MIJIN TACE 3 NA HAJ. HAFSAT C. SODANGI (Mrs. Abdullahi Yunus Dabai) HAKKIN MALLAKA Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat Chindo Sodangi ne. (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) 17/1/2013 07035586299 GODIYA Godiyar ga Allah take, Subhanahu wata'ala, Masanin yau da gobe, Gwani Mai Hikima, wanda yayi halitta tasa duka bibiyu, mace da namiji, ya kuma halicci mutum da aljan don su bauta mishi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga cikamakin Annabawa Shugaban Manzanni, Annabin tsira, Annabin karshe Muhammad (S.A.w), da Alayensa da Sahabbansa, da wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe Alkiyama. Bayan haka, ina mika godiyata ga Makaranta littattafaina, wadanda kullum sakonninsu basu yankewa a gare ni, suke ma kara min hima wajen ganin na fiddo musu da sabbin takardu. Na gode da hakurinku a kaina, na kuma gode da kulawarku kan rubutuna. Ubangiji ya saka muku da mafificin sakamako. Na gode. Hafsat Chindo Sodangi 17/1/2013 2 SADAUKARWA Sadaukarwar kullum ta Iyayena ne saboda kulawarsu da tarbiyarsu a gare ni. Alhaji Chindo Muhammad Sodangi, da Hajiya Fatima C. Sodangi, Allah ya saka muku da mafific sakamakonsa, amin. TUKUICI Tukuicin littafin na wana ne. Mallam Lawal Chindo Sodangi (N.S.I.T.F. Abuja) da Amaryarsa Zuhuriyya Ibrahim Usman Ubangiji ya baku zaman alfiya da kwanciyar hankali, amin. YABO Babayo Yusuf Dabai Ahmad Bello Sodangi Na gode FATAN ALHERI GA Hajiya Aisha Garba Mai Kwano Hajiya Lubabatu Illelah Hajiya Fatima Usman Muhammad (Nigerian Defence Academic Kaduna) Na gode. 3 JINJINA Jinjinar taka ce Abba. Aliyu Chindo Sodangi da Amaryarsa Saliha Yusuf (Ardo). Ubangiji ya zaunar da ku lafiya, ya kuma rufa muku asiri, amin summa ámin. KUNA RAINA Hajiya Maryam Dan Hassan (Mami) Hajiya Aisha Balarabe (Jazan) Hajiya Hafsat Mustapha Fatiman Hamzą Isah (Batulu) Hujiya Mariya Saleh Tsafe Hajiya Fatima Abbas Salmanduna Na gode. GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA Hajiya Sameerah Gambo Dage-dage Na gode. INA SONKI Asma'u Bello Nazir Allah ya raya ki da Imani. INA SANE DA KU Na'ima Nura Bashir Galadanci (A.K.T.H. Kano) Fatimah Yusuf Hashidu (Mrs Hon. Jibrin) 4 Sumayya Ibrahim Sumayya Baba Idris Fatima Ibrahim Zaria Alawiyya Ado Unguwar Dorayi, Kano Na gode BAN MANCE DA KE BA Hajiya Atti Manzo, Marubuciyar littafin nan na(Sarauniyar Zuciya) Allah ya kara basira. GAISUWAR BAN GIRMA Hajiya Bilkisu Ibrahim Na-Bature (Mrs Salisu Ahmad Funtua) Allah ya kara lafiya, amin. MANUFA Bana nufin habaici ko yi da wani cikin lamarin rubutuna, yi kawai nake yi don isar da wani sako. Na roki masu ganin kamar an yi da su, don Allah suyi hakuri. Na gode. 5 Littattafan SODANGI: - Uwar Miji - Naga Ta Kaina - Wayyo Duniya - Rabon Kwado... - Cikar Alkawari Tabbataccen Al'amari Yi wa Wani... - Abu Naka... - Nufin Allah - Garin Banza... Gani Gare Ka - Me Za Mu Ce Da Maza? - Biyan Bukatar Rai Kifi Na Ganinka... - Da Kamar Wuya... - Daga Kin Gaskiya... - Shamaki - Mai Uwa... - Hattara Mata Da Kicin Dinsu - Mata Masu Duniya - Duk Daya Kyautata - Ayi Dai Mu Gani.. - Wacece Ni? Wata Fuskar... - Mijin-Tace 6 MIJIN-TACE. 3 Tuni zuciyata ta tsayar min da cewar ba zan bi Ado ba, don kuwa na gane zabin da zai fi dacewa da ni shi ne zabi na zama da Mahaifiyata da dangina, ba zai yiwu in tafi in bar innata cikin bacin rai da bakin ciki da damuwa da kewa mara misaltuwa ba. Kowa yasan Innata, yasan babu abinda take so irina. Shi da kanshi Ado ya tabbatar min da cewar tsananin son da Innan take yi min ne ya sanyata saurin yafe mishi laifukan da yayi mata a baya, kafin auren namu. Ta kuma yi gaggawan maida shi da a wurinta, ta hanyar kyautata mu'amalla a tsakaninsu, ta girmama al'amarinshi ta hanyar bani umarni na in kyautata mishi. To in kuwa har haka ne shi da kanshi yasan wannan, to ai shima bai kamata ya zartar min da hukuncin tafiya kauye ba, in dai ba hakan yana cikin ajandar su ba ne shi da Mama. Tunda dama da gayya Marnan ta zabe shi ta ce a ba shi ni. Don haka ban yarda da su yarda na dari bisa dari ba, don haka ba zan bishi ba, zan zabi zaman gidanmu ne in rabu da shi yayi tafiyarshi, in rabu dashi in rabu da fitinar Mama, ba zan taba yarda 7 soyayyarshi ta wata uku da yaudare ni ba in rabu da Innata, in rabu da ita cikin &unci da bakin ciki bayan nasan soyayyar da take yi min ita ce ta gaskiya, ita ce ta asali, ita ce wacce bata karewa saboda babu algus ko wani magudi a cikin ta, don ba yi min ita take yi don taga wani abin sha'awa a gare ni ba. Ado kuwa fa? In ma har da gasken ne yana sona, to ya fara son nawa ne a daidai lokacin da watan amfanina ya kama a wurinshi, ya fara sona ne a daidai lokacin da aka bashi shawarar karbar aurena tunda tun zuwana gidanshi sau daya ban ga wata alamma da ta nuna yana nufin nuna min tsana ko kiyayya ba. Tun zuwana a cikin kokarin shawo kaina yake, don ya samu zaman lafiya da kyakkyawar mu'amallah a tare da ni, amma kafin wannan lokacin babu irin wannan mu'amallar a tsakaninmu, in kuwa haka ne to zan iya cewa da wata lagwada da ya hango wacce ya gane in yayi wasa ya rasata kanshi ya yi wa asara. Ta hanyar tsiya da nuna fin karfi kuma yasan ba zai taba samunta ba, tunda ni da shi ai kar-ta- san-kar ne, ya sanni na san shi, don haka yayi gaggawar watsar da makaman fada ya nemi hanya 8 ta rarrashi da kyautatawa ba gare ni ni kadai ba, har da ita me haifiyata da kuma sauran dangina. In kuma har nace Ado ya canza ra'ayin shi ne a kaina ya janye daga taimakon 'yar uwarshi kishi ta hanyar wulakantata don su kara sanya mahaifiyata cikin karin bakin ciki kan wanda suka saba sanya ta? To ba sakarci yayi ba, don kuwa nasan maza da yawa za su iya yin irin nashin a kaina, tunda ko da ban taba daukan kaina na jefa cikin kyawawan matan da kyansu ya kai ya kawo ba, saboda ganin kyawawan yan uwana da nake tare da Su, su Aliya da Atika, wadanda su din dukkansu farare ne so, ga su kuma da dogon gashi tunda su kama da Innata suka yi. Na sani tun ina yarinya 'yar karama nasha jin Innar tawa tana gaya min cewar ba fin ki komai suka yi ba, ai bakar fata ba muni ba ne, Babanku ai kyakkyawan mutum ne, ban kara yarda da hakan ba sai da na girma na zama cikakkiyar budurwa, na ganni a tsaye sanbal har ban bukatar sanya dogayen takalma, saboda tsayin nawa ya ishe ni. Sai dai kawai in yi hakan wani lokaci don nishadi, ga ni da kyawawan idanuwa masu tsananin fari da wadatacciyar girar ido da gashin idon, sannan ni din ba 'yar siririya ba ce, ina kuma da 9 cikakken kirji gami da damammen ciki da ya sanya kudurina ya samu damar fitowa, gashin kaina ba mai tsayi ba ne, amma a cike yake gashi kuma da laushi. Ga shi bakar fatar tawa tasha gyara saboda Inna bata yarda in shafa wani mai ba tare da ta zauna tayi mishi hadi na musamman ba, ba wai don fatar ta canza daga launinta na bakin ba, a'a sai dai don ta kara laushi tayi kyau. Sannan kuma ga ni ma'abeciyar tsabta da kamshi a kowane lokaci, sai nake ganin tamfar wadannan dalilai su ne suka janye Ado suka yi dalilin da suka hana shi jarumtakar ci gaba da taimakon 'yar uwar tashi fadan kishin kamar yanda ya saba, sai yaga maimakon yayi hakan a karshe ya rasa ni, gara mishi ya rike auren shi in yaso ko ma menene zai biyo baya bai damu ba. To in kuwa haka ne, ai son nashi yana da dalili, sabanin na Inna da shi makaho ne, yin shi kawai take yi sona kawai take yi a kowane hali nake kuma ba za ta daina ba, don haka ba zan bar ta in bi wani Ado ba. Haka nan don nace ba zan bishin ba, ba wani laifi nayi ba, zai je ya samu wata a gaba. Sannan cikin dangin shi zai koma ban da haka ma juna biyu 10 ne da ni, zan haifan mishi da ko 'ya yazo ya dauka, wannan ba karamar riba ba ce a wurinshi. Sannan zai tafi ne tare da iliminshi da yayi arnfani da dukiyar ubana ya nema, ai ko da ya dawo mishi da abubuwan shi da ke wurinshi bai dawo mishi da ilimin ba, ya rike wannan balle ace shima ya ajiye Babana ya samu ya rabawa nashi ya'yan da sakarci ya hana su yin karatu. Don haka ba zan bishi ba, ko don in dandana mishi bakin cikin rasa ni bayan ya soni ba zan bishi ba, tunda bai so ni a lokacin da ya dace ya sonin ba, ya so ni ne bayan ya taimaki 'yar uwarshi sun gallawa Inna, sun gana mata azaba ita da 'ya'yanta. Ya so ni ne bayan na gama wahala a hannun Mama, na gama azabtuwa da azabar dukanta, bai so ni a lokacin da nake bukatar taimako ya taimake ni ba, don haka ba zan bishi ba. Sannan na riga ia sani ko ban bishi ba ba zai sake zama tare da Mama ba har yayi mata irin biyayyar da yayi mata ba a baya, don kuwa ya riga ya kamu da sona matsanancin son da ya ba shi dama da kuzarin iya yin fito-na-fito da ita kaina. Don haka ko don in dandana musu wannan takaicin dukan su ba zan bi shi ba. Ina cikin wannan zancen zucin, kalaman Mama 11 suka katse ni, suka dawo da natsuwata ga kallo da sauraron ainda ke faruwa a tsakar gidan namu. Daga ido nayi na kalli Ado a dalilin jin irin kalaman da Mama ke yi mishi. A durkushe yake irin durkuson da yafi kama da ace dan kiris mutum yake jira ya ruga a guje, makwal wuyanshi sai kai kawo yake yi a tsakanin wuyanshi, yayin da idanuwanshi suke kaina ko Rifta su baya yi. "Dama ka hakura ka fidda ranka a kanta, ka kwantar da hankalinka ka samu natsuwa da yafi maka, don kuwa ba za ta bi ka kauye ba, uwarta ma ba za ta yarda ka daukan mata ita ka kaita kauye ba. Sun dai cuce ka ne kawai suka yi maka irin surkulle-surkullensu da tsatsube-tsatsuben su suka mallake ka suka yi maka dandani-haukaci, saboda sun san baka taba sanin mace ba sai akan yarsu, don haka suka kidimaka, to ba ita kadai ba ce a haka. Kar kaga kanmar ba za ka sake samun irinta ba, dubu suna nan kamarta wasu ma sun fita da yawa ma kuwa." Bata Yahya ya kalli Mama cikin wani irin yanayi da yafi kama da na jin kunyar kalaman nata, ya ce "Ke madajan wadanne irin kalamai ne 12 wadannan ki ke furtawa a cikin mutane na rashin mutunci da rashin ganin girman mutane?" Ta ce, "Ah'ah, bar ni kawai in gaya mishi gaskiya, in ya hadiyi zuciyata a kanta ya mutu ma to shi kadai ya yi wa kanshi asara, tunda uwarshi kam ai ta riga ta dade da mutuwa, ni kuma ya riga ya nuna min iyakata a kanta, ya watsa min kasa a ido, ya kunyata ni ya tozarta ni a gaban makiya kuma abokan gaba yasa su sun yi min dariya, to ai babu wani abu a tsakanina da shi a yanzu tunda an yi mishi ingiza mai kantu ruwa ya yarda. Wai har ni ka ke dawowa da kayayyakina da suke wurinka akan wannan ja'irar yarinyar, shu'uma, yarinyar da kwanannan ta gama yi maka gori a kan kauyancinka, tana fadin ta godewa Ubangiji ita gidan ubanta gida ne mai albarka, kowa yazo cikinshi zai ci arziki ya koshi ya murje, ya goge, yasa sutura ya fita daga kauyancinshi. In ba wanda ya san shi ba babu mai kallon shi ya gane ina ne asalin shi yake? Shi yasa ita ko bakunta bata barin gidan ubanta taje yi a na wasu. Ba Humaira ba ce ta furta maka wadannan kalaman?" Ta zuba mishi ido tana kallonshi, sanin da nayi cewar gaskiya ne daga bakina maganganun suka fito yasa nima na zuba mata nawa idanuwan 13 ina kallonta. Tsana ne karara ya bayyana a idon Mama, zai yi wuya a yau in har da akwai sauran wani abu naso ko tausayi a tsakaninta da shi, to me yayi mata? Ko kuwa don kawai ta ce ya saki aurena ya ce a'a? To in har haka ne yasa a yau Mama ta tsane shi to anya Mama tana yin so kuwa? Ko kuwa dai ita din takan so mutum ne kawai a gwargwadon irin amfanin da take yi da shi? Ai baka tozarta ni ba kanka ka tozarta ka tsiyata kanka don ka burgeta, ta cc zata bi ka ba kuma zata bi kan ba kai ne ka zabe ta ka bar ni amma ita ni ba za ta zabe ka ta bar uwarta ba, ko kuwa Humaira? Ta juyo da kallonta gare ni, za ki iya yin rashin hankalin zaben namijin da ba shi da tabbas ki bar iyayenki uwa da uba tunda kin san su ba sa son tafiyar taki? Ado ai dan kauye ne, kauyen kuma babu wanda bai san shi ba, a nan sai ko ke din sussuka ne da surfe gami da nika kafin aci abinci gidan su Ado kuma wani irin gida ne da giran shi ya hana shi yin fasali. Don ko katangar arziki basu samu arzikin yi mishi ba, gasu da wani irin yawa mara sha'awa, sannan wai don rashin adalci duk mutanen gidan 14 nan suna ci ne a tukunya guda daya mace daya kuma ke tuka shi, ko karya nayi nuku? Ta zuba mishi ido tana kallonshi, ya girgiza kai a hankali cikin natsuwa nuna alamar ba karya tayi ba, gaskiya ta fada, ta gyada kai nuna alamar gamsuwa da amsar da ya ba yar tare da fadin kin ji ba? Shina ya ce ya karya nayi bà. Kalaman batanci da tozartawa da Mama ke'ta faman furtawa a kan Ado, anyi-anyi da ita koama ta daina ta ki, sai suka sanya ni canza ra'ayina naga ko ba zan bishi ba to ba a gaban Mama kuma zan faii hakan ba, tunda na gane abinda take son ji daga gare ni keren, don taji dadin tozarta shi ta yanda zai kunyata yayi bakin ciki. Ke Hajiya da kin bar yarinyar nan ta zabi abinda ta zaba, don musan abinda muke ciki." Bai sauraronta shirun nata ba balle ya gane tabi umarnin nashi ko bata bi ba? Ya dawo da zancen nashi gare ni. "Ke Aisha wanne ki ka ga za ki yi? Za ki bi mijin naki ne ko ba za ki bishi ba?" Na daga ido cikin natsuwana kalli Mallam Harisu makwabcinmu da yayi min wannan tambayar, na ce mishi "Zan bishi Baba." Ina fadin hakaa dakin ya dauki kabbara mai 15 karfi tare da hamdala, daga wurin Ado da Liman, Mama kuwa kurma ihu tayi da iya kacin karfinta, tamfar wacce wani mugun abu ya samu, tana fadin ita kam ta shiganga, to bara kada ta mutu ta bar rai a duniya, wayyo!! ita magadan an kwace mata dan uwanta an shiga tsakaninsu an rabata dashi, ina ma dai ace taji kashedin da wannan yarinyar tayi mata? Baba Yahya ya ce, "Kaltume ba? Ni da kina ji da mugun nufi iri-iri da ba ki aiwatar da shi ba, amma ga ki nan ga irin abinda ki ke shukawa." Babana ya yi maza ya mike a fusace a'a Alhaji, kar ka ce zaka yi wa Mama baki, in dai akan wannan ja'irar yarinyar ne, ai gata nan ga wanda ta zaba din, ba dai a kanshi ta wulakanta ni ba? Na ce kar ta zabe shi ta zabe shi? To in ta bi shi suka tafi ta tafi kenan har abada ba za ta sake tako min cikin gidana ba, kuma ma in naga dama inyi mata baki ta lalace tabi duniya, kowa ya huta, tunda ban ga amfaninta ba, tunda tasa Mama take irin wannan kukan. Nima da iyakacin karfina na soma kuka ina birgima ina shure-shure, Babana zai yi min baki ina zan shiga ni 'yasu? Hankalina yayi matukar tashi, na rasa in da zan sa kaina in ji dadi, na rasa wanda zan matsa kusa da shi in rada mishi cewar ni fa ba 16 da gaske nake yi ba, zabin da nayi na cewar zan bi Ado nayi hakan ne kawai don in sanya Mama bacin rai, amma babu wanda zan iya fuskanta da maganar tawa ya saurareta." Gaba daya wuri ya hargitse, hankula sun kai matuka wajen tashi, Baba Yahya da Babana sai faman rirrike su ake yi saboda Babana ya koma taya Mama zagin Inna da danginta da take yi, yana tayata kiransu munafukai masu raba dan uwa da dan uwa, shi kuma Baba Yabya yana rama musu To ma na fasa tunda akan wannan.. Cikina ya bada wani irin sauti na kulułulu!!! saboda tsoron kalmar da zai karasa zancen nashi da ita, sai naji ya katse zancen nashi ya ce, na fasa ba in da zata zabin da tayi zabin banza ne, ban yarda ba, ba za ta bishi ba, a zuciyata nace tafi nono fari, Baba da haka kayi tun farko ma da ba a tsaya wannan kace-nacen din ba, tunda dai ni din ai mallakinka ce. Zancen Baba Yahya ya katse ni da na ji yana fadin, wannan ai shi ne karya ba za ta zabi mijinta ka hana ta bibn shi ka kashe mata aure ba, saboda kawai matarka tana son ganin hakan, in zaurawa ka ke son gani a gidanka ai gasu nan ka samu." Mama ta sake kurma wani uban ihun, wai Baba 17 Yahya ya yi wa 'ya'yanta gori, bai saurare ta ba balle Babana, ganin shi kawai naga yayi ya damko hannuna yana jana zuwa inda Ado ke makure a jikin bango. "Yau ka ce kana son tafiya da matarka?" Da sauri Ado ya ce mishi "Eh." Baba yana jin haka yayi maza ya danka mishi ni a hannunshi, tare da fadin "Gata nan Ado na baka ita ku tafi, ka ike min ita amana ka sani iyayenta ma hakuri da su muke yi, to balle kuma ita yarinya ce yar karama." Ado yayi maza ya kama hannun nawa ya rike da iyakacin karfinshi, tanfar yana tsoron kar a kwace mishi ni. "Wuce ku tafi." Ya bani umarni mai karfi, daidai lokacin da Babana yake ta sakin wasu maganganu masu tsanani su Mallam Harisu suna ta faman bashi hakuri, na kalli Baba Yahya ina kuka, na ce mishi "Ba zan bi shi ba Baba, ba zan bishi ba, ni dama ba da gaske nake yi zan bi shi..." Wani irin gigitaccen mari ya dauke ni dashi, sai da naga waikiya ta haske ni gaba daya, Ado yayi maza ya kankame ni a jikinshi da sauri yana baiwa Baba Yahya hakuri. "Kayi hakuri Baba, kayi hakuri." Yana kuma tattare ni da fadinshi don gudun kur hannun Baba 18 Yahyan ya sake kawowa gare ni, gigitaccen marin da Baba Yahya ya kifa min ya katse min komai, hatta kukan da na dade ina yi, na daina shi na koma zare ido saboda ban taba jin mari mai tsananin wannan ba. Ado ya tasa ni a gaba, muna fita daga gida ina jin Baba Yahya yana fadin, "Ai ko za ki shide ba shure-shure ba sai ya tafi da ita, ai ba zai zabe ta ya bar ki ke da mijinki da duk abinda ki ke ganin kun mishi ya ce ita kadai yake so sannan ku hana shi ita ba, yana sonta tana son shi ke ki ka kulla auren da nufin sharri don ki cutar da ita, kisa shi ya wulakantata. Amma' abin mamaki sai gashi zaman da yayi da ita na kwanaki tamanin da bakwai kacala sun sa shi ya zabe ta ita kadai ya barku ke da mijinki da duk abin da ku ke ganin kuna dashi. A kofar gida Ado yana kokarin shigar da ni cikin motar da ke tsaye tana faman jiranshi wadda shatarta ya dauko, sai ga su Liman da Mallam Harisu, har da Baba Yahya sun fito. Mallam Harisu da Limar suka wuce, Baba Yahya yana yi musu godiya. Shi kuwa Baba Yahya yazo ya tsaya jikin motar hannayenshi duka biyu ya saka cikin 19 aljifayen shi ya fito da duk abinda ke ciki ya mikowa Ado tare da fadin sai kayi hakuri da wannan baka ba da lokacin da za'a yi maka shirin tafiyar taku ba. Hannu biyu Ado ya saka ya karbi abin da aka bashin cikin ladabi na gode Baba, Ubangiji ya kara girma." Baba Yahya yana tsaye a kofar gidanmu har motarmu ta bace daga unguwarmu, Ado yana ganin motar ta bar kan titinan daga cikin gari ta fada kan babbar hanyar da ta nufi Kano ya saki wani irin sansanyar ajiyar zuciya tanfar dai da a tsorace yake, ko yana tunanin za'a biyo shi ko a tare shi a kwace ni. Lokaci mai tsawo yana cikin wata irin matsananciyar natsuwa kafin daga bisani naga ya shafa fatiha, don haka na gane addu'a yayi yana shafa fatihan kuwa ya juyo gare ni, kamo ni yayi da hannayenshi duka biyu ya jawo ni ya kwantar da ni kan kirjinshi, ya kuma dora hannunshi guda daya a jikina don ýa tilasta