebi bata ta6a ji yace ba, amma yau ita yake kira da Naseeba? Ya ilahi, yaba ta tausayi ama dole ta ya gane abunda yake yi ba me kyau bane, tace "kaga matsalar ka ko? Baka son gaskia, da an fara gaya maka gaskia sai ka tsaida mutum, ita gaskia kwara daya ce kuma daci gareta, Listen now, i am going to make this Straight to you, Incase you dont know, Aljannar namiji yana k'asan tafin Mahaifiyar shi, sai ya bita zai samu shiga, sai da Manzon Allah ya kira Uwa so uku kafin ya kira Uba so daya, ko kasan duk wanda ya sa Mahaifiyar sa kuka be ganin daidai? Ka san iyakar hawayen da tayi a kanka? Kasan zunuban da kake kwasa a ranar da tuna da kai ta zubda hawaye? Ya Illahi! i dont have to lecture you on this, kai kasan wannan abun amma fushi ya hanaka ganin hakan, ka ta6a tambayan kanka? Shin yanda nake ma Iyayena musamman Mahaifiya ta ina kyauta wa? Duk abunda ta mun tun ina cikin ciki har girmana ta chanchanci abubuwan da nake mata, kai ko me tayi, She's still your Mother, ko kisan kai tayi, she'll remain your mother, balle something you are not sure of, something no one is sure of, You didnt bother to find the truth, kai an maka laifi, ba wanda ya kuma isa ya ce kayi, ask yourself if this is the way you want your children to treat you when they're grown. Don abun da kayi shi zaai maka wallahi, fiye da ma wanda kayi, dole a maka, If you're not measuring up, it's not too late. You can make a change this very day. Uwa ta fi karfin wasa Wallahi, ka tashi ka fusknaci matsalar ka tun kan dare ya maka, tun kan ka wayi gari ace ba kai ko ita a duniya, Only then zaka higa damuwan da yafi wannan matsi i've said my peace" ta na kuka ta ciro paper da biro tayo rubutu, ta ajiye mai a cinya, tace "gashi this is her address, bance kaje ba, you decide what to do with it, ina so kayi tunani, ka tuna Who is your mother" ta share hawayenta ta bude motar ta fita tabar Rafeeq zaune kamar gunki. Hannu ya sa a kai ya damk'i gashin kanshi, Jijiyar kanshi kamar ta fito, Nan ya soma tunanin halin da ya iske Mami a ciki, sai ya tuno ծaծծaծan lokuttan da sukayi da Mami Daddy and Rafee'ah ad a Family, Ya tuna wacece Mami, abunda be taba yi ba, kanshi ya hau sarawa, ya kusa Minti 30 bayan fitar Nasiba yana hawaye, hawayen da ya rasa na meye, ya kunna motar shi ya fita a guje kamar be shirin tashi Sama" Nasiba ta fito daga maboyarta tace "Allah ka sa yaji, Allah ya tsareka R- Lema". _Malali Kaduna_ Shigowar ta kenan daga Gidan Ummin Anan, ta mik'a musu Coolern Danwake, don yau Danwake tayi, ta kalli agogo taga k'arfe 3:16, tace kaii bari inyi bacci kafin laasar tayi, kan kujera ta dan kishingiծa ji tayi motsin mutum tana dan kallo kofar ta ga Mutun tsaye, jiki na 6ari ta mik'e tsaye, ta kasa yarda da abun da idonta yake gane mata, baki na rawa ta nuna shi da yatsa tace " Rafeeeeeeq" A hankali yace "Mamiiiii" Da sauri ta runtse ido daidia digar hawayenta tana adduar kar ta farka da wannan mafarkin da takeyi, yau Rafeeq ne ke kiranta da Mami? Ba zata so ta ta6a tashi daga barcin nan ba, takowa yayi kusa da ita ya sa hannu ya share mata hawayen da ke zuba a idonta, jin an tabata yasa ta gane ba nafarki bane, a hankali ta bude idon ta fes kan fuskar shi da ta koma ja, girgiza mata kai yayi, da sauri ta rungumeshi tana kuka, "Rafeeq, Rafeeq my Child, Rafeeq ka yafe mini, Rafeeq na hallaka rayuwar ka, Rafeeq ka yafe mini DonAllah" shima kukan yakeyi sosai, kukan da be taba irin shi ba, yace "Mami meyasa? Mami Why? Why? Why?, Mami meyasa zakiyi haka?" ta dago da sauri tace "Wallahi bansani ba, bansani ba Rafeeq, ni nasan banda mafita, Allah kadai ne gatana shi kadai yasan me ya faru a wannan ranar, amma Wallahi bansan komai da ya faru a ranar ba i totally have no idea, please believe me my son" Zuciyar shi ta tambayeshi Wai kai dama tun farko meyasa ka yarda da Mamin ka zata iya aikata abu makamancin hakan, ita da kullum take maku Nasiha kan ku nissanci Zina, wata Zuciyar tace da idonka ka ganta" da sauri ya kawar da tunanin nan, ya sake rungume ta, yace "it doesnt matter anymore, ba zaki iya aikata hakan ba, i was blind to see, we all were blind to see the good in you, but not anymore, I swear on my Dead Sister whoever did this to you will pay" tace "Aa Rafeeq kadaina irin rantsuwar nan, be da amfani, ba kyau, kuma dont let anger have control over you, calm down" Yayi ajiyar Zuciya yace "Mami, whatever i said to you in the past, please forgive me, i dont mean any of it, i was stupid to forget who You are, someone said in har kina fushi dani ba zan taba ganin daidai ba ki yafe min" "Shhhh my baby, ba ka min komai ba, I got you, i always do" ta jawo hannun shi ta zaunar dashi ta dinga shafa hannun shi tana murmushi tana ganin komai kamar mafarki, tace "kasan me na dafa? Ya girgiza kai, tace "Danwake" yaui dariya yace kina son danwake har yanzu? Tace "kai ka koya min danwake" ya tashi yace barin zubo mana ko? Ya shiva kitchen ita kuwa ta dubi gabas tayi sujjada (Sujjudush Shukur) tana me godia ga Allah da ya dawo da danta gareta, saura Baban shi da take adduar Allah ya sa shima ya fuskanci gaskia, Rafeeq ya zubo musu Danwaken ya kawo parlor ya ajiye a kan Carpet, ya rik'o hannun Mami ya zaunar da ita a k'asa ya koma ya dibo mai da yaji a kwano yazo ya zauna, haka suka fara ci yana sa mata a baki tana sa mai a baki, hawayen farinciki sukeyi duka, har dai Rafeeq ya koma lallashin Mamin shi har suka gama, ya kwashe kayan ya shiga daki yayi alwala yayi Azahar ya ja su Jam'i sukayi laasar, nan suka hau labarin duniya. "Allah sarki Nasiba, Nasiba Alheri Ce Rafeeq, Nasiba Alheri ce a garemu duka, ko ba ka fada ba nasan ita ce Silar zuwan ka Kaduna" murmushi kawai Yayi yace "Mami ke ina kika santa? tace "tashi muje gidansu yanzu" yace "aa i want to spend more time with you" tace ba nisa makota ne yanzu zamu dawo, suka nufa Gidansu Nasiba, Daidai shigowar Abbi, Rafeeq na ganinshi yaje ya rungume shi, Abbi ya bubbuga bayanshi, ya ji dadin ganin Rafeeq haka, Lallai in ciwo cuta ce to tabbas addua Magani ce, yace "Jiki yayi kyau Rafeeq, Allah ya sa a dace yayi murmushi" "ina Mutuniyar taka? Nenen ka?" guntun tsaki yayi chan kuma yayi murmushi ya kwashe labarin abun da ya faru jiya ya basu, Dukkansu dariya suke tayi, Abbi ya girgiza kai yace "nace ma Nenen ta daina biyewa yara ta ki ji, ita jinta takeyi kamar yar shekara 15" suka sa daria. Anan yazo ya hau kan Rafeeq, Rafeeq ya daure fuska beson yara, amma ganin idon Abbii da Ummi a kanshi ya sa shi yin yak'en dole, Anan na matukar kama da Nasiba, yace ka san Adda Seebin Nene? Kai kawai Rafeeq ya gyada, to ka tafi dani gurin su" Rafeeq ya mik'e tsaye yace "Idan anyi hutu kaji" ya kalli su yace "Ina so in koma Katsina yanzu" Mami ta zaro ido tace "Feeq 5 saura fa" yace "eh Mami" Abbii yace "da dai ka bari gobe" yace "Gobe zanyi test karfe 8" nan dai suka mai Allah ya tsare hanya, ya ja hannun Mami suka wuce Gida, sun dade suna magana, tace "R-Lema anya ba zaka bari sai gobe? 6 har tayi fa" yace "zan tafi dai, your prayer keeps me moving" bmya rungumeta kafin ya sake ta ya shige mota da sauri don ganin zata fara kuka. Nan ya dauki hanyar Katsina ta bishi da Addua "Rafeeq Allah ya tsare hanya ya kaimin kai lafiya, yasa ka iske su lafiya Amin" _Layout Katsina_ 11:45pm A gajiye likis ya shigo Unguwar, duk ya gama gajia, ya wahala Mota ta tsaya mai gurin Dabai, Unguwar Shiru ba ka ganin kowa waje, abunka da Unguwanin yan gayu kowa na Gidan shi ya kulle, daga nesa ya ke hango hayak'i na tashi kan katangar wani Gida, yace "toufa, wannan hayakin daga ina, ko da ya kusanto gidan sai ya ga Gidan Nene ke ci da wuta, ai be san lokacin da ya fita daga motar ba, Gidan na ta ci da Wuta, ya rasa me zaiyi, da sauri ya dinga kiran wayar Nasiba, tana ringing baa dauka, duk ya bi ya damu, ya nufa k'ofar da niyyar ya bude ya ji wani irin zafi, ya ja da baya, ya fashe da kuka, Uncle Zaid ya fara kira, Zaid be dauka ba a lokacin yana toilet yana wanka, Yayi tsaki cikin kuka ya kira Maalesh, Maalesh ya daga " Guy howfa u never sleep?" cikin rudani yace "Nasiba, gidansu na ci da wuta" "What" inji Maalesh, gani nan zuwa, ya latse wayar, Rafeeq ya dinga kwankwasa ma makotan su Nasiba don suma Katangar ta hau ci da wuta, nan yayi tunanin yan kwana-kwana(Fire fighters), ai kafin ya samu taimako daga Makota k'ila gidan ya k'one kurmus, hannu na rawa ya latsa numbern Daddyn shi" a lokacin yana kwance ba dai bacci yakeyi ba, yana tunanin Wani abu ne da be san meye ba, ya ga kiran Rafeeq, ya daga da Mamaki "Ibn Zaid ya akayi da daren nan haka?" baki na rawa cikin kuka yace "Daddy, Daddy" Ya tashi a firgice yace "What isit son? Calm down and Talk to me" da k'yar yace "its Nasiba and Neh-Neh" zumbur Daddy ya mik'e yace "me ya samesu?" gidan su na ci da wuta, Daddy bansan me zanyi ba" Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Stay still son gani nan zuwa, i'll make some phone calls" ya tashi ya zumbura malummalum dinshi kan dogon wandon da ke jikinshi, ya dialo numbern shugaban Fire Fughters ya sanar dashi komai suka bashi tabbacin yanzu zaa su fito don ceton su" Zaid ya kira Rafeeq bayan ya fito daga wanka, amma Rafeeq be dauka ba, a lokacin makocin su ya bude gida ya fito da yaranshi maza sun fara zuba ma Gidan Nene ruwa, amma kamar ana k'ara rura wutan, Maalesh ya kira Zaid ya sanar dashi, hankali tashe ya bar Hotel din ya nufo gidan Nene, a tare yan Fire fighters da Daddy suka iso, sai Maalesh, Rafeeq ya rasa sukuni, tuni Yan kwanakwana suka kuna injin suka kashe wutan Gidan Nene, Hankalin su a Tashe, Rafeeq ya dinga bubbuga gidan Nene amma ba alamun akwai me rai a ciki, Da K'arfi yace duk sun mutu kamar wani zautace, Maalesh cike da tashin hankali yace "Noo ba su mutu ba, we just need to get in" Rafeeq ya kalli yan kwanakwanan yace "Someone should break the Goddam Door" sai ya fashe da kuka, Zaid na fitowa daga motar ya nufo su, Rafeeq na ganinshi ya rungume shi, Zaid ya dinga bubbuga bayanshi yana kiran they'll be fine, Rafeeq yace "Noo Uncle, i cant loose them both, i cant" Daddy ya taba bayan Rafeeq yace "Rafeeq ka gani an 6alla kofar, yanzu zasu firdosu a kai su Asibiti, InshaAllah they are going to be fine" Rafeeq ya waiga ya ga Jamian sun 6alla k'ofar a sittin ya ruga gidan ana rirrikeshi yana fizgewa ya kutsa kai ciki, Zaid bi bayanshi Daddy da Maalesh suka rikeshi, Zaid cikin tashin hankali yace "No he cant get in there be da facial mask, Rafeeq ka fito please" Attishawa ya fara yi amma be fasa kutsa kai ba, ko da ya isa har ya ga sun dauke Nene kan Gadon marasa lafia sun saka mata Oxygen zasuyi waje da ita, sauran kuma suka nufa Nasiba, bangaje su yayi ya nufe ta yana Attisahawa da Tari ya Ciccibi Nasiba kamar jinjira, ba alamun numfashi a tattare da ita, fadi yake "Hey hang in there, i cannot loose you too, i lost Rafee'ah" kamar mahaukaci yake sunbatu ya fita da ita, be tsaya ko ina ba sai motar shi, baya ya sakata, ya shiga ya ja Motar, Maalesh na kwala mai kira amma ina sam baya ji, Officer yace da Daddy "ku tsayar dashi, she needs First Aid, Oxygen zamu saka mata, she needs it now, Daddy yace i'm sure Asibiti zai kaita" Officer yace "i'm afraid kafin a kaita Asibiti maybe ta mutu". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Kin chanchanci Yabo a guna Masoyiyar Asali, Wannan page din naki ne Ag😘 Pg5⃣1⃣ Yana tuk'i yana kallon bayanshi hawaye na zuba, sambatu yakeyi, "DonAllah kar ki tafi ki barni, Rafee'ah ta yafi, kema kar ki tafi, bansan me zanyi ba in kika mutu, Ya Allah kar ka dauki ranta, Allah ka dauki nawa instead" ireiren maganganun da Rafeeq keyi kenan, Sanyi ACn Motar ya sa Nasiba farfadowa, tari ta hauyi ai da sauri ya juya ya kalleta, wani murmushin da be san lokacin da ta subulo ba ya sake tare da taka birki ya tsaida motar, fita yayi ya koma baya, hannunta ya rik'o Yace "Naseebah, Naseeba are you Ok?" tari ta shiga yi ba sassautawa ta zame hannunta daga nashi tace "I'm fine, ina Nene?" yace "Tana chan gurinsu Uncle Zaid" Nasiba ta shiga tuno abunda ya faru tiryan tiryan, tace "Hamma mu koma donAllah, Nene na chan ban san halim da take ciki ba" yace"karki damu nasan Asibiti zasu kawota, right now i need to take you to a hospital" tace "please mu koma, i'm fine now, i just need Water" da sauri ya dauko mata ruwa a gaban Seat, ya bude ya bata ta kwankwada" cikin sigar lallashi yace "Listen to me, zan kaiki Asibiti a duba ki, Neh-neh kuma is in safe hands, barin kira su in gaya musu kin farfado mu hade a Asibitin" Maalesh ya kira, "Maalesh kuna Ina?" cikin damuwa yace gata nan zamuzo "Alheri Clinic don ya fi kusa" "bata farfado ba?" Wallahi kuwa feeq, gatanan ko numfashi batayi" Rafeeq ya cije hak'oranshi, yace mu hade Asibitin ni na kusa ma" sukayi Sallama, Seebi tace ya jikin Nenen? Rafeeq ya fita ya koma matukin direba tare da cewa "gata nan zasu kawo ta wanchan Asibitin". ***** Daidai isowar Ambulance, aka fito da Nene aka shiga da ita ciki already Daddy ya kira Dr aka yi da Nene Emergency, da kyar aka samu suka tsaya daga waje,Seebi kuwa ta k'i yarda a bata gado acewarta ba inda ke mata ciwo, Dr's suka buga nan suka ta6a nan ba alamun Nene Zata motsa suka dukufa da aikinsu a matsayinsu na Kwararrun likitoci. Bayan 'yan mintoci Likitoci suka fito fuskar su ba Annuri. Dr Sami yace "i'm so sorry, we couldnt save her" luuuuu Nasiba ta zame k'asa ta zauna dabas, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun inji Daddy, Zaid Ya dora hanayensa duka biyu akai, Maalesh ya fara matsar kwallah, Wtf? Inji Rafeeq, ya chakume shi, what do You mean by you couldnt, save her huh? Dr Umar yace "kuyi hakuri, kamar tana da Athma, kuma ta shaki hayak'in Sosai, kuyi hakuri Addua kadai take buk'ata" Bangaje shi yayi ya shiga dakin duk suka biyo bayanshi banda Nasiban da Hawaye ke ambaliya a fuskarta, Nene ta rasu? Nenenta? Inalillahi, Nan da nan ta chanza kammanni sabida kuka, tausayi Mahaifinta da Goggonta da ke Jigawa ya kamata, suna mugun son Nene (kamar yanda Iyalan Zailani keson Tsoho, lols) kuka takeyi sosai me hade da Sheshek'a, ta kasa yarda da Nene ta Rasu. Rayuwar da sukayi ya fara dawo mata, ta mik'e Zumbur ta shiga dakin. Kwance ta ga Nene an rufeta da zanin Gado, Uncle Zaid ta fara kallo, har yanzu be sauke hannunshi daga kansa ba, yana kuka mara sauti, Alhaji habib be daina Salallami ba, Maalesh na kuka, Rafeeq na kwance kan jikin Gawar Nene yana kuka, Neh-Neh DonAllah ki tashi, DonAllah, Neh-neh kin zama wani Jigo a cikin Rayuwata, na k'i yarda kin mutu, in kika mutu bansan ta yanda Zan cigaba da Rayuwa ba ke a cikinta, Neh-Neh Ina sonki, ki tashi na yarda ki cigaba da cemin Dunkum, zan amsa sunan, ba zan k'ara miki tsaki ba, zan dinga shan Maganin nan, zanyi duk abunda kikeso, DonAllah ki tashi, Allah kar ka kashe min Neh-neh nah, Allah ka tada min ita I love you Neh-Neh. wani kukan me tsuma rai Nasiba ta fashe dashi, duk sun tausaya ma Rafeeq, Wai dagaske Nene ta Rasu? Shikenan ba Nene? Numfashinta taji ya kusa daukewa itama. "kai ni Dallah daga ni,ka wani danne min kahon Zucciya, ko sai ka k'ara sani?" da mamaki ya dago ya kalleta yace"Neh-Neh??" tana yunkurin tashi Maalesh yayi saurin taimaka mata ya zaunar da ita, murna gun Rafeeq baa magana ya subuce da dariar murna "ku Bata mutu ba Wallahi bata mutu ba" Sujjudushukur Nasiba da Uncle zaid sukayi don godewa Allah, Alhaji Habib ya fita don kiran likita yana hamdala, daya bayan daya ta bi su da ido tace "wai ya? Ko cema ku akayi na mutu ne da kuke ta wannan abun? Dr Sami da Dr Umar suka shigo da mamaki, sun tabbatar da zuciyarta bata bugu kafin suka sanar da Yanuwanta, to ya akayi haka? Ikon Allah ne, Dr Sami ya soma dube dube a jikin Nene, Yace "Blood of Jesus has healed her, she is a strong fighter" Nene ta katse shi tace "wai gwajegwajen nan na meye? Kalau fa nike, zaka zo ka tasani gaba kana man turanci, Daga gani kai kace musu na mutu, haka kurun ka tada wa 'yan jikokina hankali" duk sai da sukayi Daria banda Rafeeq da ya daure fuska wai ba abun daria bane(ikon Allah ku ji min Rafeeq da ya gama fita hayyacinshi don ance ta Mutu) Dr Sami ya kalli abokin aikinshi yace "Dr Umar what is she saying?" Dr Umar yace "Shes thanking God that Shes still Alive, go to the Office i'll take it from here" Dr Sami ya fita daga Ofishin. Ya kalleta da Murmushi yace "Sannu Mama, kiyi hakuri dogon Suma ne kikayi, Wallahi mun dade a kanki, Duk wata kafa ta sadarwa ta tsaya a jikin ki, saida muka samu tabbacin hakan kafin muka sanar dasu" tace "da kuka tabbatar kaine a zaune yanzu? Nace kaine a zaune? Toh ban mutu ba, bawai tsoron mutuwar nike ba, ku dai san aikin ku, ku san me zaku dinga fada ma mutane, yanzu da bakin labarinku ya sa Zuciyar Jikata bugawa ta shek'a lahira fa? Ni na mik'e ita ta mutu to me akayi kenan? Anyi ba ayi ba, ana muku kirari da likita bokon turai, to bokon kashi dai tunda ba ku san aikinku ba" nan ya shiga bata hak'uri tace su zaka ba hakuri, sai in yafe maka" yayi murmushi yace da su "Daddy suyi hakuri" murmushi sukayi sukace bakomai. Bayan nan aka fara diramar sama Nene Drip tace kwatakwata ita bata san Zancen ba sai dai a sallameta, Seebi tace "Wai Nene ki tsaya mana a sa miki drip din" tace "naki, ke ki zo a saka miki" Rafeeq ya daure fuska, "Uncle Zaid please talk to this Stubborn Old Woman" yayi daria yazo yace "Nenenmu kiyi hak'uri ki bari a saka miki drip din, kinga ko an sallameku yanzu ba inda zaku zauna a gidan don kusan komi ya k'one, da lallashi da lalama Nene ta yarda aka sa mata drip din. "*** A dan tsorace Rafeeq yace "Ku tsaya ku tsaya? Ku tsaya! Ina Ayman? Nene tace sai yanzu ka tuna da ita? To kar ka damu tana gun Kakar ka, dazun Baban ta ya kaita kwana, ashe Soyayyar k'arya ake mata tunda sai da aka Neh-neh ta watsake aka tuna da ita, Rafeeq ya murtuk'e fuska, Zaid yace "kaii Nene, kinsan in ka rude abun da ke gabanka kawai kake gani, amma ba me tantaman Soyayyar Rafeeq ga Ayman, Nene tace sai ni don ya fi so na, yau naga tashin hankalin su O'eh, Maalesh yace "a fadi suna mana", tace "da Dunkum nike ai yasan dashi nike, tashin hankali yau Su dunkum har da su i lobi me Neh-neh, to nima i lobi you Dunkumeh, ai na rok'i Allah kar ya kasheni sai ya nuna mana auren mu" Alhaji Habib na daria yace "Aurenku ke dawa? Tace "yo ni da Dunkum mana, ai sai na Auri Dunkum" Duk suka fashe da Daria banda Rafeeq da ya hada gabas da Yamma kamar be ta6a daria ba. "You cant sleep with them you know?" Cewar Maalesh, "Why cant i?" inji Rafeeq, Daddy yacei "Aa Rafeeq gida zamu tafi, ga Nasiba nan she cant look after her" yace "She's not well too, itama she needs someone to look after her" "Aa Hamma i can, i'm fine ba abunda ke damuna" Rafeeq yace "Shuttup you are not fine" Zaid yace "IkonAllah" Rafeeq be sake magana ba ya zaro wayar shi daga Aljihu ya latsa waya, ringing biyu ta dauka cikin magagin Bacci "Hello Mom" Mom din Maalesh tace "Son ya akayi ne da daren nan?" "sorry na tadaki, Hajjo fah?" ta kalli Agogon gefen gadonta tace for goodness Sake Rafeeq shes Sleeping, baka duba agogon bane kafin ka kira, this is 12:15am, guntun tsaki yayi yace "sorry mom, but you need to wake her up, an sake kwantar da Neh-neh kla Asibiti Maalesh yanzu zaizo daukanta, thanks Mom Love you bye" be jira ta amsa ba ya kashe wayan tare da kallon Maalesh, Maalesh kaje ka dauko Hajjo, Dad Uncle Zai ku tafi gida, I'll be here har sai Hajjo tazo". Kamar Shine Babba duk sukace Okay Maalesh ya fara tafiya, Kafin su Daddy, dama Nene Already tana bacci. A waje Daddy ke cema Uncle Zaid Rafeeq ya damu sosai, damuwar da yayi kan Nene da Seebi ya ban Mamaki, Zaid yace "ba wani abu bane kawai dai ya girgiza da Gobaran nan, na san Mutuwar Rafee'ah ta dawo mai Sabuwa, ya zata zai sake wani rashin ne, don kasan Ya dauki Nasiba kamar 'yaruwarshi, kuma duk da ba sa shiri da Nene, yana sonta Sosai" Daddy ya jinjina kai. A lokacin Zaid ke ba Daddy labarin abun da ya faru tsakanin Saude da Nene, yace " tohh abunda ya faru kenan, dazun naga bakinta ya kumbura da na tambayeta sai cewa tayi a tayi da bango ashe da walakin goro a miya, ta san basu kyauta ba shiyasa bata gaya mim abun da ya faru ba, bakomai Nenen tayi daidia" sukayi daria. ***** "Ya ki ke jin kanki yanzu, akwai abunda ke miki ciwo, ko yake damunki?" tayi murmushi tana mamakin wannan hali na Rafeeq, lokaci daya zai nuna damuwarshi kan abu, a wani lokacin kuma sai ya nuna shi be da damuwa ko kadan, kamar yanzu ne, yanda yake tambayar ta kamar ance sai ya tambayaeta dole, tace "Ba abunda ke damuna Kar ka damu" a takaice yace "ban damu ba" tayi murmushi tace "Liar, ka tabbata baka damu ba?" ya mata shiru, itama tayi shirun chan sai yace "Naje Kaduna" da sauri ta kalleshi, "da gaske kaje Kaduna?" be amsata ba yace "Anan yace in gaidaki, Murmushi me sauti tayi sannan ta fara hawayen farinciki, yace "Maminki na gaida ki, wai ku maida mata Babynta haka, she's missing her enough" dariyan farinciki ta fara tana Hamdala, tace " Thank you Hamma Rafeeq" a ranshi yace "meyasa take min Godia?" ta sake cewa "I'm proud of you" Murmushin gefen baki yayi ya tashi ya barta zaune ya koma chan kusa da Nene ya zauna, ko wannen su da sak'e sak'en da yakeyi. Bayan kwana 3 Cikin 'yan kwanakin nan Uku, Nene ta tabbatar ita *'Yar Gata Ce* (Miemee Babe's Novel) don ko Zaid, Maalesh da Alhaji Habib na kyautata mata, Rafeeq ya rage zuwa Asibitin ya kanzo da daddare, Hajjo na kula da Nasiba da Nene. Miemee da Usheey sunzo duba su Nene Tun daren da akayi Gobarar Mak'ale ya kira uwar dakinshi ya sanar da ita ai ya cika aiki, ya cinna ma Gidan Nene wuta, Wutar da Suka kunna da Petir, Saude tayi daria tace "that Old witch, yanzu sai inga iskanci, dama Alkawari na miki cewa zaman katsina sai ta gagareki". Ko da safe sai da suka fita su 3 suka ga gidan Nene a k'one, murna kamar su zuva ruwa a k'asa su sha, Meema ta san aikin Saude ne banda Aneesa da tayi zaton Allah ne ya saka musu. Zaid ya ji dadin Shiryawar Rafeeq da Maminshi, sai da yayi Azumin Godia ga Allah, dama Alwashi yaci na duk randa Rafeeq ya daidaita tsakanin shi da Maminshi, to zai jera kwana 5 yana Azumi don nuna jin dadinshi. A safiyar Yau Nene ta sa Darun sai an Sallameta, Nasiba da Hajjo suna ta bata hakuri kan ta bari sai ta k'ara jin Sauk'i, ana haka sai ga Rafeeq da Daddy da Zaid sun shigo da Dr Umar, Yauwa Dafta, yau sai ka sallameni, Dr yace "dama Mama abun da nazo kawo miki kenan, takardar Sallama, tace "yo ni ai ko ba takardar Sallama tafiya ta zanyi" yayi daria yace "balle akwai ba" Alhaji Habib yayi daria yace "Ina kwana Nene? Ya karfin jiki" tace "Ahh Jiki garas ya kuke da iyalin?Rafeeq ya gyatsine fuska a ranshi yace "Neh-nehn nan no getam for kunya, wani Iyali kike tambayar shi? Wanda kika Lafta?" ya amsa mata, Suka gaisa da Zaid da su Nasiba, ta kurawa Rafeeq ido don jin ya gaisheta, ganin ta tsare shi da ido ne ya sashi cewa "Sannu Fah" "Ahau, dama wayace ana chanza wa tuwo suna? Me hali be barin halinshi" duk sukayi daria. Daddy yace "Toh Nene an Sallame ku, Gidanki kuma ba inda zaku fake, na dai sa an kwashe abubuwan da basu ci da wuta ba, sauran kuma an kauda su, ko kuna da inda zakuje ku zauna Kafin a gyara muku gidan?" tace "Muko ke da inda zamu, Kaduna zamu wuce, lokaci yayi da dai da zama zai kaini Bariki Garin Gwamna, Mahammadu bayanda beyi in koma chan ba, har ga Allah bansan garin, amma tunda dalili yasa, dole chan zamu tafi" Daddy ya jinjina kai yace "toh karatun Seebi fa?" tace wani karatu? Ta samu ta ceci rayuwarta da k'yar, ai Gun Iyayenta zan maidata" Nassiba ta bata rai, ai wallahi Nene ba zata datse mata karatu ba, zatayi Magana Zaid yace "Ai Nene tunda dai ta fara karatun a barta ta kammala, ai sun kusa fara Jarabawa, kuma in ta koma chan Abun zai shafi Karatun ta, kuma Semester ya ja da an kama mata hostel" Daddy yace "idan ba Matsala Nene ku na iya zama a gidana Kafin a gama gyara Gidan ku" a tare Rafeeq da Seebi sukace "What?" Daddy ya kallesu yace, eh, saboda kar ayi affecting karatunki" Zaid yace "this is a nice idea" Nene tace shin "Anya zaman mu a gidanka zaiyiwu kuwa?" Zaid yayi saurin cewa "me zai hana?" Rafeeq yace "this is a bad idea, Daddy please dont, dont make them live there, please, haba Daddy, do you want our house to turn to a battlefield? Do you have any idea what she did to Aunty Saude and Aneesa? Please that Dont" Nasiba ta kalleshi da mamaki, duk da ba taso su Zauna a gidansu Rafeeq, bata ji dadin yanda yake nuna beso su zauna da su ba, kamar yana k'yamarsu irin an hada su da kashi ko wani abu, Zaid ya wurga mai Harara Nene ta k'ulu sosai duk ds ba ji me yace ba ta san beyi naam da maganar babban shi ba, da bata yi niyyar zama a gidan ba, amma tunda Rafeeq ya kuskure yayi turanci, to sai sun zauna, sai dai ya hadiye zuciya ya mutu, tace "Toh Alhaji zamu zauna, Allah bamu zaman lafia" Amin ya fada cikin jin dadi, yace "da Office zanje amma mu tafi gidan, Rafeeq ka kai Hajjo Gida kace da Mom dinku mungode, Zaid ya ba hajjo 5k tayi godia, Hajjo ta bi bayan Rafeeq da tuni ya bar gurin don bacin rai, Zaid da Seebi suka bishi da ido me yayi zafi haka?. ********* Fitowar Aneesa ke nan daga cikin gida zata bude mota ta tafi School taga Shigowar Motar Daddy da Uncle Zaid, ta tsaya tana kallon su har suka k'araso, ta nufi Motar Daddy ta Bude "Daddy kayi mantuwa ne? Yace "Aa Aneesa" ganin Uncle Zaid ya bude booth yana fito da kaya ya sa ta kallonshi, "good Morning Uncle Zee, wadannan kayan fa?" yace "na bak'i ne" Kallon gilashin Motar tayi ta ga Nene zaune a bayan Mota, Wani ihu ta sa kamar mahaukaciya, bata bar ihun ba, Su Saude da Meemah suka fito sun zata wani abun ya sameta, "Anee baby me ya faru" ba ta bar ihun ba, sai dai tana nuna cikin motar da yatsa, Nene tace "Nunani kikeyi kinga dodanniyar cikin mafarkin ki ko?(your worst nightmare) to bari in fito ki ganni da kyau, Nene danAllah ki zauna kar ki fita, ina Nene bata ji rokon da Seebi keyi ba ta fita daga motar. Ai tuni cikin Saude da Meema ya duri ruwa, da sauri ta jufi Mijinta "Alhaji Me zan gani haka? Me sukeyi a gidan nan?" yace "Sunyi Gobara ne, zasu zauna a gidan nan har sai an gyara gidansu" da masifa tace wani Gidan? Ba dai wadannan ba wallahi, ko ni ko si" ran Daddy ya 6aci, yace "Sai dai ke ki bar musu gidan, don Wannan Gida na ne, kuma ina da damar kawo duk wanda na ga dama, a lokacin da nakeso, Nene ku mu shiga ciki" suka shige ciki duk suka bar su tsaye" Gaban Saude kamar ya bude don bugawa, yau ita Alhaji ke mayar ma magana? Yau ita take cewa ga yanda zaayi yana mata musu, har yana mata barazanar ta bar gidan? Ta shiga ukunta Lallai akwai Sakel, Tana tunanin idan gidan su Nene ya k'one zasu koma k'auye su bar Katsina, su rabu da Family dinta, bata taba tunanin abu zai rikide ya koma mata haka ba, ai da ta sani da bata sa an k'ona gidansu ba, da ta sani tayi maganinsu ta wani hanya, Tana tunanin ta yada k'wallon mangoro zata huta da k'uda, ta na gudu gara ta fada gidan Zago, wannan shine ta gudu bata tsira ba, gashi ta kwan a ciki, yanzu wa gari ya waya?? (Shin ya kuke ganin Zaman su Nene a gidan Lema). _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Asslam Alaikum, Ina mik'a Godia ta ta musamman ga dukkanin masoya KE ALHERI CE, Ina Godia Matuk'a Ga Adduar Samun waraka da kuka tayi ga Mahaifiya ta, Allah ya bar Zumunci ina kuma me farin cikin sanar daku cewa Tana ta samun Sauki, Allah ya saka maku da ALHERI masu kirana ta waya da masu turo Sak'onin su Via Sms da ta Whatsapp da ma wanda basu samu daman hakan ba, Allah ya bar Zumunci. #grateful #1love. A big Thank You to Aunty Sis❤ Thank you for comforting me through my rough days. This Page is For You Sister Fatima Wada (Maman Meema)💘💘💘 Pg5⃣2⃣ Tashin Hankali Saude ta shiga don ganin Dakin Marigayiya Rafee'ah Daddy ya basu Nasiba, ta hade hannayaenta saman K'irjinta tana neman Mafita. _Boka na kan tudu_ ya fado mata a rai, ta tuna haduwar su ta k'arshe basu wanye lafiya ba har tayi ikiirarin ba zata sake neman shi ba, yanzu dole ta neme shi tun kafin dare yayi mata don tasan shi zai share kukanta. Haka ta daddafa ta kai Washegari da su Nene a cikin rumfa guda tayi ma garin Kano Asubanci tafiar da ko Aneesa bata san tayi ba. Daddy ya kalli Nene yace "Ya k'arfin jiki ya kuma Bak'unta?, tace "Alhamdulilah, ni dama ba abunda kr min ciwo" Nasiba ta gaida Daddy ya amsa mata, Daddy yace toh Nene ni zan fita gurin Aiki, akwai kalaci a Parlorn k'asa ku sauka ku ci abunda ranku keso" Nene tace to shikenan Zamu sauka, Allah ya biyaka da Alherinsa, ya amsa da Amin, har ya dan juya zai bar dakin yace "Nene ince ba wani abunda kuke buk'ata ko?" shiru tayi Tana nazari, chan tace "akwai, ina da bukatar kudi" a razane Nasiba ta kalleta, kallon Haba Nene, bayan sun tanadar musu da komai na bukata, mesa xata tambayeshi wani abu kudi ma for that matter, ba tare da bin ba'asi ba Daddy yayi saurin sa Hannu Aljihu ya bata 15k yace ga dubu sha biyar sun isheki? Tace "sunyi yawa ta amsa ta zari dubu takwas ta mik'a mai sauran kudin yace ta barshi a hannunta bazai amsa ba, tace " Kai Amsa, dubu takwas ya isheni" hannu ya sa ya amsa, ya tashi zai fita tace " ko ta wurin Filin Samji zaka ka dan ajiye ni wani gu?" Nasiba ta dafe kai cike da takaicin Nenenta, yace "Muje sai a ajiyeki, da sauri ta suri Hijab dinta ta bi bayan Alhaji ba tare da ta kula Nasiba ba. Nasiba ta juya kai cike da jin haushi. ***** Sunyi dan tafia kadan gaba da Filin Samji Daidai Asshifa Medical Center tace "yauwa aje ni nan, yace da direba yayi parking, yace "Nene Asibiti zakije daba akai ki na Dr Dara ba?" tace "kaini nafi gane na Hausa, barin shiga, daga nan sai in taka inje 'Yarkutungu in siyo Zogale" "A siyo Zogalen dani" ya fada yana daria tace "toh sai kadawo Allah bada Saa" ya amsa ta juya ta shiga cikin Asbitin Musulunci da suka shahara gun magance abun da ya danganci 'Jinnu, Sihiri, Ciwon K'ashi da makamancin haka'. ******* Zaune take gaban Malamin, tace "dama nace maka zan dawo, yanzu shine ya ajiyeni anan ma" Mallam yace "to da baki shigo dashi mun mai yan tambayoyi game da matar tashi ba don mu samu saukin Magance lamarin" Nene ta nisa tace "ai Mallam baka gane ba, Zargin matarshi nakeyi, kuma ban sanar da kowa ba, shiyasa na ke so a ban maganin da Asirin ta zai tonu, don Wallahi ban yarda da wannan Sauden ba" Mallam yace " toh shikenan, kamar yanda na gaya miki kudin Kwanaki dubu 7 da dari takwas ne" tace "toh mallam, ta bude 'yar pos dinta ta ciro dubu takwas ta mika mai, Mallam ya bata chanjin dari 2, ya dauko wani dan galan, da abun cikin be wuce rabin galan din ba, yace " Wannan hadin magunguna ne kalakala, a dinga mai amfani dashi wurin girki, InshaAllah gaskia zata baiyana, zai tunano komai in ma an batar mai da saninshi ne, Nene tayi godia ta mai Sallama ta fito ta wuce Kasuwar 'yar kutungu a siyo Zogale har da sansamin Zogalen tace "zata shuka a gidan A.Habibu tunda ta lura yana son Zogale, kawai in yayi tsawo sai a dinga katsa ana dafa mai yana sha har ruwan Zogalen tunda maganine. Kusan a tare suka iso gidan, Nene daga ina hakan, har kinji sauk'i kin fara fita? Zaidu bawan Allah, kasuwa naje, ya kalli Galan din hannunta, zaiyi magana yayi shiru a ranshi yace "k'ila jik'on su ne na tsofi" suka k'arasa ciki, yace "ai ni yanzu Kaduna zan wuce, gwara in koma hakan, Mami tana ta mitar a maido mata diyarta, Nene tayi daria, tace " ai ta ma yi k'ok'ari, ai da nasani na dan yi mata 'yan siyayya a 'yar kutungu" yace "ah haba bakomai" Nasiba ta lek'o tace "Uncle Zaid ina kwana? Yace "Ahh, na zata kin tafi School ai" tayi murmushi tace "sai 12 nake da lectures" ya kalli agogo yace ai is almost 11, in kin shirya sai inyi dropping dinki daga chan sai mu wuce" ta dan kalleshi, ina zaku wuce? Nene tace "Kaduna zasu koma yau ta fada tana murmushi" ba tare da ta kalli Nene ba tace "Allah sarki har an gama hutu, ina Ayman din?yace tana chan gidan Baba Tj daga nan sai mu biya mu dauketa sai mu wuce" Meema ta shigo Dakin jin muryar Zaid "Uncle Zee, kazo gidan baka neme ni ba? Ya dan rausayar da kai yace " Yanzu na shigo ya kike? Tace " living with some lunatics, i cant be fine" Nene ta tsargu ta hade girar sama da ta k'asa, tace "Ina fata ba dani akeyi ba" da sauri Zaid yace "Aa nenen mu, ya kawar da maganar da cewa Nasiba je ki shirya" Nasiba ta shiga ciki Nene ta rufa mata baya, ya maida duban shi ga Meema, ina Aneesa? Aneesa ta tafi School, Aunty fa? Tace ta dan je ta dawo. Ta zauna kusa dashi, ta sausauta murya tace "Uncle Zee ba zan fasa rok'onka ba, DonAllah give me a chance in nuna maka kalar son da nake maka, ina sonka, tun ina 6oyewa har na kasa, ina sonka sosai, ka aureni, ni zan zame na Ayman Uwan da ta rasa, zan dauketa kamar ni na haifeta, please ka taimakeni" ta karasa maganar kamar zatayi kuka, Sosai Zaid ya tausaya mata, ba zai bata hope ba tunda be son ta ko ծis, kuma be som ya mata k'arya, gwara ya fito mata k'arara ta san matsayinta, ya dan kwantar da murya yace "Meema, kiyi hak'uri, i only love you like a sister, no strings attached, and i'll take care of you kamar yanda zan kula da loved ones dina, please ki bar maganar aurena kinji? Allah zai baki me sonki wanda ya fini komai kinji? Kuka ta fashe dashi, Zaid beson kuka ko kadan ya hau lallashinta yace "kiyi shiru, i am sorry, i dont want to lie to you" da sauri ta mik'e ta fita daga Parlorn. ******* "Wai wannan fushin da kike tayi na uban meye? Wani abun aka miki kike ta faman nuk'ura? Nasiba ta kalli Nenenta tace " Haba Nene, saboda me zaki amsa kudi gun Daddyn su Rafeeq? Bayan wurin kwana da suka bamu, sun biya mana duk wata bukkatun mu, don me zaki ce ya baki kudi? Nene ta tsura ma Nasiba ido, tace "kin gama? Wai ni Seebi me kika daukeni ne? Makwadaiciya ko wacce bata da godiar Allah eyi? Kin tsaya kinga dalilin da ya sa na amshi kudi gunshi, to in ma kallon kwadaiyaya kike man to ki chanza tunani" kinga wanchan galan din, ta nuna gallon din da hannunta, Magani ne ciki, maganin karya duk wani sihiri da ke jikin biladama da yardan Ubangiji, ina da tabbacin akwai shiri jikin Uban Rafeeq, kwanaki na je wurin me Asshifa na fada mishi zargi na yace akwai Maganin da zai hada mai na dubu takwas, duk sihirin jikin mutum zai kare, to ni ina naga Dubu8, ai ko hakora na na saida ai bazasuyi dubu3 ba, yanzu gaya min laifi ne don ya bani kudi na siyo mai magani? Naga ai shi zai amfana " Nasiba ta sauke Numfashi, tace "kiyi hakuri Nene, nayi zaton wani abun ne, kuma ai da kin bari don yana zuwa amsan Magani gun Mai Arriyadh" tace "ke ni rabani, ai ba laifi bane in an raba k'afa, Magani ai dace ne, Allah sa a dace Amin" "barin shirya kafin Uncle Zaid yace in fito". *Wudil* "Yau na shiga uku na, na kan tudu ya mutu?" a rude Saude ke maganan, matar ta dafa kafadunta tace "Hajia, ai in gaya miki, kusan wata 7 kenan da mutuwar na kan tudu, Bukkar shi ta kama da wuta, ko tokan shi be tsira ba, da na kanzo gunshi, amma tunda na ga Na kan tudu yayi mutuwar wulakanci na koma ga Allah, Kema ina baki shawara ki koma ga Allah, abunda Allah zai miki Boka be isa ya miki ba Wallahi, Saude tace ke dalla rufa min baki ba waazi nace ki min ba, ni ba ragguwar mace bace, ni jaruma ce, i dont give up" matar ta ta6e baki, bata fahimci turancin ba tayi gaba ta bar Saude tana jimamin mutuwar Na kan tudu, yanzu take tambayar kanta, meye abunyi?. *UMYU Katsina* Fitowar su Lectures kenan, sun nufi busstop, Miemee tace "Kar ki ga don kina gidansu kice zakiyi tolerating shit dinta, Wallahi i wont forgive you in tace miki 'a' bakice mata 'b' ba, Usheey tayi daria tace " Sai da haka don na lura Aneelema na da izgili" Seebi tayi murmushi "ku kwantas ba ruwana ma da ita balle ta shiga sabgata, ban ma bada chance din mu hadu, akwai komai a dakin da aka bamu, to fita ma be dameni ba balle mu hadu ai ta chechekuce" Miemee tace "Oops, ai na ma manta da The Boss, Nenenmu bata daukan Nonsense, ba zata yarda ko hararki ayi ba" tare sukayi daria. Jin horn ya sa su juyawa, ganin Motar R-Lema ya sa Miemee tamk'e fuska, ga Hamma kuzo mu shiga ya ajiye mu" cewar Seebi, Miemee tace "aje lafiya ni bus zan shiga gata baa cike ba" Seebi tace "haba mana Miemee love kizo muje" tab kinsan dai idan ya gaya min daci zan gaya mishi madaciya ko? Usheey tace ba ma zaayi haka ba, mu dai mu kama kanmu in mun shiga, da k'yar sukayi Convincing miemee. Zuwa tayi ta bude k'ofar gaba taji shi a rufe gagam, Kasancewar Motar Tint ce bata ganin na ciki, Usheey tace kizo baya su biyu ne, Suka shiga bayan a tare. Maalesh ne ke tuk'in sai Rafeeq a kujera me zaman banza, Ya Maalesh ina wuni? Ushee ma ta gaidashi, ya amsa fuska a sake da "Lafiya lao yan makaranta ya School? Suka amsa mai, "Hamma ina wuni?" dauke kai yayi kamar be ji ta ba, bata damu ba don inda sabo ta saba. Maalesh ya kalli Miemee ta side mirror da ta hade girar sama da ta k'asa, yace "Ammata ba gaisuwa?" Seebi dake tsakiyarsu tayi saurin muntsinin Miemee tace "Sannun ku?" murmushi yayi yace "Sannunmu, meyasa kike daure fuska? Ko lectures ne ya bata miki rai? Ko rana din ne? You are beautiful, dont let anything ruin your day Okay? Gajeren Murmushi Miemee tayu, Ushee da Seebi