⚡ _Heedayah_ ⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 All thanks to Allah SWT for the privilege to start this book.... My special greetings to my lovely Mum Hajiya Hajarah, and all my small mums😍 my siblings and cousins ain't left behind too, ina son ku gaba daya.... My Isiaka Safia I greet u too, and my lovely fans that have waited so long for Khaleesat Haiydar... ina maku barka da sllh, Allah ya amshi ibadunmu baki daya, ga *Heedayah* I know u all will love it, coz I Khaleesat is already in love with it 😊 No disappoinment In sha Allah 😉 1..... Wani d'an matsakaicin daki ne da aka xagaye da tsadaddun labulaye, dakin na dauke da katifa babba, sai kayan kallo daga gefe, sai cushion tsadadde guda daya, Dattijuwar da baxata haura hamsin da biyar ba dake xaune dakin tayi tagumi tace "Toh mu dai baxa mu gaji da addu'a ba, Allah ubangiji ya bata lafiya, watan gobe kenan dai ake sa ran komai xai yi dai dai koh?" Matashiyar matar dake gefenta ta d'an yi murmushi tace "Haka dai likitocin suka ce in sha Allah, sai dai kinsan kana naka ne Allah na nasa, amma wnn aikin shine na karshe da xa ayi mata idan Allah ya yrda, sai kuma fatan Allah ya sa a dace" Yakumbo tace "In sha Allahu xa a dace, abinda kullum gaya ma Allah muke, kaf dangi bbu mai irin laluran nan balle ace ko gado ne, sam bbu shi a danginmu gaba daya, ko ke akwai a naku??" Dariya matar tayi tace "A'a Yakumbo" Yakumbo tace "Atoh, Allah dai ya raba bawa da wahala ke ma kuma Allah ya sauke ki lafiya, Indiyan xa a kara komawa kenan ayi aikin?" Matar tace "Ameen, ehh can xa mu je" Yakumbo tace "Toh in sha Allahu karshen wahalan kenan" Matar tace "Allah ya sa" agogo Yakumbo ta kalla tace "Anya tafiyar nan taku na nan yau kuwa Amina, shiru shiru har yanxu Umar din bai xo ba" Amina ta kalli agogon ita ma tace "Kuma na kirasa daxu ban samesa ba, ina jin meeting suka shiga, kila sai gobe dama na cire rai yau" Yakumbo tace "Atoh, ku bari kawai sai gobe yamma yayi, sai kace wa inda ake kora, ga hanyar nan da ba kyau gari ya xama abinda ya xama mucuta ta ko ina...." Amina tace "Haka ne" Yakumbo tace "Naji wai matar Salihu na ta neman ki da fada ko? Kar ki kuskura ki kulata gayyar mayu ne, har ita Asama'un ma ki bar kulawa duk haushin ki suke ji suna ganin kin fi su walawa gidan miji, ba su san Allah ne ya baki ba" Amina tayi murmushi bata ce komai ba, Yakumbo ta kara da cewa "Kuma wai sai kiyi ta boye yarinya kar su gani, wai haka?" Amina ta kalleta tace "Aa ba gaskiya bane, ke kanki shaida ce Yakumbo tun tana yar yarinya ba a fiye fito da ita cikin jama'ah ba, a ko da yaushe tana daki tare da ni ko mai kula da ita, ko malamarta, har yau 'yan anguwa basu wani san kalan Heedayah ba, da kyar ki xo gidan ki ganta a parlor, to sau tari idan anyi baki har su tafi ma baxa su ganta ba shine ake ganin kamar boye ta muke kar a ganta" Yakumbo tace "Toh ai gwara haka, haka kawai baka san bakin wani ba, ayi ta sa ma yarinya baki, gaskiya kun yi dubara, ki rabu da su suce duk abinda xa su ce, lafiyan yarinya shine gaba kan komai" Amina dai bata ce komai ba, Yakumbo tace "Har bokon ma a gida ake mata kenan?" Amina tace "Ehh har islamiyya" Yakumbo tace "To madalla, ae gwara hakan, Ke leko yar mutane naji shirun yyi yawa, Allah ya sa dai gantalallun yaran makotan nan nawa ba shigowa suka yi suka yi waje da ita ba" Da sauri Amina ta mike tana leka tsakar gidan tace "Heedayah??" Jin shiru ta fito tsakar gidan, Katon Babyn robanta da take combing gashinta kadai ne kan tabarma da comb din sai hularta amma babu ita, Yakumbo ta mike tace "Ni da nasan sai sun shigo sun ja ta, Amma wa ennan yara iyayensu sun haifi jaraba kawai, yara kauyawa bbu kamun kai kawai malam..." Dawowa Amina tayi dakin ta dau Hijab dinta sannan ta fita waje, Yakumbo na biye da ita tana cewa "Ni dai Allah ka rufa min asiri ba rafi suka ja ta suka kai ta ba in shiga uku, yarinya dai ba ido ba, daga kawo min ziyara shaidan ya fake ta nan yayi abinda ya ga dama tawa ta sameni ina xaman xamana...." Tun Mahaifiyar Heedayah na daurewa ana shiga bukkokin makota duba Heedayah a kauyen har taji hankalinta ya fara tashi sosai ganin babu alamar yar tata.... Yakumbo dai sai salati take xabgawa a rikice tana yafa gyalen da ya ki xama tana cewa "Toh me xance ma kanina Umaru jama'ah?? Ina xan ce yar sa ta shiga?" Wata mata ce tace "Daxu fa naga sun yi hanyar kasuwa da su Hinde da Bibalo, har da fatu, kusan dai su shidda suna rike da hannun ita yarinyar" Yakumbo ta saki salati tace "Toh kuwa wllh Ubanta a Habuja yake kuma duk iyayensu xae sa a daure idan abu ya samu yar sa, ita fa kadai garesa sae ynxu da uwar ke da sabon ciki, shekararta goma sha biyu, kuma ba idanuwa gareta ba, to a kan me gantalallun yara xasu ja ta su tafi da ita kasuwa, uwayensu xa su siya mata a kasuwar? Tun shekaranjiya da suka xo kauyen nn nake ja ma ja'iran yaran nan kunne ganin ynda suke makale mata har da masu wasa da gashin kanta nake ce masu su fita harkarta, ita dai ba fuskarsu take gani ba balle ace, to wannan wani irin bala'i ne, hanyar kasuwan nan da babu kyau sace sace yyi yawa, haba jama'ah??" Tuni duk aka watse aka dau hanyar kasuwa aka bar Yakumbo tsaye ita kadai tana kumfar baki, can dai ta bi su da sauri ganin sun yi nisa. Yara ne duk mata kusan su biyar karkashin bishiyar mangwaro sai mata biyu dake saman bishiyar suna tsinkar nunannun mango suna jefowa kasa matan dake kasa suna kwasa suna xubawa a karamin buhu, wata yarinya ce warce duk baxata wuce sa'aninsu ba tana durkushe hannunta rike da mango tana sha, daya hannunta kuma na rike da rigar fatuu don ita ke mata jagora, fara ce sosai, kana ganinta kasan jinin Fulani ce don gashinta dake bude ko hula babu ma ya shaida haka, idanuwanta farare ne kal kamar Madara tana kifta su a hankali kai kace ras take ganin kowa a wajen, sai dai babu abinda take gani banda duhu, wajen duk ya kauraye da surutun yaran dake tsinkar mangwaro xa su kai kasuwa su siyar, wata bakar mota ce ta ja tayi parking a wajen, duk suka juya yaran, lkci daya kattin maxaje biyu suka fito motar da sauri, gudu yaran suka yi har da Fatuu da ta warce rigarta daga hannun Heedayah, na saman bishiyar ma duk suka diro suka ruga aguje, Heedayah ta saki mango din hannunta ta dinga waige waige a tsorace, maxan suka bi bayan yaran suka samu kamo uku daga cikinsu, Heedayah ta mike ita ma suka daga ta suka saka cikin motar, kan kace me driver ya ja motar da gudu suka bar wajen. Gaba daya ihu yaran ke yi cikin motar har da Heedayah dake ta kwala ma Mahaifiyarta kira tana cewa "Ammina...." Wanda ke xaune a baya ya ciro bindiga yana nuna masu da jajayen idonsa fuskarsa a murtuke ya daura hannu a lebbansa alamar su yi shiru, lkci daya su ladi duk suka yi shiru sai rawa jikinsu yake, Zulai har da sakin fitsari a gun, Heedayah ce kadai bata fasa ihun da take ba, Mutumin ya shake wuyarta yana nuna mata bindigar yace "Ohh ke baxa ki rufe mana baki ba koh?" Jikin Ladi na 6ari tace "Bata gani" Mutumin ya shiga kare mata kallo sannan ya gyada kai yace "Kuma duk yanxu xaku daina gani" yana fadin haka duk ya rufe ma sauran ido da kyalle, Heedayah da ta ki yin shiru kuma ya dinga buge mata baki yana marinta, hakan kuma bai hanata ci gaba da ihu ba tana lalube laluben inda xata fita, daga karshe jin taki shiru wanda ke xaune gaba ya miko masa wani leda yace "Bada mata a fuska" hakan kuwa aka yi, nan da nan kuwa ko ina yyi tsit a motar, a hankali Heedayah ta fada jikinsu Ladi. A hanya mutan kauyen suka hadu da su Hinde da sauran matan da suka samu guduwa, Nan su Hinde na kuka da ihu suka fada masu abinda ya faru, da hanxari wasu mata biyu suka rike Ammin Heedayah dake neman sulalewa nan kasa, ta fada jikinsu a sume. Yakumbo ta saki wani salati da karfi ko ina na jikinta na rawa, cikin kidimewa ta dinga cewa "Ai shkkn tawa ta kare, na shiga uku na lalace, kar ace min yan kinnaping ne ko yan yankan kai suka dauke Heedayah, me xance ma kanina jama'ah???" Ta fashe da matsananin kuka xata fadi kasa ita ma aka rikota, ana ta salati iyayen sauran yaran da aka dauke ma suka dinga kuka suka bi bayan maxan da suka nufi gun da abun ya faru. Tafiyar kusan awa daya mutanen suka yi da su Heedayah a mota kafin su fita hanyar kauyen gaba daya kasancewar hanyar bbu kyau, sannan suka yi parking gefen jaji don tafiyar minti ashirin kawai xasu kara su isa wani checking point a gaba, wasu mutane ne suka fito daga dajin bbu kyan gani kana ganinsu kaga axxalumai, Mutumin dake bayan mota ya sakko da sauri ya fiddo su Ladi aka tasa keyansu cikin dajin bayan an kunce kyallen idonsu, daya daga busassun mutanen da suka fito daga dajin na kallon Heedayah yace "Wannan fa" Mutumin na kokarin fiddota yace "Daukarta xa ku yi, xata daga mana hankali muka badata da powder" busasshen Mutumin yace "Ai baxai yiwu bane, wnn uban tafiya xaka ce a dauketa, ku kashe ta kawai a jefar a nan, mu yi wucewar mu" A fusace Mutumin yace "Mu kasheta bayan yara goma muka yi alkawari yau, duk bbu sa'a sannan mun samu yara hudu kace mu kashe daya.... Kuma dole dai ku dauketa don makauniya ce wai" Yana fadin haka ya direta kasa ya shige motar driver ya ja suka bar gun a guje" tsaki Mutumin yyi ya dau Heedayah kai kace dabba ce irin daukan da yyi mata suka shige dajin dake da manyan torns, ga duhu don Magrib ya gabato...... ⚡ _Heedayah_ ⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 2...... Bayan tafiya that seems endless da kafa suka bullo ta wani titi inda wata mota ke jiransu, nan suka shiga aka ci gaba da tafiya, gaba daya yaran kana ganinsu kasan sun gaji sosai, Heedayah dai har lkcn dabata farka ba, sai kusan goma suka iso wani karamin Uncompleted building, mata da maza ne sun kusa 6 yashe a wani daki da bbu hasken kirki sbda karamin window ne a dakin daga can sama, Nan aka tura su ladi da Heedayah da ta fadi kasa ko motsi bata yi, Wani wanda da alamar shine babba cikin yan bindigan dake wajen yana rike da bindigarsa ya kalli wanda ke gadin mutanen shi ma da bindigarsa a hannu yace "Ya ku ka yi da mutanan wancan Mutumin a waya?" Ya kalli wanda yake nuna masa yace "Ae kawai bbu alamar xasu bada kudaden nan, sun ma daina daga kiran" Bai rufe baki ba ogan nasu ya harbe Mutumin da ake magana a kai, hakan ya kidimar da mutanen da ke xaxxaune gun, barin matan, sound din harbin ya farkar da Heedayah ta fasa wani ihu tana kokarin mikewa tsaye wata mace dake xaune kusa da ita ta jawota da sauri ta rufe bakinta a jikinta, Ogan ya dinga ma Heedayah wani kallo sannan ya kalli Mutumin gefensa yace "Is she among the kidnapped?" Mutumin ya girgixa kai da sauri yace "Aa yan kauye ne, su hudu muka dauko a kauyen jiya, ba kace ana son body parts ba" Mutumin ya karasa gun Heedayah ya dagota daga jikin matar yana kare mata kallo da kyau, ya girgixa kai yace "Yar wani babba ce wnn, it will have been good she's kidnapped, but anyway, ana bukatan parts din ma" Yana fadin haka ya turata ta fadi kasa, janye gawar Mutumin ogan yasa aka yi aka fitar waje, sannan duk Yan bindigan suka fita aka garkame kofar. Ladi ta kankame Zulai ta dinga rusa kuka tana kiran sunan Babarta, wata mata ta mike ta nufesu ita ma tana hawayen, nan ta shiga lallashin su tana kwantar masu da hankali da sauran mutanen wajen, kai kana gani kasan duk karfin halin lallashin nasu suke yi. Matar dake kusa da Heedayah sai kokarin daga Heedayah take ganin kamar suma tayi..... Sai kusan asuba Heedayah ta kuma farkawa, ta mike xaune da kyar tana laluban inda take tace "Ammi??" Jin shiru bbu muryar Mahaifiyarta kamar ko da yaushe sai mutane a kwance tana ta6a su ta janye hannunta da sauri, muryar Zulai taji a hankali tace "Kiyi shiru yar birni yan yankan kai ne suka sace mu, kiyi shiru kar su shigo" Tsit Heedayah tayi da farko, sai kuma ta fasa ihu tana kwala kiran Ammi, wani da ke sallah ya sallame ya taho kusa da ita da sauri gudun kar mutanen su shigo don babu abinda suka tsana irin a dinga masu ihu, karamin aikinsu ne su kasheta in har suka shigo, lallashinta ya dinga yi yana ce mata xata koma gida in sha Allah, ita kuwa sai cewa take "Aa ni a kai ni gun Ammina da Abbana yanxu...." Nan dai ta tada wa enda suka samu bacci aka dinga hiaikin lallashinta a d'an dakin, Cikin kuka take ce masu xata yi fitsari, aka nuna mata wani karamin kofa dake cikin dakin, Ladi tace "Yo ai bata gani" furucin Ladi ya sa duk aka tsaya kallon Heedayah, wata mata ta mike a sanyaye ta kama hannunta ta kai ta bayin. Har aka yi asuba gari ya waye Heedayah shesshekar kuka take a hankali, can ya ta6a matar dake kusa da ita cikin kuka tace "Aunty yunwa nake ji" Matar ta kuma jawota jikinta cikin sanyin murya tace "Yanxu xa a kawo abincin idan Allah ya yrda" sai karfe goma aka bude kofar dakin, duk kowa yyi tsuru tsuru ana addu'a a xuciya, Mutane uku suka shigo ko wanne ya saita bindiga, kamar ko da yaushe facemask na fuskarsu, sai wani mutum da shi ma fuskar tasa ke a rufe dake rike da babban leda me dauke da kananun bread, daga inda yake tsaye ya dinga jefa ma kowa da ledan pure wata daya, ya jefa ma Heedayah dake ta bin duk inda ta ji sound din faduwar bread da ido, Zulai ta mike xata dauka ta bata ya mata wani mugun kallo ta cikin mask din fuskarsa da ke nuna idonsa kadai, jiki na rawa tace "Yo ai bata gani ne" kallon Heedayah ya sake yi, gashi dai fararen idanuwanta a kansa kuma ace bata gani, wani tsawa ya mata yace "Sa hannunki ki dauka da kanki" Heedayah da tayi mugun tsorata ta fara laluben inda xata ga bread din amma bata gani ba don bayanta yake, karasowa yyi cikin dakin bindigar sa a hannu, duk occupant din dakin suka rike numfashi ganin ya nufo Heedayah da ta hakura da laluben inda bread yake ta sunkuyar da kai, dukawa yyi ya dau bread din ya mika mata yace amsa, tana laluban inda yake, ya kamo hannunta ya sa mata bread din, tana kallon direction din da ta ji hannunsa idanuwanta cike da kwalla a hankali tace "Thank you" ajiye mata ledan ruwa daya yyi ya bar sauran bread din ya mike ya fice daga dakin sauran yan uwansa suka bi sa sannan suka garkame kofar, matar dake kusa da Heedayah ta rungumota hawaye na zuba idonta ita ma, ta amshi bread din ta kunce mata ledan ta mika mata. Zulai da Ladi dai tuni suka handame bread din suna zare ido. Ammi ce kwance gadon asibiti da drip a hannunta, da ido kawai take bin mutanen dake cikin ward din, she looks so sick, Yakumbo na can wani gefe xaune kan kujera tayi tagumi idanuwanta duk a kumbure, wani matsanancin kuka ta saki tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, Allah kai kasan yanda xaka yi da axxaluman bayin nan naka, Ya Allah ka rufa min asiri 'yar Dan uwana ta dawo cikin koshin lafiya, wllh Ita kenan garemu..." Kanwar Ammi dake Ward din ita ma ta fashe da kuka sosai, haka ma sauran mutanen ciki, Mahaifin Heedayah dai na xaune kusa da Ammi yana rike da hannunta, shi ma ko kadan tashin hankali bai boyu a fuskarsa ba, kawai ta maxa yake, Yakumbo ta mike tana hade hanya ta fice ward din kamar xata shide don kuka tana cewa "Shkkn ni dai tamu ta kare, ita kenan gare d'an uwana fa, na cikin ma anyi barinsa sbda wnn tashin hankali, wannan wani irin xalunci ne ake yi haka a duniya ni Khadijah, Allah ka tsine ma duk wanda ya raba mu da Heedayah, Allah ka isar mana, ka dawo mana da ita cikin aminci...." Kanin Abban Heedayah ya mike ya bi bayanta shi ma dai trying hard to control his tears. Kusan la'asar aka bude kofan dakin da su Heedayah ke ciki, ja baya kowa ya dinga yi a tsorace, Heedayah ta mike xaune daga kwancen da take tana kallon inda taji karan budewar kofa, su hudu suka shigo, ko wanne da bindiga, Ogansu na nuna wani matashi yace "Kai taso xaman ka ya xo karshe a nan, Yan uwanka sun yi abinda ake bukata" tashi yyi da sauri yana hamdala sauran mutanen wajen sai hawaye, haka aka fitar da shi, ogan na nuna wani a cikin sauran yace "Kai yan uwanka na raina mana hankali, xuwa gobe idan basu yi complying ba xa mu aika ka barzahu kowa ya huta...." Yana fadin haka ya kalli wanda ke gefensa yace "Cikin yaran nan ka fito da guda daya a cire abinda ake bukata, me siya na kan hanya anjima, gobe da yamma ma akwai me xuwa zai siya" yana fadin haka ya fice, sauran suka bi bayansa, Mutumin daxu da ya kawo masu bredi ne kawai bai fita ba sai wanda aka sa ya dauko yarinya daya ya dinga bin yaran da kallo, Mutumi dai mai bredi ya nufi Zulai ya dagata ya fice tana ihu tana sakar masa fitsari, d'an uwansa ya bi bayansa ya garkame kofar, bbu abinda mutanen cikin dakin ke yi banda hawayen tashin hankali, Heedayah ta dinga waige waige jin ihun Zulai, matar dake kusa da ita ta rungume ta tana kuka sosai, cikin kuka ita ma tace "Aunty ina xa su kai ta??" Matar dai bata ce mata komai ba sai kuka. Washegari har kusan yamma basu samu an kawo masu bredin ma da ake kawo masu ba, Heedayah ta fada ma matar kusa da ita tana jin yunwa ya fi a kirga tun matar na ce mata xa a kawo abinci har ta gaji ita ma tayi shiru, kusan la'asar aka bude kofar wajen, mutumin da ke basu bread ne ya shigo da buhun bread da ruwa, nan duk ya jefa ma kowa, har bread din ya kare amma bai ba Heedayah ba, matar dake kusa da ita har xata yankar mata nata, Mutumin ya karasa ya daga Heedayah cikin kaushin murya yace "Mu je ki amshi naki" cikin rawan baki matar tace "A'a ko in yankar mata a nawa ba cinyewa xan iya yi ba, baxan ma ci ba...." Wani mugun kallo ya dinga mata hakan yasa tayi tsit jikinta na rawa, juyawwa yyi ya nufi kofa da Heedayah dake ihu tana kiran Ammi tana gatsa masa cixo a hannu, bayan ya fita ya rufe kofar, ya toshe bakinta yace "Ke xan halbe ki yanxu idan baki rufe min baki ba" Tsit tayi ko ina na jikinta na rawa tana kallonsa kamar dai tana ganin fuskarsa, xagawa yyi ya canxa hanya yanda sauran yan uwansa dake xaune a baya baxa su gansa ba, cikin hanxari ya karasa bayan wani karamin bukka da suke ajiye makamansu ya ajiyeta bayan Bukkar ya durkusa yana kallonta yace "You don't move, ki tsaya nan har in dawo idan ba haka ba, I have gun...." Kai kawai take gyada masa a tsorace tana komawa baya, ya mike da sauri ya koma inda Yan uwansa ke xaxxaune ana xuke xuke ana buga karta, Makullin mashin dake rataye jikin bishiya ya dauka yace "Xan je amso ruwa in dawo yanxu...." Wani daga cikinsu ya kallesa yace "Oga na hanya da customer fa" yace "Ehh yanxu xan dawo ai" har ya nufi gun da suke ajiye babur dinsu sai kuma ya juya da sauri ya sake komawa dakin da ya dauko Heedayah ya bude ya shiga yana masu wani kallo yace "Ko da an tambayi yarinyar nan kuce ta mutu an fitar da ita...." Tsuru tsuru suka yi suna kallonsa ya juya ya fita ya kulle kofar. Daga haka ya nufi machine ya hau ya tada, a guje ya bar wajen, dai dai inda ya ajiye Heedayah ya tsaya, sai xare ido take tana kalle kalle, ya daga ta ya daura gaban machine din yyi speed off, gudu kawai yake a dajin kamar mai race din motorcycle, tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi suka shigo cikin gari sosai, a hankali yake tafiya yana kalle kallen jama'ah dake ta kokarin rufe wajajen sana'arsu kasancewar Magrib ya gabato, sai kuma ya tsayar da machine din ya kashe, sauke Heedayah da tashin ta bacci kenan yyi, ya ajiyeta nan gefen hanya yana kallonta, laluba wajen ta shiga yi, jin ya sake kunna bike din da sauri tace "Noo, Are you leaving me??" juyar da Machine dinsa yyi ya dau hanyar da ya fito with speed, ta fashe da kuka sosai tace "Noo" ⚡ _Heedayah_ ⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 3..... Heedayah ta fi minti biyar a tsaye tana Shesshekar kuka, jin bbu alamar xai dawo ta fara tafiya a hankali tana yi ma kanta jagora da hannuwanta biyu, da tayi tafiya kadan sai ta tsaya, ihun da taji aka yi wajen ya sa ta tsaya a mugun tsorace, ji tayi kamar an hankadata da katon abu ta fadi kasa, tun tana jin surutun jama'an wajen sama sama har ta daina ji kwata kwata. A hankali Heedayah ta bude ido tana laluba inda take kwance, muryar namiji taji a gefenta yana cewa "Alhamdulillah she is back (Ta farfado....)" Ya kamo hannunta yana mata sannu murmushi dauke fuskarsa, kanta da yyi mata nauyi kawai take gyadawa tana kokarin mikewa xaune, ya komar da ita ya kwantar yace "A'a bari likita ya xo ya duba ki, bari in kirasa, ina xuwa ynxu" ita dai kai kawai take gyadawa, ba a dau lkci ba sai ga mutumin ya dawo da likita, directly Heedayah ke kallon fuskar likitan, ya sakar mata lallausan murmushi wanda bata san ma yana yi ba, likitan ya xaunar da ita ya dafa goshinta yace "Ya jikin baby girl?" Kifta ido ta shiga yi tace "Where am I? (Ina ne nan?)" Yana murmurshi yace "Hospital dear, fatan dai babu inda yake maki ciwo" kanta ta nuna masa, yace "Xai daina in sha Allah, xa a baki magani yanxu" shi dai wanda ya kirawo likitan kallonsu kawai yake, A hankali tace "Xan yi fitsari" likitan ya saukar da ita kasa, yana nuna mata kofar bandaki, hannunsa ta kama, yace "Xa ki iya dear, walk gently now (Kiyi tafiya a hankali....)" kin motsawa tayi, sai kuma a hankali tace "I can't see (Bana gani)" da mamaki likitan da Mutumin da ya kawo ta asibitin ke kallonta, likitan yace "Why? is the eyes paining you? Idanuwan suna maki ciwo ne" Ta girgixa masa kai yace "Toh yi tafiyar ki da kanki" ta rike hannunsa gam kamar xata yi kuka tace "Ae ni bana ganin hanyan" sosai hankalin likitan ya tashi, haka zalika Mutumin dake Ward din da ya mike shima yana kallonta, don gaba daya tunaninsu a lkcn ta dalilin accident din ne vision dinta ya samu matsala, Banda innalillahi wa Inna ilaihi raji'un bbu abinda Mutumin ke furtawa yana kallon Heedayah. Likitoci sun fi biyar a kan Heedayah, all trying to figure out where the problem is, ko wannensu na kokarin gano inda matsalar take amma abu ya ci tura, ita dai sai bin duk inda ta ji motsi take da manyan idanuwanta, duk da ba ganinsu take ba, daga karshe dai aka ba Mutumin da ya kawota shawara kawai ya kai ta asibitin ido, ba karamin tashi hankalin wannan mutumin yyi ba, haka dai ya biya bill din asibitin ya dau Heedayah xuwa asibitin ido dake nan cikin garin kano. Dai dai lkcn da suka shiga haraban asibitin motar optician din dake duba Heedayah tun da aka haifeta har kawo lkcn da aka yi referring dinsu india kuma na fita daga asibitin. Mutumin dake rike da hannun Heedayah bayan ya sauketa daga motar ya duka dai dai fuskarta cike da damuwa yace "Daga yaushe kike daina gani Little girl? What was the last thing u saw? Meye abu na karshe da kika gani?" Tayi shiru sai kuma tace "Nima ban sani ba" Damuwa ne sosai fuskarsa, yace "Toh daga ina kike jiya da magariba kuma ina xa ki? Where are ur parents? Ina iyayen ki" Shiru tayi, staring at him kamar tana ganinsa, nan ya shiga tantaman ganin da tace bata yi, ganin yanda take masa kallon cikin ido ya kai yatsunsa har kusa da idonta yaga bata rufe ba har sai da ya taba lashes dinta, kikkifta idon ta shiga yi, yace "ki min magana, Where are ur parent? Ina iyayenki" Ta girgixa kai tace "I don't know, (Nima ban sani ba)" da mamaki yace "Baki san inda iyayenki suke ba, ina xa ki jiya?" Ta fashe da kuka tace "Nima ban sani ba, kawai an saka ni a mota aka wuce da ni, sai na ji an sake hawa da ni bicycle kuma ynxu ban san inda aka kawo ni aka ajiye ni ba" rasa abun cewa yyi yana kallonta, can dai yace "Ya sunan garin ku?" Tace "Abuja" ya xaro ido ganin dai a garin kano suke ynxu, yace "Ya sunan baban ki?" Tace "Abba" yace "Abba??? Mamarki fa?" Cikin rawar murya tace "Ammi" Innalillahi ya dinga nanatawa a ransa, sai kuma yace "Abuja ya sunan anguwan ku?" Tace "Abuja ne" mikewa yyi just as confused as she is, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna goma na safe, yana rike da hannunta yana mata jagora suka shiga asibitin, Ba su suka fito ba sai kusan Azhar after series of Diagnosis da ya tabbatar da she was born with the blindness, a haka aka haifeta, kuma tana stage din operation din karshe kenan wanda xa ayi mata idan ba ayi nasara ba she will remain blind till the end (Xata xauna a makauniyar ta har karshe...) Alhaji Ahmad na rike da hannun Heedayah xuwa gun motarsa a haraban asibitin, bai ta6a shiga rudani irin na ranan ba, to ina xai kai wannan yar baiwar Allahn, kara kallonta yyi yaga bata wuce autarsa Rabi'ah ba, yanxu ina xai samo iyayenta ko wani wanda ya santa??? Yanke shawarar kai ta police station kawai yayi, yasan su xa su san yanda xa su yi da ita, driving kawai yake absentmindedly ya ji Heedayah tace "Abba, yunwa nake ji" ya d'an kalleta yana ci gaba da tukinsa yace "Me xa ki ci?" Tace "Shayi da bredi da kwai" sake kallonta yyi sannan ya dauke kai, Mintuna kadan ya rage ya isa nearest Police station, sbda yunwan da tace tana ji ya dau wata hanyar daban xuwa wani restaurant, abinda ta ce take so ya sa a kawo mata, ya tabbatar shayin ba xafi sosai sannan ya bude mata bread din da kwai ya mika mata, ganin yanda take ta lalube lalube kar ta kwa6ar da shayin ya mike ya koma kusa da ita, feeding dinta yayi har ta ce ta koshi, Banda kallonta bbu abinda yake yi cike da tausayinta, Bai taba ganin irin haka shi dai ba, yar karamar yarinya da makanta, tace "Abba..." Ya shafa kanta yace "Daughter" murmushinta me kyau tayi tace "Thank you" Bai ce komai ba, Amma naxari me iri iri yake yi a ransa, bayan few seconds ya kalleta yace "Ya sunanki?" Tace "Heedayah" Ya lumshe ido ya bude yace "Heedayah baki san anguwan ku a Abuja ba? Ki tuna da kyau ki gaya min daughter" Tace "Abuja ne gidanmu" ya girgixa kai ya mike yace "Tashi" tashi tayi ya kama hannunta kasancewar ya biya bill din suka fita xuwa gun motarsa, bayan sun bar Restaurant din, ya dau hanyar police station, Yana rike da ita suka shiga ciki, Bai bata lkci ba bayan yayi report ya bar Heedayah tare da su don yana da meeting da xai shiga karfe daya kuma a ranan yake son barin garin kano, sai dai har ya isa inda xa shi hankalinsa ya ki kwanciya, gaba daya ya rasa sukuni.... Washegari karfe takwas a police station yayi ma Alhaji Ahmad to be sure an samu iyayen Heedayah duk da yasan da kyar hakan ya faru a rana daya kawai, Bayan sun gaisa da policemen dake wajen suka sanar masa an kai ta orphanage for the meantime, shiru yyi na few seconds kafin yace "Shikenan, nagode...." Wani police officer yace "We will try our best in sha Allah, an kuma riga da an fara broadcasting tun jiya, so hopefully she will get back to her parent soon, (xa mu yi bakin kokarin mu na ganin ta koma ga iyayenta)" Alhaji Ahmad yace "Allah ya sa hakan" Sallama yyi masu ya bar station din. Ammi dake xaune saman gado a dakin asibiti da take ta kai hannunta xuwa na Mahaifin Heedayah dake xaune gefenta sai dai yyi nisa tunanin da yake, juyawa yyi ya kalleta, hawayen da ke gefen idonta ya gangaro cikin sanyin murya tace "Muhammad pls let nothing happen to my daughter, plss nothing shud happen to Heedayah, (Kada wani abu ya sami Heedayah) ku dawo min da yarinya ta" Uncontrollably ta fara kuka, tun xuwansu asibiti kwana biyu kenan sai yau tayi magana, Alhaji Muhd ya na rike da hannunta trying his best to be strong yace "Nothing dear, I mean nothing will happen to our daughter, (Babu abinda xai sameta) in sha Allah, zata dawo garemu soon da izinin Allah, hukuma na bakin kokarinsu, ki kwantar da hankali don Allah" Kuka kawai take bata ce komai ba, she looks so weak, ya sake hannunta ya fita don kiran likita. Da yammacin ranan Alhaji Ahmad ya gama shirin komawa kaduna, sai da ya bar gida sannan yyi deciding kafin ya tafi ya fara xuwa orphanage da yan sandan suka ce masa an kai Heedayah, Bai yi wani wahalan shiga gidan marayun ba bayan ya nuna Identity dinsa, ya dinga bin yaran dake wasa a waje da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kan Heedayah dake rakube can gefe ita kadai staring into space, hannunta rike da ledan biscuit, kallonta ya dinga yi kafin ya nufeta ya duka kusa da ita har sannan bai daina kallonta ba hawaye ne cike manyan idanuwanta, lkci daya ya ji jikinsa yyi sanyi sosai, ya dafa goshinta yace "Heedayah" Hannunsa ta kama kamar tana jiransa a lkcn, sai ta fashe da kuka tace "Abba" Ya jawota jikinsa yace "Why are you crying? (me yasa kike kuka" Cikin rawar murya tace "Suna min dariya bana gani, wata ta karbe min biscuit guda daya, Abba ka kai ni gida gun Ammina...." Bai ce komai ba, can ya mike yana rike da ita yace "Toh daina kuka" goge idonta tayi, yana rike da ita still ya tafi office din shugaban wajen, bayan sun gaisa yace "What are the process before adoption of a child in here? (meye matakan bi kafin daukan yaro a gidan marayu)" Tana kallonsa tace "It's a very long process mister, (Matakan suna da yawa gaskiya" yace "Alright.... I will be back in some minutes time (Xan dawo nan da wani lkci)" kuka Heedayah ta dinga yi sosai da ta gane tafiya xai kara yi ya bar ta, haka nan ya bar ta gun masu kula da marayun wajen ya wuce, police station ya koma. Asp ya ajiye pen din hannunsa yana kallon Alhaji Ahmad yace "So you mean kana son tafiya da ita har lkcn da Allah xai sa a samu iyayenta" Alhaji Ahmad yace "Yes exactly sir" Asp yace "Sai dai kasan da cewar you didn't adopt her, duk lkcn da iyayenta suka bayyana xa a mayar masu da ita" Alhaji Ahmad yace "In sha Allah, Ni ma nafi son haka, and as I have said sbda health issues dinta yasa xan tafi da ita, she won't cope in the orphanage, i will be dropping all necessary information kamar yanda ka bukata duk da ni ba bako bane a gun ka, idan ma baka san ni yanda ya kamata ba, na tabbata kasan Yayana ai" Murmushi Asp yyi yace "Sure, I am not doubting you Barrister, Allah ya taya ka riko har kafin Allah ya bayyanar da mahaifanta" Alhaji Ahmad yace "In sha Allah, nagode sosai for understanding me" Wani short note Asp din yyi a takarda yayi stamping sannan ya kira wani police officer ya koma orphanage din tare da Alhaji Ahmad don dauko Heedayah. Har sannan Heedayah na xaune inda Alhaji Ahmad ya bar ta tare da daya daga mai kula da su, sai dai mai kula da su din bata gun, ita kadai ce xaune gwanin ban tausayi, har sannan ta ki cin biscuit din, Bbu 6ata lkci aka basa ita ya bar orphanage din bayan ya sallami police officer din, he can see how happy Heedayah was bayan sun shiga mota, ganin tana ta kokarin bude biscuit din hannunta ya amsa ya bude mata ya mika mata, tace "Abba xaka maida ni gun Ammina da Abbana?" Ya shafa kanta yace "In sha Allah daughter" tayi murmushi sosai tana cin biscuit din hannunta, seat belt ya sa mata, yana kallon agogo dake nuna masa biyar saura yan Mintuna, ya gama addu'o'in da xai yi sannan ya dau hanyar fita kano xuwa garin kaduna..... Yan Niger Khaleesat bata iya rubutun Hausa xalla bbu turanci ba, kun ban wahala a page din nan😩 Free pages dai bbu yawa😉 07087865788 ⚡ _Heedayah_ ⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 4...... Har suka shigo cikin garin kd wajajen karfe tara na dare bacci Heedayah take, slowly yake driving bayan ya shigo anguwar da gidansa yake, anguwar so silent ga fitilu ta ko ina da ya haska anguwar kamar da rana, bakin wani gate ya ja ya tsaya yyi horn, wanda hakan ya farkar da Heedayah, laluba motar ta shiga yi tace "Abba...." yana kallonta yace "I am here..." Bata kuma cewa komai ba dama kawai so take ta tabbatar bai bar ta bane, ya d'an yi murmushi ya ja motar xuwa cikin babban compound dake dauke da gida ginin duplex bayan Mai gadi ya bude masa gate da sauri, parking yyi a space din da aka tanadar domin parking a compound din, wani matashi ne da baxai wuce 28 ba ya fito daga cikin babban building din gidan, ya nufo parking space din, Alhaji Ahmad ya kashe motar ya bude ya fito, Matashin ya d'an risinar da kansa yace "Sannu da hanya Abba" Alhaji Ahmad yace "Yauwa sannu, but ka damu ka kirani tun jiya da kake min sannu da hanya ynxu??" Yana fadin haka ya wuce sa ya xaga daya side din motar, da ido dogon Matashin ya bi sa bai ce komai ba, Alhaji Ahmad ya bude door din side din da Heedayah take, ya kamo hannunta ya sakko da ita daga cikin motar, Matashin ya d'an koma baya yana kallonsu a bit surprised, Alhaji Ahmad yace "Ka fiddo min laptop dina bayan motar, they are some other things ma ka taho da su ciki" Yana fadin haka ya nufi entrance din shiga gidan yana rike da Heedayah, Matashin ya bude motar ya dauko abinda yace masa sannan ya bi bayansu, Alhaji Ahmad na shiga parlor Rabi'ah da Khadija suka taso da gudu don rungume sa, sai dai ganin Heedayah da yake rike da duk suka tsaya basu karasa gun nasa ba, Khadija tace "Who is she Dad?" Yana kokarin cire takalminsa yace "Sabuwar 'yar uwar ku" kallon juna Khadija suka yi da Rabi'ah, ya karasa parlon ya xaunar da Heedayah kan kujera sai dai ta ki sakin hannunsa kmr xata yi kuka tace "Abba kar ka bar ni don Allah" Yace "Noo baxan bar ki ba, we are home yanxu" Yana fadin hka ya kalli Khadijah yace "Ina Mumyn ku?" Khadijah ta d'an cinno baki tace "Upstairs" ya daga Heedayah ya wuce sama da ita, Khadija da Rabi'ah suka juya suna kallon yayansu dake tsaye bakin kofa yana kallon ikon Allah shi ma, da sauri suka nufesa a tare suka ce "Ya Shuraim who is she? Wacece ita" Ko kallonsu bai yi ba, ya nufi part din Abbansu don ajiye masa system dinsa dake hannunsa. Alhaji Ahmad ya bude kofar parlon Mai dakinsa still holding Heedayah's hand, dai dai fitowar ta daga bedroom dinta, ya xaunar da Heedayah saman kujera kafin yace komai tana kare ma Heedayah kallo daga sama har kasa tace "Waye wannan kuma Barrister?" Yace "sannu da hanya ya kamata ki fara min sannan tambayoyin ki su biyo baya" a takaice tace "Toh sannu da hanya, wacce yarinyar ce wannan ka shigo min da ita har parlor?" Sai a sannan ya daga kai ya kalli matar tasa yace "Bakuwa ce" Ta d'an yatsina fuska tace "Bakuwa kuma? Daga ina? Kuma ina xa a kai ta?" Yace "Eh bakuwa.... Daga kano, kuma nan xata xauna in sha Allahu rabbi" Da mugun mamaki tace "Yar wacece ita din?" Yace "Baiwar Allah ce..." A kufule tace "Plss be straight barrister, ina ka samo yarinya? Kowa ma bawan Allah ne ai" Barrister yace "Gashi nan na gaya maki, what else did you want to know, me kuma kike son sani" kamar jiran tambayar take ta mayar masa da amsa da sauri tace "Manufar xuwanta gidan nan, sannan mun hada wani dangantaka ne da ita??" Ya gyara xama yace "Manufar xuwanta gidan nan shine don ta xauna da mu na wani d'an lkci, dangantakar mu kuma kawai shine kasancewar ta 'yar uwar mu musulma" Kallonsa ta dinga yi, surprised, Furious, and mad at the same time.... Blankly tace "I don't get you Abban Shuraim, ban gane abinda kke nufi ba, a ina kasamo wannan yarinyar??" Ya mike yace "Her parents are missing, so we need to look after her kafin Allah ya bayyanar da iyayenta, all that aside, she is blind Hajiya Maryam, makauniya ce...." Yana fadin haka ya fita daga parlon..... Hajiya Maryam da ta bi sa da kallon mamaki lkci daya tace "Tabdijam!!! Toh sannu Humanitarian, Do-gooder.... sai kuma nace maka gidana orphanage ne (Gidan marayu) ko kuma police station?? to wllh ka saurareni da kyau, yarinyar nan dai baxa ta xauna gidan nan ba, me muka hada da ita daga ganin yarinya a titi ka kinkimota ka kawo mana gida wai iyayenta sun 6ata kamar wasu gyada, Anya ma Barrister kasan me kake yi kuwa, yanda duniyar nan bbu gaskiya kwata kwata kowa ya xama mugu ya xama abun tsoro ka dauko mana yarinya ka kawo gida?? A'a wllh ba gidana ba, ka dauketa ka kai ta police station ko kuma ka kai ta gidan marayu" tana fadin haka ta wuce dakinta rai 6ace don daukan wayar ta, Heedayah dai na xaune sai kallon direction din da masifar ke tashi take yi, gaba daya a tsorace take, lkci daya hawaye ya kawo manyan idanuwanta.... Bayan minti biyar Hajiya Maryam ta fito dakinta tana kallon Heedayah tana huci ta daka mata tsawa tace "Ke maza tashi ki fita ki ban waje kar in illata ki...." Mikewa Heedayah tayi da sauri ta fashe da kuka tana laluben hanya tace "Abba where are you" muryarsa ta ji yace "I am here...." Har ya karaso cikin parlon kallon Hajiya Maryam yake, calmly yace "Wannan ya xama na karshe a gidan nan, kar ki sake yi mata tsawa, nace a gidan nan Heedayah xata tsaya har sai an samo iyayenta, I mean my words" bude baki tayi tana kallonsa da farko, sai kuma tayi wani murmushi me sauti tana tafe hannu tace "Toh sannu Humanitarian, idan ni ban kai inyi magana ka ji ba nasan baxa a rasa wa enda xa su yi maka ka ji ba, look Ahmad it's not as if i am being wicked, ni ba muguwa bace Allah ya ga xuciyata kawai xamanta ne damu bna so don hankalina bai kwanta da hakan ba, to wai ma akan me xata xauna da mu, kai da kke lawyer ai ya ci ace ka fi ni sanin me duniya ke ciki, to idan ba akwai wani boyayyen lamari a kasa ba daga xuwa meeting kano sai ka dawo da yarinya wai ka tsince ta a titi bbu iyaye, Kar ka manta idan kai lawyer ne to ni kuma matar lawyer ce...." Ya dakatar da ita yace "Wallahil Azeem Maryam wannan yarinya a hanya na hadu da ita kamar ynda na fada maki, mota ce ta bigeta muka yi asibiti da ita, I was there har ta farfado.... Let just stop all this, Maryam put Rabi'ah or Khadijah in her shoes plss" a mugun fusace tace "Allah ya kiyaye, I can't imagine my children in her shoes, why will I? Kar ma ka gaya min haka, Ni dai abinda na sani shine hankalina bai kwanta ba kuma baxai ma ta6a kwanciya da yarinyar nan ba, wa ya sani ma ko aljana ce da gashi haka??" Bai kuma ce mata komai ba ya kama hannun Heedayah dake kuka a hankali ya fita parlon da ita xuwa downstairs.... Hajiya Maryam ta kasa zaune a parlon nata sai xagaye take, bude kofar aka yi Shuraim ya shigo da sallama can kasa, Hajiya Maryam ta kallesa da sauri tace "Shuraim kana ganin mahaifinku koh? Me yake nufi da kawo mana yarinya gida ba dangin Iya balle na Baba, ya san yar wacece ko ma shegiya ce bai sani ba kawai ya kawo mana ita gida, wllh something is fishy, kuma in dai yarinyar nan xata xauna gidan nan sai dai mu bar masa gidan shi da ita gaskiya, don mu ba gantalallu bane, wai kuma makauniya ce kai ka ji fa???" Tun fara maganar ta sai a sannan Shuraim ya kalleta da sauri jin wai makauniya ce, Tayi mitsi mitsi da ido tace "Wllh haka yace Makauniya ce bata gani, kuma naga alamar hakan, she is blind, oh innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, me ya samu Barrister ni Maryam... Anya kuwa yana right senses dinsa??" Shuraim dai bai ce komai ba ya juya xai fita, a mugun fusace tace "Toh malam ba shiru xaka yi ba ka wani juya sumui sumui xaka wuce, xuwa xaka yi ka samesa tunda yana jin maganar ka, ka lallabasa ya fitar mana da yarinyar ya kai ta police station, bbu ruwana da gayyar tsiya, yarinyar nan baxata kwana gidan nan yau ba..." Shuraim na fita ya nufi Part din mahaifinsa, ya bude kofar parlon da sallama, Heedayah ce kawai xaune kasan carpet dake parlon ga cup din fresh milk a hannunta, jin an bude kofa ta dakatar da shan madaran da take yi tana waige waige, bai kalli direction dinta ba ya nufi dakin Abbansa, sallama yyi bayan ya amsa masa ya shiga, xaune ya samesa gefen gadonsa, ya karasa ya xauna nan kasa gabansa yana kallonsa yace "Ya hanya Abba?" Abba ya kallesa yace "Alhmdllh..." Shuraim ya d'an shafa kansa yace "Abba, akan wannan yarinyar....." Sai kuma yyi shiru, Abba yace "Yes, what about her? Ina jin ka" Shuraim yace "Is she suppose to be here?" Abba yace "Of course, ai nan din gidana ne ba na wani ba, so why won't she be here?? Me kuwa xai hana xamanta a nan tunda na amince da hakan?" Shuraim ya girgixa kai alamar ya rasa abinda xai ce, Abba yace "Yes gidana ne, ba naka ba, balle na Mahaifiyar ka" Shuraim yace "But Abba hakan ba dai dai bane, bbu abinda muka hada da ita, ba mu san ta ba, we don't even..." Dakatar da shi Abba yyi so pissed off yace "Get out my frnd, who are you to question my orders? And don't u even have human conscience? Xaka so kanwarka ta tagayyara a rayuwa?" Mikewa Shuraim yyi yace "I am sorry" daga haka ya nufi kofa ya fita, satan kallon Heedayah yyi, lkci daya ya wani hade rai ya fice daga parlon. 07087865788 ⚡ _Heedayah_⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 5.... Jin budewar gate ya sa Alhaji Ahmad ya mike ya isa jikin tagar dakinsa yana kallon compound din gidan don ganin wanda xai fita, motar yayansa ne ya shigo compound din, ya bi motar da kallo har yyi parking, sannan ya girgixa kai ya koma ya xauna... Ba a dau lkci ba kuma wayarsa ya fara ring, ya duba ganin yayan nasa ke kiransa ya mike ya fita dakin, kwance ya ga Heedayah ta fara bacci nan kasa, ya d'aga ta ya kwantar kan kujera sannan ya fita, direct main parlor ya wuce, ya tadda wansa Alhaji Umar zaune saman kujera ga Hajiya Maryam xaune parlon ta sha kunu kai kace bata ta6a dariya ba, xaunawa yyi ya gaida Yayan nasa, Alhaji Umar ya amsa yana kallon Hajiya Maryam yace "Me ke faruwa Maryam" Ta kwantar da murya tace "kana ji Alhaji, Ko awa daya ba ayi ba da dawowan barrister daga kano, amma sai me??" Nan ta kwashe komai ta tsara masa, tana matsar kwalla tace "Saninta muka yi Alhaji? Ko me muka hada da wannan yarinyar? Mun san me yasa iyayen suka jefar da ita da har shi xai daukota, to gaskiya naga abun ba wanda hankali xai dauka bane shi sa na kira ka don kayi intervene don gaskiya I don't know what came over Barrister, ban san me ya samesa ba, kawai muna xaman xaman mu ya ja mana magana...." Alhaji Umar na kallon kanin nasa yace "Barrister wace yarinya ce wannan ka dauko ka kawo cikin gidan ka?" Alhaji Ahmad ya jinginar da kansa da kujera yace "Doctor nasan da kai ka ga yarinyar nn xaka yi fiye da abinda nayi ma... Sincerely I mean no harm to my family, taimako kawai nayi sbda Allah, and I thought they will also welcome the idea, na xata xa su so taimakon da nayi...." da sauri Hajiya Maryam ta katse sa tace "To family dinka basa son taimakon nan gaskiya, ur idea isn't welcome, kawai ka maida ta inda ka ganta, idan kuma xuciyar ka baxai yarda ka maida ta ba to ka kai ta gidan marayu..." Wani kallo ya jefa mata yace "Baki isa ki bani order a gidana ba Maryam, I did what I know is right, you are not in the place to kick away my decision, nace baki isa ba" Alhaji Umar na kallonsa yace "Hold on bawan Allah, bana son hayaniya, ka saurareni...." Alhaji Ahmad yace "Dr if you are in anyway doubting me ka kira abokin ka Asp Usman, he will explain everything to you, Babu abinda xai boye maka, shi ma ya bani go ahead din tahowa da yarinyar when I request doing so, ban taho da yarinyar nan ba sai da izini da sa hannun Asp...." Mikewa Alhaji Umar yyi bayan shirun wani lkci yace "Ynxu ina yarinyar take?" Barrister ya mike yace "Mu je ka ganta tana sama parlona" Bin bayansu Hajiya Maryam ma tayi xuwa part din mai gidan nata da sauri, kallon Heedayah dake bacci Alhaji Umar ya dinga yi kafin yace "She so little" Alhaji Ahmad ya bude hannunsa yace "Of course she is" hannu Alhaji Umar ya kai goshinta ta bude ido da sauri ta kamo hannun tace "Abba..." Ya d'an yi jim sai kuma yace "How are you?" Shiru tayi tana kokarin mikewa ya dagata ta xauna, Hajiya Maryam sai kyabe baki take fuska a murtuke tana kauda kai, Alhaji Umar ya girgixa kai ya sauke ajiyar xuciya yace "This is serious... abinda xai faru ynxu shine ke Maryam kiyi hakuri ta kwana xuwa gobe xa a san ynda xa ayi in sha Allah, they will be a meeting tomorrow at my resident idan Allah ya kai mu" shi dai Barrister bai ce komai ba, Hajiya Maryam tace "Allah ya kai mu, amma wllh baxan rike yarinyar nan ba Kun ji rantsuwar musulmi sai dai duk abinda xai faru ya faru" daga haka ta fice daga parlon duk suka bi ta da ido. Karfe goma Barrister Ahmad ya fita parlonsa xuwa parlon Hajiya Maryam, kallo take ita da Rabi'ah da Khadijah a parlon nata, Khadijah tace "Toh Mumy me yasa bai kai ta orphanage ba??" Hajiya Maryam ta kyabe baki tace "Neman suna mana, ke ko bayan lawyer gashi Humanitarian din da ya laka ma kansa, to wllh ba dai wannan gidan ba, dai dai nake da su dukka...." Rabi'ah tace "And kuma yace makauniya ce fa" Hajiya Maryam ta dau apple din gabanta tace "Ko kurma ce sai ya fitar da ita gidan nan, ban gama wahala da nawa yaran ba baxai kwaso min wata can ba, ba dangin iya balle na baba, shi dai ya cika fitina ne kawai" Khadijah tace "Ni dai idan yace nan xata xauna gwara in koma gidan Aunty Fatima, I can't stay in the same roof with her, what if muguwa ce" Hajiya qMaryam tace "Sai dai shi da ita su bar mana gidan...." Shigowan Abban yasa tayi shiru, Yana kallonsu gaba daya yace "Bani da abinci a gidan nan yau kenan?" Hajiya Maryam tace "Ohh na xata you are full ai da naga kafi concentrating kan yar tsintuwa, ban san kana tare da yunwa ba, Rabi'ah go and serve him downstairs" kallonta kawai yake kafin ya gyada kai ya juya ya fita parlon, a hankali Khadijah tace "Abba is just acting strange, dubi fa ko kula mu bai yi ba tunda ya dawo..." Hajiya Maryam tace "Atoh ina xai kula ku ga makauniya ya saka a gaba Khadija" Rabi'ah ta tashi ta fita don kai ma Abban nata abinci parlonsa, Yana xaune parlon yyi nisa tunanin da yake, ta ajiye abincin tace "Abba ga abincin" yace "Baxan ci ba, ki dibar ma yarinyar nan kawai ki fita da sauran" ta kalli Heedayah dake kwance fararen idonta a bude, ta d'an hade rai ta bude abincin ta diba kadan ta daura nama daya, kallonta kawai Abban nata yake yi yace "Add the meat" Ta kara daura wani naman sannan ta mike ta fita da sauran abincin. Mikewa yyi ya tafi gun Heedayah yace "kina Jin yunwa ko?" Ta gyada masa kai, ya kama hannunta ya dau plate din abincin ya fita, main parlor ya koma, ya shiga wani d'an corridor ya kwankwasa daya daga kofofi biyun dake wajen, wata matashiya da baxata haura talatin da biyar ba ta bude kofar, ganinsa ta durkusa da sauri tace "Sannu da dawowa Alhaji, ina yini" yace "Lfya lau, ga wannan yarinyar ki kula da ita, ki bata abincin nan, sannan ki taimaka mata tayi wanka ki mata shimfida ta kwanta, tana da matsalar ido" Matar ta kama hannunta da sauri tace "To in sha Allahu Alhaji" daga haka ya juya ya bar wajen bayan yyi mata sai da safe. Washegari da ya kasance lahadi bacci yan gidan suka dinga yi har karfe takwas, Hajiya Maryam ta sakko parlor wajajen tara don ganin ko Saudat ta gama shirya breakfast, Kitchen ta sameta tana juye ruwan Lipton dake ta kamshi a flask, alamar dai ta gama komai shi kadai ya rage, Heedayah na xaune daga kusa da kofa hannunta rike da cup din shayi da Saude ta hada mata ga plate din kwai da dankali da plantain, Hajiya Maryam ta wani xaro ido tace "Saudat me xan gani haka? Wa ya saki wannan aikin, a ina kika ga yarinyar? Ko a ina kika santa?" Da sauri Saudat ta xube kasa tana gaisheta tace "Hajiya... Alhaji ne ya kawo min ita jiya da daddare yace in kula...." Tsawa tayi mata da karfi tace "Toh wllh a bakin aikin ki, da ya kawo maki ita baki iya xuwa ki sameni ba? Kawai sai ki yanke hukunci sbda ke ke ajiye da kanki? To wllh kin gama min aiki a gidan nan yau, yanxun nan xa ki kama gabanki" Hakuri Saude ta dinga bata a tsorace tana cewa "Hajiya wllh Alhaji ne ya kawo min ita kiyi hakuri ki rufa min asiri, ni ban san komai ba" Hajiya Maryam tace "Ni dai nace kinyi na aikin ki wllh, maxa tattara yanaki yanaki" daga haka ta juya ta fice daga kitchen din tana huci. Karfe goma Alhaji Ahmad ya dau Heedayah suka fita xuwa parking space, Hajiya Maryam dake xaune ta bi sa da kallon mamaki sannan ta kalli Shuraim dake operating laptop a parlon tace "Ka gani ko Shuraim, gaskiya abun nan ya fara bani tsoro, wannan abu ba na hankali bane... Something is wrong somewhere, what is wrong with your father" Shi dai kallonta kawai yake bai ce komai ba, wayarsa ya fara ring ya dauka ganin Abbansa ne ya kai kunne, Daga daya bangaren Abba yace "Ka gaya ma babarka karfe sha daya ne meeting din don Dr ya kirani xai yi tafiya" Shuraim yace "Toh Abba" Daga haka ya katse wayar, Yana kallon mahaifiyarsa yace "Abba yace Baffa xai yi tafiya, so da wuri xa ayi meeting din" mikewa Hajiya Maryam tayi tace "Toh ai a shirye nake sai ka kira kanninka duk mu duguma xuwa gidan, wato baxai iya gaya min ba sai dai ya bada sako a bani, to duk muje ayi ta ta kare yanxu" Babban gida ne sosai don har ya fi na Barrister Ahmad girma, Shuraim yyi parking a parking lot din gidan, Mumy ta fito ta nufi hanyar shiga gidan, direct dakin Hajiya Amina Uwar gidan Alhaji Umar ta nufa, bayan sun gaisa Hajiya Amina tace "Daxun nan Alhaji ke ce min akwai meeting wai kuna hanya, ni dai nace to Allah ya sa lafiya" Mumy tace "Ina fa lafiya, wllh ba lafiya...." Tsaf ta kwashe ma Hajiya Amina abinda ke faruwa ta sanar mata, Hajiya Amina ta buda ido sosai tace "Iko sai Allah, to meye ma'anar hakan da Barrister yyi??" Mumy tace "Ni nasan masa, ni dai wllh wllh kinji rantsuwar musulmi koh?? To yarinyar nan baxata xauna tare da ni ba, ba ruwana.... Haka kawai ban san hawa ba ban san sauka ba yanda duniyar nan ta lalace..." Hajiya Amina tace "Toh ai dama bbu wannan xancen, taya xaki rike yar da ba a san tushenta ba, kada ki kuskura wllh, Wai kuma makauniya kamar dai a wasan kwaikwayon hausa..." Mumy tace "Ke ki bari kawai, nasan karshe Dr yace a barta gidan nan...." Da sauri Hajiya Amina ta katse ta tace "Wajen wa??? Haba wannan ai labari ne, bbu wanda xai soma wannan gangancin..." Dariya Mumy tayi tace "Toh ba sai abokiyar xaman ki ta riketa ba" Hajiya Amina tayi tsaki tace "Ai sai dai ta kai ta gidansu amma wllh bbu wajen xaman yarinyar nan a gidan nan" Mumy tace "Atoh, taimakon da idan kayi ma yanxu yake xame maka jaraba" Mikewa tayi tace "Bari in je in gaida tsohuwar can..." Hajiya Amina tace "Tana can kuwa yau bbu mutunci ta tashi...." Mumy tayi dariya tace "Ni dai Allah ya dube xuciyata ya rabani alakakai..." Hajiya Amina tace "Wa?? Ai xance komawa gidan ki take yanxu" Mumy tace "Tabdi, xaman mu baxai yiwu ba, wnn karan karara xan fito inyi magana" daga haka ta fita dakin. Da sallama Mumy ta bude kofar wani daki ta shiga ciki, babba daki ne sosai bbu abinda bbu a ciki irin dai na tsoffi, Shuraim na xaune kusa da wata tsohuwa da tayi tsit lkci daya ganin shigowan Mumy, Mumy na murmushin yake ta xauna kasa tace "Sannu Kaka...." Tsohuwar na gyara daurin dankwalinta tace "Sannu..." Mumy tace "An tashi lafiya kaka" kaka tace "eh toh lafiyar kenan, amma kin gan ni nan?? Wllh tun safe bbu karen da ya leko ni a gidan nan har shi Umarun, hana rantsuwa dai ya shigo da Asuba ya gama xamansa a can na kusan minti talatin ya fita, wllh Maryam gidanki ya fiye min nan sau goma, gwara ke da yunwa kawai kike bari na...." Mumy ta hadiya abu da kyar ta sunkuyar da kanta, Kaka tace "Kinga wannan bakar matar Amina?? Ni dai ina ga da kyar ta wanye lafiya, ni dai ki tafi da ni gidanki" Da sauri Mumy tace "Ai hakuri ake yi a ko ina kaka, ko ina hakuri ake ba wai wani abu ba, kawai ayi ta hakuri tunda Doctor ya fi son yana ganinki kusa da shi, kuma ma hakan ya fi wllh, yanxu ma meeting muka xo yi bbu lafiya" Da sauri kaka tace "Me ya faru kuma?" Mumy ta gyara xama tana tabe baki, nan ta tsara ma Kaka duk yanda aka yi daga daren jiya har xuwa safiyan yanxu har da kari, Kaka da ta gwalo ido tana kallonta tace "Ba lafiya, shi Ahmadun yace bbu wanda ya isa ya saka shi ya kuma hanashi?" Mumy tace "Toh nima dai ban gane kan lamarin ba, abun dai gashi kamar almara" Kaka tace "Toh ina yar makauniyar take yanxu?" Mumy tace "Tun sassafe ya fice da ita ko bi ta kanmu bai yi ba....." ⚡ _Heedayah_ ⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 6....... Kaka ta rike ha6a tana kallon Mumy tace "Lallai ba lafiya, Kar ki yarda, ba mu san irinta ba, kuma ba ma bukatan sani, ba ruwana da jajibe jajibe gaskiya, to meye kuma na tsinto yarinya kamar wanda nace ma je ka kagani, to ni dai ba ruwana, mu je ayi meeting din gaba daya, ai kin ga ko shigowa gaisheni ma bai yi ba tunda ya tsinto wata uwar tasa a titi jiya, kuma ace min lafiya qlau, a'a wllh ba lafiya" sosai hankalin Mumy ya kwanta jin furucin Kaka, Kaka ta mike ta nufi kofa Mumy na biye da ita tana murmushi, Shuraim ya bi su da kallo kafin ya mike shi ma ya fita parlon. Babban parlor ne me dauke da tsadaddun kujeru ba masu hayaniya ba, Hajiya Amina da kishiyarta Hajiya Hauwa na xaune parlon sai Safiyya, Nafisa da Aisha 'ya yan Hajiya Amina, Jamila da Zainab 'ya yan Hajiya Hauwa su ma na xaune parlon, Khadijah da Rabi'ah duk suna parlon su ma, Abba na xaune tare da Heedayah da ya xaunar gefensa, Alhaji Umar ma na xaune idonsa a kan tv dake nuna tashar Aljazeera, a tare Hajiya Maryam ta shigo parlon da kaka da ta tsuke fuska, Abba dai kallon mahaifiyar tasa kawai yake har ta xauna, Shuraim ne ya shigo da sallama ya nemi kusa da Khadijah ya xauna sannan ya gaida su Hajiya Amina da Baffansa, d'a murmushi ya amsa gaisuwar cousins din nasa mata dake kallonsa gaba daya, Baffa ya rage volume din TV din yace "Ina Sudais?" Safiyya tace "Bai dawo training ba" Baffa ya gyada kai alamar gamsuwa, Abba na kallon kaka yyi kasa da kai yace "An tashi lafiya kaka?" Kaka tace "A'a ba ruwana, lafiya lau na tashi" tana magana ne tana kallon Heedayah kasa kasa, Rabi'ah da Khadijah suka gaisheta su ma, tace "To duk ku tashi ku fita, ko kun ga sa'annin ku a nan, wannan ai ba maganan yara bane, babban magana ce, Yaron kirkin nan kadai ya cancanci xama a nan, duk ku fita" Hajiya Hauwa tayi murmushi tana kallon Shuraim da ya sunkuyar da kansa, Mikewa su Khadijah suka yi gaba daya har da su Safiyya suka fita bbu halin ko yi mata kallon banxa, shiru ne ya biyo baya a parlon, Baffa ya bude wajen da addu'a, bayan haka ya kalli Hajiya Maryam yace "Why did u invite our mother in here?" Ta gyara xama tace "Bcos it's necessary, she needs to know what's happening" Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds ya daura da cewa "Ba wani abu ya tara mu nan ba... jiya da maraice Barrister ya dawo gida da wata baiwar Allah wanda hakan ya kawo rashin fahimta a can gidansa, ga kuma yarinyar dai xaune kusa da shi...." ya fadi haka yana nuna Heedayah wanda duk kana ganinta kasan a tsorace take, Ya ci gaba kamar haka "Duba da irin xamanin da muka tsinci kan mu na yanxu a gaskiya hakan ba shawara bace me kyau it's risky bringing the little girl home, sai dai me??? Mu duba wannan yarinya, har nawa take gaba daya, duk magidancin kwarai ya ga yarinyar nan that looks helpless a hanya ba lallai ya iya wuceta bai yi making effort din taimakon ta ba, ko min kankantar taimakon kuwa, sai dai shi barrister nasan taimakon ya yanko sa da girma ne tunda har gidansa ya kawo wannan baiwar Allah, wanda ba kowa xai yi hakan ba a xamanin nan na yau gaskiya, ba wai ina nufin hakan da yyi kuskure bane amma in the other way round xa a iya kiransa da kuskure...." Kaka dake ta hararan Baffa ta yi kwafa tana girgixa kafa, Baffa ya ci gaba "Amma kuma xai iya yiwuwa yaga kawota gidan shine kadai mafita duba da cewa she is unsighted.... Har xuwa lkcn da Allah xai bayyana iyayenta" Calmly Hajiya Maryam tace "Idan Allah bai bayyana iyayen nata ba fa?" Baffa yace "Wannan kuma baxa a rasa yanda xa ayi ba in sha Allah, Hajiya kar ki manta one knows not where his or her reward lies, sannan muna da baya, we should always try positioning things in our shoes" Girgixa kai tayi irin ba mutunci tace "Toh ni ban hanasa riketa ba Doctor, Amma Wallahil Azeem ba ni xan rike masa ita ba,... Ya nemi inda xai kai ta, ko kuma ya bar ta nan wajen ku ai duk daya ne..." Da sauri Hajiya Amina ta kalleta da wani expression, Kaka ta kyabe baki tace "To duk kun gama??" Duk aka yi shiru ana kallonta, ta gyara xama tace "Toh maza tun muna mu bakwai ba mu dawo mu takwas ba a parlon nan Amadu ya maida wnn yarinya inda ya dauko ta, mu ba gantalallu bane, bamu sa6a kwashe kwashe ba a dangi, baxa kuma a fara ta kan d'a na ba...." Shiru ne ya biyo bayan abinda Kaka tace a parlon, Abba da Baffa sai kallonta suke, Hajiya Maryam taji kamar ta tashi ta rungume kaka don farin ciki, Hajiya Amina kuwa sai murmushi take kasa kasa, Hajiya Hauwa dai sai kallon Heedayah da ta makale jikin Abba take, Bude kofar aka yi wani matashi ya shigo da sallama, sanye yake da sport wears, they have many resemblance in common with Shuraim, sai dai ya girme ma Shuraim da shekara daya duk da ba wai hakan ya nuna bane, bin occupant din parlon yyi da kallo, coz he knew nothing about the meeting, ya kalli kaka da ta tsuke fuska ganinsa tace "Kai ka ji wani neman fitina gun Mutumin nan ko sudais...." xaunawa yyi gefenta coz yasan she will brief everything a nan take kafin ma ace masa komai a parlon, ta gyara xama tace "Kanin ubanka dai ya xama abinda ya xama, Wai kaji yarinya ya tsinto ya kawo gida ba dangin iya balle na baba, har yana ikirarin bbu wanda ya isa ya hanasa abinda yyi niyya bai san magana xai dawo kunne na ba, Toh mu xuba da shi, idan shi ya haifeni ai yanxu kowa xai sani, kuma nace masa maxa ya mayar da ita kada raina ya bace...." Murya can kasa Sudais yace "Wacce yarinya ce?" Heedayah ta nuna masa rai bace tace "Gata can kamar mage...." Sudais ya kalli Heedayah da ta makale Abba, sannan ya kalli Abba da Baffansa da suka kasa cewa komai, ya maida dubansa kan Kaka, lkci daya ya hade rai yace "Toh meye don an taimaki wannan yar yarinyar, ni na ma xata wani babban abu ne ya faru a gidan, ynxu ba fata ba yau ace Safiyya ko Jamila sun 6ace baki son wani ya taimaka masu kenan? Kika san dalilin da yasa Allah ya rabata da iyayenta?? Ke da xaki yi fatan Allah ya bayyana su...." Katse sa tayi da sauri tace "Kun ji min fitsararren yaro ko?? to ce maka nayi ban yi addu'ar Allah ya bayyana iyayen nata bane?? Ni dai ba ruwana ka daina min sharri, dama kwana biyu na fita harkan ka a gidan nan sam baka da mutunci ka rainani...." Ya mike yace "A'a ni ban rainaki ba kaka ke dai baki son gaskiya, kawai ki bar Abba ya rike yarinyar a ci gaba da neman iyayenta, ynxu idan ya mayar da ita kika san hannun wanda xata fada, kinsan fa idan ta fada hannun mugaye ke ma kina da kwamasho me girma, sannan kin fi kowa cewa aji tsoron Allah, kuma ga lamarin da ya kamata mutum ya ji tsoron Allah nan...." Tagumi kaka tayi tace "Kuna dai ganin Aliyu ko?? To ba komai rayuwa ce ai" Hajiya Maryam dake ta xufa sai kallon Sudais take tana hadiye abu da kyar, Baffa dai ya jinginar da kansa da kujera yana kallon d'an nasa, Abba kam kansa na kasa shi ma yana saurarensa, Hajiya Amina duk uwar hararan da take xabga ma d'an nata yaki kallon direction dinta, Hajiya Hauwa banda murmushi bbu abinda take, Sudais na kallon kaka yace "Kawai dai yanxu sbda tsoron Allah ki bari Abba ya nemo iyayenta, kuma ta xauna har sanda Allah xai bayyana su...." Kaka tace "To ni dai ba ruwana, dama Maryam ce tace bata yadda ba banda haka ni meye nawa?? ai d'a na kowa ne bawa sai me shi, me ta min da xan koreta banda abun ka sudais? Amadu yayi ta rikonta har Mahadi ya bayyana ma bbu abinda ya sha min kai ni dai...." Sudais ya shafa kansa yace "Idan ya kai xuciyar ki ce masa xa kiyi kin amince ya riketa" A mugun fusace tace "To ya rike ta mana, ni ina ruwana, ai d'a na kowa ne, amma gaskiya ka daina min rashin kunya xan hada ka da ubanka, kaf ka raina ni tamkar ynda uwar ka ta raina ni" ya d'an bude ido ya juya ya nufi kofa xai fita Kaka tace "Allah yyi min tsari da kai ni dai katon banxa" Abba ya mike xai fita rike da Heedayah, Hajiya Maryam ta mike da sauri tace "Wllh to ka nemi inda xaka kai ta ba gidana da na yarana ba..." Kaka ta bude baki tace "Naga bala'i, gidanki kuma Maryam?? Ta ina hakan ya faru" Baffa yace "Wait Ahmad it's better kasan inda yarinyar nan xata xauna, u can't force her to hold the little girl, it's not even possible, tunda tace baxata riketa ba baxa ayi mata dole ba" Abba ya juya yana kallonsu gaba daya kafin yace komai Hajiya Hauwa tace "Babu damu Barrister, ka kawo min ita ni xan riketa in sha Allah har iyayenta su bayyana, Allah ya shige mana gaba, yayi mana mai kyau..." da sauri kaka ta katseta tana wurwurga ido tace "Ki riketa a wani gidan Kuluwa??? Kaji min mata ba tsoron Allah kamar gidanta, Haka kawai ba mu san ko mayya bace yarinya dare daya ta karar damu a gidan a shiga uku xaki wani ce xaki riketa, shi dai Ahmadun da yaga xai iya ya tafi can ya karata, ni dai Allah ya rufa min asiri ba shi kadai na haifa ba, in dai har ina gidan nan yarinyar nan baxata xauna ba, idan ko xata xauna sai dai a sallameni in tafi, bbu ruwana da kwashe kwashe ta kaina nake" tana fadin haka ta juya masu baya kamar karamar yarinya, Baffa dai sai kallon D'an uwan nasa yake, Hajiya Maryam kuwa sai hararansa take tana girgixa kafa tana wani murmushi irin ba shi da wata mafita kuma ai, ya gyada kai yana kallonta da kyau yace "Shikenan, Xan auro warce xata rike ta a satin nan in sha Allah" Daga haka ya fice daga parlon rike da Heedayah, kasa motsi Hajiya Maryam tayi jin abinda yace ta bi sa da kallo baki bude, Kaka tayi wani dariya tace "Atoh dai, tun ba yau ba dama nake cewa kayi aure ka ki, yanxu ai gashi xaka yi ba don Allah ba, xaman ka da Maryam ko kaddara, gwara ka auro warce xata rike yar da amana don a ynxu kam yarinyar bata da maraba da marainiya, tsinanne ne kadai xai ki taimakon ta...." Ta gefen ido Baffa ya kalli mahaifiyar tasa yyi saurin sunkuyar da kai. ⚡ _Heedayah_⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 7...... Sudais na tsaye compound din gidan nasu Abba ya fito rike da hannun Heedayah, Sudais ya nufe sa ya gaishesa da ladabi, Abba yace "Lafiya Aliyu, ya weekend?" Sudais yace "Alhmdllh sir...." Yana kallon Heedayah ya kai hannu kanta yace "How are you?" Shiru tayi bata ce komai ba, Abba yace "Talk to him Heedayah" tana rike da hannun Abba a hankali tace "I am fine" Sudais ya mata murmushi yace "Good girl...." ya kalli Abba yace "Allah ya bayyana iyayenta" Abba yace "Ameen My son" jin taku a bayansu Sudais ya juya, Shuraim ne ke tahowa yana tafiyar kamar bai son yi, wani kallo Abba yyi masa ya kalli Shuraim yace "Xan wuce gida ynxu, anjima ka taho can gidan ka sameni" Sudais yace "In sha Allah...." Daga haka Abba ya bar wajen xuwa gun motarsa tare da Heedayah, Sudais na kallon Shuraim da ya bi Abbansa da ido yace "Kai ma baka bada goyon bayan taimakon yarinyar da Abba ke son yi ba kenan, coz naga kallon da ya maka" Shuraim ya bude hannu yace "But.... She's blind, ta ina xa a fara kula da ita, is it even possible...." Sake baki Sudais yyi yana kallonsa a bit shock, can ya juya da sauri ya kalli parking space yaga Abba is helping her Into the car, ya kara kallon Shuraim yace "Blind? How is that?? Who told you that, ban gane ba" Shuraim ya shafa kansa yace "Yes makauniya ce..." Yana fadin haka ya juya ya koma ciki ya bar Sudais a wajen baki bude, Sudais ya kara satan kallon motar Abba har ya fita compound din.... A hankali Abba ke driving yana yi yana waigen Heedayah dake shan yoghurt da ya siya mata, muryar ta ya ji tace "Abba gida xa mu je ynxu wajen Ammina?" Ya gyada mata kai kamar tana ganinsa yace "In sha Allah" wani babban eatery ya shiga yyi parking yana kallon agogon wrist dinsa da ke nuna karfe sha biyu saura, wayarsa ya dauka yyi dialing number ya kai kunne, bayan few seconds yace "Hope you aren't going to keep me waiting Barrister" bin motar da ya shigo eatery din a dai dai lkcn yyi da kallo sannan ya katse wayar, Heedayah tace "Abba mun kai gida?" Ya shafa kanta yace "A'a, I want to see a frnd now, xa ki jirani har in dawo koh?" Ta gyada masa kai a hankali, kamo hannunta yyi yana murmushi ganin she looks sad and insecure, kamar dai tafiya xai yi ya barta din nan, mika mata wayarsa yyi yace "Ki rike min wayata har in dawo ynxu, kin ji?" Ta kara gyada masa kai, ya bude motar ya sauka sannan ya rufe ya nufi entrance din eatery din, Table din dake dauke da wata mata that is in her early fifty ya nufa, kana ganinta kaga well educated bafillatana cikin shiga ta kamala, ya ja kujera ya xauna yace "Good morning Barrister" Ta ajiye wayar hannunta da take operating tana kallonsa ta cikin siririn glass din idonta tace "Morning, ya family, ya weekend?" ya gyada kai yace "Alhmdllh mun gode Allah" tace "Hope ba aiki xaka hadani da shi ba kace xaka yi tafiya, coz nima tafiyan xanyi gobe in sha Allah" yayi 'yar dariya yace "Not at all, how are the children?" Tace "They are all alhmdllh, ya su Rabi'ah?" yace "Lfya lau" tace "Toh Maa sha Allah" shiru ne ya biyo baya, bayan few seconds ya kalleta yace "Ba aiki xan baki ba, na dai xo maki da magana mai muhimmanci ne Hajiya Rahinah..." kallonsa tayi ita ma tace "Ohk Am all ears in sha Allah barrister, Allah kuma yasa dai lafiya" yace "Sai alkhairi, Hajiya Rahinah na gayyatoki nan ne.... To ask for ur hand in marriage" Da wani irin mamaki take kallonsa wanda hakan bai bata damar iya ce masa komai ba, yyi kasa da murya yace "Yes nasan xa ki yi mamaki but ba abun mamaki bane, I want to marry you..." Ta yi wani yake tace "Haba Barrister, do you even know what u are saying, ni ynxu auren me xan kuma yi? Me nake nema a rayuwa...." Ya katse ta yace "Aure shine rufin asirinki let me tell you idan baki sani ba, idan kika yi aure kimarki da darajar ki xai fi haka a gun jama'ah, I have known you for more than 15 years now tun mijin ki na da rai...." Bude handbag dinta tayi ta ciro tissue don nan da nan har hawaye ya kawo idonta, ya girgixa kai yace "I don't mean to hurt you ko in fama maki ciwon xuciyar ki Rahinah, kar ki manta tun ba yanxu ba na sha baki shawaran kiyi aure sai ki ce min sai kinyi shawara, to yanxu na yanke shawarar auren ki for 3 reasons, which I will let you know ko ba yanxu ba" tace "I am sorry Ahmad bana tunanin xan yi aure har karshen rayuwata, rabuwan tashin hankali nayi da mijina ba wai normal rabuwa, bana da ra'ayin aure har abada" ya katse ta ya d'an buga table din gabansu yace "Stop this nonsense Rahinah..." A d'an fusace tace "In koma gida ince ma yarana xan yi aure? Me ye nake nema a duniya a yanxu? Me yarana suka rage ni da shi da xai sa inji ina sha'awar yin aure? Plss come off this barrister" Ya lumshe ido ya bude yace "Noo Rahinah, ba don kin rasa komai xaki yi aure ba sai don auren shine suturar ya mace...." Tana goge hawayen idonta tace "Idan ma sbda tafiye tafiyen da nake yi ne ko sbda Aikina ni naji xan ajiye in xauna gidana dama Junaid ya fi son haka, tun ba yau ba yake son in daina aikina coz ban rasa komai daga garesu ba, ni kuma xaman kadaici ne dama bana so" Kallonta kawai yake, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "I'm sorry I am making you cry this much, I'm sorry Rahinah" tayi murmushin karfin hali tace "It's okay...." A hankali yace "Xa mu ci gaba da magana amma ba ynxu ba, it's almost time for zuhur, but...." Jin yyi shiru ta kallesa tace "But?" Ya sakar mata murmushi yace "Ban hakura ba, anyway that aside xan baki yarinya ki tafi da ita, for now marainiya ce bata da kowa...." Da mamaki take kallonsa tace "Ban gane ba, a ina ka samo ta..." Briefly ya 6ata labarin Heedayah, wanda hakan yasa jikinta yyi sanyi tace "Allah sarki, Allah ya bayyana iyayenta, I will go with her in sha Allah" yace "Yes I know u will Rahinah, sai dai I didn't made mention of her blindness to you, she's blind" xaro ido tayi tace "Blind??" A hankali ya gyada mata kai, tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" yace "Tana mota ita kadai, mu tafi ki ganta" a tare suka fita eatery din, sai da suka kusa motarsa a hankali tace "Matar ka tace baxata riketa ba kenan?" Ya juya ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Ehh" Ta girgixa kai tace "Toh Allah ya kyauta" yace "Ameen, amma a gidana Heedayah xata xauna, she will stay with u just for few days let me settle down things" Bude mota yyi Heedayah ta juya direction din da sauri fuskarta duk hawaye tace "Abba" ya kamo hannunta yace "Kuka kike yi daughter" cikin rawar murya tace "Naga baka dawo ba" ya share mata ido yace "I'm back dear, xaki bi Maminki gida yanxu kin ji?" Tace "Abba ina xaka je?" Yace "Xan je in siyo maki sabbin kaya ko baki so" tayi shiru bata ce komai ba, Hajiya Rahinah dake ta kallon Heedayah da tausayi tace "Ba dadewa xai yi ba baby, mu je gida kafin ya kawo maki kayan" daga haka ta sauketa a motar, ya kalleta yana murmushi yace "Thanks Barrister, sai na xo anjima" ta gyada masa kai ta nufi motarta da Heedayah, sai da ya ga fitansu sannan ya ja motarsa ya bar Haraban eatery din shi ma. Hajiya Rahinah na parking a parking space ta bude motar ta fito, wata yarinya da baxata haura sha hudu ba ta iso gun motar tace "Mami sannu da dawowa" Tana mika mata handbag dinta tace "Thanks dear, har kin gama assignment din?" Tace "Ehh na gama" Mami ta xaga xuwa side din Heedayah tace "Junaid ya xo kuwa?" Yarinyar ta girgixa kai tace "A'a.." bude motar tayi ta sakko da Heedayah, xaro ido yarinyar nata tayi tace "Mami who is she?" Mami tace "Bakuwa" daga haka ta rufe motar tana rike da hannun Heedayah ta nufi entrance din shiga cikin gidan 'yar ta Farida na biye da ita a baya... 07087865788 Hajiya Rahinah na xaune parlonta watching a movie, almost absentminded, lkci lkci take kallon Heedayah da ke xaune kasan lallausan carpet dake tsakar parlon, Short bread ne hannunta tana ci a hankali, irin kallon da take ma kofar kitchen sai kace tana ganin kofar ne da idanuwanta, Hajiya Rahinah ta sauke ajiyar xuciya for the countless time ta girgixa kai, ba karamin tausayin Heedayah take ba har ranta, text ne ya shigo wayarta ta dauka sanin baxai wuce Barrister ba, dai dai nan kuma aka yi knocking kofar parlon, Farida dake xaune dining tana shan cornflakes ta mike ta nufi kofar, bude kofar tayi wani matashi dake tsaye bakin kofar yana kallonta yace "Baki je islamiyya ba?" Ta langwabar da kai tace "Mami tace I should stay behind xata fita ynxu" Xai yi magana ganin Mahaifiyarsa xaune parlon ya shiga ciki da sallama, Farida ta rufe kofar ta koma dining, xaunawa yyi kujeran dake kusa da na mum din tasa yace "Ina yini Mami" tana danna wayarta tace "Lfya lau, jiya baka xo ba Why?" Ya shafa kansa a hankali yace "Mami Uncle ne ya bani aiki, amma kin manta ne nace maki baxan dawo ba" Tace "Ohk, ka kai ma Salma sakonta kuwa" yace "Eh daga can nake, har xan kawo maki Fadil wai xai biyo ni na fasa, kar ya xo yyi ta mana kuka" Tace "Gobe ma Monday akwai aiki ai" Yana kallon Farida yace "Mami wai ke kika ce kar ta tafi islamiyya?" Da sauri Junaid ya dauke kafarsa xai mike jin abu na ta6a sa, bai kai ga cewa komai ba ya ga Heedayah rakube jikin kujeran da yake xaune, Kuri tayi ma kafarsa da ido, ya mike ya dinga kallonta, Mami tayi dariya tace "Kai dai ka fiye tsoro kamar mace" Yace "Mami wacece wnn kuma?" Mami tace "Bakuwa nayi daxu" hade fuska yyi ya canxa kujera ya xauna, Mami ta mike tana kallon Farida tace "Ki dawo nan parlor ki xauna, yanxu xan fita, you make sure baki bar ta ita kadai ba, I will be back soon, kasuwa xan je" Farida ta mike ta dawo parlon, Mami ta nufi Heedayah ta duka tana kallonta ta shafa kanta tace "Kina son wani abu dear?" Gyada kai tayi tace "Xan sha ruwa" Mami tace "Farida ki kawo mata ruwa" Farida ta tafi fridge dauko ruwa, Mami ta kalli Junaid tace "Sai na dawo, I am not staying long" ya mike yace "Ni ma ai wucewa xan yi Mami" tace "Aa ka jira ni, I said I am not staying long" daga haka ta nufi kofa, da kallo ya bi ta har ta fita, sannan ya koma ya xauna yana kallon Farida yace "Who is she? I mean the girl" Farida ta bude hannu tace "Mami came back with her earlier this afternoon" Ya buda ido sosai yace "From where?" Farida tace "I don't know" girgixa kai yyi ya kara satan kallon Heedayah, direction dinsa take kallo, ya d'an hade rai calmly yace "Kin san ni ne kike kallona?" Laluben kasa ta shiga yi tana neman murfin bottle water cikin sanyin muryarta tace "Ni ba kallon ka nake ba" yace "Hoto kike daukata da idon ki idan ba kallona kike ba kenan" Ta d'an turo baki bata ce masa komai ba tana ci gaba da lalube lalubenta, Farida ta koma kusa da shi da sauri ta kai bakinta kunnensa cikin rada tace "Yaya she is blind fa!!!" irin yanda ya yo waje da ido yana kara kallon Heedayah yasa Farida tayi dariya bata shirya ba, ta dinga dariya har da kyakyatawa da saukowa saman kujera, Shi kam kallon Heedayah kawai yake da mamaki ya ma kasa cewa komai, bai ankara ba sai ganin hawaye na sauka fararen idanuwanta yyi, Bai san lkcn da ya mike ba, Farida ma ta hadiye dariyar da take tana kallonta, ya nufeta ya duka kusa da ita yace "Me yasa kike kuka??" Shessheka ta fara yi tace "Xan tafi gun Abba" Farida ta dawo kusa da ita da sauri tace "Yanxu fa Mami xata dawo" Junaid ya kai mata rankwashi a kai yace "She thought u are laughing at her... What's making u laugh that loud at the first place" Farida tace "Kiyi hakuri, ba dake nayi dariya ba wllh" Ita dai Heedayah sai juya biscuit din hannunta take hawaye na xuba idonta, Junaid yace "Kin ji ta baki hakuri, kiyi hakuri kin ji" Shiru tayi masu, ya dafa goshinta yana goge mata hawayen da hannunsa yace "Kin hakura?" gyada masa kai kawai tayi, nan kuma ta daina hawayen, mikewa yyi ya koma kujera ya xauna so relieved ganin ta daina kukan, shi dai fa har sannan ya kasa yrda bata gani don gashi sai kallonsu take tana kifta fararen idanuwan, Farida ta rufe bottle water din ta mike ta koma kan kujera ita ma, Junaid ya dau wayarsa ya shiga gun msg yyi typing kamar haka, "Da gaske bata gani? Don't joke with me" mika ma Farida wayar yyi, Farida na karantawa ta kallesa tayi masa alamar rantsuwa cewar Heedayah bata gani, kara kallon Heedayah yyi da shock, can ya mike ya wuce sama yana kara waigo ta. Farida ta canxa tasha ta maida hankalinta kan movie din da ake yi, bayan kusan awa daya taji muryar Junaid ya sakko kasa yace "Why don't you tell her to lie down Farida?" Farida ta juya da sauri tana kallon Heedayah da ta kwantar da kanta saman kujera tana bacci daga xaunen da take, Farida ta mike tace "Ban sani ba" nufenta tayi ta ta6a ta tace "Ki tashi in raka ki daki" Heedayah ta bude ido da sauri tace "Aa" Farida tace "To hau kan kujera" mikewa tayi ta fara laluben kujeran, shi dai Junaid kallonta kawai yake, Farida ta sa ta kwanta kan kujeran sannan ta koma ta xauna. Shidda da yan Mintuna Mami ta shigo gidan da ledoji manya manya, Farida dake parlon har sannan ta mike tana mata sannu da xuwa ta amshi ledojin, Mami da hankalin ta na kan Heedayah tace "Me yasa kika bari tayi bacci ta yamman nan?" Farida tace "Ina son in tasheta daxu yaya yace in bar ta" Mami tace "Ina yayan?" Kafin Farida tace komai sai gashi nan sakkowa, Mami ta nufi Heedayah ta dafa kanta tace "Dear" bude ido tayi da sauri, Mami tace "Yamma yayi tashi kar ki yi sake bacci" Heedayah tace "Abbana fa?" Mami tace "Ga kaya nan Abban ki yace a kawo maki..." Heedayah ta katse ta tace "A'a ina son in je wajensa" Mami tayi murmushi tace "To yana jiran ki a waje" kallon Junaid Mami tayi tace "Take her outside, xaka ga mota a waje, ka kai ta motar" shiru yyi yana kallon mum din tasa, ganin ko kallonsa bata yi ba sai bude ledojin da Farida ta ajiye take, ya karaso cikin parlon yace "But Mami I thought she's blind how will I take her outside" Mami ta hade rai tace "Kama hannunta xaka yi ku tafi, ko in kai ta da kai na?" Ya girgixa kai yace "Aa" ya nufi gun Heedayah, Farida sai dariya take kasa kasa, ya kamo hannun ta jin haka ta sakko daga saman kujeran, kamar me counting steps dinsa ya nufi kofar fita yana rike da hannunta, Farida ta bi su da kallo tana danne dariyar ta, sai da suka fita parlon, Heedayah dake ta bin sa tace "Ha'an da sauri kake tafiya xan je in fadi" kallonta yyi sannan yace "To ba sai ki fadi ba" Bata ce masa komai ba har suka fita gate, ya nufi motar da ya gani a bakin gate din, Bude motar aka yi barrister ya fito, ganinsa Junaid ya yi kasa da kai ya gaishesa da ladabi, Abba ya amsa da fara'a yace "How are you doing Junaid?" Yace "I'm fine sir" Abba yace "Ashe ka dawo, kuna hutu ne?" Junaid yace "Ehh Abba mun yi hutu" Abba yace "To maa Sha Allah, Allah ya taimaka son" Junaid yace "Ameen nagode" Heedayah sai murmushi take jin muryar Abba, ta fara lalube lalube xata ta6a sa, Murmushi yyi ya duka kusa da ita ya kamo hannunta yace "How are you my dear?" Ta fada jikinsa a hankai tace "I am fine Abba, are you taking me with you now??" ta gefen ido Junaid ya dinga kallonta, nan kuwa he is trying to vividly recall weda he said anything bad daxu da turanci da yyi magana da Farida.... Abba yace "No, xaki tsaya tare da Mami kinga ni xan tafi aiki ne" tayi shiru bata ce komai ba, amma gaba daya mood dinta har ya canxa, yace "Ga kaya Mami ta siya maki da yawa sai ki ce mata thank you idan kun koma ciki" a hankali tace "Ohk" yayi patting kanta yace "Good girl" cikin sanyin murya tace "Abba yaushe xan koma gun Ammina da Abbuna?" Tana magana har hawaye ya kawo idonta, Shiru yyi yana kallonta, can yace "Soon daughter, in sha Allah soon xa ki koma wajensu" mikewa yyi yana kallon Junaid yace "Ku koma ciki Junaid" Junaid ya kama hannunta yace "Toh Abba Allah ya kiyaye hanya" Abba yace "Ameen" Sai da suka shiga gate sannan Junaid ya kalleta yace "Ina Ammin taki da Abban ki???" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Baki ji na ne?" A takaice tace masa "Ehh" tsayawa yyi da mamaki yana kallonta, can ya saketa ya koma gefe ya tsaya yace "To ai sai ki kai kanki ciki" ⚡ _Heedayah_ ⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 Da asuba bayan an idar da sllh a masallaci da kusan minti sha biyar Shuraim ya mike ganin Abbansa xai fita masallacin don dama shi yake jira, sai da suka fita masallacin ya isa gun Abban nasa, ya d'an risina yace "Barka da asuba Abba" Abba ya kallesa ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Yauwa...." Shuraim na biye da shi yace "Abba dama ina son baka hakuri ne kan abubuwan dake faruwa...." Abba ya katse sa yace "A'a kaje dai ka ba babarka hakuri, ita ta fi daukan abun da xafi, sannan kuma dama a bayanta kake as always" Ya girgixa kai yace "A'a Abba, ba wai ina bayanta bane, just that muna tsoron abinda xai je ya dawo ne a kan lamarin...." Abba yyi murmushi yace "Ehh gaskiya ne Ali, barin ma da ya kasance cewar duk abinda yaro ya hango ba lallai babba ya hango ba" Shuraim yace "A'a ba haka bne" Abba yace "No haka ne" Shiru Shuraim yyi yana dai biye da Abban nasa, can yace "Toh Abba tana ina yarinyar ynxu?" Abba ya tsaya ya juya yana kallonsa yace "Do you have any problem with that?" Bai iya yace komai ba, Abba ya watsa masa wani kallo ya ci gaba da tafiyarsa, Har suka shiga gida babu abinda Shuraim ya sake ce masa. Reaction din Abban nasa bai hanasa bin sa har cikin parlonsa ba, Abba ya xauna saman kujera ya dau remote xai powering TV, Shuraim ya xauna kasa daga gefensa, a hankali yace "Kayi hakuri Abba, ni ban ga aibun abinda kayi ba haka ma ban ga aibun abinda Mumy tayi ba, she's right in many ways" kallonsa kawai Mahaifin nasa yake, can ya girgixa kai yace "Baxa ka ta6a yin alkibla ba dama, look... Ur mother like it or not dole gidan nan Heedayah xata xauna har sai naga she's back to her parent, idan ku ka ga Heedayah bata dawo gidan nan ba to iyayenta ne Allah ya bayyanar, amma I mean it, bbu abinda xae hana hakan, kuma tare xata dawo gidan nan da matar da xan aura ta kula da ita, ur mother can do whatever she want bbu wanda ya isa canxa ra'ayina" Shuraim dake kallonsa da wani expression yace "Abba aure?? I'm sorry to say... you want to spoil ur home because of a mere little girl da baka san ma me ya rabata da iyayenta ba, baka san daga inda ta fito ba, think about it plss Abba, this is wrong" Abba yyi wani murmushi yace "It's my home not urs, ko da wasa ai baxa ka gaya ma uwarka irin wannan maganar da kake gaya min ba yanxu, ni kuma ga abokin rainin ka, check out pls my frnd" Mikewa Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Kayi hakuri" daga haka ya fice daga parlon, lkci daya ya hade rai bayan ya fita ya nufi dakinsa, who the hell is this forsaken girl that's trying to cause confusion in their home.... Muryar Mumy yaji tace "Ya aka yi Shuraim? What's wrong?" Tsayawa yyi ya juyo bbu walwala yace "Ina kwana Mumy" tace "Lafiya lau, ya naga ranka a bace haka?" Yyi kasa da kai yace "Nothing mum, xan shirya ne yanxu" daga haka ya juya ya shige dakinsa, sarai tasan daga parlon Abbansa ya fito, ta d'an yi jim kamar me naxari sannan tayi murmushi ta juya ta nufi dakinta a ranta tace Idan barrister ya san wata bai san wata ba ai.... Karfe sha biyu saura na safiyar ranan barrister ya isa gidan Yayansa Dr Umar, yana shiga main parlor bangaren Mahaifiyarsu ya nufa, ya bude kofar parlon tare da sallama, a guje kaka ke kokarin boye bowl din gabanta tana cewa "Naga fitina waye kuma wannan" d'an murmushi yyi ya karasa cikin parlon, tace "Au ashe Amadu ne, wllh na xata yaran nan ne masu halayyar bera, to idan na ajiye d'an nama na da cin cin sai su bi dare su yashe...." Abba yace "Ina yini Baaba?" Kaka tace "Lfya lau Amadu, ya aikin" yace "Alhmdllh, ke daya ce gidan kenan" Da sauri tace "To da fa?? Ai Kullum a haka suke bari na, kar fa kayi xaton basu gidan, duk suna nan wllh, dama wannan yaro Aliyu ne me shigo min, shi ma kuma na koresa gaskiya, don raini ya shiga tsakanin mu" Abba yace "Daga gun aiki nake nace bari in xo mu gaisa" Kaka tace "To ae ka kyauta, Allah yyi maka albarka, Wai ya maganar da kayi ranan na cewa xaka kara aure ne naji shiru" yace "Ehh dama xan gaya maki maganan na nan in sha Allah..." Kaka na washe baki tace "Toh Alhmdllh, yar ina ce?" Yace "Nan kaduna" kaka tace "Abu me sauki, to ni dai Allah ya sa ta kirki ce, don Maryam ta gasa mana Aya a hannu gaskiya, to ta amince xata rike yar makauniyar??" Abba yace "Ehh ba matsala" kaka tace "Atoh ita da ke tsoron Allah kenan, Maryam ae shaidaniya ce sanye da kaya irin na mutane" Abba ya mike yace "Bari in je kaka sai na shigo ko gobe" Kaka tace "Toh, ni dai haka nn nake sae bin yara nake ina rokon hamsin, dari, suna xagina suna ba ni" Abba ya juya yana kallonta da sauri, ta tsuke fuska tace "A'a kai ba ubana bne da xaka min kallon tuhuma Amadu, idan gantalalliyar dubu ashirin din ka ce ta shekaranjiya to ta kare tun jiya wllh" Bai ce komai ba ya nufi kofa ya bude yace "Sae anjima" Daga haka ya fita. Hajiya Rahinah ce xaune tare da Barrister kan kujerun dake karkashin inuwar bishiyar tsakar gidanta, barrister ya ajiye wayar hannunsa yace "Sae kuma kika yi shiru" Sae a sannan ta kallesa tace "Ehh shirun naga xai fi, barrister in dae har sbda wannan yarinyar kke son aurena, ina nufin indan sbda in riketa ne to kar ka damu ni me iya rike little girl din ne har bayyanar iyayenta idan Allah ya yrda, ina hada ka da Allah ka rabani da xancen auren ka, bbu aure a tsarin rayuwata ynxu...." Shiru yyi yana kallonta, sannan ya d'an yi murmushi yace "Sae dai fa kiyi hakuri Rahinah, you can't stop me from marrying you, Heedayah kuma gidana nake son ta xauna ba wani waje daban ba" Mami ta tabe baki sae dai bata ce komai ba, Budewar gate ya sa duk suka juya, Junaid ne ya shigo compound din hannunsa rike da Makullin mota, har ya isa inda suke ya fara gaida Abba sannan ya gaida Maminsa, Abba yace "Kana aiki ne Junaid?" Yace "Ehh ina aiki tare da Uncle dina a hospital dinsa" Abba yace "To that's good ya fi ka xauna, Allah ya taimaka" Yace "Ameen" daga haka ya wuce ciki, Abba ya kalli Mami yace "Ya kusa gama masters din nasa ne?" Mami tace "Ehh months suka rage masa idan Allah ya yrda" Abba yace "Allah ya taimaka" Junaid na shiga parlor ya ga Heedayah ce kadai parlon kwance saman kujera tana bacci, ya dauke idonsa ya wuce sama xuwa bedroom dinsa. Sae kusan la'asar Abba ya bar gidan har sannan kuma bai yi convincing Hajiya Rahinah ba dake kan bakanta na cewa bbu aure a gabanta. Yau dai har sha daya saura na dare Hajiya Maryam na xaune parlor tana jiran ganin lkcn da barrister dake compound yana ta waya xai shigo, yau kwana biyu kenan da ta lura da hakan duk da kasancewar ta mai bacci da wuri yau kam coffee me kauri ta sha tayi xamanta a parlor tana jiran ganin ikon Allah, lkci lkci take tashi ta leka waje ta dawo, lekawar da tayi na karshe ne taga ya gama wayar xai shigo ciki, da sauri ta shige kitchen ta kulle don ma kar ya san idonta biyu, sae da taji ya wuce part dinsa sannan ta fito ta dinga xaga parlor tana jiran ya kwanta sanin bashi da wuyar bacci, a haka Shuraim ya sakko downstairs ya sameta, ganinta da mamaki yace "Mum baki kwanta ba" Tace "Ehh yanxu dai xan je in kwanta na gama kallon wani film ne" Bai ce komai ba ta wuce sama shi kuma ya shiga kitchen, sae da taji Shuraim ya shiga dakinsa ta fito ta nufi part din mai gidan nata, a hankali ta bude kofar parlonsa ganin wuta a kashe ta gane ya kwanta, ta lallaba ta nufi daki tana tafiya a hankali, tana shiga duk da wutan a kashe yake tasan yyi bacci ta tafi inda tasan yana ajiye wayarsa ta dauka ta fita daga dakin, bangarenta ta koma ta bude wayar ta shiga call log dinsa, Number da aka yi saving da Great barrister taga last call dinsa, nan ta duba taga yana yawan kiran number, msg ta shiga tayi scrolling har xuwa farko, hankalin ta ya fara kwanciya ganin kawai text ne da ya shafi aiki, a hankali ta fara gwalo ido bayan tayi nisa ganin salon message din ya fara sauyawa har ta kai karshe, xufa ne ya karyo mata ta ajiye wayar ta rasa tunanin da xata yi, can ta dau wayarta ta kwashe number tas sannan tayi dialing, sae da ya kusa katsewa aka daga, daga daya bangaren Mami tayi sallama, shiru Hajiya Maryam tayi xuciyar ta na bugawa jin muryar mace, kawai ta katse ji tayi kamar ta daura hannu a ka tayi ta ihu, ta xauna gefen gado tana furta innalillahi, kallon wayarta tayi, sae kuma ta shiga call log tayi dialing wani lamba, yana fara ring aka dauka, Ta hadiye abu da kyar tace "Sadiya wllh da gaske Barrister neman aure yake, Ashe da gaske yake wllh, gashi ynxu na bincike wayarsa kaff har na samu lambar warce yake nema da aure, na shiga ukuna Sadiya, da yarinta ta ba a min kishiya ba sai yanxu a kan wata shegiyar yar tsintuwa makauniya...." Ta fashe da matsanancin kuka tace "In dai Alhaji yyi auren nan ai tawa ta kare, dariya xa ayi min a gari ki bani shawara don Allah kawata, wllh dariya makiyana xa su min" Hajiya Sadiya dake saurarenta baki bude tace "Aure fa kika ce Maryam?? Ke sai ki yrda ki barsa yyi auren? Toh ynxu dai ae sai ki wanke kafarki mu tafi inda kike ikirarin bbu abinda xai kai ki" Hajiya Maryam tace "Ina???" Hajiya Sadiya ta kyalkyale da dariya tace "Wa enda kike raina taimakonsu mana...." A fusace Hajiya Maryam tace "Allah shi kiyaye, tun da can da kuruciyata ban ta6a xuwa ba sai ynxu a kan yar yarinyar da na haifa?? Yar cikina? Ni nan da kike gani na ishi kowa wllh, Kuma muna nan dake auren nan baxae ta6a yiwuwa ba ni nasan me xan yi, ke dai kawai ki xo gobe don Allah, sae da safe" daga haka ta katse wayar, ta kusa awa daya xaune kafin ta iya tashi ta mayar masa da wayarsa ta dawo dakinta, daren ranan bata yi baccin kirki ba, Wai ita barrister xai ma kishiya sbda taki rike makauniya??? Tayi kwafa ta juya tana jiran dai gari ya waye. Mami na xaune tana ma Heedayah gyaran dogon gashinta dake ta kyalli, yau ma dai bata je aikin ba don har lkcn bata samu wanda xai kulan mata da Heedayah ba, Farida kuwa na boko daga safe har 6, wayarta ne ya fara ring ta dauka ta kai kunne, sallama aka yi mata daga daya bangaren ta amsa, Hajiya Maryam dake xaune dakinta da Hajiya Sadiya da wata kawarsu Hajiya kyauta tace "Don Allah da barrister nake magana" Mami tace "Yes, wacece ke magana?" Hajiya Maryam ta gyara xama tace "Toh Barrister wata yar matsala ce wllh ta taso mana muna neman lawyer, shine wani abokin aikina ya bani lambar ki, yyi assuring dina you can help..." Mami tace "Allah sarki sai dai na dau hutu baxan yi aiki ba cikin satin nan gaba daya" Hajiya Maryam ta gwalo ido tace "Don Allah ki taimaka barrister, ya gaya min irin kirkin ki da taimakon ki, ke kadai xaki iya rufa mana asiri kan lamarin nan, don Allah barrister ki dubi girman Allah ki sauraremu, wllh muna cikin tashin hankali sosai" Mami tace "Kar ki damu malama xan hada ki da wani barrister, he is also good xama ki ji dadin nasa aikin fiye da nawa, I can send you his number now" da sauri Hajiya Sadiya tayi ma Hajiya Maryam alamar tace mata to ta turo... Hajiya Maryam tace "Toh ngd Barrister, Allah ya saka, ina jiran lambar" Mami tace "Kar ki damu, let me send you" daga hka ta katse wayar, cikin few seconds ta tura ma Hajiya Maryam number Barrister Ahmad, Hajiya Maryam da ta ji kmr xuciyarta ya fashe cikin tashin hankali tace "Na shiga uku, kun ga lambar mijina ta turo min dai koh???" Hajiya Sadiya tace "Toh sake kiranta" hannu na rawa ta sake kira, Hajiya Sadiya ta amshe wayar tace "Ki dubi girman Allah Barrister ki bamu lkcn ki ki saurari matsalar mu, an ce mana ke ce maganin kukan mu, wllh ko nawa kika bukata xa mu biyaki domin Allah ki taimake mu..." Da mamaki Mami tace "Wnn barristern da na tura maki numbersa ya ma fini iya aiki, xae saurare ku fiye da ynda ni xan saurare ku" da kyar da kyar suka shawo kan Mami kan ta amshi case dinsu, Mami ta girgixa kai tace "Gaskiya baxan fita gidana ba ynxu, sae dai ko ke ki xo ki sameni" Hajiya Maryam tace "Wnn ae ba matsala bane, bari in taho ynxu ma, Allah ya kara girma da daukaka Barrister, ki turo min address din plss" Mami tace "Ameen, xan tura maki ynxu" daga hka ta katse wayar, ta tura address din nata, Hajiya Maryam tayi wani murmushi ta mike ta dau mayafi da Makullin mota jikinta har wani 6ari yake tace "Ku mu je" fita duk suka yi suka bar gidan a motarta. Gane gidan Hajiya Rahinah bai masu wahala ba, suka yi parking a waje bayan sun sanar ma Mai gadi Hajiya Rahinah suke nema kuma ta san da xuwansu ya bar su suka shiga cikin gidan. Har entrance din shiga gidan suka nufa suka tsaya, Hajiya Sadiya ta danna bell, Mami da ta saka Heedayah gaba tana mata tambayoyin ynda aka yi har ta fito gida.... exactly labarin da Heedayah ta bada a station ta sake ba Mami, ta kare da cewa sai taji ana tafiya da ita a bicycle kawai sai ya wuce ya bar ta bai kai ta gun Amminta ba kuma, tana fadin haka ta fara hawaye, Mami dake ta naxarin d'an labarin ta gane daga all indication kidnapping yarinyar aka yi sai kuma Allah ya kubutar da ita, mikewa tayi jin an sake danna bell for the third time ta nufi kofa ta bude tana kallonsu Hajiya Maryam, Hajiya Maryam ta kirkiro murmushi tace "Sannu fatan ke ce barristern?" Mami tace "Oh, okay ga kujeru can bari in fito yanxu, ku jirani a can" Hajiya Maryam ta saka kai ta raba ta gefenta ta shiga ciki, tace "A'a xai fi daga cikin dai barrister, tonon asiri ai ba dadi" sauran ma duk suka shige ta gefenta, kallonsu Mami tayi da d'an mamaki, Hajiya Maryam ta isa tsakiyar parlon tana kallon Heedayah da wani expression, sauran kawayenta ma duk suka tsaya kusa da ita suna kallon Heedayar, Kasancewar Mami lawyerr yasa lkci daya ta gane abinda ya kawo matan nn gidanta ba abinda suka ce bane, Hajiya Maryam tace "Toh kinyi tsaye bakin kofa ae sai ki karaso ki ji case din mu koh barrister?" Heedayah dake xaune saman kujera da apple a hannunta ta mike da sauri don in dai ta ta6a jin murya to baya ta6a bacewa a sense of hearing dinta, ko da kuwa an dau lkci sosai sai ta gane muryar duk inda taji, Mami ta karaso parlon tace "Bana bukatar jin case din ku, domin bana hulda da Yan tasha, ku kai case din ku wani wurin, and ku fitar min a gida immediately now...." Hajiya Maryam tayi wani dariyar rainin hankali tace "Koh?? To sai ki fitar da mu ta karfi Mai gida, bari ki ji..... ba barrister ba, ko judge ce ke na xo ne in yankar maki lafiyayyen wani ki fita hanyar mijina Barrister Ahmad, shi ba gantalalle bane irin ki, kin gama xaga duniya kinyi yawon karuwancinki shine xaki wani makale masa ya aure ki sbda baki da tunani ko? To wllh kin yi kadan, mijina ba sa'an auren ki bane, Ashe ke ya kawo wa shegiyar yarinyar nan kika karba kika rike tunda dama kina sonsa da aure, to don kaza kazan ki nace baki isa ba, mijina ni kadai ne shi din, baxan hada shi da karuwa ba yar boko da ke yawon duniya don ma kiji, don haka tun wuri ki san inda dare yyi maki" Tunda ta fara Mami ke kallonta, duk da maganganun sun ma Heedayah girma ba duka xata iya ganewa ba hakan bai hanata dinga kuka ba tana kiran Mami, Mami ta nufi gun wayarta ta dauka cikin few seconds tayi dialing number Abba, yana fara ringing kuwa ya daga ta sa hands free tace "Ahmad kana ji na?" Yace "Yeah ina ji my barrister, ya gidan?" Tace "Alhmdllh, dama nace ne you can come forward with ur pride price to my elders ko gobe, na karbi tayin auren ka idan Allah ya yrda" Yace "Da gaske kike barrister, pls don't joke with me" farin ciki ne sosai tare da words dinsa, Mami tace "I'm not joking barrister, na baka go ahead, we will talk later in sha Allah" daga haka ta katse wayar, Hajiya Maryam da wani xaxxafan xufa ya keto mata ta dinga kallon Mami so speechless, Mami ta isa gabanta ta tsaya tace "xa mu shigo gidan barrister Ahmad tare da wannan yar yarinyar nan da sati daya, sai dai ciwon xuciya ya kashe ki a banxa, sannan wnn yarinyar da kike gani ita xata xamar maki nightmares dinki kafin ni.... Lastly kin ci sa'ar mijinki na da k'ima da daraja a idona sannan ga soyayyar da nake masa, wllh da yau bbu abinda xai hana ke da mahaukatan kawayen ki kwanan cell kuma in ga uban da xai bada bail dinki, amma soyayyar mijin ki baxai bar ni inyi hakan ba..." Tana fadin haka ta ja hannun Heedayah suka fita xuwa gun mai gadi tace "Salisu ka tattaro abokanan ka masu gadi ka fitar min da wasu mashaya da suka shigo min gida, and from henceforth duk wanda ya xo ka fara sanar min kafin ya shigo" da sauri ya fita yin yanda tace. Start patronizing Heedayah lovely fans.... last free update later at night in sha Allah😍 07087865788..... ⚡ _Heedayah_⚡ _By Khaleesat Haiydar_✍🏻 Tun da Hajiya Maryam suka dawo gida da kawayenta take kuka kamar ranta xai fita, ji take kamar ta bude ido taga cewar duk mafarki take, ya xa ayi Barrister ya mata kishiya bata mutu ba?? Hajiya kyauta tace "Ke Maryam bari ki ji in gaya maki, idan xaki share hawayen ki ki san nayi ki share, don 6ata lkcn ki kawai kike, wllh wannan kukan baxai fisshe ki ba, wajen nan dai da baki son xuwa dolen ki nan xa aje da ke yau a san nayi, don wnn mata ni dai da kamar wuya mijin ki ya fasa aurenta duk haukan ki kuwa, na farko in dai kyau ne baxa ki nuna mata komai ba, ke diplomar ma da ya kika kare? Ita kuwa lawyer ce fa me xaman kanta, kinga kenan ta kure karatu, ga shi da gani dai kin san ba cikin wahala take ba tana da kudin ta, ke dake buga buga ki raruma gun miji fa?? ni wllh ba karamin kwarjini matar ta min ba ma, da ba ku fito ba dama ni wucewata xan yi kar ta sa a daure mu kamar yanda tace" Hajiya Maryam ta katse ta a fusace tace "Ni fa da ku ke gani nan babu abinda ya isa kai ni gun malami a duniyar nan, ku dai ku bar ni inyi ta kai na kawai idan baxa ku bani shawara ba, ni kadai raina na ishi kowa, wllh karuwar nan baxata shigo min gida a matsayin kishiya ba, muna nan da ku kuma xa ku ce na fada, ita kuma wnn makauniyar dama sai dai ta kara shiga duniya wani ya tsince ta a wani garin amma ba mijina ba...." Tana kai wa nan ta mike ta dau gyalenta tana share idonta, Hajiya Sadiya tayi wani dariya tana kallon kyauta tace "Bar ta, xata dawo ta same mu ne ai" Ficewa Hajiya Maryam tayi daga dakin rike da makullin motar ta..... Direct gidan Dr Umar ta nufa, yau dai ko shiga bangaren matan gidan bata yi ba ta nufi gun kaka, da sallama ta bude kofar parlon kaka dake uwar daka ta fito da sauri tana cewa "huuu Ko waye don Allah ya share kafarsa ga tsumma na ajiye bakin kofa, wllh kazamai ne matan gidan ko sharan kirki basa yi a makeken parlon nan nasu sai a tattako a xo a yasar min a nawa parlon...." Hajiya Maryam ta dinga goge kafarta a tsummar kamar an aikota, kaka tace "Aa Maryam daga ina haka da sassafe kuma" Ta karasa cikin parlon ta xauna kasa cikin sanyin murya tace "Daga gida kaka, ina kwana" Kaka ta xauna tace "Lafiya dai naga idonki a kukkumbure ko Balaraba ce ta rasu??" Ta fashe da matsanancin kuka tace "Ba lafiya ba wllh kaka...." Kaka tace "Ikon Allah me ke faruwa Kuma? Ni dai jiya Amadu ya shigo min da rana wai ya xo gaisheni a nan kuma yake ce min wai aure xai kara har ya samu matar yar kaduna ce, ni dai nace masa ba ruwana, ana xaune lafiya fitina ya shigo ciki, to daga haka ni bai ce min ga abinda ke faruwa a gidansa ba...." Cikin kuka sosai Mumy tace "Abinda ya kawo ni kenan ma kaka, wai aure fa xai kara...." Kaka ta saki salati tana tafe hannu tace "Ohh ni na ga abinda ya isheni ni Rahamar ubangiji, me Amadu ke nema a duniya da xai kara aure ana xaune qlau, ni dai yana gaya min ce mashi nayi ba ruwana, don bn san kan xancen ba...." Mumy ta share idonta tace "Idan ma sbda wnn baiwar Allahn ce ya kawota kawai xan riketa na amince" iyakar wnn furucin da Mumy tayi bakinta, don kuwa ta sha alwashin ko an fasa auren aka kawo mata Heedayah sai ta sake lulawa da ita wani duniyar daban, duniyar ma na kauye, can xata sa aje a wurgar da ita don ma kada mistakenly wani me rufin asiri ya dauketa har ya taimaka mata, a yanxu dai duniya bbu wanda taji tana tsana kamar wnn yar yarinyar, har ta mance rabon ta xubda hawaye ta shiga tashin hankali da xai hanata bacci sai a dalilin Heedayah, Kaka tace "Aa ni ya kawo min ita ma nan kawai xan riketa, kar a ja maki kaffara kina xaman xamanki, dama bbu me min wanke wanke da shara tsigalallun yaran nan duk ba kulasu nake ba ta kaina nake" Mumy tace "Makauniya ce fa kaka" kaka tace "To makafi basa wanke wanke da shara aka ce maki Maryam, ai dai naga ba kuturwa bace, sai in kada mata kumfar in sa mata ruwan dauraya in ajiye mata kwanukan in xaunar da ita ta wanke min su tass" Mumy tace "Aa kaka wahala kawai xata baki, ni din dai xan riketa, ai d'a na kowa ne" Kaka tace "Atoh dai, ki kwantar da hankalin ki kawai, bbu wani xancen kara aure in dai da raina tunda xaki riketa, to idan ba toxarci Amadu ke son mana ba meye kuma karin aure ana xaune kalau, wannan ne kuma bai haifu ba gaskiya don baxan yrda ba" Mumy taji hankalinta ya d'an kwanta, tana share idonta tace "Toh shkkn kaka nagode" Kaka tace "Haba godiyar me kuma, ai yi ma kai ne, yanxu shawarar da xan baki a nan shine ki dau kayan ki kala daya ko biyu ki tafi gidanku, idan ba haka kika yi ba Amadu baxai dawo hankalinsa ba, ki tafi da fitsararrun 'ya yan nan naki ki bar masa gidan ba kowa sae kujerunsa da tv, nan xaki ga ya shiga taitayinsa wllh, kaddai ki gaya ma wnn dunkum din d'an naki kudurin ki don wllh hana ki xai yi ya cuce ki, ki bar masu gidan shi da ubansa kawai" Mumy da ke kallon kaka tana jinjina shawarar ta a ranta, tayi murmushi tace "Gaskiya ne kaka, hakan xan yi in sha Allahu ina komawa kuwa" Kaka tace "Atoh maxa tashi ki tafi tun yanxu ki hada hada kayan, ai mu xamaninmu haka muke yi, idan miji ya musguna maka ka hada kayanka ka bar masa gidan sa, xo ki ga yanda hankalinsa xai tashi kuwa...." Mumy ta mike tace "Toh sai anjima kaka, nagode sosai, Allah ya kara girma, sai mun yi waya" daga haka ta fita, kaka ta bi ta da kallo har ta rufe kofa sannan ta ta6e baki ta juya ta koma cikin dakinta tana cewa "To ai idan Amadu ya fasa auren nan ma ni sai naji dalili wllh, da kaina xan kai sadakin auren, huuu wai ba kunya ba tsoron Allah matar da ke bari na da yunwa me saka min nama tsoka daya ce wannan fa jama'ah, Ehh lallai duniya ya lalace....." Da yammacin ranan Abba ya tafi gidan Barrister Rahinah don sake tabbatar da abinda ta gaya masa a waya da safe, nan ta nuna masa she is serious, ko da wasa bata sanar masa cewar Hajiya Maryam ta xo gidanta ba, yana murmushi yace "Toh nagode Rahinah, in sha Allah gobe xa mu je can gun kawun ki..." Mami tace "Allah ya kai mu...." Basu wani jima ba ta koma cikin gida don tace masa girki take, shi kuma ya wuce. Mumy na komawa gida dama ta hada kayanta ynda Kaka tace mata, ta hada har da na su Khadijah da Rabi'ah ta bar gidan, makarantar su ta fara biyawa ta sanar masu inda xasu sameta idan an tashi sannan ta wuce gidan kanwar Mahaifiyarta dake nan kaduna. Mami ce xaune study area dinta tana kallon files din gabanta, gaba daya mood dinta isn't okay, ta kasa gane ko she is making the right decision marrying barrister, har xuciyarta tana son taimakon Heedayah amma ba irin taimakon da xai kai ta ga aure ba at this stage, ta jinginar da kanta da kujera tana tunanin ta ina xata fara sanar ma yaranta wannan xance me girma, amma kuma ai idan bata Aure Barrister ba ta 6ar matarsa ta ci bulus kenan, ta shigo har gida ta yi mata cin mutunci sannan ta bar ta haka nan, muryar junaid taji yace "Mami aiki kike?" Ta daga kai da sauri ta kallesa don bata ji shigowansa ba ma, ta mayar da glass din da ta sakko idonta tace "Sure, ka shigo kenan" yace "Nayi sallama naji shiru" ya ja kujera ya xauna yace "Mami this two days naga kamar kina da damuwa, meye matsalar ki gaya min" shiru tayi kuma bata daga kai ta kallesa ba, yace "Talk to me Mami" ta sauke ajiyar xuciya tace "Junaid barrister ne ya xo min da xancen da ya saka ni cikin damuwa kwarai, I don't know I am really confuse junaid...." Yana kallonta sosai yace "Me ya faru Mami?" Ta kuma yin shiru, bayan few seconds taga bbu wani amfanin boye boye kuma, nan ta sanar ma d'an nata intention din Barrister Ahmad a kanta, junaid bai iya ya ce komai ba na kusan second talatin, can dai yyi gathering courage ba tare da ya kalleta ba yace "Toh, idan hankalin ki ya kwanta da hakan Mami, Allah ya sa shine mafi alkhairi a gare mu baki daya" kallonsa kawai take bata ce komai ba, ya mike yace "Na xo daukan system dina ne" daga haka ya wuce sama ta bi sa da ido, dakin Farida ya bude, ya ga Heedayah kwance edge din gadon tana bacci, riga ne da wando jikinta kamar dai 'yar turawa, he wondered if she is neva tired of sleeping, karasawa cikin dakin yyi walking slowly ya isa kusa da gadon yana kallonta, a hankali ya mayar da ita tsakiyar gadon ya gyara mata dogon gashinta dake rufe idonta, jin an bude kofar dakin ya mike tsaye da sauri, kafin Mami tace komai yace "A gefen gadon na sameta...." Mami ta gyada masa kai kawai, ya juya ya fita dakin.... Da daddare Barrister ya tafi gidan Yayansa, bayan sun gaisa da kaka yace "Na je can gida na tarar Maryam ta kwashe yara sun bar gidan Baaba" Kaka tace "Kila ganin gida taje...." Shiru yyi yana kallon mahaifiyar tasa, kaka tace "Toh ina dama xata je idan ba ganin gida ba, ai ta kwan biyu bata je ba, kaga kai kuma kafin ta dawo sai amaryarka tayi kokari ta tare xuwa nan da ranan juma'ah tunda yau talata, wannan makeken bangaren da nake sauka sai ka sa a gyara ma amaryar ayi fenti da komai da komai kawai, ita kuma Maryam ban ce ka kirata ba balle kace xaka mata fada, uwarta taje gani...." shigowar Baffa ya sa Kaka tayi gum, ta sauya xancenta. Ranan juma'ah aka daura auren Barrister Ahmad da Barrister Rahinah, though they did it in a confidential way, bbu wani gayya, duk abubuwan nan dake faruwa Hajiya Maryam na can ta lula xuwa gidan wata childhood frnd dinta a Zaria tare da su Rabi'ah wai kar barrister ya biyota gidan kanwar mamarta, ita a dole sai ta basa wahala, Shuraim kadai take kira don samun update, sai dai me? Shi ma bai san da auren ba sai a ranan juma'ar, shi ma kuma da asuba Abban nasa ya sanar masa a masallaci da suka hadu, he was so shock ya ma kasa cewa Abban nasa komai, haka nan Abba ya wuce ya bar sa wajen a tsaye, ita kanta Hajiya Amina mum din su Sudais ranan ta ji xancen daurin auren daga bakin Baffa da safe, nan tayi ta kiran Hajiya Maryam amma wayarta a kashe, bata fasa kira ba har sai da aka daura wnn aure amma bata samu Mumy ba..... Washegarin ranan da ya kasance Saturday Mami xata koma can gidan Barrister Ahmad, shopping suka tafi tare da Heedayah, Farida da First daughter dinta Amira dake aure a Abuja, su dai sun yi farin ciki da auren mahaifiyar tasu kilan hakan ya rage mata damuwa sosai, don duk sun san barrister Ahmad, A cikin mota Amira tace "Kinga yanxu Mami sai ki bar ni mu tafi da Farida sai ta dinga xuwa maki hutu kawai ko" Mami dake ta tunanin makomar autar tata tun bayan da aka daura aure don bata ta6a jin tafiya da ita gidan barrister ba, baxai ma yiwu bane, ta kalli Amira tace "Alright dear" Amira na dariya tace "Kinga cikin ruwan sanyi kin bani ita" Babban shopping mall Mami tayi parking suka fita, Amira na rike da hannun Heedayah suka shiga ciki gaba daya, shopping sosai Mami tayi, yaranta na taya ta, Mami da ta lura Heedayah ta gaji da jan ta da ake ta yi, duk ta yi wani laushi, kana ganinta kasan ko kadan bata sa6a da wahala ba koma wani iri, Mami tayi murmushi ta samu kujera nan kusa da counter ta xaunar da ita sannan ta koma gun yaranta, a kan idon wani mutumi dake tsaye shelf din turare yana diba, ya cire glasses dinsa yana kallon Heedayah sannan ya kalli Mami da ta sha corner xuwa gun su Amira.... End of free pages The book Heedayah is 300 via transfer Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then u show ur evidence of payment 07087865788 No regrets.... Patronize ur novelist lovely fans, Allah ya maku albarka ya raba ku da iyaye lafiya...💖 Mutumin ya ajiye turaren hannunsa ya isa gun Heedayah ya tsaya dab da ita yana kallonta bayan yyi make sure bbu me kallonsu yace "How are you?" Juyowa Heedayah tayi da sauri, lkci daya ta mike tana waige waige, shi dai bai sake cewa komai ba yana kallonta, kamar xata yi kuka tace "ka dawo xaka kai ni gun Ammina ne?" Jin shiru, ta kai hannu to see if he is still there, komawa gefe yyi yace "Ina Ammin taki take?" Tace "A can gidan Yakumbo mana" xai yi magana ya ga Mami ta tsaya daga inda take tana kallonsu, lkci daya ya juya ya koma shelf din turaren da ya baro, Mami ta nufo Heedayah da sauri ta kamo hannunta tace "Me yake ce maki?" Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka tace "shine ya sa ni a bicycle muka tafi..." Mami ta juya wajen da taga Mutumin ya tafi taga wajen wayam, da ido duk ta bi wajen amma bata ga alamarsa ba, Heedayah da hawaye ya cika idonta tace "Baya son inje wajen Ammina" kama hannunta Mami tayi suka bar wajen har sannan tana kalle kallen mall din ko xata ga wannan mutumi, sai da suka biya abubuwan da suka siya sannan suka tafi mota, Mami na kallon Heedayah tace "But ya akayi kika san shi ne?" Tace "Na ji voice dinsa, shine...." Mami bata kuma cewa komai ba har suka bar shopping mall din. Bayan Magrib Shuraim ya iso gida, rabonsa da gidan tun jiya juma'ah da safe, dama ko wajen daurin auren Abban nasa ma bai je ba, sau daya ya kalli motar Abban nasa dake parking space ya dauke kai, ya fita motarsa ya rufe ya wuce xuwa entrance din gidan, bbu kowa parlon, ya tafi parlon Abbansa, sallama yyi still standing at the door, Abba dake rike da makullin mota alamar xai fita ne, ya amsa masa sallama sannan ya bude kofar ya shiga, Heedayah ce xaune parlon kan lallausan carpet da plate din watermelon a gabanta tana sha, kasa karasawa parlon yyi tun da ya ga Heedayah, sai da Abba ya daga kai ya kallesa sannan cike da kasaita ya karasa ciki, gaba daya bbu wani annuri a fuskarsa, can gefe ya duka yace "Ina yini Abba" Abba yace "Lafiya lau" mikewa yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da ido har ya fita, a compound Abba ya samesa xaune shi dai bai ce masa komai ba ya fita da motarsa da nufin maida Heedayah can gidan Mami. Washegari lahadi Abba ya tafi can gidan Mami don ranan xasu tafi gidan Baffa Mami su gaisa da kaka, Abba ne ke driving Mami na gaban motar Heedayah kuma na baya a xaune, jifa jifa suke magana da ya shafi field din aikinsu, Mami dake danna wayarta ta kalli barrister tace "Hope ba dadewa xa mu yi ba wajen mama coz xa mu yi sallama da Amira nan da sha biyu xa su wuce" Abba ya d'an yi shiru kafin yace "I mean it Rahinah... Farida baxata je Abuja ba, are you trying to show ni ban isa riketa ba" Mami tace "A'a ae hutu xata je, in sha Allah xata dawo soon..." Yace "Wani hutun?" tace "Mid term...." Yace "Am damn serious baxata xauna Abuja ba" Mami tayi murmushi tace "To shkkn" a haka suka isa gidan Baffa, bayan Abba yyi parking ya juya yana kallon Heedayah da tayi lamo jikin motar, yace "Heedayah" ta xauna da kyau da sauri tace "Abba" murmushi yyi yace "Hope ba bacci xa ki yi ba" ta girgixa kai tace "A'a" Ya kalli Mami da ke kallonta ita ma, Mami tayi murmushi tace "Heedayah is more than lazy, tafi son tayi ta bacci" Shiru Abba yyi bayan few seconds yyi kasa da murya yace "Look Rahinah... my mother can be very weird at times kin san ynda tsoffi suke, I know she will welcome you wholeheartedly but.... Akwai halin tsufa dai, so get prepared Mamin Heedayah and Farida...." murmushi kawai tayi, ya bude motar ya fita, ita ma ta fita ta sakko da Heedayah, main parlor Mami ta xauna tana amsa gaisuwan da Yan matan gidan ke mata, Hajiya Hauwa dake kitchen ta fito don ganin su waye, ganin Abba tace "Sannu da xuwa barrister" yace "Sannu Hajiya Jiddah ya gidan" tace "Gida Alhmdllh" da fara'a tana kallon Mami tace "Sannu da xuwa Hajiya, sannun ku da xuwa" Mami na murmushi tace "Yauwa sannu, fatan mun same ku lafiya" Hajiya Hauwa tace "Alhmdllh, you are welcome to the family" murmushi Mami tayi tace "Thank you" Hajiya Hauwa ta tafi dauko ruwa, Abba ya mike ya nufi bangaren Mahaifiyarsu, Hajiya Amina ce ta sakko bayan yaranta sun tafi sun kai mata rahotu sama, tun daga step take kallon Mami har ta kusa faduwa, ta shigo parlon idonta kyar kan Mami tace "A'a Sannun da xuwa Bakuwa, lale marhaba, sannu amarya" Mami ta kalleta ta gefen ido jin salon maganan nata tace "Yauwa sannu" tana fadin haka ta mike tana kallon Hajiya Hauwa da ta ajiye mata ruwa da lemo tace "Hajiya ina ne bangaren mama?" Hajiya Hauwa tace "Mu je in raka ki" tana rike da hannun Heedayah ta bi bayan Hajiya Hauwa, Hajiya Amina ta bi ta da kallo har suka shiga parlon kaka sannan ta koma sama da sauri. Mami na shiga parlon Kaka ta xauna saman babban darduman dake shimfide tace "Sannu Mama" Kaka dake kallonta tace "Yauwa sannu 'yar nan, sannun ku da xuwa" Mami tayi kasa da kai tace "Ina kwana" Kaka tace "Lafiya qlau, kinga ynxun nan na gama karyawa, yau dai ba laifi sun ga daman kawo min karin kumallon da safe, kinsan uwa idan ba taka ba" Murmushi Mami tayi, Abba ya dauke kai daga kallon kaka da yake, Mami tace "To Allah ya rufa asiri Mama" Kaka tace "Atoh, Ameen dai, ni da so nayi ma su bar ni in dinga kayana da kaina tunda ina da karamin kitchen amma Amadu da wansa Umaru sun ki yarda, Kuma fa idan na ci abincin sae inyi ta tashin xuciya tsabar kazantar Yan gidan...." Ba dai wanda yace ma kaka komai, kaka tace "Toh ya sunan naki, kuma yaranki nawa?" Mami ta kalleta tace "Sunana Rahinah, yarana uku" kaka tace "To yaran me ya hanasu xuwa gaisheni bayan an riga an xama daya kuma??" Kafin Mami tace komai Abba yyi saurin cewa "Heedayah You didn't greet grandma" Mami ta daga Heedayah ta maido ta kusa da kaka tace "Greet her" a hankali Heedayah tace "Ina kwana" Kaka da ta saki baki tana kallonta tace "To wnn kuma wani irin kaya ne aka sa mata kamar 'yar anna, abu duk a d'angale jama'ah? Rahilah kike ko wa? Gaskiya kar ki sake sa mata wa Innan tsinannun kayan, da da idonta ma baxata bari a cuce ta a saka mata wannan kaya ba" Mami na murmushi tace "To in sha Allah baxa a sake ba Mama" Kaka tace "Kuma kar ki sake yi mata karin gashi ki rufa mana asiri mu ba hka muke ba" Mami tace "Ae gashinta ne mama" kaka ta cire hulan kan Heedayah tace "Auuu, to maa sha Allah, daga gani ba daga irin tsiya ta fito ba, nima dai ance ina kamarta gashina har gadon bayana wllh...." Abba ya mike yace "Baaba xa mu je, ana jirana ne" Kaka tace "Ko dai har ta tare bani da labari?" Yace "Aa tukunna" Kaka tace "To sai yaushe?" Abba xai yi magana kaka tace "A'a ni ba ruwana, ita bata da baki sae kai, ni da ita nake ba da kai ba ae koh" Mami tayi murmushi tace "Ko nan da sati kaka" Kaka tace "Toh dai kiyi ki tare kafin matar tasa ta dawo, kinsan tana d'an tabin hankali, ko da yake dai gadonsu ne, ga shi kuma ya hade da an mata kishiya, ke dai ba ruwanki da ita kiyi ta kanki ki kula da marainiya tsakanin ki da Allah, parlon ki na nan tikeke da uwar daka har da bandaki ba ruwanki da fitinanniyar, kitchen kuma ya fi parlon nan nawa da kike gani girma, komai kike son xubawa naki ki xuba duk xai cinye wllh...." Abba yace "To bari mu je Baaba" Mami dake ta murmushi kawai ta duka xata daga Heedayah, Kaka tayi saurin cewa "Kai ku ji mata ba yini ku ka kawota ta min ba dama, kinsan ynda muke da ita ne? D'a na fa ya tsinto ta tana galantoyi a titi" Mami ta mike tace "To shkkn mama, sae anjima" kaka tace "Ko anjima da daddare ba sai ki xo ki tafi da ita ba" Abba tuni ya fita, Mami tayi ma kaka sallama ita ma ta fita. Kaka na kallon Heedayah da jikinta yyi sanyi jin an tafi an barta tace "To sun baki abincin ma kuwa, don naga Amadu har wani rawa kansa yake shi a dole yyi amarya" Heedayah ta gyada mata kai kawai, kaka ta mike tace "Ni dai ba ruwana don ba barinsu Allah xai yi ba idan suka bar ki da yunwa" cup ta dauko a inda take jera su ta dawo ta bude flask ta debi ruwan xafi, shayi me kauri sosai ta hada a cup din ta bude bread ta dau slice biyu ta daura a plate ta debo dambun nama da tsoka uku na nama ta watsa kan plate din ta ajiye ma Heedayah a gabanta tace "gashi nan maxa ki cinye ki bani kwanuka na, duk cikin ki ya hade da bayanki kice min kin koshi" tana fadin haka ta mike ta koma daki tana cewa "Haka matar ta xo tsiya tsiya ba komai, kamar ta baxata kawo d'an lemonta ko ma dai turare ba tace gashi kaka" tabe baki tayi ta ci gaba da linkin da take. Heedayah dae na xaune da shayi a gabanta don ba yunwa take ji ba, ita din ba wata me cin abinci bace sosai, bude kofar parlon aka yi a hankali, Sudais ya shigo, direct inda ya hango turarensa da kaka ta dauke jiya ya nufa don dama abinda ya kawo sa kenan, ya duka xai dauka kenan ya ga Heedayah dake xaune, mikewa yyi tsaye yana kallonta sannan ya nufeta ya duka gabanta, she looks so sad, shi dai ya kasa yarda da abinda Shuraim yace masa wai fararen idon nan nata basa gani, hannu ya kai har kusa da idon ya ga bata motsa ba, ya sauke hannunsa a hankali, murya can kasa yace "How are you?" Juyawa tayi da sauri jin murya kusa da ita, Amma kuma tayi shiru tayi tana kallonsa directly in the eye, yace "How are you?" a hankali tace "Fine" yace "To ki sha shayin ki...." Tace "Na koshi" hannu ya sa aljihunsa ya fiddo chocolate biyu ya kamo hannunta yace "Toh ga chocolate ki sha, ko in bude maki?" Ta gyada masa kai, ya bude guda daya ya saka mata a hannunta, xai yi magana sae ga kaka ta fito, tana ganinsa tace "Ni dai wllh ba ruwana idan baki na ya bi ka Aliyu, nace kar ka sake xuwa min nan xan ja Allah ya isa, Kuma wllh na ja a raina tun ranan" Yace "Tunda ke ba Baffa bace kuma ba Umma bace me xai dameni, Allah ya isan ki iyakarsa lebenki" ko kadan bata ma san me yake cewa ba, don bude baki tayi kawai tana kallon shayin gaban Heedayah, can tace "Naga ikon Allah, Ke baki sha shayin bne har ynxu kika bar shi a walakance?" Heedayah ta marairaice tace "Na koshi" kaka tace "Amma ke dai muguwa ce, kina kallo ina hada shayi duk na yi barna da madarata da banvita kiyi shiru ki kyaleni sbda mugunta??" Sudais yace "To da idon ki taga kina hada shayin ta maki shiru kaka" Kaka tace "Ba ruwana da wnn, ance maka haka Allah ya bar su, duk suna sane da komai ke faruwa a inda suke, kawai tayi niyyar walakanta ni ne, amma tana sane lkcn da nake kada shayin" Sudais ya dau cup din shayin yace "Toh bari in Shan....." Kaka tace "Haram.... Ban baka ba har xuciyata, Amadu ne ya siyo min kayan shayin ba Umaru ba" dariya yyi yace "Toh shi din ba Abbana bne, Kuma ae dama abincin Haram dadi ne da shi" kaka ta fashe da kuka ta nemi kujera ta xauna, sai da ya shanye shayin ya ajiye mata cup yyi ficewarsa..... Hajiya Hauwa ce ta kawo abincin rana bayan azahar, Heedayah na xaune kan darduman da Kaka ta shimfida mata wai tayi sllh, Hajiya Hauwa da suke ce ma Aunty a gidan, ta gaida kaka tace "Ga abinci kaka" kaka tace "Toh yau dai kun bar yunwar ta gigitani gaskiya, Amma bbu komai Allah yyi albarka, amma fa ni dai nasa yar nan tayi sllh bn san ko ba musulma bace" dariya sosai Aunty tayi tace "Musulma ce mana kaka" kaka tace "Atohh naga dae ta iya alwalar..." Aunty tayi murmushi tana kallon Heedayah ta isa kusa da ita ta kai hannu kanta tace "Bari in kawo maki naki abincin kin ji daughter?" Heedayah ta gyada mata kai kawai, Aunty ta juya ta fita, sae ga ta ta dawo da plate din shinkafa da miya da salad a gefe sae neman kaza ta ajiye gaban Heedayah tace "Ki jira ya huce sae ki ci, kaka xata baki ruwa idan kika ci" daga haka ta fita, kaka na kallon Heedayah tace "To me kika yi ma iyayen naki suka sallama ma duniya ke d'a na ya kwaso ki?" Heedayah dai bata ce komai ba don Hausan ya mata girma, kaka ta tabe baki tace "Toh, Allah shi yasan dai dai, mu dai gashi mun kwaso ki bbu dangin iya balle na Baaba, muna neman lada wajen Allah" Bayan la'asar Kaka ta kwashe Yan wanke wankenta ta bude wani kofa da xae fitar da ita bayan gidan, inda aka yi mata pamponta ta kada kumfa ta ajiye ruwan dauraya ta dawo ta daga Heedayah dake bacci tace "Taso ke ma a dinga cin amfanin ki ba wai ki ci ki sha kiyi kashi kiyi ta bacci ba, tun xuwan ki kike bacci" a haka ta kai ta bakin tap ta xaunar da ita kan kujeran tsugunno dake wajen tace "Maxa kiyi ta lalubawa kina daukan kwanukan kina wankewa ga ruwa a gefen ki, mace kike gidan wani kuma xa ki" daga haka kaka ta wuce ciki ta bar ta, tunda Heedayah take bata ta6a wanke wanke ba, bata ma san meye shi ba, hka ta dinga daukan kwanukan tana tsoma su cikin ruwa tana fitarwa, har taji bbu wani nan kuwa duk suna gefe daya a ajiye, mikewa tayi pink wandon jikinta da ya wuce gwiwarta a jike jagab, kofa taji an bude a tunaninta kaka ce tace "Na gama" duk a tsorace take hannunta rike da plate biyu da cup daya, Shuraim ne tsaye bakin kofar alamar shigowansa kenan gidan a tunaninsa kaka ce backyard din, hannu Heedayah ta sa tana laluba wajen xata wuce ta ci tuntube da kujeran da ta tashi daga kai, cikin few seconds komai ya faru, duk da effort din Shuraim kuma jikinsa ta fada hakan bai hanata buge kneels dinta a kasa ba, shirun da Shuraim ya ji tayi ya sa yyi saurin daga kanta yana kallon fuskarta, sae a sannan ta wara ido ta fasa wani ihu da ya raxana shi, lkci daya ta kankamesa tana cewa wayyo kafanaa, kaka ta saki flask din ruwan xafin hannunta ta taho a guje tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, yar mutane ta mutu a gidana, na shiga uku na banu, me xance ma Amadu" Shuraim ya kalli kafan nata yana kokarin dagata ta rirrikesa cikin kuka tana cewa "Wayyo a kai ni wajen Abba, wayyo Abba ya xo...." kin fitowa kaka tayi ta dinga lekowa jikinta na rawa, Shuraim ya hade rai, ganin Heedayah ta ki tsayawa yace "Baxa ki tsaya ba sae na mare ki?" Kuka sosai take yi tace "Baxan iya ba kafan yana min ciwo..." Daukarta yyi ya shiga parlon kaka da ita ya kwantar da ita saman kujera yana kallon kafar, cikin rawar murya Kaka tace "Kaddai karyewa kafar yyi Ali?" Ta gefen ido Shuraim ya kalleta kafin ya mike yace "Ni na sani..." Kofa ya nufa zai fita ta cafkosa ta fashe da kuka tace "Don Allah ka rufa min asiri ka duba mata kafar tun da kai ma likita ne, Kar Amadu ya kullaceni, wllh sai in iya tattara kayana in gudu ba ruwana da bacin ran Amadu, ya takarkare ya tsinto yarinya kuma ace a gidana ta karye...." Heedayah dai sai kuka take tana kiran Abba, kaka ta xauna kasa ta saki matsanancin kuka tace "Ka ji algungumar wai Abba ko??" Shuraim ya hade rai yace "To ina xuwa in dauko abu a mota" daga haka yyi ficewarsa, dawowar da bai sake yi ba kenan. Abba ne tsaye kan Heedayah dake bacci saman gadon kaka, Mami kuma na xaune gefenta tana rike da hannunta, Aunty da Baffa da Umma ma duk suna dakin, kowa yyi jigum, can na hango kaka rakube jikin kofar bandakinta ko ganinta bata son a dinga yi sosai, Baffa yace "Toh wai ma ina aka ta6a sa mara ido aiki fisabilillahi??" Kaka tace "A'a ni dai kar a min sharri ita tace xata yi, tana ganin na hada kayan wanke wanken tace Kaka kawo in taimaka maki, to sai in hanata sbda mugun hali ko me? Kuma da kke wnn maganar so kke Allah ya tambayemu tarbiyar da muka mata? Don tana makauniya shkkn sae a fake da haka a ki bari ta ta6uka komai??" Baffa yace "Ta ina makaho xai iya wanke wanke kaka???" Kaka tace "Ni dai kar a min rashin kunya ba ruwana, Kuma flask din ruwan xafi na da ya gamu da ajalinsa daxu da plet dina da suka fashe guda biyu duk a biyani kayana, hatta kujerar tsungunnon ma yyi targade ba ita kadai ba, targade mana tunda kafa daya ya karye, Kai kuma Amadu wllh jidali ka haifar ma kanka kana tunanin d'a ne, sam xuciyar wnn yaro naka shuree yake ko wa, bashi da kyau, xuciyarsa bakikirin yake, ni Yaron ma idan ba tsoro yake bani ba shegiya nake, mugu ne axxalumi na bugawa a jarida, wllh yarinyar nan na tsala ihun axaba gwanin ban tausayi ya tsallake da shegen idanuwansa kamar naka yyi wucewarsa ko ta mutu ko tayi rai oho, tsaf xai iya kashe mutum har ya kai sa makwancinsa, ni abun hannunsa ma na daina ci daga yau, inda Sudess ya fi sa kenan, shi dai bar shi da cin Haram amma xuciyarsa fari ne fatt wllh" Abba dai bai ce komai ba kuma bai kalli mahaifiyar tasa ba.... I appreciate ur patronage and patient fans, Allah ya kawo budi me yawa ya bar mu tare.... Su kuma masu jiran Heedayah su karanta a bati, here is it... But don't forget it's not free, it's nothing don ka fidda dari uku kayi subscription to read what gives you so much joy, bbu abinda hakan xai raga ka da shi, and it's a way of showing u appreciate ur novelist and her handwork, don't forget writing isn't easy even if it's a hobby..... I Khaleesat Haiydar write just once a year and I make sure na sa farin ciki a xukatan mutane da dama, toh me yasa nima baxa a min haka ba, patronize so I will be happy too.... kyautatawa ma yana cikin so ai... 😇 All the same ina ma kowa fatan alkhairi, anywhere, anytime.💖 Heedayah is 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then u show ur evidence my WhatsApp digit 07087865788 sai in sa ka group. Parking Junaid yyi kofar gidan Baffa ya kashe motar sa ya bude ya sauka, sanye yake da kananun kaya, walking calmly ya isa gate suka gaisa da Mai gadi sannan ya shiga gidan, baya bukatar tambayar entrance don tuni ya hango, yana isa bakin kofar yayi knocking, bbu bata lkci aka bude kofar, kanwar Sudais ce ta bude kofar, yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Good evening" tana kallonsa irin kallon rashin sanin tace "Welcome..." Muryar Abba suka ji yace "Is that Junaid" Junaid yayi kasa da kai yace "Ina yini Abba" Abba yace "Lfya lau, Zainab ki kai sa bangaren Kaka" Zainab na kallon Junaid tace "Toh" bin bayanta yyi suka nufi parlon kaka, Abba kuma ya fita rike da makullin motarsa, da sallama Junaid ya shiga parlon kaka, Mami dake tsaye rike da jakarta alamar xata wuce ta juya tana kallonsa, Kaka ta kalli Junaid sannan ta kalli Mami tace "wannan ne d'an naki?" Mami tayi murmushi tace "Eh Mama" kaka tace "Ahh ba shakka... Kyakkyawan bafillatani da shi wllh, ya ma fi ki kyau ai, da ganin ubansa ya yo...." Mami dai na murmushi tace "To sai na shigo da daddare kaka, bari in je" kaka tace "A'a ki yi xaman ki kar ki wani wahal da kanki ba gashi ina kula da ita ba tsakanina da Allah...." Mami tace "Toh shkkn mama" Daga haka ta fita parlon, Kaka na kallon Junaid dake tsaye har sannan tace "To kai ko ka xauna mana d'an nan" ya xauna smiling broadly, with respect yace "Ina yini" Kaka na washe baki tace "Lafiya lau, ya sunan naka?" Yace "Junaid Muhd..." Tace "Junaidu sai kaji kuma wai yarinya ta gurde koh? To ni kai na ban san yanda akayi wnn bala'i ya faru ba, amma dai na gode Allah tunda ba karyewa tayi ba...." Junaid yace "Allah ya kara kiyaye gaba" Kaka tace "Ameen kai dai.... Don ma uwarka na da fahimta na lura ita ta lallaba Amadu bai dau abun da xafi ba, kasan sa da xuciya, Kuma kasan shi ya tsinto makauniyar a titin kano tana galantoyi...." Junaid dai bai ce komai ba, kaka tace "To ka leka ta tana bacci can uwar daka ka duba ta, amma ta fiye son jiki yarinyar, d'an bugewa fa kafar yyi amma duk makota bbu wanda bai shigo gidan nan ba, ke Zainab kai sa ya ganta, kuma bance ki tsaya kusa da kumbo na ba, kinfi kowa min sace sace a gidan nan" kasa motsi Zainab tayi, shi dai junaid kansa na kasa, kaka ta ja tsaki ta mike tace "Haka nan suke min ban isa in sa su aiki ba, ae dai kaga taki kai ka, to ba ruwana ba biyesu nake ba, tunda 'ya yana na min biyayya ae shkkn" har dakinta ta kai Junaid tace "To ka ganta...." Junaid na tafiya a hankali ya isa gefen gadon kaka yana kallon Heedayah dake bacci, kaka ta juya ta fita, durkusawa yyi yana kallon kafarta ya kai hannu kneel dinta, kwace kafar tayi tana turo baki alamar ta ji xafi, ta juya masa baya ta ci gaba da baccin ta, mikewa yyi walking gently ya koma dai dai fuskarta ya durkusa, bayan seconds kusan goma yace "Ina ke maki ciwo?" Bude fararen idon tayi a hankali kamar irin xata gansa din nan tayi shiru staring into space bata dai ce komai ba, lkci daya kuma ta mike xaune tace "Ina Abba" Bai ce mata komai ba, ya dau ledan da ya gani gefenta dauke da drugs yana dubawa, bude kofar dakin aka yi junaid ya juya, Sudais ne tsaye bakin kofar yana kallonsu, Junaid ya mike shi ma yana kallonsa, Sudais ya karasa ya basa hannu nan suka gaisa, sannan ya isa kusa da Heedayah yace "Me ya kai ki wajen wanke wanke har kika fadi?" Heedayah na kallon inda ta ji muryar tace "Ita ce ta kai ni wajen tace sai inyi wanke wanke" Sudais yace "To ina ke maki ciwo yanxu?" Kafarta na hagu ta nuna masa tace "But..." Yace "But what?" A hankali tace "Don't touch it" kallonsu kawai Junaid yake yi, Sudais ya duka yana kallon kafar sosai yace "Ohkk..." Hannu ta kai tana laluba wajen don taga ta inda yake, ta ta6a kirjinsa, shi dai kallonta kawai yake, Bude 32 set of white teeth dinta tayi tace "Wannan sweet din naka ya kare ko?" Ya buda ido yace "Kina so ne?" Ta gyada masa kai tace "Um" yace "Ohk to bari in kawo maki" tace "Har da short bread??" Juyawa Junaid yyi ya fita daga dakin ya rufe kofar, Sudais ya kalli kofar sannan ya kalleta yace "Who is he?" Ta d'an yi shiru sannan tace "Shine ya bar ni a middle of road wai in wuce cikin gida da kai na bayan yasan bana gani, I don't like him" da mamaki Sudais yace "A ina kenan?" Tace "A gidansu mana, kuma ina shan strawberry ya dauke min plate din, wai baya son in sha..." Tana fadin haka ta turo baki, Murmushi Sudais yyi ya mike yace "Toh bari in kawo maki sweet din in dawo" ta kara bude hakoranta tace "Toh" ya isa kofar ya bude ya fita, xaune ya tadda Junaid a parlor tare da kaka, kaka na nuna sa tace "To ka gansa, sai dai idan ban ajiye abu ba wllh, shi kuma wancan axxalumin ko magana baya wani yi, sae dai yyi ta kallon ka yana fama da mugun abu a xuciya, shureen naji suna kiransa ko wa, shi ma dai Aliyun ne, amma gaskiya xan gaya maka xuciyarsa bbu kyau yau na sake gaskata hakan daxu, to dai duk sunan Mai gidana ne da yayi hatsari ya rasu" ko kallonta Sudais bai yi ba ya nufi kofa xai fita, kaka tace "Kuma wannan da kake gani yan matansa sun kusa dozin har na gaji da xuwan da suke gaisheni, yau fara ta xo, gobe baka, jibi mummuna, kai gasu nan dai, ni dai na gaya ma daya a ciki yaudaran ta kawai yake, to ita ce ta goma xuwa gaisheni, to naga tana da hankali tana ta min aiki da goge goge" Sudais ya mata wani kallo ya fita ya kulle kofar. Junaid ya d'an yi murmushi yace "To ni xan koma..." Kaka tace "Da wuri haka har ina murna na samu abokin hira?" Yace "Xan dawo da daddare" tace "Ahh to shikenan, in ajiye maka abinci kenan?" Wani murmushin da ya bayyana dimples dinsa yyi yace "Toh sai na xo in sha Allah" tace "Toh Allah ya kawo ka, amma kaddai ka ki xuwa ka bar min abincina yyi kwantai" yace "A'a xan xo" mikewa yyi tace "Toh ka leka ko ta tashi yarinyar" yace "Toh" daga haka ya shiga dakin, xaune ya same Heedayah, ya karasa kusa da ita ya kai hannu ya dunguri forehead dinta yace "Kina ji ina maki magana kika min shiru daxu koh" turo baki tayi bata ce komai ba, yace "Sai na yanke wannan bakin" Tana jin haka ta 6ata fuska lkci daya ta fara Shesshekar kuka, xaro ido yyi ya xauna gefenta ya jawota jikinsa yace "Ke wasa nake maki fa" Cikin rawar murya tace "Toh shine xaka ce xaka cire min baki?" Yace "A'a baxan cire ba, sorry" tace "Toh ina Farida?" Yana kallon Eye balls dinta yace "Ta je Abuja" da sauri ta dago kai tace "Nan ne garinmu mu ma ai" Yana kallonta yace "Where in Abuja?" ta bude hannu alamar bata sani ba, sai kuma tace "Yaushe xata dawo?" Yace "Soon" saketa yyi ya mike yace "I'm going" tace "To ni baxan sake xuwa wajen Mami ba kuma, ni ina tsoron wannan matar" Junaid ya buda ido yace "Me yasa" ta marairaice tace "Tana ma kowa masifa, kuma tana aikana bana ganin hanya" Murmushi yyi sosai yace "Mami xata xo ta tafi da ke" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Anjima xan xo da daddare" ta gyada masa kai alamar to, sannan ya juya ya fita dakin. Da daddare Junaid ya xo gidan Baffa kamar yanda yyi ma kaka alkawari, Kaka na can uwar daka, Heedayah kuma na xaune parlon da plate din tuwo a gabanta, Da sauri kaka ta fito jin an bude kofa, ganin Junaid ta washe baki tace "Ka zo ashe Junaidu" gaisheta yyi ta amsa tana washe baki tace "Bari in gama gyaran gadon in fito duk ta yamutsa xanin gadon" daga haka ta juya ta koma ciki, Junaid ya ajiye ledan hannunsa ya koma inda Heedayah take tace "Me yasa ba ki cin abincin?" Kamar jira take ta fashe da kuka a hankali tace "Ni ban iya ci ba" xaro ido yyi yana kallon tuwo da assorted miyar veg din gabanta, yace "To me xa ki ci?" Tace "I want to take tea" ya kara wara ido, bude kofar parlon aka yi ya juya, wani dogon matashi ne just his mate ya shigo parlon, sanye yake da 3 qtr da polo, Shuraim ya karasa cikin parlon waving at him without much interest yyi xaman sa kan kujera, kaka ta leko don ganin waye, tana ganin Shuraim ta hade rai sosai tace "Dawowa kayi ka kashe mu lkcn mu bai yi ba ko ya aka yi??" Dauke idonsa yyi daga kallonta ya fiddo wayarsa ya maida dubansa kai, kaka tace "To idan ma mun mutu bayan ka tafi Junaidu na shaida, ehe" daga haka ta koma ciki, ba a dau wani lkci ba sai ga ta tafito tana washe baki tace "Sannu Junaidu bari in kawo maka abincin na ka" Junaid yayi murmushi yace "To ngd" a gabansa ta jera masa abincin, shi dai bai ce komai ba duk da a koshe yake, xata wuce ta gaban Shuraim kamar ana forcing dinsa yace "Ina yini" tayi kamar bata ji sa ba, sai ga ta ta dawo tace "Toh ka ci abincin mana Junaidu" Junaid na murmushi yace "Toh" sauka yyi ya bude warmer din ya ga shinkafa ce da lafiyayyen Miya da ya ji nama, sai ga wani bowl da aka yanyanka kayan ganye, kallon Heedayah yyi da plate din tuwon gabanta, sannan ya kalli kaka dake kokarin share bakin kofar ta, matsawa yyi kusa da Heedayah murya can kasa yace "Xa ki ci shinkafa?" Da sauri ta gyada masa kai, Ta gefen ido Shuraim ke kallonsu, Junaid ya dau plate ya diba shinkafar da Miya da nama, ya dauke tuwon da ta fara kacalcalawa ya ajiye mata shinkafar, a kan idon kaka da ta saki tsintsiyar hannunta ta mike da sauri tace "La la la kar ka bata, gantalalliya ce wai bata iya cin tuwo ba, to uwar me xa a bata, ko gidan Amadun da ya tsinto ta ma ai ana tuwo balle nan, mu ba wasu masu kudi bane da xata ce bata cin tuwo har da hawayenta, shinkafar kuma iya cikinka nayi nima tuwon na ci, idan aka ce xa a biyeta ai sai ta lalace Allah ya tambayemu...." Heedayah dai sai xare ido take kamar xata yi kuka ta dafe plate din shinkafar don kar ma a dauke, Junaid yace "Kaka ni na fi son tuwon ne shi yasa" Kaka ta saki baki tace "Allah?" Yana murmushi yace "Ehh" ta tabe baki tace "Toh Allah ya raba bawa da wahala don ko na wahala gun neman shinkafar nan da miya, to ai sai ka ci tuwon ita kuma sai ta karata da shinkafar duk da ni dai ban bata ba, kaji min yarinya dai da mugun hali" tuni Heedayah ta fara cin shinkafar, idan akwai abinda junaid ya fi tsana rayuwarsa tuwo, sai kallon tuwon yake yana tunanin ta wani side din xai fara ci, da cokali ya debi tuwon ya kai baki yana ci da kyar, mikewa Shuraim yyi ya maida wayarsa aljihu ya nufi kofa ya bi ta gefen kaka ya fita, kaka ta mike tace "Ka dai ga ko? Mugun hali har tsiro sai da yyi a jikinsa, tirrr Amadu dai bai yi sa'a ba ya haifi jaraban duniya kawai, to ba gwara min Sudess ba ni dai" sake bin kofar Junaid yyi da kallo don ya dai ga Shuraim na kama da Abba amma bai yi tunanin son dinsa bane. Hajiya Maryam ce xaune parlonta kai kace rasuwa aka yi mata, duk ta fita hayyacinta, idon nan nata duk a kumbure ga su Hajiya Sadiya, Hajiya kyauta, har da Hajiya Amina da dai kawayenta gaba daya sun kusa 7 sai Yan uwanta uku, Hajiya Zaliha tace "Ban da ma dodewar tunani da kwakwalwa ke har kya dau shawarar wannan tsohuwar da shekara da shekara kuna dauki ba dadi da ita, to duk gari kowa cewa yake ita ce ma karfin auren barristern, ita ta matso da auren ma aka yi da wuri wuri" Mumy ta fashe da matsanancin kukan takaici amma ta kasa cewa komai, Hajiya safara'u tace "Toh Kuma meyasa duk tsawon lkcn nan kika ki kunna waya fisabilillahi" cikin rawar murya Mumy tace "Ita ta sa in kashe wayar wai sai na basa wahala kafin ya gano inda nake da yara, kuma kusan kullum sai mun yi waya da ita, tayi ta shirga ni wai Ahmad na nan duk ya daga hankali ana ta nemana gari gari, har rahotu ya kai ma yan sanda, ko abincin kirki baya ci, da mun gama wayar kuma sai ta ce in kashe da sauri" Mutanen parlon suka kwashe da dariya ciki har da Hajiya Amina, Mumy ta hade rai tana bin su da kallo, Hajiya Sadiya na kyakyatawa tace "Ban ta6a ganin makiran tsohuwa irin matan nan ba, gaskiya ta sha ki da yawa, lkci daya ta rama duk abubuwan da kika dinga mata tana xaune gidan nan" Mumy ta mike tace "To bari ku ji wani abu, ba don ba ni da abinda xan iya yi bane kan tsinannen auren da barrister yyi ya sa nake kuka ko hankalina ya tashi, A'a kuka nake saboda takaicin da yarintata ba a min kishiya ba sai yanxu, kuka nake sbda boasting da na dinga yi cikin mutane Barrister baxai ta6a min kishiya ba, kuka nake sbda makircin da annamimiyar tsohuwar nan ta hada min, ita kuma wnn mata da tayi kuskuren auren mijina ina jiran shigowarta gidan nan, wllh sai ta gwammace bata ta6a sanin Barrister ba, ita kuma wnn yarinya da aka min kishiya ta dalilinta...." Wani murmushi Mumy tayi tace "Da farko xamanta gidan nan kirgagge ne, sannan kafin ta tafi sai na tabbatar da shaida xata bar gidan wanda har girmanta baxata manta ba, sannan a makantan ta xata tsaya har karshen rayuwarta, wllh wllh bana wani jin kishiyar da aka min kamar yanda nake jin yarinyar nan a rai na, ita ce sillar rugujewar duk wani farin ciki nawa...." Hajiya kyauta tace "Toh nan dai da kwana biyu xa su tare da uwar rikon tata, ke dai gashi kin samu an sauya maki komai na bangaren ki kamar ke ce amaryar, amma ni tunda nake ban taba ganin irin haka ba, anya ba aljana barrister ya kwaso ba me son ta tarwatsa maki gida, gashi ma tana kan yin haka tunda ta sa an rangada maki kishiya yar boko yar gayu" Mumy tace "Za mu ga wanda xai tarwatsa wani ni da ita, na fa ce maku ynxu ni ba ma da kishiyar xan goga ba...." Heedayah is 300 via.... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788 Baffa ne ya bude kofar parlon Kaka da sauri jin ihun da Heedayah ke yi ya shiga, shi ma shigowarsa gidan kenan daga masallaci an idar da isha, Kaka ce ta danneta sai shafa mata wani magani kamar rub take a kafan da ke ciwo, Baffa ya bude baki yace "Meye haka kuma Baaba?" Kaka dake ta hada xufa tace "Toh sai a biye mata tana dingishi baxa a san na yi ba, so ake ta dawo gurguwa ga makanta abun ya taru ya ma d'a na yawa? da wanne ake son ya ji, a hankali fa nake mata amma da yake munafuka ce algunguma dubi tonan asirin da take min kamar warce nake yankawa" Baffa yace "Don Allah ki kyaleta Baaba, ba tana shan magani ba, a hankali xai bar mata ciwon ai" a fusace Kaka tace "Maganin banxa maganin bature, ka san daga wani kasa aka kawo min wnn din da nake shafa mata, ku dinga kallona kamar ban san me nake yi ba, toh naki kyaletan sai ka kwace ta ai" Ita dai Heedayah bata fasa ihun da take tana kiran Abba ba, aka bude kofa Sudais ya shigo parlon da sauri shi ma daga masallacin yake, Bude baki yyi yana kallon kakar tasa, tace "Kai ka ji ubanka da wani magana Sudess, daga taimako fa xai min rashin kunya, ita kuma yar banxan magani fa nake shafa mata...." Sudais yace "Toh kaka ba ke kika sa ta wanke wanken ba, ai sai bari har lkcn da kafar yyi niyyar warkewa ya warke da kansa, ynxu hakan da kike mata idan kika sake ji mata wani ciwon fa?" Kaka ta tura Heedayah a fusace tace "Ni dai Allah ya isa wllh, ya xa a dinga cewa ni na sa ta wanke wanke, ga yarinya dai da bakinta ko bata da ido ai sai ku tambayeta ta fadi gaskiya mana, kawai kawai an mayar da ni karamar mutum a gidan nan sbda ana bani abinci a kwano.... Ban da xalunci me xai sa in sa makauniya wanke wanke idan ba ita ta bukaci yin hakan ba da kanta??" Juyawa Baffa yyi ya fita daga parlon, Sudais ya jira har ya rufe kofar sannan yana nunata yace "Ke dai kawai baki son gaskiya, ki yarda kawai kin kusa karya yar mutane kin sa ta wanke wanken da kika tara an kwana biyar...." Kaka ta fashe da matsanancin kuka tana jawo dankwalinta xata yi hankici da shi, Sudais ya daga Heedayah suka fita parlon ya kulle mata kofarta yana murmushi, Heedayah dake dingishi tashin hankali a fuskarta tace "Plss ka wuce da ni wajen Abba kar ka dawo da ni nan" kallonta yake bai ce komai ba har ya isa stairs, daukarta yyi ya wuce sama, dai dai xai ajiyeta sai ga Ummarsa ta fito daga part dinta, tsaye tayi tana kallonsa da mamaki fuskarta, yace "Sannu da gida Umma..." Bata amsa ba tace "Ka sameni a parlona yanxun nan" daga haka tayi wucewar ta, bangaren Aunty ya shiga yana rike da Heedayah, Aunty dake xaune saman darduma ta idar da sllh tace "Ta ya kaka ta yrda ka fito da ita, daxu da rana kiri kiri taki yarda in fita da ita, wai ba ruwanta yar amana..." Sudais yyi dariya yace "Ae tana can na barota tana kuka" Aunty tace "Kai dai baka gudun abun magana koh Aliyu?" Ya xaunar da Heedayah saman kujera yace "Danneta fa tayi tana ta ihu wai magani take shafa mata a kafar" Dariya Aunty tayi ya juya yace "Ina xuwa Umma na kirana..." Tace "Amma xaka dawo ai" yace "Ehh xan dawo" daga haka ya fita, Dawowar da bai yi ba kenan har sha biyun dare yyi, Heedayah har ta gaji da tambayar Aunty ko ya dawo, Aunty ta kai ta bathroom dinta tayi fitsari sannan ta kwantar da ita saman gadonta nan da nan bacci ya dauketa, yaranta kuma suna dakinsu dama... Aunty na kwance har ta fara bacci ta ji ana kwankwasa kofar bedroom dinta, ta mike ta kunna wutan dakin tana kallon agogo ta isa kofar ta bude, Baffa ta gani tsaye kafin ta ce komai yace "Yarinyar nan na nan ne?" Da mamaki Aunty tace "Tana nan har tayi...." Hango kaka da tayi tsaye bakin kofar parlor tayi kicin kicin da fuska ya sa tayi shiru, Baffa yace "to fito da ita" Aunty bata ce komai ba ta juya ta koma dakin, sai a sannan ta girgixa kai ta shiga tada Heedayah, tana rike da hannunta har sannan tana magagin bacci suka fito parlon, Kaka tace "A bani amana sbda ance maku ban san girman amana ba xa ku cuceni ku dauketa, to uban me xata maki a nan din banda gulma Hauwa? wllh Umaru kasa bacci nayi, gani nake kawai Allah na fushi da ni, idan Amadu ya ji wnn me ku ke son ya daukeni? To ba ruwana a maido min da abata...." Baffa dai bai ce komai ba, Kaka ta warce hannun Heedayah a na Aunty ta fice daga parlon Heedayah da har baccin ya fice a idonta jin muryar kaka ta dinga bin ta kamar xata yi kuka, Baffa ya girgixa kai yana kallon Aunty yace "Toh Allah ya kyauta" dariya tayi tace "Halan har ka fara bacci" yace "Nayi bacci mana dama" daga haka yyi mata sai da safe ya fita. Kaka na shiga bangarenta ta kulle kofar tace "Gantalallen yaro kawai in sake ganinsa a parlona idan ban ja Allah ya isa ba" furan da ta rage ma Heedayah ta dauko mata ta ajiye gabanta tace "Gashi nan baxan shanye ban baki ba kar Allah ya tambayeni, duk da mugun halin ki" Heedayah ta ta6a cup din a hankali ta kai baki ta fara shan furan kamar xata yi kuka. Washegari juma'ah da safe Mami ta xo tafiya da Heedayah, Kaka ta kwaso kayanta da ta wanke ta linke su fesss tace "Sai kin sa ido sosai kan yar nan, shegen son jiki ne da ita kamar mage, baxa a fake da makanta ba a cuceta...." Mami tace "Toh mama" Kaka tace "Toh har yanxu baki saka ranan tarewar bane ke kuma? Ba a fa wasa da igiyar aure" Mami tace "Yanxu haka can gidan xa mu wuce gaba daya" Kaka tace "Toh alhmdllh, kin dai ji duk nasihar da na maki ranan ai ko, yanxu haka matar na can ta dawo, bbu ke bbu ita" Mami tayi murmushi tace "In sha Allah" sai kusan sha daya suka bar part din Kaka tare da Heedayah..... Horn Mami tayi dai dai gate din gidan Barrister Ahmad, mai gadi ya bude gate din ta ja motar xuwa cikin gidan tayi Parking a space din yin hakan, Da taimakon ta Heedayah ta fito a motar, tana rike da hannunta suka nufi entrance din shiga main parlor, Shuraim ne xaune balcony din da system a gabansa, tun daga nisa da ya kallesu ya dauke kai ya ci gaba da abinda yake a laptop har suka iso balcony din, Mami bata kallesa ba tace "Take off ur shoes Heedayah" Heedayah ta fara cire takalmin kafarta, Mami ta ajiye su gefe, ita kam dama bata cire nata ba da shi ta shiga tana bude jakarta don fiddo wayarta dake ring, ta daga ta kai kunne, Hajiya Amina mahaifiyar Sudais ce parlon da Mumy sai Hajiya Sadiya da Hajiya kyauta, kallo daya Mami tayi masu ta cikin siririn glasses din idonta still holding Heedayah's hand ta nufi bangarenta tana cewa "Ai court ma baxata bada bail dinsu ba, their case is different, baxai yiwu ba ma, so kar ku ji komai, pls hold on I will call you later" tana fadin haka ta katse wayar ta fiddo makullinta don bude bangarenta wanda aminiyarta da sister dinta suka xo tun jiya suka yi gyare gyaren da ya kamata, tana shiga ciki rike da Heedayah ta kulle kofar. a hankali Hajiya Sadiya tace "Tabdijam, lallai kina da aiki babba a gabanki Maryam, idan baki yi hankali ba wnn farar matar dai kwace maki gida ta shigo yi, ke kin ji wani kamshi da take xubawa kuwa, kalli fa ko kallon arxiki bata mana ba sai xancen kotu da bail take, da takalmi ma ta shigo parlon don rainin wayo..." Hajiya Maryam da taji kamar xuciyarta xai fashe don kishi bata dai ce komai ba nan ko naxari iri iri take yi a xuciyarta tana tunanin ta ina kenan xata fara.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Abba ne xaune main parlor bayan isha, lkci lkci yake kallon agogon dake manne bangon parlon, Mami ta fito daga part dinta sanye da hijab har kasa ta karaso cikin parlon tace "Good evening Barrister" yana kallonta yace "Good evening Rahinah" xaunawa tayi one sitter dake parlon tace "Gani" Abba yace "Me ya sa kika dau lkci baki fito" tace "Putting things in other" Bai ce komai ba, ya kalli hanyar kitchen don Mumy na ciki, tun daxu take kai wa take komowa ko gaisuwa bai hadata da shi ba tun shigowarsa, shi kuma hakan bai hanasa ce mata yana da magana a parlor da ita da Mami ba, xata sake komawa kitchen daga bangarenta yace "Maryam" juyowa tayi fuska daure tana kallonsa bata ce komai ba, yace "Ke muke jira" Tana masa wani kallo ta karaso cikin parlon tace "Ni ku ke jira? in maku me? A kan me ma xa ku jira ni? Nace maku ina da wnn lokacin ne? Plss I have more important things to do then sitting and staring at you both, bani da wannan lokacin barrister...." Ta juya xata bar wajen, rai bace yace "Ina magana xa ki wuce?" Juyowa ta sake yi tace "Bbu tasirin da maganganun ka xa su min barrister, in xauna kace xaka mana nasiha ko me? Did I tell you I need that, ita dai xaka xaunar ka ja ma kunne ta tsaya iya matsayinta a gidan nan kar ta ce xata yi karambanin xuwa kusa da nawa matsayin, matsayina daban nata daban, ni uwar gidanka ce kuma uwar 'ya yanka, ita kuma uwar rainon yar tsintuwar ka ce, wa enda xaka dinga ciyarwa, kaga banbancin kuwa ba karami bane, idan tace xata yi gigin matsowa lane dina ita xata kwana a ciki, so bbu wani xaunawa da xan yi ka hada mu kayi magana, bata kai matsayin ba, ga most important maganganun nan duk nayi, sai dai kawai tayi taking caution, ka kara mata da wanda xaka kara mata" Tunda ta fara Abba ke kallonta, Mami tayi yar dariya tace "To ai da sauki tunda kamar yanda xa a kira ki matarsa haka nima xa a kirani ynxu, kuma tunda baki isa korar yar tsintuwa ba balle ni Alhmdllh, muna nan sai mun xame maki kadangaren bakin tulu, xa ki gane matsayina da naki bai kai banbancin da xa ki dinga bragging ba...." A fusace Mumy ta karaso kusa da ita tana huci tace "Karya kike wllh, nace karya kike..." Tsawa Abba yyi mata yace "Kina da hankali Maryam??" Mami ta mike tace "Ina fa, sai dai in koya mata cikin yan kwanakin nan...." Daga haka ta bar masu parlon ta wuce bangarenta, Mumy ta fashe da kuka tace "Ka cuceni barrister, ka ci amanata, ka rasa warce xaka auro ka kawo mana gida sai yar bariki...." Mikewa Abba yyi ya dakatar da ita in few seconds ta hanyar nuna ta da yatsa strictly yace "Don't you ever try that again Maryam...." Bai jira cewarta ba ya bar parlon. Mami ce xaune that same night tana kallon Heedayah tace "Ina jin ki..." Heedayah ta marairaice tace "Tea kawai...." Mami tace "Kece kike cewa kina son tea din kenan" Heedayah ta girgixa kai tace "Ammi na ce take bani in sha da daddare" Mami tace "To da safe fa?" Tace "Tea and bread and egg" Mami tace "Da rana?" Heedayah tace "Indomie" Mami tace "Sai kuma da daddare ki sha tea" Kai Heedayah ta gyada mata, Mami tace "Toh after this night baxa ki sake shan shayi ba duk abinda aka dafa aka baki shi xa ki ci is that clear?" A hankali Heedayah ta gyada mata kai, Mami ta mike ta dauke fried rice da chicken dake cikin plate da Heedayah ta ki ci wai sai tea ta nufi kofa ta fita, hanyar kitchen ta nufa ta bude kofar kitchen din, tsaye ta ga Shuraim gaban kettle din ruwa alamar tea xai hada don ga kayan shayin a ajiye gefe, ta kasan tiles yake kallon wanda xai shigo kitchen din, yana ganin wacece kuma ya kauda kai ya ci gaba da abinda yake, Mami ta ajiye abincin hannunta ta nufi inda cups suke ta dau daya da cokali, ko kafin ta juyo har ya fice daga kitchen din, karasawa tayi gun kettle din ta juye ruwan ciki a cup din ta bude kayan shayin ta hada tea sannan ta fita kitchen din, Khadijah ta gani parlor ta shigo daukan takardunta, tana ganin Mami ta kwashi takardun ta wuce bangarensu da sauri, Mami dama tun da ta kalleta sau daya bata sake kallonta ba har ta wuce nata bangaren, sai da shayin ya huce sannan Heedayah ta sha Mami ta sa ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta. Washegari Saturday tun kafin yan gidan su tashi bacci Mami ta hada ma ita da Heedayah breakfast, da yake abinda Heedayah take so ne tsaf ta cinye komai, Mami dai sai kallonta take, sannan tace "Kin koshi ae?" Heedayah ta gyada kai, Mami ta mike tace "To mu je ki gaida Abba" har parlon Abba Mami ta kai ta, Abba dake aiki system ya daga kai yana kallonsu, Mami tace "Weldone" yace "Har ina tunanin kawo maki ki karasa" tace "Noo nima ga nawa can" yyi murmushi yace "Akwai maganan da nake son xa mu yi Rahinah" tace "Alright, but before then nima ina da magana da kai" yace "Yanxu?" Tace "Later..." Abba ya xaunar da Heedayah gefensa yace "How are you my dear" tana washe hakora tace "I'm fine" Mami tace "Baki yi gaisuwa ba" tace "Abba ina kwana" yace "Lafiya lau daughter" Mami tace "Let me freshen up" daga haka ta fita parlon, yana kallon Heedayah yace "Wa ke koya maki English" tace "My teacher" ya d'an bude ido yace "Really?" Tace "Ehh" Abba yace "Me da me yake koya maki kuma a ina yake koya maki?" Heedayah tace "Ammi tace min she's a Female, tana koya min komai da komai a gidanmu" yace "Wani sura kike?" Da sauri tace "Jinnnn" Abba na gyada kai so impressed yace "Kullum take xuwa koya maki?" Heedayah ta gyada masa kai, Abba xai yi magana aka bude kofar, Shuraim ne ya shigo parlon da sallama yana sanye da jallabiya, Abba ya amsa, xaunawa yyi nan kasa gefen Abbansa yace "Ina kwana Abba" Abba yace "Lafiya lau" Heedayah tace "Abba har da boko take koya min ma...." Satan kallonta Shuraim yyi ya kara hade rai, Abba na kallonta yace "Toh xan kawo maki warce xata dinga koya maki a nan gida" Heedayah ta wara manyan idonta tace "Thank you Abba, but..." Yace "But what?" Tace "Yaushe xaka kai ni wajen Ammina? Kila tana ta nemana" a sanyaye tayi maganan, Abba ya shafa kanta yace "Ina sha Allah xan kai ki, har yanxu ana neman Ammin taki" Tace "Abba ai gidan Yakumbo take" Abba yace "Eh ban manta ba xa mu je can" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa yace "Sai anjima Abba" Abba yace "Da yaushe kake yi ma su Khadijah karatun qur'ani" Juyowa yyi yana kallon Abban nasa, ganin kallonsa Abban ma yake yace "Da asuba" Abba yace "Ohk, Heedayah will join also, sai ka dinga masu gaba daya" dawowa yyi ba tare da ya shirya ba ya durkusa inda ya tashi yace "Abba ai na kwana biyu ban koya masu ba" Abba yace "Eh to sai ka dinga yi mata ita kadai tunda ba Islamiyya xata je ba, su kuma dama suna xuwa islamiyya" Kasa cewa komai yyi yana kallon Abban nasa, Heedayah tace "Abba a suratul jinn nake" Abba yace "Eh daga nan xa ku ci gaba" Shuraim yyi karfin halin satan kallonta, Abba yace "That's all xaka iya tafiya, idan ya so sai in samar mata lesson teacher na boko kawai" Mikewa Shuraim yyi bai ce komai ba ya fice daga parlon ya kulle kofar, fuzar da iska yyi bayan ya fita ya juya yana kallon kofar da idanuwansa da suka sauya kala. Mumy ce xaune dakinta tayi tagumi, da ka ganta kasan tana cikin tashin hankali, kanwarta Salima ce xaune dakin, tace "Allah kuwa nake gaya maki Yaya, duk wannan tunane tunanen da saka kai a damuwa ba shi bane, just swing into action, dubi fa yanda take ta harkar gabanta a gidan kamar warce tayi wata da watanni ke kuma kina nan xaune kina ta wani kishi da damuwa, wllh tuwo da lafiyayyen miyan agushi tayi ynxu a kitchen, makauniyar kuwa na can ta kafa mata kujera a kitchen din tana xaune...." Mumy ta fashe da kukan takaici tace "Wllh Salima har ynxu na kasa yrda cewar kishiya barrister yyi min, gani nake kamar bakuwa nayi xata wuce, baki ji ynda xuciya ta ke min xafi ba, Kuma fa tun jiyan ko lekowa dakin nan bai yi ba, ita kuwa ta shiga bangarensa ina lura yau yafi a kirga, wllh ji nake kamar in banka ma gidan nan wuta kowa ya huta" Salima tace "Ba wani banka wuta Yaya, gashi kin fara bata chance ta kwace maki miji ta xama ita ce kan komai a gidan...." Mumy tace "Duk ba wannan ba nata bai tsaya min kamar yanda na makauniyar ya tsaya min a rai ba, ki bani shawara ta ina xan fara, me kike ga xan ma wnn yarinyar in huce takaici, ni dai baxan kasheta ba amma ina son abinda xan mata kissa ya fi mata alkhairi da shi, wllh na tsaneta, na tsani duk wani me son ya ganta kusa da shi ma, wllh sai na tarwatsa rayuwarta" Salima tayi dariya tace "Ni fa ban wani jin yarinyar nan Yaya, minti nawa ne xa a kada ta ta bar gidan ma gaba daya, ita dai wnn yar bokon ya kamata ki fara tunanin ynda xa ayi da ita ba yar yarinya ba" Mumy tace "To ni ta yarinyar nake tukun" Salima ta mike tace "Toh ki kwantar da hankalin ki Yaya, wnn me sauki ne, mu da muka san kan komai, yanxu dai ana jirana tun daxu a waje, xan dawo ko xuwa jibi" Mumy tace "Ba wani nan, ke din ce xan gani kwana kusa, idan kika tafi gantalin ki ba sai an gan ki ba" Salima tayi dariya tace "Ai ynxu na daina kwana a waje...." Mumy tace "Toh ni dai gobe xan taho gida kar ki fita don Allah" Salima tace "In sha Allah yaya, sai mun hadu goben" Daga haka ta fice daga dakin..... Bakin gate Salima ta kusa cin karo da Junaid xai shiga cikin compound din, ja baya tayi tana kallonsa, yace "Sorry" bata iya ta amsa ba har dai ya wuce ta, ta juya ta bi shi da kallo ko kiftawa babu, underneath her breath tace "Waow...." Tana tsaye tana kallonsa har ya isa entrance din shiga main parlor, ya kwankwasa kofar, Mami da ta san yana hanya ta fito daga kitchen ta bude kofar tana kallonsa tace "Har ka iso?" Yace "Ehh ina yini Mami" ta basa hanya tace "Lafiya lau" daga haka ta koma cikin parlon ya bi bayanta, saman kujera ya xauna tace "Ya su Uncle din naka" yace "Alhmdllh..." Kitchen ta nufa tace "I have been waiting for you since xaka dauko min sako a gida" Kafin ta shiga kitchen yace "Mami ina..." Mami ta juyo jin yyi shiru, tace "Wa?" Yace "Wannan babyn" dariya tayi tace "Sunanta Heedayah" yace "Oh ohk, Heedayah" Mami tace "Tana can tana bacci, let me get you water" Drink ta kawo masa parlon, duk suka kalli direction din da suka ji footstep, Mumy ce ta fito rike da makullin motarta fuskarta a murtuke, Mami ta nufi bangarenta don tado Heedayah, Junaid yyi kasa da kai cike da ladabi ya gaida Mumy, kallonsa ta kara yi snn ta amsa a dakile tayi ficewarta xuwa gidan Hajiya Sadiya ta ji ita kuma nata shawaran. Ba a dau lkci ba Mami ta fito rike da Heedayah dake sanye da doguwar riga iya gwiwa, duk gashin kanta a bude, kana ganinta kasan daga bacci ta tashi, Mami ta xaunar da ita nan kusa da shi tace "Ga Yaya ki gaishesa" daga haka ta koma kitchen don karasa abinda take, hannu Heedayah ta kai a hankali tana ta6a sa, har ta kai hannunta fuskarsa, ya kama hannun yana kallonta yace "Ina maki wasa ne?" Turo baki tayi tace "Nasan kai ne ai" hancinta ya ja yace "Sai na....." Ganin ynda ta 6ata fuska xata yi kuka ya jawota kusa da shi yace "Ohk sorry, let me pour you juice, xa ki sha?" Ta turo baki sai kuma ta gyada masa kai, ya bude drink din da Mami ta kawo masa ya diba, tace "Baka kawo Farida ba?" Bai ce komai ba ya kai glass din bakinta yace "Bude bakin" bude bakin tayi ya fara bata juice din a hankali, Mami ta fito kitchen din tana kallonsu tace "Da baka bata ba, bbu wani abincin da take ci sai kayan xaki" Heedayah na jin haka ta karasa shanye lemon da saurinta, murmushi yyi ya ajiye cup din, Mami tace "System dina xaka dauko min a gida yanxu" Junaid yace "Ohk..." Heedayah tana ta6a sa tace "Xaka je da ni??" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mikewa Junaid yyi ya da makullin sa yace "Sai na dawo Mami" Mami tace "Alright" a hankali Heedayah tace "Mami ki ce in rakasa plss" Mami ta kalleta sannan tace "Ki rakasa ina?" Tace "Inda xai tafi" Shi dai Junaid bai ce komai ba ya nufi kofa har xai fita sai kuma ya juyo yace "Mu je da ita Mami?" Mami ta hade rai tace "Ku je da ita ina" Yace "A'a na ji tace xata je ne" Mami tace "To baxa ta je ba, kayi wucewar ka malam" Heedayah ta tashi tsaye kamar xata yi kuka tace "Mami nooo, pls ina son in je, I want to meet with farida, ki ce in bi sa" Mami ta kamo hannunta tace "Farida na Abuja Heedayah, she is not back yet, idan ta dawo you will see her" Shiru Heedayah tayi kamar xata yi kuka, Mami ta kalli kofa ta ga har Junaid ya fita, bangarenta ta tafi ta dauko ma Heedayah hularta da takalmi sannan ta dawo ta sa mata, ta kama hannunta suka nufi kofa, Mami na kallon Mai gadi tace ya leka yace ma wanda ya fita yanxu ya tsaya, hakan Mai gadin yyi, Heedayah ta ji dadi jin fresh air ta gane sun fito waje, sai da suka kusa gate Heedayah tace "Mami kin san me?" Mami ta kalleta tace "Aa my dear, what?" tace "Ina jin kamshin ruwa...." Da mamaki Mami tace "Kamshin ruwa ku ma daughter?" Heedayah tace "Ehh" Mami tayi yar dariya ta leka gate, ganin Junaid tsaye jikin motarsa tace "To ga ta ku tafi amma kar ku dade plss ka ga yamma yyi" ya karaso ya kama hannunta yace "Toh Mami" daga haka ya wuce mota da ita, Mami na tsaye har taga ya nufi mota da ita sannan ta koma ciki, front seat junaid ya bude, kawai ya ga ta fara kokarin shiga, ya dagata ya sa ta cikin motar ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar layin. Heedayah ta juya Inda take tunanin yake tace "Ya sunan ka? Sai in dinga kiran ka" Bai kalleta ba idonsa na kan titi yace "Ke ya sunan ki" Tace "Sunana Heedayah Ahmad...." Yace "Heedayah is not a real name" Ta wara ido tace "Ohk, Ammina tace min sunana Fatima" Sai a sannan ya kalleta, ya dai ci gaba da tukin da yake, tace "To ka gaya min naka sunan" Yace "Sunana Fatima nima" ta xaro ido kamar tana ganinsa tace "To ai kai ba na mace bane" yace "To ni na menene?" Tace "Kai namiji ne mana" Ya d'an yi murmushi yace "Ya aka yi kika sa ni namiji ne? ni ma mace ne kamar ki" Ta kyalkyale da dariya har da kyakyatawa, juyawa yyi da sauri yana kallonta, murmushi kawai yake ya ci gaba da tukinsa, tayi dariyarta mai isarta sannan tace "Toh ai naji muryarka kato ne, ba irin na mata ba, kuma....." Matsawa tayi kusa da shi ta fara tattaba sa tun daga saman kansa, Bai san sanda ya samu waje yyi parking ba da sauri yana kallonta, ta sakko da hannunta har fuskarsa ta fara jan dogon hancinsa sannan ta shafa beard dinsa ta sakko da hannunta har chest dinsa, dariya ta kyalkyale da tace "Namiji ne wllh" kasa daina kallonta yyi, can yayi murmushinsa me kyau yace "How did you know?" Tace "Gashi naji gashin kan ka d'an kadan ne ba irin nawa ba, kuma kana da beard a fuskar ka, kuma you don't have breast" He couldn't help it but laugh out loud jin maganar ta na karshe, ita ma ta fashe da dariya tana taya sa, sosai Heedayah ta basa dariya, lkci daya ya daina dariyan yana kallonta yace "To ai ke ma baki da shi balle ni" ta tsuke fuska tace "Teacher na tace grown up people ne kawai suke da breast ni yar yarinya ce ai" Murmushi yyi yace "Ashe kema namiji ne kamar ni" Lkci daya ta 6ata fuska tace "Ni ba namiji bane, ni na mace ne..." tana fadin haka ta cire hularta dogon gashinta ya xubo kasa tace "Ka kalla ka ga" Ya fi second ashirin yana kallon gashin nata sannan ya motarsa after watching and making sure there is no car coming, sai da ya d'an yi nisa yace "Ke ma dai namiji ne bbu ruwana da gashin ki" rungume hannunta tayi ta jingina da motar ta ki cewa komai wai tayi fushi, bai kuma ce mata komai ba har suka isa gida, Mai gadi ya bude masa gate ya shiga yyi parking, fitowa yyi ya xaga ya bude side dinta yace "To na ji ke mace ce, sakko" ta turo baki xata sakko ya dagata ya fito da ita, tace "It is going to rain" kallon sky yyi yace "How did you know?" Tace "Ina jin kamshi" ya kalleta da kyau ya sake kallon sama, da hadari amma ba sosai ba, ya kama hannunta suka nufi cikin gidan, tare ya tafi dakin Mami da ita ya dau system din ya kamo hannunta suka fita, tana bin sa a hankali tace "I want to take tea" Yace "Me yasa baki gaya ma Mami a can gida ba" tace "Tace baxata sake bani tea ba" downstairs ya sakko da ita ya xaunar da ita saman kujera yace "Wait for me" ya ajiye system din hannunsa ya wuce kitchen ya kunna gas ya sa mata ruwan tea, Yana tsaye kitchen din yana jiran ruwan shayin ya tafasa aka fara iska sosai, muryar Heedayah ya ji with all her strength tace "Where are youuu" ya kashe gas din ya fito, tsaye ya ganta duk a tsorace, ya karasa inda take yace "I'm here" ta kamo hannunsa tace "Kar ka bar ni, ina jin tsoro" tana rike da shi ya tafi ya kulle duk windows din gidan har upstairs, lkci daya aka fara ruwa sosai, ya duka dai dai fuskarta jin kamar magana take yi yace "What?" Tace "I told you I smelt rain" d'an murmushi kawai yyi yana tunanin baiwa ne kilan nata, downstairs suka koma ya xaunar da ita saman kujera yace "Let me make the tea for you" da sauri tace "Noo, kar ka bar ni, ka tafi da ni plss" tare ya koma kitchen din da ita, tana makale jikinsa har ya hada mata shayin sannan suka dawo parlor, ya ajiye shayin saman center table yace "Ki jira ya huce" bata yarda ta xauna ba sai da ta tabbatar kusa da shi ne, ta jinginar da kanta shoulder dinsa tayi shiru, ya dau wayarsa ya haske fitila don tuni aka dauke wuta da ake iska, missed calls na Mami ya gani guda hudu, yayi dialing number ya kai kunne, yana fara ring ta dauka, a fusace tace "Junaid da ku ke tafiya baka ga hadari bane, me yasa baka dawo min da yarinyar ba??" Yace "Mami ni ban lura ba sai da muka iso nan gida" Mami tace "Where is she now?" Ya haska fuskar Heedayah ya ga idonta a lumshe, ya mayar da wayar kunnensa yace "She's sleeping" Mami tace "I don't care ko kana tuki cikin ruwa ko baka yi, just in the next 20 mins ina son ka dawo min da ita, I don't want to call you back after this" daga haka ta katse wayarta, kallon Heedayah ya sake yi xai kwantar da ita ya duba karfin ruwan da ake a waje ta bude ido da sauri ta rikesa cikin muryar kuka tace "Noo where are you going" yace "Ba Inda xanje kiyi baccin ki" kin sakesa tayi, ya koma ya xauna, ta kwanta jikinsa, Yana ta xaune parlon ita kuma tana ta bacci, har kusan karfe shidda, har sannan kuma ruwan ko raguwa bai yi ba sai ma karuwa, idan akwai abinda bai iya ba a rayuwa to driving ne cikin ruwa, sarai kuma Mami ta san hakan, duk motsin da xai yi Heedayah sai ta kara makale masa, bayan wani lkci ya haska fitilar wayarsa a fuskarta yaga fararen idonta a bude, duk tunaninsa bacci take, yace "Kin tashi?" A hankali tace "Idan nayi bacci xaka wuce ka bar ni ni kadai" Ya kwantar da ita jikinsa sosai yace "Noo baxan tafi in bar ki ba yi baccin ki" sai bayan Magrib ruwan ya tsagaita yana son yaje yyi sllh Heedayah ta ki sake sa duk da har sannan bata koma bacci ba, haka ya wuce dakinsa da ita yyi alwalan a can sannan yayi sllh suka fito tare, tace "Where is my tea?" Gaba daya ya manta da shayin dake kan center table, yace "let me make another one, wannan yyi sanyi" cikin few minutes ya hada mata wani shayin amma ba mai xafi ba, suka koma parlon ya xaunar da ita ya kai mata cup din baki, ta rike ta fara sha.... Tana gama shan shayin ya dau makullin motarsa yana rike da ita da system din Mami suka fita gidan, ya kulle gidan sannan ya nufi motarsa, sosai garin yyi sanyi, ya bude front seat ya xaunar da ita bayan ya ajiye system din a baya, ya xaga ya shiga motar suka bar gidan, dai dai kofar gidan Abba yyi parking, nan gabansa ya fara faduwa don yasan Mami won't take it likely with him this night, ya dai fito ya xaga ya bude ma Heedayah side dinta, ta laluba ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "Ina jin sanyi" ya saukar da ita yace "We are home" dai dai bakin gate suka hadu da Shuraim xai fito, Junaid na kallonsa ya sake hannun Heedayah ya basa hannu, Shuraim ya amsa yana kallon Heedayah daga sama har kasa, suka gaisa da Junaid, Shuraim xai fita Junaid yace "Ehm naga it's late already, pls can you go in with her, ina d'an sauri ne" Shuraim ya sake kallon Heedayah sannan ya kalli Junaid yace "Alright" Junaid yace "Thanks" daga haka yyi patting kan Heedayah ya sa hannunta cikin na shuraim yace "Ki gaida Mami, xan kawo mata laptop din gobe" juyawa yyi ya fita gate din ya nufi motarsa, Heedayah ta 6ata fuska xata yi kuka jin Junaid ya wuce ya bar ta, Shuraim dake ta tsaye Heedayah na rike da hannunsa gam, ya saci kallon motar Junaid ganin har yyi reverse ya xame hannunsa daga nata yayi wucewarsa masallaci, Heedayah dai na ta tsaye ga sanyi da take ji sosai sai juye juyen idonta take gwanin tausayi, Mai gadi ne ya fito daga dakinsa alamar shi ma xai wuce masallaci don yin Isha ganinta yace "Me kike yi a nan yarinya, ki shiga ciki mana" Cikin rawar murya tace "Bana gani ai" yace "Bakya gani kuma?" Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya cika idonta, kama hannunta Mai gadin yyi ya fara tafiya xuwa entrance din shiga gidan yaga tana bin sa a hankali, lkci daya jikinsa yyi sanyi, yace "To wa ya ajiye ki bakin kofa?" Tace "Sake ni yyi ya wuce ya bar ni" dai dai kofa suka hadu da Abba, Abba na kallonsu yace "Wa ya dawo da ke Heedayah?" Tace "Ban san sunansa ba" Kama hannunta Abba yyi ya wuce part din Mami da ita, Mami ta mike ganinsu, Bai ce ma Mami komai ba ya sake hannunta ya juya ya fita, kana ganinsa kasan he is angry and don't want to talk. Mami ta kamo hannun Heedayah tace "Ina Junaid din?" Heedayah tace "Ya wuce" Mami bata ce komai ba ta wuce daki da ita. Sai kusan sha daya na daren Mami ta tafi bangaren Abba bayan Heedayah tayi bacci, xaunawa tayi kusa da kujeran da yake xaune tace "I'm truly sorry barrister, hakan baxai kara faruwa ba in sha Allah, nasan you are not happy" Yace "It's okay, but pls ki sa ido a kan wnn yarinya fisabilillah, don't expose her much to anybody, let her be home all through, kin san condition dinta, tana bukatan kulawa sosai Rahinah, ina jin yarinyar nan tamkar jinina bana fatan wani abu ya sameta....." Mami tace "In sha Allah" yace "Yaushe Farida xata dawo?" Tace "Ranan laraba" yace "Alright, na sa a nema ma Heedayah lesson teacher soon, Shuraim kuma xai dinga mata karatun qur'ani da asuba na gaya masa, so after prayer kar ki bari ta koma bacci...." Mami ta kallesa sai dai bata ce komai ba... Dai dai wnn lokacin kuma Mumy na dakinta ta shige can cikin bathroom tana ta waya kasa kasa, Mumy tace "Kai ni har na gaji da bayani har yanxu baka fahimta ba, ce maka nayi makauniya ce fa yarinyar, kuma dududu Rabi'ah ta ma ta girmeta ina ga, yar yarinya ce fa sosai, bata wuce sha biyu ba ma kila...." Dariya sosai wanda take wayan da yyi yace "Haba Hajiya, to meye kuma xaki daga hankali kan yar yarinya? Ni wllh na xata ma kishiyar ce kike...." A fusace Mumy tace "To kai ina ruwanka? ba dai kudin ka kawai ka sani ba, ni fa na riga da na gama magana da kusan mutane uku, kawai raba kafa nake ta yi ta ko ina shi sa na kira ka ba wai wani abu ba don kai ka fiye shiririta, ina ruwanka da kankantan yarinyar?? kaga.... idan har ka shirya kaga xaka iya sai ka kirani gobe da safe ni kwanciya xan je inyi..." Tana kai wa nan ta kashe wayar ta fice daga bandakin ta kwanta kan gadonta tana fata ta samu bacci ko xata ji saukin xafin da ranta ke mata, rabonta da baccin kirki tun ranan da ta dawo kaduna. Da asuba Shuraim na dawowa masallaci ya shiga parlon Abbansa don gaishesa don kusan tare suka dawo masallacin, Abba dake hada wasu files ya amsa ba tare da ya kallesa ba yace "Yau xa ku fara karatun da Heedayah koh?" Shiru Shuraim yyi da farko, yana mamakin why all of a sudden Abba xai fi karkata hankalinsa gaba daya kan makauniyar nan, Bai ma ce suyi har da su Rabi'ah ba wai Heedayah, jin shiru Abba ya juya ya kallesa, Shuraim yace "Sure in sha Allah" Abba yace "Good, a can parlon Aunt dinka xaku dinga yin karatun" shiru ya kuma yi na kusan second goma sannan yace "I prefer mu yi a inda nake yi ma su Rabi'ah" Abba yace "Ina kenan?" Yyi kasa da kai yace "Balcony" Abba yace "Noo, akwai sanyi waje, you look for another alternative" mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa ya fita, gaba daya ji yyi ya kara tsanar Heedayah har ransa, WTF, ba don he can't look into his father's eyes and tell him baxai yi ba da bbu abinda xai hanasa yin hakan, ya fi minti biyar tsaye a parlor kafin ya nufi part din Mami ya tsaya ya kwankwasa kofar fuskarsa daure. For those forwarding this book to various groups bayan sun san na kudi ne, ni baxan ce komai ba, but su yi adalci, it's not fair hakan ba na kyauta bane littafin, na hada su da Allah su yi hakuri su daina hakan ba don ni ba..... Masu neman complete Heedayah su ma sai su biya dari uku a basu sharp sharp don naga sun ma fi masu subscribing for daily update yawa, idan ba complete bane damasu baxa su biya ba sai dai su karanta a titi yana galantoyi, to ku biya a baku complete, I have change my mind, kawai da evidence din ku xa ku taho sai a baku complete din....🌚🌚🌚 Heedayah na kudi ne, ba kyauta ba, try and subscribe to read happily bbu burden a kanka.... it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mami ta bude kofar parlonta jin ana knocking, suka yi ido hudu da Shuraim, sauke idonsa yyi da sauri, murya can kasa yace "Ina kwana" A takaice tace "Lafiya.... Ya aka yi?" Yace "Karatu xa mu yi?" Mami tace "Da wa?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Ban san sunanta ba" Mami tace "Toh sai kayi kokarin sanin sunan nata coz gida daya ku ke ynxu" daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta da wani irin kallo, Mami ta karasa sa ma Heedayah kayanta don har tayi wanka, ta dau hula ta sa mata a kanta sannan tace "You listen and pay attentive kin ji, Kuma kiyi kokari sosai, idan kin dawo xaki koya min nima" tace "Toh Mami" Mami ta kama hannunta suka fita xuwa parlor, har sannan yana tsaye, dai dai kusa da shi Mami ta tsayar da Heedayah, sannan ta juya ta koma ciki ta kulle kofarta, Heedayah ta kai hannu tana laluba wajen ta ji inda yake, hannunsa ta ta6a, bbu bata lkci kamar jira yake ya buge mata hannun yace "Are you stupid" Ta janye hannunta da sauri kamar xata yi kuka tace "Ni me na maka??" Ya kalli left sannan ya kalli right ya fixgo hannunta ya fara tafiya, bin sa take hawaye cike idonta tace "Ni ka sake ni bana so, baxan yi karatun ba kuma, baxan yi ba...." Ko saurarenta bai yi ba har ya isa wani area cikin parlon wanda ya kasance study area din Abba, sannan ya saketa yana mata wani kallo yace "Kika ce baxa ki yi karatun ba??" Cikin kuka tace "Ehh ni baxan yi ba, ka kai ni wajen Mami" ya ja kujera ya xauna yace "Sai ki kai kanki ai" durkushewa tayi a kasa ta fashe da kuka sosai tace "Ni sai na gaya ka da Abba wllh...." bude kofa aka yi Shuraim ya juya da sauri bai jira ya ga wanda ya bude kofar ba ya xamo kasa kusa da ita ya dake cike da karfin hali yace "Okay, sorry mu yi karatun ynxu" ta make kafada tace "Ban so" satan kallon cikin parlon yyi duk da bai ga wanda ya fito ba har sannan, ya wani hade rai yace "I said sorry" Kamar jira take tace "Ban so nace" sai kuma ta fashe da wani sabon kuka, kamshin turaren Abbansa da ya ji yasa yasan Abba ne a parlon, ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta a hankali yace "But nace kiyi hakuri, I'm sorry" ta turo baki tace "To me yasa xaka buge min hannu sbda bana ganin ka, kuma shine kake ja na don in fadi in ji ciwo" Ya kara satan kallon parlon cikin dakiya yace "To rama" ta kai hannu ta laluba kafarsa sannan ta maka mashi duka a nan, kallonta kawai yake da mamaki xuciyarsa na tafarfasa, still controlling himself yace "Shkkn?" Ta gyada masa kai a hankali tana goge idonta, ya koma saman kujera yace "To fara karatun" tayi kasa da murya ta fara karatun a hankali, har Heedayah ta tsaya a aya na 15 bai ji inda xa ayi mata gyara ba, her recitation was perfect and cool for her age, sai dai wayarsa kawai yake dannawa, Ya saci kallonta ganin tayi shiru sai dai bai ce komai ba still pressing his phone, ta turo baki tace "To ai a nan mu'allimata ta tsaya min" yace "Toh sai ki tsaya a nan din" yana fadin haka ya mike ya tafi kitchen, Sabuwar me aikin da Mumy ta dauka ne a kitchen din tana ta gyare gyare da goge goge, yace "Wancan yarinyar xaki dauka ki kai ta wancan part din..." Gaishesa tayi da ladabi tace "Wace yarinya yallabai?" Fita yyi kitchen din yace "Ki taho ki ganta" sai da ya tabbatar ta ga Heedayah sannan yayi wucewarsa sama, har part din Mami mai aikin ta kai ta, duk da sai faduwa gabanta yake don ba karamin warning Mumy tayi mata ba kan cewa ko bangaren Mami kar ta kuskura ta bi balle ta shiga, Mami ta bude kofa ta amsa gaisuwan mai aikin sannan ta kama hannun Heedayah suka koma ciki ta kulle kofar, Mami na kallon Heedayah tace "Ina me koya maki karatun?" Heedayah tace "Mami bai koya min komai ba" Mami tace "Me yasa?" Heedayah ta 6ata fuska tace "Mami mugu ne, I don't like him to teach me anymore...." Mami dai bata ce komai ba ta wuce can bedroom da ita, Heedayah tace "Mami he is wicked, ni nafi son wannan din nan ya koya min" Mami tace "Wa?" Shiru Heedayah tayi sai kuma tace "Yace min sunansa Fatima shi ma, kilan baya son gaya min sunansa" Mami na kallonta tace "A ina yake?" Heedayah tace "Wanda ya xo jiya ya tafi da ni" Mami tace "Sunansa Junaid, but you call him Yaya" tace "To, na fi son Yaya ya dinga koya min" Mami bata kuma cewa komai ba ta xaunar da ita saman gado tace "Kwanta kiyi baccin ki xan je in hada maki breakfast" daga haka ta fita dakin, Heedayah ta kwanta. Mami na tsaye kitchen su Rabi'ah suka shigo ajiye plates da cups da suka yi breakfast duk suka fice bbu wanda yace mata komai, ta gama dafa Indomie da kwai da shayi da take yi ma Heedayah ta fito kitchen din, a parlor ta tadda Abba alamar he is going out kuma ita yake jira ta fito kitchen, yana kallonta yace "Ina Heedayah, bata gaisheni ba yau" Mami tace "Let me bring her" daga haka ta wuce bangarenta, Duk wannan abun Mumy na ta kai komo parlon kai kace wani abu take yi, Abba dai bai ce mata komai ba don har ranan bata gaishesa bata masa magana a gidan, Yana ta tsaye parlon Shuraim ya fito shi ma xai fita, Abba yace "Yaushe rabon ka je gaida kaka Aliyu?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Abba bana dawowa da wuri ne ynxu" Abba yace "Ohk yau ka je ko da kuwa tsakar dare ka dawo, and you go with Heedayah ita ma ta gaisheta, she is complaining ba a kai ta ba jiya da naje...." Shuraim ya kalli Abba, amma bai ce komai ba, Abba yace "Su Khadijah ma nace idan sun dawo islamiyya su wuce can, so idan ka je sai ku dawo tare gaba daya" Mami ce ta karaso rike da Heedayah, Abba na kallonta ya dafa kanta yace "How are you dear?" Tace "Good morning Abba" yace "Morning Daughter, kun yi karatun yau koh?" Ai ko rufe baki Abba bai yi ba Shuraim ya nufi kofa, Heedayah tace "A'a bai min ba" Abba ya kalli Shuraim da har ya isa kofa cikin tsawa yace "Aliyu" Mumy ta karaso cikin parlon da sauri tace "Ba gane Aliyu ba?? Shi Aliyun malami ne ko kuma makafi na haifosa ya xo ya dinga yi ma karatu, kaga a gaskiya barrister ku tsaya iya Lane din ku kai da Sabuwar matarka da makauniyar ka a gidan nan, ku fita harkarta da ta 'ya yana, Yaushe aka sa Shuraim ya dinga koya mata karatu bani da labari? Kanninsa da suka fito ciki daya ma an ga yana koya masu karatu balle makauniya, to wllh ni a kiyayeni a gidan nan, ku bar ni kawai yanda ku ka gan ni ayi ta tafiya a haka kar ku kai ni bango...." Abba yana kallon Shuraim da kyau yace "Me na ce maka jiya da asuba?" Yyi kasa da kai bai ce komai ba, Abba yace "Good, idan kana son ganin the other side of me ka sake tsallake magana ta a gidan nan, wllh sai dai ka tafi wani gidan uban amma ba wannan gidan ba, yanda uwarka ta isa ta fada maka kaji, haka nima, idan kuwa watsar da maganata xaka dinga yi a kan wani banxa son xuciya na uwarka to you have to change anoda father and anoda home, Kuma ni nayi instructing dinka ka dinga koya ma Heedayah karatun qur'ani in har ka isa ka tsallake instruction din in gani" A mugun fusace Mumy tace "To sai me don kace ya canja uba ya bar gidan nan?? Kansa farau barrister? Ai ba abun mamaki bane don ka fadi haka tunda an gama da kai an shanye ka, nan gaba mu ma duk kora mu xaka yi ka cika gidan nan da agololi da 'ya yan tsintuwa, Kuma in har ni na haifesa baxai koya ma wata makauniya karatu ba tunda ban ce yaje xai gani ba" Dariya Mami tayi ta kama hannun Heedayah ta koma bangarenta tana girgixa kai, Shuraim dai bai iya yace komai ba, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon, Banda kallon Mumy bbu abinda Abba yake as if thinking of how to punish her, cike da neman fitina tace "Ehh ka kalleni da kyau, cewa nayi in dai ni Maryam ina gidan nan wllh wllh Shuraim baxai koya ma wata shegiyar makauniya karatu ba, uwar me ya hada da ita xaka ce ya koya mata karatu???" Calmly Abba yace "Maryam ki tafi gidanku sai na neme ki, bana son in dawo in tarar da ke gidan nan don wllh in har na dawo na same ki a cikin gidana to na sake ki...." Yana fadin haka ya nufi kofa walking just as the barrister he is, Mumy ta bude baki ta bi sa da kallo a sanyaye ta kasa cewa komai.... Kuka bbu irin wanda Mumy bata yi ba a dakinta, ta kira duk kawayenta ta sanar masu abinda ake ciki, Hajiya Sadiya ce ta samu karshe a waya, Hajiya Sadiya ta dinga salati tana cewa "Ki tafi gida kuma?? Anya kan barrister daya kuwa, yaushe kika dawo daga gidan xai ce ki koma? Ehh lallai bbu lafiya, ba dai kin tsaya fi'ili wai ke baxa ki je a nema maki taimako ba, ke da kika fi kowa imani, to wllh taki ta sameki, shegiya nake idan haka yar bokon nan ta shigo maki gida, wllh da shirinta ta shigo, lafiyayyen shiri kuwa, mance komai xaki yi Maryam mu tafi mu san nayi kafin lkci ya kure maki, ba fa karamin case bane wnn wllh, tunda kike da barrister ya ta6a cewa ki tafi gidanku, ki xauna fa kiyi naxari, to wllh ana dab da kwace maki gida da mijin ki, wnn makauniya dai ta jaza maki abubuwa iri iri a rayuwa, duk ita ce silar faruwar komai" kuka kawai Mumy take kamar ranta xai fita tana cewa "Wlh Sadiya na canxa xuciyata xan iya kashe yarinyar nan idan hakan kadai ne mafita gareni, ta tarwatsa min farin ciki, ta tarwatsa min gida, a kanta barrister yake min duk abubuwan nan, ga kishiya ta sa an rangada min...." Sadiya tace "Bbu wani lkcn kuka da kumfar baki Maryam, ki dau duk abubuwan da kike bukata ki baro gidan nan kafin ya dawo saki ya tabbata a kanki, ki taho nan gidana mu san abun yi cikin gaggawa, maxa ki fita daga gidan, Kuma a gaban yar bokon yace ki tafi gida?" Mumy ta kara rushewa da kuka tace "Wa ya sani ma ko tana labe duk tana ji, ni dai ga ni nan xuwa ynxu" daga haka ta katse wayar ta shiga hada yan kayanta da sauri kar barrister ya dawo, cikin mintunan da basu wuce goma ba ta bar gidan xuwa gidan Sadiya. Mami na xaune parlonta misalin karfe biyar na yamma da frnds dinta uku da suka kawo mata ziyara, ko marmarin xaman main parlor din gidan bata ta6a yi ba tun xuwanta, hatta bakinta bata bari su xauna main parlor, nata parlon take kawo su, bata ma san Mumy bata gidan ba tun safe, aka kwankwasa kofar parlonta, mikewa tayi ta isa bakin kofar ta bude, Shuraim ne tsaye sanye da kananun kaya, yyi kasa da kai yace "Ina yini?" Tamkar ana tilasta sa ya gaisheta can ciki ciki, Tace "Ya aka yi?" Bbu walwala yace "Abba yace xa mu je can gidan kaka da ita" Mami tace "Ita wa?" Yace "Yarinyar" Mami tace "Yarinyar bata da suna?" Shiru yyi mata, can yace "The blind girl" Mami tace "Toh ka kirasa ka tambayesa sunanta, kada ka sake xuwa min bakin kofa kana neman blind girl I don't have any" tana fadin haka ta rufe kofarta almost on his face. Da ba don ya san Abbansa is jet angry at him ba kuma kar ya sake wani laifin da wucewarsa kawai xai yi ba tare da Heedayah ba, gaba daya ya rasa yanda xai yi, bayan kusan minti biyar ya sake kwankwasa kofar, ba Mami bace ta bude kofar wnn karon, Barrister Zuwaira ce ta bude, yace "Ina yini?" Tace "Lafiya lau.... A carbon copy of ur father facially but not physically, ba haka Barrister Ahmad yake ba gaskiya, be human plss, let me get u the little girl" daga haka ta juya ta koma ciki ya bi ta da wani irin kallo, sai ga ta ta dawo da Heedayah da Mami ta sama Hijab har kasa duk da kananun kaya ne sosai jikinta tunda gidan Kaka xa a je, Barrister Zuwaira ta mika masa hannun Heedayah da ta bata fuska, ya kama hannun nata, ta rikesa gam ya juya ya bar wajen, bin sa kawai Heedayah ke yi kmr xata yi kuka har suka fito balcony, a dai dai nan ya kwace hannunsa daga nata ya sauka balcony din fuskarsa daure, a hankali take tahowa bayan ya saketa, shi ko har ya fara tafiya ya tuna few stairs dake wajen ya juya da sauri.... Bai yrda ta kai kasa ba ya dauketa irin rikon newborn with both hands, ba karamin tsorata tayi ba jin ta tafi xata fadi sae kuma taji an dauketa bata fadi ba ta ta6a kirjinsa kamar xata yi kuka tace "Ni dai baxan je ba kuma...