#LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode MATAR HABIBI 1 (Free page) Daya tashi zaune, saurarawa yayi, wai ko kunnuwanshi ne suke son yaudararshi, da gaske sallame sallah ne yakeji "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..." Ya furta yana janyo wayarshi, ya duba lokaci, karfe biyar da minti goma sha biyu, cikinshi yayi karar daya tabbata ta yunwa ce tunda daren jiya ba wani abincin kirki yaci ba, sai kuma cikin nashi ya sakeyin wani sauti, wannan karin na tashin hankali ne, ya kuwa diro daga kan gado cikin hanzari yana bude kofar dakin shi ya nufi hanyar da zata sadashi da dakin Jamila, ko tunanin ya zurfafa ba zai iya tuno ranar da Jamila ta makara ba, in ba don ita ba ai da ya tabbata makota sun sakashi a jerin mazan da ba'a gani a masallaci sallar asuba "Jamilaa..." Ya kira bayan ya tura kofar dakin nata, a kwance ya ganta kan darduma, jikinta sanye da hijabi ruwan toka, ta dunkule jikinta waje daya, alamar da tayi sallah bacci ya dauketa a wajen, karasawa yayi yana dan bubbugata hadi da sake kiran sunanta "Jamilaa" Motsawa tayi da sunan Allaah a bakinta, tayi hamma tana kokarin mikewa "Lafiyarki kuwa yau?" Karasa mikewa zaune tayi "Sallah nayi fa, ina lazumi ashe bacci ya kwasheni ban sani ba" Dan karamin tsaki Baffa yaja jin tana lafiya "To kuwa yau babu kanta, dan wallahi mun makara" Dauke da tashin hankalin da Jamila ta aro ta shimfida kan fuskarta tace "Subhanallahi, makara kuma?" Tana mika hannu ta dauko wayarta da take kan gado "Wallahi kuwa..." Bayan ta duba ta kalle shi tana fadin "Kayya, baccin daya daukeni ne, kasan kuma ba alarm nake sakawa ba tunda na rigada na saba tashi" Kai Baffa ya dan dafe ya sauke hannun shi "Allaah Ya kyauta, amman akwai damuwa, saboda ba wani abin kirki naci ba jiya, ga aikin da yake gabana a shago yau, ni anya ma na tabayin dorere a rayuwata?" Sai taji zuciyarta tayi mata wani iri, tausayin shi yana neman danneta, sai kwakwalwarta ta dawo mata da maganar shi "Nifa ba karamin taimako na kikeyi ba tunda kike tashina, badan ke ba ai in ta matar nan ne sai dai inyi dorere..." Gabaki daya dan tausayin sai taji ya murmushe "Ai shikenan haka Allaah Ya nufa, sai ka samu kaje kayi sallah, lokaci na tafiya, bari in shiga bayi..." Ta karasa maganar tana mikewa, tana jin yanda yake binta da kallo, sai bayan ta shiga bayin kuma tukunna taji karar budewa da rufewar kofar dakin nata, alamar ya fita. Ta danyi mintina biyu kafin ta fito, saita cire hijabinta ta koma kusa da Nana da take ta bacci, har yanzun kirjinta yayi mata nauyi. Tun da ta auri Baffa, bai taba gajiyawa wajen nuna sha'awarshi ta auren mace fiye da guda daya ba, shisa ma ta sakawa ranta salama, duk kuwa da yanda take da zafin kishi. Wani lokacin bayan tayi masa addu'ar karin yalwar arziki sai taji kamar ta koma tace Allaah karya bashi da yawa, iya wanda zai ishesu hidimarsu batare da sun takura ba, amman banda na karin aure. Wata rana sai taba kanta dariya, lokacin daya fara gini, haka ya daukota akan mashin dinshi yazo ya nuna mata, ta dinga kallon yanayin tsarin gidan cike da sha'awa, musamman da yake fada mata za'a dora bene, saboda yanason yayi part biyu "Aikuwa saman nake so" Ba zata manta ba yayi dariya yace mata "Idan kuma amarya zansa fa?" Taji dirar maganar har tsakiyar kanta, amman saita dake ta amsa shi da "Sai ta zauna a kasan, ni kuma ina sama, ai dai naci arzikin kasancewa uwargida da akasha gwagwarmaya da ita a bani zabin inda nake so ko?" Dariyar dai Baffa ya karayi batare da yace mata komai ba. Kuma lokacin daya kammala ginin kasan, aka fitar da kafar benen akayi dakin da komai, sai suka tashi suka dawo, watanni takwas kenan, yace mata a nutse yake so saman ma suna ciki ana ginawa, da duk karsashin dawowarsu sabon gida, harma da kujerun da ya sake mata duk ya rage saboda tana tunanin kowanne lokaci zai iya rakito aure, amman da taga ko bulo ba'a shigo dashi ba saita fara sakin jiki. Amman gab da azumi ta fara kula da canzawarshi, shi mutum ne da inya shigo gida to yakan ajiye wayarshi ne ya zauna ya biyewa yara suyita shiririta. Kuma itama din akan zauna da ita a taba hirar, amman lokaci daya inya dawo, to yana manne da waya yana dannawa, sai kayi masa magana nawa baiji ba, hankalinshi yana kan wayar, da bata damu ba, saida ya fara tashi yana barin dakin in tana nan aka kirashi, tasan yanayin aikin shi, yana mu'amala da mutane kala-kala, kuma ciki harda mata, sau nawa suke kiranshi a waya, wata rana ma ba amsawa kawai yakeyi a gabanta ba, a lasifika yake sakawa yayi maganarshi a nutse. Saita kara ganin wayar bawai da daddare bane kawai, har da asuba. Baffa da ana idar da sallah zai shigo gida danya koma bacci, amman sai gari ya fara haske ma wani zubin kafin ya shigo, ko inya shigo din ya wuce dakin shi ya turo harya murza mukulli. Shi yasa Jamila sanin cewa wata tayi mata kutse cikin rayuwar miji, da ta ganshi rike da wayar sai taji zuciyarta nayi mata zafi, babu abinda yake dawo mata sai lokacin da yake neman aurenta, kalamanshi, yanda yake riritata kamar kwai, saita hasaso irin wannan riritar wata take samu, wani abu daya jima da mutuwa a tsakaninta dashi, amman taji dadi saboda a lokacin azumi na karatowa, tasawa ranta zata tsaya ta kara kyautata duk ibadunta a cikin watan, sai tayi addu'a sosai. Kuma hakan ne ya faru, har a sujjadarta rokon Allaah takeyi daya saka mata salama idan har Baffa nada rabon zama da wata matar bayan ita. Sai gashi ta fara samun sauki "Allaah Kasa kar mijina ya juyamun baya, Allaah Kasa kar in taba wulakanta a idanuwanshi, Allaah Kasa kar mutuncina ya zube a idanuwanshi, Allaah Kasa kar matar da zai auro ta cutar dani koni in cutar da ita, Allaah Ka rabani da kishin da zai zame mun fitina koya hanani zaman lafiya" Haka take jerowa tana sake maimaitawa duk sallah, duk wani motsi ma da zatayi, tasan Baffa, ko tace ta dauka ta gama sanin shi, shekaru bakwai ko tace takwas in za'a hada da lokacin da yake nemanta, ko kadan bata taba hasaso zai kasance cikin irin mazan nan masu kushe matansu a wajen 'yan matan da suke nema ba, tana can gurfane kullum tana addu'ar karta wulakanta a idanuwanshi, batayi tunanin hadawa da addu'ar kar ta wulakanta ta sanadinshi ba sam, tunda akwai wani wulakanci daya wuce ace mijin daya kamata ya kare maka mutuncinka shine yake zubar maka dashi? Abin yayi mata zafi matuka, kuma inda ma ya tsaya iya abinda tayi din da zaifi mata, sai gashi kirikiri ya yanko karya a cikin wata mai girma irin Ramadan "Hmm..." Ta furta a fili ko yanzun dinma, farkon aurensu ta dauka shine zai dinga tashinsu sallah, da yake ta saba gidansu har kananun yara ma sai an tashe su da asuba, mazan haka Baba zai tattarasu su wuce masallaci, to da lokaci yayi take bude ido, ko da bata sallah kuwa saita farka, tun tanayin luf da ita tana jiranshi harta gane in dai ta biyewa Baffa to zata daina yin sallar asuba a cikin lokacinta, saita tashe shi shima. Amman wai yau dadin soyayya yasa shi rufe ido yana zabgawa budurwa karyar cewa wai indan itace da sai dai ya dingayin dorere, budurwar da sai bayan ta tashe shi, yana zaune ma yana sahur zataji vibration din wayar alamar ta kirashi, ko taji ringing din wayar idan ya manta bai sata a silent ba. Shisa ta daukarwa kanta alkawari har azumin ya kare ta daina tashin shi, zata barshi da budurwar tashi, duk da ba karamin danne zuciyarta tayi ba kafin ta iya kin tayar dashi din, tunda ita ba sahur takeyi ba, sai dai tasha ruwa, da daddare take cika cikinta. Shikuma Baffa in an kira sallah ya sha ruwa ya tafi masallaci, koya dawo sai dai ya dan sha kayan ruwa, baya iya sakin jiki yaci abinci sai ya dawo daga tarawih. To jiyama daya dawo ta hada masa komai, sai waya ta dauke masa hankali, lokaci zuwa lokaci zaiyi murmushi mai sauti, tun tana danne zuciyarta har tace masa "Abincinka yana hucewa fa, daka hakura ka gama ci saika danna wayar" Cikin halin ko in kula yace mata "Kwashe kawai, ba yunwa nakeji ba yau, naci anjima idan Allaah Ya kaimu" Haka ta kwashe komai tanajin kamar ta fisge wayar ta kwala da kasa, balle da aka fara jera masa kira ya kalleta yana fadin "Akwai gajiya sosai a tare dani, ga kaina na dan yimun ciwo, inaso in samu bacci sosai yau" Tasan a fakaice so yakeyi yace mata ba sai taje dakinshi ba, tunda yanaso ya sake yayi wayar shi da budurwa, da wannan takaicin ta kwanta, shine ma abinda ya kara mata karfin gwiwar komawa daki abinta bayan tayi brush tasha ruwa. Haka tayi nafilarta, tayi addu'o'inta, ta zauna zuciyarta nata bugawa, tana kuma kasa kunne ko zata juyo motsin Baffa, amman shiru, har aka kira sallah, saida tayi, tana zaune tana azkar din safe ta juyo takun tafiyarshi, tayi maza ta kwanta ta jirashi, tana kuma aiwatar da diramar data shirya zatayi. Tun tana tunane-tunane har bacci ya kwasheta, rigimar Nana ce ta tasheta wajen karfe takwas da rabi, saita mike gabaki daya, tayi mata wanka, ta shiryata, tukunna ta hada mata shayi ta zuba mata a kofinta ta bata, ta kama hannunta zuwa dakinsu Asaad, ta lekasu, bacci sukeyi daga shi har Arif din. Idan akwai abinda take kara godewa Allaah akai shine yanda in dai babu makaranta sukeyin baccin safe, tana yawanjin iyayen yara na korafin yanda suke tashi da sanyin safiya idan babu makaranta, amman ita dai Allaah Ya duba mata. Ta gyara musu labulen dakin, taja hannun Nana suka nufi kitchen, saida ta zaunar da