ni kwanciya kan kirjin nashi. Cikin natsuwa ya soma yi min magana. "Kin taba ganin wanda ya zabi yin aure ya tozarta? Ai abubuwa guda uku Aisha, Ubangiji ba ya tozarta mai yin su, alkawari ne ma yayi cewar 20 zai taimaki mai yin su, na farko a cikin su shi ne aure, sai Jihadi sai kuma bawan da aka rubutawa biyan wata ka'ida don ya samu 'yanci ya zama da, don haka babu abinda zai same ki sai alheri. Wata irin tafiya muka Yi wacce bazan iya tsayawa ina bada labarinta ba saboda tsananinta, ya kai duk in da ya kai, daga ni har Ado babu wanda bai wahala ba, iyaka dai shi ya yi tashi wahalar ne cikin farin ciki da gamsuwar samun yanda yake so, babu kuma wata alama ta damuwa a fuskarshi, yayin da ni kuma nayi tawa wahalar cikin matsananciyar damuwa ga bacin rai ga ciwon ciki mai tsananin gaske. Ado ya rarrashe ni ya gaya min duk wata magana da zai gaya min, har ya gaji yayi shiru ya zuba min ido, amma ban daina kukan da nake yi ba,. babu abin da yafi damuna irin tafiyar da nayi na bar Innata da na san haka zabin da zan yin zai zama daj ban yi shi ba. Na za6i bin Ado don in batawa Mama ita kadai rai daga baya in an tashi in sulale in yi tafiyata in ki komawa gidanmu, sai na tabbatar ya bar garin tunda nasan ba zai sake zama ba, gashi hakan ya jawo min al'amura masu tsananin gaske, na farko ya haddasa 6acin rai mai tsanani tsakanin Babana 21 da Amininshi Baba Yahya, a dalilin furta kalmomi masu zafi da Baban nawa ya fusata yayi tayi a kaina da mahaifiyata, da ma danginta gaba daya. Hakika nayi wauta mai tsanani da nayi nufin 6atawa Mama rai ba tare da na tunawa kaina cewar bacin ran Mama yana nufin ɓacin ran Babana ne ba, sannan hakan yayi sanadin da ni din zan bi Ado kauyensu alhalin m din ban san komai game da zaman kauye ba, ba kua duk wadannan ne suka fi kuntatawa zuciyata ba, irin tafiyar da nayi na bar Innata, ko a wane hali take ciki ko a wane matsayi ta dauki tafiyar tawa? Wannan shi ne abinda yafi damuna. Motar ta sake yin tsalle ta sake faduwa cikin wani ramin a karo na biyu, nima na sake yin maza na kankame marata da hannayena duka biyu tanfar dai yanda nayi a farkon fadawar nata, haba Malla Haruna a rinka kokarin kaucewa ramukan nan mana. Mallam Haruna ya dan yi tsaki kadan alamar shia ba a son ranshi ba ne hanyoyin namu ne sai hakuri in ban da haka da gangan ai mutum ba zai rinka fadawa cikin ramukan ba don Sukurkuta mishi motar zasu yi babu halin kayi ƴar tafiya sau daya sau biyu sai ka raba abin da ka samu tare da 22 makanikai. Ni kam Suna maganarsu ina jin su ina kankame da cikina ina sauraron abinda zai sake faruwa, tunda daga sanadin fadawa ramin farko ne cikina ya urda ya kama ciwon da nake ta fama da shi. Da kaina na lallaba na sake jingina jikina a jikin Ado, maimakon jawo nin da yake yi ina ki saboda dunkulewar da naji marata tayi a wuri daya,, da sauri Ado ya dora hannunshi a jikina ya kara tallabe ni na kwantar da kaina a kirjinshi ya cusa hancinshi da bakinshi a kan nawa ya dan sumbace shi kadan. A hankali kuma cikin natsuwa da kuma sanyin murya ya soma yi min magana a hankali. "Ina son ki Aisha." karo na biyu kenan da na taba jin sunan nawa sak a bakin Ado kafin yau, bai taba ba da Humaira ya saba kirana, ban damu ba duk abin da za a fada a fada, in ma dandani haukaci akayi min oho, ni kam ina so, ina sonki ban kuma zabe ki don in 6atawa wani rai ko don in ba wani haushi ba. Ban zabe ki akan lalura ko akan kuskure ba, na zabe ki ne don ina sonki don na riga na gane rabuwa da ke ba zai haifar min da da mai ido ba, don haka na zabi rabuwa da komai da kuma kowa 23 don in same ki ke kadai, don nasan abinda kawai zan yi kenan in samu kwanciyar hankali da nutsuwar da nake bukata. Don haka ban ga dalilin wannan bakin cikin da ki ke tayi ba, in don tsoratarwar da aka yi tayi miki ne a kan kauye da kuma gidanmu ni din ai namiji ne Humaira, nayi miki alkawarin babu wata wahala da zata dunfaroni in barta takai ga taba min ke face sai nasa dantsena na tare miki ita. Ai ban rabo ki da gidanku da iyayenki don in wahalar da ke ko don in zama sanadin wahalarki ba, na rabo ki da su ne don ina son rayuwa tare da ke, ina son ganinki a tare da ni, ina son mallakar jikin nan naki, tó a na menene za ki yi ta wannan 6acin ran? Ko kina so ne ki nuna min cewar ke din ba kya sona? Ko kuma ba kya bukatata? Tabbas na sani ba zan iya amsa wadannan tambayoyin na Ado da kalmar eh ba, in dai har gaskiya nake nufin fadi. To amma iyayena fa? Musamman ma Innata, Inna tuna girma da darajarsu da kullum mai babban allo yake gaya min da kashedin da yake yi min a kansu, na ba a karo tsakanin kwai da dutse. Sai in ga don in zauna da su lafiya in rabu da su kuma laiya zan iya hakura da duk wani abinda 24 nake so amma ina amfanin wannan abin da ya faru tsakanina da su a yau? Na tafi Babana yana ta furta munanan kalamai a kaina, Inna kuwa ko sallama bamu yi ba balle in san halin da take ciki, amma Ado wai kar in tsananta bakin ciki. To me zan yi? dariya? Nan da nan naji haushin shi ya kama ni saboda ganin da nayi tanfar kanshi kawai yake so.. "Dan sha ruwan nan ki jika bakinki, in ma ba za ki ci wani abu ba kin ga ai tunda ki ka yi amái ba ki sake cin wani abu ba, na ce uh'uh. Kalaman Ado a kowane lokaci na rarrashi ne da fadin maganganu masu dadi, don dai ya samu yaga hankalina ya kwanta, ni nasan babu abin da kalaman Baba zasu yi miki don kuwa baki yi mishi komai ba, fushi yayi da fushin wani, Inna kuwa nasan ba za ta taba jin zafinki ba, balle tayi fushi da ke, balle har taje tana yi miki wasu munanan kalamai. Nayi Imani a daidai wannan lokacin da take jin kalaman dan Baban yake fadi a kanmu ita tana yi mana addu'a ne tana neman mana kariya daga duk wani sharri ko wata fitina, tana kuma neman mana alheri wu Ubangiji shi ne kuma abin da zai same mu Humaira." 25 Mun iso Kano ne misalin karfe shida da kwata, shirye-sbiryen saliar magriba ake tayi don a wannan lokacin ita magriba din ana yinta ne shida da rabi a mafi yawancin wurare. "Samu wuri mai kyau ka tsaya Mallam Hlaruna, sai mun yi sallar magariba da Isba'i mu wuce." Mallam Haruna yayi maza ya ce, "Kai a'a Mallam Ado, kar muyi haka don kuwa muna da sauran tafiya mai tsawo ban da haka ma ina ganin tanfar gara wannan hanyar da muka baro a bayanmu, kan wanda zamu hau nan gaba." Ado yayi murmushi ya ce, "Ina ganin dai ka dade baka je Katsina ba Mallam Haruna, in ba haka ba ai mu hanyoyinmu masu kyau ne." Kofar wani gida Ado ya kai ni, sai da yayi sallama da mai gidan suka gaisa sannan ya roke shi in shiga wurin iyalinshi in yi sallah, don a kan hanya muke, ya ce babu komai. Na shiga shi kuma ya koma sai da na idar da sallar naja carbina na jira nayi Isha'i bai dawo ba, na huta naji dadi sosai don ban saba irin wannan doguwar tafiyar ba, bas taba yin ta ba. Iyakacina giyade, ban taba wuce nan ba, sa zuwa can maigidan ya shigo yana gayawa iyalinshi wadanda suka yi matukar karrama ni cewar 26 bakuwar nan ta fito suka ce to, suka rako ni har kofar zaure sukamiko min leda mai dauke da robar da suka cika min da kunun aya, nasa hannu biyu na karba nayi musu godiya. Ado ya tasa ni a gaba zuwa in da motar mu take, ina shiga ciki na zauna ya miko min wasu kwayoyi guda biyu tare da kwalbar Coke ya ce "Karbi ki sha saboda aman da kike yi." Ban yi mishi musu ba na karba nasha, ya fita akan zai maida kwalbar, bai dawo ba sai bayan minti ashirin da biyar. Mallam»Haruna yayi tsaki har ya gaji. "Dabai fa mutumin nan ya ce zamu je, amma yake yi mana irin wannan bata lokacin." Gabana ya yanke ya fadi jin sunan garin da Mallam Harunan ya ambata, ban taba jin sunan garin ba, iyaka kuma dai ban ce mishi komai ba, tunda ba abokin magana ba ne. Ado ya dawo rike da ledoji guda biyu ya mika wa Mallam Haruna daya, ya ajiye mana daya Mallam Haruna ya karba yana godiya, yana ganin dankwaleliyar kazar da ke ledar tashi ya mance abin bacin ran da Adon yayi mishi, duk da tabbacin da Adon ya bani na ba zan sake yin amai ba komai naci, ban yarda naci koman ba, in ban da kunun 27 ayan da mutanen nan suka bani wanda yayi min dadi ba kadan ba. A wannan lokacin na dan samu natsuwa da kuma saukin da nayi bacci, wata kila don sanyin dare da ya sauka wata kila kuma don saukin aman da na samu, gashi har na samu nasha kunun aya ya zauna amin. Ban sha wahala ko naga tsananin tafiyar ba kamar yanda direban ke ta magana don kuwa na farka ne a inda naji Ado yana ce min "Kin faraka a daidai Humaira, daga wannan garin da ki ka ga muna wucewa sai kaute guda daya ne a gabanmu (Tukunya) daga shi sai (Dabai). Can baya kuwa in da muka baro, kin yi bacci ne a kusa da garin (Dayi) daga nan sai Malumfashi sai Kafur sai Sabuwar Kasa, sai Gozaki sai Dabai, to amma kin san akwai kananan kauyuka a tsakanin garuruwan sai a hankali za ki san su." A zuciyata na ce, in na zauna a garin kenan, don ni kam a zuciyata ina ganin tanfar babu abin da ya dace dani irin komawa gida in je in roki Babana da Innata gafara kan bacin ran da na san na sanya Su. Ado ya saki wani lallausan murmushi bayan yayi ajiyar zuciya, tare da hamdaia ga Ubangiji. 28 "Ga Dabai Humaira mun iso." A hankali ya soma rada min a kunnena, bude ido ki ga garin mijinki Humairah gari da zai zamo shi ne garin 'ya'yanki, ina son Dabai Humaira, ba wai don garina ba ne kawai, a'a mutanen garin mutane ne masu neman na kansu, masu karamci da ganin girman juna. Mutanen Dabai jarumai ne manoma ne wasu da yawa kuma 'yan kasuwa, in ta fannin ilimi ne kuwa muna da manyan Malaman addini a ta bangaren bokon ma ba a bar mu a baya ba, mutanen mu da yawa suna nan warwatse cikin ma'aikatun Gwamnati suna aiki tun daga LocalGovernmnent har zuwa State da kuma Federal. A daidai lokacin da Ado ke ta faman wasa min garin nasu na bude ido tarwai, wai domin in ga abinda yake gaya min din, tunda an yi sa'a farin wata ya haske ko ina. Ban ga komai ba in ban da dogayen bishiyoyin da ya ce min na kuka ne, sai ko filayen da yake ta nuna min yana fadin duk nan da ki ke gani ba jeji ba ne, gonaki ne na mutane. Bari damuna ta zauna sosai ki ga abin mamaki, a zuciyata na ce ka gani dai. Shi garin Dabai gari ne da yayi sa'a babbar hanya ta ratsa shi, ta ko ina kin ga wannan hanyar da muka biyo'ai kin ga garuruwan da muka baro a 29 bayanmu, to» näii gabanmu in ta wuce Dabai zata wuce, mararrabar Danja ta tafi har Hunkuiyi taje Basawa ta isa Zariya, kin ga ta tafi har Kaduna kenan. In kuwa a mararrabar Danja ki ka tsaya ki ka bi hanyar da tayi dama, to za ki isa kauyen Dan Mai gunta ki wuce kije har Danjan, in kuma ki ka nufi hagu to zaki je garuruwan Kudan daga nan kije har Makarfi in ki ka fada babban titi ma sai ya maida ke har Kano, ita ce ma hanyar da yan kasuwanmu suka fi amfani da ita." Ya sake kallona cikin murmushi yana fadin "Ba za ki gane dadin Dabai da karamcin mutanenta ba sai na gaya miki cewar mutanen da suka san Dabai din da irin halinta suna yi mata kirari da cewar ce Dabai dabaibaye bako, maida bako dan gida ya manta garinsu, ta magaji mai alamar samu. Ban taba tankawa Ado maganganunshi ba tunda muka baro gida, don haka wannan ma ban amsa ba, na dai san kawai yana son garin nasu da kuma jihar tasu ta Katsina don yanzun nan ne zan ji ya ce wa Mallam Haruna a'a ai mu nan Katsina babu wannan, to ban tsananta jin mamakin shi ba, don kuwa nima ina son jihata ta Bauchi da garinmu na Giyade da kuma unguwarmu ta Nasarawa 30 Jahun. "Rage tafiya sosai Mallam Haruna ka kumna sanyawa na baya alamar barin hanya nan gabanka kadan ta gefen damanka akwai hanyar da ta shiga ciki, ita za ka bi." "Yan daidaikun mutane ne a waje saboda dare ya riga yayi nisa, amma mafi yawancinsu Ado yana shaida su alamar dai bai taba rabuwa da al'amuran garin nasu ba. "Bi ta nan gefen kayi dama sosai, akwai katuwar bishiyar kuka, ta gefen ta zaka wuce kiyi yamma irin bayanin da Ado ya rinka yi kenan har muka iso inda yace to, ga Masallaci can fari nan kawai zaka tsaya. Muna tsayawa Mallam Haruna yayi murmush ya ce, "Kai Mallam Ado kasan garin nan Ado ya taya shi murmushin ya ce, garina ne fa, ga ruwa nan a randa ga lbandaki can gefe in zaka taba ruwa bari mu shiga in fiddo maka da abinci." Mallam Haruna yayi maZa ya ce, kai ai ni a koshe nake, a dai bani wurin kwanciya kawai. Ado yasa hannu ya dauki jaka guda daya dakke bayan motar ya rataya akan kafadar na kuma san da ita kadai ya iso garin ya tasa ni a gaba muka nufi cikin gidan, muna fita daga zauren wanda babba ne sosai ga kuma wani daki a cikin shi. 31 Sai ga wani shamaki da ya shiga tsakanin mutanen zauren da ganin cikin gida daga bayan shaakin hanyoyi ne da suka nufi sasan da ke gidan, gaskiya ne girman gidan su Ado ya wuce a tsaya yin bayani. SW Kinga ga hanyar sasan u nan, wancan sasan Baba Halliru ne shi da 'ya'yanshi wancan na Baba Ubangida shima shi da nashi ya'yan wancan nasu Baba Tukur ne shima da nashi iyalin mu dai je kawai yanzu ba za ki gane komai ba sai an kwana biya kin gane kan gidan da mutanen ciki tukuna. A zuciyata nace hu'un. paR Muna dosan sasan da ya ce min shi ne nasan ya kwala sallama sai kawai naji wata murya ta asa daga cikin wani daki tana kuma tambayar Adamu ne a cikin tsohon daren nan? Yayi murmushi ya ce mishi eh Baba, mutumin da Ado ya kira da sunan Baba ya fito rike da sanda a hannunshi ba dai don tsafi kam sai dai ko don wani dalili don da karfinshi na ganshi. Yana ganina yasa hannu ya rufe baki nuna alamar mamaki da wannan yarinyar ku ke tàfe? Ya ce mishi eh Baba, sannu da zuwa Aishatu, nima nayi ta amsawa don girmamawa. Kaga halin mata ba? Sufa babu wani babba 32 babu yaro a cikinsu, in ka biye musu kunya za su baka. Ado yayi murmushi ya ce, me ya faru Baba? Ya ce to ai uwar taku bata nan tana can taje Kauyensu na Tukunya zata kwana saboda yau ana kamun wata jikar su, in ban da rashin hankali irin nata da nima na biye ta shi babba yana yin nesa da wurinshi ne tunda ya san yana da baya da yawa. Ado ya ce, ai babu komai Baba, Baba yaja tsaki ya ce, in ban da lalura irin ta girma me za'ayi da zaman mace daya ne? Ado ya sake wani murmushin ya ce ai Humairah ba gobe zata tafi ba, ba kuma jibi ba, zata dawo ta same ta babu damuwa, ya ce auto shi kenan amma ai ba dai haka aka so ba. Makullin dakin nan a kusa yake ni ko Baba? Baba yayi maza ya ce, eh ai cikinshi nake wuni tunda sorona ya fadi, ya ce haka ne fa Baba an gaya min soronka ya fadi ya bude dakin muka shiga, komai a gyare yake a kintse, dakin yasha leda ga katifa timemiya a shimfide ga kujerar kwanciya can gefe akwati ne shia mai kyau a rufe na tabbatar komai na cikin dakin na Ado ne. Muna shiga ya sauke jakar kafadar shi ya bude ta ya fiddo fitilar chaji ko batir ya kunnata ko ina ya dauki haske sosai. 33 A to, tunda ka ki ka sanya mana wutar lantarki a gida mu ma mu rinka ganin haske irin naka na birni, ai ka rinka yawo da fitila a Jaka, wata mata ce da ta ja ta toaya a bakin kofa tayi wannan maganar tana ganin dakin ya gauraye da haske kuma ta karasa shigowa cikin dakin ta durkusa kamar wata karamar yarinya. Da gefen Adon ya harareta ya ce, mijinki fa me ya hana shi jawowa? Tayi murmushi tare da langabar da kai ta ce waiyo bai da shi ne, ya ce eh bai da shi, amma ai a hakan yake iya karo aure ko? Ta sake wani murmushin kafin ta sake cewa waiyo!! wannan ai rabo ne. Ado yayi maza ya ce, haka ne. Tayi maza ta kalle ni cikin fara'a, kin ga rabu da mijinki kin ji ke dai sannu da zuwa abinki na ce mata yauwa, na kuma fara gaisheta saboda ganin zata iya girmana da shekarun da suka kai tara ko ma goma. Kai gani kafin ki fara tambayar mutane abin da za su ci don ke aikinki kenan tayi maza ta sake langwabewa ta ce ehhhyi, ni ai cin ne sna'ata, sai in ga kamar kowa ma haka yake. Yayi maza ya girgiza kai ya ce a'a ke kadai ce, ta ce au to, to na ji to ku da wanne ku ke farawa? Ya ce wanka don ba ki iya karbar baki ba ne yasa 34 ba ki gane hakan ba, ta ce au to to naji zan gyara ko da yake dai munan da yake mu yan kauye ne ci ne gaba da wanka ya ce, eh to ai kin san mu 'yan birni ne, ta ce haka ne. To bari in samo ruwan zafi nan da nan ta fita, tana barin dakin ya daga ido ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min Ruwailah kenan, matar yaya Jafaru ce ai kin san yana yawan zuwa wurina, na gyada kai nuna alamar na gane shi, ya ce to shi ne babban wanmu a nan sasan shi ne dan Baba Tanimu na farko wanda yaje ya karbar min aurenki amma ai kin san ni ni kadai ne wurin mahafina ko? Na girgiza kai a hankali, nuna alamar ban sani ba, ya ce to ni kadai ne. Ya ci gaba da abinda yake yi na kaye-kaye da gyare-gyare tanfar dai ba a cikin dare muka shiga dakin ba. Ruwailah ta dawo da ruwan zafi a bokiti da wani kuma a flaks dinta da ta dauka a dakin, ga kuma wani kunshi cikin leda da ta ajiye a gefe, wai yana yi muku sannu da zuwa. Ado ya yi tsaki ya ce, kai ke kan ba ki da kirki, yanzunnan sai da ki ka tashi bawan Allahn nan a cikin tsohon daren nan ki ka yi sanadin fitarshi waje? Ta ce, oh oh, ba ma a wurina yake ba, to amma da bai fitan ba da wa ya sauke maka 35 mutumin da kazo dashi din? Ado ya rike baki nuna'alamar mantuwa, ya ce na shagala ina kallon Humaira, kin san ni in ina tare da ita to sunana ne kadai ban iya mancewa da shi. Ruwaila ta kyalkyale da dariya ta ce, ai kuwa dai ma kayi kokari tunda ba ka mancewa da sunan naka a nan sanu. Sabon soso da sabulu da brush da abin wanke baki da sabon tawul ya fiddo daga cikin jakar tashi ya miko min na karba nabi bayan Ruwailah da ta daukan min ruwam muka je ta nuna min ban dakin. Na dawo daga wankan na samu kwanukan abinci iri-iri, ya kalle ni ya ce min wannan kunshin na gasasshen nama ne Yaya Jafaru ya sayo miki, ga furar da Baba ya bayar da nono Ruwailah ta dama miki, ga kuma tuwon dawa miyar kuka shima mai dumi ne ta dumamo da wanne za ki fara? Na ce kowanne, ya kalli Ruwailah da ke ta faman bubbude min kowanne in gani ya ce mata ba kin gama naki ba, to kije mana kuma sai da safe, ta ce am wai jira nake yi ta gama mu tafi can wurina ta kwanta. Yayi maza ya ce, wasa kenan, tabar dakin mijinta da mijin nata a ciki taje ta kwana a wannan 36 tsohon dakin naki? Ta ce, to ai shi kenan sai da safe Amarya. Nayi murmushi na ce mata to ki huta gajiya. Tana fita Ado ya kalle ni ya ce wannan atishawan da kike tayi fa don kin yi wanka a bayan gidan da babu rufi ne baki saba ba, ban amsa mishi ba amma cikin zuciyata nima na yarda hakanne don maimakon in ji dadin wankan da nayi sai naji kamar sanyi ya kama ni. Naci tuwo sosai don yayi min dadi laushinshi da dankonshi yayi banban da irin tuwon da na saba, nasha ruwan tea mai cçitta naci nama kadan na gyara na kwanta bayan na shafa mai nasa rigar baccina wanda itama shi yazo da ita. Na kalle shi cikin natsuwa nayi mishi magana wanda tun fitowarmu ban yi mishi ba saboda na gane babu komai cikin jakar tashi in ban da kayayyakin amfanin da ya saya saboda ni na ce to da ban biyo ka ba fa yaya zaka yi da kayan nan? Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, ban taba daukar za ki iya kin bina ba, na dauka ke ma kina sona. Muna kwance ni da Ado akan katifar yana gefenshi ina nawa sai dai mu dukanmu babu wanda ya samu yayi bacci, ya daga ido cikin natsuwa ya 37 ce min Humairah ba ki ga kamar kasa yin baccin nan da muka yi alama ne na muna jin marmarin juna ba? Nayi maza nace mishi, a'a bana ji ya sake daga ido ya kalle ni ya ce, to ai ni ina ji, nayi maza na tsuke fuska na ce mishi ba fa na zabi biyo ka da nufin in biyo ka ba ne. Cikin natsuwa ya ce min ai na sani, na sake tsuke fuska na ce, to ko da na biyo ka akan kuskuren ba zaa zan yi ba, komawa zan yi. Ya sake cewa na sani, ya sake saurarawa ko zai ji zan sake fadin wata magana, sai yaga nayi shiru. Sai naga yayi murmushi kafin ya ce min to amma ai ko za ki koman tunda ba ki kai ga tafiyar ba ai ina ganin ba zai hana in nace nayi marmarinki kiyi min yanda ki ka saba yi min bä ko kuwa. Nayi maza na kara tsuke fuska, kafin na ce mishi a'a, ya ce to shi kenan sai da safe. Washegari tun safe Goggo Ayalle ta dawo gidan a dalilin aiken da Baba Tanimu yayi na a dauko ta, tana dawowa kuwa ta maida ni dakinta, wunin ranar har dare ban gane na gama gaisawa da mutanen gidan nan ba saboda yawansu. Don haka kowa na gani kawai sabuwar gaisuwa nake yi mishi, sai in shi ne ya ce min ai 38 dazu mun gaisa in ce mishi to. Karba sosai Goggo Ayalle tayi min, ta yi ta ina taka saka dani, komai hannunta ya kai kan shi in dai ta daga taga naci ne miko min shi take yi, ungo ki ci, sai in ni ce naga zan kwari kaina in ce mata na koshi. Sau goma kuma in ta kalle ni zata yi murmushi ta ce, oh haka rabo yake har da rabon aurenki cikin al'amuran da suka kai Adamu garin nan suka zaunar dashi, kin san shi rabo ba karamin al'amari ba ne. Sai kawai nima in taya ta murmushin da take yin sai dai ban ce mata komai, can anjima kuma sai ka ji tana sake tambayata in ce ko dai manyan duka lafiya? In sake cewa lafiyarsu kalau, tamfar dazu bata tambayí lafiyar tasu ba. A haka muka wuni har dare ina idar da Sallar Isha'i ta kalle ni ta sake nuna min gadon da na wuni akai ta ce min hau kiyi barcinki ki huta gajiya, kar yan hiraa suce zasu dame ki, na ce to. Na sake dalewa gadon nayi kwanciyata, zuwa can naji Ado yana kirana, nayi kamar ban ji shi ba, ya matso kusa da kofar Goggo yana tambayarta. "Goggo Humaira tana kusa ne?" Goggon tayi maza ta sauka daga nata gadon ta 39 leka tana tambayarshi wani abu ka ke so ne Adamu? Ya ce a'a Goggo, sai da safe. Abin da kawai ya fada kenan sai na jiwo Baba Tanimu daga dakinshi yana fadin "Yau ga wani al'amari, wannan fa shi ne girman kwabo. An gira ba ayi hankali ba, yaro yana kwalawa matarshi kira kina ji tayi shiru ba kiyi mata magana ba, ya taso yazo har kofar dakinki yana tanbayarki ita kin ce wai in wani abu yake so ya gaya miki, to in ita yake so fa? Na ce in yana da bukatarta ne ma ya gaya miki? Goggo tayi maza ta ce au, to ai bangane ba ne. Ke Aisha tashi-tashi je ki maza mijinki yana kiranki." A kan dole ta fito da ni daga dikin na shiga dakinmu na samu Ado yana zaran jiran shigowan nawa, gasasshiyar kaza ne a gabanshi, a gefenta kuma flaks ne na ruwan zafi, ban kalle shi ba na wuce na hau katifa nayi kwanciyata, ya biyo ni da kallo fuskarshi ta bayyanar da rashin jin dadin shi kan yanda nayi. Yayi karfin hali ya hadiye fushinshi tashi mana Humairaa nayi kamar ban ji ba, yayi tayi min magana nayi shiru kamar ba dani yake yi ba, ke ni fa kin san bana son irin wannau wulakancin na ayi 40 tayi miki magana kina yin banza da mutane, ban tanka mishi ba, ban san yanda aka yi ba sai kawai naji ya cafko hannuna ya murde. A firgice na kwallara kara saboda zafin da naji, na kuma yi maza na kame bakina nayi shiru saboda funawar da nayi cewar a bakon wuri muke ko kuma ni din ni bakuwa ce. Daga cikin dakin Baba Tanimu da ke makwabtaka da namun naji an yi gyaran murya alamar dai yin kashedi. Ado ya hakura ya gyara ya kwanta, ni kuwa naci gaba da zama a kan katifar ina kukan sharbe tare da shisshika a hankali sai dai shi Ado shiruu kawai yayi amma yana ji na. Ana cikin haka wani irin hadari ya taso mai matsanancin iska da guguwa da rugugi mai tsananinn firgitarwa har wani bai iya cin motsin wanda suke tare, sai in yayi motsi ne da karfi nayi maza na gyara na kwanta da nufin yin shiru kamar yanda shima Adon yayi, sai kawai naga ya juyo gare ni. "Kin fasa kukanne?" Nayi kamar ban ji shi ba, Ni fa yau ba zan iya irin kwanan da muka yi jiya ba." Ya miko hannu zai taba ni, nayi maza na ce mishi "Gaskiya ni fa ba zama nazo.yi ba, ko yau 41 dinnan da ina da kudin mota da tafiyata nayi." Ina gama fadin hakan ya cafke ni, bai saurari ihun da nake yi mishi ba saboda yasan ba zai kai ga kunnen Baba Tanimu ba. Sabuwar iskar da ke kadawa ga tsawa da rugugi, watakila ma ya dade yana baccin shi, gane hakanne yasa ni barin ihun na koma yi mishi bayani. "Ni gaskiya tun da muka zo fa cikina yana ciwo, ban gaya maka ba ne kawai." Bai saurara ba. Na kwana da matsanancin ciWon cikin da yay dalilin da na kwana ina murkususu daga kan katita in koma kasa, na rasa in da zan sa kaina in ji dadi, nayi kuka har na hakura nayi shiru. Ado yayi nadamar abin da ya faru tsakanina dashi, yayi nadamar tilasta min da yayi a haka muka kwana daga ni har shi babau wanda ya samu runtsawa. Ana fitowa daga sallar Asuba muka kama hanya zuwa asibiti da ni dashi da Yaya Jafaru da Ruwailah, saboda tun dare ya shaidawa Baba Tanin halin da nake ciki, tun daren kuma Yaya Jafarun yayiwo aron mota wurin wani abokinshi don ma Baba Tanimu ya hana tafiyar daren ne yaa ce a hakura ayi sallah tukunna. Asibitin Malunfashi ya kai mu, shi ne wai yafi 42 girma a nan kusa, gwajin farko da Likitan tayi min tayi bayanin ciki ne ya lalace ya fita daga cikin mahaifa, sai dai bai shiga ya fadi ba, saboda haka zasu wanke shi ya fita don in ba haka zan yi ta wahala da shi kafin ya kai ga fita. To amma me ya kawo haka Likita? Ado ya bukaci sani, tayi ta lissafo dalilai ciki har da tafiya mai tsanani ko kuma bacin rai ko aiki mai wahala shi yasa yawanci muke hana mata masu karamin ciki ko kuma cikin da ya riga ya kai watanni bakwai yin irin wadannan abubuwan, ku kuma maza muke rokonku da ku rinka tausaya musu. Daga Ado har Yaya Jafaru da Ruwailah sun gamsu da jawabin nata. Aka yi min wankin ciki aka sallamo mu bayan La'asar, duk da Ado yaso a bar ni in kwana wai a kara kulawa dani sosai aka ce babu gado. Mun iso gida gab da magriba, kai tsaye dakin Goggo Ayalle aka kai ni, wacce ta yi fada mai tsanani akan wankin cikin da taji an yi min, ina dalili yarinya ko haihuwar fari bata yi ba za aje ana kakaba mata karfen nasara a ciki? Da da ni akaje ai da ban bari anyi hakan ba. Gaba daya hankalin Ado yayi matukar tashi da abin da ya farun, ina jin Baba Tanimu da daddare 43 yana ta ba shi hakuri, ita rayuwa fa haka take, a kullum mutumin kirki ba ya zama ba tare da ana jarraba shi ba, ba ka fita daga cikin wannan ba ga kuma wannan ya sake zuwa. To kayi hakuri kar kuma ka ee zaka yi saurin gayawa iyayenta tunda ga irin rabuwar da ka ce kun yi dasu. Naji Ado ya ce, "A'a Baba, ba zan iya boyewa mahaifiyarta halin da take ciki ba, tun muna asibiti nayi waya na gaya mata, ban dai sake gayawa kowa ba; amma ita kam na gaya mata, ya ce to shi kenan tunda kaga hakan yafi. Kwanana bakwai a dakin Goggo Ayalle tana ta faman tarairayata, Baba Tanimu kuma da su Baba ubangida suka yi ta bayar da kaji ana yankawa ana yi min farfesu, har ma cikin kajin Goggo ta cire wata yar budurwa da ta bata sha'awa ta ce ba za ta yankata ba, bar min ita zata yi in yi iri. A zuciyata na ce, uhun ni kam ai ba.zama nazo yi ba. A wadannan kwanakin babu wata mu'aallar arziki tsakanina da Ado, ko gaisuwarshi ban cika amsawa ba. A cikin kwanakin ne kuma na lura ya daina zama a gida tun bayan fitan da suka yi da Baba Tanimu ba a sake wayar gari na ganshi a 44 gidan da safe ba sai gab da Azahar, ana yi sallar La'asar kuma zai sake fita sai kusan faduwar rana ya dawo. Ban san ina yake zuwa ba, ban kuma tambaye shi ba don a yanzu ko kallon shi bana yi, fatana da tattalina bai wuce in samu kudin mota ba in kama hanya in yi tafiyata. 31Rannan ya dawo kusan Azahar ya shigo dakin na Goggo, duk da yana ganin naji sauki har ma nayi kyan gani, sai ya tambaye ni ya ya jikin naki dai Humaira? A lalace na ce mishi da sauki, ya kalle ni cikin natsuwa. "Amma kin ga yayi miki daidai a hakan da ki ke yi Humaira? kina mu'amallah da kowa lafiya amma ni da na kawo ki babu?" Na kalle shi a sakarce na ce mishi, "To ka maida ni mana in da ka dauko nin." Ya ce, to babu laifi ya wuce ya fita. Ran da na cika kwana goma rannan Baba Tanimu yasa Goggo ta sani na koma dakin namu, ita kam taso ne a bar ni in yi arba'in. Zaman da na yi a dakin Goggo ya sani fahintar gidan sosai da kuma mutanen gidan. Sassa guda hudu da ke gidan suna karkashin dattawa hudu ne wadanda su ne asalin yayan maigidan su kuma dukan su uba daya ne ya haife 45 su, amma uwa daban-daban, babban cikinsu shine Baba ubangida sai Baba Halliru sai Baba Tanimu kafin Baba Tukur shi ne karaminsu.. A duka sassan nan guda hudu akwai iyalai musu yawa su dattawan gidan kuma suma suna da nasu matan, Baba Ubangida shi ne mai mata Goggo Turai wacce take sana'ar kokon safe, Baba Halliru shi ne mai Goggo Jaku ita kuma tana furar sayarwa mai dadi Baba Tanimu Goggo Ayalle ita kosai take yi itama da safe. Sai Baba Tukur, shi kuma tashi matar ita ce Goggo 'yar neto ita kuma tana gaudan sayarwa. A kowane sassa na gidan akwai yaran mata masu yawa saboda kusan duk 'ya'yan gidan maza masu aure ne wadan da basu yi ba 'yan kadan ne mafi yawancin masu auren kuma mata bibiyu ke gare su masu dai-dai din basu da yawa, kamar ma ba su dade da yin nasu auren sosai ba. Yanda duk tsofaffin gidan ke da sana'o'insu haka suma yaran matan gidan suke da hasu sana'o'in tun daga mangyada, manja, gyadar miya, maggi, gishiri, Alala, dan wake, gasu nan dai birjik Wasu har dinki wasu kuma har aikatau da su wanki amma dai kowa da abin da yake yi gwargwadon karin injin shi. 46 Kiwo kuwa a gidan ba a magana duk yawan Tumaki da Awaki da Kajin kuma abin mamakin shi ne kowa yána shaida nashi. Gaba daya sassan nan guda hudu kuma akwai mace guda da take kamar ita ce shugabarsu a sassan Baba Tanimu dai Ruwailah ce matar Yaya Jafaru ta farko, a sasan Baba ubangida da kuma akwai Furera matar Yaya Baidu itama uwargida ce. Sasan Baba Halliru akwai Gaje matar Yaya Jumare, itama uwargida sai sasan Baba Tukur nan kuma Tanbai matar Yaya Amiru akwai Uwale, itama uwargida, gaba daya wadannan matan hudu sun zo gidanne a kusan lokaci daya, ma'ana babu bambancin lokaci mai yawa a tsakanin aurarrakin nasu dukansu kuma suna da amare da kuma matan kannen miji. Haka nan gaskiyar Mama ne gaba daya gidan tukunyar abincinsu na dare gaba daya ne da rana ne dai kowa zai yi abin da zai ci shi da iyalinshi a wurinshi amma na dare a hade yake duk kumna wanda ke da girkin ranar to shi ne mai ba da hatsin da za ayi amfani dashi dama duk abinda za a nema Goggo Ayalle kuma ta shaida min cewar in mace tayi girki sau daya to kwana ashirin da biyar take yi bata sake ba. 47 Ai kuwa kin ga dole suyi ta neman kudinsu tunda basu da wani aiki na ce haka ne, a zuciyata kuwa cewa nayi yaran mata ashirin da biyar kenan a gidan. Muna nan zaune a dakinmu ni da Ado, zaman babu wani dadi. Kallon shi bana yi balle in san me yake ciki, shima baya takura min akan komai zuba min ido kawai yake yi babu abin da nake fata irin nera talatin-talatin din da Baba Tanimu yake bani kullum safiya, ya ce wai in sai abin da nake so in karya da shi da kuma ashirin-ashirin din kokon da Baba ubangida yake bani. Ita kuma Goggo Turai ta ce kai haba, bakin. wannan yarinyar dai ita kadai ace sai na amshi kudinta? Je ki ki rike kudinki kin ji? Don haka kunu da kosai ba saye nake yi ba, sai nake tara hamsin-hamsin din ina fata su ishe ni kudin motar tafiya gida in sulale in yi tafiyata. Rannan na wuni ina murna na kirga kudina sun kai dubu daya har da dari daya ina lissafin kwanakin da suka saura kudina su gama cika sai kawai nazo zan ajiye wata nera hamsin din naga babu komai sai wata tsohuwar nera hamsin itama wata kila bai ganta ba ne sanda ya kwashe su. Nayi kuka rannan har na gaji ban kuma iya cin komai ba 48 saboda tsananin bacin rai. Ado ya dawo gab da Azahar ya same ni a haka, ya juya ya fita bai zauna ba, bayan Sallar Isha'i mna ya shigo dakin da niyyar kwanciya ya same ni ina ta faman kuka, wuri ya nema ya zauna bayan yaje yayi wankanshi ya dawo. Ban kalle shi ba balle in san me yake yi, sai naji yana magana alamar waya yake yi, gaisuwa ta ladabi da natsuwa naji shi yana yi, don haka na kasa kunne ko zan gane da wa yake maganar, sai naji yana cewa. "Gaskiya Inna na gaji da karyar da nake yi miki ne, cewar muna nan lafiya, a gaskiya ba hakan ba ne, ina jin salatin da Inna ta soma yi, ban san me ta ce ishi ba, sai naji ya ce mata gata, nayi kamar ba zan karba ba sai naga to ni kuma a wa? Inna ta ce, a bani waya in ki karba? Ina karbar wayar na kaita kunnena naji muryar Innata gaba ya yanke ya fadi nan take na soma yi mata kuka bata yi min fada ba kamar yanda nayi zaton zata yi magana ta soma yi min cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Ban ji dadin yanda ki ke yi wa mijinki ba to da wanne zai ji? Da halin da yake ciki ko da rashin lafiyarki da yayi ta fama da ita? Ko da bacin ran 49 abin da ki ke yi mishi? Matar kirki kuwa ai bata haka, ita takan taimaki mijinta ne a duk lokacin da tasan yana bukatar taimakonta, ta rufa mishi asiri a inda tasan yana bukatar rufin asirinta. In ta san yana cikin tashin hankali kuma ta kwantar mishi da hankalinshi, sannan in ba ki sani ba wannan abin da kike yi ba shi kadai ki ke tozártawa ba har da ni, don kuwa kina kokarin nunawa wadanda basu sanni ba ne su san yanda nake tunda ai ita 'ya wakiliya ce ta uwarta. In kiyi halin kwarai ace kin samu tarbiyaa a gidan ku in baki yi ba a gane uwarki ba mutuniyar kirki ba ce kar in sake jin an ce min baki kyauta ba, in dai ba kina so raina ya baci da ke ba ne, tana fadin hakan ta kashe wayar. Sunkuyar da kaina kasa nayi, nayi shiru ban iya cewa Ado komai ba, iyaka dai ranar mun kwana lafiya amma ko kusa da ni bai zo ba, balle ya ce zai taba ni, ina wurina yana nashi. Washegari da Asuba yana idar da Sallah Asuba ya shigo ya tashe ni ya wuce ya fita, sai dai maimakon sai Azahar in ga ya dawo, wajen sha daya naga shigowarshi. Ya koma gefe yana cire ranbut din kafarshi da hand glove din hannunshi mahadin ranbut din. 50 Naji Baba Tanimu daga daki yana ce mishi "Ka dawo ne Adamu?" Ya ce mishi "Eh Baba, na dawo." Ya ce "Sannu da kokari ka ji? Ubangiji ya yiwa kokarin ka albarka." Yayi murmushi ya ce Amin Baba." Ya shigo cikin dakin namu ya same ni ma Zaune. Ya kakalle ni yayi murmushi, ya ce to ko ke fa? Kin yi wankanki kinyi fes da ke, na sani ba kya jin dadin mu'amalla da kayan da ki ke amfani da su tunda sunyi miki karanci da yawa dogayen riguna biyu ne kawai, sai zanin da ki ka zo da shi a jikinki. Kiyi min hakuri a yanzu, na katse shi ta hanyar fara gaishe shi, yana gama arnsa gaisuwar ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, samo min dumamen tuwo wurin Goggo Ayalle, na ce to, na tashi na tafi cikin zuciyata ina tunanin tun zuwanmu gidan kwanaki ashirin da daya da suka wuce ban taba lura da cin shi ko shanshi ba, ban kuma taba dora tukunya a murhu don yin girkin rana ba, tunda kowa yana abincin ranarshi. Ni dai nasan duk abin da Goggo Ayalle zata ci zata bai haka nan ma Yaya Ruwailah tunda nima yanzu yayan nake kiranta. Na dawo da kwano mai dauke da tuwon da aka dumama shi tare da miyar shi a wuri daya na ajiye 51 mishi na koma gefe na zauna sai ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min baki bani cokali ba, nayí maza na kalle shi saboda sanin shi ba mai cin tuwo da cokali ba ne. "Da cokali za ka ci?" Ya ce, "Eh, dashi na ke ci yanzu saboda hannun nawa ba na jin dadin cin tuwon da su." "Me ya same su? mu gani." Bai yi magana ba ya ware min tafin hannayen nashi. Tsigar jikina tayi matukar tashi tayi wani yarrrr! hankalina yayi matukar tashi da yanda naga hannun Ado gaba daya hannun nashi bororo ne ya. duru ruwa, wani wurin ma ya fashe ya zamą miki babu dadin gani. Fuskarta a yamutse saboda yanda hankalina yayi matukar tashi na tambaye shi me ka ke yi hannunka yayi haka? Shirun da yayi bai ban amsa ba yasa na sake tambayarshi Noma? cikin nutsuwa ya kalle ni ya ce min, in nayi noma menene Humaira? Ni ba namiji ba ne? Ni fa ba wannan ne wahala a wurina ba, wahala a wurina bai wuce ki ki yarda mu zauna lafiya ba, amma in za ki yarda mu zåunna lafiya ki gamsu da kokarina ki yarda da cewar in ban yi miki ba, ba ni da shi ne. Kiyi min hakuri ai ba zan gane ina wahala ba 52 sai in rinka ganin tanfar abin da ya dani a matsayina na namiji kawai nake yi in kuwa haka ne kin ga bai zamo min wahala ba. Ban iya cewa Ado komai ba saboda kukan da soma yi ban taba hira na gane matsananciyar ramar da yayi ba sai a yau, na dai san nai Goggo Ayalle tana yawan fadin yaron nan Adamu ya zube. Amma ban lura na gane irin zubewar ba, sai a yanzu. Tashi yayi yaje ya dauko cokalin ya dawo ya zauna ya soma cin tuwon, ni in don ni ki ke kuka to ki share hawayenki, in kina so in san kina tausayina to in ina tare da ke ki bar ni in samu kwanciyar hankalin da nake bukata. Yaua gamawa ya tashi ya sake fita, nima na share hawayena na tashi naje sasan Baba Halliru wurin Goggo Jaku na gaisheta, na ce mata Goggo yau zan karbi furar da kullum ki ke cewa bana zuwa ina karba, tayi murmushi ta ce, kai ai kuwa dai kin kyauta yar nan, gata kuwa an gama mulmulata. Ta miko min tayi shar gwanin sha'awa, sai Kamshi take yi, gata nan debi maza yanda zai ishe ki nasa hannu na debi guda hudu ta ce ke tafi can da kwauro, za ki yi wa kanki, ta sake watso min 53 guda shida a cikin kwaryar da ke hannuna nayi mata godiya na tafi. Nura na kira ko Zulai yaya, Yaya Ruwaila ne gaba daya suka taho na ce to ke Zulai je ki ki huta kai Nura yi sauri kaje bakin kasuwa ka sayo min nono, ya ce to. Ina zaune ina dama furar ina tunanin kai! Dabai akwai fura, amma babu nono. nono ruwa-ruwa? Na jawo robar yougort din da ke dakin na bude shi na juye a cikin damammiyar furar na gaurayata na rufe. Ana yin Azahar Ado ya