MIJIN-TA-CE 1 NA Haj. Hafsat C. Sodangi (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) Haqqin Mallaka (m) Haj. Hafsat Sodangi Copyright© Haj. Hafsat Sodangi GODIYA Godiyata ga Allah take Subhanahu wata'ala, mai kowa mai komai, gwani kuma mai hikima wanda ya yi halitta tasa duka bibiyu, ya kuma halicci mutum da Aljan don su bautata mishi. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa, shugaban Manzanni, Manzon tsira Manzon rahama Annabin qarshe Muhammad (S.A.W) da Alayensa da Sahabbansa da waxanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar Alqiyama. SADAUKARWA Sadaukarwar littafin ta Makarantanshi ne, na kusa da na nesa na gode qwarai da kulawarku, Ubangiji ya saka muku da alheri, amin summa amin. TUKUICI Tukuicin littafin na Kabiruna ne. KABIR CHINDO SODANGI (A.T.B.U Bauchi) Haqqin Mallaka: Haqqin mallakar littafin GORO Goron naki ne Goggona HAJIYA RAKIYA BABA SANI a Bukuru  BUGAWA A COMPUTER: NAFI'U SALISU 08021225160, 07054584199 E-mailaddress:nafiusalisu47@yahoo.com Litattafan Marubuciyar: Uwar miji Naga ta kaina Wayyo duniya Rabon kwaxo.. Cikar alqawari Tabbataccen al'amari Yi wa wani Abu naka.. Nufin Allah Gani gare ka.. Kifi na ganinka... Me zamu ce da maza? Garin banza.. Biyan buqatar rai Hattara! Da kamar wuya.. Daga qin gaskiya.. Mata masu duniya Shamaki Mai uwa... Duk xaya Mata da kicin xinsu Wacece Ni? Ayi dai mu gani.. Kyautata Mai Uwa... Mijin-Tace MIJIN-TA-CE “Humaira! Humaira!! Humaira!!! Bata jin wannan kiran ne ko kuwa?” daga can cikin gidanmu nake jiwo waxannan maganganun. Abinda yayi dalilin da na fasa shiga cikin gidan na qara ja da baya na tsaya ina sauraron mai maganar. Cikin takaici da vacin rai na yanda ita kullum babu dama ta kira wani ta xan sa shi wani abu don ni ma in xan samu in huta komai sai dai ta kira Humaira. Can cikin zuciyata na sake jan wani mummunan tsaki a daidai lokacin da haushinta ya sake kama ni a dalilin zuba wa kwanon dake hannuna ido da nayi, cikin takaici nace sai kace ba ita ta aiken ba, tun kafin in kai ga kawo mata aiken da tayi min xin har ta mance tana sake nemana don ta sake aikena tanfar dai babu kowa a gidan sai ni. Maimakon in hanzarta shiga cikin gida in kai mata aiken nata, musamman da yake ina jin yanda ta kasa daina qwala wa sunan nawa kira, sai kawai naja na tsaya cikin zauren na maqale jikin bango ina sauraro tare da yin tsokaci kana wasu al’amura da suka addabi zuciyata. Ko yaushe ne ni ma zan samu in xan huta in samu in rinqa watayawa irin na sauran yaran gidanmu, in mallaki ‘yancin rayuwa irin na yanda nake ganin sauran ‘yan uwana suna dashi? A kullum zuciyata ta xan samu wani sarari ko wata dama da zata yi min wata tambaya, to ba tayi yi min tambayar da ta wuce waxannan tambayoyin, yaushe ne ni ma zan huta? Yaushe ne ni ma zan samu ‘yancin rayuwa irin wacce sauran ‘yan uwana ke da ita? A lokacin da nake yarinya ‘yar qarama, na xauki halin da nake ciki na takura da qunci da rashin hutu tanfar hakan ya same ni ne a dalilin ni xin ni ce qarama cikin yaran da suka kai munzalin moro. Don haka sai nayi ta fata da buri waxanda suke biye da ni su kawo sanda za su karve ni, amma daga baya sai na gane a’a ba haka ba ne tunda ai akwai wasu qannen nawa da tazarar watanni goma ne kawai a tsakanina da su. Kamar irin su Suwaiba, kuma su xin ba ayi musu irin aiken nan da ake yi min na sayo min kuka, sayo min daddawa, sayo min kanwa, komai ma dai ba kuma wannan ne yafi komai vata min rai ba, sai irin wai ko a gida xaya abubuwan da ake buqata suke to ba za a haxa min aiken ba, sai na kawo xaya a sake maida ni. Duk a dalilin dai wai kar a ganni a zaune ina hutawa, ko sanda nake yarinya ‘yar qarama wannan jeka-ka-dawon kan ci min rai, to balle yanzu da na soma sanin abinda ke min ciwo, ga kuma wasu qannen nawa da yawa da suka taso bayana waxanda su ba hakan ake yi musu ba, waxanda su suke ma da ‘yancin a aike su su ce ba za su ba. Babana Malam Surajo mazaunin unguwar Jahun ne dake cikin jihar Bauchi, Jahun gaba take kaxan da Nasarawa, in har ka biyo ne ta qofar Nasarawa ne, gaba xaya ta nan kewayenmu har unguwannin dake kewaye damu mutane da yawa sun san shi, sun kuma san gidanmu. Saboda kasancewar shi xin a shekarun da suka gabata yana cikin ‘yan kasuwar da kasuwa ke kai musu, ko a yau xin nan kuwa da ake faxin harka ta xan ja mishi baya yana cikin rufin asirinshi daidai gwargwado. Sanda na soma wayo a gidanmu ina yarinyar qarama, na buxe ido ne na tarar da Babana da Matanshi na aure guda biyu, wato uwargida Hajiya Majadan wacce gaba xaya gidan har mutanen unguwa ake kira Mama. Sai kuma Innata wacce akan sakaya sunanta da nayi qoqarin yi nasha tabka da bulala akan wai ni xin fi’ili ne dani da kuma sanabe iri-iri don haka nima na haqura na shiga sahu wajen gantsara mata sunanta da ake kiranta dashi Gambo. Mama ita ce uwargida a gidanmu, auren saurayi da budurwa aka yi musu ita da Babana, tana matuqar jin d axi da kuma gadara da hakan, da kuma alfahari da uwargidancin nata. Zan ma iya cewa a wurin Mama, gani take tanfar duk wata mata da ba auren saurayi da budurwa suka yi da mijinta ba, to gani take tanfar auren matar ba wani aure ba ne na sosai, in ma ‘ya’ya ta haifa to ‘ya’yan da ta haifan sun fi kama da gasu nan dai gasu nan, amma ba wani ‘ya’ya masu ‘yanci ba. Wataqila hakan ne ma dalilin da yasa a lokacin da ‘ya’yanta mata suka zama ‘yanmata suka kawo munzalin aure ta kasa ta tsare, tayi qememe ta qi yarda da mutanen da Babana ya kawo su aure su. Dalili, wai su xin masu mata ne ‘ya’yanta ba za suje suyi bau tar ‘ya’yan wasu ba, samari gal a leda zasu aura, don haka akan dole Babana ya yarda Kaza taja Zakara. Ya xaurawa ‘ya’yanshi Anti Sha’awa da Anti Kaltume aure da samarin da uwarsu take so. A kullum Mama cewa take yi da kaje ka samu ai gara a zo a same ka, duk tsiya an zo an same ka a gidanka da ‘ya’yanka da mijinka ai babu wata tsiya da za a kawo maka, dole kuma abi tsarin da a ka zo aka same ka akai, tunda dai mijinka ne, gidanka ne, to wane fi’ili za a kawo maka? Mama mata ce mai nuna isa da gadara ga kuma mulki, zai yi wuya qwarai rana ta fito har ta kai ga komawa ga Ubangijinta baka ji ta tana yi wa kanta kirari ba, kusan kullum sai ta faxa, “Alhaji mijina ne, auren saurayi da budurwa aka yi mana ni da shi, aurenmu aure ne na soyayya babu wani abin shi da ban sani ba, haka shima nawa. Aurenshi nayi tun bai da ko kwabo tun ‘yan wandunan sakawanshi basu wuce guda biyu ba nake tare da abina, don haka babu wata matar da zata shigo min gida a dalilin ita da iyayenta sun hangi arziki da rufin asiri ta ce zata kawo min wani fi’ili. Ba zai yiwu ba, ba zan yarda ba, shima maigidan ba samun shiga za’ayi ba a wurinshi, yauwa duk wacce ta hango min mijina tayi sha’awar shigowa taci arzikin da ta hanga to zata zo ne tayi zaman haquri, in har ta matsu da zaman in kuwa ba ta matsu ba sai tayi gaba kamar yanda wasu da yawa suka yi da suka gane ba za su iya ba.” Duk waxannan kalamai na Mama da takan furta kamar wasa kamar shaqiyanci da iyakacin gaskiyarta take yin su, haka nan kuma al’amarin yake a hakan kuma ake zaune babu musu ko jayayya kan maganganun nata. Babana ba ya iya musu da Mama, baya jayaiya da ita kullum a to yake a wurinta, gashi kuma tayi sa’a yana matuqar gudun vacin ranta kan abin da take so kuma to kullum zai iya sakin ra’ayinshi ya koma nata don neman zaman lafiya. Xan qaramin misali kuma shi ne, yanda ya haqura da bayar da auren ‘ya’yanshi Sha’awa da Anti Kaltume ga mutanen da yake ganin sune suka dace ya bada su ga waxanda Mama take so, duk kuma da gaba xaya ‘yan uwanshi da aminanshi ba su so yayi hakan ba. Innata dake zaune da Mama da mijinta kuwa haquri take yi, haqurin kuma ba kaxan ba, don kuwa in ban da tana da tsayayyun iyaye waxanda suke da tasiri mai qarfi a kanta da bata iya yin shi ba. Ita Innan ‘yar gata ce ta qin qarawa a gidan su Yayu ne da ita maza da mata masu yawa, gashi kuma dukkansu ji da ita suke yi ‘yar auta ce wurin mahaifinsu Mallam mai babban allo a wurin mahaifiyarta kuwa ma ita kaxai ce mace. Kyakkyawa ce qwarai, a lokacin da tayi ‘yanmatancinta babu wanda bai san da labarin kyanta ba, musamman ma a unguwarsu ta qofar Dumi, unguwar da a farkon auren Babana da Mama a can suka zauna da ya gina gidanshi na farko a Jahun, shi ne ya taso ya dawo nan kafin daga bisani ya gina gidan da muke ciki a yanzu, wanda manne yake da tsohon gidan namu. Da yawan mutanen da suka san Innata da irin gatancin dake gare ta suka kuma san halin zaman da take ciki a gidan namu kan ce wai har da rabon haihuwa cikin abinda ya zaunar da ita. Mallam mai babban allo Malami ne mai karantatarwa yara da manya suna xaukan karatu a wurin shi. Yana da matanshi na aure guda biyu, Hajiya ‘yar dubu ita ce uwargida, ita ce kuma uwar manyan ‘ya’yan gidan gaba xaya su Alhaji Maikuxi, Alhaji Malam, Alhaji Kawu, Inna Aisha, Inna Hajara, gasu nan dai da yawa gaba xayansu sun girmi Innata nesa ba kusa ba, don ma ‘ya’yansu sune sa’o’inta wasu ma da yawa sun girme ta. Saboda ita mahaifiyarta Hajiya Turai an bashi aurenta ne a shekarunshi na girma bayan rasuwar matarshi ta biyu ta rasu ita Hajiya Turai ‘ya’ya uku ne da ita Kawu Hassan da Husaini sai ko ita Gambonsu. Matan Mallam mai babban allo zama suke yi na girma da mutunci ita Hajiya ‘yar Dubu ta kama girmanta itama Hajiya Turai tana kame da kanta tana kuma girmama Hajiya ‘yar Dubu saboda ta girmama kanta shima Mallam yana iya qoqarin shi wajen ganin gidanshi ya zauna lafiya. Don haka sai komai ya tafi bai xaya gaba xaya ‘ya’yansu kuma suna girmama su saboda mahaifinsu yana da girma a wurinsu. Tasowar da Innata tayi a cikin gidansu cikin wani yanayi na shagwava mai tsanani saboda rashin kwabo da sangarcewa yasa Alhaji Maikuxi yasa hannu ya xauke ta daga cikin gidan ya maida ita nashi gidan gaban matarshi Kubra wacce a lokacin take da ‘ya’yanta maza guda uku, wato Abdullahi da ake kira Abba sai kuma Auwal da Ahmad. Ita kuwa Hajiya Kubra tayi mata riqo na gaskiya da amana ta hanyar bayar da ingantacciyar tarbiya tare da sauran ‘ya’yanta waxanda suka girmi Innan da wasu masu yawa da suka biyo bayanta. Inna ta taso cikin gidan Alhaji Maikuxi tanfar ita ce babbar ‘yarshi mace, itama Baba take kiranshi tanfar dai shi ne ya haife ta, don haka daga baya ne qwarai da yawan ‘ya’yanshi dama sauran mutane suka san cewa ita xin qanwarshi ce ba ‘yarshi ba. A lokacin da ta zamo budurwa kuwa ba zai yiwu in kwatanta yanda ta zamo ba, don kuwa ba qaramin gata Alhaji Maikuxi ya nuna mata ba. Manema sosai tayi duk da bai yarda ya bada damar aje gare ta ba, saboda jan da yayi ya tsaya kan cewar karatu zata yi. Sai dai Mallam mai babban allo bai goyi bayan hakan ba, hasalima shi ne ya bada umarnin bayar da auranta ga Babana saboda kamun qafar da Baban nawa yayi da Almajirin mai babban allo Alhaji Yahaya, wanda shi kuma Aminin Babana ne, tare ma suka taso tun suna ‘yan yara. Duk da bin umarni ne yasa Alhaji Maikuxi aurar da Innata a wannan lokacin saboda kwata-kwata shekarunta goma sha biyar ne, gashi kuma gaba xaya an san Mama da irin matan da ta kora a gidanmu da ma raxe-raxen da ake yi na fin qarfin Maigidan da ake cewa tayi. Kowa cewa yake yi zata ne kawai ta dawo ‘yar qaramar yarinya zata yi mata sanadin zawarci bai hana Alh. Maikuxi kashe dukiyarshi mai yawa wajen hidimar auren nata ba. Inna ita kaxai a gidanmu, xakunan kwana uku ke gare ta gami da makaxexen falo mai xauke da toilet a cikin shi. Hajiya Kubra ce taja ta tsaya kan sai an bata wannan wurin kafin ayi bikin, kasancewar gidan namu a lokacin sabo ne gashi kuma Babana yana matuqar son auren, ga kuma sulalla a hannunshi, yasa yayi musu yanda suke so xin duk da irin tashin hankalin da ya fuskanta daga wurin Mama. Su kuma su Hajiya Kubra da mijinta ba suyi qasa a gwiwa ba, suka shaqe mata wurin nata da kayayyakin alatu gami da gadaje irin na alfarma. Alhaji Maikuxi yana matuqar sona a dalilin tsananin son Innata da yake yi, wasa dani yake yi irin wasan Jika da Kaka, don kuwa ya dage kan cewa Innata ‘yarshi ce, don haka sai na daxe ban gane cewar ba shi ne mahaifinta ba, sai a wani lokaci da wani abu ya faru. Rannan ne cikin dare na farka a xaya xakin Inna damu ‘ya’yanta muke kwana a ciki sai na jiwo muryar Babana yana magana cikin yanayi mai qarfi, alamar dai akwai vacin rai cikin maganar tashi. Sannu a hankali da na saurari maganar tashi sai na gane tuhumar Innata yake yi yana tambayarta dalilin da yasa Mama tasa ta aiki bata yi ba? Ban jin bayanin da Inna take yi mishi, don magana take yi a hankali cikin muryarta mai sanyi, sai daga baya da maganar tayi tsanani ne na jiwo ta tana cewa, to tunda kace ita bata qarya me yasa in ta gaya maka magana ba zaka yi hukunci ba kawai sai kazo kana tuhumata? Babana ya ce, ai haka ma za ki ce? Ta ce eh, saboda in ta riga ta faxi nata zancen ko na musa baka yarda.” Ya ce, “To kar kuma kice an zalunce ki.” Ta ce, “Uhun, zalunci kam ai a cikinshi nake raye, sai dai kuma na sani da sannu mai sakayya zai saka min, don kuwa ba zan yafe ba.” Inna tana faxin haka naji saukan dukan Babana a jikinta, wai tayi musu Allah ya isa shi da Mama. Tuni jikina ya shiga rawa ina ta karkarwa akan gado na rasa yanda zan yi in taimaki Innata, tunda bayan saukar dukan farko da naji wasu masu yawa ma sun biyo bayan shi. Nayi kamar in miqe in fita falo don dai ya ji motsina ko zai saurara sai kuma na tuna da gaya mishin da Mama take yi wai ni xin zamana a wannan xakin lave nake yi musu, komai suke yi shi da Innata ina jin su. Don haka ya hana ni kwana a nan ya fito dani tsakar gida saboda tana son ganin ta rage qarfin mu’amallar dake tsakanina da Mahaifiyata, wacce ta tabbatar cewar ni ce farin cikinta na wannan lokacin. Bisa wannan dalili yasa nayi shiru, na sake komawa na qara lavewa kan gadon namu sai dai hawaye da suke ta gudu kan kumatuna. Ban san dalili ba, Inna ta qi kuka wanda in da tayin wataqila da dukan da yayi matan bai yi tsanani haka ba, don wataqila yaso tayi kururuwa ta yanda Mama zata yi abinda ke faruwa don tasan shi xin yayi hukunci kan qarar da ta kawo mishi. Duk da Babana ya daina dukan nata, ban kuma ji wani motsinta ba, kwana nayi idona biyu ina kuka, don haka ina jin buxe qofar da yayi ya fita sai nima nayi maza na diro daga kan gadonmu na fito na shiga wurin Inna don ganin halin da take ciki. Cikin rawar jiki da rawar murya saboda kukan da nake yi na ce mata “Sannu Gambo.” Bata amsa min ba, sai ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min “Xauki Aliya da Sa’adatu ki xora su suyi fitsari ki wanke musu baki.” Nayi maza na ce mata “To” naje nayi yanda tace xin, har na idar da Sallah na zo na gaisheta bata motsa ba daga yanayin da na barta, ban daxe da tsayawa a wurin ba sai kawai ga Hajiya Kubra ta shigo cikin zurmemen hijabinta. Ga dukkan alamu daga idar da Sallahrta ta Asuba ta fito, ga alama kuma ita Innan ce tayi amfani da wayarta ta hannu ta kira ta. “In ce ko dai lafiya Faxima?” sunan da take kiranta dashi kenan, ta ce “Eh, lafiya Umma.” Na durqusa na gaishe ta na juya na fita, musamman ma da yake ban ganta cikin yanayin fara’a da walwalar da na saba ganinta ba. Don haka na koma xakinmu na zauna ina tunani, tunanin da zan iya. Shekaruna na quruciya shekaru ne da ba zan iya furta komai ba game da Babana, don kuwa shekaru ne da nayi su cikin wani yanayi na fuskantar wasu al’amura da ko kaxan bai dace yarinya mai shekaruna ta ma san su ba, balle ta fuskance su. Kan kace meye wannan? Tuni ‘yan uwan Inna sun cika mana gida, su Inna Aisha, Inna Balki, Inna Hajara, gasu nan dai birjik, wasu na kuka wasu na sakin maganganu a tsakar gida don neman a tanka ayi wacce za’ayi, a wannan lokacin ne na fahimci lalle abinda ya farun ba mai sauqi ba ne. Tuni Mama ta bar tsakar gida ta koma falonta, ta kuma yi maza ta kame bakinta tayi shiru bata tankawa baqaqen maganganun da wasun su suke saki ba, don tasan karonta dasu. Ana cikin haka na sake jin sallamar Baba Yahaya a tsakar gidanmu, Hajiya Kubra tana jin sallamar tashi ta fito cikin hijabinta, cikin natsuwa ta nemi wuri ta zauna a qasa cikin ladabi ta gaishe shi, kafin ta soma yi mishi magana cikin yanayin girmamawa, na cewa Alhaji ya gaya maka ina nemanka ne saboda in bi umarnin da ka bani na duk abin da ya faru a cikin gidan nan, kai ne farkon wanda zan gayawa ba shi Alhajin ba. Ina bin umarnin naka ne kamar yanda nake bin na Baba da ya hana ni fitar da Faxima daga xakinta ba da izinin mijinta ba. Baba Yahaya ya gyaxa kai nuna alamar gamsuwa da maganar tata, kafin daga baya ya tambaye ta wani abin ya sake faruwa ne? ta ce “Eh to, ni kam ai ban san komai ba, tunda baya kai qara kan laifukan da ake yi mishin, sai dai yayi hukunci na ganin dama saboda ganin komai yayi yana sharewa qalau. In ban da haka me Faxima zata yi wa mutum yayi mata irin abinda ake yi mata a gidan nan.” nan da nan ta shiga share hawaye tana faxin a roqan mun shi kawai ya bani ita muje gida, inna yi jinyarta ta warke masan abin da muke ciki.” Ya xan yi shiru kaxan kafin ya ce mata “Hajiya shi babba fa da haquri aka san shi, kin kuma sani sarai ita mace komai gatanta bata da wata darajar da ta wuce ace a xakin aurenta take zaune.” Ta ce mishi, “Haka ne.” Ya ce, “To ina dalili, shi Alhaji Surajo komai qanqantar abinda ya faru a gidanshi tsakaninshi da yarinyar nan ba za ku bari maganar ta q are a tsakaninsu ba sai kun shiga? Sai kun yiwo gayya kun cika mishi gida? In ita Gambo bata laifi ne? kuma don ‘yar gata ce a danginta da ke da Alhaji Maikuxi sai ace ba shi da iko a kanta? Tuni Hajiya Kubra ta soma kuka sosai tana fyace majina, ta ce “In tayi laifi Alhaji sai ayi mata duka har da targaxe? Kuma menene laifin nata, ta qi yiwa matarshi aiki? Mai aiki na kawo mata ne? Yanzu mu da ku ka auro wasu matan a bayan mu haka muke yi musu? Inna Hajara ta leqo daga cikin xakin tana gaishe shi, sannu da zuwa Mallam, nan da nan ya xaga ido ya kalle ta ya ce, ai kuma duk kun zo ne kuna ciki? To duk ku fito, koma ciki ki gaya musu nace duk ku fito ku bar gidan nan. In na bar nan kuma zan je in gaya wa Mallam har da ku a rura wutar fitinar dake aukuwa a gidan nan.” Nan da nan suka yi ta fitowa suna tafiya saboda sanin matsayin Baba Yahaya wurin Mallam mai babban allo, matsayin da tuni ya maida shi ya zama xan gida, kuma mu’amalla da shi a matsayin xan uwa. Yana tsaye a wurin har suka gama wucewa bai kuma fasa faxan da yake yi musu ba, sai da yaga sun qare ne ya kalli Hajiya Kubra dake zaune a qasa cikin ladabi tana sauraronshi ya ce mata. “Kiyi haquri Hajiya, kiyi haquri na kuma roqe ki kar kije ki ce zaki gazawa Alhaji Maikuxi munin al’amarin tunda shima bai san haqurin ba.” Gambo dake da ‘ya’ya mata huxu a jere, Kubra in aka barku ke da mijinki kuka yi yanda kuke so xin kun yi mata adalci? Ai ke uwa ce ba sia na tsaya yi miki dogon