🌺 *HAMDAH* 🌺 *WASA FARIN GIRKI!!*âœðŸ? *NA* *RASHEEDA S DIRECTOR* _(Book 3)_ _(Bismillahirrahmanurrahim.) Alhamdulillah ina yiwa Ubangiji buwayi gagara misali godiya da ya kuma bani iko a karo na uku nakuma dawowa domin kawo muku cigaban labarin HAMDAH ina rokon Allah ya bani ikon kammala shi lafiyaðŸ‘ðŸ»_ (Afwan a karshen book 2 nasaka (After 1 year) I'm so sorry typing ero ne👌ðŸ») Littafin na siyar wa ne ki biya ki karan ta. domin biyan kuÉ—in littafin sai ka-ki tuntuÉ“i wannan number 08034690723 🅿ï¸?1 Bayan wani lokaci. Tuni ai kin hajji ya karato gamasu niyya tuni aka fara shirye-shiryen tafiya ai kin hajji. kan kace me kasar Saudiyya tacika tayi makil da al'ummar Musulmi. yanzu bama samun wani zama kullum muna hanyar zuwa bautar Ubangiji, ba dare ba rana kullum Bappa na tasani gaba wani sa'in tare muke tafiya da su Naseem da Nasmah,wani sa'in kuma na barsu wa Mammaa mahaifiyar Ukhtee kawata da nayi anan cikin masarautar Saudi jika ga Masarautar Saudi. dan tare muke tafiya da Ukhtee ita kuma Mammaa ciwon kafa ke damun ta bana bazata samu daman fita afara aikin hajji da itaba. acewar ta sai an zurfafa ibada sosai kan lokacin Abdul Malik yayan Ukhtee da yake karatu can jami'ar Madina yashigo zai fita da ita guraren ibada a kan keken zama irin na masu ciwon kafa. kasan cewar na yaye su Nasmah kuma suna cin komai gashi sun saba da matar sosai, shi yasa wahalar su ta É—anyi min sauki ko zamu fita ban cika tafiya da suba.... cikin yarda da buwayar Ubangiji aka kamla ai kin hajji na wannan shekaran lafiya.â˜? tuni mahajjata suka fara komawa kasashen su,nan muma muka fara shiri damin ko mawa kasar mu. ana gobe jirgin mu zata É—aga. tun safiyar ranar jama'ar dake cikin masarautar sukayi ta zuwa sallamar mu. duk wan da yazo sai ya nuna baison tafiyar mu wasu ga fuskokin su wasu kuwa sai sun kai ga furtawa. Ukhtee da Mammaa da tun safiyar ranar muke tare da su a side É—in mu, suka tirje wai sam sai dai Bappa ya barni a nan, ai ko nan kowa yace ya barni shi ya tafi bayan wani lokaci sai na koma. ni dai dariya kawai nake binsu da shi, sai dai zuwa yanzu jikina yayi sanyi ganin yan da Ukhtee take kuka. bilhakki ta rungume Nasmah tana faÉ—in bazan tafi ba. Bappa ko ido yake binsu da shi cike da mamakin ganin zunzurutun kauna gun waÉ—an nan larabawan. ana cikin haka kiran Mahmoud ya shigo wayar Bapp. nan yake sanar wa Bappa yasami masaniya daga shugaban kasar mu anfara duk ayyukan dana lissafa kuma bazai É—au wani lokaci ba insha Allah za'a gama, Bappa yayi fatan alheri kana yakashe wayar. koda naji labarin daga bakin Bappa nayi matukar mamaki dan ni har yau ganin abun nake kamar wasa bazai yiwu ba. Bappa ya mai da hankalin sa kan mutanen da suke cikin parlour'n, abun da ya lura shine suna matukar son ba'i musamman wata kabilar, bugu da kari wan da Allah ya É—aukaka a cikin su, babu garin da zai waye wasu daga wasu unguwanni daban-daban wasu kuma daga É—an garuruwan dake gefen gari basu shigo ganina ba, na zamo abun kallo da hira a gurin su, haka zasuyi ta hotuna da ni da su Naseem. numfashi Bappa ya sauke ganin gabaki É—ayan su kalma guda suke nanatawa.. dun dole Bappa ya amsa musu badun yaso ba da sharaÉ—in zasu sako ni a jirgi nan da É—an kwanaki kaÉ—an. ai kuwa ihun murna Ukhtee ta sake ta rungume ni tana sunbata. gaba ki É—aya parlour'n yakaceme da murna... washegari da misalin karfe 4 na asuba jirgin su Bappa ya É—aga suwa kasar mu ta gado wato Nigeriaâ˜?. kafin ya tafi sai da yayi ta min nasihohi da jan hankali mai ratsa jiki.. tun da Bappa ya koma kusan kullum sai munyi waya ta wayar Ukhtee har da su Inna wuro. Alhmdllh bazan ce komai ba game da zamata anan cikin masarautar Saudi batun samin kula da tarairaya ni da Æ´aÆ´ana kuwa ba'a magana... A can kasar Nigeria cikin garin Bauchi state. Na'ima ce da kawar ta Raliya,tafe cikin mota suka É—au hanyar wani asibiti dake nan cikin G.R.A wan da shine Na'imar ke zuwa awo. Raliya ke jan motar Na'ima na zaune a gefen mai zaman banza. Raliya ta É—an muskuta ta dubi kawar tata kana ta mai da idanun ta kan titi tare da faÉ—in "Aminiya yanzu yanda kika tsaran nan kina ganin hakan zai yuwu kuwa baza'a sami wata matsala ba dai ko?". Na'ima tasauke numfashi tare da gyara zaman ta cikin karfafawa da gaskata muradin ta tace "Kada ki damu aminiya Nice fa Na'ima baza'a sami wata matsala ba tabbas zai yiwu zai yiwu, yau É—in nan kuwa zan haihu, Raliya ina cikin haÉ—ari dole ne kawai na ai watar da hakan, kinsan kuwa jiya da daddare muna kwance da SALEEM yaÉ—aga rigata yana duban cikin yace shi har yanzu baya ganin garman cikin ciki wata 7 amma har yanzu bai taso ba, kin san me yafi firgitani kuwa?". tayi tambayar tana duban Raliya. Raliya ta girgiza kai cikin takai ci taci gaba da faÉ—in "Aminiya sunan wancan É“atacciyar yarin yar, ya kira min har da min misali da ita, wai lokacin da take da ciki bai cika wata huÉ—u bama amma yaÉ—an taso". ido Raliya ta waro tace "What! ya akayi har ya iya tunota? to gaskiya kawata kada kiyi wasa". Na'ima cikin damuwa da bakin cikin tuno da HAMDAH da SALEEM yayi tace "Shiyasa nake son bin duk wata kofar da zaibi ya tuno da wancan banzar É“atacciyar da ko a muce ko a raye oho, duk wata kofar zanbi na toshe duk da nasan bayida wani kataÉ“us, ko da ya tuno tan ma, amma ni kwata-kwata bana son na rikajin kwatankwacin irin sunan ta a bakin sa, bakiji abun da boka yace min ba, yana son yara sosai hakan zai iya yin tasiri wajen rika tuno ta da ita da abun da ke cikin ta duk da hakan ba wani abun damuwa bane amma ni dai sam bana son jin kalmar sunan ta kan laɓɓan sa, to ko yau da safen nan ma muna kwance dashi yaÉ—aga rigata yana shafa cikin yace wai anya abun da ke cikin nan yana da lafiya kuwa shi baya ganin yana girma, nace masa ai jikina yabi Allah ya taimaka ma ina da tumbi,ke nifa kullum a narka abinci nake aciki na in kika ga abincin da nake ci yanzu wai dun kawai tumbi na ya kara girma, yanzu Raliya cikin nan wata 7 ne yana daf da shiga wata 8 yazama dole na É—au mataki in ba hakaba komai zai iya É“aci, kin ga wancan hatsabibiyar kanwar tasa Rafee'at ranar da muka haÉ—u a gidan su har habai ci take min wai mai cikin tuwo, ni har na fara zargin ko ta gane ne". Raliya ta saki dariya har tana dukan sitiyarin motar tana faÉ—in "Ai wannan Rafee'at É—in shegiyar gaske ce sai ana taka mata burki". dai-dai nan suka isa get É—in asibitin, hon Raliya tayi mai tsoron bakin get É—in yawan gale musu get. a gefe in da aka tanada dan ajiye motoci suka faka suka fito suka nufi cikin sibitin. kofar wani office direct suka nufa tare da yin knocking, daga cikin office É—in aka basu izinin shigo wa. wanda ke cikin office É—in yana zaune cikin shigar likitoci yana ganin su ya washe baki tare da faÉ—in. "A'a manyan kasa kune tafe?". cikin fari da ido Raliya taja kujerar da ke fuskantar sa ta zauna tana faÉ—in. "Kanana dai ai kune manyan kuna zaune AC na ratsa ku kuÉ—i na shiga yadda yakamata me yamuku saura?". Na'ima ma kujerar taja tazauna kana suka shiga gaisawa, suna É—an taÉ“a hira da dariya sakanin su da kagan su kasan tabbas sunyiwa juna farin sani. Dr Mukhtar Lawan abokin su Na'ima ne sosai abota ne na tun a makaranta duk kanin su gar tasan garne, duk wani iskanci da sheke ayar da sukayi lokacin suna makaran ta tare sukeyi, har kuma yanzu wani kullin tare suke tufke shi. acikin su shine kaÉ—ai yaÉ—an maida hankali kan karatu har yake cin moriyar karatun da yanzu yake a matakin Dr, asibitin mallakin sa ne wan da mahaifinsa yagina masa bayan zamowar sa Dr. duk hirar da suke Dr Mukhtar idanunsa a kan Raliya,yakafe kirjin ta da ido wan da É—inkin rigar jikin ta ya bayyanar da nonuwan ta kusan rabi a waje. fiki-fiki yayi da ido cikin yanayin shiga tarkon Raliya yadubi Na'ima kana yace "Na'ima kawarki Raliya takini fa taki na ganta kwata-kwata yanzu ko waya na kirata muÉ—an haÉ—u taki ta bani da ma mu haÉ—u, sabo da tasami manya wan da suka fimu bata hurÉ—a da mu". yakarashe maganar da mai da idanunsa kan Raliya wacce tadaÉ—a bankaro kirji tana wani fari da ido. dariya Na'ima tayi tace "Kai haba aminiya ai ko ba komai dai zakizo wannan haÉ—aÉ—É—en office É—in kiÉ—an rika É—ebe maba kewa." fuska Raliya ta yamutsa cikin salon kwarewa a harkar bariki takuma bankaro kirji yayin da yatsarta guda ke saman wuyan ta tana É—an yawo da shi har zuwa kirjin ta, ta saman nonuwan ta,ido ta kanne a kansa kana tace. "Dr kenan ku abun naku ai sai a hankali in ka shirya yanzu Na'ima ta wuce ta bamu guri amma yanzu zaka ajiye min rabin miliyan anan shima É—in dai-dai azo sallama ne". tanuna saman table É—in gaban sa. ido ya waro da karfi ya furta "500k ai ko ai kina na wata guda bai kai rabin miliyon ba". dariya duka suka saka. Dr Mukhtar yace "Ina kinji ko Na'ima kawar ki tafi karfi na sai dai mugani kawai mu latse baki, ko za'a É—an taimaka min naÉ—an lallasa ne basai ciki ba iya waje kawai". yakarasher maganar da dariya haÉ—e da tsigar zolaya. baki Raliya ta taÉ“e tana faÉ—in "Yanzu dai muyi abun da yakawo mu, Dr muna da damuwa fa". Na'ima ta karÉ“i zancen da faÉ—in "Kwarai kuwa Dr akwai matsala". yace "Wani damuwa kuma ai ni a tunani na yanzu bakuda wata sauran ragowar damuwa ke Na'ima da kike da SALEEM a hannun ki". "A'a Dr gaskiya da saura nasame shi kam amma da saura munaso mukuma samin shi sosai yazamo nawan da gasken gaske". zaman ta ta gyara da kyau ta daÉ—a fuskantar shi kana tace "Dr yau nazo haihuwa". ido yawaro yace "Haihuwa kuma antaÉ“a haihuwar da ba ciki?". yafa da dariya sai kuma yakuma sakin dariyar shakiyyanci yace "To ai cikin naki baikai na haihuwa ba tukun". wani goron numfashi ta sauke kana ta daÉ—a gyara zaman ta da kyau tace "Dr tunani na kenan ranar da cikin nan zaikai na haihuwa, ace ciki yayi wata tara yaya zanyi narasa yanda zanyi, rabon da naji wani abu yasani shiga damuwa irin haka na mance, Dr taya zanyi nasami É—a kune manya aikin kune kunfimu sanin yadda za'ayi". jakar hannunta ta aje gefe kana taÉ—aura hannayenta biyu kan teburin gaban su sannan tacigaba da faÉ—in. "Ko nawa ne zan biya har idan nima bukatata zata biya". ÆŠan shiru yayi yayin da yake É—an juyawa kan kujerar da yake kai, sannan yasauke numfashi kana yace "Gaskiya wannan buka taki babbace a gaskiya yanzu samin É—a a cikin asibitin nan da kamar wuya, yanzu an saka matakan tsaro iri-iri, kinsan kwanaki fa munyi ta shari'a da wasu mutane wan da mukayi musu canjen É—a,munyi ta samin matsala dan ma allah ya rufa asiri, amma mezai hana tun da kince kinason É—an cikin gaggawa kije gidan marayu, gidan marayu yakamata kije, akwai wan da suka haifi Æ´aÆ´a zaki iya samin wan da yau ma ta haifa ta yar aka samu aka kai shi gidan marayun, to inaga kije ki É—auka a can É—in zaifi". kai Raliya ta jinjina alamun gamsuwa da shawarin nasa tace "Eh gaskiya hakan ma kawai za'ayi gidan marayun zamuje mu samo É—an acan kagama babu wanda ya isa ya zarge mu, sukuma hukumar gidan marayun zamusan yadda zamuyi da su tun da akwai Æ´aÆ´an banki". Shiru Na'ima tayi yayin da ta zurma cikin tunani naÉ—an wani lokaci kana ta ce "To shike nan amma kuna ganin baza'a sami wata matsala ba ko?, dan nifa bana so maganar tafita naso ace munyi shi anan sakanin mu basai ansako wasu ciki ba". Dr Mukhtar yace "Ai samun É—a a gidan marayu shine kawai mafita kuma rufin asiri, tun da jakar ku na cike da makullin kulle bakin wasu ai an gama, idan mukace a nan ne zamu samu to za'a iya samin matsala dan har yanzu asibitin nan idon hukuma yana kansa sun saka ido sosai suna jiran suji wani abun yakuma fita su sami mafakar hujjojin da suka tara, wan da naki bada damar hujjar tasu tayi aiki idan da kuÉ—i meye bazamuyi ba". ido Raliya ta kanne tace "Wai wan da kayiwa ai kin nan nawa ne yabaka haka?". wani munafukar dariya yayi kana yace "Miliyan 10 tabani kuma ko wani wata ina É—aukar albashi daga gurin ta". "Bayan 10 million tana kan baka wani kuÉ—in kuma?". Na'ima tayi maganar da fuskar mamaki. yace "To ai kin wasa nayi mata kaÉ—an fa yarage yataÉ“a nawa aikin dan ma Dad yatsaya da gaske kan lamarin, canjin É—a ai bakaramin kasada bane, jigo na canza mata da shi É—a na miji na musan ya mata da mace, to kuÉ—in wasa suke samu a kasar nan 10 million wani kuÉ—i ne agurin su, duk wata 300k nake É—au ka a gurin ta tukuicin godiya." dariya suka sheke da shi cikin muryar dariya Na'ima tace "Kai Mukhtar wlh bakada dama shine ko É—an salalan nan babu." "Haba wani salala ke me zakiyi da kuÉ—i yanzu kinada jakar kuÉ—i a gefen ki, kinada ABDALLAH IDRIS ABDALLAH me kuma zakiyi da kuÉ—i, ai nine abun a taimaka dan ko Raliya kuÉ—in da take samu bani samun irin sa". mikewa Na'ima tayi tana faÉ—in "Kace dai bazaka bamu ba kawai musan in da muka ajiye ka, aminiya tashi mutafi gidan marayun nan yanzu ba'a bori da sanyin jiki". zai yi magana sai kuma yayi shiru sakamakon hayaniyar da yaji ke É—an tashi daga can waje da alama a cikin parlou'n asibitin ne in da mutane ke zama dan jiran ganin likita. wata nurse ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izinin shigowa, É—an rusunawa tayi tace "Sir gawasu sun zo da alama haihuwa ce sai dai basuzo da kayan haihuwa ba, nace sukawo kuÉ—in kayan haihuwar sunce basuda kuÉ—i,nace to su koma suzo da kuÉ—i sunki tafiya, kuma yara ne dukan su nayi ta tuhumar su ina iyayen su sunyi shiru na ce suje su kira babba san nan su taho da kayan karÉ“ar haihuwa ko kuÉ—in kayan tunda akwai anan sunki tafiya,kuma da alamu labour take sosai zata iya haihuwa cikin mintuna kalilan gasu can zaune a parlour sunki tafiya." Dr yace "Yara kuma? akira su su shigo." tace "Okay sir." tajuya da sauri ta fita, jim kaÉ—an suka shigo, tana gaba Æ´ammata biyu na biye da ita É—aya da ciki rukuku É—ayar kuma tana tallafe da ita, sanye da uniform ajikin ta. da kaga mai cikin da alama nakuda take sosai dan sai tauna baki da yarfe hannu take tana ta faman zubda kwalla da faÉ—in "Wayyo nashiga uku." Dr yadubi wacce suke tare da mai cikin yace "Me yake faruwa wace matsalar ke tafe da ku?." tace "Haihuwa tazo shine na rako ta." Na'ima da Raliya kuwa ido suka zubawa yaran wan da akalla shekarun su bazai wuce 16 ba. Dr Mukhtar yace "Ke kaÉ—ai kika rakota haihuwar ina iyayen ku?". shiru yarinyar tayi tana duban mai cikin da sai daÉ—a shiga yanayin nakuda gadan-gadan take. sai kuma ta dubi likitan cikin rauni tace "Iyayen ta suna gida nima kawai tazone tace narako ta asibiti." É—an shiru Dr mukhtar yayi idanunsa a kansu kana yace "To ina mijin ki?." yayi maganar idanunsa akan mai cikin. duk kanin su shiru sukayi sai raba ido suke, ido ya kure su da kyau yakuma faÉ—in "Nace ina mijin ta? ita kaÉ—ai zata taho haihuwa babu wani babba ko shi mijin baisan haihuwar yataso bane kirashi a waya yanzu yazo dan bana karÉ“ar haihuwa sai an ajiye kuÉ—i an kuma sa hannu tukun". Cikin kame kame Æ´arrakiyar tashiga faÉ—in "Um..um mijin..ta..mijin ta." sai kuma tayi shiru. duban mai labour É—in yayi da kyau yace "Kirawo mijin ki yanzu yazo kice masa bazamu karÉ“e kiba har sai yazo." kasa tayi da kanta batare da tace komai ba sai hawayen da ke cigaba da sauka a idon ta, girgiza kai yayi kana yace "Ba miji kenan wannan ciki ba uba baya da uba ko?". da sauri Æ´ar rakiyar ta gyaÉ—a kai tana tsilli-tsilli da ido kamar an tare É“era kana cikin in-ina tace "Wlhy likita tsautsayi aka samu bata da miji, kuma yanzu iyayen ta sun kore ta da sukaga tana labour sun ce tafita musu a gida taje can ta haihu ba a gidan suba, shine tazo gidan mu nikuma naga kamar zata mutu shine na rakota asibiti, dan Allah likita ka taimaka mata." gaba É—aya suka zuba musu ido. wani murmushi Raliya ta sake. ido Na'ima ta bita da shi dan tasan ma'nar murmushin nan nata tace "Aminiya sabon shiga harka ko?". baki Raliya ta taÉ“e tare da faÉ—in "Oh yaro man kaza har yaushe zakayi sake irin haka ta kasance, ka É—aukar wa kanka wahala shi ba mai uba ba wahalarka a banza, uban titi da bazai kalleka cikin halin labour yace ma sannu ba, tuni ban wanke shi na zubar ba in ma yasami shiga kenan mttss". taja wani dogon tsaki tare da faÉ—in "Kara mar Æ´ar iska bata san yan da zatayi iskancin bama." Dr Mukhtar da Na'ima kasan cewar suna kusa ne suna juyo duk abun da take fata akasin su da suke tsaye a sakiyar office É—in. Dr Mukhtar yayi murmushi tare da faÉ—in "Ko zaki sata a hanya ne idan ta sauke kayan dake jikin ta". harara ta dalla masa tare da kuma jan wani gajeren tsaki. Dr Mukhtar ya mai da duban sa kan yaran sannan yace "To a gaskiya bazamu karÉ“i haihuwar ba, na É—aya babu kuÉ—in karÉ“ar haihuwa sannan babu wani babba a tare da ku, bazamu karmi haihuwar ba saboda gudun matsala, bugu da kari kuma É—an bashi da uba, muzo mu karÉ“i haihuwa wani abu ya faru azo a dakatar min da asibiti gaskiya yanzu na daina irin wannan kasadar gaskiya kuje kawai kuje wani asibitin." Da sauri Na'ima da Raliya suka juyo a tare tare da yiwa junan su kallon-kallo, sai kuma da sauri Na'ima ta juyo gun Dr tace "Dr a taima musu a karÉ“i haihuwar ni zan biya kuÉ—in duk wani É—awai niyar da za'ayi ni zan biya, zan kuma tsaya wajen ganin ba'a sami wata matsala ba, aje a kaita labour room." kai Dr Mukhtar ya jinjina kana yace "Okay." yadubi nurse É—in yace "Akai ta labour room. tace "Okay sir." tajuya da sauri tana faÉ—in "Kubiyo ni." suka fita dukan su mai labour'n da kawar tata. suna fita da sauri Raliya ta dubi Na'ima zatayi magana Na'ima tayi saurin soma yiwa Dr mukhtar magana. "Dr irin su ne idan suka haihu suke kashe É—an, har idan akabar ta ta tafi bazataje wani asibitin ba wani gun zataje ta haihu ta kashe É—an, ko kuma ta jefar da shi to ni ina son abun da zata hai fa har idan na miji ne." Dr mukhtar yayi wani dariya tare da faÉ—in "Ai tun É—azu na fahimci hakan ai tun da naga kuna wannan kallon-kallon Na'ima Raliya bakuda kyau sai an haÉ—a da wanka, ai na san hali tun a makaranta har idan kukayi wannan kallon-kallon to wata tsiyar za'a kulla." dariya suka sheke da shi suka tafa kana shima ya miko hannu suka tafa da shi dukan su. zaman sa zagyar da kyau sannan yace "To meye kaso na a ciki?." Na'ima tace "Kana da kaso mai tsoka yanzu dai kaje ka bata kulawa ta haihu kuma kayi fatan namiji zata haifa, yau nima zan haihu." yace "kwarai kuwa har an shiga dake labour room". dariya suka saka dukan su. Nan sukayi ta wasu magan ganun su sakanin su batare da ni naji ko fahimtar me suke nufi ba.. Bayan awa uku, kukan jariri ne ya soma tashi daga cikin labour room, Na'ima da Raliya da har yanzu suna zaune a office É—in Dr Mukhtar suka wani saki murmushi, lokacin da sakon Dr Mukhtar yashigo wayar Raliya wato tex message yana sanar musu da abun da aka haifa, ciki murmushin mai kunshe da ma'anoni da dama Raliya tace "Kai sannu Na'ima kin sauka lafiya kai gaskiya haihuwa akwai wuya kinsha fama yau." itama wani dariya ta sake cikin kware wa a zunzurutun makirci da hatsabiban ci tace "Na haihu yau ni Na'ima gaskiya haihuwa a kwai wuya". darika suka kuma shekewa sukatafa. Dr Mukhtar da yanzu shigowar sa office É—in bayan ya amshi haihuwar, zama yayi kan kujerar sa yana faÉ—in "Gaskiya yau ba sauki oga SALEEM ya haihu um wayaga oga SALEEM da É—a abun ba sauki hhhhh". "Shima yazama baba ni kuma mama". Na'ima ta faÉ—a tana wani faÉ—i. nurse ce tayi knocking tashigo taÉ—an dukar da kai tana faÉ—in "Sir an gama kimsa komai sai dai har yanzu tana bledin, munyi iya kokarin mu bai tsaya ba ko zaka zo ka duba ta." kai ya girgiza kana nurse É—in ta fita da sauri, a tare Na'ima da Raliya suka mike ganin Dr shima ya mike sukabi bayan sa. dukan su suka shiga É—akin da aka tanada domin haihuwa. nan da nan yasoma baiwa yarin yar taimakon gaggawa ganin yan da jini ke fita a jikin ta, batare da É“ata lokaci ba tadawo cikin hayyacin ta ,jinin kuma ya tsaya. jaririn da nurse's suka gyara shi suka kunshi cikin É—ankwalin mahaifiyar sa sai musu-musu da kuka yake ga dukkan alama niman abinci yake, nurse ta É—ago shi ta maso gaban gadon da mamarsa take, wan da a Æ´an min tunan da ta sami kanta bayan Dr yabata taimakon da ya kamata har ta iya mikewa tazaune. tamika mata shi tana faÉ—in "Ga abun da kika haifa nan kuma da alama niman abinci yake gashi bakuzo da flas ba, bare a bashi ruwan zafi ya sha." kin karbar sa tayi sai kukan da ta fashe da shi. kawar ta da suka zo tare ita ta karÉ“i É—an tashiga jijjiga shi, wayar ta dake cikin aljuhun wandon makarantar jikin ta yasoma kara alamar shigowar kira,da sauri takai hannunta guda ta cusa cikin aljuhun wan donta, É—aya hannun kuma ta gyara rukon jaririn da kyau ta zaro wayar. ido ta waro kan screen É—in wayar murya cike da tsoro tace "Mama." sai kuma da sauri taÉ—aga kiran takai wayar kunnen ta tare da yin sallama. É—an shiru tayi sai kuma tace "Mama gani nan dawowa an tashi ne bansami abun hawa ba shine yasa na tsaya". tana sauke wayar da sauri tadubi kawar tata tace "Mama ce takira ni taga lokacin tashi yayi har yanzu ban koma gidaba, bayan ko makarantar ma banje ba,ni sai yanzu ma na ga agogo tun É—azu lokacin tashi yayi, tofa zantafi gida yanzu yaya zamuyi ina tsoro kada Baba yadawo yasamu ban dawo ba, kema zaki tafi gida ba kawai tun da yanzu kin haihu? muje na rakaki gidan ku nima sai na wuce gida, karfa Mama tasa yayu na su biyo ni kin san fa in nakai wannan lokacin sawa take aje a nimo ni". tana maganar ne cikin tsaro sosai. itako mai jego kuka kawai take takasa cewa komai. Dr yace "A'a taya za'ayi ta tafi yanzu bayan yanzu ta dawo hayyacin ta,sai mun daÉ—a ganin yanayin jikin nata kafin mu sallame ta, yanzu kam ma allurar da akai mata zai fara ai ki in tayi bacci ta farka mukaga yanayin karfin jikin ta sai mu sallame ta, yanzu dai ke kije tun da ke a na kiran ki." to tace da sauri ta mika mata É—an, yanzu ma kin karÉ“ar É—an tayi. Raliya ce ta karÉ“i É—an a hannunta tace "To kije kawai." ai ko tafita da sauri. bayan fitar ta Dr Mukhtar ya dubi yarinyar yace ta kwanta ta sami bacci, a hankali ta gyara kwanciyar ta,su kuma suka fita suka koma, office É—in sa. suna zama Na'ima tace "Bani É—an na ganshi." Raliya ta mika mata kyakkyawa fari kuwa da shi, sai dai yaron bashida girma É—an kankani ne hakan kuwa bazai rasa nasaba da rashin samun kulawa da ya kamata tun aciki ba. takafe shi da ido tana wani irin murmushi tana É—an jijjiga yaron. after 4 hr. hakan kuwa yayi dai-dai da farkawar yarinyar da ta haihun a bacci, alhmdllh taji karfin jikin ta kwarai. nan tanimi tafiya gida nurse tazo ta sanar wa Dr yace taje ta kira ta. tare nurse É—in suka shigo da yarin yar,ya nuna mata kujera ta zauna kana yacewa nurse É—in taÉ—an basu guri, nan ta fita tajawo musu kofa. duban yarinyar yayi kana ya ce "Inane gidan ku". cikin kame-kame tashiga faÉ—in "Um..um..gidan mu gidan mu." sai kuma tayi shiru. da kyau yakuma duban ta sannan ya ce "Bana son wani É“oye-É“oye nasan wannan É—an bashi da uba cikin shege ne dan haka kawai tan bayar ki nake ki bani amsa inane gidan ku?." kwalla ta matse tare da mutsutstsike yatsun ta kana ta soma magana, "Gidan mu yana..yana Unguwar Bakaro". kai ya jinjina yace "A Bakaro kike?." ta gyaÉ—a kai, Raliya ta jinjina kai kana ta ce "Ah to shikuma uban É—an a ina yake shima a Bakaron yake?". tace Eh. "To yan zun ina zakije keda É—an idan kika fita daga nan?". Raliya tayi mata tambayar tana dubam ta, shiru tayi tare da musutssuke yatsun hannunta. Dr Mukhtar yaÉ—an tsura mata ido kana yace "Yanzu ina zaki kai É—an idan aka baki shi?." kuka tafashe da shi tana faÉ—in "Wlh idan na tafi da shi gida yan kani za'ayi wlh iyayena sun ce sai sun yanka ni yanzu ma in na koma gida nasan suka na za'ayi idan na tafi da shi zasu yanka ni". kuka take sosai tana faÉ—in zasu yanka ta, Na'ima kuwa carap tayi tace "To ni zan rike miki É—an ni ina son shi nasan idan kika fita yaddashi zakiyi ko ba haka ba?". tafaÉ—a tana duban ta. da sauri yarin yar ta gyaÉ—a kai tace "Wlh in natafi da shi gida ne za'a yanka ni in naje dashi gida ne." Na'ima ta ce "To ya isa, in kika je da shi gida ne za'a yanka ki idan kika fita da shi daga nan kuma yaddashi zakiyi to ni ina son shi zan rike shi". hannu ta saka ta buÉ—e jaka ta ciro kuÉ—i masu yawa gudan dubu-duba ne a É—aÉ—É—aure É—auri uku,wacce a kalla ko wani É—auri guda yakai 100k ta mika wa yarin yar tana faÉ—in "KarÉ“a in kinje kya nima abun da zaki rika ci wan da yakamata masu jego suci, ba sai kin jira iyayen ki sun yi miki ba tun da nasan cewa bayimiki zasuyi ba, da ma ace É—an da uba ne tun da bashi da shi kuwa ba mai saurarar ki, gashi sai kije kiyi jego shikuma É—an ina son shi zan rike shi, dan bazan iya zuba ido ina gani azalinci É—an da baiji ba baigani ba ku mutane kurika jin tsoron Allah, É—an da bai san komai ba aje a jefar da shi ko a kashe shi." da sauri yarin yar ta mika hannu ta karÉ“i kuÉ—in har hanunta na rawa ganin yawan kuÉ—in, kana ta yimusu godiya ta mike da sauri ta fita, har takai bakin kofa Na'ima tace "Idan kikaje gida aka tanbaye ki ina abun da kika haifa sai kice yana ina?." "Ya mutu tun a ciki!." tayi maganar cike da karfafawa tana daÉ—a dunkule makudan kuÉ—in da ta bata. murmushi Na'ima tayi tare da faÉ—in "Da kyau." da sauri yarin yar tayi waje ta haye abun hawa ta wuce gidan su cikin zillumi da tsoro.. bayan fitar yarinyar Raliya da Dr Mukhtar suka tuntsire da dariya, cikin muryar dariya Dr Mukhtar yace "Kin ji Na'ima har da É—an guntun wa'azin ta wai ku mutane kurika jin tsoron Allah tun da kin samu a sama ai dole kijefo wa'azi ciki hhhhh." "In da kuÉ—i meye bazan samu ba kai bakaji takashe É—an nata tun a ciki ba, wannan kuma ni na haifa." tayi maganar tana leko fuskar yaron da yake baccin sa. Dr mukhtar ya gyara zama tare da sauke numfashi sannan ya ce "To yan zu ya za'ayi ne?." tace "Dr ni da na haihu kuma me yazaunar da ni a nan a kaini labour room mana." dariya ya sheke dashi Raliya ma dariyar tayi tana faÉ—in "Ai kuwa mai jego a gado yakamata a same ta a kwance ba'a zaune a office É—in likita ba." nan suka mike suka nufi labour room bayan sun gama shirya duk yan da abun zai tafi. suna shiga ta haura gado ta kwanta, tayi shame-shame kamar wacce ta haihu da gaske. Waya Na'ima ta mikawa Raliya tace "Kirashi a waya". Raliya ta amsa ta danna number SALEEM......! Mommyn Twins ce 🌺 *HAMDAH* 🌺 *WASA FARIN GIRKI!!*âœðŸ? *NA* *RASHEEDA S DIRECTOR* _(Book 3)_ Littafin na siyar wa ne ki biya ki karan ta. domin biyan kuÉ—in littafin sai ka-ki tuntuÉ“i wannan number 08034690723 🅿ï¸?2 Wayar tayi ta ringing har ya yanke bai É—aga ba, ta dubi Na'ima tace "Bai É—aga bafa. " ta ce "Sake kiran shi kin san shi ai murÉ—aÉ—É—en mutum ne idan baiyi ra'ayi ba bazai É—aga ba yanzu haka wayar tana kusa da shi É—agawar ne dai baiga dama ba." kuma kiran nasa tayi namma har ya yanke bai É—aga ba, sai da ta kirashi har sau uku a na huÉ—u ne ya É—aga. ganin ya É—aga kiran takai wayar kunnen ta tare da faÉ—in "Asslamu'alaikum SALEEMA Raliya ce muna asibiti da Na'ima tahaihu." SALEEM dake zaune a office yana ta tarkasa Æ´an kayakin sa dan locin tashin sa yayi har ya wuce ma, Æ´an wasu aiyuka ne suka tsaida shi. yamike zumbur yana faÉ—in. "Haihuwa kuma? yaushe cikin nata yakai na haihuwa cikin ya fita kenan?." yajero tanbayar da alamun hankalin sa a É—an tashe yake. ta ce "Eh haihuwa ce ba fita cikin yayi ba sai dai bakwaini ta haifa É—a na miji." numfashi yasauke jin akasin abun da yake zato,shi gaba É—aya jin lamarin na bazata ya mantar da shi zata iya haifar cikin tun da yakai wata bakwai, ya ce "Ina jaririn yake yanzu yana cikin wani hali yana dai lafiya ko?." "Eh gashi can a cikin kwalba." katse wayar yayi batare da yace komai ba, Na'ima da take jin duk abun da yake faÉ—a kasan cewar tasa wayar a amsa kuwa ne ta ce "Lallai ma wannan wato shi ta jaririn yake bazai fa taÉ“a sauyawa duka ba." dariya Raliya tayi tare da faÉ—in "SALEEMA kenan miskili kafi mahaukaci ban haushi bafa zai sauya ba dan kuwa a jinin sa yake." SALEEM na kashe wayar, wayar Mamie ya kira, zaune Mamie take da su Aunty Rafee'at Aunty Jaleela da su Ummi kiran sa ya shigo. bayan sun gaisa yake faÉ—a mata Na'ima ta haihu. "Haihuwa." Mamie tafada da karfi kana ta ce "Wani irin haihuwa ciki wata bakwai." ya fuskanci yanayin da yashi ga lokacin da Raliya ta sanar masa da haihuwar shi Mamie ta shiga yanzu. yace "Eh ta haihu bakwaini ta haifa tana asibiti ma yanzu." "To Allah ya raya." Mamie ta faÉ—a a takaice tare da kashe wayarta. gaba daya hankalin Æ´an cikin parlour'n yakoma kan Mamie, Ummi ce da sauri tace "Wa ta haihu Na'ima ce?". Mamie tace "Wai haka, wai ta haihu". Mamie ta faÉ—a tana taÉ“e baki. Ummi ko baki ta washe tana fadin "Ikon Allah, kaji ikon Allah ko to Allah dai yasa abun da aka haifa nacikin koshin lafiya". baki Mamie takuma taÉ“ewa tare da faÉ—in "Ina kuwa zai zama cikin koshin lafiya ciki wata bakwai sai dai yabada wahala dai". a É“angaren Aunty Jaleela ma fuska ta yamutsa tana faÉ—in "Gayyan wahala dai ciki wata bakwai ai ba arziki." "Ina kuwa arziki duk uban iyayi da cikin ashe dai rabin halitta za'a haifo ba arziki." Aunty Rafee'at ta faÉ—a, tana tura É—ankwali gaban goshi. duk kanin su in ka gansu babu wani mai farin ciki da jin daÉ—in haihuwar, akasin Ummi da fuskarta ke É—auke da annuri bakin ta ya kasa rufuwa sai faÉ—i take "Kai masha Allah Allah dai ya raya mana." mikewa Ummi tayi tana cigaba da faÉ—in "Kai masha Allah zamu wuce asibitin ba yakamata mu tafi asibitin yanzu". Mamie ta kawar da kai gefe tare da faÉ—in "Ummi'n Fauzan ni gaskiya ba yanzu zanje asibitin nan ba gaskiya inaga kamar ina da abun yi, ai dare yayi yanzu ga magriba yakawo kai." Ummi ta girgiza kai tana faÉ—in "Kai Mamie'n Nusaiba yakama ta dai muje yanzu ace babu wani nashi a can gaskiya baiyi ba." fuska Aunty Rafee'at takuma yamutsawa tana faÉ—in "Um ni kamma kucire ni a tafiyar dan yanzu Abba'n Adeel zaizo ya É—auke mu." dakuwa Ummi tayi mata tare da faÉ—in "Maza tashi kushirya ke Jaleela tashi maza muje". Aunty Jaleela da tazo har wuya ta kwaÉ“e fuska kana tace "Ni wlh ina ji ma kamar kar inje dan nima Daddy'n Fadeel nasan zai zo yanzu." haÉ“a Ummi ta rike tana sallallami da kyar dai ta tirsasa musu ta samu suka fita, suka nufi asibitin bayan sun sanar wa su Abbu. A asibitin suka tadda SALEEM shima isowarsa kenan a tare suka shiga cikin asibitin. direct É—akin hutu suka nufa in da nurse tayi musu jagora zuwa ciki,take sanar musu da cewa an mai da Na'ima can domin ta huta. nan suka tadda Na'ima kwance tana ta sauke numfarfashi Raliya na tsaye a kanta tana ta yi mata sannu. da sauri Ummi ta matso in da take tana faÉ—in "Sannu sannu kinji Na'ima, kin sami kanki kalau?". dakyar ta buÉ—e baki cikin yanayin mutum yasha wuya murya can kasan makoshi tace "Lafiya lau." Mamie ko kallo É—aya tayi mata kana tace mata Sannu. namma da kai ta amsa. Aunty Rafee'at kam ko kallo bata ishe taba, Aunty Jaleela ce ma a sama tace mata sannu ita ma. Ya SALEEM da ya naÉ—e hannu a baya yana tsaye tagurin kafafun ta yadan dubeta kana yace "Ina yaron yake?". Raliya tace "Yana can ansashi a kwalba. kai ya jinjina cikin yanayin nan nasa, ya maida duban sa kan nurse É—in da ta yimisu jagora yace "Muje a nuna mana in da yake, ina Dr yake?". ta ce "Yana office". fita sukayi duka har da Raliya, Raliya tayi saurin shigan office É—in Dr tare suka fito da shi, ya mikawa Ya SALEEM hannu suka gaisa ba yabo ba fallasa Ya SALEEM ya amsa masa gaisuwar, kana ya gaida su Mamie sannan ya wuce dasu É—akin da aka ajiye