ita akan kujera irin ta katakon nan a cikin kitchen din tukunna ta hada wanke-wanke. Ta gama tana goge wajen Baffa ya fito, ya shirya cikin kananun kaya, fuskarshi fayau, yayi kyau kamar ko da yaushe, zuwa yanzun kuma ta tabbata bawai a idanuwanta bane kawai Baffan yake da kyau, tunda gashi nan ya haska a idanuwan wata ma "Sannu da aiki" Yace mata, ta amsa shi da "Yawwa Babansu..." Kamar yanda ta lakaba masa, shikuma ya kirata da "Mamin yara" In yanajin nishadi, gaisuwar safen da basuyi ba dazun ita tayi masa ya amsa a sanyaye yana dorawa da "Zan fita, saboda nasan aiki nacan ya cushe mana" A jikin doguwar rigarta dinkin bubu ta kara goge hannuwanta da suke da danshi tana fitowa daga kitchen din "Allaah Ya tsare Ya bada sa'a" Ta fadi tana rakashi har wajen mashin dinshi, ita ta bude masa gate tunda ba maigadi ne dasu ba, saida ya fita ta mayar da gate din ta rufe, ta koma ciki. * Karfe shida da kwata tagama komai tunda ba wani abu mai wahala tayi ba, doya fa kwai ta soya, tayi zobo, tana da sauran dafaffen nama, tayi miyar ganye, dan wannan tun safe ma tayi ta, saita tuka tuwon shinkafa dai-dai cikinsu, kuma ita da wuri take fara aikinta koma meye zata dafa kuwa, bataso ana shan ruwa tana kitchen sai dai bacin rana, sai su Asaad da Nana da suke binta, Asaad nata yi mata surutunshi kan abinda batajin ta fahimta gabaki daya, wani tsohon labarine akan yanda littafinshi ya bace a Islamiyya Tana kwasar komai zuwa falo, Arif yana nan zaune akan kafet yana kallon MBC3, Baffa kuma yana kan doguwar kujera a kwance kamar gawa, ko mintina goma baiyi da shigowa ba, sannu da zuwan da tayi masa ma da kai ya amsa, daga shi har mashin din kamar zasu tuntsire, idanuwan nan sun shige ciki, yayi zuru-zuru, ko dasu Nana suka dinga masa oyoyo ma dan rikesu yayi kadan batare da yace komai ba "Kuzo nan Babanku yau ya gaji, karku dame shi" Sai suka kyale shi din kuwa "Ka tashi an kusa kiran sallah" Tace tana kokarin danne dariyar da take neman kwace mata "Barni a kwancen nan, ki dai cikamun jug da koma menene kikayi mana na sha dan Allaah, ki matsomun dashi kusa, ki kuma zubamun abinci, yau inaga a gida zanyi Magriba" Saida dariya ta kwace mata, tun asali daman Baffa bashi da jumurin yunwa, dan azumi daga Ramadan, sitta shawwal sai kuma na arfa yakeyi, bayansu baya karayin wani azumi "Karka bada maza mana" Cewar Jamila tana karayin dariya "Ke ba zaki gane ba..." Dakinta ta shige bayan tasa su Asaad da Nana sun zauna kusa da Arif, ta dauro alwala tukunna ta fito, bata biyewa Baffa ba, ta samu kofi madaidaici, ta zuba masa zobo, sannan ta hada masa doyar ma a plate. Ya kuwa tashi zaune yana karbar kofin "Wai har yanzun ba'a kira ba?" Kafin ta amsa sukaji kiran sallar kuwa, nan da nan ya kwankwade zobon hannun shi, jikinshi har rawa yake lokacin daya sauke kofin ya dirarwa doyar "Baba kaci a hankali, babu kyau cin abinci da sauri ko Mami?" Asaad ya fadi "Bari ka fara azumi tukunna Asaad" Dariyar dai suka sake bawa Jamila, ta tashi ta tafi dan ta gabatar da sallar magriba yanda zatayi buda bakin cikin natsuwa. Sanda ta dawo a kwance ta samu Baffa "Kwanciya ka sakeyi?" A hankali yace mata "Cikina ke juyamun" Wani abu na rashin jin dadi ya tsarga mata, cike da tausayawa take ta jera masa sannu, doyar ma data dorawa buri saita kasa ci da yawa, ta dai zubawa yaran, zobo daman kowa na da robar shi da take zuba musu saboda a kofi za'a iya zubarwa a sakata aiki. Itafa ba haka taso ba, kawai dai taso ya dan sha wahala ne kadan, azumin ya gasa shi, bawai yayi ciwo ba. Sai gashi sallar Magriba a gida yayita, ya samu ya lallaba Isha'i saboda Tarawih. Daya dawo yasa ta zuba masa tuwo, saita tashi dansu Asaad da wuri suke kwanciya, kuma saita tsaya tana biya musu addu'ar bacci suna maimaitawa duk da sun haddace, ta karayi musu wata tukunna, ta goya Nana, dan itace take hirar dare wani lokacin Sanda ta koma falon Baffa ta samu rike da wayarshi, da alama ranshi a bace yake, tana zama yana mikewa ya nufi dakinshi, tana juyo yanda ya turo kofar garam kamar itace ta bata masa rai "Allaah Ya kyauta..." Jamila ta fadi, ta sauko Nana, ta janyo kulolin gabanta, a cikin kwanon da yaci tuwon ta zuba itama, tana ci tana bawa Nana itama, suka gama ta sake goya Nana dan tanaso ta kimtsa wajen kafin su kwanta. Kuma hasashenta ya zama gaskiya, ran Baffa a bace yake. Gabaki daya yau tunda ya fita shago komai ya rincabe masa, ya samu yaran shagon nashi sunata aiki, danma sun rufe karbar dinkin sallah tun saura sati biyu azumi, kuma shi yayiwa kanshi alkawari tuntuni, duk runtsi ba zai dinga kwana a shago yana dinki ba. Suna cikin aikin aka dauke wuta, tun jiya Gen dinsu yaketa wata qara, yau ma sai yaki tashi, daya kira Sani dan yazo ya duba musu sai yace masa sunje wata gaisuwa baya ma cikin garin Kano, sai yammaci, zaizo ya duba bayan shan ruwa, dan haka dole yayi abinda bayaso, aiki da keken dinki wanda bana wuta ba. Zuwa la'asar duk ya zazzage dan abinda yayi saura a cikinshi, ga ciwon cinyoyi da yakeji duk sun rike, kwata-kwata baima samu natsuwar danna waya ba, yama manta a silent ya sakata har sai bayan ya dawo daha Tarawih din nan, sai abin ya fado masa, ya riga yasan dole zai sha mita wajen Aziza. Yana duba wayar kuwa ya samu ta kirashi babu adadi, ga sakonni ta text da WhatsApp ta bar masa har yana rasa ta inda zai fara karantasu, sai kawai ya fara da tura mata da gajeran sako "Ayimun hakuri Babe, yau abubuwane suka rincabemun a shago, wayar kuma tana silent. Nayi missing dinki da yawa" Saida ya tura ya fara bin nata sakonnin, sai kuma zuciyarshi ta buga daya tuna yau yayi mata alkawarin zuwa yayi buda baki a wajenta, tun kwanaki biyar da suka wuce sukayi wannan tsarin, ya tabbata ta shirya masa shagali, lokaci daya yaji ranshi ya baci, musamman ma da ta dawo masa da sakon daya tura da "Ka kusa? Inata jiranka tun dazun. Gashi har tara saura" Yana shirin kiranta ne Jamila ta shigo, shisa ya tashi ya shiga dakinshi yana addu'ar Allaah Yasa karta biyo bayanshi, yasan halinta da naci wani zubin "Dan Allaah kiyi mun hakuri Aziza, dan Allaah..." Yake fadi cikin magiya da kwantar da kai saboda yanda Aziza ta birkice masa, kamar ma kuka takeyi "Ni ba sai kaci anan ba, kazo ka dauka kawai dan bansan yanda zanyi da abubuwan nan dana shirya maka ba" Muryarshi ya karayin kasa da ita "Na fada miki da zazzabi na dawo, yanzun haka ina cikin bargo a kwance, dan Allaah kiyi hakuri, ki sakamun komai a firij, na miki alkawari gobe In Shaa Allaah zanzo da wuri ma" Wani shiru ya ratsa a tsakaninsu kafin tace "Hmmm..." Gabaki daya a gajiye yake jinshi, bayajin ma yana da cikakke karfin fita da mashin din daya riga ya shigo dashi, balle harya falla unguwarsu Aziza "Ke kinsan babu yanda za'ayi haka kawai da gangan inyi missing din abubuwan da nasan kin shiryamun, kinsan yaushe rabon da inji wani abu mai dadi a bakina?" Cike da shagwabarta da take kara narkar dashi tace masa "Habibi saboda zuwanka fa nace yau 'yan gidama suci albarkacinka nayi tortilla da sauce din kwai" Duk da in za'a tsire shi baisan meye tortilla din ba, amman yanda ta fade shi tanayi kamar zata taune harshenta yasa Baffa hasaso wani abu da yaji naman kaza a cikin kanshi, ga kuma kwai data kira "Duk ki ajiyemun dan Allaah..." Bai sauke wayar ba saida ya tabbata Aziza ta hakura, musamman daya fara dauko mata hirar daya kula tafi faranta mata rai akan komai, hirar yanda in ta shigo gidanshi zata wanke masa takaicin rashin iya girkin Jamila, za kuma ta zame masa fitilar daya jima yana nema, a takaice dai, Baffa yace mata "Kina saka inaji kamar sai yanzun zanyi aure Aziza, kamar banma san iya abubuwan da na rasa ba sai yanzun da kika shigo rayuwata..." * Maza nawa ne irin Baffa? Mata nawa ne irin Jamila? 'Yan mata nawa ne irin Aziza? Kun shiryawa wannan tafiyar kuwa? #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. 9035723778 Opay Lubabatu Sufyan Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani * Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode MATAR HABIBI 2 (Free page) Yau kam fuskarshi ta nuna rashin jin dadinshi sosai "Nifa naji wani Malami na wa'azi in dai har sallar dare zatasa ka makara gara ka hakura da ita" A nutse take kallonshi "Babansu ai ana maganar sallar asuba ne, yau kuma bamu makara ba yanzun ma ake shirin tayarwa" A hasale ya amsa ta da "Amman ai mun makara sahur ko? Kinsan irin wahalar da na sha jiya kuwa Jamila? Gaskiya kisa alarm a wayarki yau" Kai ta jinjina masa "Kaje karka makara sallah" Kamar ba zai tafi ba sai kuma ya wuce, ta tabe baki, jiya bayan ta kwantar da Nana tayi mata addu'a sosai, da batayi niyyar zuwa dakinshi bama, sai kuma ta sake kayan jikinta zuwa doguwar rigar bacci da ta wuce har kwaurinta, ta kara goga humra, ta nemi hula ta saka a kanta sannan ta tafi, a kwance ta sameshi yana danna waya, da yake wutar dakin a kunne take saita kashe, tabi hasken wayarshi har zuwa kan gadon, kafin ma ta gyara kwanciyarta yace "Nifa a gajiye nake ba wani abu zan iya yi miki ba" Maganar tayi mata bambarakwai, a lokaci daya kuma wani abu yazo yayi mata tsaye a makoshi, tasan shi din ba wani mabukaci bane ta wannan fannin, saboda kaso tamanin cikin dari na lokutta itace take binshi, kuma tasan tana iya kokarinta wajen yin gyara, shi ba ma'abocin bada kudi bane ba, sai ayi watanni kyautar kudi bata gifta a tsakaninsu ba, ko roka tayi kuwa