*_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 1_ *_Free pages_* ________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. _________________ A tsari da tarihin rayuwa ƘADDARA MADUBI ce. Domin tana sakaka kallon kanka a ɗan adam kuma bawan da rayuwarsa ba ikonsa bace. UBANGIJI ya halicci duniya da halittun dake rayuwa a cikinta daban-daban, wanda suke a zahiri, da wanda ya baiwa kansa ilimin sani shi kaɗai. Sai dai a dukkan halittunsa ya tabbatar mana ƊAN ADAM mai daraja ne. Musamman idan mukai dubi da ayoyi da suka zo cikin Alkur'ani mai girma.         Bawai hakan na nufin sauran halittunsa basu da muhimmanci ba, a'a kai dai DAN ADAM ya baka wannan darajar, ya kuma fifitaka, idan muka duba Suratul Baqarah. Yayin da ALLAH ya ce wa mala’iku zai halicci khalifa a ƙasa (wato Adam), kuma ya umurci su su yi masa sujada, abin da ya nuna fifikon mutum fiye da mala’iku (sujuda ta girmamawa ba ta ibada ba). Bai barmu a mutanen kawai ba, sai ya rabamu a jinsi guda biyu, NAMIJI da MACE. sannan ya yomu a BAƘIN FATA da FARAREN fata. Ya yomu a YANKUNA DABAN-DABAN. Ya kuma banbantamu a ADDINAI DABAN-DABAN. Ba iya nan kawai muke ba, yarukan bakunan mu ma daban-daban suke, ta yanda wani idan zai kwana magana wani bai san mi yake faɗi ba koda zaginsa yake kuwa. Ba'a nan kawai muka banbanta ba, yama wasu ARZIƘI, wasu DUKIYA, wasu ILIMI, wasu BAIWAR SARRAFA HARSHE ko yin AIKI tuƙuru daga gaɓɓansu da ƙarfin daya azurtasu da shi. Samun ɗaya daga cikin wannan bashi ke nuna maka kafi wane DARAJA ba. Dan zai iya yinka mai ARZIƘI a DUNIYA, ka tashi talaka a lahira, talauci irin na rasa ƙyawawan ayyuka da rashin samun ƙyaƙyƙyawar MAKOMA. Zai iya yinka TALAKA a DUNIYA a lahira ka tashi mai tarin arziƙi da AYYUKANKA da samun kyakkyawar makoma. Zai iya yinka mai ILIMI, a lahira ka tashi ILIMIN bai amfaneka da komai ba domin baka amfanar da kanka da shi ba bisa kyakkyawar hanyar data dace da iklasi a DUNIYA. Zai iya yinka JAHILI, amma ka tashi a ƙyaƙyƙyawar MAKOMA saboda baka cutar da kowa ba a duniya, baka kuma bi mummunar hanyar da zata RUGUZAKA ba wajen yin ayyuka saboda RIYA (Rahama ta ALLAH ce). Wannan kaɗan ne daga cikin RAHAMARSA ga bayinsa.       A yanda DUNIYA take kamar ƙwallon wasa a ido, haka RAYUWAR kowane ƊAN ADAM take a NASARA ko FAƊUWA. Yanda kwallon ke a hannunka kusa da idanunka babba, haka girman matsalolinka da damuwarka da nasararka suke a zahirin idanunka da ZUCIYARKA. Idan ka harbata nesa da kai takan koma ƙarama, haka idan ka yarda UBANGIJI shine mai ƙaddarawa da bada sakamako sai ka dinga kallon wannan damuwar taka da matsaloli da jarabawoyi ƘARAMA kamar yanda kwallon nan dake nesa da kai take ƙarama.      Banbancin kawai girma da ƙarantar kwallo a idanu muke ganinta ƙwaƙwalwa ta auna mana. Amma girman jarabawa da matsalolin rayuwa muna kallonsu ne a ZUKATANMU da KWAKWALWAR MU baki ɗaya.       Bara mu taƙaita domin ku fahimci inda ainahin shimfiɗar tamu ta dosa kai tsaye, dan karmu shagala lokaci na gudu ba kuma mu yake jira ba. Abinda kawai nake so mai karatu ya auna anan minene ainahin RAYUWA? WANENE SHI? MAI ZAI KOMA A WATARANA? MINENE ƘARSHENSA A ƘARSHEN RAYUWA?.      Ki yarda, ka yarda a cikin kowace RAYUWA akwai farin ciki, akwai jarabawa, akwai nasara, akwai faɗuwa, akwai ƙalubale, akwai mafari, akwai ƙarshe, akwai mina aikata mina bari a bayana?. Dukansu kuma suna ƙunshe ne a cikin wannan rayuwar taki ko taka guda ɗaya tak da ba'a hannunka take ba, yanda ba'ai shawara da kai yayin halittarka ba, sai da ka girma ma kasan wanene kai? Haka baza'ai shawara da kai wajen tabbatuwar waɗan can abubuwan na sama ba. Domin a dukkan ni'ima da rahamar da UBANGIJI ya baka babu wacce kake biyansa da KUƊI. Ibada ma idan kayi kai kakema kanka gata bazaka rageshi da komai ba, ba kuma zaka ƙareshi da komai ba. Dan haka mu tafi kai tsaye kawai a wannan labari mai suna KIƊA A RUWA! MAI MAGANIN DODO. da zaizo gareku a wannan lokacin, mu kuma hango darasin da yake mana hannunka mai sanda akai domin mu fahimta, mu ilimantu, mu nishaɗantu, mukuma wa'azantu idan hakan ta kama...... •>•>•>•>•>•>• .....17/5/20013.....       ......Motse-motse yake ɗan yi da surutai cikin barci, har takai wanda ke a kusa da shi yana iya jin komai. Gashi yayi sharkaf da zufa a goshinsa duk da ba yanayi ne na zafi ba. Hasalima wani ɗan karan sanyi ake zuwabawa irin mai hazo ɗin nan da iska mai kwaso ƙasa ta buɗe mutane.      Da mamaki wanda ke kusa da shi da littafi a hannunsa yana dubawa ya ɗan zuba masa ido, sai kuma ya kai hannu ya taɓa shi yana kiran sunansa amma ko motsi. Littafin hannun nashi ya ajiye, zuciyarsa na ƙara shiga ruɗani da tsoro. Ba wannan ne karo na farko da abokin nashi kuma amini ke shiga cikin wannan halin ba a cikin barci, wani lokacin har sai ka fara fassara al'amarin nashi kamar na mai aljanu, kuma sam ba aljanun bane ba, in dai har zai kwanta barci mai nauyi a ƴan shekarun nan da wahala ya tashi bai shiga wannan yanayin na mafarki ba, duk da bai taɓa faɗa masa irin mafarkin da yake yi ɗin ba shi ya fahimci mafarkine mai nauyi da ban tsoro....        Sosai ya girgizashi kam yanzu, bayan ya janye bargon da yake ciki kalar army green, tare da shafa masa ruwan gorar dake gefensa a fuska. Wani nannauyan numfashi ya kawo tamakar mai dawowa daga suma, sai kuma ya ɗan furzar ya sake jan wani kaɗan kafin ya buɗe idanunsa a hankali.       Masha ALLAH na ambata ganin wasu kyawawan idanu tamkar ba na namiji ba. Da farko abokin nashi da shima ke kallonsa ya zubama ido, sai kuma ya kauda gefe yana yunƙurawa ya tashi zaune yana jingina da jikin tantin da suke ciki. Riga ce armless data kama ginannen jikinsa kalar army green, sai wando 3-quater irin kakin sojoji. Duk da a zaune yake kallo ɗaya zai tabbatar maka da sojan ne na gaskiya kuma tsayayye, dan kuwa jikinsa irin na lafiyayyun tsayayyun jaruman sojoji ne da zasu iya tunkarar kowane harmutsi musamman na nuna ƙarfin ƙwanji.       Abokinsa da ya zuba masa ido ya ɗan girgiza kansa, sai kuma cike da kulawa ya ce, “Da ace ina da damar matse bakin nan naka da baya son motsawa yayi magana da nayi hakan dan sanin wane irin mafarki kakeyi a shekarun nan, dake saka ka a wannan yanayin, *_Zak-Shadow_* duba fa yanda kake zufa tamkar wanda yake a filin daga, amma kuma akan mafarki, wannan al'amari na bani mamaki da tsoro”.        Wani ɗan kallon fishaa yay masa slowly da idanunsa ya kuma janye, batare da yayi maganar da yake so yayi ɗin ba ya miƙe abinsa. Nace oh oh! Wato fa da gaske a sojojin ma akwai SOJA, akwai kuma SOJI. Kai daka kalla wannan kasan yaci sunansa na Zak-Shadow, har hamar ya dace a ƙara masa da ILIYA ƊAN MAI KARFI. Dan kuwa mazan faman ne fa a mazansu da kayar da su ƙasa sai an haɗa da babban shirin haɗin gwiwa. Cikin yanayinsa na rashin gaggawa da hayaniya ya saka tausasan slippers baƙaƙe dake a gaban gadon daya tashi, batare daya sake kallon abokin nashi da yay tagumi yana binsa da idanu ba ya nufi ƙofar tantin da suke ciki, sai da ya ɗan ranƙwafa sannan ya fice.     