bayani ba, kin san komai zai yiwu ne ku kaita inda zaku mantar da ita waxannan ‘ya’yan nata? Kin fi kowa sanin ba zai yiwu ba, to kiyi haquri kawai ki kuma rinqa kwavarta duk da dia kin qi uarda da cewar ‘yarki mai laifi ce, amma hakan ba zai sa kuma kullum ki rinqa goyon bayanta ba, don gyara kayanka Kubra ba fa ya zama sauke mu raba, haka nan kana qin naka ne don duniya taso maka shi. Ta ce, “To Alhaji na gode, Allah ya saka da alheri.” Ya ce, “Amin.” Ya wuce ya fita ita kuma ta koma xakin Innarta, ta gyara abubuwan da suke buqatar gyara, duk da watsewar da dangin Inna suka yi aka bar Hajiya Kubra ita kaxai, Mama ta kama kanta sosai tana can wurinta ta kame daga yawan zirga-zirga balle aje ga sakin maganganun da ta maida yin hakan xabi’arta ta kullum. Ana cikin haka ne Baba Yahaya ya sake dawowa tare da wata Dattijuwa Sidiya, kowa ya santa ita da mijinta gyaran targaxe da karaya suke yi ita ya kawo ta shiga ta gyarawa Inna targaxen da Babana yayi mata ta fito ya maida ita. Rannan a gidanmu Hajiya Kubra ta wuni sai da tayi sallar Magariba aka zo aka xauke ta, Inna ma ta wuni a kwance ga dukkan alamu kuma lafiyarta ta rasa shi yasa ta wuni a kwance nima na wuni rannan ina hidimar xakinmu bata yi ta addabata da yawan aike ba balle aje ga tabkata da dukan da aka saba yi min kullum. Washegari da sassafe sai ga Baba Yahaya da Alhaji Mai kuxi, ga dukkan alamu kuma daga Masallaci suke tunda su xin makwabtan juna ne, unguwarsu xaya can suke wajen Makama New Axtention. Baba Yahaya ne ya fara shigowa gidan, Babana ya fito daga falon Mama wanda dama nan ne wurin zamanshi ko da kuwa shi xin a xakinta yake. “Sannu da zuwa Alhaji.” Baba Yahaya ya amsa kafin ya ce mishi “Ni da Alhaji Mai kuxi ne.” Nan da nan yanayin Baba ya sauya, ya ce “To bari in buxe muku falona mana.” Ya ce mishi “A’a, izini ya ce in zo in roqar mishi a wurinka yana so zai shigo ya duba Gambo.” “To, to ai shi kenan.” Baba ya sake faxi cikin wani yanayi ya kuma wuce ya shiga wurinshi. Har tsakar gidanmu Alhaji Mai kuxi ya shigo, Innata ta fito ta durqusa tana gaishe shi, bai wani tsaya wajen amsa gaisuwar tata ba, zuba mata ido ya yi yana kallonta. “Sannu Faxima, sannu kin ji. Sannu da qoqari.” Shi kuwa Baba Yahaya yana gefe yana kallon shi, shiga cikin Gambo ta miqe ta koma ciki suka kama hanyar fita waje, yana cewa. “Baba Yahaya ba ka yi min adalci ba Alhaji, ka zalunce ni ka sani na kawo yarinyar nan in da ba za a yi mata adalci ba, bayan kasan komai amma duk da haka kaje ka haxa ni da Mahaifina. To nima na ce ban yafe ba, ku haxu ku rufe ni da duka tunda itama abinda ta faxa kenan aka yi mata wannan zaluncin.” Baba Yahaya ya ce, “To naji muje.” Ya tasa shi a gaba suka fita. Rashin jituwa mai tsanani ne ya nemi shiga tsakanin Alhaji Mai kuxi da Alhaji Yahaya waxanda ban da ‘yan uwantakan da Mallam Mai babban allo ya haxa a tsakaninsu su xin makwabtan juna ne a unguwa xaya sannan a kasuwama shagunansu kusan wuri xaya suke. Alhaji Mai kuxi yaja ya tsaya kan bai duba kusanci da zumuncin da ke tsakaninsu ba, yasa Mahaifinshi ya tilasta shi bada qanwarshi ‘yar qaramar yarinya a inda yasan ba za ayi mata adalci ba, saboda ya fifita son amininshi a kanshi, sai da mai babban allo ya tsawatar. Tun daga wannan lokaci Mama ta shiga sakin maganganu masu zafi a tsakar gida saboda ta gane Babana ya xauki matakin daina yin duka ko da ta kai mishi qarar Innata sai dai kawai ya yi magana da fatar baki, abinda ita kuma ba haka taso ba, tunda ita qa’idar ta ne kullum sai taje ta ce mishi ga abin da aka yi. Ko kaxan Mama ba ta so Babana ya xauki irin matakin da Babana ya xauka ba na kamewa daga yin duka don kuwa kusan kullum sai na jita tana yada magana a tsakar gida. “Ni fa kar mutum yaga wasu guntayen iyayenshi marasa girma da sanin darajar Surukuta sun zo sun yi wa Alhaji burga ya tsorata yayi zaton ko ni ma a tsoracen nake.” Ta tave baki ta ce, “Ko kaxan ni xin nan a gidana rashin jini ne rashin tsagawa, baka shiga sabgata ba ba ruwana da kai, amma kana doso ni da rashin mutuncinka, to kama ka zan yi in naxa maka dukan tsiya ba mai Kuxi ba ko mai dala ne ina daidai dashi duk da a gaban Innata take furta irin waxannan kalaman, ta kuma san da ita take yi bata xaga ido ta kalle ta ba, balle ta tanka mata. Amma duk da haka wai bata tsira rannan akan ruwan bunu ruwan tin da babu komai cikin shi sai ganyen tea. Mama ta ce, “Wai Innata ta kwashe wa ‘ya’yanta ita ta basu xan qanqani. Nan da nan kuwa ta shiga zage-zage, Babana ya leqo yana tambayarta “Menene ya faru ne?” Ta galla mishi uwar harara ta ce, “Ai don ka ji ina cewa zan bata kashi ne yasa ka zaburowa ka fito kana tambayata? To ai ko kana tsaye zan yi hakan, don na gaji da irin cin kashin da ake yi min a cikin gidannan, zan yi in gani ko nima za’ayi min irin wuju-wujun da aka yi ta yi da kai.” Ta zubawa Inna ido tana mata kallo irin na wulaqanci. “Ke nan ga ‘yar gwal ko? Ki zo gidan mutane kina musu rashin kunya da rashin mutunci saboda iyayenki, ba su yi miki tarbiya ba in an tava shi su ce za suyi wa mutane iskanci, to ni ba Alhaji ba ce babu ruwana da iya shegensu maganinki zan yi ba Mai Kuxi ba, aje a turo min mai babban allo in ya tashi zuwa kuma kar ya zo da allon katako ya zo dana qarfe. Inna ta kasa haquri ta ce, “A’a me iyayena suka yi miki? In dai akan wannan ruwan tin ne gashi nan na juye miki.” Garin juye ruwan ti wani ya xallu a qafar Mama, nan da nan ta qara fusata wai Inna ta qona ta, ta shiga xura wa iyayenta ashar. Inna ta juya ta nufi xakinta tana faxin “kiyi ta zage-zagenki ni kam ai kowa ya ji abinda kike faxa yasan bada iyayena mike yi ba, tunda kowa yasan su yasan su xin ba mutanen banza ba ne.” Abinda kawai ta faxi kenan Mama ta bita ta jawo ta tana tambayarta su waye ne na banzan? Bata kai ga bata amsa ba ta rufe ta da duk ta turmushe ta a qasa ta hau kanta ta danne tana ta faman naushinta da kyar Babana ya samu ya xagata a kanta, ya kaita xakinta tana ta faman huci tana zage-zage. “Haka kawai kaje ka xauko masifa ka kawo min cikin gida, ba dole in tsaya in yi maganinta ba, tunda kai ka kasa?” yana fi towa daga xakin Mama ya kai min maka, kafin ya daka min tsawar da ta katse min komai. “Me aka yi da ki ke qur ma wannan ihun kina nema sai kin tara min Jama’ar unguwa a gidana?” Shiru nayi na bi Babana da kallo har ya shiga wurin shi, an daki Innata an farfasa mata baki da hanci alhalin ba wani laifin ku zo ku gani tayi ba, amma ina kuka ya make ni ya ce, wai ba ayi komai ba. A hankali na faki idon mutane na fita na bar gidan namu na taka da qafata na tafi har Makama extention naje na gaya wa Hajiya Kubra abinda ya faru duka, ta ce “To babu laifi zauna ki karya kiyi wanka ki sauya kayan jikinki, sai ki koma gidanku.” Na ce mata “To.” Ina dawowa gida na samu Inna cikin wani yanayi, ko dukan da Babana ya yi mata wanda gaba xaya dangin Inna suka yi ta kai-kawo akai suna faxin maganganu bata ji jiki irin wannan ba, iyaka dai a wancan ta samu targaxe a hannu shima kuwa ta kare dukan da ya kawo mata ne da hannunta. Cikin zuciyata na ce, “Wato dai da banbanci tsakanin dukan miji da kuma na kishiya?” Ban san yanda aka yi ba, Baba Yahaya ya ji abin da ya farun da yamma sai gashi yazo gidan, don jin abinda ya faru. A gaban Babana Mama tayi wa Baba Yahaya wanki irin na babban bargo, ko dama can kuma nasan ta daxe tana da cikinshi don ko maganarshi zata yi bata ambaton sunanshi sai dai ta ce mishi munafuki. Haka bata zuwa hidimar gidanshi wai shi da matanshi sun ci amanarta, Baba Yahaya yana ganin haka ya juya ya fita ya bar gidan ya barta tana ta zage-zagenta, tana haxawa har da abokin nashi wato Baban namu, har tana ce mishi wai tunda shi ya kasa to ita zata yi mishi maganinsu. Tana nan tana jiran zuwan Alhaji Mai kuxi, zata nuna mishi bai da wayo, zata gaya mishi magana irin wacce bai tava ji ba, zai gane shi xin qyalle shi kawai ake yi da wata tevar shi kamar qullin kayan wanki.” Har Babana ya gaji yasa kai ya fita ya bar gidan Mama bata gaji tayi shiru ba, sai tambaya take yi a kanki na fara ganin kishiya? Guda nawa aka yi min? ke ce ta shida, ke ki ka fi kowa? Shafaffiya da mai, ki zo min gidana ki ce za ki gallabe ni, ke xin banza! Ai tunda abin ya zama haka, to za mu sa qafar wando xaya tunda kuma na gano abin naku tsiya ne da kuma rainin hankali, to zan tasa ki a gaba zan ga yanda za’ayi kiyi zaman gidan nan, sai dai ko in shi mai kuxin ne zai zo ya taya ki zaman ko?” Ana cikin haka sai ga Hajiya Kubra ta shiga cikin gidan tana faxin, “Mama ja’ira Mama mara mutunci, Mama mai rashin kunyar qarya, to don kin daki Faxima sia me? Sau nawa ki ka haife ta? Don kuma yi kanki don xan girman da take baki kina rainawa ya qara zubewa, hakan kuma ba zai hanata sake haxa shimfixa da mijinki ba, sai dai ma ta qara. Tsohuwar banza kawai mara mutunci.” A fusace Mama ta fito tana tambayarta “Ke ce ki ka zo baki turo Mai kuxi ba?” Hajiya Kubra ta ce, “Ai sai kan abinda yafi qarfina ne ki ke ganinshi yaje ke kuwa ni ce zan yi maganinki sakaryar banza wacce uwargidancinta bai amfani mijinta da komai ba sai qarin fitina. Sakaryar tsohuwar da ta rasa masu zaunar da ita su gaya mata gaskiya.” Ban san yanda aka yi ba sai kawai naga Hajiya Kubra tayi jifa da gyalen da take yafe dashi kan kace meye wannan tuni danbe mai tsanani ya kaure a tsakaninta da Mama, sai ji kake yi xixim-xixim-xixixim!! Don kuwa su dukkan su ma’abota qiba ne da kuma jin qarfi, sai dai kan ka ce meye wannan Hajiya Kubra ta kai Mama qasa tim! Abinda ya firgita gidan gaba xaya ni da kaina jikina rawa yake yi. Habiba da ta kasa haqurin kayen da aka yi wa uwarsu, ta sunkuto tavarya da gudu tazo zata rafkawa Hajiya Kubra, cikin kuskure da rashin dace sai kawai ta sake timawa Mama tavaryar a gefen fuskarta da iyakacin qarfinta, daga ita har Mama lokaci xaya suka qurma wani irin ihu mai tsananin firgitarwa. Habiba tayi waje a kixime tana neman taimako. Hajiya Kubra tana jin za su shigo tayi maza ta xaga Mama dake kwance jina-jina ta sulale tayi ficearta, ta bar Mama tana yiwa makwabta rantsuwar Alqali ne kawai zai shiga tsakaninsu, su kuwa suna faxin “Abin dai kam bai yi daxi ba, a gefe kuma sai dariyar Mama suke yi don babu wanda bai san abin da gidanmu yake ciki ba. Jinya sosai Mama tayi har da su zuwa asibiti, da su xaukan hoto duk rantse-rantsen da ta yi tayi na xaukan mataki da kai magana kotu duk ya tashi a banza, iyaka dai ta sake tasa Babana a gaba da fitina wai shi xin ya gajiya an shigo har cikin gidanshi anci mutuncin iyalinshi bai yi komai ba. Kan haka har ta kira iyayenta suka zo suka sanya Babana a gaba ina jin shi yana mayar musu da bayanin yanda aka yi duka, su xin ma dai basu gamsu da shirun da Baban yayi ba, sun ce in yana haka a gidanshi ai sai ayi abinda babu kyau, duk da dai sun gaya wa Mama rashin kyautawarta kan cin mutuncin abokin mijinta da tayi a gaban mijin nata. Tun daga rannan kuwa ban sake ganin Mama tana yunqurin dukan Inna ba, don Hajiya Kubra ta gaya mata in ta yi miki laifi ki faxa, amma duka tsakaninki da ita babu in kuwa ki ka yi ganganci ki ka yi, to nima zan yi miki irin wanda na iya, don ba baiwarki ba ce matar mijinki ce irin amfanin da kike yi mishi irinshi itama take yi mishi. Ba kuma sai na ce miki yana sonta ba, tunda kina ganinta da ciki kina ganinta da goyo, don haka kin yi kaxan fitinarki ta rabata da mijinta.” Waxannan baqaqen maganganu na Hajiya Kubra sun sosawa Mama rai, don na ji ta tana nanata su a gaban Babana yafi sau nawa. “Ni ina Humaira taje ne?” maganar da na sake jiwowa kenan daga cikin gidanmu, wacce tayi dalilin katse min tunanina, na dawo kan abinda nake ciki a lokacin baqin ciki da takaicin Mama suka sake lulluve ni, don kuwa kowa ya sani zan yi mu’amalla da Mama ne kawai bisa tsoro, amma ba don so da qauna ba. Wannan dalilin ne ma ya sanya ni na zamo mai iya kwaikwayon Mama da al’amuranta duka babu wani abin da yake yin shi xabi’ar ta ne wanda bana kwaikwayon shi. Ko a yanzu ma kuwa tsayawa nayi na shiga kwaikwayon maganar tata. “Humaira.” Na’am, zo ga wanki, to na yi, Humaira, na’am zo ga shara, to nayi, Humaira, na’am zo ga aika, to na yi. Humaira, na’am zo…….” “Mama ki ke kwaikwayo?” da iyakacin qarfinta tayi min tambayar, nayi maza na bar abinda nake yin cikin kaxuwa na zuba mata ido ina kallonta, tsoro ya bayyana a fuskata. Habiba ce yata da nake bi ta xakin Mama, wata ashirin ne tsakanina da ita, abinda kullum Mama take nanata gaya min kenan. A duk lokacin da wani abu ya shiga tsakanin mu zata jaddada min ko sanda uwarki tazo gidan nan ta samu Habiba ne watanta goma sha xaya, ke kuwa wata tara daidai tayi ta haife ki, don kamar a hannunta ta shigo dake. Bisa wannan bayani da Mama take yi minne ya zama dole in yi wa Habiba ladabi da biyayya, irin wanda bata yi wa uwata xaya bisa gomanshi, tunda zata aike ni ta sani aiki ta yi min hukunci, ita kuwa tawa uwar bata isa tayi mata ba. Sannan biyayyar da nake yi matan ban sa an sata tayi min adalci ba, wuni take yi tana jibgata da duka, ko da kuwa daga zaman cin abinci ne ko a wurin wasa, saboda Habiba na haqura da duk wani abin da ya shafi wasa, saboda yanzun nan zata rufe ni da duka, ko da kuwa ba da ita nake wasan ba, saboda rashin ‘yanci irin wanda nake ciki. Ni har Suwaiba qanwar Habiba dake xakin Mama wacce ita xin na girme ta da watanni tara dukana take yi, ban kuma isa in ce zan rama ba, sai Mama da Habiba su rufan min suce wai cin zalinta zan yi. “Mama ki ke kwaikwayo, za ki gama da gamonki kema kin san saura.” Tayi maganar cikin yanayin jinjina kai alamar wai zan ji jiki kenan. Na zovara baki na vata rai sosai, abinda nayi ya bata haushi har ta kawo hannu da nufin buge min bakin nawa, nayi maza na kave hannun nata tare da faxin. “A’a me nayi miki? Ban yafe ba.” Tayi maza ta sake kawo min wani bugun, nima na sake cewa “Ban yafe ba, muguwa kawai azzaluma.” Ado ya leqo cikin zauren, “Kai kuzo nan Mama tana kiran ku.” Ado shi ne yaron da Mama ta xauko daga qauyensu ta kawo shi gidanmu ta ajiye, ita da Babana suka haxu suka maida shi xan gatan gidan, saboda irin son da Maman take yi mishi. Qanin ta ne uwarsu xaya uba kuwa kowa da nashi, a wancan lokacin da ta kawo shi, shi xin ba kowa ba ne face wani xan dogon yaro xan siriri xan baki, xan bagidaje-bagidaje, kana ganin shi kasan daga qauye yake, ko gajiya da aiki bai yi, don ya saba yin wanda ya fishi. In kuma aka cika mishi kwano da abinci ya cinye shi tas, amma sannu a hankali sai aka wayi gari Ado ya murje ya zama qosasshe ya zama wankan tarwaxa, ya zama xan gaye, ba zaka tava ganinshi ka gane bai daxe da fitowa daga qauyensu ba. Kan kace meye wannan? Sai gashi ya zama santalelen saurayi saboda ya samu ya xare kan dukiyar Babana, ba wannan ne abin da yafi komai qona min rai ba, irin zuwa gidan mu da ya yi da takardarshi ta kammala karatun Secondary wacce ko credit xin da ake nema bai gama samu ba, amma ya gyara jarrabawar a gidanmu ya tafi (Federal Poly) yayi diploma ya sake dawowa ya shiga (A.T.B.U) yayi karatun digiri xin shi. Amma gaba xaya nawa ‘yan uwan maza waxanda dukansu Maman ce ta haife su suna zaune a gida suna sakarci, sun qi karatu sun kuma qi tsayawa kan al’amuran Babana, su taimake shi kan harkokin kasuwancinshi sai Ado ne dai akan komai, amma wai Mama tana kallo hankalinta kuma a kwance bata da wata matsala. Komai na gidanmu Ado ne yayi matuqar shiga ran Babana, bai gajiya da yabonshi, yanzu zaka ji shi yana cewa “Jarumin yaro ne mai tsayuwa kan al’amuranshi gashi kuma komai kasa shi zai yi maka.” Mutanen da suka san gidanmu suka kuma san Mama da xan uwan nata sun san Mama da Ado sune babbar matsalar da Babana yake fuskan ta amma ba rashin kasuwa ba. Sai dai ita Mama kullum takan danganta matsalar kasuwar Baban nawa da yawan aure-auren da take cewa yayi, musamman wai auren shi na baya-baya wanda aka rufe mishi ido yayi ta kwasar dukiyarshi yana bayarwa. Tun farko zuwan Ado gidanmu ba wani jituwa nake yi da shi ba, saboda bai tava shiga harkar Innata ba, bai tava samun lokacin xaga ido ya kalle ta ba balle ya samu na lokacin gaisheta, haka nan ‘ya’yanta bai mu’malla da su iyakar shi Mama da ‘ya’yanta. Don haka nima sai na zamo bana kallon shi, bana shiga harkokin shi, bana gaishe shi, bana sauraron shi don nima bana son shi. Itama Mama mai ‘yan uwa ce da yawa, sai dai duk jama’ar da suka santa sun san bata wata mu’amalla ta ku zo ku gani da kowa sai da ‘yan uwan da ta haxa uwa da su, bata damu ba ko uwa xaya uba xaya ko uwa kawai in dai uwa tana ciki to shi kenan. Bisa wannan ne ma ta zamo ‘yan uwanta na wurin uba ba kasafai suke zuwa mata ba, saboda komai nisan garuruwansu da suka baro bata yarda baquntar su ta wuce ta kwana uku sai ka ji tana yada magana tana faxin da aka ga ka zama mutun ne fa ake nemanka, amma kana qarami menene ba ka gani ba?” “Kwaikwayonki take yi Mama.” Muna shiga ciki abinda Habiba ta fara faxi kenan. “Kwaikwayo kamar yaya?” tayi tambaya don buqatar qarin bayani, Habiba ta samu damar da ta tsaya rattaba bayani sosai da sosai na abinda ta tarar ina yi. “Maman take yi wa wannan iya shegen?” Babana ne ya qara yin wannan tambayar, na xan kalle shi kaxan can cikin zuciyata na ce tanfar dai yau ba a wurin Innata yake ba, kullum nan ne wurin zamanshi ko da kuwa girkin na wanene amma ita Innata ko girkinta ne, to sai ya faki ido yake shiga wurinta in dai ba qararta aka kai mishi ba zai je yayi mata hukunci nan ne zaka ga ya shiga kai tsaye. Babu ruwan shi da wa ke da haqqi saboda Mama bata yardar mishi baiwa mai haqqi haqqin shi ba. Abubuwan da Habiba ta kwatanta da suka bayyanawa Babana cewar maganar Mama da tafiyarta na tsaya ina kwaikwaya, ya baiwa Babana takaici mai yawa, zuba min ido yayi yana kallona, cikin takaici da baqin rai mai yawa, irin kallon da naga ya yi min xin ya sanya ni nima na waiwaya baya don ganin waxanda suke tsaye. Ado ne da Habiba waxanda su dukan su biyun ana cewa za’a kama ni za su yi sanadin da za a yi hakan. “To ba dole tayi ta kwaikwayona ba, Habiba ai samu tayi duk abinda take yi ai ta sani gata gareta mai yawa a gidan, ga ta kuma ‘yar lelen Baba.” Ta qarasa maganar cikin wani yanayi da ita kaxai tasan abin da take nufi da hakan. Babana ya ce, “Ba fa na son kina yi min irin wannan maganar a gaban yara, ni na ce miki ina da wata ‘yar lele?” Mama ta ce, “Uhun, Alhaji kenan, bari dai in ja bakina kawai in yi shiru tunda ba ni da ikon yin magana, sai ka hayayyaqo min a gaban yara tunda ni ce marainiyar yaronka. Amma in ban da haka iya shegen da wannan yarinyar nan take yi a gidan nan in da wani ne wanda ba a tsoron uwarshi da danginsu ai da bai kwashe qalau ba. Sai dai nima ba ina ganin laifinka ba ne kan hakan da kake yi, da azo ana tuhumarmu kan abin da bai taka kara ya karya ba, ai gara muyi ta haquri da ita.” Da irin waxannan kalaman kullum Mama ke