bako da yaushe yake bata ba, saima kaji yana mitar "Kin cika kashe kudi Jamila, meye zaki siya da baki dashi a gida?" Amman kyautar da 'yan uwanta suke mata lokaci zuwa lokaci tunda sun san ba sana'a takeyi ba, a ciki take dauka tana siyan magungunan mata, maganin sanyi kam wannan baya yanke mata sam ko dan yanda ake kara jaddada amfanin yawan shanshi ga mace ko da bata da aure balle kuma mai aure. Da kanta a WhatsApp ta fice daga cikin groups da dama na matan aure saboda yanda in an samu wata mai maganin matan, suka siya aka gwada za'azo ayita sharhi, kaji wasu suna bada labarin yanda miji ya manne musu, wata ma zatace "Nifa da niyyar kwana biyu yazo, amman kinganshi nan yana maganar ya kamata ace wannan komawar dani ya koma" To ita kuwa duk wani doki da rawar kai a wannan harkar Baffa yayi mata itane a cikin watanni ukunsu na farkon aure kafin ta fara laulayin cikin Arif da yazo mata da zafi, daga baya kuma sai taga kamar abin koya fita daga ranshine, yanayin wannan hirar da take gani tsakanin mata, ita kuma inta siya tayi amfani dashi sai taga dai babu wani canji ta bangaren Baffa, saima ita da wasu magungunan zata ga kyansu, wasu kuma inta sha idan sun cika bauri ta wuni cikinta na murdawa. Sai kuma takeji kamar ta daina burgeshi yanzun, wannan soyayyar duk ta disashe. Amman duk da haka kai tsaye bai taba bude baki ya fada mata magana mai zafin ta yau ba. Idan ma gajiyar yayi to zai kyaleta ne ta shige jikinshi sosai ta kwanta. Yanda gwiwoyinta sukayi mata sanyi yasa ta kasa tashi tabar masa dakin, zuciyarta ta dinga mata zafi, musmaman ma data ga ya juya kwanciyar shi yana matsawa ya bada tazara a tsakaninsu. Ta rufe idanuwanta da sukeyi mata yaji-yaji, bata kasance cikin mata masu saurin kuka ba, asalima abinda zai saka hawayenta zuba ba karami bane ba, ta dinga jero duk wata addu'a da tazo bakinta ko zata samu saukin zafin da kirjinta yakeyi, ashe bacci ne ya dauketa a haka, bata sani ba sai data fitsari ya tasheta tunda ta daddaki zobon da tayi babu laifi. Bataga alamar Baffa a kusa da ita ba, saita dauka ya shiga bayi, shisa ta nufi kofa ta bude da nufin tafiya dakinta, kuma har zata wuce saita dinga juyo karar kiran wayarshi daga falo. Da mamaki ta nufi falon, yana kwance kan doguwar kujera yana bacci, ga wayar nan a kasa da alama subuce masa tayi bai sani ba, daman Baffa da bacci, sau nawa ko kiranshi akayi ita kiran saiya tasheta shi yana baccinshi. Ta karasa ta dauki wayar, sai dai tana dauka kiran na yankewa, zata ajiye masa a gefenshi sako ya shigo, kuma da yake ko a mukulli take zaka iya karanta sakon ta saman inka dan taba, haka kawai taji tanaso ta karanta, anyi saving din lambar da "AZ" kawai. "Habibi bacci kayi ko? To bari in tashi inyi sallah in rokar mana Allaah Yasa next azumi kana gefena zakayi baccin nan" Wani duhu-duhu ya nemi rufe mata ido, musamman da wani sakon ya kara shigowa "Ina sonka sosai. Allaah Ya kulamun da kai Habibi Na, sai anjima In Shaa Allaah dan yau gara na kwana a zaune da in bari kayi dorere" Daman haka kishin yake? Duk wanda take zato tanaji a baya karya ne, yanzun ne tasan yanda yake. To taya mata suke iya danne shi? Ya suke kallon mijinsu ya ketare ya tafi dakin wata matar batare da zuciyarsu ta kama da wuta ta kone ba? Ita gata, sako kawai tagani amman zuciyarta kamar tana gab da zama toka saboda yanda takejin tana ci da wuta. Sai gashi tanajin alamar hawaye suna neman zubo mata, ta ajiye masa wayarshi inda ta ganta a kasa, ta wuce dakinta da kudiri daya. In Shaa Allaah har a karasa azumi nan da kwanaki bakwai ko takwas ta gama tashin shi Sahur, ita AZ din saita tashe shi kafin azumi na gaba din da zasuyi tare saita dora daga inda ta tsaya a wannan din. Yau ko dar bataji bama, dan daya shigo dakinta bankan-bankan lokacin ma da hijabinta a hannu "Ke Jamila wai wanne irin abune ya sameki yau ma?" Ya fadi bayan ya turo kofar "Kasan goman karshen nan, sallah jima inayi, sai na dan kishingida sai yanzun na tashi naji anata kiraye-kirayen sallah, to alwala nayi ma yanzun nake shirin zuwa in tasheka" Taji ranta yayi mata sanyi-sanyi ganin nashi ran a bace, a nutse tayi sallarta ta idar tana zaman Azkar. Tana idarwa ta koma tayi kwanciyarta. * Wajen Azahar tana zaune tana firar dankali, Nana kuma ta gama kukan faduwar da tayi da keken Arif ta buge bakinta har saida yayi jini, shine ta samu take baccin wahala, tayi mata shimfida anan tsakar gidan. Da yake gidan inka shigo gate, akwai wata yar haraba da har mota ma za'a iya parking dinta kuma a samu waje, sai ka kara shigowa wata kofa da zata hadaka da cikin gidan, daka shigo kofar akwai dan filin tsakar gida da ba wani girma ne dashi ba, daga gefe kitchen ne wadatacce anyi masa kanta mai kyau daga ciki, da yake itama ba wani tarkace ne da ita ba sai tsarin kitchen din yayi kyau. Akwai karamin bandaki a tsakar gidan, sai kuma wata kofa da inka shiga itace zata sadaka da falon Jamila, a cikin falon akwai daki daga hannun dama, inda ta mayar dashi dakin yaran, sai kuma daga hannun haggu dan dogon corridor ne da zai sadaka da dakuna guda biyu da suke kallon juna, daya na Jamila, dayan kuma na Baffa, kowanne daki kuma da bayi a ciki. Tsarin gidan yayi kyau, dai-dai na masu rufin asiri. Sai dai yanda Baffa yake gaya mata tsarin saman ne yasa taji son wajen ya kara kamata, tunda yace a falon har wajen dining za'a fitar, sannan kuma kitchen a ciki za'ayi shi shima, ba kamar na kasan da yake a waje ba. Irin dai tsarin gidajen 'yan gayu. Abinda kawai take so da kasan shine tsakar gida, dan ita tanaso ta fito taga sararin samaniya lokaci zuwa lokaci, bawai kullum kana cikin daki ba. Har mamakin irin gidajen da basu da tsakar gida kwata-kwata takeyi. "Mami waken duka zan tsince? Akwai yawa fa" Asaad ya fadi cike da kosawa, tayi 'yar dariya. Shi Arif in dai akwai kallo tofa bashi da lokacin komai tunda yarone marar hayaniya, komai nashi da sanyi-sanyi yakeyi. Asaad kuwa irin yaran nan ne masu kulafacin uwa. Baiki duk inda tasa kafarta ya mayar da tashi ba, gashi da son aiki, shisa bata rasa abinda zata bashi ya tayata ko danma ya zauna waje daya "Duka zaka tsince dan albarka, kayi maza kagama in baka ka dakamun maggi" Aikuwa saiya kara maida hankali, dan yanason ta bashi dakan abu a karamin turminta, kwankwasa gidan da akayi yasa ta ajiye firar dankalin taje ta bude, tun daga kofar suka fara gaisawa da Rufaida. Wata mata guda daya da tun ranar da suka dawo unguwar suka fara mutunci saboda kirkinta, itama tace basu fi shekara biyu da dawowa unguwar ba, tana da yaranta hudu "Dan Allaah ki taimako mun da flavor in kina da milk zansa a kunun aya, ragowar Intee ta mungular mun dashi" Cewar Rufaida bayan sun gaisa da Jamila "Allaah Ya shirya mana yaran nan, gashi kai ba abin ka jibgi kudinka ba" Kai Rufaida ta jinjina "Inka biye musu ai karyasu zakayi 'yan albarkar" Daki Jamila ta shiga tana barin Rufaida da Asaad da yake gaishe da ita, tunda dan karamin firij din nata a falo yake, data ajiye shi nan tsakar gida rana ta hanashi abin kirki, a kitchen kuma ya cike mata waje, saita mayar dashi falo tayi masa waje tunda falon wadatacce ne. Data fito ta kawo mata ne take ce mata "Kinga wata gumba ce aka kawomun naji dadinta wallahi, kin aiko Arif ya karbar miki na manta dana fito miki da ita" Tabe baki Jamila tayi "Dan Allaah ki rabani da 'yan shaye-shayen nan ina azumina" Hararta Rufaida tayi "Wannan gumbar yanda kikasan kina shan madara da kantu haka zakijita, kefa mazan yanzun saida gyara" Yanayin fuskar Jamila dai inka gani kasan yau zancen bai zauna mata ba sam, saima yake tuno mata da wulakancin da Baffa yayi mata jiya "Wannan duk baya hanasu karo aurensu insun tashi" Dariya Rufaida tayi sosai "Allaah Ya shiryaki wallahi, to ke ina ruwanki da karo aurenshi? Daman ai bawai zaki gyara bane dan karya karo aure, a'a taki mafitar zaki duba, ki gyara dan ki samu naki matsayin a wajen shi, in kika tsaya wallahi 'yan matan nan na yanzun da suke da ido a tsakar kai sai su sa kwabarki tayi ruwa" Dan jim Jamila tayi tana tauna maganganun Rufaida din, wata irin shakuwa ce ta shiga tsakaninsu kamar sunyi shekaru tare, dan Jamila zatace ita dai a yanzun bata da kawa kamar Rufaida, kuma sukan tattauna matsalolin da ba'a rasa duk wata mace dashi, musamman ta maza, su ba juna shawara "Hmmm..." Jamila ta iya fadi, kuma yanayinta yasa Rufaida ta fahimci cewa tana da damuwar da bataso ta fito fili ta fadi "Karki yarda ki bar mijinki a hannun wata, musamman ma yarinyar da duk wani feleqe da takeyi kokarinta ta taddoki ne, kibari inta shigo sai kiyi lokacinta, amman yanzun kam ki kara rike mijinki" Haka Rufaida ta dinga bata shawarwari kala-kala har saida taga tana aminta da maganganunta, ta kuma kira Arif tace ya bita ya karbo mata gumbar. Rufaida na fita bata jima ba, dan dawowar Arif kenan shima ya ruga daki dan ya cigaba da kallon shi, taji wayarta na ringing, ta dauka tunda tana nan ajiye a kusa da ita. Baffa ne, ta daga tasa a kunne hadi dayin sallama "Mamin yara" Ya fadi daga dayan bangaren yanasa tayi murmushi, kafin kuma ta amsa ya dora da "Daman zanji ya kuka wuni ne? Ina yaran? Kinata aiki halan?" Sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta, akace abubuwan da mata suke so daga wajen mazajensu ba masu yawa bane ba, kulawa komin kankantarta na daga cikin wannan abubuwan, ta manta rabon da haka kawai Baffa