Babbar magana, jeji ne iya jeji da babu alamar wani gari ko motsin halittu na mutane a kusa. Idan ka cire ɗan sansanin da suka kafa nasu na sojojin mai Tanti biyar kacal. Uku manya ne sosai da zai iya cin sojoji da yawa. Guda biyun sune ƙananu madaidaita. Guda ukun manya da ɗanyan ƙaramin suna a kusa da juna ne, ɗayan da Zak-Shadow ya fito a ciki yana gefe guda ne a ware ƙarƙashin wata ƙyaƙyƙyawar bishiya ƙatuwar gaske. Sosai garin yayi hazo na yanayin sanyi har baka iya hango abinda ke ɗan nesa da kai da ƙyau koda bishiyoyi ne, a gurin yashine shimfiɗe mai ƙyau da ɗaukar idanun mai kallo, ga tsafta, dan gabansu kaɗan akwai ruwa kwance dake rayuwa a wajen, dan haka ya zama matattara dabbobin jeji dake zuwa shan ruwa, wani lokaci kuma harda masu haɗari amma suka zo suka kafa sansani a wajen saboda ƙarfin hali irin na soja.       (Sojojinmu ALLAH ya ƙara muku lafiya da nisan kwana a duk inda kuke🙏).      Babu yawan sojoji a waje, dan basufi a ƙirga ba dake ɗan kai-kawo da bindigu a hannu sai wasu a zaune, da alama ƴan jiran kota kwana ne.         Fitowar Zak-Shadow ya saka wanda ke jikin tantin daya fito nutsuwa da sauri, tare da ƙamewa yayi salute nashi cike da girmamawa yana sake risinar da kai ƙasa, dan da gaske Zak-Shadow zakine a wajen na sama da shi ma ba naƙasan kawai ba. Idanunsa kyawawa masha ALLAH ya zubama sojan na sakanni, sai kuma ya maida ga sauran da ƙamshinsa ya fargar da su, suma duk sun nutsu, wasu a cikinsu jikinsu har tsuma yake yi. Jin shakkar Zak-Shadow a jinin duk wani matashin soji daya sanshi yake, badan ya kasance azzalumi ba, sai dan kasancewarsa tsayayyen mutum da baya ɗaukar shirme akan aikinsa da gaskiyarsa, kana take doka ko gaskiya ya ɓallaka ya ɗora gaɓa-gaɓa wannan abu ne mai sauƙi a wajensa.      Sai da ya gama ƙare musu kallo tsaff batare da yace uffan ba yay wucewarsa cikin takun bajinta na ma'abota ƙarfin jiki. Numfashi suka shiga saki a hankali, dan tunda ya fito kowa ya riƙe nashi a maƙoshi gudun shiga tarko. Sai kuma suka shiga ɗan kallon juna suna gulma da idanu, dan buɗe baki dai ayi magana tamkar taro match ɗin da babu yawan ƴan wasa ne..........✍🏼      _(🤣To bana kuma wa muka kwaso ne? Nima fa masu karatun wannan Zak-Shadow ya fara razana ni🤭, kota yaya labarin ma zai rubutu oho🥱😆. Kudai kuyi addu'a kawai kar ku ji ana karya Bilyn ku gaɓa-gaɓa ana ɗorani🤥.)_     ________________👇 *_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 2_ __________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 ________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv __________________ ........A gaban ruwan nan da kowa yasan wajen zuwansa ne in har ba suna akan aiki ba ya iso, ya ɗan bi wajen da kallo cike da nazari, sai kuma a hankali ya furzar da huci mai ɗan nauyi da nuna damuwa. Dai-dai nan wani matashin soja ya iso wajen hannunsa ɗauke da roba cike da dawa. Ɗan kallonsa Zak-Shadow yayi, sai kuma ya miƙa hannu ya amshi roban dawar alamar baya buƙatar wata magana. Cikin girmamawa sojan ya bashi, ya juya yabar wajen. Tamkar tsuntsayen dake rayuwa a wajen sunji ƙamshin dawar ne, sai gasu suna sauka ɗaya bayan ɗaya a gabansa. Karo na farko yay wani ɗan murmushin gefen baki, tare da ɗibar dawar a hannunsa ya shiga watsa musu, ai kafin wani ɗan lokaci tsuntsaye kala-kala sun cika wajen, shiko yana cigaba da watsa musu dawar. Abin sha'awa harda masu sauka akan kafaɗarshi. Dan dai-dai nan ma wata ƙyaƙyƙyawa mai adon ja da blue a jikinta ta taso fiirrr ta sauka akan kafaɗarsa ta haggu. Juyawa yay a hankali ya zuba mata ido, kai da ganin kallon da yake mata kasan tunaninsa ya tafi wani waje ne kuma daban.         