tunzura Babana tasa shi yayi abinda take so, yayi min hukunci irin na azabtarwa, saboda babu abinda ta tsana a rayuwarta irin ta ganni ina zaune lafiya ko da kuwa ba wani walawa nake yi ba. Shi kuma Babana ya kasa tunawa kanshi cewar su dangin Inna basu tava zuwa sun same shi kan wani abin da shi ko Mama ko wani can daban ya yi min ba, duk kuwa da sun saba ganina da tabon duka iri-iri a jikina, su kullum maganarsu kan tsaya ne kan abin da ya shafi ‘yarsu. Sai ya yi ta biyewa Mama yana gana min azaba, ko da yake dai nakan gwammace nashi hukuncin komai tsananin shi akan na Mama, tunda ita bayan duka shaqe ni take yi ta tattara ni wuri xaya ta hau kaina ta zauna, wai sai na ji nauyinta, ita xin kuma ba qaramin nauyi ke gare ta ba, don kuwa jibgegiyar gaske ce. Miqewan da naga Babana yayi, ya sanya ni juyawa da gudu da iyakacin qarfina, don nayi zaton kama ni zai yi, wajen juyawan nawa na banke Habiba dake bayana, shi kuwa Ado na kwantara mishi kwanon dake riqe a hannuna, man gyaxan dake ciki kuma ya kware mishi a fuska da jiki gaba xaya. Mama ta kama salati tana faxin, “Wai ga wani abin al’ajabi, wai ga abin mamaki ni majadan naga abinda ya ishe ni yake kuma nema yafi qarfina.” “Kamo min ita Ado, kamo ta maza in baka bulala ka hukuntata, ja’ira kawai mara kunya.” Babana ne mai wannan maganar, yayin da ita kuma Mama take faxin. “Wannan shi ne wani zance kai baka hukunta al’amarin gidanka ba sai Ado? Kaja mishi kawai qarin baqin jini itama ba so suke su buxe ido su gan shi ba a cikin gidan nan.” Babana ya biyo ni tsakar gida inda nake tsaye ina ta faman vari, ina kuma kuka saboda na riga na tsorata da abinda zai same ni. Innata kuwa tana sunkuye tana wankin kayan ‘ya’yanta bata xaga ido ta kalle ni ba, balle ta ce “Me ke faruwa? Amma sai Babana ya shiga cewa shaqiyancin banza shaqiyancin wofi, mu nan gidan ba a kawo mana shaqiyanci dama kin yi maza kin bari don masu koya miki ba riba zasu ci ba, wahala kawai zasu yi ta ja miki.” Yana gama faxin hakan ya shiga shirva min bulalar dake riqe a hannunshi, wacce yasa Suwaiba ta miqo mishi, na shiga ihu ina buga tsalle ina faxuwa a qasa don tsananin gigicewa. Sai da Mama ta tabbatar na jigata ne ta fito daga falonta tana faxin “Ni fa bana son irin wannan ja min maganar da ka ke yi, kai kasan halin ja’irar yarinyar nan sarai ba a tava ta ba ma ihu take yi don dai ta qulla wa mutane sharri a unguwa ace to ga ta can ana azabtar da ita, tunda tasan muna tsakanin ‘yan sa ido to balle kuma an tava ta.” Yana huci yake faxin “To ina ruwana da maganarsu, za su hana ni yin hukunci a gidana ne?” Mama tasa hannu ta karve bulalar daga gare shi tana faxin, “Ai kuwa dai magana abin a guje ta ne tunda ko kai xin ma kana dai faxa ne kawai, in ban da kana gudun maganar ai wani iya shegen da ba ayi shi a gabanka kana kallo ba. Bata kuxin mangyaxan ni ta sayo min tunda wancan xin a gabanka ta kifar dashi, kana kallo.” “Nawa ne kuxin?” Ya tambaya tare da qoqarin fiddo da wasu kuxin daga aljihun shi, ta ce “Kwalba biyu ne.” daga ni har shi barin abinda muke yi muka yi muka kalli Mama, ni na bar kuka na zuba mata ido shi kuma ya tsaida hannu a aljihunshi ya bar zaro kuxin. “Kwalba biyu ne?” ya buqaci sani, tayi maza ta xaure fuska ta ce, “To zanyi mata qarya ne ba gata ba? Tambaye ta mana. Ni kam ko da Babana bai yi kuzarin tambayata ba qiris ya rage in buxe bakina in qaryata Mama, in ce gongoni ne biyu ba kwalba ba. Sai kuma naga yin hakan ba zai amfane ni da komai ba, tunda ba zai hana Babana biyan kuxin kwalba biyun ba, ni kuma sai in sake shiga cikin wani matsanancin hali, don cewa Mama zata yi na qaryatata a gabanshi yana kallo, ko ma ace Inna ta ce ta sani yin hakan tunda ni kullum laifina na Inna ne, ita ke sa ni komai in dai na sharri ne ko kuma danginta. “Ke da masu koya miki iya shege ba zan yi maganin ku, zan sa qafar wando xaya daku.” Abinda ya ci gaba da gaya min kenan. Bayan ya miqa wa Mama kuxin ita kuwa ta karve su ta juya tayi tafiyarta, bata sake aiken nawa ba wai kar in je in sake kifar mata, can cikin zuciyata kuwa nasan ba sake saye zata yi ba. A kullum irin kalaman da Babana kan furta kenan an koya min halin tsiya an yi min huxubar banza, an cusa min xabi’ar da ba za ta amfane ni ba, zai yi maganin mu alhalin shi xin bai tava kama wani ko jin wani yana yi min xaya daga cikin waxannan abubuwan da yake faxa ba. Illa iyaka dai abinda ita Mama take gaya mishi kenan. Kan hakan ne ma ni ko magana baya yi in dai wadda ta shafi muhimmin abu ne a gabana, sai ta nuna mishi ni ta hanyar yin zunxe ta ce mishi dama dai kayi shiru tunda ga ‘yan baka nan a kusa. Amma ta yarda yayi a gaban su Habiba, waxanda a wajenta wasa zaka ji suna faxin Babanmu ya ce, kaza ya ce kaza da maganar zata fito kuma ya zamo ba wacce ake son ji ba ne sai Maman ta ce mishi ai ta hana shi sakin bakin shi a gabana ya qi ne yasa ta zuba mishi ido. Gidanmu gida ne da ake da qarancin ‘ya’ya maza, ko a xakin Mama mai gadaran uwargidanci da ‘ya’ya maza guda uku ne mazan, mata kuma biyar. To balle ita Innata da ko xaya namijin bata dashi, sai mata guda huxu. To amma su mazan waxanda guda biyu sun ci ace sunyi nisa, Baba da kuma Ibrahim don sune a gaban su Anti Suwaiba da Anti Kaltume waxanda a lokacin aurensu Babana yayi komai don ya burge Mama, ya basu mazan da suke so su da uwarsu, alhalin shi ba sune zavin shi ba, ya kuma kashe maqudan kuxi wajen hidimar auren nasu a kayan xaki da walima gami da ciyar da mutane. Don shi dai ma mijin Anti Suwaiba ko qwaqqwarar sana’a bai da ita, amma Mama taja ta tsaya sai shi tunda shi ne saurayi ai shima Baban namu lokacin da ya aure ta ba komai ke gare shi ba, in ban da ‘yan jamfofinshi guda biyu. To amma duk da haka da taro ya watse sai Mama ta buxi baki ta ce, wai wannan hidimar da Baba yayi bata yi rabin wacce yayi ba a hidimar auren Innata da yayi, har rayuka suka kai ga vaci kan hakan. Sannan a hakan a irin soyayyar da Mama ke yi wa ‘ya’yanta na ace su wasu ne a gan su ace sun burge a kalle su ace babu wasu sai su, Baba da Yaya Ibrahim sun qi karatu tana kallon su babu boko babu Arabi, sai gata a gabanta Ado yazo daga qauye yayi karatu har yau xin kuma ba barin karatun ya yi ba. Yana karatun yana kuma kasuwa ya tsunduma kan shi cikin al’amuran Babana tsundum, mutanen da suka san yanda lamurran gidan namu yake tafiya, faxi suke yi, “Ko da qoqarin Mama wajen samun shigar qanin nata cikin lamurran Babana, to jaruntakarshi kuma ita ce kan gaba wajen saman mishi fada mai yawa.” Duk wata aika da Babana zai yi to Ado ne, shi ne yake wanke mishi kayanshi, ya goge mishi su, daga zuwan Ado gidanmu ne Babana ya daina kaiwa masu wanki da guga kayanshi. Shi ke wanke mishi mota, ya share qofar gida ya sare bishiyoyi in ganyensu ya yi yawa, waxannan ayyuka kuma ya kan yi su ya gama kafin fitowar rana, ba kuma sa shi ake yi ba, shi yake sa kanshi, gashi ya iya girmama Babana, dama duk wani mutumin da ya yi nufin girmamawa. Daga haka ne Ado ya samu shiga wajen Babana, da ma Dattawan unguwarmu duka. Sannu a hankali-sannu a hankali sai ga Ado a shagunan Babana sai kuma Baban ya gwammace zaman adon a kan nasu Yaya Ibrahim da ma sauran yaran shagon. Saboda jaruntakar shi ta wajen aiki da tsayuwa akan gaskiya, daga baya ne da ya lura ya gane ya riga ya samu shiga mai yawa, ya shiga kwashe mishi dukiya suna kashe-mu-raba shi da Mama. Amma su su Yaya Ibrahim ta qyale su suna yawo kan Baburan da ta saya musu da kuxinta da Babana ya yi magana kan hakan da tayi sai ta ce “Kai Alhaji kenan, kai baka saiwa yara ba bayan ga sa’o’insu nan da ma waxanda ba su kai su ba na abokanka wa su har motoci iyayensu suke sai musu.” Ya ce, “Da suka tsaya suna yiwa kansu abin arziki ba? Suna bin umarnin da iyayensu suke ba su in da suma sun tsaya kan karatunsu kamar yanda waxancan xin suka tsaya me zai hana in saya musu? Ai taimakon kai ne da kullum ka baiwa yaro kuxin motar zuwa Makaranta da na kasuwa, ai gara ka dunqule ka samar mishi abin hawa, to su waxannan basu tasa komai a gabansu ba sai la…” Tayi maza ta katse shi ta hana shi qarasawa, ta hanyar faxin “A’a, kar kayi musu baki gara kai, yauwa shi karatun boko ai ba shine kaxai hanyar samun arzikin duniya ba, da shi kaxai ne kai ma da baka samu ko kwabo ba.” Ta juyar da fuskarta can gefe ta daina kallon inda yake. Tun Babana yana yi wa su Yaya Ibrahim da Baba faxa kan abubuwan da suke yi na qin karatu da yawan abokai har ya gaji ya watsar, wataqila ganewa yayi hakanne zai fi komai saman mishi zaman lafiya. Jarumtaka guda xaya da yayi dai ita ce, ta hana su zuwa kasuwa su zauna mishi a shaguna, ita kuwa ko a jikinta sai su wanke goma su tsoma biyar, qa’ida ne kuma wanda ya kai musu abincin ya koma ya kwaso kwanukan in sun gama ci a kuma yi musu shara. Abokansu kuwa sun fi kowa mutunci a wurin Mama, don a bayyane yake bata shiri da mafi yawancin abokan Baba na tun ba Baba Yahaya ba ta ce, babban munafuki kenan. Ana cikin haka suka tasa Mama a gaba wai su a bar su su koma xaya gidan na Babana wanda Ado ke ciki, tunda Baba baya so abokansu suna shigowa gida. Da farko Babana bai yarda ba, amma Mama ta dage to menene ba gashi manne jikin wannan ba ga kuma Ado a ciki? A dole ya haqura suka koma, nima na xan ji daxi duk da dai ana tura ni kai musu abinci, xebo kwanuka da yi musu shara. A fili yake gaba xaya ‘ya’yan Mama daga matan har mazan da ma ita Maman kanta basa sona ba kuma sa iya voyewa, babu halin in xan zauna a cikinsu sai ka ji suna cewa. “Haka kawai muna zaman zamanmu Babanmu yaje ya auro mana wannan matar tazo ta haifan mana wannan shegiyar.” Da zan xago ido in kalle su don sanin ni da uwata suke zagi, sai ka ji sun daka min tsawa, “Daina kallona in ba haka ba in buga miki ranqwashi.” Wata ranar ko nayi maza na kawar da kan nawa na daina kallon nasu sai sun bi ni da ranqwashin. Ko kaxan ba ni da farin jini a gidanmu, nafi kowa baqin jini a ‘ya’yan xakin Innata, na fi su kuma wahala don ni kam kullum a cikin fitina nake, a cikin azaba r duka ba wurin Mama da ‘ya’yanta kawai ba, har wurin Baban nawa. Gaba xaya cewa suke yi wai ni muguwa ce kuma munafuka halina iri xaya ne da na Innata, in yi ta kallon Inn ata ina tunanin yanda halin nata yake, tunda ni ban tava sanin muguntarta ba balle kuma munafurcin. Sai dai kuma abin mamaki, duk da wannan matsi da tsana da nake fuskanta a gidan mu wurin dangin Innata, farin jini ne da ni. Tun ma ba wurin Alhaji Mai kuxi da Hajiya Kubra ba. Tun kuma ba wurin Mallam Mai babban allo da uwar gidanshi Hajiya ‘Yardubu ba, ita kam Hajiya Turai yanda ba kula Innata take yi ba haka nima ba wani shiga harkata take yi ba. A mafi yawanci ma nakan shiga gidan mai babban allo ban leqa xakinta ba in gama in tafi, sai da shi mai babban allon ya koya min bin ta xakin ta in gaishe ta. Su dangin Inna kullum sukan danganta tsanar da ake nuna min a gidan namu da yawan son Innata da kuma tausayinta da aka san ina yi. Donni kam kullum cikin tausayin Innata nake, ban sani ba ko shi ne dalilin da su kuma suka maida ni ‘yar lelensu, ba komai ba ne a wurinsu suyi min sayaiya ni kaxai su bar su Atika da Aliya da Sa’adatu. Kwata-kwata shekaru goma sha uku ne da auren Innata cikin waxannan shekaru kuwa ‘ya’ya shida cif ta haifa, gaba xayanmu kuma mata ne mu huxu muna nan a raye, biyu kuwa babu su. Ni da Atika da Aliya dama a jere muke, sai Zainab da Kubra su babu su, sannan Sa’adatu. Yawan haihuwar Inna ba qaramin damun Mama yake yi ba, duk da cewar da take yi wai mai haihuwar ‘ya’ya mata zalla bai san daxin haihuwa ba tunda shi wai mai son haihuwar xa namiji ne, to amma kuma duk da matan da take haifan ba ta iya zuba ido ba sai da ta xauki matakin shiga tsakanin Inna da mijin nasu. A wannan lokacin ne Mama ta kawo wata qa’ida ta wai in kana goyo to ba za ka yi girkin gida ba, ba kuma zaka je gun miji ba, ko shi xin yazo wurin ka. Kowa yasan don Mama taga haihuwa ta tsaya mata ne yasa ta fito da wannan qa’idar, to amma tunda wanda aka yi domin shi ya yarda itama Innata bata tanka ba, don haka hakan ake yi. Innata bata da miji sai dai ba girki ne bata yi ba, kamar yanda aka ce na wai mai goyo taji da hidimar goyonta, don kar taje tana girki tana qazanta. To amma kuma kusan kullum sai Mama tayi cefane ta ajiye ta fita unguwa ta bar ma Innata girkin da ba nata ba ne tayi. A farkon tasowata xauka nayi kwata-kwata Babana bai son Innata saboda ganin abubuwan da ke gudana a gidan baya iya magana da Inna ko kallon inda take baya yi. Baya sauraron ta komai nashi ko hidimar shi Mama ce, itama kuma Innan bata xaga ido ta kalli abinda ake yi, sai daga baya da na soma wayo na soma fahimtar al’amura sosai, sai na soma yarda da maganganun da mutane da kuma makwabtanmu masu sa ido kan lamurran gidan namu ke yi. Cewar ai babu yanda za’ayi Babana ya ajiye kyakkyawar mace mai kyan diri da kyan halitta irin Innata, bugu da qari ga tsabta da yawan ado sannan ya ce bai sonta, sai dai kawai ya kasa mu’amalla da ita a zahiri, saboda an sha gaban shi. To ilai kuwa, ina soma wayo sai na soma yarda da cewar ba son Inna ne Babana ba ya yi ba, akwai shakku ne mai yawa tsakaninshi da Mama, na kuma qara yarda da hakanne a dalilin ganewar da nayi cewar Mama tana sanya qafarta waje tabar gida da sunan tafiya unguwanninta da kusan kullum sai taje je su. To shi kuma zai dawo cikin gidan ya baro kasuwarshi kenan sai ya tabbatar ta kusa dawowa sannan zai fice ya bar gidan ya koma shago. Yana shigowa gidan kuma zai nufi wurin Inna, wurin da bai rabuwa da tsabta da qamshi saboda ita xin mai tsabta ce, iyayenta kuma masu yi mata hidima ne bata neman komai ta rasa har turaren xaki da na jiki da namu na yara kawo mata ake yi. Baba yana shigowa gida in dai Mama bata nan to zaka ji yana magana cikin natsuwa “Ina Fatima take?” ko kuma ya ce, “Ke Humaira ina Mamanku? In gaya mishi sai ya nufi inda take xin. Sai dai Inna bata sauraron shi. Innata mai kyau ce, gata da kwalliya ga tsabta duk da nasan ta ne a shekarun da tayi fama da matsalolin aurenta saboda fin qarfin da kishiya ta yi wa mijinta, hakan bai hana ni sanin kwalliyarta ba. Haka nan mutanen da suka san farkon zuwanta gidan basa gajiya da faxin kai ai farkon zuwan yarinyar nan gidan nan anyi wani abu a wurin, ga kyau ga ado ga yauqi ga murmushi ga ta kuma da girmama mutane. Rannan ma Mama bata nan tun safe ta bar gidan ita da su Suwaiba. Babanmu ne ma ya xauke su a motarshi ya tafi dasu wai anyi mata haihuwa, ni da Inna ne kawai a gida sai ko Sa’adatu. Suma su Atika sun tafi Makarantar allo, ni na taimaki Innar ta gama`aikin abincin ranar da Mama ta tafi ta bar mata. Sai da mukk kammala kooai ta shiga xakknta don yin wanka, ni kuma na tsaya ina gyaaa kicin xin da muka yi aikin a ciki. Yayin da sa’adatu ke bayana tana ta tsala uban kuka, muna cikin haka sai ga Babana ya shigo. “Ke Humaira ina Innarku take?” nayi maza na ce mishi sannu da zuwa Baba, wanka take yi. Ado ya shigo ya ajiye kayan cefanen da yazo dashi, Babana ya kalle shi ya ce mishi, koma shagon sai an yi sallah sai ka zo ka xauke ni. Cikin ladabi ya ce mishi, to ya juya ya tafi, shima Babana ya shiga wurin Innata, bai daxe da shiga ba naji Innan tana cewa, ina kike? Kawo min ita, na ce to, naje zan kai mata ita. Tana zaune kan kujerarta ta kwalliya a gaban mudubi yayin da Babana ke tsaye a bayanta yana magana a hankali tare da kallon abinda take yi na gyaran gashinta. Ke fa halina dake kenan, ke fa halina da kenan babu halin in dawo gidan nan saboda ke sai kin vata min rai, to ka daina dawowa mana, tayi maganar a wani yanayi da ya sanya ni hanzarin cewa, gata don su san na shigo xakin. Har ta miqa hannu zata karve ta sai kuma ta ce min shiga ban xakin can kiyi mata wanka sai ki kawo min ita don kar ta vata min jiki. Na ce to, na je yin abinda tace xin duk da kukan Sa’adatun. Ina cikin yi mata wankan naji Babana yana cewa, wai me kike nufi ne da waxannan abubuwan? Ta ce abinda nake nufi kenan mu zauna kamar yanda aka ce mu zauna. Ya fara magana kamar zai yi faxa ban san dalili ba sai kuma naji ya canza yana cewa ke baki da wayo, tayi maza tace eh, ai nima na sani. Zo ki ji abinda zan gaya miki, bata kai ga bashi amsa ba na fito da Sa’adatu zan bata ita har lokacin bata gama shafe jikinta da mayukan dake kan madubin nata ba, waxanda ni na kawo mata su daga gidan Alhaji Mai kuxi. Ke tafi da yarinyar nan Babana yayi maza ya daka min tsawar da ta sani nayi maza na juya na bar xakin na fito tsakar gida ina rarrashinta daga baya mana goyata na nufi zaure naja na tsaya ni kaxai jikina sai faman vari yake yi saboda tsoron abinda zai faru tsakaninsu, tunda na fara jin Baba yana cewa ai tunda kin ce ba kya jin rarrashi to kuma wannan abin da ya shafe ki ne kin san dai baki isa… Ban yarda na ji qarshen maganar ba saboda tsananin tsorarta da nayi na kar in ji ya nufe ta da duka. Lokaci mai tsawo Baba ya xauka bai fito daga xakin ba tun ina tsorace har dai na haqura na shiga sabgogina tunda itama Sa’adatun ta haqura tayi barci. Sai zuwa can naga ya fito ya shiga wurin ya xan daxe kafin ya sake fitowa yazo zai wuce mu a zaure ya kalle ni ya ce min, kai mata ita ta shimfixe ta nayi maza na ce mishi to. Ina shiga xakin Inna gabana ya sake faxuwa, saboda kukan da na same ta tana yi, gashi kuma gaba xaya kwalliyarta dama gyaran gashinta sun lalace. Tasa hannu ta karvi Sa’adatu suka kwanta tare tana bata nono, ni kuma na fito na shiga kicin don bin umarnin da ta ba ni na xora mata sanwan abincin dare. Kullum qa’idar Babana kenan Mama tana barin gida zai dawo ya samu Inna ko da kuwa dawowar nashi zai zama dalilin faxansu, ya tafi ya barta tana ta kuka ya gwammace yin hakan. Har a wurin dangin Baba Innata ba wani farin jini ne da ita ba saboda Mama ta riga ta saye su da ‘yan kyaututtuka gashi kuma ita Innan a cikin kulle mai tsanani take, don ko nan da can Babana bai barinta taje. Koda kuwa abinda ya shafi danginta ne sai dai in dolen ta kai dole, ‘yan uwan Babana da suke son Inna sune waxanda suka haxa uwa da uba da shi waxanda Mama take mu’amalla da su ta koma vangaren ‘ya’yan da yake uba xaya dasu. Don a cewarta na uwa xaya uba xayan su da uwarsu ma’ana kakarmu kenan basa nufinta da komai sai sharri don su suka fi kowa son ganin Baba yana aure. Tsiyar mutum ba zai sihirce mata yaya ya mallake mata su ba. Duk da halin da zaman Inna ke ciki a gidanmu na rashin ‘yanci da rashin walwala ga rashin damar yin mu’amalla da miji a bayyane sai dai komai a xarare koma a tsorace, hakan bai hana kishin Mama tsananta a kanta ba. Kullum qawayenta suka zo ko wasu ‘yan uwanta da take yarda ta tattauna sirrinta dasu to hirarsu bata wuce hirar Inna. Idon su a kanta yake, hankalinta da tunaninsu gaba xaya wurinta yake tafiya. Rannan ina jin ta ita da aminiyarta Hajiya Anwamu, kai wannan ja’irar yarinya da an barta ta samu sakewa a gidan