suka matse hannun juna irin suna sonyin gulman nan amma ba chance, haka Maalesh ya cigaba da tuk'i Binibini sai ya kalli Miemee ta mirror, yana sakin murmushi, sometimes kuma ya tsomata cikin firar su da Seebi, Rafeeq najin Maalesh ya lura da taketaken shi amma be ce komai ba, don ya san Maalesh da playing Mata, kuma ya zaayi yana son Seebi kuma yana flirting da Miemee yayi dan guntun tsaki. Wayar shi ta hau ruri. Ya dauka ya soma magana kamar baya so "Kun wuce din? Ina Angel?Okay Safe journey". Ikon Allah inji Miemee a ranta, shikuma haka yake 3sentences har ya gama waya lallai "Uncle Zee din ya wuce ne?" cewar Maalesh, "Uhm" kawai Rafeeq yace. Haka suka kai Miemee har gida, Miemee tace thanks ta bude motar, wanda ma ta ke sha ma maganin be san tanayi ba, Maalesh yace "excuse me" ya bi bayanta duk suka bishi da ido, yace "Beautiful, Allah sa ban bata miki rai da surutu na ba? Tace " No kar kadamu" yace "no na damu" tayi murmushi tace "Ka shiga ku tafi suna jiranka" ya dan marairaice yace "DonAllah in amsa numbernki gurin Nasiba?" tayi murmushi tace "ba laifi" "awwn thanks beautiful ya kashe mata ido tare da komawa cikin motar" ba wanda ya ce mai k'ala ya ja motar suka bar Unguwarsu Miemee. Sai da suka gama Fira da Baba Maigadi wanda duk rabin Firar gardama ne tace kai ni bari in shiga ciki in dan yada kafadata kafin Seebi ta dawo, Baba Maigadi yace "toh Aminene ta" Nene tace "Wallahi kwalelenka na fi karfinka, ni sai me lamozin (limousine) sukayi Daria duka, ta wuce, sai da ta shiga ciki sannan ta tuna da Sansamin Zogalen da ta siyo don ta shuka, tace " barin dauko in shuka kafin na mance" ta shiga ta dauko, ta wuce baya inda take ganin shukokin flowers da kayan itatuwa (Garden) tana waigawa taga gatari tace "yauwa ta kwana gidan Sauki" ta dauko daga gefe ta fara hak'a rami, ji tayi ta finciko da wani abun, toufa tace "a hankali tare da duban abun me kama da k'ulli, tace "wannan k'ullin na meye? Ta dauka ta warware a hankali, laya ce da yar takarda an rubuta ~Aisha Habibu~ da larabci an sokeshi, Nene tace "wacece Aisha kuma?wata Zuciyar tace "ko sunan Mamin Rafeeq ce?" tayi murmushi tace "Haba biri yayi kama da mutum, ni na san wallahi ba a banza ba Saude, babban kuskurenki daya da kika bar Nenen Seebi ta zauna a gidan ki, a hankali duk zan warware duk wani muggun tuggu da kika k'ulla, mafarin kenan, da ni kike zancen. ********* Rafeeq ya kalli Maalesh dake kwance rigingine kan gado yana waya da Miemee bayan da suka sauke seebi ya amsa numbern a gunta, har ya gama ya dago Rafeeq na lura dashi, chan ya cire baki yace "Lesh, me kake nufi ne wai kai?" Maalesh ya dan kalleshi da mamaki yace "guy bangane ba, me kake nufi?" dan guntun tsaki Rafeeq yayi yace" ka amsa numbern wannan yarinya mana, yanzu kazo kana waya da ita" Maalesh ya dan bata fuska yace "do you have a problem with that? Rafeew ya harzuk'a yace " Tun farko mesa zaka ce kana son Naseebah idan kasan you wont ask her out ba, why? Na baka number don kace min kana sonta har kace aurenta kake sonyi, ko dama yaudara ce? meyasa ba ka fada mata ba? Kullum kana damunta da waya, kana kasheta da words dinka, ka sata tana ta jiran tsammani, and yanzu don cin fuska ka tambayeta numbern friend dinta, Seriously Lesh?Why? Tell me why?" Ya karashe maganar shi a dan fusace, Maalesh ya dan kallo Rafeeq shima a fusace yace "Why Rafeeq? You want me to tell you why? Fine! Its Because of you Feeq, i didnt ask her out because of You, You R-Lema" a firgice Rafeeq yace "Bangane ba, me kake nufi saboda ni? Kar ka manta i gave you her number" darian takaici Maalesh yayi yace "Eh ka bani numbern ta saboda baka san your true feelings for her ba, ba ka san cewa she's your Happiness ba, you are blindloving her, why cant you realise it? Kana mata wani makahon so da kai karan kanka baka san kana yi ba, You love her Feeq" Cike da tashin hankali Rafeeq ya wurgar da Roban ruwan, ya tashi a fusace ya cukume rigar Maalesh, yace "Inji uban wa yace maka sonta nakeyi? Are you crazy Mahmud Ahmad? You know me better than anyone, No girl is worth my love, I cant fall for her, cant fall for any girl, Ba macen da ta isa in so ta" Maalesh ya katse shi "Why? Saboda kai ba mutum bane? Sabida kai baka da Feelings? You are inhuman? Or your Humanity is shutdown, you think you dont have right to love? Who are you to say you cant love anyone? Rik'on da ya mai ya sake matse mai wuya cikin daga murya yace "duk me zakace kace , ban damu ba, ba yarinyar da ta isa in sota because I'm Rafeeq Freaking Lema" _Bibilicious Biebee_ 👧KE ALHERI CE🙇‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Get Well soon Aunty (Maman Sultan)💘. Allah ya baki lafiya Amin. Pg5⃣3⃣ Darian takaici Maalesh yayi, yace "yes you are Rafeeq freaking Lema, i know, the guy that cares about nothing, na san kai ko waye, nafi kowa saninka, which is Why nagano exact feelings dinka towards Seebi, Saboda Kai na bar Seebi, saboda kai maganar So bata ta6a hada mu ba ba wai don bana sonta ba, aa sabida na lura kafini sonta, ka fini bukatar ta, Shuttup Maalesh, ka fara hauka ne wai? Me zanyi da wannan yarinyar? Ce maka tayi ina sonta? Ko kuma meye? She means nothing to me, na dauketa a 'yaruwa ta, shes like Rafee'ah to me, nothng more nothing less" Maalesh ya katseshi "Ofcourse, naga alama, ai naga lokacin da wuta ya kama gidansu ka fita daga hayyacinka kake ta sambatu ba wani abu bane wannan ko? Ko da yake ba sai na tsaya gaya maka ba, kai da kanka ka san what you want, like it or not, you are deeply in love With Seebi" Zuciya ta ci Rafeeq ya dunkule hannu ya kai ma Maalesh Naushi a baki, nan take ya fasa mai baki, Maalesh ya taba yaji jini, Murmushi yayi yace" yanzu ka gasgata min Zance na, kana Son Seebi, in ba haka ba mesa zaka damu kanka har haka?why are you affected With what i said? idan ba haka abun yake ba, me zai dameka? Har kana tada jijiyoyin wuya? Har ya kaika ga naushi na, It only means onething, you love Seebi this much" Fuskar Rafeeq yayi ja sosai, zuciya na tunzura shi, Rafeeq ya sake daga hannu zai kai ma Maalesh mari, Maalesh yayi saurin rik'e hannu tare da ture shi iyakar k'arfin shi, Rafeeq ya zube k'asa, ai kuwa ya tashi da zafin nama ya wawuro Maalesh da fada haka suka kama dambe iya karfinsu, suna nushin juna, abunda basu ta6ayi ba kenan Dambe, iyakacinsu gardama da chachan baki, abun be taba kaisu ga fada har haka ba. *********** "Ai kuwa Asirin ki ya tonu, don k'ona wannan layar zanyi, duk asirin ya kone tare da layar" har mu zaa nuna ma hatsibibanci, mu ba boka ba mallam muke maganin mutum" mitar da Nene take tayi kenan bayan fitowar ta daga garden rik'e da layar zata shiga cikin gida, daidai wani daki taji alamun Hayaniya, kamar fadafada, ta shaida Muryan Rafeeq da na Maalesh, da sauri ta k'arasa dakin ta bude gami da doka uban salati "Lailahaillah, me zan gani haka? Dambe? Kuna cikin ganiyar Samartakan ku kuke dambe? Zaku rabu ko kuwa? Inaaa sam ba su san tana yi ba, dambe fa sosai sukeyi, kowa da tashi kalar Zuciyar, Ta ajiye karikitan hannunta a gefe ta shiga tsakaninsu tana raba su, Maalesh ya dan ja baya amma Rafeeq sai k'ara wawurar Maalesh yakeyi suka cigaba da damben, ba yanda batayi su rabu ba sun k'i, har dai ma Rafeeq ya yi kuskuren hanbarin Nene a gefen fuska, ta ko ji zafi sosai, tace "bala'in nan, daga rabo na samu kasona? Ku ba ku san ku bari ba ko?ta waiga ga Rafeeq tace "Ana baka hakuri kak'i bari ko? Kai me zuciya, har warewa kakeyi don ka saba dambe ko, to kar ku fasa, ku jirani inje in dawo, in kun fasa damben kun ci uwarku duka, ku jira ni nace" ta durkusa ta kwashi tarkacenta ta fita tana tsuma, wurim baba maigadi taje taga baya nan ya tafi masallaci, ta wuce baya inda ta shuka zogale ta hango gatarin da tayi amfani dashi. ta hau cire kayan jikinta tana fadin "har ni za a nuna wa dambe, Allah kasa kar su fasa" sai da Nene ta cire Zani da rigar da ke jikinta ya rage daga ita sai fan guntun Buje(Skirt), ta dauki Gatarim ta cire wurin tsinin(blade) gatarin ya koma kamar tabarya, nan tayi cikin gida tana huci kamar Zakanya. "Yihuhu ina Dunkum din yake, ba ka fasa ba ko? To gani nan zuwa, yau sai nayi k'ullin k'ullin kubura da kai, yau ko ni ko kai". A lokacin ba su bar damben ba, cikin ikonAllah Allah ya nuna wa Maalesh Nene ta gefen ido, kallo daya yayi mata ya dauke kai, gabanshi ya fadi, a ranshi ya ke tambayan kanshi anya Nene na da hankali kuwa? Ba da ban dan guntun siketi din dake jikinta ba da yace zindir take, cikin seconds din da be wuce Goma ba Maalesh ya gama tunanin nan, da sauri ya bangaje Rafeeq ya fice a guje, a zaton Rafeeq Maalesh ya ji tsoro ne shiyasa ya gudu, da azama ya bishi don kamo shi, ya ci karo da Nene wanda ta yo dakin gadangadan, ai da gudu ya rufe daki ya shige toilet tare da sa Key, tsakaninshi da Allah be gane ko wacece ba, duk zaton shi gamo yayi, bugu daya Nene ta ma k'ofar dakin Rafeeq ya bude, ta shiga dakin tana dube dube ta na fadin "ina dunkum din yake, ka fito mana, in ba ga tsoro ba, yau ko ni ko kai, yau sai na cire maka duk wani abun da ke kanka" jikin Rafeeq rawa yakeyi, ta hujin makullin toilet yake kallon Nene sosai ya firgita da yanayinta,tsoro ya hanashi gane ko wacece. Addua ya hauyi a zuciyar shi, na Allah ya kawo mai dauki, Allah ya cece shi daga wannan Zararriyar matar" Fitsari yaji na neman kubce mishi sakamakon Bugun da yaji Nene na ma K'ofar toilet din" baki na rawa yace "Lord have Mercy" karaf kunne Nene, ai ko ta tunzura, ta cigaba da bugun k'ofar nan da Gatari tana cewa "Ni kakeyi wa Turanci?" Jikin Rafeeq na kyarma, a hankali ya shiga kiran "Mamiiiii" (Manage this zan cigaba daga nan😬) 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Cikin Masoyan Biebee Isa harda Tsofi💚 wannan abun ya min dadi. Ina mik'a gaisuwa ta musamman gareki, Kakar mu Hajia Saje❤ at your age i never thought you'll have time to read This Story of mine, I was so happy and excited when i was told by your granddaughter (Benazir) that you are a Fan of My Story, which is why i'll make you Friends with Nene😉 Thank You Hajia Saje❤, Allah ya Albarkaci Zuri'ar ki, ya k'ara miki lafiya da tsawonci rai da kwana. KE ALHERI CE This Page is for you Grams Hajia Saje❤ Pg5⃣4⃣ Toilet Saude ta fada ta je ta tsatso wankan ta, tare da sa wata rigar bacci, ta duba agogo taga k'arfe 9 saura lokacin shan Tea din Alhaji ne, dabara ta fado mata, tunda ruwan tea din sai an sa kayan k'amshi kamar su citta, kannanfari, na'a na'a da green grass sai lipton, to me zai hana ta dafa mai ruwan nan ta watsa kayan k'amshin ciki ta kaima ya sha tunda ba ganewa zaiyi ba? Haka ta dauki gallon dinta ta nufa kitchen ta tafasa wannan ruwan ta zuba kayan k'amshin ta juye a flask, ta dauki dan guntun mug tayi dakin Alhaji Habib. Ta shiga da Sallama, zaune yake yana kallon News Line a NTA, ya dago ya kalleta, haka kurum yaji be don ganinta, da k'yar dai ya amsa Sallamar ta, ta janyo dan guntun table ta ajiye flask din da cups, tace "Alhaji Na ina wuni?" ba yabo ba fallasa ya amsa mata,yace "ina kikaje Saude? Duk yau ban ganki ba? Ta fara indainda, wai tana cikin gari, Mamar kawarta ta rasu, shine taje zaman makoki" ban isa ki gaya mim inda zaki bane? Ni fa ke aurenki Saude, bazan dauki fita irin haka ba, duk inda zakije daga yau sai kik nemi izini na, no matter how urgent it is, am i clear?" Mamaki ya baiyana fuskarta, abunda bata taba gani ba, a ranta tace komi zai zo k'arshe once ka sha ruwan nan" ta marairaice face dinta tace "Am sorry Alhaji na, kayi hakuri, ba zaa kara ba" ga night Tea dinka kasha barin tsiyaya maka" kafin yace wani abu Sallamar Nene ta doki kunnuwansu, Alhaji ya amsa mata, Saude ta murtuk'e fuska, Daddy yace Nene har kin dawo? Tana washe baki tace "Ai na gaya maka abun ba wuya, gashi har na hada ta ajiye flask dinta nan kusa da flask din Saude, Saude ta kalleta da mamaki tare da murtuk'e fuska tace "miye wannan?" Nene tace "Shayin buzaye ne" Saude ta dauke flask din Nene tace "Alhaji baya shan irin shayin nan, baya buk'ata" "Aa ni nace mata ina so, inaso in sha yau, tace min irinshi take sha, shiyasa bata ciwon jiki, shine nace nima ina so wataran in sha, ta shaida min tana da abun hadin, nace aa tabarshi don nasan sai an hura garwashi, bayanda ban yi da ita ba tace ita sai ta min, ashe har ta hado, kai amma Nenemu nagode sosai" Alhaji ne yayi maganar. Nene ta chafe da cewa "ai nagaya ma ba wahala, ina sauka k'asa naga wutan da yan baya sukayi abincin dare ba be mutu ba, na dan dibo na dinga rurawa, daman na siyo mangal (kaskon karfen) a kasuwa jiya don duk dare sai na sha" ran Saude in yayi dubu ya 6aci tace "Alhaji, you cannot take this thing, i made your Tea for you, you dont know what ingredients she used, they might be bad for your health, dont forget you are allergic to such things" yace "Saude it would be very bad if i dont take this, she used her strength and energy to make it for me, i dont want her to feel bad" Nene ta hade fuska, uban me suke cewa?, ita zaa yo wa turamci daga abun azziki? Harda Shi Alhajin k'aton banza, Ta mik'e fuu zata kwashe flask dinta, da sauri Alhaji yace "Aa Nene ki bar min donAllah zan sha" "aa kadai sha na matarka kar ta sake turance ni" yace "Aa Nene DonAllah ki bar min, naki zan sha" nan ta fara Fara'a ta ahiga tsiyaya mai Tea dinta da ya sha Magungunan Asshifa, Ran Saude a 6ace ta mik'e fuuuu ta bar Parlorn. Sosai Alhaji Habib yaji dadin Shayin buzayen, ya kumayi santi, jin haka ya sa tace gobe zata mishi da sassafe don ya sha yayi godia sosai, suka danui fira kadan kafin ta mai bankwana ta tafi daki don yada k'afada. Da takaicin Nene Saude ta kwana, Tsohuwar na ci mata tuwo a k'warya, amma bakomai, gobe rana ce, gobe Dole zai sha ruwan magamin nan don Da kanta zata shiga kitchen ta mishi Lunch kasancewar gobe Weekend. *Mafarki* _2:45am_ "Ubangiji Allah kadai zai saka miki abun da kikayi ma Family dina, ke da kakarki Alheri ne a garesu, Abu daya ya rage kiyi, ina So ki shiga dakin Daddy, akwai wani gagarumin sihirin da akayi a cikin dakin, shine dalilin da ya sa Auren su Mami ya dade a rabe, ina da tabbacin in kika ga wannan Asirin komai zaizo k'arshe, Asirin na nan a----" Jijigar da Nene ke yi wa Nasiba ne ya katse mata mafarkin da takeyi,Nene ke famar fadin "ke Seebi tashi, ina kika ajiye min tochila na?" Nasiba ta buga tsaki da k'arfi, ji takeyi kamar ta rufe Nene da duka, saboda bata karasa jin Umurnin Rafee'ah ba, so tayi ta tambayeta ta hanyar da zata bi ta shiga dakin Daddy ba tare da sanin kowa ba, amma Nene ta shiga tsakani, pillow kawai ta daga ta ciro ma Nene torchlight ta ajiye mata ba tare da tace mata komi ba don takaici, ta juya tare da jan bargo tana me rok'on Allah Allah ya sa ta sake Mafarki da Rafee'ah. 1:00pm *A hanyar Kaduna* Maalesh ya gangara k'asan Titi sakamakon taka k'usan da yayi, kiris ya rage ya k'arasa Zaria, gashi be da Spare tyre, ya rasa yanda zaiyi, ya koma cikin mota ya doka tagumi yana tunanin ya zaiyi. Daga nesa ya hango motar Lesh, mamaki ya kamashi, to me ya keyi a nan? Kd zaije ko Abj? Dan guntun tsaki yayi yace "thats non of my bussiness" niyyarshi ya tafi ya barshi a gun don be son yi mishi magana, amma wata zuciyar ta hanashi yin hakan, don be san me ya tsaida shi ba, ya gangara yayi parking baya motar Maalesh, idan shi ya kai ga Tayan baya da yake a sace, guntun tsakin ya sakeyi yare da bude bayan booth dinshi ya ciro wani spare tyre, ya dauko kayan aiki duk cikin booth dinshi, ya gangaro dasu daidai tayar, daga cikin motan Maalesh ya ji ana kwance taya, yayi saurin lek'owa ganin Rafeeq ya sa shi dauke ido, don har yanzu yana fushi dashi, R-lema ya cigaba da cire wannan tayan, ya chanza dayan, ganin wannan ya mai tauri yana bukatar taimako ya sa Maalesh karasawa gunshi ya taimaka suka murde tayan ba tare da sun kalli juna ba, don kowa cike yake da danuwanshi, Rafeeq ya mik'e ya kakkabe hannunshi, cikin backseat din motar Maalesh ya hango bottle water ya bude ya dauka ya wanke hannun shi ya koma motar shi ba tare da yace komai ba ya ja motar shi yayi gaba, Maalesh ma be bi takanshi ba ya sa Tayan a Booth da kayan gyaran ya shiga mota ya bi bayan Rafeeq a guje. A tare suka iso Kaduna, Maalesh ya kira Uncle Zaid yace "mai ya iso, gashi zai k'araso gidanshi" Uncle Zaid yace"Aa Mahmud bana gida, ina Gidan Maminku, kasan Malali ai? Yace "eh" "to in kazo ka kirani" yace "toh" ganin Rafeeq yayi hanyar Malali ya san cewa chan ya nufa ba tare da ya kira Uncle Zaid ba ya bi bayan Rafeeq har suka iso gidan Mami. ******* A tare suka shiga gidan Mami tafito ta hadesu duka ta rungume, tana me murnar ganinsu duka, Ta ja hanayensu har parlo ta zauna, ta kallesu tace "Ayman na bacci kafin ku isheni da tambaya" murmushi sukayi a tare. Zaid ya iso ya gaisa dasu ta hanyar musabaha, yace "ya akayi ka gane gidan Mahmud? Ya danyi shiru sai yace " na bishi a baya ne" Mami ta gabatar musu da abincin da ta dafa musu, nan Rafeeq yafara narkewa wai yayi tuk'i hannun shi na ciwo,sai dai ta bashi a baki, haka mami ta biye mai ta dinga bashi abincin a baki, Zaid da Maalesh sun saba ganin haka a gunsu kafin abubuwan su rinchabe, har suka gama. Zaid ya kallesu duka yace "Ku saurareni, na son kuna mamakin dalilin da yasa nake nemanku ko? To lemme go straight to the point, ina lura da kalan kallon da kuke wurgar junanku dashi, ina sane da ba kwa magana, ina so ku sanar dani meye damuwar ku? Meye matsalar ku? Meye dalilin da ya sa abunda bakuyi shi a yarinta ba kuka fara shi da girmanku? Ina nufin meyasa kukayi dambe jiya? Ku bani amsa" Mahmud me ya hadaku? Maalesh ya kalli gefe yace bakomai Uncle Zee, ya juya ga Rafeeq ya tambayeshi, sha amsar kenan da ya bashi, ba yanda Zaid be yi ba don ya ji musababbin yin fadar su amma sunki bashi dama, sunki gaya mai komai. Mami tace "Ina ga tunda sunk'i magana ba sa son mu san meke tsakanin su ne, they chose to leave it to theirselves, nidai abu daya zance muku, you guys grew up together asif you're Siblings, dalilin ku Families din mu suka zama best of Friends more of relatives, and now kun dauko wasu halaiyar da ba naku ba? Bansan meya hadaku ba, bansan waye yafi gaskia a cikinku ba, but what ever it is, Fix it, kar in sake ji, kar in sake gani, idan na sake naji kun sake Dambe kai ko chachar baki ne zan sa6a muku sosai, kunsani ni ba bakuwar ku bace, i wknt take this, ina so ku shirya kanku right away". Ta tashi ta shige daki, Zaid ya zira key dinshi shima ya fita waje ya rage su biyu ne kachal a Parlorn. Kusan mintuna 20 ba wanda yace ma wani k'ala, ba me niyyar magana, kamar daga sama Maalesh yaji maganar Rafeeq cikin sanyin yanayinsa, inda yake cewa "You asked me why? I will tell you why, Everything is because of Uncle Zaid, Saboda Uncle Zaid, i cannot love Naseebah, because of Uncle Zaid i cannot accept that i love her, because of Uncle Zaid i cannot let my feelings out. That is why Lesh, thats the reason". Maalesh yayi murmushi yace "nasani Feeq, amma kasani ban bar maka Seebi ba don ka bar ma Uncle Zaid ba, na bar maka ne saboda i want you to have her, na son kafini sonta, kafini bukkatar ta, kun dace da juna, AKWAI LOKACIN da zai zamana cewa Seebi ce farincikin ka, ko da yake itace farincikin ka. Idan har baka yi abunda ya kamata ba, wato ka sanar da ita abunda ke ranka, you'll leave me no choice But to compete with Uncle Zaid, don ni kai na bar ma wa, ba shi ba, because i love you, i want the best for you, you've suffered and gone through alot, now is your time to be Happy" Wannan murmushin nan nashi na gefen baki dai yayi yace"Oh Maalesh, ashe kana so na har haka, okay listen closely, Uncle Zaid Mahaifina ne, shi ya rada min suna, duk wani wahalana Shine tun ina karami, har girma na, hakan ne yasa Babana yake min lak'abi da Ibn Zaid, Uncle Zaid na son duk wani farincikina, yana gudun bacin rai na, da wannan k'addarar ta fada a kaina, he's the only person that never thought of giving up on me, he stood by my side through my worse and rough times, he understands me better than anyone, he never judged me, he tolerated me, he took care of my Mom,he's done alot for All of us and Sacrificed alot. Ka gaya min Lesh, ya kamata in so abun da yake so? Ya kamata in yin butulci akan hallarcin da ya dade ya na min tun ina zanin goyo? Ya kamaceni da in so kaina har haka? Wallahi i can give my life up for him, i can Sacrifice my happiness for him, balle Naseebah" ya danyi guntun murmushi yace "Uncle Zaid ya fini sonta, ya fini kaunarta, ya fini buk'atar ta, ko don Ayman, da take buk'atar Uwa, i'm sure Naseebah zata kula da ita kamar diyarta" muryar shi na rawa ya danne ya koma zolayar yace "in banda abunka ni ai ban isa aure ba kasani ka girmeni fa yet you are just 25, i am jusy going to waste her time, shikuwa he's ready, kuma zai kula da ita fiye da yanda wani zai kula da ita" chan kuma ya koma magana dagaske "I love Uncle Zaid, i want the best for him, Lesh, help me do this please" Maalesh ya ja dogon numfashi ya sake, yace "Gaskia ne, Uncle Zaid ya chachanci fiye da haka, Alright, Uncle Zaid can have Seebin Nene" Murmushi Rafeeq yayi ya rungume Maalesh tare da fadin "Thank you, brother from another mother" su ka dinga bubbuga bayan juna. Rafeeq be ji wani darr din gaya Maalesh maganganun nan ba, don yasan Su hak'a su burne ne a gurin ne ba me jin zancen nan, He's sure Maalesh ba zai gaya ma kowa ba. °°°°°∆∆∆°°°°° Mami ta fito daga daki, ta gama jin zancensu, sun dan firgita ganin ta fito, ta zauna a tsakiyar su, tace "dama abunda ya hadaku kenan? Ta shafa sajen Rafeeq tace " I am proud of you R-Lema you are indeed your Father's Son, Ina Alfahari da kai, kasan cewa koda son Seebin Nene zai kasheka ba zan taba baka goyon ba, ba don komai ba sai don Zaid, Rafeeq gaya muku yanda Zaid yake a gurina bata Lokaci ne, amma zan baka tabbaci daya, banda Iyayena, Zaid ya fiye min kowa da komai a duniyar nan, Zaid ya sharen hawayena da kukana, Zaid ya tsaya dani lokacin da nake bukattar wani ya tsaya tare dani, I cannot ever repay him for what he's done to me, Rafeeq nafi son farinicikin Zaid akan naka, akan nakowa ma" ta daga hannayenta sama tace "Allah na gode maka da ka bani d'a mai hankali da tunani, Allah nagode maka da baka bari son zuciya ya rufe mai ido ba, ta riko hannunshi tace Thank you Feeq, nagode da baka tsaya competition da Kawun ka ba, You sacrificed Love for Family, remember thats what you do for your Family, ka zamto Fitila k'ona kanka ka haska wani ,ina Alfahari dakai Rafeeq Habib Lema" Allah ya muku Albarka duka, ta rungumesu tana hawayen farinciki. *KATSINA* Dadi tamkar ya kasheta ganin ta gama hada So6o da Shinkafa da miyan Vegetables din ta da ruwan Asirin da ta amso, a ranta tace "Yau Alhaji sai yanda nayi dakai" ta gyara zaman dankwalinta dama taci kwalliyarta ta dauki tray tayi hanyar Parlorn Alhaji Habib dashi. Ta shiga da Sallama, Sandarewa tayi sakamakon ganin Nene da Alhaji Habib zaune a kan Carpet inda Nene ke k'ara zuba mishi danbun Tsakin masara da yaji Gyada da Zogale a ciki dama har, ya cinye plate guda wannan k'ari ne, parlorn sai k'amshin Danbu yakeyi Saude ta k'araso da masifa "me zan gani haka? Alhaji ga Abincinka nan na kawo maka fa?" yace "Saude karki damu, Nene ta min Danbu, ba zan iya tuna last dana ci dambu ba, wallahi yayi dadi, kema you should eat" ta kallesu kallon wulakanci, ta dai daure tace "ga Sobo nan kasha toh" bakinshi cike da dambu yana tauna ya na nuna mata wani jug din da ke gefe yace "ai Nene ta min Kunun Zak'i bakiji dadi ba, ko zaki sha" Waiyo takaici kamar ya kashe Saude, ji takeyi kamar ta runtuma Ihu, tsohuwa ta tsaneta kamar me, ji takeyi kamar ta kasheta, fuuu ta koma kitchen ta dire tray din tana huci kamar Zakanya. *Kaduna* Abii ya ji dadin ganin su Maalesh, ya kuma ji dadin ganin Chanji sosai gurin Rafeeq, Abi yace "Ko kunje gurinsu Nene? Suna lafiya ko?" subul da bakan Maalesh ne ya gaya mishi maganar gobara, Ummi da Abii suka sake salati, basu san da zancen ba, "ince dai ba abunda ya samesu? Ba su gaya min ba wallah, kuma yawancin kullum sai munyi waya," Rafeeq yace "Lafiyan su kalau, suna nan gidanmu, Daddy ne yace kar a gaya muku saboda kar a tashi hankalinku, kuma ai ya sa an fada gyaran gidan, so please kar ku tada hankulanku" Abbi ya jinjina kai, yace "to ku yaushe zaku koma Katsinan?" Maalesh yace sai mun kai Jibi ko Talata" "to shikenan in ba matsala ina so in biku don kwanciyar hankalina" *Katsina* Bata hak'ura ba, ta sake daura ma Mijinta abincin Dare da ruwan maganin nan, Tuwon Semovita ne miyan Kuka, bata taba mishi ba da hannunta sai dai ta sa ayi, amma da yake yanzu bukatar ta take so ta biya ta zage ta tuke tuwon nan sosai. Bayan Sallar Isha'i ta kwashi kayanta a tray ta nufi parlorn Mijinta, ranta fadi k'al don bata ga gilmawan Nene ba, don ma damar nan da ta samu duka ruwan magamin ta juye a cikin tuwo da miyan, ta shiga da Sallama. Damm kakeji alamun fashewar Tanagaran, Saude ce ta sake Tray din da ta dauko sakamakon ganin Nene da tayi zaune kan kujera Alhaji Habib kuma daga gefe ya na ta zak'ar danwake. Fuuuu ta tako gunsu idonta ya rufe ta shiga zazzago ma Nene masifa "Wai meye haka ne? Wai ba za ki daina dafa ma Mijina Abinci ba? Meyasa kike yin aikin da ba naki ba? Hakkina ne in kula da mijina, cinsa da shansa sun rataya a wuyana, ki tsaya a matsayinki na Alfarma da aka muku na wurin zama, zak'ewarki ta fara wuce gona da iri" Alhaji Habib yace "haba Saude, ina laifin wanda ke kula da naka? Menene laifi don Nene ta bani Abinci?, kin tsaya kina mata rashin kunya, kar ki manta bake ba ko ni ta isa ta haifa please ki kula" Saude ta shiga tafa hannayenta "Wonders shall never end, Alhaji you are making me feel like i am sharing You with this Old thing" chan kuma ta saki daria tace "Ehwo, kar dai son shi kike? In sonshi kike kuyi aure mana a raba mana kwana kowa ta san matsayinta, don naga shishigewar ta yi yawa" sai a sannan Nene tayi magana tace "Yaro Man kaza, Saude kenan, ai ke baki isa in hada miji da ke ba, da kinzo lokacin da nike Aminene Mamman da bakiyi kuskuren yin zancen nan ba, kuma da yanzu misali zance zan auri Mijinki Wallahi ko iskar da ya debo ki ba zai kalla ba, ba zaki iya Kishi da ni ba, don indai bariki ne baki sam hanyarta ba, ni na biya Allo na, kuma na wanke shi, ki kula ki san kallar maganganun da zaki man" ta na kaiwa nan ta wucewarta don in ta tsaya tana iya kaima Saude Hannu, kuma ba zataji dadi na idan Alhaji Habib ya bar ganin kimarta. Ran Daddy bace yace "Saude are you out of your senses? Meya shiga k'wak'walwarki da har kika iya yin maganar nan, You are unbelievable" ya buga tsaki ya wuce daki shima, ita kuma Saude ta durkusa ta rushe da wani irin uban kuka. 7:14am Tunanin ta ta Ina zata fara shiga dakin Daddy har ta soma bincikar dakin bata tare da an ganta ba? Dabara ta fado mata ta mik'e ra shiga parlorn Daddy da Sallama ta ganshi Zaune da Nene suna Karin kumallo, k'osai ne da koko, Seebi na mamakin Nene yanda tayi katokato tayi kanekane tayi kakagida da kula da Abincin Alhaji Habib kamar itace matar shi, ta girgiza kai ta gaidasu, ya amsa mata cikin sakin Fuska, tace "Daddy ina fatar kana jin dadin Weekends dinnan" yace "Sosai ma, Nenenki tana cika da Abinci, baki ga har na fara tumbi ba" Nene ta chafe ai ni nan da ka ganni, ba daga baya ba na iya kula da mutane" Seebi ta kawar da Zancen kafin Nene ta 6allo musu ruwa tace "Daddy grant me the priviledge to make your room for you,i've been doing nothing ever since our stay, please dont say no" Nene tace "Uban me kike cewa? Ta danyi yak'e tace cewa nayi ya bani dama in gyara mai daki tunda yau Lahadi ba abunda nakeyi" Nene ta yashe hak'ora tace kinyi tunani" yayi murmushi jin dadi yana ganin Nasiba kamar Rafee'ah, yace "Seebi, you are my Daughter, like Rafeeq, kina da damar shiga inda ranki yakeso da sanda kikeso a gidan nan, balle dakin Daddynki, ki shiga ki gyara mun kinji?" Nasiba tayi murmushi ta shiga tana godia ga rabbi. "Oh Allah make it easy for me, Allah ka taimakeni ka nuna min abunda nake nema, ta shafa adduarta" nan ta fara da kewaye ta wanke toilet din tas, bayan ta duba duk lungu da sak'on Kewayen bata ga Komai ba, ta dawo daki, bata tsammani za a saka Wani abu a cikin Wardrobe, nan ta hau neme neme daga nan daga chan jawo nan, jawo chan, wayam, har ta fara gajia ta shiga gyaran Gado, haka kurum hancinta ya jiye mata wani wari, ta shiga shinshine shine, tayi Imani warin nan daga k'ark'ashin Gado yake, da k'yar ta samu ta daga katifar gadon me nauyin tsiya, gabanta ya fadi da ta hangi wani yar k'aramar tukunyar k'asa da aka daure da wasu zare, jikinta ya hau rawa, ya zatayi yanzu? Nan ta shiga karanto adduar da ta shigo bakinta tana k'arafafa ma kanta guiwa is now or never, Dole tayi jihadin dauko ko menene, nan ta samu wani kwarin guiwa tayi bismillah ta dauko tukunyar nan,da k'yar ta samu ta maida katifar tayi laying dinshi duk hankalinta baya jikinta, tayi saurin saka tukunyar a dustbin din dakin ta fita, har yanzu suna Zaune inda ta bar su, baki na rawa tace barin je in dauko zubar da bolan nan sai in kunno turaren kamshi, Daddy yahi murmushi yace "Bless you My Child" Kallo daya Nene ta mata ta san bata cikin hayaccinta batayi yunkurin binta ba, Hijab tayi sauri ta saka ta fita daga cikin gidan, jiki na rawagudu gudu sauri sauri ta bar gidan, ko lura da Baba maigadi batayi ba, ta samu Keke Napep. Da k'yar ta lalubo magana "Arriyadh Islamic Medicine zanje" yace "ki shigo" suka hau titi jikinta be bar rawa ba, cikin ikon Allah isarta tayi daidai da zuwan Mallam Usman, ya kalleta yace "Nasiba lafiya naganki da sassafen nan? Ince dai Rafeeq lafiyar shi lau?" bata iya bashi amsa ba sai dai ta mik'a mai dustbin din hannun ta, yana lek'awa ya shaidi Tukunyar nan ta tsafi ne, ya kalleta yace "ki kwantar da hankalinki Nasiba, you are safe, no harm may come to you here" Ajiyar Zuciya ta sake me k'arfi, mai gadi ya bude musu Asibitin suka k'arasa tare, wani daki ya shiga bayan ya umurce Seebi data tsaya waje, Mallam yayi 'yan adduoin shi tare da sakin wannan tukunyar kasa, nan take tukunyar ta fashe, wani ruwa me doyi tare da wasu kadangaru suka gani guda bakwai, kandangarun masu rai, k'okarin guduwa sukeyi Mallam ya shiga Karatun kurani mai girma, amma idan yayi nan sai wasu suyi chan a guje, be so su bar dakin, don in suka bar dakin akwai Matsala, Tun Mallam na fafatawa da kadangarun nan har ya fara gajia, ya dan bude murya yace "Mallam Salis dauko mun recorder din nan ka kunno ta ku ku're volume" jiki na rawa Mallam Salisu ya nufi office din, ganin kamar zai bata lokacine mallam ya vigaba da karanto Amanar Rasulu, Wani k'arfin guiwan da bata taba ji ba yazo mata lokaci daya, bata san lokacin da ta bude dakin da Mallam Usman ke ciki ba ta shiga tana karanta Ayatul kursiyy da karfi, tana kaiwa k'arshe ta bi Mallam da karatun Suratul Jinn suka hada baki wurin karatun nan, cikin ikon Allah K'adangarun nan suka fara wani irin ihu, chan suka fara fashewa sai kuma suka fara ci da wuta, Mallam da Seebi basu bar karatu ba, har sai da suka k'one kurmus ko toka ba'a gani. Daidai lokacin da Alhaji Habib yaji kanshi ya mai nauyi ya mike tsaye tare da rik'e kai, Ya fara ganin Nenen bibbiyu, dakin na juya mai, abubuwan da ya mance su yake tunanowa chan kuma ya zube k'asa, kuma sai ya tashi a zabure Dda k'arfi yace "AISHATU". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg5⃣5⃣ Nene tace "Alhaji Lafia? wacece Aishatu?" Alhaji Habib ya k'ura wa Nene ido kamar me son tunano wani abu, cikin sanyi yace "Ina zuwa Nene" ya zura takalman shi, ya wawuro key ya fita daga gidan, Nene ta bishi da ido tace "toufa Allah ya sa lafiya" ****** Zamewa tayi ta zauna a k'asa tana maida numfashi, tunda uwata ta haifeta, bata taba ganin abu makamancin na yau ba, ta sha jin irin labaran nan a littatafai, amam bata yi zaton haka abun yake ba, Mallam yace "Sannu Nasiba, kinyi k'ok'ari, ina mai murnan sanar dake cewa Asirin da akayi don Alhaji ya kare, Zuri'ar Lema sun yi dacen samunki a rayuwansu, kina musu wannan hidimar ba tare da sanin su ba,KE ALHERI CE NASIBA, Nasiba ta share hawayen da ke gangarowa ta k'ak'alo Murmushi tace "Nagode Mallam, Allah ya saka maka da Mafificin Alherinsa, ya raya zuri'ah" yayi murmushi ya amsa da Amin, Sosai yaji dadin adduointa, yace "tashi ki tafi gida" sukayi sallama ta wuto gida. ******** Guiwarta ta shiga Sosawa, don ta soma jin k'aikayi a wurin, da k'aikayin yayi yawa ta daga doguwar rigarta don ganin me yasameta a guiwan, wani k'urji ta gani a gurin kamar fitsarin gwauro, tayi tsaki ta shiga lailaya gurin don k'aikayin ya soma yawa, Meema tace "Sis lafiya kuwa? Ya naga kina soshe soshe? Tace "ke wani dan iskan kurji ya fito min a guiwa, sai dan banzan k'aikayi" Eyyer sannu Mom, barin dauko miki piriton kisha, zai bar kaikaryin" cewar Aneesa tare ea mikewa. ******* "Habibullah Lafiya? Yau kaine a gidan nan? Lafiya ma dai? Ya naganka haka da Farar Saffiyar nan?" baki na rawa yace "Mama ina Aishatu?" Mama ta murtuk'e fuska tace wata Aishatun?" cikin rawar jiki Alh Habib yace "Mama ku gafarceni, nasan nayi laifi gagarumi, amma ki taimakeni ki gaya min inda take, wallahi ina da bukkatar ganinta yanzu" Mama ta kalleshi galala, tacs "Habibu kenan, tin randa ka saki Aishatu shekara da watanni kenan baka ta6a zuwa gun mu gaishe mu ba, baka zo ka ga lafiyar mu ba, balle kace tana ina, ka tambayi lafiarta, ko makamancin haka, ai inace Habibu ko da baka auri Aisha ba mu Iyaye ne a gunka, amma da yake ba mu isa da kai ba, dukda Rabon da Allah ya baku na 'ya'ya, bamu ci albarkacin su ba, so hakan ma yanzu ba ruwanka da mu, ba kai kayi aure ba? Ba ka dauke mu komai ba, sai ka je chan, ba kai ba Aishatu" Hawayen da yake 6oyo ne suka shiga reto a fuskar shi, Muryan Baba Tijjani yaji inda yake cewa "Ke Lami, ya da daga murya da Sasafen nan?" ganin Alhaji Habib durkushe gaban Maman Mami ya sa shi mamaki, "Habibullah a gidan nan?" Yauwa Alhaji ka ganshi nan, don ya raina mu, ya raina mana azziki sai yau ya zo neman Aishatu, dube shi nan"nan ta cigaba da zazzaga Masifa, ta inda take shiga ba ta nan ta ke fita ba, da Baba Tj ya ga abun nata yayi yawa ya kalli Daddy yace "yi tafianka Habib, zan neme ka" kamar wani k'aramin yaro ya rausayar da kai Alamun a tausaya mishi, Baba Tj yace "kar ka damu, Zan kiraka" jiki ba k'wari ya fice sum sum. Nan Baba TJ ya tasa Mama gaba yana mata Nasiha, bw kamata tayi haka ba, godia ya kamata tayi da ga maido Habib kan turbar gaskia, shi dama ya san ba yin shi bane, nan ya cigaba da mata Nasiha. ********* Hawayen kunci yake tayi, Ji yayi ba zai iya wani kwanan ba tare da ya Dora Aishatu a kanshi ba yau duk inda take sai ya ganota, he'll be with her again ya fada toilet dom yin wanka, dole zaije duk wani Gidan da ya san Aisha na zuwa nemanta. Nasiba ta fito daga wanka ta na shafa mai Nene ta shigo dakin, tace ke kuma daga ziddo shara kikayi wani gurin, ina kikaje ne?" Seebi tace "ina fa? Ina nan mana" Nene ta harareta tace to banfi minti 10 da barin dakin nan ba, na ga bakya nan, na fita har k'asa nemanki, ban ganki ba, don ki renan wayau zakice kina nan" Seebi dai tayi shiru ta cigaba da shafa man ta, don tasan ta k'ara magana tsafe Nene zata dago ta. Nene ta fice daga dakin ta sauk'a k'asa gun Baba maigadi, don taya shi zama, bayan 'yar mahawarar su, ya kece mata ya lura Alhaji na cikin Matsala, dazun ya fita da damuwa, yanzu kuma ina ganin damuwar shi ta k'aru, bansan me ya auku ba ,Nene tayj dan jim ta mik'e tace ina zuwa. ***** Hannu bibbiyu ta iske shi yayi tagumi tace "Alhaji Lafiya? Ya na ganka haka?" kamar jira yakeyi, ya fashe da kuka, yace "Nene nayi kuskure, nayi kuskure babba, wallahi bansan ya akayi na saketa ba, bansan ya akayi ban nemeta duk tsawon lokacin nan ba, bansan ya akayi na mance duk wani abu da ya dangance ta ba, bansan ya akayi na daina tunanin ta ba, gashi ban san inda take ba yanzu, bansan inda zan shiga nemanta ba, bansan ta inda zna fara ba" Nene ta tausaya mai sosai, ta shiga lallashin shi, tana bashi baki, chan kuma ta danyi jim sai tace "wai wa kake nufi? Wai Mamin su Dunkum? Jin yanda take magana ya sashi daga kai, yace "eh ita" ta shiga tafa hanayenta tace "toh share hawayenka, kakarka ta yanke sak'a, na san inda take" zumbur ya tashi baki na rawa yana mamakin ina Nene ta san Aishatun shi? Ya kawar da mamakin shi ya shiga tamabyar ta inda take, Nene tace "ai ni sai dai in mutum be gaya min matsalar shi ba, da ikon Allah zan magance mai" ba wannan yake son ji ba, yace donAllah ki gaya min, tana ina? Wani hali take? tace "ina zuwa" ta fita daga Parlorn sai gata ta dawo da Seebi, Seebi na tambayarta lafiya? tace "Ke ko ba Mamin dunkum kike bani a waya mu gaisa ba?" Seebi ta kalli Nene ta juya ta kslli Alh Habib da ya zura mata ido yana neman jin Amsarta, ta gyada kai tace "itace" Nan ya rude, "tana ina? Ya take? Is she alright? Seebi my child, tell me where is she now? Where can i find her please?" Nasiba tace "Daddy calm down, shes fine, tana Kaduna" "Kaduna? Gun wa? DanAllah kice min batayi aure ba" Nasiba tace "batayi Aure ba, she's been waiting for