sake shigowa nayi mishi sannu da zuwa, ya amsa. Na jawo kwanonon fura na mika mishi ya kalle ni da walwala a fuskarshi ya ce to ke fa? Na ce ai na sha, ya ce eh, amma ba zai taya ni musha tare ba ai. Na zauna muna shan furar tare har muka gama, muka dan yi hira kadan sai na kalle shi na ce mishi, "To ka dan kwanta mana ka huta." Ya ce in kwanta Humaira? Nayi maza na ce mishi eh, ya ce to za ki yi min tausa ne? Na gyda mishi kaina nuna alamar eh. Yayi maza ya mike akan katifar nima na bi bayan shi na soma yi mishi tausa ina yi mishi danna ina bin gabobin jikinshi ina matsawa cikin hikima, 54 shi kuma yayi lamo ya lumshe idanunshi nuna alamar jin dadi. A hankali kuma yana furta wasu kalmomi da ni kadai ke iya jin su, bacci mai nauyi Ado yayi bai farka ba har sai da na tashe shi, wajen karfe hudu da rabi na yamma abin da bai taba yi ba tunda muka zo, ya kwanta da rana yayi bacci. Da daddare rannan muna hira ni dashi ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min ni kuwa Aisha in ban da kar in yi ta takura miki har in yi ta kai ki bango ban sani ba da na roke ki kiyi min wata alfarma, na ce ta menene? Ya ce dakin nan da muke zaune a ciki ne bana son shi, duk da nawa ne. Na ce, ni na gane saboda gininsu ma ya banbanta da na sauran dakunan gidan shi da na Baba da na Goggo Ayalle. Bai bani amsa ba sai ya ce min nan din a takure nake, ba zan iya sakewa nayi kusa da Baba da yawa ba zan iya zama dashi duk wani motsina yana ji ba, shi ne nace da za ki yarda da mun fita daga ciki mun koma wasu tsofaffin dakuna da ke ta can baya, babu kowa a wurin sa muyi zamanmu zuwa lokacin da zan samu halin samar miki wurin da zai dace da ke." A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to mu 55 koma mana. Ya zuba min ido yana kallona, babu damuwa? Na ce to ai ba daki na biyo ba, ba kuma shi nazo nema ba, ni a wurina kai ne muhimmin abu, kai na biyo kai ne mijina a yanzu kuma zan iya zama da kai a duk in da ya kama. Kwana uku kawai da yin wannan maganar tamu Ado ya gama gyaran dakunan da da shara ake zubarwa a wurin ya kwasheta fes ya gyara wurin ya tsabtace shi ya gyara dakunan gyara na musamman ya sai buhun siminti ya toshe duk in da yake bukatar a toshe shi. Ina jin Baba Tanimu yana yabon kyan aikin da Adon yayi, amma ban san kyan wurin ya kai haka ba sai da Adon ya kira ni naje na gani, dakuna uku ne a wurin gaba daya yayi musu gyara na sosai, kowane daki ya maida shi abin da yake son ganin ya zama guda daya, ya gyara shi a matsayin dakin kwana daya dakin dahuwa, wato kicin daya kuma bayan gida na sosai da za'ayi amfani da shi akan komai sannan ya killace wurin da wata yar katanga. Yayi mata kofar shiga dan karamin tsakar gidan kafin ka shiga 'yan kananan dakunan ni dai wurin ya ban sha'awa, yayi murmushi ya ce to yaushe za ki dawo ciki? Na ce ko yanzu, ya yi 56 murmushi ya ce, to shi kenan. Baba ne yasa Ado daukan katuwar katifar da ke dakin da muke din, don haka ya sayo mishi 'yar karama. Randa na tare a sabon dakin namu tsaf na same shi ya malale shi da leda yasa katifar yayi mata shimfida ga akwatinshi a gefe sai Jakar da yazo da ita da 'yan tarkace kadan, dakin dahuwa kuwa yasa risho har da tukwane guda biyu da yan tarkacen kayan aiki kadan, food flask da dinner set da kuma wasu kwanuka. Ga bokitaye da randa da dai wasu tarkace, ga kuma kayan abinci dan daidai gwargwado ko a ina yaké samun kudin da yake kashewa? oho! tambayar da na.yi wa kaina kenan, a zuciyata dai nasan babu abin da yafi min ban dakin nan dadi, don na samu kebabben wuri har da bayan gidan hadakan da ban saba da shi ba yake sani jin kiyan yin wanka. Nayi maza na kammala abubuwan da zan yi nayi wanka saboda jin dadin ganin bandakin na zauna na shafa mai nayi gyara irin yanda na saba yi a gida, gaba daya dakin ya gauraye da kamshin kayan shafan da nayi amfani da su. Ado bai shigo ba sai da yayi sallár Isha'i shima 57 yana shigowa bandakin naji ya shiga yana wankan, Cikin zuciyata na ce ashe shima da kwiyan wankan yake ji, don tunda muka zo ban gan shi yana wankan dare ba, yana shigowa dakin ya sanya hannayenshi duka biyu ya sure ni. "Kina lissafin kwanakin aiko? Kina lissafin kwanakin da nayi ina hakuri ina fama da shan jar kanwa da lemon tsami? Tuni na langabe mishi na sa shi ya mance duk wata damuwa in har yana da ita da kuma wahalar da yake wuni cikinta, wanda nasan ya manta rabon da yayi irinta, duk wani abin da nasan zan yi wa Ado rannan da zai sa shi jin dadi ko farin ciki nayi mishi. Na kuma yi matukar yin hakuri da shi, ban Duna mishi gajiyawata ko korafi kan al'amuranshi ba, ba don komai ba sai don zuciyata ta riga ta yarda ta amince da cewar Ado mijina da na kuduri aniyar zama dashi a kowane hali yake ciki in taimake shi, in ba shi hadin kan da da yake nema a tare da ni, in jiyar da shi dadi gwargwadon abin da zan iya yi. Saboda na yarda na amince sona yake yi da zuciyarshi guda daya dawo da ni kauyensu da yayi kuma ba laifi ba ne gurinshi na asali yazo da ni mafi yawancin wahalar da yake yi kuma na yarda 58 mati yawancinta tawa ce. Sallar Asuba ya fita yayi ya dawo ya same ni nima ina sallar, nayi zaton komawa zai yi ya dan kwanta kafin ya fita tunda ni dai nasan kashi uku bisa hudun daren idonshi biyu ne, amma sai naji ya ce min ni na tafi bai ma jira amsawata ba. Na idar da sallata na koma na kwanta, sai da na dan yi bacci kafin na tashi na duba abin da muke da shi na abinci na gama gyaran wuri da tsabtace shi, nayi wanka nazo na shirya abin karyawa, na karya na gyara jikina na jawo kofar wurina na rufe don kar kaji su shiga suyi mana ta'adi. Na fita naje na gaida manyan gidan duka kafin na wuce can tsakar gida wurin haduwar matan gidan. inda ake da babban fili sosai da ke dauke da wurin girki a can nesa ga runbuna a can wani gefen ga in da ake aikace-aikacen wanki ko wanke- wanke, wani gefen can kuma daka ake yi da nika ga kuma wata katuwar rumfa da ke tsakanin wasu manyan bishiyoyi in da ake zama ana yin hira. Zaman tsakar gidan nan yafi komai dadi, don wuni ake yi ana raha ana barkwanci ana kwashewa da dariya, shagala nayi a cikinsu ana tayi ina kallo har ina taimakon masu daka da yin tankade, ban ankara ba sai naji ana kiran sallar azahar. 59 Gaba daya aka watse kowa ya nufi wurinshi don yin sallah, kofata tana rufe kamar yanda na barta a zuciyata na ce yau ma Ado bai dawo ba kenan, na idar da sallah naje na karbo fura nazo na dama na ajiye mishi na koma wurin matan gida, na ce ba zan iya zaman kadaici ba, in ya dawo ya kira ni ko kuma ya sha furarshi ya tafi. Ado bai shigo ba sai bayan 'sallar magariba, ban taba ganin tashin hankali da bacin ranshi irin na rannan ba, kina nufin ba za ki iya zaman wurinki ba? To me yasa ki ka yarda ki ka dawo? Kina nufin ai ba zan dawo gida in same ki a wannan dan tsukakken dakin namu kina zaman jiran dawowana ba? Sai in ina son ganinki in biki cikin mata ina kwala miki kira? Ke ba ki san hakkina ba? Ba ki san abin da za ki taimake ni da shi ba? Fura ce zan rayu a kanta Humaira? ba ki ga kamar dandanon abincinki a bakina zai yi matukar yin amfani a gare ni ba? To bari in gaya miki dama kin bi a hankali wannan taron nasu da ki ke gani-randa suka tashi tambayar junansu gulma suka sa dake a ciki abin zai baki mamaki, ke baki taba zaman gidan yawa ba duk fitinar da ki ka sani a gidanku wasan yara 60 ne. Gabana ya yanke ya fadi, jin da nayi Ado ya kira fitinar gidanmu wasan yara na ce to ai gara ka maida ni gidan namu, abin da kawai na fada kenan Ado yasa hannu ya make ni, kina hauka ne? Na ce kina hauka ne da kullum za ki rinka kallona kina cewa in maida ke gidan naku ke kina da gidan zuwa ne? Ko ba ki ji abin da maigidan ya fada ba sanda ki ka zabi biyo ni? Ya ce kar ki sake taka gidanshi saboda ya yafe min ke bai da sauran bukatarki." Dukan da Ado ya yi min bai 6ata min rai ya daga min hankali irin wannan maganar da ya soka min ba saboda gaskiyar abin da Babana ya gaya min ya gaya min. Nayi kukan bakin ciki har na gaji a kasa da kwanaki talatin na barin iyayena da nayi na biyo shi har ya fara goranta min abin da ya farun. Tabbas Ado namiji ne dama kuma nasha jin Mama tana cewa shi namijin ba dan goyo ba ne, a gabanshi kuma ma ta fada ta ce namijin ai ga ki nan gashi nan. Rannan dai kam kwanan da muka yin ba mai dadi bane, don haka yana fita sallar Asuba na duba inda 'yan kudina da nake tarawa suke, don yau kam 61 nayi niyya ko ba za su kai ni gida ba in dai za su raba ni da garin Dabai, to zan tafi in yaso nasan yanda nayi na karasa gida. Ban ga komai a wiirin ba sai nera hamsin saura. ya kwashe kwana biyu muna cikin wani hali ni dashi, rannan ya dawo da yamma ya same ni, kin gani Humairah mu biyu ne ni da ke a nan, ya kamata in wani abu ya faru a tsakaninmu na rashir jin dadi in na ba ki hakuri ki hakura, ba zai yiwu ace kullum sai na kai wa Inna maganar za ki hakura ba, in dai ba so ki ke mu rinka tayar mata da hankali ba. Kuka na soa yi sosai da sosai, kiyi hakur na sani ban kyauta ba da nayi miki gori, to amma ke kin ga yayi miki daidai kan maganar da ba ta taka kara ta karya ba ki rinka cewa in maida ke gidanku? Ai ya kamata ace ni da ke mun fahimci wani abu a tsakaninmnu, shi ne zaman namu bana rabuwa ba ne ba kuma na wulakanta juna ba. Tsawon lokaci yana yi min maganarsu na rarrashi da ban baki har dai ya samu ya gawo kaina na hakura, muka shirya. Tun daga wannan lokacin na rage shiga can cikin gida don yin hira da matan gidan sai dai kawai in gari ya waye in shiga in gaishe su dukan su in 62 dawo wurina in gama aikina in gyara komai in yi wanka in gyara jikina, duk da 'yan kayan nawa har yanzu guda uku ne sai lodin rigunan baccin da babu damar in sanya su da rana sai da daddare in yi mana abin karyawa irin wanda naga ina, so don komai na abinci Ado kawowa yake yi, komai tsadarshi kuwa. Agada, Doya, Dankali, Wake, Kuskus, Indomie, kwai, manja, Mangyada, Manshanu, Shinkafar tuwo saboda masa da kuma ta wara duk ina da su ina kuma da kayan tea zan kuma tashi da safe in je in kar6o kunu da kosai, don ko ban je ba za a biyo ni da shi, don haka nake girmama su in je da kaina. Shi kuwa Ado ka'ida ne kome nayi na karyawa to sai na karbo mishi dumame wurin Goggo Ayalle ya fara dashi kafin ya ci wani abin. Kullum zai baro gonarshi sha daya ya dawo gida, yana dawowa zai tube kayan jikinshi ya shiga bandaki yayi wanka, ni kuma sai in tsoma su a ruwa in wanke su in shanya in wanke mishi ranbut din nashi na hannu da na kafan in jefa su kan rufin dakin namu su sha rana, sai da yamma in kwashe su. Yana fitowa daga wankan zan sanya mishi 63 tabarma a inuwan dakina ya hau kai ya zauna in gabatar mishi da abin da na tanadar mishi. Yana ci muna hira yana bani labarin gonar tashi, mafi yawancin lokaci in muka zauna a wurin zai yi wuya mu tashi bai nanata gaya min maganar da ya saba gaya min ba, ina so in samu damar dda zan nuna miki halarcina Humaira, ina so in samu damar da zan nuna miki cewar ni din da namiji ne. In ya gama abin da zai yi ya kama hanya ya fita sai kuma in sake zama in shirya mana abinda zai dawo da azahar ya ci, hakan kuma bai hana ni tanadar mishi furar da zai sha bayan yaci abincin." Da daddare kuwa food flaks din mu nake dauka in kai wurin da ake kwashe tuwon darea zuba mana namu in yi musu sannu da aiki in dauka in kawo mana in zuba mana manshanu da yaj1 muci ba tunda ya hana ni cin abincin hadaka da su ba, ban dai kara tsinkewa na lamarin gidan yawa na kara tsorata da zaman gidan yawa ba irin ranar da aka wayi gari a gidan ana tuhumar Ade 'yar dakin Yaya Furera wai tayi gulma. Ade kuwa kishiyar, Ruwailah ce ranar ne na gane su matan gidan ba shugabancin matan sasansu suke yi ba, a'a group ne kawai daga kowane sasa ka ke in kana so zaka shiga kan hakan ne ma nake 64 ganin tanfar gaba dayansu kowacce kokari take ta janye ni in shiga nata group din. Ni kuwa kashedin da Ado ya yi min da kuma ganin abinda ya faru a ranar don ma anyi sa'a Yaya Baidu yana gida, shi ne ya fito yayi tsawar da kowacce ta shiga taitayinta da ba a san abin da zai faru ba, yasa na kara tsorata na kara kama kaina. Sannu a hankali ma sai na daina zuwa karbo mana tuwon daren, ina yi mana namu saboda kullum Ado yana yi. min maganar ke ba taya su aikin komai ki ke yi ba, amma sai kin je kin karbo musu tuwon su, in nayi abincin daren dai ban sawa kowa, amma na rana gaba daya tsofaffin gidan nake sanya musu, su kuma yaran matan wacce ta aiko danta ko tazo ta ce in zuba mata in zuba mata, wacce bata aiko ba shi kenan. Don abin da ya ce kenan, sai ko yaran gida da na gama suna wurina. Yarda da bin ka'idojin Ado da nayi sai suka yi dalilin da na samu wata irin rayuwa a tare dashi wacce ta fahintar dani cewar ita mace ba wai tarin dukiya ko wani kyale-kyale ne yake samar mata farin ciki da kwanciyar har kalin rayuwarta ba, a'a mijinta kawai. Kullum ni da Ado a cikin tarairayar juna muke, yana gudun bacin raina ina gudun nashi, yana 65 tattalin farin cikina kamar yanda nima nake tattalin nashi, duk da matsanancin aikin da yake fama da shi a gonakin shi ramar shi tayi matukar raguwa, saboda yana da kwanciyar hankali a gida ina kuma tarairayarshi da abinci mai kyau. Rannan muna daki da daddare ni da shi, hadari ne ya taso a gari ganga-ganga, tuni na fara sabawa da irin wannan hadarin mai yawan iska da rugugi gami da tsawa, shafa maina nake yi ban fasa ba, na ce mishi kai-kawo hadarin nan ba irin namu ba ne na can. Idon shi yana lumshe ba tare da ya yarda ya bude su ba, ya ce min eh ai ko ruwan ma ba daya ba ne, in kin lura ai mun baro can ne damuna ta riga ta kankama sai muka zo nan muka tarar lokacin ake shuka. Na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi idon naka yana ciwo ne? Bai yarda ya bude suba ya ce min to ko ba sa ciwo Humairah tunda ki ka zauna kika bar kirji a waje ai dole in yi maza in rufe su in dai ba so ki ke in kasa cika alkawarin da nayi miki na cewar shekaran jiya waccan da wacce ta wuce da jiya da yau da gobe duk za su zamo ranakun hutu ne a gare ki ba, don ki san in aka yi min alheri nima na iya irin nawa alherin. 66 Nayi murmushi na ce eh, gaskiya ne kar ka bude kai dai to dan bani hannunka in sa shi yayi min wani aiki. Ba tare da ya bude ba yayi maza ya miko hannun yana laluben in da nake tare da fadin ungo shi Humairah ungo hannun nawa karbe shi ki sanya shi hidimar da ki ke ganin ta dace da shi ina kama hannun nashi na ji Ado ya yi wani irin ajiyar zuciya mai sanyi ban sake ganin yanda aka yi ba sai ganina nayi a gefen shi a kwance ya zagaye ni da hannayen shi duka biyu tare da yi min tambayar. "Kin san wani abu ne Humaira?" Bai jira na ba shi amsar na sani ko ban sani ba, sai ya soma rattabo min bayaninshi, ke din mai alheri ce, alherinki kuma yawa ne da shi saboda kina da kirki ga ki da abin arziki iri-irni, in ki ka ga dama sai ki sa mutum ya rinka ganin tanfar babu ma wanda ya kai ki abin arziki, balle ya iya fin ki. Ban kula zancen na Ado ba, iya ka dai nasan in dai barin shi ya yi yanda yake so shi ne kirki, ko alheri to na yi mishi. Muna cikin irin wannan zaman mai dadi ni da shi wara magana ta taso a cikin gida, Ruwaila ce take yawan yi min magana akan kankane ni da Ado yake yi, yana hana ni mu'amalla da kowa cutata 67 yake so yayi dama haka tsofaffin maza suke yi ma matansu, don su hana su fahimtar komai. Shi Adamu ai ba yaro bane ga sa'o'inshi ne da ke garin nan suna shirin yin surukai, ko ma daukan jika kwanannan, don haka ga adashe nan na kafa ki zo ki shiga, na ce ai ba zai bar ni ba, ta gallà min harara "Ke ko iya zama da miji baki yi ba? Ai kamewa za ki yi daga gare shi ba a sakan mishi jiki haka sakakaka ba, in ki ka ga ya matsa sai kema ki bijiro mishi da taki bukatar. u da muke da shashun kishiyoyi ma muke yin hakan muci nasara balle ke ke kadai? In ki ka saban mishi da yanda ku ke din nan ai wahala za ki sha tunda in ke kin yarda da hakan wata ba za ta yarda ba, kin kuma san ana yin kaka in ya saida amfanin gonarshi kishiya zai yiwo miki." Kirjina ya bada sautin rugugugu! ban sani ba ko itama ta gane tsananin tsoratar da nayi ne yasa ta yin murmushi, ta ce "Lah, to wannan ai ba wani abu ba ne, mu nan ai haka ake yi kaka tana yi in aka cika runbuna da hatsi, to abinda yai saura sai akai kasuwa a sayar sai ki ga an kawo miki wacce zaku ci hatsin tare shi kenan." Ta sake kallona ta ce min, to balle ko mijinki da wahalar damunar nan bata hana shi manne miki 68 ba, ai kuwa kin san ya huta da kaka akwai magana, na kuma ji Yayanshi yana cewa yayi noma ba kadan ba, in kaga irin aikin da yake yi ma sai ka ga tanfar da gayya yake yi. Sammako yake yi ya riga kowa tafiya, sannan duk a can ake baro shi, na ce mishi babu wata gayya so yake yi yayi gini ya kuma kara wani auren, ai kuwa dolen shi yayi aiki tukuru." Na zuba mata ido kawai ina kallonta don kuwa ban taba jin maganar da ta dame ni ta daki zuciyata ba irin cewar wai Ado zai yi min kishiya, to ni kuwa kenan ribar me naci a biyo shin da nayi? Ta salke kallona cikin natsuwa ta ce, yarinya kamar ki ya kyale ki kina yawo cikin wasu zulunbun dogayen riguna da tun suna baiwa mutane sha'awaa har sun daina sun maida ke kin zama tanfar wata tsohuwar Babarbariya." Kalaman na Ruwailah sun yi matukar yin tasiri a zuciyata, musamman da ta tabbatar min da cewar su al'adar mazansu ne ma in sun cika runbu da hatsi, to abinda ya saura in an kai shi kasuwa aure ake yi. Don haka nan na kame sosai daga yawan sakewa Ado fuska, al'amura suka yi matukar sauyawa a tsakaninmu, da yazo zai taba ni sai in ce 69 mishi cikina na ciwo, sai yayi maza ya kyale ni. Rannan dai ta kure, mun kai wajen sati uku a haka tunda safe Ado yake yi min magana, rarrashina yake yi a dalilin bai son tilasta ni saboda abin da ya taba faruwa a tsakaninmu, ganin da nayi ya matsu kwarai mu fahirnci juna ya sani bijiro mishi da maganar adashen da ake yi a gidan, wanda ni kadai ce bana yi. Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, "To kina da sana'a ne Humairah? Adashe ai na mutane masu sana'a ne, ke ba ki da sana'a ni ba wani abu nake yi ba in ban da maganar gonar nan, gona kuna ci mun kudi take yi bata fara bani ba, yanzu ne nake neman aikin koyarwa tunda na gaya miki na mika takarduna ba kuma zan yi wani aiki de va wiice koyarwa ba a yanzu, saboda ina son in jarraba yin noma sosai. Ni yanzu fatana da addu'a ta bai wuce mukai lokacin da za a yi girbi asirinmu bai tonu ba. Na rantse miki Humairah rutin asirin Ubangiji ne kawai yake tafiyar mana da al'amuran sai ma ganin kamar zata kure sai kuma in ga wata hanyar tazo ai, wani lokacin ma ba da gangan nake kwashe miki kudinki ina bar miki nera hamsin ba, Kurewa take yi. 70 Kiyi hakuri kin gane? Nasan kina hakuri dani, amma ki kara maimakon in ji wannan rarrashi da bayanin da yayi min, na riga naji zuga zugan da aka yi min cewar su din ma'ana, 'maza' ba ayi musu sassauci mai yawa sai su raina mutum. Don haka sai na kara daure fuska na kara 6ata rai na ce, to sai muyi hakuri duka, na kawar da fuskata gefe. Abin da kawai na fada kenan, sai ya fahici abin da nake nufi, muyi hakuri duka? Na ce, eh, me kenan hakan yake nufi? Na sake bata rai na ce, ko ma menene? Ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, waye ya koya miki wannan iskancin ? Nayi kamar ban ji shi ba, ya ce to ai da sai ki gaya mata naki mijin ba irin nata ba ne. na ce uhn, na mike da nufin fita in bar mishi dakin, sai kawai naji ya kamo hannuna ya murde da karfi, sai da na kwallara kara mai tsanani, amma bai sake ni ba. Ai babu in da za ki tafi sai kin gaya min wacece take koya miki wannan iya shegen? Ruwailah ko? Sai naci abu kazanta, in bata yi hankali da ni ba, ha'a me tayi maka zaka zage ta? Kau na ji, ya wanke ni da wani irin wawan mari, nayi maza nasa daya hannun na dafe wurin, ai in ba ki gaya min wacce tasa ki kiyi min wannan 71 wulakancin ba, za kiyi mamakin abin da zai faru yau." Na soma mutsu-mutsun kwatar hannuna naga hakan ba zai yiwu ba wahala kawai nake karawa kaina bai kuma kula kukan da nake yi ba, balle ya damu da cewar rana ce mutanen gida zasu iya jin abin da muke ciki. Wulakanci irin wanda Ado yayi min rannan bai kwatantuwa, murde ni yayi ya yi abin da yaga ya yi mishi daidai sannan yasa kai ya fita ya bar gidan da azahar tayi ma ya sake dawowa, babu kuma wata mu'amulla ta rarrashi ko sassauci a tsakani na rasa in da sa kaina in ji dadi, ga shi kuma bsbu halin in kai kara in maganar ta fto ban san me Zai faru ba. Ba kuma zan iya gayawa Inna ba in ce tayi mishi magana, nasan zai iya gaya mata abin da ya hada mu, na kuma san zata yi fushi mai yawa don na saba jin ta tana cewa dabi'ar matsiyatan mata kenan su ne wadanda ba za su gaya wa mazansu bukatunsu ba, sai a lokacin da suka ga sun matsu da su. Don haka na lallaba na samu Ado ina kuka na ce mishi kayi hakuri Kawu ka daina irin wannan mu'amullar dani. Ya dago ido ya kalle ni ban san yenda aka yi 72 ba, tausayina ya kama shi cikin natsuwa ya ce min ya wuce amma ki gaya mata tayi hankali da ni ko wacece? In ita bata sani ba ke kin sani cewar Mama ita ce mafi darajar mutum yau a wurina tunda bani da uwa ba ni da uba su Baba Tanimu ne iyayena. Ita ta rike tayi min gatan da nayi karatu na koyi al'amura masu yawa na rayuwa, amma sa nayi jaruntakar rabuwa da ita don in zauna dake ya sake zuba min ido yana yi min kallo mai tsanani, shi ne za'a saki kiyi min abinda ki ka san zanyi bakin ciki? In ana son cutar da ni sai a hada kai da ke? Yanzu in an san ina sonki sai ayi amfani dake? Ni in ina da hali sai kinyi adashe? Me zan yi da kudin? Hankalina yayi matukar tashi jin kalaman Ado nayi matukar jin kunya da Nadama na abin da nayi mishin kuka sosai na soma yi ina bashi hakuri don kuwa na san ba karamar wauta nayi ba dana ji irin wannan zugan na kuma yarda nayi amfani da ita. Na dade sosai ban iya sakin jikina sosai da Ado ba saboda naji kunyar abinda nayi mishin ba kadan ba duk dai shi din bai sake yi min wata magana ba ko kuma nuna min wani abu. Ana cikcin haka rannan ya dawo da rana, wasu takardu ya ciro a aljihunshi ya miko min, nasa 73 hannu biyu na karba ina dubawa tun kafin in kai ga gama karantawa ya ce min naje nan Government Day Secondary School Dabai nayi magana da Princepal din ya yarda za ki soa zuwa satin nan. Kije kiyi karatu ki samu takardar ki yafi min wunin da za ki rinka yi a gida bana nan ana koya miki abin da ba zai min daidai ba, da na bari ne sai badi don in ga na soma yin wani abu, to amma sai na tuna kuma ai 'Though Times Never Last but though people do." A haka na soma zuwa makarantar (S.S. 2) aka sanya ni, babu kuma abin da Adon bai saya min ba na karatuna, tun daga uniform, sandal, safa, har zuwa littattafai na karatu. In nayi shiri Zan ta in sanya dogon hijabina akan uniform din sai na shiga cikin makaranta in cire in shiga aji in mun taso ma in mayar. Tunda na shiga makaranta na soma koyon jarumtaka kan al'amura masu yawa nayi matukar rage baccina, kullum na kan tashi ne da wuri in yi mana abin karyawa da abincin da zamu dawo muci da rana, in zuba a cikin food flask kafin in yi wanke-wanke, in yi wanki in yi shara in yi wanka. Karfe bakwai nayi kuma zan sanya kayana in dora hijabina in je in gaida su Baba da su Goggo, 74 da sauran mutanen gida, in fita waje in samu Ado yana jiran fitowata bayan ya rurrufe mana wurinmu mu jera mu tafi sai yaga shigata makaranta sai ya wuce gonarshi. Yana kuma daidaitan lokacin tashin mu ne ya taso daga gonarshi ya biyo min ta makaranta mu dawo gida tare, da daddare in mun gama abinda muke yi kuma yana duba takarduna yaga aikin da aka yi mana ya yi min gyara kan abin da ban gane ba. Zaman lafiyan da aka lura aka ga ya samu tsakaninà da mijina ne ya bayyana a cikin gida, wanda ban samu hakan ba sai da na yarda ni ce a kasa shi ne sama da ni, sai da na yarda da barin son raina na koma bin nashi, na koma karbar umarnin komai daga gare shi, na koma rayuwar yi nayi bari na bari ko da kuwa ina son barin ko kuma ina kin yin da aka ce in yin. Misali, ko a cikin gida ina son shiga cikin mata 'yan uwana in dan yi mu'amalla da su in dan ji dadi a raina, amma tunda yake min ya hana ni žaman gindin bishiya don hira, na ce mishi, to na kuma bari ko baya nan bana zuwa. Tunda ya hana ni bin dakunan mutane matukar ba wani dalili mai kwari ne ya kai ni ba, na hakura 75 na daina sai ko dakin Goggo Ayalle. sKullum ni kadai ce a wurina, in ba shi din yana gida bane kowane lokaci a cikin hidimarshi nake, tunda daga wankin yan suturunshi da adana su da tattalin abin da zai ci hakan kuma bai hana ni ba shi lokacina a duk lokacin da ya bukaci hakan. Ana cikin hakanne kawai na soma jin maganganu suna yawa a cikin gida, wai ni din fin karfin shi nayi, bai da wani katabus bai iya yin komai sai abin da nasa shi, ko kuma na hana shi, wai ai tunda na iya raba shi da Hajiya Majadan duk alherin da tayi mishi, to babu wani wanda ba zan iya raba shi da shi ba. Ina jin maganganun na gane daga inda suka fara fitowa, cikin zuciyata na ce don ta gane na daina daukan shawarwarinta ne, gara ita, nata mijin yana da irin wannan juriyar ni nawa in na ce zan yi mishi haka ba kwashewa kalau zan yi ba. Na dai kudiri aniyar zama lafiya da kowa ba na son fitina, don kuwa nasan babu alheri a cikinta, tashin hankalin Mama kawai da ta tasa mu a gaba shi ne yayi dalilin barowarmau gida muka taho nan, to ta wadannan bataliya fa? A wannan lokacin aka sake fito min da wata dabi'a, duk wacce zata yi wanka ko zata yi taya bahaya 76 sai tazo wurina ta ce wai a nan zata yi. Wuni suke yi suna layin shiga bayan gida, kuma duk yanda na kai da wanke shi sai sun 6ata shi yayi ta wari, wani lokaci har cikin daki, don tuni da nayi hakuri da su akan sabon halin nasa. To Ado ya ce bai yarda in hana su, in gaya musu cewar shi din ya hana su shiga wannan bayan gidan ya ce in gaya musu su rinka wanke hasu, suna gyarawa don su rinka jin dadin shiga ko ni din da irin barin wannan din da kazanta da ba su zo sun shiga ba. Ni kam ban iya gaya musu ba, ina jin kunya don mafi yawancinsu sun girme ni nesa ba kusa ba, shi kuma yana ganin wata tazo ta shiga ni yake balbalewa da fada, sai da nayi sa'a maganar ta kai ga Baba Tanimu. Shi ne yayi kashedi mai kari kar ya sake ganin wata taje ta zaga a wurina baya son iya shege da neman magana. A wannan lokacin har a gabana a kuma kan idona za a rinka tsaki ana cewa a hau, to namiji kuma, wacce bata san shi ba ai ita ce bata san sh ba, mu kan ai sun shamu un warke, muna nan da ke za ki zo kina zubar mana da hawaye sanda zai yi miki halin nasu mu ce muma bamu sanki ba 77 amarya muka sdni. Kusan kullum sai an ce min an ga Ado gidan Mallam Korau yaje tadi, rannan dai na daure na samu Adon na tambaye shi cikin natsuwa na ce mishi ni da gaske ne wai kana neman yar gidan Mallam Korau? Bai wani kalle ni sosai ba ya ce min Menene in ina neman nata? Na ce a'a na dai tabaya ne kawai don in sani ya ce ba uwardakinki ce ta gaya miki ba, ai ba zata yi miki karya ba, watakila dai kina ganin ne tanfar gonar tawa ba, za ta rike min ku ku biyun ba ko? Ban sake ce wa Ado komai ba, amma wani irin al'amari ne naji ya taso min ya tokare ni a kirji, wani irin nauyi ya saukar min a kirjin, zuciyata tayi matukar kunzi, karo na farko da naj! in wannan abin a tare da ni. Kishi mai tsanani ne ya kama ni, na tabbatar wa kaina da cewar aiki ne babba a kaina, in har ya tabbata Ado auren nan zai yi tun daga. wannan lokacin na soma sa ido akan lokutan fitanshi da kuma na dawowanshi tare da tunann io a wane lokacin yake zuwa wurin nata? Zuciyata ta soma raya min cewar wata kila daga yin sallar Isha'i ne tunda kullum bai dawowa 78 gida bayan Isha in sai yayi zama na awa daya da minti goma sha biyar ko kuma da minti talatin. A farko ya ce min yana zaman yin karatu ne wurin Limamin Masallacin unguwar, na kuma yarda. To yanzu kam na gane ba gaskiya ba ne, loba ni kawai yake yi, tadin shi yake zuwa. Don haka rannan da zai fita Masallaci don sallar Isha'i; na ce mishi in an yi sallar Isha'i ka shigo gida don ban yarda da wannan munafukar makarantar taka ba, babu kowa a ciki sai kai kadai. In ban da munafurci wane karatu ne ba za ayi shi ido na ganin ido ba, kullum sai dare yayi? Zuba min ido yayi yana kallona, a hankali ya bude baki ya ce min, makarantar tawa ce kuma munafuka yau Humaira? Nayi maza na ce mishi, eh, kana nema ne ka maida ni wata yarinya 'yar kankanuwa. Ka shanya ni a gida da sunan kana wurin Mallam alhalin kai kana can ne wurin tadin ka. Ya ce, To shi kenan, ke ba yarinya Rankanuwa ba ce, tunda kin yi kokari kin gano ni, to amma ai kuma ina jin ban taba yi miki karyar zan zauna da ke ke kadai ba, balle ki ce na 6oye miki. A kullum kuma ina kokarin gaya miki cewar ni 79 din namiji ne, shi kuma namiji ai kin san imijin mata hudu ne. Kalaman nashi suka kara fusata ni, na soma sake mishi maganganu masu zati, musamman ma da na tuna eh, gaskiya ne shi din kullum a cikin alkawarin zai nuna min shi namiji ne, wato dama abin da yake nufi kenan? Ba. mu gama fita daga cikin wannan maganar ba tunda bai yarda zai daina zaman waje bayan Sallar Isha'i ba, sai kawai na dauki wayar Ado ina bincike a cikinta. Text din yanata na soma gani, yayi maza ya fige wayar daga hannuna, nan take kuma ya kama yi min fada ""Kina fa nemana da fitina, kina nema sai kin takura min, yaya ne haka? Ya ya za ki tsananta min bincike bayan kin san an hana? Na soma yi mishi kuka saboda a wannan lokacin na riga na gane gaskiya ne yana neman aure? Kenan gaskiya ne duk wahalar gonar nan da yayi da juriya da taimakon da nayi tayi mishi kudin a dawainiyar aurenshi zasu tafi? Hannu biyu na dora a kaina nayi kuka har na gaji bai yarda ya sake shigowa dakin ba. Washegari tun safe na tatt a na bar mishi 80 wurin, na koma dakin Gogori Ayalle nayi kwanciyata, zuwanshi uku in dawo wurinmu zai zauna muyi magana ta gaskiya, ni da shi ban yarda ba. Har kusan yamma ban koma ba, anyi sallar La'asar ya shigo ya zo ya same ni, "Zo muje kiyi mana girkin abinda zanmu ci mana Humaira, na ce mishi kaje ka kawo yar gidan Mallam Korau ta girka maka. Ya zuba min ido yana kallona cikin natsuwa, kiyi hakuri mana Humairah na ba ki hakuri na kara ina ce ni duk girman laifin da ki ka yi min hakuri daya ki ke bani in ce na hakura? Na daga ido na kalle shi, kayi min wulakanci akan wata 'yar iska? Yayi murmushi, "To ai na ce kiyi hakuri." Ban tanka mishi ba sai ya juya ya fita, Bai wani dade ba ya sake juyowa zai dawo, sai kawai naji Ruwaila tana ce mishi, ai kai kuma yau taka ta sae ka tunda ka yarda ka bata mata rai, baka da šauran zama lafiya tsugune ta kare maka tunda ka bari aka yi fushi da kai. A zuciyata na ce, kai wasu da rashin zuciya suke, tanfar dai bata gane irin sharewar da Ado yayi mata ba kusan kowane lokacin a cikin nemanshi da magana take. 81 Sai kawai naji ya ce mata, eh ai ta isa ne kin san ni din a hannunta nake, wata matar don ta yi wa miji fushi ai shirme tayi, tunwa wanda tayi domin shin ba zai kula ba, balle ya bi baya. Abin da kawai ya fada kenan, tayi matukar fusata da maganar tashi ta shiga sakin maganganu, ai kai ma ba haka kawai ka ke wannan zaryar ba. Ka ke ganin a kanta zaka iya batawa da kowa, ai rashin imani suke gwadawa tunda abin da ba a sha suke wankewa suna ba ku. Maimakon yayi shiru tunda ya ji inda ta maida zancen nata, sai naji ya ce, ni na yafe mata, ba kuma rashin Imani aka yi min ba, da bakina sai in yi yanda ake so tunda ai nawa ne. A mafi yawancin lokaci, nakan hakura da abubuwa masu yawa sosai inyi ta hakuri dasu saboda sanin da nayi cewar gaba daya matan gidan nan idonsu a bude yake akan al'amarin zamanmu ni da mijina. Tunda Ado da Ruwaila suka yi wadannan maganganun gashi dai a zahiri wàsa suka yi irin na matar wa da kuma kanin miji, amma can cikin al amarin nasu sun kulle wani abu Ruwaila dai 1a nanata maganar yafi a kirga. Ana cikin haka, raninan na amsa kiran da 82 Goggo Ayalle tayi min da sassafe, Ado bai fita ba ya jira in je in dawo don ya ji kiran akan menene? Me ta ce miki? Yayi min tambayar tare da bina da kallo zuwa in da na zauna. A hankali cikin natsuwa don kar ya dauki maganar da tsanani nace mishi kan maganar girkin ne. Wani lalataccen ashar ya wulwulo ya antakawva Ruwailah, zan sa kafar wando daya da matar nan, wai ita tana son takurá min ne ko? Nayi maza na fara bashi hakuri, ba fa ita ba ce. Da sauri ya ce ke matsa can, ke me ki ka sani? Tlo ka gani ma dai kawai ni kam kayi hakuri na gayawa Goggo zan karbi girkin. Da sauri ya tanbaye ni mene? Za ki karbi girki ki ka ce musu? To kje ki karba ta kuma kisan yanda zaki yi dasu ni babu ruwana. Tunda na gane kin fi jin tsoronsu da ni, kin kuma fi jin maganarsu da tawa. Kuka na soma yi mishi sosai da sosai, to ya ya zan yi? Iyayenmu ne in naji maganarsu ko naji tsoronsu nayi hakan ne saboda girma da darajarka a wurina ba zan 1ya jayaiya da su. Goggo ta ce, "Ci gaba da kin shiga girkin nawa zai zamo sanadin da kowa zai 1ya warewa ya ce 83 baya ciki, in nayi haka kuma ban kyauta musu ba, don wannan girkin nasu yana cikin alamomin hadin kan gidansu. Gaba daya suna ci daga tukunya guda, to sai kuma in ce mata ba zan yi ba? Shiru Ado yayi cikin nazari da tunani kafin jimawa can ya dago ido ya kalle ni ba za ki iya aikin ba Humaira ba, kuma zasu taya ki ba don wannan haduwar da ki ke ganin suna yi kowadanne suna taya 'yan group din su ne. Ke kuma ba kya cikin na kowa, sannan cefanen gidan nan ba karamin abu ba ne, ni kuma a halin yanzu ba zan iya ba saboda a halin da nake ciki kina gani sarai kullum kara maneji nake yi. Ban yi miki bayani ba ne, don,ba ki yi magana ba, ba ki kuma nuna min damuwar ki ba duk wani abin da nake kashewa yanzu ba nawa ba ne, rancensu nayi. Hannu biyu na dora a kaina na ce rance? Bai kula ni ba sai yaci gaba, to zan rinka cin bashi ne ina yin cefanen da bai zaa min wajibi ba? In suka yi hakuri ma ai nima ba zan bar abin haka kawai ba, tunda duk masu cin abincin nawa ne ba sai an ce min in yi ba. Ni kam kuka na rinka yi saboda na tsani bashi, 84 gai nake tankar shi ne karshen fitina tunda naji Malla mai babban Allo yana yawan neman yin magans kan Hadisan da suka yi mini da gaggauta biyanshi in har mutu ya cilka ana bin shi, kai ni kam ban son bashi. Kukan da nake tayi yasa Ado tsayawa yi min bayani Ke bashin fa ba wanda za'a matsa min ba ne wurin Haruna naje na karba wannan abokin nawa da nace miki tare muka yi Secondary School. Yana gamawa shi ayayenshi suka yi mishi aure, har na ce miki yanzu matanshi uku da 'ya'ya birjik yana kuma ta hidimarshi. Duk da Ado yasha bani labarin abokinshi Haruna na rowan bargo ban ji dadin bashin da yace min yaje ya karba a wurinshi ba da nayi tunani sosai ma sai na gane har 'yan atamfofin Nicharm din da ya sayo min guda biyu yazo min dasu a dinke, wai in dan sabunta a kudin da ya rantan ya sayo min su. Ke ba fa ni kadai ne nake cin bashi ba utane da yawa ana bin su bashin da bai dadi shi ne wanda ka karba bayan kasan baka da hanyar biya, ni kuwa ina da shi. Damuwar da ya gani a tare da ni ce tasa shi yi min wannan bayanin, tabbacin da Ado ya bani na 85 bashi da halin da zai yi cefanen gidan nan in girkin yazo kaina yayi matukar tayar min da hankali. Duk da ni din ba mai yawan yin addu'a ba ce, sai na dukufa nayi ta karanta wata addu'a da mai babban allo ya bani ita, ya ce min addu'ar Nana Aisha' ce (R.A) a kowanne lokaci. Wani lokaci ma in na zauna ina yi na rinka kenan sai Ado ya gaji da ganina a zaune ya sure ya dora a katifa yana daiyar cewar da nayi mishi mai babban allo ya ce min mai yawan karanta addu'ar baya talauci. Shi kuwa Ado sai ya ce nin, in ya kama sana'a ko? Ko kuwa haka kavwai za su Zubo mishi? Ban kula shi ba, iyaka dai ban daina ba. Rannan mun tafi Makaranta da safe shi kuma ya wuce gonarshi kan hanyar tatiyar tamu dai ya bani tabbbacin a satin nan zai fara dibar masararshi ya sayar ko da bata gama karasawa ba, tunda ba zai sake zuwa wurin wani neman wani rancen ba. Na ce mishi, to in dai ba ya zama dole ba kar ya yi hakan, ya kara hakuri kawai Na shiga aji ya wuce ya tati, ina aji ina tunanin Ado, irin wahalar da ya yi wa gonarshi ya sonmna diban masararshi a yanzu ba karamin asara ba ne tunda ba duka ne tayi ba wacce tayin ma bata yi 86 wani kwari ba. Ana tashinmu na fito ban ganshi a inda yake jirana ba, na dan tsaya kadan ko zai karaso ban gan shi ba naga za'a watse a bar ni ni kadai nia na biyo hanya na dawo. Ina bullowa lungun gidan mu naga wata lafiyayyar mota a tsaye a kusa da Masallaci mai lambar Abuja, ban sake kallonta ba, na wuco na nufi cikin zauren gidanmu muka yi kaci6is da shi Na daga ido na kalle shi har ya dawo yayi wanka yasa T-shirt da wandon shi masu kyau wadanda ma ba kasafai yake sanya su bayana kuma kamshin turarenshi. Ban san dalili ba sai naji haushinshi ya kama ni nan take na soma yi mishi kuka, shi ne baka biyo min ba ka dawo gida? Ina kukan ina tambayarshi, to kiyi hakuri mana Humaira, ki tsaya mana kiji abinda yasa nayi hakan in ban da uzuri ba ki gamsu ba sai kiyi hakan ki. Daga cikin dakin zauren nan na jiwo wata murya tana tambayar Ado to kai tsoron kukan nata ka ke yi ne? Da gudu na fada dakin jikin mai babban allo na kwanta shi da Baba Yahaya ne a ciki. Mai babban allo ya ture ni yana fadin "Ke 87 matsa can ja'ira, shagwababbiyar wofi, kar ya baro ki