ita da mijinta da ban san yanda ta zama ba. Mama ta kalli inda Inna take shanyar kayan ‘ya’yanta da ta wanke a daidai lokacin da Anwamu ke cewa, ni fa ba kyanta ne yafi komai qona min rai ba, game da ita uh’uh, tsabtarta tafi komai vata min rai. Mace mai tsabta majadan ke da mummuna ce jan hankalin miji ne da ita, to balle wannan shi yasa na ke gaya miki daina barin yaran nan suna tara miki kayan dattinsu a xakinki kowacce ta tuve to ta wanke kawai. Ta xan ja tsaki kaxan kafin ta ce uhun, ai mazan nan suna qwararmu. Sai da suka ga mun fara kaiwa inda muka kai sannan suka xebo tsala-tsalan ‘yanmata ‘ya’yan cikinsu suka kawo mana, yanzu wannan in ka ce zaka sa wa miji ido a kanta ai sai ranka ya vaci. Shi yasa ni a gidana har sayar mishi da girkina nake yi, ko in bashi kyauta ta cikin hikima kuma in san yanda nayi na fanshe ta wata hanyar, tunda in ya kwana wurin nawa ma menene? In ban da kayan vacin rai. Mama tayi maza ta qyalqyale mata da dariya, ta ce tafxijan ai ba zan iya irin wannan sakarcin naki ba. Ta kwashe bayani tsab na sabon tsarin da ta kawo a gidan na cewar mai goyo bata da miji bata kuma da girki saboda xawainiyar goyonta. Hajiya Anwamu ta ce, anya Majadan a hakan kuwa ake har yanzu? Qwarai kuwa, in ji Mama, ai tunda ta haifi ‘yar nan har yanzu ban vata girki ba, shi kuma kin san ba ma mai irin wannan fitinar ba ne, da dai an yi. Amma yanzu ko harkokin cuxewar kasuwar nan da ake ciki ai ta isa ta hana mazannan namu kuzari. Anwamu ta ce haka ne jimawa kaxan ta sake waiwayawa ta kalli inda Inna take zaune tana taje gashin kanta data gama tsefewa ta ce uhun, ni kam da za’a bar ni da na ce yarinyar nan ciki ne da ita. Mama ta zabura da sauri alamar kaxuwa ta ce ciki? Kai haba wane irin ciki to a ina ma ta gan shi? Ita ba fita take yi ba balle in ce suna haxuwa a wani wuri shi kuma ba dawowa gida yake yi ba in bana nan tunda ai ko da nake fita unguwa da yaran don bana barin su balle ace sune zasu yi girkin dana bari ai kullum ina tambayar Ado da bana nan kun zo gida ne? Sai ya ce min ni dai nazo na kawo cefane Inna ce Alhaji fa? Sai ya ce a’a shi bai lura ba. Cikin zuciyata nayi mamakin jin yanda duk da baiyananniyar qiyayyar da ado ke yiwa Innata ya qi yarda ya gayawa yarshi gaskiyar abinda yake faruwa tsakanin Innan da mijin su in bata nan. Mama ta sake kallon Aminiyar tata ta ce, mata ai kin san ita xin bata rabo da shafe-shafe kullum a cikin shi take shi yasa nake cewa ita xin ba wata fara ba ce mai ne kawai ya maida ita haka. Hajiya Anwamu ta ce, to ba zan yi miki musu ba, amma ni dai nasan matar da aka hana miji ya kama hannu tsabtarta da ban take da irin ta wannan yarinyar. Kalli kyan kitson da ta tsefe ke da kike da mijin kalli kitson da yake kanki. Cikin zuciyata na amince da cewar ita Hajiya Anwamu mata ce mai auna komai a mizanin hankali, don kuwa ni da kunnena nasha jin Babana a irin ranakun da yake dawowa wurin Inna in Mama bata nan yana cewa Inna. Nafa ga ji da ganin wannan kitson a canza min shi a kuma zizara min lalle in gani in xan ji daxi, wani lokaci ma zan gan shi yana vata kuxi masu xan auki yana cewa ki sayi sabbin under wears ki kuma bada sabbin xinkuna tunda nasan kina da zannuwan da ba a xinka ba. A duk lokacin da yayi irin waxannan maganganun kuwa to ko da bata tanka mishi ba, to zaka ga tayi abinda yace xin, za kuma ta nuna mishi in an kawo. Don haka nima na yarda yawan kwalliyar Innata har da yawan kulawar Babana na voye. To sai dai ita Mama duk da wannan hannunka mai sanda da aminiyar tata tayi mata don ta lura tasa ido ko zata yi sa’a ta gano abinda ke gudana ta qi yarda ta mace to taja ta tsaya kan cewar ai shi Babana ba ma zai kwatanta wani abu makamancin abinda ake za ton ba, don yasan karonsu da ita. Ban da haka ma ta riga tayi sa’a ba abinda yake gudu irin vacin ranta in ban da haka ai da zama da waxannan bai zamo mai sauqi ba a wurin kullum fa sai tsohon nan ya zo gidannan wai yazo ganinta sai kace shi kaxai ne ya haifi ya a duniya. Ai kin san dai ba haka kawai yake yi mana wannan zaryar ba. Hajiya Anwamu ta riqe baki nuna alamar mamaki ta ce ai fa kam da walakin wai goro cikin miya, kin kuma san shi fa duk ‘ya’yanshi da jikokin shi da ake aurarwa inda duk suka je ai karve gida suke yi in ban da nan xin. Mama ta gyaxa kai alamar jin daxin cewar da aka yi ita kaxai ce ta gagara. Mama da ‘ya’yanta sun qi sun kuma tsani ace wai ni xin kama da Babana nake yi, balle ma ni yayi suvutan baki yace ai duk gidan nan babu mai kama da Alhaji Surajo irin Humaira sai kaga ta taso da faxanta kuma da iyakacin gaskiyarta faxin zata yi rai a vace tana faxin wannan ai wulaqanci ne. A ce duk ‘ya’yan da aka haifa a gidan nan ba a samu mai kama da Alhaji ba sai akan wannan mummunan yarinyar, to ta ina kamannin nasu yake? Ku nuna min don in gani. Duk da wannan baloqoqo da zare ido da Mama ke yi don hana faxin kamannin nawa da mahaifina su can wurin dangin Inna sun dage kan wai ban xauko komai na Mahaifiyata ba, har ma basa gajiya da bayar da labarin wani abinda ya faru sanda Innan take goyona suyi ta dariya. Wai ana hidimar aure ne a gidan Alhaji Mai kuxi sanda ya auri amaryar gidan ta yanzu Furera Jama’a sun cika sai aka shigo dani ana tambayar ina uwar wannan yarinyar take? Mai tambayar qanwa take wurin mai babban allo, don haka Inna tayi shiru tana kallonta bata ce mata gata ba. Sai da Hajiya Kubra tazo wucewa taga abinda ke faruwa shi ne ta kalli Inna tayi mata dakuwa, ta ce shaqiyancin banza kina kallo ana tambaya ina uwar yarinya ba za ki sa hannu ki karve ta ba sai kiyi shiru kina kallo? Sai a lokacin ne mai tambayar ta kalli Inna ta ce yau ga abin mamaki, Binta ce ta haifi wannan baqar yarinyar? Gaba xaya aka kwashe da dariya tayi murmushi ta ce Ubangiji ya rayata ya kuma sa mai albarka ce aka ce amin. Ko kaxan ni xin bana kama da mahaifiyata, don kuwa yayin da Inna take fara sol, ni xin baqa ce. Inna mai dogon gashi ce ni kuwa gashin kaina matsakaici ne sai dai akwai laushi da santsi da kuma cika kai. Inna dara-daran idanuwa ke gare ta, ni kuwa nawa madaidaita ne, sannan ita siririya ce ni kuma ba ni da jiki bani kuma na ma xarata tsayi kaxan, to amma duk da haka su Mama sun ce Inna ba da ita nake kama ba, to a danginta na samo kamannin nawa. Rannan muna kwance kan gado xaya ni da Innata yayin da su Atika da su Aliya suke xaya xakin nata donni kam duk in da Inna take ba na iya barin wurin ko da kuwa Babana yana nan sai in shi da kanshi ne ya kore ni. Kan hakanne mutanen gidanmu suka qulla mata sharri har ya bazu mutanen waje ma suka ji wai duk cikin ‘ya’yanta tafi sona har ma wai bata haxa son nawa da na kowa. Ni kam cikin zuciyata cewa nake yi aniyar kowa zata bishi, in ma mai faxan yana faxa ne don ya haddasa mata matsala cikin ‘ya’yan nata mun san duk xaya muke a wurinta. Inna kamar ki bani gashin ki tayi maza ta juyo ta kalle ni cikin yanayinn murmushi ta ce na ki fa? Na xan yi magana cikin natsuwa na ce ai nawa ba mai yawa ba ne irin naku ke da su Atika, su kam sun ji daxi kama dake suke yi. Su masu kyau farare sol-sol ni kuma baqa mumm….kan in qarasa tayi maza ta xaure fuskarta nima nayi maza nayi shiru waya ce miki baqi muni ne? Ta zuba min ido tana kallona, sannan ta xan saki fuska kaxan ko kaxan baki da muni ba kuma zaki yi ba, ko kin ji ana ce miki mummuna kar ki sake damuwa ki dai kuxura ranki cewar za ki natsu ki zama mutuniyar kirki mai kamun kai da natsuwa. Mai girmama na gaba da ita, mai jin maganar iyaye, mai maida hankali akan karatunta mai jin tausayin qannenta, kin ji ko? Nayi maza na ce mata to Inna, ta juya ta ci gaba da kwanciyarta zuwa can sai naji ta ce min, kin fara girma yanzu kuma ke xin mai manyan varage ne, amma duk da haka ina so kiyi karatu tunda ni ban samu damar yi ba, don haka kar ki yarda ki kula kowa kiyi karatunki kawai nace mata to. Yawan maganar karatu da Inna kiyi min yasa na zamo ko a bani kuxin Makaran ta ko kar a bani to zan taka da qafata in tafi Makarantar secondary ta qofar fada inda muke karatu. In na tashi kuma sai in qarasa gidan Malam mai babban allo in ci abinci in huta in na yi Sallah in zo gabanshi in biya karatuna na Alqur’ani da kuma littattafan sannan sai ya bani kuxin mota in shiga in dawo gida. Kan hakan ne Mama take cewa Babana wai ba ina zuwa makarantar don nafi kowa son karatun bane a’a ina zuwa ne saboda gidan mai babban allo, su kuwa su Habiba ba su da kowa a wurin shi yasa suke fashin zuwa. Rannan na dawo gida daga Makaranta da yamma babu kowa cikin gidan sai Innata sai kuma Babana shi kuwa na san ya dawo ne a dalilin yasan Mama da ‘ya’yanta basa zuwa, nayi zan shiga falon Inna sai na ji Babana yana cewa kai kukan mata sai a barku. Wato ashe duk ta sani a gaban nan da aka yi a kanki bin ta bai ishe ki ba? Ke kin fi so dai kiyi ta ganina cikin fitina? Ki voye ciki a jikinki wata bakwai ba za ki gaya min ba sai yau? Alhalin kuma na tambaye ki yafi sau nawa in akwai shi ki faxa don a san yanda aka yi dashi tunda ina amfanin fitina? Inna ta ce babu, to yanzu yaya za’ayi kenan? Ta sake ce mishi ai ban sani ba kai nake sauraro. Ya ce to kin ga ni bana son abin da zai tayar min da hankali. Ina ganin asibiti kawai zamu tunda kema gashi ko yaye yarki baki yi ba, bata ma tafiya, uhun, sannan ana ganewa sai ace ba ki da miji amma ga ki da ciki yaya kenan? Inna ta ce, kana nufin kenan a cire? Ya ce eh to kin san wani abin dole kan saka kayi shi ba don kana so ba, ni fitina ce bana so. Ta ce, to ai sai ka gaya mata kawai cewar ba naka ba ne, yayi maza ya daka mata tsawa ta hanyar tambayarta wane irin zancen banza ne wannan? Nan take ta soma kuka tana faxin ita ya maida ita gidan su ya taimake ta ya mayar musu da ita tunda ita bata da halin zuwa da kanta su barta ta zauna. Inna ta urunce da kuka gaba xaya tana faxin ya mayarwa iyayenta da ita tunda akan tsoron kar matarshi tasan tana da ciki zai iya kaita wurin haluka hankalin Babana yayi matuqar tashi. Ya shiga faxin ni Binta? Ni da bakina na ce ki zubar da ciki? Na ce muje a san menene abin yi? Nayi sallama a bakin qofar sau biyu kafin ya amsa na shiga ina wucewa zuwa xakinmu shi ma yayi maza ya fita wataqila dama zaman ya ishe shi. Washegari kuwa da safe sai kawai ga qaton cikin Inna ya baiyana tanfar dai dama wani abu take sa wa tana xaure shi manyan riguna da hijaban da take sanyawa ma yau taki zani da riga ta saka da tayi wanka bayan ta gama kwalliyarta ta fesa turare ta kuma shiga zirga-zirga da kaiwa da kawowan da ta saba ba a xauki wani lokaci mai tsawo ba kuma na ji Mama tana wani irin firgitaccen salati a tsakar gida. Wannan menene ki ke son nuna min shi Fatima? Ciki ku ka yi ban sani ba? Lalle yau za’ayi abinda za’ayi a gidan nan, dama cin amanata kuke yi kuna satar kwanana?” Inna kam bata tanka mata ba, aikinta kawai take yi. Mama kuwa sai faman zuba ashar take yi tana faxin “Su Habiba su fita su kira mata Babanmu, duk inda yake.” Inna ta bar tsakar gidan ta dawo xakinta tayi zamanta, na kuwa san in ban da tasan ba zata tava Inna ta kwana lafiya ba, da ta gwada yin hakan. Rannan cikin dare ba mu san abin da ya faru ba, iyaka dai da sassafe naga Babana ya shigo xakin Innata, na ji shi yana ce mata “To buqatarki ta biya Binta kin nunawa Mama cikinki kin tayar mata da hankali, kin yi sanadin da tayi yaji ta bar miki gidan, shi kenan ko? Inna ta ce, “Tana da gata ne tana da wurin zuwa ni da ba ni da wurin zuwan ba gashi…” yayi maza ya katse ta “Muje can xakina sai muyi magana.” Inna tayi maza ta ce wa? Tafxijan. Rannan Baba ko tsakar gidanmu bai leqo ba, yana xakin Inna suna ciki su biyu gaba xaya hidimar gidan ni aka bar wa har abincin rana sai bayan Azahar na ganshi ya fito ya shigo wurin shi yayi wanka ya tafi Masallaci. Da ya dawo ya ci abinci ne na ji shi yana cewa, “Bari in je kasuwar in ga abinda suke ciki.” Ta ce mishi “To, a dawo lafiya.” Har washegari Mama bata dawo ba, a dalilin Babana bai je biko ba duk da aiken da aka yi na ana neman shi, gidanmu ya zama gwanin daxi sai murmushi yake yi yana hirarshi maimakon da da kowane lokaci fuskarshi a xaure. Kwanan Mama biyu sai ga Baba Yahaya ya dawo da ita. Da alama shine yaje bikon ta kuma biyo shi duk da cewar da take yi shi xin munafuki ne. Mama ta dawo gida cikin wani qarin zafin ita kanta dai kana kallonta kasan tana cikin vacin rai mai tsanani, ban da haka kuma kallo xaya zaka yi wa fuskarta ka gane ashe ba qaramin gumurzu suka yi da Baban namu ba kafin ta tafi. A tsakar gida Babana ya zauna shi da Baba Yahaya da Maman suna maida magana, don Maman ce ta nemi ayi hakan duk da shi da ya kawo ta cewa ya yi to ni na tafi Allah ya kiyaye na gaba.” Ta ce, “A’a ai gara ka tsaya ka ji abin da abokin naka yake yi.” Mama ta maida bayanin komai dalla-dalla na yanda aka yi taga Inna da ciki alhalin ita xin bata da kwanan miji. Baba Yahaya ya kalle ta ya ce, bata da kwanan miji kamar yaya? Ta sake rattabo mishi wani bayanin har dai ya fahimci komai. Sai dai maimakon yayi magana kan cin amana da zaluncin da ta ce anyi mata, na satan mata kwana a kai wa wata sai reshe ya juye da Mujiya. Baba Yahaya ya soma yiwa Babana magana cikin vacin rai mai tsanani, ba laifin Hajiya Majadan ba ne duk abinda yake faruwa a gidan nan Alhaji laifinka ne. Da ka kasa tsayuwa da qafafunka ka zama kaine mai zartar da hukunci a cikin gidanka. Yanzu ace an zartar da hukuncin hana ka baiwa binta haqqinta na kwana har sai ka saci jiki ka shiga wurinta don kawai bata girki? Girkin me nene? Ita mace dole ne sai tayi girki kafin ayi aure da ita? Yarinyar nan guda nawa take da kake yi mata irin wannan zaluncin? Har yau xin nan fa bata cika shekaru talatin ba tana da shekara goma sha shida ne aka baka ita. Yaya za’a rinqa gana mata azaba ana wulaqantata kana kallo? Maimakon ayi maganar da zata zamo mai daxi ga Mama sai kawai aka shiga yin wadda haqurinta ya kasa jura, ta shiga gaggayawa Baba Yahaya maganganu. Ya kalle ta ya ce, ba laifinki ba ne shi ya bar ki ki ka zame mishi haka, da har ki ke ganin matarshi da ciki kina tuhumar shi yanda aka yi.” Yayi ficewar shi ya bar su nan a zaune. Mama ta shiga bori da zage-zage, tana faxin wasu irin maganganu tamfar dai ba daga bakin babba mai shekarunta suke fita ba, Babana yana jin ta bai ce komai har lokacin mai tsawo. Ban san yanda aka yi ba sai kawai na ji ya daka mata tsawa mai qarfi ya ce, “Ya isa haka. Ya kuma ishe ki haka kin gane?” abin mamaki sai kawai na ji Mama tayi xib, tayi shiru. Cikin zuciyata na ce, “A’a ashe dai itama tana xan tsoronshi ina ma dai ace kullum irin wannan tsawar yake yi mata da wasu abubuwan da yawa, ashe da bata yi su ba. Babana ya shirya ya fita ya bar gidan, ni ma naci gaba da abin da nake yi ban san abin da nayi ba sai kawai na ji Mama ta zo ta fincike ni tana jana zuwa xakinta. Tuni na saki kwanon dake hannuna ya faxi na shiga kuka ina magiya ina bata haquri, don kuwa nasan karonmu da ita a kullum nakan gwammace ta haxa ni da Babanmu ya buge ni duk da tsananin dukan nashi don shi duka kawai yake yi min baya shaqe ni. Mama kuwa bayan shaqa ma sai ta ce sai ta hau kaina ta zauna. Duk da magiyar da nake yi mata bata fasa ba, can cikin xakinta ta kai ni ta shiga gana min azaba tana yi kuma tana cewa wai ke ga shegiya ko? Na bar muku gida kuna murna ke da uwarki, to na dawo zan kuma yi maganinku.” Gajiya Mama tayi ta qyale ni don kanta, babu wanda ya zo ya qwace ni, tunda ba ma kowa a cikin gidan in ban da Inna da sauran yaran gida, ita kuwa Inna ko meye za a yi min bata yin magana. Da kyar na fito na dawo xakin Innata na kwanta ban iya fitowa ba sai wajen yamma. Ina fitowa su Habiba suka kalle ni suka kwashe da dariya suna faxin ta ji jiki ban kula su ba. Tunda Mama ta dawo Babana ya sake kama fuskarshi ya tsuke tanfar ba shi ne ya wuni yana murmushi ba, jiya da shekaranjiya, yana dawowa ya shiga xakin Mama suka yi maganganunsu, kuma ya fito yazo ya shiga xakin Innata ranshi a xaure. “To ai sai ki fito kizo ki xora abincin dare ko, ko shima ba za kiyi ba ne za ki bar mutane da yunwa kamar yanda ki ka bar su da rana?” Inna ta kalle shi ta ce, “A’ah ni ce kuma mai girkin ba gata ta dawo ba? Ya yi maza ya ce, “A’a ba za ta yi ba karvi girkinki kawai tunda dai taimakonki da aka yi aka hana ki yin girkin ya zama laifi a kanshi ake kiran mutane azzalumai.” Inna ta kalle shi kawai ta juyar da fuskarta gefe, bayan taja mishi wani irin mummunan tsaki, sai dai kafin takai ga gama tsakin nata yayi maza ya wafce bakin nata da duka. A kixime nayi tsalle nayi waje ina qurma ihu, saboda razana. Inna da ta wuni cikin wani yanayi da na kasa fahimtarta za kuma a buge ta, ban san yanda aka yi ba na gan shi ya fito yana cewa, in ba za ki fito kiyi girkin ba sai a zauna haka, waye mai qananan ‘ya’ya a gidan in ba ke ba? Rikici yayi yawa a gidanmu, gaba xaya an daina yin girki, Mama ta qi yi itama Innan ta qi. Gaba xaya gidan babu daxi, gaba xaya an shiga wani hali na wani yanayi. Ni da kaina na qara shiga wani yanayi na tsoro saboda irin kallon da Mama ke yi min, Babana sai jin haushin Inna yake yi, yana faxin wai dama abin da take son ganin ya same shi kenan, shi yasa tayi abin da tayin gashi kuma ya ce ta karvi girki ta qi ta ce ba zatayi ba, tunda dama can ba a bata girkin ba sai yanzu? Rannan da sassafe ya shigo xakinmu bai ma tsaya amsa gaisuwar da take yi mishi ba, ya ce mata, shirya kije gidan ku.” Ta ce, kai madallah, ya juya ya fita ni kuma na soma kuka yayin da ita kuma ta shiga shirya xakinta tana kwashe kayayyakinta masu daraja tana kai su xakin kwananta tana kuma gaya min abinda take so in rinqa yi wa qannena, ni kam ko amsawa ba na yi saboda kukan da nake yi. Ta gama kintsa komai ta kulle wurin ta jefa xan makullin a jakarta sannan tayi shirinta tamfar wacce zata unguwa, ta xauki jakarta ban sani ba ko kukan da taga ina tayi ne ya sa ta ce min xauko min jakar muje ki raka ni sai kiyi sauri ki dawo ke Atika kar ku fita ko ina, suka ce to.” Muka fito sai da muka yi wa Mama sallama bata wani amsa ba muka wuce muka fito qofar gida muka shiga Taxi zuwa gidan Alhaji Mai kuxi, sai dai savanin yanda ni da Inna muka zata cewar Babana ya ce taje gida ne da wata manufa ta barin gidan. Ashe qararta ya kai wajen Alhaji Mai kuxin. Faxa mai tsananin Alhaji Mai kuxi yayi mata, tayi ta kuka bai kuma fasa yin faxan ba, haka nan bai bata wata dama ta cewa ga abinda aka yi mata ba. Sai bayan fitarshi ne ta samu ta yi wa Hajiya Kubra bayanin komai, ta yi dariya ta ce ai in baka iya tsiya ba to ba ka yi wa kanka ba, ashe kema kin iya iya shege? To amma ai da ya baki umarnin karvar girki sai ki bi ba kema ki bijire ba. Wato shi babu wacce zai tanqwasa ta tanqwasu kenan? Ba ki kyauta ba ai kin rama abinda tayi miki yaushe rabon Mama da yin yaji in ban da wannan karon? Ki koma xakinki in kun je kuma ki ka samu bata xora girkin ba ke