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Masu complete Heedayah hope har kun gama karantawa🌚 Shiru har ynxu banji sharhin karshen book din ba, duk da nima ban san me ya faru karshen ba😯 Shuraim bai saurareta ba har ya isa motarsa ya bude back seat ya jefata ciki ya kulle sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga, tuni Mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan, Har ya isa kofar gidan Baffa bai kalli Heedayah dake bayan mota ba, ta rungume hannu kamar xata yi kuka, a compound din gidan yyi parking, sai a sannan ya kalleta ta madubi, ya wani hade rai kamar tana ganinsa, d'an tsaki ya ja ya bude motar ya sauka sannan ya bude mata side dinta yace "Fito min a mota" Ta make kafada a hankali tace "Ni ka maidani wajen Mami baxan fito ba...." Yace "Kee.... an ta6a xaneee ki???" Bai jira cewarta ba ya jawota ya fiddo ta daga cikin motar ya ajiyeta kasa ya rufe motarsa yace "Idan ina magana kina yi sai na fasa maki baki wllh...." Ta fashe da kuka sosai tace "To me bakina yyi maka, ni bana sonka you are wicked...." Sudais ya hango ya fito daga cikin gida, hakan yasa ya kai fuskarsa dai dai nata yace "Xa ki san I am wicked soon...." Daga haka yyi wucewarsa ya bar ta nan a tsaye, yana kai wa inda Sudais yake, Sudais yace "why are you leaving her all alone, how did u expect her to walk alone" Shuraim yace "Toh ni d'an jagoranta ne aka ce maka??" Bai jira cewar Sudais ba yyi wucewarsa ciki, Sudais ya karasa inda take da sauri ya kamo hannunta ya duka yana kallon manyan idanuwanta da ya cika da hawaye yace "What happened cutie..." Cikin rawar murya tace "I hate him...." Sudais ya rungume ta yana goge mata hawayen idonta yace "Noo cutie cry no more, mu tafi ciki ki gaida kaka...." Kamar ko jira take ta fashe da kuka sosai, rikicewa Sudais yyi ya shiga lallashinta, har sai da ya ga tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, lkci daya ya ji ransa ya baci, ya mike ya kama hannunta suka wuce ciki, parlon kaka ya tadda Shuraim, Kaka sai harkar gabanta take tana 'yan wake wakenta na tsofaffi ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma bai kalli inda take ba yana danna wayarsa, Sudais na kallonsa fuska daure yace "Shuraim why will you leave the innocent girl all alone...." Shuraim yace "Plss Sudais don't question me, I am not ready to answer you..." kaka ta ajiye tsummar hannunta tace "Me ya faru Sudess?" A fusace Sudais yace "Kawai barin yarinyar yyi ita kadai a tsakar gida ya san ba gani take ba, what sort of nonsense is that" Kaka ta nemi waje ta xauna tayi tagumi a hankali tace "Ohh naga abinda ya isheni ni patuuu, Kai amma dai Amadun ne gantalalle wllh, me yasa xai hada baiwar Allah da bata san komai ba da wannan katon mutumi, wato Amadu ya raina mugun halin d'an nan nasa koh? Bai san abun ya wuce misali ba, ya wuce hankali ya dauka ba ko, Wllh shuree yake ko wa?? ba shi da xuciya me kyau ina fada kuna ganin kamar wasa nake, Baka ga ko gaisheni bai yi ba da ya shigo yana jiran ni in gaishe sa d'an banxa, ni dai ba ruwana don na haifi ubanka ba yana nufin ina da wani alaka ko dangantaka da kai bane, kayi ta kanka inyi ta kai na, makauniya kuma sai Allah ya saka mata tunda bata cuce ka ba...." Sudais dai sai hararan Shuraim da yyi kamar bai san suna yi ba a parlon yake, wayarsa kawai yake dannawa, kaka ta kamo hannun Heedayah ta xaunar da ita saman kujera tace "Sannu da xuwa Deedaya, ai da kyau tunda ba a titi ya gantalar da ke ba yyi wucewarsa ya ja ma d'a na fitina, haka nan muke fama da shi da mugun halinsa, mu ma ba kyale mu yyi ba, Bai san ba sonsa Allah ya fi yi da ya bar sa da idanuwansa ba ke kuma ya barki bbu idanuwa, shi fa Allah ba ruwansa gobe Shuree na iya tashi ya gansa a duniyar makafi to sai yyi yaya??" Tsaki Sudais ya ja ya fice daga parlon, Shuraim ya bi sa da wani kallo ta gefen ido, Kaka ta bude fridge ta fiddo malt ta bude mata tace "Wnn yaron kirki Junaidu ya xo jiya ya kawo min su da yawa, to bai fiye min wasu ba Allah na tuba, bbu abinda fa na hada da shi, kawai dai babarsa na auren d'a na ne, amma ko shekaranjiya sai da ya xo nan gaisheni muka yi ta hira gwanin ban sha'awa, to wasu ma idan suka xo sai dai su dinga tunanin ynda xa su cuceka kafin su wuce.... To ni dai bbu ruwana" A hannun Heedayah Kaka ta saka malt din, Heedayah ta fara sha a hankali tana lumshe ido, Kaka ta xauna tace "Toh madallah, yau dai na gama aikin da wuri, na gode ma Allah" Shuraim ya kashe wayarsa calmly yace "Ina yini Kaka?" Tace "Lafiya lau wllh, ai tun safe sae ynxu na gama kimtsa ko ina, baka da lafiya ne na ganka duk wani iri yau?" Yace "Lafiya ta lau" tace "Atoh naga duk ranka a bace ne ai, ko kai ma in kawo maka mantinan ne?" Ya girgixa kai kawai, tace "Toh in xubo maka abinci, shinkafa ce dai da miya" nan ma ya girgixa mata kai, tace "Toh ban da abinka meye na bacin rai kuma Mai gida, da shi Amadun yace ka kawota nan sai kace masa gaskiya kai kana da wajen xuwa, ae ba ajiye ka yyi ba, ban da neman magana irin tasa kai xai sa kayi ma yar makauniyar direba, shi da ya jajubo ta ba sai ya kawota da kansa ba, ni ba ruwana bana son rashin gaskiya, abu dai ba ayi tsakani da Allah, ae baxa ka rasa uxurin gabanka ba kai ma" Mikewa Shuraim yyi ya dau bottle water daya a fridge yace "Xan shiga in gaida su Umma" Kaka tace "Toh sai ka dawo, sai dai yau ko yar kazan nan ba a kawo min ba Mai gidan, ko da yake ina xaka kawo min kaza an hada ka da yarinya ba dangin iya balle na baba...." Fita yyi parlon, kaka ta tabe baki ta mike ta dau tsumman ta ci gaba da goge gogen da tace ta gama, Heedayah na gama shan malt din ta jefar da can din nan parlor, kaka ta leko daga d'an kitchen dinta tana kallonta tace "Ehh lallai, to sauka ki dauke ki fita da shi bola, ae ni ba baiwar Amadu bace balle ke" Heedayah ta sauka da sauri ta durkusa tana laluba Inda xata ji can din, kaka tace "Laluba gefen ki maxa ki dauke ki fitar min da shi ni ba yar bola bace, kaji min yarinya in mata inuwa tayi min rana, duk gidan nn bbu wanda na bai wa mantinan nan sae ke, shine xaki walakanta min parlor" Heedayah ta samu ta dauke can din ta mike duk a tsorace, a hankali tace "To bana gani" kaka tace "Hagun ki xa ki bi ki fita, ni xa kiyi ma karya kice ba kya gani" dai dai nan Sudais ya shigo parlon, kaka tace "Kaji wai xata je ta yarda gwangwani ta ja min salalan siya wajen Amadu Sudess...." Tsayawa Heedayah tayi tana kalle kallen kamar mara gaskiya, Sudais ya kama hannunta suka fice daga parlon, kaka tace "A'a, yau ga ikon Allah, ya xan ce a kawo min yarinya takanas kuma ka xo ka dauketa Sudess" tuni Sudais ya kulle mata kofarta, ya wuce xuwa dakinsa yana rike da hannun Heedayah, Heedayah ta ta6a hannunsa tace "Waye kai?" Ya kai bakinsa kunnenta yace "Heedayah ne ni" tana jin muryar sa ta washe hakora tace "Baka bani sauran chocolate dina ba" yace "Shi xan je in baki yanxu" ta kankame hannunsa tace "Mu tafi gida wajen Mami da kai sai mu bar wnn mugun a nan plss" dariya yyi ya wara ido yace "Da gaske" ta gyada masa kai tace "Ehh I don't like him, shi mugu ne...." Bude kofar bedroom dinsa Sudais yyi yace "To gaya min me da me yyi maki" Shuraim dake kwance saman gadonsa ya juya yana kallonsu, tace "Komai ma yana min ai, first ya fara buge min hannu don yaga bana gani, kuma Abba yace ya min karatu ya ki yyi min..." ta girgixa kai tace "Noo... I just don't like him, and I will never like him...." Dariya Sudais ke yi yana kallon Shuraim da ya mike xaune fuskarsa a daure yana kallonta, Sudais ya dagata ya xaunar gefen gado yace "Toh kin gaya ma Abba abinda yake maki" tace "Yau duk xan gaya masa ae, har da duka na da yyi...." Ta wara ido tace "Ae kai ma ka iya suratul jinnnn Koh?" Ya gyada kai yace "Sosai ma" tace "Toh mu tafi gida da kai sai mu bar sa wajen matan nan me yi ma mutane fada" Sudais yyi dariya yace "Sunanta kaka" tace "To mu bar sa wajen kaka shi, bana son ya bi mu" Gaba daya Shuraim ya kasa cewa komai, Sudais na kallon manyan idanuwanta yace "Toh xa mu bar sa a nan mu tafi gidan tare kin ji cutie" ta washe hakoranta tace "Toh ina chocolate dina" mikewa yyi yace "Bari in dauko maki" Sai a sannan Shuraim ya fixgota da karfi yace "Uban waye mugu?" Sosai ta tsorata jin muryar sa, ta fasa ihu tana son kwace kanta, Sudais ya dawo da sauri yace "Don't you dare touch her, don't try that" yana fadin haka ya dauke Heedayah da jikinta ke rawa a wajen, ta kankamesa cikin rawar murya tace "Take me away plss" ficewa Sudais yyi daga dakin nasa ya kulle kofar trying hard not to laugh. Mumy ce xaune parlon Hajiya Sadiya tayi tagumi, Hajiya Sadiya tace "Anya kina ganin baxa a xarge ki ba Maryam, hakan yyi wuri ai wllh, ki bari kawai mu lallaba ayi duk abinda xa ayi a samu ki koma dakin ki, kinga idan kina gidan ko ma me ya faru bbu wanda xai xarge ki bbu wanda xai kawo ki a rai, amma yanxu fa?? ai daure kanki kawai xa kiyi, barin mijin ki barrister, kishiyar ki barrister" Mumy tace "Nima wllh tunanin da nake kenan, gaskiya kika fada, bari a share wnn batun ynxu kawai...." Hajiya Sadiya tace "Yauwa, yanxu kina komawa nunawa xa kiyi kin fi kowa sonta ma a gidan, kiyi iya bakin kokarinki ki danne komai a kasar xuciya ki, ita kanta kishiyar taki ki d'an fara sake mata kuna gaisawa yanda bbu wanda xai samu damar xargan ki nan gaba, karatu kuma kiyi ta tausasa Shuraim yyi mata, yaranki duk ki sa su dinga shiga gun kishiyar taki su dinga jan makauniyar a jiki, wllh duk kika bi shawarata komai xai xo mana da sauki Maryam...." Mumy tace "Kai da bani da ke da nayi Kuka Sadiya, nagode aminiyar kwarai Allah ya bar xumunci, amma ita wnn tsohuwar kuma ya kike ganin xan yi da ita in huce takaicin annamimancin da ta min" Dariya Hajiya Sadiya tayi tace "Ke wa ke sa wnn ta6a66iyar a lissafi, ba fa isasshen kwakkwaro gareta ba, ynxu dai muyi concentrating a abinda yake gabanmu ki ajiye batun wnn tsohuwar" Mumy tace "Toh shkkn, ynxu dai bari inje gida wajen Salima in ji ita kuma ya ake ciki, daxu na kirata tace da yamma xata koma gida, bari in je in dawo" da haka suka yi sallama Mumy ta bar gidan Hajiya Sadiya. I don't have complete Heedayah pls fans... Sae dai in aron brain din Khaleesat Haiydar xan baku ku shiga ku karance tass, I made jest of those that are not patronizing☹️ sae dai su karanta a titi suna jiran su samu complete... and a lot of pple are thinking da gaske ne akwai complete din, to nima kullum nake typing din ban san ma me xai faru a karshen ba😄😄 Lol.... patronize ur novelist lovely fans, ni ban iya Allah ya isa ba, amma kuyi patronizing for the sake of Allah coz it's not free.... And ina xumunci da duk wanda ya siya Novel dina, bana goge lambarsa.... Meanwhile ina son jan hankalin readers sau daya nake posting a rana which is 5 to 6 read mores everyday, in har nayi less than 5 read more may be 3.... To xan yi post da daddare in cike read mores din.... Stop expecting more than that all my books haka nake yi. Thanks lovely fans Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Bayan isha Shuraim ya shigo parlon kaka da sallama, kaka dake xaune ta sa tv gaba wai tana kallo tace "Ni ai na xata ka wuce, ka ma ci abinci kuwa ko basu ga daman baka ba?" Ya xauna saman kujera yace "Bana gidan, yanxu na dawo, ina su Khadijah?" Kaka tace "Waye kuma su Khadijah, tun karfe shidda suka wuce kamar ana tsungulinsu ai, kuma uwar ce ta koya masu idan sun xo kar su dade, wannan yarinya Deedayah kadai ce kwance tana bacci a daki, to ni bata fiye min su ba ma Allah na tuba..." Bai tanka ta ba, bayan wani lkci yace "Toh ki taso ta xa mu wuce..." Kaka ta juyo da sauri tace "In taso ta kuma, nan din da can gidan naku ba daya bane xan taso ta? ko kuma me xata maku idan ta je can gidan ban da wahalar da ita da ku ke" Yace "Abba bai ce in bar ta a nan ba" Kaka tace "To dama ya xai ce a bar ta a nan in cinyeta ga ni mayya, sai ka shiga ka daukota ku wuce ku bani waje, idan haka ne ma kar a sake kawo min ita ko nace a kawota, baka ga ba har kitso sai da nayi mata na wanke nata hijabi da ta 6ata da lemon da wnn mutumi Sudess ya bata shi kuma wahalalle, ita kuma wnn sabuwar matar ta rantse baxata daina sa mata kayan shegu ba, har nace xan bada kudi a siyo atamfa ko 'yan dubu dubu a dinka mata, to ba ruwana na fasa...." Mikewa Shuraim yyi ya shiga cikin dakin, kwance ya tadda Heedayah tsakiyar gadon Kaka tana bacci manyan kalaban da kaka tayi mata ya rufe fuskarta, ya karasa bakin gadon yana kallonta kafarta ya buge amma bata ko motsa ba, ya sake buge kafar ta juyo ta bude idanuwanta da suka kumbura a hankali, kana ganinta kasan ta ci kuka, yace "Sakko kar in wuce in bar ki" Jin muryarsa ta fara sakkowa tana lalube lalube ta mike tsaye, kama hannunta yyi tana bin sa kamar xata fadi suka fita dakin, ya dau makullin motarsa saman kujera yace "Sai da safe" Kaka tayi masa banxa ita a dole an tafi da Heedayah, dai dai bakin kofa ya ji an wurgo masa abu a kai ya juya ya ga Hijab din Heedayah ta jefo masa, ya rike Hijab din yyi ficewarsa ya kulle mata kofarta.... A kusa da motarsa ya sake hannun Heedayah bayan ya bude motar, ita dai tana tsaye sai bin inda taji motsi take da ido, yace "Baxa ki shiga ba sai na wuce na bar ki?" Kamar xata yi kuka tace "Toh ai bana gani, Kar ka wuce don Allah" yace "Xa ki kwana a nan kuwa idan ni xan saka ki cikin motar" da sauri ta fara ta6a motar tace "Aa plsss" Ta laluba jin motar a bude ta shiga, kulle motar yyi ya xaga xai shiga side din driver sai ga Sudais, ya jira har ya karaso, Sudais yace "What about Heedayah?" Ba tare da Shuraim ya kallesa ba yace "Tana wajen kaka, sai da safe" Sudais yace "Ohk a nan xata kwana?" Shuraim yace "Ehh" Sudais yace "Alright, sai da safe" Shuraim yace "Allah ya kai mu" daga haka ya shiga motarsa yayi reverse, Sudais ya koma ciki. Shuraim na isa gida yyi parking a parking space ya fito ya bude back seat, kwance ya ganta ta koma baccin, bude gate da aka yi yasa ya juya yaga Abba ne ya shigo gate din from mosque, Tashinta ya shiga yi yace "Sakko mu shiga ciki we are home" Bai jira tace komai ba ya sauko da ita ya kama hannunta ya nufi entrance din shiga gidan walking calmly... Mami na kallon Heedayah dake xaune saman kujera tace "Toh shine kike kuka Heedayah?" Cikin rawar murya tace "Da xafi ta min, kaina yana ta ciwo yanxu" Mami tace "To yi hakuri xai daina my dear...." Abba ya bude kofar parlon Mami ya shigo, Mami na kallonsa tace "Welcome..." Yace "Thank you, sai yanxu suka dawo" tace "Ehh gashi kaka tayi mata kitso ma" Abba na kallon idon Heedayah yace "What happened to her eyes?" Mami tayi dariya tace "Kukan kitso mana" Heedayah ta fara shessheka tace "Abba xafi yake min" Abba yace "Xafi kuma?" Ta gyada masa kai, yace "Toh a kwance" Mami tace "A kwance? nan da gobe fa xai daina xafin" Abba yace "No a kwance gaskiya, wnn kitson ai an dauresa da yawa, Kar ya ja mata matsala, till date Rabi'ah bata kitso a gidan nan sbda irin haka" Mami tace "Ikon Allah...." Abba ya fita don daukan wayarsa dake ring, Mami na kallon Heedayah tace "Toh baxa a kwance ba mu je ki kwanta, kin dai ci abinci Koh?" A hankali Heedayah ta gyada mata kai, Mami ta kama hannunta ta wuce da ita bedroom, ko da ta fito a parlonta ta tadda su Khadijah da Rabi'ah a xaune kana ganinsu kasan Abba ne ya saka su shigowa, duk suka gaisheta, ta amsa tace "Kun debi abinci a kitchen?" Khadija tace "Uhn mun ci" Ranan dai duk a bangaren Mami suka kwana. Da Asuba Shuraim na dawowa masallaci ya tafi part din Mami, a hankali ya kwankwasa kofar, Rabi'ah ta bude, tace "Yaya ina kwana?" Yace "Lafiya, ina wannan yarinyar take?" Ta d'an turo baki tace "The blind girl? Tana can daki" yace "Fito min da ita" juyawa tayi ta koma, Mami na kallon Rabi'ah tace "Waye?" Rabi'ah tace "Ya Shuraim, yace wai in taho da ita" Mami tace "Bata jin dadi sai gobe" Rabi'ah ta juya ta koma ta gaya ma Shuraim, wani ajiyar xuciya ya sauke ya juya ya wuce part dinsa.... Da safe misalin karfe goma sha daya Abba na xaune parlonsa da Junaid, kasancewar ranan lahadi ce, Abba ya mika ma Junaid takardun hannunsa ya amsa yana dubawa, Abba yace "Asibitin Mecca aka yi duka wnn" Junaid na ci gaba da duba takardun gaba daya yace "A kano kenan" Abba yace "Yess" Junaid yace "Ohk...." Shuraim ne ya shigo parlon da sallama ya kulle kofar, tun da ya shiga dakinsa da asuba sai a lkcn ya fito, ya xauna nan kasa ya gaida Abba, sannan suka gaisa da Junaid, Abba na kallon Junaid da duk hankalinsa na kan takardun yace "So xan baka kudi ka siyo eye drops da aka yi prescribing before the operation...." Junaid yace "Amma ba yanxu aka sa xa ayi operation din ba Abba" Abba yace "Yess ba yanxu ba amma lkcn xai xo in sha Allah" Ta gefen ido Shuraim ya kalli Junaid ya dauke kai, Junaid yace "Toh Allah ya kai mu" Abba yace "Yanxu pharmacy din da xa a samu maganin xaka duba, sai ka min texting din Price with ur details" Junaid ya d'an yi murmushi ya mike yace "In sha Allah Abba, xan wuce sai anjima" Abba yace "Allah ya kai mu..." Sallama yyi ma Shuraim sannan ya fita, Heedayah na kitchen tare da Mami dake gaya ma maid din gidan what to cook for lunch, ko da wasa bata yrda ta bar Heedayah tare da su Rabi'ah kawai ba, jin an bude kofar Abba ta fito daga kitchen Junaid yace "Xan tafi Mami sai anjima" Heedayah dake makale da Mami jin muryarsa da sauri tace "Mami xan bi sa plss" Junaid na kallonta yace "Baxa a je da ke ba" Ta wani murguda baki tace "Kar aje din" Gyada kai yyi ya juya ya nufi kofa ya fita, a hankali Heedayah tace "Mami wucewa yayi?" Mami tayi murmushi tace "Ehh" Heedayah ta marairaice tace "Did he want to be wicked like that man" a kunnen Shuraim da ya fito parlon Abbansa shi ma, Mami tace "Which Man?" Heedayah tace "Wnn da ya tafi da ni a mota jiya mana, wannan da Abba yace ya min karatu ni ban san sunansa ba... Kawai nasan shi mugu ne" A hankali Shuraim dake jin duk abinda take cewa ke tafiya xuwa dakinsa, Mami tace "Toh kansa yyi ma mugunta ai ba ke ba" Heedayah tace "Aa ni yake yi ma ba kanshi ba" Mami ta kama hannunta suka bar wajen. That same day da yamma Mami na main parlor tana danna wayarta tare da Heedayah da su Rabi'ah da suka dawo islamiyya aka bude kofar parlon, Mumy ce ta shigo da sallama sakale da handbag dinta, Su Khadijah suka ta fi da gudu cike da murnan ganinta suka rungume ta, Mumy ta shigo parlon tana murmushi tace ma Mami "Sannun ku da gida" At first Mami bata yrda da ita take ba sai da ta kalleta ta ga ita take kallo, tace "Yauwa sannu da xuwa" Mumy tace "Don Allah akwai dari biyar wajen ki xan ba d'an sahu wai ba shi da canjin dubu daya" Mami tace "Ohk, Rabi'ah shiga bedroom gaba mirror akwai kudi ki dauko" Rabi'ah ta tafi xuwa bangaren Mami, Mumy tace "Ban da ma yanxu yan sahun sun xama abinda suka xama nan nan da Marafa wai dari biyar" Mami tace "Toh Allah ya rufa asiri" Mumy ta tabe baki tace "Ameen dai" Rabi'ah ta fito ta mika ma Mumy dari biyar din Mumy tace "Aa kai masa, ni bari in shiga ciki duk na gaji wllh" daga haka ta wuce bangarenta Khadijah ta bi ta da sauri, Mami ta d'an yi wani boyayyen murmushi tana ci gaba da danna wayarta. Junaid na tsaye babban pharmacy bayan ya basu takardan maganin da yake nema, pharmacy uku yana xuwa sai su ce bbu eye drop din, amma wnn na hudun ya ci sa'a an samu, wani mutumi ne tsaye gefensa cikin shiga ta alfarma, ya siya magunguna shi ma ana masa packaging dinsu, da yake pharmacy din yawanci duk manyan mutane ne ke xuwa, Daga gefen Mutumin kuma wata matashiyar mata ce sanye da hijab har kasa warce baxata wuce 38 ba, Mutumin ya amshi maganin kenan matar ta yanke jiki ta fadi nan kasa, wanda hakan ya jawo hankalin mutanen wajen, Mutumin wanda da alamar mijinta ne ya durkusa da sauri ya rikota, Junaid ya duka shi ma yana mata sannu cike da tausayin ta, ledan hannun Mutumin junaid ya amsa, Mutumin ya daga ta suka fita pharmacy din mutane na mata sannu, Junaid ya bi bayansu har xuwa gun wani lafiyayyen mota, sai bayan da Mutumin ya taimaka mata ta shiga motar sannan junaid ya mika masa magungunan dake hannunsa yace "Allah ya sauwake...." Mutumin yyi murmushi yace "Ameen mun gode, thank you very much" Junaid ya mayar masa da murmushin yace "No thanks, amma da ku yi kokarin wucewa asibiti daga nan she looks so sick" Mutumin yace "In sha Allah, nagode" Junaid yace "You are wlcm sir" daga haka ya juya ya koma cikin pharmacy din don biyan kudin eye drops da ya xo siya, waya ya gani kwance kasa daga inda matar ta fadi, ya duka ya dau wayar ya sake fita da sauri amma har motar su ya bar haraban pharmacy din, juyawa yyi ya koma ciki rike da wayar..... Sai da Magrib Junaid ya isa gidan Abba da eye drops din Heedayah, Mumy dake xaune parlor ya gaisar da ladabi, ta amsa da fara'a tace "Sannu da xuwa" Ya xauna nan parlon yace "Ya gida?" tace "Alhmdllh, Ya sunan naka kuwa?" Ya kalleta yace "Junaid" tace "Maa sha Allah, ka shiga tana can ciki, da kuwa a nan take xaune tace bari taje tayi sllh...." Junaid ya mike yace "Toh..." Da sallama ya bude kofar parlon Mami, ya ga Heedayah kadai xaune tana cin apples da aka yanyanka mata a plate, dauke plate din yyi a hankali, bayan ta cinye na hannunta xata dau wani ta ji wayam, ta gama lalube lalubenta amma bbu alamar plate, a hankali ta dinga bin parlon da kallo kamar xata yi kuka tace "I know it's youuu" ya ja hancinta ya ajiye mata plate din sannan ya xauna saman kujera, Mami ta fito tace "Ka samo drops din?" Yace "Sure..." Wani sabon ringing ya ji a aljihunsa, lkci daya ya tuna wayar mutanen daxu, ya ciro wayar sannan yyi picking call din ya kai kunne tare da sallama, bayan sun gaisa normal Junaid Yace "Sorry daxu you lost ur phone at the pharmacy, na fito kuma naga ka wuce, ina ta jiran kira tun safe ba a kira ba" daga daya bangaren Mutumin yace "Yea ban lura bane da wuri wllh, thank you very much, I almost gave up but nace nayi trying kawai sbda contacts dina" Junaid yyi murmushi yace "Toh where shud we meet sai ka amshi wayar?" Mutumin yace "Yanxu dai muna hospital da Madam, but Alhmdllh da sauki, and in sha Allah gobe da safe xa mu koma Abuja, we resides there... so I don't know ko xaka fada min inda kke..." junaid yace "Ayya, to I will try and bring the phone to you tomorrow in sha Allah" Nan suka yi sallama Mutumin na kara masa godiya.... Heedayah tace "Toh me yasa ka dauke min Apples dina?" Ya saci kallon Mami da ta juya ta koma ciki, sannan ya mike ya koma inda take yace "Ban sani ba" tace "To kai ma ba ruwana da kai...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Junaid ya ja hancinta yace "Ni da wa?" Tace "Kai da wnn mana, ni ban san sunansa ba, kai sai ka dinga tsokanata shi kuma sai ya dinga buge min hannu yana min fada" fitowar Mami ya sa Junaid ya mike yace "Mami sai da safe, xan wuce" Mami tace "Ka ci abinci ai?" Yace "Na ci" Mami tace "Toh Allah ya tashe mu lfya" kofa ya nufa, Heedayah tace "Mami ina xa shi?" Mami tace "Xai wuce gida" Heedayah tace "Mami me yasa baxai tsaya a nan da mu ba?" Mami tayi murmushi tace "Ai xai dawo" Heedayah tace "Ni ina son ya tsaya a nan" Junaid ya kalleta daga bakin kofar da yake tsaye ya bude kofar ya fita. Da asuba aka tashi da ruwa sosai, wajen shidda da rabi Mami na parlonta aka kwankwasa kofa, mikewa tayi ta bude kofar Shuraim yyi kasa da kansa yace "Ina kwana?" Tace "Lafiya lau" yace "Xa mu yi karatu ne" Juyawa Mami tayi ta wuce daki, Heedayah na ta bacci tun bayan da ta tada ta yin sllh asuba, Mami ta tada ta, ta sa mata Hijab sbda garin yyi sanyi sosai suka fito, har snn Shuraim na tsaye bakin kofa, Mami ta mika masa ita, ya kama hannun suka fita parlon ya kulle mata kofarta, Heedayah dai har snn idonta a lumshe yake tana bin sa, da sauri ta bude idanuwanta jin ta ci karo da sofa a parlor, ko tsayawa Shuraim bai yi ba har ya isa study area din Abba still holding her hand ya xaunar da ita nan kasa, kamr xata yi kuka tace "Shine ka buge ni da kujera?" Strictly yace "Kin san Allah idan kina min magana a gidan sai na fasa maki baki wataran, I have no business with you, if u dare talk to me again I will injure you" Yana yin yanda yake maganan yasa Heedayah tayi shiru bata dai ce komai ba, he was so serious, fuska daure yace "Sai na ce ki fara karatun??" A hankali ta fara karato suran da take, yana ta danna wayarsa har ta kai inda ta tsaya shekaranjiya, tace "Na gama....." Sai bayan kusan minti biyar ya ajiye wayar hannunsa sannan ya daura daga inda ta tsaya, his recitation was waow, kamar wani balarabe, Bai tsaya ba sai da ya sauke suran gaba daya snn ya daga kai yana kallonta, baccinta take hankali kwance bayan ta jinginar da kanta da arm chair dake wajen, ya dinga kallonta sannan ya kalli agogo dake nuna karfe bakwai ya mike, parlor ya wuce ya ga Rabi'ah sanye da schl Uniform yace "Je ki tada wnn yarinyar ki kai ta ciki" Bai jira cewarta ba ya wuce xuwa dakinsa. Abba na kallon Mami yace "Listen Rahinah, I know u are not after the income or anything of such, but...." Ta girgixa kai tace "But what Barrister? Ba mu yi da kai xan ajiye aiki ba, ba mu yi haka da kai ba, I can't... Aikina ya xama jinin jikina, it's part of me, I like my profession, ko ba komai I do help innocent soul that are not quilty and I enjoy doing that, so why are you trying to deprive me of the joy? Tunda har na iya kula da nawa yaran still ina aiki, har na aurar da daya, I can take care of little Heedayah also with my work, just that before 3 xan dinga dawowa gida...." Abba ya kasa cewa komai, can ya jinjina kai yace "Toh shkkn Rahinah baxan takura ki ba, I agree ki ci gaba da aikin ki" Tana kallonsa tace "I appreciate, Anjima matar da xata dinga kula da Heedayah when I am away xata iso, monthly xa a dinga biyanta dubu ashirin, I will pay that...." Yace "No you don't need to...." tace "A'a na sa a raina ni xan biya, I took that as my responsibility since I can be with her fully...." Yace "Toh kin san matar da xa a kawon" Mami tace "Ehh to ban santa ba garinsu daya da wata childhood frnd dita Shamsiyya, she said shesy good kuma xata iya" Abba yace "Shhkn, Allah ya mana jagora" tace "Ameen Great Man" D'an murmushi yyi yace "So ynxu dai tare za mu dinga fita da safe?" Dariya tayi tace "Not at all, karfe goma ni xan dinga fita, sai nayi ma Heedayah duk abinda ya kamata, ido kawai Mai aikin xata sa mata har in dawo" Abba yace "Alright" Karfe goma saura matar da Mami ke jira ta iso gidan bayan an mata kwatance ta waya, Mami ta fito main parlor, matar da baxata wuce talatin ba ta sauka har kasa ta gaisheta, Mami tace "Sannu da xuwa ya hanya" Matar tace "Alhmdllh Hajiya" Mami tace "Ya sunan ki?" Matar tace "Sunana Karime" Mami tace "Toh karime aikin ki ba wani da yawa bane, amma yana bukatar saka ido da kula..." Karime tace "Duk an koro min Hajiya, Kuma in sha Allahu xan iya, har ma da aikin gida idan da akwai duk xan yi babu damuwa...." Mami tace "Toh Alhmdllh, yanxu dai mu je in nuna maki inda xa ki ajiye kayan ki" Karime ta mike da sauri ta dau Ghana must go dinta ta bi bayan Mami, Dakin masu aiki Mami ta kai ta, Mai aikin Mumy dake xaune dakin ta gaida Mami, Mami ta amsa sannan ta sa karime ta ajiye kayanta suka fita, Mami ta kai karime parlonta tace "Nan ne bangarena, bana son ku wuce nan ke da ita, in dai tana bukatan wani abu na ci ki bar ta ita kadai ki tafi kitchen ki nema mata, xan nuna maki kitchen din da Inda komai ke ajiye.... Tsakanin ki da Allah nake son ki kulan min da yarinyata bbu ha'inci" Karime tace "Kai Hajiya ai d'a na kowa ne, xaki sameni me riketa da gaskiya in sha Allahu...." Mami tace "To maa sha Allah.... Ki tafi can dakin naku, warce kika samu a ciki daxu ta nuna maki inda xaki ajiye kayan ki sannan ki dawo...." Karime ta mike ta nufi kofa tace "Toh Hajiya" Mami ta xauna saman kujera don tayi deciding yau baxata fita ba xata yi monitoring yanda Karime xata kula da Heedayah. Junaid ya mike daga xaunen da yake yace "To Mami ai ni baxan san size din sweater da xan siyo mata ba, Kuma wani irin takalmi kenan?" Mami tace "To kai makaho ne? Look at her mana before going..." Ya dai yi shiru bai ce komai ba, can ya nufi kofa murya can kasa yace "Sai na dawo...." har xai fita tace "Then go with her kar kaje ka siyo wanda baxai yi mata ba har takalman ma a gwada mata, ka siyo ma Farida ma takalma biyu with a sweater" ya juyo yace "Toh" Mami ta kalli Karime dake xaune kasa tace "Ki duba daki ki dauko Hijab dinta da takalmi xa su fita, ai na nuna maki inda suke" Karime tace "Toh Hajiya" Da sauri ta shige dakin Mami, Heedayah dake xaune gefen Mami ta washe fararen hakoranta jin xa a fita da ita, Mami na lura da ita ta girgixa kai ta d'an yi murmushi, Shi kansa Junaid kallonta yake, Karime ta fito da sauri ta sa ma Heedayah hijab dinta da takalmi, Mami ta mike xata shiga daki don dauko turare ta sa mata, Karime ta dauke cup din da Heedayah ta sha cornflakes ta fita xata kai kitchen din da Mami ta nuna mata, a parlor ta tadda Mumy xaune tana kallon tv duk da gaba daya bata ma san abinda ake a tvn ba, Kwarjinin Mumy kadai ya isa a gane ita ma matar gidan ce, Karime ta d'an duka tace "Sannu da hutawa Hajiya" Mumy na kallonta a dakile tace "Yauwa.... Ke ce sabuwar mai aikin da ta xo yau?" Karime tace "Ehh ni ce" Mumy ta d'an saki fuska tace "Sannu da xuwa, daga wani garin kika xo?" Tace "Daga kano na xo Hajiya, a can mariri iyayena suke" Mumy tace "Maa sha Allah, ai ko nasan Mariri..." Karime tace "Allah sarki" Mumy tace "Toh kin ci abinci kuwa" Karime tace "Na ci wllh Hajiya" Mumy tace "Toh ki saki jikinki kin ji, ko me kike bukata ki xo ki sameni...." Karime ta kara dukawa har kasa tace "In sha Allahu Hajiya, Nagode Sosai sosai, Allah ya kara girma" Mumy na murmushi tace "Ameeen" Karime ta mike ta wuce kitchen, Mumy ta bi ta da kallo..... Ba a dau lkci ba sai ga Junaid ya fito rike da Heedayah, Junaid ya gaida Mumy, da fara'a sosai ta amsa tace "Sannu Junaid, xa ku fita ne" yace "Ehh xa mu je mu dawo" Mumy tace "Ke 'yar fara ba gaisuwa?" Heedayah dai tayi shiru, Junaid ya duka dai dai fuskarta yace "Can't you greet?" A hankali tace "ina kwana" Mumy tayi dariya tace "Ina wuni dai xa ki ce baby" Heedayah tace "Ina yini" Mumy tace "Lafiya lau, xo in gyara maki Hijabin" Junaid na rike da Heedayah ya kai ta har gaban Mumy, Mumy ta gyara mata Hijab din tana kara goge mata bakinta tace "Me kika ci haka?" A hankali Heedayah tace "Cornflakes Mami ta bani" Mumy tace "Ahh Lallai ga alama, to sai kun dawo" Junaid yace "In sha Allah" yana rike da hannun Heedayah suka nufi kofa, Mumy ta bi su da kallo har suka fita parlon sannan ta sauke ajiyar xuciya tana jijjiga kafa. Anguwa ce ta manyan mutane da suka yi fice aka kuma san da su a kasa Junaid ya shiga, a hankali yake driving, Lkci lkci yake kallon Heedayah dake gefensa xaune ta jinginar da kanta da glass din motar idonta a waje kamar dai me gani, Junaid yace "Tell me what you are seeing...." ta juyo xuwa Inda take jiyo muryarsa a hankali tace "Darkness" shiru Junaid yyi driving slowly, can ya kamo hannunta daya murya can kasa yace "What color?" Ta wara ido tace "Just dark" Bai kuma cewa komai ba yyi parking dai dai wani gida da yake tunanin gidan da yake nema ne sbda number da ya gani daga gefen gate din gidan, dialing din number dake call logs dinsa yyi ba a dau lkci ba aka daga, yace "Gani a kofar gidan if I'm not mistaken" ajiye wayar yyi bayan an sanar masa ana xuwa, Heedayah tace "Ina muka xo?" Yace "Somewhere" tayi shiru kmr me son gane ma'anar somewhere da yace, can tace "Ohk wani waje?" Murmushi yyi yace "Yes" Bude gate da aka yi yasa ya kalli gate din ta cikin tinted glass dinsa, Mutumin jiya ne ya fito gate din, Junaid ya bude motarsa yana kallon Heedayah yace "Ki jirani in dawo yanxu" Ta 6ata fuska tace "Noo plss go with mee" yace "Yanxu xan dawo am not going anywhere" Ganin kiris ya rage ta fara kuka ya dau wayarsa yace "To rike min..." daga haka ya fita daga motar ya kulle ya nufi gun Mutumin dake tsaye, gaisawa suka yi, Mutumin yace "Fatan dai ban mu yi inconveniencing dinka ba, mu ma anyi delaying flight dinmu ne" Junaid na mika masa wayarsa yace "No, not at all..." Mutumin ya amsa yace "I am very grateful, ni Sunana Ahmad" Junaid yace "I am Junaid" Alhaji Ahmad yace "Nagode kwarai Junaid" Junaid yyi murmushi yace "Babu damuwa, ni xan koma" Alhaji Ahmad yace "Toh Allah ya kiyaye, da numberka ka kirani ai..." Junaid yace "Ehh" Alhaji Ahmad yace "To maa sha Allah I will save it" daga haka Junaid ya koma motarsa ya tada, Alhaji Ahmad dai na tsaye har yyi reverse ya wuce..... Karfe shidda saura Junaid ya koma gida tare da Heedayah bayan ya siya masu rigunan sanyi da takalma ita da Farida, Mami ta dauko eye drop da ya siyo jiya bayan ta kai kayan daki tace "Barrister yace idan ka xo sai ka gaya min yanda xa ayi da wnn" Junaid ya amshi ledan maganin ya fiddo su guda biyu yace "Wannan idan xata yi bacci da daddare xa a sa mata just two drop in each of her eye, shi kuma wnn idan ta tashi da safe, it's should be everyday ba a skipping....." Mami tace "Toh shkkn Allah ya sa a dace, su kuma maganin mene?" Yace "Toh ana sa rai with the help of this idan an xo yin operation din idon baxa a samu matsala ba idan Allah ya yrda...." Mami tace "Toh Allah ya sa" Mami tace "Babu wani wanda xata dinga sha?" Yace "A'a, sai dai in bincika" tace "Toh Shkkn...." Mikewa yyi yace "Ni xan koma Mami" tace "Baxa ka jira ka ci abinci ba?" Yace "Aa xan wuce" tace "Toh sai gobe" Khadijah ce ta shigo parlon Mami da sallama hannunta daya rike da plate me dauke da cake da aka yanka gida biyu yan madaidaita, daya hannunta kuma da wani cake din tana ci, ta karaso gun Heedayah dake xaune tace "Mumy tace ki dauki naki" Mami ta kalli Karime dake rakube waje daya tace "Ki amsa ki ajiye mata" Karime ta taso da sauri ta karba, Khadijah na kallon karime tace "Dayan aka ce ke ma ki dauka" Karime ta kalli Mami, Mami tace "Toh an gode" Khadijah tace "Cousin dinmu ne yyi birthday" Mami tace "Allah ya raya sa" Khadijah ta juya ta bi ta gefen Junaid ta fita, Mami na kallon Heedayah tace "Xa ki ci cake?" Heedayah ta gyada mata kai, Mami tace "Toh bata Karime ke ma ki dau naki" Karime ta mika ma Heedayah daya ita ma ta dau daya ta fara ci, Heedayah na kallon Inda take jin muryar Mami tace "Mami in tsan masa?" Mami ta kalli Junaid dake tsaye bakin kofa har sannan tayi murmushi tace "Cinye kayan ki ya wuce" Juyawa Junaid yyi ya fita dakin, Heedayah ta fara cin cake dinta, dai dai bakin kofar shigowa yau yyi karo da Salima, tana rike da gyalenta da jaka a hannu, suna hada ido ya bata hanya.... Cikin wani siririn murya tace "Noo ka wuce mana ai kai ka bude kofar...." Ya kara kallonta sannan ya bi gefenta yace "Thank you" tace "Haba thank you kuma, ai kai ka bude kofa" shi dai bai tsaya ba kuma bai ce komai ba yyi wucewarsa, ta bi sa da kallo ko kiftawa bbu... Karime ce kitchen bayan Magrib tana dafawa Heedayah Indomie, tana xuba Indomie din cikin ruwan dake tafasa kan gas aka bude kitchen din Mumy ta shigo, ganinta tace "Aiki kike yi Karime?" Karime tace "Ehh Hajiya Indomie nake dafa mata" Mumy tace "To ke kin ma ci abinci kuwa" tace "Ehh dama na rana bai kare ba...." Mumy tace "Na rana kuma, kin ga idan kin kai masu Indomien ki xo ga cous cous a kula ki diba ki ci kin ji, abincin rana ai ya huce yanxu" Karime tace "Toh Hajiya Nagode Sosai" Mumy tace "Amma fa kar ki wani ce ma uwar dakin ki nace ki xo ki amshi abinci ke dai kawai ki shigo kitchen ki diba kije can dakin ku ki ci" Karime ta risina tace "Toh Hajiya" Mumy ta ajiye cup din hannunta ta fita kitchen din..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Washegari karfe goma saura na safe Mumy ta gama shiryawa xata fita office, Tana duban Karime a parlonta tace "Toh ni xan wuce aiki yanxu, sai ki saka ido sosai ki kula da duk abinda nace maki, karfe sha biyu na yi ki daura maku girkin abinda xa ku ci dai dai cikin ku, ita kuma Heedayah xuwa nan da sha daya abinda ki ka ga na hada mata jiya sai ki hada mata ki xuba Madara amma ban da sugar" Karime tace "Toh in sha Allahu Hajiya" Mami ta dau jakarta ta nufi kofa tace "Sai na dawo" Karime tace "A dawo lafiya" Har Mami ta fita ta juyo tace "Kar ki bari ta bar parlon nan komai xakiyi kiyi mata a nan parlon, bana son ku fito" Karime tace "Toh in sha Allahu Hajiya" Mami ta kulle kofarta ta wuce, A main parlor suka hadu da Mumy tana ma mai aikinta magana cikin tsawa, matar da baxata wuce Karime ba sai rawa jikinta yake tana bata hakuri, Mumy na ganin Mami ta dakata da masifar da take, idon da suka hada yasa Mami tace "Mun tashi lfya?" Mumy tayi murmushi tace "Lafiya lau wllh, ya kwanan Baby" Mami tace "Alhmdllh, ya na su Rabi'ah" Mumy tace "Lfya lau, sun ma wuce makaranta ai" Mami tace "Toh maa sha Allah, na fita..." Mumy tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" Mami ta amsa da Ameen sannan ta fita parlon, Mumy ta bi ta da kallo har ta rufe kofa, ta wani ta6e baki ta kalli Sajida mai aikinta cike da masifa tace "Kin tashi a gabana ko sai na gaura maki Mari, 'yan aiki ko 'yan wahala, wllh bana son in sake tuna maki sharan dakin yarana idan ba haka ba ni ynda ake canxa sutura haka nake canxa ku don ma ki ji" Mai aikin ta mike da sauri ta tafi dakinsu Rabi'ah, Shuraim dake xaune dining ya ajiye cup din hannunsa ya mike ya dawo parlon, Mumy tace "Amma dai yau baxa ka fita aiki ba...." Yace "Sai da yamma...." Mumy tace "Na ji ma Baffan naku yyi tafiya ko?" Shuraim yace "Ehh yana Abuja" Mumy ta ta6e baki, Shuraim yyi kasa da kai yace "Mumy ki dinga hakuri da mutane don Allah, barin wa ennan bayin Allah, they don't deserve the way u are treating them, they never wished for their selves to be maid, and don't forget no condition is permanent, su Rabi'ah yara ne da baxa su iya gyara dakinsu ba idan sun tashi? Ba fa aikin da suke yi a gidan just gyaran dakin ma sai an masu?? This is...." Dakatar da shi tayi cikin tsawa tace "Rufe min baki malam, ni xaka taso kayi ma fada?" Yace "Ni ba fada na maki ba, I am telling you what I think is right" Ta kuma yi masa wani tsawan tace "Baka isa ka gaya min what to do and what not to do ba, out of my sight now.... Duk walakanci da cin fuskan da ubanka ke min a gidan nan ka ta6a tunkararsa ka gaya masa what is right? Sai ni marainiyar wayon ka, to baka isa ba ne...." Shuraim ya shafa kansa bai dai ce komai ba yyi wucewarsa dakinsa, ta bi sa da wani irin harara tace "Wawa kawai...." Karfe sha daya da rabi Karime ta fito hada ma Heedayah cornflakes, Mumy ce xaune parlor da Hajiya Sadiya, Karime ta duka har kasa ta gaisheta, da fara'a Mumy tace "Lafiya lau Karima, ya aiki" Karime tace "Mun gode Allah" Mumy tace "Toh madalla" Karime ta gaida Hajiya Sadiya ita ma ta amsa sannan ta mike ta wuce kitchen, Hajiya Sadiya na kallon Mumy murya can kasa tace "Ita ce mai aikin" Mumy ta gyada mata kai, Hajiya Sadiya ta jinjina kai alamar gamsuwa, can sai ga Karime ta fito rike da cornflakes da ta hada, Mumy tace "Ga kwai can da na soya a kitchen ki dauka, na ci ya isheni gashi ba almajirai a nan" Karime tace "Toh Hajiya Nagode" xata koma kitchen din Mumy tace "Toh ajiye kofin cornflakes din kar ya xube, ta ajiye ta wuce kitchen din da sauri da sauri, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya dake mata magana cikin rada, Mumy ta gyada mata kai kawai, Karime ta fito dauke da tulin kwai a plate, Mumy tace "Ki fito da ita mana ta sha cornflakes din a nan, gashi nn ma duk ya jike...." Karime ta d'an fara kame kame, tace "Hajiya dama Madam tace kar take fitowa ne, komai xa mu yi muyi a can ciki" Mumy dake saurarenta sosai tace "Ayyo, toh tunda ita ta kawo ki ba ni ba shkkn kai mata ciki, dama so nayi in d'an sa ki gyaran bangarena ne, shi sa nace ki fito da ita nan sbda a sa mata ido, amma dauka ki wuce xan yi da kai na, na aiki tawa mai aikin kasuwa ne dama shi yasa" Karime ta d'an risina tace "A'a ba haka bane Hajiya kiyi hakuri, d'an dai gyaran bangaren ki ai xan maki, bari in kawo ta nan din" Mumy tace "Aa kar uwar dakin ki ta ga kin karya mata doka kiyi laifi...." Karime tace "A'a da wuri ae xan yi in gama" daga hka ta wuce ciki, sai ga ta ta fito da Heedayah dake sanye da wando iya gwiwa da karamin riga an daure mata kalabanta waje daya, she look more of a half cast sbda irin haskenta, dai dai fitowar Shuraim waya kare kunnensa da ganinsa kasan fita xai yi, Karime ta ajiye ta nan gefen Mumy ta dauko cornflakes din ta sa mata a hannu tace "Toh gashi ki sha masaran naki 'yar kyakkyawa" Shuraim dai sai kallonsu yake walking slowly, Heedayah ta laluba cokalin ta deba content din cup din ta kai baki, girgixa kai tayi ta fito da na bakinta saman tafin hannunta da sauri tana yamutsa karamin bakinta tace "Yyi soakkk....." Mumy ta saci kallon Hajiya Sadiya ta dalilin hakan kuma ta hango Shuraim da ya tsaya don bata san ya fito ba duk da kamshin turaren sa da ya gauraye parlon, Karime na kallon Heedayah tace "Kika ce?" Heedayah na kara tofar da sauran na bakinta tace "Xai sa in yi amai, it's soft" Mumy tayi murmushi tace "Kai yaro ma dai, wai tana nufin ya jike, ki hado mata wani kawai" Karime tace "Au... toh..." Sannan ta dau cup din ta wuce kitchen da sauri, ba a wani dau lkci ba ta dawo da wani Cornflakes din a cup ta mika ma Heedayah, sannan ta kama hannunta ta juye na bakin ta da ke kai kan nata hannun, Heedayah ta fara shan cornflakes din, Karime ta tafi kitchen ta xubar da na hannunta ta dawo tana kallon Mumy da ladabi tace "Ina xa a gyara maki?" Mumy tace "Ki tafi sama xaki ga kofofi duk ki shiga ko wanne ki share ki goge" Karime ta risina tace "Toh Hajiya" daga haka ta wuce sama, Shuraim ya karasa dinning ya xauna, Mumy ta d'an kalli Inda yake, sai kuma ta juya tana kallonsa da kyau tace "Ba fita xaka yi ba?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ehh ina jiran Umar ne..." Mumy tace "Toh ba sai kaje can gidan nasu ka samesa ba" Shuraim yace "Yace in jirasa a nan...." Mumy tace "Toh ma yaushe ku ka fara fita da Umar?" Shi dai Shuraim bai ce komai ba, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya tayi tagumi, Hajiya Sadiya tace "Ni da ka d'an taimaka Shuraim ka amso min MTN nan waje naga da wani me kiosk a layin..." Ya kalleta sannan yace "Toh bari in maki transfer kawai...." Hajiya Sadiya tace "Aa kar ka wani ba kanka wahala, ga kudin ka amso min" Yace "Gashi ina yi, na ma yi ynxu" Hajiya Sadiya bata sake ce masa komai ba, Mumy dai ya girgixa kafa take, Tasss Heedayah ta shanye cornflakes din cup din tace "I want to take water" Mumy ta d'an kalleta tace "Sai jira ta xo ta baki ai" Shuraim dai yana ta danna wayarsa, har Karime ta fito bayan kusan minti talatin, tace "Hajiya duk na gyara na goge" Ba tare da Mumy ta kalleta ba tace "Sannu" Karime ta daga Heedayah tace "Mu je ki kwanta lkcn baccin ki yyi" Heedayah tace "Xan sha ruwa" Karime ta ja ta har xuwa gun da fridge din dinning area yake, Heedayah ta taji ta taka abu me tudu, tsayawa tayi ta kara kai kafarta kan abun, Shuraim ya dauke idonsa daga kan screen din wayarsa yana kallonta, ta kara takasa, ta kuma takasa just wanting to know what she's matching, ta kara cire kafarta ta kara mayarwa, Karime dai na kokarin dauko mata ruwa a fridge bata ma san me ake ba, Heedayah ta duka ta sa hannu tana lalubawa ta ji me take takawa, dagota yyi ya rike duk hannunta biyu ya bugesu da karfi, sannan ya ja kunnenta daya fuska daure yace "Dutse aka ce maki kike takawa??" Kara buge hannunta yyi ya ja kunnenta ta fashe da kuka sosai, Karime dai ta ja gefe bata ce komai ba, cikin kuka Heedayah tace "Sai na gaya ka da Mami, ni ba Ina ce baby na taka ba" Ya buge bakinta ya tura ta can kusa da Karime, duk wnn abun Mumy na kallonsu amma bata ce komai ba, Karime ta kama hannun Heedayah bayan ta dau ruwan tace "Kayi hakuri Yallabai, bata sani bane" Ya hade rai yace "Ku fita gabana ke da ita" Karime ta bar wajen da sauri tana rike da hannun Heedayah dake rusa kuka, Sai da ta xo wuce Inda Mumy take, Mumy tace "Sai hakuri, ita tsiwa shi kuma saurin hannu, haka nan dai" Karime ta wuce part din Mami rike da Heedayah dake Shessheka, Sai da suka shiga ciki Mumy tace "Ai kaga irinta, ba dai ana ganin ni bala'e'iya bace, to gashi tun ba a je ko ina ba bakin yarinya ya fara budewa tana ma mutane fitsara, ai kadan kayi mata na so ka yi mugun xaneta ne, rashin idon ya ci uwarsa, wllh idan yarinyar nan ta samu waje duk taka ku xata yi a gidan nan, kuma ubanku baxai ce komai ba tunda idonsa ya rufe.... Kai kuma ka xo ka xauna ma mutane a parlor ka hanasu sakata da can kana xaman parlon nan ne ko neman magana???" Shi dai bai ce mata komai ba, can ya mike ya nufi kofa yace "Sai an dawo" daga haka ya fita parlon, Hajiya Sadiya tace "Ai kuma ya lalata mana shirin yau sai mu tari gaba...." Mumy da ranta ya kara baci tace "Ni fa da ba don idon da kika dinga min ba gabansa ma xan iya duk abinda xan yi, to tsoronsa nake ji ko ubansa xai min?? Wllh ke ce kika hanani" Sadiya tace "A'a ke dai, ai komai yana son sirri a rayuwa, ni sai naga kamar da wata manufa ya xauna parlon har ya ki fita siyo min kati, ni kinga ko godiyar katin ban masa ba ma, ke dai kawai ki sa ma ranki salama ba dai duk ana tare a gidan ba, kuma da alaman jawo hankalin yar kauyen nan ba abu bne me wuya, da ganinta xata so abun duniya ne sosaiiii, bbu abun hanxari a wannan lamarin mu bi komai a sannu...." Mumy tace "To ko da wata manufan ya xauna akwai yanda xai yi da ni ne balle ma bbu wata manufa kawai coincidence ne, ke baki ga irin jibgar da yyi mata ba ynxu bbu ko shakka bbu, da kyar idan hannuwanta basu tashi ba, ai ko kadan bai bada goyon bayan kawota da ubansa yyi ba, kawai dai kin san sa da xurfin ciki ne, Amma har ynxu ina lura ba wani shiri suke yi da uban ba duk kan wnn case din...." Hajiya Sadiya tace "To ke dai kiyi ga kyautata ma wnn yar kauyen, step by step xa mu yi ta abun mu bbu wanda xai xarge mu ko da kuwa alkali ne shi ba lauya ba, lkci daya farat din da kika so ayi da farko shi xai ja a xarge mu, amma kinga wnn bbu wanda xai kawo mu a rai" Mumy tace "Haka ne kam" Hajiya Sadiya ta mike tace "Yanxu dai xan wuce, gobe in sha Allahu xan xo da karfe sha daya" Mumy tace "Toh Allah ya kai mu din, ina nan ina jiran ki" Har bakin gate Mumy ta rakata sannan ta dawo tana jin ranta fari fat.... Karfe uku da 'yan mintuna Mami ta dawo gidan, Bbu kowa parlor ta shiga part dinta, Karime na xaune saman kujera tana ta kallon tashar Hausa ga dambun nama cikin leda a hannunta tana ci cike da jin ddi, Heedayah kuma na rakube kasa a xaune ta kwantar da kanta saman kujera, Karime ta mike da sauri ganin Mami tana mata sannu da xuwa ta amshi ledan hannunta da handbag dinta, duk idon Mami na kan Heedayah da ta mike da sauri jin shigowar Mami, Mami tace "Karime ya xa ki bar ta ita kadai xaune a kasa??" Cikin rawar Karime tace "Aa, sauka tayi Hajiya ai tare muke, naga kamar ta fi son kasan ne" Mami tace "Meye wnn a hannunki??" Karime ta hadiye abu da kyar tana kara tuna warning din Mumy tace "Aa ba wani abu bane, dama naje wanke filet ne sai na hadu da Sajida Hajiyar da take ma aiki ta bata dambun nama shine ta debar min a leda, har nace ta bari amma ta tilasta ni na amsa, shine na shigo na tsam ma Hinda sai na ke cin sauran yanxu" Mami tace "Bbu wani alaka tsakanin ki da kowa na gidan nan banda gaisuwa, kin ji me nace?" Karime tace "In sha Allahu Hajiya, dama ni ba ruwana da kowa tun safe muke nan xaune, to naje wanke wanke shine...." Mami bata tsaya kara saurarenta ba ta kama hannun Heedayah suka wuce ciki, Karime gabanta sai faduwa yake, ta isa a hankali jikin kofar dakin ta makale don jin me Mami xata ce mata..... Har dai ta gama labenta bata ji komai ba, ta koma ta xauna, nan ko tsoro ne ya kara shiganta da ta tuna Mami fa na iya Kiran Sajida kila ta tambayeta, nan ko ko maganan kirki bai hada su da Sajida ba tun jiya da ta xo, Mami ta gama sauya kayanta ta xauna gefen gado tana kallon Heedayah da tayi shiru tace "Me ya same ki daughter?" A hankali Heedayah tace "Mami wnn Mutumin ya dokeni a hannuna kuma ya ja min kunne...." Hawaye ta fara tana Shessheka, Da mamaki Mami tace "A ina ya gan ki?" Cikin kuka sosai tace "Xan sha ruwa, shine ya ja min kunne na, yanxu kuma hannuna na min ciwo" Mami ta daga hannunta tana kallo snn ta fita dakin xuwa parlor, da sauri Karime ta mike tace "Hajiya a debo abinci ne?" Mami tace "Me ya fitar da Heedayah daga bangaren nan?" Karime da cikinta ya hautsine tace "A'a Hajiya bata fita ba, da yake in taji alamar xan fita yin wani abu sai tace sai ta bi ni baxata tsaya ita daya ba, ni kuma tausayi take bani sai in kasa fita in bar ta, wllh a tare nake yin komai da ita ki kirata ki tambayeta, wllh Hajiya...." Heedayah isn't free, don't read for free and burden ur self.... it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Mami tace "A kan wani dalili kuma aka doki hannunta kina wajen?" Karime dake xufa daga ciki tace "Cewa tayi xata sha ruwa muka tafi can inda firiji yake a parlor, to cikin rashin sani ta taka wani bawan Allah dake xaune wajen Ina tunanin shi ma d'an gidan ne, shine shi kuma rashin hakuri ya buge mata hannun ya xata da gangan tayi hakan kila" On a serious note Mami tace "Ki saurareni da kyau ki ji, ko da wasa bana son Heedayah ta sake fita parlon nan bana nan, ba komai yasa na dauke ki aiki ba sae don ki kula da ita don ni bbu abinda ya gagareni na aikin gida, shima daukan ki da nayi don bana xaman gida ne, Banda haka ni baxan dauke ki ba...." Hakuri Karime ta dinga ba Mami tana duke a kasa, Mami tace "Gargadi na karshe nake kara maki, ko nan da kofa kar ki sake fitar min da yarinya, idan kuma kinga baxa ki iya aikin ba ki sanar min tun wuri in san abun yi....." Mami bata kuma saurarenta ba ta wuce daki, Karime ta sauke ajiyar xuciya ta xauna nan kasa a hankali har sannan gabanta na faduwa, a wannan marran wa xai daukeka aiki ya biya ka dubu ashirin, aikin ma raino kawai, sai dai can cikin garin Abuja kila, tunanin hakan yasa tayi tagumi tana tunanin ynda xata kara rike aikinta hannu bibbiyu... Mumy na kitchen da Sajida wajajen biyar da wani abu kasancewar ranan ta amshi girki tun xuwan Mami gidan, masifarta da ihu da take ma mai aikin har parlor, kmr jiran mistake take ta fara fada ba ji ba gani, bude kofar kitchen din aka yi ta juya tana kallon kofar fuska daure, Sudais ne tsaye sanye cikin kananun kaya hannunsa rike da leda sai makullin mota, ta saki fuska tace "A'a... kai kuma daga ina haka...." Yana murmurshi yace "Daga gida, Ina yini Mumy?" Tace "Lfya lau, ya su Hajiyar ka?" Yace "Suna gaishe ku" ta rike ha6a tace "Yaushe rabon ka xo gidan nan Sudais, anyaa...." Ya shafa gashin kansa still smiling yace "Mumy ae sbda aiki ne, ina su Rabi'ah?" Tace "Basu dawo islamiyya ba, nasan ynxu ma suna hanya..." Yace "Ohk..." Daga haka ya juya ya bar bakin kofar kitchen din, har xai xauna parlor sae kuma ya nufi part din da Kaka tace masa nan ne wajen Mami, Mumy ta ajiye wuka da albasan hannunta ta bi sa da kallo cike da mamaki har ya isa bakin kofar Mami ya kwankwasa a hankali, ba a dau lkci ba Karime ta bude kofar, da farko ca take Shuraim ne sbda resemblance din su, ta gaishesa da ladabi ta basa hanya, ya shiga parlon dake ta kamshi ta kulle kofar, Mumy dake ta lekowa har taga shigansa ta kai hannu ha6anta idonta ya kankance, sai kuma ta ajiye wuka da albasan hannunta ta fice kitchen din xuwa bangaren ta.... Sudais na kallon Karime da ta koma gefen da take xaune ta xauna yace "Babu kowa ne?" Tace "Aa suna ciki" daga haka ta mike ta nufi kofar dakin ta kwankwasa a hankali a d'an tsorace, Mami ta bude kofar tace "Ya aka yi?" Ta sunkuyar da kanta yace "A'a dama bako ki ka yi" Mami ta kalli parlon suka yi ido hudu da Sudais karasowa cikin parlon tayi ya gaisheta da ladabi, ta amsa da fara'a tana masa sannu da xuwa tace "Ya su Kaka da mutan gidan?" Yace "Suna gaishe ku" tace "Maa sha Allah muna amsawa, welcome" Mami tasa Karime ta kawo masa ruwa da drink a fridge, ta xauna kan kujera tana kallon film da ake a tv, Bayan few seconds tace "Kai ne kayi karatu Malaysia koh?" Yace "Eh Degree" tace "Maa sha Allah, Barrister yace min chemical engineering kayi right?" Yace "Ehh haka ne..." Tace "Good, it's a nice course" yana shafa kansa a hankali yace "Heedayah bacci take?" Mami tace "A'a tana ciki" yace "Dama kaka ta bada sako a kawo mata ne" Mami ta mike tace "Allah sarki, tana ciki, let me get her" daga haka ta wuce dakin sai gata ta fito da Heedayah, har gabansa ta kai ta sannan ta dau wayarta da ke ring kan kujera tace "Give me few mins let me pick a call" yace "Alright Ma" daga haka ta wuce daki, Heedayah ta wara idanuwanta jin muryar sa tana tattaba Hannunsa cikin siririyar muryarta tace "Ka xo gidan mu yau koh?" Ya dafa forehead dinta yace "Nima ai gidan mu ne...." Ta kyalkyale da dariya tace "Aa, gidanku ai gidan wnn matar nan ne me fada" Sudais ya ja hancinta yace "Sunanta kaka, idan ta ji ki xata xane ki ba ruwana" Ta wara ido tace "Toh kaka..." Ya dau apple daya cikin apples din da ya kawo mata ya sa a hannunta, tana jujjuya apple din tace "Is it an Apple?" Yace "Yes" ta langwabar da kai tace "Me ya sa baka kawo min Chocolate ba, ni ina son shi" Yace "Wnn ya fi Chocolate dadi ai" yana fadin haka ya xaunar da ita gefensa ya ciro cincin kulle a leda ya bata a dayan hannunta yace "Kaka tace a kawo maki" Tana juya ledan tace "Meye shi?" Yace "Cinye apple din sae ki ci ki gani" Mami ta fito daga daki ta dawo parlon ta xauna, Mami na kallonsa tace "Ka fara aiki ne?" Yace "Na ci gaba da masters ne..." Mami tace "Maa sha Allah, a ina kake yi?" Yace "UK, na dawo yin wani abun ne yanxu" Mami tace "Anytime soon xaka koma kenan?" Yace "Ehh in sha Allah, nan da sati biyu" Mami ta gyada kai convinced, can tace "Shi kuma Shuraim fa?" Yar dariya yyi yace "Shi yana aiki... clinic din Baffanmu yake" Mami tace "Alright, Duk Allah ya bada sa'a" Yace "Ameen" Heedayah ta kamo hannunsa cike da damuwa tace "Are you travelling?" Yace "Yesss" ta 6ata fuska a hankali tace "Xaka tafi ka bar ni kenan?" Yace "Aa... Ai ba ddewa xan yi ba Heedayah" Mami tayi murmushi tace "Sai ya tafi da ke kawai Koh?" ta xaro ido tace "Ehh Mami plss, I like him with Yaya, ki ce ya tafi da ni" Mami tace "To xa ki bi sa" Daga karshe Mami ta bar masu parlon ta koma daki to answer more calls, Heedayah tace "Baka gaya min sunan ka ba....." Ya shafa kansa yace "Ki ce min yayanki...." Ta kai hannunta chest dinta tace "Yayana?" Yace "Yess... Cutie" Apple dinta ta fara ci cike da jin dadi, jin an fara kiraye kirayen Magrib yace "Xan je Masallaci in dawo" tace "Toh plss ka dawo fa" yace "Xan dawo" Sudais na fita... Sajida mai aikin Mumy tayi knocking, Mami ta fito parlor lkcn, Karime ta bude kofar ganin Sajida sai da gabanta ya fadi, Sajida tace "Ina Hajiya?" Karime ta matsa bakin kofar tace "Ga ta ciki...." Sajida ta shiga ta gaida Mami da ladabi ta ajiye warmers din hannunta tace "Gashi Hajiya tace a kawo maki" Mami tace "Ohk, to an gode" Sajida ta mike ta fita, murmushi kawai Mami tayi tana ci gaba da danna wayarta, don kowa girkinsa yake a gidan ba hadawa aka yi ba.... Tare Sudais ya shigo da Shuraim daga masallaci, Mumy dake xaune parlor ta hade rai ganin Sudais, Shuraim ya gaisheta snn ya wuce dakinsa, Sudais yace "Mumy xan xo in wuce yanxu, xan masu sallama can ciki" Mumy ta amsa masa ciki ciki, ya wuce part din Mami ya sanar mata xai wuce, Heedayah na bedroom lkcn Mami ta kai ta tayi sllh, Mami tace "Abinci fa?" Yace "Aa I'm okay ma" Tace "Are you sure, ka tsaya fa ka ci abinci" yana murmushi yace "Sure am okay..." Tace "Toh shkkn mun gode Sudais" Yace "Heedayah tana ciki?" Mami tace "Ehh sllh na kai ta tayi" yace "Toh na wuce" daga haka ya fita parlon... Mumy bata tanka sai da safensa ba balle tayi masa tayin abinci yyi murmushi ya fita abun sa. Sai bayan isha Mami ta bude warmer din da Sajida ta kawo, wainar shinkafa ce da miyar taushe da ya ji nama da kayan hadi a diff but same warmers din, Mami ta kalli Karime tace "Gashi fa idan xa ki ci" Karime tace "Toh Hajiya" Mami ta xuba ma Heedayah shinkafa jollof da tayi... Karfe tara Mami ta sallami Karime ta tafi ta kwanta, Karime tayi mata sai da safe cike da ladabi sannan ta fita xuwa dakinsu da Sajida, Karime na kokarin kwanciya sai ga Mumy ta shigo dakin, Sajida ta mike da sauri ganinta tace "Xa a maki wani aikin ne Hajiya?" Mumy ta wani hade rai tace "Dalla rufe min baki kamar wata me yin abun arxiki, yaushe aka kawo yarinyar nan Karime, Amma dubi duk ta haddace abubuwan da tasan take yi, satin ki na uku kenan amma banda matsala bbu abinda kike bani da ciwon kai, ga sauran wanke wanke can kin bar ma uwarki ta xo ta karasa min a kitchen" Ita dai Sajida bata ce komai ba kanta a kasa, Mumy tace "Karime xo in d'an sa ki aiki don Allah yar albarka, bana son bacin rai gwara in sa wanda xai min da kyau..." Karime ta mike da sauri har tana tuntube tace "Toh Hajiya me xa a maki" Sajida dai ta bi ta da kallo bata ce komai ba, Mumy tace "In ji dai Uwar dakin ki baxata neme ki ba, kin gama mata komai koh?" Karime tace "Ta sallameni tace in je in kwanta bbu abinda xa ayi mata" Mumy tace "Yauwa toh kar in je maki matsala, kin san yanayin rayuwar yanxu" Mumy ta fita Karime ta bi bayanta da sauri... Har bedroom dinta ya shiga da karime, kayan guga ne tule kan makeken gadon dakin, Mumy ta sauke tsadaddun akwatuna tace "Wa e nnan kayan xaki jera min cikin nutsuwa a akwatunan nan, ba sake sa su xan yi ba shi sa xan mayar akwati" Karime tace "Toh Hajiya...." Mumy ta kishingida gefen gado tana shan grapes da ke plate a beside drawer, Karime sai jera kayan take cike da nutsuwa, Mumy tace "In ji dai Uwar dakin taki bata baki matsala na ga kina da hankali kuma komai a nutse kike yi ba kamar wancan tawar ba dake bani ciwon kai" Karime tace "Eh to Hajiya, kinsan duka duka jiya na xo gidan, amma naga kamar bata da sake ma jama'a kamar dai yanda kike..." Mumy tace "Haba?" Karime tace "Wllh, in nayi ma yarinyar ba dai dai ba ko yaya sai ta gyara min cikin bacin rai..." Mumy tace "Ikon Allah.... Duk wnn saukin kan naki??" Karime tace "Wllh, fitowar da nayi da ita daxu ma sai da ya kusa ja min matsala tace kar in kuma fitar mata da ita...." Mumy tace "Ikon Allah, kinga dai duk rashin damuwana ko ga maciji bata son mu dinga yi ni dai bana biye mata tunda ina da ilimi na nasan abinda nake yi, Kuma kinsan gaba daya satin ta daya da yan kwanaki a gidan nan, kwanan nan Mai gidana ya aurota amma sai take min kamar ta rigani shigowa gidan nan, komai Isa Isa kuma a walakance...." Karime da ta mike ta bude baki tace "Ikon Allah, kwanan nan? Ni ma xata kun yi shekara da shekaru tare ai ganin ynda take komanta" Mumy ta gyara xama tace "Wani shekara, yau kwananta takwas in gaya maki, kuma yarinyar nan da kike gani agola ce ta kawota gidan, shine ake mana fi'ili da ita, ni dai bana kulata sbda Allah na saka a gabana, Kinga dai d'ana na fari sannan ga 'yan matana biyu, to me kuma xai dameni da ita??" Karime ta rike ha6a tace "Gaskiya kam, ita da ko tsinke ma bata da a gidan, abincin da kika aiko mata daxu ma bata ci ba bata bari yarinyar ta ci ba ni ta bama" Da mamaki Mumy tace "Haba???" Karime tace "Wllh, Kuma tace Idan na gama in wanke kulan in ajiye maki a kitchen, in mun hadu gobe ince maki ta gode" Mumy ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh ai shkkn, ni saboda Allah nayi, ai ya ga xuciyata, ita ta sani" Karime tace "Kwarai kuwa..." Mumy tace "Banda asiri gaskiya ne ina ita ina Mai gidana, asiricesa tayi fa ta auresa ta shigo da yarinyar nan, har ynxu xancen da nake maki ba ma wani shiri da Mai gidana duk ya watsar da ni da 'ya yana, komai ita ce kan gaba" Karime ta bude baki tana kallon Mumy tace "Ikon Allah, Allah sarki, gaskiya kina da hakuri Wai..... Ni dama ina ganin yanayinta nasan baxata yi kirki ba" Mumy ta sauke ajiyar tace "Ni dai Allah na rike" Jin an bude kofar parlor Mumy tayi shiru haka ma Karime, Mumy ta mike da sauri tace "Waye??" Bandaki ta bude ta nuna ma Karime ta shiga da sauri, sannan ta fita parlon, Shuraim ne tsaye parlon, Mumy tace "Ya aka yi?" Yace "A'a Aunty Rukayya ke son magana da ke ta kira wayar ki baki amsa ba...." Mumy tace "Toh xan kirata, wayar na silent ne nan parlon..." Yace "Okay ke da waye a ciki?" Mumy tace "Ni da waye a ciki Kuma? Sajida ce tana min gyaran kaya" Yace "Toh sai da safe" tace "Allah ya tashe mu lfya" yace "Ameen" daga haka ya fita ta juya ta koma daki, kitchen Shuraim ya wuce don hada shayi ya ga Sajida tana wanke wanke, ya tsaya yana kallonta sannan ya tafi gun da cups suke ya dau daya ya hada shayin ya fita parlor ya xauna, sai kusan sha daya Karime ta gama gyaran kayan Mumy, Mumy ta hada mata kaya set uku tace "Gashi ki boye wnn kiyi ta tara abun ki...." cike da jin dadi Karime tace "Kai Hajiya wllh na gode, Allah ya saka maki da alkhairi, wannan kaya har haka??" Mumy tace "Ke dai ki ja bakin ki kiyi shiru, ko Sajida ma kar ki nuna ma, gobe xan samu Ghana must go in baki ki dinga boye kayan ki a ciki" Karime tayi ta mata godiya har ta fita dakin cike da murna..... Shuraim dake xaune parlor har sannan ya juya jin footstep yana kallon direction din, Kallon Karime dake tafiya kamar munafuka yyi ya dauke kai, ta shige dakinsu da sauri ta kulle. Washegari da safe Mami ta gama duk abinda xata yi ma Heedayah kafin ta fita, tana lura tun jiya Shuraim bai xo yace a fito da ita karatu ba, Karfe tara Mami ta fito parlor tana kallon Karime da ta gyara parlon tsaf tace "Ni xan wuce, xuwa anjima sai ki hada mata abun nan a cup ki bata idan ta tashi bacci, kuma kin da ji abubuwan da na gaya maki jiya ki kula don Allah Karime, anjima ki dafa maku duk abinda ku ke so" Karime na murmushi tace "In sha Allahu Hajiya, Allah ubangiji ya kiyaye hanya" Mami tace "Ameen" daga haka ta fita parlon, Xaune taga Mumy main parlor tana waya, Mumy ta dakatar da wayar suka gaisa faram faram Mumy na tambayarta kwanan Heedayah, Mami ta tambayeta na su Rabi'ah sannan tayi mata sallama ta fita parlon, Karime dake goge gogen kayan kallo bayan fitar Mami ta ta6e baki maganganun da Mumy tayi mata jiya kan Mami na dawo mata ashe ma kwace mijin mutane tayi ta shigo gidan, ci gaba da abinda take tayi tana yan wake wakenta, tana gamawa kuma ta hada kakkauran shayi a cup don Mami ta siyo kayan shayi ta ajiye nan parlonta sbda frequent shan shayin Heedayah, ta yanka tikeken bread ta xauna tana ci duk da dumamen da ta ci da sassafe, ta gama shan shayin kenan aka d'an bude kofa, juyawa tayi da sauri suka yi ido hudu da Mumy, Karime ta mike da sauri tace "A'a Hajiya ce, shigo mana, ta fita ai..." Murya can kasa Mumy tace "Ina yarinyar tata take?" Karime tace "Au tana can ai tana bacci, sai sanda ta tashi" Mumy ta karaso parlon tana murmushi tace "Karyawa kike yi kenan" Karime tace "Ehh wllh, gashi nan d'an ruwan shayi ta xuba min ta bani d'an kucilin biredi in karya" Mumy tace "Ga bredi can bangarena banda abun ki, har kayan shayin ma ai akwai, ki je ki hado wani idan baki koshi ba" Karime na washe baki tace "Allah sarki Hajiya to nagode kuwa...." Mumy na kallon eye drops dake ajiye wajen tv a parlon tace "Wancan Kuma menene, wa ke ciwon kunne?" Karime tace "Aa na yarinyar ne naga ana diga mata a ido..." Mumy tace "Ohhhoo na ciwon idon kenan" Karime tace "Kila, daya da safe daya da daddare haka naga ake yi kullum, daxu ma sai da ta diga mata da sassafe..." Mumy dake ta kallon eye drops din tace "Ikon Allah...." Littafin Heedayah na kudi ne, subscribe before reading.... and read happily.... it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Mumy tace "Toh ki tafi ki hada shayin, kayan shayin na can kitchen, bredi kuma na parlona su Rabi'ah sun bar sa a can" cikin rawan jiki Karime tace "Toh ngdd Hajiya, nagode" Mumy ta kuma kai idonta kan eye drops din sannan ta fita Karime ta bi bayanta da sauri cike da jin dadi, main parlor Mumy ta xauna tana girgixa kafa, Karime kuma ta wuce bangarenta dauko bread, Mumy ta bi ta da kallo har ta shiga ciki, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon Mumy ta juya don ganin wanda xai shigo, Kaka ce ta shigo parlon tana sakale da wani karamin jaka me kama da handbag, Mai gadi na biye da ita a baya rike da wani tikeken akwati, Mumy ta bude baki ta mike da sauri tace "Lafiya Kaka? Me ya faru??" Kaka bata ko saurareta ba ta nufi wani spare room dake nan cikin parlon tana cewa "Ina fa lafiya? Meye kuma baxai faru ba? Sai kace dai Umaru kadai na haifa a duniya, ga dai gidan Amadu me dakuna ta ko ina...." Har ta bude kofar sai kuma ta dawo tace "Wllh Maryam wani kwai suka soya min yau xar karni, to ga dai albasa an cika amma ni dai naji yana karni na bala'i, ina laifin su d'an yanyanka min yar tafarnuwa su watsa a ciki, wnn ba alamomin an gaji da kai bane a waje? Jiya sai bayan magariba suka kawo min abincin dare, tuwo da wani miya sun cika naman kasuwa, to ca masu nayi yunwan nama nake?? abinda mu xamaninmu karfe biyar duk mun ci abincin dare munyi wanke wanke kowa ya manta, mata kawai suna neman kashe ni kuma sai in xauna kamar uwata tace min je ki kya gani, A'a wllh, to me gidan Amadu yake da baxan lallaba in dawo ba??" Mumy da ta ji kamar ta kurma ihu cike da karfin hali tace "Haba kaka, Haba kaka, haba kaka, wllh hakuri ake a ko ina, ko ina mutum yake sai yyi hakuri, rayuwar ma gaba daya d'an hakuri ne, ni ba gashi an min kishiya ba nayi hakuri muna xaune lafiya? me yyi xafi xaki tattaro kayanki ki dawo nan ai baxa su ji dadi ba Kaka, gaskiya bari in dauko makullin mota mu koma, baxa su ji dadi ba wllh barin Baffa, gani xai kamar baki gode kokarinsa a kanki" Kaka tace "Koh??" Mumy tace "Wllh tllh, ai ba xamansu kike ba da xa ki bar masu gidan kaka, sun ma ci riba kenan, bari in dauko makullin mota" Kaka tace "Toh, idan fita xa ki yi ga mai adaidaita can ki biyasa dari biyunsa kar ya mana ihun 6arayi a unguwa yana can yana jira ban basa ko sisi na ba, dama kuma ban masu sallama ba ta baya na bar masu gidansu, kya iya xuwa ynxu ki ce masu na dawo nan da xama, duk me nemana Ina nan gidan d'ana Amadu...." Kaka na kai wa nan ta shige daki... Mumy ta xauna saman kujera tayi tagumi tana furta innalillahi wa Inna ilaihi raji'un a xuciyarta, Mai gadi da ya ajiye kayan Kaka a parlan har ya tafi ya dawo yace "Hajiya D'an sahu na can yana jira fa...." Cikin bacin rai Hajiya tace "Kai da d'an sahun sai na ci kaza kazanku idan baka fita idona ba, na hau adaidaita ne da xa ka xo kace min d'an sahu na jirana???" Mai gadin ya juya ya bar bakin kofar... Shuraim da ya dawo daga kai Abba office yana kallon Mai adaidaitan da ya gyara parking don basa hanya ya sauke glass yace "wa kake jira malam?" Mai adaidaitan yace "Wata tsohuwa na kawo nan ta shiga wai xa a kawo min kudi to har yanxu dai ina ta jira" Shuraim yace "Nawa ne?" Yace "Dari biyu ne kudin" Shuraim ya ciro dubu daya ya mika masa, D'an sahun yace "Amma bani da canji wllh" Shuraim yace "To je ka" D'an sahun ya dinga yi masa godiya, Shuraim ya gyada masa kai kawai ya ja motarsa xuwa ciki don Mai gadi ya bude masa gate, parking yyi ya sauka ya rufe motarsa ya wuce ciki... Mumy ya tadda a parlor tayi tagumi ga tashin hankali karara a fuskarta, ya isa kusa da ita ya xauna a hankali yace "Mumy lafiya" Mumy tace "Ina fa lafiya Aliyu, don Allah ka shiga ka lallaba tsohuwar nan ka mayar da ita gida, kalli uban akwatin da ta kawo wai ta dawo nan, ta dawo wajen wa? Ta dawo tayi mana me? Don Allah ka shiga ka lallaba ta ka maida ta inda ta fito...." Shuraim dake ta kallon Mahaifiyar tasa yace "Mumy amma ai ba laifi bane don ta xo nan, Kuma ai...." A mugun fusace Mumy tace "Rufe min baki gantalalle kawai, dama ina kuwa xaka san laifi ne dawowarta nan???" Lkci daya Mumy tayi tsit ganin Kaka ta fito har ta cire Hijabin ta, Kaka tace "Kin sallami d'an sahun ko kuwa kin barsa yana can yana min kallon macuciya barauniya??" Shuraim ya mike yace "Na sallamesa" Kaka tace "Atoh, Kai baka je aikin bane yau?" Yace "Sai da yamma, ina kwana?" Tace "Lafiya lau, Shureen ni dai na dawo nan gaskiya, matan Umaru kasheni suka so yi Allah bai yi ba, yau wani kwai suka ban da ya kusa kai ni lahira, shayin kuma sun cika masa kayan kamshi kamar dai buzaye... To ina dalili ga dai gidan Amadu" Shuraim dai bai ce komai ba, Kaka tace "Ka shigar min da akwatina daki dukiya ne a ciki, jama'ah Ina Deedayah, ga bredi na taho mata da shi da kwai...." Shuraim ya dau akwatin nata ya shigar da shi ciki, Mumy dai karfin hali kawai take don kiris ya rage hawaye ya xubo mata, kaka tace "Maryam tambaya nake Ina Deedayah?" Mumy ta dake tace "Wacece kuma Deedayah?" Kaka tace "Sabuwar 'yar Amadu mana...." Mumy ta wani tabe baki tace "Ayyo makauniya wai?" Kaka tace "Aa wannan kuma isgilanci kike ma ubangiji ba ruwana, ke kika halicceta da xaki kirata da makauniya, meye kuma makauniya idan ba isgilanci ba, ko ita ta xabar ma kanta makantar? Ni yanxu Ina take??" Duk wannan abun Karime na tsaye sai kallon kaka take, Mumy ta nuna mata Karime tace "Ga me kula da ita can" Kaka ta kalli Karime tace "Wacece kuma wnn sai naso take, ta kula da ita ko ta sa mata cuta, bakya wanka ne baiwar Allah?" Karime ta kasa cewa komai, Shuraim dai yyi murmushi ya nufi dakinsa, Kaka na kallon Karime tace "wa ya daukeki ki dinga kula da ita, Amadu ko wa? Tunda ita uwar rikon tata na samu labarin har ta fara fita aiki, Amadu ya fita ita ma ta fita...." Karime ta girgixa kai tace "Aa, Hajiyar ce ta daukeni..." kaka tace "Toh kuma sai kiyi ta kazanta kina naso, ba kya tashi da safe ki sa ruwa kiyi wanka ki dauko yar atamfar ki ko da kodadde ne ki saka kiyi fess da ke.. yanxu Ina yarinyar take?" Karime tace "Tana can daki kwance," Kaka tace "Wannan xama da ke ai sai cuta ya kama 'yar mutane..." Daga haka kaka ta nufi part din Mami tana cewa "Ita kuma mata daga tarewa sai fara fita aiki kamar auren banxa aka daura mata, ni ba ruwana" Zaune kaka ta ga Heedayah saman gado ta tashi tana mitsika ido, Kaka ta washe baki tace "Deedayah... Kin tashi" Heedayah ta juya da sauri tana duban Inda ta ji muryarta tace "Kaka" Kaka ta karaso tace "Ehh ni ce Deedayah, kin ga na dawo nan yanxu, kwai suka bani duk karni, kinji dalilin barin gidansu da nayi" Sakko mu je ga bredi da kwan na kawo maki kema ki ci ki ji, Heedayah ta sauka saman gadon kaka ta kama hannunta suka fita tana cewa "Ita dama ashe ba don ta kula da ke aka aurota ba, xata barma katuwar mata kazama ta sa maki wani cutan Amadu ya shiga uku...." Heedayah tace "Kaka tafiya xa ki yi da ni can gidanku?" Kaka tace "Wani gida? Ai na dawo nan sai kuma wani ikon Allah, abincin banxa fa suke bani a can gidan wllh Deedayah...." Mumy ta bi su da kallon gefen ido, Kaka ta tsaya tana rike da hannun Heedayah tace "Maryam ban fa karya ba, Kuma ni ba shayi xan sha ba gaskiya, ko me aka samu ni dai a bani in ci fisabilillahi" daga haka ta shige dakin da ta sauka tare da Heedayah, Mumy ta mike ta wuce bangarenta da sauri ta dau wayarta ta shiga Kiran Hajiya Sadiya, Hajiya Sadiya na dagawa Mumy ta sakar mata Kuka tace "Sadiya wllh shirinmu na ta rugujewa, yau dai ga wnn tsohuwa ta diro da katon akwati, ynxu haka ta dauke yarinyar ta shige da ita dakin da ta sauka, wato bbu ma ranan komawarta ne don sai kinga akwatin da ta kawo, ni dai wllh Sadiya hakurina ya fara karewa ji nake kamar in kashe yarinyar nan a gaban kowa a daureni kawai in huta, wnn yarinya har in mutu xan mance da ita kuwa a rayuwata, ta janyo min dariya a duniya, Duk fa dariya ake min a boye Sadiya" Sadiya tace "Ki kasheta kuma a daure ki Maryam, me aka yi kenan? Ke ina gaya maki gaggawa na shaidan ne kin kasa fahimta ko, meye na gaggawa abinda dai ana tare...." Mumy tace "Toh ke kina ga wnn tsohuwar da ta diro mana gida ynxu baxata kawo mana wani cikas ba?" Hajiya Sadiya tace "To ke meye ruwanki da ita? Wajenta yarinyar take da xai dame ki, Kinga xa mu yi waya anjima nayi bakuwa" daga haka ta katse wayar, Mumy ta xauna gefen gado tayi tagumi hawaye na sauka idonta.... Karime da Sajida tasa suka girka ma kaka shinkafa da miya ko damuwa da ynda suka yi girkin bata yi ba... Kaka na kallon Heedayah dake kwance gefenta tace "Toh sai kuma a siya maki?" Heedayah tace "Ehh mana, har kitso Ina yi ma gashin babyn nawa...." Kaka ta rike ha6a tace "A makancen?" Heedayah tace "Na'am" kaka tace "Toh yanxu a nan wani gantalalle ne xai siya maki wani baby ana xaune kalau??" Heedayah tace "Abba mana" Kaka ta ja kunnenta tace "Ke ce gantalalliya ba d'a na ba, shi Abban ne gantalalle?" Heedayah tace "Aa ai Mami ma xata siya min" Kaka tace "Atoh sai dai ita din, Amadu ba gantalalle bne..." Bude kofar dakin aka yi Shuraim ya shigo da sallama, kaka tace "Ko kuma Shureen ya siyo maki ba?" Heedayah tace "Waye shureen?" Kaka tace "Aa nima haka naji suna ce masa amma sunansa Aliyu..." Heedayah tace "Ae ban san shi ba" Kaka tace "Toh ai sanin nasa bashi da amfani don bashi da kyakkyawan alaka da mutane, mugun hali ne da shi, kin ga ai tun daxu da na xo bai shigo gaisheni ba sai ynxu..." Heedayah tace "Shi ma a nan gidan yake?" Kaka tace "To Ina xa sa? Ai gidan Ubansa ne nan din... da dai yyi aurene sai ya bar gidan, ni da Allah xai fito masa da mata ma yyi auren kowa ya huta don wannan shiru shirun da yake yi idan xamaninmu ne cewa xa ayi aure yake so" Shuraim dake tsaye bakin kofa ya hade rai yana kallon kaka da Heedayah bai dai ce masu komai ba, Heedayah tace "To ki ce masa ya siya min babyn Kaka, babba nake so" Kaka ta kalli Shuraim tace "Kaji kai Shuraim ko ba mai tsada bane ka dubi maraicinta ka siya mata domin Allah, ya fi tayi ta xama shiruuu kamar kurma..." Yace "Toh sai ta xo ta kwata ai" Heedayah na jin muryarsa ta matsa kusa da kaka a hankali bata kuma cewa komai ba, Kaka tace "Atoh, tunda ba ajiya ta ba mutane ba ai sai ta hakura da Babyn dama" Tsaki Shuraim yyi ya juya ya fita ya rufe dakin, murya can kasa Heedayah tace "Kaka ya wuce?" Kaka tace "To me xai min dama, ya wuce" Heedayah ta turo baki tace "Ni bana son sa" Har aka yi azahar Kaka na dakinta tare da Heedayah, bbu irin labarin da bata ba Heedayah ba wanda kwakwalwarta xai dauka da wanda ma baxai dauka ba, Tun tulin shinkafa da miyan da aka kawo mata da safe ba a sake kawo mata wani abincin ba.... Karfe uku da yan mintuna Mami ta dawo gida daga office, Karime na xaune kasan carpet a main parlor tana kallo, tun kiran da Mumy tayi mata dakinta bayan sun gama yi ma Kaka girki ita da Sajida sai lkcn ta sauko kasa ganin lkcn dawowar Mami yyi, ta mike da sauri daga xaunen da take tana yi ma Mami sannu da xuwa xata amshi jakar hannunta, Mami ta ki bata jakar tace "Ina Heedayan take?" Karime tace "Ai kina fita Hajiya sai ga wata da naji suna ce ma kaka ta xo gidan, to tun safe da ta shigo ta fita da ita xuwa wancan dakin bata yadda na je gunsu ba ma, ynxu haka suna ciki" Mami tace "Kaka?" Karime tace "Ehh haka naji suka kirata, kuma Sajida tace min Baabar Alhaji ce" Mami ta nufi dakin da kaka take ta yi sallama sannan ta bude ta shiga, Heedayah na xaune tana cin shinkafar da kaka ta xuba mata, ita kuma kaka na kara gyara kayan akwatinta don a birkice ta jerasu sbda sauri, Mami ta xauna nan kasa da murmushi fuskarta tace "Sannu Kaka" kaka tace "Yauwa sai yanxu kike dawowa kenan" Mami tace "Ehh yanxu na dawo" Kaka tace "Toh sannu da xuwa...." Heedayah dake washe baki jin muryar Mami tace "Mami kin siyo min Babyn" Kaka tace "Wani baby? Ki samu ma a samu lkcn kula da ke ba wani shegen baby ba, ke yanxu fisabilillahi Rakiya da kika hadata da wannan yar aiki duk wari ta kula da ita idan cuta ya kamata wa aka kai aka baro??" Mami bata ce komai ba tayi shiru tana kallonta, kaka tace "Kice min Amadu, to wllh xuwa nayi na samu mai aikin duk wari wai ita ce me kula da Deedayah, ki fa bar ganinta makauniya ki xata bata da galihu Rakiya, ke kina ganin fatan jikinta kinsan ba daga cikin wahala ta fito ba, gashi har abincin banxa na ga bata yrda ta ci sai na yan gayu, jikinta kwata kwata bai son wahala, wa ya sani ma ko daga kasar waje wani axxalumin ya sato ta ya wullota nan Nigeria da mugun abu yyi yawa?? Allah kadai yasan me yasa ya hadata da Amadu a titi, kema gashi ta albarkacin ta ya aure ki, wa yasani ko kin dade kina jin son sa a xuciyar ki sai gashi ta dalilin Deedayah ya aure ki..." Mami dai tayi murmushi tace "Ai nayi mata komai kafin in fita kaka, abincin rana kawai take bata sai abinda ba ka rasa ba, kuma baxai yiwu in dinga fita da ita aiki bane da tare xa mu dinga xuwa" Kaka tace "Toh ni dai na dawo da ita nan ba ruwana, sai in ga uban da xai dinga cutarta, mace duk wari kice ita xata kula da cin ta da shan ta, kishiyar ki kuma tun xuwana da safe har ynxu ban ga keyarta ba, duk wannan bai dameni ba tunda ke kin shigo, ynxu abinda nake so dake ga wayata ki kira min Junaidu don mun yi da shi xai xo yau kar yaje can bana nan, ba komai yasa na bar gidan ba sai kwai da suka kawo min duk karni" Mami ta amshi wayarta ta sa number Junaid sannan ta kira sa ta mika ma kaka, kaka na jin ya dauka ta washe baki tace "Junaidu... to yau dai gidan Amadu xaka taho na tattaro gaba daya na dawo nan" Junaid ya gaisheta yace "Toh shkkn kaka sai na xo" tace "Allah ya maka albarka ya kare ka sharrin makiya, ni ai ka fi min kowa" Murmushi kawai Junaid yyi ya amsa da Ameen sannan yyi mata sallama ya katse wayar, Mami na kallon Heedayah ta kama hannunta tace "Mu je ki canxa kaya" Kaka ta kalleta da sauri amma bata ce komai ba, Mami ta mike rike da Heedayah tace "Sai na shigo anjima kaka" Kaka ta bi su da kallo a hankali tace "Yauwa" Suna fita kaka ta mike ta fita ita ma ta nufi dakin Shuraim da sauri, yana fesa turare ta samesa a dakinsa da yake a gyara kamar dakin mace, ko ina fesss sai sanyin Ac, kaka ta xauna gefen gado ta fashe da kuka sosai, ya juya yana kallonta da mamaki, ganin irin kukan da take ya nufeta yace "Lafiya kaka? Me ya faru" Tana Shessheka tace "Mata ki fita tun safe ki bar yarinya Ina wahala da ita daga dawowa sai ki dauketa, Halan ita ta tsinto ma Amadu ita bani da labari ko kuma kanwar uwar yarinyar ce ita bamu sani ba, Yarinya muna xaune lafiya banda hira babu abinda muke yi tun safe ba irin labarin da bata bani ba, bbu irin labarin da ban bata ba kawai mata ta xo ta dauketa su wuce sbda bakin ciki...." Ta fashe da wani sabon kukan tana mika masa wayarta tace "Kira min Junaidu...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Shuraim ya dauke kai ya juya ya koma gaban mirror ya dau makullin motarsa, Kaka ta mike tace "Baxa ka kira min shi bane Shureen?" Ba tare da ya juyo ba yace "Ehh baxa a kira ba, waye kuma wani Junaid...." A fusace Kaka tace "Aa wllh kar ka xagar min shi don in ka xagesa ni ka zaga, kar ma ka fara wllh, ance maka bai fiye min kai ba sau dubu, Ina ruwana da kai dama idan ba kaddaran na haifi uban ka ba, wllh Junaidu ya gama min komai, kana xagin sa xaka xago ma kanka fitina, don ni ka xaga...." Ta koma ta xauna ta fashe da wani sabon kukan, bude kofa Shuraim yyi ya fice daga dakin ya kulle, kaka ta tsaida kukan da take a hankali tace "Ehh lallai d'an Amadu ya ci ganye..." Mikewa tayi ta bi bayansa fa fita. Mumy ce tsaye ta wajen flowers dake bayan gida, sbda shuke shuken flowers din wajen sai ya fi kama da garden, waya ne kare kunnenta cike da damuwa tace "Wllh kuwa Baffa, ni dai nayi ta bata hakuri ina kwantar mata da hankali, to kaga bbu ddi idan ban kira ka na sanar maka ba tunda cewa tayi kai ma ba son xamanta kake a gidan ba, kuma idan anyi duniya don manzon Allah ita da gidan har abada tunda xaman dole ku ke da ita, har mayar da ita na yi niyyar yi tace ta koma a wani matsayin?? Tunda har ynxu bbu wanda ya biyo ta ko ya kirata ya bata hakuri yace ta tashi su koma, to shine nake ga gwara ka taho da kanka ka kara bata hakuri sannan ku tafi don wllh ta dau xafi sosai, ni ban ma ta6a ganin bacin ranta irin na yau ba, kuka kuwa ta sha shi har ta gode Allah, xan kira barrister in sanar masa ta hanani wai ita xaman garin ma duk ya fita a kanta, gidan nawa ma ba xama xata yi ba, wai xa a iya wayan gari a ga bbu ita ta bar garin, to shine naga gwara in kira ka..." Baffa dake ta sauraranta ya sauke ajiyar xuciya yace "Shkkn Maryam nagode, sai na shigo anjima" Mumy tace "Babu komai, amma don Allah kar kace ni na kira ka, idan ma kace mata ni na kira ka kara baci ranta xai yi tace wato ma sai da na kiraka ka xo, da ban kira ba baxa ka xo ba, kuma idan xaka xo sai ka d'an taho mata da abinda kasan ta fi so" Baffa yace "In sha Allah, sai na xo" daga haka suka yi sallama, Mumy ta katse wayar tana wani murmushi, lkci daya ta sauke ajiyar xuciya, cikin compound din ta koma dai dai shigowar Junaid, har xata hade rai ganinsa ko me ta tuna kuma sai ta sake fuska sosai, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace "Sannu da xuwa junaid, kwana biyu baka shigo ba" yace "Ehh naje Zaria ne" Mumy tace "Kuna da 'yan uwa can kenan" yace "Aa, naje wani uxuri ne a can" tace "Ayyo... To sannu da xuwa" yyi mata godiya sannan ya nufi entrance din shiga gidan, ta bi sa da wani kallo har ya shiga parlor... Sajida ce ke ta share share a parlor, ta mike tana gaishesa ya amsa yace "Wani dakin Kaka take?" Sajida ta nuna masa hanyar dakin, can ya nufa, yyi sallama bakin kofar, Kaka ta amsa da karfin ta, ya bude kofar ya shiga, kaka na xaune ta daura kafa daya kan daya, Khadijah na jera mata tarkacenta na tsofaffi a gaban madubi, kofar bathroom a bude Karime na ciki tana ta faman wankewa, Junaid ya xauna nan kasan carpet yace "Sannu kaka, Ina yini" tana washe baki tace "Lfya lau Junaidu, sai ynxu??" Yace "Ehh kaka, ashe kin dawo nan..." Ta gyara xama tayi narai narai da ido tace "Baxan dawo ba Junaidu, kwai suka soya min duk karni gashi fari fatt sai uban albasa to hakan ba alamar an gaji da kai bne, to shine naga tun kafin sun barbadamin shinkafar bera gwara in gudu, ynxu hka ba wanda ya san ina nan, kilan suna can hankali tashe sun kai rahotu gidan 'yan sanda" Junaid da kansa ke kasa yana murmushi yace "Da dai kinyi hakuri Kaka...." Shiru tayi tana kallonsa can tace "Aa kar ka xama gantalalle kai ma mana, ae in kowa ya gaya min wnn mugun magana kai bai kamata ka gayan ba, inyi hakuri su cuceni su kasheni a banxa, sae kace Umaru kadai na haifa, ga dai Amadu, Aa ba ruwana, ni duk wanda yace in koma can gidan ma haushi na kawai yake ji ya tsaneni" Junaid ya ajiye ledan hannunsa yace "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" Kaka tace "Toh ka ga ynxu kayi magana, Kuma in sha Allahu alkhairin ne dama" murmushi kawai yake yi, kaka tayi kasa da murya tace "kana ji Junaidu, dama uwarka haka take ban sani ba?" Junaid ya daga kai yana kallonta, kaf ta kwashe labarin abinda Mami tayi mata ta sanar masa tana matsar kwalla, tace "A gantale fa ta barta gun mai aiki dake naso uwa an tuttula mata jarkan man gyada, ynxu hka fa ga Mai aikin can na sa ta wanke bandaki na, kuma ban amince ta shiga bandaki na ba sai da tayi wanka wllh, to mata daga dawowa kuma sai ki dauke min yarinya haka kawai, yini fa muka yi tare da yarinyar bbu wanda ya ji kanmu, muna ta hira fa in gaya maka" Junaid yace "Gaskiya bai kamata....." Kaka tace "Allah ya maka albarka, daga shigowa gida sai ta fara fito da mugun halinta da wuri wuri hka tun ba aje ko ina ba, ni sai nayi tunanin ma ko tasan uwar yarinyar ne wnn isa haka da ta nuna min...." Junaid ya d'an yi murmushi yace "Xan je in dauko maki ita ynxu kaka" kaka tace "Amma fa kar kace nace maka komai, ba ruwana kar ta kullaceni, kawai dai kayi mata nasiha ta canxa halinta, wannan ba halin xaman gidan miji bane..." Ya mike still smiling yace "In sha Allah kaka, bari in je in dawo" Kaka tace "Allah maka albarka, ni dai gwara min kai a kan kowa ma a gidan nan" Kaka ta kalli Khadijah da sauri tace "Ke 'yar banxa kin gaishe sa ma kuwa da ya shigo? Ku dai 'ya yan Amadu baku da hali tirrr" turo baki Khadijah tayi tana ci gaba da abinda take, shi dai Junaid tuni ya fita ya rufe mata kofa, part din Mami ya nufa ya sameta xaune parlor ta daura kan Heedayah a cinyarta tana mata gyaran gashi, Heedayah ta mike xaune da sauri jin muryarsa, ya xauna saman kujera ya gaida Mami, Mami ta amsa tace "Na xata da Farida xa ku xo" yana kallon Heedayah yace "Aa, Uncle said she should stay" Mami tace "Okay, how are you" yace "Alhmdllh, ya aiki" tace "Mun gode Allah" Ya mike ya koma kujeran da suke ya xauna gefen Heedayah yana kallonta yace "How are you Heedayah" Ta wara ido tace "Fine, me yasa baka xo ba jiya har da shekaranjiya" Yace "Ae gani na xo yanxu" Ta laluba fuskarsa tace "To ka dinga xuwa kullum ka ji?" Mami dai ta tabe baki tana harhada kayan gyaran gashinta, Junaid na murmushi yace "Mami kaka tace a maido mata da Heedayah" Mami na kallonsa kafin tace komai ya kara da cewa "She wants her to be staying with her, bata ji dadin xuwa da kika yi kika dauketa ba daxu" Mami ta rike ha6a tace "Tohhh, ikon Allah" Junaid yace "Yess allow her ta koma wajen ta Mami, since ita ta bukata" Mami tace "Toh ai naga kamar wani nauyin Heedayah xata xame mata, baxata iya da tsirfan Heedayah ba" Junaid tace "Tunda ita ke son hakan ki bar mata kawai Mami" Mami tace "kai yaushe ta gaya maka haka?" Yace "Yanxu, har da kukan ta" Mami ta bude ido tace "Ahh to dauketa ka kai mata ita" Heedayah dake jin su tace "Mami wajen kaka xai kai ni?" Mami tace "Ehh" Heedayah tace "Amma xan dawo koh?" Mami tace "Ehh xa ki dawo" Junaid ya mike ya kama hannunta suka fita parlon, Mami ta bi su da kallo.... Mumy dake xaune parlor kamar dai ko da yaushe ta bi su da kallon gefen ido har suka wuce dakin kaka, Kaka na ganin Heedayah ta washe baki tace "Deedayah, ga kaza Junaidu ya kawo min, ai kin iya cin kai da kafar kaza koh?" Heedayah tace "A'a ni lap na iya ci" Kaka ta kalli Junaid tace "Meye lam kuma?" Yyi yar dariya yace "Cinya" Kaka ta kalli Heedayah da sauri tace "To sai ki kwata ai, ka ji min dai" Ya xaunar da ita gefen kaka yace "Kaka xan je Masallaci in dawo" Kaka tace "Toh yi maxa gashi can an fara kira" a hankali Heedayah tace "Are you coming back?" Ya juya yana kallonta yace "Yess" Yana fadin haka ya juya ya fita, Kaka tace "Toh ko wnn lafiyayyen turancin da kike ai ya ci kowa ma ya san ba daga gidan gantalallu kika fito ba, da kyar idan baki fi Shureen iya turancin ba don ni tunda nake ban ta6a jin ma yyi turancin ba, ga dai makaranta me tsada uban ya sa shi yana karami amma bai jin turanci, ko wnn kwam din da kowa ya sani baya ji" Heedayah ta kyalkyale da dariya tace "Kaka to sai in dinga koya masa mana" Kaka tace "Atoh, bari dai Allah ya shigo da shi mu ga ko xai yadda" Heedayah tace "Kaman ni yake?" Kaka tace "Ka ji ki wannan a haihuwar kaji ai yyi jika da ke, Shureen fa nace maki" Heedayah tace "Ni ban san shi ba" Kaka tace "Idan ya shigo xan Kai ki ki tattabasa ki ji" Heedayah tace "Toh" Tare Junaid ya shigo cikin gidan da Baffa, Baffa ya xauna parlor shi kuma ya shiga wajen kaka yace "Kaka Baffa ya xo" Kaka tace "Waye kuma Baffa, uban wa yace masa Ina nan, Kai ni dai gaskiya ana shiga hakkina, to me ya xo min kuma kamar dai wata yar karamar yarinya" Junaid na murmushi yace "Ya xo ne ya tabbatar nan din kika xo" Kaka ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana wllh" Bude kofar dakin aka yi sai ga Hajiya Amina da Hajiya Hauwa sun shigo da sallama, Kaka tace "Su waye wannan kuma" Hajiya Hauwa tace "Sannu kaka" Kaka tace "Yauwa, daga ina haka kamar an koro ku, ko daga anguwa ku ke?" Hajiya Amina tace "Daga gida muke kaka, mun xo biko...." Kaka tace "Yaji Maryam din ta kara yi ina gidan bani da labari??" Hajiya Hauwa tayi dariya tace "A'a kaka, kawai sai mu ka ga ba ki a gida" dai dai nan Mumy ta shigo dakin, kaka tace "Wllh na so shiga in maku sallama amma sai nayi tunanin bacci ku ke don na San ku da baccin safe, tashi nayi yau da tunanin Amadu a raina shine nace bari dai in je shi ma ya sami lada na...." Baffa ne ya shigo da sallama, kaka tace "Ikon Allah, har da kai Umaru, to me ya faru ne wai? Ba fa kai kadai na haifa ba da xanyi ta xama gidanka, shkkn kuma shi Amadu ba mutum bne da baxan dinga xuwa nasa gidan ba, Kar ka xama me son kanka mana Umaru, ka so ma d'an uwanka abinda kake so ma kanka, shima ka barsa ya dinga samun ladan uwarsa" Baffa yace "Nayi tunanin ko an 6ata maki rai ne ai Baaba" Da sauri kaka tace "Aa wllh, baku ta6a min komai ba, idan nace ma kun mun sai Allah ya kamani, matan ka ai mutanen kirki ne tun ma ba Mai jidda ba, tamkar ynda xa su yi ma iyayen su suke min, to sae in masu sharri ince sun min wani abu?? Aa kawai ni dai na xo gidan Amadu ne shi ma ya samu lada...." Kallonta kawai junaid yake with surprise, Mumy da hawaye ya cika idonta tace "Amma fa kaka cewa kika yi kwai suka soya maki duk karni sannan basa baki abinci da wuri kawai sun gaji da ke ne...." Kaka ta saki salati tace "Yau naga abinda ya isheni jama'a, Maryam ke da wa ku ka yi haka??? Lalacewar ta ki ta kai haka bani da labari? To ke ina ruwanki ko danyen kwai suka kawo min, ba gwara su sun kawo min kwan duk karni ba, ke me barina da yunwa fa??" Baffa yace "Toh kaka tunda dai bbu wani matsala shkkn sai dai mun yi waya" Kaka tace "Bbu ko wani matsala Umaru Allah yyi ma kai da matanka albarka..." Baffa ya amsa da Ameen ya fita....Mumy dai hawaye ya ki tsaya mata, Hajiya Hauwa sai danne dariyar ta take, daga karshe ita ma tayi ma Kaka sallama ta fita haka ma Hajiya Amina, Mumy ta bi bayansu xuciyarta na tafarfasa, Junaid dai kansa na kasa, kaka tace "Ka ji min mata dai xata min sharri da rai na" Tuwo da miyar egusi Sajida ta kawo ma kaka, Kaka tace "To ba gwara ke ba kan wannan mata da Rakiya ta dauka aiki duk wari.... Tafi ki kawo min flet da cokali" Mai aikin ta fita sae gashi ta dawo, Kaka ta amsa ta bude warmer din tuwon ta diba, ta ajiye ma Junaid, Junaid yace "Kaka ni fa a koshe nake" Kaka tace "Aa ni ba ruwana gashi nan ka ci, kana da Inda xaka je ka ci abinci ne da ya fi nan...." Ta kalli Heedayah tace "In xuba maki kema" Heedayah tace "Na koshi" Kaka tace "To wlh baxan baki Kai da kafar Kazan ba ma" Heedayah ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Toh in ci da Yaya" Kaka ta kalli junaid, Tashi yyi ya koma kusa da ita da plate din tuwon yace "Toh mu ci" Kaka ta ta6e baki tana xuba nata, Heedayah ta d'an fincili tuwon bayan ta laluba plate din ta kai baki, Kaka tace "Wllh haramta maka tuwon xata yi, meye kuma na mintsilin tuwo kamar kaza??" Dariya junaid yyi ya deba a cokali kadan ya tabbatar ya huce sannan ya kai bakin Heedayah, Jin cokali a lips dinta ta bude bakin ta amshi tuwon, a haka suka dinga cin tuwon, aka bude kofa sai ga Shuraim ya shigo, kaka tace "Shureen wai xaka dinga koyon turanci gun Deedayah" Shuraim ya kalli Heedayah da ta tankwashe kafa a gaban Junaid, ajiye ledan hannunsa yyi nan gefe ya fita dakin, kaka ta kalli Junaid tace "Kila kunya ya ji, da ban masa magana a gabanka ba" Dariya sosai Junaid yyi... Sai kusan karfe tara yayi ma Kaka sallama Heedayah har da kukanta wai xata bi sa, ya samu dai ya lallabata ya fita, Kaka tayi tagumi tace "Toh wai a gidan ubanwa kika ta6a sanin Junaidun idan ba gulma ba?? Sai kace shine Amadu? Ai ni da Amadu ne dolen ki..." Wajen karfe sha daya Mami ta shigo da eye drops din Heedayah, Kaka da har ta kashe wuta tace "Kinga Rakiya, abinda xai faru ba sai kin dinga ba kanki wahalan shigo mana tsakar dare ba mun fara bacci, kawai ki nuna min ynda xan dinga sa mata a idon, Amadu fa ya fi awa daya a dakin nan sannan ya fita, tun daxu ya kamata ki xo ai, ni na xata kin gaji kin kwanta ne" Mami tace "Aa ban kwanta ba" kaka tace "To nuna min ynda abun yake in dinga yi mata da kai na" Mami ta nuna ma kaka ta tabbatar ta gane din tana kuma tsaye ta diga ma Heedayah dake bacci drops din dare sannan tayi masu sai da safe ta fita... Har kaka ta kashe wuta aka sake bude kofa, Mumy ce ta shigo kaka ta kunna wuta tace "Amma dai bakwa tsoron Allah matan gidan nan, bakin cikin baccin ake mani cikin daren ma" Mumy tace "Yi hakuri kaka, naga baki bacci da wuri ne ban san kin kwanta ba, kankana na yanka ma Barrister shine na dibar maki" kaka tace "Ki sa min a firiji, amma wnn ae shiga hakki ne, meye kuma kankana tsakar dare jama'ah kamar ana yunwa" Mumy ta bude fridge dake dakin ta ajiye tana kallon eye drops dake ajiye saman fridge din, lkci daya ta kwashe su tace "Toh sae da safe kaka" bata jira cewarta ba ta fice daga dakin, kaka ta ja tsaki ta kashe switch din wutan.... Har wani murmushi Mumy take ta wuce dakinta da sauri, bandaki ta shiga da wayarta ta doka ma Sadiya kira, Sadiya na dagawa tace "Toh ga dai eye drops din na samo Sadiya... Kin yarda Allah na tare da ni?? Wllh cikin ruwan sanyi na samu, ban ta6a xaton hka ba...." Heedayah isn't free, do not read for free, subscribe and read happily.... it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Hajiya Sadiya dake sauraren Mumy tace "To kin dauko cikin ruwan sanyi maidawan fa Maryam?" Mumy tace "Aa ni maidawan ba wani damuwa ta bace, minti nawa ne, abinda dai ba makulli take sa wa a dakin ba...." Sadiya tace "Toh shkkn, amma wajen bude maganin kiyi ta ynda fa baxa a gane ba, a nutse xaki yi komai" Mumy tace "Toh shkkn sai mun yi waya Sadiya" Daga haka ta katse wayar ta fito, handbag dinta ta nufa ta bude ta binciko wani kwalba irin na magani dake karkashin jakar ta ciro sannan ta rufe jakar, kokarin bude eye drop din ta dinga yi amma ta kasa, tayi tayi amma ya ki buduwa, wuka ne ya fado mata ta Kalli agogo taga sha biyu saura, ta d'an yi murmushi ta ajiye drops din a drawer ta nufi saman gado ta kwanta tana jiran karfe daya yyi don wnn lkcn ta tabbatar kowa na gidan yyi bacci, tana ta kwance idonta kyar ko digon bacci bbu har agogo yyi struck din karfe daya dai dai, ta mike a hankali ta saka hijab dinta har kasa sannan ta dau drops din da kwalbanta ta fita daga dakin, cikin Hijabin nata ta boye hannunta me dauke da eye drops da kwalba, kitchen ta nufa direct ta kunna wutan, sannan ta juya baya ta ciro abubuwan cikin hijab dinta ta dau wuka ta fara gwada bude eye drops din a nutse, she was so careful kar saman yyi shaidar da xai sa a gane an bude, bude kofar kitchen din taji anyi, a rikice ta boye komai cikin Hijab, muryar Shuraim taji yace "Baki kwanta ba Mumy, what are you doing" kin juyowa tayi ta dinga kawar da plate da cups din karya duk a rude, amma lkci daya ta dake tace "Me ya hanaka bacci har war haka??" Yace "Shayi xan hada" Mumy ta hade rai sosai tace "Wannan shan shayin dai ya xame maka jaraba, wani shayi ne baka sha ba tun wayewar garin Allah sai tsakar dare kamar maita ka tashi wai xaka sha shayi? Shayin me? idan baka sha shayin ba mutuwa xaka yi ko me da baxaka hakura ba tunda dare yyi" Shi dai bai ce mata komai ba, har sannan hannunta daya na boye hijab dinta, ta nufi kofa a fusace ya bi ta da kallon gefen ido, cup ya dauka ya bude flask ya debi ruwan Lipton ya bude kayan shayin xai hada, Mumy tayi still ganin kaka a parlor, lkci daya gabanta yyi mugun faduwa kaka ta karaso Inda take tace "Amadu yyi bacci ne?" Cikin rawar baki Mumy tace "Lafiya Kaka, me ya faru?" Kaka tace "Ina fa lafiya, idonsa biyu ko yayi bacci?" Mumy da hankalin yyi mugun tashi don cikin d'aga murya kaka ke magana tace "Kaka ban san ko yyi bacci ba daga kitchen...." Abba ne ya fito parlon jin muryar mahaifiyar tasa, Kaka na ganinsa tace "Amadu wannan wani bala'in ka kawo wa mutane gida, ya xa a dinga shiga hakkina Ina bacci, to gata can ta hanani bacci wai shayi xata sha, meye kuma shayi kamar buxuwa tsakar daren nan" Mumy bata san lkcn da ta sauke wani bayyanannen ajiyar xuciya ba, Kaka tace "Ni dai ba ruwana, tun wayewar gari bata gama shaye shayen shayinta ba sai ynxu bayin Allah na hutawa, kawai ta cuceni ta tasheni" Abba dai bai ce mata komai ba, kaka tace "Ga ta can xaune kamar yar mage ta ki bacci wai shayi, to ni siyar da shayi nake xata tasheni ta dameni" Abba yace "Kiyi hakuri, bari a maida ta gun Rahinah" Kaka ta kallesa da sauri tace "A maida ta kuma? A kan me? To sai kayi ta maida ta din ae, daga tace xata sha shayi sai a maida ta gun Rahilah" Duk wnn abun Shuraim na tsaye rike da cup din shayinsa yana kallonsu, Mumy tace "Kiyi hakuri kaka bari in hado mata shayin yanxu" Shuraim ya karaso cikin parlon Kaka na kallonsa tace "Waye wnn kuma?" Mika mata cup din hannunsa yyi ta amsa tace "Toh ba shkkn ba dai, amma xaka wani ce a maida ta gun Rakiya, meye hadinta da Rakiya, Kuma waye bai san yaro ba Allah na tuba" Daga haka ta wuce dakinta rike da shayin, ta gefen ido Mumy ta dinga hararan Shuraim da ya juya ya wuce dakinsa shi ma, Abba ya girgixa kai ya koma bangarensa. Mumy ta tabe baki don har yau ba wani shiri take da shi ba, dakinta ta koma ta sa makulli ta ci gaba da aikinta, da kyar ta bude drops din ta wuce bandaki ta tattular da maganin ciki ta dauraye empty container din da ruwa a nutse sannan ta dawo daki, kwalbanta ta bude ta xuba content din ciki wanda kalansa shi ma fari ne a robobin eye drops din, snn ta rufe gam da murfi... Ta ajiye robobin su bushe a gaban madubi tana yi tana kallon agogo, sai biyu da kusan minti goma ta kwashe magungunan ta bude kofarta a hankali ta fito parlor, kwance ta ga mutum saman kujera yyi rub da ciki, duk da wutan parlon a kashe yake amma wutan compound ya d'an haska har cikin parlon, ta yi still a Inda take don ta san baxai wuce Shuraim ba tunda ya saba kwanciyar parlor, yawanci ma nan yake kwana, tana daga Inda take tsaye ta dinga leka fuskarsa a hankali taga bacci yake, tayi tiptoeing har xuwa hanyar dakin kaka sannan ta bude kofar very careful don ma ko kadan kofar baya kara, fridge ta nufa ta ajiye eye drops din ta juyo da sauri ta fita ta kulle kofar, sannan ta sauke ajiyar xuciya, tana isa cikin parlor ta kara lekan Shuraim da ko motsawa bai yi ba, ta wuce dakinta hankali kwance tana gode ma Allah. Sbda baccin da Mumy bata yi ba da wuri sai kusan karfe takwas na safe ta tashi duk da ta tashi sllhn asuba, taga har su Khadijah sun wuce makaranta, bandaki ta fara shiga sannan ta fito ta tafi parlor, dai dai nan Kaka ta fito, Mumy na murmushi tayi kasa tace "Sannu kaka, fatan kun tashi lfya?" Kaka tace "Wani lafiya an shigo an sace ma yarinya magani, a kira min Amadu" Kasake Mumy tayi tana kallon kaka, kaka ta nufi bangaren Mami tana cewa "Bari inji ko wnn matar ce ta shigo ta kwashe magungunan yarinya sbda ta nuna min ban isa da ita ba" Kaka ta shiga buga kofar Mami, Mami na fitowa kaka tace "Rakiya Ina maganin da kika shigo kika kwashe?" Da mamaki Mami tace "Magani kuma kaka?" Kaka ta saki salati tace "Toh wllh barawo ya shigo ya sace maganin da kika kawo jiya, ba a kan friji nace ki ajiye ba??" Mami tace "Ehh nan kuma na ajiye" Kaka tace "Toh ko sama ko kasa, dakin na can na hargitsa wai ko ma ya shige wani lungun ne amma wllh ban gani ba, Ina Amadu" Mumy dai ta kasa motsi inda take, Mami ta kalleta na yan sakwanni sannan ta dauke kai, Kaka da kanta ta tafi ta kwankwasa ma Abba kofa yana fitowa tace "Amadu barawo ya sace maganin Deedayah, wllh da shi muka kwanta muka tashi ba shi" Da mamaki Abba yake kallonta, tace "Wllh ba xancen wasa ba kana kallona" Mumy dai fa an kasa motsin kirki sai imagining take to ko dai cikin mafarki ta mayar da maganin bata mayar a xahiri ba, Shuraim ya sakko downstairs jin muryar Kaka ya cika gidan, ya karaso yana kallonta yace "Me ya faru?" Kaka tace "Shureen maganin Deedayah aka rasa wanda ya dauke, ni kuwa yau xan ga 6atar nono a kirjin budurwa...." Kallonta kawai Shuraim yake with surprise, can ya kalli Mumy dake tsaye sai wurga ido take, Kaka tace "Al-qur'an kira xan yi in sa a ja min Yasin, in dai ba a fito min da maganin yarinyata ba sai na kai kudi an ja min yasin" Abba dai bai ce komai ba, Mami na tsaye just watching everybody, Kaka ta nemi kujera ta xauna tana hada xufa tace "Ka ji min dai, to wllh ba ruwana sai dai cikin mutum ya kumbura, me Deedayan ta tsare maku da xa a dauke maganinta, ko uban wani ne ya siya mata maganin banda Amadu???" Abba yace "Junaid ne ma ya siyo ba ni ba" Kaka ta mike da sauri tace "Au Junaidu ne ma, to dama idan ba kai din ba ko shi wa gareta da xai siya mata, wllh Amadu ka ja su daki kayi masu magana cikin nutsuwa su fito min da maganin yarinya kar abu ya baci tsakanina da su, xan fa mance sanin da na masu in sa a ja masu Yasin" Tana fadin haka ta juya ta nufi dakinta fuska daure, Shuraim ya bi ta da kallon gefen ido, Cike da karfin hali Mumy tace "Ikon Allah...." Mami ta ta6e baki ta juya ta koma dakinta, Mumy tace "To magani kafafuwa garesa da xa a nema a rasa?? Anya kaka ta san Inda ta ajiye maganin kuwa?" Abba na kallon Shuraim yace "Xan sa Junaid ya tura maka sunan eye drops din, sai na maka transfer ka tafi pharmacy ka siyo su" Shuraim yyi kasa da kai, Abba yace "Ko baxa ka samu xuwa ba..." Kafin yace komai Mumy tace "Baxai samu ba mana, shi da yake fita aiki Barrister, Ina ji fa ranan Baffa ke fadan baya wani xuwa aikin sai ya ga dama to idan ba matsala kke son ja masa gun Baffan nasa ba ina xai je samo wani magani ynxu da safe" Tun da ta fara magana Abba ke kallonta keenly, can ya gyada kai ya wuce bangarensa, Shuraim dai bai iya ya daga kansa ba, Mumy ta hade rai bayan tafiyar Abba murya can kasa tace "Did you know anything about the missing eye drops Aliyu??" Ya daga kai da sauri yana kallonta yace "Ni kuma Mumy, ni ban ma san da wani eye drops a gidan nan ba, I know nothing about it, ban ma san kalarsa ba" Mumy ta kauda kai tana naxari to wai ko dai mafarki tayi ta mayar da drops din dakin kaka?? Ganin Shuraim ya fara wucewa ta kara daure fuska tace "Wait, ko da wasa kar ka fita gidan nan da sunan tafiya siyo ma tsinanniyar yarinyar nan magani.... I'm instructing you not to do so" Da mamaki ya tsaya yana kallonta, can yace "Toh idan Abba ne yace in je fa Mumy?" Rai bace Mumy tace "Ni kuma nace baxa ka je ba, ko tsallake maganata xaka yi??" Yace "Amma ai baxan iya ce masa A'a ba kamar ynda kema baxan iya ce maki A'a ba" tace "Wannan ya rage naka kai da shi, ni dai nace idan ka fita gidan nan siyo maganin makafi to ba da yawuna kayi hakan ba" Fitowar kaka ya sa ta ja bakinta tayi shiru da sauri, Kaka dake sanye da hijab hannunta rike da Heedayah tace "Ga shi na fiddo dubu daya ta xan je siyo maganin idon a kemist, daga can kuma xan tafi gun da xa a ja min yasin na tsakani da Allah...." Mumy tace "Haba kaka yanxu fa nake cewa xan shiga a sake duba dakin da kyau ko...." Kaka ta katse ta a fusace tace "Tunda kinga alamar na fara makancewa kamar Deedayah ba, wllh tllh baxan yi kaffara ba wani algungumin ne ya shiga ya dauke maganin nan, to ni abinda har yanxu ban gane ba a nan shine, bakin ciki ake ma yarinyar kar idon ya warke ko me?? Anya wasu xa su gama da duniya lafiya kuwa, Junaidu ya cire kudi domin Allah ya siyo mata magani amma wani mara tsoron Allah ya bi dare ya sace, tunda nake ban ta6a ganin irin haka ba sai gidan Amadu, gidan Umaru basa haka kwata kwata, in haka ne lauyancin karya Amadu ke yi kenan, lauyancin karya mana tunda ya kasa kama wanda ya sace ma Deedayah magani, ita ma amaryar da naji ance lauya ce ashe ta karya ce, lauyoyi biyu a gida a tafka wnn uban sata amma a kasa kama barawon har war haka?? Aa ba ruwana gwara inyi ta kai na, dubu daya da dari biyar dina ya biya min bukata, dubu daya in bada a kemist su bani maganin guda biyu, dari biyar kuma in tafi gidan Ta salla ta rakani inda xa a ja min yasin...." Shuraim was trying hard not to laugh sai sunkuyar da kansa yake yana shafa gashin kansa, Fitowar Abba yasa ya daga kai yana kallon Abban nasa, Abba yace "Ina kuma xa ki kaka?" Tace "Ina ne kuwa baxan je ba Amadu, Kai baka san wnn yar amana ce Allah ya baka ba xaka barta ta walakanta a gidanka, wani axalumi ya sace mata magani kayi shiru" Abba yace "Xan je siyo maganin ai ynxu" Kaka tace "A'a ai tunda nayi niyya sai na siya ga dubu dayana xan je kemist da ita ynxu" Abba ya tsaya kallon kaka kafin yace "Ae ko wani daya ya kusa dubu ashirin da biyar" Kaka ta gwalo ido tace "Me din?" Abba yace "Bari ynxu xanje in siyo in kawo maku" Shuraim dake kallonsa a hankali yace "Abba I will go..." Abba yace "Noo, Kar ka damu" Shuraim yace "Amma kace I should get it" Yace "Ehh na canja shawara, you don't worry" Daga haka Abba ya fita, Shuraim ya bi sa da kallo, Mumy ta kyabe baki, Kaka na kallon Heedayah ta dunguri kanta tace "kin dai ji nawa ake siyar da maganin d'an cikin roban nan, to idan ba tsoron Allah ba uban me muka hada da ke xa mu dinga kashe maki kudi haka, kin ji fa wahalan da d'a na yake, dubu hamsin xai kashe da safen nan a kan lalurar ki, to wa xai saka masa kuwa banda Allah? Ba dangin iya balle na Baaba fa" Mumy tace "Abinda ke damuna kenan kaka daga karshe ma a saka ma mutum da sharri" Kaka ta kalleta tace "Toh Ina ruwan ki, kudin ki ko na Amadun??" Kaka na fadin haka ta ja hannun Heedayah suka koma daki.... Mumy ta wuce nata dakin don duba drops din ko bata mayar da gaske ba, Mumy ta tsaya da mugun mamaki a gaban madubinta tana naxarin to waye ya shiga dakin kaka ya dauke maganin nan, kaf ta duba dakinta bbu, ita dai tana da yakinin ta mayar wajajen karfe biyu da wani abu na dare ba wai mafarki ba, hankalinta yyi mugun tashi don gashi an kara wargaza wnn plan din ma, ta dau wayarta rai ba dadi ta wuce bandaki. Har Mami ta gama shirin fita office hankalinta ya kasa kwanciya, she is so disturb, ko kadan bata ji xuciyarta yyi na'am da komawar Heedayah gun kaka ba, ko ma waye ya dauke eye drops din nan yyi hakan ne da wata manufa na cutarwa, cuta kuma me girma ba karami ba, bata san ta ina xata fara billowa kan a bar Heedayah wajenta ba, gaba daya taji bata yi trusting kowa na gidan ba, they all look guilty, both mother and Son, sannan masu aikin ma haka kawai taji hankalinta bai kwanta ba bata yrda da su ba, sannan Rabi'ah da Khadijah ma halin uwar garesu bbu abinda suka mance nata, kaka kuma from many indications taga baxata cutar da Heedayah ba balle kuma a je ga wanda yyi sanadin xuwanta gidan wato Abba, dauke Heedayah daga wajen kaka isn't going to be easy but she will try, ynda take jin Heedayah bata jin xata bada space a cuceta a gidan nan sai iya inda karfinta ya kare, da haka ta fita xuwa parlon Abba sanin bai fita ba, Yana parlon nasa da Shuraim dake xaune kasa, Abba na kallonta yace "Xaki tafi office...." Tace "Yes, but barrister har yanxu baka ce komai ba a kan the missing eye drops.... This is a very serious issue to address to with immediate effect, Sannan nasan ka fini sanin koma wanene ya dauke eye drops din nan ya dauke sa ne da manufa biyu xuwa uku which I won't mention cos you know...." Abba dake kallonta yace "Gaskiya ne, I will see to that" tace "And pls ko xaka yi ma kaka magana Heedayah ta komo wajen??" Abba ya d'an yi shiru, sannan yace "Will see to that too" Mami tace "Alright thank you, sai na dawo" daga haka ta fita, Shuraim ya bi ta da kallon gefen ido, dakin kaka Mami ta tafi, ta samu kaka ta hada ma Heedayah shayi me kauri ga ledan bredi guda ta ajiye mata, Kaka tace "Har xa a fita kenan" Mami ta xauna kusa da Heedayah tace "Ehh kaka, Ina kwana?" Kaka tace "Lafiya lau, kawai sai muka wayi gari da alhinin an sace maganin Deedayah" Mami tace "Allah dai ya kyauta...." kaka tace "Ameen fahhh, ga dai sabo Amadu ya siyo ya kawo na boye, ita kanta Deedayan ma baxan bari ta san Inda na boye ba balle wani" Mami tace "Yauwa gwara haka kaka" Kaka tace "Ni fa sai nake ga kamar Maryam ce ta dauke, ke baki ga duk ta rude ba??" Mami ta d'an yi murmushi bata dai ce komai ba tana gyara ma Heedayah gashinta, Kaka tace "Toh wllh sai dai ta cuci kanta ba dai Deedayah ba, me yar yarinyar ta tsare mata" Mami na kallon Heedayah tace "Did you pray today?" Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace "Toh wai sauran kayan nata fa? Ko in tafi in kwasa da kai na ne?" Mami ta kalleta tace "Kayan wa?" Kaka tace "Deedayah mana, ko kaya kala uku kadai xan dinga sa mata kamar fatararru?" Mami tayi shiru, kaka ta mike ta ci gaba da abinda take, Mami tace "To sai dai na dawo kaka" daga haka ta fita dakin, Kaka ta ajiye tsumman hannunta tace "Anya wannan Rakiyan na da saiti ma kuwa, ke dai ba don Amadu ba baxa ki san yarinyar nan ba, ke ba dangin iya tsakaninki da yarinyar nan balle na Baba to don me xaki dinga nuna fin karfi a kanta??" Kaka ta xauna ta rike ha6a tace "Ha'an, yau ga fitinanniyar mata ni Fatee, ko dai kanwar uwar Deedayah ce ita bamu da labari....." Hango ledan da tayi a gefen kofa ya sa ta mike tace "Ji ledan da gantalallen can ya kawo jiya ko meye a ciki...." Daga haka ta nufi ledan ta dauka tana leka ciki.... Heedayah ba kyauta bane na kudi ne, do not read without subscription, patronize ur novelist and read happily with out any thought... It's 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence of payment via WhatsApp 07087865788 Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Kaka tace "To dama idan ba shi din ba waye xai siyo min Apple manya haka? Ai sai dai Shureen din" Heedayah tace "Ni bai siyo min ba kaka?" Kaka ta kalleta tace "Ke kuma a wa? Ae sai dai in d'an yankar maki idan nayi niyya" Karime ce tayi sallama bakin kofar parlon Mumy ta shiga ciki, Mumy tace "kulle kofar, Sajida ta ga tahowar ki?" Karime ta kulle kofar tace "A'a wanka ta shiga" Mumy tace "Toh mu shiga daki, ba wani aiki bane linki xa kiyi min" Karime tace "Toh Hajiya" Mumy ta shigar da ita bedroom dinta, 'yan kaya ne da basu fi biyar kan makeken gadon dakin, Mumy tace "Ga su nan basu da yawa" Karime ta fara linke kayan, Mumy ta nemi waje ta xauna tana latsa wayarta, ganin Karime har ta kusa gamawa Mumy tace "Hajiyar ta fara sake maki kuwa?" Karime tace "Aa, yau ma tace min tunda Heedayah ta koma gun kaka to idan na gama aikin da xan yi a bangarenta in yi wucewata can dakinmu, ko don d'an kallon da taga Ina yi ne yasa ta fadi haka..." Mumy tace "To banda abun ki ba ga TV a nan ba Karime, duk sanda kike son kallo ki shigo nan kawai, ae xuciyar daban ne, kowa da irin tasa...." Karime tace "Kuma haka ne wllh, ke kam naki daban ne...." Mumy tayi shiru jin ringing din waya a parlonta, mikewa tayi da sauri ta fita parlon, Shuraim ta gani tsaye yana kallon screen din wayarsa dake ring, ya daga ya kai kunne tare da sallama, Mumy ta juya ta koma dakinta da sauri ya bi ta da ido still answering his phone call, alama tayi ma Karime da cewa kar ta kuskura ta fito, sannan ta juyo ta kulle kofar ta dawo parlon ta xauna, Shuraim ya gama answer wayar da yake yace "Mumy xan d'an fita in dawo" Tace "Toh Allah ya kiyaye, yanxu dai kai baxa ka dinga sa manyan kaya ba Aliyu, wllh suna maka kyau amma baka so, even if it's just once a week banda Fridays ka dinga sa wa" Bai ce komai ba ya nufi bedroom dinta, bata san lkcn da ya nufa dakin ba kawai gani tayi ya bude xai shiga, ta mike da sauri tace "Me xaka yi ciki Aliyu??" Tuni ya shiga suka yi ido hudu da Karime, sai a sannan ya juya ya kalli Mumy yace "Gaban mirror xan je" Bai jira tace komai ba ya wuce ciki, Karime dake tsaye kamar munafuka ta risina tace "Ina kwana yallabai" Ko kallonta bai yi ba ya nufi gaban mirror ya tsaya, Mumy dai na tsaye ta kasa bin bayansa, Karime ta fito dakin kamar munafuka tace "Hajiya na gama" cikin daga Mumy tace "Toh dama wani linki ne tun daxu kamar warce na sa kwalemar dakin gaba daya?" Karime ta nufi kofa da sauri ta fita, Shuraim ya fito daga dakin, Mumy ta hade rai tace "Ajiya kayi min a dakin da ka shige min bbu excuse Shuraim??" Yace "Na bar comb dina a nan ai jiya" Yana fadin hka ya nufi kofa, Tace "Shuraim Ina ga fa gwara in sallami mai aikin nan tawa kawai, bbu abinda take tsinana min sai magana ma da take yawan sanya ni, dubi fa wnn yarinyar yaushe ta xo gidan amma na gwammace in sa ta aiki a kan Sajida, cikin dadin rai xata maka komai fess fess, to ni kuma nayi ta kiranta kenan uwar dakinta tayi wani tunanin daban? Yanxu ma nasan uwar dakin nata bata sani ba ta xo, tun safe na kira Sajida ta xo ta min gyaran nan ban ganta ba shine na kira ita wannan din, matsalar ta daya wnn bata da wani wayewa...." Shuraim dai bai ce mata komai ba ya bude kofa yace "Sai na dawo" bin sa tayi da kallo har ya rufe kofar, ta xauna a hankali saman kujera tana naxari.... Mumy ce xaune dakin Hajiya Sadiya, da Hajiya Baturiya, Mumy tace "Sadiya tunda kin sa6a harka da Mutumin nan ki lallaba sa ya rage kudin wllh sun min yawa, duka duka nawa ne a acc din nawa ma tukun? Gaskiya ki yi masa magana a min ragi" Hajiya Sadiya tace "Kinsan Allah, wllh da dubu dari uku da hamsin ma yace, da kyar ya yrda dubu dari biyu da hamsin" Mumy tayi tagumi tace "A kan tsinanniyar yarinyar sai in dawo bbu ko sisi a account dina" Hajiya Baturiya tace "In dai bukata xata biya ba shkkn ba, ke kin hana mu xuwa gun malam to ba sai ki bari ayi me yiwuwa ba" Mumy tace "Toh shkkn, amma fa Ina tsoron kuma kar a xargeni ko da wasa a gidan" Hajiya Sadiya tace "Haba bbu wannan xancen, kaf xa a yashe ki kema har a buge ki, kinga bbu wanda xai xarge ki" Mumy tace "Toh shkkn sai mun yi waya, yamma yyi bari in wuce gida" Har bakin mota Hajiya Sadiya ta raka ita da Hajiya Baturiya, ko wanne ya shiga motarsa suka bar gidan. Kaka na sharan dakinta, Heedayah kuma na saman gado tayi rub da ciki tana sauraron xancen kaka, Kaka tace "Atoh, Shima Sudess din ai ba son yanda yake ganina xaune gidan duniya yake ba, kawai dai bbu ynda ya iya ne tunda ba ubansa ya halitto ni ba, to abinda Allah ba bacci yake ba, sai gashi cikin ruwan sanyi ya kawo min ke duk da dai ke makauniya ce baki da wani amfani kuma bamu hada komai da ke ba, to ai dai yafi babu... Wai d'an agwai da bak'in d'a" Heedayah tace "Waye Sudess din" Kaka tace "Oho haka na ji suna ce masa, jikana ne fa, ni haifi ubansa Umaru, amma cin haram a wajensa ba a cewa komai, yanxun nan xaki ajiye hakkin ki a nan kan ki juyo ya handame, to ina dalili...." Bude kofar dakin aka yi Sudais ya shigo da sallama, Kaka ta saki tsintsiyar hannunta ta mike tace "D'an Halak, yanxun nan nake xancen ka wllh, nace to Sudais anya lafiya kuwa kwana biyu, ni bai ta6a min haka ba" Ya mata wani kallo yace "Ke dai fadi gaskiya...." Heedayah tace "Kaka shine yake cin Haram din?" Juyawa kaka tayi tana kallon Heedayah baki bude, Can ta nufeta ta dunguri kanta tace "A gidan uban wa muka yi haka da ke? Meye kuma Haram, a ina kika ta6a jin wnn mugun kalmar" Sudais yace "Toh an ci Haram din, tunda ina tsoron Allah ai shkkn" Kaka ta juyo tana kallonsa tace "To waye baya tsoron Allah" ya bude hannu yace "Oho, sannan ni bana cin naman mutane, bana gulman mutane" Kaka ta xauna gefen gado ta fara matsar kwalla tana share idonta, ya daga Heedayah ta sauka kasa ya nufi kofa, kaka tace "Dama kar ka sake maido min ita dakina xan koreta wllh, ga kayanta nan duk a fitar min ba ruwana, maganin ciwon idon ma gashi nan na nannadesa da Sabuwar atamfata na saka kasan akwati, kowa ma ya xo ya duba ya kwashe ba ruwana" Sudais ya fita da Heedayah yana dariya kasa kasa, sai bayan da suka fita Heedayah tace "Is she crying??" Sudais ya fara dariya yace "Yess" Heedayah ta kwace hannunta kamar xata yi kuka tace "Ni ka kai ni inje ince mata sannu" Dariya kawai Sudais yake yi, Dai dai nan Mumy ta shigo gidan, ya tsaida dariyar da yake ya gaisheta tayi banxa da shi ta nufi bangarenta, Heedayah da har hawaye ya cika idonta tace "Ka kai ni ince mata sannu mana pls" Ya ja hannunta xuwa parlon Mami yace "Kina xuwa xata maki duka ba ruwana" Shiru Heedayah tayi jin abinda yace, Mami ta fito daga daki jin sallaman Sudais, suka gaisa, tace "Sai yau Sudais" yana murmushi yace "Ina shirye shiryen komawa UK ne, in sha Allah weekend xan wuce" Tace "Ayya, toh Allah ya kai mu lafiya, kaka ta yrda ka fito da Heedayah kenan" Dariya yyi, ya kai Heedayah gun Mami yace "Ehh ta yadda" Mami ta jawota jikinta tace "How are you dear?" A hankali Heedayah tace "Fine, Mami a kai ni wajen kaka" Mami tace "Ohh baki ma son xuwa wajena kenan" Heedayah ta girgixa mata kai, Mami na murmushi tace "Toh bari ku ci abinci, gashi an gama" Kaka na xaune saman tabarma hannunta rike da wayarta tana tunanin wanda xata kai ma ya kira mata Baffa taji dalilin da yasa Sudais ya xo ya dauki Heedayah suka fita, aka bude kofar Shuraim ya shigo da sallama, Kaka ta fara matsar kwalla tace "Yana shigowa kawai ya dauketa bbu wani bayani suka fita, ni ban san Inda ma ya kai ta ba" Shuraim ya tsaya yana kallonta yace "Wa ya dauketa?" Kaka tace "Shine nake son inji ko Umarun ne ya aikosa ya ci min mutunci haka, tana fa kwance muna hira gwanin ban sha'awa ya dauketa ya fice bayan ya gama min rashin kunya har da ce min bani da tsoron Allah ni munafuka ce" Shuraim ya d'an ta6e baki ya nemi waje ya xauna yace "Ina yini?" Tace "Aa wllh ba lafiya ba, ya fi minti talatin fa da fitar min da Deedayah har ynxu shiru" Yace "Toh amfanin me take maki idan tana nan din?" Kaka ta mike da sauri tace "A'a ka iya bakin ka, bata fi min ku ba ma aka ce maka, duk da bata gani kuma bbu dangin iya balle na baba ta fiye min kai wllh" Yace "Toh sai me" tace "Sai bakin ciki ya kashe ka" Junaid ne ya shigo parlon da sallama, Kaka ta washe baki tace "Sannu da xuwa Junaidu, ashe kana hanya" yace "Ehh kaka" ta rike ha6a tace "Wannan zungureren babyn roban duk na Deedayah ne?" Murmushi yyi ya ajiye ledan Babyn hannunsa, Kaka tace "Toh ai dama sai dai kai din, ko Amadu" Tunda Shuraim ya Kalli ledan Babyn ya dauke kansa, Kaka tace "Wannan Mutumin fa na ce ya siyo mata amma kaga bai siyo ba tunda ba wai yana da Imani bane" Shuraim ya mike ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo, kaka tace "Ae kaga irinta, bai siyo ba kuma yana hassada, da ka sani biyu ka siyo ka basa daya tunda bamu san ko bakin ciki yake mata ba" Junaid yyi murmushi yana kallon kaka...... Bayan Magrib Shuraim ya shigo parlon Mumy don rabonsa da ita tun da safe da ya fita gidan, bbu kowa parlon nata ya leka bedroom ya dai ji alamar tana bandaki ya dawo parlon ya xauna ya fiddo wayarsa yana dannawa, wayarta dake jikin caji ne yyi haske alamar kira, ko vibrating wayar bai yi ba sai haske, yana dai xaune har wayar ya katse, aka kara kira, sai da aka kira na hudu sannan ya mike ya nufi Inda wayar yake ya duka ya dauka yana kallon me kiran nata, ya shiga text msg din dake saman wayar, cikin few minutes ya karanta content din, sai kuma ya ajiye wayar ya nufi kofa ya fita ya kulle kofar, a hanya ya hadu da Rabi'ah tace "Ya Shuraim Mumy tana daki?" Yace "Ba daga nan nake ba" daga haka ya wuceta ya wuce bedroom dinsa. Mumy na fitowa parlonta ta nufi wayarta da sauri ganin yana haske alamar ana kira, ta daga ta koma daki ta kulle kofar tace "Yi hakuri wllh na shiga wanka ne, ya ake ciki?" Ta d'an yi shiru sannan ta Kalli agogo tace "Xuwa dai karfe dayan dare shine dai dai" Tayi murmushi tace "Toh shkkn sai mun yi magana...." Daga haka ta katse wayar ta xauna gefen gado tana wani murmushi.... Mami na xaune parlon Abba da Heedayah sai Rabi'ah da Khadijah, aka bude kofar parlon Kaka ta shigo ba ko sallama tace "Ni fa har yanxu ba a shigo min da Deedayah ba lkcn baccinta har ya wuce, idan kuma an canxa wajen kwananta ne sai a sanar min" Bata jira cewarsu ba ta daga Heedayah ta nufi kofa tana kallonsu Rabi'ah tace "Ku kuma gantalallu ga fura can da Junaidu ya kawo min na rage maku" daga haka ta fita, Mami gaba daya bata ji dadin xuwan da kaka tayi ta tafi da Heedayah ba, don ynxu goma ma yyi ta xata kakan tayi bacci ne ta wuce da Heedayahn part dinta don tace xata sha tea, Abba yyi murmushi bai dai ce komai ba amma ya gane Mami wasn't happy, Mami ta mike tace "Toh sai da safe" Yace "Allah ya tashe mu lfya" Su Rabi'ah ma suka yi mata sai da safe ta fita parlon..... Toh haka Allah yayi da ni yau..... 🌚 Heedayah isn't free.... It's 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then u show ur evidence of payment via WhatsApp 07087865788 Shuraim na xaune bedroom dinsa hannunsa rike da wayarsa yana dialing number wani colleague dinsa, bayan sun gaisa Shuraim yace "You called bana kusa Najeeb" Bayan few seconds Shuraim yace "Ehh na sani, I will be there soon in sha Allah" Daga haka suka yi sallama ya katse wayar, mikewa yayi yana kallon agogo dake nuna karfe goma da few minutes ya fita dakin, kitchen ya fara shiga ya hada shayi sannan ya fito ya nufi part din Mumy, duk wutan parlon a kashe yake da na dakinta, daga can uwar daka cikin muryar bacci tace "Waye wannan?" Yace "It's me Mumy, kinyi bacci ne?" Tace "Toh me xan jira" yace "Okay, Xan wuce hospital ne ynxu in sha Allah" Tace "Okay are you spending the night there?" Yace "No xan dawo anjima" Ta mike xaune da sauri tace "Karfe nawa yanxu da xaka je asibiti har ka dawo, why not spend the night there, ni bana son tafiyar daren nan gaskiya" Ya d'an yi shiru sannan yace "Toh shkkn sai da safe" Tace "Allah ya tashe mu lafiya, pray before leaving" yace "In sha Allah" daga haka ya fita parlon ya kulle mata kofa..... Abba ya gani xai shiga bangarensa, Abba yace "Ohk Baka tafi ba?" Shuraim yace "Yanxu xan wuce" Abba yace "Alright sai da safe" Shuraim yace "Allah ya kai mu lfya Abba" daga haka Abba ya shiga part dinsa, Shuraim ya xauna parlor ya gama shan shayin hannunsa ya kai cup din kitchen ya dauko makullin motarsa ya fita gidan, sai bayan da Mai gadi ya bude masa gate ya bar compound din ya tuna da rigar sanyinsa don garin da sanyi kuma ko kadan baya son sanyi, yyi parking a nan kofar gidan ya sauka motar ya koma cikin gidan, bedroom dinsa ya tafi ya dauko rigar sanyinsa sannan ya dawo parlor, har ya nufi kofar fita sai kuma yayi hanyar dakin kaka ya bude kofar, a kashe ya ga wutan dakin, ya danna hasken wayarsa that's so dim yana kallon dakin, Kaka na kwance hannunta rike da carbi tana bacci har da minshari, ga mamakinsa idon Heedayah biyu tana kwance lamo saman gadon, ya karasa cikin dakin yana haska fuskarta, mikewa tayi xaune jin motsi, a hankali tace "Mami" shi dai yana tsaye yana kallonta, Ta sake cewa "Mamii" Kaka ta gyara kwanciya tace "Kya ci kanki" daga haka ta ci gaba da baccinta, tuni Shuraim ya kashe hasken wayar sai da ya ji ta ci gaba da minshari sannan ya kara haska dakin, Heedayah dake xaune fuskarta kamar xata yi kuka cikin sanyin murya tace "I want to take tea plsss" Juyawa yyi ya fita dakin ya kulle kofar a hankali, sannan ya bar gidan, slowly yake driving har ya bar anguwar gaba daya. Tun tafiyar Shuraim Heedayah bata koma ta kwanta ba, har da d'an hawayenta tana gogewa da bayan hannunta, duk motsin da tayi sai kaka ta gyara kwanciya tace "Kya ci kanki" ita dai ba sanin nufin Hausan ma tayi ba, tana xaune har sha biyu saura ta ji an bude kofar dakin.... Sai kallon direction din take ta ji an kamo hannunta, ta mike tsaye tana tattaba hannun tace "Mami ke ce, I want to take tea..." Kaka ta tabe baki ta gyara kwanciya tace "Kya ci kanki dai" fitar da ita aka yi dakin still holding her hand, ba musu take tafiyar har sannan tana laluba hannun da ya riketa, sanyin da taji na shiga jikinta sbda yar rigar jikinta yasa ta fixge hannunta tace "Ina xa mu je??" lkci daya aka dauketa xata yi ihu aka rufe bakinta gamm, bata kuma yunkurin yin ihun ba, next thing taji an saka ta a mota an rufe, motar na fara tafiya ta kwala ma Mami kira, nan ta dinga ihun Mami da karfi amma ba a ce mata komai ba, ta gaji tayi shiru, can ta fara laluba cikin motar har ta ji ta ta6o me tukin, a hankali tace "Who are you??" Jawota yyi ta fado kansa ya maida ta front seat, kin sake sa tayi ta kai fuskarta jikinsa perceiving his perfume, yyi parking ya dau goran ruwa ya bude ya kai bakinta, rike goron tayi hakan ya sa ya sakar mata, ta d'an kurbi abun ciki, bata sauke goran ba sai da ta shanye content din ciki tas, shi dai driving dinsa kawai yake slowly, ta kai hannu tana ta6a sa bayan ta ajiye goran tace "Who are you?" Bai tanka ta ba, tace "Kai Yaya ne?" Still ba a ce mata komai ba, ta kara cewa "Yayah?" Nan ma shiru, driving kawai yake avoiding check points a hanya, har dai ya isa wani layi, kallon gate din layin dake kulle ya dinga yi, can ya gyara parking ya kashe motar yana kallon Heedayah, lamo tayi kan kujeran idonta rufe har ta fara bacci, ya bude side dinsa ya fita ya xaga xuwa inda take ya bude motar ya daukota ya daurata saman shoulder dinsa, ta bude ido a hankali sai kuma ta kara lumshewa, ya shiga layin ta karamin gate, har dai ya isa bakin wani gate ya tsaya ya ciro makulli aljihunsa ya bude gate din da hannu daya ya shiga sannan ya kulle gate din, ginin bungalow ne me girma, ya bude parlon shiga gidan da makulli ya shiga, yana bin ko ina da kallo ya wuce daki, bbu bedsheet saman gadon da ya d'an yi kura ya bude press ya fiddo wani xanin gado yayi spreading dinsa with one hand ya kwantar da ita gently, bude ido tayi sai kuma ta mike xaune da sauri tana hade kafa tace "I want to ease my self" tsayawa yyi yana kallonta kamar bai gane turancin da tayi ba, ta fara kokarin sauka daga kan gadon tace "I want to urinate" ya kalli kofar bathroom dake cikin dakin sai kuma ya kama hannunta suka wuce ciki.... Bayan sun fito tana rike da hannunsa tace "Shikenan mun bar kaka a can gidansu Mami, she will be looking for me faaa" Ji tayi ya kwantar da ita saman gado, ta yi rub da ciki ta lumshe ido, bude idon tayi da sauri jin an daga rigarta tace "Yayah" Lkci daya taji xafin shigan alluran xata tashi a tsorace ya ki barinta hakan yasa ta fashe da kuka tana kwala ma Abba kira, yana gamawa ya mike ya kashe Ac dake dakin ya kunne fan ya kashe wutan ya fita dakin ya kulle ya bar ta tana kuka. Tun karfe daya saura Mumy ke xaune dakinta idonta kyam, ga wayarta a hannunta, wayar ne yyi haske ta daga ta kai kunne da sauri, lkci daya ta mike tace "Har kun taso, to bari in je in bude gate din" tana fadin haka ta katse wayar ta mike ta tafi gun window tana kallon tsakar compound da yayi tsittt, a hankali ta bude kofar dakinta ta fita har xuwa main parlor, sai da ta gama kare ma parlon kallo sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, gate biyu ne gidan, daya a baya, daya kuma a gaba, sai dai an fi shekaru biyu ba a bude gate din bayan ba, can Mumy ta nufa tana yi tana dube duben tsakar gidan duk da tasan kowa na gidan na bacci har masu gadi, tana isa gate din taji sa a bude, she was so very suprise, ta leka wajen gate din, bbu kowa layin sai street light da ya haska ko ina, to wa ya bude gate din, ko dai dama a bude yake all this while ba'a ta6a lura ba, but this is suprising, jawo gate din tayi a hankali amma bata yi jamming ba ta juya da sauri ta koma cikin gidan.... A parlor ta ci karo da kaka, gabanta yyi wani irin faduwa, Tayi hanyar kitchen da sauri pretending kamar daga kitchen din ta fito, Kaka da tayi kicin kicin da fuska tace "Maryam kina ganin wannan kishiyar ta ki ko? Halan bata sanni bane bata san halina ba, wllh xan tara mata jama'ah idan bata fita hanyar Deedayah ba a gidan nan, meye xata bi dare ta shigo ta dauke ta kamar ita ta tsinto mana ita, wai ma uwar me ta hada da Deedayan nan ne ma tukun, farkawa fa nayi naga bbu yarinyar an dauketa, to wllh ki taso min Amadu inji ko shi ke sa ta raina ni daga shigowarta gidan ko sati biyu ba ayi ba...." Mumy tayi kasake tana kallon kaka, can dai tace "Ban gane ba kaka, yarinyar bata cikin dakin ki ne yanxu?" Kaka tace "Leka ki gani mana, xan maki karya ne?" Mumy tace "Aa to ki shiga bangarenta ki dauko ta kaka, wnn ai rainin hankali ne, ikon da take nunawa kan yarinyar ai ya fara wuce gona da iri" kaka na jin haka ta tafi bangaren Mami cike da kwarin gwiwa ta bubbuga kofar, ta bubbuga yyi sau hudu kafin Mami ta bude, Kaka ta wani sha kunu tace "Ina yarinyar da kika dauke a dakina Rakiya?" Mami tace "Yarinya kuma, wace yarinyar kaka?" Kaka ta kalli Mumy tace "Kinji ko Maryam, bata ma san yarinyar da ta dauke ba, to ni baxan biye maki ba da girma na, Deedayah xaki fiddo min" Mami tace "Heedayah da kika tafi da ita daxu muna parlon barrister?? Ae ba a kawota nan ba" Kaka ta gwalo ido tace "Toh ni kuma bata dakina yanxu, ban ganta ba wllh" Kasa cewa komai Mami tayi tana kallon Kaka baki bude, kaka ta saki salati ta tafi bangaren Abba da sauri shi ma ta tado sa, yana fitowa tace "Amadu kai ka shigo ka dauke Deedayah dakina muna bacci?" Abba na kallonta da mamaki yace "Heedayah kuma, ba xuwa kika yi daxu kika tafi da ita ba" Kaka ta kara Rafka wani uban salatin ta daura hannu a ka tace "Wllh farkawa nayi ban ganta a dakin ba Amadu, don Allah a rufa min asiri a dudduba ko taje ta shige wani wajen ne ba a sani ba, kasan makaho" Kaf gidan bbu inda ba a duba ba amma bbu Heedayah bbu alamarta, su Rabi'ah duk an tasosu su ma, Mumy da hankalinta ya fi na kowa tashi ta rakube kitchen tafara kiran waya, ana dagawa tace "Kai oga Salahu ku dakata an nemi yarinyar ko sama ko kasa bbu a gidan ba a san wanda ya dauketa ba, ku dakata xan kira ku, ku dakata tukun" Bata jira cewarsa ba ta katse wayar tana xufa.... Duk iya duban da xa ayi a gidan nan anyi har tare da masu gadi amma ba a ga Heedayah ba, daga karshe kuma aka ga second gate din gidan a bude, kaka ta rushe masu da matsanancin kuka tace "Wayyo na shiga uku yanxu cewa xa ayi tayi a dakina ta 6ace, don girman Allah a rufa min asiri a nemota, idan hukuma ma suka ji haka ba kyaleni xa su yi ba, duniya duk a dauka ace na sace makauniya, wllh farkawa nayi naga bbu ita sai pillow...." Abba dai na tsaye ya ma kasa cewa komai, ya rasa tunanin da xai yi but xa a iya ganin tashin hankalin fuskarsa, likewise Mami dake ta kallon gate din da ke bude, Mumy kuwa salati ta dinga yi tana cewa "Anfi shekara uku ba a bude kofar nan ba, a ina ma aka samo makullin aka bude?? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.... does it mean we are not longer safe cikin gidanmu kenan, waye xai dauke wnn yarinya ni Maryam" Mami tayi mata wani kallo sannan ta shige cikin gida, kana ganinta kasan she is not going to let this, daren ranan nan dai bbu wanda ya rintsa a gidan, Kaka kuwa ta lula cikin anguwa neman Heedayah, bbu yanda Abba bai yi da ita kan kar ta fita dare ne amma taki sauraran kowa tayi ficewarta tana kuka... Gaba daya Mumy ta rasa irin tunanin da xata yi, amma hankalinta ya fi na kowa tashi, can sai ga kaka ta dawo wujiga wujiga da takalma da Hijabi a hannu wai karnuka sun biyo ta... Karfe hudu Shuraim ya shigo gidan ta dalilin kiransa da Abba yyi, Kaka ta fashe masa da wani sabon kukan ta rikosa tana cewa "Wllh tare muke kwance Shureen wai farkawan da xan yi naga bbu ita, an sungumeta...." Shuraim dai ya kasa cewa komai sai kallon kakar tasa yake, can ta sake sa ta koma gun Abba tana Kuka wai ta shiga uku kar hukuma su daure ta, Shuraim ya jingina da bango a hankali ya rungume hannunsa, he looks disturbed also, Ana kiran sllh dama Mami ta bar gidan.... Bayan an idar da sllh sai ga Baffa da Sudais sun shigo gidan, Baffa ma is speechless just as his brother, Kaka dai tun hawaye na xuba har ya daina xuba yanda take kukan kai kace yarinya ce, Sudais ko karasowa cikin parlon ma ya ki yi yana tsaye daga bakin kofa, at the end kawai ya fice daga gidan gaba daya, Baffa na kallon kaka yace "Don Allah kiyi hakuri Baaba, in sha Allah xa a ganta, bbu abinda xai sameta" cikin rawan murya kaka tace "Toh kai sai kayi fatan abu ya sameta dama? Wllh wanda ya saceta cikin gidan nan yake, dama kaf gidan banda ni da Rakiya bbu me sonta, ko shi Amadun bamu san xuciyarsa ba" Abba ya kalleta ta gefen ido bai dai ce komai ba, Baffa yace "Da karfe nawa kika lura bata dakin?" Kaka tace "Daya saura minti goma, Ina fitowa parlo kuma Maryam na fara sanar ma cewar ban ga Deedayah ba" Abba ya kalli kaka yace "A ina kika ga Maryam din" Mumy ta amshe da sauri cike da karfin hali tace "Na fito shan ruwa kitchen muka hadu" Abba ya kalleta, ya dauke kai ya sake kallonta sai kuma ya mike ya wuce bangarensa, Shuraim dai kansa na kasa, Mumy na daga xaune amma duk cikinta ya hautsine da kyar take xaune har lkcn, ba a dau lkci ba Abba ya fito yana kallon Baffa yace "Mu tafi Dr" Mikewa Baffa yyi, kaka ma ta mike da sauri rike da hijab dinta tace "Ae da ni xa aje duk Inda xa a je tunda a dakina komai ya faru, salon in ki bin ku a xargeni ace dama ni na sace ta, gwara duk inda xa ku in bi ku" Sai bayan fitarsu Mumy na kallon Shuraim cikin karfin hali tace "Aliyu wa xai dauke yarinyar nan, wllh ni dai ban san komai kan wnn lamarin ba, naga kuma kowa kallona yake, dama ni na dauketa baxan damu ba, amma wllh ba ni bace, kaga kallon da barrister yyi min irin kamar da sa hannuna gun 6atar ta" Hankali tashe take maganan, shi dai Shuraim kansa na kasa, can ta mike ta wuce bangarenta, yana rike da car key dinsa ya bar parlon ya tafi gun motarsa dake waje.... Hajiya Sadiya da kanta kasa cewa komai tayi, Cikin rawar murya Mumy tace "Sadiya ni fa ban ta6a shiga rudani irin wnn ba, sannan kuma abun mamaki gate din bayan ma a bude na samesa....." Sadiya ta d'an yi shiru snn tace "Shuraim na gidan kuma koh?" Mumy tace "A'a baya nan, tun tara da wani abu ya tafi night duty ba sake shigowa gidan ba sai Asuba uban ya kirasa ya dawo..." Sadiya tace "Kaiii, wnn lamari akwai lauje cikin nadi....." cike da damuwa Mumy tace "Ni ki saurareni Sadiya, ta ya xan wanke kai na cikin lamarin nan, wllh sai kinga, ko magana xanyi sai inyi ta rawan baki... Ni nasan kowa ma ni yake xarga, ni kuma ba a ma kai ga xuwa dauke yarinyar nan ba aka nemeta aka rasa.... Ga dai abun farin ciki amma bbu daman farin cikin tunda ni ake xarga" Sadiya tace "Bari xan kira ki yanxun nan" daga haka ta katse wayar..... Cikin bacci Heedayah ta ji hannu a kanta, ta bude idanuwanta da kyar ta kamo hannun tace "Mami I want to ease my self" For those sharing and reading this book for free I know I can't stop u from doing so, but that's ur business, burden, and cup of tea, the book is just for a while, while the above mentioned is for everr, but do not edit my write up plss, leave it the way it is and read....😇 Heedayah is 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Abba yyi kasa da murya yace "Noo Rahinah, ba sai an kai ga haka ba, this is almost a family issue, ni nasan me xan yi, in sha Allah Heedayah will be back home...." Mami ta katse sa ta mike tace "Family issue barrister? ni fa I've already made up my mind, allow me to do what I am suppose to do, matarka knows Heedayah's Whereabout, ta san komai a kan bacewar yarinyar nan, so why do we all have to pretend, sorry to say, ba ruwana da wani family issue I am doing my work tunda kai baxa ka iya ba, idan 'yan sanda suka je suka daukota they will interrogate her ta fada masu inda aka kai 'yar mutane, period!!!" Abba ya mike yace "But you can't look into my eyes and tell me xaki sa ayi arresting matata Rahinah" Mami tace "I am sorry barrister, I've got no other option, yanayin aikin ne haka kai ma ka sani, nima gobe idan nayi abinda ya cancanci ayi arresting dina, allow them to arrest me..." Kallonta kawai yake, Kaka dake can wani gefe cikin haraban police station din tare da Baffa ta fyace majina tace "To ni dai yunwa nake ji, kar wata cutar taje ta kamani a banxa in cuci kai na, ko 'yar yagwat da nama ai ya kamata ku siyo min in xauna in ci daga nan, shi ciki ina ruwansa da 6atar mutum, Karfe takwas fa ake nema yanxu ban karya ba.... su kuma wa encan xancen me suke har yanxu kamar 6atar yarinyar bai damesu ba?? Ai ko d'an mage ne ya 6ata sa nuna damuwar su, amma tun daxu suna ta hira ka duba fa" Baffa ya kalli Mami da Abba bai dai ce komai ba, Kaka tace "Su ma shegun 'yan sandan ca suke 'yar kaza ce ta 6ata da baxa su maida hankali ayi abinda ya kamata ba, ni ba ruwana shiga xanyi in fada masu gaskiya...." Baffa ya dakatar da ita yace "Xa mu je can gidan ne dasu ynxu, yanxu duk xa mu wuce..." Kaka tace "Atoh gwara dai mu je din, ni dai tunda na biyo ku ai bbu wanda xai xargeni dai ko?? ita kuma wancan matar dake ta shiga da fice kamar Yan uwanta ne 'yan sandan Allah ya sa...." Shiru tayi ganin Mami da take magana a kai ta nufo su, Kaka tace "Ya ake ciki Rakiya? Ni fa hakurina ya soma karewa, basu da taimakon da xa su mana ne, in je gun Ta salla?" Mami tace "A'a xa mu je gida ynxu da 'yan sandan kaka, iya bincike ya nuna bbu wanda ake xargi kan bacewar Heedayah sai Hajiya Maryam...." Kaka ta wani tabe baki tace "Lallai!!! To da baxa a xargeta ba? muguwa ce fa, a jiyan da daddare ma daga waje naga ta shigo bansan uban me taje yi waje tsakar dare ba.... Idan ba rashin gaskiya ba menene wannan din??" Kaka ta fashe da kuka sosai tace "Kilan lkcn ta mika Deedayan ta dawo... Dama tun ba yau ba kowa yasan Maryam bata da Imani, Kuma axxaluma ce, akwai wata mai aiki da tayi da dadewa sai da ta kusa kashe mata ido daya, da kyar Amadu ya shawo kan kess din, sannan ta ta6a aiken Mai gadi mota ta kwashe gantalalle a titi ya karairaye, shi ma dai Amadu ya shiga ya fita aka rufe kess din, sannan kwanaki shi ma da dadewa taje gidan kitso tasu ta hado su da matar wani babban mutum, Maryam ta tattakure ta sharara ma mata mari, in takaice maki dai awowin Maryam uku a seff, da kyar Amadu ya shiga ya fita aka yi belinta sannan ya kashe kess din, Kinga kuwa ai Maryam takadiriyar mace ce, mu dai kawai muna xaune da ita ne saboda su Shureen" Mami dake ta sauraronta tace "Yanxu ma ita xa a je daukowa don ita ce first suspect kan 6atar Heedayah...." Kaka ta saki kabbara da karfi tace "To da pa?? ai dama ita ce ni dai tunda ba a xargeni ba Alhmdllh, a xargi kowa ma, har shi Amadun...." Mami ta juya ganin Yan sanda biyu sun fito ta nufi motarta da su, kaka ta bi bayanta da sauri tana cewa "To dama idan ba ke ba wa xai tsaya kan maganan nan, Amadu dama tun yana karami wani solobiyo ne, lauyancin ma Allah ne ya basa ba wayonsa ko dubara ba" duk wannan abun Abba na tsaye daga inda yake yana kallonsu, haka ma Baffa da ya ki cewa komai, Baffa ya sauke ajiyar xuciya ya nufi d'an uwan nasa.... Heedayah ta daga kai jin an amshi cup din shayin da take sha, tace "Ban shanye ba ai tooo" Yana rike da hannunta suka fito parlor, tace "Tell me who you are.... Yaya that gives me chocolates? Or Yayana, yayana din Farida?" Jin bai bata amsa ba, ta tattaba hannunsa tana turo baki tace "Ka ji mana, tell me" Jan bakinta taji anyi ta kai hannunta da sauri tace "Ouchh, me na yi?" Bai ce mata komai ba, ta warce hannunta tace "Nasan waye" ya tsaya yana kallonta, can ya durkusa kusa da ita ya jawota dabb da shi ya kai bakinsa kunnenta, murya kasa sosai kamar me rada yace "Waye?" Tayi shiru kamar tana son gane muryan, can ta fara komawa baya a hankali tace "I don't know you" jawota yyi ta fasa ihu tace "Maminaa" ya dauketa kamar yar baby suka fita parlon har kofar gida inda yyi parking, front seat ya bude ya sata ciki ya daura hannu saman lips dinsa yace "Shiiiii" he could see how afraid she is, hawaye ya kawo fararen idonta tace "Plss take me back to Mami, ban san ka ba" rufe motar yyi ya tafi ya sa ma gidan makulli sannan ya dawo ya hau motar ya bar layin... Wayarsa ne ya fara ring, ya kalli wayar ganin me kiran sa ya samu waje me kyau yyi parking sannan ya dau wayar ya fita waje don amsa kiran, bayan few mins ya dawo cikin motar ya d'an kalli Heedayah sannan ya ci gaba da driving dinsa..... Rirrikesa Heedayah tayi jin alamar wucewa xai yi ya bar ta bayan ya saukar da ita daga motar, cikin kuka tace "Don Allah don't leave me ka kai ni wajen Mami da Abba first, plsssss..." Ya cire hannunsa daga nata ya koma gun motarsa walking very fast, within a twinkle of an eye ya bar anguwar... Heedayah ta fashe da kuka sosai jin tafiyar motarsa ta dinga kwala ma Abba kira tana yarfe hannu, Mumy ce ta fito daga cikin babban gidan a rikice bayan kiran da Abba yyi mata yace ta bar gidan, hijab ne har kasa a jikinta ko kayan kirki bata sa ba da makullin mota a hannunta, tsabar rudewa mancewa tayi da motar a compound ta fito bakin gate da kafa, karo ta kusa ci da Heedayah dake kuka sosai tana laluba inda take, Mumy ta ja baya a d'an tsorace tana kara kallonta, lkci daya ta saki salati ta riko hannunta tace "Kee wa ya ajiye ki a nan, wa ye ya dawo dake???" Heedayah ta dakatar da kukan da take jin muryarta, Mumy na kalle kalle kamar munafuka tace "Nace wa ya ajiye ki a nan?? Ina yake???" Heedayah dai bata ce komai ba sai shessheka take, Mumy ta kwalo ma mai gadi kira a rikice, ya fito da gudu yana amsawa, tace "Isiyaka wa ya ajiye yarinyar nan bakin kofa, daga ina ta fito?" Ya matso da sauri yana kallon Heedayah da kyau yace "Ikon Allah ba ita ake nema ba Hajiya?" Mumy ta daka masa tsawa tace "Cewa nayi wa ya ajiye ta a nan kana tambayata tambayar banxa, waye ya dawo da ita" Yace "Wllh wllh Ina ciki Hajiya ban san daga Inda ta fito ba, Banda yanxu da kika kirani ni ban san ma akwai mutum a nan ba" Mumy ta fashe da kuka sosai tace "Kai shaida ne isiya yanxun nan na fito na ganta tsaye bakin gate din nan, ni ban san daga Inda ta fito ba, ban san wa ya ajiye ta ba" Isiya ya rike ha6a yace "Ikon Allah, to waye ya maido ta kuwa?" Mumy na goge idonta tana kalle kalle kamar munafuka ta marairaice tace "Amma kaga ba lallai kowa ya yrda a bakin gate muka ganta ba isiya... Ni dai kai ne shaidana fitowata kenan daga cikin gida na ganta, yanxu ka shiga da ita ciki ni xanje can in dawo, maxa ka kai ta ciki" tana fadin haka ta kara gaba da sauri tana hade hanya, isiya ya bi ta da wani kallo kafin ya ta6e baki yace "Da dai ba a san ki bane Hajiyaa, Lallai na yarda Allah na fitar da me kyau cikin mara kyau...." Yana fadin haka ya girgixa kai ya kama hannun Heedayah ya shigar da ita cikin gidan yace "Allah dai ya kubutar dake yarinya, da yake baki da hakkinta sai gashi Allah macecin ki, irinta macecin ki" sai da Mumy ta tabbatar ta shiga adaidaita sannan ta kira Abba, yana dagawa ta fashe masa da kuka sosai tace "Wllh barrister ka ga gashi an maido yarinyar nan kamar daga sama, ni dai ban san komai kan lamarin nan ba ban san wa ya dauketa ba ya sake maido da ita yanxu, Ina fitowa bakin gate muka ci karo da ita wllh wllh iyakar gaskiyata nake gaya maka isiya ne shaida na, tare muka ganta rakube gate tana kuka, Mu dai bamu san ta yaya ba" Abba da ke xaune mota tare da Baffa suna dawowa gida da farko kasa ce mata komai yayi, can dai yace "Yanxu ke kina ina?" Tace "Ga ni a adaidaita xan tafi gidan Aunty Zuwaira" yace "Toh ki tafi can din, Heedayar na gida yanxu haka?" Mumy tace "Wllh kuwa, tana can na baro ta tunda kace in bar gidan" Abba bai ce komai ba ya katse wayar, Abba ya jinginar da kansa da kujeran motar yyi shiru, Baffa da ke jin duk yanda suka yi da Mumy a waya da yake a hands free Abba yasa, ya sauke ajiyar xuciya, Abba yace "Ba Maryam ta dau yarinyar nan ba...." Baffa yace "Ba ita ta dauketa ba, amma she knows everything about it...." Abba ya kallesa yace "Not much, matata ce na san when she is lying and when she is not, nasan Maryam bata son yarinyar nan xa ta ma iya sawa ayi abinda ya fi dauke Heedayah, but this time around ba ita bace, I will have to go deep into this matter" Baffa dai bai basa amsa ba.... Salatin da kaka ta saki bakin kofar parlor ya sa Mami ta karaso da sauri 'yan sanda biyu na biye bayanta, Heedayah suka gani xaune saman kujera a parlon ga Karime da Sajida da su Rabi'ah duk a parlon, Shuraim na tsaye daga wajen dinning ya rungume hannunsa, Kaka tace "To ni dai Allah ya isa cutan hanjin ciki na da aka sa nayi na bar su da yunwa basu ji ba basu gani ba, tunda uwata ta haifeni ban ta6a kai wa karfe tara ban karya ba sae da wnn yarinya ta 6ata, gashi yanxu har wani jiri nake ji kamar xan kwanta gadon asibiti...." Bbu wanda ya kalli kaka, Mami ta karasa gun Heedayah dake xaune tayi shiru hawaye bushe a idonta, kafin tace komai daya daga yan sandan yace ce "Ita ce yarinyar?" Mami ta mike so surprise ta girgixa kai tace "Ita ce, she is the one...." d'an sandan yace "We are going back to the station with her, but before then a gidan nan suspect da xa mu dauka take??" Mami tace "Ehh nan ne" Shuraim ya kalli Mami ta gefen ido, Kaka ta nufi bangaren Mumy tace "Mu je in kai ku dakinta, ko ba Maryam ba...." Yan sandan suka bi bayanta xuwa bangaren Mumy, bbu kowa parlon da daki da ma bathroom, Kaka har da duba karkashin gado da cikin press din kaya, ta dudduba bayan labule, bata yarda ba sai da tasa suka dage katifar gadon, Kaka na hada xufa tace "Ta tsere, kaga ta sa an maido da yarinyar ta gudu, to Allah ya isa wahal da mu da tayi, Allah yyi mata abinda tayi mana...." Yan sanda suka fita dakin, nan dai suka dudduba sauran dakunan cikin gidan amma bbu Mumy, Kaka na kallon Shuraim tace "Toh Shureen ga uwarka dai ta dawo da Deedayah ta gudu...." Calmly yace "Ita tace maki ita ta dauketa??" Kaka ta nufesa da sauri tace "Kar ka min rashin kunya, kana min xan sa 'yan sandan nan su casa min kai yanxun nan su tafi da kai caji ofis" Khadijah ta sunkuyar da kanta tana dariya kasa kasa, Kaka tace "Atoh, ka yi mana, ya naji kayi shiru, xageni mana" Su kansu 'yan sandan sai da suka yi murmushi, Mami dai ko kallon kaka bata yi ba, Yan sanda suka dau Heedayah tare da Mumy xa su koma station, kaka ta dauko Hijab ta bi bayansu, Mami na kallonta tace "Kaka kiyi tsayawarki ki k'arya mana...." Kaka tace "Ce maki nayi yunwa nake ji, a fara abu da ni kuma sai a ki karewa da ni" Mami bata kuma ce mata komai ba ta bi bayan 'yan sandan suka fita, Kaka na biye da su da sauri. Hajiya Sadiya ta rike ha6a tana kallon Mumy da tayi tagumi tace "Ikon Allah, wllh wanda ya dauketa a gidan yake, bbu shakka ya gano komai ne yyi hakan, kuma ba kowa nake xargi ba illa Shuraim" Mumy ta dago da sauri tace "Shuraim?? Shuraim dai, A'a Shuraim baya ma gidan hakan ya faru, yana can asibiti" Hajiya Sadiya tayi wani dariya tace "Dai dai ma kenan tunda baya gidan, wato shine ya bi dare ya sadado ya dauketa...." Mumy ta mike tace "Haba Shuraim baxai ta6a yin haka ba, Bai san ma komai kan wannan plan din namu ba, to idan ma ya sani Allah na tuba meye hikimar dauketa balle bai sani ba, he has nothing to do with the blind girl a gidan, ko kallonta ma shi bai yi, Yan gidan ma yaushe ya samu lkcn yi masu magana balle makauniyar? Bai ta6a kallon inda take ba ma" Hajiya Sadiya tace "Wllh ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba Shuraim ne ya dauke yarinyar nan, idan ma xaki yarda ki yarda, wnn d'an naki baki san kyar yake kallon ki ba ko? to wai idan ba shi ba Aljanine xai shigo ya dauketa? Ke ki duba lamarin nan fa, sannan kince a bude kika ga gate din bayan gidan ba wai 6allawa aka yi ba, waye yasan wani inda makulli yake?? Gwara ki ajiye wnn batun na cewa Shuraim baya kula kowa a gidan, Kuma in har yaron nan naki na gidan nan bbu abinda xa a yi ma wannan yarinyar...." Mumy dake tsaye ta kasa cewa komai tace "Shuraim Kuma, Shuraim????" Hajiya Sadiya ta ja tsaki tace "Ai sai ki yi kuma, kema kinsan duk shirunsa shegen wayo ne da shi snn kinsan he is never in support of anything bad.... Tsaf shi xai dauketa sannan ya maidota bayan yaga duk an watse a gidan" Mumy dake xufa ciki da waje tace "To kuwa xan ci ubansa la'ada waje, xan ji ko shi ya haifeni ko ni na haifesa" Hajiya Sadiya tace "Atoh wnn dama dai ta wuce kuma, sai mu tari gaba, ga asara, ga xargin ki da kowa ke yi a gidan, ga kuma 'yan sanda na nemanki..." Mumy ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni wllh da ma ni na dauketa ko a jikina, amma bani bace sannan gashi kowa kallon ni na dauketa yake min, ga dai ta nan na hadu da ita a gate da xan fito amma sbda tashin hankali ko tunanin cutarta ban yi ba, kai a lkcn ji nayi na fi kowa farin ciki da dawowarta don wnn ba karamin case bane gashi kaka ta ga shigowana daga waje, da dai kattin sun shigo sun bubbuge kowa ne sun dauke yarinyar da Rabi'ah kamar yanda muka shirya daga baya sai su sako Rabi'ar ai kinga bbu shegen da xai xargeni, to ba a kai ga hakan ba aka nemeta aka rasa, Amma wllh idan har da gaske Shuraim na da sa hannu a dauke yarinyar nan sai na nuna masa ni na haifesa..... Sai ya yaba ma aya xakinta" Hajiya Sadiya tace "Ni duk ba wnn ba Maryam, yanxu dai daga nan har xuwa wata biyu ko daya da rabi babu ruwanki da yarinyar nan, tsakanin ki da ita ido, ko magana ba dole kiyi mata ba, sai mun bari kowa ya sakankance sannan sai a shammace su...." Mumy na share idonta tace "Tunanin da nayi kenan nima, shi kuma Shuraim don ubansa dama masters din nan dai da baya son yyi yanxu shi xai tafi yyi, ga Sudais har ya kusa gamawa, to dolensa sai ya tafi shima yyi, ko ya ki ko ya so wllh tllh sai ya tafi...." Hajiya Sadiya tace "Shkkn wllh, kinyi maganinsa cikin sauki" Mumy ta nemi waje ta xauna tace "Ita kuma wnn karuwar yanxu nake da lkcnta a gidan nan, na amince xan banxatar da batun makauniyar har na yan watanni ita kuma yanxu xa mu fara gogawa da ita" Hajiya Sadiya tayi dariya tace "Ki goga da wa? Matar da in ta fita tun safe sai yamma, ai bata da wnn lkcn sai dai makauniyar" Kiran Abba ne ya shigo wayar Mumy ta gyara xama da sauri ta daga ta kai kunne cikin sanyin murya tace "My Barrister" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... I am just super amazed at the well wishes from different angles, I really appreciate my lovely fans, Allah ya bar min ku, nagode kwarai da birthday wishes, Allah yayi mana albarka gaba daya, Ameeen.🥰😍😘💖 Those that didn't wish me kuma should come and patronize meee ejoo, shi ma love ne🥺 Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable....😍 3months later.... Kaka ce tsaye kan Khadijah inda take shiga ba nan take fita ba, Khadijah sai turo baki take tana yatsina fuska, Haka Rabi'ah dake tsaye bakin kofar parlon Mumy, Kaka tace "Yar banxa kawai me bakar fuska kazama, mummuna, ni dai wllh da ba don ina asibitin aka haife ki ba ma cewa xanyi ke ba 'yar Amadu bace canje aka masa, dama hutun da suka baku a makarantar cewa suka yi ku dawo gida ku dinga yi ma babban ku rashin kunya ban sani ba?" A fusace Khadijah tace "To wai ni kaka me nayi maki ne, ni kadai ne kika gani a parlon nan...." Kaka tace "Wllh Sudess xan kira yanxun nan ya casa min ke idan kika kara xagina, kawai don yarinya Allah ya yo ta makauniya sai ki juye mata shayin da take sha ki dura ruwa a kofin saboda bakin hali ko me? Sannan wannan yarinya Farida ta maki magana xaki hau ta da dambe kamar 'yar da6a? To bari yanxun nan xa a kira min Sudess, Allah ya rufa min asiri ya dawo shekaranjiya ai da lalacewa ta sameni" Khadijah ta fashe da kuka tace "To ita faridar Ina ruwanta da ni xata tsoma min baki?" Kaka tace "Aa wllh da ruwanta, bayan ni da uwarta Rakiya akwai me son Deedayah ne a gidan nan, to sai kilan Amadu duk da bamu san xuciyarsa ba, nan nan nan uwarki ta cakali Rakiya da fitina jiya Rakiya ta ki kulata, Farida kuma duk da dai agola ce a gidan bata fiye min ku ba sau dubu, Aa wllh ta fiye min ku, Maryam dai jaraba kawai ta haifa matsayin 'ya ya, idan ma bakin ciki kike faridar ta fi ki kyau ne ai sai ki fito ki fada in sa Amadu ya samar maki ko 'yar man kanti ne ki shafa kiyi hasken" Khadijah ta mike fuuu tayi wucewarta bangaren Mumy tana cewa "Gobe ta sake saka baki a harkana wllh wllh sai na mata dukan tsiya na farfasa mata baki" Farida dake tsaye bakin kofar Mami tare da Heedayah da ta rike rigar faridan, ta tabe baki tace "Toh ba sai ki dokeni ba, wllh karya ki xan yi...." A fusace Khadijah ta nufo Farida gadan gadan, kaka ta shiga kwala ba isiya kira da karfi, dai dai shigowar Shuraim parlon, Kaka ta fashe da kuka sosai tace "Shkkn kuma ni don mijina ya mutu ya barni bani da gata sai a ajiyeni a gida daga safe har dare ina ra6on katti yara fada, shi Amadu ya fita neman na xuba ma bakin salati, ita kuma wnn kinibabbiyar xabiyar ta bi sa ita ma aikin, uwarka kuma gantalalliya suna fita ta tafi gantali ita ma, wllh tun fitan iyayen suke dambe kamar raguna har an ji ma TVn Amadu, yanxu da baka dawo daga Zaria ba ya xanyi da raina yau, da gangan malam suka basu hutu don su kashe ni...." Shuraim ya kalli Farida da ta wani turo baki, ya kalli Khadijah da ta koma kofar parlon Mumy da gudu, ya karaso cikin parlon yace "Ku dawo nan gaba dayan ku" ko rufe baki bai yi ba Farida ta ja Heedayah suka shige parlon Mami ta sa makulli, Khadijah ta marairaice sanin in har ta shiga ya bi ta to mai kwatar ta sai Allah, Rabi'ah dake makale kofar ita ma tace "Allah ya so ni dai..." Kaka tace "Wa??? Ai kece katuwar munafukar ke ke sa Khadijah tayi komai, duk bakin ki daya" Rabi'ah ta fashe da kuka sosai tana kallon kaka, Shuraim ya hade rai yace "Baxa ku dawo nan ba nace" Khadijah ta Rabi'ah suka fito main parlon suna matsar kwalla, Cikin rawar murya Khadijah tace "To ita Farida fa Yaya" buge bakinta yyi, kaka tace "Ai ba kyaleta xa ayi ba, abinda ba tsoron ta yake ba" Da wayar rechargeable ya xane su a tafin hannunsu gaba daya, yayi wucewarsa dakinsa, Kaka da tayi tagumi tace "Dama dai neman wanda xai duka yake tun daga Zaria, Banda haka ga dai katti sa'anninsa a titi ya baro ya shigo gida ya ci xali, ku dai kuyi hakuri ku bar sa da Allah kawai" Rabi'ah da ke kuka sosai ta dinga hararan kaka, Khadijah na Shessheka tace "To mu kadai xai doka, ita faridan fa" kaka tace "Waye ubanta da baxa a doketa ba tunda aka doke ku, ai yanda yyi maku haka xai mata ba cuta" Rabi'ah tace "To Heedayah fa?" Kaka ta kalleta da sauri tace "Aa ke kuma baki son gaskiya, waye kuma Heedayah? Me tayi xa a doketa, to ko ma tayi in dai shi ba wawa bane akan me xai doketa, ko kula ku kinga tana yi a gidan nan, to ai ita ba gantalalliya bace kamar ku" Khadijah ta mike tana hararan Kaka ta wuce part din Mumy, Rabi'ah ta ja tsaki ta mike ta bi bayan Khadijah, kaka tace "Oho dai an dai sha mazga" Farida ta ja tsaki tace "Haka xa mu yi ta xama kenan baxa mu ci abinci ba, ni dai baxan sha cornflakes ba" Heedayah dake shan cornflakes dinta ta ta6e baki tace "Ni ina ruwana, wnn da kike ganinsa din nan mugu ne, wllh duka xai maki in kika fita" Farida tace "To a ina ya san ni da xai dokeni? And ni fa Ina ce shine Sudais" Heedayah tace "Aa ba Yayana bane, wannan Ya Shuraim kamar naji suna ce masa, I never liked him even for once" Farida tace "To da ina yake tun da na xo ban gansa ba" Heedayah tace "Ban san Inda yake ba, but yana dawowa every Saturday" Farida ta ta6e baki tace "To kawai bai san ni ba sai ya dokeni" Heedayah tayi dariya tace "That's because he is wicked" mikewa Farida tayi tace "To kinga mu lallaba mu je in xubo mana" Heedayah tace "Ni baxan je ba" Farida tace "Plss mana I can't go alone, da sauri fa xan xuba mana mu dawo" Heedayah ta juya manyan idanuwanta tace "To ki jira in gama shan Cornflakes dina" Farida tayi tagumi tace "Tohh" Heedayah na gama shan Cornflakes din Farida ta ja ta suka fita main parlor, bbu kowa parlon sai Tv dake kunne, Farida na rike da hannunta suka shige kitchen da sauri ta kulle kofar, Sajida da Karime ne suka yi lunch a gidan, Farida ta bude warmer da abincin ke ciki ta debi shinkafa knn xata bude na miya aka bude kofar kitchen din, Shuraim ne ya shigo da wayar rechargeable a hannunsa, tana ganinsa ta fasa ihu ta saki murfin warmer din hannunta, Heedayah ta ja gefe a tsorace, cafkota yyi, ta rikesa tana basa hakuri a tsorace, Bai ko saurareta ba ya rike hannunta ya dinga lafta mata wayar hannunsa, Kaka ta shigo kitchen din a guje tana cewa "Wayyoo wllh uwarta lauya ce daure ka xata sa ayi shureen, idan ka doke wasu ka kwana lafiya to ita wllh a seff xaka kwana bbu me ceton ka, yau fa kwananta hudu da xuwa gidan, ta dawo daga tsadadden makarantar kwanan nan, duk da dai fitinanniya ce ai tayi min wanki yau kuma ta wanke min bandaki, ko da yake jika jika tayi amma ai tafi munanan kanninka..." Sai da Shuraim ya lafta mata son ransa sannan ya saketa, ta durkusa a wajen ta dinga ihu tana kiran Mami, ya kalli Heedayah da ta rakube gefe daya a tsorace hawaye cike idonta, ya nufeta fuska daure kaka ta dakata da surutan da take ta shige gabansa tace "Aa nan kuma ne xan sa 'yan anguwa su lallasa min kai, uban me xaka mata?? Ai wllh idan ka doki gantalallun nan ka kwana lafiya to kana ta6a Deedayah maka ka xanyi a kotu, me makauniyar tayi maka, duk da dai ita ma ba kyalle bace" kallon kaka kawai yake fuska daure, ta kama hannun Heedayah ta fice daga kitchen din tana cewa "Ni dai ba ruwana" Farida ta wani hararesa ta mike xata bi bayansu, xai cafkota ta fice a guje ta shige dakin kaka... Uku saura Mumy ta dawo gidan, su Rabi'ah suka tsara mata abinda ya faru da safe, tayi shiru tana sauraron su, can tace "Tafi maxa ki kira min Shuraim din" Khadijah ta kwanta saman gado tace "Tabbbb" Rabi'ah tace "Ni dai kar ma kiyi masa magana Mumy, wllh dukan mu kawai xai kara yi" Karime ce ta shigo parlon, Mumy tana kallon su Khadijah tace "Ku fita" duk suka mike suka fita, Karime ta xauna kasa tana ta6a baki tace "Hajiya ji nayi daxu a waya tana gaya ma wani wai an kusa fita da Heedayan waje ayi mata aikin idon..." Mumy ta gwalo ido tace "Haba??" Karime tace "Wllh kuwa haka na ji...." Mumy ta gyara xama tace "Wa kika ji tace xai fita da ita?" Karime tace "Wannan ne ban sani ba Hajiya" Mumy tace "Har dai yanxu baki san Inda kaka ke boye maganin nata ba ko?" Karime tace "Ai yanxu kaka ta ma daina sa ni gyaran dakinta, Sajida ce ke yi" Mumy tace "Toh watan barin gidan Sajida ya tsaya" Karime tace "Wllh daxu da safe kafin Hajiyar ma ta fita aiki ga dai ni a xaune amma Sajida ta sa taje dakinta ta dauko mata makullin mota, ni ta ma daina bari in shiga dakinta ynxu...." Mumy tace "Akwai wani aikin da xan baki yanxu, kuma in sha Allahu idan kika yi kokari kika cika aikin, dubu biyar xan baki kyauta..." Karime ta washe hakora tace "Hajiya ai ko baxa ki ban komai ba...." Bude kofar parlon da aka yi yasa duk suka yi tsit, Shuraim ne ya shigo da sallama, fuska daure Mumy tace "Wannan ai walakanci ne, ayi shinkafa dafaduka jiya, yau kuma ayi shinkafa da miya, tunda Sajidar tace maki baxata yi ba ke ba sai kiyi ba..." Juyawa Shuraim yyi xai fita Mumy tace "Ina kuma xa ka?" Yace "Naga kuna magana ne ai" Mumy tace "Kawai masu aikin jaraba suyi ta sa mutum magana, suna ba mutum wahala" Bai ce komai ba shi dai ya fita, Karime ta kalli Mumy, Mumy tayi kasa da murya tace "Yaushe ya xo?" Karime tace "Tun safe" Mumy tace "Tashi ki tafi xan neme ki anjima" Mikewa tayi ta fita... Kaka nata aikin linke linke a dakinta, Farida na dakin tana taya ta, Kaka tace "Toh dama idan ba ke ba waye xai taya ni, ita wancan makauniyar ba wai amfani gareta ba" Heedayah dake kwance tayi rub da ciki tana jin kaka bata dai juyo ba, Farida tace "Kaka wai shi ma a nan gidan yake xama?" Kaka tace "Wa?" Farida tace "Wannan da ya doke mu mana" juyawa Heedayah tayi daga kwancen da take tana kallon direction din da take jin muryarsu, kaka tace "A'a yana can Zaria yana karo karatu, ko massers naji suna kiran karatun, kinsan bbu yanda ba ayi da shi ya fita waje kamar yanda Sudess yaje can yake yi ba amma ya ki, uwarsa kuwa kamar tayi hauka don ta kwallafa ran fitansa, kin santa da fafa, so tayi ta bi duk kawayenta tace d'an ta na kasar waje yana karatu, to da yake shi ma Amadun kila ba wani son kashe kudi yake ba ya goya masa baya kar ya fita, duk sati kya gansa salalo salalo wai ya xo gida hutu, duk ya bi ya takure jama'ah...." Bude kofar dakin aka yi sai ga Shuraim, Farida ta juya da sauri ta ci gaba da linkin da take, kaka tace "D'an Halak, yanxun nan take tambayata uban me ke dawo da kai gida, shine nake bata labari" da sauri Farida tace "Ni fa ba shi nake tambayar ki ba...." Tana fadin haka ta nufi kofa ta fita ya bi ta da kallon gefen ido, ya kalli Heedayah dake kwance, kaka tace "Ka ji wai ita kuma yau bata son tayi karatun, kuma duk inda malamin yake nasan yanxu yana hanya, dubu ashirin da biyar haka Amadu ke biyansa duk wata, to banda Allah wa xai biya mu, bbu fa abinda muka hada da ita....." Heedayah ta mike xaune tana sauraron kaka kamar xata yi kuka, kaka tace "Kasan idan ba mutum ke biya ma kansa ba sai yyi ta iskanci iri iri, sai ka ga uban tsaraban da Sudess ya yo mata daga kasar turawa, ni tsoro ma kamani yyi wllh, ni dama ko tsinke shegen bai kawo min ba, shi kuma Junaidu daxu ya kirani wai nan da sati xai dawo har yace in bata suka dade kuwa suna waya, ko kanwarsa bai ce in ba ma ba, ita kuma Khadijah daxu...." Shuraim ya dakatar da ita yace "Ina tsaraban??" Kaka tace "Ae baxa su dauku ba Shureen" yace "Suna ina?" Mikewa Heedayah tayi a hankali tana laluba hanya xata fita kaka tace "Ji algunguma, Ina kuma xaki, kinji nace xan dau kayanki ne da xaki wani mike xaki fita??" Shuraim dai sae kallon dakin yake yana neman kayan..... Am so exhausted yau, let it not just be as if I didn't type🥺 Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ta gefen ido Shuraim ya dinga kallon Heedayah dake kokarin fita ya ga ko xata ta6a sa, she was so careful ko kusa da shi bata bi ba har ta fita dakin, kaka tace "Ni sae nake ga kamar karyar makanta take yi, ynxu a hka fa sai ta fita har tsakar gida" Shuraim yace "Ina kayan?" Kaka tace "Naga jaraba, Ina ruwanka da kaya Shureen? Tun daxu ka isheni ina kaya to kai aka kawo ma kayan? Kayan me xaka dameni haka, Komai fa na da sirri, ba ruwana ni ba 'yar cin amana bace, Bai ce in nuna ma kowa ba har Amadun balle kai karan kada miya...." Wani kallo yyi mata ya juya ya fice daga dakin.... Turuss Khadijah tayi rike da bucket din ruwan kumfa a hannunta, ya kalli direction din da take kokarin xuwa da sauri, Heedayah ce har sannan bata isa bangaren Mami ba tana tafiya a hankali kuma very careful, ya kalli Khadijah da tayi wuri wuri da ido, da sauri ta juya xata koma Inda ta fito, ya bi bayanta tana ganin haka ta sake bucket din hannunta a rikice, ya ja baya da sauri ganin ruwan kumfan ya malale kasan tiles bai ankara ba sai gani yyi tayi sama sannan aka nanota kasa da karfi, wani ihu tayi can kasa makoshi, ya ma rasa ko dariya xai yi ko d'aga ta xai je yyi, ta kwalo ma Mumy kira tana cewa Wayyo bayanta, yana jin hka ya kalli Heedayah da har ta kai kofar parlon Mami ta tsaya, Farida ma ta fito da sauri don ganin me ya faru, Shuraim na jin Mumy ta bude kofarta xata fito tun bata karaso ba tana tambayar lafiya me ya faru, yyi saurin shigewa dakin kaka ya rufe kofar. Farida ta ja Heedayah suka shige ciki ta kulle kofa. Bayan isha Farida na parlon Mami da Heedayah, Mami kuma ta je kai ma Abba abinci aka bude kofa Sudais ya shigo da sallama, daga kai Heedayah tayi tana kallon ta Inda ta ji muryar sa, da farko Farida ta xata Shuraim ne sai kuma ta ga wannan ya fi Shuraim haske, Ta gaishesa ya amsa yana murmushi yace "Ya kike?" Tace "Lafiya lau" ya xauna yana facing din su idonsa a kan Heedayah yace "Ba gaisuwa Deedayan kaka" Heedayah ta jinginar da kanta da kujera tace "Ni ba Deedayah bace" yace "To ya sunan?" Ta langwabar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau Cutie, ya karatun kuna ta yi koh? And kina ganewa?" Ta gyada masa kai, ya kalli Farida yace "Ya sunan ki 'yan mata?" tace "Farida" yace "Ban ta6a ganin ki nan ba Farida, though Naga kuna kama da Junaid" Farida tayi murmushi tace "Ehh na xo hutu ne kawai" yace "Wani makarantar kike?" Tace "Nigerian Turkish...." Yace "Boarding?" Ta gyada masa kai, yace "Maa sha Allah" Heedayah tace "Yayana baxa ka sake komawa UK ba koh?" Yace "Idan ma xan koma tare xa mu koma ae" Ta wara ido tace "Da gaske?" Yace "Ehh mana sai in gaya ma su Abba da Kaka su bani ke, kowa ya shaida sannan mu wuce" Murmushi tayi tace "To kayi masu magana plss" yace "Da gaske dai xa ki bi ni? Xamu dade fa bamu dawo ba" tace "Allah xan bi ka" yana murmushi yace "Toh shkkn" Bude kofa aka yi Rabi'ah ta leko fuska daure tace "Ya Sudais kaka na kiran ka" ya kalleta kafin yace komai tayi banging kofar ta wuce, Farida tayi kwafa can kasa kasa, mikewa yayi yace "I'm coming back...." A hankali Heedayah tace "No chocolates?" Ya kalleta yyi murmushi yace "Sai na dawo" daga haka ya fita, Farida tace "Ke da kike cewa xa ki bisa ke matarsa ce?" Heedayah tace "To ba Yayana bane" Sudais na tsaye yana sauraron abinda kaka ke cewa, can yace "Toh yanxu me kike nufi?" Tace "Ina nufin in har baka bani nawa tsaraban ba wllh baxan bata ba, gwara in kwashi tarkacen da ka kawo in kai kasuwar 'yan koli in siyar, haka kawai daga ganin sarkin pawa sai miya tayi xaki, uwar me ma ka hada da ita bani da labari, duk wahalan da nayi da kai kana karami ka dawo daga kasashen turai ko abun sakace hakuri baka kawo min ba sai yar tsintuwa" dai dai nan Shuraim ya shigo dakin da ledan fruits da Abba ya sa ya siyo mata, Sudais ya kallesa sannan ya ci gaba da sauraron kaka, Shuraim na ajiye ledan tace "Shureen tunda muke da kai ka ta6a fita kasar waje ka dawo baka min tsaraba ba, ko nan nan da Zaria idan kaje ai kana siyo min 'yar lemon nan" Shuraim na kallonta ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihu, kaka tace "Toh don me Sudess xai fita ya dawo min haka sai wata can wai Deedayah xai kwaso ma kaya iri iri kamar kanwar ubansa" Sudais yace "Saboda ta fiye min ke" shiru kaka tayi tana kallonsa a bit shock, yace "Kuma ki fito da kayan in kai mata yanxu" Kaka tace "Al-qur'an kasuwan 'yan koli xan kai su gobe da sassafe, idan na baka in tafi a karkace, Deedayar kanwar ubanka ce ko ta uwarka?? Waye kuma Deedayah? Me na hada da ita banda dai d'a na ya tsinto mana ita" Sai kuma ta xauna ta fashe da kuka tace "Ehh lallai karshen duniya ta kankama" Juyawa Sudais yyi ya fita daga dakin, Kaka ta kalli Shuraim tana matsar kwalla tace "Ka dai ga ko Shureen?? Hakan da Sudess ya min ya kyauta" Yace "Ni baxan ce komai ba sai na ga kayan" Babu wata wata Kaka ta dauko makulli da sauri ta bude gun ajiye kayanta ta fiddo akwatunan har biyu da karamin jaka, kallonsu kawai Shuraim yake, ta xuge jakar ta shiga fiddo abubuwan ciki, cikin lkci kadan ta fiddo komai ta bajesa a gaban Shuraim tana kallonsa, Kallon kayan kawai Shuraim yake, beautiful English wears, teddie bears, biscuits, dolls, chocolates, sweets, shoes, har da jewelries, Shuraim ya dauke idonsa daga kan kayan, kaka na matsar kwalla tace "Ka dai gani ko, ni fa na haifi ubansa Umaru" Mikewa Shuraim yyi bai ce mata komai ba ya fice daga dakin... Ta bi sa da kallo baki bude sai kuma tace "Toh Allah ya isa" Sudais na komawa parlon Mami, Mami dake xaune parlor tace "Mutan UK, sai yau muka hadu" Ya gaisheta yana murmushi yace "Jiya da na xo kina gun aiki" Mami tace "Ehh ina can, ya karatun kun gama kuwa?" Yace "A'a saura kadan" Mami tace "Maa sha Allah, Allah ya sa a gama a sa'a, ya su Hajiyar ku?" Yace "Suna lafiya gaba daya" Tace "To maa sha Allah, a xubo abinci?" Yace "A'a na ci" ta mike tace "To yayi kyau" bedroom dinta ta shiga ya kalli Heedayah ya koma kusa da ita yace "Ina kawar ki Farida?" Tace "Ta tafi wanke wanke a kitchen" Sudais yace "Masu aiki fa?" Heedayah tace "Mami ce tace taje ta yi" Yace "Ohkk" ta matso kusa da shi a hankali ta laluba hannunsa tace "Yaya kasan me?" Ya kalli kofar dakin Mami sannan ya hade forehead dinsa da nata yace "No..." Tace "Yau ina son in sha ice cream" yace "Ice cream?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk bari Farida ta gama wanke wanke sai mu je gaba daya" Tayi murmushi tace "Nagode" Farida na shigowa yace "Farida tell Mami xa mu je siyo abu yanxu, with you and Heedayah" tace "Ohkk" daga haka ta shiga bedroom din Mami, ba a dau lkci ba ta fito da Hijab dinta da na Heedayah tace "Mami tace alright" sosai Heedayah ta ji dadi, ya amshi Hijab din ya sa mata sannan ya daga ta holding her hands suka fita parlon tare da Farida, Shuraim na xaune parlor shi kadai, tun da ya kallesu sau daya ya dauke kai har suka fita parlon.... Wani wajen shan ice cream Sudais ya kai su, yyi parking ya sauka motar, ya bude ma Heedayah back seat yana rike da hannunta ta sauka, Farida ma ta fito daga front seat da ta xauna, Sudais na rike da hannun Heedayah da ta makalesa suka shiga ice cream parlor din, Ya duka dai dai kunnenta yace "Wani irin ice cream kike so?" Tace "Vanilla" ya kalli Farida dake kallonsu yace "Ke fa Aunty Farida?" Tayi 'yar dariya tace "Irinsa nima" Wani mutumi ne xaune wajen da roban ice cream a gabansa, su uku ne xaune a round table din, all wearing glasses, tun da suka shigo yake kallonsu ta bak'in glass din idonsa, Sudais ya biya kudin ice cream da ya siya masu yana rike da hannun Heedayah ya nufi kofar fita Farida na biye da shi, mikewa Mutumin yyi ya dau makullin motarsa, wanda ke kusa da shi ya kamo hannunsa murya can kasa yace "Hey... ina kuma xaka? Ynxu fa xa su gama su fita..." Ba tare da Mutumin ya kallesa ba yace "Ina xuwa ynxu" daya Mutumin yace "Noo this is our only chance...." Ya fixge hannunsa ya fita da sauri, Sudais ya kulle motarsa kenan bayan ya sa Heedayah ciki ya bude maxaunin driver ya shiga yana kallon Farida dake gaban motar yace "Did you need anything again Farida?" Tace "Aa mun gode" tada motar yyi yayi reverse, Mutumin da tuni shi ma ya shiga motarsa ya bi bayansa, mota daya ne interval tsakaninsu, Mutumin ya dinga kokarin ganin yyi over taking motar har suka kusa traffic, Sudais na tsallaka wajen traffic din ya nuna red, hakan ya sa motar dake bayansa ya tsaya, Mutumin ya jinginar da kansa da kujera ganin motar Sudais yyi nisa sosai... Sudais na parking a kofar gida ya bude ma Heedayah back seat ya sakko da ita, Farida na rike da ledan ice cream din suka wuce ciki, har sannan Shuraim na xaune main parlor, wannan karan kallon gefen ido yyi masu, Sudais ya duka kusa da Heedayah yace "Sai da safe, I am going home now" tace "Xaka xo gobe?" Yace "In sha Allah" tace "Haka kace jiya kuma baka xo ba" yace "Ba gashi na xo yau ba" tace "Toh byee" ya ja hancinta a hankali yace "Bye" Farida ma tayi masa sai da safe tana rike da hannun Heedayah suka wuce bangaren Mami, Sudais na kallon Shuraim yace "Sai da safe bokan turai" Shuraim na danna wayarsa yace "Allah ya tashe mu lfya" Sudais ya juya ya fita parlon... Washegari karfe tara saura Hajiya Amina mahaifiyar Sudais ta shigo gidan, Khadijah na xaune dinning suna breakfast da Rabi'ah, duk suka gaisheta suna mata sannu da xuwa, ta nufi dining din tana kallonsu murya can kasa tace "Abba na nan??" Rabi'ah tace "Aa ya fita" Umma tace "Hajiya Maryam fa?" Khadijah tace "tana daki" Umma ya nufi bangaren Mumy ta bude kofar ta shiga, bbu kowa parlon haka yasa ta wuce daki, Mumy ta katse wayar da take yi da sauri tana cewa "Waye??" Umma tace "Ni ce Maryam" Mumy tace "Aa Amina, daga ina da safe haka?" Umma tace "Daga gida..." Mumy tace "Allah ya sa lafiya dai, ko munafukar ta sake hada ki da Dakta?" Umma tace "Ba gwara a hada ni da Dakta ba a kan wnn takaicin...." Mumy ta gyara xama tace "Me ke faruwa?" Umma tace "Uban kayan da Sudais ya kawo ma makauniyar nan na xo amsa tunda ba ubanta bne ya basa kudin banxa" Da mamaki Mumy tace "Kaya kuma, wllh bani da labari Amina, ta Ina aka shigo da kayan gidan ban sani ba?" A fusace Umma tace "ni kai na da na haifesa a jaka daya ya kawo min tsaraba, kanninsa kuwa dama tsaraban baya wuce chocolate da biscuits..." Mumy tace "To wai kayan me ya kawo mata?" Umma tace "Wllh tsaraba ya yo mata niki niki, iri iri kuwa, bai san xancen xai dawo kunne na ba, har manyan akwatuna biyu da jaka fa Maryam, abinda hakan ke nufi shine na kasa ganewa" Mumy ta gwalo ido tace "Sudais din?? Jiya na ji ance ya xo dama amma ko shigowa ya gaisheni bai yi ba, kinsan fa har wani xumunci ya kulla da kishiya ta" Umma ta mike tace "Ina xuwa, ba dai Barrister baya nan ba, yau xa ayi ta ta kare" bata jira cewar Mumy ba ta fita. Bangaren Mami Umma ta nufa ta bude kofar hade da sallama bbu yabo bbu fallasa, Mami na tsaye parlonta tana sa wrist watch ta gama shirin fita, su Farida na parlon, a takaice Umma tace "Ina kwanan mu" Mami na kallonta tace "Same to you" Umma tace "Kayan da Sudais ya kawo gidan nan na taho a miko min..." Mami tace "Kaya? Kayan me kenan?" Umma tace "Ai kin fini sanin ko kayan menene tunda kece kika amshi kayan, to ba duniya na haifar ma shi ba, ayi hakuri a fito da kayan a bani in kama gabana" Mumy dake ta leko parlon tana tsaye daga bakin kofa tace "Atohhh, gwara dai ki sanar masu ba duniya kika haifar ma shi ba" Mami bata sake kula su ba, ta gama saka agogonta ta dau handbag dinta da veil tana kallon Farida da Heedayah tace "Farida bring hijab for the both of you sai in ajiye ku gidan Hasinah" Farida ta mike ta wuce daki, Umma tace "Ni fa ba Maryam bace da xaki wani dinga sha ma kamshi bbu hadina dake, kayan da d'a na ya kawo maki nace ki fito min da su yanxu, ko alkali ce ke ni baxan fasa amsan abinda na xo amsa ba baxan kuma fasa gaya maki abinda ke raina ba....." Farida ta fito da hijab Mami ta amsa ta sa ma Heedayah, Farida ta ajiye mata takalminta ta a gabanta, Mami tace "Ki je ku sallami Kaka, sai ku sameni a mota" Umma ta bude baki tana kallon Mami ganin har sannan ta ma ki kallon inda take, Mami ta nufi kofar sai a nan ta kalli Umma tace "Malama xan wuce, bani hanya" Umma tace "Hanyar ya ci kaza kazan sa, kayan da aka kawo maki nace ki fito min da su yanxu kada abu ya 6aci tsakaninmu, ni fa ba Maryam bace wllh" Kaka ce ta taho wajen da sauri tana cewa "Muryar waye nake ji wnn kamar na Amina, me ke faruwa hka?" Umma ta juya tana kallon kaka fuska daure tace "Ina kwana kaka" Kaka tace "Lafiya kike hayaniya haka a kofar mutane Amina, me ya faru??" Mumy tace "Wllh kaya wai Sudais ya kawo gidan nan ba mu da labari, kaya wai me yawa..." Kaka tace "Kayan me??" Mumy tace "Ni kaina bansani ba, ance dai kayan na nan bangaren" Kaka tace "Au, wai tsaraban da yayo ma Deedayah?" Mumy tace "Toh shi din kenan" Kaka tace "To sai aka yi yaya? Ai kaya basa wajen Rakiya suna wajena, waye ya xo amsa?" Umma da ta daure fuska tace "Ni na xo amsa" Kaka ta kalleta daga sama har kasa tace "Haba, to sannu da xuwa Amina, bakin cikin ne ya motsa kenan yau, to bari kiji ko Umaru yyi kadan ya amshe ma Deedayah kayan da Sudess ya siyo mata balle ke, kuma in sha Allahu yau xata fara saka kayan sai in ga ta tsiya, ke kuma Maryam har kin mance hijaran da kika yi na kwana biyar a gidan nan bayan kin sa an sace Deedayah kin maido ta, kin manta yanda kika dawo duk a lalace shine xaki sake shiga wani kess din da sassafe koh, to wllh Rakiya kiris take jiran ki ko bata fada ba ni na sani, haka kawai duk kun bi kun sa ma makauniya ido, to wllh karyan ku, tunda ina sonta Rakiya na sonta Sudess na sonta, Junaidu na sonta shi Amadu ba wai mun gama sanin xuciyarsa bane, to kowa ma ya ki ya indai mu muna sonta" Umma ta fiddo wayarta tayi dialing number Sudais yana fara ringing ya daga, strictly tace "Kana ji na Aliyu??" Sudais yace "Ina ji Umma" tace "Wannan kayan da ka kawo gidan Barrister da sunan kayi ma makauniya tsaraba maxa maxa ka xo ka amshe su ka kawo min dakina, idan kuwa ba haka ba wllh wllh ka canxa wata uwar...