jaririn wan da yake karkashin kulawar na'urori.. Can suka hango jaririn cikin kwalba wan da ake saka jariran dabasu kai watannin haihuwa ba, yanata wutsul-wutsul da kafafunsa. murmushi Raliya tayi a kasan ranta dan ganin shirin su yana tafiya yan da ya kamata. da sauri Ya SALEEM ya karasa jikin kwalbar yana leka cikin kwalbar. su Ummi ma gaba É—ayan su suka karaso jikin kwalbar, Ido Mamie ta kurawa jarijin da ake kiran sa da bakwaini gashi dai ba wani girma yake da shi ba É—an kankani ne, sai dai yanayin sa da wayon faskarsa ya girmi na bakwaini. kai ta girgiza tare da juyawa ta kalli likitar tace "Wannan shine bakwaini an ya ma kuwa anyi lissafin cikin nan dai dai ko dai tara ne an É“ata lissafin kaga yaron da wayon sa." da sauri Raliya tace "Bai cika tara ba bakwai ne ai ko jiya ma sai da mukayi lissafin watannin da ita, yau kuma sai ga haihuwa kingan shi ai É—an misilili da shi". Ummi tace "Ai kuwa gashi É—an kankani irin su idan suka tashi girma sai an gansu dan sai anci tuwo an koshi kafin a iya É—aukar su". Ya SALEEM kam duk baya jin su dan ya gama shagalta da kallon yaron wai shine yau da É—a, wannan É—an nasa ne, wani murmushi yayi a kasan ransa wan da har sai da yabayyano kan fuskarsa. Aunty Rafee'at data kafe yaron da ido tarr sai lokacin tayi magana. "Wai wannan yaron shine bakwaini gaskiya wannan baiyi kamada bakwaini ba sai dai in ku kuka É“ata da lissafin". tayi maganar cikin gatsali. wani kallon sama da kasa Raliya ta bita da shi. Aunty Rafee'at ma irin kallon ta wasa mata tare da girgiza kai tana cigaba da yi mata wani kallon shekeke, sannan ta juya ta fita a cikin É—akin bayan ta gama ai kawa Raliya kallo masu cike da ma'anoni da yawa.. ko minti 30 basuyi a asibitin ba Mamie tace sutafi, haka dai suka fita suka koma gida. Haushi da bakin ciki kamar Na'ima tayi yaya, wai ace kalar gaisuwar da surukar ta zata yi mata kenan, babu wani gaisuwa mai nuna tausaya wa babu wani nuna farin cikin samo mata jika da tayi. Raliya tace "Ni da É—ina da ke gajen hakuri dan Allah kibar wannan maganar kiyi shiru, ke kam dai ba kin haihu ba ina ruwan ki da su, wan da kika haifa masa ne idan ya miki zakiji zafi,ina ruwan ki da su ba wa É—an su kika haifa ba, can ta matse musu ke meye damuwar ki, kinga wannan shegiyar yarinyar zan nuna mata ni Æ´ar bariki ce cikakkiya ma kuwa ciki da waje na, wai shegiyar Rafee'at É—innan kinga wani kallon da take min, kinga wani kallon da take min kuwa, zan nuna mata halina bata sanni bane." Na'ima tace "Him in dai wannan Rafee'at É—in ce ta wuce sammanin ki, wannan yarin yar da kike gani nima inada cikin ta kuma zanyi maganin ta, zan je musamman gurin boka domin yamin maganin ta, zatagane da ni take rabu da ita mance da ita dan wlh sai ta gane kuskuren ta." Jin an murÉ—a handle yasasu yin shiru da zancen nasu, Na'ima ta gyara kwanciyar ta kamar É—azu, ta daÉ—a marairace fuska da shagwaÉ“e fuska. ya karaso bakin gadon yadube ta kana yace "Ya jikin?". cikin makirci da salon iya kirsa tace "My SALEEM kaga É—an mu ko,ya bani wahala yaron nan, É—an ka yabani wahala My SALEEM da kyar na iya haifo shi." gefen fuskarsa ya shafo tare da naÉ—e hannun sa É—aya a bayan sa, "ÆŠa na." yafaÉ—a a kasan zuciyar sa yayin da yake jin wani abu yana tsarga masa mai kama da farin ciki, can karkashin kasan zuciyar sa kuwa, jin wani abu mai nauyi yake yana kokarin tasowa sai kuma yanayi biyun suka shiga kokawa da junan su, yayin da farin cikin ya danne wancan nauyin da yake jin nauyin sa na yau yafi na kullum. har sai da yakai hannu ya dafe kahon zuciyar sa. daga Na'ima har Raliya ido suka zuba masa ganin yan da ya dafe kirjin sa da karfi tare da rumtse idanunsa, wani abu ne ya gilma masa cikin duhuwar kwayar idanunsa da suke a rufe, wani irin bugawa kirjin sa yayi kamar an fizgi zuciyar sa, sai yarika ganin wasu abubuwa guda uku masu haske suna yi masa yawo cikin ido yayin da bugun zuciyarsa ya tsanan ta, dai-dai lokacin da yaga abun suna daÉ—a tunkaro sa tamkar suna tahowa gare sa, a zahiri kuma idanunsa a buÉ—e. sai kuma a sannu suka rika yin nesa dashi sai da sukayi nesa dashi sosai kana duhu takuma gilmawa sakanin su. cikin tsananin karfi ya ware idanun sa, jin muryar Na'ima tana faÉ—in "Ya dai My SALEEM?". hannayen sa biyu ya cusa cikin sumar kansa kana ya burzar da wani huci mai zafi daga bakin sa "I'm sorry." ya faÉ—a tare da juyawa yabar É—akin da sauri, yayin da yake jin zuciyar sa naciga da yi masa nauyi, acikin Æ´an kwanakin nan hakan yana yawan faruwa da shi akai-akai, musamman in ya kwanta bacci yarika irin wannan mafarkan kenan, sai yari ganin haske guda uku suna dumfaro shi sai sunzo daf da shi sai su bashi baya yayin da duhu kuma zatazo ta mamaye hasken. abun da yake gani cikin mafarkin sa shi ke kokarin zuwa masa a zahiri, to ko bacci yafara a tsayen har ya fara mafarkin?. yarika jefowa kansa tambayoyin da bashida amsar su.. Bayan sa Na'ima tabi da kallo cikin takai ci, a tunanin ta É“arin jiki zaiyi idan yaji ta haihu, idan yaga É—an kuma murna zai yi ba adadi, sai kuma gashi sai wani shashshan kamshi yake,batare da ya nuna farin ciki da hakan ba. A can kuwa bayan komawar su Mamie suna tare a parlour kowa na faÉ—an albarkacin bakin sa. Mamie kam sam taji wannan É—a bai kwanta mata a rai ba, kwata-kwata taji É—an baya cikin ranta, tana yi masa wani irin kallon da ita kaÉ—ai tasan ma'anar sa. Aunty Rafee'at fuska ta yamusa ganin su Fauzan da Nusaiba na ta murna wai matar Ya SALEEM ta haihu zasu sha suna tace "Dalla kurufa mana baki, ni wallahi wannan É—an ma kwata-kwata bai min ba wlh ya É—auko jinin uwar sa, ni bai min kama da bakwai niba haka bakwaini yake,sau nawa nake ganin Æ´aÆ´an da ake haifarsu wata bakwai sai ace wai wannan É—an wata bakwai ne, to can ta matse mata sai taje ta ta fama taje can tayi ta haifar bakwaini ita ta sani". kai Mamie ta girgiza. Aunty Jaleela tace "Ai wlh nima Aunty Rafee'at É—an baimin kama da É—an bakwai ba, sai dai idan ko sun É“ata lissafi ko kuma wani munafurcin ta ke kullawa ciki yafi wata bakwai tace bakwai to meye amfanin hakan, meye na cewa ciki wata bakwai bayan tasan cikin yafi bakwai É—in". Ummi ko cemusu tayi "To ku in ban da abun ku ta yiwu ta É“ata da lissafin ne in mutum ya É“ata da lissafi kam shi zai rika lissafi kuma alhalin ba haka bane, ai ba wani abu bane kakan iya É“ata da lissafi, kuma ai ana iya haifar wata bakwai yayi rai me lafiya ma yatashi har yafi É—an wata taran kwari da kuzari, kar ku mance fa a asibiti ta haihu in ba bakwai ba taya za'ayi a sashi a kwalba likitan ai yafiku sanin me yake, Allah dai ya rayashi da imani". "To amin". cewar su dakaji amin É—in kasan baikai can kasar zuci ba... Bayan kwana uku tun da sukaje sau É—aya basu kara zuwa ba sai ranar da ta cika kwana uku shima da kyar Ummi tasa Mamie suka koma asibitin, anan suka tadda Æ´an gidan su Na'ima, nan ma basu wani jima ba suka baro asibitin. satin su Na'ima biyu a asibitin, zaune suke da kawar ta Raliya Na'ima ta dubeta tana faÉ—in "Kai Raliya wlh nagaji da zaman asibitin nan haka, wai shin dole ne sai mun yi wata biyu a asibitin nan, dole wai saimunyi wata biyu wlh nagaji da zaman asibitin nan, wai dole ne har sai É—an yacika wata tara kafin mu koma gida, gaskiya asan yan da za'ayi kije ki sami Dr asan yan da za'ayi gaskiya, wlh nagaji da zaman asibitin sati fiyu fa ina nan,gaskiya kije ki same shi asan yan da za'ayi nakoma gida." Raliya tace "Gaskiya nimafa nagaji da sintirin yau asibiti gobe asibitin nan,kullum kenan mutum na hanyar zuwa asibiti alhalin duk kanin ku lafiyar ku lau, jariri yana nan yana shan madarar sa ke kina nan kina narkar abincin ki, nikam mafa inada wasu a hannu wlh ina da wan da na karÉ“i kuÉ—in su, akwai wan da na karÉ“i kuÉ—in sa na kwana uku gashi nan ko wuni É—aya bamuyi da shi ba, sakanina da shi da daddare mu kwana shi da yaso muje Abuja muÉ—an shana, gaskiya bari naje na samu Mukhtar asan yanda za'ayi ki koma gida, nasamu naje su fanshi kuÉ—in su". ta karashe maganar tana mikewa tsaye ta fita ta nufu office É—in Dr. Bayan Raliya sun gama tattaunawa da Dr Mukhtar yace "To gaskiya akwai yadda za'ayi zata iya komawa gida abisa ita ta tirsasa tagaji da zaman Asibitin, nikuma sai na bada wasu shawarwarin da zata É—auru akai bayan ta koma gidan". nan suka tsara yan da abun zai tafi. a ranar da yamma suka sami sallama suka koma gida, bayan shariÉ—oÉ—i da shawarwarin da Dr ya bata a gaban Æ´an uwan ta da kuma gogan wato SALEEM. Tun da suka koma gida yaron kullum a kwance yake idan akazo barka ma sai tace ba'a É—au kar sa sabo da likita yace, kada a rika yawan sa masa hannu, sai dai azo a ganshi a kwancen kawai acikin bargon da kullum yake dukunkune a ciki. haka tayi ta rainon É—an da masu da ita da É—an ma'aikatan ta da kuma Æ´an uwan ta, koda waÉ—an da suke kanta sukaga nonon ta ba ruwa basu kawo komai ba sai cewa sukayi ai dama gaka wasu matan suke sai an nimi magani. tuni aka nemo maganin wanke nono da ku ma ruwan nono, kan kace me ruwan nono yakawo tashiga shayar da É—a. lokacin da suka cika wata biyu,wato É—an yacika wata tara kenan washegari tahaÉ—a wani gagarumin taro. biki irin na masu ji da naira, biki akayi na gani na faÉ—a naira tayi kuka, ranar SALEEM katuwar saniya ya yanka da katon rago, yaron yaci sunan baban Na'ima. ko da taji sunan da ya raÉ—a masa sam bata so ba dan taso yayi wa babansa ne takwara. yace mata shi halacci yayi mata yasa wa É—an sunan mahaifin ta. ranar kuwa kaÉ—an ya rage Raliya suyi faÉ—a da Aunty Rafee'at kan cewa da Aunty Rafee'at tayi yaron ma ko kama da su baiyi ba duk da kuwa girman da yake ta karawa,amma ko alamar kama da su bayayi sai dai in ya É—auko zuriyar uwar sa dan ko kama da uwar tasa ma baiyi ba. shike nan kawai suka kama zasuyi faÉ—a, wai akan me yasa Aunty Rafee'at zatace haka ai duk wan da yaga É—an yaga SALEEM, dan kuwa farin SALEEM É—in ma ya É—auko tun da kuwa yayi kama da uban sa ai ba sai yayi kama da dangin uban sa ba. cikin masifa da bala'i da tsagwaran bariki Raliya take maganar. Aunty Rafee'at ma kuwa bata yi mata da sauki ba tayi mata wankin babban bargo. Allah ma ya taimaka Ummi tazo sunan ita ta raba faÉ—ar. ta kora Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela tace duk su tafi an yafe musu sunan, dan ganin abun na daÉ—a girma dan har Aunty Jaleela tashiga faÉ—ar.... After 1 year Acan kasar Saudi Da sauri na fito daga cikin bedroom cikin hanzari jin kiran da Ukhtee take kwaÉ—a min, abakin kofa mukayi kiciÉ“us da ita, fuska na kwaÉ“e ganin tana yi min dariya "Ni gaba É—aya kin firgita ni na É—auka wani abun ne". nayi maganar cikin harshen larabcin da nake É—an tsinta a gurin ta. murmushi tayi tare da ruko hannuna tace "Zo ki gani ga É—an'uwan ki yazo shi yace nayi mishi magana da ke". tayi maganar ne cikin yaren ta da kuma yanayin da zan fahimta, dan yanzu ba laifi nakan fahimci abun da ake faÉ—a da larafci har nakan iya É—an gwamusa wa wajen yin magana da bashi da tsawo mafi sauki. ta janyo ni muka nufi parlour. turus nayi ganin wan da yake zaune a parlour'n su Naseem da Nasmah sun zagaye shi sai zuba masa surutu suke. sai kuma nayi murmushi tare da karasowa cikin parlou'n ina faÉ—in "La Uncle Mahmoud kai ne yaushe ka zo?". dan yanzu kunyar kirashi da sunan sa nake. shima murmushin yayi yana faÉ—in "Ban jima da isowa ba,Naseem yace min kina bacci da zaije ya taso kine nace a'a yabar hajiya ta huta". baki nawashe ina zama kan kujera jin abun da ya faÉ—a nace "Uncle Mahmoud kenan wai hajiya, hajiya kuma". yace "Eh mana hajiya kai, taya za'a taso hajiya a bacci lokacin tashin ta baiyi ba ai dai gara abar hajiya tayi bacci da kyau da kyau". dariya kawai nayi kana nace "Sannu da zuwa ya hanya? yasu Bappa da Inna wuro da Fatu". yace "Hanya lafiya lau, sai dai badaga gida nake ba, amma dai Duk suna Lafiya". Naseem da Nasmah suka mike a jikin sa sukabi bayan Ukhtee aguje sukayi side É—in Mammaa. janyo table É—in da ya É—aura system É—in sa a kai yayi, yajuyo shi ta gabana yana faÉ—in "To hajiya komai fa ya kammala, shiya sa ma na dako musamman tun daga Nigeria zuwa nan na sarnar miki ki kuma ganewa idonki, ba sai an kira ki a waya an sanar miki ba." Ido na kurawa system É—in, ganin bidiyoyi sunata bayyana cikin system É—in, masu É—auke da tamfasa-tamfasan gidaje wane a turai motoci gidajen mai masallatai makarantu haÉ—e da kamfanoni da dai sauran su. cikin tsananin mamaki na dubeshi nace "Wannan fa Uncle Mahmoud?". nayi tambayar ina nuna cikin system É—i. yace "Ah ai kin ki ya kammala wakilci a ka naÉ—a ni domin a kawo miki kiganewa idon ki musamman nataso domin shi". da É—in bin mamaki nakuma kallon hotunan dake bayyana kan system É—in kana na maida dubana gareshi nace "WaÉ—an nan É—in?." yace "Kwarai kuwa sune,nakine sun kammala yanzu ke kawai muke jira ki koma abubbuÉ—e su, sannan kuma ba a gari É—aya akayi su ba a state da dama ne nacikin kasar mu Nigeria, ga jerin sunayin garirruwan da akayi gine ginen a cikin sa". ya daddanna system É—in,sai ga sunayen garuruwan sun bayyana da kuma abubuwan da akayi a kowa ni garin. yace "Kin ga yanzu zaki koma Nigeria a dai-dai dan kullum sai Bappa yayi maga, yanzu ma yace mu dawo tare sai dai ni bagida zan koma ba zan wuce Uganda tare da abokan aiki na, akwai wani abun da zamuje muyi a can". kai na jinjina dan nifa har yau ganin abun nake kamar wasa nace "Him..Him.." kasa magana ma kawai nayi sai Him. nake ta faÉ—a ina kallon ikon Allah,yayin da nakeyi wa Ubangiji buwayi gagara misali tasbihi a can kasar zuciya ta. rufe system É—in yayi kana yace "Kin ga abubuwa yan da suka kammala ko, ko mai masha Allah, yanzu wani suna kike ganin za a sakawa kamfanoni da gidajen mai dai duk sauran kaddarori, wani suna kike ganin ya dace a saka musu, domin idan akaje yin katin gayyata da sanarwa ayi amfani da wannan sunan, da zai zamo shine sunan duka kaddarorin". Shiru nayi yayin da na saka yatsa na guda kan kuma tuna nayi sama da ido na alamun tafiya duniyar tunani, tare da É—an kyafkyafta idon. kana nayi kasa da idon cikin washe baki nace "Yauwa na tuno sunan da nake so a saka masa *HAM'NAS*". nayi kaganar cikin zakuwa ina cigaba da washe baki. yanayin yadda nake maganar sai da ya bashi dariya ya ce "To meye ma'anar *HAM'NAS* É—in kuma". fuskata narufe da tafin hannuna cikin muryar dariya haÉ—e da zakuwar jin yadda na haÉ—a kalmomin suka tafi normal nace "Kaga ma anar sa, HAM sunana ma'ana HAMDAH, NAS kuma Naseem and Nasmah". dariya sosai ya sake yana faÉ—in "Kaga yarin ya mai basira, tabbas wannan suna yayi kuwa ba shakka *HAM'NAS* Co Fitroleum Nigeria Limited *HAM'NAS* Intranational School Of Science And Technology *HAM'NAS* Store Complex *HAM'NAS* Clinics *HAM'NAS* International Hospital, Eh ba shakka lallai sunan yayi *HAM'NAS* Allah ya taimaka yayi jagora". tsabar zakuwa kasa kuma cewa komai nayi sai baki na da yakasa rufuwa..â˜? A ranar da yamma Mahmoud ya wuce Uganda........â˜? Mommyn Twins ce HMD 🅿ï¸?3 Yau juma'a babban rana, ranar da duk kanin al'ummar musulmi suke farin cikin zuwan sa, al'ummar Annabi suna ta kai komo hada-hada da shirye-shiryen tafiya masallaci domin sallar juma'a. da sauri Ummi tafito daga cikin bedroom É—inta sanye da mayafi akanta, fuskarta É—auke da yelwataccen annuri, da ka ganta kasan tana cikin matsanancin farin ciki. da sauri ta nufo bakin kofa, lokacin Fauzan yasako kansa da gudu kaÉ—an yarage yayi karo da Ummi, Ummi ta ce "Kai Fauzan bazaka rika yin abu cikin nutsuwa ba ko." baki ya washe yana waigen bayan sa da faÉ—in "Yau wa Ummi direba yadawo daga masallacin nace masa yafito da mota zai kai ki unguwa." yana maganar yana waigen bayan sa yana wurga hannu alamun zakuwa, sarai Ummi tagane shi so yake ya bita dan tun kan afita a sallah yake fita dubo direba ko yadawo, dan ko masallacin shi baije ba dan ko da tace masa yaje masallaci cewa yayi wai shi a gida yau zaiyi sallah. fita Ummi tayi tana faÉ—in "To naji." bayan ta yabi da sauri yana faÉ—in "Ummi nima zan biki Ummi dan Allah kije dani kin ga wancan Juma'ar da É—ayan wancan juma'ar bakije da ni ba, akwai bashin tafiya unguwa biyu da bake je da ni ba." "Tafican da alla kai ko ina za'aje sai an je da kai kai mata ne, da Nusaiba zamuje kai sai ka jira idan Abba ko Abbu'n ku suka dawo sai kayi musu rakiyar." kafa yashi bubbugawa yana biye da ita a baya tare da faÉ—in "Ummi nikam dai kije dani ina ranar da Nusaiba kuka je." suna isowa tsakar gidan Mamie da Nusaiba suna fitowa, dagudu Fauzan yaje in da suke yaruko hannun Nusaiba da take gyara mayafin ta da ta fito dashi rike a hannu tsabar sauri, jan ta yayi kusa da Mamie yana faÉ—in "Allah yau bazaki je ba dani za aje Mamie rike min ita kar ki sake ta sai nashi mota mun tafi." Mamie tace To cikin muryar dariya ganin yan da ya janyota tana torjewa kamar masu kokawa, Ai ko Mamie na rike ta yajuya a guje yayi gun mota yana dariya da faÉ—in "Yarinya yau badake za aje ba agida zaki zauna." kukan shagwaÉ“a tasake tana jan hannunta dake rike a hannun Mamie tana faÉ—in "Ai wlh dani Ummi zata tafi da kai namace ce sai ka rika bin mata unguwa, Mamie sake ni kuma sai na maka duka." yana isa jikin motar ta zille a hannun Mamie tarufa a guje suka kama rige-rigen shiga mota. tana faÉ—in "Da kai mace ce kuma ai Ummi tace dani zata rika zuwa unguwa." "Allah baki isa ba yaukam dani za a tafi ai sau uku ana tafiya dake unguwa ni ba a tafiya da ni sai naje." yayi maganar yana shigewa cikin motar a guje, itama shigewa tayi ta É—aya barin tana cewa "Bazan taÉ“a zama a gida ba sai dai kai ka zauna." Ummi kam baki ta rike tace "Oh yaran nan sai shegen son yawo duk in da mutum zai je sai kun bishi kamar jakka." dariya Mamie tabisu da shi. da sauri direba yafito yabuÉ—e wa Ummi kofa tashiga, da sauri Nusaiba ta dawo gefen ta yazamo sun sata a tsakiya. sunata yiwa junan su gwalo direba yaja motar suka fita bayan Mamie tayi musu a dawo lafy. koda suka haura titi direba ya juyo ya dubi Ummi yace "Hajiya ina zamu fara zuwa?." yayi tambayar ne dan yasan rana irin ta yau wato ranar ko wata juma'a Ummi tana fita zuwa asibitoci kan titi in da mabarata suke zama dakuma masallaci in da mabarata suke zama, domin basu sadaka a kowace ranar juma'a, dan haka yake da tabbacin wannan fitar ma zuwa guraren zasuyi dan iwar haka suke fita. Ummi tace "Babban masallaci zamu fara zuwa." yace "To Hajiya." nan yajuya akalar tafiyar izuwa babban masallaci. suna isa direba yagyara parking a gefe, Ummi tafito rike da jakarta, yayin da Fauzan da Nusaiba suka rufa mata baya, ta isa in da mabarata suke jere a bakin masallacin, ta buÉ—e jakarta tarika ciro kuÉ—i tana raba musu, tana bin kowa layi-layi tana mika musu sadaka. duk wanda ta mika masa sai ya kwararo mata addu'a da fatan samun biyan bukatun ta na alkhairi ga mahaliccin ta. duk wan da ta bawa idan yayi mata wannan addu'ar sai kaga ta saki wani murmushi tare da fatan tabbatu war hakan acikin zuciyar ta. akasin da da idan sunyi mata addu'ar saboda raunin dake zaune cikin ruciyar ta har sai ya kai ga tayi kukan zuci, tana ji ina ma Ubangiji yakarÉ“i addu'o'in nasu da wanda take hana idanun ta bacci acikin kowani dare, ya kare mata É—iyar ta a duk in da take. gaba É—aya yau É—in nan ta tashi ne cikin farin ciki da jin daÉ—i tana jin kanta cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa, wan da ita kanta batasan na mene ne ba. Haka tarika binsu tana raba musu cike da shauki da jin daÉ—in da yagama baibaye zuciyar ta, har sai da ta tabbatar da kowa ya samu, kafin ta koma cikin mota tana jin su suna daÉ—a bin ta da addu'o'i mai kara mata nutsuwa da kwanciyar hankali. daga masallacin kuwa titi-titi suka fara bi in da mabarata ke zama suma tarika mika musu sadaka. kana suka wuce asibiti, har sai da kuÉ—in da ta fito dashi yakare kafin tacewa direba su koma gida.... *(a can kasar Saudiyya cikin masarautar Saudi)* Da sauri nafito daga cikin bathroom ina gyara gashin kaina dana wanke yazubo ya rufe min fuska har bana iya ganin hanya, cikin hanzari na nufi gaban mirror karamar towel in dake rike a hannuna na naÉ—e shi a kaina ina tsane ruwan dake É—iga daga gashina. kana na É—au na'urar dake busar da gashi nabusar da gashin, batare da ya bushi duka ba, nabaza shi ta baya domin iska yakarasa busar da shi. zama ta na gyara na É—au mai nasoma shafawa a jikina. daga cikin mirror nake hango su Ukhtee ita da su Naseem sun sata a tsakiya sai surutu suke zuba mata, suyi da hausa su gwama da larabci abun ka da kwakwalwar yaro sukam tuni suka fini ji da iya mayarwa ma. kai na jinjina a raina nake cewa "Kai waÉ—an nan yara da surutu suke ko surutun wa suka É—auko?." ko É—azu dasuke ta zuwaba Mammaa surutu sai cewa tayi wai ni suka gado, niko ina nake da surutu irin haka. idan kaji maganar su kamar wan da sukayi shekaru huÉ—u wan da ko shekara uku basu cika ba saura wata huÉ—u nan gaba. nayi murmushi kawai tare da girgiza kai, ganin Naseem yajuya fuskarta gareshi in zayi magana Nasmah ma haka. wai su in zasuyi magana ala dole sai mutum na kallon bakin su in bai kallaba sun rika juyo da fuskar shi kenan. wayan Ukhtee ne yashiga kara taÉ—ago wayar tana dubawa kana ta maida duban ta gareni, daga cikin mirror'n muke kallon juna, ganin ta mai da kallon ta kan wayar namike da sauri dan nasan ni ake kiran ganin yan da tayi zuruu tana kaloon wayar tawani langwaÉ“ar da kai, da sauri na isa bakin gadon, ina faÉ—in "Bappa ko?". kai ta gyaÉ—a tare da mika min wayar, na amshi wayar na É—aga kiran tare da kara wayar a kunne. "Assalamualaikum Bappa." daga cikin wayar Bappa yace "Ke HAMDAH me kike yi ne har yanzu baki shirya ba." da sauri nace "Ina kan shiri Bappa yanzu nafito daga wanka ina kan shirin, ina shafa mai ne yanzu." yace "Kada fa ki tsaya wani dogon shafe-shafe kisaka kaya kawai kada jirgi ya tashi ki rasa jirgi kada ki tsaya shiririta irin na rannan." "To Bappa yanzu zan gama". nakashe wayar ina mai jin wani farin ciki. wan nan karon bazan yi wasa ba kamar na wata guda da ya wuce, haka nayita lalawai har jirgi yatafi a bun sa, wannan karon kam ba Bappa kaÉ—ai keson komawa ta ba ni kai na inason komawa kasata, hankali na gaba É—aya yakoma kasata yanzu. ina so najini a cikin ta, ba naganni cikin kasata kaÉ—ai ba, ina so naganni cikin ahalina duk da nasan hakan ba abu mai sauki bane, har idan Abba bai sauka daga fushin da yake dani ba. Mika mata wayar nayi ina kokarin juyawa, wani kiran yakuma shigowa. murmushi nayi ganin Bappa ne yakuma kiran, da safiyar nan kiran sa na shida kenan kan nayi sauri kada jirgi yatafi. "Hello Bappa". nafaÉ—a ina kai wayar kunne na, muryar sa na jiyo yana faÉ—in "Kada ki É“ata lokaci dai kinji ko, kisaka kaya kawai kada ki rasa jirgi ki hanzarta." nace "To Bappa." na sauke wayar na mika mata da sauri na koma gaban mirror, a gaggauce nakarasa shafa mai sai pauda da man baki. na mike da sauri na isa bakin gado in da dama nan nacire kayan da zansaka na aje na É—auka na sa, dan sai da na shirya su Naseem da Nasmah kafin na shiga wanka, shiyasa shirin yayi min sauki. tun da Bappa yakira waya nalura da yanayin Ukhtee gaba ki É—aya yanayin ta ya sauya tayi wani ziruu da ita, kai na kawar dan bana son muhaÉ—a ido da ita, dan yanayin nata zai iya sa jikina ya mutu. cikin hanzari na kammala saka kayana, ina cikin sa kayan ban kai ga gamawa ba Bappa yakuma kira. Nan ma kuma faÉ—in nayi sauri yace, cikin hanzari na kammala saka kayan. Na dubi Naseem da Nasmah ina faÉ—in "Kutashi muje ko." ido Naseem ya kura min yayin da hannayen sa biyu ke dafe da kuma tun sa kana ya ce "Mommy mataiyaci amuje?". Nasmah ma tace "Tayan kaya amuje ko Mommy?." kai na girgiza musu nace "Ba siyan kaya ko masallaci zamu je ba, kasar mu zamu koma can kasar mu in da aka haife mu." ido yaran suka ware suna kallona kana Naseem yakuma cewa "Mommy kasar mu in da aka haife mu?." yy maganar yana zura yatsarsa cikin baki alamun mamaki irin na yara. kai na gyaÉ—a masa tare da ruko hannunsu ina faÉ—in "Kutashi muje." dan nasan idan nabi na surutun su sai mu makara anan har Bappa yakuma kira. Ukhtee kuwa tuni idanunta suka kawo ruwa kan kace me hawaye yafara sauka, hannunta na rike cikin rauni tare da girgiza mata kai dan nima idanuna sun fara tara kwalla. cikin harhaÉ—a larabci nace "Dan Allah Ukhtee kar kisa jikina yayi san yi, baga waya ba zamurika magana ai tafiya ba mutuwa bace ai dai bamu rabu ba tun da akwai waya zamu rika gaisawa, bakin ce zaki zo kasar mu ba?." kai ta gyaÉ—a min alamar Eh nace "To dan Allah kada ki karya min guiwa da tafiyar kizo muje kin ga Bappa sai kira yake." jiki a sanyaye ta mike. koda muka fito parlour sai gani nayi babu akwatin kayan mu in da nafito da shi na ajiye É—azu bayan nagama shirya mana kayan mu. nan Ukhtee take sanar min direba ne yashigo ya É—auka. koda muka fita farfajiyar masarautar, a tsaye jikin mota muka tadda direba da alamu mu yake jira. da sauri na juya na nufi side É—in su Ukhtee dan yiwa Mammaa sallama, narika bin part-part na masarautar ina yi musu sallama duk in da na shiga sai na fito da Æ™walla dan suma da kwallar suke rako ni,haka narika bin side mafi kusa da mu ina yi musu sallama dan idan nace zanbi na nesa da mu sai na kusan sai na É“ata lokaci mai tsawo ban gama ba. daga karshe nashiga can cikin masarautar in da lokacin da mukazo aka canza diamonds É—in nan aciki. direct cikin katafaren parlour wan da aka kawata shi da adon zinari mai matukar É—aukar ido muka shiga, adalin shugaba na zaune a mazaunin sa na alfarma, yayin da Alkur'ani ke gaban sa yana bita cikin nutsuwa. a gaban sa muka rusuna, cikin ladabi nayi masa barka da war haka,kafin nakuma cewa wani abu ya É—aura hannunsa a kai na yana yimin fatan isa kasata lafiya, nayi mamakin yan da yasan abun da ya kawo ni dan ni a zato na bai san da tafiya ta ba. naji daÉ—in addu'o'in da yayi min kwarai da gaske, na mike cikin jin daÉ—i yayin da jikar sa wato Ukhtee ta rufamin baya, bayan itama ta gaishe shi, gaba É—aya cikin parlour'n suka shiga yimin fatar isa gida lafiya ina amsawa da amin har muka fita. a jikin mota na tadda su Mammaa cikin matukar bege kowa sai hawaye yake har sai da suka sa hawaye na ya karu. direba na ganin mu yayi saurin buÉ—e motar yariko hannun su Naseem yasa su cikin motar, rungume juna mukayi da Ukhtee muka saki kuka a tare, gaba ki É—aya gurin hawaye suke babu mai iya rarrashin wani, zame jikina nayi cikin sauri nashige cikin mota, direba yatada motar. motocin da suke jere a gaban mu guda uku sai wasu biyu a bayan mu, motar farko mai tambarin masarautar haÉ—e da jiniya, shi ya fara fita, kafin biyu suka bi bayan sa sai kuma motar da muke ciki. motoci biyu da suke bayan mu suma suka biyo mu, kamar dai ranar da muka shigo masarautar sai gashi yauma a haka muka fita. muna isa airport batare da É“ata lokaci ba muka shige cikin jirgi, nan motocin suka juya. bada jimawa ba jirgin ta É—aga... Bayan wasu Æ´an awanni jirgin mu yasamu sauka cikin yar dar Allah da buwayar sa, cikin babban birnin tarayya Abuja da ke cikin kasata ★NIGERIAâ˜?. bayan saukar jirgen da kamar minti 15 fasinjojin ciki suka fara sauka. da sauri ganin Naseem da Nasmah sun mike kan kace me sun rufa da gudu sunyi bakin kofar fita in da mutane keta sauka, cikin hanzari na rufa musu baya da sauri ina faÉ—in "Kai kutsaya fa kar kuje ku faÉ—i." ai ko da gudu suka fara sauka daga matattakalar jirgin suna dariya. bayan su nabi ina dariya ganin inda suke sauka cap-cap-cap daga matattakalar kamar zasu kefe kasa ina cigaba da faÉ—in. "Zaku faÉ—i fa kutsaya." kan kace me sun sauka kasa, sauri na kara ina sauke kafata kan shinfiÉ—aÉ—É—iyar kasan kasata abun alfahari na Æ™asata Nigeria, naja wani irin numfashi tare da shakar daddaÉ—an iskar dake kaÉ—awa acikin Æ™asata. ganin suna kokarin cigaba da gudun nayi hanzari na ruko su tare da faÉ—in "Idan yaro ya faÉ—i yayi min kuka zan kara masa." baki suka washe cikin kyakyata dariya Naseem yace "Mommy baya mu faÉ—i ba." goshin sa na dungure nace "Zaku faÉ—i mana in zaku faÉ—in zaku sani ne wan nan gudun da kuke ai sai dai kuji ku a kasa kuzo nan ku tsaya." na janyo su gefe guda. Daga can gefe guda da sauri aka buÉ—e wata motar da suke jere É—an nesa da mu, wasu mutane biyu suka fito da sauri suka karaso in da muke, sannu da hanya sukayi min, na amsa ina kokarin janyo su Nasmah mu matsa gefe, daya daga cikin su ya mika min waya, kallon wayar da yake mika min É—in nayi kana na mai da duba na kansa, kai ya É—aya tare da faÉ—in "Ana maga na." ya fada yana kallon kan screen É—in wayar, a hankali na sake Nasmah dake rike a hannun dama ta na amshi wayar, shikuma yayi saurin ruko hannun ta yaÉ—an matsa gefe kaÉ—an in da É—ayan mutu min ke tsaya ya harÉ—e hannu da bakin gilashi a aidon sa, a sannu nakai wayar kunne na tare da yin sallama, daga cikin wayar akace "Barka da isowa kasa Nigeria ki bisu su isa da ke masauki." É—an shiru nayi kamar naso nagane muryar mai maganar, sai kuma na sauke wayar batare da nace komai ba na mika masa wayar. a hankali na soma tafiya suna biye da ni har gurin mota, da sauri É—ayan ya buÉ—e min murfin motar muka shiga in da tuni suka saka jakar mu cikin motar. jere motocin suka fita kamar yan da aka kawo mu airport a can kasar Saudiyya. muna fita daga cikin airport É—in muka É—au hanya, shiru nayi cikin motar ina raba ido cikin Æ™asata yayin da zuciya ta ke kunshe da É—in bin farin cikin gani na cikin Æ™asata, ina jin wani farin ciki tabbas Æ™asata abun alfahari na ne. munyi tafiya mai nisa kafin muka isa wani katafaren hotel, hotel ne irin wan da manyan kusoshin kasa suke sauka a cikin ta... Awani haÉ—eÉ—É—en É—aki aka sauke mu sai da suka rako mu har bakin kofar room É—in kafin suka juya, wan da ke rike da jakar mu kuma yashi ga ya ajiye, kana ya miko min waya yace "Ana magana." na amshi wayar a raina nake faÉ—in "To yanzu kuma ina zai kuma cewa na bisu." a sannu nakara wayar a kunne na sai jin muryar Bappa nayi yana faÉ—in "HAMDAH sannun ku da hanya ya gajiyar hanya." washe baki nayi dajin muryar Bappa da sauri nace "Laaa Bappa mun iso lafiya kalau Bappa kana ina?." nafaÉ—a ina washe baki cike da murna jin muryar Bappa da nayi yace "Kuhuta ku kwanta ku huta sosai ina nan zuwa." nace "To Bappa." na mika masa wayar ina cigaba da washe baki, mutumin ya fita tare da jamin kofa, numfashi na sauke tare da bin É—akin da kallo, na isa bakin gado na zube bakin gado, in da tuni Naseem da Nasmah suka haye gadon sai salle suke. kokarin tuÉ“e kayan jikina nake dan so nake naÉ—an watsa ruwa, naji ana knocking mayafi na naÉ—auka na mayar jikina, na mike na nufi kofar na buÉ—e ma'aikacin hotel É—in nagani tsaye rike da babban tray, baya naja na bashi hanya yashigo ya dire try É—in kan table kana yafita na mai da kofar narufe na murza key. na dawo bakin gadon na tuÉ“e kayana nashige bayi, wanka nayi sosai nafito na tuÉ“e su Naseem suma nayi musu wan kan. bayan na shirya su nima na sauya kaya, kana na zuba mana abinci mukaci. muna gama ci muka koma gado... bayan haka da kamar awa 2 akayi knocking na mike naje na buÉ—e, É—aya daga cikin mutanen da mukazo tare nagani tsaye yace "Madam kun kammala zamu iya tafiya?". kai na gyaÉ—a masa, juyawa nayi dan kiran su Naseem sai ganin su nayi a bayana suna kokarin fita daga É—akin, mutumin ya ruko hannunsu nikuma na koma na É—au mayafi na nabi bayan sa muka fita.. tun daga bakin get É—in da muka iso na fahimci banki muka zo dan gashi a rubuce (First bank) buÉ—e baki nayi a raina nake faÉ—in "To me mukazo yi a banki." bakin na rufe jin yana faÉ—in "Bismillah fito muje ko." sai lokacin na lura ashe ma har sun fita har ya buÉ—e marfin É“arin da nake ban sani ba, a hankali na zuro kafafuna waje na fito. direct cikin bankin muka shige batare datsaida mu ko bincike ba, akasin jama'ar da nagani tsaye bakin bankin an tsaida su an hana su shiga. tun da nashiga cikin bankin aka bani gurin zama ban motsa ba, duk wani cike-cike da kai kawo wasu suke tayi su da wan da mukazo da su, sai dai abun da yakamata ni nayi da kaina shine nake tashi naje nayi, awa 1 da zuwan mu aka kammala komai aka bani ATM, muna fita daga bankin zato na masauki za'a maida mu sai ganin mu nayi a get É—in wani banki, shima kusan mintunan da mukayi a bankin da muka baro mukayi a nan É—in kafin muka kammala, nan ma da ATM É—in bankin muka fita. ina mai jin mamakin kuma zuwan mu wannan bankin. mamaki na bai karu ba sai da nakuma sin tar kaina cikin wata banki, wunin ranar muka kare ta a bin bankuna dan sai da muka je banki biyar kuma duk wan da mukaje da ATM É—in sa muke fita.. sai yamma liss muka dawo masaukin mu, a gajiye na zube bakin gado in da É—aya daga cikin mutanen da muka tafi da su yashigo da su Nasmah, wata laidar dake rike a hannunsa ya mika min yana faÉ—in "Gashi ance na baki." bin laidar nayi da kallo kana namika hannu na amsa shiku yafita, zamata na gyara tare da zuba ATM É—in da suke hannuna kan table É—in gabana. a sannu nashiga buÉ—e laidar dan ganin abun da ke ciki, kwalayen wayoyi ne har guda biyu nagani ciki a sannu na ciro su ina jujjuyasu, rabon da narike waya haka a hannuna a matsayin nawa har na mance, sai kuma cikin hanzari nashiga buÉ—esu dan tun ban ciro su ba wayoyin suka tafi da ni, da sauri na ciro cazar wayoyin duka namike cikin hanzari naje na saka su a cj, ina saka wa kuwa suka nuna min acike suke, da sauri na dawo in da na tashi na kunna wayoyin, ai ko ina kunna wa sai ji kake É—uÉ—ut-É—uÉ—ut alamun shigowar message alert akai-akai. ido na kurawa musu ganin alat ne na kuÉ—i suke ta shigowa, na bankunan da muka buÉ—e É—azu, ido na zubawa sarautar Allah ganin kuÉ—aÉ—en da suke ta shigowa ni bama zan iya kiyaste adadin su ba. sai da naji wayoyin sunbar kara kafin nashiga latsa su, contacts nashiga da sauri sai gani nayi babu number ko É—aya, jiki a sanyaye nake kallon wayar, abu na farko da ya fara zuwar min shine lokacin da Abbu ya siya min waya yasaka min number family na aciki,haka narika bin lambobin Æ´an'uwa na ina kiran su. hawayen da yagangaro kan fuskata na share ina mai jin kewar ahalina, a sannu na mike na isa in da jakata yake na buÉ—e naciro number Ukhtee da ke rubuce a takarda, na saka cikin wayat kana na dannan mata kira, tana É—aga wa dajin nice mai kiran atare muka saki ihun murna. hira mukayi tayi da ita har magriba kafin na mukayi sallama... Kasan cewar ina fashin sallah gado na haye nayi kwanciya ta cike da kewar ahalina daya baibaye ni lokaci guda... washe gari da rana Bappa ya iso Abuja, nayi murna matuka da ganin sa har nake jin wani É“ari na kewar ahalina dana kwana dashi ya yaye da ganin sa. isowar sa ba da jimawa ba muka bar cikin hotel É—in har da kayan mu. wani katafaren gida mai matukar kyau da tsaruwa gida ne babba wan da girmansa yakai ya kawo tsarin sa gwanin burgewa, a bakin ramÉ“asheshen get É—in gidan motar gaban mu ya tsaya, wan da mutanen da suka É—auko mu a airport da wan da muka haÉ—u dasu a banki jiya dakuma wasu karin mutun biyu da yau nafara ganin su, sune acikin motar, motar da muke ciki ke biye da su, sukayi hon, abakin get É—in ramÉ“asheshiyar gidan........