you all this while, tana nan tana jiranka Daddy" Wani Murmushi ya sake yace "I am coming for her, tell me ina kika santa?" tace "Mak'otan mu ne a Kaduna" Allahu Akbar, i shall go to Kaduna now" har ya juya cikin daki ya juyo ya kalli Seebi, yace "KE ALHERI CE a gareni Seebi thank you" Nene tace "Kadunan zakaje? Aikuwa dama ina so inje inga Mahammadu, ko zan biyoka?" cikin Nishadi yace "me zai hana, ai kawai kije ki shirya Nenenmu", "wani shiri zanyi? ai a shirye nake" Seebi tayi raurau kamar zatayi kuka, tace "Nene na zaki barni a nan ne?" Nene ta zaro ido tace "Rufa min asiri in mutu maza su rufeni, ya zanyi gigin barinki gurin dangin matsafa? Ai kafata kafarki, muje ki shirya" Seebi ta zaro ido tace bangane dangin matsafa ba, Nene ta tabe baki, tace "Zan shak'a miki muje mu shirya". Parlorn sama ya iske su, yace "kun shirya? tace "ai sai tafia kawai" yace "to bismillah" yace "bari in shiga inyi ma Saude Sallama in gaya mata na tafi Kaduna" da sauri Nene tace "ai ta fita yanzu tace sauri takeyi shiyasa ba zata tsaya kuyi bankwana ba, amma tana mana Allah ya tsare" Baki Sake Seebi ta tsaya kallon Nene da take ta karanto k'arya, Sauden da ke cikin daki ita da Aneesa sun koma Baccin safe, Meema kadai ce ta fita, ran Alhajk ya 6aci, baya son fitan da Saude ke yawan yi, tsaki yayi yace "mu tafi" Nene kuwa Allah allah takeyi su tafi don bata san Alhaji ya gana da Saude, gudun kar a samu Matsala balle idan ta san gurin tsohuwar matarshi zaije. Nan suka fito a tare suka shiga bayan Sienna, Alhaji ya kwalawa direban shi kira, Baba maigadi ya wangale Gate, Nene ta wangale baki tana ma baba Maigadi Byebye. Waya ga kauyus a Sienna. KADUNA (Toh kuyi hakuri da wannan, Lokacin wahalan Wuta yazo, muna Samun matsalan wuta so ina rashin Charge, zan cigaba daga nan InshaAllah) 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg5⃣5⃣ Nene tace "Alhaji Lafia? wacece Aishatu?" Alhaji Habib ya k'ura wa Nene ido kamar me son tunano wani abu, cikin sanyi yace "Ina zuwa Nene" ya zura takalman shi, ya wawuro key ya fita daga gidan, Nene ta bishi da ido tace "toufa Allah ya sa lafiya" ****** Zamewa tayi ta zauna a k'asa tana maida numfashi, tunda uwata ta haifeta, bata taba ganin abu makamancin na yau ba, ta sha jin irin labaran nan a littatafai, amam bata yi zaton haka abun yake ba, Mallam yace "Sannu Nasiba, kinyi k'ok'ari, ina mai murnan sanar dake cewa Asirin da akayi don Alhaji ya kare, Zuri'ar Lema sun yi dacen samunki a rayuwansu, kina musu wannan hidimar ba tare da sanin su ba,KE ALHERI CE NASIBA, Nasiba ta share hawayen da ke gangarowa ta k'ak'alo Murmushi tace "Nagode Mallam, Allah ya saka maka da Mafificin Alherinsa, ya raya zuri'ah" yayi murmushi ya amsa da Amin, Sosai yaji dadin adduointa, yace "tashi ki tafi gida" sukayi sallama ta wuto gida. ******** Guiwarta ta shiga Sosawa, don ta soma jin k'aikayi a wurin, da k'aikayin yayi yawa ta daga doguwar rigarta don ganin me yasameta a guiwan, wani k'urji ta gani a gurin kamar fitsarin gwauro, tayi tsaki ta shiga lailaya gurin don k'aikayin ya soma yawa, Meema tace "Sis lafiya kuwa? Ya naga kina soshe soshe? Tace "ke wani dan iskan kurji ya fito min a guiwa, sai dan banzan k'aikayi" Eyyer sannu Mom, barin dauko miki piriton kisha, zai bar kaikaryin" cewar Aneesa tare ea mikewa. ******* "Habibullah Lafiya? Yau kaine a gidan nan? Lafiya ma dai? Ya naganka haka da Farar Saffiyar nan?" baki na rawa yace "Mama ina Aishatu?" Mama ta murtuk'e fuska tace wata Aishatun?" cikin rawar jiki Alh Habib yace "Mama ku gafarceni, nasan nayi laifi gagarumi, amma ki taimakeni ki gaya min inda take, wallahi ina da bukkatar ganinta yanzu" Mama ta kalleshi galala, tacs "Habibu kenan, tin randa ka saki Aishatu shekara da watanni kenan baka ta6a zuwa gun mu gaishe mu ba, baka zo ka ga lafiyar mu ba, balle kace tana ina, ka tambayi lafiarta, ko makamancin haka, ai inace Habibu ko da baka auri Aisha ba mu Iyaye ne a gunka, amma da yake ba mu isa da kai ba, dukda Rabon da Allah ya baku na 'ya'ya, bamu ci albarkacin su ba, so hakan ma yanzu ba ruwanka da mu, ba kai kayi aure ba? Ba ka dauke mu komai ba, sai ka je chan, ba kai ba Aishatu" Hawayen da yake 6oyo ne suka shiga reto a fuskar shi, Muryan Baba Tijjani yaji inda yake cewa "Ke Lami, ya da daga murya da Sasafen nan?" ganin Alhaji Habib durkushe gaban Maman Mami ya sa shi mamaki, "Habibullah a gidan nan?" Yauwa Alhaji ka ganshi nan, don ya raina mu, ya raina mana azziki sai yau ya zo neman Aishatu, dube shi nan"nan ta cigaba da zazzaga Masifa, ta inda take shiga ba ta nan ta ke fita ba, da Baba Tj ya ga abun nata yayi yawa ya kalli Daddy yace "yi tafianka Habib, zan neme ka" kamar wani k'aramin yaro ya rausayar da kai Alamun a tausaya mishi, Baba Tj yace "kar ka damu, Zan kiraka" jiki ba k'wari ya fice sum sum. Nan Baba TJ ya tasa Mama gaba yana mata Nasiha, bw kamata tayi haka ba, godia ya kamata tayi da ga maido Habib kan turbar gaskia, shi dama ya san ba yin shi bane, nan ya cigaba da mata Nasiha. ********* Hawayen kunci yake tayi, Ji yayi ba zai iya wani kwanan ba tare da ya Dora Aishatu a kanshi ba yau duk inda take sai ya ganota, he'll be with her again ya fada toilet dom yin wanka, dole zaije duk wani Gidan da ya san Aisha na zuwa nemanta. Nasiba ta fito daga wanka ta na shafa mai Nene ta shigo dakin, tace ke kuma daga ziddo shara kikayi wani gurin, ina kikaje ne?" Seebi tace "ina fa? Ina nan mana" Nene ta harareta tace to banfi minti 10 da barin dakin nan ba, na ga bakya nan, na fita har k'asa nemanki, ban ganki ba, don ki renan wayau zakice kina nan" Seebi dai tayi shiru ta cigaba da shafa man ta, don tasan ta k'ara magana tsafe Nene zata dago ta. Nene ta fice daga dakin ta sauk'a k'asa gun Baba maigadi, don taya shi zama, bayan 'yar mahawarar su, ya kece mata ya lura Alhaji na cikin Matsala, dazun ya fita da damuwa, yanzu kuma ina ganin damuwar shi ta k'aru, bansan me ya auku ba ,Nene tayj dan jim ta mik'e tace ina zuwa. ***** Hannu bibbiyu ta iske shi yayi tagumi tace "Alhaji Lafiya? Ya na ganka haka?" kamar jira yakeyi, ya fashe da kuka, yace "Nene nayi kuskure, nayi kuskure babba, wallahi bansan ya akayi na saketa ba, bansan ya akayi ban nemeta duk tsawon lokacin nan ba, bansan ya akayi na mance duk wani abu da ya dangance ta ba, bansan ya akayi na daina tunanin ta ba, gashi ban san inda take ba yanzu, bansan inda zan shiga nemanta ba, bansan ta inda zna fara ba" Nene ta tausaya mai sosai, ta shiga lallashin shi, tana bashi baki, chan kuma ta danyi jim sai tace "wai wa kake nufi? Wai Mamin su Dunkum? Jin yanda take magana ya sashi daga kai, yace "eh ita" ta shiga tafa hanayenta tace "toh share hawayenka, kakarka ta yanke sak'a, na san inda take" zumbur ya tashi baki na rawa yana mamakin ina Nene ta san Aishatun shi? Ya kawar da mamakin shi ya shiga tamabyar ta inda take, Nene tace "ai ni sai dai in mutum be gaya min matsalar shi ba, da ikon Allah zan magance mai" ba wannan yake son ji ba, yace donAllah ki gaya min, tana ina? Wani hali take? tace "ina zuwa" ta fita daga Parlorn sai gata ta dawo da Seebi, Seebi na tambayarta lafiya? tace "Ke ko ba Mamin dunkum kike bani a waya mu gaisa ba?" Seebi ta kalli Nene ta juya ta kslli Alh Habib da ya zura mata ido yana neman jin Amsarta, ta gyada kai tace "itace" Nan ya rude, "tana ina? Ya take? Is she alright? Seebi my child, tell me where is she now? Where can i find her please?" Nasiba tace "Daddy calm down, shes fine, tana Kaduna" "Kaduna? Gun wa? DanAllah kice min batayi aure ba" Nasiba tace "batayi Aure ba, she's been waiting for you all this while, tana nan tana jiranka Daddy" Wani Murmushi ya sake yace "I am coming for her, tell me ina kika santa?" tace "Mak'otan mu ne a Kaduna" Allahu Akbar, i shall go to Kaduna now" har ya juya cikin daki ya juyo ya kalli Seebi, yace "KE ALHERI CE a gareni Seebi thank you" Nene tace "Kadunan zakaje? Aikuwa dama ina so inje inga Mahammadu, ko zan biyoka?" cikin Nishadi yace "me zai hana, ai kawai kije ki shirya Nenenmu", "wani shiri zanyi? ai a shirye nake" Seebi tayi raurau kamar zatayi kuka, tace "Nene na zaki barni a nan ne?" Nene ta zaro ido tace "Rufa min asiri in mutu maza su rufeni, ya zanyi gigin barinki gurin dangin matsafa? Ai kafata kafarki, muje ki shirya" Seebi ta zaro ido tace bangane dangin matsafa ba, Nene ta tabe baki, tace "Zan shak'a miki muje mu shirya". Parlorn sama ya iske su, yace "kun shirya? tace "ai sai tafia kawai" yace "to bismillah" yace "bari in shiga inyi ma Saude Sallama in gaya mata na tafi Kaduna" da sauri Nene tace "ai ta fita yanzu tace sauri takeyi shiyasa ba zata tsaya kuyi bankwana ba, amma tana mana Allah ya tsare" Baki Sake Seebi ta tsaya kallon Nene da take ta karanto k'arya, Sauden da ke cikin daki ita da Aneesa sun koma Baccin safe, Meema kadai ce ta fita, ran Alhajk ya 6aci, baya son fitan da Saude ke yawan yi, tsaki yayi yace "mu tafi" Nene kuwa Allah allah takeyi su tafi don bata san Alhaji ya gana da Saude, gudun kar a samu Matsala balle idan ta san gurin tsohuwar matarshi zaije. Nan suka fito a tare suka shiga bayan Sienna, Alhaji ya kwalawa direban shi kira, Baba maigadi ya wangale Gate, Nene ta wangale baki tana ma baba Maigadi Byebye. Waya ga kauyus a Sienna. KADUNA Rafeeq ya iso gidan Uncle Zaid da misalin k'arfr 9:30 na safe, dauke yake da breakfast dinshi da Mami ta hada musu, shi yace zai kawo ma Zaid tunda ba zai samu zuwa yin break din ba a gidan Mami wai kanshi na ciwo. Rafeeq da mamaki ya ga Zaid garas yana kallon TV ya dai daure yace"Good Morning uncle Zaid" ba tare da ya kalle shi ba yace " Ka tashi lafiya? Ina Mahmud?" "Lesh ya tafi gaida wani Uncle din Mom a Unguwar Dosa" Zaid yace "Serve me" Rafeeq ya kalli Uncle Zaid kamar me son gano wani abu tattare dashi amma ya kasa gane komi, ya shiga zuba mai Tea a cup, ya zuba mai Dankali da wainar k'wai ya tura mai kusa dashi, Zaid ya dan gyara zama tare da cewa "Thanks" Rafeew ya zauna kusa da shi ya dauki remote control ya sauya channel, shi kuwa Zaid ya duk'ufa da yin kalacin shi. ******* "I know you love her" Rafeeq ya dan kallo shi yana tunanin ba da shi Uncle Zaid yake ba, amma ganin shi yake kallo ya sa shi gane dashi yake, tare da yamusta fuska yace "What?" Zaid yayi murmushi yace "you love her right? Ya k'ara turbune fuska yace "Wai wa?" ba tare da shakku ba Zaid yace "Seebin Nene kake so" Rafeeq cikin borin kunya ya mike a zafaffe, what nonesense uncle Zaid? What are you saying?" nake son wa? Wannan yarinyan? Me zanyi da ita? This is ridiculous" Murmushi me sauti Zaid yayi yace "Chill Feeq, theres no need to get upset, ba abun tada jijiyoyin wuya bane, na san kana sonta, i heard everything you discussed with Mahmud Yesterday, dama na dade da Zargin hakan, amma ban taba tunkarar ka da maganar ba, naji komai Feeq, so kwantas kaji" Kai ya dafe da hannu biyu, takaici kamar ya kar shi, Uncle Zaid ya ji su kenan? Theres no need to lie, theres no need at all, Rafeeq yace "Uncle Zaid, abun da kaji jiya is Nothing, donAllah kar kayi zaton wani abu, i'm so sorry ka yafe min, i cannot love her, shiyasa ma ba ruwana ni da ita, Uncle Zaid please kar ka dauka wani abun ne" Zaid ya rik'o hanayensa biyu yace "Ya Isa boy, Calm down, ni fa baka min laifi ba, listen to me, I was happy da naji zancen nan jiya, it got me thinking the whole of yesterday, like tunda kana cikin hali ma k'unci da duhu, kuma da kanka ka hango haske da farincikin ka, to me zai hana mi baka abun da kake so, we Always want your Happiness Rafeeq Lema, and if Seebi makes you Happy Rafeeq then you can Have her na barka maka ita, all you have to do is Ka gama School kaje Service, and i get you married then, i know itama tana sonka" "Enough, enough Uncle Zaid, you dont have to to this, waya ce maka tana sona? Tsaya ma what if she loves me too? Sai me? Sai me in itama tana sona? Kana tace wa kabar min ita,For crying out loud I am just 24, ban isa Aure ba, ko Soyayyar zamani kake so muyi da ita? Tunda ni ba aurenta zanyi ba, maganar gaskia, You love her so much Uncle Zaid, i know it, you took care of her, ka damu da damuwarta she's very good for you,she deserves you, and you deserve her, zata kula min Da Angel dina, bana son Angel tayi kukan maraicin uwa, nasan Nasiba zata kula da ita as if shes her own, zata zama Uwa gareta, you and Nasiba suit eachother please Uncle Zaid stop this now kajih?" Zaid yayi murmushi yace "Boy, ba wani abu bane don naso Yarinyar da kake so, ba wani abu bane don na kula da ita, ba wani abu bane don na damu da damuwarta, we can take it as i did it for you, i loved her for you, i took care of her for you, yanzu na bar maka abunka, is now your time to care for her and love her, and like i said, sai ka gama Service zan maka Aure, kaga itama a Lokacin karatun ta ya mik'a, i want the best for you, i want you to be Happy" fuskar Rafeeq ta fara sauyawa zuwa Ja, ya murtuk'e yace "for how long will you keep choosing My happiness over yours Uncle Zaid? Sai yaushe zaka daina Danne farincikin ka saboda nawa? For how long? Listen Umcle Zaid, you've made alot of sacrifices for me i know, now is time to make sacrifice for you, its time for you to be Happy" Zaid ya girgiza kai yace "No Rafeeq, please No" Rafeeq ya dan sassauta murya muryan chan k'asa, yace "Will you for once stop thinking about Rafeeq lema? I'll be fine, eventually, think about yourself for once Uncle Zaid, its Time for you to be happy" Zaid ya girgiza kai yace "Listen to me Feeq" Rafeeq ya katse shi ta hanyar daga mai hannu muryar cike da fushi yace "no you listen to me, Kasanni fiye da kowa, you want me to be Happy? Then Marry her, that would make me Happy, idan ko ba haka ba, Na rantse da Allah, idan baka auri Nasiba ba, to wallahi bazan aureta ba, you cant have her, Lord Help me! i cant have her as well, do everyone a favour and Lets not lose her both, with all due respect Uncle Zaid, this is my warning to you". Yana kaiwa nan ya juya ya bar Parlorn ya bar Zaid tsaye cike da mamakin Rafeeq. *12:05pm* "Assalam Alaikum" Mami ta fito da sauri jin muryan wata kamar Nasiba, ta fito rik'e da Serving spoon don tana kitchen tana Abincin Rana, "Waalaikum Salam, ga diyata ga diyata" ta rungume Nasiba, Nasiba na ta dariya" Mami ta kalli matar da ke tsaye bayan Nasiba, ta na da tabbacim itace Nene don tsananin kamarta da Baban Anan, tace "sannu da zuwa Nene" Nene ta amsa da fararta, Ayman ta fito daga parlorn da gudu ta ma Nene oyoyo don ta ganr, Nene ta dagata sama tana mata tawai" ku zauna Nene, Seebi tace "Aa Mami, isowar mu kenan, ko gida ba mu shiga ba, nace bari mu fara yo wa nan" Mami tace "Allah sarki, bari In gama Abinci zan shigo" Nene zatayi magani Nasiba tayi saurin cewa "Actually Mami, there's someone outside who wants to talk to you" Mami tace ni? Waye? Nasiba tace "Yana neman izini shigowa" Mami tace shigo dashi, barin in sako Mayafi, tace "toh shikenan" ta ja hannun Nene da ke rik'e da Ayman suka fita, ita kuma Mami ta shiga cikin don dauko mayafi. ******* "Toh Alhaji Habibu, kayi ta maza ka shiga, ka nuna mata kai namiji ne, kar karaya da duk abunda zaka ji ko zaka gani, ka karanta Li illafi kuraysh, Allah ya sa komai ya zo da Sauk'i" cewar Nene, Daddy ya jinjina kai yace "InshaAllah Nene, komai zai zo da sauk'i" Seebi tace "Goodluck Daddy, she's waiting for you". Ya shiga gidan su kuma suka wuce gidan Abbi. ********* Ta fito tana gyara zaman gyalenta, ta shiga da Sallama, k'amshin turarenshi ya daki hancinta, da sauri ta dago kai ta kalli Mutumin da ke zaune kan kujera, Haske kyau da Kiban da ya k'ara be hanata ganeshi ba, hannunta ta sa a idonta ta murje su don gani take mafarki takeyi, ko kuma gizon da ya saba mata ne, har yanzu yana zaune be lura da shigowarta ba, gani tayi shi din ne, daidai nan ya dago kai ya ganta, da sauri ya tashi tsaye, murya da jikinshi na rawa yace "Shatu nah" wasu zafaffan hawaye suka soma kwaranyowa daga idaniyarta. Shima hawayen ya keyi, sai da sukayi me isar su kafin ta juya ciki ba tare da sunyi magana ba, "Shatu na DonAllah ki tsaya" ya bita har cikin kitchen din, Abincin ta ta ke juyewa a Cooler tana share hawaye. "Aishatu, nasan na miki laifi, na son na bata ran ki, nasan na miki ba daidai ba, amma ki yarda dani, Everything happened sooo fast, bansan dalilin da ya sa na yanke hukunci cikin fushi ba, bansan dalilin da ya sa na Sakeki ba, Wallahi na yarda dake, na san ba zaki aikata wannan mumunnan aika aikan ba, duk da abun a Sark'e yake Allah kadai zai warwareshi, bansan na furta miki kalmar Saki ba, sometimes inaji a jikina kamar controlling dina akeyi" Mami ta share hawayenta ta kalleshi a raunane tace "Habibi, meyasa sai yau kazo? I've waited for you my life" Kneel down yayi da cewa "Wallahi i dont know why i never cme back for you, i'm sorry for taking so long, but i'm here now, i'll be with you again and Nothing can seperate us now" ita dai Mami kuka takeyi, ta san tayi missing tsohon mijinta sosai kuma idan ba shi ba ba zata iya rayuwar Aure da wani ba, tunda har ya bata hak'uri na sakinta da yayi, da rashin binciken da beyi ba dukda ya ga abu clearly, dukda ba wanda zai fidda ta daga kangin Sai Allah, to meyasa ba zata yafe mishi ba? Ai tunda be k'yamaceta ba, itama bazata k'yamace shi ba, a hankali tace "ka tashi donAllah be kamata ka durkusa min da guiwowin ka ba, Na yafe maka Habibi, ka yafe min, Wallah bansan komi da ya faru a wannan ranar ba" da sauri ya mik'e tare da hugging dinta, for the first time in a very long time suka sauke numfashi a tare, sunyi missing juna, yace "shhh, kar kice komai, na san ko ke wacece Shatu na, amma na miki Alkawarin gano gaskian lamarin" tace "its been long Habibi let it go" yace "Never, i'll see to it that whoever is behind this will pay" wani tunani yazo ma Mami, da sauri ta raba jikinta da nashi, tace "Sorry, we cant touch eachother, ba aurenka a kaina" kanshi ya dafe yace "Oh Allah, now i cant even touch my wife?" tayi murmushi tace "Your ex wife, bazawara ce ni, ina da zaurawa da yawa, mai rabo ka dauka" ta k'arashe tana mai zolayar shi, ya harareta yace "me wuri yazo me tabarma ya nade, inshort i cant wait any longer, Nearby mosque za a daura auren mu bayan Azahar, ba zan iya bari har in koma Katsina ba" Mami ta tabe baki tace sai Walliyi na ya amince" Daddy yace "Walliyin ki? Wanene shi? Na san dai walliyin ki ya rasu" Mami tace "Zaid ne Waliyyi na" Daddy ya kalleta da mamaki yace "Zaid? Wani Zaid?" Murmushi tayi tace "Zaid Iro Lema My saviour" "bangane ba?" gyara tsayuwarta tayi ta kwashe labarin tun randa ta bar gidan shi zuwa yau, hawaye yakeyi yana k'ara rok'on ta gafara, wani Son Zaid na k'ara shiga ranshi, be taba tunanin Zaid na da kaifin tunani kamar haka ba, Lallai Zaid ALHERI ne, wayarshi ya ciro tare da dialling Numbern Zaid, ringing sukaji kusa dasu a tare suka waiga, Zaid, Rafeeq da Maalesh tsaye a kofar kitchen, Zaid yace "Welcome back to your Senses brother" sukayi daria, Daddy yace dole kayi welcoming dina, ya rungume Zaid sosai, yace "Thank you Brother, Allah ya biyaka" Murmushi yayi ya kallo Mami yace "kuka ya k'are ko Mami? Tayi Murmushi tana share hawayenta, ganin sabon kuka zata fara Feeq yyi saurin cewa "What a reunion in the kitchen" Sukayi daria, ta kalli Daddy tace "kuje Parlor i'm coming out with lunch" Daddy ya kalleshi yace "Okay Zaid and His sons Out you go " sukayi daria duka suka fice. Taimaka mata yayi da tray din, ita kuma ta dauko sauran kayan suka fito Parlor, Rafeeq ya kalli Mahaifansa, yanda ya gansu ya ji dadi, hakan ya faru ne saboda Uncle Zaid, me zai ma bawan Allahn nan ya ji dadi shima, dole ya samo mai farinciki a duk inda yake" ******** Su biyar zaune a Kan dinning suna cin Abinci like before, Daddy yace "R-lema nikam yaushe ku kazo Kaduna? Kamar ba zai tanka ba yace "Jiya" "oh shine ba ka min sallama ba?" a tak'aice yace "lokacin da na fito baka tashi bacci ba" Zaid yace "Mami kinga Nenemu ko?" tace "aikuwa na ganta, waya gaya maka tazo?" yace "Ai da mukayi waya da Seebi ta shaida min sun rako Yaya gunki ita da Nene" Rafeeq ya zaro ido yace "Wait, Neh-neh na Kaduna? " Ehmana" Daddy kai ka kawota? Saboda mene? Daddy do u have to bring her along? Omg, dole in koma Katsina like right now" Rafeeq my child me yayi Zafi haka?"Mami that woman is the most craziest person i've ever seen, she's Delusional " Mami taba ta rai tace "ka min shiru, tsaraka ce? Dont talk about her like that, me ta maka ne? Maalesh ya chafe, ya basu labarin haduwar su ta k'arshe da Nene daria sukeyi sosai banda Rafeeq da ya daure fuska don shi be ga abun daria ba, Daddy yace " Yihuhu ina dunkum din yake" aiko suka sake tuntsirewa da daria, Rafeew ya tashi ya dibi abincin shi a plate ya bar musu wurin" Zaid yace kunga ku rabun min da Yaro na ko ince ba zan bada Auren ba" da sauri Daddy yayi shiru Mami da Maalesh na daria k'asa k'asa. ****** Bayan Zaid ya shaida ma Baba Tj komai, Baba Tj yace "Zaidu ai kaine Uban Aishatu yanzu, na baka wuk'a da nama, duk yanda kayi daidai ne" Zaid yaji dadi, baba Tj ya sa musu Albarka. Bayan Sallahr Azahar ne Mutanen Unguwar Malali da suka halarci Sallahr Azahar a Massalcin ne suka Shaida Auren Aishatu Tijjani, da Angonta Habib Iro Lema bisa sadaki Naira dubu 50. Inda Zaid ne Waliyin Amarya, Abiin Seebi ne Waliiyin Ango. Daddy baki ya ki rufewaji yakeyi kamar yau ne aurenshi na farko. 4:30pm Nene ta tasa Mami a gaba tana mata fadan Sakaci da addua, da yanda ta bari har aka kulla mata sharri bata ji bata gani ba, da yanda ta jefa rayuwar danta a garari, "to salan in kin koma yanzu ki k'ara Sake, har a sake kulla maki wani mugun sharri, sai fa kin mike tsaye don kina da kishiya, ai mu ba boka ba Mallam muke cin uban mutum, ta inda Nene ke shiga ba tanan take fita ba, in kunga yanda takeyi sai ku rantse da Allah ita ta haifi Mami ko kuma ta dade da sanninta kamar ba yau suka fara ganin juna ba, A ganin Nene Sakacinta ne Ya sa aka mata Asiri kalakala, duk da bata fito tace masu ga abunda ta sani game da Saude ba, sun dago wani abu, amma ko wa ya share" Nasiba na Allah allah kar Nene ta ballo musu ruwa, ta cigaba"ai akwai magungunan da zan baki, sai dai mun kebe don kawar zaman taki 'yar yi ce" kunya ya kama Ummi, Seebi da Mami, don Nene ta fara sakin layi, Surutun ta suka fara isar Rafeeq gashi Daddy ya hanashi fita, ya buga tsaki tsut hankalin ta ya koma kanshi, tace "Kai dunkum dangin tsaka, ka fita idona, kar ka sake min Tsaki, kar ka ga ka tsira wanchan karan, yanzu na ritsa ka sai dai uwarka ta sake haifo wani d'an"duk suka rike dariar su, Zaid yayi murmushi yace "Nenenmu da har ina cewa Ke zaa kai yar zaman dakin Rafeeq?" tace "Yo ai duk matar da ta auri Dunkum ta zama abar tausayi, don Zama da dunkum Sai Ni, ni kadai na san maganinshi, amma idan ya auri mace shirushiru kamar Seebi zata mutu da bakin ciki, don irinsu akwai kunsa bakinciki, kyanta ya samu irin mu" Ummi tace "to ko ke za a aura mai?" "Ai Ko wallahi da duk dare sai na kulleshi daki na ci ubanshi" Abbi da kamar ya nitse kasa don kunya yace "Nene ba na hanaki irin maganganun nan ba?" ta kallo danta galala tace "Nabari, ubana Mamman" Zaid yace "kiyi hakuri Nenenmu" tace "yiriri angon bana, nayi hakuri, kuma dai tsaya ai tunda an hadu haka ai gwara a sa bikin su Zaidu bawan Allah da Seebina ko? Daddy yace "Ashe soyayya akeyi su Baban Rafeeq" Zaid ya rasa ta cewa, Daddy yace "Abu yayi dadi, barin ji ta bakin diyata, Kinason sa Seebi?Nene ta chafe tace"tsohon zance, in kaji yandatake narke mai tana wannan abu a waya sai ka rike baki, da baka sha wahalar tambyarta ba" Seebi kamar k'asa ta tsage ta shige ciki, Nene ta gama kasheta, Abu yayi kyau, to Mallam ya kagani? A sa bikin yanzu?" Abbii yace duk yanda kukayi daidai ne, Daddy yace to tunda gamu duka anan, sai a saka ko? Zaid yayi saurin cewa" Yaya, donAllah minti daya". ******* "Wani irin magana ce wannan kakeyi Zaid? Wa zai ma Rafeeq aure yanzu? DonAllah bar zancen nan, banson shashancin banza, kai Nasiba take so, kuma kai zan bata, shi kuma idan ya isa aure ya samo wata chan ko yar gidan wanene zan aura mai ita" Daddy ya shige ya bar Zaid a k'ofar parlo, ba me fahintar shi. A nan aka sa biki bayan nasiba ta gama Level 1, dukaduka be wuce Wata Daya da kwanaki ba, Abbi yace "Alhaji da ka bari anyi komai a tsanake, ina ganin kamar wata 1 yayi kusa" Daddy yace "kar ka damu Mallam, daurin aure kawai nake bukata kazo, don bikin nan na YAR GATA CE, da dan gata" sukayi daria, Rafeeq ya dago ya kalli Seebi, itama shi din take kallo, suka k'urawa juna ido sun kasa karantar junarsu. ******** "Shatu na ina muka kwana? Ni bazan barki nan Kaduna ba, don ba zan iya hure rashin ki a kusa dani ba kina da option din inda zaki zauna, ki zabi Daya daga cikin gidajen da zaki zauna a Katsina, don gobe zamu wuce gaba ki daya saboda karatun yaran nan" Mami tayi murmushi tace "Habibi na, ba sai na zabi ko wani gida ba, I want to live where it all started, nan Main house din, There are lot of Wonderful Moments i shared with all my loved ones there I want to live there again, that is if my room is not Occupied yet" ya rungumeta yace "your Room is waiting for you, Thank you shatu, i love you so much" i love you more Habibi" yace "We leave tomorrow" WasheGari * Katsina* Tun daga bakin gate Nene ke rangada Guda, bayan ta Nade Mami cikin lafaiyarta,Ummi na rike da Hannun Mami, Mom din Maalesh da hajjo suka iso gidan, dama Maalesh ya kirata lokacin da suka shigo KT yace "tazo gidan su Rafeeq tarban k'awarta" ta rungume kawarta suna hawaye, Nene tace "Hajia yau ba ranar kuka bane yau ranar kunsawa wasu bakin ciki ne" kamar ya?" matsa ki gani, wanda be da hanci ya ja gefe, Nene ta shiga rangada guda, Hajjo ta tayata gabaki daya suka kama hanyar shiga gidan. "Meema me nakeji haka?" Sis guda ne!" anya gidan nan ne kuwa? Jin gudar na matsowa kusa ne ya sasu tabbatar da hakan, Saude ta sauko da kgar daga kujera don zuwa ganin ikon Allah, Meema tace "Sis ina zakije da wannan kafar taki duk ya ja ruwa" Bata kulata ba, ta shiga dangyasawa tana cije baki ta fita daga dakin, ji tayi gudar na kusantosu, sai ganin Nene tayi da wasu mutane biye a bayanta,banda Seebi ba wanda ta shaida, Saude ta daka wata uwar tsawa "Ke jarababiyar tsohuwa, wani salon iskanci ne wannan? Zaki shigo mana gidan kina guda, sai kace gidan biki wanda suka dauko Amarya" Nene tace "banda abunki ai duk inda akaji guda an sna da Amarya a gun" Saude cikin rashin fahimta tace bangane ba, ina fa zaki gane bayan kanki cunkushe yake da duhu, to Amarya ce aka kawo, Amarya Habibu Lema, Kuma ta shigo kenan, ba boka mallam tuggu, kisisinar da zai fiddata, ta shigo kenan, mutu ka raba takalmin kaza, wanda be iya ganin hakan sai fita dan uban mutum" gaban Saude ya yanke ya fadi, ta kasa gasgata zancen Nene, Alhaji ba zai taba yi mata haka ba, amma ta lura akwai wacce aka lullube, ta maida hankalinta kan wacce ke lullube da farin lafaya, a ranta tace Amarya? Zuciyarta na dukkan tara tara ta taka har gaban su, ta sa hannu ta yaye mayafin, Yanda kukasan taga Dodo haka ta sake mayafin da sauri tare da ja da baya, gani takeyi kamar Gezau, wata ta gani kamar Aishatu, haba ba ita bace, idonta ne, Na kan tudu yace ba zata sake taka gidan ba, jin muryar Nene tayi inda take cewa " ita din dai ce, Nana Aishatu Masoyiyar Asali, wacce k'addara ta rabata da gidanta, kuma Allah ya maidota, bawani dan buta uban da ya isa ya fidda ta kuma" Saude cikin kidima ta sake ihu tace "Aishatu, kai k'arya ne, ba ita bace" Mami tayi murmushi tace "Nice Saude, Nice" Luuuuu Saude ta fadi k'asa sumammiya. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) This page is for all Members of JUST NOVELS, Baby nice and above all Sadeeqah Ummu Sudais, ILY'lls Oceans and Galaxies❤ Pg5⃣6⃣ Duk sukayo kanta, Alhaji Habib yace "Ku taimaka a kaita Asibiti" Nene tace "wani Asibiti? Ai kawai ruwa zaa yayyafa mata" Meema tayi saurin dibo ruwan fridge, Nene ta karba ta watsa mata ruwan sanyi nan, Saude ta farfado idonta fes kan Mami, sake zabura tayi zata tashi, Meema ta maidata ta kwantar a k'asa, Mami ta tsugunno zata dafa Saude, Saude tayi zumbur tare da nunata kar ki tabani, wallahi kar ki tabani, Aljanna ce ke, it cant be, ance ba zaki sake dawowa ba?" duk kallon mamaki suke mata, Meema tayi saurin cewa "Wallahi Daddy tundazun Sis ke ta sambatu, ina jin Zafin ciwo ne, don wani Katon Maruru ya fito mata a guiwa" Daddy yace Allah ya kyauta, ai sai ki mikar da ita ki wuce da ita daki, Ya shigewar shi ciki, Zaid yace da su "ko muje Asibiti ne?" da sauri Saude ta girgiza kai tace "ai taje" Nene ta ta6e baki tare da cewa "mun rike Allah da Annabi, ku mu shiga daga ciki ko?" Mom din Maalesh ta ja Mami cikin gidan bayan Mami tayi adduar shiga Gida. **** "Yo ai tunda ba a kai ga shara da gyaran dakinta ba ai ina ga dakin Mijinta kawai zaa safketa ko?" cewar Nene, Maman Maalesh tace "hakan ne daidai, in yaso a gyara mata daki daga baya ta koma" Dakin Alhaji Habib suka shiga da ita, bayan sun dan jima suka mata Sallama, Uncle Zaid ya dauki Ummi Da Ayman ya kaisu gidan Baba Tj don chan za su zauna, Nene da Seebi da suka shiga dakinsu don huta gajia. ******** "Na shiga uku na, tawa ta same ni, Meema ya zanyi da mutanen nan? Aishatu ta dawo, komai ya jagule, nasan yin wannan Shegiar tsohuwar, nayi nadamar sawa a kona gidansu don yanzu Reshi ya juye da majuyi. Ni gaskia ba zan iya bari Aishatu ta kwanta da mijina ba, zuwa zanyi in lumama ta wuk'a ta mutu, na tsaneta na tsaneta" Saude ce ke wannan furucin cikin yanayin da ya firgita meema, bata ta6a ganin Yayarta a wannan yanayi ba, Firgici da Tsoro take gani kwance a idonta, tace "Sis ki k'okarta ki kwanta, komai zai zo a sauk'ak'e, gobe zanyi maganin abun, trust me Sis". Saude ta dan jigina da pillow kamar me bacci". ****** Aneesa batayi wani tashin hankali ba data dawo daga makaranta taji labarin dawowar Mami, hasalima murna tayi don ta tuna da, Mami ta kasance me kyautata mata, har Parlorn Daddy taje ta rungume ta, tana mata sannu da zuwa, Daddy yace " kice ma Saude bayan Isha'i tazo ina nemanta" tace "ok Daddy" ta fice ko da ta sanar da Mummynta Saude ta haruzka, don me Aneesa zata je gun Aishatu, tayi fadan ta zage Aneesa tas, karshe ma Aneesa ta buga tsoki ta bar dakin, ko a jikinta don ita bata tsoron fushin mamarta. Sak'e sak'e saude ke tayi, bata san me zatayi ba, idearta duk ta k'are, duk wata dabararta ta bace bat ta cije yatsa ta datsa lebe duk don ta samu sausauci amma a banza, Meema ta bata shawara tayi acting kamar ba matsala kafin da safe ta nemo mafita. Har wurin k'arfe 9 ba Saude ba Labarinta, Alhaji Habib ya latsa wayarshi ya kirata, K'in dauka tayi sai da Meema ta rada mata wani abu a kunne, kafin ta dauka tana cika tana batsewa, yace "Saude ina nemanki a dakina" a takaice tace "banda lafiya" yace "SubhanAllah, kafar ne har yanzu? Gani nan zuwa" ya latse wayar ta kalli Meema, Meema tace "lets use this opportunity ki kwanta ki ta juyi matsayin baki lafiya, kinga zai tsaya wurinki" ta dan mata rada a kunne" Saude ta jinjina kai tace "Plan dinnan zaiyi aiki". **** "Shatu nah, Saude ce bata ji dadi ba ina so in je in dubota" Mami ta dan hade wani bakin miyau tace "Haba Habibi, matarka bata Lafiya shine sai ka tsaya tambayan wani izini, donAllah tashi muje mu ganota" Daddy ya ji dadi tare da rik'o hannun Mami suka nufi Dakin Saude. Kwance take kan gado tana ta mutsumutsu, ya k'arasa Gadon ta tare da kiran sunanta, ta rungume hannunshi ta na wani kukan munafurci, Mami ta kauda kai, yace "Sannu Saude, k'afar ne? Allah ya sauwake ya baki lafia" Mami tace "Sannu Sauda, Sannu" Alhaji yace "Ko muje Aisbiti?" cike da makirici da kissa tace "A bari da safe sai aje, i'll b fine cike kawai dai Alhaji Please stay with me, kar ka barni ni kadai" ya dan kawar da kai gefe, yace ba ga Meema da Aneesa ba?" Saude ta marairaice tace "Please Alhaji, dare daya ne" cike da makirci Saude ta kalli Mami tace "Yaya ba zaki damu ba ko ya kwana a nan, ina bukatar taimako da kulawarsa" Mami tayi murmushi tare da mikewa tace "karki damu, yana iya tsayawa, mudai burinmu ki warke ki samu sauki, Allah ya baki Lafiya sai da safen ku" ba tare sa ta kalli Daddy ba tayi hanyar fita, Ji yayi kamar ya kurma ihu, meye hakan Aishatu tayi? Shi da yaci burin daren yau, ya zaayi ta amince ma Saude haka? Aishatu batayi missing dinshi ba, tunda bata damu dashi ba, ranshi na k'una, zuciyar shi na tafasa, da ta san yanda yayi kewarta da bata tafi ta barshi zaune ba" ******* Tafiya takeyi kawai bata san inda take jefa kafarta ba, saboda wani bakin kishi da ya turnike ta, tayi kewan Habibinta sosai, ba halin kasancewa tare dashi a wannan daren ji tayi an dafata" a dan firgice ta dan kallota, Nene ta daga mata gira "Yadai? Ina zaki kika bar mijin ki? Ashe ke sakarya ce? Nazata ke wayis ce ashe ke kauyis ce, mtsw, wai nan fa bariki akai miki, an kwace miki miji a wayance don kar ku kasance tare, Aishatu, na gaya miki BARIKI IYAWA" Mami dai ta kasa ce ma Nene komai, Nene ta ja hannun Mami suka koma dakin Saude da Sallama" Saude da har ta mik'e Zaune tana ma Alhaji Shagwava shikuma yana ta basarwa, tana ganin Mami da Nene ta hade rai, Nene tace "Alhaji ya na ganka anan? Daga zuwa inje in dawo" Alhaji yace "Wallahi jikin Sauden ne" tace "to ai gani na dawo, kasan ni ta aika a ka kira mata, wai jikinta na ciwo ko akwai dabarar da zan mata namu na tsofi, shine naje neman Robb don zan shafe mata a baya don ta samu saukin ciwon jikin ashe har ka zo mata bankwana, to ai sai ka tashi ka bi amaryark dare nayi" baki wangale Saude ke jin K'aryar da Nene ke shatatawa, Mamakin wannan duniyancin tsohuwar nan takeyi, zatayi magana Nene tayi saurin cewa"Toh ku tashi Alhaji, ina so in shafe mata jiki, don taji dadi, InshaAllah zuwa Safiyya ta warke" Kamar jira dadsy yakeyi yayi zumbur ya mik'e, Saude zata mik'e Nene tayi saurin danna mata harara, Da sauri Alhaji yace "Sai da safenku, Allah ya sauwake" ya fita da sauri,Mami na mamakin yanda Nene take rarafk zance, Nene ta katse mata tunani tace "Zaki bi mijin ki ko sai kin gama sakin bakin? Sum sum Mami ta fice, Nene ta juyo ga Saude ta kashe mata ido, ta juya ta fita. Ihu Saude ta sake, ihun takaici, ihun bakin ciki, ta na tsananin kishin mijinta, gaskia ba zata iya barinshi tare da Mami ba a wannan dare, dole tayi maganin abun amma ta yaya? °1:23am° Saude ta kasa bacci, abun duniya ya mata yawa, idanunta sun soye duka, ba alamun bacci, kallo daya zaka mata kaga tsantsar tashin hankali a tattare da ita, gaskia ba zata iya ba, Allah kadai ya san me Habib da Aishatu keyi, wani abu ta tuna, shaidan ya mata huduba, zumbur ta tashi, ta manta da maruran da ke kafarta masu mata Azaba, tana dangyasawa ta fita ta nufi kitchen, Wuk'a ta zaro, don ita Wallahi kashe Aishatu zatayi, haka ta dinga hada hanya don gani tayi wurin da duhu sosai, bawai don ba wuta ba a tunaninta k'ila Bulb din corridor din ne ya mutu, tana jan k'afa har k'ofar da zai sadata da Dakin Daddy, dagowar kanta ke da wuya ta ci karo da gamon ta, Wani halitta ne tsaye daidai k'ofar parlorn Daddy kamar Maiguard, sanye da Likafanni Fari, fuskar nan bakirkirin ga wani abu saman kan kamar k'aho, daskarewa Sauda tayi don Firgici, Tsuuu kakeji Saude ta saki Fitsari, wannan halittar ta fara kusanto Saude, habawa k'afa me na ci ban baki ba, Saude ta arta a guje ta shige daki a sittin bayan ta jefar da wukarta, ta datse da mukulli tana maida numfashi, Nene ta fashe da daria ganin yanda Saude ta tsure, tace "Shegia, ashe k'aryar iskanci takeyi, harda tsula fitsari, to ina nan ina gadinsu, ba abunda zaki musu, ni zanyi gadinsu har sai sunyi kwana 7, sai sun murji amarcin su" Nene ta sake fashewa da daria ta shige dakin su, tare da cire farin Kayan jikinta ta fada toilet don wanke fuskarta da ta sha Bak'in gawayi. Haka Saude tayi kwanan Zaune a tsorace. Bayan kwanaki 5 °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Yan Kaduna sun koma, banda Ayman da ke gurin Nasiba, cikin yan kwanankin nan Daddy ya dan yi kiba, an gyara ma Mami Dakinta, har ta tare, sai Amarcinsu suke sha kamar wannan ne aurensu na fari hankalinsu kwance Allah na karesu, Nene na gadinsu ba tare da saninsu ba. Meema ta bar gari ta zage gun bin gidajen bokaye don samo ma Yayarya mafita, Saude kuwa ta fara zarewa don duk a lokacin da tayi niyyar kulla ma Mami Sharri tsakar dare sai ta ci karo da Nene wacce tayi badda kama zuwa wannan mumunnar Hallitar da Saude ta ma lakabi da Fatalwa, Saude ta fara Zarewa, ta fara susucewa, Ga Maruran kafanta sai girma suke k'arawa da yawa, abubuwa sun rinchabe sun ma Saude Yawa duk ta sa damuwa a ranta, ta fige ta fita hayyacinta. *UMYU Katsina* Ki kirashi donAllah ya maidaki Gida Seebi, ba fa ki da lafia, baki ta dan cije alamun tana dan jin zafin ciwon tace "Ku bari kawai, zai daina with time, haba abunda an riga da an saba" Usheey tace "Tab, dama ana sabo da ciwo? tace "bari nidai sai na kirashi in ma Zagina zeyi yayi, ta dauki Wayar Seebi ta latso Hamma na ta kira, Ba yanda Seebi zatayi da Miemee da Usheey. Yayi ringing har ya katse bai dauka ba, Usheey