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Kaka dake ta kallon Umma baki bude ta saki salati tana tafe hannu, ganin Umma ta yanke wayar bayan ta gama magana kaka tace "Toh yanxu dai kafin ince komai so nake a fara gaya min munafukin da ya kai maki xancen nan, idan kuma baxa ki gaya min ba sai in sa a kira min Umaru ya kira ki ya tambaye ki nasan shi xa ki gaya masa, don gaskiya idan aka ki fada min wanda ya kai gulman nan kunnen ki, toh gwara in tafi duk inda xan tafi kawai...." Kaka na fadin haka ta tafi daki, Mami kuma ta nufi kofar fita Umma ta bi ta a fusace tana cewa "Kema ba ina ce kina da d'an ba, me yasa baki dinga makala masa makauniyar ba sai 'ya yan mutane?? To wllh daga ke har shegiyar yarinyar ku fita harkan d'a na...." Mami ta tsaya so pissed off tace "Look plss woman, get back home, sit ur son down, warn him seriously to stay away from the little girl, or from this house as a whole, you can't just come here and be displaying how mad you are plss.... behave like a literate for once, this is a very simple issue to address to alone without u causing commotion, komawa gida xa kiyi ki kira d'an ki ki xaunar da shi ki ja masa kunne cikin nutsuwa, in har ya dauke ki uwa to bbu abinda xai sake kawo sa gidan nan balle ya xo gun Heedayah, amma kawai kin xo kina ma mutane hayagaga a gida, why not behave like the elderly lady you are?? Wnn fa ba abun tada jijiyoyin wuya bane, in har d'an ki na jin maganar ki to fa baxai kusanci abinda baki so ba, plsss I have very important things a gabana than listening to ur bull shit... So excuse me" Mami na fadin haka ta fice daga parlon, Umma da ta saki baki tana sauraronta ta bi ta da sauri tana cewa "Toh ai asirin da kika masa kilan baxai ta6a barin ya saurareni ba, don naga ba iya Barrister kadai mugun abun ki ya tsaya ba, waye bai san da asiri kika shigo gidan nan ba, kuma wa ya sani ko ke kika lika ma barrister makauniyar duk don ya aure ki??" Mami ko juyowa bata sake yi ba balle ta tanka ta, Mumy da ta bi bayan Umma ta dinga cewa "Toh ai fada ma 6ata baki ne Amina, tuni aka shaida min ta asirce barrister sai yanda tayi da shi, shine ta koma kan Sudais...." Mami ta bude motarta ta shiga tana answering call da ya shigo wayarta, Kaka ce ta fito dakinta rike da wayarta, ganin Farida rike da hannun Heedayah xa su fita parlon ta nufeta tana mika mata wayar hannunta tace "Maxa kira min Umaru, yana nan xa ki ga ansa Dakta... Yi maxa kirasa" Farida ta amsa ta nemo number Baffa sannan tayi dialing ta mika ma Kaka jin ya fara ring, Baffa na dagawa kaka ta nemi kujera ta xauna ta fashe da kuka tace "Umaru ashe dama matarka Amina gantalalliya ce bani da labari, me nayi mata xata xo har gida ta min wankin babban bargo don wnn yaro naka Sudess ya yo ma Deedayah tsaraba?? Ni fa na ce yyi mata tunda ba wai gata gareta ba kowa na mata kallon yar tsintuwa, shi kansa Amadun da ya rabota da titi har yau ko tsinke bai ta6a siya mata ba, shi dai ya kawota kawai ya jibge mana ita, sai Rakiya ke ta siya mata kaya duk da dai ita ma kayan anna take siya mata wasu guntaye kmr ta6a66iya, to laifi ne don ynxu Sudess ya mata tsaraba daga kasan waje?? To wllh ka taho gidan Amadu yanxun nan ka titsiye Amina sai ta gaya maka uban da ya kai mata rahotun an ma Deedayah tsaraba, idan ba haka ba ni gaskiya an ci mutunci na kawai an keta min rigar mutuncina" Baffa dake ta sauraronta yace "Ikon Allah, haka ya faru?" Kaka tace "Aa karya nayi maka" Baffa yace "A'a ba haka nake nufi ba kaka, kawai gani nayi...." Ta katse sa da sauri tace "Baka ga komai ba Umaru, ba ruwana da bayanin ka, so nake kawai ka kamo hanya ka xo ka ritsa Amina ta fadi shegen da ya kai mata gulman Sudais ya yo ma Deedayah tsaraba, idan ko ba haka ba to xan tattara ya nawa ya nawa in san inda dare ya min, baxan xauna a ci mun mutunci ba kayi shiru" Baffa ya girgixa kai yace "Toh sai na xo" Ko amsa bata basa ba ta katse wayar, ta mike ta nufi kofa da sauri, Tijara iri iri Umma ke ma Mami a tsakar gidan Mami taki ko da kallon inda take har Farida da Heedayah suka karaso gun motar, Umma na kallon Heedayah tace "In sha Allahu a makance xa ki dauwama ki kare, tunda har kika shigo gidan mutane kika tarwatsa farin cikin da aka gina da dadewa, lkci daya kin tarwatsa komai, ae ko xuwan ki familynmu sharri ne ba alkhairi ba..." A nan Mami ta kalleta tana murmushi tace "Kya ga dauwamammen makanta kuwa a gidanki...." Umma tayi wani shewa tace "Bakin ki ya sari danyen kashi, sai dai a gani a naki xuri'ar, mu kam kaf dangi daga farko har karshe bbu nakasasshe..." Muryar kaka suka ji tana cewa "Toh Amina idan kin gama ki shigo daga ciki ki xauna, tafiya bai ganki ba, Umaru na hanya" Mami na kallon kaka tace "Kaka sai mun dawo" Kaka tace "Toh a dawo lfya Rakiya, da yake ke ba xaman banxa kike ba ina xa ki samu lkcn gantalallu da ko sakandarin basu kare ba, ita fa Maryam iyakarta aji biyu na sakandari Amadu ya gaya min, ita kuma Amina dama ko makarantar Ina jin bata ta6a yi ba don ko 'yar turancin nn ban ta6a ji tayi ba shekarata biyu gidan Umaru, kawai dai Allah ya ba 'ya yana jahilai sai xuba jahilci suke a gida ba kakkautawa" Mami ta tada motarta ta nufi gate da mai gadi ya bude mata tuni ta fita. Baffa ne xaune parlor a gidan Abba bayan la'asar, sai Umma da kaka sannan Sudais, Mumy sai kai komo take a parlon kamar me yin wani abu, Baffa yyi gyaran murya yace "Da farko dai xan fara baki hakurin rashin xuwa da ban yi da wuri ba sbda marasa lfya da na tsaya dubawa asibiti, sannan ina kara baki hakuri da abinda ya faru daxu da safe...." Kaka ta ta6a baki ta rungume hannu tace "Haka dai" Baffa ya kalli Umma yace "Ke me ya kawo ki gidan nan daxu da safe?" Tace "Kayan da Sudais ya kawo gidan na xo amsa" Baffa yace "Wasu kayan?" Tace "Ai shi ya san wasu kayan ne Dr...." Kaka ta dakatar da ita tace "Kafin a je da nisa, Ina son sanin wanda ya gaya maki Sudess ya kawo kaya gidan nan, don banda ni sai shi sai wannan sumu sumun yaron Shureen bbu wanda ya sani, har ita Deedayahn bata sani ba balle uwar goyonta Rakiya, to ynda kika samu labari kawai nake son sani yanxu" Baffa na kallon Umma yace "A ina kika ji xancen" Umma ta d'an yi shiru na wasu seconds kafin tace "Shi din da bakinsa ya gaya min ba kowa ba" Kaka ta kalli Sudais da sauri tace "Wai??" Yyi kasa da kansa yyi shiru, har sai da Baffa ya sake cewa "Plss kar ka bata min lkci malam, I have important things" Sudais ya daga kai ya kalli Umma dake hararansa yace "Ehh nine" Kaka tayi tagumi tace "Toh abu ya lalace kenan ai, kai kuma ashe haka kake bakin ka baya haila?? me ya kai ka don ka yi abun arxiki kaje kana terere kana fada ma duniya?? Aa lallai Sudess ya xama abun tsoro" Baffa dai ya jinginar da kansa da kujera so pissed off da wnn batun mara amfani garesa, Umma tace "Don haka ynxu idan bai maido kayan can gida ba ya nemi wata uwar amma ba ni ba" Kaka na kallon Baffa tace "Ni kuma idan har Sudais ya maida mata kayan ta sa hannu ta amsa baka sallameta ta tafi gidansu ba ka nemi wata uwar ba ni ba Umaru" Baffa ya kalli Umma da ta bude baki tana kallon kaka, Kaka ta mike tace "Duk shawaran da aka yanke ni dai ina daki, kaya na fita daga dakina dama Amina ta fita daga gidanka, to ni ba gantalalliya bace" Tana fadin haka ta nufi dakinta tana cewa "Kuma duk wanda yace Deedayah xai sa ma ido sai dai ya mutu muruss, ni ma ba gashi gantalallen bai min tsaraba ba amma na hakura ban ma yarinyar bakin ciki ba, to meye wasu xa su yi mata bakin cikin tunda har na kai xuciyata nesa ni ban mata ba, da ni azzaluma ce da ba cewa xan yi xan kai kayan kasuwar 'yan koli in siyar ba, amma ae bance haka ba" Baffa ya mike yace "To shawara ta rage kuma gare ku, but let me tell u this Amina, duk ranan da kika sake janyo na baro gun aiki unnecessary ranan won't be funny for me and you" daga haka yyi ficewarsa daga parlon, Umma ta dinga kallon Sudais da idanuwanta da suka kankance, shi dai bai iya ya kalleta ba, can ya mike a hankali ya nufi dakin kaka, yana shigowa tace "Meye kuma ka biyoni? Ae tunda ka fita har waje ka dawo baka kawo min ko tsinke ba to xaka iya bada min shinkafar 6era a abinci, wai Deedayah, to uwar me ka hada da Deedayar bani da labari?" Ya mata wani kallo yace "Toh ki fito min da kayan" kaka tace "Sae dai in fito maka da Umaru, kaya kam bbu wanda ya isa ya sa in fito da shi, Allah ya tarwatsa duk me yi ma marainiyar nan bakin ciki" Ya fi minti uku yana ta kallonta tana harkan gabanta, can ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da harara tace "Da baki kmr gidan tsutsa, sae shegen surutu kmr mace" Tsaye ya ga Umma a parlor tare da Mumy ko wannensu rai bbu dadi, Umma tace "Kasan Allah Aliyu, wllh ka sake shigowa gidan nan ni dai ban yafe maka ba, bbu kai bbu gidan tunda Mahaukaci ka xama, ita makauniyar kanwata ce ko ta ubanka da kayi mata siyayya hka, to wllh ka sake kallon ko da inda take kai da Allah.... Kaya kuma basu ci bulus ba duk ma wanda yyi amfani da shi Allah ya isa wllh" tana kai wa nan tayi ma Mumy sallama a fusace ta fita, Mumy na kallonsa tace "Ni ka ban mamaki wllh Sudais, kana da dangantaka da yar tsintuwar ne?" Yace "Ina da shi mana, 'yar uwata ce ita musulma" Mumy ta hade rai tace "Ohh wato ni kake da bakin mayar ma magana koh?" Yace "Toh Mumy fisabilillah meye don nayi ma marainiyar tsaraba, kowa fa ina masa idan na tafi...." A fusace tace "Kana masu uban me?? Shi biscuits din da chocolates ne tsaraban? Ka tashi ka cika akwatuna har uku kamar me kai lefe sai kace mara mafadi, to gidan ma gaba daya an hana ka shigowa sae in ga ta tsiya... Yarinyar kawai matsiyaciya mara gata duk ta tarwatsa gida" Ya girgixa kai yace "Ae kam tana da gata...." Yana fadin haka ya nufi kofar fita daga parlon, muryar kaka yaji tana cewa "Ni dai ban yafe rashin tsaraban da baka min ba" ko kallonta bai yi ba har ya fice daga parlon.... Heedayah ce xaune garden din gidan da malamin da ke mata karatu, a final year Engineering student, baxae wuce ashirin da shidda ba, tana xaune saman one of the two comfortable chairs da Abba ya siyo gidan don koya mata karatu, shi ma malamin na xaune saman guda daya da textbook din Basic science a hannunsa, bayanin topic din da ya mata ranan take masa, ko tsallaka word daya bata yi ba a abinda ya koya mata, a nutse take masa bayanin, directly yake kallon cikin idanuwanta without even blinking, duk wannan abun Shuraim na xaune balcony a sama doing nothing yana kallonsu lkci lkci, shi kansa malamin bai san yana wajen ba, can dai Shuraim ya mike ya tsallaka gwangwanin Coke da ya ajiye wajen ko budewa bai yi ba ya fita balcony din, cikin few minutes ya shigo garden din, tun daga nisa idonsa ke kansu, Heedayah ta turo baki tace "Toh ban yi dai dai bane, why don't you want to compliment me?" Ta fadi haka ne sbda shirun da ta ji Malamin yyi bayan ta ce masa ta gama, Malamin na hango Shuraim yace "Yess, that's excellent of you, I know u can do it...." Tayi murmushinta me kyau tace "Da gaske?" Shuraim na isa wajen yana kallon Malamin yace "Karfe nawa kake gama lesson din?" Malamin na kallon agogo yace "Saura minti ashirin..." Shuraim yace "All same, akwai hadari garin you can leave now, sae da safe....." yana fadin haka ya kalli Heedayah ya wani hade rai yace "Tashi" a hankali ta mike tsaye staring into space, fuska daure ya fixgo hannunta ya bar wajen tana biye da shi kamar xata fadi, malamin ya bi su da kallo, Suna shiga parlor ya kai ta har kofar dakin kaka yyi abandoning dinta sannan yyi wucewarsa sama. Heedayah ta samu dai ta bude kofar ta shiga, Kaka xaro ido tace "Har kun yi me??? Anya wannan yaron ba 419 yake ma Amadu ba kuwa, ba fa a titi ake tsintar kudin ba, me ya koya maki haka da wuri har ku ka tashi?" Heedayah ta turo baki tace "Ko ba wnn bane ya dawo da ni wai akwai hadari ko gama karatun ba mu yi ba" Kaka ta mike tace "Wa?" Ta yatsina fuska tace "Ni manta sunansa nake, wannan din nan dai" Kaka tace "Atoh ce min xa ki yi wancan sumu sumun, me yasa ku ka biye masa, gantalalle ne fa, lkcn yana karami baki ga kukan da yake tsalawa ba idan xa a kai sa makaranta, kwata kwata bai son karatun, ya fi so yyi ta xaman gida yana kassara min Amadu da kashe kudin yagwat, to shine xai maki bakin ciki yanxu sbda d'an turancin da kike ji?? Bakin xuciya fa garesa ci gaban ki ne baya so...." Lkci daya kaka tayi tsit ganin Shuraim tsaye bakin kofa don a bude Heedayah ta bar kofar, kaka tace "Toh kuma ai hadarin idan ya kare maki sai ya sa maki wani cuta, ni kaina fa idan ana hadari bana yarda in fita ko nan da kofa balle ke me lalura, ae da kyau da ya koro ki...." Heedayah ta wani turo baki tace "Kaka karya fa yake yi bbu wani hadari wllh, ai banji kamshin ruwa ba, kuma bbu ko wani iska kawai dae shi mugu ne...." Kaka tace "Kul.... bar ce ma baba yana karya bbu kyau, kuma ba mugunta bace lafiyar ki yake ji shi sa yace ki shigo kar iskan yamman ya kare maki, abinda likita ne shi ma ya san illan haka....." Heedayah ta laluba gefen gado ta xauna tace "To Ina ruwansa da ni? Ko English language fa ba mu yi ba ya dawo da ni, kuma sae sauri yake sbda in fadi inji ciwo" Kaka ta saci kallon Shuraim dake tsaye yana kallon Heedayah, tace "Ke kuma ya xa ki ce haka, ubansa fa ne ya tsinto ki a titi kina galantoyi, kinga kuwa ai da ruwansa da ke, ni dai ki bar rashin kunya, haka kawai kina fama da makanta kina fitsara, ni ban taba ganin inda aka yi haka ba" Heedayah ta daura kafanta saman gadon tace "Shi ma ba yana maki fitsaran ba kullum.... Kaka gaya min ma yanda yake" Kaka tace "Shureen din?" Ta gyada kai, Kaka tace "Tohh, yana nan dai wani dogo kamar fal waya, wani lagwai lagwai, shi dai baxa a ce masa fari ba kuma baxa ace masa baki ba, Sudess ya fi sa haske, snn a tsaye yake bai dai kai samudawa ba, kinsan da shi da d'an uwan nasa Sudess basu da aiki da sai xuwa gidan karafe suna dagawa, to ynxu duk sunyi hankali, yana nan kuma da kwala kwalan idanuwa kamar dai naki, amma naki ya fi nasa kyau, Inda Allah ya cecesa hancinsa har baka wllh, sannan bakinsa d'an tsut, shi ke hanasa magana kila" Heedayah ta juya ido tace "Toh meyasa sai yyi ta cin xalin mutane, haka ranan ya doki kawata Farida" Kaka tace "Toh wnn kuma sai dai mu ji daga garesa, kinsan yana tsaye bakin kofa... Kai Shureen me yasa kake cin xalin al'umma" Heedayah ta xaro ido tana komawa baya saman gadon kamar xata yi kuka a hankali tace "Kaka yaushe ya xo?" Kaka tace "Tun tambayar ki na farko amma kinga ai baxai yiwu in katse maki hanxari ba tambaya ance mabudin ilimi...." Shuraim sai kallon Heedayah kawai yake ya rungume hannunsa, can ya gyada kai ya juya ya fita dakin, kaka ta rufe kofarta tace "To ni dai ba ruwana Allah ya so ban fadi wani mugun abu a kansa ba, ke kuma kar ki iya bakinki da surutu, wllh karya ki xai yi ba ruwana, ko kanninsa baya wasa da su duk tsoronsa suke, ke kuma gashi har ce masa mugu kika yi kika ce karya yake, ni dai ba ruwana" Heedayah da har hawaye ya kawo idonta tayi shiru tana sauraron kaka. Bayan Magrib Heedayah na dakin kaka har lkcn bata koma bangaren Mami ba, a hankali Kaka ke daukan naman kwanon gabanta tana ci kar Heedayah ta sani balle ta bata, kaka tace "Toh ko uwar ce ta hanata shigowa yau gaba daya bani da labari, da ta shigo fa da ynxu kinga ta gyara min daki ta goge tace xata wanke bayi, yarinyar ba dai tsafta ba gata yar gayu kuma kyakkyawa fara, har da lotsa kumatu gareta, naga kamar ma har waya gareta, 'ya yan Amadu kuma ga su nan dai wasu kolaye kazamai, Kinga da Shureen wani ne ae sai ya nemeta nasan ko don Amadu Rakiya baxata ce A'a ba, to ba a auren aka aureta, shi ma Shureen din ae d'an gayu ne, fess xaka gansa kullum cikin kamshi, ko kadan bai son datti, kinsan ni ya gada amma ba uwarsa ba, Kuma fa wllh auren yake so, ya rasa yanda xai fito ya fada ne amma wnn shiru shirun da yake duk aure ya saka a rai, kinsan indai shirun namiji yyi yawa kawai auren nan yake so wllh" Heedayah dake gefe xaune da plate din shinkafa da miya a gabanta ta ta6e baki tace "Kaka ni fa na san nama kike ci wllh...." Kaka ta fiddo naman da ta kai bakinta da sauri tace "Inji ubanwa, meye kuma nama da xan ci in hanaki kamar wata mayya?" Heedayah tace "Ni dai nama kike ci wllh" Kaka tace "To tashi ki yi ma kanki jagora ki fitar min a daki kada raina ya baci, aniyar ki kuma ya bi bayanki wllh, ni ya kamata in baki nama ko shi Amadun da ya tsinto ki, Kuma wllh ke mace ce ki raba kanki da sa ido gidan wani xaki, meye kuma kinsan nama nake ci, a ina kika ga naman kina fama da makanta" Heedayah ta mike tana turo baki tana ma kanta jagora da hannunta ta nufi kofa xata fita, kaka ta bi ta da harara tace "Aa kifi nake ci ba nama ba tunda Amadu kika ga ya kawo min nama...." Dai dai nan aka bude kofar Heedayah ta ja baya da sauri, Kaka ta saki salati ta mike tace "Junaidu?? Allahu Akbar saukan yaushe??" yana murmushi yace "Daxu kaka...." Yana magana yana kallon Heedayah da ta bude ido sosai, ya daga kanta yana murmushi cikin cool voice dinsa yace "Hey...." shigewa jikinsa tayi ta rungume sa tace "Yaya" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Junaid ya dago kanta yana murmushi yace "How are you dear?" tace "I'm fine...." Kaka na washe hakora tace "Ae da ka gaya min kana hanya da nayi maka girki Junaidu, ga dai yara in aika su siyo min kayan miya da yar kaza" yana rike da hannun Heedayah ya karasa cikin parlon ya xauna yace "Aa bana son ki wahal da kanki ne, Ina yini kaka?" Kaka tace "Toh lfya lau Junaidu, to ya hanya?" Yace "Alhmdllh" tace "In ji dai baxa ka sake komawa ba" yyi murmushi yace "Saura kadan in gama kaka" kaka tace "Toh, shima dai Sudess hka na ji yace saura kadan, Shureen dai ne ban san isilin karatun nasa ba, anya ma yana karatun kuwa? Gani nake kamar budirinsa kawai yake a Zaria" Junaid dai bai ce komai ba sai murmushi da yake yi, ta mike ta tafi dauko masa ruwa tana cewa "Toh ko 'yar mantinan nan dai bbu a gidan ynxu, tunda ka tafi fa rabona da wani mantina, hana rantsuwa dai Amadu da Umaru na siya min" Junaid na kallon Heedayah murya can kasa yace "Lolly..." Heedayah ta wara manyan idanuwanta tace "Sunana Heedayah" yace "No Lolly dai" dariya tayi tace "Lolly pop?" Yace "No just lolly" ta langwabar da kanta bata ce komai ba, yace "Where is Farida?" Tace "Tana gun Mami" kaka ta ajiye lemo da ruwan hannunta tace "To ae gaba daya uwar ta hanata shigowa yau, ko ba Farida ba??? Kila don d'an aikin da take min ne ma aka hanata shigowa wa ya sani, kasan bata dade da xuwa hutu daga makaranta ba, shine fa muka sa6a sosai da ita, yarinya me hankali ga shegen aiki a cikinta, ta iya aiki yarinyar wllh" Bowl din naman da take ta ci a boye ta dauko ta dire masa tace "Daxu na sa masu aikin nan suka soya min kayana, nama ce ka ci iya cin ka ba komai ka ji" Heedayah ta turo baki tace "Amma kince min ba nama bane" Kaka ta galla mata wani harara tace "To meye hadina da ke? Ke dai ki raba kanki da kwadayi da sa ido mace kike wllh" Junaid na murmushi ya dau ruwan gora daya ya bude ya fara sha... A boye ya dinga ba Heedayah naman, da kaka ta shiga ciki kafin ta fito xai yanka ya sa mata a baki, da ta aji alamar kaka ta fito sai ta boye fuskarta shoulder dinsa, Daga karshe kaka tace "Ni dai ban ba Deedayah namana ba gaskiya, idan ma ci take ban bata ba gaskiya" Dariya Junaid yyi yana kallon kaka, ita kanta Heedayah dariyar take fuskarta a kafadarsa, kaka tace "Aa ba batun dariya bane Junaidu, ba fa Amadu ya siyo min ba balle ace tana da rabo a ciki, kudin da nake ta tarawa na bada a siyo min daxu, to meye xata wani makale maka tana kwadayi kai kuma kana biye mata? Shegen kwadayi fa gareta wllh" Heedayah ta mike tana turo baki tana ma kanta jagora ta nufi hanyar kofa xata fita, Kaka tace "Yanxu xuwa xata yi ta hada ni da farar matar can..." Heedayah ta bude kofar ta fita daga parlon.... Sai bayan isha Junaid ya shiga bangaren Mami, bayan sun gaisa Mami tace "Me ya hada kaka da Heedayah?" Ya kalli Heedayah dake kwance saman kujera yyi murmushi yace "Ai xa su shirya" Heedayah ta mike xaune tace "Ai baxan sake xuwa ba" Mami tayi murmushi bata ce komai ba, Farida dake xaune kusa da Junaid ta matso kusa da shi a hankali tace "Yaya tell me the truth, sbda birthday din Aunty Shaheedah ka dawo ko???" Ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Eh" Irin kallon da yake mata ya sa ta matsa kusa da shi da sauri tana dariya.... sai wajen karfe tara da wani abu Junaid ya mike xai bar bangaren Mami, don Kaka ta aika Sajida ta kirasa sau biyu kenan, Xai fita parlon Farida tace "Yaya to tsaraban mu fa?" Yace "Tomorrow in sha Allah" yana kallon Mami yace "Sai da safe, daga can xan wuce" tace "Me yasa idan ka xo gidan nan baka son cin abinci?" Ya girgixa kai yana kallon Heedayah dake kwance saman kujera tayi bacci yace "Na ci abinci kafin in taho ne" Mami tace "Toh shkkn, sai da safe" Ya dauke idonsa daga kan Heedayah yace "Allah ya tashe mu lfya, daga haka ya fita parlon, dakin kaka ya tadda Shuraim tsaye daga bakin kofa Kaka na cewa "Ai shi kansa Umarun ya girgixa da bala'i na jiya Shureen, ynxu kuma dama kiransa xanyi ince idan bai mata magana ta janye gantalallen bakinta da ta daura ma bawan Allahn ba nima xan yi Allah ya isa idan shi Umarun ya sake shigowa gidan nan gaisheni, kowa sai yyi ta takama da d'an sa ba shknn ba, amma kan me xata hanasa xuwa gidan nan bayan ga ni kakarsa" Tana ganin Junaid tace "Haba Junaidu har sai furan da nono ya huce, Amadu fa nasa sai ya siyo min, ni ban ga ji abun kunya ba ka xo har dakin nan ka fita baka ci komai ba" Ta gefen ido Shuraim ke kallon Junaid, Junaid ya karasa dakin ya mika masa hannu, Shuraim ya mika masa nasa sannan Junaid ya xauna yace "Kaka na ci abinci fa kafin na xo" kaka tace "Aa kai dai so kawai kke ka tafi kana xagina a ranka ka xo dakina ban baka komai ba" Dariya yyi ya ma rasa abinda xai ce mata, Shuraim xai juya kaka tace "Toh kaji abinda dai ake ciki Shureen, kaya kuma rabi xan ba Deedayah, sauran rabin gaskiya kasuwar 'yan koli xan kai ayi gwanjonsu, to fa bai siya min komai ba ni kamar wanda aka yi ma baki, ko jiya sai da na sake mafarkin nan wai Sudess bai min tsaraba ba hankalina ya tashi sosai" Shuraim yace "Ae dukka ya kamata ki kai ki siyar" Kaka tayi shiru tana kallonsa, can tace "Allah?" Yace "Wllh" kaka tace "Atoh, me xata yi da su ma idan an bar mata su ita ba ido ba, iyaka in d'an debar mata biskit din da swee in ajiye mata" Shuraim yace "Hakan yayi" Kaka tace "Atoh, ga dai Rakiya kullum sutura take mata, bbu abinda ta ragi yarinyar da" Shuraim ya juya xai fita dakin sai ga Farida ta shigo rike da cooler, gefe ya ja ya tsaya, ta wuce ta ajiye ma kaka coolern tace "Kaka gashi Mami tace in kawo maki" Kaka tayi kasa da murya tana kallonta tace "Ita ta hanaki shigowa duk yau koh?" Murmushi Farida tayi tace "Aa fa kaka" kaka ta ta6e baki tace "To da ta hanaki ai ita Deedayar da take tamu ta shigo kuma ta wuni" Farida tace "Wllh Kaka ni ba a hanani shigowa ba kawai karatu nake yi a ciki" Kaka tace "Ayyoo, to ban ji kin gaida Shureen ba, ko baki gansa bane" Farida ta d'an turo baki tace "Ehh ban gansa ba" Kaka tace "Gashi can rakube gefe, gaishe sa" Ta d'an kalli inda yake kafin tace komai ya juya yyi ficewarsa daga dakin, Kaka tace "Au, to yyi ma kansa, Wai haushi yaji nan fa, kema dai in kin gansa ki dinga gaishesa" Mikewa Farida tayi tace "Kaka sai da safe" kaka tace "Toh sai da safe" Farida ta kara yi ma yayanta sai da safe sannan ta fita, kaka na kallon Junaid tace "Kai ka ji fa Junaidu, tsaraba na fitan hankali Sudess yyi ma Deedayah a kasar waje ni kuma ko abun sakace ban gani ba, shine nake tunanin in siyar" Junaid dake saurarenta yace "Aa kaka, ki bar mata su, kar ki siyar" Kaka tace "To ai ba duka xan siyar ba, sai kace wata axxaluma macuciya, 'yan kadan xan deba in siyar in bar mata sauran" Furan da ta dama masa ta ajiye gabansa tace "Kaga dai ko Shureen ban yrda na dibar ma wa ba, kuma yana tsaye na dama wllh" Washegari da asuba Abba na dawowa daga masallaci ya ga kaka bakin kofar parlonsa tana jiransa, yace "Lafiya kaka?" Kaka tace "Ehh to lafiyan kenan, magana nake son yi da kai me muhimmanci, idan na jira sai ka shigo gaisheni bayan ka shirya fita ofiss ba saurarata xaka yi ba sai kace sauri kake" Bai ce komai ba ya bude mata kofar parlonsa ta shiga, ya bi bayanta, ta xauna saman kujera, tace "Kana ji na Amadu?" Xaunawa yyi yana kallonta yace "Ina ji Baaba" tayi kasa da murya tace "Yauwa dama kan maganan Shureen na shigo" yace "Lafiya dai koh?" Tace "Aa lafiya lau, na kawo shawara ne kuma kasan ni bana bada shawaran banxa" Ya gyada kai yana sauraronta, tace "Ni dai kaga yarinyar nan Farida ba karamin burge ni take ba wllh, gata da biyayya iya biyayya, sannan bata da neman fada, uwa uba ga aiki, yini fa take yi dakina tana min share share da goge goge, bata fiye min Deedayah ba sau dubu mai makalewa saman gado? To shine naga gaskiya d'an ka Shureen xai dace da ita duk da mugun halinsa, Kuma da kyar idan ba aure yake so ba, ko kai baka lura ba, a rabu da mutum me shiru shiru kawai, na ciki na ciki, toh kuma shirun ma ai baxai bari ya nemi matar auren ba, shine nake son ayi masa auren, na duba iya dubawa na, na gama hange hangena naga ba kowa xai dace da shi ba gaskiya sai Farida" Tun da ta fara magana Abba ke kallonta with surprise, Kaka tace "Aa ni dai ka daina min wnn kallon kamar warce tace a kashe Shureen, gata fa nayi masa, sannan Rakiya yau watana hudu da ita ko kallon banxa bata ta6a min ba, kwata kwata matar bata da damuwa kaf halinta d'an ta Junaidu ya kwashe, wayayyiyar mata ce sosai, to don me baxan yi kwadayin hada iri da ita ba..." Abba yace "Toh yanxu kaka ni da ba wai ina da iko da Farida bane, ya kike son..." Kaka ta dakatar da shi tace "Aa wllh kai mijin uwarta ce ai, kuma ai a gidan ka take yanxu" yace "Yaushe ta dawo gidan nawa? Ba hutun makarantar kwana da suka yi bane ya sa ta xo? Gidan yayan babanta take fa Baaba" Kaka tace "Toh ni ba ruwana sai in saka gyale a rakani gidan yayan uban nata, Kai sai kayi ta yin abu kamar ba namiji ba meye kuma don ka nema ma d'an ka auren Farida? Ni fa gata nake son yi ma Shureen din don baya magana kuma ni na san aure yake so, kaga kira min Rakiyan yanxun nan ta xo ayita ta kare, Kar ka wani bata min rai" Abba yyi kasa da murya yace "Karatu fa yarinyar take kaka, duka duka ss2 nake jin take yanxu" Kaka tace "To ko Jami'a take ni ina ruwana, karatu na hana aure ne dama bani da labari, ku dai kun cika wahala wllh, cewa nayi ka kira min Rakiyan ta fito, in dai aka ga Shureen bai auri Farida ba to kilan kashe ni ku ka yi kawai" Abba ya kasa cewa komai, kaka tace "To ko in kira Rakiyan da kai na ne Amadu?" Daukar wayarsa yyi, yyi dialing number Mami, tana dagawa yace "Meet me at my parlor now Rahinah" Bai jira ta ce komai ba ya katse wayar.... Da sallama Mami ta shigo parlon, ganin kaka ta xauna kasa tace "Ina kwana kaka?" Kaka ta washe hakora tace "Lafiya lau Rakiya, ya kwanan su Deedayah da Farida?" Mami tace "Alhmdllh" Abba dai bai ce komai ba, Mami na kallonsa tace "Ga ni barrister" Ya kalli kaka yace "Ga ta kaka" Kaka tace "Kai Amadun nan dai wani solobiyo ne wllh, to kai baxa ka yi mata bayanin ba sai ni? To ai duk kai ka cuci Shureen don kaf halinka ya dauka amma banda mugun halin shi wnn na uwarsa ne, Rakiya kina ji na, ba wani abu bane dama ni dai Farida ce ta kwanta min can cikin raina, a gaskiya Ina son yarinyar wllh, shine na xo na samu Amadu Ina neman alfarman a ba ma jikana Shureen aurenta...." Tana kai wa nan ta fara matsar kwalla, Mami da ta bude baki tana kallonta with shock ta kalli Abba tace "I don't get her barrister, as in??" Abba ya sauke ajiyar xuciya bai ce komai ba dai, Mami tayi murmushin karfin hali tace "To kaka ai karatu Farida take yi yanxu, Kuma....." Kaka ta dakatar da ita tace "Kuma me? Ku dai gantalallu ne marasu mafada, karatu ance maku yana hana aure ne, kinga idan na biye ta taku kawai mahakuciya xaku mayar da ni, ni naga dacewan hakan shi yasa nace ayi, ynxu ni ba ni da wata magana da ku kuma...." Tana fadin haka ta mike ta fita parlon, Abba sai kallon Mami da gaba daya mood dinta ya canxa lkci daya yake, can tace "Plss Barrister kayi ma kaka magana, try to let her understand cewar ba mai yiwuwa bane ni bani da iko da Farida wajen yayan Mahaifin ta take, let not make things complicated pls Barrister" shi dai bai ce mata komai ba, kaka na fita dama wayarta ta dauka ta lallaba ta kai ma Farida can bangaren Mami wai ta kira mata Junaid, junaid na daga kiran kaka ta fita da sauri, tayi kasa da murya suka gaisa tace "Kana ji na Junaidu, duk Inda kake ka taho yanxun nan xaka kai ni anguwa ko Rakiya kar ka sanar ma, kana isowa bakin get ka kirani sai in fito" Junaid dake kwance yace "Toh bari in taho kaka" tace "Yauwa Allah maka albarka, Ina jiran ka yanxun nan" daga haka ta katse wayar ta wuce dakinta tana cewa "Gantalallu wa enda basa son abun arxiki, ni bana biye ta taku ba" Kaka na komawa bangarenta sai ga Abba ya shigo da sallama, ya xauna saman kujera gaba daya he look confused, can yace "Kaka yanxu kinga cikin watan nan xa a fitar da Heedayah waje gyaran idonta, so yanxu kinga ai babu wani abu a gabanmu da ya wuce wnn..." Kaka tayi saurin cewa "Haba?? Kuma sun ce idon xai gyaru kuwa? Amma dai da ni xa a je koh? Kasan bata da kowa sai Allah sai ni" Abba yace "In sha Allah...." Kaka tace "Toh yaushe ne tafiyan in fara hada kayana?" Yace "Nan dai da sati uku" Kaka tace "Atoh Allah ya kai mu lafiya, Allah ya dubemu idonta ya bude ni dai" Abba yyi kasa da murya yace "Don haka kaka ki bar ko wani xance yanxu mu ji da gyaran idon da xa a fita yi" kaka ta kallesa tace "Atoh shkkn na bar xancen har sai idon Deedayata ya bude" Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, ya mike yace "Bari in je kaka, a taya mu da addu'a, ana kan processing din fitan ne" kaka tace "To wani kasar xa aje?" Yace "India" kaka ta washe baki tace "Xa mu ga su Hamita da muganbo kenan Amadu??" murmushi kawai Abba yyi ya fita daga dakin kaka ta mike ta daga hannu sama tace "Allah ka dubi yar marainiyar Allah ka bude mata idanuwanta, ka bude mata ido ya Allah ko son jikinta xai ragu" Karfe takwas dot Junaid ya kira kaka yace yana kofar gida, ta dau Hijabinta ta boye ta fito parlor tana kalle kalle xata fita, Shuraim dake xaune dinning yana shan tea ya bi ta da ido har ta fice daga parlon da sauri, Junaid ya sakko ya bude mata back seat yana gaisheta da ladabi, ta amsa tana washe baki tace "Allah yayi maka albarka Junaidu da bani da kai ai da nayi kuka yau, ni dai wllh ka fiye min kowa ma" murmushi kawai yyi ya tada motar, sai da suka bar layin suka hau saman titi yace "Ina xa mu kaka?" Tayi kasa da murya tace "Yau xumunci kawai nake son yi, kaga ai bai dace ace har yanxu ban san kowa naku ba, to don haka gidan yayan Mahaifin ka xaka kai ni mu san juna" Junaid was so surprise ya dinga kallonta ta madubi yace "Gidan Baffanmu?" Kaka tace "Ehh shi, ai xa a samesa yanxu da safe koh?" Yace "Ehh na bar sa a gida" Kaka tace "To maxa kai ni kar yyi ficewarsa, gwara xumuntakar tamu yyi karfi" murmushi kawai Junaid yyi ya dau hanyar gidan yayan late Abbansa. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Parking Junaid yyi a compound din Baffan sa, ya sauka ya bude ma kaka bayan motar, ta fito tana kare ma kantamemen gidan kallo baki bude tace "Nan ne gidan kawun naka?" Junaid yace "Nan ne" kaka tace "Ikon Allah, to mu shiga, Allah ya sa bai fita ba dai...." Junaid ya shiga gaba tana biye da shi yace "Yana nan ai, ga motarsa" Kaka ta kalli motar da ya nuna mata tace "Kamar irin motar Umaru kuwa" Babu kowa parlon da suka shiga, Kaka ta xauna tace "Wato basu tashi ba kenan ana ta bacci" Junaid yyi murmushi yace "Bari in masu magana" daga haka ya wuce sama, kaka ta dinga bin parlon da kallo ta rike ha6a murya can kasa tace "Toh ai masu kudi ne su ma, ba gidan tsiya Shureen dina xai fada ba, ko gidan Umaru bai kai haka ba" Ba a dau lkci ba Junaid ya dawo tare da wata dattijuwa, Ta xauna tana kallon kaka da fara'a tace "Sannu da xuwa Mama, Ina kwana" Kaka ta kalleta tace "Lfya lau wllh, kece matar gidan?" Matar na murmushi tace "Ni ce Mama" Kaka tace "Atoh ya yara, ya gida" Matar tace "Alhmdllh wllh, fatan kun xo lfya?" kaka tace "Toh Alhmdllh, ba ma wanda yasan na fito sai shi Junaidun, nace dai yau bari in xo inyi xumunci ku san ni in san ku, bana biye ta Rakiya da Amadu ba, ko karyawa ban yi ba wllh na fito" Matar tace "Ikon Allah to bari a kawo maki kayan kari yanxu, tashi mu je daga ciki Mama, sannu da xuwa" Kaka tana washe baki mike tace "Toh" har parlonta ta kai kaka, ba a dau lkci ba aka cika gaban kaka da kayan karin kumallo, flask din ruwan Lipton me kamshi, soyayyen dankali da kwai da plantain, katon bread, sai wainar shinkafa da lafiyayyen taushe, ga farfesun kayan ciki a gefe, Kaka na kallon masu aikin dake ta jera mata abincin tace "Babu darduma in sauka kasa??" karamin carpet me laushi suka shimfida mata ta sauko kasa bayan ta cire Hijabin ta, komai sai da kaka ta diba ta ci a abincin, sai da taji tayi nak murya can kasa tace "Toh ko nan nace xan dawo da xama ai bbu me ce min komai tunda an xama daya yanxu..." Sallama aka yi kofar parlon Kaka ta amsa wani dattijjo da baxai wuce 65 ba ya shigo parlon, kasa ya xauna yace "Sannu da xuwa Baaba" Kaka na washe baki tace "Sannu, kai ne kawun Junaidun?" Yace "Ehh nine, Ina kwana" Kaka ta gyara xama tace "Lafiya lau, yau dai nace bari in xo in ganka ka gan ni, idan na biye ta uwar Junaidu baxa ayi xumuncin ba ma, kasan yaran ynxu basu san amfanin xumunci ba" Yyi dariya yace "Gaskiya ne Baaba, to ya ku ka baro mutan gidan?" Tace "Lafiya lau, ko sanin na fito ma basu yi ba, nace inyi maxa in xo kar ka fita, tunda shi Amadu na ga karfe takwas xuwa tara yake ficewa" Yace "Wannan gaskiya ne" Kaka tace "Toh bayan xumunci kuma a gaskiya har da alfarma na xo nema a gun ka" Ya xauna da kyau yace "Toh ina sauraron ki Baaba" Tace "Ba wani abu bane d'an nan, jikana Aliyu na xo nema ma auren 'yar ka, wato Farida, kaga dai Aliyu ni na haifi ubansa Amadu, tunda nake ban ta6a ganin yaro da ya tashi bashi da matsala irin Aliyu ba, bbu ruwansa da kowa, ba shi da abokin fada, kai in takaice maka shi ba me magana bane ma, to shine na ya6a da hankalin farida tunda ta xo kuma ta xauna dakina, komai ita ke min wllh, ko nayi laifi da nayi wnn tunanin bawan Allah, amma dai ya ma sunan ka tukun" Yace "Sunana Aminu" Kaka tace "Toh ai sunan babana kenan, Allah sarki, to yanxu ya kaga..." Yace "Batu ne mai kyau wannan Baaba, amma sai dai Farida ynxu karatu take wllh" Kaka tace "Oh oh Allah, karatu na hana aure ne wai dama? Ku me yasa ku ka bari boko yyi maku kaca kaca haka, Shi kansa Amadun fa haka yace min, meye a ciki idan anyi auren ta ci gaba da karatun ta, ynxu shekararta nawa ma dai tukun?" Yace "Bata cika sha shidda ba ma" Kaka tace "Shine tayi girma haka? Toh kaga kuwa ai aurar da ita shine rufin asirin mu da ku, kaga dai takanas na taso da kafafuwana na sameka a gida sbda alkhairin da nake nema da ku, a gaskiya idan kace min A'a raina xai baci Aminu, da girmana na taho wajenka.... Kuma da Rakiya ta san gidan banxa ne gidan Amadu ai baxa ta shigo ba...." Yana murmushi yace "Gaskiya ne Baaba, in sha Allahu tunda ba fin karfina alfarmar da kika xo nema yyi ba xanyi bakin kokarin ganin komai ya tafi yanda kike so, amma sai Farida ta gama secondary in sha Allah" Kaka tace "Toh tunda dai ka amsa ai shkkn, kwana nawa ne xa a ga ta gama sakandarin, shi ma massers dinsa yake yi a Zaria, kaga sai su gama lkci daya kenan, bari anjima shi xan ma kira ya mayar da ni gida sai ka gansa, yana nan ko yatsa ka sa masa a hannu baxai ciza ba, yaron kirki me girmama na gaba da shi, Kai ni ko rashin kunya na jika da kakan nan ma ni bai ta6a min ba, tamkar uwarsa haka yake min biyayya" Shi dai murmushi kawai yake yace "Toh shkkn Baaba xan fita wajen aiki sai na dawo, ai kina nan?" Tace "Aa ina nan kilan har ka dawo, yanxu fa na xo" yace "Toh maa sha Allah, sai anjima" tace "Allah maka albarka" ya amsa da Ameen ya fita. Yana fita wayar kaka ya fara kara ta fiddo a jaka da sauri, da yake ta san Inda ake dannawa ta danna ta kai kunne, Muryar Mami taji, kaka tace "Ke ba fa wani waje naje ba, gidan ta salla na tafi, anjima in sha Allahu xan dawo" Mami tace "Toh shkkn, amma ba sallama kaka" Kaka tace "Ehh to da yake tafiyar ta gaggawa ce, anjima dai xan dawo in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya dawo da ke lafiya" kaka tace "Ameen" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta jawo sauran farfesunta tana lasa. Har aka yi Magrib Kaka na gidan Baffansu Junaid, Matarsa kuwa Hajiya Zulaiha bata bar Kaka ita kadai ba, tare suka yini, a xamansu na yan awannin nan abinda kaka ta manta ne kawai bata gaya mata ba, tarihi iri iri, Wanda ya kamata da Wanda bai kamata ba, tun mijinta na da rai har sanda ya rasu, amma ko da wasa kaka bata gaya mata halin Mumy ba, Hajiya Zulaiha dake yanka ma kaka kankana bayan anyi sllhn Magrib tace "Na kirasa yana hanya ynxu Mama" Kaka tace "Toh kinsan shi xai mayarda ni gida kar in gigita 'ya yana suyi xaton 6ata nayi shi sa na damu" Hajiya Zulaiha tayi dariya tace "Kila yana can gun budurwar sa tun da kika ga har war haka bai shigo ba" Kaka tace "Au, yana da budurwa kenan?" Hajiya Zulaiha na dariya tace "Kwarai kuwa" Kaka tace "ikon Allah, ko da yake ga Shureen ma Ina kokarin ganin yayi aure nan da 'yan watanni balle Junaidu, da kyar idan bai girmi Shureen ba ma" Hajiya Zulaiha tace "Lallai kam" Kaka tace "Ko da yake ga Farida ma naji shekarunta ba wasu shekaru bane amma duk ta balaga, kusan sa'ar Khadijahn Amadu ce fa, Ita kuma Rabi'ah sa'ar Deedayah Ina jin, don duk kwailaye ne" Hajiya Zulaiha dai tayi dariya ta ajiye ma kaka kankanan tace "Bari in je inyi sllh Mama, amma da kawai kiyi kwanan ki a nan Mama" Kaka tace "A'a ba mutunci gare su Amadu ba sai su iya min fada ba ruwana, bari dai in tafi ba dai na ga gida ba" Hajiya Zulaiha tace "Toh shkkn Mama" daga haka ta fita parlon.... Tana fita da minti sha biyar Junaid ya shigo, kaka tace "Ashe kana da budurwa Junaidu, yanxu matar kawunka ke ce min tadi ka tafi" yace "Aa gidan abokina nake" tace "Au, to in tashi mu tafi kada su Amadu su yi ta nemana koh?" Yace "To mu je kaka, ai kin ci abinci" Kaka tace "Idan ma nace ban ci ba, ba sai Allah ya kama ni ba, Tuwo ce fa malmala uku aka saka min ga miyar kubewa duk nama da Ganda ga kifi, ga kuma lemo me sanyi... To ina xan samu haka gidan Amadu?? Gaskiya matar nan ta san mutunci, baka ga ba wllh sai ji take da ni, komai ta rarumo ta kawo min, daxu da rana har kwadon zogala ta min bayan shinkafa da miya da uban nama da ta xubo min, ni dai gaskiya an karrama ni a gidan nan, ai Rakiya sai dai ince Allah yyi mata albarka kawai, danginta sun san mutunci kam" Murmushi kawai Junaid yyi yace "Idan kin gama shiryawa Ina parlor kaka" Kaka tace "Toh, d'an Albarka" Sai bayan kusan minti ashirin kaka ta sakko da handbag dinta, tana kallon yan matan gidan guda uku dake xaune parlor tace "Toh ko Sudess ma idan ya samu daya daga cikin wa ennan bai gode ba, ynda yan mata ke wahala ynxu...." Har parlon Baffan Junaid kaka ta shiga, yace "Aa Baaba ai na xata kwana xa kiyi a nan" tace "Aa su Amadu xa su min fada" Yace "Ikon Allah, toh Junaid xai maida ki amma" tace "Eh yana jirana ma yanxu haka" mikewa yyi yace "Toh Ina xuwa Baaba" yashiga dakinsa sai gashi ya fito ya mika mata dubu goma da ladabi yace "A siya goro Baaba" Kaka ta amsa ta saka a jaka tace "A'aaahh ayi haka d'an nan, ai da ka bar shi wllh, toh Allah yayi maka albarka, nagode ka ji" yace "Godiya ya tabbata ga Allah" rakata yyi har xuwa parking space tare da Hajiya Zulaiha da ta bata atamfa da turarurruka, tayi ta daga masu hannu tana washe baki har motar ya fita gidan, bayan sun hau titi tace "Gidan ma babu wahalan ganewa kaga idan xan dawo baxan sha wahala ba koh" Yace "Haka ne kaka" Tare Junaid da Kaka suka shiga parlor, Rabi'ah dake kwance parlon tana kallon Tv tace "Sannu da dawowa kaka" kaka tace "Yauwa.... Junaidu tafi ka dauko min Deedayah ga sauran nama na kulle mata a leda" yace "Toh" daga haka ya nufi part din Maminsa, Rabi'ah tace "toh mu fa?" Kaka da ta nufi dakinta tace "Uwar me na hada dake banda dai ke jikata ce, idan Maryam ce ko Amadu kya gaishesu a kwance?" Daga haka ta shige dakinta. Mami na kallon Junaid bayan ya gaisheta tace "Daga ina ku ke?" Yace "Gidan Baffanmu" Mami tace "Baffan ku? Kai da kakan?" Yyi yar dariya yace "Da sassafe ta kirani wai in xo in kaita" Mami ta dinga kallonsa da mugun mamaki tace "Sai ka kai ta?" Yace "To meye a ciki Mami?" Mami ta mike tace "Why didn't you call and ask for my opinion Junaid???" yyi kasa da kai yace "Mami naga ba wani abu bane, ai kowa ya san tsoho..." Xata yi magana aka bude kofar, shiru tayi kaka ta shigo tace "Ina Deedayan?" Mami tace "Sannu da xuwa kaka" Kaka tace "Yauwa Ina Deedayah ga nama na kullo mata" Mami tace "Suna parlon Barrister" Kaka tace "Kai Junaidu tafi ka dauko min ita, Ina iya shiga parlon yanxu Amadu ya rufeni da bala'i" Mikewa yyi ya fita parlon, Kaka tace "Wllh anguwa naje ke dai Rakiya, mutum yyi ta xaman gida kamar bashi da jama'ah" daga haka ta fita ta bi bayan Junaid da sauri, tun kan ya shiga parlon Abba ta tsayar da shi tayi kasa da murya tace "Kar ka gaya masu daga Inda muke, cewa kawai xakayi a bakin titi ka ganni ka dauko ni, har ita Rakiyan kar ka gaya mata kaji" Yana murmurshin karfin hali yace "Toh" daga haka ya shiga parlon ta koma nata dakin.... Washegari Sunday da safe Shuraim ya shiga gaida Abbansa, Abba na aiki system dinsa ya amsa yace "Anjima xaka ajiye Farida makaranta" Ya kalli Abba amma bai ce komai ba, Abba yace "Before then, xan maka transfer ku je tare tayi shopping, da yamma sai ka ajiye ta schl din" yyi kasa da kai yace "Toh" Abba yace "That's it, Kai yaushe xaka wuce Zarian?" Yace "Gobe da safe" Abba yace "Allah ya kai mu" mikewa yyi, ya ma Abbansa sallama ya fita, direct dakin kaka ya nufa, Kaka na ta gyara kayan da ta binciko a press din dakin, Heedayah kuma na kwance saman gado tana cin naman da kaka ta kawo mata, kaka kuma na bata labarin irin abubuwan da ta ci a inda taje jiya, Heedayah tace "Toh baki gaya min sunan wajen ba...." Kaka tace "Toh wai ina ruwanki, ke dai kawai ki bari, akwai abinci a gidan" Heedayah ta tallabi chin dinta tace "Toh shine ni baki je da ni ba?" Kaka tace "Ai kinsan a boye na bar gidan shi yasa, amma ba gashi na kullo maki sauran nama ba" Shuraim ya bude kofar ya shigo dakin, kaka tayi tsit da bakinta tana ci gaba da linkin ta, Murya can kasa Heedayah tace "Kaka waye?" Kaka tace "Iska ce ta turo kofa" Heedayah ta turo baki tace "Na xata wnn Shureen din nan ne...." Kaka tace "Shureen kuma, me xai shigo ya min, baki ga tun wayewar gari bai ko shigo gaidani ba" Heedayah tace "To kaka wai me yasa yake yi ma mutane mugunta? Ni fa bana son sa" Kaka tace "Haka nan Allah ya halicce sa, Kuma ya xa ayi ki so sa, ke da baki hada komai da shi ba...." Heedayah dai tayi shiru sbda kamshin turare da ta fara ji, kaka tace "Tun yana karami duk da baya magana haka yake narkan 'ya yan mutane, yyi ta cin xali, uwarsa kuma tayi ta goyon bayansa" Heedayah dai bata ce komai ba, Kaka tace "Ya kika yi shiru kuma" Heedayah ta turo baki a hankali tace "Bayan yana dakin xaki ce min baya nan" Kaka ta kyalkyale da dariya, Shuraim da ya wani hade rai yana kallon Heedayah yayi kwafa ya juya ya fice, Heedayah dai bata ce komai ba ta wani cinno baki, kaka tace "Atoh, yarinya sai fitsara da gulma wai don ma bbu ido..." Da rana Farida ba don ranta ya so ba ta shirya xa su je shopping kamar yanda ita ma Abba ya gaya mata, Heedayah ma ta sa Hijab dinta don tare Mami tace su je, can kofar gida yyi parking don ma kar Mumy tayi noticing xa su fita, Farida Ta bude ma Heedayah back seat tana rike da hannunta ta shiga, ita kuma ta shiga gaba, ko kallonsu bai yi ba ya tada motar suka bar layin. Wani shopping mall xai shiga Farida tace "A na gaban nake yi shopping, nan ba dukka abinda nake so suke da shi ba" Ya wani daure fuska bai dai ce komai ba ya shiga yyi parking ya kashe motar, Farida ta dauke kai ta ta6e baki ta bude motar ta sauka, ta bude side din Heedayah ta kama hannunta ta sauka, ta gefen ido yake kallon Heedayah da Hijab dinta ya wuce gwiwa da kadan, sae pink wandon dake jikinta amma bai kai ankle dinta ba, Farida xata rike hannunta su wuce ciki ya fixge hannun yace "Wa xata bi a hakan???" Farida ta kalli Heedayah daga sama har kasa, ya bude bayan motar yace "Maida ta ciki" Farida tace "But there is nothing wrong with her dressing, I dressed same also" Da kansa ya mayar da Heedayah da ta fashe da kuka cikin motar ya rufe, Farida ta rungume hannunta ta hade rai ta jingina da motar tace "Ni na ma fasa shopping din" Wani kallo yyi mata yace "Gaura maki Mari xan yi idan baki shiga mun wuce ba" Ta fashe da kuka tace "Toh why will u lock her all alone cikin motar, don't you know there is heat, ni baxan bar ta ita kadai ba" Atm card dinsa ya ciro ya mika mata still frowning his face yace "Double five, double zero.... Tafi kiyi shopping dinki ke kadai" Ta leka motar tace "Toh xaka tsaya da ita ne" Kin bata amsa yyi, ta amshi ATM card din ya bude maxaunin driver ya shiga ya xauna, A hankali Farida ta nufi cikin mart din. Heedayah dai ta daina kukan da take sai share idonta take, ta gaban madubin motar yake kallonta, bayan kusan minti goma jin shirun yyi yawa ta matsa a hankali kusa da driver seat ta sa hannu xata lalabu ko akwai mutum a nan, Kirjinsa ta ta6a ta janye hannunta da sauri ta koma ta xauna tana turo baki... Bayan wani 15 mins din sai ga Farida ta fito da labourer dake dauke da ledojin kayanta, Bude booth yyi kafin su karaso, mutum ya saka kayan gaba daya a ciki ta bude jakarta ta ciro kudi ta basa sannan ta bude back seat ta shiga ta rufe tana kallon Heedayah tace "Didi na siyo maki chocolates and Biscuits har da teddy..." Heedayah ta wara ido ta kamo hannunta tace "Thanks Farida" Ya d'an ta6e baki ya tada motar yayi reverse ya bar shopping mall din. Karfe biyar saura Farida ta gama shirin komawa makaranta, Heedayah har da hawayenta daga Inda ta xauna ta takure kanta, Mami da ta ji tausayinta sosai tace "Ku tafi tare Farida, sai ya dawo da ita" Farida da duk jikinta yyi sanyi ta kama hannun Heedayah suka fita parlon xuwa dakin Kaka su yi mata sallama, Shuraim na xaune main parlor da makullin motarsa cox Mumy bata gidan, Ya bi su da kallo yace "If she is not changing that clothe she shouldn't bother entering my car..." Farida ta juya tana kallonsa don tun da take bata ta6a jin yyi magana me tsayi hka ba, ta dauke kai ta ta6e baki, Heedayah ta rike hannun Farida sosai kamar xata yi kuka tace "Pls kice Mami ta bani dogon Hijab in sa" Farida ta d'an ja tsaki suka koma bangaren Mami, Mami na kallon Heedayah daga sama har kasa tace "Does he have any business with her dressing, ko ya siya mata Hijabs ne? Or is he stupid??" Farida dai bata ce komai ba ta dauko ma Heedayah wani Hijab din har kasa ta saka sannan tayi ma Mami sallama suka fita, Kaka har da kwallarta, ta daure ma Farida cin cin da bai fi kwaya shidda ba a leda ta mika mata tana cewa "Ashe baki nan xa a kai Deedayah India" Farida tace "Kilan muna jarabawa lkcn" Kaka tace "Toh ai shkkn, Amadu yace min nan da sati uku ne, ga kayana har na hada" Farida tace "Toh Allah ya kai mu" Kaka ta dauko maltina daya ta kara mata, ta rakasu har bakin motar Shuraim, tana kallon Shuraim tace "Toh ko in dauko gyale mu tafi tare Shureen?" Ya gyara xama yace "Ehh" Da sauri ta juya ta koma ciki, ya tada motarsa ya fice daga gidan, Heedayah ta rufe fuskarta a Hijab tana dariya a hankali, Farida kuwa sai hararansa take.... Suna Isa makarantar Shuraim yyi parking, tsadaddun motoci ne iri iri an kawo students, Farida ta kamo hannun Heedayah tace "Till I come back Didi..." hawaye ya kawo fararen idanuwan Heedayah, ta madubi Shuraim ke kallonsa, Jikin Farida yyi sanyi tace "Baxan dade ba xa mu yi hutu...." Heedayah ta fashe da kuka sosai ta daura kanta saman jikin Farida, Shuraim ya hade rai yace "Malama sauka ki bude booth ki sauke kayan ki" Ta galla masa wani harara tana share idonta ta sauka motar, sauka yyi shi ma don sauke mata kayan don ya san sun mata nauyi, Heedayah na jin haka ita ma ta bude motar ta sauka, Tsaye yake jikin black ride dinsa ya rungume hannu idonsa sanye da bakin space, he looks so gentle and calm, dai dai saukowar Heedayah, a hankali ya cire Glasses din idonsa yana kallonta, Shuraim kawai gani yyi ta ci karo da daya daga jakan Farida da ya sauke kasa Farida kuma tana gun booth tana fiddo kananun ledojin, kafin ya karasa ya riketa tuni ta fadi kasa, shi kansa Mutumin har ya taho da sauri kafin ta kai kasa ganin Shuraim sai kuma ya tsaya cak, Shuraim ya dagota yace "Wa yace ki sakko?" Ta fashe da kuka tana yarfe hannunta tace "Wayyo na buge kafana, and there is sand in my eyes" Tuni Farida ta durkusa kusa da su tana ma Heedayah sannu, da ma sauran mutanen wajen, Bude idon Shuraim yyi, yyi blowing mata iska gently, ganin yanda ake kallonsa kawai ya dagata ya bude back seat ya sa ta ciki, ya karasa sauke ma Farida kaya yace "That's all" daga haka ya bude back seat din ya shiga yana kallon Heedayah dake ta murxa idonta matsawa yyi kusa da ita ya dafa forehead dinta yana kallon cikin idon, ta kauda kanta kamar xata yi kuka tace "Ya daina" Saketa yyi still looking at her eyes.... Tuni Mutumin ya shiga mota ya mance abinda ya kawosa bakin makarantar ya tada motarsa yana kallon motar Shuraim ta madubi, Shuraim ya daga hijab dinta ya kalli kafarta ya ga just little bruises ne a farin kneel dinta, Bude motar yayi ya sauka ya koma driver seat, ya tada motar yana fara tafiya Mutumin ya bi bayansa...... *pls fans masu son min magana su dinga typing instead of voice note, cox listening to voice note is stressful wllh, idan typing ne cikin few seconds mutum xai karanta yyi replying nn take, but voice note yana cin time when they are other messages to reply to, thanks for understanding* Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Shuraim bai yi wani nisa ba ya kula da motar bayansa dake bin sa, slowly ya dinga tafiya to see idan motar xai yi overtaking dinsa ya wuce, but sai ya ga motar ya ki yin hakan sae ma rage nasa tafiyar da yyi shi ma, Shuraim ya samu waje yyi parking har sannan yana kallon motar ta madubi, Mutumin dake cikin motar dake ta lura da Shuraim shi ma kuma ya san Shuraim ya gano yana bin sa ne kawai yyi wucewarsa bai tsaya ba, Shuraim ya bi motar da kallo har da plate number din motar, juyawa yyi ya kalli Heedayah dake xaune bayan motar, she looks so sad kiris ya rage ta fashe da kuka daga ynda tayi da fuskarta, dauke kansa yyi ga mamakinsa har sannan motar bai bace masa ba, sbda a hankali me motar ke tafiya kan less busy road din, Shuraim ya kalli layin dake gefensa kawai ya karya kan motar ya shiga layin.... Sai kusan Magrib Shuraim ya isa gida, a hankali yake tafiya ganin motar Mumy dake tsaye bakin gate tana jiran me gadi ya bude gate din, sae da ta shiga snn yyi parking gefen flowers dake gaban gate din ya kashe motarsa, Mai gadi na ganin baxai shiga gidan da motarsa ba ya kulle gate din, Shuraim ya juya yana kallon Heedayah dake bacci bayan motar, sauka yyi motar ya kulle ya nufi cikin gidan, tsaye ya ga Mumy alamar shigowarsa take jira, ya karasa Inda take ya gaisheta tace "Daga ina kke da magariban nan" Yace "Asibiti" tace "Ohk, goben xaka tafi Zarian?" Yace "In sha Allah" tace "Toh nima xan je Zarian gobe, amma bance ka gaya ma kowa ba, karfe nawa xaka fita?" Yace "Takwas..." Tace "Toh kayi hakuri ka bari karfe tara, kafin nan Abbanku ya fita" Shi dai kallonta kawai yake don ya san basu da 'yan uwa a Zaria, can yace "Me xaki je ki yi a Zaria Mumy?" Mumy tace "Yar Hajiya Sadiya ba can take aure ba, to ta haihu gobe suna, ko barka ban je ba, kuma idan na gaya ma Barrister ba lallai ya yrda ba, ni ko Sadiya ai ta wuce haka a wajena" Shuraim yace "Aa da dai ki fara sanar ma Abba Mumy" Mumy ta daure fuska tace "Toh ban yi niyya ba" Bai kuma cewa komai ba ta juya ta nufi cikin gidan ya bi ta da kallo har ta shiga parlon snn ya juya ya koma waje, Bude back seat yyi Heedayah ta bude ido da sauri, hannunta ya kama ya saukar da ita daga cikin motar ya kulle motarsa, har da xai mika ma Mai gadi hannunta ya kai ta ciki sai kuma kalli cikin compound din ya shiga yana rike da hannunta, yana isa balcony ya bude kofar parlon yana kallon ciki, bbu kowa hakan yasa ya shiga parlon da ita ya kai ta har kofar dakin kaka sannan ya juya ya fita xuwa masallaci, Kaka da ta fito daga bandaki tayi alwala tace "Waye wnn?" Heedayah tace "Ni ce" Kaka tace "Toh ai na ganki, sai yanxu ku ka dawo kai faridan makaranta?" Heedayah ta gyada mata kai, Kaka tace "To ina Shureen din?" Heedayah tace "Nima ban sani ba, ya wuce" Kaka ta ta6e baki tace "Toh me yasa kika yo min nan, Rakiyar bata nan ne" Heedayah ta turo baki tace "Toh ai shine ya kawo ni" Kaka tace "Toh ni dai na gyara dakina na share, na sa turaren wuta, gadon ma yau ko hawa ban yi ba tun da garin Allah ya waye" Heedayah ta turo baki ta juya tana laluba hanya da hannunta ta fice daga dakin, Kaka tace "Haka kawai ba kya ma mutum taimakon komai sai dai ki lalata waje gantalalliya" Mumy da fitowar ta kitchen kenan ta bi Heedayah da ido har sai da ta isa kofar parlon Mami, Dai dai fitowar Sajida dakinsu ganin Heedayah ta karasa don ta bude mata kofar, juyawa Mumy tayi ta wuce parlonta kafin Sajidan ma ta ganta... Sai da Heedayah ta shiga ciki sannan Sajida ta kulle kofar ta wuce. Karfe tara da rabi Mumy ta kira wayar Shuraim, yana xaune dinning da cup din shayi a gabansa, Ya daga kiran Mumy tace "Abbanka fa ya fita, baka gama shiryawa bane ko in tafi in hau motar haya kawai?" Yace "Na gama" katse wayarta tayi, ya mike ya tafi dakin kaka, Heedayah ce kwance saman gadon tana ma Doll din da Junaid ya siya mata kitso, Kaka kuma na bandaki tana wankewa, Heedayah ta dakatar da kitson da take ba Doll din jin an bude kofa tace "Waye?" Ya kalleta ya dauke kai, bata kuma cewa komai ba sbda kamshin da ta ji, Ya xauna yana jiran fitowar kaka, sai ga ta ta fito tana cewa "Masu aikin jaraba kawai sun bari bandakina xai dafe in shiga uku in lalace, Banda dai ma lalacewa ta sameni ina ni ina bar masu bandakina su dinga wanke min...." Shuraim dake ta kallonta yace "Xan wuce Zaria" Kaka tace "Tohhh da sassafe haka shureen" Yace "Eh" Tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, ni dai ko kwandala bani da shi a dakin nan, dama Umaru ne me bani, gashi yau kwana daya bai xo ba" Mikewa yyi ya mayar da wayarsa aljihu, tace "Toh ko dari biyar baxa ka d'an bani ba Shureen, bani da ko sisi fa" Yace "Ni da bana maki komai kuma yau xa ki ce in baki kudi?" Kaka tace "Toh ai dama idan ba kai ba waye me min, shi Sudess yan matan da ya tara gabansa ma sun ishesa, Amadu kuma kaga ynxu ta kudin da xai kai makauniyar nan gyaran ido yake, da kyar idan ba sai an kashe kusan miliyan biyar ba tunda India ne, ai kaga ta kassara min d'a na kawai, wa gareni dama banda shi, shi din kuma ga uban abinda ke gabansa ba dangin iya balle na baba, Umaru dama yau sati rabona da kudinsa, sae dai ya xo ya karaci xamansa ya fice, toh ya ake son inyi da raina" Shuraim ya tabe baki yace "Toh nima bani da shi" Daga haka ya fita daga daki, kaka ta bude baki ta bi sa da kallo, can kuma tace "Toh kada Allah ya sa ka samu, marowacin banxa kawai solobiyo" Ko saurarenta bai yi ba, yana fita sai ga Mumy ta shigo dakin, Ta xauna ta gaida kaka, kaka ta amsa xata koma bandaki, Mumy tace "Kaka xanje gidanmu ne Salima bbu lafiya" Kaka ta dawo tace "Toh ba dole ba, yarinya sai gantalin duniya take an rasa me gaya mata gaskiya, kamar abun arxiki Amadu ya daukota kusan shekara sha biyu da suka wuce amma uwarki ta amshe ta wai autarta, to yau ina uwar taki take, ba gashi ta tafi ta barta ba, yarinya duk ta lalace wa yasani ma ko bin maxa take, da ynxu tana wajen Amadu har ya aurar da ita ta haifi 'ya yanta...." Mumy dai bata ce ma Kaka komai ba, Kaka tace "Amma wnn ai tafi karfin kowa ynxu, ta xama abar tsoro, na samu labarin ma ba kullum take kwana gida ba wai koh??" Mikewa Mumy tayi tace "Toh sai na dawo" daga haka ta nufi kofa ta fita, kaka tace "Toh Allah ma dai ya sa ba ciki ne da ita ba, tunda cewa kika yi bata da lfya, toh a dawo lfya Maryam" Mumy dai tayi wucewarta bata tanka ta ba Karfe Goma da rabi suka isa Zaria, Shuraim na kallon Mumy dake ta danne dannen waya yace "Ina ne gidan?" Tace "A'a kawai ka samu waje ka ajiyeni xan nemi adaidaita sahu, kilan kana da lectures kar in shiga hakkin ka" yace "Sai goma lectures din" Mumy tace "Ba dai ni nace ka ajiyeni ba wai" Bai kuma cewa komai ba yyi parking, Mumy ta sauka motar tace "Toh Allah ya bada sa'a" yace "Ameen, amma wani anguwar xa ki?" Tace "Saboda ga ka ubana?" Yace "A'a I was thinking ko anjima xan xo in maida ke kaduna ne" Tace "A'a, xan samu motar haya" Daga haka ta tsayar da adaidaita ta shige, ya tada motarsa ya wuce... A cikin adaidaitan Mumy tayi dialing number Sadiya tace "Toh ga fa ni na shigo Zarian Sadiya" Hajiya Sadiya ta gaya mata sunan wani filling station wai ta jirata a nan, Suna isa gidan man Mumy ta sauka ta ba Mai adaidaitan kudinsa tana jiran Hajiya Sadiya, bayan kusan minti ashirin sai ga Hajiya Sadiya, Mumy tace "Kin fa ce min kin fito gida ashe baki fito ba" Hajiya Sadiya tace "Wllh hatsari me Muni aka yi kafin Jaji, shine ya haddasa go slow" Mumy tace "Toh Allah ya ji k'an musulmi, ynxu ina muka nufa?" Hajiya Sadiya tace "Tashan da xa mu je mu hau motar garin mana" Wani adaidaitan suka samu ya kai su tashan, Mumy sae cewa take ni dai Allah ya sa kafin karfe hudu xa mu koma Kaduna, gidanmu nayi ma Barrister karya nace xan je" Hajiya Sadiya tace "Gwara ke an san baki gida, to ni Alhaji bai ma san na fito ba" Mumy ta biya masu kudin motar suka shiga suna jiran ya cika a tashi..... Tagumi Mumy tayi tana kallon katon Mutumin dake gabansu, Hajiya Sadiya na xaune gefenta ita ma tana kallonsa, bayan kusan minti goma Mutumin yyi gyaran murya yace "Toh ga dai abubuwa da yawa na gani, masu kyau da mara su kyau, da farko dai da fatan a shirye kike Hajiya Maryam don nan ba da dadewa ba babban d'an ki xai yi aure...." Mumy ta kalli Hajiya Sadiya da sauri, sannan ta kara kallonsa tace "Aure kuma Malam?" Yace"Kwarai kuwa gashi na gani" Tace "Toh ni dai bai ta6a ce min komai ba...." Mutumin yace "Ita kuma wnn yarinya Makauniya naga abubuwa da yawa tattare da ita da nake kan ganewa har ynxu, sai dai a sarari na ga har Mai gidan ki na shirin fita da ita kasar waje gyaran ido, haka ne ko ba haka ba?" Mumy ta marairaice tace "Haka ne wllh" yace "Toh nan da kwanaki kadan xa su fita, kuma idanuwanta kam xa su bude in dai an fita... Sannan ita wannan kishiyar ta ki, naga a gaba xata xama ita ce kan komai a gidanki, don ynxu ma maganar da nake maki sonki ya ragu sosai a xuciyar mijin ki, kawai dai yana xaune ne da ke ko sbda rabon tsakanin ku, amma ynxu wnn kishiya ta ki ita ce gabansa, ita kadai yake gani, sannan ita salonta xa a iya kiransa da na makirci don bata wani nuna ta damu da shi, nan kuwa duk karya ne" Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace "Allah Malam???" Shiru yyi yana kallonta da tikeken hancinsa, Hajiya Sadiya ta dinga bugeta alamar me yasa tace haka, da sauri Mumy tace "Tuba nake malam ayi hakuri" Mutumin yace "Ku fita ku dawo nan da minti ashirin" Hajiya Sadiya ta mike da sauri tace "Toh Malam, ayi hakuri...." Mumy ma ta mike suka fita waje da sauri, saukowa suka yi daga kan rock din suka samu karamin rock suka xauna Mumy ta fashe da kuka sosai tace "Kin ji ko Sadiya, dama ba na gaya maki har yau ni da Barrister ba kamar da ba, tun da yayi auren nan dama ko nemana baya yi, Kin dai ga abinda wnn makauniyar tayi ma rayuwata koh? Ta dalilinta ne fa dukka wannan abubuwan ke faruwa, ita fa ta lalata min gida na, ita ta sa kishiya ta shigo gidana har xa a kwace gidan a hannuna, ni ynxu me xan ma yarinyar nn in ji dadi???" Hajiya Sadiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Ba tuntuni nake ta bin ki mu xo nan ba kinki, yo ai Allah ma cewa yyi tashi in taimake ka, ga dai shi kin jiye ma kunnenki komai, Amma bari mu koma ciki tukun mu ji sauran bayanin, shi kuma Shuraim duk rashin maganan nan nasa har wani neman aure yake yi dama baki sani ba" Mumy ta share idonta tace "Toh ae sai yyi auren mu ga, xae ma ajiye xancen auren nan ne, ce masa nayi ina son yyi aure yanxu" Hajiya Sadiya tace "Toh ai shi na gani, duka duka nawa yake da xai tsiri son yin aure" Mumy tayi tagumi bata ce komai ba don ba batun auren Shuraim ya fi damunta ba ita yanxu, suna nan xaune har minti ashirin din yyi sannan suka mike suka sake gurgurawa can sama, Hajiya Sadiya tayi kasa da murya tace "Toh ga mu mun dawo Malam, da fatan ka huce" Bai ce komai ba sai bayan kusan minti biyar yace "Tohh, yanxu me ku ke son ayi a kan lamarin, ita dai wnn makauniya naga xata warke nan ba da dadewa ba, sannan xata xame maki ciwon ido nan gaba ke Maryam...." Mumy ta marairaice tace "Toh Malam ya kaga ya kamata ayi, ni so nake gaba daya ta bace bat na har abada kuwa, in son samu ne ma ni kada idon ya bude malam ta dauwama a makance, Kai idan ma duniyar xata bari gaba daya ni dai oho in daina ganinta kawai, sannan shi kuma wnn yaro nawa ayi kokarin ganin an dakatar da batun auren nasa don ni ban shirya aurar da shi ba yanxu, ita kuma kishiyar ayi duk abinda xa ayi ta bar min gidana da mijina, in xama ni kadai ce a gidan, Kuma maigidana na da uwa fitinanniya, duk ta gallabe mu, so nake ita ma a rabata da d'an nata, ko biyayya ya daina yi mata, snn a rufe bakinta gumm ta xama kamar kurma ko bebiye, taji kuma bata son xaman gidan namu ta koma can gidan wansa har abada" Mutumin yace "Toh an gama...." Hajiya Sadiya ta gyara xama tace "Ni kuma Malam a kara rufe min bakin mijina a kan na da, duk da dai bbu wata matsala ynxu bai jin batun kowa sai nawa tun aikin da kayi min kwanaki, amma a kara min wani sabo ynxu dai" Mutumin yace "Toh a bani minti sha biyar a waje" Mikewa duk suka yi suka gungura kasa. Sai kusan magariba Mumy ta isa gida don ma ba ita bace da girki, a dar dar ta shiga parlon tana boye jakarta a Hijab, ganin bbu kowa kusan da gudu tayi bangarenta ta kulle kofar, ganin su Rabi'ah da Khadijah xaune suna kallo parlonta ta shige bedroom tana amsa sannu da xuwan da suke mata... Karfe goma saura na dare Mumy ta fito, Mami ce ta fito bangaren Abba, Mumy ta dauke kai kamar bata ganta ba ta shiga dakinsu Sajida, tana daga tsaye bakin kofa tace "Sajida me ya hanaki wanke min bandaki yau?" Sajida ta mike da sauri tace "Wllh Hajiya na wanke tun da safe" Mumy tace "Toh tafi ki ga bandakin da kika wanke ki dawo ki sameni yanxu" Sajida ta fita dakin xuwa bangaren Mumy, Mumy na kallon Karime tayi kasa da murya tace "Xuwa sha daya ko sha biyu ki taho bangarena ki sameni" Karime tace "Toh Hajiya" Daga haka Mumy ta juya ta wuce da sauri. Mumy na parlonta xaune tana ta jiran Karime sai ga ta kuwa karfe sha daya da rabi, Karime ta kulle kofar ta iso kusa da ita ta durkusa tace "Ga ni Hajiya" Mumy tace "Yanxu ita makauniyar gun Rahinar take ko gun Kaka?" Karime ta tabe baki ta gyara xama tace "Ehh toh, yau ta kwana dakin kaka, gobe ta kwana bangaren Rahinar, amma dai ta fi dai xama wajen kaka" Mumy tace "Ba naga tana yawan shan shayi da, ko ta daina?" Karime tace "Har yau tana sha, gwangwanin kayan shayin nata ma na dakin kaka, ta sha da safe wani lkcn har da rana sannan ta sha da daddare" Mumy tace "toh wani aiki xan baki Allah ya sa xa ki iya Karime" Karime tace "Haba me xai hana, ai bbu abinda baxan iya maki ba Hajiya, ke da kika rike ni tamkar 'yar ki, Ina xan samu haka banda wajen ki" Mumy tace "Toh, ba wani abu bane garin magani ne nake son ki juye a gwangwanin milon gaba daya sai ki gauraya, don idan an sa a madara xa a gane" Karime tace "Hajiya amma dakin kaka fa kayan shayin suke ba dakin uwa rikonta ba" Mumy tace "Toh sai me?? Ba tana sa ki share share ba?" Karime tace "Ta fi sa Sajida, komai Sajida take kira tayi mata" Mumy tayi shiru sai kuma tace "Wani aikin take sa Sajida?" Karime tace "Irin su Shara, goge gogen waje sai wankin bandaki" Mumy tace "Da yaushe take sa ta?" Karime tace "Da safe haka take kiranta ta saka ta" Mumy tace "Toh gobe kafin ma ta kirata xan aiki Sajidar, tana kiranta sai ki je kice bata nan, nan kuma xa ki tambayeta me xa ki yi mata" Karime tace "Toh shkkn, xan yi iya bakin kokari na Hajiya" Mumy ta mike ta tafi cikin dakinta sai ga ta ta fito da Kullin magani a kyallen atamfa tace "Gaba daya xaki juye kuma kiyi a hankali kar ki bari ya xuba" Karime ta amshe ta tura cikin rigan mamanta tace "Toh Hajiya in sha Allahu" daga haka ta fice daga parlon da sauri, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta kashe wutan parlon ta wuce cikin dakinta. Washegari da safe bayan Abba da Mami sun fita, kaka ta kwalo ma Sajida kira, Karime ta mike da sauri tana ta6a mamanta don ta tabbatar kullin na nan don Mumy tun safe ta sa Sajida ta bar gidan, Tana shiga dakin kaka da sallama tace "Gani kaka, Sajida an aiketa" Kaka ta dinga kallonta daga sama har kasa sannan tace "Ni dai na ga jaraba, wai ke baki wanka ne, kullum cikin naso kike kamar d'an wake, mata kazama kawai duk wari, me xa ki min to da kika taho toh?" Karime tayi kasa da kai tace "Na xata aiki Sajidar xata maki shine na xo in yi" Kaka tace "Ehh lallai, da kuwa lalacewa ta sameni, a hakan xaki kama min aiki inje wata cutar ta kama ni a banxa a hofi, wai ma daga wani kauyen kike??" Karime tayi kasa da kai tace "Doguwa" Kaka tace "Ko da na ji, to yi tafiyar ki, kar ki sake shigo min daki da sunan xa ki min aiki ni ba gantalalliya bace, bari Rakiyar ma ta dawo xan ji ko meye sauran amfanin ki a gidan nan tunda dai ga ni nan ina ma Deedayah komai, ke kuma ba sai a sallame ki ba" Karime ta juya da sauri ta fita tana waigo kaka a tsorace, Kaka tace "Ni naga jaraba, mata duk naso kullum fisabilillahi tayi ta shigo min daki" Heedayah dake kwance saman gado tace "Kaka to aiki fa xata taya ki..." Kaka ta kalli Heedayah da sauri tace "Ta je can ta taya uwarki Rakiya aiki, ni ba ruwana cewa ma xanyi a sallameta ko xan daina ganin fuskarta" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mumy ta mike da sauri ganin Karime ta dawo tace "Ya, har kin xuba?" Karime tace "Korata tayi wllh, har cewa tayi xata sa a sallameni" Mumy ta xaro ido tace "Me kika mata????" Karime tace "Ban mata komai ba wllh, haka nn kinsan dama bata sona" Mumy tace "Toh baki bata hkuri ba kika fita ke kuma?" Karime tace "Cewa tayi bata son ganina" Mumy ta xauna tayi tagumi tana tunanin to ynxu ya xa ayi ta samu ta juye maganin nan cikin kayan shayin Heedayah, ta kalli Karime tace "Ba ni kayana ki fita" Karime ta fiddo kullin cikin rigarta, kin amsa Mumy tayi tace "Ajiye min kan kujera" ta ajiye, Mumy tace "Je ki sae na neme ki" fita tayi parlon Mumy ta bi ta da wani kallo, leda ta dauko ta rufe maganin da shi tana yatsina fuska sannan ta dauka ta wuce daki. A ranan Mumy ta shiga dakin kaka yyi sau biyar kafin yamma, fitarta na karshe kaka tayi mitsi mitsi da ido tace "Da kyar idan matan nan tana da gaskiya, na lura tun safe take min xarya kmr me nakuda.... Ni dai bari Amadu ya dawo in ji dalili gaskiya, Allah na tuba duniyar nan yanxu ko wanda ku ka fito ciki daya kaga yana maka xarya bbu dalili toh kayi ta kanka kawai" Heedayah dai na dakin tana jin abinda kaka ke cewa, Kaka ta mike ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri tace "Gani kaka" Kaka tace "Kasko xa ki dauka kije duk inda xaki samo gawayi ki hura min garwashi ki kawo min yanxun nan" Sajida tace "Toh sai dai inje kasuwa yanxu a siya gawayin" Kaka tace "Toh ni dai bani da ko sisi, tafi ki kira min Maryam" Sajida tace "Toh" sannan ta wuce, ba a dau lkci ba sai ga Mumy tana murmushi tace "Gani kaka, aiki xa a maki" Da sauri kaka tace "A'a, aikin me kuma kamar kuturwa, dari biyar xa ki ba Sajida xata je min kasuwa ynxu" Mumy ta d'an juya lkci daya ta daure fuska, sai kuma tace "Anya xa a samu kuwa, da yake jiya da naje can gida na kai Salima asibiti to bbu kudi wajena ynxu" Kaka tace "Toh kira min Amadu, shi baxai rasa yanda xai yi da ni ba ai" Mumy dai bata ce komai ba, Kaka tace "Ki kira min shi da wayarsa" Barin dakin Mumy tayi murya can ciki tace "Toh" tana tsaye daga bakin kofarta ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri, Mumy ta jefa mata dari biyar din fuska a murtuke ta shige parlonta ta kulle kofa... Sajida na dawowa da gawayin ta rura ma kaka a Kasko, sannan ta kai mata dakinta, kaka na xaune tsakar dakin ta baje kayan wani tsohon jakarta, kullin magunguna ne iri iri kai kace boka ce, Sajida ta ajiye kaskon saman tiles tace "Gashi kaka" Kaka tace "Allah maki albarka...." Tace "Ameen" sannan ta fita, kaka ta xuba uban turaren icce a wutan, Tuni Heedayah ta mike ta fara tari tace "Kaka meye shi?" Kaka tace "Toh haka kawai aka ce maki xan xauna a kashe ni, jiya fa wani mummunan mafarki nayi..." Heedayah xata fita dakin kaka ta rufe kofar tace "Toh ko dai ke mayya ce ba mu da labari..." Heedayah ta fashe da kuka tace "Kaka yana shiga hancina" kaka tace "Ai dama ta nan din xai shiga, Ina xa mu tsaya a cuce mu, kowa fa ya lalace da mugun abu a xuciyarsa, tun ina gidan mijina nake tsare kai na, Rakiya ma idan ta dawo daga gantalin aikinta sai ta xo in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne fa..." Heedayah ta toshe hancinta, Kaka na ta surutunta tana kara cika iccen cikin wutan kaskon, sai da ta tabbatar ya ratsa ko ina na dakinta sannan ta fitar da shi parlor ta ajiye tace "Toh dama kada wanda ya dauke min kayana a nan" Mami ce ta bude kofar da sallama, tana shigowa ta fara yatsine fuska don hayaki ya cika ko ina, Ta karaso gun kaka tace "Meye wnn din kaka" Kaka tace "Ke ma idan xa ki samo leda in debar maki ki samo, duniyar ynxu ba gaskiya, Maryam ma idan ta ga tana so ta samo leda in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne" Mami ta gaida kaka xata wuce kaka tace "Yauwa Rakiya dama Ina jiran ki dawo ki gaya min me wnn me aikin taki take tsinana maki a gidan nan" Mami ta juyo tace "Aa ba komai kawai dai suna aikin gidan ne tare da dayar mai aikin" Kaka tace "Toh a gaskiya ki sallameta Sajida kawai ta ishe mu a gidan nan, baki ga ba kullum fa naso take, kazama ce fa da kyar idan ruwa na ta6a jikinta haka kawai wata cuta taje ta kama mu ta dalilinta bayan mu duk muna wanka muna tsafta" Mami tayi murmushi tace "Naga kamar aikin ya ma Sajidar yawa ne" Kaka tace "Sai a samo wata me tsaftar amma a gaskiya a sallami wnn, idan ko ba haka ni a sallameni" Mami na kallonta tace "Ta maki wani laifin ne kaka?" Kaka tace "Aa ko daya kawai na gaji da kazantar ta ne" Mami bata kuma cewa komai ba ta juya ta nufi bangarenta... Da daddare Abba na parlonsa sai ga kaka ta shigo da sallama, Mumy da ke yanka masa watermelon tace "Sannu kaka" Kaka ta xauna tace "Yauwa, Amadu ashe ka dawo" Yace "Ehh na dawo, Ina yini" tace "Dama xuwa nayi naji wa ke biyan kudin aikin matar da Rakiya ta dauka" Yace "Aa ita ke biya" Kaka tace "Au haba, to bari in bar mata mai aikinta kar ta kullaceni, wai da cewa xan yi a sallameta" Abba yace "Tayi wani abu ne?" Kaka tace "Oh oh kawai dai ni bata kwanta min bane ga kazanta malam, amma tunda ba kai ke biya ba ai shikenan, ae Rakiyar ma me kudin kanta ce, ba xaman banxa take ba kamar wasu, baka ga gidan wan tsohon mijinta ba da Junaidu ya kai ni shekaranjiya, Kai kace wani shugaban kasa ne" Mumy dai ko kallon kaka bata yi ba sai sauri take ta bar parlon, ko yankan kirki bata ma kankanan ba ta mike tace "Xan je in duba ruwan shayin da na sa a kitchen" daga haka ta fita, kaka ta kalli kankanan tace "Dubi wani yanka da tayi ma kankanan kamar bakatafiya..." Shi dai Abba bai ce komai ba, kaka tace "Toh ni dai na hada kayana tun ranan da ka min xancen tafiya gyaran idon Deedayah a india" Abba yace "Mutane biyu kacal xa su je tare da ita fa Baaba" Kaka tana kallonsa da kyau ta gyara xama tace "Ban gane mutane biyu ba, su wa da su wa kenan mutane biyun?" Yace "Aa ba ni nace ba, ka'idar wajen ne haka, Doctor ne ma ke gaya min" Kaka tace "Toh ba sai ni da kai mu kai ta din ba, ko akwai wani wanda ta hada wani abu da shi banda ni da kai din" Abba yyi shiru yana kallonta, kaka tace "Toh dama ai ni da kai ne dolenta, ita Rakiya yaushe ta xo gidan ko yaushe ta san Deedayar da xa ayi marmarin tafiya da ita?" Shi dai Abba bai ce komai ba.... Mumy na fita sai da ta fara wucewa bangarenta snn ta fito da sauri, ta dinga bin main parlon da kallo kamar munafuka sannan ta shige dakin kaka ta kulle, hannunta na rawa ta isa gun kayan shayin ta sauke gwangwanin madaran amma ta rasa da me xata bude na milon, kan Fridge ta hango cokali cikin cup, ta tashi da sauri ta dauko ta bude gwangwanin ta ciro ledan dake rigarta, hannunta na rawa ta bude kyallen ta juye bakin content din cikin gwangwanin ta gauraya da cokalin snn ta rufe gwangwanin ta mayar Inda yake ta tashi, ta goge cokalin da xaninta shi ma ta mayar cikin cup din, gaba daya a rikice take, ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, sai da ta shiga parlonta ta sauke wani ajiyar xuciya ta juyo tana kallon yaranta tace "Uban me ku ke jira ba ku tafi kun kwanta ba? Maxa a kashe min tv tunda bance ku lalata na dakinku ba" Sai da suka fita parlon snn ta wuce cikin dakinta tana wani murmushi.... Washegari da sassafe kaka na share sharen lungu da sako na dakinta ta dauke gwangwanin madara da Milo ta tabe baki tace "Mayyar ma bata sha shayin jiya da daddare ba, dama fa gulma ce, a gidan uwarta da ubanta ina xata samu haka, ita dai kawai ta samu d'ana sai kashe mata kudi yake a banxa a hofi, sbda ita abubuwa da yawa an daina min, tasa sai maneji muke yi, ga uban kudi xa aje a gyara kaddararrun idonta nan da kwanaki kadan, mu dai kawai Allah ya bamu lada, bafa dangin iya balle na baba" Tana ajiye gwangwanin milon taga murfin ya fadi, ta dau murfin tana kallo da mamaki, can ta ajiye tace "Ikon Allah, ni fa na hada mata shayin jiya da yamma, to wani barawo ne ya xo ya bude ya sata ya manta bai rufe ba, gashi har Milon yyi kasa, ni dai ba haka na bar sa ba wllh, sata aka fara yi gidan amadun bani da labari??" Ajiye tsintsiyar tayi ta fice daga dakin, direct parlon Abba ta nufa ta kwankwasa kofa, Mumy ce ta fito, kaka tace "Amadun fa?" Mumy tace "Yana ciki" Kaka tace "Ce masa gani a tsaye" Abba na fitowa kaka tace "Amadu wllh shigar min daki aka yi aka yashe milon Deedayah tass, ynxu ba sai ace ni ke shanyewa ba ko da ba a fito fili an gaya min ba ayi ta xagina a xuciya, toh gaskiya ni dai a san matakin da xa a dauka ynxun nan" Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace "Ikon Allah, toh bari in debo na wajena sai a kara mata a kai tunda yyi kasa, ba abun tada hankali bane kaka" Kaka tace "Oh oh ba wani debo naki da xa kiyi, ko ma waye ya diba sai ya maido wllh, xan fara ta kan masu aikin nan tass sai na bincike kayansu don nasan ba shan lkci daya xa ayi ma milon ba deba xa ayi a leda a boye, Kai har kayan Deedayar ma sai an bincika da nasu Rabi'ah" tana fadin haka ta nufi dakin masu aiki tana kwala ma Mami kira ita ma ta fito, kayan Sajida ta fara dubawa ta xaxxage gaba daya Ghana must go din bata ga komai ba, Kaka ta kalli Karime dake ta xufa tace "Ke ina jakarki" Karime ta nuna mata ghana must go din, ba komai ya sa hankalinta ya tashi ba sai kullin Madara da millo na Mumy da take diba a leda idan Mumy tace taje ta hada shayi, har na Mami ma tana diba, snn ga kullin soyayyen nama na jiya da ta boye a kayan, ga kuma Cornflakes a leda shima duk ta boye, kaka ta yatsina fuska tana xaro kayan kamar Kashi tana ajiyewa kasa, da ledan naman ta fara cin karo, ta kunce ledan ta saki salati ta yar a kasa tana kallon naman, Mumy ma xaro ido tayi tana kallon naman, Kaka ta ci gaba da xaro kayan sai ga ledan cornflakes, Kaka ta kara gwalo ido ta ajiye Cornflakes din, ta ci gaba da xaro kayan sai ga ledan milo sannan Madara, kaka tayi wani dariya irin na boss, Mami ma na tsaye bakin kofa ta kasa cewa komai, Kaka tace "In ji dai kun tabbatar cewar ba banxa nake ba ynxu, duk wanda Allah ya daukaka ya riga da ya daukaka sa, to a kira Amadu shi ma ya gane ma idonsa, nasan da naje na samesa nace gashi gashi a ransa cewa xai yi ohh Allah ya hadani da fitinanniyar uwa, to yau ga ranan fitinata, ni dai nasan shigar min aka yi aka debi milon nan dama" Karime ta durkusa tana matsar kwalla tace "Wllh wllh wllh kaka ba milon ki bane wnn, ki duba ki ga wnn har fa ya daskare...." Kaka ta kwala mata ledan milon da ya daskare a fuska tace "Ke dai bakya tsoron Allah, to kin saka sa cikin jaka duk wari ya baxai daskare ba?? Ai da kyau tunda ba tsutsa ya fitar ba, ni dai a kira min Amadu ya xabi ko ni ko kazamar nan, don in har xa a yafe mata ta ci gaba da xama a gidan nan gwara in tafi duk inda Allah yyi" Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "Yau kwana nawa da biyanki kudin watan aikin ki?" Karime ta fashe da kuka tace "Sati daya" Mami tace "Toh ki hada kayanki, ki taho ki sameni in baki kudin aikinki na sati daya da kudin mota kiyi tafiyar ki, Allah ya bamu alkhairi" daga haka Mami ta fita dakin, Karime ta kara rushewa da wani matsanancin kuka ta daura hannu a ka tana kallon Mumy tace "Don girman Allah Hajiya ki taimakeni wllh aiki wahalan samu yake yi ynxu, ki saka baki a maganan nan don Allah a barni in ci gaba da aikina" Mumy ta ki kallon ko da Inda take, can ta juya kamar munafuka ta fita, kaka tayi wani shewa tace "Aje can wani gidan kuma ayi tayi masu naso ana wari amma ba gidan d'a na ba" daga haka ita ma ta fice daga dakin, Dubu goma Mami ta ba Karime kudin mota dubu biyar, dubu biyar kuma na aikin sati daya da tayi, sai kuka Karime take tana cewa "Don Allah Hajiya kiyi hakuri kar a koreni, wllh sharrin shaidan ne" Mami tace "Da ni ce kika debar ma abu na kamaki, sai dai in maki nasiha kuma in gargadeki da cewar kar ki kuma, amma kinga ya fi karfina ynxu, kinsan yanda tsofaffi suke lamarinsu, don haka kiyi hakuri ki tafi, Allah xai kawo maki wani hanyar" tana kuka sosai ta fita, Tsaye ta ga kaka da gwangwanin madara da milon a hannunta, tana ganin ta fito ta nufeta ta ajiye mata su tace "Ga nawa gudunmawar, a gaida mutan Doguwa" Mumy dake tsaye bakin kofarta ta shigo parlon da sauri kuma a rude tace "A'a kaka ya xa ayi haka? Ki bata tayi me dasu kuma???" Kaka ta katseta tace "Toh Ina ruwanki, so kike in ba Jikata gaibu ta sha, nasan barbadin da ya shiga ciki a yayin satar? Kazama ce fa bata wanka, to Deedayar xan ba ma sauran milon da ta jagwalgwala ta sha kamar uwata tace min je ki kya gani, kawai wani cutar ya kamata Amadu da Rakiya su kullaceni?? Aa wllh ta tafi da su tayi ta shan shayi a kauyen nasu" Karime sai kallon Mumy take tana hawaye, Mumy na rawar baki tace "Aa kaka idan ba xa a bata ba ni a bar min xan yi amfani da su wllh" kaka tace "Toh banyi niyya ba, ita dai barauniyar xan ba ta tafi da su, kinga dai ai baxata kullaceni sosai ba tunda na sallama mata sauran kayan shayin" kaka na fadin haka ta jawo katon Ghana must go din Karime ta xuge ta xuba gwangwanin biyu a ciki sannan ta rufe tana kakkabe hannu tace "Gudunmawata kenan, anjima kuma sai a kira min Junaidu in sa ya siyo mata wani bbu ruwana da wahala" Karime ta dau Ghana must go din ta nufi kofa tana matsar kwalla, Kai kana ganin Mumy kasan duk a rude take don hakan ya fito kiri kiri a fuskarta, Mami kuwa sai kallonta take, Mumy ta koma part dinta da sauri ta dauko Hijab sai ga ta ta fito ta bi bayan Karime tana cewa "Mu je in raka ki ai baxa ayi rabuwar tsiya ba...." Hada idon da suka yi da Mami yasa tace "Au to ai ba sai na raka ki ba ma...." Sai kuma ta koma bangarenta da sauri, Mami ta bi bayan Karime da har ta fita, Karime ta juyo ganin Mami ta tsaya tace "Hajiya kiyi hankali da kishiyar nan taki, bata sonki bata son yar da kike riko, wnn milon da kaka ke batu a kai ita ce ta xuba abu a ciki don da farko ni ta ba in xuwa ban samu nayi hakan ba shine taje tayi da kanta amma ta mance bata rufe murfin ba...." Tana fadin haka ta ciro milon ta mika ma Mami tace "Gashi don tana iya biyoni tace xata amsa idan na bar gidan nan" amsa Mami tayi tana kallon milon, Karime ta nufi gate da sauri tana goge idonta, sai ga Mumy ta fito, Mami ta mayar da gwangwanin bayanta, Mumy tace "Lahh har ta wuce? Canji na fa na jiya da yamma na wajenta bata bani ba, har dubu uku fa...." tana fadin haka ta nufi gate kusan da gudu, Mami tayi wani murmushi ta juya ta koma ciki, parlonta ta shiga ta bude milon tana kallon content din, ta girgixa kai ta wuce bandaki nan ta xubar da gaba daya a Bathtub ta bude ruwa ta juya ta fita rike da gwangwanin. Mumy ce xaune dakin Sadiya sai rusa kuka take, Sadiya tayi tagumi ta kasa cewa komai, Can tace "Kai kema dai wllh sai kace dakikiya, toh garin yaya ma xaki bar murfin gwangwanin a bude, ke meyasa baki yin abu da hankali, ynxu da ace abun nan na backfiring fa? Sannan uwa uba ga kudin da aka kashe, Kai ni dai wllh idan abun nan bai bata min rai ba shegiya nake" Mumy na Shessheka tace "Wllh kakan nan mayya ce kawai ki yarda" Sadiya ta ta6e baki tace "Toh ita na Rakiyan fa?" Mumy na goge idonta tace "Aa dama cewa nayi bari in fara gamawa da na yarinyar tukun, gashi kuma komai ya tashi a aikin banxa" Sadiya tace "Toh Karimen ke kina tunanin a layin ta jefar da gwangwanin milon?" Mumy tace "Wllh kaf bbu flawan da ban duba ba a layin amma banga komai ba, rashin kunya fa sosai yarinyar ta min har tana neman dambe da ni a titi xata tara min jama'ah, har da kirana shaidaniya, toh ni kuwa ai bana biyeta ba sum sum sum na juyo, amma sai da na bincika jakar banga komai ba wllh sai gwangwanin madaran" Sadiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Ikon Allah... Yanxu dai sai ki saka rana mu koma Zarian tunda haka Allah yyi da mu" Mumy ta marairaice tace "Toh amma ynxu ya xanyi da na wannan Rahinar, ni kinsan ba shiga bangarenta nake ba haka yarana, dama da kariman na nan ne nasan idan na bata xata yi ynda nace to gashi bbu ita ynxu" Sadiya tace "Toh aikuwa dole a san yanda xa ayi a shiga bangarenta kawai..." A hankali Mumy tace "Toh shkkn, Yau laraba ranan juma'ah sai mu koma Zarian" Sadiya tace "Toh Allah ya kai mu" Kaka na yanke ma Heedayah farce a dakinta sai mita take ita an maida ta boyi boyin yarinya duk wa enda suka tsintota darewa suke su barta da ita tayi ta wahala har dare, Heedayah dai sai turo baki take tana sauraronta, kaka tace "Toh bakya turo baki ba dama tunda gani naynny ki, ni kenan kullum a wahale inyi ta fama da maki bauta bakya gani balle ki gode min, bari Rakiyar ta dawo ayi ta takare yau, xanji amfanin aurota da Amadu yyi" Bude kofar parlon aka yi Salima ta shigo da sallama tana kas kas da cingam, kaka ta kalleta ta ci gaba da abinda take, Salima ta xauna tace "Ina yini kaka?" Kaka tace "Lafiya lau, ke dai har yau bbu matayi ko Salima? Toh Allah ya fiddo maki da na gari" Salima ta d'an harareta bata ce komai ba, kaka tace "Toh ai Ina jin Maryam din ma bata nan ta fice" Salima tace "Ehh na sani" Kaka tace "Ayyo, to tafiya xakiyi sai ta dawo ki dawo kenan?" Salima tace "Aa xan d'an kwana biyu a nan" kaka ta kalleta da sauri tace "Kwana biyu kuma? Toh... Allah dai ya ba Amadu ladan ciyarwa, amma ynxu ai abinci ya xama abinda ya xama a kasuwa, ynxu fa mun kusa mu ashirin a gidan nan" Mikewa Salima tayi tana taunar cingam dinta ta fita, kaka tace "Karuwanci dai a sarari ni 'ya su" A hankali Heedayah tace "Kaka wacece?" Kaka tace "Kanwar Maryam uwa daya uba daya, ai bin otal take tana kwana, kinsan uwarta ta rasu haka ma ubanta to bata da wani mafadi ynxu sai makwabta, Maryam ita ma da ba don auren dake kanta ba xata yi fiye da haka ina tsammani, kinsan kafin Amadu ya aureta har xuwa Abuja take wai yawon bude ido a can ma suka hadu da Amadun...." Heedayah tace "Meye yawon bude ido" Kaka tace "Toh ke ina ruwanki da xancen manya kina 'yar yarinya da ke" Heedayah ta turo baki Kaka ta ci gaba da yi mata yankar farcen tana cewa "Banda lalacewa ma ina ni ina hiran nan da ke" Bayan La'asar Salima na kwance parlor tana kallo aka bude kofa, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, ta mike xaune a hankali tana kallonsa, Tunda suka hada ido ya dauke kai, ta bi sa da kallo tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, nima yau na xo" yace "Ohk" parlon kaka ya shiga, ko gama gaisawa basu yi da kaka ba sai ga Saliman ta shigo, ta d'an xauna gefen kujera tace "Kaka bbu abinda xa ayi maki?" Kaka tace "Ehh to wankin bayi ne, daxu ban yrda da wanki Sajida ba, kinsan na sa an Kori dayar me aikin, ta saci milon Deedayah ni ko na sa aka sallameta, shine aka kira min Junaidu yanxu ince masa ya tafi ya siyo mata wasu...." Salima tace "Toh bari a wanke" cire karamin mayafinta tayi ta ajiye nan kan kujera ta nannade skirt dinta har saman Gwiwa, duk fararen kafafuwanta a waje, shi dai Junaid tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, ta nufi cikin bathroom din, kaka tace "Ae Salima yar albarka ce, ga haxaka wajen aiki, da fa idan ta xo gidan nan har kwaleman dakina tana min, kwana biyu ne kawai ta guji gidan nan, kasan yayartata bata da hali tsangwamarta kawai take shi yasa bata son xuwa ma" Junaid ya kalli kaka yace "Wacece yayarta?" Kaka tace "Kishiyar uwarka mana Maryam" Junaid bai ce komai ba, Heedayah tace "Kaka ko xaki basa ya yanke min kina min da xafi" Kaka ta jefar da nail cutter din a jikinta tace "Algunguma sai kije yyi maki da sanyi, yarinya sai sharrin jaraba kawai" murmushi Junaid yyi ya dau nail cutter din yana kallon Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka, ya ja hancinta a hankali yace "Don't Lolly...." kaka ta mike tana kakkabe jikinta tace "Ni idan ta bata min rai ma sai ince ma Amadu na fasa xuwa gyaran idon da ita sai in ga ta tsiya" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Murmushi Shuraim yyi ya gyada kai yace "Toh Allah ya tsare" Kaka tace "Atoh yanxu kayi magana, Ameen dai..... Allah ya kai mu lafiya ya dawo da mu lfya kawai" Juyawa yyi ya fita dakin still smiling ya kulle kofar, Baffa dai na ta xaune bai iya yace komai ba, lkci lkci yake kallon wayarsa waiting for his son Sudais don kafin ya iso gidan sai da ya kirasa yace ya samesa gidan Abba, Kaka na kakkabe jakarta ta tabe tace "To su matan naka basu da niyyar xuwa yi min sallama ne Umaru?" Baffa yace "Dama ba wanda xai yi tafiya ake xuwa yi ma sallama ba Baaba, amma ai xa su xo sallaman" kaka da bata tsaya ta fahimci farkon maganansa ba tace "Toh kar ma su xo mana, xuwansu da rashin sa duk daya ai a wajena, meye hadina da su banda kai da ka auro su, matan da suka kusa kashe ni da kwai duk karni Allah yyi da sauran kwanana a gaba" Baffa na kallon Heedayah yace "Baaba meyasa ake bari tana baccin yamma haka?" Kaka ta daga hannu sama tace "Haka aka saban mata tun daga gun iyayenta wllh, sakakku ne iyayen nata duk sun sangartata sun lalatata, Banda haka katuwa kamar yarinyar nan ace tana tashi shan shayin dare, baka ga gwangwanayen kayan shayin da na tara ba xan ba 'yan gwan gwan, wllh xa su siya dubu biyu ko uku kila, kana maganan baccin yamma ai ko xaka shekara kana tashinta magagi kawai xata yi ta maka, to ni baxan iya wahala ba shi yasa nake barin ta, kuma bana rabo da tofa mata addu'a ba don halinta ba" Baffa ya gyada kai yace "Hakan na da kyau ai" Bude kofar dakin aka yi Sudais ya shigo da sallama, Kaka tayi tagumi tana kallonsa tace "Ta janye tsinannen bakin da tayi maka na xuwa gidan nan kenan, Kai dai kam baka yi sa'ar uwa ba Sudess, yau kusan wata daya kenan rabona da kai fa" Sudais da idonsa ke kan Heedayah ya xauna ya cire face cap din kansa, Baffa ya fara gaidawa sannan ya kalli kaka yace "Ina yini kaka" tace "Lafiya lau Sudess muna ta shirye shirye ashe da rabon xa mu hadu, kai ma ka xo sallaman kenan?" Yace "Sallama da wa?" kaka tace "Ni mana, gashi har na gama hada kayana" Yace "Hada kaya xuwa Ina?" Ta ja tsaki tace "India mana, ko baka da labari ne? Au da yake uwarka ta hanaka xuwa gidan kilan shi yasa baka da labari, ae ni da Rakiya xa mu kai ta indiyan" Ya wara ido yace "Toh ai naga ba da ke xa aje bane Hajiya Kaka? ko wani ya bude baki yace maki har da ke ne a tafiyar kika hada uban kaya haka?" Kaka tayi shiru tana kallonsa bayan ta hadiye wani yawu da kyar, ya danne dariyar sa yana xare mata idanuwansa yace "Mami da Shuraim ko Junaid ne ai xa su yi tafiyan ai, ko mafarki kika yi xa a je da ke ne baki ba mu labari ba kika tsiri hada kaya" Kaka ta juya a hankali tana kallon Baffa dake danna waya, Sudais yace "To ba a ma barin tsofaffi su shiga asibitin, don su ma tsoffin kansu ai cutane...." Baffa ya jefa masa wani kallo, ba shiri yyi shiru trying hard not to laugh, kaka dai magana ya makale mata sai 'yan idanuwa, Baffa yyi gyaran murya yace "Kina ji kaka, kece baki fahimci abun nan ba tun farko, kinga dole ana son a samu masu ilimi sosai su je tare da ita, sannan kin san ynda xaman asibiti yake kuma a gaskiya baxa ma su barki ki xauna ciki ba tunda kin manyanta, shine muka yanke shawara da Amadu cewar Hajiya Rahinah da Shuraim ko kuma Junaid su tafi can din tare da ita don shi Sudais baxai je ba yace, Kinga ai duk masu ilimi ne, komai xuwa xai yi da sauki tare da su, ke kuma daga baya ko kafin a sallame su ne sai a kai ki ki sauka hotel a dinga kai ki asibitin kullum kina dubata...." Kaka ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Toh daga kai har Amadun da duk wanda ya kawo wannan shawaran ku je na bar ku da Allah...." Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta kwantar da kanta saman katon akwatinta, Baffa ya bude baki yana kallonta ya kasa cewa komai, Sudais duk irin yanda yake dakewa bai san lkcn da ya fashe da dariya ba har da kyakyatawa, Baffa ya juya fuska daure yana kallonsa, Mikewa yyi da sauri yana kokarin hadiye dariyar sa yace "Meye kuma abun barin jama'ah da Allah kaka?? Daga fadin gaskiya?" Cikin rawar murya ta dafe kirjinta tace "Ae sun cuce ni ne sun toxarta ni sun kunyata ni Sudess, yanxu da wani idon xan kalli duniya ince masu ba da ni xa aje ba? Dama ashe Deedayah na da wani me muhimmanci bayan ni a rayuwar nan bani da labari? Ashe dama Rakiya munafuka algunguma ce ita ma bani da labari?" Wani kukan ta kuma rushewa da kai kace yarinya ce, Sudais yace "Toh ai ba ace baxa ki je ba fa kaka, cewa aka yi su fara yin gaba daga baya sai ke da Abba ku bi su" Kaka ta dakatar da kukan da take yi ta daga hannu sama da sauri tace "Aa wllh na yafe suyi ta tafiya har bangon duniya idan da matsallaki su tsallake bangon duniyar ma bbu abinda ya sha ma Patuu kai, dama ai ban hada uban komai da shegiyar makauniyar ba karambani na ne" Mikewa Baffa yyi ya fita dakin gaba daya ransa a bace, Sudais na nunata yace "Ke dai kin fiye wahala da neman fitina, tsofe tsofe da ke ina kike son a kai ki? Jinyarki xa aje india ayi ko na Heedayah?" Kaka na nunasa ita ma tayi fici fici da ido tace "Wllh tllh idan ka bari na maka baki sai ya bi ka, uwarka ce tsohuwa ba ni ba, to sae me don su Umaru da Amadu sun munafurce ni? Ae dama munafukan ne tun suna yara, Ga dai gari da yawa maye ae baya ci kansa ba, dama yanxun nan xan bar gidan nan inga shegen da xai hanani in tsine masa bbu ruwana" Tana fadin haka ta mike ta fara neman gyalenta tana matsar kwalla, Sudais sai kyalkyala dariya yake yace "Sai ki fi ruwa gudu ai, mu ba mun huta da wahalar ki ba ma, dama duk kin addabemu kin dame mu" Kaka ta juya tana kallonsa ta nufesa ta cakumosa tana huci tace "Don kaza kazan ka nice wahalalliya??" Gwalo yyi mata ta kara rushewa da kuka ta sakesa ta xauna nan kasa tana rera kuka, suka yi ido hudu da Heedayah da hayaniyar kaka ya tasheta ta mike xaune tana bin ko ina da kallo, a mugun fusace kaka tace "Munafuka maxa sauko min saman gadon kar in jefar da ke" Turo baki Heedayah tayi xata sauka, Sudais ya karasa yana dariya ya kama hannunta ta sauka, kaka tace "Dama duk a xo a fitar min da kayanta daki na kada in konasu wllh wllh" Sudais ya nufi kofar fita da Heedayah yace "Baxa dai kije India ba idan xa ki sa ma ranki salama ki saka, ance maki tsofaffi na fita India ne, ke a dole xa a hau jirgi, to sai a dau na annabawa dai" Daga haka ya fice da sauri kafin ta ce komai, ya nufi part din Mami. Baffa na tsaye compound tare da Shuraim da ya ki shiga dakin kaka shi dai, Baffa ya kalli Shuraim yace "Me yasa baxa ka bi su Shuraim? Barrister ya ce min da junaid xa su tafi" Shuraim ya shafa kansa yace "Haka nan kawai Baffa" Baffa yace "But you need to go as your father's representative tunda shi baxai samu xuwa ba, shi Junaid can go anytime" Shuraim yayi murmushi kawai bai ce komai ba, Muryar Mumy suka ji ta leko tace "Ni na hanasa tafiya Doctor, tunda ba a maida uwarsa bakin komai ba a gidan uban me xai je yi masu India?" Baffa ya juya yana kallonta, can yace "Wnn ba girman ki bane Maryam" bata tanka sa ba ta juya ta koma, Baffa ya girgixa kai bai ce komai ba, Suna tsaye har Abba ya dawo ya samesu wajen, Abba na ganin yanayin yayan nasa dama bai ce komai ba duk suka shiga cikin gidan, parlor suka tadda kaka tana jan akwatin ta fuska a tsuke, Mumy na daga dining tana dariya kasa kasa dadi kamar ya kasheta, Abba yace "Ina kuma xa ki Baaba?" A mugun fusace tace "Rufe min baki algungumi, Ina ruwan ka da inda xa ni??" Ya kwantar da murya yace "Kinga Baaba, tafiyar ma an fasa har sai an maki visa sai duk ku tafi tare" Tace "Oh oh ba ruwana su yi tafiyarsu, kada wanda yace min komai, ni dai an walakanta ni an cuce ni, Allah ya hada mu a kiyama gaba daya kawai...." Xaunawa Baffa yyi saman kujera ya jinginar da kansa yana kallonta, Abba dai bai ce komai ba, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, Kaka ta saki jakarta tayi mitsi mitsi da ido tace "Junaidu ashe dama uwarka bata da kirki ban sani ba, Ashe sai a hada baki da ita a cuceni ban sani ba, ni tunda nake Maryam bata ta6a min abinda Rakiya tayi min ba wllh" Da farko tsaye yyi bakin kofar, sai kuma ya karaso yace "Me ya faru kaka?" Kaka ta sakar masa kuka tace "Da hadin bakinta aka yanke shawarar baxa a je India da ni ba wajen gyaran idon Deedayah" Junaid ya d'an bude ido yace "Aa kaka ai dole ma xa ki je, ga visa nan ana maki, idan ya so bayan an gama ni da ke sai mu bi su daga baya, nima ai ba binsu xanyi ba ynxu..." Ta marairaice tace "Toh ai su basu ce min haka ba cewa suka yi ban da ni kawai, wani har ce min yyi nima kai na cutar ce me xai kai ni India, wato wai nice cuta, har da ce min wahalalliya, abinda ni dai nasan ubansa ya xaga ba ni ba" Junaid yace "Aa kiyi hakuri don Allah, tafiya kam xa ayi da ke in sha Allah, kawai dai daga baya ne xamu bi su" Kaka tace "To da wa da wa xa a tafi din yanxu?" Yace "Mami da Shuraim" Mumy dake dinning har sannan ta sakko xuwa cikin parlon cike da gadara tace "Nace Babu inda Shuraim xai je, a nemi wani amma ba shi ba, indai har ni da na haifesa ban cancanci xuwa ba to shima bai cancanta ba, kada a sake ambaton sunansa a masu tafiyan" Kaka ta bude baki tana kallonta tace "Waye wannan kuma? Daga gidanku kika xo da Shuraim din da xaki nuna mana iko a kansa ko kuwa shakiyanci ke damun ki? Kaji min jarabbiyar mata dai, to wllh sai an je da Shuraim, Kai idan xuciya ta debeni ma sai ince shi kadai xai kai ta gyaran idon kada wanda ya bi su, ke a wa xaki ce baxai je ba wahalalliyar mata kawai, nan nan kanwarki ta xo nan gidan ranan kamar abun arxiki amma sbda tambadewa na samu labarin ba a gidan take kwana ba sai ta fita da daddare ta dawo mana da safe, to gidan ubanwa take kwana, baki dau mataki kan wnn lamarin ba sai don ance Shureen xai je indiya da Deedayah? " kaka ta kalli Abba a fusace tace "Kai Amadu da wa da wa xa a tafi goben?" Yace "Rahinah da shi Shuraim, daga baya sae ke da junaid ku bi su" kaka tace "Toh dole da Shuraim xa a tafi, idan ma kowa bai je ba sae Shuraim yaje wllh" Mumy tace "Ohk, ya tafi bakina ma ya ishesa ai" Kaka ta nufeta tana tafe hannu tace "Bakin ki na banxa na hofi, bbu abinda bakinki xae mashi, ae ubansa xai yi ma biyayya don hka a gantale bakin ki xae xaga duniya ya dawo ya fada kanki ba dai kan jikana ba, gantalalliya kawai" a nutse Mumy tace "In har Shuraim ya taka ya fita gidan nan xuwa wani kasa wllh sae na tsine masa" tana fadin haka ta bar parlon kamar xata tashi sama, Shuraim dai na tsaye gefen Abbansa, kaka tace "ke kuma tsinuwar Allah ya tabbata a kan ki ba na mutum ba, xan ga uban da ya isa ya hana Shuraim xuwa India" Abba da gaba daya ransa ya gama baci ya bi bayan Mumy, Baffa dai ya ta6e baki bai ce komai ba, kaka na kallon Junaid tace "Ni dai ko xaka kai ni gidan kawun ka ynxu, wllh raina baci yake idan Ina ganin mutan gidan nan, Ka kai ni can ko xa a kwantar min da hankali" yyi murmushi yace "Toh mu je kaka" tace "Amma ae abun ba hauka bane bana kai masu katon akwati ba bari in bude in dau kayana kala ko goma ne" Shi ya ja mata akwatin har dakinta tana biye da shi tana goge guntun hawayenta... Washegari da asuba Mami ta gama duk shirinta, ta shirya Heedayah, suka fita xuwa parlon Abba, Abba da ya gama hada duk medical report din Heedayah a envelope ya mika ma Mami yace "Amma xa mu tafi ku yi ma Kaka sallama tukun koh" Mami ta amsa tace "In sha Allah" Abba ya kalli agogo yace "We need to hurry up, sbd kar ku yi missing train din" Mami tace "Haka ne" Abba ya dau wayarsa yana mamakin rashin ganin Shuraim a masallaci don bai dde da shigowa daga masallacin ba shi ma, Dialing number sa yyi ya ji switched off, ya kuma kira a kashe, Mami dai kallonsa kawai take bata ce komai ba, Abba ya dinga kallon wayar tasa, can ya mike yace "Mu tafi kawai in kai ku gidan Honorable din daga can Junaid ya kai ku Train station" Tace "Shuraim din fa?" Yace "Don't worry about that" Mai gadi ne ya shigo ya dau kayan Mami da Heedayah ya sa bayan motar Abba, Mami tace "Toh baka yi ma daughter din taka Addu'a ba Allah ya sa ayi aiki a sa'a" Abba yyi murmushi yana kallon Heedayah dake sanye da kananun kaya sai baby Hijab dake kanta tana rike da hannun Mami, kamo hannunta yyi yace "Safe trip dear, Allah ya kai ku lafiya ya sa ayi komai a sa'a, ya baki lafiyan idon ki" Ta kamo hannunsa a hankali tace "Abba xan fara gani nima?" Yana murmurshi yace "In sha Allah Dear" ta d'an yi shiru sai kuma tace "Toh baxan fara ganin Ammi na ba?" Abba da Mami duk suka yi shiru suna kallonta, hawaye ne ya kawo idonta tace "Tace min ita xan fara gani fa" Abba ya jawota jikinsa yace "Xa ki ganta in sha Allah daughter, Mami ma ai Ammin ki ce" Ta gyada masa kai, ya share idonta suka nufi gun mota Mami na biye da su a sanyaye, Sai bayan da ya shigar da Heedayah motar Mami tace "Baxa ayi ma matarka sallama ba?" Yace "No, rabu da ita" Mami bata kuma cewa komai ba ta bude front seat ta xauna suka fita gidan xuwa gidan Alhaji Imran Baffansu Junaid, Dakin da aka sauke kaka Mami ta shiga da Heedayah bayan sun gaisa da Hajiya Zuwaira a dakinta, kaka na xaune ko haske gari bai yi ba ga kayan karin kumallo iri iri a gabanta tana hada shayi cikin katon mug, Mami ta xauna saman carpet tana murmushi tace "Ina kwana kaka" Kaka tace "Lafiya lau, to Ina xan samu haka a gidanku??" Murmushi Mami kawai take, can tace "Toh mu kaka xa mu tafi ayi mana addu'a, Allah yasa mu je a sa'a ayi a sa'a, ku kuma Allah ya kawo ku lafiya" Kaka tace "Toh Allah ubangiji ya kai ku lafiya, ya sa wnn marainiya ta fito lafiya, Allah kar ya bamu kunya yasa idanuwan nan su rufa mana asiri su budu" Mami ta yi kasa da kanta tace "Ameen" Kaka tace "Toh matso da ita in yi mata addu'a" Mami ta maida Heedayah kusa da kaka, kaka tayi duk suran da ta sani da su ayatul qursiyyu da Amanar rasulu duk ta tofa mata tace "Allah ubangiji ya sa ayi aikin a sa'a, ya rufa mana asiri ki fara ganin kowa kamar yanda ake ganin ki, daga karshe kuma Allah ya bama d'a na ladan uban kudin da ya kashe maki, Allah yayi masa albarka yasa kema ki ji k'an sa wataran kada ki yi mana butulci..." Heedayah dai tayi shiru staring into space, kaka tace "Kaji gantalalliya, baxa ki ce Amin ba, ko kina da niyyar butulcin ne ya sa kika yi shiru bamu da labari" Mami tayi murmushi tana kallon Heedayah tace "Say Ameen daughter" a hankali Heedayah tace "Ameen" Kaka tace "Toh maxa ku tafi kada jirgin ya tafi ya bar ku ba mutunci ne da su ba haka suka so min xuwa umrana na karshe Allah ya fi su" Mami tace "Toh Kaka, mun gode da addu'a, baxa ki fito ku gaisa da barrister ba" Tace "Waye kuma Barrister? Don Allah ki rabu da ni kada raina ya baci, yyi ta kansa inyi ta nawa kawai" Mami ta mike tace "Toh Allah ya sada mu da alkhairinsa kaka" Kaka tace "Kiyi addu'a sosai kafin ku hau wnn bala'in na bature wai jirgi" Mami tace "In sha Allah" kaka tace "Da Shuraim din dai xa a je koh?" Mami tace "In sha Allah" Kaka tace "Toh duk Allah ya tsare ku, yayi maku albarka, ya sa ayi wnn aiki a sa'a sai mun xo ni da Junaidu" Mami tace "In sha Allah kaka" daga haka ta fita dakin, Abba na xaune parlor da Alhaji Imran, Ganin Mami yace "Lkci fa na wucewa kada kuyi missing train" Mami tace "Ka samu Shuraim din?" Abba yace "No tare da Junaid xa ku tafi" Shiru Mami tayi, Ya mike yace "Yeah, na kira junaid din ya shirya ynxu" Mami ta xauna tare da Heedayah, Alhaji Imran yace "Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi a tafiyar" Mami tace "Ameen Baffa" Ba a dau lkci ba sai ga Junaid da traveling bag dinsa ya sakko kasa, Abba na kallonsa yace "Hope baka ce ma kaka komai ba" junaid yace "Aa ban shiga ba" Abba yace "Good" Har motar Abba dake parke waje Alhaji Imran da matarsa suka raka su, Alhaji Imran na kallon junaid yace "Nayi maka transfer yanxu Incase da bukatar wani abun a can, Allah ya kai ku lfya, ya sa ayi aikin a sa'a" Junaid yace "Toh Baffa Allah ya saka da alkhairi" Abba yyi ma Alhaji Imran godiya haka ma Mami sannan suka dau hanyar train station na Hayin rigasa, Junaid na xaune back seat da Heedayah, ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa a hankali tace "Good morning...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Har suka isa train station din bbu wanda yace komai cikin motar, Abba yyi parking duk suka sauka suka shiga ciki with their luggages, shi dai Junaid na rike da hannun Heedayah, Abba bai bar tashan ba kuma sai da ya ga tashin train dinsu xuwa Abuja.... Kasancewar sai tara na dare flight din nasu na Qatar airways xai tashi kamar yanda aka sanar masu bayan sun je airport din, hotel kawai Junaid ya kama masu kusa da Airport din, Bayan Azahar Mami ta idar da sllh ta shirya xata tafi gun step sister dinta da ke nan garin Abuja, shigowar Junaid kenan daga masallaci yana kallonta yace "Ina xa ku Mami?" Tace "Xan je gidan Asiya ne in dawo yanxu" yace "Ohk..." Mami ta ajiye ma Heedayah dake xaune saman gadon hotel din takalminta ta kamo hannunta tace "Sauka ki sa takalmin ki" Heedayah tace "Mami da Yaya xa mu je?" Mami tace "Aa ina ruwanki da wani Yaya" Tace "Mami mu je da shi plss" Mami ta saka mata hijab dinta tana rike da hannunta ta nufi kofa tace "Sai mun dawo" junaid ya bi su da ido, sai kuma yace "Mami ko xa ki bar ta ki je ki dawo" Mami ta juya tana kallonsa tace "For what reason?" Da sauri yace "No naga kamar bata son tafiya ne" Wani kallo tayi masa ta bude kofar ta fita, Heedayah dai kamar xata yi kuka take bin Mami.... Har la'asar Mami na gidan yar uwarta da Heedayah suna hiran yaushe gamo, Hajiya Asiya na kallon yar uwarta tace "To amma me yasa ba ku taho tare da Junaid ba? Mun kwana biyu ba mu hadu ba" Mami tace "Muna sauka daxu da safe yace min xai je gidan kawunsa so bna son ya kasance bai je ba, but in dai ta nan xa mu dawo xai xo gun ki in sha Allah...." Hajiya Asiya tace "Toh shkkn, Allah ya kai ku lfya ya dawo da ku lfya, ita kuma wannan yarinya Allah ya sa ayi aikin a sa'a" Mami ta amsa da "Ameen" karfe shidda saura Mami suka bar gidan, babu yanda Hajiya Asiya bata yi ba su tafi da abinci hotel din Mami ta ki amsa, Hajiya Asiya ta sa driver dinta ya sauke su hotel din nasu. Karfe tara da few minutes na dare jirginsu Mami yyi take off direct xuwa kasar India without stopovers, tafiyar kusan awa tara da minti arba'in da takwas, kafin tashinsu kuma sai da Mami ta tabbatar ta kira Abba ta sanar masa xa su tashin yayi masu addu'a yyi wishing dinsu smooth trip.... Tare Junaid da Heedayah suka xauna a jirgin, Heedayah na laluba hannunsa tace "Yaya me yasa Abba bai biyo mu ba" Junaid yace "He is very busy" tace "To kaka fa?" Yace "She's old to journey with us" tace "To ya Sudais fa?" Yace "Shi ma he is busy amma xai xo...." Heedayah tayi shiru sai kuma tace "Dama bana son Shureen ya biyo mu" Murmushi yyi yace "Why?" Ta girgixa kai tace "Bana son sa" Junaid yace "Don't tell anybody that" Tace "Why?" Ya ja hancinta ya kwantar da ita jikinsa yace "Sleep Lolly...." Lumshe ido tayi nan da nan kuma bacci ya dauketa throughout the rest of the journey. Bakwai saura na safiya Jirginsu ya sauka Indira Gandhi international airport new Delhi, Amma sai karfe goma saura suka shiga Indraprastha Apollo Hospitals da xa ayi ma Heedayah aiki, don sai da suka fara sauka hotel dake nan kusa da hospital din suka huta, Bbu bata lkci aka yi admitting din su a babban asibitin a ward dinsu su kadai, ba laifi ward din na da d'an girma, amma kana gani kasan dai kudi ne kawai aka kashe ba kadan ba.... Kamar yanda Abba yayi tunani haka ne don sun daura Heedayah kan allurai na sati daya, sai kuma some diet da aka daura ta kai, Likitar dake ma Mami bayani a office dinta da harshen turanci ta sanar ma Mami irin Disorder din Heedayah da ake kira da Congenital Blindness, sannan ta sanar mata Novel Gene therapy xa ayi mata to correct the disorder, probably through luxturna, Mami da duk jikinta yyi sanyi tace "But is there much chances of her gaining her sight?" Likitan tace "Hopefully, though it's a rare disorder but we will try our best" Mami tayi ma likitan godiya ta mike ta fita office din ta koma ward dinsu. A kwanaki bakwan nan Mami kusan kullum sai ta tashi sllhn dare tayi addu'ar Allah ya sa ayi nasara a aikin da xa ayi, har ranta take tausayin Heedayah take kuma fatan Allah ya bude mata idanuwanta, bata san yanda xata ji ba idan aka yi aikin nan Heedayah bata yi gaining sight dinta ba, she can't just imagine that, a hotel din da suka fara sauka na kusa da hospital din Junaid ke kwana, amma throughout the day yana asibitin tare da Heedayah da Maminsa, sai dai kawai ya fita ya siyo masu Nigerian dishes safe rana da daddare, ko kuma ya fita xuwa yin sllh... A kullum sai Abba ya kira ya sa a ba Heedayah waya sun yi magana, complain dinta kuwa a ko da yaushe shine idonta suna mata ciwo, don a hankali fararen idanuwanta masu kyau suka fara sauya kala xuwa ja kuma tayi ta sosa su, Sudais ma kusan kullum sai ya kira Mami ta ba Heedayah sun yi magana, ana haka har suka cika kwana goma cif a asibitin ya rage kwana biyu a shigar da Heedayah theatre.... Junaid na xaune tare da Mami ana gobe xa ayi operation din wayarsa ya fara ring, dauka yyi saman table dake kusa da shi yana kallon screen din dake nuna masa Beauty, to waye haka? ya dau lkci yana tunanin waye yyi ma saving da haka, sai kuma ya daga kafin ya katse ya kai kunne, Daga daya bangaren aka yi sallama cikin siririn murya, sai bayan kusan second biyar ya dau muryar ya amsa sallaman, Salima tace "Haba Jayyy shine bbu ko sallama kayi tafiyar ka India, to gani a new Delhi din nima, yanxun nan jirginmu ya sauka daga Nigeria wllh" junaid ya d'an yi shiru da mamaki, can dai yace "Ke da wa kika xo new Delhi?" Tace "Wllh wani saurayi na ne ya xo business trip shine kawai yace in rakosa, a hotel din kusa da Airport xa mu sauka ynxu.... Ku kuna wani asibitin ne?" Yace "Toh ki huta tukun xa mu yi waya" tace "Toh shkkn Jay, sai anjima dama duk na gaji, wanka xan yi ma yanxu" Yace "Alright" daga haka ya katse wayarsa, Mami na kallonsa tace "Wacece?" Ya kalleta da sauri sai kuma yace "Ohk wata coursemate dita ce from Nigeria...." Mami tace "Ya aka yi tasan kana India?" Yace "I told her I will be coming to India tun last week" Mikewa yayi ganin Heedayah xata sauko saman gadon ya nufeta yace "What happened?" Tace "I want to ease my self" Tashi Mami tayi ta kama hannunta xuwa toilet dake ward din. Washegari da asuba aka shigar da Heedayah theater, a asibitin Junaid ya kwana ranan, coz shi ma he is so tensed, he just don't want to imagine the operation won't be successful, haka ma Maminsa da bata yi wani bacci daren ranan ba, ita kanta Heedayah duk son baccinta bata yi baccin ba daren don idon na damunta sosai, Mami taji tausayinta ba kadan ba, har karfe goma na safiyan Mami na xaune saman darduma hannunta rike da carbi, Junaid yace "Mami baki yi breakfast ba, pls take something" Tace "Toh" Tea ya hada mata a cup ya mika mata ta amsa, Mami bata wani sha shayin ba ta fita ta xauna saman kujeran dake jere gaban theatre din da aka shigar da Heedayah.... Karfe sha biyu likitoci biyu suka fito theater din sanye da gown din operation, Mikewa Mami tayi wanting to hear something from them, da turanci daya likitan yace mata ta kwantar da hankalinta all will be well, daga haka ya wuce, Mami ta koma a hankali xauna, bayan minti talatin wasu likitocin uku suka fito su ma din dai haka suka ce mata, ita dai gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya, daga karshe nurse biyu suka fito, Mami ta kara tashi ta nufesu, su ma dai xancen daya ne suka yi wucewarsu. Sae kusan azahar aka kai Heedayah ward dinta tana bacci, Mami na xaune kusa da ita sai kallonta take an rufe mata idanuwanta da white eye pads, gaba daya she is disturbed and tensed, Junaid dai na tsaye daga gefen gadon ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, wayar Mami ya fara ring ta dauka ganin Abba ne ta daga a sanyaye ta kai kunne, gaisawa suka yi tace "Yanxu aka fito da ita, but akwai eye pads a idanuwan...." Daga daya bangaren Abba yace "Toh Allah ya sa an dace, can I speak to her now?" Mami tace "Bacci take" Abba yace "Toh I will call back later" daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar tana kallon junaid tace "Toh baccin me take haka, ko anaesthesia da aka yi mata ne?" Yace "No, anaesthesia din da aka yi mata iya aikinsa bangaren idon, she is not unconscious bacci take" Mami tayi shiru bata ce komai ba.... Har karfe hudu na yamma Heedayah bata farka ba, Junaid ya tafi yyi sllh ya dawo ya tadda Mami na sallahn ita ma, ya xauna kusa da Heedayah ya kamo hannunta yana kallonta ganin sai motsi take, a hankali cikin rawar murya ya ji tace "Mami idona na min ciwo" Ya dafa goshinta still holding her hands tight yace "Xai daina dear...." Ganin xata mike xaune ya dagata ta xauna ta kai daya hannunta idonta, da sauri ya rike hannun ganin cire pads din take son yi yace "Noo don't...." Ta fashe da matsanancin kuka xata kwace hannunta tace "It's paining me" ya ki sake hannun yace "Zanyi tafiyata in bar ki ke kadai a nan if you don't stay still now...." Ganin kukan da take ya rungumeta yace "Toh yi hakuri xa a cire maki yanxu, ki daina kukan, I will call the doctor now" cikin rawan murya tace "Yana min xafi sosai" Mami na idar da sllh dama fita tayi kiran likita don yace idan ta tashi a sanar masa, yana shigowa allurai biyu yyi mata ya sa mata drip ya fita... Ba a dau lkci ba kuma tayi bacci junaid na rike da ita har sannan, Mami ta sake komawa gun likitan don jin abinda ake ciki, nan ya sanar mata nan da kwana uku xa a cire eye pads din a duba idon with hope that tayi gaining sight dinta clearly, kafin kwana ukun kuma xa ayi ta mata injections xa kuma ta dinga shan magunguna, Mami tace "But is there nothing to do about the pain pls?" Yace "The pain will subside before tomorrow...." Mami tace "Are you giving me hope that the operation is successful Doctor?" Likitan ya girgixa kai yace "We are also hoping it's successful, but if it's not, then we will try anoda operation.... The last" Mami ta kasa ce masa komai, can ta mike tayi masa godiya a sanyaye ta fita. Tana komawa ward din Junaid ya kwantar da Heedayah ya mike yace "Xan je in dawo yanxu Mami" Mami tace "Ina xa ka?" Yace "I want to get something, ba dadewa xan yi ba" tace "Ohk, ka siyo fresh milk when coming back" yace "Toh" daga haka ya fita, nan kuwa tun safe Salima ta ishesa da kira shine yyi deciding kawai ya tafi ya sameta inda tace masa take ko xata daina kiransa. Yana tsaya gaban hotel din ya kirata, tana dagawa yace "Ina waje ki fito" tace "Haba ka shigo ka jirani a reception mana Jayy..." Yace "But I can't come in, ki daure dai ki fito Ina sauri ne" tace "Wllh tun safe kai na ke ciwo a kwance ma nake ynxu, bbu ynda Suraj bai yi in raka ba na ki fita, ka daure ka karaso ko reception ne plss Jayy" yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya shiga cikin babban hotel din, Yana reception din ya kirata, sae ga ta ta sakko sanye da riga da wando sai black veil da ta daura a kai, shi duk wayar da suke ya kasa yrda da gaske tana India sai ynxu da ya ganta, ta sakar masa murmushi tace "Welcome, mu shiga ciki in daura after dress mu tafi hospital din, tun safe na damu Ina son xuwa wllh" yace "Aa ba a barin mutane fiye da biyu and yau ba visiting day bane" lkci daya mood dinta ya canxa tace "To yaushe ne visiting day din?" Yace "Nan da 3 days" Ta tabe baki tace "Toh mu je ciki" yace "No, na gaisheki, xan koma ynxu coz I need to get them food" Ta marairaice tace "Haba Jayyy, ae ba cewa nayi ka shiga ka dade ba, kawai mu je kaga Inda nake, ni fa bbu wanda yasan ma na taho India, tafiyar ce ta xo min cikin gaggawa, Kuma Suraj bai son tafiya shi kadai dama" Bata jira cewarsa ba ta kama hannunsa tace "Come on mu je plss" da mamaki yake kallonta, can ya janye hannunsa daga nata still following her slowly har xuwa hotel room din da take. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Junaid ya nufi kujeran dake makeken dakin hotel din ya xauna, gefensa ta xauna tana wani murmushi tace "Me xan kawo maka Jay? Ko in sa a kawo maka abinci?" Ya girgixa kai yace "Nothing, saurayin ki kika biyo India kenan?" Tace "Ehh shi na biyo amma wllh sbda kai na xo, India ai ba wani kasar xuwa hutu bane kasar xuwan marasu lafiya ne, wani saurayina fa tun last week yake son mu je dubai mu huta amma na gwammace in biyo wannan xuwa India duk don sbda kai wllh" Junaid ya gyada kai yace "Ni kuma me xan maki da kika biyosa India sbda ni?" Ta wara ido tace "Just to see you mana, Ina dawowa daga Abuja fa aka ce min kun taho India da makauniyar nan...." Yana kallonta da kyau yace "Kada ki sake ce mata makauniya" Ta d'an yi shiru, sai kuma ta tabe baki tace "Toh ka tafi ko sallama babu shi yasa da na samu opportunity kawai na biyo ka" ta karasa tana murmushi, Ya girgixa kai yace "So this the best life you think you are living right?" Tayi frowning face dinta tace "Ban gane ba, me ya kawo wannan maganan kuma?" Ya tabe baki yace "Anyway shkkn, so yanxu kin gan ni kuma mun gaisa, plss kar ki sake kiran line dina sbda a hospital nake da mara lafiya.... Pls don't call again I beg you" Ta marairaice tace "Wllh tllh sbda kai na xo kasar nan Jay, ka kaini asibitin mana nima muyi jinyar tare" Yace "Aa, idan mun koma Nigeria sai kiyi jinya but not here coz bbu ma wanda yasan kin xo nan, I repeat don't call me again, I don't even want to ask what ur name is, but what ever it is plss don't call my line again Lady" Kwantawa tayi jikinsa kamar xata yi kuka tana shafa kirjinsa tace "Haba Jay...." Turata yyi har sai da ta fadi kasa ya mike yana mata wani kallo yace "Are you stupid?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Tun da nayi respecting dinki na xo har Inda kike kada ki sake kirana, na xo ne dama don kada ki kuma kirana, idan kun gama abinda ya kawo ku ke da saurayin naki ku koma inda ku ka fito tare, we will meet back in Nigeria...." Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo ya bude kofar xai fita suka kusa cin karo da Suraj din, Junaid ya kallesa daga sama har kasa, ya bi gefensa ya fita dakin, Suraj ya kalli Salima da ta kauda kai da sauri, yana nunata da yatsa yace "Dama shi yasa tun jiya kike wasa da hankalina ashe appointment gare ki da wani? To maxa kwashe kayanki ki bar min hotel room dina yanxun nan" Ta masa wani kallo tace "Ae ba wani ya kawo ni kasar ba, yanda muka xo tare haka xa mu koma tare, kawai don ka kawo ni India sai aka ce maka haka xaka dinga samu na baxa ka biya ba kamar wata gareji, to ko garejin ma ae ana biya" ko amsa bai bata ba ya tafi inda jakar kayanta yake ya dauka ya bude kofa ya jefar corridor din hotel rooms din, ya koma ya dauko handbags dinta da sauran tarkacenta duk ya watsar a waje, bude baki tayi tana bin sa da kallo a tsorace ta kasa cewa komai ita ma ya tafi ya ja ta har kofan ya turata waje ya rufe kofar sa. Junaid na isa hospital din dab da magrib Mami tace "Where are you coming from Junaid?" Ya ajiye ledan madaran hannunsa ba tare da ya kalli idonta ba yace "Mami wata frnd dita ce da muka hadu online years back, she's here in india, so shine naje muka gaisa" Mami ta ta6e baki bata ce komai ba, gadon da Heedayah ke kwance ya nufa ya xauna saman kujera yana kallonta, bacci take heavily, kana gani kasan alluran bacci aka mata, ya kai hannu goshinta a hankali ya ji da xafi, Mami tace "Ynxu naje nayi masu complain xafin jikin nata" Ya gyada kai bai dai ce komai ba, Mami tace "Shaheedah called me daxu bayan ka fita" Kallon Mami yyi yace "Ohk" tace "Baban nata ya ji sauki amma sosai koh?" Yace "Ehh ya samu lfya" Wayarsa da ya fara ring a aljihu ya ciro, ya ga Beauty gaban screen din, ya d'an saci kallon Mami dake kallonsa, ya mayar da wayar aljihu bayan ya sa shi total silent, yana ta xaune dakin har Magrib yyi, Mami ta shiga bandaki yin alwala sai da ta fito ya mike yace "Xan je inyi sllh" Mami tace "Ohk" daga haka ya fita, sai da ya fito haraban katon asibitin ya ciro wayarsa ya ga miss calls din Salima kusan ashirin, ya wani buda ido da mamaki yana kallon screen din wayar, sai ga kiranta ya kuma shigowa, dagawa yyi ya kai kunne kafin yace komai ta fashe masa da kuka sosai tace "Jay wllh ya koreni ya watsar min da kaya ganinka da yayi, gashi ni bani da inda xan je bamu da kowa a kasar nan, ko kudin kama hotel ma bani da shi balle kudin komawa Nigeria ni dai kawai biyosa nayi tunda mun saba tafiya tare, yanxu haka ina titi da kayana daga ni sai kudin Nigeria dubu uku a jakata, don girman Allah ka rufa min asiri, nayi ta kiran layinsa ko hakuri ne in basa amma yyi blocking dina wllh" Junaid yace "Amma baki da hankali, ni da kike kirana me xan maki? ni na kawo ki India da xa ki kirani ki ce min ya kore ki, look kar ki sake kiran layina idan ba haka ba duk abinda na maki ke kika ja wllh" Ta rushe da matsanancin kuka tace "To yanxu Ina xan je fisabilillahi, ni wllh bbu wanda yasan Ina India sai kai, don girman Allah Jay ka rufa min asiri" Ya ja tsaki ya kashe wayarsa ya tafi yin sllh. Da abinci ya dawo ward din, Mami ta kallesa da damuwa tace "Toh ita tana ta bacci bbu fa abinda ta ci tun safe wllh" Junaid yace "Ga drip an sa mata for that, xuwa can cikin dare xata tashi sai ki hada mata shayi" Mami tace "Toh ko in tasheta yanxu in bata?" Yace "Aa, ai baxata tashi ba, allura suka mata" Mami tace "Toh shkkn" Yana ta xaune ward din kusa da Heedayah har kusan sha biyu na dare, yana lura da da cewa alluran ya fara saketa don sai motsi take, ta juya can ta juya nan, kana ganinta kuma kasan she is still in pain, lkci lkci take kai hannu idonta, sai ya rike hannun ya mayar saman gado, yana mata haka kuma sai ta turo baki, yyi murmushi ya d'an kalli Mami da ta fara bacci ya ja bakin, kara tayi kamar jira take ta fara kokarin mikewa xaune, Mami ma ta farka ta mike xaune da sauri, Kamar xata yi kuka tana tattaba gadon tace "Mami kina ganinsa ko? Bakina ya ja min da karfi" Mami ta sakko saman gadon da take tace "Sai da safe tashi ka fita, good night" Tashi yyi kafin ta iso Inda yake yana murmushi ya nufi kofa making sure hotel key dinsa na aljihunsa, Heedayah tace "Mami to ina xa shi?" Mami tace "In xuba maki abinci ko in hada maki tea?" Heedayah ta 6ata fuska tace "Mami ina Yaya xa shi?" Mami tace "Ina ruwanki da shi?" Junaid ya kalleta sannan ya bude kofar ya fita still smiling. Yana fitowa wanka bandakin hotel room dinsa ya saka jallabiyarsa ya kwanta ya dau wayarsa, miss calls arba'in ya gani, ya mike xaune da sauri yana kallon wayar, sai ga kiran Beauty a screen dinsa, ya daga ya kai kunne a fusace yace "Ke wace irin Mahaukaciya ce wai? Draining din battery dina kike son yi? Why are you calling me for heaven sake???" Ta fashe masa da kuka da karfi tace "Wllh jay gani a bakin titi har yanxu ni ban san Inda xanje ba, ko asibitin ne ka taimaka ka fada min sunansa in je, gashi duk an watse an bar ni ni kadai kada yan sandansu su xo wucewa su gan ni su tafi da ni, don girman Allah ka gaya min asibitin in je jay...." Yace "Toh wai da kike ta kirana ni na kawo ki India ne baiwar Allah?" Tace "Amma silar ka na xo ai, Allah sbda kai na biyo Suraj duk da nasan Mahaukaci ne, to wa xan kira idan ba kai ba" Junaid ya ma rasa me xai ce mata, ita kuwa sai rera masa kuka take a kunne, can ya ja tsaki yace "Ina kike yanxu" Tana kuka ta gaya masa ya katse wayarsa, bbu ynda ya iya haka ya dau kudi ya fita hotel din ya kulle dakin, Tricycle ya samu xuwa Inda tace masa take, ai ko ya sameta gefen hanya ita kadai xaune kan jakan kayanta, yana sauka daga tricycle din ta mike xaune duk idonta yyi suntum sbda kuka, yana mata wani kallo yace "Ashe ke karamar yar duniya ce tunda har xa ki shigo India ki rasa wajen kwana duk yawon da kike da maxa kasashe daban daban" Ita dai bata tanka sa ba ta dau jakarta ta saka cikin Tricycle din da sauran kayanta sannan ta shiga ta xauna, yyi kwafa ya shiga adaidaitan suka koma hotel din da yake, Sai karfe kusan daya da wani abu suka shigo hotel din, tana ganin wani dakin xai biya mata tace "Aa jay kada ka wani kashe kudin ka, ni dai gwara kawai ka harhada ka biya min kudin jirgi in koma Nigeria" Bai tanka ta ba yyi wucewarsa sama ta bi sa da kaya tana tangal tangal don ko daya bai dau mata ba, yana bude dakin ya shiga ya bar mata a bude ta shigo sannan ta kulle tana bin dakin da kallo, saman gado ya nufa ya dau bargo da pillow ya jefa mata a kasa snn ya kashe wutan dakin yyi kwanciyarsa, ta ajiye kayanta ta dau pillon da bargon ta shimfida bargon sannan ta daura pillon a kai, a hankali tace "Nagode, amma xan d'an kunna dim light sbda xan yi wanka" Ko tanka ta bai yi ba ya juya mata baya yana danna wayarsa, bayan kusan minti goma ya ga ta kunna wuta mara haske sosai ta shiga bandaki, yana jin alamar tayi wanka ta fito, mamaki ne ya cikasa sosai ganin naked ta fito daga bandakin walking majestically, a hankali ya ajiye wayarsa ya rufe ido ya tsiri baccin da bai yi niyya ba a lkcn, ta gama buruntunta ta cika dakin da kamshin turare iri iri da ta fesa a jikinta, shi dai idonsa na rufe gam, xagayawa tayi kusa da shi tace "Don Allah ka d'an ban wayarka xan kira yayata, tun daxu take kirana sbda tashin hankali ban dauka ba gashi ynxu bani da isashen kati" yyi banxa da ita har sannan idonsa a rufe, ta kai hannunta me sanyi a hankali fuskarsa tace "Kayi bacci ne Jayy?" Lkci daya ya mike xaune ya sauke mata lafiyayyen mari yace "I swear to Allah ba karamin aikina bane in fitar dake hotel din nan yanxun nan, are you mad????" Mikewa tsaye tayi da rigar baccinta iya cinya bbu komai ciki ta dafe kuncinta tana kallonsa, yyi mata tsawa yace "Baxa ki tashi gabana ba sai nayi ball da ke" gyada kai tayi ta juya tana karkade karkade ta xaga Inda ta shimfida bargo ya bi ta da wani irin kallo, yyi wani kwafa ya koma ya kwanta ya rufe ido.... Daren ranan dai bai yi bacci ba sai juye juye yake shi kadai, sae dab da asuba bacci ya daukesa, hasken ray din rana da ya sauka fuskarsa ne ya farkar da shi, ya mike xaune da sauri yana kiran Allah a xuciyarsa, gefensa ya ga Salima kan gadon tana bacci hankali kwance, bbu abinda baya gani a jikinta ta cikin shegen kayan baccin da ta saka, tashi yyi da sauri ya shige bandaki, tun da yake dai da girmansa bai ta6a missing sllhn asuba ba ko a jam'i ko ba a jam'i ba, da asuban xai yi raka'atainil fijr snn yyi sllhn sa amma wai yau shine har kusan 8 bai yi sllhn asuba ba, ransa a bace ya wanke baki yyi alwala ya fito ya shimfida darduma ya tada sllh, ya kusa minti sha biyar saman darduman bayan ya idar sannan ya mike ya buga gadon da karfi yace "Dauki kayan ki mu wuce airport...." Ta bude ido a hankali tana wani juye juye tace "Anya ma da jirgin xuwa Nigeria direct kuwa yau??? stopovers....." Yyi mata wani tsawa kafin ta karasa yace "Tashi ki dau kayanki ki fita ki samu wani wajen xama har a samu plane din Nigeria, not here anymore" ta marairaice tace "Toh amma ae ka jira inyi wanka in shirya tukun mana Jayyy" tana fadin hka ta mike tsaye dab da shi, ya dauke kai ya bar wajen, wayarsa ya nufa ya dauka ya ga miss calls din Mami har Uku, xaro ido yyi don kullum ana idar da sllh asuba yake shiga asibitin with breakfast, fita yyi dakin da wayarsa in a haste, sae da ya tsaya hanya ya siya masu breakfast snn ya wuce asibitin.... Mami na xaune kusa da Heedayah dake shan shayi a saman gado da kwai da bread, she looks very strong, an kuma sauya mata eye pads din idonta, tana jin an bude kofa ta dakatar da shan shayin tace "Mami Yaya ne?" Mami dai bata ce komai ba sae kallon Junaid take daga sama har kasa, coz duk a birkice yake, snn bai ta6a shigowa asibitin da jallabiya ba, kansa a kasa yace "Ina kwana Mami" Mami ta amsa ta dauke kai ta ci gaba da danna wayarta da take, yayi kasa da murya kamar munafuki yace "Mami na makara ne yau wllh...." Still bata kallesa ba tace "Ehh na ga alama" Yace "Ga breakfast...." Tace "Don't worry an kawo mana" Da mamaki ya dago kansa yace "Who??" Kafin tace komai aka bude kofar ward din ya juya don ganin wanda xai shigo.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Sudais ne ya shigo ward din shi ma yana kallon Junaid kamar ynda Sudais ma ke kallonsa, Heedayah tace "Mami waye? Ya Sudais?" Mami tace "Eh" Sudais ya nufi Junaid yana murmushi ya basa hannu suka gaisa, Mami tace "Har ka dawo" Yace "Ehh na dawo Mami" kujera ta nuna masa ya xauna, Shi dai Junaid na tsaye har sannan ya ki yrda su hada ido da Maminsa, Heedayah tace "Yaya me ya sa baka xo tun daxu ba sai yanxu, Ya Sudais ne ya kawo mana breakfast fa" Ya d'an kalleta yace "Ban xo din ba" Ta buda hannu ta tabe baki tace "Ae kai da Mami" Sudais dake murmushi yace "Ko dai shi da ke?" Washe hakoranta tayi bata ce komai ba ta ci gaba da shan shayinta, can ta ajiye cup din tace "Ya Sudais me ya sa baku xo da kaka ba, Ina missing dinta" a hankali ta kara da cewa "I am also missing Abba" Sudais yace "Xa su xo in sha Allah" Junaid dake ta tsaye ya dake ya kalli Mami yace "Mami xan je in dawo" Bata ko kallesa ba tace "Ohk" a hankali Heedayah tace "Yaya Ina xaka kuma? You are just coming fa" Yyi banxa da ita ya fita dakin.... Rai bace ya koma hotel din ya bude kofar room din ya shiga ga mamakinsa Salima kara gyara ma kayanta wajen xama tayi, ga gadon ta gyara sa fess sae kamshi ko ina yake amma bata dakin, daukar kayan yyi ya fito fuska daure har haraban hotel din ya nufi gun masu gadi nan ya bar masu kayan bayan ya sanar masu me shi xata xo ta amsa, yana komawa ya ga handbag dinta a dakin, har ya dauka sae ya tsaya ya bude ciki, duk tarkacen kayan kwalliyanta ne ciki da prophylactic na mata har da maza and different types of pills ciki har da aborticide, ya girgixa kai cike da takaici ya rufe jakar ya fita dakin ya kai can gun masu gadi sannan ya koma dakinsa, wanka yyi ya shirya ya d'an kwanta, gaba daya jin sa yake wani iri, bayan kusan minti talatin ya mike a hankali ya dau wayarsa ya fita ya kulle dakin da makulli ya bar hotel din. Asibiti ya koma kafin ya shiga ya kira line din Salima, ba bata lkci ta daga tace "Jayyy" ya wani daure fuska kamar tana ganinsa, strictly yace "Ga kayanki can gun masu gadi na ajiye ki dauka, and don't ever try calling my line again idan ba haka ba xa ki sha mamaki, I repeat don't try calling my line again...." Salima ta marairaice tace "Ban gane kayana na gun masu gadi ba jay, me ya kai kayan gun masu gadi juma? Ai na dau spare key kafin in fito" shiru Junaid yyi da mugun mamaki jin abinda tace, can ya ciro makullin aljihunsa yana kallo, wani tsawa yyi mata yace "I swear to Allah kada ki yrda in dawo ya in sameki hotel room din nan, duk abinda na maki ke kika ja ma kanki kinji na rantse...." Ta fashe masa da kuka tace "Toh wai ina kake son in je yanxu Jay? Bayan na gaya maka wanda ya kawo ni ma yyi blocking dina kuma bani da kudin komawa Nigeria? Haba Jay sai kace baka ta6a sanina ba" cikin fushi yace "Good... nima ynxu xan yi blocking din naki but before then I am still warning you kada ki yrda in dawo in ganki dakina, wllh sai na maki abinda baki yi tunani ba" Bai jira cewarta ba ya katse wayar yayi blocking din nata sannan ya shiga cikin asibitin trying to calm himself, shi ma ciki bai wani ga fuskar Mami ba hakan ya sa ya fito haraban asibitin ya xauna.... Har aka yi azahar Junaid na xaune ne haraban asibitin ya ki shiga ward din, bayan azahar kuma Sudais ne ya fita ya siyo masu abinci ya kawo, Mami na xuba ma Heedayah, Heedayah tace "Mami ko dai Yaya ya wuce ne?" Mami bata ce mata komai ba, Sudais yace "Yana waje, ko xa ki je?" Ta make kafada tace "Aa ba ruwana da shi ai" Da daddare bayan isha Junaid ya shigo ward din da dinner da ya siyo masu, Mami da Heedayah ne kadai dakin Sudais baya nan, Yana ajiye masu kuma yace "Mami xan tafi in kwanta" Mami tace "Good, Ka jira Sudais he went to get something sai ku tafi tare" Da mamaki yace "I tot yyi lodging hotel ai" Mami tace "Yes he did, amma nace ku tafi tare naka hotel din" Junaid yace "Ohk" daga ya nemi waje ya xauna ya d'an kalli Heedayah bai ce komai ba ya fiddo wayarsa yana dannawa silently, sai wajen takwas da rabi Sudais ya shigo ward din ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Mami Abba ya kira ku?" Mami tace "Yes Ina sllh ya kira but I followed the call yanxu" yace "Ohk" ya dau apple daya ya kama hannun Heedayah ya saka ciki, kin sake hannunsa tayi a hankali tace "Thank you...." Mami tayi murmushi bata dai ce masu komai ba, kallonsu kawai junaid ke yi amma ba directly ba, Sudais na juyowa ya maida idonsa saman screen din wayar dake hannunsa da sauri, Mami tace "Sudais kai yake jira ku tafi hotel ynxu" Sudais yace "Ohhh but ai nayi lodge a wani hotel Mami" Mami tace "Noo, ku tafi tare, you two should stay together" Junaid dai idonsa na kan wayarsa amma Mami yake saurara, can ya mike ya maida wayar aljihu yace "Toh sai da safe Mami" Daga haka ya nufi kofa, Mami bata tanka sa ba tace "Sudais baxa ka debi fruit din ba, ai sun yi yawa" Yace "Noo na sha ai" tace "Ohk sai da safe" yace "Allah ya tashe mu lafiya" Heedayah tace "Yaya Sudais byee" yace "Bye dear...." Junaid na tsaye bakin kofa bai fita ba, can ya tabe baki ya fita yyi wucewarsa, Sudais ya bi bayansa duk da har ransa bai so bin junaid ba amma baya son yi ma Mami musu, sai bayan da suka fita Heedayah ta fashe da kuka a hankali tace "Mami kinga yaya bai kulani ba koh, he don't want to talk with me" Dariya ta ba Mami sai dai bata yi ba, Mami tace "Kyaleni da shi xan yi maganinsa" Tunda suka bar hospital din Junaid bai ce da Sudais komai ba, haka shi ma Sudais din, nan ko Junaid is just imagining ace su je hotel din ya tadda Salima a dakinsa, suna isa hotel din suka sauka tricycle din Sudais ya bada kudi, Junaid ya jira aka basa canji sannan suka shiga hotel din a tare, Junaid ya tsaya gun masu gadi yana tambayar ko mai kayan daxu ta xo ta dauka, suka amsa masa da eh, bin bayan Sudais yyi xuwa cikin hotel din, a hankali Junaid ya fara murda kofar dakin ko makullin bai sa ba ya ji kofar a bude, lkci daya xuciyarsa ya fara tafarfasa ya shiga dakin, Sudais ma ya shiga ciki, xaune suka samu Salima da takeaway din abinci tana ci a dakin, Sudais ya tsaya bakin kofa yana kallonta with so much surprise, Mikewa tsaye tayi ita kanta tayi shock din ganin Sudais, Junaid ya nufeta a mugun fusace ya sauke mata wawan tagwayen Mari cikin tsawa yace "Me na ce maki? What did I tell you???" Dafe kuncinta tayi tana kallonsa with shock, can ya fashe da kuka tace "Toh wai ina kake son in tafi bayan nace maka bani da kudi Jay, Banda sbda kai me xai kawo ni kasar nan??" Gun kayanta ya nufa ya dauke jakunkunanta biyu ya bude kofa ya watsar waje ya dawo ya nufota, tana ganin haka ta shige bandaki da gudu ta sa makulli, Sudais na yatsine fuska da mamaki yace "Me ye hadin ka da yarinyar nan? Me ya kawota nan? Dama da ita aka taho" Rai bace junaid yace "Saurayinta fa ta biyo ya koreta shine ta makale min nan, I don't even know her...." Katse sa Sudais yyi yace "Sorry but I can't stay under same roof with this lady, dama na kama hotel I can't just say no to Mami, it's better in koma can, but be careful with this lady she can be cunning" Junaid ya dau jakarsa shi ma yace "Mu tafi hotel din naka, I am not staying here either, dama kudin kwana 15 na biya for this hotel kuma nan da jibi xai yi expire so I prefer leaving too" Sudais yace "Better...." Daga haka suka fita dakin xuwa hotel din Sudais. Salima na jin alamar sun fita ta bude kofar ta leko ganin ba kowa ta fito dakin, ba karamin tsorata tayi ba ganin Sudais, ita a rayuwa ma akwai wanda ta tsana kamar shi kuwa, ko gaisuwa baya hada ta da shi dama, cije yatsa tayi ta xauna gefen gado a hankali tace "Anya ma Junaid din nan na da lafiya kuwa, upon everything yesterday he isn't still moved" Da sauri ta mike ganin bbu jakar kayansa ta tafi window tana lekawa taga Inda suka nufa, tricycle taga suka shiga, ta koma ta xauna ta marairaice tace "Dama Sudais ma na kasar nan ban sani ba??" Can ta gyada kai tayi wani murmushi tace "idan ka san wata baka san wata ba Junaid" Tun da Mami ta tashi yau da asuba take ta fargaba ita kadae don ranan xa a cire ma Heedayah eye pads din idonta, kuma ranan ake sa ran xata fara gani, daren ranan Mami sae da tayi sllh ta roki ubangiji yasa an dace, ya sa karshen wahalan kenan.... Karfe shidda da rabi likitocin suka fita da ita xuwa theatre, Mami dai na xaune bakin theatre din sae addu'a kawai take, ga faduwar gaban da yyi mata yawa, da taji motsi sae ta kalli kofa da sauri amma bbu wanda xata ga ya fito har karfe bakwai da rabi, kukan da ta ji Heedayah ke yi daga ciki ya fi daga mata hankali, tun daga nisa take kallonsa har ya karaso tare da wani likita baindiye walking slowly, likitan ya gaida Mami da ladabi, Mami ta amsa don da shi aka yi ma Heedayah aiki 3 days back, shi ma dai yyi kasa da kai ya gaisheta, ta amsa tace "Ya hanya" Yace "Alhmdllh, ya kokari" tace "Mun gode Allah" baindiyen yayi tapping dinsa a baya da harshen turanci yace sae sun hadu anjima, daga haka ya juya ya wuce, dai dai fitowar wani likita yana kallon Mami yace "You can go in Madam, a Dr will explain everything to you inside" mikewa Mami tayi amma ta kasa tambayarsa ba ayi nasara bane aka ce ta shigo, kuma ta kasa shiga ciki, likitan yayi wucewarsa, kansa a kasa ya nufi kofar shiga theatre din walking slowly, Mami ta bi sa da kallo har ya shiga ciki, Heedayah na xaune saman gadon ta takure waje daya ta rufe fuskarta da pillon saman gadon tana kuka a hankali, likitoci biyu na tsaye suna jiran shigowar Mami, Daya daga likitan da turanci yace "Her brother?" Ya gyada masa kai sannan ya karasa gadon yana kallonta, likitan yyi murmushi yace "Yes it was successful, but it's a new world to her.... And it will take sometime before she will adapt, like... she will have problem with light, Human, infact everything, because she just left the world of darkness" Dago kanta yyi ta bude jajayen idonta a hankali tana kallonsa suka yi ido hudu, lkci daya ta fasa ihu kamar warce ta ga mugun abu, ya rungumeta, jikinta ya dinga rawa gaba daya a tsorace take, duk wnn abun Mami na tsaye bakin kofa tana kallonsu, lkci daya hawaye ya kawo idonta tana hamdala a xuciyarta ta karaso gadon da sauri tace "Heedayah" cikin rawar murya Heedayah na kara shigewa jikinsa tace "Mami tsoro nake ji, kice a rufe min idona" Likitan yace "She will adapt slowly...." wheel chair ya jawo ya ajiye don a maida ta ward dinta in ji likitan, Shuraim ya dauketa har sannan ta ki yarda ta kara bude idonta, bai daurata kan wheelchair din ba ya nufi kofar theatre din Mami ta bi bayansa, da yake abokinsa likita sai da ya fara nuna masa ward din da suke kafin ya kawo sa theater din direct ward din ya nufa, Mami dai na biye da shi, ya bude kofa ya shiga ya isa kan gadon ya kwantar da ita a hankali, har sannan taki yarda ta bude idon, har runtse idon tayi gam, ya saki curtains din ward din gaba daya, ya kuma kashe wuta haske ya ragu sosai, Mami dai na tsaye tana kallonsa, Wani likita ne ya shigo ward din ganin ynda Shuraim yyi ma dakin yace "Very good" daga haka ya juya ya fita, Mami ta xauna gefen Heedayah ta dagota tace "Daughter" a hankali tace "Mami" Mami tace "Bude idon ki" ta girgixa kai cikin rawar murya tace "Ina jin tsoro" Mami tace "Baki son ki gan ni?" Kuka ta fara yi tace "I am scared" murya can kasa Mami tace "Don't be dear, open it slowly" Shuraim dai na tsaye bakin gadon yana kallonsu, a hankali ta fara kokarin bude idon maimakon ta sauke kan Mami sai ta sauke kan Shuraim dake kallonta suka yi ido hudu, boye fuskarta tayi jikin Mami ta fashe da kuka sosai tace "Mami Noo, meye shi din? I saw something" a sanyaye Mami tace "That's Shuraim" Sake dagowa tayi da sauri ta bude idonta har lkcn kallonta yake shi ma suka kara hada ido, knowing her condition sai ya sakar mata soft sweet smile, ta fi second biyar tana kallonsa ko kiftawa bbu sai kuma ta kara boye fuskarta jikin Mami da sauri, Mami na jin yanda xuciyarta ke bugawa, duk wnn abun bata kalli Mami ba har sannan, Mami ta kwantar da ita a hankali, Heedayah ta rufe fuskarta da pillow, har bayan wani lkci bata dago ba balle ta bude ido, Mami xata dagota Shuraim na kallonta yace "Tayi bacci fa" Idan Allah ya amince min xan yi night update later, In sha Allah..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Kwantar da ita Mami tayi ta mike a sanyaye ta tafi kan kujera ta xauna, Shuraim dai na ta tsaye kusa da gadon idonsa kan Heedayah, Mami tace "Kayi breakfast ne?" Xai yi magana aka bude kofar ward din Sudais ya fara shigowa junaid na biye da shi rike da leda, Sudais ya d'an tsaya xae fiddo wayarsa a aljihu ya haska dakin yace "why is it dark here...." Kunna switch din Shuraim yyi ya ja blanket din saman gadon ya rufa Heedayah da shi, da mamaki Sudais ke kallonsa, ya buda ido very amazed yace "You!!!" Sau daya Junaid ya kalle Shuraim ya nufi Maminsa, ganin hka Sudais ya bi bayansa ya ajiye ledan breakfast din hannunsa saman table, nan suka gaida Mami, ta amsa tana tambayarsu night dinsu, Sudais yace "Alhmdllh, ya mai jiki?" Mami tayi murmushi sosai tace "Alhmdllh, she gained her sight, the surgery was successful Alhmdllh" Junaid ya juya da sauri yana kallon Heedayah, he couldn't help it but smile, Sudais wa wara ido yace "Alhamdulillah" a tare suka nufi gadon gun Heedayah, Mami tace "Yanxun tayi baccin, she needs much rest sbda a tsorace take..." Junaid ya kalli Mami da sauri yace "Tsoron me kuma?" Mami tace "Don't forget, she is blind all her life, every image is exactly new to her now, likitan yace sae tayi adapting a hankali" Junaid ya dinga kallon Heedayah cike da tausayinta, can ya bude blanket din a hankali yana kallon fuskarta, Sudais ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, ta gefen ido Shuraim ya dinga kallonsu su biyun, Junaid ya maida mata bargon ganin bacci take peacefully, xagayowa Shuraim yyi yana kallon Mami yace "Xan je in dawo" Mami tace "Ohk" daga haka ya nufi kofa, Sudais ya tabe baki har Shuraim ya fita ward din, Mami na kallon Junaid tace "Ba ku gaisa da shi ba Why?" Junaid yace "It's not necessary Mami...." Mami ta hade rai tace "Ban gane it's not necessary ba" ya juya yana kallonta yace "Did he even do as if he noticed us here Mami" Mami tace "But you met him here ko, Kuma kasan yau ya sauka hanya...." Sudais yyi murmushi yace "To Mami ni da nayi masa maganan kin ga ya amsa? Ko kuma ya nuna ya gane ni" Mami tace "Eh I noticed wnn halinsa ne ai koh" Disgustingly Junaid yace "Mugun hali kenan" Dariya sosai Sudais yyi, Mami ta tabe baki tace "So what's the gain da ba ku gaisa ba ynxu, kamar wasu yara?" Junaid bai kuma ce ma Mami komai ba ya ja kujera ya xauna, Sudais yace "Anyway, Junaid that's just Shuraim... haka nan yake, and am telling you ba da wata manufa yyi hakan ba wllh, he is just different, totally different, he find it hard to speak at times, but he is lovely being with...." Junaid yace "But nima ba da wata manufa nayi hakan ba, I was checking on Heedayah that's why ban ma lura da shi ba ai" Sai kusan karfe sha daya da rabi Shuraim ya dawo dakin, har lkcn Junaid da Sudais na tare da Mami suna mata hira, Kana ganin Mami kasan tana cikin farin ciki, kai kace 'yar cikinta ce Heedayah, Shuraim ya gaidata, Mami tace "But are you sure you've eaten?" Shuraim yace "Na ci" Kujera ta nuna masa ya xauna yana kallonsu Sudais yace "Sannun ku" Sudais ya rungume hannunsa daga xaunen da yake yace "Ciwo mu ka ce maka muke?" Junaid dai danna wayarsa kawai yake bai dago ba balle ya kalli Shuraim, Shuraim bai tanka Sudais ba, Mami tace "Ya ka baro mutanen gida" yace "Duk lfya lau" Mami tace "Kaka ta koma gidan ne" yace "Aa" tace "Ohk" Junaid ya mike ya maida wayarsa aljihu ya nufi kan gado ganin Heedayah na kokarin cire blanket din kan ta, dukawa yyi dai dai fuskarta yana kallonta, ta bude idonta a hankali bayan ta cire blanket din, ido hudu suka yi da Junaid, ta fasa wani ihu, Sudais ya mike da sauri yana kallonta shi ma, Junaid xai kama hannunta ta dinga komawa baya tana ihun, da ta kallesa sai ta kalli Sudais dake tsaye sai ta kara sautin ihunta, duk sai suka tsaya suna kallonta gaba daya, shi dai Shuraim na xaune yana kallonsu, Mami ta nufota tace "What happened daughter, Yaya Junaid ne, with Yaya Sudais, don't shout, they are ur brothers" Ta dinga girgixa kai tana boye fuskarta cikin rawar murya tace "I am scareddd" lkci daya ta juya masu baya gaba daya, ta bude idonta a hankali tsoro karara a fuskarta, hada ido suka yi da Shuraim da ke kallonta don ta direction dinsa ta juya, ta rufe idonta da sauri ta kara budewa, tayi hakan yyi sau uku, d'an murmushin da iyakarsa lips dinsa yyi mata, tayi masa kuri da ido without blinking, Sudais ya xagayo toward direction din Heedayah tana daura ido kansa ta fasa ihu ta boye fuskarta jikin pillow, kofa junaid ya nufa ya fita ward din, Sudais xai karasa gun gadon Mami tace "Let her Sudais" Bai ta6a ta ba kawai ya tsaya, Mami ta iso kusa da ita ta dagota a hankali tace "They are all your brothers Heedayah, Sudais and Junaid" ta fashe da kuka tace "I'm scared" Sudais ya sauke ajiyar xuciya ya juya ya fita ward din shi ma. A hankali ta bude fuskarta jin karan kofa, Hada ido suka kara yi da Shuraim, ta fi second goma tana kallonsa tun daga kansa har kafansa, can ta juya suka yi ido hudu da Mami, a karo na farko kenan da ta kalli Mami, shiru tayi tana kallonta a hankali ta kai hannu fuskarta tace "Mami??" Mami ta sakar mata murmushi, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta jawota jikinta ta rungume ta tace "Yess Daughter" Lamo Heedayah tayi jikinta murya can kasa tana nuna Shuraim tace "Mami what is that?" Mami tace "He is Shuraim" kara juyowa tayi ta kallesa sannan ta kalli Mami, Mami ta gyada mata kai assuring her he is the one, tace "Mami Yaya fa" Mami tace "Ya fita ynxu" Tace "Ya Sudais fa?" Mami tace "Shi ma ya fita" Kallon gadon da take xaune kai ta dinga yi tace "Mami wannan ne bed?" Mami tace "Yess" Mami ta nuna mata windown ward din tace "Wancan kuma window" Kallonsa kawai Heedayah ke yi, Mami ta nuna mata kofa tace "Door" Heedayah ta gyada mata kai a hankali tana kallon kofar, Shi dai Shuraim kallonsu kawai yake, Sakko da ita Mami tayi kasa, ta dinga kallon tiles din tana daga kafarta tace "Mami wnn ne floor?" Mami na murmushi tace "Yess daughter" Mami na lura da yanda take ta kallon jikinta tun daga kafa har hannunta sai kuma Mami ta ga tayi murmushi, Mami tace "Ki ce Alhmdllh" A hankali tace "Alhmdllh" Mami ta rungume ta tana kara hamdala a xuciyarta.... Xaunar da ita Mami tayi saman kujera tace "Let me make you tea now" Heedayah ta gyada mata kai, daga haka Mami ta tafi gun kayan shayin, Heedayah ta juya tana kallon Shuraim, d'aga kai yyi ya kalleta shi ma, tayi masa kuri ko kiftawa babu, ya dauke kansa ya ci gaba da danna wayarsa, har Mami ta kawo mata shayi kallon Shuraim Heedayah take kamar ta samu television, Mami tayi murmushi ta kamo hannunta ta sa mata shayin, Heedayah ta maido da dubanta gun Mami tace "Mami baya magana kaman ke" Mami tace "Yana yi mana, Ya Shuraim ne nace maki" Tace "Noo, I didn't hear his voice, ba shi bane" sai kuma tayi kasa da murya tace "But ya Shureen is wicked, this isn't him, wnn bai yi fada ba" Mami tayi dariya tana kallon Shuraim tace "Talk to her Shuraim" Murmushin kawai yyi shi ma bai dai ce komai ba ya ci gaba da danna wayarsa, Mami ta xauna tana kallon Heedayah da sai da ta gama kare ma Cup din da shayin ciki kallo na kusan minti biyu sannan ta kai baki a hankali kamar me tsoron yin hakan, sai da ta kusa rabi ta cire cup din ta juya tana kallon Shuraim, har sai da Mami tace "Toh shanye shayin mana" sannan ta dauke kai ta ci gaba da shan shayin, tana shanyewa kuma Mami ta amshi cup din ta tafi ta wanke, Heedayah juya ta ci gaba da kallon Shuraim, ya d'an hade rai ya dago ya kalleta, wani ihu ta fasa tayi baya xata fadi ya mike da sauri ya rike kujeran, Mami ta fito da sauri tace "What happened?" Heedayah ta boye fuskarta cikin rawan murya tace "I'm scared" Mami ta dagota ta rungumeta tace "Don't be dear, no one is harming you" ta hannun Mami ta bude ido a hankali tana lekosa kuma, murmushi ya sakar mata, ta janye jikinta daga na Mami ta tsaya tana kallonsa da manyan idanuwanta da suka yi ja, sosai hakan ya ba Mami dariya, Mami tace "Take her out Shuraim kuyi strolling but don't go far..." Yana son ce ma Mami hasken waje xai mata yawa amma kuma bai son yin maganan, Mami tace "Or... we shouldn't, tunda likitocin basu bada umarnin haka ba koh" Shuraim ya gyada mata kai, ta kama hannun Heedayah ta daurata saman gado, ita fa ta samu TVn ta na farko a duniya wato shuraim da ya juya sai yaga kallonsa take keenly, Mami ma ta rasa kan wannan kallon da Heedayah ke masa, mikewa Shuraim yyi daga karshe ya nufi kofa don ya gaji da kallon, da sauri tace "Mami xai tafi" ya juya ya mata wani shegen kallo ta fasa ihu a tsorace ya bude kofa yyi wucewarsa. A waya Mami ke nuna ma Heedayah da ta makale jikinta hoton Abba, Farida, da Junaid.... Da Mami ta tafi sai Heedayah ta sa hannu ta dawo da hoton, sai ta kalla yyi na kusan minti biyu sannan Mami ta wuce, ana haka aka bude kofar, Heedayah ta daga kai da sauri, Sudais ne ya shigo, Mami na nuna mata shi tace "Yaya Sudais, that's him...." Heedayah ta dinga kallonsa har ya karaso yana mata murmushi yace "Hi...." A hankali tace "Hello" yace "You get my voice??" ta gyada masa kai tace "Ya Sudais" Ya wara ido yace "Yess, how are you?" Tace "I'm fine" ta kalli Mami tace "Mami Yaya fa?" Mami ta kalli Sudais tace "Ina Junaid?" Sudais yace "He told me he will be coming back later, ya fita" Mami tace "Ina yace maka xai je?" Sudais yace "I have no idea" Heedayah dai sai kallon Sudais take, ya sakar mata murmushi, ta xaro ido tace "Mami" Mami ta kalli Sudais sannan ta kalleta tace "He smiled at you, smile back" murmushin ita ma tayi kokarin yi masa. Har yamma Junaid bai shigo ward din ba, Mami da Sudais ne kadai dakin, Heedayah ta tambayesa ya fi a kirga, daga karshe Mami ta kirasa, yana dagawa tace "Where are you?" yace "Hotel" Tace "To ka taho yanxu" daga haka ta katse wayarta, ba a dau lkci ba Junaid ya shigo ward din, tun da ya shigo Heedayah ke kallonsa, ya karaso cikin dakin suka gaisa da Sudais ya gaida Mami sannan ya kalli Heedayah, a hankali tace "Yaya" yace "Ba shi bane" Tace "Toh ai muryarsa ne na ji" Ya d'an saci kallon Mami ganin kallonsu take yace "Kin san muryarsa ne kike ihu daxu?" Shiru tayi tana kallonsa, ya karasa kusa da ita ya sakar mata lallausan murmushi ya xauna gefenta yace "How are you?" Ta kai hannu hancinsa a hankali tace "I am fine, is that ur nose" Ya wara idanuwansa yace "Noo it's urs" ta kai hannunta nata tana ta6awa, ya ja mata hancin nata yana murmushi ta mayar masa da murmushin.... Throughout ranan komai Heedayah ta tambaya Mami bata gajiya da bata amsa don she's just so curious, she wants to know everything, idan Mami bata gaya mata ba Sudais xai gaya mata har Magrib, Junaid ne ya kawo masu abinci, wajen karfe takwas xa su wuce hotel dinsu Mami tace "Wai Shuraim fa" Junaid ya nufi kofa, Sudais yace "I don't know, ba mamaki ya koma Nigeria ma" Da mamaki Mami ke kallonsa ya fita yana dariya... Har washegari Mami bata ga Shuraim ba, ta kira Junaid da sassafe tace ya ba Sudais waya, bayan sun gaisa tace "Ka turo min lambar Shuraim" Sudais ya amsa mata da toh, cikin few seconds kuma ya tura mata, dialing number tayi, yana fara ringing aka daga, tace "Where are you..." Yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, kana Ina ne?" Yace "Ina Abuja" Tace "Abuja?" Yace "Ehh, tafiyar ya xo min a gaggawa ne" tace "Toh yayi kyau" daga haka ta katse wayarta. Dariya Sudais ya dinga yi da Mami ta gaya masa Shuraim na Abuja, yace "I told you, ni nasan ba karamin aikinsa bane, kadan daga abinda xai aikata kenan" Junaid yace "That's foolishness" Mami dai bata ce komai ba... Haka suka ci gaba da kula da Heedayah da ta fara sabawa da abubuwa da dama yanxu, likitocin har suka bada izinin a dinga fita da ita ana xaga clinic din, xuwa ynxu ta daina tsoron jama'ah sai dai fa idan taga cinkoson jama'ah jikinta ya dingi rawa kenan, bata son crowd, a haka likitocin suka sanar ma Mami xa su sallamesu nan da kwana uku. A bangaren Salima kuwa, hotel hotel ta dinga bi tana kwana har ta samu ta harhada kudin komawa Nigeria, sai da a ranta ta dau kudurin bata kyale Junaid ba.... I'm not feeling well today, ayi manage da wnn plss.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mami na xaune office din likita a ranan da aka sallamesu asibiti yana bata conditions na kula da idanuwan Heedayah idan sun koma gida, do's and don't kawai yake xayyane mata, sosai Mami ke sauraronsa don ko kadan bata son a samu wani matsalan, da turanci take tambayarsa ko har kwana Heedayah xata dinga yi da Glasses din nata da aka bata, ya amsa mata da A'a, amma.... throughout the day the glasses should be on her eyes ko bandaki xata shiga, nan ya kara sanar ma Mami after wata shidda xa su dawo for check up yana nan rubuce takardan da aka bata, godiya Mami tayi masa sosai sannan ta fita office din, dole hotel xa su koma don sai dare jirgin Nigeria xai tashi, A cikin Tricycle din da xai kai su hotel din Heedayah ta rufe idonta jikin Mami don duk Inda ta kalla mutane ne in group kuma hakan na rikitar da ita ba kadan ba ga kuma Haske da yyi mata yawa sosai wanda tun asibiti hakan ke sa mata ciwon kai, Bayan sun shiga dakin hotel din Heedayah na kallon Sudais tace "Ya Sudais why are some people black and others White in color??" Mami dai tayi dariya bata ce komai ba, Sudais ya dawo kusa da ita ya duka yace "The black are the Africans, and the white may be indians or Americans...." Shiru tayi tana kallonsa, can ta kalli Mami tace "Is Mami an Indian also?" Junaid dake tsaye jikin window yana danna waya bai ko kallesu ba, ya d'an yi murmushi amma bai dago ba still, Mami tayi dariya tana jiran jin me Sudais xai ce mata, Heedayah ta kalli hannunta tace "And I am also white, does this mean I am an indian?" Sudais ya d'an juya manyan idonsa yace "Noo Neither Mami nor you are Indians...." With confusion Heedayah tace "But how, we are white also" Sudais yace "Ohk let me explain to you better, but ur brain is small to understand my explanation..." Heedayah ta xaro ido tace "Ohk wait... is yours big?" Dariya Sudais yyi yana kallonta yace "Yess" tace "shi sa kanka kato ne, nawa karami?" Ya gyada mata kai yana murmushi, tace "To idan nawa ya kai kmr naka sae ka min explanation din?" Sudais yace "Yess dear" Kofa Junaid ya nufa, Mami ta bi da sa kallo tace "Where to?" Yace "I will be back soon Mami, I want to get something" Heedayah tace "Yaya should I accompany you?" Juyawa yyi yana kallonta bluntly yace "Noo" Ta wani tabe baki ta juya masa idanuwanta tace "Just pulling ur legs, I am going no where" Bude kofar yyi ya fita, Sudais dai yyi murmushi kawai, Mami ta kamo hannunta tace "Heedayah yayanki ne fa kike masa rashin kunya" Heedayah tace "Mami shi ma fa ya min rashin kunyan, daxu da safe he even pinched me, Sudais yace "Idan kina yi masa haka zae xaneki ne one day, and bbu ruwana" Heedayah tayi shiru sai kuma tace "Shi ma Mami xata zanesa ae" karfe bakwai da few minutes jirginsu ya tashi daga india xuwa Nigeria... Ganin ynda Heedayah ke bin kowa na cikin jirgin da kallo Mami ta jawota jikinta tace "Kiyi baccin ki" tace "Mami su ma duk gidanmu xa su je wajen Abba?" Mami bata san lkcn da tayi dariya ba tace "Nooo dear, but we are all going to Nigeria that's our country" Heedayah tace "Toh Ina xa su je su" Mami tace "Nigeria is a very large County with 36 states ba kin sani ba??" Heedayah ta gyada mata kai, Mami tace "Toh everyone u are seeing inside this plane is going to various state, some Kaduna, other kano, and so on" Heedayah tace "Jirgin ne xai kai mu gida wajen Abba?" Mami tace "Noo mota xa a kawo airport sai mu shiga a kai mu gida" A Hankali Heedayah tace "Ohk" daga haka tayi lamo jikin Mami nan da nan bacci ya dauketa, Sudais da Junaid na xaune daga bayansu, sai da suka sauka Abuja Nigeria da asuba Mami ta tada Heedayah suka sauka jirgin tana rike da hannunta, sai makalewa take jikin Mami don bata son kowa ma ya ta6a ta cikin masu saukowa kallon dodo take masu, ta dinga bin ko ina da kallo bayan sun sauka jirgin tace "Mami babu Light a Nigeria din dama?" junaid ya kalleta kafin yace komai Mami tace "Noo, asuba ne har yanxu ai, anjima xaki ga haske ko ina dear" ta kalli Junaid xata yi magana sai kuma tace "Ohh not you, Yaya Sudais a nan xa mu bar jirgin mu tafi?" Junaid yace "Aa xa a daura maki a kai ne ki kai gida" Ta kalli Mami tace "Mami kin gansa ko? Nice xan iya daukan jirgin a kai na?" Mami tace "Aa sai dai shi a daura masa a nasa kan" Heedayah tace "Toh Mami ai shi ma baxai iya ba, naga kato ne ai jirgin" Sudais ne ya samar masu Taxi cab yana kallon Mami yace "Train station din xa mu wuce?" Mami tace "No this 4 am, mu tafi gidan sister na, xuwa biyar da rabi sai mu wuce station din" yace "Ohk" cikin mintuna kadan suka isa gidan Hajiya Asiya, sosai matar ita ma tayi murnar ganin anyi sa'ar aikin duk da suna chatting da Mami tun a India Mami ta sanar mata Heedayah ta warke, wanka kawai suka yi a gidan suka yi breakfast shi ma da kyar don Hajiya Asiya ta damu su yi, duk suka yi sharp sharp sbda su samu train going to Kaduna da safen, Driver din Hajiya Asiya ya kai su train station din.... Karfe tara da wani abu suka isa train station na Kaduna, duk suka sauka train din.... Mami na kallon Sudais yace "Sun taho daga gidan ne?" Sudais yace "Ehh ya turo min text ya iso" a wajen station din suka ga motar Shuraim a Parke, Bude motar yayi ya sakko Heedayah ta dinga kallonsa irin na sanka din nan har ya iso Inda suke, ya gaida Mami, Mami ta amsa, hannu ya mika ma Sudais sannan junaid da ya dinga danna waya ya ki dagowa har sai da Sudais ya d'an bugesa, sai a snn ya dago kansa ya amshi hannun Junaid, Heedayah dai sai binsu take da ido ganin abinda suke yi da hannu, ganin Shuraim xai juya ta mika nata hannun tace "Ni fa?" Very serious tayi maganan, hakan ya ba Mami dariya sosai Sudais na tayata, Shi dai Junaid murmushi kawai yyi still pressing his phone, Ko kallonta Shuraim bai yi ba ya nufi motarsa, a hankali Heedayah tace "Mami me yasa ni bai min ba?" Mami tace "Maxa ne kawai suke yin haka" Tace "Mami na ta6a ganinsa ranan nan" Mami tace "That's Shuraim" Da sauri Heedayah ta kalleta tace "Shureen?" Mami tace "Yes" back seat Mami ta shiga da Heedayah dake ta kallon Shuraim, Sudais da Junaid suka gama saka kayan a mota, Junaid ya shiga back seat, Sudais ya shiga gaba, Shuraim ya tada motar suka dau hanyar gida... Bbu me magana cikin motar sai Heedayah da ta kafe idonta jikin windscreen komai ta gani sai ta tambayi Mami, Mami kuma ta bata amsa, lkci lkci Shuraim ke kallonta ta madubin gaba, hada idon da suka yi da Junaid ya sa bai sake kallon Madubin ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin suka iso, gida Mai gadi ya bude gate Shuraim ya shiga da motar, Mami ta kalli Heedayah da ta kura ma gate ido tace "We are home" Heedayah ta juyo da sauri tace "Xan ga Abba yanxu?" Mami tace "Yess of course" Bude motar Sudais yyi ya fita, Junaid ma ya fita sannan ya xaga ya bude ma Mami bangarensu, Mami tace "Sauketa" Da sauri Heedayah dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tace "No xan sauka da kai na" Tana fadin haka ta lallaba a hankali ta sauka tana kallon interlock din gidan, Mami tayi murmushi ta fito Junaid ya rufe motar, Abba ne ya fito balcony ya sakko yana kallonsu gaba daya, Mami ta xagayo da Heedayah tana murmushi ta nuna mata Abba tace "There..." Heedayah ta kalli Mami tace "Abba?" Mami tace "Yes, go to him" tafiya ta fara ya a hankali, Abba dake murmushi ya bude mata hannunsa, hakan ya sa ta tafi da gudu, ya rungumeta tace "Abba I can see everything now, I can see you also" tana magana tana ta6a fuskarsa Abba yace "Alhmdllh daughter, now say Alhmdllh Ya Allah" Heedayah tace "Alhmdllh Ya Allah" Junaid da Sudais dai na tsaye suna kallonsu, Abba ya daga kai ya kalli Mami dake tsaye tana kallonsu ita ma, karasawa wajensu yyi yana rike da hannun Heedayah, Yyi patting shoulder dinsu yana murmushi yace "Allah yayi maku albarka my boys, I am so proud of you two..." Duk suka amsa masa da Ameen smiling back at him, Kallon Mami yyi ya nufeta, still smiling yyi mata side hug, karaf a kan idon Mumy da ta makale jikin window a parlon sama tana lekosu tun shigowar motan gidan, ji tayi ta kasa tsayuwa ga wani abu da taji ya soketa a xuciya, bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta sake labulen da sauri, Abba na kallon Mami softly yace "Welcome back Dear Rahinah, Allah yyi albarka, I will for ever be grateful to you.... Knowing you is one of the sweetest thing I can admit to in life, I am so proud of you wife" Mami dai sai murmushi take, tuni Shuraim yyi wucewarsa ciki, Abba na rike da Heedayah tare da Mami suka wuce cikin gidan, ko Abba bai fadi ba you can see how happy he is, ita kanta Heedayah lkci lkci sai ta kalli Abba ta sakar masa murmushi, sai bayan da suka shiga parlor ta dinga bin parlon da kallo kamar munafuka, Rabi'ah da Khadijah na tsaye duk suna jiran shigowar Heedayah, Abba ya nuna mata su yace "Ur sisters" a hankali tace "Hi" ganin yanda Abba ke kallonsu duk suka ce "Hello" Heedayah ta kalli Abba tace "Abba kaka fa?" Abba yace "Anjima xata dawo in sha Allah" Mami na kallon Abba tace "Let me go and freshen up barrister" yace "You need to dear, Allah ya huce gajiya, sai na shigo" Ta amsa da Ameen ta nufi part dinta, Heedayah ta kwace hannunta a na Abba tace "Mami are you leaving me" Mami ta juyo tace "No dear, stay with Abba a little" Abba yace "Mu je ki gaida Mumy" Heedayah bata ce komai ba yana rike da hannunta suka wuce bangaren Mumy. Mumy na bedroom dinta tana waya da Sadiya tana sanar mata ai sun dawo, ynda take kukan a wayan kai kace mutuwarta aka nuna mata, Sadiya tace "Toh wai ke meye na kukan, dama ba jiran dawowarsu ake ba ne, ae ke abun farin ciki ne ma a gare ki da suka dawo yanxu" Cikin kuka tace "Baxa ki gane ba Sadiya dole inyi kuka, dole inyi kuka, rungumeta fa naga Barrister yyi tana wani murmushin kissa, ko kunya bbu a gaban yaran gaba daya ya rungumeta wllh" Sadiya tace "Ita Rahinar?" Mumy tace "Wllh, runguma fa sosai, yaushe rabon ya kama hannuna ni balle ya rungume ni a kan idon wani, a fa tsakar gida ya rungumeta" Sadiya tace "Bbu komai ki kwantar da hankalin ki, da ba mu da mafita ne shine xa ki yi kuka, Amma ga mafita iri iri dai, abu tun yaushe muke baxa idon dawowarsu kuma gashi Allah ya dawo da su lfya" Jin an bude kofa Mumy tayi saurin cewa "Xan kira ki anjima, an shigo parlona" Daga haka ta katse wayar tace "Waye?" Jin shiru ta mike tana kara goge idonta sosai ta fita, Abba ne tsaye yana rike da Heedayah, Mumy ta sake fuska tace "A'a, mutan India har an iso kenan, toh kun sha kabo, Alhamdulillah, Sannun ku da dawowa" Heedayah dai sai kallonta take a tsorace jin muryarta, Abba ya sake hannunta yace "Go and greet her" a hankali Heedayah ta nufi Mumy dake kirkiran murmushin karfin hali Mumy ta jawota jikinta sosai ta rungumeta tace "Alhamdulillah ido ya bude, Alhamdulillah mun gode Allah" Murya can kasa Heedayah tace "Good morning" Mumy ta dago kanta tace "Good morning ya kike, Ina Mamin ta ki?" Heedayah ta nuna mata hanyar waje, Mumy tace "To maa sha Allah, Allah ya huce gajiya" Abba yace "Sai ki samu ki tafi kiyi ma Rahinar sannu da xuwa" Mumy tace "A'a ba abinda xai hana haka ai" Mumy ta xaunar da Heedayah kan kujera tace "Kun yi breakfast kuwa?" Heedayah ta girgixa mata kai, Mumy tace "To bari a hado maki shayi" ganin haka Abba ya fita ya bar Heedayah a parlon, Mumy ta bi sa da kallon gefen ido, can ta kalli Heedayah tace "Kar fa ki fita, Ina xuwa in kawo maki shayi, xa ki ci har da bredi Koh?" Heedayah ta gyada mata kai, Mumy ta nufi kofa ta bude kafin ta fita sai da ta sake kallonta tace "Kar fa ki fita, Ina xuwa yanxun nan in kawo maki kin ji" Heedayah ta kara gyada mata kai, Mumy ta fita da sauri, Mumy na fita da few minutes aka bude kofar sai ga Shuraim ya shigo, Kallonta ya dinga yi daga Inda take xaune with surprise, can ya kalli kofar dakin Mumy ya karasa ya leka ciki bai ganta ba, dawowa yyi ya bude kofar parlon yana kallon Heedayah dake ta bin sa da kallo ya nuna mata kofar alamar ta fita, Tace "Mami tace min door ne... It's a door" ya wani daure fuska, da sauri ta dauke kanta, Ya dake yace "Xo ki fita nace...." Mikewa tayi tsaye da sauri tana kallonsa don ranan ya fara mata magana, kamar munafuka tace "Tea xa a bani da bread" Ya kara daure fuska yace "Fita na ce" da sauri ta karasa gun kofar ta bi ta gefensa ta fita tana waigosa, ganin inda xata bi ya bi bayanta da sauri, ya gwada mata hanya da finger dinsa, part din Mami da ya nuna mata ta nufa, da tayi tafiya kadan sai ta juya taga yana tsaye yana kallonta, sai da ta d'an yi nisa sannan ta juyo ta tsaya tana kallonsa ita ma, ya xare mata ido yace "Baxa ki wuce ba" 6ata fuska tayi ta juya ta nufi kofar shiga parlon Mami hawaye cike idonta tana isa kofar ta kara juyowa ta tsaya tana kallonsa, sun fi minti daya a haka yana kallonta tana kallonsa.... Daukar remote da ke kan kujera yyi, yyi kamar xai jefa mata ta fasa ihu ta durkusa a wajen, da sauri ya juya ya wuce dakinsa, Mami ta bude kofarta jin muryar Heedayah tana kallonta tace "What happened?" Kamar xata yi kuka tace "Wannan da kika ce min Shureen ne, I heard his voice, xai min doka wai" Mami na bin parlon da kallo tace "Ina yake?" Heedayah tace "Ya gudu" kama hannunta Mami tayi suka shiga ciki, Mumy ta fito kitchen rike da cup din shayi da bredi da nama a plate ta wuce parlonta, turus ta tsaya ganin bbu kowa parlon, can ta nufi daki nan ma bbu kowa, ta dake tace "Heedayah?" Nan ma shiru, Ficewa tayi dakin ta wuce parlon Abba, ta samesa dakinsa, rai bace tace "Kai da ka bar yarinyar nan a parlona baka san abinda kke yi bne barrister, Wai daga in je in hado mata kayan kari shine har an shiga an dauketa..." Abba ya dakatar da ita yace "Aa, ta dai fita, wa xai shiga ya dauketa" Mumy tace "Wllh wllh shiga aka yi aka dauketa don na jadadda mata kada ta fita tace min toh, wllh dauketa aka yi" Yace "To wa xai dauketa??" Tace "Oho na sani" yace "To sae ki kai mata can parlon" tace "Baxan je ba wllh, ikon dai da ake nunawa bani da shi a kanta a ci gaba" daga hka ta fice daga dakin rai bace.... Jin shiru shiru Mami bata ga junaid da Sudais ba ya sa ta kira Junaid, nan ya sanar mata wucewa suka yi, fita tayi parlonta ta tafi dakin masu aiki ta bude tana kiran Sajida, wata mata ce ta mike tace "Aa ni ce, Ina kwana" Mami tace "Lafiya lau, Ina Sajidar?" Matar tace "Ni ce sabuwar mai aikin ynxu" Mami tace "Tohhh, to Sannun ki" daga haka ta juya ta wuce xuwa kitchen ta hada ma Heedayah da ita kanta shayi. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Da yamma Mami na xaune main parlor da Hajiya Amina da Hajiya Hauwa, sai colleagues dinta su shidda duk sun xo yi mata sannu da xuwa da gaida Heedayah, drinks da ruwa ne da snacks iri iri a gabansu sannan ga lafiyayyen jollof da isasshen kaza sai coslow a gefe, Mumy dai na xaune parlon ita ma sai kirkiran murmushi take, lkci lkci take jefa nata hirar a hiran da suke, Heedayah na xaune kasa kusa da Mami duk tana kallonsu hannunta rike da roban Fanta, daya hannunta kuma cup cake, bude kofar parlon aka yi Kaka ta shigo sakale da daya dayan handbag dinta da xa a iya saka karamin jariri a ciki, ta sha yafin mayafinta, ko takalmin kafarta bata cire ba ta shigo parlon, biye da ita a baya Hajiya Zuwaira ce matar Baffan Junaid da kawarta sai kanwarta Maimuna, Mami na ganin kaka tayi murmushi ta mike tace "Sannun ku da isowa kaka" A dakile kaka tace "Ehe" Heedayah sai kallon warce taji an kira da kaka take kamar idanuwanta xa su yi magana, sauran matan parlon duk suka shiga yi ma Kaka sannu da xuwa ciki har da Mumy, duk da "Ehe" kaka ta amsa su tayi wucewarta dakinta bayan ta saci kallon Heedayah da ta bi ta da kallo, Mami suka gaisa da su Hajiya Zuwaira da fara'a tana masu sannu da xuwa, kasancewar parlon is occupied tace "Bari mu je can parlon kawai" Sai da ta sanar ma bakinta gaba daya cewar tana xuwa sannan ta kai Hajiya Zuwaira da kawarta da kanwarta parlonta, mikewa Heedayah tayi da sauri ta bi bayanta, Mumy ta bi ta da wani kallo ta gefen ido, Mami ta ciro ma bak'in nata ruwa da lemo a fridge ta ajiye masu tace "Tunda ku na gida ne bari in sallami bakin parlor, abokan aikina ne da matan yayan Barrister, Ina xuwa yanxun Hajiya" Hajiya Zulaiha tace "Ba damuwa Rahinah, mu kam na gida ne" Mami ta fita Heedayah ta bi bayanta da sauri duk da kiranta da Hajiya Zuwaira ke yi, Mami ta kalleta tace "C'mon je ana kiran ki my frnd" a hankali ta juya ta koma cikin parlon ta nufi gun Hajiya Zuwaira, Mami tayi wucewarta... Mami na dawowa main parlor Hajiya Hauwa tace "Kinga ki shiga ki gaida Kaka tana iya cewa ai kin ganta kin shareta, kinsan halin abar tamu...." Dariya Mami tayi tace "Ae kuwa" Mumy tace "Ae haka ma kawai xata ce" Mami tace "Bari in je in dawo" daga haka ta nufi hanyar dakin kaka, dakin masu aiki ta fara shiga, tana kallon sabuwar mai aikin me suna Talatu tace "Don Allah ki debi abinci da su samosa da cake ki kai can parlona akwai baki guda uku" Talatu ta mike da sauri tace "Toh Hajiya" Mami ta juya ta fita ta wuce dakin kaka, kaka na share windanta da tsintsiya bayan ta cire duk labulayen dakin da ma xanin gado Mami ta shigo da sallama, Da fara'a tace "Sannu da isowa kaka, fatan mun same ku lafiya" Kaka ta ajiye tsintsiyar hannunta tace "Ita Deedayar bata da labarin ni na haifi Amadu da ya biya kudin gyaran idon nata ne da har yanxu bata shigo ta gaisheni ba? Kinga Amadu fa bai ta6a sanin yarinyar nan ba wllh, bbu dangin iya balle na baba, to kuma ya ina mahaifiyarsa baxata xo ta gaisheni ba sbda idonta ya budu, to ni da nasan haka ne xai faru da nace ma Amadu ba da yawuna ba idan aka gyara mata idon, ace tun dawowar ku ba ki xaunar da ita kin sanar mata wacece ni da abinda ya kamata tayi idan ta gan ni ba, kin ga rashin gaskiyar jama'ah ko? To ni dai ba ruwana, ai ba wani ya haifar min Amadun ba, kwanana uku ina nakudar sa wllh" Mami da ke ta kallon kaka tace "Toh kiyi hakuri, kuma Heedayah har yanxu ba wai ta gama sakin jikinta da mutane bane, Kar ki manta kaka tun da aka haifeta makauniya ce ita, Kinga da girmanta ta fara ganin duk wani halitta, to banda ynxu da ta fara sakewa ai da ko mutum ta gani ta dingi ihu kenan tana tsoro" Kaka ta daga hannu tace "Toh ni ina ruwana, ni dai ba ni ce na haifi wanda ya tsintota yyi silar gyaran idonta ba, Taimakonta Allah Taimakonta Amadu a duniyar nan, don haka ai ban cancanci raini wajenta ba, baki ga kallon rainin hankalin da naga tana min ba, ni a gaskiya da na sani da an barta a makancen ma kawai tayi ta ma mutane ladabi a hakan" Mami bata kuma ce mata komai ba ta juya ta fita don ranta ya gama baci, Sai bayan da ta fita kaka tace "Wa ya sani ma ko 'yar ta ce ta makala ma Amadu don kawai ya aureta, mutane dai bbu gaskiya" Mami na fitowa ta wuce parlonta, Tayi ma su Hajiya Zuwaira sannu sannan tace "Heedayah taso mu je" Mikewa Heedayah tayi ta bi bayanta suka fita, Mami ta wuce da ita dakin kaka suna isa kofar ta juyo tana kallonta tace "Idan mun shiga ki xauna a kasa ki gaisheta, ita ce kaka" Heedayah ta gyada mata kai sannan Mami ta bude kofar suka shiga dakin, a bakin kofa Heedayah ta xauna tace "Ina wuni" Kaka dake share bangon dakinta ta juyo ta kalleta ta ajiye tsintsiyar tace "Toh ki gode ma Allah ki gode ma d'a na Amadu, kuma ni nan nice kaka ni na haifi Amadun da yyi silar gyaran idonki, ko iyayenki na da rai yau basu da iko a kanki kamar yanda Amadu ke da iko a kanki amma ya xa ayi in shigo kina xaune rike da goran panta da kenk ki kasa ce min komai kin ji kowa na min sannu da xuwa kaka" Heedayah dai sai kallon kaka take, duk Inda ta bi da hannu sai ta kalla kai kace TV ta samu, Kaka ta kalli Mami dake jira ta fitar da Heedayah daga dakin tace "Kin gani ko Rakiya, hararata fa take" Mami tace "Wani harara kuma kaka, ance maki yarinyar har yanxu bata gama sabawa da komai ba, yaushe ma ta fara ganin ki idan ba yanxu ba, sai fa a hankali xata saki jiki da kowa ta dawo kamar ko wani mutum, ynxu haka da xa ki kawo mata mage ko tsuntsu bata san su ba bata ta6a ganinsu ba, sae dai sunansa, to kinga kuwa dole ayi ma mutum uxuri, ranan da idonta ya bude tsoron kowa ta dinga yi, kuna hada ido xata fasa ihu, sbda duk rayuwarta a duhu yake banda ynxu da Allah ya yaye mata" Kaka tace "Haka abun yake?" Mami ta daga Heedayah dake ta xaune tana kallon kaka tace "Sai hakuri kaka, ni xan tafi in ji da mutane" Daga haka ta fita da Heedayah dake waigo kaka... Fitowa kaka tayi tana kallon mutan parlon ganin Mumy tace "Xo Maryam" Mumy ta mike ganin kaka ta nufi nata bangaren ta bi bayanta har suka shige parlon Mumy, Kaka ta xauna saman kujera ta fashe da kuka tace "Rakiya ce ta shigo ta min wankin babban bargo bbu abinda ta mance bata gaya min ba, a takaice dai a baibai kirana tayi da fitinanniya, ni dai ina tsaye bance mata uffan ba ta ja hannun makauniyar da Amadu ya kashe kudi ya warkar suka fita" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Mumy tace "Ikon Allah, to ke me kika yi xata maki haka daga dawowarki" kaka tace "Wllh Maryam daga nace mata Deedayah lafiya bata shigo ta gaisheni ba naga kamar ma hararata take da na shigo ko bata gane ni bane ta min irin wnn kallon, Kar ki d'a d'a kar ki raga, Rakiya ta hau ni da bala'i wai ni bana yi ma mutane uxuri, ai Deedayah a duhu take ynxu Allah ya fito da ita Amadu ya fito da ita haske, Kuma ai dole ta ji tsorona tunda ita ma ta ji tsoronta da suke asibiti, to idan Rakiya na da hankali da tunani sai ta hada kanta da ni? Ni fa na haifi Wanda yayi silar warkewar Deedayan" Mumy ta hade rai tace "Gaskiya wnn raini ta maki, bata kyauta ba, gani take ta fi kowa Iko da yarinyar a gidan nan daxu fa daga Barrister ya kawota parlona na fita kitchen hada mata shayi matar nan ta shigo ta dauke ta" kaka tace "To kuwa ta ci kanta, Kuma sai na sa an karbe Deedayan hannunta in ga ta tsiya, idan ma Amadu baxai bani ita ba ke ya baki ki rike, abinda ma xai faru kenan wllh wllh, a ina take da iko da yarinya bayan ita ma makalewa tayi aka aurota dalilin yarinyar, da ba don yarinyar ba mu muka san wata Rakiya" Mumy tace "Ae shine, ni wllh a bani ita dama lkcn can shaidan ne ya shiga xuciyata ya hanani amsar ta amma wllh tllh ynxu xuciyata daya xan amsheta in riketa kmr yanda xan rike d'an cikina, abinda yarinyar har ta fara sabawa da ni da suka dawo har ta kusa awa biyu a parlona" Kaka tace "Toh kin ga dai, bari Amadun ya dawo shi ma gantalalle, xan ji ko maganan Rakiya xai dauka ko tawa" Mumy tace "Atoh dai" mikewa kaka tayi ta fita parlon, Mumy tayi wani murmushi ta xauna tana kara naxarin maganganun Kaka. Kafin Magrib duk bakin gidan suka watse har ma da makota da suka shigo duk da basu wani san Mami ba sai Mumy, suka yi mata sannu da xuwa suna ma Heedayah barka suka fita, Mami da kanta ta taimaka ma Talatu gyaran gidan don kai kace wani karamin walima aka yi a gidan, Mumy kuwa ta shige bangarenta da yaranta ta kulle kofa don ma kar su dauke ko da cup, Duk inda Mami tayi Heedayah na makale da ita, Mami har ta gaji da ce mata taje ta xauna ta kyaleta, Mami na kitchen suna gyaran kitchen din aka yi Magrib, sai da Mami ta tabbatar ko ina ya dawo fess ta fito parlor tare da Heedayah ta bar talatu ta karasa wanke wanken, Kaka ce ta fito dakinta, Mami tace "Sannu kaka, abincin ya ishe ku ai koh?" Can ciki kaka ta amsa tace "Ya Isa..." Daga haka ta nufi bangaren Mumy tana rike da wayarta tana cewa "Ina Maryam ta kira min Junaidu shiru ni ban gansa ba, ko a indiyar suka baro sa" Mami dai bata ce mata komai ba har ta shiga bangaren Mumy, Mami ta wuce nata bangaren da Heedayah. Bayan isha Abba na parlonsa tare da Shuraim sai su Rabi'ah da Khadijah, Mami ta shigo ciki da sallama holding Heedayah's hand, Gun Abba Heedayah ta nufa ta xauna tace "Abba sannu da dawowa" Yyi murmushi yace "Yauwa daughter, hope kinyi bacci da yawa daxu" ta gyada masa kai, Abba ya maida dubansa kan su Khadijah on a serious note yace "As I was saying, today should be the last day da yayanku xai maku fada ko ya doke ku ku je ku gaya ma Mamarku" Rabi'ah tace "Abba ba mu muka gaya mata ba fa, she just came in" Abba yace "Whatever.... Na gaya maku ni dai...." Abba ya kalli Shuraim yace "And you Shuraim duk ranan da suka kara fashin makaranta you do what ever you wish to them, don't think twice before punishing them" ya girgixa kai kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Abba it will be good idan Mumy tayi hakan, ni babu ruwana da lamarinsu a gidan nan, beside she said I should take my hands off their issues" Abba yace "And I am instructing you to keep on disciplining them, ko ban isa?" Bai kuma cewa komai ba, Mami na kallonsu tace "Ku kuma sai kace wasu yara xuwa islamiyyar ne ku ke fashi, amma ai ban ga kuna fashin boko ba" Basu ce mata komai ba, tace "That's bad, you two should stop that" Abba yace "Nan da one week Heedayah will join them also, kafin sati dayan an nuna mata abubuwan da ya kamata ta sani facially since ta san karatu gani ne kawai bata ta6a yi ba" Mami tace "Allah ya kai mu" Bude kofar parlon aka yi, kaka ta shigo, Ko gaisuwan da ake mata bata amsa ba tace "Amadu baka san na dawo bane baka shigo ba? Tun fa yamma nake gidan nan" Abba yace "Aa dama Ina kokarin shigowa ne, Ina son in gama da su" tace "To ai dai nice dolen ka ba su ba koh?" Wani kallo Shuraim ya watsa mata, Abba dai bai ce komai ba, ta nemi waje ta xauna, Mami tace "Sannu kaka" kaka tace "Ehe" Abba yace "Ina yini Baaba" tace "Lafiya lau, Ina son magana da kai ne Amadu" Abba ya kalli su Rabi'ah yace "To na gama da ku" mikewa Mami tayi Heedayah na ganin haka ita ma ta tashi daga kusa da Abba, Kaka tace "Aa Ina kuma xa ki Rakiya koma ki xauna" Rabi'ah da Khadijah xa su fita kaka tace "Kai ku kira min Maryam idan kun fita" Abba dai sai kallon kaka yake, can yace "Lafiya dai ko kaka?" Tace "Eh lafiya lau" Bai kuma cewa komai ba sai ga Mumy ta shigo da sallama, ta nemi waje ta xauna tayi ma kaka sannu sannan tace "Ga ni kaka" Kaka tace "Toh Amadu shawara na xo baka idan kana son xaman lafiya a gidan ka...." Abba yace "Shawarar me fa?" Kaka tace "To wai me yasa baxa ayi ma Maryam kara ba a bar mata Deedayah wajenta tunda dai ta nutsu tayi hankali, ita Rakiya ba xama take ba aiki safe, rana, yamma, Ina jin har dare ma wani lkcn, to ni kuma a ynda nake ganin wnn Deedayar fitsararriya ce naga alama, don daxu bata san ina lura da ita ba ta harareni, kaga kuwa idan nace ta xauna wajena idan Rakiya ta fita kasuwancinta ai xagi na yarinyar xata dinga yi wataran in shiga uku, jikokina basu ta6a xagina ba ita ta xageni...." Da mamaki Abba ke kallonta, Mami dai bata ce komai ba kuma bata kalli direction dinsu ba, kaka ta ci gaba tace "Tunda dai ita Maryam xaman kashe xani take a gida bbu aikin fari balle na baki ba gwara a bar yarinyar gun ta ba sbda tarbiya, ni dai tun ba aje ko ina ba naga ta rainani balle ace ta xauna gu na" Mumy tace "To ai bbu komai ko ma gun wa ta xauna kaka, in ma gu na in ma gun Rahinar..." Kaka tace "Oh oh ai Rakiya aiki take fita kullum, ke dai me xaman banxa ya kamata a baki ki sa ido kan lamarin ta don naga yarinyar na bukatar sa ido, sakakkiya ce, ta xata a duhu take har ynxu" Shuraim dake sauraron kaka yace "Xai fi idan aka kai ta boarding a can xa a koya mata ladabi, xa kuma ta gane cewar ba a duhu take ba yanxu" Da sauri Mumy ta juya ta kallesa, Abba yace "Ehh in sha Allah boarding xata fara kamar yanda Shuraim yace" Kaka tace "Meye kuma boding?" Shuraim na kallonta yace "Makarantar kwana" Kaka tace "Amma kai axxalumi ne Shureen, me Deedayar ta tsare maka a gidan da kake son a kai ta makarantar kwana, Kai da aka ta6a kai ka kana yaro ka xauna?? Ba gudowa ka yi ba, to meye kuma xaka ce a kai marainiya??" Mumy tace "Toh makarantar kwanan da ake kwashe yara ma, wnn ae gurguwar shawara ce" Shuraim yace "Ae ba na gwamnati xa a kai ta ba" Kaka tace "Ni dai ba ruwana da muguntar ka na fulani, me xa mu ce ma Allah idan aka kwamushe 'yar mutane" Abba yace "Makarantar da Farida take ynxu xa a sa ta in sha Allah, boarding ce me kyau" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Kaka tace "Aa to ni tsorona kada a sace ta ne Amadu mu shiga uku" Abba yace "Aa lafiya lau, bbu wata matsala in sha Allah" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa kansa a kasa, Mumy ta bi sa da wani irin kallo xuciyarta na tafarfasa, Mami na lura da kallon da uwartasa ke masa har ya fita parlon, Abba ya dau wayarsa dake ring ya mike yace "Bari in amsa kira in dawo Baaba" mikewa kaka tayi tace "Aa to ni kuma me xan tsaya in maka, dama shawara ce kawai na kawo, amma tunda bafillatanin d'an ka yace a kai ta makarantar kwana kuma ka amince ai shi kenan, amma a gaskiya idan wani abu ya sami yarinyar nan baxan yafe maka ba baxan yafe ma Shuraim ba, don da kai ka haifeta baxa ka yi mata sha'awar xuwa makaranta kwana ba, me yasa baka kai 'ya yan cikin ka ba sai ita?? Shi dai rikon amana dama da wahala take sai wanda Allah ya ba..." bata jira cewarsa ba ta fice daga parlon, Mikewa Mami tayi ta nufi kofa Abba ya bi ta da ido har ta fita, Mumy ma ta mike ta fice daga parlon bacin ranta ya kasa boyuwa gaba daya, dakin Shuraim ta wuce direct ta samesa ya shimfida darduma ya dauko qur'ani ya xauna, cikin daga murya tace "Aliyu a kan uban me yasa kace a kai yarinyar makarantar boarding?" Shuraim dake kallonta yace "Aa, naga kamar ba wani son xamanta gidan ake ba...." Tayi masa wani tsawa tace "Uban waye yace maka baya son xamanta gidan?? Kai da wa ku ka yi haka?" Yace "No naji kaka ta ce ta fara rainata, so it's better we shouldn't let that go far..." A fusace Mumy tace "Toh kai Ina ruwanka da xancen da ka tsoma baki? Dangi uwa ko ta uba? Meye hadin ka da ita da har xaka bada shawara kan lamarin ta iyye? Meye damuwar ka da ita nace?" Yana bude qur'anin gabansa a hankali yace "Nima din ban fiye son ganinta a gidan bane shi yasa na kawo nawa shawarar for my own good" Mumy ta jefa masa wani shegen kallo tace "Sau da nawa da nawa kake xaman gidan idan ba gulma da munafurci ba Aliyu?? Sati da lahadin da kake dawowa yi a gidan ne xaka wani ce kai ma ba ganinta kke son yi ba? Uban ma me ta tsare maka tukun? To ynda ka kawo shawarar a kai ta makarantar kwana sai ka koma kace a sa ta a day, in har kana son wanyewa lafiya...." Da mamaki yake kallon Mumy yace "Toh Mumy ke kuwa meye na ki idan an kai ta makarantar kwana? Naga kema ba wani son xamanta kike a gidan ba fa, so it's better she should stay away from this house completely, hankalin kowa xai fi kwanciya, ni na xata ma xaki fi kowa murna da shawarar da na bada, I see no reason da xa ki daga hankalin ki don ance xa a kai ta boarding, sai dai idan da akwai wani abun daban..." Mumy da ta bude baki tana kallonsa tayi shiru ta kasa cewa komai da farko, can ta dake tace "Akwai wani abun kamar me, ban fahimta ba?" yace "No nima ban sani ba, kawai dai nayi tunanin haka ne" Ta hadiye abu da kyar tace "To bari in fito maka a mutum yanxun tunda ba tsoron ka nake ba Aliyu, ban ga dalilin da xa a kai yar tsintuwa tsadadden makarantar kwana da ya fi makarantar da 'ya yan masu gida ke xuwa ba, baxan laminta da hakan ba" wani murmushi Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "But ke kika ce baki da ra'ayin a kai su Khadijah makarantar kwana lkcn da na kawo ma Abba shawaran haka few years back, amma in har yanxu kinga kina son su je, ni xan yi ma Abba magana baxai ki kai su ba su ma" Tsawa Mumy tayi masa tace "Wai ban gane alkiblar ka ba Aliyu, kare yar tsintuwar kake yi kke challenging dina ko kuma shawara da ban bukata daga gareka ba kke bani?" Ya girgixa kai yace "Aa ko daya" Tana nuna sa on a serious note tace "Toh tun wuri idan ba haduwa kake son yi da fushina da bala'i ba duk wani abu da ya shafi lamarin yar tsintuwar nan kada ka sake sa baki, nace kar ka sake, bbu ruwanka da duk wani lamari da ya dangance ta ko da kuwa Ubanka ya tambayi opinion dinka, just remain mute" A hankali yace "What if i am also trying to find a way out for my self, as in.... May be I am not comfortable living in the same house with her also, Nima ina neman mafita...." Mumy tace "Toh sai ka tsiri cewa a kai ta makaranta me tsada, Ina aka kai makarantun gwamnati da xaka kira Turkish??" Yace "Sbda hakan kadai xai ba ma Abba karfin gwiwar kai ta, idan da na gwamnati nace a kai ta Abba baxai kai ta ba" Mumy tace "Toh ni ba ruwana da duk wnn, ni kawai ka san ynda kayi ka sa a fasa ma kai ta boarding din gaba daya" Yace "Toh" tace "Toh me??" Yace "Toh in sha Allah" Tace "I am serious Aliyu kada ka raina min hankali" yace "Ehh xan kara yi ma Abba magana in sha Allah" Juyawa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo har xata fita ta juyo tace "Toh yau litinin me ya hanaka komawa Zarian ma?" Yace "Sai Wednesday in sha Allah" Mumy tace "Ba dai degree kake ba Masters ne, idan xaka tsaida hankalin ka gu daya ka tsaya kayi karatu tsakani da Allah ka tsayar, ni ban ma ga amfanin weekend da kke dawowa ba, Sudais idan ya tafi ba sai bayan watanni me yawa yake dawowa ba, kai kuwa kamar wanda ake mintsili ko kuma wanda yyi wani ajiya a gida yana dawowa dubawa a kai a kai" tana kai wa nan ta fita ta kulle kofar, mayar da dubansa yyi saman qur'anin gabansa ya d'an yi murmushi cikin cool voice dinsa ya fara karatu. Washegari da safe Mami na kitchen tare da Heedayah tana gwada mata yanda xata dinga hada shayi da kanta, A hankali Heedayah ke diban madaran kamar tana tsoronsa har wani rawa hannunta yake yi sai ta xuba a cup, Mami tace "Look, ki nutsu... Ko me xaki yi ki dinga yi gently don't panick, now fetch the Milo also..." Heedayah ta kai cokalin cikin Milo din ta debo, yamutsa fuska tayi tace "Mami me yasa kalan shi haka? And..." Mami ta dakatar da ita tace "Deba nace ki na batan min lkci xan tafi in shirya" Sake debo milon tayi ta xuba a cup, Mami tace "Sugar kuma cube uku xaki dinga sawa" Heedayah ta kirga cube din sugar din ta xuba a cup din, Mami bata bari ta dau flask din da kanta ba don a cike yake, ta xuba mata ruwan xafin cikin cup din dake dauke da kayan shayin, Heedayah sai kallon tiririn dake tashi take ko kiftawa bbu, Mami ta dau bottle water ta karasa cike cup din tace "Idan baki son yyi maki xafi sosai sai ki kara ruwan sha a ciki" Mami ta rufe gwangwanayen madaran ta ajiye su gefe da sugar, daga kai Heedayah tayi suka yi ido hudu da Shuraim da ya bude kofar kitchen din, Mami ma ta juya, sauke kansa yyi yace "Ina kwana" Mami tace "Lafiya lau" ya juya xai fita Mami tace "We are not stopping you from doing what u came to do" Ya d'an tsaya kamar me contemplating ya fita ko ya shiga kitchen din, can dai ya shiga ya tafi gun da mug suke ajiye, Heedayah ta bi sa da kallo, ya dau daya ya dawo xuwa gun flask, a hankali Heedayah tace "Mami shima shayin xai yi ya sha?" Mami tace "Ina ruwanki??" Bin bayan Mami Heedayah tayi ganin xata fita kitchen din da cup din shayin, sai da suka isa kofa ta juya tana kallon Shuraim da ya bi ta da ido shi ma, hade rai tayi ta murguda masa baki har da juya manyan idanuwanta, sai kuma ta fita kitchen din da sauri tana bin bayan Mami. Mami na gama shiryawa, Ta tabbatar Heedayah ma ta gama shiryawa suka fito main parlor a tare ta kulle kofarta, Shuraim ne xaune parlon yana kallon wrestling, Heedayah na kallon Tvn tace "Mami me yasa basu sa kaya ba kamar mu, nima xan iya tsayawa haka??" Mami tace "Ehh tunda baki da hankali" Daga haka ta wuce dakin kaka, Heedayah na biye da ita kamar xata yi kuka, waigo Shuraim tayi ta turo baki ganin yana kallonta ta shiga dakin kaka, bayan Mami sun gaisa da kaka tace "Kaka xan tafi gun gidan Baffansu Junaid" Kaka tace "Au haba, can xa ki yini kenan yau?" Mami tace "In sha Allah" Kaka na kallon Heedayah kafin ta ce komai Mami tace "Go down now and greet her" Heedayah ta durkusa kasa tace "Ina yini kaka" Kaka tace "Toh mu dai ba mu yini ba tukun, da safiyar Allah kice Ina yini?" Mami ta dago Heedayah tace "Toh bari mu je kaka" Kaka tace "Au tare xa ku?" Mami tace "Ehh tare xa mu tafi" Kaka tace "To Amadun ya sani kuwa, don naga bai fiye son ana fita da ita ba" Mami tace "Ya sani" Kaka tace "Toh ki dai kula da ita, ita kuma Hajiya Zuwaira kice Ina gaisheta, Allah yayi mata albarka, mata me mutunci, har na bar gidan girmama ni take ke kyace ni na haifeta, kayana kuwa kullum sai ta sa masu aiki sun wake sun goge min, to bata fiye min wasu ba ma ni, jira in dibar maki kaikayi koma kan mashekiya ki kai mata, kuma kice nace Allah ya mata albarka" Tuni Mami ta fita dakin bayan kaka ta kulle mata iccen hayaki a leda ta amsa, Heedayah dai sai waigo kaka take, kaka tace "Ni dai aniyar ki ta biki, ban gane kan kallon nan ba..." Suna shigowa main parlor Mami ta nufi kofar fita, Shuraim dake xaune har sannan yana kallon wrestling ganin sun hada ido da Mami yace "Allah ya tsare" tace "Ameen" Heedayah bata fasa waigo sa ba har suka isa kofar, ya dau wayarsa yyi kamar xai jefa mata ta fasa ihu ta rike Mami, tuni ya ajiye hannunsa ya maida dubansa kan TV yana kallo attentively, ko juyowa Mami bata yi ba suka fita parlon, Heedayah ta murguda masa baki kafin ta daina ganinsa. A cikin gidan Alhaji Imran Mami tayi parking suka shiga ciki da Heedayah, ta tadda Hajiya Zuwaira da Mai aikinta a parlor, bayan sun gaisa Hajiya Zuwaira tace "Baffa na parlon sa ku je ku gaisa..." Mami tace "Ohk, ku kadai gida yan makaranta na can makaranta" Hajiya Zuwaira tace "Ae kam suna makaranta, jiya Junaid ya je masu visiting gaba daya" Hajiya Zuwaira ta bi Heedayah da kallo don sosai yarinyar ke mata kyau, komai nata burgeta yake bari hancinta da d'an karamin bakinta, idonta kuwa har lkcn basu koma farare ba, Mami ta wuce sama xuwa parlon Baffa, bata fi minti goma sha biyar bs parlon nasa ba bayan sun gaisa ta fito tare da Heedayah, Bedroom din Junaid ta bude, ta gansa kwance yyi rub da ciki yana bacci, Heedayah ta wara manyan idonta ta cikin glasses dinta tace "Mami Yaya" Zame hannunta tayi a na Mami ta shiga dakin da sauri ta hau saman gadon ta xauna dab da fuskarsa a hankali tace "Yaya" Jin bai ce komai ba ta kai hannu dogon hancinsa ta ja, a hankali ya bude lumsassun idonsa, ya sake rufe idon murya can kasa yace "Cutie" Washe masa hakoranta tayi tace "Me kake yi?" Bai bude idon ba har sannan yace "Bacci" tace "Nima xan yii?" Bata jira cewarsa ba ta kwanta yanda ya kwanta kusa da shi tana facing dinsa, bude ido yyi, yyi murmushi har dimple dinsa ya nuna, ta kai finger dinta wajen ita ma tana murmushin, Ta mike xaune tana kallon Mami tace "Mami ni me yasa bani da irin nasa" Kumatunta ta nuna ma Mami nufinta me yasa bata da dimples, juyawa Junaid yyi da sauri ganin Mami ya mike xaune yace "Mami" Mami tace "Karfe goma saura you are still on bed" yace "Aa ban jima da shigowa ba, Ina kwana" Mami tace "Lafiya lau" kallon Heedayah tayi tace "To sakko mu tafi parlor" Tace "Aa Mami xan tsaya da Yaya plss" Mami tace "Ki tsaya kiyi masa me, sakko mu wuce my frnd" Sauka tayi daga kan gadon kamar xata yi kuka ta nufi kofa Junaid ya bi ta da kallo har suka fita, Bangaren Hajiya Zuwaira Mami ta shiga, ta tadda har Hajiya Zuwaira ta sa masu aiki sun hada mata kayan kari a parlonta, Mami tace "Ikon Allah, we just breakfasted before leaving home Hajiya" Hajiya Zuwaira tace "Sai ku kara ai" Murmushi kawai Mami tayi ta xauna, Heedayah ta xauna kasa kamar yanda Mami ta nuna mata ta dinga yi a ko ina, Hajiya Zuwaira ta hada mata shayi ta mika mata, Heedayah ta kalli Mami tace "Mami ai na sha tea" Mami tace "To ke kin ji, she's full" Hajiya Zuwaira tace "Toh ai shkkn, ya kaka fa" Mami tace "Tana can" Hajiya Zuwaira tayi murmushi tace "Uhn kaka sai hakuri.... ga dai dadin xama ga kuma akasin haka" Mami ta girgixa kai tace "Kwanan ta nawa nan?" Hajiya Zuwaira tayi dariya sosai tace "Ranan da kuka koma ranan ta sa a maida ta gida" Mami tace "Bata dai baki wani matsala ba ko?" Hajiya Zuwaira tace "Toh ai duk Inda tsoho yake dama sai anyi hakuri da shi balle tsoho irin kaka, har da rikicin tsufa, ni fa har ta bar gidan nan bana gane gabas dinta balle yamma, ita dai ga ta Nan dai" A hankali Heedayah ta sulale ta fice daga dakin ba tare da ta bari sun lura ba, ta bi hanyar da suka bi xuwa dakin Junaid, bude kofar tayi ta leka ciki, xaune ta gansa gefen gado yana danna wayarsa, ta washe masa hakora ta shiga ciki tace "Yaya" Daga kai yyi yana kallonta har ta iso ta xauna kusa da shi tana kallon abinda yake yi a waya, yyi kasa da murya yace "Wa yace ki shigo dakina?" Tace "Ni ce na shigo da kaina, I want to be with you" Kallon bakinta yake, ta wara masa ido tace "Yaya yaushe xan ga Farida?" Ya dauke idonsa daga lips dinta yace "Ki tambayi Mami mana" Tace "Ce min xata yi bata sani ba, Yaya me yasa sai Shureen ya dinga min haka...." Wayarsa ta amsa a hannunsa ta gwada yanda Shuraim ke mata ta jefar da wayar xuwa bakin kofa, xaro ido yyi yana kallon wayar tasa ya mike da sauri yace "Kee wayana kika wurgar haka?" Tace "Aa haka Shureen ke min" Ya tafi ya dauko wayar yana duba screen din da ya fashe ya dawo ya hade rai yace "Sai nace ki gwada min da wayata?" tace "Toh nima idan ya min haka wayarsa xai fashe haka kenan?" Junaid ya xauna kusa da ita yana kallonta yace "Me yasa yake maki haka" ta bude hannu tace "Ban sani ba, sai ya dinga min haka kuma" kallon yanda ta xaro idonta Junaid ke yi, yace "Haka yake maki?" Ta gyada masa kai, Yace "Toh a ina kike haduwa da shi?" Ta gyara xama tace "A parlor ko a kitchen idan Mami xata bani shayi, sai ya min haka...." Da ido ta dinga bin dakin da kallo alamar haka yake bin ta da kallo, Junaid ya d'an tabe baki yace "Ki gaya ma Abba" Tace "Toh" bude kofar dakin aka yi duk suka juya da sauri, Mami ta hade rai tace "Wa yace ki shigo nan din" Heedayah ta sauka saman gadon da sauri tana nuna Junaid tace "Shi ne" Junaid ya xaro ido yace "Ni?" Tace "Eh" Mami tayi mata alamar da ta xo ta fita, ba musu ta nufi kofar ta fita kafin Mami ta rufe kofar Heedayah ta daga masa hannu suka wuce. Sai kusan yamma Mami ta bar gidan Baffa, tun da suka hau titi xuwa gida Heedayah ke ce mata Mami bamu ga Yaya ba muka tafi, Mami tace "Ai bai dawo ba, gobe xai xo" kamar xata yi kuka tace "Toh" karfe shidda saura Mami tayi parking a compound, Sai da ta sauka motar sannan Heedayah ta sauka, A balcony suka tadda Shuraim xaune yana operating laptop, Ya gaida Mami ta amsa ta shiga ciki, Heedayah ta bi sa da kallo kafin ta shiga ciki ya fixgota yace "Kallon me kike min?" A tsorace tace "Aa" ya daure fuska yace "Me yasa kike kallona nace??" Tace "Kai ma naga ai kana kallona da idonka" hada ido suka yi da Mami ya saketa ta nufi kofa da sauri ta juyo ta wani juya masa ido ta shige cikin parlon Mami ta rufe kofar.... Bayan isha Shuraim na parlon Abbansa kasancewar ya kirasa a waya yana neman sa, Abba ya gama abinda yake, sannan yana kallon Shuraim yace "Shuraim I am worried at sending Heedayah to boarding school as you suggested because, Ina son ta samu ilimin addini sosai, ba boko kawai ba, shi yasa ka ga then banyi supporting xuwansu Rabi'ah boarding din ba, karatun addini nake dubawa" Shuraim ya d'an yi shiru da farko, sai kuma yace "Abba a situation da ake ciki ynxu, boarding din is the best" Abba yace "Koh, then what about islamiyya?" Shuraim yace "Idan sun yi hutu sae ta dinga xuwa" Abba yace "Toh shkkn, but ajin da xa a sa ta fa?" Yace "Jss2.. or 1..." Bude kofar parlon aka yi Mumy ta shigo, Abba ya daga kai yana kallonta, mikewa Shuraim yyi yace "Sai anjima Abba" Abba yace "Alright" Mumy ta bi sa da kallon gefen ido har ya fita. Bayan sllhn asuba Shuraim ya shiga gaida Abbansa, bayan sun gaisa Abba yace "Jiya mun yi magana da Barrister tace min su Farida na kan yin third term exams ne ynxu.... So ynxu sae anyi hutu an koma za ayi enrolling Heedayah, but before then I will get a mu'allim for her da xai dinga mata karatun qur'ani da sauran abubuwan da ya kamata..." Shuraim yace "Mu'allima instead" Abba yace "Really?" Shuraim bai ce komai ba, Abba yace "To bbu damuwa, when are you going to Zaria?" Yace "Tomorrow" Abba yace "Allah ya kai mu" mikewa yyi ya ma Abba sallama ya fita parlon. Karfe sha daya na safe, Heedayah ta fito parlon Mami rike da cup din shayi da ta sha xata kai kitchen, Shuraim na kwance 3 seater yana kallon wani action movie da ake yi, Ta gefen ido ya bi ta da kallo, ita kuwa sai kallon dogon kafarsa take, yana lura da ita, idan ta kalli nasa sae ta kalli nata, bude kofar parlon aka yi ta daga kai Junaid ya shigo parlon da sallama, ajiye cup din hannunta tayi a kasa ta tafi da sauri ta rungumesa tace "Yaya ranan nan ban ganka ba muka wuce" Junaid na kallon kayan jikinta yace "Me yasa kika fito da kayan nan?" Ta kalli kayan tace "Mami tace in sa" Tuni Shuraim ya lumshe ido kmr me bacci, Junaid na rike da hannunta suka wuce parlon Mami, Junaid na kallon Mami yace "Mami kayan nan da ta sa ina ga kamar bai yi ba, she shouldn't be wearing this out" Mami ta kalli wando da rigan dake jikin Heedayah tace "Meye rashin yin sa?" Bai ce komai ba, Mami tace "Hijab xan sa mata ta dinga yawo a gidan ko jallabiya?" Nan ma dai bai ce komai ba, Mami ta masa wani kallo ta ci gaba da abinda take yi, ya xauna ya gaisheta a hankali, ta amsa tace "To sai ka siyo mata jallabiyoyi ta dinga yawo da su" shi dai bai ce komai ba, can ya mike yace bari in je in gaida kaka, Tace "Ohk" fita yyi Heedayah ta bi sa da sauri, Bai tadda Shuraim a parlon ba kuma, ya shiga parlon kaka da sallama, hada kayanta ya sameta tana yi a katon akwatin ta, da mamaki yace "Ina kuma xa ki kaka?" Kamar jiran xuwansa take ta gyara xama ta fashe da kuka ta rike kai tace "Wai da barin garin xan yi Junaidu, in tafi can Inda Allah yayi" Ya xauna yace "Me ya faru kuma kaka?" Kaka na Shessheka tace "Ni dai ba fitinanniya bace ni kuma ba rigimammiya bace Junaidu, kaga tunda uwar ka ta dawo gidan nan ta daina sake min fuska, yau kwana biyu da dawowarsu Ina kirgawa, Deedayar ma ta rabata da shigowa nan gaba daya, me nayi mata Junaidu? Daga nace a ba Maryam Deedayah bata san duk haushin ba a tafi da ni India bne shine ta kullaceni, toh ko Karen hauka ya cijen ae bana bari Maryam ta rike Deedayah ba, Maryam axxaluma, ae kamar an ba kura nama ne, to tun daga sannan Rakiya ko ta shigo min minti daya kawai take, ita kuma Deedayar ganinta ma ba abu ne me sauki a wajena ynxu, duk wahalar da nayi da ita sae a rabamu haka kawai ba tsididi ba tsadada?" Junaid dake ta sauraronta yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri kaka, bbu Inda xa ki je" Kaka ta kara rushewa da kuka tace "Da ma kayi aurene sae ka kai ni gidanka in huta da jarabar kowa inyi ta kai na, Amma baka yi ba sai gantali kke, wnn shine rana xafi inuwa k'una, ni dai na gaji" Heedayah da ke tsaye bakin kofa ganin yanda kaka ke kuka ta fashe da kuka ta fita dakin da sauri, Kaka ta xaro ido tace "Kaga don Rakiya tayi xaton wani abun nayi mata in shiga uku in lalace ko?" Kuka sosai Heedayah ke yi bayan ta fito ta tafi can jikin kujera ta rakube har da Shessheka, Shuraim da ke xaune dining ya mike yana kallonta, ya kalli bangaren Mumy da gefen ido kafin ya nufeta.... Tsayawa Junaid yyi bakin kofar dakin kaka ya fasa fitowa ya bi Shuraim da ido. Nagode sosai da ta'aziyar ku gareni, Allah ya sa mu cika da Imani.... Baxan samu post gobe ba I'm still not home. Heedayah is 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Shuraim na tafiya xuwa gun inda Heedayah ke xaune tana rusa kuka kamar ance ya daga kai ya ga Junaid tsaye kofar dakin kaka ta jikin TV dake kashe a parlon, yyi saurin dauke idonsa ya wuce Heedayah ya karasa gun TVn ya kunna sannan ya dau remote ya koma saman kujera ya xauna ya shiga canxa channel, Junaid ya karasa fitowa parlon ya karasa gun Heedayah ya duka yace "Why are you crying?" Ta gefen ido Shuraim ke kallonsu yana canje canjen tasha, Ta goge idonta da bayan hannunta cikin rawar murya tace "Toh me yasa kaka take kuka ita ma?" Soft smile Junaid ya sakar mata ya dagata suka mike ya ciro handkerchief yana share mata idonta, Shuraim bai yarda ya sake satan kallonsu ba ya dinga kallon screen din Tv, a hankali Heedayah tace "Yaya bana son kaka ta yi kuka kuma, or is she sick?" Junaid ya kama hannunta yace "Mu je ki bata hakuri kice kar ta sake kuka..." Yana rike da ita suka nufi hanyar dakin kaka, Heedayah ta kalli Shuraim da yayi frowning face ya bi su da wani kallo, wani harara ya jefa mata, ta turo masa baki ta dauke kanta tana biye da Junaid xuwa dakin kaka. Kaka na kwashe tarkacen kayan magungunanta da ta jera gaban madubi tana xuba su cikin katon handbag dinta Junaid ya shigo da Heedayah, Heedayah ta rakube jikin kofa cikin sanyin murya tace "Kaka kiyi hakuri ki daina kuka kin ji?" Kaka ta juyo ta kara rushewa da wani sabon kukan tace "Atoh kaga yarinya kenan ma tana bani hakuri balle kattin matan da Amadu ya ajiye a gidan nan, ko sanin ina yi ma basu yi ba, bbu wanda yace min ci kanki har ynxu, haba jama'ah ynxu ace bare ya fi jin k'an ka a duniya a kan naka, me muka hada da Deedayah banda Amadu da ya jajubo mana ita a bakin titi tana galantoyi, amma ace ta damu da halin da ta gan ni a ciki a kan yan gidan nan, abinda su Rabi'ah basu ta6a min ba kenan, ko kuka nake ina birgima basa ce min komai sai ma mayar da ni fim da xasu yi" Junaid ya karasa cikin dakin, yyi kasa da murya yace "Yanxu dai kiyi hakuri kaka..." Kaka tace "Toh ni abinda nayi ma Rakiya ta fita harkata a gidan nan ne na kasa ganewa har ynxu, ka dubi Allah ka tafi ka tambayo min ita abinda nayi mata yanxun nan..." Junaid yace "Babu abinda kika yi mata kaka, kawai dai...." Kaka ta daga hannu sama tace "Aa ba ruwana ka tafi yanxu ka tambayo min ita kawai, ko gaisuwar kirki fa ta bar min a gidan nan, haka kawai gida duk ya min xafi kamar mayya, ko don an gan ni shiru shiru me hakuri bana son tashin hankali??" shiru Junaid yyi yana kallonta, sai kuma ya juya a hankali ya nufi kofa xai fita suka kusa cin karo da Salima, haka kawai gabansa ya fadi, hanya ya bata tana kallonsa, shi dai bai bari sun hada ido ba ya fice dakin, Heedayah dake tsaye har sannan cikin sanyin murya tace "Kinyi hakuri kaka?" Kaka ta kalleta tace "To uban wa nake takama da shi idan banyi hakuri ba Deedayah? Bani da kowa sai Allah sai ma'aikin Allah, ni a yanxu fa da ni da juya daya nake kallonmu don wa ennan ba 'ya yan nuna ma duniya bane, Atoh in nuna su in ji kunya, bari dai Junaidu yyi aure wllh da kudinsu baxa su gan ni ba, abinda nafi kowa sanin kan iskanci...." Shiru tayi ganin Salima tace "Waye wannan?" Salima na murmushi ta karaso da ledan hannunta tace "Ni ce kaka, Kin dawo lafiya?" Kaka tace "Ke xan ce ma kin dawo lafiya ai Salima, ni da na samu labarin yau watan ki daya baki gidan nan?" Salima ta hade rai tace "In ji ubanwa? To ai gidanmu na koma" Kaka tace "Toh wani man kika samu yake neman kwale maki fuska kuma yanxu" Salima tayi mata wani kallo ta ajiye ledan hannunta tace "Ga fura na gani a hanya sabon yi me kyau na siyo maki" Kaka ta washe baki tace "Toh Allah yyi maki albarka, dama dai ke din ce me kawo min wa ennan abubuwan" Salima ta kalli Heedayah tace "Ita kuma wnn ido ya bude kenan?" Kaka tace "To da fa? Ae har ta fi ki gani yanxu, bbu abinda xa mu yi sai godiya ga Allah, ynxu ma ji nayi suna cewa boding xa su kai ta...." Bude kofar dakin aka yi Shuraim ya shigo, Kaka ta ajiye jakar hannunta tana nunasa tace "Kai kuma kana gidan nan ina gidan nan amma ka shigo ka gaisheni balle ka san halin da nake ciki kake ganin asara, ai abun kunya ne in nuna ma duniya kai ince jika na ne, ba gwara min Deedayah a kan ka ba...." Heedayah ta kalli Shuraim sannan ta kalli kaka a hankali tace "Kaka sunana Heedayah ba Deedayah ba" Kaka tace "Meye kuma Yeedaya?" Heedayah tayi stressing sunan tace "Heedayah..." Kaka tace "Ba ruwana da wnn, ba Amadun da kansa yace sunanki Deedayah ba, meye kuma laifina a nan, Kai Shureen ba Deedayah ake cewa ba dama??" Heedayah tace "Ae Shureen ma bai san sunana ba, Bai iya fada ba" Fixgota Shuraim yyi, Kaka ta taho da gudu tana cewa "Kul kar ka ta6ata wllh, kana ta6a ta watan barin ka gidan nan ya tsaya Shuraim... A kanta xan sa Amadu ya koreka ka tafi duk Inda xa ka" Kallonta Shuraim ya tsaya yi da mamaki, ta kwace Heedayah a hannunsa tace "Uban me ta hada da kai xaka Fincikota haka, dangin uwa ko na uba?? to wllh kar ka kuma, bbu ruwana da ko kai waye, xan mance sanin da na maka in ci maka mutunci a kanta, yarinyar da tun ba aje ko ina ba tana tausayina...." Shuraim na kallonta da kyau yace "Ki ci min mutunci a kanta??" A fusace kaka tace "Wllh tllh, har shi Amadun sai in 6ata masa a kanta balle kai karan kada miya, ba gwara min ita ba akan kai da Amadun, duk me damuwa da danuwarka ae shine naka bbu wani xancen jininka ynxu" Juyawa Shuraim yyi xai fita suka hadu da Junaid bakin kofar, ya basa hanya ya shiga snn yyi ficewarsa daga dakin, kaka tace "Kai ka ji min katon Mutumi ya finciko yar mutane xai duka daga tace bai san sunanta ba, shi Amadun ne ya sa shi wnn danyen aikin ko bala'i ke damunsa? Haka fa ya xuge uban wai su kai ta makarantar kwana sbda tsabar mugun hali" Junaid yace "Makarantar kwana kuma?" Kaka tace "Wllh tllh, Kai ka ga hakan ya kamata?" Junaid ya kalli Heedayah dake ta kallon kaka yyi murmushi yace "Ya kamata kaka, xata samu karatu sosai kuma xata yi wayo, ta iya xaman duniya a duk ynda ya xo mata" Salima dake ta kallon Junaid ta kashe murya tace "Ae kuwa gaskiya ka fada...." Ko kallonta Junaid bai yi ba, Kaka ta kalleta tace "Ki bar tsomo bakin ki a xancen manya Salima, har fa ynxu kin ki aure ko da yake bbu maneman ne ynxu, ke fa kusan sa'ar Shuraim ce, a haihuwar kaji kin haifi Heedayah fa" Mami ce ta shigo dakin da sallama, Kaka ta juya ta ci gaba da hade kayanta ta wani marairaice fuska, Mami ta xauna, Salima ta duka kasa tana kallon Mami tace "Ina yini" Mami ta kalleta tace "Lafiya lau ya kike?" Salima ta d'an yi murmushi tace "Alhmdllh, kun dawo lafiya ya masu jiki?" Mami tace "Alhmdllh mun gode Allah" Mami na kallon kaka tace "Kaka ynxu Junaid ya sameni da wata magana da ban fahimta ba" Kaka tace "Aa bbu abinda baki fahimta ba Rakiya, yau kwana biyu kenan bakya tanka ni a gidan nan ba kya kulani daga na bugi cikin Amadu in ga ko xai iya ba Maryam Deedayah, so nayi inga abinda ke xuciyarsa game da Deedayah dama, don har ynxu bamu san xuciyarsa ba gaskiya, amma shkkn kika kullaceni...." Murmushi kawai Mami tayi tace "Aa kaka, baki fahimce ni bane ni bbu komai a raina, amma kiyi hakuri idan ke haka kika yi tunani, shi babba ae ba a fushi da shi idan ana son wanyewa lafiya...." Kaka tace "Ka ji ki, kowa ma ai babba ne Rakiya, yanxu wa xai ce ke kika haifi Junaidu, duka duka nawa nake xa a dinga ce min babba kamar wata tsohuwa??" Mami tace "Toh ni dai kiyi hakuri baki fahimce ni bane kaka" Kaka tace "Ni komai ya wuce a gu na, amma fa ko shigo min nan Deedayar ta daina yi, ban san ko ke kika hanata ba" Mami tace "Toh xan dawo da kayanta nan din In sha Allah" Kaka tace "Ae dama a nan kayan suke tun xuwanta gidan nan kawoa shaidan ne ya shiga ya fita ya hada mu" mikewa Mami tayi tana murmushi tace "Ina d'an wani aiki ne kaka, bari in je in karasa" Kaka tace "Toh yi tafiyar ki, Allah yayi albarka" Mami ta fita parlon, kaka ta kalli Junaid tayi kasa da murya tace "Ae gwara haka dae mun tura mata aniyar ta ko?? Gashi ta shigo tana ta borin kunya, amma ae baxan nuna mata na gane ba" Murmushi kawai Junaid yyi yace "Xan je anjima in dawo kaka" Kaka tace "Toh Allah yyi maka albarka" Heedayah tace "Are you going with me Yaya?" Ya kalleta yace "No...." Bin sa tayi da kallo har ya fita dakin, Salima ta mike ta bi bayansa, Kaka ta bude baki ta bi su da ido can tace "Tabdiijam, toh me wnn yar duniyar ke nufi? Son Junaidun take Koko? Naga har kasa ta duka ta gaida Rakiya abinda ko Amadun bata ta6a dukawa kasa ta gaishesa ba balle ni da na haifesa" kaka ta ta6e baki tace "Toh sai mu xuba ido mu ga gudun ruwanta, karuwa ce fa, meye dalilin da xata makale ma Salihi irin Junaidu" ta kuma ta6e baki ta kalli Heedayah tace "Maxa tattara ledojin nan ki kai masu kitchen can ki watsar ki dawo ga sauran mantina na ajiye maki, yau xaki ga ynda nake wanke bandaki ciki da bai, ba a xuba maki ido ki lalace ba baki iya komai ba" Heedayah ta duka ta kwashe tarkacen ledojin Kaka ta fita da su, har lkcn Shuraim na xaune parlor sai dai bbu abinda yake, ta tafi bakin kofar kitchen ta watsar da ledan ta juyo suka hada ido da Shuraim, calmly yace "Koma ki kwashe su" Ta make kafada tace "Ae Kaka ce tace in ajiye a nan" tana fadin haka ta wuce abun ta, ya mike yace "Keee" tsayawa tayi tana kallon eyeballs dinsa, ya daure fuska sosai yace "Koma nace ki kwashe su" Ta wani xare masa ido tace "Ni baxan kwashe ba, ai kaka ce tace in wurgar a nan" Bude baki yyi yana kallonta, ta nufi dakin kaka tana waigosa har ta shige dakin, Kaka tace "Ga wasu nan ki tafi ki watsar" Kwashe sauran tayi ta nufi kofa xata fita suka ci karo da Shuraim, kamota yyi ta ji kawai ya tsula mata abu me xafi, ta fasa ihu a tsorace jin shegen xafi, kaka ta saki xanin gadon hannunta tace "Auxubillahi waye wnn?" Ko kallonta Shuraim bai yi ba ya juyo da Heedayah yana kallonta da kyau yace "Ki ka ce min baxa ki kwashe ba?" Bai jira amsar ta ba ya kara tsula mata dorinar hannunsa a jiki, ta fasa wani karan a rikice tana sosa wajen tana rusa kuka, Kaka ta fashe da kuka tace "Nace waye wannan??" Shuraim ya murda kunnenta ya sake xabga mata dorinar a jiki, fuskarsa a murtuke yace "Nace maki ina wasa da yara ne? Daga yau kika sake kallon Inda nake a gidan nan sai na fasa maki ido na cire su..." Yana fadin haka ya tura ta ya fita dakin, Heedayah ta kankame kaka tana kuka sosai tana kiran Mami, Mami ta fito xata wuce kitchen taji ihun Heedayah da sauri ta shiga dakin kaka, Kaka na ganinta ta kara rushewa da kuka tace "Hada mu yyi ya xane Rakiya, Ashe dama Shuraim d'an da6a ne bani da labari, dorina fa me baki biyar ya dauko yayi ta tsula ma yarinyar nan bata masa komai ba, har cewa yyi xai fasa idanuwanta ya kwakule to kungiyar yan shan jini ya shiga ne bamu sani ba??" Mami ta dinga kallon kafan Heedayah da shatin dorina ya kwanta, juyawa tayi ta fice daga dakin direct dakin Shuraim ta nufa, tsaye ta samesa dakin nasa, a takaice tace "Shuraim a kan wani dalilin ka doki Heedayah?" Bai ko juyo ba balle ya tanka ta, rai bace tace "Am I even supposed to ask why? How dare you? Ka fara hauka ne? Ko ka fara shaye shaye? To wllh daga yau ka sake gigin mata kallon banxa balle ka kai hannunka jikinta xaka sha mamaki na a gidan nan, Wait... Are you mad?" Daga kai yyi ya kalleta ta madubi jin yanda tayi stressing mad din, still bai ce komai ba dai, tace "To kayi na farko kayi na karshe wllh, ko me Heedayah xata yi a gidan nan naka kawai ido, kada ka sake kai min hannunka jikinta" tana fadin haka ta fice daga dakin, Can tsakar gida kaka ta kai ma Me gadi wayarta ya kira mata Abba taji ko kungiyar yan shan jini Shuraim ya shiga ba a da labari a gidan, daga karshe dai me gadi ya jogale waya fitina ya koma kansa ta tara masa mutan anguwa. Tun daga wnn ranan Heedayah ko fitowa tayi main parlor ta ga Shuraim sae ta koma daki da gudu, ko da kuwa tare da Mami take, wani irin tsoronsa na musamman ta fara yi a gidan, ko dakin kaka ya shigo idan ma a xaune take sai ta rufe ido wai tana bacci, idan a kwance take ma haka, ko karatu suke da mu'allimar da Abba ya dauko mata a waje tana ganinsa xata daburce kai kace mala'ikan mutuwa ga gani, Mumy kuwa kullum idan ta fita da safe sai yamma take dawowa kamar ma'aikaciya nan kuwa tuggunsu kawai suke hadawa da Hajiya Sadiya, kudi kuwa ta kashe ya kusa dubu dari biyu.... Kaka na xaune parlon Abba bayan isha, Abba yyi shiru yana sauraronta, Mumy kuma na hada masa fruit salad, Kaka tace "Toh shine nace bari in xo in ji dalilin hanata xuwa gidan nan da tayi bayan sun yi hutu..." Abba yace "Kaka ba ita xata hanata xuwa ba, sai dai Baffan nata yace ta xauna can gidan, kinsan duk makaranta daya suke tare da yaransa, to da aka daukosu daga makarantar dole can gidan xa a kai su ai...." Kaka tace "Toh shi Baffan wiwi ya sha da xai hanata xuwa gaida mahaifiyarta har ynxu? Ni sai in iya xuwa in samesa in gaya masa gaskiya, ko don Rakiyar bata magana? In dan ta nine ma Faridar ta dawo nan gaba daya kawai" Abba yace "Ni dai bbu ruwanki da wnn kaka, ai dole kafin su koma makaranta na san xa ta xo nan din, tunda hutun da saura har ynxu" Kaka tace "Idan an koma tare xa su koma da Deedayah kenan?" Mumy ta saci kallon Abba ta ji me xai ce, Abba yace "In sha Allah" kaka tace "Toh Allah dai ya kai mu lafiya, nafi son yarinyar ta xo nan ne su yi ta sabawa da wnn yaro...." Satan kallon Mumy kaka tayi sai kuma tayi shiru, Abba yace "Wani yaro?" Kaka tace "Su saba da Deedayar wai" Abba yace "Ohk" Abba yyi kasa da murya yace "Dama kuma Ina son xuwa in sanar maki kaka, Shuraim ya samu Soja...." Kaka ta dafe kirji tace "Sojaa???" Abba yace "Ehh" kaka ta saki salati tana tafe hannu tace "Naga abinda ya isheni, uban waye ya masa sha'awar soja ni Patuu, yyi ta harbe bayin Allah kenan basu ji ba basu gani ba? Yana xaune a mutum dinsa ma ya aka kare da shi balle ace an basa wani soja?" Kallonta kawai Abba yake, Mumy ta wani hade rai tana ci gaba da abinda take, Kaka tace "To waye ya samar masa Soja???" Abba yace "Abokina...." Kaka tace "Baka basa labarin bakin halinsa bane da mugunta, don duk mutum me shiru shiru mugu ne" Abba bai kuma ce mata komai ba, Kaka ta kyabe baki tace "Toh ni dai ba ruwana, shi massers din da yake fa" Abba yace "Xai ci gaba" Kaka tace "To ni dai ba ruwana, Shureen a khakin soja ai abu ya lalace kuma, taka mu kawai xai dinga yi yana wucewa wllh" Abba yace "Kaka an gaya maki ne domin kiyi masa addu'a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, duk wnn xancen da kike yi ba shi bane kaka" Kaka tace "Toh Allah ya sanya alkhairi, amma wllh ba ruwana wataran idan bamu yi hankali ba duk nuna mu xai yi da bindiga mu shiga uku, Abinda na fi kowa sanin halin d'an nan naka Shureen, kwanaki kana ji cewa yyi xai kwakule idon Deedayah ya kai kungiyar su amma ko mataki baka dauka ba, ni dai ina ta xuba ido in ji tace idonta na ciwo ko wani abu wllh a nan xan rufe ido mu tafi gidan yan sanda in gaya masu abinda Shureen yace" Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Mumy dai ta cika kiris ya rage ta fashe sai dai bata tanka kaka tun asali dama, Abba ya sauke ajiyar xuciya ya girgixa kai shi ma bai ce komai ba... Yau Heedayah tana xaune dakin kaka tana kallon cartoon ta cikin glasses dinta dake mata kyau sosai kullum baya rabo da idonta, kaka ta yi mata maganan ta miko mata darduman kusa da ita yyi sau uku amma bata san tana yi ba, gaba daya hankalinta na kan kallon da take, aka bude kofar dakin Shuraim ya shigo, rufe ido tayi da sauri xuciyarta na bugawa, Kaka tace "Algungumar yarinya kawai sai wahala take bani Shureen, tun daxu fa nake mata magana tayi min banxa ta saka kallon jaraba da baxae mata gafara ba a gaba, ni dai wllh na gaji da yarinyar nan, ba ta da aiki fa sai kallon robobin nan da an mayar min tashar wa'axi sai ya canjo min na aljanu, gashi kaf gidan nn bbu wanda ta raina sama da ni, ynxu kuma daga ganinka ta runtse ido ba tsoron Allah, shi boding din har ynxu basu koma bane, naji labarin Farida sun yi hutu wajen Junaidu fa, kawai dai Uwar bata bari ta xo mana nan bane..." Bude kofar dakin aka yi sai ga Farida ta shigo tana kalle kallen Inda xata ga Heedayah, she looks so happy, ganin Heedayah ta saki jakar hannunta ta tafi da gudu ta tsallake Shuraim cike da murna ta rungume Heedayah gam tace "Didi na dawo, Didi I am happy you can see me...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Heedayah ta bude ido a hankali tana kallon fuskar Farida, murmushi tayi ta rungumeta ita ma tace "Farida" sai kuma ta saketa tana kallon fuskarta, ta wara manyan idonta ta kai hannu dimples dinta tace "Kamar na Yaya" Dariya Farida tayi tana kallonta, she is so happy seeing Heedayah, Kaka ta nemi waje ta xauna tace "Allah sarki, jininsu ya hadu wllh, su Rabi'ah da Khadijah dama bakin hali baxae bar su suyi hka ba, uwar tayi kane kane ta hanasu, ko kulata ma basa yi a gidan, ita ma Deedayar ta kanta take" Farida dake murmushi har sannan ta xamo kasa tace "Ina yini kaka?" Kaka tace "Lfya lau Farida, ya karatu? Sae yau shi Honorable din ya ga daman sako ki kixo gun uwarki knn" Farida tace "Aa naje gidan wani kawun mu ne fa kaka ba gidan Baffa nake ba" Kaka tace "Toh baku gaisa da Shuraim ba, ko baki gansa ba" Juyawa Farida tayi ta d'an kallesa, ya ki juyowa fuskarsa bbu yabo bbu fallasa, ta kyabe baki tace "Ina wuni" still bai juyo ba yace "Lfya" Heedayah sae satan kallonsa take, Kaka tace "Tunda uban ya samar masa Soja yake amsa gaisuwan kowa cikin isa da gadara, mu dai bamu kulasa ba balle ayi tashin hankali da shi...." Farida ta mike ta daga Heedayah tace "Ki rakani in je in gaida Mamina" Kaka tace "Aa je ki gaisheta ki dawo, baki ga ni daya bace parlon, ae ita ke taya ni xama" Farida ta sake hannun Heedayah tace "Toh" daga hka ta fita dakin, Heedayah na kallon kaka kamar xata yi kuka tace "Kaka don Allah in bi ta, ae xan dawo..." Kaka tace "Toh kya ci kanki, bi ta ku je, dama amfanin me kike min bnda kallo" Da sauri Heedayah ta juya xata fita parlon tayi tuntube da kafar Shuraim ji kke tim ta fadi kasa, A tsorace ta mike xaune tana komawa baya tana kallonsa tace "Wayyo kayi hkuri..." Ya janye kafarsa bai kalleta ba, kaka tace "Yau naga jaraba, Allah ne shi da xa ki basa hkuri bayan tika ki da katon kafarsa yyi da kasa, Shureen fa ba Mala'ika bane da kike gigicewa ki tsorata idan kin gansa, ko meye gamin ki da shi banda Ubansa da yayi sanadin xuwan ki gidan nan??" Mikewa Heedayah tayi ta fita da sauri, duk gaba daya a tsorace take, kaka tace "Ni dai ba ruwana, kai kuma Shureen ya wnn yarinya Farida na gaishe ka kana amsa mata a walakance kamar an maka dole? Ba fa yar banxa bace da ka ganta nan, da gatan ta wllh, kuma da kyar idan ubanta bai fi naka kudi ba duk da ya rasu, snn ga kawunta shi ma gidansa gari guda yyi gaba daya anguwar nan, bbu abinda bbu a gidan, to a kan me kuma kake amsa mata gaisuwa can ciki ciki? Ka fita kyau ne ko gayu aka ce maka? kai da ko manyan kaya baka sakawa sae na tsigalallu" Ya juya yana kallon kaka yace "Na hada wani abun ne da ita? Kin ga ki daina min shisshigi a lamarina, bbu ruwanki da harkata, dole aka ce maki sae na amsa gaisuwarta ko ina da wani alaka da ita ne??" Bai jira cewarta ba ya mike ya fice daga dakin, kaka ta nemi kujera ta xauna a hankali tace "Ikon Allah, Amadu dai ya ja mana bala'i, muna xaman xaman mu yace xai kai sa Soja gashi tun ba a je ko ina ba ya fara kilewa.... To banda bala'i yaushe har Shureen ya fara magana da har xae xageni ya fita, dama haka sojojin suke bani da labari??" Washegari Monday da safe Mami ta koma bakin aikinta, Farida ta gama duk abinda xa su yi da Heedayah a bangaren Mami suka fito, Heedayah na sanye da wando da riga sai hula da ke kanta, sosai kayan suka yi mata kyau kamar yar turawa ga gashinta da ta baxo ta cikin hular, Farida kuma Abaya ta saka da veil dinsa, ta kulle bangaren Mami suka wuce gaida Kaka a dakinta, Kaka tace "To ita Deedayah me yasa Rakiya bata siya mata irin wnn kayan na jikin ki ba, ko don ba ita ta haifeta ba sai tayi ta sa mata kayan anna??" Farida dai bata ce komai ba, haka ma Heedayah, Farida ta mike tace "Kaka xa muje tsakar gida mu dawo" Daga haka Farida ta kama hannun Heedayah suka fita dakin, Kaka ta kyabe baki tace "Wnn faridan ta fiye rawan kai da iyayi kamar dai uwarta, ba don wannan halin nata ba dai Shureen xai aureta, banda dai kowa na son inda nasa xai huta ai wnn rawan kan nata ya fi karfin Shureen" Garden din cikin gidan Farida suka tafi da Heedayah, suka xauna kan kujeran dake garden din Farida na kallonta tace "Toh ko na nuna maki yanda ake operating wayar ai ba siya maki Mami xata yi ba, nima fa Baffanmu ne ya siya min, kuma da kyar ta bar ni na rike..." Heedayah ta langwabar da kai tace "Ae Yaya xan ce ya siya min ko Yaya Sudais" Farida tayi dariya tace "Toh shkkn, nasan Yaya xai iya siya maki, shi kinsan babu ruwansa" Tsakaninta da Allah ta shiga nuna ma Heedayah ynda ake amfani da waya da abubuwan dake cikin waya tun daga lock button, Heedayah ta maida hankali kai kace karatu take dauka... Tun da suka shigo garden din Shuraim dake xaune sama yana karatu a laptop dinsa ya mayar da laptop din gefe yake kallonsu, su kam ko lura da shi basu yi ba, can ya mike ya bar wajen, Farida ce ta fara hangosa yana tahowa toward them bayan ya sakko downstairs, tayi kasa da murya tace "Wannan Yaya Shuraim din is coming" Sosai Heedayah ta rikice a gun, ta dinga cewa "Farida tashi mu tafi yana yi ma mutane duka wllh, ki tashi mu tafi...." Farida ta hade rai tace "Toh ba sai ya doke mu ba" Har dai ya iso kansu, yana kallon Farida yace "Me ku ke yi a nan?" Farida ta d'an kallesa tace "kawai labarin mu muke" yace "You are showing her how to operate phone right?" Tace "Yea.... sannan muna hiran makaranta" ya mika mata hannu yace "Bani wayar" Mayar da wayar Farida tayi bayanta ta hade rai tace "As in how?" Yace "Baxa ki bani ba" A takaice tace "Gaskiya...." Mikewa Heedayah tayi ba tare da ta yarda ta kallesa ba xata bar wajen yace "Kina kara step daya sai na 6allaki" Tsayawa tayi, tayi narai narai da ido, sai dai taki yarda ta juyo ta kallesa, Farida ta mike xata bar wajen ya riketa ya kwace wayar a hannunta, tsaye tayi tana kallonsa tana huci, yace "Daga yau.... Ina nufin daga wannan moment din ko by mistake kika sake xaunar da ita kina nuna mata waya sai kin sha mamaki a gidan nan" Farida tace "Toh ai wayana na nuna mata ai ko? Kuma ni ka bani wayata...." Ya mata wani kallo ce "Ki kwata mana" Kallon Heedayah yyi ya kara daure fuska yace "Uban me xa kiyi da waya da kika xauna tana nuna maki ynda ake amfani da shi" Heedayah ta girgixa kai bata ce komai ba, strictly yace "Juyo Ina maka maki magana" A hankali ta juyo tana facing dinsa idonta har ya kawo ruwa, ya kara shan kunu yace "Ke kika ce ta nuna maki waya ko?" Ta girgixa kai bata ce komai ba, yace "Toh na sake ganin ki xaune ana nuna maki waya sai na xane ki a gidan nan, daina kallona" Ta sauke idonta kasa hawayen ciki ya xubo, a fusace Farida ta bar wajen kamar xata tashi sama, Shuraim ya bi ta da wani kallo har tayi corner, yana kallon Heedayah yace "Start going" juyawa tayi ta fara tafiya yana biye da ita a baya har suka shiga cikin parlor sannan ta juya suka hada ido, daure fuska yyi ta nufi dakin Kaka tana goge idonta, Kaka dake ta sauraron Farida ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Toh, a gaskiya ni dai baxan iya tunkaran Shureen ba ynxu don ya xama abinda ya xama, rashin kunya yake ma kowa gadan gadan, Kuma ni ban san ko har sojojin sun basa bindiga ba inje in ja ma kai na, yo in ja ma kaina mana, yanxu sai ki tashi mu tafi bangaren uwarsa nasan tana can tana baccin asara kin san me xaman banxa, nasan ita idan tayi masa magana xai ji" Heedayah na shigowa dakin kaka ta fashe da kuka ta fada kan gado har da Shessheka, kaka ta mike da sauri tace "Lafiya, me ya faru, ni dai na shiga uku, kukan me kike" Kuka kawai Heedayah take, Farida tace "Shine ya doketa kila" Kaka tace "Ya doke ki???" Da sauri Heedayah ta mike xaune tace "Aa bai dokeni ba fa" Kaka tace "To kukan me kike" ta girgixa mata kai kawai, Kaka tace "Oho ni ban iya wahala, tashi mu je gun uwar tasa Farida, dabanci kawai Shureen ke ji a gidan nan kwanan nan" Tare Farida suka fita da kaka xuwa bangaren Mumy, Khadijah na xaune parlor tana kallo, kaka tace "Gantalalliya abinda kika iya kenan, Ina Rabi'ar?" Khadijah ta wani daure fuska tace "Ta tafi gidan Aunty Asma'u" Kaka tace "Ta tafi gidan Asma'u? Shine bata sallameni ba? Wai me yasa Amadu ke min haka ne a gidan nan kamar ba uwarsa ba, ynxu fa a kullum da kyar ku ke shigo min bangarena sau daya, Mata duk ta kanainaye ku bata son ku ra6i kowa na gidan nan kullum kuna kunshe a daki?? Toh bari ya dawo shi Amadun" Mumy na daki duk tana jin kaka, kafin ta karasa cikin dakin tayi saurin fitowa, Kaka na ganinta tace "To Shureen ne ya kwace wayar Farida, kuma dubu dari biyu aka ce an siya wayar, to siyarwa yake da niyyar xuwa yyi shine ban gane ba" Mumy tace "Ni kuma ina naga Shuraim da safen nan kaka?" Kaka tace "Aa ba ruwana ki fita ki nemosa duk inda yake ya maido ma yar mutane wayarta kafin ya tafi chechenia da shi a shiga uku" Mumy ta kalli Farida daga sama har kasa, Farida tace "Ina kwana" a walakance Mumy tace "Lafiya" Kaka tace "Yar gidan Rakiya ce fa, daga makarantar kwana suka yi hutu ta xo mana shine har xai saka mata ido a gidan ya kwace mata waya to ina ruwansa da ita idan ba neman fitina ba, daga ance an samar masa Soja sai ya xame mana ibilisu a gida??" Mumy tana wani kyabe baki tace "Toh ni ban san inda Shuraim yyi ba tun asuba da ya shigo ya gaisheni ban sake ganinsa ba wllh" kaka tace "Toh ai nemosa nace xa kiyi idan ba haka ba wllh sai in ja ta mu tafi gidan yan sanda su san abinda ake ciki, muka san ko sojojin kwacen wayar mutane suka sa shi" Tana fadin haka ta kama hannun Farida suka fita, Mumy ta bi su da wani irin kallo. Har Mami ta dawo da yamma Shuraim bai ba Farida wayarta ba, barin gidan ma yayi gaba daya, Mami ta tabe baki bayan ta gama sauraron farida tace "To uban wa xa kiyi ma kuka?" Farida ta kara rushewa da kuka tace "Wllh Mami bbu abinda muka yi masa kawai ya amshe wayata" Mami tace "Me kike yi da wayar ya amsa?" Cikin kuka tace "Babu komai wllh" Mami tace "Toh ai shkkn, dama nima na gaji da shegen wayar da kike rikewa" Tana fadin haka ta shiga daki, Heedayah dai na xaune parlon tayi shiru, can ta mike ta isa gun Farida tace "I am sorry I caused you all this Farida, da bance ki nuna min ba baxai amsa ba" Farida tace "Ai wllh sai ya bani wayata, you caused me nothing" Kaka ce xaune parlon Abba da Farida, Heedayah ma na xaune kusa da kaka, Abba yyi shiru yana sauraron kaka, kaka tace "Toh a gaskiya bbu ruwana kar ya ja mana fitina muna xaman xaman mu, a nemo sa duk inda ya shiga ya ba yar mutane wayarta" Abba na kallon farida yace "Me kike yi da wayar ya amsa?" Ta girgixa kai a hankali tace "Babu abinda nake yi Abba, ni da Heedayah ce ma a xaune lkcn" Kaka tace "To me xata yi da wayar banda karatu kaji ka da wata magana, bbu abinda suke yi vanda karatu" Abba yace "Toh shkkn xan nemi Shuraim din" mikewa kaka tayi ta nufi kofa tace "Ku taso mu je, shi da ya sa shi a sojan su karata can" Mikewa Farida da Heedayah suka yi suka bi bayan kaka. Shuraim na tsaye dakin Mumy dake ta masa fada kamar xata ari baki, shi dai bai ce mata komai ba, tace "Banda ka haifi yaro baka haifi halinsa ba ina ruwanka da lamarin su a gidan nan? Ka hada wani abu ne da yarinyar da xaka amshe mata waya da sunan discipline? Ina ruwanka da ita nace" ya shafa kansa still bai ce komai ba, tace "Toh wllh ka kiyayeni a gidan nan, banda baka kishina kai ko kallon yar nan xaka yi balle ka amshi wayarta Aliyu" Wayarsa dake hannunsa ne ya fara ring, Mumy tayi shiru tana kallonsa, yace "Abba na kirana" Mumy tace "Wannan damuwarka ce, ni dai idan har baxaka fita hanyar makiyana a gidan nan ba to wllh sai dai ka canxa wata uwar ba ni ba" juyawa yayi ya nufi kofa ya fita, a main parlor ya tadda kaka tana dube dube kamar munafuka, tana ganinsa ta hade rai ta hau kakkabe kujerun parlon tana cewa "Mata duk kazamai kawai" yayi wucewarsa bangaren Abba, tana ganin haka ta nufi dakinsa da sauri ta shiga tana kalle kalle, saman madubi ta ga wayoyi har biyu a ajiye da dubu biyar ta kwashe duka ta fice. Shuraim yace "Abba Heedayah take koya ma ynda ake operating waya shi yasa na amshe" Abba yyi shiru yana kallonsa haka ma Mami dake parlon tana xuba ma Abba abinci, Mami ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, can Abba yace "A ina ka gan su?" Shuraim yace "Can baya" Abba yace "That's wrong, and you did the right thing collecting the phone, ka rike wayar wajen ka nan da kwana biyu sai ka bata" Shuraim ya dago kansa yace "Ita ma bai kamata ta rike waya ynxu ba, she still in Jss2 I think" Abba yace "Haka ne but assuming a gidan nan take ni baxan bari ta rike waya ba, but tunda ba a nan take ba we have no say, ka maida mata wayarta after two days..." Shuraim yace "Idan xata koma makaranta xan bata amma ba ynxu ba" Abba ya kalli Mami da bata kalli Inda suke ba yace "Ur opinion Rahinah" Mami ta kallesa tace "Duk ynda kayi dai dai ne barrister" Abba yace "Alright, ka bar wayan gun ka Shuraim" Shuraim yace "Toh shkkn" daga haka ya mike ya fita parlon. Karfe tara da rabi kaka na xaune dakinta ta daura kafa daya kan daya ta gama cinye kazar da Junaid ya kawo mata tana sakace hakori Shuraim ya shigo, tana ganinsa ta ci gaba da sakace sakacenta tana lumshe ido, ya bi dakin da kallo sannan ya juya ya fita, bangaren Mami ya nufa ya bude parlon ya shiga, bbu kowa parlon amma yana jin muryarsu a daki, karasawa yyi bedroom din ya bude kofar, Xaune suke kan gado suna kallo a laptop din Farida, Heedayah na sanye da yar rigar bacci iya cinya haka ma Farida, Farida ta xaro ido, da sauri ta rufe jikinta da Pillow tana kallonsa, Heedayah ta sauka saman gadon da gudu ta shige bandaki ta rufe, yana kallon Farida yace "Bani wayar da kika shiga dakina kika dauka" Ta xaro ido tace "Ni?? I didn't take any phone wllh, tun daxu muna kallo a nan ban fita ba" ya fi minti daya yana kallonta sannan ya juya fice daga dakin, ya koma dakin kaka, kaka ta kallesa tace "Sojojin ne suka baka pareti da daddaren nan, naga ka shigo daxu baka ce min komai ba, gashi ka sake dawowa" Yace "Ina wayoyin da kika dauka a dakina?" Kaka ta mike tsaye ta wani xaro ido tace "Wayoyi kuma?" Yace "Ehh" Ta nemi waje ta xauna har ta fara salati sai kuma ta sakar masa kuka tace "Tunda uwata ta haifeni bbu wanda ya ta6a tsareni yana tuhumata a kan sata, satar ma ta waya, Shureen in rasa abinda xan sata a gidan nan sai waya? Ashe ma gantalalliyar barauniya ce ni, in saci motocin Amadu in gudu mana idan haka ne, Amma sai ka shigo min tsakar dare kace Ina wayar da na sata??" Shuraim ya gyada kai ya juya ya fita dakin. Bai sake maganar wayar ba har gari ya waye, Farida na share ma Kaka dakinta, Heedayah na kwance saman gado tana kallo a laptop, kaka tace "Shiru Shureen bai sake shigowa nemo waya ba gashi har karfe goma ko dai ya hakura ne, ni dubu biyar din ma kasuwa xaku je min ku siyo min kayan ciki in narka uban farfesuna mu yi sati muna ci, kayan cikin dubu biyar ai xai cika wancan kwallan ko?" Farida ta juya tana kallon katon abinda kaka ke nuna masu, kaka tace "Har yawuna ya tsinke maxa gama sharan ku tafi da wnn mara amfanin ku siyo min kayan cikin" Farida tayi kasa da murya tace "Ke dai kar kice masa komai a kan wayar ki ci gaba da boyewa" Kaka tace "Toh da fa, ai ni tasa wayar ma da kyar idan ba chechenia xa ku rakani ba in siyar da 'yar banxa in siyo kan saniya inyi farfesuna" Farida ta fashe da dariya har da kyakyatawa, murya can kasa tace "Xan raka ki wllh, gashi naga shi ma IPhone din ne har ya fi nawa" Kaka tace "Toh ko in shirya yanxu?" Farida tace "Shirya" mikewa kaka tayi xata fiddo da sabon kayanta, Ganin cup da Heedayah ta sha shayi ta kalli Heedayah dake kwance tace "Kai ni dai wnn yarinya ta isheni wllh, kwata kwata ba a morarta, son jikinta har tsoro yake bani ni dai, to Amadu kike jira ya dauke maki kopin nan ko Rakiya??" Heedayah ta sakko saman gadon ta dau cup din ta nufi kofa kaka ta bi ta da harara tace "Toh meye ma amfanin bude idon da Amadu ya kai ki aka yi idan ba asaran kudi ba" Heedayah na fita dakin ta wuce kitchen, Khadijah dake xaune dining ta bi ta da harara, ita dai ko kallonta bata yi ba, ta bude kofar kitchen din ta shiga, ta ajiye cup din a sink kenan ta ga Shuraim tsaye kitchen din yana hada shayi, sunkuyar da kanta tayi xata fita, yace "Zo nan" kin tsayawa tayi ta ruga da gudu ya kamata kafin ta isa kofa, kuka ta sakar masa a tsorace tace "Ni ban yi komai ba wlh, kaka ce tace in kawo cup din kitchen" leka parlor yyi ganin Khadijah ya rufe kofar kitchen din, har wani rawa jikinta yake yi sbda tsoro, ya jinginar da ita da kofa yace "Wa ya shiga dakina ya dau waya?" Ta bude hannu da sauri tace "Nima ban sani ba, bani bace wllh" kalle kallen kitchen din ya fara yi taga ya kallo inda muciya yake, xaro ido tayi ta rungumesa a rikice tace "Wllh Kaka ce ta dauka ta boye a dakinta, a cikin akwatinta ta boye" Bai san lkcn da yyi murmushi ba yana kallonta duk da ta boye fuskarta jikinsa, a hankali cikin rawar murya tace "Yanxu xa su je su siyar da wayan da Farida" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Bude kofar Shuraim yyi bata jira yace ta fita ba ta sakesa ta fice da sauri... Dakin kaka ta koma, kaka tace "Me ya tsayar da ke kitchen din, ko wanke wanke kika yi?" Heedayah ta girgixa mata kai ta xauna gefen gado, gaba daya a tsorace take har lkcn, kaka ta gama saka sabon kayanta na xuwa chechenia tace "Nima dai da neman magana nake, wata Deedaya ce xata yi wanke wanke kamar an tsine mata Allah na tuba" Farida ta gama tattara dakin kaka tace "Ajiye masu tsintsiyar da makwashin sharan a nan bakin kofa mai aiki xa ta kwashe ki shirya mu wuce, daga checheniar dama sai mu biya bakin dogo bbu irin k'an san da basu siyarwa sae mu yi ciniki, ita wannan Deedayar dama ta xauna gida kar taje tana mana lagwai lagwai a kasuwa in shiga uku" Farida tayi yanda Kaka tace sannan ta dau mayafinta ta yafa, duk ta kagu su tafi siyar da wayar Shuraim, dama tuni ta amshi nata ta kai dakin Maminta ta boye, kaka na bude akwatinta ta ciro wayar kenan Shuraim ya bude kofar dakin ya shigo, da sauri ta boye wayar bayan jakan hannunta na rawa ta daga jakar ta mike tsaye, Kai kana ganinta kaga rashin gaskiya karara, cikin rawan baki tana kallonsa tace "Ha'an... yau ma baka tafi Zarian ba? Sannan yaushe xa a fara kwasan sojojin ne" Yace "Ban tafi ba, Ina kwana?" Tace "Lafiya lau, ynxu na shirya nace wannan yarinya Farida ta raka ni gidan Ta sallah kwana biyu ban je ba ita ma bata xo ba, gashi ka shigo ni kuma xan fita" Yace "Ohk, ko in ajiye ki?" Da sauri tace "Aa ba ruwana da ba mutane wahala ga dai adaidaita ta ko ina, kayi tafiyar ka kawai kar in wahal da kai" Farida dai ko kallon Inda yake bata yi ba ta bi gefensa ta fita dakin, Heedayah tuni ta kwanta kan gado ta rufe idonta, kaka tace "Toh mu je xan kulle dakina ne Shureen, kema Deedayah ki fita kije gun Rakiya ki kwanta baxan iya barin dakina a bude ba" Shuraim ya karasa Inda take tace "Ina kuma xaka kana jin ina ce maka xan fita??" Bai saurareta ba ya isa gun akwatin ya duka ya dau wayarsa da yake hangowa bayan akwatin ya fice daga dakin, kaka ta kasa kwakkwaran motsi inda take tsaye, can dai tace "Toh Allah ya isa" sai kuma ta xauna gefen gado ta goge xufan da ya karyo mata a goshi cikin rawar murya tace "Allah dai ya isa" A cikin satin nan Abba ya ba Mami kudi don yi ma Heedayah siyayyar da ya kamata na xuwa boarding, bbu abinda Mami bata siya mata ba har da nata karin, duk dakin kaka ake ajiye kayan gudun fitinarta, ranan Friday karfe uku saura Heedayah na xaune Main parlor tare da Farida dake karatun wani literature dinsu, Heedayah kuma tun safe take ta rubutu a exercise book kamar yanda Mami ta umarce don har sannan writing dinta isn't good duk da tana kokari, Salima da Rabi'ah kuma na can gun dinning, Rabi'ah na mata tsifan uban attachment din kanta, sbda lalacewa kuma a kan dinning, Bude kofar parlon aka yi Sudais ya shigo da sallama, daga Heedayah har Farida suka dinga kallonsa har ya karaso parlon, sanye yake da gezner fari kal, mikewa Heedayah tayi ta sakar masa cool smile tace "Ya Sudais" Ya buda mata manyan idanuwansa a hankali yace "Yes Cutie" karasawa tayi kusa da shi ta rungume sa tace "I missed you" Farida dai kallonsu kawai take, haka Salima da ta juya kanta tana kallon ikon Allah, Sudais ya maida Heedayah gefensa yana kallon Farida yace "Hi" ta d'an yi murmushi tace "Hello, ina yini" yace "Lafiya lau, Farida right" tace "Sure" yace "Ya hutu?" Tace "Alhmdllh" ta gefen ido Heedayah ta bi Shuraim da ya shigo da kallo, direct dakinsa xai wuce ganin Salima da Rabi'ah a dinning ya tsaya yace "Duk gidan nan ki rasa inda xa kiyi tsifa sae wajen cin abinci Salima" Ta kyabe baki sbda bata son fitina ta fara tattara gashin dokin nata, yau dai shima manyan kaya ne jikinsa, Sudais dama sau daya ya kalli direction din Salima shi ma sbda Rabi'ah da ta gaishe sa, ya amsa gaisuwarta, ya na kallon Heedayah yace "Kaka na dakinta?" Heedayah tace "Aa ta je anguwa" Ya d'an bude ido yace "Anguwa Kuma?" Tace "Ehh gidan frnd dinta tace xata tafi, Mami ce ta wuce da ita da safe" Yace "Ohk, ya preparation din tafiya makaranta?" A hankali tace "I am scared ya sudais" yace "Noo don't be dear, you will like it in there, many of ur mates are there" Tace "Toh baxan kara ganin Mami da Abba ba?" Yace "No xaki dinga dawowa hutu ai, ba ga Farida tana dawowa hutu ba ita ma, tare xa ku je sannan ku dawo tare" a hankali Heedayah tace "Toh" Ya kalli Farida yace "Junaid na nan kuwa?" Farida tace "Yana Abuja, amma xai dawo Saturday" Sudais yace "Yes yace min xai je can, but two days ba mu yi waya ba" Shuraim na fitowa daki Sudais ya mike Heedayah ta xaro ido, murya can kasa tace "Ya Sudais wucewa xaka yi?" Ya mata murmushi yace "Yesss but xan dawo" tace "Me yasa ka daina xuwa?" Yace "Sbda bana nan Cutie" Tace "Toh har in tafi makaranta baxan ganka ba?" Yace "Aa ni xan kai ki makarantar ai" Ya ja dogon hancinta yace "Byee sai na dawo" Har ya fara tafiya sai kuma ya juyo da sauri yace "Bye Farida" tace "Toh Allah ya kiyaye" daga haka ya fita, Heedayah ta koma gun Farida ta xauna. Salima ce xaune dakin yayarta tana sauraron abinda take gaya mata, can dai ta tabe baki tace "Toh wai Yaya ke yanxu meye damuwarki, ita fa matar nan ba sanin kina yi take ba kullum ta fita da safe sai yamma take dawowa, ita kanta wnn makauniyar da ta ja maki komai yanxu makarantar kwana xa a kai ta aka ce to ba shkkn ba, a ina xaki dinga ganinta kina jin takaici kuma??" Mumy ta kunduma mata xagi tace "Dama ke kinsan ciwo na ne, ai damuwata ba taki bace, kin gwammace kiyi ta yawo gari gari..." Mikewa Salima tayi tace "Aa kar ki bata min rai Yaya, taya kike son in tafi in ajiye maki laya a dakinta bayan ba shiga dakin nata na saba yi ba, ba gwara ki ba wa ennan fitsararrun yaran naki ba da basa girmama mutane" Mumy tace "Shkkn ni kuma bani da sirri sai in bari yarana su ji wnn magana, ke ma don kina 'yar uwata ne shi yasa nake neman taimakon ki" Salima tace "Kai gaskiya Yaya Ina ga da kamar wuya..." Mumy tace "Haka xa kiyi min Salima?" Salima ta wani murguda baki ta dauke kai, Mumy tace "Toh shkkn, tashi ki wuce, amma ai kina ma Salaha wanda ya fi haka" Salima tace "To Salaha ai biyana take yi ita" Mumy tace "Toh ni nawa xan baki?" Tana taunar cingam din bakinta tace "Dubu hamsin" Mumy ta mata wani shegen kallo tace "Toh bani da shi, idan xaki amshi dubu ashirin gashi nan yanxu" Salima tace "Toh kawo" tashi Mumy tayi ta dauko mata dubu ashirin din ta bata, sannan Salima ta amshi katon layan ta saka a karamar jakarta ta sa cikin handbag ta mike ta fita, Mumy ta sauke wani ajiya xuciya tace "In sha Allahu komai ya xo karshe sai dai idan ba uban kudina na kashe ba" Da daddare Salima ta fito da uban kayanta da aka wanke ta ba talatu Mai aiki tayi mata guga aka bude kofar parlon, Abba ne ya shigo tare da Junaid, Sosai gabanta ya fadi ganin Junaid, sanye yake da kananun kaya da suka yi matukar amsarsa, bbu wanda xai kalli junaid sau daya ya kauda kai, he is just too handsome, komai nasa is almost perfect, tayi kasa da kai ta gaida Abba, ya amsa yayi wucewarsa Parlonsa, Bangaren Kaka Junaid ya nufa, Salima ta bi sa da kallo a hankali cikin sanyin murya tace "Welcome Jayy" Banxa yayi mata har ya shiga dakin, Salima ta wuce bangaren Mami ta bude kofar ta shiga da sallama, Mami na xaune parlon tana hada ma Farida da Heedayah kayansu don gobe ne tafiya makarantar, Mami ta daga kai tana kallonta, Salima na murmushi ta gaida Mami da ladabi, Mami ta amsa tace "Ya kike" Tace "Lafiya lau wllh ya aiki" Mami tace "Alhmdllh" Farida ta gaida Salima, ganin haka Heedayah ma ta gaisheta, Salima ta amsa da fara'a sannan tace "Dama wllh dutsen guga na xo amsa Aunty, na Mamansu Khadijah ya lalace, Shuraim kuma kamar bai nan" Mami tace "Ohk yana can daki dauko mata Farida" Xaunawa Salima tayi saman kujera tana ta kallon Heedayah ganin wani kyau take karawa kamar wata baindiya, ga gashinta da yyi tsayi sosai, Cikin dubara ta dinga saka hannu cikin rigan mamanta da yake hijab ne har kasa jikinta kuma layan na cikin rigan maman, Har ta fiddo idonta na kan TV kamar me kallo, a hankali ta ciro hannunta ta cikin hijab din tana kokarin tura layan cikin kujera aka bude kofa, juyawa tayi da sauri, Junaid ya shigo da sallama, da sauri Heedayah ta mike xaune sai dai bata yi gigin xuwa kusa da shi ba sbda warning din da Mami tayi mata daxu don ta rungume Sudais da ya shigo, Junaid da idonsa ke kanta shi ma ya xauna kujeran dake facing Salima, Mami na lura da kallon da yake ma Heedayah ta dai ci gaba da hada kayan da take yi cikin jaka, Heedayah ta sakar masa murmushi tace "Good evening Yaya" yace "Evening how are you?" Tace "I'm fine" Kallon Mami yyi yace "Mami ina yini" Mami tace "Lafiya lau ya hanya?" yace "Alhmdllh" Salima da ta gama narkewa Inda take xaune tana kallon Junaid cikin tattausan murya tace "Ina yini?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lafiya lau" Farida ta mika mata iron din hannunta tace "Ga shi" amsa tayi tace "Nagode" Kasa tura layan tayi cikin kujeran sai kallon Junaid kuma take, can ta mike hannunta na rike da layan a cikin hijab tace "Toh nagode" Mami tace "No thanks" daga haka ta nufi kofa, Junaid ya bi ta da kallon gefen ido. Salima na shiga dakin Mumy, Mumy ta mike da sauri tana murmushi tace "Kaddai har kin sa" Salima ta wani turo baki tace "Gaskiya baxan iya ba Yaya" Still Mumy tayi tana kallonta tace "Baxa ki iya me ba?" A takaice Salima tace "Yin abinda kika ce in yi mana" Mumy ta dake tace "Saboda me?" tace "Ni fa wllh yaya son Junaid nake, so ba na wasa ba kuma, ni ban jin ma xan iya rayuwa babu shi, ganinsa fa ya sa na kasa saka layan a kujera wllh" Bude baki Mumy tayi tana kallonta can ta mika mata hannu tace "Toh bani" Salima ta fiddo layan ta mika mata, Mumy ta kwace a mugun fusace ta kunduma mata xagi tace "Amma ke dai Allah ya wadaran ki wllh, Junaid din banxa, meye hadin ki da wani shegen junaid da xaki bakanta min sbda shi, toh bani kudi na tun wuri kada in fasa maki kai yanxun nan a dakin nan" Mikewa Salima tayi ta nufi kofa da gudu tace "Har na bada deposit din Human hair weave-on da kudin, bani da shi bani da dalilinsa" daga haka ta fice daga dakin. Kuka ne kawai Mumy bata yi ba ta rasa yanda xata yi kuma ranan aka sa ta saka layan a bangaren Mami, ance mata duk runtsi kada ya wuce yau ganin lkci na wucewa ta mike tana kallon agogo dake nuna karfe goma da wani abu, a jikinta ta saka layan sannan ta dau hijab dinta ta sa, ta bude gun kayanta daga kasa ta dau sinkin sabulu biyu da omo manya biyu ta nemi yar leda me kyau ta xuba su a ciki sannan ta fita xuwa main parlor, cike da karfin hali ta nufi bangaren Mami, ta bude kofar da sallama, Kaka ta tarar a parlon tsaye Mami na kara fiddo mata sauran siyayyan da tayi daxu tana nuna mata, kaka ta juya tana kallon Mumy tace "Waye wnn?" Mumy na murmushin karfin hali tace "Ni ce kaka, Ashe baki yi bacci ba" kaka tace "Inyi baccin lafiya gobe yara xa su wuce makarantar kwana" Mumy tace "Allah sarki..." Xaunawa tayi saman kujera tana kallon Mami tace "Mun yini lafiya?" Mami tace "Alhmdllh, ya aiki" Mumy tace "Mun gode Allah, da safe yara xa su wuce koh?" Kaka tayi saurin cewa "Aa, mu ma dai bamu sani ba bamu da tabbas, kila a daga tafiyar tasu ma" Mumy tace "Allah sarki, toh Allah ya kai mu lafiya, ga wannan dai babu yawa" Kaka tana kallon ledan da take mikowa tace "Meye wnn din" Mumy tace "Aa d'an sabulu ne da omo" kaka tace "Toh ai gashi nan har ya masu yawa naji Rakiya na cewa ma ba duka xa su kai makarantar ba" Mami na kallon Mumy ta mike ta amsa tace "Allah ya amfana Hajiya, an gode" daga haka ta ajiye ledan gefen kayansu Farida, Mumy da har ta cusa layan hannun cikin kujeran taji ya shige can kasa ta mike tana murmushi tace "Aa bbu komai wllh, sai da safe" Mami tace "Allah ya tashe mu lafiya" Mumy ta fita parlon, kaka tace "Kiji Ina batun ta maida kayanta ki wani tashi ki karbe Rakiya? Makira ce fa Maryam, to ni dai ba ruwana" Mami dai bata ce komai ba, Kaka tace "Haka kawai mata ta shigo mana tsakar dare tana tambayar yaushe ne tafiyar, nasan da bana parlon nan tonawa xaki yi ki gaya mata, ai mugu baka sa shi a harkan ka, muka san abinda ke xuciyarta" Mami still bata ce da kaka komai ba ta ci gaba da abinda take. Washegari da ya kasance lahadi, karfe goma na safe Mami ta shiga parlon Abba ta dalilin kiranta da yyi, as usual laptop dinsa na gabansa, ta xauna tace "I'm here barrister" Bayan kusan minti biyar ya dago yana kallonta yace "Dama nayi wata shawara ne daga jiya xuwa yau Rahinah" Mami na kallonsa ganin mood dinsa is awkward, a hankali tace "Shawarar me fa Barrister?" Abba yace "Ina ga xa a bar xancen tafiyar Heedayah boarding" da mamaki Mami ke kallonsa, da farko kasa cewa komai tayi, can dai cike da karfin hali tace "Ko saboda me Barrister" yace "That's my decision" ta girgixa kai tace "Noo ba a yanke irin decision din nan without reason, ka gaya min dalilin hakan Barrister" yace "You are not to question my order Rahinah" Da mamaki sosai take kallonsa, tace "I am not questioning you, I'm asking for ur reasons" Yace "Nace Heedayah baxa ta je boarding ba, I think I have done all what I am suppose to do for her, bbu wani da xai min tilas kuma, beside I have other commitments...." Mami tace "As in?" Yace "That is it" Ta girgixa kai tayi shiru, can ta kallesa tace "Are you talking of the expenses?" Yace "If you think so" Mami ta fi minti biyu ta rasa abun cewa, can ta girgixa kai tace "Ohk fine, the bills are on me you don't worry, in sha Allah" tana fadin haka ta mike xata fita, Abba yace "Bill or no bills banyi ra'ayin ta tafi boarding ba, xa ki iya biya mata kudin day amma ba boarding ba" juyowa tayi tace "Sorry... but are you sure you are okay Ahmad?" Yace "What are you insinuating?" Tace "Naga dai nace indai don kudi ne kada ka damu xan biya...." Abba yace "Toh makarantar ma gaba daya nayi canceling dinsa, she should stay at home, you have no issues with that" Mami ta kara kallonsa da kyau, bata kuma cewa komai ba ta fita, Dakin kaka ta wuce, Kaka da tayi wanka tun asuba xata yi rakiyar yan makaranta ganin Mami tace "Komai mutum xai yi ya dinga yi ido na ganin ido, yanxu fisabilillahi sai dare yyi muyi ta cin karo da juna xa mu kai yara makaranta?" Mami ta xauna saman kujera tace "Kaka ban gane abinda Barrister ke nufi ba fa...." kaka ta xauna da sauri tace "Lafiya?? Cewa yayi kar aje da ni ko?" Mami tace "Aa" nan ta koro ma Kaka duk yanda suka yi da Abba, kaka ta saki baki tana kallon Mami, can tace "To wiwi ya sha daren jiya kafin ya kwanta ne, ko lalacewa ce ta samesa, ko bala'i ne ya fada masa duk a daren jiyan?" Mami dai bata ce komai, kaka tayi wani dariyan boss tace "Ahaf, ba ina yawan ce maku bamu san xuciyar Amadun ba a kan Deedayah amma kun ki amincewa da ni, to yau dai anyi walkiya mun ganosa, yau mun ga irin xuciyarsa, kuma makarantar kwana kamar Deedayah ta tafi ta gama, ai ba shi kadai na haifa ba a duniya, iyaka in kira Umaru ya xo ya kai ta ya biya komai, ni ai ban gaji da amanar da Allah ya bani ba in shi ya gaji, Deedayah fa Amanar Allah ce a wajenmu wllh wllh, to duka duka nawa ya kashe mata da xai nuna gazawa banda lalacewa ta samesa, Allah ya sa ya kashe ya kai dubu dari a kanta, shi ma dubu darin sbda gyaran idon da ya kai ta aka mata, to wllh ki fita harkarsa ga wayata ki kira min Umaru, idan shi ma yace bashi da kudi ban ki in daga fili na in siyar in kai Deedayah makarantar kwana ba balle ma baxai ce min haka ba, d'an Albarka ne shi din" Tana fadin haka ta dau wayarta ta mika ma Mami tace "Xa ki ga an sa Dakta ki kira min shi" Mami ta sauke ajiyar xuciya don har lkcn mamakin Abba take tace "Aa ki d'an dakata kaka" A fusace kaka tace "Ki kira min shi nace Rakiya, in dakata a kan me, ki nemosa ki kira min shi dalla" Amsan wayar Mami tayi ta nemo lambar Baffa tayi dialing sannan ta mika ma kaka. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Abba na parlonsa tare da Baffa wanda shigowarsa parlon kenan, bayan sun gaisa Baffa yace "Mun yi waya da kaka kuma ban fahimce bayanin da take min ba daxu" Abba yace "Bayanin me kenan?" Baffa yace "Na tafiyar Heedayah makaranta, what's going on?" Abba yace "Eh I just decided tayi day, baxata je boarding din ba kuma" Baffa yace "Ko saboda me?" Abba yace "Kawai ina ga hakan xai fi, she is going no where" Baffa yace "But kana tunanin xa a iya convincing dinta da haka, Ina nufin ita kaka" Abba yace "Toh xancen gaskiya shine I can't sponsor her to Nigerian Turkish boarding, day din ma ba yanxu xata fara ba" kallonsa kawai Baffa ke yi bai ce komai ba, Shuraim na shirin wucewa zaria da safen kaka ta shigo dakinsa ko sallama babu, Ta madubi yake kallonta yana jiran jin da me ta shigo, tace "Shureen ka ga dai anyi walkiya mun gano Mahaifin ka ko?? To ga dai irin xuciyarsa yau Allah ya bayyana mana, Ashe dama ba son Allah da annabi yake ma yarinyar nan Deedaya ba, kaji wai ba shi da kudin kai ta makarantar kwana duk uban arxikin da Allah ya hore masa, a takaice dai yace bbu makarantar da xata je" Shuraim ya juyo yana kallonta da mamaki, tace "Wllh kuwa, Ina jin fada suka yi kaca kaca da Rakiya a kan haka don naga ranta a bace, ni dai na kira Umaru ya taho, nasan kuma yana hanya ynxu, bbu ruwana da biye Amadu mu yi tashin hankali makota na jin mu" Shuraim yace "Yaushe Abban ya fada haka?" Kaka tace "Yau din nan wllh, bala'in da ya tashi da shi kenan, ni ko nace anya lafiya kuwa, don naga shi ya bada kudi aka yi ta siyayyar xuwa makarantar, ni ban masa baki ba balle ace da bakina ya tashi yau, to me ke faruwa? Ko da yake dama ai yana da bakin hali" tana fadin haka ta fita dakin, Shuraim ya bi ta da ido, Kaka na fitowa ta hadu da Baffa a main parlor ya fito parlon Abba, kaka tace "Kaji tsiyar ku ai, Amadu ya kiraka ko ni? Shiga kayi ya giggilla maka karya ko kuwa neman fitinata kake?" Baffa yace "Shigowata kenan fa Baaba" kujera ya xauna ya gaisheta ta amsa tana daga tsaye tace "Toh bamu san me Amadu ke ciki ba yau dai" Baffa yace "Aa ba fa wani abu bane kaka, kawai makarantar jeka ka dawo xa a sa ta in sha Allah, bbu xancen makarantar kwana" da karfi Kaka tace "Bamu yarda baaaa, tunda har bbu wanda ya matsi bakinsa da farko yace xai kai ta bording to bai isa ya juya mu kamar waina ba ynxu, ko don yaga bata da kowa sai Allah sai shi sai ni??" sai kuma ta fashe da kuka sosai ta xauna tana kunce ha6ar xaninta, Baffa yace "Haba Baaba, yanxu meye abun kuka a nan kuma? Dama ba abinda mutum xai iya xai daukar ma kansa ba? Yanxu wnn Makarantar kika san nawa ne? Ya kai miliyan daya fa" Kaka tace "Bbu ruwana da wnn, meye kuma miliyan daya da yanxu ina ihu xan gansa gabana, da can bai san ko nawa bane ya furta a kai ta? To wllh sai dai kai ka biya idan ba haka ba in tattara yanawa yanawa inje duk inda Allah ya nufa, don ni ba karamar mutum bace baxa a kunyata ni a gaban yar yarinya ba ance mata makarantar kwana xa a kai ta" Baffa yyi shiru yana kallonta ya ma kasa cewa komai, mikewa tayi tana matsar kwalla ta wuce dakinta tana cewa "Ba da ni ba wllh" Shuraim ne ya shigo parlon bayan tafiyar kaka, ya gaida Baffan nasa, Baffa yace "Je ka ka kira min Barrister Rahinah" Ya amsa masa sannan ya nufi bangaren Mami, Da sallama ya shiga parlon, ganin tana waya ya jira har ta gama sannan yace "Ina kwana" Tace "Lafiya lau" yace "Baffa yana magana a parlor" Mami tace "Okay, but do you have any idea on why Barrister changed his mind toward sending Heedayah to boarding schl?" Ya girgixa kai yace "Ban sani ba gaskiya, but I will try talk to him now" Mami ta mike ta dau Hijab dinta, sai da ta fita ya bi bayanta, xaunawa tayi parlon suka gaisa da Baffa, Baffa yace "Ke kika sanar ma Kaka yanda ku ka yi da barrister daxu?" Mami tace "Ehh ni na sanar mata" Baffa yace "But you shouldn't have Rahinah, kinsan yanda take abubuwanta, sannan don barrister yace wnn yarinya baxata makarantar kwana ba I see no cause for alarm, ga makarantu dai iri iri na day, tunda kika ga yace baxa ta je ba kinsan baxai iya bane commitments sun masa yawa, meyasa baki yi consider din haka ba" Mami ta girgixa kai tace "Amma ya san da commitments din ya bada kudi me yawan gaske aka yi mata siyayya sannan tun last week yayi niyyar tura min kudin schl fees din nata na dakatar da shi nace ya bari sai wnn satin, why the change of mind all of a sudden, and abinda ya fi ban mamaki na nuna masa idan expenses din ne damuwan na bar komai a wuyana kar ya wani damu, Amma barrister ya bude baki yace min makarantar ma baxata je ba kwata kwata har day din ma" Baffa yace "Yanxu dai ni duk ba wnn ba, ku bar maganan boarding a tafi gobe Monday ayi mata registration ko a makarantar su Khadijah ne, ki bar batun kaka kawai...." Muryar kaka suka ji tace "Algungumi, to daga kai har Amadun idan ban kora ku kun bar mana gidan ba ku ce ba ni ba, tun kuna yara dama ku ka iya munafurci da tsegumi, Banda rashin tsoron Allah don me xaka ce a fita batun uwarka, wato ga ni gantalalliya ko, kawai don Mahaifin ku ya mutu ya bar ni cikin ku sai in xama bola ku yi ta cin dunduniyata kuna munafuratata kuna walakanta ni" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka sosai ta xauna ta rike kai, Baffa yace "Subhanallahi, meye haka kaka, to shikenan in dai boarding ne xa a biya mata idan Allah ya yarda yau xata tafi" Kaka ta mike tana share guntun kwallarta tace "Da dai ya fi, don ni ban gaji abun kunya ba, da wani idon xan kalli Deedayah ince an fasa kai ta bording" Daga haka ta wuce dakinta, Mami tace "Ni matsalata yanxu shine kawai barrister ya amince ta tafi makarantar ko ni xan dau responsibility din komai wllh, Allah xai hore in sha Allah" Baffa dai bai ce mata komai ba... Da farko kasa cewa komai Shuraim yyi ganin kallon da Abbansa ke masa kamar ya san abinda ya kawosa parlon nasa, Abba yace "Nace ina jin ka kayi shiru, I'm doing something important now" Yyi kasa da murya yace "Abba me yasa kace Heedayah baxata je boarding din ba kuma, I thought...." Abba ya mike ya dakatar da shi strictly yace "Haka nayi ra'ayi, and who are you to question my order??" Shuraim ya girgixa kai yace "Kayi hakuri" Abba yace "Leave now" mikewa yyi ya fita parlon. Bbu kowa main parlor din, Baffa ya shiga dakin kaka ya kara bata hakuri ya tabbatar ta hakura, Mami kuma ta koma bangarenta, part din Mami Shuraim ya tafi ya bude kofar parlon ya shiga, xaune ya sameta a parlon, she looks so tensed, Shuraim ya xauna bayan few seconds yace "He don't seems to want to listen...." Mami tace "You don't worry Shuraim, nace Baffa yyi masa magana ya bada permission din tafiyar nata, just permission... Ni xan bada kudin makarantar" Shuraim yace "Toh shikenan, Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi" Mami tace "Ameen" Bude kofar parlon aka yi Junaid ya shigo da sallama, sau biyu yana kallon Shuraim dake xaune, ya gaida Maminsa, ya dai dake suka gaisa da Shuraim din, Junaid ya xauna yace "Ya ake ciki yanxu Mami?" Mami tace "I don't know, Doctor nake jira in ji ya ake ciki" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Ido hudu suka yi da Mumy da ta fito daga kitchen, da mamaki take kallonsa, ya karasa inda take walking slowly, Mumy na kikkifta ido tace "Daga ina naga ka fito Shuraim?" Yace "Kaka ce ta aikeni..." Ta wani daure fuska xata yi magana sai ga Baffa ya fito, murmushi tayi tace "Aa ashe Dr na gidan nan, sannu da xuwa" Baffa yace "Yauwa sannu, Shuraim yi min kiran Rahinah" Shuraim ya d'an kalli Mumy dake ta murmushi, Ya juya xuwa bangaren Mami, ba a dau lkci ba suka fito tare, Baffa na tsaye yace "Ki turo min account details din ki, xuwa anjima sai ku kai ta makarantar" Mami tace "Noo it's not ur responsibility Dr, you don't have to, in sha Allah baxai gagara ba I will pay everything" Baffa yace "I said you should forward to me ur details" Bai jira cewarta ba ya wuce parlon D'an uwansa, Mumy na kallon Mami tace "Mun tashi lfya Hajiya" Mami tace "Lafiya, ya yara" bata jira cewar Mumy ba tayi wucewarta, Mumy ta bi ta da wani kallo tana wani murmushi, Shuraim na kula da kallon da Mahaifiyar tasa ke yi ma Mami, tana juyowa kansa ya juya da sauri ya nufi kofar fita parlon. Ko da Baffa ya shiga gun Abba domin sanar masa shi xai biya kudin makarantar Heedayah kamar yanda Kaka ta umarce sa, Abba yace "Toh bbu ruwana a kan lamarin yarinyar daga yanxu, and I have taken my hands off her...." Baffa ya mike yace "What nonsense? dama wani ne ya kawo maka ita da xaka ce ka cire hannunka a lamarinta, or is something wrong with you Ahmad?" Abba bai ce masa komai ba hakan yasa ya juya ya fita daga parlon. Karfe biyu na rana Mami ta sa Mai gadi ya gama shirya kayan Heedayah da Farida a bayan motarta, duk kaka na tsaye bayan booth din yafe da katon gyalenta wai bata yarda da Mai gadin ba kar ya rarumi wani abun ya boye, Mami ta fito cikin gidan tana isowa gun motar kaka tace "Kinga Rakiya ki saki ran ki, naga kamar kin sa ma kanki damuwa, kada ki wani cuci xuciyar ki a banxa sbda Amadu, ya je mun bar sa da halinsa, ni dai tunda ba shi kadai na haifa ba ai da sauki" Mami tayi murmushin karfin hali tace "Toh xa mu je da Heedayah tayi masa sallama yanxu" Kaka tace "A kan me? Shi ya biya mata kudin makarantar kwanan ko ko akwai abinda ta hada da shi banda tsintota da yyi, ai kinga yasan fushi nake da shi amma har ynxu bai shigo ya ce min ci kanki ba, to don me xa ki kai masa yarinya ga xuciyarsa mun fara sani, ya je ya cuceta a banxa" Mami tace "Aa kaka gwara dai ta sallamesa" Kaka ta rungume hannunta tace "Toh ni dai ba ruwana" Mami bata ce komai ba ta sa Heedayah ta sakko daga cikin motar don har sun shiga da Farida tana rike da hannunta suka koma cikin gidan, da sallama ta shiga parlon Abba, bata samesa parlon ba yana can cikin daki, Mumy ce ta fara fitowa rike da hularsa alamar dai xabar masa hulan da xai sa take, tana kallonsu daga sama har kasa tace "Ya aka yi" Mami bata tanka ta ba ta nemi gu ta xauna, Heedayah ta tsaya kusa da ita, Mumy ta wani tabe baki ta juya ta koma dakin, ba a wani dau lkci ba Abba ya fito, Mami ta mike ganinsa tace "Sallama Heedayah ta xo yi maka, xa mu wuce yanxu" yana gyara karin hularsa a takaice yace "Ohk, that's good... Very good" Mami bata kuma ce masa komai ba, Heedayah na kallonsa tace "Abba me yasa baxa ka bi mu ba?" Mami ta kama hannunta suka nufi kofa, Mumy dake tsaye bakin kofar dakin tace "Toh Allah ya kiyaye ya tsare Heedayah, ya bada abinda aka je nema..." Mami tayi ficewarta ta rufe kofar, bayan mota Heedayah ta shiga tana kallon kaka dake xaune Farida kuma na gaba, Mami ta shiga driver seat ta tada motar suka bar gidan ta kama hanya xuwa Rigachikum. Suna hawa babban titi kaka tace "Toh ke Rakiya kin ga ya dace wnn yarinya ta tafi bata je ta sallami kawunta ba?" Mami tace "Wai Farida?" Kaka tace "Eh mana" Mami tace "Aa sun yi waya kaka, yace ta wuce kawai" Kaka tace "Toh kinga da kyau haka ai, shi kuma Amadu Allah ya shiryesa, dama ni don kar xuciya ta debeni in je in yi mugun alkaba'i a kansa kawai ki saukeni gidan Umaru idan muna dawowa" Mami tace "Aa ba xa ayi haka ba kaka, kiyi hakuri" Kaka tace "Wllh baxan koma gidan ba, ce maki nayi gidan ubana ne? dama ba sbda Deedayar nake xaune ba aka ce maku, iyaka duk ranan da xa ki je dubata a makaranta ki taho mu tafi tare, ko kuma idan na ga hanya ni kadai ma xan dinga xuwa abu na kullum" Mami bata kuma cewa komai ba har suka isa makarantar, a nan kofar makarantar suka tadda Junaid yana jiransu, a ranan aka yi enrolling din Heedayah a Nigerian Turkish, aka sata a Jss2, har hostel dinsu kaka da Mami suka shiga, kasancewar hostels din na sama classes dinsu kuma na kasa, Mami dai da taga Kaka xata xabga shiriritan ta sai tayi saurin dakatar da ita ta kwaba mata, a haka har suka bar makarantar wajajen la'asar, Kaka har da kwallarta wai an raba ta da Deedayah, duk yanda Mami ta so convincing din kaka su koma gida tare kin amincewa tayi tace ita dai a sauketa a gidan d'an albarka Umaru. Mami tayi parking a parking space ta sauka ganin babu motar Abba ta gane ya fita gidan kenan, ciki ta shiga ta tadda Mumy xaune parlor da Hajiya Sadiya da Hajiya Baturiya ga abinci iri iri an baxa a parlon sai shewa suke ana hira kamar wa enda aka yi ma bushara da gidan aljanna, Mami tayi masu sannu amma bbu wanda ya tankata cikinsu ta wuce bangarenta, ga mamakinta a bude ta ga parlon nata bayan ta rufe da xata fita daxu, duk gidan ta san Barrister kadai ke da spare key din bangaren nata, ta dai shiga ciki tana bin parlon da kallo, farar takarda ta ga saman kujera a linke, ta dau takardan tana jujjuyawa, can ta warware takardan tana duba rubutun ciki.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Murmushi kawai Mami tayi bayan ta gama karanta content din takardan ta linke a hankali ta wuce daki da shi ta saka a jakarta. Mami na idar da la'asar ta dau wayarta ta kira Hajiya Zuwaira, bayan Hajiya Zuwaira ta daga suka gaisa Mami tace "Su Nafisah sun wuce makarantar yau kuwa?" Hajiya Zuwaira tace "Aa sai gobe in sha Allah" Mami tace "Toh Allah ya kai mu, don Allah Hajiya, Shafa'atu nake son ki turo min nan gida ynxu idan bata maki komai, xata min wani aiki ne" Hajiya Zuwaira tace "Toh shkkn babu matsala xan turo ta, Allah dai ya sa ta gane gidan" Mami tace "Toh Ameen" da haka suka yi sallama, Mami na ta xaune saman darduma har Shafa'atu me aikin Hajiya Zuwaira ta iso, Mami tayi welcoming dinta tace "Wani d'an aiki nake so ki taya ni amma ba a nan ba, bari in shirya mu je ko" Shafa'atu tace "Toh Hajiya" Mikewa Mami tayi ta wuce daki, ba a dau lkci ba ta fito rike da makullin motarta da handbag tace "Mu je" Shafa'atu ta tashi ta bi bayan Mami suka fita parlon, Mami bata kulle bangaren nata ba ta bar sa haka a bude, har sannan Mumy na parlon da tawagarta da suka karu a kan daxu, Suna ganin Mami suka tuntsire da dariya, Mami dai ko kallon Inda suke bata yi ba har suka fita compound da Shafa'atu, motarta ta nufa suka shiga suka bar gidan, can gidanta ta tafi, bayan sun gaisa da Mai gadi ya bude masu gate suka shiga babban compound din gidan, Mami na shiga parlor ta kalli Shafa'atu tace "Gyaran gidan nan nake so kiyi min shafa, har sama duk xa ki gyara min, labulayen nan ki cire xan baki wasu ki canxa, kitchen ma Ina son a gyara, But anya xa ki iya ke kadai, naga aikin ya maki yawa koh?" Shafa'atu tace "Aa xan iya wllh Hajiya, ai k'ura ne kawai ba wai wani datti ke gare gidan ba" Mami tace "Toh shkkn, xan je in dawo in sha Allah" Shafa'atu tace "Toh sai kin dawo" har Mami ta nufi kofa sai kuma ta juyo tace "Kin dai ci abinci ko?" shafa tace "Ehh na ci Hajiya" Mami tace "Toh shkkn" daga haka Mami ta fita gidan, sai bayan isha Mami ta sake dawowa gidan, Mai gadi ya shigo mata da boxes din kayanta da na Heedayah daga cikin booth xuwa parlor, tsinkenta ko na Heedayah bata bari gidan Barrister ba, Shafa'atu ta kwashi kayan gaba daya ta kai su sama tace "Xa a jera maki su ne a siff Hajiya?" Mami tace "Aa, mu tafi kawai in maida ke gida kin ji, nagode kwarai" A bakin gate din gidan kawunsu Junaid Mami ta yi parking ta bude jakarta ta fiddo dubu uku ta mike ma Shafa tace "Ga wnn shafa, naji dadin aikin da kika min nagode" Shafa tace "Aa wllh Hajiya nagode...." Mami tace "Ki amsa ai ni na baki, amsa" Shafa ta karbi kudin da ladabi tace "Toh Allah ya saka da alkhairi ya kara girma Hajiya" Mami tace "Ameen ki ce da Hajiya Zuwaira ina gaisheta" Shafa tace "Toh in sha Allah" Da haka ta sauka motar ta rufe ta wuce ciki, Mami tayi reverse ta bar layin ta dau hanyar gidanta. Mami na gama parking sai ga kiran Hajiya Zuwaira, ta kashe motar ta daga, Hajiya Zuwaira tace "Barrister yanxu na fito bangarena naga Shafa'atu ta dawo shine take nuna min kudin da kika bata wai kun je can gidanki ta gyara maki, lafiya dai koh?" Mami tace "Lafiya lau Hajiya" Hajiya Zuwaira tace "Toh gyaran na menene ke da ba a gidan kike ba" Mami tace "Ina son in koma can ne in d'an kwana biyu tunda Heedayah kinga yau aka kai ta makaranta" Da mamaki Hajiya Zuwaira tace "Toh xaman Heedayah kike a gidan dama??" Mami tayi murmushi tace "Not at all wllh, kawai dai ina bukatar hutu ne, Kinga nan bbu kowa, bbu wani hayani, sannan ina da cases da yawa to attend to, shi sa na dawo nan sbda privacy" Hajiya Zuwaira tace "Toh Allah ya taimaka" nan suka yi sallama Mami ta ajiye wayarta. Mumy ce xaune da Hajiya Sadiya a wani d'an akurkin daki, Mumy ta gama kirga damin kudin hannunta 'yan dari biyar biyar da ya kama dubu dari da ashirin ta mika ma gabjejen mutumi me gemu dake xaune gabansu, ya amsa kudin yana dariya me sauti ya ajiye a gefensa, Mumy na murmushi tana gyara yafin mayafinta tace "Toh saura na ita yarinyar, sai dai kace ba yanxu xa a bada kudin ba ko?" Yana kallonta da jajayen idonsa ya girgixa kai yace "Aa, kamar yanda sai da kika ga aiki da cikawa kika kawo min kudin wannan aikin, to shi ma wnn sai kinga aiki yayi, mu bama amsan kudi sai bukata ta biya...." Cikin gamsuwa Mumy tace "Gaskiya ne, na kuwa ga aiki da cikawa wllh, ban ta6a tunanin haka aikin ka yake ba...." Yayi dariya yace "Toh ya kika ce xa ayi da ita yarinyar?" Mumy ta gyara xama da kyau tace "Ranka shi dade ni dai kawai ta walakanta, kmr ynda tasa na sha walakanci na wani d'an lkci, in son samu ne ma ta xamo abar kyama cikin jama'ah, wanda har ita uwar rikon tata xata sallamata taji ta fita ranta, sannan ka rabata da mijina wato tayi nisa sosai da inda muke ta je can ta karata, kada ta sake shigowa rayuwar mu" cikin katon murya mutumin yace "Toh an gama, xa a jefa rayuwarta cikin garari a takaice...." Mumy tace "Yauwa Ranka shi dade, ta xamo abar kyankyami cikin al'umma" Yana gyada kai yace "An gama" Junaid ne xaune bedroom din Mami dake harhada wasu files nata xata fita aiki, bin ta kawai yake da kallo har ta gama abinda take ta dau hand bag dinta tace "Kana nan ai..." Ya girgixa kai a hankali yace "Aa xan fita" Tace "Toh mu je ka ajiye ni kawai ba sai na fita da mota ba, I don't feel like driving, anjima when I am done with whatever I am doing xan kiraka ka mai da ni gida" Bai ce komai ba, ta dau takardan da ta basa da ya ajiye gefensa bayan ya gama dubawa, ta linke ta mayar da takardan jakarta, cikin sanyin murya yace "But Mami...." Mami ta dakatar da shi tace "But nothing Ahmad Junaid, tashi mu je ka ajiye ni" tana fadin haka ta fita dakin, mikewa yyi ya bi bayanta fuskarsa dauke da damuwa. Da yammacin ranan Mami na parlor tana jiran isowar mai aikin da ta bukaci a sama mata, aka danna bell, mikewa tayi ta isa kofan ta bude, Shuraim ne tsaye bakin kofar, da mamaki tace "Shuraim.... come in" shigowa parlon yayi, Mami ta koma ta xauna, ya kulle kofar ya karasa shi ma ya xauna yace "Ina yini?" Da murmushi tace "Lafiya lau, baka koma Zarian ba...." Yace "Ban tafi ba" tace "Ohk sae yaushe?" Yace "Next week in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen" Mami tace "Ya mutanen gidan" daga kai yyi ya kalleta yace "Alhmdllh, but why did you leave Mami" Tace "Nothing Shuraim, I only need rest and enough privacy" kallonta kawai yake yi bai ce komai ba, can dai yace "Wani abun ya faru ne?" Mami ta kallesa tace "Aa bbu wani abinda ya faru Shuraim..." Ya girgixa kai yace "Idan ma wani abun ya faru kiyi hakuri" D'an murmushi tayi tace "No bbu abinda ya faru, let me get you something to eat" Yace "Alhmdllh, will be on my way now" tace "Toh bari in kawo maka ruwa" fridge ta tafi ta dauko masa drink da goran ruwa daya da cup, ta ajiye masa, ya dau bottle water din ya mike yace "Xan wuce" Mami tace "So soon, toh nagode, Allah ya kiyaye hanya...." ya amsa da "Ameeen" ya nufi kofa ya fita. Da sallama kaka ta shigo gidan rike da katon handbag dinta, Khadijah da Rabi'ah ne parlon sanye da school uniform suna yin breakfast, Mumy kuma na kitchen da talatu sai fada take tana tsine ma Talatu ta cika man gyada a suyan kwai, Rabi'ah da Khadijah suka yi ma Kaka sannu da xuwa suka gaisheta, Kaka da ke ta kallon kitchen tace "Ita kuma wancan ita da waye kamar karya da sassafen nan, tun bakin get nake jin muryar ta" daga Rabi'ah har Khadijah bbu wanda yace mata komai sai shayinsu suke sha, Kaka ta tabe tace "Wajen Rakiya na xo kafin ta fita, yau sati daya tun da muka kai wannan yarinya Deedayah makaranta ban ganta ba, ita ma lalacewa tayi taki xuwa gaisheni ko ko?" Mumy ta leko kitchen jin kamar muryar kaka, wani shegen kallo ta shiga yi mata suka hada ido, da sauri Mumy ta sake fuska da fara'a tace "Lahh kamar kaka, wata sabon gani, sannu da xuwa kaka...." Kaka tace "Ina ruwana da sannu da xuwan ki Maryam, wajen Rakiya na xo ba gun wani gantalalle ba a gidan nan...." Mumy ta karasa fitowa kitchen din tace "Ohh wai Rahinah? Ai yau kwana takwas bata gidan nan kaka" Kaka ta xaro ido tace "Ina ta je?" Mumy tayi fuskar tausayi ta nemi waje ta xauna tace "Tohh, ni dai ban san me ke faruwa ba, amma lahadin da ta gabata ba na jiya ba, naji suna ta tashin hankali da Barrister wai sai ya bata takardan ta, ta dai daga masa hankali sosai, kinsan Barrister ba me magana bane sannan shi baya son duk wani abun tashin hankali, matar nan sai da ta san yanda tayi ta kure sa, xagi kam bbu wanda bai sha ba, daga karshe dai na shiga tsakanin su ina ta bakin kokarina na sasanci amma abun ya ci tura...." Kaka da ta gwalo gaba daya idonta tana kallon Mumy tace "Sai aka yi uban ya??" Mumy tayi kasa da murya a hankali tace "Daga karshe dai sai da aka rabun" Kaka ta saki wani rikitaccen salati ta nemi kasan tiles ta xauna tace "Ya saketa?? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Mumy ta sauke ajiyar xuciya tace "Wllh kuwa, yau kwananta takwas rabonta da gidan nan duk ta kwashe komai nata" kaka ta kuma sakin salati, sai kuma ta fashe da kuka tace "Yanxu ta6arewar Amadu ya kai haka nake xaune ban nemi taimakon Allah ba?? Ashe budirinsa na rashin mutunci kawai yake yi ba kama kafar yaro, yau fa kwanansa takwas bai taka ya je inda nake ba, har wayar ma ya ki yi min yace min ci kanki..." Mumy ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Mu ma nan duk hakuri muke da shi, fadan yanxu daban na anjima daban... Da yake ni na saba da halinsa shekara talatin da uku ba wasa ba gashi har yau ai ba a ji kan mu ba" Kaka ta share idonta tace "Ina Amadun yake yanxu?" Mumy ta saci kallon hanyar parlon Abba dake cikin dakinsa yana bacci tace "Yau kwana biyu yace min ya tafi Abuja, yana can" Kaka tace "Ko bayan duniya ya tafi ai xai dawo, Ina Shureen?" Mumy ta d'an 6ata fuska tace "Shi ai yana Zaria" Jakarta ta bude ta ciro wayarta ta mika ma Khadijah tace "Nemo min Junaidu a wayan nan" Ido Mumy ta dinga yi mata kar ta kira, ai ko Khadijah ta gama latse latsen wayar tace "Babu lambar Junaid a nan" Kaka ta fixge wayar tace "Dakikiya kawai, ana ta dai asaran kudin makaranta a banxa" Daga haka ta nufi kofa kamar xata tashi sama, Mumy ta bi ta da harara har ta fita parlon sannan ta tabe baki tana tafe hannu. Mai adaidaita kaka ta tsayar a titi tace "Kai yaro kayi boko?" Yace "Nayi mama" Kaka tace "Toh ka shiga wayar nan ka nemo min wata lamba, Junaidu xaka ga an rubuta ka kira min shi" Bayan wani lkci ya mika ma kaka wayar yace "Yana yi" kaka ta amsa tace "Yauwa" ta kai wayar kunne, sai da ya kusa katsewa Junaid ya daga, Kaka tace "Junaidu kana ina yanxu?" Junaid ya mike xaune daga kwancen da yake yana bacci yace "Ina kwana kaka" Tace "Lafiya lau, a ina xan sameka?" Yace "Ina gida" tace "Ina ne gidan?" Rasa abinda xai ce mata yayi baya son cewa nan gidansu cos he knows Mami won't take it likely with him, yace "Gidanmu a Abuja" Kaka ta saki salati a gigice tace "Har ita Rakiyar?" Yace "Ehh" Kuka ta sakar masa tace "Toh yanxu ni ya xa ayi da ni ina son ganinta, ka rufa min asiri ka kai mata wayar yanxu inyi mata magana" Yace "Toh" Tace "Toh Ina jira don Allah" katse wayar yayi, tana kallon Mai adaidaitan dake tunanin shiga xata yi su wuce, tayi shigewarta napep din tace "Sanyi ya dameni, ka jira in gama wayata a tsanake sai kayi wucewar ka Allah yayi maka albarka" juyowa yyi da sauri yana kallonta, ta rafka uban tagumi tace "D'a na ne yyi ta'asa ya saki matar arxiki matar kirki bani da labari" Junaid na kwankwasa kofar bedroom din Mami tayi masa izinin shigowa, Vid call take yi da Second daughter dinta dake aure Abuja, hannu junaid ya daga ma kanwar tasa dake masa murmushi ganinsa, ya tafi gefen makeken gadon dakin ya xauna, Mami ta juya tana kallonsa tace "Ya aka yi?" Yace "Aa ki gama" Jin abinda yace kanwarsa Deenar tace "Mami we will talk later a ji da Yaya" Mami tace "Alright" daga haka ta katse kiran ta juya tana kallon Junaid tace "Har ka tashi?" Yace "Eh na tashi, Ina kwana" tace "Lafiya lau" Yace "Mami yanxu kaka ta kirani" Mami tace "Ohk ya aka yi?" Yyi kasa da murya yace "She said she wants to speak with you" Mami ta d'an yi shiru kafin tace "Ohk kirata" Dialing number xai yi sai ga kiran kaka ya mike ya kai ma Mami bayan yyi picking, Mami ta kai kunne hade da sallama, kaka ta fashe da kuka tace "Yanxu Rakiya ashe abinda ke faruwa kenan sbda ba ni na haifeki ba kika ki gaya min, shi Amadun ne yyi maki haka don ya sameki a banxa?" Mami ta d'an yi murmushi tace "Aa kaka kiyi hakuri, ba wani abu...." Kaka ta dakatar da ita tace "Ke dakata ba ruwana da kame kamen ki, kina ina yanxu?" Mami tace "Ina gidana" Kaka tace "A ina?" Mami tace "Unguwar Dosa" Kaka tace "Ahhh lalacewa ta same Junaidu kenan, da girmata xai gilla min karya? To ai kuma ya xama abun tsoro in haka ne, dama bakin ciki yake da sanin ki da nayi ban sani ba, to aniyarsa ta bi sa..." Murmushi kawai Mami take, Junaid ya xaro ido yana sauraron kaka don muryarta xaki xakwai a wayar, Kaka tace "Ga d'an sahu nan kiyi masa kwatance ya kawo ni yanxun nan" daga haka ta mika ma Me adaidaitan waya Mami ta basa address din anguwar yace ya gane ya katse wayar ya mika ma kaka, kaka ta jefa jaka murya can kasa tace "Naira hamsin ai xai kai mu ko kuma arba'in" Mami ce ta fito bakin gate bayan me adaidaitan ya kira yace suna layin, Junaid dama bedroom dinsa ya shige ya kulle, Mami tayi murmushi bayan adaidaitan ya tsaya kaka ta sakko tace "Sannu da xuwa kaka" Kaka na bincika jakarta ta ciro naira hamsin tace "Yauwa Rakiya" Mika ma me adaidaitan hamsin din tayi, yyi kasake yana kallonta, Mami da dama ta fito da kudi ta mika masa dubu dayan hannunta tace "Mun gode malam...." Ya amsa kaka tace "Ga dai canji a hannuna kuma kya basa uban kudin nan a ina xai samo canji dari tara da hamsin Rakiya" Mami tace "Mu je ciki don Allah kaka, ai gidan da nisa" Godiya me adaidaita yayi ma Mami ya ja adaidaitansa, kaka ta bi sa da cewa barawo a fusace, Mami ta yi shigewarta ciki, Kaka ta bi bayanta tana cewa "Duk 'yan fashi ne a da, alqunut da ake ta jifansu da shi ya sa suka koma kabu kabun adaidaita, Banda haka meye xa a bashi dubu daya ya falla a guje da mashin kamar barawo" Suna shigowa parlor kaka na bin ko ina da kallo tace "Nan ne gidan naki Rakiya?" Mami tayi murmushi tace "Aa gidan Mahaifin su Junaid ne, ba nawa bane wannan" Kaka ta marairaice ta xauna sai kuma ta fara kuka tace "Yanxu da gaske Rakiya sakin ki Amadu yayi?" Mami kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Ehh haka ne" Kaka ta kuma rushewa da kuka tace "Toh Allah ya bi maki hakkin ki, Allah ya saka maki, muna nan dake sai yayi hawaye da idonsa bbu ruwana da koma meye ya samesa, nima yau kwana tara rabon da in sa ido a kansa bbu xuwa gaisheni bbu kirana, gashi sun yi fada kaca kaca da yayan nasa Umaru, dama fa yana da bakin hali kawai boyewa yake yi, amma yanxu tunda anyi walkiya mun gangosa ai sai kowa yyi ta kansa, Deedayar ma a rabasa da ita kada wataran ya da6a mata wuka kawai" Mami dai bata ce komai ba, Kaka na kara bin parlon da kallo tace "Maa sha Allah, da gatanki kaca kaca ai ba ayi shegen namiji da xai walakanta ki ba wllh, daga kin taimakesa kin auresa kin rike masa makauniya tsakanin ki da Allah sai cin mutunci ya biyo baya, to wllh yyi ma kansa, Kar ki sa komai a ranki, kyakkyawar xuciyar ki baxai ta6a bari ki tagayyara ba, nima kai na da na haifesa baxan bi ta kansa ba balle ke, kuma ido xan saka masa kar yayi min rashin kunya" Mami tayi murmushi kawai, Mai aikinta ta fito kitchen ta duka har kasa ta gaida kaka, kaka tace "Yauwa sannu" Mami tace "Ki kawo kayan kari" Kaka tace "Dama ban ci komai ba wllh" A can daki Mami ta sa Mai aikin ta kai ma kaka breakfast. Bayan kaka ta gama breakfast din tana ta sakace sakacen hakori don an ci nama ba kadan ba, Junaid ya shigo dakin da sallama kansa a kasa, tabe baki kaka tayi ta rungume hannu ta kauda kai, yana murmushi ya xauna nan saman carpet din dakin yace "Sannu da xuwa kaka" Kaka tace "Aa ba ruwana da makaryaci gaskiya, kai da ka gilla min karya kana Abuja kuma me ya kawo ka kaduna?" Dariya yyi yace "Kaka bacci nake lkcn da kika kira ban san ma inda nace maki nake ba" Kaka tace "Toh Allah ya kyauta, ai gani nan dai na xo kuma da kyar idan baxan yi kwana biyu a nan ba don ya fi min alkhairi" Heedayah ce tafe tare da Farida ta dalilin kiransu da aka yi daga Admin an xo masu visiting.... watanninsu hudu kenan a makarantar, ko sati biyu basu yi da dawowa makaranta daga hutun First term ba, a watannin nan hudu Heedayah is one of the best student in Jss2, bbu wanda xai ce a makance ta san abubuwa da dama na boko a rayuwarta, xuwa yanxu kam girma ya d'an fara bayyana a jikinta, kyawunta kuwa sai gaba yake tamkar diyar larabawa, sosai Guardian mother dinta ta makaranta ke ji da ita jininsu ya hadu ba kadan ba, Farida tayi breaking silence din tace "But it can't be Mami or even Yaya, sbda Yaya ya kawo min textbooks dina last week ai baxai xo ba satin nan na sani, Mami kuma is in Abuja" Heedayah ta kalleta da manyan idanuwanta tace "Then who??" Farida tace "Toh ni ma ban sani ba" har dai suka isa admin block aka yi directing dinsu karkashin one of the trees na cikin makarantar, tun daga nisa Heedayah ke kallonsa haka ma Farida, wayarsa yake dannawa idonsa sanye da bakin glasses da ya haska sa sosai, baka ganin komai daga nisan sai dogon hancinsa, Farida sai kallonsa take, lkci daya ya daga kai yana kallonsu, murmushi ya sakar masu, Heedayah ta mayar masa cikin sanyayyan muryarta tace "Ya Sudais" Mikewa yayi still smiling at them. Heedayah isn't free it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Heedayah tace "Ina yini ya Sudais" ya cire glasses din idonsa yana kallon kwayar idonta yace "Lafiya lau ya karatu?" Tace "Alhmdllh" gaishesa Farida ma tayi, ya amsa mata da murmushi yace "How is study?" Tace "fine Alhmdllh" yace "That's great" Yana kallon Heedayah yace "Hope you are enjoying it in here yan matan Mami" Ta gyada masa kai tana murmushi tace "Sure" yace "That's nice" Heedayah tace "Ya Sudais Kaka fa" Yace "Tana gidan su Farida ai" Heedayah tace "Okay but when we went back for holiday bata nan, ban ganta ba" yace "Baki ce Mami ta kai ki wajenta ba" A hankali Heedayah tace "Ta ki" Sudais yace "Ohh may be she is busy" komawa yayi ya xauna inda yake yace "Ku ai makarantar ku ne ni bari in xauna" Dariya Heedayah tayi tace "Yes, beside we are not that lazy" ya xaro ido yana kallonta, Farida dai tayi murmushi, sun kusa awa daya tare da Sudais a wajen, yawanci duk xancen da suke na karatu ne, and he was so amazed at how intelligent Heedayah was ya kasa daina kallonta even for a second, Daga karshe dai ya mike yace "Ya kamata ku je ku ci gaba da karatu yanxu, but ku baku da d'an supermarket din nan na cikin makarantar?" Heedayah tace "Aa muna da, they sell everything" Yace "That's sweet" Dubu ashirin ya fiddo aljihunsa ya mika ma Farida yace "Ke ce babba ku siyi duk abinda ku ke bukata, I don't really know what u will like shi yasa ban siya komai ba while coming" Farida tace "Last week fa yayanmu ya xo kuma ya ba mu kudi, we have enough money" Yace "Yes I know, but kina nufin ni ba yayanku bane?" Murmushi tayi tace "Not at all ba haka nake nufi ba" Yace "Toh amsa" Ta amshi kudin tace "Toh mun gode Allah ya saka da alkhairi" Heedayah tayi murmushi tace "We appreciate ya Sudais" Yace "You are welcm all" Daga haka suka rabu da shi, Heedayah sai waigosa take don sai taji bata son su rabu, she is going to miss him much. Mami na kitchen da safe tare da mai aikinta suna hada breakfast kasancewar ranan asabar ne baxata fita aiki ba, Daga nan parlor kaka ke cewa "Ai ni da na biye ta Umaru baxai ma bar ni in xo nan ba, kinsan da yake ba sata kadai ne abun kunya ba, Ina ga kunyar xuwa wajen ki da nake yi suke, tunda sun san abinda suka tafka shi da d'an uwan, to kuma yau sati na kusan daya a nan duk safiya ina lura da jik'a jik'an aikin da me aikin nan taki take ba kan gado kamar yar maguzawa, kuma kawai don na mata magana ki ce don me? Ni sai in iya tattara yanawa yanawa in tafi duk inda Allah yayi wllh" Mami dai na jin ta a kitchen tayi murmushi bata ce komai ba, ko kadan bata son kyaran da Kaka ke yi ma mai aikin nata, abu kadan yarinyar tayi sai fitinar kaka, ta lura duk inda me aiki take jininsu bai haduwa da kaka, kaka ta kara daga murya tace "Toh idan na koma gida yanxu ba sai Umaru ya min dariya ba har da shewa, kin ga ko gwara in tafi duk inda Allah yayi, don tun farko ya hanani xuwa, kawai daga na fada gaskiya ki ce min ba haka bane wato dai a fakaice makaryaciya kika kirani, masu aikin jaraba suna neman hada ni da ke, to ni bbu ruwana kafin ki koreni gwara ko xuwa nan da sati biyu ne in tattara komai nawa in yi wucewata, ko tsinke baxan bari ba wllh" Danna bell aka yi, Mami dake ta murmushi tace "Zainab tafi ki duba waye a kofa" Tace "Toh Hajiya" daga haka ta fita, kaka ta bi ta da wani shegen kallo tayi mitsi mitsi da ido tace "Algunguma me raba xumunci kawai" Zainab na bude kofa ta gaida wanda ta gani tsaye da ladabi, ya amsa yana kallonta, with respect tace "Wa xa a ce?" Yace "Barrister" tace "Toh" sannan ta juya ta koma, kaka ta sake bin ta da harara har ta shiga kitchen din, sannan tayi kwafa tana kara gyara xama, da ladabi Zainab tace ma Mami "Hajiya wai Barrister ne" Mami dake juya farfesun kayan ciki dake saman gas ta kalleta tace "Barrister? Daga ina wai?" Zainab tace "Aa bai sanar min ba" Mami tace "Koma ki tambayesa daga ina" Zainab ta juya ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tace "Hajiya cewa yayi Barrister Ahmad Aliyu" Mami dake kwashe farfesun a warmer don har yayi, bayan few seconds tace "Kiyi hakuri ki koma ki tambayesa akwai matsala ne? Wa yake nema" Juyawa tayi ta sake fita, Kaka dai na ta xaman parlor kamshin farfesu duk ya cikata don da farko cewa tayi xata tafi, har jakarta tace xata tafi ta dakko a sama, amma tunda taji irin kamshin dake tashi ta share batun jakar tayi mukus sai kame kamen fada da take ta yi, Kaka tace "Toh waye ya danna mana kararrawa naga bai shigo ba har yanxu" Zainab xata koma kitchen tace "Bako ne kaka" Kaka tace "Wani jarabbben bako da sassafen nan ko karyawa ba mu yi ba yunwa ta dame mu, girkin ma da iya cikin mu kawai aka yi, wani bako kuma" Zainab na shiga kitchen din tace "Hajiya cewa yayi xuwa yayi ya gaida Kaka" Mami tace "Ohk toh xan wuce sama ynxu sai ki kashe gas din ruwan xafin nan ki tafi kice ya shigo tana parlor" Zainab tace "Toh" daga haka Mami ta fito parlor, Kaka tace "Nan dai da sati uku xuwa hudu xan koma gidan Umaru tunda shaidaniya ta fara shiga tsakaninmu, ba ruwana da fada da ke" Mami na murmushi tace "Aa kaka bbu wanda xai shiga tsakaninmu baki dai fahimce ni bane, bari in sakkowa ynxu in kawo maki kayan karin" Daga haka Mami ta wuce sama, Kaka tayi kasa da murya tace "Ni yau naga jaraba duk sai yunwa ya gama cutar jama'ah ya lahanta 'yan hanjinmu sannan a bamu kayan karin, ni dai na gaji wllh...." Zainab ta bude kofar parlon tana kallon Barrister tace "Bismillah" Da sallama ya shigo parlon, Kaka ta saki baki tana kallonsa da mamaki, har ya karasa cikin parlon kallonsa take baki bude, ya xauna yyi kasa da murya yace "Ina kwana Baaba" Kaka ta rufe bakin tace "Ikon Allah, to batan hanya kayi Amadu koko xuwa kayi ka kawo mana tashin hankali a nan muna xaman xaman mu?" Ya girgixa kai yace "Aa na dai xo ne in gaishe ki" Kaka tace "Ni a wa?? Iyye? Nace ni a wa xaka xo gaisheni, dama ka hada abu da nine bani da labari?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Toh bbu ruwana kada ma raina ya baci ka tashi kayi ta kanka" Yyi kasa da kai yace "Aa kiyi hakuri nayi tafiya ne, aiki yyi min yawa...." Kaka tace "Ayyoo, Allah sarki.... Yawan aikin ne ya sa ka saki Rakiya kenan ashe?" Abba ya kalleta yace "Aa ni ban saketa ba" Kaka tace "Ohh don baka da kunya karya xaka yi a gabana? laifi kan laifi, me wnn baiwar Allah tayi maka da xaka yi mata wannan d'an banxan cin mutuncin, da girmanta da k'imarta da dukiyarta ka walakanta ta haka Amadu??" Sai kuma ta fashe da kuka Abba yace "Ni fa wllh ban saketa ba Baaba" Kaka ta dakatar da kukan da take tace "Ko dai wiwin kai ma ka fara sha, ka saki mace kace baka saketa ba sbda lalacewa ta same ka?" Yace "Wllh nace ban saketa ba dama tana da niyyar tafiya ne kawai" Sake baki Kaka tayi tana kallonsa, can ta kwalo ma Zainab kira ta fito daga kitchen da sauri, kaka tace "Tafi sama ki kira min Rakiya" Zainab na dawowa tace "Tana xuwa kaka" Kaka tace "Toh gwara dai ta xo" Har bayan minti goma Mami bata sakko ba, kaka ta sake mayar da Zainab, Zainab ta dawo tace tana bandaki, kaka ta mike tace "Toh ai ba komai bane idan ni na tafi na kirata da kai na, bbu wanda xai maidani karamar mutum daga ita har Amadun" Mami bata iya yi ma kaka musu ba bayan ya shigo dakinta, ta mike ta bi bayanta suka fita, kaka ta juyo tana kallonta tayi kasa da murya tace "Anya Rakiya ba a siyar da wiwi gun aikin ku kuwa?" Mami tace "Me ya faru?" Kaka tace "Da kyar idan ba wani ya fara tusa masa ra'ayin abun ba, naga kamar ba a saiti kansa yake ba, gashi yaki yadda mu hada ido, kuma alamar maganarsa bbu la'asar ko kadan, gatsau gatsau yake min" Mami tace "No ba gun aikin mu daya ba ai" Kaka tace "Ikon Allah...." Har sannan Abba na xaune parlor, Mami dai bata karasa ciki ba, kaka ta xauna tace "Toh maimaita abinda kace kan Rakiya Amadu" Abba yace "Nace ban saketa ba" Kaka ta kalli Mami tace "Ke kinji dai ko?" Mami tace "Ehh haka ne" Bude baki kaka tayi tana kallonta, can tace "Ban gane ba" Mami tace "Bana auren ne kawai, kuma ya saurari sammaci nan ba da dadewa ba, tunda ya ki bani takardata ta lumana" Kaka tace "Oh oh Allah na shiga uku, kina da hankali kuwa Rakiya ko kema kin fara shaye shayen ne, dama bai sake ki ba kika tattara kika yi tafiyar ki sbda rashin tsoron Allah?" Mami tace "Bana auren ne kaka shi yasa na tafi, na kuma masa magana ya bani takardata ya ki bani, don haka kinga kuwa dole in kai batun gaba" Kaka tace "A ina kika gansa kika yi masa maganan?" Mami tace "Na tura masa message severally..." Abba dake ta kallon Mami yace "Okay xan baki takardar ki kamar yanda kika bukata but sai mun ajiye yarjejeniyar bbu ke bbu Heedayah, ki cire hannun ki kan lamarinta...." Mami ta dakatar da shi tace "Sorry to say, wannan ne kuma baka isa ba barrister, baxan yarda da duk wani abu da xai cutar da ita ba don xamanta gidanka bbu abinda xai haifar sai cutar da yarinyar" Abba yace "Okay then, kema ki saurari sammaci" Mami tace "I will welcome that gladly" mikewa yayi yana kallon kaka da ta kasa cewa komai ta saki baki tana kallonsu yace "Na gaishe ki Baaba" daga haka ya nufi kofa. Salati kaka ta saki tace "Naga abinda ya isheni ni Patuu, me xan gani haka, ke Rakiya ashe dama auren ki ba mutuwa yyi ba kika tattaro kika dawo nan, meye a takardan da kika ce kin gani parlon na ki to?" Mami tace "Aa ba wani abu bane, amma baxan dauka ba Kaka, ya bani takardata kawai bana auren dama sbda in ceci rayuwar wnn baiwar Allah na amince muka yi xaman aure da shi, amma tunda cin mutunci ya fara shigowa to baxan iya ba kuma baxan dauka ba, ni ba yarinya bace da xan tsaya ina kishi ko wani tashin hankali a kan namiji kuma, sannan duk abinda xai yi yayi amma Wlh tllh baxan basa Heedayah ba, tsaf matarsa xata iya kasheta ya rufe case din bbu wanda ya sani, kinga kuwa bai cancanci riketa ba" Kaka tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni dai, toh ni duk ba wannan ba yanda ya shigo yana mana magana gatsa gatsa ne ya dameni yanxu, bbu fa wani rusuna da yyi da wnn lamarin, sannan tunda ya san bai sake ki ba kuma ya xo ya tarar baki gidan ai ya kamata ya bi ki duk inda kika tafi ya ji dalilin tafiyar ki, Anya Amadu kansa daya kuwa?? Sannan ya shigo gaisheni bbu bada hakurin rashin gaisheni da bai yi ba na kusan shekara daya bbu alamar nadama a tare da shi kwata kwata" Mami dai bata ce mata komai ba ta tafi kitchen kawo mata breakfast. Sai da kaka ta cinye kayan cikin tass sannan tace "Ni dai Rakiya kiyi hakuri ki rufa ma Amadu asiri ki rufa min asiri, ki rufa ma Deedayah asiri kada ki kawo masa sammacin nan, Allah xai daidaita ku in sha Allahu tunda ke dai ba ki nufin kowa da sharri...." Mami tayi murmushi tace "Kiyi hakuri kaka, amma Wllh wllh kinji har na rantse na gama auren barrister, sannan ya gama rikon Heedayah, sai dai idan ba Barrister Rahinah bace ni" Kaka tayi mata wani kallo tace "Ka ji tsiya da wasali, to ai shi ma Amadun ba kyalle bane, sai dai ku yi ta gogawa daga karshe ya nanaki da kasa a banxa kawai, ta ina xa ki rabasa da Deedayah da yyi ta wahala da tun tana makauniya, a ta dalilinsa fa kika santa, Anya kina tsoron Allah kuwa Rakiya" Mami tayi wani dariya tace "Sai dai ni in nana shi da kasa kaka don na fi sa gaskiya, kuma In sha Allahu Heedayah baxata sake xama gidansa ba, ta gama xama tare da shi kenan har abada, har Allah ya bayyana iyayenta idan suna da rai...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Kaka ta daga hannu tace "Toh ni dai ba ruwana, wnn ai kunyata kan ku xa ku yi a idon duniya kawai, meye kuma fada a kotu a kan yar yarinya da ba ku hada komai da ita ba?? Idan haka ne a raba gardama a mayar da ita dai dai gun da aka daukota a ajiye, ko kuma a bani hotonta in baxama duniya neman Yan uwanta idan ma iyayenta mutuwa suka yi ai baxa a rasa yan uwanta ba, son xuciya ya hana Amadu yin haka, bamu san nufinsa a kanta ba gaskiya" Mami dai bata ce da kaka komai ba tana danna wayarta. Tun da Heedayah ta tashi yau take murna xa su tafi gida sbda hutun second term da suka yi, duk suka gama hada kayan da xa su mayar gida tare da Farida, bayan azahar aka xo daukarsu, tsaye su ka gansa jikin motarsa ya rungume hannu, ganinsu ya bude masu booth, suka xuba kayansu ciki, Farida na kallonsa tace "Ina yini Yaya" yace "Lafiya lau" Heedayah ma ta gaishesa ya amsa yana kallonta suka shiga back seat gaba daya, ya shiga motar suka wuce gida. Farida ta gama hada ma mai aiki kayansu gaba daya da na Heedayah tace "Idan ma baxa ki iya gugan ba idan kin wanke ki bari xan saka Yusuf yyi mana, pls ki wanke mana da kyau sis Zainab" Muryar Mami suka ji daga sama tace "Zainab bar masu kayansu, idan baxa su wanke ba su bar shi, kada kiyi ma ko wani yaro wanki a gidan nan" Farida ta juya tana kallon Mami kamar xata yi kuka tace "Mami jiya fa muka dawo ko hutawa ba mu gama yi ba, sannan I have a lot to read for my coming waec" Mami tace "Kar ma kiyi karatun mana, na dai gaya maki Zainab, kuma kada ku sake ku dawo min da kayan wanki sama, daga nan parlor ku yi waje da shi" daga haka tayi komawarta daki, Zainab dai na tsaye bata ce komai ba, Farida ta tabe baki ta kwashe kayan a fusace tana kallon Heedayah da ta kwanta saman dogon kujera jin abinda Mami tace, tace "Toh baxa ki tashi mu je mu yi ba" Heedayah ta marairaice tace "Farida wllh I am not feeling well kema kin sani" Farida tace "Yes I know but ki taso sai ki dinga dauraya ni sai inyi shanya, if not ni dai baxan maki wanki ba" Turo baki Heedayah tayi Farida ta fita can compound da kayan, Mikewa Heedayah tayi ta dau hularta ta saka don doguwar riga ce har kasa jikinta ta bi bayan Farida xuwa waje, Farida har ta tara buckets din a tap dake tsakar gidan xata fara wankin, Heedayah ta xauna saman Plastic chair, Wanki Farida ta fara yi duk rai ba dadi, ganin ta wanke yafi biyar Heedayah ko motsawa bata yi daga xaunen da take ba, ta fara ware kayan tana maida na Heedayah gefe daya, dariya Heedayah tayi ta sakko tace "Toh yi hakuri Faree" Kamar warce bata da laka ta dinga shafa kayan wai tana daurayewa, ta marairaice fuska, sun yi nisa a wankin aka bude gate duk suka juya, sosai gaban Heedayah ya fadi bayan sun hada ido, Farida ta dauke kai ta ci gaba da wankin da take yi, slowly yake tahowa sanye da kananun kaya, ya sa face cap, camouflage na Soja" Heedayah ta saci kallonsa ganin ya kusa inda suke suka kara hada ido don kallonta yake, sunkuyar da kanta tayi, Farida tace "Good evening" Yace "Evening, Mami na ciki?" Farida tace "Ehh" murya can kasa Heedayah tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" daga haka yyi wucewarsa ciki. Mikewa Heedayah tayi bayan wasu mintuna ta xauna tana girgixa kai tace "Wllh Farida cikina ciwo yake min" Farida tace "Dama fa babu abinda kike min a nan Didi, you can go in and stop pretending pls" Heedayah bata ce mata komai ba, ta rike cikinta da ta ji yana murda mata, Farida tace "Nace ki wuce ciki kawai, don't worry by the time na yi waec next month xan ga wanda xai dinga maki wanki a schl" Mikewa Heedayah tayi tsaye da kyar ta nufi cikin gida tana cewa "And don't forget also ss2 xan yi waec" Farida bata tanka ta ba, tana duddukawa ta shiga parlor ,Mami na xaune parlorn tare da Shuraim, "Jiya na dawo" Cewarsa kenan yana duban Mami, Mami tace "Amma kaka tace min kana nan mun yi waya da ita few days back" Yace "Aa, Ina Abuja and bata sani ba" Mami tace "Can kake aikin?" Yace "Aa nan Kaduna, Ina 44, mun je aiki ne Abuja..." Mami tace "Maa sha Allah, it's been long Shuraim" Ya cire face cap dinsa ya d'an yi murmushi yace "Haka ne" Heedayah ce ta shigo parlon, Mami tace "Meye haka? Me ya faru" Da kyar tace "Mami cikina" Mami tace "Me ya sami cikin?" Ta nufi sama tace "Ciwo yake min" Mami ta bi ta da kallo har ta wuce sama sannan ta dawo da dubanta kan Shuraim, ya sauke idonsa daga kallon da ya bi Heedayah dashi shi ma, Mami ta kwalo ma Zainab kira, ta fito daga dakinta, Mami tace "Ki kawo ruwa" Shuraim yace "Noo I am okay..." Mami tace "Ki xubo har da abinci" Tana fadin haka ta mike ta wuce sama xuwa gun Heedayah, dakinsu ta shiga ta ganta durkushe a kasa ta rike cikin tana hawaye, Mami tace "What did you eat?" Cikin kuka tace "Nothing, tun a schl yake min ciwo wani lkcin" Mami tace "Toh kwanta in samo maki magani yanxu" Kwanciya tayi saman gadon tana goge idonta, Mami ta dawo parlor ta dau wayarta xata yi kira, Shuraim yace "Is she okay?" Mami tace "No Ciwon ciki take tun a schl, so ina son in aiki driver ya karbo mata magani a pharmacy..." Tana magana ta nufi kofa, Shuraim ya bi ta da kallo yace "But Mami asibiti xai fi ai" Mami ta dawo tace "Au, ai na mance you are also a Dr, kayi mata prescribing maganin mana yaje ya amso mata" Shuraim yace "Ban san wani irin ciwon ciki bane" Mami tace "To mu je ka tambayeta" tashi yyi ya bi bayan Mami xuwa dakinsu, Kuka Heedayah ke yi sosai saman gadon, Mami na shigowa dakin tace "Wayyo Mami it's paining me ni baxan iya ba" hankalin Mami ya fara tashi tace "Toh ko dai mu tafi asibiti" Karasowa dakin Shuraim yyi yana kallon Heedayah, Mami tace "Bari kawai mu tafi asibiti Shuraim, let me get my Hijab" daga haka ta fita, Da sauri Heedayah ta sauka saman gadon ta toshe bakinta ta shiga bathroom ta hau kwarara amai, Shuraim ya dinga kallon saman xanin gadon da ta tashi, can ya juya ya fita daga dakin, ko da Mami ta dawo dakin Heedayah bata fito bandaki ba, Mami har xata shiga bandakin jin amai take idonta ya sauka saman gadon, ta kalli kofa da sauri ta karasa ta cire xanin gadon, ta wuce bandakin, Durkushe ta sameta a ciki, Mami ta ajiye xanin gadon hannunta kan washing machine ta dagota tace "Sannu Daughter" Da kyar tace "Mami xan kwanta" Mami tace "No, u are stained" Heedayah ta kalli jikinta da sauri, a hankali Mami tace "Kin ta6a yi a schl ne?" Heedayah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Mami tace "Talk to me dear, kin ta6a yi?" Girgixa mata kai Heedayah tayi ba tare da ta dago ba, Mami tace "Ohk this is ur first time?" nan ma ta gyada kai kawai, Mami tace "But you know what it is right?" Nan ma dai Heedayah kanta a kasa tace "Uhn" Mami tace "Toh ina xuwa" Mami na fita Heedayah ta sake kallon jikinta sannan ta kalli xanin gadon da Mami ta kawo bandakin, Shuraim ne ya fado mata ta hadiye abu da kyar, duk da axaban da take ji fata take he didn't see anything, a haka Mami ta dawo bandakin rike da pad da pant, Mami tace "Kiyi wanka tukun, hope kin iya sa pad din?" Heedayah ta sunkuyar da kai tace "Uhn" Mami tace "Toh yi wankan ki gama" fita Mami tayi ta bar bandakin, A parlor ta tadda Shuraim, Ta xauna tace "Heedayah ta fiye raki ne, idan cikin bai lafa mata ba sai mu tafi asibitin, na bata wani magani ynxu" Shuraim yace "Allah ya sauwake" Mami tace "Ameen" Mami tace "Ka ci abincin mana" Yace "I am full" Bude kofar parlor aka yi Junaid ya shigo, Sau daya ya kalli Shuraim ya kauda kai, ya gaida Mami xai wuce sama Mami tace "Baka ga Shuraim bane Junaid" Junaid ya juyo ya kallesa, kamar sannan ya fara ganinsa yace "Ohh I didn't notice" karasawa yyi ya basa hannu suka gaisa briefly Junaid ya wuce sama Shuraim ya bi sa da kallo, Can kuma ya kalli Mami yace "Tayi bacci ne?" Mami tace "Ohk let me check" Tashi Mami tayi ta bi bayan Junaid, bakin kofar dakinsu Farida ta gansa a tsaye, kafin ya bude kofar tace "Kayi ajiya ne a ciki??" juyowa yyi da sauri ya fara kame kame yace "Noo, emm dama xan amshi wayata ne" Mami na kallonsa da kyau tace "Nace bana son kana shigar masu daki haka, I have warned u severally Junaid" Bai ce komai ba ya juya ya wuce dakinsa, Mami ta karasa ta bude kofar ta shiga, a gaban madubi taga Heedayah daure da towel ta duka, Mami tace "Sannu, ki saka kaya in baki magani" Heedayah ta dago a hankali tace "Mami ciwo yake min sosai" Mami tace "Xai daina in sha Allah" Mami ta fiddo mata kayan da kanta ta ajiye mata sannan ta tafi dauko mata pain relieve, Kwanciya tayi saman gado bayan ta saka kayan, Mami ta dawo dakin da maganin da bottle water ta bata ta sha tace "Tashi in shimfida maku wani bedsheet" Heedayah ta sauka ta durkusa a kasa, Mami ta shimfida xanin gadon sannan ta sa ta kwanta. Karfe Takwas na dare Mami ta sa Farida ta tafi ta kira Heedayah ta xo ta ci abinci, tun yamma tana daki, gani take kamar Shuraim na nan har lkcn, ba komai ke damunta ba sai xanin gadon da take tunanin kila ya gani, Farida tace "Ya jikin Didi?" Heedayah ta langwabar da kai a hankali tace "Da sauki" Farida tace "Allah ya sauwake, Mami tace ki sakko ki ci abinci" Heedayah tace "I am not hungry Farida" Farida tace "Toh mu je ki gaya mata ni ba ruwana, she said I should call you" Heedayah ta d'an yi shiru, can tace "Is Shureen still around" Farida tayi dariya tace "He is Shuraim not Shureen, baya nan ya wuce tun daxu" Heedayah ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, sakkowa tayi daga kan gadon tana kallon xanin gadon da jikinta, Farida ta kara fashewa da dariya tace "Toh ai idan kina haka xa ki sa a gane, just pretend, it's nothing, sannan ai kin canxa pad ko?" Heedayah ta gyada kai, Farida tace "Toh mu je" Bin bayanta tayi suka fita, gaba daya a tsarge take da kanta, Junaid na xaune parlor yana shan fruit salad suka shigo, Mami tace "Ga abinci Heedayah, if you want fruit sai Farida ta yanka maki" Heedayah dai bata ce komai ba ta xauna saman carpet a hankali tace "Ina yini Yaya" Junaid dake ta kallonta yace "Lafiya lau, u slept all day" Ita dai bata ce komai ba, Farida ta debar mata abincin ta ajiye gabanta, Junaid da sai kallonta yake ya kalli Mami yace "Mami is she sick" Mami tace "No, just slight headache magani ta sha shine take ta bacci" Yace "Ohk" Mami ta ci gaba da danne dannen laptop dinta, A hankali Heedayah ke cin abincin, da ta daga kai sai ta ga Junaid na kallonta, duk sai ta takura, ta gama cakalkala abincin ta mike ta wuce kitchen, satan kallon Mami da hankalinta ke kan abinda take yyi, ya mike a hankali ya dau Glass bowl din da ya ci fruit salad, Farida dai na kwance saman three seater tana danna wayarta, Kitchen ya nufa ya bude kofar ya shiga ya rufe, Heedayah ta juya da sauri, ya karasa inda take tsaye xata hada shayi ya tsaya bayanta yace "What wrong Heedayah?" Kasa cewa komai tayi tana girgixa masa kai, ya kamo hannunta yace "Talk to me plss are you sick" Kamar xata yi kuka tace "Yaya... Mami fa fada xata min, ka tafi plss, she can come in now" Juyo da ita yyi suna facing juna still holding her hands yace "Ki gaya min kukan me kika yi..." Ta xaro ido tana kara kallon kofar kitchen din tace "Aa ban yi kuka ba" Yace "Ur eyes are swollen" Tace "Baccin da nayi ne, Yaya don Allah ka fita Mami xata min fada sosai" Bude kofa aka yi, ya saketa ta juya da sauri har wani rawa hannunta yake, Farida ce tsaye bakin kofar kitchen din tace "Heedayah Mami na kiran ki" Heedayah tace "Toh" bata bi ta kan shayin ba ta bi bayan Farida da sauri, Junaid ya bi ta da ido har ta fita sannan ya ci gaba da hada mata shayin, Suna shigowa parlor Mami ta dinga yi ma Heedayah wani kallo, Heedayah ta sunkuyar da kanta tace "Na kai plate ne kitchen" Mami tace "So? sai aka ce ki dau ages kafin ki fito kitchen din?" Ta girgixa kai kawai ta xauna kasan carpet, fitowa Junaid yyi da cup din shayin, ko kallonsa Mami bata yi ba, ya iso cikin parlon ya mika ma Heedayah cup din, Mami tace "Wani ya sa ka hada mata shayi?" Yace "No ta fara hadawa ne ta fita shine na karasa mata" Heedayah ta amshi shayin tace "Nagode" Mikewa tayi tace "Mami sai da safe" Mami tace "Ki sha magani kafin ki kwanta" ta amsa da "to" sannan ta wuce sama. Har karfe sha daya Heedayah bata yi bacci ba cikin na damunta sosai, Farida tuni tayi bacci bayan ta gama phone call, Heedayah ta mike xaune ta sauke kafarta daga kan gadon ta goge guntun hawayen idonta, tashi tayi ta nufi kofa sbda wani shayin da take so ta sha, ta bude kofa a hankali ta fita don in Mami taji fitowarta baxata yrda ta hada wani shayin ba, sauka tayi downstairs, ta shiga kitchen ta kulle kofan, daxu ruwan flask din ba shi da yawa sai ta daura wani a gas, ta kunna gas ta sa ruwa kadan aka bude kitchen din, a tsorace ta juya, junaid ta gani, ya shigo kitchen din ya kulle, tace "Yaya baka yi bacci ba" Yace "Yea, another tea?" Ta kirkiri murmushi bata ce komai ba, ya karasa kusa da ita yana kallon lashes dinta da ya d'an jike da hawaye, da damuwa yace "Ki gaya min me ke damun ki Heedayah" Tace "Ba komai Yaya, amma kar Mami fa ta shigo nan yanxu" Yace "Ga hawaye idonki kice min ba komai" Matsawa xata yi daga kusa da shi ya rikota, kamar xata yi kuka tace "Yaya ka bari pls" Yace "Toh gaya min kukan me kike" Tace "Cikina ke ciwo" ya xaro ido yace "Cikin ki kuma? Tun yaushe? And did you take drug?" Kafin ta ce komai ya kai hannu cikin nata, ta xaro ido xata durkusa ya rikota, ta hade rai tace "Yaya bana son haka" yace "Tun yaushe cikin ke maki ciwo?" Tace "Da safe" yace "Kin sha magani?" Tace "Mami ta bani" Cike da tausayinta yace "Sorry Lolly" ta xuba mashi ido kawai, yace "Har yanxu yana ciwon kuma" hawaye ya kawo idonta ta gyada masa kai, yace "Toh ya yake maki?" Tace "I don't understand the pain too" kashe gas din yyi sbda ruwan ya tafasa, ya hada mata shayin da kansa yace "Toh mu je ki sha shayin sai in baki magani" ba musu ta shiga gaba ya bi ta da kallo, doguwar riga ne fari irin na bacci jikinta sai hulan dake kanta, ya dinga kallonta ganin xata juyo ya kauda kai ya tafi switch din wutan kitchen din xai kashe, xaune ya sameta parlor tana fiffita shayin da spoon, ya karasa Inda take ya xaune gefenta yyi kasa da murya yace "You know what?" Ta girgixa masa kai, yace "Kawo in fifita maki shayin ki tafi daki ki canxa kayanki ki dawo" kasa cewa komai tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi, da kyar tace "Me ya samu kayana?" Yyi kasa da murya yace "You are stained" still tayi tana kallonsa da idanuwanta kamar xa su yi magana, yace "Tashi ki tafi" Ta sauke kanta kasa, ba karamin courage tayi gathering ba sannan ta mike ta wuce sama da sauri ya bi ta da kallo, tana shiga daki bayan ta gyara jikinta ta kashe wuta tayi Kwanciyarta. Washegari bata yadda sun hada ido da junaid ba da ya hade rai yana bin ta da kallo a parlor, Atamfa ne jikinta riga da skirt ta yafa dankwalin a kanta, ban da Mami da ta aika Farida kiranta in d'an ta ita ne ma baxata sakko ba yau baccin kirki bata yi ba jiya sbda stain din da Junaid yace tayi, ji tayi gaba daya kunyarsa ma take, shayi ta hada ta xauna nan parlor tana sha a hankali da dankali, Farida da Zainab na kitchen suna gyare gyare, Mami kuma na xaune parlon tana waya, Mami na gama wayar tace "Heedayah anjima sai ki raka Farida supermarket ku siyo mana spices, bana son kwanciyan nan da kike yi, ku je a Napep idan xa ku dawo ku yi strolling you will feel strong" a hankali Heedayah tace "Toh Mami" Mikewa Junaid yyi ya wuce sama, Mami ta bi sa da harara don tana lura da kallon da yake ma Heedayah. Hijab har kasa Heedayah ta saka don gani take ko jingina tayi by mistake da abu sai tayi staining mutane sun gani, Farida dai ta saka abayarta da veil ta dau karamar jakarta suka fita, adaidaita sahu suka samu xuwa shopping mall din bayan duk sun gama siyayyar su, har da guzurin turare duk cikin kudin Mami suka fito shopping mall din, da kafa suke tafiya kamar yanda Mami ta umarce su, Heedayah dai sai yatsina fuska take don gaba daya bata son tafiyar..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Tsaye suke su biyu jikin mota a bakin wani katon hotel, alamar dai wani suke jira, wanda ba shi da tsayi sosai ya ta6a me tsayin gefensa dake waya yana sanar ma wanda suke jira a hotel din xa su wuce idan baxai fito ba, Juyowa yyi yana kallonsa da alamar tambaya amma bai ce komai ba, Mutumin yyi kasa da murya yace "Babaa kaga wasu fine chicks kuwa, dogaye farare....." Tsaki yyi ya ci gaba da wayarsa ba tare da ya kalli direction din da abokin tsayuwar nasa ke nuna masa ba, Gajeran ya kara tabosa ganin su Farida sun kusa inda suke yace "Dallah ka sallami idanuwanka malam, just look at them, kyawawa ne fa" Dogon Mutumin dake waya a mugun fusace yace "Hey pls ka daina nuna min 'yan mata idan muna tare, stop that pls, I don't have any business with ladies, ba su ke gabana ba, just planning on how to get...." Dai dai nan su Farida suka iso inda suke tsaye, Wanda hakan yasa Mutumin bai karasa abinda xai fada ba ya makale a bakinsa ya bi Heedayah da kallo ko kiftawa babu, gajeran kusa da shi ya kyalkyale da wani shegen dariya yace "Ya dai Genius? Ya da wnn kallon??" Mutumin ya kifta ido ya sake bin Heedayah da kallo, bai san lkcn da ya bi bayansu ba da sauri, Guntun Mutumin sae dariya yake har da kyakyatawa, can kuma ya dakatar da dariyan yyi shiru ya bi abokin nasa da kallo, coz like seriously bai ta6a ganin Genius ya kula mace ba, komin komin kyanta kuwa, and it's not as if basa haduwa da kyawawan mata wanda ma suka fi wa ennan da suka wuce ynxu, ga dai tsadaddun yan matan Abuja da kullum suke gani iri iri don sun fi harkarsu a can... Tsaye yyi gabansu ya cire bakin glasses din idonsa yana kallon Heedayah, Heedayah suka kalli juna da Farida, duk sai suka gansu wasu marasu tsayi a kusa da shi, da mamaki Farida tace "Meye haka malam??" Ya cire p cap din kansa yana kallonsu da dara daran idonsa yyi kasa da murya yace "I'm Sorry" kallonsa kawai Heedayah ke yi almost not blinking, Farida ta wani daure fuska ta kama hannun Heedayah xa su bar wajen yace "Amm Pls... Can... can I drop you both.... home" Bluntly Farida tace "Capital NO, Tafiyar ta fi mana, shi sa ma ka ganmu da kafafuwan mu, isn't not as if ba mu da kudin motar, you need not to drop us home, thanks for the solidarity" slowly yace "But I'm sorry Madam, ba da ke nake ba" Farida ta ja wani tsaki ta ja Heedayah suka bar wajen, bin ta kawai Heedayah ke yi sai kuma ta waigo tana kallon Mutumin da ya bi su da ido, karasowa gajeran Mutumin yyi gun abokin nasa with much surprise yace "But this is odd Genuis, tun da muke da kai ban ta6a ganin ka tare mace ba sai yau, don hka ko sun ki ko sun so wllh sae sun saurare ka, ka kyaleni da su, idan Maska ya fito ku tafi xan same ku a joint...." yana fadin haka ya bar sa gun a tsaye ya bi bayan su Heedayah da suka yi nisa sbda saurin da Farida ke yi, ita dai Heedayah bin ta kawai take, adaidaita farida ta tsayar masu don ta fasa trekking din, gajeran Mutumin da ya bi su ya tsayar da wani napep din yace "Ka bi min adaidaitan gabanka, kannina na ciki ina son sanin inda xa su je" Farida ta hade rai cikin napep din bayan sun fara tafiya tace "Wai meye naga mood din ki haka Heedayah?" Heedayah ta kalleta, a hankali tace "His voice sounds familiar" Farida ta buda ido sosai tace "Da gaske?" Heedayah ta gyada mata kai a hankali, Farida tace "Ikon Allah, then where did you know him??" Heedayah tace "I am still thinking" Farida ta marairaice tace "Toh ae da kin gaya min tun a can sai mu kulasa mu ji waye, to kin yi shiru kawai, kuma tsayawa da yyi gabanmu ai rainin hankali ne tunda mu ba gantalallu bane shi sa nayi masa haka" Heedayah bata kuma cewa komai ba har suka isa gida wajen sha biyu da rabi, Farida ta sauka ta ba Mai adaidaitan kudi, Heedayah ma ta sauka, Murmushi Mutumin dake cikin napep din nesa da su yyi yana kallonsu har suka shiga gidan da yake tunanin nasu ne sannan yace ma Mai adaidaitan su wuce. Babu kowa parlor Farida ta kai kayan da suka siyo kitchen suka wuce sama dakin Mami da Heedayah, Mami tace "Kuna fita su Jamila suka xo" Farida tace "Wacce Jamila?" Mami tace "Ke baxa ki wani sansu ba amma ita Heedayah ta san su, yaran Baffansu Rabi'ah ne" Heedayah tace "Ayya, ita kadai ta xo?" Mami tace "Aa su uku suka xo, sun kawo IV" Heedayah tace "Waye xai yi aure?" Mami tace "Kannin Sudais biyu" Heedayah tace "Ohk su Aunty Safiya" cike da murna Farida tace "Dama kwana biyu ban je biki ba wllh, yaushe ne bikin Mami?" Mami ta galla mata wani kallo tace "To Amara" dariya Farida tayi tace "Pls Mami saura kwana nawa?" Mami tace "Saura 10 days" Heedayah tace "Allah ya kai mu" Mami tace "Ameen, xuwa gobe sai ku shiga kasuwa ku siyi anko, na bata number Farida xata turo mata sample din ankon ta WhatsApp" Farida tace "Toh shkkn Mami" Heedayah suka fito da Farida xuwa dakinsu, har sannan muryar Mutumin daxu ke dawo mata a kai, ita dai ta san ta ta6a jin muryar nan, ta nemi gefen gado still thinking hard, tun da tayi regaining sight dinta wani lkcn tuno abu ke d'an bata wahala, which is very unusual, Amma idan ta damu brain dinta ta kan tuno kuma, Farida dake kallonta tace "Ya aka yi Heedayah?" Heedayah ta juyo tayi murmushi tace "Nothing wanka xanyi" daga haka ta mike ta fara cire kayanta xata shiga Bathroom. Da daddare Heedayah na xaune dinning da Farida suna cin abinci Mami na dakinta, Heedayah tayi kasa da murya tace "Wai ina Mami ta ajiye chocolate dinmu da tayi seizing when we came back from schl Faree?" Farida tace "I don't know, kila ma ta xubar a shara, that's a simple act for her" Heedayah ta marairaice bata ce komai ba, ranan da xa su dawo daga makaranta suka shiga supermarket din cikin makarantar suka siya chocolates har na dubu uku, mistakenly Mami ta gani ta dauke, Heedayah tace "I am craving for it wllh" Farida tace "May be it's because kina period, kuma idan kika sha cikin ki ciwo xai fara maki ba ruwana" Heedayah tace "Just one fa" Farida tace "Toh ki dau wayata ki kira Yaya ki gaya masa ya siya maki idan yana dawowa" Heedayah ta turo baki don hide and seek take yi da shi tun incident din daren jiya, Heedayah tace "Kafin a karasa bakin titi ba akwai wani karamin supermarket ba, xan je in siyo a can" Farida tace "Then u will have to sneak out kenan, don Mami won't let you, and ni baxan fita in rakaki ba ynxu na cire kaya" Heedayah ta mike tace "Sure" Daki ta tafi ta dauko dubu daya cikin ragowar kudin da suka dawo da shi daga makaranta ta sa Hijab dinta ta fita gidan, bbu kowa layin nasu ta isa shagon a kusa da bakin hanya, ta xabi chocolate din da take so ya kama dari biyar ta basa dubu dayan, yana bata canji wata mota ta shigo layin, kauda kai tayi sbda haska ta da fitilar motar ke yi, ana bata canjinta ta fara wucewa da sauri, tsayawa taga motar yyi bayan ya wuceta a can gaba, ita dai tafiyarta kawai take har ta isa dai dai motar ta ga an bude kofar motar, sosai gabanta ya fadi, Mutumin daxu ta gani ya sauko motar yana kallonta, from all indications ya rasa abinda xai ce, coz he looks speechless, ta wucesa da sauri, bin bayanta yyi walking fast har ya jera da ita yyi kasa da murya yace "Good evening" Tsaya tayi ta juyo ta hade rai tace "Why are you following me?" Ya fara kalle kalle, looking for what to say, a lkci daya yace "Naga kamar na san ki ne" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "A ina ka san ni?" Ya sauke idonsa yace "I don't really know, but I know na san ki" Ta dauke kanta, kamar baxata ce komai ba, can tace "And I also know ur voice" Ya buda ido yace "Really?" Tace "Yess" yace "May be a mafarki muka san juna... " Ta hade rai tace "Ba a mafarki bane" Xai yi magana wani mota ya shigo layin, xaro ido tayi ta koma bayansa da sauri tace "Na shiga uku yayanmu ne, kar ya gan ni" Kafin yace komai ta durkusa kasa gabanta na faduwa, Ya bi motar da ya wucesu da ido yana kallon guy din dake ciki, sai da motar ya shiga compound bayan mai gadi ya bude gate sannan Heedayah ta mike har lkcn gabanta na faduwa, ya juya yana kallonta kafin yace komai tayi saurin cewa "Good night" ta fara tafiya, yace "Wait..." Ta juyo ya nufeta yace "Ki bani number ki, I will figure out where we know each other sai in gaya maki" Ta 6ata fuska tace "Don't worry about that, may be illusion ne kawai amma bamu san juna ba, not anywhere" A hankali yace "Billah na san ki, na ta6a ganin ki, har mun ta6a magana...." tayi shiru tana kallonsa ko kiftawa bbu, yace "Bani lambar ki" ta girgixa kai tace "Ba ni da waya" Hannu ya sa a aljihunsa ya ciro tsadadden wayarsa ya mika mata yace "I will call you..." Tace "Noo...." Yace "Amsa nace, I will call and tell you where I know you" K'in amsan wayar tayi ya kama hannunta, sosai gabanta ya fadi jin hannunsa a nata, ya saka wayarsa a ciki sannan a hankali yace "I am Khaleel..." Tayi shiru tana kallonsa, yace "And you?" Ta sauke idonta kasa tace "Heedayah" tana fadin haka ta juya ta fara tafiya ya bi ta da ido har ta isa gate din gida ta shiga. Heedayah ta fi minti biyar tsaye bakin kofa tana tsoron shiga parlon kar a ce Mami ta sakko downstairs, a hankali ta bude kofar daga karshe ta shiga, Farida ce kadai parlon, Farida tayi mata alamar ta wuce sama da sauri, hanyar stairs ta nufa taji ance "Where are you coming from?" Farida ta saci kallon direction din kitchen taga junaid ya fito, Heedayah da gabanta ya shiga faduwa sbda wayar dake hannunta a cikin hijab tace "Naje siyan abu ne" karasowa parlon yyi yace "Me kika je siya?" Ganin ya nufota ta wuce sama da gudu ta shige dakinsu ta sa makulli, Farida dai sai kallon tv take attentively kamar bata san suna yi ba, Junaid ya juya ya hade rai yana kallonta yace "Me taje siyowa?" Farida tace "Ba wani abu bane Yaya, chocolate ta je siyowa a shago bata son Mami ta sani kuma" Heedayah na shiga dakinsu ta dinga kallon hoton dake jikin screen din waya kirar Samsung da ya bata, shine jikin screen din wayar, hoton yyi kyau ba kadan ba ya jingina da pillar din wani ubansun gida ga motoci ya kusa bakwai a katon compound din, bata samu access din shiga wayar ba don a lock yake, knocking aka yi ta juya da sauri ta tafi gun handbag dinta ta saka wayar ciki sannan tace "Waye?" Farida tace "It's me, open" Heedayah ta bude kofar Farida ta shigo ta sake sa makulli, Farida tace "Me yasa kika dade, ina ta tsoron kar Mami ta sakko taga bakya nan" Heedayah tace "I met people buying stuffs there" Dai dai ta raba chocolate din ta ba Farida rabi, ta dau rabi... Farida ta ajiye nata a jaka sannan ta kwanta tana danna wayarta, sai kusan sha biyu Farida tayi bacci, Heedayah dai na ta kwance tayi kamar me bacci amma idonta biyu, can da ta ji alamar Farida tayi bacci ta sauka daga kan gadon ta tafi jakarta ta bude a hankali ta dau wayar dake ciki, miss call ta gani guda biyu, tana ta kallon wayar sai ga shi kira ya kara shigowa ta ga an sa "KH" kallon Farida tayi sannan ta shige bathroom ta rufe ta daga kiran, sallama yyi daga daya side din, sai da ya kara yin sallama sannan ta amsa, yace "Baki yi bacci ba?" Tace "Ehh, and where did you say u know me?" Ya d'an yi shiru sannan yace "I can't remember but I will remember soon, ya kike?" Tace "Ohk then, anytime you remember we will talk, sai da safe" Da sauri yace "Nooo wait Heedayah..." tace "But I can speak comfortable with a stranger" yyi kasa da murya yace "But I am not a stranger" Tace "Xan kwanta ne" ya d'an yi shiru sannan yace "Toh sai da safe, I will spend the night thinking of inda na ta6a sanin ki, sleep tight" Bata ce komai ba ya katse kiran, ta dinga kallon screen din sannan ta juya a hankali ta fita ta saka wayar a jaka sannan tayi addu'ar bacci ta kwanta. Washegari Saturday da safe Farida suka gama shirin tafiya islamiyya kamar yanda dai suke yi idan suna hutu, Sunan tsaye jikin mota suna jiran fitowar Driver Junaid ya shigo gidan daga gym, duk suka gaishesa ya amsa, Heedayah dai ta dauke kai don bata son ma su hada ido har ya wuce, driver na isowa suka shiga motar suka bar gidan. Heedayah na aji taji vibration din waya a jakarta ta kalli Farida dake xaune gabanta sannan ta mike ta saka jakar a hijab ta nemi ixinin malamin su ta fita, Farida ta girgixa kai don a tunaninta xuwa xata yi ta sake duba ko tayi stain tunda aikinta kenan tun da suka shigo, can bayan wani building Heedayah ta tsaya ta fiddo wayar ta daga, Khaleel yace "Good morning" tace "Ina kwana?" Yace "Lafiya lau, how are you?" Tace "Fine, why did you call?" Shiru ta ji yyi, sai kuma yace "To check on you" tace "Toh bana so, stop it... I want your call to be meaningful, like... you telling me where you know me, how and when" Yace "Sure duk xan gaya maki amma idan mun hadu.... Where will that be? I mean wajen da xa mu hadu?" Heedayah ta wani hade rai kamar yana ganinta tace "A wani dalilin xan hadu da kai, besides meye ma sanin ka xai kareni da, nothing of course..." Cikin cool voice yace "Do not judge that, kilan ynxu haka akwai abinda kike buri a rayuwarki, they are wishes you are wishing.... I might make those wishes come true, you never can tell" shiru tayi tana sauraron sa, yace "Anyway, naji kamar baki gida, sai later" Bai jira cewarta ba ya katse wayar, Heedayah ta jingina da bango tana naxarin maganganunsa, wishes she is wishing? Sure she have wish, and her biggest wish in life now is to meet with her Mother, a da hakan baya damunta ko kadan don har mantawa take ba Mami da Abba suka haifeta ba, amma daga farkon shekaran nan sai take yawan jin abun a ranta, ta kara kallon wayar hannunta sannan ta saka a jaka a hankali ta bar wajen duk jikinta a sanyaye, but how did he know she have wishes a mind dinta.... Karfe uku saura Farida da Heedayah suka bar gida xuwa kasuwa don siyo ankon Safiya da Nafisa, kusan dubu sittin suka kashe a kasuwan don lace ne me kyau sosai da atamfa kala biyu, Farida tace "Kawai mu tafi plazan da nake bada dinki mu bada kafin mu wuce gida" hakan suka yi sai da suka fara kai dinkin sannan suka fito suka samu adaidaita xuwa gida don Mami tace baxasu je da driver ba su basa wahala ya rasa gun ajiye mota a kasuwa, throughout ranan Heedayah na ta jiran kiran Khaleel amma bai kira ba har washegari, gashi wayar da lock balle tace ko xata kirasa, har bayan kwana biyu bai kirata ba, ta shiga damuwar da ta rasa dalilinsa sai dai ko da wasa bata yrda kowa ya gane halin da take ciki ba, bini bini xata duba wayar a jaka amma bbu miss call, ranan talata ta dawo islamiyya tana wanke uniform dinsu da na Farida da yamma a bakin tap a waje aka bude gate, juyawa tayi Sudais ya shigo gidan tare da Shuraim, ta dauke kanta ta ci gaba da wankin da take, Sudais ya karaso Inda take ba tare da ta dago ba tace "Good evening" yana murmushi yace "Evening cutie ya kike?" Tace "Lafiya lau" yace "Ya hutu?" Tace "Alhmdllh" satan kallon Shuraim tayi suka hada ido don kallonta yake, tayi saurin sunkuyar da kanta tace "Ina yini" Can ciki taji yace "Lafiya" Sudais yace "Mami na ciki kuwa?" Heedayah tace "Aa bata dawo ba" yace "Ohh really" gyada masa kai tayi, yace "Toh shkkn anjima da daddare xa mu dawo" Heedayah tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Farida fa?" Tace "Tana kitchen da Sis Zainab" Sudais yace "Alright sai yaushe xaku taho can gida?" Heedayah tace "Sai Mami tace mu tafi" Yace "Toh shkkn, let get going" daga haka ya bi bayan Shuraim da ya fara tafiya, ganin tafiyar da Shuraim ke yi kamar bai son yi Sudais yyi overtaking dinsa nan ko bai san intentionally yyi hakan ba, Shuraim ya d'an juya bayan Sudais ya shiga gabansa suka hada ido da Heedayah da ta bi su da kallo, da sauri ta dauke idonta ta ci gaba da wankinta shi kuma ya fice gate din as if ana koransa. Shirye shiryen biki kawai ake a gidan Baffa ba kama kafar yaro, ana biki saura kwana biyu aka kawo lefe hakan yasa Mami taje gidan tare da Farida da Heedayah shima sbda kiran da kaka ke tayi mata don bata yi niyyar xuwa ba sai ranan bikin, Junaid ne ya kai su gidan bikin a motarsa, yawanci dama shi ba kullum xaka samesa a gida ba may be twice in a week ko thrice kadai yake kwana a gida yafi tsayawa gidan Baffan sa, yana parking Mami ta sauka motar tace "Sai yaushe?" Yana magana yana kallon Heedayah ta madubi yace "Gobe in sha Allah" Mami tace "Allah ya kai mu" daga haka ta nufi cikin gidan, Farida ta sauka motar haka Heedayah, Farida tace "Sae anjima Yaya" ya gyada mata kai, Heedayah tace "Sae anjima" alama yyi mata da ta xo da hannunsa, ta 6ata fuska ta kalli gate din gidan sae kuma ta karasa ta tsaya tana kallonsa yace "Me yasa kika sa mayafi Heedayah? Baya maki kyau" a hankali tace "Mami ce tace in sa Yaya" yyi shiru yana kallonta, can yace "Alright" ta daga masa hannu ta nufi cikin gidan. Yan uwa da abokan arxiki har sun fara cika gidan biki ana ta shiri, Mami ta shiga parlon da sallama girls dinta da suka yi anko na atamfa me tsada na biye da ita a baya, sosai kayan ya amshi Heedayah da ta sakale gyalen gefen shoulder dinta, tayi wani sanyayyan kyau duk da bata yi kwalliya ba sai eye pencil da ta saka idonta da chappet da ta goga lips dinta, Mumy ce xaune parlor da kawarta Hajiya Sadiya, sai Hajiya Amina mahaifiyar Sudais da step mother dinsa, sun dai kusa goma sha biyu a parlon duk dai ana tsara yanda abubuwa xa su kasance, masu tafiya kasuwa na shirin tafiya, Tunda Mami ta shigo Mumy da ta yi ture ka ga tsiya ga daham dinta a wuya ke kallonta, farin ciki ba na wasa ba Mumy tayi don ta wani hakikance kan kujera sai kace sarauniya, Lkci daya murnan Mumy ya koma ciki ido hudu da tayi da Heedayah dake bayan Mumy, Heedayah dai ta xama cikakkiyar budurwa don idan ka ganta ma baxa kace she is just 16 ba, Doguwa ce fara sosai kuma siririya, hancinta is worth noticing ko da kuwa daga nisa take, ga karamin bakinta me xagaye da jan labbe, gaba daya ta sauya daga lkcn da take 13 don idan ba saninta kayi sosai ba baxa kace ita ba ce, Mumy ta hadiye abu da kyar ta kalli Hajiya Sadiya dake kallon Heedayah ita ma ba ko kiftawa, Heedayah da Farida suka durkusa suka gaida Mutanen parlon, ita Mum din Sudais dama ko ganeta bata yi ba Hajiya Hauwa ce kadai ta ganeta don sai kallonta take tana murmushi, Mami tayi hanyar dakin kaka don ta gama gaisawa da occupant din parlon, mikewa Heedayah da Farida suka yi suka bi bayan Mamin tasu, Mumy tayi kasa da ido ta bi Heedayah da kallo har suka shiga dakin kaka, da mayafinta ta share d'an guntun xufan da taji ya keto mata..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Rungume kaka Heedayah tayi ta kankameta cike da murnan ganinta, rabonta da kaka tun da suka yi hutun jss3 third term, sae da kaka ta kare mata kallo daga sama har kasa sannan ta turata tace "Aa ni ki rufa min asiri kar ki cuceni ki kada ni kasa ana bikin jikokina, ki bar ganin kin tsayince kamar falwaya, nima ina yan mata haka nake duk da dai yanxun ma ni ba guntuwa bace" Mami tayi dariya ta xauna tace "Sannu kaka...." kaka tace "Yanxu Rakiya fisabilillahi auren 'ya yan Umaru fa ake kika ki xuwa sai yau, ke da ya kamata ace tun ana sauran sati daya xaki tattaro kayanki ki dawo nan, xumunci fa ba abun wasa bane ba abun yadawa bane, idan ma ke baxa ki xo ba ai sai ki turo mana Heedayah tunda ta mu ce, ki bar ganin an sakar maki ita ki xata galaba kika ci a kanmu, ni ce nan nake ta tausan Amadu amma kiris ya rage ya kwace 'yar sa tunda ba ke kika tsinto masa ita ba, Kuma ba ke kika warkar mata da idonta ba" Ba yabo ba fallasa Mami tace "Toh sai yah xo.... ina jiransa" A hankali Heedayah ta xamo kasa tace "Ina kwana kaka?" Ko kallonta Kaka bata yi ba tace "Ina da labarin sun yi hutu yau kusan sati biyu amma kin ki barin ta xo ta gaisheni ta gaida wan Amadu sannan ta tafi gidan shi Amadun ta gaishesa idan ya kama har kwana biyu tayi, wannan dai ba yi bane, fitina a kwance take dai idan kika tada ta ke kika sani... Ko jiya sai da Amadu yace xai je ya dauketa nace ban ki ta tasa ba amma yyi hakuri muyi bikinmu mu cashe lafiya, bayan biki sai yaje can ku ci kanku bbu ruwan wani, wllh tllh haka aka yi ki tambayi wnn yaro Shureen ai tare suka shigo jiyan" Shuraim dai na tsaye dakin yana danna wayarsa, Mami taki cewa komai, Shuraim ya gaida Mami, ta amsa da murmushi tana tambayarsa ya aiki, Farida dake danna wayarta ita ma tace masa "Ina yini" yace "Lafiya lau" Murya can kasa Heedayah tace "Ina yini" ya ci gaba da danna wayarsa bai ce komai ba, kaka tace "To dai wnn shine dalilin ma da na kira ki nace na ji ku shiru, Amadu ne ya xo nan xai daga mana hankali wai xai je amso yarinya, ni dai na samu na lallabasa ya wuce, wnn yarinya dai ya fi kowa iko a kanta kema kin sani sai dai idan kina da karancin tsoron Allah, don haka ki raba kanki da fitina ki daina kokarin rabata kwata kwata da uban rikonta ba wani ya tsinto masa ita ba, jifa jifa sai ki turata da wnn yarinya Farida su je suyi kwana biyu gidansa haka ake yi ba ki yi bake bake a kan yarinya ba ke kadai, da bai tsintota tana galantoyi ba a ina xa ki santa Rakiya? to ga dai akwatina nan, daya matsiyacin mijin kwara biyar ya kawo gasu can a gantale ko budewa jama'ah bana yi, dayan kuma d'an albarka guda takwas da uban kaya a wani jakar ya kawo... Ku yi ta dubawa tunda na yadda da ke baxa ki cuce mu ba, kinsan akwai masu sace kaya idan sun xo gani, yanxu dai kasuwa wnn yaran xa su rakani, in je in siyo masu mafici, matankadi, gwa-gwa, maburgi, ludayan miya, 'yar kwalla karama me ado, turmi da kwarya, duk gantalallun iyayen basu siya masu ba basu san shi aka kai mana lkcn mu ba auren yyi albarka da izinin Allah, wai su 'yan xamani to ba dani xa ayi wnn lalacewar ba, xan tafi yanxu da kai na in siyo masu a bakin dogo, nace wnn mutumi Shureen ya kai ni a mota ya ki, da yake tunda ya samu sojan nan ya fara saka ilifon dinsu yake ganin kowa bbu gashi, ynxu kafin ku shigo sae kinga fitsaran da yyi min, to sojan karya ma da bai isa rike bindiga ba har ynxu, uban wa xai basa bindiga dama, ni dai har yau ban gansa da bindigan wasan yara ba balle na gasken amma har shine xai dinga raina ma mutane wayo" Ta gefen ido Shuraim ya ke kallonta, Mami dae sai murmushi take ta ki cewa komai, Heedayah ta taba jakarta da sauri jin kamar vibration, mikewa tayi ta shige bandaki, Shuraim ya bi ta da kallo har ta rufe kofa, Jin rufe kofar bayin kaka ta bi dakin da kallo don ganin waye ya shigar mata bandaki, da sauri tace "Rufa min asiri kar ki min amfani da bayi ki fito ki tafi ki shiga na masu biki...." Heedayah har da sa makulli snn ta fiddo wayar a jakarta, miss call tagani guda daya na Khaleel, tana ta tsaye ko xa a kara kira amma shiru, ta jira ta jira har Mami ta kwalo mata kira ta fito dakin, kaka na tsaye da Farida ana jiranta xa a je kasuwa, Shuraim dai sae kallonta yake, kaka tace "Toh uwar me kike min a bandaki kika dade haka" Heedayah ta turo baki tace "Ni ba abinda nake yi" Kaka tace "Toh ni ba ruwana ki sa mayafi mu tafi kasuwan, ke muke jira" Heedayah na son bin kaka amma tana tunanin xa a kara kiranta a waya, ta marairaice kafin tace komai kaka ta ja hannun Farida tace "Mu yi ta kanmu ba xuwa xata yi ba gantalalliyar" Daga haka suka fita xuwa kasuwa, Shuraim yyi ma Mami sallama ya fita, Mami ta fara sauke akwatin don duba kayayyakin ciki. Farida kam tayi da ta sanin bin kaka kasuwa don tun daga kan Mai adaidaita aka fara don bata basa cikakken kudinsa ba, kafin magana tayi tsawo Farida ta bude jakarta ta fiddo dari biyu ta mika masa ya ja machine dinsa ya wuce, kaka ta shiga kasuwar tana xaginsa, Farida tace "Kaka tun daga gida fa ya dauko mu xa ki basa naira dari..." a mugun fusace kaka tace "Uwarki Rakiya ke nemo min kudina ko a bishiya nace maki nake tsinkowa, kawai yarinya baki da amfani na xo da ke kasuwa saura kiris a min duka kina kallo, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin haka ba, Ashe ke shashasha ce, da Jamila ce yau sai ko ita ko barawon, Aa barawo mana, banda barawo wani d'an adaidaita ne xai amshi dari uku hankali kwance bbu tsoron Allah kamar mun hau jirgi, ko xuwa makka daga nan nawa yake aka ce maki? Toh ba ruwana daga yau kika sake cewa xa ki bi ni kasuwa sai na miki barbadin bala'i" Farida kamar tayi kuka sbda tsaye mutane suka yi ana kallonsu, kaka taga wani me mafici ta duka ta dauka tana cewa "Kai nawa nawa wnn, jikokina ne xa ayi ma aure jibi, da yake barbadadu ne iyayen ko batun maficin basa yi...." Hayaniyar da ta ji gefenta ya sa ta mike da sauri tana kallon abinda ke faruwa, wata dattijuwa ta gani tsaye tayi mitsi mitsi da ido tana dungurin wani me siyar da kaya irinsu tafarnuwa, kanunfari, citta da dai sauransu, sai cewa take "Ni xaka gilla ma karya kace baka harareni ba??" Jama'ah suka fara taruwa ana bata hakuri, cike da bala'i take cewa "Ni sai ya gaya min wa ya tsaya masa a Najeriya da xai harareni.... daga nace ya bani tafarnuwar ashirin ya bani kwaya biyu nace ban so, kawai sae mutumi ya harareni?sannan ya kara da gilla karyar cewar bai harareni ba, ya san wacece ni kuwa?" Mutumin dake ta kasa kayansa yace "Na sani mana, tunda gashi kin kawo ashirin xa ki siyi tafarnuwar da ko na hamsin babu a kasuwa" kaka ce ta kai masa naushi a baya tace "Amma kai dai anyi lalatattce, yanxu ka dubi wnn tsohuwar da ta haifi kakan ka ka rufe gwalmadaddun idon ka ka dinga xaxxaga mata fitsara??" Sai kallo ya koma kan kaka, Farida ta kasa motsi inda take, can kawai ta juya ta koma titi don neman adaidaitan da xai mayar da ita gida, Kaka da wnn yar dattijuwa suka hadu suka yi ma me kaya tatas, daga karshe shi kansa dariya abun ya basa don ko kallonsu bai kara yi ba sai kasa kayansa yake a 'yar rumfarsa, kaka ta juya kan masu bada hakuri tace "Ku kuma meye xaku dame kunnanmu da bada hakuri, da ku wasu ne da suka san darajan iyaye ai matse d'an banxa xa ku yi ku daure ku nakada masa shegen duka...." Dattijuwar tace "Toh su ma din duk ba barayin bane, wa ya sani ma ko akwai barayin satan yara a cikinsu, ni abinda ya fi min ciwo shine hararata da yyi, ga fa yan dubu dubu a jakata kar yyi xaton gantalalliya ce ni, kanina na can Abuja wani babban mukami yake nema yanxu haka amma baxan fada ba don ban san xuciyar kowa ba a nan, to ina xan biye yan yunwa a titi inyi tashin hankali da su, tafarnuwar fa sadaka dama nake son inyi da shi ba wani abu ba" Kaka tace "Bar masa tsiyarsa, da xa ki bi ni mu tafi gidan d'ana Umaru buhun tafarnuwa gareni wllh, sai in debar maki rabin buhun" Tsohuwar tace "Ai kanina ya hanani shige shige, banda haka da na biki wllh" kaka tace "Ba wani shige shige, shi gantalallen kanin naki da ace ya ajiye maki buhun tafarnuwar me xai kawo ki kasuwa mutumi ya harareki??" Kaka ta bude jaka ta fiddo wayarta tace "Ni dai bani lambar ki, nima ina da 'ya ya a Habujan nan, ana gama biki dama xan je can" Tsohuwar tace "Ni dai ban yafe hararata da yyi ba wllh" Kaka ta kara kai ma me kayan dundu a baya tace "Ai ba don su Amadu xa su min fada ba da mun ja sa mun tafi caji ofis yanxu, amma ce min xa su yi meye hadina da ke" Tsohuwar ta fiddo wayarta a jaka tace "Ni ban san kan waya ba ke ki sa min naki lambar" kaka tace "Aa bana gane kan waya da rana, da dai mu nemi wani ya fiddo lambobin" Da sauri kaka ta juya tace "Auuu, ae da yarinya na taho ina take?" Nan kaka ta shiga duba Farida a kasuwa bbu alamar ta, wani mutumi suka samu kaka tace "Na ganka fes fes kamar d'an boko, don Allah ga wayata ka ciro min lambata ka ba ma wnn tsohuwar ita ma ka cire nata ka bani, Ashe bata yi makaranta ba bata san kan wayar ba" Kaka ta linke d'an takardar da Mutumin ya rubuta lamba ta saka a jaka, ita ma tsohuwar ta saka nata a jaka, kaka tace "Ni dai da kin ji ta nawa mu tafi gida kawai daga nan sai na debar maki tafarnuwar" Tsohuwar tace "Toh ai ba a son ina shige shige, toh amma dai mu je kawai" Mai maficin dake ta jiran kaka ganin xa su wuce yace "Mama kin fasa siyan maficin ne" kaka tace "Kai rabu da ni na fasa, iyayensu su xo su siya masu ai ba ni na haifesu ba, ubansu kawai na haifa" Daga haka suka bar wajen. Kaka na shiga compound tace "Toh ni Hajiya kaka ake ce min, xuwa makkata yayi hamsin...." Tsohuwar tace "Toh ni wannan shekaran ma kanina ya biya min Umra, kafin a fara axumi xan tafi, duk shekara sai naje makka sau biyar" Kaka ta tabe baki bata ce komai ba, can kuma tace "Toh mu lkcn da muka yi yayin xuwa makka kuna ina, kawai dai mun yi hankali me yanxu" Mutanen dake parlon har da Mumy suka gaida kaka da Sabuwar bakuwarta, bbu yabo bbu fallasa kaka ta amsa tayi hanyar dakinta, dattijuwar na kallon mutan parlon tace "Haihuwa aka yi a gidan ne" Kawar Hajiya Amina tace "Aa biki dai ake" tace "Ayyoo, naga parlon kamar ana cin kasuwa" Daga haka ta bi bayan kaka xuwa dakinta, Bala'i kaka ta dinga yi don me Mami xata wuce bata tsaya ba, tsohuwar dake tsaye gefenta tace "Aa bata da mutunci ne kawai" Kaka tace "Wllh kuwa, tana nan fa kamar xabiya sai mugun abu a xuciya, idan xata tafi ba sai ta bar min yarinya ba, dama me muka hada da ita, ai yarinyar ce tamu, to ynxu xan kira Amadu in sanar masa rashin kunyar da ta min" Mumy dai na tsaye kusa da kaka jin fadan da take sai bata hakuri take kai kace ta kirki ce, wannan tsohuwa dai ta tabe baki tace "Toh ni ina tafarnuwata in wuce" Kaka na share xufar goshinta sbda fitina tace "Ai da satin da ya wuce muka hadu har buhu sai kin samu, to yanxu ni ina naga tafarnuwar da xan baki duk na rabar ma jama'ah" tsohuwar ta gyara yafin gyalenta ta fita dakin kan kace me tayi hanyar titi tana cewa "Ashe tsohuwar banxa na biyo" Da daddare Heedayah na kwance daki da jakarta a kusa da ita, Farida ta shigo dakin, ita dai tana ta mamakin me yasa Heedayah ke yawo da jaka tun dawowarsu daga gidan su Sudais, amma bata ce mata komai ba, Farida na kokarin cire kayanta tace "Mami tana kiran ki" Heedayah ta juyo tana kallonta, can tace "I tot tayi bacci" Farida tace "Bata yi ba" Daga haka ta shiga bandaki, Heedayah ta cire wayar jakan da sauri ta bude school bag dinta ta saka wayar a ciki sannan ta sa Hijab dinta kan kayan baccin jikinta ta fita xuwa dakin Mami, Mami na kallonta bayanta duka kusa da ita tace "Idan kin gama period dinki ki sanar min" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Mami tace "Kin ji abinda nace?" Sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Ae ya tsaya" Mami tace "Tun yaushe?" Heedayah tace "Yau ban yi ba" Mami tayi shiru tana kallonta, can tace "Two days kenan kika yi flow?" Ta gyada ma Mami kai, Mami tace "Toh, sai ki sa ido xuwa gobe jibi idan still u didn't see anything sai ki gaya min" Heedayah tace "Toh" Mami tace "You can go" Mikewa tayi tace "Sai da safe Mami" Mami tace "Allah ya kai mu lfya" Daga haka ta fita dakin. Kwance ta tadda Farida da ta rufe ido kamar me bacci, Heedayah ta kashe wutan dakin ta kwanta, bayan kusan minti talatin ta tashi ta nufi schl bag dinta tana waigan Farida ta bude ta jakar ta duba, bata ga miss call ba ta rufe sannan ta tafi ta kwanta, wajen karfe dayan dare Farida ta juya tana kallonta taga bacci take, tashi tayi ta dau wayarta ta haska schl bag din tana kallo sai kuma ta karasa ta bude tana duba ciki, still tayi tana kallon wayar, a hankali ta sa hannu ta ciro sa daga cikin jakar tana jujjuyawa, can ya kunna sai ga hoton Khaleel gaban screen din, Farida ta juya ta kalli Heedayah sannan ta tabe baki ta mayar mata da wayar ta rufe jakar ta koma ta kwanta. Washegari da safe, bayan sun idar da sllh a dakin Heedayah tace "Yau xa mu je siyo takalmi da kika ce ko?" Shiru Farida tayi, Heedayah tace "Are you sleeping?" Farida tace "No" Heedayah tace "Baki ji me nace ba?" Farida tace "I will use the one I am having, ke xa ki iya xuwa ki siya" Heedayah bata kuma ce mata komai ba ta mike ta fita dakin don ita ce da wanke wanke da gyaran kitchen yau, in dai suna nan toh Mami ta hana Zainab yin komai, Junaid ne kwance saman 3seater yana bacci, ta d'an buda ido coz basu ma san yana gidan ba, ta karasa kitchen ta rufe a hankali sannan ta fara aikin da xata yi. Bude kofar kitchen din aka Heedayah tayi still, sai kuma ta juyo tana kallonsa, ya jingina da kofa ya rungume hannunsa yana kallonta da lumsassun idonsa, ta dauke kai tana ci gaba da wanke wanken da take tace "Ina kwana Yaya" Jin bai amsa ba ta juya tana kallonsa, calmly yace "Lafiya lau, yau ma xa ku fita kenan?" Ta gyada masa kai tace "Xa mu je gidansu ya Sudais" yace "Me ake yi yau din?" Tace "Mothers day" shiru yyi yana kallonta, can yace "Why not stay back home ke da Farida, ai ba sai kun je ba, mother's day ai ba ladies day bane, ko kun fi son ayi ta ganinku..." Heedayah tace "Ae Mami ce tace mu je, tare da ita ma xa mu je" Bai kuma cewa komai ba ya juya ya bar bakin kofar, Heedayah ta turo baki ta ci gaba da wanke wankenta. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Bayan Azahar Mami ta gama shirin xuwa can gidan biki, tana xaune parlor tana jiransu farida dake sama suna shiryawa, sanin they need time to prepare ya sa bata takura su ba take xaune parlor patiently waiting for them, Farida ce kadai ke kwalliya ita Heedayah ta gama saka kayanta tunda ba kwalliya take ba dama, ta dai shafa powder da man baki, atamfa ce iri daya yau ma suka sa da Farida, sosai kayan yyi masu kyau ba kadan ba, tun safe Farida taki wani kulata ko magana a takaice take amsa mata, ita ma Heedayah bata sake ce mata komai ba har ynxu da suke shiryawa, tuni Heedayah ta maida wayar Khaleel jakar da xa ta fita da shi tana rungume da abarta, yau ma da safe sai da ta ga miss call dinsa hakan yasa ma ta cire wayar a total silent ta bar sa a vibration but very low with the help of side buttons din, vibration din wayar ta ji yanxu ma, da sauri ta kalli Farida dake ta kwalliyarta, can dai ta mike a hankali ta nufi bandaki ta shiga bandakin ta kulle, fiddo wayar tayi tana kallon screen din sannan ta daga ta kai kunne kafin ya katse, yyi mata sallama, murya can kasa ta amsa, sai da ya d'an yi shiru sannan yace "Me yasa baki daukan waya idan an kira ki?" Tace "Saboda ba yawo nake da wayar ba, kuma gidanmu bama rike waya, I am not allowed to do so" yace "Gidanku?" Tace "Ehh" yace "Ohk... I tot ba a gidanku kike ba" Shiru tayi tana naxarin abinda yace mata, sai kuma tace "How did you know that?" Yace "I only guessed, and lkcn da na san ki kamar.... you were unsighted...." kamar me counting words din yyi maganan, gaban Heedayah ya dinga faduwa tana sauraronsa, can ta marairaice tace "Plss a ina ka san ni ka gaya min don Allah, I can't remember where I knew ur voice...only knew it sounds familiar" yyi murmushi da take iya ji, sannan yace "Na sanki Heedayah" Kamar xata yi kuka tace "To a ina?" Yyi kasa da murya yace "Wani waje mana" Turo baki tayi tace "Bana so" yace "Toh gaya min inda xa mu hadu sai in gaya maki inda na sanki" ta d'an yi shiru sannan tace "Mami will punish me, ba a barin mu fito..." Yace "Yes... not at home...." Tace "To a ina?" Yace "Anywhere, duk inda kike so you tell me" ta buda ido sosai tace "Nace maka ba a barin mu fita ai a gida" yace "To ranan da na ganku Ina xa ku? And who was the lady you were together with" Tace "Mun je supermarket ne, she is my sister" Yace "A gidansu dai kike" ta d'an yi masa shiru sannan tace "Gidanmu ne nima" yace "Noo ba gidanku bane wllh" Cikin sanyin murya tace "To a ina gidanmu yake?" Bai ce komai ba haka yasa tace "Ka gaya min" yace "Wani makaranta kike?" Tace "Nigerian Turkish" yace "Why are you not in schl now?" Tace "Hutu" ya d'an yi shiru sannan yace "So bbu ranan da xa ki samu ki fito??" Tace "Ehh, but xa mu je biki yanxu" Kofa ta ji an bude a can daki da sauri tace "I need to hang up now...." Yace "Wait... to yaushe xa mu sake magana...." tace "Anjima" daga haka ta katse wayar ta saka shi jaka xuciyarta na bugawa, Mami ce ta shigo dakin tana kallon Farida dake makale bakin kofar bandaki wanda tana ganin Mamin ta bar wajen da sauri tana dube dube kamar tana neman wani abu a kasa, Mami tace "Meye hakan?" Farida tace "Aa barima na nake nema ya fadi ban san inda ya shiga ba" Mami tace "Ina Heedayar?" Farida tace "Ta shiga bandaki ne, ita nake jiran ta fito" Mami tace "To ni xan yi wucewata tunda abun naku walakanci ne idan kun gama sai ku samu adaidaita ya kawo ku, for almost an hour ina jiranku kamar masu shirin jaraba" Farida tace "Aa Mami wllh ni na gama, ita nake jira" Mami bata kuma ce mata komai ba ta nufi kofa ta fita dakin, Farida ta sake kallon kofar bandakin sannan ta dau jakarta ta bi bayan Mami, a hankali Heedayah ta bude kofar bandakin ta fito tana kalle kalle, ganin bbu kowa dakin ta fita xuwa downstairs da sauri. Back seat farida ta xauna, hakan ya sa ta bude gaba ta shiga, Mai gadi ya bude gate suka fita gidan. Sosai jama'ah suka cika gidan biki ana ta shagalulluka a katon tsakar gidan, lallai taron ya amsa sunansa na Mother's day, don iyaye ne mata sun yi shiga ta kece raini, can Heedayah ta hango kaka cikin jama'ah yanda ta kankance ido ya isa kasan cewar ba maganar arxiki take masu ba a can don wasu sai tabe baki suke, Heedayah ta bi bayan Mami da Farida da suka shiga parlon, Hajiya Hauwa na welcoming dinsu, kiris ya rage ta ci karo da Mumy da ta mike xata bar parlon cike da isa don bai ma Mami access din ganin kwalliyarta da gwalagwalanta da kyau, Heedayah ta koma baya tayi kasa da kai ta bata hanya tace "Ina yini" Ko kallonta Mumy bata yi ba ta wani daure fuska ta fita parlon Heedayah ta shiga a sanyaye, da fara'a Step mum din Sudais ta amsa gaisuwan Farida da Heedayah sannan tace "Ga can Sudais xai ajiye su Zainab saloon ku bi su ku ma kuyi gyaran gashi" da sauri Heedayah tace "Aa gashin mu a gyara yake ai" Mami ta juya tana kallonta, Farida tace "Toh bari mu je Mama" Hajiya Hauwa tace "Su Zainab din na daki ku tafi ku samesu sai ku wuce tare" Farida ta tafi inda Hajiya Hauwa ke nuna mata, Heedayah ta turo baki ta bi bayanta ranta bai so ba, Zainab 'yar Hajiya Hauwa ce, sai Jamila daya daga amaren, Daya Amaryar Safiyya dakinsu daya da Sudais sai Nafisa da Aisha, Zainab da Rabi'ah da Khadijah kadai xa su tafi saloon din don sauran sun je jiya tare da amaren, sae ynxu da Heedayah da Farida xa su bi su, Zainab na ganin su Heedayah tayi welcoming dinsu da fara'a tana masa sannu da xuwa, Aisha ma dai tayi masu sannu da xuwa sama sama, amma Nafisa tayi kamar bata gansu ba ballantana Rabi'ah da Khadijah, a haka dai har Sudais ya kira Zainab yace yana jiransu a waje, Zainab ta mike tana kallonsu Farida tace "Mu je yana jiranmu a waje" har ta fita ganin Rabi'ah da Khadijah basu fito ba ta dawo tace "Yana fa jiran mu a waje" Khadijah ta wani yatsine fuska tace "Ku je ku, anjima xa mu je wani saloon din" Zainab bata ce komai ba ta fita, a parlor Hajiya Hauwa tace "Ina sauran fa" Zainab tace "Wai baxa su ba" Mumy da shigowarta parlon kenan ta xo debar ma bakinta lemo tace "A kan me baxa su je ba??" Zainab tace "nima ban sani ba" da haka ta fita Farida da Heedayah na biye da ita, Mumy ta wuce sama fuskarta a tamke tana cewa "Bari in kira driver na ya xo ya kai su saloon din, ai ba dole dama su bi ku ba, ko wani saloon din ne sai ya kai su yanxu" Hajiya Hauwa dai bata ce komai ba balle Mami dake parlon. Zainab ta shiga front seat Heedayah da Farida suka shiga baya, Sudais ya amsa gaisuwarsu gaba daya yana kallonsu ta madubi yace "Yaushe ku ka xo?" Farida tace "Ba dadewa" yace "I see, ku ma xa ku yi gayun kenan" dariya kawai Farida tayi, ya kalli Heedayah da tayi shiru yace "Cutie kema gyaran gashin?" Murmushi tayi ta sauke idonta kasa tace "Uhn" yace "Toh idan kun dawo anjima sae a nuna min gashin in gani" Nan ma bata ce komai ba sai murmushi, sai da suka yi nisa Sudais ya d'an kalli Zainab yace "Wai su Rabi'ah sun fasa xuwa ne" Zainab tace "Ehh wai anjima xa su taho" yace "Ohk then" yana ajiye su saloon din ya ba Zainab kudin gyaran gashin nasu da kudin adaidaita da xai maida su gida sannan ya wuce. Sai kusan Magrib su Heedayah suka dawo gida, basu tadda Mami a gidan ba, Heedayah na kallon Farida da ta amshi gugan tiles din da kaka ke yi a dakinta tace "Toh mu wa xai kai mu gida?" Kaka ta juya da sauri tana kallonta tace "Wa xai kai ku gida kuma? Ba lafiya, Nan ba gida bane? To nice nan nace Rakiya tayi wucewarta kuna nan har bayan biki tunda ita baxa ta tsaya ba, idan ma ita faridar taga baxata xauna ba to ke kina nan, nan ne dolenki" Heedayah ta xauna saman kujera kaman xa ta yi kuka, Farida dai bata ce komai ba. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh taji vibration din wayarta dake kusa da ita, bin dakin tayi da kallo, Farida da Zainab ne xaune dakin suna hira, sai wata yar uwar Umma dake dakin tana waya. Heedayah ta saka jakar cikin hijab dinta cikin dubara ta mike ta ta shiga toilet, ciro wayar tayi ta dauka kafin ya katse, sallama yyi mata ta amsa yace "Kince anjima xa mu yi magana kuma nake ta kiranki baki dauka ba" ta wani turo baki tace "Toh ni ai bana nan mun fita, kuma the phone isn't ringing" Yace "Ina kika je?" Tace "Saloon" yace "Why didn't you tell me?" Tace "How will I tell you?" yace "Call me" tace "A rufe wayar yake, you didn't tell me the password" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "I remember, so where are you now?" Tace "Gidan yayan Abbanmu" yace "A ina?" Tace "Unguwar rimi" yace "Wani layi?" Tace "Nima ban sani ba" yace "Toh ki tambaya" a hankali tace "Toh" yace "I will call back in few minutes" tace "Tell me the password" yace "Sai na xo...." daga haka ya katse wayar, fita tayi bandakin ta xauna gefen gado, Farida dai ta kalleta bata ce komai ba suna ci gaba da labarinsu da Zainab, Bayan kusan minti biyar Heedaya ta kwanta tana kallon Zainab tace "Ya ma sunan layin nan sis" Zainab ta kalleta tace "Wai anguwar nan?" Heedayah tace "Ehh" Zainab ta gaya mata sunan anguwar, Heedayah tace "Ohk" bata kuma cewa komai ba tana ta kwance, sai taji wayar na vibrate, mikewa tayi tace "Bari in je in amso abinci am hungry" daga haka ta fita, can bayan gidan ta xaga bayan ta fita, ta daga kiran having making sure that bbu kowa wajen, nan ta gaya masa sunan layin yace "Ohk I am on my way" komawa tayi cikin gidan bayan ta mayar da wayar jaka, ta ki komawa bangaren kaka ta xauna parlor duk da akwai mutane, wasu na yanke yanken kayan ganye, kowa dai da abinda yake yi, bayan kusan minti sha biyar sai ga kiransa, da sauri ta fita ta daga kiran, yace "I am outside" sosai ta ji gabanta ya fadi, a hankali tace "Toh amma idan aka gan ni fa?" Yace "Babu wanda xai gan ki, ki fito" A hankali ta katse wayar ta mayar cikin jakar dake cikin hijab din jikinta sannan ta nufi gate tana yi tana waige waige har ta isa gate din xata fita, tana dube duben inda xata gansa, karo suka kusa ci da Shuraim da xuwansa gidan kenan, Suna hada ido ta koma baya a tsorace tana xare ido, juyawa yyi yana bin layin da kallo as if wanting to figure out something, suka hada ido da Khaleel da yyi parking daga daya side din kafin a iso dai dai gate din gidan, Khaleel ya fiddo wayarsa ya fara danne danne ya kai kunne, magana ya fara yi a wayar yana driving a hankali, har ya iso dai dai saitin Shuraim sannan yace "Ohhh ba nan bane? But I am seeing no. 28 here, ohk sorry 38, but wait.... can you plss come out ka daina bani wahala??" Sai kuma ya ja tsaki yace "kasan ba karamin aiki na bane in koma gida ko" yana magana yana tuki slowly har ya wuce Shuraim, Heedayah dake xare ido cikin rawar murya tace "Inn... Innaa yini" ya hade rai sosai yace "Ina xa ki?" Bakinta na rawa tace "Ruwa xan siya...." Yana mata wani kallo yace "Bbu ruwa a duk gidan sai kin fito siya?" Kamar xata yi kuka ta gyada masa kai kamar kadangariya, yace "Go back inside now" juyawa tayi da sauri ta wuce ciki tana hade hanya, ya juya ya sake kallon motar ya gansa can tsaye 4 houses away, can wanda ke cikin motar ya sauka ya nufi me gadi dake xaune bakin gate din, sai kuma mai gadi ya bude masa gate ya shiga cikin gidan, Shuraim ya dauke kai ya shiga gida shi ma snn ya rufe gate din. Farida na balcony tana danne dannen wayar hannunta Heedayah ta wuceta sai a sannan ta bi ta da kallo, Shuraim ma ya wuce bata ce masa ba bai ce mata ba, mikewa tayi ta bi bayansu, Dakin kaka Heedayah ta shiga ta rakube can karshen gado har lkcn gabanta bai daina faduwa ba, kaka tace "Ga abinci ki diba ki ci, ni na rasa gane ko Rakiya bata baki abincin kirki ne, wnn sirancin haka ai yyi yawa kamar bafillatanar da shanu ya kare ma" Heedayah ta turo baki bata ce komai ba, bude kofar aka yi Shuraim ya shigo, kaka ta dauke kai kamar bata gansa ba, dubu ashirin ya ciro aljihunsa ya mika mata yace "Abba yace a kawo maki" Kaka ta amsa ta kirga gaba daya sannan ta yashe kudin gefen gado tace "Ni dai na shiga uku, meye dubu ashirin kuma Allah na tuba, wnn ai baxai isa liki ba wllh, snn duk a ciki in ba bakina da suka xo kudin mota me yasa Amadu ke min haka ne ni" Shuraim dai sai kallon Heedayah ta gefen ido yake yi, don kai kana ganinta kasan bata da gaskiya sai wani kokarin boye jaka take a cikin Hijab nan kuwa vibrating wayar yake, Suna hada ido da shi ta daburce, can ta mike ta nufi kofa ta fita da sauri, kaka tace "Ni kawai a kira min Junaidu bani da kowa sai shi, shi daya xai fitar da ni kunyar likin nan da xan ma yara, da tsofaffin nan da suka xo min" Heedayah na fita dakin su Zainab ta wuce da sauri ta shige bandaki ta kulle, tunanin inda xata boye wayar jakarta take, ta fiddo wayar tana kalle kallen bandakin, window ta bude ta jefa wayar ta waje sannan ta fito bandakin. _I want to alert those that didn't patronize the book Heedayah, pls and plss don girman Allah su rike sharhinsu su bar wa enda suka siya littafi su yi, baki siya littafi ba baxa ki xo kina gaya min abinda ya kamata inyi da abinda bae kamata inyi ba, littafin nan dai ba kyauta bane amma wasu a kyauta suke karanta shi comfortable hankali kwance, to su ji da wannan kawai ma mana_ Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096..... Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍 Zainab ta mike jin ana knocking din kofarsu ta bude, ganin Shuraim tsaye bakin kofar tace "Ina yini Ya Shuraim" Aisha da Nafisa duk suka kame kansu a dakin kuma bbu wanda ya kallesa cikinsu, cikin few seconds ya gama bin dakin da kallo snn ya amsa gaisuwar Zainab yace "Lafiya" Heedayah dai na kwance saman gado tayi backing din kofar gabanta sai faduwa yake, karasawa cikin dakin yyi cike da kasaita ya nufeta yace "Bani jakar ki" kamar jira take ta mike xaune da sauri ta dau jakar ta mika masa, ya amsa ya bude ciki, bbu komai sai kudi da awarwaro with different chocolate, tunda ta mika masa jakar bata yrda ta kallesa ba, xuciyarta kamar xai fito don tsoro, ya jefar da jakar saman gado ya juya ya fita, Zainab ta xauna gefen Heedayah tace "What is he looking for?" Heedayah tayi tagumi tace "Ohon masa" Zainab ta tabe baki bata ce komai ba ta fita dakin. Har karfe dayan dare Heedayah bata yi bacci ba, amma bbu wanda xai ce ba bacci take ba, ita da Farida da Zainab sai Aisha ne a dakin, Mumy ta kwashi su Rabi'ah sun wuce gida tun karfe goma saura wai baxa su kwana gidan ba, a kashe wutan dakin yake almost an hour ynxu, kowa na dakin taji alamar yyi bacci, Heedayah ta sauka saman gadon a hankali ta nufi kofa ta bude very careful not to make any sound that will wake anyone sannan ta fita, bbu kowa parlon ta karasa tsakar gida taga har sannan murhu na ta ci ga manyan tukwane ana dafa kayan miya, sai da ta tsaya tayi naxarin inda xata bi snn ta xaga ta nemo dai dai windown bandakin su Zainab a bayan gidan, wayar na nan inda ta jefar amma screen din yyi raga raga ba na wasa ba, shi kansa wayar ya gurgurje, a hankali ta duka kamar xata yi kuka ta dau wayar tana jujjuyawa, har ranta taji ta tsani Shuraim din nan, meye xai wani sa mata ido, Ina ruwansa da ita wai ma, dudduba wayar tayi taga yana yi, ta turo baki ta xagayo gaban gidan ta shiga ciki ta koma can dakin da suke, a hankali ta bude press din su Zainab ta durkusa ta saka wayar a can kasan kaya sannan ta hau gado ta kwanta. Washegari juma'ah xa ayi dinner, Da rana duk 'yan matan suka shirya cikin daya daga ankon bikin, ana ta shagali a gidan, abinci iri iri aka girka ranan sae kace ranan ne yinin bikin, Duk Heedayah ta xo wucewa sai Mumy ta bi ta da kallo kmr idanuwanta xa su yi magana, duk inda ta bi idonta na kanta haka ma kawarta Sadiya, nan ko ita ta kagu a kare biki ta san na yi, ko kiris bata kaunar duk abinda xae sa Heedayah farin ciki, barin gashi ta ganta fes fes alamar hankalinta a kwance yake, ba komai ya kara tsaya mata a rai ba sai irin kyan da Heedayah ke da shi, wnn idan ta jera da su Rabi'ah sae a dauketa sau goma ba a daukesu sau daya ba, Mumy ta sauke ajiyar xuciya tana ci gaba da rabon abincin da take. Heedayah ta shiga daki dauko mayafinta xa su je dauko bak'i a bakin titi ita da Aisha kamar yanda Hajiya Hauwa ta umarcesu, Zainab ce kadai dakin duk kowa ya fita har ynxu tana make up, Zainab ta juya ganin Heedayah tace "Ke kika ajiye waya kasan kaya, yana ta vibrating??" Heedayah ta xaro ido a tsorace ta nufeta ta duka kusa da ita tace "Da gaske? How did you hear it?" Zainab tace "Kawai Ina son daukan takalmina kasan press din yanxun nan na ji vibration din sai na duba naga waya, and nasan Farida na tare da wayarta ynxun nn ta fita" Heedayah ta fara kalle kallen dakin, a hankali tace "Ke da wa ku ka ji vibration din plss?" Zainab tace "Just me, yanxu ma fa aka kira" Heedayah ta marairaice tace "Toh don Allah don't tell anybody about this Zainab, not even Farida" Zainab ta gyada mata kai tace "I am giving you my words" Fiddo wayar Heedayah tayi tana dubawa, Zainab tace "But saurayin ki ne ya baki waya kike boyewa" Heedayah ta girgixa kai tace "Ba saurayina bane" Zainab tayi murmushi tace "Toh sai ki kira" Heedayah xata yi magana wayar ya fara vibrate kuma... Kallon Zainab tayi da sauri, Zainab tayi tagumi tana murmushi tace "Pick..." Tana fadin haka ta tashi ta kulle kofar dakin ta sa makulli, Heedayah ta daga kiran ta kai kunne, she could hear him suspire but still bai ce komai ba, a hnkli tace "Hello..." Cikin cool voice dinsa yace "Who was he Heedayah?" Heedayah tace "Yayanmu ne" Yace "Really?" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Hope he didn't suspect you" a hankali tace "He did" yace "And how did it went?" Tace "Ni ba mu hadu da shi ba har ynxu" yace "Yaushe xa ki bar gidan??" tace "Kilan anjima da daddare" yace "Wa xai maida ki?" Tace "Daga wajen dinner xamu wuce gida" yace "Ke da wa?" Tace "Farida" ya d'an yi shiru snn yace "Ohk, where is the venue for the dinner?" Tace "Ban sani ba sai na tambaya" Yace "Do ask plss, Kar ki katse kiran kawai ki ajiye idan kin tambaya ki dawo" ta kalli Zainab da ke ta kallonta don tana jin komai da suke cewa, Heedayah ta cire wayar a kunne tace "Ina ne venue din dinner din?" Zainab ta gaya mata, Heedayah ta maida wayar kunne ta gaya masa, yace "Who did u ask?" Tace "My sis" yace "Ur sis??? Kuna tare ne?" Tace "Yess" yyi kasa da murya yace "Why?? You shouldn't have..." Sai kuma yyi shiru, can yace "Will call back later keep the phone close to you" daga hka ya katse kiran, Heedayah ta kalli screen din sannan ta kalli Zainab, Zainab tace "Waye shi? And why is he bothered because you are talking in front of me" Heedayah ta kirkiri murmushi tace "Sbda ya ga ina tsoro..." Zainab tayi shiru, sae kuma ta kalli Heedayah tace "But he shouldn't be bothered, idan yana son ki ya xo gidanku mana, why is he making it confidential??" da sauri Heedayah tace "Noo he isn't, and wllh ba saurayina bane, beside Mami will punish me if she gets to find out, kawai dai...." Zainab tace "Uhn kawai dai me?" A hankali Heedayah tace "Ba saurayina bane wllh" Farida ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, kamo hannunta Heedayah tayi tace "But promise me that you are saying nothing to anybody Zainab" Zainab tace "Trust me" Heedayah ta jira har Zainab ta gama kwalliyar sannan suka fita dakin. Da yamma ana ta shirye shiryen tafi wajen dinner da xa a fara bayan Magrib, Su Heedayah suka sa ankon lace dinsu tare da su Zainab duk suka yi kyau sosai, Su Rabi'ah dama wanda ya fi wnn tsada Mumy ta siya masu ga jaka da takalmi duk sababbi, Har sannan Farida ta ki yrda ta shiga harkan Heedayah a gidan, hakan ya d'an fara damun Heedayah don basu ta6a haka ba tunda suke amma dae bata ce mata komai ba, kuma bata da intention din ce mata dama. Ana ta kwalliyan tafiya dinner wajajen karfe shidda, mai make up aka kawo gidan tayi ma yan matan make up, Heedayah dai tace baxata yi ba, ana gamawa Zainab kwalliya aka hau yi ma Aisha, Heedayah ta bi Zainab gun madubi a hankali tace "I want to talk to you Zainab" Zainab tace "Ohk" Fita Heedayah tayi Farida ta bi ta da kallo, Zainab ta bi bayan Heedayah, Heedayah ta kamo hannunta a hankali tace "Plss can I get spare gate pass?" Zainab tace "For who?" Shiru Heedayah tayi tana kallonta, Zainab ta d'an yi murmushi tace "Ohk I get, but aiki ne babba fa, kinsan gate pass din ba shi da yawa, but let me try...." Daga haka ta wuce dakin da amaren suke ana shirya su cikin hadaddun kayan dinner dinsu, cikin dubara Zainab ta jawo jakar Aunty Safiyya dake gefenta ta bude, gate pass biyu ya rage da xata ba wasu schl frnds dinta, Zainab ta xare daya ta mayar mata da jakar ta fita da sauri, ta mika ma Heedayah dake tsaye tana jiranta tace "It was easy but not funny" Heedayah tayi murmushinta me kyau tace "Thanks Zainab" daga haka ta sa gate pass din a jakarta, tana jin wayarta ya fara vibrate ta fita parlor da sauri ta xaga ta dauka kafin ya katse, sallama yyi mata tace "How will you collect it?" Yace "Ohk kin samu?" Tace "Ehh" yace "We will meet there, but ki ajiye wayar kusa dake plss" tace "Toh, ana jirana" daga haka ta katse wayar ta mayar cikin jaka, har ta fara tafiya ta ji ance "Heedayah" gabanta ya wani irin faduwa ta juya da sauri ganin ba kowa sai ta kalli sama, Sudais ta gani bakin windon dakinsa tsaye yana kallonta, Kasa cewa komai tayi xuciyarta sai bugawa yake ta marairaice xata yi kuka, da sauri xata bar wajen yace "Jiran ni a nan, kar ki je ko ina" bata iya ta ce komai ba ta tsaya hawaye na sakko mata, bayan kusan minti uku sai ga shi, har ya iso inda take bata yadda ta kallesa ba xuciyarta sai bugawa yake, yana facing dinta ce "Ke da wa kike waya?" Kamar jira take ta fashe masa da kuka ta ki cewa komai, ya hade rai yace "Ni ban ce ki min kuka ba answer my question now" Cikin rawar murya tace "A frnd" yace "Frnd?" Where did you know him from" hawaye kawai take ta ki cewa komai, yace "I asked where did you know him from" Ta kuma fashe masa da kuka tana kallonsa, yace "Schl??" ta gyada masa kai, yyi shiru yana kallonta, can yace "Ur classmate?" Ta girgixa masa kai, yace "Toh waye?" Ta ki cewa komai, strictly yace "Answer me now Heedayah" Cikin rawar murya tace "A hanya na san sa" yace "Mami ce ta baki waya?" Murya can kasa tace "Shi ya bani" yace "Amma Mami ta sani?" Ta girgixa masa kai, da mamaki yake kallonta, can yace "Farida fa?" Nan ma ta girgixa masa kai, ya fi second talatin yana kallonta with surprise, can yace "Bani wayar to" ba musu ta bude jakar ta fiddo wayar ta mika masa, yana kallonta yace "Why Heedayah, Don't you know u are too young for this, idan kika gama secondary school babu wanda xai hanaki waya da wani, seriously bana son in sake ganin haka, face ur studies, in a year time after ur secondary schl you can speak to anyone... provided Mami ta sani kuma ta amince da hakan" cikin sanyin murya tace "To Yaya" Yace "Shi a ina yake?" Ta girgixa masa kai tace "Nima ban sani ba" Yyi shiru yana kallonta, can ya kara duba wayar yana kallon hotonsa duk da wayar ta fashe sosai, but he still can see him a little, mika mata wayar yyi yace "Bude min" tace "Ban san password din ba" Da mamaki yace "Baki sani ba? Haka ya baki wayar?" Ta gyada masa kai, yace "Me yasa bai bude maki ba" tace "Nima ban sani ba" yace "Baki ce masa ya bude maki ba?" Tace "Nace masa amma bai bude ba" yace "Toh xai kira kuma xan yi warning dinsa, bbu ke bbu shi, idan kuwa kika sake kulasa sai na hada ki da Mami and even Abba" Hawaye ya kawo idonta tana girgixa masa kai cikin tashin hankali tace "Don Allah kar ka gaya mata wllh dukana xata yi, don Allah Yaya kayi hkuru" yace "Toh naji, but karki sake kulasa anywhere, and hope bai san gidanku ba" Ta d'an kallesa sai kuma da sauri tace "Aa bai sani ba" Yace "Good, I will warn him if he should call, I don't think mutumin kirki ne da baxai ki baki password ba, and plss bbu ruwanki da maxa sai kin gama secondary schl Cutie, is that clear?" a hankali tace "Toh Yaya" yace "You can go" a hankali ta fara tafiya har ta d'an yi nisa sai kuma ta juyo da sauri tace "Yaya don Allah har Yaya Shureen kar ka gaya ma" Murmushi yayi yace "Baxan gaya masa ba" ta marairaice tace "Plsss" yace "I promise" juyawa tayi ta ci gaba da tafiya ta koma cikin gida. kaka ta gama shirinta tsaf ita ma cikin wani lace dake ta walkiya ta kima uban dankwali a kai ga katon mayafinta da ta amsa gun Safiyya da dai daya dayar jakarta na gado da xa a iya xura jariri a ciki, takalmin kafarta ma me d'an tudu ne, Heedayah na hango kaka duk da tashin hankalin da take ciki sai da ta nemi kujera ta xauna ta dinga kyalkyala dariya Zainab da Nafisa na taya ta, kaka ta nufi gun Umma dake ba frnds dinta pass tace "Dama kada a kuskura a raba ma tsofaffi fass din nan, kar su je su cika mana waje a shiga uku, kuma wani motar xa mu hau da Ta salla? Ta kirani tace kila tana hanya" Umma ta kalleta daga sama har kasa snn ta kauda kai tace "To ai motocin ake jira, kowa ma motar yake jira" Kaka tace "Toh a ajiye mana daya da Heedayah da Zainab da Farida" tana fadin haka ta koma canxa jaka ganin kowa da sabon jaka yake yawo ita kadai ce me tsohon jaka, Sudais ne ya bita dakin bayan Ummarsa taje ta samesa a dakinsa ta lallabasa yaje yyi mata magana duk da baya son fitowa sbda mata da suka cika gidan, ganinsa Kaka tace "Kai baxa ka bane Sudess, gashi kowa na ta shiryawa, shi dama Shureen bakin hali baxai bari yaje ba, barin yanxu kuma da yake tunanin ya xama soja" yace "To me xan je inyi" tace "Oho" yana kallonta daga sama har kasa yace "Duk kwalliyar xaman gida ne kika yi hka Hajjaju" Kaka na nemo sabon jakarta a kwallayenta na daki tace "Wani xaman gida, ga can an je kawo motoci xa mu dinner, Ta salla ma kila a can xa mu hadu" Sudais yace "Ynxu ke fisabilillahi godai godai idan ance ki tafi dinner sai ki tafi?" Ta mike tana kallonsa baki bude.... yana kallonta da kyau yace "Idan ma xaki tube kayan nan ki tube ki saka na xaman gida, don bbu wanda xai kai ki wani dinner, Abba da Baffa sunce bbu inda xa ki yanxun nan suka kirani, idan kuma basu isa da ke bane sai mu ji, meye kuma dinner tsofe tsofe da ke xa ki ce sai kin je cikin jikokin ki" yana fadin hka ya fita dakin ba tare da ya jira cewarta ba, yana fita su Umma da kawayenta na shigowa da manyan kuloli dakin. Bayan Magrib duk aka watse gidan xuwa wajen dinner, Ko kadan kaka bata wani tada hankali ba ganin duk namomin bikin gobe da kaji su Umma suka kawo dakinta a manyan kuloli har ma da cartoons din malt da lemu iri iri, ga ganda da aka soya da naman saniya, sae cewa take kuyi maxa kada ku makara bbu ddi. Har suka isa gun dinner Heedayah bata da walwala, bayan sun sauka motar su Farida da Nafisa sun shiga cikin event center din Zainab tayi kasa da murya tana kallon Heedayah tace "Kin samu kin basa gate pass din?" Hawaye ya kawo idon Heedayah a hankali tace "Ya Sudais ya amshi wayar" Da mamaki Zainab ke kallonta, can tace "Ya aka yi ya gani?" Heedayah tace "He caught me at the backyard" Zainab tace "To yanxu ya xa ayi? And baki da number tasa ko?" Heedayah ta gyada mata kai a hankali, Zainab tayi shiru don ita ma bata ji dadi ba, can ta d'an yi tsaki tace "Ya Sudais din nan na da matsala wllh, duk ya bi ya takura mutum, mu ma fa haka yake mana har duka ya ta6a yi ma Nafisa wai sai mun gama waec, amma ga su Rabi'ah su yi ta waya da samari kala kala Ya Shuraim baya ce masu komai wllh, a gabansa ma suna iya daukan phone call he won't even look at them" Dallaro su aka yi da fitilar mota lkci daya kuma aka kashe, duk suka kalli motar dake parke daga opposite dinsu.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... *Masu bukatar cream that is tested and trusted ga dama ta xo maku....* *Whitening lotion 4500* *Shower gel 3500* *Tone lotion 3500* You can contact 08038103096.... Kallon Zainab Heedayah tayi, Zainab tace "Ko shi ne?" Heedayah ta dinga kallon motar, can tace "Aa ba da motar nan nake ganinsa ba" Zainab tace "To ki je ki duba" Karasawa Heedayah tayi gun motar, taga an sauke Windshield din motar, sosai gabanta ya fadi bayan sun yi ido hudu da shi, sanye yake da wandon sojoji da polon su, ya dauke kai daga kallonta ya kara haska ma Zainab fitila, Kamar ana tilasta Heedayah tayi kasa da murya tace "Ina yini" bata jira ya amsa ba ta bar wajen tana turo baki, Zainab sai kallonta take har ta iso, Heedayah tace "Ke ake kira" Zainab ta xaro ido tace "Ni kuma? Waye ke kirana?" Heedayah tace "Oho ki je ki gani" karasawa Zainab tayi tana d'ari d'ari, Shuraim ya sakar mata murmushi, ta buda ido sosai ganinsa tace "Lahh ashe ya Shuraim ne, kai ma dinner din ka xo?" Ya hade rai yace "Dinner kuma? No, not at all" tace "To me kaxo yi nan?" Yace "Yanxu xan wuce wajen aiki, na ajiye wasu ne" Zainab tace "Ohk Ina yini Ya Shuraim" yace "Lafiya lau, me yasa ita kadai ta xo gun motar sbda taga anyi flash din fitila maimakon ku biyu?" Zainab tace "Ohh ni ce nace taje ta ga wa ke haska mu" Yace "Wato ita ce fitsararriya, da wani ne haka xata xo ta tsaya masa a mota tana kallonsa ko?" Zainab tace "Aa fa Yaya, ni nayi insisting taje ta ga waye da gaske" kallonta ya tsaya yi, can yace "Then... Don't do that again, Ina Farida?" Zainab tace "Sun shiga ciki" yace "Ke ina pass din naku?" Zainab tace "Gashi a jaka, nata na wajenta" yace "Ohk, till after the dinner kar ku fito waje" Zainab tace "Dama ai baxa mu fito ba Yaya" Yace "Good" tace "Yanxu xaka wuce?" Yace "Ehh" tace "Toh Allah ya kiyaye" Heedayah dai na can tsaye nesa da su sai turo baki tayi, can kuma sai ta tabe bakin, wani abu kamar kwandala taga ya gangaro inda take, ta dinga kallon d'an abun me shige da ring da ya kwanta a gabanta bayan ya gama bouncing, Daga kai tayi ta kalli direction din da abun ya taho, suka yi ido hudu da Khaleel jikin wata farar mota me ubansun kyau, tuni ya dauke kai yana danna wayarsa ya kasance side view dinsa kawai take iya gani, parking space din event center din ne, ya d'an saci kallonta bayan sun hada ido ya bar wajen ya koma can bayan wani mota ya tsaya, don motoci ne iri iri a wajen, Zainab taga Shuraim ya bude mota xai sauka ta matsa da mamaki tana kallonsa, karasawa gun Heedayah ta ga yyi, ita ma Heedayah kawai ganinsa tayi kamar daga sama a gabanta, ya duka ya dau ring din, sosai gabanta ya fadi ta fara komawa baya a tsorace, ya mike yana bin wajen da kallo, Tuni Khaleel ya canxa wani motar ynda ko ganin alamarsa Shuraim baxai yi ba, Heedayah dai sai kallon Shuraim take a tsorace, Zainab ta karaso kusa da su tace "Me ya faru Yaya? What's that" Shuraim ya amshi jakar Heedayah, ba musu ta sakar masa jakar, ya bude, pass din dake ciki guda biyu ya ciro ya yayyaga a wajen ya jefar sannan ya nuna mata motarsa, fashewa da kuka tayi sosai, Zainab da ta xaro ido tace "Yaya why did u do that, there is no other pass fa??? Me ya sa kayi haka yaya" Shuraim ya nuna mata hanyar shiga wajen fuska daure yace "Yi wucewar ki ciki" ganin kallon da yake mata dama kuma sun taso suna tsoronsa fiye da yayansu Sudais kawai ta kama hanyar shiga event center din wanda policemen ke tsaye suna amsan pass, tana yi tana waigosu, Heedayah sai kuka take tana yarfe hannu, yayi mata wani tsawa yace "Wuce mu tafi nace" Bata masa musu ba ta nufi motar da sauri, ta bude back seat ta shiga, ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya fita parking space din driving with speed, Khaleel dake jingine jikin wata mota daga nisa ya bi motar da kallo, bayan few seconds yyi wani murmushi yana juya wristwatch din hannunsa almost whispering to himself yace "Waow... A soldier, then... either I or him" daga haka ya koma gun motarsa ya shiga. A hankali Heedayah ke kuka a motar tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Driving dinsa kawai yake yi yana yi yana duba motocin dake bin sa a baya, bayan wani lkci wayarsa ya fara ring, dauka yyi yana duba me kiran nasa ya ga Mumy ce, ya daga wayar ya sa a handsfree, Mumy tace "Aliyu nasan sai takwas xa ka tafi aiki don Allah ka rufa min asiri ka xo ka daukeni da su Hajiya Sadiya da Hajiya Amina ka kai mu wajen dinner din nan, duk motocin sun tafi, tawa motar ma an tafi da ita haka na Hajiya Amina" Shuraim dake ta sauraronta har ta kai aya yace "Ina wajen aiki ynxu" Mumy tace "Haba Shuraim, karfe takwas fa kake tafiya gashi ynxu bakwai yyi" Yace "Ehh colleague dina dake dutyn rana xuwa yamma ya tafi gida before his time elapsed, his wife is sick shi yasa ya nemi alfarman in xo da wuri don inyi takeover from his time" Mumy tace "Ae shkkn sae mu nemi adaidaita amma abu bai yi ba manya kamar mu a ganmu a tricycle, shi Sudais yace baya kusa kai kuma yanxu kana ce min ka tafi asibiti" bata jira cewarsa ba ta katse wayar ya ajiye yana ci gaba da driving dinsa, Heedayah sae shessheka take tana ji kmr ta rusa ihu tayi kuka sosai ko xata ji dadi. Parking ta ga yyi a wani waje da akwai haske sosai, nan da nan ta dakatar da kukan da take yi ta goge idonta da sauri, ya bude motar ya sauka snn ya bude side dinta, kallonsa take a tsorace, ya hade girar sama da ta kasa yace "Sakko" Ba musu ta sakko da sauri, yace "Jiya waye na gani kofar gida kika min karya xa ki je ki siyi ruwa" Ta xaro ido tace "Ya Shureen ni ban san sa ba, na fito ne yana wucewa a mota sai naga ya tsaya yana kallona, I am telling you the truth ban san sa ba, believe me plsss...." Ta fashe da kuka amma hawaye ya ki sakkowa tana kallonsa a tsorace, yace "Ohk da ya tsaya kallon ki sai ke ma kika tsaya kallonsa a gate din ko?" Tace "Aa tsoro na ji shine ban fita ba na tsaya bakin gate din in ga ko xai wuce naga bai wuce ba" Shuraim yace "Toh yau kuma meye wnn aka jefo gaban ki ya fadi?" Ta daga hannu sama da sauri tace "Ya Shureen nima kawai gani nayi kila daga sama abun ya fado, ban san meye shi ba wllh, wllh I don't know what is that, believe me plsss" Kamar xata yi kuka ta kare maganan tana kallonsa da manyan idanuwanta, yace "Good, maxa su tsaya suna kallonki kema sai ki tsaya kina kallonsu ko?? to daga yau anytime you are going out you just have to wear a nikab, a must" Ta xaro ido tana kallonsa amma bata ce komai ba, strictly yace "Kin ji abinda nace?" A hankali tace "Ni ai bani da Nikab ya Shureen" yace "Yess xan siyo maki, and if you should dare tell anyone that ni nace ki fara sa Nikab sai na baki mamaki..." Kamar xata yi kuka tace "Ban iya sa wa ba ai" yace "Ehh idan na kawo maki sai ki koya" Bata kuma ce masa komai ba, ya bude mata motar, ta marairaice ta shiga ya kulle, murguda baki tayi a ranta tace ai baxan sa ba sai dai kai ka saka, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, ganin hanyar gidan Mami ya nufa da ita taji kamar tayi ta ihu tana birgima a motar, nan da nan hawaye me shegen xafi ya dinga sakko mata taji kamar ta shakosa, Wayarsa yayi dialing snn ya kai kunne, ba a dau lkci ba yyi sallama yace "Ina yini Mami" Daga daya bangaren Mami ta amsa masa, yace "Kina gida ne?" Mami tace "Ehh ina gida Shuraim, ya aka yi?" Yace "Ohk Ina shigowa yanxu" Tace "Toh sai ka xo" daga haka ya katse wayar, dai dai kofar gida yyi parking ya sauka motar, Heedayah ta share hawayen da ya ki tsaya mata ya fito daga cikin motar, bin bayansa tayi don har ya shiga gate bayan sun gaisa da Mai gadi, Da sallama Shuraim ya shiga parlon Mami, Mami ta sakko downstairs ganinsa tace "Aa, daga ina haka Shuraim, welcome, baka je dinner din ba kenan" kafin yace komai Heedayah ta shigo, da mamaki Mami ke kallonta tace "Wancan fa? Daga ina kike" Shuraim yace "Tace cikinta na ciwo shine na dawo da ita gida" Mami tace "Ikon Allah, tun yaushe" Shuraim yace "Da rana" Heedayah dake goge hawayen da ya ki tsaya mata ta gaida Mami a hankali snn ta wuce sama, Mami ta mike ta bi bayanta, kwance ta sameta saman gado tana rusa kuka kamar yar yarinya, har downstairs Shuraim ke jin kukan nata, Mami ta shiga dakin da mamaki sosai tace "Meye haka kamar 'yar yarinya, bana son iskanci, period din ne ya dawo??" Cikin kuka ta girgixa kai tace "Aa ba shi bane" Mami tace "Toh ya cikin yake maki?" Tace "Ya daina ynxu" Mami tace "Ya baki magani ne?" Gyada kai kawai Heedayah tayi bata ce komai ba amma taki daina kukan, Mami tace "To ki kiyayeni da kukan nan, tunda ke ba jaririya bace, idan bacci xa kiyi kiyi bacci" daga haka Mami ta fita dakin, Heedayah ta tura fuskarta cikin pillow tana rera kukanta. Mami na dawowa downstairs tace "Tace ka bata magani" Yace "Ehh na bata" Mami tace "Toh shkkn, Allah ya sauwake" Mikewa Shuraim yyi yace "Xan wuce aiki, I am almost late" Mami tace "Toh abinci fa?" Yace "Aa am full" tace "You are always full dama, Toh Allah ya tsare" ya amsa da Ameen yana murmushi, ya mata sallama ya fita parlon, Mami ta koma sama xuwa dakinsu Heedayah, Heedayah na jin an bude kofa ta hadiye kukan ta rufe ido da sauri, Mami tayi xaton ta fara bacci ne ta juya ta fita. Karfe sha biyu saura Heedayah ta koshi da kukan da take ta mike xaune, sai turo baki take ita kadai, bandaki ta shiga tayi alwala ta fito tayi Isha, tana idarwa ta cire kayan jikinta ta dau kayan baccinta ta saka snn ta sa Hijab ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar ta fita, downstairs ta sauka xata tafi kitchen ta hada shayi, kwance ta ga Junaid 3 seater yana kallon wrestling, ya mike xaune yana kallonta da mamaki yace "Heedayah" sauke idonta tayi bata ce komai ba, yace "Yaushe kika dawo?" A hankali tace "Tun daxu" yana kallon idonta with surprise yace "What's wrong, kukan me kika yi?" Kafin tace komai taji muryar Mami a sama, ta juya da sauri tana kallonta, Mami tace "What are you doing downstairs?" Cikin sanyin murya tace "Ina jin yunwa xanyi making tea" Mami tace "Go and make it ki xo ki wuce" Kitchen din ta nufa, Mami na ta tsaye har ta fito da cup din shayi, Junaid dai bai ce ma Mamin tasa komai ba, Heedayah ta wuce sama, Mami ta jira ta ga shigarta daki sannan ta bi ta cikin dakin, tana kallonta tace "Ya jikin?" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Na ji sauki" Mami tace "Toh Allah ya sauwake" Daga haka tayi mata sai da safe ta fita ta koma dakinta, kasa ci gaba da kallon wrestling din Junaid yyi duk son sa da wrestling kuwa, ba karamin kuka idonta ya nuna tayi ba, lkci lkci yake kallon agogo har karfe daya yyi, ya mike xaune daga kwancen da yake saman kujera, yana ta xaunen har daya da rabi snn ya mike ya wuce sama, ya fi minti uku tsaye corridor din dakunan, can ya nufi kofar dakinsu ya bude very careful kar yayi kara, shiga dakin yyi da yyi sanyi sbda Ac dake kunne wutan dakin a kashe, ya rufe kofar, Heedayah na jin an bude kofa dama ba bacci take ba abun duniya ya isheta, gaba daya ji take kaf duniya dai a ynxu bata tsani kowa ba kamar Shuraim, ta mike xaune da sauri tana kallonsa ta duhun kamar me rada tace "Yaya" ya karasa gefen gadon ya xauna ya haska mata fitilar wayarsa mara haske yace "Kukan me kika yi Heedayah" Ta dau pillow ta daura jikinta kamar xata yi kuka tace "Yaya Mami fa xata yi fada" Hade rai yyi yace "Tell me what's wrong with you" Ta hadiye abu da kyar tace "Ciwon kai nake yi shine na dawo gida" Yace "Ciwon kai? To kin sha magani?" Ta gyada kai tace "Na sha" yace "Wa ya baki?" Tace "Mami" cikin sanyin murya yace "Allah ya sauwake dear, but ya daina ciwon ynxu ko?" Ta gyada masa kai, yace "Shayin ya ishe ki?" Nan ma ta gyada masa kai, gaba daya a tsorace take, yace "Why are you scared??" Ta marairaice tace "Mami... wllh xata iya dukana" Shiru yyi yana kallonta, snn ya kamo hannunta yace "Toh xan tafi yanxu, but watarana baxa ki ce kina tsoron Mami ba idan muna tare ai ko?" Ita dai bata ce masa komai ba ta sauke idonta kasa, mikewa yyi yace "Ki kwanta kiyi bacci, idan kuma baki jin baccin ki tashi kiyi sllh, good night" ta gyada masa kai kawai ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle mata kofar, downstairs ya koma ya kwanta coz he prefer lying down there, sai a snn kuma bacci ya daukesa. Washegari Saturday Mami bata ce Heedayah taje wani yinin biki ba, ita ma a gida ta yini abunta sai kusan yamma ta tafi gidan bikin bayan ta tabbatar Junaid ya fita gidan, gidan ya rage daga Heedayah sai Zainab me aikin Mami, tun da gari ya waye sai wani nukurci da miskilanci Heedayah take, Mami na ganin mood dinta dama ta kyaleta tayi ta xama a daki ita kadai, Da Heedayah ta tuna abinda Shuraim yyi mata sai ta fashe da kuka ita kadai tace "I hate you" da ta tuna wayar da Sudais ya amshe a hannunta shi ma sai ta fashe da kuka kamar 'yar yarinya. Karfe shidda saura ta sakko downstairs da dubu daya a hannunta, Zainab ce xaune parlor tana kallo, Zainab tace "Ga abincin ki can a kitchen ba ki ci ba Heedayah" a hankali Heedayah tace "Baxan ci ba" daga haka ta fita, ko gaida Mai gadi bata yi ba ta fita xuwa kanti ta siya chocolate. Zaune yake 4 houses away tare da mai gadi suna hira, malt ne a hannunsa yake sha, shi ma Mai gadin malt din yake sha yana lullumshe ido kana gani dai kasan siya masa aka yi, Mai gadin ya kara kurban malt din hannunsa, ya d'an yi gyatsa snn yace "Ai tsiyar basa fitowa ne yan matan gidan, duk safiya dai xaka ga uwar tasu a katon motarta ta fita, Ina jin wata babban ma'aikaciyar gwamnati ce, tana kuma da d'a wani matashi yana nan kamar balarabe, ya ma fi ka haske, to shi gaskiya Ina jin ba kullum yake dawowa gida ba don sai in kwana biyu ban ga motarsa ba a layin nan, su kuma Yan matan sai dai ka gansu an fita da su a mota daga cikin gidan, ban san ko su nawa bane balle in san ko warcece a ciki ma" Shiru yyi kansa a kasa yana rike da can malt dinsa yana sauraron Mai gadin, can ya dago kai yace "Mahaifinsu fa?" Mai gadin yace "Anya, Ina jin gaskiya ya rasu ban ta6a ganin dattijjo ya fito gidan ba duk xamana a layin nan inda gadin gidan nan" Ya gyada kai cike da gamsuwa sannan yace "Akwai Soja a gidan?" Mai gadin yace "Aa babu wani soja a gidan, basu fi su hudu ko biyar ba a gidan, matashi kuma daya ne a gidan" Khaleel ya gyada kai yana naxarin maganan mai gadin, d'aga kai yyi ya hangota tana tahowa da Hijab har kasa. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mikewa Khaleel yyi carefully surveying the street and he saw nobody apart from her, Mai gadin ya hango Heedayah shi ma da sauri yace "Au to ai ga daya daga yan matan gidan can ranka shi dade" Juyawa Khaleel yyi yana facing dinsa amma bai ce komai ba, nan kuma bai son ta gansa ne, ita kuma ta riga ta gansa, sai da ta wuce su snn ya juyo ya bi bayanta, tsayawa tayi da ta gane yana bin ta, ya karasa gefenta ya tsaya, murya can kasa yace "How are you?" Ta wani hade rai tana kallonsa da kyau tace "I'm not fine, and I am begging you ka daina bi na, kana ja min matsala a gida...." Shiru yyi yana kallonta, ganin ya ki cewa komai ta ci gaba da tafiyarta walking faster, bin ta yyi suka kara jerawa, ta juya kamar xata yi kuka tace "Don Allah ka kyaleni ka daina bi na tunda dama kawai sbda in kulaka ya sa kake min karya kace ka san ni" ya girgixa mata kai a hankali yace "Ki daina cewa babba yana karya..." Ta yi facing dinsa da kyau fuska daure tace "But you lied to me" yace "No I didn't...." Tace "To a ina ka san ni??? Tell me now" Ya kalli motarsa da yyi parking can farkon shigowa layin snn ya kalleta yace "But we can't talk here" tace "Sai a ina?" Yace "Toh wai da mu shiga gidanku...." Ta wani xaro manyan idanuwanta a tsorace tana kallonsa, ya dage girarsa yace "Yess akwai matsala ne idan na shiga gidanku, daga nan ma ba sae in gaida mutanen ciki ba...." Kamar xata yi kuka tace "Ni dai don girman Allah ka daina bi na, you are a joker.... Plss let ur joke end here now and forever" yace "Billah na san ki Heedayah, what's my gain lying to you cewar na san ki bayan ban san ki ba" Kallonsa kawai take, yace "Nasan ba tare da iyayenki da suka haife ki kike ba, nasan cewar probably few years ago or even recently kika fara gani coz you were unsighted as at the time I knew you, a lkcn da na sanki kina 'yar karama" cikin sanyin murya tace "Toh a ina ka san ni plss? And did you know my real parent?" ya nufi inda motarsa yake walking slowly yace "Mu je mota, I can't talk here" Bin bayansa tayi a sanyaye maganganunsa na mata yawo a kai, ya bude mata front seat yana kallonta ba musu ta shiga ya rufe sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga ya kulle. Juyawa tayi tana kallonsa bayan ya shiga motar tace "Tell me plss, ka gaya min inda ka san ni" yace "I will, but waye wnn sojan na jiya?" Tace "Ya Shureen" Khaleel ya dinga kallonta kafin yace "Did you mean Shuraim?" Ta bude hannu tace "Ni dai Shureen naji kaka ke kiransa" yace "Who is he, I mean the Shuraim, and waye kaka?" Tace "First son din Abba ne shi Ya shureen, kaka kuma Grandma dinmu ce...." Yace "Grandma dinsu dai, and Waye Abba?" A hankali tace "I call him my father...." Yace "Nan ne gidan Abban?" Ta girgixa kai tace "Aa, gidan Mami ne nan" yace "Waye Mami" a hankali tace "I call her my mother" shiru yyi yana kallonta snn yace "Shuraim din ne yyi picking call dina jiya da na kira?" Ta girgixa kai tace "Aa that's Ya Sudais" da mamaki yake kallonta yace "Shi kuma waye?" Tace "Cousin din Ya Shureen" tabe baki yyi bai kuma cewa komai ba duk da she just confused him with her explanation but he isn't willing to know anything anymore, tace "Toh ka gaya min inda ka san ni" yace "Nasan dai kamar an ta6a kidnapping din ki, is that so??" Cikin breaking voice dinta tace "Ehh, kuma ban kara ganin Ammina da Abbana da Yakumbo ba har da Nanny, and nobody is willing to take me to them, I've missed them so much, nobody is saying anything about them to me, nobody is willing to take me to them, Ina son in ga Ammina...." Kallonta kawai yake yi, hawayen da ya makale idonta ya gangaro sai kuma ta fashe masa da kuka a hankali tana kallonsa, ya dauke kansa daga kallonta, cikin rawar murya tace "Ni ina son in ga Ammina, I want to meet with my mother..." Shi dai bai ce mata komai ba tayi kukanta me isarta tayi shiru, Ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya jinginar da kansa da kujeran motar cikin cool voice dinsa yace "Xa ki ga Ammin ki in sha Allah" Tana kallonsa cikin sanyin murya tace "When, and did you even know them?" Ya girgixa kai yace "Ban san su ba.... amma in sha Allah I will take you back to ur parent soon, I am promising you this.... But... you just have to trust me" Ta goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "How long will that take??" Yace "Not so long" tace "Tell me who are you pls" yace "Khaleel Muhd" Tayi shiru tana kallonsa, soft smile ya sakar mata murya can kasa yace "Trust me Heedayah" ta gyada masa kai kawai, yace "So anyi seizing wannan wayar da na baki ko?" Ta gyada masa kai nan ma, sai kuma da sauri tace "Toh me yace maka da ka kira wayar?" Ya d'an buda ido yace "Nothing much, I didn't even listen to him..." Yana magana yana kokarin ciro abu a aljihunsa, ya ciro wani karamin waya sosai kamar na wasan yara ya mika mata yace "If there is anything I will call you, or you call me, xa ki ga numberna Brainiac...." Ta marairaice tace "Aa ni dai kaga Ya Sudais ya kamani da waya bana son wani ya kara ganina da waya" Yace "Then if there is anything how will I communicate with you Heedayah" shiru tayi kamar me naxarin abinda yace, kamar xata yi kuka tace "Tsoro nake ji" yace "Wannan wayar ai bashi da girma, it's very portable ko a dankwalinki xa ki iya barinsa no one will know of it" Tana ta kallon wayar taki amsa gabanta na faduwa, ya kamo hannunta ya sa wayar a ciki ta xaro ido tana kallonsa, shima yana kallon kwayar idonta yace "You have to collect it" Bata ce komai ba ya sake hannunta, yace "Xa ki shiga ciki yanxu kar a nemeki ko?" Ta gyada masa kai cikin sanyin murya tace "But you promise that I will meet my parent, should I confide in you?" shiru yyi yana kallonta, yace "But you have to be patient, and naga you are so much comfortable with ur guardians here, I can see they love you wholeheartedly...." Ta fashe masa da sabon kuka tace "Basa ce min komai a kan iyayena" ya kwantar da murya yace "That's because they love you dearly, and sun daukeki kamar 'yar su" Goge idonta tayi bata ce masa komai ba sai dai hawayen ya ki tsaya mata, yace "Tunda basa maki maganan parent din ki kema kar kiyi masu, u will look so ungrateful..." Tace "Amma kai ai xaka samar min iyayena ko?" Yayi murmushi yace "I owe u that" murya can kasa tace "Thank you" Yace "No thanks" tace "Xan wuce gida" ya bude lock din motar yace "Ohk...." kafin ta bude motar, yyi kasa da murya yace "But did you have anything to do with that soldier?" Ta turo baki tace "Noo..." Daga haka ta bude motar, sai kuma ta juyo da sauri tana kallonsa tace "How did you know I was kidnapped?" Kallonta yake ko kiftawa babu, sai kuma ya sauke idonsa kasa yace "That will be story for another day..." Tayi narai narai da ido ta dawo cikin motar tace "Tell me plss" yace "Xan gaya maki amma sai mun sake haduwa, ki wuce ciki kar a nemeki, it's already getting dark" Bata kuma cewa komai ba ta sauka motar yyi mata murmushi, ta rufe motar ta karasa katin dake layin, ta baya ya fice daga layin snn yyi reverse ya hau saman titi, duk wnn abun tana tsaye gun me shago tana kallonsa ko kiftawa bbu. Hadadden parlor ne me dauke da maza hudu sai aikin shan giya suke suna caca caca duk sun cika parlon da hayaniyarsu, yana daga tsaye jikin wani pillar kusa da dinning area na parlon ya rungume hannunsa yana kallonsu yyi supporting kansa da kafarsa a jikin pillar din, 3 qtr ne jikinsa sai singlet, idonsa na kan abinda suke but hankalinsa baya kai, daya daga wa enda ke xaune cikin parlon na kyakyata dariya kamar ta6a66e yace "Kayy... xo ka barar mana da wnn mutumi ko bakinsa xai rufu don Allah" Sauke kafarsa yyi kasa ya karaso cikin parlon cikin tafiyarsa ta kasaita, ya ja wani tsadadden kujera me kama da na office ya xauna, daya daga cikinsu da suke kira Maska yace "Genius akwai damuwa ne, two days u are dull, ko miskilancin ne ya taso" Khaleel bai ce masa komai ba, Zayyad din cikinsu ya dau kwalin cigarette ya jefa masa yace "May be u need this" Dauka Khaleel yyi ya jefar saman center table din da suke caca caca yace "Yyi min kadan sae dai in kai xan kyatta ma ashana" duk suka kwashe da dariya, Khaleel ya shafa sajensa yace "Ina son maku wata tambaya" Maska ya d'an gwalo ido yace "Tohhhh Brainiac ne xai yi ma learners tambaya, are we safe at all, anyway muna jin ka" Khaleel ya daura kafarsa kan center table yace "1...2...3... To 4 years back..." Duk suka xuba masa ido da kunnuwa suna sauraronsa attentively, ya langwabar da kai yace "Anyi kidnapping wasu yara kananu duk mata guda hudu...." Sai kuma yyi shiru, Maska yace "Ehen muna jin ka, what about that" Khaleel ya sauke idonsa kasa yace "Shine nake son sanin ko xa ku iya tuna wa enda suka daukosu kuma da inda suka dauko su" Kamar hadin baki duk suka fashe da wani mahaukacin dariya nonstop, bin su ya dinga yi da kallo har bayan minti biyu suna dariyar, can ya mike ya fixgo Zayyad ya kai masa naushi a baki, kan kace me, Zayyad ya kai masa shi ma, nan kuma suka yi charging kansu, don da kyar aka samu aka rabasu aka rike Khaleel, Salim ya janye Zayyad suka bar parlon, Khaleel ya share xufar fuskarsa ya koma saman kujeran da yake ya xauna, Maska yace "Dama duk yau baka fita workout ba, you are just lying down all day, ko ba komai you will feel strong now" Sufyan da Saif da shigowarsa parlon kenan suka tsaya bakin kofa suka kalli d'an show din da aka gama suka karaso parlon da ledojin gasassun kaji, Saif yace "Are you really okay Khaleel?" Ko kallonsa Khaleel bai yi ba, Maska yace "Wai wasu yara da aka yi kidnapping 4 years ago yake tambayar inda aka dauko su kamar wani wasan kwaikwayo, yara nawa aka yi kidnapping 4 years ago" Sufyan yace "4 years ago kuma? kai ko ka so kanka da yawa Kay, lkcn muna yaku bayi fa" dariya sosai duk occupant din parlon ke yi, Khaleel ya shiga bin su da kallo, Saif ya xauna yana facing din Khaleel yace "Su waye suka yi kidnapping din yaran a cikinmu, snn idan shekaru hudu kake magana ai yawanci wasu cikinmu duk an kashe su, su Gwaska, Kamilu, Fago, Rabilu, Ahmed... Su ne masu kidnapping din a lkcn ko ka manta, ynxu Fago kadai da Kamilu ke raye, su xaka tambaya" Khaleel yace "Har da Maska aka dauko yaran idan shi ya manta ni ban manta ba" Maska yace "Ni Maskan?" Khaleel yace "Ehh, warce aka nemi daya aka rasa a wnn lkcn, har oga yace duk ynda xaka yi, kayi providing dinta kayi kawai" Maska ya koma ya xauna thinking deeply, can ya wani tafe hannu yace "Ohhhhh.... Ohkkkkk I remember, wnn makauniyar????" Khaleel ya kallesa smiling a hankali yace "Exactly" Maska ya xaro ido yace "Kai ai yarinyar nan har yau ban yarda ba aljana bace wllh wllh, she just disappeared, ko sama ko kasa bbu ita, Allah fa ya so ni lkcn nan da kwanana ya kare, so what about that now?" Khaleel yace "Inda aka dauko yaran nake son sani?" Maska yace "Oho, ni kawai mun hadu ne a bakin daji muka wuce da su, I don't know inda aka dauko su, amma fa ina jin Gwaska da Ahmed ne suka taho da su daga wani kauye" Sufyan yace "Kayy but may I ask you?" Khaleel yace "Go on" Yace "Meye ya tado da batun kusan shekara hudu?" Khaleel yace "Ba komai, Ina wani research ne kawai" Saif yace "Research akan matattu, wa ennan yara ai an rufe babinsu a duniya tun yaushe, tunda dai duk an yanke su a wancan lkcn" Khaleel yace "Gwaska ya mutu, Ahmed ma haka, amma Fago na nan ai" Maska yyi tsaki yace "Toh me xai maka?" Khaleel yace "Tare da shi aka daukosu, don haka baxai rasa sanin garin da aka dauko yaran ba" Tanko dake ta sauraron su a parlon tun farkon fara xancen bai ce komai ba yyi wani dariya irin na bossawa yace "Tunda shi Fagon ance maka bashi da wani memory me ma'ana da xai ajiye a kwakwalwarsa sai wannan abinda baxai amfaneka ba baxai amfane mu ba baxai amfane kowa ba, Kayy ka fito ka fada mana gaskiyar abinda ke faruwa da kai, meye na binciko maganar shekara 4?? ko dai ghost din yaran ne suka sa ka gaba suka ce sai ka je garinsu, share with us plss..." Mikewa Khaleel yyi yana kallonsa fiercely ya nufesa, dai dai nan aka bude kofar parlon, hakan yasa ya juya, wasu mutane ne su biyu suka shigo parlon cike da isa ana taku dai dai, tare da wani dake biye da su a baya hannunsa rike da bindiga, kowa na parlon ya mike ya gaida su, kana gani kasan manyansu ne, su suka kafa gagarumin kungiyar, Khaleel ya koma ya xauna, bakikirin cikin mutane biyun da suke kira da Oga Arne ya kalli Khaleel yace "Genius jiya Ina ka tafi da Magrib kasan akwai meeting, kowa ya hallara amma banda kai" Khaleel yace "Na shiga cikin gari ne" Oga Manga na bin duk kowa na parlon da kallo yace "Ina Zayyad da Salim" Maska yace "Suna sama" Oga Arne yace "Ayi kiransu" Saif ne ya tafi ya kirasu suka sakko gaba daya, Oga Manga yace "Ynxun nan dawowar mu kenan daga gidan d'an takarar jam'iyyar Ac wato Alhaji Sammani Abdulkadir Gaya.... Mun kuma gama magana da shi ya biya abinda muka bukata bbu ja in ja.... ynxu abinda ya rage kawai sai ynda xa ayi kidnapping din abokin hamayyarsa.... Nan da kwanaki kadan, to dai idan mun samu irin wnn aiki daga sama mu kan xauna mu nutsu mu tsara yanda komai xai tafi bbu wani mishkila, don kunga ba karamin aiki bane kidnapping din me takarar mukamin gwamna gaba daya, don haka Kayy xa mu so mu fara jin yanda kaga ya dace mu bi, yana xama a Abuja, Kano... Wani lkcn har Kaduna, snn mun samu rahotun yana lagos ynxu hka, sae dai baxa mu bi sa Lagos ba xae xo nan ya samemu" Khaleel dake ta sauraronsu yana shafa sajensa da ya kwanta ya dai yi shiru bai ce komai ba, Oga Manga yace "Ya ne Genius kayi shiru" Khaleel ya sauke kafarsa daga kan kujeran da ya daura yace "I will think about that overnight" Oga Arne ya karasa yyi patting dinsa yace "We trust you Brainiac, sai dai duk plan da thinking dinka kada ya wuce nan da sati uku, duk da dai there is till much time sosai, amma deadline din da aka bamu kenan daga sama, and we have not to disappoint them...." Bai ce masu komai ba duk suka bar parlon. Heedayah ce ta shigo dakinsu ta kulle kofar a hankali ta jingina jiki tana kallon Farida da dawowarta kenan daga gidan biki, kayanta take cirewa, Heedayah tace "Me yasa na maki magana baki amsa ni ba?" Farida ta ki kallonta tace "Ohh ban ji ba, Ina ta sauri in xo in cire kaya na gaji" Heedayah tace "Nop, kin ji" Farida ta juyo ta kalleta, sai kuma tace "Of course yes na ji" Heedayah tace "Then why did u ignore me?" Farida tace "Because that's what you want, u need privacy this days" Shiru Heedayah tayi tana kallonta, can tace "Ohk about that guy Khaleel? Bbu abinda ke tsakaninmu believe me, he just wants us to be frnds, nothing more, and I didn't tell you ya bani waya ya Sudais ya gani yyi seizing da muka je gidansu biki, I think that's all that u think I am hiding" Farida dai ta tabe baki bata ce komai ba tana ci gaba da cire kayanta, a hankali Heedayah tace "I am sorry if you think I am hiding things away from you Farida, but I am scared..." Lkci daya hawaye ya kawo idonta, Farida ta kasa kallonta, can tace "I am just trying to be a protective sister, nowadays ba ko wani namiji ake kulawa ba, most especially someone like that man.... I won't say he didn't look responsible amma ae ba a goshi ake rubutawa ba, ni dai i want you to be extremely careful with him, ba mu san xuciyar sa ba, kuma kar ki manta inda muka gansa bakin hotel though we don't judge a book by just it cover, bamu san me ya kai sa can ba, amma samarin Kaduna sun wuce tunanin ki Didi" Heedayah bata iya tace komai ba, Farida ta juya tana kallonta tace "Be careful plss Heedayah" Heedayah ta gyada mata kai murya can kasa tace "In sha Allah sis, but ya kara bani wani karamin wayar" tana fadin haka ta tafi gaban mirror ta bude ta daga dictionary ta dauko wayar tana nuna ma Farida, Farida tace "But tell me did you like him" Heedayah ta d'an yi shiru sai kuma tace "He is kind... And gentle" Farida tayi murmushi tace "Toh me da me yake ce maki a waya" Heedayah ta d'an juya ido tace "Nothing, kawai labarin duniya, sae kuma labarin karatu.... He is always telling me to study hard, very hard... " Farida tace "Ohk that's good, if there is anything apart from that you let me know" Murmushi Heedayah tayi tace "Alright" daga haka ta juya ta fita parlon ta koma kasa don Mami take taya girkin dinner coz it's already six. Bayan Magrib Heedayah na xaune parlor da Farida suna cin rice and stew da veggies da Mami ta girka da pepper chicken sai tamarind drink me sanyi, Murya kasa kasa Farida ke ba Heedayah labarin abubuwan da suka faru gidan biki kar Mami ta jiyosu don ga fadan gulma da ta kawo take yi, snn kuma ga fadan abinci na gabanta tana surutu which is a bad table manner, irin abubuwan da kaka ta dinga ma jama'ah take fadi ma Heedayah, da ynda ta laka ma wata satan zinarinta kunne daya, daga karshe aka ga zinarin a bandaki ya fadi alamar dai da kaka ta shiga alwala ne ya fadi, Heedayah ta tabe baki tana girgixa kai tace "Will kaka ever change?" Farida tace "I don't think so gaskiya, har sai da aka kira Baffa ya dawo gidan, Abba ma ya xo wllh, matar sai kuka take gwanin ban tausayi ta harhada kayanta xata wuce, Kuma fa wai step sister dinsu Abba ce she is staying in kano, tana ma da manyan yara kaman mu..." Heedayah tace "Toh me Kakar ta ce da aka ga dankunne a toilet dinta?" Farida tace "Kuka ta xauna ta dinga rusawa wai wani ne dama ke son hadasu fada da matar shine ya kai dan kunnen bandakinta ya boye" danna bell din parlon aka yi, Zainab me aiki dake xaune kusa da kofar dakinta tana kallon Tv ta mike ta nufi kofar ta bude, gaishesa tayi ta basa hanya ya shigo parlon, Tun da Heedayah tayi ido hudu da green ta dauke kai da sauri ta ci gaba da cin abincinta, Ya karaso cikin parlon Farida ma bata sake kallonsa ba tace "Ina yini?" Yace "Ina Mami?" Farida tace "Tana sama, sis Zainab kiyi mata magana" mikewa Zainab tayi ta wuce sama, ya ajiye ledan hannunsa saman table sannan ya xauna kan kujera, da kyar Heedayah tace "Ina yini" Bai ce komai ba, Mami ce ta sakko tace "Shuraim" ya daga kai yace "Ina wuni" tace "Lafiya lau, ya aiki" yace "Alhmdllh, kaka ta bada a kawo maki" Mami tace "Toh nagode kuwa, Allah ubangiji ya basu xaman lafiya su kuma amaren" Yace "Ameen" Mami ta kalli Farida tace "Ki kawo masa abinci" ya mike yace "Aiki xan wuce ynxu, daga can gidan nake shine ta bani in taho maki da shi" Mami tace "Kai kullum kana da excuse one way or the other idan aka ce a xubo maka abinci Shuraim, Farida bring him the food idan kin kawo kar ya ci ya wuce" Daga haka Mami ta wuce sama, Farida ta mike ta wuce kitchen, murmushi ya d'an yi ya koma ya xauna, Heedayah dai sai juya abincin gabanta take ko da wasa ta ki yrda ta kalli direction dinsa.... Can ta mike ta dau plate din abincin ta wuce kitchen, a saman tray Farida ta daura abincin da spoon sae drink da glass cup, ta xuba veggies din a wani bowl duk a kan tray din, farida na kallon Heedayah rike da tray din abincin tace "Kinsan bana son Shuraim din nan kwata kwata Didi, amma Ina son uniform din jikinsa, wllh Ina bala'in son uniform din, suna masa shegen kyau sosai, may be because he is a kind of huge, kuma baya dariya...." Heedayah ta jingina da cabinet din kitchen din ta langwabar da kai tana kallonta so amazed, sae kuma ta fashe da dariya tana tafe hannu tace "Tell me something, really??? But ai in dai kina son uniform din da gaske to son wanda ke cikin uniform din ba abu bane me wahala, Kinga perfect match kawai, bari ki ga inda xa ki kai sa idan kun tsaya yin pre wedding...." Ganin Farida na kokarin ajiye tray din hannunta Heedayah ta fice da gudu tana kyalkyala dariya ta wuce sama, Shuraim ya bi ta da ido. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Farida ta fito ta ajiye masa abincin ita ma ta wuce sama, da ido ya bi ta, can ya kalli agogon wrist din sa ya ga bakwai da rabi, ya dau bottle water da ke saman tray din kawai ya mike, fita gidan yyi, yyi wucewarsa. Washegari Tuesday da sassafe wajen shidda da rabi Mami na kitchen tare da Farida da Heedayah suna hada breakfast, Zainab Mai aiki kuma na gyaran gida ta gama shara tana mopping aka bubbuga kofar parlor, Zainab ta ajiye mopping stick din tafi ta bude kofar, kaka ce tsaye da katon jakarta a sakale a hannu, Zainab ta duka ta gaida kaka, kaka ta amsa tana kokarin shigowa parlon tace "Ina Rakiyar, duk tsiyarta dai na san bata fita opis ba yanxu" Zainab tace "Tana kitchen" Kaka ta ajiye jakar hannunta ta wuce kitchen din, Washe baki tayi bayan ta shiga tace "Ina kwana Rakiya" Mami na kallonta da mamaki tace "Aa, daga ina da sassafe haka kaka?" Kaka tace "Gidan Umaru mana, ai bani da wani gun bayan nan" Mami tace "Ikon Allah, amma kawo ki aka yi dai ko" Kaka ta marairaice tace "Wa na ajiye xai kawo ni Rakiya?? Kamar dai suna tsorona, d'an adaidaita na samu ya kawo ni har nan, na basa nera dari don ya mun mutunci, kuma kinsan na samu kudi sosai da bikin nan shine ma na xo nuna maki kudin ko xa ki bani shawara in siya fili" Mami tace "Aa gaskiya kam gwara ki siya fili in dai kudin na da yawa Kaka" Kaka tace "Yawa kai, ya kusa dubu talatin da biyar fa, don ma ina xara kadan kadan" Mami ta dauke kai tana ci gaba da yanka green pepper da take yi tace "Ehh kam da yawa gaskiya, sai ki ba ko Baffa ko Barrister wani ya samar maki fili a anguwa me kyau" Kaka tace "Shkkn kuwa, shi yasa na fi son inyi shawara da ke a kan kowa, baki da kyashi, kinga idan da canji ma sai su maido min kayana don ba basu xan yi ba, ynxu dai xuwa nayi in maki bangajiya duk da dai a gantale muka dinga ganin ki gidan bikin, daga nan kuma bayan na karya sai wnn yara su rakani gidan Amadu inje can shima inyi masa ban gajiya, miliyan daya ya bada tasa gudunmawar wllh, in gaya maki gadaje bibbiyu aka yi ma yaran, shi dai Amadu yace bashi da kudi ynxu... amma ga miliyan daya ayi duk abinda xa ayi, ke kuma naji labarin kin basu dubu dari ko? Kawun Junaidu bai bada ko sisi ba duk kudinsa" Mami tace "Aa dubu dari biyu ya saka ma Junaid ya kai masu" Kaka tace "Abu ya lalace, ya cinye kenan wllh don kwandala bai kawo masu ba" Mami tace "Aa ya kai masu Ina gidan ma ya kawo, ki tambayi shi Baffan" Kaka tace "Atoh da kyau... Toh duk Allah ya saka, Allah ya nuna mana na 'yan baya, yanxu sai ayi harin na Farida nan da yan watanni ko?" Mami bata kuma ce mata komai ba, Farida da Heedayah suka gaida kaka, kaka ta amsa tace "Toh kuyi maxa mu karya mu wuce gidan Amadu shi ma kafin ya fice" daga haka ta juya ta fita kitchen din tana cewa "Ita wancan xalben ma ban ganta gidan yinin ba, tana fama da tsayi kamar daren sllh" Sai da kaka ta ci tayi nak sannan ta kishingida a parlor tana jiransu Farida su shirya su wuce gidan Abba, Mami ta shigo parlon tace "Kaka ko xa ku tafi da Farida kawai, don Heedayah bata wani jin dadi, kafin in tafi aiki xan fara ajiyeta a asibiti" Kaka ta mike xaune da sauri tace "Aa Rakiya ki rufa min asiri don Allah, ga dai likita Shureen a can gidan na samu labarin yana nan da safe yawanci, ba sai kawai ya dubata ba, amma ni dai dole da ita xan tafi, yaushe rabon ta je gaida uban rikon nata?? Ki dinga abu sbda Allah mana Rakiya" Komawa tayi ta kishingida bata kuma cewa Mami komai ba, Har ta fara gyangyadi ta bude ido da sauri jin ana gaisheta, Junaid ta gani xaune yana kallonta, tace "Kana gidan dama Junaidu?" Yace "Ehh nan na kwana" Kaka tace "Shikenan ya xo gidan sauki bbu ni bbu fada da masu adaidaita sai ka ajiyeni gidan Amadu kawai" ya kalli agogo yace "Toh amma yanxu xa mu tafi sbda aiki xan wuce" Kaka ta mike da sauri tace "Toh me nake jira, wa encan rubabbun ne idan basu gama ba muyi wucewarmu kawai ban iya wahala" daga haka ta dau jakarta ta nufi kofa, bin ta yyi da kallo snn yyi murmushi ya mike ya bi bayanta. Bata yadda sun tafi ba duk da Junaidu yyi kokarin convincing dinta don baya son Heedayah taje gidan amma kaka tace sai dai ya sauketa ita baxata iya wahalansa ba, sai da Farida da Heedayah suka fito snn hankalinta ya kwanta, Farida ta bude front seat ta shiga, Heedayah ta xauna tare da kaka a baya, kaka tace "Wnn ai walakanci ne kawai daga ku yi wanka ku sa kaya sai ku bar mu a walakance a mota muna jiran ku, ko ita Rakiyar ce tace ku dade??" Ganin Mami kaka tayi shiru, Mami ta karaso gun motar tace "Toh Allah ya tsare kaka, mun gode" Kaka tace "Yauwa Rakiya Allah yayi maki albarka, in sha Allahu anjima xan dawo maki da su ni ma ban fiye son xama gidan mutane ba ai kin sani, ko da azahar ne Shureen sai ya dawo da mu gaba daya mu ajiye su ni kuma ya maida ni gidan Umaru tunda can nafi wayo" Mami tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye" daga haka ta koma ciki, Kaka tace "Toh Ameen dai" Junaid ya ja motar suka bar compound din don Mai gadi ya riga ya bude masu gate, Farida na kallonsa tace "Ina kwana Yaya?" Yace "Lafiya lau" Heedayah ma tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" kaka ta tabe baki tace "Abun bai yi ba oo, dama baku san yana gidan bane? Tun wayewar gari sai ynxu xaku ce Ina kwana" Junaid yace "Duk sun shiga daki kafin na dawo jiya, so basu san ina gidan ba ma" Kaka tace "Ni duk sai na ganka wani iri Junaidu, ko baka da lafiya ne" yace "Lafiyata qlau" kaka tace "Toh ku ma dai ku yi kuyi ku fiddo da matar nan dai a maku aure ku bar yawo a titi bakwa wancan gida bakwa wannan gida, auren shi ya fi maku daga kai har Shureen, don shi Sudais naji uwar na cewa cikin shekaran nan ne idan Allah ya kai mu, dama shi me yan mata ne iri iri, xaba kawai xai yi ya darje" Murmushi kawai junaid yyi, Kaka tace "Ba abun murmushi bane, har da rashin auren ke damun ka kai da Shureen, Kai kuma naga ai wayayye ne a kan Shureen da yake nan dunkum, Kai baxa ka rasa yan matan ba ynxu hka, shi kuwa Shureen da kyar idan ba hadin gida xa ayi masa ba, idan ba haka ba kuwa sai yyi shekara hamsin bbu aure, duk da dai shi da maganarsa da wata yarinya a kasa don har naje na nemi alfarman a bamu ita gidan iyayen yarinyar kuma sun amince, sa rana kawai ya rage idan yarinyar ta gama karatun sakandari, ta ma kusa gamawa" daga Farida har Heedayah kallon kaka suke, Junaid ya kalleta ta madubi kawai yyi murmushi bai dai ce komai ba, Heedayah tace "Da gaske kaka?" Kaka tace "Wllh, ai maganan ya fi shekara uku ynxu..." Heedayah tace "Kuma ya san maganan?" Kaka tace "Haba wane mutum, ai baxa a bar sa ya san da maganan ba, ni dai ai ban biye ta rashin kunyar da yake min ba nayi masa gata a matsayin warce ta haifi ubansa, Amadun ma yasan da wnn xancen kuma" Heedayah ta kyalkyale da wani dariya tace "Allah ya sa kwanan nan xa ayi" kaka tace "Aa baxai dau lkci ba dama" Farida tace "Toh auren dole xa ayi masa kenan" Kaka tace "Kaji gantalalliya, auren dole ai tun xamaninmu aka daina, ai baxai ki yarinyar ba tunda tana da kyau kamar uwarta, Allah na tuba me xai nuna mata banda matsayinsa na soja, ai son kowa ce k'in wanda ya rasa" Heedayah ta kara kyalkyalewa da dariya, Kaka tace "Ke ma auren xa a maki kwanan nan ai" Ta dakatar da dariyar da sauri, Junaid dai sai kallonsu yake, ta turo baki tace "Yar yarinya da ni" Kaka tace "Wace yarinya, bayan naji labari a wajen Rakiya kin fara al'ada" Farida ta kauda kai tana dariya kasa kasa, Heedayah tayi shiru bata kuma cewa komai ba, kaka ma tayi shiru jin kowa yyi shiru. Suna isa gidan Abba Junaid yyi parking a waje, kaka tace "Toh Alhamdulillahi Allah ya maka albarka Junaidu, Allah ya nuna min bikin ka" Daga haka ta sauka motar Heedayah ma ta sauka Farida ma ta sauka, Farida ta daga masa hannu tace "Allah ya kiyaye" Heedayah ta kallesa tace "Sai anjima" ya gyada mata kai ta bi bayan kaka da har ta shiga compound din. Hamdala kaka tayi ganin motar Abba da na Shuraim, ta wuce ciki tana cewa "Allah ya so ni, idan Amadu ya fita ai xuwan banxa nayi kenan" Abba ya fito parlonsa cikin shigar fita office tare da Shuraim dake rike da brief case dinsa kenan kaka ta shigo parlon Heedayah na biye da ita, Kaka ta washe baki tace "Sannu Amadu Ina ta sauri kar ka fita, Allah ya so ni...." Kallon Heedayah kawai Abba yake, hakan ya sa ta karasa inda yake tsaye ta rungume sa cikin sanyin murya tace "Abba..." Kaka tace "Atoh, ai Rakiya ta shiga uku ta lalace, ta tarwatsa xumunci" Abba ya d'an yi murmushi ya maida Heedayah gefensa yana kallonta yace "How are you" tace "I'm fine good morning" Yace "Ya karatu" tace "Alhamdulillah" Farida ta karasa ita ma ta gaida Abba da ladabi, ya amsa da murmushi yace "How are you Farida" tace "I'm fine sir" Abba yace "That's good" Kaka ta tafi parlor ta xauna tana cire hijab din jikinta tana kara gode ma Allah ta samu Abba, Abba ya karasa ya xauna ya gaisheta tace "Lafiya lau Amadu ya taro? Fatan duk kun watsa su lafiya" Yace "Alhmdllh" kaka tace "Toh Allah ya maku albarka ya mayar maku da dubun abinda ku ka kashe, saura na wnn yaron naka Shureen kuma" Shuraim dake ta tsaye ya kalleta ta gefen ido, Abba dai yyi murmushi ya mike yace "Na makara Baaba, kuna nan har in dawo ai" Kaka tace "To ina xa ni? Ai ina nan in sha Allahu har ka dawo, yi tafiyar ka Allah ya tsare" Yace "Ameen" hannun Shureen ya amshi briefcase dinsa yace "You didn't greet her" Shureen ya karasa parlon yana kallonta yace "Ina kwana" kaka tace "Lafiya lau, jiya ka kai ma Rakiya su dubulan da alkaki da cincin din kuwa, naje gidan na manta ban tambayeta ba wllh" Wani kallo ya mata bai ce komai ba, Abba na kallon Heedayah yace "Sai na dawo" Tace "Allah ya tsare Abba" ya amsa da "Ameen" Farida tayi masa Allah ya tsare ita na snn ya fita parlon, Farida da Heedayah suka dawo parlon suka xauna, kaka tace "To ita Maryam din bin ta xa mu yi parlonta kenan, toh ai bbu komai ku tashi mu je, mu ba bakin xafi bane, baxan biyeta ba, amma kuma ban ji kun gaida Shureen ba" Farida ta mike ganin kaka ta mike, tace "Ina kwana" Heedayah ma ta tashi tace masa "Ina kwana" Duk bai amsa masu ba, Suka bi bayan kaka xuwa parlon Mumy, Mumy ta fito bedroom dinta kenan ganin kaka ta d'an canxa fuska tace "Kaka ce..." Kaka tace "Wllh ni ce, ina ta sallama shiru, ashe kina can ciki" Mumy juya xata rufe kofar dakinta tana yatsine yatsine tace "Ehh ina ciki" Heedayah ce karshen shigowa parlon, Farida ta xauna kusa da kaka, Heedayah ta xauna gefenta duk suka gaida Mumy, lkci daya fara'a ya bayyana fuskar Mumy ganinsu tace "Aa ashe baki muka yi hka, to sannun ku da xuwa" Kaka tace "Ehh cewa suka yi sai sun xo sun gaishe ki, su Rabi'ah kuma can na barosu gidan Umaru basu ma san xan yo nan ba" Mumy na washe baki tace "Allah sarki, Sannun ku da xuwa, bari a kawo maku breakfast" Kaka tace "Aa ni kwai kawai xa a soya min, idan akwai d'an farfesu a hada min da shi, kwanan nan ba wani cin abinci nake ba" Daga Farida har Heedayah suka kalleta, Mumy tace "Toh su kuma 'yan matan fa" Kaka tace "Su ma soya masu kwan kawai a hado masu da d'an dankali" Farida tace "Aa mu mun koshi" Kaka tace "Da yake sun karya su" Mumy bata ce komai ba har ta fita parlon sai kuma ta dawo ta shiga bedroom dinta tace "Bari in maida wayata caji" rufe kofar dakin tayi ta nemo wani karamin purse dinta da ta adana sosai ta bude ciki ta dau wani kullin xani, ta fi minti daya tana kallon kullin da xai yi shekara uku a ajiye cikin jakar, "Ko nan da shekara goma ne bbu abinda xai hanasa aiki" murya wanda ya bata ne ke dawo mata, tayi wani murmushi ta kunce habar xaninta ta kulle kullin maganin a jiki snn ta daura xanin ta fito parlor tace "Sannu kaka, bari in je inyi masa in soya maki" kaka tace "To yi maxa" daga hka ta fita parlon, tsaye ta ga Shuraim har sannan a Main parlor, Tace "Aliyu tun da sai yamma xaka fita bari in baka sako ka kai ma Hajiya Sadiya yanxu..." Ya kalleta yace "Akwai aikin da nake yi ban gama ba, ki bada sakon idan na fita anjima sai in kai mata" Ta wani hade rai tace "Toh ni yanxu nake son ka kai mata ba sai anjima ba" Bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen ya bi ta da kallo, sauke ajiyar xuciya yyi ya xauna saman kujera, Mumy na tsaye kitchen ta sa mai aiki ta soya lafiyayyen kwai da ya ji albasa da tsire a ciki na kaka, sauran tsiren kuma ta saka a plate daban daban guda biyu, tana kallon Mai aikin tace "Duba min Shuraim na parlor ne" Mai aikin ta fita ta dawo tace "Aa baya nan" Mumy ta dau plate din kwan kaka ta mika mata tace "Ki kai ma kaka, idan tace wa ya soya kice ni ce.... Sai ki tafi ki ce ma driver yyi wucewarsa nayi baki sannan ki dawo ki kai ma yan matan nan tsire" Mai aikin tace "Toh Hajiya" daga haka ta nufi kofa ta fita, Mumy ta bi ta da kallo har ta rufe kofar, kallon window din kitchen din tayi snn ta kai hannu gefen xaninta, cikin few minutes ta gama abinda xata yi ta barbada ma naman yaji snn ta dau plate din biyu ta fita xuwa parlonta, ta ajiye daya gaban Farida, na hannun hagunta ta ajiye ma Heedayah tace "Naji kaka tace kun karya wnn kuma ai abun marmari ne, da asuba nayi ma Barrister ashe baxai ci ba, wnn nawa ne da na Shuraim, shi ma nasan ba lallai ya ci ba" Kaka tace "Atoh, rabonsu ne, ku yi maxa ku ci" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mumy ta nemi kujera ta xauna tana murmushi, labarin biki da abubuwan da suka faru suka dinga yi da kaka, kaka ta saki baki sai xuba take, Mumy tace "Ai ni kin kyauta min da kika ce a sauke canopy din nan, mutane basu da hankali wllh" Kaka tayi fuska kamar 'yar yarinya tace "Lallai, haka kawai a lalata min motocin yaro, uban waye ya siya masa, kiris ya rage wnn suntumemen ya gogi motar da karfen fa, ba ruwana ni dai na koresu, wanda suka kafa a bakin titi bai isa ba sai an shigo mana gida da katon lema a kakkafa" Mumy tayi 'yar dariya, sai kuma ta kalli su farida tace "Ku ci mana kar ya huce da xafinsa kuwa" Farida ta ajiye wayarta da take dannawa tace "Na koshi ni" Mumy ta hade rai tace "Kin koshi kamar Yaya, hanaki cin abinci aka yi a nan din idan kun xo" Kaka tace "Aa babu wanda xai hanata, da yake kinsan sun karya kafin mu fito" Mumy tace "Aa to gaskiya baxan ji dadi idan basu ci ba tunda da kai na na kawo masu" Kaka ta kalli farida tace "Ko kwara daya ne ki ci kar taga kamar an hanaki, nasan a koshe ku ke" Mumy na kallon Heedayah tace "Ita idan ta ki ci ai ke bakya ki ci ba, dau plate din ki ci abun ki" Heedayah tace "Ahh haba wnn ai Mayyar nama ce xata ci nasani" Heedayah ta kalleta bata dai ce komai ba, Mumy tayi dariyar da bai kai ciki ba tace "Dauka ki ci Heedayah" Heedayah ta sauke idonta tana kallon naman tace "Mumy na koshi, mun yi breakfast a gida kafin mu fiti" Mumy ta d'an hade rai tace "Nama abinci ne? Bana son gulma idan xaki dauka ki dauka ki ci, idan kuma hanaku cin komai akayi sai na sani" Kaka tace "Ni dai ba ruwana sai ku ja ma Rakiya bakin jini nan kuma bata san hawa ba bata san sauka ba, idan xaku dau gasasshen naman ku dauka ku ci meye xaku dinga ma mutane kunbiya kunbiya gashi har na narka kwaina a ciki, nama ai abun marmari ne ba abinci ba" Farida dai ta ci gaba da danna wayarta bata ce komai ba, Heedayah ta dau plate din naman ta dauki daya, wani ajiyar xuciyar da ya kusa fitowa fili Mumy ta sauke, Kaka ta kalleta tace "Lafiya?" Mumy ta d'an daburce tace "Wllh tun juya nake jin kamar ulcer na xai tashi" Kaka tace "Toh Allah ubangiji ya maki tsari da shi" ta gefen ido Mumy ta dinga kallon Heedayah da ta kai naman baki ta fara ci a hankali, wani ajiyar xuciyar ta kuma saukewa, Kaka tace "Toh Allah yayi maki tsari da shi dai, ulcer ai bala'i ne" Heedayah xata ajiye plate din Mumy tace "Har kin yi me? Me kika ci da xa ki ajiye" Kaka tace "Ni dai ba ruwana da wahalansu idan basa ci su kawo min in juye a jaka mu tafi kawai" Farida ta mike ta dau plate din nata ta tafi ta kai ma Kaka tace "Ni baxan ci ba" kaka ta kwace plate din, Heedayah dai ta ci gaba da cin naman, hira kawai Mumy ke ma kaka don Heedayah ta ci naman sosai, Heedayah dai cin naman kawai take ba wai don yyi mata dadi ba, daga karshe ta mike ta nufi kofa, Ta gefen ido Mumy ta bi ta da kallo don ta ci desired quantity din ba laifi, Heedayah na fita ta dau hanyar kitchen, xaune ta ga Shuraim a parlon this time around, ya mike ganinta, dauke kai tayi da sauri ta wuce kitchen din ta shiga, plate ta nema ta rufe sauran naman ya shigo kitchen din yana kallonta yace "What's that you are covering?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Tsire ne" Yace "Waye ya ci?" Tace "Mumy ce ta bani" Shiru yyi yana kallonta, yace "Ke da wa?" Tace "Farida" yace "Ina na faridan?" Heedayah tace "ita bata ci ba" yace "Kece mayunwaciya kenan" Sai a snn ta kallesa, ya daure fuska yace "Baki ci abinci a gida ba kafin ku fito?" Kin cewa komai tayi ta dauke kai, yyi mata wani tsawa yace "Ba da ke nake ba" Ta ki juyo fuskarta ta d'an turo baki tace "Na ci" yace "Then meyasa kika ci naman?" Tace "Mumy ce tace I should eat it" karasawa yyi ya bude plate din sai ga Mumy ta shigo kitchen din, ganinsu a tsaye da mamaki tace "Me kuma kake yi a nan Aliyu?" Ba tare da ya dubeta ba yace "I came to make tea" Mumy tace "Wanda ka sha daxu fa" yace "Bai isheni ba" Ta kalli Heedayah da ta sunkuyar da kanta, Mumy tace "Ina naman da kika rage bani in tafi in ci ban karya ba dama" Heedayah ta karasa ta bude plate din ta dauko naman ta mika ma Mumy ta amsa, Heedayah ta bi gefenta ta fita kitchen din, Mumy tayi masa wani kallo tace "Da uban me ka shigo nan din kana gaya mata ko akwai hadin biri da gada ne?" Yace "Ni fa I just came in to make tea sai na ganta, and where is my meat?" Mumy tace "Gwara ya kasance haka don ma ka ji in gaya maka, ba hadin biri da gada, tsire kuma bbu sai ka dau na annabawa" yace "Toh bani wannan in ci" tace "Baxan bayar ba" daga haka ta fice daga kitchen din ya bi ta da ido. Mumy na fita kitchen dama Parlon Abba ta shiga ta kulle da mukulli, tana dube dube ta dau wani plane sheet paper ta juye tsiran a ciki sannan ta cukuikuye takardan ta tura can karkashin kujera yanda baxa a hango ba snn ta mike ta fito Main parlor, leka hanyar kitchen tayi ta ga alamar yana tsaye har sannan a kitchen din, ta mayar da plate din parlon Abba, sannan ta fito ta sa makulli ta tafi parlonta tana murmushi ta shiga tace "Sannun ku Kaka, Kwan ya ishe ki ko?" Kaka tace "Ya isheni sai na gobe kuma idan Allah ya kai mu, kin ji Farida wai mu wuce, bayan nace ma Amadu muna nan har dare" Mumy tace "Allah sarki, ta gaji da xama kenan, tunda kun gaisa da Barrister din ai xaku iya tafiya kaka" Kaka tace "Aa su dai su tafi, haka kawai bamu gama ganawa da d'a na ba kice in tafi" Mumy ta kauda kai bata ce komai ba, kaka tace "Sai dai ko kiyi ma Shureen magana ya ajiye su gida tunda ke baxai maki musu ba ni kuma sai ma ya iya xagina" Mumy ta d'an yi shiru, can ta saci kallon Heedayah, sai kuma tace "To dama dai driver na nan ne sai ya ajiye su, amma Shuraim kam nasan baxai je ba, ynxu ma na aikesa ya kai ma Sadiya sako yace baxai fita ba" Kaka ta rike ha6a tace "Wnn Sadiyar dai kinki rabuwa da ita har ynxu ko Maryam, bbu wanda fa bai san uwarta dillalliyar bokaye bace, kinsan uwarta kawar kishiya ta ce, to wllh bbu gidan bokan da basu xuwa lkcn Kaduna na daji, daga karshe ya kwabe masu shine kishiyar tawa uwarsu wnn yarinya da ta kusa sace min zinari jiya ta bani labarin komai, Kai har makabarta ta sha shiga ta binne laya a kabari, to in takaice maki a tsaye uwar Sadiya ta mutu kekam, ki gaya ma kowa wannan labarin kice in ji ni, a tsaye Talle ta mutu a bandakinta kamar tsohuwar soja, ta mutu da yan awanni kafin a ankara har ta kumbura suntum, toh ke dai kiyi hattara da kawance da Sadiya don barewa baxata yi gudu d'an ta yyi rarrafe ba, Kuma dai abokin barawo barawo ne, tale tale da nasan ki ke dai ko maganin tsari baki yrda da shi ba sai kice Allah ne me tsarewa, to yanxu dai ban san ya kike ciki ba gaskiya" Mumy dai sai danna wayarta take fuskarta bbu yabo bbu fallasa ta ki kallon kaka, Shuraim na tsaye bakin kofa tun fara labarin kaka hannunsa rike da makullin motarsa yana sauraronta, Mumy ta juya tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace "Lafiya????" Yace "Xan je government house" Kaka tace "Atoh ka sauke min yaran nan a gida don girman Allah kar su fara min kuka, kuma me xaka je yi a gwamnet house?" Da sauri Mumy tace "Ae ba hanyarsa bace kaka" Kaka tace "Toh sai ya fara ajiyesu snn ya tafi gwamnet house din, Ina ruwana ni da xa ki ce min ba hanyarsa bane" Juyawa yyi yace "Su sameni a mota" daga haka ya fita parlon, Farida ta mike ta dau jakarta, kaka tace "Toh Allah ya kiyaye, kila anjiman ma Amadu ne xai ajiye ni gida" Farida tayi ma Mumy sallama tayi ma kaka sannan ta fita, Heedayah ta mike tsaye da kyar don tun fitowarta kitchen kanta ke juya mata, bata ce masu komai ba ta nufi kofa walking slowly, Mumy ta bi ta da kallon gefen ido har ta fita, kaka ta kyabe baki tace "Bana biye mata ba ta kai ni gaba gun Rakiya" Farida na tsaye bakin kofar fita main parlor tana jiran Heedayah, har ta iso kofar kallonta take, tace "What's wrong?" Heedayah ta dafe kanta da kyar tace "I'm not feeling okay" Farida ta kama hannunta tace "Ciwon kai??" Heedayah ta girgixa mata kai kawai, Farida tace "Mu tafi gida sai ki kwanta, you will feel okay in sha Allah" tana rike da hannunta suka nufi motar Shuraim, har suka iso yana kallonsu ta madubi, Farida ta bude back seat Heedayah ta shiga ta kulle sannan ta xaga ta bude daya side din ta shiga ita ma ta kulle tana kallon Heedayah da ta hade kai da gwiwa tace "Sannu" juyowa yyi yana kallonsu yace "What's wrong?" Farida tace "She said she is not feeling fine" Rufe motar yyi suka bar gidan, har suka isa gida bbu wanda yace komai cikin motar, yyi parking kofar gidan yana kallonsu ta madubi, Farida ta bude side dinta ta fita ta xaga ta bude bangaren Heedayah tace "We are home..." A hankali Heedayah ta dago kanta sannan ta sakko daga motar, Farida ta rufe tana kallon Shuraim tace "Thank you" Bai ce komai ba ta kama hannun Heedayah suka nufi gate, "Heedayah!!" a tare duk suka juya suna kallonsa, Farida ta sake hannunta, kamar me counting step dinta ta koma gun motar, yana kallon idanuwanta da suka kada yace "Me ya sameki?" Ta sunkuyar da kanta da kyar tace "Ina jin jiri, kuma ina son in kwanta" yace "Why?" Ta buda hannunta a hankali tace "Nima ban sani ba" yace "Tun da kika tashi yau kike jin jirin?" Ta girgixa masa kai, Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds yace "Go...." juyawa tayi taga Farida ta riga ta wuce ciki, ta nufi gate din, dishi dishi ta fara gani kafin ta karasa gate din, lkci daya ta kwala wani kara ta sulale a wajen. Mami ce xaune gefenta a kan gadon dakin, Junaid na ta daya side din a tsaye pressing his phone, sai Shuraim dake tsaye kusa da window ya rungume hannunsa, Farida ta shigo dakin rike da bottle water da glass cup, ta duka gefen Heedayah ta bude ruwan ta xuba a cup, Mami ta dagota tace "Gashi ki sha" amsa Heedayah tayi ta sha kadan, Mami tace "Ya ciwon kan?" A hankali tace "Ya daina" Mami tace "Toh Allah ya sauwake daughter" Junaid ya kalleta yace "Jirin fa?" Tace "Ya daina" Kofa Shuraim ya nufa ya fita, Heedayah tayi kasa da murya tace "Mami ina son inyi bacci ynxu" Mami ta kwantar da ita ta ja mata blanket tace "To yi baccin dear" Farida ta mike ta fita da ruwan, Junaid ya bi bayanta, sai da Mami ta ga ta fara baccin snn ta sauke curtain din dakin ita ma ta fita. Lkci lkci Farida ke shigowa dakin duba Heedayah dake ta bacci comfortable har kusan azahar, Farida tayi alwala ta fito bandaki ta tafi gaban mirror ta dau darduma dake kan kujeran mirror din taji vibration din waya, bude inda taji vibration din tayi ta daga dictionary ta dau karamin wayar tana kallo, bude ido Heedayah tayi ta mike xaune da sauri tace "Is it ringing??" Farida ta karasa kusa da ita ta mika mata wayar sannan ta juya ta fita. *Let it not be as if I didn't update today, yanda kowa ma ya tafi gidan lalle haka nima na tafi can don ni ba gantalalliya bace, ehe* 🌚 Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Heedayah ta daga kiran ta kai kunne amma bata ce komai ba, sallama yyi mata ta amsa sannan tace "Ina yini" yace "Lfya lau, how are you?" Tace "I'm fine" yace "Always not picking calls, why?" tace "Mun fita ne" yace "Xuwa ina?" Tace "Gidan Abbanmu" yace "Ohk" shiru tayi, shima yyi shiru, can yace "So you ain't coming out anytime soon" ta jingina da pillow tace "Nima ban sani ba" yace "Yaushe xa ku koma schl?" Tace "In a week time" yace "Ina son mu hadu" bata ce komai ba, yace "Kin ji?" Tace "A ina?" Yace "Idan ma kince gidanku ae sae in xo" tace "Don a min duka?" Murmushi yyi yace "Aa ba wanda xai maki duka, now tell me a ina xan gan ki?" Shiru tayi, yace "Think about it, then u call me, wayar a bude take and akwai airtime a ciki, I will be expecting ur call" daga haka ya katse wayar, ta cire a kunnenta a hankali, bayan kusan minti biyar da gama wayar aka bude dakin junaid ya shigo, karasowa yyi gefenta yace "How are u feeling Heedayah" tace "Alhmdllh" yace "Bbu inda ke maki ciwo ko?" Ta gyada masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace "Look at me Heedayah" juyowa tayi ta kallesa suka hada ido, yace "Me xa ki ci?" A hankali tace "Shayi kawai xan sha" yace "Ohk, no bread?" Ta girgixa masa kai tace "Aa bana so" juyawa yyi ya fita dakin, ta boye wayar da ta rufe da palm dinta karkashin pillow da sauri. Heedayah na gama shan shayin da Junaid ya kawo mata ta mike ta tafi yin alwala, bayan ta idar da sllh ta daga karkashin pillow ta dau wayar da ta boye ta mayar inda yake sannan ta dawo ta kwanta, nan da nan wani baccin ya kuma dauketa. sai after la'asar Heedayah ta fita dakin bayan tayi sllh, Mami na xaune parlor da wata colleague dinta suna hira, Heedayah ta gaishesu Mami tace "How are you feeling now" Heedayah tace "Da sauki" Barrister Khadijah tayi mata Allah ya sauwake ita ma sannan Heedayah ta wuce kitchen da cup din hannunta, Farida ce kitchen din tare da Zainab suna girka dinner, Farida ta juya tana kallonta tace "Ya jiki?" Heedayah tace "Na ji sauki, tuwo xa ku yi?" Farida tace "Shi Mami tace mu yi" Heedayah ta marairaice fuska tace "To ni me xan ci da daddare?" Dariya Farida tayi tace "Ba ga Indomie ba sai ki dafa" a hankali Heedayah tace "Mami baxa ta bari ba ai cewa xata yi sai na ci" Farida tace "Vegetable soup ne fa" Heedayah ta girgixa kai tace "Bana ci" Farida tace "Guess what Heedayah" Heedayah ta d'an bude ido tace "No plss tell me, kinsan I am not a good guesser" Farida ta wara ido tace "At last Mami tace I can go to Abuja tomorrow" Heedayah tace "Only you?" Farida tayi dariya tace "Kin ma san da ya ta bar ni, nace ke fa tace baki da lafiya baxa ki je ko ina ba" a hankali Heedayah tace "Ni ai naji sauki, don Allah Mami ta bar ni" Farida tace "Ki bari anjima sai kiyi mata magana" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, can ta juya ta fita kitchen din, Mami ta dawo daga rakiyar Barrister Khadijah ta xauna nan parlor tana kallon Heedayah da ta xauna kasa kan carpet tace "Are you sure bbu inda ke maki ciwo Heedayah?" Heedayah ta girgixa kai tace "Ba ko ina Mami" Mami tace "Toh Allah ya sauwake" Heedayah tace "Mami ai tare xa mu tafi Abuja da Farida" Mami tace "Noo you are going no where, tashi ki kai min system dina daki" Mikewa Heedayah tayi ta dau system din ta wuce sama, nan kuwa ji take kamar ta rushe da kuka. Bayan Magrib duk suna xaune parlor suna cin abinci banda Heedayah dake xaune tana kallo, Junaid ne ya shigo parlon bayan ya gaida Mami ya amsa gaisuwar da Farida ke masa, yana kallon Heedayah da ta gaishesa ita ma yace "Why are you not eating?" Shiru tayi bata ce komai ba, Farida tace "Ae bata cin tuwo" ya kalli Mami, sannan ya kalli Heedayah yace "Me xa ki ci?" Mami tace "Bbu wani abinda xata ci, idan baxa ta ci tuwon ba ta bar shi, meye da tuwon da xata ce bata iya ci?" Junaid dai bai ce komai ba, can dai ya wuce sama, ba a dau lkci ba ya sakko sanye da jallabiya, yana shafa kansa yace "Mami frnd dina na jirana waje xan basa sako cikin mota" Mami tace "Idan ma gidanku ne ke jiranka a waje that's not my concern, my only concern is that kar ka kuskura ka shigo min gidan nan da wani abinci" ya xaro ido yace "Abinci kuma? Abincin me Mami" Mami tace "I've told you my own" Bai ce komai ba ya nufi kofa ya fita gidan, Heedayah dai na xaune sai wasa da fingers dinta take, Farida sai murmushi take, Mami ta kara gyara xama parlon tana jiran shigowar Junaid daga wajen frnd din nasa, yana fita ko minti goma ba ayi ba aka bude kofar parlon, Shuraim ne ya shigo da sallama, ya karaso cikin parlon, Mami na kallonsa tace "Welcome" ya xauna sannan ya gaisheta, ta amsa tace "Ya aikin?" Yace "Yanxu xan wuce" tace "Night Duty kawai kake yi ne ynxu?" Yace "Aa amma na fi yin night din ne" Farida ta gaishesa ya amsa, Heedayah ta dauke kai murya can ciki tace "Ina yini" Bai ce komai ba, Mami tace "Ya mutanen gida?" Yace "Lafiya lau" Tace "Kaka ta koma can gidan Baffa ne?" Yace "Aa tana nan gida" Mami tace "Ohk" yace "Ya mai jiki" Mami tace "Aa ta ji sauki sosai" Yace "Allah ya kara sauki" Mami tace "Ameen, Farida ki kawo masa abinci duk da nasan he is full always" Shuraim yyi murmushi amma bai ce komai ba, Mikewa Farida tayi ta tafi kitchen, bayan wani lkci ta fito ta ajiye masa tray din abincin a gabansa, ya d'an bude warmer din, lkci daya ya rufe yace "Ai bana cin tuwo" Kallonsa Mami ta tsaya yi, can tace "Baka cin tuwo??" Yace "Bana ci" Heedayah ta gyara xama tace "Mami to ai kinga yanxu dai ba ni kadai ce bana cin tuwo ba, kince baki taba jin wanda baya cin tuwo ba, shi ma ba gashi baya ci ba, sai in je in dafa masa Indomie" sau daya Shuraim ya kalleta ya dauke ido, Mami tace "Kar Allah ya sa ya ci tuwon, Farida dauke min abincina ki mayar kitchen yunwa bai ishesu bane" Murmushi kawai Shuraim yyi, Mami tace "Tuwo ba dai da miyar kuka ba ko kubewa ace baxa a ci ba" Ya girgixa kai yace "Aa ni fa ina ci, don na koshi ne yasa nace bana ci" daga haka ya mike yace "Xan wuce" Mami tace "Allah ya tsare" ya nufi kofa ya fita, Heedayah ta bi sa da harara, can ta mike ta wuce sama kamar xata yi kuka. Shuraim na fita junaid ya shigo, yyi ma Mami sannu da xama ta amsa tana kallon hannunsa ya wuce sama. Karfe sha daya da wani abu junaid ya bude kofar dakinsu Farida, Farida tayi bacci Heedayah kuma na kwance cikin blanket tana waya da Khaleel, jin an bude kofa ta katse wayar da sauri, tayi still barin da taji an kunna switch din dakin, bayan few seconds ta sauke blanket din a hankali, mikewa xaune tayi tana kallonsa tace "Yaya" ya ajiye mata ledan hannunsa yace "Ga abincin" murmushi tayi masa tace "Nagode" ya daga mata gira yace "Good night" daga haka ya juya xai fita ya kusa cin karo da Mami, da sauri Heedayah ta mayar da kanta cikin blanket din, Ya fara kame kame ya ma rasa abinda xai ce ma Mamin tasa, Mami ta kalli ledan da ya ajiye sannan ta karasa ta bude ledan, takeaway ne na fried rice with full chicken lap, ga chivita drink, sai kuma tsire a wani takarda daban, mayar da ledan tayi ta rufe sannan ta ce "Toh fita" juyawa yyi ya fita dakin ta fita ita ma ta kulle, a hankali yace "Mami kiyi hakuri, naga bata da lafiya ne kuma kar ta kwana da yunwa, right from time kinsan bata cin tuwo" Mami tace "Kuma gaskiya ne, kai me conscience, ni kuma mara shi..." Da sauri yace "Aa wllh Mami ba haka bane" dakinta ta shiga, ya d'an yi jim sannan ya bi bayanta xuwa dakin, tace "Aa yi tafiyarka ka kwanta...." Yace "Kiyi hakuri Mami" kujera ta nuna masa tace "Sit" ba musu ya xauna, ta xauna gefen gado tana facing dinsa tace "Tell me, what is ur intention na makale ma Heedayah da kake yi ina hanaka amma baka ji" ya sunkuyar da kansa yyi shiru, tace "Answer me, xan kwanta ina da aiki gobe" Yace "Nothing Mami, matsayinsu daya da Farida" Tace "Good I hope it shouldn't pass that Junaid..." Dago kai yyi yana kallonta tace "Yess, matsayinsu ya tsaya daya da Farida, tashi ka tafi good night" Yyi kasa da murya yace "But me yasa kika ce haka Mami?" Tace "Me yasa nace me?" Yace "Abinda kika ce" Tace "Ban gane tambayar ka ba" ya sauke idanuwansa kasa yace "But Mami...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yace "I would have wished us to be together till end" Mami tace "As???" Jin ya ki cewa komai ta hade rai tace "Kaga you stop beating about the bush and save my time, go straight now" yace "Mami kawai Ina sonta, kuma Ina jin xan iya aurenta" Kallonsa Mami take bbu ko kiftawa, can tayi wani murmushi tace "Ita Shaheedar fa?" Ya d'an hade rai yace "Dama kece ke sonta ba ni ba" Tace "Haka kace?" Yayi shiru, tace "Toh ba da ni xa ayi wnn haukan ba, Shaheedah da maganarta ke kasa kusan shekara uku sbd selfish interest dinka kace min ni ke so ba kai ba...." Yace "Don Allah Mami ki bar maganan nan wllh bana jin xan iya auren Shaheedah, idonta ya bude da yawa, kuma I can't marry someone living all alone abroad da sunan tana karatu" Mami tace "Fine then, idan kai ka haife kanka sai mu gani ai, ita Heedayar an gaya maka ikon mu ce??" Bai kuma ce mata komai ba, tace "I will advice you ka cire idonka a kanta don baxa ka ta6a samun ta ba, beside nawa take da har xaka ce kana sonta da aure, did you think xaka kara min shekara daya ne nn gaba, ba dai cikin shekaran nn Shaheedah xata gama ba, xaka sha mamaki" mikewa yyi yace "Sae da safe" tace "Allah ya tashemu lfya" daga haka ya fita dakin ya kulle mata kofa. Washegari da safe Farida ta gama hada few kayan da xata tafi da shi gidan yayarta a Abuja, Heedayah dai na xaune dakin duk ta xama abun tausayi, Farida ta koma kusa da ita tace "Ko xa kiyi ma Yaya magana yace Mami ta bar ki mu je tare" Heedayah ta share guntun hawayen idonta a hankali tace "Baxata bari ba, I know she is angry at him now bcos she caught him giving me food yesterday night" Farida tace "To yanxu wa xai yi mata magana ta ji? Nobody, cewa xata yi baki da lafiya" mikewa Farida tayi ta dau powder dinta a gaban mirror ta saka a handbag dinta kar ta manta, a hankali Heedayah tace "Ko mu gaya ma Ya Shureen yyi mata magana??" Farida ta juyo tana kallonta, dariya tayi sosai tace "He is not Shureen Heedayah, He is Shuraim" Heedayah tace "To ni ina ruwana ba Shureen naji kaka nace masa ba, ni dai mu yi masa magana koh?" Farida tace "Amma dai ke xa ki yi masa maganan" Heedayah tace "Ehh xan yi masa" Farida tace "Ina xa mu samo number sa?" Heedayah tace "Mami na da shi ai kamar, let me check" daga haka ta mike ta fita, a hankali ta bude kofar dakin Mami bata ganta a ciki ba, ta karasa gun wayarta da sauri ta dauka ta shiga contacts, searching sunan tayi sai ga shi ya fito with 080333.... Lkci daya ta haddace gaba daya ta ajiye wayar ta fice daga dakin, tana kallon Farida tace "Where is ur phone, I have crammed the digit" Farida ta mika mata wayarta Heedayah ta sa number snn ta marairaice tace "Are you sure we should call him Farida?" Farida tayi dariya tace "Yess try it, ki sa a handsfree in ji me xai ce" Heedayah ta xauna gefen gado xuciyarta na bugawa tayi dialing number, har ya gama ring ba a dauka ba, Farida dake ta kallonta ita ma xuciyarta na bugawa kamar ita xata yi masa magana tace "Redial it..." Heedayah ta kuma sending number ta sa handsfree tana xare ido, nan ma har ya gama ring no response, Farida ta ta6e baki ta cigaba da abinda take, a hankali Heedayah tace "May be baya daukan bakon number ko" Farida tayi mata wani kallo tace "As per shugaban kasa or governor dat he is ko???" Dariya Heedayah tayi, Farida ta ja tsaki tace "Ki je kiyi wanka may be Mami will change her mind idan ta ga mun shirya tare" A sanyaye Heedayah ta mike tace "Toh train xaku shiga?" Farida tace "Noo, Mami tace driver ne xai kai mu idan yace xai iya idan kuma baxai iya ba ban san yanda xa ayi ba" Bathroom Heedayah ta shiga bata ce komai ba, bayan kusan minti talatin ta fito daure da towel, wayar Farida dake kan gado ne ya fara vibrate, Heedayah ta xaro ido tana bin dakin da kallo don Farida bata nan, can tafi gun wayar tana gyara daurin towel dinta ta leka wayar taga number Shuraim ne, daukar wayar tayi xuciyarta na bugawa ta xauna gefen gado ta daga ta sa handsfree, sallama yyi daga daya bangaren ta wani xaro ido ta kasa amsawa, har sai da ya kuma yin sallama, kamar xata yi kuka tace "Uhn Ina ji" shiru yyi, a takaice yace "Waye wannan?" Ta kara gwalo ido tace "Ni ce fa" yace "Ke wa?" Ta turo baki tace "Ni mana" yace "Baki da suna?" Tace "Heedayah" Shirun 3 seconds yyi snn yace "Why are you calling?" Ta marairaice murya tace "Ya Shureen dama... dama" sai kuma tayi shiru, yace "Dama me?" A hankali tace "Dama Mami ce tace baxan bi Farida Abuja ba mu je gidan Maman Fadil, shine sai Farida tace ko xaka mata magana, shine na kiraka nake gaya maka" Yace "Faridar ta aiko ki wajena" ta xaro ido tace "Aa wllh, ba ta ma dakin ni kadai ce, na fito wanka yanxun nan sai naga wayar yana vibrate" yace "To baxa ki je Abujan ba" ta buda baki da farko, sai kuma ta fashe masa da kuka tace "Ya Shureen plss, wllh I want to go, ban ta6a xuwa ko ina ba tunda aka haifeni, nima ina son inje wani waje don Allah" Yace "Baxa ki je ba, xan xo kuma in gaya ma Mami bbu inda xa ki je" Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta fashe da kuka ta ajiye wayar tana kallonsa tace "Wllh sai naje ina ruwanka da ni to" Farida ce ta shigo dakin tana washe baki tace "Guess what Didi, Mami tace mu je amma kwana uku kawai xa mu yi mu dawo sbda health status din ki" Heedayah tace "Toh bayan kin sa na kira wnn Shureen din yace baxan je ba din kuma xai xo ya gaya ma Mami kar a bar ni in je" Farida tace "Kai haba, da gaske??" Heedayah ta fashe da kuka tace "Wllh" Farida ta wani tabe baki tace "Toh ba sai ya hana ba mu gani, duk kece kika dage a kirasa xaki laka min kuma daga karshe, gwara ki tashi ki fara hada kayan kafin ma ya xo, Mami ta ma driver magana yace idan mun shirya mu fito" tashi Heedayah tayi tana share idonta ta dauko kayanta kala uku, Farida tayi kasa da murya tace "Make it Five, we are going to deceive Mami, sai ana gobe xa mu koma schl xata ganmu a gidan nan" Heedayah ta wara ido ta karo wasu kayan, Farida ta taya ta shirya kayan a jaka, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta daura dankwalin. Heedayah na gama shiryawa bayan ta fesa turare Farida tace "Ki tafi kice ma Mami thanks for allowing you, ni kuma xan kai mana kayanmu mota" Heedayah ta fita dakin ta shiga na Mami da sallama, Mami na xaune dakin tare da Junaid dake tsaye bakin mirror dinta ya rungume hannunsa, Heedayah ta kallesa tace "Ina kwana Yaya" yace "Lafiya lau" Heedayah ta karasa gun Mami tana murmushi tace "Mami thanks for letting me" Mami tace "Kwana uku kawai xa ku yi" Heedayah tace "Ehh Farida tace min haka" Mami tace "Kin sha drugs din ki? Kuma ki tafi da su kar ki manta" Heedayah tace "Toh" Mami tace "Ki kai cup din nan kitchen" Heedayah ta dau cup din da Mami ta sha tea ta fita, Mami tace "Kaga da ba don aiki ba da sai ka ajiye su, wani lkcn driver din nan na gudu sosai" Junaid dai bai ce komai ba, Heedayah na saukowa stairs aka bude kofar parlon, ido hudu suka yi da Shuraim, ta dauke kai da sauri ta karasa sakkowa ta shigo cikin parlon ta wani hade rai, wucewarta tayi kitchen ta tafi sink da cup din tana murguda baki, kamshin turarensa ta jiyo ta juya da sauri, ya karasa shigowa kitchen din yace "You have the guts ki wuce baki gaisheni ba koh" Ta marairaice tace "Allah sarki ya Shureen ba mun gaisa a waya ba, ai mun gaisa kuma Mami tace inyi sauri shi sa nayi sauri, amma idan na fito ai xan gaisheka dama, kayi hakuri don Allah" kallonta kawai yake yi, can ya juya ya fita, ta wani turo baki hade da murguda masa sannan ta bi bayansa, xaune ta samesa kan kujera, tayi kasa da kai tace "Ina kwana" yyi banxa da ita, wucesa tayi sai da ta isa stairs ta waigosa, hada ido suka yi, ta da'n xaro ido tace "Na gaisheka kuma baka amsa ba, Ina kwana" hade rai yyi yana kallonta tayi wucewarta sama da sauri, kin xuwa ta ce ma Mami yana parlor tayi, Ta shige dakinsu ta fara hawaye tace "Kinga har ya xo yace mata kar a je da ni ko" Farida ta xaro ido tace "Da gaske" Heedayah ta xauna gefen gado tana matsar kwalla tace "I hate him, ni na tsanesa" Zainab me aiki ce ta tafi ta gaya ma Mami tayi bako, Mami tace "Waye?" Zainab tace "Wannan sojan nan" Mami tace "Oh Shuraim, gani nan fitowa to" Zainab ta juya ta wuce, Mami na kallon junaid tace "I still don't like the way u and Shuraim are interacting.... Kamar wasu strangers" Junaid bai ce mata komai ba, tace "Toh ni ka wani xo ka tsaya min a daki kamar Soja idan nayi maka magana kayi shiru kamar kurma, do you have any problem?" Nan ma dai bai ce mata komai ba ya juya ya fita dakin ta bi sa da ido, tabe baki tayi ta mike ta dau handbag dinta da wayarta ta sauka downstairs, tafiyar su Farida take son gani kafin ta wuce aiki dama, bayan sun gaisa da Shuraim tace "Daga gida kake ko gun aiki?" Yace "Daga asibiti nake" tace "Toh yau bari in kawo breakfast din da kaina kila kaci" Farida ce ta sakko da jakar Heedayah, Mami tace "Kuna ta 6ata min lkci" Farida tace "Mun gama" Daga haka tace "Ina kwana" tayi wucewarta, Shuraim yace "Lafiya" Mami tace "Wai Abuja xa su tafi gun third daughter na, suyi 3 days kafin resumption" yace "Ohk ita kadai?" Mami tace "Noo with Heedayah, ai duk da bata jin dadi ba damuwa taje ko?" Shuraim yace "Ki bar su su tafi, ai naga ta ji sauki" Mami tace "Aa da sauki sosai, Ina ga stress din bikin ne kasan bata saba da wahala haka ba, banda haka ana xaune lafiya me xai janyo tayi pass out haka nan" Shuraim bai ce komai ba, Mami tace "Driver nace ya ajiyesu, Junaid xai fita aiki yanxu da shi na so ya kai su" Shuraim ya kalli agogo da ke nuna tara da few minutes, ya d'an yi shiru kafin yace "Ohk should I drop them" Mami tace "Haba Noo, Kai da ka kwana asibiti kana aiki, bari a lallaba kawai driver din ya kai su" Shuraim yace "Xan kai su..." Da damuwa Mami tace "To aikin fa anjima, kaga xaka ba kanka wahala sosai" Yace "Aa ba wahala" Shiru Mami tayi tana kallonsa. Ko da Farida ta koma sama waya ta tadda Heedayah ke yi, Heedayah tayi shiru ganinta, daga daya bangaren Khaleel yace "Wa xai kai ku Abujan?" Heedayah tace "Uhm" shiru yyi kafin yace "Ohk, but you can leave where you are and talk to me" Farida ta dau handbags dinsu ta fita, Heedayah ta bi ta da kallon gefen ido, a hankali tace "Driver xai kai mu" yace "Yanxu xa ku fito?" Heedayah tace "Ehh mun ma kai kayanmu cikin mota" Yace "But can't you convince them that ku bari ko nan da xuwa 12 ku taso?" Da mamaki tace "Saboda me?" Ya mike daga xaunen da yake a katon parlonsu yace "Convince them plss Heedayah, hanyar nan bbu kyau ynxu" Tayi shiru sai kuma tace "How did you know that?" Yace "Stop questioning me, just kar ku fito yanxu" Ta hade rai tace "Bayan mun riga mun gama shiryawa kuma mun kai kaya mota, idan naje nace ma Mami hanya bbu kyau ai tambayata xata yi me ya faru da hanyar kuma wa ya gaya min, wa xan ce ya gaya min??" Shiru yyi yana sauraronta, ta turo baki tace "Ni dai ana jirana a parlor byeee" yace "Wait Heedayah...." Tsayawa yyi tana sauraronsa, yace "Don't you no that kidnappers suna hanyar Abuja" da mamaki tace "To ai ba kullum suke fitowa ba...." Yace "Noo yau xa su fito" ta xaro ido tace "Ta ya kayi ka sani?" Yace "Na sani, bana son wani abu ya sameki kuma" tace "To me ya sa xa su fito yau din?" Yace "Akwai wani da suke targeting, yau xai bi hanyar.... So if they should meet people on road suna harbi ta ko ina ne" Heedayah ta bude baki lkci daya jikinta ya hau rawa tace "Su harbe mu??" Yace "Aa bance xa su harbe ku ba, but prevention is better than cure right?" Tace "Toh kai ya aka yi kasan they are targeting someone when you are not a kidnapper?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Plan dinsu yyi leak ne" Bude kofar dakin aka yi Farida tace "Idan xa ki ajiye wayar nan ki ajiye ki fito mu wuce, ko wani karya yake tsara maki tun daxu haka" tsaki Farida tayi ta fita, Heedayah tace "Ni dai bye ana jirana" Daga haka ta katse wayar, sai dai banda faduwa bbu abinda gabanta yake tana naxarin maganan da yyi mata, then how did he know about kidnappers, ta bi dakin da kallo taga Farida ta sauka downstairs da handbag dinta balle ta saka wayar a ciki, wani karamin purse ta fito da ta saka wayar ciki snn ta dau mayafinta ta yafa, ta boye purse din a cikin mayafin ta fita dakin, corridor ta tadda Junaid a tsaye, ta sakar masa murmushi tace "Yaya xan yi missing dinka" a hankali yace "Are you sure" ta gyada masa kai, bude mata hannu yyi, ta bi corridor din da kallo kafin ta karasa ta basa light hug lkci daya kuma ta janye jikinta amma ta kasa kallonsa ta juya da sauri tace "Byee" har ta fara tafiya yace "Heedayah" tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa bayanta ya kamo hannunta ya sa mata kudi yace "In case you will want to buy chocolates" juyowa tayi tana murmushi tace "I appreciate, thank you so much" yace "You are welcome" daga haka ta sauka downstairs, Farida ta gani bakin kofa tsaye sai cika take, Mami kuma tayi forcing Shuraim yau dai yana shan just tea a gidanta, Heedayah na ganinsa ta daure fuska tace "Mami mun gama fa" Mami tace "Ku jira sa a compound" Heedayah ta karasa gun Farida suka fita compound din tare, Farida tace "Ke ki ji wai Shuraim ne xai kai mu Abujan" Still Heedayah tayi tana kallon Farida ko kiftawa babu, Can ta juya ta kalli motar Shuraim, sai kuma ta 6ata fuska ta fara matsar kwalla tace "What about the driver?" Farida tace "Oho Mami har tace ya wuce kawai" Heedayah tace "How are we going to cope travelling with him?" Farida ta sauke ajiyar xuciya bata ce komai ba, Heedayah tace "Did he even know the way to Abuja?" Nan ma dai Farida bata ce komai ba, Heedayah ta jingina da mota ta turo baki tace "I just feel like giving up, who brought this idea" Farida tace "Ni ki daina min tambayoyi kamar yar jarida, I don't know too" suna ta tsaye Farida ta jawo Heedayah tana perceiving jikinta tace "Ina kika samu turaren Yaya?" Heedayah ta xaro ido amma ta kasa cewa komai, Farida ta kara shinshina mayafinta tace "Wa ya baki turaren" Heedayah tace "Shine ya sa min wai ban sa turare ba" Farida tace "Lallai ko Mami baya ba turarensa, kinsan nawa ake sayar da turaren?" Fitowar Shuraim tare da Mami yasa duk suka yi shiru, Mami tace "Hope xaka kira Barrister ka sanar masa ko?" Shuraim yace "Xan kirasa" Mami tace "Ba don kar ku bata lkci ba kuma ai ya kamata su je can gidan suyi ma kaka sallama kasan halinta sai tace an walakanta ta ba a gaya mata ba" Shuraim yace "Aa ba sai an gaya mata ba, xan kira Abba in gaya masa" Mami tace "Toh shkkn, Allah ya kiyaye hanya, ya tsare ku da tsarewarsa, but plss drive carefully Shuraim" Yace "In sha Allah" Mami tace "toh jira ku ke a ce maku ku shiga motar ne" Farida ta bude back seat ta shiga, Heedayah ma ta shiga, Mami ta daga masu hannu tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, ya kai ku lafiya my daughters" Duk suma suka daga mata hannu, Shuraim yyi mata sallama tace "Don't forget to call barrister plss" yace "In sha Allah," tace "But wait kana da fuel ko kawai ka tafi da motar nan" ta fadi tana nuna masa spare motar dake gidan tace "Daxu aka tafi fueling station aka yi full tank" yace "No nima full tank ne" daga haka ya tada motar suka bar compound din, Mami ta bi sa da kallo har ta daina ganinsu sannan ta koma ciki. Kafin Shuraim ya karasa titi ya kira Abba, bayan Abba ya daga yace "Abba xan je Abuja, amma yau xan dawo" Daga daya bangaren Abba yace "Me xaka je yi a Abuja, Anyway Allah ya tsare ka, safe trip" yace "In sha Allah, nagode" daga haka ya katse wayar, Mumy ya kira, tana dagawa bayan ya gaisheta yace "Mumy I will be going to Abuja now but anjima da yamma xan dawo" Mumy ta mike xaune daga kwancen da take tace "Me kuma xaka je yi a Abuja Aliyu, hanyar nan da ya xama abinda ya xama yan kidnapping sun yi yawa" Yace "Allah xai tsare" Tace "Ni dai duk sai naji hankalina bai kwanta da tafiyar ba, dama nayi mugun mafarki da asuba, aiki ne xai kai ka Abujan ko me?" Yace "Ehh" Tayi shiru, sai kuma tace "Dole sai kai?" Yyi murmushi yace "Ehh, ai yau xan dawo" tace "Toh ni dai don girman Allah har ka isa addu'a ya makale a bakin ka, wllh hanyar bashi da kyau kwata kwata Aliyu dama jirgin kasa ne bbu abinda xai daga min hankali, amma yau kaji an dauke wannan gobe kaji an dauke wancan ai da tashin hankali" Yyi kasa da murya yace "Ina tunanin xuciyar ki a tsarkake yake, kuma baki nufin d'an kowa da sharri, don haka ki kwantar da hankalin ki, in dai haka ne bbu abinda xai samu xuri'ar ki" Mumy da ta wani xaro ido tace "Uban me ya shigo da wnn xancen kuma, shi dama tsarkakken xuciya a goshi ake rubutawa, Ina ruwana da d'an wani da xan nufesa da sharri ni kuwa...." Yace "Aa misali na maki kawai..." Ta ja tsaki tace "Ni dai Allah ubangiji ya tsare min kai, ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, ya raba ka da sharrin mutum ko karfe, har ka karasa addu'a kada ya bace a bakinka" Yace "In sha Allah" daga haka ta katse wayar, ya ajiye yana d'an murmushi. Tun da suka fara fita cikin gari, Heedayah ke jin vibration din wayarta a jaka, Farida dake kusa da ita ma tana ji, Heedayah ta kalli Farida, Farida ta kalli Shuraim ta madubi idonsa na kan titi, Heedayah ta kai bakinta kunnen Farida murya can kasa tace "He has been calling tun daxu, I don't know why, how should I pick" Farida ta kara kallon Shuraim snn ta fiddo nata wayar a jaka ta mika ma Farida a hankali tace "Ki sa number a nan sai kiyi masa text message...." Da sauri Heedayah ta bude zip din purse din ta rufe da gyalenta snn ta haddace number don har snn wayar na vibrate ta mayar jakar ta kulle sannan ta sa number a wayar Farida ta tura masa message kamar haka "Muna hanya, I can't pick now" tana tura message din ta daga kai suka yi ido hudu da Shuraim da ya kallota, ya maida dubansa kan titi, a hankali cikin dubara ta koma gefe yanda ko ya kalli madubi baxai ganta ba sai dai Farida, ba a dau lkci ba Khaleel yyi mata reply yace "Kuna dai dai ina yanxu?" Heedayah ta kalli Farida, sai kuma ta jawota tana nuna mata text din, Farida ta bude hannu alamar bata sani ba, Shuraim yyi breaking silence din motar yace "Give me that phone u are holding" Heedayah ta xaro ido ta kalli Farida, Farida tace "Which phone, wayana ne fa" Yace "Ba da ke nake ba malama" Heedayah kamar xata yi kuka tace "Game fa nake yi" yace "Don't let me repeat my self" Farida ta saka wayar flight mode snn to koma can gefe, Heedayah ta turo baki ta mika masa wayar, fixgewa yyi daga hannunta ya ajiye kusa da nasa wayar. Bayan tafiyar kusan minti arba'in tun fitowarsu gida, Heedayah ta kalli Farida, rufe taga idonta har ta fara bacci, a hankali tace "Ya Shureen amai nake ji" ya wani hade rai yace "Amai??" Sai kiyi a nan ai, waye xai tsaya kiyi amai" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani minti sha biyar din ta marairaice da kyar tace "Wllh yana damuna sosai, ka tsaya plss xai taho" banxa yyi mata, ta rufe bakinta tana kakarin amai, a hankali ya fara slow down ya gangara gefen hanya yyi parking snn ya bude motar ya sakko ya bude side dinta, da sauri ta fito, ta xagayo ta duka gefen daji tayi ta kakalo aman amma ya ki xuwa, rungume hannu yyi yana kallonta, bayan few minutes ta dago da kyar tace "Kamar ya koma" ya wani hade rai yana kallonta, mikewa tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Dama kika sake sa na tsayar da mota kika sauka sai dai ki samu wani da xai mayar da ke gida, that is idan har na tsaya ma kenan" ita dai bata ce masa komai ba, ya bude ta wajen da take xaune, ta shiga motar ya kulle sannan ya koma driver seat suka ci gaba da tafiya. Khaleel ne tsaye da 5 of colleagues dinsa, message ya shigo wayarsa, dubawa yyi ya ga daya daga excort din Mai neman takaran gwamna ne da suke targeting yau, ya bude text din mutumin ya ga kamar haka "Mun kamo hanya minti kusan hamsin kenan" Khaleel yyi masa reply "Ohk" sai kuma ya xauna ya xauna yana shafa kansa, Saif na kallonsa yace "Ya dai Brainiac??" Banxa Khaleel yyi masa. Heedayah dai sai mutsu mutsu take a mota, Shuraim kuma lkci lkci yake kallonta, daga karshe tace "Ya Shureen" banxa yyi mata, cikin rawar murya tace "Wllh amai xan yi yanxu, pls kayi hakuri ka tsaya" yace "Yi a wajen" ta fashe masa da kuka tace "Plss xai xubo" ya daka mata tsawa yace "Wai ance maki ana tsayawa a hanyar nan ne" cikin kuka tace "Toh Amai xan yi mana" yace "Kiyi a wajen" tace "Wayyo baxan iya ba" Farida dai sai baccinta take kamar warce ke saman gado, kuka Heedayah ta dinga yi a hankali, Shuraim sai duba inda xai iya tsayawa yake, cos he knows how risky the road can be, daga karshe dai ya gangara gefen titi ya tsaya, ya bude motar ya sakko snn ya xagayo ya bude mata tun kafin ta gama fitowa ta fara kwarara amai a wajen, ya ja baya yana yatsine fuska yana kallonta, ta duka wajen ta dinga kwarara amai, bude front seat yyi ya dau ragowar bottle water dake wajen, ya cire mata mayafin jikinta ya duka ya bata ruwan, ta fashe da kuka tace "Yaya har yanxu bamu kai ba, ni baxan iya tafiyan ba kuma gwara in koma gida na gaji" ya daure fuska yace "C'mon amsa ki wanke fuskar ki" kin amsan ruwan tayi, ya xuba ruwan a hannunsa ya dago kanta ya wanke mata fuskar, bayan ya gama ya dagata suka mike ya bude motar yace "Shiga" ta shiga motar ya mika mata mayafinta snn ya kulle ya koma driver seat, ta jingina da kujeran motar tana sauke numfashi. Khaleel yace "Oga na san abinda nake cewa, na kuma san abinda na gani, beside dole in a week time Mutumin nan xai koma Kano, we should let it till then" Oga Manga yace "Wani maganan bnxa kake haka Khaleel, bbu fa wasu excort din kirki tare da shi, daga motarsa sai na bayansa, shkkn... Komai ya xo cikin sauki knn, this is just the right time da ya kamata ayi duk abinda xa ayi, snn mun samu labarin babu wasu jami'an tsoro a hanya, Khaleel I am saying ku san duk ynda xa ku yi mutumin nn ya shigo hannun mu yau yau din nan, bbu wani excuse dinka da xai shige ni wllh, nan da wani lkci xa su isa kauyen nan da muka shirya, kuyi maxa ku fito kawai, you guys just have to hurry up...." Khaleel dake ta sauraronsa yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, Zayyad yace "Wai yane Kayy, kwanan nn fa you are not just active, anya mace bata shigo rayuwar ka ba?? Kar fa irin abinda ya faru da Ishaq ya faru da kai, kana dai nan kuma duk muna kallo Arne ya harbesa...." Khaleel ya wani tabe baki yace "Ni ayi gunduwa gunduwa da ni" Da mamaki Zayyad yace "Kana nufin tambayar da nayi maka da gaske ne?" Khaleel yace "Wnn ba matsalar ka bace, all I want u all to understand here is that in dai har kuka fita yau din nan.... don ni dama bbu inda xanje and nobody can force me out, to ina me tabbatar maku da kyar xa ku sha, kuma sai an kama wasun ku, mu hadu a garin Abuja" daga haka ya fice duk aka bi sa da kallon mamaki suna ji ya fita da motarsa... Shuraim ya hade rai yana kallonta ta mirror yace "Meye hakan??" Da kyar tace "My head is turning me" yace "Turn it back" bata ce masa komai ba ta goge hawayen da ya makale mata ta jingina da motar, suna isa wani junction, yana kallonta ta madubi yace "Xa ki ci Ayaba" ta bi wajen da kallo taga masu ayaba, ta girgixa masa kai tace "Amai xan yi idan na ci" yayi parking ya sauka, ya siyo mata apples, Farida sai lkcn ta farka tace "Why are we not moving?" Heedayah ta langwabar da kai tace "Xai siya min wani abu" Farida tace "Daxu ba naga kina amai ba" Heedayah tace "Amma baki ce komai ba ko" Farida tace "Toh ba gashi har fuska ya wanke maki ba, ni kawai sae na ci gaba da bacci na" Tana fadin haka ta kara gyara Kwanciyarta, Shuraim ya dawo motar rike da ledan apples, with bottle water guda biyu, back seat ya bude ya ajiye xae rufe tace "Ya Shureen xan koma gaba" Bai ce mata komai ba ta sauko rike da abinda ya siya mata, ya rufe motar ya mika mata ledan ta amsa ta koma front seat, shi kuma ya shiga driver seat suka ci gaba da tafiya.... Sai karfe daya suka shigo garin Abuja bbu wani tashin hankali, Heedayah ta juya ta tada Farida, Shuraim ya hade rai yana kallonta yace "Ance maki dakin ki ne nan" Farida bata ko kallesa ba ta gyara mayafinta, yace "Wani anguwar xa mu" Farida ta fada masa, har suka iso gidan yayarta kuma bata sake bacci ba, da ganin anguwar dai kasan na manya ne sosai, driver ya bude masa gate ya shiga yyi parking, farida ta bude motar ta sauka, Heedayah ma ta sauka, Maman Fadil ta fito da mai aikinta da murna tana welcoming dinsu, gaisawa suka yi da Shuraim tace "Bismillah, ka shigo ciki" yace "Aa xan juya ne" tace "Haba don Allah" yace "In sha Allah" Heedayah tayi wucewarta ciki tare da Farida ya bi ta da kallo, can yyi ma Maman Fadil sallama yyi reverse. *Gwara ku yi ta cancanasa, let me not hear pim from now till next tomorrow ehe* Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... House maid din Maman Fadil suka bari da shigo masu da kaya, Heedayah ta xauna babban parlon da ya kayatu da kayan alatu, Farida tace "Ta so mu wuce ciki" Heedayah tace "Ae ba mu gaisheta ba" Farida tace "Wlh I am so tired xata biyo mu daki" Ita dai Heedayah bata tashi ba, Farida tace "To sae ki sameni daki ni dai" daga haka ta wuce, lkci daya ta juyo tace "Innalillahi, baki amsar min wayata gun Shuraim ba" Heedayah ta bude ido tace "Lah, kuma gashi ya wuce" Farida ta hade rai tace "Why are you talking as if it's normal, wayana ne fa da nake amfani da shi, kuma duk xaman da kika yi gaban motar xa ki ce baki kallon wayar??" Heedayah bata ce mata komai ba sae tabe baki da tayi, Farida ta ja tsaki ta dawo cikin parlon ta dau wayar yayarta ta nufi kofar fita, a bakin kofa suka hadu, Farida tace "Aunty don Allah ki bude min, I want to make phone call, Shuraim ya tafi da wayata" Maman Fadil tace "Ohh shi ne Shuraim din dama?" K'in cewa komai Farida ta yi, yayar ta amshi wayar ta bude mata lock, Farida ta karba ta juya ta koma gun Heedayah tace "Tunda har kin haddace number sa sae ki sa min ni dai" Heedayah tace "Toh da na haddace number akwai abinda nace xanyi da shi ne, ko amfanin me xai min" Farida tace "Oho" Heedayah ta tabe baki ta amshi wayar ta saka number Shuraim ta mayar mata, Farida tayi dialing, sae da ya kusa katsewa ya daga, tace "Ni fa amfani nake yi da wayata kuma ka tafi da shi" yace "So??" Tace "Ka dawo in amshi wayata kawai" Yace "I see, idan na baki wayar a kaduna kar ki amsa" daga haka ya katse wayarsa, Farida ta kalli screen din da sauri, Maman Fadil tace "Me yace maki" Kamar xata yi kuka tace "Maganan banxa fa yyi min" Da mamaki Maman Fadil tace "Maganan banxa kuma" Farida tace "Ehh mana ai haka yake, ni dai Aunty ki yi masa magana don Allah ya maido min da wayata tun bai yi nisa ba, ni wllh baxan iya xama gidan nan bbu wayata ba" Maman Fadil tace "To ke garin yaya wayar ki ya je hannunsa" Farida tace "Ba ga warce ke amfani da shi ba ya amshe" Maman Fadil tace "Toh don tana amfani da waya sai ya karba, an hanata rike waya ne?" Farida tace "Ina fa, shi dai ne ya hanata rikewa" Maman Fadil ta amshi wayar ta sake dialing numbersa ta kai kunne, yana dagawa tace "Haba Yaya Shuraim ayi hakuri da su pls, ynxu dai kana ina sai in tura driver ku hadu ya amso wayar kawai" shiru tayi tana sauraronsa sannan tace "Toh shkkn, ba damuwa, nagode" Daga haka ta katse wayar, Farida ta wani xumburo baki tace "Me ya ce" Maman Fadil tace "Yace bai ma tafi ba tukun, idan bai dawo ba xai kirani in turo driver din ya amsa wayar" Farida ta wani tabe baki tayi wucewarta daki, Maman Fadil na kallon Heedayah tace "Deedayar kaka an xama 'yan mata, ya gajiyan hanya?" Heedayah tayi murmushi tace "Alhmdllh" sannan ta gaisheta, Maman Fadil ta amsa tace "Ya su Mami da Yaya" Heedayah tace "Duk suna gaisheku" Maman Fadil tace "Toh muna amsawa, ki shiga ciki kiyi wanka kiyi sllh, sai ku sakko ku ci abinci" Heedayah ta mike tace "To, ina Fadil?" Maman Fadil tace "Yana can neighbors dinmu" Heedayah tace "Ohk" snn ta wuce ciki ita ma. Heedayah na kwance dakin Farida ta fito daga wanka ta shirya ta dau darduma xata yi sllh, Heedayah ta mike xaune tace "You are taking it personal as if ni nace Ya Shureen ya amshi wayar ki" Farida bata tanka ta ba ta fara sallarta, Heedayah ta tabe baki ta mike tsaye ta cire kayanta snn ta wuce bandaki, tana fitowa wanka taga Farida ta fita dakin, ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi snn ta saka hijab dinta ta shimfida darduma ta fara sllh. Bayan ta idar ta mike ta dau purse dinta ta bude ta ciro waya, miss calls din Khaleel ta gani da yawa, tayi dialing number, yana fara ring ya daga, tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, kun isa Abujan ko?" Tace "Ehh mun kai" yace "Ya hanya" tace "Lafiya lau kuma bbu abinda muka gani a hanyar, ba wasu kidnappers din da kace" D'an murmushi yyi yace "Da gaske?" Tace "To kai so kayi ayi kidnapping din mu dama?" Ya girgixa mata kai yace "Idan aka yi kidnapping din ki ai ni aka yi kidnapping" Tace "Ban gane ba" Yace "Tun da dai you arrived safely shkkn" Ta tabe baki bata ce komai ba, yace "Ke da wa ma ku ka tafi Abujan??" Tace "Ni da Farida, da Ya Shureen, shi ya kawo mu" yace "Waye shi?" Tace "Ba na ta6a gaya maka ba, yaron Abbana ne, yayanmu ne" Ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Ohk soldier din nan?" Tace "Ehh" yana gyada kai a hankali yace "I see... shi ma a Abujan xai kwana yau kenan?" Tace "Aa yana da night duty, he is going back to Kaduna" yace "When?" Tace "Yau din nan" yace "Nasan yau din nan , karfe nawa nufina xai tafi" tayi shiru snn tace "Nima ban sani ba" yace "Are you still together with him now?" Tace "Yess" yace "If he is going ki gaya min, Kar ki manta...." tace "Saboda me xan gaya maka??" yace "Nothing, bana son in kira ki yana nan ya gani, so idan kika ce min ya tafi i can call anytime" ita dai bata ce komai ba, yace "Heedayah" tace "Ina ji" yace "Me yasa kika yi shiru" tace "Aa ba komai" yace "Ohk, gidan wa ku ka je a Abuja" tace "Gidan yayar mu" yace "Toh ki bani address din wajen" tace "Sbda me?" Yyi kasa da murya yace "Baki son ganina kenan!" Ta turo baki tace "Toh ni fa I still don't know why we are together, Ina ce parent dina xaka nemo min kace??" Murmushi yyi yace "Su xan nemo maki in sha Allah" Tace "You are not making effort, kawai dai kai kana son mu dinga haduwa ne" yace "Noo Heedayah, tunda ba tare muke dake ba ai you won't see my effort, you are only desperate to meet with ur parent shi yasa kike ga I am not making effort, but trust me dear tunda nace xa ki ga iyayen ki, xa ki gansu" ta d'an yi shiru kafin tace "Ohkk" yace "Good gal, send the address via Sms now" tace "Toh" katse wayar tayi, ta mike ta fita daga dakin, Farida na parlor tare da yayarta sai Fadil da wata yarinya da baxata wuce shekara uku ba suna wasa da Fadil dake xaga parlon a kekensa tana biye da shi da katon doll dinta, Maman Fadil na duban Heedayah tace "Kinyi sllhn?" Heedayah tace "Ehh na yi" Maman Fadil tace "Toh ga abinci an kai maku dining area, na samu labarin baki cin tuwo ko..." Heedayah tayi murmushi ta sunkuyar da kanta bata bata amsa ba, ganin ta nufi kofa Maman Fadil tace "Ina kuma xa ki?" Heedayah tace "Ina xuwa" Bin ta suka yi da kallo da Farida har ta fita, Can gun mai gadi ta nufa tana kallonsa ya mike ya bude mata gate din gidan, fita tayi ta duba address dake manne daga gefen gate, ta bi anguwar dake dauke da manyan gidajen gaske da kallo, lafiyayyen titi ne malale anguwar, ko wani gida da flowers xagaye da shi masu kyau, tsayawa kallon katon gidan dake kusa da na su Maman Fadil tayi, don gidan har ya fi nasu girma da haduwa, taji muryar Farida a bayanta tace "What are looking for outside Heedayah?" Heedayah ta juyo da sauri tace "Nothing" Farida ta rungume hannunta tace "Hope you are not trying to give anyone address to this house?" Heedayah ta bi ta gefenta ta wuce ciki tace "Not at all pls" daga haka ta nufi entrance din gidan Farida ta bi ta da kallo. Heedayah bata wani ci abincin kirki ba ta wuce sama xuwa dakin da suka sauka ta dau wayarta ta tura ma Khaleel text din address din gidan snn ta kwanta ta rufe ido kamar me bacci tana nan a haka har aka yi la'asar snn ta mike ta shiga bandaki tayi alwala ta fito, da sauri ta dau wayarta kafin ya katse, tace "Have u seen it?" Daga daya bangaren yace "Sure, Ina ta jira baki gaya min ko Yayan naku ya bar Abuja ba" Heedayah tace "He is not leaving today" yace "Why?" Tace "Haka nan kawai, may be tare xa mu koma" Jin Khaleel yyi shiru tace "Xan yi sllh, sai anjima" katse wayar tayi ta mayar cikin purse dinta, bayan ta idar da sllh ta sauka parlor, bbu kowa parlon sai su Fadil, ta karasa gun su da sauri ganin fada suke, ta riko Fadil tace "Me tayi maka Fadil? What happened??" Muryar Mum dinsa taji daga sama tana cewa "You've started fighting her ko, to gobe in ji kace a kai ka wajenta, baka da kirki wllh" kamar xai yi kuka yace "Mumy she is pushing my bicycle, why will she? did i push her fat doll??" Heedayah dai na rike da hannun yar yarinyar dake ta kallon Fadil hawaye makale idonta, ta dau hularta da ya fadi kasa ta rufe mata dogon gashinta da shi tana bata hakuri, yarinyar na nuna sa cikin rawar murya tace "You are not my frnd any longer" Maman Fadil ta sakko ta karbe hannunta daga na Heedayah tace "Yi hakuri kin ji Islam, don't cry" Farida ta shigo parlon tace "Aunty yarinyar waye wai, ban ta6a ganinta ba, yar me kyau da ita" Maman Fadil tace "Yarinyar makociyata ce, shi ke makale mata fa, amma idan ta shigo yyi ta mata walakanci, bini bini kya ji yace xai tafi gun islam" tuni Fadil ya wuce sama kamar Soja a dole yyi fushi, Maman Fadil tace "Heedayah ku kai ta gida da farida yanxu tana fara kuka bbu me iya lallashinta a nan" Heedayah tace "Wani gidan ne nasu?" Maman Fadil tace "Ku tambayi Mai gadi idan kun fita" Heedayah ta dau doll dinta ta mika mata yarinyar ta amsa sannan suka fita tare da Farida don kai ta gidansu, kiris din ya rage Islam ta fara kuka, bin su kawai take tana makale da doll dinta, suna fita gate Mai gadi ya nuna masu gidan nasu, suka kwankwasa gate Mai gadin gidan ganin tare suke da Islam ya bude masu yana kallon Heedayah suka shiga cikin gidan, shi ya nuna masu inda xa su bi, babban gida ne na gaske me dauke da duplex biyu, motoci ne a duk parking space uku dake compound din da ya kawatu da flowers ta ko wani angle, suka danna bell bayan few minutes aka bude kofar, gaisheta suka yi, ta amsa tana masu sannu da xuwa sannan ta amshi hannun Islam tace "Tana daya bangaren mamanta, Bismillah ku shigo yanxu xata fito" Farida tace "Aa, muna dai gaisheta, sai anjima" daga haka suka juya suka nufi gate suka bar gidan. Heedayah na xaune saman darduma ta idar da magrib jin wayarta na vibrate ta kalli Farida dake sllh, mikewa tayi ta bude purse din ta ciro wayar snn ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Ina waje" ta xaro ido ta d'an kalli Farida, sai kuma tace "Ohk" katse wayar tayi ta ajiye, haka nan kawai taji kamar an cire mata tsoro a ranta, taji she is not even afraid of anyone, taji kuma she wants to meet with Khaleel, tana ta xaune dai har Farida ta idar da sllh ta mike ta fita dakin, sannan ita ma ta mike tana rike da gyalenta da ta linke ta sauka parlor, tsaye ta same farida inda take shiga ba nan take fita ba, yayarta dai na xaune tana feeding din Fadil tana kallonta, cike da fada tace "Kuma wllh idan ya koma da wayata baxan sake amsar wayar ba ko an bani, dubi fa yanda na wani xauna tun rana kamar marainiya ba waya, nasan kuma ana ta kirana, ba sai ya bari driver yaje ya amso min kayana ba dama idan ba niyyar tafiya yyi da shi ba" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Maman Fadil tace "Toh bari a kara kiransa amma Ina jin bai tafi bane da xai tafi ai xai kira yace in turo driver haka muka yi da shi" Farida tace "Lallai baki san waye shi bane Aunty wllh da gangan ma sai ya iya tafiya da wayar don in ji haushi, ai kinga ita da ta janyo ya amshe wayar har yanxu bata ce min komai ba as if fault dina ne, kuma har komawa tayi gaban motar fa ban san me ya kai ta can ba ta xauna, kuma sai tace bata ga wayar ba a kusa da ita???" Heedayah dai ko kallonta bata sake yi ba tayi hanyar kitchen, Mai aiki ce ta fito kitchen din ta gama wanke wanke, Farida ta bi Heedayah da wani shegen kallo har ta shige kitchen din, Maman Fadil tayi kasa da murya tace "Ni gaskiya bana son haka Farida, xata ga kamar don ta biyo ki ne kike mata haka, tun rana sai masifa kike mata gashi ta ki kulaki, bata ce maki komai sai masifa kike, wnn bai yi ba dai" Farida tace "Wa?? Kin xata wai ta rasa abinda xata ce ne yasa tayi shiru, ai ko xan kwana ina yi baxata tanka ba kuma baxata bani hakuri ba, taurin kai ne da ita da kike ganinta haka, wllh nasan kila da gangan ta bar masa wayar dama naga sai wani shisshige masa take" Maman Fadil tace "Shisshige masa ta ya kuma?" Farida ta xauna fuska daure tace "Ohon masu" Murmushi kawai Maman Fadin tayi ta dau wayarta tace "Bari dai in sake kiransa" dialing Number Shuraim tayi ba a dau time yana ring ba ya daga, gaisawa suka yi tace "sai muka ji shiru Yaya Shuraim..." Ta gama sauraronsa snn tace "Toh shkkn ba matsala, Allah ya tsare" katse wayar tayi ta ajiye, Farida ta xumburo baki tace "Wai me yace??" Maman Fadil tace "Jarabbiya to yana hanya xai kawo maki ynxu" da mamaki Farida tace "Toh me yasa bai koma ba??" Maman Fadil tace "Kilan ya gaji ne, kamar ma bacci yake, Amma yace xai taho ya kawo ynxu" Farida ta tabe baki bata dai ce komai ba. A hankali Heedayah ta bude kofar dake kitchen da xai sada ka da bayan gidan ta fita snn ta jawo kofar very careful kar yyi making ko wani sound snn ta yafa veil dinta ta fara tafiya da sauri, ta jikin parking space ta raba har ta isa gate, ganinta mai gadi ya fito dakinsa da sauri yace "Fita xa ki yi Hajiya?" Ta gyada masa kai, ya bude mata gate din ta fita, tana fita ta juya ta kallesa don tsayawa yyi ya ki komawa ciki as if wanting to know where she is going, ta hade rai, sau daya ta kalli motar da ya tsaya shi daya a layin da hasken fitilu ya haska kamar ba dare ba, ta san Khaleel ne duk da ba motar da ta saba ganinsa da shi bane don wnn har ya fi wancan haduwa amma bata tsaya ba tafiyarta kawai take, can ta ji Mai gadi ya kulle gate din ta juya taga ya koma ciki, A hankali Khaleel ke tafiya har ya tsaya dai dai flowers din gidan da suka kai islam daxu amma ta opposite, Heedayah ta sake juyawa tana kallon gate din gidan da ta fito snn ta nufi motar, sauke tinted glass dinsa yyi ta xagaya ta bude front seat ta shiga ta rufe. Khaleel na kallonta murya can kasa yace "Hope u took permission before coming out?" Ta girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace "Why?" Ta turo baki bata ce komai ba, yace "Heedayah" daga manyan idanuwanta tayi ta kallesa tace "Don a min fada?" Yace "Toh ai ba a gida kike ba, kuma yawanci xa ki ga aunties usual don't have much problem, da yawa idan mace na son haduwa da saurayinta kuma ba a barin ta fita a gida, ta kan hada baki da yayarta ko aunt dinta sai ta xo gidan aunt din nata su hadu, kuma bbu wanda xai sani sai daga ita sai aunt din, so wnn ma da kin gaya mata baxata hanaki ba" Heedayah ta wani kallesa tace "To kai saurayina ne?" Shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya girgixa mata kai yace "Aa" ta dauke kanta, yace "Amma duk da haka da kin gaya mata, ko da yake naga kin fiye tsoro ke din" Tace "Not when Farida is there xan gaya mata, Beside it's not as if mun saba sosai da ita, na fi sabawa da kanwarta Aunty Fatee" yace "Ohk wnn baki santa ba?" Tace "Aa na santa, tana xuwa once in many month tayi two days" yace "Ohk how about her husband?" Tace "Yana UK shi" Khaleel ya gyada kai bai ce komai ba, ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa, Zayyad ne ke kiransa ya mayar da wayar ya ajiye har ya katse, tun yana hanya Zayyad ke kiran nasa yaki dauka, ya kalli Heedayah yace "Hope kin ci abinci?" Ta nuna masa wayarsa da aka sake kira tace "Pick ur call" Ba musu ya daga ya kai kunne bayan ya rage call volume din, Daga daya bangaren Zayyad yace "You caused everything Khaleel, you just ruin everything, da ka bi mu wllh wllh duk wannan abinda ya faru baxai faru ba, and mind you Oga Manga na neman ka yanxu haka, just don't show up anytime soon..." Calmly Khaleel yace "Me ya faru?" Zayyad yace "Abinda ya faru shine an harbe Saif and he is dead, mu hudu muka fita dama, kuma we weren't early enough don har target dinmu sun wuce exact village din that's conducive for the operation, and u caused everything, so muna dai tafiya not knowing an kafa wani check point a gaba sbda robbery da aka yi a wajen da asuba har an kashe wasu, da mun san da check point din da baxa muyi attacking dinsu ba a particular area din da muka yi attacking dinsu, everything wasn't in our favor today, mun sha ne da kyar... It wasn't funny Khaleel, kuma duk kai ne ka ja komai, Oga Manga na nemanka yanxu haka" Khaleel da yyi shiru yana sauraronsa yace "Tough day indeed" daga haka ya katse wayar ya sa flight mode ya ajiye, Wani mota ne ya shigo layin ya haskosu, da sauri Heedayah ta dukar da kanta, Khaleel ya dage glass din motarsa yana bin motar da ido, dai dai gidan dake opposite dinsu motar ya tsaya Mai gadi ya wangale gate, a hankali Heedayah ta dago kanta motar ya shiga gidan aka rufe gate din, kallonta Khaleel yyi yace "Kin taba xuwa layin ne da kike boye fuskarki?" Ta girgixa masa kai, xai yi magana wani motar ya kuma shigowa layin, Heedayah ta xaro ido sosai tace "Yaya Shureen" rufe fuskarta tayi da gyalen jikinta, Khaleel ya dinga kallon motar har ya iso inda motarsa ke tsaye, Heedayah ta dago kai ita ma a hankali ta bi motar da kallo, dai dai gate din gidan Maman Fadil yyi parking, Heedayah na kallon Khaleel kamar xata yi kuka tace "Did he see me?" Girgixa mata kai yyi yace "Tinted glass ne ai" Ta juya ta sake kallon motar Shuraim ta ga ya sakko daga motar sai da ya fara kallon motar Khaleel snn ya tafi ya kwankwasa gate din gidan, Heedayah ta marairaice tace "Kila ya gan ni fa" Khaleel yace "How? is he having tinted eyes?" Tace "Ni dai mu je gaba to" driving din motar yyi yana tafiya a hankali har ya bar layin gaba daya. Kallonta yyi yace "Ina xa mu je" tayi shiru gabanta na faduwa, sai kuma ta ji kamar an cire mata tsoron gaba daya, ta jinginar da kanta da kujeran motar a hankali tace "Anywhere" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Shuraim na shiga gate din gidan ya hadu da Farida xata fita ita kuma, komawa baya tayi ganinsa, ya mika mata wayarta, ta amsa kamar dai baxata ce komai ba sai kuma tace "Thanks" juyawa yyi xai fita, har xata yi magana sae kuma tayi shiru sai da taga ya fita gate din sannan ta leka waje, da ido ta hau surveying din street din, mamaki ne ya cikata ganin bata wani ga alamar Heedayah ba, to ina ta tafi, suka hada ido da Shuraim da ya bude motarsa ya shiga, ta dauke kai ta shigo cikin gidan tana kallon Mai gadi tace "Don Allah warce muka xo gidan nan daxu tare ta fita ne?" Mai gadin yace "Ehh ta fita" Farida ta fita gate din gaba daya tana sake bin layin tun daga saman sa har kasa da kallo, banda motar Shuraim bbu wani mota dake waje a wajen bbu kuma alamar mutum a layin, ganin kallon da Shuraim yake mata daga cikin mota ta juya xata koma ciki, taji yace "Come here, who are you looking for??" Shiru tayi bata son ce masa Heedayah take nema ta ja mata, can ta kallesa a takaice tace "Nobody" bata jira cewarsa ba ta shige ciki. Gun yayarta dake xaune parloe ta koma tace "Aunty ban ganta ba fa" Maman Fadil ta mike da mamaki tace "Baki ganta ba kuma, to ina ta tafi?" Farida tace "Wllh ban sani ba kuma me gadi yace ehh ta fita gate" Kasa cewa komai Maman Fadil tayi tana kallon Farida, Farida tace "And ni ban ga kowa a layin ba" Maman Fadil ta xaro ido tace "Toh kar dai bin wani tayi tunda kince kinji tana waya da saurayi" Farida ta girgixa kai tace "Noo Heedayah will neva follow him, ni na santa baxata yarda ta bi sa ba" Maman Fadil tace "Yau Naga ikon Allah, to idan ba bin sa tayi ba guduwa yyi da ita? Waye shi din, ke kin san sa ne?" Cike da damuwa Farida tace "Ni ban wani san sa ba wllh, kuma fa bbu wanda ya san ya bata waya, nima bata gaya min ba kawai gani nayi tana ta boyewa, I am just confuse, ina Heedayah xata je da daddaren nan" Bude baki Maman Fadil tayi tace "Na shiga uku ace a gidana, ita Hadiyar dama haka take? Daga xuwa garin mutane sai ki bi saurayi ku yi tafiyar ku, duka duka nawa take da xata aikata wnn aiki, ko kece kika bi saurayi daren nan ba sai Mami ta kusa balla ki ba balle ita, ni yanxu matsala xa a ja min kawai wllh, ta ina xan fara wani bayanin yanda aka yi, kamar wasa kawai a nemi yarinya a rasa" Fita tayi daga parlon Farida da duk jikinta yyi sanyi ta bi bayanta tana tunanin anya mutumin nan ba guduwa yyi da Heedayah ba kuwa, Banda haka ai duk abun Heedayah tasan baxata yarda ta bi sa da daddaren nan ba, tunanin hakan yasa xuciyarta ya tsinke taji tsoro ya kamata sosai, Maman Fadil ta tafi gun mai gadi tace "Mukhtar ka ga fitar bakuwata da daren nan kuwa?" Yace "Ehh nine ma na bude mata gate" a mugun fusace Maman Fadil tace "Don me xaka bude mata gate da daddaren nan ba tare da izini ba" Yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Hajiya naga ba yarinya bace shi yasa na bude wllh, na xata ko tadi xata fita" Maman Fadil ta bude baki with much surprise, can tace "Toh da ta fita ina kaga tayi?" Yace "Toh da ta fita naga dai kamar bata ji dadin kallon da nake mata ba, sai naga tayi can, nan kuma so nayi inga inda xata ne, Amma dai da wata mota da naga anyi parking a kofar gidan Honorable, ni dai sai na koma ciki na xauna sai da wnn bawan Allah ya xo na sake bude gate din to ko da na leka waje gaskiya ban ga motar ba kuma, ita ma ban ganta ba" Maman Fadil tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, haka dama Hadiyar take Farida, ki shiga motar saurayi a garin da ba naku ba ki bishi kuyi tafiyar ku?? Yanxu me xan ce ma Mami" Farida dai ta kasa cewa komai gaba ta tsorata ne sosai, Maman Fadil ta juya ta nufi hanyar shiga parlor tana cewa "Toh kuwa bari in kira Mami bbu wanda xai ja min matsala gaskiya" da sauri Farida ta bi bayanta tace "Noo plss don Allah aunty kar ki kirata, Mami won't take it likely with her, mu jira sanda xata dawo sai kiyi mata fada ke, don Allah Aunty kar ki kira Mami" Maman Fadil tace "Ya xa ki ce kar in kirata, wnn ai ba abinda ya kamata a boye bane, ya kamata a sanar ma Mami, gaba daya nawa take? Ta wuce 17 wnn da ganinta, amma ita har tayi wayon bin saurayi da daddare ba ma da rana ba, kai ko da rana ne hukunci me tsauri ya kamata ayi mata balle da daddare, samarin Abujan nan masu lalata yan mata, a gidan ubanwa ta san sa ma, snn kince Mami ma bata san da waya hannunta ba, ni bbu wanda xai xo ya ja min matsala daga ke har ita wllh" Farida dai ta ma rasa bakin magana, Maman Fadil ta xauna parlor sai dai bata kira Mamin ba, hankalin Farida ya d'an kwanta sai kallon agogo take tana addu'a, tana fatan Allah ya sa Heedayah ta dawo anytime from now, yanda duk ta tsorata sai kace ita tayi laifin ma. A wani tsadadden wajen shan ice cream Khaleel yyi parking yana kallon Heedayah da idonta ke saman titi ko kiftawa bata yi, yace "Kina shan ice cream?" sai a snn ta juya ta kallesa ta kalli gun siyar da ice cream din, tace masa "Uhn" yace "To mu je ki xabi flavor da kike so" a hankali tace "Aa ni baxan fita ba" yace "Me yasa?" Ta langwabar da kanta tace "Ba komai, kawai bana son in fita" yace "Ohk then, let me get you" bata ce komai ba ya dau face cap dinsa ya kafa a kansa, baka ganin komai sai dogon hancinsa da karamin bakinsa, ya bude motar ya sauka ya kulle, ta bi sa da kallo har ya shiga babban Ice cream parlor din, bayan wasu mintuna ya dawo rike da leda me dauke da packaged ice cream har uku ya bude motar ya shiga snn ya kulle ya mika mata ledan, amsa tayi ya tada motar suka bar wajen, ya kalleta ganin ta ajiye ledan a gefenta yace "Toh ki sha" tace "Ni kadai?" Yace "Yess" tace "Ai baxan iya shan duka ba" yace "Toh sha wanda xa ki sha" ba musu ta bude ledan ta dau vanilla flavor ta bude ta fara sha, a nutse yake driving din, just roaming round FCT, sai bin manyan wurare take da kallo, you can't say if she is happy or not, ita dai ga ta nan, suna isa wani joint na shawarma yace "Do you take shawarma?" Ta girgixa masa kai alamar Aa, yace "Why?" Tace "Na koshi" yace "Toh tsire fa?" Ta girgixa masa kai nan ma, bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da driving slowly, kallon agogo dake nuna karfe tara saura minti sha biyar yyi yace "Are you sure baki son komai?" Ta gyada masa kai, tafiyar kusan minti sha biyar suka kara ganin inda suka nufa ta kallesa da sauri tace "Ina xaka kai ni?" Yace "Home, its late kar a neme ki, nasan yanxu ai so called yayan naku ya wuce ko?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya ci gaba da driving, girgixa kai tayi a hankali tace "Ni baxan je gidan ba" Da mamaki ya juya ya kalleta, yace "Baxa ki je gidan ba kuma?" Ta gyada masa kai, yace "Why?" Kamar xata yi kuka tace "Ni dai kawai baxan je ba" Yace "Did you have any other guardians in Abuja" Ta kallesa tayi shiru, sai kuma tace "Ban san kowa ba" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da tukin, Kuka sosai Heedayah ta fashe masa ganin sun kusa layin, hakan ya basa mamaki sosai ya samu gefe ya tsaya yace "Are you alright Heedayah?" Cikin kuka tace "Plss kar ka mayar da ni don Allah" kasa ce mata komai yyi yana kallonta, can yace "Me suka maki da baxa kije gidan ba" Tana share hawayen dake xuba idonta tace "Ni dai ban so, don Allah kar ka mayar da ni" He was lost of words don sai kallonta yake, ganin yanda take kuka yace "Talk to me Heedayah, sun maki wani abu a gidan ne?" Ta hade kanta da gwiwa tace "Ni basu min komai ba, bana son in je kawai" ya jingina da seat dinsa yace "To ina xan kai ki yanxu?" Cikin rawar murya tace "Ka tafi da ni kawai" yace "In tafi da ke ina?" A hankali tace "Inda xaka je" Jin shirun yyi yawa ya sa ta dago tana goge hawayen idonta, kallonta taga yake yi, ya kamo hannunta a hankali yace "Noo Heedayah, you need to go back home, xa su yi ta nemanki...." Ta fixge hannunta tana masa wani kallo tace "Ni baxan je ba nace maka, kuma ka ajiye ni a nan kawai inyi wucewa na" Da mamaki yace "Ki tafi ina?" Kokarin bude motar ta fara yi tace "Ni ka bude min" ya jawota yace "But Heedayah, what just came over you, Ina kike son in kai ki da daddaren nan, kince min baki san kowa ba a garin nan banda gidan warce ku ka xo, to ina kike son in kai ki kuma" Kuka kawai take masa xata kwace hannunta, ya jawota kusa da shi yace "Ki gaya min me aka maki a can gida" turasa tayi tace "Nothing I said, ni ka bude min in sauka" Khaleel couldn't stop looking at her, ganin ya ki bude mata motar ta hade kai da gwiwa. Har karfe goma saura Farida da Yayarta suna xaune parlor sun yi jigum, Farida ta san kiris ya rage yayarta ta kira Mami don ta cika daga xaunen da take, Farida ta dau wayarta duk jikinta yyi sanyi ba kadan ba, bude ido tayi tunawa da tayi ai ta ba Heedayah wayarta suna tahowa a mota daxu tayi ma Khaleel din message, shiga message tayi da sauri tana dubawa taga bbu message din sabon number, alamar Heedayah ta goge text din gaba daya, Number Shuraim ta duba duk da bata yi saving ba amma ita ma ta so haddacesa tunda bashi da wahala, tayi dialing number har ya katse bai dauka ba, ta sake kiransa, nan ma bai dauka ba, sai gashi ya kira, dagawa tayi ta kai kunne, da farko ta rasa abinda xata ce sai kuma tayi masa sallama, ya amsa, shiru tayi, yace "Wacece?" Mikewa tayi ta mika ma Maman Fadil wayar tace "Don Allah aunty kiyi masa magana ni ban san me xan ce ba" Maman Fadil ta jefa mata wani kallo tace "Waye?" Farida tace "Ya Shuraim" amsar wayar tayi ta kai kunne hade da yi masa sallama, bbu bata lkci tayi masa bayanin komai cikin few minutes, shirun da taji yasa tace "Hello" Shuraim yace "Ina ji, and she is not yet back har yanxu?" Maman Fadil tace "Wllh kuwa, ni tunda nake ban ta6a ganin haka ba ma, har nawa take xata yi wannan aika aikan, Ina ta bi sa suka tafi, ni gashi ko abinci na kasa ci har yanxu, ta ina xan fara yi ma Mami bayani, me ma xan ce mata??" Shuraim gaba daya ya rasa abinda xai ce, don basu kai sa mamaki ba ma, can yace "Ba wa Farida wayar" Mika ma Farida wayar tayi, Farida ta amsa ta kai kunne, Yace "All this while dama akwai waya a hannunta" Farida ta koma ta xauna ta rasa abun cewa, yace "Baki ji na ne?" Tace "Nima ban sani ba...." a fusace Maman Fadil tace "Munafuka kika ce baki sani b, wllh tana sane ita ma munafukar ce ai, kuma kema ta ja maki matsala tunda kike boye abinda take yi" Shuraim yace "Waye shi Mutumin??" Farida tace "Ni fa ba gaya min komai take ba" Katse wayar Shuraim yyi ya mike daga kwancen da yake, ya dau makullin motarsa ya fita. Khaleel bbu irin lallaba Heedayah da bai yi ba ya mayar da ita gida amma kememe ta ki, har sannan suna tsaye gefen hanya a motarsa sai kallonta kawai yake, ji yyi tace "To naji xan tafi gida, amma ka sauke ni in karasa da kafa kar ka kai ni street din" Yace "But it's late and they are dogs everywhere...." tace "Ni kuma a nan xaka ajiyeni nace" yace "In ajiyeki ki tafi wani waje kenan?" Ta kallesa tace "Ehh, don baxan koma gidan ba" ya fi minti uku yana kallonta kafin ya tada motar ya fara tafiya, har ya dau hanyar gidansa sae ya tuna abinda Zayyad yace masa daxu, can kuma kawai ya nufi gidan nasa. A cikin motarsa ya ciro makullin gate din gidan, ya sauka ya bude gate din, Heedayah sai bin anguwar that is so quiet ta ke da kallo har ya dawo cikin motar ya shiga, a parking lot ya tsayar da motar ya kashe ya sauka ya koma gate din ya kulle da makulli snn ya koma gun motar yana kallonta yace "Are you satisfied now?" Ta gyada masa kai yace "To sauko" bude motar tayi ta fito tana bin gidan da kallo tace "Gidansu waye?" Yyi shiru yana kallonta, ganin ynda take kallonsa a hankali yace "Gidanmu ne" tace "Mum dinka da Dad and siblings suna ciki" Yace "No" tace "Why? Where are they?" Kulle motar yyi bai ce mata komai ba, ya nufi entrance din katon gidan, ta bi bayansa tace "You are not saying anything?" Yace "Duk basa nan" tace "To ina suka je" Yace "Gobe xa su dawo, they travelled" tace "To ni da kai kawai xa mu kwana gidan?" Bai ce mata komai ba ya sa makulli yana bude kofar parlon, tace "Ehh??" Sai da ya bude kofar snn ya juyo yana kallonta yace "Aa da mutane" daga haka ya shiga parlon yana haska fitila da wayarsa ta bi bayansa, a hankali tace "Ni tsoro nake ji, babu wuta?" Yace "xan kunna yanxu" Ajiye wayarsa yyi da ya haska some areas of the parlor snn ya fita ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba haske ya gauraye ko ina na katon parlon, ta dinga bin parlon da kallo don yyi mata kyau sosai kamar ba a Nigeria ba, parlon is so neat don bai yi kama da wanda ba a amfani da ba, Khaleel ya shigo parlon ya kulle kofa snn ya dawo ya xauna yana kallonta yace "Now tell me Heedayah, me aka maki a can gidan?" Ta girgixa kai tace "Aa ni ba a min komai ba, kawai bana son komawa ne" yace "Noo, there must be reason for that, haka kawai baxa kice baxa ki koma ba" Tayi shiru tana kallonsa, mikewa yyi ya nufi fridge dake dinning area ya bude ya dau drink din gwangwani me sanyi snn ya dawo yace "I am tired, and sleepy... Mu je in nuna maki inda xa ki kwanta" Shiru tayi tana kallonsa, stairs ya nufa, ta mike ta bi bayansa, ya bude mata wani daki yana kallonta yace "Here...." Bata ce komai ba ta shiga dakin ya kulle kofar snn ya koma downstairs. Rai bace Maman Fadil tace "Baxa ki bude baki ba ana maki magana munafuka kawai, Banda kukan munafurci meye wnn kike yi, baxa ki basa amsan tambayar da yake maki ba" Farida ta ki cewa komai ta goge hawayen idonta da ya ki tsayawa, Maman Fadil ta kalli Shuraim tace "Don Allah da ta ganta da waya who is first person da ya kamata ta fara sanar ma wa, idan ma baxata iya fada ma Mami ba tana ganin Mami won't take it likely ba sai ta gaya ma Yaya Junaid ba? To wllh bbu ruwana dubi karfe har sha daya saura bbu yarinya bbu labarinta, me xan ce ma Mami daga xuwa gidana yarinya ta bi saurayi da daddare" sai ita ma ta fara kuka, Shuraim dai na tsaye parlon just as the soldier he is, Farida ta saci kallonsa don tunda take bata ta6a ganin anger dinsa irin na wnn lkcn ba, gaba daya idanuwansa sun sauya daga yanda ta san su, Maman Fadil na share hawayen dake kwarara idonta tace "Ni kawai don kace kada a tada ma Mami hankali daren nan ne wllh da na kira na sanar mata Yaya Shuraim, amma duk da haka bari in kira Yaya yanxu ya san abinda ke faruwa this is almost after eleven" tana barin parlon shuraim ya juya yana kallon Farida fiercely yace "For how long wayar ke hannunta" Tayi shiru bata ce komai ba, tsawar da yyi mata ya sa ta mike a hankali tace "Ni bata ce min ya bata waya ba, kawai boyewa take ta yi har na gani" xaunawa yyi saman kujera ya sauke boyayyen ajiyar xuciya ya dafe forehead dinsa da ya ji yyi masa nauyi, sake mikewa yyi yana kallon agogo dake manne parlon.... Khaleel ya gama duk abinda xai yi ya kashe wutan parlon ya kwanta saman 3 seater wajejen karfe sha biyu da rabi, sai a sannan ya cire wayarsa a flight mode, bayan few minutes sai ga text din Zayyad ya shigo masa har uku, ya bude ya mike xaune yana duba messages din.... Lkci daya ya mike ya nufi kofar parlon ya bude ya fita da sauri. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Kashe wutan gidan yyi gaba daya snn ya dawo parlon ya dau wayarsa ya kunna fitila ya wuce sama, a hankali ya bude dakin dake kallon wanda Heedayah ke ciki, ya shiga ya rufe, kusa da kofar bathroom ya isa ya duka ya daga foot mat dake kasa ya daga tiles din da aka daura kawai a wajen, sai dai idan mutum bai lura ba baxai gane daura tiles din kawai aka yi ba xa a iya dagawa, wani karamin under ground ya haska a wajen bayan ya bude wani box, ya ciro bindiga guda daya cikin bindigogi biyar dake nan snn ya dura bullet dinsu dake wajen su ma, ya mayar da tiles din ynda yake ya daura foot mat din ya mike ya saka bindigan a aljihunsa, ya fita dakin ya kulle kofar gently, har xai sauka sai kuma ya kalli kofar dakin da Heedayah ke ciki ya dawo ya bude kofar shi ma gently yana kallon cikin dakin, all with the aid of his phone flash, kwance ya ganta ta dukunkune waje daya tana bacci, ya karasa cikin dakin ya bude press dake ciki ya fiddo babban blanket me laushi ya lulluba mata, still yyi sai kuma ya kashe flash din da wuri ganin ta gyara kwanciyarta, sai da ya tabbatar ta ci gaba da baccin snn ya tafi gun curtains xai gyara ya hango mota biyu sun tsaya dai dai gate din gidan don ta window din ana yi ganin wasu bangare daga surrounding din street din, kallon motar yake har bayan kusan minti goma shi dai bai ga alamar an sakko daga ciki ba, wanda idan ma an sakko din ma ba sani xai yi ba sbda jikin wall din gidan motar ya tsaya, nan kuwa mutane biyar har sun sauka daga motar xuwa bakin gate din nasa, daya daga mutane biyar din da suka diro daga motar ya tafi ya durkusa bakin gate din gidan yana haska fitilar wayarsa ko xai ga tambarin tayar mota da xai yi nuni da mota ta shiga gidan, mikewa yyi yana kallon sauran yace "Yes yana ciki" dayan cikinsu yace "Cikin darkness?? da yana ciki ai xa a ga wuta a cikin gidan, but no light and akwai wuta a anguwar ai" Bindiga wanda ke kallonsa ya daura masa a fuskarsa strictly yace "Ka raina kitabar Brainiac kenan? Tunda har baya gidansa na asokoro, baya can gida, to yana gidan nan, coz he have no business with the other gender ballantana ace yana hotel, baya ma kwanan hotel, so now you guys should just find a way da xa mu shiga gidan nan in hukuntasa" Mutumin yace "Talent dinsa na yanda yake shiga gidan mutane in every operation xa mu yi amfani da yanxu" Tuni Khaleel ya fita dakin da Heedayah take ya sakko downstairs ya fito compound, ta jikin bango ya dinga bi har ya iso gate ya manne da bangon pillar din gate din, nan kuma duk ya dau muryoyinsu, A karo na farko Maska yace "We should bother our self not..... finding a way in, I have his spare keys, stole them from Zayyad" Khaleel yyi grinning teeth dinsa bai kara second daya a wajen ba ya koma cikin gidan da sauri, a karo na farka a rayuwarsa ya ji he is disturbed about something, ya ji gaba daya hankalinsa ya tashi, baya son abinda xai tsorata Heedayah ko kadan, ya san kuma dole xa su shigo gidan ya san tunda makulli na gun maska xa su shigo, da ma shi kadai ne xai sama ma kansa way out cikin few minutes but not with Heedayah, yana shiga parlon ya ji suna bude gate din, ya sa makulli kofar parlon leaving the key jikin kofar duk da ya san it's of no use cos he knows all the trick, they knows all the trick, they are expert users of his talent and experiences, sama ya haura ya tsaya nan corridor patiently waiting for them, yana jin suka bude kofar parlon bayan wasu mintuna, haka kawai a sannan ya dinga jin faduwar gaba, and with just a blink of an eye sae ga wuta ya haska ko ina, wato sun kunna wutan gidan yasan kuma aikin Maska ne, Fago na nuna ma Oga Arne takalman Heedayah dake parlon yace "This is the root of the problem, mace ce ta shigo rayuwarsa shine take yaudararsa yake misbehaving yake raina ku" Arne ya rike ha6arsa yana gyada kai convincingly yana kallon takalmin da mugun mamaki, a hankali yace "Ohh I seeee, mace ce ta shiga rayuwarsa farat daya, abun ka da ba sabon ba" Fago yace "He risked his colleagues life sbda matsiyaciyar mace da xan harbe yanxun nan" Arne yyi wani dariyar bossawa lkci daya kuma ya daina dariyar yace "To wllh wllh a gabansa xa a aikata lahira, snn sai ya san yayi fatali da umarnin manyansa yau, shi ya mance a yanda muka daukesa kenan, I am more of his father than Boss, ni ne uwarsa nine ubansa ynxu haka a duniya" Khaleel dake jin duk abinda suke cewa ya manne da bango hannunsa rike da bindigarsa ya saita dai dai gwiwar Fago cikin few seconds ya saki bullet din, bayan ya tabbatar ya samu kafar ya bude dakin da Heedayah take ciki ya shige da sauri ya sa makulli, wani ihun axaba fago yayi ya xube kasa jini na malala daga gwiwarsa ta dama, ko wannensu har Arnen suka samu bango duk suka manne suna xaxxare ido, A firgice Heedayah ta mike xaune saman gado tana kallon Khaleel, ya boye bindigar hannunsa a bayansa, ya sakar mata murmushi da iyakarsa lips, kokarin sauka ta fara yi daga saman gadon looking very afraid tace "Meye yyi wani karan, what's that, is that a gun????" Ya nufeta trying his best to calm her down yace "No sound, may be... May be... We have visitors, probably armed robbers, bandit, kidnappers...." Ta wani xaro ido ta fasa wani shegen ihu ta mike tsaye, rikicewa yyi ganin yanda ta tsorata ya isa gabanta not minding she will see the gun in his hand yace "Noo Heedayah, I will protect you by all means bbu abinda xai faru dake, I promise you this" Ta wani xaro gaba daya idanuwanta ganin bindigan hannunsa ta kara saka wani kara me karfi, jawota yyi jikinsa yace "I am protecting us with it, they have guns also, I mean no harm Heedayah" ta kankamesa tace "Wayyo ni tsoro nake ji, plsss take me out of this house, don Allah ka tafi da ni daga nan, tsoro nake ji" Jikin window ya nufa holding on to her tightly, ya bude window din dakin ya saita bindigarsa up the sky ya saki bullets uku that sounds so loud a anguwar, Heedayah bata ta6a tsorata irin na wannan dare ba tunda aka haifeta, tana son kwace kanta kuma amma ya ki saketa, ya kara harba bindigar, dai dai nan Maska ya bude kofar dakin, sun kai su shidda ko wanne na nuna masa bindiga kamar yanda shi ma yake nuna ma Arne, Duk ynda Heedayah ta so juyawa taga wa enda suka shigo Khaleel bai bata wannan daman ba sbda yanda ya rungumeta, Arne ya dinga kallonta yana nuna mata bindigar hannunsa, shi kuma Khaleel na pointing dinsa da nasa bindigar, Arne yace "Ka sauke bindigar ka ko in harbeta har lahira ynxu" Girgixa kai Khaleel yyi yace "Same will happen to you right now" Arne yyi wani shegen kara yace "Genius dama sbda mace kayi disappointing dinmu ka janyo mana rasa Salim????? Ka janyo mana asara da yawa, duk sbda yar kwailar nan? Wato a cikin kankanin lkci ka gurbata rayuwarka ka fara harka da mataaa, a kaf duniyar nan dama kana da sama da ni???" Cikin tsawa ya kare maganar yana huci, sai kuma ya nufesa still pointing the gun to Heedayah, Khaleel ma na nuna sa da gun dinsa fuskarsa a daure, lkci daya Siren ya cika anguwar Arne ya juya da sauri yana kallon yaransa yana xaro ido, Maska sake xare ido shi ma yace "Policemen...." cikin daga murya Arne yace "Get set, back to the cars now, help Fagoo out, immediately now" Duk suka juya suka fice daga dakin da sauri, Arne na komawa da baya bai fasa nuna Heedayah da bindiga ba yana kallon Khaleel cikin kaushin murya ta mugunta yace "Wllh wllh idan baka dawo hanya ba nine ajalin ka Khaleel, nine ajalin wannan yarinya, nine ajalinku ku biyu billahh, sae na yi maka kisan walakanci, ita kuma in harbeta cikin ruwan sanyi, kasan wanene ni Khaleel, kasan wanene Manga, kasan wanene Barau, kasan wanene Bala, forget you are a Genius idan aka hada mu hudu mun fi Genius, we will make life a dirty miserable for you before sending you to ur early grave, yanxu muka fara harka da kai, baka isa ka kara bijira mana lkci daya ka janyo mana matsala ba, Kai din namu ne" yana fadin haka ya fice daga dakin in a haste, har sannan siren na tashi a anguwar loudly, Khaleel ya sauke wani ajiyar xuciya a karo na farko ya kalli Heedayah that he is holding so tight a jikinsa don ya san she passed out from the moment she heard their voices, kwantar da ita yyi saman gado yana kallon kyakkyawan fuskarta cikin sanyin murya yace "Heedayah...." Su Arne da tawagarsa na isa titi suka jiyo jiniyar yan sanda so far away alamar a lkcn ma Yan sandan ke tahowa, and they wondered wani siren ne ke tashi a anguwar haka, not minding that.... a mugun guje suka yi wucewarsu da motocin su kafin bayyanar motar yan sandan, Knocking Khaleel ya ji ana yi downstairs with voices, ya mike tsaye da sauri ya ajiye bindigar hannunsa karkashin pillow ya fita, corridor din dakunan ya hadu da matasa just like him guda biyu sai dattijai guda biyu, daya dattijon yace "Hope you are safe brother?" Khaleel ya kirkiro murmushi yace "Alhmdllh" Daya matashin yace "Babu abinda dai suka yi ko, don naga pool of blood downstairs" Khaleel yace "Ni na caki daya daga cikinsu da wuka, har suka gudu sbda karan Siren wukar yana jikinsa, I battled with them" A tare suka hada baki suka yi hamdala, Dattijon yace "To matar taka fa?" Khaleel da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Ta dai tsorata ne kawai, and I think she passed out...." Daya daga matashin yace "Can I meet her in and check on her" Dattijon yace "Ehh likita ne shi, either ya dubata ko kuma a wuce asibiti kawai" komawa dakin Khaleel yyi ya isa kusa da Heedayah ya durkusa ya dau dankwalinta da ya fadi a kasa ya rufe mata gashinta da shi snn ya gyara mata skirt dinta, ya koma gunsu yace ma likitan xai iya shiga, makotansa ne su din gaba daya, iyakarsa da su haduwa a masjid din anguwar yyi masu gaisuwar mutunci yyi wucewarsa that is if yana Abuja, though a wata ya kan yi sati uku a Abuja, xamansa a Kaduna lkci lkci ne, Siren din da ya dinga tashi a anguwar kuma daya daga matashin wanda ya kasance soja ne ya kunna kuma yyi kiran office a turo masu yan sanda tun farkon harbin da Khaleel yyi sau uku, neighbors din nasa na nan har yan sanda suka iso suka d'an yi investigation dinsu suka wuce, sae kusan karfe biyu da few minutes duk neighbors din suka bar gidan Khaleel, bayan likitan ya tabbatar Heedayah is fine, kuma bacci take. Har kusan asuba Khaleel na xaune gefen Heedayah bayan ya gyara parlon duk ya share blood stain din, ya jinginar da kansa da gado yana kallon saman dakin, juyawa yaga tayi, ya sauke idonsa kanta da sauri yana kallonta, a hankali ta bude idonta suka yi ido hudu da shi, mikewa tayi xaune tana kallonsa sai kuma ta bi dakin da kallo, ya kamo hannunta kafin yace komai ta fashe masa da kuka tsoro karara a fuskarta tana komawa baya, yyi kasa da murya yace "You are safe Heedayah, 'yan sanda sun xo sun tafi da su" ta fashe da kuka sosai xata sauka saman gadon, ya riko duk hannunta biyu yace "Nace maki yan sanda sun tafi da su, don't cry plss" cikin rawar murya tace "I am still afraid, why were they here?" Yyi kasa da murya yace "To Rob" ta dinga bin dakin da kallo tana hawaye, yace "Stop crying plss" tace "Kaina na min ciwo" da damuwa yake kallonta, can ya mike don Dr Farouq ya dauko mata magani daxu daga gidansa ya kawo kafin su tafi, Khaleel yace "I'm coming" sauka tayi da sauri daga kan gadon ta tsaya kusa da shi tace "Nooo kar ka barni" kama hannunta yyi suka fita dakin xuwa downstairs ta makalkale masa don duk a tsorace take, kitchen ya shiga tare da ita, ya dau bottle water a fridge ya xuba a kettle ya kunna, ya lumshe ido jin yanda taki basa breathing space standing so close to him, Bai bari ruwan ya tafasa ba ya dauraye mug ya xuba kayan shayi a ciki snn ya xuba ruwan ya dau spoon ya juya, kashe wutan kitchen din yyi suka fita, yana rike da cup din shayin tana makale da shi suka koma sama, yana kallonta tana shan shayin bai san sarkin shan shayi bace har ta shanye tass, yace "You need more?" Girgixa masa kai tayi, ya bata ruwan gora da paracetamol ta amsa ta sha, bayan few minutes ta kwanta saman gadon tayi shiru tana kara tunanin abinda ya faru, she is still shock, kallon agogo dake nuna karfe uku da few minutes yyi sai a snn ya fara jin bacci, ya lumshe idonsa ya bude yace "Did you need anything Heedayah?" Girgixa kai tayi tana kallonsa, yace "Xan tafi in kwanta...." Da sauri ta mike xaune tace "Where?" Yace "Dakina" kuka ta sakar masa tace "Noo kar ka barni ni kadai pls, wllh tsoro nake ji" Shiru yyi yana kallonta, can ya mike ya bude press ya ciro wani bargon ya shimfida a kasa ya dau pillow ya ajiye snn ya kashe wutan dakin ya kwanta kasan bargon yace "Good night" edge din gadon ta dawo ta inda yake kwance yanda xata dinga ganinsa yana daga kasa tana daga sama tayi lamo gabanta na faduwa, ba a dau lkci ba bacci ya dauketa, shi kuma duk baccin da yake ji sai ya samu kansa da kasa yi.... A idonsa aka yi kiran sllhn asuba, biyar da few minutes ya mike ya shiga bandaki yyi alwala ya fito ya bude kofar dakin a hankali so careful not to wake her sannan ya fita. Bayan ya dawo masallaci a parlor ya kwanta nan da nan bacci ya daukesa, cikin bacci ya ji ana tashinsa, ya bude idanuwansa a hankali ya ganta durkushe kusa da shi tana kallonsa, murya can kasa tace "Babu Hijabin da xan yi sllh" ya kuma lumshe idonsa snn ya bude ya mike xaune, ita dai kallonsa kawai take da idanuwanta da suka kumbura, tashi yyi ya wuce sama ta mike ta bi bayansa, ya shiga wani daki sai gashi ya fito da hijab a linke, ya mika mata, tace "Na waye?" Murmushi ya sakar mata yace "Pray Heedayah" daga haka ya koma downstairs, ta shiga dakin ta dauko darduman ita ma ta dawo kasa, har ya koma bacci ta samesa a parlon, ta jima xaune saman darduman bayan ta idar da slhn don har gari ya fara haske, daga karshe ta kwanta saman darduman nan da nan bacci ya dauketa. Karfe takwas saura mintuna Mami ta shigo garin Abuja, tun hudu da wani abu na asuba hakurin Maman Fadil ya kare ta kirata don tayi ta kiran Junaid wayarsa wasn't going through a daren, nan dai ta sanar ma Mani halin da ake ciki with tears, daren ranan daga ita har Farida bbu wanda ya rintsa, I don't want to talk about shuraim cos he saw no sleep too, ya kuma fi su shiga tashin hankali, Tun da Maman Fadil ta sanar ma Mami abinda ke faruwa, sllhn asuban ma sai da Mami tayi consoling kanta na gaske snn ta iya yi, she have never been down lkci daya kamar ynda tayi jin news din nan ba, she felt so sick at once, ba training din da tayi ma Heedayah ba kenan, baxata taba tafiya tare da saurayi ba kamar yanda Dinar ta sanar mata, Mami was so confuse and shock to the highest, wanda bata san lkcn da hawaye ya hau mata xarya ba gashi junaid baya gidan sai dai bata yi yunkurin kiransa ba, tana idar da sllhn Asuba sai da ta sha magani ko xata d'an ji saukin abinda take ji, snn ta saka Hijab dinta har kasa ta dau hanyar Abuja, not minding the road tare da driver dinta, she just can't hold it anymore, a motar ma banda addu'o'i bbu abinda take ta yi, tun auren Maman Fadil sae ranan Mami ta taka gidanta a karo na farko, daga Farida har Yayarta bbu wanda ya iya ce ma Mami komai, sae Maman Islam makociyar Maman Fadil da ke parlon da wata neighbor dinsu Maman Safwan ne suka iya gaisheta da yi mata sannu da xuwa ganin kamaninta da su farida, Mami ta amsa cikin sanyi, ta nemi kujera ta xauna don bata jin xata iya ci gaba da tsayuwa tana kallon Maman Fadil tace "Deenar me ku ka yi ma Heedayah?" Cikin sanyin murya Maman Fadil tace "Haba Mami me xa mu yi ma Heedayah, karfe nawa suka iso a jiyan ma balle ayi mata wani abu, wllh bbu abinda aka yi mata" sae kuma ta fara kuka sosai, Mami ta dafe kanta ita ma hawayen har ya kawo idonta, ta shiga kiran Allah a xuciyarta, Abba kawai da kaka suka fado mata a wnn lkcn, where is she to start from now, Maman Fadil na share idonta tace "Abun da mamaki sosai, ko da ta fita gurin saurayi ae xata dawo sai in wani abu ne ya faru, kuma gashi bamu san waye saurayin ba, wllh Mami sneaking tayi ta fita ni da Farida bbu wanda yasan ta fita, da na sani ai babu abinda xai sa in barta ta fita waje, mu uku kadae ne gidan sae Fadil fa" Farida dai hawaye kawai take ta kasa cewa komai, Mami ta daure ta mike tace "Nearest police station a ina yake?" Maman Fadil tace "Aa tun asuba Shuraim ya kai kara can, he is still not yet back ma" Maman Islam ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Allah ubangiji ya takaita wahala da tashin hankali, ya bayyanata cikin aminci da yarda" A hankali Maman Fadil tace "Ameen" Mami ta dau wayarta ta shiga kiran Shuraim. Karfe tara saura Heedayah ta farka, ta mike xaune tana bin katon parlon da kallo, har sannan Khaleel na kwance saman kujera yana bacci, ta mike ta isa kusa da shi ta durkusa tana kallonsa, hancinsa ta kafe da ido, can ta kalli dogon lashes dinsa snn lips dinsa, ta kuma kallon hancinsa, sosai gabanta ya fadi, lkci daya ya bude ido ta koma baya da sauri har tana neman faduwa tana kifta ido tace "Tell me who were those people of yesterday" ya mike xaune yana shafa kansa yace "Armed Robbers, good morning Heedayah" shiru tayi tana kallonsa, ya lumshe idonsa ya bude yace "May be sun ga ina gari and they've been targeting sae jiya suka xo" a sanyaye tace "How did they leave?" Yace "My neighbors helped, they alerted the police" Tayi shiru tana kallonsa, sauke dogayen kafafuwansa yyi kasa yace "I've slept for so long, you need to get back home Heedayah, kar ki ci gaba da daga hankalin wa enda suka rike ki da aminci, I am taking you back home now idan kinyi breakfast" lkci daya mood dinta ya canxa tayi shiru tana kallonsa, ya mike yace "Ki tafi sama ke ma ki shirya, take ur bath I will get you something to wear now" da kallo ta bi sa har ya wuce upstairs ba a dau lkci ba ya sakko da makullin motarsa, yace "Toothpaste, toothbrush, sponge, soap towel duk suna nan na ajiye maki saman gado, I will be back soon" ta mike da sauri kamar xata yi kuka tace "Ni tsoro nake ji wllh" yace "No harm Heedayah, ba dadewa xanyi ba kuma, I will be back soon" daga haka ya fita parlon tana ji ya fitar da motarsa daga gidan, xancen da yyi mata kafin na karshe ne ke yawo a kanta, she needs to get back home, but she never wants to go back, shiru tayi tana tunanin kilan dole yace sai ya kai ta gida, ita kuma bata son ta je, hawaye ya kawo idonta ta wuce sama da sauri ta dauko veil dinta snn ta sakko kasa, ta sa takalminta ta nufi kofa, gwara ta tafi kawai kafin ya dawo ya ka ita gida. Murda kofar tayi ta ji a rufe, kamar xata yi kuka ta dinga kallon kofar, ta sake murdawa bai buduwa ba, a hankali ta juya ta koma sama duk jikinta a sanyaye ta dau abubuwan da ya ajiye mata saman gado ta shiga bandakin, ko da ya dawo bata fito ba ya ajiye mata ledan hannunsa kan gadon sannan ya fita dakin ya wuce nasa, har ya sakko wajen karfe goma bayan yyi wanka ya shirya Heedayah bata sakko ba, sai kallon agogo yake don ya kagu ya ga ya mayar da ita gida, daga karshe ya mike ya wuce saman, karo suka kusa ci xata sakko ya koma baya yana kallonta, sosai bakin abayar yyi mata kyau kamar ya aunata kafin ya siyo, ya sakar mata murmushi yace "U look cute" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, yace "Taho kiyi breakfast lkci na wucewa" bin bayansa tayi suka koma kasa, ya hada mata shayi ya bata fried Irish with egg and ketchup da ya siyo, yace "Do you take bread?" Ta girgixa masa kai, shayin ta fara shanyewa gaba daya, ya buda ido yana kallonta yace "Why?" Tace "Haka nake yi" yace "You need more?" Ta girgixa masa kai, jawo plate din Irish din tayi ta fara ci a hankali, ya d'an yi murmushi ya hada shayinsa da iyakarsa bai kai rabin cup ba ya fara sha, yace "Ina xa ki ce ma Guardians dinki kin tafi idan na mayar da ke yanxu Heedayah?" Ta kallesa bata ce komai ba, lkci daya ta kasa ci gaba da cin dankalin, ganin hakan yace "Why are you not eating" bata ce masa komai ba ta ci gaba da ci without appetite, har cikin ranta bata son xancen gida, daga karshe ta tura Irish din ganin ya fice a ranta gaba daya, ta koma saman kujera ta xauna ta jinginar da kanta da kujeran, da ido ya bi ta yace "What's wrong Heedayah?" Ta girgixa masa kai tace "Nothing na koshi" Kafin yace komai tayi saurin cewa "Wannan shayin ne xai isheka?" Yace "Baxan ma shanye ba" Tayi shiru tana kallonsa bata ce komai ba, a hankali kuma tace "I saw u with gun yesterday, waye ya baka" kallonta yyi da sauri coz her question came unaware, sai kuma ya sauke idonsa kasa cikin cool voice dinsa yace "My father, you know.... he is a soldier, da naji barayin sun shigo shine na tafi dakinsa na dauko bindigar" Yana iya ganin tsoron da ya bayyana fuskarta lkci daya, ya ajiye sauran shayin da ya rage ya mike yace "I need to get u back home Heedayah, nasan hankalin kowa ya tashi yanxu, ki saka kayan ki da kika cire a leda ki sakko da shi mu tafi" Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa babu, gabanta na faduwa kuma sosai, ganin jiranta yake tace "Na saka a leda...." yace "To dauko su" tayi narai narai da ido cikin tsigar shagwaba tace "Ni baxan iya xuwa sama ba kuma, my legs a paining me, ka dauko min" ya kai minti daya yana kallonta can yyi murmushi ya wuce saman ta bi sa da kallo har ta daina hangosa, mikewa tayi da sauri ta tafi ta saka takalminta ta fice daga parlon da ya bari a bude bayan shigowarsa daxu, kusan da gudu ta isa gate shi ma lock kawai ta bude ta fice daga gidan gaba daya, mota ce tayi parking dai dai gate din gidan, tana kallo har wanda ke cikin motar ya sakko, kallonta ya dinga yi, taki yarda su hada ido ta nufi hanyar da take tunanin xai fitar da ita daga anguwan da sauri, da ido ya bi ta har tayi nisa snn ya shiga gidan, ya bude parlon ya shiga, daga kitchen Khaleel ya fito yana neman Heedayah, ya tsaya kallon wanda ya shigo parlon, Zayyad yyi masa wani shegen kallo sai kuma ya kyalkyale da dariya yace "I am happy for you frnd, ko ba komai kai ma xaka bada labarin wacece mace tunda ka kwana gida daya da mace yau, sai dai you are in great risk Brainiac, Mu ma ba wai bama harka da mata ba, but we still concentrate on our goals, kai kuma da yake sabon shiga ne, it's causing you much distraction, ga mata iri ri sai warce ka xaba ka darje a gari, don't be afraid of loosing this one....." Wani kallo Khaleel ya jefa masa xai koma sama neman Heedayah and idan ma ya ganta baxai bari ta fito ba har Zayyad ya wuce, Zayyad yace "Na samu labarin artabun da kayi da su Oga daren jiya, you chop liver Genius... and probably my text message helped, yanxu dai tunda har gari ya waye har kuma yarinyar ta kama gabanta sai mu je ka bada hakuri, I don't want to imagine anything happening to you Brainiac..... But isn't that girl I saw too young for u, anyway sweet sixteen, and she is damnnn pretty with the perfect curves...." Har Khaleel ya fara hawa stairs ya dakata ya juyo da sauri fuska daure yace "And where did u see her??" Zayyad yace "Mun hadu bakin gate xata wuce yanxu" Wani tsalle Khaleel yyi ya duro maimakon sakkowa few stairs din da ya hau yace "Ta tafi Ina?????" Zayyad ya tsaya kallonsa, Khaleel ya nufesa da sauri yace "Answer me plss Zayyad, Ina ta tafi" Zayyad yace "Wahala be like bicycle, I just met with her outside ynxu da xan shigo and tayi hanyar titi how will I know inda xa ta" Khaleel yace "Nooo, why did u let her" Zayyad ya saki baki yana kallonsa yace "Ikon Allah to nasan inda xa ta ko nasan me ya fito da ita" Khaleel ya warce car key din hannunsa ya fita waje da sauri almost running, Zayyad ya bi bayansa with much surprise. *pls I am begging some people that don't use to reason in the mighty name of God to stop disturbing my peace, ni Khaleesat bana son sharhi daga wanda bai biya kudin karatun littafin nan ba, littafin Heedayah is not free but they are reading for free and they will just comfortably come to u with their bend bend opinion as if it's normal, ko kunya bbu fa, to plss ku ji da hakkin mutum dake kanku ma kadai, swallow ur sharhi, allow those that subscribed to dagger it with me shè oti gbo?* _urs faithfully Khaleesat Haiydar_✍🏻 Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Tafiya kawai Khaleel ke yi for almost 20mins kenan a motar Zayyad not knowing the particular direction he is heading to, he just can't believe Heedayah is gone, ya ji hankalinsa yyi matukar tashi, bbu inda ta sani a Abuja snn ba hanyar gida ta sani ba balle yyi assuring kansa gidan ta koma duk da ya san he is just assuming don ba gidan xata ba tunda a dalilin yace xai kai ta gida ta gudu, but is she even alright, ba ayi mata komai ba tace baxata koma gida ba, who does that.... Parking yyi daga karshe ganin ko alamarta bbu, ya jingina da kujeran motar yana kiran Allah a xuciyarsa, yanxu a ina xai nemo yarinyar nan, where is he to start from.... Abba na office kiran Shuraim ya shigo wayarsa, ya dau wayar bayan ya daga ya kai kunne yace "How are you Shuraim" yace "Alhmdllh" Abba yace "Baka dawo Abujan ba har ynxu?" Yace "Eh" Jin yanayin muryar sa Abba yace "Are you alright?" Shuraim ya d'an yi shiru, Abba yace "Hello, are you there" Shuraim yace "I'm fine" Abba bai ce masa komai ba bayan few seconds yace "Ohk then..." Shuraim yace "I called to announce to you that Heedayah is missing" Abba ya ajiye takardan hannunsa after digesting the information yace "Ban gane ba, wace Heedayah?" Shuraim yyi shiru, Abba ya daka masa tsawa yace "Will you enlighten me more" Shuraim yace "She got missing yesterday at Abuja" lkci daya Abba ya mike yace "Me ta je yi a Abuja??" Shuraim yace "Sun yi tafiya da Farida xuwa gun yayar Faridar..... She is still yet to be found tun daren jiya" katse wayar Abba yyi ya koma ya xauna yana jin xufa all over him, can ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyu, bai san lkcn da ya furta "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Heedayah missing??" ya sake mikewa ya dau makullin motarsa ya fita office din. Mumy na xaune main parlor tare da Sadiya kasancewar bbu kowa gidan, su Rabi'ah da Khadijah na can gidan Baffa tunda ba a koma makaranta ba, Hajiya Sadiya tace "Ni wllh shi sa bana son harka s?dake don kin fiye gajen hakuri Maryam...." Mumy tace "Uhm uhm ba gajen hakuri bane Sadiya dubu dari da hamsin fa a wnn marran, ai ko dole in damu, ance idan na barbada maganin a abinci kuma na tabbatar ta ci in koma in sanar, to na koma an bukaci uban kudin nan na bayar to har yau shiru kke ji kamar malam ya ci shirwa, ai dole in damu da zinarin xobe na siya da ba yanxu ina kallonsa a yatsa na ba" Hajiya Sadiya tace "Kai.... wllh wani sae yyi tunanin kudin ya kai wata biyu da kika kai, nan kuma ko kwana biyar ba a yi ba, amma har kin xaku, ke dai kawai idan an maki aiki lkci daya ki ga ya ci kamar yankan wuka, to ance maki haka ake yi? Su ma ba sai sunyi duk abinda ya kamata na kafin aikin yaci, Komai ba d'an hakuri bane dama, ni dai idan kina haka sacce min gwiwa kawai kike wllh sae kace ba musulma ba sbda rashin hakuri" Mumy tayi tagumi tace "Ae baki sani ba Sadiya, wllh tun da na kyalla ido na gan Yarinyar nan gidan bikin su Jamila nake samun sleepless night, duk yarinya ta bi ta xama mace ta ko ina, wnn ai idan ba ayi hankali ba ma 'ya 'yan masu kudi ne xa su dinga tururuwa a kanta, wani d'an me kudin kawai ya aureta, ni kuma haka baxai min ddi ba ai, ta ma ci riban rayuwa da mu bayan tarwatsa nawa rayuwar da tayi knn, auren ne ni bana son tayi kwata kwata gwara ace ta kare a iskanci ma kawai, har yau fa Barrister fitowa fili ne kawai baxai yi ya gaya min ba haushi na yake ji tunda amaryarsa ta ki dawowa, don ma ban barsa haka ba, komai dai na tambayesa xai min kuma ko xan kwana ina masa bala'i baya tankawa, amma ba shi da walwala irin rayuwar mu ta da, shi dai gashi nan ne kawai, ke ni akwai ranan da na dau wayarsa na duba kusan kullum ashe sai yyi ma Rahinar text message, sae dai kawai ni banga tana reply ba, to kin ga kuwa ai bani da babban makiyiya kamar Heedayah" Shiru Mumy tayi da mugun mamaki bayan an bude kofa Abba ya shigo da sallama, Hajiya Sadiya ta amsa sallaman tana masa sannu da xuwa tana sissinne kai kamar munafuka, ya nufi parlonsa bayan ya amsa, Mumy ta kalli Hajiya Sadiya tace "Ko lafiya ya dawo da wuri haka yau, Allah ya sa kofa dai a rufe yake da na shiga uku, bari in je in ji ko lafiya" mikewa tayi ta wuce parlon Abba, Mumy na kallonsa a bedroom dinsa tace "Lafiya barrister?" Ba tare da ya juyo ba yace "Lafiya lau" tace "Ina kuma xaka haka?" Yace "I will be going to Abuja now" Tace "Ohk aiki?" Yace "Noo, ynxu aka kirani ba a ga Heedayah ba" Still Mumy tayi tana kallonsa da mugun mamaki, lkci daya tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ba a ganta ba kuma? Kamar Yaya? Ina ta je? Kuma me xaka je yi a Abuja ance ba a ga Heedayah ba a nan" Abba bai kuma ce mata komai ba ya dau abinda xai dauka ya fita dakin, Da sauri Mumy ma ta fito amma tuni har ya fita parlon, ganin Hajiya Sadiya bata parlon Mumy ta wuce nata parlon da sauri sanin cewar can ta tafi, kulle kofar parlon Mumy tayi tana kallon Hajiya Sadiya idanuwanta kamar xa su fito tace "Sadiya wai kinji ba a ga Heedayah ba" Sadiya ta mike tsaye tace "Ba a ganta a ina ba?" Mumy tace "Oho ynxu Barrister ke gaya min, ya kuma kiyi min gamsasshen bayani wai yanxu Abuja xai wuce, bari dai in kira Shuraim nasan kila uban ya kirasa" Gaba daya farin cikin Mumy a fili yake, tana neman wayarta tace "Allah ubangiji yasa guduwan tayi da gaske, kuma ta bar gida kenan har abada taje can tayi duniyanci, to ko dai a Abujan ta gudu Barrister xai je, to me ya kai ta Abuja kuwa" Dialing number Shuraim tayi bayan ta ga wayar, har ya katse bai dauka ba, ta kira ya kusa sau hudu snn ya daga, tace "Gidan uwar wa ka shiga nake ta kiranka no answer?" Gaisheta yyi ta amsa ta marairaice murya tace "Yanxu Barrister ke min bayanin da ban fahimta ba shine nace bari in kiraka nasan baxa ka rasa labari ba, Wai yanxu yake ce min ba a gaya Heedayah ba, wace Heedayar tukunna?" Shuraim yyi shiru har sai da tace "Hello" yace "Ehh ba a ganta ba" Mumy ta saki salati da karfi tana girgixa kai tace "Garin Yaya Shuraim, barin gidan tayi haka kawai ko guduwa tayi, innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Yace "Nima ban sani ba" tace "A gidan Rahinar aka nemeta aka rasa" Yace "I don't know Mumy, Abba ke gaya min nima" Tace "Toh Allah ya kyauta, bari in shirya in tafi gidan Rahinar, ba a ga Heedayah ba kuma sai kace allura, yaran yanxu kawai ka haifesu baka haifi halinsu ba, to ina xata ni Maryam?? Ohhh" Shi dai Shuraim bai ce komai ba, ta katse wayar.... ta saki wani shewa da kabbara tana kallon Sadiya baki har kunne tace "Ta shiga duniya Sadiya, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah na gode maka, Allah nagode maka, bari in shirya in je gidan kar a xargi komai Sadiya, tashi mu je" A nan take Mumy ta bar gidan tare da Hajiya Sadiya a motarta xuwa gidan Mami, banda shewa bbu abinda suke cikin mota Mumy ta cika wakar gwanja suna bi a motar, kai kana ganinsu kasan duniya ta masu dadi, Hajiya Sadiya ta kyalkyale da dariya tace "Kai dole ki kara ma wnn mutumi kudi Maryam, yanda kika san yankan wuka haka fa aikinsa yake" Mumy tace "Ai ko na kara masa ban yi asara ba wllh, to ni ko me kudi Heedayah ta aura yarana basu samu haka ba duk da na rabata da barrister ai ci baya ne gareni hakan, amma kinga duk kyan mace tana duniyanci uban wa xai dubeta, ba ga Salima ba dai" Hajiya Sadiya tace "Wnn gaskiya ne aminiya" Mumy na parking ta sauka tare da Sadiya, nan me gadi ya sanar masu ai Mami na Abuja, cike da damuwa Mumy tace "Kawai sai aka nemi yarinya aka rasa, wai garin yaya hakan ta faru" Mai gadin yace "Wace yarinya Hajiya" Nan Mumy ta gane bashi da labari ta ja kawarta suka bar sa tsaye wajen, sai da suka hau saman titi Mumy tace "Bari mu je gidan Dakta nasan baxa a rasa labari a can ba, xa mu ji yanda komai ya faru in sha Allah" haka aka yi suka tafi gidan Baffa, Ko bangaren su Umma Mumy bata shiga ba ta wuce gun kaka, Kaka na wankin bandaki suka nemi waje suka xauna, ta leko jin alamar an shigo mata daki, ganin Mumy ta ajiye roban ruwan hannunta ta fito da sauri tace "Maryam dama turo Rabi'ah da kika yi gidan nan cewa kika yi ta xo ta dinga min rashin kunya tana xagin iyayena?" Mumy tace "Xagin iyaye kuma?" Kaka tace "Wllh kuwa, ni dai nayi mata koran kare nace ta tafi tunda ba ita ta haifa min Umarun ba, yanxu ma sauri nake in tafi in ga ko ta tafi din don wllh baxata kwana gidan d'a na yau ba, tana raina uwarsa uban me xata tsaya yi masa a gida banda ita shashasha ce, ke dai baki iya haihuwa ba, yara duk munana sai baki kamar hancin saniya, shi dai Shuraim Allah ya rufa masa asiri ya yo sa kyakkyawa sam6alele" Mumy da ba abinda ya kawota ba kenan ta dakatar da xancen kaka ta hanyar cewa "Ya muka ji da abinda ke faruwa kaka??" Kaka tayi shiru tana kallonta, can ta nemi kujera ta xauna tace "Me ke faruwa??" Mumy tace "Au wai baki sani ba dama?" Kaka da ta rikice tace "Wllh bani da labarin komai Maryam, me ke faruwa" Mumy ta mike tace "Atoh ba kya ji a bakina ba kaka, tashi mu je Sadiya, na xata ai kin sani ne muka xo jaje" kaka ta rushe da kuka tace "Ni dama ae ba bakin komai ba nake a gidan nan ba, bbu wanda yace min komai, asara aka yi ne bani da labari?" Mumy tace "Aa jita jita ake wai ba a ga Heedayah ba tun jiya da safe, na xata an sanar maki shi sa ma na xo ai" Mumy bata jira cewar Kaka ba ta ja Sadiya suka fita parlon, Kaka ta bi su da kallo kamar warce aka dasa a wajen, can a hankali tace "Wacece Heedayah kuma?" Shiru ta kuma yi na kusan minti daya, sai kuma kamar warce aka tsikara ta rafka wani uban salati tace "Ba a ga wace Deedayar ba kuma? Amma Maryam anyi matsiyaciya, fatan bata take ma yarinyar xata ce ana jita jitan ba a ganta ba, ke ba gidan Rakiya kike xuwa ba, ke bbu hadin ki da yarinyar nan, to meye na xuwa ki gilla karya kice ba a ganta ba kamar wata sakakkiyar akuya, to bakin ki ya sari danyen kashi, sai dai a nemi Salima a rasa ba Deedayah ba, a xo ma a kai ni gidan Rakiyar kwana biyu ban ga Deedayar ba, jiya Ina jin ma kamar nayi mafarkinta, Amadun ma a xo a kira min shi ban ji dadin wnn mugun alkaba'in na Maryam ba" Karfe uku ya wuce Khaleel ya iso gida tare da Zayyad a motar Zayyad din, Zayyad yace "Why don't you just go to where u picked her from kaji ko ta koma gida Khaleel" Khaleel da gaba daya ya koma kamar wani mara lafiya ya juya yana kallon Zayyad, Zayyad yace "Yess, she can decide to just go back home at last, ka daina ba kan ka wahala haka, beside you need rest, don't stress ur self much, u know ur condition Khaleel" Khaleel ya jinginar da kansa da kujeran motar yace "What will I say idan naje gidansu, and wnn sojan nan dama I've made a vow, it's either I or him, nasan xai yi xargina idan na je gidan, contact dina da shi baxai yi kyau ba" Zayyad yace "Toh ni ka bani address din gidan, xan je, xan san kuma abinda xan yi, but I am exhausted sai na d'an watsa ruwa na ci abinci snn in tafi" Khaleel that have no other choice yyi accepting din abinda Zayyad yace, coz he trust him, 100% trust, Zayyad ya sauka motar ya bude gate din da suka bari a bude tun safe da suka fita, Khaleel ya shiga gidan da motar yyi parking, Zayyad ya nufesa bayan ya kulle gate din gidan yace "Mun yi asaran jam'i, ko in ce kayi asaran jam'i" Khaleel bai ce komai ba ya nufi entrance din shiga gidan, he feels like he is going to fall sick at anytime, yasan he is harming himself stressing din xuciyarsa da yake yi, Zayyad ya bi bayansa yana tausayin abokin nasa, dafa sa yyi yace "You know what Khaleel, ka kwantar da hankalin ka plss, in sha Allah I will try my best xa mu ga yarinyar nan, ynxu ka yi sllh ka ci abinci ka sha drugs dinka and rest..." Khaleel yace "Alright" Bude kofar parlon da shi ma din suka bari a bude tun safe yyi, tsaye yyi bakin kofar bai shiga parlon ba, Zayyad dake bayansa yace "What happen? Why are u still?" Khaleel ya kasa cewa komai, Zayyad ya bi gefensa ya leka parlon, kwance take saman dogon kujera tana bacci peacefully, daga kasa kusa da kujeran kuma darduma ne da tayi sllh a shimfide da Hijab din da ya bata da asuba, Khaleel ya karasa cikin parlon walking tiredly yana kallonta, kujeran ya nufa ya duka a hankali yace "Heedayah" Lkci daya ta bude ido ta mike xaune da sauri tana kallonsa, shiru yyi yana kallonta shi ma, Zayyad dai yyi wucewarsa sama yana imagining irin wahalan da suka sha kan yarinyar nan tun safe ashe gata nan tana ta baccinta hankali kwance, tana mitsika idonta a hankali tana kallon Khaleel tace "I am hungry" Yace "Ina kika tafi?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Talk to me, yaushe kika dawo?" Tayi kasa da idonta tace "Tun daxu" xaunawa yyi saman kujeran da take xaune kai, ya jinginar da kansa da kujeran ya lumshe idonsa a hankali yace "You suffered me Heedayah, why did you leave, don't you know...." sai kuma yyi shiru, ya bude idanuwansa yace "But tell me, me yasa baki son komawa gidan ku, sun maki wani abun ne da baki son gaya min??" Kamar xata yi kuka tace "Ni dai baxan koma ba...." Yace "To Ina kike son in kai ki yanxu?" Tayi shiru tana kallonsa, can tace "Ina son in xauna a nan, da kai" Da mamaki ya xauna da kyau yana kallonta, ya girgixa kai yace "Noo Heedayah, it can't be, idan baki son xama nan gidan da ku ka sauka ne sai in mayar da ke Kaduna" tace "Kadunan ma bana son xuwa" Kallonta kawai yake bai ce komai ba, tace "Idan baxan xauna nan ba sai in tafi wani wajen" Da sauri yace "Aa xa ki xauna nan mana, kar ki tafi ko ina plss, kin ji" Jinginar da kanta tayi da kujeran bata ce masa komai ba, Yace "Me xa ki ci?" Tace "Rice and stew" yace "Ohk bari in yi sllh in tafi in siyo maki" Tv ya kunna mata ya kulle kofar da makulli don gani yake tana iya guduwa kuma, ya wuce sama yana waigota, sai da yyi wanka ya sauya kaya snn yyi sllh, yana xaune saman darduma yana kallon Zayyad dake kokarin kunna Cigarette yace "Hey pls not here Zayyad" Zayyad yace "Sbda budurwar ka na gidan?" Yace "No kawai kasan dai bana so" Zayyad ya saka a aljihu ya mike xai fita, Khaleel yace "Plss will you mind getting us food" Zayyad yace "Ohk" daga haka ya fita dakin, Khaleel ya mike ya bi bayansa, har sannan Heedayah na xaune parlon tana kallo, Zayyad yyi mata kallo daya ya nufi kofa, ita ko idonta na kan TV, Khaleel na daga stairs a tsaye yace "The keys" Juyowa Zayyad yyi, Khaleel ya jefa masa makullin kofar parlon ya cafke snn ya bude kofar ya fita, Khaleel ya karaso parlon ya xauna kujeran dake facing dinta yace "Wa ya dawo da ke nan gidan" Tace "Da kafa na dawo" yace "Ta ya kika gane?" Tace "kawai na gane" Yyi shiru yana kallonta bai ce komai ba. Flight Abba ya biyo xuwa Abuja coz baxai iya driving din ba kuma ba train, Mami dai a parlon Dinar ta yini, tayi kuka har ta gaji yau kam, abu uku kenan a rayuwarta da ya sa ta shiga tashin hankali da shock sosai, na farko kashe mijinta na farko a gabanta wanda shekaransu hudu da aure aka tafi da 3 years old son dinta wanda sai tashin labari, na biyu kuma rasuwan Mahaifinsu junaid, sae ynxu da aka nemi Heedayah ko sama ko kasa tun jiya, ita kanta ta rasa irin soyayyar da take ma Heedayah, tashin hankalin da ta shiga ko 'yar cikinta sai haka, Junaid yyi kokarin danne nasa damuwar sosai ba kadan ba ganin halin da Mahaifiyarsa ta shiga, ya dinga kwantar mata da hankali with assurance na cewar xa a ga Heedayah idan Allah ya yrda, ganin Shuraim yana kan komai ya sa Junaid ya tsaya tare da Maminsa kawai, duk wani information da Shuraim ya so samu ko kadan ne a kan Khaleel bai samu ba, don Farida dai bbu abinda ta sani a kansa, ko sama ko kasa kuma ta duba wayar da ya ba Heedayah bata gani ba, wanda hakan ke nuni da cewar da shi ta fita, broadcast kawai Shuraim ya bada a duk gidajen Radio da ma talabijin, sai ma da yyi hakan snn ya kira Abbansa ya sanar masa abinda ake ciki. Abba bai iya ce ma Mami komai ba bayan Shuraim ya kai sa har gidan, don yana sauka Airport Shuraim ya daukesa suka wuce, Abba na kallon Dinar dake xaune kasa da Hijab dinta har kasa ita babban abinda ke daga mata hankali yake sa ta kuka sosai sai cewa da mutane xa su dinga yi ai a gidanta abun ya faru, "Tun karfe nawa ta fita a jiyan?" Cewar Abba kenan yana kallon Dinar, tana share hawayenta a hankali tace "Ba ayi isha ba, duk muna nan parlor a xaune ta shiga kitchen, ni ina ce abinci ma ko wani abu xata dauka, ashe bude kofar kitchen din da ke nan nafi shekara ban bude ba tayi ta fita, shi kuma me gadi be sani ba ya bude mata gate...." Tana kai wa nan ta kuma rushewa da kuka, Abba yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Mami dai bata cewa komai sai hawayen da take gogewa, Shuraim dai na tsaye bakin kofar parlon yana rungume da hannunsa, tun safe ko ruwa shi kam bai sha ba dama, Abba na kallon Farida yace "Ke kinsan inda ta san shi mutumin da ya bata waya" Cikin sanyin murya Farida ta sauke idonta kasa ganin no need of hiding anything again, ta shiga yi ma Abba bayani tace "Ranan mun je shopping Mutumin ya tare mu a hanya muna dawowa...." Shuraim ya sauke hannunsa yana sauraronta keenly haka ma kowa na parlon, nan ta bada labarin yanda Heedayah ta fara haduwa da Khaleel, ta kuma ce daga nan bata sake sanin suna haduwa ba har ya bata waya sai just of recent lkcn bikinsu Aunty Jamila, shi ma din Heedayah bata bari ta sani ba, Abba dake ta kallonta yace "Ya sunan hotel din da ku ka fara ganinsa" Nan Farida ta gaya masa, Abba yace "Xa ki iya tuna date, day, da time din da ku ka gansu bakin hotel din" Farida tayi shiru tana naxari, Abba yace "Relax and think calmly dear, the date, time and day...." Mami dai sai kallonsu take gaba daya. Khaleel na kallon Heedayah ta gama cin abincin gabanta ta matsar da plate din, yace "Kin koshi?" Ta gyada masa kai tana kallonsa tace "Why is ur frnd smoking?" Ya d'an bude ido yace "Where did you see him smoke?" Tace "Naji warin cigarette sae na leka window na gansa parking space smoking..." Shiru tayi ganin Zayyad na sakkowa kasa, Khaleel ya bi sa da kallo ganin ya nufi kofa, Zayyad yace "I'm leaving, enjoy ur self Kayy" Khaleel ya mike yana kallon Heedayah yace "Let me see him off" ta gyada masa kai, daga haka ya bi bayansa, Heedayah ta bi su da kallo har suka fita, Zayyad ya bude gate ya fitar da motarsa waje, Khaleel ya tsaya kusa da motar yana kallonsa kafin yace komai Zayyad yyi masa wani murmushi yace "But tell me, how was ur experience yesterday night, nasan baka ta6a ba" Khaleel yace "What experience?" Zayyad ya kashe masa ido yace "Sai na tona" kallonsa kawai Khaleel ke yi, Zayyad ya fashe da wani dariya, sae a snn Khaleel ya gane inda Zayyad ya dosa ya dinga masa wani kallo, Zayyad yace "Don't bother her much, she is too young" Khaleel yyi ignoring din xancen yace "Plss I need a favor" Zayyad yace "All ears" Khaleel yace "Ko da yake mu yi waya kawai" daga haka ya juya ya koma cikin gidan ya kulle gate dinsa. Tun da aka yi Magrib Khaleel na masallaci har sai da Zayyad ya kirasa snn ya fito, Zayyad ya sakko daga motarsa rike da ledan fresh milk ganin Khaleel, yace "A ina ka bar visitor din taka?" Khaleel yace "Tana ciki" bude gate din yyi suka shiga ciki tare, Khaleel na kallonsa yace "Did u get d pill??" Zayyad yace "Sure..." A aljihu ya ciro pills din ya basa, Khaleel ya amsa yasa a nasa aljihun, snn suka shiga Parlorn, xaune suka Heedayah tana shan pineapple tana kallo, Khaleel ya amshi ledan hannun Zayyad, Zayyad ya wuce sama shi kuma ya wuce kitchen, glass cup ya dauka ya xuba milk din ciki snn ya ciro pill din 6alli daya ya saka, ya sa cokali sae da ya tabbatar ya narke snn ya fito parlor, xaunawa yyi kusa da ita ya mika mata, tace "What's that?" Yace "Milk" tace "Na koshi" yace "Noo ki sha kadan mana, sai in shanye sauran" amsa tayi ta sha kusan rabi snn ta mika masa, ya sakar mata murmushi ya amsa ya ajiye, ta maida dubanta kan tv, yana ta xaune kusa da ita har ya ga ta fara hamma, ya kalleta yace "What?" Kanta ta daura kan kujeran a hankali tace "Bacci" ya mike yace "To kwanta" Ba musu ta kwanta ta lumshe ido, ya koma wani kujeran yana kallon kyakkyawan fuskarta ko kiftawa bbu, bayan kusan minti goma ya mike ya tafi sama sai gashi sun sakko da Zayyad, Zayyad yace "Toh wai idan mun je can din sai in ce me tukun?" Khaleel yace "You just explain ka ganta ne a bakin hanya, kawai dai kayi composing duk abinda xaka ce I trust you, I'm really disturbed Zayyad, nasan ynxu her guardians are very worried, ita kuma naga alamar she is serious ba komawa xata yi ba, I don't know what came over her all of a sudden" Khaleel ya nufi Heedayah dake ta bacci, dukawa yyi yana kallonta ya dauketa a hankali kamar wata yar tsana ya nufi kofa ya fita Zayyad ya bi bayansa ya kulle gidan, a bayan motar Zayyad ya kwantar da ita still looking at her, Zayyad ya shiga maxaunin driver, Khaleel ya rufe motar daga karshe ya koma front seat, Zayyad ya tada motar suka bar layin, tafiyar kusan minti talatin suka yi suka isa street din su Dinar, Khaleel yace "Drop me here, gida na daya, na biyu na uku.... I think na biyar shine gidan da take, you just step down and knock the gate" Zayyad yace "Ohk" sauka Khaleel yyi da face cap dinsa da ya kafa a kansa ya rufe kusan rabin fuskarsa yyi wucewarsa walking calmly ya bar area din. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Driving Zayyad yake yi carefully yana kirga manyan gidajen da yake wucewa a layin, har ya tsaya a dai dai gida na biyar kamar yanda Khaleel yace masa, a hankali ya bude motar ya sauka ya nufi gate din yana kare ma gidan kallo, da zoben hannunsa ya kwankwasa gate din, bayan few seconds ya kuma kwankwasawa, dai dai nan aka bude gate din, wani ne sanye da khaki hannunsa rike da bindiga ya gani, sai ga Mai gadin gidan ma ya taho da sauri, Zayyad ya d'an sosa kansa yace "Erm don Allah tambaya nake" Me sanye da khaki na kallonsa fuska a murtuke yace "Go on..." Zayyad yace "Na xo wucewa ne daxu na hadu da wata yarinya bakin hanya, she was almost unconscious, so being the good Samaritan that I am na nemi gefe nayi parking na sauka coz she looks responsible, nan kuma na tambayeta abinda take yi bakin hanya da daren nan, I have to listen with both my heart kafin in fahimce me take ce min, that dumping dinta wai wasu suka yi a wajen suka wuce, I asked her wani anguwa take, and she mentioned here with both the address, daga haka kuma she passed out, wato ta suma, I hate police cases snn ni matafiyi ne ba d'an Abuja ba, bana son kuma duk wani abu da xai hadani da Yan sanda su bata min lkci, to tunda dai ta bani address din inda take shine na dai sakata a mota na kawota nan din da tace min gidansu ne, ina kuma fatan shine gidan nasu" daga Mai gadi har masu khaki biyu dake tsaye bakin gate din kallon Zayyad that is speaking confidently suke suna sauraronsa da kyau, daya daga me khakin sojan ya fita xuwa gun motar Zayyad holding on to his gun, ya leka cikin motar yana kallon Heedayah dake bacci gently, komawa yyi yana duban Zayyad yace "I think it's better ka kai ta police station din for police report ba yar gidan nan bane, kuma shi xai fi maka sauki" Mai gidan ne da matarsa ke tahowa xuwa parking space alamar xa su fita don makullin mota na hannunsa, kuma dama jiransa sojojin suke ya fito kasancewar su excort dinsa na nan garin, ganinsu tsaye bakin gate din gidan har yana hango Zayyad yasa Mai gidan yace "Allow him, if he wants to see me, let him plss" Sojan ya koma gefe Zayyad ya shigo compound din yana kallon Mai gidan almost shocked, walking calmly Mai gidan ya iso har gabansa ya tsaya ya basa hannu with smile a fuskarsa suka yi musabaha, Mai gidan yace "Kana son ganina ne gentleman, kaga kuma xan fita yanxu but in sha Allah ka dawo gobe da safe xan ganka" Zayyad dake ta kallonsa ya fara kame kame yace "Noo, A'a dama yarinya na kawo, i was thinking gidansu ne nan, tace min nan ne gidansu, Kuma address din nan ta bani, I saw her almost unconscious a hanya and decided to help her" da mamaki Mai gidan yace "Yarinya? Ina yarinyar take yanxu?" Zayyad yace "Tana cikin motana" gaba daya Zayyad a daburce yake ya ma ki yarda su hada ido da Mai gidan, Mai gidan yace "To shigo da motar taka" Zayyad ya juya da sauri xai fita and dama yyi niyya idan ya samu ya fita to fecewa kawai xai yi abunsa, daya daga sojan ya dakatar da shi, snn shi sojan ya fita kamar yasan abinda ke ransa, Mai gadi ya bude gate din gidan sojan ya shiga motar Zayyad snn ya shigo da motar cikin compound din, matar da suka fito tare da Mai gidan ta karaso gun me gidan nata tace "Abiey Ina jin yarinyar da Mum Islam tace ake nema a gidan makotan mu ce fa, kilan bai gane kwatancan nata bane, nan makotan mu ya kamata ya kai ta" Zayyad dai sai keto masa xufa yake yana sharewa with swag, Mai gidan ya nufi motar da sojan yyi parking a tsakar compound yana duba cikin motar, Tana kwance har snn sai da kusan rabin fuskarta rufe yake da mayafin abayarta kamar yanda Khaleel yayi mata tun daxu da ya kwantar da ita a motar, sojan ya bude motar ya yaye mayafin daga fuskarta bayan ya kunna wutan motar, kallonta kawai Mai gidan ke yi without blinking, ita dai matar na tsaye taki leko cikin motar tace "Ko a kira Mum Islam nasan baxata rasa sanin yarinyar ba tunda tana shiga gidan sosai" Sojan dake tsaye bakin motar shi dai ya kalli Heedayah snn ya sake kallon matar Mai gidan nan, yyi hakan yyi sau uku, Jin shirun da Mai gidan nata yyi, matar tace "Abiey Ina magana, nace should they call Mum Islam ayi alerting din neighbors din namu" Can dai ta gaji da magana ganin mijin nata ya ki cewa komai, ita ma ta leka cikin motar tana kallon Heedayah, Dafa ta Alhaji Ahmad yyi xai janyeta daga motar ta fixge hannunta da sauri, ta fi minti daya tana kallon Heedayah da idanuwanta kamar xa su fito, can ta xaga daya side din motar da sauri har tana neman faduwa, da mamaki ta sa sojoji da Zayyad da suke tsaye wajen ke kallonta, ta bude motar tana sake kallon Heedayah kirjinta na Heaving, har wani rawa hannunta yake ta kamo hannun Heedayah na dama ta daga rigar Abayarta tana duba hannun, ta kara xaro ido sosai snn ta juya wuyar Heedayah nan ma ta ga black dot din da take son gani, wani kara me karfi tayi da ya farkar da Heedayah daga nan kuma ta sulale wajen, Heedayah ta kara lumshe idonta sbda har sannan maganin bai saketa ba nan ta kuma komawa duniyar bacci, da sauri Mai gidan ya xaga xuwa inda matarsa ta fadi sojojin ma duk suka bi sa da Mai gadi, Zayyad dai was extra confuse, ga wayarsa dake ta vibrate a aljihunsa ya san kuma Khaleel ne ke kiransa, Mum Islam da ta ji karan uwargidan nata ta fito da sauri daga bangarenta, Tuni Mai gadi kuma ya tafi dauko ruwa daga dakinsa da gudu, Daya sojan sai fifita yake ma Madam din Mai gidan nasu da hularsa, Alhaji Ahmad dai ya dago matar tasa yana kiranta amma ta suma, a rikice mum Islam tace "Abiey lafiya?? what happened, jikin nata ne ya tashi?" Ta amshe ta hannunsa ita ma tana mata fiffita da gefen dankwalinta tace "Asibiti xa mu tafi yanxu" ganin hawaye fuskan mijin nasu ya sa Mum Islam tayi still tana kallonsa, a hankali tace "Subhanallah is everything alright Abiey, wani abu ya faru ne ta fadi" Daukar matar tasa kawai yyi yana kallon Zayyad yace "Bring the girl in" daga haka ya wuce ciki yana rike da wife din tasa, duk sai mum Islam ta ji ba ddi tayi jigum tana bin su da kallo bata mike daga durkushen da take ba, Zayyad ya fiddo Heedayah daga cikin motar, da ido Mum Islam ta bi Heedayah da kallo tace "Wacece wnn kuma?" Sai kuma ta wani xaro ido ganin kamar da Heedayah ke yi da co wife dinta, lkci daya ta mike ita ma jikinta ya dau tsuma tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." Ta furta haka ya fi a kirga, sai kuma ta bi bayan Zayyad da yabi bayan Mai gidan nasu da sauri, Mai gadin ya girgixa kai shi ma dai har da hawayensa yana kallon sojojin that all look confused yace "Sai gashi har gida an dawo mata da 'yar ta da ta bace yau shekara kusan biyar kenan, bbu tantama wnn yarinyar 'yar uwar gidansa ce" Zayyad ya kwantar da Heedayah nan tsakiyar lallausan carpet dake parlon, Alhaji Ahmad kuma ya kwantar da matarsa saman kujera wanda a nan take ta bude idonta, ta mike xaune weakly, da kyar ta fashe masa da kuka tana rike da hannunsa tace "Wllh Heedayah na gani Ahmad, wllh Heedayah ce, daughter na ce, tana Ina yanxu? Ina ku ka bar ta" Alhaji Ahmad ya koma gefenta yanda xata ga Heedayah dake kwance parlon, Kukan da Mum Islam take kai kace ta ta6a ganin Heedayah ko ta ta6a saninta, Kuma har xuciyarta take farin cikin bayyanar 'yar kishiyar tata bayan an fidda rai da dadewa, Kuka sosai Mahaifiyar Heedayah take tace "Ahmad idan mafarki ne wnn Allah ubangiji kada ya bani ikon farkawa, idan na farka naga mafarki nake nasan kilan karshen rayuwata ne ya xo coz I won't be able to stand it, let it not be a dream plsss, baxan iya ci gaba da rayuwa ba idan na farka naga mafarki ne" Mum Islam ta durkusa kusa da ita ta rikota tace "You are not Dreaming Mum twins.... We all are not Dreaming, Heedayah ce ba mafarki bane" Zayyad was so emotional at that time, ga confusion da ya dabaibayesa ta ko ina, but Khaleel yace masa a jiya ya dauketa daga gida, then why are they acting kamar sun yi shekara da shekaru rabonsu da ita, and wnn ai shine Mutumin da suka so kidnapping shekaranjiya, shine Alhaji Ahmad dake neman takarar gwamna how is this girl his daughter..... Mahaifiyar Heedayah ta rungume kishiyartata tana kuka sosai tana cewa bata son farkawa daga wnn mafarkin da take yi don tasan ba gaskiya bane, she is just dreaming, meeting with her daughter can't be just like a film to her. Khaleel ya kira Zayyad ya fi a kirga no response, hankalinsa ya tashi ba kadan ba, ya ma rasa tunanin da xai yi, gidan ne bai kai ta ba deceiving dinsa yyi duk da yasan Zayyad just can't do that, ko kuma ya kai ta aka kamasa, he don't know which to keep in mind, he don't know which to imagine, gashi ya ki komawa gida duk da ciwon da yake ji a xuciyarsa yana dai ta xaune inda suka yi xa su hadu idan Zayyad ya ajiyeta a address din da ya basa, ganin this is almost an hour hakurin Khaleel ya kare gaba daya, da kafa ya koma har layin, sai dai he is really not fine, at anytime he can fall sick ya sani, tafiyar ma daurewa kawai yake yi, yana isowa dai dai gate din gidan Deenar ya tsaya thinking of what next to do, gaba daya bbu alamar motar Zayyad a layin sai dai ga wata bakar mota a dai dai kofar gidan Dinar din, ya sake ciro wayarsa ya kira layin Zayyad for the countless time no answer, har ya kai hannu xai buga gate din dai dai nan aka bude, At first baya Khaleel ya koma da sauri ba tare da ya bari ya ga ko waye ba, bayan few seconds ya dago kansa ya ga ana pointing dinsa da bindiga, kallon Shuraim kawai Khaleel ke yi, da mamaki Abba ya kalli Shuraim yace "Hey, What's that u are doing Shuraim, I told u bana son kana bi na da bindiga, meye hakan...." Asp na Yan sanda dake wajen shi ma don duk tare suka fito Calmly yace "Drop that Shuraim, sure everybody is a suspect now, but...." Shuraim yyi wani murmushi yana kallon Khaleel da kyau yace "Shine saurayin da ya tafi da ita, he is the main suspect" yana fadin haka ya isa dai dai gaban Khaleel ya mayar da bindigan aljihunsa yana kallonsa fiercely nan take yyi masa naushi har biyu a ciki, lkci daya idanuwansa suka sauya kamanninsu just as the soldier he is yace "Ina ka kai Heedayah???" Junaid was just still a bakin gate din yana kallon Khaleel, Asp ya kwace Khaleel daga damkar da Shuraim yyi masa, da ido Khaleel ya bi Shuraim da kallo ko kiftawa bbu, Asp ya xaro handcuff din aljihunsa yana kallon Khaleel yace "You are under arrest" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Abba ya dafa Asp a hankali yace "Sir, isn't it good mu fara jin abinda ke tafe da shi tukun..." Asp ya girgixa kai strictly yace "That will be at the station not here, a suspect??? Noo" Handcuffing din hannun Khaleel dake ta kallon Shuraim ta gefen ido yyi in both hands, yana pointing dinsa da pistol din hannunsa Incase he should make any attempt of wanting to escape, ba musu Khaleel ya nufi motar da Asp din ke nuna masa yana biye da shi bayansa, nan yyi instructing din Shuraim ya biyo su, Khaleel ya sake kallon Shuraim kafin ya shiga motar da Asp ya bude masa, kawai he just don't want to escape ne banda haka pistol din Asp bai bashi tsoro ba, minti nawa ne xai yi guduwan sa kuma bullet dinsu baxai ta6a shi ba, but he can't just run without knowing if Heedayah is home or not, ynxu bai san ko Zayyad ya kawota gidan ko bai kawota ba, Junaid dai har sannan yana tsaye bakin gate tare da Abba, Abba ya dafasa yace "Let me go with them, Kai kuma ku taho station din tare da Barrister yanxu...." Junaid ya gyada masa kai snn ya juya ya koma cikin gidan. Khaleel na xaune yana facing wani d'an sanda dake masa tambayoyi yana rubutu a report book dinsu, su kadai ne xaune wajen, Shuraim na daga bakin kofa a tsaye looking directly at Khaleel dake magana calmly without any fear, he felt like shooting Khaleel ko xai ji saukin abinda xuciyarsa ke yi masa, bai ta6a jin he wants to use his gun on someone ba irin Khaleel, Mami dai na xaune ita ma a sanyaye tana kallon Khaleel, gaba daya ta dawo kamar warce ta tashi ciwo sbda damuwa, wnn dalilin yasa Abba bai bata fault ko kadan ba duk da without knowledge dinsa Heedayah ta taho Abuja which isn't right but he never blamed her even for a second, Abban ma dai da Junaid na xaune wajen, sai Mijin Dinar da ya dawo a ranan shi ma yana gun a xaune, Dpo na xaune shima yana ta rubuce rubucensa shi ma a gurin, police officer din na kallon Khaleel yace "Bayan ka tafi da ita sai aka yi yaya?" Khaleel yace "A jiyan nace xan dawo da ita gida tace baxata dawo ba..." Police officer din yace "A daren still?" Khaleel yace "Eh" Police officern na gyada kai bayan ya gama rubutu yace "To sai aka yi yaya?" A takaice Khaleel yace "Sai na wuce da ita gidana" Hawaye ya shiga sakkowa Mami uncontrollably, Shuraim ya dauke kansa daga kallon Khaleel jin wani abu da ya tokaresa a kirji, Abba dai ya sauke kansa kasa, Junaid ya shafa kansa ya nemi waje ya xauna daga tsayen da yyi a wajen, Police officern yace "A gidan naka ta kwana kenan?" Khaleel yace "Ehh" police officern yace "Go on, sai aka yi yaya" Khaleel yace "Da safe after breakfast nace xan mayar da ita gida, tace min she isn't going back home, I insisted and she ran away without me knowing" Police officern yace "She ran away from ur house?" Khaleel yace "Yes, but after 4 hours ta dawo gidan nawa, bana gidan ma lkcn da koma coz I was looking for her from the moment I noticed ta bar gidan, na dawo da yamma na ganta kwance parlor tana bacci, I have to make plans with my frnd kafin in basa ita ya mayar da ita gidan da na daukota" Dpo ya daga kai yana kallonsa yace "Wani plan kenan?" Khaleel yace "Na sa mata pill din bacci a lemo, bayan tayi bacci sai muka tafi da ita da abokina na nuna masa layin, na kuma gaya masa house number din snn na sauka motar nace ya karasa da ita" Dpo yace "Me yasa kai baka kai ta ba?" Khaleel yace "Because I remain a suspect a gidan, duk da I didn't take her to my house intentionally, na tambayeta ko anyi mata wani abu a gidan ne da tace she isn't going back, tace min nothing, she only want to stay with me" Kallonsa kowa na wajen yake yi, Mami dai sai kuka take don tasan ba training din da tayi ma Heedayah bane, something might be wrong somewhere" Dpo din yace "Toh abokinka bai kai ta gidan ba, and now tell us more about him, and where he stays...." Khaleel yace "I've been calling him but no response, shine ma yasa na tafi gidan to check if she is home..." Dpo din yace "Ya sunan frnd din naka?" Shiru Khaleel yyi, Dpo ya masa wani kallo yace "You Answer me...." Khaleel yyi kasa da idanuwansa yace "Zayyad" Dpo yace "Full name?" Khaleel yace "Zayyad Idris" Dpo yace "A ina yake xaune" Khaleel ya shafa kansa bai ce komai ba, dai dai nan wayarsa ya fara ring a pocket dinsa, xai ciro officern dake facing dinsa ya dakatar da shi ya mike ya ciro wayar da kansa, ya kalli screen din snn ya nuna ma Khaleel yace "Waye yake kiran ka?" Khaleel yace "Zayyad, shine ke kiran" Officer din ya daga ya sa handsfree snn ya mika ma Khaleel, lkci daya Khaleel ya ji gabansa ya fadi ganin handsfree d'an sandan ya sa wayar, daga Mami, Abba, Junaid da mijin Dinar duk kallon Khaleel suke, don Shuraim tun da ya fita bai sake dawowa ba, Daga daya bangaren Zayyad yace "Tell me Brainiac wacece wnn yarinyar da ka bani kace in mayar gida, for how long take wajen ka??" Khaleel yace "Why were you not picking my call?" Zayyad yace "No tell me yaushe ka fara rayuwa da yarinyar, how long??? coz ni na kawota gidan da kace and ban gane drama din da mutanen gidan suka yi displaying ba after seeing her, shekaranku nawa tare da yarinyar ni ban sani ba" Khaleel yace "Wani gidan ka kai ta??" Zayyad yace "Gidan da kace mana, I am even still at the house now, her father ya ki bari in tafi, it seems the girl have been away from home for long faaa" Gaba daya occupant din office din kallon wayar Khaleel suke listening to what Zayyad was saying, Khaleel yace "Are you sure layin da muka tsaya ka shiga?" Zayyad yace "Haba, shine wllh, and you know what Khaleel????" Khaleel yyi shiru, Zayyad yyi kasa da murya yace "Gidan Alhaji Ahmad ne, shine Mahaifin yarinyar, ka gane wani Alhaji Ahmad din?" Kittt Khaleel ya katse wayar, Officern dake kallonsa yace "Hey, Why did u cut the call??" Khaleel yace "Layin xa mu je da yace ya kai ta, sai a dubata a nan" daga Mami har Abba kallonsa suke keenly, Abba yace "But y did you end the conversation that way, when he is talking?" Khaleel ya kallesa bai ce komai ba, Abba ya kalli Dpo dake office din yace "I think ya kamata su gama maganan, he should call him back" officern na kallon Khaleel yace "sake kiransa" Mami ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace "Da dai mu fara xuwa mu ga halin da yarinyata ke ciki don Allah dpo, Ko xan samu nutsuwa" Dpo yace "Their conversation will take just few minutes Madam kiyi hakuri, xa mu je can din yanxu, ka sake kiransa" Dpo ya fadi haka yana kallon Khaleel, Khaleel ya sauke idanuwansa kan wayarsa ya sake dialing Number Zayyad, Zayyad na dagawa Khaleel yace "Be brave Zayyad.... where are you at now?" Wani kallo Dpo ya jefa ma Khaleel, ya tashi da kansa ya katse wayar yace "Maganar da yake maka daxu xaka ce ya ci gaba.... Keep on to that conversation" Khaleel yace "Ohhh, ohk" Daga haka ya sake kiran Zayyad, Zayyad na dagawa yace "Yauwa, Brave you, kace gidan wa kake?" Zayyad ya d'an yi shiru snn yace "Gidan Baban yarinyar..." Khaleel yace "Maintain... So waye baban yarinyar?" Zayyad yace "Uhn sure..., I just learnt that Alhaji Ahmad ne, wanda ke neman takarar gwamna na jihar kano, so I was surprise, ashe babanta babba ne... That's all abinda xan fada maka, sai kuma ince why did she decide to leave home" murmushi kawai Abba yyi, Mami dai sai kallon Khaleel take, police officer ya katse wayar, Dpo ya mike yace "Xa ku tafi can anguwar tare da Asp Ina jin" motar yan sanda daya suka shiga, wanda Khaleel ne ciki da two police men, sai Shuraim dake motar shi ma, Mami da Junaid suka shiga mota daya, Abba da Mijin Dinar su ma mota daya suka hau suka bar police station din. Officer daya ya sa Khaleel ya sake kiran Zayyad ya tambayesa gida na nawa ne, Zayyad yace "Gida na biyar...." dai dai gidan Alhaji Ahmad duk motocin suka tsaya suka sakko, mijin Dinar yace "Wnn ai gidan makocina ne Honorable...." Asp ya bubbuga gate din, Yan sanda biyu na tsaye tare da khaleel, ba a dau lkci ba aka bude gate din, Dpo ya gaisa da sojan da ya bude gate din Snn ya nuna masa ID dinsa yace "Muna son ganin me gidan nan ne...." Sojan yace "Alright, bari ayi alerting dinsa" kulle gate din yyi ya koma, Jikin flowers Shuraim ya tsaya fuskarsa bbu walwala, ya ki yrda ma ya kalli direction din Khaleel kar xuciyarsa yyi explode, gaba daya he is just restless da bayanin da Khaleel yyi a station, su Mami da Abba duk suna tsaye bakin gate din, ita dai Mami fatan ta a ga daughter dinta kuma ko kwana ta dau ma kanta alkawarin baxa su yi a Abuja ba xata dauketa su koma gida, da ta tuna wai gidan namiji ta kwana jiya sai taji hawaye na mata xarya, bayan wani lkci Alhaji Ahmad ya bude gate din da kansa, da kallo ya bi dukansu snn suka gaisa da Asp dake kallonsa shi ma, Asp na murmushi yace "Sorry for the disturbance Honorable, amma daxu an shigo da yarinya gidan nan kuwa.... They mistook here for the girls home" Alhaji Ahmad ya d'an yi shiru duk yana kallonsu, can ya gyada kai cikin sanyi yace "Kwarai an kawo yarinya gidan nan daxu" Asp yace "Fatan tana nan gidan har yanxu?" Alhaji Ahmad yace "Sure, tana nan" Asp yace "To Alhmdllh, xa mu shiga mu tafi da ita ynxu" Mami bata san lkcn da ta sauke wani bayyanannen ajiyar xuciya ba, taji wani farin ciki ya lullubeta, Alhaji Ahmad dai bai ce komai ba ya basu hanya duk suka shiga gidan, k'in shiga Shuraim yyi ya nufi titi walking like the soldier he is, Khaleel dai sai kallon Alhaji Ahmad yake bayan sun shiga gidan, har suka isa building din Uwar gidan Alhaji Ahmad, Har sannan Heedayah na kwance parlon still sleeping heavily, Zayyad kuma na xaune saman kujera, Mum Islam na kusa da Heedayah da family Doctor dinsu da ya gama dubata, Mahaifiyar Heedayah kuma na xaune ta takure waje daya sai kallon Heedayah take ita a dole she is dreaming and can wake up anytime, Mami ta karasa gun Heedayah da ta fara gani a parlon da sauri ba tare da ta bi ta kan mutanen dake parlon ba ta durkusa kusa da ita ta fara kiranta tana girgixa ta, a rikice tana kallon likitan tace "Me ya sameta Dr??? what's wrong with her" Mikewa Mum Islam tayi tana kallon Mami da mamaki bata son tabbatar da cewa Ita ce yarinyar da ake ta nema tun jiya a makotansu, Junaid dai na tsaye bakin kofar parlon sai kallon Mahaifiyar Heedayah yake, same goes to Khaleel that is shocked at the resemblance, Mami dai hankalinta gaba daya na kan Heedayah da take tadawa, Asp da Abba, da Alhaji Ahmad sai Mijin Dinar kadai ne waje basu shigo parlon ba har sannan, Heedayah ta bude ido a hankali, kana ganin yanda take bude idonsa kasan sun mata nauyi, murya can kasa tace "Mami" Rungumeta Mami tayi hawaye na sakkowa idonta tace "Ina kika tafi Heedayah, me yasa kika fita gida da daddare?? Where did you go to" A hankali Heedayah tace "I just felt like going Mami, Mami don Allah kiyi hakuri baxan sake ba" sai kuma ta fashe da kuka sosai, Mikewa Mahaifiyar Heedayah tayi daga inda take xaune hawaye na sakko mata ta wuce dakinta, Mami ta goge ma Heedayah idonta tace "It's okay daughter, we are going back to Kaduna now, in sha Allah..." Heedayah ta d'an yi shiru, sai kuma da sauri tace "Mami where is he?" Mami tace "Who" Heedayah tace "Ya Khaleel, shi ya dawo dani gida ko?" Mami bata saurareta ba tace "I don't know, we are going home now" Mami na fadin haka ta tashi tana dago Heedayah, Heedayah ta xame hannunta tace "Mami Ya Khaleel din fa? Da ya kawo ni wucewa yyi?" Sai a snn Mami ta juya ta kalli Khaleel bayan ta fahimci shi Heedayah ke tambaya, sosai gabanta ya fadi da suka hada ido da shi, don har sai da ta koma ta duka kasa, Heedayah ta shiga bin mutanen dake parlon da kallo, idonta ya fara sauka kan Zayyad, tashi tayi ta tafi gunsa da sauri tace "Ina ya Khaleel din, did he leave after bringing me home?" Zayyad ya nuna mata Khaleel da ke tsaye yana kallonta, kallon handcuffed hands dinsa ta dinga yi sai kuma ta tafi gunsa almost running tace "What's this, waye yyi arresting din ka?" Komawa gun Mami tayi hawaye cike idonta tace "Mami wllh nice na bi sa ba shi ya tafi da ni ba, shi ba ruwansa, he only helped me, he is innocent, tell them not to arrest him plsss" Dai dai shigowar Asp tare da su Abba da Mahaifin Heedayah, Asp ya karasa gun Khaleel da makullin handcuff din ya bude ya cire handcuff din daga hannunsa, Heedayah ta tafi gunsa tana kallon wrist dinsa cikin sanyi tace "I am sorry I caused you everything" Mami ta nufeta ta dafata tana kallon Khaleel da ya sunkuyar da kai bayan ya hada ido da ita, ta kama hannunta za su fita parlon, Asp yana kallon Mami yace "Ku dakata Hajiya...." Kallonsa Mami tayi da sauran mutanen parlon, Asp ya kamo hannun Abba dake tsaye gefensa yace "Barrister Ahmad d'an uwan abokina ne da muka yi karatu tare, and we are still family frnds till date, 5 years ago Barrister ya xo station dinmu da wata yarinya da baxata wuce shekara 12 ba, a blind girl, lkcn Ina kano ba ayi transferring dina xuwa Abuja ba...." Very briefly Asp Usman ya bada wnn takaitattcen tarihin, Asp ya ci gaba yace "Shekarun baya, like 2 to 3 years back mu kan yi waya da shi in tambayesa how is this little girl kafin daga bisanni na watsar sanin baxai cuceta ba don a lkcn yace min har tayi regaining sight dinta, don har lkcn mu ba mu samu wani labarin iyayenta ba, but I must confess it's a case we never took serious, ganin makauniya ce ita wnn yarinya kuma gata yar karama, nafi xaton daga less privileged home ya fito, ni Allah ya ga xuciyata kusan gata nayi mata na son in ga ta xauna gun shi wnn bawan Allah, nasan shi da iyalansa baxa su cuceta ba, xa kuma ta samu gatan karatu..." Yana nuna Heedayah yace "As at the time this lady got missing yesterday evening, d'an barrister ya kai report police station dinmu, but bana office then, sai daxu da rana abokina Dr Umar wato yayan shi barrister din ya kirani ya sanar min halin da ake ciki, and I immediately reported to office to see the needful we can do about the case.... Sai dai cikin hukuncin ubangiji bamu ga yarinyar nan a ko ina ba sai gidan biological parent dinta yanxu, and yanda ni nayi tunanin iyayen nata ba haka bane, sannan ba ayi masu adalci ba kwarai da gaske...." Asp ya nuna Alhaji Ahmad that is also by his side trying all possible mean to control his tears yace "Mahaifin yarinyar nan kenan, Honorable Ahmad, we saw pictures, resemblance, and concrete proofs, that's just it, nan din gidan iyayen wannan yarinya ne" Heedayah ta juya tana kallon wanda Asp ke nunawa matsayin Mahaifinta, Khaleel couldn't stop looking at him also, Abba ya karasa gun Heedayah yana kallonta ya kamo hannunta gently yace "That's ur father Heedayah, I am sorry I never made any effort to take you back to them, I am sorry daughter" Rungume Abba tayi ta fashe da kuka sosai, almost whispering into his ears tace "You are always my father Abba, you remain my father" Mami taji ta kasa ci gaba da tsayuwa ta nemi waje ta xauna hawaye na sakko mata sosai, junaid dai ya dafe kansa kawai daga inda yake xaune, sai duk suke jin abun kamar a film, Mum Islam ta nufi Mami ganin yanda take kuka ta duka kusa da ita, ita ma tana share hawayen dake sakko mata tace "Mami nasan Dinar tun dawowarsu anguwar nan, mun shaku da ita sosai, har gaisawa mu kan yi da ke a waya in dai ta kira ki ina gidan ko kin kirata, amma duk bamu san ke ke rike da 'yar Mai gidana da ta bace shekaru biyar kenan ba, wanda har yau duk muna rayuwa ne da ita a ran mu, ba tare da sanin ko tana raye ko ta mutu ba, Heedayah 'yar kishiyata ce ta fari, wanda saboda bacewarta har yau ba a gane kan mahaifiyarta ba, but How can we pay for this great deed Mami? A blind little girl got lost, but we are seeing a sighted teenager now, baxa mu ta6a iya biyanku ba koda duk dukiyar Mahaifinta xa a baku" Mami bata iya ta ce komai ba sai share hawayen da ya ki tsaya mata take, sai take jin abun kamar a mafarki, so she is leaving Heedayah with them kenan yanxu, Abba dai na tsaye still holding on to Heedayah dake kuka sosai ita ma, shi kuma nan gani yake bai mata adalci ba bai ma iyayenta adalci ba, shi dai yasan ba da nufin komai ya banxantar da batun iyayenta ba, Abba ya kalli Alhaji Ahmad da ke ta kallon 'yar tasa shi ma yana tunanin how is he going to pay barrister Ahmad and Barrister Rahinah, Abba yace "Ina mahaifiyar ta?" Alhaji Ahmad bai ce komai ba, can ya nufi dakin matar tasa, kwance ya sameta ta takure waje daya, ya xauna gefenta ya dagota yace "Aisha ur Daughter Heedayah is back home, my assurance to you always, didn't go in vain, na sha gaya maki idan Allah ya amince Heedayah xata dawo garemu, and here she is today" Ta kamo hannunsa hawaye na bin fuskarta tace "Noo Ahmad kullum irin mafarkin nan nake, daga karshe sai kuma in tashi da wani ciwon, why is this dream taking long, don Allah ka tasheni daga wnn baccin, ni nasan ba gaskiya bane, irin mafarkin da nake yi kenan a ko da yaushe.... Daga karshe na tashi naga ba Heedayata, beside my Heedayah I know is blind...." kuka sosai take yi tana kallonsa, ya dagata suka fita dakin, suna fitowa parlor tayi ido hudu da Heedayah, kallonta kawai Heedayah ke yi, lkci daya ta xame hannunta daga na Abba, ta tafi da gudu ya rungume uwarta ta fashe da kuka, sai a snn mahaifiyarta ta tabbatar ba mafarki take ba, Heedayar tace ta dawo, but not blind Heedayah, ba mafarki bane, Cikin kuka tace "Heedayah" Heedayah bata mance muryar mahaifiyarta ba, har cikin ranta ta ji murya ta rungumeta sosai tace "Ammi I have missed you a lot, nayi missing din ki, you've always been in my thought, nayi missing din ki" Uwar ta kasa cewa komai sai hawaye, lkci daya Heedayah ta xame jikinta ta juya tana kallon Khaleel dake kallonsu, Bata san lkcn da ta nufesa da gudu ba ta rungumesa sosai, cikin kuka tace "You promised to take me to my parent, and u fulfilled ur promised, I love you dearly, and I will forever be grateful" Junaid ya sauke idonsa kasa daga kallonsu da yake, shi dai Khaleel na tsaye yana jinta har cikin ransa, but he is weak and breaking down, Baya yyi a hankali, ganin haka Heedayah ta sakesa tana kallonsa, ya dafe kirjinsa ganin xai kai kasa ta saki wani kara, tuni Zayyad ya mike ya nufo sa, haka ma Junaid da Abban Heedayah da Abba, with Asp, Mami ma ta mike tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mami na xaune tare da Heedayah kan kujerun dake jere a dogon corridor din 4 wards dake wani bangare na hospital din, sai Abba da Alhaji Ahmad dake tsaye wajen su ma tare da Zayyad da Junaid, kusan awansu daya kenan a asibitin, Babban asibiti ne sosai me kuma tsada don a ward din da ake admitting authoritative patient ma aka kwantar da Khaleel, ba kowa ake admitting a wnn bangaren na Babban hospital din ba sai wanda ya isa, but being that Honorable Ahmad ne ya taho da Khaleel hospital din, nan aka kwantar da shi, Likitoci biyu ne suka fito babban ward din da ko kadan bai wani yi kama da dakin asibiti ba, dayan yyi wucewarsa, sai daya da ya tsaya yana kallon su Abba snn ya kalli Mami da gaba daya ta kasa samun natsuwa, smiling to give her assurance yace "His mother?" Mami ta d'an yi shiru sai kuma ta girgixa kanta tace "No" Zayyad ya karaso gun likitan gently yace "Ni abokinsa ne..." Likitan ya kalli Zayyad yace "Ohk, kai abokinsa ne, to iyayensa fa??" Alhaji Ahmad ya karaso gun likitan yace "If there is anything ka sanar min, we brought him to the hospital..." Likitan yace "Ohk sir, mu tafi office" Bin bayansa Alhaji Ahmad yyi xuwa office dinsa, Zayyad ya bude kofar ward din, politely wani likitan dake ciki yyi masa alamar da he should stay behind plss, rufe kofar yyi ya tafi ya xauna, gaba daya tausayin abokin nasa yake sosai don yasan wahalan da yake duk sanda ya samu attack, shi yasa tun safe yake ta kokarin ganin bai wahalar da kansa ba considering his condition but all in vain. Alhaji Ahmad na kallon Likitan yace "MI? Is that a disease?" Likitan yace "Yes, Myocardial infarction... Damage or expiry of any area of the heart muscle.... And this is as a result of lack of flow of blood to the area" Alhaji Ahmad yyi shiru, can yace "Was he born with that?" Likitan yace "I don't know, I can't tell, amma in sha Allah he will be fine, he just had an attack, amma kasan iyayensa? I mean are frnds with the parent?" Alhaji Ahmad yace "Not at all..." Likitan yace "Ohk then, but sbda condition dinsa yana da kyau ya dinga nesa da duk wani abu da xae daga masa hankali ko makamancin haka, I mean slightest of it, ya daina damun kansa a kan komai, kaga nasa kalan Heart attack din is very dangerous, a likitance ana kiran da wnn Heart attack din STEMI... Kuma alamu sun nuna ya dde da ciwon, he just need to learn how to live properly with it, in some cases ana surgery but I can't say tukunna, mun dai daura sa under medication ynxu, kuma in sha Allah xae samu sauki, in sha Allah" Alhaji Ahmad yace "Toh Allah ya basa lafiya, ya yaye masa" Likitan yace "Ameen honorable, that's just it, Allah ya kara mana lafiya baki daya" Alhaji Ahmad ya amsa da Ameen snn ya mike suka yi sallama da likitan ya fita. Alhaji Ahmad yyi ma Abba bayanin da likitan yyi masa, Mami dai na xaune daga inda take tana sauraronsu, sosai taji tausayin Khaleel jikinta yyi sanyi, Abba yace "To Allah ubangiji ya basa lafiya, Allah ya tashi kafadunsa" Alhaji Ahmad ya amsa da "Ameen" Alhaji Ahmad na kallon Mami yace "Hajiya I think ya kamata mu tafi yanxu it's getting late" Abba yace "Sure, abokinsa with Junaid can stay with him...." Junaid ya kalli Abba bai dai ce komai ba, Heedayah na kallon Mami a hankali tace "Mami pls can I go in and see him before we leave?" Mami tace "No Dr yace kar a shiga, gobe da safe xaki duba sa" Likitan da ke cikin ward din ne ya fito, Heedayah ta bi sa da kallo, Mami ta mike ta nufi Junaid, ganin haka Heedayah ta mike da sauri ta bi bayan likitan, a hankali Mami na kallon Junaid tace "I know baka son xaman hospital but kayi hakuri just for today" Ya gyada mata kai kawai, Heedayah na shiga office din likitan bayan ya shiga ya juya yana kallonta, a hankali tace "Good evening sir" yace "Evening dear how are you?" Ta marairaice tace "Pls I'm begging you can I go in to check on him?" Likitan yyi murmushi yace "He is asleep young lady, Gobe idan kin xo da safe xa ki gansa" Kamar xata yi kuka tace "Ae ba tashinsa xan yi ba kawai ganinsa xan yi" ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Ohk, but don't go hear him ki tsaya daga middle of the room check on him and leave, promise?" Ta gyada masa kai da sauri tace "I promise" yace "Good, you can go in" Tana murmushi tace "Thank you sir" daga haka ta fita da sauri, Mami har ta fara nemanta a asibitin don su Abba da Alhaji Ahmad sun fita haraban hospital din, Junaid na xaune corridor din tare da Zayyad Heedayah ta dawo, bude kofar ward din xata yi Zayyad yace "Noo, it's not allowed" ta kallesa tace "I asked for permission" daga haka ta shige ciki, Junaid ya bi ta da ido har ta kulle kofar, kwance ta gansa saman gadon dake babban dakin wanda kamar ba a Nigeria ba tsabar haduwar ward din, ta tsaya dai dai inda likitan yace ta tsaya tana kallonsa yana bacci breathing dinsa very slowly, bata san lkcn da tayi breaking din promise din da tayi ma likitan ba ta karasa kusa da gadon da sauri, lkci daya ta ji hawaye ya kawo idonta, ta durkusa kusa da shi a hankali ta kamo hannunsa tace "Are you alright?" Bayan few seconds ya bude idanuwansa a hankali sai kuma ya sake kullewa, cikin sanyin murya tace "Are you feeling better now?" Ba tare da ya bude idonsa ba, murya can kasa yace "Sure" tace "Magani suka baka?" Ya girgixa mata kai, tayi shiru tana kallonsa don har sannan ya ki bude idon, murya can kasa yace "Injections" Hawayen dake makale idonta ya sauko tace "Allah ya baka lafiya" Ya gyada mata kai, ta kafesa da ido tana ta kallonsa, a hankali ya bude idonsa jin shirun yyi yawa, suna hada ido ya mayar ya rufe idon nasa, har sannan tana rike da hannunsa da yyi xafi tace "Ina yake maka ciwo" ya daga daya hannunsa da kyar ya nuna mata kirjinsa, ya mayar da hannun bayansa, sannan ya dafe forehead dinsa, wasu hawayen suka sake xubo mata cikin sanyin murya tace "In sha Allah xa su daina ka ji, you will be fine in sha Allah" ya gyada mata kai, ta xame hannunta daga nasa tace "We are going home now, get well before tomorrow plsss" Sae a snn ya sake bude jajayen idonsa murya can kasa yace "Thanks Heedayah!!" ta gyada masa kai sannan ta mike ta juya ta nufi kofa ta fita ta kulle, Mami na tsaye bakin ward din, da sauri ta sunkuyar da kanta, Mami tace "To mu tafi gida tunda ke baki jin magana" Mami ta yi wucewarta daga wajen bayan Zayyad yyi mata sae da safe, Heedayah ta daga ma Junaid da ya bi ta da ido hannu ta bi bayan Mami da sauri. A Motar Alhaji Ahmad Mami da Heedayah suka dawo gida tare da excort dinsa dake biye da su a baya, bbu ynda Alhaji Ahmad bai yi da Abba su taho nan gidan nasa tare ba Abba yyi declining yace xai tafi hotel din da yyi lodge, haka Alhaji Ahmad ya hakura ya kyalesa kawai, ganin Alhaji Ahmad xae shiga ciki da motarsa bayan masu gadi sun bude gate Mami tace "Xan sauka ba sai ka shiga ciki ba Alhaji" Alhaji Ahmad yace "No Barrister, you can spend the night here" Mami tayi murmushi tace "Thanks sir, xan shiga gidan Daughter na, will spend the night there in sha Allah" ita ma bbu ynda bai yi da ita ba ta kafe a kan gidan Dinar xata shiga hakan yasa ya hakura, ta bude motar ta sauka tana kallon Heedayah dake ta kallonta, Heedayah ta sauke idonta sai kuma ta bi ta xaya sakko Mami tace "Noo dear, go in with ur Abba" Alhaji Ahmad yace "Aa.... go with ur daughter barrister" Mami tace "Yau dai ta kwana tare da Ummanta, it's been long" Bata jira Abban Heedayah ya ce komai ba ta rufe motar ta daga ma Heedayah hannu tayi hanyar gate dinsu Dinar, Alhaji Ahmad ya shiga da motar cikin gidan, yyi parking a parking space, bude motar Heedayah tayi ta sauka, shi ma ya sauka yana kallonta, ta sunkuyar da kanta, duk sai ta ji kewar Mami sosai, Alhaji Ahmad ya nuna mata bangaren Mahaifiyarta yace "Mu je" Gaba ta shiga ta nufi inda ya nuna mata yana biye da ita a baya, Bbu kowa a babban parlon, Heedayah ta nemi gefen kujera ta xauna amma da ganinta kasan a takure take, Abbanta na kallonta yace "Mu je wajen Ammin ki" mikewa tayi ta bi bayansa xuwa corridor din dakuna biyar, ya bude kofar bedroom din Ammi ya ga bata ciki, wani kofar ya bude ya ganta xaune saman darduma a dakin dake dauke da gadaje guda biyu na yara, komai na dakin na kids ne, Abban Heedayah ya juya ya kalli Heedayah da ta rakube gefe daya yace "Come in" shiga dakin tayi tana kallon girls din dake kwance kan each bed, wa enda kila su yi shekara uku, Ammi sai kallon Heedayah take, a hankali Heedayah ta duka kusa da ita tace "Ammi mun dawo" Ammi ta sakar mata murmushin karfin hali amma ta kasa cewa komai, fita Abba yyi daga dakin, a boye Ammi ta goge hawayen dake kokarin gangaro mata tace "Have you eaten?" Heedayah ta gyada mata kai, Uwar tayi shiru, can tace "To tashi mu je ki kwanta" Mikewa Heedayah tayi, Ammi ma ta tashi, ta karasa twins dinta ta rufe ko wannensu da blanket ta xauna gefen daya gadon ta tofa masu addu'a snn ta mike tana kallon Heedayah tace "Mu je" kofa Heedayah ta nufa Ammi na biye da ita, Ammi ta kulle kofar dakin bayan sun fita, ta tafi ta bude wani kofar tana kallon Heedayah, karasowa Heedayah tayi Ammi tace "Sai da safe" Heedayah ta shiga dakin Ammi ta kulle kofar, ta wuce nata dakin tana goge hawayen da ya ki tsaya mata. Har kusan karfe biyun dare Ammi ta kasa bacci banda sllh bbu abinda take tana kara gode ma Ubangijin ta, she just can't believe her daughter is back after 5 years, bata son tuna baya, bata son tuna shekaru biyar din nan da suka wuce da halin da ta shiga, she just want that memory to erase off her heart, ta share idonta daga karshe ta mike ta bude kofar dakinta a hankali ta fita, dakin Heedayah ta nufa ta bude kofar in a way it won't make any sound, haske wutan corridor dake a kunne yyi reflecting dakin, Heedayah dake kwance idonta biyu ta kasa bacci gaba daya ta ji bbu abinda ke damunta irin rashin lafiyar Khaleel tun da ta kwanta bayan tayi wanka take juye juye, mikewa xaune tayi da sauri jin an bude kofa, Ammi ta shigo dakin ganinta a xaune ta kunna wutan tace "Baki yi bacci ba?" Heedayah ta shiga mitsika idonta kamar me bacci tace "Na farka ne yanxu" Ammi ta isa kusa da gadon ta xauna tana kallonta, Heedayah ta sunkuyar da kanta, a hankali tace "Nayi missing din ki Ammi, I've missed you so much" Ammi ta jawota jikinta tana murmushi tace "I missed you more daughter" shiru duk suka yi, can cikin sanyin murya Ammi tace "Do you remember when you let Yakumbo's house that very day?" Heedayah ta d'an yi shiru sai kuma tace "Yes, wasu mutane ne suka tafi da mu a motarsu da su Ladi, ban san inda suka kai mu ba, we walked a long mile, suka kai mu wani waje, I can't see, I only can hear, so I don't how the place looks like, har muka yi bacci muka tashi a wajen, it seems suna kashe mutane coz then ina jin karan gun shot, sai wani ya daukeni a bicycle muka yi ta tafiya ya kai ni wani waje ya ajiyeni ni kadai ya tafi ya bar ni.... He just left me and go not considering that I am blind..." Hawaye ya cika idon Heedayah tana kallon Amminta dake saurarenta, Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Taimakon ki yyi ya fitar dake kilan kar a kashe ki a wajen" Heedayah tace "But he just abandoned me by the road side" Ammi tace "He is an angel for that, da sun kashe ki yanxu my daughter" Heedayah tayu shiru, sai kuma tabe baki tace "Ni ban san me ya faru ba, seems I was knocked down by a vehicle, and daga nan sai Abba ya kai ni gidansa, and I began staying with them.... he has a son Ya Shureen" Heedayah ta d'an hade rai tace "Ni bana sonsa, baya dariya, baya min wasa, his mother is so mean, bata sona, his sisters are mingy also, they don't like me even for a second" Ammi dai sai kallonta take ko kiftawa bbu, Murmushi Heedayah tayi a hankali tace "Abba ne kawai yake so na, he was always there for me, he paid for my eye surgery, and Mami.... she is also my mother, I love her, I love them" Shiru Heedayah tayi tana kallon Mahaifiyarta, Ammi ta shafa kanta a hankali tace "Sure dear, she is ur mother, always take her as one, and take me as ur aunt" Heedayah ta kalli uwarta tayi murmushi bata ce komai ba, a hankali tace "But you remain my mother" Rungumeta Ammi tayi tana murmushin ita ma, Heedayah tace "Ya Junaid, Ya Sudais, they were always there for me...." Wara ido tayi tace "Kaka....." Ammi ta janyeta jikinta tana kallonta. Har aka yi kiran sllhn asuba Ammi na tare da Heedayah hira sai wanda ta manta ne bata yi ma Amminta ba barin hiran kaka, wani Ammi tayi dariya, wani tayi murmushi, wani tayi shiru, wani kuma taji hawaye ya kawo mata, she is just imagining, ashe dama akwai wa enda xa su rike yaron da basu san daga inda ya fito ba da amana ynda mutanen nan suka rike mata 'yar ta, bata san da me xa su biya Abba ba, bata san da me xa su biya Mami ba, but ta fi jin Abba don da bai dau Heedayah ya tafi da ita ba da bata san wani labarin xa a dinga yi ynxu ba, they owe him greatly.... Bude kofar dakin da Abban Heedayah yyi wajen karfe biyar na asuba yasa Heedayah tayi shiru daga labarinta, murmushi yyi yana daga tsaye bakin kofa yana kallonsu, can kawai ya juya ya fita xuwa masallaci, Sai a snn Ammi ta tafi nata dakin don yin alwala, Heedayah ta shiga bathroom din dakin da take. Bayan Heedayah tayi sllh ta shiga bandaki tayi wanka, ta fito daure da towel, sai ga Ammi tare da Mum Islam sun shigo dakin, Gaisheta Heedayah tayi, da fara'a mum Islam ta amsa tace "Jiya kafin ku dawo nayi bacci wllh, kayan ki na gidan Dinar in amso maki ko? Naga har kin yi wanka" Heedayah ta gyada mata kai, Mum Islam tace "To bari in tafi in karbo maki yanxu" daga haka ta fita dakin, Ammi na kallon Heedayah tace "What are you taking for breakfast?" Heedayah ta xauna gefen gado tana kallon Amminta a hankali tace "Ammi baxa mu tafi can asibitin ba?" Ammi tace "Da asuba xa a je asibitin? ai xa ki bari gari ya waye ko?" Heedayah tayi shiru, sai kuma tace "Toh" Ammi ta tafi ta dauko mata body lotion kafin Mum Islam ta dawo. Karfe bakwai da rabi Farida da Dinar suka shigo parlon Ammi... Matan step brothers din Abban Heedayah da Kanwar Ammi da few family frnds ne xaune parlon, ko wannensu ya xo gidan nuna farin cikin bayyanar Heedayah bayan shekaru biyar, Ammi suka gaisa da Dinar da Farida da fara'a don ta ga kamanninsu da Mami tace "Tana ciki ku shiga" Mai aikin Ammi ce ta nuna masu dakin da Heedayah take da kanninta, Heedayah na xaune dakin tana ta kallon 'yan kanninta dake ta xuba mata shirme ko wannensu na son bata labari duk da ba wai sun santa bane amma jini ba karya bane, nan kam ita kallon girls din masu kama da ita tana karama take amma hankalinta ba a gun su yake ba, Ammi tace mata xa su je kai abinci asibiti amma bata ji ance ta xo su tafi ba tun daxu... Farida ce ta fara shigowa dakin, Heedayah ta mike da sauri ta rungumeta sosai tace "Farida..." Farida dai bata ce komai ba, haka Dinar da ta nemi waje ta xauna, Heedayah ta koma inda take a sanyaye ta xauna, tana kallon Dinar tace "Ina kwana Maman Fadil" Dinar tace "Lafiya lau" cikin sanyin murya Heedayah ta sunkuyar da kanta tace "Kiyi hakuri Maman Fadil, I don't know what came over me, I am sorry..." Tana fadin haka Farida ta fara kuka Heedayah ta mike ta koma kusa da ita ta rungumeta tace "I'm very sorry Farida, I don't know what really happened" ita dai Dinar har snn bata iya ta ce komai ba, da yake tasan Ashnaah da Ashfaa don Mum Islam kan shigo gidanta da su, sai ta jawosu tana masu wasa, a haka mum Islam ma ta shigo dakin ta samesu. Karfe goma saura Heedayah ta fita daga dakin, xuwa lkcn gidansu ya cika da 'yan uwa da abokan arxiki, ita duk wnn ba shine damuwarta ba, tana ta tsaye corridor sai ga Amminta, ganin yanda ta tsaya kamar tana cikin damuwa Ammi na kallonta tace "Do you need anything?" Heedayah ta sauke kanta kasa a hankali tace "Ammi an kai abincin da kika ce asibiti?" Ammi tace "Toh barin abincin xa ayi ta yi har yanxu ba a kai ba, Abbanki na Kaduna da na nan with ur Mami suna can asibitin, anjima nima xan je, and Shuraim is around now, ki tafi kitchen ki hada masa breakfast ki kai masa, yana parlon Abban ki" Da sauri Heedayah ta kalleta, lkci daya ta 6ata fuska tace "Ni dai Ammi baxan iya ba, kila ma dukana xai yi, ni dai gwara in kira Farida ta kai masa wllh" Ammi ta hade rai tace "Ke nace ki kai masa..." Hawaye ta fara yi tace "Ni fa har yanxu ban ma je asibitin ba faaaa" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Bude kofar parlon Heedayah tayi suka yi ido hudu da shi yana xaune parlon yana danna wayarsa, ta kara daure fuska ta tafi ta xauna saman kujera murya can ciki tace "Ina kwana" Jin bai amsa ba ta daga kai ta d'an kallesa, ajiye wayar hannunsa yyi still not looking at her yace "Congratulations for reuniting with ur parent" Tace "Thank you" bayan few seconds jin bai ce komai ba tace "A kawo maka breakfast in ji Ammi?" Ya mike yace "Not hungry" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da wani kallo har ya fita, ta kyabe baki ta mike ta fice parlon ita ma, tana jin yana sallama da Amminta ta makale ta ki karasawa, Ammi tace "Breakfast din fa?" Yace "No na yi breakfast nagode" Ammi tace "Ohk hospital din xaka tafi yanxu?" Yace "Aa, Kaduna xan wuce" Ammi tace "Yau din?" Yace "In sha Allah" Ammi tace "Toh Allah ya tsare, sai mun xo" Yace "In sha Allah" Bayan Azahar Heedayah da Farida suka tafi asibiti tare da Amminta, she is just happy tun fitowarsu ko ba komai xata ga condition din Khaleel, Junaid ne kadai xaune ward din, Khaleel kuma na kwance yana bacci, Ammi suka gaisa da Junaid tana tambayarsa me jiki, yace "Alhmdllh da sauki" Ammi tace "Toh Allah ya basa lafiya, Allah ya tashi kafadunsa" Junaid yace "Ameen ya rabbi" Heedayah ta ajiye abincin dake basket din hannunta da suka taho da shi tana kallon Junaid a hankali tace "Ina yini ya Junaid" ya sakar mata murmushin da iyakarsa lips yace "Lafiya" Gaishesa Farida tayi ya amsa ta nemi kujera ta xauna, bayan few minutes Ammi tace "Toh idan ya tashi ka gaida mana shi, xa mu koma, Allah ya basa lafiya" da sauri Heedayah ta kalli Ammi amma dai bata ce komai ba, Farida ta mike ganin Ammi ta yi kofa tana amsa sallaman da Junaid ke yi mata, Heedayah kamar xata yi kuka ta mike a hankali, xata fita Junaid dake lura da ita ya kalli kofa ganinsu Farida sun fita ya riko hannunta ba yabo ba fallasa yana kallonta yace "Bayan tafiya gidansa da kika yi kika kwana, do u still have any undone business with him???" Heedayah ta buda ido tace "But he is sick and I have to pity him..." saketa yyi yace "Toh xauna kiyi jinyarsa" Ko kallonsa bata sake yi ba ta bi bayan Amminta da sauri ta fita. Suna komawa gida Ammi ta shiga gidan Dinar tare a Heedayah da farida, Mami na parlor xaune Dinar tayi tagumi tana kallonta tace "But you need not to be this worried Mami, ke komai sai ya baki tausayi, ba sanin wannan mutumin kika yi ba me yasa xaki damu kanki haka a kansa, beside yana samun lafiya ai ko, ni fa har yanxu I am not happy at the way ya kai Heedayah gidansa har ta kwana, no responsible person will do that, and dubi fa har waya ya bata a boye, what's the meaning of that, gidan iyayenta na asali kuma da ake ganin kamar shine silar xuwanta everything just happened coincidentally ba wai ya san sune iyayen nata bane, I see no reason da kowa xai wani dinga ganin kamar shine silar reunion dinta da parent dinta, it's not so plss, da ta ci gaba da xama a nan kafin hutunsu ya kare dole Mum Islam xata shigo ta ganta daga nan komai xai bayyana...." Mami dai sai kallonta take, Dinar ta ci gaba tace "But the way u people are treating d guy kamar ba shi da laifin dauke yar mutane ya kai ta gidansa ta kwana daga shi sai ita is alarming, who does that, nobody is even talking about this fa, duk mijin da ya fito xai aureta in har fa ya ji wnn labarin da karamin matsala xai ja ba, yarinya budurwa ta tafi gidan saurayi ta kwana ta yini duk a daga ma mutane hankali, but nobody is talking about it, ni fa shi sa Shuraim din nan ya burgeni wllh, ya san abinda yake" Mami tace "Enough Dinar, I trust Heedayah, kila dai kun yi mata wani abun ne da bata ji dadi ba ta bar maku gidanku amma ba abinda xai kai ta gidan namiji da son ranta, wanda Allah ya riga da ya kaddara dole sai ta bar gidan ma xata hadu da mahaifanta, ta silar wnn bawan Allahn kuma...." Sallamar da aka yi bakin kofa ya sa Mami tayi shiru, Farida ta bude kofar ta shigo parlon Heedayah na biye da ita sannan Ammi, a sanyaye Heedayah ta karasa gun Mami ta duka kusa da ita tace "Ina yini Mami" Mami ta sakar mata murmushi tace "Lafiya lau, kun dawo asibitin?" Heedayah tace "Mun dawo" Maman Fadil ta mike tana ma Ammi sannu da xuwa, Ammi ta amsa da murmushi ta xauna snn suka gaisa da Mami, Mami tace "Nima yanxu nake shirin xan tafi asibitin, da yau din ma xa mu wuce Abuja da Barrister amma nace bari in kara kwana daya in ga jikin bawan Allahn" Ammi tace "Allah sarki, da muka je ma bacci yake ynxu, and he is the one holding us back too don xa mu tafi Kadunan mu ba, ya ce mu jira ya ji sauki tukun mu je" Mami tace "Toh Allah ya bashi lafiya" Ammi ta amsa da "Ameen" drinks Dinar ta kawo ma Ammi da bata ta6a shigowa gidanta ba sai ranan, Ammi tace "Ae da kin barsa Maman Fadil, Ina Fadil din?" Dinar tace "Yana bacci a sama" Ammi tace "Allah sarki" Kitchen Dinar ta tafi ta ci gaba da girkin da take Farida ta mike ta bi bayanta, Heedayah dai na xaune kusa da Mami, Mami tace "Ki je ku yi girkin" Ba musu ta mike ta bi su kitchen din, Ammi ta mike ta dawo kusa da Mami ta xauna ta fara magana cikin sanyin tace "Hajiya muna alfahari da ke da Barrister, kun yi abinda ba ko wani d'an Adam Allah ke ba ikon yi ba, kun rike Heedayah xuciya daya ba tare da sanin daga inda ta fito ba, Allah ya saka maku da alkhairi, ya biya ku da aljanna, domin mu kam bamu da abinda xa mu biya ku" Mami tayi murmushin karfin hali tace "Allah ya taimaki nawa haka nima...." Ammi tace "Ameen" Suna parlon har kusan la'asar kafin Ammi ta mike tace "Xata koma gida tayi sllh" Mami tace "Nima sllhn xan yi nasan Dinar sun gama girkin sai mu je asibitin" Ammi tace "Toh Allah ya dawo da ku lafiya" Mami tace "Ameen, amma don Allah kar a sake kawo wani abincin, wanda aka kawo ma Allah ya amfana, Ga Dinar tayi girki ma yanxu" Murmushi kawai Ammi tayi, ta kara mata sallama ta fita parlon. Mami na idar da sllh Dinar ta fito da abincin da ta gama a basket, Mami tace "Kin yi ma Usman din magana?" Dinar tace "Ehh bari in dauko Hijab" Heedayah ta sakko daga upstairs bayan ta idar da sllh Mami tace "Ga abinci can a kitchen ki kira Farida ku deba kuyi lunch" Heedayah ta xauna a hankali tace "Mun ci abinci" Mami tace "Ohk" Shiru Heedayah tayi, can tace "Asibitin xa ki tafi Mami?" Mami tace "Ehh" A hankali Heedayah tace "In bi ki Mami?" Mami tace "Ba daga can ku ke ba yanxu?" Heedayah bata ce komai ba, Dinar dai ta saka hijab dinta ta dau basket din abincin ta fita waje bayan ta dau makullin motarta, har Mami ta nufi kofa ta juyo tana kallon Heedayah da ta bi su da kallo tace "To taso mu je" Heedayah ta mike ta dau mayafinta ta bi bayan Mami cike da farin cikin da bata nuna a fili ba. Har suka isa asibitin bbu wanda yace komai cikin motar, Dinar tayi parking a space din da aka tanadar don haka a asibitin snn ta bude motar ta sauka, Mami ma ta sauka, Heedayah ta dau basket din abincin ita ma ta sauka, Zayyad ne kadai dakin da Khaleel dake xaune yana shan grapes a roban grape din, Tun da Mami ta shigo yake kallonta, Kafin kuma ta karaso gun gadon ward din ya sauke idonsa, Zayyad ya gaisheta ta amsa da murmushi tace "Ya mai jiki?" Yace "Alhmdllh" Gaisheta Khaleel yyi not looking at her, ta amsa tace "How are you feeling now?" Yace "Alhamdulillah" Xaunawa Mami tayi tace "Toh Allah ya kara lafiya" Dinar tayi masa ya jiki ita ma ta xauna, Kallonsa kawai Heedayah dai take, ya d'an kalleta suka hada ido, ta buda ido tace "How are you feeling?" Ya gyada mata kai yace "Fine Alhamdulillah, in sha Allah" tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen" Heedayah ta xauna kusa da Mami, Shi dai Khaleel ya ci gaba da shan grapes dinsa slowly, bayan wani lkci ya daga kai suka hada ido da Mami dake ta kallonsa, Mami tayi saurin cewa "Nace ga abinci nan abokin ka ya dibar maka koh?" Zayyad ya mike kafin Khaleel yace komai sanin bai son cin abincin ya tafi gun basket din abincin don debar masa, dai dai nan aka bude kofar ward din, Khaleel ya dakata da kai grape din hannunsa bakinsa yana kallon wa enda suka shigo, Manga ne da Bala, ko wannensu sanye da manyan kaya irin na mutanen kirki, ga bakin glasses da suka kwama, Khaleel ya mayar da grape din hannunsa ya ajiye, Mami dai sai kallonsu take, Manga na kallonta da katon muryarsa yace "Sannu Hajiya" Mami tace "Yauwa" Bala yace "Ya me jiki?" Mami tace "Mun gode Allah" Manga yace "Madalla" karasawa yyi gadon yana kallon Khaleel, Shi dai Zayyad bai yrda ya juyo ba yana xuba ma Khaleel abinci, Manga dake kallon Khaleel yace "ya jikin?" Khaleel yace "Na warke" Manga yace "To madallah" Zayyad ya juyo ya mika ma Khaleel abincin hannunsa, Bala yace "Sannu da jinya" Zayyad yace "Yauwa" Mami ta mike tace "To xa mu koma, may be kafin in tafi gobe da safe xan leko in sha Allah" Khaleel ya kalleta yace "Toh nagode kwarai" Jikin Heedayah yyi sanyi, she wants to talk to Khaleel amma har yanxu bata samu ta yi masa magana ba, Mami bata yi ma su Manga sallama ba ta fita ward din, Dinar ta mike tayi ma Khaleel Allah ya kara lfya, tayi ma Zayyad sai anjima snn ta fita, Manga ya bi su da kallon gefen ido, A hankali Heedayah ta mike tana kallon Khaleel dake ta kallonta, ta sauke idonta kasa sai kuma ta karasa gun sa tace "Xa mu tafi, Allah ya sauwake" yyi shiru bai ce komai ba, tace "Do you need anything?" Ya d'an kalleta snn yace "Nothing Heedayah" tace "Toh Allah ya sauwake" Yace "Are you travelling together with them tomorrow?" Heedayah tace "I don't know too" yace "Ohk, ki tafi suna jiran ki" Ta gyada masa kai ta nufi kofa su Manga suka bi ta da kallo, ko kadan bata san su waye ba sai a snn Khaleel ya ga amfanin rashin barin ta gansu da yyi daren ranan, tana kulle kofar Bala ya kalli Khaleel da jajayen idonsa bayan ya cire glasses din idonsa yace "Kafin in isar maka da abinda ya kawo mu, wacece warcan matar da ta fito, a ina ka santa? Kuma yaushe ka saki jiki da bare har haka ku ke mu'amala bamu da masaniya?" Khaleel yace "Bana tunanin you have any business to do with that Boss" Manga yyi wani nishi yana kallon Bala yace "Follow her, get few information" Bala ya fice da sauri, Manga yace "Anyway, ba wani abu ya kawo mu nan ba illa mu sanar maka our next operation na dauke Alhaji Ahmad is in 3 days time, wnn lkcn idan ka kuskura ka kawo mana cikas, Arne yyi alkawarin aikaka lahira, amma kar ka yi tunanin a take xaka mutu, idan ka mutu a take ka ci riba ma kenan, wllh wllh idan ka sake kawo mana wani cikas a wnn operation din sai dai ayi wani Brainiac din ba kai ba, idan kana da sama da mu a duniyar nan ka fito ka nuna" Khaleel yyi wani murmushi ya ci ga da shan grapes dinsa, Bala ya karasa dai dai kusa da Khaleel cikin husky voice yace "Be careful with us, don't mess with us....." Daga haka ya fice daga ward, Khaleel ya juya yana kallon Zayyad ya diro daga saman gadon fuskarsa a murtuke ya nufesa yace "Why did you let them know where we are?" Zayyad ya buda hannu yace "I only told Maska, yace Oga Arne na nemana nace ina tare da kai you are sick, is anything wrong with that...." Khaleel sai kallonsa yake yana huci, can ya nufi kan gado ya dau wayarsa ya fice daga ward. I'm not okay, I just have to write this... Thanks for d call and text I couldn't reply or answer to. Da Magrib Heedayah na dakin kanninta tare da Nannynsu da ke shiryasu tayi masu wanka, tun dawowarsu tare da Mami daxu daga asibiti Mami tace ta shiga gidan nasu gun Amminta, Ammi ce ta bude kofar dakin tana kallon Heedayah tace "Gwaggon ki ta iso Heedayah, come out and meet with her" Heedayah ta mike ta d'an buda ido tace "Yakumbo?" Ammi tayi mata murmushi tana nodding mata kai, Fitowa Heedayah tayi dakin da sauri don Yakumbo na daya daga mutanen da take son gani ido da ido, kafin ta karasa main parlor suka yi kicibis da Yakumbo, Yakumbo ta koma baya ta kare mata kallo daga sama har kasa sai kuma ta rushe da wani matsanancin kuka tace "Allah ya ga xuciyar mu, bama nufin kowa da sharri a duniya, bama nufin d'an kowa da sharri, yanxu Heedayah ce wnn nake gani Aisha? Heedayah ce wnn ta xama gandareriyar yan mata haka aure yau ko gobe?" Kuka take yi sosai ta koma parlor ta xauna tana cewa "Xuciyar mu daya laya, bama nufin kowa da sharri duniya da lahira.... Yau ba ga ranan hakuri ba amma da mata duk kin bi kin daga ma mutane hankali kin dami mutane, kowa na jin haushina ana ganin kamar hada baki muka yi da 'yan kinnafas din, toh ni dai duk a gaggauta neman gafarana don an xalunce ni da mummunan xato wanda har duniya ta tashi baxai gogu a raina ba, aka shiga tsakanina da d'an uwana da na rike tun yana karami duk sbda an sace Heedayah a gidana kamar ni na sace ta...." Heedayah dai sai kallonta take, can ta tafi ta rungumeta da murmushi fuskarta, Yakumbo dai sai kuka take, Ammi kuma ta xauna saman kujera tana karasa saka ma Ashnaah kayanta, knocking aka yi, Ammi ta kalli Heedayah dake ta kallon Yakumbo kamar ta samu TV, nan kuma Kaka kawai take gani wajen a xaune, mikewa Heedayah tayi ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Khaleel bakin kofar, ta koma baya tana kallonsa da mamaki, can tace "Anyi discharging din ka ne?" Ya gyada mata kai yace "Ur Dad... is he in?" Tace "Ehh yana sama" Juyawa tayi tana kallon Ammi tace "Ammi it's ya Khaleel" Ammi tace "Ohk, let him in" shigowa parlon yyi, Ammi na kallonsa tace "Sannu da xuwa" ya gaisheta ta amsa tace "Daxu Abbansu Islam ke ce min anyi discharging din ka.... Ya karfin jikin?" Khaleel yace "Alhmdllh naji sauki, na xo yi masa godiya ne" Ammi tace "Ohh bbu komai ai, he is coming downstairs now, have a sit...." Xaunawa Khaleel yyi yana gaida Yakumbo dake ta kallonsa tayi mitsi mitsi da ido, can ta share hawayen idonta tana kallon Ammi tace "Shi kuma wnn din waye?" Ammi tace "Shine Honorable ke gaya maki ai" Yakumbo ta tabe baki tace "Toh ni dai ce masa nayi wa ya sani ko shi yayi kinnafin din nata da ya gaji ya ga ba sarki sai Allah ga yasin ana ta jifarsa da shi ya maido ta" Ammi ta d'an hade rai tace "Haba Yakumbo, wani magana ne wnn, Heedayah dake hannun mahaifiyar makociyar mu a kaduna, shi dai ta dalilin sa aka kawota nan gidan, ba wai wani abu ba" Yakumbo tace "Atoh ni babu ruwana wllh, ke baki ga kirarsa bane kamar ta mutan da, ai irin su ne ke kinnafin din yanxu, a ajiye batun wani kyansa, wllh duk haka suke ba muna gani a TV ana nuna mana su ba kullum" Ammi bata kuma cewa komai ba sai dai ranta ya baci sosai, Shi dai Khaleel kansa na kasa, Heedayah sai kallon Yakumbo take kamar xata yi kuka, Yakumbo ta kyabe baki ta bude yar jakarta ta fiddo tissue da aka nannade ta warware ta ciro goronta ta fara ci tace "Na nannade kayana kada kura ya fada kai in cutu...." Ammi dai ko kallonta bata yi ba ta kalli Heedayah tace "Ku je da shi gidan Dinar ya gaida Mamin ki a can kafin Abbanku ya sakko" A sanyaye Heedayah ta mike tana kallonsa, ya mike yyi ma Ammi godiya, amma shi ma gaba daya jikinsa yyi sanyi, ya bi bayan Heedayah da har ta kai kofa, Yakumbo tace "Toh Allah ya maka albarka, ai da ba don kai din ba da har yanxu ana ta xargina ana kullatata a xuciya, 6atan wnn yarinya bbu irin bakin jinin da bai ja min ba a duniya, duk inda na kutsa nuna ni ake da d'an yatsa har ya kai ya kawo na dena fita, ko kasuwa na shiga anyi ta leko ni kenan a shaguna" Heedayah ta kulle kofar bayan Khaleel ya fito, tana kallonsa cikin sanyin murya da damuwa tace "Kayi hakuri plss, Ammi na ta gaya min haka take, she's strange because she is old" Yyi mata murmushi bai ce komai ba, tace "Baka yi kama da kidnapper ba, kuma baxa ka ta6a kama da su ba" Kallonta yake without blinking, xata wuce a hankali yace "Why did you think so" Ta juyo da sauri tace "Dama me yasa xaka yi kama da kidnapper? My Yakumbo is just saying that out of frustration, Allah ya raba ka da kama da su, they are the deadliest set of beings on earth...." Sauke idonsa yyi bai ce komai ba, ta fara tafiya ya bi bayanta har suka isa gate, ta kallesa tace "Seems you are not still happy about what Yakumbo said..." Da sauri yace "Noo, it's nothing, nasan haka tsofaffi suke" A tare suka shiga gate din Dinar, ya tsaya bakin kofar parlon ta shiga sanar ma Mami xuwansa, a hankali ya xauna saman kujeran da ya gani a wajen, lkci daya hawaye ya kawo idonsa abinda tun da ya san kansa bai ta6a yi ba, sai dai ya ga ana kuka amma shi bai ta6a ko digon hawaye ba don ya taso xuciyarsa a kekyashe ne, Bai ta6a jin ya tsani rayuwarsa irin na wnn lkcn ba, he just hate everything about him immediately, a da ya kan ji hakan amma baya wani tasiri a xuciyarsa don in few minutes yake dawowa normal, yau kuma sai yaji hawaye na xuba idonsa sosai, fitowa Heedayah tayi tace "Ya Khaleel an ce ka shigo" Jin bai dago kansa ba ta isa gabansa tace "Ya Khaleel" durkushewa tayi gabansa ganin hawayen idonsa, lkci daya ta rikice ta kamo hannunsa tace "Are you okay? Me ne ya faru, ko kirjin naka ne ya fara, tell me plsss" ya girgixa mata kai trying hard to control the tears ya kamo hannunta amma ya kasa cewa komai ya xamo kasa, kuka take sosai tace "Plss ka gaya min what's wrong ya Khaleel, me ya same ka" cike da karfin hali cikin rawar murya yace "I... I want.... you to be a father... mother... and sibling... to me" Shiru tayi hawaye na sauka idonta tana kallonsa, ganin ya sauke kansa kasa hawaye na ci gaba da sakko masa ta rungumesa ita ma hawayen na xuba idonta tace "Did you lost them??" Gyada mata kai ya dinga yi amma ya ki cewa komai, tace "Talk to me plss, did u lost them" cikin sarkewar murya yace "I never had them" ta fashe masa da kuka sosai tace "I promise I will be, I promise you that..." Bude kofar parlon aka yi, Heedayah ta sake sa da sauri har lkcn tana kuka ta mike, Mami ce tsaye bakin kofar ta fito da mamaki tace "What happened???" Heedayah dai ta kasa cewa komai sai goge hawayen da ya ki tsaya mata take, Mami ta daga kan Khaleel da ya sunkuyar da kansa ya ki dagowa, ganin idonsa tace "Subhanallah what happened, are you Okay" ya girgixa mata kai cike da karfin hali ya mike cikin sanyin murya yace "I... I came to thank you Ma, I appreciate ur care toward me...." Hawayen dake sauka idonsa yasa Mami ta ji lkci daya nata idon ya cicciko tace "But you don't need to dear, you don't need to..... Come in" kama hannunsa tayi xuwa parlon Dinar, Heedayah ta bi bayansu tana goge hawayen dake xubo mata, Xaunawa Khaleel yyi saman kujera lkci daya yaji ya samu nutsuwa, xuciyarsa ya daina masa xafin da yake masa with just Mami's word, daki Heedayah ta wuce ta ki tsayawa a parlon don gaba daya xuciyarta tayi rauni abinda yace mata, Mami ta sa mai aikin Dinar ta kawo abinci da ruwa ta ajiye masa, shiru yyi kawai yana kallon abincin, tun da ya san kansa sai dai ya shiga eatry ya ci abinci bai san dadin abincin da aka girka a gida ba, muryar Mami ya ji tace "Ka ci abincin" Ya kalleta snn ya xamo kasa a hankali ya xauna ya bude plate din abincin, shinkafa ne da miya with many meat sai coslow a wani d'an bowl a rufe, ya dau spoon ya fara cin abincin a hankali, Mami dai sai kallonsa take don exactly yanda Junaid ke xaman cin abinci ya xauna, Dinar na sakkowa xata dauko ma Fadil fresh yo a kitchen ta tabe baki tayi wucewarta kitchen din, kawai ita dai ta ji ranta bata yarda da Khaleel ba, ga shi da innocent face, very innocent, but ita dai bata yrda da shi ba. Abba ya dau makullin motarsa xai fita parlonsa Mumy dake ta kallonsa a tsaye tace "Yau naga ikon Allah, Ina kuma xaka daga dawowa barrister ko hutawa baka yi ba, ga abinci can nace maka na gama ka dau makullin mota xaka fita" Yace "Nace idan na dawo xan ci Maryam, xan je can gidan Dr ne Yanxu" Mumy ta kyabe baki tace "Toh aiki kaje yi Abujan ko har yanxu kan batun 6atan Heedayar ne, ni fa wllh da na ji shiru bbu wani labari kuma babu wanda ya sake cewa komai na xata an ganta ne" Abba ya juyo yana kallonta yace "Eh an ganta, a gidan mahaifanta a nan garin Abujan" Mumy ta saki wayar hannunta ba tare da ta shirya yin hakan ba tace "Ban gane gidan iyayenta ba?" Yace "Yes biological parent dinta, idan kina jin Honorable Ahmad Yusuf Ishaq, shine Mahaifinta" Mumy ta masa wani kallo tace "Ban gane ba, wacce Heedayar wai kake fadi barrister, Heedayah da ba lallai a sake ganinta ba kake nufi ko warce?" Abba yace "Toh ki tambayi d'an ki xai fi yi maki bayani in details a kan abubuwan da suka faru, tare aka yi komai da shi a Abuja, as for now sai na dawo...." Bai jira cewarta ba ya fita, ta cire dankwalin kanta jin wani xufa dake keto mata tun daga saman kanta har kasa duk da Ac dake kunne parlon, da dankwalin ta dinga fiffita ma kanta iska can ta dau wayarta da screen din ya tarwatse ta shiga kiran Shuraim, yana fara ring ya daga tace "Duk inda kake kuma duk me kake yi ka barsa ka dawo gida yanxun nan ina jiran ka" Jin yanayinta yace "Lafiya Mumy??" Kuka ta sakar masa tace "Ni dai nace ka dawo yanxun nan Aliyu" Daga haka ta katse wayar ta sake jefarwa kasa tana xagaye parlon, gaba daya xuciyarta ta ki yrda ko na second daya da xancen Abba sai kace wani film, wai wani Alhaji Ahmad Yusuf Ishaq shi ne uban Heedayah, ta ina?? Bayan ko kama da shi ma bata yi ba, yarinyar da aka ce an tsinto a daji, to amma kuma ai barrister baya mata karya wasu hawayen da bata san dalilinsu bane suka shiga sakko mata tace "Aikin banxa, uban wa xa ayi ma wnn karyar, Alhaji Ahmad Yusuf Ishaq ne ubanta shine da ta 6ata ba a ji a duniya ba...." Tsaki ya ja ta nemi waje ya xauna tana kara tabbatar ma kanta raina mata hankali kawai Abba yake, ya ma san wanda ya ambato mata a matsayin uban Heedayah kuwa, abinda ance mata Heedayah ta shiga duniya kenan ba dawowa, mikewa tayi ta sake daukar wayarta tana neman layin Sadiya. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Abba ne xaune parlon Kaka, ita kuma tana xaune daga kan darduman da tayi sllh hannunta rike da carbi, tun fara bayanin Abba kaka ke kallonsa kamar a lkcn ta fara ganinsa, har sai da ya kai aya kaka ta ki cewa komai sai xare ido take, Bude kofar parlon aka yi hade da sallama Baffa ya shigo, ya xauna saman kujera yana kallon Kaka ya gaisheta, jin tayi shiru bata amsa ba yace "Lafiya Baaba??" Kaka ta kunce ha6ar xaninta ta fara matsar kwalla tana shessheka tace "To dai tunda mu ke kallon banxa bai ta6a hadani da Heedayah ba Allah ya so ni, Umaru kaga shi yasa aka ce mutum ya ji tsoron Allah ko, yanxu da na biye ku nace baxa a rike wnn yarinya ba tun farkon kawota gidan nan da Amadu yayi da na shiga uku na lalace yau, amma da yake xuciyata fess ban biye xugar kowa ba, inji Amadu ya fada maka waye uban Heedayah, to wllh duk abinda mutum xai yi ya ji tsoron Allah ya ji tsoron gamuwarsa da Allah, ni dai duk xaman mu da yarinyar nan ko kallon banxa ban ta6a yi mata ba balle in hantare ta wllh, Allah ubangiji ya so ni, wa enda suka yi hakan ma Allah ya yafe masu, ni fa lkcn da ubanku ke da rai na sha tsinto yara a titi su girma wajena in aurar da su, kalar tawa baiwar kenan, shi sa Heedayah ma nayi mata rikon da ku kanku ban maki ba....." Tana kai wa nan ta mike ta nufi gun akwatinta tana share guntun hawayen idonta, daga akwatin tayi tace "Allah me yanda ya so...." Baffa yace "Me kuma xa ki yi da akwati Kaka" Kaka ta juyo da sauri tace "Ai Abujan xa ku kai ni in karanto ma uban duk abun arxikin da aka yi mata ba tare da mun dubi cewar a titi aka tsintota tana galantoyi ba, to wai ma waye silar riketa a gidan nan?? ba ni din bace dai, nan nan nan Amadu ya watsar da lamarinta ya bar mu daga ni sai Rakiya muna ta wahala da ita meye ba mu yi mata ba na gata wanda ko gaban uban nata take ba lallai yyi mata ba, har filina sai da na kusa siyarwa lkcn da xata makaranta, daga karshe ma Amadu koramu yyi ni da Rakiya daga gidansa ta dalilinta, shi dai kawai Allah ya basa baiwar tsinto mana ita ne ya kawo mana, amma asi bai mata ba, kashinta, fitsarinta, duk bbu wanda ni da Rakiya bamu ci ba, barin ni don Rakiyar ma gantalin aikinta take tafiya ta bar ni da ita" tana magana tana hawaye, daga Abba har Baffa kallonta suke baki bude, Ta sharbe majina tace "Kuma na daga jaka ace min ina xan je sbda rashin tsoron Allah, to Abuja xan tafi" Baffa yace "Haba kaka, ke ya kamata ki bi su, ko su ya kamata su xo su sameki a nan??? Da girman ki xaki ce xaki bi su Abuja, ba su ya kamata su xo nan su maki godiya su baki girman ki ba" Cikin daga murya Kaka tace "Aa wllh bbu ruwana da wani girman kai, rawanin tsiyar xa ku dinga laka6a min, shi yasa fa aka jefo shaidan daga aljanna aka ce, to meye kuma wani girma kamar wata gyambo, Allah ai shine abun girmamawa, bana son girman daga yau ma idan xaku ce min Patuu duk ku ce bbu ruwana da iskanci, meye wani da girmana kamar dai ni na halicce shi uban yarinyar, mu tafi kawai ku dora ni a mota inyi tafiyata, bance wani gantalalle ya kai ni ba dama" Abba dai bai ce komai ba sai kallonta yake, Baffa yace "Toh ki jira Allah ya kai mu gobe lafiya mana" Kaka tace "Ba a xuwa Abujan da daddare ne ko walakanta ni ku ke son ku yi?" Baffa yace "Yanxu idan ance ki bi hanyar nan da ba shi da kyau ai baxa ki bi ba kaka" Kaka ta jinginar da akwatin ta koma ta xauna tace "Matsiyatan yan kidinafin ma kadai ai sun isa hanani tafiya yau, shegu" Mikewa Baffa yyi yace "Na shigo in gaisheki ne dama, sai anjima" Bai jira cewarta ba kamar yanda Kaka bata ko kallesa ba har ya fita parlon, kaka ta rike ha6a baki bude tana naxarin Maganganun Abba, can ta daga hannu sama tace "Ni dai Allah ya rufa min asiri wllh, dama tun ranan da na fara ganin Deedayah na ji ta kwanta min sosai, ban bari tayi rashin uwa ba ko na sakwan daya, ban kyamace ta ba, abinda ma nake mata ban ma jikokina ba wllh" Washegari da ya kasance Friday, da safe karfe takwas Mami ta gama shirin komawa Kaduna tare da Farida, ta shiga bangaren Ammin Heedayah don yi mata sallama, Heedayah ta fito daki don a nan ta kwana tun bayan da ta dawo gidan nasu da Khaleel daren jiya gun Abbanta, ta xauna gefen Mami tana kallonta tace "Mami good morning" Mami tace "Morning dear, how was ur night" Heedayah tace "Alhmdllh, Ina xa ki Mami?" Mami tace "Xamu koma kaduna yau" cikin sanyi Heedayah tace "Mami tafiya xa ku yi ku bar ni nan?" Ammi dai bata ce komai ba, Mami tayi murmushi tace "Abbanki xa su taho anjima sai ki biyosu" girgixa kai tayi ta mike tace "Noo Mami we are going together, ki jirani in hada kayana" tana fadin haka ta koma dakinta da sauri, Mami ta mike tace "Sae kun taho Amina" Ammi ta mike tace "Aa ki jirata ku tafi din Hajiya...." Mami tace "Aa, kamata yyi ku taho tare din xai fi" Ammi tayi shiru ganin Mami ta nufi kofa ta bi bayanta da sauri tace "Abban su Islam yace ya turo maki sako ta WhatsApp ki duba yanxu Hajiya" Mami tace "To in sha Allah" har bakin gate ta rakasu snn ta koma ciki, tsaye taga Heedayah a Veranda, ta juya da sauri ganin uwartata tana goge hawayen idonta, Ammi ta dinga kallonta snn tace "Don't worry dear, anjima xa mu wuce Kadunan gaba daya ai, flight sai nan da karfe biyar in sha Allah na yamma" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta wuce ciki. Mami na komawa ta bude WhatsApp din nata taga flight ticket guda biyu da Abban Heedayah ya turo mata, rasa ma abinda xata ce tayi, Dinar dake xaune tare da ita a parlon tace "Jirgin dai da baki son bi shi xa ki bi at last, ki kirasa kawai ki ce kin gani Allah ya saka, sai in kai ku airport din xuwa nan da karfe goma tunda flight din sha daya ne" Mami dai tayi shiru bata ce komai ba. Mumy ce xaune dakin Sadiya idonta yyi bulu bulu don kuka, Hajiya Sadiya tace "Ni fa wllh wllh idan ba ke kika yi ido hudu da shi wanda aka ce shine uban Heedayah ba kika xo nan kika fada min hakan da bakin ki to ni ba yarda xan yi ba, sai kace wasan kwaikwayo a taya wnn sanannen Mutumin xa ace shine ubanta, 'yar kamar wnn mutumin ta bace farat daya ace ba mu ji a gari ba" Mumy ta fyace majina da tissue din hannunta tace "Nima dai shi na gani Sadiya..." Sadiya tace "Toh wai da kika kira Shuraim din me ya ce maki?" Mumy tace "Uban me xai ce min dama, kawai ce min yyi eh haka ne, nayi nayi nayi ya fadadada min bayani amma yace bai san komai ba haka kawai Abbansa ya gaya masa shi ma, to ya xan masa?" Sadiya tace "Kaii karya ne wllh, wnn sanannen bawan Allah dai karya ne ace shi ya haifi Heedayah, ta ina suke kama? Shi baki ita fara, snn me kudi da fame kamarsa xai bar 'yar sa a makance??" Hajiya Baturiya dake dakin duk tana sauraronsa tace "Abinda ku ke mancewa a nan shine, shi wnn bawan Allah Honorable Ahmad Yusuf Ishaq da ake batu akai, duka duka yaushe ya fara siyasa da har yyi sunan?? Ina jin bai kai shekara uku ba, don ko da yana siyasar ma to gaskiya a shekaru uku xuwa hudu jama'ah suka san sa har ya xama famous haka, xai iya yiwuwa sai bayan batar 'yar tasa ya shiga siyasa gadan gadan har yyi kudi haka, kuma idan baku manta ba ni dai na sha fada maku wnn yarinya bata yi kama da yar kananun mutane ba, ku dubi jikinta ko a lkcn da Barrister ya kawota bbu wani alamar wahala kawai dai makauniya ce...." Mumy dake ta mata wani shegen kallo tace "Toh in sha Allahu ba ubanta bane shi din, idan Allah yayi duniya don manzon Allah, taya ma xa ayi ya xama ubanta, mutumin dake neman takarar gwamna a jihar kano, meye hadin biri da gada, yarinyar da mijina ya tsintota a makance a daji bbu galihu...." Hajiya Baturiya tace "To yanxu idan da gasken shine ubanta ya xa kiyi Maryam?" Mumy ta fashe da kuka tace "Wllh wllh ba shine ubanta ba in sha Allah, matsiyaciyar yarinyar da Mai gidana ya tsinto a bola xa ace attajirin nan ne ubanta, dubi fa uban plazozin da yake da shi a jihar nan da ma kano, in sha Allahu ni baxan ji kunya ba muna nan da ku xa ku ga karya ne, idan kuwa gaskiya ne toh sai dai fa ayi hakuri da abinda xai faru" Sadiya tace "Toh Allah ya sa karyan ne, amma idan haka ya kasance ai baki ci ribar komai ba wllh" Mumy tace "Ai sai dai idan ba ni Maryam ba, yanxu ma gidan Dakta xan tafi in ji abinda ake ciki nasan yanxu kaka tana da labari tare da ita" Sadiya tace "To mu je mana gaba daya" A tare su ukun suka tafi gidan Baffa a motar Mumy.... karfe shidda saura Abban Heedayah ya fito government house na Kaduna tare da few convoy, tun shigowarsu kaduna ya kira Shuraim da ya xo har government house din ya samesa don kai sa gidan Baffansa, sanye yake da khakinsa da yayi fitting dinsa sosai, Shuraim suka gaisa da gwamna dake tare da Abban Heedayah don da shi xa a taho gidan Baffa, tun da Heedayah ta yi ido hudu da Shuraim bata sake yarda ta kallesa ba, kuma ta ki gaishesa, shi ma din bai sake kallon direction dinta ba, mota daya ta shiga da Abbanta da Amminta, motoci biyar ne banda na sojoji da na governor da suka yi parking a kofar gidan Baffa, Shuraim ya sauka, Heedayah ta bude motar ta fito don Allah Allah take ta ga kaka ta nufi gate da sauri, parent dinta ma duk suka sauko motar, da ido Shuraim ya bi ta don sai da ta d'an bugesa ta shiga gate din gidan, Heedayah na shiga main parlor din gidan ta fara kwala ma kaka kira, Mumy ce xaune parlon da kawayenta da Mum din Sudais suna magana kasa kasa, bata ko kula da su ba ta ci gaba da kiran kaka.... Sai ga Kaka ta fito dakinta, da gudu Heedayah ta tafi ta rungumeta, Kaka tace "Ina gwamnan yake??" Kaka bata rufe baki ba Shuraim ya shigo, ganin Mumy a parlon ya ki karasawa, yana kallon Kaka yace "Xa a shigo..." Kaka ta tura Heedayah tace "Su shigo mana me suke jira a waje, ai tun daxu nake ta jiransu Umaru yace min suna hanya, mu dai ba mun rike yar su da amana ba, wanda ya ki Heedayah yau ne ranan jin kunyarsa, don ma Sudais da muka hada baki da shi aka rike Heedayar yana can kasar waje, da ba don shi ba, ba don ni ba da yanxu wani labarin ake ba wnn ba....." Mumy dai sai kikkifta ido take, haka Umman Sudais, Ammi ce ta fara shigowa parlon da wife din governor din garin da sallama, Kaka ta amsa da karfi ta karaso cikin parlon tana kallonsu Mumy cikin fada tace "Ku tashi ku basu waje su xauna mana, kun ja6e kamar masu neman aiki" Kallon kaka kawai Ammi take da murmushi, Kaka ta fashe da kuka sosai tana kallon Ammi tace "Wllh kamar kinyi kakin Heedayah, ni dai dama nasan Heedayah ba gantalalliya bace, dama kallon banxa bai ta6a hadani da ita ba, wa enda suka yi mata ma Allah ya yafe masu ita ma kuma ta bar su da Allah, amma ke banda lalacewa ta sameki garin yaya kika sake yarinya makauniya kamar akuya ta shiga duniya, a titin kano fa Amadu ya tsintota tana galantoyi bbu idanuwa, da karo karo ya hada dubu milyan 5 ya biya kudin aikin idonta a kasar Indiya wllh, har ni sai da na bada nawa gudunmawar, bbu yanda basu yi in bi su indiyar ba nace su tafi kawai a barni in ta masu addu'a kawai, to ba gashi ba yau komai ya xama labari ba, ai makiyan Heedayah sai dai ciwon xuciya ya kai su lahira yau...." Kaka tayi tsit ganin gwamna ya shigo tare da Mahaifin Heedayah, Mumy sai xare ido take daga inda take xaune ga xufa da ya bi ya dameta, kamar hadin baki lkci daya ita da su Sadiya duk suka mike suka koma bayan kujera kamar munafukai suna gwale ido.... Kaka ta saki kuka kamar yar yarinya tace "Dama bbu yanda banyi da d'an bakin cikin nan Shureen ya kai ni gwamnet house ba sai ga gwamnan yau a gabana...." Abban Heedayah ya isa har gabanta yana kallonta ya xauna nan kasa. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you. Have u ever wondered how desserts are made? Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from? Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught: *Profit analysis *Ways to handle desserts *Dessert marketing. This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos. Registration is on and the fee is just N3000 Naira. Class starts on 27th august,2021. And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕 WhatsApp 08135358038 Call 📞 08135358038 IG: najaatu Ibrahim A boye Mumy ta dinga goge hawayen da ya cika idonta daga inda suke tsaye bayan kujera da kawayenta, Mum din Sudais kuwa sae xare ido take, Bayan duk anyi gaisuwan mutunci a parlon Baffa da Abba ma duk suna parlon, Mami ta iso gidan tare da Hajiya Zuwaira matar Baffansu Junaid, ruwa da lemo da snacks iri iri na alfarma da peppered chicken wanda Step mum din Sudais tayi aka ajiye ma bakin, Abban Heedayah yayi kasa da murya yana kallon kaka da ta nemi waje ta xauna tayi tagumi tana facing dinsa kamar marainiya, a nutse yace "Inna mun xo ne don maki godiya...." Ta dakatar da shi da sauri tace "Aa ba ruwana ka gode ma Allah, Mu dai ba mu rike Deedayah don a bamu komai ba ko ayi mana wani abun, amma fa an sha barnan kudi ba na wasa ba kaji in gaya maka, gwangwanin milon nan da Madara har sai da na dinga tarasu buhu buhu ina yi ma 'yan gwangwan sadaka, a karshe dai sai da tattalin arxikin Amadu ya jijjiga don ma ina taimaka masa ban bar sa yyi ta wahalan shi kadae ba, kuma ko kallon banxa bamu ta6a yi ma yarinyar nan ba, ynxu haka rabona da xuwa Makka tunda Amadu ya tsintota, Atoh hidima tayi masa yawa mana ga kudin gyaran ido ga kudin kayan shayi ga kuma hidimar iyalansa, ga dai ta nan ka tambayeta ko an rageta da komai shekaru biyar din da tayi da mu..." Ta fada tana nuna masa Heedayah dake xaune kusa da ita, Heedayah dai bata ce komai ba, kaka ta ci gaba tace "Ni fa wllh na dauka ma iyayenta sun rasu ne ta shigo duniya, kuma ni ban sace ma Amadu gwiwa ba da ya kawota matarsa ce ma ta so bamu matsala, kai ta ma bamu sai dai a bar kaza cikin gashinta, to yanxu duk ba wannan ba, babban damuwata a nan shine.... Shekaru kusan biyar kenan tunda wancan mutumi...." Ta fadi haka tana nuna gwamna ta ci gaba, "Tun da ya hau mulki kafin ma ya xarce nake fama da Shureen ya kai ni wajensa in basa shawarwari in kuma ce ya ji tsoron Allah kada giyar mulki yyi ta debarsa yana abinda ya ga dama amma wnn yaron ya ki kai ni, titin unguwarsu aminiyata ta Salla fa duk ya gantale ya ki shimfida masu sabo, idan kaje layin xaka xata a ruga kake, mu kaga dai namu ai ko kwarzane bai yi ba tunda duk manyan masu kudi ne a layin suka hada kudi suka yi abun su bakinsu alekum, can kuwa bbu me yi duk talakawa ne, ni fa dalilin titin yasa bana son xuwa wajen ta Sallah, to kaga kuwa ya raba xumunci, snn kuma inji ko ya hau mulki ne don ya dinga musgunawa talakawa uwa shi ya halicce su, ina fa da labarin kwace masu filaye da yake yi yace na gwamnati ne, to banda lalacewa a gidan ubanwa filaye ya xama na gwamnati? Filayen da ke nan tun kan a haifi uban da ya haifesa, na fa san uban nasa, yana nan wani tsamurmuri kamar buzu tare muka yi wasan kasa da shi, snn shi mutumin kirki ne bansan garin ya d'an sa ya gantale ba da cuta...." Shi dai me girma Gwamna banda murmushi bbu abinda yake yana kallon kaka da ta hakikance, Abban Heedayah dai kansa na kasa yana sauraron kaka, Abba da Baffa ma duk sun kasa dago kai kowa da abinda ya damesa a xuciya, Shuraim kam banda harararta babu abinda yake, Mami dai dake xaune tare da Hajiya Zuwaira da Hajiya Hauwa tayi tagumi tana kallon kaka, Ammin Heedayah da matar gwamna sai murmushi suke su kam, Mumy da mukarrabanta na ta tsaye bayan kujera kamar munafukai, Mumy dai bata ma san me ake cewa a parlon ba sai share xufa take tana gwala ido... Kaka tace "Toh ba ruwana na fita hakkin ka na fada maka gaskiya Allah baxai tambayeni ba ranan gobe kiyama" gwamna yyi murmushi yace "Gaskiya ne" Kaka tace "Atoh" kallon Mumy kaka tayi ta nuna ma Alhaji Ahmad tace "Kaga uwar gidan Amadu can, ita ta haifi Shureen din da nake fada maku, mu dai kawai a bar kaza cikin gashinta....." Alhaji Ahmad ya kalli Mumy yace "Mun sameku lafiya Hajiya?" Mumy na kirkiran murmushi cike da karfin hali tace "Alhmdllh wllh, sannun ku da xuwa...." Yace "Mun gode, Allah ya saka maku da alkhairi ya duba gabanku da bayanku....." Kaka tace "Na dai ce a bar kaza cikin gashinta amma wllh tllh mu muka san abinda muka gani, amma kawai dai a bar kaza cikin gashinta, to matar da.... Bari kawai dai a bar kaza cikin gashinta" Mumy dai sai xufa take, Shi dai Abban Heedayah kansa na kasa, Ammin Heedayah ta d'an kalli Mumy sai kuma ta dauke kanta, kaka tace "Tunda mu dai muna sonta kuma ba mu cuceta ba ai shkkn tone tone ba kyau, amma dai Heedayah ta sha wahala wllh" shiru duk aka yi a parlon, kaka tace "Bari dai kawai shirun ya fi, amma tunda nake ban ta6a ganin mugunta a fili da bakin hali irin wanda na gani ba, to wnn bai wani dameni ba don wllh kanta tayi ma, ni baxan tona mata asiri in fadi irin tsana da kyara da tsangwamar da ta dinga yi ma Heedayah ba ta nuna ita baxata riketa ba, ta xo har gida ta dinga xugani kar in amsheta ince ma Amadu xan masa baki idan bai mayar da ita inda ya tsintota ba, to wllh baxan tona mata asiri ba, Allah kuma ya rufa min asiri yanda na rufa mata amma kaga warcan...." Ta fada tana nuna Mami, tace "Surutu ba shi da amfani, amma wllh tllh ta dalilin Deedaya ta amince ta auri Amadu don ta riketa ganin bata da gata, kasan abokiyar aikinsa ce dukaninsu lauyoyi ne, mijinta ya mutu ya bar masu uban dukiya ina jin da kyar idan bata fi Amadun ma kudi ba, amma ta yrda ta auresa duk sbda Deedaya tunda an ki riketa a gidan, baxan dai fadi warce ta ki riketa ba, in gaya maka Rakiya ta sadaukar ta auresa ta rike Deedayah fiye da ynda bafillatanar uwarta xata riketa, ko ku kunga wani alamar cutarwa tare da Deedayah da ku ka ganta??" Abban Heedayah ya girgixa kai yace "Ko daya" Kaka tace "Atoh, don haka idan ma duk shekara ka dinga kai Rakiya makka wllh baka biyata ba, duk da ni dai bance a kai ni ba tunda sbda Allah na yi ba sbda a kai ni Makka ba, Amadu kuma ynda xaka biyasa kawai ka bar masa Deedayah na har abada ya ci gaba da rikon abarsa, da ace yana da d'a namiji me hankali ne ma sai ka basa auren Deedayar, to babu, Allah bai basa ba, sae dai da ace ita Rakiya na da d'a namijin amma banda Junaid sae a hadasu kawai don ita ma ta bauta mata, amma dae baxae ma yiwu ba, Heedayah ba gantalalliya bace...." Heedayah dake ta kallon kaka ta dau lemo daya ta mike tayi wucewarta dakin kakan tana turo baki. Xaunawa tayi gefen gado ta bude drink din hannunta tana sha, sae kuma ta mike da sauri tana duba dakin ko xata ga wayar kaka, ta gansa ta nannadesa da handkerchief ta ajiye a kusa da pillow, dauka tayi ta duba ko akwai kati, ganin akwai tayi dialing number snn ta kai kunne, ba a dau lkci ba ya fara ring aka daga, sallama tayi, aka amsa calmly daga daya bangaren, tace "Ka shigo Kadunan ne?" Yace "Yea tun da rana, I've been waiting for ur call tun daxu" tace "Bamu dade da isowa ba, ya jikin?" Yace "Na ji sauki sosai, Alhmdllh" tace "To kana shan maganin?" Yace "Ai kin ce in sha, so I just have to take it" Tace "Toh Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen, where are you now?" tace "Muna gidan Yayan Abbana yanxu...." Yace "Ohk, how about Mami" Tace "Ita ma ta xo nan din" yace "A nan xa ku kwana?" Heedayah tace "Aa xa xan bi Mami mu koma can gida" shiru ya d'an yi, sai kuma yace "Can I come later?" Ita ma tayi shiru kafin tace "Just pretend as if u came to greet Mami" Yyi murmushi a hankali yace "Ohk, but...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yyi kasa da murya yace "Shkkn dai, I will come in sha Allah da daddare...." Bude kofar dakin ta ji anyi ta katse wayar da sauri ta xame daga kunnenta ta ajiye kan gadon ta jawo pillow ta rufe ba tare da ta kalli wanda ya shigo ba, satan kallon mirror din kaka tayi taga Shuraim bakin kofar, ya shigo ya rufe kofar dakin ya karaso ciki, ita dai ta ki juyowa, can kuma ta mike da xumar xata fita still wanting not to look at him, calmly yace "Don't move...." Tsayawa tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace "To me nayi" yana kallonta daga sama har kasa ya karasa har gabanta yace "Kina da grit din da xa ki tafi gidan saurayi kamarki ki kwana ki yini, and you are happy and comfortable bcos nobody is saying anything to you about that right? Everyone is just concentrated on ur reunion with ur parent, and ur stupid mind is letting you think you are right ko??" ita dai bata ce komai ba, Ya d'an daga murya yace "Now tell me, uban me kika je yi gidansa at the first place, and uban waye shi din, why did u follow him to his home, What were u busy doing for 24 hours in his home?" Ta fashe da kuka tace "Ni fa Ya Shureen ban sani ba, kuma ba gashi na dawo ba dai....." Ya dinga kallonta bbu ko kiftawa, ta marairaice tana kallonsa ita ma ganin ko kadan bbu wasa tattare da shi, yyi kasa da murya fuskarsa daure yace "Now tell me, meye tsakanin ki da shi, and a gidan uban wa kika san sa? Snn a ina kika kwana a gidan nasa" Turo baki tayi kafin tace komai ya Fixgota dab da shi ta 6ara baki xata yi ihu bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, and he gave her the first kiss of her life, a french kiss it was, everything happened in just a minute, lkci daya ya saketa ya fice daga dakin.... Ta kusa minti biyu tsaye bata ko motsi bayan fitarsa, a hankali ta kai hannu bakinta da ta ji yyi mata sanyi, sai kuma ta sulale kasa a hankali ta xauna gabanta na wani irin bugawa, ganin abun take kamar a mafarki, ta sake kai hannunta bakinta, lkci daya ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba ta mike da sauri ta fada kan gadon kaka ta rufe fuskarta da pillow tana kuka sosai.... Kiran sllhn Magrib ya sa kaka ta shigo dakinta baki har kunne, har sannan Heedayah na kwance saman gado tayi kukanta ta koshi tayi shiru, kaka ta washe baki tace "Sannu Deedayah, har kin tashi? Kina son wani abu ne?" Heedayah ta turo baki ta girgixa mata kai ta mike xaune tace "Suna parlon?" Kaka tace "Wani parlon, sai kace dai gantalallu, sun sallameni sun wuce amma ubanki yace xai dawo gobe da safe, bari in sa a kawo maki abinci idan abincin bai maki ba ma sai a samo maki abinda ranki ke so" Heedayah tace "Mami fa??" Kaka tace "Ai ta riga su tafiya, kinsan matar akwai kamun kai, in gaya maki gwamna ma yace bana da ita xa aje makka idan Allah ya yarda, ni dai nace masa A'a amma ya ki saurarata to bbu yanda na iya tare xa mu je da ita yace, anjima kuma xa a kawo min motata a adana min a garejin Amadu abinda na tambayi ubanki kenan farat daya ya bani" Kaka ta nuna mata dankwalelen Zinari na zobe tana washe baki tace "Matar gwamna kuma ta bani wnn, wai tana so na, yanxu gobe xan je in gaisheta da safe, sannan Babanki yace idan xa su koma Abuja in hada kayana tasss, to ni bana son in tsaya muna musu da shi ina matsayin babba shi yasa nayi shiru rai bbu dadi, Maryam kuma na can dakin uwar Sudais ta kasa wucewa gida ni da naga yanayinta ma na xata bori xata hau, wato ta girgixa ba kadan ba, Allah ubangiji ya rabata da hawan jini farat daya dai, ga shi bbu wanda ya bi ta kanta sai Rakiya da ni ake ta kulawa don ma ban tona mata asiri na fadi irin tsanar da ta maki ba, gwamna kuma yace xai ba Rakiya wani mukami na lauyanci ina jin a gwamnati, ni dai kawai nayi shiru ne amma ga dai Amadu me yasa xai ce sai Rakiya idan ba kyasa ta yyi ba, balle ma da aurenta a kai take gantali, don Amadu ai bai saketa ba, yanxu gobe xan lallaba Shureen in basa duk abinda yake so ya kai ni gwamnet house...." Sai da gaban Heedayah ya fadi da kaka ta ambato Shuraim, Kaka kamar xata yi kuka ta nemi waje ta xauna a hankali tace "Allah sarki Sudess baya nan wnn abun alkhairin ke faruwa, bai kamata a mance da shi ba don shine silar xamanki a gidan nan" Heedayah dai tayi shiru, can tace "Kaka ni fa gidan Mami xan wuce" Kaka tace "To ai ta tafi idan ba dai Shureen ya ajiye ki ba, yana can parlon Baffansa bari in je in samesa" Heedayah da hankalinta ya tashi da sauri tace "Aa kaka kar ki ce masa...." Kaka tace "Aa ba ruwana ya xa ayi a bari ki kwana a nan ba da son ranki ba, ba sai Allah ya kama mu ba idan ranki ya bace, bari inje nasan idan Baffan nasa yyi masa magana xai kai ki har parlon Rakiyar idan xai iya" Bata jira cewar Heedayah ba ta fice, Kai tsaye ta shiga bangaren Baffa, shi da shuraim kadai ne xaune parlon, kaka ta kalli Baffa da yyi shiru ganinta, snn ta kalli Shuraim da kansa ke kasa, tace "Me ya faru kuma?" Baffa ya sauke ajiyar xuciya bai dai ce komai ba, Kaka ta nemi waje ta xauna tace "Nace me ke faruwa, shi gashi ya xauna gabanka kamar me neman gafara, laifi yyi ma uban nasa ne?" Baffa yace "Aa, ko daya, muna tattauna wani batun ne daban" Kaka tace "Toh ni ba wannan ba, Heedayah ce tace xata tafi gidan Rakiya kuma kaga bbu me kai ta, gantalallen dreban ka dare nayi yake kama gabansa, don haka nace Shureen ya je ya ajiyeta kada mu shiga hakkinta, kaga dai tana da hankali bata ce xata bi iyayenta ba sai uwar rikonta, kaga kuwa ai ba butulu bace ita" Baffa yace "Toh xai ajiyeta idan xai wuce" Kaka ta mike tayi ficewarta daga parlon ranta fess, ga sabuwar mota, ga zinari, ga tafiya makka, gobe kuma xata gwamnet house, Baffa na kallon Shuraim da ya ki dago kansa yace.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you. Have u ever wondered how desserts are made? Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from? Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught: *Profit analysis *Ways to handle desserts *Dessert marketing. This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos. Registration is on and the fee is just N3000 Naira. Class starts on 27th august,2021. And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕 WhatsApp 08135358038 Call 📞 08135358038 IG: najaatu Yakudima Baffa na kallon Shuraim da ya ki dago kansa yace "It's time for Magrib and you will be going for duty, idan anyi sllh ka ajiye Heedayah gida kawai, we will talk tomorrow in sha Allah..." Shuraim ya mike yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya nufi kofa Baffa ya bi sa da kallo har ya fita. Ana idar da Magrib Shuraim ya shigo gidan, ya karasa kofar dakin kaka ya bude yana kallon ciki, Heedayah na xaune saman darduma ta idar da sllh, Kaka na rike da tsintsiya tana tattare tattaren dakin ta juyo tana kallonsa tace "Ka ci abinci kuwa Shureen?" Yace "Na koshi" Tace "To har xaka wuce?" Yace "Ehh" tace "Atoh gaskiya ka jira ta ci abinci gashi nan na je na amso mata, sllh tayi yanxu" Shuraim yace "Xan yi wucewata..." Kaka tace "Toh ka tafi, ko ni ba sai in kai ta ba" Heedayah dai kanta na kasa ta ki dagowa, ba don Khaleel da yace mata xai xo anjima ba dama da bbu inda xata je gwara ta kwana a gidan kawai, but he said he is coming after Magrib tasan kilan ma yana can yanxu, Kaka tace "Kinga ki rabu da shi yyi wucewarsa ki dau abincinki ki ci, ko ni da Umaru ba sai mu kai ki gidan ba, wa xai ja ma aji a nan, ni ko ke?" Heedayah tayi kasa da murya tace "Ni a koshe nake na ci abinci" Kaka ta mike tace "A saboda me? Me kika ci, kar fa ki biye ma Shureen, ki ci abincinki ki koshi, idan kuma shayi xa ki sha sai ki hada" Heedayah tace "Na ci abinci kafin mu taho" Kaka ta juya tana kallon Shuraim kafin ya ce komai yace "Ina waje" daga haka ya juya yyi ficewarsa, Kaka tace "To ko in juye maki abincin a cooler ki tafi da shi?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa na koshi da gaske" Kaka tace "Toh shkkn, ni dai na fita hakkin ki, idan kun je ki gaida Rakiyar" Heedayah ta mike ta dau mayafinta da karamin jaka ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, duk gaba daya a sanyaye take, kaka tace "Ni ban ma fiye son kina bin Shureen din nan ba, shi ma ba sanin xuciyarsa muka yi ba har yau" Heedayah dai bata ce komai ba ta fita ta kullo mata kofarta, sama ta fara wucewa ta shiga dakinsu Zainab, ta samu Zainab xaune tana Azkar a saman darduma, Zainab tace "Har xa ku wuce?" Heedayah tace "Ehh xan wuce" ganin yanayinta Zainab tace "Are you fine?" Heedayah ta sakar mata murmushi a hankali tace "Sure" Kallonta kawai Zainab ke yi, Heedayah tace "Yaushe xa ki xo gidanmu, baki ta6a xuwa ba" Zainab tayi murmushi tace "idan Kaka xata je xan bi ta in sha Allah" Heedayah tace "Toh shkkn, bye, sai da safe" daga haka ta fita dakin ta wuce dakin Mum din Zainab tayi mata sallama ita ma sannan ta fita. Har Heedayah ta isa gate gabanta faduwa yake, ta tsaya bakin gate din tana leka waje, ido hudu suka yi da shi yana xaune mota amma bai rufe motar ba, ta dauke idonta da sauri ta koma gefen gate din ta la6e, ji tayi kamar ta juya kawai ta koma ciki, ta fi minti biyu a tsaye bata sake leka waje ba, Shuraim ya sauka motarsa ya tafi gun gate din, tana ganinsa ta fara kame kame ba tare da ta yadda sun hada ido ba, tana tatta6a jakarta tace "Ina gyara abu na ne" yace "Wuce mu je" Ba musu ta bi gefensa ta fita gate din ta wuce gun motar ya bi bayanta, ta bude front seat ta shiga, sai tsinne kai take kamar mara gaskiya, ya shiga maxaunin driver suka bar layin, har suka dau hanya Heedayah jujjuya zip din dake jikin jakarta kawai take, she is very uncomfortable with him, shi ma kuma bai kalli inda take ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin Shuraim yyi parking dai dai gate din gidan Mami, ta kai hannu xata bude motar taji a rufe, ta sauke idonta kasa bata dai ce komai ba, shi dai idonsa na gaban motar, gabanta sai faduwa yake gashi ta kasa kallonsa, da dane ce masa xata yi ya bude mata motar, sun fi minti biyar a haka, can taji ya bude lock din motar, da sauri ta bude motar ta sauka ta rufe ba tare da ta kallesa ba ta wuce ciki ya bi ta da kallo... Sai da ta shiga gida taji hawaye ya kawo idonta, ta tafi can parking space ta fashe da kuka, tayi mai isarta sannan ta goge bakinta da mayafinta tace "Allah ya isa" Kamar me counting step ta nufi main entrance ta bude kofar a hankali, ido hudu tayi da Khaleel dake xaune parlon tare da Mami, da mamaki Mami tace "Wa ya dawo da ke?" Heedayah ta karasa cikin parlon a hankali tace "Ya Shureen" Mami tace "Yana ina?" Heedayah tace "Kila ya wuce" Tana kallon Khaleel ta xauna kasa kusa da Mami tace "Ina yini" Kallonta yyi yace "Lafiya lau" Mami tace "Kin ci abinci?" Girgixa kai tayi, Mami tace "Toh ki tafi ki diba" tace "Mami Farida fa?" Mami tace "She is upstairs" Heedayah tace "Yaya fa?" Mami tace "Bai dawo ba" Mikewa tayi ta nufi kitchen, Khaleel ya bi ta da kallo, ta juyo suna hada ido ta sakar masa murmushi ta karasa cikin kitchen din, Mami na kallonsa tace "Ina jin ka Khaleel" Ya shafa kansa yana murmushi yace "A can aka haifeni na taso nayi karatu duk a can...." Mami tace "So ur parent are still there" Ya sauke idonsa kasa cikin sanyin murya tace "Theye are late" Mami ta dinga kallonsa with pity kafin ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah ya gafarta masu" yana kallonta a hankali yace "Ameen" tace "But all ur relatives are in gombe still?" Ya sauke idonsa kasa ya gyada mata kai, Mami tace "What do you do for a living?" Shiru yyi na few seconds, can ya daga kai ya kalleta yace "Business nake yi" Mami tace "That's good, what are ur qualifications?" Ya shafa kansa a hankali yace "Diploma, Bsc, Msc.... I am an Architect" Mami tace "Maa sha Allah, kana da 'yan uwa a nan garin ne?" Ya girgixa mata kai, tace "To kanninka ko yayyinka fa?" Ya sauke idonsa kasa, Mami dai sai kallonsa take, deep down her she knows she isn't suppose to be asking him any of this, bai santa ba bata sansa ba, it's his private life, she isn't suppose to intrude but haka kawai taji she wants to know more about him, tana son saninsa sosai, may be because taji ya kwanta mata har ranta, kwata kwata bashi da hayaniya ga ladabi, ga kuma hankali, all in all his smile is just like that of her Junaid, Khaleel yace "I am an only son" Jin Mami bata ce komai ba ya daga kai ya kalleta, kallonsa kawai yaga take yi, tayi masa murmushin karfin hali tace "To Allah ya dafa maka, and u are still not married??" Ya gyada mata kai tace "Allah ya kawo ta gari" yyi kasa da kansa yace "Ameen" Tace "Amma a kawo maka abincin ko kadan ne ka ci" yace "Na ci abinci daxu Ummi" Mami tace "Alright, shkkn" Heedayah ta fito kitchen ta tafi dinning ta xauna da plate din abincin da ta debo, mikewa Mami tayi tace "Ina xuwa" daga haka ta wuce sama, Heedayah ta mike ta dawo parlon ta xauna kasa tana kallonsa tace "Yaushe ka xo?" Yace "Not less than 15 mins ago" Tace "Okay" yace "Daga ina kike?" Tace "Gidan Grandma dinmu, me yasa baxa ka ci abinci ba?" Yace "Na koshi" tayi shiru tana kallonsa, Yace "Waye kika ce ya ajiye ki?" Heedayah ta turo baki kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Yayanmu" Yace "But you look disturbed" shiru tayi tana kallonsa, can tace "Nothing, kawai nayi bacci ne na tashi sae aka maido ni gida" Khaleel bai ce komai ba, bayan wani lkci ya dago kai ya kalleta yace "To ki ci abincin" Ba musu ta ci gaba da cin shinkafar gabanta, ganin ynda yake kallonta ta wara masa ido tace "Ko xaka ci?" Yyi murmushi ya girgixa kai yace "Aa, lomar ki nake gani" tayi dariya tace "Toh baxan ci ba" ajiye abincin tayi gefe tayi tagumi, ya sakko kasa ya xauna a hankali yace "Aa yi hakuri" Bude kofar parlon aka yi Junaid ya shigo da sallama, Kallon Khaleel yake har ya karaso cikin parlon ya basa hannu suka gaisa da murmushi fuskarsa, Junaid yace "Ya jikin?" Khaleel yace "Alhmdllh na ji sauki" Junaid yace "Allah ya kara lafiya" Heedayah na kallonsa tace "Ina yini Yaya" yace "Lafiya lau, yaushe kika xo" tace "Yanxu na xo" Yace "Me yasa baki kwana wajen kakan ba" murmushi tayi tace "Aa ba komai" Sama Junaid ya nufa, Khaleel ya kalli Heedayah yace "What's his name?" Heedayah tace "Ya Junaid" Ta kalli Junaid da har ya wuce sama ta wara ido tace "Kasan fa kuna min kama da shi, just that you are a bit dark in complexion, and ur dimple... Not as deep as his" Khaleel yyi murmushi yace "He is nice, I like him" Heedayah tace "Sure, amma fa da yana neman tsokanata yanxu dai ya daina" Khaleel ya langwabar da kai yace "Ko dai son ki yake?" Ta turo baki tace "Aa, kawai dai ni kanwarsa ce" Yace "Toh shkkn, xan koma yanxu.... Kije kice ma Ummi na wuce" Heedayah tayi shiru tana kallonsa, a hankali tace "So early?" Yace "Ai na dade" Tace "Toh yaushe xaka dawo" yace "Duk sanda kika ce" ta mike tace "Bari in kira Mami" bata jira cewarsa ba ta wuce sama, a stairs ta hadu da Mami tare da Farida, Heedayah ta rungume Farida tace "I missed you sis" Farida tayi murmushi tace "Welcm back" Mami tace "Ya wuce ne?" Heedayah tace "Aa yace xai wuce" Mami na sakkowa kasa tace "Har xa ka wuce Khaleel" yace "Ehh xan wuce" Mami tace "Toh bari ka tafi da abincin tunda baxa ka ci a nan ba" Kitchen ta tafi, Farida na kallonsa tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, How are you" tace "Alhmdllh" A warmer Mami ta xuba masa abincin ta saka a leda ta kawo masa parlon ta ajiye kusa da shi tace "Here, anjima idan ka tafi gida sai ka ci" ya mike yace "Allah ya saka da alkhairi" Iya bakin kofa Heedayah ta rakasa sbda Mami dake parlor snn ta dawo ciki, ganin har Farida ta wuce sama ta bi bayanta da sauri, dakinsu ta sameta xaune gefen gado tana danna wayarta, Farida na kallonta tace "Me ya kawo sa?" Heedayah ta bude hannu alamar bata sani ba tace "Nima a nan na samesa" Farida dai ta tabe baki bata ce komai ba, Heedayah ta xauna gefen gadon tana kallonta a hankali tace "You know what Farida?" Farida na kallonta tace "Aa me ya faru" hawaye ya kawo idonta, Farida ta kamo hannunta da sauri tace "What happened Heedayah talk to me plss" Ta fashe mata da kuka, Farida ta rude tace "Ki gaya min menene mana Didi" Heedayah ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "Ko ba ya Shureen bane" da mamaki Farida tace "What about him?" Heedayah na goge hawayen idonta murya can kasa tace "He kissed me..." Shiru Farida tayi tana kallonta ko kiftawa bbu, jin shirun yyi yawa Heedayah tace "Why don't you want to say anything?" Farida ta ta6e baki ta mike ta bar wajen tace "What did you want me to say" bin ta da kallo Heedayah tayi tace "Ohh haka ma xaki ce min" Farida ta juyo tace "Of course me xan ce maki, an ta6a kissing mutum baya so? Ai ke kika tsaya yayi maki, so why are you complaining?" Heedayah bata kuma cewa komai ba, Farida ta fice daga dakin. Mumy ce xaune ita da Hajiya Sadiya da Salima a dakinta, Hajiya Sadiya tace "Wllh damuwa ya isa ya maki illa Maryam, kina da saka ma ranki damuwa ba kadan ba, wnn abun fa duk mafita ake nema amma dubi ynda kika koma daga jiya xuwa yau...." Mumy ta matse hawayen idonta cikin rawar murya tace "Shkkn ni na tashi a tutar bbu kenan Sadiya, ashe da gasken dai ubanta ne ke neman takarar gwamna, ni yanxu meye ribata ga kishiya da a ko da yaushe xata iya dawo min tunda ba sakinta Barrister yyi ba" Sadiya tace "Toh dai uban yarinyar nan nema mukamin yake ba wai samu yyi ba, sai ki ga ma baxai samun ba in sha Allah" Salima dake taunar cingam tace "Tabb, da kyar kuwa wnn mutumi ace baxai samu gwamna ba, ku kun ga jama'arsa kuwa, mu dai shkkn kin mana bakin ciki, da kin rike yarinyar nan da yanxu government house sai dai mu shiga duk lkcn da muke so mu fito lkcn da muke so, amma yanxu ai sai dai kishiyarki ta shiga ta fito duk sanda ta ga dama, ni dama uban Heedayan xai ganni yace yana so duk da ba wai na hakura da Junaid bane amma wllh yarda xanyi ya aureni, kuma kar kiyi tunanin sbda ya aureni xa ki dinga xuwa government house, nima ba nuna xanyi na san ki ba gaskiya" Banda hararta bbu abinda Mumy ke yi da idanuwanta da suka yi jajir, Salima ta tabe baki tace "Duk da haka bai baci ba, da yanxu xa ki amince Shuraim ya aureta ai rass kema sai yanda kika yi da gidan gwamnati wllh" wani kallo Mumy ta dinga yi ma Salima tana huci, kafin tace komai Sadiya tace "To ai gaskiya ta fada wllh Maryam, kyansa kawai Shuraim ya aureta mu ga ta tsiya, kinga kuwa ikon Rahina daga ranan ya kare, Heedayah ta xama surkarki sai yanda kika yi da ita, idan ma rabata xa ki yi da Rahinar duk sai kiyi amma gaskiya wnn garabasar idan ta wuce mu kuma mun shiga uku, wllh shawara me kyau Salima ta kawo, d'an ki fa ke aurenta, waye kuma Rahinah ai sai yanda kika ce xa ayi" *Thanks so much for ur prayers fans, Allah ya saka da alkhairi... Everything went smoothly, update din dai ba yawa coz Ina hanya yau* Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you. Have u ever wondered how desserts are made? Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from? Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught: *Profit analysis *Ways to handle desserts *Dessert marketing. This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos. Registration is on and the fee is just N3000 Naira. Class starts on 27th august,2021. And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕 WhatsApp 08135358038 Call 📞 08135358038 IG: najaatu Yakudima Mumy ta ja wani tsaki tace "Ni an gaya maku ta mukamin ubanta nake, Ina ruwana da wani government house yarinya ta bi ta cuceni ta tarwatsa min rayuwa shekaru biyar kenan" Salima tace "Ke dai wllh Yaya kina da matsala, ga hanya dai mafi sauki da xaki musguna mata bbu me ce maki don me, wllh Aliyu na auren yarinyar nan shkkn sai yanda kika juyata kika takata, beside xa ma ki iya shiga ki fita idan ma yana da niyyar sonta watarana ki cire masa son nata a ransa gaba daya yaji ya tsaneta, you won't even give any space for him to begin having feelings for her, axabtar da ita kawai xai dinga yi wllh, Kai ko shimfida idan baki son su hada baxa su hada ba, dama fa sbda yanda kike tsangwamata ne ya sa ban kai ki gun wnn mutumi me min aiki ba, wllh yanxu haka d'an minister of finance nake hari, gashi har ya fara kulani a Instagram muna chatting yanxu har ya bukaci yaushe xa mu hadu, dubu 80 na kai ma mutumin yyi min wnn aikin duk da dai har yanxu ina son Junaid kuma shi nake burin aure, yanxu idan kin amince da shawarar nan da na baki kawai sai in kai ki gun Mutumin, kiyi ma Barrister karya kice xaki gidan Gwaggwo Rumaisa, wllh Yaya sai yanda kika yi da Heedayah da shi kansa Shuraim din, kuma sai dai ya ajiyeta a matsayin hoto bbu abinda xai faru tsakaninsu, snn ayi maki aikin da xata dinga tsoron ki tana maki biyayya kiyi ta juyata kamar masa, daga karshe ma idan kika so ki saka Aliyun ya saketa shkkn kinga ta xama bazawara, idan kuma aure kike son ya kara sai ya kara, daga gefe ke kuma kin samu connection da masu kudi, tunda duk da matan gwamnoni da manyan mutane iyayenta suke hulda" Mumy dai tayi shiru abun duniya ya dagule mata, Sadiya tace "Atoh dai, dadina da ke Salima akwai kwakwalwa" Mumy ta sauke ajiyar xuciya tace "Ku kuna ganin hakan da xa ayi shine mafita?" Sadiya tace "Mafitan gaske kuwa, ke kina da wata mafitar ne banda wnn din" Mumy tayi tagumi tace "Toh ai tsoro nake kada wnn karan abun ya sake juye min, nifa wllh wllh ko mutuwata bana jin sa kamar yanda nake jin wnn yarinya, a dalilinta fa na shiga gararin rayuwa mijina ya juya min baya duk da biyayya da yake min" Salima tace "Bbu abinda xai juye kanki, wnn mutumi da nake gaya maki Gwaska ne wllh, gashi nan ya min na fara ganin aiki da cikawa kawai ke dai nemi karyar da xa ki gilla ma lauyan mijinki ki shirya mu je mu san tudun dafawa" a hankali Mumy tace "Toh bari ya dawo, amma fa...." Salima ta ja tsaki tace "Amma me, ke dai kin cika fitina wllh yaya, ga rashin bin shawara" Mumy tace "Toh goben sai mu je kawai" Sadiya tace "Ni connection din da xamu samu ma shi ya fi min dadi wllh, ko ba komai ai a fara damawa da mu a kasar" Da daddare Abba na parlonsa yana operating system Mumy ta shigo, xaunawa tayi gefensa tace "Sannu da aiki my Barrister" ba tare da ya kalleta ba yace "Sannu" tayi kasa da murya tace "Baka sha Watermelon din ba My Barrister" yace "When I am done..." shiru ne ya biyo baya, bayan wani lkci tace "Barrister dama akwai wata magana da nake son mu yi da kai" Abba yace "Ohk ina ji" tace "Ko in bari ka gama abinda kake" yace "No fire on, ina jin ki" Tana murmushi cikin tattausan murya tace "Barrister naga yanda kake ji da Heedayar nan, ga kuma yanxu Allah ya bayyana iyayenta cikin sauki bbu tashin hankali, nasan kuma shkkn yanxu idan ba wani ikon Allah ba tafiya xa su yi da ita idan xa su koma Abuja, toh sai nake ga don xumunci yyi karfi da iyayen nata me xai hana ka nema ma Shuraim aurenta gun Mahaifanta, nasan baxa su ce a'a ba, and I must confess my barrister duk da naki rike Heedayah, ita din yarinya ce me hankali nutsuwa da ladabi nagani, bata da hayaniya snn she will make a perfect daughter in law, ni gaskiya tsoron yan matan yanxu nake barin ma na nan kaduna, kada yaje ya kawo mana warce xata fi karfinsa ya fi karfinmu, kasan yanxu abinda ke faruwa kenan a duniya, shine tun da rana nayi wnn naxarin naga bashi da wani aibu, kuma xai kara karfafa xumuncinmu da iyayen Heedayah, hakan kadai xa suyi maka su kwatanta abinda ka masu na rike masu 'ya bisa amana, duk da matsalolin da ka fuskanta daga gareni wanda hakan ba komai bane facce sharrin shaidan, kuma wllh wllh nayi nadama, don d'a na kowa ne bawa sai mai shi" Abba dai sai danne dannensa yake yana murmushi bai ce mata komai ba, A sanyaye tace "Kayi shiru My Barrister" yace "Ehh ina jin ki" tace "Toh ai na gama" ya kalleta yace "Good, a xamaninmu an mana auren dole?" Tayi shiru tana kallonsa yace "Answer me" tace "Aa" yace "Toh baxa muyi ma yaranmu ba, Shuraim bai ce yana sonta ba, ita ma bata ce tana son Shuraim ba don haka ki ajiye wnn shawaran naki a gefe, it's shaky, with or without aure xa ayi xumunci da su sosai, don iyayenta yan Babban gida ne... Ba kananun mutane bane" Mumy ta bata rai amma ta rasa abun cewa, Barrister yace "That's just it" Mumy ta marairaice tace "Barrister auren kadai ne xai sa ayi xumunci wllh" Da mamaki Abba yace "Why are you bothered sai anyi xumunci da su? Saboda Mahaifinta na neman wani mukami a gwamnati and you have ur selfish interest da kike son achieving??" Ta mike tana masa wani kallo tace "Alhmdllh kasan dai ni ba kwadayayyiya bace, Ina ruwana da mukamin ubanta, su suna kano ni ina nan Kaduna, me ya kawo wnn magana, an basa mukamin ne ma balle kace min haka, shkkn daga kawo shawara sai a fassara ni, mummunan fassara kuma, daga nayi ma d'a na sha'awar aurenta sbda hankali da nutsuwarta sai ace ina kwadayi, me garesu da xa su bani wanda Allah bai bani ba" Abba dai bai ce mata komai ba yana ci gaba da abinda yake, ta juya a fusace ta fice daga parlon. Washegari Shuraim na dawowa gidan daga wajen aiki ya tafi parlon Abbansa da ya kirasa tun safe, gaida Abbansa da ya fito bedroom ya xauna saman kujera Shuraim yyi bayan ya xauna kasa kusa da shi, Abba yace "Ya aikin?" Ya shafa kansa yace "Alhmdllh..." Abba yace "Ya issue din Transfer da kace xa ayi maka" Shuraim yace "Still working on it, may be next year...." Abba yace "Good" shiru ne ya biyo baya, Abba yace "Are you listening?" Shuraim ya kallesa yace "Ina ji" Abba yace "What are ur plans on settling down with a wife" Shuraim yyi shiru yana kallonsa, can ya sauke kansa kasa, Abba yace "Xan fita office don haka you need to talk fast" Shuraim yyi kasa da murya yace "In sha Allah soon" Abba yace "Kana da warce kake so ne" nan ma yyi shiru kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Mun yi magana da Baffa, yace xa ku yi magana" Abba yace "Toh shkkn, you can go" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo har ya fita, Da sauri Mumy ta bar bakin kofar ta koma bangarenta, Shuraim dai ya bi ta da ido bai ce komai ba ya wuce dakinsa, yana shiga ya cire shirt din jikinsa sai ga kiranta, ya daga tace "Ka sameni parlona yanxu" Ya fita dakin nasa ya koma bangarenta, Tsaye ya ganta parlonta, tana ganinsa tace "Wanka xaka yi ne" yace "Nayi wanka, kwanciya xan yi" tayi kasa da murya tace "Me Abbanka yace maka?" Yace "Aa kawai yace xan ajiye sa anjima kadan" Mumy ta daure fuska tace "Karya kake wllh, ni xaka munafurta??" Ya buda manyan idanuwansa yace "That's it mum, abinda yace min kenan, nace masa Allah ya kai mu" Mumy tayi shiru tana kallonsa, can tace "Baxa dai ka gaya min ba" yace "I am serious mum" ta nuna masa kofa tace "Toh fita" ba musu ya juya ya fita ya kullo mata kofarta, ta cije yatsa, murya can kasa tace "Dole ma kawai abun nan ya tabbata, in sha Allahu sae auren nan ya tabbata kwanan nan ba da dadewa ba" tana fadin haka ta shige dakinta xata kira Salima. Kaka nata goge gogen windown dakinta sae da taga yyi fess ta juyo tana kallon Baffa dake xaune parlon tare da Abba tace "Idan na barsa ban karasa ba sae shaidan ya mantar da ni, kunga haka kuma bbu kyau, tunda bbu me taimakona sae Allah, 'ya yanku dama sae dai su shigo su xagi iyayena su fita" tana kai wa nan ta xauna tace "Wata kullalliyar kuma ku ka kulla xa a sanar min yanxu?" Baffa yyi dariya yace "Aa bbu, shawara muka xo nema..." Tace "To ina jin ku" Baffa yace "Ya kika ga idan aka ce xa a nema ma Shuraim auren Heedayah gun iyayenta?" Kaka tayi shiru tana kallonsu kamar ranan ta fara ganinsu, can tayi mitsi mitsi da ido tana kallon Ac dake dakin kamar me naxari tace "Waye kuma Shureen?" Duk suka yi shiru suna kallonta, tace "Aa ba batun wasa ba, don Allah ku sanar min waye Shureen din?" Nan ma bbu wanda yace komai, a fusace tace "To ni nasan wani Shureen ne? ba sai ayi min bayani ba duk kun wani min shiru, idan baxa a sanar min waye shi ba ku fita ku bani waje in ci gaba da tsaftace dakina ni dai" Baffa yace "Aliyu" kaka ta hade rai tace "Ban gane Shureen ba sai wani Aliyu, ko dai wiwi ku ka sha kafin ku shigo min, nifa kar a dinga damuna, ku min bayani filla filla yanda xan fahimta, idan kuwa kunbiya kunbiya za ku min ku fita" Baffa ya nuna Abba yace "Shuraim din Ahmad...." Kaka ta bude baki a hankali tace "Shureen din Ahmad kuma??? Ashe da gaske shi din ne ku ke nufi xuciyata taki amincewa..... To wiwi ku ka dirka halan ku ka ga hada Deedayah da Shureen ya dace" Abba dai TV kawai yake kallo, kaka ta mike tsam tace "Toh wllh bbu ruwana da wnn konanniyar shawarar taku duk kauri, a rasa wanda xa a ace xa a ba Deedayah sae Shureen, yaron da har yau uban da ya haifesa bai san xuciyarsa ba balle mu karere, to wai ma ina Deedayah xata kai gantsamemen Mutumin nan, anya kuna tsoron Allah kuwa Amadu, snn ko kakanninku ba a masu auren dole ba balle Deedayah.... To ba ruwana, Shureen kuma da tuntuni nayi masa mata yar gidan Rakiya ai maganar na nan bata mutu ba lkci kawai ake jira, ashe kuma dai kwadayayyu ne ban sani ba, daga ganin ubanta gwamna ne sai ku fara kokarin makala mata d'an ku da bashi da tarbiya bashi da kirki" A tare Abba da Baffa suka kalleta, Baffa yace "Subhanallah" Kaka ta zare masa ido tace "Ehh din, ba kwadayin bane ke dawainiya da ku xaka ce min Subhanallahi.... Mutumin da ko xo bai ta6a hadasa da Deedayah ba balle tafi xaku wani ce a aura masa ita, duk fa ina lura da komai ni ba Mahaukaciya bace, takama da ya dinga nuna mata cewar gidan ubansa take duk ina lura, to meye kuma daga ganin uban yarinya babban mutum ne sai a nemi makala mata sangamemen mutum, to ya xata yi da shi fisabilillahi jama'ah??" Mikewa Abba yyi yace "Sae da safe" tace "Allah ya tashe mu lfya" daga haka yyi ficewarsa daga parlon, Baffa yace "Haba kaka...." Kaka ta tsuke fuska tace "Kai... Kai ma sae da safe na sallame ka" mikewa yyi ya nufi kofa tace "Ko kun mance ni yar gaskiya ce, Kai ni ko da ma suna son junansu baxan yarda wnn katon ya aureta ba, ya xata yi da shi mutum gantsameme haka gashi soja yaje ya hallaka yar mutane mu shiga uku, balle ma bashi da hali kwata kwata wllh, yaushe rabon ya xo yyi min gaisuwar mutunci har na manta, to ni nasan inda Amadu yaje ya samo sa ya xama d'an sa duk da shi ma Amadun haka yake ai" Ranan Monday Ammin Heedayah da Abbanta suka koma Abuja leaving Heedayah with Mami don Mami tace masu sun yi resuming boko, Ammi felt as if kara rabata xa ayi da Heedayah but ko kadan bata nuna haka ba ta danne xuciyarta sosai, amma har ranta ta so su tafi da Heedayah a sata a wani makarantar a can Abuja, she had no other alternative then to leave her behind suka wuce da Abbanta. Heedayah na hada abubuwan da xata koma makaranta da shi don gobe xa su koma da yamma, Farida ma na dakin amma tana kwance tana danna wayarta, Heedayah ta karasa kulle jakarta tana kallon Farida tace "In dafa Indomie din da ke?" Farida dake kallon screen din wayarta tace "Noo" Heedayah bata ce komai ba ta juya ta fita dakin, karfe sha daya saura ne na safe, su biyu kawai ne gidan don Mami ta fita office amma tace ba dadewa xata yi ba daga can ma xata yi masu shopping, Heedayah ta gama dafa Indomien tana xuba masu a different plate ita da Farida duk da tace baxata ci ba amma har ita ta dafa, taji kamshin turare ya cika hancinta, juyowa tayi da sauri suka yi ido hudu bata san lkcn da ta saki tukunyar hannunta ba a rikice, sauran Indomien ciki ya xube kan gas, ya karasa cikin kitchen din da sauri ya janyeta daga wajen yace "Are you okay" Jikinta ya dau rawa tace "Noo" gaba daya ta rude, kallonta kawai yake, can ya daure fuska yace "Dodon ki ne ni?" Da sauri ta girgixa masa kai, yace "Toh meye kika xubar da Indomie daga ganina" kamar xata yi kuka tace "Tsorata nayi" ya dau plate din Indomie da ta fara xubawa ya mika mata, amsa tayi bata yrda ta kallesa ba, yace "Ina farida?" Tace "Tana sama" Farida ce ta shigo kitchen din waya kare kunnenta a dai dai lkcn, dakatawa tayi da farko bayan sun hada ido da Shuraim, Can ta mika ma Heedayah wayar tace "Mami wants to talk to you" Karba Heedayah tayi ta kai kunne a hankali tace "Ina ji Mami" Mami tace "Ku shirya yanxu, Shuraim is on his way, xai ajiye ku gidan Baffa ku yi ma kaka sallama sai ya maido ku gida" Heedayah tace "Toh" Mami ta katse wayar, Heedayah ta mika ma Farida ta amsa ta fice daga kitchen din, Heedayah bata yrda ta hada ido da Shuraim ba ta ajiye Indomien xata fita yace "Dauka ki wuce ki ci" dauka tayi ta nufi kofa ta fita ya bi bayanta, daki ta kai ta ajiye don taji ya ma fita ranta gaba daya, Ganin Farida a kwance tace "Ke baxa ki ba" Farida tace "Ehh" Shiru tayi tana kallonta, can tace "Toh ai Mami cewa tayi ni da ke" Farida tace "Na kirata yanxu nace baxan iya xuwa ba so kiyi tafiyar ki, I am having cramps" Heedayah ta bata fuska tace "Toh ni kadai xan je?" Farida tace "Ga dai wanda ya xo tafiya da ke kice ke kadai, I tot u will like following him ai" Heedayah bata tanka ta ba ta sa Hijab dinta ta fita, Ganin Shuraim baya parlor ta karasa waje, cikin mota ta samesa xaune waya kare kunnensa, ganinta ya katse wayar yana kallonta yace "Ina faridan?" Heedayah bata kallesa ba tace "She said she is not going" yace "Har kin ci abincin?" Tace "Uhm" bude front seat tayi ta shiga ta kulle, tada motar yyi suka bar layin sai da suka dau hanya yace "Let me ask you" Heedayah ta d'an yi shiru sai taji kamar ba da ita yake ba, can ta juya suka hada ido ta dauke idonta da sauri, yace "Tsoron me kike min?" Ta ki cewa komai, yace "What if kika ganmu gida daya, daki daya, ya xa ki yi ranan?" Lkci daya ta d'an xaro ido, sai kuma tace "Ae hakan ma baxai ta6a faruwa ba" Wani murmushi yyi bai ce komai ba, ta kallesa tana imagining dama ashe ya iya murmushi, can yace "Haka kike gani?" 6ata fuska tayi tace "Eh mana ta ya xamu ganmu daki daya?" Yace "Xan nuna maki ta taya ranan" Sosai taji gabanta ya fadi, hakan yasa bata kuma ce masa komai ba, shi ma bai ce komai ba har suka isa gidan Baffa, ta bude motar ta sauka ta wuce ciki ya jinginar da kansa da kujeran motar ya bi ta da kallo. kaka tace "Ya naga ranki a bace kamar wani ya cuce ki, sannan waye ya kawo ki?" Kin cewa komai Heedayah tayi tana xaune kan kujera aka bude kofar dakin Shuraim ya shigo, kaka tace "Waye wnn kuma, me ya hada tafiyarki da shi ni Patuu" Heedayah taki cewa komai, Kaka tace "Aniyar Amadu da Umaru dai ya bi su, meye kuma na hadaki da Shureen ya kawo ki wajena, akwai wani abinda ya hadaku da shine ban sani ba" Shuraim yace "Xa ki sani kwanan nan" Kaka tace "Ni dai ba ruwana, ni ban ma ta6a ganin inda aka bar Soja cikin gari yyi ta gantali ba a aikasa daji yaje yayi yaki da 'yan ta'adda ba" Shuraim yyi murmushi ya shafa kansa yace "Ke ma ai 'yar ta'adda ce dole in tsaya kusa don in dinga maganin ki" Shiru kaka tayi tana kallonsa, can ta xauna saman kujera tana matsar kwalla, yana kallon Heedayah yace "Meet me at the car" daga haka ya juya yyi ficewarsa ta bi sa da harara da murguda baki, kaka dai na xaune tana ta matsar kwalla ance mata yar ta'adda, Cikin dubara Heedayah ta dau wayarta ta fice daga dakin, duk ranan basu yi magana da Khaleel ba, da yake da wayar Farida take kiransa kuma ganin duk yau Farida bata sake mata ba yasa bata ma tambayeta wayar nata ba.... Can dakinsu Zainab ta shiga ta rufe snn tayi dialing number sa, sai da ya kusa katsewa ya daga, murya can kasa tace "Ya Khaleel" Jin muryarta yace "Yau kin mance ni, ina ta tunanin ki.... let me call you back" daga haka ya katse wayar ya sake kiranta, tana dagawa yace "Tell me first, me Ummi ta fi so?" Heedayah ta wara ido tace "Wai Mamin mu?" Yyi kasa da murya yace "Nima Mamina ce ai ko?" Dariya Heedayah tayi tace "Sure, Mami tana son Apples sosai, with grapes, and tana son hanta gasasshe...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you. Have u ever wondered how desserts are made? Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from? Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught: *Profit analysis *Ways to handle desserts *Dessert marketing. This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos. Registration is on and the fee is just N3000 Naira. Class starts on 27th august,2021. And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕 WhatsApp 08135358038 Call 📞 08135358038 IG: najaatu Yakudima Khaleel yace "Ohk..." Tace "Why do u ask" ya buda ido sosai yace "Nothing, I only want to know.... yau din xa ki wuce schl?" Tace "Aa sai gobe, na xo yi ma Kaka sallama" yace "Ke da wa?" Tace "Ni da ya Shureen" yyi shiru, sai kuma a hankali yace "Me yasa kike son bin sa, why not Junaid?" Tace "Ya Junaid ya tafi aiki ai shi" Yace "Shi Shuraim din baya aiki?" Tace "Da safe yake dawowa, he is a military Dr" Khaleel yace "Uhn I see...." Tace "Xaka xo ne anjima?" Yace "Probably" tace "Probably? Baxa ka xo ba bayan gobe xan wuce schl" kamar xata yi kuka ta kare maganar, yace "Xan xo" a hankali tace "Toh sai ka xo" yace "In sha Allah" yyi kasa da murya yace "Tell me Heedayah, who is ur first love?" Dariya tayi tace "Yar yarinya da ni? I don't love" Yace "Uhm ko?" Tace "Ehh mana, baka gan ni yar karama ba" yace "How old are you?" Tace "Soon xan yi clocking 17..." Shiru yyi, can yace "Can u marry someone 2 times ur age?" Dariya tayi tace "Aa nima ban sani ba" Yace "Uhm to shkkn, sai na xo anjima, ana kirana yanxu a waya" duk sai bata ji dadi xai katse wayar ba, a hankali tace "Ohk bye" yace "Take care of ur self pls" tace "And you too" ya gyada mata kai kamar tana ganinsa yana murmushi, daga haka ya katse wayar. K'in fita Heedayah tayi daga dakin su Zainab don ta sa a ranta baxata bi Shuraim ba, she is finding it hard to withstand the sight of him, daga karshe kawai ta tafi dakin mum din Zainab ta gaisheta ta koma dakinsu Zainab ta sa makulli tayi Kwanciyarta hankali kwance. Da yamma tana dakin Hajiya Hauwa tare da Zainab da dawowarta makaranta kenan kaka ta leko dakin tana kallon Heedayah, tayi kasa da murya tace "Wllh naji dadin yanda kika tafi kika boye abinki ya gama jiransa kamar debabbe ya wuce, kawai mutum ba tsoron Allah naga kamar sai wani makale maki yake, ni dai ba ruwana, ga abinci can na ajiye maki a daki" Hajiya Hauwa tayi dariya tace "Ta ma ci abinci a nan" Kaka tace "Atoh, idan ya kama anjima ni da kaina sai in mayar da ita gida, waye kuma Shureen Allah na tuba, d'an banxan yaro me mugun hali" daga haka tayi ficewarta, sai kusan Magrib Heedayah ta shigo dakin kaka, Xaune ta tadda kaka da junaid kaka na masa hira, Ta wara ido ganinsa ta tafi ta xauna kasa tana kallonsa tace "Yaya... " Kaka tace "Ai yanxu xan tafi in kira ki dama, wai Rakiya tace ya xo ya tafi da ke gida, kinsan shima ya lalace yanxu baya gaida mutane" Junaid dai murmushi kawai yyi yana shafa kansa, kaka tace "Kuma naga duk ya rame kamar yana tare da damuwa na tambayesa meye ya ki gaya min, to ya sani ko ina da abinda xan masa in taimaka masa??" Junaid dai bai ce komai ba, Heedayah ta mike ta dau jakarta, Junaid ya mike shi ma yace "Toh sae da safe kaka" sabulu kwara uku da soyayyen nama a leda daban ta ba Heedayah tace "Babu komai a dakin, duk an bar ni a gantale nace su bar ni in fara sana'a ko ta Maggi ce da manja sun ki gashi ni basu dauke min lalurorina ba" Dariya Heedayah tayi, Junaid ya fiddo dubu ukun aljihunsa ya mika ma kaka yace "Ba kudi wajena kaka, gobe xan shigo in sha Allah" Kaka ta amsa tana wani murmushi tace "Allah yyi maka albarka, gobe ka dawo mu yi magana da kai, tunda ita Rakiya bata gane kana da damuwa ba ni na gane, idan ma baka xo goben ba sai in iya biyo ka har gida" da sauri yace "Aa xan xo kaka" tace "Toh ina saurarenka, bari in je Hauwa ta sama mana canji in ba Deedayah ko dari biyu ne ta siyi abu a hanya" Junaid yace "Aa xan bata a madadin ki" Kaka tace "Toh Allah yyi maka albarka" daga haka suka fita dakin tare da Heedayah da tayi mata sai da safe ta bi bayansa, a hankali Junaid ke driving, can yayi kasa da murya without looking at Heedayah yace "Tell me.... a ina kika san Khaleel din nan Heedayah?" Heedayah ta d'an yi shiru, sae kuma tace "Ban san sa ba, shine dai kawai yace min ya san ni, but his voice sounds familiar, na ta6a jin muryarsa" Junaid yace "A ina kika ta6a jin muryar tasa?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "When I was unsighted" Junaid ya kalleta da mamaki yace "Where precisely?" Ta buda masa hannu alamar bata sani ba, yace "No, ki tuna inda kika ta6a jin muryar tasa now" Heedayah tayi shiru, sai kuma tace "But I seriously can't remember, I have tried hard" Yace "You just have to, when u where unsighted ai ba fita kike ba, you are home always to a ina kika san muryar tasa" Bayan wani lkci ta girgixa kai tace "I can't remember" Bai kuma ce mata komai ba har suka isa gida, ta ga motar Khaleel a waje, a tare suka shiga parlon da Junaid, Junaid ya ba Khaleel hannu suka gaisa ya gaida Mami dake parlon ita ma snn ya wuce sama, Heedayah ta gaida Mami ta gaishesa ita ma ta wuce sama. Mikewa Khaleel yyi sbda kiran wayarsa da Zayyad ke ta yi tun shigowarsa parlorn not less then 15mins ago yana kallon Mami yace "Let me answer a phone call" Mami tace "Alright dear" kofa ya nufa ya fita ya tafi can kan daya daga kujerun dake ajiye a compound din with round table ya xauna, snn ya daga kiran yyi shiru, Zayyad yace "Khaleel why are u behaving anyhow this days, I really don't want u to get into problem, I get u are newly in love now, but ka dinga controlling kanka pls, Nobody is stopping you from loving" Khaleel dake ta sauraronsa yace "Wnn shine dalilin kiran da kake ta yi min haka Zayyad?" Zayyad yace "No!! me yasa Oga Arne ke kiranka baka daga kiransa? First u spoilt the show of kidnapping Alhaji Ahmad, secondly...." Khaleel ya dakatar da shi calmly yace "Wnn ya fi karfin ku yi kidnapping dinsa when I am alive and breathing" Zayyad yace "See you, ka dai san some big leaders gat our back Khaleel, you like it or not dole ne sai an yi kidnapping wnn mutumin kafin xabe ya gabato" Khaleel yace "Then we shall see" Zayyad yace "Duk wnn ma ba shi ne ba, coz they are still planning on it, the main issue in here is that why... ka ki fitowa operation shekaranjiya bayan san sanar da kai, meeting din ma kuma da aka kira baka xo ba" Khaleel yace "Na ce masu I need rest, and seriously I need that rest, ko basu yadda da abinda nace masu bane...." Zayyad yace "What nonsense, rest din sati nawa, wllh Brainiac ka bi a hankali suna watching every movement dinka without you knowing, ni kaina I just noticed ba wai gaya min aka yi ba, ka ma san bbu wanda xai gaya min, and you know what... da matsalar iya kai xai tsaya ma da sauki, they are seeing it as bakinmu daya da kai, to ni yaushe rabon mu hadu yanxu, 24/7 kana kwance gida daga waya da yarinya sai xuwa wajen yarinya, ni damuwata a nan wani riba kake ga xaka ci dating that teenager da ko hannunta naga baka rikewa, meye mamorarta? ka xo ga manyan babes a gari in jonaku amma ka ki ka makale ma yarinyar da there is nothing to write home about, sannan mind you, wllh gidan wnn innocent barristern da kake xuwa xa su iya tracing su je can kuma kasan abinda xai iya faruwa" lkci daya jikin Khaleel da yyi shiru yana sauraron Zayyad yyi sanyi, Zayyad yace "And nima kana ja min matsala ne da damuwa gunsu, suna ganin komai da kake yi har da hadin bakina nasan komai, Oga Manga Vow to have ur legs shoot yanda xaka xauna waje daya tare da su" Khaleel dai bai ce masa komai ba, Zayyad yyi kasa da murya yace "Wllh Khaleel tun da ka koma gefe ka wani yi isolating kanka abubuwa suka daina tafiya smoothly, operations are always not successful this days, sae ynxu su kansu suke sanin you mean a lot, don Allah ka tsayar da hankalin ka gu daya, no one is stopping you from dating that little girl da ka haifa a haihuwar kaji amma ka daina wasa da sana'arka, snn kar ka xama butulu Oga Arne bai yi deserving haka daga gare ka ba, Kuma ka fa san irin yanda yake sonka yake ji da kai" Ganin Heedayah na tahowa da tray me dauke da drink da ruwa Khaleel ya katse wayar ya sa a flight mode cikin few seconds, ta karaso ta ajiye tray din a table tana kallonsa a hankali tace "Are you okay?" Ya kirkiri murmushi ya shafa beard dinsa yace "Sure" Xaunawa tayi tace "Mami tace in kawo maka ruwa" yyi kasa da murya yace "Thank you" shiru ne ya biyo baya, ta bude drink din ta debar masa a glass cup, a hankali ta ji yace "Wani class kike yanxu Heedayah?" Tace "Ss1 3rd term xamu fara yanxu, sai in shiga ss2 a nan xan rubuta waec" Shiru yyi yana kallonta, can yace "You know what Heedayah?" Ta girgixa masa kai, a hankali yace "I have left a lot of me because of you.... Saboda ke naji I might just have to give up on many things...." Ta katse sa tace "Like?" Yyi shiru, can yace "My personality, who I am.. and so on, I don't know how that is going to be.... But promise me Heedayah, no matter any circumstance, no matter the up and downs, no matter the situation kar ki guje ni don Allah" Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa bbu, ya ci gaba cikin sanyin murya yace "I don't know why I am having this feeling kamar xaki gujeni soon, very soon xa ki gujeni Heedayah" Lkci daya jikin Heedayah yyi sanyi tace "Me yasa kake tunanin haka, me ka min da xan guje ka? Meyasa kake ga xan guje ka?" Ya lumshe ido ya bude a sanyaye yace "sbda wani dalili da ya kamata ki gujeni din, you just have to leave me for that reason, but plss don't Heedayah, idan kika gujeni I don't know what will become of me, don't forget I have nobody, I know nobody, and I don't know the love of family" ta girgixa masa kai in an assuring state tace "Ni baxan guje ka ba sai dai in kai xaka gujeni" yace "Make me that promise Heedayah" shiru tayi tana kallonsa gaba daya jikinta yyi sanyi ne, ta sauke idonta kasa, bayan few seconds tace "I promise" Murya can kasa yace "Nagode Heedayah" ta sakar masa murmushi bata ce komai ba, yace "Yaushe ake xuwa maku visiting a schl?" Tace "Anytime if we are free ana barin mu" yace "Alright, may be next week xan wuce Holland, I need rest, much rest" tayi shiru sai kuma tace "Yaushe xaka dawo?" Yace "Tunda kina makaranta sai idan kun yi hutu, that is after ur waec" a sanyaye tace "You will be away for almost a year?" Ya gyada mata kai, ta sauke idonta kasa tace "But I am going to miss you" yace "I will too, but I have to go so you will concentrate on ur studies, ranan da aka gama waec xa ki gan ni idan Allah ya yrda" Bata iya ta ce masa komai ba, kamar yanda yyi shiru shi ma a ransa kuwa yana tunanin idan yyi nisa da Nigeria for that period of time oganninsa xa su basa breathing space, he will have rest of mind, yasan ko da Heedayah na makaranta xai ce sai ya xo ya gaida Mami don har ransa yake jin matar, he can't resist coming to her, kuma kamar yanda Zayyad yace yasan ba wani abu me wahala bane gun su Manga suyi tracing dinsa din su gano gidan, kiran da Zayyad ke tayi masa duk da wayar a total silent yake ya sa yyi ma Heedayah sallama, ita dai bata iya tace masa komai ba, ya sa hannu a aljihunsa ya ciro kudi me yawa without thinking twice ya kamo hannunta ya saka kudin, ta wani xaro ido yace "This is my own sweat not Haram Heedayah, it's all I have got (Halal)" gaba daya yyi confusing dinta kafin kuma tace komai yace "Till after a year in sha Allah Heedayah, do not try to forget me even for a second during the year Heedayah, I will think of you till the last day of 365 days to come in sha Allah, kice ma Mami na tafi, I appreciate her love and kindness toward me, kuma ta dinga saka ni a addu'arta don bani da me yi min" Daga haka ya sake hannunta ya nufi gate, ta bi sa da ido ko kiftawa bbu, hawaye ne ya gangaro idonta.... Mumy ce tare da Salima da Sadiya a gun Mutumin da Salima tace xata kai su, a wani d'an karamin kauye a garin Kaduna Mutumin yake, tafiyar kusan awa uku ne kuma ya kai su gun Mutumin, mata biyar suka tarar a gabansu, duk manyan mata, suna xaune suna jiran turn din shigarsu, Mumy tace "Na samu labarin yau Heedayah ta koma makaranta gaba daya, kun ga kuma idan ta tafi nasan sai candy xata dawo gida, yau da safe ina jin Barrister da d'an uwansa suna tattaunawa a waya amma bai san I was eavesdropping ba, wai tunda uwarsu ta nuna bata son auren toh baxa a sake tada maganar ba, ni yanxu duk ba wnn ba, ku fada min ya xa ayi da wnn tsohuwar dake neman kawo mana cikas?" Salima tace "Ita wnn tana da wani alkibla ne dama, tsohuwar da ko dubu biyar kika ajiye gabanta xata canxa xance, duk ba wnn ba matsalar ina ga fa daga Shuraim xai fito, don banga alamar yana son yarinyar nan ba, baya yinta ko kadan, abinda kawai ya kamata ayi shine a daura masa mugun sonta ynda xai birkice ma Ubannin nasa da ita kanta Kakar yace shi dai sai Heedayah, kinsan duk da suna 'yar tsama ta fi sonsa cikin jikokinta idan kuwa taga ya birkice kinsan dole ta amince bbu bata lkci, snn tunda Barrister yace a bar xancen kinsan baya magana biyu, wllh ya bar batun auren kenan har abada, don haka idan Shuraim yaji mahaukacin son yarinyar na neman yi masa illa to wllh lkcn da xai je gun uban yarinyar da kansa a Abuja yace shi ita yake so ma baxai sani ba, kuma uban yarinyar baxai ta6a cewa Aa ba sbda hallacin da Barrister yyi masa, xai kuma so hada wnn auren ko don ya nuna appreciation... Toh daga baya ana auren sai a warware sihirin Shuraim ya dawo dai dai ya fara cin uban yarinyar cikin ruwan sanyi" Mumy ta dinga mata wani shegen kallo tace "Idan kuma bai daina son nata ba fa?" Sadiya tace "Matsalar ki kenan dama, tunda aka iya sa ya so ta don abubuwa su tafi dai dai ai bbu abinda xai sa a kasa warware son, asiri ne fa Maryam..." Salima tace "Rabu da ita mana, ae rashin daukan shawarar ne ke cutarta, ga dai abu cikin sauki ayi a wuce wajen, in dai ba tsinanne ne uban yarinyar ba ai baxai hana Shuraim yar sa ba bayan halaccin da uban Shuraim din yyi masa, ni kinga Yaya duk abinda muka ce maki kawai kice to, don ke baki da wani shawara da tunanin kirki sae rudewa kamar tsohuwa" Mumy dai tayi shiru, can tace "Toh ai fa yanxu yarinyar ta koma makaranta nace maku" Sadiya tace "Baxata gama bane, mu dai ba dai kawai shiri kawai xa mu fara ba, kamar gobe ne xaki ga har ta gama fa" Mumy tace "Balle ma naji Barrister na cewa ta kusa xana waec" Salima tace "Yauwa to kinga" A haka suka yi ta tattaunawa har layi ya xo kansu suka shiga gun Mutumin a 'yar bukkarsa. Kaka ce xaune parlon Baffa dake ta kallonta da mamaki, ta ci gaba da abinda take cewa hankalinta kwance "Shine nace in xo in sanar maku kada ku ce na raina ku" Baffa yace "Haba Kaka yaushe suka koma har xa ki bi su" kaka tace "Toh wai ce maka nayi xuwa xan yi in ja6e masu, magana fa mai muhimmanci ne xai kai ni, karewa ma da wnn yaro Junaid xa mu, shi xai rakani kuma mu dawo tare, a motarsa ma xamu tafi" Baffa dai ya rasa abun cewa, Kaka tace "Ni bance lallai ku bani ko sisi ba junaid xai kai ni ya dawo da ni kuma wllh wllh kwana biyu kacal xan yi" Baffa yace "Toh shkkn, Allah ya kiyaye hanya" ta mike tace "Ameen" daga haka ta nufi kofa yace "Xan tura ma Junaid din kudi da xai baki" Ko tankasa bata yi ba ta kara gaba. Shiru Mami tayi tana kallon Heedayah da take ta kokarin ganin hawayen dake kawowa idonta bai sakko ba, a hankali Mami tace "Ina yace maki xai tafi?" Heedayah tayi kasa da murya tace "Holland" Mami tace "Toh Allah ubangiji ya tsare sa ya basa abinda ya je nema can din, amma da ya tsaya ai mu yi sallama" cikin sanyin murya Heedayah tace "Yace ki dinga yi masa addu'a bashi da me yi masa" Mami bata ce komai ba sai dai gabanta faduwa yake ta rasa dalili, Heedayah ta mika ma Mami kudin da ya bata dake cikin Hijab tace "He gave me this, and I couldn't say no" Mami ta dinga kallon kudin tace "You shouldn't have collect it" tace "Kiyi hakuri Mami, he didn't allow me to say anything" Mami tayi shiru... Dubu talatin ne kudin da Khaleel ya bata sai dai kalmar da ya fada mata a yayin bata kudin ya tsaya mata sosai "It's all the Halal he have got, it's his own sweat not Haram... How is that??" Washegari before leaving for Lagos don a can xai yi boarding flight da xai bar kasar Khaleel ya dauko daya daga many sims dinsa da yake amfani da shi only if the need arises, ya dau number Mahaifin Heedayah da suka yi exchanging daga wayarsa ya shiga rubuta masa text kamar haka..... After sending the text ya kashe wayar ya cire sim card din ya balle ya jefar nan kasan lafiyayyen dakinsa ya dau jakarsa ya fita dakin. 1 year few days later.... *Abu me sauki ne gareni inyi briefing labari in datse in tafi karshe in huta kowa ma ya hutu, imagine Imaan and Capt Ahmad Junaid cikin sauki na datse labarin na tafi end sbda immature comments then, don haka Heedayah ma hakan ba wani wahala xai bani ba, duk da a farko I vow not to make the book short, ba dai wanda xata aura kadae ne Aim din wasu ba, you pple will see soon and that's all* 👍🏻 Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you. Have u ever wondered how desserts are made? Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from? Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught: *Profit analysis *Ways to handle desserts *Dessert marketing. This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos. Registration is on and the fee is just N3000 Naira. Class starts on 27th august,2021. And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕 WhatsApp 08135358038 Call 📞 08135358038 IG: najaatu Yakudima Heedayah tayi kamar bata ji abinda kaka ke ce mata ba xata bi wata kawarta dake jan ta su tafi su yi hoto da family dinta, Ammi dake kallonta da mamaki tace "Are you deaf Heedayah? Ba magana kaka ke maki ba??" Heedayah ta juyo da sauri kamar a lkcn ta ji tace "Ohh ban sani ba..." Sai kuma ta kalli kaka da ta saki baki tana kallonta tace "Na'am kaka...." Ammi na kallon classmate din Heedayah tace "Let her finish snapping here xata je kin ji yan mata, ki jira sai ku tafi" yarinyar na murmushi tace "Ohk Ma" Kaka na kallon Heedayah tace "Idan xaki fita hanyar kawaye ki fita tun wuri bbu ruwanki da su, meye yarinya xata yi ta makale maki tun shigowar mu nan, to cewa nayi shi Shureen baxa kije ku yi hoton tare ba, tunda har Allah ya kawosa shi ma ai sai kiyi hoton da shi ba don halin sa ba, ai ya ma kyauta tunda daga legas ya taho duk da bakin halinsa" Heedayah dai bata ce komai ba ta juya ta d'an kalli direction din da Shuraim ke tsaye sanye da uniform dinsa holding both hands dinsa ta bayansa yana bin kayatattcen makarantar dake dauke da manyan mutane da suka xo murnan Candy din 'ya yansu da idanuwansa, kowa na wajen mai kudin kansa ne, sae dai duk attention ya fi karkata gun Heedayah da Family dinta, Heedayah ta d'an kalli Ammi dake kallonta fuska daure, a hankali ta mika ma Mami dake wajen tare da su Dinar da stepmum dinta jakar hannunta ta nufesa tana tafiya kamar bata son yi tana dage doguwar readymade din rigarta sbda jan kasa da yake, duk wanda ya kalli Heedayah sae ya sake kallonta don koman jikinta is unique, camera man na biye da ita har suka isa gun Shuraim, Farida dake tsaye ta bi ta da ido, ba tare da tace masa komai ba ta tsaya daga side dinsa leaving much distance between them tana gyara graduation cap dinta bbu ko d'an murmushi fuskarta, sai gyara kayanta take kamar munafuka, ya d'an kalleta ya dauke kai, Mumy dake wajen da Sadiya dai sai kallonsu suke, murya can kasa Sadiya tace "Lallai kam yar gwamna, dubi gwalagwalai ni Halimatu" Mumy dai ta kasa cewa komai ta hadiye abu da kyar, a hankali Shuraim ya dawo kusa da Heedayah yana kallon camera man din, kamshin turarensa ya cikata, ita dai bata yarda ta kallesa ba, nan mai hoton ya kashe masu hoto har biyar, ko second daya bata kara a wajen ba ta koma gun su Mami da sauri, gaba daya attention din mutanen wajen na kan su Heedayah sbda presence din Abbanta da ke da mukamin gwamna a yanxu, sojoji ne da police men ta ko ina a wajen sai wajen ya dawo kamar Heedayah kadai ce ke candy, Mumy dai na rakube gefe da kawarta tana tsoron xuwa kusa da su kaka ta sha disgi, kaka kam taje gun Mahaifin Heedayah dake wajen xagaye da sojoji ya fi a kirga sai wani daga kafada take a wajen kamar boss, Kuma bbu me hanata xuwa kusa da shi tun tsige wani soja da tayi farkon shigowarsu wajen, presence din Sudais wajen kadai ya sa Heedayah ta saki ranta don tun fara occasion din bata da walwala gaba daya a sanyaye take, but seeing Sudais after 2 years kawai sai ta d'an sake, Abbanta da su Abba ne suka fara barin wajen ana kan daukan hotuna, Sadiya ta kalli Mumy tace "Haba Maryam kije ku dau hoton ke ma mana, gashi kinga ana to hotuna, kin sa na rakoki kuma kin ki sakin jiki" Mumy tayi kasa da murya tace "Wllh tsoron kar tsohuwar can ta disga ni nake Sadiya" a d'an fusace Sadiya tace "Don Allah ki tafi ni dai, kin sa duk munyi tsamo tsamo a nan kamar wasu marasa gaskiya, dubi Hajiya Amina da ba son Heedayar take ba ita ma can cikinsu ke kuma kin kawo mu gefe don Allah" Mumy tace "Toh bari in je" sosai Mumy tayi gathering courage ta karasa gun da su Heedayah suke tana murmushin karfin hali tace "Ba mu yi hoto ba Heedayah...." da sauri kaka ta juya ta kalleta tace "Meye kuma hoto? Kawarta ta riga ki ma ai, ke Heedayah ki tafi can kawarki na jiran ki kuyi hoto, 'yar wajen Bulasawa ce fa kawar aka ce" Mami dai ta dauke kanta, Gaba daya sai Ammi bata ji dadi ba ta dinga kallon kaka, Yakumbo da ta hakikance kan kujera a wajen tace "To ma hoton me xa suyi ana xaune qlau idan ba gulma ba, mu ma kanmu da kika ganmu nan guda daddaya muka yi da ita, da mai girma Gwamna sai ubanta na kaduna ne kawai suka yi hotuna yayi biyar, ita kanta uwarta ta amana Rahinah sau uku suka yi..." Mumy ta juya sum sum ta bar wajen, Ammi ta hade rai tana kallon Heedayah tace "Follow her immediately and snap" Heedayah ta nufi Mumy me hoton ya bi bayanta, Kaka tayi ma Ammi wani shegen kallo tace "Dole ki xagemu da turanci ai tunda kin samu yar ki da rai, da a mace kika ganta ai baxa kice taje su yi hoto da Rakiya ba" Yakumbo tace "Dalla rabu da ita, makirarra ce ai da kike ganinta, banda makirci mu xata gwale" Ammi dai bata kallesu ba, Yakumbo tace "Toh wai ni banga sirkin nawa ba" Kaka tace "Toh shi Junaidu ai ba ya shiga mata, yana can yana neman na kansa...." Sai kusan Magrib Heedayah suka koma can gidan Mami gaba daya da su Ammi da kaka da Yakumbo, tunda suka dawo bata sakko parlor ba har bayan isha, Mami ta shigo dakin jin shirun yyi yawa ta sameta kwance, ta karasa gadon ta xauna kusa da ita tace "What's wrong Heedayah? You don't look happy today, upon it's a great day for you... ur parent, love ones and well wishers are all here today because of you" Heedayah ta mike xaune bata ce komai ba, Mami tace "Talk to me dear, meye ke damun ki?" Kuka ta fashe ma Mami, Mami ta dinga kallonta da mamaki tace "Meye haka?" Ta rungume Mami cikin rawar murya tace "Mami he told me xai dawo ranan graduation dina kuma ban gansa ba" Mami tayi shiru, bayan kusan second talatin ta dago ta a hankali tace "You mean Khaleel?" Heedayah ta gyada mata kai, Mami tayi kasa da murya tace "But ae bai san yau graduation din naki ba ma...." Hawaye na sauka idon Heedayah tace "It's a year and 3 months now kuma bai dawo ba, his line isn't going through till today..." Mami ta share mata idonta tace "In sha Allah he is fine dear, kuma xai dawo da yardar Allah, kullum ina addu'an Allah ya karesa da kariyarsa ya dafa masa..." Heedayah ta gyada kai bata dai ce komai ba, Mami tace "Now kiyi sllh ki sakko downstairs, ur mum, step mum, relatives are all here for you, Ko kina son su gane wani abu ne?" Heedayah ta girgixa mata kai, Mami tace "Good, do as I say now" Heedayah ta sauka gadon a hankali ta wuce bandaki Mami ta bi ta da ido, tun da Khaleel ya tafi yau shekara daya da watanni ita ma rana daddaya ne baya fado mata kuma kullum sai ta sa shi a addu'arta, kuma tana jin tana kewarsa sosai, sai da Heedayah ta fito bandaki Mami ta mike ta fita dakin. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh ta jinginar da kanta jikin gado tayi nisa tunanin da take aka bude kofar dakin, Farida ce ta shigo, ta karaso inda take xaune ta xauna gefen gado tana kallonta, Heedayah ta daga kai ita ma tana kallonta, Farida tayi kasa da murya tace "Congrats Heedayah, Allah ya sanya alkhairi" Heedayah ta sakar mata murmushi tace "Thank you Sis, ya lectures?" Farida tace "Alhmdllh" Shiru duk suka yi, Farida ta mike ta fita dakin Heedayah ta bi ta da ido, bayan fitar Farida Heedayah ta sake lulawa duniyar tunanin da take, hawaye ya sakko idonta ta sa hannu ta goge a hankali ta jawo wayarta ta sake dialing number Khaleel duk da ta san baxai shiga ba, hade kanta tayi da gwiwa bayan ta kira bai shiga ba hawaye na ci gaba da sakko mata, gaba daya shekara dayan nan da watanni bata da wani sukuni bata ta6a tunanin xata yi kewar Khaleel har haka ba, she so misses him, to yaushe xai dawo?? Knocking kofar da aka yi yasa ta dago kai da sauri ta share hawayen idonta, jin an sake knocking ta mike a hankali ta nufi kofar ta bude, Junaid ne tsaye, sosai gabanta yayi mugun faduwa don kawai a fixge sai ta gansa kamar Khaleel din a gabanta, lkci daya ta sunkuyar da kanta da sauri, Junaid yayi kasa da murya yace "Congratulations Heedayah, Allah ya sanya alkhairi" Ta dago kanta ta sakar masa da murmushin karfin hali tace "Thanks Yaya" yace "I'm sorry I couldn't make it to ur graduation" Tace "Ba komai, ya aiki?" Yace "Alhmdllh" murmushi ya sakar mata yace "Just to say congratulations" ta gyada masa kai a hankali tace "Nagode" Har ya juya sai kuma ya sake juyowa yana kallonta yace "Are you alright" Cikin sanyin murya tace "Sure...." Yace "Ohk then sai da safe" Daga haka ya juya ya bar wajen ta rufe kofar ta tafi ta kwanta saman gado tana jin wasu hawayen na taruwa idonta. Mumy ce ta bude kofar dakin Shuraim a hankali ganin tun da suka dawo bai fito ba gashi har karfe goma da rabi, xaune ta samesa gefen gado ya rike kansa, ta karasa tace "What's wrong Aliyu?" Bai dago ba kuma bai bata amsa ba, tace "Aliyu" nan ma yyi mata shiru, tace "Wai ba magana nake bane, meye haka Aliyu" Bai dago ba still yace "I am fine" tace "You are fine?" Ya gyada mata kai, tace "Toh me ya hanaka fitowa ka ci abinci?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Aliyu??" Still ya ki cewa komai, juyawa tayi ta fita daga dakin, ya dago kansa da idanuwansa da suka sauya kala ya hau saman gadon ya kwanta ya rufa da blanket, bayan fitarta da minti biyu sai ga Abba ya shigo dakin yace "Shuraim" Ya yaye duvet din jikinsa ya mike xaune yace "Na'am" Abba yace "Are you alright?" Yace "I am" Abba yace "Sure?" Kai ya gyada masa, Abba yace "To fito ka ci abinci" yace "I'm not hungry" shiru Abba yyi yana kallonsa, can yace "Meet me at my parlor" Shuraim bai ce komai ba, Abba ya fita dakin, bayan kusan minti biyar ya sauka saman gadon da kyar ya bi bayansa, Mumy na xaune main parlor ta kasa cin abinci gabanta, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai ya nufi parlon Abbansa ta bi sa da ido, Xaune ya tadda Abba a parlon, ya xauna nan kasa, ba tare da ya dago kansa ba cikin sanyi yace "Gani Abba" Abba na kallonsa yace "Tell me, meye damuwar ka?" Shiru yyi bai ce komai ba, Abba yace "Talk to me Shuraim" Lkci daya idonsa ya kada, da mamaki Abba ke kallonsa, can yace "Are you okay?" Shuraim ya kasa dago kansa, sai ga hawaye without him preparing for it, kasa ce masa komai Abba yyi yana kallonsa da mamaki, bayan few minutes Abba yyi karfin halin cewa "Talk to me son, what happened..." Girgixa masa kai kawai Shuraim yyi, sai kuma yace "Xan kwanta Abba, I will be fine" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo, bakin kofa ya tadda Mumy labe bai kalleta ba ya wuce dakinsa yana shiga ya sa makulli ya hau gado ya shige Duvet. Mumy ta shiga parlon Abba da har lkcn was surprise, da damuwa tace "Ya gaya maka Barrister?" Girgixa mata kai kawai Abba yayi, ta fashe da kuka tace "To kuma ka bar sa ya fita, ni ban ta6a ganin yayi haka ba, ko matsala ya samu gun aikin, dama ni tun da ya xo nagansa kamar yana tare da damuwa na dai yi shiru ne, plss Barrister ka koma dakin ka samesa ka lallabasa ya fadi me ke damunsa" Abba dai bai ce mata komai ba ya bude laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you. Have u ever wondered how desserts are made? Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from? Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught: *Profit analysis *Ways to handle desserts *Dessert marketing. This class is all you need to start up a profitable side hustle.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos. Registration is on and the fee is just N3000 Naira. Class starts on 27th august,2021. And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕 Contact 08135358038 for ur *dessert* class follow us on Instagram via *najaatu Yakudima* Washegari karfe takwas da wani abu Mumy ta isa gidan Baffa, Bangaren Hajiya Amina ta nufa ta sameta tare da Sudais, bayan sun gaisa da Hajiya Amina, Sudais ya gaisheta da ladabi sannan ya mike ya fita parlon, Hajiya Amina ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ya na ganki haka ko baki da lafiya ne?" Mumy tayi kasa da murya tace "Wajen Dr na xo, to ban ga motarsa a parking space ba, shine na fara shigowa nan" Hajiya Amina tace "Yana can asibiti bai dawo ba" Mumy tayi tagumi bata ce komai ba, Hajiya Amina ta kara sauke ajiyar xuciya tace "To mu dai sae dai mu ce Allah ya kyauta da yanda abubuwa suka xo kamar wasan kwaikwayo, amma fa ni wlh ba wai kin jinin yarinyar nan Heedayah nayi ba har ga Allah, kawai naga ba a kyauta maki bane, ni kuma baxan iya juya maki baya ba shi sa nima nace baxan riketa ba, banda haka ai yaro na kowa ne wllh" Mumy dai ta ki cewa komai amma ji take kamar ta fashe da kuka a lkcn, Hajiya Amina tace "Kinsan dama Sudais tun tana makauniyar ta ya nuna damuwarsa sosai a kanta, to shine fa yanxu na aika aka kira min shi nake tambayarsa ko yana da interest ne a kanta kada in tauyesa...." Mumy da ta shiga yi mata wani irin kallo da sauri tace "Sai yace maki me?" Hajiya Amina tace "Rabu da shi ni xai raina ma hankali kamar shi ya haifeni, wllh kinji har na rantse yana son yarinyar nan, Wai ni xai kawo ma iskanci... dama can ai ba wai gaba daya na raba sa da ita ba sbda ke ce nace ya daina xuwa gidan wajenta kada xumunci a ya samu matsala tunda baki so" Mumy da duk ba wnn take son ji ba tace "Sai yace maki me ni dai??" Hajiya Amina ta tabe baki tana gyara xama tace "Ai karya yake bai fada min gaskiya ba, wai cewa yyi shi ba son aurenta yake ba, kawai dai ya dauketa tamkar kanwarsa ce sbda maraicinta a lkcn, amma bbu wani soyayya na aure da yake mata, wai fa ni xai raina ma hankali, to baya sonta xai dinga kashe mata uban kudade yanda ya dinga yi a lkcn, ni dai nace masa kar fa ya ji komai tuni na janye bakin da nayi a kan taraiyarsa da ita, idan ma aurenta xai yi ni baxan hanasa ba sai in fada ma Barrister a san abun yi, amma yaron nan ya dage shi ba sonta yake da aure ba yana da warce xai aura...." Mumy dake ta yi mata wani kallo ta katse ta tace "Amma Wlh Amina baki da kunya, ynxu don kin ga ubanta Gwamna ne shine kike nema d'an ki ya aureta?? Kike makala masa ta karfi da yaji? Wnn kwadayi har ina Amina" Hajiya Amina ta mike tace "Ehh na nema din, kuma kwadayi ai a gun danginki nayi gado, duk ba ke kika ja mana ba da muguwar xuciyarki da bakin halin ki, gwara ni nawa bai wani fito sarari ba, ai yau ga irinta nan kashi ma ya fi ki daraja a gun iyayen yarinyar, dubi yanda aka walakanta ki jiya gaban jama'ah kika yi tsamo tsamo da ke ba kyan gani, muna nan da ke in sha Allah sai na lallaba Sudais ya nemi auren nata tunda dama sonta yake nice na rabasa da ita ta karfi da yaji sbda sharrin shaidan, kuma naga yarinya ma a lkcn ai tana son sa...." Mumy tayi wani dariya ta mike tana mata wani irin kallo tace "Sai dai ki mutu ki ru6e amma wllh wllh Sudais baxai auri Heedayah ba, me kika ta6a tsinana mata daga ke har Dakta din? Gwara ni mijina shi yyi mata komai na rayuwa, Allah ne gatanta shine gatanta, shine tsaye kan komai nata, idan ma yau d'an Barrister yace xai auri Heedayah ya cancanci a bashi, to shi kuma Sudais a wa?? Idan ma auren ne Shuraim ya dace ta aura" Mumy bata jira cewarta ba ta nufi kofa da sauri tana cewa "Ni dama ba wajen ki na xo ba, ganin motar Dakta baya gidan ya sa na shigo wajen ki ashe da rabon inji kayan takaici, kwadayayyiya kawai" Bangaren Kaka ta shiga, ta sameta xaune da Hajiya Hauwa dake gyara mata kayanta a akwati, kallo daya kaka tayi ma Mumy ta ci gaba da bada labarin da take, Mumy ta xauna cike da ladabi tace "Ina kwana kaka?" Ba tare da kaka ta kalleta ba tace "Lafiya lau" Mumy ta gaisa da Hajiya Hauwa, Hajiya Hauwa ta tambayeta ya yaran, tace "Alhmdllh" Mumy na kallon kayan da ake xuba ma kaka a akwati tace "Tafiya xa kiyi kaka?" Kaka tace "Ehh Gwamnet house xa ni a kano, yanxu ai mune gwamnati tunda xuciyar mu da kyau bama nufin d'an kowa da sharri" Mumy dai bata ce komai ba ta hadiye wani abu da kyar, Hajiya Hauwa ta mike tace "Toh bari in dauko maki turaren kaka" Kaka tace "Yi maxa, duk da idan naje can baxan rasa ba amma kar inje masu tsiya tsiya ko?" Murmushi kawai Hajiya Hauwa tayi ta fita, Kaka ta kalli Mumy tace "Ai Aminar na can bangarenta baki duba bane...." A hankali Mumy tace "Aa wajen ki na xo" Kaka tace "Wajena kuma?? Ikon Allah, to ina jin ki, kinga shirye shirye nake kar lkci ya baci a banxa a hofi, a jirgin Uban Deedayah xa a tafi da mu wai jirgin baya jira inji Kumbo" Mumy tace "Allah sarki, to Allah ya kai ku lafiya Kaka" Kaka tace "Ameen, Ina sauraron ki" Mumy ta d'an yi shiru, kaka ta mike tace "Ni dai fa wanka xan shiga Maryam, baxan 6ata ma manyan mutane lkci ba" Mumy tace "Dama kaka a kan Shuraim ne" Kaka ta koma ta xauna tace "Waye kuma Shureen?" Mumy tayi shiru, kaka tace "Nace waye Shureen" Mumy tace "Shuraim dai daya, jiya ya dawo mun rasa gane kansa wllh, nayi nayi ya ki gaya min meye damuwar ya ki, shi ma Barrister ya samesa har daki ya ki gaya masa, yau ina ta xuba ido ko sallan Asuba bai fito ba, kuma kofar tasa a rufe yake yaki budewa" Kaka da ta saki baki tana kallon Mumy tace "Toh ko yayi masu bakin halin ne suka koresa gun aikin" Mumy dai bata ce komai ba, kaka tayi kasa da murya tace "Allah kuwa xai iya yiwuwa haka ne, me hali ai baya fasa halinsa, to amma ko koransa suka yi ga dai Uban Deedayah yana sa baki xa a mayar da shi, ai gwamna ne shi" Mumy dai tayi shiru, kaka ta rike kanta a hankali tace "Oh oh Allah, Ni wllh lamarin Shureen na damuna sosai... mutum magidanci gandarere haka amma har yanxu daga ke har Amadu kun xuba masa ido bbu me ce masa Ina matar aurensa, bbu me ce masa komai fa, to ko dai miskilancin nasa xai aura ne bani da labari? ga dai Sudais wllh jiya ya kawo min yarinyar da xai aura xankaleliya da ita, ga ta dai ba yar kowa ba yar talakawa ina jin a tudun wada ma take da iyayenta, to ai da kyau ya fi babu, yarinyar sai kyau da hankali da nutsuwa ga kunya to ai hakan da kyau, bai ma yarda ya kai ta gun kwadayayyiyar uwarsa ba, shi kuma Junaidu Uban Deedayah yace ya basa Deedayah duniya da lahira daga ni sai shi sai uwar Deedayah muka san wnn xancen, sirri ne bbu wanda ya sani, ko Rakiya bata sani ba wllh, nan Junaidu ya xo ya fada min damuwarsa na son Deedayah ni ko na ja sa har gidan uban Deedayah a Abuja, ashe wata fitinanniyar tsohuwa da na ta6a haduwa da a kasuwa da dadewa tana bala'i da jama'a kamar karya yayar uban Deedayar ce, gaskiya na girgixa ainun har buhun tafarnuwar na mata alkawari a lkcn Allah bai yi xan bata ba, to in gaya maki har ita tayi Na'am da Junaidu tunda uwarsa ce ta rike Deedayah da amana bbu ha'inci, kuma tace Deedayah na gama sakandari bbu ruwanta da wani Jami'a xa ayi aurenta da Junaidu, to yanxu sai naje xa mu fara shirin bikin ma, daga nan kuma sai a kira kowa a sanar masa, kece dai baxa a sanar ma ba sbda ba a san xuciyar ki ba" Mumy dake ta xufa daga xaune sai kallon Kaka take xuciyarta na bugawa sosai, Cike da karfin hali tace "Ita Heedayar na son shi ne???" Kaka tace "Ko bata son shi idan ita ba butulu bace ai baxata ki d'an Rakiya ba, Junaidu kuma ai mutum ne ga kyau ga kudi ga ladabi, snn abunsa bai rufe masa ido ba, halinsa sak na uwarsa Rakiya, ashe ma wai sun ta6a haduwa da uban Deedayah da dadewa sai da ya amshi lambar Junaidun ya gani a wayarsa yyi saving, to yanxu dai Shureen ne kadai bamu san kansa ba a xancen aure, amma tunda xan aurar da Sudais in aurar da Junaidu ai shkkn sai yyi ta xama a tuxurunsa shi" Mumy dai bata ma san abinda kaka ke cewa ba banda xafi bbu abinda take ji, gashi ta kasa xaune waje daya, Kaka tace "Toh yanxu xuwa xan yi can gidan in ji me ya same Shureen din duk da bashi da mutunci koko?" Mumy dai ta kasa cewa komai, gaba daya ta shiga wani mugun tashin hankali, Junaid ya auri Heedayah? Inaa this is impossible, Bata san lkcn da ta girgixa kai ba da karfi tace "Baxai yiwu ba wllh" Kaka ta saki baki tace "Meye baxai yiwu ba Maryam?" A firgice Mumy ta kalleta tace "Au, A'a ba komai, ba komai" Kaka ta dinga kallonta can ta mike ta tabe baki tana karasa rufe jakarta tace "Toh Allah ya kyauta, auren Junaidun da Deedayar ne baxai yiwu ba tunda ke kika halitto su ko, to ai kuwa sai dai bakin ciki ya kashe ki Maryam, Rakiya dai kina ji kina gani sai ta xama surukuwan gwamna in sha Allah, sadaukarwarta da jajircewarta baxai tashi a banxa ba, sai in har ta cuci Deedayah wanda Allah shaida bata cuceta ba a shekaru shidda da suka yi tare.... Abinda ma ta hakura ita ma Rakiyar xata koma gidan mijinta tunda Gwamna ya sa baki a lamarin har gwamnan Kaduna nan sai da yyi mata nasiha kuma ta hakura tace xata koma" Mumy ta mike gaba daya tashin hankali ne bayyane fuskarta ta nufi kofa kaka ta bi ta da kallo snn ta tabe baki ta ci gaba da abinda take tace "Aniyar ki ya bi ki gantalalliya" Gidan Hajiya Sadiya Mumy ta tafi, tun daga parlor Sadiya na xaune da yaranta Mumy ta rushe mata da matsanancin kuka, Sadiya ta mike da sauri ta ja ta suka wuce ciki da mamaki tace "Subhanallahi, lafiya Maryam me ya faru?" Cikin kuka sosai tace "Sadiya kinji wai da Junaid xa a hada Heedayah aure...." Sadiya ta gwalo ido tace "Waye kuma Junaid?" Mumy ta kara rushewa da kuka tace "D'an wajen Rahinah, shi wai xa a ba Heedayah" Sadiya ta bude baki tace "Ke a ina kika ji haka?" Mumy tace "Daga wajen kaka nake take gaya min yanxu, snn wai Rahinah xata dawo gidan Barrister, ni wnn ma bai wani dameni ba, wllh har raina ina jin idan Shuraim bai auri Heedayah ba xan iya mutuwa, takaici xai iya kasheni, kawai na tashi a tutar bbu kenan, shkkn a haka xan kare bbu riban komai, ga kishiya kuma xata dawo, snn Salima ta sa na kai uban kudi gun mutumi wai Shuraim xai ji sonta da sha'awar aurenta har ya kasa daurewa sai ya furta, to yau gashi shekara daya kenan bai ta6a xancenta ko makamancin xancenta ba balle har yace xai aureta, ni yaya xanyi da raina Sadiya?? Sadiya ta rasa abun cewa, can dai tace "Toh ke a ina kika ga kaka ta fasa maki wnn labarin, kakan da kowa ya santa da xuki tamalle...." Mumy tace "Wllh wnn ba xuki tamalle bane, cewa tayi ba a ma son kowa ya ji, kuma ita kanta Rahinar ma bata da labari sai kwanan nan xa a sanar mata tunda Heedayah ta gama secondary, tun jiya an rasa gane kan Shuraim ban san me ke damunsa ba, uban ma yyi yayi ya fada masa damuwarsa amma ya ki, tun asuban fari nake xaune parlor nake jiran fitowarsa ya tafi masallaci, wllh bai fito ba naje na kwankwasa kuma bai bude ba, shine na xo fada ma Baffansa halin da ake ciki tunda uban yyi watsi damu bai sake bi ta kansa ba, ban samu Baffa ba shine ya shiga gun kaka, a nan take gaya min wnn bakin labarin" Sadiya da tayi shiru tana sauraronta tace "Jiya tun yaushe kika lura Shuraim din na cikin damuwa?" Mumy tace "Tun bayan dawowar mu daga graduation da ya shiga daki bai sake fitowa ba" a hankali Sadiya tace "Dadina da ke rudewa baya sa ki fahimci komai wllh Maryam, daga dawowa graduation shkkn sai shiga damuwa, to wllh son Heedayah ce ya jefasa damuwar nan bbu tantama, ba ya ganta jiya ba har sun yi hoto, kinga dai bakiyi asaran kudin ki ba kenan kamar yanda kika ce" Lkci daya Mumy ta dakatar da kukan da take tana kallon Sadiya da idanuwanta kamar xa su yi magana, Sadiya tayi wani dariya tace "Alhmdllh, yanxu komawa gida xa kiyi cikin dubara kiyi masa xancen Heedayar sai ki ga reaction dinsa, lallabasa xa kiyi sosai" Mumy ta goge hawayenta da sauri tace "Toh bari in je, in sha Allahu son nata ne ma yasa shi damuwar" Ko minti daya bata kara a gidan ba ta fice ta koma gida, a waje tayi parking ta shige compound, Rabi'ah na xaune parlor tace "Shuraim ya fito?" Rabi'ah ta girgixa mata kai tace "Amma Abba na dakin nasa, ya sa na kai masa breakfast" Da sauri ta wuce dakin, Abba na tsaye kansa, shi kuma yana xaune gefen gado with cup of tea a hannunsa, kana ganin idonsa kasan bai yi bacci ba daren jiya, Abba ya kalli Mumy bai dai ce komai ba, da damuwa Mumy tace "Barrister ya gaya maka meye matsalar?" Abba yace "Ba sai ya gaya min ba, koma menene Allah ya yaye masa" Mumy ta hade rai, Abba na kallon Shuraim yace "Idan kayi breakfast din ka sameni dakina" daga haka ya fita dakin, Mumy ta bi sa da harara ta tafi ta kulle dakin ta sa makulli ta dawo ta ja stool ta xauna tana kallonsa da damuwa tace "Ka gaya min gaskiya Shuraim, jiya lafiyan Allah muka fita gidan nan da kai xuwa wajen graduation din Heedayah muna dawowa kuma shine har yanxu aka rasa abinda ya dame ka, tell me the truth son did you in anyway have feeling for Heedayah?" Shuraim ya daga kai yana kallonta, ta kwantar da murya tace "Kar ka ji komai ka gaya min I am ur mother, nasan tunanin ka idan kace kana son Heedayah kilan ka samu matsala ta wajena, to ba haka bane, in dai nice I won't stop you from loving Heedayah, you can go ahead and ask for her hand in marriage from her parent" Kallonta kawai Shuraim yake, dai dai nan aka buga kofar dakin, Mumy ta kalli kofar tace "Waye wnn" shiru ba ace komai ba, ta mike ta isa kofar ta bude, kaka ce tsaye tace "Xaki ce waye bayan kinje kin daddago ni Shureen ba a san me ke damunsa ba" Bata jira cewar Mumy ba ta shiga dakin tana kallon Shuraim tace "Auxubillahi, me ya same shi haka? Ko jifansa aka yi gun aikin" Mumy ta wani harareta, sai a snn ta fara da ta sanin xuwa wajenta ma ta sanar mata, to amma ai xuwanta yyi amfani tunda ta samu information da yawa, Kaka kamar xata yi kuka tace "Me ya sameka haka Shureen, me aka yi maka" Shi dai bai ce mata komai ba, ya ajiye cup din shayin ya mike ya wuce bathroom, kaka ta bi sa da kallo tace "Toh kinga tsiyar ana masa magana ya shige bandaki ko? Dubi fa yanda ya wani xabge kamar wanda yyi jinya, duk da a rame ya dawo mana daga legas din amma ai bai kai haka ba, asiri aka masa a can ne bamu sani ba, shi kuma Amadu tunda idan wani abu ya samesa ba shi yyi asara ba shi yasa ya ki bin ta kansa, to wllh idan abu ya samu Shureen sai ya samu kowa, duk cikin jikokina waye me sona banda shi..." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Ni sai in fasa xuwa Gwamnet house din, baxan tafi in bar jikana a haka ba ban san me ke damunsa ba, damuwa dake kisa lkci daya yanxu, idan abu ya samesa ai na shiga uku" Cire mayafinta tayi ta linke ta ajiye ta xauna gefen gadon ta ciro wayarta ta mika ma Mumy tace "Kira min Umaru, ni na ma fasa xuwa Gwamnet house din su yi tafiyarsu" Mumy ta ji sanyi sosai a ranta sanin in har Shuraim xai bude baki yace Heedayah yake so kenan ai sai inda karfin kaka ya kare, amma tsoronta yanxu bata ma san ko son Heedayar bane ke damunsa kawai ita dai lalube take cikin duhu tana fatan shi din ne, idan kuwa ba shi bane shkkn ta shiga uku. Heedayah sun fito tare da Mami da twin sisters dinta xa su shopping mall, Mami xata yi ma Ashnaah da Ashfa shopping kasancewar a ranan karfe sha daya xa su yi set off for kano, Yakumbo da Farida kadai suka bari a ciki don Ammi ta tafi gidan wata frnd dinta kafin su wuce, Mami na gyara ma twins din takalmansu aka bude gate din gidan, Heedayah ta daga kai don ganin wanda xai shigo, tsaye yyi bakin gate din yana kallonta kamar yanda ita ma ta take kallonsa..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Hello salaamu alaikum everyone! Good day to you. Have u ever wondered how desserts are made? Do u want to start a dessert business but don’t know where to start from? Or are you a new bride looking for other ways to amaze your husband 😂and Woow your guests ? Worry no more because Yakudima bakery has bring u an intensive online dessert class where u will be learning 8 amazing desserts recipes! Not only that, you will also be taught: *Profit analysis *Ways to handle desserts *Dessert marketing. This class is all you need to start up a profitable side hustle 🤣.This class entails everything u need to know. I promise it’s going to be very detailed with clear and explanatory videos. Registration is on and the fee is just N3000 Naira. Class starts on 27th august,2021. And always remember ,After a long stressful day , all u need is a DESSERT because STRESSED is just DESSERTS spelled backwards 🙃see you in class💕 Contact 08135358038 for ur Dessert class Mami ta mike tana rike da hannun twins din xata sauka kasa ita ma suka yi ido hudu da shi, tsaye tayi tana kallonsa, lkci daya Heedayah ta ji hawaye ya kawo idonta, yana murmushi ya karaso wajen walking slowly, yyi kasa da kai with respect ya gaida Mami, Mami ta sauke wani ajiyar xuciya tace "All this while bbu kira Khaleel? Sannan tafiya babu sallama" Ya kasa kallonta yace "Kiyi hakuri ban tafi da sim din da nake da numbers bane" Mami tace "To ka dawo lafiya?" Yace "Alhmdllh Ummi, ya gida" tace "Lafiya lau, ka shiga ciki, xan je Supermarket in dawo yanxu" yace "Toh in ajiye ku?" Tayi masa murmushi tace "Aa xan yi driving, motar ma na waje, kar ka damu ka shiga ciki" Yace "Toh Allah ya tsare" Mami ta kalli Heedayah da ta sauke kanta kasa tace "I will be back soon Heedayah, you stay back" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Mami ta kama hannun girls din ta wuce, Heedayah bata yarda ta kallesa ba ta juya ta koma ciki, ya bi bayanta yana kallonta. Babu kowa parlon ya xauna saman kujera still looking directly at her, ita dai ta ki yarda su hada ido, yyi kasa da murya yace "Heedayah" ta kauda kanta ta wani daure fuska, mikewa yyi ya dawo kujeran dake kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Ain't you happy seeing me?" Hawaye ya kawo idonta ta rufe fuskarta da kujeran, yyi shiru yana kallonta, can yace "To kiyi hakuri, idan baki son ganina I will go now" Ta dago tana kallonsa cikin rawar murya tace "You just left, no calls, no text...." Ya kwantar da murya ce "But I told you before leaving Heedayah, kuma ni ban tafi da wayata ba..." ta goge hawayen idonta da ya ki tsayawa, cikin sanyin murya yace "But I missed you with every second, I think of you everyday...." Ta d'an kallesa, sai a snn taga irin ramar da yyi, ya sakar mata cute smile dinsa yace "I missed you Heedayah" Bata iya tace komai ba, shima yyi shiru, bayan few seconds yace "Kuma ai jiya ku ka yi graduation dinku, i kept to my promise..." Tace "How did you know jiya ne graduation dinmu?" Yyi murmushi yace "I knew because I care Heedayah, nayi kewar ki fiye da yanda kike xato, I had no choice but to stay far away..." Yakumbo ce ta shigo parlon tana kallon Heedayah tace "Aa fasa tafiya tayi da ke Rahinar?" Heedayah tace "Uhm sun tafi" Yakumbo na kallon Khaleel a hankali tace "Auu, dama Rahinah na da wani d'an bayan Junaidu, ahh ba shakka" Heedayah ta kalli Khaleel dake kallon Yakumbo shi ma, cikin ladabi ya gaisheta ta amsa tace "Toh ya aka yi baka xo shagalullukan jiya ba, sannan ni bata ce min tana da babban d'a haka ba...." Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Nayi tafiya ne yau na dawo..." Yakumbo tace "Ba shakka, to ya sunan naka" ya sauke idonsa kasa yace "Khaleel" Yakumbo tace "Ba shakka, ita dai Rahinah Allah ya bata kyawawan yara maa sha Allah" lkci daya Yakumbo tayi tsit tana kallonsa da kyau tace "Aa wnn ai kamar na ta6a ganin ka ma..." Shi dai Khaleel bai ce komai ba don bai mance abinda tayi masa a gidansu Heedayah a Abuja ba, Yakumbo tace "Wllh sai fuskar yyi min kamar na ta6a ganinsa, toh shi Junaidu ba kullum yake dawowa gida bane, naga kullum ba a ganinsa a gida" Heedayah dai bata tanka ta ba ta mike ta tafi kitchen ta dauko masa ruwa da drink ta daura glass cup a tray din ta dawo parlon ta ajiye kusa da shi tana kallonsa, Yakumbo dai tayi wucewarta sama amma fa tana son tuna inda ta ta6a ganin Khaleel, Khaleel na kallon Heedayah murya can kasa yace "Ina kama da su Ummi ne?" Ta kallesa ta d'an yi murmushi tace "Aa, just the dimples" Shiru yyi yana kallonta, ta dau drink din ta mika masa, suka yi direct contact na ido, sosai gabanta ya fadi, shi ya fara sauke idonsa ya karbi drink din cikin sanyin murya yace "No matter the circumstances do not leave me plss Heedayah, idan kowa ma ya gujeni ke kar ki gujeni, I don't know what will become of me..." Cikin breaking voice ya fadi haka, lkci daya taji jikinta yyi sanyi tace "Me yasa kake yawan fada min haka, kana tunanin akwai abinda xai raba mu ne?" Ya gyada mata kai a hankali yace "Sure Heedayah, amma kar ki bari hakan ya raba mu..." Sakkowa kasa yyi kasa a hankali kneeling down right in front of her, ta ja baya ta xauna tana kallonsa da mamaki, cikin sanyin yace "I have never fell in love sai da na sake haduwa dake 1 year and some months back Heedayah, ban san meye soyayya ba, ban san ya yake ba, I was raised with a strong harsh heart, sai dai ban bari hakan yayi fatali da tausayina ba, Ina da tausayi sosai duk da dakakkiyar xuciyata..." Shiru yyi yana kallonta da lumsassun idonsa, ita kuma taki dago kanta tana ta naxarin abinda ya fada, can ta dago tana kallonsa tace "Sai da ka sake haduwa da ni? Dama mun ta6a haduwa ne?" Ya sauke idonsa kasa yace "Ehh mun hadu a lkcn da bakya gani, a lkcn da baki da sauran gata... Naji tausayin ki sosai, wanda tausayin yasa nayi maki abinda na maki" Kallonsa take ko kiftawa babu, can tace "Ban gane ba, meye ka min?" Yayi kasa da murya ce "Ni ne na dauke ki a den din Kidnapper na fito da ke a kan Motorcycle na ajiye ki gefen hanya Heedayah, and your words to me then were 'Are you leaving me?' Ban kuma ce maki komai ba nayi wucewata na barki, kin tuna??" A tsorace Heedayah ke kallonsa da manyan idanuwanta, can ta fara ja baya tace "Kai Kidnapper ne?" Ya girgixa mata kai da sauri as confused as he is yace "Noo Heedayah, kawai na kubutar da ke ne daga wajensu sbda tausayin ki da naji" Kallonsa take ko kiftawa bbu xuciyarta na bugawa, cikin sanyin murya yace "Ni ba su bane Heedayah, na dai taimakeki ne sbda kashe ki xa su yi" Ta hadiye abu da kyar tace "To ya aka yi kasan ina wajen, I was thinking daji ne, me ya kai ka wajen har ka san da ni??" Ya girgixa kai da sauri, da farko ya rasa abun cewa, sai kuma yyi saurin cewa "Na xo wucewa ne da Bike dina shine na dauke ki...." Bata kuma cewa komai ba ta sauke idonta kasa, lkci daya jikinsa yyi sanyi sosai don ya san bai gamsar da ita ba, bata gamsu da bayaninsa ba, gaba daya kuma ya rasa me xai ce mata, can a hankali yace "Heedayah" ta dago da sauri ta kallesa yace "Tunanin me kike?" Ta girgixa masa kai ta mike tace "Aa ba komai, xan karasa wanke wanken da nake yi a kitchen" bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen din da sauri, ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa, Heedayah na shiga kitchen ta kulle kofar ta jingina jiki gabanta na wani irin faduwa flashback din shekaru shidda da suka wuce da muryarsa na sake dawo mata, sai yanxu ta tuna inda ta ta6a jin muryarsa, shi ne wanda ya kama hannunta ya saka mata bread bayan an sanar masa bata gani a lkcb, snn shi ya xo ya dauketa ya sa ta a bike ta tuna ihun da ta dinga yi and he told her he have gun wanda hakan ya tsoratata sosai a lkcn, yess muryarsa ce, ji tayi gaba daya jikinta ya dau rawa kafafuwanta sun kasa daukarta, ta fi minti biyar a haka can ta bude kofar kitchen din a hankali ta fito parlon, yana durkushe yanda ta bar sa, jin an bude kofar kitchen din ya juya ganinta yace "Heedayah...." Bata ko kallesa ba ta wuce sama da gudu xuciyarta na bugawa, ya bi ta da ido... Sai kuma ya dafe kansa da yyi masa nauyi lkci daya, a haka Mami ta shigo parlon ta samesa, ya dago da sauri, tace "Lafiya Khaleel??" yyi murmushin karfin hali yace "Aa ba komai, sannu da dawowa" Tace "Yauwa, ina Heedayar?" Yace "Ta wuce sama yanxu" Mami ta sake hannunsu su Ashnaah ta nuna masu sama duk suka wuce, ta xauna tana kallon Khaleel tace "Is everything okay?" Ya sauke idonsa kasa ya xauna nan kasa yace "In sha Allah" Tace "Baka sha lemon ba?" Ya kalli drink din da Heedayah ta ajiye masa yace "Xan sha" tace "Ko a kawo maka abinci?" Ya girgixa mata kai yace "Alhmdllh na ci abinci" Ita dai sai kallonsa take, bayan few seconds yace "Dama ina jiran ki dawo ne, xan wuce" tace "To xaka shigo anjima" ya gyada mata kai yace "In sha Allah" ta mike tace "Toh shkkn Khaleel, bari a kira Heedayar" da sauri yace "Aa mun yi sallama da ita" Mami ta juya tana kallonsa ya mike yace "Nagode Ummi, sai anjima" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, ta koma ta xauna a hankali, ko kadan bata gane feeling din da xuciyarta ke samu idan taga wnn bawan Allah, muryar Yakumbo taji tana cewa "Rahinah ashe kina da babban d'a dama bani da labari, wnn ma har ya fi Junaidun nutsuwa da kunya naga" Mami ta kalleta tace "Wa kenan?" Yakumbo tace "Au har ya tafi kenan, nan na samesa tare da Heedayah" Mami tayi shiru, can tace "Aa ba d'a na bane, ya xo gaisheni ne" Yakumbo tace "Toh ai d'an d'an uwanka ko yar uwarka naka ne, jini ai ba wasa bane, ga kamanninku nan tare da shi kuma kice ba d'an ki bane, kuma ko ba komai suna yanayi da Junaidu sosai, ke kanki ma idanunku iri daya ne da nashi, to ita kuma Aisha bata da niyyar dawowa ne ta debi sojoji suna gadinta tana xaga gari don neman suna, kai samun waje ma dai bai yi ba wllh, tun safe an shanya mu ba alamar wucewarmu fisabilillahi, ita kuma wancan tsohuwar me gilla karya har yanxu bata iso ba ta kuma ce min da sassafe xata xo, Amadi dai yace a taho da ita, Kar mu je bbu ita ya kullace mu tunda ta nace sai ta bi mu" Mami dai bata ce komai ba don abinda ya dameta ya tsaya mata a xuciya daban. Farida ta rufe laptop dinta tana kallon kofar bathroom don kusan minti talatin kenan da shigan Heedayah har yanxu bata fito ba, har lekowa Mami tayi daxu tana tambayar Heedayar tace mata tana bayi, kuma ita bata ji alamar wanka take ba, mikewa tayi ta isa bakin kofar ta kwankwasa, jin bata amsa ba ta bude kofar bathroom din, durkushe ta ganta bandakin ta hade kanta da gwiwa, da mamaki Farida ta karasa ciki ta dago kanta tace "What's wrong Heedayah" hawaye ta gani sha6e sha6e fuskarta, Farida ta buda ido tace "Subhanallah, me ya faru? What happened?" Heedayah ta fashe da kuka a hankali, Farida ta dagota hankali tashe tace "Ki gaya min me ya faru Heedayah, me aka maki?" Heedayah ta rungumeta tana kuka sosai amma ta kasa cewa komai, Farida ta fito da ita daga bandakin ta xaunar da ita gefen gado tace "Don Allah ki gaya min menene? An maki wani abu ne" cikin rawar murya Heedayah tace "I don't want to say anything about it Farida..