kuyi rashin girki a gida ai wulaqanci ne ta ce to, muka kamo hanya muka dawo gida. Muna shiga xakinmu Inna ta ce min in je in gyara mata kicin, ban kuma san abinda ta tuna ba ta ce min ke dawo, taje ta kama aikinta da kanta, ta gama girkin aka kaiwa Mama abinci ta ce ta qoshi, suma su Habiba haka. Ta gama komai ta kintsa ta dawo xakinta tayi sallar Magriba ta zauna taja carbi sai da tayi Isha’i sannan ta shiga tayi wanka ta fito ta shafa mai tasa su Atika suka je suka kwanta, mu ma muka hau gado zamu kwanta sai ga Babana ya shigo. Fuskarshi a xan sake, yana xan dube-dube kina fa jin daxinki Binta, sai kawai ki kalelece jikinki da xakinki ki tasa ‘ya’yanki a gaba kuyi kwanciyarku cikin qamshi babu abinda ya dame ki da miji ba kya nemanshi saboda ba ki damu da shi ba. In dai ‘ya’yanki suna kusa da ke to shi kenan zance ya qare, musamman ace ga Humaira, ta ce eh to su na mallaka sune nasan da wuya ace an yi nasarar raba ni da su a zihiri da baxini, amma miji fa? In na qwallafa rai a kanshi ai sai in yi ta wahala tunda ba zan same shi a lokacin da nake so ba. Yayi murmushi ya ce, qarya kike yi ki ce in kin neme ni ba za ki same ni ba, ba ki neme nin ba ma ina kawo miki kaina duk da vata min ran da kike yi, ban tava bari kin rasa ni ba, wurina girki kawai aka hana ki amma ba a hana ki mijinki ba, kuma da aka hana ki girki da kwanan ai ba kiyi magana kin ce ba ki yarda ba, shiru ki ka yi nima na taya ki yin shirun. Inna ta ce, kai dai ai sha’ani, ya ce to shi kenan ai sha’anin zance dai kuma ai ya qare, tunda gashi yau kin karvi girki ga ni kuma a xakin naki. Ban san yanda aka yi ba wataqila sai lokacin Babana ya ganni a bayan Inna don tsawa na ji ya daka min ya kuma shiga yiwa Inna faxa, ina dalilin da take barina ina shigowa nan xakin ina kwanciya bayan ga sauran ‘yan uwana a can. Sum-sum na tashi na fita. Tuni aka koma wani irin zama tsakanin Mama da Babana sai su suka san irin shi duk kuwa da cewar shi xin baya iya shiga xakin Innata akan idonta, ko da kuwa girkin nata ne, ko da daddaren ne ma yakan shigo ne bayan ya xan faki idonta. Amma duk da haka bata gamsu ba tunda dai tasan yana shigan, a wannan lokacin bata da wani zance da ya wuce na kowa ya ji tuwo-tuwo da ita miya ya sha. Ai wannan cin mutunci da aka yi mata in bata rama shi ba to ba iyayen da suka haife ta ne iyayenta ba. Inna kuwa bata kulawa ko dama can kuwa ba xabi’arta ba ne tunka maganganun Mama sai in ya zame mata dole, haka nan kowane lokaci Babana ya shigo xakinta. Ba ta ce mishi don me? Ko kuma sai yanzu? Sai dai kawai tayi amfani da wannan damar wajen ganin ta kyautata mishi kamar yanda Hajiya Kubra tayi mata umarni. Inna tayi girkinta na kwana biyu ta fita girkin Ado ya kawo cefane babu alamar Mama zata karvi girkin tayi na fito daga xaki zan je aikan da Innan tayi min sai na ji Adon yana ce mata. “Haba Mama, gidan nan fa ko an qi ko an so gidanki ne, yaya za ki rinqa yin abubuwan da kowa zai gane akwai matsala tsakaninki da Baba, kin ce za ki yi maganinta na ce eh, yana da kyau kiyi hakan to kuma sai kiyi ta qin yin girki? Bayan kin san babu abinda Baba ya qi irin hakan? Yanzu wannan abin da ya farun ba murna suke yi ba? Kuma don kin ganta da ciki bata da kwana sai me? Sai ki xaga hankali? Shi Baba fa ina ganin kamar in aka cika mishi ciki zai iya xaukar matakin da babu daxi, ki wastsake kawai ki koma hidimarki, ki sake kama mijinki, ki tattare abinki ki riqe kar kiyi sakacin da zata samu wata dama a kan shi, don haka kar ki bari yau mu dawo daga kasuwa ba kiyi girki ba, abin ba zai yi kyau ba in da hali ma sakwara za ki kirva don na ji ya ce min yana marmarinta. Ki san yanda ki ka yi ku ka daidaita in yaso sannu a hankali sai kiyi maganin nata cikin ruwan sanyi daga ita har wannan mara kunyar ‘yar tata. Nayi maza na kauce na bar wurin don kar su hango ni, Mama ta ce a kamo mata ni, cikin zuciyata na qara qin Ado na ce, ina ma dai Tanko aka sanya mishi ba Adam ba, tunda halin shi yafi kama da halin mata baya gyara sai zuga gashi da taya kishi maimakon ya zamo mai ba da haquri. Kan in dawo daga aika sai kawai na samu Mama kace-kace a kicin tana aikin girki, naje na faxi aikan da aka yi min xin na zo na shiga kicin na soma taya Mama aikin girkin abincin daren da zata yi tunda in ba hakan nayi ba sai in shiga wani hali alhalin su Habiba ko suna kallonta ta nayi ba taya ta suke yi ba. Ni kam bana iya qin taya ta don ina tsoron Mama ina kuma tsoron azabar da take gana min. Tunda Mama ta shawo kan Baba suka daidaita sai kuma al’amura da yawa suka yi ta vullowa, a yanzu in tayi girki to xan qanqani take sawa Innata, mu ma ta xan minxira mana su kuwa su Suwaiba ta tura su xakinta ta zuba musu yanda suka ga dama in mun zo mun ce ba mu qoshi ba sai ta ce kuje ku sha ruwa. Da yake an ce muku akwai wata baiwar uwarku a gidan nan da zata rinqa yi muku girki kuna wage bakunanku kuna xurawa, duk zaku ci uwa ku daga ku har uwar taku ba dai ta ce itama ita ce ba? Ni da ku ne a gidannan ni kam tunda naje neman qari ta rattaba min wannan bayanin ban sake komawa ba, da na gane kuma Inna kan ba mu nata ne ita ta haqura sai na daina ce mata ban qoshi ba, suma su Aliya na hana su tunda dukanmu muna da wayon mu. Rannann na farka cikin dare a firgice saboda xaxa min dukan da naji anyi, “Ke tashi ki koma can xakin.” Nayi maza na buxe ido jin maganar Hajiya Kubra, me kuma ya sake faruwa? Tambayar da ta zo cikin zuciyata kenan. Sai kawai na ganta riqe da jariri sabon haihuwa, nan da nan na wastsake saboda sanin Innata ta haihu. Nan da nan na shiga murna ina farin ciki, Hajiya Kubra sai murmushi take yi alamar itama tana farin ciki. Babana ya leqo “Sannunku da qoqari Hajiya.” Tayi maza ta ce, ‘yauwa sannu Alhaji.” Ya ce, “Babu matsala dai ko?” ta ce, a’a babu lafiyarta qalau haka nan xanta, ya yi maza ya ce na’am ta ce eh ai xa namiji muka samu gashi nan kamanshi xaya da Humaira, ya yi murmushi ya yi addu’a ya juya ya fita. Mama ta turo kai cikin falon daidai Inna tana fitowa daga wanka ta ce, “ai ke kaxai ki ka haihu a xaki baki kira kowa ba? Lalle yarinyar nan kina jin wani abu. Hajiya Kubra tayi murmushi ta ce, “Ba ita kaxai ba ce ina ciki.” Mama ta xan kaxu alamar bata san Hajiya Kubra tana ciki ba, ai kina ciki ne Hajiya? Ta ce eh, ai nazo suka shiga gaisawa. Inna tana zaune tana shan kamun gyaxan da Hajiya Kubra ta dama mata, Babana ya sake leqowa babu wani abinda ake buqata ko Hajiya? Tayi murmushi ta ce, a’a babu, tanfar dai ace gaskiyar Mama da ta ce Babana mai xabi’ar son haihuwar xa namiji ne, kusan ace mancewa yayi da Mama tana gidan ya shiga zirga-zirga da kai-kawo na sintirin ganin jariri da tanbayar lafiyar maijego. Gari na wayewa dangin Inna suka kama zirga-zirgar kaiwa da komowa, da suka saba kan kace meye wannan sun cika gidan sai hidimarsu suke yi cikin farin ciki da annashuwa don ma dai suna tsoron Mallam mai babban allo don ya ce in suka sake zuwa gidan aka yi faxa da su to zai hana su zuwa in ban da haka da ba qaramin iya shege suka yi wa Mama ba. Da Azahar rannan Babana yana xakin Mama nima ina ciki ina gyara mata farcenta sai kawai na ji ta ce mishi a qa’ida fa wannan xan ba naka ba ne, don kuwa shege ne tunda s atan kwana aka yi aka je gun uwarsa. Nan da nan Babana yayi fici-fici ya vata rai ya shiga yin tsaki yana faxin wannan wane irin zancen banza ne? bai ma xauki wani lokaci ba ya tashi ya fita ya bar mata xakin. Jego mai d axi Inna ke yi saboda Hajiya Kubra tana tare da ita, nan take wuni nan take kwana tana kula da ita da komai nata, Sa’adatu tana wurin Inna Balki tun ranar da aka yi haihuwar ta tafi da ita gidanta, gashi komai a wadace Babana yake bayarwa babu kuma halin Mama ta tauye shi. Rannan ma ta shigo xakin saboda ganin jariri da uwarshi, ko sun tashi lafiya saboda sanin Hajiya Kubra na nan suna hira da ita, tana riqe da shi a hannunta sai kawai ta ce wa Hajiya Kubra mazan nan da ki ke ganinsu fa munafukai ne, ba su da gaskiya ko ta anini. Tayi murmushi ta ce mata, ba duka ba ne, Mama ta ci gaba da yi mata bayani don ta gamsu da maganarta, har tana kawo mata misali da abinda ya auku na gidanmu, ta qare maganar tata da cewar to ko ke Hajiya ai ina ganin sai kin yi haquri da waxannan amaren naki yara.” Hajiya Kubra ta sake wani murmushin kafin ta ce mata, to kin san shi haqurin iri-iri ne, kamarni kin ga amaryata ta farko sa’ar Binta ce, tunda an yi auren Binta da wata uku ne kawai ya yi nashi auren. Shekara xaya da rabi bayan nan kuma ya qarato bana shiga harkarsu da mijinsu in dai bana sa zasu yi wani rashin hankali in tsawatar musu ba. To shima ya sani ya san na kame girmana, don haka yana bani girmana suma suna bani girmana saboda sun san mijinsu ba zai yarda su kawo min raini ba, tunda ban raina kaina a gabansu ba. Mama ta ce haka ne, haka ne abin yake, tayi sallama ta fita. A waxannan kwanakin yake kawai Mama take yi amma kana kallon idonta kusan sai da ta gama kuka a xaki sannan ta fito. Kwana uku da haihuwar, Baba Yahaya ya rako Alhaji Mai kuxi suka zo gidanmu ganin jariri, rannan a falon Babana suka sauka ni Hajiya Kubra ta baiwa yaron naje na kai musu sai fara’a yake yi yana qarawa shi kuwa Babana yana gefe shima da alamun farin ciki a tare dashi. Ya kalle ni yana murmushi, kin yi qani Aisha, sai dai shima baqi ne irinki, Alhaji Yahaya yayi dariya ya ce, to ai gaskiyarsu suma waxanda suka yi farin ai karanbani ne ya kai su. Shi kam Alhaji Mai kuxi wasa da ‘ya’yan Inna yake yi tanfar jikokinshi don ya ce Inna ‘yarki ce, Inna ta shigo ta durqusa ta gaishe su, ya tambaye ta ina ‘yar uwar taki take? Babana ya ce mata, biya ki gaya mata ga Alhaji yazo. Mama tazo itama suka gaisa da ta juya zata tafi sai ya ciro kuxi masu yawa ya bani ya ce in kai mata a sai mana alewa, na ce to. Naje na kai mata su. Na dawo na karvi jaririn na kai xakinmu. Ko da Babana bai yi wa Inna zannuwan goyo ba, Mama ta hana ta ce duk sanda Inna ta haihu yayi mata zanin goyo, to hatta kayan jariran da yayi sai yayi mata itama don har da gangan Inna ke irin haihuwar da take yi saboda tasan in ta haihun zai kwashe kuxin abincin mutane yayi ta kashe mata. To duk da hakan yayi hidima, goro murza-murza a wadace gami da butter mint da dabino mai yawa, ga ragunan suna tima-tima masu kama da ‘yan Maruqa. Ga abincin suna iri-iri kuma mai daxi, ‘yan uwan Innan ne suka xauke cefanen da aka kawon suka yi don sun saba zuwa sunan Inna su kai yamma Mama bata ba su abincin suna ba a dalilin wai ba a gama ba, don haka wannan karon ba su ma saurare ta ba. Wunin rannar Inna da ‘yan uwanta da na Babana da abokan arziki suna hidimar suna, ita kuwa Mama bata da aiki sai baiwa mutane labarin yanda aka yi aka haifi yaron tana faxin wai shege ne. Tunda satan girki aka yi aka same shi, tun tana bada labarin ga masu sauraronta har taje tana baiwa masu yi mata dariya, uwargidan Baba Yahaya Hajiya Haran wacce ta yi wa sunan hidima mai yawa a dalilin wai mijinsu aka yi wa takwara. Kallon Mama tayi a sakarce ta ce mata, dama dai kin bar bada labarin nan don kuwa kanki ki ke tona wa asiri, ina ruwan wannan jariri da abinda aka yi da zai zama shege? Ko dama a waje aka yi cikin nashi balle a aure? Sannan gashi nan tubarkalla tanfar amanshi Alhaji Surajo yayi. Nan da nan ta soma sake mata mata maganganu don dama ita da Mama ta ciki na ciki ne kawai. Kullum Maman takan ba da labarin Hajiya Haran a matsayin maciyar amana, wai duk da irin amincin da ke tsakaninsu ita ce ta jagoranci komai da aka yi na neman auren Innata. Ita kuwa Haran ta ce aminci ba zai hana ta bin umarnin mijinta ba ta kuma yi duk abinda zata yi don ta nunawa Mama tana tare da ita don su ci gaba ita Maman ce ta qi. Hajiya Haran ta kalle ta tayi murmushi, ta ce “Mama kenan, to ai ba ni na kar wannan zomon ba ko ratayen shi kuma ba a bani ba balle ya zama sanadin faxa a tsakaninmu, tunda ke kin saba. Ba’a hidima a gidanki a rabu da ke lafiya saboda zubar da girma, ta ci gaba kuma da sabgoginta tana kuma zaune a falon na Mama bata fita ba sai in wani abu ya kama taje tayi ta dawo. Can a xakin Inna kuwa wata gwanar ajiyar ce tazo da kaset xin da Muhammadu Shatan dangi yayi wa Babana da Inna waqa, lokacin aurensu. Don haka tuni matasa-matasan cikinsu suka miqe sai faman taka rawa suke yi. Da yamma rannan kowa ya zo yayi wa Inna salamma zai tafi ‘yan uwanta za su kawo kyauta su bashi na qunshin goro da minti da dabino gami da cincin, babu ruwansu da cewar kai wanene? Da daddare rannan a xakinmu bayan watsewar Jama’a babu masaka tsinke saboda tarin kaya na sutura da na amfani, atamfa-atamfa turmi ashirin Inna ta samu mafi yawancinsu masu kyau. Don ko daga gidan Baba Yahaya wanda sunanshi aka sanyawa yaron manyan super biyu aka kawo mata da rigunan yaro guda bakwai gami da sauran tarkace, ga kuma wasu lesuna da shadda da material guda goma can gefe waxanda Alhaji Mai kuxi ya yi mata. Rannan yanda Hajiya Kubra ta wuni cikin hidimar kai-kawon ganin abin da ake yi haka har cikin daren bata huta ba, qoqari take yi wai taga ta samar wa komai muhallin da ya dace dashi. Ni kam sai murna nake yi bini-bini sai in matsa jikin Innata in xauki yaro ko in zuba mishi ido ina kallon shi, ji nake tanfar kar Hajiya Kubra ta tafi, musamman da yake tunda ta zo babu wanda ya zungure ni balle ya doke ni. Ko wannan fitinanniyar aikar ma an rage yi min ita. Washegarin suna da sassafe su Anti Ramla da Anti Sajida matan Baba da Abba surukayen Hajiya Kubra suka sake dawowa, kamar yanda tayi musu umarni suka zo suka qarasa gyara komai suka kuma soye ragunan suna ta kasabta komai ta baiwa kowa nashi gaba xaya makwabta da dangi har qauyen su Babanmu Giyaxe sai da ta bayar ta ce a kaiwa Mahaifiyarshi tare da goro da minti da kuma turamen atamfofi biyu. Mama ma aka bata nata tare da turmin super guda xaya amma wai sai ta dawo da zanin ta ce a bar wa maijego kawai ta xaura. Da yamma rannan Hajiya Kubra ta koma gida bayan tafiyar surukayen ta kafin ta tafi kuwa sai da na ji ta tana jaddawa Inna cewar lalle ne ta kula da kanta da kuma ‘ya’yanta ta ce, to. Washegari da sassafe tun Innan bata sauko daga kan gadonta ba Mama ta aiko wai ta fito ta baiwa jama’a abin karyawa. Inna ta leqo tsakar gida ta ce mata ina kwana? Da kyar ta buxe baki ta amsa sai da tayi ta sake, ta kalle ta cikin natsuwa ta ce “Mama ko za a ba su na yanzu ni in yi na anjima tunda ai na gama daga abincin dare ne muke canjin girkin. Ta ce, yau an baki daga na safe in kuma ba za ki yi ba ne sai ki faxa.” Ta ce, to, ta koma xakinta ta bani umarnin kintsa mata shi da baiwa qannena ruwan wanka ita kuma ta sanya suwaita da hijabi ta fita. Inna tana kicin tana aikin abin karyawa ni ina xaki ina jin Mama tana cewa tunda ki ka san zuwan gun miji a kowane lokaci ai ya kamata ki san hidimar gidan shi ma a haka nan kuma gidana ne yanda naga dama haka zan dama a kuma sha dole gidana ne ni da mijina da ‘ya’ya ki ka zo ki ka same mu ni da mijnin da ‘ya’yana. Kin ga zai yiwu ki ce za ki kawo min wani fi’ili? Ai sai dai kawai in kin ga ba za ki iya ba kiyi gaba kamar yanda saura suka yi. Inna ta dawo xakinta tana murmushi ta bani kuxi ta ce in sayo biredi da madara. Nayi maza naje na kawo mata, nan da nan ta gama abinda zata yi ta rabawa jama’a, ta bani na Mama na kai mata. Na dawo kenan Habiba ta biyo bayan ta zo ta tsaya qerere akan Inna da ke yiwa xanta wanka, ta ce mata in ji Mama wai wannan abin karyawar da ki ka basu kunu da qosai za ki rinqa yi, ta ce mata “to”. Rainin da Habiba ta yi wa Inna yana ci min tuwo a qwarya, sai dai babu yanda zan yi, tsoronta nake ji saboda kusan kullum sai tayi mini duka. Rannan ban san laifin da nayi ba sai kawai na ji Mama ta qwala min kira, da sauri na amsa naje in ji kiran sai kawai ta ce min in shiga can cikin xakinta. Naja na tsaya ina faxin “Mama me nayi? Mama kiyi haquri.” Ta ce, “Ba zan yi ba ta waiwaya ta kalli Ado dake gefenta ta ce mishi shi kenan je ka sai ka dawo. Ya tashi ya tafi ba tare da ya ce mata uffan ba. Ta tasa ta biyo ni cikin xakin tana faxin, ai dama tara ki nake yi ina kallon iya shegen da kike yi sarai kin xauka zasu xauwama min a cikin gidanne? Mama ta soma kama hannayena tana naxewa ta kwantar dani a qasa ta haxa da qafafuwana ta danne ta hau kaina ta zauna da iyakacin qarfinta, ta shiga mintsinin cinyoyina ina ihu ina faxin waiyo Mama, waiyo numfashina don tasan ta toshe min kafar hanci guda xaya. Numfashin da nake samu baya isa ta nishi yafi damuna ba tsananin nauyinta da azabar mintsinin da take yi min ba, ya tsaya nunfashin ki mutu don uwarki sai me ba na rage mugin irin da ake tara min a gida ba? Azaba ta ishe ni na kuma gane da gaske Mama bata damu ba don numfashin nawa ya tsaya ba ban san yanda aka yi ba sai kawai jina nayi na kama mazaunanta dake daidai bakina da haqorana da iyakacin qarfina. Ihun da Mama ta qurma mai tsananin qarfi shi ne wataqila yayi matuqar firgita ni, har ban san yanda aka yi ba sai kawai na ganni tsaye a tsakar gida ina huci cikin tsananin firgita don tsoro, ganewan da nayi na kuvuta ba kuma a girma da arziki na kuvutan ba, wani mummunan abin nima nayi mata ya sani kartawa da gudu na nufi gidan Mallam mai babban allo. Ina tsugune gaban Mallam sai zare ido nake yi bayan na gama mayar musu da bayani, Hajiya ‘yardubu ta ce kai wannan zalunci da rashin tausayi da yawa yake, amma babu komai wata rana ba za ta yi ba.” Mallam ya xan yi murmushi ya ce, “Itama yarinyar ai da nata laifin, haka kawai za a kama ta da duka ne bata yi komai ba? Ai ba ita kaxai ba ce.” Hajiya ‘yar dubu tayi maza ta ce, uh’uh Mallam, babu wanda bai san lamarin gidan nan ba, kai dai ayi sha’ani kawai.” Mallam ya ce, “To Allah ya kyauta, ta ce amin. Abinci kawai Mallam ya bari naci yasa Hajiya ‘Yar dubu ta taso ni a gaba ta dawo dani gidanmu, gabana sai faxuwa yake yi, yayin da ta tasa ni muka shiga wurin Mama. Maman tana kwance tana ganin Hajiya ta miqe ta zauna tana yi mata sannu da zuwa, suka gaisa ni kuma ina durqushe. ‘Yarki ce tazo mana gida da wani bayani na rashin hankali, shi ne na ce to bari dai in dawo miki da ita in ji gaskiyar lamarin, tunda dai ai banza bata kai zomo kasuwa, sannan sha’anin nan na ‘ya’yan yau maganarsu ba abin kamawa ba ne, in dai ba zahiri aka gani ba.” Mama tayi ta bayani na kame-kame har tana gayawa Hajiya wai na cije ta a mazaunai, ta ce a’a shi ne abin mamaki cizo a mazauni kuma? Tayi maza ta bar maganar ta shiga tambayarta Mallam da sauran mutanen gida, wataqila ta gane abinda bayanin nata yake nufi. Na shiga wani hali na tsoron kar Mama ta ce zata kama ni akan cizon da nayi mata, bata yi hakan ba wataqila don maganar ta yayatu da yawa har gidan Baba Yahaya an ji, ya kuma yi wa Babana magana kan irin dukan da ake yawan yi min alhalin na riga na fara girma. To sai dai Habiba duk inda muka gamu sai ta buge min baki wai ladan cizon Mama da