ya kirata a waya. In kuwa ya kira to sako zai bata, ayi masa wani abin, ko ita ta kirashi suna bukatar wani abu, da takan kira inya tafi dan taji ya ya isa shagon sai yace mata "Daman shikenan abinda zaki fada? Kai kema dai kina da rigima, sai kace wanda zai bace a hanya" Irin wannan sage gwiwar da yakeyi mata kan abubuwa da yawa yasa ta hakura ta yakicewa kanta yi masa su tunda basa burgeshi. Ko kuma ita dince ta daina burgeshi ba zata iya cewa ba "Bama aikin da nakeyi, dankali ne nake ferewa" Ta fadi muryarta cike da annashuwa "Akwai saura ne har yanzun? Ko in bada a karo sai a kawo muku?" Kai ta girgiza tanata murmushi "Akwai fa, kasan shi saurin lalacewa yakeyi, kuma azumin ma yazo gangara" Tunda ita dankalinma baya cikin abubuwan da suke burgeta, saita soya shi sau nawa bataci ba "To shikenan, kinga dinkunan nan da yawa, daman ince miki karki wahalar da kanki yau ba zan dawo gida da wuri ba, mun nemi wani abin muci anan. Kiyi abinci mai sauki kawai na sahur" Lokaci daya taji wani abu ya haska cikin kanta "Me kake so a dafa maka?" Dariya yayi "Kome kika dafa ai kinsan zanci" Saita jinjina kai "Zan dan fita anjima to tunda ba zaka dawo da wuri ba" Dariyar ya sakeyi "Kafarki ce take kaikayi daman, Allaah Ya tsare, ki dauki dubu biyu a dakina inda nake ajiye kudi saikiyi kudin mota..." Ta fara jera masa godiya "Wai ina ma zakije matar nan?" Saita kama dariya "Badai kace kabarni ba?" Shima dariyar yakeyi "Bazan biye miki ba, bari inyi aikina koma ina ne a dawo lafiya. Ki kula da kanki dai, kar kuma ki dade" Ta jinjina kai, saida tasa hannu tana share wata yar kwallar farin ciki, yaushe rabon data jita cikin nishadi haka? Yaushe rabon da Baffa ya biye mata suyi hira cike da kulawa irin wannan? Harta manta, waya kuwa ko history ta duba na shekara daya basuyi wayar data wuce yan sakanni ba dashi, tunda yana gama fadar abinda zai fada yake kashewa batare ma daya jira tace wani abu ba, hira kuwa tunda ya gane mayi da 'yan matanshi inya dawo ta yanke a tsakaninsu, saita kirga magana nawa take hadasu inya dawo gidan kafin su kwanta. "Asaad ajiye tsintar waken nan haka..." Tace tana tsame hannunta daga cikin dankalik ta tafi ta dibo cefane ta hau gyarawa, bayan ta wankesu, ta dauko wani kwali da busashen kifi yake a ciki, Yayanta Kabiru ne ya kawo musu tsarabar shi daga Jos inda yake aiki, da yawa ta diba ta zuba a wata tukunya ta yanka albasa ta zuba citta da tafarnuwa, dan Allaah Yayita da jin karni matuqa, in zatayi amfani da kifin saita fara tafasa shi haka ta zubar da ruwan, tukunna ta zauna ta gyara shi ta cire kan da kaya. Cikin wani lokaci sai gashi ta gama miyarta mai yawa. Yau kam yanda ya faranta mata rai, itama saita faranta mishi. Zata bashi mamaki, kayan buda baki zataje ta kai masa har shago, yaran shagon nashi ma sai bakinsu ya canza yau, ba zata bari yanda baiyi sahur ba, yayi buda baki a wahale. Shinkafa da miyar kifin zatayi, ta soya dankalin da wainar kwai, sai ta hada musu lemon citta, ta sauko wasu kulolinta da bata taba amfani dasu ba, a ciki zata shirya komai, haka wasu filet dinta masu kyau ta dauraye, ta fiddo robobin da taketa boyo don irin haka, Rufaida ce ta bata su guda goma, design dinsu yayi kyau matuka, shisa ma ta adana, yau ga ranar amfani dasu tazo, shawarwarin Rufaida na dazun suka dinga mata shawagi Haka kawai da zata biyewa zuciyarta da bakin kishi taje ta illata mijinta, a yanzun dai in wani abin ya same shi ai ita da yaranta sune da asara ba AZ din ba Sai dai a lokacin da Jamila take aikinta cike da nishadi da son farantawa Baffa Haka a gefe daya Baffa yake cikin nishadi da dokin ganin Magriba tayi dan yaje yaga abinda Aziza take ta fadin ta tanadar masa...! #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. 9035723778 Opay Lubabatu Sufyan Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani * Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode ********************** ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** ************************* ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ************************** MATAR HABIBI 3 (Free page) Wannan shagon na yanzun, guda biyu ne ya siya, da 'yar karamar plaza ce, akace mai ita ya rasu, to cikin yaran bayan an raba gado sai wasu suka siyar da nasu kason, wajene mai kyau, kuma a bakin hanya. Bayan ya siya a hankali saiya rushe katangar data raba shagunan, aiki yayi masa sosai, kusan duk wani tari daya dingayi da nufin siyan mota a wajen gyaran shagon suka tafi. Aka fadada shi, akayi musu dan karamin bandaki a ciki, saboda yaran shagon nashi idan aiki ya kacame musu, sukan kwana, da yake Baffa mutum ne mai tsantsani, bayason amfani da bandakunan plaza din sam. Har yar doguwar kujera aka saka a cikin shagon daga gefe. Da shigar kananun kaya ya fito daga gida, sai kawai cikin yaran shagon nashi, Isma'il da yanzun zaice ma yana neman finshi kwarewa a harkar dinkin nasu na maza, gashi shi harda na mata ma yakeyi, ya dauko masa yadin daya manta ya siye shi yana fadin "Oga Baffa nafa gama maka dinkin nan" Ya karba, yadine ruwan toka mai duhu, irin masu laushin nan, ba wani abu akayi a jikin dinkin ba, amman yayi kyau matuqa, hannun dogo mai links, sai maballai a jiki, yasha guga, sai kamshin turaren sa Isma'il din yake amfani dasu a jikin duk wani kaya da zai dinka sukeyi, sai yaji ai wannan kayan sune ma yakamata ace ya saka anjima in zaije wajen Aziza. Haka kuwa akayi, yana ganin shida tayi ya shiga bandakin nan, yayi amfani da soso da sabulun da suke dashi ya kara wanke kafafuwanshi da babu abinda sukayi, har fuska ya wanke, inda ace shi din ba kumama bane ba wanka zai karayi, to komin zafin da akeyi saiya sirka ruwa yake iya wanka. Haka ya dauki mai da yake ajiye a saman wata yar shelf din katako da akayi, ya murza a hannuwanshi da kuma kafafuwa, sauran ya murza fuska, ya daura alwala, tukunna ya dauki kayan ya saka a cikin bayin Yana fitowa ana fara kiran sallar magriba, Usman ya mika masa ruwa mai sanyi da dabino, yayi Bismillah ya fara cin dabinon tukunna yasha ruwan "Oga Allaah dai yasa ba zance zakaje ba, irin wannan shan wanka da magribar nan" Cewar Rabi'u dayake mikewa daga kan kekenshi "Kaga wani sa'ido ko?" Baffa ya fadi yana murmushi "Da gaskiyarshi fa Oga, ba zamu bari a hada baki damu ayiwa Maman Arif haka ba, kai Isma'il kaine kayi dinkin nan, kamar a kunnenta" Dariya Isma'il yayi yana daga hannuwa sama alamar saranda "Ku rufamun asiri, ni na dauka ma cikin kayan sallah ne wallahi" Kai kawai Baffa ya jinjina "Wato dai in na lura daku, kamar bayan Jamila zakubi" A tare suka hada baki suka amsa, ciki kuwa harda Abbati da bai cika magana ba, dan shi saida ya dora da "Nan Madam take shaqaro kuloli da abinci ana aiko mana, so kakeyi a janye mana tallafi?" Maganar taba Baffa dariya sosai "Ni sallah zanje, ku kuka sani" Suma sallar suka wuce bayan sun rufe shagon, da yake akwai masallaci a nan gefensu. Ana idarwa Baffa ya fadawa Usman akwai inda zashi, in dai wani abin ya taso sai su kirashi a waya, ya dauki mashin dinshi bayan ya turawa Aziza sakon cewa yana hanya, sai lokacin ma ya kula da cajin wayarshi saura 2%. Tunda yaje shago da safe bai sakata a caji ba, daman kuma jiyama haka bacci ya dauke shi da dare suna chatting da Aziza bayan wayar da suka sha, wayar da itace ma tasa shi ya barowa Jamila dakin nashi ya dawo falo. Addu'a yakeyi kar wani ya kirashi wayar ta mutu kafin ya karasa, dan bayason saiya nemi wanda zai aika a kira masa Aziza, gara dai ya kirata a waya. A ranshi ya dinga zabga tsaki, shifa abinda ya tsana da unguwar nan ta Rijiyar Lemo kenan, musamman wannan layin 'yan chanan, kamar babu layin daya kaishi yawan kwatoci, jiyan nan ya bada aka wanke masa mashin dinshi tas, wani lokacin har mamakin yanda za'ace yarinya kamar Aziza tana irin wannan unguwar yakeyi. Ko a cikin layin nasu ma gidansu ne kadai mai katoton gate. Sai dai bayan ya karasa, ya samu waje a gefe yayi parking din mashin dinshi yana kara kallon unguwar tasu, cike da mutane anata hada-hada, ga masu awara nan da dankali waje-waje, an zagaye su layi danqam. Baiyi mintina uku ba Aziza ta fito, kamshin da take zabgawa ya wanke masa duk wani takaicin bata mashin dinshi da yayi. Daya kalleta kuwa saida ya tsinci kanshi da rokon Allaah daya hore masa halin karasa gininshi ko zai samu ya mallaki Aziza kafin wani yazo yayi masa shigar sauri, bakinta daya sha jambaki ja ya kara fito masa da hasken fatarta tar da kwan lantarki ya haske masa kamar don shi aka bar wuta "Kinyi kyau" Ya fadi yana mata murmushi, ta danyi far da ido kafin ta saukesu cikin kunya "Zaka fara ko Habibi?" Yanayin yanda tayi maganar yaji duk ya susuce, shifa wannan abubuwan, yanayin yanda take lankwasa murya in zatayi magana, 'yar shagwabar da takeyi masa, kwarkwasar nan, sai yaita kallon Jamila yana tunanin yanda akayi tun farko bai taba kula bata da wannan abubuwan ba, ya dinga zurfafa tunani, daman ko lokacin kafin suyi aure haka take? Ko kuma daga bayane ta canza tunda tanajin aita same shi bata bukatar ta dinga yi masa irin wannan abubuwan "Kazo mu karasa ciki" Cewar Aziza, bai kuma yi mata musu ba, yau ma kamar duk zuwan da zaiyi, ya shiga tunanin yanda za'ayi a shiga da mota gidan nasu Aziza. Inka shiga karamar kofar jikin gate din, baifi kayi taku hudu ba zaka samu katanga data raba gate din da cikin gidan nasu, sai