a makaranta ya dawo shi kadai akan me? Duk tsiyarki da wayonki mata hudiu zai yi ba da ke kadai zai zauna ba, nayi murmusha na cee oho, ni dai nayi gaba, Baba Yahya ya taya ni murmushin tare da fadin gaskiyarki Aishatu. Na gyara zama na gaida Baba Yahya cikin ladabi da girmamawa, yana kallona sai murmushi yake yi alamar dadi ya kama shi. "Karatu ki ke yi?" Na ce mishi "Eh Baba." Ya sake wani murmushin ya kalli Ado Ubengiji ya yi muku albarka ya rufa muku asiri ko in e ya kara don ya riga ya rufa sai neman kari. Ado ya ce amnin Baba. Na kalli mai babban allo ina murrmushi "Ina su Hajiyoyinki?" Ya taya ni murmushin tare da fadin kalau din su, ba su ma san zamu zo ba." Na sake kallon Baba Yahya na ce "Baba ba ku gaya wa kowa ba ne? Baba Yahya ya ce, ai babu wanda ya sani jiya da daddare ma da Yayanku yazo nan gidan shi da Atika nayi kamar in gaya musu sai kawai na fasa. Nayi murmushi na ce dukansu lafiyarsu kalau Baba? Ya ce kalau dinsu Aliya dai zata tai aikin Hajji ita kuma Atika cikin dake gare ta yasa ba a yi 88 maganar tafiyar tata ba. Dadi ya kama ni jin alherin da 'yan uwana suke ciki. Na sake kallon Baba Yahya cikin natsuwa na ce mishi oh Baba, ashe zaku zo dubani da sauri ya ce zamu zo mana Humairah, zamu zo mana mu gan ki. Na kuma ji dadin zuwan da nayin ba kadan ba nazo na same ki kina karatu, mijinki ya maida ke makaranta don kiyi ilimi shi kuma naje gonarshi na gani wannan noma da wannan yaro yayi ya wuce abin mamaki sai abin tsoro. Zuciya dai ita ce mutum, shi yasa Manzon Rahma (S.A.W) ya ce, in ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, in kuma ta Baci to dukkan jikin ne ya baci. Na dan yi murmushi saboda jin dadin gamsuwwar da ya ce sunyi na ganinmu cikin natsuwa na ce mishi Baba har kun je gonar ne?. Mai babban allo ya ce ai mu ta can muka fara don da muka yi tambaya gonar tashi aka kaimu, ai mijinki ya zama sarkin noma. Na sake wani murmushin daidai Ado ya sake shigowa da wani kwanon a hannunshi. Baba Yahya ya kalle shi cikin natsuwa daidai yana ajiye kwanon ya ce mishi kai mu fa mun riga mun koshi, wannan gaudan da ka kawo mana ba 89 cin wasa muka yi mishi ba. Ai rabon ma da in ci gauda mai dadin na yau har na manta matanmu na can ba su iya irin wannan girke-girken ba. Ina jin sun tsunduma hira da Ado akan maganar gonar tashi nayi maza na nemi izininsu na shiga gida naje na tube uniform dina na daura sabuwar atamfata. Na gyara nayi tsaf, na yafa sabon gyalena na dauko abincin da na tanadan mana muci, in mun dawo. Na hada da abin shan da nayi na ajiye cikin randar kasa na dora a tire na hada dasu plate cokali da kofuna, na dawo nayi sallaa a bakin kofar suka amsa. Na shiga na tsuguna na ajiye tiren mai babban allo yana kallona yana cewa, amma ai kina jin Babanki yana cewa sarkin noma mun koshi ko? Ban asa mishi ba, na kalli Baba Yahya cikin yanayin da zai tausaya min, na ce mishi Baba wannan abincina ne da nayi da hannuna, kuci ko ba yawa. Nan da nan ya ce, zuba mana muci Aisha, nayi maza na jawo plate-plate zan fara zubawa, mai babban allo yana fadin "Ka ji wai tana jaddada da hannunta tayi kamar hannun nata ya wani iya ko 90 kuma dabanne. Ado yana murmushi yana fadin, kai dai bari ka ji kawai Mallam. Ina zuba musu abincin, Baba Yahya yana kallona. Burabuskon gero ne da miyar taushen da taji busasshen kifi da tantakwashi, sai kamshi suke yi daga shi har miyar. Na zuba musu a plate na zuba musu miyar sosai na mika musu, Baba Yahya ya kai lomar farko ya tsaya ya sosa kunnenshi da dan makullin motarshi kafin yaci gaba da kai loma bakinahi. Jimawa can, sai naji yana tambayata Ke da ki ke sammakon zuwa makaranta Aishatu, da wanne lookaci ki ke wannan girkin?" Kan in yi magana Ado ya soma yi mishi bayani har yana ce mishi ban cika gane ina wahala mai yawa ba Baba, saboda Humairah wata irin yarinya ce mai hakuri da juriya. Duk abin da zata ji ta taimaki abokin zamanta shi take yi, babu yanda za'ayi in dawo gida bata gamsar de i ba, tana kuma tsusayin wahalata. Matsalarta daya ce, Baba kullum a kanta muke fada da ita, Baba Yahya yayi murmushi saboda ganin rin kallon da Adon yayi min yasan zolayata yake so yayi. Ya ce, kishi ne da ita Baba kishin ma na rashi 91 hankali, in ba haka ba.... Mai babban Allo ya karbe maganar, don haka Adon yayi shiru shia yana sauraron shi. Yayin da Baba Yahya yake ta faman murmushi, ni kam tsuke fuska nayi na sunkuyar da kaina kasa, ai duk tsiyarta sai kayi hudun nan don kayi biyu ma'ai ba wani kokari kayi ba. Kana girbe amfanin nan naka, ka samu wata santaleliyar fara ka hada, kaga sai ya zama kana da baka ga kuma fara ka kawo. Baba Yahya yayi dariya ya ce rabu da su kin ji Humairah ke dai ki kara kokari akan wanda mijinki yake bada labari kin ji ko? Na ce, to Baba. Na kwashe kwanuka na fita dasu na dawo don yin sallama da su, ina durkushe Baba Yahya sai faman sanya mana albarka yake yi, zan je in baiwa uwarki labarinlku. Na sake wani murmushin, kudi ya miko bandir din Naira hamsin-bamsin guda biyu sababbi, "Rike wannan ki rinka zuwa makaranta da su." Nasa hannu biyu na karba nayi mishi godiya, suka fita suka tafi ina leke ina ganinsu tsaye tare da su Baba Tanimu da sauran mutanen unguwa. Na koma na shiga gida ina ta murnar kudin da Baba Yahya ya bani cikin zuciyata, ina fadin shi kenan ajiye su zan yi in girkin ya zo kaina Ado ya 92 samu abin da zai yi cefane dashi. Jimawa can sai ga Ado ya shigo murmushi yake tayi, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi sun tafi? Ya sake wani murmushin ya ce sun tafi Humairah, ni a rayuwata ko me zan cewa Baba Yahya? Oho! Nayi murmushi na ce mutumin kirki ne amma Baba Yahya kadai mai babban allo fa? Yayi murmushi ya ce, dukansu Humairah, amma Mallam ai kin san ganinki yazo yi, na ce ai haka kace? To bari sai na gaya mishi. Yayi dariya ya ce, "Yi hakuri." Na mika mishi kudin da Baba Yahya ya bani, ina murmushi ""Ga shi nan ka samu kudin cefane in girkin ya zo kaina. Wani irin lallausan murmushi ya sake kafin ya daga gefen katifa ya rinka fiddo min bandir din dari bibiyu sai da ya ajiye guda biyar, Zubawa kudin ido sosai nayi ina kallonsu, a ina ka same su? Ya ce a ina na samne su kuma? Ban da wurin Baba Yahya. Sannan ko mai babban allo bai ga lokacin da ya bani ba. Baba wani irin mutum ne mai iya martaba mutum ya sake kallona cikin murmushi mashin zan je in sayo mana don in hutar da ke tafiyar kafan da kike yi zuwa makaranta kullum da dawowa. Asabar da Lahadi kuma in dan rinka daukanki muna fita kina ganin kauyuka da kasuwanni. 93 Na kalle shi cikin natsuwa na ce, ni na yafe kaje ka biya bashin da ka karba in sun ragu ka rike don cefanen abincin gida. In gonarka takai kayi girbi in ka gama biyan sadakin aurarrakin da zaka yi in wani abu ya ragu ka sayi mashin din. Yayi dariya ya ce, wai wa ya ce miki zan yi aure ne? Na galla mishi harara na ce, uhun ba ina jin mai babban allo yana ce maka kar ka yarda in tsufar da kai ni kadai ba? Yayi dariya mai karfi ya ce, kai Humairah! Ke kam ban san iyakacin kishinki ba. Don haka yau bari in yi miki wani alheri tukuicin zuwa mai babban allo gidana, in hutar da ke in kwantar miki da hankali, don ki sakata ki wala kiyi abin da ki ke so, aure ko? Ya zuba min ido yana kallona cikin natsuwa da walwala kafin ya ce a yanzu a wannan halin da muke ciki ba zan yi shi ba, ban ce miki kwata-kwata ne ba zan yi ba, a'a a wannan lokacin ne ba zan yi ba. Don haka kar wata ta sake ce miki an ganni wani wuri bani ba ne, in kuma lokaci yayi na in yin to ni da kaina ne zan gaya miki. Don ina fatan in yi ne a lokacin da ke da kanki za ki gamsu da cewar eh, ya dace in yi in ba, wannan halin na samu ba, ba zan yi miki kishiya ba Humairah to me zan yi da ita? 94 Duk da cewar da nayi wa Ado kar ya sayi mashin sai daya saya don irin na matasa, yana kawo mashin din gida su Baba da su Goggo suka sa albarka ya shigo ya ce min ki shirya in rana tayi sanyi za ki raka ni Ruwan bago muje in kaiwa Mallam Haruna kudinshi. Daga nan kuma tunda yau ranar Lahadi ne sai mu tsaya a kasuwar "Sundu' muyi sayayyar abin da ba mu dashi na kayan abinci, na ce mishi to. Da yamma na shirya nayi kwalliya da daya atanfar tawa itama Nicharm ce amma nayi kyau sosai, na yi wa mutanen gida sallama naje na dale bayan mashin din Ado, wanda tunda na gan shi nake ta faman murmushi. "Ke ba ki san yanda tafiyar kafan nan da ki ke yi yake ci min rai ba ne." Abin da yake gaya min kenan, lokacin da na sa hannu biyu na kankame shi kamar yanda ya yi min umarni. Muka fara tafiya, sai da muka tsaya a Sundu muka yi sayaiya muka ajiye a wata runfa muka wuce zuwa Ruwan Bago. Gidan Mallam Haruna, ni na shiga wurin iyalinshi na shiga wurin uwargidan Hannatu, don Ado ya ce min ita yafi sani, nan sauran matan suka same ni muka yi hira da su, sai da ya gama ya aika a kira ni. 95 A hanya muna dawowa Ado yana bani labari, kai biyan bashi da dadi Humaira, kai da ka biya ka ji dadi shima wanda ka baiwa ya ji dadi. Balle shi Mallam Haruna ma bai dauka zan maida mishi da kudin ba. Nayi maza na ce don me? Ado ya ce mutanen yanzu fa ba wani damuwa da biyan bashi suka yi ba. Na ce, hu'un, ai kuwa dai suna daukarwa kansu jidali. "Kinga iyalin Haruna ko? Ga gidanshi ga ya' yanshi gashi yana noman nan, yana kuma taba kasuwanci. Komai nashi gwanin sha'awa ko? Na ce ni ban sani ba, na dai san kawai bai fika komai ba. In dai ba yawan matan nashi ba ne yake ba ka sha'awa, to, to shi kenan mu bar maganar, na ce eh gara mu bari. Ana cikin haka rannan girki yazo kaina, kafin zuwan ranar kuwa babu abin da Ado bai tanada ba na kayan amfani, tunda ga bokitaye, robobi, kwanuka, kore, ludaya, cokala suna kammale. Ina tashi da safe na kammala ayyukan wurina, nayi duk abin da zan yi na jira Ado ya dawo kamar yanda yayi min umarni, gabana sai faduwa yake yi, ina dai ta faman addu'a. Kar fa ki ce za kije kiyi wahala mai yawa ga buhun shinkafa can na kawo, in kinga ba za su 96 taimake ki ba sai ki juye ta kawai gaba daya, ki juye mata abin hadinta akai in ta nuna za'a ci. Nayi murmushi na ce mishi, to na fita. Ina fike da tsintsiyar zabori a hannuna don share wurin yin girkin, da kuzarina na fita sai dai ina dosar wurin na susuce. Tun daga nesa dai na hango buhun shinkafar da Ado ya kawo a kwance a kasa, ga kwandon tumatur, attaruhu, albasa da tattasai, ga galan din man gyada da ledar maggi da su kori da sauran kayan hadin da ya san ina amfani da su. Ina dosar wurin naji matan gidan suna shewa suna fadin "Lalle yau za'ayi sha'ani shinkafa? Matar so zata yi girki, Ruwaila kuwa sai cewa tayi mutanen birni ne yaushe za su je suna taba dawa? Ai sai mu. Nayi kamar ban ji su ba, na gaishe su suka amsa na wuce naje na kawar dá buhun naja shi na jingine shi, na kama sharan wurin na share shi tas na kwashe tokar da take murhu. Naje na debo itace na kawo wurin, ban ankara ba sai kawai naga gaba daya sun sulale sun watse sun barni ni kadai a wurin ko wanda zan yi wa tambaya in wani abu ya daure min kai babu. Na leka tukwanen da zan yi amfani da su babu wanda aka wanke gaba daya kayan wanke-wanken yana tare a bakin rijiya, randunan da ake tara ruwan 97 girkin ma babu komai a ciki. Don haka na tafi wurin Ruwailah tunda ita ce ta riga kowa karbana a gidan sannan kusancin da ke tsakanina da ita ma yafi yawa. Cikin natsuwa na kalle ta na ce mata babu ruwa a' randunan kuma ina so ki hada min itacen murhun don wutar ta kama sosai. Sai kawai naga ta zuba min ido tana kallona cikin wani yanayi "Dama kin mike kin yi aikinki tunda kema ba taimakon wasu kike yi ba. Al Da zai yiwu kema kice sai an taimake ki ba, in zaman jikin miji ne babu mijin da baya so á zauna mishi sai dai in bai samu ba ya hakura. Don babu wata matar da mijinta ba ya sonta, tunda duk daya muke amfanin da ki ke yi wa mijinki shi nake yiwa nawa mijin, shi ko wace mace ma take yi wa nata kin gane? Na ce mata eh, na juya na tafi, na nufi bakin rijiya tana fadin au, tafiya ki ka yi tun ban gama yi miki bayanin ba? Ban sake sauraronta ba. Na dauki guga na jefa cikin rijiya da nufin debo ruwan da zan yi aikin da shi, sai ga Ado ya shigo wurin, abin da ban ta6a ganin yayi ba tun zuwanmu, tun da yasan wurin zaman mata ne. "Ke me ki ke yi a wurin nan? tambayar da ya soma yi min kenan, ban iya amsawa ba saboda in na 98 ce zan y1 magana zan yi kuka. Ajiye gugar ki tashi a wurin, na ci gaba da jawo gugar, tunda na riga na cikota da ruwa ga nauyi. Ajiyeta kuma yana nufin ta koma cikin rijiyar. Ganin da yayi ban ajiyeta ba ya sanya shi Rarasowa wurin yasa hannu ya karbeta daga gare ni, wannan rijiyar da ba a ganin cikinta ne za ki zo kina jan ruwa a ciki?" Ya dangwarar da gugan a kasa ruwan da na jawoo din ya kife, ya wuce ya fita. Ina tsaye ina tunanin abinda zan yi sai naji wata a cikin matan da şuke dakin Ruwailah tana ce mata wai fa matan so zasu yi girki a gidan nan maza sai zirga-zirga'suke yi. Ta ce, ai zai ga tsiya ai sai dai ya cire rigarshi yayi mata girkin, haba ina amfanin namiji ya susuce ya zama 'MIJIN TACE' kamar Ado ya laface akan wannan yarinyar ya záma sai yanda tayi dashi, wai har yana cewa suna aka tara. To da me tafi wata? Gaba daya suka kwashe da dariya suna fadin to shi ba tashin ya sani ba. Taja wani mummunan tsaki da ke kara baiyanar da tsananin bacin ranta, ai ni da su ne a gidannan zasu ga tsiya, zan ga yanda za'ayi sujr dadin zaman, sai dai in zasu tattara su koma in da suka fito, ko da yake dai can din ma koro su ita Hajjyar tayi. Tana tayin maganganun bata san Ado ya shigo 99 ba, yaran Almajirai ya kirawo ya kirawo guda biyu wadanda dama sanannu ne a gidan Hamza da Bala, ya nuna musu tarin wanke-wanken da.aka tara vace musu su wanke su kuma debi ruwa su cika randuna suka ce mishi to. Daga muryar da yayi ya kira Furera, shi ya fahimtar da Ruwailah mai rantsuwar Ado zai ga tsiyar da zata yi mishi tasan yana wurin nan.da nan tayi tsit. Furera ta fito tana gyara daurin dan kwalinta tana murmushi lafiya yau maigidan yake yawo a wurin da mata suke girki? Ko ba ya koshi ne?" Bai saki fuska ba balle ya rama mata wasan da tri nishi, sai ya ce mata taimakona nake so kiyi ki hadawa Humaira wuta ki kuma tsaya ki kula da girkin ko ba za ki iya ba? Da sauri ta ce, to me zai hana? Ya ce to na gode. Yajuya zai tafi tayi maza ta sake ce mishi in dama ba kana so ta zauna a wurin don ta ga aikin ba ne ai da tayi tafiyarta.ma za'ayi. Ya sake cewa to na gode, ya wuce ya tafi, na tsaya zan taya Furerah aikin da ta unguma da hannu bibiyu zata yi, sai kawai ta kalle ni cikin murmushi ta ce ke tafi ki je wurin mijinki kin ji? Kiran da Ado ya yi wa Furera ya danka mata aikina a hannunta ba karamin abu ba ne wurin 100 Ruwailah, don a zahiri ne kawai suke abokan juna na kut-da-kut, amma a 6oye abokan adawa ne. Don ita Furerah ma ita ce uwar dakin amaryar Ruwaila ban da haka kuma ita din bata yi zaton zai iya yin hakan ba, don ganin ba sasansu daya da Furare ba. Sannan ita Ruwailah ban da zumuncin ita mata wanshi ne na sasa daya akwai kuma zumunci na jini, don haka ta dauka dole dai ita zai nema. Ina tare da Ado a daki da daddare nayi mishi kwalliya da sabuwar rigar baccin da ya zo min da ita daga Zaria, sai kamshi nake yi, yayin da shi kuma yake zaune daga shi sai dogon wandonshi na Track Suit. Yana tashe da laptob din shi Intenet ya shiga yana bincike kan noma irin na zamani, ni kuma ina kwance a gefenshi nayi filo da gefen cinyarshi ina kallon abin da yake yi. Yana kuma kara yi min bayani kan abin da na tambaye shi, sai kawai Furera tayi sallama a bakin kofa, ya amsa ya ce mata shigo mana. Nayi maza na tashi na zauna na jawo dankwali ina daure kaina. Suka gama gaisawa, sauran kayannan ne na kawo, ga shinkafa mudu zai kai bakwai nayi amfani da mudu ashirin da biyar ne ga... ya katse ta, je ki da su Furerah da rana sai ki girkawa yaran wurinki, tayii 101 ta godiya ta tashi ta tafi. Tana fita ya ture laptop din nashi gefe yasa hannu biyu ya jawo ni jikinshi, kin san yau kuwa yau wata uku daidai tun da ki ka yi rashin lafiyar nan." Dan langabe nuna yana yin zolaya na ce mishi bana lissafi, ya dan rage fara'ar shi ya ce to ni ina yi wani lokaci kuma nakan tambayi kaina, to ko dai nayi kuskuren ne. Kamar yadda Goggo ta ce, nayin da na bari aka yi miki wankin cikin? Nayi maza nace mishi baka yi ba ban yi ba? Na ce mishi eh, baka yi ba, lokaci ne kawai bai yi ba, Kankame ni yayi da iyakacin karfinshi yana tambayata, to yaushe ne lokacin? Kin kuwa san haihuwar da aka yi wa Malla Haruna ta shekaranjiya, ita ce ta sha bakwai? Na ce, uhun! To sai me? ya zuba min ido yana kallona, ina sonki Humaira, ko ace dandani-haukaci ki ka yi min ko ace wani abu aka wanke aba ni nasha, ni na gode da hannuma ma in aka bani zan iya kaiwa bakina insha kin ji? Ban tanka mishi ba, kiri-kiri a gidan nan Ruwailah tayi dalilin da aka radawa Ado sunan 'MIJIN-TACE' wai shi din ta ce, ne wai bai da katabus sai yanda aka yi dashi. Ado da nake ganinshi jarumi in na ce jarumi ina 102 nufin akan komai ma shi din jarumin ne. wajen neman halal din shi wajen tsayuwa kan ra'ayinshi a gida ne kuwa ko a waje musamman ace ra'ayin nashi akan gidanshi ne. Tunda nasan kullum nai ce nake bin umarninshi nake kuma barin ra'ayina in koma nashi don mu zauna lafiya amma wai shi ne MIJIN-TACE da zuciyata tayi kunci na tsunduma cikin tunani mai tsanani, saboda bakin cikin kira min jarumin mijina MJIN-TACE. Da tunani ya tsananta gare ni, sai na tunano Babana, na tuna marasa mutuncin unguwarmu har nuna mana gidanmu da dan yatsa suke yi suna fadin wai gidan mijin tace kenan, nace to ko dai shima ba mijin tacen ba ne sharri kawai ta kama ni a dalilin tausayin shi da yafi matukar kamani. A hankali cikin zuciyata na shiga fita da addu'ar ina ma dai ya huce ya daina fushi dani, don wata rana in samu damar zuwa gabanshi don in roke shi gafara kan laifin da nayi mishi? Tunda Furera ta karbe ni hidimar girkin abincin gida sai take ta kokarin sanya ni cikin al'amuranta misali haihuwa ko baki da suka dangance ta zata gaya min ta ce in gayawa maigida in ya bar ni sai muje tare don mu saba da jama'a tunda shi mutum shi ne babban arziki in bai bari ba babu damuwa in ce 103 mata to. Rannan kanwarta da suke ciki daya ta haihu tazo har dakina ta gaya min nace mata wanan kam dani za'aje tayi murna sosai. Ado yana dawowa na bashi labari, ya ce to in lokacin ya matso sai ki tuna min, na ce to. In ka samu sarari sai ka saya min rigar yanmata in bata don mace aka haifa. Ya ce min to, yana fita kuwa sai ga shi yazo min da riga mai kyau na kai mata tayi ta murna. Tun ana jibi suna na tuna mishi ya ce to, ina ta murna nima zan fita unguwa tare da matan gida abinda ban taba yi ba ana gobe sunan ma na tuna mishi bai yi magana ba. Washegarin suna ina gama aikina nayi wanka na zauna nayi shafa na gyara jikina, yayi tsaf sai kamshi nake yi na dako sabbin-under wears dina na sanya tunda su kam ban taba rashinsu ba. Duk rashin kudin Ado ba taba fashin sayen under wears rigunan bacci da man shafawa ba, ko turare. Ina tashe da atanfata dana ciro don daurawa, cikin zuciyata ina tunanin Ado, tunda ya fita da safe bai dawo ba, gashi har rana ta fito, mutan gida kuma duk sunyi shirin tafiya baya nan, zuciyata ta raya min in har aka ce in fito ba dawo ba, tafiyata zan yi tunda ya san da maganar sanda na gaya mishin, kuma ba 104 musu yayi ba. Ina cikin wannan tunanin sa gashi ya shigo rike da leda mai dauke da robar yourgout da kuma fura a ciki. Ungo dama in na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi, ko za kayi hakuri ne kawu duk sun riga sun gama shiri, ni kadai suke jira ka kuma san matan gidannan kara ce dasu, in hidimar mutum daya ta tashi sai kaga duk an dunguma an rufa mishi baya. Ya ce, eh ai kirki ne da su, na ce eh, sai kawai naji ya ce min, amma ba da wadannan sabbin under wears din za ki ba ko? Wadannan ai kin san don kaina na saye su me yasa za ki bude su bananan'? Na daga ido na kalle shi ya bata rai sosai ji kuma irin kamshin da. kike yi a haka ki ke shirin tafiya gidan sunan? Wannan ma ai rainin hankali ne cikin natsuwa da sanyin murya na ce kayi hakuri ka barni in tafi na yau, tunda nasa mata rai, in yaso na gobe ka hana ni." Ya ce, a haka a kamshin da kike yi? Ai alhaki ma sai yayi miki yawa, gara kawai ki sake wankan, na ce to. Ina cewa to din ya matso jikina, to zaki yi wanka mara dalili ne. Humaira bayan kin yi shafan nan mai kyau ai bari ki ga hikimar da za'ayi ai gara kawai a yi mai dalili sai kiyi kawai gaba daya kan nan ma kowa ya gama shirinshi maimakon kije kiyi ta jiransu. 