â˜? Mommyn Twins ce HMD WASA FARIN GIRKI!!!âœðŸ? _(Book 3)_ 🅿ï¸?4 Asannu a ka wangale tamfatsetsen get É—in gidan, motar gaban mu yakusa ciki, a hankali direban dake jan mu ya danna hancin motar cikin gidan, a tsakiyar farfajiyar gidan duk suka faka motocin, a sannu na zuro kafafuna waje, "Ya ilahi ya littahi". abun da na furta kenan lokacin da na dai-dai ta tsayuwa ta a cikin gidan, bin gidan nashiga yi da ido har ina wai ga gefe da gefe na. gaba É—aya gidan da tsaruwar sa yatafi da ni, tsaruwan gidan yawuci misali komai an tsarashi a inda ya kamata yana ajiye a in da ya dace,gida ne babba mai É—auke da part har huÉ—u, daga gefe can gabar da gidan side ne guda É—aya sai kuma gefe ta hannun dama shima side ne guda sai kuma gefen hagu shima side É—aya, sai dai Æ´an madaidaita ne ba wasu manya ba. daga tsakiyar gidan kuwa wani side ne na musamman wan da yazamo sauran side É—in sun sashi a tsakiya shi kam gini ne mai hawa É—aya babbane ya tsaru iya tsaruwa, daga saman side É—in har kasan sa yaji ado da gilasai masu ban mamaki an kawata shi tamkar a turai,daga kasa kuma an zagaye shi da wasu flaw's masu matukar kyau da É—aukar ido, gaban side É—in wani shinfiÉ—aÉ—É—iyar swimming pool ne wan da aka kawatashi da rubber grass malaye har bakin kofar shiga side É—in. gefe can kuma parking space ne É—auke da lafiyayyun motoci da suka kai guda uhu a cikin sa, daga farin shiga gidan kuma gefe da É—akin mai gadi masallaci ne shin fiÉ—aÉ—e agun, sai kuma É—akuna guda É—ai-É—ai a jere guda uku a gefe da masallacin ta can. Maganar Bappa naji yana faÉ—in "Muje ciki ko HAMDAH." da sauri nadawo daga duniyar kallon gidan dana tafi, da murmushi kan fuskarsa dan ganin yan da na tafi gaba É—aya na shagalta da kallon gidan. na ce "To Bappa". a hankali nabi bayan su side É—in da ke gefe ta hannun dama muka nufa a hankali nake taka kafata ina cigaba da baza ido cikin gidan har muka isa cikin side É—in. masha Allah É—an madaidaicin side É—in ya tsaru matuka. side ne mai É—auke da 3 bedroom ko wanne da banÉ—aki a cikin sa, É—an madaidaicin parlour haÉ—e da dinning da kitchen da komai da komai, an tsara komai yan da yakamata duk wani abun bukata an tanadar babu abun da babu. É—akunan cikin parlour'n muka rika shiga wan da komai akwai hatta gadon É—akunan duk da shinfiÉ—ar su, sunsha lafiyayyun bedsheets. bayan mungama zagaye cikin side É—in gaba É—aya, muka fita É—ayan side É—in dake gefen hagu muka shiga, shima kamar wancan side É—in yaji komai. kowa sai faÉ—in masha Allah yake, nidai kasa magana nayi sai binsu nake inata baiwa idona abinci sabo da gaba É—aya yanayin tsarin gidan yatafi dani. daga nan É—aya side É—in dake can gabar da gidan muka nufa, shima tsaruwan sa da tsarin sa kamar sauran part biyun nan, koda muka fito daga cikin part É—in baki na washe nadubi Bappa dake ta faÉ—in "Kai komai yayi masha Allah komai fa yayi yadda yakamata". baki nakuma washewa ina faÉ—in "Kai wlh Bappa gidan nan Allah yayi kyau kaga fa nan irin wancan can ma irin wancan kai tsarin gidan yayi kyau komai iri É—aya, sai dai kawai kalolin kayan cikin sune daban-daban". dariya Bappa yayi kana yace "Da gaske gidan yayi kyau ko?." "Wlh kuwa Bappa." nafaÉ—a da sauri ina cigaba da washe baki, shima dariyar ya kuma yana girgiza kai kana muka rufawa mutanen baya in da suka nufi wannan kayatacce rantsatstsen babban side É—in nan dake a tsakiyar gidan wan da yazamana da sauran side É—in sun sashi a tsakiya. a hankali muka isa bakin kofar da sauri É—aya daga cikin mutanen ya isa bakin kofar side É—in wan da yake na glass ya É—aura hannunsa gefe kan wasu madannai ya daddanna sai ga glass É—in yafara bada sauti É—an baya yaja kana ya dubeni yace "Bismillah Madam É—an zo ki tsaya a nan." ya nuna min kan step É—in da yasauka akai wan da saika haura kansu kafin ka isa bakin kofar,step ne guda uku, nuna kai na nayi alamar ni?. yace "Eh." a hankali na matso na haura kan step É—in, daga in da yake yamika hannunsa yakuma danna wasu lambobin kana yace na É—aura hannuna kan nan yanuna min wani É—an zagaye da hoton yatsu, a sannu nakai hannuna na dai-dai ta yatsuna kan zanen yastun, nan yafara bada sauri É—it-É—it sai kuma yakuma danna wata lambar data fito mai alamar Okay. nan take kofar tazuge gefe ai ko da sauri na É—aga hannuna. ya juyo yana duba na kana yace "Madam wannan kofar special ne mai amfani da zanen yatsune mutum É—aya ke amfani da shi, sai kuma wancan". yanuna wata kofar dake gefe ya isa gurin muma mukabi bayan sa,ni dai cikin rashin fahimta nake jin sa, yace "Shi wannan common door ne kamar yanda aka sani kowa zai iya amfani da shi." ya murÉ—a handle É—in kofar yabuÉ—e muka shiga ciki. sai gamu mun bayyana cikin wata katafaren parlour ya ilahi ya lilahi, har bansan san da na furta "Kai! amma wannan duk yafisu kyau!". nayi maganar cikin hakikance gaskiyar abun da ke cikin zuciya ta wan da maganar fitowa kawai tayi, Bappa ko karamar dariya yayi tare da jijjiga kai. suma sauran dariya suka bini da shi, nan muka fara kusawa cikin katafaren parlour'n, baki da hanci gaba É—aya na buÉ—e wajen kallon katafare kayataccen parlour'n, faÉ—an tsaruwar sa da misalta tsarin parlour'n ma ba zai misaltuba, yaji kayan alatu da more rayuwar duniya tsaruwan sa ya zarce sauran side É—in da muka shiga babu haÉ—i ko kaÉ—an. bedroom É—in dake cikin parlour'n muka rika shiga É—aya bayan É—aya, bedroom ne zafafa har guda huÉ—u masu É—auke da tsalatsalan bathroom, daga gefe da parlour'n kuwa katon dinning area ne sai kitchen babba a gefe. sama muka hauwa wan da shi kanshi step É—in haurawan sama abun kallo ne domin kuwa shima an kawatashi na musamman. wow masha Allah shima tsarin saman kamar kasan sai dai banbancin kalolin kayan dake cikin su, kalar kujeru da labulayen bedroom and parlour kasan white and ash da É—an ratsin lemon-green. saman shima 4 bedroom ne a cikin sa kalan kayan bedroom and parlour'n kuma white and sky-blu. Antsara komai yadda yakamata sai tashi da sassanyan kamshi mai haÉ—e da kamshin sababbin kaya yake. kai gidan ya haÉ—u fa nidai bakina yakasa rufuwa wajen kallon tsaruwan gidan, bayan mun gama zaga lungu da sako na saman muka gangaro kasa anan muka yada zangon mu cikin parlour'n kasa. Kowa sai yaba kyau da tsaruwar gidan yake, É—aya daga cikin mutanen yadube ni kana yayi gyaran murya sannan ya ce "Madam komai yayi ko? komai ya miki wannan gidan yayi miki? kokuma mu isa wani gidan?." kallon sa nayi cikin rashin faminta sai kuma na maida dubana ga Bappa danaji yana faÉ—in "Duk da dai bataga sauran ba amma ga yanda take ta washe bakin nan ai ba a magana." da sauri nace "Bappa gidan..". bai bari na karasa ba yace "Gidan ki wannan gidan duk girman ta nakine akwai kuma ire-iren su suna nan". ido na waro kamar a mafarki nakejin zancen, "Wannan ya miki?". mutumin yakuma jefo min tambayar, kai nashiga gyaÉ—awa da sauri sai kuma naruko hannun Bappa ina faÉ—in "Eh wlh yayi-yayi Allah Bappa gidan yamin kyau sosaiiiii". Dariya Bappa yayi yace "To sake min hannu kada ki É“ala". ai ko sauran mutanen ma suka rika dariyar ganin yan da nake washe baki ina jijjiga hannun Bappa, Naseem da Nasmah dariya suka rikayi suna tsalle jikin Bappa kamar wan da sun san abun da ake. Mutumin yacigaba da faÉ—in "To masha Allah wannan side É—in shine naki a yanda aka tsara ginin gidan, sauran kuma ke kikasan yan da zakiyi da su, yanzu mu zamu koma mubarki ki huta zamu dawo zuwa gobe, domin sauran baya nai." Sukayi mana sallama suka fita, suna fita, na dubi Bappa ina waro ido nace "Bappa wai da gaske wannan gidana?". Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in "DaÉ—ina da ke akwai shirme." hannu nashiga tafawa ina faÉ—in "Kai wlh gidan nan yayi min mugun kyau." ya ce "To sai ki goyashi kuta yawo tun da dai naki ne." ido na waro tare da sa dariya nace "Bappa gidan zan goya?." kanshi ya jinjina yana murmushi. rungume Naseem da Nasmah nayi cikin tsananin farin ciki, sai kuma na sake su. da sauri nace "Bappa ina su Inna wuro da Fatu?." yace "Suna can ruga". nace "Bappa shine bakazo da su ba kace su dawo nan suzo mu zauna da su a nan, kaji Bappa." nafaÉ—a ina jijjiga hannun sa, "Kaji Bappa kace su zo". nakuma faÉ—a ganin yayi shiru bai ce komai ba, yace "A'a HAMDAH su zauna acan zan koma ai nima". ido nakuma warowa da karfi nace "Bappa ni kaÉ—ai za'a barni a wannan gari gudan, da ni kaÉ—ai zan zauna a gidannan ai dani daku zamu zauna." nayi maganar ina nuna cikin parlour'n "Tap Allah bazan iya zama ba dan Allah Bappa kace su dawo nan, wannan gidan ai tsoro zai rika bani ni kaÉ—ai a cikin sa, kaji Bappa?." nafaÉ—a ina bubbuga kafafuna a kasa. "To babu damuwa zasu zo amma ba yanzu ba." na ce "Bappa sai yaushe." ya ce "Bari dai mana a gama Hajiya HAMDAH." dariya yake bani in naji ance Hajiya HAMDAH, ai ko na washe baki, yace "To meyasa bakisa hakorin hajji ba acan?." "Kai Bappa,hhhh to zan sa in na kuma komawa." "Allah ya kai mu ai kamar yanzu ne shekara zata kuma zagowa Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya." yayi maganar yana mikewa tare da cigaba da faÉ—in "To ni bazanje masallaci gashi ana ta kan kiran sallah, mutumin zo muje muyi sallah". da sauri Naseem ya mike ya roko hannunsa suka fita. Da sauri na mike inata daÉ—a waigen cikin parlour'n inshiga wan É—akin in fita inshiga wancan haka narikayi, daga nan kuma naja hannun Nasmah muka haura sama ina faÉ—in "Bari naje na zaÉ“i bedroom É—in da yafi min." koda muka haura É—akunan duka na shiga kana nazaÉ“i É—aki É—aya, nan cikin bedroom É—in nabuÉ—e bathroom É—in sa na shiga mai girma da tsaruwa kamar É—akin kwana. kayan jikina na tuÉ“e duk da ban jima da yin wanka ba nacika ruwa cikin basin nashige ciki, lumshe idanuna nayi ina jin daÉ—in ruwan na ratsani, najima sosai a ciki kana na wanke jikina da sabulu mai sanyin kamshi da nagani cikin bathroom É—in, sannan nafito. Na sami Nasmah gaban mirror ta É—auki janbaki sai murkawa take a bakin ta. dariya nayi ina faÉ—in "Oh wannan yarin ya ke kam akwai ki da son janbaki". itama baki ta washe tana cigaba da kwaÉ“ula janbakin a bakin ta. da sauri na sauka kasa akwatin kayan mu na janyo nadawo É—akin, a sannu na isa gaban wardrobe dan na shirya kayan ciki, ina buÉ—e wa ido na ware cikin wardrobe É—in ganin kaya ashake a ciki, kama daga kan leshi atamfa material shadda dogayen riguna iri-iri, sai dai ba a É—inke suke ba,a hankali na zaro É—aya daga cikin dogayen riguna wan da suke jere gefe guda masu kyan gaske, na dawo gefen Nasmah na zauna, kana na sauya kayana da dogon rigar nan... Tsabar farincikin da nake jin kaina ciki yau bazai misaltuba, muna zaune har su Bappa suka dawo muka sauko parlour'n kasa muna É—an taÉ“a hira dakuma kallon tv. duban Bappa nayi sai kuma kamar an zabure ni na mike ina faÉ—in "Bappa ina zuwa." sama na haura in da na aje karamar jakata ta hannu na É—auko na buÉ—e jakar naciro wayoyin da jiya aka bani wan da tun da na kunna su nakuma kashewa najefa cikin jakar, dakuma ATM É—in da jiya aka bani su a banki, nadawo in da Bappa suke da sauri nace "Kagani Bappa jiya mutanen nan suka É—auke ni sukayi ta kaini bankuna sukayi ta buÉ—e min account, muna dawowa kuma suka bani waÉ—an nan wayoyin ina kunna su kawai Bappa kaga kuÉ—in da sukayi ta shigowa kawai kuÉ—i sunata shigowa cikin accounts É—in". nayi maganar ina wawwaro idanuna alamun tsantsar mamaki. Murmushi Bappa yayi irin nasu na manya kana yace "HAMDAH kenan ai kuÉ—in kine yake shiga cikin asusun bankin ki, duk wani abun da kikaga yake faruwa duka, duk waÉ—annan mutane dasuke ta zirga-zirga da É—awainiya da ke, duk umurnine daga sama, duk kanin su an É—aurasu ne jagora akan lamarin, shiyasa kikaga duk waÉ—an nan abubuwa suke faruwa duk abun da kikaga sunyi umurnine, sunce min ma gobe idan Allah yakai mu za'a fara kai ki guraren da akayi ayyuka wato guraren kaddarorin ki, kije ki gaggansu gobe za'a fara tafiya shiyasa sukace kihuta yanzu." kai na jinjina alamun gamsuwa, ikon Allah abun kamar a mafarki yake zuwar min. knocking É—in da ake ne yasani mike wa nanufi kofar da nafi zaton tanan ake knocking É—in, na isa jikin kofar na buÉ—e, wani nagani tsaye rike da basket har guda biyu a hannunsa, É—an risinar da kai yayi alamun girmamawa kana ya É—ago yayi min barka da warhaka, na amsa kana yace min order ne daga hotel É—in su akace yakawo nan gidan, kai kawai na girgiza kana nabashi hanya yawuce ciki. dinnig table ya isa ya aje kayan abincin kana yayi mana sallama yafita. muna nan zaune a parlour sai wajen la'asar mukaje mukaci abincin, daga nan Bappa yakuma fita domin zuwa Masallaci shida Naseem. Washegari da safe kamar yan da mutanennan suka ce zasu zo suka iso, suna zaune a parlour nikuma ina ciki domin kimsa su Naseem, ina gama kimsasu muka sauko nan muka É—unguma. yau munsha yawo kaman kaman domin kuwa tundaga unguwar muka fara, wani gida mukaje sakanin sa daÉ—an rata da gidan da muke ciki, sannan muka wuce wasu unguwanni biyu duk kanin su da gidaje É—ai-É—ai, wan da an gama musu komai suna kulle,suka nunnuna min dakuma tabbacin nawa ne, nasha mamaki kwarai daganin manyan gidajen wai kuma a matsayin nawa. daga nan wani tsalelen gidan mai muka je tun daga can nahango ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) wan da aka rubuta da manyan harufa a saman gidan man, tunga nesa zaka iya hango shi É“aro-É“aro. idanuna na lumshe tare dayiwa Ubangiji buwayi gagara misali tasbigi a kasan raina kana na buÉ—e, Mun zaga gidan man na yaba da tsarin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba, daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu É—auke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu É—auke da sunan ( *HAM'NAS International HOSPITAL* ) suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba. daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kanin su da tambarin *HAM'NAS* International School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba. Zuwa yanzu kam nidai komai ganin sa nake kamar almara nafara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke faÉ—a min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu.. Damin Bappa narikayi nace nidai yasa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun, yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba, haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije É—auko su nace yace musu kada suzo da komai, dan cikin side É—in dana matsawa Bappa sai ya zabi É—aya daga cikin side É—in gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side É—in. hakan kuwa a kayi ranar da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika É—aukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su. a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su, dan su anan Abuja suke gun ai kin sa. nan muka wuni da su wunin ranar yayi min daÉ—i matuka, sai narika jin su tamkar wani É“ari ga ahalina, ganin su yaÉ—an rage min kewa da begen family na. Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi tafiyar, da sassafe muka É—auki hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai É—aya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, É—aya motar kuma mutane huÉ—u ne a cikin ta suna gaba muna biye da su. mun isa cikin garin Kano da misalin Æ™arfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu, gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni. bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka É—au hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari muka nausa Katsina. Sati biyu muka É—auka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da karÉ“a mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi, lokacin da motar mu tashiga cikin Bauchi state, tashin hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin É“ari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen zufa yashiga keto min, hankalin Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda, cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar Æ™waÆ™walwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare min a kai, kunnuwa na tamkar ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga faÉ—in "Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mutafi wayyo Allah na". kaina nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa. cikin É—aga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace "Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!". gudu direba ya kara bai tsaya ba sai da muka fita a garin, gabaki É—aya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki, Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi gaba É—aya. A hankali narikajin abun da nake jin na sassauta har ya washe. numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da faÉ—in "Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama". yadubeni da kula yace "Sannu ko HAMDAH". kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai. "Zai bari insha Allahu". yayi maganar tare da buÉ—e tafukan hannunsa yasoma karanto Suratul (Khafi) aya goma na farkon surar haÉ—e da ayatul Qursi'yu ya tofa kana yashafamin a kan. cikin yar da da buwayar Allah naji ciwon kan na sauka. Ko da muka shiga jahar plateau state, farkon shiga garin Jos NARKUTA. wasu zafafan kwalla ne suka gangaro kan fuskata tuno da Mama mai awara, da sauri nayi yinkurin yin magana a tsaya amma abun mamaki sai naji harshe na yayi min mugun nauyi gaba É—aya jikina ya sake babu alamar karfi tattare da ni, abun da na fahimta tun lokacin da nayiwa Bappa maga shigar mu Bauchi zan kuma wata maganar naji na kasa, har kuma yanzu ina jin yanayin... da daddare muka shiga Abuja, da kyar da taimakon Bappa na iya sauka cikin mota muka shiga ciki. Inna wuro ta firgita da ganin yanayi na, ko da Bappa yayi mata bayanin abun da ya faru, hankalin ta yayi masifar tashi, yace ta taimaka min naje na kwanta, shikuma yafita can ya dawo da É—an karamin Æ™warya da magani a ciki yabawa Inna wuro yace "Kibata tasha babu komai insha Allah zata ware garin ne kwatakwata basa so tashiga sai dai tayi nesa da shi sun mance cewa Allah baya bacci". Inna wuro tace "Ikon Allah wannan irin shiga sakani sai sakayyar Ubangiji". ko da Inna wuro ta bani maganin inasha bada jimawaba bacci yaÉ—auke ni, ranar a kaina ta kwana, Fatu kuma tana tare da su Naseem a É—aya É—akin dake kusa da nawa. washegari kuwa cikin yarda da buwayar Allah namike garau... muna tare a parlour ni Inna wuro Fatu dan har lokacin basu koma side É—in suba, labarin garuruwan da mukajejje narika basu ina washe baki da faÉ—in "Allah Inna wuro bakuga abubuwan yan da sukayi kyau ba kai har da garin da ban taÉ“a zuwa ba". nayi maganar ina washe baki, dariya suka rika min, nan Bappa yashigo ganin jikina shima yazauna mukayi ta hira.... bayan kwana biyu Mutane biyu daga cikin jagororin nan suka zo su da wasu mata guda biyar sukace na zama a cikin su wan da zasu rika yi min ai ki, mata ne irin wan da suke karkashin paundation, irin waÉ—an da mazajensu suka sake su dakuma wan da mazajensu suka rasu, akan É—auke su ai ki irin gidajen masu kuÉ—i É—in nan, a cikin su na zaÉ“i guda uku dasukafi kwanciya min a rai, kana nace zan gwada ai ki da su. É—aya na É—auke ta a matsayin mai kula da su Nasmah dakuma kula da tsaftar side É—in, na biyun kuma mai girka abibci, sai kuma É—ayar na turawasu Inna wuro ita zata rika kula da tsaftar side É—in su dakuma girkin su. nan suka kuma gabatar min da masu maza wan da nazo nasame su a cikin gidan, direba sai mai baiwa fulawa ruwa shi zai rika wanke mota, sai mai gadi dakuma mai kula da tsaftar farfajiyar gidan gaba É—aya. mun zauna da su na É—an wani lokaci na fahimci mutane ne masu kirki da rukon amana. Haka rayuwa tacigaba da tafi, tuni akayi bikin buÉ—e masana'antu da masallatan nan manyan shuwagabannin Nigeria sun halacci torurrukan sun kuma bada gudummawar su kwarai da gaske wajen ganin an É—ibi ma'aikata masu inganci. Bayan wani lokaci Tuni aka damkamin ragamar duk wasu kaddarori na ni nake bada umurnin ayi da kuma kar ayi, har kuma yanzu muna tare da jagororin nan su suke sanya ido kan ganin komai yatafi dai-dai. tuni nasa aka baiwa Fatu uniform a É—aya daga cikin makarantu na, dan dama acan rugar ma tana karatun ta tacigaba a nan. Zaune nake a parlour ina dudduba jerin sunayen mata da matasan da nasa a É—iba, a karkashin paudasion É—ina domin basu tallafin wasu kuÉ—aÉ—en da zai jamusu jari domin dogaro da kansu, matasa hamsin da kuma mata hamsin,na tura da kuÉ—aÉ—en tallafin izuwa asusun *HAM'NAS* paudasion. a hankali na mike tsaye tare da yin mika haÉ—e da salati, wayoyina na tattara haÉ—e da sabuwar system É—ina, na haura sama, kan bedside na ajiye su kana na haye gado dan bacci nake ji, ina so nayi baccin kafin su Naseem su shigo dan suna can side É—in su Bappa. har na kwanta na tuna da akwai maganar da nake so muyi da Bappa kan wani Company na murza karfe da ake gina shi a Lagos, mikewa nayi na fita dan ina so muje ziyarar gani da ido acikin satin nan. da gudu Nasmah ta shigo tana faÉ—in "Mommy kin ga Naseem ko jai camin jiji". Naseem shima dagudu yashigo yana binta da abun yana dariya, Fatu na biye da su tana dariya da faÉ—in "Naseem kabari kar ka sa mata". da sauri nakarasa sauka kan step na rungumo Nasmah dake falfala gudu kamar zata kife kasa nace "K.......!â˜? Mommyn Twins ce 5 "Kai Naseem me zaka sa mata kai ka bari zata faÉ—i fa kabari." nayi maganar ina É—ago Nasmah cak na rungume ta a jikina, shiko dariyar yake yana matsowa in da muke ya É—aga hannun sa sama tare da yin É—agelgel da kafa, yana washe baki, na ce "Idan ka zo nan sai na mare ka, zo kagani zo ka samata kagani, dariya sosai yarika yana faÉ—in "Mommy dan tamata ne dan ta mata wannan." "To ka samata kagani sai na maka bulala." kiran Talatu mai kula dasu nashiga yi ina faÉ—in "Talatu zo ki kaishi wa É—awisu ta cakwaÉ—e shi tun da dai shima sa mata jiji zaiyi." Talatu ta iso da sauri tana faÉ—in "Ayi hakuri Hajiya kar a kaishi wa É—awisu zata cake shi, zo nan Naseem kada kasa mata ko, so kake a kaika wa É—awisu ta cake ka,zo ko É—an lele na mene ne zaka sawa Nasmah É—in?." É—an karamin tafin hannunsa da ya dunkule ya buÉ—e kaÉ—an ya nuna mata kana ya kuma dun kulewa yana cigaba da dariya, "Lalala shine zaka sa mata?." cewar Talatu tayi maganar haÉ—e da dariya, kai ya gyaÉ—a yana washe baki, duban Fatu nayi ina faÉ—in "Wato Fatu keda Naseem kuke sawa Nasmah ta abin tsoro ko? to bazata sake wasa da ku ba." dariya Fatu tayi tare da faÉ—in "Allah Adda HAMDAH kin ga bansan in da yasamo ba kawai ganin sa nayi ya shigo da shi a hannunsa,malam buÉ—e takarda ne fa." "Au malam buÉ—e takarda ne ya É—auko shine yake so ya sa mata to bari yagani sai an kaishi wa É—awisu shima, shine baki karÉ“a ba ko Fatu kika tayashi tsoratar da ita." "Allah Adda HAMDAH binshi nake na karÉ“a shine yagudu." Talatu ta É—auke shi tabuÉ—e hannunsa taciro abun tana faÉ—in "Kawo shi nan a yasar da shi kada ka saka mata kaga tana jin tsoro, kaima kada ka sake É—auka a hannun ka." tana rike da hannunsa tafita waje ta yasar da shi kana suka dawo ciki. karaso wa cikin parlour nayi na zauna kan kujera tare da zaunar da Nasmah kan cinya ta, na dubi Fatu nace "Fatu Bappa na ciki ne?." tace "A'a yafita". sai kuma ta turo baki gaba tare da faÉ—in "Adda HAMDAH nifa wannan sunan Fatun nace ki dai na faÉ—in shi, Fatun nan fa a can Ruga ne fa ake kiran Fatun nan tun da yanzu mutum yazo birni har yanzu ayi ta ce mishi wani Fatu, gaskiya Adda HAMDAH ni wlh na canza suna Fatu ai duk su Inna wuro ne suka wani lankwasa min suna yaya Mahmoud dake shi a birni yake ai Fatima yake cemin,haka jiya wata Æ´ar ajin mu tana ta min dariya wai ni Fatu, aradun Allah na canza suna ko a ajin mu ma na faÉ—a na canza suna". dariya muka tuntsire da shi, Talatu tace "To Fatu man yan gari me kike so ace miki kenan?". "Ai sunana da yawa masu daÉ—i ma, Nana, Fatima, FaÉ—imatu, Faty Zarah duka gasunan masu daÉ—i sai a rika cewa mutum wani Fatu kamar rugo". nace "To lallai kam kamar kin sani da ma kam wannan sunan bai dace da ke ba yanzu dai kawai Faty za'a rika ce miki." tace "Yauwaaa Adda HAMDAH Faty wlh yama fi amma kuna ta cemin wani Fatu kamar rogo". "Hhhhh Faty kenan Allah bakida dama". tace "Yauwa Adda HAMDAH gashi kin iya faÉ—in sunan dai-dai mai daÉ—i". kai kawai na girgiza ina dariyar ta. tace "Zo muje muyi wasan mu o Nasmah." nace "O'o kuje bazata biku ba kuje kusata kuka bazata biku ba kam kutafi ku." "Allah bazan barshi yasa mata ba". fuskata na kawo dai-dai fuskar Nasmah nace "Zaki bisu?". kai ta gyaÉ—a "To muje daga gun na duba ko Bappa ya dawo". nafaÉ—a ina mikewa na direta kasa tare da ruko hannunta muka nufi side É—in su Inna wuro. a parlour muka tadda Inna wuro Bappa bai dawo ba sai na zauna muna É—an taÉ“a hira da ita. muna nan zaune har Bappa ya shigo yazauna muka cigaba da hirar da shi, acikin hirar nake yi masa maganar yace kwarai kuwa ya dace kam aje domin a ganewa ido, in yaso satin sama sai a je, duk da akwai idanu da yawa akan lamarin. nace "Toh Allah yakai mu." muna zaune sai ganin Naseem mukayi ya kin kimo school bag É—in Faty, a tsakiyar parlour'n ya zauna ya tuttuÉ—e littatafan cikin jakar kasa ya É—auki littafi guda ya buÉ—e yana ta gwalaÉ“e wai shi yana karatu. dariya duka muka saka, Faty ko da gudu ta mike taje ta tattari litattafan ta tana ta faÉ—in "Kai kasan meye a ciki ka iya karatu ne". Inna woro tace "To ai karatun yake baki gani ba". cikin muryar dariya nace "Um karatu yake ko gwalaÉ“e har da wani mike kafa kamar mai karatun gaskiya." "Ah to gaskiya za'a saku a makaran ta tun da har ka iya É—auko littafi kazauna ka buÉ—e kana karatu". cewar Bappa yana yi masa dariya. "Wlh Bappa nima dama ina so a turasu makaranta amma a sona sai sun cika shekara uku da rabi, amma gashi nan bakin su ya buÉ—e kawai sutafi yanzu." Bappa ya jinjina kai kana yace "Kwarai kuwa ya kama ta kam tun yanzu, tun da ga bakin su nata kan buÉ—e wa a kai su makaranta yakarasa buÉ—ewar a can".... A cikin satin akayi musu komai da komai nashiga makaranta, sai dai wata makarantar daban badaga cikin nawa ba, dan *HAM'NAS* International School Of Science Of Technology. suna da nisa saka nin mu, duk da dai shima makarantar da aka sasun yana da É—an nisa sai dai baikai su nisa ba, Islamiyar da a kasasu kuma anan unguwar tamu yake. ranar da zasu fara zuwa kuwa zo kaga murna wajen su, da misalin karfe 7 na safiya Talatu taga ma shirya su tsaf, Zulai kuma ta shirya musu lafiyayyen breakfast É—in su. ina rike da hannun su muka fito in da Talatu ke biye da mu rike da school bag É—in su da baske, parking lot muka nufa, tun kan mukaraso Yakubu direba dake goge mota yayi hanzarin buÉ—e marfin motar, cike da ladabi yaÉ—an duka yana faÉ—in "Barka da safiya Hajiya." "Yauwa barka." nafaÉ—a cikin É—an jin nauyin yan da suke yimin idan zasu gaida ni, duk kanin ma'aikatan gidan sun girme min nesa ba kusa ba wasu ma sun haife ni sun juya,nakan ji nauyi a duk san da sukayi min irin wannan gaisuwar. Nasmah naÉ—aga nasaka ta cikin motar, Naseem kam cemin yayi shi da kan sa zai shi, Talatu tayi dariya tana saka musu school bag É—in cikin mota tace "Naseem iyayen rigima kai bazaka bari a saka ka ba da kan ka zaka shi ka girma ashe". kai ya gyaÉ—a yana gyara zama tare da faÉ—in "Eh nagima da kaina naciga." tace "To babban zance ke kuma Nasmah yaushe zaki girma?". Nasmah ta cuno É—an karamin bakin ta gaba tace "Gobe dan gima ai". murmushi nayi tare da shafa gefen suskar ta nace "Au ke sai gobe zakiyi girman naki?". kai ta gyaÉ—a tana murmushi, kansu na shafa dukansu nace "To sai an dawo ayi karatu sosai kunji". sukace to. direba yaja mota ina É—aga musu hannu suma suna daga min mai gadi yawangale get