kuma wata kofa da ba'a sakawa kyaure bama, nan zaka shiga, wani dan surkukin soro ne da su biyu ma in suka tsaya shi da Aziza a ciki tsaf yan hisba zasu samu sabon case, sai dai suji ana tambayar lambar wayar iyayensu, don da wahala jikinsu ba zai gogi na juna ba saboda kankantar shi, a gefe kofa ce da take a rufe, bai taba ganinta a bude ba, sai kuma dayar kofar da zata sadaka da wadataccen falon da suke zama suna zance a ciki. Aziza ce a gaba yana biye da ita, tun daga bakin kofar kamshin turaren wuta yayi masa sallama kamar ya shiga Maiduguri. Yaji wani sanyi na ratsa shi, kasala da gajiya duk suka rufar masa, suna kara tuna masa da ya kamata shima yasa AC a gidanshi, ko da iya dakinshi ne kuwa. Ya zauna a daya daga cikin kujerun dakin da sallama a bakinshi yana ba Aziza dariya duk da ta amsa, ta dora da "Ina wuni, an sha ruwa lafiya? Ya aiki?" Ya sauke numfashi yana amsawa, hankalin shi yana kan kwanonin da aka shirya a tsakar dakin, bawai abinda ke ciki yake hasashe ba, kwanonin ne sukayi masa kyau matuka, dan bai taba ganin irinsu ba. Aziza ta sauko ta fara budewa, kamshi ya cika hancin shi, saida ta mike ta dauko wata darduma mai kyau, tukunna ta shimfida masa tana fadin "Ka sauko Habibi, nasan bakaci komai ba" Saukowar yayi ya zauna, yana kallon fararen yatsunta da jan lalle a jikin faratan, yayi saurin maida idanuwanshi kan farantin yana jan Istigfari saboda tunanin da yake neman kutso masa cikin kai "Kice mun ba wahalar da kanki kikayi ba kika sake shirya wani abin, ai nace jiya ki sakamun a firij" Saboda shifa wannan tortilla din data kirane a ranshi har yanzun, so yake kawai yaga daga inda zata bullo "Ya zanyi dakai tunda baka zo ba? Kuma kasan Mummy ma zatayi mun fada tace ya za'ayi in baka abincin jiya" Ta fara mika masa wani dan karamin kwano da wani abu a cikin narkakke da dan barbadin wani ganye-ganye a ciki. Ya karba yana kura masa ido na dan sakanni kafin ya duba sauran tarkacen da take ta kiciniyar dibar masa, shi dai baiga biredi ba, abinda yake hannun shi kuma yayi masa kama da butter "Nasanka da son dankali, gashi anci maiko tunda azumi ne shine nace gara inyi maka mashed..." Yaji kalmar, kuma yasan turanci ne, a dan abinda yakeji dai ya kasa fassara shi balle hadinshi da abinda yake hannunshi, ya dai karbi cokalin da ta mika masa ya dibo yana kaiwa bakinshi da Bismillah, ba don korar shaidan ba, don neman sa'a kar bakinshi ya kunyata shi yaki karbar wannan abin. Hakan kuwa ya faru, shi dai yaji galmi-galmi, amman baiyi masa yanayi da abinda zai iya ci ba. A yunwar da yakeji ai gara ma ta bashi kunu akan wannan mashed abin. Gudun karya bada kanshi ya dinga turawa yana hadiyewa yana rokon Allaah Ya kiyaye shi da bacin ciki, saboda cikinshi bai cika son bakon abu ba. Har wani numfashi ya sauke lokacin daya ajiye dan kwanon ta bashi filet "Bari inzo Habibi, dan Allaah ka cinye komai" Cewar Aziza tana tashi, yaji dadin bashi wajen da tayi, tana ficewa kan tsiren da yake ciki ya fara, yayi masa dadi sosai, yaso ace shine yafi komai yawa, sai kuma yaci samosa da spring rolls, shima sunyi masa fiye ma da tsiren, kamar ya bude sauran kwanonin ya kara haka yakeji, ya dauki lemon data tsiyaya masa ya kurba, akwai sanyi, amman dai bai gane ma dandanon lemon ba, yayi masa wani daci-daci saiya ajiye "Sufa 'yan gayu harshensu ma kamar daban yake dana sauran mutane" Ya raya ma ranshi, yanata barin abinda yake tunanin yamballs ne daga karshe saboda soyayyar da take tsakaninsu, idan Jamila tayi wuni yake yana ci, ya kudurce a ranshi zai siyi doya gobe tunda ta fada masa sauranta ne ta soya musu jiya, ya dan ajiye filet din yana, daya dauka dai sai yaji shi sakat a hannunshi, gashi da girma, amman baiyi masa nauyi kamar yanda ya sani ba. Sannan daya kalla da kyau ma, bayan abin kamar ba kwai bane ba, yadai yi kyan suya, sai kawai ya jefa shi a baki duka yana taunawa. Sai yaji kamar kubewa ce a tsakiyar, gabaki daya komai da yaci ya nemi dawo masa, ba arziki ya fito dashi daga bakinshi, sai kuma tunanin inda zai saka shi ya dinga masa yawo, cikin hanzari ya mike kamar zai kifa yana ficewa ya tura kyauren gidan ya jefa shi ya dawo ya zauna, lemon daya ajiye ya dauka ya kwankwade saboda zuciyarshi da taketa hargitsawa Gabaki daya ba haka ya hango yau din ba, sai yakejin inama jiyan yazo, ya tabbata abinda ta shirya masa jiya yafi na yau nesa ba kusa ba, kawai dai ita din da kuma kwalliyarta ne suka danne masa rabin disappointment din, sai gata ta dawo dakin da sallamarta tana dorawa da "Afuwan Habibi, kasan Matar Officer na gidan, yau nan tayi buda baki, nasan yanzun mijinta zaizo daukarta, akwai ajiyarta a wajena" Matar Officer kamar yanda Aziza take kiran Yayarta Jalila dashi, daga Jalilar sai ita, tazarar shekaru biyu ce a tsakaninsu, sai dai Jalilar tayi aure da wuri, dan yanzun haka ma yaranta uku. Kuma daga yanda Aziza take yawan maganarta, akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu "Haba ni da kin gama cikamun cikina, ga aiki na baro a shago, anya ma zan iya asham yau?" Sai tayi dariya ta karasa cikin dakin sosai tana zama a gefenshi "Baka cinye ba, ga cheese balls dinma baka cinye ba, kuma saboda kai nayi" Ta karasa cike da rashin jin dadi a muryarta "Cikina ya cikane sosai, naci daya dan yayimun kyau a ido" Sai ta dan saki fuska "Aikam sai in juye maka ka tafi dashi" Baiyi musu ba, wannan ai mai sauki ne saiya cillar dashi a hanya koya samu wani almajiri ya bashi. Koma wanne abu dai, hira suka dingayi cikin nishadi. Ana fara kiran sallah yace mata "An kiramu" Ta turo baki "Bangaji da ganinka ba" Murmushi yayi "Ni akace na gaji da ganinki ne? Gashi da wahala in sake samun damar zuwa kafin sallah idan Allaah Ya kaimu" Aikuwa tayi kwal-kwal da idanuwa har yana hango kyallin hawaye a cikinsu, duk yaji ya susuce "Kar muyi haka dake Babe, ga waya fa, ga video call" Hawayen ta bari suka zubo "Wanne video call? Abinda daka shiga gida baka yarda muyi saboda matarka, bayan nima yanzun ina da hakki akanka tunda ai aurena zakayi..." Da sauri yace "Inji wa ya gaya miki saboda ita ne? Nifa na isa da gidana, abinda nake so shi zanyi" Aziza taja hanci tana kara narke masa "To me yasa idan na kiraka baka dagawa? Aiko ba zakayi magana ba saika daga in ganka" Ya jinjina kai "Zan dauka, shikenan? Dan Allaah ki share hawayen nan bana sonsu" Duk da haka saida ya kara bata lokaci yana lallashinta da yi mata alkawura kala-kala duk da yaji an tayar da sallah. Ya ajiye mata dubu goma cifa, sababbin yan dubu-dubu. Yaji dadin yanda ta manta da hadashi da wannan cheese ball din. Daya fito ne ma sukayi kicibis da Jalila tana tsaye, bayanta goye da karamin Jawad, sai Jabir da Jafar da suke gefenta, ga wata katuwar leda data ajiye a gabanta, zuciyar Aziza ta tsinke, kar dai har yanzun Balarabe baizo ya daukesu ba "Habibi ga Adda Jalila ku gaisa" Cewar Aziza cikin karfin hali ganin idanuwan Baffa akansu ya fara sauka, ta kalli Jalilan tana fadin "Matar Officer ga Habibina" Duk da Baffa yasan ya girmeta haka ya dan rage tsaho yana gaishe da ita, ta amsa shi fuska a sake "Kinga kila ma ciki zan koma, yanzun Officer ya kirani wai kaman ya taka abune tayarshi tayi faci" Jalila ta fadi "Babur din Baba ne yayi faci?" Jabir ya fadi yana kallonta cikin maganarshi da bakowa bane yake ganewa, Aziza tayi saurin kallon Baffa da alama baiji abinda akace bama, dan hankalinshi naga masallaci da har anyi raka'ar farko, tunda da alwalarshi yacewa Aziza "Bari kiga inyi sallah kafin in wuce, lafiya kalau mashin dina idan na barshi anan?" Kai ta daga masa da sauri, dan unguwarsu tana da tsaro sosai duk kuwa da yawansu, akwai karancin sace-sace musamman irin wannan lokacin ma da jama'a suke hada-hada. Baffa na shigewa tana juyo karar mashin din Balarabe tun daga kan kwanar layinsu kamar babu salansa a jiki, suka hada ido ita da Jalila cike da takaicin da har yau basu daina shakarshi akan wannan mashin din nashi ba. Saikuwa gashi nan ya karyo kwanar, kana hango sabon uniform dinshi shar "Officer take aure ashe, soja ne ko dan sanda?" Baffa ya taba tambayarta da tace masa tana gidan Jalila din tana kiranta da Matar Officer, farko-farkon haduwarsu, babu shiri ta katse hirar da fadin "Minti daya Habibi" Ta kashe wayar, tunda ai ba zata sharo masa karya ba, idan aurenta zaiyi dole wannan likon zai cire, ta ina zata fara ce masa Balarabe dan karota ne?. Ko gaisawa bata tsaya sunyi ba, dan kafin ya karaso ta cewa Jalila "Adda sai munyi waya" Ta shige gida abinta. Baffa kuwa ana sallar nan kamar an kara zazzage masa hanji haka yakeji, gashi limamin nan kamar ya zabi yayi tilawa ne a sallar asham din, kafafuwan Baffa har sanyi sukeyi kafin ayi ruku'u. So kawai yakeyi a idar ya karasa gida ya dirarwa koma menene Jamila ta tanadar masa, Allaah Yasa tayi zobo, dan yau jinshi yakeyi kamar baisha abinda ya kai masa inda ya kamata ba. #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. 