ta sake kiran layin shi, a ringing na 3 ya dauka, yabkara wayar a kunne ba tare da yace komai ba, Usheey tayi saurin cewa "ina wuni?" ya danyi jim, wannan ba muryan Naseeba bane, yace "Yeah" "um um dama Seebi ce bata dan jin dadi, tunda safe take fama da ciwon ciki har yanzu, kuma lectures zamuyi 4-6 tace zata tsaya amma ya kamata ace ta sha magani ta dan huta a gida"cike da damuwa a ranshi yace "Oh Allah why is she sick" a fili kuwa cewa yayi "kuna ina?" da sauri tace "Bayan theatre" dif ya kashe wayar, Miemee tana na Usheey daria tace "ai gwara da ke ce kika kirashi, dani ce ya katse ma waya da yaji ba dadi" Usheey tace "Toh ko we should get her on a bus, sai in rakata, na yafe Lectures din yau din" Miemee tace "muje Kawai, mayi attending nextweek" Seebi tace "ku barni please, zai daina, kar kuyi missing lectures saboda ni pls" kafin daya daga cikinsu ya k'ara magana Wayar Seebi tayi ruri, Usheey ta dauko wayar ganin Hamma ya sata dauka da sauri ji tayi yace "ku matso da ita" ya katse wayar, ya yace? "Cewa yayi a matso da ita, which means yana kallon mu, Miemee tace ga motarshi chan, Usheey tace "Oya Seebi, kiyi k'okari ki tashi ga R-Lema chan yazo, suka taimaka mata suka nufi motar, Idonshi fes kanta, cike yake da damuwa, ji yake kamar ya fito ya taimaka mata, ya dai daure ya zauna cikin mota ya k'wama Glass a ido yanda ba zasu gane yanayin yake ciki ba. Sun so sata a baya amma tak'i bata so ya gano me ke damunta, tace su sata gaba,haka sukayi, suka rufe, be ce musu komai ba ya ja motarshi ya tafi, kallo daya ya mata ya dauke kai, Seebi na da dauriya, haka ta dinga cicijewa tana mutsitsika baki alamun zadi, har ranshi ya ke jinta, Da alamu tana shan wahala, ya na tausaya mata sosai, ya dinga driving, Seebi duk'e a gaban mota idonta lumshe Rafeeq ya dan juyo ya kalleta, kamar yayi kuka yakeji, a hankali yace "Sannu Kinji?" tadan kalloshi ta gyada kai, gani yayi gwara ya tsaya ya sai mata magani, don in taje gida kwanciya zaa sata tayi ko kuma wannan lunatic grandma ta bata wasu maguna marasa dadi, a hankali yace "Naseeebah, Me ke damunki?" ta dago a daburce ta rasa me zata ce mai, daure fuska yayi dan guntun Tsaki yace "Period pain ne?" waiyooo Allah k'asa bude Seebi ta shige, kunya ya rufeta ta rasa me zata ce mai, tsakin ya sake yi ya maida hankalin sa kan tuk'in sa, chan kuma ya kira Mamin sa Waya "R-Lema yadai?" Kamar bazai yi magana ba yace "Mam, First Aid for Mentsrual Pain, drugs? Anything?" ta danyi shiru chan tace "ba a cika san ana shan kwayoyi ba, its better to use natural remedy, like Hulba, Khal tuffah in hot water, hot water bottle" Mami ta shiga zanyano mai sunayen magunguna kala kala, Rafeeq ya danyi guntun tsaki yace "Mam-Mam, its an emergency, just name a thing, Mami tace "ok kane ma mata Khal tuffa cider vinegar sai hot water bottle sai ayi using dinshi" "Thanks Mam" zai kashe tace "Rafeeq wacece bata da Lafiya?" a takaice yace "Naseebah". Waiyo Allah na is she alright?" Mami zanje in siya Mata maganin, sai mun dawo Gida" "Toh Feeq ina mata Sannu" ya kashe wayan, ya dan waiga ya ga Nasiba ta dan jingina kan kujerar, ya danyi parking ya dan rankwafo ta wurinta har tana jin saukar numfashin sa, ya kwantar mata da kujerar yace "kwanta kinji?" haka ya wuce ya siya mata duk abunda Mami tace ya kaita gida, ya taimaka mata da jakkarta, Mami ta sauko da sauri ta rungume Seebi tana mata Sannu, Nene tace "wannan ciwon Marar naki na fara tsorata dashi,Muje ga ruwan Zafi na dan dauraye ki" Rafeeq ya mik'a ma Mami ledar magungunan, Mami tayi sauri ta shiga kitchen da hado mata da dan ruwa mai dan Zafi. √√√√√√√√√√√ Kula suke ba Nasiba kamar wata k'wai, Ba Daddy ba Rafeeq ba Ba Nenen ba, Zaid ma da ke Kaduna yana kira, binibini Rafeeq zai lek'o ya ganta tana bacci sai yayi murmushi ya juya, ya ci karo da Nene a wurin juya, Nene ta daga gira "yadai Dunkum ya da mana lek'e?" ya danyi tsaki yace "Ya jikin Naseebah?" ta ta6e baki tace "ni bansan wata Naseebah ba" ya dan kalleta da mamaki tace "nadai san Nasiba Seebin Nene" cikin rashin gane inda ta dosa yayi tsaki zaibi ta gefenta ya wuce tace "ni dai bansan ko a Amuruka a ka haifeka ba, naga iyayin ka ya soma yawa, in banda fi'ili da felek'e sunayen mu na da turanci ake fadansu, kace Mam, Neh-neh, oh ni Aminene diyar Mamman, har Nasibar ma da turanci kake fadarta? Wai Naseeebah" ta kwaikwayi muryarshi tana gyatsine, tsaki yayi me Sauti ya wuce ta tace "woo dangin tsaka". ******* Kasa hak'uri yayi, ba inda zaije cikin daren nan, ga Maalesh yaje Kano, yana son sake ganinta, yana son Sanin in jikinta yayi sauk'i,ya kalli Mami, "How's she?" Mami tace "Taji sauki kam don yanzu nan ta bar Parlorn Nan" "wai Naseeebah?" inji Nene ta fada tana daria, yasan shi take kwaikwayo bece komai ba ya mik'e ya fita, Daddy na cewa "Nene sai na hadaki da Zaidunki, kin sa ma danshi ido" sukayi ta daria. ******* Saude ta kulle kanta cikin daki tana ta kuka ta k'agara ta ga dawowar Meema taji yanda suka k'are, tana fatan dacewa, Aneesa tace "Mommy, wai ba zaki bari a kai ki Asibiti ba? Wannan kurjin sub ki warkewa, sai karuwa suke tayi suna fashewa ga wari, nidai gaskia bazan kara matse miki ba" Saude tace "Sorry my Baby, nasan gaji, karki damu Auntynki kawai nake jira, da ta dawo komai zaiyi daidaita, trust me my child". ********* "May i come in?" da bata saurara da kyau ba, da bataji me yace ba, da Sauri ta latse wayar da takeyi da Miemee tace "Hamma shigo" tana dan gyara dankwalin kanta, ya shigo kan stool din madubi ya zauna cikiciki yake magana kamar ance dole sai yayi, yace "cikin ya bari?" cike da kunya tace "Eh ya bari" yace "Sannu fa" tayi murmushi yace "I'm hungry" da sauri ta mik'e tace "i'll cook you dinner" ya yamutsa fuskar sa yace "No no no, bana son cin Solid food at night, tashi ki rakani in har kinji sauk'i" da sauri tace "i'll just get ready" smilling yayi yace "good girl" ya fita. Ta bishi da ido tana mamakin shi, duk ya bi ya sauya, damuwarshi k'arak'ara a kanta, ta bude Sif ta ciro Hijab ta bi bayanshi. Soli Center suka nufa, "oya fito" ya umurceta, cikin sanyinta ta fita tana tafia a hankali, duk ta raina kanta ganin irin mutanen da ke wurin, bata tunanin a garin Katsina akwai irin wuraren nan, ko don bata fita ne oho, tana bin ko ina da kallo, wurin ya hadu, tana ganin yanmata da samarin su, Har suka iso Shawarma&Pizza Spot, yayi ordering, Pizza da Shawarma, tace "Hamma ba yunwa kakeji ba, kwadayi kakeji" murmushin gefen baki kawai ya mata, yace "Muci Anan?" ta marairaice tace "No please" don ta raina kanta da kallon da 'yan gurin ke binta dashi, ya lura yace "Oya rik'e, i am not your Boy" ta amsa ledojin hannunshi, Rafeeq be da tausayi, suna tafia yace "do you need anything? Tace "No Thanks" suna tafia zasu koma cikin mota Sukaji ance "R-Lema" a tare suka juya, wata hadaddiyar budurwa suka gani Rafeeq ya zaro ido yace "Nanjeee? Omg" ai ko wacce aka kira da Nanjee ta rugo da gudu ta rungume Rafeeq shima rungume ta yayi suna jin dadin ganin juna, Gaban Nasiba ya yanke ya fadi, meye wannan? Wacece wannan rungume da Hamma Rafeeq? Zuciyarta na bugu da sauri, duk ta dabarce ta shiga yanayi ganin Rafeeq da wata, hankalinta yayi matuk'a gun tashi, da sauri ta dauke ido ta matsa gefe don kirjinta na barazanar fitowa " OMG R-freaking Lema, What are you doing here?" murmushi kawai yakeyi ya kasa cewa komai don be san me zai cemata ba, mamaki ya cika ta, don ta san ba haka yake ba, ya cika surutu a da, amma yanzu sai basarwa yakeyi, tace "lookat you, what happened to you kamar ba R-leman da na sani ba" share maganan yayi yace "Yaushe kika dawo daga States? tace "wallahi last week nagama Masters na and all, ina Maalesh? Maalesh na Kano Wallahi, "I've missed you guys wallahi" "same here" "who is she R-Lema, your girl? Ya tsina fuska yayi Shaf ya mance da Seebi da ke tsaye kamar gunki, ba tare da ya kalleta ba yace "She's so not my type ke kin sani, shes my cousin" Seebi na jin haka, No reason taji hawaye na sauka daga fuskarta, Nan aka kira wayar Rafeeq ya matsa gefe yana receiving wayar, Nanjee ta matso kusa da Seebi, ta sa hannu tana share hawayen Fuskar Seebi, tace "Haba k'anwata why are you crying?" Seebi ta wayance tace "Aa ba kuka nakeyi ba" dont lie to me, i caught you crying, tell me you have feelings for R-lema huh? Tell me" daburcewa Seebi tayi tana girgiza kai, tace "No No is not what you are thinking, wani abu ya shigar min ido ne" Nanji tayi murmushi tace "bansan ya kuke da R-lema ba, but i can say you have feelings for him, You got Jealous when you saw us together, dont worry, i am not a threat, R-lema was my Bestfriend, and Maalesh was my crush lokacin muna Secondary School, so you dont have to worry about me, Kina sonsa, i can say that for sure" Nasiba ta rasa bakin magana, bata taba zaton wani ko wata zai fuskanci abunda takeji game da Rafeeq ba, tayi Alkawarin barin abun a ranta har mutuwarta, tace "Sorry Aunty is not what you are thinking" Nanji tayi murmushi tace "kanwata think about it, Rafeeq ya min yaro da na miki snatching" ta fada tana daria ita kuwa Seebi ta rasa yanda zatayi, Feeeq ya dawo yace "Oya lets get going Mami ta kira tana tambayarki" Nanji Babe bari mu tafi, sukayi shaking hands tareda exchanging Numbers, Seebi ta kallesu ta gefen Ido, Allah ya sauwake kuna diyan musulmai kuna taba juna kamar muharamai" ta murguda baki, fuu ta wuce gun mota don wani abu da takeji me kama da Kishi, Nanji na kallonta tayi daria ta wuce gun Saurayinta dama tare suke. ********** Tun a mota ya ga yanayinta ya chanza, ba kamar da sukazo ba, amma yanzu ta hade rai sai fushi takeyi, ko me aka mata oho, yaso ya mata magana amma ya shareta har suka zo Gida, yana parking ta bude k'ofa zata fita yayi saurin rik'o hannun ta yace "Whats your Problem?" a dan masife tace "i dont have any" baki bude ya kalleta, ashe ta iya fushi, to me yayi zafi haka? Tab" ta wuce ta bar mai ledojinshi, ya daga kafada yace "matsalarki" ya wuce Dakinshi. Da fushi ta shiga gidan tana ta mita cikin zuciyyarta, ba kowa a Parlorn K'asa ta hau sama daidai Dakin Saude taji ana magana k'asa k'asa, ta so wucewa don lab'e haramun ne, amma zuciyarta ya haneta, ta kasa kunne sosai ta gane Aunty Meema ce da Saude ke magana amma bata jin me suke cewa, a tsorace ta dan tura k'ofar a hankali, ta kutsa kai ciki ta labe tsaf takejin Su, jikinta ya fara rawa sakamakon abubuwan da kunnuwanta suke jiye mata: "Wallahi Sis cikin kwanaki Shidda gidajen Boka shabiyar naje garuruwa daban daban, duk magana daya suke gaya min, wai ba abunda zasu iya miki" da Sauri Nasiba ta ciro wayarta ta danna record. "Yanzu shikenan tawa ta sameni, yanzu ya zanyi da Alhaji? Gashi Aishatu ta dawo na san sai yanda tayi dashi, Matsalata Aneesa, ya zanyi da ita? Yanzu idan Alhaji ya fadi ya mutu bata da gadonsa, ya zanyi in sa ya bata k'addarorinsa, da ace ta hanyar Sunna muka haifi Aneesa da nasan tana da gadon Hafiz, gashi Hafiz be bar mata komai ba, kai ni tau na shiga uku" da sauri Nasiba ta toshe bakinta, tana fadin inalillahi wa ina ilaihir rajiun, yanda ta shigo haka ta fito a tsorace, jikinta na rawa ta ci karo sa Nene, Nene tace "meye haka jikin ki ke rawa kamar Mazari? Ya akayi? Ko gamo kikayi? Seebi ta ja hannuj Nene zuwa daki, ta rasa me zatace, Nene tace "wai meye? Zaki gaya min ko sai na je dakin Sauden naga me kike ma rawar jiki don naga da ga chan kike" da sauri tace "Aa nene, kar kije bari kiji" ta mata Playing abunda tayi recording, "tohhhh maganar kenan? Shi Hafiz din waye? Seebi tace " Yayan Uncle Zaid ne, ya rasu" toh Shine Uban Aneesar kenan, kuma Shegia ce, to ko sun sani? Anya bana tunanin sun sani, bari dai muga" Nene ta mik'e Seebi tayi saurin kamota, ina zaki? Haba Nene tada fitina zakiyi tsakaninsu? DonAllah kar kije, Nene ta lailayo ashar ta watsa ma Seebi, tace "Uban meyasa kikayi rakodin din, ni ban guri dalla" ta fita da wayar Seebi a hannu" Seebi ta daura hannu a kai "La i'llahailallah lahu take maimaitawa Hafiz Lema ne Baban Aneesa? Kuma ba ta hanyar Aure suka haifeta ba? Gashi Nene ta je fallasa asirinsu, anya tayi daidai kuwa da ba Nene wayar? Da sauri ta bi bayan Nene. Nene bata tsaya ko ina ba sai dakin Aneesa, Aneesa ta kalleta galala tace " Meye? Zaki shigo min daki? Nene tace "yi hakuri, DanAllah zuwa nayi ki latsa min inji wannan rakodin din" kamar ba zata karbi wayar ba ta karba, ta yi playing recoding din da tagani" K'arara muryar Mamarta taji tana wannan furucin ta zaro ido tace da Nene meye wannan? Ko Kinsan Babanki Shine Hafiz Lema? Ko kinsan ke Shegiya ce? Ihu Aneesa ta rusa, Na shiga Uku, ni Shegia? Ai ko a sittin ta diro daga kan gadin ta fita waje tana bige Seebi da ke kokarin riketa, wucewa tayi dakin Saude, Saude da Meema na kan Gadi, Aneesa ta danne kan Saude, duk ta chanza kamar wacce Aljannu suka shiga, tace "Saude Aminu ki gaya min da babanki, Ni diyar Hafiz Lema ce? Hafiz Lema ne Baba na? Dama ni shegia ce?" _Bibilicious Biebee_ (donAllah kuyi hakuri, kunji ni shiru kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon Makaranta da muka koma, Karatu ya tasoni gaba wallahi ga matsalar wuta da muke fama da ita, kuyi min uzuri, nima so nake nagama wallahi, kunsan halin Karatu. DonAllah ku cigaba da Hakuri nagode..) 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg5⃣7⃣ Cikin k'ak'ari Saude tace "Aneesa ki dagani, You are hurting me, ki cika min Wuya" Meema tayi tayi ta k'waci Saude daga hannun Aneesa amma ta kasa, Nene a ranta tace "ku k'arata chan" Mami da Daddy suka shigo da sauri, Daddy yace "Meke faruwa nan ne?" ai Nene ta mik'a ma Daddy wayar Nasiba yayi Playing recording din nan, idan shi ya kada yayi jazir, ya Kalli Saude da Aneesa cike da Tsana, Daddy ya juya ya bar Dakin, Mami ce ta k'arasa gunsu tana ririk'e Aneesa, Aneesa Calm down, let your Mom go, please" a hankali Aneesa ta zame k'asa tana gurshek'en kuka me tsumma rai, Sauden ma Kukan takeyi, tace "Aneesa my child, ki saurareni" Aneesa tace "Saude ki daina min magana, ni ba diyarki bace, ashe ni shegia ce? Ba ta hanyar aure aka sameni ba? Kikayi min k'arya Babana ya rasu, Allah ya isa, Allah ya isa, na tsaneki Saude, i wish i have a different Mother" Mami tayi saurin taran Aneesa tace "Haba Aneesa, ki daina magana haka, Musulmi na kwarai shine wanda yake rungumar k'addarar sa da hannu bibiyu, me kyau ko mara kyau, DonAllah muje ki sha ruwa ki huta, kar ki sa abun a ranki". Fuu ta fita kamar zata tashi sama, Mami ta kalli Saude ta dan yi mata alamun tayi hakuri kafin ta wuce, Saude ta daura hannu a kai ta rusa ihu, Shikenan Asiri na Ya tonu, banda sauran Mutunci a idon kowa, Meema tawa ta k'are ya zanyi?" Meema ta hau lallashinta. Safa da Marwa Alhaji Habib ke tayi a tsakar dakinsa, Wannan wani irin musiba ce, ya zaayi Saude ta iya wannan cin Amanar? Ta yaya Saude zata musu haka? Taya zata Aure shi bayan tasan cewa Hafiz ne Baban 'yarta, Mami ta shigo ta dafa kafadar shi "Habibi, donAllah ka kwantar da hankali, daure ka sha ruwa gashi nan" Alhaji Habib yace "Shatu Sauda taci Amanata" "Shhh, ka sha ruwan nan, everything is going to be fine InshaAllah" ya karba Cup din hannunta ya kurba, "Sakinta zanyi, ba zan iya zama da ita ba wallahi" "DonAllah dont make any descision yet, you are Angry, kar kayi abunda zakayi dana sani" "da nasani? Shatu da nasani fa? Don na saketa? I never loved her, God i didnt even know why i got married to her, itama kwadayi ne yasata Aurena, idan ba haka ba meye zata dinga maganar Gado, gaskia ba zan iya zama da matar nan ba, ta zalunceni, Sakinta Zanyi, and Hafiz? How could he do this to us? "DonAllah ya isa Habibi, Hafiz ya rasu, please dont say bad about him, Allah ya gafarta mishi ya rahama mai, and if you have the slightest respect for me, ba zaka saki Saude ba, zaka cigaba da Aurenta ko don Aneesa, diyar k'aninka" "Shatu kar ki man haka" Mami ta rungime Mijinta tana shafa kanshi kamar k'aramin yaro tace "Please Habibi, do it for me, Please". ******* A daren Ranar, Saude, Aneesa, da Daddy ba su samu sun runtsa ba, Washegari Aneesa ta ki bude k'ofa, Mami tayi kwankwasawr duniar nan, amma taki ta bude. K'arfe 11:30 Uncle Zaid ya shigo gidan, Tun daren Jiya Daddy ya kirashi ya sanar dashi, abun ya firgita Zaid Sosai, amma beyi wani mamaki ba, ya Umurta duka 'yan gidan Su hallarci Parlorn Daddy, har su Nene karere, bayan Meema ta gunguro Saude kan Kujerar guragu, Duk ta fita hayyacinta, kafar nan ta faara rubewa, ga wani wari, Zaid yace "Ina Aneesa?" Mami tace ta kulle k'ofa tun jiya" Zaid ya mik'e ya wuce Dakin Aneesa ya shiga kwankwasawa, "Anee open the door, Uncle Zaid ne please" "Go away i dont want to see anybody" Anee Please kizo ki bude mim k'ofa, nine Uncle Zaid, K'anin Babanki" a hankali ta bude kofar tare da Rungume Zaid, be hanata ba, kuka take tayi sai da tayi me isar ta kafim ya jata har toilet ya wanke fuskarta kafin ya rik'o hannunta har Parlor inda suke Jugum jugum kamar Gidan Rasuwa. ******* "Uncle Zaid bana son ganin wannan Matar a rayuwa ta, Na tsaneta, na tsaneta, tayi Zina ta haifeni, ni bazan zauna rumfa daya da ita ba" Aneesa ta fashe da kuka me tsuma rai, duk sai ta basu tausayi, Saude ta gungura kekenta gaban Aneesa, tace "ki yafe min, ki sani whatever i did, was because of you, i did it for you to have a better life, i did it because i Love you" cikin tsawa tace mata "k'arya kikeyi, Makaryaciya, you never loved me, coz if you do, you wouldnt have given birth to me, you were a slut, and thanks to you, i'm a bastard" ta juya zata bar Parlorn da gudu Saude tayi saurin mik'ewa zata bita, ta turgude ta fadi, wani ihun wahala ta sake Mami, Meema da Seebi sukayi Kanta, Daddy Dauke kanshi yayi, Rafeeq dama latselatsen wayan shi yakeyi, Zaid yace "Feeq je ka fiddo mota, mu kaita Asibiti" Feeq yayi kamar be ji ba" Zaid ya sake cewa "Rafeeq Lema, i said je ka dauko mota zaa kaita Asibiti" Rafeeq ya mike tare da zare earpiece din kunnen shi, ya kalli Zaid yace "No Uncle Zaid, ni ba zan dauko Mota akai any bitch Asibiti ba, besides I never liked her" ya wuce ya bar Parlorn, Zaid yayi saurin Kallon Alhaji Habib, Shi ko ya daga kafada alamun be damu ba, shima ya mik'e ya shige daki, Zaid ya kalli Mami yace "barim dauko mota, kuyi k'okarin sauko da ita". Bayan Sati 2 Cikin kwanakin nan Sha hudu, kallo daya zakuyi wa Saude ku san cewa tana cikin Azaba da Musiba, don k'afarta ya gama Rubewa, har aiki akayi amma kamar an jangwalo wani abun, don kafar tayi damadama, ko so daya Daddy be zo ya dubata ba, kullum sai sunyi Fada da Mami kan sai yazo dubata amma yak'i, Aneesa ma idan ka mata maganar dubota sai ta hau Zage zage, Mami ce d a Seebi ke kula da ita harta Meema tayi watsi da lamuran Yayar tata, sai ta ga dama take zuwa Asibitin, Mami kuwa ko so daya bata taba gazawa da kula da Saude ba, Zaid ne ke Biyan duk wasu kudin da aka kashe a asibitin. Dr ya kira Mami Office dinshi yace "I am so sorry to tell you, k'afar Sauda Ya rube, bai da wani amfani, idan aka barshi a hakan zai yi causing trouble to the other leg ne, So ina ba da Shawarar a yanke kafar, ayi mata Aiki me kankat" Mami ta dafe k'irji tace "A yanke k'afar fa kace" Dr yace "Its the best solution, ana iya samata k'afar roba, amma kuje kuyi Shawara". ********** Waya ta kira Zaid ta shaida mai yace" Ba matsala amma ta tuntubi Sauden, shi yana wani aiki ne idan ya samu sarari zai lek'o Katsinar" ko da ta tuntubi Sauden da maganar Sosai ta firgita, taci kukanta harta godewa Allah, wai yau ita Saude me ji da kanta, me takama da duk abunda take so sai ta sameshi ko ta halin k'ak'a wai ita ake cema zaa yanke ma k'afa, lallai Duniya Budurwar wawa, to ya zatayi idan bata amimce ba zai shafi dayan kafar, ga wahalar da take ci, gwara kawai a yanke, tana hawaye tace "Yaya a yanke kawai zan ma fi samun kwanciyar hankali, nagaji da wahalar da kafan nan ke bani". °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° A GURGUJE Bayan An yanke k'afar Saude ta dan yi kwanaki a Asibitin ta dawo Gida, an bata Crutches na tafiya, har yanzu Aneesa ba ta sauko ba, Daddy ma ba ruwanshi da ita, sai da Mami tayi dagaske kafin ya lekata so daya, shi bek'i ya saketa ba, don ya mugun tsanarta, Mami ta shaida mai Ai don Diyarta zaiyi. Saude tayi mugun shiga taitayinta, yanda taga Alhaji ya banzatar da rayuwarta, ya nuna mata cewa da ita da banza daya suke, ita har ga Allah tana sonsa. Mami ta samu Aneesa a daki wata rana bayan ta dawo daga School, Mami tace "Aneesa, komai yayi zafi maganin shi Allah, nasan Saude ba ta kyauta ba, ba kya tunanin cewa abubuwan zasuyi mata yawa? Kin dauki gaba da ita, watan ta kusan 1 a Asibiti ba kije kin dubo ta ba, Sannu be taba hadaki da ita ba, Aneesa horon da kika mata yayi tsanani, Uwa uwa ce, ko ya take, donAllah kije ki sassamta da ita ko ta samu sauki, nasan hankalinta a tashe yake, i was once in her shoes, Rafeeq turned his back against me, banji da dadi ba please Have Mercy on her, go talk to her" Aneesa ta share hawayenta ta san tana matuk'ar Son Mamarta, amma what she did was unforgiveable. Ok kawai tace ma Mami. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• "Kanaji ko? Kwana 1 na baka, ko ka kawo min cikon kudina, ko wallahi in sa Guys su min gunduwa gunduwa da kai, you cannot run away from me, wherever you go, i will find you and i will Kill you, i want my Money" Ya hadiye wani mugun bakin miyau, duk Iskancin shi ya san Steve ya fishi, yayi dana sanin Shiga Chachar nan, da beyi Chacha ba k'ila da ya rage Bashin 2million din da Steve ke binshi yace " Sorry Iga Steve, i'll get you your Money, kayi hakuri" Steve yace "Ka sanni, kasan me zan iya yi, get my money Ready or else, hmm" ya kashe wayar, cikin shi ya duri ruwa, da sauri ya lalubo Numberta. "Fatara me tada Tsohon Bashi, Aminiyata ya kike?" a tsure tace *Mak'ale, meyasa ka kirani, we dont have any Bussiness left, kar ka sake kirana, You might get me into trouble, danAllah kar ka sake kirana" dif ta kashe wayar, tana waigen bayanta Allah yasa ba wanda ya jita, wayarta ya sake ringing har ta katse bata dauka ba, ya sake kira ta dauka a masife " Ke Sauda, butulu, ni zaki kashe ma waya? Kar ki kawo min Iskanci mana, haka kurum da ina kiranki ne? Kudina zaki ciko min, na sha miki aiki kina bani rabi baki ban rabi ba, nasan ina binki bashi fiye da 7million, amma na bar miki 5, ki bani 2million ciki, i need it, its an emergency, kuma ina sonshi kafin gobe" cike da rudu tace "Makale me kake cewa ne? Are you insane?, banda sauran Alaka da kai, please ka rabu dani, i am a born again person, ina so in saita rayuwata, i want to start new, so Please ka rabu dani, kar ka sake kirana" wani mugun daria Mak'ale yayi yace "Nice Joke Sauda, kinsan dai na fiki tasha ko? Ni zaki cema you are a born again hahah Sauda bani ke da wuta ba amma na san ke 'yar wuta ce komin tuban da kikayi, kin dade kina tsula tsiyarki, mtsww, yanzu ba wannan ba, Kudina nake so, someone is threatening me, if i go down i promise to drag you down with me, idan baki son Asirin ki ya tonu ki hada min kudina kafin Gobe wallahi in ba haka ba, komi zai iya faruwa" dif ya katse kiran,Zufa ya fara jike kayan Saude, ya zatayi? Ai ba zata taba bari asirinta ya tonu ba, wanda ya tonun ma tsautsayi ne, tana cikin tararrabin nan ne Meema ta shigo dakin tana zuba uban k'amshi, Saude a razane ta kalli Meema tace "Meema akwai Matsala, i need your help, Makal'e ke min barazana, wai zai tona min Asiri idan har ban bashi 2millionn ba donAllah ki taimakeni, bana tunanin a Account dina zan samu ko da 100k" Meema ta kalli Saude galala tace "Sis are you crazy?ke matar the great Habib lema baki da kudi sai ni? Please stop this nonesense now" baki wangale Saude ke kallon Meema da mamaki, yau ita Meema ke ma magana Gatsau? tace "Maryam nike ma magana haka?after all i've done for you? I took care of you tun kina k'arama and now don banda wata mamora kike min magana yanda kika ga dama" Meema tace "nifa kin dameni, haba, gori zaki min don ina zaune a gidan Mijinki? To karki damu i'm leaving and never coming back, dama son Zaid ne da burin samun Shi ya sa ni zama a gidan nan all this while, amma naga banda chance din samunshi kwatakwata bana gaban shi, to banga amfanin zamana a gidan nan ba, bayan inada Sugar daddies din da zasu ingata rayuwa na da kuruciyata, da kyau na, na hakura da Zaid, ba zan lallace kanshi ba bayan inada Future , so zamana a gidan nan be da amfani" ta juya da sauri saude tace "No No Meema donAllah Dont Go, dont leave me like this, i need you now more than ever, you are the only one i have left, kema ni kadai gareki, pleaee kar ki tafi" Meema ta kalleta a tsaye tace "Sorry sis, i cant do anything for you" Aneesa tace "Aunt Mee, you are leaving? Why?" Meena ta daga kafada tace "Anee take care of your Sis, ni na shiga dunia, i'll come back when i acheived what your Mom wasnt able to Acheive" ta banga k'ofa ta fita, Saude ta rushe da wani irin kuka, Aneesa ta karasa gunta don lallashi.. ****** "Saude kin hada min kudina ko kuwa?" jiki na rawa tace "Kayi hakuri i need more time" da tsawa yace "I dont have any time left, once 2 yayi clocking it would be the end of me, and you are my last hope, so i ask You nicely ina zanzo in karbi kudina?" cike da tausayin kanta tace "Mak'ale, inada ATM's biyar, ina jin kudin cikin duka zasu kai 400k, ga Sark'a na da yan kunne sai a saida, na san zasuyi 500k, in aka harhada nasan zasuyi 1million, ina kuma da Gona duk sai in baka ka har hada" Mak'ale yayi Murmushi yace "Good Girl, yanzu kikawo min, ina ta wurin Magama" Saude ta fashe da kuka yace yadai? Tace "Mak'ale banda k'afa, k'afa ta daya, an gundule dayan?" cikin halin ko in kula yace "Really? Yanzu ki ba Meema kayan kawai ta kawo mun" "Meema left me Jiya" haan to ya zaayi? "Ya zan samu kaya na ne? Ina diyarki?" da sauri tace "keep my daughter outof this" "So tell me how can i get my Shit?" tace "Shi nake tunani ni idan na fito they'll be suspicious" yace "i'll come get it" tace "no you cant come over" yace "like you have an option, nagaya miki need to get the whole shit kafin 2, and this is past 12, the earlier the better, if you are worried i'll be caught kar ki manta waye mak'ale, i'll gt everything under control like always, ki tuna duk aikin da kika sani bantaba failing dinki ba, so dont worry i gt my ways" ba dan hankalinta ya kwanta ba tace "Ok". ******* Dawowar shi daga School kenan, a gajiye yake don a yau ya ga Project dinshi, Cikin gida ya shiga, ba kowa a Parlorn k'asa Sai Saude da mak'ale yace ta harhada mai komai gashi nan zuwa, ganin Rafeeq a wannan lokacin ya tada mata hankali, amma ganin be nuna ya ganta ba ya sata dan kwantas, hayewa sama yayi yana kiran "Mam". Doguwar riga jallabiya ce jikin Mak'ale, yayi rolling da gyale, ya k'wama bakin glass wanda ya mamaye fuskar sa, ba ka taba gane shigar maza yayi, a bakin gate yace da Baba Maigadi suna ciki? Yace " Hajia babba ko karamar? A takaice yace babbar yace eh ta na nan, Makale ya shiga gidan yana taku kamar mace, kai tsaye Saude tace tana Parlorn kasa da ya shigo zai ganta, kawai sai ya amsa ya ware, a saukake batare da kowa ya ganshi ba, kan Mak'ale a kasa ya shiga, ko magana basuyi da Saude ba ya amsa k'aton Envelop din hannunta ya juya ya fita, Saude ta sake ajiyar Zuciya ganin ba wanda ya ganshi har ya bar Parlorn, a ranta tana tunanin dabara irin ta mak'ale. Da sauri sauri Makale ke tafiya a farfajiyar gidan, karaf ya ci karo da wani abu, ko da ya dago wata tsohuwa ya gani, Nene ta yashe Baki tace "ikon Allah, saurin me kikeyi ne haka da baki kallan gabanki in kina tafia? Iye? Makale ya sadda kai, Nene tace" ko da yake ya zaki ga gabanki bayan sanye kike da wannan bakin tabarau din?". Daddy da Uncle Zaid suka shigo gidan dama tare suke da Nene ta dai riga su shigowa inda sukuma suka tsaya a waje suna dan magana, daga gidan Nene suke, su ne dubo Ginin ne, A k'asa sukaje. A lokacin kuma Fitowar Rafeeq kenan daga cikin gida, ya sa Mamin shi dafa mai indomie, ya ga Nene na ma wata Mita, tsaki kawai yayi yace "this woman, she annoys everyone, har bak'in ma bata barsu ba" yayi hanyar Dakinshi ya ga Rigimar Nene wai sai ta cire gilashin Matar nan, ya tsaya ganin ikom Allah wannan karfin halin Nene na bashi mamaki, ina ruwanta da Glass din da matar ta saka? Makale na dan karewa ba dama ya sa hannu ya bangaje Nene don kayan dake hannunshi, Nene ta ci nasarar cire Glass din fuskar Mak'ale.Nene na daria tace"Diyata ya na ga fuskarki kamar ta gardi?" Fuskar da bazai ta6a mantawa ba ko anyi shekara dubu, fuskar da ta jefa rayuwarshi cikin Garari, Fuskar da ta sashi cikin K'unci da Ukubar Rayuwa. Tafia yake be ganin gabanshi idonshi a rufe, ba abunda yake gani sai bakar ranar da bazai taba mantawa ba, komai ya dawo mai sabo, ba su san da zuwan shi ba, sai da Mak'ale yaji an rike mai k'ugu anyaye gyalen kanshi, Nene ta dan daka tsalle tayi baya tare da karanto "Summa Alaiyna bayana" na shiga uku me zan gani haka? Gardi da shigar Mata, Idon ryafeeq ya kada yayi Jazir, tabbas shine, aiko Mak'ale ya zubda kayan hannunshi zai Arta a guje Rafeeq ya damk'o shi ya sauke mai nushi, Nene tace "Barawo ne ko dunkum? Ci Uwarshi Wallahi" Alhaji Habib daUncle Zaid suka karaso, "Rafeeq meye haka?" Rafeeq be bashi amsa ba Alhaji Habib ya hada ido da Mak'ale, baki na rawa Ya nuna shi da yatsa "me kakeyi anan?" Mak'ale ya kaima Rafeea Nushi, da sauri Rafeeq ya cikashi shi kuma ya zabura zai gudu, Nene ta hango dan gatarin da kwanaki taso ladabatar da dunkum a gefe da sauri ta dauko ta wurga ma Mak'ale, cikin saa ta sameshi a Bayan kai, Mak'ale ya zube a k'asa, Rafeeq na is gunshi kamar ance ya sa hannu a bayan wandon Makale, yana sawa kuwa sai ga Bindiga. ******* Baba Maigadi yazo da Igiyar Shanya, aka daure Mak'ale tsaf, Rafeeq ya shiga dukkanshi, Alhaji Habib ya kira jamian Tsaro, Rafeeq yayi tsaki yace "we dont have time for this, ya shak'o wuyan Mak'ale, "Uban me kakeyi a dakin Mamina 3/12/2014?" Mak'ale yayi shiru, tare da kawar da kai gefe" Daddy yace "ka bamu amsa kafin police suzo, sukazo ba zakaji da dadi ba" Mak'ale ya ki magana, Nene ta kwala mai wannan gatarin a taakiyar ka, tace kana magana ko sai na rotsa ka?" Mamakin tskhuwar nan yake, anya Mace ce kuwa, wani riko da ta mai dazu ya zata kattai suka kamashi. Akai akai mak'ale yayi magana yayi shiru, Zuciyya taci Rafeeq ya zaro bindigar Mak'ale ya nunashi da ita, yace "Iswear to God, ka fadamin me kake yi ranar a Dakin Mami na kuma waya saka ko in harbeka" a tsorace Zaid yace "Feeq, calmdown hand the gun over" Rafeeq yace "tell me or i shoot" Mak'ale yayi murmushi yace " You cannot shoot me Boy" "İ Am no Boy, i am Rafeeq Freeking Lema" Rafeeq ya saita kafar Mak'ale ya harba ji kake tasssss, İhu Nene ta sake, Mami da ke kitchen tayi salati tare da kashe gas ta sauko, Aneesa a kidime ta firo daga dakinta tayi kasa Gaban Saude ya yanke ya fadi, what the hell just happened? Gabanta na dukan chalugude ta lek'a window abunda idonta ya gane mata ne yasa ta sakin fitsari, shikenan "Asirinta ya tonu, ya zatayi? Mafitar ta daya, ta bar gidan kafin su ankara da ita, Crutches dinta ta hau dogarawa cikin sanda ta hau saukowa, inshaAllah kafin Mak'ale yayi wata magana ta bar gidan. Mami Ta tsure ganin Rafeeq yayi harbin, burinta taje ta kwace bindigar hannushi da yake sake kokarin harbin wani, Daddy ya janyeta ya rungume. Rafeeq ya saita zuciyar Makale "Dont underestimate me,Tell me now or i wont miss your Heart, start talking" cikin jin zafi da Azaba Mak'ale ya fara magana "Sauda ce, Sauda ce, itace ta sa mata magani a drink dinta tayi bacci, ni kuma na shigo dakin nayi acting kamar wani abu ya shiga tsakanin mu, itace ta sani, itace ta sani na kawo mata poison don ta sama yaran mijinta har macen ta mutu, itace ta sa na Kashe Hafiz Lema, itace ta sani na sa ma wani Gida wuta last 2months, itace..... "İnallilahi wa ina ilaihir rajiun kawai kakeji" kuka Mami, Aneesa, Uncle Zaid da Daddy keyi Sosai banda Rafeeq da idonshi ya k'ekashe, "Jaruban chan" cewar Nene. Cikin karaji Rafeeq yace "Saudeeeeee yau zan kasheki da hannuna" murya na rawa Aneesa tace "Yaya Rafeeq, Yaya Rafeeq, ga Saude chan, gata chan zata gudu" dum a tare suka kalli hanyar gate, ashe suna tsaye ta zo ta wuce ta gabansu, gashi har ta bar gidan, da gundulelen kafarta take cilla kafar da crutches tana tafia sauri sauri, Rafeeq ya danna a guje Mami na kwala mai kira ko waigiwa beyi ba, Mami tace Habibi ku tsaidashi kar yayi kisa donAllah, Zaid kuje, Daddy da Uncle Zaid suka bi Rafeeq a baya. Kuka takeyi tana dogara Sandarta tana tafia da sauri, daga gefe taga wani Me Keke Napep na fitsari hango makullan tayi jikin Napep din, da sauri ta k'arasa gun Keke Napep din ta shige, ta tada, tayi ribas ta bar gurin a Sittin, Me Napep ya ji Alamun an tada mai Abun Hawa da gudu ya zira wandon shi, kafin yayi aune sai gani yayi wata mata Me k'afa daya ta sace mai Machine" Jamaa ku taimakeni ta sacen a daidaita sahu" Rafeeq ya karaso ya shiga halbin tayar Napep dinnan amma ina be sameta ba, ya harbi iska da hannunshi, dan Achaba ya tsaida, shima ya janye shi ya wurgar dashi a kasa ya hau kan Machine din ya burka ya bi bayan Saude Mai Keke Napep.