suka fita.. Kwana uku kullum cikin É—oki suke zuwa makarantar ranar na huÉ—u kuwa É—oki tafara kare wa, ina kwance sai ga Nasmah ta shigo da gudu É—aure da É—an karamin towel É—in wankan su tahaye gado ta É“oye a baya na tana faÉ—in "Ni bajan je school in ba." zanyi magana sai ga Naseem shima da wandon uniform ajikin sa babu riga, sai muryar Talatu daga bakin kofa tana faÉ—in "Kai Naseem kazo nakarasa saka maka kayan". mikewa nayi zaune ina faÉ—in "A'a yaya ne tsaya mana". ai kan kace me shima ya É—ale gadon cikin cuno baki gaba Nasmah ta daÉ—a laÉ“ewa jikina tana faÉ—in "Ni Mommy bajan je School in ba". ido na waro ina duban Naseem shima da yake faÉ—in "Nima bayan jeba". kai na langwaÉ“ar gefe nace "Oh yanzu wa School É—in kuke gudu ne, bazaku je ba kuma, yaushe ne kuka fara zuwan da har zaku fara fashin sa?, kuna ji ko kuzo ku je makaranta". kafaÉ—a suka make alamar o'o, rungumo su nayi dukan su ajikina ina murmushi kana nace "Ina kallon da mukayi jiyan naaan na sojojin naaan, to waye meson zama irin su a cikin ku?". da sauri Naseem ya mike a jikina yana washe baki tare da nuna kanshi yana faÉ—in "Nine-nine". "Yau wa to har in kana son kazama soja to ko sai kaje makaranta, kaje makaranta kayi karatu sosai daga nan zaka zamo soja, in kuma baka so to kazauna kawai a gida ina baka so kazama sojan zauna abin ka kada kaje School". kai yashiga girgizawa da sauri yace "A'a a'a Mommy ina so to danje School in nine toja". "Yauwa to kada ka sake cewa bazakaje School ba dan soja baya fashin School, Nasmah ta kefa? baki son zama sojan ne?." da sauri tace "Ina to." nace "To ke bama soja zaki zama ba Dr Nasmah ce a nan, ina kina so kizamo likita kirika yiwa mutane allura." ta gyada kanta da sauri, nace "Yauwa kinga in kikaje makaranta kikayi karatu da yawa to zaki rika yiwa mutane allura". kuma gyaÉ—a min kai tayi da sauri tun kan in karasa maganar, murmushi nayi ina shafa kansu. kallon kofa nayi tare da É—aga murya nace "Talatu kawo musu uniform É—in su saka". daga can bakin kofar in da take tsaye ta waje ta amsa da to kana taturo kofar tare da sallam, nakarÉ“i uniform É—in nafara sakawa Naseem rigar sa wan da shi dama ta saka masa wandon shine yagudu,gyara masa zamar rigar nake ina faÉ—in "Um kaga soja wannan yaro zai iya rike bindiga in ya girma ya zama soja". baki yarika washewa yana É—aÉ—É—aga kafaÉ—a da faÉ—in "Nine toja ai nine toja". "Ai kam ga sojan gasken gaske". a haka nagama kimsashi kana nasakawa Nasmah ita ma inata faÉ—in mata itace Dr zata rika yiwa mutane allura. nariko hannun su muka fito parlour nan muka iske Zulai da kayan break É—in su, Talatu kuma ta É—auko musu School bag É—in su, muka nufi parking space, da murna suka shige cikin motar Naseem sai faÉ—i yake nine toja, Nasmah kuwa ta dube ni tace "Mommy ni meye?". kumatun ta naja nace "Kece Dr me yiwa mutane allura". sai washe baki suke cike da murna direba yaja motar suka tafi. Wani sati na gewayo wa muka fara shirin tafiya ziyarar gani da ido nan muka É—auki hanyar zuwa Lagos, sai dai wannan karon bantafi da su Nasmah ba saboda School, ni da Bappa da wasu jagorori biyu muka tafi, mun isa Lagos lafiya awani kayataccen hotel akayi mana masauki, mun isa yau washegari muka nufi Company da ake ta kan ginashi tamfatsetsen Company wan da girman sa ya kai ya kawo, an kai ni gurare da dama acikin sa an nunnuna min, masha Allah komai yayi saura kaÉ—an a kammala. a gajiye muka koma masaukin mu kansan cewar da kafa akayi ta yawo damu acikin Company'n. kayan jikina na tuÉ“e nashiga baya na watsa ruwa kana nafito na sauya kaya na haye gado dan na É—an huta, waya ta na É—auka na laluÉ“o lambar Talatu bugu É—aya ana biyu ta É—aga, da sallama bayan mun gaisa nace "Ina mutanen naki?". tace "Gamu nan muna tare da su a parlour muna kallo, ungo Naseem karÉ“a ga Mommy tana magana." tasaka masa wayar a kunne, "Mommy da mu biki kijo jike da mu". murmushi nayi jin muryar Naseem nace "To zan zo naje da ku, kuna karato sosai ko?". kai ya gaÉ—a, Talatu tace "Ka amsa da baki ai bata ganin ka". yace "Eh." "To a dage sosai, bawa Nasmah wayar." ya mika mata Nasmah tace "Mommy kina ina, damu biki kije da mu". nace "Nasmah to zan dawo nazo naje da ku kinji." "Mommy yaushe zaki jo?." "Gobe zan dawo naje da ku kinji". to tace, haka sukayi ta zuba min surutu da gwalaÉ“en su ni ma ina biye misu kun kai minti 30 a haka daga bisani na kashe wayar. na gyara kwanciya ta dan bacci nake ji. kwanan mu uku a Lagos muka juya Abuja. Yau asabar ba makaranta muna tare da Æ´aÆ´ana a parlour munata sharholiyar mu cikin farin ciki da jin daÉ—e, duban daular da nake ciki a rayuwa da nake yin ta yan zu nayi, Allah yabani duniya ya É—aga ni ya É—aukaka min daraja ta, a lokacin da duniyar ke kokarin suÉ“uce min a lokacin da rayuwa ta tazomo tamkar kwai a cikin tray, wan da yazamo baki-baki saura kiris ya suÉ“uce kasa ya tarwatse. numfashi na sauke lokacin da tunanin Inna ta ya zomin, wasu zafafan kwalla ne suka zubo min, Allah sarki Inna ta tabbas na yarda wani hanin ga Allah baiwa ce, ya É—auke ta a lokacin da nake tsananin bukatar ta arayuwa ta, lokacin da duniya ta juya min baya lokacin da narasa madafar dafawa lokacin da na gwammaci mutuwa ta da rayuwa ta. ya É—aukaka darajata abayan bata nan ya azirtani da arziki mai tarin yawa, wa zai iyayin duk wannan in banda *RABBUSSAMAWATI WAL'ARDI*. Allah sarki Inna ta Allah yakai haske kabarin ki ya sa mutuwa yazame miki hutu. wasu kwallan nakuma sharewa lokacin da na kuma tunawa da wata uwar wato Mama mai awara, Allah sarki rayuwa ta cito ni lokacin da duniya tafara wasan kwallo da ni, matar data jajirce wajen ganin an ceto rayuwa ta gun haihuwa, da awancan lokacin bata samo kuÉ—in da za'a min cs ba wata kila da yanzu na mutu da ni da su duka aciki, tarike ni tamkar É—iyar da ta haifa a cikin ta. lokacin da tayi nisa wajen ceto rayuwa ta sai ta tsuÉ“uce min. sai gashi yau Bappa yamaye gurbin su, yazame min uba kuma uwa, ya jajirce yatsaya kan lamari na yazamo silar isata matakin danake yanzu, matar sa ta zame min uwa Æ´aÆ´an sa suka zame min yan'uwa. Rungume su Naseem nayi a jikina ina jin wani irin kuna, rumtse idanuna nayi da karfi jin kaina yana wani irin tsara min, lokacin da tunanin abun da yayi silan rabani da ahalina yashiga yimin yawo a kwakwalwa da zuciya ta. zunbur na mike nashige bedroom É—ina, sam bana son narika tunawa da hakan duk ranar da na tuna nakan kwana cikin kunci da bakin ciki da matsanancin ciwon kai, dan ranar zan kwana ina kuka. Zubewa nayi kan kado nakife fukata jikin pillow, kai na rika juyawa ina ta fafutukar son na mance da tunanin, amma ina sai daÉ—e tahomin yake, da karfi cikin karaji narika faÉ—in "Wlh Allah Abba ban taÉ“a ai kata zina ba, Ya SALEEM ba wani É—a na mijin daya taÉ“a sani na mace bayan kai, duk da karancin shekaru na Inna ta ta tsoratar dani haÉ—e da kyamatar dani illan dake cikin zina, Ya SALEEM kai ka sanar dani mene ne aure, a lokacin da kuma nasan mene ne auren akayi min kagen zina aka kuma sheganta min Æ´aÆ´a, bazan taÉ“a aikata zina ko da ace bani da aure bare ina da shi É—in." wani irin kuka ne ya tsuÉ“uce min, na kankame jikin pillow'n ina cigaba da kuka mai tsanini. nakai tsawon awa guda ina kukan kana da kyar na sai-saita zuciya ta na baiwa kai na da kai na hakuri, kana nagyara kwanciya ta wan da ba bacci nayi ba, sai tulin tunani daban-daban. har yamma ina nan kwance, ganin tunani yana kokarin kassara ni sai na mike nanufi side É—in su Bappa, a can na iske su Naseem, har dare muna can sai wajen bayan sallar isha kafin muka koma side din mu. zuwa lokacin kam naji saukin damuwa ta kwarai dan su Inna wuro sun yaye min shi da hirarsu mai É—ebe kewa. Washegari Lahadi ma ban yarda na zauna a side É—i na ba da sassafe na wuce part É—in su Inna wuro acan mukayi breakfast, a nan nawuni muna hirar mu cikin jin daÉ—i. Yau Monday da misalin karfe 7 narako su Nasmah har sai da naga tashin su kafin na koma ciki, ina gama abun da zanyi nawuce side É—in su Bappa, ina shiga bayan mun gaisa Bappa yake cemin "Dama yanzu nake da shirin niman ki, kan ai kin masallacin nan ne harfa an rigada an gama shi, wan da aka bashi kwangilar jiya yake sanar min da cewa an gama." da murmushi sosai kan fuskata nace "Kai masha Allah kai amma dai ai kin yamin sauri wlh." Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in "In dai da kuÉ—i a kasa komai cikin sauki yake zuwa, in dai da kuÉ—i ai komai mai sauki ne Allah dai yaba da ikon cin jarabawar da yayi dan shi kanshi arziki babban jarabawa ne, yakan kai mutum wuta yakan kaishi aljanna, kuÉ—i kamar takwabi yake idan kayi jahadi da shi shigar aljanna mai sauki ne idan ka ai kata É“arna da shi shiga wuta mai sauki ne, Allah yasa mudace." Amin Amin. duk muka amsa da shi cikin washe baki nace "Bappa masallacin nan fa nagina ne saboda Inna duk ladar arika kai mata kabarin ta, shima asibitin da yanzu ake gina shi idan a ka gama komai kyauta za'a rika yi duk ladar arika kai mata cikin kabarin ta". "Masha Allah masha Allah". abun da Bappa da Inna wuro suka rika faÉ—a kena. Bappa yace "Ubangiji Allah ya tabbatar mana da hakan Allah yajikanta da rahama ya kai mata dukkanin ladan kabarin ta ya kyautata namu bayan nasu, kai sannu HAMDAH kinyi tunani kwarai da gaske Allah ya saka miki da mafificin rahama." Amin. nace ina mai jin sanyi da daÉ—in addu'ar da yake min. Muna nan zaune a parlour ban ankara ba sai gani nayi karfe 12 har da É—ori, wayata na É—aga da sauri ina faÉ—in "Ikon Allah lallai guri babu wuya dubi 12 har ta gota an yama Yakubu yadawo kuwa bari dai na kirashi naji." nayi maganar ina laluÉ“o lambar sa, wayar tayi ta ring bai É—aga ba, nakira yakai sau biyar bai É—aga ba, na sauke wayar ina faÉ—in "Oh to ya ajiye wayar a ina ne shi ga lokacin É—auko su Nasmah daga School yayi, gashi nayi ta kiransa bai É—aga wayar ba." Bappa yace "Ko ina ya aje wayar to shi, ina yaje haka ayi ta kirashin baya É—aga wa". nace "Wlh É—azu ne na ai keshi gidan Hajiya Firdausi matar ministar Bukar, akwai wasu kayan da tayi min tallar su wan da tayi odar su daga jamani, to sun yi min na tura da kuÉ—in to É—azu take faÉ—a min direban ta baya nan ko zan turo nawa direban ya amso min, shine na tura shi to gashi har yanzu bai dawo ba nayi ta kiran shi ma bai É—auka ba". nayi maganar ina kuma É—aga wayar nakuma niman lambar sa. Hajiya Firdausi matar ministan Abuja ne, na yar da idan Allah yayi maka rufin asiri babu irin mutanen da bazaka gani ba ka kuma yi tarayya da suba, ire-iren irin waÉ—an nan matan manya muna hulÉ—a da su sosai wasu sun girme min nesa ba kusa ba, wasu ma sun haife ni sun juya amma haka muke cuÉ—an ya da su. Mikewa nayi da sauri ganin na kuma kiran sa har sau biyu nan ma bai É—aga ba, nace "Bappa bari naje kawai na É—auko su har yanzu bai É—aga wayar ba, kar suyi ta jira kasan mutumin ka yanzu haka yana kan musu rigimar zai dawo gida". Bappa yace "Maza hanzarta kam ga guri nata kan tafiya". da sauri nafita ina shiga side É—ina mayafi kawai na yafa dan dama a kimtse nake na É—au É—aya daga cikin makullen mota da suke cikin drower, da sauri na sauka na nufi parking space. kana nashiga motar nayi wa motar key, tun kafin na karaso bakin get maigadi ya wangale min get yana fadin "Adawo lafiya". Saboda yanayin gosulo na bata lokaci sosai a hanya dan har karfe É—aya ta cika har ta É—an gota, kafin nan na isa makarantar su. tun kafin nakaraso get É—in makarantar, na zubawa kofar makarantar ido sosai dan ganin wasu yara rike a hannun wani mutum "Kamar su". nafaÉ—a a file, nayi saurin isowa gurin, da mamaki nazuba musu ido ganin suÉ—en ne, yana rike da su suko sai washe baki suke, shikuma mutumin yana ta tafiya da su yana nufar wata mota dake fake taÉ—an can gefe da get É—in makarantar, yayin da yake ta girgiza kai alamun yana jin surutun da suke ta zuba masa. cikin hanzari na isa gefe nafaka cike da mamakin ganin nufar motar yake gadan-gadan na É“alle marfin mota na fita da sauri, cikin hanzari nasoma bin bayansu ina faÉ—in "Kai Naseem Nasmah!, malam ina zaka kaisu kuzo nan ku wuce mutafi". mutumin bai juya ba sai su yaran ne suka juyo sai kuma suka kawar da kansu suka juya suka cigaba da tafiya suna cigaba da zuba masa surutu. da sauri nasha gaban su gani yan da suka batsar kamar basu sanni ba nace "Kai ina muku magana kuna jina ina zakuje kuwuce mutafi malam ina zaka kaisu?". sai sannan mutumin yaÉ—an dukar da kansa dai-dai tsawon su kana yasoma magana "Kunsan ta ne?." batare da yaÉ—ago ko ya dube ni ba ya ce "Ke a ina kika sannu bamu hanya mu wuce." ido na waro cike da mamaki jin abun da yafaÉ—a tare da mamaita kalmar nasa "Nasan su? nasan su fa kace, da alla malam ka sake su ina magana kana cigaba da tafiya da su." gefe na ya gota batare da yace komai ba ya karasa jikin motar nima da sauri na rufa musu baya ina cigaba da faÉ—in "Kai malam ina tambayar ka ina zaka kai su wai kana tambaya ta nasan su ne, ni zaka tambaye ni nasan sune, tambaya ta kake nasan su? dalla kasake min yara muwuce,ina ne zaka dasu kake nufar cikin mota da su?, idan baka sake suba yanzu-yanzu zan kira maka hukuma anan." baiyi magana ba sai mika hannun sa yayi yabuÉ—e marfin motar, yaÉ—au ko kwalin chocolate yaciro chocolate guda huÉ—u yabawa Nasmah biyu ya baiwa Naseem biyu kana yace "To ga tsarabar ku kuci wannan yanzu, wannan kuma sai kusa a aljuhu." yafaÉ—a yana cusa musu wani chocolate É—in cikin aljuhun wandon su. da mamaki nake kallon su ganin yan da sukayi tamkar basu sanni ba, sai murna da tsalle suke suna faÉ—in "Ye am bamu da yawa ye am bamu da yawa." cikin takaici nakai hannu zan fisge chocolate É—in, da sauri mutumin ya janye su gefe kana yaÉ—ago kansa tare da zuba idanun sa cikin nawa, wani irin dirrr naji a cikin jikina tamkar jan wutan lantar ki.......! Mommyn Twins ce 6 Yan da idanun sa yasarkafu cikin nawa haka babu zato ko sammani shi yasani shiga yanayin, sai kuma na gyara tsayuwa ta da kyau, wani kallo yake bina da shi daga sama har kasa kana yace "Na É—auka kafin kiran hukuma ihu zaki yi ta yi kitara jama'a kice ga É“arawo yazo satar yara, ke ba'a yi miki ihu ba har ke zaki wa wani ihu? karfe nawa ne yanzu wai wannan lokacin ne lokacin zuwa É—aukar yara a makaranta,abar yara can kowa ya watse sai su kaÉ—ai a cikin makaranta, sabo da baki san abun da kike yi ba an turaki É—aukar su kin tsaya kin É“ata lokaci a hanya kina damuwar ki wata kila ma kinbi gidan kawayen ki kin gama sharholiyar ki, kafin nan kika zo wai ke a hakan kinzo É—aukar su a makaranta, karfe nawa yanzu?. karfe nawa ne yanzu?!". yakuma nanata tambayar, yana maganar ne ida nunsa a kaina da kuma alamun jaddada tambayon da yake jefa min, gashi dai maganar cikin faÉ—a yake yin sa amma lamÉ“ansa a hankali suke motsawa. dogone yana da faffaÉ—ar kirji da zubin kakkarfan maza, fuskarsa na É—auke da É—an siririn saje wan da ya zagaye fuskar nasa har zuwa É—an gemun sa da bai wuce rabin kamu ba, irin gemun da gayu suke bare. baza a kirasa da fari soll ba sanna kuma ba baki bane, hasken sa dai-dai. kwantaccen gashin kansa baki sitif yasha gyara mai tsamtsi da tsulÉ“i sai wani yal-yal yake, sabo da iskar dake kaÉ—awa. Kaina nakawar gefe tare da murguÉ—a baki nashi a wanne zai zauna yana wani masifa to ina ruwan shi ne ma. É—an rutsunawa yayi yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran kana ya dubi ko wannen su yace "Idan kunje gida kuce wa Mommyn ku kada a sake turo Aunty ku ta É—auko a School a rika ai ko me wayo yarika É—auko ku, wan da bazai barku kuyi ta shan wahala a nan ba, kunji ko?." kai suka gyaÉ—a suna ta faman shan chocolate "Yauwa to kuje gida sai gobe zan kawo muku wani chocolate É—in, kada ku man ta in kunje gida kufaÉ—a wa Mommy kada a kuma turo wannan Aunty'n naku É—aukar ku a School a aiko mai wayo." yayi maganar yana yi musu alama da suje in da nake yana binsu da murmushi, ido na waro cikin masifa nabuÉ—i baki zanyi magana, dai-dai lokacin mota ta faka gefen mu, da mugun gudu, Yakubu direba yafito da sauri ya iso in da muka yana faÉ—in "Ranki shi daÉ—e Hajiya wlh gosulo ne yatsare ni tun É—azu babu ta yan da zanbi na koma da baya na canza wata hanyar, gaba da baya motoci suka sani a tsakiya,jibi kumatu na har mari nasha dana nimi in juya dan na canza hanya, Hajiya a gafarce ni, wlh gosulo ne, ita kuma wayar sam na mance jiya da zankwanta bacci nacire ta a kara yau har gari yawaye kuma ban mai da kararta ba, Hajiya ayi hakuri da Allah." maganar yake tamkar zai zuba guiwowin sa a kasa yana tafa bayan hannun sa a cikin É—aya tafin hannunsa alamun roko, banyi magana sai juya wa nayi nanufi gun motar dana zo da ita, dan wannan mutumin yakure É“ata min rai. Muryar Yakubu naji yana faÉ—in "A'a ranka shidaÉ—e ina wuni barka da warhaka." bude motar nayi nashige ciki batare da naji amsa gaisuwar da yake yi masa ba. sai juyawar sa nagani yamatsa jikin motar sa yana kokarin bude marfin gidan baya, da sauri a ka buÉ—e gidan gaba wani ya fito cikin hanzari yarigasa kai hannu jikin kofar yabuÉ—e, kana yaÉ—an ja dabaya ya bashi hanya yashige motar ya mai da murfin ya rufe, kana shi kuma yakoma mazaunin direba yaja motar sukayi gaba. Yakubu yakamo hannun su Naseem ya kawo su motar da nake yabuÉ—e gidan baya yasaka su, yace "Hajiya bari na rufe wancan motar sai na kaiku gida a wannan na hau abun hawa na dawo na É—auki wanca É—in." yajuya da sauri ya nufi in da motar da yazo da ita yake, fita nayi nakoma baya in da su Nasmah suke, yana kulle motar yadawo yashiga mazaunin direba yaja motar. Munbar harabar makarantar da É—an nisa kana na juyo na dubi su Nasmah dasuka gama kwaÉ“e jikin su da chocolate, ganin ina kallon su sai Nasmah ta miko min na hannuta tace "Mommy akici". cikin masifa nace "Ai sai kun sha duka ba kun iya kwaÉ—ayi ba bakusan mutum ba kuka ma binsa, waya sani ma ko mai satar mutane ne yayi gaba da ku wata kila ma badun na iso da wuri ba da yanzu yayi gaba da ku, yaje yayi kuÉ—i da kanku, idan kuka kara ganin mutum baku sanshi ba kuka bishi sai na zane ku, bare har ya baku abu ku karÉ“a sai na yanke hannun ku, yajaku mota zaiyi gaba da ku Allah ya so ku ai da kuna can Allah kaÉ—ai yasan halin da kuke ciki, badun na iso da wuri ba, É—an rainin hankali wai arika ai ko mai wayo yarika É—aukar ku to ina ruwan sa ma daku tukun, mttsss." nayi maganar tare da jan tsaki. baki Naseem yawashe cikin É—an sallen murna daga zaunen da yake yace "Ai Daddy yace dai caya mana mota." wani irin faÉ—uwar gaba naji da ya ambaci sunan Daddy da sauri nace "Kai Naseem waye kuma Daddy?." Nasmah ce ta caÉ“e zancen da faÉ—in "Daddy daya bamu chocolate yace dai cayamin jigi haida mota da chocolate da yawa." da karfi jin yan da zuciyata ke tafarfasa kai na ke sara min nace "Kai ya isa! idan na kara jin kalmar wani Daddy a bakin ku sai na fasashi, ku bani chocolate É—in nan." nafaÉ—a ina karÉ“e chocolate É—in hannun su na zuge glaas É—in motar nayi wurgi dashi. maganar Yakubu najiyo wan da tashin hankalin da nashiga ciki yanzu sama-sama nake jiyo shi yana faÉ—i "Hajiya ai shi wannan mutumin bamai satar yara bane mutumin kirki ne, shine Ahmad Tijjani Sabil mai kamfanonin nan wan da ake nuna shi agidajen talabijin, ai ko É—azu dana kawo su makaranta na tarar da motar kamfanin shi tana sauke kujeru dawasu kayan amfani na makaranta,ai kin sa kenan yana da yawan taimako kuma taimakon sa yafi yawa a inda yara suke." "Ahmad Tijjani Sabil." na mai-mai ta sunan a raina ina ta son tuna in da nasan sunan, sai a lokacin na tuna É—azu da safe ake labarai a kansa a gidan tv anan nataÉ“a jin sunan. Naseem yace "Ai nima Daddy yace dai taya min mota in tuka akaina." cikin tsawa nace "Ban ce kada naji wani ya kara min maganar wani Daddy anan ba?, rufamin baki idan ka kara sai na fasa ma baki bari ka gani." Yakubu kuwa ci gaba da zuba yake wan da ma gaba É—aya hankali na baya cikin motar da jikina gaba É—aya. Muna komawa gida nakira *HAM'NAS* Store Complex nace a kawo min motar wasan yara guda biyu da wasu kayan wasa, batare da É“ata lokaci ba motar ShopRite É—in ya iso, a É—akin kayan wasan su aka jibge musu, ihun murna suka sake ganin motocin cikin tsallen murna Naseem yace "La iyin motan da Daddy yace dai taya mana babba." da sauri na mike daga kan kujerar da nake zaune cikin É—akin kayan wasan su, hannayen su duka na riko nadawo na zauna, inajin zuciya ta na min mugun É—aci da kuna a duk san da naji sun furta kalmar Daddy a bakin su, duban su nayi dukan su nace "Kuna ji ko Naseem Nasmah?, shi wancan mutumin ba Daddy'n ku bane baku sanshi ba kuma ku bakuda Daddy, nice Mommy'n ku kuma nice Daddu'n ku bakuga na siya muku mota ba, idan kuka sake faÉ—ar Daddy bazan sake siya muku mota ba, kuma zan sa akwashi waÉ—an nan ma a tafi dasu, baku da Daddy nice Daddyn ku kunji ko?." kai suka gyaÉ—a nace "To maza kuje kushiga motar ku." ai ko da sauri suka ruga in da motar suke suka shiga, ina tare da su a É—akin sai zaga É—akin suke a cikin motar, suna dariya. numfashi nasauke ganin suna cikin farinci sosai, Nasmah ta danna motar ta motar tatafi tsuu zata garu da jikin garu-bango da sauri na mike na tafi da gudu na taro ta, na ciro ta ciki ina faÉ—in "To ya isa haka muje kuyi wanka kuci abinci sai kuma anjima zan sa afito muku da shi can tsakar gida kuyi wasan acan." nayi waje da su. Yau Juma'a da wuri Talatu tagama yi musu shirin makaranta, narako su har sai da motar kaisu makaranta yafita kafin na juya a hankali, gaba É—aya yau jikina baya min daÉ—e a hankali na isa bakin swimming pool na cire takalmata gefe na zauna bakin swimming pool É—in na zura kafafu na ciki, a hankali nake motsa ruwan da kafata ina É—an lilashi ciki, wasu hawaye ne masu É—umi suka zubo kan fuskata banyi kokarin sai da su ko danne zuciya ta daga abun da take jiba, tun jiya nake jin kai na cikin yanayin ina so nayi kuka ko zanji sassaucin abun da nake ji cikin zuciya ta, sai dai ban sami damar yin kukan ba saboda su Naseem, sam bana so nasaka musu rauni cikin zuciyar su, dan aduk san da irin wannan damuwar ta taso cikin zuciya ta zama nake a É—aki nayita kuka, aduk san da sukaga ina kuka sun rika tambaya ta me ya same ni idan nayi shiru ban basu amsa ba ko nace musu babu komai suma sai su fashe da kukan su rungume ni muyita kukan. tabbas ina ganin rauni da damuwa aduk san da hakan tafaru agare su, duk da kuwa kasan cewar su yara wan da basu san komai ba, amma nasan akwan atashi idan hakan yaci gaba da faru zasu tashi da abun a ransu, nasan É—aci da kunar dake tattare da kuncin ganin UWA cikin damuwa game da É—an ta, dan kuwa shike hanani sukuni a koda yaushe. wasu hawaye ne masu zafi da kuna suka cigaba da wanke min fuska cikin jan sheshsheka nashiga faÉ—in "Ummi na kizauna gidan Abba Ummi bazan taÉ“a yafewa kai na ba har idan nayi sana diyyar barin ki gidan Abba, Ummi na zancigaba da yin nesa dake har idan hakan zai sa ki cigaba da zama gidan Abba." kuka sosai ya kwace min cikin muryar kukan nacigaba da faÉ—in "Abba wlh ban ai kata zina ba ban taÉ“a ai kata zina ba, Abba zan cigaba da yin nesa daku har idan hakan zaisa Ummi na tacigaba da zama agidan mu, bana so nayi maraicin uwa batare da tabar duniya ba, Abbu Mamie Ya Masa'ud Auny Rafee'at Aunty Jaleela Nusaiba Fauzaun, kewan ku da begen ku yana hanani sukuni,kullum da ku nake kwana cikin raina, shin haka kuma kuke kewata ina son ku ko da yaushe ina tare da ku a cikin zuciya ta, ku yar da dani wlh Æ´aÆ´ana ba shegu bane, wlh Allah ban taÉ“a zina ba, Allah sarki Inna ta da kina nan da kin faÉ—a musu kalar tarbiyyar da kikayi min wan da ko da agidan karuwai zan zauna bazan yi iskanci ba, bazan yi ba, bazanyi ba, Ya SALEEM Ya SALEEM Ya SALEEM me na tare muku kai da matar ka meyasa zaka rabari da *MAHAIFIYA TA* karabani da ahalina me nayi muku, me yasa zaka sheganta min Æ´aÆ´ana tsaftatattu ka dan ganta su da wani uba wan da bansan ko waye shiba, duk hakan na menene da har sai ka kazanta min Æ´aÆ´a? Æ´aÆ´a na ba kazan ta bane kamar yadda ka faÉ—a Æ´aÆ´ana tsaftatattu ne bazan taÉ“a yafe maka Ya SALEEM bazan yafe maka b...." Kuka ne yaci karfi na nakifa kaina da guiwa na nayi ta kuka kamar raina zai fita. najima sosai zaune a gurin ina ai kin kuka, mai cike da kuna da bakin ciki. da kanshi hawayen ya tsaya badun na tsai da shi ba, sai dai kukan zuci danake, a hankali na mike cikin matsananciyar ciwon kai wan da dakyar nake iya buÉ—e idona duka sabo da zafin ciwon kan, na nufi ciki. direct bedroom na shige kana shiga bathroom wanka nayi nafito na sauya kaya na zo na kwanta bakin gado, karatun Alkur'ani na kunna cikin wayata a hankali nake bin karatun, a sannu narika jin zuciya ta tana samin salama da nutsuwa, a hankali narika jin bacci na fizgata ta, na lumshe idanuna. can cikin baccin da ya É—auke ni da nisan ta baifi na minti 20 ba. najiyo muryar su Nasmah, da gudu suka haye gadon suna faÉ—in "Mommy mun dawo Mommy mun dawo." ida nuna na rumtse da É—an karfi dan har lokacin kai na bai bar yimin ciwo ba, mike wa zaune nayi jin sun zube a jikina na É—ago su ina faÉ—in "Wai har kun dawo? amma dai ba'a tashi ba ko." nayi maganar ina duban agogo, karfe 12 har da rabi,nayi mamakin gani in da lokaci yatafi har haka, ranar yau karfe 12 saura suke dawowa har sun dawo anyi musu wanka an sauya musu kaya. lallai najima ina kuka har ban san lokaci yatafi har haka ba, tausayin kaina ya kamani, É—an guntun kwallar da ke kokarin sauka a idona É—aya nayi saurin kai yatsata na tare shi kana na gyara zama ta ina faÉ—in "Ashe dai lokacin tashin naku yayi, to yaya karatu yau ansha wasa ko." nayi maganar ina shafa kansu. baki Nasmah ta washe ta mike tsaye a kangadon tace "Mommy yau Aunty'n mu tayi mana haka." tarike kugu tare da girgizawa, dariya nayi ina faÉ—in "Au kice yau Aunty rawa tayi muku." "Ba haka bane haka ne". Naseem yafaÉ—a tare da mike wa yarike kugu yasoma tsalle. ido na ware nace "Kai kuce yau kunsha rawa." cikin tsallen yace "Eh ai hadda chocolate ma." tsai da tsallen da yake yayi sai kuma ya dira a godon da gudu yafita sai gashi ya dawo da School bag É—in sa, a tsakiyar gadon ya zazzage School bag É—in sai ga Chocolate masu yawa haÉ—e da littattafan sa sun zubo, da mamaki nace "Yau kuma Talatu kayan zaki tacika muku a jakar." nakai hannu na É—ibo chocolate dasuka kai guda biyar kala daban daban, ga kuma wasu a gaban sa, da É—an mamaki nake kallon su dan asanina babu kalar waÉ—annan chocolate É—in acikin kayan cime-cimen su kalar nasu ba irin wannan bane. "Kai Naseem a ina ka samo waÉ—an nan chocolate É—in?." nayi maganar ina duban sa, da sauri Nasmah tace "Nima akwai nawa." ta dira agadon da gudu tayi waje, Naseem ko bai bani amsa ba sai kokawar buÉ—e laidar chocolate É—in yake. ta shigo da school bag É—in ta itama ta zazzage, nace "Kai wai waya baku wannan abun haka, Talatu Talatu." nashiga kwaÉ—awa Talatu kira dan na fara tunanin ko rikici sukayi mata gun shirya su tabuÉ—e wani katon É—in chocolate É—in daban. Naseem da yakai Chocolate É—in baki ya kutsura yana É—aga kafaÉ—a alamun yana jin daÉ—in abun yace "Daddy yace mucinye wannan duka dai kaya mana wani." "Ai yace idan ka kaiÉ“a min baye kaya maka ba ni de bani da yawa." cewar Nasmah tana kai wan da ta É“are baki. Ido da baki na waro da mamaki tuno wan da suka taÉ“a kiran sa da Daddy a makarantar su nace "Wani Daddy mutumin nan ko?, a ina kuka san shi dan gidan ku da har zaku rika ce masa wani Daddy." Naseem daya cika chocolate a bakin sa yace "Ai Daddy yace kuma dai jo ya auke mu ya kai mu can guyin kifi babba." cikin tsawa nace "Bana ce muku kada wani yasake baku abu ku karÉ“a ba? ashe bakuji ba so kuke nazane ku ko?, bana ce muku nice Daddyn ku nice Mommy'n ku ba, shi ba Daddy'n ku bane, baku san shiba shima bai sanku ba, bakuda Daddy nice Daddy'n ku, kuna jina dai ko?." nariko kunnuwan su ina jijjigawa a hankali, suka gyaÉ—a kai. shiru nayi tare da komawa na jingina bayana da jikin gado jiki a sanyaye nashiga maganar zuci "Kuhi hakuri Æ´aÆ´ana ni zan cigaba da zame muku uwa kuma uba a duniyar na." jin kwalla nakokarin zubomin nayi saurin dakatar dashi... A ranar nasa aka kawo musu chocolate dawsu kayan makulashe aka kara kan wan da yake gida. washegari ranar asabar bamu wuni a gida ba yawon guraren shakatawa muka tafi, ni Faty Naseem Nasmah da kuma Talatu, sai direba. sai yamma muka dawo niki niki da kayan makulashe, washegari ranar Lahadi ma muka kuma fita, shima sai yamman muka dawo a part É—in su Inna wuro muka yada zango sai bayan isha muko koma side É—in mu, ai ko muna shiga su Nasmah suka É“ingire da bacci. koda gari ya waye dakyar nata da su Talatu ta tafi da su dan yimusu wan ka da shirin makaranta, dan tare jiya muka kwana da su. kamar kullum na rakosu muna É—agawa juna hannu suka fita. ina komawa ciki wanka nayi nashirya cikin les copie colour da É—an ratsin gold ajiki, da misalin karfe 10 da rabi nasauko kasa da mayafi akai na sai Æ´ar karamar jaka mai É—auke da wayoyina da wasu Æ´an kuÉ—i dana saka ciki, dinning area na nufa, in da na tadda Zulai tagama shirya komai na breakfast, a É—an gaggauce nayi breakfast É—in, ina yi ina duba agogo, dan fita zamuyi da Bappa zuwa asibitin da ake ginawa dasunan Inna ganin yan da ai kin ke tafiya, ina saurin ne dan jiya nace mishi karfi goma da rabi zamu tafi nasan kuma yanzu haka yagama shiri ni yake jira. koda na fita a kofar masallaci dake ta nan cikin gida na taddashi zaune, na karaso in da yake tare da gaida shi, daga nan muka shige mota muka nufi asibitin. masha Allah asibiti yayi kyau saura kaÉ—an a kammala aiki, bamu bar asibitin ba sai wajen karfe 12:20pm nacewa Yakubu muwuce makarantar su Nasmah mu É—auko su. Abakin get É—in makarantar Yakubu ya faka mota yafita da sauri yana faÉ—in "Bari naje na fito da su". yayi cikin makarantar da sauri, muna nan zaune can yafito da sauri kamar zai kife kasa yakaraso gefen da nake yace "Hajiya wai an zo an É—auke su." ido na waro da mamaki nace "Wa yazo ya É—au kesun bayan kai muna tare da kai ina ce kai ne me zuwa É—aukar su." Bappa yace "Zancen banza kai wani direban akayi musu sabo ne da zaizo É—aukar su? ko dai bakaji abun da suka faÉ—a da kyau bane?." yace "Wlh haka mai gadin yafaÉ—a Bappa." da sauri Bappa ta buÉ—e motar yafita ai ko nima da sauri nafita narufa masa baya har ina haÉ—awa da sassarfa. babu kowa cikin makarantar sai mai gadi da masu kula da tsaftar makarantar sai shara da goge-goge suke, hankali tashe Bappa ke tambayar mai gadi, mai gadin yace "Ai ko minti goma basu da tafiya ba duk É—azu muna tare da su anan da wasu É—aliban mota tazo tafaka nan bakin get suna ganin motar suka zuba a guje zuwa gurin motar suna murna, da naso hanasu dan ganin ba É—aya daga cikin irin motocin da ake zuwa É—aukar su da shi bane, to ganin yan da suke ta murna sukayi gun motar a guje yasa nayi tunanin É—aukar su a kazo, dama badaga gida akazo É—aukar su ba!." maigadi yakarashe maganar yana buga kirji. Yakubu da gumi yafara keto mishi kamar zai fashe da kuka yace "Ina ni ke zuwa É—aukar su kuma gani a gaban ka sai kuma hajiya wata rana,ko mutumin yasako irin fuskata ce ya zo." Bappa yace "Amma kuwa abun da mamaki amma ya kamata lokacin da kaga ba É—aya daga cikin motocin da ake zuwa É—aukar su da shi bane yazo kama yayi kaje kaga ko waye ne,amma wani abun mamakin da kace wai sun je gurin motar da gudu kuma suna murna to ko wani ne daga gida yazo É—aukar su tun da sun