9035723778 Opay Lubabatu Sufyan Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani * Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode MATAR HABIBI 4 (Free page) Adai-daita na ajiyeta, ta dauki katon kwandon data hada komai a ciki, don da taga almajiri ma shi zata ba ya dauka ya tsallakar mata dashi saita bashi ko Naira dari ne sadaka. Kwandon yayi mata nauyi, haka ta kinkima saboda wani mai mota daya gansu a tsaye, mata su wajen biyar saiya daga musu kafa suka samu suka tsallaka, sai nishi takeyi, ta ajiye kwandon a kasa dan ta numfasa. Ta godewa Allaah da tabarwa Rufaida har Nana. Da yake ba kwiya gareta ba, su Asaad na dauke mata hankali ta samu ta silalo, ai da taji a jikinta da daukar wannan kwandon. Yanda Baffa yace ba zai dawo da wurin nan ba, sai kaga har goma ta wuce ma kafin ya shiga gida, tasan yana son shan ruwan shayi wani zubin, saita hada masa shi yasha kayan kamshi. Shisa kwandon ya kara nauyi. Kamar ance ta juya, ta hangi Baffa yana daukar mashin dinshi, sai dai ba kayan daya fita dasu bane a jikin nashi, yadi ne yanzun, kuma daga inda take taga yayi kyau duk kuwa da bai saka hula ba. Babu yanda za'ayi ta ware baki ta kwala masa kira, bata kuma fito da wayarta ba. Hakan yasa ta dauki kwandon, nauyin shi na hanata sauri yanda ya kamata, sai dai kafin ma ta karasa Baffan ya haye mashin dinshi yayi gaba, tunda baya ya bata ya fice ta dayan bangaren shisa bai ganta ba "To ko dai gida zai koma?" Wata zuciyar ta raya mata, sai tayi tunanin ta karasa shagon taji. Haka kuwa akayi, Abbati ne ya fara ganinta tunda yana bakin kofar shagon a tsaye da kankana a hannunshi "Maman Asaad" Ya fadi yana dorawa da gaisheta a daburce "Naganshi ya fita ma yanzun, kar dai gida ya koma, yace mun zaku dade yau a shago saboda akwai ayyuka" Sai Baffa ya juya yana kallon Isma'il cikin neman dauki, dan shi karya bata cikin dabi'unshi, ko da kuwa ta kare kaice, kalamai ma gabaki daya basa yawaita a bakinshi. "A'a um...yaje ya dawo ne" Cewar Isma'il shima sarkin maganar yau da alama ya rasa ta cewa, kuma hakan nada nasaba da yanda Jamila takeyi musu kwarjini. Macece da nagartarta take shimfide akan fuskarta. Yanayinsu, da kuma yadin jikin Baffa ta hada waje daya a cikin kanta, kwakwalwarta ta dai-daita mata lissafin. Shisa ya kirata yau kenan? Shisa yayi mata kirki? Saboda zaije zance wajen AZ dinshi kenan, acan zaiyi buda baki kome? Ita tana can tana kitimillin hada masa, banda ruwa da dabino bata saka komai a cikinta ba tanata sauri ta fito, ashe tana da rabon ta cika cikin nata taf da bakin ciki. "Na bar yara a makota, ga kayan buda baki nan, bari in wuce" Saboda jikinsu a sanyaye yake su duka, kamar sune suka saka Baffa tafiya zance a ranar yau, sai suka kasa wani yunkuri har Jamila ta juya, ta tare napep, zuciyarta na wani irin tafasa. Numfashi kawai take maidawa har suka isa, dari biyar din data bashi ma ca tayi ya rike canjin ta wuce ta shiga gidan Rufaida, taji dadin samunta ta tayar da sallah dan kwata-kwata bata son wani dogon surutu, ta sabi Nana tana riketa a hannu ta cewa su Asaad "Ku taso mu tafi" Bata san ko muryarta bace ko yanayin fuskarta yasa duk suka shiga hankalinsu. Tana zuwa kofar gida kuwa ta samu Yayarta Yasmin da take tsaye tana danna waya "Yanzun nake shirin juyawa dan nagaji da kwankwasa kofa..." Murmushin karfin hali Jamila tayi "Kai su Maman Danjuma babu hakuri" Yasmin din tayi dariya. Tun haihuwar Yasmin ta biyu, ta kwallafa rai akan idan namiji ne za'a saka sunan mahaifinta Abubakar, har shafa cikin take tana fadin Assadiqu kamar yanda take da niyyar kiranshi, ta shiga watan haihuwarta, Kanin mijinta ya rasu, kawai tana haihuwa da yayi masa huduba, bata kawowa ranta ba Abubakar din ya saka ba, sai ranar suna taji ana "Ashe yaro sunan margayi yaci, Allaah Sarki Ya'u" Ta tabbata da ba'a zaune take ba sai jiri ya tikata da kasa, ita tun yana da rai ma ba shiri sukeyi ba, duk da ance babu kyau tado da halayen mamaci musamman wanda ba nagartattu ba, shi kam mutum ne mai tsugudidi, sannan ya saka mata ido ainun, duk wani husumi da zai taso tsakaninta da dangin mijin nata in aka bibiya shi ya kitsa zancen. Kamar mace haka yake da gutsiri tsoma. Da yake kuwa ranar Juma'a ne ta haihu, saita fara kiran yaron da Danjuma, wani suna da mijin nata da dangin shi suka tsana saboda sunce akan meye zata boye sunan yaro, shima mijin da yayi magana sai tace masa "Ni da nayi dakon wata shida, nayi nishin nakuda ai ayi mun alfarmar kiran yaro da sunan daya kwantamun ko? Tunda ban hana kowa ya kirashi da sunan da aka rada masa ba" Haka dole ya hakura ya kyaleta, tunda yasan hali, jan maganar kamar neman zunguro sama da kara ne tunda har batace masa ta tafasa ba akan sauyin sunan da aka samu. Tun daga lokacin ta tashi daga Adda Yamin a wajen kannenta ta koma Maman Danjuma, tun suna kiran sunan da zolaya har yanzun kusan kowa ma haka yake kiranta dashi. Gidan Jamila ta bude suka shiga, su Arif suka gaishe da ita "Mu karasa ciki mana" Kai Yasmin ta girgiza "Keni ba zama zanyi ba, Yaya Babangida ne ya hadani da aiki, ga sakonki nan" Cewar Yasmin tana mika mata ledar data shigo da ita, kafin ta fara kokarin sauke jakar kafadarta, sai ga wuta sun kawo, daman fitilar caji ce da take dorawa sama, ita ta haske tsakar gida, saita wuce daki da yara ta kunna musu tv ta dawo, Nana ce kawai ta makale taki sauka. Kudi ne Yasmin ta mika mata, tasa hannu ta karba "Kudin dinkin kine yace a baki" Haka kawai sai taji hawaye ya balle mata, wani irin rauni ya mamaye ta "Jamila, ikon Allaah, meya faru kuma?" Da sauri tasa hannu ta goge hawayen, kawai tana hasaso tarin kauna da hadin kan da suke dashi, yanda ta fahimci ba sai iyayenka nada kudi bane kake kasancewa dangata, ita kam 'yar gata ce, sun taso cikin tarin kulawa, yanzun gashi aure ya rabota da gidan nasu, ya kuma sakata yunwar wannan kulawar. Tunda in ba yunwarta da takeyi ba, wayar kasa da mintina biyu da sukayi da Baffa itace fa tasa ta son faranta masa "Wai menene? Kinsan banason wannan shirmen banzar naki" Yasmin tayi maganar cikin fada, amman zaka iya tsintar damuwa a kasan muryarta. Saboda tasan halin Jamila, abinda zaisaka hawayenta zuba ba karami bane ba, akwai kujerun roba guda hudu, wata cikin wata daga can gefe, Yasmin ta karasa ta dauko guda daya, duk da batayi niyyar zama ba "Kiyi mun magana tunda dai ai baki da wanda suka fimu" Numfashi Jamila taja tana saukewa "Baffa ne" Ta fadi, Yasmin ta kalleta tana jiran karin bayani "Zance ya tafi" Sai Yasmin din taja wani dogon tsaki "Shine kike shararar hawaye sai kace wanda ya nakadawa duka, to in ba daukar kafa ba ke ina ruwanki da zancen shi?" Wasu hawayen suka ciko idon Jamila "Adda bafa dan ya tafi zancen bane ba, kayan buda baki na shirya masa na tafi na kai saboda yace mun zai dade bai dawo ba, na samu ya tafi wajenta" Kureta da ido Yasmin tayi "Da yace miki zai dade sai yace kiyi abinci ki kwashi kafa ki kai masa?" Ta girgiza kai "Shegiyar kankanba ce irin taki kenan" Tayi shiru "Ke yanzun waye yace miki anayi wa maza wannan kankanbar? Ai kina budurwa ne kafin ya sameki, shine zaki burgeshi da irin wannan iyayin, amman yanzun tunda ba sakaki yayi ba gara ki rufawa kanki asiri, in ba kina neman ciwon zuciya bane ba" Fada sosai Yasmin tayi mata kafin ta dora da lallami, ta nuna mata duk taji, ta kuma lallasu, haka sukayi sallama, ta rakata tana dawowa. Ta duba ledar, lace ne mai kyan gaske sai atamfa kala biyu, sai kuma shadda da tasan ta Baffa ce. Da yake Yaya Babangidan yanzun kasuwa nayi dashi, kuma shi din mutum ne mai son hidimtawa dangi, babu ruwanshi da kana dashi, inya tashi zaiyi maka, su matan har mazajensu yake hadawa. Ta tattara duka ta shige dakinta dasu ta adana. Kamar yanda Yasmin ta fada mata ne, ita ta kai kanta, babu wanda ya aiketa. Amman ta kasa daina jin takaicin wai saboda yana so yaje zance ne yau yayi mata kirki. Tana da hakuri, amman tasan idan bata rama wannan abin da Baffa yayi mata ba, zata jima dashi a rai. Ta samu tayi sallar isha'i da asham, ta dan zuba abinci kadan taci, tazo ta dauki su Asaad da sukayi bacci a falo ta kaisu dakinsu, tana tashin kowanne yayi fitsari, tukunna tayi musu addu'a, Nana da take goye a bayanta itama tayi bacci, taje ta kwantar da ita. Taji ana kwankwasa gida, wani abu ya taso mata, haka ta sauka taje ta bude masa, ta kuma danne zuciyarta tayi masa sannu da zuwa "Kece da sannu ai Mamin yara, ya naji gidan tsit, ko har sunyi bacci" Data kalle shi, yanda yadin yayi masa kyau bai hanata ganin bakin shi ba, sai takejin kamar dariyar da yakeyi mata dinma duk ta yaudara ce yau. Shikuma ganin irin kallon da takeyi masa yasa shi saurin cewa "Kinganni da yadi ko? Hmm, kwata na fada, Allaah Ya taimaka Isma'il ya dinka mun wannan yadin, na samu na canza, kayan na can ma shago na manta dasu" Baffa ya karasa maganar yana gyarawa mashin dinshi zama "Da mashin din ka fada kwatar?" Jamila ta tsinci kanta da tambayarshi duk kuwa da shiru taso yi "A'a fa" Ya fada da sauri "Da naje azahar ne" Sai wani guntun murmushin takaici mai sauti ya kwace mata hadi da mamakin yanzun ne Baffa ya koyi shararo karya haka, ko kuma tunda can ne itace dai bata maida hankali ba. "Allaah Ya kara tsarewa" Ta furta tana wucewa ta shige daki, bata kuma tsaya ko ina ba sai dakinta, ta haye gado, tana shirin kwanciya ne Baffa ya turo kofa, ta daga kai ta kalle shi "Abinci na Mamin yara, bakiji yanda cikina yake daurewa ba" Zuciyarta tayi wani tsallen murna a cikin kirjinta, ta danyi 'yar dariya "Yau kuma zolayar taka ce ta motsa, wanne abincin kuma Babansu? Banda wanda nasan yau har makotanku a shago sai sun samu rabonsu" Ya dan diririce yana juya maganarta, yana juya maganarta, sai yayi dariya shima duk da kuwa bai gane me take nufi ba "Ni dai a dawomun da robobin dana zuba zobo