(Lols) _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) (Afuwan Habibties, Ina k'ara baku hakuri a kan rashin jina da kukeyi akai akai, Makarata ke boyeni wallahi, karatu ya fara Zafi, i spend more time in School than in House, nima na k'agara na gama wallahi, So ku cigaba da hakurin da kukeyi dani, Nagode, Saura Cinguli👌🏼) Pg5⃣8⃣ Wuta kawai Saude ke ba ma Napep dinnan, ita kanta tana Mamakin yanda take Sarrafa Napep dinnan, ta madubi ta hango Rafeeq na binta a acha6a, sosai ta k'ara gudu, Abun ya ba Rafeeq mamaki me k'afa daya da Jan Napep haka shima ya kara gudu, Round din dandagoro(hanyar Barin Katsina)Saude tasha inda tayi tafia kadan kafin ta fita daga cikin Katsina, Relay sukeyi sosai ita da Feeq, har sai da suka bar Katsinar baki daya, Jamaan Annabi sai binta sukeyi da Kallo, wasu suce ko Lafiya?, ganin zata mai nisa ne ya sa shi k'ure gudun babur dinnan, a lokacin sun bar gurin taron Mutanen, cikin ikonAllah ya kamo Saude, aikuwa ganin hakan yasa ta fita daga Napep din tana neman guduwa, daidai wani Kango take nufa, Rafeeq ya sauka daga kan Machine din, ya bita a baya, to k'arfi ba daya ba, gata da k'afa guda, nan da nan Rafeeq ya isketa. Cikin Saude ya kada, ta kalli Gabas da Yamma, bata ga halitta ko daya ba, tasan tata ta k'are bata ga ko digon imani a idon Rafeeq ba, tasan kasheta zaiyi, yana ko Chapkota ya wanketa da Marin da bata taba tunanin a iya rayuwarta wani ya taba mata irin shi ba, yace "Wannan na Mamin mu ne" ba ta gama tunani ba ta sake jin wani Mari a dayan kumatun yace "This is for Rafee'ah" ya kai mata Nushi a ciki yace "This one too, is for Rafee'ah" ya kwashe kafarta ta zube a k'asa, ta saki ihu sanda gulalliyar k'afar ta daki k'asa, yace "Wannan ma na Rafee'ah ne" ya zaro Bindiga daga cikin Aljihun shi ya saita kanta dashi yace "And this one also is for her" Tsuuu Saude take Fitsari, yau ta hango k'abarinta, baki na rawa jiki na 6ari ga Azabar da takeji a jikinta, tana kuka ta ke cewa "Kayi man Rai Rafeeq, kuyi hak'uri ka gafarceni" Idonshi ya rina yayi Ja, wannan Family is the First and the Last Family da zakiyi ruining, tunda kika shigo Rayuwar mu, abubuwa suka chanza, alot of people suffered because of you Saude, a dalilin ki na fita daga hanya Madaidaiciya, a dalilinki Mami da Daddy suka rabu, You killed Rafee'ah, Kin kashemin Rafee'ah ta" sai ya fashe da kuka da ya tuna Rafee'ah, da irin halin ko in kula da ya dinga nuna mata, yace "kuma na san Ke kika kashe Matar Uncle Zaid? Mom din Ayman?, shiyasa i'll show you no mercy, Jininki ya Halasta, i'm going to kill you right now" ai kuka take majina faceface a hancinta, "Wallahi bani na kasheta ba, why would i ever kill her? DonAllah kar ka kasheni, i have to stay Alive for Aneesa" Rafeeq ya saita yace "Goodbye Saude, May all your Evil die with you along" ya ja kan bindigar, yayi pulling trigger ya tattaro dukka bacin ranshi don ya samu kwarin guiwar Harbinta. "Rafeeq Dont shoot" Muryar Daddy sukaji daga gefe yana fitowa daga mota shi da Uncle Zaid, Rafeeq ya kallesu ta gefen ido, yayi guntun tsaki ya maida hankalinshi ga Saude, Uncle Zaid ya daga hannuwanshi sama yana fadin "No, no Rafeeq kar ka harbeta, lets settle this right, Police sunzo, let them take it over frome here please son" siren din Police kawai kakeji, Polis ne suka iso bayan su kuma Motar Mami ce, tare take da Nene da Aneesa da Seebin da dawowar ta kenan daga makaranta taga wannan tashin hankali, kallo daya zakai musu kasan cewa a Tsure suke. Mami tace "Rafeeqqqq ka ajiye Bindigar nan" da tsawa yace "She killed Rafeeah, i wont let her getaway with it" wani Police inyamiri yace " shes not getting away with it, i promise you this, just hand over the Gun Rafeeq Lema" Rafeeq ya nuna Police din da bindigar yace "Dont come any closer, stay where You are, dukkan ku kar wanda ya matso kusa dani, she has to pay for what she did to my little sister, duk ku ja baya" yanda Rafeeq yake magana ne ake ganin kamar zautace, idonshi da fuskar shi sunyi Ja, be ganin kowa burinshi ya ga ya kashe Saude. A hankali a dan tsorace take takawa zuwa gareshi, a gajiye take limis, ta sha wahalar Makaranta yau, a hankali ta furta "Hamma Rafeeq, put the Gun down, you are not a killer, put it down please" a tsawance yace " Shut the Hell up Naseebah, 'Yaruwata ta kashe, zan kashe ta itama, i'll avenge Rafee'ah's Death" da sauri Naseebah tace "No please Hamma na, kar ka kasheta, ka ajiye bindigar, you think Rafee'ah would be happy? She wouldnt want any blood to spill in your hands, She wouldnt be Happy if you kill for her, Rafee'ah ba zata taba jin dadi ace yau ka kashe rai ba, duk munin halaiyar Rai, daraja ne dashi, ba zan so ka kashe Rai ba, i wont let you do that" ta matsa kusa dashi tace "Enough Is Enough Please give me the Gun" sosai ya tsura mata Ido, kamar ba zai Sake ba, ya Sako bindigar a k'asa, wani Jami'in tsaro ya zo ya dauki Bindigar Da Handkercheif, Wasu kuma sukaje suka sa ma Saude Handcuffs, suka Sunkuceta kamar wata diyar roba Nene tace "Ofisa minti daya" suka tsaya, Nene tayi hanzarin karasawa kusa da su, duk suka zuba mata ido, tana zuwa daidai Sauda kuwa ta daga Hannu ta kamtse ta da Mari. Duk suka bude baki cike da Mamaki Nene ta nuna ta da yatsa tace "Ki k'ara sawa a k'ona Gidan wani kiga" duk sukayi daria, haka a ka tura Saude bayan Motar Police, Bayan sun Ja Napep da Achabar nan a Bayan wata Mota, suka wuce da su. Zaid ya kalli Nasiba ya sakar mata Murmushi, murmushin kinyi k'okari, itama Murmushin ta maiyar mai, Zaid mamaki yakeyi tun da yazo nan yake ba Rafeeq hakuri kan ya ajiye bindigar nan yayi banza dashi, amma yaji magana daya da Nasiba tayi, meaning he loves her so much da har zai take maganar shi da na Daddynshi dana kuma Maminshi, Zaid ya raya a ranshi cewa "Sai na Aura maka Nasiba InshaAllah Rafeeq". "Oya ku wuce Gida Shatu, ni da Zaid zamu je Police Station din". Haka duk suka shige mota sukayi Gida, 'yan motar Uncle Zaid kuma suka wuce Police Station.. Bayan Kwana Uku. Saude na nan a Prison, abun duniya ya isheta, bata lafiya sosai tun da aka kawota, Ciwon jiki ne, da Ciwon ido, tun Iskar Napep dinnan ya shige mata Ido, gaba da gabanta Cell mates dinta sun rainata, haka suke lakada mata na jaki, dalilin da ya sa aka maida ta wani kazamin daki dake gefe, warin ma ya ishe bawa, balle kazantar da ke ciki, sai taji Sauk'i zaa makata gaban Kotu don a yanke mata hukunci.. *Bayan wasu 'Yan Sattitika* A cikin kwanakin nan kuwa, wani sabon Kwanciyar Hankali ya shigo Gidan Alhaji Habib Lema, Basu da wata Damuwa, Suna zaune da junansu cikin Aminci da kwanar juna, Harta Aneesa suna janta a jiki don kar ta ga kamar an Wareta, Matsalarta Rafeeq, ita ta hakura da shi don ta san ya mata nisa ya mata fintinkau, amma kallon Azziki baya mata, abun na damunta, Mami ta ritsashi a daki tace kaga " R-Lema, bana son abunda kakeyi? Why are you blaming Aneesa fo what happened? Ai komai ya wuce tunda Saude is behind bars, ba laifinta bane, please ka daina blaming dinta she's your sister ka daina kaji yaro na?" Rafeeq ya dan daure fuska a hankali yake magana "Mami ni bansan irinki ba, for all her Mother did, you still consider her as your daughter, lemme remind incase you've forgotten, Her Mom is a Monster, shes not human, She doesnt Deserve to be Human, She killed your Only daughter" Mami tace "haba Rafeeq Yar Adam ce we all make mistakes, ka daina cewa She's not human" yace "Lord of Mercy, why cant you see what i'm Seeing? Sanyin ki yayi yawa, after all she did to this Family? Mami tell me What can define this? Framing you with Adultery and Fornication. Having baby with the Younger brother then Marrying the Older brother and killing her child's Dad afterwards tell me Mami is this Human? What she did was unforgiveable" tace "Rafeeq na san ta saba mana ta saba ma Allah, ba ta kyauata ba ko kadan ba, amma tunda yanzu tana nan a kurkuku ba shikenan ba, and shes going to pay for all she did, when she recovers zaayi Sentencing dinta, what i'm saying is kar ka bari fushin da kake yi da ita ya shafi Aneesa please" Rafeeq dai ya daijita ne kawai. Sai da Mami tayi dagaske kafin Rafeeq ya fara amsa gaisuwar Aneesa. An gama Gyaran Gidan Nene ya koma Sabo dal, Mami ta rok'eta da Allah kan suyi zaman su nan a tare da ita, don sun Saba sosai, Nene tace "Ahhh Wallahi aa Gidana zan tafi, kawai sai in ta zama Gidan 'ya'ya? Aa zaman da nayi ya isa haka, nafiso in koma chan ni da Seebi ta, Mami tace " Tabdi, ai Seebi na nan har nan da Wata 1 da Rabi, anna zaayi Aurensu da Zaid, Daddynsu ya Amshe miki ita, amma tunda kince zaki goma Gidanki barin je in gaya ma Daddy kince a Aura miki Maigadin Lema sai ku zauna A tare" Nene ta zaro ido tace " Ke Aishatu ki fita idona, haka na ce miki? Wani aure zakuyi man ana zaune kalau? Auren buta ko me? To walle ki fita idona, tam na gaya miki, ai sai muyi ta zama har ki gaji dani, kuma kin ja ma kanki Habibu zan sake ma Aure" Mami ta fita tana daria sosai. Busy Rafeeq da Nasiba suke, saboda Exams dinsu da ya k'arato, a lokaci guda Kuma wani Son junar su na shiga cikin jinin jikinsu, Rafeeq yace da ranshi if you kee on seeing her, you'll only Love her More and you wont fulfill your only Dream, which is to Make Uncle Zaid Happy, Dole ya daina haduwa da ita ko don Uncle Zaid, ya kagara ya gama Makaranta, da ya gama zai ware ya bar k'asar, don yasan Uncle Zaid he would stop at nothing har sai ya aura mai Nasiba shi kuwa idan har Uncle Zaid be aureta ba shima ba zai aureta ba, saidai suk su rasa. Alk'awarin da ya daukar ma kanshi kenan, haka a fannin Nasiba, ita dai tasan Tana mugun ganin girman Uncle Zaid, tana jinshi a ranta kamar Babanta, kunyar shi takeji, kwarjininshi ya mata yawa, Hallarci, So da k'aunar da ya musu ita Da Nenenta zai sa ba zata ta6a butulce mai ba, duk da ba wani Son Soyayyar da take mishi amma ganin girmanshi zai sa ta Aureshi ta kula mishi da tillon diyarshi, ko tana so ko bata so, dole Ta Auri Uncle Zaid, Dole ta yakice Rafeeq Lema a ranta, bata taba zaton tana ma kanta irin Son da take ma R-lema ba, tana me tausaya ma kanta, ta kasance me Son maso wani koshin wahala. Dole ta nisantar da kanta daga R-Lema, don yawan ganin da take mishi ne ya ke k'ara mata sonshi. *********** Rayuwa Kenan, Gaskiar Hausawa da sukace Ramin K'arya K'urarre ne, In zaka gina ramin mugunta ka ginashi dan k'arami, kuma komai nisan Jifa kasa zai dawo, Kuma duk wani abu da ba a ginashi ta hanyar Allah ba, to ba a ganin daidai, K'aryar Saude ta k'are, ba ta da saurin gata, Cikin lokacin kalilan Saude ta koma watta halitta, abubuwa sun mata yawa. Skin Disease har uku, K'azuwa, sankarau da kezbi, hakan ya sa ta koma kamar bushahshen kwado. Sai Idonta daya ya tsiyaye, mai lafiyan kuma ya kamu da ciwon polio mai kwantsa da Yana. Ga kuma ciwon ga6obi a guri uku; bayanta, wuyanta da kwankwasonta. Sai kuma basir mai tsiro gaba da baya. Shi ya sa ta tsani kanta, duk ta koma wata hallita daban, jinya take tayi, da wannan wuri ya warke sai wani ciwo ya baiyana har Allah Allah take Alk'ali ya yanke mata hukunci, don a halin yanzu tafi son mutuwarta fiye da komai. Kotu Kotu ta cika Makil, Iyalan Habib Lema zaune a kujerar gaba don jin hukuncin da zaa yanke ma Saude, a ka fito da ita, da kyar Mami ta shaida ta, duk ta jeme ta kanjame, wasu kuraraji a jikinta ba kyan gani, ga ido daya a makance. Hat tanta ta tausaya mata, Aneesa ma kukan takeyi, Nene ko sai tabe baki. Bayan Saude da Mak'ale sun Ansa laifin su, Alk'ali ya yanke ma Mak'ale hukunci Kisa ta hany,ar rataya bayan kuma ya tona asirin Abokanshi da suka kashe Hafiz Lema tare, Saude kuwa hukuncin Daurin rai da rai da kuma horo mai tsanani, wato Life Imprisonment with hard labour, Ihu d kururuwa ta dinga yi, tana fadin "Alk'ali, dama ka sa a kasheni, donAllah kunkasheni da me zanji? Da cututukar da ke damuna ko da Wannan hukuncin? Na tuba, ni ko Kisa ta hanyar rataya ne ku min, ko harbi na zakuyi kuyi, donAllah kar ku barni da Rai, ku kasheni, Please end my Suffering, li want to die" haka Saude ta dinga Ihu tana sambatu, da yawa ta ba tausayi a kotun nan, ko da Nene taji wasu mata Na cewa ta basu tausayi tace "don ba ku san abubuwan da tayi ba, haka ta dan basu labari a takaice, matan nan suka tabr baki tace, ya mata daidai, Ai duniya Makaranta, abunda ta shuka ne take girba. Ba na tunanin zata k'ara Sati biyu a raye don Wannan kurarrajin jikinta ba na warkewa bane" Nene tayi daria tace "yauwa yan gari" Mami kuka Seebi kuka Aneesa Kuka, Rafeeq na ganin haka ya tattara su ya maida gida don ko kadan bata bashi tausayi ba, yana ganin hakan ne daidai ita, baya so ta mutu don yasan mutuwa hutu ne a gareta, gwara ta tsaya da ranta bakin ciki ya cinyeta. Biki Saura Sati Biyu *Mafarki* (Afuwan. Abunda ya samu kenan. Zan cigaba, ina Makaranta☹☹☹ Masu min mgn ta prvt da ban samu nayi replying dinsu ba ba Afuwan.abubuwan da yawa) 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀      NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) This page is for all Members of JUST NOVELS, Baby nice and above all Sadeeqah Ummu Sudais, ILY'lls Oceans and Galaxies❤ Pg5⃣9⃣ Biki Saura Sati Biyu *Mafarki* Daria sosai sukeyi, Rafee'ah tace "Kakar ki na da abun daria, Allah dai ya ja kwana" Seebi tace "Ai zama da Nene sai hak'uri, wanda zai zauna da ita sai ya kai zuciya nesa, don haka zata dinga dasa miki kayan haushi, idan Nene ta k'unsa miki wani abun to sai kinyi kuka" Aiko Rafee'ah ta tuntsire da daria, sai da tayi me isarta kafin ta tsagaita, ta kamo hannun Seebi, ta murza a hankali ta na me Kallonta cike da So da k'auna, chan kuna ta rungume ta sosai ta na shafa mata baya tace "KE ALHERI CE Nasiba Muhammad, kin cika min buri na, Everything is now in place, now i can rest in peace, kin gama min komai, Allah kadai ne zai biyaki da daukacin Zuriar ki, kun kasance Haske a cikin Zuriar Lema, kun kasance abun kwatance a Alumma, kinyi Jihadi, kin sadaukar da Rayuwarki akan mutanen da baki san ko su waye ba, dalilin ki abubuwa da dama Sun faru, Ina Alfahari dake, Ina kuma miki Fatan ALHERI, Allah ya hadaki dauwamamiyar farin ciki, Allah ya tsare ki da Yayana" Seebi tace "Allah sarki Sis Rafee'ah, zaki sani kuka, Amin ya Allah, ke kika bani hope a Lokacin da nake zaton hakan ba me yiwuwa bane, Wannan shine kallan tawa Jarabawar, ba dabara ta ba wayau na" ba zan gaji da gaya miki *KE ALHERI CE* ba" Seebi na daria ta rungumeta tace "Kema Alheri ce Sister Rafee'ah, without you, none of these would have Happened" itama Rungumeta tayi ta na shafa bayanta a hankali, chan tace "Nasiba, This the last time you'll see me, Its been a priviledge to know you though i didnt get to spend more time with you, i wish we met while i was still Alive, but Nevertheless I Thank Allah for making these all possible, Cikin ikon shi, Izzar shi da Zatin shi ya sa kike mafarki dani, Ba abunda zance sai Alhamdulilah" Nasiba kuka takeyi sosai, tace DonAllah ki tafi, you've become part of me, dont leave me please" "Ohh Nasiba, dont cry Habibty, ina ma laifi we met for the 4th time? You'll miss me but abun zai zo miki da Sauk'i, tunda gaki ga Hamman mu, in kina tare dashi, zaki dinga ji kamar kina tare dani ne, you'll see him in me" Seebi ta wurga idonta ta sama tana cewa "That your Arrogant pompous Brother, he makes me sick" Daria Rafee'ah tayi sosai tace "Alright enough, i have to go now, but ina da Sak'o ga kowa" ki gaya ma Daddy nace " Ya gina Massalatai da Islamiyoyi da Rijiyoyi, ya kuma dinga Sadaka da bada Zakkah, ya kuma dinga Ciyar da Marayu " Nasiba tayi Murmushi ta maimaita abunda Rafee'ah tace, kamar a kunne Daddy zan gaya mai" tace yauwa Mami kuma kice nace ta cigaba da Hak'urin da na santa dashi, ta kula da Mijinta, ta zama Mace ta gari, kar rudun duniya ya sa ta shagala, kar Kawayen Banza su sata bin bokaye don Mallakar miji ko wani abun daban, ta Tsare Ibadunta, ta rik'e Adduoin InshaAllah zata ci ribar Rayuwa" kamar dazun Nasiba ta sake Maimaita abun da Rafee'ah tace, Fee'ah ta cigaba da cewa "Uncle Zaid the Noble Gentleman,wanda zai kuntata ma kanshi don ya faranta ma wani, kice mishi Allah kadai ya san yanda zai biya shi, Allah ya Saka mishi da Alherin sa, Ya raya mishi Takwara ta, ya bashi mata ta gari wacce zata kula dashi kamar yanda ya dade yana kula da mutanen da ke kewaye dashi, Allah ya biyashi da gidan Aljannah" haka Nasiba ta sake maimaita abunda Fee'ah tace, Rafee'ah tayi daria tace My Next message is for Nene, kice mata nace "Ba kamarta, Allah ya hada mu a gidan Aljannah Firdausi" Seebi tayi daria ta maimaita, Lastly Hamma na, kice mai nace "Stop getting angry Easily, Dont get Mad at anything, dont be Sad anymore, Live your Life, and Be happy, I love you so much Hammana" haka Nasiba ta maimaita sak'on Rafeeq, "And you, i dont know if i'm supposed to ask you this, because you've done alot for me and My Family, but i really want you to do this, I want you to take very good care of Hamma Rafeeq, i want you to love him for the rest of your life, Please" Sister Rafee'ah me kike cewa ne haka? Wannan hakkin matar da zai aura ne, how am i supposed to take care of him for the rest of my life? I'm getting married In 2weeks time, i cannot promise you this, i'm sorry i cannot do this, i shall take care of my Husband" Murmushi me kayartar da Fuska Rafee'ah tayi, ta lumshe ido a Hankali tace "Goodbye Nasiba, Be Happy" "Wait Sister Rafee'ah, kar ki tafi donAllah" ************ Cikin Barcinta taji ana shafar k'afarta, bata son tashi daga mafarkin don tana sa ran sake ganin Rafee'ah, amma sai dai kash tasan Rafee'ah ta tafi kenan don baccin ya fita daga idonta, a hankali ta bude idonta ta sauke su kan mutanen da ke tsaye kanta, cikin hanzari ta mik'e tsaye tana mitsitsika ido,ta bisu da ido, ta kai dubanta ga Nenenta tace "Lafiya Nene?" Nene tace "Sambatu kikeyi cikin bacci Seebi, kamar kina magana da wata cikin mafarkin ki, ina Sallahr Dare naji kawai kin fara maganganu, na zo daka miki duka amma ko shurawa bakiyi ba, haka na tsaya kanki jin kina ta turanci na dinga miki addua, dana ga abun ba me karewa bane ya sa na je na kwankwasa ma su Aishatu nace baki da lafia, tun kafin su karaso ta kira Dunkum da Zaidu bawan Allah tace su zo a kaiki Asibiti, shine ma fa mukazo dob cicinbar ki, sai Mukaji kina wani magana Sai Zaidu yace a tsaya yaji kamar ana son Isar da Sak'o a garesu, tsaf muke jin Amsar da kike badawa amma ba ma jin abunda ake ce miki" Seebi ta tashi tsaye tana salati, Mami ta matse hawayen ta tace "Nasiba da Rafee'ah kikayi mafarki ko?" kanta a kasa ta daga kai alamun Eh" Mami tace "For howlong kike mafarki da ita, saboda yanda naji kike magana kamar you two are so close to eachother" "Nayi mafarki da ita So 4 ko 5" Allahu Akbar, inji su, Rafeeq ya matso kusa da ita, ya tsura mata ido, yace "Naseebah tell us everything you know, kar ki boye mana komai" Nasiba ta kwashe komai tun farkon Mafarkinta da yanda ta nemi Alfarma taje ta biya mata bashi a makaranta, da yanda tasa bincikar Rayuwar R-lema, da yanda ta sa ta shiga rayuwar shi, da yanda ta taimaka mata gun tona Asirin Saude har zuwa rana ta yau da duk sukaji komai" Allahu Akbar kakeji da kirari ga Ubangiji Allah, abun Mamaki kamar Almara, ba su taba jin irin haka ba ko a Mafarki. Rafeeq ya rasa tunanin me zaiyi ya rasa sukuni, Wacce iri ce Naseebah? She did alot for him, how he wish he could show her love and Appreciation, he loves her so much, and after this wani girmanta ya karu a idonshi, wani sonta ya sake ratsa shi, wani kaunarta ya shige shi, hawaye ya zo mai da sauri ya juya ya bar dakin, Zaid ya bishi da ido ya na tunanin wannan abun Mamakin" Daddy yace "Nasiba My Child, Allah ya miki Albarka, naji Sakkon diyata Rafee'ah kuma InshaAllah gobe zan fara aiwatar da yanda tace Allah Kuma ya gaffarta mata ya sa Aljanna ce makomarta" duk suka amsa da Amin, Daddy yace "Oya muje mu kwanta is getting late" Mami tace "No, i'll sleep close to my daughter today" Daddy yace "Babanta kuma fa?" Mami tayi daria tace "yaje hutu" duk suka sa daria, Daddy ya fita, Mami ta kwanta gefen Seebi tana shafa kanta, Nene ta shimfida Bargo a k'asa tace "ki maidata ciki karshen shigewa jikinta". Akwati Set1 (Guda 6) Mami ta hada, komai ya ji, Mami tace " idan zaka wuce Kaduna sai ka tafin ma su Ummin Anan dashi, duk da tace ba sai an kai ta gani ba, amma yakamata a bata hakkinta na uwa" Nene tace "Ni da kun bi ta tawa tunda Ran Jumaa zasu zo ba sai an sha wahalar kai kaya Kaduna ba" Mami tace dai a kai musu su gani. Su Miemee da Usheey sunzo ganin lefe, suna ta murna don Seebi tayi Goshi, kaya sai sambarka, nan suka ritse Uncle Zaid a Parlor suna zolayar shi, dariya kawai yakeyi, Miemee tace "Uncle Zee ya maganar Dinner? Kasan dai biggest hall of them all zaa kama mana, Soli Center nake ma bayani, yayi daria yace "Kar ku damu, ga Son nan kuyi magana dashi, zai yi komai" Meemee ta waiga taga Rafeeq na shigowa Fuskar nan murtuk'e, a ranta tace "kai dai ka sani". Bayan Kwana Biyu KADUNA "Yaya Destiny brought Nasiba And Rafeeq Together, They belong to eachother, Ba ka tunanin dalilin da ya sa Allah ya kawo Nasiba garemu don ta auri Rafeeq ne, Nasiba da Rafeeq suit eachother, ko ban fada ba ka san Nasiba na Son Rafeeq, Mami kinsan dacin rabuwa da masoyi, please lets not deprive them of their chance to be Happy, lets help them be together, if you are worried and concerned about me, kar ka damu, i'll be fine eventually, mata da yawa a gari, i'll get one" Alhaji Habib yace "Zaid nagaya ma Times without Number cewa zan aura ma kowa Rafeeq but not Nasiba, Nasiba taka ce, Rafeeq is not worth her, he'll only hurt her da miskilancin shi, and Shes like a daughter to me, ba zan sa rayuwarta cikin kunci ba, shiyasa zan aura mata kai, kaine zaka kula min da ita" ran Zaid ya fara 6aci yace "Yaya you always tell me that you'll do anything for me, and Mami kullum cewa kikeyi kina so ki biyani for all i did to you, you all want to make it up for me, So this is what you'll do to make it up for me, Get Rafeeq married to Seebi, haka kurum zakuyi ku biyani duk abubuwan da na muku" Mami da Daddy suka kalli juna, Daddy yace "Zaid why are you so Stubborn, ban san ka da haka ba, i'm sorry i cannot do this" Mami ma tace "Sorry, Zaid ask for anything but not This" Rafeeq da ya shigo dakin Daddy ya gama jin duk abunda suka tautauna kasancewar wayar a Handsfree yake yace "ko sun amince ni ba zan amince ba, ba zan taba hada kaina da kai ba" cikin bacin rai Zaid yace "waya sa bakin ka Rafeeq? Who is asking for your opinion, shut the hell up boy, God!! you all make me sick" Dif Zaid ya kashe wayar ya cillar da ita kan kujera yana safa da marwa cikin Parlo, why is it that noone seems to understand? Shi gaskia ba zai shiga tsakanin masoyan nam ba, ya lura da irin son da Nasiba ke ma Rafeeq, ya lura bata sonsa, kuma ko kadan beji haushinta ba, ko kadan be ji kishin Rafeeq ba, tsaki yayi ta yanda zai bullo wa Yayanshi da Matarshi, ko ta halin k'ak'a bazai auri farincikin Rafeeq ba, a fusace ya bude fridge din Parlorn shi ya ciro kwalbar ruwa ya bare marfin ya cillar da ita ya kafa kai ya fara kwankwadar ruwan. "Assalam Alaikum" wata zazzakar murya tayi sallama a k'ofar parlon tare da shigowa lokaci guda, fesar da ruwan bakinshi yayi tare da sakin robar a kasa sakamakon kwarewar da yayi, wata hallita ce tsaye da Bak'ar Jallabiya, kamar Maman Ayman, sai dai wannan tafi Maman Ayman haske, tafita kyau, tafita dan kauri da tsawo kadan, kamar Balarabiya, dam Gaban shi ya yanke ya fadi sakamakon hada idon da sukayi, lokaci guda ya ji shi a wani yanayi me wuyar fasaltuwa, rabon da yaji irin wannan yanayin an jima, yayi ta maza ya saita tunanin shi ya taka daf da ita, kamshinta ya bugi hancinsa, ya lumshe ido wani natsuwa na shigar shi, Ya tsura mata ido yana son gane wani abu game da ita, , itama shi din take kallo da sauri ta kawar da tunanin da takeyi game dashi, don duk yanda take zaton shi ya wuce nan, ya zarta tunaninta, da ta ga Kallon ba me k'arewa bane ta cira baki tace "Ina wuni, donAllah ina neman Zaid Lema" cikin sanyin jiki ya lumshe ido yace "Ni ne, how may i help you?" a tsaye tace "Sunana Zainab Sani Sister din-- bata karasa ba yace "Sistern my late Wife, Safiyya" tace "Exactly" yace "Ban sanki ba, but i've heard about you from her, and da kika shigo ina ta kallon ki, da kikayi magana kuma na ga tsantsar kamar da kikeyi da Ita" cike da k'asaita tayi Murmushi, da ya lura 'yar aji ce, sai shima ya ari fuskar dansa Rafeeq (lol) yace "So why are you here? ta kalleshi da mamaki tace " I'm not here for you, i'm here for my daughter, i came to take her with me, its time for her to Live with her Mother's Family". Da mamaki Zaid yace "What??". _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀      NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg5⃣9⃣ (This Line is for all the Amazing Sisters that Sacrificed their Happiness for their Nieces and Nephews, i'm talking about the Sisters that gt Married to their Late Sister's Husband. Only Allah Can Reward them💙) "Eh kaji ni sarai, nazo in tafi da Rafee'ah Aymana ne, jiya na dawo k'asar, an gaya min cewa Aure zakayi, Ba zan yi gangancin barin ta wurin ka ba, ba zan bari ta fukanci wahalar MATAR UBA ba, ba zan bari tayi kukan rashin uwa ba, shiyasa zan dauketa. Kallonta Sosai Zaid keyi, Sosai ta burgeshi, yanayin maganar ta, bata shakka ko tsoro, yanda ta nuna son da take ma Ayman ya burgeshi, da ta ga kallon da yake mata sai tace "Mallam ka dauko min diyata, sauri nakeyi" Zaid ya murmusa, yace "Ga dukkan alamu kina Son wannan diyar taki" tace "So fiye da kaina ma" yace "Good, amma kiyi hakuri, ba zan iya ryauwa ba Ayman ba, na rasa Mamarta ba zan iya juren Rashin ta ba itama, kiyi hakuri ba zan iya baki ita ba" Zainab ta bata rai tace "Bangane ba" ya yi Murmushi yace "Baki gane hausar ba? Oh ashe balarabiya ce, gashi ni ban iya turanci ba balle larabci, hakuri kawai zakiyi, ba zan iya naki Ayman ba, Kuma idan nayi aure Amarya ta zata rik'e min ita, yanzu haka ma ba ta tare dani a garin Kaduna, tana chan garin Katsina tare da Amaryar tawa" Idon Zee suka ciko da hawaye, ta sausata murya tace "Please ka taimaka ka bani ita, ina so in kasance tare da ita, ina sonta Sosai" Zaid ya girgiza kai tare da Murmushi yace "Nope, ai ina jin ganinta ma zai miki wahala balle ta zauna tare da ke, kinga ba ma lallai bane Mijinta ya Amince da ita ba" da sauri tace " Wallahi banda aure, kuma kafin inyi sai na tabbatar Mijin da zan aura ya amince zai riketa ya dauketa a matsayin Uba" yace "Tabdijam, da Mahaifinta a raye, har sai an nemi izini wani? Wannan ma na daya daga cikin dalilan da zai hana in baki ita, ba zan baki ita ba gaskia" ran Zainab ya gama 6aci tasan in ta k'ara bude Baki zata iya fashewa da Kuka, ta sa6i jakkarta ta juya ta bar Parlorn ranta a jagule, Zaid kuwa Murmushi yayi Sosai. ********** Tana isa Gida ta fada kan Mamanta ta fashe da kuka, Maman ta hau lallashi tana cewa "Zainab me yasa ki kuka? Me ya faru? Wani abun ya samu Aymana?" cikin kuka tace "Umma, cewa yayi ba zai bani ita ba, wai Amaryar shi zai ba ita, yanzu haka Aymana na Katsina ita zata kular mishi da ita" Umma tayi Murmushi tace "Zainab dama sai da na gaya miki Zaid ba zai yarda ya baki Aymana ba" "wai ma Umma tun da Safiyya ta rasu mesa baki gaya min ta bar diya ba? Eh Umma? Meyasa kuka boye min ta bar diya, haka Aurenta, sai dai naga hotuna a IG, gashi har diyarta ta fi shekara, haba Umma me ya sa kuke min haka ne?" Umma tace "Zainab hakuri zakiyi, umurnin babanku ne, ya san halinki, kina iya cewa zaki dawo, kuma Lokacin kina tsaka Da rubuta Jarabawa, kuma in kika dawo kika ga Aymana kina iya cewa ba zaki koma ba, ko kuma ki nemi a baki ita ki tafi da ita, shiyasa yace in har aka bari kika dawo, sabon tashin hankali kowa zai shiga, kuma Zainab ki kwantar da Hankalinki, Zaid mutumin kirki ne, yana da Amana, ya kan kawo mana Aymana shi da Marikiyar Ayman, mutanen kirki ne wallahi, kar kiji fargaban komai, Zaid zai kular miki da diyarki" "Umma ba shi nake ji na, ina tsoron Matar Uba, ina tsoron Kar ta sha wahalarta, shiyasa nake so ya bamu ita, ai mu ke da hakkin riketa" Aa fa Zainab, shi ke da hakki, sai yanda yayi da ita" kafin Zainab tace komai sai jin Sallama sukayi, k'anin Zainab ya shigo yace "Umma ga Yaya Zaid nan a waje" Umma tace "Bismillan shi, ya shigo" Zainab ta 6ata rai tace idan be bani ita ta dadi ba, zan maka shi Kotun Musulunci" Daidai da Shigowar Zaid fuskar nan kamar kullum dauke da Murmushi, A ladabce ya durkusa har k'asa ya gaida Umma, Umma ta amsa mai cikin sakin fuska da girmamawa. Zainab ta hadiye fuska ta na karkada k'afa. Murmushi Zaid ya sake yi yace "Umma ashe 'yan makaranta sun dawo?" Umma ta kallo Zainab da ta hade girar sama da k'asa tace "Aiko dai su Dr Zainab an dawo" Zaid yace "Ahhh ashe Dr ce" Umma tace aiko Likita ce, jiya ta dawo ta kammalla karatun Likitamcin ta gaba ki daya, saura Housemanship da zatayi a Barau Dikko" Zaid yace "Allah sa Alkhairi" "Amin Amin" Abba ba ya nan ko? Umma tace "Ya je Government House" su ka danyi shiru na wani dan Lokaci kafin Zaid yace "Umma sai gashi Likita ta zo min da wani zance" Umma tace "ina ruwan Zainab, jiya ta dawo, daga ce mata Mijim Marigayiya Safiyya ma zai yi aure nan da Sati biyu, Kai Mu'allim sai kace nan za a kawo mana Aymana? Sai ta tambaya wacece Aymana, kasan ba a gaya mata Safiyya ta bar diya ba, ai fa tun da ta ji ance Diyar Safiyya ce take ta ruwan Wulakanci tun jiya, wai zata je ta daukota, ya zaayi mu bar maka yarinya, wacewace ita sai ta amso ta" Zaid ya fadada Murmushin sa, yace "Umma zan bata Aymana idan tana so" Umma da Zainab suka zuba mai ido, Zaid ya maida dubanshi ga Zainab da ta zuba mai idanuwanta, yace "kwarai kuwa, zan baki Ayman ki rayu da ita, har girmanta, har tsufanki, Aure kawai zai rabaku da ita" ba ta san sanda Murmushi ya kubuce mata, tace "Nagode Sosai, Allah ya biya ka, Allah ya ji kan Sofie, nagode da ka Amince zaka bani ita, Allah ya baku Zaman Lafiya da Amaryar ka" yayi Murmushi tare da cewa "Amin, amma fa da Sharadi daya, i have a condition" da Murmushi a fuskarta tace "Koma meye zanyi, tell me" a takaice yace "Marry me" idanuwanta ta gwalalo, tace "What?" ba tare da wani fargaba ba yace "Ki Aureni, and Ayman is yours" ta mik'e tsaye tace "Are You in your right sense? In bacci kakeyi ka tashi, bazan taba aurenka ba, ta ya ma zaayi in auri Mijin Yayata? Tabdijam, don nace ka ban diyarka zakace in aureka? You are using the love i have for your Daughter to use me, To ba zan aureka ba, ba zan auri Mijin Yayata ba" Murmushin dai yayi yace "Ina Yayar taki? Ba ta rasu ba? Idan tana da rai zance ki Aureni ne? Ai Aure tsakanin mu be haramta ba, and kuma if theres anyone Safiyya would like me to get married to is defintely You, for the sake of our Daughter" Wani kallo ta ke binshi dashi, tace "ko ma meye ne, ba zan aureka ba, ba zaayi wannan cin amanar dani ba". "Zaid" cewar Umma da ta gama nazarin Zaid da Zainab , Zaid ya maida dubansa ga Umma, Umma tace "Bari in dan ga Zainab" ta mike tare da jan hannun Zainab suka wuce Daki. Daidai da shigowan Abban, "Ahh Zaid Sannu da Zuwa, ka dade da zuwa? Ya na ganka kai kadai?" Zaid ya durkusa har kasa ya gaida Sirikin shi, suna ganin mutuncin Juna, Zaid yace "na dan jima, yanzu Umma ta shiga ciki ita da Zainab" Abba yace "Toh toh, barin shiga inji". Dakin Umma ya shiga, ya tarar Umma na Ma Zainab fada ko da ya tambayi ba'asi, Umma ta danar dashi abun da ke faruwa, Sosai ya ji dadi, don har ranshi yana Son Zaid, yana son sake Hade iri da shi. Zama yayi sosai yana me kallon Zainab chan yace; "Zainab ki saurareni da kyau, wannan Mahaifiyar ki ce, Ni ko Mahaifinki ne, ba zamu so wani abu ya sameki ba, kuma Hak'k'ina ne in za6a miki Mijin Aure, Zaid Namiji ne da ko wane Uba zai so ya za6a ma diyar shi shi a Mijin Aure, Zaid na da kirki, ni ba talaka bane amma duk wata Zaid sai ya aiko da Motar Abinci duk wani nauinka Abinci yana kawo mana, tun daga lokacin da yake neman Yayarki har zuwa rana irinta yau, Zaid na da kirki da mutunci da kuma girmama na gaba, Shekarar shi daya da dori Yayarki bata taba cewa ya mata ba daidai ba, Zainab idan nace zan gaya miki irin Kirkin Zaid to zamu dade ina miki magana daya, ke ba wani tsaiyayye ba, ba kya kula Samari, ba kya sauraronsu, da ta ni ne da tun kam ki gama karatunki na miki Aure, amma saboda ba wani tsaiyaye na bari kika kammala, Zainab ba zan miki Auren dole ba, amma in kin nemi shawara ta, to Zaid Mijin Aure ne, Allah shi ya kawo miki Zaid a lokacin nan, kuma tunda shi ya bukaci ki aureshi ai ta kwana gidan Sauki, ba zaki ce ana so a hadaki da wani ba, shi ya kawo kansa, na yarda dashi dari bisa dari, sannan kuma kina maganar Zaki ci Amanar Safiyya, me ya kawo cin Amana? Kar ki manta ta rasu ta bar diya, kuma na san ba zata so diyarta ta sha wahalar Matar Uba ba kamar yanda kika ce, zata so ke ki kasance tare da ita, da Mijinta, Shawara ce" Shiru tayi Alamun maganr Mahaifinta ya shigeta, Umma ma ta sake k'arfafa mata guiwa, Abba yace "Maza Autan mata, je ki kuyi magana kinji" cikin kunya ta tashi ta fita. Zaune ta ganshi yana bin hotunan Parlorn da ido, nan ta samu ta k'are mai Kallo Tsaf, Haddade ne son kowa kin wanda ya rasa, ya hadu iya haduwa, komai na sa yayi, to meyasa zata ki'sa? A hankali ta k'arasa tare da Sallama, ya amsa tare da mikewa ya na wurga mata Murmushi, ya karaso kusa da ita, tana tsaye har suna jin hucin juna, yace "So??" cikin sanyi ta tace "You like smilling alot" Murmushin ya sake sakar mata yace "Dont i have reason to Smile? I'm with you afterall" Murmushin kunya takeyi, yace "So? Will you Marry me?" a hankali tace "Yes i'll Marry you" Murmushi suke sakar ma Juna, ji sukayi kamar sun shekara da haduwa, wani So da kaunar junansu ke shiga jinin jikinsu, wani Shaukin k'auna ke shigar Zaid, be taba jin wannan yanayin a tare dashi ba. Ta samu kwarin guiwan cewa "Mu zauna" suka zauna su ka tsura wa juna Ido, a hankali tace "Yaushe zan ga Ayman? Yace $whenever You are ready" tace "A shirye nake yanzu" yayi daria yace "yamma yayi, ki bari Gobe sai muje ko? Alright?" ta gyada kai cikin murna. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Zaid Matar da zaka aura nan da Sati Biyu fa?" cewar Abba, Zaid yace "Matar Rafeeq ce, Rafeeq zata aura" duk suka kalleshi suna neman karin bayani, Abba yace "Toh a katin daurin Auren da a ka kawo min sunanka ne a jiki" Zaid yace hakane, amma abun da ya faru shine ita yarinyar da Yaro na suna matukar son junan su, cikin rashin sani aka sa ranar da ni, Ko da Allah be kawo min Zainab ba, gaskia na fasa Auren yarinyar, don D'ana take so bani ba" Karaf Zainab tace "Kai fa? Kana sonta?" duk suka bita da ido, itama sai taji kunyar maganar da tayi, yace "Ina sonta, amma sai bayan haduwar mu dake na san cewa irin son da nake ma Rafeeq nake mata, ba irin So na Aure ba" wani dadi ya lullube ta, Abba yace "Toh yanzu ya kake so ayi?" yace "Abba, so nake in gabatar da Maganar ga Yayana, sai a hade Auren da na Rafeeq din nan da Sati Biyu" Abba yace "Wannan gaggawa haka?" Zaid yace Abba ba Gaggawa bane, saidai in kana da bukattar yin bincike a kaina, sai ayi abu a tsanake " Abba yace "Haba Zaid, bincike na me? Zaid ai kai ba bak'o bane, mun sanka mun san kai ko waye, ba sai anyi bincike ba, ba komai zamu shirya nan da Sati Biyun, zan kira kawunta in sanar dashi, Allah ya sa Alkhairi". Sosai Zaid yaji Dadi yace " Gobe InshaAllah zanje Katsinar don yi magana da Yayana da Magabacin mu" "Allah ya kaimu" inji su Umma, Cikin In ina Zainab tace "Abba nima ina so inje Katsinar don ganin Aymana" Abba yace "Toh uwar azarbabi, ba inda zakije, ki bari har ya kawo miki ita" "Abba Please kar ka hanani, kaga ban taba haduwa da ita ba, i cant wait till two weeks, Please Abbana" Abba yace " "Abba zuwan ta zai taimakeni gurin yi ma Yayana bayani, a yi hakuri a barta taje" Abba yace "I know she's safe with you, Allah ya kaimu goben ya kuma tsare Hanya" Zaid ya ji dadi sosai sukayi Sallama da niyyar Gobe zasu wuce Katsina. WASHEGARI KATSINA (Sorrynku, ku cigaba da min uzuri, Same excuse din dai ne, zaa cigaba daga nan InshaAllah) 👧KE ALHERI CE🙇‍♀      NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) CIGABAN5⃣9⃣ Gaba ki dayan su suna Zaune a Parlorn k'asa suna lunch, Ayman na kan cinyar Seebi ta na bata a baki, ba tare da ya kalleta ba yace "Dame dame zaki buk'ata a hidimar bikin?" a takaice tace "Nima bansani ba" ya tsagaita cin Abincin ya kallota kamar ba zaiyi magana ba chan yace "bangane baki sani ba, ba naji wannan friend dinki tace meye meye ba" Mami da Daddy da suke binsu da ido suka kalli juna suja bata baki, sun lura da Rafeeq yanzu abu kadan yake harzuk'a shi, Mami tace "Rafeeq, ai ba haka akeyi ba, ba da ita ya kamata kayi magana ba, ai ga Aneesa nan, ko kuma friends dinta zaka sama sai kuyi maganar komai" ya dan bata rai "Ni ba wurin wata da zanje, suna da Hayaniya gasu da damuwa, Bari zan ma Lesh magana, sai ya same su" Nene dai ta ta6e baki, ba ta son tanka musu, don yanzu zata sake layi shiyasa tayi shiru". Sallama Zaid yayi a tare suka amsa, ya kusto kai yayi dining area inda yake jin surutan su da karan plates da chokula, Daddy yace "Zaid, kaine a tafe? Kai ba kajin sintiri a hanya ko? Ka dauki hanyar Katsina zuwa Kaduna kamar Tafiyar minti 30, kai ba ka gajiya ne? Kullum kana hanyar Katsina, shekaran jiya fa ka tafi" Nene tace "Yanzu dai ya iso Lafiya, ai shikenan, Mita na ne? ya ajiye Mata ai dole ya ke zuwa ganinta ko" Yak'e kawai Zaid yayi, Mami tace Sannu da Zuwa Zaid, Aneesa da Seebi sukace "Sannu da zuwa Uncle Zee" ya amsa cikin sakin Fuska, Rafeeq ya dago kai suna masu hada ido da juna, ya sakar mai da Murmushi Yace "Kazo Lafiya?" "Lafiya lau Boy" Mami tace "Oya Zauna ka kwashi Gara, nasan kana nan da yunwa" yace "Eh Mami, amma ba ni kadai bane, mu biyu ne" "kai da waye? Ka barshi waje? Haba je ka shigo dashi" Murmushi yayi ya fita, suka cigaba da cin abincin su, chan ko sai gasu sun shigo, Zaid a gaba, Zainab a baya tana tafe sum sum, sanye take ta Hadaddar Jallabiya, K'amshin turarenta ya sa su dagowa gabaki daya suka zuba mata ido, Zaid na zuwa ya sa Hannu ya dauki Ayman ya mik'a ma Zainab ita, Zainab ta amsheta ta rungumeta take taji hawaye sun fara bin kuncinta, abun mamaki Lamo Ayman tayi a jikin Zainab, bata yi mata k'uiwa ba, Sosai ta matse Ayman a jikinta tana jin so yarinyar har 6argonta. Nene tace "Zaidu bawan Allah, wannan fa?" yayi Murmushi ya kalli Mami yace "Sister din Marigayiya Safiyya ce, shekaran jiya ta dawo daga Makaranta" Allah Sarki inji Mami da Alhaji Habib, Sannun ki da zuwa, kun sha hanya, ya su Mamarku? Ya kuma k'arfin hakuri? Allah ya ji k'anta ya rahamshe ta" Zainab ta amsa gaisuwar Mami, sannan ta Mata gaisuwar Rafee'ah, ta gaida Nene ds Alhaji Habib, Seebi da Aneesa suka gaidata, with a big smile on Rafeeq's face ya gaida Zainab, farat daya ta mishi, ko don ta na son Angel dinsa ne? Matashiya ce da ba zata wuce Shekaru daya da shi ba, 24 zuwa 25. Mami tace "Zauna kinji Zainab mu ci Abinci" Zaid ya Ja kujerar baya ta zauna shima ya zauna don cin Abinci. Bayan sun gama cin Abinci suka hadu a Parlor, Ayman har tayi bacci jikin Zainab, Zaid ya kalli Alhaji Habib da Mami, yace "Erhm,Yaya, Mami, dama na kawo Zainab ne don taga Ayman da kuma in sheda muku cewa zan aure ta, ba wai don tana k'anwar Safiyya ba, aa saboda dai ina sonta" Rafeeq ya zaro ido yana mamakin furucin da Uncle Zee keyi, Mami ta dan razana a ganinta kamar cin fuska ne ga Nasiba, ace tun Kafin Aurenta har an fara maganar yi mata Kishiya Mami ta k'irkiro Murmushi, Daddy ya yi ta maza yace "Zaid, ina ganin ai kamar its too early, ya kamata ku k'ara fahimtar junanku, da ka bar wannan maganar an cigaba da Maganar ka da Nasiba, nan gaba sai ayi maganar Zainab din tunda ka nuna kana sonta, mu kuma abun da kake so zamu maka" Gaban Zainab ya yanke ya fadi, kar mutanen suk'i amincewa da ita, gashi ta bari Son Zaid ya mata Kamu ba na wasa ba, har ta fara tausayin kanta. Jin muryar shi tayi yace "Aa Yaya, zan aureta in the next two weeks, ba zan iya bari har mu kai wani lokaci ba tare da juna ba". "Kai Zaidu Bawan Allah kalle ni nan, ni tsarar kace? Ko don kaga ina daga maka k'afa shiyasa kake son Takani? Seebi ta maka kama da wacce zaka Wulakanta? Kai ka samu farar mace ko? Dangin larabawa zaka ma Seebina Wulakanci? In banda Wulakanci ya zaka fara maganar Auren wata tun kafin ka aureta? Don cin fuska kace rana daya zaa daura? To wallahi ka fita idona in rufe, ban ta6a watse maka karama ba, banso in fara yau, ina ganin girmanka, ka ja dan gemunka kayi fatali da wannan magana ta auren wata" Seebi ta dago cikin nauyin baki tace "kiyi hakuri Nene, ba komai Wallahi, bakomai don ya aure mu Lokaci guda, Uncle Zaid Allah ya sa Alheri" "ke dallah rufe min baki, me kika sani, banza samna kawai, in banda banza wa ke bada goyon baya a mata Kishiya? Bazan hanashi Aure ba, amma