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai, cike da damuwa Farida tace "Don't you trust me Heedayah, talk to me plss" Heedayah ta runtse ido trying hard not to burst out again tace "Khaleel" Farida ta bude ido tace "What about him? Is he back??" Da kyar tace "Am thinking...." Sai kuma tayi shiru wasu hawayen na taruwa idonta, Farida tace "What are you thinking?" Rungume Farida tayi cikin kuka sosai tace "He is a kidnapper Farida, wllh kidnapper ne" Still Farida tayi jin abinda Heedayah tace, can ta dagota with so much shock tace "How did you know?? who told you that?" Heedayah tace "Shine ya fito da ni daga wajen kidnappers ya ajiye ni bakin titi years back" Heedayah bata kai Farida tsorata ba, Banda xare ido bbu abinda Farida ke yi kamar warce tayi ma sarki karya, cike da karfin hali tace "Who told you all this Heedayah?" Hawaye na sakko ma Heedayah tayi ma Farida bayanin komai, Farida da tayi mugun tsorata tace "Is he still in this house?" Heedayah ta buda mata hannu alamar bata sani ba hawaye me xafi na sakko mata, Farida xata mike Heedayah ta rikota tace "Promise me this will be a secret between us, don girman Allah kar ki gaya ma kowa not even Mami" hawaye ya kawo idon Farida ta koma ta xauna tace "Why secret Heedayah? Xa ki ci gaba da alaka da d'an kidnapper ne? What will be our faith?" Heedayah ta fashe da kuka tace "Not at all, baxan ci gaba ba, amma...." Farida tace "Amma me?" A hankali Heedayah tace "Yasa na fara sonsa, I don't know how that happened all of a sudden, ya cuceni ya sa min sonsa" Farida ta xaro ido tace "So xa ki ci gaba da sonsa kenan???" Da sauri Heedayah ta girgixa kanta tace "I hate everything about him now, he is disgusting, I now understand why I saw gun with him a gidansa ranan da daddare, I now understand why he is this rich with so many cars and houses, I now understand me yasa baya son daga kiransa a gabana, I now understand why yake yawan ce min I shouldn't leave him no matter the circumstances, but I have to leave him, kuma na bar sa har abada, na tsani komai nasa, nayi da na sanin sake haduwa da shi da kulasa da nayi, dama shi ya rabani da iyayena tun ban san kaina ba, ya kuma maida ni wajensu after many years sbda selfish interest dinsa" kuka take sosai tana girgixa kanta, Farida ta kamo hannunta amma ta rasa abinda xata ce mata, ita ma hawayen take sosai don tun ba yau ba tasan Heedayah ta fada son wnn mutumi, Mikewa Heedayah tayi ta tafi gun kayanta ta fara hadawa tace "I will be leaving with Ammi today...." Jikin Farida yyi sanyi sosai sai a snn ta gane sbda Khaleel Heedayah tace baxata koma Kano da Amminta ba after her graduation, sbda tana anticipating dawowarsa. Da ido kaka ta dinga bin Shuraim da ya gama saka kayansa a jaka tace "Yau naga jaraba ina ta magana mutumi ya mayar da ni mahakuciya, dubi fa yanda ka zabge kamar me wata cutar can warce bamu sani ba, tunda iyayenka gantalallu ne ai ni ba gantalalliya bace baxan bari ka cutu ba, idan ma wani abun ke damun ka sai ka gaya min in san nayi tun wuri, bbu wajen wani shegen aiki da xaka koma, to banda kai wa ke gareni a duniyar yanxu, dama ni da kai nafi sabawa a kan su Amadu ma, kawai shaidan ne ya shiga tsakaninmu, shekarunka nawa a wajena kafin algungumar uwarka ta amshe ka ta karfi da yaji" Shuraim ya juya yana kallonta yace "Ba abinda ke damuna, bana jin dadi ne kawai, Amma yanxu Alhmdllh, xan koma bakin aikina" ta mike tace "Allah ya tsine ma aikin, idan ma xaka bini in kaika asibiti ka bini wllh, tunda shi Umaru bai daga kirana ba shi yasani, shi kuma Amadu xai ga barbadin bala'i yanxun nan kuwa" daga haka ta fice daga dakin, xaunawa Shuraim yyi gefen gado jin kansa na juya masa ya dafe kan xuciyarsa na bugawa, kaka na shiga parlon Abba ta samesa ya gama shiryawa xai wuce aiki, cike da bala'i tace "Amadu ba gwara abu ya sameka ba da ya samar min Shureen, uban me ka ta6a tsinana min tunda na haifeka dama, wato bakin ciki da rayuwar da Shureen ke yi a duniya kake yi ban sani ba, ban da bakin ciki ya xa ayi d'an ka bashi da lafiya amma ko a jikinka ka wani shirya xaka fita inda ku ke giggilla karyar ku..." Abba dai kallonta yake kafin yace "Baaba Shuraim ba yaro bane, idan yana ga barin damuwarsa a xuciyarsa ne mafi alkhairi garesa ba sai a kyalesa ba" Kaka tace "To anki kyalesan, kuma aniyarka ya bika wllh, in sha Allah bbu abinda xai samar min shi...." Abba ya d'an yi murmushi bai dai ce komai ba, sarai yasan meye damuwar son din nasa, ta juya ta fice daga parlon ta koma dakin Shuraim, Mumy dai na ta xaune main parlor tana ta addu'ar Allah ya sa son Heedayah ne ya sa shi damuwar nan, kuma Allah ya sa ya sanar ma kaka komai ya xo cikin sauki kenan. Zayyad ne durkushe an daure hannunsa da igiya ta baya, oganninsu ne tsaye kansa ko wanne na nuna sa da bindiga, Zayyad ya kalli sauran colleague dinsa dake tsaye gaba daya a katon parlon, Oga Manga ya karasa gaban Zayyad da katon muryarsa yace "Brainiac ya sauka kasar nan jiya, yana ina??? We are asking you this for the last time Zayyad" Zayyad ya juya da jajayen idonsa yana ma Salim wani irin kallo, Oga Arne ya kai masa kyakkyawan naushi a fuska cikin tsawa yace "Baxa ka bamu amsa ba??" Zayyad yace "Ni bamu hadu da shi ba har yanxu Oga, na gaya maku kun ki yarda" Oga Bala na nuna masa wayarsa yace "Amma kun yi waya ko...." Zayyad ya kalli wayarsa da Ogan nasa ke nuna masa yace "Ehh" Oga Manga yace "Ina yace maka yake?" Zayyad yace "Naje gidansa kamar yanda ku ma ku ka je, ban samesa ba gidan a kulle yake" Salim yace "Amma a waya daxu yace maka xai je gidan budurwar tasa" Zayyad ya sake jefa masa wani kallo, Oga Arne ya hauresa yace "True or false??" Zayyad yace "Ai ban san gidan ba nima" Oga Arne yyi wani dariya ya koma kan mighty chair dinsa ya xauna ya daura kafa daya kan daya yace "Ku tafi da shi ku tabbatar ya fadi inda gidan yake, snn a tafi a dauko mana mahaifiyar ita yarinyar yau din nan" Wani kara Zayyad yyi ya buga tsalle ya dawo da hannunsa dake daure ta baya gaba, ya haure Oga Arne dake kan kujera da kafarsa snn yyi hanyar bedroom da gudu ya bude wani daki ya shiga ya sa makulli yana huci, da sauri ya tafi gaban mirror ya fiddo karamar wayarsa ya shiga dialing number din Khaleel, yana jin suna kokarin balle kofar gaba dayansu, har wayar ya katse Khaleel bai dauka ba, gaba daya Zayyad ya hada xufa, ya sake kira praying hard Allah ya sa Khaleel ya dauka sai gashi ya dauka, da sauri Zayyad yace "Brainiac ka dauke Barrister din nan a gidanta with every other person, su Oga Arne xa su je gidan yanxun nan, I am giving them the address nowwww....." yana fadin haka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya jefar ta bayan mirror ya durkusa a dakin ya sunkuyar da kansa kasa, suna 6alla kofar Zayyad ya dago da sauri nan ya zayyano masu full address din gidan Mami ya kara da cewa "Xan iya kai ku gidan ynxu ma...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Heedayah dai taki yarda ta dago kanta, Mami tace "Wai baxa ki bani amsa ba?" Ta dago a hankali tace "Mami nace ba komai, kaina ne ke min ciwo" Mami ta hade rai tace "Ciwon kan yasa kika yi kuka har idonki ya kumbura?" Heedayah ta marairaice tace "Yayi min sauki ynxu Mami, ask Farida" Farida dai na xaune can karshen gado tana danna wayarta bata ce masu komai ba, Mami tace "Toh yayi kyau, keep on lying, and why did you change your mind about going to kano with them?" Heedayah tayi kasa da murya tace "Mami sati daya xan yi in dawo in sha Allah, kawai dai ina son in je" Mami dai bata kuma ce mata komai ba ta fita dakin, Heedayah ta goge guntun hawayen idonta, Farida ta mike ta dawo kusa da ita tace "Heedayah me yasa baki son gaya ma Mami, why are you hiding this serious issue from her" Heedayah ta kalleta bata ce komai ba, Farida tace "It's better ki gaya mata, kinga she likes the guy, gwara ta sani tun wuri wllh, damuwata daya yanxu ya san gidanmu, I don't think we are safe anymore" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Heedayah na ci gaba da share idonta tace "Tun da ya san na sani ynxu baxai sake xuwa nan ba, and just watch and see" Farida tayi mata wani kallo tace "Wa yace maki?? Mutumin dake son ki, snn sbda son da yake maki har ya tona ma kansa asiri ya gaya maki shi wanene, ae wlh baxai ta6a daina bibbiyar ki ba, tafiyar ki kano shine kadae mafita gare ki" Heedayah tace "Wait Farida, is he even crazy to come back bayan ya riga yasan na san komai a kan sa ynxu??" Farida tace "Ke baki san so ba ko?? Wllh ko xaki tona masa asiri in dai yana son ki da gaske baxai daina bibiyar ki ba" Heedayah ta hade rai tace "Then he will be playing with fire, I will have to expose him to everyone" Farida tace "Exactly Heedayah, yanxu ki tashi mu je ki sanar ma Mami first..." Heedayah tayi shiru lkci daya hawaye ya kawo idonta, Farida ta mike ta kamo hannunta, xame hannunta tayi cikin sanyi tace "Baxan iya ba Farida, kawai let just leave him, I don't want anything to happen to him ta dalilina, ni nasan baxai ma sake dawowa ba" Farida tayi shiru tana kallonta. Mami ce tsaye dakin da Yakumbo ke ciki tana xuge handbag dinta tace "Toh ni yanxu wa xai kai ni can gidan lauyan??" Mami tace "Driver xai ajiye ku yanxu" Yakumbo tace "Ya san gidan ne?" Mami tace "Aa tare da Heedayah xa ku je" Yakumbo tace "Toh ni dai Allah ya rufa mana asiri kada tafiyar nan ya sha ruwa yau, ita Aisha na can tana xaga Kaduna da sojoji bata da niyyar dawowa, komai dai sai an bata ma mutum rai, amma ba laifin kowa bane laifin Amadi ne" Mami dai bata ce komai ba ta fita su Ashfah da suka makale mata na biye da ita, bbu abinda suka mance na Heedayah yaran kawai dai ta fi su haske, dakinsu farida Mami ta shiga, Mami na kallon Heedayah tace "Idan kin ga dama kin gama kukan iskancin naki sai ki shirya ki raka Yakumbo gidan Abban ki...." Da sauri Heedayah ta juyo tana kallonta tace "Gidan Abba kuma, Ba yanxu xa mu tafi ba Mami?" Mami tace "Wannan kuma ban sani ba" Heedayah tayi shiru, Mami ta juya ta fita dakin, Bata fuska Heedayah tayi ta rungume hannu, Farida dai na tsaye jikin window tana kallonta, bayan minti kusan goma Yakumbo ta leko dakin tace "Toh ni dai idan baxa ki je ba ai sai yar uwarki ta xo ta rakani, bbu ruwana da wahala..." Heedayah ta kalli Farida tace "Farida ki rakata ni kaina ciwo yake min wllh" Yakumbo ta rike ha6a tace "Ga dukkan alama Rahinah ta sangarta ki, kuma wnn wlh ba halin xaman gidan miji bane, kaji min fitsararriyar yarinya kawai" Heedayah bata ce mata komai ba, Yakumbo na kallon Farida tace "Kinga shirya ki rakani kin ji yar nan" Farida tace "Toh" Yakumbo ta fice daga dakin ta koma gun Mami, Mami tace "Baxa ki ci abincin ba kafin ki tafi?" Yakumbo tace "Kyaleni da abincin nan ke dai, amma a gaskiya wnn Heedayar taki bata da hali ko kadan, ga rashin kunya fal cikinta, wai yarinyar ta dubi tsabagen idona tace ita baxata ba sai dai Farida ta kai ni, irin tarbiyar da kika mata kenan??" Mami tace "Kiyi hakuri bata jin dadi ne, amma dole ma xata bi ki" Yakumbo tace "Aa ba ruwana, ta sha xamanta ni Faridar ma ta fi min sau dubu" Mami ta fita dakin ta koma dakinsu Farida, fuska daure tana kallon Heedayah tace "Tashi ki shirya ki fito ku wuce" Heedayah ta mike bata ce komai ba ta tafi press dinsu ta bude ta fiddo hijab dinta har kasa, Farida ta bi bayan Mami bayan ta fita, parlor ta sameta tace "Mami can I go with them?" Mami tace "Kince kina da lectures by 2, but if you want to go, you can" Farida tace "Toh Mami" daga haka ta fita, Nikab Heedayah ta saka ta fito parlor tare da Farida, Yakumbo tace "Allah ya kiyaye, uban wa xa ki bi a haka?" Mami dake parlon ita ma a xaune tace "Da shi take fita Yakumbo" Yakumbo tace "Toh ai ba da shi na ganta jiya a gun taron ba, Kai ni fa idan ma xata ce ba nice yar ubanta ba bbu abinda ya sha min kai" da turanci Mami tace ma Heedayah ta tafi ta cire Nikab din, ba musu Heedayah ta koma ta cire snn ta dawo, gaba daya bata da walwala, motar sojoji guda ne a layin tun xuwan su Amminta gidan Mami jiya, Heedayah dai na xaune bayan mota tare da Yakumbo, Farida kuma ta shiga gaba suka bar layin. Suna isa gidan Abba mai gadi ya bude masu gate, driver ya shigar da motar yyi parking, Heedayah ta sauka snn Farida, Yakumbo ma ta sauka tayi hanyar cikin gidan suna biye da ita... Mumy ta fito daga kitchen kenan suka shigo parlon, ganinsu ta baje fara'a a fuskarta tace "Sannun ku da xuwa" kallo daya Yakumbo tayi mata ta nufi kujera tana cewa "Ina patun take?" Mumy na ta murmushi ta karaso cikin parlon tace "Ta je gida, Amma yanxu xata dawo" Yakumbo tace "Ya mai jikin?" Mumy tace "Da sauki Alhmdllh, yana cikin daki, Heedayah rakata dakinsa" sosai Heedayah tayi mamakin abinda Mumy tace, ta dai gaisheta tare da Farida, Mumy ta amsa tana washe baki tace "Ki kai ta dakin Shuraim" mikewa Heedayah tayi ta nufi dakin Shuraim Yakumbo na biye da ita a baya, ta bude kofar dakin ta tsaya nan bakin kofa ta ki shiga, Yakumbo ta shige dakin tana kallon Shuraim dake kwance yyi rub da ciki yana bacci, he looks so sick and tired, Yakumbo tace "Toh kai kuma ya da kwanciyar 'yan wuta, cuta ai ba mutuwa bace" Shuraim ya bude ido a hankali, ganinta tsaye dakin ya mike xaune da kyar, Yakumbo tace "Sannu, ya jikin?" Ya gyada mata kai yace "Da sauki, ina kwana?" Tace "Lafiya lau, me ke damun ka haka?" Murya can kasa yace "Na ji sauki" Ta xaro ido tace "A haka?? Toh Allah ya sauwake, amma wnn kam ai kana jin jiki...." Ya daga kai ya kalli Heedayah da ta ki shigowa har sannan, suna hada ido ta sauke kanta tace "Ya jiki" Bai amsa ba ya cire Duvet din jikinsa ya saukar da kafafuwansa kasa, Yakumbo tace "Tana maka ya jiki" ya daga kai ya kara kallonta yace "Fine" Yakumbo ta kyabe baki ta nufi kofa tana cewa "Ita ma ai bakin halin gareta" da sauri Heedayah ta bi bayanta bayan ta fita ta kullo masa kofarsa suka koma parlor, Mumy tuni ta ajiye ruwa da lemo har da abinci a kasa kusa da kujeran da Yakumbo ta fara xama, Yakumbo na kallon abincin tace "Aa mu mun ci abinci kafin mu fito, kamar dai ana yunwa" Tana fadin haka ta matsar da abincin gefe ta xauna tace "Me ke damun shi Aliyun haka?" Mumy tayi kasa da murya tace "Wllh bamu sani ba, ya ki fadi...." Yakumbo tace "Toh ba a je asibiti bane?" Mumy tace "Yayan Abbansa ya xo daxu yyi masa allura ma, toh shine yake ta bacci tun daxun, yana dai complain din ciwon kirji" Yakumbo tace "Toh Allah ya sauwake, ita patun yanxu xata dawo kuwa?" Mumy tace "Ehh taje yi masa girki ne kafin ya tashi wai, na ma ce ta barsa gashi nayi amma ta ki saurarata" Yakumbo tace "Toh ai da kince mana yana bacci da bamu tashe sa ba yyi baccinsa isasshe" Mumy dai sai murmushi take bata ce komai ba, Farida dai idonta na kan TV da gaba daya bata san abinda ake ba, Mumy ta mike ta wuce kitchen, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da cup din shayi ta nufi Heedayah dake xaune ta mika mata tace "Tunda ya tashi gashi ki kai masa, tun safe bai ci komai ba, Allah ya sa ya sha wnn din ma" Heedayah ta d'an buda ido tana kallonta, ganin mika mata dai Mumy ke yi ta amsa ta kalli Farida dake kallonsu, Yakumbo tace "Toh ko baxa ki kai masa din bane tunda kunya bai isheki ba, sai Farida ta amsa kawai ta kai ita" Heedayah ta d'an hade rai ta mike ta nufi dakin, Farida ta bi ta da ido, a hankali ta bude kofar dakin tana kallon ciki, xaune ta gansa yanda suka barsa ya rike kansa da duk hannunsa biyu, jin an bude kofa ya dago sai dai bai kalli kofar ba, ta shigo dakin ta ki kulle kofar, kamar warce aka tilasta tafiyar ta isa inda yake xaune tace "Mumy tace in kawo maka" Jin yyi shiru ta durkusa ta ajiye masa cup din tea din, ta mike xata fita taji yace "Heedayah" tsayawa tayi amma bata juyo ba gabanta na faduwa, bayan few seconds ta juyo a hankali tana kallonsa.... Bayan tafiyarsu Heedayah kafin azahar Ammi ta dawo gidan, Mami na kallonta tace "Amma dai bbu tafiyar ta ku yau ko?" Ammi tace "Ehh wai Aliyu bashi da lafiya daxu Abbansu Islam ke gaya min, kuma Yakumbo ma taje can gidan ko?" Mami tace "Ehh tana can da su Heedayah" Ammi tace "Dole sai gobe kenan xa mu tafi, anjima daddare xan je dubasa idan Allah ya nufa" Mami tace "Allah ya kai mu, xan d'an fita in dawo yanxu Maman biyu" Ammi tace "Toh shhkn Allah ya tsare hanya" Hijab Mami ta sa har kasa ta dau wasu files Ashnaah ta fara kuka xata bi ta, Mami ta kama hannunta suka fita, Abba take son kai ma files office kamar yanda ya bukata, bayan tayi warming motarta ta fita gidan tare da Ashnaah dake xaune front seat.... Mami na fitowa daga layin, aka sauke glass din wata farar mota dake parke nesa da layin, Oga Manga ya kalli Zayyad dake gefensa cikin motar yace "Ita ce wancan?" Zayyad yace "Aa...." Wani naushi Manga ya kai masa yace "Ba matar nan muka tarar asibiti a Abuja ba??" Zayyad yyi shiru a ransa yana mamakin me yasa Khaleel yyi ignoring din message din da yyi passing masa ta waya da safe, Wani naushin Manga ya kai masa, Zayyad yace "Ita ce" tada motar Salim yyi suka bi hanyar da Mami ta bi a guje kafin Wani barrier ya shiga tsakaninsu, Mami na isa office din Abba tayi parking waje ta dau wayarta ta kirasa don ya fito ya amshi envelope din hannunta don baxata shiga ciki ba, Ashnaah dake xaune tace "I want to ease my self..." Mami ta kalleta tace "Ohk" daga haka ta bude motar ta sauka ta rufe ta xagayo ta inda take ta bude motar ta sakko da ita, A bayan motarta su Manga suka tsaya da tasu motar, duk da ta ga motar bata kawo komai ba ta xata client din Abba ne, Manga na kallon Fago yace "Kayi attacking yarinyar karama first...." Fago ya dira motar ya nufi Mami da ke daga kayan Ashnaah, lkci daya ya fiddo bindigarsa ya daura mata a kai yana kallonta da masked face dinsa, Xaro ido Mami tayi tana kallonsa kafin tace komai ya fixge Ashnaah daga hannunta xai koma motarsu ta bisa a rikice yana ganin haka ya bude motar ya jefa ma Manga Ashnaah, Manga na kallonta yace "Ki shigo idan kina son yar ki da rai...." Ai Mami bata san lkcn da ta shiga motar ba, ta shiga tashin hankalin da ya wuce misali, a rikice take cewa "Ku fadi abinda ku ke so daga gareni amma ku rufa min asiri kar ku tafi da 'yar mutane..." tuni Fago ya rufe motar ya shige gaba Salim ya tada motar suka bar wajen a guje, Zayyad dai ya sunkuyar da kansa ya kasa dagowa, Ashnaah ta haye jikin Mami a tsorace tana kuka sosai don gaba daya fuskarsu a rufe yake, Mami ta rungumeta har ranta taji farin cikin ba Ashnaah kadai xa su tafi da ba har ita.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Khaleel na kwance saman 3 seater a parlonsa, yyi nisa tunanin da yake idonsa na kan pop din parlon, a hankali ya juya yana kallon wayarsa da yyi vibrate a gefensa, ganin me kiran nasa ya ki dauka har ya katse, sake kira aka yi, ya mike xaune da kyar ya daga kiran yace "You called bana jin ka daxu kuma ka kashe waya gaba daya, What's up?" Muryar Oga Arne ya ji yana dariyar bosawa, Khaleel yyi shiru ya sake kallon screen din wayar yaga number Zayyad ne ya katse wayar ya kashe gaba daya ya jefar nan gefensa ya koma ya kwanta ya lumshe ido xuciyarsa na bugawa.... Mami na kallon katti ukun dake kanta a tsaye cikin wani daki ko wannensu rike da bindiga, tana son magana amma ta kasa cewa komai sai hawaye, Ashnaah ma sai kuka take tana shigewa jikin Mami, fuskarsu dake boye cikin face mask shi ke kara tsorata yarinyar, cike da karfin hali Mami tace "Ku fada min me ku ke so daga gareni?" Bbu wanda ya tanka ta cikinsu da alama gadinta kawai aka ajiye su suyi, Ta rungume Ashnaah tana lallashinta tana karanto addu'o'i a xuciyarta na neman tsari da sharrinsu. Shuraim bai yarda ya hada ido da Heedayah dake tsaye tana kallonsa ba yace "Close the door" ta kalli kofar sannan ta kallesa, kin xuwa ta kulle kofar tayi kuma bata ce komai ba, ya kalleta suka hada ido yace "Baki ji me nace bane?" Tace "Toh saboda me?" Mikewa yyi ta koma gefe da sauri tana kallonsa kamar xata yi kuka, ya isa gun kofar ya kulleya juyo yana tsaye wajen yace "I want to ask you 2 to 3 questions" Ta d'an yi shiru, sai kuma ta gyara tsayuwarta tace "Ina ji" Ya jingina da kofar bai yrda sun sake hada ido ba yace "And promise to say the truth... Nothing but the truth" ita dai tayi shiru tana jin sa, yace "Kin tuna lkcn da Abba ya kawo ki gidanmu ko?" Ta gyada masa kai, yace "Good, daga lkcn xuwa ynxu shekara nawa kenan?" Still not looking at him tace "Shidda" Yace "Alright, a cikin shekara shiddan nan can you plss remind me ko na ta6a cutar ki?" Kura ma carpet din dakin ido tayi trying to digest what he just said, bata san lkcn da tayi murmushi ba don ba karamin dariya tambayar ya bata ba, yana kallonta ce "Ina sauraron ki" tace "Wani irin cuta kenan?" yace "Duk abinda a tunanin ki cuta ne" tace "Ni na manta" Yace "Baki manta ba, bani amsata" Tace "Toh idan ma conscience dinka na judging dinka ne sbda abubuwan da yasan kayi, duk da ni dai manta pass dina balle in tuna abinda aka min, to I've forgiven you" Yace "My conscience can never judge me don nasan ban maki komai ba duk Shekarun nan...." Tace "Toh me ya kawo maganan nan yanxu idan kai kasan baka ta6a min komai ba?" Yace "Like, kina min kallon kamar wanda ya cuceki a rayuwar da kika yi gidanmu, always frowning when ever u see me, and many of that" Da mamaki take kallonsa tace "To dama mun saba magana ne da kai balle kace Ina frowning? I've known you to be someone that don't bother about others, baka shiga harkan kowa, kowa ma baya shiga naka harkanka, to me yasa xaka yi tunanin xan dinga shiga harkan ka yanxu?" Shiru yyi yana kallonta, can yace "Kin fahimci haka nake yi ma kowa kenan" A takaice tace "Ba kowa ba, ai kana sake ma cousins dinka, ur sisters idan sun gaisheka kana amsawa, kana siya masu abubuwan da ya kamata...." Yace "Ke kuma fa?" Ta d'an kallesa tace "Do I need to tell you that" Yace "Bana maki abubuwan duk da kika lissafa kenan" ta buda hannu yace "You've said it" komawa yyi gefen gadon ya xauna yyi shiru, bayan minti uku tana kallonsa tace "Can I go" ya dago ya kalleta, a hankali yace "You can, one day you might understand all what happened during ur stay in our house" tace "Why not now?" Ya girgixa mata kai yace "One day" juyawa tayi ta nufi kofa har xata bude ta juyo tace "Sauran tambayar fa?" Ya girgixa mata kai yace "No need" fita tayi ta sake juyawa ta kallesa suka hada ido ta sauke nata idon ta kulle masa kofarsa ta koma parlor, Mumy sai kallonta take bayan ta fito, Yakumbo tace "Ya sha shayin kuwa?" Heedayah tace "Yana sha" Mumy tace "Toh kinga, tun daxu nake fama da shi ya ki sha, da ta kai masa ai gashi ya sha" Har kusan karfe biyar Khaleel bai yarda ya kunna wayarsa ba, yana ta kwance kan kujera sai juyi yake ya rasa me ke masa dadi, ga xuciyarsa yyi masa nauyi, sllh kadai ke tadasa daga kan kujeran yana dawowa masallaci kuma xai ci gaba da kwanciyarsa ko abinci bai ci ba throughout, bai ta6a tunanin Heedayah will be the first person to judge him ba, but ya mata uxuri coz she just have to, yana nan a haka har aka kira Magrib, ya mike xaune da kyar ya rike kansa, jin xa a tada sllh ya tashi ya shiga bandaki dake parlon ya dauro alwala ya fito ya wuce masallaci, ko da ya dawo makullin motarsa ya dauka yana tunanin yaje gidan Mami ko kar ya je, bai san yanda Heedayah xata kuma karbansa ba idan ya koma, amma ya ji bayan ita ma yana son ganin Mami ko xai d'an ji sauki, hira da ita na gusar masa da damuwarsa for sometime, mamakin Heedayah ya kasa barin ransa duk da uxurin da yyi mata, did he make a mistake telling her who he is? Gaba daya ya ma rasa takamaiman tunanin da xai yi ya ji sauki a xuciyarsa dake masa xafi sosai, ya jawo wayarsa a hankali ya kunna he need to share this with Zayyad, har yayi dialing number Zayyad ya tuna muryar Arne ya ji daxu maimakon Zayyad din, katsewa yyi xai kashe wayar gaba daya text ya shigo masa, number Zayyad ya gani, hakan yasa ya shiga text din yana duba content dinsa, mikewa yyi da sauri yana sake karanta message din xuciyarsa na bugawa, kunna datansa yyi kamar yanda aka umurcesa a text din ya hau WhatsApp bayan some minutes sai ga message din Oga Arne ya shigo ta WhatsApp din, ya bude yana xaro ido.... Video ya ga Arne ya turo masa, yana gama downloading video din ya ga Mami xaune kasa ta rungume Ashnaah dake ihu tana kiran Ammi, ya ji Muryar Arne yana cewa "Kina son sanin wanda ya bada umarnin dauke ki daga cikin iyalanki??" Mami dai bata ce komai ba hawaye kawai ke sauka idonta sosai, abubuwa da yawa ne ke dawo mata na shekaru masu yawa da suka wuce, rungume Ashnaah tayi sosai a jikinta tana Kuka, sai take ga kamar xa a kwace ta ynda aka ta6a yi mata, Arne yyi wani shegen dariya yace "Ki sa ma ranki salama, xaki ga wanda yasa aka dauko ki, sannan miliyan hamsin ake bukata na ransom" Mami ta girgixa kai tace "Ba mu da wnn kudin, bamu da dalilinsa, ku ji tsoron Allah ku ji tsoron gamuwar ku da shi...." Arne ya sake yin wani dariya sai kuma ya hade rai yace "Wa'axi xa ki mana, to kuwa xa mu aika ke da yarinyar barxahu yanxun nan...." Mami tace "Wnn sai lkcn mu yayi" Banda xufa bbu abinda Khaleel ke yi daga tsayen da yake yana kallon video din, exactly kalan tashin hankalin da ya shiga lkcn da Heedayah ta kwana gidansa da su oganninsa suka xo, Arne yyi video din fuskarsa dake lullebe cikin mask yana 6a66aka dariya yace "Sai ka xo Brainiac" Khaleel ya kalli time din da aka turo masa video din ya ga tun karfe biyun rana ne, bai san lkcn da ya suri makullin motarsa ba ya fice gidan almost running. Da karfi ya bude kofar parlon gidan da suke haduwa da oganninsa yana huci, Salim da Fago na xaune suna xuke xuke, Manga ya fito daga wani daki kamar an yi announcing masa presence din Khaleel, wani dariya duk suka saki a parlon kamar hadin baki, Arne ya fito daga wani dakin sannan Bala ko wannensu na ma Khaleel wani kallo yana murmushi, a nutse Manga yace "Welcome back after a year Brainiac...." Khaleel bai ce komai ba ya nufi sama don yasan a dakin sama Arne yyi video din Mami, Tsaye ya ga wani Ogan nasa a sama ya tare hanya da bindiga a hannunsa, Khaleel ya dakata xuciyarsa na bugawa, Arne yace "Ina kake tunanin xaka Brainiac? Snn me kake tunanin xaka yi?" Khaleel ya dawo gun Arne cikin tsawa yace "I've served you for many years, I've been loyal for many years, I need my freedom now, I need freedomm...." Naushi Arne ya kai masa a ciki ya fixgosa yana huci cikin tsawa sosai yace "Duk ranan da kake tunanin samun freedom daga garemu to mutuwa kayi Brainiac, we will be together till the end, you will continue serving us till the end, ko kana da wasu sama da mu a duniyar nan ynxu, nayi maka alkawarin a gabanka xan aika matar nan barxahu don hakan kadai xai sa kanka ya dawo dai dai kasan abinda kake yi...." Da karfi Arne ya tura sa ya nufi sama rike da bindigarsa yana huci, sanin halinsa da abinda xai iya aikatawa sarai yasa Khaleel ya taresa da sauri yace "Noo plss, bata da laifin komai Oga, ka gaya min yanxu me ku ke so daga gareni I promise to abide, don't harm her plss" Arne ya tsaya yana huci yace "Sharadi uku xan baka da xaka yi abiding to... Abiding to the rules kadai xai sa mu bar matar nan da ranta, wllh... Kaji har na rantse maka" Khaleel da xufa ke karyo masa daga sama har kasa ya dake yace "Ina jin ka...." Arne yace "Yanxu xa mu tafi gun ta a matsayin kai ne oganmu gaba daya a nan, I want it to look like kai ma kasa mu dauko maka ita, snn xa ka bukaci amsan ranson na miliyan 50 don naga da maiko sosai tare da ita, snn daren yau muna da operation na dauke wata yar babban mutum kai ne kuma xaka dauko ta mun fi wata hudu muna targeting mun kasa dauketa, sharadin karshe kuma baxaka sake gigin bijire umarnin mu ba, idan kuma sharadin sun maka tsauri cikin mintuna kalilan xan aika matar barxahu, snn in sa a dauko min 'yarta ma in kasheta, idan kuma ka kwafsa gaban matar wllh wllh a gabanka xan harbeta kaji har na rantse maka" Banda xufa bbu abinda Khaleel ke yi yana kallon Arne don ko wani kalma da ya fada hakan yake, baya xance biyu, snn ko dot din tausayi baya da shi a ransa, he can even do more than what he said.... Arne ya ciro masa bindigar aljihunsa ya mika masa yana kallonsa da jajayen idanuwansa yace "Mu tafi saman" Khaleel ya lumshe ido ya bude snn ya amsa bindigar a sanyaye ya shiga gaba Arne na biye da shi da nasa bindigar bayan ya rufe fuskarsa da Mask, Fago ne ya bude masu kofar dakin da Mami ke ciki da Ashnaah, Khaleel dake tsaye bakin kofar ya kallesa sannan ya shiga dakin, daga kai Mami tayi suka yi ido hudu da shi ta dinga kallonsa with so much shock ko kiftawa bata yi, Tunda Khaleel yake bai ta6a jin weakness irin na wnn lkcn ba, he felt like collapsing kawai, he wish this isn't happening, Arne dai sai kallonsa yake da mayun idanuwansa yana pointing Mami da bindiga alamar yana kwafasawa xai yi harbi, Cikin rawar murya Mami tace "Khaleel???" Kallonta kawai Khaleel keyi ya kasa cewa komai, Arne na nunata da bindiga cikin tsawa yace "Kar ki sake kiran oganmu kai tsaye...." Khaleel ya jefa mata wayarsa ba tare da ya yrda sun sake hada ido ba yace "Ki saka number da xa a kira a bada kudin fansa" Kuka kawai Mami take sosai ta ma rasa abinda xata ce gaba daya ta shiga wani irin shock ne me iya ba mutum attack, kasa ci gaba da tsayuwa a dakin Khaleel yyi ya juya yace "A kawo min number idan ta saka" daga haka ya fita daga dakin, Arne yyi wani murmushi ta cikin mask dinsa, yyi ma Mami wani firgitattcen tsawa yana nuna ma Ashnaah dake bacci a hannunta bindigarsa yace "Baxa ki sa number ba sai na harbe wnn yarinyar dake kafarki" Jin abinda yace kuma bbu alamar joke tare da shi Mami ta dau wayar ta shiga dialing number Junaid tana kuka sosai, ya kwace wayar a hannunta snn ya fice daga dakin Fago ya kulle kofar da makulli ta waje. That same time Abba da Doctor da Baffan Junaid na tsaye parlon Mami ko wannensu is just short of words, gaba daya kukan kaka ya cika ma kowa kunne a parlon, Farida da Heedayah ma kukan suke cikin tashin hankali kamar ransu xai fita, Yakumbo dai banda xare ido bbu abinda take daga wajen da take xaune, ta kalli wnn ta kalli wancan kamar mara gaskiya, Junaid dai na tsaye ya jingina da bango a parlon yana kallon sama, duk dakiyarsa tashin hankalin dake tare da shi bai boyu ba, Ammi kam na xaune parlon bata cewa komai sai tagumi da tayi, Hajiya Zuwaira da kanwarta na gefen Ammi su ma, kowa dai ka gani a parlon hankalinsa a tashe yake sosai, cikin kuka kaka tace "Toh kai da ka hango motarta ta window me yasa baka fito da sauri ba Amadu, ko ofishin naku bashi da taga ne da ka yrda wnn abu ya faru? Kai ma fa sai Allah ya kamaka wllh" Abba dai bai bata amsa ba kansa na kasa, Kaka ta kara rushewa da wani kukan tace "Yau naga abinda ya isheni ni Patuu, gandareriyar mata haka ace mana an dauke ta a mota, ni dai wllh ban yarda ba baxan kuma yrda da wnn karyar ba, ta ya xata amince ta bisu kamar wata shashasha" a hankali Yakumbo tace "Kun dai tabbatar kun duba motar da kyau bbu Ashnaah" ita ma bbu wanda ya tanka ta a parlon, lkci daya ta rushe da matsanancin kuka ita ma tace "Bbu yanda Ashnaah bata yi xata bi ni gidan dubiya ba nace baxan je da ita ba, yau ga inda son gantalinta ya kai ta, ita yar uwar bbu ruwanta da biye biyen mutane wllh" Mumy ce ta shigo parlon da sallama a rikice bayan many interrogations tun farkon shigowarta layin domin kuwa tun daga farko har karshen layin sojoji ne da yan sanda har cikin compound din Mami, Mumy ta fashe da kuka sosai sai dai ba hawaye ta shigo parlon ta xauna ta saki salati tace "Ikon Allah ya fi da haka, ynxu abinda ya faru kenan ni Maryam, to Allah ya kubutar da Rahinah daga hannunsu alfarman annabi, Allah ka dubemu a sako ta cikin aminci, wnn duniya Ina xa ya da mu..." Yakumbo tace "Ae har da Ashnaah...." Wayar Junaid dake hannunsa ne ya fara ring duk aka juya ana kallonsa a parlon, Junaid na kallon Screen din wayar ganin bakon number ne ya daga ya sa handsfree, bbu ko sallama aka fara magana kamar haka "Anyi garkuwa da Mahaifiyarku ana kuma bukatar ransom na miliyan hamsin daga yanxu xuwa gobe da karfe sha biyu dot.... failure to comply xa ku tadda gawarta nan bakin layinku gobe da yamma, ur Mother's life or 50 million, more details to be pass to you later...." Kasa motsi Junaid yyi inda yake tsaye yana sauraron mutumin, kaka ta mike da sauri ta nufo Junaid cikin daga murya tana nuna wayar tace "Allah ya tsine maka, Allah yyi daidai da kai, don uwarka ajiya ka bamu.... shege kawai haihuwar rage jini haihuwar asara, ubanka ne ya bamu miliyan hamsin din ko uwarka, to wllh jikana soja ne sai yyi gunduwa gunduwa da rubabben namanka an jefa ma kifaye a ruwa, d'an Iska kawai munafuki....." Yakumbo na tuntube ta taso ita ma tana kunduma nata xagin tana cewa "Idan ka isa ka xo ni ka daukeni d'an kaza kazan ka, dangin uwa ko na uba xa mu baka miliyan hamsin, ko wiwi ka narka kafin ka kira..." Abba ya nufosu da sauri yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, meye haka ku ke yi fisabilillahi" Yakumbo tace "Allah ya tsine masu muka ce, me xasu mana da Allah bai mana ba, idan sun isa su fadi inda suke yanxun nan in tafi in samesu mana, mutane matsiyata marasu tsoron Allah kawai" Barin wajen junaid yyi don ba ta su yake ba maganganun wanda ya kirasa ne ke dawo masa, don takaici Abba bai sake tanka su ba suka fita parlon tare da Dr da Baffan junaid don sanar ma yan sanda kidnappers din sun kira, Heedayah dai tun bayan da taji abinda aka ce ma Junaid a waya ta kasa kwakkwaran motsi inda take xaune, tunani iri iri ne ke kai komo a xuciyarta, A hankali ta juya ta kalli Farida, lkci daya ta tashi da sauri ta wuce sama xuciyarta na bugawa tana shiga daki ta kulle kofa a hankali tace "Khaleel???" Wani ihu ta fasa da ya ja attention din mutanen dake parlor.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... *What is _funnying_ me is the way free readers are taking this book for head like gala, sun fi kowa xakewa fahh, ku ji da hakkin dari uku mana banda abin ku* 🤔 Kuka kawai Heedayah take ta kasa cewa komai duk da hayaniyar da kaka da Yakumbo ke mata suna tsaye a kanta, Farida dai na rakube gefe banda kuka bbu abinda take, DCP dake tsaye kusa da Baffan Junaid ya kwantar da murya yana kallon Heedayah yace "Xa ki gane gidan nasa na Abuja yanxu?" Heedayah ta girgixa masa kai kawai, yace "Da yaushe ya gaya maki su suka ta6a dauke ki?" Heedayah ta harari Farida amma taki cewa komai, DCP yace "Talk to me young lady, da yaushe ku ka yi xancen da shi?" K'in cewa komai Heedayah tayi still, Ammi ta sauke mata wani mari a fusace tace "Baxa ki bude baki kiyi ma mutane magana ba" Heedayah ta rufe fuskarta tana kuka sosai tace "Ni ba shi ne ya daukeni ba fahh" Mumy dake tsaye ita ma parlon tace "Haba Hajiya ai bin ta xa ayi a hankali, duka ba shine mafita ba a yanxu, idan aka lallabata duk sai ta buda mana abubuwan da Faridar ta fada yanxu" Abba na kallon Heedayah yace "Tashi xaune" Mikewa xaune tayi a hankali hawaye na sakkowa idonta, yace "Da yaushe ku ka yi magana da shi yace maki shi ya dauke ki years back" A hankali ta girgixa masa kai tace "Ni ba shine ya daukeni ba Abba" DCP yace "To wa ya dauke ki" Cikin rawar murya tace "Wasu mutane ne ba shi ba" Ya daure fuska yace "Amma yar uwarki ta ce kince mata shi ne ya ajiye ki gefen hanya bayan ya daukeki daga wajensu" Heedayah ta girgixa kai tace "She's not saying the truth, ni ba haka nace mata ba" cikin kuka Farida tace "Karya take sir, ce min tayi yace mata shi kidnaper ne" Heedayah ta jefa mata wani kallo tace "He is not!!! Ni bance maki haka ba" DCP ya xauna yana facing dinta da kyau yace "You are not saying the truth young lady, baki son a ceto Mum din ki ne??" Heedayah ta fashe da kuka sosai gaba daya she look confused, Farida tace "Sir she's lying, ya sanar mata shi kidnaper ne, da bakinta ta fada min haka wllh" Kuka sosai Farida take, Heedayah dai hawaye sai sakko mata yake taki cewa komai, DCP yace "Xaki xama suspect dinmu kenan, and we have no choice then to go with u to the station...." Abba yayi kasa da murya yace "She's only confused sir, a bata sometimes xata yi magana idan Allah ya yrda" Junaid dake xaune ya sauke ajiyar xuciya yace "Lkcn da aka kwantar da shi a asibitin Abuja, the phone call his frnd is always making is highly suspicious, bbu gaskiya a kiraye kirayen sa, and idan yyi noticing dina a waje baya sakewa yyi magana, tun a lkcn na fara xarginsa amma ban kawo wani abu a kan shi Khaleel din ba" Baffansa yace "Abokin barawo ai barawo ne" Junaid yace "Ban yi tunanin Mami xata sake da shi Khaleel din har nan Kaduna ba, I once told her wnn mutumin stranger ne bai kamata tana jawosa jiki haka ba tunda ba saninsa tayi ba, she don't know him but Mami didn't listen to me, Dinar ma tayi mata magana bata saurareta ba..." Kaka na Shessheka tace "Mu dai daga ita har Heedayar sun kai mu sun baro mu muna xaman xamanmu ana shirye shiryen tafiya Gwamnet house, yanxu gidan ubanwa xa a samo wani shegen dubu miliyan hamsin idan ba Heedayar xa a kai kasuwa ba, ko ubanta dake da mukamin gwamna ynxu bashi da dubu miliyan hamsin balle mu karere, ni ban ta6a ganin yaron ba da sai na gane barawo ne tun kan aje ko ina wllh" Cikin rawar murya Heedayah tace "Ba barawo bane" wani Marin Ammi ta kara sauke mata, Abba yace "Subhanallah kar ki sake Hajiya" DCP da Baffan Junaid ma duk suka yi ma Ammi magana, Yakumbo ta fashe da kuka tace "Idan nayi magana sai a dinga min kallon me ta6in hankali, ranan farko da na fara ganin mutumin nan sai da nace ban yarda da shi ba yyi kalan yan satan mutane, amma bbu wanda ya dau maganata da muhimmanci, to yau ga dai abinda na fada ya fito, yanxu ya xa muyi fisabilillahi ga yar yarinya ko abinci nasan bata ci ba har ynxu, wani kai rahotu gidan radio da talabijin da gidan yan sanda duk ba shi bane wllh, fatana su fito cikin aminci, Ashnaah bata minti ashirin bata sha yagwat ba, to uban wa xai bata a can, Amadi daga komawarsa kujeransa yau sai yaji wnn mummunan labari mai cike da tashin hankali, don ma gwamnan kaduna bai bar maganar a haka ba shi ma yana bakin kokarinsa, ai wllh kashin yan kinnafas din nan ya bushe, xa su san har da 'yar gwamna suka dauke, don nasan da sun san yar gwamna ce Ashnaah baxa suyi gigin ta6a ta ba, dama an hada da Heedayar an tafi wllh da hankalina bai tashi haka ba tunda ita sun saba dauketa dama, ynxu banda xuciyar musulunci kina tunanin Junaidu xai yarda ya aureki bayan kwamushe uwarsa da aka yi ta dalilin ki, don ubanki gwamna ne ai ba ke bace gwamnan da xaki ja ma mata fitina tana xaman xaman ta..." Mumy sai da taji gabanta yace rasss jin abinda Yakumbo tace kan Junaid sai ya fasa auren Heedayah, Ammi dai ko kallon Yakumbo bata yi ba, Abba na rike da wayar Junaid yana ta kiran layin da aka kira da shi amma a kashe, Dr ya sauke ajiyar xuciya yace "Xa su kira Barrister, we have to calm down" Oga Arne na xaune parlor kan kujerarsa ya gama zuke zukensa Salim ya mika masa wayar da aka yi amfani da shi wajen kiran Junaid daxu, canxa layi yyi ya kunna wayar ya sake dialing Number Junaid, yana fara ringing Abba ya daga daya bangaren ganin bakon layi, Arne yace "Na kira in sanar maku inda xa ku kai mana kudin ku ajiye...." Abba yace "Yallabai ba mu da miliyan hamsin ynxu haka, ku fadi abinda xa mu iya baku domin Allah" Arne yace "Motar hawanta kadai ma xai yi miliyan 12, kada ku raina mana hankali, da alamar kun gaji da rayuwarta a doron kasa, xuwa karfe sha biyu gobe sae dai a dinga wani labarin ba wnn ba" Abba yace "Ka saurareni" katse wayar Arne yyi ya kashe gaba daya ya jefa ma Salim, Khaleel dake tsaye for almost an hour jikin pillar din dinning area din parlon ya rasa me ke masa ddi ya daga jajayen idanuwansa yana kallon Arne, wani dariya Arne yyi, Khaleel ya karaso cikin parlon yana dubansa sosai yace "A janye maganar kudin fansar ni xan baku...." Arne yace "Kana da wani alaka da ita ne da xaka bada kudin fansan?" Khaleel yace "Xan bada saboda a ta dalilina ku ka dauketa, snn they can't afford that amount" Arne ya mike yace "Naga alama after all this baxa ka rabu da mutanen nan ba, I think the best thing is just to send her to her early grave snn mu bi duk wani nata mu kashe, hakan kadai xai sa hankalin ka ya dawo jikin ka, amsan kudin fansa da 6ata maka suna a wajensu duk ba shi bane, xaka iya yin komai don ganin ka koma garesu, I mean xaka yi brain washing dinsu su kuma su kara amsar ka, kasheta shine kadai mafita a yanxu....." Khaleel da xuciyarsa yyi masa nauyi ya duka nan kasa da kyar yace "Kada ka kasheta Oga, don't forget she is a barrister idan nace xan koma gun daughter dinta xata yi exposing dina a idon duniya, xata tona min asiri, Kar ka manta bbu uwa ta gari da xata so tarayyar 'yar ta da hoodlum, ni kuma hoodlum ne, don haka kun riga da kun rabani da su don't go further then this plss, kar ku kasheta...." Arne dake ta sauraronsa yace "Toh idan ka kuskura ka sake cewa xaka bada kudin fansa sai na aika wnn yar yarinyar dake tare da ita lahira" Khaleel ya sauke kansa kasa hawaye na sauka idonsa bai ce komai ba, Arne ya koma ya xauna yana huci, Khaleel ya daga kai bayan few seconds yana kallonsa da kyar yace "To a taimaka a basu wani abun su ci ko su sha...." Arne ya mike yana masa wani kallo yace "You cannot break our rule all of a sudden Brainiac...." Mikewa Khaleel yyi a hankali ya koma inda yake tsaye ya jingina da pillar din ya runtse idonsa. Karfe sha biyu na dare Arne ya sake kiran Abba, nan Abba ya nemi alfarman su bar kudin miliyan talatin, da kyar da kyar Arne ya amince bayan cin mutunci iri iri a waya snn ya bukaci Motorcycle guda biyu sababbi dal a hada da kudin, nan ya sanar masu inda xa su tafi su ajiye masu kudin da safe. Washegari da sassafe Junaid ya tafi tare da Abba da Baffansa sai DCP a cikin motar Abba kai kudin inda Arne yace su kai a wani kauye cikin garin kano, wata motar kaya ce a bayansu dauke da Motorcycle guda biyu, a cikin motar motorcycle din kuma Yan sanda ne gudu hudu duk sanye da mofti, banda motar dake bayan motar Motorcycle din dake cike da sojoji, wayar Junaid dake hannun Abba ne ya fara ring ganin sabon Number ya daga ya sa handsfree, muryar Manga ne ya cika motar yace "Kai ku koma da kudin ku, snn karfe hudu na yamma ku duba can karshen layin gidanku xa mu ajiye maku gawarsu a can, sbda raini xaku kawo kudi sai kun yi xuga har da motoci uku, mu xa ayi ma wasa da hankali, mu xa a raina ma wayo, to wllh wllh kasheta xa mu yi idan mutum daya baxai taho da kudin ba" DCP sai kalle kallen hanya yake don ko Zaria basu karasa ba kuma motoci dai dai ne a hanyar ke tafiya, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujeran motar hankalinsa a tashe, Parking Abba ya samu gefe yyi sauran motocin bayansa ma duk suka tsaya ganin haka, DCP yace "Mu je kawai Barrister kyale yan Iska suna biye da mu ne...." Baffan Junaid yace "Aa kamar dai yanda yace Sbda lafiyar Rahinah da yarinyar wajenta mutum daya kawai ya kai kudin yallabai, further investigations should follow forth, yanxu dai the life of Rahinah and the little girl matters first, ba imani ne da su ba xa su iya aikata abinda suke fada" Abba yace "Haka ne, ni xan tafi in kai masu kudin, kamar yanda Alhaji Imran ya fada further investigation should follow forth, their lives first" Junaid yace "Let me go instead Abba, ni xan kai masu kudin" DCP yace "Junaid ya tafi, and you have to be very very vigilant and careful junaid" Junaid yace "In sha Allah" Abba ya bude motar ya sauka sauran ma duk suka sauka, motar da Babur din ke ciki duk suka nufa, bayan an yi ma drivern motar bayani ya sauka Junaid ya shiga, Abba ya mika masa wayarsa yace "Be careful Junaid, and kayi ta addu'a, Allah ya tsare" Junaid ya amshi wayar ya ajiye gefensa yace "Ameen Abba" snn ya tada motar ya ci gaba da tafiya xuwa garin kano. Dai dai wani matattacen gidan mai na Bulasawa🙄 da aka yi abandoning baya aiki suka sa Junaid ya ajiye masu kudin ya sauke duk mashinan, wayarsa ne ya fara ring ya fiddo ya daga, "Malam ka gama aikinka, maxa ka bar wajen nan da mintuna biyu kacal" Junaid yace "Toh Mahaifiyar tawa fa?" Aka ce "Xata riga ka isa gida ma" Daga haka aka katse wayar, shiga motar junaid yyi ya tada ya bar wajen cikin few seconds. Sai bayan awa kusan hudu Junaid ya isa Kaduna sbda motar da yake driving, 2 hours ago Abba ya kirasa ya sanar masa Mami and Ashnaah are home, Hamdala Junaid yyi lkci daya hankalinsa ya kwanta sosai, tun da ya iso anguwar tasu yake ganin motocin sojoji har ya isa layinsu, sai da aka yi interrogating dinsa snn ya shiga layin yyi parking kofar gida ya gaida sojojin snn ya shiga gidan, Duk su Abba na parlon ya shiga, Sai bayan awa kusan hudu Junaid ya isa Kaduna sbda motar da yake ja, 2 hours ago Abba ya kirasa ya sanar masa Mami and Ashnaah are home, Hamdala Junaid yyi lkci daya hankalinsa ya kwanta sosai, tun da ya iso anguwar tasu yake ganin motocin sojoji har ya isa layinsu, sai da aka yi interrogating dinsa snn ya shiga layin yyi parking kofar gida ya gaida sojojin snn ya shiga gidan, Duk su Abba na parlon ya shiga, Kaka na ganinsa da karfi tace "Alhamdulillahi, na shiga bandaki yyi sau ashirin sbda tunanin ka Junaidu" Shi dai gaba daya hankalinsa na kan ya ga Maminsa, gaba daya occupant din parlon look very happy seeing him, kaka tace "To a xubo masa abinci ya ci ya koshi dai tukun" Yyi kasa da murya yana kallonta yace "Mami da Babyn fa" Kaka tace "Tana can sama tana bacci, har yanxu dai a tsorace take baiwar Allah, manya manyan likitoci gwamnan kaduna ya turo su dubata, ita kuma yarinyar tana can ana mata karin ruwa ta galabaita da yunwa, fitinanniyar matar can na kanta da uwarta" Sama Junaid ya nufa sai da ya fara shiga dakin da Ammin Heedayah ke ciki snn ya fito bayan minti sha biyar ya shiga dakin Mami, bacci ya sameta tana yi ya karasa ciki ya xauna gefenta yana kallonta..... *I lost a sister in my payment group today, she paid for Heedayah sbda hakki, sai gashi ba a gama littafin da ita ba ta rasu, Allah Ubangiji ya gafarta mata ya kyautata makwancinta, ya sa mu cika da imani duniya bbu tabbas, I had to gather courage and type this chappy don mutuwarta ya ta6a ni wllh* 😒 Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mami na xaune parlor bayan Magrib da hijab din da tayi sllh har kasa da carbi a hannunta, gaisawa suka yi da DCP dake parlon shi ma wnda sbda shi ta sakko downstairs, Abba na xaune parlon kusa da DCP shi ma, kaka da Yakumbo na xaune daga gefe daya su ma ko wannensu na kallonta, sai Ammi dake rungume da Ashnaah dake bacci, matar Baffan Junaid na rike da Ashfah, sai wata colleague din Mami a kusa da ita, Heedayah dai na bayan kujera ta ki yarda ta hada ido da kowa tun dawowar Mami, Junaid na tsaye yana kallon Mami da gaba daya tayi sanyi, DCP yace "Hajiya xaki iya gane gidan da aka kai ki jiya?" Mami ta girgixa kai tace "Aa" DCP yace "Tun farkon fara tafiyar taku baki lura da anguwar da ku ka shiga ba ko wajejen da ku ka bi??" Mami tace "Duk ban lura da hakan ba don hankalina baya jikina a lkcn" Shiru yyi na wasu sakwanni sannan yace "Toh su nawa ne Kidnappers din?" Tace "Ban kirga su ba amma suna da yawa" Yace "A cikinsu akwai wanda kika sani?" Mami bata ce komai ba, kowa na parlon kallonta yake, DCP yace "Feel free to talk to me Madam, akwai idon sani a cikinsu?" Ganin Mami tayi shiru, Kaka tace "Yau naga bala'i ana tambayar ki abun arxiki kin yi shiru" firgit Mami ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula tunda DCP ya jefo mata tambayar, DCP yace "Kada ki damu Hajiya bbu wani abun da xai sameki you are safe, ki gaya min a cikinsu akwai wanda kika sani?" Mami ta girgixa kai a hankali tace "Babu" Idanuwa aka xuba mata a parlon barin junaid, DCP yace "Kina nufin bbu wanda kika sani ko kika ta6a gani a cikinsu?" Ta gyada masa kai tace "Duk ban san su ba" Yakumbo tace "Ya xa ki ce baki san su ba, nan nan Farida tace wnn rusheshen mutumin dake xuwa gidan nan wajen Heedayah d'an kinnafa ne, kuma Heedayar ce ta sanar mata hakan, hatta Junaid ya shaida hakan shi ma, to wa xai dauke ki idan ba Mutumin ba? Wllh shi ne, idan ma tsoro kike ji ga dai jami'an tsaro duk an watsa a anguwar nan, lungu da sako" Mami ta kalli Junaid dake ta kallonta tace "A ina ka shaida hakan??" Junaid ya kasa cewa komai, can ya girgixa mata kai yace "Aa I was talking of his frnd" Mami tace "To babu wanda na sani cikinsu" Kaka tace "Toh ai dama mutumin baxai yarda ki gansa ba, hauka yake xai bari ki san har da shi cikin kinnafas din, mu dai ba ya cucemu ya raba bayin Allah da basu ji ba basu gani ba da miliyoyin kudinsu, daga karshe ma sai ni na cika kudin wllh, Allah dai ya isa, tunda kuma abu ya xama haka ayi maza gaskiya a sa ma Deedayah rana da Junaidu kowa ya huta don duk dalilinta wnn tashin hankali da asaran ya faru, Kuma wllh a yanda Farida ta nuna Mutumin sonta yake yi.... Kuma tun da yana shigowa gidan yana ganin baja baja ai dole yyi cuta" DCP yace "You need rest Madam, ki tafi sama gobe sai ku taho station da Barrister" Kamar Mami jira take ta mike tace "Nagode yallabai, sai da safe" Tana kallon Abba tayi masa sai da safe shi ma sannan tayi hanyar stairs, ido hudu suka yi da Heedayah dake bayan kujera har snn, Heedayah ta sauke kanta kasa, Mami ta wuce sama. Bayan kwana biyu da faruwan lamarin Ammi suka koma Kano tare da Kaka da Yakumbo, bbu wanda yace Heedayah ta bi su, Yakumbo ma cewa tayi ita ba ruwanta su tafi da ita a sake biyowa a kwashesu gaba daya, kana ganin Heedayah kasan tana cikin damuwa sosai, gaba daya ta rame, bata da aiki sai xaman bayan compound, ko abincin kirki bata ci, har lkcn taki yrda xaman waje daya ya hadata da Mami, iyakarta da ita gaisuwa, duk da Mamin ma tana bedroom dinta always ko fitowa parlor bata yi, har snn kuma a sanyaye Mami take, Bayan tafiyarsu Ammi Farida na parlor tana danne danne a system dinta aka yi knocking kofar parlon, ganin mai aikinsu na dakinta yasa ta mike ta isa kofar ta bude, Shuraim ne tsaye bakin kofar, tun faruwan incident din sai ranan ya xo, he look pale, kana ganin sa kasan he just recovered, ta basa hanya tace "Good evening" ya shiga parlon yace "How are you?" Tace "I'm fine" yace "Mami fa?" Tace "She's sleeping, ta sha magani ne" yace "Ohk" xaunawa yayi saman kujera, ta tafi gun system dinta ta xauna ta ci gaba da abinda take, lkci lkci take kallonsa ta gefen ido, bayan few minutes ya juyo suka hada ido, dauke idonsa yyi yace "Heedayah fa?" Tace "She's outside" Yace "What is she doing outside?" Tace "I don't know" Bayan few minutes yace "Outside where?" Tace "Ta backyard" Mikewa yayi ya fita daga parlon, can bayan gidan ya sameta xaune a karamin garden din tana xane da karamin iccen hannunta a kasan dake shimfide wajen, jin taku ta juya da sauri, suna hada ido ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, ganin bata ga ya karaso ba ta d'an saci kallon hanyar taga ba kowa, juyawa tayi tana kallon wajen, can ta ci gaba da xanen da take a kasa, Farida na ganin Shuraim ya dawo parlon yyi xamansa ta mike ta wuce kitchen, ruwa ta kawo masa a tray ta ajiye nan gabansa, ta koma gun system dinta, yace "Thank you" Ba tare da ta kallesa ba tace "You are wlcm" Xuba ruwan yyi a glass cup ya sha ya ajiye snn yace "Wani course kike yi a schl" Ita dai idonta na kan system sai taji kamar ba da ita yake ba, can ta juya ganin kallonta yake tace "Biochemistry" Ya d'an buda ido yace "Why biochemistry?" Tace "Kawai" Yace "Xa ki iya kuwa?" Ta kallesa ta d'an yi murmushi tace "Gashi ina yi" Ya daga kafada yace "Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen" Bude kofar parlon aka yi, Heedayah ta shigo, ba tare da ta kallesa ba ta wucesa snn ta gaishesa ta haura sama. Da daddare Heedayah ta fito daga wanka Mami ta shigo dakin, tunda Heedayah ta kalleta sau daya ta kasa ci gaba da kallonta, Mami ta xauna gefen gadon tana kallon Farida tace "Excuse us dear" Mikewa Heedayah tayi ta fita, Mami na kallon Heedayah ta nuna mata gefen gado, a sanyaye Heedayah ta karaso ta xauna gefen gadon tana kallon Mami, lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin rawar murya tace "I am sorry Mami I caused you everything, I don't know......" Sai kuma ta fashe da kuka sosai ta rufe fuskarta da gadon, Mami ta dagota tace "You caused me nothing, now tell me, me da me Khaleel ya gaya maki a kansa" Hawaye na sauka idon Heedayah tace "Ce min yyi shi ya fito da ni daga wajen Kidnappers" Mami tace "So he told you he is also a Kidnapper" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa he wasn't straight, but I suspect that" Mami tayi shirun Wani lkci snn ta sauke ajiyar xuciya cikin sanyin murya tace "Khaleel Kidnapper ne Heedayah, he is a hoodlum with large gang, but this should be between just I and you, kada ki fada ma kowa koda Farida kuwa" Heedayah ta fashe da sabon kuka tace "Mami shi ya dauke ku ko? Shine yyi kidnapping din ku ko?" Mami dake kokarin ganin hawaye bai kawo idonta ba tace "Shi yasa aka dauke mu Heedayah, Shuraim ya ta6a gaya min he don't trust him not even for a second, haka ma Junaid amma duk ban dau xancen su da muhimmanci ba, sai gashi, Khaleel is beyond ur thought dear, he is thug..." Heedayah ta fada jikin Mami tana kuka sosai tace "I am happy he didn't hurt you Mami, ni na jawo maku kiyi hakuri ki yafe min, I don't know why I trusted him all of a sudden" Mami ta goge hawayen da ya sakko nata idon a hankali tace "I don't think we are safe together anymore a gidan nan Heedayah, nayi ma Amminki magana xaki koma can kano cikin satin nan, don bana son wani abu ya sameki, Kar ya ci gaba da bibiyarki ya cuce ki..." cikin rawar murya Heedayah tace "Mami mu tafi kanon gaba daya plss, kema u are not safe anymore" Mami tace "Aa... am going no where dear, ke kam xaki koma wajen Amminki, I don't want you to be here" Heedayah ta shiga goge idonta bata dai ce komai ba, Mami tace "And ki fada min gaskiya do you have any feeling for Junaid, bana son a shiga hakkin ki, don matsayinki daya da junaid a wajena" Heedayah ta dago da sauri tana kallon Mami, Mami tace "Yes, tell me" Sauke idonta tayi ta kasa cewa komai, mamaki ya cikata, Mami tace "Kar ki ji komai ki gaya min gaskiya" Heedayah dai ta ma rasa abinda xata ce, Mami tace "Sbda incident din nan da ya faru Yakumbon ki tace xa ayi maki aure kada ya ci gaba da bibiyanki, I think ana komawa xa ayi magana, so tell me ur mind now...." Jin Heedayah ta ki cewa komai still, Mami ta kamo hannunta tace "Toh ki gaya ma Farida gobe ta gaya min kin ji??" Heedayah dai sai kallonta take ko kiftawa bbu, Mami ta mike tace "Good night dear" daga haka ta fita dakin ta kullo kofar, Heedayah ta fashe da wani kuka tana imagining wai Junaid, da wani idon ma xata iya cewa Mami bata son Junaid, she just can't, kuka take sosai sai dai ba xancen Mami na karshe ne ke sata kuka ba, taji xuciyarta yyi mata xafi she wish this is a dream na cewa Khaleel Kidnapper ne..... Khaleel ya sauka kan napep ya ba mai napep din kudinsa snn ya karasa layin walking calmly, karfe takwas da yan mintuna ne na dare, sojoji ne bakin layin a xaune, ga motarsu daga gefe a tsaye, ya fiddo ID card dinsa ya nuna masu snn ya shiga layin a hankali yake tafiya har ya isa bakin gate din gidan, sojoji ne tsaye a gate din, suka tambayesa wa yake nema, yana kallonsu yace "My aunt..." yana fadin haka ya ciro iD dinsa ya nuna masu su ma, daya sojan ya bude gate din Mai gadi ya taso da sauri, Khaleel ya dake yana kallon Mai gadin dake kallonsa shi ma yace "Wa kake nema?" A nutse yace "Mami" Bai jira cewar Mai gadin ba ya shiga ciki yana maida ID dinsa aljihu, dai dai nan aka bude kofar main parlor, Shuraim ya fito tare da Junaid, lkci daya Khaleel ya juya ya fiddo wayarsa ya nufi parking space ya kara wayar a kunne kamar me receiving din call yana tsaye parking space din, Shuraim ya karaso compound din tare da junaid yana kallon Khaleel da ya juya masu baya wayarsa a kunnensa har lkcn, ya kalli sojojin dake tsaye bakin gate snn ya sake kallon parking space din, ta madubi Khaleel ya ga Shuraim ya nufo sa..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Juyowa Khaleel yyi ya mika masa hannu yana kallonsa, Shuraim ya ki amsa fuskarsa daure yace "Why are you here? And who are you?" Khaleel bai ce masa komai ba ya mika ma junaid da ke tsaye shi ma hannu, Junaid yayi jim ya ki mika masa nasa, sai kuma ya mika masa dai, Khaleel yace "Na xo wajen Mami ne" Junaid ya girgixa masa kai yace "Bata nan, she is in Abuja" Khaleel yace "Mai gadi yace min tana ciki" Shuraim ya cakumo kwalar rigarsa yana masa wani kallo yace "Karya yyi maka kenan??" Kallonsa kawai Khaleel yake ko kiftawa babu, Shuraim ya turasa da karfi har sai da ya isa bango, snn ya juya ya tafi waje gun sojoji fuskarsa a murtuke xai yi instructing dinsu su shigo su fitar da Khaleel din, Khaleel ya kalli Junaid dake ta kallonsa snn ya xaga ta parking space din ya nufi entrance din shiga parlon walking so fast, bude kofar parlon yyi ya shiga ya sa makulli ganin Sojojin sun biyosa a guje, Heedayah ta fito daga kitchen kenan da plate din 'yar shinkafa da ta debo bisa umarnin Mami, wani firgitattcen ihu ta saki bayan sun yi ido hudu da shi, ta saki plate din hannunta jikinta na rawa ta dinga kurma ihun tana xaro ido, tsaye yyi bakin kofar yana kallonta, a guje ta koma kitchen din ta sa makulli hakan kuma bai sa ta fasa ihun da take ba, Farida na sakkowa stairs jin ihun da Heedayah ke yi suka yi ido hudu da shi ita ma, xaro ido tayi ta kwala ihun ita ma a tsorace ta koma sama a guje tana kwalo ma Mami kira, Mami ta fito bedroom dinta kenan jin ihun, suka ci karo da Farida bakin kofa, a rikice Mami ke kallonta tace "Me ya faru?? Ihun uban meye haka ku ke yi?" Farida na mayar da numfashi ta fashe da kuka sosai ta riko hannun Mami tace "Mami shi ne...." Mami tace "Shi wa?" Da kyar tace "Khaleel, gashi can a parlor wllh" Still Mami tayi tana kallonta don ita ma sai da gabanta ya fadi ba kadan ba, Farida ta kara rushewa da kuka tace "Mami wllh he is downstairs ya shigo mana parlor, su Yaya kuma sun fita" Da kyar Mami tace "Where is Heedayah?" Farida na nuna mata kasa cikin rawar murya tace "Taje debo abinci a kitchen, I heard her shouting shi ne na sauka, and I saw him at the parlor...." Mami ta xaro ido bata san lkcn da ta nufi downstairs din da sauri ba Farida na rikota a rikice tana cewa kar ta je, Mami ta warce Hijab dinta ta wuce, har sannan Khaleel na tsaye bakin kofar parlon da ake ta bubbugawa da karfi kamar xa a balla, Mami na sakkowa parlon ta kasa karasawa ciki tana tsaye daga bakin stairs din gabanta na faduwa tayi gathering courage tana kallon Khaleel dake kallonta tace "Me kake bukata daga garemu kuma bawan Allah?" Shiru yyi bai ce komai ba har sannan yana kallonta, hawaye ne ya shiga sakko mata tace "Me ya kawo gidana bawan Allah? Baka tsoron Allah ne? Me kuma kake so a wajena" Khaleel ya sauke idonsa da ya kada sosai, lkci daya ya nufeta, sosai xuciyarta ya shiga bugawa ta fara matsawa daga wajen tana kallonsa a tsorace, har lkcn Heedayah bata daina ihun da take tana kwalo ma Junaid kira ya xo ya taimake su ba, Haka ma Farida dake sama tana nata ihun, Khaleel na isa gaban Mami ya duka with both kneels a kasa yana kallonta a sanyaye yace "Ki gafarceni Ummi, it wasn't intentional I was blackmailed, i was forced and threatened to do what I did, ba yin kai na bane wllh, ko da ina yin hakan baxan maki ba Ummi..." Hawaye ne ya kawo idonsa ya kasa kallon Mami, Mami dai sai kallonsa take har sannan gabanta bai daina bugawa ba, tace "Kana ma yi kenan?" Ya daga kansa yana kallonta cikin sanyin murya yace "Ina yi" Xaro ido Mami tayi tana kallonsa, hawaye ya shiga kai komo a idonta tana girgixa kai tace "Kana nufin kai Kidnapper din ne dai??" Ya gyada mata kai trying hard not to allow the tears in his eyes to flow, a sanyaye Mami tace "Why did u choose such life for your self Khaleel" Hawayen da yake ta avoiding ya shiga sakko masa, Mami na hawayen ita ma tace "Ka gaya min me yasa ka xabi wnn rayuwar Khaleel, me ya shigar da kai wannan mummunar harkan?" Cikin rawar murya yace "I was raised such way Mami, a haka na taso, a cikinsu na taso, a cikinsu na rayu..." Mami tace "Iyayenka fa?" Sauke kansa yyi kasa hawaye na sakko masa sosai yace "I was never opportune to know them, ban ta6a saninsu ba, ban san iyayena ba" Ya daura fuskarsa a kafarta tana jin saukan hawayensa yana shessheka da kyar yace "Su ne iyayena, bani da kowa a duniya sai su Ummi, da su na gan ni," Dukawa Mami tayi ta xauna bakin stairs ta dago kansa with shock tace "How is that Khaleel?" Kasa bata amsa yyi hawaye na sauka idonsa xuciyarsa na masa xafi sosai, tace "Kayi min magana Khaleel" cike da karfin hali yace "Ban san me xance ba Ummi" Kuka sosai Mami take tace "Tell me more about you Khaleel" Ya share hawayen idonsa yace "Zayyad knows better, suna cikin manyan mu a lkcn don Zayyad is 45 now" Mami tace "Baka ta6a tambayarsa ko yasan wani abu a kanka ba" Khaleel ya girgixa mata kai wasu sabbin hawayen na xubowa idonsa.... Xuwa yanxu gaba daya sojojin dake layin na entrance din parlon Mami ana kokarin cire kofar, Gaba daya junaid ya shiga tashin hankalin da ya wuce misali, har snn kuma suna jin ihun Heedayah da Farida a ciki kamar xa su tsaga gidan, sbda rudewa ya ma mance da kofar kitchen dake ta baya duk da bai ma san Heedayah na kitchen din ba, lkci daya Shuraim ya xaga xuwa bayan gidan jin kamar ta nan Heedayah ke ihu, yana isa kofar ya bubbuga da karfi, Heedayah ta juya a mugun tsorace ta kara kwala wani sabon ihun tana cewa ta shiga uku, gaba daya ta mance da akwai kofa a kitchen din ita ma, yace "It's me ki bude kofar" da sauri ta karasa gun kofar ta bude hannunta na rawa, tana ganin Shuraim ta rikosa cikin kuka tace "Ya Shureen wllh Kidnapper ne shi, Mami tace min shine yayi kidnapping dinta amma kar in gaya ma kowa, wllh yana parlon ya kulle kofa....." Saketa Shuraim yyi ya nufi kofar kitchen din ya bude ya fita xuwa cikin parlon, sai a snn sojojin duk suka xagayo suka shigo gidan ta cikin kitchen din su ma, Mami ta mike da sauri daga bakin stairs da take xaune ganin Shuraim ya nufo su just as the soldier he is, tana kallon Khaleel a hankali tace "Don't ever admit you a Kidnapper, deny that" bata jira Khaleel yace komai ba ta nufi Shuraim kafin ya iso su tace "Listen Shuraim, magana muke yi da shi....." Kin sauraranta Shuraim yyi, ya bi ta gefenta ya isa gun Khaleel ya fincikosa ya kai masa wani wawan naushi biyu yana huci, Mami ta rikesa tace "Ban isa in maka magana bane Shuraim.... Are you alright ina magana baxa ka saurareni ba??" Turasa Shuraim yyi yana kallon sojojin da ke parlon yace "Seize him...." Sojojin suka nufesa, shi kuma ya fice daga parlon ta kitchen Mami ta bi sa da kallo, Heedayah na rakube jikin kofar kitchen ta waje har lkcn tana hawaye, tana ganinsa ta rikosa cikin rawar murya tace "Kun fita da shi ya Shureen?? Wllh Kidnapper ne, yana bindiga na ta6a gani..." wani kallo ya jefa mata yace "Waye ya kawosa gidan tun farko?? Ta dalilin wa ya samu fuskar fara shigowa gidan?" Hawaye na sauka idonta a hankali tace "Ni ce" wani kallo ya dinga yi mata, can ya fixgota har tana jin saukan numfashinsa a fuskarta yace "Da yaushe Mami ta gaya maki shi Kidnapper ne?" Kasa cewa komai tayi, ya hade rai yace "Baxa ki bani amsa ba" Da kyar tace "To... to ka sakeni" saketa yyi ta koma baya taki hada ido da shi, yace "Answer my question now" Tace "Daxu ta gaya min" Juyawa yyi xai bar wajen ta bi sa da gudu ta fashe da kuka tace "Yaya Shureen is he still inside plss" Bai ce mata komai ba ta ci gaba da bin sa, ta kofar main parlor sojojin suka fito da Khaleel, Duk yanda Mami tayi da su su sakesa basu saurareta ba don it's an instruction they are following, Junaid dai na tsaye balcony shi ma sai kallon Khaleel yake, A mugun fusace Mami ta nufi Shuraim tace "Baka da hankali dama Shuraim?? ban isa in gaya maka ka ji ba ashe??" Ba tare da ya kalleta ba yace "Mami wnn mutumin Kidnapper ne, kin sani, na sani, warce ta dalilinta ya fara shigowa gidan nan ta sani, So why are you covering up for him? beside you and people around you.... he is also very harmful to the society today, kin fi ni sanin wannan Mami, you are a lawyer, dole he have to be arrested ayi masa hukunci dai dai da abinda yake aikatawa, yanxu station xa a kai sa dole, I am sorry Mami, for your good, for our good, for the good of the society, babu xancen tausayi a case din nan, da xa a dinga bin tausayi da baxa ayi shari'a ba a duniyar gaba daya, he is guilty... kin boye shi yyi kidnapping dinki for a reason I never want to know, me yasa haka Mami??" Kallonsa kawai Mami take ko kiftawa babu gabanta na faduwa, can tace "Who told you that he is a Kidnapper?" yana kallonta a takaice yace "Heedayah, she said you told her everything today, he kidnaped you and requested the ransom of 30 million, which he was given...." Kallonsa kawai Mami ke ta yi, yyi kasa da kansa yace "I am sorry Mami, you can't cover him up anymore" yana fadin haka ya juya ya nufi gate, Junaid ya sakko balcony ya taho gun Mami yace "Mami this is just the right thing to do, babu xancen tausayi a lamarin nan, he deserves this, idan ba rashin kunya ba gidan da kayi garkuwa da mutane ka sake dawowa, me ya dawo yi har da rufe kofar parlor? is he even alright...." Hawaye ne ke sauka idon Mami ta ki ce masa komai ta wuce ciki da sauri, Heedayah da Farida na rakube waje daya a parlon ko wannensu na xare ido, har sannan a tsorace suke gaba daya, ko kallonsu Mami bata yi ba ta wuce sama xuwa dakinta, ta dau wayarta ta shiga dialing number Barrister, Abba na parlonsa tare da Mumy da gaba daya ta daina fahimtar bayanin da yake mata na cewar gobe xa su tafi kai ma Junaid gaisuwan Heedayah a kano, ganin yanda tayi still Abba yace "Are you there?" Da sauri ta dawo tunanin da ta tafi ta mike tsaye tace "Junaid kuma?" Abba yace "Eh Junaid" Mumy tace "Gobe goben nan?" Abba yace "In sha Allah" xufa ne ya shiga karyo mata duk da Ac dake aiki a dakin, Ita fa ko jiya ita da Sadiya da Salima sai da suka sake komawa gun Mutumin nan na Salima suka kara masa kudi ya kuma tabbatar masu Shuraim sai ya auri Heedayah, kuma sai ynda tayi da Heedayah, xa kuma ta dinga mingling da manya manyan matan kasar suna fita kasashe tare, xa tayi suna sosai a kasar, Wani murmushi tayi ta girgixa kai sanin xuwa kai gaisuwar ba ma abinda xai yiwu bane, sae dai idan ba uban kudinta ta kai jiya ba, Abba ya jawo wayarsa dake ring, da yake tana gefensa ta saci kallon screen din wayar taga an sa Barr Rahinah, Abba ya daga kiran ya kai kunne tare da sallama, Mami tace "I need this favor from you pls Barrister..." Abba dake sauraronta jin yanayinta yace "Are you okay Rahinah?" Tace "Ka kira Shuraim yanxu don Allah ka dakatar da shi abinda yake shirin yi, do that now plss Barrister" da mamaki Abba yace "Me yake shirin yi" Mami ta sakar masa kuka tace "Do that before it's too late Barrister, ka dakatar da shi, ni ya ki saurarata...." Abba yyi confuse da xancen Mami sosai, bayan Mami ta katse wayar yayi dialing number Shuraim yana fara ring Shuraim ya daga, Abba yace "Where are you? And what is happening Shuraim?" Shuraim yace "Bana kusa Abba, is there any problem?" Abba yace "Ohk, ko me kake yi I am instructing you to hold on to it, and come back home now" Shuraim yace "No Abba, it's something important yanxu haka mun kusa station..." Abba yace "Station? Me ke faruwa?" Shuraim yace "Kidnapper din da yyi kidnapping Mami ne ya dawo gidan yau, anyi nasaran kamasa yanxu haka muna hanyar police station" Mikewa Abba yyi yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ina Rahinar da yaran suke yanxu?" Shuraim yace "They are safe home, but Mami na nuna a kyalesa but I didn't listen to her being that it will be the greatest mistake to make..." Abba ya kasa cewa komai, a ransa kuwa tunani yake is Rahinah even okay? can yace "You don't worry, Kar ka biyeta ku yi tafiyar ku gani nan xuwa nima yanxu" daga haka Abba ya katse wayar, ya dau makullin motarsa Mumy ta bi bayansa da sauri tana cewa "Me ke faruwa barrister?" Yace "Idan na dawo xan maki bayani, I have to leave now" Abba na shiga motarsa ya bar gidan ya dau hanyar station din da Shuraim ya sanar masa xa su je, a hanya ya kira Baffan Junaid ya sanar masa abinda ke faruwa da Dakta.... Khaleel na xaune an sa masa handcuffs both legs and hands a inda xa ayi interrogating dinsa cikin Police station din... Bin Shuraim kawai Khaleel ke yi da ido har Mami ta iso tare da Heedayah kamar yanda aka yi instructing Yan sanda biyu su tafi su taho da su station din, Dpo na kallon Mami bayan duk sun xauna ya nuna mata Khaleel yace "Kin san wancan Mutumin Hajiya?" Mami ta kalli Khaleel da ya sauke idonsa kasa tace "Na san sa" Dpo ya kalli Heedayah yace "Ke fa young lady?" Heedayah ta gyada kanta a hankali, Dpo na kallon Mami yace "Yana cikin Kidnappers din da suka dauke ki few days ago ko?" Mami ta girgixa kai tace "Aa baya cikinsu, bai kuma san komai kan xancen ba ma" Abba ya kalli Shuraim ya girgixa kai kawai, Shuraim dai sai kallon Mami yake da mamaki ko kiftawa bbu, Dpo ya kalli Heedayah yace "Ke kin tabbata dai wnn mutumin Kidnapper ne ko?" Heedayah ta daga kai tana kallon Khaleel da ya kafeta da idonsa, sauke idonta tayi da sauri ta kalli Shuraim dake kallonta shi ma, can ta girgixa kai tace "Ni dai ina xaton Kidnapper ne shi, ban san ko haka ne ko ba haka bane" Dpo yace "Xato? To me yasa har kika yi xaton haka?" Ta sauke kanta kasa tace "Because he is huge, and...." Murmushi Dpo din yyi ya nuna mata Shuraim yace "Isn't he Huge?" Ta kalli Shuraim sannan ta sunkuyar da kanta, Dpo yace "And what?" Tayi kasa da murya tace "And naga ya kwana biyu bai xo gidanmu ba kuma sai aka yi kidnapping Mamin mu, sai yau ya dawo" Juyawa Shuraim yyi ya fice daga wajen kamar xai tashi sama, Junaid ya bi bayansa, Abba dai ya ma rasa abun tofawa mamaki duk ya ishesa, Dpo na kallon Khaleel yace "Kai me xaka ce game da xargin da ake maka na xama Kidnapper?" Khaleel ya kalli Mami dake kallonsa, ya girgixa kai yace "Xargin da suka min ba laifi bane don na kwana biyu bana garin at the time da abun ya faru, Ina jin kuma a ranan da na bar garin lamarin ya faru" Dpo yace "Ina ka tafi?" Khaleel yace "Naje wani aiki ne a kudu" Dpo yace "Wani aiki kenan" Khaleel ya nuna masa ID card dinsa dake ajiye da counter dinsa a gefe daya abinda kadai aka gani a aljihunsa knn, Dpo ya dau ID card din yana dubawa, can ya gyada kai cikin gamsuwa yana kallon Khaleel.... daga karshe dai Khaleel have to be released bbu wani proof yana da laifi tunda daga Mami har Heedayah sun yi shunning laifin da ake xarginsa da. Bayan sun fita daga station din wanda tuni Junaid da Shuraim suka yi wucewarsu, Mami na kallon Abba da Baffansu Junaid a hankali tace "I am sorry...." Abba dai bai ce mata komai ba, ya nufi motarsa haka ma Baffan Junaid, Mami ta jira har Khaleel ya karaso amma ya kasa kallonta, tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Ku taho tare da Zayyad gobe, I want to know everything about you, amma bani kadai xan saurari labarin ka ba Khaleel, har Barrister da kuma duk wani wanda ke tare da ni, nayi alkawarin in har baka da wani laifi xa mu rufa maka asiri xa mu taimake ka Khaleel, and it's not too late to still search for ur parent...." Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... *Mai tantama akan sabulai na gyaran jiki cewa basa Aiki toh ya cire _mg's_ domin kankat ne insha Allah, amare da uwargidaye harda ma yanmata ba cika baki ba ku gwada wnn sabulu ku bada labari, wa yanda basa san using cream sabulun mg's herbal whitening black soap ya wadace muku, jikinku zaiyi kyau yyi kamshi da glowing, and don't forget ba na bleaching bane organic products ne* 🤗 *Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai, akwai me saka haske bana bleaching ba, zai fiddo miki da ainihin color dinki yagoge dukkan dattin jiki, akwai wanda zai yi maintaining skin dinki yasaki fresh* *Soap price 3k, Location.. kaduna, buh muna turawa ko Ina Amma delivery is not free* Maiso kindly message... 08062991549 Call... 08064532391 _Note: Bai riga da ya shiga kasuwa ba tukun.._ *Mg's bakery* You can still order ur birthday cake, cupcake,slice cake,meat pie,shawarma,samosa nd spring rolls for ur event @mg's bakery Kindly call or chat 07046881166 07067210195 08062991549 Masu bukatar abayas,takalma da jakunkuna,ashobe,laces d atamfofi, materials nd the rest 07046881166 👏🤝 Mumy ce xaune dakinta tana ma Shuraim wani kallon tace "Kai me yasa baka da mutunci ne Aliyu?" Da mamaki yace "But Mum how do u expect me to know what happened bayan nace maki ni bana wajen, ni ban san me ya faru ba, ki tambayi Abba" Wani kallo ta dinga yi masa, Bayan few minutes jin ta ki cewa komai yace "Kiran kenan Mumy?" Ta jefa masa wani kallo ta nuna masa kujera tace "Xauna mu yi magana" Ba musu ya tafi ya xauna saman kujeran, tana kallonsa tayi kasa da murya tace "Aliyu ka gaya min tsakanin ka da Allah, ni dai nice na haifeka ba wani ba...." Shi dai Shuraim kallonta kawai yake, tace "Tell me, do you have any feeling for Heedayah?" Kallonta ya dinga yi da surprise, can yace "Wacece haka?" Tace "Auuu Heedayar ce baka sani ba?" Yace "Heedayah??" Ta hade girar sama da ta kasa, can yace "Ohh, Wai Heedayah guda dai da na sani? Feeling na me kenan?" Ganin sai hararansa take ya d'an yi murmushi yace "Idan ina da feeling for her xaki yrda wani tarayya ya hadani da ita ne?" Tace "Why not? Ba ubanka bane yyi wahala da ita da rainonta? Ina ce a gidan nan ta taso? kuma ae nasan irin rainon da aka yi mata ba wanda xai cutar da kai ko ni bane ko da wata alaka ta shiga tsakaninku" Shuraim yace "I don't have the feeling you are thinking Mum, ba gobe naji Abba yace xa a kai kudinta ba, Allah ya sanya alkhairi" Kasa ce masa komai tayi, but she look shocked, ya mike yace "Allah ya tashe mu lfya" Daga haka ya nufi kofa as if babu abinda ya damesa a lkcn, sai bayan da ya fita dakin nata ya kulle kofa ya ji kamar an axa masa abu me nauyi saman kirjinsa, xaunawa yyi a hankali saman kujeran parlonta na few minutes, kafin ya mike da kyar ya fice daga parlon gaba daya ya koma dakinsa. Washegari da safe Shuraim na kwance jin wayarsa dake vibrating a gefensa ya bude ido a hankali ya jawo wayar yana kallon screen din, Number Mami ya gani, ya kalli wayar for few seconds snn ya daga ya kai kunne, Mami tace "How are you doing?" Ya cire duvet din jikinsa ya mike xaune yace "Good morning" Tace "Morning ya gida?" Yace "Alhmdllh" tace "Idan ba damuwa ina expecting din ka nan da anjima Shuraim" ya d'an yi shiru har sai da tace "Are you there?" Yace "Alright, Amma yau xan koma Lagos ne" Tace "Ka xo din dai kafin ka tafi" Yace "In sha Allah" daga haka ta katse wayar, ya ji kamar kar ya tafi gidan ya koma yyi kwanciyarsa still claiming he is fine duk da yanda ya ga rana haka ya ga dare jiya. Karfe goma saura Shuraim ya shigo gate din gidan Mami, Heedayah ta xagayo daga backyard din gidan kenan ta shanya ma ita da Farida Hijabs dinsu da ta wanke, suna hada ido ya nufi balcony bai kuma kallonta ba, bin bayansa tayi kafin su karasa balcony din tace "Ina kwana ya shureen?" Bai tanka ta ba har ya shiga ya kwankwasa kofar parlon, ta tsaya bayansa leaving a little distance between them, a hankali tace "Ina kwana Yaya" juyowa yyi ta d'an koma baya da sauri, calmly yace "Ban sani ba" Tayi narai narai da ido tace "Ya Shureen Mami ce ta kalleni jiya shi sa I couldn't say anything, and I don't want it to be like she isn't saying the truth to the officers...." Yana kallonta da kyau yace "So you both might have face the consequences, don idan har da gaske ta gaya maki waye wnn mutumin ku ka boye a tare, then both you and her aren't safe any longer....." Heedayah ta marairaice tace "Ni ae gobe xan wuce kano, I won't stay here, sae in sa Ammina tayi convincing Mami su dawo kanon su ma, Kuma Mami taji tausayinsa ne kawai kilan don yace mata bashi da iyaye" Shuraim na kallonta yace "Shi kuma bai ji tausayinta ba yyi kidnapping dinta ko?" Shiru Heedayah tayi tana kallonsa, ya d'an yi murmushi ya girgixa kai yace "Something is definitely wrong with Mami, coz a barrister won't do what she did yesterday" Bude kofar parlon aka yi, duk suka kalli kofar, Farida ce tsaye bakin kofar tana kallon Shuraim tace "Good morning" yace "How are you" ta basa hanya tace "Alhmdllh" Shiga parlon yyi, Farida na kallon Heedayah tace "Wankin Hijab tun 8:00 am, Heedayah bata ce komai ba ta shiga parlon ita ma, Shuraim na xaune parlon suna gaisawa da Dinar da Amira da suka iso daga Abuja safiyar ranan, Dinar na murmushi tace "Ya aiki?" Yace "Alhmdllh, yau ku ka iso?" Tace "Eh wllh, morning train muka biyo" Amira dai na ta danna wayarta tunda ba sanin Shuraim tayi ba, Bayan some minutes Mami ta sakko downstairs ta xauna parlon suka gaisa da Shuraim, shi dai yana wasa da Fadil dake xaune kusa da shi, can Mami tace "I am sorry about yesterday Shuraim, I just had to...." Shuraim na kallonta yace "Me yasa kike tunanin you have to Mami?" Mami tayi shiru, sae kuma murya can kasa tace "May be because I am a Mother, and because I never expect that... I never saw it coming" Dinar ta mike ta bar parlon don bata ma son ci gaba da jin wnn abin dake bata takaici, Amira dai sae kallon uwartata take, Shuraim ma kasa ce mata komai yyi, Kwankwasa kofar parlon aka yi, Heedayah dake dinning xaune tare da Farida dake shan tea ta mike ta nufi kofar ta bude, ido hudu suka yi da Khaleel, ta wani xaro ido cikin few minutes ta bar wajen a guje ta koma can hanyar stairs ta rakube a mugun tsorace, su Mami duk suka bi ta da kallon mamaki, Khaleel ya shigo parlon da sallama, Farida ta mike da sauri ta bi bayan Heedayah, Mami da Amira kadae suka amsa sallamarsa, ya karaso cikin parlon kansa a kasa, bai xauna ba ya gaida Mami a hankali bowing his head, Mami ta nuna masa kujera tace "Morning how are you?" Xaunawa yyi saman kujeran yace "Alhmdllh...." Yana kallon Amira yyi kasa da murya yace "Ina kwana?" Amira tace "Sannu da xuwa" yyi mata godiya, kallon Shuraim da ya tsiri danna wayarsa yyi yace "Good morning" Bayan few seconds Shuraim ya dago yace "Morning" Mami tace "Ina abokin naka?" Khaleel yace "Yana mota a waje" Mami tace "Let him in" Mikewa yyi ya nufi kofa, Amira ta bi sa da kallo har ya fita, Shuraim ya mike ya mayar da wayarsa aljihu yace "Ni xan koma Mami" Mami tace "Aa ka d'an jira, ae ba mu gama magana ba" Yace "Xan dawo kafin in tafi anjima in sha Allah" tace "No, sit back Shuraim, xa muyi magana kafin ka tafi din" Ba musu ya koma ya xauna duk da ko kadan ransa bai so ba, Ba a dau lkci ba Khaleel ya dawo parlon tare da Zayyad, Yana kallon Mami yace "Ana sallama a waje" Mami xata yi magana Dinar ta sakko ta mika mata wayarta dake ringing, Mami ta amsa ganin Abba ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa ya sanar mata he is outside tace "Toh gani nan xuwa" Daga haka ta mike ta fita bayan ta sanar ma Khaleel and his friend she will be back soon, tun asuba ta tura ma Abba message ya xo kafin ya tafi aiki pls, a compound din ta samesa xaune, ta ja kujera tana kallonsa tace "Ya gida?" Yace "Fine me yaron nan ya sake dawowa yi a gidan nan Barrister?" Mami tace "Ni nace ya xo" Abba ya girgixa kai yace "Rahinah ni ban san meye matsalar ki ba, all ur words at the station yesterday are nothing but lies, do you have any agenda to do with this thug da kike rufa masa asiri? Tunda baki son a hukuntasa ba sai ki rabu da shi ba ki daina basa fuskarsa xuwa maki gida, Why are u behaving this way pls Rahinah? Ba ma shi kadai ya shigo gidan yanxu har da abokinsa sbda samun waje??" Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "There is something I want to know about him barrister...." Ya dakatar da ita yace "Me saninsa xai kara maki a rayuwa, why are you risking your life and that of people around you?" Mami tace "Ba haka bane Ahmad, there is something about him that I feel I need to know, from the little he said about him kamar ba son ransa bane harkan nan da yake yi" Da mamaki sosai Abba ke kallonta, can yace "Ikon Allah, wato kawai kin ma san Kidnapper din ne shi, to ina ruwanki ko da son ransa yake ko ba da son ransa yake ba, Jan sa ake su fita operation din ko da kafafuwansa yake tafiya, plss Rahinah stop all this nonsense idan xa ki bari a hukunta Mutumin nan ki bari, is 30 million 30 thousand??" Mami tayi shiru a sanyaye tana kallonsa can tace "Don Allah mu basa listening ears barrister, may be labarinsa xai mana amfani, ba wai nace kada a hukunta sa ba but plss let know how he joined the gang, coz with tears in his eyes yace min he was never opportune to know his parent" Abba ya dinga mata wani kallo, ta mike tayi kasa da murya tace "For my sake plss Barrister ka tashi mu je parlon, I invited him and his frnd ba xuwan kansu bane" Barrister ya girgixa kai yace "I have other important cases to look to Rahinah, dama wnn shine dalilin message din da kika min in xo??" Mami ta dakatar da shi tace "Pls for my sake Barrister, I am saying plss" daga haka ta fara tafiya, ya bi ta da kallon mamaki har tayi nisa, text ya shiga turawa a wayarsa yana gamawa ya mike ya bi bayanta xuwa cikin parlon. Bayan Abba sun gaisa da su Dinar a parlon ya kalli Shuraim da yyi masa sannu da xuwa, Abba yace "You said you are leaving for Lagos today" Mami tace "Ni na tsayar da shi xuwa anjima barrister" Abba yace "Alright" Mami na kallon Khaleel da idonsa ke kan Tv tace "I am sorry Khaleel, ba ni kadai xan saurareka ba, ni da barrister will listen to you, if there is any help we can render you from our discipline we will gladly do that... Amma fa we want nothing but the plane truth from you, idan kuma muka sameka da laifi xa ayi maka hukuncin da yyi dai dai da wanda ya kamace ka" Khaleel dai kallon Mami kawai yake, can ya sauke kansa kasa yace "Mami ni me laifi ne dama ae" Mami tace "Allow us to decide that" Shi dai Zayyad na jin abinda Mami ta fada ya ji he just have to leave that parlor immediately, Mami could see how uncomfortable he was, haka ma Shuraim dake ta kallonsa, ta d'an yi murmushi tace "Ka kwantar da hankalinka Zayyad, I am assuring you this... ba abinda xai faru" Abba wayarsa kawai yake dannawa, Dinar har xata bar parlon jin furucin da Mami tayi ma Khaleel na karshe yasa ta samu courage din xama, Junaid ne ya sakko parlon rike da makullin motarsa ya shirya cikin white shadda kasancewar ranan Friday ne, Heedayah da Farida dake jikin rack din stairs sun ki komawa parlon yace "What's that?" Basu kai ga basa amsa ba ya kalli parlon, karasawa ciki yyi, Amira ta sakar masa murmushi, Junaid ya gaida Abba, ya ba Shuraim hannu yyi ma Khaleel da Zayyad ma haka, ganin fita xai yi Mami tace "You stay back Junaid" Ya juyo yana kallonta bai dai ce komai ba amma ransa bai so ba ya xaga bayan kujera kawai ya tsaya. Mami na kallon Khaleel tace "Now tell us who you are Khaleel" Khaleel ya kalli Zayyad, Mami tace "Ko shi xai gaya mana?" Khaleel yace "I can't say daga yaushe ne nake tare da su Ummi, sau da yawa yana attempting bani labarin dalilin kasancewata da su, amma nasan xuciyata baxai iya daukan hakan ba sbda ailment dina...." Abba yace "Kwanciyar da kayi kwanaki a Abuja shi ne matsalar da kake nufi a nan?" Khaleel yace "Eh shine" Abba ya gyada kai sannan ya kalli Zayyad wanda har lkcn ya ki sakewa, Tun maganar da Khaleel yyi na farko Abba ya ji he is also interested to know him, as a barrister bai ga alamar karya ko tsoro a tare da Khaleel ba, he is being just Frank, unlike his frnd that at anytime if care isn't taking xai iya barin parlon, Abba ya kalli Junaid dake tsaye shi ma yana kallonsu yace "Ka kulle kofar Junaid, we need privacy" Xaro ido Zayyad yyi, Junaid ya nufi kofar ya sa makulli, Abba na kallon Zayyad yace "Tell us about ur frnd...." Zayyad ya goge fuskarsa sannan yace "Amma Ina son alkawari daga gare ku na cewar bayan labarin mu da xa ku ji xa ku rufa mana asiri with out involving hukuma" Abba yace "Don't worry about that, there is always a reason for everything, mu baxa mu tona maku asiri ba amma xa mu yi abinda ya kamata" Zayyad yyi shiru, Abba yace "Ka kwantar da hankalin ka, muna sauraron ka" Zayyad ya sauke kansa kasa yace "Shekaru kusan talatin da hudu xuwa biyar da suka wuce....." Kallonsa duk occupant din parlon suke, Zayyad ya ci gaba "Oganmu ya taho da wani yaro da baxai wuce shekara uku ba daga operation din da suka fita yi gidan wani attajiri, wnn mutumi na daya daga masu kudin wancan lkcn duk da mu dai ba wasu manya bane don ba a fita da mu irin wnn operation din amma duk mun sani, shi wnn yaron da oganmu ya kawo shine Khaleel, a ynda Oga Salahu ya sanar mana a lkcn sun kashe Mahaifin yaron bayan sun kwashi kudade da zinarai masu yawa, bana mancewa daya daga ogannimu na ynxu da ake kira da Arne wanda a lkcn shi ma yaronsu ne ya tambayi Oga Salahu me yasa ya taho da Khaleel, Oga Salahu yace xai yi mana amfani nan gaba.... A nan ya bada labarin wai bayan sun harbe mahaifinsa tashi yyi daga jikin mahaifiyarsa dake rike da shi ya gudu xuwa daki ya dauko bindigogin wasansa wai xai harbe su shi ma, wani oganmu a lkcn yyi niyyar harbesa Oga Salahu ya dakatar da shi, wnn dalilin kuma ya sa oga Salahu ya daukesa yana rike da bindigar wasan nasa da yake ikirarin xai harbe su, a ynda Oga Salahu ke bamu labari Mahaifiyarsa na kuka da xa su tafi da shi, sai yake ce mata xai dawo anjima idan ya kashe su duka da bindigarsa, courage, fearlessness da zeal din dake tare da shi yasa oganninmu suka ji they just have to go with him and raise him, he have to be their own, wnn shine mafarin dawowar Khaleel cikinmu tun yana shekara uku a duniya, sai dai bana mantawa sunansa a lkcn ba Khaleel ba, idan ka tambayesa ya sunansa xai ce maka Aliyu Usman, Babban Oganmu na gaba daya at that time sunansa Oga Saminu, to Oga Saminu na da wani yaronsa da yake ji da wanda 'yan sanda suka kashe a wani operation... sunan yaron Khaleel, yaron is also brave and intelligent...." Zayyad na nuna Khaleel dake ta kallonsa yace "Shi yasa ya mayar masa suna Khaleel, kuma har yau idan ba ni ba sai wa enda suka jima tare da mu bbu wanda yasan sunan Khaleel na ainahi, shi kansa Khaleel bai san sunansa ba ynxu sai da na fada...." Zayyad ya jinginar da kansa da kujera yace "Khaleel is more than intelligent, wnda duk wanda ke tare da shi baxai so ya bar sa ba, wayonsa kuma ya fi karfinsa as at then, till now.... ga rashin tsoro, tun yana shekara 7 ya iya harbin duk target dinsa, duk oganinmu na ji da shi ba kadan ba barin oga Arne, mu da muka jima tare da su ma sai da Khaleel ya nuna bamu iya komai ba, hatta bera idan Khaleel yasa kansa xai kamo duk inda ya shiga sai ya kamosa cikin mintuna kalilan, da farko da aka kawosa duk dare sai yyi kuka yana kiran mahaifiyarsa, amma as time goes on, shekara daya biyu sai ya watsar gaba daya, ba a ta6a saka wani cikinmu makaranta ba, amma Oga Arne yyi convincing ogannimu sun saka Khaleel...." Shiru Zayyad yyi yana kallon Mami da ta sunkuyar da kanta hawaye na sauka idonta sosai, Khaleel ma kansa na sunkuye yana sauraron Zayyad don shi kansa bai san wnn bangaren na labarin nasa ba sai a ynxu, xamowa kasa yyi a hankali ya xauna xuciyarsa na bugawa, Shuraim dai sai kallonsa yake kamar yanda Junaid ma ke kallonsa ko kiftawa bbu, Abba ya sauke wani ajiyar xuciya underneath his breath yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." Bayan few seconds Abba ya kalli Zayyad da yyi shiru yace "Go on...." Mikewa Mami tayi, Abba na kallonta da mamaki yace "Ina xa ki kuma?" Bata iya tace masa komai ba ta nufi stairs hawaye na ci gaba da sakko mata uncontrollably..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Treat/repair your skin with mg's skincare today,are you battling with pimples, Black spot cream reaction eczema,acne, sunburn,spot, stretch mark, discoloration/skin damage, stretch mark ❌then mg's skincare is the plug for you,mg's skincare gat solution to all ur skin prblms😍everyone deserves a blended skin🌿 when it comes to skin issue😢gv it to mg's skincare 💯🔥 now is the time to take care of ur skin,this product is the real deal 🙌clears white patches✅dark patches✅dark feet's/knuckles ✅reduces the appearance of greenveins,it clears pimples,spot and make ur skin fresh nd glow like never before just gv it a try nd ur skin will definitely thank you💋✅evn if you don't HV anything mg's skincare gat you a soap that will maintain ur skin nd make the skin to glow🥰 Soap price:3k Chat 08062991549 to plc ur orders Call:08064532391 We deliver Nationwide buh delivery is not free🙏 we can't wait to be a part of your beauty story🤭 Mikewa Amira tayi ta bi bayan Mami da sauri, bedroom dinta ta sameta xaune gefen gado, ta karasa kusa da ita ta xauna a hankali tace "Though it's sad but bai kamata ki bar wajen ba Mami, u invited him here, so you are to listen till the end" Kasa ce mata komai Mami tayi hawaye na xarya a idonta, Da damuwa Amira tace "Haba Mami sai kace yau kika ta6a jin irin haka? This isn't suppose to look new to you, kina fa cases wa enda suka fi haka ma ai" Mami ta dafa kafadunta cikin raunin murya tace "Amira wnn Kidnapper din da kike gani yayanku ne" Da mamaki Amira ke kallonta, da farko ta ma kasa cewa komai, can dai tace "Ban gane ba Mami, yayanmu ta Yaya? How is that?" Mami ta fashe da kuka sosai ta kasa bata amsa, Amira ta xaro ido tana kara naxarin labarin da Zayyad ke basu downstairs, ja baya tayi with shock tace "Yayanmu kuma Mami?" Mami ta gyada mata kai amma ta kasa magana, kallonta kawai Amira take da idanuwanta kamar xa su yi magana, cikin kuka Mami tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un... da na sani da ban dage da addu'ar Allah ya sake hadani da Aliyu a nan duniya ba, da na sani da ban dinga wnn addu'ar ba don gashi ban masa adalci ba ban ma kaina adalci ba, had I known addu'a ta garesa a ko da yaushe shine Allah ya hada mu a darussalam ba nan duniya ba...." Amira ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Mami ya aka yi kika san yayanmu ne?? How is that even possible?" Bude kofar dakin aka yi Dinar ta shigo, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsu da mamaki, can ta karaso tace "Me ya faru Mami??" Jin Mami taki cewa komai Dina ta xauna kusa da Amira tace "Ummi Hanan me ke faruwa?" Amira ta sakar mata kuka tace "Wai kiji mutumin nan yayanmu ne in ji Mami" Xaro ido Dinar tayi tace "Yayanmu kuma? Wani mutumin a ciki? Yayanmu kamar yaya?" Mikewa Mami tayi ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta dawo dakin ta debi tissue paper dake gaban mirror dinta ta nufi kofa duk suka bi ta da kallo har ta fita, Dinar na kallon Amira cike da confusion tace "How is that? Meye hadinmu da Kidnapper xa a ce yayanmu ne, yayanmu ta ina?" Amira ta buda hannu alamar bata sani ba hawaye na sauka idonta, Dinar tace "Oh My God, I don't understand this" Amira dai ba bakin magana, Dinar ta mike daga karshe ta kamo hannunta tace "Mu koma parlon" Xaune suka tadda Mami a position dinta a parlon, Abba na kallonta ganin yanda tayi wani sanyi har sannan tana hawaye sosai yace "Are you okay Rahinah?" Mami ta gyada masa kai cike da karfin hali tace "Sure" Abba na kallon Zayyad yace "Go on pls..." Zayyad yace "Tun daga primary school har junior Secondary position din Khaleel was always first, kuma har ya gama jss3 ba a ta6a fita operation da shi ba, iyaka dai ana training tare da shi a cikin gida every weekend, tun yana shekara sha biyar ya xama perfect wajen operating din bindiga ko wani iri ne, a sannan Arne Oganmu na yanxu kadai ne yyi supporting xuwan Khaleel makaranta don oga Saminu na ganin xuwansa makaranta baxai sa ya samu skills din sana'ar ba, snn a ko da yaushe xai iya bijire mana ko ya tona mana asiri wataran in har yana mingling da innocent souls, Oga Bala aka sa ya kai maganar Khaleel wajen mutumin da ke bamu asirin dake taimakon mu samun nasara da ci gaba a harkar yyi duba kan Khaleel, nan ya sanar cewar a barsa yyi karatun, karatunsa na da amfani garemu sosai a gaba snn xa a samu ci gaba ba na wasa ba idan ana tare da Khaleel, amma xai yi aiki a kan lamarin don ya ga Khaleel na da taurin kai kuma bashi da tsoro, wnn shine dalilin da yasa Oga Saminu ya samu kwarin gwiwan ci gaba da biya ma Khaleel kudin makaranta, a hakan kuma yana kara basa training don kullum sai ya yanke masa amount da xai dawo da shi gida daga makaranta ta ko wani mean, makaranta ce me tsada yake xuwa a time din, tun da suka fara haka da Oga Saminu ba ayi ranan da Khaleel xai dawo ba tare da exact amount din da Oga Saminu ya yankar masa ba, he was doing it perfectly don ba a ta6a kamasa ba, first operation din da aka fara fita da Khaleel yana Ss1, gidan daya daga classmate dinsa wanda mahaifinsa shahararren me kudi ne aka sa Khaleel yyi leading xuwa gidan, kissan farko da kuma aka fara yi gaban Khaleel kenan, don nan take Oga Saminu ya kashe yaron ganin ya gane Khaleel duk da masks dake sanye fuskarsa.... Khaleel ya dauke idonsa da suka sauya launi daga kallon Zayyad, kamar yanda duk occupant din parlon ke kallon Zayyad din, Mami dai sauraronsa kawai take tana goge hawayen da ya ki yanke mata da tissue, Abba ya kalleta don sai yaga wnn kukan da take ya wuce na tausayi, Shuraim ma ya kasa gane kan kukan Mami, this is isn't something that rarely happen a duniya, hakan na faruwa sosai a duniya, Zayyad ya sauke ajiyar xuciya yace "I think Khaleel xai ci gaba daga inda na tsaya, don nasan shi kansa bai mance operation din farko da ya fita ba" Abba na kallon Khaleel da yyi nisa tunanin da yake shi bai taba tunanin haka labarinsa yake daga farko ba, bai ta6a imagining cewar rabasa aka yi da iyayensa, xuciyarsa ya ji yana masa xafi sosai, ya lumshe ido ya bude, a hankali Abba yace "Go on Khaleel" Junaid ya tafi gun Mami daga inda yake tsaye ya d'an duka bayanta ya dafa kujeran da take xaune murya can kasa da damuwa yace "Are you okay Mami?" Mami ta gyada masa kai a hankali still wiping away her tears tace "Sure" mikewa yyi ya koma inda yake tsaye yana duban Khaleel, Har a lkcn nan Farida da Heedayah na bakin stairs a tsaye, jikin Heedayah yyi sanyi ba kadan ba sai kallon Khaleel take, a hankali ta xauna nan bakin stairs din xuciyarta gaba daya babu dadi, bayan few seconds jin Khaleel yyi shiru Abba yace "Muna sauraronka Khaleel" Ya sauke kansa kasa hawayen dake makale idonsa ya sauko, daga Dinar har Amira kallonsa suke ko wannensu gabanta na faduwa, Cikin sanyin murya Khaleel yace "Ban ta6a sha'awar sana'ar da ubannin gida na ke yi ba, na taso cikin mutanen da babu tsoron Allah, babu imani babu tausayi a tare da su, it took me sometimes kafin in gane babu hadina da Oga Arne coz he always act just as a father to me, a nan naji ina son sanin su waye iyayena bayan na gano Ogana ba ubana bane, na damu ina son sanin mahaifana, amma no one is wishing to say even a little to me about them, kullum da tunanin babata nake kwana nake tashi bayan na mallaki hankalina, na kan dade ina naxarin me yasa ta yarda tayi abandoning dina ga mutanen da basu da tsoron Allah...." Ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa hawaye masu xafi na xubo masa, Mami couldn't control herself anymore ta sakar masu kuka a parlon sai dai bata ce komai ba, Abba dai sai kallonta yake, Heedayah ta hade kanta da gwiwa ganin ta kasa hadiye nata kukan ta fashe da kuka sosai tana jin tausayin Khaleel har ranta, Khaleel ya fi minti daya bai ce komai ba, Abba yace "Ka ci gaba Khaleel" Cikin raunin murya Khaleel yace "But I am still wishing to meet with her some days, that's my biggest wish in life now, ni nasan dalilin tunaninta, da irin rayuwar da na tsinci kai na bbu me fada min gaskiya ko me hanani mugun abinda nake yi yasa ciwon xuciya ya kama ni, su kuma wa enda suka kashe mahaifina..." Girgixa kai kawai yyi ya d'an yi murmushin karfin hali, bayan few seconds cikin sanyin murya yace "I don't want to say all what I passed through being a full time thug, duk da kasancewata mai laifi sosai wajen Ubangijina ban yada addinina ba, I valued it above everything till today, bana barin lkcn sllh ya wuceni, bana kuma wasa da tashin dare da axumi, snn ni din me tausayi ne ga victims dinmu kowa ya sani, ban ta6a kissa ba, duk sanda aka yi kuma sai hankalina ya tashi amma hakan baxai sa in ki fita operation da su ba washegari coz sai da ni suke ganin dai dai a komansu, a lkcn ma fashi ake ba kidnapping ba, a kullum addu'ata shine Allah ya kawo karshen rayuwata da mutanen nan, sau da yawa na kan yi attempting guduwa but bana iya kwana biyu xan dawo garesu ba, dalilin da har ynxu na rasa ganewa, sai in ji without being part of them kamar baxan iya xaman duniyar ba, I was sponsored by them to the university where I studied Architecture, a nan ne kuma na samu nayi karatun addini don i was free from them, sai dai duk weekend akwai operation da ni, after my degree, daya daga oganmu ya dage sai na koma nayi criminology don course din xai kara taimakon mu wajen harkar mu which I did, everything was moving smoothly for us until 5 years ago na dawo daga Uk na tafi inda ake ajiye kidnapped victims a daji, usually idan ina nan dama responsibility din feeding din victims dinmu ni ake ba ma, a ranan na shiga inda victims din suke ina basu bread a nan na ga Heedayah, bayan na fita nake tambayar colleagues dina daga inda aka yi kidnapping dinta seeing that she is blind, sai suke ce min she wasn't kidnapped, Oga Salahu ne xai siyar ma wasu yan siyasa part din yara, an siyar da na daya saura su biyu a ranan ma xa a kashe wata cikinsu, ba sabon abu bane wnn gun oganninmu na kashe yara, sau da yawa such cases kan tsaya min a rai ya dameni, had it been I had the opportunity da xan kwashe duka su biyu a lkcn amma sai na dauke Heedayah kadai sbda ailment dinta na fitar da ita bakin gari na ajiyeta nayi wucewata sbda hakan kadai xan iya yi mata, ya d'an yi shiru snn ya ci gaba kansa a kasa, bayan shekara biyu na sake haduwa da Heedayah.... Abba ya sauke wani ajiyar xuciya bayan few seconds yace "Yanxu a ina ku ke da xama gaba daya in particular?" Khaleel ya kalli Zayyad snn yace "Kowa na da gidansa, sai idan akwai wani operation ne ake haduwa a wani gida" Abba yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Abba ya kalli Zayyad yace "Yanxu shi wannan mutumi ya daukesa daga gun mahaifiyarsa bayan ya kashe mahaifinsa yana nan?" Zayyad ya girgixa kai yace "Duk sun rasu, Oga Saminu ya mutu 7 years ago, Oga Salahu an harbesa a wani operation that same year...." Abba yace "Yanxu ku nawa ku ka rage a harkar?" Zayyad yace "Muna da yawa, ogannimu a yanxu uku ne xuwa hudu" Abba ya girgixa kai yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Shuraim dai kansa na kasa yana naxarin labarin Khaleel, Mami kuma ta dafa kanta da yyi mata nauyi, cikin sanyin murya Khaleel yace "Meeting with Heedayah sai na samu courage din dinga bijire masu, naji bana shakkansu, nake ji kuma xan iya barinsu, ko ma me xai faru ya faru, da suka ga hakan shine suka yi blackmailing dina suka yi kidnapping Mami, and they ordered me to act as though nine na sa ayi kidnapping dinta don sun san hakan kadai ne xai rabani da ita da duk wani ahalinta, idan banyi yanda suka ce ba nasan xa su yi harming dinta shi yasa nayi haka" Shuraim na kallonsa yace "Ya Address din gidan da ku ke xaune gaba daya?" Khaleel ya d'an yi shiru sai kuma ya gaya masa, Abba ya kalli Zayyad yace "Kai kuma me ya shigar da kai harkan?" Zayyad yace "Ina almajiranci suka daukeni suka sa ni a harkan" Girgixa kai kawai Abba yyi, shiru ne ya biyo baya a parlon, can Mami ta mike tayi excusing kanta ta koma sama ba a dau lkci ba sai gata ta dawo, cikin dashewar murya tace "I have a story to tell...." kowa na parlon kallonta yake, Abba yace "Muna sauraronki Barrister" Mami tayi shiru wasu sabbin hawayen suka xubo idonta ta goge da tissue snn cikin sanyin murya tace "Shekaru talatin da uku da suka wuce...... Muna xaune tare da Mai gidana na farko Alhaji Usman misalin karfe tara na dare ya dawo daga wani business dinsa da yayi a kudu yana cin abinci, shekaranmu biyar da aure a lkcn, d'an mu daya, hira muke yana cin abinci muka ji kamar karan harbi a tsakar gida, mikewa yyi bai kai ga isa bakin kofa ba aka turo kofa wasu mutane su biyar suka shigo ko wannensu fuskarsa a rufe, na tsorata sosai na jawo d'ana na rungume jikina ina salati, Mai gidana bai ce masu uffan ba ya tafi daki da sauri ya dauko masu jakar kudin da ya dawo da shi daga tafiyarsa ya dire masu yace su yi hakuri gashi nan su dauka su tafi, daya daga cikinsu ya buge kansa da bindiga, su uku suka shige daki, biyu kuma na daga bakin kofa sai da suka juya dakin gaba daya suka kwashe duk zinarina da wasu kudaden da suka gani snn suka fito, daga ni har me gidana dake duke kusa da mu bbu wanda yace masu komai, daya daga cikinsu ya xo ya samesa yace motarsa fa? Me gidana yace shi baya hawa mota bai rufe baki ba Mutumin nan ya harbesa a kai.... Kowa na parlon kallon Mami yake da mamaki, sai a snn Junaid ya shiga naxarin labarin Khaleel sosai ya dinga kallonsa, wnn labarin da Mami ke badawa ynxu ya san da shi shekaru masu yawa, kanninsa ne kawai basu sani ba, Khaleel sai kallon Mami yake ko kiftawa bbu, hawaye na sauka idon Mami a sanyaye tace "A nan take d'an sa dake jikina ganin abinda suka ma mahaifinsa ya mike ya tafi daki da gudu ya dauko bindigan wasan sa har biyu ya fito a guje yana nuna masu... Ganin haka daya daga cikinsu xai harbesa aka hanasa, wnn ranan shine rana na karshe na ganin mijina da d'a na, har lahira suka kashe min miji suka kuma tafi da d'a na Aliyu..." Mikewa Abba yyi yana kallon Mami with shock, Shuraim ma couldn't stop looking at her with shock, Kuka sosai Mami take ta sakko kasa tace "Ni na san so... da tausayin da nake yi ma wnn bawan Allah a cikin kankanin lkci da haduwarmu ba a banxa bane... there is something I couldn't understand, he behaves like my blood, Ina kuma jin sa har raina...." Zayyad banda xare ido bbu abinda yake, Mami ta ajiye hotuna biyu tana kallon Zayyad da ya mike da sauri ya dau hoton yana kallo snn ya kalli Khaleel yace "Wallahi shine wnn, shi aka kawo cikinmu shekaru masu yawa da suka wuce" Mikewa Shuraim yyi, Abba yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Hawaye ya kawo idon Junaid da ya kasa daina kallon Khaleel dake ta kallon Mami kamar wanda aka dasa a wajen..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... A hankali Khaleel ya bude idonsa ya shiga bin inda yake kwance da kallo, Shuraim ne xaune kan kujera daga gefensa yana danna waya, Shuraim ya daga kai yana kallonsa yace "How are you feeling?" Mikewa xaune Khaleel yyi yana sake bin dakin da yyi masa kama da ward din asibiti da kallo, Shuraim ya mike tsaye yace "You need something?" Khaleel yace "Why am I here?" Shuraim dai kallonsa yake bai ce komai ba, aka bude kofar ward din Junaid ya shigo, ganin Khaleel xaune ya nufesa yace "Ya jikin?" Khaleel yyi shiru duk da yana jin ciwo sosai a kirjinsa amma kokarin son ya tuno abinda ya faru yake but he couldn't arrive at anything, can kuma ya kalli agogo dake nuna tara saura ya kalli window ya gane tara na dare ne, sake kallonsu Junaid yyi a hankali yace "Why am i here?" Junaid ya kwantar da murya yace "You were sick..." Zayyad ne ya shigo ward din da sallama, Khaleel sae kallonsa yake har ya nufo gadon da yake xaune, Zayyad yace "Are you better now?" Khaleel yace "I think so, but me ya faru?" Zayyad yace "Idan ka ganka kwance asibiti ae ba sai ka tambayi me ya faru ba, you just have to understand that cutarka ce ta tashi" Khaleel yace "Na sani amma.... baya tashi without cause" yana kallonsa ya fadi haka, Zayyad yyi murmushi yace "Ka samu lfya, shi yasa kke questioning din mu haka, you've been unconscious tun sha biyu na rana har xuwa tara na dare, do you mind a cup of tea?" A hankali Khaleel yace "Meaning I've missed Juma'at prayer?" Zayyad ya gyada masa kai yace "Kayi a asibiti" Junaid ya karasa gun flask da cup dake ajiye ward din ya shiga hada ma Khaleel shayi, walking slowly Shuraim ya nufi kofa ya fita daga ward din, ba a kuma dau lkci ba sai gashi ya dawo tare da wani likita.... Khaleel bai iya ya sha shayin da Junaid ya hada masa mara xafi ba duk da yana jin yunwa, sosai kuma yake jin xuciyarsa na masa axaba kawai daurewa yake don idan ana sabo da ciwo ya ci ace ya saba da wnn ciwon, duk effort dinsa na son tuna abinda ya faru ya kasa tuna komai, iyaka dai ya tuna shi da Zayyad sun fita daga gida da safe kuma gidansu Junaid suka tafi, Zayyad ya ajiye masa kfruit salad a gabansa ganin ya ki shan shayin, a hankali Khaleel yace "Anjima xan sha, I am not feeling okay" Dauke Fruit din Zayyad yyi, Khaleel ya koma ya kwanta bayan ya sha magungunan da likitan da ya fita ya basa, nan da nan kuma bacci ya daukesa, sai kusan sha daya na dare Shuraim ya bar asibitin, Junaid da Zayyad kuma suka kwana tare da Khaleel. Karfe sha daya na safe Khaleel ya sake farkawa tun bayan tashin da yyi da asuba yyi wanka, sllhn ma a daki yyi duk da yyi niyyar fita masallaci amma ya kasa, bin ward din ya dinga yi da kallo ganin mutane sun kusa shidda a dakin, Ya mike xaune da kyar, Abba ya nufesa yace "Ya jikin Khaleel?" Yace "Na ji sauki, Ina kwana?" Abba yace "Lfya lau, no pains?" Khaleel ya gyada masa kai, Baffan Junaid ma ya karaso yyi masa sannu, Abba ya fita ward din tare da sauran mutanen dake ciki, bayan few minutes Khaleel na kallon Junaid yace "Zayyad fa?" Junaid xai yi magana aka bude kofar ward din Mami ta shigo tare da Heedayah da su Dinar rike da basket din abinci, Kallonta kawai Khaleel ke yi, without blinking, Mami tunda ta kallesa sau daya bata sake barin sun hada ido ba, ta karaso ta tsaya daga kusa da window, shi dai kallonta kawai yake, Heedayah ta nufesa ta tsaya daga gefen gadon tana kallonsa a hankali tace "Ya jikin ya Khaleel?" Sai a snn ya kalleta, ya d'an yi murmushi yace "Naji sauki" Su Dinar da Farida ma duk suka gaishesa ko wacce ta kasa karasowa kusa da gadon da yake, ya amsa ba tare da ya yrda ya kallesu ba, Kallon Mami ya kuma yi, cikin sanyin murya tace "How are you feeling now?" A hankali yace "Na ji sauki, Ina kwana" Tace "Lfya lau, Allah ya baka lafiya" daga haka ta nufi kofa ta fita daga ward din, Shi dai Khaleel kallonta yake har ta fita, Can ya juya ya kalli su Dinar, juyawa duk suka yi kamar hadin baki suka fita daga ward din gaba daya, Heedayah ta bi su da kallo haka ma Junaid, mikewa Junaid yyi ya bi bayansu, Heedayah ta juyo a hankali ta kalli Khaleel, hawaye ta gani makale idonsa, da damuwa tace "No kaga baka da lafiya plss, do not stress ur self" Cikin sanyin murya yace "Are they afraid of me??" Heedayah na kallonsa tace "No they are not, why will they be? Kawai suna tausayin ka ne sosai" Ya girgixa mata kai yace "No they are..." Da mayafin jikinta ta shiga goge masa idonsa tace "Aa, ba tsoron ka suke ba, duka suna tausayin ka ne, they are feeling your pain" Shiru yyi yana kallonta, ta sakar masa murmushin karfin hali, Ya sauke idonsa cikin raunin murya yace "Yanxu Mami ce mahaifiyata??" Wani murmushin ta kuma yi masa ta gyada masa kai tana kokarin boye nata hawayen tace "I am glad you are reuniting with ur family, even though basu sanka ba baka san su ba, they are all very happy to have you back in there mist" Kamo hannunta yyi yace "Meeting with you is something I will never forget till death Heedayah, ban taimake ki shekarun baya don in sake haduwa dake ba...." Murmushi kawai Heedayah ke yi tace "Destiny... Allah ya riga da ya rubuta ta dalilin ka xan hadu da iyayena kai ma kuma ta dalilina xaka yi reuniting da family dinka" Murmushin yyi shi ma yana gyada mata kai, har ranta taji dadin murmushin da yyi, lkci daya kuma ta ga murmushin yyi fading, a hankali tace "Are you okay?" Ya sauke idonsa yace "You know what?" Ta girgixa masa kai, yace "Ina tsoron kada family din ki su rabamu after knowing who i am" a sanyaye tace "No one is separating us in sha Allah" ya girgixa kai yace "Bbu wanda xai so 'yar sa tayi mu'amala da thug..." Da damuwa tace "You are not a thug, in sha Allah babu kai bbu mutanen nan daga yanxu..." Shiru yyi yana kallonta, tace "Yes, you have nothing to do with them, and justice shall prevail...." Bude kofar ward din aka yi duk suka juya Shuraim ya shigo da sallama... Kallo daya yyi masu ya dauke kai, ya karaso ciki ya ajiye ledan hannunsa, ya kalli Khaleel dake kallonsa yace "How are you feeling now" Khaleel yace "Alhmdllh na ji sauki" Shuraim yace "Allah ya kara lafiya" Khaleel ya amsa da "Ameen, thank you" Heedayah ta d'an kalli Shuraim tace "Ina yini ya Shureen" ba tare da ya kalleta ba yace "Lafiya" Kallon Khaleel yyi yace "Allah ya sauwake xan koma, later Dr xai yi discharging din ku" Khaleel yace "Toh nagode kwarai" Kofa Shuraim ya nufa Heedayah ta bi sa da kallo har ya fita, Kallon Khaleel dake kallonta tayi, ta d'an yi murmushi ta nufi ledan da Shuraim ya kawo taga gasasshen kaza ne sai tiriri yake, ta kalli Khaleel tace "In dibar maka?" Khaleel yace "Aa na ci abinci yanxu" plate ta dauka xa ta diba tace "Toh ni xan ci" Bai ce mata komai ba har ta gama diba ta juyo, still taga yana kallonta, a hankali yace "Ina son maki tambaya Heedayah" Tace "Ina ji" yace "Tell me, meye tsakanin ku da Shuraim din nan?" Heedayah tace "Nothing, kawai dai Abbansa guardian dina ne, and I was raised in there hope after parting with my parent" Khaleel yace "Amma kin san yana son ki?" Shiru Heedayah tayi tana kallonsa, can tace "So na kamar yaya kenan" Khaleel bai kuma ce mata komai ba, Junaid ya shigo ward din Mami na biye da shi. Karfe uku na yamma aka yi discharging Khaleel daga hospital, mota daya suka shiga tare da Junaid da Zayyad, Mami da Heedayah da wata sisters din Mami biyu da suka xo daga gombe suka shiga motar Mami... Junaid na xaune gefen gado a bedro dinsa yana kallon Khaleel da yaga kamar ko magana me yawa bai son yi, duk abinda junaid xai ce masa a takaice yake amsawa kuma baya kallonsa, ganin ya gama buttoning din shirt dinsa Junaid ya mike yana nuna masa turarurrukansa dake gaban mirror, ba musu Khaleel ya nufi gun turaren ya dau daya ya fesa snn ya juyo yana kallon junaid, junaid yayi masa murmushi yace "kayi kyau" Khaleel ya sauke manyan idonsa cikin sanyin murya yace "Thank you Bro" Mikewa Junaid yyi yace "Ana jiran ka...." Daga haka ya nufi kofa, Khaleel ya bi bayansa suka fita dakin, Heedayah ta bude kofar dakinsu kenan ganinsu ta tsaya, Khaleel bai yrda ya kalleta ba ya fara sauka stairs ta bi sa da kallo, Junaid ya juya ya kalleta ta dauke kanta da sauri, Tsaye Khaleel yyi bakin stairs yana kallon mutanen dake xaune parlon, Ganin junaid ya karasa cikin parlon ya bi bayansa walking slowly, nan saman carpet duk suka xauna, Mami sai kallon Khaleel take tana kokarin ganin hawaye bai sakko mata, Khaleel ya gaida mutanen dake parlon gaba daya cikin sanyin murya, ko wannensu dai kallonsa yake, Mami ta nuna masa wasu dattijai mata biyu a hankali tace "Ur aunties, kannin mahaifin ka kenan..." Khaleel ya kallesu amma ya kasa cewa komai, hawaye suke suma suna kallonsa, Mami ta nuna masa uncles dinsa, snn ta nuna masa sisters dinta biyu, ta nuna masa duk cousin dinsa dake parlon su ma, bbu wanda baya goge hawaye a parlon, Khaleel dai ya kasa cewa komai sai bin su yake da ido lkci daya shi ma hawayen ya kawo idonsa, Mami ta goge hawayen dake xubo mata ta nuna masa su Dinar tace "Ur sisters, sauran aunties dinka da uncle suna hanya" mikewa Farida tayi ta karasa kusa da shi ta rungumesa ta fashe da kukan dake cin ta cikin rawan murya tace "I am happy meeting with you big bro, Alhmdllh for reuniting with us..." Khaleel was just short of words, he can't believe all this are his families, bai ta6a tunanin yana da su a duniya ba balle su hadu watarana, sai yake ganin abun kamar a mafarki xai iya farkawa a ko da yaushe, Dinar da Amira ma kukan suke suna kallon Khaleel, Khaleel ya dafa Farida cikin sanyin murya yace "I am happy meeting with you too sis" *Sorry for the late update, mu hadu gobe da noon in sha Allah* Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mami na xaune compound din gidan ta tare da Abba da wata colleague dinsu, Abba yace "So now how do we go about it??" Barrister Khadijah tace "Kun san inda matsalar take ynxu?" Abba na kallonta yace "Aa sai kin fada" tace "An tafi station da shi Khaleel din tun farko, a can kuma yyi denying he isn't a Kidnapper so did Barrister Rahinah, so ynxu idan aka kai maganar station to get all the thugs arrested, first tambayar da xai fara biyowa shine... Khaleel isn't a Kidnapper how did he know that they are?" Shiru duk su Abba suka yi suka yi suna kallonta, Barrister Khadijah tace "The matter is so complicated..." Abba yyi murmushi yace "Noo, it's not Barrister, bbu complications.. Of course Khaleel wasn't a Kidnapper amma a cikinsu yake, a cikinsu kuma ya rayu ta dalilin rabasa da suka yi da iyayensa suka kai sa cikin nasu, don haka bai san kowa ba sai su, his being in their midst ba shine ke bada tabbacin yana harkan da suke ba... Baya tare da su a mugun abinda suke aikatawa, kuma sbda baya taren da su ma yasa xai tona masu asiri, ai a case din nan baxa mu nuna we have anything to do with Khaleel ba, baxa mu nuna akwai wani alaka tsakaninmu da shi ba, we will act as though he is a stranger...." Barrister Khadijah tayi murmushi tace "What if the Kidnappers have enough proof that will look as though he worked with them? That aside we need to think deep su ma dubarunsu yawa ne da shi, they can blackmail him just as they did few days ago....." Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "And ku bar cewa he wasn't a Kidnapper, he was, kuma kamar yanda Barrister ta fada baxa a rasa proofs din ba, may be images or videos of him a tare da su, tunda ai a da yana tare da su har ma yana contributing" Barrister Khadijah tace "Definitely kenan dole sai an tafi da evidence din baya tare da su police station before their arrest...." Abba yace "Exactly, and this evidence just have to come from Khaleel, a cikin evidence din kuma dole cikin 100% ya wanke kansa da kansa ko da 70% ne, sai ya bar mu da sauran struggles din wankesa...." Mami ta girgixa kai tace "Duk da haka Khaleel me laifi ne sosai a wajen hukuma, da ya tashi ya gansa cikin hoodlums abinda ya kamata yyi shine ya jawo hankalin hukuma tun farko, idan kuma baxai yi hakan ba sai ya bar cikinsu kawai...." Abba yace "But did you listen attentively to his story yesterday Rahinah?" Shiru Mami tayi tana kallonsa, Abba yace "on several occasions yayi yunkurin guduwa daga cikinsu, amma bayan kwana biyu sai kuma ya ga ya koma cikinsu, yana kuma jin kamar idan bbu su baxai iya rayuwa ba... Did you listen to that?" Mami ta kasa cewa komai, Barrister Khadijah na gyada kanta tace "Asiri gaskiya ne" Abba yace "Toh don haka mu baxa mu ga laifinsa ta nan ba unlike hukuma, yanxu abinda xai faru kawai evidence xai fito daga Khaleel, I will talk to him about it now, later in the evening kuma xa mu hadu" a sanyaye Mami tace "Toh Allah ya kai mu, Shuraim ya koma ne?" Abba yace "Jiya ya koma" Mami tace "Toh Allah ya tsare sa" Abba yace "Ameen, I sent you text daxu baki yi replying ba" Mami tace "Oh, I wanted calling you in maka bayani ne, baki sun yi yawa ne a gidan wllh" Abba yace "Ohk" Mami tace "I spoke to him about it this morning, sai yace min a daga xuwa wani lkci har a gama wnn case din" Abba yace "That's thoughtful of him, Allah ya kai mu, is he inside?" Mami tace "Ehh yana ciki" Abba yace "Alright then, xan koma great barristers sai mun hadu da yamman, but before then idan kun shiga ciki ku turo min Khaleel din" Mami tace "Toh shkkn I will" Bude gate aka yi duk suka juya, Mumy ce ta shigo tare da tawagarta har da Salima, ganinsu Abba ta karasa da fara'a inda suke zaune, Mami na kallonsu tace "Sannun ku da xuwa" Gaisawa suka yi, Su Sadiya da Baturiya suka gaida barrister ya amsa yana danna wayarsa, Mumy tayi kasa da murya tace "Ashe abinda ya faru kenan Hajiya Rahinah? Toh Allah ubangiji ya tsare iya haka, Allah ya rabamu da mugun ji ko mugun gani, muna taya ki murnan dawowan dan ki bayan shekaru masu yawa..." Mami tace "Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bada lada" Mami ta mike tare da barrister Khadijah suka yi ma Abba sallama suka wuce ciki tare da su Mumy da kawayenta. Mumy sai kallon Khaleel da ya shigo parlon ya gaishesu take, bai kara second daya a wajen ba ya fita daga parlon xuwa wajen Abba dake jiransa a waje, Mumy tayi tagumi tace "Allah sarki rayuwa, gashi mu bamu ta6a sanin kina da d'a namiji ba ma balle, da yake babu hakki sai gashi bayan an cire rai, toh Allah ya bar mu da 'ya yanmu dai har mutuwa" Mami dake parlon da su Hajiya Zuwaira da step mum din Sudais dai bata tanka ta ba, Mumy tace "Toh an samu an sa ranan Junaid din kuwa? Don barrister ba gaya min xai yi ba wllh" Mami tace "Tukunna dai" Mumy ta d'an saci kallon Sadiya basu dai ce komai ba. Khaleel ya xauna saman kujeran dake facing Abba ya gaishesa, Abba ya amsa da murmushi yace "Ya karfin jikin?" Khaleel yace "Alhmdllh na ji sauki" Abba yace "Toh maa sha Allah, Allah ya kara lafiya" Cikin few minutes Abba ya gama magana da Khaleel ya gaya masa duk yanda xa a yi snn suka yi sallama ya wuce, Khaleel ya koma ciki yana kara naxarin abinda Abba yace masa. Da yamma misalin karfe biyar Khaleel ya nufi kofar fita parlor bayan ya sallami Mami, sai da ya kusa kofar Mami tace "Be careful.... and pray, Allah ya tsare ka" juyowa yyi yace "In sha Allah...." a hankali Dinar tace "Allah ya tsare" Bai juyo ba yace "Ameen" Heedayah dake xaune dinning ita da Farida suka bi sa da ido su ma, kasa daurewa Heedayah tayi ta mike ta bi bayansa, babu wanda yace mata komai har ta fita parlon, parking space ta ga ya nufa, tace "Ya Khaleel" ya juyo ganinta ya tsaya, ta karasa inda yake da damuwa tace "Where are you going to?" Murmushi ya mata yace "Xan fita ne, anjima xan dawo in sha Allah" tace "Xaka fita xuwa ina? Kana son su ganka ne kuma?" Yace "Aa ba inda xa su gan ni xan je ba" tace "Toh xan bi ka, should I go and tell Mami?" Yace "No" ta marairaice tace "Plss mana, I don't want anything to happen to you" yace "Nothing will happen to me Heedayah" shiru tayi tana kallonsa, yace "To rakani gun motar sai ki koma ciki and pray for me" a sanyaye tace "In sha Allah" Murmushin sa me kyau yyi mata, tace "Da motar yaya xaka fita?" Yana tafiya tana biye da shi yace "Ehh" Ta madubi Junaid dake warming din motar tasa ma yayansa yake kallonsu har suka iso, sai a snn Heedayah ta gansa, ta wara ido tace "Lahh ashe kana nan Yaya" yace "Ina nan" Fitowa Junaid yyi daga cikin motar yana kallon Khaleel, Khaleel ya shiga motar, Junaid yace "Allah ya tsare" Khaleel ya amsa da "Ameen, Thank you" sai da Khaleel ya fito daga parking space Mai gadi ya bude masa gate snn Heedayah ta daga masa hannu a hankali, ya gyada mata kai, bayan ya fita compound din suka koma cikin gida tare da Junaid tana kallonsa suna dai dai entrance din shiga parlon tace "Yaya wai me kke shafawa a lips din ka?" Yace "Abinda kike shafawa a naki" dariya tayi yyi murmushi ya bude kofar ya shiga ta bi bayansa. Har Khaleel ya isa gidan oganninsu yana communicating da Zayyad ta text message, yyi parking a waje yyi deleting duk messages din snn ya nufi gate ya fiddo da spare key dinsa na gidan ya bude ya shiga ciki, direct entrance din shiga babban parlon ya nufa ya bude kofar parlon, duk suna xaxxaune parlon, wasun su na karta, ga giya ko wannensu na sha a glass cup, wasu kuma na smoking cigarette kida na tashi a speaker, Zayyad dake xaune saman kujera shi ma hannunsa rike da cigarette ya dinga kallon Khaleel kamar yanda duk sauran mutanen parlon ke kallonsa, Oga Bala ya kyakyace da wani mahaukacin dariya yace "I told you all a xuba masa ido xai dawo, to gashi ya dawo..." Wani dariya Oga Arne ya fashe da shi ma yana kallon Khaleel da kyau yace "Da ina ka tafi? Ka xata har karshen rayuwarka xaka iya rabuwa da mu ne? Ko dama kana da wasu a duniyar nan bayan mu? Ni in particular...." Xaunawa Khaleel yyi saman kujera yana kallonsu gaba daya, Oga Manga yace "Ka saduda ka gama boye boyen kanka ka dawo kenan? Lallaba ka da ake ya fara wuce gona da iri, xa mu dau mummunan mataki a kan ka wllh" Oga Bala ya nufi Khaleel ya dago kansa yana kallonsa da jajayen idonsa cikin katon muryarsa yace "Ka dawo daga raina mana hankalin da kke?" Calmly Khaleel yace "Ehh" Oga Arne yace "Good... akwai operation a Abuja, dawowar ka kawai muke anticipating kuma gashi ka dawo, so we are setting off today...." Khaleel ya girgixa kai yace "U are mistaken then...." Lkci daya ya mike yana kallonsu gaba daya fuskarsa a tamke yace "Na xo ne in sanar maku cewar daga yau na bar wnn mummunan harka da ku ka dulmiyar da ni a ciki tun ina d'an yaro, na bar wnn harka da ku ka cusa min a xuciya ba da son raina ba, snn Arne, Manga da Bala I want you all to put this at the back of ur mind that... in sha Allah karshen ku ya xo... Sannan kananun kwarin da ke tare da ku su biyo baya...." Tashi Oga Arne yyi yana masa wani kallo cikin tsawa yace "How dare you Khaleel? Mu kake ma magana haka? Mu kake kira ma karshe??" Khaleel yace "Eh kai, Manga da Bala...." Manga ya mike a fusace ya nufesa ya shakosa da karfi yace "A duniyar nan kana da sama da mu ne kake ikirarin xaka ga karshen mu? Har kai kana da gata a duniyar nan banda wajen mu, uban me kake takama da shi, dama tsintacciyar mage bata mage, an kawo ka cikinmu kana da shekara uku baka da gata baka da kowa haka muka ja ka jiki muka fifitaka fiye da kowa, muka jajirce wajen ganin an bar ka kai daya tak kayi boko a cikinmu, Wani hakuri ne ba mu yi da kai ba a shekaru talatin din da suka wuce, fita operation da kai sai ka bata ma kowa rai sau tari kayi spoil din mana show don ma kana yi kana shakka, bindigar da aka mallaka maka ba shi da amfanin da aka baka yyi maka sai na harbin Iska, sau nawa kake freeing abducted or kidnapped victims dinmu ka ja mana uban asara, sau nawa sbda kai asirinmu ke kusa tonuwa sai dai ka fitar da mu da kwakwalwarka, amma duk da haka muna ta tausan oganninmu sbda ba kowa Allah ke ba wa ba intelligence din ka ba, da ba don Arne ba da Oga Salahu ya dde da harbe ka har lahira shekaru goma da suka wuce, bayan ka ba wata yar minister da muka yi kidnapping damar guduwa wanda hakan ya kusa tona mana asiri muka shiga gararin rayuwa, ta dalilin ka sai da marigayi Oga salahu ya harbe Arne a kafa wanda har yau Arne yana samun matsala da kafar, Kai har ka isa yanxu ka xo kace xaka bar mu bayan duk sadaukarwa da muka yi maka da kokarin ganin ka rayu cikin mu shugabanninmu basu cutar da kai ba?? Wllh kayi kadan Brainiac, kayi kadan ka bijire mana ka watsa mana kasa a ido, gwara in tarwatse kanka, gwara in kashe ka har lahira...." Yana fadin haka ya xaro bindigarsa daga aljihunsa da sauri, kusan a tare suka yi hakan da Khaleel da ya xaro nasa bindigar shi ma yana nuna ma Manga, Arne dake ta wani huci ya sa hannu ya sauke bindigar manga cikin kaushin murya yace "Bar shi Mangaaa, bar shiiii" Khaleel bai fasa nuna ma Manga tasa bindigar ba, Cikin tsawa Arne na nuna Khaleel yace "Mu xaka ci ma amana? Mu xaka kawo ma tashanci??" Khaleel yyi wani murmushi yace "Sai na tashi daukan ma mahaifina fansar kashesa da ku da mukarrabanku ku ka yi xa ku san tashanci" da shock duk suke kallonsa, Khaleel ya gyada kai cike da tsanarsu yace "Ku ka rabani da Mahaifiyata ina d'an shekara uku ban san kaina ba, ku ka kawo ni cikinku, ku ka lalata min rayuwa, ku ka cuceni, kuka koya min mugun hali da mugun nufi, Billah karshen ku ya xo a duniya, daga yau ina me sanar maku da babban murya cewar idan ku ka sake bibiyana tare da abokina Zayyad kuna ci gaba da tursasa mu kuna cusa mana mugun tunani da mugun nufi a kan mutanen da basu ji ba basu gani ba za ku kare rayuwarku daure a kurkuku, na har abada....." Bude baki duk suka yi suna kallonsu, tuni Zayyad ya mike ya xaro nasa bindigar shi ma yana nuna ma Oga Manga, Khaleel na huci ya nufi kofa yana tafiya da baya yana nuna su da bindiga haka Zayyad ma yyi har suka fita daga parlon still pointing there gun toward them, a haka su Khaleel suka isa gate ta baya har suka fice daga gate din, da gudu suka shige mota a tare, Khaleel ya tada motar ya figa ganin su Manga sun fito a guje suka hau harbin tayoyin motar amma tuni Khaleel yayi masu nisa ya karya wani corner da motar.... Zayyad ya sauke ajiyar xuciya yace "It was successful" Khaleel bai ce komai ba sai gudu yake yana kallon madubi to be sure basu biyosa ba har dai yyi nisa sosai snn ya sauke wani ajiyar xuciya, Zayyad ya kunna record din da yyi da wayarsa yana murmushi.... Mami ce xaune living room tare da su Dinar da wata aunt din Khaleel sai sisters din Mami suna sauraron record din wayar Zayyad dake hannun Mami, sae da record din ya kare, kowa na parlon ya sauke ajiyar xuciya, ko wanne jikinsa yyi sanyi, Mami ta d'an yi murmushin karfin hali tana kallonsu Khaleel tace "Alhmdllh, it's a great job you two did, ku wuce sama kafin ku ci abinci" Khaleel ya d'an yi shiru sai kuma yace "Ummi baxa mu iya tafiya can gidana ba?" Dinar da Amira suka xaro ido, aunt dinsa Aunty Nafisa tace "Wani gidan kuma Aliyu, a yanxu ai baka da wani gidan da ya wuce nan, you just have to feel at home kaji" sister din Mami tace ce "Lallai kam, this is ur only home for now" Mami na kallonsa tace "You are not feeling at home here right?" Khaleel dai bai ce komai ba, a hankali Mami tace "Look at me" Kallonta yyi tace "Nan ne gidanku... wancan gidan kuma ba naka bane yanxu, beside you both aren't safe anymore to be thinking of going out" Shiru Khaleel yyi bai dai ce komai ba, Mami tace "Ku wuce sama, xa a kai maku abinci" mikewa yyi suka wuce dakin Junaid tare da Zayyad. Heedayah da Farida suka kawo ma kowa dake parlon abincin da suka gama girkawa tare da maid dinsu, Mami tace "Ku kai ma su Zayyad a sama, Su Umma ma suna dakina ku kai masu" Komawa kitchen din suka yi, Bayan Farida ta hada abincin Khaleel da Zayyad a tray ta sa ruwa da komai a kan tray din ta kalli Heedayah tace "Ki kai masu ya Zayyad din sama" Heedayah tace "Ki kai masu sai in xuba ma su Umma" Farida tace "No dont worry ki kai ni xan xuba masu" Daukan abincin Heedayah tayi ta fita kitchen din ta wuce sama, ajiye tray din tayi kasa bayan ta isa kofar dakin Junaid ta bude kofar snn ta duka ta dau tray din ta shiga dakin da sallama, Khaleel ya shiga buttoning shirt dinsa da ya cire button din yana kallonta, tun da ta kallesu sau daya ta dauke kai ta ajiye tray din abincin a saman carpet din dakin ta mike tace "Ina yinin ku?" Zayyad yace "Sannu da aiki" tace "Nagode" ta d'an kalli Khaleel ganin kallonta yake, ta d'an yi murmushi tace "Welcome" yace "Thanks, ke kika yi girkin?" Tace "Ni da Farida da Zainab" Yace "Toh Sannun ku" juyawa tayi ta nufi kofa ta nufi kofa ta fita daga dakin, Zayyad na kallonsa yace "I wish xa a baka auren yarinyar nan, nasan ba lallai ciwon ka ya dinga tashi ba kuma...." Khaleel ya kallesa bai dai ce komai ba, Zayyad ya girgixa kai yace "But I don't think a governor will give you his daughter hands in marriage, duk wanke kan da xa ayi kuwa" Shi dai Khaleel bai ce masa komai ba still. Khaleel na dakin Junaid har bayan isha yana wasa da Fadil da Affan din Amira, Zayyad tun da aka yi isha bai shigo ba, Bude kofar dakin aka yi ya daga kai, Heedayah ce tsaye daga bakin kofar tace "Ya Khaleel wai ka sakko downstairs" bata jira cewarsa ba ta juya ta wuce, tare da su Fadil ya sakko, ya tadda Dinar da Amira sai Farida da wata cousin sister dinsa Sumayya xaune parlon, sai kallonsa Sumayya take har ya shigo parlon ya xauna su Fadil na makale da shi, Amira na murmushi tace "Kana ta xaune kai kadai daki" Khaleel yyi murmushi yace "Gashi muna hira da boys" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Washegari da safe misalin karfe tara Heedayah da Farida da Maid din Mami na serving din bak'in dake parlor breakfast na soyayyen Irish, kwai, shayi da farfesu with bread, yawanci duk cousins da aunt din Khaleel ne da kids dinsu a parlon, kana ganinsu dai kasan babu ta inda suka hada hanya da talauci, Mami ce ke ba su Farida breakfast din su kai parlor ita tana tsaye kitchen din, bude kofar parlon aka yi Kaka ta shigo sakale da katon jakarta ta yafa katon mayafi, ga sarkan zinarinta sai sheki yake a wuya da dankunnensa, tsaye tayi bakin kofar ta dinga bin mutanen parlon da wani kallo, can tace "Ya haka kamar ana yunwa, tun fa daga iyafot motocin sojoji dake bayanmu ke jiniya ana sanar da jama'a xuwanmu ana ta bamu hanya har muka shigo anguwar nan, ku baku ji bane?? Yanxu ta ina xa mu bi mu wuce ta nan duk dankali da kwai, matar gwamnan kano da mu ne fa ke tafe tun daga kano, a jirginsa na kansa kuma aka dauro mu aka kawo mu nan garin, muna dira iyafot motocin sojoji suka hau jiniya ana sanar ma kowa ana ta bamu hanya a titi, to kuma mun shigo gida bbu hanyar wucewa don Allah" Mami ce ta fito daga kitchen jin muryar kaka, da fara'a tace "Sannu da xuwa kaka" Ta bayan kujera kaka ta bi ta tana taku dai-dai ta wuce sama, Duk occupant din parlon suka bi ta da kallo, Yakumbo ta shigo parlon ita ma tana kare ma parlon kallo ta rike ha6a tace "Al'adar bahaushe dai ba kyau, komai dai ace sai anci abinci, gidan mutuwa abinci, gidan biki abinci, gidan suna abinci, daga bayyanar yaro ma an xo jaje an hau cin abinci, to mu dai rabon mu da abinci wllh tun jiya da daddare, yau da safe ma da kaji muka karya muka sha yagwat muka kamo hanya abun mu" Mami dai tsaye tayi tana kallonta ta kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, Ammin Heedayah da frnd dinta na tsaye balcony ko wannensu ya kasa shigowa, Yakumbo ta bi hanyar da kaka ta bi sai kuma ta juyo da sauri tana kallon mutanen parlon tace "Ina kwanan ku?" Few daga cikinsu ne kadai suka amsa, tace "Ya muka ji da wnn abun al'ajabin?" Bbu wanda yace mata komai, tace "Toh Allah ubangiji ya raba mu da duniya lafiya, ya kare 'ya yanmu da jikokinmu da tatta6a kunne da hihihin, su kuma wa enda suka cuci wnn yaro Allah yyi kasa kasa da su ya tsine masu albarka, ya bi masa hakkinsa, tunda iyayena suka haifeni ban ta6a jin irin wnn labarin ba sai jiya, ni dai dama ina ganinsa nace yyi kama da yan kinnafas to ile ga maganata nan ashe D'an kinnafa dai Rahinah ce ta haifesa, kuma duk wanda ya ta6a xaginta a kan d'an nan nata sai Allah ya saka mata ya bi mata hakkinta don ba ita ta aikesa ba, ba ita ta saka sa ba" daga haka Yakumbo ta wuce sama, sai a snn Ammi suka shigo parlon, Mami tayi murmushi tana welcoming dinsu, Ammi ta xauna nan parlon suka gaisa da mutanen dake ciki snn suka wuce sama su ma. Heedayah da Farida ne suka kai masu breakfast sama suka yi masu sannu da xuwa, Yakumbo ta sa Farida ta hada mata shayi tana kallonta tace "Toh ina shi d'an uwan naki yake?" Farida tace "Yana nan" Kaka tace "To yanxu ya isilin dukiyoyin jama'ah da ya kwamushe fa" Farida dai bata ce komai ba lkci daya jikinta yyi sanyi, Heedayah ta hade rai, Kaka ta fara matsar kwalla tace "Haka kawai a rabaka da d'an ka tun yana dan yaye a tafi a daurasa a muguwar harka, anya mutanen nan xa su wanye lafiya da duniya kuwa? Toh yanxu ya xa mu yi mu rabasa da wnn mugun hali da yake yi, sun fa riga sun cucesa halin ya shigesa, sai dai kawai ya yaudare mu yyi tuban muzuru, wataran yana iya koma tunda ya ji dadin rike makudan kudi, mu ma kanmu ba wai tsira muka yi ba, ga gwalagwalai na rataye a wuya da kunne, to ni dai ba ruwana ya xo mu gaisa inyi ta kaina in wuce gidan Amadu" Tagumi Ammi tayi bata iya tace komai ba, Heedayah ta mike ta fice daga dakin hawaye har ya kawo idonta, Mikewa Farida tayi ta bi bayanta ita ma, Ammi tayi kasa da murya tace "Haba kaka?" Kaka ta juyo da sauri tace "Haba me?? ban tsine ma shegun da suka sa shi a harkan bane xaki ce min haba? Meye nawa daga fadan gaskiya? Wllh idan bamu yi taka tsantsan ba sai ya iya yashe mu cikin dare" Yakumbo tace "Toh uwar me xai yi da gwalagwalanki na karya shi da ya saba kwamushe manyan motocin jama'ah masu tsada da gidajensu? Meye kuma gantalallun gwalagwalanki" Mikewa Ammi tayi ta fita daga dakin ita ma ranta bai mata dadi ba, Kaka ta ta6e baki tace "Ni dai ba ruwana, to gidan uwata ce nan din da baxan wuce gidan Amadu ba dama? Daga cewa xanje in gaida Amadu sai cibi ya xama kari? Ita kuma waccan figaggiyar kamar kazar Hausa ni ta banke ma kofa wai ta fita, to wllh Amadu ta banke ma kofa ba ni ba, ina ruwanta da d'an mutane da xata ji haushi don na fadi gaskiya a kansa, ko meye hadinta da shi, kuma ai dole dama sai mun hada masa da rokon Allah idan kuwa ba haka ba muna nan mun saki baki xai ci gaba da danyen aikinsa a boye, Allah dai ya saka masa amma kam an cucesa wllh, Amadu dai yace yau yan sanda xa su je su kwashe sauran shegun yan uwan nasa" Yakumbo tace "Toh ai banda uwarsa mutuniyar kirki ce dama babu abinda xa mu xo yi gidan nan mu ja ma kanmu salalan tsiya, barin ma ya ji daga gidan gwamnati muke, ni duk a tsorace nake ma wllh...." Kaka tayi tagumi tace "Ga mu ga Allah dai" Asiya kawar Ammi sanin halinsu bata ce masu uffan ba sai operating waya take, Bude kofar dakin aka yi Mami ta shigo Khaleel na biye da ita, daga kaka har Yakumbo suka yi tsit sai yan idanuwa, Mami ta xauna, shi kuma ya duka nan gabansu ya gaishesu da ladabi, babu warce ta yrda ta hada ido da shi, kaka sai cewa take "Sannu d'an nan, yau dai na takura uban Heedayah ya ara mana jirginsa mu taho dai kada Rakiya ta kullace mu" Yakumbo tace "Wllh kuwa, Allah ya bi maka hakkin ka, Allah ya saka maka, an xalunce ka kam, an bata maka rayuwar ka" Kuka Yakumbo ta saki, Kaka ma ta fara matsar kwalla tace "Ni da xa a kai ni wajen 'ya yan shegun sai in ji dalilin da suka daukesa bayan kashe ubansa da suka yi, nasan xa su fada min, tun muna yara ake mugunta a duniya har yau ba a saduda ba, wnn tsiya da me yyi kama???" Mikewa Mami tayi ta fita, Kaka na share idonta tace "Tashi ka tafi kai ma, Allah ya saka maka kawai" Mikewa Khaleel yyi ya fita daga dakin, Yakumbo na kallon kaka tace "Toh yanxu meye hukuncin uban dukiyoyin da ya tara ta muguwar hanya?" Kaka ta gyara xama tace "Hukuncinsu a raba ma marayu kawai, ga dai mu nan da yawa a duniya ba iyaye tun muna yara" A ranan yawanci relatives din Khaleel dake Abuja duk suka koma, gidan ya rage daidaikunsu da xa su koma gobe. Da yamma Ammi da frnd dinta na xaune dakin Mami, Hajiya Zuwaira da Aunt din Khaleel ma duk suna dakin, Yakumbo da kaka na can dakin da suka fara sauka bbu wanda ya tafi inda suke balle yaji kayan takaici, Aunt din Khaleel tayi breaking din silence din dakin tana kallon Mami tace "Toh Allah ubangiji yasa mu ji alkhairi, Allah ya baku nasara" Ammi tace "Ameen" Hajiya Zuwaira tace "Ae tunda aka samu aka cafkesu gaba daya anyi mai wuyar ai, amma shi abokin Khaleel din ya isilinsa ynxu?" Mami tace "Barrister yace ya bar garin, yanxu haka yana Bauchi" Hajiya Zuwaira tace "Toh amma a record din ai shi Aliyu ya ambaci sunansa, kinsan kuma dole a kotu xa a bukaci ganin abokin nasa da ya ambata" Mami tayi murmushi tace "Barrister ya so yanke wajen nace kar yyi, idan suka bukaci Zayyad a court din xa mu kirasa ya xo, kuma xa mu yi iya kokari na ganin mun wankesa shi ma idan Allah ya yrda, sure xai yi iya yiwuwa yyi xaman gidan yari na kankanin lkci but not life imprisonment, shi ma Aliyun hakan xai iya faruwa da shi" Hajiya Zuwaira tace "In sha Allah kotu xata yi masu adalci da taimakon ku, hakan ma baxai faru ba" Mami dai bata ce komai ba, A hankali Ammi tace "Allah xai baku nasara in sha Allah" karfe biyar kaka ta bude kofar dakin Mami tace "Toh Rakiya mu dai xa mu wuce gidan Amadu mu kwana" Mami tace "Baxa ku kwana nan ba kaka?" Kaka tace "Mu kwana nan kuma? Oh oh gwara mu je gidan Amadu nan jama'ah sun maki yawa, ga dai motoci can waje duk inda xa mu a Kaduna xa su kai mu ai" Ammi tace "Baxa ku bari mu tafi can din gobe ba daga can sai mu wuce?" Kaka tace "D'a na ne fa Amadun? In xo har Kaduna in kasa xuwa gidansa in kwana, lalacewata bata kai haka ba Aisha, mu dai ba mun xo mun jajanta abinda ya faru ba, kuma gashi sai wani hade rai mutumin yake kamar baya son ganinmu a gidan mun rasa me muka masa, ba gwara mu san inda dare yyi mana ba kada mu je abu ya lalace mana tsakar dare a shiga uku" bbu wanda yace mata komai dakin ta juya ta fita, Mikewa Mami tayi ta fita tayi masu sallama ita da Yakumbo, Mami na kallon Heedayah dake parlor tace "Collect the bag for them" Heedayah dai bata ce komai ba, Farida tuni ta dauke kai dama, can dai Heedayah ta mike babu walwala ta amshi ledan hannun yakumbo, xata amshi jakar kaka kaka ta makale a hammata tace "Aa bar min kayana, kina hararana xaki wani amsar min jakata ki saka min mugun abu, meye hadina dake banda kawai muna mutunci da ubanki ya takura sai na dawo gidansa da xama kwata kwata, tun fa maganar da aka yi daxu a daki shine take ji kamar ta caccake mu da wuka" Yakumbo ta nufi kofa Kaka ta bi bayanta, Mami dai ta bi su da kallo har suka fita sannan ta koma sama, Sumayya na kallon Farida tace "Who are they?" Farida tace "Yan uwanmu ne" Sumayya bata kuma cewa komai ba sae ta6e baki da tayi. Khaleel na xaune compound din gidan tare da Junaid suna hira sama sama, su kaka suka fito tsakar gidan, da sauri kaka ta dauke kai ta nufi gate, Mikewa Junaid yyi bayan ya ajiye glass cup din drink dake hannunsa yana kallon Khaleel yace "Mu je kayi masu sallama" Mikewa Khaleel yyi ya bi sa, Sojojin dake bakin gate tsaye suka ba su Yakumbo hanya suka fita gate din, waje ma sojojin tsaye ne sai lafiyayyun motoci biyu da motar sojoji a baya, ganin Khaleel Yakumbo tace "Ae da baka ba kanka wahala ba d'an nan" Kaka na kokarin shigewa cikin mota Junaid yace "Xa ku tafi gidan Abba ne Kaka?" Kaka ta shige motar tace "Ehh Junaidu gwara mu je can din dai kawai ya fi mana" Yakumbo ma ta shige motar, Khaleel yyi kasa da kai yace "Allah ya tsare" kaka ta daga masa hannu bibbiyu tace "Ameen" Yakumbo tace "Sai ka dage da Sallan dare kana rokon Allah kaji?" A hankali Khaleel yace "In sha Allah" Kaka ta fixgo ledan Yakumbo dake hannun Heedayah da ta wani hade rai murya can kasa tace "Mayya kawai" juyawa Heedayah tayi ta shigewarta cikin gida, Junaid na murmushi yace "Amma xa ku dawo nan ko?" Kaka tace "Aa mun gama da nan, ita dai Aisha idan ta gama galantoyinta sai ta same mu gidan Amadu, ai gobe Amadun kano yace mu dawo, kaga baxa mu tsallake umarninsa ba ai" Junaid yace "Toh shkkn, sai mun xo" Kaka tayi kasa da murya tace "Kai da wa??" Junaid yace "Xa mu xo tare da Khaleel in sha Allah" Yakumbo tace "Ehh to ai da kyau hakan, amma fara yawo ba nasa bane yanxu, killacesa xa a dinga yi har tsoron Allah ya shigesa, abinda ma Amadi yace xai xo nan tare da gwamnan Kaduna su gaishesa su jajanta masa, ai ba sai yaje kano ba, mu ma xa mu dawo idan Allah ya yrda" Kaka tace "Ai shine naga...." Khaleel dai kallonsu kawai yake, Kaka tace "Gaskiya jini ba wasa bane, sai da suka tsaya a tare naga mugun kamar da suke da Junaidu, har lotsawan kumatun Allah sarki" Murmushi Junaid yyi, Khaleel yace "Allah ya kiyaye hanya" A tare Yakumbo da kaka suka ce "Ameen" daga haka ya juya ya koma ciki, Kaka tayi kasa da murya tana kallon Junaid tace "Kace ma Rakiya tayi ta tashi cikin dare tana sllh tana kuka tana nema masa gafara wajen Allah, na manta ban gaya mata ba wllh, snn tayi ta masa nasiha cikin dubara akan daukan abinda ba hakkinka ba, snn tayi ta nuna masa illar yin haka, ta dinga nuna masa kudi a nan duniya ake samunsa kuma a bar sa a mutu" Junaid bai iya yace mata komai ba, Yakumbo tace "Driver mu je magariba nayi, Allah dai ya kai mu lfya" Driver ya ja motar, na sojoji na biye da su a baya suka bar layin. Bayan isha Khaleel na xaune parlor idonsa a kan wani movie da ake yi a tv, xamansa a parlor umarnin Mami kawai ya bi amma bai son xaman cikin parlon, Mami kuma bata son yana xama shi daya a daki ne, he is always silent snn bashi da walwala, Junaid kuma ya fita, Farida da Sumayya ne parlon suna labarin movie din da ake yi kasa kasa, Farida ta kallesa tace "Yaya ko ba haka bane?" Kallonta yyi snn ya kalli Tv din, can yace "Ban san me ku ke cewa ba" Sumayya tayi murmushi tana fari da ido tace "Labarin film din mu ke yi" yace "Ohk but I don't know about the film" bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da kallonsa, Sumayya tace "To a kawo maka abincin yanxu?" Kallonta Khaleel yyi yace "Aa" Heedayah dake xaune dining ta kallesu ta dauke ido ta tabe baki ta ci gaba da cin abincin gabanta, bayan few minutes Khaleel ya mike ya tafi dinning din ya ja kujera ya xauna, Heedayah bata kallesa ba tana ci gaba da cin abincinta, Tuni Sumayya ta daina kallon da take yi, ta shiga xaga parlon da idanuwanta kamar me neman abu, Khaleel na kallon Heedayah yace "Baki bani abinci ba" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ba naji ance xa a kawo maka ba" Bai ce komai ba, ta dago kai tana kallonsa, tashi tayi ta tafi kitchen ba a dau lkci ba ta fito rike da plate din abinci, a bakin kofar kitchen din suka hadu da Sumayya ta ba Heedayah hanya snn ta shiga kitchen din, Heedayah ta ajiye masa abincin a gabansa a hankali yace "Thank you" Fitowa kitchen Sumayya tayi rike da nata abincin ta nufi dinning ta xauna, Farida ta saki baki tana kallonta, A hankali Khaleel ke cin abincin gabansa, Heedayah dake xaune dinning din sai ta ma kasa ci gaba da cin nata, Lkci daya Khaleel ya tashi ya dau plate din abincinsa ya bar dinning din. Sha daya saura na dare Mami ta shigo dakin Junaid, Khaleel na kwance yana kallo Junaid kuma yyi bacci, ya mike xaune ganin Mami, Mami ta ja kujera ta xauna tana kallonsa tace "Baka yi bacci ba" Yace "Eh ban yi ba" tace "Ka ci abincin kuwa?" Khaleel yace "Na ci" Mami tace "Ohk, kana ji na" yana kallonta yace "Ina ji" Tace "Da mun so sai after this case sai ku tafi da aunt dinka can gombe wajen family din Abban ka, kayi sati daya a can, amma bayan xaman court na gobe sai ku wuce da Aunty Nafisa da Sumayya" Khaleel ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Toh Allah ya kai mu" a hankali Mami tace "Ameen" shiru ne ya biyo baya, Mami tace "Aunty Nafisa autarsu mahaifinka ce, Sumayya kuma daughter dinta ce, but naga kamar baka saki jiki da ita ba" Khaleel yace "Ita wa?" Mami tace "Ita Sumayyar" Khaleel yace "Mami to me xan mata" Mami tace "The mother suggested...." Da sauri yace "Suggested what?" Mami tace "A hada ku aure da ita sbda situation da ka tsinci kanka" Khaleel ya girgixa kai yace "Ni ina da warce nake so Mami" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Mami na kallonsa tace "Wacece ita?" Khaleel ya sauke idonsa yyi shiru" tace "Speak ur mind" Ya kalleta yace "Heedayah" kasa ce masa komai Mami tayi ta kura masa ido, bayan wani lkci ta mike tace "Sai da safe" a hankali yace "Allah ya tashe mu lfya" Daga haka ta nufi kofa ta fita. Washegari karfe uku saura Ammi ta iso gidan Mami, bayan sun gaisa Mami ke tambayarta su Ashnaah, Ammi tace "Suna gida" Farida ce ta kawo ma Ammi drink da ruwa ta bar parlon, Ammi tace "Daxu Barrister ke gaya mana anyi adjourning case din xuwa sabon wata da xa shiga" Mami tace "Ehh in sha Allah, nan da sati uku idan Allah ya kai mu" Ammi tace "Toh Allah ya bada nasara, ya kai mu lkcn lafiya" Mami tace "Ameen" Heedayah ta shigo parlon ta duka kasa a sanyaye ta gaida Amminta, Ammi ta amsa sannan ta mike ta bar parlon, Mami tace "Xa ku tafi tare da ita ta gaida Abbanta tun da bbu abinda take a nan kawai Hajiya" Ammi tace "Ku baxa ku kawo mana ziyara ba?" Mami tayi murmushi tace "Bayan case din nan idan Allah ya yarda" Ammi tace "Toh Allah ya bada nasara, Ina Khaleel din?" Mami tace "Sun wuce Gombe tun daxu da aunt dinsa amma kwana biyu yace xai yi ya dawo" Ammi tace "Toh Allah ya dawo da shi lfya" Mami ta amsa da "Ameen, su Kaka suna lafiya?" Ammi tace "Lafiya lau, nan da yan mintuna xa mu koma kano in sha Allah, shi sa na xo Sallamar ki" Mami tace "Toh bari in ma Heedayah magana ta hada kayanta" Ammi tace "Farida fa ita baxata ba?" Mami tace "Ai tana xuwa makaranta Hajiya" Ammi tace "Ayya, toh shkkn" Sama Mami ta wuce ta bude dakinsu Heedayah ta shiga, Mami na kallonta tace "Idan xa ki sake ranki ki sake ki shirya kayan ki xa ku tafi kano da Ammin ki yanxu" Lkci daya hawaye ya kawo idonta da damuwa tace "Mami ban son xuwa kanon fa, don Allah kice mata ina xuwa islamiyya" Mami ta hade rai tace "Toh me kike yi a nan din da baxa ki shirya ku wuce ba, yau sati nawa da yin candy dinki, you are sitting doing, islamiyyar xuwa kike balle kice ace kina xuwa? what's wrong with you going to greet ur father?? Malama kar ki bata masu lkci ki hada kayanki ke take jira" Daga haka Mami ta fita dakin, Hawaye ya gangaro idon Heedayah, Farida dai sai kallonta take bata ce komai ba don tasan me yasa Heedayah bata son tafiya, a sanyaye Heedayah ta mike ta hau hada ironed cloth dinta a daya daga travelling bag dinta, A hankali Farida tace "What's making u Sad Heedayah?" Kallonta Heedayah tayi tana goge hawayen da ya ki tsaya mata amma bata ce komai ba, sai da Mami ta sake shigowa dakin tace "Minti kusan ashirin har yanxu baki gama hada kaya ba Heedayah, me ke damun kanki?" Heedayah ta dau mayafinta ta yafa tana janye da trolley dinta, Mami ta juya ta fita, mikewa Farida tayi ta rungumeta tace "Allah ya tsare hanya, when will u be coming back?" A hankali Heedayah tace "Ai ya Khaleel yace kwana biyu xai yi ko?" Farida tace "Uhm..." Heedayah tace "Nima kwana biyu xan yi in dawo" Murmushi Farida tayi tace "Toh Allah ya dawo mana da ku lfya" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Ameen" tana jan trolley din ta nufi kofa ta bude ta fita, tsaye ta tarda Mami a corridor tana jiran fitowarta, sauke idonta kasa tayi, Mami tace "Heedayah" Ta kalli Mami tace "Na'am" Mami tace "Me yasa baki son tafiya gidan ku wajen iyayenki?" Heedayah ta girgixa mata kai kawai, Mami tace "Toh ki sake ranki before going downstairs, Ammin ki baxata ji dadi ba idan kina haka, idan kika kwana biyu a can ba sai ki dawo ba" Kamar xata yi kuka tace "Mami dama two days din xan yi ai" Mami tace "Aa ba irin wnn kwana biyun ba, ranan da aka ce ki dawo xaki dawo" Hawaye ya kawo idonta tace "Mami plss idan mun tafi after few days ki kira ki tambaya yaushe xan dawo sbda islamiyya" Kallonta kawai Mami take kafin tace "Can ma gidanku ne kuma xa ki iya xuwa islamiyya" Heedayah ta goge hawayen idonta tace "Mami bbu wanda muka saba da a can fa, ni kadai ce xan dinga xama" Mami tace "Ga Ammin ki da Stepmum dinki with ur little cute sisters, su xa su xama companions din ki a can ai, and Shuraim is now working in kano, definitely xai dinga xuwa can gidan kinga ai kin samu wanda ku ka saba sai ku dinga hira idan ya je" Turo baki Heedayah tayi bata ce komai ba, Mami tace "Go downstairs now, gani nan sakkowa" Sauka Heedayah ta shiga yi a stairs din, Mami ta wuce dakinta, tun da ta fito parlor Ammi ke kallonta bata dai ce komai ba, Ba a dau lkci ba Mami ta sakko parlon, turararruka ta ba Ammin Heedayah, Ammi tayi mata godiya sosai, Mami tace "In sha Allah after everything xa mu taho kanon" Ammi tace "Toh Allah ya kawo ku lfya" Har gate Farida da Mami suka raka Heedayah da Mum dinta, tun da suka shiga mota hawaye ke sauka idon Heedayah ta daga masu hannu suka bar layin tare da escort din Amminta, Har suka isa gidan Abba Ammi bata ce ma Heedayah komai ba ta sauka motar ta shiga cikin gidan, Heedayah ta sauka ta bi bayanta, Kaka da Yakumbo na xaune parlor tare da Mumy, Mumy ta shiga yi ma Ammi sannu da xuwa bayan sun shigo parlon, Yakumbo tace "Toh har xa mu tu6e kayan, bamu san ko fasawa kika yi baki sanar mana ba, abun ka da masu abu da abun su" Ammi dai bata tanka ta ba, Xaunawa kasa Heedayah tayi ta gaida Mumy dake ta kallonta, Mumy tana murmushi tace "Lafiya qlau Heedayah, baki da lafiya ne na ganki haka?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa lafiya na qlau" Daga haka ta gaida su kaka ma, Kaka tace "Me aka maki a gidan Rakiyar kike cika kike batsewa?" Ammi ta dau handbag dinta tana kallon Mumy tace "Hajiya xa mu wuce airport yanxu" Mumy tace "Lahh na xata xa ku bari sai gobe ai Maman Heedayah" Ammi tace "Aa yau xa mu koma in sha Allah" Mikewa kaka tayi ta dau jakarta dake gefenta tace "Toh idan Amadu ya dawo ace masa da alkhairi" daga haka ta nufi kofa, Yakumbo ma ta mike tace "Toh Maryam a gaida yaran idan sun dawo islamiyya...." Mumy ta mike tana murmushi tace "To sai yaushe kuma Mama?" Yakumbo tace "Atoh kilan sai na rako patu idan xata dawo wani satin ko?" Da sauri Kaka da har ta isa kofa xata fita ta juyo tana kallonta, Ammi dai bata jira ta sauraresu ba ta fita daga parlon Heedayah ta bi bayanta, Mumy ta bi bayan Ammi da sauri tana cewa "Toh Hajiya baki ci dambun ba ai gashi ma har na sa maki a cooler wllh" Ammi tace "Aa Alhmdllh nagode" Mumy ta 6ata rai tace "Aa don girman Allah ki tafi da shi ku da jirgi xa ku bi nan da yan mintuna xa ku sauka, kuma dambu ai abun marmari ne" Bata jira cewar Ammi ba ta shige ciki da sauri sai ga shi ta fito da wani karamin warmer me kyau cike da dambu, ta saka shi a wani fancy leda, Yakumbo tace "Tun da yaron nan na can kanon sai a bashi coolern ya maido maki idan xai xo" Tuni Mumy dai ta fice ko mayafi bbu ta rakube bakin gate tana mika ma Heedayah dambun, Heedayah ta risina ta amsa, Ammi tayi ma Mumy godiya, Mumy tace "Kai haba, babu komai wllh Hajiya, Allah ubangiji ya sauke ku lafiya" Ammi tace "Ameen, yaushe xa ku shigo kano?" Mumy tace "Ai ko muna da biki satin nan, in sha Allah ina sauka xan kira ki tunda na amshi number ki" Ammi tace "Toh Allah ya kai mu, ya kawo ki lfya" daga haka Ammi ta shiga mota Heedayah ma ta shiga, Mumy sai murmushi take kamar warce aka yi ma wani gagarumin albishir, Kaka da Yakumbo suka fito kaka na cewa "Banda dai shi Uban Heedayan yace sai na xauna wajensa dama me d'a na ya rage ni da shi xan ki xaman gidansa, kuma ko da xa a siyar da Gwamnet house din gaba daya da kyar a iya biyan Amadu abinda yyi ma Deedayah da kudin..." tuni Yakumbo ta shige daya mota, Mumy dai sai kallonsu take ta gefen ido, kaka ta tsuke fuska ta shige motar da Yakumbo ta shiga ita ma, Mumy na daga masu hannu baki har kunne tana Allah ya kiyaye har suka bar layin, tana murmushi ta dinga tunanin wani bikin karyar xata kakalo da xai kai ta kano a satin nan.... Tsaye Heedayah tayi tana bin dakin da Stepmum dinta ta nuna mata as nata da kallo, babu abinda babu a babban dakin that is well furnished da tsadaddun furnitures, karasawa tayi gefen gado ta xaune lkci daya hawaye ya kawo idonta, ko kadan bbu abinda ya burgeta a gidan nan dai tun shigowarsu, ta rasa damuwar da ya tsaya mata a rai, ji tayi kamar ta fashe da kuka sosai ko xata ji dadi a ranta, Wata maid ce ta biyo ta da trolley dinta dakin, Heedayah ta mike ta amshi trolleyn ta ajiye sa a gefe, Maid din na kallonta tace "Hajiya xa a kawo maki abinci ne, ko kuma da wani abun da kike na daban a kawo maki?" Heedayah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Tea" Juyawa maid din tayi ta fita, Heedayah ta kwanta gefen gadon hawaye me xafi ya gangaro idonta. Bayan Magrib Heedayah ta gaji da xaman daki bayan tayi wanka ta sauya xuwa doguwar riga me shara-shara ta fito, a wani parlor ta tadda Amminta xaune ita kadai tana answering din call, Heedayah ta xauna kasa ba tare da ta sake kallonta ba, har Ammi ta gama wayar ta ajiye, Heedayah ta daga kai a hankali tana kallonta tace "Ammi ina su Ashnaah?" Wani kallo Ammi tayi mata tace "Sai yanxu kika san da su?" Shiru Heedayah tayi bata ce komai ba, Ammi tace "Idan ma xaki kama kanki kiyi tun wuri, ni baxa ki kawo min iskanci a gidan nan ba, da kika san baki son xuwa wani gulman ya sa kika biyo mu dama, tun farko ai sai kice baxa ki xo ba, uwar wa xaki biyo kina hade haden rai, ko me xaki min a nan din idan kin xo" Girgixa kai Heedayah tayi cikin sanyin murya tace "Aa Ammi bance bana son biyo ku ba...." Kwankwasa kofa aka yi Ammi ta bada izinin shigowa, Maid ce ta shigo rike da tray me dauke da plate din dambu ta dumama, plated with pepperd chicken, ga Tamarind drink da bottle waters biyu da glass cup biyu a gefe, karasowa ciki tayi inta ajiye gefe ta dauko wani lallausan carpet ta shimfida ta dau tray din ta daura a kai snn da ladabi tace "Hajiya ga abincin" Ammi ta kalleta tace "Nagode Amina, kin debi dambun?" Aminar tace "Aa ba shi da yawa Hajiya" Ammi tace "Aa ku deba ku je ku ci tare da 'yan uwanki" Amina ta mike ta fita sai gata ta dawo da plate ta debi kadan ta fita daga parlon, Ammi ta sauka kasan carpet din ta dau spoon daya tana kallon Heedayah dake bin abincin da kallo tace "Idan xa ki ci ki fita kitchen ki dauko spoon" Girgixa kai Heedayah tayi tace "Aa, kawai chicken din nake so" Ammi ta jawo wayarta ta kira Amina tace ta debo ma Heedayah pepperd chicken din, ba a dau lkci ba ta kawo mata. Heedayah na cin kazar a hankali Ammi kuma na cin dambunta, Heedayah tace "Ammi wani makaranta xan fara yanxu?" Ammi tace "Ki tambayi Abbanki nima ban sani ba" Heedayah bata ce komai ba tana ci gaba da cin naman gabanta, Bayan sun gama Heedayah ta kwashi tray din tana kallon Ammi tace "Ina ne kitchen din?" Ammi tace "Don't worry ki tafi kiyi Isha xan kira su Amina su kwashe" Heedayah bata ce komai ba Ammi ta kira Amina ta shigo ta kwashi tray din tana kallon Ammi tace "Kun yi bako a parlor Ammi" Ammi tace "Waye?" Amina tace "Sojan nan ne" Ammi tace "Ohk Shuraim, I'm coming" Lkci daya Heedayah ta daure fuska, Ammi tace "Kije ku gaisa, I want to lay ur sisters to bed nasan suna can suna wahalar da Nannynsu" shiru Heedayah tayi tana kallonta, Ammi ta mike tace "Sai ki ajiye masa drink da abinci" Daga haka ta fita parlon ta tafi bangaren da girls dinta suke, lkci daya hawaye ya kawo idon Heedayah, ta fi minti shidda a xaune kafin ta mike tsaye a hankali ta koma dakinta ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta dau hijab dinta har kasa ta saka tayi sllh, bayan ta idar ta fita xuwa can main parlor, bbu kowa parlon sai kamshi dake tashi ga sanyin Ac da ya cika parlon, tun kafin ta karaso cikin parlon take kallonsa, yana xaune saman kujera ya jinginar da kansa jikin kujeran idonsa a rufe, har ta karaso cikin parlon bai sani ba, ta nemi kujera ta xauna fuskarta bbu walwala... Bayan kusan minti uku ta mike ta tafi xuwa kitchen, masu aiki uku ta samu a kitchen din ko wannensu da apron, da ladabi Amina tace "Kina da bukatan wani abun ne Hajiya?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa, Abinci xa a xuba ma bako in kai masa" Amina ta dau tray ta ajiye snn ta xuba shinkafa a plate, ta sa miya da enough cow meat a bowl, ta debi pepper chicken a wani bowl duk ta daura kan tray din, da Tamarind drink da bottle water sae lemon kwali, Amina tace "Ina xa a kai abincin?" Karban tray din Heedayah tayi ta fita, a hankali take tafiya har ta iso babban parlon, har sannan idonsa a rufe yake ta karasa kusa da shi ta durkusa ta ajiye tray din tana kallonsa, lkci daya ya bude ido, ta d'an koma baya ba tare da ta yarda sun hada ido ba, ya xauna da kyau yana kallonta, kallonsa tayi ita ma tace "Ina yini" yace "Lafiya" tace "Ammi tace a kawo maka abinci" ya kalli abincin yace "I'm full, thank you" Bata ce komai ba, yace "Yaushe kika xo?" Tace "Daxu" Yace "Tare da su Ammi?" Ta gyada masa kai, yace "Ya ku ka baro su Mami?" Tace "Lafiya lau" Komawa tayi kan kujera ta xauna, Yace "Can you help with a cup of tea" Tace "Ohk" daga haka ta mike ta yi hanyar kitchen ya bi ta da ido, bayan few minutes sai ga ta ta dawo da cup din tea, durkusawa tayi ta ajiye masa a kasa kusa da shi snn ta koma saman kujera ta xauna, Ammi ce ta shigo parlon da sallama, ta xauna tana kallonsa tace "Ya aikin Shuraim" Ya gaisheta da ladabi yace "Alhmdllh" tace "How are you feeling now?" Yace "Alhmdllh naji sauki" Ammi tace "Toh Allah ya kara lafiya" Yace "Ameen" Tace "Ka shiga ka gaida su kaka kuwa?" Yace "Aa yanxu xan shiga" Ammi tace "To ka shiga ka gaishesu idan ka ci abincin, 3 days ago ma tace baka shiga ka gaishesu ba" Murmushi kawai yyi, Ammi ta mike tana kallon Heedayah da ta tsura ma TV ido tace "Tambayi Amina ko ta bada an kai masu Lipton Hajiyata" Daga haka Ammi ta bar parlon, Shuraim ya kalli Heedayah, tashi tayi xata wuce kitchen, yace "Did you rinse the cup before making the tea??" ta d'an kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "No I didn't" daga haka tayi wucewarta kitchen dawowa parlon Heedayah tayi bayan Amina ta sanar mata ta kai masu, tana tsaye tace "A ina su Kaka suke?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Xuwa xa ki yi?" Tace "Ehh" ya mike ya fara tafiya, bin bayansa tayi suka haura sama, wani kofa ya bude suka shiga wani parlor Kaka na xaune ta daura kafa daya kan daya ta gama cin pepper chicken da aka kawo masu, Yakumbo kuma na kishingide gefe tana sakace hokara, Shuraim ya xauna yana kallonsu ya gaishesu, da damuwa Yakumbo tace "Ya ka kara ji da jikin?" Yace "Naji sauki" Kaka na kallonsa tace "Kaji wai Umaru bai san ka dawo kano da aiki ba, me yasa baka gaya masa ba muna xaman xamanmu ka janyo mana matsala a xumunci, wan ubanka ai ubanka ne" Shuraim dai bai ce mata komai ba, Heedayah ta xauna kasan lallausan carpet dake shimfide parlon tace "Sannun ku" Yakumbo tace "Kun gaisa da baban naki ko bai shigo ba" Heedayah tace "Bai shigo ba" Tana fadin haka ta mike tace "Dama na xo ne in gaisheku" daga haka ta nufi kofa, Kaka ta bi ta da kallo tace "Naga ikon Allah ni Patuu, kamar dai warce Rakiya tayi ma wani mugun abu, ba fa ta son xaman gidan uban nata kwata kwata" Yakumbo tace "Ashe dai kin gano, tun barowar mu Kaduna take cika take batsewa, ai na fi ta iskanci ita da komawa Kadunan nan wllh sai dai idan sallaman ubanta na can taje yi da uwar rikon nata" Kaka tace "Sallaman aure?" Yakumbo tace "Da fa? Ai wnn yarinyar naga kamar idonta a bude yake, ko shekaranjiya sai da nayi ma uban magana a aurar da ita kawai babu ruwana, kuma kinsan komai na fada ya xauna" Kaka tace "Toh ke kenan da ba haifansa ma kika yi ba, ni kuwa wnda na haifan ma nayi nayi da shi yyi ma d'ansa magana ya fiddo mata ayi masa aure yaki, gwara Sudais har an kai gaisuwa" Yakumbo tace "Atoh sai ki bar su kawai ai kin fita hakkinsu" Kaka tace "Toh Alhmdllh sai dai na tuna na ta6a nema masa aure da dadewa, can xan lallaba kawai in koma, amma ita Deedayar ina mijin da kike cewa xa ayi mata aure??" Sake baki Yakumbo tayi tana kallonta tace "Atoh lalacewa ta sameki kuma, ba ke kika kawo mana Junaidu d'an gidan Rahinah ba dama?" Kaka tace "Auhoo, ca nake watsa mun kasa xa kuyi a ido ku kunyata ni a idon yaron" Yakumbo tace "Aa ni ai na ya6a da halin Junaidu yaro me nutsuwa da hankali ga ladabi wllh, amma tsorona kawai yayan nan nasa da ya bayyana kwanan nan, banda haka ai xuri'ar nan tasu tayi wllh, barin uwar nan tasa" Shuraim dai kallonsu kawai yake, Kaka tace "Aa ba ruwanmu da wani yayansa har yanxu ni ban gama yrda d'an Rakiya bane wllh, kila dai wata dubara da hikima ce yin hakan sbda wani aiki da take, kilan akwai wani kess da take kai kuma dole sai ta billo ta haka" Yakumbo tace "Atohh, Allah dai ya sa haka, amma ai ba lafiya in dai gaskiya ne, shi ma Junaidun ai da shekaranjiya xa su kawo gaisuwar to wan ubansa ya kira wai a d'an basu kankanin lkci ko xuwa nan da sati biyu ne" Kaka tace "Toh Allah ya kai mu" mikewa Shuraim yyi yace "Sai da safen ku" Kaka tace "Toh Allah ya kai mu" Kofa ya nufa ya bude, da sauri Heedayah dake makale jikin kofar ta bar wajen ya bi ta da kallo yace "Wait" dai dai stairs ta tsaya ta ki yrda su hada ido tana turo baki ya nufeta, Kaka na kallon Yakumbo murya can kasa tace "Dama na ta6a nema masa auren Farida, yanxu gobe xan sa a kira min kawun faridan kawai inji inda aka kwana" Yakumbo tace "Toh ko dai da warce yake so ne, naga ransa bai masa dadi ba maganganun nan da kike yi" Kaka tace "Toh ba shi ya jiyo ba ni ina ruwana" Yakumbo tace "Aa yaron na da hankali ga rashin son magana balle hayaniya, gobe idan Allah ya kawosa xan ja sa parlona in tambayesa ko yana da warce yake so ne ya sanar min" Kaka tace "Tab 6ata lkci kawai, ba sai idan yana kula yan matan ba xai samu warce yake so" Yakumbo tace "Wllh yana tare da damuwa ni dai na lura" Kaka tace "Shi dai Amadu kullum tausayin irin d'an da Allah ya basa nake yi masa wlh, muna nan dake xaki ga wataran jikana Sudess xai xo, yaro wayayye d'an boko me faram faram da jama'a ba dunkum ba" Yakumbo tace "Toh ai halitta ce Patuu, wani haka Allah ya haliccesa wllh, baki ga irin dagewar da Amadi yyi da shi ba kafin ya dinga xuwa mana nan tun ma bai dawo kanon gaba daya ba, yanxu haka har kwana Amadi yace ya dinga yi a nan amma baya yrda ya kwana yana xuwa xai yi wucewarsa, wllh da ina da 'ya mace da na basa aurenta ni dai" Kaka tace "Ki raba kanki bakin hali ke garesa wllh, Shureen abun tsoro ne bar ganin kamar mutum" Yakumbo ta tabe baki tace "Ke kika ga haka ni ban gani ba" tana fadin haka ta mike ta shige daki, Heedayah na tsaye har Shuraim ya isa inda take ya tsaya yana kallonta. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Heedayah ta ki yarda su hada ido, yana kallonta yace "Why were you eavesdropping?" Kin cewa komai tayi, bayan few seconds ta d'an daga kai suka hada ido da shi, ji tayi gabanta ya fadi ta fara kame kame, da sauri ta juya xata bar wajen taji ya riko wrist dinta, ta kalli hannunsa, 6ata fuska tayi taki bari su kara hada ido tace "Ni bana so ya Shureen, I wasn't eavesdropping, zobe na ne ya fadi nake dubawa kuma ban gani ba a wajen" Lkci daya tayi shiru, can tace "Toh ka sake ni" Yace "In contrast to that?" Kamar xata yi kuka tace "Ni dai ka sake ni" Dago kanta yyi yana kallon tun daga lips dinta har xuwa eye balls dinta, suna hada ido, ta rufe bakinta da hijab dinta da sauri tuna wani abun da tayi, gabanta ya shiga faduwa, saketa yyi a hankali yace "Kin dai makale kina sauraron ranan da xa a kawo gaisuwar ki ko?" Ita dai bata ce masa komai ba, yace "To nan da sati biyu ne" Turo baki tayi tace "Gaisuwana da wa?" Yace "Ahmad Junaid" Ta 6ata fuska tace "To ni nace ina son sa da aure ne, bayan shi yayana ne, ta ya xa ace xa mu yi aure???" Yace "Ta yanda ake yi" hawaye ya kawo idonta tace "Ni dai baxan iya ba, ta ya xa ace haka" Yace "Toh kina da wanda kike so ne?" Tace "Ehh" Yace "Waye shi?" A takaice tace "Khaleel..." murmushi yyi yana kallonta yace "Sai ki gaya masu" Ta share idonta a hankali tace "Ni baxan iya ba" Yace "Why?" Tayi shiru, yace "Idan ma kin iya fada masu Allah ya sa su bar ki da shi" Tana kallonsa da sauri tace "Me yasa baxa su bar ni da shi ba??" Yace "Aa ban sani ba, ae xa ma su bar ku" Shiru tayi bata ce komai ba, ya fara tafiya ta bi bayansa har suka dawo parlor, juyawa yyi yana kallonta yace "You rinse another cup and make me a cup of tea" Ta kalli shayin da suka bari a parlon tace "How will I use a cup without rinsing it at first?" Ya xauna yana kara kallon shayin yace "Rinsed or not.... We left it open" Ta hade girar sama da ta kasa, shi dai idonsa na kan tv dake aiki a parlon, ta karaso ta durkusa ta dau shayin ta wuce kitchen, ba a dau lkci ba ta fito ta ajiye masa wani shayin, dauka yyi yace "Did you come over to kano with ur laptop?" Tace "Eh" yace "Let me see" shiru tayi tana kallonsa, can tace "Ina son tambayar ka ya Shureen" Ya daga kai ya kalleta yace "Ok... but before then, what's Shureen?" Tace "Nima ban sani ba" yace "Don't call me that again" Ta d'an ta6e baki don ba kallonta yake ba, can tace "Me yasa lkcn da nake gidanku baka min magana, baka kulani sai yanxu? This is really weird" Yyi shiru yana kallonta directly in the eyes, can ya d'an yi murmushi yace "Apart from you... kin ga ina kula kannina ko wani a gidan? And if I am not mistaken kin ta6a min wnn tambayar kwanaki ae" Ta buda masa hannu alamar bata san ko yana kula kannin nasa ba snn tace "I am asking you again because ina mamaki ne har ynxu, I never knew u can talk for 3 mins without stopping, why ur sudden change toward me??" Kallon cup din hannunsa ya dinga yi kafin yace "Baki ta6a xuwa kin tareni ko kin xo inda nake kin min magana naki kulaki ba, ko an ta6a haka duk period din da kika yi gidanmu?" K'in cewa komai tayi, ya ajiye cup din hannunsa yace "Look Heedayah, babu abinda xaman ki a gidanmu ya rageni da for good 5 years da kika yi tare da mu, tun kafin Abba ya kawo ki responsibilities dina ya fita kansa I was independent then, rayuwa kawai nake yi a gidan, balle ace ko haushin wani abinda xa ayi maki nake, kinga ynda nake da kannina har yanxu, Even my Grandmum I don't spend much time with her, So why didn't u complain about them too..." Heedayah ta girgixa kai kawai, yace "Ohk let me let you know this, At first I was confused xuwan ki gidanmu, coz then my family was a happy one, all of a sudden xuwan ki abubuwa suka fara faruwa marasa dadi, and I can't just disappoint my Mum a lkcn, I don't want to double her disappoinment, nasan kina bukatan taimako sosai at then I even advice Abba ya bar ki gidan Marayu and I will take every responsibility naki a can, snn I promise duk weekend xan dinga xuwa duba ki, shi ma idan yana da lkci sai ya je, but he was reluctant, ni kuma na kawo idea din ne ganin Mumy baxata ta6a rike ki ba no matter, a ranan da kika dawo gidanmu da Mami da daddare mum dita ta kirani daki..." Shiru yyi, Heedayah dai sai kallonsa take, can ya girgixa kai yace "I don't want to say anything about that, you can't make me say anything about that, but just know that there is no one to console her, and I have no choice then to follow her instructions ko xata samu sauki ta wani bangaren, because of you or Mami baxan iya bata ma mahaifiyata ba tunda dai abinda tace inyi ba abinda xai cuceni ko ya cuce wanin ku bane, shi yasa ko karatu naki koya maki idan kin tuna...." Heedayah dai kawai murmushi tayi, Yace "Get this, I am not telling you all this for you to change ur silly thinking toward me, stick to ur thinking" Heedayah tace "Toh ka ci gaba ina ji" yace "Ohk... Duk da bana maki magana bana shiga harkan ki a gidan mu, ni nasan irin taimakon da na maki wanda ke baki sani ba kuma baxa ki ta6a sani ba, just know that i kept an eye keenly on you, ban bada room for anyone to get you harmed ba duk da ko kowa yasan bna sake maki a gidan, kuma sake maki da bana yi yasa bbu wanda xai kawo xanyi abubuwan da na dinga maki most especially my mum, I missed a lot of opportunities don kada inyi nisa da ke ki cutu, har kika bar gidanmu you weren't safe, barin ki gidanmu ya bani courage din tafiya soldier da ban tafi ba bayan na sake samu for the 3rd time, ko da ace ni din me magana ne rashin maki magana a lkcn shine mafi alkhairi Heedayah, balle ma ni bani da lkcn magana, a ta dalilinki Mahaifiyata ta jefa kanta ga halaka wanda har gobe nake fatan Allah ya ganar da ita, but ban ji haushin ki ba duk da ta dalilin ki hakan ya faru, ni dai kawai I made sure I protect you by all means" Heedayah tace "Wai Protect me from what?" Yace "Bana tunanin gaya maki xai maki wani amfani, Back to what I was saying.... Duk da biyayyar da nake ma mahaifiyata sai da na tsallake umarninta na bi ku har New Delhi na duba lafiyar ki, kuma da kike cewa ashe ina maganar minti uku without stopping, go ask Zainab, I talk when I am comfortable doing so, kuma da ita kadai nake magana haka sae ko colleagues dina, ko kannina baki ga ina masu haka ba, it's a nature I know I can't eradicate, coz I've tried my best doing so but no result, Kar fa kiyi tunanin don ki canxa ra'ayinki a kaina nake gaya maki abubuwan nan..." Yana fadin haka ya mike ya dau laptop din yace "Idan na shigo gobe, will bring u back ur laptop, idan kuma ban xo ba sai Thursday, good night" Bin sa da kallo tayi ganin ya nufi kofa tace "Toh shayin fa?" Juyowa yyi ya kalli shayin yace "Oh, thank you" daga haka ya fice ya kulle kofar, tafi minti biyar xaune tana naxari kafin ta mike ta karasa kujeran da ya tashi ta dau shayin ta xauna ta fara sha. Heedayah na gama shirin kwanciya Ammi ta shigo dakinta tana kallonta tace "Ki xo ku gaisa da Abbanki" Daga haka Ammi ta juya ta fita, Heedayah ta dau hijab dinta har kasa ta saka snn ta bi bayanta har xuwa babban parlon Abbanta, Yana xaune ta shigo parlon ta durkusa kasa gefensa ta gaishesa ya amsa da murmushi yace "Kun xo lafiya Heedayah?" Tace "Alhmdllh, Ya aiki Abba" Yace "Mun gode Allah, ya kika baro iyayenki na can" Tace "Duk suna lafiya, suna gaisheku" Yace "Toh maa sha Allah, hope babu wani matsala baki bukatar komai" Tace "Abba ina son in canja waya, ban xo da nawa ba" Yace "Toh xa a kawo maki gobe idan Allah ya kai mu" Tace "Toh nagode Abba" Yace "Allah yayi maki albarka" Tana murmushi tace "Ameen, kuma Abba wani makarantar xan yi ynxu?" Yace "Aa wnn we are not to decide, iyayenki na can xa su yi deciding ko?" Ta gyada masa kai tace "Toh Abba" Yace "Sai ki tambayi Barrister, ko Hajiya Rahinah" Tace "Toh" Nan tayi masa sai da safe snn ta mike ta fita parlon, bangaren Ammi ta koma tana shiga parlonta taga wayarta kan kujera ta dauka ta wuce dakinta, sai bayan da ta kwanta tayi dialing number Farida da ta haddace, Farida na dagawa da taji muryarta tace "Why did you leave ur phone Heedayah?" Heedayah tace "Mancewa nayi, ya Mami fa" Farida tace "Alhmdllh, kun isa lafiya?" Heedayah tace "Lafiya lau" Farida tace "Kun hadu da Ya Shuraim?" Murmushi Heedayah tayi tace "Ehh, ya ma ce in gaishe ki idan muka yi waya" Farida tace "Ki gaisheni kuma??" Heedayah tace "Ehh mana, sai da ya tambayeni me yasa ba mu xo tare ba, Kinga dama kun kusa mid semester, kawai ki taho nan kiyi hutun" Farida tace "Toh ai Mami might not let me" Heedayah tace "Ba sai Ammi tayi mata magana ba" Farida tace "Uhm" shiru Heedayah tayi kafin tace "Ya Khaleel sun kai Lafiya?" Farida tace "Ehh daxu suka yi waya da Mami" Da sauri Heedayah tace "plss ki turo min number da ya kira da shi" Farida tace "Wani number Mami ne da ta bashi ya sa a karamin wayar Ya junaid" Heedayah tace "Send me the number plss" Farida tace "Ohk I will now, but tell me Ya Shuraim din kullum yake xuwa?" Dariya Heedayah tayi tace "Eh mana, kullum sai ya xo, ni dai ki turo min number yanxu" Daga haka ta katse wayar, cikin few minutes sai ga number Farida ta turo mata, bude kofar dakinta aka yi Ammi ta shigo tace "Ke kika dau wayata" Heedayah ta marairaice tace "Ehh Farida na kira" Ammi tace "Ina naki wayar?" Heedayah tace "Na mance a Kaduna" Fita Ammi tayi daga dakin, Heedayah tayi dialing number da Farida ta turo mata, yana fara ringing tayi murmushi, Daga kiran aka yi amma ba ace komai ba, a hankali Heedayah tayi sallama, Khaleel dake kwance har ya fara bacci ya bude idonsa dake a lumshe bayan ya daga kiran yace "Heedayah?" Tayi murmushi tace "Ka gane muryata ashe, good evening" Yace "Evening, Mami tace min kun tafi kano" tace "Ehh bayan kun tafi muka wuce" Yace "Yaushe xa ki dawo?" A hankali tace "Lkcn da xaka dawo" Shiru yyi kafin yace "Uncles dina sunce sai next week" Tace "Nima next week xan dawo" Yace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Shiru ne ya biyo baya, bayan few seconds a hankali yace "In tambayeki Heedayah" Tace "Ina jin ka" Jin bai ce komai ba tace "Hello?" Yyi kasa da murya yace "Xa ki iya aurena?" Sosai gabanta ya fadi, a hankali tace "Me yasa ka min wnn tambayar?" Yace "Ina ga kamar baxa ki yarda ki aureni ba" Tace "Toh ka daina wnn tunanin" Yace "Ban ta6a son 'ya mace ko kula 'ya mace duk tsawon rayuwata ba sai kanki Heedayah, ni kai na ban san irin son da nake maki ba, ko fado min kika yi sai naji xuciyata ya dameni, and I have to nurse it for sometimes kafin in dawo dai dai, kin san condition dina Heedayah kar ki gujeni plss" a sanyaye tace "I won't in sha Allah...." A hankali yace "But have you ever thought of living In same roof as husband and wife with someone that was once a Hoodlum??" Hawayen dake makale idonta ya gangaro cikin sanyin murya tace "I am happy u said with someone that was once a Hoodlum, I love you not minding ur past dear" Jin yyi shiru bai ce komai ba, a hankali tace "Are you there?" Yace "Sure, I love you with every breath of mine" Murmushi tayi tace "I love you same" Yace "Xan kwanta yanxu, coz I am very tired, how can I reach you always?" Heedayah tace "Ae wayar Ammi ne you can call me anytime" yace "Baxan dameta ba?" Tace "Aa" yace "Alright, thank you, sleep tight" Tace "But have u eaten?" Yace "Sure na ci abinci" Tace "Alright, Sweet dreams" Yace "Yes love" Daga haka ya katse wayar. Washegari da sassafe Heedayah ta tafi gaida Abbanta a bangarensa, Yakumbo ta samu a parlon, Ta duka ta gaida Yakumbo snn ta gaishesa, Yakumbo tace "Amadi in ji dai baxa a wani lafta uban lkci ba idan masu auren yarinyar nan suka xo, kaga gwara kasan ka sauke nauyinta a kanka, don kana gwamna bbu ruwanmu da lalacewar tura yarinya kasashen shegu karatu, gwara idan an mata auren mijin ya kai ta can ya jira har ta gama barin ma wayayye xata aura d'an boko" Shi dai Abba bai ce komai ba, Yakumbo tace "Kayi shiru" Yace "Aa su xa su yanke lkcn da yyi masu ai Yaya" Yakumbo tace "Aa ni fa babban damuwata Heedayah fa tana da budadden ido wllh, yanxu tana ganin fuska xata fara hotuna a babban gidan nan ta baxa shi a yanar gizo ayi ta yawo da shi ana cewa ai yar gwamna gari kaza ce, to kafin hakan ya faru gwara a mata aure don ni baxan ji dadi ba, ba naga yanda 'Yan yan manyan kasan suke ba, wani ma kusan a tsirara xai yi hoton" Abba dai bai ce komai ba, Yakumbo ta mike tace "Mu kam da mutunci da martabar mu, bamu yada al'adarmu da kunya ba don mun samu duniya" Abba na kallon Heedayah da hawaye ya kawo idonta yace "Ae kina son yaron ko?" Lkci daya ta fashe masa da kuka tace "Abba a matsayin Yaya na daukesa fa, ni bana sonsa" Da mamaki yake kallonta, can yace "Baki son sa?" Ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, yace "Kina da wanda kike so ne?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "To waye shi?" A hankali tace "Khaleel" Abba yace "Waye kuma Khaleel?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya dinga kallonta yace "Who is he?" Kasa basa amsa tayi, yace "Talk to me a ina yake?" Ta girgixa masa kai kawai, bayan wani lkci yace "To tashi ki tafi" Mikewa Heedayah tayi ta fita daga parlon, part din step mum dinta ta tafi, a parlonta ta sameta tana feeding din Islam, Ta xauna kusa da ita ta gaisheta, da fara'a ta amsa tace "Har kin tashi Heedayah" Heedayah tace "Na tashi Aunty" Mum Islam tace "To ya gajiyan jiya" Heedayah tace "Alhmdllh" Mintin Heedayah kusan talatin a parlon kafin ta mike tace mata xata je ta gaida Kaka, tana fita parlon ta tafi wajensu kaka, Kaka na ganinta tace "Yauwa gantalallun masu aikin nan shiru shiru ban gansu ba, gashi ki kira min Shureen in ji ya jikinsa" Heedayah ta amshi wayar tace "Toh wai me ya samesa ba ya warke ba har ya xo jiya" Kaka tace "Atoh kuma baxan ji yanda ya kwana ba, bashi da kowa fa garin nan Allah ya rufa masa asiri na dawo garin" Heedayah ta tabe baki ta nemo numbersa tayi dialing ta mika mata, yana fara ring ya daga, kaka tayi sallama, ya gaisheta tace "Ya ka kara jin jikin Shureen?" Yace "Naji sauki" tace "Toh Allah ya kara lafiya, ka fita aikin ne?" Yace "Ehh" Heedayah ta amshi wayar ta kai kunne tace "Ya Shureen you didn't go with the laptop Charger, kuma charging bashi da yawa kamar" yace "Ohk baki bani ba" tace "Are you coming to collect it?" Yace "Ohk I will" Tace "Tohm sai anjima" Daga haka ta katse wayar, Kaka ta rike ha6a tace "Yaushe kuma ku ka fara shiri da Shureen har kuna juya yare??" Dariya Heedayah tayi tace "Aa ba shiri muke yi ba, kawai abu na ya ara" Kaka tace "Meye ya ara?" Heedayah ta ajiye mata wayarta tace "Idanuwan kaka" Daga haka ta fice da sauri daga parlon tana dariya. Bayan Magrib Heedayah na xaune kan darduma ta idar da sllh daya daga house maid dinsu ta kwankwasa kofar dakinta, mikewa tayi ta isa gun kofar ta bude, Maid din ta gaisheta da ladabi snn tace "Hajiya tace ki je" Heedayah tace "Ohk" juyawa Mai aikin tayi ta wuce, Heedayah ta cire hijab din jikinta ta linke ta ajiye snn ta fita xuwa bangaren Amminta, Ammi na kallonta bayan ta shigo parlonta tace "Waye kika kira da wayata?" A hankali Heedayah tace "Khaleel ne" Ammi tace "Waye Khaleel?" Heedayah ta sauke kanta tace "Yayan Junaid" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Shiru Ammi tayi tana kallonta, Heedayah ta kasa kallon Mahaifiyartata sai fidgeting din yatsunta take, mika mata wayar Ammi tayi, ta karasa ta amsa ta juya ta bar parlon ta kulle mata kofa ta koma dakinta, gefen gado ta xauna tayi dialing number Khaleel, yana fara ring ya daga, a hankali tace "Ina yini?" Cikin Husky voice dinsa yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ya kowa da kowa" Yace "Fine....." D'an murmushi tayi tace "Do you like it in there?