dan Allaah" Jamila ta fadi, zuciyar Baffa ta buga, kar dai abinci ta aika musu dashi shago? "Bari dai insa wayata caji" Yace mata yana ficewa daga dakin, zuwa yayi yasa wayar tashi a caji, ya kunnata, ya dan zauna a wajen yana jira ta gama kawowa, sai ga sakonni, na Aziza, sai kuma Isma'il, da hanzari ya fara bude na Isma'il din "Inata kiran wayarka a kashe, yanzun Madam tabar shagon nan, ta kawo mana kayan buda baki, amman dai munce mata kaje ka dawo" A fili ya furta "Inalillahi wa ina ilaihi raji'un" Bayan ya karanta sakon, a yanda yasan Jamila, ya tabbata abinci ne niqi-niqi takai, kuma anan gida din wanda zata bari ba mai yawa bane ba, tunanin karyar da zaiyi mata ya samu ko da taliya ce ta dafa masa yakeyi, saboda da gaske yunwa yakeji. Haka ya bar wayar batare daya ko bude sakonnin Aziza ba, ya sake komawa dakin Jamila ya ganta tana duba drawer din gefen gado "Me ake nema?" Batare data dago ba tace masa "Paracetamol zan hadiya, kaina ke ciwo" Ya danyi jim "Sannu, kuma da zuwa nayi ince a zubamun abinda aka rage, kinsan yan shagon nan, musamman Isma'il, shiya fita da plate yan shagon Rahusa suka ganshi, nan suka tattaro suka zo, dan abinda nacin ba mai yawa bane ba, anayi asham duk ya zazzage" Sai lokacin ta kalle shi, amman ya kasa hada ido da ita "Aikuwa babu wani abu sai abincin Sahur dinka, shisa na zuba muku shi da yawa daman, ko da baku kadai zakuci ba, kuma da yake banma zaci yanzun zaka dawo ba" Yayi shiru, itama tayi shiru "Bani shi inci kawai yanzun din, da sauran biredi? Ko shayine sai in sha anjima din" Ta jinjina masa kai, tana mikewa, acan kitchen din ta zuba masa a filet, ta samu dan karamin kwano ta zuba masa miyar, tana dan saka masa kifin kadan, duk kuwa da yawan da yake dashi a cikin miyar, ta daukar masa pure water da kofi, a falo ta same shi zaune, ta ajiye masa komai a gabanshi "Ko dan zobon bai rage ba Jamila?" Tayi 'yar dariya "Ai kam dai bai rage ba, mun shanye ni da yaranka" Ya kalli shinkafar "Bari inje in samu maganin nan in sha in kwanta ko zan samu bacci" Da sauri Baffa yace "Kisa alarm dan Allaah karmu sake makara" Ta jinjina masa kai kawai tana wucewa batare data amsa ba, haka ya tashi da shinkafar tas, miyar tayi masa dadi, ya dinga cancana dan kifin da yake ciki kamar karya kare. Ya sha ruwan yaje ya kwanta, sai lokacin ya dauki wayar shi yana kiran Aziza. Hira sukayi sosai, harda video call din da yayi mata alkawari, duk da bai bari video call din yayi nisa ba, ko dan dare ne, gashi ba hijabi ta saka ba, duk da baya ganin komai banda wuyanta sai kuma gashin kanta da yake kwance luf har akan goshinta,hular data saka ta dan zame baya. Gashi duk ta narke sai shagwaba takeyi masa, yaji ya fara susucewa, kuma tunda watan azumi ne, yasan bashi da halin labewa bayan shaidan. Haka yayi mata sallama yace zai kwanta, kuma kwanciyar yayi, amman cikinshi daya murda ne ya saka shi tashi babu shiri yayi bandaki, wasa-wasa kafin karfe biyun dare ya shiga bayi yafi sau takwas, danma Allaah Ya taimake shi cikinshi bai fara ciwo ba, da yazo ya kwanta dai sai yaji jikinshi yayi laushi matuka, kamar duk yinin ranar baici komai ba, yasan dole ya lallaba Jamila anjima ko indomie ce ta dafa masa ta soya masa kwai kamar guda biyar yayi sahur dashi, dakyar ya samu bacci yanata mafarkin abinci Abinda Baffa bai sani ba shine Jamila bata kwanta da niyyar tashin shi ba... #LubnaSufyan ✨ #WomenOfWords #09035723778 Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram 10/12/2024 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano. 9035723778 Opay Lubabatu Sufyan Saika turo shaidar biya ta lambar da take sama. Nagode da addu'a'inku, nagode kuma da kwarin gwiwar da bakwa gajiya da bani * Duka littafin nan sadaukarwa ne ga Marubuciya Aisha Shafi'i, idan kunci karo da littafin nan, kun nishadantu, kun karu ta kowacce irin fuska, ku rokawa mijinta Isma'il Rahmar Allaah, ku roka mata sauki da juriyar rashin shi, ku rokawa yarinyarta rayuwa mai albarka. Nagode MATAR HABIBI 5 (Last Free page) Kudin da Baffa ya bata ta kirga bayan tafiyarshi, saita tabe baki, saboda ta raina dubu goma, kamar yanda ta raina kayan sallar da yayi mata, musamman lace din. Ko Mummy da ta ganshi saida tace "Wannan lace din ai karami ne Aziza, ba zai wuce dubu sha biyar ba" Aikuwa dansu tabbatar haka ta dauki hoton shi ta turawa kawarta da take siyar da kaya tana tambayarta, ita a wajenta ma dubu sha uku da dari biyar ne "Inya baki wasu kudin a hankali saiki tarasu ki hada ki dauki babban shi" Haka Mummy ta bata shawara. Jaka da takalmin dai sunyi mata kyau sosai. Taji sanyi da ba da Baffa kadai ta dogara ba, sauran samarinta sunyi mata hidima kamar yanda suka saba. Kawai matsalar zuciyarta ce, itace ta narke akan Baffa, saboda tana tunanin fata da kuma bakin Mummy ne yake binta, ita take yawan fadar "Kefa ba matar kananan yara bace ba, In Shaa Allaahu ke din matar babban mutum ce" Manyan mutanen ne suke binta kuwa, masu kudi, dattijai da suka kusan haifarta dama wanda suka haifi kamarta sau babu adadi. Tana son rayuwar hutu da jin dadi, amman fa auren tsoho bai taba burgeta ba komin kudinshi. Duk kuwa yanda take ganin jin dadi shimfide a fuskar Mummy din idan sun hidimta mata, wani zubin ko don Mummy ta huta sai taji kamar ta duba wanda suka fi dama-dama a cikin maneman nata, a lokacin ne kuma ta gane da yawansu ba auren bane ya kawosu. Alhaji Sadisu ne kawai yayi mata maganar aure da kanshi, shikuwa matanshi uku a yanda ya fada mata, uwargidanshi ta rasu, da ita yake so ya cike ta hudu. Shikuwa ko bai fada ba ta tabbata ya ba saba'in baya. Ba tajin tarin dukiyar shi zasu lullube mata shekarun shi. Samarin kuma da suke tareta bata ma bata lokacinta akansu, tunda ta tabbata ba aurenta zasuyi ba. Baffa shine namiji na farko da yazo wajenta taji ya kwanta mata har cikin ranta, duk kuwa da taso ace yafi haka kudi, saboda Mummy da ta tabbata Baffan ba zaiyi mata ba, ya aka kare ma lokacin auren Jalila da Balarabe. Shisa Mummy ta tattara burinta da fatanta kacokan akanta. Aziza itace 'ya ta hudu a wajen Marigayi Malam Ayuba da matarshi Rahanatu. Shi din Bafullatani ne dan asalin garin Adamawa. Neman kudi ya shigo da iyayensu garin Kano, da kuma rabon suma din arzikinsu yana nan Kanon. Rahanatu kuma 'yar Dawakin tofa ce ta asalin garin Kano. Haka iyayenta duka 'yan Kano ne. Ta taso cikin gidan yawa, mata hudu, su kuwa yaran gidan sun bawa talatin baya. Haihuwa ake a gidansu da ta zama gasa, duk da mahaifinsu ba mai karfi bane ba. Dan 'yana aiki ne a gidan sarki, da yana cikin masu gadi, da yake mutum ne shi mai shisshigi da tusa kai, haka ya dinga shiga da fice har saida aka maidashi bangaren kula da dawakai. Sannan wannan shisshigin nashi yasa yake samun alkhairi babu laifi tunda gwani ne kwarai wajen koda duk wani ahali na gidan Sarkin. Kusan a cikin yaran gidan, Rahanatu itace tafi kowa haske da manyan idanuwa, hakan yasa mutane suke cewa tafi kowa kyau, da yake za'a iya cewa ta biyo halin mahaifinta, saita kara da iyayi da kuma son ace wata ce, da ta kafa rigima da naci saida aka sakata a makarantar bokon da har mazan gidan ba damuwa sukayi da ita ba. Ta kuwa rungumi fadin rai ta dorawa kanta, duk inda zata zauna saita san yanda tayi ta fadi cewa ita jinin sarauta ce. Yaran unguwa da aka taso tare kullum cikin gulmar wannan karya ta Rahane suke tunda mafadaciya ce ta gaske ba'a isa ayi a gabanta ba. Ko Rahanen ma ta hana a kirata dashi sai Rahanatu. Tana aji uku a sakandire ta hadu da Ayuba, dan gaye dai-dai da zamanin shi. Yana da shagon saida kayan masarufi. Gashi Bafullatanin usul, fari sol dashi. Cikin kankanin lokaci akayi bikinsu, yana kuma yi mata hidima har ya zarta karfinshi wani lokacin saboda yanda take da son harkar karya. Dai-dai gwargwado tsaye yake kansu. Data nemi komawa makaranta bai tauyeta ba, dakyar dai ta hada takardun sakandire, dole ta hakura, sabodq hidimar gida data yara. Tana da cikinta na biyar ya rasu, bayan gajeriyar jinya. Wannan rasuwa ta kidima Rahanatu, gashi daga shagon nan sai gidan daya bar musu. Yara kanana, tunda a lokacin Khalifa ne kawai yake da shekaru goma, Anwar takwas, Jalila shida, sai Aziza uku, dan ta samu tazarar shekaru 3 ne a wannan karin. Bayan ta haihu ta samu namiji sai aka mayar masa da suna Ayuba suna kiranshi da Nur. Sai ga takardun sunyi mata rana, shige-shigen mahaifinta da mutanen daya sani, sai gashi an samar mata aikin rubuta kati a Asibitin Aminu Kano. Kuma bata zauna haka da aikin ba, duk wata sana'a da zata kawo mata karin kudi bata sanya da ita. So take yaranta su haska sufi na kowa a unguwar tasu, su samu ilimi tunda ita dai taga ranarshi. Rayuwar karyar dai data dorawa kanta, Malam Ayuba kan nuna mata rashin jin dadin shi akan irin rayuwar lokacin da yake da rai, tunda yanayi mata komai, bayason yanda dai idonta yake kan wasu a cikin kawayenta, tana so ta taddosu ko ta zartasu. Yanzun da kasa ta rufe masa ido, ga aikin data samu, sai abinda yayi gaba. Cikin yaran nata biyar kuwa, Khalifa ne ya fita zakka. Ya samu karatu zuwa NCE, yana aikin koyarwa, yanzun haka yana da mata da yaro daya. Ko kadan Khalifa bayason irin rayuwar da Mummy kamar yanda suke kiranta takeyi, ta kuma dora kannenshi akai. Ga Anwar nan, yana BUK a yanzun haka, saboda shi yace daman ba zai iya FCE ba, kusan yafi kowa jin kai a cikinsu, saboda shine sak ya