nayi. Rannan na dawo daga gidan ‘yar Inna Balki da aka gama bikinta wacce kuma take matuqar sona Ruwaila. Ina rungume da jakar ledar da ta bani kayanta kala biyu masu kyau da kayan kwalliya dangin su janbaki da hoda da gazal da man shafawa, gami da turare na zuba a ciki ina ta murna nazo zan wuce Habiba dake tsaye da qawarta a waje sai kawai tayi maza ta tare ni ta kaiwa bakina duka. Na ce ban yafe ba, ta sake kai mishi wani dukan na sake cewa ban yafe ba, zata sake sai qawar tata ta ce mata “Haba Habiba, wane irin cin zali ne wannan? Don kawai kin ga tana yi miki shiru-shiru?” Da sauri Habiba ta ce, kar tayi shiru ta rama mana taga irin yanda zan yi fici-fici da ita, kwanannan ma zamu yi maganinku don Mama tasa Babanmu yayi aure har ma ta samo mishi budurwar har an kai sadaki zaku sani. Sum-sum na wuce na shiga gida, gabana sai faxuwa yake yi jikina kuma yayi matuqar yin sanyi don kuwa ko ban san komai ba ban kuma isa komai ba rayuwar gidanmu ta riga ta karantar dani cewar kishiyar uwa ba qaramar aba ba ce, sannan ganin Habiba tana murna ya isa ya fahimtar dani cewar don mahaifiya ta za’ayi auren. Duk da kashedin da Inna tayi min na jin magana in zo in gaya mata da na shiga xakinta kasa yin shiru nayi, durqusawa nayi gabanta da gwiwoyina duka biyu na ce mata Inna Habiba ta gaya min wata magana ki bar ni in gaya miki. Ta ce, to gaya min, na kwashe bayanin duka nayi mata ta xan yi shiru zuwa na wani lokaci kafin ta ce min babu komai kar ki damu kanki kin ji ko? Na ce mata to, ina ce kina yin addu’o’in da na koya miki? Na ce mata eh, ta ce to ai shi kenan. Da daddare Babana ya shigo wurinta saboda ranar ma girkinta ne, bata wani canza mishi ba, wai don ta ji labarin yana neman aure ina jin shi yana tambayarta wai ni menene amfanin gadon jariran can da aka sai miki ne? Yasa hannu ya xauki yaron da muke kira Baba qarami ya maida shi ciki ya kwantar, ban san yanda suka yi da Inna ba iyaka dai da safe bayan mun kammala komai muna zaune a xaki ni da ita sai ta ce min. “Da gaske ne Babanku zai yi aure har ma wai bikin ya matso, Mama ce ta hana shi gaya min wai don kar in hana auren ni da Babana.” Na zubawa Inna ido ina kallonta, ban ma san abinda zan ce mata ba, sai ta sake ce min babu komai kar ki wani damu ranki na ce mata to. Kwana biyu da yin haka na ji Babana yana cewa Innata ga wannan kiyi haquri, ki sayi wani abu ko bna ita Mama ta ce bata buqatar komai nawa, ita auren kawai da zan yi ya ishe ta farin ciki.” Inna ta ce, haka ne tayi shiru, to amma dai ai kin san babu wata mata da…” Inna tayi maza ta ce, mishi uh’uh mu bar wannan zancen kawai, na gode, Allah ya qara buxi, ya ce to amin ya fita. Bayan fitar tashi ne ta aike ni in kaiwa Hajiya Kubra kuxin daga nan kuma in ce mata in ta samu lokaci ta tamb ayi izini tazo tana son ganinta. Zaman lafiya sosai aka shiga yi tsakanin Inna da Babana, maimakon tayi mishi borin jin zafin auren da zai yi sai kawai tayi kamar bata ji ba, tunda Mama bata maganar ba ta kuma taso ta ji, shima Baba a wannan lokacin hidima sosai ya yi wa Innar saboda jin daxin haqurin da tayi. Tunda bai saba ganin hakan ba wurin uwargidan da za’ayi wa amarya, don haka sai yayi ta qoqarin ya nuna mata cewar bata da matsala a auren nashi, ko da yake dai ni nasan can cikin zuciyar Inna akwai damuwa ta dai haqura ne kawai ta danne don kar ta tonawa kanta asiri, tunda tasan bata da ikon hana auren. Sati biyu ne kawai bayan wannan lokacin sai muka wayi gari ana yin buki a gidanmu, Mama sai kawai da kawowa take yi cikin murna da farin cikin Babana ya sake auren budurwa. Sai murmushi take yi tana faxin wannan ai ni ba kishiya ba ce a wurina ya ce, nima zan yi mata irin adalcin da uwar Fatima take cewa tana yiwa kishiyoyinta tunda ita ba za ta yi min irin cin zarafin da Fatima tayi min ba tunda iyayenta ba su yi mata irin tarbiyar da na Fatima suka yi mata ba. An sha biki a gidanmu ba kaxan ba, Inna dai bata wani yi gayyata ba a dalilin wai bata daxe da yin hidimar suna ba, amma dai duk da hakan ‘yan uwanta sun taru suna kuma bata shawarwari iri-iri. Ana kammala biki sai manufofin Mama nasa Babana yayi aure suka fara baiyana, cewar ita ta sa shi kuma ba zargi ba ne da kanshi ya faxa cewar Mama ta ce qara auren nashi ne kawai zai kawo zaman lafiya kuma in ya duba da kyau ma ai zai ga gaba xaya abokan shi ma mata uku-uku ke gare su ba biyu ba. Tun daga ranar da aka yi buxan kai ya haxa su gaba xaya a xaqin Mama don yi musu nasiha kan zaman lafiya da muhimmancin qarami yabi babba Mama ta ce in shi babban ya bi nashi na gaban ko? Zaman lafiya kuwa ai a wurinka yake tunda kaine mai gida in ka tsaya kan hana zalunci da kuma tsoma yara cikin zaman kishi, amma fa sai kaso hakan tunda ni kam ina ruwana? Ai ni ‘yar kallo ce, menene ban gani ba cikin sha’anin kishiya da sanabenta? Ai babu wani dare da jemage bai gani ba sai na ranar mutuwarsa. Baba ya ce, haka ne to yanzu tunda ku uku ne yaya ku ke gani zaku ci gaba da kwana bibbiyun ne ko kuwa zaku canza? Ta ce, to sai suyi magana amma ni kam ai ba zamu raba ka da wannan yarinyar ba tayi min quruciya da yawa, kaje can kawai kayi sha’aninka ni na bata nawa girkin in ka yi kwana biyu a wani wuri sai kayi huxu a wurinta. In gari ya waye dai kazo mu mu mu gaisa mu tattauna al’amura tunda kasan duk cikin su babu wacce takai ni sonka tunda su duk Alhaji suka aura ni kaxai ni ce nan matar Surajo.” Babana yayi murmushi alamar jin daxi ya ce, to kuma kin san haka kya ce kin yafe musu ni? Ta ce oh’oh ai ba komai, ka saki jiki kayi hidimar ka Alhaji, ai mun riga mun zama xaya. Ya gyaxa kai alamar yarda, ya ce haka ne, haka ne Majadan, ta ce to menene? Ai na riga na ci dubu sai ceto. To hakan aka yi, Innata a matsayinta na wacce aka yi wa Amarya ita ce ta xauki nauyin yiwa Amarya girki na kwanaki bakwan da ango ke yiwa Amarya, ta sake yi mata girkin kwana biyun da Mama ta bata kyauta. Sai nan ta yi wa kanta nata girkin bayan Baba ya yi wa Amarya kwana tara ya dawo wurinta. Ya sake komawa wurin amarya ta sake jerawa amaryar girkin kwana huxu a jere nata dana kyautar da aka yi mata, sannan ta sake yiwa kanta da ya zo wurinta daya fita zai koma wurin amarya ne ta ce to yau kam a baiwa amarya cefanenta, ta fito ta yiwa kanta girki itama zata huta saboda goyo ke gare ta. Babana ya ce, ai kin yi qoqari kwana goma sha bakwai fa kika jera kina yi ke kaxai sau xaya kuma ban kama ki da laifin yin girkin maguxi ba, Allah ya saka miki da alheri, ta ce amin. Ya fita ya tafi, ba mu san yanda aka yi ba sai gashi ya dawo wai ba zai yiwu ace tun yau an baiwa amarya girki ba wannan wane irin kishi ne? ‘Yar yarinya ‘yar qanqanuwa ace ba za ayi mata girki ko na wata biyu ba. Inna ta ce, ai fa kana ta juya ta gyara ta yi kwanciyarta ya yi faxanshi har ya gama ya fita bata tanka mishi ba. Mama ta fito ta karvi girkin tana faxin ai ba zai yiwu ba ace wannan ‘yar yarinyar ta shiga kicin don ana jin haushinta a xora mata xawainiyar da bata isa yi ba, tunda dai ni ce babba a gidan ai dole in shiga hidimar girkin nata. Inna tana daga kwance ta ce, babbar banza ba, nayi maza na kalle ta don ba xabi’arta ba ce faxin irin waxannan maganganun. Nan take cinta a zuciyarta. Mama kullum takan yi wa amarya girki nata da na kyautar da tayi mata sai dai kuma qwandala bata miqa mata cikin canjin cefanen da ke raguwa, mu kuma ta koma min xira mana abinci kamar yanda dama ta faro a baya. To na da ma da sauqi don zata yi kwana biyu ne Innan ma ta kwana biyu to yanzu ita kaxai kwana huxu take yi, ga amarya fitsararriya babu alamar kunya ko tsoro a tare da ita ga alama kuma ta riga taji labarin Inna kafin zuwanta. Don haka da shirinta sosai ta shigo cikin gidan, ba kuma yarinya qarama ba ce kamar yanda ake faxa, don kuwa ba za ta rasa shekaru ashirin ba, zuwa da biyu ba kuma wani karatu ta yi ba, mijinne dai bai samu ba sai a lokacin. Tuni amarya ta gundure ni na rasa yanda zan yi da zuciyata in ji daxi, na tsane ta na tsani duk wani al’amarinta saboda tasa min uwa da tayi a gaba da rashin kunya iri-iri. Babu damar Inna tayi wani motsi sai kawai ka ji ta tana sake mata maganganu. Mama kuma tana qara zugata tana faxin, a to ai karen bana shi ne maganin zomin bana, in ni anyi min na qyale dole don kar ace girmana ya zube yarinya kam ai ba za ta yarda ayi mata takun da ake yi min ba. Wani irin kishi mai tsanani ya kama ni game da amarya saboda ganin yanda aka xauke ta aka fifitata akan Innata, take kuma ci wa Innar tawa tuwo a qwarya. Babana kuma yake zumuxin ta yake faman zirga-zirgan wurinta sai ko wurin Mama, xakin Innata bacci ke kawo shi a dole wataran ma ya qi zuwa wurin nata ya shige nashi wurin yayi kwanciyarshi. Zuciyata ta kai matuqar zafi game da abubuwan da nake gani, gashi kusan kullum sai naga idanuwan Inna a kunbure alamar vuya tayi ta yi kuka. Rannan na amsa iran Babana a falon Mama suna zaune dukansu na durqusa ina sauraron maganar da yake yi min. Wannan ba uwarki ba ce da kike kiranta da sunanta? Na sunkuyar da kaina qasa nayi shiru can cikin zuciyata kuwa cewa nake yi, to ai nima tawa uwar da sunanta kowa yake kiranta, ban kuma tava ji an yi wani tsawa kan hakan ba. Zuciyata ta tafi wajen tunanin lamurra iri-iri, don haka ba sosai nake fahimtar maganganun da ake ta yi min ba, na dai san kawai na ji kashedin da Baban yayi min na in ya sake jin na ambaci sunan Zubaida da bakina to zan san bolko miya ne, ke Zubaida ko bana nan ta kira ki da sunanki kizo ki gayawa Mama in na dawo zata yi min bayanin komai. Ta ce, to, cikin wani yanayi na shagwava, ni kam a wannan lokacin in ban da Innata tana cikin gidan, wataqila da gudu nayi na bar gidan saboda yawan vacin ran da nake samun kaina a ciki. Na daina ambaton sunan Zubaida sai dai kuma bana kiranta wani Anti, in mu’amalla ta haxa ni da ita magana kawai nake yi mata, ta yanayin da zata gane da ita nake yi ba sai na ambace ta ba. Rashin jituwa mai tsanani ya shiga tsakanina da ita saboda gaba xaya bata shakka ko shayin sakin bakinta ta gayawa Inna maganun ban za na rashin mutunci. Ko kuma ka ji ta tana yi wa Inna gori kan wasu abubuwan da zaka kasa sanin inda ta samo labarinsu. Haka kawai kuma sai tayi yaji in Babanmu ya dawo sai ace mishi wai Inna ce take yi mata wulaqanci da barazana. Sai ya tura Mama taje mishi biko in ta dawo ayi ta rattabo mishi bayanai. Wani lokaci ma bayanin yana qarewa Babana zai kama ni ya naxa min dukan tsiya ya kuma gaya min cewar in har ban daina biyewa Innata, ina taya ta baqin kishinta ba to ni da ita ne zamu bar mishi gidan don ba zan yarda da abinda zai kawo rai ba kan iyalinshi ba gara kawai ya kori mutum ya tafi ya bar mishi gida a zauna lafiya. Rannan Inna tana wanki tana matsewa tana ajiyewa a qasa, kusa da bahon xin wankin nata saboda sai da ta wanke wurin da zabor yayi tas kafin ta fara wankin ni kuma ina gefenta ina wanke-wanken da Mama ta sani a ina kuma yi mata magana a hankali sai kawai ga Zubaida ta fito daga xakin Mama tazo ta keta tsakaninmu ta taka wankin da Inna ke tarawa da qafarta mai sanye da takalmi. Inna ta miqe ta tsaya tana kallonta ta ce aiya Zubaida wannan kaya da kika taka na riga na wanke su, sai kawai naji ta ce an taka xin menene? Ko shure su nayi na watsa su me zaki yi? Tana faxin hakan kuma sai kawai naga ta shure tarin kayan sun watse sunyi xai-xai a qasa mai datti. Ban san yanda aka yi ba, sai kawai na samu kaina da tambayar ta ha’a wannan wane irin abu ne haka? Ta wanke kayanta kin taka tayi magana kin watsar mata da qarfinki? Ta ce an watsar ko kina da abin yi ne mai uwa? Ta miqo hannu ta murxe min baki ta saki don kawar da kan da na yi bakin nawa ya suvuce daga yatsunta ta sake miqo hannu zata sake. Na kaiwa hannun nata duka da iyakacin qarfina. Lah, ni kika buga? Da qarfi tayi tambayar Inna tana faxin ki bari ki qyale ta kawai kije xaki, amma ina? Idona ya riga ya ru fe don haka Zubaida na sake kawo min duka ban tsaya ba rarumarta kawai nayi da wani irin qarfi da ban tava sanin ina da shi ba na jefar da ita cikin kwanukan wanke-wankennan. Ga zaton Mama duka zata yi min in aka yi danben, don haka tana ganin mun fara ta bar falonta, ta shige can cikin xaki. Inna tana kiranta tazo ta raba don ita kaxai ba za ta iya ba, ta qi kulawa. Sai data ji Zubaidan da kanta tana ihu saboda mummunan shaqan da nayi mata sannan ta fito a guje, ta xaga ni akanta. Ta kuma yiwa Babana waya ta ce mishi maza-maza ya bar abinda yake yi yazo gida gani nan ni da uwata mun taru zamu kashe mishi amarya. Inna tayi murmushi kawai ba ta ce komai ba ni kuwa can cikin zuciyata na riga na gamsu don haka ban damu da hukuncin da za a zo ayi min ba. Babana ya zuba min ido cikin matsanancin vacin rai bayan ya gama sauraron jawabin Mama na cewar ni da Inna ne muka taran mata. Ya ce “Ke Binta.” Gabana yayi mummunan faxuwa ga zatona cewa zai yi ta bar mishi gida ko ga takardar saki ya bata. Sai na ji ya ce zan sa qafar wando xaya dake a gidannan ba dai kina baqin ciki da abinda nake so ba, to ai kuwa kin rinqa vacin rai kenan za kuma mu haxu a daidai. Tashi min daga nan ki koma xakinki don bana son ganinki a yanzu.” Inna ta miqe ta fita ta bar ni a tsugune a zuciyata ina farin cikin ganin abinda nake tsoron akan Inna bai faru ba, don haka duk wani abin da zai faru to ni kam in dai a kaina ne zan yi haquri da shi. Ke kuma Humaira bar min gidannan tunda ba kya jin maganata tafi duk inda ki ka ga dama na bar musu ke.” Na fito gida sanye da jiqaqqen hijabina ina kuka saboda ban tava tsammanin irin hukuncin da Babana zai yi min kenan ba, na kora daga gida, na xauka dukana kawai zai yi ya bar ni in yi zamana tare da Innata. Gidan Baba Yahaya na tafi baya nan a gida don haka nayi zamana kamar yanda Baba Hairan ta umarce ni. Bayan na gama rattaba mata bayanin komai. Ai kaxan ya fara gani in dai bai yi himma ya gyara lamarin cikin gidan shi ba. Ci abinci kije kiyi wanka in kin gama kije ki duba cikin kayan ‘yan uwanki ki zavi wanda zai yi miki daidai.” Na ce “To” ban san yanda aka yi ba ina zaune ina shafa mai ta juyo ta kalle ni, Salati mai tsanani naji ta saka wannan wane irin tabo ne haka a jikinki? Na xan yi murmushi na sake zubawa tabon ido ina qarasa vare waxanda basu varu da kyau ba wake yi miki irin wannan duka Humaira?” Na sake wani murmushin kafin na ce mata, Mama da Babanmu, ta ce tirqashi, taja bakinta tayi shiru. Baba Yahaya kuwa yana dawowa ta kai ni gabanshi ta mayar mishi da bayanin komai yayi min faxa sosai akan danben da aka ce mishi nayi da Zubaida kafin yayi tsaki ya ce, kai Alhaji Surajo lamarinshi sai shi. Gida ba doka ba oda? To ya ya za’ayi a zauna lafiya? Baba Hairan ta ce, ai duk Mama ce ta dama gidan nan, kalli jikin yarinyar nan ka gani ta matso tana qoqarin kwaye rigar dake jikina, wai yaga tabban, ni kuwa ina qi saboda qirjina cike yake da nonuwa na riga na shekara goma sha shida. “Barta kawai Hairan, ai na riga na san komai babu wani laifin Majadan da nake gani, nashi yafi yawa don shi ya bnar damar shi ta cewar shi ne Maigida mai wuqa da nama a hannunshi ya bar ta take yi mishi kwavar da taga dama. Yanzu wannan abu da me yayi kama, ace ‘yarka tayi danbe da matarka ina alherin haka? Wa kuma gari ya waya? Sannan wai ya zartar da hukuncin korarta, to taje ina? In ban da tayi hikimar zuwa nan xin da wani wuri ta nufa da wa gari ya waya? Kwanana huxu a gidan Baba Yahaya kafin ya dawo dani gida a dalilin wai Baban nawa yana nemana. “Ka gyara zaman gidanka Alhaji, ka fita cikin wannan ruxani da ka sanya kanka kai da iyalinka, musamman ma ‘ya’yanka abin zai dame ka fa don in ba sa’a kayi ba zumunci zai yi wuya a tsakaninsu. Baba ya ce “To su wa zasu sha wahala? Ai sune qanana, ba shi ke nan ba tunda dama uwarsu da danginta ne basa so ayi zumuncin don su sake koya musu mugun abu suna qoqarin ganin sai sun watsa min haxin kan gidana. Baba Yahaya ya ce, ai gidanka bai tava zama cikin haxin kai ba Alhaji, yau in da da fitina aka fara wannan zaman da wannan rikicin da sai ka ce to gara itama duk juyi iyayenta a tsaye suke akan zaman nata in ban da haka ai da tuni zaman naku ya zama labari kamar yanda na sauran matan ya zama.” Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min shiga gida Humaira kar in sake jin wani abu ya sake faruwa tsakaninki da wata mata musamman ma ita Zubaida, dukkansu iyayenki ne dukkansu ki rinqa girmama su saboda matan ubanki ne kin ji ko ba ki ji ba?” Na ce mishi na ji, to in ki ka sake ni da kaina ne zan yi miki hukunci don ba zamu yarda ace ‘ya’yanmu ‘yanmata suna mana danbe da matanmu ba, wannan lalacewar ai ta kai in da dai. Babana yayi kwafa alamar dai har lokacin yana cikin tsananin vacin rai game da lamarin. A wannan lokaci mun shiga hali mai tsanani a gidanmu ban da maganar faxan da nayi da Zubaida wacce yaja ya tsaya kan shedar da Mama ta bayar ce gaskiya cewar Innan ce ta kwashewa Zubaida qafa yasa na kada ita. Ita Innan da shi kuma suna cikin wani rikicin na zaman hirar da Babana yake yi a xakin Mama sai sha xaya ko sha biyun dare kafin ya shiga xakin mai girki. Gari na wayewa kuma can wurinta zai sake komawa a dalilin wai ita tayi kyautar kwananta. Inna taja ta tsaya kan tunda ba ita aka yi wa kyautar kwanan ba, to kuma babu abin da zai tauye mata kwanakin girkinta. Sai abin ya tsaya can a tsakaninsu ita da wacce ta yi wa kyauta kan haka dai nasan ta kulle mishi qofa yafi sau goma shi kuma yayi mata duka har sau biyu. Rannan dai aka wayi gari Inna bata nan a gida babu kuma wanda yasan lokacin da ta fita. Mama da Zubaida sai maganganunsu suke yi a tsakar gida na nuna murnarsu kan abinda ya faru. Ni kuwa ina xakinmu ina yiwa qannena hidimar da ta dace in yi musu don hatta Baba qarami bata tafi da shi ba, na gama basu kunun da na dama musu kenan Mama ta kira ni ta bani abin karyawar gida tana kuma zagina kan munafurci na da kuma ware qannena da wai nake yi ina nuna su kaxai ne nawa. Har dai na koma xaki ban ji Zubaida ta tanka mata ba savanin da da itama kanta zagin nawa take yi a yanzu kuwa ni da ita mun shiga taitai juna bana shiga harkarta ko xaga ido in kalle ta bana yi, itama bata shiga tawa ta kuma rage yiwa Inna irin hawan qawarar da da take yi mata. Ina zaune a xakinmu ni da qannena su suna kallon katun xin (AVATAR) da na sanya musu yayin da ni kuma nake ta faman share-share da goge-goge kamar yanda kullum muka saba yi da Inna. Can cikin zuciyata kuwa tunaninta nake yi itama ta tafi gidansu kawai taje tahuta da wannan wahalar da take ciki tabar mu kawai tunda mu gidanmu ne a cikin ta aka haife mu mu zauna muyi ta shanta amma kuma da na tuna yin hakan yana nufin ba zamu sake zama wuri xaya da ita ba sai kawai na ji hawaye suna gudu a idona. Babana ya shigo xakin ya same ni ina kuka ya yi kamar bai ga kukan da nake yi ba ya ce min, “Yauwa ki kula da su kin ji ko?” na ce mishi “To.” Yasa hannu a aljihu ya ciro kuxi ya bani ya ce, ki voye wannan in kuma buqatar wani abu ki sai muku na ce mishi to. Har yayi kamar zai fita sai ya sake juyowa cikin murya qasa-qasa ya ce min, ina Innarku ta ce miki zata tafi? Na ce bata gaya min ba, na ji kukan Baba qarami ne kawai na fito na gan shi shi kaxai a kwance. Kwana biyu a jere babu Inna babu dalilinta, an neme ta gaba xaya bata nan. Bata gidan mai babban allo bata gidan Alhaji Mai kuxi yayinta maza da mata duka an je bata nan gaba xaya hankula suka tashi ko ba a gaya min ba kuwa nasan Babana yana cikin waxanda suka fi kowa damuwa. Don na ji yana cewa Mama abin nan kamar wasa fa an nemi Binta ba a ganta ba, ta yamutsa fuska ta vata rai ta ce ai sai kuyi ta nema abinda dama take so kenan da yake ku kuma kun iya xaurewa qarya gindi in ba haka ba yarinya ce qarama balle ace ta vata? Tayi maza ta riqe baki ta ce, au, haka fa in ba a yi neman da kai ba, Alhaji Mai kuxi ga kuma munafukin abokinka, taja bakinta tayi shiru, zuwa can ta sake cewa ai ace ma kana da tsayaiye da daxi sai kayi ta dama tsiyarka yanda kaso dole a qyale ka ayi ta bi in ba haka ba ai ina? Ta sake yin shiru, shima ya tashi ya fita ya bar mata gidan. Kwana biyar da barin Inna gida na fito da safe ina goye da Baba qarami don ko Ali ya da Atika baya yarda su tava shi sai ni, a qofar gida naga Babana yana tsaye naje zan wuce shi tunda dama naje na gaishe shi. “Zo nan Humaira.” Da sauri naje na same shi na ce mishi, gani Baba. Ya yi kamar zai fasa gaya min maganar da zai gaya min xin sai kuma ya ce min yanzu in na shirya zanje wajen maganar Innarku.” Da sauri na ce mishi Baba an ganta ne? ya ce eh, dama ashe tana can ne sabon gidan Alhaji Abba dake can bayan (C.B.N Quarters) can ya kaita ya voye ta kin san dama ba wani mutunci ne dashi ba tunda ya wayi gari ya gan shi da kuxi a hannu na lura yana yiwa mutane kallon banza na fitar harkarshi. Kin san kuxi a hannun yaro in ba mai natsuwa ba ne sai ya shiga aikin rashin hankali da wulaqanta na gaba dashi, don ko gidan nan da yake zuwa wurin Innarku ba gaishe ni yake yi ba sai in ta qure mun yi kacivis dashi. Shi yasa ma nake ganin tunda shi ne mai xaure mata gindi take yi min iya shegen da take yi min to ina ganin zan haqura da ita ne kawai don in samu ma gidana ya zauna lafiya musamman ma da yake Mama tayi min alqawarin zata kula min da ku. Na kalli Babana na ce mishi, to Baba Allah ya zava mana mafi alheri, na wuce shi na tafi. Da daddare har na turo qofa na rufe na kuma kullewa Inna qofarta da take kwana bayan na kintsa shi na kuma tattara duk wani abu mai daraja na shigar mata ciki, gaba xaya sun yi barci nima abin da ya hana ni kwanciya ina damawa Baba qarami kunun da zan ba shi ne in ya tashi cikin dare. Sai kawai naji ana tava qofa nayi maza naje na buxe, Innata na gani. Tsalle nayi ina ihu na qanqame ta. Mama ta leqo da sauri ta ga abinda ke faruwa, ta ce au kece ki ka dawo? Ta ce, eh mana ina wuni? Bata tanka mata ba ta juya gun Babana wanda nima sai lokacin na gan shi a tsaye a tsakar gidan ga alama dai tare suke, ta ce mishi uhun ai dama tunda naga ba ka dawo ba na ce kana can wurinsu. Gaba xaya suka rurrufe mishi qofa ya dawo xakin Innata wanda ban so hakan ba, naso ace ya yi zamanshi a can don nima in samu in shaqi qanshin jikinta da na daxe ban ji ba. ‘Yan kwanaki kaxan xin da Inna tayi bata gida har ta xan canza, ta yi girkinta na kwana biyu ta fita cikin kwanakin kuwa Babana baya hirar dare a xakin Mama iyaka dai ya shiga da safe su gaisa kamar yanda yake yiwa kowacce sai kuma da rana in ya dawo, nan ma nanne wurin zamanshi. Amma da daddare yana shigowa daga Masallaci in anyi sallar Isha’i wurin Inna yake shigowa, Mama kuwa sai yada maganganu take yi shi kuma in ban da harara da tsaki babu abin da take yi mishi. Kwana biyu da dawowar Inna Hajiya ‘Yar dubu tazo gidanmu ina xakin Mama ta shiga suka gaisa ta fita ta nufi wurin Innata tana barin xakin Mama ta kalli Zubaida ta ce mata wani maganin uban ya sake bayar wa a kawo mata duk zanci abu kazansu ba dai da ni suke yi ba. Na tashi nima na fito xakinmu nazo don in qara gaida ‘yar dubu sai na same ta tana cewa, Inna wannan hanqoro da ake yi na kashe miki aure fa ba gata ba ne. Da ma kin yi haquri kin zauna a xakinki kin daina kai qara da faxin maganganu da ya fiye miki daraja yanzu irin maganganun da wannan yaron yayi ta gayawa mijinki da ya zuciya ya ce ya haqura da wa gari ya waya? Duk wani gatan da za’ayi miki yanzu ya wuce ayi miki tattalin yanda za’ayi ki zauna a xakinki tare da ‘ya’yanki? Ke mai ‘ya’ya mata? Huxu ne fa dake a jere ga su nan reras, don ma sauran babu kuma don zafin rai irin naku na ‘ya’yan yau da ba a gaya muku gaskiya xanki mai wata bakwai da za ki tafi ai sai ki goyo abinki ki tafi dashi. A’a ke ga mai zafin rai kin ajiye shi kin tafi to dube su shi da wacce ki ka bar wa xin yanda suka zama, su ‘ya’ya in gaya miki in suka kintsu suka zama mutanen kirki ne suke zama na kowa da kowa, amma in suka lalace to na mai su ne shi kaxai. Dama kin yi hankali kin yi karatun ta natsu ki gane vata kanki da baqin kishin gidanku ya kamata kiyi ba ta waxannan yaran ya kamata kiyi ki tsaya kiyi musu tarbiya ki tsaya musu da addu’a, Ubangiji ya raya miki su ya kuma basu mazan da za su riqe su. Shima wannan yaron Mallam yana nan yana jiran shi don Alhaji Yahaya yaje yaga yawa Mallam irin baqaqen maganganun da ya rinqa gasawa mijinki sakaryar yarinya kawai shashasha mara wayo. In sake jin kin kai wata magana can gidanku za ki gamu da ni, in kina da matsala ki kai wurin Mallam Yahaya tunda ba shi da wani daban a cikinku, ta tashi ta fita ta bar Inna tana ta faman kuka, nima jikina yayi sanyi. Can cikin zuciyata na xan ji tausayin Baba karo na farko da na ji hakan a game da shi, ko waxanne irin baqaqen maganganu Alhaji Mai kuxin ya yi ta gasa mishi oho. A wannan lokacin sai na samu kaina da jin tausayin Babana, maimakon tsananin jin z afin shi da da nake yi, a yanzu sai na gane ma fi yawancin abubuwan da suke faruwa a gidanmu ba sonsu yake yi ba, illa iyaka dai ba shi da yanda zai yi an riga an sha gabanta. Ta haka sai na koyi daina ganin anyi abu in gayawa Inna in ta ganan wa kanta kuma in bata haquri in naga da Babana a cikin abin kuma in ce mata kar kiyi faxa dashi Inna daina gasa mishi maganar da zata vata mishi rai. Kinga dai kin hana shi hirar xakin Mama ya daina duk da tsananin hakan a wurin shi tunda kina jin irin habaice-habaicen da take yi. To qyale shi haka komai yayi, kiyi haquri ta ce min to. Ta haka sai Inna ta riqe kwanakin girkin ta guda biyu sune nata in ta shige su zata yi komai don farantawa mijinta in ta fita kuma bata sake xaga ido ta kalli Baba balle har ta gane wane abin haushin yayi? Gashi tunda muka yi wannan tsiyar da Zubaida tana shakkar gaya wa Inna magana, sai dai kuma wani abin can daban, don haka har yanzu Mama bata gamsu ba daina zuwa hira xakinta ran girkin Innata ba qaramin tayar mata da hankali ya yi ba. Ban san yanda aka yi ba sai kawai gani nayi Babana ya sake taso ni a gaba kan maganar gaida Zubaida, Inna ta ce min rinqa gaishe ta na ce mata to. Kullum zan tsaya a qofar xakinta in gaishe ta ko kuma a tsakar gida, wata ran ta amsa wataran tayi kamar bata ji ba. Rannan na fito daga xakinmu da safe naga Mama da Babanmu akan qatuwar tabarma sun haxu har da Zuwaira suna karyawa. Na tsuguna na gaishe su dukansu har na miqe zan tafi sai Mama ta ce. “Humaira mai gaisuwa yau da yake da Babanku a wuri ita ma Zubaida ta ci arzikinshi an gaishe ta.” Nan da nan Babana ya tunzuro ai bata gaishe ta ko? Mama ta ce uhun to ai gata nan kusa da kai menene na tambayata ni? Ya juya wajen Zubaida da tanbayar ta gyaxa kai ta ce mishi eh. Nan da nan ya shiga banbami yana faxin za ki gani zan nuna miki duk abinda ki ke yi ina qyale ki ina yin hakanne kawai don kaina ba don tsoron wani ba, ba kuma wani ne yake sa ni nake yin abinda nake yin ba, don na ji ana cewa wai ni bana amfani da ra’ayina sai na wanda aka tsara min. Akan gaida Zubaida ne aka kafa min dokar da ta hana ni zuwa Makaranta gaba xaya tun daga ta boko har zuwa ta allo saboda wai ina qarasawa can gidan su Innata wai kuma a can xinne ake koya min mugayen halayen da kullum nake fitowa da sababbi. Ko ba a gaya min ba ni na san Mama ce tasa aka hana ni zuwa Makaranta daga baya ma aka ce an cire ni don dama tunda muka zo aji biyar muka yi jarrabawar kwalifayin aka ce ni kaxai ce naci, ni kaxai ce Gwamnatin jiha zata biyawa jarrabawar (WAEC) da (NECO), su su Habiba da Suwaiba sai dai in iyayensu sun matsu da su rubuta su su biya musu ko kuma su sake maimaitawa zuwa baxi. Ta sanyawa karatun nawa qahon zuqa ta tsani ganin na shirya zan tafi Makaranta tunda su su Habiba sun daina zuwa sun ce son kai aka yi musu saboda Malaman namu sun san Mallam mai babban allo. In tsaya cewa nayi baqin cikin hana ni karatuna ma vata lokaci ne kawai tunda ina son yin shi Inna ma tana so in yi gashi yazo qarshe aji shida nake. Inna ta kalle ni ta ce, to ke ki rinqa sammakon zuwa gaishe ta a gabanshi mana don ya yarda kina gaishetan, ya barki ki rinqa zuwa karatunki. Na ce ba zan sake gaishe ta ba Inna ya hana ni yin karatu don na daina gaida ita in rayu cikin jahilci shi kenan ina ce sai buqatarshi ta biya. Tayi maza ta ce hauka kike yi ne da kike gaya mishi irin waxannan maganganun, naja bakina nayi shiru illa iyaka ban iya hana hawayen da ke zuba gudu a idanuna ba, Inna tayi tayi in canza daga matakan da na xauka na daina gaida Zubaida har Maman ma sai in jera kwana biyu ni ba ta ga idona ba. Rannan ina jin ta tana cewa wata qawarta muu ai ta riga ta riqa, kin san ita ‘ya mace in ta riga ta xanxani garxin namiji to shi kenan rashin kunyarta sai ta buwaya. Qawar tata tayi dariya ta ce, Mama kenan wannan wani namiji ta sani? Rashin kunyar ‘ya’yan yau dai kawai, da in suka riga suka fara girma sia kaga kamar menene? Balle wannan ja’irar yarinyar da kullum ka ganta ka ra kyau take yi tanfar wata mai rikixa. Ai da gani ake tanfar qannenta za su fita, amma kin gani da yake dai kawai shi mai kyau to Allah ke ganin dama ya yi shi, ga kuma uwa uba tsabta da iya kwalliya. Mama ta ce uh, ai ku ku ke qara zugata amma in ba zuga ba to wa tafi kyau cikin yaran gidan? Nan in da kike ganinta ma lakaci guda xaya bata dashi in dai na kirki ne to ina kyau yake? Abinda kullum ake yi min gori dashi kenan rashin saurayi shekaruna goma sha bakwai a dunmiya amma ban tava saurayi ba ko a gida ko a hanya wani bai tava tsare ni ya ce min ke ‘yanmata ji mana, wa sunanki, sonki nake yi ba a tava yi min hakan ba sai dai in ga sa’annina da ma waxanda ba su kai ni ba da yawa ma nafi su kwalliya dama kayan kwalliyar don ni xin ma’abociyar ado ce da kuma kayan adon saboda Hajiya Kubra da dangin Inna da suka maida sai min kayan kwalliya tanfar ni kaxai ke gare su. Ko da Babana ya daina hirar dare a xakin Mama ran girkin Innata hakan ba yana nufin babu matsala ba ne, a’a suna nan birjik basa ma lissafuwa, babba daga ciki dai akwai minxira mana abincin da Mama ke yi kusan kullum a cikin neman abin da zamu ci Inna take. Babu kuma halin Mama ta xora tukunya itama ta xora ba ma zai yiwu ba, don haka sai dai ayi ta kame-kame, gashi kuma wai Mama ta ce sun yafewa Babana hidimar qanana-qananan abin buqata na gida dangin su omo, sabulun wanka da na wanki. Man shafawa har su kayan Sallar yara saboda wai hidima da nauyi sun yi mishi yawa, kowa ya yi wa ‘ya’yanshi kan hakanne yasa Inna ta ce to ko za a rinqa yin wadataccen abincin da yara zasu rinqa qo shi. Tun kafin Babana ya yi magana Mama tayi, Mama ta ce ai yanzu nan duk irin abincin da ake yi a gidan nan yara sun ce miki basa qoshi? Tirqashi, ina yaran suke? Su zo nan su gaya min su wanene ba sa qoshin? Yanzu ashe a irin qoqarin da Alhaji ke yi na ganin asiri ya ruhu har da wani mai qorafi akan abinci? Baba ya ce, ai Binta kam akwai qorafi akwai mita, akwai fitina. Ta dai ce ga abinda aka yi mata yauwa! Ko ga abinda ba ta yarda dashi ba uhun! Mama ta ce, to kaga, maimakon suzo suna yawo dakai a gari suna vata maka suna tunda su zuriyarsu bata rufin asiri ba ne raba girkin nan kawai kowa ka ba shi nashi. Baba ya ce, a’a ai sai dai suyi abinda zasu yi amma ba zan raba girkin gidana ba. Ta ce, ai kuwa da ka raban da yafi maka ni da Zubaida muna haxe tunda ita ai ba mai matsala ba ce, tunda tazo gidannan ka ji tayi da wani in ban da su da suka matsa mata? Ya ce haka ne, ta ce to ware ka bamu namu itama ka bata nata taje tayi tayi tana baiwa ‘ya’yanta suna ci suna qoshi. A haka aka raba girkin gidanmu, Inna ita da ‘ya’yanta su kuma girkin su yana haxe ita ce kuma mai yi tun daga ranar da aka raba girkin kuma ya zama komai Babana ya kawo tanfar wawashe shi ake yi. Tun daga hatsi zuwa kayan haxin, Babana da komai suyo shi yake yi ya ajiye sai aka ba shi shawarar daina sayen komai wai ya rinqa bada kuxin kawai ya kuma yarda kuxinsa biyun namu duk da ba ninka mu suka yi ba a yawa sai dai wai su xin manya ne, a kullum aka bamu kuxin namu sai mun zauna ni da Inna mun yi ta lissafin yanda zamu yi mu sarrafa su ta hanyar da za su ishe mu, amma ina! Ta yanda duk muka juya su basa wuce abin karyawa sai ko kuxin awon hatsi kuxin cefane kullum sai ta nema ga sabulun wanka da wanki ga man shafawa duk waxannan al’amura da Mama ta kawo Babana sai ya mance da cewar ita manyan ‘ya’ya ke gare ta, ga kuma uwa uba qaninta akan dukiyarshi wanda kuma a cikinta suke yin komai. Don haka maimakon Inna ta samu sauqi sai ya zama kullum matsalolinta qaruwa suke yi, kullum ka ganta a rame ramarta kullum qara yawa take yi. Inna mai xabi’ar wanki kullum sai ta zama yanzu tarawa take yi sai randa ta samu omo ko sabulu tayi ban kuma san dalili ba, ko Baba ya gane a yanzu babu abinda Inna take so ne irin zaman gidan nashi. Kusan kullum sai ka ji shi yana kafa mata wata sabuwar doka tare da faxin zaman nan fa ba dole ba ne in da takura a ciki a bar shi, tuni ya daina cin abincin da muke girkawa a dalilin wai bakin shi baya iya cin abinda bai da xanxan. Don haka kullum Mama ce mai ba shi abinci, zancen kar ya yi hira a xakin ta ma kuma duk bai taso ba. Tuni ‘yan uwan Inna suka ja suka tsaya kan sai lalle ta fita ta bar gidan wai azabar da ake gana mata tayi yawa, in miji yana son mace ai duk yanda ya kai da tsoron wata matarshi bai yi mata irin wannan azabar. Tashin hankalin da su Inna Balki yayinta mata suka zo gidan suka yi yasa Babana yin amfani da shawarar da Mama ta bashi na kai maganar gaban mai babban allo ko don ya jarraba dattakunshi ya gani tunda yayi alqawarin randa duk suka sake zuwa gidan aka yi faxa dasu to zai haramta musu zuwa gidan. Yana zuwa kuwa ya zartar da wannan hukuncin har kuma akan Hajiya Kubra da take matsayin uwa rta, sai ta nemi izininshi gaba xaya ‘yan uwan Inna suka xauke qafarsu suka kuma xauki mataki mai tsanani a kanta wai mijinta ya hana su zuwa wurinta. Ita kuma tana zaune bata fito ba in ya soma daga baya ta koma amma dai sun san ta nuna rashin jin daxinta kan wulaqancin da yayi musu, don haka duk wani taimako dake zuwa daga wurin ‘yan uwanta ya katse, ba sa ma zuwa balle su ga halin da take ciki. Ita kuma dama ba zuwa take yi ba, balle kuma yanzu da haka ta faru ko ta tambaye shi zuwa wurinsu sau ashirin baya bari in yaga zata matsa ma sai ya ce da izinina dai na hana in kuma kin ga za ki da naki izinin shi kenan.” Mallam mai babban allo ne kawai yake xan kewayo mu yazo mana da xan abin hasafi har ma ya bamu kuxi sai ko Baba Yahaya. Burin Inna a wannan lokacin bai wuce taga an yi aurena ba, tana gidan kullum ta kan gaya min in Allah yasa naga an yi bikinki lafiya to zan koma gidanmu zan koma wurin iyayena da dangina ba zan iya rayuwa babu su ba, in na ce to Inna su kuma su Atika fa? Sai ta ce uh’uh, su ko na bar su babu komai ba za su samu kansu cikin matsala mai yawa ba kamar ke, yanzu ina nan ma yaya? Balle kuma ace babu idona a kusa?” A yanzu duniya tayi matuqar yiwa Mama daxi sai wani irin qiba take qarawa a daidai lokacin da Inna ke neman lami ta baiwa ‘ya’yanta ta dai samu suci su qoshi kar su kwana da yunwa, wata rana bata samu. Ita Mama ta daina cin naman saniya sai kaji saboda Ado ya karve ta cefane, ita da bakinta naji ta tana gayawa qawayenta ai ita yanzu ta huta, Ado ke yi mata komai tun daga ce fane zuwa sauran hidimominta ‘yan kuxin da Alhaji ke bayarwa ajiye su kawai take yi saboda ba ni banin yara, qa’ida ne in sun miya da kaji da daddare to da safe kuma za su karya ne da farfesun kifi ko na bindi. Gashi kuma ba za su zauna a falonta su karya ba sai ta ce wai ina dalili? Gara dai a baza qatuwar tabarma a tsakar gida kowa ya baje, nan za su baje har da Babanmu da zai ga wucewar Sa’adatu ya xan gutsuro wani abu cikin abinda suke ci ya miqa mata sai ta ce Alhaji kenan, to kasan abinda suka ci a xakinsu? Ta manta cewar ko da ma me muke ci xin muna da haqqi cikin nasun tunda da kuxin ubanmu ake yi, Ado bai da wata harka ko sana’ar da zai saman mishi kwabo in ban da zaman shagunan Babanmu da yake ji ko kuma zuwa mishi aika zuwa aikan da zai yi wuya ace sau goma ba a dawo an ce ga wani abin da ya samu kuxin da aka yi akan da su ba. Haka kuma dole Babana zai haqura don kar Mama ta tambaye shi Alhaji ba ka san asara ba ne? to wane bincike zaka tsaya yi a kanta in dai ba so ka ke kayi abinda zaka zobe ladanka ba? Na tsani Ado, na tsani in xaga ido in ganshi a cikin gidanmu gani nake tanfar har da shi cikin abubuwan da suka yi dalilin shigar mu da Innata cikin halin da muke ciki, gashi don raini da wulaqanci sai ya shigo gida ya gaida Mama da Zubaida ya juya ya fita bai gaida Innata ba. In har da wani abinda na qi na kuma tsana cikin zuciyata to bayan Mama qanin nata ne. Rannan ina xakinmu a kwance cikin dare ban san Babana ya shigo xakin Inna ba, don a yanzu ranar da yaga dama ne kawai yake zuwa wurinta, ko da kuwa kwanan nata ne sai ya shige wurinshi yayi kwanciyarshi. Salatin shi na jiwo da qarfi tare da jan tsaki mai tsananin qarfi, kafin ya soma faxin “Kai wannan fitina da yawa take, ni Surajo naga abin da ya ishe ni, kin gani Fatima, tun dai ni a wurinki na gajiya ba kya ganin qoqarina bare alherina komai nawa a raine yake a wurinki, bani da fita a wurinki ba ni da shi a gun danginki kiin zo kin same ni cikin iyalina kin takura mana kin tasa mu a gaba da dokoki komai aka yi ki ce baki yarda ba kin watsa min haxin kan gida kin raba min kan ‘ya’yana sannan a hakan baki gamsu ba. To in kin ga har yanzu kina da matsala to za ki koma gidanku ne kawai, donni na gaji na gaji abin ya ishe ni haka. Ya balle qofar ya fita cikin daren har ya isa xakin shi bai daina mita da faxin maganganu ba. Inna ta miqe tana haxa kaya a cikin daren nan fito na same ta tana yi tana kuka wataqila yau ma so take ta tafi ban sani ba, tana ganina ta soma share hawayenta na ce mata kar ki