san mun fita har da direba?." ni dai kasa magana nayi sai É“ari da jikina yake cikin matukar tashin hankali tuni idanuna suka kawo ruwa kan kace me hawayen suka fara sauka. murya na rawa Yakubu yashiga tafa hannu da salati yana faÉ—in "Dama ance yanzu masu garkuwa da mutane sun canza salo akwai wani abun da suke yi sai dai kaga mutum na ta binsu kamar ya sansu harsu tafi da shi, wayyo Allah Naseem da Nasmah ko dai sune." cikin gwalalo ido mai gadi yace "Wayyo Allah nashiga uku wayyo ai kina shikenan dama ance idan aka sami matsala to abakin ai kina, ashe dama tsarin da masu garkuwa da mutane suka fito dashi kenan? shi yasa yarannan sukayi ta tsalle kamar doki suka ruga in da motar take, ashe jansu ake taciki kamar kuran karfe." É“arin jikina ne yakaru yayin da zuciya ta ke bugawa da karfi gudun hawaye na yakaru. Bappa yace "Kai ya isa haka Falyakum khairan au yasmuq, in sha allahu babu abun da zai faruku muje gidan mugani wata kila daga gida ne akazo aka É—auke su tun da sunsan bama gidan." yadube ni yana cigaba da faÉ—in "Kice Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." kalmar nashiga nanatawa kana muka juya gun mota, muka bar maigadin nan tsaye yana ta rafka salati dafaÉ—in shikam yau yasan ai kin sa yazo karshe har in sace yaran akayi. acikin mota Bappa yarika zuba addu'o'i yakuma hanani kukan danake shirin yi yace nayi ta faÉ—in Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un. a haka muka isa gida. Muna isa Yakubu yayi hon maigadi ya wangale get yana kokarin wucewa parking lot nace "Ka sauke mu anan." dan gani nake kamar motar bata tafiya da sauri tsabar tashin hankali. tun kan ya dai-dai ta parking muka fito daga motar maigadi yakaraso yana mana sannu batare da dukkanmu mun amsa ba Bappa yayi saurin cewa "Wayaje ya É—auko su Naseem a makaranta a cikin ku?." maigadi yace "Gaskiya babu wan da yaje É—auko su dan tun da kuka fita ma babu wan da yafita, yau kam sunsha zama a makaranta Yakubu yayi hanzarin zuwa É—auko su." "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un an ce anzo an É—auke su kuma kace ba wan da yafi tun fitar mu an sace su kenan." nayi maganar tare da fashewa da kukan da Bappa ketasa ni danneshi, nacigaba da faÉ—in "Ina suke ina suka shiga waya É—auke su.". maigadi ya walalo ido tare da faÉ—in "Iye! ansace su!." Bappa yace "Ka tabbatar da babu wan da yafita." yace "Wlh babu wan da yafita tun fitar ku ina bakin get É—in nan........! Mommyn Twins ce 7 HMD WASA FARIN GIRKI! Littafin na siyar wa ne kibiya ki karan ta my no 08034690723 Mai gadi yashiga jan hanci yanaci gaba da faÉ—in "Sam babu wan yafita ai da nasani dana shiga ciki naje na karÉ“i makullin mota naje na É—auko su ai, na É—an iya mota ba sosai ba amma da wasu su É—auke su gara ni naje a haka na É—auko sun, wasu matsiya tane masu niman jaraba suka É—auke su, duk tai makon da akewa mutane baiyi musuba har sai sun haÉ—a da sata, wayyo Allah Naseem wayyo Nasmah, ashe da rabon ragowar shayi da nama gobe bazan shaba, kullum sai sun kawo min na haÉ—a da nawa duk na kallame." zuwa yanzu tashin hankalin Bappa yafara bayyana yashiga faÉ—in "Kanu innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Allahumma ahjirni fi musibati²." bakina na toshe da tafin hannuna jin kuka mai sauti yana son suÉ“uce min najuya ina kokarin barin gurin Bappa yakira sunana najuyo ina hawaye yace "Je ki zauna kada ki É—aga hankali sosai na tabbata zasu kira kuma bazasu cutar da su ba dan kuÉ—i suke bukata za'a kuma basu babu komai." kai kawai na gwaÉ—a najuya nasoma tafiya, maigadi yabiyo ni yana cigaba da jan hanci yace "Anyi bako Hajiya." ban iya juyowa ba bare nabashi amsa Bappa ne yace "Ina bakon?." yace "Gashi can a mota yana shigowa kuma kuka shigo," "Wanene?." cewar Bappa, yace "Gashi can cikin mota ai da naso hanashi shiga ganin baiyi kama da irin waÉ—an da za'a dakatar ba shine na barshi ya shigo." yayi maganar yana nuna wata mota dake fake gefe a farfajiyar gidan. Bappa ya girgiza kai kana ya soma tafiya yana faÉ—in. "Ana cikin wani hali ta ya za'ayi a saurari wani bako." Cikin matukar da muwa da tashin hankali nake tafiya, "Me zaisa su É—auke su in dai kuÉ—i ne akan su É—auke su ni da sun faÉ—a min ko nawa ne zan basu, me yasa suka zaÉ“i su cutar da yaran da basujiba basu gani ba. wlh Allah sai yabi musu kadin su tun suna ciki ake cutar dasu da zaluntar su, har suka fito duniya." wasu zafafan kwalla ne suka rika wanke min fuska bana ko iya ganin gabana, tunani na É—aya awani hali suke yanzu.. Bappa har ya wuce motar da mai gadi yace masa bako ne ciki, sai kuma ya dawo sanin da yayi kan cewa bako rahama ne, gilashin motar ya kwankwasa, a hankali aka zuge glass É—in. cikin matukar mamaki Bappa ke lallon mutumin da waÉ—an da ke tare da shi, yana zaune a mazaunin direba waya na rike a hannunsa yana ta faman latsawa, Nasmah na zaune a gefen sa tasaka kanta jikin kafaÉ—ar sa tana ta cin chocolate, Naseem kuwa na zaune a gefen mai zaman banza rike da waya a hannunsa yana buga game yana kuma taunar chocolate. cikin tsananin matukar mamaki Bappa ke cigaba da kallon mutumin da mamakin ganin sa tare da su Naseem, tabbas bazai taÉ“a mance wannan fuskar ba, mutumin daya samar musu da ingantaccen ilimi a rugar su,mutumin da ya yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin an cafke Æ´an ta'addan da suke shiga rugar su suna kaÉ—a musu shanukai su kashe musu makiyaya. cikin girmamawa mutumin yashiga gai da Bappa, Bappa ya amsa fuska É—auke da annuri yana yi masa kallon sani, shiko mutumin ga duk kan alamu bai gane shiba, cike da al'ajabin ganin su tare da su Nasmah Bappa yace, "Ikon Allah kai ne nan tare da su Naseem da muke zaton ko Æ´an garkuwa da mutane ne suka É—auke su." da sauri Bappa ya juya yana faÉ—in "HAMDAH taho gasu nan." cak naja na tsaya dai-dai lokacin dana ke kokarin É—aura hannuna jikin kofar side É—ina, najuyo da sauri, magana Bappa yaci gaba dayi yana nuna cikin motar. "Gasu nan cikin mota Allah yayi ikon sa." dagudu na nufo gun motar ina share hawaye na da bakin mayafi na, ina isa gun motar nawuce gaban Bappa da sauri batare da duban cikin motar ba duk da glass É—in motar a sauke take, hankali na nakan murfin motar dana saka hannu ina kokarin buÉ—e motar sai jin ta nayi a rufe, da sauri na É—ago karaf idanun mu ya haÉ—u da juna, da mamaki nake kallon sa sai kuma nan take naji raina ya É“aci, mutumin da yace wai arika turo mai wayo yarika É—aukar su Naseem a school ba ni ba, wan da kuma suke kiran sa da Daddy yayi ta tara musu chocolate kamar sun zama shazumame sar kin shan zaki. fuska na É—aure tamau ina duban su Nasmah nace "Ku sauko nan!." nayi maganar cikin tsawa da zare idanuna. Bappa yaÉ—an matso yana faÉ—in "Wlh mun shiga tashin hankali sosai da akace wani mota daban yazo ya É—auke su ba É—aya daga cikin motocin gidan nan ba, mungama zaton masu garkuwa da mutane ne, suka É—au ke su." kai ya jinjina tare da yin murmushi wan da yayi sana diyyar bayyanar kyakkyawar dimple É—in fuskar sa, batare da yayi magana ba ya kai hannu ya buÉ—e marfin motar, baya na É—an ja kaÉ—an ya buÉ—o marfin, ya zuro kafafun sa waje, Nasmah dake gefen sa yaÉ—ago ta cak yafito da ita ya aje ta kasa, kana asannu yafito daga cikin motar,tsayuwar sa ya gyara kana yaÉ—an sunkuya jikin kofar yamika hannu cikin motar Naseem ya rike hannun nasa yaÉ—ago shi cak yafito da shi, sai da ya ajiye Naseem kasa kana ya É—ago da murmushi yace. "Idan za'a cigaba da barin su har kowa ya watse a makaranta ba'a je ana É—aukar su kan lokaci ba to kuwa zasu iya fuskantar hakan,domin su masu garkuwa da mutanen babu ta in da basa nan." kai Bappa ya jinjina cike da gamsuwa da maganar sa kana yace "Tabbas kuwa, Allah yashiga sakanin nagari da mugu." a kufule nace "Babu ranar da ba'a zuwa É—aukar su kan lokaci in ban da ranar da nayi ta kiran Yakubu bai É—aga ba, sai kuma yau, yau É—in ma ai bawani makara akayi ba tun da karfe 12:50pm muka isa makarantar kuma karfi 12 da rabi ake tashin su, kuma tun kan É—alibai su watse mai gadi yace aka É—auke su, to ashe dai ba'a makara zuwa É—aukar su, ana zuwa É—aukar su tun shabiyu ajira su har sai an tashe su a É—auko su a dawo da su, babu wani É“ata lokaci a zuwa É—aukar su, kai kuwuce mushiga ciki!." nayi maganar cikin haÉ—a haushi biyu zuwa uku, akan me zaice ba'a zuwa É—aukar su kan lokaci. sannan kuma wace dalilin ne yasashi zuwa É—aukarsu ina ruwan shi dasu dakuma rayuwar su, yasa nayi kuka da tunanin ansace su ne. sannan ganin yan da yaran suka manne masa sai kiran sa da sunan dana hanasu suke. tun da nafara maganar idanunsa akaina yayin da yake shafa sajen fuskar sa, kafaÉ—a yaÉ—aga kana yace "Kinyi kokari, kiyi wayon sanin hakan tukun dan da kaÉ—an kikafi yaran wayo." ido na waro amma lallai mutumin nan yana da rainin wayo karo na biyu kenan da yake cemin wai bani da wayo, yaran dana haifa yake cewa wai dakaÉ—an nafisu wayo. wani kallo na watsa masa tare da murguÉ—a baki nace "Allah yasa wayon suka fini, mece ce matsalar ka?." nayi maganar tare da kuma murguÉ—e baki. Bappa yace "Um to hakane kam amma ana zuwa É—aukar su akan lokaci sai dai É“acin rana, amma akiyayen shiyafi, mun gode sosai, in sha Allahu za'a kara azama wajen zuwa É—aukar su." hannunsu na fizgo ina faÉ—in "Kuzo ku wuce ina magana kuna tsaye." najanyo su fuuu muka nufi ciki anan na barsu shi da Bappa, cikin haushin jin Bappa yana saurarar sa, har shi zai gwada wa mutane yan da zasuyi da rayuwar su, ina ruwanshi, irin mutane masu shegen shishshigi kan abun da bai shafe su ba. sai da muka shiga parlour kafin na sake hannun su, na zauna kan kujera, ina duban su sukam ma ko a jikin su sai wata tsafgar su suke. kunnuwan ko wannen su na rike naÉ—an murÉ—a da karfi, suka haÉ—a baki wajen cewa "Wayyo Mommy." nace "Sai na sinke kunnen har idan baku dai na abun da na hana kuba, wato duk hanaku da nake tayi bakuji ba ko shine yau abun naku yagirma har da binsa, kunsan shi ne? baku san mutum ba kukama binsa har da shiga motar sa, ina kuna so a yanka kanku ne?." kai suka girgiza da sauri tare da faÉ—in "A'a-a'a Mommy." nace "To ban hanaku ce masa Daddy ba bana ce muku ku bakuda Daddy nice Mommyn ku nice Daddyn ku ba?, ban ce kada wani ya sake baku abu ku karÉ“a kuci ba?, shine har yau zaku bishi kushiga motar sa, kunsan shine?, to sai nayi muku duka yau sai na kaiku wa É—awisu ta caccake ku bari ku gani." namike tsaye tare da ruko hannun su ina cigaba da faÉ—in "ÆŠawisu kawai zan kai ku wasu sune zasu yin maganin ku." kuka suka sake da karfi suna faÉ—in "Wayyo Mommy kai ki kai mu." "Ai bazaku bari ba sai na kai ku gurin su su hana ku da kansu." nayi maganar ina jansu. ihu sosai suke suna faÉ—in "Mommy mun bayi." komawa nayi na zauna kan kujera ganin sun tsorata sosai najasu jikina na rungume su, ina faÉ—in "To kuyi shiru nafasa kai ku amma idan kuka kara sai na kaiku, zaku kara ko?". kai suka girgiza da sauri nace "Kada ku sake zuwa gurin wan da baku sanshi ba bare har kushigs motar sa, kuma kada ku sake ce masa Daddy shi ba Daddyn ku bane nice nan Daddyn ku kunje jo?." kai suka kuma gyaÉ—a wa suna jan shashsheka. a hankali narika shafa kansu cikin tsananin tausayin su, wasu zazzafan kwalla ne suka ciko ido na, ban dakatar da su ba har sai da suka gangaro kan fuskata ta, nakai tafin hannuna na goge, yayin da nake daÉ—a mannna kan su a kirjina, ina jin tausayin su na daÉ—a shiga na. maganar zuci nafara yi yayin da zazzafar hawaye mai cike da É—in bin kuna ke cigaba da zuba a ido na. "Kuyi hakuri bana so ku sanya wa ranku abun da babu shi a rayuwar ku, nafiso ku tashi da sanin cewa bakuda shi ni zan zame muku garkuwa uwa uba." daÉ—a rungume su nayi ina jin kuna cikin raina lallai tabbas ba shakka anyi min tabo mai muni ni da Æ´aÆ´ana wan da bazan taÉ“a mancewa da shi a rayuwa ta ba. kwallar idanuna na share tare da kokarin danne damuwa ta. É—ago wa nayi jin sallamar Bappa na amsa ina mai cigaba da kokarin danne damuwar dake azalzala ta cikin zuciya, naÉ—an gyara zamata cikin dabara na share ragowar hawayen idona, ya karaso ya zauna. huf su Nasmah suka mike a jikina Naseem daya dubi Bappa yace "Bappa Daddy fa yana waje?." sai kuma ya juya da sauri yana faÉ—in "Dan je guyin Daddy." ido na ware da mamaki kamar ba yanzu nagama masa barazana har da kukan sa ba amma gashi ya tashi yana faÉ—in zai je gurin mutumin. Bappa yayi murmushi da faÉ—in "Dawo nan mutumina, ai yatafi." yafaÉ—a yana ruko hannunsa kana ya cigaba da faÉ—in "Yaro kenan shi kamar dabba yake duk mai kyautata masa to zakaga yana son kasan tuwa da shi, wlh nayi mamakin ganin Ahmad Tijjani Sabil, nakuma yi mamakin ganin sa tare da yaran nan, koda yake hakan ba abun mamaki bane." da É—an mamaki na dubi Bappa jin sunan mutumin a bakin sa, Bappa ko daÉ—a faÉ—aÉ—a murnushin dake bayyane kan fuskar sa yayi kana yaci gaba da faÉ—in "Yaron kirki ne sosai kinga ma bai ganeni ba sai da nayi masa tuni, ai wannan yaro Allah dai ya masa albarka yakawo babban gudunmawa cikin rayuwar mu a Ruga, ya inganta mana rayuwa yakawo haske cikin rayuwar mu kwarai da gaske, lokacin da É“arayin shanu suka addabe mu babu dare babu rana, sukashe mana makiyaya su kaÉ—a mana shanukai, kwasam sai Allah yajefo mana shi, wata rana yazo rugar mu a matsayin bako watan sa guda tare da mu, ranar da yazo É“arayin shanu suka shigo rugar mu, suka saci shanukai suka raunata mana makiyaya Allah yatakai ta kwanan su na gaba, sai dai mun rasa makiyayin mu guda É—aya kuma mun san su suka sace shi, ya kwashe su yakai su asibiti cikin gari, ranar hankali yatashi muka É—au aniyar É—aukar mataki da kanmu. ranar da ya cika sati uku, har lokacin É“arayi basu kara kawo mana hari rugar muba sai dai rugar da muke makota da su, da yammacin ranar an je kai masa abinci kamar yadda aka saba sai aka iske shi da wani makiyayin mu cikin É—akin da aka bashi yake kwana ciki, makiyayin da muke tunanin É“arayin shanun nan sun tafi da shi, ya É—aÉ—É—aure shi, yanata gana masa azaba da wani irin na'ura. wan da yakai abincin yakurma ihu nan da nan jama'a suka taru munyi mamakin ganin makiyayin mu tare da shi yana bashi azaba,nan Æ´an gari suka rika cewa a kashe shi ashe shima É“arawon shanu ne muke tare da shi. cikin tsawa yace duk mudakata yace kunzo nan kuna ta wani har gowar ku mara amfani kuje ku tare Æ´an ta addan da suka dunfaro rugar ku domin kona ku su kuma tafi da dukiyar ku. cikin rashin fahimtar abun da yake nufi muka shiga kallon junar mu, shiko ci gaba da baiwa makiyayin mu azaba yacigaba da yi, dai-dai lokacin kuwa muka soma jin karar bindiga daga can nesa, nan fa hankali yatashi jama'a suka fara kokarin watsewa domin É—aukar makamin kare kansu. wani irin gigitaccen kara makiyayin nan ya saka lokacin da ya datse masa yasar hannun sa guda, cikin tsawa yace masa, Ta wani kusurwa zasu shigo,? su nawa ne kuma?, wasu irin bindigogi ne a hannunsu?!!. cikin tsananin jin azaba yasoma magana cikin matukar wahala yashiga bashi amsar tambayar dayayi masa. munyi matukar mamakin jin abun da makiyayin nan yafaÉ—a to me haka yake nufi?, a lokacin bamu sami damar jin amsar tambayar muba, sai muryar AHMAD Tijjani Sabil mukajiyo da karfi yana faÉ—in. Kowa ya koma gidan sa kada wani yafito waje,duk abun da zakuji kada ku fito. kamar yadda yafaÉ—a kuwa haka mukayi batare da musu koni man jin ba'a si ba kowa yayi gidan sa, sai dai bamu zauna haka ba kowa da makami a hannusa domin kare kai. ranar tashin hankalin da muka shiga ba zai faÉ—u ba, dan muna shiga gida Æ´an tadaddan nan suka karaso cikin rugar mu, wasu suna kunce dabbobi wasu kuma suna ta harbi. shigowar su dakamar minti ashirin, muka jiyo jiniyar sojoji ta ko ta ina suka sanya rugar mu a tsakiya. nan suka shiga bata kashi ranar kamar rugar mu zata fashi dan harbin bindiga, an É—auki tsawon mintina 30, kafin kikaji guri yayi tsit. sai hayani ya da magana da turanci haÉ—e da hausa ake, can aka fara magana da abun sauti irin wan da hukuma suke magana da shi domin sanar wa ko bada umurni wa al'umma, aka ce kowa ya fito, nan muka fito cikin É—ar-É—ar duk da asanar wan nasu sun sanar mana da cewa hukuma ne ke magana, amma a tsorace muke kuma bamu fito haka kawai ba sai da makaman mu, domin kare kai, duk da kuwa munsan su bindiga ne a hannusu mukuma akasin haka sai dai munsan Allah yana tare da mu. koda muka fito ganin hukumar ne da gaske nan hankali yaÉ—an kwanta kaÉ—an, Allah yabasu nasarar cafke Æ´an tadaddan nan wasu daga cikin su sojojin sun harbe su gasu kwance cikin jini, wasu kuma gasunan kwance a É—aÉ—É—aure bindigogin su a zube a gefe. Ahmad Tijjani Sabil yana tsakiyar hukuman nan yayin da wannan makiyayin namu ke kwance a gabansa shima a É—aÉ—É—aure. bayan jawabi da ban hakuri da hukumar nan sukayi mana, da alkawarin bamu kariya da tsaro, suka tattari Æ´an ta'addan suka saka su cikin mota, Ahmad ya É—aga wannan makiyayin namu yatura shi cikin mota, nan wasu daga cikin sojojin suka tafi da Æ´an ta'addan suka bar motan soja guda. ranar acikin rugar mu suka kwana suna bamu tsaro kwanan su uku kafin suka tafi, Ahmad kuwa bai bar rugar ba har sai da yagina mana makaranta da asibiti yazuba mana malaman asibiti dana makaranta, makarantar ne ma Fatu take ciki, tun daga lokacin muke samin tsaro sosai, munyi matukar farin ciki da zuwan Ahmad cikin mu dan kuwa ya tallafawa rayuwar mu kwarai da gaske, har rana mai kamar ta yau ba'a kuma shiga rugar mu da sunan sata ba." Numfashi na sauke cike da alhinin labarin da Bappa ke bani nace "Ikon Allah to shi wannan makiyayin naku yaya iyayen sa sukayi dajin shima É—an fashin ne, yanzu ku duk zaman ku da shi bakusan shi ma É—an fashi bane?". yace "Sam bamusan É—an fashi bane, to ai shi asalinsa ma ba bafulatani bane, zuwa yayi rugarmu tun yana yaro yace zai rika yi mana kiwo muna biyan sa, shekaru 16 muna tare da shi, muka bashi duk wani yar da ashe macuci ne bamu sani ba, yana ha'intar mu, har sai da Allah ya turo mana Ahmad Tijjani Sabil." kai na jinjina cike da mamaki ina faÉ—in "Tab lallai to shi ya akayi yasan É—an fashi ne shi da yazo bai jima ba, ku da kukayi shekara da shekaru da shi baku sani ba?." Bappa yace "Wlh duk kanin mu kowa abun da yayi ta faÉ—a kenan bayan komai ya lafa, sai dai bamu sami amsar tambayar ba, dan ko shi Ahmad É—in da muka tambaye shi bamu sami wani kwakkwaran amsa ba, sai muma muka bar shi bamu tsanan ta masa tambayar ba, munji daÉ—i da farin cikin da Allah ya nufa shi zai zame mana karshen matsalar mu." Bappa yana maganar ne cikin nuna tsantsar farin ciki da jin daÉ—i... na ce "Lallai kam to Allah ya tsare na gaba." ya am sa da amin amin kana yamike yana faÉ—in "Bari na shiga ciki." yana tafiya naruko hannun su muka haura sama... Yauma kamar kullum narako su Naseem ina tsaye har sai da naga fitar su, kana na koma ciki, wanka nayi ina gama kimsawa nayi breakfast, wan da nasa Zulai takawo min shi cikin É—aki, ina gama breakfast É—in nahaye gado dan bacci ne a idanuna ban farka ba, sai wajen karfe shabiyu saura Æ´an mintina dabasu fi 20 ba, wayata na janyo na kira Number Yakubu, kasan cewar yau juma'a da wuri ake tashin su, bugu É—aya ana biyu ya É—aga, nace "Kayi maza kaje ka É—auko su Nasmah." yace "To Hajiya da ma nima yanzu ina kan goge motar kenan yanzu zan tafi." "Kabar wani goge mota katafi kaje ka É—auko su." nayi maganar tare da kashe wayar, mikewa nayi nashige bathroom nayi wanka tare da dauro al'wala, ina fita na sauya kaya. ganin lokacin salla da saura sai na nufi kofa nafita kasa na sauka. Talatu da Zulai duk suna parlour'n suna ganina sukayi min sannu da fitowa,na amsa ina yi musu yaya aiki, suka ce alhmdllh, an tsaftace gurin ko ina yayi tsaf sai kamshe ke tashi. ina jin matukar daÉ—in zama da su sabo da suna baiwa aikin su kulawa sosai. a É—aya daga cikin kujerun parlour'n na zauna, tare da saka idanuna kan TV ganin shirin da ake. zamata baifi da minti 10 ba najiyo muryar su Naseem daga kofa ta waje suna kwaÉ—a sallama, kallon kofar nayi da murmushi akan fuska ta, suka turo kofar da gudu suka shigo suna faÉ—in "Mommy mun dawo Mommy mun dawo." faÉ—aÉ—a murmushi na nayi tare da faÉ—in "To sannun ku da dawowa." in da nake suka taho da gudu na buÉ—e hannuna suka faÉ—o ciki na rungume su, ina dariya da faÉ—in "An yi karatu sosai dai ko?." kai Naseem ya gyaÉ—a. nace "To madallah." na dubi Nasmah nace "Likita na anyi karatu sosai ko?." itama kai ta gyaÉ—a tana washe baki, Naseem ko baki ya turo yace "Mommy ni baki ce min tojan ki ba." cikin muryar dariya nace "Oh soja na." shima dariyar yayi cike da jin daÉ—in sunan dana kira sa da shi. Nasmah ko mikewa tayi a jikina tarike kugu tare da jujjuya idanun ta tace "Ai nafi Naseem yin kayatu da yawa yana ta wasa da wani yayo, ni nayi kayatu da yawa dan yika yima mutane ayyuya kuma." ido na waro yan da take yi da ido ya bani dariya nace "A.a.a Naseem É—in wato wasa kaje ka zauna kake yi ba karatu ba ko?". nayi maganar tare da rike haÉ“a ina kallon sa, yace "Hum kaiya ne take yi, nayi kayatu da yawa kuma Daddy yace nayi kayatu da yawa idan nayi da yawa da yawa, yace dai jo ya auke mu a gida." Nasmah tace "Um ai Daddy yace ni ne dai jo ya auke ni nafika kayatu da yawa, ai nayi mishi kayatu da yawa ma yau kuma." Naseem yayi kamar zai ture ta yana faÉ—in "Ai nima nayi ma Daddy kayatu da yawa." ido na waro da mamakin kin sunan da suke ambata sunan da nayi ta musu barazana kan kuma faÉ—ar sa, nace "Kai kurafa min baki, wani Daddy'n." nayi maganar cikin tsawa dan ni a tunani na ma wani ne daban ba wancan mutumin da na kwaÉ“e su da shi ba. Yakubu da yashigo rike da school bag É—in su yakaraso ciki Talatu ta amshi jakar tayi cikin bedroom É—in su da shi, ya washe baki da faÉ—in "Ai Hajiya Ahmad Tijjani Sabil suke nufi, ai ina isa na iske su tare da shi abakin get din makarantar su tare da shi, naji yana tambayar su karatu suna ta zuba masa karatun da aka musu, nace kai ashe fa yaran nan za'ayi masu ilimi ne anan wlh kuwa." yayi maganar yana mai cigaba da washe baki. fuska na tsuke sosai tare da mai da dubana kan yaran kana na mike tsaye na ruko hannun su na janyo su muka haura sama, muna shiga É—aki na sake su ina faÉ—in "Ni Æ´asu yazan yi da yaran nan wato ku bakwa ji, duk abun da zanyi ta faÉ—a muku bazaku jiba shi wannan Ahmad yake ko wane wlh dole na É—au mataki a kansa, idan bana É—au mataki akan lamarin ba zai rushe min ginin danake ta gina shi, yana ta kokarin rushewa ya haka ne kam, ina ruwan shi da su meye haÉ—in shi da su da zai rika sanya musu wani ra'ayi a cikin zukatan su." Duban yaran nayi nama rasa wani irin masifa zan musu, ko da na musu ma abanza gobe zasu kuma, zubewa nayi bakin gado da tunanin yan da zanyi na É“ullo wa lamarin, yazama dole na É—auki mataki kan lamarin idan ba hakaba, to kuwa tabbas ginin da nake ta kokarin gina shi domin yayi karko to kuwa zai iya rusa min shi, tabbas zan É—auki mataki kansa, "Amma mene ne mafita?. nayi wa kai na tambayar ina gyara zama ta, "Mafitar kenan kawai ki canza musu makaranta." zuciya ta ta bani amsa, kai na jinjina da gaskata abun da zuciya ta ta faÉ—a min, hakanne kawai mafita ta yadda zasuyi nesa da shi, idan kuma ba haka ba to kuwa abun da nake ta kokarin cire masu kwaÉ—ai tar sa a zukatan su shine zai faru, dan kuwa in har hakan yaci gaba da faruwa zasu tashi da sanin wani mahaifi a ransu wan da bana son su san haka, nice nan uwa kuma uba a rayuwar su, sam bana son su tashi da jin cewa zasu sa mi uba ni zasu cigaba da jina uwa kuma uba a rayuwar su. bana so su sanyawa ransu abun da baza su samu ba a rayuwar su, to mene ne amfanin sanya wa ransu hakan, gara kawai su san cewa ba su da uba, su ji a ransu ni ce uban nasu kuma ni ce uwan su. wannan kaÉ—ai shine mafita in sauya musu makaranta in nesan tar da su daga gare shi, in ma koyarwa yake a makarantar imma mene ne baya sake ganin su bare ya cigaba da cusa musu wani ra'ayin, ai dai sun rabu bashi basu, bazai sake ganin suba suma haka bare su sake kiran shi da wani Daddy, "ÆŠan rainin wayo har da cewa surika ce masa wani Daddy, sai kace wani uban su ko meye gamin sa da su oho." naja dogon tsaki tare da yin kwafa kana na mike, nashiga tuÉ“e musu uniform É—in su, ina faÉ—in "Ku da shi É—in duk zanyi maganin ku." bathroom na jasu da kai na nayi musu wanka yau, muka fito na saka musu wasu daga cikin kayan su da yake bedroom É—ina, sai da na nagabatar da sallar azahar kana na janyo su muka sauka kasa. dinning area muka zarce bayan munci abinci najasu muka tafi part É—in su Inna wuro, nan muka tarar da Faty ita ma dawowar ta daga school kenan, nan muka yada zango mukata hira... da yammacin ranar zaune nake a parlour'n sama na É—ago wayata na laluÉ“o number shugaban makarantar su Naseem.....! Mommyn Twins ce 8 Nan nake shai da masa bukata ta nakan canza su Naseem makaranta. shugaban makarantar nasu yace "To ba bubu da muwa amma dan Allah muna so musan dalilin da yasa ake son sauya musu makarantar ko kuma makarantar tamu babu koyo ne yan da ya kamata?". nace "Ko kaÉ—an ba haka bane ba kawai dai ina so ne na canza musu makarantar ba wai kodun rashin koyo ba, ai ba za'a ce makarantar ku babu koyo ba, yara suna fahimta sosai, kawai dai yaÉ—an yi nisa ne." yace "To in dai kuwa haka ne to dan Allah kada a ciresu a makarantar gaba É—aya, akwai É—aya makarantar mu dake wata unguwa mafi kusa da ku in dai kina so sai a maida su can É—in, ranar Monday idan suka zo sai ayi transfer É—in su can É—in." shiru na É—an yi cike da nazarin maganar sa, sai kuma nace "To shi kenan a mai dasu can É—in." har munyi sallama zan kashe wayar yayi saurin cewa "Dan Allah Madam a daure a kawo su sai a kaisu wancan makarantar, idan akace an cire su gaba É—aya kokon to zai shiga zukatan iyayen yara zasuyi zaton ko wani matsala ce mai girma aka samu cikin makarantar, tun da bawai barin garin zakuyi ba, zamu iya samun dakilewar customer, adai duba lamarin da kyau Hajiya." "Babu damuwa in sha Allah za'a kawo su sai a kai su wan can É—in." godiya yashiga yi min kana mukayi sallama na kashe wayar. Ina sauke wayar number Ukhtee na kira yayi ta ringing ba'a É—aga ba,nakuma mai da kiran shima har yakusa yanke wa kafin ta É—aga, da sallama. na amsa cikin harshen larabci nace "Oh kai Ukhtee ina kika aje wayar haka ina ta kiranki baki É—aga ba?, ko yanga kike min an ce miki ni saurayin kine." dariya tayi tare da faÉ—in "Saurayi kuma haba dai kedai wayar tana bedroom ne nikuma ina parlour, nama shigo É—aukar abune cikin É—akin naji wayar tana ring, ai da haka zaki ta kira ma ban sani ba, ya kuke ina yarana suke?." "Lafiya lau duk muna lafiya, yaran ki suna can gurin Bappa sunki biyo ni suna can suna damin sa da surutu, ni nagaji da hirar ne nadawo side É—ina naÉ—an huta suna can." larabcin nake ina ta haryaÉ—a shi. dariya tayi jin yan da nake ta kwamusa larabcin, tace "Oh kin dawo kasar ku yaren kasar ku yana so ya korar miki da yaren kasar muko?." nima dariyar nayi tare da faÉ—in "Ashe kin gane inata yi da kyar amma fa su Naseem sunanan da shi a bakin su domin makarantar isilamiyyar su larabci zalla ake, shi yasa yake nan zaune a bakin su." tace "Kai naji daÉ—i wlh gara ai su zauna da larabcin a bakin su, ke kizauna da yaren kasar ku tun da shi kika zaÉ“a." nace "To ya zanyi mahaifa ta dole naso yare na ke ma ba kina son yaren kiba?." tace "Sosai ma." "Oh to shine nima baki so naso nawa yaren." mukayi dariya. hira kukayi tayi sosai da Ukhtee wani maganar idan nayi ita zata gyara min shi dan larabcin bai gama nuna baki na ba. sai can da jinawa mukayi sallama. Yau Monday kamar yan da nasa ba na rako su Nasmah gun mota, Yakubu dake goge motar yayi saurin buÉ—e motar nasaka su ciki,bayani na yiwa yakubu kamar yan da mukayi da shugaban makarantar su idan sun je za'a haÉ—a su da wani domin yayi musu jagora zuwa É—aya makarantar. ina tsaye ina É—aga musu hannu har suka fita... Kai tsaye Yakubu yaÉ—au hanyar makarantar, kamar koda yaushe hira yake da yaran yanata washewa da dariya kamar yan da suma suke ta washe baki. suna isa bakin get É—in makarantar yayi parking yafito, kana ya buÉ—e musu suka fito, suna fita suka shige cikin makarantar direct office suka nufa daga nan aka haÉ—a su da wani malami da zai kai su É—aya makarantar, suka fito tare. suna fita bakin get É—in school É—in, wata lafiyayyi zazzafar mota tayi parking a gefe, tun kan motar ta kakarasa parking Naseem yafara murna yana faÉ—in "Laa ga Daddy yazo laa ga Daddy yazo." Nasmah ma kuwa ihun murna ta sake tare da sa gudu sukayi gurin motar. da sauri ya buÉ—e motar ya fito yaware hannayen sa ai ko da gudu suka shige jikin sa ya rungume su, duk suka saki dariya har dashi, kana ya mike yashiga É—aga su yana cillasu sama sai kya-kya ta dariya suke. sai da yayi wa kowannen su haka har sau uku kana yadire su kasa, Yakubu ya karaso in da suke yana washe baki da faÉ—in "Ranka shi daÉ—i barka da war haka." amsa wa yayi fuska a sake sai dai gaba É—aya hankalin sa na kan su Nasnah da suke ta zuba masa surutu. shima wannan malamin da aka haÉ—o su da shi ya karaso yana faÉ—in "Barka da zuwa yellaÉ“oi." yace "Yau wa, yaya ji da É—aliban?." malamin yawashe baki tare da faÉ—in "Muna kai kam." yace "Masha Allah." malamin ne ya dubi yakubu da kuma yaran yace "To muje ko." yayi maganar yana duban motar su. sai a lokacin Ahmad ya É—ago da kallon sa kan yaran yadawo da shi kan su Yakubu kana yace "Ina kuma za'a je ba makaranta za'a shiga ba?". yayi maganar yana shafa kan su Naseem. malamin yace "A'a zamu tafi da sune É—aya makarantar mu." duban sa Ahmad ya kuma da alamun tabbayoyi É—auke a fuskar sa, kana yace "Wacce makarantar kuma?." yace "ÆŠaya daga cikin makarantar mu ne za'a mai da su." da fuskantar mamaki Ahmad yace "Har sun gama wannan makarantar ne da za'a tura su wata makarantar daban?." kai malamin ya girgiza tare da faÉ—in "A'a ai za'a sauya musu makarantar ne anyi musu transfer can ne." É—an shiru Ahmad yayi kana yace "Malam É—in yana ciki?." kai malamin ya gyaÉ—a tare da faÉ—in "Eh yana ciki." yace "Okay to muna zuwa." yafaÉ—a tare da gyara rukon Naseem da Nasmah a kowani hannun sa guda, ya janyo su suka shige cikin makarantar. Malamin ya dubi Yakubu dake ta washe baki yace "Wai nikam da ma Æ´aÆ´an Ahmad Tijjaji Sabil ne kake kawowa makaranta?." Yakubu ya daÉ—a washe baki yace "A'a Æ´aÆ´an me *HAM'NAS* Company ne fa." "Au Æ´aÆ´an mai *HAM'NAS* Company ne to shi Ahmad Sabil dangin su ne? lallai Allah mai yin yan da yaso yahaÉ—a family guda da tarin dukiya." Yakubu yace "Eh Æ´an uwa ne." yafaÉ—i hakan ne kawai dan bashi da amsar bashi, dan shi kansa bai isa yace suna da dangan taka ko basu da shi ba, a matsayin sa na mai ai kin gidan ba lallai dole yasan dan gin gidan ba, san nan kuma baya so ya disga kan sa gaban malamin, ko ba komai shi ma za'a rika yi masa kallon wani... suna nan tsaye zuwa can Ahmad yafito shi kaÉ—ai batare da yaran ba. ido suka zuba masa ganin yafito shi kaÉ—ai, yakaraso in da suke, duban malamin yayi tare da faÉ—in "Ka koma kacigaba da koyar da É—aliban ka, kai kuma ka koma gida ka dawo da wuri ka É—au ke su." yakara she maganar da duban Yakubu. Yakubu yace "Ranka shi daÉ—e hajiya tace na tsaya sai mun kai su kafin na komo gida." Yace "Kar ka damu kaje ka abin ka." yace To. yashiga mota in da tuni malamin ma yakoma cikin makarantar. shiko Ahmad a hankali ya isa jikin motar sa ya shige ciki... Da misalin karfe 12 a hankali na mike