saidai ya zabi daya, Saidai a fara daura Aurenku in kin haihu yana iya Auren" Nene ta karashe ta na me hararar Zainab da ta gama tsorata da Nene, Mami tace "Kiyi hakuri Nene, da Nasiba aka fara Sa Rana, da ita zaa fara daure Auren" Zaid ya dafe kai yace "Nene wallah ban isa in Wulakanta Nasiba ba, ya zaayi in Wulakanta ta? Ina mata tanadi ne, tanadin da zata fi kowa Farinciki da faruwar shi, ina so taji dadi har karshen rayuwarta, na sa ma mata wanda zai so ta ya kula da ita fiye da ni, na gano wanda ya fi ni sonta, na kuma gano ina ma Nasiba So irin na Uba da Diya ne" Seebi da Rafeeq suka tsura ma Uncle Zaid ido, Rafeeq fargaba ce, fargaban wanda Uncle dinshi ya samo ma Nasiba, Nene tace "Zaid me kake nufi ne na kasa gane komai, meyasa kake maganar Wani bayan ga ka?" a takaice yace "Saboda ba ni zan aureta ba" duk suka ware ido "Rafeeq zai aureta, Ya fi ni sonta, ya fi ni k'aunar ta, kuma zai kula miki da ita fiye da zatonki" Nene ta murtuk'e fuska tace "Waye Rafeeq?" Zaid yayi Murmushi yace "Dunkum Naki" Nene ta dafe kirji tace "Allah ya tsari Kakata Laminde, Dunkum din zan baiwa Nasiba, koo a mafarki" kan Rafeeq a k'asa, ya shiga duniyar tunani, son Uncle Zaid na ratsa shi, Uncle Zaid ba zai ta6a hutawa ba sai ya mallaka mishi Seebi, da me zai saka ma bawan Allahn nan?. Ai Nene in gaya miki, Dunkum dinki na son Seebi yanda baki tunani, kuma nagane ta na sonshi, shiyasa zan aura musu junan su, kuma kinsan kin fi son farincikinta fiye da na kowa ko? to Rafeeq ne farincikin ta, kar ma ki shiga tsakani don tun Asali Seebi bata taba so na ba, tana dai ganin girma na ne shiyasa ta amince da Aurena, in kin musa gata ki tambaye ta" Nene ta kalli Seebi, tace "Ke Seebi wai haka? Wai dunkum kike so" Nasiba ta daburce ta fara girgiza kai alamun aa,bata san yanda aka gane cewa tana son Hamma Rafeeq ba" Nene tace "magana zakiyi ki na gyada kai kamar k'adangaruwa" Nan ta k'ara rudewa, "E- aa, aa bana so" Nene ta ta6e baki, tace "Ja'ira, ba ta iya k'arya ba, duk yanda tayi k'arya sai ka dagota, Aishatu son shi takeyi Wallahi, amma kin bada ni wallahi, ki rasa wa zaki so sai Dunkum? Dunkum fa Seebin Nene, yo ni ko a k'afa aka daura min Dunkum ai sai na kwance" Rafeeq ya dago kai ya kalli Nene, suka galla wa juna harara. Zaid yayi murmushi yace to Alhamdulilah yanzu dai Tare zaa daura Aurenmu, sai A fara Shirye shirye, Daddy yace "Zaid think of what you are doing, ya zaayi Rafeeq yayi aure yanzu? He will only hurt her with his attitudes, dont do this" Zaid ya kallo yayan shi yace "Yaya, this is my descison, Rafeeq is My Son, and i can get him Married whenever i want" Alhaji Habib ya ja baki yayi shiru, Mami ta dan ji wani Sanyi a ranta da abu yazo da sauki da haka, dama bawai ba ta son Rafeeq da Seebi bane, aa tana dai Son saka ma Zaid hallacin da ya mata. Zaid ya ma Mami ido, Mami tace "Zainab tashi mu shiga ciki ko? I know you must be tired" Zainab tayi Murmushi Ta mik'e Aneesa ta karbi Ayman da ke bacci a hannunta ta hau da ita sama din kwantar da ita, Daddy ya bi bayan Mami, Zaid ya Mik'e yace "bari naje na dan watsa ruwa donAllah Nene ki dan kwada min Zogale yanzu" Nene ta galla mai harara Zaid ya fice yana daria. Baka jin komai sai k'aran Ac din da ke Parlorn, kamar ba wasu hallittu a ciki, tana nan durkushe a k'asa, shima daga dayan gefen yana durkushe a k'asa, Nene ta kalli wannan ta kalli wannan, da ta ga zaman bana k'arewa bane sai ta tashi ta fita, to hakan ma bayan fitar ta, sai da suka fi 15mins, ba wanda ya tanka ma danuwansa, Seebi sai wasa take tayi da 'yan yatsunta, shi ko tarrarabin yanda zai fara mata magana yakeyi, sai ya bude baki zai yi magana sai ya kasa, kirrr yaji wayanshi alamun shigowar message daga Uncle Zaid, ya bude message din *"Drop the Ego, Pride and Whatsoever, Tell her how much she mean to you, Tell her how much you love her"* Rafeeq ya karanta message din yayi dan guntun tsaki, shifa abunda ke bashi wahala kenan bayani da baki, ta ya zai fara mata wasu surutai, ya sake sakin tsakin. Bayan nan ma wani mintuna goma suka k'ara shudewa, Nasiba ta aiyana a ranta ba zai mata magana ba, Uncle Zaid yayi kuskure da yace Feeq na sonta, ta mik'e tsaye tayi hanyar Sama, be an kara ba sai ganinta yayi zata fara taka bene, guntun tsaki yayi yayi saurin shan gabanta, ya zuba mata daradaran idanuwanshi cikin nata, da sauri ta runtse ido, wani kallo yake binta dashi, yana k'are mata kallo, nishadi na shigar shi, cikin kasan mak'oshinsa a hankali ya furta "Naseeebahh" a hankali ta soma bude idonta ta sauke su fes a kansa, ba zata iya jure kallon shi ha ta kawar da kai gefe, toh anzo gurin, besan me zai ce mata ba, sun kusa minti bakwai a tsaye ya rasa ta inda zai fara magana, sai ya bude baki zai ce wani abu sai ya kasa, da ta gaji da tsayuwa tace "Hamma zan hau sama, ka dan matsa daga hanya" Rufe idonsa yayi ya fara zubo zance kamar Radio, shi kansa be san me yake fada ba ga abunda yace "Nikam Soyayyah bata cikin kaya, love was Really not my thingy, I was a real time Player, banda burin Love, because a gani na bacin lokaci ne, I had more than a Hundred Girlfriends, banda Damuwa ko kadan, all i do is Eat, Pray, Sleep, Dump a girl, Repeat... Why? Because i am Rafeeq Freaking Lema. A rana daya mata fiye da goma za su kawo min kansu su bani kansu tun kafin na shiga Jami'a, amma sai Allah yayi ni ba mazinaci bane, Allah ya jarabbeni da k'addarori da dama, na shiga halin Bakin Duhu ta yanda na cire rai daga rahamar Allah, duk da haka abun baya damuna, i enjoyed myself being the IDGAF (ban damu da kowa ba, lols) about anybody, not even my Dad, the only humanity left in me was the love of My Uncle Zaid, Ibada ma a lokacin zan yi ta, amma ba kamar yanda ya kamata ba, Sallah ma sai na ga damar yinta nakeyi, na shiga Halaka fa ba tare da na nuna damuwa ta a hakan ba, Rana daya Allah ya jefo ki cikin rayuwata dalilin Sanadi, Sanadin Alkhairi, Naseebah, tun farkon haduwar mu dake na san Akwai Dalilin da ya sa ki ka shigo rayuwata, tun farkon haduwar mu na fara ganin haske a rayuwata, Damuwar wani ba damuwata bane ba, amma damuwarki damuwata ce, na fara damuwa da lamarinki, duk yanda na so in k'untata miki, ina kasawa, theres Something about you that i just dont know how to put it, amma All i know is KE ALHERI CE, you are a Blessing, you and your Entire Family, and let me say Something that i've never said to you in a Nice way, THANK YOU, Thank You Naseebah Muhammad". Zatayi magana ya katse ta hanyat cewa "Shhh, ban gama ba, thats a short story, And this, i dont know how to put this, i am not good in expressing myself, from What i noticed, Baki da Damuwa, baki da Hayaniya, Baki da matsala ko kadan, Unlike your Neh-neh" Murmushi mai sauti tayi, ya sausauta murya cikin murya me kama da Rad'a yace "Ina Sonki Seebin Nene, Ina Sonki Sosai" wasu zafafan hawaye taji sun fara sauko mata, Hawayen Farin ciki, rudewa yayi ganin tana fitar da hawaye, guntun tsaki yayi ya ciro Handky daga cikin Aljihun shi, "Lord of Mercy! Fine! Ba kya sona shiyasa kike kuka, ki share hawayen ki, kiyi hak'uri, I know what to do, Zan bar garin kafin daurin Auren, don nasan Uncle Zee ba zai taba saurarena ba idan nace na bazan aureki ba, kinga idan bana nan ba zaa daura auren ba" a ranta tace "What is his Problem? Why is he acting so stupid? Tana so tace mishi tana sonshi, tana so ta gaya mishi tana son aurenshi, amma dole ta share shi ko don ya cire wannan zafin rai din. Ta goge fuskarta, yace "Cry nomore, forget all i said, kawai consider everything i said a mistake" haushi ya tunik'e ta, ra6awa tayi ta gefenshi ta hayewarta Sama ba tare da ta ce dashi komai ba. Guntun tsaki yayi ya bi ta sama da sauri, don gani yake idan ya barta ta tafi he's lost her forever, kuma baya son wannan damar ta wuce shi, Sake shan gabanta yayi, ta daure fuska tace "Lafiya? Hannun ta ya kamo ya rik'e, ya murza a hankali, kasa kwace hannunta tayi, sai dai ma ta runtse idonta, don tana iya hawaye, a hankali yace "Baby" da sauri ta vude idonta yace "please dont go, dont leave me, I love you so much Wallahi, i want to be with you, i cant live without you, You are my Forever" wani murnan dadi ya risketa. Bari ta dan ja ajinta, sai ta yi k'okari wucewa yayi saurin tare ta, ji yayi ya ba kanshi haushi meyasa ba zai barta ta tafi ba, meyasa ba zai barta ta wuce ba, yana da Pride but shes stomping on his Pride, yana Son k'yaleta, amma son da ya ke mata ya wuce nan, daure fuskar shi yayi tamau, yace "Baby listen to me, i dont care if you love me or not, all i want is fr you to be here, all i want is your presence, I just want to be with you, i dont know much about Love, but what i believe is that 'You don't have to be in a relationship before u love somebody' i hid my love for you for a long time, i dont regret loving you withou you knowing, i dont mind keeping it much longer without admitting it to you, because thats the way I love, I love inside my heart Thats the way i show my love. i love you so much, i love only you, Oh God! Enough of this, i've said enough, i am not asking you to Love me back, I know i'm one hellof a guy, but all i want is for you to please Stay with me, stay around." Kasa magana tayi saboda wani yanayi da ta shiga, da ya lura da hakan ya sake kamo hanayenta ya murza a hankali yace "You have the whole day to think about it, I'll respect all your decision but please don't choose to leave me, I'll be a better person for you, I'll make you believe in me, I can be what you want me to be, I'll make you see that I can be anything, you want from me I promise" ya saki hannunta ya sauka k'asa ita kuma ta haye Sama tana jin wani farinciki Mara misaltuwa. A k'asa yayi kicibus da Nene, da alamun La6e ta musu, wani Murmushin me k'ular da mutum Nene ta ke ma Rafeeq, ya tsaya daf da ita ya murtuk'e fuska kamar ba shi yanzu taga yana kwantar da kai ba, yace "Ya akace?" tayi daria tace "Miskili kafin Mahaukaci ban haushi, kai Dunkum kar ka ga turanceta ka gama yi, na fahimci komai wallahi, ashe nima ina jin turanci bansani ba sai yau, ka tona Sirrin dake ranka, to na daiji komai, ana so ana kaiwa kasuwa, ai Seebi ba irin matan da aka yaudara bane, Allah ne ya kamaka" ta dinga surutu har ya fara ji kanshi na sarawa, ya dode kunnensa yace "Kina da Hayaniya, haba ki dinga shiru mana" ta daga kafada tace "Shikenan, da zan je in shawo maka kanta ne, ta amince ta aureka amma tunda baka so kaga tafiya ta" ta juya "Oh Shit" yace ya bi bayanta tare da rik'o hannunta yace "Haba Neh-neh, kiyi hakuri kinji?" Nene a shek'e da daria tace "to ka gaya min tsakani da Allah kana sonta?" da sauri yace "I love baby more than life itself" ta mai wani mugun kallo ta dai san me I love you ke nufi,amma sauran surutan ne ba tagane ba tace "Uban me kace?" "Oooops ina nufin ina sonta sosai, fiye da komai" ta yashe baki tace "Nima i lobiyu Dunkum" Idonshi ya kada a sama kafin ya rungumeta yace "Sunana Rafeeq" tace "har abada sunanka Dunkum" Ya saketa yace "Neh-Neh ki bar ce min Dunkum" ta buga tsaki tace "Kai ni fa sunana Nene, ka daina ce min wata Neh-neh kamar wata mallamar Choci" ta sake tsakin ya kalleta yayi guntun Murmushi yace da ita "Dunkuma Dangin Tsaka kawai" aiko Nene ta bishi da gudu ya ruga a guje. "Lesh kana ina?" i've got some good news for yah, alright i'm coming" Mota ya ja Sai Farm house dinsu Maalesh, suna hadewa Rafeeq ya rungume Maalesh, Maalesh yace "Guy howfa? Na dade banga ka cikin irin farincikin nan ba" cikin Doki Rafeeq Yace "Aurena da Naseeebah in 10days time" Are u kidding me? No i'm not wallahi, nan Feeq ya kwashe komai ya gaya mai, Sosai Maalesh yayi murna tare da bashi tabbacin Nasiba na son shi Kawai yaje ya fara shiri, Maaleah yace "Naseebah is a blessing, we have to make her Marriage a meomorable one, dama na san da shirye shiryen su don dama sun sa zatayi aure, So yanzu dai muje mu ga Miemee don k'ara shirya abun, Rafeeq ya daure fuska yace "kaje dai, wannan yarinyar shes lousy, ta cika Hayaniya" Maaleh ta daure fuska yace "danubanka thats my girl, bansan iskanci" Rafeeq yayi daria yace what a perfect match, dukkanku kuna da hayaniya" Maalesh ya kaimai duka. *******••••••******** "Alright, i know you dont like me, as a matter of fact i dont like you too, but since you are Baby's friend and my Bff's girlfriend, i have no choice than to put up with you" Miemee ta harareshi, tace "Wallahi da zan ba Seebi Shawara taji da nace kar ta yarda ta aureka, now i have to tolerate you" Maalesh yace "oya, Feeq, Beautiful ya isa, Enough of this arguments, gwara muyi shirin abunda zai birge kowa a bikin nan, ba fada na hada ku kuyi ba, dole sai kunyi settling differences dinku" Miemee tace "Fine, barin kira Ushee sai mu hade muyi planning bikin". Washegari Uncle Zaid ya koma Kaduna don fara shirye shiryen gyaran Gidanshi, Ilu Direba kuma ya kai Mami, Nene da Zainab Kano, Kasuwa sukaje don hado Lefen Zainab, Mami tace ki saki Jikin ki ki zabi duk abunda kike so, kar kiji komai in abu ya miki ki dauka kawai, haka suka hado lefe Akwati 6, a ranar suka dawo Katsina. Inda WasheGari Kuma Nene da Mami da wasu Yan uwan Mamin suka nufa Kaduna don kai Lefen Zainab. Gidan shiru daga Aneesa Sai Seebi, yana shigowa ya haye Sama straight, Aneesa ya gani tafi to daga dakin su Nene, ya mata rada is she inside? Anee tayi Murmushi tace "she's in, Goodluck" ya shiga a hankali, ta ja ganinshi tayi wuf ta mik'e tsaye, ya tsareta da idanu, sai ya ga ta k'ara kyau, yace "Baby, ya kike?" cikin muryar da bata san tana da irin shi ba tace "nika bar ce min Baby" yace "Saboda ba kya so na? da sauri tace "Ni ka bar cewa bana sonka" yace "Kina So na?" tace "Ni na hallicceka da zan ce bana sonka?" ya danyi jim, da wata ke wana shi haka da tuni ya ba banza ajiyarta, amma Nasseba ce, ba zai iya shareta ba. Yace "I came for my answer, na baki kwanda daya kiyi tunanin, ki gaya min" ta fara jan aji kamar shi a gurin, tace "Toh tunda Uncle Zaid ya matsa sai anyi auren, ai banda choice ko? Dim yaji wani iri, yace " So You are accepting because of Uncle Ziad? Kai tsaye tace "Ina ganin girman shi i cant say no to him" yace "Baby, i dont care if you are getting married to me For the sake of some, like i said ba ina so ke ki soni bane, i just want me to be loving you, to take care of You, and to give you the best things in life, thats all i ask, amma if really zaki chuta da Aurena, ki gaya min, Wallahi ba zaayi ba, don kinsan your happiness is all i want, amma please kar ki gujeni, ke kadai kikasan yanda zaki zauna dani, ke kadai ki ka shanye abubuwa da dama game dani, Please Baby" duk ya bi ya susuce, ya mugun k'askantar da kanshi, kamar ba Rafeeq Freaking Lema ba, tausyain shi ya kama ta a hankali, ga ta kuma bata dauki duniya da zafi ba tace "Hamma Rafeeq, Please kar ka k'ara hadani da Allah, ka wuce matsayin ka tsaya ka ta rok'ona haka, zan Aureka" Wani farinciki ya lullube shi, shi fa wani abun ma be san yanayi ba, So Makaho ne, idonshi ya rufe, be ji be gani ya shiga Murna, da bata ja baya ba da ya rungumeta, yace "I Love you Baby, say you love me too Please" kunya ya kamata tace "Barin shiga Toilet" ta fada toilet ya yi wani Murmushi ya waiga kan gado ya ga wani dan karamin Ribbon pink color, ya dauka yayi kissing kafin ya bar dakin. *Satin Biki * Nene ta nemi izinin komawa Gidanta gun Alhaji Habib, Saboda yanuwanta na nesa da na kusa da zasu zo bikin, Alhaji Habib ya sa aka bude gidan aka share Nene da Mak'arabanta suka koma chan don ba su Mami space su ma danginsu sun fara zuwa, Gwaggon Nasiba da ke Jigawa tazo, tunda tazo ta hau gyara Nasiba ciki da waje, Ranar Talata aka fara Events, Waazi akayi a Multipurpose, inda Malama Zahida (Mrs Muhammad) ta waazantar da su, ta ja ma Nasiba kunne kan bin miji da shawarwari da dama. Ranar Laraba kuwa Bridal Shower ne, Miemee ta fi 1 daya tana ma Seebi kwalliya, bayan ta saka wata Azababen gown milk color ta daura karamin Crown a kanta an baza gashin da ya sha Stretching a baya, Nasiba sai da ta tsorata da ta ga kanta a Mirror, tayi wani irin Masifar kyau, bata taba irin wannan kwalliyar ba, ta kalli Miemee tace "wai haka zan fita gurin nan?" Miemee ta harareta, to uwar ustazai, ko a kawo miki Nikab ne?" Usheey tayi daria tace "Nasiba kar ki damu, daga yau shikenan, mu je suna jiran mu" Seebi tace "Wallahi Nene ba zata bari na fita haka ba" Usheey tace kuyi gaba, barij je in janye hankalinta don naga ta rako wasu su gaida Mami" Takalma Me tsini ta saka tana tafia kamar wata bishiya, suna sando kar Mami Ko Nene su gansu, Miemee na jan hannunta iya kuka tana tafia dakyar sakamakon takalman ta, ba ta ankara ba taji ta bige wani abu, baki bude yake kallonta, Wai Naseebah ce nan? Kallon kallo suka tsaya yi, Miemee ta tabe baki tace "Muje Seebi, friends na chan na jiran mu" bakin Seebi na rawa tace "Ok" zata ra6a shi ta wuce ya kamo hannunta, wani yar taji, Miemee zatayi magana yace da ita, "ki tafi, zan kawota" Miemee tace please "Yaya Rafeeq, sauri fa muke, past 5" yayi dan guntun tsaki ya kawar da kai gefe, shi be saki hannun Seebi ba shi be ce komai ba, Seebi tace "Sorry Miemee, ku tafi ga mu nan zuwa" Miemee tace "Argh, Wallahi Mijinki dinnan sai a hankali"tayi gaba, Rafeeq ya wani wana kanshi a sama, Wani mayatacen kallo ya bita dashi, duk ta bi taji kunya ta tsargu, baki na rawa tace " Hamma, suna jirana, tun dazun suke min waya, we need to go please" matsowa yayi daf da ita ya kai bakinshi kan kunennta tare da fadin "You are a Blessing Baby(KE ALHERI Ce), I Love you with all My heart" Aikam jikin Nasiba ya hau kyarma, ba ta son yana kusanto ta haka, ya lura da halin da yake ciki, ya kashe mata ido yace "Yadai Baby?why are you blushing? Do you want me to kiss you?" ai da sauri ta juya har tana turgude wa, yace "Hey easy mana kar ki fadi, wasa ne" ita dai bata da sukuni sai da ta ga ta yi nesa dashi, still dai cikin motar haka ya dinga binta da kallo har suka iso Soli Center idan zasu yi Bridal Shower din. Yace "Oya Baby, have fun ina nan ina jiranki" Ta kalleshi tace"Hamma ka tafi ba maza" yace "I know, Event din mata zalla ne, an gaya miki da harda maza zan bari ki fito haka ne? Ina nan ina jiranki je ki gama" tace "Haba Hamma, ka tafi donAllah zamu koma da Su Miemee" yace "Alright Fine, Sai kin gaya min magana me dadi" ta runtse ido tace " Alright Baby, you go now, i'll see you later" cikin murna yace "What did you just called me? Baby?" Kunya ta ji zata bude k'ofa ta fice ya kamo hannunta, ta na waigowa ya kashe mata hoto, bata shirya ma hoton ba, amma tayi mugun kyau, ya musu Selfie, Sun hadu sosai a hoton, wayarta yayi k'ara tace "Hamma lemme go please" yace "I love you kinji?" cikin k'osawa tace !Naji let me go please" ya kai hannunta kan bakinshi yayi kissing, ta waro ido yace "yadai?wannan zare ido haka? Alright Bye, Call me when you are done" ya mata unlocking k'ofa ta fita, Su Miemee na jiranta a Entrance suna shiga aka sa ihu, Bridemaids sun sha kyau sun gaji, haka aka fara gudanar da bridalshower. WasheGari kuma Iyalan Gidan Lema da Seebi suka wuce Kaduna banda Nene don jamaa sun Mata yawa, A ranar zaayi Arabian Night din Aunty Zee da Uncle Zee, sun isa wurin k'arfe 1, Straight Gidan Su Aunty Zee sukayi, an karbe su cikin mutumci, Mami ta shiga Sallah, Umma ta sa aka raka Seebi gidan da Amare suke, inda Ake yaryara ma Aunty Zee Lalle ja da Baki, sunji dadin ganin juna, Aunty Zee tace "Yauwa ga dayar Amaryar nan, ita nace zaki ma wa" Me lalle tace "aiko ga ta nan tayi shanb'ar suka dara". Arabian Night Larabci kawai kakeji na tashi, saboda K'awayen Aunty Zee da sukazo daga Sudan Maza da Mata don tayata murna, Ko wanne ka gani da Jallabiya jikinsa, Seebi ta sa Jallabiya baka tayi kyau Sosai, ta bi Amare gurin Dinner, motar su ta tsaya, ta fito, Wayarta taji yayi Ringing ta ciro Baby na ta gani, tana dauka yace "Uhibukki kasiran ya habibty" daria tayi sosai, yace "kinyi kyau sosai Baby" tace "Da larabci zaka fada hakan ma" yace "Na farkon ma Uncle Zee ya gaya min, and i really cant remember" daria tayi tace "Munzo gurin dinner" yace "ai ina kallon ki kinyi shigar larabawa" waige waigen idan zata ganshi ta farayi, yace "Duba hagunki, ta na duba wa kuwa sai ganin shi tayi kan wani Black RangeRover spot, rabin jikin shi zaune gaban motar, k'afar shi kuma a waje, " Ta'al hoona Baby" Daria tayi tace stop embarassing me, kai keyi nike jin kunya" oh hakane? Barin zo in baki kunyar da kyau" ji yayi an buge mishi baki, Uncle Zaid ne, yace 'Kai baka da kunya ko, a gabana?" ya turo baki "Uhmmn baby kinga Uncle Zaid" Kirjinta ta dafe "Inalillahi Hamma wai gaban Uncle Zaid kake wayar nan ji yanda kake magana kamar wani baby?" toh ai babyn ne ko? Babynki" Uncle Zaid ya kaimai duka ya kauce yana daria, karbe wayan yayi daga hannun shi, yace "Seeebi Zooo nan" sallalami ta fara tace Uncle Zaid kayi hakuri ba zamu sake ba, byebye Aunty Zee na nema na" diff ta kashe wayar don kunyar Uncle Zaid da ya lullubeta, haka kurum Hamma ya sa ta jin kunya. Zaid yace "Baka da kunya ko Son?" Rafeeq ya kama kunnen shi yace "Sorry papa, shes just so beautiful, i cannot resist her" Uncle Zaid ya tabe baki yace "Thank God Matana tafi ta kowa" Rafeeq yace "Wallhi Baby ta fi Aunty Zee kyau" "haba Rafeeq kar ka rantse, Kalleta fa chan, kamar Balarabiya" Rafeeq ya ta6e baki yace "Fari kawai tafi baby" Uncle Zaid yace za ma ka dawo hanya, Oya muje tunda sun k'araso" suka fita, Sanye suke da Farar Jallabiya iri daya, sun yi kyau, kamar wasu abokai, suka karasa gun Amaren, Nasiba na daga gefen Aunty Zee, Suna hada ido da Rafeeq ya kashe mata ido, ta kawar da kai da sauri ta na smilling, "Aunty Zee kinyi Kyau Sosai" cewar Rafeeq, tayi Smile tace "Thank You Son" ya daga Ayman ya chafe yace Angel you look beautiful too ya mata kiss a kumatau, suka shiga Hall din a layi bayan an sa kusu wak'ar Sudan. Tafiya yakeyi kamar wanda aka ma dukkan tsiya, yayi doro wai duk cikin Gayu ne, aikuwa yanmatan gun duk idansu kanshi, Nasiba ta lura da wani Kallon Da Wata k'awar Aunty Zee Emjay (Talatuwa)Ke binshi dashi, cike da kishi Nasiba tace "Aunty Emjay, He's just 24, jin girmeshi fa" lols. Haka aka watse daga dinner bayan an bar tarihi. Washegari da Sassafe Mami, Ummi da Seebi, da wasu Friends din Naseebah su Softie, Maryam Aqeel, Jamie jamie, Azyza, Mufeen, Friends dinta na Secondary School Suka wuce Katsina, don yau Mami zatayi Yinin Bikinta a chan Katsina. Tun Sati kafin bikin Daddy ya nemi Alfarma kan a raba Bikin Uncle Zee da na Rafeeq, saboda ba zaiyiuw a zo Kaduna a daura Auren Aunty Zee ba kuma a koma Katsina daura Auren Rafeeq ba, kuma ba yanda zaayi a hade bikin don Mutanen Daddy na Katsina na Abban Zee na Kaduna, shiyasa aka yanke hukuncin fara daura Auren Uncle Zee. Bayan Sallahr Jumaa, daukacin Alumaar Musulmi suka Shaida Daurin Auren Zaid Iro Lema, da Amaryarsa Zainab Sani, bisa Sadaki naira dubu 50 lakadan ba ajalan ba. Bayan Reception.Daddy, Uncle Zee, Rafeeq da Maalesh suka dauki hanyar Katsina, Maalesh ke tuk'i, Rafeeq a kusa dashi, Sai Daddy da Uncle Zaid a baya **** A lokacin Gidan Mami na chan Mak'il ana yinin biki (Mothers Day) Farfajiyar ya sha Decoration, MC Lubna Sufyan aka dauko tun Daga Lagos don yin MC, yan kidan kwarya nayi, Mommyn Maalesh (Umm Eeman) sai chashewa take tayi tana ruwan kudi, Mami dai sai dai tayi lik'i amma ba dai rawa ba, Su Miemee Suka jawo Nene wai sai tayi Rawa, da Nene ta sake wani shewa sai ko ta fara rawan Allah bakace, Ummi kunya taji sosai, Seebi ko da ke zaune kan kujera sai dariar Nene take tayi, har kusan bayan Ishai kafin aka watse, sai da Nene ta bi Bayan masu kidin kwaryar nan tace suzo Gobe gidanta, don ita gobe bayan Daurin auren take nata yinin Biki. Sun ko amince zasu zo. Bayan Isha'i suka iso Charanci, Daddy yace Maalesh maida min Companion Fm, takwas tayi inji Labarai me katsinar ke ciki, Rafeeq yace "Daddy wai dama akwai gidan Radio a Katsina ne? Maalesh yace " Dan rainin wayau kana nufin baka san Akwai Gidan Radio a KT ba? No wonder Nene tace maka no radio a gida" sukayi daria har Rafeeq yace "That woman never cease to amaze me" Maalesh na tuning Stations din suka ji ana shelar *Mallama Aminene Maman na farincikin gaiyatar ku zuwa Yinin Bikin Jikarta Nasiba Muhammad Seebi, da Angonta Rafeeq Habibu Lema Dunkum" be bari an karasa ba ya latse Radiom ta mutu, tare da dafe kai yace "Lord of Mercy, this woman is my Worsttttt nightmare" aiko duk suka tuntsire da daria banda Rafeeq da ya hade girar sama da ta k'asa. _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀      NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) Pg6⃣0⃣ Ya kallesu yayi dan guntun tsaki, yace "Ba abun daria bane, duk yanda na so to get along with her, i just cant, shes Annoooooying" Daria Daddy yayi, Uncle Zaid yace "shiyasa nace zata zauna maka 'yar zaman daki" Rafeeq ya gwalo ido yace "Wa? Aikuwa da wata rana na mata dukkan tsiya" Maalesh ya bude baki yace "Nenen?" Rafeeq yace "Ita fah" Maalesh yace "aikuwa kamar a kunnenta" "in ka fasa tsoron ta nakeji ne dama?" Maalesh ya fashe da Daria yace "Aa fa guy, kar fa kamanta randa tayi shirin Buje da gatari a hannu ka tsorata fa" Rafeeq yace "Randa tayi shigar 'Yan daba dai, everyone in my shoes will do the same, daga ganinta ta ta6a Daba" Zaid ya murtuk'e fuska yace "Rafeeeq" da sauri Feeq yace "Sorry". Haka suka iso Katsina Lafia, straight Guest House suka nufa inda aka ajiye Abii da mutanen shi, Suna sauka Rfaeeq ya Sanfe ya tari Achaba ya haye sai Gidansu inda aka gama Mothers day, da sauri Feeq ya hau sama, haka ya dinga k'etara Mata har ya shiga dakin Seebi, wayam be ga kowa ba, ya lek'a dakin Mami, Zaune Mami take da Friends dinta su Mom din Maalesh da wasu yana ganinsu yayi saurin juya wa, don bai san surutu, amma kash Mom din Maalesh ta ganshi tace "Come here boy" sum sum ya shiga dakin kamar wanda yayi k'arya, Mom tace Yadai? Murya k'asa k'asa yace "Mom Naseebah nake nema" ta harareshi tace "If i slap you ehn, baka ga Aunties dinka ba? Cant you greet?" dan guntun tsaki yahi ya kallesu tare da Turo baki yace "Ina wuninku" duk suka amsa cike da faraa" ya juyo ga Mom din Maalesh yace "Mom where is she?" Mom ta ja kunnenshi tace "Listen to me boy, you are not to see the Bride sai bayan an daure Aure kaji ai?" Rafeeq ya turo baki kamar zaiyi kuka ya kalli Mami da fuskar tausayi ta ta6e baki tace "Kai da ita ba ruwana" juyawa yayi yana tafiar yara idan an hanasu abu, Mom din Maalesh tayi daria ta kalli Friends dinsu tace "Kun ganshi ko? Shine fa Angon, wai Amaryar sa ya ke nema" su ka kalli Mami "wai dagaske Hajia Aishatu?" Mami tayi daria tace "gashi Mom dinshi ta fada". Duk mamaki ya lullubesu. "Yauwa Anee, ina Baby?" Aneesa tace "Yaya Rafeeq ta tafi gida bayan an gama Mothers Day" ya dan bata fuska, wani Gida?" "Gidan Nene mana" "Oh shit!" ya fada tare da yin hanyar k'asa da gudu yana mita. °°° Gidan Nene cike da dangi, kowa da abunda yakeyi wasu daga ciki kuma ana yankar Alaiyahu da zaayi Miyar Yinin Biki, wasu na 6are Ledar tuwo, su Nene kuwa an shige Dangi ana ta labari a lokaci guda kuma tana bada Umurni. Be san gidan cike yake ba, Cikin muryan shi yayi Sallama tare da kusta kai lokaci guda, Nene kadai taji Sallamar sa, sai ganinshi kawai sukayi a kansu, yayi nadamar shigowa da ya ga idanuwa sun mai chaaa, ji yake kamar ya juya, haka ya tsaya musu k'ikam, shi be juya ba, shi be ce dasu komai ba, Goggon Seebi tace "Wanene wannan ya shigo mana gida ba Sallama" Daure fuska yayi tamau, Nene tace "Ya fayi, haka yake sallamar sa kamar Wusir, Dunkum kike gani, Dangin Tsaka, Miskili yafi mahaukaci ban haushi" inji inna tani "Toh fa Shikuma fa?" "Shine fa Angon Seebi" wata Yayar Ummi tace "Ahh Nene kice duk kirarin nan ba a banza ba, ashe kishi kikeyi, Ya dauki Seebi yace beyi dake" Nene ta ta6e baki tace "Ni me zanyi da Dunkum? Ai Sai Seebin da ta ga zata iya" da Ummi suka hada ido, ta mishi Inkiya da ya gaida su, guntun tsaki yayi, a hankali yace "Ina wunin ku" suka amsa da faraa, Kakkanin Seebi suka fara jan shi da wasa, Yak'e me kama da Kuka yakeyi, nan ya samu ya sanfe daga gidan. Tsaki ya buga da k'arfi da ya kira Wayar Seebi karo na 6 ya ji shi kashe, shi gaskia ba zai iya kwana be ganta ba, Wayar shi ya zaro ya latso Wayar Uncle Zaid "Boy ya?" Cikin Marairaicewa yace "Ba gani nazo gidan Neh-neh ba, na ga Mata sunfi 60, wai a gidan Neh-neh zasu kwana, kuma Baby na cikin su, duk sun matse ta, sun takura mata" Uncle Zaid yace "Boy ban san rigima, ba daga yau shikenan ba?, Danginta ne" Kamar Zaiyi kuka yace "Please Uncle Zaid, do something" ajiyar zuciya yayi yace ya kake so ayi to? Cike da shagwaba yace "Ni ta koma gida" Zaid yace "Ohh saboda ka hanata sukuni ko?" da sauri yace Aa Wallahi, ni da zan kwana Gidansu Lesh " Good inji Zaid ya latse wayar ya kira Wayar Nene, "Halo Zaidu Bawan Allah, ango, kayi hakuri ban hallarci bikin ka ba, Yanuwa na daga k'auye sunzo ne"Murmushi yayi yace "bakomai Nenen mu, ya taro? Ya jamaa?" "Alhamdulilah ya naku?" "Lafiya lao Nene, nace dama Seebi da k'awayenta su je chan Gida su kwana, an gyara musu daki Biyu" Nene bata kawo komai ranta ba tace "kamar ka san a gwamutse muke, bari ko su shirya su koma chan" bata kashe wayar ba ta shiga kwadawa Seebi Kira ta shirya su koma Gidan Lema. ********* "Baby" jin muryar shi kawai tayi a tsakar Gida, Friends dinta sukace "lahh ga Ango" Mur ya sha, saida Seebi ta harareshi kafin yace "Sannun ku fa" su ka amsa sunso Magaanr tasu yayi Nisa, amma ba hali, Nasibah tace "zamu shiga ciki" yace kije ki rakasu ina jiranki" zatayi magana ya tsareta da idanun sa, Alright tace tayi cikin gida da Friends dinta, shi ko dakinsa ya shiga ya ciro Key din motarsa ya bude ya shiga tare da kunna AC, ya ga fitowarta, yana ganin yanda take dube dube ta window da alamun shi take nema,horn ya mata da ya dan firgita ta, a hankali ta tako ta side dinshi, a taka'aice yace "Get In" tace "Hamma Please"kallonta kawai yayi, ta san maanar kallon da ya mata da sauri ta zagaya ta bude motar ta shiga, Gyara zamanshi yayi ya maida hankalin shi kachokam kan ta, yana binta da kallon so da k'auna, sadda kanta tayi k'asa, ya sa hannu ya kamo hannayenta duka biyu da suka sha zanen Lalle, ta yi ta kwace hannunta ta kasa, ya fi minti 3 a haka shi be tanka ta ba, da k'yar bakinta ya lalubo " Ina jin Bacci" Murmushi yayi yace "Baby, kin kashe wayanki, kin hanani ganinki and now kina jin bacci? Oya zo ki kwanta" ya karashe tare da nuna chest din shi, Ido ta ware tace "Hamma"yayi Murmushi yace "Alright, kije ki kwanta, I love you so much baby, I got you, I got Us" Smile tayi tare da fadin "Goodnight" ta bude murfin k'ofa zat fita ya rik'o hannunta daya ya kai bakinshi yayi kissing, Lokaci daya Seebi ta daburce, ya sake hannun tare da cewa "Goodnight Baby" da sauri ta fita ta bar Motar tayi cikin Gida, shikuma ya ja Mitar ya fita daga Unguwar ya nufa Unguwar su Lesh. SATURDAY 11:30AM Massalacin Commasie Cike ciki da bai, har toshe Hanya akayi saboda chunkosa, Manyan Mutane k'usoshin k'asa, yan Siyasa, Yan Kasuwa Yan Uwa da Abokan Arziki zaune Cikin Massalacin, Abbii na gaisawa da mutanen shi, suna mai Murna, Liman yazo, ana jiran zuwan Waliyyin Ango, har 12:30 ba alamun su, Daddy cikin bacin rai ya ciro Waya ya danna kiran Uncle Zaid, yana dauka Daddy ya rufe shi da Fada, kai Zaid kar ka maida mu k'ananun mutane mana, ka tara mu a nan, ka k'i zuwa, kowa fa na da abun yi haba" daddy na iya jiyo Sautin Murmushin Zaid, yace "Kwantas Yaya, i had to make sure My Son is looking Good, yanzu dai juyi daman ka, gamu muna kallon ka" Da sauri Daddy ya kallo Daman shi, Aiko sai ganin Zaid yayi sanye cikin Shiga ta Alfarma, Babbar riga ce Milk color, Rafeeq a kusa dashi wanda ke sanye da Farar Shadda da ta sha Bakkin Aiki harda Baban riga, sai Maalesh da ya sa Skye blue Shadda shima da Babbar rigar shi, Wani farinciki ya ziyarci Zuciyar Daddy, ya dade be ga tilon danshi cikin wannan farin ciki ba, Dukda fuskar sa Murtuke yake, kallo daya zaka mai kasan yana cikin farinciki Mara Misaltuwa, Tafiya sukeyi cike da Tak'ama da Isa, suka je har gaba suka samu wuri suka Zauna bayan Zaid ya nemi Afuwan mutane na Latti da sukayi. Liman ya fara da cewa Ina Waliyyan Maauratan? Su matso gaba, Uncle Zaid da wani d'an k'anin Nene suka matsa Gaba, Aka buk'aci Sadaki, Zaid ya sa Hannu cikin Aljihu ya ciro bandir din 1000, dubu Dari, bayan anyi yanda Addinin musulunci ta tanada, nana Dubannin Mutane suka Shaida Auren RAFEEQ HABIB LEMA da Amaryar sa NASIBA MUHAMMAD Bisa Sadaki naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba, Rafeeq ya ji hawaye a kuncinshi da sauri ya goge ya zaro Wayarshi tare da tura mata Text, nan aka shiga gaigaisawa ana taya juna Murna, Rafeeq ya ji dadin ganin Old Friends dinshi a gun Daurin Aure, na University dana Secindary, yasan aikin Maalesh ne, daga nan suka zarce KATSINA MOTEL inda zaayi Reception. Tun Safe suka dawo gidan Nene, Gida ya cika Makil, tun wurin 8 aka fara zuwa yinin biki, Nene tayi kyau abunta cikin shiga ta Lifaya, sai wani kankanba take ma kawayenta tsofi irin ita jikarta ta dangwalo arziki, ana ta ba ciki hakkinsa, Abinci sai wanda ka zaba, Amare na rawan kidin kwarya, Nene na tayasu, Nene ta kalli Miemee tace "Miemee Yar gayu je ki hankado min Seebi yanzu" da sauri Miemee tayi hanyar Dakin. Usheey ta mik'o mata Wayar ta, don ta ji kamar Alamun shigowar Sak'o, tana duba wayar ta ga BABY ne, da sauri ta bude Sak'on *"YOU ARE MINE"* abunda ke ciki sak'on kenan, wani Farinciki ya ziyar ce ta a hankali ta zame ta yi Sujjudushukur don nuna Godiar ta. Usheey tace "yadai? Cikin Sanyin jiki tace "An daura" Miemee ta shigo k'uryar tace "wai me kukeyi ne? Nene tace kar ku bari ta iske ku Wallahi, ku fito bak'i nata zuwa" Usheey tace "Sorry Sallah mukayi" Miemee tace donAllah ji an daura miki Dankwali kin kwance" Seebi tace "Alwala fa nayi" Miemee ta harareta ta hau gyara mata dankwalin kanta, suka fita Masu kidan kwarya na ganinsu suka fara wak'ar *giringibishi*. Yinin Bikin Nene yayi Armashi Har wurin bayan Laasar ba a bar zuwa ba, anan ne aka kira Nene aka sanar da ita 'yan daukar Amarya zasu zo, Nene ta lek'a chan k'urya ta ga Seebi rakube tana Kuka kamar ranta zai fita, zuviyar Nene ta karaya, ta dai dake tace "Ke kika ce kina so, da ba kice kina so ba da ba a baki dunkum ba, to kuka na me? Tashi muje inkai ki gun Babanki ya miki fada da Nasiha" Aiko Seebi ta sake fashewa da kuka, ta ba Nene tausayi sosai, nan ta samu ta shiga lallabata har ta ja ta sukayi Parlo inda Abbii da Kawu Magaji ke zaune, Nene ta aika aka kira mata Ummi, aka gurfanar da Seebi gaban Abbi, Nene tace "to Mahammadu ga Seebi nan kai mata fada" Abii yayi hamdala yace "Toh Seebin Nene Allah yayi yau na ga Aurenki, Seebi, duk me hankali zai yi duba ga lamarin Aurenki, kin shiga rayuwarsu a Matsayin wata Haske ba tare da ke kanki kin sani ba, Haduwarki da Rafeeq har zuwa yau itace K'addaraki, abubuwan da kikayi domin shi, shine Jarabawarki, ki kasance me boye sirrin Mijinki, Abubuwan da suka faru, na dadi da na rashin Dadi, hakan ya zama ishara gareki,, ina Miki gargadi da ki rike gaskia da Amana, kin taimaki Mutanen nan, suma sun taimake ki, Suna sonki Sosai, Kar ki zama butulu, ki kaunce su da zuciya daya, na sanki da hakuri, ki kara a kan wanda na sanki dashi•••• Nasiha me ratsa jiki Abii ta cigaba da yi ma 'yarsa, tana kuka yanayi, Ummi nayi, sai da ya gama Nene ta sa Ummi daura mata kan na Abii, Kawu Magaji ya mik'a Ma Seebi Sadakin ta yace "ga Hakkinki" Seebi kasa amsa tayi sai dai Nene ta sa hannu ta amsa, suna cikin haka sai ga yan daukar Amarya sunzo, Suna Guda sosai, dangin Mami da dangin su Daddy yan Azare ne sai Mom din Maalesh, Bayan an gama yan surutai aka basu Amarya Nene ta yana Lifayar ta zata bi bayansu, wata abokiyar wasanta tace "Kai Aminene ba dai binsu zakiyi ba?, ke fa ce Uwar Amarya" Nene tace "Yo saboda me? Ai wallahi kafata kafar Seebi in gaya miki" ta bi bayansu da sauri. Gidan Habib Lema akayi Da Seebi, dama chan zata fara Zama cewar Uncle Zaid saboda dalilin shi daga shi sai Rafeeq suka sani, sun dai ce ma Mami tun Kafin ayi Bikin nan zata zauna, saboda haka nan akayi da Amarya, ba abunda ke tashi sai Guda, Sama akayi da ita aka kaita Dakin Mami, kan tsakiyar Gadon aka ajiyeta, inda take kuka a Hankali. *********************** "Sweet Zee ka huta kaji? Bana so wata ta ganka ta lik'e maka a Dinner dinnan a Son" Cewar Aunty Zee da ke kwance rigingine tana waya da Mijinta, Uncle Zaid yayi dariya yace "Cute Zee ki kwantar da hankalin ki, ba wacce zata ganni, kowa ya san nima fa Ango ne, dont worry kinji Cute Zee? I'll keep myself for you alone, I love you so much, Gobe First thing in the Morning zan taho, i cant wait to set my eyes on you" Murmushi me sanyi tayi kalamanshi sun kwantar mata da Hankali, Sallama sukayi bayan ya shaida mata zai dinga tiro mata Pictures da Videos ta Whatsapp. "Beautiful Akwai Sauran Gate Pass a gurinki" Miemee tace "Handsome Wallahi duk sun k'are, Wasu Friends din Seebi 'yan Zauren Biebee Isa da Miemee Bee Novels group sukazo kuma duk na rabe musu Gate Pass din" "and kuma dukkansu sai da kika basu?" Miemee tace "duka Wallahi,Friends din Amarya me, daga wurare daban daban, garuruwansu nesa da na kusa suka zo, they mean alot to Seebi, kaga dole a sama musu gate pass" "Alright ba Matsala, barin je in shirya Ango, Please ki cema Friends dinku su shirya, Immediately Isha zaa zo ayi kwasa daya a tafi, kinsan abun ba African Time, saboda harda su Daddy da Friends dinshi, so Everything has to be on time" Miemee tace "Alright Handsome baka da Matsala, ana chan ana Makeup din Amaryar, mu kuma a shirye muke ku muke jira" "Alright bae, i love u". Me too bye. A kan idon Nene Mami ta ba Ummin Seebi gate pass da yawa tace "gashi ke da mutanen ki" Ummi tace yanzu sai munje?" Mami tace "Ehmana, duk zaaje har Alhaji da mutanen shi zasu, kinga kema harda Abii dinsu zaki" sukayi daria duka. 