tafi Inna, za ki je gida ne ki haihu a can? Kin san dai in kin tafi yanzu ba bin ki zai yi ba, ‘yan uwanki kuma ba za su dawo da ke ba, kiyi haquri ki daina gaya mishi damuwarki kiyi mishi shiru kawai, ba ke ma kina da abinda kike shiryawa ba? Ta gyaxa kai nuna alamar eh, na sake ce mata to kiyi haquri ta ce min to. Na koma xakinmu na kwanta cikin zuciyata tunani nake yi burin Inna bai wuce ta yi ta haqurin zaman gidanmu har zuwa lokacin da zata ga an yi aurena, in yaso sai ta tafi, ita a ganinta don ta bar su Atika ba komai ba ne don su basu da irin matsalar take ganin ni ina da ita. To amma yaushe? Yaushe za’ayi auren nawa tunda ni ko saurayi guda xaya ban tava yi ba, ban tava samun saurayin da ya kalle ni ya ce min ke ‘yanmata ji mana, me sunanki? Ni fa sonki nake yi ba balle a ce an zo qofar gidanmu ana kirana balle har a biyo ni da wani xan hasafi kamar yanda kullum nake ganin ana yi wa su Habiba a kowane lokaci naga Mama tana nuna wa Inna irin hasafi da ake yi wa su Habiba wanda a ciki zanga har da sabulayen wanka da na wanki har ma da su omo sai in ji zuciyata tana cewa ina ma nima in samu saurayin da zai rinqa yi min irin wannan kyautar da Innata ta huta da tara wankin da take yi tunda nasan tara wankin yana cikin lissafin damuwoyinta. Amma Mama sai ta nuna mata ta kwashe su duka ta yi tafiyarta da su ba za ta bata ko qwalli xaya ta ce ta wanke kayan qannen su Habiba ba, duk da addu’o’in alherin da take yi musu in ta ganni tanfar dai wacce ake yi wa qwalele. Rannan cikin dare Inna ta haihu yau ma xa namiji muka sake samu ni da ita mun yi murna Baba qarami shima ya samu xan uwa sai da na tayata ta yanke wa yaron cibiya ta yi mishi addu’o’i ta naxe shi a zani ta bani shi na kwantar dashi na juye mata ruwa taje wanka na dawo na naxe ledar da ta shimfixa ta haihu akai na goge komai na gyara shi tsaf. Na kawo mata ruwa don ta wanke shi ta kalle ni ta ce min wanke shi ki koya nace ah Inna ai ba zan iya ba ta ce koyi na zauna na wanke shi tsaf ina yi ina canza mishi ruwa har sau uku da na gama na shafa mishi man da muke shafawa na kuma sanya mishi riga cikin rigunan Baba qaramin da Inna ta adana don shi kam bai samu an sai mishi komai ba. Na kalle ta na ce, mata to me za ki ci? Ta ce babu komai ai bana jin yunwa tausayinta ya yi matuqar kama ni don na riga na saba ganinta tana cin abinci da na sha mai yawa idan ta haihu sanin da tayi ba mu da komai a xakin shi ne ya sanyata ce min ba ta jin yunwa. Naje na tsiyayo ruwan xumi a flask na sa mata suger kaxan da lipton na kawo na bata ta karva ta kwankwaxa, ta ce min to sannu je ki ki gaya musu na ce to naje na qwanqwasawa Mama qofa. Babana ya fito daga xakin Zubaida saboda jin qwanqwasa qofar da nake yi, yaya lafiya? Na ce mishi Inna ta haihu, Mama ma ta buxe ta haihu ne ko zata haihu? Na ce mata a’a ta haihu ne.” Ita da Babana suka yi hanzarin shiga xakin na tsaya a tsakar gida sai da naga sun fito daga xakin sannan na shiga. Washegari da sassafe Hajiya Kubra ta iso gidan saboda aiken da aka yi musu cewar Inna ta haihu, a wannan haihuwar gaba xaya dangin Inna babu wanda ya leqo ta daga Hajiya Kubra sai ko Hajiya ‘Yar dubu, sau biyu ina jin Inna tana gayawa Babana cewar tana so a sanya mata sunan Babanta wato a yi wa Alhaji Mai kuxi takwara, amma ranar sai kawai na ji Mama a tsakar gida tana faxin wai Ado aka yi wa takwara, don haka sunanshi Adam. Ai kuwa dai Mama a irin hidima da xawainiyar da yake yi da gidan ai gara da ki ka sa aka yi mishi takwara, in ji Zubaida. Cikin zuciyata na rasa abinda zan ce iyaka dai sai naga kai ni kam babu ma dai abinda ya dace da ni illa in fidda raina kan tunanin aure da ma sha’awarshi. Tunda ma na riga nayi sa’a bani da samarin tunda in dai ma aure irin na gidanmu ne nima haka za aje ayi min irin yanda nake ganin ana yi wa mahaifiyata, to ai ina ganin barinshi kawai shi ne zai fiye min sauqi tunda bana ganin kamar zan iya irin haqurin da take yi. Duk da vacin ran da na samu akan sunan da aka sanyawa yaron nayi wanka nayi kwalliya saboda Innan bata xauki sanya mishi sunan Ado da wani zafi ba, ta ce kowane mutum da sunanshi yake zuwa. Da hantsi na fito bayan nayi kwalliya sosai don in ma muna rashin komai to ni kam bana rashin kayan kwalliya gidan Anti Ramla nayi nufin zuwa don babu wani abin armashi da na gani a sunan namu, sai nazo wucewa ta falon Mama karaf sai na ji tana ce wa manyan qawayenta da suka riga suka zo mata sunan, ai bata ga komai ba tukuna ai sai na nuna mata ni xin ni ce ai sai na sata tayi nadamar auran mun miji da tayi. Gaba xaya suka kwashe da dariya cikin zuciyata na ce, oh’oh ko me zata yi wa Inna wanda ya zarce wanda take yi mata a yanzu oho? Tausayin Inna ya sake kama ni da na tuna duk da halin da take ciki bata nadamar auren Babana da tayi na kuma tabbatar a zuciyata ko ma me Mama zata yi ko tasa ayi mata ba za ta iya sata tayi nadamar da take cewa zata sa ta tayin ba. Tunda ita da bakinta ta ce min bata nadamar aurenshi domin ta haife mu a tare dashi, don haka ta gamsu da koma menene. To ban san me Mama ta faxa musu ba, wataqila don na shagala da tunani to amma na ji Hajiya Anwamu tana ce mata uh’uh Mama, uh’uh kar ki fara, kar kiyi wannan abinda kike shiryawa, ba don komai ba sai don kowa yasan wannan yarinyar ita ce uwarta. Kinga kuwa tura in ta kai bango to bata cika daxi ba, ita kuwa wannan yarinya da kike kallonta yanda fa bata yi kama da uwarta a halitta ba haka nan ko kaxan halinsu ba xaya ba ne don haka qyale mata ‘yarta kawai ai kin samu ina laifi wata da nakuda wata faxin sunan xa? Ban da haka ban da haka ko hana ‘yan uwan yarinyar nan zuwa in da take da ki ka yi ai ya ishe ta. Ina fita waje Habiba da Suwaiba na gani suma sun sha kwalliya kamar in wuce su in yi tafiyata sai na tuna maganganun da na bar uwarsu tana faxi, don haka sai na matsa kusa da su na same su. Suwaiba dai tuni ta riga ta tsorata dani, don sau biyu ina yi mata dukan tsiya. Na isa wurin kenan sai na hango Ado yana fitowa daga cikin gidansu yasha kwalliya yayi matuqar yin kyau, kallo xaya nayi mishi na kawar da idona daga gare shi. Na kalle su na ce musu, me na ji ku kuna fa xa xazu? Habibna ta ce, abinda ki ka ji muna faxin shi… kan ta gama nayi maza na café bakin nata nufina wai in yi mata yanda itama da take yi min, sai Ado yayi maza ya qaraso yana faxin. “Kai, kai ku bari ku bari, ke fa fitinanniyar yarinya ce.” Yana maganar yana nuna ni da xan yatsa, na galla mishi harara na yi mishi wani lalataccen kallo na sama da qasa sia da na murguxa mishi baki kafin na ce mishi daxin abin dai a gidan ubana nake fitinar duk iyayin mutum bai da yanda zai yi dani tunda shima zaman cin arziki yake yi. Bina da kallo Ado ya yi, kallo kuwa mai tsananin cikin kaxuwa da mamaki bai tava sanin zan iya yin abin da nayin ba. Nasa kai na wuce nayi tafiyata, daga shi har su Habiba babu wanda ya ce min qala. Ban dawo gidan ba sia da yamma, nazo na samu Hajiya Kubra tazo ta tafi ga kuma kayan da ta kawowa Inna zannuwan da ba su wuce goma ba, sai kayan jarirai babu wani yawa suma sai dai ta kawo mata kuxi masu xan auki wai ta riqe a hannunta saboda hidimar yara. Tun ban gama zama ba Inna ta soma tanbayata me yaron nan yayi miki ki ka zage shi? Na ce shi yazo ya gaya miki na zage shi? Ta ce a’a su Habiba ne suka gaya wa Mama shi ne ta ce min in gaya miki kar hakan ya sake faruwa. Don haka kar ki sake, na ce an zagi Ado Inna suyi abinda za su yi an zage shi, Inna ta zuba min ido tana kallona zata yi min magana na ce mata kar kiyi min faxa akan shi Inna ki bar ni kawai ‘yan abu kazan uba na sake mulmulo wani ashar xin na antaka musu. Shiru tayi tana bina da kallo saboda ita ba mai son tashin hankali ba ne, na nemi wuri nayi kwanciyata ba tare da da na gaya mata hirar da na ji Mama da qawayenta suna yi ba. A yanzu Habiba ma shakkar haxuwarmu wuri xaya take yi, don ta gane babu abinda nake so irin danbe ya haxa mu ta kuma riga ta tsorata da waxanda take ganin mayi, don haka ta daina shiga harkata balle aje ga tsokana. Rannan mun haxu da Ado a wajen wani biki da abokan Baba suka haxa ‘ya’yansu aure, don qara qarfafa zumuncin da ke tsakaninsu, dukanmu mun je har da su Habiba mun kuma sha kwalliya don mu a gidanmu kwalliya muke har da ta gasa. A yau xin kuma na burge qwarai don har da zinari nayi adon saboda Hajiya Kubra ta dawo daga Ummara, don haka ta sayo min xan kunne da sarqa har da zobe masu kyau da kuma girma qirar Dubai. Cikin kuxin Innata dake hannunta wanda take sawa ana juya musu, to Ado ma yana cikin abokan ango ya kuma sha kwalliya don ya iya sanya sutura mai tsada gashi kuma kwalliyar tana yi mishi kyau, don ya riga ya qoshi ya zama saurayi mai kwarjini da nagarta. Wata yarinya da muke tare da ita Sadiya ita ce ta ce lah, su Humaira ga kawunku sai da na waiwaya bayana muka haxa ido dashi sannan na juyo na kalle ta ba kuma tare da na ji kunyar Habiba dake tsaye a gefenta ba, na ce mata uh’uh Sadiya ba kawuna ba dai kawun su Habiba ne, ai ni babu wani abin da ya haxa ni da shi in ban da zaman cin arziki da yake yi a gidanmu.” Sum-sum Sadiya tayi ta bar wurin don ta san Ado ya ji abin da na faxa su kuma suna girmama shi saboda ya iya kama kanshi, ita kuwa Habiba ta kama fuskarta ta tsuke alamar rashin jin daxi, sai dai bata tanka ba. Nima na ci gaba da harkokina, ana buxe falo aka soma neman ‘yanmatan da za su taka rawa na fita, ba tare da na damu da tsayuwar Ado a wurin ba, don dai in nuna mishi bai da wata kima a wurina. A wannan lokacin kusan kowane lokaci Mama bina da kallo take yi cikin takaici da kwafa ban dai san dalili ba ko tasa mata ‘ya’ya da nayi a gaba ne su Habiba da Suwaiba waxanda a baya suka yi matuqar takurawa rayuwata tana kallo, oho. Sati guda da gama bikin gidan su Sadiya ranar ma ranar wata Juma’a ce, nayi niyyar zuwa gidan Mallam mai babban allo wanda na daxe ina nerman izinin zuwan wurin Babana bai bani ba sai yau. Don haka kwalliya sosai na yi na fito daga gida. Ado da wani abokinshi Nasiru suna tsaye a inuwar bishiyar qofar gidan mu, ina jin sanda Nasiru ya cewa Ado kai kai kai yarinyar nan haka ta zama? Ado yayi maza ya kawar da kanshi can gefe ga barin kallona. “Menene na wani kai kai kai? Sai ka ce ka ga wani abin da baka tava sani ba, in ka naso ka wai kayi magana shi ke nan dama ba wani saurayi ne da ita ba, ‘yan uwanta gaba xaya sun samu manema har an kawo sadakinsu amma ita babu kowa babu wani malalacin.” Nasiru ya ce, ai yarinyar ce kwarjini ne da ita gata bata bada fuska in ka dunfareta da nufin yi mata magana ma dole ka daina don gabanka faxuwa zai rinqa yi. Ya yi tsaki ya ce, ka zama ragon maza kenan, don haka tunda kana cikin waxanda take faxar wa da gaba to bari zan yi maka iso a cikin gidan in yaso ko baka zo taxi ba nasa a xaura auren a kawo maka ita har gida sadaka.” Nasiru yayi dariya ya ce, wannan shi ne zance ka dai yi ne don ka ji ta bakinta tun yaushe ne ma aka daina yin sadaka da ‘yanmata balle kuma irin wannan mai tsadar.” Ado ya ce, in na dai an daina yin sadaka da ‘yanmata to wannan kam zan iya sa wa a baka ita, in kuma kana musu to zuba ido kawai kaga abin mamaki. Wucewa nayi na tafi zuciyata a cike da vacin rai mai tsanani a dalilin jin maganganun cin zarafi da Ado yayi min a gaban abokinshi babu abinda yafi komai qara min vacin ran kuma irin sanin da nayi cewar duk maganganun nashi akan gaskiya suke. Bani da saurayi su Habiba da Suwaiba an kawo sadakin aurensu sannan shi xin da zai nishaxi ya ce wa Mama yana son a baiwa Nasiru abokinshi ni, ina ganin babu abinda zai hana ayi hakan tunda shi ne Mama, Mama kuma ita ce Babana. Har na isa gidan mai babban allo ban gama wastsakewa daga wannan vacin ran ban gama wastsakewa ba sai dai ina shiga wajen shi na soma murmushi a dalilin son da yake yi min, ina isa gabanshi vacin raina yake gushewa. Fura na samu yana sha, don haka na zauna muka sha tare ina mitar babu sugar ni ya barni in sa koxan kaxanne shi kuwa yana faxin ai ba zai yiwu ba don ba zan bar ki ki vata min ita ba sai dai in ki kawo wani abin in xiban miki naki sai ki sa duk abinnda kike son sakawa, na ce a’a tare da kai zan sha ya ce to kuwa sai kisha mara sugar. Ya gama shan furar yana kallona ina qarasa, sahan wacce ya bar min sai naga yayi murmushi na ce mishi menene Mallam? Ya ce kallonki kawai nake yi ina tunaninki sai aukin kwalliya da iya lanqwasa amma har yanzu ban tava ganin wani yazo ya gaishe ni ba a cewar ke kika turo shi na ce azo a gaishe kan? Yayi maza ya ce zan qosa mana Aisha in ta samu aka kan dake xin ai zata samu xan wani sauqin. Na ce uh ni in ban da saboda Inna da kuma gorin da ake yi min mafa Mallam ni auren nan ba wani son shi nake yi ba. Ya xan gyara zama kaxan ya ce aure kuwa ai abin so ne Aishatu, Ibada ne kuma rufin asiri ne ina ce kina karanta surorin da na ce miki kullum? Na ce eh Mallam kullum sai na karanta (Yasin) in karanta (Arrahaman) in karanta (Waqi’a) sannan in karanta (mulk). Yayi murmushi ya ce, madallah ashe qoqari ne da ke to rinqa haxawa da (La haula wala quwata) qafa casa’in da tara take yi qarami daga cikin magungunan nata shi ne baqin ciki na ce to Mallam na gode, muka xan yi hira na miqe na ce mishi bari in shiga ciki in gaishe su don in zo in tafi ya ce min to. Na gama abinda zan yi a cikin gida na dawo wurin mai babban allo zan yi mishi sallama sai na same shi tare da Alhaji Abba, wasa dani da yake yi tun ina ‘yar qaramata ya sani sakewa nima nake wasan dashi a matsayin ‘yar Inna da xan kawu don shi ya ce Inna uwa ce ba ‘ya ko qanwa ba. Na kalle shi cikin murmushi na ce, ah, ka ce ka ji nazo ne ka biyo ni? Ya yi wata irin dariya kafin ya kalli mai babban allo ya ce ni Mallam in ce ko dai wannan irin kwalliya da ake tsalawa tana biyan kuxin sabulu? Mallam yayi dariya ya ce, to ina fa na sani tunda ni har yanzu ban gani a qasa ba, ya qyalqyale da dariya jin daxin abin da Mallam xin ya faxa, ya ce to ko dai ni zan soma zuwa gaishe kan ne kawai Mallam don ka gani a qasan? Mallam ya ce a to ga ka nan ai ga ta ku ku kasan saura. Alhaji Abba ya kalle ni cikin yanayin murmushi da zolaya ya ce, Yaya ko zan fito ne kawai muyi ‘yar gida ko kuwa Mallam? Mallam ya sake cewa, ato, ai ga ka nan ga ta nayi murmushi na ce sha kurumin ka ni na da ka ke kallona gal a leda zan aura. Mai babban allo ya ce uhun’uhun ka ji sakarcin nata ba? Da wani gal a leda da ya wuce wanda zai riqe auren yaga darajar iyayenki? Ban kula zancen na mai babban allo ba don naga zancen yana nema yayi nisa. Un, ban kuxin mota Mallam ni zan koma gida don Babana ya ce kar in yi yamma sosai. Eh, ai yana da gaskiya Mallam yashiga dube-dube yana qoqarin tattaro duk kuxinshi ya bani kamar yanda ya saba yi kullum. Alhaji Abba ya karkace yana qoqarin cusa hannunshi cikin aljihun wandonshi, qyale ta kawai Mallam bari in karve ka ba da kuxin motar nan a yau tunda ga dukkan alamu ma na fika ganin kyan kwalliyar tata ta yau. Ya zaro kuxin da bai qirga ba ya miqo min nasa hannu biyu na karva, bai bari ya ji godiyar da nake shirin yi mishi ba sai ya ce min cewar da ki ka yi ni ba gal a leda ba ne ba fa ba zai hana ni biyo ki gida don taxin ba, bari in yi kwaskwarima in zo ki gani ki ga yanda zan zo miki a wani santalelen saurayi za ki gane wannan qatuwar rigar da nake sanye da ita, ita ce ta hana ki gane ni xin na ma fiye miki gal a ledan ba. Mai babban allo sai faman dariya yake yi yana faxin har da su kwaskwarima a ciki kenan, ka yarda kai xin ba gal xin ba ne tunda sai ka haxa da kwaskwarima. Suna dariyarsu ni kuwa na sunkuya na tsince ‘yan kuxin da Mallam ya riga ya fito dasu, shi kuma sai faxi yake ka ganta ko? Ba kaga irin halin nata ba sai ta haxa har da nawan ta kwashe. Na isa gida gaban Innata cikin farin cikin gamuwa da Alhaji Abba da nayi, tuni na man ce da takaicin maganganun banza da Ado yayi min sanda zan tafi, na samo mana kuxi Inna na gamu da Alhaji Abba ina murmushi nayi mata bayanin komai na xebo kuxin daga cikin jakata, kin gansu? Na nuna mata itama tayi murmushi ta shiga yi mishi addu’a na gama lissafa su dubu goma sha uku ne na sake wani murmushin na ce mai kuxi ne Abba ko qirga su bai yi ba ya bani. Ta sake wani murmushin cikin jin daxi ta ce, eh ai shi arziki haka yake ba daga yawan shekaru ba ne kyauta ce kawai daga mai bayarwan na ce haka ne. Na dunbazu wasu kuxin na miqe zan fita don na saba in mun samu kuxi bani kawai Inna take yi ta ce in sayo mana abinda nasan shi ne muhimmi, ina za ki da waxannan kuxin? Cikin natsuwa tayi min tambayar na ce mata sabulun wanka da na wanki zan sayo mana masu yawa don su daxe basu qare mana ba, sai ko biskit da indomie saboda su Baba qarami ba ta yi magana ba shiru tayi alamar ta amince kenan, na wuce na fito da nufin sayo abinda zan je sayowa. Sai kawai na hangi Ado a falon Mama sun haxa kai suna qus, qus, qus, ga alama kuma basa son wani ya ai abinda suke tattaunawan, gabana ya yanke ya faxi kar dai maganar da Ado yayi xazu a waje mai kama da shaqiyanci ne yake shirin mai da shi gaskiya? Har naje na dawo ba su gama maganar ba, hankalina ya yi matuqar tashi don kuwa nasan Mama da Ado za su iya yin komai a kaina, don Innata tayi baqin ciki, tunda sun riga sun tsarawa kansu cewar ni xin bata haxa ni da kowa ba cikin ‘ya’yanta. Nan da nan hirarrakin Mama da qawayenta da nayi ta ji suka rinqa dawo min, roqon da suke yi ta bar wa Innata ‘yarta kar ta sake jefa ta cikin wani baqin cikin, ko ba a gaya min ba kuma nasan ba kowa ba ce wannan ‘yar ni ce. To ga Ado ga kuma abinda na ji ya fito daga bakinshi gashi kuma na gansu suna tattaunawa, irin tattaunawar da suka saba yi in suna shirin qulla wa Inna wata qullalliyar. A xakinmu na rasa yanda zan yi in gaya wa Inna da nake ciki tunda ita kuma a yanzu damuwarta ta ragu in ma bata gushe duka ba ta samu abinda za ta baiwa ‘ya’yanta su ci gobe da jibi da gata da citta, don haka sai kawai na wuce naje na hau gado can cikin zuciyata ina tunanin me zan yi wa Ado? Me zan yi mishi in nuna mishi cewar ni ma xin ta Maman ta ce kowa ya ci tawo da ita miya yasha. A yanzu kam madan ni kam ina ganin kamar zuciyata ta kai wani matsayi da bata da wani wanda ta qi ta kuma tsana take jin zafin shi take neman samun damar xaukan fansa a akan shi irin Ado. Washegari da sassafe Innata ta amsa kiran da Babana yayi mata a xakin Mama a gaban kuma Maman har ma da Zubaida. A gaban Maman kuma da Zubaidan ya baiwa Innata wa’adi na kwana uku wai in fiddo da miji ya haxa mu da su Habiba yayi mana don ba zai yi auren Habiba da Suwaiba ya bar ni a cikin gidan ina zaune ina zubawa matanshi rashin mutunci ba. In ma dai mu bi wannan umarnin da ya bayar ne na kawo mijin cikin kwanaki ukun da ya ambata ko kuma mu tattara mu bar mishi gidan. Mu ci gaba cikin yardar Allah a littafi na biyu tare suka fito. HAFSAT C. SODANGI 07035586299 18/7/2012 28/8/1433 Hijira