Mafarkinsa ne ke dawo masa daki-daki tamkar Film da ake kallo zaune a cinema. Ba yau bane farko a garesa yin mafarkin, amma duk sanda yayi yana koma masa ne kamar sabo, kamar kuma a ranar ya fara yinsa, ga mafarkin a duk sanda zai yi shi cikin maimaita masa kansa yake abin kamar wani sihiri koma mi zai kirashi oho. Shekararsa bakwai da wasu watanni kenan da fara wannan mafarki, tun daga randa suka fara shigowa wannan jeji (2006) akan aikin da suke kai har zuwa yanzu lokacin yana ma a matsayin Major. Sun yo nisa sosai da jejin sukaci karo da wasu gayyar mata tafe da kayayyaki a kansu har da yara anata raira waƙar aure, ganin motocinsu da kayan jikinsu na kakin sojoji ga bindigu a hannu ya saka mutanen firgita suka shiga watsar da kayan kansu suka kwasa da gudu, masu ihu nayi masu kururuwa nayi. Sai mace ɗaya mai tsohon ciki data tsaya cak a hanyar, lallai itama a tsoracen take, sai dai da alama bazata iya gudun bane ba saboda ciki. Idanunta a rufe suke ga zufa ta gama wanke mata jikinta dake rawa. Duk abin nan dake faruwa kallo ɗaya yay musu ya maida kansa ga jaridar da yake dubawa, sai da abokinsa, koma ace amini da ya zama ɗan uwa na jini dake gefensa a motar da suke su biyu rak sai driver ya furta, “Ikon ALLAH irin wannan cin gudu kamar kunga dodanni! Ita kuma wannan halan cikin jikinta ne ya hanata gudun..?”       A karo na biyu ya ɗan ɗago a hankali jin furucin Imran ɗin, akan matar dake tsayen ya sauke kyawawan idanun nasa da kullum suke a juye da sirkin ja kamar wani mai afa ƙwaya, baya ganin fuskarta saboda ta juya musu baya, atamface a jikinta kalar blue da zanen barewa yallow. Zanen atamfar shine a matsayin gyale data lulluɓa, sai fanteka madaidaiciya a kanta dake haɗe kusan guda goma. Ƙafarta takalman danƙo ne da ake kira ɗan-madina suma blue. Tunaninsa ya katse sakamakon fitar wani yaron sojansu inda matar take yana mata tsawar data sakata daburcewa har tana neman zubar da kayan kan nata. Shi kansa baima san ya ɓalle murfin motar ba ya fita, sai ganinsa yay kawai a gabansu. Yaron sojan ya ƙame da sauri yana salute nashi, sai kuma ya nuna matar cike da takaicinta zai fara masa bayani kawai sai yaga ya ɗan duƙa a gaban matar. Ba shi dake tsaye inda suke ba har waɗan da ke mota sai da suka firgita, ai tuni suka shiga rige-rigen fitowa a motocin harda Imran, yo oga kwata-kwata ya fito su ubammi zasu jira yi kuma. Zak-Shadow dake a gaban matar cike da tsigunnon ƙasaita kaɗan ya motsa lips ɗinsa ya ce, “Kiyi haƙuri”. Da wani kalar sauri ta ɗago tana kallonshi, dan gaba ɗaya ta gama ƙarasa susucewa tunda ya duƙunnu gabanta, sai taji ma ai gara na farkon da wannan mai kama da mala'ikan ɗaukar ran. Kalmar ‘Kiyi haƙuri’ daya ambata ta matuƙar jijjiga mata zuciya kwarai da gaske, dan ba abinda tai zato ba kenan. Numfashi ta sauke mai nauyi, sai kuma cikin sanyin murya da rawar baki ta ce, “Ku su waye dan ALLAH? Dan bamu taɓa ganin irinku a wannan yankin ba shiyyasa sauran ƴan uwana suka firgita”.     Kallonta kawai yake baice komai ba, fin minti ɗaya kafin ya furta amsar da kowa baiyi zaton zai batan ba. “Mu sojoji ne, masu bada garkuwa ga al'umma da ƙarfin ikon ALLAH.”      A mamakinsa sai yaga tayi murmushi mai ƙayatarwa tana ƙara sauke ajiyar zuciya da sharce zufar data jiƙeta da mayafinta. Ta ce, “ALLAH sarki, lale marhabun da shigowarku wannan yankin namu, dama haka sojojin da muke ji ana faɗa a redion Tanimu suke?. Lallai yau na yarda SOJA MAZAN FAMA, SOJA GA WUTA GA YAƘI. ALLAH ya ƙara kareku bisa ƙyawawan aikin ku, ya baku nasara da kariya daga duk wasu mugaye. Tunda na fara jin labarin aikin ku nake fatan ALLAH yasa na haifi ɗa namiji idan Tanimu zai tafi birni yaje da shi ya saka shi a makarantar sojoji shima ya zama soja. Amma tunda yau har gaku a wannan yanki namu in sha ALLAHU in dai namijin na haifa zan nemoku a wannan jejin ko badaɗe ko ba jima na baka amanar yarona ka koya masa wannan aiki na jarumai. Dan daga ganinka kai mutumin kirki ne jarumin kwarai ɗan gaske”.       