na shige bayi wanka nayi haÉ—e da É—auro al'wala nafito,nashirya cikin wani doguwar rigar atamfa pauda da man lip kawai na goga sai turare dana fesa a jikina, a hankali na isa jikin window labulen window'n naÉ—an janye shi gefe tare da zuge glass. ido na kurawa furannin da suke ta kaÉ—a wa gwanin ban shawa, idanuna na sauke can bakin get jin karar buÉ—e get É—in, da murmushi nake kallon kofar, dan nasan su Naseem ne suka dawo, É—an gimtse annurin fuska ta nayi ganin ba motar kai su makaranta bane wata motar ne daban ta shigo. a sannu motar ta isa ta gyara parking a gefen farfajiyar gidan, an É—au tsawon minti 10 kafin aka buÉ—e motar, ido na waro cikin tsananin mamaki da shiga shoc ganin wan da yafito daga cikin motar, cikin matukar kufula nake kallon sa yayin da yazaga É—aya gefen ya buÉ—e, sai ganin Naseem da Nasmah nayi sun fito daga cikin motar suna ta washe ba ki. "What! me nake gani haka, yaran da nasa a canza musu makaranta domin sa wai bin su yakuma yi?." cikin matukar É“acin rai nasaki labulen da sauri na juya nafita a É—akin na nufi kasa, da sauri na ke sauka har ina haÉ—a step cikin hanzari nakarasa sauka nayi waje da sauri. Suna tsate jikin mota sai zuba masa surutu suke shiko sai binsu da murmushi mai haÉ—e da dariya yake, tun kan na karaso in da suke nashiga faÉ—in "Kai malam wai meye hakan ne, wai meye gamin ka da yaran nan ne kam?!." dai-dai lokacin na iso in da suke, kugu na rike cikin masifa nacigaba da faÉ—in "Meye da lilin ka na wani shishige musu da kake kana ta wani cusa musu wani ra'ayi meye nufin ka da su?." maganar nake a tsai-tsaiye kuma cikin É—aga murya cikin masifa nakuma faÉ—in "Bana bukatar wani ya raÉ“e su da manufa irin naka kagane ko malam?." tun da na fara maganar ido kawai ya zuba min batare da yace komai ba, idanun sa kan lip É—ina, a sannu yaÉ—an yi baya ya jin gina bayan sa jikin mota hannayen sa ya sarkafe a kirjin sa, harshen sa yaÉ—an zuro waje yalashi pink lip É—in sa, har lokacin fuskar sa na É—auke da murmushi wan da dimple suka daÉ—a kawata annurin fuskar sa. cikin kuma É—aga murya na dubi su Naseem nace "Idan baku wuce kun shiga ciki ba na rantse sai na É“aɓɓala yaro anan gurin ku wuce mutafi nace!." nafaÉ—a ina nuna musu hanya. Nasmah tace "Mommy ja mu jo." ido na waro wato ma na jira su kenan sai sun gama abun da suke. shiko wani murmuahi yakuma sakewa. tsayuwar sa ya gyara tare da duban yaran kana ya mai da duban sa kai na sannan yafara magana "Zaki É“alla su?." ya faÉ—a tare da kuma sakin wani murmushi kana ya É—an sun kuya yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran ya dubi ko wannen su yace "Kuje ciki ayi muku wanka kuci abinci ku kwanta ku huta kuyi bacci idan kun tashi kuyi karatu gobe zan tambaye ku karan tun da kukayi kun ji ko?." kai suka gyaÉ—a masa suna faÉ—in "Tom." yace "Yauwa to maza a je ciki." Naseem yace "Daddy dakajo anjima?." kai yagyaÉ—a yana mai cigaba da wannan murmishi wan da kamar da shi aka gina fuskar sa yace "Sosai ma zan zo mana." Cikin hatsala haÉ—e da É“acin ran ganin yau ma kamar na ranar da na same su tare da shi a kofar makarantar su, ina nayi musu magana sukayi kamar basu san ni ba, sai shi da suke ta biye masa suna bashi amsar duk abun da yace musu, bugu da karin bacin raina kiransa da sunan dana hane su a gabana. cikin tsawa nace "Kai Naseem me nace maka waye Daddy'n ka wato bakaji ba ko, ban ce muku kada ku kuma cewa wani Daddy ba, wato duk maganar da nake muku aban za bakwa ji ko, idan naji kasake cewa wani Daddy sai na fasa maka baki,wuce mutafi nace!." ko da nake masifar harlau idanunsa a kai na, sai ya saki wani murmushin gefen baki yayin da gefen kumatun sa na dama ya lotsa, har kuma lokacin yana rike da kafaÉ—ar su. a sannu yaÉ—an sun kuyo yadubi Naseem kana yakuma dubi Nasmah kana yakuma sakin wani murmushin sannan yace "Naseem Nasmah mene ne ma suna na?." suka haÉ—a baki wajen cewa "Daddy Daddy tunan ka." yace "Kai yaran nan to Allah yayi muku albar ka, to maza ku tafi ciki ayi muku wanka kuci abinci maza kuje." ya faÉ—a yana tura keyar su. ai ko da gudu suka yi ciki suna dariya, ganin rainin wayon nasu da yawa yake wato umurnin sa ma zasubi ba nawa ba. nadube shi tare da rike kugu nace "Kai malam kana ji ko, kada ka sake zuwa in da yara na suke kada ka sake kasake zuwa in da suke, kada ka sake cusa musu ra'ayin cewa wai kai Daddy'n su ne, kai ba Daddy'n su bane basuma san ka ba, ni ban gayyaci wani acikin lamarin Æ´aÆ´ana ba,karabu da harkar yara na idan kuma ba haka ba wlh zan É—auki tsatstsauran mataki a kanka, kada ka kuskura ka sake zuwa in da yara na suke, kada ka sake yi musu karya kan abun da ba haka bane, bana kara kan haka dan Æ´aÆ´ana nice kaÉ—ai uwan su kuma uban su, dan Allah malam kada ka sake cusawa Æ´aÆ´ana wannan gurguwar ra'ayin, ka gane ko?!." na karashe maganar da nuna masa yatsa haÉ—e da murguÉ—a masa baki, na juya a hatsale ganin duk maganar da nake madadin ya shiga taitayin sa sai ma daÉ—a sakin wannan murmushin nashi yake. tafiya na soma cikin fushi dan nalashi takwabin yau sai na zane yaran nan tun da har ni zasu gwadan wani yafi ni muhimmanci agurin su har zasu ji maganar sa akan nawa. sai jin maganar sa nayi daf dani "Kece uwan su kuma uban su to ya akayi kenan hakan ta faru, ke kika ba kan ki cikin kenan,faÉ—a min da ma a she mace tana bawa kanta ciki da kanta, dama a she uwa tana bawa kanta ciki ita kaÉ—ai batare da uba ba??." wani irin juyi nayi jin sautin sa kusa dani batare da zato ko sammani ba, maganar yashige ni tamkar shigar shoc cikin jini na, wani irin mugun kallo na watsa masa tare da jan dogon tsaki, najuya na nufi kofar side É—ina da sauri... shiko bayana yabi da wannan murmushin kana ya juya yashige motar sa yaja yabar gidan. Koda na shiga banbi takan su Naseem ba dan nasan koda na yi musu hukuncin danayi niyyar ma bashi zai sa su dai na abun da na hanasun ba, sai kawai nashige É—aki nazube bakin gado, kamar an zabure ni kuma na mike na isa gaban mirror in da wayoyi na suke ajiye, number Yakubu na kira, nafara zazzage masa masifa "Wato Yakubu dana ce kaje ka É—auko su shine bakaje ba kabar wannan É—an rainin wayon mutumin wai Ahmad yake ko wa yaje ya É—au ko su ko?, idan ka gaji ne kafaÉ—a sai a sallame ka." da sauri yatari numfashi na da faÉ—in "Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh yanzu haka ina hanyar dadowa ne ina ma kokarin kiran ki kenan sanar miki sai ga kiran ki, naje makarantar aka ce min yazo ya É—auke su, ai Hajiya baki sani bama É—azu da zamu kai su sabon makarantar yazo ya mai da su cikin makarantar yace mutafi mu barsu anan." ido na waro da É—inbin mamaki mai haÉ—e da mugun É“acin rai, ban san san da na dakawa Yakubu tsawa ba nace "Dalla malam ya isa ni da kai na nace ayi abu kan Æ´aÆ´ana sannan wani can daban yazo yace ba hakaba kai kuma ka yarda, umurnin sa kabi kenan? ok to ka wuce gidan sa daga nan kaje can yacigaba da baka umurnin!." nakashe wayar rai É“ace, "Lallai ma wato ashe ma ba'a kai su makarantar ba shike nan ya hana ko me?." Afusace na danna number shugaban makarantar yana É—agawa nace "Malama ya zan ce ga abun da nake so sannan kuma wani yazo ya hana kuma ku amin ce, to gaskiya daga yau bazama su sake zuwa makarantar ba ma sun fita kenan." da sauri yace "Ranki shidaÉ—e mahaifin su ne yazo yace kada a canza musu makarantar bawai yin kan mu bane." kashe wayar nayi jin raina yadaÉ—a É“aci. dogon tsaki naja tare da yin kwafa nama kasa cewa komai saboda sabar bakin ciki,sai dai naci alwashin daga yau baza su sake zuwa makarantar ba, zan mai da su *HAM'NAS* International School Of Science And Technology. After 1 week Tsawon sati guda agida suka yishi ranar Lahadi nasa aka kawo musu uniform na *HAM'NAS* International School Of Science And Technology. washegari Monday da misalin karfe 7 aka gama kimsa su tsaf, muna tsaye a parking space, daga can na É—agawa Faty hannu da fito war ta kenan daga side É—in su, nayi mata alama da tayi sauri, ta Kara so da sauri, tace "Ina kwana Adda HAMDAH." murmushi nayi tare da faÉ—in "Lafiya lau antashi lafiya." "Lafiya lau." tafaÉ—a tare da duban su Nasmah tace "Yau yara sun koma School É—in mu." hannun ta Nasmah tarike taÉ—ago kanta tana duban ta tace "Aunty Faty School inku akwai lilo?." Faty tace "Eh har da abun zame-zame da mota mai lilo da doki mai lilo." tsalle Naseem ya tuma yana faÉ—in "Yeee nine zan shiga moto in tuka ku." dariya duk mukayi, na dubi Yakubu dake ta faman goge mota, nace "Dan Allah kabar goge motar nan haka in ba halitta zaka sake masa ba, kutafi haka kada kasa su makara,kuma dai kaji abin da na faÉ—a maka wlh aka kuma samin wata matsalar duk wani hakuri da magiyar ka bazai maka amfani ba." nayi maganar ne cikin jin haushin sa na rannan dan da kyar na hakura da hakurin da yayi ta bani. da sauri ya bar goge motar yabuÉ—e marfin motar yana faÉ—in "Zo ku shiga Naseem, wlh hajiya in sha Allahu baza a sake samin wata matsala ba, wancan rabar ma tsautsayi ne, dakuma ganin shi babban mutum ne a kasar nan shiyasa ban masa musu ba, dan gudun kada yasa a kwashe ni akai ni gidan maza, dan musu da babban mutu awannan zamanin haÉ—ari ne." tsaki naja tare da faÉ—in "Kabari zai kai ka karshen É—auri kenan." najuya naso ma tafiya ina É—agawa su Nasmah hannu da cigaba da faÉ—in "Kadai ji abun da na faÉ—a maka." yace "Kwarai Hajiya, ai daga yau bazaki sake jin wata masala ba." ban kuma bi ta kan sa ba nawuce part É—in su Inna Wuro." A parlour na tadda su Bappa suna breakfast na zauna nima bayan mun gaisa Inna Wuro tazubo min kayan breakfast ta turo min gabana, nan nashiga ci muna É—an taÉ“a hira. Bappa yace "Mutanen sun tafi makaranta ko?." nace "Eh sun tafi." Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in "Yanzu kam an bar kuka idan za'a tafi." "Dama ai rashin sabo ne yanzu kam an saba." cewar Inna wuro. Bappa yace "Hakane kam wai me yasa ne aka sauya musu makarantar ko yayi musu nisa ne? ko da yake *HAM'NAS* International School yafi shi nisa, me ya sane?." "Babu tsaro yan da yakama ta a makarantar shi yasa." nafaÉ—a a takaice. Inna wuro tace "Hakkum gaskiya sabo da Allah kam ya kamata su kara sa ido kan É—aliban su, susan duk wani wan da zai kawo É—alibai yakuma zo É—aukar su, duk da dai ranar Malam yace min mutumin kirkin nan ne Ahmad Tijjani Sabil yaje ya É—auko su ake tunanin ko masu garkuwa da mutane ne, amma dai ya dace sosai su sa ido kan É—aliban su." kai kawai na jinjina batare da nace komai ba,akasan raina kuwa faÉ—i nake "To waya sani ma ko mai satar mutanen ne dole zan sa jami'an tsaro cikin gidan nan tun da har ya fara shiga cikin gidan nan yana leken asiri." maganar Bappa dana ji shi ya kashe min zancen zucin danake "HAMDAH har yanzu banji kin ce komai ba kan maganar mu ta rannan, Yakamata yanzu kam kiyi aure ki fidda miji na gari kiyi aure, domin darajar ki yadaÉ—a ninkuwa, kwanakin can munyi maganar nan bakice komai ba, daraja da kimar hace baya É“ata cika cif har sai tana tare da abokin rayuwa wato mijin aure." tea É—in da na kurÉ“a ne nahaÉ—iye shi da kyar, sam bana son jin wannan kalmar gaba É—aya naji nakoshi da abincin a hankali na mai da cup É—in na aje kana a hankali nasoma magana. Bappa aure kuma, ai ni bazan yi aure ba rayuwa ta a haka tafi min." yace "A kul É—in ki kada na sake jin wannan maganar, a wannan shekarun naki zaki ce baza kiyi aure ba, nutsuwa bata taÉ“a cika sai da abokin rayuwa, kiyi na zari sosai ga abokan kasuwancin ki da suke zuwa gidan nan, ko wannan Alhj Muttari nan ai mutumin kirki ne ko ranar yaso yimin zan cen sai dai bai fito muraran yayi maganar ba, in yaso sai ku dai-dai ta kiyi auren ki kamalar ki ta daÉ—a cika." Inna Wuro tace "In ban da HAMDAH ma ai mutane basu taru sun zama É—aya ba, dan wani abu yafaru da rayuwar auren ki na fari bashi zai sa nan gaba yakuma faruwa ba,ai Allah baya taÉ“a jarabtar bawan sa da abun da bazai iya ba, duk kuma musulmi an sanshi da karÉ“ar kaddara me kyau ko mara kyau, ki gode masa ta hanyar kuma kara yin wa ni auren." "Hmm." kawai nace dan bana jin kamar abun da suke faÉ—an zai kasan ce, har can kasan kololuwar raina bana jin zan kuma aure, babu abun da natsana a yanzu kamar aure. meye acikin auren ban da tashin hankali da musifa, in dai har aure nutsuwa ce kamar yan da suka faÉ—a to gara na tabbata ni bani da wannan nutsuwar. Duk wani nasiha da jan hankalin da su Bappa suke jin su kawai nake,dan a yanzu babu abun da nafi tsana ma kamar aure!. sai da na bari suka gama yi min nasihar kafin na mike nace dasu zanje na É—an kwanta kafin su Naseem su dawo, abin cin da ban karasa ci ba kenan nafito. ina fita daga side É—in wata mota na shigo wa cikin gidan, a hankali na ke tafiya har na iso in da motar tayi parking kasan cewar dole sai nabi ta hanyar kafin na wuce side É—ina, ina isa dai-dai in da motar take sai ji nayi an.......! Mommyn Twins ce 9 An buÉ—e murfin motar, baya na É—an yi da sauri dan kaÉ—an ya rage marfin ya bige ni, kasan cewar nazo daf da motar sosai. da sauri na É—ago dan ganin wan da ke cikin motar, ido na waro da É—inbin mamaki ganin mutumin da su Nasmah suke cewa Daddy ne, tsayuwa ta na gyara ganin yazuro kafar sa waje yafito daga cikin motar,baki na buÉ—e cikin masifa ganin yan da yayi kusan bige ni da murfin motar sa, "Malam ya haka baka ganine?." nayi maganar ina yi masa kallon sama da kasa. tsayuwar sa ya dai-dai tare da mai da murfin motar ya rufe, kana yashiga nuna min yatsa tare da kaÉ—a yatsar yasoma magana. "A kan wani dalili zaki rika birkita wa yara Æ™waÆ™walwar su, kinyi yunkurin sauya musu School abaya, ba'a baki dama ba shine kika ajiye su a gida tsawon sati guda, sannan kika sauya musu Makarantar, ilimi kike so su samu ko kuwa birkita musu Æ™waÆ™walwa kike son yi, kada ki kuma yunkuri da tunanin sauya musu makaranta kan wani dalilin ki mara amfani, idan kuma ba haka ba." sai yayi kwafa tare da kaÉ—a yatsar sa. kamar daga sama nake jin maganar nasa mamakin sa da furucin sa suka sani gyara tsayuwa ta ina yi masa kallon kacika mai karfin hali. "Dakata malam." nafaÉ—a ina É—aga masa hannu, kana nacigaba da faÉ—in. "A kan dalilan su Æ´aÆ´ana ina da ikon yin komai da su, dalilina mai amfani, kada ka kuma cewa dalilina bashi da amfani tun da baka sanshi ba, Æ´aÆ´a nawa ne nike da ikon yin komai kansu, malam kafita daga rayuwar Æ´aÆ´ana kana ta yau darar su da danganta su da kai, da suna mai kama da uba, Æ´aÆ´ana basu da uba kuma basa bukatar uba domin bazai yi musu amfanin komai ba, rayuwar su a haka tafiye musu rayuwa da uba sau dubu dan bashi da wani amfani a gare su." sassauta maganar da nake nayi tare da haÉ—e hannaye na biyu kana nacigaba da faÉ—in "Dan Allah kafita daga rayuwar Æ´aÆ´ana kada ka yaudare su da wannan kalma ta uba, dan basu da uba kuma basa bukatar uban, kuma ba shegu bane Æ´aÆ´ane tsaftatattu mafiya daraja." Afusace yashiga matso ni, ganin yan da yanayin sa ya sauya gaba É—aya, sai na shiga ja da baya, shiko maso ni ya cigaba da yi tare da nuna ni da yatsa, yana huci kana yasoma magana cikin É—aga murya "Idan kika sake cewa basu da uba sai ranki yayi mummunar É“aci, idan kika kuma sako kallamr yaudara sakani na dasu!..." sai yayi kwafa tare da kaÉ—a yatsar sa alamun gargaÉ—i, mamakin ganin karfin halinsa muraran nake, wai ni da Æ´aÆ´ana ake nuna min iyakata a kansu, bil hakki da gaskiya yake maganar dan kuwa fuskarsa ta nuna, niko baya na kuma ja ganin yan da ya matso ni sosai yana maganar kamar zai kai min hannu, wani irin kallon shekeke nabisa da shi sannan na ce "Idan ba yaudara bace mene ne, kana cusawa yara abun da babu shi, cikin rayuwar su, ina sanar maka da hakan ne sabo da matsaltawan ka kansu, na dai faÉ—a maka kafita daga tsafgar Æ´aÆ´ana idan kuma ba haka ba zan sa ayi maka gargaÉ—in da zaka fi fahimta." ina kai wa nan najuya. Shan gaba na yayi a fusace cikin muryar da yake nuni da tsantsar gargaÉ—i ya ce "Yazamo na karshe fitar kalmar nan daga bakin ki, idan kika sake kika sake furta kalmar durkuso cikin rayuwar su, bazan sa ayi miki hukunci ba ni zan yi miki hukunci da kai na! ki sake nanata kalmar basu da uba kigani!." yayi maganar cikin fusataccen amon sauti, a zaburi namatsa gefe dan maganar nashi ta shige ni rabon da ayi min ihu da tsawa irin haka har na mance, shiyasa abun yazo min a sabo. ba zato naji kafata ta ta dama ta wuce cikin abu kamar rami, da sauri na juyo sai kawai na tafi luuu gaba É—aya, idanuna na rumse da karfi ina jiran najini a kasa, sai jina nayi zundum cikin ruwa, kara na Æ™walla wan na hakan yayi sana diyyar wucewan ruwa cikin bakina, fafutukan niman numfashi nashiga yi, da niman ceton kaina, duk buÉ—e bakin da zanyi sai ruwa ya wuce ciki, nayi-nayi na iya mike wa tsaye na kasa, duk da kuwa zurfin ruwan idan zan shiga da kafata iya kirji na yake zuwa min. Shiko Ahmad da sauri ya faÉ—a cikin swimming pool É—in ganin yan da ta ke bubbuga hannu da yin sama da shi da alamun niman ceto. hannu na ya ruko da karfi ya É—ago ni yamikar da ni tsaye. ruwan da ke kunshe cikin bakina dana ki haÉ—iye shi dan cikar da ciki na yayi, na furzar da shi tare da sauke tagwayen numfashi, ina damke cikina da ruwa yacika shi, a wahalce na na É—ago hannuna É—aya na share fuskata tare da tattaro gashi na daya rufe min fuska, na mai da shi baya, ida nuna na sauke kansa, dai-dai lokacin daya kai hannu ya share ruwan dake fuskar sa, sai a lokacin na lura ruwan dana furzar daga baki na a fuskar sa na fesa. shima idanun sa a kai na tun daga gashin kaina yake bina da kallo har kasa, kasan cewar rana ya taso ya haske cikin ruwan ana iya kallon abun da ke kasan ruwan. dogon tsaki na ja dan nakasa magana tsabar haushi, bugu da kari yan da cikina ya cike tam da ruwa. a hankali na soma tafiya cikin ruwan har na isa bakin gaÉ“ar gun matattakalar shiga da kuma fita daga cikin swimming pool É—in, a sannu na soma hawa maganar sa na jiyo, "Ki tsaya a taimaka miki kirage ruwan da kika sha." cigaba da haurawa ta nayi batare da waige ko tsayu ba, ina karasa fita da sauri nayi hanyar part É—ina jin zuciya ta na tashi, cikin sauri na shige cikin side É—in direct sama na haura, ina shiga bedroom É—ina da sauri nashige bathroom, ai tun kan na karasa bakin toilet nafara sheka amai tsakiyar bayin, zallar ruwa narika aman sa. da kan sa aman ya tsaya kamar yadda yazo bazato ba sammani, numfashi narika sauke wa ina tallafe da cikina da yanzu nake jin sa wayam, sai dai É—an murÉ—ar da yake min. a daddafe na tsaftace bayin na tuÉ“e kayan jikina da suka jike gaba É—aya na wurgasu cikin wishing machine, nafito doguwar riga mara nauyi na zura, kana na isa bakin gado na zauna ina mai cigaba da sauke numfashi, tsaki narika ja a-kai-a-kai tsabar haushin da nake jin kaina ciki, har lokacin kasa iya furta komai nayi. idan na tuna ruwan da na hambuÉ—a a cikina sai naji kamar nayi ihu, sauki na ma É—aya jiya-jiyan nan nasa aka fidda ruwan dake cikin swimming pool É—in, aka wanke cikin sa a ka kuma zuba wani, ban kuma yi amfani da shi ba. wani dogon tsakin naja yayin da na kai bayana na kwanta kan gado. mamakin karfin hali da takaicin mutumin nan suka rika zuwar min, wai ni yake yiwa gargaÉ—i kan Æ´aÆ´ana, ya kuma yi sanadiyyar faÉ—uwa ta cikin ruwa, badun kwanana na gaba ba wata kila da yanzu ana kan shirin kai ni makwanci. Dole nasa jami'an tsaro cikin lamarin dan ban amin ta da mutumin nan ba, awani dalili zai rika shiga min cikin gida kai tsaye har yarika yimin barazana kan Æ´aÆ´ana. Mikewa zaune nayi tare da É—aukar waya ta, number Mr Aliyu nakira wato P.A na, ko da ya É—aga bayan mun gaisa na É—aura da faÉ—in "Mr Aliyu ina so a saka min jami'an tsaro a gidan nan." da sauri ya ce "Madam meke faruwa akwai matsala ne?." yayi maganar cikin nuna damuwa sosai kana yaci gaba da faÉ—in "Ai Madam tun farko shiyasa nace azuba jami'an tsaro gida kamar wannan dole sai da manyan Security masu rike da bindiga, kikace abar mai gadi kaÉ—ai ma ya isa, ina kuwa zai isar wa gida kamar wannan, yanzu kuwa zan fita in sha Allahu anjima zamu zo da su." na ce "To Allah ya kaimu." nakashe wayar, ina katse kiran kiran Bappa na shigowa, na daga da sallama daga cikin wayar Bappa ya ce "HAMDAH ko kina bacci ne?." na ce "A'a ba bacci nake ba Bappa." ya ce "To kizo yanzu maza." da sauri na mike jin yana faÉ—in haka ya kashe wayar. cikin hanzari na nufi side É—in su Bappa da sauri na dan Bappa bai taÉ“a min irin wannan kiran ba nasan komai akayi akwai wata masalar, da ire-iren waÉ—an nan tunanin nashige cikin side É—in. turus naja na tsaya yayin da jikina ya kama É“ari ganin Yakubu durkushe yana kuma rungume da uniform É—in su Nasmah, cikin tsanani tashin hankali na karaso cikin parlour'n gaban Yakubu natsaya cikin rawar murya da kuka keson kwace min na ce "Ina yara na?!." nayi maganar cikin rawar murya sosai tuni hawaye yacike ido na. Bappa da ke zaune kan kujera ya dube ni tare da faÉ—in "Zo zauna nan HAMDAH." yanu na min kujerar da ke kusa da shi, ban iya bin umurnin Bappa ba dan kuwa hankali na yakai kololuwa wajen tashi, duba da yan da Yakubu yake É“ari yakuma rungume uniform É—in gam-gam. Inna Wuro ce ta mike tazo taruko faÉ—ata ta jamyo ni ta zaunar da ni kan kujerar, tuni hawayen da suka cuko idona suka fara zuba. Bappa ya girgiza kai yana faÉ—in "Muma mun shiga irin yanayin nan da kika shiga a yan da yashigo mana kamar an rakoshi a guje, tam bayar da na fara mishi shine ina yaran suke ganin uniform É—in su a hannun shi, da kyar ya iya ba mu amsar suna nan kuma suna makaranta, yaji tsoron ya tinkare ki kai tsaye shiyasa yazo nan." kai Yakubu yashiga gyaÉ—a wa yana É—an rarrafowa da guiwar sa yana kuma faÉ—in "Dan Allah dan Annabi Bappa Malam ka rokar min afuwar ta wlh duk yan da naso na hana faruwan haka bai yuwu ba, wlh fin karfi aka nuna min muraran." Bappa ya katse shi ta hanyar É—aga masa hannu ya ce "Ya isa." kana Bappa ya juyo da kallon sa gare ni ya ce "Lokacin da suka fita zai kai su makaranta a hanya suka haÉ—u da Ahmad Tijjani Sabil ya sai da su, yake tambayar su ina zasuje ganin ba hanyar makarantar su suka nufa ba, sannan kuma ga wata uniform É—in daban a jikin su, to shine shi Yakubun ya shai da masa in da zasu, shikuma Ahmad yace kada ya kuskura ya kaisu wannan makarantar yawuce ya kaisu wan can makarantar su, to dai a takaice tare suka tafi da shi wancan makarantar da aka cire su yasa aka basu wani uniform, yakuma tuÉ“e musu najikin su shine yabashi wan da yacire musun yace ya mai do shi gida, to shine ya dawo hankali tashe yakuma ji tsoron yaje ya tinkare ki da batun shine ya zo nan, kafin na kira ki sai da na kira shi Ahmad É—in sabo da ina da lambar sa dan ranar da yazo nan na karÉ“i lambar sa, ashe dai zatayi amfani gaba akuma irin wannan ranar,shine na kira sa dan ji dalilin sa na yin hakan, ya bani tabbacin dalilin sa na yin haka, kuma na gamsu, yace yawai ta canza musu makaranta a karancin shekarun zai iya birkita musu Æ™waÆ™walwa gara abar su idan suka gama can É—in kan lokacin sun daÉ—a wayo sai suyi gaba, kuma nima nayi nazari naga hakan yafi abarsu a can É—in, nayi masa maganar dalilin ki na canza musu makarantar yace za'a kara tsaro sosai babu wata matsala." Yakubu da tun da Bappa ya soma maganar yake ai kin gyaÉ—a kai da buga bayan hannun sa cikin É—aya tafin hannun sa, yayi kalar tausayi, Bappa na gama maganar shima ya É—aura da faÉ—in "Wlh tallahi Hajiya na rantse miki da Allah, ba laifi na bane, na dage wajan ganin ba'a kuma samin wata matsala ba kamar yadda nayi miki alkawari, wlh Hajiya dana buÉ—e baki zanyi masa musu dawani yafito daga cikin motar sa, ya shake ni sai da naji kamshin kabari, shi ya hana mutumin da yanzu na sheka, ki gafar ceni Hajiya ki tai maka kibar ni a bakin aiki na." Numfashi na sauke jin akasin abun da nake tunani yafaru a kansu, dan Ni nagama tunanin hatsari sukayi sun mutu shine yakawo kayan su gida. duban Bappa nayi ina shere hawayen fuska ta nace "Yan zu Bappa ka amin ce da abun da yafaÉ—a kenan?, to shi ina ruwan shi da su me ya shafe shi da lamarin su da har zai rika shiga, har fa Daddy yake cewa surika ce mishi meye gamin sa da su." murmushi Bappa yayi irin tasu na manya kana ya ce "To in ban da abin ki HAMDAH ai wan da ya nuna yana son naka yagama yi maka komai a rayuwa, kuma da kike cewa yana shiga lamarin su basu kaÉ—ai ba lamarin koma waye yana shiga, idan baki mance ba na taÉ“a baki labarin sa nazu wa rugar mu da yayi, muma ba lamarin mu yashiga ba yakuma jiÉ“anci lamuran mu, yayi silar magance mana wutar fitinar da take ta kunno mana, ko jiyan nan da daddare munkalli labarai gidan TV wasu iyaye sun fito suna mika masa godiya kan gudumawar da ya bada kan Æ´aÆ´an su, su iyayen ma basu ma sani ba Æ´aÆ´an ne suka dawo gida suke faÉ—a musu alkhairin da yayi musu, a makarantar gwamnati suke karatu ya cire su ya mai dasu na kuÉ—i, sannan kin ce meye gamin sa da su, ke da kike taimakon bayin Allah meye gamin ki da su?, ai shi tai mako basai wan da kasani kake taimaka masa ba, duk wan da Allah ya sa da rabon sa yafaÉ—o ta kansa sai ka taimaka masa ladan ka na gurin Allah, shiya sa Allah ya halittomu kala biyu mai kuÉ—i da kuma talaka hakan kuma jarabta ce, idan kai me kuÉ—i ne kayi kokarin cin jarabawar da yayi maka, wato kajikan na kasa da kai, ka kuma tsare dokokin Allah, to da yardar Allah babu shakka zaka shiga aljanna ta sanadiyyar jaraftar ka da yayi da arziki, idan kuma kai talaka ne, karike talaucin ka kabi dokoki Allah, kai ma zaka wuce aljanna da yar dar sa. shi tai mako ba sai wan da kasani kake yi masa ba. kiran sa da sunan uba kuma da suke yi, ai duk É—a nagari shike daraja nagaba da shi yakira sa Yaya wan da ya haifesa kuma yakira sa da sunan uba, wan da yayi jika da shi yakirasa da Kaka, abun alfahari ne É—anka yazamo daga cikin irin waÉ—an nan Æ´aÆ´an, ba ai bu bane dan sun kirasa da suna Daddy tun da yakai ya haife su, zaki so ace Æ´aÆ´an ki suna da rashin kunya ko basu da tarbiyya?." Shiru nayi batare da nace komai ba. murmushi Inna Wuro tayi,dan ta fahimci in da maganar tawa ta dosa, kana tace "HAMDAH kenan ai laifin wani baya shafar wani." kana ta kawar da zancen da faÉ—in "Sai kiyi wa Yakubu hakuri ya dai na wannan tafa hannu da É“arin jikin da yake." da sauri Yakubu ya daÉ—a rarrafo wa gaban mu yace "Whl Innar Gida kada kiga shakar da mutumin nan yamin, tsaro biyu ne suke girgiza ni a jikina, tsoron kada Hajiya ta kore ni daga ai ki na, da kuma tsoron wannan basamuden mutumin da suke tare da Ahmad Sabil daya makuren makogaro." yayi maganar yana É—aga wuyar sa da nuna mana in da ya shako san. dariya duk sukayi ban da ni dana murmusa kawai. na yar da da dukkanin maganar da Bappa yayi, sai dai inajin abune me wuya na iya jure wa dajin kalmar uba na fita daga bakin su Naseem. Bappa yacewa Yakubu ya tashi ya tafi anjima yaje ya É—auko su a makarantar. ya mike yana zuba godiya yayi waje. Haka su Bappa sukayi ta jana da hira bani na bar side É—in ba sai wajen karfe 12, gani lokacin dawowar su Naseem yayi nayi musu sallama nakoma side É—ina. komawa ta bada jimawa ba su Nasmah suka shigo a guje, kalmar da suka fara furta min shine Daddy'n su ya ce gobe zai zo ya É—auke su a mota. ban iya ce musu komai dan ko na faÉ—an ma abanza ne... A É“angaren Ahmad Tajjani Sabil, tun da yabar gidan tuki yake kamar mai koyon tukin, a haka ya iso bakin wani katafaren get me girma da tsaruwan gaske, yayi hon batare da É“ata lokaci ba a ka wangale masa katafaren get É—in, a sannu ya dannan hancin motar sa ciki, ya ilahi ya lillahi gida ne mai matukar girman gaske, alkalami na bazai iya zana girma da tsaruwan gidan ba, FAN'S na barku ku hasasho da kanku. a hankali ya isa parking lot in da motoci da suka kai guda biyar ke jere agun ya yayi parking, a sannu ya buÉ—e motar yafito, daga can wasu matasa guda uku suka iso in da yake da sauri, suna faÉ—in "Barka da dawowa master." hannu kawai ya É—aga musu tare da yi musu murmushi, batare da yace komai ba, yasoma tafiya a hankali ya iso ba kin wata kofa, jiki ba kwari ya tura kofar yashiga da sallama É—auke kan laɓɓan sa. wata kyakkyawar mace fara Æ´an duma-duma ce ke zaune cikin katafaren kayataccen parlour'n, tana ganin sa ta ajiye wayar dake rike a hannun ta, ta mike da sauri, ta nufo shi da É—an sassarfa, tun kafin ta karaso ya buÉ—e hannayen sa ta shige cikin jikin sa ta rungume shi, hannayen sa ya haÉ—e yazagaye bayan ta tare da manna mata kyakkyawan sumba a goshi, ido ta lumshe tare da buÉ—e wa lokaci guda, kana ta É—ago kanta ta mannan masa kiss a kumatu. yan da tayi shima haka yayi, ya lumshe idon tare da kuma buÉ—e wa, itako hannun ta tayi sama da shi ta sakalo wuyan sa taÉ—an langwaÉ“ar da kai gefe kana ta soma magana cikin shagwaÉ“a "Aboki ka mance da nine?." ido ya waro da alamun maganar tata tayi girma, baki ta cuno gaba tace "To shine nayi ta kiran ka a waya baka É—aga ba, kuma baka neme ni ba tun da ka fita, ni da na nime kan kaki amsa kiran." maganar take cikin shagwaÉ“a kamar zata fashe masa da kuka. kuma tun ta ya kama yaÉ—an ja kana ya ce "Na isa naki É—aga kiran ki kinga wayar da na fita da ita É—aya wayar tana gida ai." yayi maganar yana nuna mata wayar dake rike a hannun sa. murmushi tayi tare da faÉ—in "Ai har da nayi fushi." hannun sa ta ruko tana faÉ—in "Toho muje kayi wanka." ta janyo hannun sa sukashi ge cikin wani kayataccen bedroom, suna shiya da kanta ta tuÉ“e masa kayan jikin sa, boxes kaÉ—ai ta bari takuma janyo hannun nasa sukayi cikin bathroom. Ta taimaka masa yayi wanka suka fito É—aure da towel a kugun sa. lokacin an fara kiraye-kirayen sallar azaha jallabiya ya zura ya jasu sallah nan cikin É—akin, ko da suka idar, zaman sa ya gyara ya jingina da jikin bayan sa da jikin garu-bango yana lazumi, ido taÉ—an tsura masa kana sai kuma ta mike ta fita jim kaÉ—an ta dawo É—auke da tray mai girma a hannun ta, a gaban sa ta dire, kana tashiga buÉ—e kulolin da suke kan tray'n har guda uku, wani daddaÉ—an kamshi ne suka fara tashi daga cikin kulolin, nan da nan É—akin ya kaure da kamshin lafiyayyun girkin. tazuba cikin plt tare da saka cokula guda biyu, ta gyara zaman ta da kyau ta maso gaban sa, in da ta saka plt É—in a tsakiyar su, suka rika cin abincin gwanin ban sha'awa sunayi suna É—an taÉ“a hira da zolayar junan su, a haka har suka kammala, takwashe kayakin ta mai da su kitchen, ko da ta dawo ta taddashi ya koma gado, yana É—an danne-danne a waya. kimsa in da suka É“atan tayi kana tazo bakin gadon ta zauna, dai-dai in da kansa yake, ta gyara zaman ta da kyau ta É—ago kansa ta É—aura kan cinyar ta, yayin da ta cusa hannunta cikin sumar kansa tana É—an yamutsa shi cikin tsalon sa mutum yayi bacci. aje wayar dake rike a hannun sa yayi, kana yayi sama da hannun sa ya shafi gefen fuskar ta, a hankali cikin muryar jin baccin da yafara ziyar tar sa, ta sanadiyyar abun da take masa, ya ce "Kawa nayi bacci kenan?." kai ta gyaÉ—a tare da faÉ—in "Eh nasan ka gaji." numfashi ya sauke kana yayi kasa da hannun sa yadaÉ—a gyara kwanciyar sa da kyau a hankali yashiga sauke numfashi. batare da É“ata lokaci ba bacci yayi gaba da shi da taimakon yan da take sarrafa gashin kansa da wasu sassa na jikin sa. sai da ta tabbatar da baccin nasa yayi nisa, sannan ta É—aga kansa a hankali ta janyo pillow ta saka masa kana ta mike tafita, domin sanya ido kan aikin da masu aiki suke gudanar wa a gidan... Da misalin karfe uku da rabi ya farka bathroom ya faÉ—a can yafito ruwa na É—iga daga jikin sa da alama wanka yakuma, gaban wardrobe ya tsaya yaciro kaya wani dakakken yadi ne wan da daganin sa ma kasan bana wasa bane sai dai manyan kam. bayan ya saka ya isa gaban mirror turo kofar a kayi daga cikin mirror yazubawa kofar ido, lallausan murmushi ya sake wan da sai da kumatun sa suka lotsa, lokacin da suka haÉ—a ido da ita tacikin mirror, baki ta É—an turo gaba kana ta tako zuwa in da yake, ta É—aura hannun ta kan hannun sa daya É—aura kan turare yana kokarin É—auka, ta amshi turaren sannan ta dube shi tare da faÉ—in "Shine zaka yi wanka baka neme ni na taya ka bako?." kai yaÉ—an langwaÉ“ar sannan ya ce "Nayafe miki ai nasan kin sha wuya wajen sani yin bacci." turaren ta É—ago tafara fesa masa a jiki sannan tace "Babu wani wuya gun ai kin lada ni dai wayo kayi min ka hanani samin wannan ladar." "Kinfa tara ladan nan da yawa amma rabawa zamuyi ko?." yayi maganar cikin tsigar zolaya yana kuma jan kuma tun ta. kafaÉ—a ta make ta ce "Naki wayon naka yafi nawa yawa ai." dariya suka sakar wa junan su. sai da ta fisa masa turaruka wajen kala uku kana ta gyara masa zaman hular kansa, ta ce "Kafito sosai fa." "Haba original mirror ai ba ma sai naga wannan jebun ba." yafaÉ—a yana nuna mirror. murmushi tayi kana taÉ—an tsura masa ido sai kuma ta ce "Aboki me ke damun ka?." tayi masa tambayar cikin nuna tsantsar kulawa. da sauri ya ce "Wani abun kika gani ne, to ni kuma me zai dame ni bayan ina da ke." ya kai bakin sa kan goshin ta tare da mannan mata kiss. numfashi ta sauke tare da É—an yin shiru tana nazartar yanayin sa, kana ta ce "To shike nan muje na rakaka katafi masallacin gashi ana kan kiran sallah." Hannun ta ya damke cikin nasa cikin son kawar mata da shakkon dake hangowa kan fuskar ta ya ce "Babu komai fa." da sauri ta katse shi da faÉ—in "Ban kuma cewa komai ba fa muje katafi masallaci......"