105 Babu halin in ce zan yi musu dashi kan bukatar tashi sai ya ce kan tafiyar zan sabawa umarnin da yayi min, saboda haka nayi hanzarin sallama mishi kaina ban tsaya ja mishi rai 'ba, don nima yayi saurin sallamata. Sai dai abin takaicin shi ne, ina shiga hannun Ado na mance da komai, ya sanya ni ciki wani hali da ya kidimar dani, ya hanani tunani balle jin wani motsi. Ban sake tunawa da komai ba balle in tuna a cikin sauri nake don kar in yarda in biye mishi, sai bayan da na ganshi kwance a gefena kokarin ne na tuna abin da ke gabana. Zunbur nayi na mike cikin sauri na mufi ban daki nayi wanka da ruwan sanyi aazo ina shiri hankalina a tashe saboda shirun da gidan yayi min yayi yawa da sauri. Na sanya kayana ba tare da na tsaya shafa ba na' fita naje don in gani ko sun gaman suna jiraa nawwa babu kowa a gidan gaba daya sasan babu kowa sai yar gidan Fureran budurwa Hasiya. Na ce ke Hasiya tafiya suka yi basu gaya min ba? Ta ce sun gaya miki baki ji ba ne? Na ce sun gaya min wa ya gaya min? Ta ce ni ta aika sau biyu ina yi miki magana ba ki ba. Na dawo daki raina a bace gululun bakin ciki sai 1O6 yawo yake yi tsakanin wuyana da makogorona, na dawo daki har lokacin Ado yana nan a yanda na bar shi barci ma yake shirin yi bakin ciki da takaicinshi suka kama ni har ban san lokacin da na soma kuka ba. Cikin sauri ya bude ido yana tambayata menene? Ban kula shi ba, balle in tsaya yi mishi magana ba ki da lafiya ne? Ban kula shi ba, menene ya same ki? Na ki yin magana har ya gaji ya dawo kan hanya sunyi gajin hakuri ne. Haka suka tafi suka bar ki? Ban amsa ba yayi maza ya mike bari in yi wanka in zo in kai ki ke da ki ke da babur ma menene abin 6acin rai a ciki? Nayi shiri Ado ma ya shirya muka fita ya burga mashin na hau bayan shi muka kama hanya a yanda duk suke fada kauyen Tukunya kusa kwarai take da Dabai. Muna tafiya naga bamu je da wuri yanda nayi zato ba, na ce mishi har yanzu ba mu zo Tukunyar ba? Yayi maza ya ce min Tukunya dama ki ka ce zamu? Nayi maza na ce, to da ina ka ji na ce? Ya ce Randa na ce, a'a ban da Tukunya akwai wani kauyen ma Randa ne a nan kusa? Ya ce min eh, na ce to ai Tukunya na ce maka ya ce, to ai Tukunya na ce maka ya ce to ai babu damuwa bari mu gaida wadannan sai muje Tukunyar 107 na ce to. Ya tsaida mashin din shi gaban wani gida mai tsananin tsabta ga ko'ina an dabe shi an kuma share shi gwanin sha'awa. Wani farin Dattijo mai wadatar farin gashi a fuskarshi yana zaune kan farin buzunshi a gindin wata katuwar bishiya mai yawan gaske. Yana rike da carbinshi a hannunshi yana ja, cikin natsuwa Ado ya kalle ni ya ce min, "Gidan Kawo' kenan wannan da ki ke hange shi ne Baba Sambo. Sanda mahaifina yake raye bai da wani Aminin da ya fi shi, kin kuma san an ce mu sadar da zumuncin iyayenmu ko bayan ba sa raye ko? Nayi maza na ce eh, haka ne. Muka karasa gaban dattijon nan cikin yanayi na giramawa yana gane Ado ya gyara zamanshi cikin fara'a da murmushi, ya amsa sallamar da Adon yayi mishi, ya kuma shiga yi mana sannu da zuwa, Ado yana amsawa. Can kusa dashi yaje ya tsuguna yayin da ni kuma na tsuguna daga baya, amma yana hangena tafin hannunshi ya dora akan Ado tanfar wani dan yaro a hakan ya ke yi mnishi magana, da alamar dai akwai shakuwa da kulawa a tsakaninsu. Wannan ita ce iyalintaka? Ya dago ido yana kallona cikin nuna alamar jin dadi, sannu kin ji 108 yarinya, sannu Aishatu, sannu kin ji sannunku Ubangiji yayi muku albarka, ya kuma jikan Mallamn Sulaimanu." Ado yayi maza ya ce, "Amin Baba." Ya ce, "Kar ayi wasa da yi mishi addu'a, amfanin barin da a duniya kenan, ka kuma san kai kadai ya bari." Ado ya ce, haka ne Baba. Muka dan yi hira, Ado ya ciro kudi ya bashi, ban san nawa ne ba, yayi tasa mishi albarka har nima yazo ya burga mashin din shi muka hau muka tafi. Wata hanya ya biyo da ni da bangane ba, wasu gine-gine nake gani da ban taba ganinsu ba, nan kuma ina ne? nayi mishi tambayar cikin natsuwa ya ce min "Dabai mana Humaira, ban biyo da ke ta inda ki ka saba bi ba ne." Tuni na shagala ina kallon gidaje da layuka har da su kwalta a shimfide cikin unguwanni, ga rijiyoyin burtsatse a ko ina, na ce kai Kawu, Dabai din nan ma fa ba wani kauye ba ne, ai ban san haka take ba sai yau. Dubi gidaje har da tunkunan ruwansu, ga titina ga fanfunan burtsatse birjik, ga lantarki har mutane da yawa sun sanya a gidajensu, mas'alar dai kawai ba ku da babbar kasuwa. Wani irin lallausan murmushi Ado ya saki cikin natsuwa naji ya ce min, sannu. A hankali dai in nayi 109 sa'a Dabai zata yi miki halin nata ta dabaibaye min ke, ta maida ke 'yar gida har ki mance garinku. Kin ga shi kenan sai muyi zamanmu mun huta da kowa sai in kuta jin ana cewa an yi mafarkin anje gida an ga an canza kofar gidan ko anje gida anga Sa'adatu balle kuma aje ana mafarkin anje gida Baba yayi kora da sanda. Tsuke fuska nayi na ce, ai ni ba zan taba mancewa da garinmu ba, kuma ma ai ta nan wurin ne in da ba kauyen ba ne ta can wurinku ku kauye nel? kan mu karasa gida muka yi fada da Ado, don haka nan da na ganshi ya kafe mashin din a kofar gida na ce ba zan sauko daga kai ba sai ya juya ya maida ni Tukunya kamar yanda yayi alkawarin kai ni. Ya soma rarrashi yaga alamar ba zan yarda ba, sai kawai naji ya ce min, kine dai so ne kawai ki nuna wa mutanen da suke zaune gindin bishiyoyin can cewar eh da gaske ne kin fi karfina. Kin ga sai suma su yarda da magánar da matan cikin gida suke yadawa cewar ni din MIJIN-TACE ne, ban sani ba ko Ado ya gane irin dukan da wannan kalmar ke yi wa zuciyata ne in an fade ta yasa ya gaya min hakan, don a firgice na sauko daga kan mashin din na shige cikin gida, naje na tsaye bakin kofa ina jiran yazo ya bude min in shiga. Sai dai a gidan ban yarda kun zauna lafiya ba, 110 saboda na riga na gaji da yanda yake tsattsare ni yana kokarin hana ni mu'amallah da kowa da kowa, har da mutanen da nake tare dasu, wadanda matan yan uwanshi ne. Muna cikin wannan rikicin, Ado ya samu aikin koyarwa a Makarantar Secondaryiyanmata ta DANJA', shi kenan sai murnan samun aiki yasa muka shirya. A farkon samun aikin murna nayi ba kadan ba, saboda ni da shi addu'a sosai muka yi akan aikin, saboda irin bayanin da ya rinka yi min cewar, aikin koyarwar shi ne aikin da yafi so a wannan lokacin, saboda irin alherin da ke cikinshi. Za ka koyar da yara mutanen da suke sune za su girma, su zama al'uma ta gama shi a wurinshi babu wani aiki da yafi koyarwa dadi, da kuma muhimmanci aikin ne mai lokaci ga kuma. lokuta daban-daban na hutu wanda zaka iya aiwatar da wasu l'amuran naka da basu shafi Makaranta ba a lokacin. Koda dai a wannan lokacin da muke ciki, ba wani muhimmanci hukuma da wasu Jama'ar gari suke baiwa Malami ba, shi a wurinshi darajar Malami ba sai wani ya ce gata.ba, tunda Ubangiji da kansa ya girmama shi. Irin wadannan kalaman nashi ne suka kara cusa min son aikin nashi, amma yana farawa ba a dauki 111 wani lokaci mai tsawo ba na gane ba sakandaren 'yanmata ba ne ta kamata a tura min mijin mawa ba. Don ba a je ko ina ba na soma gani wasikun yanmata da hotunansu a cikin Jakarshi ga waya akai- akai, ga text na kalamai masu dadi irin ma wadanda ban taba jin su ba. A farkon al'aarin yana rarrashina ya gaya min kalamai masu dadi da yake rage min 6acin raina, amma daga baya sai kawai ya daku wai shi ba zai dauwama kan rarashi da ban baki kan matsala guda daya ba. Don haka hanya mafi sauki ta neman zaman alfiya kawai in daina yi mishi bincike in daina taba mishi jakarshi ta zuwa aiki da kuna wayarshi in ban taba su ba ai ba zan ga abinda ke ciki ba. Kan ka ce meye wannan kuma sai ya fito da wata ka'ida ta cewar, wai shi din tafiya tana yi mishi yawa, kullum sai yaje Danja yayi aiki ya dawo Dabai. Don haka ba zai juri hakan ba, wahala tana yi mishi yawa, maimakon ace kullum yana zirga-zirga kan hanya da safe da yamma zai maida tafiyar tashi ta zaa ranar Litinin da safe. Ba zai dawo ranar ba sai ya kwana ya bada darussanshi na ranar kala ta in an tashi sai ya dawo ya kwana a gida, sai washegari aba ya koma da 112 safe ya kwana ranar ya wayi gari a can Alhamis in ba shi da wani darasi na ranar Juma'a to ranar zai dawo. Ba zai sake komawa ba sai ranar Litinin in kuma yana da shi Juma'a to sai in yi hakuri sai Juma'ar zai dawo. A farkon bayanin nashi banga wani abin damuwa a ciki ba don yayi min bayani sosai kan wahalar zirga-zirga a hanya amma yana fara aiwatar da abin a haka mutanen gida suka gane shi kenan sai aka soma kace-nace. Ya samu wata a can kenan ya ajiye, nan da nan hirar gidan ta koma hirar mazan da ke ajiye mata a waje, wato matan banza. Cabdi! Ai gara mana irin namu mazan da ke shigo mana da abokan zamanmu cikin gida suci daga abinda muke ci, shi din kuma gashi nan a tsakaninmu ya dai ishemu muna kuma kallonshi. Amma matan banza hidimar da ake yi musu ai ba irin ta nmatar gida ba ce, ga kuma ciwace-ciwacen nan na zamani." A wannan lokacin in na ce bana cikin tashin hankali to nayi wa kaina karya, gashi dai a wannan lokacin nayi matukar wadatuwa da abubuwan rayuwa, komai da Ado yasan zan bukata ko zai yi min amfani kawo min yake yi. Albashinshi na farko ma da aka fara bashi saboda 113 anyi mishi biyan na wata uku ne gaba daya kamar yanda all'adar aikin Gwammati take, kananan atamfofi masu saukin kudi masu kyau turmi goma ya saya min. Ya bayar duka aka dinke min, dinki kuma mai kyau ga takalma da gyalulluka da under wears, a wannan lokacin kuma tuni ya canza min tsarin abincina, a kowane lokaci ban rabuwa da madarar fulani da shi yasan inda yake zuwa ya samo ta. Bana rabuwa da naman kaji, bana rabuwa da kayayyakin itace dangin kankana, gwanda, inabi, lemo, ayaba, in zai kawo kumá masu kyau zai kawo min. gashi kua ya tsare mnin girkin gidan. Kullum ya zagayo kaina ko baya nan Furerah zata yi don zai sa a kawo mata kudin cefanen ya ce tasa a sayo wanda ta mafi son hakan. Jikina yayi matukar yin kyau saboda yana samun nau'o'in abincin da ya dace ya samu, amma na kasa yin kiba in maida jikina ya zama kamar asalin yanda nake kafin zuwan mu. Sai ma kara ramewa nake yi saboda kullum a cikin fargaba nake. Ni kuma gashi duk da wadatar da Ado ya samu ban koyi adana ko kwabo a dakina ba, hamsin-hamsin din da su. Baba suke bani yana ganin sun taru zai sa hannu ya kwashe in ma bai diba ba in dai ana zaune kalau ni da kaina ma zan ce mishi ga 114 Su. Sai a lokacin da raina ya soma baci ne zan rinka ganin ina ma adana abina nake yi da nayi amfani dasu na tafi gidanmu. Rannan abin ya ishe ni, bakin cikin Ado yana nema ya maidani wata iri Alhamis ya zo bai dawo ba na zuba ido ban gan shi ba cikin zuciyata na ce to watakila sai Juma'a kenan. Yayi sammakon dawowa don wani lokaci yakan yi hakan sai kawai naga Bala da sassafe ya kawo min cefane wai a gaya min sai gobe zai dawo ya tsaya daurin auren Jalo. A zuciyata na ce tafdijam! Wato ni babu abin da nasan darajarshi irin ciki, don haka cefane na gashi nan an kawo min babu fashi shi sai sanda yaga dama zai taho. A cikin gida kuwa rannan maganar da su Ruwailah suka wuni suna yi kenan, amma akan wai ban da ni ake yin hirar ba tunda ni da 'yan dakinta ma ba wata doguwar magana ke hada mu ba. Don ko nayi musu a lalace suke amsa min, ko a yanzu da rashin Ado ke sani zaman cikin gidan wani lokaci da sauran mutanen gidan muke hira, amma yan dakinta ta hana su kula ni. 'Ko da yake dai nima ko da baya nan din na stare dokarshi ta shiga dakin mutane, bana shiga dakin 115 kowa. Ina jin ta a gindin bishiya tana fadin au, to shi namiji don ka tsare shi ka hana shi yin aure ai ba wata birgewa ba ce. In har baka hana shi ganin na banza ya ce yana So ba, ta tsirtar da yawu nuna alamar kyaa, ta ce ni a yanda nake da kyaman nan ai ba zan 1ya zama da manemin mata ba. To me zan yi da shi? Ai komai zai bani gara ya bar shi ya tsare min mutuncin kanshi kawai yafi min, ni nayi sana'ata in nemi abin da zan rufawa kana asiri dashi. Sannan abin tsiyar shi ne, sma kara kullewa a can tana karakwace maka shi. In a farko kana ganinshi şau uku a sat sai a koma biyu sai a koma daya wani satin ma sai ka ji shiru. Ai gara a hada mu mu hudu a gida kishiya dai kowacce tazo Ubangiji zai bani hikima da basirar zama da ita, in ta kunso wani abin tsiyarta ma a wayi gari ya koma mata kanta ko ya kare tsakaninsu can musu ita da wanda ya kawo ta, aifa kam- aifa kam abin da yan amshin nata suke fadi kenan. Rannan da daddare Inna ce na runtsa ta karya na yi wa kaina. Washegari tun safe Ado ya dawo ya yi sa'a kuma a wurina yazo ya same ni ban riga na rufe na tati wurin hira ba. Karbar da nayi mishi bata wani ba shi sha'awa 116 ba baki da lafiya ne? na kalle shi da gefen ido na tambaye shi me ka gani? Yanayin ki ne na ganshi wani iri. Na ce ta dauro ne ka ganshi a haka ka kuma san daurowa take yi a daure AIkali. Ya ce haka ne, to ga leda nan nazo da shi juye abin da ke ciki don ba zai juri zafi ba. Na mike kamar zan juye abin da ke ledar na wuce na tafi tsakar gida abin ban sake dawowa dakin ba. A tsakar gidan kuma sai tambayeta ake yi ana fara'a ashe maigidan ya dawo? In ce eh sai ace kai madallah, hannunshi da zuwa. Ina nan wurin a. zaune sai ga Ado ya shigo suka gaisa da matan duka ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min zo mana Hunmaira, na ce to. Na tashi na bi bayan shi don komai yaya ba zan iya wulakanta mmijina a gaban wani ko wasu ba. Muna shiga ya kalle ni ya daga ido ya kalli agogo sannan ya sake kallona ya ce min, kin ga wannan abinda ki ka yi min na farko kin yi min kuma na karshe kin gane? In dawo daga wani wuri baki karbe ni ba baki yi mi abida ya dace kiyi min ba. Ki tafi ki bar ni awa guda minti sittin ina zaman Jiranki, na yau din ya zama na karshe kar ki sake. Na ce Inna sake din me zai faru? Ko me zaka yi? Ya ce to ki sake mana ba ga ki ba gani? Na juya 117 da nufin sake fita, yayi maza ya kamo ni ya murde min hannu, nayi karfi hali ban yi irin ihun da nakan yi ba alamar na riga na saba da wannan wahalar. Kar ki neme ai da fitina Humaira, bana so. Yana ta nanata kalmar alamar bai son fadan da ya gane ina so muyi. A zuciyata na ce ya san ba shi da gaskiya. In wani abu nayi miki a laifi ki gaya min bai zama min komai ba in ba ki hakuri ke kin san na saba hakan bani da wannan girman kan me nayi miki? Kullum naje aiki na dawo sai kin yi min sanadin bacin rai? Saboda kawai bana gida kina shiga cikin matan da suke cusa miki ra'ayin da ba naki ba suna koya miki abinda bai dace ba, wanda ban taba zaton zaki yi haka ba, ke da ki ka girma a gida irin naku ki ka yi karatun boko da na addini har yanzu ma kina yi. Amma wai wadannan matan ne suke koya miki abinda za ki yi wa mijinki. Kalamanshi suka sanya ni bude baki na ce mishi ni babu wata wacce take koya min wani abu, halayenka da dabi'unka ne kawai suka gundure ni. Ya dan saki fuskarshi kadan alamar bacin ran nashi ya dan ragu. Yana kallona cikin natsuwa ya ce wadanne a Ciki? Ko duka? Ban amsa ba, sai ya ce to tunda ma halayena ne matsalar ai duk ta kwana gidan sauki, 118 tunda ba cusa miki wani ra'ayi a kaina ba Magana kawai zaki yi ki ce min Ado ko Kawun da ki ke kirana halinka kaza-kaza da dabi'arka iri kaza da iri kaza basu min ba, ka canza sai in ce miki to. In kuma canzan tunda ke ma sheda ce ni mutum ne mai saurin canzawa daga wani matsayi in koma wani ko daga wani hali zuwa wani duk ina iyawa, don haka mu bar wannan maganar yanZzu anjima sai muyi ta. Yanzu zo kiyi min tausa in dan ji dadi in wastsake gajiyata ta wannan satin kin kuma san wannan karon kwana hudu nayi bana gida, maimakon daya ko biyu da nakan yi. Ko kallonshi ban yi ba kaina a sunkuye na ce mishi can inda ka baro ba. ayi maka tausar ba ne? maganar da nayin tayi matukar dukan Ado watakila bai taba zaton ina yi mishi irin wannan zargin ba, ni ayi min tausa a inda na baro Humairah me ki ke nufi? Kina yi min mummurian zato ne? na ce kana yi wa kanka, dai in ba haka ba me yake zaunar da kai? Me yake tsareka daga dawowa gidan ka? Rikici sosai muka yi saboda ranshi ya kai matuka wajen 6aci da zargin da nayi mishin. Amma duk da haka yayi kokarin hadiye fushin shi ya zaunar da ni don yayi min bayani. 