Karo na farko ya kai idanunsa akan cikin nata da yay girma sosai, sai kuma ya kauda kai batare daya ce komai ba, anutse ya miƙe gaba ɗaya yana mai tura hannayensa cikin aljihun wandon kakinsa na soji, daga sama kuwa riga ce baƙa t-shirt data kama ingarman jikinsa, yanda yay zanzaro da belt ya bama shafaffen cikinsa bayyana kwance a rigar luf. Tabbas suffarsa itace ta asalin Zaki da ake faɗa.       “ALLAH ya saukeki lafiya, mun gode da addu'ar ki garemu. Zan zo da kaina amsar amanarki! Ku bata ruwa, a ƙarbi address ɗinta”. Yay furicin ƙarshe da umarni yana barin wajen. Ba ƙaramin mamaki abin ya bama sauran sojojin ba, hatta da aminin nashi Imran kuwa. Duk da dai kowa yasan Zak-Shadow a kallon nesa ne zakai masa ganin mugu, dodo mai firgitarwa koda a kallo ne, amma yana da tausayin na ƙasa da shi da sassauci ga mata, dan ko macen soja ce tai masa laifi yanda yake mata hukunci ba daidai yake dana namiji ba. Kamar yanda ya bada umarni sun bata ruwan roba da aka ɗakko a mota, sun kuma tambayeta garin da take ta faɗa suna rubutawa. Sannan suka taimaka mata ta tashi daga faɗuwar da tayi na firgita. Sojan da yay rubutun address ɗin nata ya miƙawa Imran cike da girmamawa, amsar takardar Imran yayi ya saka a aljihu kawai, sannan yay ma yaran umarnin su koma motoci, dan tuni shi mai gayya da aikin ya koma ciki abinsa. Haka suka wuce suka cigaba da tafiyarsu suka bar wannan mata mai tsohon ciki nabin motocinsu da kallo har sai da suka ɓace mata. Tun daga ranar bai sake bi takan zancen ba, sai dai a daren kwana goma sha shida da haɗuwa da su yay mafarkin ta haihu tana miƙo masa jaririn. Abin kamar wasa ya cigaba da maimaita wannan mafarki akai-akai, kuma koda yaushe irinsa yake maimaitawar babu canji. Gashi a ƙalla yanzu shekara bakwai kenan da wata har biyu..... _______________ FAZANAMS MULTIPURPOSE PLC. *_Ina masu neman ayi musu souvenirs Na bukukuwan su dana shagalin bikin birthday da dukkan wasu taruka?_* *_Ina masu son ayi musu abinci Na gargajiya da abin sha Don farin cikin taronku?_* *_Maza ku garzayo to ga Dama ta Samu a FAZANAMS MULTIPURPOSE PLC_* _Muna yin abinci Kamar: Masa, Dambu, Alkubus, Dashishi, Dan wake, Alala, Biski da sauran su da Miya Kala Kala 🍝🍜🍲🍛🥗🥘🫕💃💃_ *Sannan Muna yin: kunun Aya, Zobo Mai flavour Kala Kala, Kunun tsamiya, Kunun gyaɗa, Tamarind drink, Kunun Zaki da sauran su🥤🧋🧃🍸🍹🍷🥂💃💃💃 _Sannan Muna yin party packs na Yara da manya haka zalika Muna yin snacks Kamar samosa, spring rolls, doughnuts, cincin Mai kwakwa, Mai flavour Kala Kala da sauran kayan makulashe irin Aya Mai sugar da Mai gishiri, Muna yin kwakumeti, Muna alawar Madara, iloka, ridi da sauran su.🧇🥪🥙🌮🫔🌯🥐🥯🌭💃💃💃_ *_Muna yin abincin sadaka ga Mai bukata muna nan a area 2 Abuja_* kuna iya tuntubata a wannan lambar👇 *08094186230* _Whatsapp Ko Kira._ _________________        Ɗan motsin da wayarsa tayi ne ya sashi sake furzar da huci, sai kuma ya sauke hannunsa dake cikin dawar nan ya cirota daga aljihu yana dubawa. Kallon wayar kawai yake babu wani yanayi dake nuna kirane ke shigo masa ya kamata ya ɗaga, harta gama ta yanke, sai kawai yay ƙoƙarin maidata aljihun, amma hanzarinsa ya katse saboda sake motsawar data shiga yi a karo na biyu. Yanzu kam hannu ya kai ya wani murza goshinsa, kafin ya sake ɗaure fuska babu alamar wasa sannan ya kai wayar kunne alamar dai da gaske kiran nashi akeyi..   “Hallo. My D!”. Wata zazzaƙar murya mai sanyi da kwantar da kai ta faɗa daga can. Shiru babu alamar zai tanka, da sauri ta ce, “Oh I'm sorry dear. Assalamu alaikum”.         “Wa'alaikissalam”.    Karo na farko jarumar muryarsa ta bayyana cikin buɗaɗɗen sauti da ƙarfin lafazi irin na maza marasa son wasa da lokaci. Itama sai ta ɗan ƙara kwantar da murya ta gaisheshi. Maimakon amsawa tambaya ya jeho mata a kausashe.       “Kiran na miye?”. Yanzu kam murya ta raunana kamar zatai kuka, ta ce, “Haba My D. Shike nan abu baya wucewa a wajenka, na baka haƙuri, na tura maka saƙo amma duk ka share ni. Dan ALLAH kayi haƙuri, nayi kuskure kuma na yarda nayi ina sake neman afuwa. Wlhy ni kewarka ma nake yi dan ALLAH kazo gareni, wata biyu fa ba sati biyu bace.”       Shiru yayi bashi da alamar tanka mata, har sai da ta fara kuka ƙasa-ƙasa tana cigaba da roƙonsa da ban haƙuri sannan ya motsa lips da ƙyar ya furta, “Naji”.        Baiwar ALLAH, dariya ta farayi cike da farin ciki, sai jera masa kalaman soyayya take masu zaƙi da taushi dake nuna tsananin kewa da begensa da take ciki. Shi ko yaƙi ya ƙara cewa komai. Cike da sake kwantar da kai ta ce, “Na faɗama Ummie?”.       “No!”.   “Ammafa itama tana kewanka D. Haka ma su Biebah kullum zancen ka ne a gidan nan, yau tunda na shiga hiranka kawai mukeyi”.        “Uhmm!”   Kawai yace. Bata damu ba ta cigaba da masa labarin ƙannen nasa, sai kuma ta koma na yaran dake tare da ita. Shi dai nashi saurare kawai, sai dai fuskarsa ta ɗan sassauta kaɗan ba kamar farko ba. Hakan na nufin koma wacece tana da muhimmanci a gareshi. Ya jima suna wayar kafin network ya fara rawa, kasancewar inda suke sai a hankali dama. Wayar ya maida aljihu, sai kuma ya ajiye robar dan dawar ta ƙare duka. Jejin ya shiga bi da kallo irin na nazari, kafin ya bar wajen gaba ɗaya ya koma cikin tantin da ya fito ɗazun..........✍🏼 _Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* *_Typing📲_* *_🫧KIƊA A RUWA.....!!🫧_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _Chapter 3_ __________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳. IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link ɗin namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Bilyn Abdull tuni na antaya🏃 _____________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ____________________ ........Ɗagowa Imran dake zaune a study table yana duba wasu takardu yay yana kallonsa. Shi ko kallo ɗaya yay masa ya ɗauke kansa, zama yay a bakin gado ya jawo takalma daga ƙasan gadon, batare daya kalla Abbas dake cigaba da kallonsa ba har yanzu ya ce, “Zanje gida”.         “Gida kuma? Lafiya dai ko?”.    “Kawai zanje ne!”. Ya faɗa a taƙaice. Abbas yasan amsar ke nan, amma sai yay shiru yana kallonsa da nazari. Eh yasan in dai yace zai je gida akwai dalili, sannan sai ya tabbatar babu wani ƙalubale da zai bari mai girma a inda suken, amma haka kawai shi sai a yau sai yaji kamar tsoro ya tsarga masa akan tafiyar tasa, sai ya kasa cewa komai. Dai-dai Zak-Shadow dake haɗa bindiga shima ya ɗan ɗago ya kalla Imran ɗin, ganin yanda ya zuba masa idanu sai ya sake tsuƙe fuska ya ɗauke kansa. Imran yayi murmushi, dan yasan ya tsani kallo. Cike da tsokana ya ce, “Anya ba kewar Madam bace ke tsikarin ka?”.       Bai kula tsokanar da yake masa ba, kansa ya ɗan girgiza kawai yana zuwa gab da shi ya ciri ƙaramar takarda ya ɗauki pen yay gajeren rubutu. Batare da yayi magana ba kawai ya tura gabansa ya nufi barin wajen, sai kuma ya juyo yana kallonsa, cikin ɗage gira sama ya furta, “Ka rage sa ido Imran, idan nayi kewar laifi ne?”.     Imran yayi dariya da faɗin, “A'a bakai laifi ba MAZAJEN FAMA, maza jeka ka ɗabbaƙa sunna abinka”. “ALLAH ya shiryeka”. Cewar Zak-Shadow. Imran ya amsa da amin yana ɗaukar takardar ya fara dubawa.         _“Bana son kowa yasan na fita, kamar yanda na faɗa maka 2 days ne, Kar abar ƙofar yamma a buɗe, dan haɗarinta yafi na sauran ƙofofi ka sani. Imran idonka ya zama sosai akan yaran nan da dukkan Captains ɗin kowanne sansani, sannan duk motsin da bai muku ba na sani, komai ƙanƙantarsa._      Takardar Imran ya ajiye ya juya yana kallonsa da faɗin, “Babu damuwa in sha ALLAHU. Amma dan ALLAH ka biya ka sayo min kilishi da gyaɗa. Zan sa a kawo maka saƙo daga gida ka taho min da shi..”       Wani kallo ya ɗago ya zuba masa, Imran daya san ma'anar kallon sai ya kwashe da dariya. “Maida wuƙar, ba ɗan aike zan maidaka ba ai ALLAH nace”.        A karo na farko Zak-Shadow ya ɗan saki wani murmushi gefen baki yana ɗauke kansa da ɗan girgizawa. Shima Imran ɗin murmushin sa ƙara faɗaɗa yayi. Yana matuƙar son aminin nasa, kamar yanda kowa yasan shima Zak-Shadow na sonsa matuƙar so ma kuwa. Dan shi mutum ne mai ra'ayin riƙau, idan baya yinka, baya yinka kawai. Idan ya soka kuma, to da gaske son naka yake. Mutum ne tsayyaye akan ra'ayi, kuma ɗan kai tsaye, baya iya kawaici akan duk abinda bazaiyi ba kuma baya buƙata. Idan har yace maka (eh) to ‘eh’ ɗin ce koda za'a kashesa, idan kuma yace (a'a) tofa ‘a'a’ ɗin ce. Zak-Shadow yasha baƙar wahala a lokacin da suke yaran soji saboda wannan taurin kan nasa a hannun manyansu. Dan a shekararsu ta biyu da fara aiki har zaman prison na sojoji yayi na wata shida saboda wata tirjiya da yayi akan umarnin wani ogansu. An azabtar da shi matuƙar azabtarwa a lokacin, dan bayan ya fito ma mutane da yawa sunyi zaton bazai sake rayuwa mai tsaho ba, amma da yake rayuwa ta UBANGIJI ce sai gashi ya miƙe, miƙewar data zama sanadin jajircewarsa a yanzu. Dan azabar da suka bashi sai ta zama kamar sun sake busar masa da zuciya ne ta yanda bai jin shakkar tunkarar kowane irin haɗari na rayuwa, daga nan kuma nasarorinsa suka fara bayyana har zuwa matakin da yake a yau.          Shi Dodo ne a idon wanda bai san ainahin halinsa ba, saboda a kallon fuska kai tsaye zaka kirashi mugu ne. Baida fara'a, bai san wasa ba koda da aboki ne. Duk wanda kaga yace maka yaga yana dariya lallai ya kai ai masa barka. Yana magana idan yaso, idan kuma bai so ba zaku iya kwashe awanni tare koma sama da haka bakinsa bai furta komai ba na hira sai dai kaji yana karatun Alqur'ani. Dan kuwa yana da addini sosai, hakama ilimin addinin. Tabbas da ace bai zama soja ba sai dai a kirashi malami, a yana sojan ma yana koyar da sojoji ilimin addini, kuma yana musu majalisi, sannan yana cigaba da neman nashi ilimin shi kansa.       Sai dai sirrin da mutane basu sani a kansa ba sai shi amininsa da mahaifiyarsa shine haƙuri. Zak-Shadow mutum ne mai haƙuri kwarai da gaske. Sannan mutum ne mai adalci da son tsayawa akan gaskiya komai ɗacinta. Yana da tausayi matuƙa musamman akan mata da yara. Zai iya saida rayuwarsa akan su. Sannan yana da kishin addini da yankinsa. Dan shi kai tsaye ma zai ce maka yana fara jin kishin yankinsa ne kafin ƙasa gaba ɗaya....         “Ka dinga tunani kamar wani mace”.     Buɗaɗɗiyar muryarsa ta dawo da Imran daga doguwar tafiyar tunanin da yayi. Cikin ɗan sauke numfashi yace, “Ai tunaninka nake yi”.        “Rashin aikin yi ne yay maka yawa da har zaka zauna tunani na halan?”.     Cewar Zak-Shadow yana ficewa a tantin. Tashi Imran yay yabi bayansa. Kamar ɗazun yaran sojin suka shiga kamewa da sake nutsuwa waje guda. Yanzu kam sunfi ɗazun yawa. Da alama wasu dama suna a cikin tantunan ne shiyyasa. Inda yake zaman yin alwala ya nufa, hakan ya tabbatar musu lokacin la'asar yayi, ruwa aka kawo masa shi da Imran, suma suka shiga haramar yin tasu musulman ciki kenan. Wanda ba musulman ba kuma suka amshi duty ɗin zagaye wajan. Koda suka idar da sallar shi da Imran sansanin suka bari gaba ɗaya, sun jima kafin can su dawo suna hirarsu. Wajen wani ɗan bukkan kara dake gefe suka nufa, koda ya buɗe buhun da akayi labule a bukkar wasu irin garƙama-garƙaman karnuka ne marasa ƙyawun gani, sai dai kallo ɗaya kai musu dole ne hankalinka ya tashi, dan babu tantama waɗan nan idan suka kama mutum sai kufan jinin jikinsa amma ko ƙashi bazasu bari ba, dan marabarsu da zakuna ƙalilanne. Aiko suna ganinsa suka fara zallo da haushi kamar wanda suke gaishe shi.     