biyo mahaifinsu, yana daga cikin matasan da suka rungumi mining din Pi lokacin da yazo, dan gani kasheni ne akan Pi, dan zaku iya raba jaha dashi idan kayi kokarin rage masa burinshi akan Pi. Haka yayi sa'a yana cikin wanda aka budewa yin kyc da wuri, saboda haka lokacin da aka fara bumburutun Pi saiya zamana ya samu kudin da bai taba rike irinsu ba. Khalifa ya bashi shawara ya samu sana'ar da zai dingayi, suka zauna sukayi magana sosai, kuma Anwar ya nuna masa ya dauki shawarar, yana komawa gida, suka zauna da Mummy ya fada mata kudurinshi na da yayi niyyar yayi musu gyara ne a gidan, sai ta rushe duk wani tsari da Khalifa ya dorashi akai, sai gani yayi an dauko gyaran gida, gini ne na zamanin da, na kasa, sai akayi masa shafen suminti, dan haka katanga akaja bayan an ware daki daya akayi masa gyara na gaske, sai katangar ta raba wannan dakin da sauran gidan ba'a gyara ba, ya siyo wannan katon gate din aka kakaba a gidan. Sauran Pi din yace ba zai siyar ba zai jira a shiga kasuwa dashi ne, dan abinda yayi saura ya fara saro gilasai, hulunan hana sallah da zobunan azurfa, daman yana dan taba siyar da takalma, yana samun rufin asiri dai-dai gwargwado dan kuwa Anwar ya iya kasuwanci, karya ce kawai takeyi masa cikas, tunda kudin maimakon yayi abinda ya kamata dasu sai a siyi turaruka ko takalma designers. A wajen Anwar dama Jalila a yanzun, da aji kunya gara an kwana da yunwa. Kawai wani hali da suke dashi su dukansu, suna son farin cikin Mummy, duk wani fata nasu na yanda zasu gatanta ne, ko Jalila tayi niyyar yin auren kudi yanda Mummy take so, sai ga Balarabe da suka fara wata irin soyayya mai tsayawa a rai duk kuwa da tarin talaucin shi. Haka Mummy naji tana gani ta hakura akayi auren. Shikuwa Auta Nur yanda duk akayi dashi haka yake binsu. Jalila a yanzun haka ta gama diploma dinta anan Kano Poly, amman ita data samu mijin daya kwanta mata sam ba zatayi wani karatu ba. Aure take so, tunda ta tasa tasan ma'anarshi, ko yaushe cike take da mafarkin auren nan. Balle data kara samun babbar waya, tana cikin group din matan sirri na Facebook, tana bibiyar manyan bloggers a manhajar Instagram, sai ta karajin tanason auren, babu kuma abinda yafi burgeta irin ace yau ta mallaki kitchen dinta na kanta, tana dafa ma mijinta abubuwan burgewa itama ta dauki hotonsu ta shiga wannan trend din da ake yayi na 'ga abinda nake ciyar da mijina'. Shisa duk shiriritarta, tunda Mummy tayi musu tsaye a bangaren boko dama Islamiyya, itace dai sai taga dama take zuwa Islamiyar lokacin, bata wasa da addu'a akan aurenta. Dan bata dagowa daga sujjada bata roki Allaah daya bata miji nagari ba, kuma tana da yakinin rokonta Allaah Ya amsa ya jeho mata Baffa. Duk da karsashinta ya rage lokacin da taji yana da aure harda yara uku, amman shi da kanshi Baffan ne ya kara mata karfin gwiwa, a bakinshi takejin shi da Jamila aure ne akayi musu na hadi, yanzun a tare da son da takeyi masa, akwai tausayi mai yawan gaske da yake bata. Ace matashi dan kwalisa kamarshi, ga rufin asiri yana dashi dai-dai gwargwado amman baiyi sa'ar mata ba. A goman karshen nan batayi wasa ba wajen addu'a, harda Mummy take hadawa idan Baffa shine mijin nata, to abin ya kwantawa Mummy a rai. Tasan duk yanda zasu so juna da Baffa, in dai Mummy bata karbe shi da budaddiyar zuciya ba, ba zataji dadin zaman yanda ya kamata ba. Ai tana gani akan Jalila, duk wani abu da Balarabe zaiyiwa Jalila sai ta kushe, ko ita kuwa ya bada aka kawowa haka zata karba tana kushe abin da Balaraben ma gabaki daya. Wani zubin ma da kuka Jalila take barin gidan saboda kwarzabar Mummy akan auren nata. Shisa ba zata taba wasa da addu'a ba ita kam, tunda tasan babu wanda zai tausaya mata sama da Ubangijinta, to kuwa gara ta gurfana a gabanShi ta kai kukanta. Yanzun a cikin kawayenta su shida, Aisha da Hassana duk sunyi aure, saura su hudu, ita, Mimi, Nabila da kuma Maryam. Sunfi dasawa da Mimi saboda yanayin rayuwarsu yazo daya, suna da son asan dasu a waje, gayu, dama karya, duk da ita Mimi suna da kudi, amman kudin nasu bai kai yanda ita take zuzutawa ba. Maryam yanzun haka ansa ranarta, Nabila ma anyi gaisuwa, shiya karawa Aziza jin kamar ta janyo Baffa yazo ayi magana tasan cewa da gaske yakeyi, yau ma sunyi zasu hadu a gidan Hassana,ita, Mimi da kuma Nabila, tunda duk Hassana dince takeyi musu dinki. Ta kware sosai, haka kuwa akayi, suna cikin hira ne, Mimi take basu labarin saurayin da tayi Nawaf "Nifa bawai baiyi mun bane ba, yanda yake isata da hirar matarshi da yaranshi shine abinda yasa duk ya fice a raina, to tunda yana son matar tashi uwarme ya kawo shi wajena?" Hassana tayi dariya "Ke dai Allaah Ya shiryeki, ai wannan alama ce mai kyau, ba wai hirar matar tashi ba da yakeyi miki, yanda yake nuna miki iyalanshi ma da muhimmanci a wajenshi, kema sai kiyi fatan idan abin ya tabbata Allaah Yasa kiyi muhimmancin nan" Kai Nabila take girgizawa "Koma menene, karka kawomun maganar matarka, babu ruwana da ita, kazo muyi hira kan abinda ya shafemu, nifa shisa sam bana son ma in kwasowa kaina mijin wata, duk yanda zakiyi dashi sai an samu damuwa, wannan makirar matar tashi saita kawowa soyayyar taku wani cikas din" Aziza da take jinsu ce tace "Bafa kowacce ba, wata ma bata da wannan muhimmancin a wajenshi, kinga kaman Habibi na, wallahi har tausayi yake bani, saboda dama can shi ba auren soyayya sukayi ba, wata dusa ce aka hadashi da ita, hakuri kawai yakeyi, shisa nake ta shiri, dan na tabbata kwace shi a hannunta ba wahala zaiyi mun ba" Wannan karin Nabila ce tayi dariyar harda kyakyatawa "Wallahi karya yakeyi miki..." Take fadi har lokacin tana dariya "Wato zama yayi yana shirya miki drama ke kuma kika hau? Auren hadin shekara mai zuwa ma kina iya ganinta da lodin shagamu, in babu kenan, ya mika mata ta karbe da hannu biyu, yazo yana shirgaki" Wannan karin su duka sukayi dariya banda Aziza da maganar ta bata mata rai sosai "Meye kuma shagamu? Kefa Nabila kina da matsala" Mimi tace "Ciki mana, ba haka suke zuwa suna samun su Aziza suna shirga musu karya ba, yanzun daya shiga gida zakiga ba zai sake waya dake ba sai gobe idan ya fito, makirin" Fuska sosai Aziza ta sake daurewa "To ni ba waya ba, wallahi har video call munyi dashi jiya da daddare, yana gidan nashi kuma balle wata waya" Hassana tayi mata wani kallo "Video call da daddare? Ita matar tashi tana ina?" Dan murmushi tayi "Nace miki fa wata dusa ce yake aure, tana can tana baccin asara mana" Aziza ta bata amsa sunayin dariya tare da Nabila, amman banda Hassana da fuskarta ke kara hadewa waje daya "Amman kinsan daga ke harshi baku kyauta mata ba, saboda abune da idan akayi miki shi ke ba zakiji dadi ba" Mima ce ta karbe zancen "Babu wani rashin jin dadi, aina dauka shirga mun kawa yakeyi, in har yana video call da ita a gida to da gaske waccen batama san ciwon kanta ba balle har tayi muhimmancin a wajen miji, idan irin wannan wawayen matan ne to fa kwace miji a hannunsu ba zaiyi wuya ba, ke dai kawai ki shiga da shirinki" Ganin kome zata fada ba zasu taba fahimtarta ba,sai tayi shiru, amman ita tayi samari masu mata, bama guda daya ba. Ita asalima bataso ka kwaso mata maganar matarka, sannan in dai ka shiga gida, tasan lokacin komawarka gida yayi, koya zaka kirata ba zata amsa maka ba, da yake da anyi isha'i in ba wani abu zatayi ba, kwanciya takeyi tai bacci, ba'a wannan chatting din daren da ita sam. Tana kokarin kiyaye kin yin duk wani abu da ba zataso ayi mata ba a matsayinta na mace to kar tayiwa wata macen. Sai ta cigaba da fere doyar da takeyi tunda daman suna tsakar gidane "Duk dani dai in ba kaddara ba auren mijin watan nan bai kwanta mun ba" Aziza ta kalli Mimi "Nifa na kasa gane wannan maganar ta mijin wata, waishi namijin inace don mace hudu aka halicce shi? Sai wata ta kwakume tace ita kadai zata rayu dashi, ni wallahi babu wani mijin wata, mijinmu dai" Nan fa musu ya kaure tsakanin Mima da Aziza da kowa yaki fahimtar dan uwanshi, ganin abin na neman zama rigima Nabila ta katse su da fadin "Kuna da fadin, yanzun fa akayi azahar, kuna nema ku karar da dan energy din naku akan gardamar da banga amfaninta ba, kowa ba sai ya auri wanda yayi masa ba" Kafin su amsa Hassana tace "Ni iskancin kawo mun dinki a kurarren lokaci ma nake so ku duka ku bari, nayi muku magana kunqi jiko, to zaku sha mamaki wannan karin" Su duka sai suka koma lallashinta, dan sun san Hassana, tsaf zata iya kin dinkawa ko da kuwa tana da lokaci, gashi sun kasa sake wani wajen dinkin, bayan kwarewar da tayi, suna samun rangwame saboda kawancen da yake tsakaninsu. Duk da haka Aziza da Nabila saida suka sake zantawa akan Baffa da suka tashi tafiya tunda hanyar su daya ce, acan ma suka bar Mima da yake ita bata da nisa da gidan Hassana din, unguwa dayace, layi biyu ne ya rabasu A lokacin da Nabila take karawa Aziza kwarin gwiwar shiga gidan Baffa, da kuma karin dabarun da zatayi amfani dasu ta kamashi a hannu, wasu dabaru da take hadawa da fatan bawai ta kama Baffa kawai ba, a'a ta jijjige Jamila daga gidan gabaki daya ta rayu ita dashi su kadai. Shikuma yana can shago ulcer din da bashi da ita na neman duk wata hanya da zasu kulla zumunta... ********************** ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** ************************* ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** **************************