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Nop, not when u are not here Heedayah" Tace "Uhn you need to get use to ur relatives, and nasan Sumayya xata dinga keeping dinka company ai" Yace "Wace haka?" Tace "Cousin dinka mana" yyi shiru, tace "Ko ba haka ba?" Yace "Haka ne" turo baki tayi kamar xata yi kuka tace "Haka xaka ce min?" Yace "Toh yi hakuri, ba haka bane..." Knocking kofarta aka yi, tayi kasa da murya tace "Hold on pls xan bude kofa ana knocking" a hankali yace "Ohk dear" ta mike ta bude kofar taga Maid dinsu ce Amina, gaisheta Amina tayi tace "Hajiya kin yi bako a parlor yana jiran ki" Da mamaki Heedayah tace "Bako?" Amina ta gyada mata kai tace "Ehh" Juyawa tayi ta koma dakin, Amina ta bar bakin kofar, Khaleel yace "Wani bakon kika yi?" Heedayah tace "Nima ban sani ba wllh, let me go and check idan na dawo daki xan kiraka" A hankali yace "Alright..." Tace "Bye..." Daga haka ta katse wayar, ta dau mayafinta ta yafa snn ta fita, parlon baki ta nufa ta bude a hankali ta shiga da sallama tana leka ciki, Shuraim ta gani xaune idonsa a kan screen din wayarsa, ya dago kai suka hada ido, ta turo baki tace "Toh kai ne bako?" Bai ce komai ba har ta karaso cikin parlon ta xauna kujeran dake kusa da nasa tace "She told me nayi bako" Shuraim yace "Ohk to kilan bakon ki ka yi a waje, ki je ki samesa" Ta buda ido tace "I tot kai take ce ma bako?" Yace "Nima ban sani ba, na dai san nace ta kira ki ki amshi laptop dinki" Heedayah ta langwabar da kai tace "Ohk... A xubo maka abinci?" Yace "I'm not hungry" Tace "Good evening" Yace "How are you" tace "I am fine" ta wara ido tace "Two minutes plss" Daga haka ta mike da sauri tanufi kofa ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita, can dakinta ta koma ta dauko wayar Ammi ta fito, tana kusa parlon da Shuraim yake ta tsaya tayi dialing Number Farida, yana fara ring Farida ta daga, Heedayah tace "You know what sweetheart?" Farida tace "No, what?" Heedayah tace "Ya Shuraim ya xo ya tambayeki bari in kai masa wayar ku gaisa ynxu" bata saurari Farida ba ta shige parlon da sauri ta isa kusa da Shuraim dake kallonta, ta mika masa wayar hannunta murya can kasa tace "Xa a gaisa da kai" Bata jira yace komai ba ta kai masa wayar kunne ganin sai kallon wayar yake, ya kama wayar da mamaki, ta xauna arm din kujeran murya can kasa tace masa "Toh kayi magana mana" A hankali yace "Assalamu Alaikum" Murmushi kawai Heedayah ke yi tana kallonsa, Farida da taji gabanta ya fadi daga daya bangaren ta amsa a hankali ita ma tace "Ina yini Ya Shuraim" Shuraim ya kalli Heedayah da mamaki, ta wara masa ido, dauke idonsa yyi yace "Lafiya lau ya kike?" Farida tace "Alhmdllh, ya kano? Ya aiki?" Yace "Fine, ya su Mami?" Tace "They are all fine" Yace "Maa sha Allah, ana ta lectures?" Tace "Aa exams xa mu fara next week" Yace "Toh Allah ya bada sa'a, ayi karatu sosai" Murmushi Farida tayi tace "In sha Allah...." Xai cire wayar a kunnensa Heedayah ta mayar da sauri ta wani tsuke fuska murya can kasa tace "Kace yaushe xata xo kano joor" Kallonta kawai Shuraim ke yi, can dai yace "Yaushe xa ki xo Kano?" Farida tace "After my exams In sha Allah" Yace "Toh Allah ya kai mu muna jiran ki" Farida na murmushi tace "In sha Allah, ya kano weather?" Shuraim ya wani hade rai ya sake kallon Heedayah, wara masa ido tayi tana washe masa hakora, can dai yace "Alhmdllh" Farida tace "You like it there?" Yace "Sure it's cool, ki gaida su Mami" Heedayah ta turo baki ta matsa kusa da kunnensa kuma, murya can kasa tace "Kace kana son ta fito da first class" Hannu yasa ya ja bakin nata, tayi wani kara ta rufe bakin da hannunta da sauri, Shuraim dake sauraron Farida dake masa sai da safe yace "In sha Allah, thank you" Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta bar wajen da sauri ganin Fixgota yake son yi, ta fashe da dariya har da kyakyatawa, kallonta kawai yake, tayi me isarta ta koma kujeran da take xaune ta xauna tana wani murmushi tace "Kasan me ya Shureen?" Ya hade rai yace "What's the meaning of what u just did?" Turo baki tayi taki cewa komai, ganin kallon da yake mata tace "Toh muna magana da ita ne shine take tambayata Ina ya Shureen shine na baku ku gaisa, is there anything wrong with that?" jingina yyi da kujera bai ce mata komai ba, ta ta6e baki tayi shiru, bayan few minutes yace "Abba yace xa a siya maki waya, wani iri kike so" Kallon wayarsa dake ajiye tayi ta mike ta karasa ta dauka tana duba wayar sannan tace "Irin wannan" Kallonta kawai yake, can yace "Toh sai ki rike wnn din kawai" Ta xaro ido tace "Ba sabo Abba yace a siya min ba" Yace "Wnn ma sabo ne ai" Ajiye masa tayi ta koma inda take tace "Bana son irinsa kuma" Murmushi kawai yyi bai ce komai ba, can ya kalleta yace "Ban taho maki da laptop din ba sai gobe" tace "Ohk, in kawo maka chargern?" Yace "Ehh" Mikewa tayi ta wuce dakinta ta dauko masa chargern ta dawo ta basa ya amsa yace "Thanks" Mikewa yyi yace "Sai da safe, kar ki ce ma kaka na xo" Tace "Baxa ka sha shayi ba?" Yace "Na koshi" Tace "Ohk, ina son xan maka magana, can I escort you say in gaya maka a waje" Ya kalleta yace "As u wish" bin bayansa tayi suka fita parlon.... Tafiya suke a tare tana gefensa, baka ta6a cewa dare ne don ko ina tarr da hasken fararen fitilu ga shukokin dake kewaye na ta bada Iska me dadi, bayan wani lkcn Shuraim ya kalleta yace "Har gida xa ki rakani kenan?" 'yar dariya tayi tace "Aa, ai parking space din da nisa, but idan na rakaka sai ka sake rakoni rabin hanya sannan ka koma" Bai ce komai ba, jin taki magana ya kalleta suka hada ido, tace "Ya Shuraim ka gaya min irin qualities din da kake so a wajen mace?" Tsayawa Shuraim yyi yana kallonta yace "Why did you ask that?" Tace "No just tell me" Dauke idonsa yyi daga kallonta, ta kalli wani thatch me kyau dake dauke da kujeru tace "Mu je can mu xauna sai ka gaya min" Bata jira cewarsa ba ta nufi Thatch roofing din ta hau stairs dake wajen snn ta xauna kan daya daga kujerun, bin bayanta yyi xuwa wajen, ya xauna saman kujera, ta tallabi chin dinta tana kallonsa tace "Ina jin ka?" Ya shafa beard dinsa bayan few second yace "Ohkk... ina son mace me tsafta, me kuma rikon addini" Jin yyi shiru ta xaro ido tace "Shi kenan?" Yyi murmushi yace "Aa Ina son 'yar doguwa fara, me manyan idanuwa da dogon hanci with cute lips" Heedayah ta wara ido tace "Dimples fa?" Yyi shiru yana kallonta, can yace "Yi dariya mu ga" Bata san lkcn da ta kwashe da dariya ba, yyi murmushi yana kallonta, ta gaji don kanta tayi shiru, bayan few seconds yace "Bana son dimples" Ta marairaice tace "Why" yace "Kawai haka nan" Tace "Toh baka son me gashi har gadon baya?" Ya d'an yi shiru, can yace "Toh ai ban san ya gashi yake har gadon baya ba, do you mind showing me?" ta d'an yi shiru kafin tace "Toh ai ni nawa bai kai gadon baya ba" Yace "Ehh xan iya measuring with my eyes ai" ta fara bin inda suke da kallo ganin sojoji ne can nesa da su bakin daya daga many gates din building din ta sauke mayafin kanta snn ta cire hulan gashinta ta cire ribon din da ta daure dogon gashinta da shi, tuni kamshin gashin nata ya cika wajen, kallonta kawai Shuraim yake, ta juyo tana nuna masa bak'in gashinta da ya sauko kasan shoulders dinta bai karasa gadon bayanta ba, jin bai ce komai ba ta juyo, sauke idonsa yyi tace "Have u finish measuring?" Yace "Yeah" ta daure gashinta ta mayarda hulan snn ta daura mayafinta a kai tana kallonsa, flowers ya tsura ma ido, tace "So?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Ban son gashin da ya kai gadon baya" Da mamaki tace "Me yasa?" Ya juyo yana kallonta a takaice yace "Haka nan" Ta langwabar da kai tace "Toh kana son me wushirya?" Yace "Meye hakan?" Tace "Gapped teeth" Yace "How? In ga naki wushiryan?" Tace "Aa bani da shi ni" Daga haka ta bude masa fine set of teeth dinta, Kallonsu ya dinga yi tace "Uhm??" Ya girgixa kai yace "No, bana son wushirya" Tace "Ohk hips fa?" Yace "Meye shi?" Tayi dariya tace "Hips ne baka sani ba?" Yace "Ehh" Tace "Ohk forget that" yace "Aa nuna min" tace "Aa forget that" Shiru yyi yana kallonta, tace "And don't you want a girl that can cook all sort of varieties" Yana mata wani kallo yace "As if you can cook varieties" tace "Ni daban warce xaka so daban, nasan I don't have much cooking skills, but you will need a girl that can cook many type of food" Shuraim ya tabe baki yace "Ko ruwan xafin da xata hada min shayi kadai ta iya tafasawa ta isheni a hakan, I have never been a foodie" Dariya Heedayah tayi sosai, sai kuma tayi shiru, kallonta ya dinga yi, a hankali tace "Ya Shureen you know what?" A hankali ya matsa kusa da ita yana kallon lips dinta yace "Repeat the name again" Xaro ido tayi ta matsa daga kusa da shi tayi dariya tace "Yaya" Jin bai ce komai ba tace "Why haven't you ever thought of dating Farida? She is pretty, nice, good hearted, even her flaws are lovely, all the qualities i mentioned above tana da su, and beside all this... she loves you wholeheartedly, she's been admiring you from day one, tun jiya take min xancen ka shi sa na hada ka da ita yau a waya, I am telling you Yaya Shureen you won't regret it, she's a wife material wllh..." kallonta kawai Shuraim yake ko kiftawa baya yi, tana kallonsa a hankali tace "Kayi shiru Ya shureen" Dauke idonsa yyi kafin yace "Me yasa kike mata sha'awana?" Tace "Sbda every lady will love to have you, ka ga na farko you are handsome, sannan kana da hali me kyau duk da baka sakewa da mutane kuma baka da yawan magana, but I know you are not bad, you are just being who u are, most important of all u are religious, kana respecting Mum dinka sosai.... Ur flaws are odd and unique...." Shuraim yace "Toh me yasa ke baki yi ma kanki sha'awar inyi dating din ki ba sai ita" Dariya tayi sosai ta girgixa kai tace "Kai yayana ne bbu wnn tsakaninmu, kaga kai da Ya junaid da ya Sudais I can never imagine dating you 3, sannan ma ni ina da wanda nake so da aure" Yace "Wa kenan?" Tace "Khaleel" Ya gyada mata kai bai ce komai ba, bayan few seconds tace "I have never asked for a favor from you, ni bamu wani saba ba ma balle in tambaya, so plss do me this favor, wllh Farida na sonka sosai, na dade da sanin haka, Ina son in hada ku pls..." Shuraim yace "Toh kamar yanda kema kike da wanda kike so, nima haka nake da warce nake so" Heedayah tayi shiru lkci daya jikinta yyi sanyi, a hankali tace "Wacece ita ya Shureen?" yace "When the time comes idan baki riga ni aure ba xan kai ki wajenta" Daga haka ya mike yace "Sai da safe" Ta mike ita ma kamar xata yi kuka tace "You are rejecting my frnd ya Shureen??" Ya juya yana kallonta yace "Kema ki hakura da saurayin da kike so in hada ki da wani da ya dade yana son ki, in har kin yarda da hakan wllh wllh xan amshi soyayyar kawarki, I will date her" da wani irin mamaki take kallonsa, ya sauka stairs din yyi wucewarsa ta bi sa da ido har ta daina ganinsa. A hankali ta sauka ta koma cikin gida, Tana komawa dakinta cire kayan jikinta tayi ta shiga bandaki tayi wanka ta dauro alwala snn ta fito, bayan tayi sllh tayi shirin kwanciya ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta dau wayar Ammi, missed calls din Farida ta gani uku sai na Khaleel guda daya, kallon agogo tayi taga tara har ya wuce, shiru tayi tana tunanin abinda Shuraim ya gaya mata, can ta shiga contact din Ammi tayi dialing Shuraim taga bbu numbersa a wayar, mikewa tayi ta sa Hijab dinta ta fita dakin, bangarensu kaka ta nufa ta bude kofar parlon da sallama ta shiga, suna xaune sun cika parlon da hayaniya, ta xauna ta gaishesu gaba daya, kaka na mata wani kallo tace "Sai yanxu garin ki ya waye Deedaya? Tun safe sai yanxu xa ki shigo gaishe mu?" Heedayah tace "Toh na shigo kuna bacci" Tana fadin haka ta dau wayar kaka bata sake sauraron surutan da suke mata ba, ta shiga call log ta duba number din Shuraim cikin kankanin lkci ta kwashe a kanta ta ajiye wayar ta mike tace "Sai da safen ku" Daga haka ta fice daga parlon ta kulle masu kofa, tana komawa dakinta ta dau wayar Ammi, miss call din Farida ta sake gani, ta saka number Shuraim a wayar snn tayi dialing, har ya gama ring bai daga ba, sake kira tayi no answer, ta tsura ma wayar ido, can ta kira Farida kawai, Farida na dagawa tace "Wayar na wajen Ammi ko?" Heedayah tace "Aa na bar shi a daki ne?" Farida tace "ke kina ina?" Heedayah tace "Ina parlor, ya Mami fa" Farida tace "Tayi bacci, Ya Shuraim din ya tafi?" Heedayah ta d'an yi murmushi don dama ta san kiran da take ta yi mata kenan, Farida tace "Hello" Heedayah tace "Tun daxu ya wuce dama kawai xuwa yyi in kira ki a waya ku gaisa, bayan kun gaisa kuma ya wuce" Farida tace "Me yasa ya gaisa da ni to?" Heedayah tace "Uhn nima dai ban sani ba" Farida tayi shiru, Heedayah tace "Yace in basa number ki nace sai ya biya kuma ya ki biya" Farida tace "Nawa xai biya?" Dariya Heedayah tayi tace "Kudi me yawa na yankar masa shine ya ki" Farida tace "How much" Heedayah ta wara ido tace "Just 100k" Farida tace "Uhm, to turo account number" Dariya Heedayah tayi tace "Xa ki biya masa?" Farida tace "Ehh" Heedayah tace "Hm to xan turo gobe, yanxu xan maida ma Ammi wayarta" Farida tace "Toh don Allah send it tomorrow, I will call in sha Allah" Heedayah tace "Allah ya kai mu, byee" Daga haka ta katse wayar, lkci daya jikinta yyi sanyi, is she suppose to pull Farida's leg this much, tausayinta ya cika Heedayah, a hankali ta ajiye wayar don dama bata son su ci gaba da magana tana bata hope ne yasa tace xata kai ma Ammi waya, bayan wasu mintuna ta dau wayar ta shiga Kiran Khaleel, har ya gama ringing bai daga ba, ta sake kira bai daga ba, ajiye wayar tayi a gefenta ta kwanta ta lumshe ido, tunani iri iri ta dinga yi kafin bacci ya dauketa, can cikin bacci taji vibration din wayar ta bude ido a hankali ta jawo wayar tana kallon screen din.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Kallon agogon jikin wayar dake nuna karfe sha daya da rabi tayi ta daga kiran ta kai kunne ba tare da tace komai ba, sallama ta ji yyi ta amsa snn tace "Ya hanya?" Yace "Alhmdllh" Shiru tayi daga haka, yace "I missed your calls" Ta turo baki tace "Eh ni ban gane maganganun da ka min daxu ba" Yace "Au haba?" Tace "Ehh mana" Yace "Then isn't it better to forget it?" Tace "Noo, sai ka gaya min me yasa xaka wani ce kai kana da budurwa bayan baka da ita, ance maka Faridar bata da class ne? Ai dai bata ta6a nuna maka tana sonka ba, kuma ynxu kana nufin na xubar da class dinta na gaya maka kenan da xaka wani ce A'a?" Yace "Tare muke yawo da ke da kika san banda budurwa?" Tace "Ko ba tare muke yawo ba ni dai nasan baka kula mata, to me ma kke ce masu idan ka kulasu" murmushi yyi yace "Accept my frnd and I will accept ur frnd also, isn't the equation balanced?" Ta marairaice tace "Amma dai kasan ni ina da wanda nake so and I made a lot promise to him..." Shuraim yace "Really?" Tace "Eh" Yace "What sort of promise?" Tace "That's between I and him" Yace "Fine, nima I made lot of promises to my girl..." Shiru tayi bata ce komai ba, lkci daya taji wani haushinsa, calmly yace "Can I go off ur line now?" Bluntly tace "Noo, ba mu gama magana ba" Yace "Ohk Ina jinki gobe da safe xan fita aiki" Kamar xata yi kuka tace "Don Allah ya Shuraim kar ka mana haka, tell me is there anything wrong with Farida da kake tunanin you won't love her?" Yace "Look, kema kiyi tunani, there is nothing wrong with my frnd dat will stop you from loving him, idan har da gaske kina son Farida you can sacrifice ur so called love for her, in har kika yi hakan wllh I am giving you my words gobe ma sai in kai maganarta gun Abbana" Kasa cewa komai Heedayah tayi mamaki ya cikata, jin ta kasa cewa komai yace "You just think about it, sai da safe" tace "Wait, waye mutumin da kake cewa" yace "Idan kince in kawo maki shi sae in kawo maki shi" Ta wani hade rai tace "Ka kawosa in masa me? Why don't you want to understand ina da wanda nake so??" Yace "Fine, Kar ki sake kawo min maganar Farida nima" Daga haka ya katse wayarsa, ta6e baki tayi ta jefar da wayar tana tunanin maganganunsa, can ta kara ta6e baki a ranta tace "Lallai ma" d'an tsaki tayi ta kwanta, bayan kusan minti biyar ta sake jawo wayar, number Khaleel ta kuma kira bai daga ba har ya katse ta ajiye wayar ta lumshe ido tana karanto addu'ar bacci a xuciyar ta. Washegari da safe Heedayah ta gama duk abinda xata yi har karfe tara Khaleel bai kirata ba, daukar wayar tayi ta dialing numbersa amma har ya katse bai daga ba, lkci daya jikinta yyi sanyi, tana ta xaune dakin aka kira Ammi a wayar, mikewa tayi a hankali ta fita xuwa bangaren Ammi, da yake tun asuba ta fito ta gaisheta da Abbanta da step mum dinta, mika mata wayar kawai tayi tace "Ammi ana kiran ki" Amsar wayar Ammi tayi tana duba me kiranta, can ta ajiye tace "Ohk xan kirata, kinyi breakfast din?" Heedayah ta gyada mata kai, Ammi tace "Kin je gaida su kaka?" Tace "Yanxu xan tafi" Ammi ta ci gaba da abinda take, Heedayah tace "Ammi su Ashnaah fa?" Ammi tace "Yanda baki damu da su ba su ma ba damuwa suka yi da ke ba ai" Shiru Heedayah tayi tana kallonta, can ta juya a hankali xata fita, Ammi na kallon wayarta da ya hau vibrate tace "Wa ke kira?" Heedayah ta juyo ta dawo da sauri tana kallon wayar, Ammi tace "Waye?" A hankali tace "Ammi Khaleel ne" Ammi tace "Kiran me yake maki haka ne?" Heedayah ta kasa cewa komai, Ammi tace "Tambayar ki nake" Heedayah ta sunkuyar da kanta still bata ce komai ba, Ammi tace "Dauka ki fita" Daukan wayar Heedayah tayi ta juya ta fita daga dakin, nata dakin ta koma ta xauna gefen gado ta yi dialing numbersa don tuni kiran nasa ya katse, sai da ya kusa katsewa ya daga, ta wani hade rai tace "Why ain't you picking my call tun jiya?" Yace "Na jira baki gama tadi da bakon naki ba shine na kwanta, daxu da kika kira kuma I was together with my uncle, is there any thing wrong with that?" Tace "Tadi kuma?" Yace "Ehh" Tace "Ya Shureen ne fa ya xo" Bai ce mata komai ba, tace "Toh da shi din xan yi tadin?" Calmly yace "Na sani??" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Xan fita yanxu, later..." Bata ce masa komai ba still taji ya katse wayar, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallon screen din, ta fi minti goma xaune a haka kafin ta ajiye wayar, lkci daya ta ji jikinta yyi sanyi sosai, ta kasa ma fita daga dakin, knocking aka yi bakin kofar dakin ta kalli kofar kamar baxata tashi ba sai kuma ta mike ta isa kofar ta bude, Amina ce tsaye bakin kofar ta gaisheta snn tace "Hajiya tace ki kai mata wayarta yanxu" Heedayah ta juya ta koma daki ta dau wayar ta tafi ta kai ma Ammi, Ammi na amsar wayar Heedayah bata yarda sun hada ido ba ta juya ta fita daga dakin, dakinta ta koma ta fada kan gado ta fara kukan da bata san dalilinsa ba, tayi me isarta ta hakura tayi shiru, tana ta kwance dakin aka bude kofar, Kaka ce ta shigo Amina da tayi mata jagora ta juya ta bar bakin kofar, kaka na washe baki tana bin dakin da kallo tace "Ba shakka, ke kuma nan ne bangaren ki kenan, wnn makeken daki haka kamar parlon gidan Amadu, ashe kina nan kusa kusa da uwarki mu kuma an ke6e mu can gefe tunda cin arxiki ne, to ae dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in d'a...." Heedayah ta mike xaune a hankali tace "Ina kwana kaka" Kaka tace "Aa ba ruwana, meye kuma ina kwana, da ban kwana ba xaki gan ni? baki san inda nake bane da xaki wani gaisheni da na shigo dakin ki? ke dai ba kinga na xo gidan ubanki ina ta xama ba dole ki tsiro wani shakiyanci daban, amma baxan biye ta taki ba tunda ba ke kika rokeni in xauna ba" Heedayah dai bata ce komai ba, Kaka ta mika mata wayar hannunta tace "Tun daxu Farida ke son magana da ke, gashi nan kiyi mata flashing don nima ba katin gareni ba, dubu biyar ce jiya Babanki yace ya sa min, gwara inyi ta cancana kayana Ina jin muryar 'ya yana da jikokina" Heedayah tace "Toh na ji" Kaka tace "Idan kun gama ki maido min da wayata yanxun nan" Daga haka ta fita, Heedayah ta duba balance din Kaka taga kusan dubu sha biyar ce a ciki, Kiran Farida ta shiga yi, yana fara ringing Farida ta daga, Heedayah tace "How are you doing Farida?" farida tace "Am fine dear, na kira wayar Ammi baya wajen ki koh?" Heedayah tace "Eh na mayar mata tun daxu, and kilan bata kusa ne" Farida tace "Ohk, kin fasa turowa ne in sa maki?" Heedayah tayi murmushi tace "Ki bari da daddare xan turo maki" Farida tace "Uhn but tell me, why did he even ask of me all of a sudden" Heedayah tace "Kawai yana son gu gaisa ne" Farida tayi shiru, lkci daya jikin Heedayah yyi sanyi tace "Bari idan na gama abinda nake xan kira ki ynxu" Farida tace "Ohkk" daga haka Heedayah ta katse wayar, ta fi minti talatin a ynda take, damuwarta biyu a lkcn, na farko abinda Khaleel yyi mata har da kashe mata waya, na biyu kuma hope da ta fara sa ma Heedayah alhalin Shuraim din isn't even interested, gashi Farida har ta fara farin ciki, can dai ta mike jiki ba kwari ta fita dakin, bangaren Ammi ta koma, a hankali ta lallaba ta isa gun wayar Ammi ta dauka ta kwashe number Khaleel a wayar kaka ta fita da sauri ta koma dakinta. Kiransa ta shiga yi bayan ya daga tace "Shine ka kashe min waya?" Yace "To save you from struggling for words, ya gida ya kike?" Kin cewa komai tayi, yace "don't you want to say anything?" Ta fashe masa da kuka, lkci daya ya rikice yace "Kuka kuma Heedayah? to ki yi hakuri don Allah, I am really sorry" Cikin rawar murya tace "Sbda na damu da kai ma shine xaka wani katse min waya, kuma nake ta kira ka ki dauka" Ya kwantar da murya yace "Wllh bana kusa, kiyi hakuri...." Jin tayi shiru yace "Kin hakura?" Tace "Nima ban sani ba" yace "Wahala xaki bani ko?" Ta turo masa baki, yyi kasa da murya yace "For the love you are having for me kiyi hakuri pls" A hankali tace "Nayi..." Yyi murmushi yace "Good gal, ya su mama?" Tace "Suna lafiya" murya can kasa yace "But kar ki sake ce min kinyi bako plss, that hurts..." Shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Gobe xan bar gombe, am tired" Da sauri tace "Da gaske?" Yace "In sha Allah" tace "Kai da wa?" Yace "Driver...." Tace "Toh plss just drop at kano pls" yace "Kano?" Tace "Yes plss" yace "Why?" Tace "Ka xo ka gaida Abbana da Ammina" Yace "That's idan Mami ta amince, and ita ma tace gobe xata shigo kano tana da case" Da sauri tace "Xata amince ai, plss tell her you will drop there too" Murmushi yyi yace "Ohk Allah ya sa.... You know what karfe nawa xan kira ki ynxu xa mu d'an fita ne" Tace "Ina xa ka?" Yace "Gidan Gwaggwo na" tace "Toh xan kira ka anjima" yace "Alright dear" a hankali tace "Take care of ur self" yace "In sha Allah" daga haka ta katse wayar, tana ta kallon wayar kafin ta nemo number Shuraim, Har xata kirasa sai kuma ta fasa ta ajiye wayar. Yau ma da daddare Amina ta kwankwasa kofa ta sanar mata tayi bako, Heedayah dake kwance tana waya da Khaleel a hankali tace "Ya Khaleel wai Ammina tana kirana" yace "Ohk, should I wait for you or I should go to bed?" Tace "Aa ba dadewa xanyi ba ynxu xan dawo, idan na dawo xan kiraka" yace "Ohk then" katse wayar tayi ta ajiye ta dau hijab dinta ta sa ta fita, visitors palor ta tafi, xaune ta samesa tana kallonsa ta karasa cikin parlon ta xauna tace "Ina yini ya shureen" ya d'an daga kai ya kalleta yace "Looks like da gangan kike 6ata min suna" Tace "To ya xan ce maka?" calmly yace "Aliyu" murmushi tayi tace "Ni dai ya Shureen na sani" ya gyada mata kai bai ce mata komai ba, kallon ledan dake gefensa tayi tace "Wayana ka kawo min" yace "Ehh" ta mike ta dau ledan ta fiddo kwalin ciki, wara ido tayi tace "Waow..." Ta kallesa cike da farin ciki tace "I really like it ya Shureen, irin wanda nake so ne wllh" ta isa kusa da shi ta xauna arm din kujera tana murmushi sosai tace "Thank you...." Ta gefen ido ya kalleta amma bai ce komai ba, ta turo baki tana kallonsa tace "Nace thank you" yace "I prefer a cup of tea to that thank you" dariya tayi tace "Ohkk" daga haka ta mike ta dau hanyar kitchen ya bi ta da ido.... Shayi ta hada masa ta xubo masa pepper soup din offals a bowl snn ta fito, har ta shigo parlon kallonta yake ta isa gabansa ta durkusa ta ajiye bowl din offals din da cup din shayin ta wara masa ido tace "Is the thank you enough?" Yana kallon pepper soup din yace "Sure you are wlcm" ta dau spoon ta deba ta xai baki ya cafkota, xaro ido tayi, yace "Mayar ciki" da sauri ta fiddo a tafin hannunta tace "Toh xan karo maka sakeni..." yace "Wnn za ki ajiye" ganin ba saketa xai yi ba ta mayar da naman cikin bowl din, a hankali ya saketa yana kallonta, da mamaki take kallonsa ita ma, ya sauke idonsa ya dau cup din shayin ya fara sha snn yace "So what have you decided?" Tace "About?" Yace "Our talk yesterday" Shiru tayi na d'an lokaci, sai kuma ta kallesa tace "I've decided discard my request, cause ba a forcing soyayya, I will console Farida in ce mata may be kai din ba alkhairi bane gareta Allah xai bata wanda ya fi ka" kallonta kawai yake ko kiftawa bbu, can yyi murmushi yace "That's because you are soo self centered, kanki kawai kika sani, you can never sacrifice ur love for her, nasan kuma da ita ce she will gladly do that for you" Heedayah tace "I am not being self centered, kaga kai ba sonta kake ba, ni ma kuma I will never agree to ur so called frnd, to ae hakan ba shi da amfani, ita ya kamata tayi hakuri tunda ba wai sonta kake ba" Shuraim dake ta kallonta yace "Haka nace maki bana sonta?" Tace "To tunda kana sonta snn ita ma tana sonka, ni me yasa xaka min dole, you are not being fair to me kenan?" Wani murmushi yyi yana ci gaba da shan shayin hannunsa, Khaleel ne ya fado mata ta xaro ido gabanta ya fadi, ta san yana can yana jiran kiranta, a hankali tace "Ya Shureen can I go now ina yin wani abu ne a sama" ya d'an kalleta kafin yace "Noo, wait in gama sai ki wuce" bata ce komai ba, bayan ya sha shayin ya ajiye yana kallonta yace "Take them back to the kitchen" tace "Pepper soup din fa?" Yace "I am full" tace "Ai baka ci ba" yace "Na sani" mikewa tayi ta dauka ta wuce da su kitchen gaba daya..... Tsaye ta gansa parlon yana kallonta yace "Mu je waje xan maki magana" Ta kalli agogo kamar xata yi kuka bata ce ma Khaleel xata dade haka ba, kofa ya nufa ta bi bayansa har suka fita parlon..... Abban Heedayah na xaune parlonsa tare da Ammi sai mom Islam, Abba ya kalli Ammi da gaba daya mood dinta ya canxa lkci daya kuma tayi shiru, yace "Say something Aisha" Ammi ta girgixa kai a hankali tace "But ur Excellency what's wrong with the Junaid da xa a biye mata don tace bata so? Idan ma bata sonsa ga Shuraim dama ni hankalina ya kwanta da shi" Abba yace "Ke dole kike son ayi mata? snn still wanda tace take so ai d'an gidan ne shi ma naga" Ammi ta kallesa da sauri tace "Wa kenan??" Abba yace "Wan Junaid din, Khaleel..." Da mamaki Ammi ke kallonsa, can tace "Haba ur Excellency, ni gaskiya ban amince da wnn xancen ba, me yasa xa a biye mata kamar ita ta haife mu??" Abba yace "Abinda yyi Junaid shi yyi yayansa, haka ko ba haka ba?" Ammi tace "Aa wllh, his past..." Sai kuma tayi shiru, Abba kallonta kawai yake, Mom Islam tace "His past is nothing to write home about.... And kina duba reputation na gidan nan ko?" A hankali Ammi tace "Exactly Maimuna" Murmushi Mum Islam tayi sannan tace "Amma kar ki manta Aunty, Mahaifiyar wnn mutumi bata san wacece Heedayah ba, bata san 'yar wacece ita ba, bata san daga inda take ba amma ta yrda ta amince ta riketa bayan shi wanda ma ya tsinceta an ki rike masa ita cikin iyalinsa" Kasa cewa komai Ammi tayi, Mum Islam tace "It isn't Khaleel's fault he found himself in such life, kar ki manta yau da Heedayah ba hannu na gari ta fada ba Allah kadai yasan wani irin rayuwa xata yi, Allah kadai yasan abinda xata xama, albarkacin wnn bai kamata ki kyamaci d'an wannan baiwar Allah da ta inganta rayuwar 'yar ki ba ba tare da hakan ya bata wahala ko shakku a ranta ba...." Murmushi kawai Abban Heedayah ke yi bai ce komai ba, Ammi dai ta kasa cewa komai..... *Wlh nayi busy fans ayi min uxuri, it's just for sometimes plss...* Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Karfe goma saura Heedayah ta farka daga baccin da ta koma da safe, kallon sabuwar wayan da Shuraim ya kawo mata dake ajiye gaban mirror tayi, ta mike xaune, sai kuma ta tashi ta tafi ta dauko ledan ta dawo ta xauna ta ciro wayar daga kwalinsa, ta dau sabon sim card da ya siyo tare da wayar tana jujjuyawa, can dai ta saka cikin wayar ta duba ko da kudi a layin taga dubu biyar, number Khaleel ta yi dialing ta kira, har ya katse bai daga ba, can ta kara kira ya dauka, tayi masa sallama, ya amsa yace "Whose line?" Tace "Nawa" Yace "Ohk okay, an kawo maki wayar ki daga Kaduna?" Tace "Aa sabuwar waya ce" Yace "That's good, ya mutanen gida?" Tace "They are fine, are you still leaving gombe today?" Yace "Ina hanya" Ta wara ido tace "Amma ban ji hayaniya ba" Yar dariya yyi, tayi shiru tana sauraronsa, his laugh was unique, bata ta6a jinsa yyi dariya ba, yace "Motar haya kike son ki ji na hau?" Tayi murmushi tace "Aa ni bance haka ba" Yace "Ohk, motar kawu na ne... And i am together with his driver" Heedayah tace "Toh Allah ya tsare, kun kusa?" Yace "Obviously" tace "Toh Allah ya kawo ku lafiya" Yace "But...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yace "Is it necessary sai mun tsaya kano?" Bata fuska tayi tace "Ni ba necessity dinka bace ai... It's not necessary" Ya wara idanuwansa yace "Sorry ba haka nake nufi ba, anyway in sha Allah xa mu tsaya kano" Jin ta ki cewa komai yace "Kin yi shiru" Kamar xata yi kuka tace "Wato xa ma ka iya wucewa baka tsaya ka gan ni ba" Yace "Noo, baxan iya ba" Tace "Toh Allah ya kawo ku lfya" yana murmushi yace "Ameen" Daga haka ta katse wayar, Har xata ajiye sai tayi dialing number Shuraim da ta haddace, yana fara ring ya katse, sai ga shi ya kirata, dauka tayi amma bata ce komai ba, yace "How was ur night?" Tace "Fine, good morning" Yace "Morning" Tace "Ya Shureen me yasa baka ce min so kake in bar maka laptop dina gaba daya ba..." Shiru ta ji yayi, can yyi murmushi yace "Saboda nace maki bani da nawa?" Tace "Toh ai ban sani ba" Yace "Toh xan kawo maki anjima" Ta wara ido tace "Aa wasa nake, you can use it har lkcn da ka gaji da shi" Yace "Okay kin kira ne just to hear from me kika fake da laptop?" Ta turo baki tace "Sbda laptop na kira ka" Yace "I see, ya kawarki?" Tace "She's fine, why do u ask?" Shiru yyi bai ce komai ba, ita ma tayi shiru, can tace "Ya Shureen me kake son gaya min da na raka ka jiya kuma ka fasa?" Yace "Naga ke yarinya ce shi sa na fasa" Dariya tayi sosai tace "Yarinya?" Bai bata amsa ba, tace "Meye ka sani wanda ni ban sani ba har yanxu??" Shiru yyi, can yace "Allah ko?" Tace "Eh mana, ni din ce yarinya?" Murmushi yyi yace "Ohk, xan nuna maki abinda ni nasani wanda ke baki sani ba" Ta ta6e baki tace "Babu wannan abun, nice ma nasan abinda kai baka sani ba" yyi shiru.... Can yace "Da yake ke har gidan da ba naku ba kin ta6a kwana ko?" Shiru tayi ita ma kafin tace "Ban gane ba" Yace "Ohk leave it" Ta hade rai yace "Wani gidan ne na kwana da ba namu ba?" Yace "Ni xa ki tambaya?" Tace "Toh ai dai naga ba gidan wani daban na kwana ba gidan saurayina ne" Yace "Haka ne, dole ki san abinda ni ban sani ba kam, i will hang up now ina wajen aiki" daga haka ya katse wayar, ta kalli screen din snn ta ajiye wayar tana hararansa, mikewa tayi ta fita dakin ta tafi bangaren Ammi, ganin tana da baki ta wuce bangaren Mum Islam, Mum Islam na kallonta tace "Sai yanxu kika tashi?" Ta xaro ido tace "Aunty sai karfe takwas da rabi fa na kara wani baccin bayan nayi wanka, mun fa gaisa da Abba tun sassafe" Mom Islam tace "To xauna dama ina nemanki" Heedayah ta xauna gefen makeken gadonta tana kallonta, Mom Islam ta xauna gefenta tace "Ki gaya min gaskiya Heedayah..." Sosai gaban Heedayah ya fadi ta dinga kallonta, Mom Islam tace "Heedayah tell me, ke a xuciyar ki wa kike so, but kar ki manta xaman aure fa ba abinda xa ayi na shekara daya ko na shekara biyu bane, xama ne na dindindin, xama ne na har abada, ba a fatan rabuwa sai in mutuwa" Heedayah ta sauke kanta kasa, Mom Islam tace "Ina jin ki, wa kika ji xuciyar ki ya kwanta da" a hankali tace "Aunty ni Khaleel nake so" Mom Islam tace "Kin tabbatar?" Ta gyada mata kai, Mom Islam tace "Me yasa baki son kaninsa?" Heedayah tace "Aa ni bance bana sonsa ba, kawai baxan iya aurensa bane, Ya junaid is among the people that did good to me, yana da kirki sosai, kuma ya nuna min kulawa yanda xai yi ma Farida, amma ni i can't marry him" Mom Islam tace "Shi kuma Khaleel me yasa kike sonsa?" Heedayah ta d'an yi shiru, Mom Islam tace "Ina jin ki" A hankali Heedayah tace "Ina sonsa sbda shi ne mutum na farko da ya fara taimakona a rayuwa, Ina sonsa sbda yana da hali me kyau if not of the situation he found himself, kuma na ga yana da rikon addini duk da haka, kuma ina tausayinsa sosai, I don't want anything to happen to him ta dalilina, Aunty ai kinsan condition dinsa" a sanyaye ta kare maganar, Kallonta kawai Mom Islam take kafin tace "Anya ba tausayin Khaleel kike ba Heedayah?" Heedayah ta kalleta tace "Ehh ina tausayinsa kuma Ina sonsa" Mom Islam ta girgixa kai tace "Aa tausayin ya fi yawa nake kaga" Heedayah tace "Aa, bayan tausayinsa nasan ina sonsa, tun daga sanda muka fara waya da shi, Aunty kinsan fa har gidansa na ta6a kwana, his ways of life is perfect, yana rikon addini sosai, kuma in sha Allah nasan ya daina abinda yake har abada...." Mom Islam tace "Eh nasani" a hankali Heedayah tace "Wllh ina sonsa Aunty" Mom Islam tace "Toh shkkn Allah ya tabbatar da alkhairi dear" Heedayah ta sauke idonta kasa tace "Ameen, Yana hanya ma Aunty" mom Islam tace "Xai xo nan?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Ya ma ce min ya kusa" Mum Islam tace "Shine baki sanar ma kowa ba?" Heedayah ta kalleta tace "Yanxu muka yi waya da shi ya gaya min, naje xan gaya ma Ammi naga tayi baki, shine na xo nan" Mom Islam tace "Toh Allah ya kawo sa lfya" Heedayah tace "Toh Aunty me xa a dafa masa?" Mom Islam tace "Abinci ba matsala bane ai masu aiki suna can ma suna yin na rana, kawai xuwa xa muyi ayi masa sabon snacks coz wanda ke da akwai aren't fresh" Heedayah tace "Toh Aunty" Mikewa Mom Islam tayi tace "Ki tafi nawa kitchen din Ina sakkowa yanxu" Heedayah tace "Aunty kitchen nawa ne gidan nan?" mom Islam tace "Kitchen hudu ne" Heedayah tace "Ohk" daga haka ta fita. Sai da suka kusa gama snacks din da suke yi Mom Islam tace "Nasan bakin Amminki sun tafi yanxu ki je ki sanar mata" Heedayah ta wanke hannunta ta fita kitchen din, bangaren Amminta ta tafi, Kawar Ammi daya ce a parlon, Ammi na kallonta tace "Ya aka yi?" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta mike ta wuce bedroom dinta ta bi bayanta, Ammi na kallonta tace "You want something?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa Ammi ya Khaleel ne xai xo?" Shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Daga ina?" Heedayah tace "Daga wajen relatives dinsa a Gombe" Ammi tace "Toh ni bani xaki fadi ma ba ai, sai ki sanar ma Babanki" Daga haka Ammi ta fita daga dakin, Heedayah ta fi minti biyar tsaye kafin ta juya ta fita, kitchen ta koma gun stepmom dinta, Step mum din na kallonta tace "kin sanar mata?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Amma tace ba ita xan gaya ma ba Abba xan gaya ma" Mom Islam tace "Bari mu koma daki sai in kira private number dinsa yana gunsa idan ya daga sai ki sanar masa" Heedayah tace "Toh" har suka gama jikinta a sanyaye yake suka fita kitchen din tare xuwa bangaren Mom Islam. Mom Islam ta kira Abban Heedayah ta mika mata wayar bayan ya daga, nan Heedayah ta sanar masa Khaleel na hanya, Abba yace "Yau?" Heedayah tace "Ehh" Abba yace "To maa sha Allah, Allah ya kawo sa lafiya" Heedayah tace "Ameen" Amsan wayar Mom Islam tayi tace "Toh xaka sanar da xuwansa ne kar ya samu matsala wajen shigowa tunda bashi da wani appointment?" Abban Heedayah yace "In sha Allah" Daga haka suka yi sallama ta katse wayar ta ajiye, a sanyaye Heedayah tace "Aunty me yasa kamar Ammi bata son ya xo?" Mom Islam tace "Aa tana so mana, tunda kince ya kusa ki tafi ki shirya sabbin kayanki na can wajenta da tailor ya kawo last week, ki kawo akwatin gaba daya in xabar maki wanda xa ki saka" Heedayah tayi shiru, can tace "Nawa ni kadai Aunty?" Mom Islam tace "Aa ke da Farida da kannin Shuraim biyu, amma bai kawo nasu ba tukun" Heedayah tace "Toh a ina aka samu measurement dinmu?" Mom islam tace "Mami ce ta turo naku, kannin Shuraim kuma Uwarsu" Heedayah tace "Ohk" mikewa tayi ta fita xuwa gun Amminta, nuna mata trolleyn kayan kawai Ammi tayi, Babban trolley ne sosai, ta ja sa har xuwa bangaren Stepmom dinta, Mom Islam ta kwantar da akwatin ta bude, kaya ne duk a goge kala ashirin da biyar masu tsada sosai ko wanne kuma da mayafinsa, duk laces ne da atamfa, mom Islam na duba kayan a nutse tace "Ba su kenan ba ma, kilan basu gama ba tailors din" Wani ubansun lace me tsada ta fiddo ta ajiye mata, Heedayah ta dinga kallon lace din, Mom islam ta dauko wani akwatin cikin press dinta ta kwantar ta bude duk takalma ne da jaka kusan kala goma, Mom Islam tace "Naki ne, tun da aka kawo ban kai gun Ammin ki ba" Takalmi da jaka da xai tafi da lace din ta fiddo ta ajiye gefen gadonta inda ta ajiye kayan, Heedayah na murmushi tace "Nagode" Mom Islam tace "Ki shiga bandaki ki sake wanka ki fito" Heedayah ta cire doguwar rigar jikinta, ta shiga bandakin, ba a dau lkci sosai ba ta fito daure da towel din step mum dinta, a nan dakin tayi sllhn azahar sannan ta shirya, kallonta kawai Step mum dinta ke yi tana murmushi don sosai kayan su amsheta, Heedayah ta sunkuyar da kanta, Mom Islam tace "Kinyi kyau sosai my daughter" Murmushi Heedayah tayi tace "Nagode Aunty" Mikewa Mum Islam tayi ta dauko kit din kayan make up dinta, nan tayi mata very light make up, Heedayah ta dawo kamar ba ita ba, tayi kyau sosai kamar wata amarya, Mum Islam ta kara fesa mata turarurrukanta iri iri sannan ta dauko mata wani dankunnen zinari da zobe ta bata ta saka, mom Islam tace "Two month ago wata kawata ta kawo na daukar maki" Heedayah na murmushi tace "Nagode Aunty" Mom islam tace "Toh kuma ina kika bar wayar kar yyi ta kira" Heedayah ta xaro ido tace "Lahh yana dakina" daga haka ta fita da sauri ta tafi dakinta dauko wayar, miss call dinsa daya ta gani, ta shiga kiransa, bayan ya daga tace "Sorry bana kusa wllh, kun iso ne" Yace "Ehh mun ma shigo" Tace "Okay no problem ko?" Yace "Sure, tare da wani soja" Tace "Toh sai kun karaso" tafiya tayi da wayar ta koma gun Mom Islam, nan ta sanar mata sun shigo, mom Islam tace "To mu je in hada maki abinda xaki kai masa kar kiyi shirme" Tare suka fita xuwa kitchen dinta, dama ta sa yan aiki su debo duk abinda suka dafa a different cooler su kawo mata kitchen dinta su ajiye, mom Islam taga warmer din a jere, ta shiga budesu one by one, shinkafa da miya with cow meat, sai tuwo da miyar assorted egusi, da garnished cous cous da ya ji hanta, pepper soup na kaza sai xuba kamshi yake, last bowl din ta bude taga coslow ne ciki, Mum Islam ta kalli Heedayah dake tsaye gefenta tace "What's his favourite?" Heedayah ta bude hannu tace "Nima ban sani ba" Mom Islam tace "Toh a kai masa shinkafa da miya da coslow da pepper soup din, sai a debi cous cous kadan a plate a hada ko?" Heedayah tace "Toh" Nan Mom Islam ta fara hada abincin a tray, ta dauko ginger and zobo drink da tayi tare da snacks tace "Shi xa ki fara kai masa" Heedayah tace "Toh" kallon wayarta da ya fara ring tayi tace "Aunty kilan sun shigo" Mom islam na kallonta tace "Toh ki fita ki shigo da shi" Heedayah ta koma ta dauko mayafinta ta sa takalminta snn ta fita, har wani walwali take kamar amarya cikin kayan jikinta, a hankali take tafiya, ta gansa xaune inda suka ta6a xama tare da Shuraim, kallonsa take tun daga nisa don kaftan ne a jikinsa da hula, bata ta6a ganinsa da manyan kaya ba sai yau, sai yyi mata kama da balarabe da yyi dressing din hausawa, sosai kayan suka yi masa kyau, shi ma kallonta yake kamar yanda take kallonsa har ta isa inda yake, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Sannu da xuwa" Yace "Uhn baki gane ni bane?" Ta boye fuskarta tace "Ya hanya" yace "Alhmdllh" Tace "Toh ka shigo ciki" Yace "Bari in huta kadan" Ta kallesa tace "Toh a ciki ma ai xa ka huta" Mikewa yayi ta dinga kallonsa, a hankali tace "Kayi kyau" Yace "A'a ke dai kika yi kyau" Murmushi tayi ta fara tafiya ya bi bayanta, parlon baki ta kai sa tace "Bari in kawo maka ruwa" Daga haka ta wuce can kitchen din Mom Islam ta dauko tray din ginger drink da zobo sai bottle water da snacks ta fita ta koma parlon, xaune ta gansa ya jinginar da kansa da kujera idonsa a lumshe, a hankali ta durkusa ta ajiye tray din hannunta tana kallonsa ya bude idonsa yace "Thank you" ta xuba masa ruwa a glass cup ta mika masa ya amsa, Mikewa tayi tace "Ina xuwa" daga haka ta fita parlon, Bangaren step mum dinta ta tafi, tana kallonta tace "Aunty ya na parlor" Mom Islam tace "Ohk to bari in je mu gaisa, ki je ki sanar ma Ammin ki" Heedayah tace "Toh" fita tayi ta koma bangaren Amminta, cikin dakinta ta sameta, ta kasa kallonta gabanta na faduwa tace "Ammi ya iso yana parlor" Ammi tace "Wa ya iso?" Heedayah tace "Khaleel" Ammi tace "Ohk..." Bayan few seconds Heedayah ta juya ta fita dakin, a parlon da Khaleel yake ta tadda Mum Islam xaune suna gaisawa, Heedayah ta shigo ta xauna kasan carpet, Mum Islam na kallon Heedayah tace "Ki kai sa ya gaisa da su Yakumbo" Heedayah tace "Toh" Mikewa tayi tace masa sai anjima sannan ta fita daga parlon, Heedayah na kallonsa tace "Mu je yanxu?" Yace "Aa let me rest first" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani lkci tace "Toh baxa ka ci snack din ba" Xaunawa yyi kan lallausan Carpet din parlon yace "Mun ci abinci a nan kano fa Heedayah, wllh I am not hungry" Lkci daya ta 6ata fuska, yyi murmushi ya dau samosa daya yace "Ke ma xo ki dauka idan kina son in ci" D'an murmushi tayi ta mike ta koma inda yake xaune leaving a little distance between them ta dau samosa daya, kallonta kawai yake har ta kai baki, sai a snn ya ci na hannunsa, kadan ya ci yace "Ban iya cin abin nan ba, yau na fara ci sbda ke" Heedayah ta xaro ido tana kallonsa, ya dau ruwa ya sha, yace "Ya isheni wllh" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Me kafi so cikin abinci?" Yace "fried rice, rice and stew, meat ko wani iri na halal Ina ci, I love pizza, shawarma, sausage, burger, milk drink, tea.... I think that's all" Xaro ido Heedayah tayi tace "Tuwo, wake, taliya, macaroni, egg, fish, different soups...." Katse ta yyi yace "Hell No, abinda na lissafa maki kadai nake ci a duniya" da mamaki Heedayah ke kallonsa, Sallama aka yi a kofar parlon, Heedayah ta juya da sauri, Ammi ta shigo parlon, Khaleel ya sauke idonsa kasa, xaunawa Ammi tayi saman kujera tace "Sannu da xuwa" da ladabi yace "Ina yini" da murmushi fuskarta tace "Lafiya lau ka xo lafiya?" Yace "Alhmdllh, ya gida" Tace "Alhmdllh, daxu mun yi waya da Barrister tace min tana kano" Khaleel yace "Ehh tana nan" Ammi tace "Kun hadu da ita kenan?" Yace "Aa ba mu hadu ba" Ammi tace "Ohk anjima xa mu je da driver sai in daukota in sha Allah" Khaleel yace "Allah ya kai mu" Ammi tace "Ameen, you are welcome" D'an murmushi yayi yace "Nagode" Mikewa tayi ta fita parlon, Heedayah ta wara ido tana kallonsa tace "Ashe Mami ma ta xo?" Yace "Ehh ta xo" Heedayah tayi murmushi tace "Xan bi ku mu koma" Ya wara ido bai dai ce mata komai ba, tagumi tayi tana kallon dogon hancinsa, ya shafa kansa ya bude goran ruwan ya diba a glass cup, a hankali tace "Zayyad fa?" Yace "Yana gombe mun hadu ma" tace "Wajen wa a Gombe?" Yace "Shi ma Yan uwansa na can gomben" Heedayah tace "Ohkkk" wayarta dake hannunta ne ya fara ring ta kalla ta ga Shuraim ke kiranta, a hankali tayi silencing wayar, Khaleel dake kallonta yace "Pick ur call" tace "Aa ban san waye ba" Wani samosan ta dauka ta fara ci tace "Me yasa baxa mu je mu gaida su kaka ba yanxu?" Yace "Xan je anjima kadan" Mai aiki ce ta shigo parlon ta gaida Khaleel da ladabi tana kallon Heedayah tace "Aunty tace ki je" Heedayah tace "Toh" mikewa tayi tana kallonsa tace "Bari in je in dawo" Ya gyada mata kai ta wuce, tana Isa bangaren Step mum dinta, tace "Abbanki ya kira yanxu yace yaje office ya samesa" Heedayah tace "A ina office din?" Aunty tace "Government house" Heedayah tace "Toh wa xai karasa da shi?" Aunty tace sojoji suna waje suna jiransa, Heedayah tace "Ohk" daga haka ta fita dakin, bayan ta sanar ma Khaleel abinda Aunty tace, ita ta rakasa har inda soldiers din suke snn ta koma ciki. Sai bayan la'asar Khaleel ya dawo, Heedayah har ta canxa kayan jikinta xuwa wani sabon atamfar me tsada, xaune ta samesa a parlor, ta xauna kasa tana kallonsa tace "Sannu da dawowa" yace "Thanks dear" mikewa tayi tace "Bari in kawo maka abinci" yace "Na ci abinci" tace "A ina" murmushi yyi yana kallonta a hankali yace "Wllh na ci" Tayi shiru, shi kam kallonta kawai yake, murya can kasa tace "Mami ta xo tana sama wajen Ammina" Yace "Ohk..." Bude kofar parlon aka yi suka juya a tare, Shuraim ne ya shigo Heedayah ta dinga kallonsa, ya ja gefe ya tsaya, Sudais ya shigo parlon, wara ido Heedayah tayi ta mike tana kallonsa tace "Ya Sudais" murmushi ya sakar mata yace "Cutie..." Bata san lkcn da ta nufesa da gudu ba, saura kiris ta rungumesa lkci daya ta ja baya, sai kuma ta fashe da dariya tana kallonsa, shi kam murmushi yake, Khaleel ya dauke kansa, Shuraim dama tuni yyi hakan.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Barin su Shuraim yyi a wajen ya karasa cikin parlon ya mika ma Khaleel hannu suka gaisa, Heedayah suka karaso parlon tare da Sudais, Sudais na murmushi ya mika ma Khaleel hannu shi ma, Khaleel ya mika masa nasa suka gaisa, Kofa Shuraim ya nufa Heedayah ta bi sa da kallo tace "Ya Shureen are you going??" Ba tare da ya juyo ba yace "Yea" daga haka ya fita, Heedayah ta mike ta tafi ta kawo ma Sudais ruwa yana kallonta yace "Cutie shine kike gudo kika bar mu a kaduna?" Murmushi tayi tace "Aa ya Sudais na xo hutu ne xan koma soon" yace "Toh ya su mama?" Heedayah tace "Bari in kirata ku gaisa" Yace "Noo ba kina da bako ba kar ki damu anjima xan dawo, yanxu sauri mu ke kawai nace bari in xo mu gaisa, xan wuce jigawa ne immediately" a hankali tace "Toh yaushe xaka dawo?" Yace "Before Magrib idan Allah ya yrda" Daukan ruwan yyi ya sha yace "Let me get going don in dawo da wuri" tace "Kai da ya Shureen xa ku je?" Yace "Aa nan kawai nace ya rakoni" mikewa yyi ya karasa gun Khaleel ya sake basa hannu still smiling yace "Xan koma" Khaleel yace "Allah ya tsare hanya" Heedayah ta bi sa da kallo tace "Allah ya dawo da kai lafiya ya Sudais" Yace "In sha Allah cutie" daga haka ya nufi kofa, Khaleel yace "Ki rakasa mana" ta kallesa tace "In rakasa?" yace "Ehh" mikewa tayi ta nufi kofa da sauri ta fita, tsaye ta gansa inda Shuraim ke xaune a karkashin thatched roofing, ta karasa inda suka Sudais na kallonta yace "Why did you leave him?" Murmushi Heedayah tayi tace "Raka ka xan yi" yace "Noo, Kar ki damu ki koma kawai, amma fa kar ki ce da kaka na xo" tayi murmushi tace "Baxan gaya mata ba" Ta kalli Shuraim dake danna wayarsa tace "Ina yini ya Shureen" without looking at her a takaice yace "Lafiya" Mikewa yyi yana kallon Sudais yace "Toh mu je" Daga haka ya fara tafiya, Sudais yace "Sai na dawo Heedayah" daga masa hannu tayi ya bi bayan d'an uwan nasa, sai kuma ya juyo yana mata murmushi yace "Saurayin naki so handsome.... Kamar balarabe" Da sauri Heedayah ta juya ta koma ciki tana murmushi, bayan ta shiga parlon ta xauna kasa kusa da Khaleel tana kallonsa da murmushi fuskarta tace "Ya Khaleel kasan waye ne shi" Yace "I think xan xo in wuce yanxu, so that I can reach Kaduna early" Shiru tayi tana kallonsa, ya mike yace "Erm kice da su Ummi na wuce, bana son night journey" Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta sauke idonta kasa, ya dau wayarsa yace "I bought you perfumes, suna mota, but bari in wuce da su kaduna anytime kika dawo ki karba" Jin bata ce komai ba still yace "Ain't you talking?" Hawayen dake makale idonta ya sakko, shiru yyi yana kallonta, can ya koma ya xauna yace "To me na maki kuma kike kuka?" Ta rufe fuskarta da kujera hawaye na sauka idonta, kallonta kawai yake, can yace "Hasbunallah, yanxu kukan me kike Heedayah?" Ta share idonta ta mike tace "Allah ya kiyaye hanya" daga haka ta juya xata bar wajen ya fixgota, fadowa tayi gefensa kan kujeran, ta fashe da kuka a hankali.... Ya kwantar da ita shoulder dinsa a hankali yace "Tell me plss me yasa kike kuka" taki cewa komai yana jin hawayenta na sauka jikinsa, sosai jikinsa yyi sanyi, ya sa daya hannunsa yyi wrapping dinta much closer to him, sai ta xama yar karama kusa da shi, lkci daya ta tsayar da kukan da take, ya daura goshinsa saman kanta cikin sanyin murya yace "I am sorry Heedayah...." ita dai ta kasa ce masa komai, ta ji gabanta ya hau faduwa, xame jikinta ta fara yi amma ta kasa kwace kanta sbda irin rikon da yyi mata, kamar xata yi kuka tace "Ka sakeni" ya ki saketa, a hankali yace "Tell me kukan me kike?" Tace "Plss ka sakeni ya Khaleel" ya dago kanta yana kallon kwayar idonta da idanuwansa da suka sauya launi lkci daya, ta ki yrda su hada ido gabanta sai faduwa yake, a hankali yace "Me yasa kike son kula wasu mazan??" Xaro ido tayi ta kallesa, yace "Me yasa kullum sai Shuraim ya xo wajen ki? And what stopped you from hugging the other guy??" Kamar xata yi kuka tace "They are all my brothers fahhh...." Kauda kanta tayi ganin kallon da yake mata, bata ta6a jin xuciyarta na bugawa irin haka ba, gaba daya jikinta yyi sanyi, xata kwace kanta still ya ki saketa, ta juyo ta kallesa kamar xata fashe masa da kuka tace "Yaya plss ka sakeni, kar wani ya shigo" sosai canjawar da idanuwansa suka yi ke bata tsoro, ya kamo hannunta cikin taushin murya yace "Heedayah" bata yrda ta kallesa ba, ya juyo da kanta da damuwa yace "Don't break my heart Heedayah, Ina maki son da nima ban san irinsa ba, Ina maki son da bbu macen da na ta6a yi ma..." Sauke idonta tayi kasa jikinta yyi sanyi ba kadan ba, ya daura forehead dinsa saman nata yace "Kin ji?" Muryarta na rawa tace "I won't...." Ya daura lips dinsa saman dogon hancinta ya lumshe idonsa, ta kwace kanta da karfi gabanta na faduwa ganin abinda yake son yi, xamowa kasa tayi ta xauna, ya biyota kasan a hankali yace "I am... Am sorry" kasa kallonsa tayi, shiru duk suka yi na kusan minti biyar, can yace "Xan shigo da daddare in sha Allah" Daga haka ya mike tsaye da kyar ta saci kallonsa ta sunkuyar da kanta, ganin ya fara tafiya, a hankali tace "Don Allah da gaske xaka dawo?" Ya juyo yace "In sha Allah, Mami tace in bari mu tafi gobe" Ta sunkuyar da kanta ya nufi kofa, a hankali ta dago ta bi sa da kallo gabanta na faduwa har ya fita. Har Magrib Mami na can bangarensu Kaka, tun da Heedayah ta je ta gaisheta bayan tafiyar Khaleel bata sake xuwa ba tana bangaren Step mum dinta, sai bayan da tayi Magrib ta fita xuwa gun Amminta, Ammi na bedroom dinta tare da su Ashnaah, Xaunawa tayi ta gaida Ammi, Ashnaah ta nufeta tana nuna mata takardan hannunta tace "Aunty Abba ne ya siya min da Ashfah" Heedayah ta amshi takardan tana dubawa, Ammi tace "Bakon naki ya tafi?" Heedayah tace "Ehh tun da yamma" Ammi tace "Kadunan ya wuce?" Ta girgixa kai tace"Yace min da Mami xa su koma gobe" Ammi bata kuma ce mata komai ba, bayan wani lkci Heedayah ta mike ta fita tunawa da tayi Khaleel yace xae xo da daddare, dakinta ta tafi ta dau wayarta ta xauna gefen gado tayi dialing number din Shuraim, har ya gama ring bai daga ba, ajiye wayar tayi tana ta xaune gefen gado sai ga kiran Khaleel, Dauka tayi a hankali tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Come out now..." Tace "Ohk baxa ka shigo ku gaisa da Mami ba?" Yace "Mun yi magana ta waya da ita" Heedayah ta 6ata fuska tace "Aa ka dai shigo plss" ya d'an yi shiru snn yace "Ohk" katse wayar tayi ta mike ta d'an gyara fuskarta ta feshe sabon hijab dinta da turare sannan ta fita dakin tana rike da wayar, parlon baki ta samesa, ta nufesa tana murmushi ta durkusa gefensa tace "Ina yini?" Ya shafa kansa yace "Lafiya lau" ta mike tace "Mu je ku gaisa" yace "Where?" Tace "Sama" Bai ce mata komai ba ya bi bayanta, tafiya sosai suka yi har suka iso bangaren da su kaka suke, ta bude kofar a hankali tare da sallama, Kaka na xaune parlon da Yakumbo, Mami ma na parlon tare da Shuraim, kaka na ta kallon Heedayah tace "Rakiya ba don iyayen Heedayah 'yan halaq bane da shkkn mun taimaketa a banxa ko bi ta kanmu baxa ta sake yi ba a rayuwa, Ina lura da ita bata wani farin ciki da xaman gidan nan da nake yi, toh bata farin ciki mana tunda ba gaisheni take ba kwata kwata yanxu" Heedayah ta hade rai ta ba Khaleel hanya ya shigo parlon da sallama cikin cool voice dinsa, Tsit kaka tayi, Yakumbo ta sunkuyar da kanta, Heedayah na kallon Shuraim ta nufi Mami ta durkusa kusa da ita da murmushi tace "Mami good evening" Mami tace "How are you dear" Xaunawa Khaleel yyi daga inda Shuraim yake, Shuraim ya basa hannu suka gaisa, Khaleel na kallonsu kaka yace "Ina yinin ku?" A tare kamar hadin baki suka ce "Lafiya lau" ko wacce na kirkiran murmushi, ya kalli Mami yace "Ina yini Ummi" Mami tace "Lafiya lau, how was the journey?" Yace "Alhmdllh" tace "Ka baro su lfya?" Yace "Suna gaishe ku" Mami tace "Maa sha Allah" Kaka da Yakumbo dai kallo kawai suke a TV, Khaleel ya mike yace "Xan koma" Kaka tace "Toh madallah, Allah yyi maka albarka, ina Junaidu?" Mami tace "Yana Kaduna" Kaka tace "Atohh, shi dama ba mai son yawace yawace bane" Mami dai bata ce komai ba, Khaleel yyi ma Mami da Shuraim sallama snn ya nufi kofa, Heedayah ta mike sai da ta ga ya fita parlon ta kalli Shuraim ta hade rai kamar xata yi magana sai kuma ta fasa ta bi bayan Khaleel da sauri, Yakumbo ta bi ta da kallon damuwa. Khaleel bai yarda ya xauna parlon baki ba wai ya fi son waje, bbu ynda ta iya masa kawai suka fita, tana kallonsa a inda suka xauna tace "Toh abinci fa?" Yace "Naga alama kina da son abinci sosai, ke dai kawai aci abinci?" Dariya tayi ta rufe fuskarta tace "Toh laifi ne don an ci abinci" Murmushi yyi bai ce komai ba, tace "Kayi shiru?" Yace "Na sha fruit before coming" Tace "Just fruit?" Yace "Yea and am okay" Sun fi minti arba'in xaune wajen daga karshe ganin yanda yake lullumshe ido tana basa labari, ta bata fuska tace "Wai bacci kake ji?" A hankali ya bude idonsa yace "Yes dear, na gaji da yawa" Shiru tayi tana kallon kyakkyawan fuskarsa, Can tace "Toh ai Abbanmu yace ka kwana nan" da sauri yace "Noo, I've already lodged a hotel" tace "Toh me yasa baxa ka kwana nan din ba" Yace "Nothing" Tace "Toh shkkn, gobe ai xaka xo kafin ku tafi" Yace "Uhn xan xo" Ta rungume hannu ta hade rai tace "Ban yarda ba" Yyi murmushinsa me kyau ya kai hannunsa a hankali kan hancinta yace "Ko mun yi auren wnn wahala kawai xaki dinga bani, kin fiye rigima" Ta rufe fuskarta da hannunta, ya mike yace "Ai ni nace maki xan shigo idan Allah ya yrda" A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" tashi tayi tace "Bari in raka ka first gate din can" Yana kallonta yace "Okay dear" a tare suke tafiya, taji ya kamo hannunta a hankali, ta kallesa bata dai ce komai ba har suka isa gate din, tsayawa yyi yana facing dinta, ta sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "Thanks for ur care sweetheart" Bata ce komai ba ya kai hannunta bakinsa yyi pecking, sosai gabanta ya fadi, ta ki yarda su hada ido, ya saketa cikin sanyin murya yace "Sleep tight dear" Ta gyada masa kai kawai ya fita gate din ta juya ta koma building din gidansu tana tafiya a hankali..... Tun daga nisa take kallon Shuraim dake tahowa, sai kuma ta tsaya har ya iso inda take tace "Why didn't u pick my call" Yace "When did you call?" Tace "To ka duba wayar" Ya fiddo wayarsa a aljihu ya shiga call log, kafin yace komai ta amshi wayar tana kallon call log din, taga bayan miss call dinta ya daga kira har uku, ta kallesa tace "Kace baka gani ba" Yace "Ohk na gani, ban ga damar dauka bane" Ta tabe baki tace "Toh ai nima ba da kai xan yi magana ba, dama naga ya Sudais bai dawo bane shi sa na ke son in tambayeka ko ya wuce ne, da ina da number sa ma baxan kira ka ba" Tana fadin haka ta mika masa wayarta tace "Sa min number sa" shafa kansa yyi a hankali yana kallon wayar da take mika masa, can ya sa hannu ya amsa, tafiya ta ga ya fara yi, ta xaro ido tace "Ina kuma xaka da wayata" Bai juyo ba balle ya bata amsa, ta bi sa da sauri tace "Ya Shureen ina xaka tafi da wayata, number ya Sudais nace ka sa min fa" ganin ya ki tsayawa kuma ya ki ce mata komai ta riko hannunsa kamar xata yi kuka tace "Ni dai ka bani wayata, ba kawai sai kace min baxa ka bada ba...." Warce wayar tayi lkci daya ya xamo daga hannunsa ya fadi kasa screen din ya tarwatse, still tayi tana kallon wayar kamar yanda shi ma yake kallon wayar, lkci daya ta fashe da kuka ta juya xata koma cikin gida ya rikota, kwace kanta take son yi tana kuka sosai yace "Ke fa kika fasa kayan ki kuma kike kuka" kin ce masa komai tayi, ganin ba saketa xai yi ba ta tsaya tana kukanta a hankali, Jan ta yyi xuwa gun da ta xauna daxu da Khaleel ya xaunar da ita ya xauna gefenta yace "Toh yi hakuri, xan kawo maki wani gobe" Rufe fuskarta tayi da hijab dinta tana shessheka, Yana kallonta yace "To baxa ki daina kukan ba?" Cikin rawar murya tace "Bayan ka fasa min sabuwar wayata" Murmushi yyi ya mika mata nasa yace "Toh ga nawa idan na kawo maki sabo gobe sai ki bani" Ta d'an kallesa ta turo baki a hankali tace "Toh sim dina fa?" Yace "Sai a mayar maki nawa wayar" Tace "Toh" amsar wayar tasa tayi tace "Da me xa a bude wajen sim din?" Yace "Ke xan tambaya" Ta bata fuska tace "Toh bani da pin" yace "Likewise me" shiru tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Ohk, let me see ur earring" Cire hannun Hijab din tayi ta bude hijab din tana nuna masa dankunnenta, ya kai hannunsa ya cire earring din daya snn ya bude wayarsa ya cire sim cards dinsa, ya bude nata ya ciro sim dinta ya maida wayarsa, nasa kuma ya saka a wayarta, daukan wayar tasa tayi ta kunna ta mika masa tace "Ka cire lock din" amsa yyi, yayi yanda tace, yana kallonta yace "Shkkn?" Ta juya masa gefenta tace "Ka maida min dankunne na" Daukan dankunnen yyi ya shiga sa mata yana kallon gefen fuskarta, ta juyo suka hada ido, sauke idonsa yyi kasa ya mike yana rike da wayarta yace "Sai da safe" Tace "Kace xaka kawo min sabo gobe" yace "Ehh" tace "Toh wani kuma nake so ba wnn ba" Yace "Sai mu je tare ki xaba" tace "Toh xan gaya ma Ammina" Bai ce mata komai ba ya fara tafiya, ta bi sa da kallo har yyi nisa, snn ta mike ta wuce cikin gida. Abban Heedayah na xaune parlonsa tare da Yakumbo dake xaune ita ma duk a firgice, Cike da damuwa tana kalle kalle tace "Amadi ni dai Allah ya gani muna cikin hatsari a gidan nan tun xuwan yaron nan, garin yaya aka barsa ya shigo mana har nan, me ya kawosa, ai shkkn duk rayuwar mu a hatsari yake ko da kuwa bariki goma xa a xube mana a nan, Mutumin da yyi shekara talatin yana abu daya ai bbu abinda baxai aikata ba, har bam sai ya iya dasa mana a nan, snn ni abinda nake son sani shine me ya kawo sa gidan ma, wajen wa ya xo, wllh na shiga bandaki yyi sau ashirin tun barin sa parlona...." Abban Heedayah dake ta sauraronta yace "Haba Yakumbo ki dinga kyakkyawan xato mana, ko don uwarsa ai ya kamata a raga masa balle tasa kaddarar ce ta xo a haka" Yakumbo ta marairaice tace "Toh ni me nace? Ka ji na xagesa ne?" Abba yace "Aa ki daina maganar nan da kike don Allah" Yakumbo tace "Toh ni dai gaskiya nayi kewar inda na fito, Ina son komawa tunda na xo na maku kusan shekara a nan, idan an sa bikin Heedayah sai in dawo bbu ruwana" Abban Heedayah yace "Ai bikin ko xa a sa baxai wuce wata uku ba" Yakumbo tace "Toh naga ai iyayen Junaidun basu xo ba har yanxu, ba sai sun xo xa a sa bikin ba? Balle ma ni duk a tsorace nake da su gaba daya ma ynxu" Abba ya d'an yi shiru kafin yace "Ba da Junaid xa ayi ba kuma" Yakumbo ta gyara xama tace "Toh Alhmdllh, ko don rikon da uwarsu tayi ma Heedayah kamar ita ta haifeta bai kamata ace da aure ma tsakaninsu ba, duk da dai na ya6a da hankalin yaron wllh, amma ni kawai abun ya fitar min a kai ne, yanxu aure ma ba tasa bace kamata yyi ya xauna yyi ta nusar da yayansa da Allah ya kubutar kwanan nan" Kallonta kawai Abban Heedayah ke yi, kafin yace "Toh da yayansa xa ayi, don ita Heedayah tace shi take so, kuma bana tunanin akwai abinda dangin Hajiya Rahinah ko Barrister Ahmad xasu bukata daga bangarena in hana ko da abun yafi karfina xan yi iya bakin kokarina in ga na kwatanta masu...." Yakumbo kallonsa take kamar bata fahimci abinda yace ba, can dai tace "Wani ne a dangin nasu yace yana son Heedayar kake nufi ko me, ni ban gane ba" Abba yace "Shi dai Khaleel din ke sonta da aure, ita ma kuma ta shaida min shi take so, Barrister ya kirani mun yi magana, Yan uwan mahaifinsa ma sun kirani munyi magana jiya, kanin mahaifinsa ma na da wani mukami a nan gombe, gidansu ba kananun mutane bane, gida ne me tarihi me kyau da usuli, ynxu xa mu jira ne a gama shari'ar da ake a kotu snn a sa rana wanda baxa a ja lkci ba idan Allah ya yrda, ni na yrda da kaddara, me kyau ko akasin haka, kaddarar Khaleel ne sai yyi rayuwa cikin gurbatattun mutane, kaddarasa ce sai sun gurbata masa rayuwa, amma ynxu Alhmdllh da Allah ya maidosa hanya madaidaiciya ya shiryesa, ni baxan kyamacesa ba kamar yanda Uwarsa bata kyamaci tawa 'yar ba, snn bana fatan wani nawa ya kyamacesa, ba laifinsa bane don ya tsinci kansa a rayuwar da yyi a baya.... In dai aurensa da Heedayah alkhairi ne garemu baki daya Allah ya tabbatar" Yakumbo ta fashe da wani kuka tace "Ba ruwana da surutunka mara kan gado wllh Amadi, idan kotu ta yanke hukuncin xa a ratayesa ko xa a dauwamar da shi a gidan yari na har abada sai ayi yaya kenan?" Abba ya girgixa kai yace "Dangin ubansa baxa su ta6a barin hakan ya faru ba, haka zalika mahaifiyarsa da ta kasance babban lawyer, snn ga mijinta da shi ma babban lawyern ne, idan kuma an ajiye batunsu... laifin Khaleel ba mai yawa bane tunda bai ta6a kisa ba" Yakumbo ta kara rushewa da kuka tace "Katon mutumi ya xauna ya giggilla maku karya yace bai ta6a kisa ba ku yrda, dama an ta6a d'an ta'adda da bai ta6a kisa ba? To wllh ni dai da ya auri Heedayah gwara kawai a kasheni" Tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Abba ya girgixa kai don darun Yakumbo ba matsala bace a wajensa, shi dai yasan bbu abinda xai hanasa bai ma Khaleel auren 'yar sa, sai in shi ya fito da kansa yace ya fasa. Heedayah ta gama saka kayan baccinta kenan taji ringing wayar Shuraim dake kan gadonta, karasawa tayi tana kallon screen din wayar taga number ne kawai, bata dauka ba ta karasa shiryawa ta kwanta kan gado ta dau wayar, WhatsApp dinsa ta bude ta shiga, messages sun kusa dari uku ta gani da ba ayi replying ba, bin messages din ta shiga yi tana dubawa, duk yawanci taga na mata ne, call ne ya shigo wayar ta ga still number daxu ne, dagawa tayi ta kai kunnenta taji ance "Isn't the number saved?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Ehh no name" yace "Toh wani labarin ku ka yi da saurayin naki yau?" Tace "Me yasa kake tambayata?" Yace "In kara maki experience" bata san lkcn da tayi dariya ba tace "Wanda baya soyayya ne xai bani experience, ashe xaka korar min saurayi" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Murmushi Shuraim yyi yace "Toh sae da safe" Heedayah tace "Ko kana yi?" Yace "Mene?" Tace "Soyayyan mana" ya girgixa kai yace "Aa sai ke" Tace "Tohm byee" katse wayar ta ji yyi, ta kalla sannan ta ajiye a hankali ta juya ta kwanta. Washegari da safe Heedayah ta samu Mami a parlon Amminta, bayan ta gaisheta a hankali tace "Mami don Allah ina son in bi ku...." Mami tace "Ki bi mu ina?" Heedayah tace "Kaduna" Mami tace "Yaushe kika xo xaki ce xaki koma Kaduna?" Shiru Heedayah tayi, Mami tace "Look Heedayah gidan ku ne nan idan xaki saki jiki ki saki jiki, bana son gulma" Ita dai Heedayah bata ce komai ba, Shigowar Ammi ya sa ta mike ta fita, a ranan karfe goma da rabi Heedayah na tsaye sai kallon Khaleel dake xaune gaban motar da xai kai su Kaduna take, Mami ta shiga bayan motar bayan ta gama sallama da Ammi da Mom Islam, a hankali Heedayah ta daga mata hannu, Sannan ta daga ma Khaleel ma, murmushi ya sakar mata ta juya ta koma ciki kar hawayen dake makale idonta ya gangaro. maid dinsu Amina ce ta kwankwasa dakinta bayan Magrib, Heedayah dake xaune saman darduma ta mike ta bude kofar tana kallonta, Amina tace "Baaba Yakumbo na kiran ki" Heedayah bata ce mata komai ba Maid din ta juya ta bar wajen, Heedayah ta koma ta dau wayarta ta fita dakin, gaba daya a sanyaye take, sosai take jin tana missing din Khaleel, a hankali ta bude kofar parlon Yakumbo bayan ta isa, Yakumbo ce xaune parlon da kaka da tayi tagumi, Shuraim ma na xaune parlorn, ta karasa ta durkusa saman lallausan carpet dake parlon ta kalli Shuraim tace "Ina yini Ya Shureen" Yace "Lafiya" Ta kalli su kaka ma ta gaishesu, bbu wanda ya amsa mata cikinsu, Bayan few seconds tace "Gani" Kaka ta saki kuka tace "Yanxu fisabilillahi Deedayah ki rasa wanda xaki ce ma iyayenki kina so sai d'an kinnafin? Ke ko me ya sameki haka kika xabar ma kanki mutumin nan ni Patuu??" Tuni Heedayah ta hade rai tace "Shi ba Kidnapper bane" Kaka tace "Aa toh wllh kin karyata ubanki, Mutumin da tun kina ficiciyar ki ya daukeki ya raba ki da iyayenki, sbda addu'ar da ake jefa sa da shi ya rasa sukuni ya fito dake daga garkensu ya yasar dake gefen titi shine xaki bude baki kice mana ba kinnafa bane???" Hawaye ya kawo idon Heedayah tace "Ni dai ba Kidnapper bane, ku daina kiransa haka" Yakumbo na kallonta da kyau tace "Toh bari kiji wllh indai da raina bbu wanda ya isa ya nuna ni yace ga surkar kinnafa, tun wuri kiyi maxa ki sauya shegen tunanin ki, kaf xuri'ar mu bbu me abun fadi da ya bar ma jika, don haka baxa ki bar mana abun fade ba, har gobe mutumin nan kinnafa ne a idona, ba komai bane mu ma ya kwamushe mu wataran" Kaka tace "Toh da fa?? Ai ynxu da kyar idan bai lallabo ya dawo nan ba yyi abinda xuciyarsa ke raya masa, ni ban yrda ya wani koma kaduna ba, yana nan makale a kano xai dawo tsakar dare, sannan wlh banda ina kunyar uwarsa ni rufe ido xanyi in gaya masa abinda ke raina, to meye hadina da shi??" Heedayah ta fashe da kuka sosai tace "Ni dai ba Kidnapper bane...." Yakumbo ta dau pillon da ke gefenta ta jefa mata a fusace tace "Kin karyata uwarki, wllh in dai ina numfashi baxa ki auri katon D'an ta'addan nan ba" Kaka ta kalli Shuraim dake danna wayarsa tace "Kai kuma an kiraka ka xo ka yi mana shari'a kayi shiru kana kallonta tana mana fitsara" Ya dago kai yace "Toh Kaka ku xa ku xauna mata da shi?" Bude baki Yakumbo tayi tana kallonsa, yace "Ita xata xauna da abun ta, kuma Kidnapper da ku ke ce masa ya ta6a kidnapping din ku ne?" Yakumbo tace "Naga abinda ya isheni...." Kaka tace "Toh tashi ka fita, na mance halinka ne ya sa na kiraka, Allah yayi maka yanda kayi mana yanxu" mikewa yyi ya maida wayarsa aljihu ya nufi kofa, Yakumbo tace "Kai xaka yrda kanwarka ta auri tatattcen tsohon d'an kinnafin idan ba mugunta ba, ashe haka xuciyarka take ban sani ba, toh aniyarka ta bika wllh" Kaka tace "Gantalalle ne fa, ni ba na mance waye shi ba na gayyatosa, ai fadan gaskiya karara sai Sudess Dan arxiki" Mikewa Heedayah tayi ta fita tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, tsaye ta ga Shuraim bakin stairs, ta fashe da wani sabon kukan, yana kallonta yace "Toh meye na kuka? Ba dai Abbanki ya amince ba haka ma Amminki?" Ta hade kanta da bango tana kuka sosai tace "Toh shine xa a dinga ce masa Kidnapper bayan ya daina???" Yace "Haka yace maki?" Juyowa tayi da sauri tana kallonsa, yace "Suna nufin idan ku ka yi aure da shi, ce maki xa a dinga yi matar tsohon Kidnapper" Tace "Ehh na yarda" daga haka ta bi gefensa xata wuce ya riko hannunta, kin juyowa tayi hawaye na sauka idonta, ya juyo da ita yace "Toh kiyi hakuri idan ma sun kiraki kar ki sake xuwa" ita dai bata ce komai ba, yace "Mu je ki amshi wayarki ki bani nawa" Ba musu ta bi sa downstairs. Mami ce xaune bedroom dinta tare da Junaid dake sauraron abinda xata fada masa don kiransa tayi a waya, Mami na kallonsa tace "Da farko na so ka da Shaheedah ka kawo excuses which I had no option then to let you stick to ur choice, kace kai Heedayah kake so, fine ka je gun iyayenta without me even knowing kuma sun nuna sun baka ita, weeks back ana da intention din kai kudi gidansu, sai abubuwa suka faru wanda ya sa aka daga, to har yanxu naji kayi shiru kan xancen baka cewa komai ba, da akwai wani abun a ranka ne??" Tunda Mami ta fara magana Junaid ke kallonta, can ya sauke idonsa kasa yace "Na hakura da ita ne kawai Mami" Mami na kallonsa tace "Ko saboda me?" Yace "Saboda yayana, I will welcome anything that will make him happy, he deserves to be happy bayan duk abubuwan da yyi passing a rayuwa, I over heard conversation dinku the other night, a wannan daren kuma na cire Heedayah a raina, bbu aure tsakanina da ita, na bar ma Ya Khaleel, Allah ubangiji ya sa rabonsa ce ita" Mami ta kasa cewa komai don tunda Khaleel ya gaya mata Heedayah yake so bata da wani kwanciyar hankali, har ranta take son duk abinda xai faranta ma first son din nata, amma kuma bata sanar ma Junaid xancen ba sbda bata son ya ga kamar ta fifita Khaleel a kansa, amma furucin Junaid yau ya sa taji hankalinta ya kwanta, Rasa ma abinda xata ce masa tayi, Junaid ya mike ya fita daga dakin. 3 months later.... Heedayah na parlon Stepmum dinta dake tsefe mata kitson da tayi mata duk da satin kitson daya bbu abinda yyi, Mom Islam ce ke ta surutun ta ita kadai Heedayah bata cewa komai, can Mom Islam tace "Are you okay Heedayah?" Da sauri Heedayah ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka, Mom Islam tace "Tunanin me kike?" shiru Heedayah tayi, Mom Islam tace "Talk to me" A hankali Heedayah tace "Nothing aunt" Murmushi Mom Islam tayi tace "Sa ranan da aka maki yau ne ya sa kike ta tunani tun daxu" Lkci daya hawaye ya kawo idonta amma bata ce komai ba, Mom Islam tace "Toh ki kwantar da hankalin ki dear, kowa ma haka ya ji yanda kike ji, amma naki shirun yyi yawa, you are suppose to be happy...." Heedayah tace "I am not sad" Mom Islam tace "Ko ranan da aka sa yayi maki kusa?" Heedayah ta dago ta kalleta kamar xata yi kuka tace "Ehh" Mom Islam tayi murmushi tace "Wata dayan ne yyi kusa?" Hawaye na sauka idonta tace "Aunty just four week fa, yar karamar yarinya da ni?" Dariya sosai stepmom dinta tayi tace "Ehh lallai kam yar karamar yarinya, to ni a ranan da Abbanki ya kai kudi ranan ma aka daura auren, kinsan Ammin ki ce ta hada mu dama" Heedayah dai tayi shiru bata ce komai ba, Mom Islam tace "Washegari kuma aka kai ni dakina, kinga ke ai an maki gata sosai har sati hudu" Heedayah ta share hawayen idonta a hankali, Mom Islam tace "Ki kwantar da hankalin ki kin ji my daughter, ba dai kina son mijin ki ba" Heedayah ta gyada mata kai, sai kuma a hankali tace "Amma ni tsoronsa nake" Dariya sosai Mum Islam tayi tace "Tsoron me?" Heedayah dai bata ce komai ba, Mom Islam tace "Shi yasa jiya kika ki dadewa da kika fita wajensa?" Heedayah ta turo baki tace "Aa shine yace min yana jin bacci" Mom Islam tace "Ayya, ya koma Kadunan shi?" Heedayah ta gyada mata kai, Mom Islam tace "Allah sarki, ni dai nutsuwarsa na burgeni kuma naji dadi da ba a samu matsala shari'ar da aka yi ba, Allah ya dubesa da yake xaluntarsa aka yi" Heedayah dai bata ce komai ba, Mom Islam ta ci gaba da kwantar mata da hankali har suka gama tsifan ta hau sharce mata dogon gashin nata kafin ta wanke. Sai bayan awa kusan biyu Heedayah ta koma bangaren Amminta bayan Step mum dinta ta gama gyara mata gashinta, Amminta ta bi ta da wani kallo tace "Kumbure kumburen uban me kike?" Heedayah ta girgixa kai tace "Ba komai" Ammi ta ci gaba da abinda take, juyawa Heedayah tayi ta fita ta koma bangarenta. Mumy ce xaune parlon Hajiya Sadiya hawaye na sauka idonta tace "Ni shkkn dai a tutar bbu na tashi wllh...." Tana fadin haka ta fashe da matsanancin kuka, Hajiya Sadiya dai ta ma rasa abun cewa, cikin rawar Mumy tace "Dama nace asirin nan bai ci Shuraim ba ku ka ce ina na fito, Salima ta sa ina ta kashe kudi a Iska, ga dai yarinya yau an sa mata rana da d'an gidan Rahinah, kamar fa almara labarin ya xo min, ban ta6a kawowa hakan xai faru ba, kuma tunda na ji kullum sai Shuraim yaje government house na xata saboda ita yake xuwa ina ta murna sun shaku yanxu ashe ashe ba haka bane, Wai ina kwance Barrister ya shigo ya sanar min xa su kai kudi da safe...." wani sabon kuka ne ya kubce mata, a hankali Hajiya Sadiya tace "Shuraim yana da tsari duk ynda aka yi, tunda bake kadai Mutumin nan ya ma aiki ba, ni da mutumin ya min aiki kan surajo ba gashi yayi ba, ko sati ba ayi ba ya saki matar saki uku ya auri warce nake so....." Mumy na share hawayenta tace "Kuma haka ne wllh, yanda dai kika fada haka ne Shuraim na da tsari, kinsan Kakar ma ba wai barin su haka tayi ba" Hajiya Sadiya tace "Toh wata nawa aka saka ranan yanxu?" Da damuwa Mumy tace "Wata daya kacal Sadiya" Hajiya Sadiya ta bude baki tace "Toh sai dai in Heedayar xa a asirce tace ta fasa kawai ko?" Hawaye na taruwa idon Mumy tace "Ta yaya? Shi wnn mutumi sai yace a barbada a abinci ko abun sha, to ina xa mu ga wata Heedayah tana gidan iyayenta, Kadunan ma ko ta xo kwana biyu take yi ta koma, balle ma tunda aka sa mata rana ma shkkn ba lallai ta xo kwana kusa ba sai bayan bikin" Sadiya tace "Wai tsaya ba d'an fashin nan bane d'an Rahinar da aka sa mata rana da?" Mumy tace "Shine dai wllh, in gaya maki sun shiga sun fita sai da suka tabbatar sun wankesa tass, su kuma abokan huldarsa duk an masu daurin rai da rai a gidan yari haka naji, lkcn shari'ar kuwa ko baccin kirki Barrister baya yi, su kusan biyar suka hada kai aka wanke Mutumin nan me laifi kiri kiri gashi a bayyane, kuma wllh gagarumin d'an Kidnapping ne fa aka ce" Sadiya da ta saki baki tace "Ikon Allah, to ya aka yi da dukiyoyin jama'ah da ya tara da mutanen da ya kashe???" Mumy tace "A karyansu wai bai ta6a kisa ba, dukiyoyin jama'ah kuma an kai gidan Marayu, ke kiji daure ma karya...." Sadiya tace "Lallai yana da masu tsaya masa ne" Mumy tace "Da fa, ance kanin ubansa wani babba ne a Gombe, snn autarsu ubansa ma wani babba take aure a gomben, snn ga danginsu Junaid su ma kinsan an sansu, uwa uba ga gwamnan kano dake tunanin xai xama surkinsa, kinga kuwa ai ba karamin wanki xa ayi masa ba" Sadiya ta rike ha6a tace "Ikon Allah" Mumy tace "Ni dai mu koma abinda ya dameni, yanxu Sadiya ya xan yi??" Sadiya tace "Asiri kawai xa mu je ayi ma Heedayar idan ma magani ya bada wanda ake son ta ci sai ki wanke kafa ki tafi government house ai bbu wanda xai ce maki don me, bbu wanda xai koreki, da ba don mijinki ba da yanxu kilan bbu Heedayah a doron kasa, kina sauka kano sai Shuraim ya shigar da ke government house din kawai" A hankali Mumy tace "Toh hakan xa ayi, tunda da sauran lkci tashi mu tafi gun Mutumin Sadiya" Kallon Mumy kawai Abba ke yi har ta gama maganan da take sannan yace "Ki dai gaya min me xa ki je yi a kano Maryam" Tayi masa wani kallo tace "Me xanje yi kamar Yaya? Kana nufin karya nayi maka kenan ko me? Nace xanje gaida kaka kace min me xanje yi a kano" Abba yace "Sati me xuwa kaka xata dawo ba sai kin je ba, bbu inda xaki je" Mumy tace "Toh wllh wllh sai naje ko da gobe xata dawo kuwa" bata jira me xai ce ba ta fice daga dakinsa xata je hada kayanta ya bi ta da kallo keenly. A ranan da safe Heedayah na babban parlon Abbanta xata yi masa sallama, ya gama wayar da yake yana kallonta yace "Kwana nawa Ammin ki tace kiyi?" A hankali Heedayah tace "Biyu" Abba yace "Toh Allah ya kiyaye hanya, xa ku je tare da Shuraim...." Heedayah tace "Ammi ta gaya min" mikewa tayi ta fita daga parlon, step mum dinta ce ta rakota gun wata rantsantsiyar mota ta shiga baya ita kadai sai driver dake gaba, step mum dinta na kallonta a hankali tace "Ki kula da kanki kinji daughter?" Heedayah ta gyada mata kai tace "Toh Aunty" Mom Islam ta daga mata hannu Heedayah ta daga mata ita ma, Kalle kallen wajen Mom islam ke yi tace "Toh ina Shuraim din" Heedayah ta bude hannu alamar bata sani ba, can Mom Islam ta hangosa cikin daya daga motar da xasu yi masu escort, Mom Islam na tsaye har motocin suka fara fita..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Basu yi awa daya suna tafiya ba motar da Heedayah ke ciki ya gangara daga tsakiyar motocin da yake yyi parking gefen titi, hakan yasa duk sauran motocin har da na gabansa suka yi parking, Heedayah ta bude motar ta sauka ta tafi gefen ciyayi ta durkusa, Shuraim ya sakko daga motar da yake ciki ya nufeta yana kallonta, sojojin ma duk suka sakko daga mota, lkci daya Heedayah ta mike da kyar tana kallonsa tace "Ya Shureen amai nake ji" Tsayawa yyi ya jingina da motar ya rungume hannunsa yace "Toh kiyi" ta koma ta durkusa sai kuma ta dago kamar xata yi kuka tace "Ya ki xuwa" gaba daya she's restless alamar aman na damunta, bai ankara ba sai gani yyi ta duka da sauri ta fara kwararo amai a kan ciyayi, ya tsaya yana kallonta, can ya bude motar ya fiddo bottle water dake ajiye kan kujera ya bude ruwan, sai da ta gama sannan ya karasa ya mika mata, ta amsa da kyar ta wanke fuskarta ta mike tana maida numfashi, ya bude mata motar yana kallonta, shiga tayi ta jinginar da kanta da kujera xai rufe motar a hankali tace "Don Allah ka shigo nan Ya Shureen, ni kadai ce" yace "In shigo in maki me?" Da damuwa tace "Ka xauna, kuma kace ma driver ya rage Ac din sanyi nake ji" Da kamar baxai shiga ba, sai kuma dai ya shiga motar ya rufe, sauran sojojin suka koma motarsu, Shuraim ya umarce driver da ya rage sanyin Ac, drivern yyi haka nan suka ci gaba da tafiya. Lumshe ido tayi daga haka bacci ya dauketa, sai da suka iso Zaria ta bude idonta a hankali, daga kai tayi ta kalli Shuraim dake danna wayarsa, ta kalli shoulder dinsa da ta daura kanta, gyara xamanta tayi tace "Ba mu kai ba?" Bai ce mata komai ba, ta karbi wayar hannunsa ya kalleta, tace "I am asking ko mun kai" yace "Ehh har mun juyo" Yana fadin haka ya kwace wayarsa, ta turo baki ta koma can nesa da shi ta xauna, d'an murmushi yyi ya ci gaba da abinda yake yi a wayarsa, bude handbag dinta dake hannunta tayi ta fiddo wayarta dake vibrate, ganin Khaleel ke kiranta sai da gabanta ya fadi, ta dai daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren yyi sallama, ta amsa, yace "How are you?" Tace "I am fine" yace "Kun taso?" Tace "Ehh mun taso" yace "Okay, ya hanya?" Tace "Alhmdllh" Yace "Ke da waye?" Ta d'an kalli Shuraim snn tace "Ba kowa, ni da driver ne" Yace "Ohk, Allah ya kawo ku lafiya" A hankali tace "Ameen" snn ta katse wayar, satan kallon Shuraim tayi suka hada ido don shi ma kallo ta yyi, ta dauke kanta ta gyara xamanta, har suka shigo kd wajejen karfe sha biyu. A hankali Heedayah ta bude motar ta sauka bayan driver yyi parking compound din Mami, Farida ce ta fito ganin Heedayah ta taho da sauri ta rungumeta, Kankameta Heedayah tayi tace "I missed you Farida" Farida tace "I missed you more Didi ya su Ammi?" Daga kai Farida tayi suka yi ido hudu da Shuraim, yace "Ya kike?" Farida tace "I am fine" juyawa yyi ya nufi gate ya ciro wayarsa dake ring a aljihunsa, Heedayah ta bi sa da kallo tace "Ain't you coming in ya Shureen?" Ba tare da ya juyo ba yace "Xan dawo" Daga wayar yyi ya kai kunne ganin Mumy ce ke kiransa, Ya gaisheta tace "Shuraim ga ni a kano ka xo ka shigar da ni government house, ina nan kofar Nasarawa gidan 'yar uwar Sadiya" Shuraim dake sauraronta yace "Bana kano, Ina Kaduna ynxu" Da wani irin shock Mumy tace "Kaduna kuma? Me kaje yi Kaduna, kuma wa ka gaya ma xaka je kaduna? To ni yanxu wa xai shigar da ni government house din?" Shuraim yace "Ki kira kaka ta sanar masu xa ki shiga" A fusace Mumy tace "To wai ma uban me kaje yi Kadunan ne baka gaya min ba?" A hankali yace "Aiki Mum" Mumy tayi tsaki tace "Toh kawai ka turo min number Maman Heedayah, kaka mutum ce da xa a kira, ni ka ji da ni ina jira" Yace "To" daga haka ta katse wayar, ya tura mata number Ammi da ta ce. Heedayah ta ja hannun Farida da ta bi Shuraim da kallo suka wuce cikin parlor, har bedroom din Mami Heedayah ta shiga ta tafi da sauri ta rungume Mami cike da murnan ganinta tace "Mami good afternoon...." Mami na kallonta tana murmushi tace "Afternoon My Daughter ya hanya?" Heedayah tace "Alhmdllh, su Ammi da Aunty sun ce a gaisheki" Mami tace "Maa sha Allah ina amsawa hope baki yi amai a hanya ba" Heedayah ta boye fuskarta jikinta tace "Nayi sau daya Mami" Mami tace "Allah ya yaye maki, ya Abban ki da su Yakumbo??" Heedayah tace "They are all fine, they sent their regards, kaka ma next week xata dawo tace amma kwana biyu kawai xata yi ta koma" Mami tace "To maa sha Allah, Allah ya kawota lfya" Heedayah tace "Mami Ya junaid fa?" Mami tace "Yana gidan Baffansa, anjima xai shigo in sha Allah" Heedayah tace "Allah ya dawo da shi lfya" daga haka ta mike tana kallon Mami tace "Xan yi sllh Mami" Mami tace "Toh kiyi wanka gaba daya, idan kinyi sllhn sai ki ci abinci" Heedayah tace "Toh Mami" daga haka ta nufi kofa ta fita ta kulle ma Mami kofarta, Tsaye ta tadda Khaleel bakin kofar bedroom dinsa yana sanye da kananun kaya ya rungume hannunsa yana kallonta, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Ina yini" murya can kasa yace "Lafiya, why did you lie to me?" Ta kallesa da sauri tace "Na me?" Shiru yyi yana kallonta, kamar xata yi kuka tace "What did i lie about?" Yace "Kince ke kadai kika taho" da sauri tace "Ehh with... with Escort" Ya gyada kai yace "Good, Sannun ku da xuwa to" Downstairs ya fara sauka ta bi sa da kallo, snn ta turo baki ta shiga dakin Farida ta kulle kofar, sai bayan da Heedayah tayi wanka ta canxa kaya tayi sllh snn ta fito dakin ta sauka downstairs, Khaleel na xaune parlon da Farida dake kusa da shi yana nuna mata abu cikin laptop, tsaye tayi bakin stairs tana kallonsu, ko lura da ita basu yi ba a wajen, Farida ta wara ido tace "Waow yaya, you are an expert, ni ma ka koya min" ya kyabe baki yace "Xaki shekara goma baki iya ba" Bata rai tayi tana kallonsa, dai dai nan ta ga Heedayah dake tsaye har lkcn, ta sakar mata murmushi tace "Ga abincin ki can dinning na ajiye maki" Heedayah bata ce komai ba ta nufi dinning din, can Khaleel ya dauke laptop din kafarsa ya ajiye kan kujera ya mike ya bi bayanta. Mumy na xaune parlon Yakumbo tare da Ammi da Mom Islam bayan an gama gaggaisawa, Kaka na kallonta da kyau tace "Toh me ya kawo ki Maryam??" Mumy ta yi yake tace "Aa biki muka yi, shine nace bari in karaso in kawo ziyara inyi xumunci snn inyi Allah sanya alkhairi ranan da aka sa ma Heedayah tunda har na shigo kanon" Kaka ta rike ha6a tace "Su xumunci manya, to amma kina da wasu yan uwa ne a kano wanda bani da labari Maryam?" Mumy ta sunkuyar da kanta tace "A'a yar uwar Sadiya ce aka yi bikinta" Kaka ta kyabe baki tace "Toh sannu da xuwa, gwara kema ki xo ki d'ana arxiki kar ayi ba ki" Yakumbo ta kyabe baki, Ammi ta mike tana kallon Mumy tace "Mu je can bangaren Hajiya" Mumy ta mike tana murmushin karfin hali ta bi bayanta suka fita parlon kaka ta bi ta da kallo tace "Kiri kiri ta ki rike Heedayah bbu irin walakancin da ba mu gani ba daga wajen matar nan, kawai dai a bar kaza cikin gashinta" Yakumbo tace "Toh ba kanta tayi ma ba, yau ba arxikin Heedayar ta ci ta shigo gidan nan ba, Banda haka meye hadin mu da ita??" Kaka tace "Kul.... Uwargidan Amadu ce, uwar Shuraim, da ba don Amadu ba kuma Heedayah kilan sai dai kullum a dinga mata addu'ar gafara gun ubangiji, Kinga kuwa ai ba laifi don ta shigo Gwamnet house" Ammi na komawa bangarenta da Mumy ta sa masu aiki suka kawo mata kayan ciye ciye da ruwa da abinci, Mumy sai kalle kalle take tana duba inda xata ga Heedayah ta billo, duk wnn abun da aka cika mata a gabanta ba shine damuwarta ba, can dai ta kalli Ammi murmushi dauke fuskarta tace "To ina Heedayar ta shiga ban ganta ba" Ammi tace "Ayya ai yau suka wuce kaduna" Mumy ta gwalo ido da sauri tace "Da wa?" Ammi tace "Ita da Shuraim suka tafi, taje yi ma iyayenta na can sallama, tunda bikin ba wani lkci me tsayi aka sa ba" Mumy taji xufa ya karyo mata tace "Yaushe xata dawo kenan?" Ammi tace "Baxa dai ta wuce kwana uku ba ina jin, duk dai yanda Abbanta na Kaduna yace" Mumy tayi wani murmushin karfin hali tace "Toh maa sha Allah, Allah ya dawo da su lafiya, nima din dai yau xan koma dama" Da mamaki Ammi tace "Yau kuma Hajiya, ai yamma yyi, ki bari gobe" Mumy tace "Aa ba mu yi da barrister xan kwana ba, in sha Allah yanxu xan wuce, dama kawai nace in xo inyi Allah ya sanya alkhairi ne" Ammi tace "Da dai kin hakura gobe Hajiya, hanyar nan bai fiye kyau ba" Mumy ta sauko kasa ta dau snacks daya tace "Aa Hajiya yanxun nan ma kuwa xan wuce, bari in d'an ta6a abincin" ko minti ashirin Mumy bata kara a government house ba ta dau hanyar park wajajen karfe uku na yamma. Shuraim na xaune parlon Abbansa yana sauraron maganan da Abba ke masa, Jin ya ki cewa komai Abba yace "Ka min shiru" Shuraim ya daga kai ya kallesa yace "Abba ni fa ban san komai kan xancen nan ba" Abba yace "Kwana biyu da suka wuce kaka ta kirani a kan batun, na kuma yi tunanin kai kayi mata maganan" Shuraim yace "Aa ni ba mu yi wata magana da ita ba" Abba ya girgixa kai yace "Toh bayan bikin Heedayah ina son inji kace min ga gidan da xa mu tafi nema maka aure, naga kamar baka san a sa maka ido ba" Shuraim dai bai ce komai ba, bayan few seconds Abba yace "Snn akan batun mahaifiyarka...." Daga kai Shuraim yyi yana kallonsa, Abba yace "Wannan karan xan dau mataki me tsananin gaske a kanta, tunda har na hanata fita gidan nan tayi disobeying dina tayi ficewarta, to ta tabbatar ba gidan nan xata dawo ba" Wayarsa ne ya fara ring, ganin number isn't saved ya dauke kai, Shuraim dai bai iya yace komai ba, Abba yace "Ina raga ma Maryam wasu abubuwan sbda ku amma bata gani, duk ina sane da abubuwa da yawa da Maryam ke yi ba wai bana sane ba, Maryam bata san annabi ya kafu ba, I am overlooking so many things a da, but today I am done...." Abba ya kalli wayarsa da aka sake kira for the second time, daukar wayar yyi ya daga ya kai kunne tare da sallama, Jin tambayar da aka yi masa a wayar yace "Ehh, who is on the line" shiru Abba yyi as if trying to comprehend the message passed to him kafin ya ajiye wayar bayan an katse yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Shuraim dake ta kallonsa yace "Lafiya Abba?" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Washegari da sassafe Mami da su Heedayah suka gama shiryawa xuwa Nigerian Army Reference Hospital Kaduna, Mami na tsaye parking space da Heedayah Khaleel ya karaso tare da Farida, Mami tace "Ba lallai a barmu mu shiga gaba daya ba, ka dauko makullin motar Junaid kai da Heedayah ku tafi tare, ni kuma i will go with Farida" Yace "Alright" daga haka ya juya ya koma ciki, Mami ta jira har ya dawo da makullin motar snn ta bude tata mota da ke a kunne ta shiga Farida ta shiga front seat, suka bar compound din, Khaleel ya shiga motar Junaid ya kunna yana warming din motar, Heedayah dai na tsaye fuskarta bbu walwala, ko kadan bata ji dadin wucewar da Mami suka yi suka bar ta ba, ya d'an daga kai ya kalleta suka hada ido, sauke idonsa yyi yace "Are you waiting for me to help you in?" K'in cewa komai tayi ta dauke kanta ta turo baki, bata ankara ba sai ji tayi ya dauketa cak, ta xaro ido a tsorace ta rikesa tace "Noo, don Allah ka bari" Bai saurareta ba ya rungumeta jikinsa, ya xaga daya side din motar ya bude front seat ya ajiyeta a hankali yana kallonta, rufe fuskarta tayi da kafarta da sauri xuciyarta na bugawa, yyi murmushi ya rufe motar ya xaga driver seat ya shiga sannan ya ja motar suka bar gidan, har suka isa asibitin bata yrda sun hada ido da shi ba, shi ma bai ce mata komai ba, ya samu wajen parking yyi parking a babban asibitin, sai a snn ya kalleta yace "Uhn wai kunyata kike ji?" Ta saci kallonta suka hada ido, yyi murmushi yace "Ki dinga cin abinci ko xaki d'an kara weight, ur weight isn't encouraging" Hararansa tayi tace "Kai ma ka dinga cin abincin, ae naga baka ci da yawa" Ya wara ido yace "Ae idan na kara cin abinci a kan wanda nake ci ke ce xaki sha wahala" Tace "How?" Ya bude motar ya sauka yana murmushi yace "Xa ki san how" Bude motar tayi ita ma ta sauka, Khaleel ya fiddo wayarsa ya kira Mami, nan ta sanar masa suna Accident and emergency wards, Heedayah na biye da shi suka nufi wajen. Mami na xaune tare da Hajiya Amina da Hajiya Hauwa, ko wannensu yyi tagumi, sai su Rabi'ah da suka ci kuka suka gode Allah, Khaleel ya gaida su Hajiya Amina da ladabi, Heedayah ma ta gaishesu, duk suka amsa, Khaleel yace "Ya mai jiki?" Suka amsa masa da "Alhmdllh" Khaleel ya fita haraban asibitin ya xauna, Heedayah dai na ta tsaye gefen Farida, ko wa na wajen damuwa ne karara tare da shi, Bude kofar ward din aka yi likitoci biyu suka fito, ba a dau lkci ba Shuraim ma ya fito ward din, har xai wuce ganin Mami ya tsaya ya gaisheta, Mami ta amsa, a hankali tace "Ya Mai jikin?" Yace "Alhmdllh" da damuwa tace "Baxa a bari a shiga ba ko?" Shuraim ya gyada mata kai ya bar wajen, Heedayah ta bi sa da kallo, slowly yake tafiyar, bata yi wani tunani ba ta bi sa da sauri, ta isa inda yake cikin sanyin murya tace "Yaya Shureen ya jikin Mumy?" Ya d'an kalleta yana tafiya still yace "Da sauki..." Bin sa tayi har suka fito ya xauna kan Concrete bench, ta xauna gefensa tana kallonsa, she could see how disturb he is, a hankali tace "Ya Shureen is it that serious?" Bai ce mata komai ba, ta dafasa tace "Talk to me" Sai a snn ya kalleta a hankali yace "You pray for her" Tayi shiru tana kallonsa, cikin sanyin murya tace "Will I be allowed to see her?" Ya girgixa mata kai, cikin kwantar da murya tace "Do not be press ya Shureen, this shouldn't oppress you, Allah xai bata lafiya in sha Allah ka ji?" Lkci daya Hawaye ya taru idonta jin ya ki cewa komai, tace "Ka ji ya Shureen" kallonta yyi amma ya kasa ce mata komai, kamo hannunta yyi a hankali yace "Ki taya ta da addu'a ke ma" Ta gyada masa kai, daga haka ya mike, pharmacy din asibitin ya nufa.... Heedayah ta bi sa da kallo, dai dai nan suka yi ido hudu da Khaleel dake xaune shi ma saman concrete bench ta side din da take, mikewa tayi a hankali ta nufesa, yana kallonta yace "Ya jikin mum din tasa?" Ta xauna tace "He said we should pray for her" Khaleel yace "Allah ya sauwake" A hankali tace "Ameen" Kamo hannunta Khaleel yyi, xata kwace ya ki saketa, ta shiga bin wajen da kallo kamar mara gaskiya, murya can kasa yace "What are your plans...." Tace "What plans?" Yace "For ur wedding" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, yana kallonta ta gefen ido yace "Kinyi shiru" A hankali tace "To ai ban sani ba, sai abinda Aunty ta ce" Yace "Ohk, jiya sai kika barni ni kadai a parlor ko...." Tace "Mami ce tace in je in kwanta" Murmushi yyi bai ce komai ba. Sai kusan sha daya suka bar asibitin har sannan kuma ba a bari sun shiga ward din da Mumy take ba, Abba kadai ne ya shiga sai shi Shuraim, duk iya dube duben Heedayah ko xata ga Shuraim bata gansa ba har suka bar asibitin, gaba daya hankalinta ya ki kwanciya, sai da suka kusa gida Khaleel ya kalleta ganin yanayinta yace "ko dai a maida ke asibitin ne?" Ta kallesa kamar xata yi kuka ta gyada masa kai, yace "Ohk" Wani layi ya shiga yyi reverse snn ya dau hanyar asibitin kuma, wajen da xai iya parking ya samu a nan bakin titin asibitin ba tare da ya kalleta ba, tana kallonsa tace "Toh xa ka dawo ka daukeni anjima?" Yace "Ehh" Tace "Toh nagode" Daga haka ta bude motar ta sauka ya dinga kallonta har ta rufe motar snn ya ja motarsa ya bar wajen, ta karasa karamin gate din shiga cikin asibitin ta shiga bayan ta gaida sojojin dake wajen, da kafa ta karasa har Accident and emergency. Shuraim ne kadai xaune saman kujeran dake gaban ward din, ya dinga kallonta har ta iso yace "What did you forget?" Ta xauna wani kujeran tace "Aa kawai ina son in tsaya nan ne" Ya girgixa kai yace "Aa da yamma ai xa ku dawo" Tace "Toh ai kowa ya tafi ya bar ni" Shiru yyi bai ce komai ba, Suna ta xaune a haka bayan wani lkci ta kallesa tace "Ya Shureen is she sleeping?" Ya girgixa kai yace "She is still unconscious" Da damuwa tace "Ta ji ciwo ne?" ya girgixa kai yace "Aa, may be internally" Lkci daya jikin Heedayah yyi sanyi sosai, a hankali tace "Toh yanxu wani treatment ake yi?" Yace "Still on scanning, kafin a gano inda matsalar yake idan akwai sai a dau mataki, Ana jiran wasu results din" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Allah ya bata lafiya" Shuraim yace "Ameen" Suna ta xaune a haka har kusan sha biyu da wani abu, Heedayah ta kallesa ganin baya daukan phone calls dinsa yace "Why ain't you picking?" Girgixa mata kai kawai yyi ya mike yace "Lkcn sllh yyi, mu je in nuna maki inda xa kiyi sllh" Tashi tayi ta bi bayansa suka nufi kofar fita. Heedayah na idar da sllh ta xauna kan Concrete bench tana jiran fitowarsa daga masallaci, muryarsa taji ta bayanta ta juya da sauri, yana kallonta yace "Me xa ki ci?" Ta girgixa kai tace "Aa am not hungry" yace "Then you need to go back home now" Ta 6ata fuska ta mike tace "Anjima idan su Mami suka xo ba sai in bi su ba tohh" Bai ce mata komai ba ya fara tafiya ta bi sa, Xaune suka tadda Abba da Baffa a bakin ward din, Shuraim ya gaishesu, Heedayah ma ta gaishesu da ladabi, Abban Sudais na kallon Shuraim yace "Ya jikin nata, har yanxu dai shiru?" Shuraim yace "Ehh, duk scans din da suka fito bbu matsala saura uku yanxu ake jira" Baffa yace "Toh Allah ubangiji ya tashi kafadunta" Shuraim yace "Ameen" Shi dai Abba bai iya yace komai ba, Baffa yace "Sun dai ki barin a shiga a ganta" Shuraim yace "Ehh amma in sha Allah idan ta farfado shkkn" Baffa yace "Toh Allah ubangiji ya tashi kafadunta ya bata lafiya" Shuraim yace "Ameen" Sai karfe daya su Baffa suka bar wajen. Karfe biyu da 'yan mintuna Shuraim ya mike daga inda yake xaune ya kalli Heedayah yace "Nace ki tafi gida kin ki tafiya.... And you haven't eaten till now" Tace "Toh ai kai ma baka ci komai ba" Yace "Toh ki tafi gida idan kin ci sai ki kawo min" Kallonsa tayi tace "Da gaske?" Yace "Ehh" Tace "Toh xan iya ganinta kafin in wuce?" Ya d'an yi shiru, kafin ya bi corridor din da kallo, sai kuma yace "Toh taso" Mikewa tayi ta bi bayansa ya bude kofar ward din ya shiga ta bi bayansa, kallon Mumy dake kwance kamar me bacci Heedayah ta dinga yi, ta kasa karasawa gun gadon, Shuraim ya karasa ya duka yana kallonta, ya fi minti daya yana kallonta kafin ya kamo hannunta a hankali, lkci daya ya sake hannun ya kai finger dinsa gefen wuyarta, xame hannunsa yyi ya mike, Heedayah dai na tsaye sai kallonsa take, kofa ya nufa ya fita daga ward din ta bi bayansa, xaunawa ta ga yyi kan kujeran dake wajen ya rike kansa, sosai ta ji gabanta ya fadi ta karasa kusa da shi da sauri, ta xauna tace "What happened Ya Shureen" Jin bai ce komai ba da damuwa sosai tace "Talk to me plss, me ya faru?" A hankali ya dago kansa hawayen dake idonsa ya sauko.... *Ya dai fi babu, wai d'an agwai da bakin d'a, but you pple shud be pitying ur final year Khaleesat* 😩 Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Komawa baya Heedayah tayi, lkci daya tsoro ya bayyana fuskarta, cikin tashin hankali tace "Yaya me ya faru tell me plss don Allah ka gaya min" Jin Shuraim ya ki bata amsa ta sakar masa kuka tace "Ka gaya min mana Yaya" Gathering courage yyi ba tare da ya kalleta ba trying to be very strong yace "We just pray for her" Mikewa Heedayah tayi tana dubansa gabanta na faduwa tace "Kamar ya?" Ya mike shi ma still ya ki kallonta ya kama hannunta suka bar wajen. Kaka ce ta bude kofar parlon da mutane ke cike a xaune, cikin mutanen parlon Yan uwan Abba ne na kusa da nesa, sai 'yan uwan Mumy, Mami ma na parlon tare da Hajiya Zuwaira da su Hajiya Amina, duk aka daga kai ana kallon kaka, kaka ta rushe da wani matsanancin kuka ta xauna nan bakin kofa tana nanata "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, na shiga uku ni Patuu, wai dama da gaske ake?? Da ma wnn mummunan labarin gaskiya ne?" Bbu wanda ya tanka mata a parlon, Kaka ta daura hannu a ka tace "La ila ha illallahu muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, yanxu da gaske Maryam ta rasu?" Ammi ta shigo parlon a sanyaye tare da Mum Islam dake biye da ita, Yakumbo dama a nan balcony ta xauna tana sharban kwalla, Heedayah dai da Farida na xaune kusa da Mami sun yi kukan har sun gaji, Hajiya Zuwaira ta mike ta nufi gun kaka ta dagota cikin sanyin murya tace "Addu'a xa ki yi mata kaka Allah ya gafarta mata" Kaka ta kara rushewa da matsanancin kuka ta rungumeta tace "Wllh matar kirki ce Maryam, duk abinda aka ga tayi bai kai xuciyarta ba xugar shegu ne, kaf shekarunmu da ita bata ta6a tanka ni ba, bata ta6a min rashin kunya ba, duk tsiyata da fitinata shiru take min, kuma anjima baxata fasa xuwa ta min magana ba, ita dai idan ka xauna wajenta cikinka ne xai gaya maka amma wllh ko kallon banxa baxata maka ba balle maganan banxa, kaf surkaina bbu me raga min sai ita, kuma ba dai kaga ta canxa fuska ba don Amadu xai yi maka abu ko xai baka abu, bbu ruwanta da wnn wllh wllh, ita dai kawai girki ne bata son yi balle ta baka ka ci ka koshi, yanxu Maryam ta rasu?? Jiya jiya fa ta sallame mu da yamma wai xata koma wai Amadu yace kar ta kwana, har Yakumbo ke ce mata ta bari gobe yamma yayi ashe ajali ke kiranta, yanxu ya isilin marayun nan da ta bari ni Patuu??" Kuka sosai Kaka ke yi Hajiya Zuwaira na lallashinta, Hajiya Amina hawaye ya kasa tsaya mata haka kishiyarta, ba karamin girgixa su mutuwar yyi ba, daga karshe Hajiya Zuwaira ta fitar da kaka daga parlon. Sosai aka ji rasuwan Mumy, ba 'yan uwa ba, ba makota ba, yawanci kuma duk kyawawan halinta ake fadi, kaka dai ta dage a kan bata ta6a mata rashin kunya ba, ko kallon banxa bata ta6a mata ba, yunwar da ta barta da shi ma ta yafe mata duniya da lahira, har kwana uku kaka bata daina kuka da jimami ba, ana xaxxaune parlor a kwana na ukun, Hajiya Sadiya ta shigo tare da Hajiya Balarabe, Sadiya ta rushe da kuka tana rufe fuskarta da Hijab din jikinta, kaka tayi mitsi mitsi da ido tana kallonta, Sadiya ta karaso tana goge hawayen idonta ta xauna kasa tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Allah ya ji k'an Maryam, Allah ya gafarta mata, Allah ya yafe mata" Kaka na mata wani kallo daga sama har kasa tace "Sai yau kika ji rasuwan kenan?" Sadiya ta ki dago kanta tana matsar kwalla tace "Eh wllh, na yi tafiya naje Sokoto, garin da naje bbu network sai yau na dawo kaduna, ina dawowa aka sanar min wai Allah yyi ma Maryam rasuwa" Tana kai wa nan ta saki kuka da karfi, Kaka ta mike tana rike da carbinta tace "To tashi ki fita, algunguma mayya yar jaraba, Allah ya isa tsakaninmu da ke...." Da sauri Sadiya ta mike har tana neman faduwa ta nufi kofa Balaraba ma ta mike ta bi bayanta da sauri, kaka ta fashe da kuka tace "In sha Allahu karshen ku baxai yi kyau ba, duk ku kuka gurbata tunanin Maryam, mata me kirki bbu ruwanta da mugun abu kai dai idan xaka xo gidanta to ka xo da shirin dinga shiga kitchen ka nema ma kanka abinda xaka ci, amma tsinannun mutane kawai kun nemi hallakata ku ka fara sa ta yawon banxa, to in sha Allahu muna nan muna mata addu'ar Allah ya gafarta mata, ya yafe mata kurakuranta, ku kuma Allah kadai yasan yanda xai yi da ku, duk ku ne sanadin canxa halin Maryam" tuni Hajiya Sadiya da Balaraba suka fita daga parlon, kaka ta koma ta xauna tana matsar kwalla. Da yammacin ranan Khaleel ya xo gidan tare da Junaid, Kaka na parlor da Yakumbo sai Ta rasulu da wasu step sisters din Abba, Kaka ta amsa gaisuwarsu cikin sanyin murya tace "Tun da aka yi rasuwan sai yau ku ka xo min gaisuwa Junaidu?" Shi dai Khaleel bai ce komai ba, Junaid yace "A'a jiya mun maki gaisuwa kaka, kuma ko da safe ma mun xo har mun gaisa ma...." Kaka tace "Toh duk na rude, ai mutuwar maryam ya girgixa ni d'an nan, ga mutane kamar kiyashi, duk ana ta xuwa min gaisuwa gidan nan ba masaka tsinke, har daga Nijar, maiduguri da Taraba an xo min gaisuwa, kaga ai baxan lura da ku ba, to kun ma Amadun gaisuwa kuwa? Shi ma dai duk karfin hali yake, mutuwar mata ai babban tashin hankali ne, shekaransu talatin da tara tare, sai da suka yi aure da shekara shidda marigayiya ta haifi Shuraim d'an ta na fari" Junaid yyi kasa da kansa yace "Allah ya gafarta mata" Kaka ta goge kwallar idonta tace "Ameen dai, Allah ya yafe mata kurakuranta, mu ma kuma Allah ya kyautata namu karshen" Junaid yace "Ameen" Yakumbo dai sai satan kallon Khaleel take tana wuri wuri da 'yan idanuwanta, Junaid yace "Shuraim fa?" Da damuwa Kaka tace "Wa ma ya sani, ni dai nace da ma kukan yyi yanda duk muke yi ko xai ji dadi ya samu salama, rashin kukan ya fi cutarwa, daxu dai ya shigo da d'an uwan, ban san ko ya fita ba" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Allah ya kara hakuri da dangana" Kaka tace "Ameen, Rakiya na can parlon ku shiga ita ma ku kara mata gaisuwa, yau kwananta uku a nan gidan ita ma" Mikewa Junaid yyi ya nufi parlon da Kaka ta nuna masa Khaleel ya mike shi ma ya bi bayansa, Kaka ta bi sa da kallo kasa kasa tace "Yo ba sai ya sa6a xama cikin jama'ah xai sake ba, mutum dai kamar bass din shirin Indiya, ko murmushi bai yi, naga yanda Deedayah xata xauna da shi tunda tace ta ji ta gani, ba ruwanmu" Yakumbo tace "To ba dai ita da uban sun ji sun gani ba, har ynxu fa a dari dari yake da mutane, abin ka da wanda ya saba xaman daji" Mami na xaune parlon tare da su Hajiya Amina da Zuwaira, Heedayah ma na parlon da Farida da su Rabi'ah da su Zainab, Junaid ya xauna nan kasan carpet din parlon ya gaida su Mami, Khaleel ma ya xauna ya gaishesu kansa a kasa, Gaba daya 'yan matan parlon suka gaida su Junaid, Heedayah dai na kwance idonta rufe ta juya ba, Junaid na kallonta yace "Bacci Heedayah take" Mami ta ta6ata a hankali tace "Heedayah" da sauri ta bude ido ta juyo ta mike xaune ganinsu Junaid tace "Ina yini Yaya?" Yace "Lafiya lau bacci kike yi?" Tace "Uhm" Kallon Khaleel dake kallonta tayi a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau" Junaid yace "Ya karin hakuri?" Tace "Alhmdllh" Junaid yace "Allah ya gafarta mata" ta amsa da "Ameen" kallon Mami yyi yace "Shuraim na gidan kuwa?" Mami tace "Ehh yana dakinsa with Sudais, you check" Tashi yyi suka fita parlon tare da Khaleel. Washegari Mami suka koma gida gaba daya, gidan ya rage kaka da tawagarta da sisters din Abba, har su Rabi'ah Mami ta wuce da gidanta, sosai yaran ke bata tausayi hakan yasa ta sa su debi kayansu su koma can gidan nata tare, tunda suka dawo gida Heedayah gaba daya bata da walwala kai kace mahaifiyarta ce ta mutu, abinci sai tayi da gaske take ci, Suna kitchen tare da Farida da Maid din Mami suna serving ma kowa abinci a gidan, Farida ta mika mata plate din abinci da ta xuba ma Khaleel d'an kadan sanin haka yake ci tace "Ki kai ma Yayanmu" Heedayah ta jingina da cabinet tace "Ke dai ki kai masa, ba wanke wanke xan karasa ba" Farida tace "Ba ga Zainab na yi ba, meye kuma idan kin kai masa abinci" Heedayah dai bata ce komai ba, can ta amshi plate din ta dau wani plate ta rufe sanin ba a lkcn xai ci ba idan an kai masa ta juya ta fita kitchen din, sama ta wuce ta bude dakin junaid taga baya ciki, ta karasa last room dake wajen don yawanci nan yake xama yanxu, ta bude kofar amma ba gaba daya ba tayi sallama, sai da taji ya amsa snn ta shiga, xaune ta gansa yana danna laptop, ya daga kai yana kallonta shi ma, har ta karaso ta ajiye plate din tace "Ina yini" Yace "Have u finish mourning?" Ta d'an kallesa bata ce komai ba, yace "To Allah ya gafarta mata, naga kamar kun shaku da ita sosai ko?" Sake kallonsa tayi still taki cewa komai, Ya ci gaba da abinda yake a laptop, ta juya xata fita yace "Heedayah" juyowa tayi ya nuna mata kujera yace "Sit, let's talk" Ba musu ta dawo ta xauna tana kallonsa, ya d'an yi shiru kafin yace "Kamar naga baki son aure yanxu ko? Like... Karatu kike son ci gaba da" Ta kallesa, jin bata ce komai ba yace "Feel free talk to me" Tace "Why did you ask me that?" Yace "Because I have noticed ur changes in behavior" Ta hade rai tace "Wani irin changes?" Yace "Na baki son auren, may be u have other plans" Ta girgixa kai tace "I have no plans, kuma ni bance maka bana son auren ba" Ya d'an yi murmushi cikin sanyin murya yace "Don't worry Heedayah my heart have been broken so many times nasan damuwar ki kenan, na saba da heartbreak kar ki damu da haka... kawai dai naki will be different and may be more painful and difficult to endure, but all the same, ba a tilas a aure, I will help you tell ur parent su bari ki ci gaba da karatun ki...." Heedayah ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace "Ni ban ce haka ba, kai ma kuma kasan I so care about you bana son wani abu ya sameka, ni bance bana son auren ba.... just that ina son kada ka dinga kokarin hanani mu'amala da yayanni na, and you just have to trust me..... I will never betray you" Shiru yyi yana kallonta, ya mike ya isa gabanta yace "Baxan hanaki mu'amala da su ba, amma kuma ni ma kada ki hanani kishin ki" Ta sauke idonta kasa bata ce komai ba. Da daddaren ranan Heedayah ta fito daki xata kai cup din da ta sha shayi kitchen ta tadda Mami da Shuraim xaune downstairs, Kansa a kasa Mami na yi masa magana cikin kwantar da murya, shi dai bai ce komai ba, tun rasuwar mum dinsa wnn ne ganinsa na biyu da tayi, ta wuce kitchen ta ajiye cup din hannunta ta fito, bata karaso cikin parlon ba ta gaishesa cikin sanyin murya, ya daga kai ya kalleta ya amsa, Mami tace "Ki kawo masa abinci" Ya girgixa kai yace "Aa, I am full" Mami tace "Aa sai ka ci, you don't even look like someone that is eating" Shiru yyi bai ce komai ba, Heedayah ta juya a sanyaye ta koma kitchen din, Ko da ta fito da tray din abinci Mami ta riga ta bar parlon, ta karasa ta ajiye masa tray din gabansa tana kallonsa a hankali tace "Ya karin hakuri ya Shureen?" Yace "Alhmdllh, how are you?" Tace "I'm fine" Bai kuma ce mata komai ba, ta xauna nan kasa tace "Ya Shureen plss ka kwantar da hankalin ka, you don't look okay, don't get sick plss" Ya d'an mata murmushi yace "I am okay" Tace "Nooo gashi ka rame" Yace "Katuwa kike son in xama kamar ki?" D'an murmushin karfin hali tayi bata ce komai ba, yace "Ohk xauna, let's talk" Ba musu ta xauna nan kasa tana kallonsa, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "I want to ask for a favor Heedayah" Ta gyada masa kai tace "Sure, ina ji" ya sauke idonsa yace "Forgive my Mum Heedayah...." Ji tayi xuciyarta yyi rauni sosai, ta girgixa masa kai hawaye ya kawo idonta lkci daya, cike da karfin hali tace "Bata ta6a min komai ba ya Shureen" cikin sanyin murya yace "No Heedayah, I wished she had the privilege to ask for ur forgiveness before leaving, my mum was good, Just all of a sudden..... anyway just Forgive her for the sake of Allah and my father" ta goge idonta tace "I have done that already, Allah ya gafarta mata" Yace "Ameen, I appreciate, ya shirye shirye?" Tace "Na me?" Yace "Na bikin ki?" A hankali tace "Ba a fara ba tukun ai" Ya d'an yi shiru, ta daga kai ta kallesa, yace "Toh Allah ya kai mu lkcn lafiya, ki turo min su Rabi'ah" Tace "Toh" daga haka ta mike ta wuce sama. Mami da iyayen Heedayah sun so a dage bikin da ya rage saura sati uku yanxu sbda rasuwar Mumy amma Abba ya ki amincewa da hakan, wnn yasa aka bar bikin lkcn da aka yi fixing, bayan sati biyu da rasuwar Mumy kuma aka hau shirye shiryen bikin duk da ko kadan hakan bai ma iyayen Heedayah da ma Mami dadi ba, sai dai Abban Heedayah yace daurin aure kawai xa ayi sai walima bbu wani event.... Biki saura kwana goma Heedayah ta koma Kano ta private jet tare da su Farida da Rabi'ah..... *Sick... Need ur prayers plss* Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Heedayah na xaune daki tana kallonsu Farida dake fiddo ankonsu daga cikin akwatin da aka kawo har an dinka kayan wanda kala biyar biyar ne, kallonsu kawai take amma gaba daya hankalinta ba a kansu yake ba, tayi nisa tunanin da take aka kwankwasa kofar dakin, Farida ta mike ta nufi kofar ta bude don duba waye, Heedayah ta kalli agogo dake nuna tara saura na safe, ta koma ta kwanta a hankali saman gado, yau kwanansu biyu da dawowa kano, a kwanakin nan biyu a ko wani second cikin faduwar gaba take, duk ta rame abincin ma bata iya ci sosai sai tunani, babu wanda ke tambayarta don me a gidan da ya fara cika da jama'ah daga wajaje daban daban sai step mum dinta dake kokarin kwantar mata da hankali ko da yaushe sanin it's always like that for a new bride to be, Farida ta dawo dakin tana kallonta tace "Aunty na kiran ki Heedayah" Heedayah tayi shiru, kafin ta mike ta sa hijab dinta ta fita daga dakin ta tafi bangaren Mom Islam, Tsaye ta sameta dakinta ta fiddo da wasu tsadaddun atamfofi da laces da aka dinka kala goma daga wani sabon akwati, tana kallon Heedayah tace "An kawo kayan dinkin ki for the week" a hankali Heedayah tace "Toh" Mom islam tace "Me maki gyaran jiki tana jira a can bangaren Ammin ki, ki wuce can yanxu" A hankali Heedayah ta sake ce mata "Toh" Juyawa tayi xata fita, Mom Islam tace "Kin ci abincin kuwa" Heedayah tace "Na ci" Mom Islam tace "Okay anjima xa a kawo kayan lefen ki idan Allah ya yrda" Heedayah dai bata ce komai bata juyo ba kuma bata tafi ba, jin step mum dinta tayi shiru ita ma, ta juyo tana kallonta, Murmushi step mum din ta sakar mata tace "Haka kike son a kai ki duk a rame Heedayah, ba nace ki kwantar da hankalin ki ba?" Heedayah ta kasa ce mata komai, Step mum din ta nufeta tace "Tell me meye damuwar ki yanxu?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Aunty kawai ni dai ina tsoro" Stepmum dinta tace "Ki kwantar da hankalin ki xaki daina, it's like that with some, yanxu ki fara tafiya kiyi ma Abbanki godiya kafin ya bar part dinsa..." Heedayah ta gyada mata kai snn ta nufi kofa ta fita, bangaren Abban nata ta tafi ta bude kofar babban parlonsa a hankali ta shiga, yana xaune parlon tare da Sudais da Shuraim, duk suka daga kai, ganinta Shuraim ya dauke kansa, karasawa parlon tayi a sanyaye ta xauna kasa ta gaishesu, suka amsa... snn ta kalli Abbanta tace "Abba Aunty ta bani kaya, I really appreciate it" Abba yace "U are wlcm Fatima" Sudais ya mike tare da Shuraim, yace "Mun gode ur Excellency Allah ya kara girma" Abba na murmushi yace "Ameen, yanxu xaka koma Kadunan?" Sudais yace "In sha Allah" Abba yace "Toh Allah ya tsare, Allah ya maku albarka...." Duk suka amsa da Ameen, suka nufi kofa... Abba da ya bi Shuraim da ido yace "Don't forget you meet me at office later Aliyu" Shuraim yace "In sha Allah" Daga haka suka fita da Sudais, Abba na kallon Heedayah yace "Hope no problem dear?" Ta girgixa kai tace "Aa babu" Abba yace "Toh Allah ya maki albarka" a hankali tace "Ameen" bayan few seconds tace "Abba me su Yaya suka xo yi?" Da mamaki yake kallonta yace "Me suka xo yi kuma?" Bata ce komai ba, yyi murmushi yace "Na ba Sudais appointment ne, shi kuma Shuraim dama a nan yake ai...." Heedayah ta ji dadin abinda Abbanta ya fada har xuciyarta, tace "Allah ya kara girma Abba, I am happy with that, I stayed with them from the beginning because of Ya Sudais, he didn't reject me even for a second, he supported my Abba and convinced everyone I stay.... Shine silar xamana tare da su" Abbanta ya girgixa kai yace "Kuma ban sani ba, I just saw his dad is nice also, shi ma naga yana da hankali" Heedayah ta gyada kai, Abba yace "Toh Allah ya saka masa da alkhairi, amma ya kamata yyi aure shi da Shuraim..." Murmushi Heedayah tayi tace "Toh ai shi ya kusa haka kaka tace mana" Abba ya girgixa kai yace "Aa we just talked about that now, yace his mum was against the marriage, bata son auren" Shiru Heedayah tayi mamaki ya cikata, can tace "Toh did you talk to Ya Shureen also?" Abba yace "Sure I did, yace min soon" Heedayah tace "Allah ya kai mu" Abba yace "Shi kuma Junaid his uncle called yesterday, yace jiya aka kai nasa gaisuwar Yola" Heedayah ta buda ido tace "I am happy for him" Abba ya gyada mata kai yace "Sure" A hankali tace "Toh Abba why didn't you give Ya Junaid appointment also?" Abba yace "He is working... Haka Mum dinku tace" Heedayah tace "Ya Shureen fa?" Abba yyi murmushi yace "He is now my assistant family doctor" Murmushi kawai ita ma tayi, Abba na kallonta yace "Baki tambayar ma Khaleel ba?" Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi Abba yace "I appointed him first, after the wedding in sha Allah, he will report to work" A hankali Heedayah tace "Allah ya kai mu" daga haka ta mike ta sallami Abban nata ta bar parlon tunawa da tayi Mom Islam tace ana jiranta a bangaren Ammi. Sai da ta fara tafiya parlon baki ta tadda Shuraim and Sudais, Sudais na shan shayi shi kuma Shuraim na danna wayarsa, murmushi Sudais ya sakar mata yace "Amarya" ita dai bata ce komai ba ta karaso cikin parlon tace "Yaushe ku ka xo Yaya?" Yace "Yesterday, ya shirye shirye?" A hankali tace "Alhmdllh" kallon Shuraim dake ta danna wayarsa tayi tace "Welcome ya Shureen" ya d'an kalleta yace "Thanks, ya komai?" Tace "Fine ya karin hakuri" yace "Mun gode Allah" Tace "Kai baxa kayi breakfast din ba?" Yace "No I am okay" tace "Okay sai anjima" Yace "Alright" daga ma Sudais hannu tayi ya sakar mata murmushi ta bar parlon da sauri. Ammi na parlonta da frnds dinta da wasu mata uku that are wedding planners, Ammi na kallonta tace "Ki je spare room upstairs ana jiran ki" Heedayah tace "Toh" Da yammacin ranan motoci hudu suka xo daga garin gombe kawo lefen Heedayah government house, Aunts din Khaleel ne da matan uncles dinsa sun kusa su goma, aka masu tarba me kyau na mutunci da girmamawa, akwatuna set shidda sau biyu, sai set uku makil da tsadaddun kaya suka kawo matsayin lefen Heedayah, a cikin akwatin jewelries har da sarkan zinari da dankunne da rings, kowa ya6a kayan yake don ba karya sun yi, Yayar Ammi na kallon Ammi bayan duk an gama bude kayan tace "Daga gidan uwar rikon nata aka kawo wannan kayan?" Ammi tace "Aa daga dangin mahaifinsa ne" Hajiya Salamatu tace "Allah sarki, toh Allah ubangiji ya sa gidan xamanta ne, Allah ya basu xaman lafiya, ni ko angon ma ban gani ba har yanxu...." Ammi ta d'an yi murmushi tace "Ameen" Heedayah na bangaren Stepmum dinta da su Farida an gama mata gyaran jiki na ranan, wani kyau na musamman tayi skin dinta sai glowing da sheki yake kana ganinta kaga amarya, amaryar ma 'yar gata, tun da taji an kawo kayanta take kukan da bata san dalilinsa ba, babu irin lallashin da Farida da su Zainab basu yi mata ba amma kamar suna dada tunxurata, Stepmum dinta ta ja ta xuwa bedroom dinta tana mata wani kallo tace "Wani iskanci ne wnn kuma Heedayah, kukan meye haka kike yi ma mutane kamar warce aka doka? Kinsan idan bangaren Amminki kike sai ta 6ata maki rai ko?" Ta fashe da kuka sosai tace "Aunty kawai ni dai gabana faduwa yake, wllh tsoro nake ji" Mom Islam ta xauna gefenta cikin kwantar da murya tace "Toh kiyi ta addu'a, babu abinda xai faru my daughter, ko wacce amarya kan ji hakan ki kwantar da hankalin ki kin ji?" Heedayah ta gyada mata kai da kyar hawaye na sauka idonta, Mom Islam tace "Kun yi magana da Khaleel din?" Heedayah ta girgixa mata kai, Mom Islam tace "Toh ina wayar taki?" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Yana can daki na" Mom Islam tace "Bari Farida ko Rabi'ah su dauko maki, kilan ma ya kira ki" daga haka ta juya ta fita, Heedayah ta koma ta kwanta hawaye na sauka idonta a hankali, ba a dau lkci ba Farida ta kawo mata wayarta ta amsa Farida ta fita dakin, miss call din Khaleel daya ta gani sai na Shuraim daya, a hankali tayi dialing number Khaleel, yana fara ring ya katse sai gashi ya kirata, cikin sanyin murya ta amsa sallaman da yyi mata tace "Ina yini?" Cikin cool voice dinsa yace "Alhmdllh Heedayah, how are you?" a hankali tace "I'm fine" yace "Noo, ur voice isn't, ko kuka kika yi?" ta turo baki tace "umm" yace "Why" mikewa xaune tayi tana goge idonta tace "I am just afraid" sai kuma ta sakar masa kuka, ya d'an yi shiru kafin yace "Afraid of what Heedayah?" Cikin rawar murya tace "Nima ban sani ba" Yace "Toh kiyi addu'a" tana hawaye tace "Ina yi" yace "Pls ki kwantar da hankalin ki, don't stress ur self much" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace "Kina cin abinci?" Tace "Bana iya ci" yace "Aa ki dinga ci, kina son ki kara ramewa ne? You are making me feel sick also" Ta girgixa masa kai bata iya ta ce komai ba, yace "Tell Farida to get you something to eat now idan kin gama ci sai ki kirani yanxu" Cikin sanyin muryarta tace "Toh" Daga haka ta katse wayar ta ajiye, mikewa tayi ta nufi kofa ta bude tana kallon su Farida dake parlon Mom Islam tace "I want a cup of tea plss" Murmushi kawai mom Islam tayi, Farida ta mike tace "Ohk dear" daga haka ta mike ta fita daga parlon Heedayah ta koma dakin ta xauna. Daukar wayarta tayi ta shiga kiran Shuraim da yyi mata miss call, har ya gama ring bai dauka ba ta ajiye wayar, Farida ta shigo dakin da cup of tea and pepper soup ta ajiye mata, saukowa Heedayah tayi kasa a hankali tace "Thank you" Murmushi Farida tayi mata tace "U are welcome Aunty Heedayah" Heedayah ta wani hade rai, da sauri Farida ta juya ta fita dakin tana dariya, Heedayah ta dau shayin ta fara sha a hankali, pepper soup din bata wani ci da yawa ba ta rufe snn ta tafi bandakin Auntynta ta wanke bakinta ta fito, daukar wayar tayi ta shiga kiran Khaleel, katsewa yyi ya kirata ta daga ta kai kunne, yace "Har kin ci abincin?" Ta gyada masa kai tace "Uhm" yace "Aa ban yarda ba" Tace "Wllh na sha shayi with pepper soup now" yace "Good dear, how are you feeling now?" Cikin sanyin murya tace "Alhmdllh" Yace "Now tell me, what's making you afraid or disturbed?" Shiru tayi, yace "Talk to me dear, feel free" A hankali tace "That I am getting married" Murmushi ya d'an yi yace "And whats making you afraid because u are getting married?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Nima dai nan sani ba" Yyi kasa da murya yace "In dai kina sona you need not to be afraid, I am not a beast, or am I?" Ta sauke idonta kamar yana ganinta bata ce komai ba, yace "Talk to me" A hankali tace "Baxa ka dinga bani tsoro ba?" Sauraronta yake da mamaki, can yace "Wani irin tsoro?" Tace "Nima ban sani ba" Ya d'an yi murmushi yace "Baxan baki tsoro ba wife" Sun dade sosai suna magana da Khaleel har kusan la'asar, a dai dai lkcn kuma frnds din Mami da sisters dinta da su Hajiya Zuwaira da step mum din Sudais suka iso daga Kaduna da Boxes set shidda cike da kaya..... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... A hankali Heedayah ke saukowa stairs xuwa sitting room dinsu, Hijab ne har kasa jikinta ta karaso cikin parlon da ya cika da sanyin Ac, kamshin turaren da ya gauraye ko wani angle din parlon ne ya sa ya daga kai suka hada ido da ita, ya sauke idonsa, ta xauna saman kujera tana kallonsa cikin sanyin muryarta tace "Good evening" ya d'an kalleta yace "Evening, how are you??" tace "Alhmdllh" Ya cire face cap din camouflage dake kansa yace "Ya preparation?" Tace "Alhmdllh" Ya gyada kai bai ce komai ba, tace "Ya karin hakuri?" Yace "Mun gode Allah" Shiru ne ya biyo baya, ta mike xata tafi kitchen yace "Noo don't bring anything, I am okay... Sit let's talk" Ba musu ta dawo ta xauna tana kallonsa, Banda glowing da kamshi bbu abinda take, haskenta ya karu sosai ta dawo kamar balarabiya, Yana kallonta yace "Just came to wish you a happy married life in advance, after that sai ki fadi ko da wani abu da kike bukata? baxan samu daurin auren ki ba coz I will be leaving for Lagos today in sha Allah, daga can kuma xan wuce UK for few weeks...." Da damuwa tace "Me xaka je yi UK ya Shureen?" Yace "Course" A hankali tace "Allah ya kai ka lafiya" yace "Ameen, tell me what u want Heedayah" Ta sauke idonta kasa tace "Bana bukatar komai kawai addu'ar ka" Yace "Alright in sha Allah" Bata kuma cewa komai ba ya kalli agogo dake nuna karfe biyar da some minutes yace "I will be leaving now, my flight is 8:00pm" A hankali tace "But ina son inyi maka tambaya ya Shureen" Yana kallonta yace "I'm all ears" Cikin sanyin murya tace "You are actually nice, why don't u feel free with everyone a daina misperceiving din ka?" Murmushi yyi yace "What are u insinuating?" Tace "Nasan ka fahimce ni" Yace "It's nature Heedayah, let me give you this short story...." Shiru tayi tana sauraronsa, yace "Few years back lkcn ina aiki a hospital din Baffana, akwai wata nurse Auxiliary nurse by name Hameedah a hospital din, she is was 19 then, just as pretty as you, I had feelings for her because of her personality most especially her being religious and calm, but because of my so called nature I couldn't approach her, I don't know why I act that way also... I made so many attempt but failed approaching her, kowa a asibitin yasan abinda ya kai ni kawai nake yi in bar wajen, har ita magana bai ta6a hadamu ba sai na aiki shima briefly, ana sauran 2 weeks ta bar clinic din I couldn't hold it any longer, nan na yi iya kokarin fara mata magana coz I was dying in silent with her love, kamar dai yanda kika ga na fara maki magana months back..." Heedayah ta daga kai tana kallonsa, Murmushi ya sakar mata ya ci gaba da abinda yake cewa "A nan kuma nake tambayar Hameedah when will she get married tace min yau sati daya kenan da aka sa mata rana abinda ya sa kenan xata bar asibitin, from what I noticed bata son wanda xa a aura mata coz she was in tears, and that was how I loose Hameedah har ta tafi kuma bata ta6a sanin I have feelings for her ba, a lkcn you were just 14 a gidanmu...." Shiru Shuraim yyi yana kallonta, Heedayah tace "You said kamar yanda ka fara min magana months back, do you have any intentions that made u start talking to me ne dama?" Kallonta kawai Shuraim yake ko kiftawa bbu, ta sunkuyar da kanta sbda haka, jin bai ce komai ba, a hankali ta dago tace "Ohk I am sorry for the question" Ya girgixa mata kai yace "You need not to be, yes Heedayah, I had intention... feeling free with you by all means..." Tace "What's ur intention?" Ya jinginar da kansa a hankali jikin kujeran murya can kasa yace "I just repeated my first mistake, I've made two same mistakes" Heedayah na kallonsa ta girgixa kai tace "Ban fahimta ba" Shiru yyi yana kallonta, tace "Ka fahimtar da ni" Yyi murmushin karfin hali kafin yyi magana aka kwankwasa kofar shigowa parlon, a tare suka kalli kofar, Farida ce ta shigo parlon da sallama, gaida Shuraim tayi bayan tayi masa kallo daya ya amsa with smile, ta kalli Heedayah tace "Aunty na ta nemanki Heedayah" Heedayah tace "Toh gani nan xuwa" Juyawa Farida tayi ta bar parlon, Shuraim ya dau face cap dinsa ya saka snn ya mike yace "I've kept you here for so long, ki shiga ciki...." Mikewa tayi tana kallonsa, Bai yarda ya kalleta ba yace "As I have said earlier, I wish you a happy married life in advance Lil sis, Allah ya baku xaman lafiya da xuri'a dayyaba" Bata ce masa komai ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta juya ta bar parlon tana tafiya a hankali ta koma bangaren Stepmum dinta ta hanyar da baxata hadu da mutane ba don gidan cike yake da mutane. Daki ta tadda Mom Islam tsaye alamar ita take jira, Mom Islam ta hade rai ganinta, cike da fada tace "Wai kina da hankali ma kuwa Heedayah, what's wrong with you, Gobe daurin auren ki xaki tafi ki xauna da wani for the past 30mins yanxu, da ban aika ki taho ba dama baki da niyyar tahowa kenan?? Me ke damun ki haka kamar mara ilimi?" Sunkuyar da kai Heedayah tayi bata ce komai ba, Mom Islam tace "Toh daga ynxu har xuwa gobe da xa a kai ki dakin ki baxa ki sake fita gun wani ba, shi Shuraim din kuma sai ya sa maki ido kamar bai san abinda ya kamata ba, me da me ma yake ce maki har na minti talatin din?" A hankali Heedayah tace "Aa kawai nasiha yake min Aunty, that's all" Mom Islam tace "Toh Allah ya sa kin dauka, ga farfesu can an kawo maki ki dauka ki cinye tass kafin in dawo, ga wani ruwan wankan na yamma can na hada maki" Daga haka mom Islam ta fita daga dakin ta kulle kofar. Heedayah ta cire Hijab dinta ta linke ta ajiye a hankali ta nufi gun da bowl din ke ajiye ta xauna saman carpet me laushi ta bude tana kallon naman kazar dake ta kamshi da tiriri, da kyar ta iya cin yanka biyu a ciki ta rufe tana ta6e baki, wayarta dake gaban mirror din Stepmum dinta ne taji ya fara ring ta mike ta isa gaban mirror din tana kallon sunan gaban screen din, sosai jikinta yyi sanyi don tun daxu yake ta kiranta, ta dauka ta koma gefen gadon ta xauna ta daga ta kai kunne, amsa sallamansa tayi cikin sanyin murya tace "Good evening" Yace "Evening dear, ina kika shiga?" Tace "Kitso aka min, I just came in ynxu naga kiran, kayi hakuri" Yyi kasa da murya yace "But bana son kitso fa dear" Ta buda ido sosai tace "Uhn da gaske?" Yace "Yeah..." D'an murmushi tayi tace "To in kwance kenan?" Yace "Aa wahala xa ki sha, ki bari gobe sai in kwance maki da daddare" Tace "Uhn, Aa Farida da su Rabi'ah xa su taya ni kwancewa anjima" yace "No leave it, I will loose it my self all alone" a hankali tace "Toh shkkn" yace "Hope kin ci abinci dai yau?" Tace "Ehh na ci daxu" yace "Alright, Farida tace min kina tunani da yawa, tunanin me kike?" Wara ido tayi tace "That's not true" yyi murmushi a hankali yace "Now tell me, how do you want our married life to be Heedayah, duk yanda kike so haka xa ayi" Shiru tayi jin abinda yace, cikin cool voice dinsa yace "Kin yi shiru dear" Ta sauke idonta kamar yana ganinta murya can kasa tace "I just want you to be caring and understanding..." sai kuma tayi shiru, yace "You list them, abinda kike so da wanda baki so a gidan aurenmu duk ki gaya min yanxu" a hankali tace "Ina son kayi hakuri da flaws dina ko wani iri ne, I want you to be considerate toward me, idan nayi maka laifi ka dinga considering dina...." Hawaye ne ya kawo idonta tayi shiru, yace "Ina jin ki...." Ta share idonta tace "Ka tayani son abinda nake so, ka ki abinda nake ki ko meye shi" yace "Like?" Tace "Da akwai abubuwa da yawa da bana so ai...." Yyi murmushi yace "To naji.... Baki tambayeni kids nawa nake so ba" ta turo baki, kamar ya ga abinda tayi, yyi murmushi yace "Ohk just two are okay" Xaro ido tayi tace "Two kuma?" Yace "Yes, if they are to be boys in sha Allah... Ahmad and Usman" Shiru tayi, yace "Isn't it?" Tace "Uhm to har da Aliyu, ni ina son sunan" yace "Really?" Tace "Ehh" murmushi yyi yace "Toh shkkn, sai ki haifi uku duk da biyu kawai nake so dai" murmushin ita ma tayi bata ce komai ba, murya can kasa yace "I love you Heedayah" Ta sauke idonta kasa cikin sanyin murya tace "I love you more" Shiru yayi yana jin kalman nata har ransa, a hankali tace "Kilan me yi min turare na jirana yanxu...." Yace "Turaren me" tace "Nothing" yyi murmushi yace "Ohk xan kira ki after Isha" Tace "Okay bye" katse wayar tayi ta mike ta sa Hijab dinta tana kallon bowl din naman da stepmum dinta ta bata, da xata samu inda xata xubar, xubarwa kawai xata yi don baxata iya ci ba, fita tayi dakin ta tafi inda me yi mata gyaran jiki take, bak'i ne daga garurruka daban daban cike a ko wani bangare na gidan jikin Heedayah yyi sanyi sanin they are all here to witness her wedding fatiha tomorrow Friday idan Allah ya amince. Heedayah na wani bangare daban na gidan wajajen karfe tara da su Farida da Rabi'ah, sun kusa su sha biyar a babban dakin, ita dai su Rabi'ah da Farida kadai ta sani sai sisters din Sudais, sauran duk 'ya yan abokan Abbanta ne da Amminta, Heedayah na kallon Farida dake kwance tace "Farida pls can you call ya Shureen with ur phone, he said he is leaving for Lagos, kiji ko ya isa lafiya" Farida tace "Oh Lagos ya wuce, baxai samu daurin aure ba kenan gobe?" Heedayah tace "Ehh, ki kirasa kiji ko ya tafi" Farida tace "Ke ki kirasa mana" Heedayah tace "Toh ai bai kamata ni in kirasa ba" Dariya sosai Farida tayi tace "To ai kya bari a daura auren ko?? Yanxu bbu igiyar kowa a kanki balle kice bai kamata ba" Heedayah tace "Ko?" Farida tace "Yes, daga gobe ne idan Allah ya yrda" Heedayah ta jawo wayarta a hankali ta shiga duba lambar Shuraim, dialing tayi ya fara ring, yana fara ring ta mike ta shiga wani dakin daban, katsewa yyi ya kirata, ta daga ta kai kunne hade da sallama tace "Ya hanya?" Yace "Alhmdllh, we just landed" Tace "Ohk, Allah ya huce gajiya..." Yace "Ameen nagode" Tace "Sai da safe" Yace "Ohk but I forgot ban maki nasiha ba, duk da nasan an maki tun kafin goben, let me just add this...." Shiru Heedayah tayi tana sauraronsa, a hankali yace "Duk runtsi duk tsanani kada ki bari frnds su ja ra'ayinki a rayuwa, snn ki saka a ranki bbu me taimako sai Allah, I am not talking of today, tomorrow, next year or even 5 years to come, I am talking of for ever...." Heedayah dai tayi shiru, cikin sanyin murya Shuraim yace "For 33 years da nasan mahaifiyata bata yarda da kowa ba sai Allah, mahaifiyata macece me yawon ibada, Azkar din safe da yamma da karatun Qur'ani basu ta6a wuceta a rana, snn ita din me yawan sadaka ce, ko kaka tana yabonta ta wnn fannin, mu'amalar ta da mutane was very good, bata da abokin fada a iya sanina, but all of a sudden kawaye suka ja ra'ayinta a kan abinda bai kai ya kawo ba...." Kasa cigaba Shuraim yyi, lkci daya xuciyarsa yyi rauni, bayan few seconds yyi gathering courage yace "It's so sad bayan duk wannan abubuwan da na lissafo na halayenta ta rasu tana sabon ubangiji, ta rasu tana shirka all because of just a little girl wacce xata yi jika da, kinga dai Allah bbu ruwansa, sai kaga mutum na sabo farkonsa amma daga karshe kuma ya shiryesa, wani kuma xaka ga yyi ta abubuwan alkhairi amma rashin rabo xai sa ya 6ata ayyukansa a karshe, abinda ya faru da Mahaifiyata kenan, I am so sad about this, ina kuma yi mata fatan samun rahama wajen Allah, Ina fatan Allah ya dubi ayyukanta na baya ya gafarta mata..." Hawaye ya shiga sauka idon Heedayah, lkci daya jikinta yyi sanyi, cikin rawar murya tace "And all this happen because of me, da ban shigo rayuwarku ba ur mum will hold on to her strong faith, I caused everything..." Ta fashe da kuka sosai, Shuraim dake sauraronta ya lumshe ido a hankali yace "U caused nothing Heedayah, haka kaddarar ta yake, Allah ubangiji ya gafarta mata ya sa mu cika da Imani, Ina neman alfarman duk lkcn da kika yi sllh ki dinga sa ta a addu'ar ki, Allah ya yafe mata....." Heedayah ta gyada masa kai hawaye na ci gaba da sauka idonta cikin sanyin murya tace "In sha Allah" Yace "My point in here is that, duk tsanani duk runtsi kada ki bari kawaye su canxa ki, kada ki raunata imanin ki sbda su, you just keep it at the back of ur mind that komai yyi tsanani a rayuwa maganinsa Allah, ynxu da Mum ta hakura ta rike ki sbda maraicin ki duk da bata so, sai ki ga sbda haka sai Allah ya dubeta cikin lkci kalilan iyayenki xa su bayyana may be in just few months time, amma sbda nunawa da tayi xata ja da Allah shi yasa duk abubuwan nan suka faru, ba a kuma ga iyayenki ba sai bayan shekara biyar, snn ta dalilin ki aka yi mata kishiya" Heedayah ta kasa ce masa komai, yace "Abu na biyu kuma in life Heedayah, ki xama me taimako da rikon amana, ki xama me pure heart, I won't go deep into this, kawai xan baki misali daya xuwa biyu.... Taimakon Mami da rikon amana da tayi maki yasa tun a nan duniya ta ga reward dinta, coz d'an ta da aka dauke shekaru masu yawa har ta fidda rai da shi sai gashi har gida, kuma ta dalilin ke da ta rike din ta gano yaron nata, did you get me?? One never knows where his or her reward lies, don haka ki xamo me tausayi da taimako... Lastly ki xama me biyayya ga mijinki, That's all I have to say to you, Allah ya baku xaman lafiya...." Ta goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "There is something you wanted telling me daxu kafin Farida ta shigo, ka gaya min yanxu don Allah" Shiru ta ji yyi, bayan wani lkci yace "It's too late, telling you or not telling you will add nothing" Ta girgixa kai tace "Aa ka gaya min don Allah ya Shureen" Jin yyi shiru tace "Ka ji?" Kallon wayarta tayi da sauri jin alamar shigowan kira taga Khaleel ke kiranta, da sauri tace "Ya Shureen ana kirana, sae da safe" A hankali yace "Alright good night" daga haka ta katse kiran da sauri ta daga kiran Khaleel, sallama tayi masa ya amsa, tace "Ina yini?" Yace "Da wa kike waya?" Sosai gabanta ya fadi tace "Aa Mami na kira" yace "Wacce Mamin?" Rasa abinda xata ce masa tayi, da sauri tace "Auntyna ce" Yace "Ohk I see" Shiru tayi, yace "Har xa ki kwanta kenan?" Tace "Uhn" Yace "Ohk sai da safe" Jikinta yyi sanyi, a hankali tace "Amma kai kace xaka kirani mu yi magana after Isha" Yace "You've exhausted all the strength to talk to me, talking to someone, gobe da safe sai mu yi maganan, sai da safe" Kuka ta sakar masa, ya mike xaune daga kwancen da yake da sauri yace "Hasbunallah.... Look now kiyi hakuri ki daina kukan nan, sai ki gaya min gaskiyan da wanda kike waya idan kina son mu shirya" Cikin rawan murya tace "Ya Shureen ne, kuma wllh nasiha kawai yake min inyi maka biyayya" Shiru yyi kafin ya d'an yi murmushi yace "To Allah ya sa kin dauka" A hankali ta dinga goge idonta, murya can kasa yace "Haka xa a daura auren gobe a kawo min ke kiyi ta kuka ki hanani bacci ko?" Turo baki tayi bata ce komai ba, yyi murmushi yace "Baxan bari kiyi kuka mara dalili ba gobe" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Washegari har karfe tara Heedayah na kwance ta lullube har kanta da duvet, babu yanda Farida bata yi da ita ta tashi tayi wanka su yi breakfast ba amma ta ki, duk 'yan matan dakin sun yi wanka wasun su sun shirya, Mom Islam ce ta shigo dakin tana kallon saman gadon tace "Au har yanxu bata tashin ba?" Farida tace "Eh ta ki tashi" Karasawa bakin gadon Mom Islam tayi ta yaye Duvet din tana kallon Heedayah, da sauri ta rufe fuskarta da pillow, Mom Islam ta xauna gefenta xata dago ta taki yarda, Mom Islam ta hade rai tace "Meye haka kike yi" Heedayah dai bata ce komai ba kuma ta ki bari a ga fuskarta, Mom Islam ta janye pillon ta dago ta tana kallonta, sosai idanuwanta suka tashi sbda kuka, Kallonta Mom Islam ta tsaya yi da mamaki, Heedayah ta sakar mata kuka ta fada jikinta tana shessheka a hankali, murya can kasa mom Islam tace "What's wrong dear?" Kasa cewa komai Heedayah tayi hawaye masu xafi na sauka idonta, Mom Islam ta mike ta dagata, har sannan rigar bacci ne iya gwiwa a jikinta, Mom Islam na kallon Farida tace "Ina Hijab dinta?" Farida ta dauko Hijab din ta mika ma Mom Islam, ta sa mata sannan ta kama hannunta suka fita daga dakin, Farida ta bi su da kallo don har ranta take tausayin Heedayah, tana lura jiya da daddaren ma bata yi wani baccin kirki ba. Mom Islam ta rufe kofarta bayan sun shiga dakinta ta xaunar da Heedayah gefen gado tana kallonta tace "Now tell me what ur problem is Heedayah?" Ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Nima ban sani ba" Mom Islam ta hade rai tace "Baki sani ba kamar yaya?" Heedayah ta bude hannu hawaye na sauka idonta cikin sanyin murya tace "I am just being afraid...." Mom Islam tace "Afraid of what in particular?" Kasa cewa komai Heedayah tayi hawaye na sauka idonta sosai, Mum Islam ta xauna gefen gadon ta jawota jikinta tace "Ki kwantar da hankalin ki daughter, you need not to be afraid of anything" Heedayah ta gyada mata kai amma ta kasa cewa komai ta rufe idonta, Mom Islam ta saketa ta mike ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka ta fito tana kallonta tace "Tashi ki shiga kiyi wanka" Ba musu Heedayah ta mike a hankali ta cire Dogon Hijab din jikinta, snn ta cire rigan baccin ta amshi towel din da stepmum dinta ta kawo mata ta daura sannan ta shiga bandakin. Tana fitowa wanka Mom Islam ta tilasta mata ta sha shayin da ta hado mata, da Irish kadan, snn ta bata hijab ta saka ta kama hannunta xuwa dakin da warce xata yi mata shiri har a gama bikin take, matar kadai ce a babban dakin tare da me make up, sai wedding planner guda daya, babban akwati ne a gefenta me dauke da kayan Heedayah kusan kala sha biyar na fitan biki, Mai make up ma ga boxes din kayan make up dinta a gefe, Mom Islam ta sake hannun Heedayah tace "Ki je a shirya ki" Ita dai Heedayah bata ce komai ba ta tsaya tana kallon matan dakin, Mom Islam ta juya ta fita ta kulle kofar. Sai kusan karfe goma aka gama shirya Heedayah cikin wani dankareren tsadadden lace da ya haska ta sosai, kana ganinta ka ga amarya, lallenta me kyau ya haska hannuwanta da kafafuwanta, very light make up aka yi mata, tayi wani sanyayyen kyau kamshi sai tashi yake a dakin, hotuna kawai ake mata amma fuskarta bbu walwala, fashion stylist din dake kallonta tana murmushi tace "It's been long da naga amaryar da bata murmushi, smile plss angel, you look enamor, one experience this moment just once in lifetime...." Heedayah ta sauke idonta a hankali ta kirkiri murmushin karfin hali gabanta na faduwa, bude kofar dakin aka yi bayan anyi knocking Farida ta shigo rike da waya a hannunta, wara ido tayi tana kallonta ta karaso da sauri ta rungumeta tightly, a hankali tace "You look like a princess Didi, kinyi kyau sosai..." Lkci daya hawaye ya kawo idon Heedayah ta kasa cewa komai, Fashion stylist din dake kallonta tace "Kar ki bata fuskanki 'yan mata, today is ur happy day, an wuce wnn era din kuka ranan biki, chill and be happy plss, sai kace ba auren soyayya ba....." Heedayah tayi iya kokarin ganin hawayen bai sauka idonta ba... Wata frnd din Ammi ce ta shigo dakin don ganin ko an gama shirya Heedayah, ta kama hannunta suka fita xuwa inda Yakumbo da 'yan uwanta suke sai kaka da tayi kane kane cikinsu, ko wacce tayi shiga na kece raini, Yakumbo sai bada labarin yanda Aisha ta haifi Heedayah take kaka na kallonta tana kyabe baki, Dukawa Heedayah tayi har kasa kanta a sunkuye cikin mayafin da aka yafa mata cikin sanyin muryarta ta gaishesu, Yakumbo da kaka ne kadai basu amsa ba sai kallonta suke kai kace ranan suka ta6a ganinta, nan ko Khaleel ne kawai ya fado masu barin Yakumbo da tayi tsuru tsuru, tsofaffin parlon sai sa ma Heedayah albarka suke, Hajiya Fa'iza ta dagota suka bar parlon, Yakumbo tayi tagumi tace "Allah ga mu gare ka" gun manyan bakin gidan Hajiya Fa'iza ta kai Heedayah duk ta gaishesu snn ta mayar da ita bangaren Mom Islam, Kwanciya Heedayah tayi dakin, Mom Islam ta karaso kusa da ita ta mika mata wayar hannunta bayan tayi dialing number tace "Amshi xa ayi maki magana" A hankali Heedayah ta mike xauna tana kallonta, Mom Islam tace "Mamin ki ce, ki amsa" Heedayah ta sauke idonta ta amshi wayar ta kai kunne, muryar Mami ta ji, ta gaisheta cikin sanyin murya, Mami tace "How are you daughter" Cike da karfin hali Heedayah tace "I'm fine Mami, ya gida" Mami tace "Kuka kike Heedayah?" Girgixa mata kai Heedayah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Aa ba kuka nake ba, Mami baxa ki xo ba?" Murmushi Mami tayi tace "In xo ina?" Heedayah tayi shiru ta kasa cewa komai, Mami tace "kar ki damu ki kwantar da hankalin ki in sha Allah xan xo" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Da gaske Mami?" Mami tace "Ehh" Shiru Heedayah tayi, Mami tace "Hope kina cin abinci dai?" Heedayah ta gyada kai tace "Ina ci" Mami tace "Toh maa sha Allah, Allah ya maki albarka my daughter" A hankali Heedayah tace "Ameen" Mami tace "Sai na kira anjima" Da sauri Heedayah tace "Ba kince xa ki xo ba?" Mami tace "Ohh haka, sai na xo" Daga haka Mami tayi mata sallama ta katse wayar tana murmushi, Mom Islam ta karba tana kallon Heedayah tace "Tashi mu je ki gaida su Abbanki, sun shigo yanxu" Heedayah bata ce komai ba, Mom Islam ta dau mayafinta snn ta kama hannunta suka bar dakin, tafiya ce sosai suka yi har xuwa inda su Abba suke, Abbanta ne da Abban Shuraim, Baffan Junaid da Abban Sudais, all with few frnds, Heedayah kanta na lullube ta nufi gun Abban Shuraim da ta hango ta durkusa amma ta kasa cewa komai, lkci daya hawaye ya shiga sauka idonta, murmushi yyi ya kai hannunsa kanta yace "Allah yyi maki albarka daughter" Cikin sanyin murya Heedayah ta gaishesa sannan ta gaishe da su Abbanta, Abban Shuraim na kallonta yace "Tashi ki je, Allah yayi maki albarka" mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, ta tadda Mom Islam wani parlon tana jiranta, mom Islam ta kama hannunta suka koma bangarenta don can ne bbu mutane da yawa, Bedroom ta kai ta xauna gefen gado, Mom Islam tace "Kun yi magana da Khaleel din?" Girgixa kai Heedayah tayi, Mom Islam tace "Ina wayar ta ki?" Kwankwasa kofar dakin aka yi, mom Islam ta karasa ta bude, Farida ce tsaye ta mika ma Mom Islam wayar tace "Ana ta kiranta Aunty" Mom Islam tace "Ohk, kar kiyi nisa Farida you will stay with her here" Farida tace "Toh" daga haka ta koma parlon ta xauna, Mom Islam ta dawo ta mika ma Heedayah wayarta, amsa tayi tana dubawa, taga missed call biyu na Khaleel, sai text message, bata shiga message din ba tayi dialing number Khaleel first, yana fara ringing ya katse ya kirata, ta daga ta kai kunne, murya can kasa tayi masa sallama, shi ma murya can kasan ya amsa yace "Ya kike?" A hankali tace "Alhmdllh and you?" Bai amsa ba yace "Where did you drop the phone?" Tace "Yana wajensu Farida, Ina dakin Aunt dina, she just brought it now" yace "Ohk hope kin ci abinci?" Jin yanda yake maganan a hankali tace "Are you okay?" Yace "Hopefully...." Shiru tayi, kafin tace "What's wrong?" Yace "I'm fine dear, you don't worry... Ban ga kwalliyar ki na safe ba" tace "Ba a turo min hotunan ba tukun" yace "Ohk" tace "Me kake yi yanxu?" A hankali yace "Just lying down" Kallon agogo dake nuna karfe sha daya tayi tace "Lying down har karfe sha daya?" Yace "Yea ynxu xan tashi" tace "Ohk, have u eaten?" Yace "Sure" a hankali tace "Ko dai baka da lafiya ne?" Yace "Ciwon kai nake yi, but I will be fine in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen, will call you later, xan shirya ynxu ana jirana" tace "But ka sha magani?" Yace "Yes, na sha magunguna na" murya can kasa tace "Toh sai anjima, Allah ya sauwake" yace "Alright dear, Ameen ngd" daga haka ya katse wayar, ta tsura ma screen din ido kafin ta shiga inbox dinta na msgs, ta fi minti biyu tana kallon message din da aka yi mata almost an hour ago kafin ta sauke idonta ta ajiye wayar, kwankwasa kofar dakin farida tayi ta shigo, tana kallon Heedayah tace "Ki taso mu je ki canxa kaya in ji Aunty" Ba musu Heedayah ta mike ta dau wayarta suka fita tare da Farida xuwa dakin da aka yi mata kwalliya, wani lace din da ya fi na daxu ta saka aka kara gyara mata fuskarta, aka yi mata hotuna snn suka fito. Karfe sha biyu Heedayah ta sauko parlon baki tare da Farida da Zainab, Junaid ne parlon da Sudais sai frnds dinsu hudu ko wannensu ya sa gezna fari kal, ta karasa a sanyaye ta gaishesu gaba daya, Junaid dai kallonta kawai yake yana murmushi yace "Aunty Amarya kin sha kyau" Sunkuyar da kanta tayi ta kasa kallonsa, Sudais ma dake tsokanarta taki yarda ta kallesa, tana son tambayar Junaid ina Khaleel ganin baya parlon amma ta rasa ta yaya, Farida dake gefenta ta kalla ta matsa dab da ita tace "How about ya Khaleel" Farida ta xaro ido tayi dariya, Heedayah ta riko hannunta da sauri murya can kasa tace "Noo, I am just asking" Farida na murmushi tana kallon Junaid tace "Yaya what of Big bro?" Junaid yace "He is outside, bai shigo ba" Farida tace "Me yasa bai shigo ba" Junaid yace "He prefer staying out" Heedayah dai bata ce komai ba, Sudais na kallon Farida yace "Good afternoon kawar amarya" Xaro ido Farida tayi ta kallesa da sauri tace "Ohh yi hakuri, Ina yini, kun xo lafiya??" yyi murmushi yace "Alhmdllh, ya taro?" Farida na murmushi ita ma tace "Alhmdllh" gaida sauran frnds din nasu Farida tayi sannan ta ja Heedayah suka bar parlon da Zainab, sai da suka hau stairs Heedayah tayi kasa da murya tace "Farida Ina son in ga Ya Khaleel" Farida tace "Ohk, let me ask a ina yake" daga haka ta koma ta tambayi Junaid, Junaid yace "A compound muka bar sa, call him on phone" Farida tace "Ohk" juyawa tayi ta koma sama, a bangaren Mom Islam ta tadda su Heedayah tace "Ya junaid yace yana waje, ko xa ki je ki samesa?" Heedayah tace "Xan iya xuwa?" Farida tace "Toh amma idan aka gan ki fa? I think it's not proper" a hankali Heedayah tace "Baxan bi inda akwai mutane ba" Farida tace "Toh shkkn, amma kar ki dade" mikewa Heedayah tayi ta yafa babban mayafinta ta fita dakin, ta inda bbu wanda xai lura da ita ta bi har ta fito daga gidan tana ta dube duben inda xata ga Khaleel.... Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Karkashin wani bishiya Heedayah ta hangosa xaune kan kujera a wani bangare na compound din, tun xuwanta wajen ya ganta shi ma, ya sakar mata murmushi bayan sun hada ido, sauke idonta tayi ta nufesa walking slowly, mikewa yyi yana kallonta har ta iso inda yake, ya buda mata hannunsa, kasa karasawa tayi da farko, can ta bi wajen da kallo sannan ta karasa kusa da shi gabanta na faduwa ya rungumeta jikinsa, lumshe idonta tayi kamshinsa ya cikata, ya daura bakinsa a kanta murya can kasa yace "You look beautiful wife" Bata iya tace masa komai ba, suna tsaye har bayan minti daya sannan ta dago kanta tana kallonsa tace "How are you feeling now?" A hankali yace "Alhmdllh am fine, where you worried?" Gyada masa kai tayi tace "But ur body is warm" yyi murmushi yace "Not like in the morning, I don't take my drugs the way I am suppose to, but naje asibiti I'm feeling much better now" Cikin sanyin murya tace "Toh Allah ya sauwake" yace "Ameen, amma kin yi lunch ko?" Ta turo baki tace "Kai abinci dai ko da yaushe" Yace "Eh mana, ke baki ganki ba kamar a huraki ki fadi" Murmushi tayi tace "Tohm na ci" a hankali ta xame jikinta daga nasa, yana kallonta daga sama har kasa yace "Kinyi kyau sosai, you look like a princess" Murmushi tayi tace "Kai ma ai kayi kyau" Yace "Noo ban kai ki ba" kallon kyakkyawan fuskarsa tayi, ya kashe mata ido ta sunkuyar da kanta da sauri tana murmushi tace "Ina son in koma ciki ynxu kar a neme ni" yana kallonta yace "Alright dear, in an hour time mu ma xa mu tafi mosque in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Ya kamo hannunta yace "I pray this will be the best for I and you, I pray it's for lifetime...." a hankali ta xame hannunta tace "Ameen" daga haka ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo, a wani d'an corridor da ta bi ta fito ta tadda Farida na tsaye tana ta jiranta, Farida ta sauke ajiyar xuciya tace "Ina ta tsoron kada Aunty ta xo tace kina ina, I don't know if it's proper da kika fita" Heedayah tace "But ai ban dade ba ko?" Farida na kallonta daga sama har kasa tace "Aa baki dade ba, turarensa ya sa maki?" Heedayah tace "Why do you ask?" Farida tace "Kamshin turaren naji kike yi" Heedayah tace "Aa ni bai sa min ba" Farida ta wara ido tace "Ko dai ko dai...." Heedayah ta turo baki ta bi ta gefenta ta bar wajen, Dariya Farida tayi tace "Mu je ki canxa kaya, Aunty tace you should keep changing after an hour" Heedayah bata ce mata komai ba ta ci gaba da tafiya Farida ta bi bayanta. Ana saukowa sallan juma'ah aka daura auren Aliyu Uthman da Fatima Ahmad a kan sadaki naira dubu dari biyu, daurin auren da ya samu halartar dumbin jama'ah daga garurruka daban daban har ma daga kasashen waje, kan kace me government house ya cika makil da bakin d'a suka xo taya murna da farin cikin wannan daurin aure.... Heedayah na xaune saman darduma tun bayan da ta idar da sllh, banda faduwa bbu abinda gabanta yake, ita kadai ce xaune dakin don Farida da su Zainab sun fita, ta kalli agogo dake nuna biyu saura, dai dai nan message ya shigo wayarta da ke ajiye gefen gado ta sa hannu a hankali ta dauko wayar tana dubawa, message din Khaleel ne ya shigo wayar, sosai ta ji gabanta ya fadi bata kai ga bude message din ba aka bude kofa dakin, Farida suka shigo tare da Zainab da su Rabi'ah, da gudu Farida ta tafi ta rungumeta sosai tace "I am wishing you a happy married life Didi, Welcome to our family once again as an in-law...." Kasa ce mata komai Heedayah tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta ta janye jikinta daga na Farida ta fashe da kuka sosai, Wata kawar Yakumbo ce ta shigo dakin ta saki wani guda da karfi tana kallon Heedayah, mikewa Heedayah tayi ta shiga bandaki ta kulle ta durkusa kasa ta rushe da wani kuka kamar warce aka sanar ma mutuwa. Sai da Mom Islam tayi da gaske da ita ta bude bandakin da ta sa ma makulli bayan kusan minti talatin, tausayinta ya sa Mom Islam ta kasa yi mata fadan da tayi niyya, Banda kallonta bbu abinda take, don har idonta ya tashi, Mom Islam ta jawota jikinta cikin kwantar da murya tace "Haba Heedayah, Why are you behaving this way?" Kasa ce mata komai Heedayah tayi hawaye masu xafi na sauka idonta, Mom Islam ta kama hannunta suka fita daga dakin xuwa nata bangaren ta xaunar da ita tana kallonta tace "Ain't you happy?" Cikin sanyin murya Heedayah tace "I am" Mom Islam tace "To ki daina kukan nan, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya da kwanciyar hankali ma har abada, kowa ma haka yaji yanda kike ji yanxu" Gyada mata kai kawai Heedayah tayi tana goge idonta, Mom Islam ta mika mata wayarta tace "Ana ta kiran ki" amsan wayar Heedayah tayi a hankali, Mom Islam ta mike ta fita dakin, Miss calls din Khaleel ta gani, ta fara shiga inbox dinta ganin msg hudu, na Sudais, Junaid, da Shuraim ne all wishing her a happy and peaceful married life, sai na Khaleel da ta bude a karshe tana duba content din nasa, lumshe ido tayi a xuciyarta ta amsa addu'o'insa da Ameen, daga haka ta ajiye wayar ta kwanta kan gadon stepmom dinta. Bayan la'asar Heedayah ta fito main parlorn su cikin wani ubansun gown da ya haskata sosai, da kyar Mom Islam ta lallabata ta fito din bayan an gama shiryata don yin hotuna, wajensu Abbanta aka fara kai ta suka yi hotuna, daga nan sister din Mom Islam ta dawo da ita bangaren Amminta suka yi hoto da Ammi da frnds dinta na nisa da na kusa da suka xo, daga nan matar ta kai ta gunsu kaka ayi hoto, duk Heedayah bata da walwala aka yi hotunan suka fito, Farida ce ta kai ta parlon baki don yin hoto da su Junaid, su kadai ne a parlon da abokansu su ma. Walima aka yi a gidan na kece raini har yamma, kafin Magrib kuma aka fara shirye shiryen tafiya da amarya Kaduna a private jet, Heedayah ta shiga tashin hankalin da ya wuce misali, kai kace tafiya xa ayi da ita gun yankan kai, sai da kukan ma ta kasa yi, Abban Shuraim da Abbanta da step brothers dinsa suka yi mata nasiha sosai, daga nan aka kai ta gun su Yakumbo, Yakumbo na kallonta tace "Ni dai da aka min aure idan ba mantawa nayi ba bbu wanda yyi min wata nasiha, a lkcn ma duniya bata waye ba balle ynxu da duniya ta waye, ke dai kawai kiyi ta kanki a gidan mijin ki...." Mom Islam ta hade rai ta daga Heedayah ta kai ta gun kaka, kaka tace "Tohh, duk da dai mu dai ba haka muka so ba, amma Allah dai ya baku xaman lafiya, sai mun hadu a Kadunan, ba dai gidan Rakiya xa a kai ki ba, ku je kawai sae mun xo" Dagata Mom Islam tayi ta kai ta gun sauran tsofaffin parlon duk suka mata nasiha sosai, snn Mom Islam ta fita da ita daga dakin, Bangaren Ammi ta kai ta, Ammi na kallon Heedayah cikin sanyin murya tace "Allah ya baku xaman lafiya, that's all I will say, idan kin je Kaduna nasan Maminki xata karasa maki sauran...." Nan sauran frnds din Ammi suka mata nasihar su ma snn mom Islam ta fita da ita daga parlon, kawayen Ammi biyu da Kanwar Ammi da kanwar Abbanta sai Farida suka shiga jet din xuwa Kaduna..... Ana kiraye kirayen Magrib motoci kusan shidda suka yi parking kofar gidan Mami. Har aka shigar da Heedayah gidan tana rungume jikin Hajiya Fa'iza, Mami ta sauko daga tana kallonta tana murmushi, Hajiya Fa'iza ta kai bakinta kunnen Heedayah tace "Ki bude fuskar ki tafi ki gaida Ummin ki" a hankali Heedayah ta bude mayafinta ganin Mami ta karasa da sauri ta rungumeta sosai, cikin rawar murya tace "Mami..." Mami tace "To kukan ya isa haka, stop it now" Gyada mata kai kawai Heedayah ke yi wasu sabbin hawayen na bin kuncinta, Mami ta shiga yi ma bakin da suka shisshigo sannu da xuwa da fara'arta, sai da duk suka xaxxauna snn ta bar su da frnds dinta da su Dinar ta wuce sama da Heedayah, bedroom dinta ta kai ta ta kulle kofar ta xaunar da ita gefen gado ta cire mayafin kanta tana kallonta tace "Ba nace ki daina kukan ba" a hankali tace "Na daina Mami" Mami tace "Toh shiga bathroom kiyi alwala ki fito" Ba musu Heedayah ta fara cire jewelries din hannunta ta mike ta nufi bandakin, Mami ta ajiye mata darduma da hijab a kai snn ta fita dakin don xuwa ta sake gaisawa da bakin. Heedayah na xaune saman darduma bayan ta idar da sllh tayi jigum tana tunanin wai yanxu ita matar Khaleel ce, a hankali ta jinginar da kanta da gado, tana ta xaune a haka Mami ta shigo dakin da warmer din abinci da plate da spoon ta ajiye gefenta, cikin sanyin murya tace "Ina yini Mami" Mami ta xauna tace "Lafiya lau daughter, ki debi abinci ki ci" Kallon abincin kawai Heedayah take bata ce komai ba, aka bude dakin frnds din Mami suka shigo gaba daya suna guda, Heedayah ta sunkuyar da kanta, Mami dai ta fita dakin, Dinar na tsaye bakin kofa sai kallon Heedayah take tana murmushi, sai da kawayen Mami suka fita dakin snn ta karaso ta xauna gefen gadon still smiling tace "Sannu Aunty Amarya, ya hanya...." Heedayah ta kasa kallonta a hankali tace "Ina yini Maman Fadil" Dinar tace "Lafiya lau dear, ya hanya" Heedayah tace "Alhmdllh" Dinar ta sauka ta dibar mata abincin da kanta snn ta kawo mata ruwa ta fita dakin, daren ranan a dakin Mami Heedayah ta kwana tare da Mamin, bacci me dadi tayi sosai, with full rest of mind don ta fi kwana uku bata baccin kirki, da asuba sai da Mami ta tasheta sllh, kafin karfe tara na safe kuma wa enda suka kawota duk sun juya xuwa kano duk da Mami bata so hakan ba, gidan ya rage daga few frnds da colleagues din Mami, su Dinar, sai Hajiya Zuwaira da kanwarta da Stepmum din Sudais. Bayan azahar Heedayah ta idar da sllh ta mike kenan tana linke darduman aka bude kofar dakin, daga kai tayi tace "Mami ur phone is...." Makalewa sauran maganan yyi ta sunkuyar da kanta da sauri ganin wanda ya shigo, sanye yake da kananun kaya, ya kulle kofar ya jingina da kofar yana kallonta, juya masa baya tayi gabanta na faduwa, ya taka ya isa dab da ita murya can kasa yace "Heedayah" kasa juyowa tayi, ya xaga a hankali xuwa gabanta ta sauke idonta kasa xuciyarta na bugawa, bude kofar dakin aka yi ya daga kai da sauri, Dinar ce ta shigo ganinsa ta buda ido tace "Lahh ashe ka tashi Yaya, Mami ta tambayeni nace baka tashi ba" Yace "Na tashi" Tace "Toh ka ci abincin kuwa??" Yace "Yea" tace "Maganin fa?" Yace "Na sha" Yana fadin haka ya nufi kofa yace "Ina Fadil?" Tace "Yana can gun Amira wllh naga yana damunka ne shi sa na ki barinsa ya shiga dakin" Khaleel yyi murmushi yace "Ae da kin bar sa" Daga haka ya fita dakin, Dinar na murmushi tana kallon Heedayah tace "Aunty Amarya wai xa ku gaisa da baki downstairs ki sakko" Heedayah bata kalleta ba ta dau mayafinta ta rufe kanta da shi, Dinar ta karaso ta kama hannunta suka fita xuwa downstairs. Har dare Heedayah na dakin Mami don Mami bata barta taje nasu dakin ba, ta gama shirin bacci xata kwanta Mami tace "Heedayah" juyowa tayi tana kallonta, Mami tace "Kije ku gaisa da Khaleel kafin ki kwanta, kiyi masa ya jiki yanxu ki dawo" Tana kallon Mami tace "Is he still sick?" Mami tace "No, He is fine now, but kije ki gaishesa" A hankali Heedayah ta dau Hijab dinta har kasa ta sa snn ta nufi kofa ta fita, dakinsa shi kadai ta tafi ta bude kofar a hankali hade da sallama, yana xaune daga shi sai singlet with 3 quarter yana danna laptop dinsa ya daga kai yana kallonta, sunkuyar da kai tayi taki yarda ta karasa cikin dakin ta gaishesa cikin sanyin murya tace "Ya jikin?" Kallonta kawai yake, ita dai ta ki yarda su hada ido, ya sauke kafafuwansa daga saman gadon ya mike ya nufota, juyawa tayi da sauri xata fita yace "Heedayah" ta kasa bude kofar kamar yanda tayi niyya, ya karasa dab da ita ya juyota yana kallonta, sauke idonta kasa tayi cikin sanyin murya yace "Mami tace kar in dade" Ya kai lips dinsa hancinta murya can kasa yace "I will love you till my last breath" ta kasa ce masa komai ta rufe idonta, jawota jikinsa yyi ya rungumeta yana jin yanda kirjinta ke bugawa, a hankali tace "Mami... she is waiting for me" ya dago kanta yana kallon fuskarta yace "Tsorona kike ji?" Da sauri ta bude idonta tace "Aa, Mami ce ke jirana" murmushi yyi yace "Hope baxata jira ki ba gobe?" Ita dai bata ce masa komai ba ya bude kofar yana mata lallausan murmushi yace "Good night love" juyawa tayi ta fita ya kulle kofar, wani ajiyar xuciya ta sauke ta koma dakin Mami da sauri washegari da yamma aka fara shirye shiryen tafiya da Heedayah gidan Khaleel wanda kanin mahaifinsa ya mallaka masa halak malak, tun ana saura kwana biyar biki aka yi furnishing gidan daga kano, babban duplex ne sosai, both sama da kasa duk an xuba ma Heedayah kaya na gani na fada, hankalin Heedayah bai gama tashi ba sai da taji Mami na yi mata nasiha wai xa a tafi da ita gidanta, duk xaton ta a gidan xata xauna da su Mami kamar ko da yaushe, nan ta rushe da kukan tashin hankali tace "Don Allah Mami a bar ni a gidan nan in dinga ganin ki kar a kai ni wani waje" Mami tayi murmushin karfin hali tace "Muna tare daughter babu me raba mu...." Da kyar aka fitar da Heedayah daga gidan tana kukan rabuwa da Maminta, kawayen Mami biyu, da sisters dinta da su Dinar da mum din Sudais da step mum dinsa da Hajiya Zuwaira suka rakata gidanta with few others, Heedayah ta makale ma Farida a makeken bedroom dinta da aka ajiyeta ciki bayan ta kara tabbatar da tafiya duk xa su yi su bar ta ita kadai, dole aka bar Farida gidan duk aka watse, Heedayah sai bin dakin take da kallo gaba daya a tsorace take, Farida dake gefenta tana ta danne dariyarta tace "Ko mu je kiga gidan naki ne da kyau?" Hararanta Heedayah tayi tana goge idonta, Farida ta fashe da dariya tace "Kilan abinda ma kike ma tsoro ba haka bane" Heedayah tace "Me nake ma tsoro?" Farida tayi dariya tace "Toh na san maki??" Heedayah bata kuma ce mata komai ba jikinta yyi sanyi. sai kusan Magrib Khaleel da Junaid suka shigo compound din gidan, Junaid ba yarda ya shiga ciki ba yana kallon yayansa yace "Sai na shigo gobe, kace da Farida ta fito mu tafi" Khaleel yace "Toh Allah ya kai mu, I tot Farida will spend the night here?" Junaid yace "Aunty tace mu taho da ita" Khaleel ya nufi kofa ya shiga gidan. Knocking kofar bedroom din Heedayah yayi sannan ya bude, Heedayah ta rufe fuskarta da sauri, mikewa Farida tayi tana murmushi tace "Sannu da shigowa big bro, ya junaid din yana waje?" Yace "Yes...." Farida bata ce ma Heedayah komai ba ta nufi kofa ta bi gefen yayan nata a hankali ta fita tana murmushi, da sauri ta sauka downstairs kafin Heedayah ta lura, Khaleel ya jingina da kofar yana kallonta, a hankali ta bude fuskarta jin ta daina jin muryar Farida a dakin, da sauri ta mike tana bin dakin da kallo tace "Yaya ina Farida?" Kallonta kawai yake, ta ji hankalinta ya tashi, kofar ta nufa da sauri xata bi gefensa ta fita ya riko hannunta yace "Farida ta wuce" cikin sanyin murya tace "Shi ne bata gaya min xata wuce ba?" Ya jawota jikinsa yace "Gobe xata dawo" Ita dai bata ce komai ba, yana rike da ita suka koma cikin dakin ya xaunar da ita gefen gadon yana kallonta yace "Ki je kiyi alwala ina xuwa yanxu" Bata ce komai ba ya juya ya fita dakin ta bi sa da ido, bayan few minutes ta mike a hankali ta bude press dinta tana kallon kayan baccin da Farida ta ajiye mata ta dauke kanta, ta dau wani dogon rigan har kasa shi ma na baccin ta ciro hijab dinta snn ta rufe press din, kasancewar tayi wanka a gida kafin a kawota, cire atamfar jikinta tayi ta linke ta ajiye snn ta sa doguwar rigar ta shiga bandaki tayi alwala ta fito, hijab dinta ta sa ta xauna gefen gadon tayi jigum, can ta kwanta ta rufe har kanta da duvet, tana jin Khaleel ya shigo dakin, ya karasa inda take yace "We have to pray Heedayah" kin ce masa komai tayi ya bude duvet din, ta bude idonta a hankali tace "Ni nayi sllh" yace "Ehh na sani, tashi kije kiyi performing ablution" ta mike xaune tace "Da alwalana" yace "To sauko" yana fadin haka ya mike ya shimfida masu darduma, jallabiya ne milk color jikinsa, Heedayah ta sauko da kyar gabanta na faduwa, nan ya ja su sllh, sun dau lkci xaune bayan sun idar yana masu addu'a, daga karshe ya juya yana kallonta ya ga idonta a lumshe, ya kai hannunsa saman kanta, ta bude ido da sauri ya sakar mata lallausan murmushi yace "I pray it's death that will do us apart Heedayah" ta sauke idonta kasa cikin sanyin murya tace "Ameeen, ina jin bacci" yace "Ohk, you have to eat something first" ta girgixa masa kai tace "I'm not hungry" mikewa yyi yace "No you are" daga haka ya fita dakin, ba a dau lkci ba ya dawo da plate din gasasshen kaza da lemon kwali, duk son Heedayah da kaza ji tayi baxata iya cin wnn ba, bbu yanda bai yi da ita ba, ta dai daure ta ci kadan, drink din ma ko rabin cup bata sha ba, ganin xai fitar da su tace "Toh kai baxa ka ci ba?" Yace "Ni naci abinci a gida" bata ce komai ba ya fita dakin, a hankali ta mike ta cire Hijab dinta ta shiga bandaki, wanke bakinta tayi ta fito ta linke hijab dinta ta ajiye sannan ta hau saman gadon ta kwanta ta rufe kanta da duvet tana karanto addu'an bacci, sai bayan kusan minti talatin Khaleel ya dawo dakin, har sannan Heedayah ta kasa bacci, amma tayi still kamar me bacci, ya dauke pray mat dake kasa ya kashe switch din wutan dakin ya karasa saman gadon ya xauna murya can kasa yace "Am I Welcome??" shiru tayi bata ce masa komai ba, ya yaye duvet din yana kallonta duk da akwai duhu dakin bata yrda ta bude idonta ba, murmushi yyi murya can kasa yace "Toh sai da safe, I will sleep downstairs since I am not welcome" Da sauri ta bude idonta, kafin ya mike ta riko hannunsa a hankali tace "Toh ai bance kar ka kwanta ba" yace "Really?" Tace "Uhn" murmushi yyi ya kwanta kusa da ita ya kai hannu saman kanta yace "Yanxu xa mu kunce kitson?" Ta girgixa masa kai tace "Bacci nake ji" yace "Toh yi baccin ki" matsawa take son yi daga kusa da shi ta koma can karshe ya rikota, ta marairaice cikin sanyin murya tace "Ya Khaleel plss am...." Bai jira ta karasa ba ya rungumeta sosai ya shiga snogging dinta passionately, rikon da yyi mata yasa ta kasa kwakkwaran motsi, ta tsorata ainun da lamarinsa a moment din, ko kadan Khaleel bai sarara mata daren ranan ba ganin take takenta, her plea and cry all went in vain, sai da ya ga tayi laushi kukan ma ta kasa snn ya kyaleta, likewise ita ma daren ranan bata bar sa yyi baccin kirki ba, ya lallasheta har ya gaji kamar yana kara tunxurata, sai da tayi bacci wajajen karfe uku snn ya fita dakin amma yaji tausayinta har ransa. Da safe driver ne ya kawo Farida gidan ta kawo masu breakfast da wani envelope babba, bayan ta gaida yayanta dake parlor da murmushi ta mika masa envelope din tace "Mami tace in kawo maka" Ya amsa yace "Ohk" tace "Yaya where is she?" Ya kalli sama sanin Heedayah take tambaya yace "She is sleeping" tace "Toh idan ta tashi ka gaisheta plss" Yace "Alright I will" tace "Sai anjima driver na jirana" Yace "kice ma Mami mun gode" Murmushi tayi tace "In sha Allah, byee..." daga haka ta fita, ya kalli agogo dake nuna karfe takwas, snn ya bude envelope din yana duba abinda ke ciki results din clinical test dinsa da na Heedayah ne da suka yi months back, ya mike ya wuce sama, bedroom dinsa ya kai ya ajiye snn ya fito ya bude kofar dakin Heedayah a hankali ya shiga, xaune ya ganta can karshen gado ta hade kanta da gwiwa, ta dago a hankali tana kallonsa da kumburarrun idonta, lkci daya ta sauke idon kasa, ya karasa cikin dakin yana kallonta yace "Kin tashi?" Kin ce masa komai tayi bata kuma yarda su hada ido ba, wasu hawaye suka taru idonta, xaunawa yyi kusa da ita ya jawota jikinsa murya can kasa yace "I'm sorry wife, I'm really sorry" kasa ce masa komai tayi tana shessheka, ya sauko da ita daga saman gadon ta ki yarda ta tsaya, kyaleta yyi ta koma ta xauna, yace "Are you okay?" Girgixa masa kai tayi, ya juya ya shiga bathroom ya hada mata ruwan wanka ya dawo ya taimaka mata xuwa bandakin. Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... Heedayah na tsaye kitchen wajajen karfe takwas da kayan baccinta da iyakarsa cinya, tana wanke dishes din da suka yi lunch jiya da breakfast din safiyar ynxu, kasancewar Khaleel bai barta tayi wanke wanken da daddare ba yasa dishes din suka yi yawa, satinsu biyu kenan a gidan amma wani xai ce sun shekara don ta saki jiki sosai, tsoronsa ma da take ta daina, Khaleel pattern of love is just amazing and cool ya iya tafiyar da mace yanda ya kamata, soyayyarsa me shiga da tsayawa a rai ce, baxa a ta6a cewa ita ce first love dinsa ba, shigowa kitchen din yyi ya karasa bayanta ya jawota jikinsa yace "Toh ba gashi na kama ki ba" Cike da shagwaba tace "Ni wllh xan gaya ma Mami kana damuna a gidan nan ya Khaleel" ya wara ido yace "Toh 'yar Mami, ya xaki ce mata?" turo baki tayi tace "Ka sakeni plss in gama aikin da nake" ya kwanta jikinta a hankali ya lumshe ido yana kissing wuyarta yace "Xa mu yi bakuwa anjima.... Is she welcome" juyowa tayi tana facing dinsa ta xuba masa manyan idanuwanta tace "Wacece?" Ya ja hancinta yace "A long time frnd" tace "Alright, Allah ya kawota lfya" yyi kasa da murya yace "Me yasa kike min rowa honey bunch???" Ta marairaice tace "Kace xa mu yi bakuwa kuma har ynxu fa ban gama gyaran gidan ba, haka jiya ka ki bari na inyi wanke wanke da daddare, I just left everywhere untidy" yace "Toh bara in taya ki mu yi sauri sai ki sallameni" turo baki tayi tana ci gaba da wanke wankenta, a tare suka gama aikin gidan gaba daya, wajen wanka sai da suka yi yar drama sannan aka yi wankan, tuni Khaleel ya shirya ya xauna dakin yana kallonta tana shafa lotion dinta kamar bata so, mikewa yyi ya amsa duk da tace bata so yace "I just have to help you" kallonsa take kamar xata yi kuka don ta san sauran, shiryawan da ba a gama ba kenan sai wajen sha daya na safe, shi ya fita ya shigo da bakuwar da baxata wuce ashirin da biyu ba, Heedayah ta sakko downstairs cikin atamfarta da ya mugun amsan jikinta, satin ta biyu gidan Khaleel tayi wani kyau ta murmure kamar ba ita ba, kallon kyakkyawan budurwar ta dinga yi har ta karaso cikin parlon ta xauna suka gaisa da murmushi fuskarta snn ta mike ta tafi dauko mata ruwa da lemo a Fridge, hira suke yi da Khaleel sama sama, ita dai Heedayah na xaune parlorn tana danna wayarta tana sauraron conversation din nasu, daga karshe ta mike ta wuce sama... Bayan few minutes Maryam na kallon Khaleel tace "Toh ni xan koma, na gaida amarya sai Allah ya sake hadamu" mikewa Khaleel yyi yace "Haba, so early Maryam?" Tace "Next time xan dawo in sha Allah" yace "Toh xaki kira driver din ne? naga ya wuce" Tace "Eh bari in kirasa" yace "Ohk I am coming" sama ya wuce ya tadda Heedayah kwance, hade rai tayi ganinsa ta juya masa baya, a hankali yace "Ki xo ku yi sallama" mikewa xaune tayi tace "Who is she?" Ya xauna gefen gadon yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Kamar yanda na ta6a kubutar dake shekaru masu yawa, ita ma haka nayi mata, yarinyar wani minister ne da baxan fada maki ba, bata tona mana asiri ba duk sbda ni, since then kuma mu ke xumunci sosai da ita a waya, always preaching and praying for me in dawo hanyar dai dai" Shiru Khaleel yyi yana kallon Heedayah dake kallonsa ko kiftawa bbu, ya sauke idonsa yace "Hijab din da na ta6a baki kika yi sallah wancan lkcn a gidana nata ne, I have many of her like that we are still frnds with till date, both male and females, Allah yayi sai mun sake haduwa dake rayuwata xai dawo sabo" Heedayah bata iya tace komai ba, ya dagota daga kan gadon yace mu je ku yi sallama, ba musu ta bi sa suka koma parlon, knocking kofa aka yi bayan sun shigo parlon a tare, Heedayah ta xauna tana murmushi tace "Na fa daura girki ki jira yyi sister don Allah" Maryam tace "Aa nagode sosai, sae kuma wani lkcn idan Allah ya yrda" Khaleel ya karasa ya bude kofar parlon, ido hudu suka yi da Shuraim dake tsaye bakin kofar with his uniform, Khaleel ya mika masa hannu with surprise din ganinsa, nan suka gaisa sannan Shuraim ya shigo parlon, wara ido Heedayah tayi ganinsa tace "Ya Shureen!!!" ya sakar mata murmushi ya karaso parlon yace "Deedayar kaka" dariya tayi ta rufe fuskarta, ya xauna saman kujera yana kallon Maryam da ta gaishesa ya amsa da murmushi, a hankali Heedayah tace "Ina yini ya Shureen" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, yaushe ka dawo?" Yace "Jiya da daddare" cike da jin dadi tace "Na ji dadi da ka xo ya Shureen, I'm so happy" Khaleel ne ya kawo masa ruwa da drink da kansa ya ajiye sannan ya xauna parlon, hira suka yi na few minutes, Maryam dake ta xaune ta kalli Khaleel tace "I will be on my way Khaleel" yace "Ohh wai da gaske baxa ki jira ki ci abincin ba?" Tayi murmushi tace "Nace next time in sha Allah" Khaleel yace "Toh ki kira driver din naki tukunna...." Shuraim dake kallonta yace "Where to?" Tace "Home" yana kallonta yace "Home din ba shi da location?" Murmushi tayi tace "GRA" yace "Ohk let me drop you" Maryam dai bata ce komai ba, ya mike yana kallon Khaleel yace "Xan koma sai wani lkcn idan Allah ya yrda, I just came to say hi" Khaleel ya mike shi ma yace "We really appreciate bro, Allah ya saka da alkhairi" Heedayah tace "Ya Shureen har yanxu su Rabi'ah basu xo ba" yace "Xa su xo" Rakasu Heedayah da Khaleel suka yi har bakin motar Shuraim dake waje, Khaleel na kallon Maryam yace "I really appreciate the vist Maryam, Allah ya bar xumunci" Shuraim ya kalleta da sauri jin sunan da Khaleel ya kirata, sae dai bai ce komai ba ya bude motarsa ya shiga, Maryam ta daga ma Heedayah hannu ta shiga front seat, sai da suka bar layin sannan Heedayah da Khaleel suka koma ciki, da yammacin ranan Sudais da Farida suka xo gidan, Heedayah tayi tagumi a bedroom dinta tana kallon Farida dake bata labari iri iri, a hankali Heedayah tace "Ni dai duk ba abinda ya dameni ba kenan Farida, all I want to know is... A ina kika samo ya Sudais har ku ka xo gidan nan tare" Xaro ido Farida tayi Heedayah ta kyalkyale da dariya sosai tace "Ke kika bi sa gidansu ko shi ya biyo ki kuka xo tare???" Farida ta jefa mata counter din hannunta tace "Ban sani ba...." Heedayah har da kwanciya sbda dariya. Sai kusan Magrib Sudais da Farida suka bar gidan, Da daddare Heedayah na kwance jikin Khaleel suna kallo a parlor ya kamo hannunta yace "Ranan lahadi xa a kawo gaisuwan Farida idan Allah ya kai mu" Heedayah ta mike xaune da sauri tace "Really?? But she didn't tell me" Ya d'an yi murmushi bai dai ce komai ba, tace "Who is she getting married to??" Ya buda ido yace "Wanda suka xo tare daxu" Heedayah ta wara ido tace "Waow ya Sudais.. I'm very happy wllh" Khaleel ya ja hancinta yace "Da gaske" tace "Ehh mana" mikewa yyi ya dauketa ya kashe TV da switches din parlon suka wuce sama tana masa kukan shagwaba wai bata so. 2 years later.... Kaka ce xaune main parlor din gidan Shuraim tayi kane kane tana bayani ga plate din farfesun da ta gama sha a gefenta, yau watan ta uku kenan a gidan taki tafiya, Maryam ce xaune gefenta tana ta sauraron jawabinta, Kaka tace "Ynda kika xauna haka kusa da ni wllh haka marigayiyar ke yi farkon da aka aurota kafin shaidan ya shiga tsakaninmu, sai dai ita bata samu ciki da wuri ba gaskiya, ke kuma gashi har kin tsufa haihuwa ko yau ko gobe, snn ynda naga kike da yawan ibada haka take ita ma da farko" Maryam dai murmushi kawai take kanta a kasa, kaka tace "Aa gaskiya mun yi rashi mu kam, Allah ma ya sani, shi sa da Allah ya ba Shureen ke, ga ki da sunan mahaifiyarsa gaki da hankali naji dadi sosai, wllh na fi kowa murna, ba gashi yanxu kamar ba shi ba tunda yana ganinki, ynxu fa idan Allah yyi mace xaki haifa ae sai dai a kirata da Maryam" Ita dai Maryam bata ce komai ba, Ganin xancen kaka ba me karewa bane nan kusa tace "Kaka bari in karasa abinda nake kada bakin su karaso sunce suna hanya" Kaka tayi tagumi tace "Ae ni ba xuwan Deedayah gidan nan ba, wnn Mayyar 'yar tata me sunan Rakiya kukan banxan ta tsaya min yake a rai, ke yarinya gaki kamar aljana amma sai fitina, Kaiii ai yarinyar nan fitinanniya ce" Dariya Maryam tayi tace "Kaka tsoronki fa take amma bata da kuka ai, ba suna xuwa ba" Kaka ta hade rai tace "Tsorona a kan me? Me nayi mata? To taje ita da Allah, gashi babu abinda ta bari na basamuden ubanta, sae dai wllh ba dai hankali ba Khaleel har ya fi min gantalallen Sudais din nan dake makale da matarsa, daga shi har matar tasa Farida basa gaida kowa a duniya, su kadae ke rayuwarsu irin na turawa, ki ji fa tunda suka xo min gaisuwar Salima da ta mutu a kasar waje duk da ban hada komai da ita ba ban sake ganin keyarsu ba, d'an nasu ma me sunan Umaru basa kawo shi gun kakanninsa balle ni karan kada miya, shi Junaid dama duk sati xaki gansa da salahar matarsa, har miya take min me kyau wani lkcn wllh, amma tunda na dawo nan shi ma sai ya ga dama, wnn d'an albarkan Khaleel kadai nake gani jifa jifa" Mikewa Maryam tayi da kyar ganin kaka ba gama xancenta xata yi ba tace "Bari in je kitchen kaka" kaka tace "Toh gwara ai kina yi kina motsa jikin, Allah dai ya raba lafiya" Maryam bata kai kofar kitchen din ba, Heedayah ta shigo parlon tare da cute Rahinarta da suke kira da Noor a hannunta, Kaka ta washe baki tace "Kabo kabo, ynxun nan na gama cewa shiru shiru baku karaso ba ko lfya ashe kuna kusa" Maryam dai sai murmushi take tana kallon Heedayah tace "Har na fara cire rai" Dariya Heedayah tayi tace "Wllh mun fara biyawa gida gun Mami ne" Kaka ta kya6e baki tace "Amadun na nan ko ya fita shi kuma daya?" Heedayah tace "Aa Abba ya fita aiki, Mami ce kadai a gida" Kaka tace "Toh ina d'an albarkan mijin naki" Heedayah tace "Yana waje" Kaka tace "Toh ya shigo mana sai kace wani bako, ni bai fiye min Sudais da Junaid ba ma, shi dama Shureen kwanan nan kora da hali yake min ba don matar na masa jan ido ba wllh" Dariya kawai Heedayah ke yi Maryam na tayata, Noor dai ta kankame uwarta sai kallon kaka take da manyan idanuwanta kamar taga dodo, Maryam ta karaso ta amsheta tace "Little Mami taho mu gaisa..." Kaka tace "Kya haifi irinta kuwa, ke baki ganta kamar xabiya ba sai tsayin gashi kamar aljana, ae kyan na uban ne, don uwarta haske ne kawai ya ceceta, daga hanci sai idanuwa" Heedayah dai bata tanka kaka ba tayi murmushi kawai, Kaka tace "Naji kun je kano, me yasa baki bar ma uwarki ta yaye maki ita ba, ga dai shi nan karamin ciki ne a jikin ki wllh" Dariya kawai Maryam ke yi tana kallon Heedayah da ta ki tanka kaka ta fita don ce ma Khaleel ya shigo, shigowar Khaleel parlon yasa Shuraim ya fito, kaka na kallon Khaleel dake xaune gabanta ya tankwashe kafa bayan sun gaisa da Shuraim tace "Tun safe wllh Shureen bai fito gaisheni ba, kilan daga nan ma ni gidanka xan koma naga kafi sanin mutuncin babba" murmushi kawai Khaleel ke yi yace "Ki hada kayan naki mu tafi" mikewa kaka tayi ta wuce dakinta ta fara hada kayanta kamar jira take, Shuraim ya kalli Heedayah yace "Toh mu mun huta yanxu kuma, sai ke da mijin ki ku shirya" Turo baki Heedayah tayi tana kallon Khaleel tace "Allah bar maku gidan xan yi kai da ita ni dai...." Maryam ta xauna ta dinga dariya, shi dai Khaleel banda murmushi bbu abinda yake yana shafa kansa, sai ga kaka ta fito da katon jakarta da handbag tace "Ku mu tafi, gidan Amadun ma ba dadin Rahinah nake ji ba" Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... _Ina bukatar addu'ar lovely fans a kan Allah ya ba ni, da duk wani me karatu sa'a, ya sa mu gama lafiya, and reap the fruit of our labor in sha Allah, special greetings to all fudite (Fed uni dutse), Khaleesat Haiydar ta gaishe ku kyauta😍_ *To those that i disappointed after I made mention of no disappoinment from the beginning of the book su gafarceni domin girman Allah ba don ni ba, I just found out that everyone is entitled to his or her point of view, snn wasu opinion dinsu kadae suka sani be it on the right track or not, duk yanda nayi I can't please everyone, it's just not possible, kuyi min adalci don ku ma kunsan haka, but ni a tunanina yanda nayi din shine dai dai don ba komai mutum ke nema ya samu ba a rayuwa, and masu tunanin xurfin ciki da miskilanci nature ne su yi eradicating wnn tunanin* _Alhamdulillah a nan na sauke littafina me taken *Heedayah* kurakuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min, darussukan ciki kuma Allah ya sa mu amfana da su, ya sa mu cika da imani, a shekaranjiya na fito da main lessons din littafin Allah kuma yasa ya xama ishara garemu baki daya_ *Na Saudakar da littafin nan xuwa ga lovely sister na Fatima M Bello, Allah ya albarkaci rayuwar ki Lil sis* _My special greetings goes to my lovely Mum Hajiya Hajarah, Allah ya bar mana ke ya daukaka ki ya kare ki Hajiya Yaya, my small momies... I greet you all with respect, and I appreciate ur encouragements from the beginning of *Heedayah* till the very end Jiddoh na godiya, my lovely siblings Ahmad, Maryam, Yahya, fatima, Baby, Haiydar, Ilham, Sudais, Fadil, papi Allah yayi maku albarka baki daya, Lovely cousins, Jamila, Ilham, Mujaheed, Khaleesat, Baby, Haneef... Allah ya raya min ku gaba daya ina sonku sosai sosai_ And My fans😍ku ne farko ku ne karshe, without you... They won't be Khaleesat Haiydar, I appreciate every atom of ur support toward me, Allah ubangiji ya cika maku burikanku na alkhairi ya raba ku da iyayenku lafiya, ya kara maku budi da daukaka, I really appreciate ur patronage and patient. Duk wanda na 6ata ma daga farkon littafin nan xuwa karshe ko na fada ma maganan dai bai ji dadi ba ya gafarceni, nima na yafe. *And those that read Heedayah for free should keep it in mind that I owe them just 300 naira* 👍🏻 Thank you thank you thank you 💖.... Taku har ko da yaushe Hauwa Bello Jiddah (Kha,leesat Haiydar) *You can kindly exit the groups if you wish*