! Mommyn Twin ce 10 Tun da yatafi masallaci bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha, dan tun san da aka idar da sallar zai koma ciki, yayi ba'i dan haka yasa akayi musu masauki a parlour'n ba'i, basu kuma bar gidan ba sai daf magriba, dan haka masallaci ya zarce sai yanzu bayan sallar isha ya shigo. ko da yashigo parlour'n babu kowa, sai sanyi me fidda daddaÉ—an kamshi ke tashi cikin parlour'n. direct bedroom É—in sa ya wuce, hular kansa ya cire ya É—aura saman bedside, kana yatafi a hankali zuwa bakin gado ya zauna, a hankali yakai bayan sa ga katifa ya kwanta rigingine, yayi pillow da hannayen sa kafar sa na kasa yana É—an lilo da shi. shiru yayi yayin da ya kurawa pop'n É—akin ido, kamar mai karantar wani abu a jiki. a hankali ta turo kofar ta shigo da sallama, ido ta kura masa na Æ´an dakikai kana a sannu ta taka zuwa bakin gadon, sai ta faÉ—a jikin sa gaba É—aya ta sake nauyin ta a kansa, ido ya waro tare da faÉ—in "Wash zata karya ni, Kawa kin kara nauyi fa." cikin muryar dariya ta ce "Allah Aboki babu wani nauyin dana Æ™ara in da nake da haka nake yanzu ma." "Tap waya faÉ—a miki ke baki ganki kwana biyu sai daÉ—a zama duma-duma kike ba, niko sai tatse ni kike." kwanciyar ta tadaÉ—a gyara wa a kansa cike da shauki tace "Kai Aboki kai ma fa baka ganka bane kayi kiba kwana biyun nan." dariya yayi yana dai-dai ta fuskar su a hankali ya manna mata kiss kan laɓɓanta. yan da suke yiwa junan su idan ka gani zaka fagimci santsar kauna soyayya shakuwa yarda a saka nin su. cike da shauki ya mirgino ta yadawo da ita kasa shi ya haye kanta, nauyin sa shima ya sake mata, yana faÉ—in "A hakan kike cewa nayi kiba jini fa babu ko nauyi kamar pepa kullum kina tsotse ni, kullum sai na tsame wani abu daga jikina na zuba shi jikin ki, taya bazaki daÉ—a kara zama wata duma-duma ba." Æ´ar karamar kara ta sake tana faÉ—in "Allah Aboki kayi nauyi wash Aboki na tuba É—aga ni." Æ´ar dariya yayi tare da shafa sumar kanta yana nan a kanta. Æ´an wasan ni suka cigaba da yi sakanin su me cike da zallar shauki da kauna, zallar soyayya da É—in bin kauna kake hangowa tsagwaran ta a tattare da su. Cikin yanayin da suke ta dube shi tana faÉ—in "Aboki ka rama É—aga ni na tashi, idan ka kara yafi haka nima sai na rama." tayi maganar tana ture shi. Æ´ar dariya yayi mata tare da mirginawa ya koma gefe yakwanta rigingine tare da yin pillow da hannayen sa biyu, ta mirgina tayi pillow da damtsen hannun sa, sai kuma ta É—ago tasaka hannun ta a kumatun ta, yazamana da guiwar hannun nata najikin katafi, in da da kyau take iya kallon fuskar sa, duban sa tayi da kyau naÆ´an sakanni kana a hankali taso ma magana "Meke da mun ka aboki?." tayi maganar idanunta cikin nashi. idanun sa ya lumshe tare da buÉ—e wa yaÉ—an ja numfashi kana yace. "Tambayar É—azu kuma har lau, to me kika gani yanzu bacci nake ji." murmushi tayi kana ta shafa gefen fuskar sa sannan ta ce "Bacci kuma him Aboki kenan, adalilin yin baccin ka na rana zaka kuma yin wani baccin ne da misalin karfe 12 na dare, yanzu karfe 8:30 saura akwa uku da rabi lokacin baccin ka yayi, sam karya baya yi maka kyau sabo da rashin iya shi da bakayi ba shi yasa ko kayi ake saurin gane ka." kokarin kawar da maganar yayi ta hanyar janyo ta jikin sa, kana ya shiga wasa da wasu sassan jikin ta, a hankali ya furta "Kawa ke baki ga in da idona sukayi ba bacci ne a cikin su, da alama dai baccin da É—azu kika sani bai ishe ni ba." ta ce "Him wai ni yau ake É“oyin wani abun, Aboki yaushe ka fara É“oye min damuwar ka, yaushe ka fara sanya hijabi sakanin sirri na da naka, duk faÉ—in da kake ni da kai abu guda ne ashe ba haka bane??, shin da ma ashe akwai wata ranar da zaka É“oye min damuwar ka, ni ce fa wacce muke tauna matsalolin mu mu magance sa batare da wani ya sani ba, ashe dama faÉ—in mu tsirrin junan mu ne da kake abun ba haka yake ba, ban taÉ“a tunanin zuwan wannan ranar ba." É—an sakai ta maganar nata tayi tare da mike wa zaune ta tankwashe kafafun ta takuma duban sa da kyau, nan take sai ga hawaye yacika idon ta, hannun sa ta ruko ta kankame shi cikin nata, ta ce "Tabbas akwai abun da yake damun ka da ma ai ni na sani akwai ranar da zatazo irin haka." hannun sa ta daÉ—a kankamewa cikin nata, taci gaba da faÉ—in "Kayi hakuri amma ka sani nafika jin damuwa fiye da kai, ni na riga da nasa ni, dama kana hana ni damuwar ne kai kana yi, idan da a ce mutum shi yake ba kan sa abu da karfin dukiya WALLAHI dana sadaukar da dukiya, WALLAHI idan dana san in da zanje na sami maganin da zansha yazamo silar haihuwa dana tafi ko da bangon duniya ce,domin samin farin cikin ka, nagaza baka É—a kayi hakuri kayi hakuri kayi hakuri!!." takuma nanata kalmar hakuri yayin da tuni hawayen idon ta suka fara zuba. Da sauri yamike zaune tare da janyo ta jikin sa yana faÉ—in "Ke meya kawo wannan maganar?, banace kada nasake jin wannan maganar a bakin ki ba?,meye na yin ta meya kawo ta yanzu kuma?, Okay so kike ki kawar da farin cikin da ke nan ko?, hauhuwa dama ashe mutum shi yake bawa kansa haihuwa?, okay kin mance cewa Allah shi yake bai wa bayin sa haihuwa?, so kike kiyi tsaÉ“o to kiyi gaggawan tuba, maza yanzu." yayi maganar yana share mata hawaye. kana yaci gaba da faÉ—in "Dai na kunan kada na sake jin wannan maganar a bakin ki, kada na sake ji idan kuma so kike ki koyi yan da zaki rika É“ata min rai to ki kara yin ta, na ce miki ina son haihuwa Allah bai nufa na samu bane, idan yaso sai ya bamu bare ma muna da su Æ´aÆ´an da muke yi musu hidima kama daga gidan marayu makarantu da dai sauran su suÉ—in ba namu bane, suma Æ´aÆ´an mu ne, mai da hawayen kinji Fara Æ´ar duma-duma ta." " kai ta shiga girgiza wa tana faÉ—in "Nayi shiru bazan sake ba ka yafe min." kai ya jinjina kana ya koma yajin gina bayan sa da jikin gado, ita ko zaman ta tagyara suna fuskantar juna ya ce "Ko ke fa fara Æ´ar duma-duma ta to na yafe." dariya tayi kana taÉ—an langwaÉ“ar da kanta cikin muryar shagwaÉ“a a hankali ta ce "Na yar da ba abun da na faÉ—a yanzu ke damin ka ba amma na tabbata akwai wani abun, zuciya ta baza ta sami sukuni ba har idan ban za mo silar kawar da damuwar ka ba, amma babu damuwa tun da ka nuna baka so na sani, yau rana ta farko daka taÉ“a É“oye min damuwar ka, ban taÉ“a tunanin akwai ranar da zata zo ka É“oye min damuwar ka ba, damuwar ka tawa ce kamar yan da yake tawa takace, ai ban san cewa haka yanzu ka É—auke ni ba shike nan babu damuwa." tayi maganar tana kokarin sauka a gadon. dakatar da ita yayi ta hanyar rike hannun ta kana yaÉ—an ja numfashi sannan ya ce "Abar shi kawai faÉ—ar shi ma bashi da wani amfani." ido ta kura masa sannan tace "Haka kace abar shi yaci gaba da damun ka da cin ka a rai ko?, kada ka mance nafi kowa sanin ko kai waye tun sati biyu da suka wuce na fara fahimtar akwai wani abun da ke damun ka, ban daÉ—a gaskata hakan ba sai yau da ka shigo gida, rungumar ka da nayi jikin ka da zuciyar ka suka tabbatar min da haka, dakuma tabbacin damuwar naka yakaru a yau, tanbayar ka danayi É—azu da zaka tafi masallaci yakuma bani amsar abun da nake zargi, babu halin da zaka shiga koda dai-dai na second 1 ne ban gane shiba." Ganin yan da ta hakikan ce tanuna damuwar ta matuka a kanshi takuma nuna É“acin ranta nakin faÉ—a mata da yayi wan da ada ba haka asakanin su. sai ya janyo ta jikin sa ya rungume, tabbas ita wata sashi ce a rayuwar sa da bazai iya É“oye mata komai na rayuwar sa ba, kamar yan da tun fari suka gina rayuwar su ta hanyar faÉ—awa junan su sirrukan su, bata É“oye masa komai kamar yan da shima baya É“oye mata, ko a yanzu dayake ta kokarin barin abun cikin zuciyarsa shi kaÉ—ai yana ta shan fama da É—awai niya da zuciyar sa dan bai saba ba sam. numfashi ya ja kana a hankali yasoma magana "Akwai wani abun da ke damu na amma sam banso na fitar ba naso nayi jarumtar iya barin sa a raina dan faÉ—ar sa sam bashi da amfani." wani numfashi yakuma saukewa kana a hankali ya cigaba da magana "Kiyi hakuri da abun da naketa É“oye shi a zuciya ta ni kaÉ—ai, wan da nagaza iya dan neshi sabo da ban saba da irin saba, yabani wuya sosai a zuciya ta, kiyi hakuri yanzu da zakiji shi a kan laɓɓana, tabbas da gaske bazan iya É“oye miki sirri na ba kokarin yin haka dana yi kuwa dan cigaba da ganin kwanciyar hankalin ki yabani wuya sosai a zuciya, nayi ta kokarin danni shi cikin zuciya ta hakan ya garara gashi bugun farko kin gano da akwai abun da yake dami na." hannun ta ya damke cikin nasa kana yaja numfashi ya sauke sannan yaci gaba da faÉ—in "Wata ranar da Company na ya tura kayan bukata izuwa wata makarantar yara, kamar da yan da kika sani a ka saba, lokacin da motar Company ya isa aka shai da min da isar sa, sai na tashi da kai na naje makarantar domin ganewa ido na kalar farin cikin da yara zasuyi kan kayan da aka kai musu wan da yawan ci kayakin wasa ne irin na yara,sai sabbin kujeru, dan nima naji daÉ—i, duk da kuwa makarantar bana Gwamnati bane, makaranta ne ma irin na Æ´aÆ´an masu kuÉ—i, lokacin da na shiga makarantar nayi arba da wasu yara guda biyu, sunata wasanni da kayakin wasan da aka kai musu, duk da yara dayawa agurin amma nafi ganin farin cikin waÉ—an nan yara guda biyun sosai cikin matukar farin ciki da kuma jin daÉ—i suke ta wasa da kayan da motar Company na ta sauke, naji daÉ—i matuka ganin farin ciki a fuska da zukatan É—aliban, amma sai dai hankali na yafi karkata kan farin cikin da ke baiyana ga waÉ—an nan yara guda biyu, kasan cewar lokacin tashi yayi nan É—alibai suka fara watsewa, wasu diraibobin su suka zo suka kwashe su wasu kuma motar makaranta ta kaisu, haka yara sukayi ta watsewa. ina nan a cikin makarantar muna magana da shugaban makarantar bayan mun gama maganar na fito, lokacin tuni students sun watse, a bakin get na tadda waÉ—an nan yara guda biyun, da lokacin da na shigo makarantar su na fara ganin su da É—in bin farin ciki kan fuskokinsu, tare da mai gadin makarantar suna zaune a bakin get. ko da na iso gurin su kan su na shafa tare da duban mai ganin na ce, yaya su ba'a zo É—aukar su bane kokuma motar makaranta zasu bi kuma naga É—alibai duk sun watse. mai gadin ya ce Ba motar makaranta zasubi ba direban su ne zai zo ya É—auke su ko mai akayi dai yanzu yana hanya, yau an É—an makara ne wajen zuwa É—au kar su. kan su na daÉ—a shafawa sai nayi waje cike da jin sha'awar yaran, ina fita kuwa sai suka biyo ni a baya, sai na tsaya naruko hannun su ina tanbayar su yaya sunan su, kai yaya sunan ka nafara tambayar na mijin sai yace min sunan sa Naseem, ita kuma macen tace min sunan ta Nasmah, nafahimci wayo sosai tattare da yaran duk da kuwa Æ™arancin shekarun su, dan bazasu wuce shekaru uku zuwa uku da rabi ba, bayan nayi musu tambayar sai suma suka mai da min tambayar. to kai ma yaya sunan ka, wayon yaran ya burge ni sosai jin yan da suma suka iya mai da min tambayar, Sai nace musu sunana Daddy, kin san wani irin yanayi nagani a tare da su lokacin da nace musu suna na Daddy?." Dan sakai ta maganar yayi tare da daÉ—a matse hannun ta cikin nasa kana yaci gaba da faÉ—in "Ihun murna suka sake haÉ—e da tsalle suka rungume ni suna faÉ—in laa kai Daddy ne irin Daddy'n su Aeeman,É—in class É—in mu, to kai Daddy'n su waye ne?, maganar yaran yasa Ni shiga wani yanayi, sai dai farin cikin danake hango wa tare da su da kuma fahimtar da nayi kalmar sunan Daddy dana furta musu yazo mu su a sabon abu ko makamancin haka, Sai na ce musu Daddy'n ku. kin san me yaran sukayi?." nan ma hannun ta yakuma damke wa cikin nashi kana yaci gaba da faÉ—in. "Da É—a rungume ni sukayi suna ta tsallen murna da nanata kalmar sunan Daddy, wani irin abu naji acikin jiki na da zuciya ta, a duk san da suka furta kalmar Daddy a gare ni, sai naji wani irin farin ciki da jin daÉ—i mara misaltuwa a gare ni, cikin kan kanin lokaci naji yaran sun shige cikin zuciya ta, har nake ji tamkar Æ´aÆ´an da na haifa ne a gaba na suke kira na da wannan suna, abun da na daÉ—a lura da yaran a lokacin sosai na ke hango jin daÉ—i irin na samun sabon abu a tare da mutum, sai suka ce min Daddy kai ma zaka bamu chocolate irin wan da Daddy'n Aeeman yake bashi. na ce musu kwarai kuwa, to lokacin akwai ragowar Chocolate a mota wan da nake baiwa yara a gidan marayu idan naje, sai na ruko hannun su nace muje na basu chocolate yana mota ma kuwa. lokacin da muka nufi gun mota, a dai-dai lokacin wata yarin ya ta iso gurin a cikin mota." Sai kuma yayi shiru batare da yaci gaba da Maganar ba. ita ko zaman ta tagyara sosai wannan karon ita ta mai da tafin hannun sa cikin nata tasar kafe yatsun su guri guda, kana ta sanya idanun ta cikin nashi, cikin daÉ—a karfafa shi da bashi kwarin guiwar gama fidda damuwar da take ganin tamkar ta yaye masa, tagyaÉ—a masa kai cike da bashi kwarin guiwar yaci gaba da da fidda damuwar da take yi masa kallon cuta ce barin sa a ransa. A hankali kuwa yaci gaba da maganar yayin da ya daÉ—a sarkafe hannun nasu sosai, ya ce "Kawa kin san me naji?, wani abun mamaki naji wan da ban san mene ne shi ba, bayan da yarin yar ta É—auke su ta tafi da su, sai na tsinci kai na cikin wani irin yanayi mai ka ma da da muwa, mai kama da son in sake ganin su, amma nafi alakanta son in sake ganin yaran ne, bayan kwana biyu sai naji tunanin nawa yanata rikiÉ—a, madadin tunanin yaran su biyu sai ya dawo uku, zuwa lokacin na gama fihimtar har da ita yarin yar nake son sake gani. nayi mamakin kai na matuka, wata rana dana fita muka kuma haÉ—uwa da su a kan hanya ta ta zuwa mittin, a tunani na ganin da nayi musu wannan rana shike nan zuciya ta zata huta da tunanin abun da bai shafe ta ba, amma ina bayan rabuwar mu da su sai naji tamkar kara min ake. Bayan wasu kwana biyun sai nasa ayi min bincike a kan su wato ita da yaran dana ke yi musu kallon kannen ta ne, nayi mamaki matuka lokacin da labarin su ya iso min, dajin waÉ—an nan yara nata ne ma ana ita ta haife su. mamaki na shi ne ganin ta kara ma sosai, nasamu cikakken labarin su, da duk kanin bayanan tarihin rayuwar su..." shiru yayi tare da jan numfashi ya sauke, sannan ya ce "Labarin su mai cike da ban tausayi na girgiza da jin lamarin, sai dai a yanzu su ba abin tausayi bane, dan Ubangiji ya zartar da ikon sa gare su..." A hankali yashiga bata labarin su kamar yan da aka kawo mishi cikakken tarihin su, bai É“oye ko rage mata komai ba kamar yadda baiyi da farko ba, bayan gama shaida masa abin da aka sanar masa a kan su sai ya cigaba da faÉ—in "Kin san wace ce wannan yarin yar?." kai ta girgiza jiki a sanyaye yayin da idanun ta suka cika da Æ™walla tap suna shirin zubowa. taji bala in tausayin su da jin labarin su jikin ta yayi matukar sanyi. ya ce "I ta ce mai Company *HAM'NAS*." ido ta waro ta ce "Mai Company *HAM'NAS* mai *HAM'NAS* Nigeria Limited?." "Kwarai kuwa ita ce." kai ta jinjina tare da faÉ—in "Allah mai iko wan nan shine sakayyar da mafificin rahama yayi mata sakamakon cin jarabawar da ya É—aura mata tabbas labarin rayuwar ta abun a tausaya ne, a da yanzu kam Allah yayi mata sauyi da mafificin rahamar sa." sai gata tana hawaye cikin matsanancin tausayin labarin rayuwar HAMDAH da taji, har da jan sheshshe ka. ta kai hannun ta share hawayen ta tare da faÉ—in "Allah kayi mana mai kyau kasa mu dace duniya da kiyama." ya ce "Amin." sai ya saki hannun ta yakoma ya kwamta tare da lumshe idanun sa. a sannu ta gyara ita ma sai ta kwanta gefen sa tare da yin pillow da damtsen hannun sa, a hankali takai hannun ta kan fuskar sa, a sannu tashiga shafa gefen fuskar sa, in da kayataccen saje ke kwance a gurin lub-lub gwanin ban sha'awa. duban sa tayi da kyau cikin kulawa a hankali ta ce "Aboki." idanun sa da suke lumshe yaÉ—an buÉ—e su a kanta sannan ya amsa da "Na'am." in da ya am sa can cikin kasan mako shin sa, laɓɓan sa ne suka motsa tanan ta fahinci ya amsa kiran nata. idanun ta cikin nashi, sannan tace "Aboki bayan sanin labarin ta kuma sai me baka karasa bani labarin ba." idanun sa ya lumshi cikin son kawar da zancen ya ce "Wani labarin kuma ai na gama baki labarin." murmushi tayi tare da faÉ—in "Baka kara sa ba da saura dan acikin duk kanin labarin da ka bani baka bani asalin gundarin labarin ba, kawai dai ka ce min kana jin wani abu a kanta mene ne shi?." "Ba ko mai fa." yafaÉ—a a takaice yana gyara kwanciyar sa, tare da juya wa ya fuskanci jikin garu, yana faÉ—in "Zanyi bacci ki tai maka min kisa yayi daÉ—i." hannun ta ta cusa karkashin gashin kansa ta bayan keyar sa, yana jin haka da sauri ya juyo dan yasan jan masa sumar zatayi da karfi bawai tayi masa yan da zaiyi baccin ba. dariya tayi tana faÉ—in "Ai da baka juyo ba Aboki yau aski zan maka." ido yaÉ—an waro ya ce "Aski da hannu." farr tayi da ido ta ce "Zan nimo abin yin askin ai taÉ“awa nake naji ta in da zan fara." ya ce "FaÉ—i gaskiya dai Æ´ar guntun muguntar ce ta motsa." dariya takuma in da shi kuma ya murmusa yana kokarin mai da idanun sa ya lumshi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar faÉ—in "Me zaka É“oye min ne iye sai fa ka karasa bani labarin nan dan baka gama bani ba." shiru yayi bai ce komai ba, Murmushi tayi tare da faÉ—in "To ni bazan karasa baka labarin, tun da yau ka aro hijabi ka sakata sakanin mu, zan yaye ta yanzu dan babu ita sakanin mu har gaba da abadan." É—an numfashi ta ja tare da cigaba da faÉ—in "Tun da ka sanya ido kanta Ubangiji yayi ikon sa,ya datsa maka sonta, a lokacin da baka taÉ“a sammanin a kwai ranar da hakan zata kasan ce da kai ba, dan kai a tunanin ka ni kaÉ—ai ce Ubangiji ya dasa maka sona cikin zuciyar ka, babu wata macen da zata kuma samin gurbi cikin zuciyar ka, ka mance da cewa Allah shi ne sarkin mulki mai yin yadda yaso da bayin sa, nasan ka da son yara amma son da kake yiwa waÉ—an nan yaran na daban ne, kana yi musu irin son da uba yake yi wa Æ´aÆ´an sa, haka ne ko?." tayi magaran tana duban sa da murmushi sosai kan fuskar ta. numfashi ya sauke kana ya janyo ta jikin sa sannan ya ce "Haka ne." ya faÉ—a dan babu É“oye-É“oye ko karya sakanin su, ko yan zu ma dayayi kokarin yin hakan sabo da wani dalilin yasha wuya sosai da fama da abun cikin zuciyar sa. wani yelwataccen murmushi ne ya baiyana kan fuskar ta, kana ta ce "Kana son ta?." kai ya gyaÉ—a alamar Eh sannan ya ce "Amma abar maganar domin bana jin zan iya haÉ—a ki da wata." gyemun sa taja, sai kuma ta É“ata fuska sannan tace "Haka Allah ya ce, bana son ka canza daga halin dana sanka baya yi maka kyau, dama kan haka kake masaltawa zuciyar ka aje damuwar da bata saba ba, shine har kake son ka koyi karya ko?, kana son ta, tun daga farkon labarin ta naji nima ina son ta ina son Æ´aÆ´an ta, ita ta musamman ce yarin ya karama mai halin man ya ba kasafai ake samun irin su a duniya ba, ni ma ina son ta, zan ku ci gaba da son duk wani abun da kake so har idan bai saÉ“awa Shari'a ba har karshen rayuwa ta zan cigaba da son sa." mike wa zaune yayi ya lankwashe kafafun sa kana ya dubi ta da É—in bin farin ciki da jin daÉ—in kasan cewar ta cikin rayuwar sa ya ce "Haki ka babu wan da yakai ni dace da samun mace ta gari, da ace kowani na miji irin ki ya samo a matsayin mata shi da damuwa ko tashin hankali bazai gansa ba har karshen rayuwa, Allah yayi miki albarka matar aljanna, faran tamin da kike Allah kema ya faran ta miki fara Æ´ar duma-duma ta." "Ameen Ameen ameeeeeen." tafaÉ—a tana jan É—an gyemun sa irin na gayun nan. sai kuma da sauri ta saki gyemun ta ce "Ka faÉ—a mata kana son ta kuwa?." kai ya girgiza ya ce "Ban faÉ—a mata ba." ta ce "To me ya sa?." ya ce "Sabo da baza ta amince ba." "Kamar ya, zakace bazata amin ce ba, baka tin kare ta da batun ba ka bata laifi." tayi maganar tana rike haÉ“a. kuma tun ta yaja kana ya ce "Um to tana da masifa tsiwar tsiya ce da ita." dariya tayi sosai tare da tafa hannu ta ce "Masifa haÉ—e da tsiwa kuma, a'a kada kayi wa kanwa ta fin tsayi." shiko murmushi yayi yana faÉ—in "Allah idan ta fara tsiwa sai kin sha mamaki." dariyar ta kuma ta ce "Zata amin ce kai dai je ka latsa ta kuma ka gani in sha Allahu zata amin ce, wata mace ce zataki tayin ka duk haÉ—uwar ta da dukiyar ta kuwa, ai mijin nawa da farin jinin sa aka halitto sa, shiyasa ma har gida ake kawo masa hari, wannan bazawarar taka ma jiya ta zo." dariya duk kanin su suka fashe da shi, zillo tayi gefe ganin yami ko hannu yana kokarin ruko ta, tasan sarai baya so tari yi masa maganar ire-iren waÉ—an nan matan da suke kawo masa hari. janyo ta yayi jikin sa ya rungume yana faÉ—in "Zakiyi baya ni." dariyar take tana daÉ—a shige wa cikin jikin sa. Kissing yashiga ai ka mata yana faÉ—in. "Hakika nayi dace da mace ta gari Æ´ar uwa ta jini kawa kuma abokiyar shawara, tabbas duk wan da yasa mi mata kamar ki yagama more yaruwar sa har gaba da abadan, ke matar aljanna ce insha Allahu da yar dar Allah zamu shiga aljanna ni da ke da kafafun mu." Baki ta turo gaba ta ce "To HAMDAH fa?." ya ce "To har da ita." mumushi tayi tare da daÉ—a rungume shi ta ce "In sha Allahu kuwa Allah ya tabbatar mana." ya am sa da amee. nan suka shiga nuna wa junan su tsantsar kauna da soyayya in da zancen ya sauya suka lula duniyar ma'aurata... Wane ne AHMAD?......! Mommyn Twins ce 11 Ahmad Tijjani Sabil shine cikakkoen sunan sa, mahaifinsa Alhaji Tijjani Sabil shahararren É—an kasuwa ne wan da ya jone da siyasa,yayi suna ya shahara a kaf faÉ—in Nigeria har ma da kasashen ketare, mutum ne adali mai gasjiya da rukon amana da son jama'a, yana da taimako matuka musamman ga nakasa dashi. matan sa biyu Hajiya Karima da Hajiya Harira. Hajiya Karima itace uwar gida shekarun su biyar da ita Allah bai sabu haihuwa ba, bayan shekaru biyar É—in yakaro aure in da ya auro Hajiya Hariri, cikin yar da da buwayar Allah tana shiga Allah yabata ciki. hankalin Hajiya Karima yayi masifar tashi, sai dai bata nuna wa a fili Æ´ar kasa take yi dan ta iya makirci, a fili kam nunawa take tana son cikin sosai. bayan wata tara Hajiya Harira ta haifo É—an ta namiji yaci suka Ahmad. Ahmad yatashi cikin gata da soyayya, tun daga kan sa Allah bai sake basu haihuwa ba. Ahmad É—a É—aya tilo ga Alhaji Tijjani Sabil, yayi karatun sa na primary da secondary a nan kasa Nigeria in da daga nan Alhaji Tijjani Sabil yaÉ—aga sa daga nan ya millashi kasashen ketare acan ya kammala karatun sa in da ya dawo Nigeria da sakamako mai kyau. dawowar Ahmad Nigeria da wata É—aya aka É—aura musu aure da Æ´ar uwar sa, wato yarin yar kanin mahaifinsa, Rasheedat, wan da dama can suna soyayya tun kafin ya bar Nigeria, a gidan su ta tashi shakuwa ce mai karfi sakanin su wacce har takai ga haifar da sosayya, yabar Æ™asa Nigeria da alkawarin aure sakanin su, dan haka yana dawowa batare da É“ata lokaci ba aka É—aura musu aure tare da gaggaru min biki, irin namasu akwai. Ahmad da amaryasa Rasheedat zama suke na amana da sansar kauna da soyayya da tarairayar junan su, basa kaunar abun da zasuyi ya É“atawa É—ayan su rai, babu wan da yake É“oyewa wanin sa sirrin sa, yar da da amin ta da suke yi wa junan su, har ya kai ga suka lankayawa junan su suna, in da Ahmad yake kiran ta da kawa dan acewar sa bashi da kawa kuma aminiyar da ya wuce ita. ita ce murfin rufe sirrin sa itace sirrin sa ma gaba É—aya. Ita kuma take kiran sa da aboki dan kuwa bata da wan da ya fishi, shine kawa kuma aminin ta. yan da suke gudanar da rayuwar su gwanin ban sha'awa. bayan wasu shekaru da auren su mahaifinsa sa wato Alhaji Tijjani Sabil yayi hasarin mota a hanyar sa na zuwa airport in da zai tafi kasar waje domin gudanar da wasu kasuwancin sa, nan take Allah ya karÉ“i rayuwar sa. Bayan rasuwar sa da shekaru biyu Hajiya Hariri wato mahaifiyar Ahmad ita ma ta rasu, sakamakon ciwon zuciyar da ya kamata bayan rasuwar mijin ta da yayi faraÉ—É—aya batare da ciwo ba. Ahmad yashiga tashin hankali rashin uwa da uba daga karshe ya fawwalawa Allah komai. Bayan rasuwar mahaifansa duk kanin ragamar dukiyar mahaifinsa da kaddarorin sa yadawo karkashin kulawar sa, shiyake kula da komai sakanin dukiyar sa da kuma dukiyar mahaifinsa. Shekaran su 8 kenan da aure Allah bai basu haihuwa ba, ko dai-dai da rana É—aya Ahmad bai taÉ“a sawa kan sa damuwa kan rashin haihuwar su ba, ya san cewa Allah ne bai kawo lokaci ba, shi yake rarrashin Rasheedat a duk san ta nuna damuwar ta kan rashin haihuwar nasu. yakan yi mata tuni kan cewa Allah ne mai badawa kuma bai mance da su ba lokaci ne dai baiyi ba. Ahmad mutum ne mai son yara duk da kasan cewar sa mutum mai son yara, bai taÉ“a tunanin kara aure wai ko dun zai sami Æ´aÆ´a ba. a duk in da yara suke zakaga ya na yawan ziyar tar gurin, kamar makarantun yara da gidan marayu, ko tafiya yake idan yaga yara sai ya tsaya ya nimi yayi musu wasa da kuma kyauta, shi yasa yawan cin taimakon sa tafi yawa kan yara da gajiyayyu, sai dai masu karfin ma bai barsu ba. Ahmad yayi suna a duk faÉ—in Nigeria tai makon sa yazaga ko ina. (Wannan kenan kaÉ—an daga cikin labarin Ahmad)â˜? A can cikin garin Bauchi Ummi Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela Nusaiba ne zaune cikin parlour'n Ummi, suna ta hira, kamar yadda suka saba a kowani makon karshen wata suna kawo wa iyayen su ziyara. suna tare cikin parlour suna ta hira, Fauzan ne yafito daga cikin bedroom É—in Ummi hannun sa na bayan sa da alama wani abun yake É“oye wa. Aunty Rafee'at ta dube shi tana faÉ—in "Autar Ummi me kake yi ne cikin É—akin ka É“ata shiru kamar baka nan?." "La wayar ki Aunty Rafee'at ya É—auka yaje ya É“oye yake yin Game da shi." Nusaiba ta faÉ—a tana rike haÉ“a da yin sama da wuya tana leka abun da yake É“oyewa bayan shi. harara ya dalla mata tare da faÉ—in "To haÉ—el ina ga wayar Aunty Rafee'at É—in can kan hannun kuje ra." huf Nusaiba ta mike dan son ganin abun da yake É“oye wan, ta bayan sa tazo ta fizge abun da ke hannun san tana faÉ—in "Ai sai naga abun da kake É“oye wan in ma abu na ne sai ka bani." rikewa yayi da karfi bata sami damar kwace wa ba ya ce "Dalla masa can idan kika yaga fa." "La Fauzan mu gani a ina ka samu." Nusaiba ta faÉ—a tana mika hannu ya bata abun da ke hannun sa, kusa da Aunty Rafee'at ya zauna in da dama nan yake zaune É—azu kafin ya tashi ya shige wani É—akin dake gefe a nan cikin parlour'n. gaba ki É—ayan su suka maida kallon su gare shi kana kamar haÉ—in baki Ummi Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Suka ce "A ina ka sami hotunan nan?." da sauri Aunty Rafee'at ta karÉ“i wasu daga cikin hotunan in da Aunty Jaleela ita ma ta karÉ“i sauran, nan take annurin fuskokin su ya É—auke, damuwa hade da É—in bin kewar wacce ke cikin hoton yadirar musu lokaci guda. a É“angaren Ummi kuwa kasa iya furta komai tayi gaba É—aya jikin ta yayi sanyi, É—an kuzarin da ke tattare da ita ya kauce. Fauzan ya ce "A É—akin da aka zuba kayan Aunty HAMDAH na samu cikin akwatin ta." "Allah sarki HAMDAH dube ta kamar a kirata ta amsa." cewar Aunty Rafee'at tana nuno wa Aunty Jaleela É—aya daga cikin hoton HAMDAH da suke hannun ta. karÉ“ar hoton tayi tana duba yayin da idanun ta suka kawo Æ™walla. wani hoton ta Aunty Rafee'at ta zubawa ido nan take sai ga hawaye shar a idon ta, murmushi tayi yayin da Æ™walla ke cigaba da zuba a idon ta, kana ta É—ago hoton ta na faÉ—in "Kaga Æ´ar gidan Inna an sha gayu, Jaleela kin tuna hoton nan?." Amsar hoton tayi ta ce "Wannan hoton kamar shine wan da ranar da mukaje Dass muka samu taje takar É“o shi nan ko?." dariya Aunty Rafee'at tayi yayin da Æ™walla ke cigaba da zuba a idon ta tace "Ƙwarai shi ne taci Æ™walliyar ta Inna'r ta ta bata kuÉ—i taje ta É—auki hoto, ta kawo kikayi ta kushe wa har Inna ta ce mu tattara mu koma in da muka fito, tun da tsiya zamu kawo mata gida, kin san Inna da HAMDAH, Allah sarki Inna Allah yayi miki rahama." Aunty Jaleela tayi murmushi tare da share wasu zafafan hayen da suka zubo mata ta ce "Ai ita ta fara taÉ“o ni wai naga hancin ta ashe dama haka yake ko Ya SALEEM É—in da ake cewa hancin su iri É—aya nata yafi nashi Æ™yau, in duba na gani ta fini Æ™yau." "Ke dai baki da hakuri HAMDAH kuma zolaya." cewar Aunty Rafee'at tana murmushi. ta ce "Allah babu waninnan Aunty Rafee'at kin san kakar ta ai bata ganin laifin ta yarin yar nan ta raina ni kamar ni wata sa'ar ta bacin na bata shekaru da yawa, ko Ummi?." ta karasa maganar tana duban Ummi dake zaune shiru. Ummi ko kai ta jinjina tare da mai da hawayen da suka ciko idon ta kana ta ce "Ganin ta ma har tayi miki rashin kunyar ai abun daÉ—i ne." kaf parlour'n yayi tsit yayin da zuciyoyin su ke kuna tunani da kewar HAMDAH yadawo musu sabo fil a zukatan su hannu Ummi ta kai ta share wasu zafafan hawaye tana faÉ—in "Ko wani hali take ciki ko a muce ko a raye Allah kaÉ—ai ya barwa kan sa sani." Sallama Abba da yanzu shigowar sa yayi, duk babu wan da ya amsa masa, har ya karaso cikin parlour'n ya zauna babu wan da ya lura da shigo war sa, ya fahimci duk kanin su hankalin su baya tare da su, yana zama kuwa dai-dai lokacin Ummi take faÉ—in, kalmar ta na karshe. shiru yaÉ—an yi yayin da yanayin sa yasau ya. gyaran murya Abba yayi, sai a lokacin duk kanin su suka juyo in da yake, nan suka shiga yi masa sannu da dawowa,kana ya mike jiki ba Æ™wari yayi cikin bedroom É—in sa... A can cikin unguwar G.R.A kuwa Na'ima na hango da kawar ta Raliya zaune cikin bedroom É—in Na'aima, daya daga cikin ma'aikatan gidan ne tayi sallama bakin kofar É—akin,suka ce ta shigo. ta shigo rike da yaro a hannun ta wan da akalla zai iya kai wa wata 11 zuwa shekara É—aya, baki Raliya ta washe tana faÉ—in "Kawo min shi nan kaga magajin gida É—a ga Abdallah Idris Abdallah in kiya SALEEM, kaga