'Toh wadannan takardun da ake rabawa na meye?" Mami da Ummi suka juya ta inda sukaji Muryar Nene, Nene ta k'araso tace "ko bakuji ba?" Mami tace "Gate Pass ne" Nene ta yatsuna fuska tace "meye haka nan?" Mami tace "Kati ne Nene, na shiga wurin Dinner, idan baka nuna ba, ba zaa barka ka shiga ba" Nene tace "ina wai?" Mami tace "Dinner kamar Walima aka hada, zaa hadu duka a ci Abincin Dare don murnan Biki" Nene tace "Tab, Munafurci ya sa ba a a gaya min ba? Ya ake abu ne ba a sanar min?" Ummi tace kiyi hakuri, dama katittikar mu ne nanz shine yanzu zan kai gida a shirya a tafi" Nene ta harari surukar ta tace "bani su nan" da sauri Ummi ta mik'a mata IV's din duka jiki na rawa, Nene ta zaro daya ta mik'a mata, tace "muje gidan, zan ba wamda ya dace yaje don kar muje su ba mu kunya, sai wanda yayi wankan Suwaga(Swagger) zaije" duk sukayi Daria, Mami tace "to Nene ku je ku shirya da anyi Sallahr Ishai zaa tafi, Nene tace bari mu je da sauri suka fita ita da Surikarta Ummi. Mami kuma ta wuce Parlorn Daddy inda aka ma Nasiba Makeup, Sanye take da Turquoise Blue Wedding gown, da dogo Veil dinshi wanda Houseofkaya suka dinka mata, Rigar ta hadu iya haduwa, Aneesa ce ke koya ma Nasiba yanda zatayi tafia gun dinner din, Mami ta shigo da Sallama, Nasiba tayi saurin Sadda kai, Mami ta isa gunta ta rungume Nasiba tace "MashaAllah Seebi kinyi kyau sosai"Murmushi kawai tayi, Wayar Mami yayi k'ara, ta dauka " Yeah Okay, we are ready as well" Mami ta kalli Lynaz me Makeup tace "Thank you Lynaz, you've transformed my daughter" Lynaz tace "thats my job maam, we bring out the beauty in you" Mami tayi Murmushi suka tarkata kayansu Aneesa tace "i'll show you the way out" Mami tace daga nan ki kira min Wayr Maalesh, Rafeeq yazo ga EventsUnlimited(masu hoto) nan sunzo, yazo ayi Post wedding pictures kafin a tafi dinner din, Aneesa tace "Ok Mami" Mami ta tsura ma Nasiba kyau, duk kunya ya kamata ya sadda kanta k'asa, Mami ta kamo hannunta tace "Nasiba Wallahi ina sonki ina jinki kamar Rafee'ah, kinyi kyau sosai, Allah ya Albarkaci Rayuwanku duka" a hankali ta amsa da "Amin". Ta k'ofar baya aka shigo da Masu hotunan, don kar a dauki hankalin mutane, aka bi dasu ta baya suka hau sama Parlorn Daddy. Bayan gaishe gaishe suka hada kayan hotunan su. Mami ta fita waje don kiran Rafeeq ko Maalesh ta ko ci Sa'a wayar Rafeeq ta shiga, " "Hello Feeq kana ina? Mam ina tsakar gida, Oya ka shigo ciki ka hayo Sama, ga Eventsunlimited nan, kazo ayi Postwedding pitures, ya marairaice kamae zaiyi kuka, Mami ta ya zan shigo, Mutane da yawa, tace "ta baya fa zaka shigo" "ni Mami i cant" tace "Ina Maalesh ya rako ka mana?" Mam Lesh yaje tattaro Friends dina yanda zasu a kwashe mutane a tafi at once" tace "Alright gani nan zuwa in taho da kai". Ta sauka kasa ta ga Rafeeq, sanye yake da shiga irinta Nasiba, manya kanya Turquoise Blue ga hularsa yayi kyau fiye da tunanin me tunani ga wani k'amshi yana zubawa, Mami ta rungume shi tare da mai kiss a kumatu, tace " Yaro na ya girma " Sake rungumeta yayi ta ja hannunshi har Sama ta sada shi da Parlorn Daddy ta turash ciki. Sandarewa yayi da ya hango Sanyin idaniyar shi daga chan gefe ana kashe mata hoto, Kallonta yakeyi cike da so da k'auna, ya shagala da kallonta sai ji yayi Me daukar hoton tace"The Groom is here, come over here" Hankalin Seebi ya koma kan Rafeeq, gani yakeyi Yafi ko wa Dace tunda yana da Seebi, itama hakan ne, don yau ya mta kyau matuk'a, a hankali ya taka har gunta yana mata kallo kasa kasa, ta sadda kanta k'asa ya sa hannun shi ya dago fuskarta ya kai bskinshi kan kumatun ta ysyi kissing a hankali, daburcewa tayi Lokaci guda ya sa hanayenshi duka hya ya rike kafadunta, idonta a runtse ta bude su a hankali, Cikin muryar rada yace "Calm down baby, i got you" Me hoto tace "Oya Romeo Shall we?" kao Kawai ya gyada mata, nana aka fara kashe musu hotuna kala kala. 8:10pm Ko wacce ta samu gurinta a Mota, Motoci aka kawo sun fi 20, yawancin Manyan duk sun tafi, Mami da Aminanta sun wuce, yanmatan ne dama suka rage, Rafeeq da Seebi a bayan Motar Uncle Zaid, Miemee da Maalesh a gaban Motar, Usheey na motar wani friend din su Maalesh Faisal, tun farkon biki suka hade, kuma da alamu suna son junan su, Nene ta shigo gidan, Da sauri tana murnan ga motoci nan basu tafo ba, dama sai da ta tabbatar ta sallami kowa a gidanta kafin ta fito, Daga dan Nesa ya hangota, a zuciyar shi yace "Neh-neh? ina take tunanin zata?" wata zuciya tace "Dinner"da sauri ya girgiza kai, In har ka bari Matar nan taje Dinner dinnan, to sunan ka sorry, zata kwafsa maka, ta bada kai gaban Friends dinka, zata ba ka kunya gaban Manya mutane, you have to stop her from coming, unless yiur name will turn to Apology" gargadin da zuciyarsa ke ma sa kenan, da sauri ya bude k'ofa yace "i'll be right back ya fice" ba su lura da ita ba, da sauri ya tare ta, ta yashe baki "Ahh su dunkum da manya kaya, ka ga kyan da kayi?" yayi Murmushin yak'e yace "ban Kai ki ba" Nene akaji dadi tace "Allah ko? Ni naga k'auna, ga motoci nan bari in dirje In shiga"Da sauri Feeq yace "No No Neh-neh, Mami tace " ki tafi mata da wasu kaya" Nene tace wasu kaya kuma dunkum?" ko dar yace ina jin kayan da zata raba wa mutane ne" suna ina? Yace Suna daki, kaje ka dauko min kar a tafi a barni" yace "wa zai tafi ya barki, ke ke da Ango" Nene ta ji dadi tace muje mu kwaso, suka jufa hanyar dakin Rafeeq, Rafeeq ya bude dakin shi, Nene ta shiga tace "ina kayan suke?" yace duba kewaye, aiko tana shiga yayi saurin fita ya sa Mukulli ya kulle K'ofar, ba ta lura ba illa ma cewa take "Ina kayan suke dunkum?" yana fita ya ma motovin gaban gida Signal da su fara tafia, aiko duka motoci suka kumna Motar su, da sauri ya hau tasu, Maalesh ya tada Motar suka bar haraban gidan fuk suna masu kunna fitilar motocin su, abun za kyau Convoy din ya hadu. Haka su ka wuce NYSC hall, inda a Nan ne zaayi Dinner. ******* "Bara'uba Salatin gwarawa" cewar Nene da ta fuskanci Dunkum ya kulleta a Dakinshi. **** A Convoy suka isa har NYSC camp Hall, suna isa Maalesh ya kira Mom dinsa yace sun iso, Mom din ta sanar da MC Lubna Sufyan, nan MC ta buk'aci kowa da ya mik'e tsaye don shigowar Amare. Dj ne da Makadi(Mai Asharalle) nan da nan DJ ya sa wak'ar Nura M Inuwa na Amarya, Mom ta fita ta hada kan Amaren, Layi ne biyu, daya dogo na mata, daya na maza, in twos zaa shiga, Feeq da Seebi a tsakiya, ofcourse Miemee ce a gefen Maalesh su ne a gaba, Ushee kuma da Faisal a bayan su, Maalesh yayi kyau sosai, kayan shigen na Rafeeq ya sa, Abokan Ango Masu jiji da kai, duk ba zasu wuce shekarun Rafeeq ba, sai shan k'amshi sukeyi, ko don sun ga suna da kyau sun hadu ne oho, Kawayen Amarya kuwan sun sha kyau sun gaji, Anko suka yi na wani atamfa mai touches din Ja, sun daura Head Ja, ga kuma Amarya da Ango sunyi turquoise blue abun duk sai ya bada color, Mom tace da Miemee oya Yarinya na ku fara shiga da taku kunji?ta kashe ma Maalesh ido, nan suka fara taku sukayi hall din, aiko sauran suka bisu a baya, Fuskar Rafeeq ba yabo ba fallasa, shidai ba Murmushi yake ba, shi kuma ba daure fuska yayi ba, Suna shiga hall din Gaban Seebi ya fadi, ganin haduwar Hall din, ga Idon Mutane kan su, Hall din babba Ne kuma cike yake Mak'il, Rafeeq ya lura da ita, a hankali ya sak'alo hannun shi cikin nata, dumin hannun shi kawai taji a nata, da sauri ta kalleshi tare, ya kashe mata ido, a hankali yace "I got you" idonta ya kai kan Ummi, Mami Abbii da Daddy a chan gaba, duk kunya ya lullubeta, Zata zame hannunta Rafeeq ya matse hannun, ya ja ta suka cigaba da tafia har sai da sukaje suka zauna wurin da aka tanada domin su, kafin aka fara gudanar da Shirye shirye, Daddyn Maalesh aka bukata don bude taro da Addua, Alhaji Habib ya zo yayi Welcome Speech(Sannu da zuwa), sannan aka bukaci Baban Abokin Ango da K'awar Amarya su fito don bada takaicecen tarihin Ma'auratan, Muhawara ya kaure tsakanin Miemee da Ushee, Miemee tace "Oya Ushee tashi jeki yi Jawabi kan Amarya" Ushee tace "Tabdi, kinsan dai bazan iya magana gaban crowd ba, ai ke zakiyi, so kije dont waste time"Miemee ta harareta tace "don ace baki da hayaniya ko?" sukayi daria, Maalesh ya taso ya zo kusa da Miemee, suka jera sukayi kan Stage din a tare, abun sai ya burge Mutane. Maalesh ya fara magana; "My name is Mahmud Ali Umar, and Rafeeq is a brother from another Mother, we've been together for 20years, Rafeeq is a•••••••• nan Maalesh ya shiga koda Rafeeq tare da mai Fatan Alheri, Rafeeq ya taso ya rungume Maalesh tare da bubbuga bayan sa ya rada mai a kunne "thank you brother". Miemee ta fara bada bayani kan Seebi, ta fadi kyawawan halaiyarta ta kare da mata fatan Alheri" aka tafa musu, MC tace kafin su tafi sai sun taka rawa, nan Surajo mai Maalesh ya fara wak'e Malesh babban aboki, da Maryam Miemee yar gayu, sin dan taka zasu koma MC tace da su "Are you a couple?" Maalesh yace "yeah we are" tace "You suit eachother" sukayi Murmushi aka tafa musu suka koma mazaunin su. Aka gayyaci Ango da Amarya a fili, Marok'i sai kirari yake ma Ango, Mom ta hau sama don Rafeeq da Seebi sunki tashi, Ita kunya, shi kuma be son hayaniya, sai da Mom ta je ta sauko dasu, Wannan karon karon Dj ne, Wak'ar Work-Rihanna ft Drake aka samu su, dukkansu tsaye sukayi, ba me rawa, Mom ta rada ma Feeq a kunne Spray her, Ta wuce ta zauna aka barsu su kadai a fili, hannu ya sa cikin Aljihu, ya ciro bandir din1k ya fara lik'a mata, kanta a k'asa, ya dinga spraying, Yana mata liki'i, nan Daddy da Abokansa suka zo suka lik'a musu kudade masu yawa, gajiya Rafeeq yayi, ya kama hannun matarsa ya ja ta suka koma mazaunin su, nan aka ba Abokan Ango da Kawayen Amare fili suyi rawa. Tagumi ta rafka hannu bibiyu tana tunanin irin dukan da zata ma dunkum idan ta samu ta fito, ita zai ci ma fuska? Don kar taje lanchin (luncheon)din shine zai kulle ta don bakin hali. Agogon dakin ta daga kai ta kall 9:15, ji tayi ana bude k'ofar dakin da Mukuli, da sauri ta mik'e ta la6e bayan labule don yau watan cin uban Dunkum ne ya shigo, fitowa tayi daga Bayan labule tace "Zaidu bawan Allah, kaine anan bakaje gun patin ba?" da mamaki yace "Nene, me kikeyi anan?" tace "ba wannan shegen yaron bane ya kulle ni a dakin don ya tsane ni, wai don kar inje partyn" Zaid yace "Wa kenan?" cikin fada Nene tace "Wa fa banda fitsararen Danka Dunkum" Zaid yace "shi Rafeeq din ya kulle ki? Saboda me to?" tace "Af Sabida ya tsanan mana" "aa Nene ki bar cewa Haka, bari in dauki abu mu tafi" ta yi Murmushi tace "Yawwa Zaidu Bawan Allah" da sauri Zaid ya bude Wardrobe ya ciro wata Envelop yace "muje Nenenmu, kai Nenen mu kinyi kyau wallahi" dadi kashe Nene tayi ihun murna tare da juyi tace "Ai nasani wallahi, kaima kayi kyau Sosai dama Zainabu ta na nan sa ta ganka" yana tafiya tana bin shi a baya yace "ai ta ganni" tace "ta ina? Ko ta zo ne? Yace " Aa Wallahi, ta Video Call, itama ta sa na makara" Nene tace "Miye Bidi'o kwal?" suka shiga Mota Zaid ya fara mata bayanin Video Call. Yanzu lokaci ne na Nishadi(Entertainment) inda aka gayyaci Baban Cinedu da Baba Ari su fito don sa Mutane Nishadi, Baba Ari ya fito ya amsa Mike ya dinga Ma Feeq Ango kirari, ya dinga zazzafo zance, har gaban Feeq yaje ya na surutai, cikin Muryar shi yace Ango Rafeeq ka sha k'amshi, me zaka ce game da wannan Rana? Ya sa mai Microphone din daidai bakin shi, kamar ba zaiyi magana ba, chan kuma sai yace "Kana da Hayaniya" aiko duka hall din aka kwashe da daria. Baba Ari yace "Abun yazo inji me tsoron wanka, Amarya Nasiba, sai kin yi dagaske don Mijin naki, erhm erhm... Aka sake kwashewa da daria banda Rafeeq da ya murtuk'e fuska, Naseebah ta kalleshi ta sake daria, ya sa hannu ya tsinguleta tayi dan ihu me k'ara. Yana daga ido idonshi ya kai kan Nene da Uncle Zaid baki bude a hankali yace "Akwai Damuwa" bacin ran Nene duk ya 6ace data ga Tsaruwar Hall din, da manyan Mutane da ke ciki, Ihu ta hada da Shewa da ta ga haduwar da Seebi da Feeq sukayi, ai da sauri ta k'arasa gunsu, tana washe Baki, Seebi ta mik'e ta rungume Nene, ta fara kwalllar farinciki, Nene ta bude baki tace "kwalliyar dubu dari da hamsin din zaki jika da hawaye? Maza Share hawayenki, ina nan tare dake" ta kalli Rafeeq tana mai Murmushi don ya mata kyaun da be taba ba, da tuno Abun da ya mata nan da nan ta galla mai harara. Mai hoto da gurbataciyar Hausarta tace "Mama siya a maka photo" Nan Nen ta pose aka fara kashe mata hoto, Nene har da rike su K'ugu duk Cikin style, sannan ta tunkude Feeq ta zauna a tsakiyar su aka musu hoto, har da dundu ta sakar mai ta baya ba tare sa Seebi ta gani ba, takaici ya hana shi Motsi. Muryar Uncle Zaid ta kauraye hall, din inda yake ba Amarya da Ango Shawara yana musu Nasiha, Nene taji wani dadi, da sauri ta bar gunsu Seebi ta k'arasa gun Uncle Zaid, cewa take "Zaidu Bawan Allah ka bani abun maganar nima nayi". "Assalam Alaikum jama'a, sunana Aminene Mamman" Rafeeq ya dafe kanshi da hanayenshi biyu cike da takaici, a hankali yace "Lord of Mercy! what is this crazy Woman doing?" Seebi ta dan rankwafo a hankali tace "Baby its your day, be happy dont be Sad" Murmushi yayi yace "Ina sonki kinji?" Murmushi kawai tayi, Nene ta cigaba da cewa "shekaru na Sittin da dori nice kakar Amarya wato Seebi, duk da wasu ba su so na zo gun nan ba, har kulle ni sukayi a cikin daki, toh Da yake ta Allah ba tasu ba, sai gani a cikin Fillin nan, hantar su sai ta fashe" ta karasge tana me hararar Rafeeq, shiko Murtuk ya dauke annurin fuskar shi, Nene ta cigaba da Surutan ta karshe ta Ma Maauranta Addua da fatan Zama lafiya, nan da nan hall ya kachame da tafi, da yawa Nene ta burgesu ta basu daria. Dj ya sa mata wak'a, tace "kai ni rabani da wannan wakar kafiran" Surajo kada min molimoli, aiko kamar jira surajo mai asharalle yake, suka fara kidi, Nan Nene ta fara taka rawar Moli Moli, nan da nan wuri ya kachame da tafi, Abii dai dafe kanshi yayi yana tunanin yaushe Nene zata bar abubuwan ta. Nene ta burge kowa, wani Abokin Daddy yace da Daddy i like this woman, this is what we call Entertainment" don shi a ganinshi Nene yar wasan kwaikwayo ce aka gayyato. A tare suka Yanka Hadadden Cake din da Ummu Sudais ta Musu, cikin kunya Seebi ta sa mai a baki, shima ya guntula ya sa ma ta, nan aka hau tafi. Dance! Dance! Dance, na Tsakiyar hall ta kacame da rawa, Yan Asharalle suyi, Dj yayi, dukkansu suna ta nuja tasu basirar, Rawa ko Nene kamar ta karya k'ugiu, lik'e kam anyi, an Watsar da kudi, (nima biebeen ku da na ga haka sai na fara rawa ina kaiwa k'asa kasa ina tsince yan dubu dubu dinnan, ban ankara ba naji Nene ta take min hannu). Daga nan kuma aka hau Refreshment, wato cin Abincin dinner din, Babu ne kawai babu cikin kayan Abincin. Nan akayi serving kowa, Kowa ya ci ya sha. Nene tace tabb"Amma Dunkum yaso in tafka asara, da bani zaayi wannan shagalin, toh Allah ya tsare ni dai daga minahuncin shi, shege sai kyau kamar shi yayi kanshi" na kusa da ita suka tuntsire da daria, Abinci ake taci, Naga Yan Zauren Biebee Isa sai cin abinci suke, wasu har da kullewa a cikin tissue lols, Rafeeq kuwa wurin ya ishe shi, so yake kawai ya ganshi a gida, ya gaji da rawa ya gaji da hayaniyar gun. Fuska ya ma Uncle Zaid, Uncle Zaid ya bashi hakuri ta ido. Haka taro ya tashi Lafiya, Komai yayi daidia, abun sai wanda ya gani, abun sai san barka. Sai fatan Allah ba Maauranta zaman lafiya. Da Asuba Zaid da Rafeeq sun dade suna Magana, Sosai yake mai fada, da Nasiha, Rafeeq yayi Murmushi yace "Uncle Zee, you dont have to worry about anything, i love Baby so much, i wont hurt her, i assure you that" Zaid ya ja kunnen Rafeeq yace "In my presence her name Is Nasiba, idan a bayan idona call her anything in kaso ka kirata da Jaririya ba Baby ba" daria Rafeeq yayi yace "Are You Jealous?" Zaid ya tabe baki yace "Ina da Zainab din?" Rafeeq yayi daria. Alhaji Habib ya shigo, bayan gaisuwa Zaid yace "Yaya yanzu fa zan wuce Kaduna" 'Ba ka bari sai Gobe?" da sauri Zaid yace "Tab" Alhaji Habib yayi daria yace "toh kai wani Gida ka zaban ma dan naka? Gwara tun wuri a je a gyara ayi furnishing ya dauki matar shi su koma chan" Zaid yace "Yaya Akwai dan shirin da nake musu, nan da lokaci kadan zakaji" "Alright" inji Alhaji Habib, Suka fice, Uncle Zaid yace da Rafeeq "kai kuma kayi ma Seebin magana, in ta amince to, in bata amince ba sai kuje ku dawo, duk dai yanda kukayi sai ka sanar dani" Ya rungume shi yace "Thank you, You are the best" "shuttup boy" sukayi daria, tare suka hau sama wurin Mami Uncle Zaid ya mata Sallama, ya ma Seebi da Aneesa Sallama, ya wuce Gidan Nene ya mata Sallama, ta mai Addua Sosai, ya dauki Abii da Ummi da Anan suka wuce Kaduna. A yau Lahadi yan Nesa suka koma garinsu, yan biki aka watse. Nene ta tarkata ta koma Gidan Lema don kwana daya da tayi ba Seebi duk sai ta ji ba dadi Sabo turken Wawa. Karfe tara na dare taji sak'o ya shigo wayarta, ta bude "Baby, I'm hungry" ta kalli Nene da ta bude baki sai surutu take mata tana bata labarin 'yan biki" ta dan muskuta, ta mik'e tace "Nene ina zuwa" Nene ta tsuke fuska tace "ina zaki da daren nan?" "Hamma zan dafa ma Indomie" Nene ta tabe baki tace "Ke Seebi ki fita idona, ke baki iya dan jan ajin nan ba, Miji ya kiraki jiki na rawa zaki kai kanki, tun kafin ki tare, wayace miki haka akeyi?" Seebi ta bude baki cike da Mamakin Nene, tace "Nene meye haka kike fada?Yunwa fa yakeji? Meye laifi don zan kai mai Abinci? Ai mijina ne ko?" Nene ta bude baki "Ehh lallai Seebi wuyan ki ya isa yanka, idon ki ya fedare, ke kin auri Dunkum, zaki gayan magana ke me Miji, ke dadi Miji, ke danubanki Mutunci nake neman miki" Wayar ta ya sake Ringing din, da sauri tayi hanyar k'ofa tace "Ni abinci nace zan kai mai ba wani abu ba" Nene ta daga murya tace "Ke kika sani, indai Dunkum ne gaki gashi". Kitchen ta wuce, tana shiga ta hango SlicedBread, tace " Yauwa" Ta bude fridge ta dauko Sardines da butter, da bama ta hade su gu guda, a gurguje ta shafa ma bread dinnan tayi toasting guda 4, ta Zuba mai Pepper Chicken din da ta ganj a cooler ta ciro Kwalin Exoctic a fridge ta sa a tray da Cup tayi k'asa dakin Rafeeq, a k'ofar Dakin tayi Sallama. Bude wa yayi ta shiga da tray din kanta a k'asa, Hijab ke jikinta amma sai ta mishi kyau sosai, hannu ya sa ya karbi tray din hannunta ya ajiye kan stool, ya riko hannunta ya zaunar da ita kan Gado, yace "Thank you" da sauri ta kwace hannunta ta mike ta isa ga Tray din ta mik'a mai Sandwich din tace "kaci, you are hungry" ba gardama ya amsa, ta tsiyaya mai lemun ya kurba, yanda yake taunawa a hankali cikin aji, sai taji ya burgeta, guda biyu kawai yaci yace ya k'oshi, ta so ya k'ara amma ya shaida mata ya ishe shi, ta mik'e ta kwashe kayan tace "to sai da safe" da sauri ya mik'e ya karbe tray din ya dire a k'asa yace "Baby i want to talk to you about Something" jin yanda yayi maganar ne ya sa ta gane maganar Muhimmiya ce, wuri ta samu ta zauna, k'asa ya zauna yana me fuskantar ta, a hankali ya fara magana; Baby, i know we had a rough start, i kept the way i feel for you for a quite a long time, ,kin shigo Rayuwata as a Blessing, you Sacrificed and did alot for me, And nagode miki for all that, Yanda Allah ya tsara, you are now My Wife, I know be kamata na sa ki ki min wani abu ba bayan abubuwan da kika min a baya, na son ba kya min son da nake miki, i'm not even sure if you love me at all, well I dont care about that, Ni ina sonki, ina kaunarki which is why nake so ki taimaka ba danni ba, ba don bakya so na ba, idan Wannan shine abu na k'arshe da zaki min ki min shi, ba zan tilasta miki kiyi abun da bakya so ba, but i'll be happy if you grant my request. DonAllah". Yanda yake magana ya sa taji tausayinshi, to me yake bukata daga gareta haka har yake rok'on ta? Kuma wai a ganinshi bata sonshi?" muryar Mimi ya fado kanta a lokacin da take ce mata "Seebi, sai kin cire kunya zaki iya zaman aure, he is your husband, take care of him or Someone will" runtse ido tayi tace "Hamma, ka daina cewa bana sonka, ko ban sanka ba ai ba zance bana sonka ba, balle kuma Yanzu da kai Mijina ne, and Please ka daina rok'ona haka, ka fadi ko me kake so, InshaAllah zan maka shi in har befi karfina ba" Sosai maganganun ta suka mai dadi, ya samu k'arfin guiwan yi mata magana, hannunta ya sake kamawa yana mursawa a hankali yace "Baby, ina so ki dauki Zuwanki UMYU Matsayin Zuwa na ba zuwan karatun ki ba, ina nufin Don ki hadu dani ne kikazo Garin Katsina Gabaki daya, i want you to Sacrifice the 1year you spent in UMYU for me, ina so Ki Hak'ura da karatun da kikeyi a UMYU" idon Naseeba ya kawo ruwa, Tayi saurin maidasu, a ganinta kishinta yakeyi shiyasa be da Raayin tayi Karatu, amma Feeq beyi kama da Mazan da ba son Matansu suyi karatu, k'ila yana da reason dinshi, Sonshi da takeyi zai sa tayi mai komai, Ko don ta k'arasa ladarta, ko ba komai Aljannarta na tafin k'afarshi, a hankali tace "Hamma na, ba sai ka rok'eni haka ba, nafa kawai Umurni ne, umurni kawai zaka bani, kace Nasiba kin gama makaranta, ba zaki koma Makaranta ba, kai Mijina ne, ba sai ka rok'eni haka ba, ko da a ce ina Level 400 ka bukaci da na yanke karatu na, wallahi ni me yi ne, balle Level 1, ban ma gama sanin kan makarantar ba, Allah ya sa hakan yafi Alheri Amin" ta mik'e tsaye zata tafi,tausayinta, Sonta da k'aunar ta suka k'ara shigar shi, nan ya sake bata babban Matsayi a cikin ranshi, yace "Baby, baki gama karatu ba, yanzu dai zaki fara, i have plan for us, Abun da ya faru a baya tsakaninmu da Saude and All, hakan ya sani tsoron Mutanen mu, baka san wanda suke kewaye da kai ba, ba ka san ma su nufar ka da Sharri ba, hakan ya sa na tsani fara sabon rayuwa a k'asar nan, ina tsoron sharrin Mai sharri, ina tsoron Hassadar mai Hassada, Ina so muyi Nesa da k'asar nan, ina so mu fara Sabon Rayuwa inda ba wanda zai matsa mana, ba wanda zai cutar da mu, inda zamu gina Rayuwar mu cikin Aminci da k'aunar juna, Na gaya ma Uncle Zaid bukata ta, sai ya sanar dani dama Zai shirya mana Honeymoon a London mu hudu, sai yace in tambayeki idan kina da raayin Zama chan, zai Samo mana gida, ki fara Karatunki, And ni in fara Masters dina, idan baki da raayi, sai muje muyi 3weeks mu dawo, toh Alhamdulilah kin Amince, So help me Lord! I'll make you Happy, you wont regret this I promise, i'm going to shower you With Love and Care For the Rest of our Lives" kallo daya zaka mata ka ga Murnar da takeyi a zuciyarta ya baiyana, Dadi ya mamayeta, Farinciki ya ziyarci zuciyarta, ina zata saka ranta don Dadi, Alhamdulilah ta gode ma Allah a cikin ranta, ji take kamar ta rungume shi, ta bashi tukwicin wannan Albishir da ya mata, wai ita yau Seebin Nene zata je London? Bata taba zaton zataje ko nan da Airport ba, Amma da yake baka cire rai daga rahamar Allah gashi Aure zai kaita London. Kashe mata ido yayi yace "Baby, we'll be there, alone, just me and you, Just Us, then i would teach you how to love me" a hankali tace "You dont have to teach me how to love you, because i Do" Wani dadi yaji a ranshi cikin wata murya me sanyi yace "You What?" gangar Soyayya ta shigeta, bata son lokacin da tace "Yes Hamma, I believe In Destiny, My Destiny is to Meet you, Marry you and be with You, I love you So much" Dadi ke mai chalugude a k'irji, Farinciki da jin dadi ya ziyarceshi, takowa yayi ya matso gaf da ita, har suna iya jin hucin Juna, a hankali ya zare Hijab din jikin ta, nan da nan ta daburce, idonta ya juya don tsoro, shikam yana son yanda idon ta ke juyawan nan idan ta tsorata da abu, murmushi yayi ya Rungumeta sosai, ido ta runtse saboda tsoro, a hankali ya rada mata a kunne "Shhhh, keep calm, I got you" lamo tayi a jikinshi, shikuma ya sa hannu ya ware ribbon din da aka daure gashin kanta, gashinta ya zubo, ashe tana da gashi haka, a hankali ya dago ya tallabo fuskar ta, bata bude ido ba har yanzu ya kai bakinshi kan nata ya bata light kiss, kafin yace "I Love you Baby, with every fibre of my being, I will love you always and Forever" murya chan ciki ciki tace "I love you More Baby" _Bibilicious Biebee_ 👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍ NA BIEBEE ISA ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA) K'ARSHE Shigowa dakin tayi tana Sallalami tana tafe hanayenta, da sauri Seebi ta ture Feeq, tana sinsina kai, shikenan Yanzu Nene zatayi Shela dasu, don tasan ta gansu, ba su san Nene gwanace ba, wayyaya ce in taso, yi tayi kamar bata ga me sukayi ba ta kalli Seebi tace "yanzu ke Seebi, wannan k'aton Gardin zaki kalla ki kira da Bebi? Bebi fa? Amma an cuci jarirai da k'ananun Yara" Seebi ta sauke sigh of relief, tana jin dadi Nene bata gansu ba, abunda bata sani ba tun sanda ta shigo Nene na la6e ta window, Seebi bata tanka ta ba ta rabata ta gefen ta wuce da sauri, Nene ta galla wa Feeq harara tace "Dangin Tsaka, an zo ana mana fankama, amma an tsaya ana ma Mata k'aramar murya" Girgiza kai yayi ba tare da cewa komai ba ya fada toilet, don yau ba zai bar Nene ta bata mishi Mood ba, yau ya na cike da farinciki mara Misaltuwa, Nene ta durkusa ta kwashe tray din ta wuce tana Murmushi, a baiyana tace "a ganin su ban ga suna Sumba ba?" lols. Rafeeq na fito wa toilet ya ciri Waya ya kira Uncle Zaid, Ringing daya ya dauka "Rafeeq Lema, why are you calling me in the Middle of the Night?" "Uncle Zaid, its to 10 fa, dare yanzu har yayi?" Oh God, did You forgot? I have a Wife Stupid" dariya yayi yace "Ohh Sorry, na manta wallahi, i thougbt har yau gauro ne kai" Zaid a k'agare yace "Shuttup and go straight to the point, Matata na jira na" Rafeeq ya ta6e baki yace "Su ma su Mata, Dama in gaya ma Seebi said Yes, ta amince" Ohhh Feeq ba zaka iya bari sai da safe ka kirani ba?, kar ka sake kirana sai bayan 1week" dif ya latse Wayar, daria Feeq yayi Ahh Su Uncle Zaid dokin shiga dakin Amarya kenan? Lols. A Gurguje Kwanci tashi ba wuya gun Allah, Rafeeq ya gina soyayyar sa a Zuciyar Seebi cikin kwanaki kadan, bai jin komai gaban kowa ya nuna mata So, in kuwa tana kusa dashi to sai fa ya rik'e hannunta, Nene tayi masifar tayi tsiyar amma a banza, don shi indai kan Seebi ne Neh-neh ta bar bata mai rai, haka dai aka Kamala komai na tafiyar su Seebi, zasu tashi ta Lagos in two days, ana Gobe zasu tafi Seebi ta fita gidansu Usheey, zasu biya gidansu Miemee ta musu bankwana, A gidan su Miemee suka kulle a daki, suna bata shawarar yanda zata rik'e Mijinta, sai ta cire kunya da sauransu. •••••••• Tun dazun yake kiranta a waya wayar bata shiga, da sauri ya dawo gida ya haye Sama, dakin Mami ya fara dubawa don yanzu tafi zama chan bata nan, sai ya lek'a kitchen, ya L'eka dakin Nene bata nan, sai Nene ita kadai, juyawa yayi ya fita cike da damuwa, Maminsa bata nan itama, ya kira Mami waya yana me tambayar Seebi, ta shaida mai da nan ta barta da Nene, Dakin Nene ya koma, zaune ya ganta tana cin dabino, tana ganinshi ta hau taunar dabinon nan kamar Chewingum da gayya, shiru yayi na kusan minti 3 kafin yayi tsaki yace "Neh-neh ina Baby?" shiru tayi kamar ba ta ji shi ba, Rafeeq ya k'ulu sosai, amma beyi zuciya ba, to ko don Yace Baby ne tak'i kulashi? Ya dan sausauta murya ba kamar dazu da yayi kamar yana mata gadara yace "Neh-neh, ina Naseebah?" nan ma Shiru ta mai, kamar ya mak'ureta don haushi, Amma ya daure ya kai zuciyarsa Nesa yace "Neh-neh mana, please ina Naseebah taje?" mik'ewa tayi tace "Haba Dunkum, haba Dunkum, ya zaka tasani gaba kanai man tambayoyin ya Uwata ta haifeni? Kazo kana min wasu surutai a ka, kana fa da Hayaniya, Kana maganar wata Bebi, ni bansan baby ba na dai san 'yar Tsana(Doll Baby), Ajiyar Seebin ka bani? Yaushe rabon da kai man magana? Yau da yake kai ke so sai gaka kana min magana, to banganta ba, fitar min a gaba" Rafeeq ya k'urawa Nene ido, ya san dai idan ya bude baki ya mata magana k'arshe ya kai ga sa mata hannu, juyawa yayi Kawai ya fita, Dadi ya kashe Nene ganin ta k'untata ma Rafeeq, har da hayewa Gado tana murna, ko ba komai ta rama Wulakancin Da ya mata ranar Bikin shi. Aneesa ya gani ta fito daga kitchen rik'e da Plate, tace "Yaya Rafeeq ya dai?" cikin doko yace "Anee ina Baby? Ohh taje gidansu Ushee, da Miemee" gudu gudu, sauri sauri ya sauka daga Saman. Daidai Haraban Gidan suka ci karo, tare take da su Miemee da Usheey, Tsayawa sukayi, straight gunta ya nufa tare da jawo hannunta, Ba tare da yace komai ba ya ja ta daki, Su Miemee suka bisu da kallo, tare da fadin "toufa" suka wuce cikin Gidan. Dakinsa ya rufe k'ofar a lokacin tsoro ya cika ran Seebi, da bango ya sadata ya mata rumfa da hanayensa, ya tsura mata ido kamar ba zai tanka ba a hankali yace "Baby kin sa na shiga damuwa, your phone wasnt going through" amda sanyi jiki tace "Kayi hakuri, naje musu Bankwana ne" to meyasa baki jira na dawo ba na kai ki, i was worried about you, and your Grandma was so Annoying, i nearly Hit her" a hankali tace "Hamma, ka dai na gigin cewa zakayi hitting Nene, i know shes annoying and she loves you" kada idonsa yayi yace "And it is you i love" da sauri ya hada bakunan su, ta tureshi iya k'arfin ta tace "su Miemee na jirana" ya rik'o hannunta yace "Oya na basu time, because in two days time, its going to be The two of us alone" bata gama saurarshi ba ta fita da gudu don yanayin shi na bata tsoro. RANAR TAFIYA Bayan An musu Nasihohi da Adduo'i, Daddy, Mami Anee, Abba da Umman Aunty Zee, Abbii, Ummi da Nene suka raka Uncle Zaid, Aunty Zee Seebi da Feeq Airport din dake Kaduna a Mando, inda zasu tashi zuwa lagos, daga lagos zasu hau Jirgin da Zai sada su da England. Sosai Seebi ke Kuka ta rungume Iyayenta Mata, ta dade Rungume da Nene, kuka sosai takeyi, duk taurin zuciya irin na Nene sai da tayi k'wallah, da taga kukanta ba me k'arewa bane, sai tace da Feeq "Kai Dunkum, zo ka janye Matarka" jin kukan yake har ranshi da k'yar ya banbareta daga jikin Nene ya doraya a kafadarsa, a hankali ya rada mata a kunne "I got you" Uncle Zaid yace "Alright ya isa hakan nan, lets get going" ya Rik'o hannun Matarshi, har sunyi gaba Nene tace "Dunkum" kamar ba zai tsaya ba, sai chan ya juyo, sai da ta harareshi tace "Ka kular min da Seebi, Kamar ba zai tanka ba yace "InshaAllah" nan suka fara daga wa juna Hannu har suka kure wa ganinsu. LEEDS BRADFORD AIRPORT A gajiye libis ta fito daga Jirgin, ta sha bacci a kafadan Feeq, Aunty Zee na ta mata daria, Feeq ya rik'o hannunta suka fara tafia, Kayansu su ka kwasa, Uncle Zaid ya tsaida musu Cab, suka shige inda yace akai su *Bradford Intl Hotel* suna isa Zaid ya kama musu Daki Biyu, Room 123 da 124 aka basu, 123 duk suka shiga suka baje, Feeq yayi ordering Abinci daga Room Service, sukayi Jami'n sallolin da ake binsu, sannan sukayi Nafila, bayan sun idar ne Zaid ya dafa kan Zainab kana ya Umurci Feeq da ya dafa kan Seebi shima, hakan yayi, Zaid ya na karanto Addua Feeq na maimaitawa, sun dade suna ma Matayensu adduoi da adduoin zaman lafia a tsakaninsu kafin suka shafa, bayan sun danyi lazimi ne Zaid ya kalli Zainab yace "muje daki ko cutie? Nasiba ta mik'e itama, Zaid yace "Ina zaki Seebi?" murya k'asa k'asa tace "Aunty Zainab zan bi" Feeq ya harareta, Zaid yayi Murmushi yace "Babyn Son, ga dakin ku nan, in kuma kin fison chan din Son ku koma, mu sai mu zauna a nan din" a daddare tace "ai na zata dakin Mata daban na Maza daban" Feeq ya fashe da daria, Aunty Zee ta kai mai Jifa tace "Oya tashi ka taya Baban ka kwashe kayanmu ku kai mana daki" Feeq yayi fuskar tausayi ya kalli Uncle Zaid zai yi magana Uncle Zaid ya mai ido, ya tashi yana turo baki kamar wani jariri, ya dauki trollyn Aunty Zee, Uncle Zaid ya dauki Jakkanshi suka fita suka barsu. "Seebi D'iyata, ki kwantar da hankalin ki, ki natsu, na lura duk a tsorace kike, Seebi Auren fa kenan, lada zaki samu in kika faranta ma Mijinki, kuma zaki samu akasin hakan in kika sa6a. Hakuri zakiyi kawai ki saki jikinki, jinji daughter? Kai kawai ta gyada mata hannun ta ta rik'o suka fita. "Kaga abunda matarka ta ja mana ko?" inji Uncle Zaid, Rafeeq yace Matarka dai, da ba tace in biyoka ba da i wont be stucked in here with you" Nidai gaskia i cant sleep without my cutie, tashi muje dakin" da sauri Feeq ya tashi suna murda k'ofar dakin sai ganin su sukayi tsaye, a tare suka sakar ma Junansu Murmushi, Aunty Zee ta hararesu duka tace "Sai ina?" cike da so da k'auna Zaid yace i was about to get my Wife, coz i cant sleep without her" shauki ya kama Aunty Zee idonta suka rufe ba ta ganin kowa sai Uncle Zaid tace "and i can live without you Sweet Zee" Rafeeq ya gyara murya yace "We want to be like you when we grow up" sukayi daria duka har Seebin, Zaid ya jawo hannun Aunty Zee ciki, ya tura Feeq waje yace "Oya Babye, Seebin Nene goodnight" ya rufe k'ofar. Daria ya basu duka, suka kalli Juna Feeq yace "Baby, Me Aunty Zee tace miki?" Hararshi tayi ta juya dakinsu ya bi bayanta yana daria. Yana shiga dakin duk ta tsorata da yanayinshi don cicibarta yayi yayi toilet da ita, tana ta zillewa, cikin bath ya direta, ta kalleshi zatayi masifa yace "Wanka zakiyi babyna" Juyawa yayi ya fita daga toilet din, Akwatin ta ya janyo ya ciro mata wata doguwar riga ta Bacci me Hannu, ya kwashi kayan shafan ta dake cikin wata jakka ya kwankwansa mata yace "ga kayanta nan, ya juya, sai da tayi kusan 15mins tana wanka ta shirya ta fito daga toilet din, chan daga Nesa ta ganshi yana latsar laptop dinshi, ba tare da ya kalleta ba yace "Baby kin fito? Uhm kawai tace dashi, ya rufe laptop din ya dauki towel dinsa ya fada toilet din shima wankan yayi, ko da ya fito ganin dakin yayi da duhu, Toilet din ya bude ,hasken toilet din ya hasko mai ita, tana chan tsakiyar Gado ta rakube, Murmushi yayi ya kunna wutar dakin, a hankali yace " Baby* ta runtse ido wai ita tayi bacci, kana ganinta kasan baccin k'arya takeyi, wucewa yayi ya shafa mai tare da fesa turarruka masu k'amshi, ya sa 3quarter da wata bodyhug, sanyi takeji amma ko don kar tayi k'warar motsi ya san idonta biyu sai ta lafe, hayewa gadon yayi, idonta ra k'ara runtse wa, bakinshi ya kai kan kunnenta, cikin salon shi yace "Baby me baccin k'arya" Zumbur ta bude ido, tace "Hammana kayi hakuri DanAllah" dora kanshi yayi kan hannunta "baby me kika min" jikinta ya fara rawa, idonta ya fito don fargaba, abun da yake so kenan ya gani a kwayar idonta Murmushi yayi yace "i love it when you get scared like this" kukan shagwaba ta fara yi, ya sake Murmushi yace"Baby me kuka ba hawaye" yana ta kallonta tana ta dramar ta, na shgawaba da sakata, ita tsakanin ta da Allah kuka takeyi, cike da so da k'auna yake kallonta, Hannu ya sa ya mata rumfa tana kwance, yace "Shhhh, Keep Calm Baby, i got you kinji?" da kyar ta gyada kanta tare da runtse idonta, bakin shi ya kai kan nata ya shiga mata hot kiss, jikinta yayi labas har ta samu courage din responding, Rungumeta yayi sosai yace "Oya baby kiyi Bacci, kwanta kinji" kasa Magana tayi, ta rufe ido, sunfi 30mins a haka, ta kasa Bacci, sabida yanda ya rungumeta ta ya yake so tayi Bacci a haka? Shi ma hakan ne, ya kasa baccin jinta a kusa dashi yana sa shi wani iri, ya kuma kasa rabata da jikinshi, sarai ya san ba bacci takeyi ba, a hankali ya kai bakinshi kan wuyarta yayi kissing, kafin ya kai kan kunnenta yace "Baby" bata amsa shi ba, illa jikinta da ya fara rawa, kara rungumeta yayi yana mata rada a kunne har ta samu nutsuwa, haka ya samu damar sarrafata son ransa, kuka takeyi mara sauti, bakinsa be daina fadin"Baby, i got you, Shhh kinji? i am not going to hurt you, keep Calm!" abun da ya ta ce mata kenan. A wannan daren maaurata 4 dinnan sun raya daren nan mai Albarka, daren da suka na lak'abi da Daren Alheri. Bakin Rafeeq ya k'i rufuwa, cike yake da nishadi, tun bayan sallahr Asuba ya kasa komawa bacci, kallonta yake tayi tun da ta koma bacci bayan Sallar Asuba, kafin ta tashi bacci ya kira Room Service ya mata Ordering Abinci, tagumi yayi hannu bibiyu yana kallon ta, yana tunanin what life would be without her, wani Sonta da k'aunarta na sake shigar shi, bakinshi ya kai kan goshinta ya bata peck, a hankali ta bude ido ta zube su kan Feeq da ya zuba mata ido, Murmushi ya sakar mata yace "Good Morning Baby, kin tashi Lafiya? Da sauri ta mayar da idonta ta rufe tana me sakin Murmushi me sanyi" yace "Thank you Baby, Thank you so very Much, ki tashi kiyi wanka, your breakfast is ready" ya lura kunyar shi takeji, a hankali ta bude idonta ta zube shi a bayn Feeq, abubuwan da suka faru jiya da daddare suka soma dawo mata" Murmushi tayi ta dan yunkura zata tashi, ta dan cije lebe, a jikinshi yaji kamar Baby na cikin ciwo, da sauri ya juyo ya ganta tana yunkurin tashi, "Sannu kinji? Allah miki Albarka, na san kina da hakuri sosai, jiya na kara tabbatar wa da hakan, Kuma ina sonki, sosai nake sonki, tashi muje kiyi wanka kinju Babyna? ko kuma i have a better idea" sabarta yayi kamar Baby ya sadata da toilet din, kamar dazun da Asuba, ruwan Zafi ya hada mata" yace "zaki iya? Ko in miki?" hararshu tayi tace dazun kai ka min?" yace "ba laifi idan na miki yanzu" da sauri tace "Zan iya, ka tafi" yace "Alright baby zan tsaya a bakin kofa if you need anything". Hannun ta ya ja sukayi Dakinsu Uncle Zaid, sukayi knocking tare da shiga, Zaune suke suna breakfast suna ciyar da junansu, Seebi taji kunyar yanda taga Aunty Zee kamar ta shuhe jikin Uncle Zaid, Rafeeq ko ko a jikin shi, cewa ma yayi "Mr&Mrs Zee may we come in?" Uncle Zaid yayi daria yace "Noo, Mr&Mrs SeebiFeeq, My Wife and I are Busy" daria sukayi gabaki daya, Seebi da Feeq suka gaidasu, a ka gaisa, Aunty Zee ta ja Hannun Seebi suka shiga chan ciki, Feeq ya zauna kusa da Uncle Zee yana cin Apple, yace "Uncle Zee kasan jiya..." Uncle Zaid be tsaya jin me Rafeeq zaice ba ya buge mai Baki yace "Shuttup boy" You are a Married Man, act like one" turo baki yayi yace "Baby kinga Uncle Zaid ko?". Wani Zafaffen k'auna sukeyi wa junan su, cikin kwanaki biyi Rafeeq ya koya ma Seebi yanda zata so shi, tun tana kunya har ta daina, bata da wurin Zama sai jikinshi, in kuma suna tafia hannun nan nasu a sak'ale da juna. ******* Da suka fita wurin da ake Sayar da bada hayan gidaje suka fara zuwa, bayan yan dube dube Uncle Zee ya kama musu gida a Morley Streets inda duk Wata zaa dinga biyan £700, to bayan a basu mukullin gidan suka je suka duba gida, 3bedrooms ne, da kitchen, Gida dai yayi, tou dinga nan suka fara zuwa Malls don siyayya, yau basu wannan Mall din gobe basu wannan, sunje Malls kamar su The westfield Broadway,The kirkgate mall, Trinity mall, White rose and Foster square, sai da suka shak'e gidan Da kayan Amfani, to yau ba suyi kwanan Hotel ba dukkansu, nan Gida suka dawo, To bayan sunyi Settling, kuma suka sake wanka, Sunyi kyau gabaki dayansu, sai da sukayi Dinner kafin suka fita yawon bude ido, National Media Museums, inda sukaje ganin abubuwan da aka fara yin films dasu in the world. Haka kullum suke fita yawon Bude ido, sunje gurare kamar bowling hall, Cineworld, da Parks kamar su, Chellow dean, Lister park and Horton park. Satin su 3 su Uncle Zaid suka fara shirin komawa Naija, sai da Uncle Zaid ya ma Seebi processing University of Bradford inda ta zabi Nursing kuma ta samu. Rafeeq kuma sai Results dinshi ya fito zai fara Msc dinshi, Su Uncle Zaid da Aunty Zee suka yi Sallama da England suka wuce Saudi Arabia don yin Umrah, kwana 10 sukayi suka koma Naija. Dadi kamar ya kashe danginsu don ganin Yanda suka chanza sukayi kyau abunsu, barin ma Uncle Zaid da ya dan k'ara k'iba, Aunty Zee na kula dashi sosai, shiyasa yake Sonta. Sai da ta hada da Kuka kafin Mami ta bata Ayman da sharadin duk hutu zaa kawota Katsina. 