A mamaki na sai naga ya ɗaga musu hannu yana faɗin, “Good Afternoon my Boys”.        Wani haushin suka ƙara yi a tare kamar masu amsa masa. Imran yay dariya da faɗin, “Kama yaran nan naka training mai wahalar gaske. Idan suna wani abun sai ka rantse mutane ne”.      Ƙaramin Murmushi Zak-Shadow yayi da ɗan taɓe baki. Idan yayi murmushi ƙyau yake masa, maybe shiyyasa baya son yi. Sun jima a wajen karnukan sannan suka fito, lokacin duhun magriba yayi. Yanzu kam sojoji ne sosai a camp ɗin, gaba ɗaya sun fito daga tantunansu, ashe a ɗazun wasu basa wajen shiyyasa, wasu kuma na barci, dan maimakon barcin dare su na rana sukeyi saboda tsaro. Tunda Imran da Zak-Shadow suka fito gaba ɗaya wajen yay tsitt kamar an musu tsawa, kowa ya nutsu. Kallo ya bisu da shi kaf ɗinsu, a ƙalla sun kai su ɗari, dan wasu basa a cikin sansanin a yanzu suna kan aiki a cikin jejin tako wace kusurwa. Wanda ke nan tare da shi bazasu wuce ɗari ba. Wucesu yay ya zauna kan dutsin da yake zaman yin alwala akoda yaushe, ai da sauri wani ya kawo masa ruwa dan in dai kaga ya zauna a wajen alwala zai yi. Daga nan kowa ne ya fara ƙoƙarin yin alwalar, sai wanda ba musulmai ba suka sake amsar dutyn zama garkuwa a yanzu ma kamar dai ɗazun. Sanin yau zai bar jejin kuma baya son su fahimta sai ya ce yanzu ma Imran ya jasu salla. Hakan baisa sun zargi wani abu ba suma, dan yana yin hakan a kowane lokaci, ba oga Imran ba har a cikinsu yaran masu addinin kan jasu salla, duk da dai duk wanda ke a ƙarƙashin Zak-Shadow duk iskancinka da sakacinka ga ibada wlhy sai ya saita maka haukan kanka. Dan in har kana cikin tawagarsa bakai ba wasa da salla, ba kai ba shaye-shaye koda na sigari ne kawai, bakai ba zama da jahilci dole ka cigaba da neman ilimin addini, shiyyasa ma ya saka musu ranakun karatu, bashi kuma kaɗai bane malamin harda wasu a cikin yaran masu ilimi na koyarwa suma, sai dai in ana kan matsannacin yaƙi ne. Hakan yasa Alhamdullah hatta wanda ba musulmai ba a cikinsu zaka gansu a nutse. Dan in ma kace zaka bijire kayi jikinka ne zai gaya maka a hannunsa..      Bayan sunyi sallar magriba Imran yay musu nasiha kamar yanda suka saba, har zuwa lokacin isha'i. Bayan an idar kowa ya miƙe suka kasu group-group dan kowa da abokansa da kuma abokan maganarsa suka kunna wuta suna hira, wasu na cin abinci. A lokacin ne Zak-Shadow ya sulale ya bar jejin, barin da da yasan sakamakon da zai so da shi da bazai yi ba. Dan kuwa tabbas wannan barin shine mafarin wata babbar ƙaddara da alkalami ya jima da rubutata a cikin rayuwarsa tun yana cikin Ummiensa.........✍🏼    *_Wace ƙaddara ce wannan? Mizai faru? Mike shirin faruwa ne da Zak-Shadow 😭. Ya labarin mace mai ciki kuma? Wace rawa zata taka mana a wannan labarin?. Amsar ku na cikin labarin KIƊA A RUWA MAI MAGANIN DODO. Kada ku bari a baku labari. Dan ni kaina Bilyn ku labarin nan tsumani yake yi💃💃💃._* _Zaku sameshi a waɗan nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER🇳🇪- (500 Fcfa)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* _Shaidar biya👇_ *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: 👇_* *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number 👇_* *+234 805 568 7449* *_Telegram Number👇_* *+234 903 234 5899* Ku ci gaba da ziyartar wannan shafin na mu ci gaba da kawo muku update kullum i marubuciyar ta saki.