Irfan É—an gidan SALEEM sai girma yake." mika mata shi ta yi ita kuma tayi waje. dariya Na'ima tayi ta ce "Kai aminiya wannan kirari haka har kinsa naji wani karin da É—i." zama Raliya ta gyara kana ta dubi aminiyar nata ta ce "Sha kurumin ki kiji daÉ—in ki wata rana kece ke rike da ragamar dukiyar SALEEM." tafawa sukayi tare da shekewa da dariya Na'ima tace "Kamar yan zu kuwa, ko yanzu ma na fara jin kamshin su." wani dariyar suka kuma shekewa da shi. kana Raliya ta dubi É—an tana faÉ—in "Wai har yanzu bai fara tafiya bane duk uban kayan in ganta lafiyar da ake tafka mishin nan?." "Sati biyu daya wuce yafara É—an takawa, ai kam yana yana ci da shan abubuwan guna jiki dan duk fitan da SALEEM zai ya idan zai dawo sai ya shigo da wani abun." Raliya ta É—ago yaron tana dudduba jikin sa tare da faÉ—in "Ai kuwa dubi jikin sa kamar É—an turawa luwai-luwai da shi sai sheki yake." shiru sukayi da maganar nasu jin an turo kofar, Ya SALEEM ne ya shigo da sallama ai kuwa yaron najin muryar sa ya fara tsalle yana mika hannu, daga bakin kofar ya tsaya lai dar dake rike a hannunsa ya aje nan bakin kofar, Raliya ta gaishe sa kai a kasa kamar mutumi yar kwarai, a takai ce ya amsa mata gaisuwar nata batare da ya dube ta ba, Na'ima ta mike tare da karÉ“ar Irfan tana faÉ—in "Oh ji yaro daga ganin uban sa yaka ma murna wai fa gurin ka yake son zuwa." tayi maganar tana nufo shi, kafin ta iso in da yake yajuya yayi waje. bin bayan sa tayi tana faÉ—in "My SALEEM barka da dawowa." "Yau wa." yafaÉ—a a takai ce tare da nufar side É—in sa tabi bayan sa. yana shiga bedroom É—in sa, wayoyin sa ya zuba su kan beside kana yashiga tuÉ“e kayan jikin sa. in da yake ta karaso cike da muryar kirsa ta ce "My SALEEM tun É—azu Irfan yake ta murnar ganin ka baka ganshi bane?." bai yi magana ba sai da ya karasa tuÉ“e rigar jikin sa kana ya mika hannu ya karÉ“i yaron, shiko sai washe baki yake, murmushi yayi masa tare da lakace kumatun sa kana ya ce "Hy ykk." baki yaron yakuma washewa. sai ya mika mata shi kana ya cigaba da tuÉ“e kayan jikin sa, yarage daga shi sai boxes kana ya wuce bathroom. baki ta taÉ“e ta gyara rukon yaron tayi waje, tana shiga É—akin ta Raliya ta dube ta ta ce "Ya naga kin dawo da shi bazaki bar sa gun uban sa suzau na ba." baki ta taÉ“e tana zama bakin gado, ta ce "Ai wannan uban nasa murÉ—aÉ—É—en uba ne ke bakiga shigo war sa da nake masa magana juya wa yayi ya fita batare da yace ko mai ba, da ace agaban wasu yayi min ai da ya dizgani dan ma Allah ya taimaka a gaban ki ne." "Wai kina so ki ce min baya karÉ“ar sa ne ko me?." "A'a yana karÉ“ar sa har ma yayi masa wasa ko kwanakin can ma dayayi ciwo yake hanani bacci É—aukar sa nake da daddare na kai masa shi su kwana, yana yi masa wasa amma yan da yake masan bai min ba, baya nuna rawan jiki irin wan da uba yake nuna wa kan É—an sa musamman idan yaro yana karami kamar shi É—in nan, wani lokaci har nayi tunanin na nime ki muje gurin boka sai kuma na shashantar da abun, dan nasan miskilanci a jinin sa yake, in baki mance ba boka ma haka yace mana, shi yasa ma kawai na dai na damuwa." Numfashi Raliya ta sauke ta ce "Har naji sanyi in dai wannan ne kawai ai bawata matsala bace, adai juri zuwa rafi, ina labarin kuÉ—in da Dr Mukhtar ya nima lokacin jinyar Irfan É—i, kai Dr Mukhtar bashi da mutunci in dai a kan kuÉ—i ne to komai ma zai iya." matso wa kusa da ita Na'ima tayi, kana ta waiga gefe da gefen ta sannan cikin kasa da murya ta ce "Ai baki sani ba shekaran jiya ya tura masa da 500k kan wancan 500k É—in nan yanzu jibi zamo koma asibitin na basa kason sa na am so nawa, daga nan kuma yakuma tsara yan da wani kuÉ—in zai kuma zuwa." dariya Raliya tayi suka tafa tace "Kai aminiya daga haifan yaron nan zuwa yanzu da ko shekara bai cika ba an tatse sa abun da ya fi 5 Miliyan." fuska Na'ima ta yamusa tare da faÉ—in "Um ai ma dai wani wahalar banza nake, kuÉ—in nan namune ni da magajin sa, da na karÉ“i wannan bazan kuma karÉ“ar wani ba, zan karÉ“e su ne a dunkule da zaran lokaci yayi." Raliya zatayi magana wayar ta ta fara ring, tsaki taja ganin mai kiran nata tare da tura wayan gife. Na'ima ta dube ta ta ce "Ya dai aminiya ba tsohon kamu kenan." ta ce "Rabu da jarabebbe sai azabar jarabar tsiya baya bada kuÉ—in arziki, ranar kusan kwana yayi a kaina yaÉ—au naira dubu 50k yabani, shine yau ma yake son muje mu kwana, ina zan iya wannan tsiyar sabon Alhajin dana yi yanzu haka mun shirya tafiya kwana da shi, account É—i na yayi nauyi yaushe zan tsaya kula irin su kananun Æ´an iska, tsabar jarabar sa wai baya gane yin harka da roba wai zai cire nace wlh kana cire wa zan fita na tafi, na isa ai na san waÉ—an da nake harka da su ba condom." dariya Na'ima tayi tana faÉ—in "Ai da kun je shima an gwada lafiyar sa sai kuce gaba da fafata wa." "Allah ya sawake min ai bana harka da talaka irin sa dubu 50k fa, ka kwana a kai na kaÉ—au naira dubu 50k ka bani kamar na zama shegiya." wani kiran da ya kuma shigo wa wayar ta ce ya katse musu hirar É—aga wayar tayi rai É“ace dan a tunanin ta wannan wan da taki É—aukar kiran sa shi yakuma kiran ta yanzu. murmushi ta sake ganin ba shi bane wan da take sumayen jin kiran sa ne, ta É—aga kiran cikin kwarewa da iya bari ki ta kara wayar a kunne. mike wa tayi tana faÉ—in "Okay I'm coming." sai ta sauke wayar a kunne, ta dubi Na'ima ta É—auki jakar ta tana faÉ—in "To alhaji na ya zo bari na tafi sai mun yi waya." tayi mata sallama ta tafi. Abujaâ˜? Yau tun tashi na nake jin jikina ba daÉ—i da alama zazzaÉ“i ne ke son rufe ni, a daddafe nayi al'walan sallar a zahar nazo na gabatar da Sallah. ina idar wa na haye gado naja bargo na rufe jikina, kasan cewar yau Lahadi babu school su Naseem suna gida, so nake na samu na É—an rumtsa kafin su shigo, ko zan samu baccin ya saukar min da zazzabin, dan bazan iya shan masa magani ba kwata-kwata bazan iya ba dan zan iya yin amai. kwanciya ta na gyara ina jan hanci na daya toshe, nasan zazzaÉ“in mura ne na ruwan sanyin dana yi ta shiga, kwana biyu ana sanyi ruwan cikin swimming pool yana yin sanyi sosai kuma haka nake shiga ciki. idanuna na lumshe a hankali ina jin kaina na tsara min, so nake nayi bacci ko zan samu zazzaÉ“in yaÉ—an sauka, batare da nasha magani ba. Nasmah ce ta turo kofa da gudu ta haye gadon ta faÉ—a jikina, ta yaye blanket É—in dana rufe jiki na har zuwa kai na, ta leko fuska ta tana faÉ—in "Mommy kina da lafiya ne?." murmushi nayi tare da gyaÉ—a mata kai, da jin kalar hausan nata, idan zata ce mutum bashi da lafiya sai tace wai yana da lafiya ne. fuska ta Æ™waÉ“e tare da mara baki ta ce "Nima ina da lafiya." tayi maganar tana shige wa cikin blanket É—in. kwanciyar ta na gyara nayi mata pillow da hannu na, na dube ta da murmushi ganin yan da take ta wani mammatse ido tana cuno É—an karamin bakin ta gaba wai ita a dole bata da lafiya. na ce "Me ke yi miki cewo?." kyakkyafta ido tayi takuma cuno É—an karamin bakin nata gaba kana ta nuna kan ta da yatsar ta. na ce "Kan ki ke yi miki ciwon?." ta ce "Eh cine yake min jafi." shafa kan nata nayi tare da faÉ—in "Sannu bari nasa Dr yazo ya baki magani ko zai bari." kai ta gyaÉ—a, mumrmushi na kuma ganin ta mai da idanun ta ta lumshi nasan bacci take ji sai na ja blanket É—in na gyara rufe mata jikin ta, ina mai cigaba da kallon fuskar ta da murmushi wato adole tun da nima bani da lafiya ita ma bata da shi, oh Nasmah kenan iyayen manyan ce. a hankali nima na mai da idanuna na lumshe babu jimawa kuwa bacci yayi awon gaba da ni. Da misalin karfe 4:30Pm na farka na É—an ji daÉ—in jiki na sabo da baccin da nayi amma dai hanci na na nan a toshe ciwon kan ma haÆ™a. ahankali nayi Æ™oÆ™arin É—aga kan Nasmah a hannun na na maida shi kan pillow sai ta farka, sai na É—ago ta nayi da ita bayi wanka nayi mata kana nafito da ita, ni ma na koma nayi. bayan na idar da sallar la'asar na saka kaya itama na saka mata, kana na ruko hannun ta muka fito, kasa muka sauka muna shiga cikin parlour'n Naseem da Faty suka shigo, zama nayi ina faÉ—in "Gara da bakuzo tun É—azu ba sai da muka gama baccin mu." dariya Faty tayi tare da faÉ—in "Kai Adda HAMDAH ai har munfito É—azu zamu zo, sai kuma muka wuce gun lilo, da mun hana ku bacci." murmushi nayi na ce "Gara da kuka tsaya can gun lelon ai da yanzu kun hana mu yin bacci ku bakuyi ba mu ku hana mu yi." Talatu data dire tray'n abinci saman kan table É—in gaban mu, ta ce "Barkan ku da hutawa, uban É—aki na muje kayi wanka naga gimbiya kam da wankan ta ta sauko, kai ne ka tsaya gun lilo ko ka É—ebo rana." tayi maganar tana ruko hannun Naseem. sukayi cikin bedroom... Washegari ya kasance ranar Monday bayan su Naseem sun tafi makaranta bacci na koma, cikin bacci naji wayata tana ring, idanuna a rufe na mika hannu na janyo wayar, na É—ago shi tare da buÉ—e idanu na kan shi, ganin sunan daya bayyana kan screen É—in wayar. yasani ware idanuna sosai, sunan shugaban makarantar su Naseem ne. nayi saurin É—aga kiran tare da kai wayar kunne, muryar sa na jiyo hankali tashe yana faÉ—in "Madam gamu a asibiti Nasmah ta." É—ip wayar ta yanke cikin tsananin firgici na mike zaune nan da nan na nimi baccin da nake ji É—in na rasa, hannunna na É“ari na dan na number sa na mai da masa kiran, yayin da nake jin kirji na na dukan uku-uku. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." na furta a fili, wayar tayi ta ring har ta kusa yanke wa kafin aka É—aga da sauri cikin matukar firgici da tashin hankali na ce "Ina Nasmah take me ya same ta?!." ya ce "Gata nan kwance ta......! Mommyn Twins ce 12 Da sauri cikin matukar tashin hankali tun kan ya karasa abun da zai faÉ—a na ce "Tamutu tamutu ko?!!." nayi maganar hankali a mugun tashe dan nagama tsinkewa da yan da naji yake maganar. ya ce "A'a Madam ba mutuwa tayi ba, dama bata da lafiya ne?, tun zuwan su School É—in Aunty'n su tace taga yanayin ta kamar batajin daÉ—i, shine ta tambaye ta sai tace mata wai kan ta keyi mata zafi, to tafita taje ta É—auko magani a office kenan ta dawo ta samu tana rike da kanta tana kuka tana faÉ—in kanta zafi, kan tayi aune ma ta faÉ—i kasa a sume, tun É—azu muna asibiti ban so kira na sanar ba sai ta farfaÉ—o amma har yanzu likitoci sun kasa shawo kan ta." "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un wlh lafiyar ta lau ta bar gida." na furta da karfi yayin da jikina ke cirawa cikin azama na duro a gadon wayar na kare a kunnena ina tambayar sa wani asibiti ne, yana faÉ—a min nakashe wayar batare da na tsaya sauraran abun da yake cigaba da faÉ—a ba. wardrobe na buÉ—e na janyo mayafi na takalmi mara tudu na saka da sauri nafita na nufi Æ™asa, bibbiyu nake haÉ—a steps,ina sauka na nufi kofa har ina haÉ—awa da sassarfa. su Talatu suna zaune cukin parlour'n da sauri suka mike ganin yanda na sauko a firgice, tambaya ta me ke faruwa suka shiga yi suna biyo ni a baya, tuni nayi waje ban tsaya basu amsa ba, har parking lot suka bini, suna tambayar abun da ya faru. sai a lokacin na ce da su "Nasmah ce ke asibiti asume." salati suka shiga yi suna tambayar garin yaya. wan nan karon ban tsaya basu amsa ba dan ji nake tsayuwa basu amsa ma É“ata lokaci ne. kan kace me sabbin Security É—in da aka zuba cikin gidan sun iso in da muke, ganin yan da su Talatu suketa rafka salati, suma duk tambayar da suke ban tsaya basu amsa ba, su Talatu ne suka sanar musu abun da ke faruwa. Yakubu nashiga kwaÉ—awa kira, da sauri haÉ—e da gudu yafito daga cikin É—akin su, da sauri na shige cikin mota, yana ganin haka ya koma É—akin da sauri ya fito rike da makullin motar cikin hanzarin yashige motar. cikin matukar da muwa da rawar murya nace "Yakubu kayi sauri ko ka bani key É—in motar ni naja." key yayi wa motar tare da figar ta aguje, da gudu mai gadi ya buÉ—e get muka fita a gidan, sai da muka haura titi kafin yake tambaya ta in da zamu nafaÉ—a masa sunan asibitin. duk gudun da Yakubu yake gani nake kamar bayayi asibitin tayi min nisa. Number da aka kira ni da shi aka sanar min da tana asibitin na kuma kira wayar tayi ta ring ba'a É—aga ba, kuka ne naji ya zo min nayi saurin toshe baki na a raina nake faÉ—in "Shike nan ta mutu." kokarin mai da kiran nake dai-dai nan najiyo muryar Yakubu yana faÉ—in "Hajiya mun iso." da sauri na É—ago dan ban san har mun iso ba. da sauri na buÉ—e motar na fito batare da na jira faÉ—in da yake bari ya zo ya buÉ—e min motar ba. da sauri haÉ—e da sassarfa nayi cikin asibitin, a kofar shiga cikin parlour'n asibitin na haÉ—u da Aunty'n su Nasmah tana kokarin fitowa cikin sauri take tafiya da ka ganta gaba É—aya hankalin ta a tashe yake. tana gani na ta juya da sauri tana faÉ—in "Madam ta farfaÉ—o amma tana ta kuka." da sauri nabi bayan ta ina faÉ—in "Ina take." tun da ga cikin parlour'n nake jiyo kukan ta, da gudu nanufi kofar room É—in da nake jiyo kukan ta ciki, wasu daga cikin ma'aikata asibitin sukayi yunkurin dakatar da ni, ban ko saurare su ba na tura kofar na sa kai ciki. ina ji Yakubu daya biyo ni yana sanar musu da ko ni waye. Likitoci har guda uku a tsaye a kan ta suna rirrike da ita sai ihu take tana bige-bige, da gudu na isa in da take na kusa sakanin su na rungume ta,sai kawai nima na fashe da kuka ina faÉ—in "Nasmah me ya same ki, me ya same ki Nasmah?!!." kuka sosai na ke ina rungume da ita, itama kukan take tana ta fisge-fisgen nan kamar wacce bata cikin gayyacin ta. Turo kofar aka yi da karfi yana gaba wani na biye da shi. in da muke suka karaso da sauri, wan da ke biye da shi É—in ya dubi likitocin da ke cikin É—akin yana faÉ—in "Wai har yanzu bakuyi wani abu a kai ba?." cike da girmamawa sukace "Sir muna kai kenan yanzu ta farfaÉ—o so taki tsayuwa Muna kan kokari ke nan mu shawo kan matsalar, ruwa za'a saka mata sai dai taki tsayuwa sau uku ana samun jijiya sai ta gauce ya É“ata, zamu nima ta kafan ta ko kai ne a saka mata, na hannayen ta kam duka mun rasa su." cikin faÉ—a Dr da suka shigo tare da Ahmad da alama shine babban su ya ce "Shirmen banza sai kace ba ai kin ku ba." sai kuma ya dubi Ahmad ya ce "Sorry Sir ko mai zai dai-dai ta insha Allah." kai kawai Ahmad ya jinjina ya É—an maso in da nake rungume da ita ya ce "To meye amfanin kukan, kin rungume ta kina kuka ita tanayi, to da wanne zata ji da ciwon da ke damin ta ko da wannan kukan naki?." hannu ya mika ya É“amÉ“are ta a jikina, sake masa ita nayi dan na rasa abun yi guda É—aya ganin yanayin nata yakuma jefani cikin kiÉ—i ma, da firgici da tashin hankali, ya É—ago ta ya saka ta a kafaÉ—ar sa ya na faÉ—in "Kun É“ula ta da yawa dubi yan da hannayen ta suka fara kumbura." "Sorry Sir ta ki tsayuwa ne." É—aya daga cikin likitocin yafa É—a. tsaki yaja kana ya ce "Me yasa tun kan ta farfaÉ—o baku ni mi jijiyar ba, sai da ta farka zakuyi ta É“ula ta." "Sorri Sir hakan bazai yiwu ba do le sai ta farfaÉ—o." tsaki yakuma ya, yana jijjiga ta da bubbuga bayan ta, yana faÉ—in "Shiiit ya isa sorry baby yi hakuri kin ji sorry sorry." maganar yake daf kunnen ta yana ci gaba da jijjiga ta da bubbuga bayan ta. baya nayi, najin gida na da jikin garu-bango, ina mai cigaba da kukan cikin yin kasa da sauti. Dr da suka shigo da shi ya ya nufi kofa yana faÉ—in "I'm coming Sir." sai yayi waje sauran likitocin suka bi bayan sa. bai yi magana ba sai ci gaba da jijjiga ta da hura mata iskar bakin sa cikin kunne yake, a hankali kukan nata yarika raguwa, sai ajiyar zuciyar da take sauke wa a kai a kai, har tayi shiru tana mai cigaba da sauke ajiyar zuciya. jim kaÉ—an likitan ya dawo wannan karon su biyu suka shigo, yana gaba É—aya daga cikin waÉ—an da É—azu suke kan ta na biye da shi rike da wasu kayakin amfani irin na ma'aikatan lafiya. Dr ya dubi Ahmad da murmushi yana faÉ—in "Ikon Allah abun da mu likitoci muka kasa yi gashi uba yayi wa É—iyar sa, baby da ma so kike sai Daddy'n ki yazo kafin ki bamu damar yin ai kin mu ko." yayi maganar yana leko fuskar Nasmah da ke lumshe da alama bacci ke son É—aukar ta. murmushi Ahmad yayi yana shafa kanta, kana ya ce "Yan zu zaku iya yi mata abun da ya kamata." Dr ya ce "Okay." ya mika hannu ya karÉ“e ta yana kokarin kwantar da ita kan gado. ai ko ta buÉ—e ido tare da sakin kuka. da sauri Ahmad ya É—auke ta yashiga jijjiga yana faÉ—in "Shiiit Nasmah ya isa yi shiru jinki." ai ko tayi tsitt,har kuma lokacin ida nunta suna lumshe. zama yayi bakin gadon kana a hankali ya kwantar da ita yana É—an jijjiga ta da faÉ—in "Sorry kwanta a saka miki magani kiji sauki ko,babu zafi yanzu a gama miki mu tafi hawa doki." alama yayi wa Dr da ya soma ai kin sa, yakuma ce masa yabita a hankali, kana shi kuma yarika shafa kanta yana yi mata magana a hankali daf da kunnen ta. a hankali likitan ya soma gudanar da ai kin sa irin na kwararren likita. bugun fari ya samo jijiya a hannun ta na dama, batare da É“ata lokaci ba ya É—aura mata ruwa mai É—auke magunguna masu karfi da inganci. nan da nan cikin sakanni kalilan bacci yayi gaba da ita. bayan likitan yagama duk abun da ya kamata ya dubi Ahmad yana faÉ—in "Allah ya sawaka in sha Allah ko mai zaiyi normal idan ta farka." ya an sa da amin kana likitocin suka fita. Numfashi na sauke mai sauti san da ido na ya sauka kan Nasmah da ke bacci tana sauke numfashi a hankali, idanuna na rumtse tare da jan sheshsheka cikin kukan da nake har lokacin, sai dai zuwa yanzu kukan nawa a hankali yake fita. cikin zuciya ta nake yiwa Ubangiji godiya ganin ta sami bacci. har lokacin yana sunkuye a kanta yana shafa kanta yayin da É—aya hannun sa ke rike da hannun ta da akayi mata karin ruwa. maganar sa najiyo yasani buÉ—e idona a kan sa. "Ke kin ishe mu da wannan koke-koken na ki, kifita waje kije kiyi sa a can kin dame mu, ko so kike ki tashe ta da Wannan kukan naki mara amfani, tun tuni yarin ya tana tare da ciwo kin barta da shi a jikin ta har sai da yayi (C), ke baki da wayon sanin yaro bashi da lafiya ne, a hakan ne kike cewa ke zaki iyar musu yaushe kikayi wayon kula da kanki bare ki kula da su." baki na murguÉ—a cikin zubda Æ™walla na buÉ—i baki zanyi magana, sai wayata ta fara ring, dago wayar nayi ina mai share hawaye ganin Bappa ke kiran, sai nayi picking call É—in na kara wayar a kunne, daga cikin wayar Bappa ke faÉ—in "HAMDAH wani asibiti ne?." ina faÉ—a masa sunan asibitin ya kashe wayar. Zama nayi kan kujerar da ke gefe na jin kafata ta gaji sosai, ina mai ai ka masa da harara ina ci gaba da murguÉ—a masa baki. magana ya soma yi yayin da idanun sa ke kan Nasmah da take ta baccin. "Wayon ki a iya nan kaÉ—ai ya tsaya, sabo da ke baki da wayon magan ce naki shine ita ma zaki barta da shi ko, dubi idon ki ke kan ki ma baki da lafiya amma baki da wayon da zaki iya magan ce ciwon naki." a fusace cike da tsiwa nace "Idan kai ke raba wayon bana so karike shi, har abada kada nayi wayo." nayi maganar ne cike da jin haushi, ban san meye damuwar sa na jifana da kalmar rashin wayo a koda yaushe a duk san da muka haÉ—u da shi ba. yabi ya ishe ni da wasu maganganu ya barni naji da damuwar ciwon Æ´ata. fuskar Nasmah ya shafa tare da sakin murmushi har sai da dimple É—in fuskar sa ya bayyana. baki na taÉ“e tare da kawar da kaina gefe, dan zuwa yanzu hankali na yafara kwanciya, bai kuma magana ba sai zaman sa daya gyara ya daÉ—a gyara rukon hannun Nasmah da ke hannunsa sakama kon É—an zaburan da tayi cikin bacci. ni ma ido na na mai da kan waya ina É—an lallatsawa. Tun daga can waje nake jiyo muryar su Bappa ina kokarin mike wa suka turo kofar, Bappa na gaba Inna Wuro Faty Yakubu da Sule direban su Bappa, suka shigo. hankali tashe Bappa yake faÉ—in "Subhanalillahi garin yaya me ya same ta haka?." dai-dai nan suka karaso bakin gadon da Nasmah take kwance. Bappa ya leko fuskar ta yana cigaba da faÉ—in "Amma ta farfaÉ—o ko." Ahmad ya ce "Eh ta farfaÉ—o yan zu dai bacci take." "Masha Allah, kaji ikon Allah ko yarin ya tabar gida lafiya sai kuma ga ciwo, kai sannu Nasmah." Inna Wuro ta faÉ—a tana shafa kanta. Bappa ya dubi Ahmad yana faÉ—in "Sannu Ahmad sannu fa da kokari Allah ya saka da alheri." murmushi yayi kana suka shiga gaisawa, bayan gaisuwa da jajen abun da yafaru Bappa ke faÉ—in "Wai haka kawai ta suma kuma me likita ya ce ke da mun ta?." Ahmad da idanun sa ke kan Nasmah dake ta baccin ta har yanzu kana ya ce "Typhoid ne har yayi mata (C) da mamaki ace wai ciwo irin haka har yayi yawa a jikin yaro irin haka ba'a sani ba, har yakai matakin da zai iya sumar da ita wai duk ba'a sani ba." Bappa ya ce "Ikon Allah amma kuwa abun da mamaki, wai da ma bata da lafiya ne HAMDAH? ko irin zazzaÉ“i a tsatstsayen nan ne take?." ya karasa maganar yana duba na. da sauri ganin yan da wannan Ahmad É—in yake taso ya mai da alhakin ciwon ta kaina. na ce "Lafiyar ta lau bata kuma zazzaÉ“i a tsatstsaye." "Kuma bata taÉ“a ce miki wani gurin ta na ciwo ba, yaro ke nan Allah sarki kuma kema baki taÉ“a lura da yanayin ta ya sauya ba." cewar Inna Wuro, tayi maganar cikin jimami da alhinin ciwon nata. "Babu wani alamar da na taÉ“a gani na ciwo tattare da ita, kuma bata taÉ“a cemin wani gurin ta na ciwo ba, in ban da shekaran jiya da nake kwance kai na na ciwo ita ma tazo ta ce min kanta na mata zafi, kuma nasan a lokacin É—in dan nima na ce kai na nayi min ciwo ne shi yasa ita ma ta faÉ—a." nakarasa maganar ina É—aga hanci sama dan ganin yan da É—an shishshigin nan keta wani girgiza kai. da sauri na mai da idanuna kan sa jin yana faÉ—in "Ashe dai ta ma faÉ—a miki bata da lafiya amma bakiyi serious a kai ba, dan ta faÉ—i kan ta na zafi lokacin da naki yake ciwo sai ya zama nata karya ne?, taya za'ayi ki fahimci hakan tun da baki da wayon sanin haka." ido na waro baki buÉ—e jin yakuma jifata da kalmar rashin wayo,wai shin wannan mutumin me yake jin kansa ne,shi ji yake yafi kowa wayo kowa yi masa kallon rashin wayo yake?. a kufule na buÉ—i baki zanyi magana, Bappa ya katse ni da faÉ—in "Ai shi yaro idan ba lura kayi da yananin saba wani É—an bashi da azancin faÉ—ar abun da ke damin sa, ko da yana jin wani gurin sa na ciwo, sai dai in kai ka gane hakan daga yanayin sa na yau da kullum, kirika lura da yanayin su tanan zaki rika fahimtar ciwon su, Allah sarki da gaske kan nata nayi mata ciwon ne sai tace yana yi mata zafi, Allah yabaki lafiya Nasmah." Amin duk aka amsa da shi, baki na tura gaba muna gaÉ—a ido dashi na murguÉ—a masa baki, wani murmushi ya sake sai da dimple É—in sa suka bayyana,ya mai da idanunsa kan Nasmah yayin da fuskarsa ke nan É—auke da murmushin nan. ido na É—an kurawa fuskar sa wan da dimple ya daÉ—a kawata shi. baki na taÉ“e ina mai É—auke idanuna a kansa... Muna nan cikin É—akin kiran sallar azahar ne yasa su Bappa fita dan zuwa masallaci, har da shi, yarage daga ni sai Inna Wuro da Faty. Inna Wuro ta shiga toilet É—in cikin É—akin ta yi al'wala tafito tace da ni naje nima nayi muje masallacin cikin asibitin muyi sallah, tun da ga Faty in muka dawo sai itama taje tayi... muna isa masallacin ana idar da sallah, su mazan suka koma ciki mukuma muka shige cikin masallacin. ko da muka idar muka koma ciki, abakin gadon na kusa da Nasmah in da É—azu yake nan yanzu ma yake zaune. zaman mu baifi da minti 20 ba akayi knocking É—in kofa, Yakubu dake tsaye ta kusa da kofar yabuÉ—e. wasu maza guda biyu suka shigo niki-niki da kayan abinci duk kanin su sanye da rigonan irin na ma'aikatar hotel. cikin girmamawa suka shiga gaida Ahmad kana suka gaida Æ´an cikin É—akin, suka dire manyan basket É—in dasuka shigo dashi, nan suka shiga zuba abinci suna mikawa kowa, da mamaki nake kallon su dan nidai a sani na ban bada umurnin kawo abinci daga wani hotel ba. maganar É—aya daga cikin mutanen naji ya na faÉ—in "Gashi hajiya." É—ago idanuna nayi daga kan wayar da nake natsawa na dube shi, plt É—in abinci yake miko min, kai na girgiza tare da faÉ—in "Nakoshi." "A'a me kikaci HAMDAH nasan tun fitar ki ba abin da kika ci." cewar Bappa yana duba na. "Bana jin yunwa." nafaÉ—a ina mai da idanuna kan wayar. "Zama da yunwa bashi da amfani wan da gashi komai yazo da sauki kici abinci itama bakiga tana baccin ta ba, sauki ce ke samuwa cikin bacci insha Allah." Inna Wuro ta ce "Insha Allahu kuwa lafiya nata kan samuwa." ni dai ban kuma cewa komai ba, plt É—in abincin suka mikawa Faty dake kusa da ni. wani É—an ma dai-dai cin basket daga cikin waÉ—an da suka shigo da su, abincin cikin sa na musamman shi suka zuba masa suka mika masa hannu ya daga tare da faÉ—in "Akarawa kowa yaci." Bappa da yakai loman abinci yahaÉ—i ye ya ce "A'a Ahmad ai wannan ma ya ishe mu maza karÉ“i ka ci wannan ya ishe mu haka ga abibci nan idan bamu koshi ba duk zamu kara, Allah ya saka da alkhairi an gode sosai Allah yakara buÉ—i." Jin yan da Bappa yake ta zuba masa godiya yasa nasan cewa shi yayi odar abincin, baki na taÉ“e a raina nake faÉ—in "Sai kace ance masa bamu ci abinci bane ko yunwa ke damin mu." wayar sa ce tayi kara yamike yafita batare da ya karÉ“i abincin ba, Bayan sa nabi da kallo "Gulma shi da yasa a kawo dan tsabar gulma shi ne yaki ci to da waya mai da mayunwata." Faty dake daf da ni ta juyo tare da faÉ—in "Adda HAMDAH me kika ce?." "A'a bada ke nake ba da wancan É—an gulmar nake." "Wafa?." ta faÉ—a tana kallon waÉ—an da suke cikin É—akin. "Ba kowa." na faÉ—a ina mai da idanuna kan waya. tun da ya fita bai dawo ba ganin ya jima sosai bai dawon ba yasa nayi tunanin ya tafi ne, gara ma ya tafin É—an shishshigi. har wajen la'asar muna nan zaune Nasmah bata farka ba zuwa lokacin kam bakin gadon na dawo na zauna. akai-akai likitoci ke zuwa duba ta, tun bayan fitar sa. ana kiran sallar la'asar su Bappa suka fita bayi Inna Wuro ta shiga ta É—auro al'wala tafito ta shinfiÉ—a sallayar da nasa Yakubu ya É—auko a mota, ina nan zaune kusa da Nasmah da har lokacin take ta kan bacci, ido na tsura mata gaba É—aya yanzu na kagu ta farka. na É—au alwashin duk likitan da yakuma zuwa zai saka wani allura cikin drip É—in dake shigan ta zan hana, dan na lura kamar shi ke da É—a sata cigaba da baccin. ban tashi ba har sai da Faty ta idar da nata sallar, kana nashiga toilet É—in room É—in bayan nayi al'wala nazo na gabatar da salla. ko da na idar ina nan zaune kan sallayar ina lazumi,da sauri na É—ago kaina jin Inna Wuro tana faÉ—in "Nasmah kin farka ne?." da sauri na mike ganin tana É—an motsa hannun ta, da sauri Inna Wuro dake gefen ta ta roko hannun nata da aka mata karin ruwa da shi take ta kokarin É—aga shi, cikin hanzarin na iso bakin gadon ina faÉ—in "Nasmah Nasmah tashi kada ki sake komawa baccin nan." a hankali ta buÉ—e idanun ta na bin cikin É—akin da kallo. sannu Inna Wuro da Faty suka shiga jera mata. É—aya hannun ta na roko da murmushi ganin idanun ta wasai naci gaba da faÉ—in "Sannu Nasmah kan naki ya dai na yi miki zafin?." fuska ta kwaÉ“e sai kuma ta fashe da kuka. "Subhanallahi yi hakuri kinji Nasmah yi shiru kinji idan kikayi kuka kan zai ci gaba da yi miki zafin fa yi shiru abin ki." Inna Wuro ta faÉ—a da alamun rarrashi. kai na gyaÉ—a tare da faÉ—in "Eh kin ji yi shiru abin ki Nasmah." sautin kukan nata takuma karawa tana ta kokarin fizge kannulan da ke hannun. da sauri ya turo kofar ya shigo , cikin hanzari ya iso bakin gadon. ta gefen da nake ya tsaya tare da ruko hannun ta da hannuna ke kai, da sauri na É—auke hannuna dan yan da ya sauke hannu nasa kan nata sai da ya taÉ“a nawa hannun. É—an matsawa nayi ganin yan da mukayi daf da juna. "Shiiit ya isa haka bar kukan nan." ya faÉ—a yana shafa kanta kana ya É—ago wayar sa ya daddanna ya kai kunnen sa "Na shigo." yayi maganar yana sauke wayar. kan ta yaci gaba da shafawa yana kuma cigaba da faÉ—in "Yi shiru bari azo a cire miki wannan abun ki huta." Cikin mintinan da basufi 3 zuwa 5 ba Dr ya shigo ya cire mata ruwan dan dama saura kaÉ—an ne ya rage, a na cire mata Ahmad ya É—ago ta ya saka ta kafaÉ—ar sa yashiga jijjiga ta har tayi shiru. bakin gadon ya zauna kana ya É—aura ta kan cinyar sa, ya dubi Faty ya ce "Fatimah haÉ—a mata tea ta sha." yayi maganar yana kallon basket É—in da ma'aikatan hotel É—in nan suka zo da shi suka tafi suka barshi a nan cikin room É—in. Faty ta ce tom. ta haÉ—o tea É—in da sauri ta mika masa, ya amsa, tare da gyara wa Nasmah zama kan kafarsa ya saka mata cup É—in a baki yana faÉ—in "Sha maza muje ki hau lilon doki daga gun kisha Chocolate ko." ai ko tabuÉ—e baki ya kafa mata cup É—in, sai da tasha fin rabi kafin ta É—aga kanta. Dr dake tsaye a gefen su yayi dariya tare da faÉ—in "Nasmah Daddy ne kaÉ—ai mai yin rarrashi a yarda ko?." Inna Wuro ta ce "Ai kam mu duk rarrashin da zamuyi sai dai ta sa mana ihu." duk sukayi dariya ban da ni da kuma shi da ya murmusa. "ÆŠan shishshigi." nayi maganar a kasan raina tare da jan guntun tsaki a fili. duk suka juyo suka kalle ni. Inna Wuro taciga da faÉ—in "Har uwar tata ma taki yar da rarrashin nata." mike wa yayi tare da sakata a kafaÉ—ar sa yasoma tafiya tare da faÉ—in "Tasan itama bata wuce rarrashin bane." yana kaiwa nan yayi waje Dr ya rufa masa baya, ido na waro tare da yin kwafa wannan mutumin sainayi maganin sa. Inna Wuro da Faty kuwa dariya sukayi. Faty ta É—auki sallayar da mukayi sallah muka nufi waje. a can farfajiyar asibitin muka iske su suna tsaye suna magana da Bappa. kafin mu karaso ya shige motar sa in da ya saka Nasmah a gefen sa yaja motar mai gadin asibitin ya buÉ—e masa get ya fita. cikin takaici haÉ—e da mamakin karfin hali irin nasa nabi bayan motar da kallo. bansan dalilin sa na son yimin shishshigi cikin rayuwa ta ba, akan wani dalilin zai tafi da ita, to ma ina zai kaita tun. maganar Bappa naji yana faÉ—in "HAMDAH muje ko." juyowa nayi sai gani nayi har kowa ya shige mota. "Bappa akan wani dalili zai tafi da ita?." ya ce "Gida zai kai ta dan taki yar da na karÉ“e ta kuma aciki ma yace min taki yarda da ku,idan ya barta zatayi ta kuka ne kuma likita ya ce ba'a so tarika kuka, sabo da ciwon kannan nata sai ya iya motsa mata, muje zamu same su a gida ma yan zu, yaron arziki mai son taimakon al'umma." da sauri na ce "Waya ce masa bukatar taimako muke." nayi maganar ina waigin hanyar da suka fita tare da murguÉ—a baki kamar yana gani na. murmushi Bappa yayi kana ya ce "Babu wan da ya ce masa ana bukatar taimako halinsa ne hakan." juyawa nayi na shige cikin mota ba tare da na kuma cewa komai. Koda muka isa gida ganin babu motar sa yasa nayi tunanin ko har ya ajiye ta ya wuce ne, da sauri nashiga ciki. Naseem da ke tare da su Zulai ya rungume ni yana yi min oyoyo. su Talatu sunayi min sannu da dawowa ya mai jiki, ban iya basu amsa ba sai tambayar su nayi "Ina Nasmah?." "Hajiya ba tana asibiti ba." cewar Zulai. kaina girgiza tare da faÉ—in "An dawo da ita gida." Talatu tace "A'a Hajiya ba'a dawo da ita ba." da sauri na juya nafita waje a sakar gida na tadda su Bappa suna kokarin wucewa part É—in su na ce "Bappa bai fa dawo da ita ba." murmushi yayi tare da faÉ—in "Zai dawo da ita je ki huta." juyawa kawai nayi badun naso ba sai dun bana so nayi masa musu. Nakai tsawon awa guda zaune cikin parlour zaman jiran dawowar ta, ganin guri ya fara rufawa magriba ta kusa sai na mike na haura sama, sai da nayi wanka na gabatar da sallar magriba kafin na sauko. nasa Zulai ta kawo min tea sai a lokacin na sa wani abu a ciki na. zuwa yanzu kam ina ji bazan iya cigaba da hakuri da sa sammanin dawo da ita ba, yunkurin mike wa nayi dan zuwa gurin Bappa, ya faÉ—a min gidan sa naje na É—auko Æ´ata. da sauri na waigo kofa jin an turo kofar parlour'n........! Mommyn Twins ce