6 Months Kasancewar yau Saturday, yau Weekends dukkansu biyun suna gida basu da Lectures, Zaune yake a k'asa inda Seebi ke zaune tsakanin cinyoyinsa, kanta kan kirjinsa suna Kallon The Originals Season 4, Wayar Seebi tayi k'ara, Feeq ya sa Pause, tare da mik'a Mata wayar, Aneesa ce "Hello Sisi ya kuke? Lafiya lau Anee ya su Mami?" "Mami nata Nak'uda tun shekaran Jiya yanzu haka suna Asibiti da Nene" Rafeeq da Seebi suka hada baki "Nak'uda?" "Ehmana, an yi zaton Haihuwar ce, ashe ba ita bace, Dr yace idan ta wuce Friday to saidai a mata aiki" Rafeeq yace "Anee, wai Mami haihuwa zatayi? Meyasa ba wanda ya gaya min? Seebi tayi sauri rufe bakinshi tace " Alright Anee, keep us posted dai, Allah ya raba lafiya" ta latse wayar, Hararar Feeq tayi tace "Saboda me zaa gaya ma? Me zakayi?" kasa yarda yaui wai Mami zata haihu, Hannu ta sa ta shafa gemun fuskar shi tace "Baby, Kana Mamaki ne? Ba abun Mamaki bane tunda mami ba ta wuce Haihuwa ba, Kyauta fa Allah ya mata, naga kamar ba kayi murna da hakan ba, Abin cikinta jininka ne, k'annenka ne, you should be happy, kaga Haihuwa zatayi, tana Buk'atar Adduar mu, mu tayata Addua, da Sauri ya daga Hannu ya fara Addua, ya shafa chan kuma y tuno da maganar da ake cewa ana mutuwa gun Haihuwa, da sauri yace " Baby, ina returning tickets din mu? We need to go back ASAP, hankali na ba zai kwanta ba, duk yanda ta so ta kwantar mai da hankalin shi amma ina, hankalin shi yayi Gida daki ya shige ya shiga bincike. Basu sanar da kowa Zuwansu ba don ma kar a hanasu, Kawai ran Jumaa suka ma Kaduna Diran Mikiya, a ranar kuma Mami ta haifi Yan Biyu, Namiji da Mace, Allahu Akbar, inji Nene, Murna Gun Daddy ba a magana, haka ya shiga kiran yanuwa da Abokan Azziki yana sanar dasu. Waya Feeq yayi ma Uncle Zee yace suna AIRPORT, sosai yayi Mamaki yace to dama gasu nan hanyar Kawo zasu wuce Katsina bari su biyo su daukesu kawai su wuce. *Katsina 8:00pm* Asibitin Alheri kawai Uncle Zee ya wuce dasu, suna shiga sai ganin Nene sukayi a harabar Asibiti, daga Nesa ta hango su Uncle Zee, ta k'araso gunsu "Ahhh Zaidu bawan Allah, an k'ara zama Uba ko k'aninka ne? Tunda kace dunkum kadai ne danka, wai kai tafiyar dare ko? kak'i bari sai gobe ku taho, sannunku dai da zuwa Zainab, Ayman Sannun ku, ta kalli Mata da Mijin da ke gefensu duk sun tsura mata ido, Feeq galala yake kallonta bata chanza hali ba, Seebi ko wai Nene bata ganeta bane kome wai?" Zaid yace "Wai Nene baki ganesu ba?" Ta kalli Rafeeq tace "Bature ne Gemu kamar dusa daga ina kuka samosu? Ita tsakanin ta da Allah baa gane Feeq ba don ya chanza kwatakwata, Zaid yace "Ki kalla Matarsa kila ki ganeta, Nene ta juya ga Seebi, Seebi sai Murmushi take tayi, wabi tsalle Nene ta daka ta rungume Seebi, tace " Wallahi Seebi nace" Seebi sai daria take tayi,wai kece kika koma baturiya, Ta dafa Feeq tace "Oh ni su Dunkum an zama magidanci, wannan Uban Gemun fa? Da k'asumbar nan wannan ai sai ka dade mata hanya" kunya ta ishi Seebi, Feeq yayi dan guntun tsaki yace "She'll never change" Ita kuma tace "Hali Zanen dutse" duk sukayi daria, suka nufa dakin da Mami ke kwance, Rafeeq na shiga dakin yaje ya rungume Mami, ko ita dai don yana danta ne ta ganeshi, amma ya chanza gabaki daya, Seebi ma rankwafawa tayi ta rungume ta suna mata Sannu, Anee na daga gefe suka Rungume juna suna Murna, Feeq cikin doki ya kalli Nurse din da ke gefe yace "Where are my Siblings?" Cikin wani abu aka ciro su, da sauri Rafeeq ya amsa baby girl din, yana wani Murmushi, Seebi ta anshi Namijin tana kiran MashaAllah, Feeq ya rungume Babyn a jikinshi yana me jin k'aunar k'annensa. Sai da su Mami sukayi Kwana 3 a Asibiti kafin aka Sallamo su, Gidan Alhaji Habib kullum cike da 'yan Barka, Mom din Maalesh in tazo tun 8 to sai 10 na dare take tafiya wata rana har Sha daya. Bayan tafiar su Rafeeq England ne Maalesh ya matsa ma Mom dinsa sai da aka kai kudin gaisuwan Miemee, yanzu rana kawai za a sa, Mom dinshi na Son Miemee sosai. Ranar Suna Yan biyu suka ci Suna SHAFEEQ da SHAFEE'AH(Aj) taron suna yayi Lafiya lao haka aka tashi cike da Jin dadi, kowa ka gani murna yake. ** ** "Guy wai wannan gemun na meye? Harda k'asumba, Seebi bata complaining? Haba mana ka rage shi" Feeq ya kalli Maalesh yace "Do you think bata son Gemun? Aikam zanje in cire, wallahi don bana son abun da bata so, kuma kasan bata taba min complaining ba" yace "kasan dai Seebi akwai kawaici, gani takeyi tunda kana so ba zata takura ma ka cire ba" Feeq ya jinjina kai yana jin son Seebi har bargonsa. Zaune take ita da Nene a daki Nene tana tambayar ta ya karatun ta? Rafeeq ya shigo dakin da Sallama, Nene ta washe baki, "Dunkum dan Ingila wai ka ga yanda Ka koma kuwa? Kamar bature ka zama Magidanci, lallai Seebi ta iya kiwo" Murmushi kawai yayi yana kallon Seebi yana aika mata sak'on K'auna, Zama yayi kan Gadon Nene tace "wai ni Dunkum wannan Gemun baka aske shi? Duk sai kayi kama da wani Osama bn laden, DonAllah ka cire, Seebi nasan ta kasa ma magana ne amma maganar Gaskia kyankyamin ka take" lokaci guda damuwa ya shiga fuskar shi, ya kalli Seebi da niyyar yace mata dama daukarta yazo yi suje Barbing Salon ta fada irin gyarar fuskar da take so yayi, Seebi ta tashi rai a bace tace "Nene haka mukayi da ke? Ni nce miki k'yankyaminshi nakeyi? Yaushe mukayi haka dake? Ta kalle shi tace "Baby ka bar abunka haka" Nene tace "ke banza in ya aske zai fi kyau" Seebi tace "ikon Allah, Mijinki ko Nawa? Ba zai aske ba Nene" Nene ta buga tsoki tace ke kika sani, ta mik'e ta fita, Feeq ya tsura mata ido, ganin Kallon da yake binta dashi ya sa ta mikewa ta dawo kusa dashi ta na shafa Gemun, yace "Baby, ki fada min gaskia, ba kya so ko? Maaleah yace kina kawaici ne shiyasa baki gaya min ba, tell me pls, in bakya so yanzu muje a maida miki yanda kikeso" Murmushi tayi tace "Baby nafison ganinka haka, yana k'ara ma girma a idon mutane, and besides i love it, so ba za ka cire ba, i want it" Rungumeta yayi yace "then i dont care about what people would say, my Baby wants it, then i shall keep it, and su Nehneh, i dont give a damn about them" Murmushi tayi tace "in banda karfin halin nene ina ruwanta? Abincin wani gubar wani" yayi daria. *A Gurguje Bayan Shekara Daya* Abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda Auren Maalesh da Miemee, Auren da ya sa su Rafeeq zuwa tun Sati 2 kafin Biki, Rafeeq da Seebi sun taka rawar gani a bikin Maalesh, Maalesh ya na nan zaune a Kaduna inda yake Aiki a NNPC, ya kuma samar ma Miemee transcript tana nan aji Biyu a nan Jamia'ar Kaduna KASU, suna matuk'ar son junansu kuma suna zaman Lafiya. Usheey fa? Usheey itama tana nan an Sa Mata biki nan da wata Biyu zasu sha Biki da Faisal abokinsu Maalesh, anan Katsina yake aiki. Rafeeq ya gama MSC dinshi a Biotech, dama shekara Daya ne, Ba yanda Seebi ba tayi ba da Feeq ya dawo Naija yayi Service amma yak'i, ya kan ce ba zai iya barinta ita kadai ba, kuma ba zai yanke mata karatu ba, so zai jira sai ta gama Karatunta sai su koma gabaki daya suyi Service din a tare. Kasancewar Rafeeq akwai shi da k'okari da k'wazo ya saye zuciyan Professor Nicklaus, Saboda k'warewar Rafeeq a harkar Biotechnology, Professor Nick yayi mai hanya lokacin da zaayi wani project, don he believe zaa samu good outcome daga Feeq, aiko it was Successful daga nan *World Bank Assisted Project* suka dauke shi aiki kan fannin *DNA Vaccine on Tryponosomiasis. Aunty Zee ta haifi danta Namiji inda yaro yaci Sunan Yayan Babanshi wato Hafiz, Abunnan ya ma Alhaji Habib Dadi, nan take ya Mallaka ma Hafiz Zaid Lema Gidan shi na Kaduna. Aneesa na son Hafiz Sosai, Ayman tayi wayau sosai har an sakata a Kindergarten, Mamarta kuma ta gama Housemanship dinta yanzu Service takeyi nan Kaduna. 'Yan Biyun Mami kuwa sunyi bulbul dasu gwanin shaawa, ga Yan biyu da farinjini, Amma kyaunsu ya shahara, sai da Nene ta fara tofa musu ruwan Addua saboda bakin mutane. Daddy ya shawarci Abii da su dawo Katsina da Zama, tun bayan Bikin su Rafeeq, yanzu Abbii da Ummi suna nan Gidan Nene, Abbi ya zama dan kwangila, dama Da Iliminshi na Architecture, shike Contract din wasu Zane zanen Gwamnati, yanzu shima ana damawa dashi. Nene kuwa tana Gidan Lema, Mami ta rok'i Abbii da su bar mata Nene, Abbii kance ai Nene ta kuce, idan kuma su Feeq suna Waya idan ta isheshi sai yace "ta tafi gidanta, tana takura ma K'annenshi da hayaniyarta" sai tace "in kaga na bar Gidan Lema, toh cema Maza akayi gani" Sai ya kalli Seebi cike da rashin Fahimtar don be gane Hausar Nene, Seebi sai tayi daria tace ta na nufin "Sai dai a fitar da gawarta, In otherwords suna nan tare Mutu ka raba" tabe baki yakeyi kawai. *** *** *** "Zaid Lema Wallahi dagaske, nakeyi, ka sa min Mata, kasan ni tun bayan Rasuwar Halima(Matar shi) Aure ya fitar min akai, Mama tayi fadan tayi Nasiha amma shiru, har tana cewa ko Aljanna ta Aureni" Daria Sosai Zaid keyi, yace "Bawani Aljanar da ta Aureka, kawai dai ka fi maida kanka Wurin Bussiness dinka da Aiki, gashi Kudi sun ma Yawa kai ba d'a ba Mata" Daria Sosai AbuSadik yayi yace "Ai shikenan yanzu na baka wuk'a da Nama, ka zaba min Mata Daidai da ni" Zaid yace "wai dagaske kake?" Abu Sadik yace"Wallahi dagaske Nakeyi" Yace "Toh shikenan, na baka Diyata Aneesa, Ajin ta Biyu a Jamia," ya ciro wayarshi ya nuna mai hoton Aneesa, nan da nan Abu Sadik ya Ji Aneesa ta mai, suna kama da Zaid abunka da Jini, AbuSadik ya ba Zaid hannu suka Kashe, Allah nawan? Kaii wannam ta hadu wallahi, ta min, amma Yarinya ce" Zaid yayi Murmushi yace kai dai kawai ka shirya muje Katsina Wannan Jumaar. Haka UncleZaid da Abu Sadik suka je Katsina ran Jumaa, sai da Zaid ya gabatar da AbuSadik a matsayin Abokin Aikinshi, kuma ya na so a bashi izinin neman Aneesa, Daddy yaji dadi amma yace "A nema So wurin Yarinya, idan ta Amince shima ya Amince ba zai ma diyarshi Auren Zumunci ba". Aneesa na zaune a daki tana chatting Nene ta shigo tace " Anusa, tashi kimtsa ga bak'o kinyi" Anee ta zaro ido, tace bak'o Kuma? Tace "ke dallah yi sauri tare suke da AnkulZaidun ku" Jiki Sanyaye Aneesa ta yafa gyalenta, tazo wucewa taji Mami na kiranta, ta karasa gunta tace "ki kwantar da hankalin ki kinji diyata, InshaAllah Alheri ne" gyada kai tayi, ta nufa Parlorn k'asa, Zaune ta gansu daga chan gefe ta durkusa ta gaida su Uncle Zaid yace "Zo nan Daughter, zauna nan" ta matsa ta zauna kusa dashi yace "ba tare da bata lokaci ba, Aneesa, kar ki manta nace miki ni Zan zaba miki Mijin Aure, ba wai don ke ba zaki iya zabar ma kanki abin da kike so ba, ba kuma don ke baki da samari ba, zan zaba miki wanda ya dace dake, wanda zai kular min da ke, you are my Responsibility, in kin yarda da hakan toh Gashi na kawo miki shi, Abubakar Sadik, Abokina ne, wurin aikin mu daya, nasan kingan shi lokacin Bikina, he's my trusted friend kuma na san zai kula dake, ki bashi hadin kai kinji diyata?" kai kawai ta gyada mai, Zaid ya mik'e ya fita don basu damar tautaunawa. Sun danyi maganar ganin bata sake dashi ba, daki ta koma. Mami ta bi bayanta, tace "Daughter ya dai? Mami Tsoho ne fa Shekarun shi 40, nidai gaskia yace ya bani time inyi tunani nidai banaso" Nene ta shigo tace "Ke dallah, Magidantan basun fi iya kaunar ba? Sun fi sanin darajar Mace, sunfi kula dasu, ki gwada ki gani zakiji dadinshi" Mami ma ta kara kwantar mata da hankali tana bata shawarwari har ta Amince. Magana ta kai gun Daddy, har ya sake kiranta don jin ta bakinta ta nuna mai ta Amince. A hankali A hankali ta fahimci AbuSadik wanda danyi ne shima, ya iya soyyaya kamar Chewinggum boys, son sji takeyi sosai, shima yana sonta, Daddy yace ya turo, dama jira kawai yakeyi don danginsa a shirye suke, nan da nan ya turo su, aka kawo kudi har rana aka sa biki wata 5. Biki ya Matso Gata Aneesa ta samu, ba nuna wariya ko kyariya, haka Mami ta samar musu Visa to Dubai don yi ma Anee kayan Kitchen, Kasancewar Shafeeq da Shafee'ah na cin Abinci Sosai, Mami ta yayesu. Biki ya matso su Feeq suka taho Naija Bikin Aneesa. Mami ta shirya ma Bikin nan, haka aka sha shagalin biki aka daura Aure, aka dauki Amarya zaa kaita Kaduna, rannar ta sha kuka kamar ranta zai fita, ta rungume Mami da Daddy ta na musu Godia, don duk duniya bata da wanda suka fisu. Haka aka kaita Tamfatstsen gidan ta da ke Unguwar Dosa. Bayan yan biki an watse Nene ta ja Seebi daki, tace "wai ya Seebi? Banji ba banga bayani ba?" Seebi ta kalleta cikin rashin Fahimta, tace "bangane ba" tsoki Nen ta buga tace "Ciki Mana" Seebi ta girgiza kai tace "Banda komai Nene" Nene ta kara buga tsokin, tace "ai nasan baki da komai din ai, sai zuba ido nake tun Wata 3bayan bikin ki shiru, Seebi kar dai Dunkum ya miki wayau ya na dirka miki maganin Daukar ciki, ku ga turawa yace be son haihuwa sai kin gama Makaranta" da sauri Seebi ta tashi, tace "Subhanallah, haba Nene, Haba Nene wani irin magana kikeyi haka, wallahi kar ki dauki Alhakin bawan Allah, Nene Allah ne be kawo haihuwar ba, shi ke bada wa, Wallahi kiyi istighfari ba daidai bane" Nene tayi shiru tasan bata kyauta ba, tace "kiyi hakuri, na damu ne, na zata kin biyewa Zamani ne kice ba zaki haihu ba sai kin shana, kar ma ki tada hankalinki kinji Seebin Nene, ai ana hakan, wasu ma sai sun kai shekara 10 da aure kafin suke haihuwa, balle ke yar shekara 1 da watanni, kar ki damu" Seebi tayi Murmushi tace dama banda mu ba, don Na san Allah na sane da mu" "to Allah ya kawo masu Albarka" ta amsa da Amin". Karo na Farko da yaji Nene ta burgeshi, tayi laifi an gyara mata kuma ta dauki Corrections. Allah sa ta daure,ya juya ya fasa shiga dakin yayi dakin Yan Biyu don musu Wasa. BAYAN SHEKARA DAYA Hajiyar Bana Hajiya Aminene Mamman sanye da hak'orin Makkanta, duk duniya bata da Kamar Zaidu Bawan Allah tunda ya kai ta dakin Allah, tunda ya biya mata kudin Makka taje ta sauke farali k'ima da darajarsa suka k'aru a idinta, Addua kawai take mishi don Zaid Alheri Ne, ta dage sai kassafa tsarabarta takeyi a gida, Akwatin kayan yara ta ma Hafiz da Aishatu diyar Aneesa, Sai kuma Akwatin dan cikin Seebi wanda Haihuwa ko yau ko gobe, sai zuwa sannu da zuwa ake mata. Mami tace da Zaid "Kasan Maganar ka kadai takeji, ka shiga ka mata bayani zatafi Amincewa, Murmushi kawai yayi ya shiga Dakin Nene, tana ganinshi tace " yauwa Zaidu bawan Allah, ga Akwatin Hafizu, da Aishatu, in zaka wuce sai ka tai musu dashi" yace "toh sun gode" ya zauna kan Gado, tace "Ya akayi Zaidu Bawan Allah? Fadin bukatar ka komicece zan maka ita in befi karfina ba" ya ji dadi sosai yace"Nene kinsan Seebi ta kusa Haihuwa, kuka ba halin dawowa Nan sabida ta kusa fara Jarabawar ta, shine nake so ko kije ki zauna da ita har ta haihu bayan Jarabawan sai ku dawo tare" Nene tace "Haba Zaidu dama wannan maganar ce sai kayi 'yar murya? Seebi tace fa, in ban kula da ita ba wa zai kula da ita, wannan Solobiyon in banda kiranta da 'yar tsana(doll baby) ba abunda ya iya, dole ni zanje? Yaushe tafiyar?" Zaid ya ji dadi Sosai yace "nan da yan kwanaki ne an gama komai". To wa zai kaini? Kai ko Aishatun?" yace "Ko daya, ke kadai zaki, mik'aki kawai zanyi ni" ta zaro ido tace "kai Zaidu Bawan Allah, in ka ganni lahira to kaini akayi, ta ya zan tafi K'asar Yahudawa ni kadai? Salan a saceni ko ai man Illah, ba dani ba sa Lallen Kaza" Zaid yayi Murmushi yace "Nene, ba wanj abu bane ba fa, kamar yanda kikayi tafiyar ki Saudi ke kadai, banbancin wannan Jirgi kawai zaki chanza, zan tura ma Rafeeq lokacin da Jirginku zai isa, kafin nan zaije ya jiraki, da kin fito zaa ki ganshi, an samu cigaba yanzu ko yaro dan shekara 5 sai ka turashi shi kadai, tayi daria tace "balleni 'yar Shekaru Saba'in ba biyu (68) sukayi daria, haka Nene ke yarda da zancen Zaid, ta dauki zancen Zaid kamar yankan Wuk'a, sai dai in beyi magana ba, nan da nan zata yarda. Nan ya cigaba da wayar mata da kai kan tafiyar. BAYAN WASU KWANAKI LEEDS BRADFORD AIRPORT. A gajiye take tafiya tana jan Akwatin ta, in ka ganta da wuya ka shaida Nene, ta Waye ta kile ta kara kyau, daga Nesa ta hangoshi washe hak'ora tayi ta kwala mai Kira "Dunkum" muryarta yaji a Sama, ya tabe baki "Here Comes My Headache"Ba ta bar shiru ba ba ta fasa kiran 'Dunkum' ba, Niyyar shi ya shareta amma da ya tuna Gargadin da Uncle Zaid ya dade ya na mai kan Nene, sai ya k'akalo Murmushi ya matso kusa da ita, ya karbi Akwatin hannun ta, bakin Nene kamar gonar Auduga, ya bude baki da k'yar yace "Sannu fa" ai fa ya tabota, "Kai Dunkum ka fita idona, in ci uban tafiar nan ni kadai in sha wahalar nan ka kallan kace min Sannu fa? Sannu fa?" ganin in ya biye mata zasu saida hali, shiru yayi ya ja Akwatin yayi gaba, binshi tayi tana Mita "Ka daiji haushi Wallahi, Dunkum kawai, Dunkum Dunkum, kana Girma kana cin K'asa, kana niyyar Zama Uba baka daina Dunkumcin ba, Dunkuk dangin tsaka, tsukakke" chak ya tsaya, Murmushi tayi na cin Nasara, burin ta kenan idan Feeq ya nuna mata be son abu tayi ta tsokanan shi, juyowa yayi a hankali da Niyyar yi mata magana amma sai ya fasa Securities din bayanta ya yafito fa hannu, da sauri suka k'arasa gunsu, Rafeeq ya fara magana ya na nuna Nene da hannun "Hello Officers, i need help from you, this is my Grandma, she's exhausted from her Journey, and shes having difficulty in Walking, you know how Annoying Old People can be, she wont let me Carry her or help her, i want you both to take her to My Car Over there, and Whatever happens you must'nt let go, keep hold of her" kai suka gyada mai Alamun sun gane, cikin Nene ya bada k'ululu da ta ga Masu Jan fatar nan sun kusanto ta, a hankali ta fara Ja da Baya, "Kai Dunkum Uban me zasu min? Uban me kace sumin? Eyi, Nene ba ta ankara ba sai ji tayi su chafkota kamar wacce tayi sata, Gabanta ya fadi da ta kalli mutanen nan sanye suke da Glass a ido so tashin hankalin da ta shiga ya hanata gane Yananyinsu, amma a zahirin gaskia Murmushi suke mata, Janta suka fara yi Feeq na ganin haka ya ja trolly dinta yayi Gaba, shikenan Feeq ya saida ta ga Nasaran nan masu jar fata mara Imani, Daga zuwanta, Shiyasa tace da Ziadu ba zata zo ba, Ashe Ajalinta ta biyo har Ingila, idon nene ya kawo ruwa, duk yanda taso hana hawayen fitowa sai da suka fito, don ta tsorata Ainun, Nene ta kwala mai Kira, "Dunkum, DonAllah kayi hakuri kar ka barni da Jar fatar nan, Dunkum ka taimaka, na tuba Wallahi, ba zan k'ara ba" banza yayi da ita ya cigaba da tafiar sa, ganin ba wanda ya damu da su, kowa harkar gaban shi yakeyi, kuma ba wanda yyi yunkurin taimakon ta, da taga dai tafiyar zaiyi ya barta da marasa Imanin nan tayi saurin cewa "Rafeeq Habib Lema, ka yi hakuri Na tuba, donDarajan Allah kayi Hakuri, na daina takura maka na bar kiranka da dangin tsaka, sunan ka Rafeeq dan Alhaji Lema" chak ya tsaya yana wani shegen Murmushi, takowa yayi har gabanta yace "Ya Sunana?" da sauri tace "Rafeeq Habibu Lema" ya sake Murmushi yace "ba Dunkum ba?" ta gyada kai tace "Ba dunkum ba, nice ma dunkumar" Yayi mugun Murmushi, duk ta tsure ta fita hayyacinta kamar ba Nenensa ba be takura mai idan ya nuna be son abu, ya kalli Securities din yace "Officers, I'll take it from here" suka saki Nene suna daga mata hannu wai byebye, da sauri ta k'arasa gun Feeq tana cewa "Mugaye Allah tsine muku" Feeq ya daure fuska yace "Me kikace?" da sauri tace "bance komai ba" yanda ta yi ne duk ya sashi daria, Har suka shiga mota Nene ba ta daina sauke Ajiyar Zuciya ba, Rafeeq ya kira Uncle Zaid yace ta iso har ya bata suka gaisa, ya tsareta da idanuwa, ta kasa gaya ma Uncle Zaid Rafeeq yayi Niyyar saidata, ko da ya tambayi ya yaji muryarta haka sai cewa tayi "Gajiya ce" haka suka iso gida. Seebi ta fito daga daki tana murna ga Nene ga Nene, gannin Seebi ya gusar mata da ko wane bacin rai da ke tattare da ita, suka rungume Juna, cikin Seebi ya mata kyau, Nene ta fara mata Fadar saka matsatun kaya ga Ciki, Rafeeq ya hade rai yace "Neh-neh, ki daina daga mata murya" da sauri Nene tace "Dama Rafeeq ba daga mata murya nayi ba, kasan matsatin kaya na takura ma Babyn da ke ciki shiyasa na ke cewa ta bar sawa" Yanda take magana ya sa Seebi gano wani abu, Rafeeq yace "Baby muje ki chanza kayan kinji?" kallom tuhuma ta bishi dashi ya dauke kai yana Murmushi ta mai kallon zamu hadu, Murya na rawa Nene tace "Rafeeq dama ince ina dakin da zan sauka?" a takaice yace "ki jira sai mun fito" da sauri tace "a fito lafiya" daria ta bashi sosai ya ja hannun Seebi sukayi daki. "Baby" Seebi ta kirashi, "Naam baby" ya amsa ba tare da ya kalleta ba, tace "kalleni nan, why is Nene nice to you? Why is she Suddenly calling You by your Name not by Dunkum? And why is she polite to you" Rafeeq yana daria yace "Baby i'm suprised to, but its a good thing she's changed" tsareshi da ido tayi yace "Fine, i did what i should have done a long time ago" Seebi tace "what is that?" "I settled her Ish" Seebi tace me kamata? Tiryen tiryen ya kwashe abun da ya faru a Airport ya gaya mata ya kare yana daria itama Abun ya bata daria sosai, ta kaimai dukkan wasa tace "Haba baby its not funny, not even in the history naji ance Nene ta tsorata da wani abu, koa Aljani baya ba Nene tsoro, amma gashi ka tsorata ta, baiwar Allah shiyasa ta tsani Turanci da Turawa" Rafeeq ya fashe da daria yace "Ai na kara sawa ta tsani Turawan, but its a good thing i did, coz my son wont grow up to hear his Great GrandMa calling His Dad Dunkum or Whatever" sosai Seebi ke daria, yace "Enough, zo in cire miki rigar muje mu lallasheta don naga ta tsorata dani". Sati Biyu Bayan Zuwan Nene Seebi ta santalo Danta Namiji, Haihuwar da Allah ya kawo mata shi a Sauk'ak'e, Farinciki Gun Rafeeq ba a magana, ya Rungume danshi yace " Welcome to The World ZAID RAFEEQ LEMA, i love you with all my Heart" Nene bata taba ganin Farincikinshi a baiyane kamar yau ba, a gaban ta da Drs ya ke ta rungume Seebi yana kissing dinta, yana mata Godia, Nene ba daman tankawa don ya mata hankali sai dai ta kallesu ta tabe baki, ko irin kawaicin nan va suyi na diyan fari" haka aka Sallamota Asibiti, har dan Aikin ya daina zuwa, kullum yana Manne da Seebi da Yaronta, be taba jin son yara irin haka ba, ba yanda Nene zatayi illa ta sa mai ido, don abun ya fara isarta, komai zaa musu a gabanshi, ya dinga wannan abu kamar kanshi farau gun Samun Haihuwa, sai tayi tsaki don kar ya jita. Zaune suke gabaki daya har Nene a Parlor, suna Video Call ta System din Feeq da Uncle Zaid, Rafeeq ya kanga mai fuskar Baby, Zaid da Aunty Zee sukace "MashaAllah, Rafeeq ka sa na tuna randa aka haifeka, you look just like him" Feeq yayi Murmushi yace "Zaid Rafeeq lema, open your eyes and see your Grandpa, Your Dad's Hero, your Dad's Saviour, Your Dad's Favourite, Your Dad's Best" Farinciki ya maimaye Uncle Zaid, bakinshi ya k'i rufuwa, don dai ya tabbatar da abun da kunnenshi yaji sai yace "What did you just called him?" Rafeeq yayi Murmushi yace "Zaid Rafeeq Lema" ya kalli Aunty Zee yace "Ga Miji nayi miki" tayi daria tace "Aikam nagode dama wannan ya tsufa ga sabon Jini" sukayi daria Hafiz ya lek'o yana ta cewa "Baby baby" duk sukayi daria. Nene tace "Zaidu Bawan Allah yaushe zaku zo?kace da ta haihu xaku zo?" yace "Eh Nene, zamuzo ranar Laraba dukkanmu Har su Yaya da Abbii, Mahmud kuma sai Jumaa shi da Iyalinshi InshaAllah" Rafeeq yace "Meye Laraba?" duk yanda ta so tayi shiru ta kasa, tace "Kai Rafeeq, ka fita idona, Kar kaga kwana biyu na sa maka ido ka dinga min wasu kamkamba da iyayi, ba fa tsoronka nike ba, don Tsiya Laraban ne baka sani ba? To bature yaci buraubashi" daria sukeyi sosai, yace "dagaske bansan meye Laraba ba" ganin iyakar gaskiar shi Yake fadi, Seebi tace "Wednessday ne Laraba baby" yace "yauwa Baby you the best, Uncle Zaid bari na baka short story, nan ya basu labarin yanda sukayi da Nene a Airport aiko suka fashe da daria, Nene ta ja kunnenshi ya tashi da sauri ta bi Rafeeq da throw pillow suna Zagaye parlorn tace " ni za kayi wa Bariki da turanci? Ashe ba saida ni kayi ba kasa na daga hankali na? Ya Rungumeta yace "ya zanyi in saida uwargida na, kinsan ina sonki Sosai" itama Rungume shi tayi tace "I lobiyu too" duk sukayi daria, tace "Zaidu BawanAllah idan ka gama murnan Takwaran da aka ma, kaje ka biya min Makarantar Yaki da Jahilci, da na dawo Turanci zan fara zuwa in koya, saboda kar Baban Zaid ya sake min irin haka" gabaki daya suka sa Daria. 5 Years Ayman yar kimanin Shekara 10 zaune tana kallon CN ta k'ura volume, Shafeeq da Shafee'ah kuma da Aishatu(diyar Aneesa),suna game Hide and Seek, duk sunyi kachakacha da Parlorn, nan pillow nan remote nan ball nan teddy, sun cika gidan da Hayaniya Zaid na gefe zaune Kawai, Ihun su ya fara isan Rafeeq dake daki, tsaki yayi ya daura Pillow kanshi, ihun Yan biyu ya cika ma Rafeeq kunne, kamar zaiyi Kuka ya zaro Wayan shi ya latso Maalesh, Ringing daya Maalesh ya dauka Rafeeq ya balbaleshi Da fada "Lesh wani irin abu ne haka?" Maalesh yace "Guy ya akayi ne?" cikin Masifa yace "Some noisy kids are Disturbing my peace, for crying out loud Today is my only Holiday in ban huta yau ba sai yaushe? Gashi Baby tana gidan ka in sun hadu da wannan Usheey din kamar kar su rabu" Maalesh Yayi Daria yace "Yanzu ya kake so ayi Oga? Ni kazo ka kwashesu duka ku tafi Gidan ka" Tabdi so kake su tsorata min Jaririyata yar kwana 2? Ka bar su nan, ai hutu suka zo ma" Dif Maalesh ya katse wayar, Rafeeq yayi tsaki ya lalubo wayar Uncle Zaid, "Hello Son yadai? Uncle Zee Yaushe zaka koma Katsina kuma?" "Katsina dai? Jiya fa nadawo kasani, what is it? Kamar zaiyi kuka yace " Uncle Zee yaran nan suna son tarwatsa min kai, suna da hayaniya, tun dazun nake so inyi bacci sunki bari na, and I'm very tired, nidai Katsina zan maidasu Gobe, ba zan iya ba" Zaid yace "Haba Son, Jiya fa suka zo, kuma Seebi ta matsa su zo muku hutu, da k'yar Mamin su ta bari na taho dasu, amma kwana daya kachal sai kace zaka maida su haba Yarona" kamar zaiyi kuka Feeq yace "Nidai i want to rest, ba kuma zasuyi shiru ba" To bari in sa Driver yazo ya daukesu akai Su Bambinos, kafin Zee ta dawo daga gidan Mahmud" Rafeeq bece komai ba Ya kashe wayar. Bayan 'Yan mintoci sai ga Sam yayi knocking, Amina mai aiki ta bude k'ofar, yace "Oga yace yazo ya tafi da yara" Amina tace oya ku shirya Uncle Zaid ya aiko a tafi dasu, da murna su ka tashi za suje Bambinos, "Adda Ayman ki bari in zauna gaba" cewar Shafeeq, Ayman ta harareshi tace "Go back my Friend" Lil Zaid yace"Aunty Angel in zauna a gaba? tace "Eh zo ka zauna My boy" Murmushi Kawai yayi ya zauna, "Aunty Angel yaushe Ammi zata dawo? Ta shafa kanshi tace "taje Gidan Aunty Mimi, Aunty Mimi ta haihu, ba zata dade ba kaji Yarona?" kai kawai ya gyada don shima yana jin wuyar Magana, haka suka tafi. Da sauri ta shigo Sallama tana kwala mai kira, "Baby" dakinshi ta fada ta ganshi kwance yayi rub da ciki zuwa tayi ta hau kan bayanshi, "ohhh Baby lemme sleep" tsalle ta fara yi kanshi har sai da ya jiyo ya kalleta ta dawo kan cinyarshi, ta rataye Hannayenta a wuyansa, tace "Baby Guess What?" ya kalleta cike da shauki yace "Sister Nasiba Lema, wont you let me sleep? Kafada ta daga alamun Aa, tace "ni sai kayi guessing" yace "Baby save me the Stress tell me" murna Fal cikinta tace "Yaya Maalesh ne yace ranar suna zai min takwara, zai sa ma Babynshi suna Naseeba" Wooooow cewar Rafeeq, Yanzu mu kayi magana fa, be ce min komai ba" Wayar shi ya jawo ya sake kiran Maalesh, Maalesh na dauka yace "What?" Rafeeq na daria yace "Ashe ni zaa ma takwara, baka gaya min ba" ta yaya zan gaya ma? Ka kirani dazun kana min fada" Seebi tace "Aini Ya Maalesh ka gama min Komai Allah ya raya Baby Nasiba" yace Amin Seebi, and ki bincika sosai Feeq ya koran miki Yan hutu su duka" Feeq yayi saurin latse wayar, Seebi ta kalleshi kallon tuhuma tace "Baby ina Yarana?" ya dan sosa k'eya yace "Baby they were disturbing and i wanted to sleep" ta harareshi sai kayi me? "Uncle Zaid ya aiko a dauke su" Aunty Zee fa na gidan Ya Maalesh fa ta na duba Mimi, ni gaskia a dawo min da su, Amanar Mami ce, kuma nasan Angel na recording duk abunda kake musu, Mami na zuwa suna zasu kai k'ararka, ni ka dawo min dasu, ta fara shagwaba" Kallonta kawai yakeyi cike da So ds k'auna, shekaru sun shude amma ba abunda ya chanza na daga Kyaunta do koman ta, kaganta ba za ka taba cewa ta haifi Zaid dan Shekaru 5 ba, mayatacen kallon da Feeq ke binta dashi ya sata hararshi tace "What?" kashe ido yayi yace "Baby lets make a Baby" ta sake hararar shi tace "Bangane ba" idonshi ya k'ankata yace "I mean lets Make Mahmud Maalesh too" baki ta murguda tace "ban fa gane ba" Rungumota yayi sosia yace yanzu zaki gane, salon da ya fara mata yasata tuntsirewa da daria. Daria Zaid keyi kamar cikinshi zai fashe, Seebi na tayashi, Rafeeq na cewa "Baby ku dagani nagaji" Zaid yayi daria yace "Papa is a Superman he cant get tired right Ammi? Seebi tayi daria tace "Right Son, Your Pa is a Superman" Feeq na nishin wahala yace "Yes i am a Superman" Seebi ta tuntsire da daria, ta san Feeq da rashin Juriya, Sauka tayi tace "Son Sauko is time to Sleep" ba gardama ya daga Rafeeq ya ma Seebi kiss a kumatu yace "Sai da Safe Ammi nah" Allah ya tashe mu lafiya, kar ka manta Adduar bacci" kai ya daga mata, yaje gun Feeq, Feeq ya daga shi Sama ya kai shi daki ya sa shi fitsari ya kwantar dashi kan Gado, tare sukayi Addua, Feeq ya mai Goodnight kiss ya kashe mai wuta ya fito. Isketa ta yayi a Parlor, yace "Sister Nasiba Lema" ta kalleshi tace "Baby na ina sonka sosai" nima ina sonki sosai Baby na" Kinsan Nextweek ne Opening din *LEMA SPECIALIST HOSPITAL* Akwai wasu Dr's yan India da Uncle Zee ya ma magana, zasu zo and zasu dinga Partime anan, Asibiti ai ya gama haduwa, ga kuma Dr Zee Lema, ga Kuma Sister Nasiba Lema" Seebi ta tafa hanayenta cikin jin Murna, tace "ka san kafi kowa iya kiran Sister Nasiba? Thank you Baby for helping me Acheive my Goal, i wouldnt be what i am today if it werent for you" "Shhhh Baby dont say Anything, i should be saying that, ba zan taba manta Role din da kikayi playing a Rayuwata ba, role din da kike kan Playing, Baby kin game min komai, you stayed with me and love me despite my flaws and imperfections, you were there with me through my tough times, you endured all my Negativity, above all you gave me the most priceless Jewel Zaid, Tell me what more can i Say Seebin Feeq? You are a Blessing, I love you So Much i cant live without You, and Hey, you gave my life a purpose, it was all about Eat, Pray, Sleep Repeat... And now It is about Seebi and Zaid, all about The Both of you, My Happiness". Rungume shi tayi ta bashi wani hot kiss, chabal ya dauketa kamar baby sukayi daki. Gabaki dayansu a Tamfatsetsen Parlon Uncle Zaid, bayan su dawo daga Zagayen lungu da Sakon Sabon Asibitin, Dan guntun Walima sukayi isu isu, aka ma Yanuwa da suka riga mu Gidan Gaskia Addua, Dr Zainab da Nurse Nasiba suka yi Alkawari ba da guddumuwa iyakar K'arfinsu domin cigabar Asibitin. Aunty Anisa ba ma son Waina da tuwo" cewar Hafiz dan Uncle Zaid, Aneesa ta rungume shi tace "me kake so babana?" Nene tayi karaf tace "Ba sa son Tuwo sai Rice" Akayi daria Aneesa tace "Barin zubo muku kunji yarana" Ayman tace "Kunsan Nehneh ta fara jin Turanci? Nene tayi karaf tace "bazasu yarda ba Aymana sai sunji munyi, ki tambayeni yaya sunana?" duk suka Zuba musu Ido suka fito gaban Kowa, Ayman tace "What is your Name? Nene harda gyara murya aka mak'aleta tace "Ma Nem Aminene Mamman" Gabaki daya Parlorn Aka tuntsire da daria. Mami da Alhaji Habib sukayi Hamdala da suga Family dinsu a haka, taji dadi tasam cewa Burin Rafee'ah ya gama cika, sai dai su mata Adduar Allah ya sa ta huta, Baby Zaid kwance jikin Uncle Zaid inda yake mai magana yace "Grandson kaje kaci Abunci da yanuwanka gasu chan" k'asa k'asa yake magana yace "Grandpa, i am not hungry" Zaid ya shafa kanshi yace "Are you sure Grandson?" "Yes Grandpa kasan Me Papa yace min about you? Uncle Zaid yace "tell me Grandson" yace "He Said You are the best There is, you are the Best There was, and The Best there will ever Be, He loves you so much" Zaid yaji wani Dadi ya rungume Takwaranshi yace "I love you and your Pa So much" Nene ta tabe baki tace maganar kenan, kai wannan Jikan naka Zaidu Bawan Allah be son mutane, be yarda da kowa da ga kai sai baban shi, kai ko Katsina sukazo ya dinga wani ja da baya baya, da yayi Gadon Miskilancin sai ya zarce shi ko cikin yara yanuwan shi baka ganinshi, sai shegen son jiki" Su Mami sukayi Daria, Little Zaid ya tabe baki ya kalli Uncle Zaid yace "She's Noisy" Nene tace "Me yace?" Rafeeq yayi karaf yace "Cewa yayi kina da Hayaniya" duk suka fashe da Daria. Nima Biebee Isa Dariar nayi na fito nace bari na bar ku haka....... TAMMAT BI HAMDULILAH Alhamdulilah! Alhamdulilah!! Anan na kawo karshen wannan k'ageggen Labari na na KE ALHERI CE, Kuskuren da nayi a ciki Allah ka yafe min kuma ku yafe min dan Adam Ajizi ne, Allah ka bamu ma su son mu tsakani da Allah, Allah ka bamu 'yanuwa masu Zumunci kamar Uncle Zaid, wanda yake Fitila k'ona kanka ka haska wanda yake so, Allah ka bamu Ladar Zumunci. Allah ka kara mana son Yanuwan mu Ameen Ya Rabb. Ina Godia da yanda kuka kasance A tare dani tun Farkon Novel din har zuwa k'arshensa, yanda kukayi Hakuri da rashin Posts na kwanaki, ina fatan kun min Uzuri saboda Uzurorina. Ina Fatan kun Nishadantu, kun Ilimantu da #KAC, kuma zakuyi koyi da abubuwan k'warai na ciki, kuyi panchakali da mara amfanin ciki. And Yeah to The Bibilicious Freaking Fans all over The World💕I Love Y'lls with Every Fibre of My Being, I Heart Y'lls To Pieces❤❤❤ #1love to All My Whatsapp Groups ❤ #1love to Nagarta Writters Association❤ My Wattpad followers @biebeeisa, Thank you for Your Votes and Comments it means alot, M Sorry i dont reply some of your messages. But Y'lls are right here in my Heart❤ I love you. Thank You! Thank You!! Thank You!!! #KAC #SeebinFeeq #SeebinNene #1love #Ana tare👻👻👻👻👻 _Bibilicious Biebee_ #Complied by Princess Aysha Muhammad