119 Tafiya nake yi Litanin in dawo T'alata in koma Laraba in dawo Alhamis ko Jumaa in kin yi lissafi da kyau za ki ga sau biyu ne kawai ko uku ba na kwana a gida a sati. A haka kuma kullum kina ganina ko kuma kiyi fashin ganina sau daya to menene? Na kuma gaya miki a gidan abokin aikina iro nake kwana wannan satin kuma jalo ya kara aure na tsaya tunda mune abokan ango. Na ce gaskiya ban yarda ba sai dai cikin biyu ka zabi daya ko dai ni in bika mu koma can ko kuma kullum kaje ka dawo cikin natsuwa ya ce min ba zai yiwu ba. Humaira kina karatu kina aji shi da ba za ki bar karatunki ba, sannan a can din ma ai ba ni da in da zan ajiye ki sannan ni in yi ta wahala ina ta zirga- zirga akan hanya ba za ki tausaya min ba, saboda wva nake aikin nan ne? nayi maza na ce mishi idon ni ne ka daina. Gaba daya ban karbi rarrashin da Ado yayi min ba, ban kuma yarda mun shirya ba, naja na tsaya kan cewar sai lalle wannan karon nima ya bar ra'ayinshi ya dawo nawa, tunda ni nayi mishi hakan wane dubu wane dari bafulatani ya ce wai cabiyar din cegiya? A haka yayi kwana biyunshi ya koma ban yarda ya taba ni ba. 120 Ranar da ya tafi Litinin na zuba idon ganin dawowarshi da yamma don in ga ya bar nashi ra'ayin ya bi nawa, ko bai bi ba? Bai dawo ba talatan ma da ya saba dawowa da yamman bai dawo ba, bai kuma aiko da cefanen da ya saba kawowa a ranar ba. Kamar yanda ya saba yi in zai yi fashin zuwa sai ya tashi wani ya ba shi duk abinda ya saba zuwa min dashi ya kawo mnin, ya kuma yi min bayani. To wannan karon shiru ban ga Ado ba. Sai ranar Alhamis da yamma, don haka ni kuma ina zaune a dakin ina jin shigowarshi, amma ban daga ido na. kalle shi ba, balle in yi mishi wata magana. Tun bayan sallamarshi da na amsa wacce itama don nasan amsatan wajibi ne yasa' nayi hakan. Ban sake daga ido na kalle shi ba, balle in ce mishi kaci kanka, kusan minti goma yana zaune bai ce min ba ban ce mishi ba, sai naga ya mike ya fita kamar zai je ya dawo ne. Nima na mike nayi abubuwan da zan yi, ban shirya ba shi abincina ba don haka ban ma shiga kicin don yin girki ba. Shiru ban sake ganin Ado ba har wajen karfe takwas na dare, sai kawai ga Bala da manya-manyan ledoji guda uku rike a hannayenshi, wai gashi ki duba abinda babu ki fada aje a kar6o. Na leka cikin ledojin, daya kayan shafe-shafena 121 ne sai su Sheltoze da Room freshner da su izal da Detol, kayayyakin amfani dai da suka dangane wannan, daya ledar ta kayan Tea ne madara Nido babban gongoni da Bounvita shima babba sai kwalin- sugar guda biyu. Dayar kuwa nama ne da kifi, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi shi fa? Wai don in san in da ya tsaya yaje na raka shi yaje ya duba aikin lambunshi daga can sai ya ce in raka shi tasha ya shiga mota ya tafi Danja. Kan uba, abin da nasan na fadi kenan, kafin nayi maza na rufe bakina, saboda tsayuwar Bala a dakin. Za'a karbo miki wani abu ne? na ce mishi a'a, jeka kawai. Yana fita na ce me zan yi in ba kuka ba? Kwana nayi idona biyu ban runtsa ba, nayi kuka har na gaji, nayi bakin ciki irin wanda ba zai kwatantu ba, wunin rannan ban fita ko 'ina ba, ina kwance a dakina ko su Goggo ban je na gaishe su ba sai da suka ga shiru ne suka biyo suka gaishe ni a cewar bani da lafiya. Sauran matan gidan ma suka yi ta zuwa, amma don fitina wai sai da Ruwaila ta gane lafiyata kalau, ina jin ta tana gayawa wata da suka zo duba ni tare cewar, kalau dinta, bakin ciki ne kawai ya ishe ta. To miji yayi mata shigo-shigo babu zurfi ya dodana mata romo a baki ta dauka a haka za su 122 dauwama yanzu kuma bata yi aune ba sai taga ba shi da lokacinta. Jiya fa yana shigowa ko gaida su Baba bai tsaya yayi ba ya juya ya tafi abinshi, yana Can wurin wancan din, ni naji kamar ana cewa ma wai ciki ne da ita sai ta haife za'a daura auren. Ni kam a wannan lokacin na sakankance na yarda na kuma mika wuya cewar bakin cikin Ado ne zai kashe ni. A wannan lokacin Goggo Ayalle da Babba Tanimu sun yi matukar kula da ni, don su a nasu ganin rashin lafiya nake yi, don ita na baiwa ma cefanen da Adon ya aiko dashi. Hajiya kuma tazo tayi min shara da duk wani abinda ya kama na tsabtace min wurina, bana cin komai sai in Goggo ta matsa min ne nake yarda in sha ruwan tea ko farau-farau din da kullum Baba Tanimu yake aiko min dashi. Na rarne nayi matukar fita hayyacina, in ban da kukan bakin ciki babu abin da nake yi, kewar iyayena da 'yan uwana da dangina, musamman Babana tayi matukar mamayar zuciyata. Babu abin da nake nadamar shi irin sanya Babana bacin ran da nayi akan Ado, gashi tun abin bai je ko'ina ba ko shekara cif ba a cika ba har alhakin shi ya kama ni, na soma ganin sakamalkon 123 abin da nayi 'kwai da dutse. Kullum bayanin da mai babban allo yake yi min kenan ya ce min basa karo, ya kan yi min irin wannan bayanin ne kuwa a duk lokacin da na soma gaya mishi abinda Baban nawa yake yi mana mu da Innarmu. Ashe ma Baban nawa mutumin kirki ne mai kuma adalci ban taba sanin hakan ba kuma sąi a yanzu, a wannan lokacin da nake dandanar bakin cikin Ado. Ran Litinin da sassafe ya zo gida babu wanda yayi zaton ganinshi a lokacin tunda ranar nema ranar da ya kamata ace ya tafi. Ni kadai ce a dakin ssai ko Hasiyan da ke kai-kawon gyara min wuri. Ina kwance a kan katifar ya wurgar da abin da ke hannunshi yazo ya daga ni ya zaunar da ni na ki zaman na koma na kwanta, kina hauka ne Humairah? Kina hauka ne da ki ka maida kanki haka? Yanzu in ban da nayi wa Bala waya ya ce min ba ki da lafiya sai kiyi ta zama a haka? Za ki kashe kanki ne? ban tanka mishi ba, tun zuwanshi da safe har Azahar ban bude baki nayi mishi magana ba. Na riga na kudurawa zuciyata in dai zuwan da ya yi ban yi mishi magana ba ne yasa shi yi min hukuncin da yayi min, to na daina yi mishi magana 124 VAvi min abin da yafi wannan tsanani. Har aka yi Sallar La'asar bai ji na bude bakina na ce wa weai wani abuba, balle yasa ran zan yi mishi na kuma ki yarda da cewar da yayi in tashi muje asibiti, Ina kallonshi ya jawo wayarshi, kalaman shi suka fahintar da ni da Innata yake yin maganar gaskiyar abinda ya faru tsakanina dashi, ya gaya mata abin da nayi mishi da wanda shima yayi bai rage komai ba. Haka nan bai kuma fara ba, da kuma halin da ake ciki a yanzu duik sai de ya gaya ata. Ban ji ita abin da take gaya mishi ba amma na ji shi yana amsa mata da to Inna sai kuma neji shi ya ce mata to gata, nayi kamar in ki kar6ar wayar sai kuma naga to in ranta ya baci fa? Alhalin bacin ran Babana shi kadai shi ne ya yi min wannan sanadin, to in ya hada har da nata fa? Ya ya zan yi? Nasa hannu na karbi wayar ina jin ta soma yi min magana naji muryarta. Sai kawai na soma kuka, kuka kuma mai tsanani ina jin itama ta gane ina cikin bacin rai mai sanani ne yasa ta talkaita maganar tata da cewar tunde dai ya zabe ni ya kawo maganar gabana ina ganin ya kamata ta kare don girmarma ni yayi. 125 Ga manya nan a gidan naku bai kai maganar gabansu ba saboda yana ganin in na gaya miki zaki ii, in kuma kin ga ba za kiyi min wannan alfarmar ba duk matar da ki ka gani a dakinta tana zaune, to hakuri talke yi. Ba kuma zai yiwu ace kina zaune da miji amma ba za ki girmama shi ba, in yaja sai kema ki ja saboda lina ganin kin isa. Wannan ba tsarin aure ba ne na Shari' a ya zama auren 'yan iska. In kuma kin ga irin shi ki ka fi sha'awa sai kiyi, sannan zan yi miki kashedin ki daina fada da shi a gaban yan uwanshi. Ki rike sirrin da ke tsakaninki da mijinki, ki gamsu da alherinshi tun ba ki kure hakurinshi ba. Inda za ki daina jin jita-jita kuma kina amfani da zato to da zai fiye miki amfani, in kin yarda da abinda na gaya miki ki bashi hakuri, na ce mata to. Tana kashe wayar na sunkuyar da kaina kasa na ce mishi, kayi hakuri, bai taba tsammanin abin da zan gaya mishi kenan ba, wata Kila jira yake yi mu gama maganar shi ya bani hakurin. Dadi ne yayi matukar kama shi yesan in na ce ta sani ba shi hakurin, dawowa kan katifar ds nake kwancem yayi ya dago ni ya kwantar a jikinshi inna tana sona Humaira, in ma dai ke ce ki ka fahimce ni 126 irin fahimtar da tayi min? Sau dava nake fadin gaskiyata ta yarda da ita, amma ke baki yarda da ni ba, yaya za'ace miki na ajiye wata mata a wani wuri ki yarda? Sannan in ban da Inna tayi miki magana ta saki ki bani hakuri ke kina shirin muyi tashin hankali ne. Ni kuma ba ki sani ba tausayinki nake ji na rabo ki da iyayenki da danginki na kawo ki cikin nawa na ajiye ki ni da ki ke ganina ban cika son muna samun matsala da ke ba. Iyaka dai ba zan yarda da wasu halayen da ki ke fito min da su ba ne don ko da ki ke jin ana ce min 'MIJIN TACE' in ma dashi ki ke lura to na rantse miki ni ba shi ba ne. Sannan masu kawo miki bayanin abinda nake yin dama ko menene? Da yake zama sanadin fada a tsakanina da ke in na nemi aure a danginsu fa za su jagoranci a bani in kuma kina ganin karya ne to. Na daure fuska na ce to a baka mana sai me? Rannan haka muka kwana da Ado maganganu masu kwantar min da hankali yake tayi min na yanda zamu fahimci juna mu zauna lafiya, ban tanka mishi ba muka yi kwanciyarmnu yana kankame dani a jikinshi bai kuma nemi komai ba daga gare ni. 127 Washegari tun daga fitowarshi Masallaci Sallar Asuba ya yi shiri ya ce min zai tafi Danja, na ceto sai ya dawo, nayi mishi addu'ar da ta dace in yi mishi, ya kama hanya ya tafi. Wunin rannan ma ban fito ba ina dakina, ina kwance kan katifata tunanin al'amura kawai nake yi a zuciyata. Hasiya tazo tayi min duk abinda ya kamata tayi min ta tafi ta bar ni ni kadai. Tuni na kudurawa zuciyata bin hanyar da zan zauna lafiya da mijina, in daina daukan zancen wani ko bin shawararshi tunda na gane hakan ba zai amfane ni da komai ba. Sai dai yayi min sanadin wahala da 6acin rai mai tsanani, babu kuma wanda zai agaza in da wani abu sai dai ma in an gane halin da nake ciki ayi ta zundena ana yi min dariya. Don haka na yanke wa kaina shawarar ajiye makaman fada in bi hanyar lallama da rarrashi da bin umarninshi akan komai in dai baya sabawa Shari'a ba ne shima kuma nasan da wuya yasa na saba shari'ar. Don kuwa mai kokari ne akan kiyaye dokoki tunda na gane abin da ake yi wa wasu mazan a kwashe kalau shi kam ba zai lamunta ba dama kuma Hausawa suna da karin maganar da suke 128 cewa, wai in da wani yayi rawa aka yi mishi kari, in wani yayi to dukan tsiya yake sha. Nayi sallar La'asar nasa ruwa nayi wanka irin wanda na dade ban yi ba, don kuwa rabona da in yi wanka har na manta, tun da bakin cikin Ado ya kwantar da ni. Ni da kaina tsamin jikina nake ji. Na fito nayi alwala don yin sallar magarib da Isha'i, sannan na zauna nayi shafa mai kyau na gyara jikina sosai tun daga gashin kaina har farcena babu abin da ban gyara ba. Sanyi ya sauka min har cikin zuciyata saboda ni' imar tsabta da na sau, kai kazanta dai musiba ce, ni da kaina na gayawa kaina hakan. Nan da nan na mike na canza zanin gadon da ke shinfide kan katifar na shimfida, wankakke, gogagge, na fesa freshner mai sanyin kamshi na kuma kunna turaren tsinke a bayan gida na jawo dan kofan tsaki gina na koma dakina na zauna ina jiran lokacin Sallar magrib tayi. Cikin zuciyata dai bani da wata matsala illa jiran in gabatar da sallolina insha tea in kwanta tunda nasan ni da ganin Ado watakila sai gobe da yamma ko kuma ma ranar Allhamis. Na idar da Sallar Isha'i na kulle kofata na dawo ina hada tean da zan sha kafin in kwanta tunda ban 129 yi girki ba ban kuma aika an karbo min abincin gida ba sai naji ana taba kofa nayi maza naje na bude don ganin ko waye? Sai naga Ado na kauce daga kofar ya shiga nayi mishi sannu da zuwa ya amsa da har kin rufe kofar ne? na ce mishi eh, yana cire kayan jikinshi alamar wanka yake shirin yi yana tabayata me ki kaa girka ne? Cikin natsuwa na ce mishi ban yi giki ba saboda ban san zaka dawo ba, in ba zan dawo ba ba za ki girka abin da za ki ci ba? Kin ga irin ramar da ki ka yi kuwa? Ya maida rigarshi ya fita. Tunda Ado ya dawo ranar Talata da yamma bai sake tafiya Danja ba yana gida bai kuma fita ko'ina in ba sallama aka yi dashi ba. Zuwa nayi na gayawa Princepla da yake akwai fahinta a tsakanin na ce mishi akwai matsala a gidana, ya ce to in je ya bani wannan satin sai na roki wani Malami ya taimaka min da darussan nawa don kar yara su cutu. Ya dago idanuwanshi ya kalle ni doon a kwance yake sanda yake maganar. Sai dai kuma gashi na dawon tun ba aje ko'ina ba har na gundure ki kin gaji dani ban tanka mishi ba don nasan me yake nufi. 130 Tun daga wannan lokacin mu'amallar Inna da Ado tayi matukar karuwa, na kuwa gane hakan ne daga yawan kiranta da nake ganin yanayi, ba zai yiwu sai rikici ya taso min a gida in rinka kiranta tana kwantar min da fitinar ba. Abinda ya gaya min kenan rannan da na ji su suna magana ban kula shi ba, na dai san kawai yana ganin girmanta da darajarta yana kuma girmamata da iyakacin gaskiyar shi. A wannan lokacin ne na gane gaba daya mataan gidan bakin su daya ne haduwa suke yi suyi maganganinsu kan abinda ya shafe ni ni da Ado. Illa iyaka kawai ita Furerah ta ki yarda ta daina karbar girkina tana yi saboda tana matukar amfana dashi. A zahiri kuma tana nuna ita babu ruwanta ni tata ce saboda alherin da nake yawan yi wa ya'yanta. Don haka sai na hada su gaba daya nayi musu jumiah guda daya dukansu ina girmama su bana kuma jin zafinsu tunda na gane damuwarsu bata wuce ta kulawar da mijina yake da ni ba. Ado bai daina zuwa Danja ya kwana ba na kuma cire raina a kan hakan randa yake gida ma mafi yawancin lokaci yakan raba dare ne biyu yana waje bai dawo ba. 131 Ban kuma damu ba duk da 'yan maganganun da ake yi in an ganni, nasan yana wurin lambunshi yana lura da yanda ake ban ruwanshi. Wani lokaci ya dawo ya samu ina zaman jiranshi, wani lokaci yazo ya samu nayi bacci, randa yaga zai tashen ya tashe ni in yi mishi abinda yake so in yi mishi. Randa yaga zai hakura ya bar ni in yi barcina, shi yasa ma mafi yawancin lokaci in naji yana tayi min kashedin kar fa kiyi bacci ki jira ni ce mishi nake yi gara dai in ka dawo ka tashen, don ba zan iya wannan dogon hirar ba a wannan duhun ni kadai. Yawan itar da nake yi wa Ado akan duhu ya sanya shi yana fara diban labun nashi ya kashe kudi mai yawa ya sanya wutar lantarki a gidan gaba daya. Ya kuma gyara katangar gidan yayi mata kofa daya, yayi wa zauren gidan kyakkyawan gyara, soronshi ya zauna daidai maimakon da da yake barazanar zubowa, amma bai yi musu gwaninta ba. Su Ruwaila wai cewa suke yi aikin banza, tun lantarki yana sabo a Dabai ba a sanya mana shi ba sai yanzu da ya zama gidan kowa da shi, kuma dubi hanyoyin nan da muke samu muna shiga makwabta 132 hankali a kwance wai don fitina yasa an toshe. Yanzu babu halin ka fita sai ka nemi izini, kai zama da fitinannen mutu dai wuya ne dashi, sai kayi hakuri. . Ni kam tunda na gane mijina na kuma gane halinshi na gane yana sona yana girmama min mahaifiyata yana tattalin yan kannena sai na. kudurawa kaina yin hakuri da shi da duk wani abin da ya shafe shi. Ban ganin yayi wani abu in ce mishi don me? balle in je ina tambayarshi dalilin da yasa yayi har akai ga jallin da zan ce ban yarda ba na daina. Shi kuma in ya ga nayi mishi ba daidai ba ya kama zai yi fada tunda shi baya iya ganin an yi bai tanka ba sai in ba da hakuri ko da kuwa ina sane nayi don ya ji in da dadi. Don haka yan uwanshi başa bata min rai komai suka yi min ban tankawa saboda na san fitinata da su ba za ta saman mishi farin ciki da kwanciyar hankali ba ni kuma abinda son ganin ya samu kenan. Rannan na dauki wayar Ado na kira Inna don mu gaisa, tunda zaman jiran fitowarshi daga wanka nake yi muna cikin hira Innar take bani labarin anyi ruwan saman farko a Bauchi jiya. 133 Nayi kabbara cikin farin ciki tare da addu'ar Ubangiji ya sanya damunar ta zamo mai albarka, ta ce min to amin. Na ce shi kenan Inna za ku dan samu saukin zafin nan da ake ta fama dashi ko ina. Don mu ma nan din zafin ne, Inna tayi murmushi ta ce to mu tun yaushe kuma muka huta da zafi? Nayi maza na ce, Inna bana ba ayi zafin ba ne sosai a Bauchi? Ta sake wani murmushin kafin ta ce min. "Hala ba ki san mijinki ya aikowa Umar mai shagon dinkishi kudi ba? Wai azo a sanyawa mai sunanshi (A.C), ai mu tun nan muka daina jin zafi. Na ce bai gaya min ba Inna, cikin zuciyata kuwa tunawa nayi da ranar da naji hirar Ado da Sa'adatu yana tambayarta mai sunanshi, tana bashi labarin ai tunda zafin nan yazo baya baccin daree kwana yake yana kuka wai shi nan ma baya son zafi. Ado yana jin anyi ruwan saman farko a Bauchi ya fitar da hatsinshi da ya noma gaba daya ya kai kasuwa ya sayar, sai dan kadan ya bari. Dama tunda' aka yi girbi ya fidda Zakka tun a gona na baiwa makwabta da 'yan uwa nasu hakkin. Ya tattara saura ya adana da niyyar sai damuna ta gabato zai kai hatsinshi kasuwa, don yayi amfani 134 da kudin wajen yin noman wannan damunar. Ado yana ta shirye-shiryen noma bana na wannan damunar da muke addu'ar zuwanta lafiya nima ina nawa shirye-shiryen na rubuta jarrabawata ta gama Secondary a lokacin nan kuwa ina da ciki wata hudu. Sai dai babu wanda ya sani don babu alamar shi ga ni kuma lafiyata kalau yan matsalolin da nake dasu ba wasu masu yawa ba ne. A wannan lokacin babu abin da nake so irin Ado ya yarda ya barni in je gida in ga iyayena da yan uwana. Amma sai in yi tayi mishi maganar yana jna baya ma amsawa sai in ya ji na matsa mishi da zancen sai ya ce min io wai me za ki jie ki yiwo ne? Da Aliya ta dawo daga aikin Hajji sun zo gidan nan ita da Atika da Sa'a har da Baba karami suka kawo miki tsarabarki suka yi miki bakunta ta kwana uku. A wannan dan tsukakken dakin naki baile ko in ce tsarabarki kike son karbowa. Inna kuwa kina jin maganarta a waya mai babban allo in yana son ganinki shi da matanshi sun san in da kike tunda yazo Hajiya 'yar dubu ma tazo to wa yai saura? Kullum yayi min irin wannan maganar bata rai nake yi in daure fuskata in ce 135 mishi su kadai ne yan uwana da dangina? Babana fa? Sai in hado da Mama don in yi mishi kara tunda na gane har yanzu yana sonta yana kuma girmamata, sauran 'yan uwana fa? Sai ce to ba yanzu ba sai ya duba yaga lokacin da ya dace. Rannan muna tare da Ado a dakinmu bayani yake yi min kan kudin hatsinshi da ya noma bara wanda sai à wannan lokacin ya sayar da kuma na lambunshi da ya sayar shima ya adana yana harin damunar bana da gonakin da yake shirin nomawa. Bana duk gonakina na gado zan noma Humairah ki taya ni da addu'a, nayi murmushi nayi mishi addu'o'in tun a gabanshi wanda kuma dama ka'ida ne sai dai in ban yi sallah ba. Haka kawai ma na kan shi da irin koKarin- shi da wahalarshi in roki Ubangiji ya sanya mishi albarka mai yawa a ciki. Muna cikin hirar ya daga ido ya kalle ni, amma a anya Humairah ba zan kure hakùrinki, in sa ki gundura da halayena da dabi'una ba kuwa? Nayi kamar ban ji shi ba, saboda tunda muka yi fadan da nace halayenshi da dabiu'unshi ne suka gunduren ya.maida maganar ta żama ka idar nenman magana a wurinshi. 136 Ban taba ganin mutum nmai son kai irina ba Humairah alherin da na samu a noman banan kawai ya ishe ni in yi miki ginin da za ki zauna a ciki ki yalwata. Amma ban yi ba, wai so nake in juya kudin in sake maida su gona wai da a irin nawa son kan so nake duk abin da ya fito daga gona in maida shi gonar a aikin da nake yi in yi tattalin da zan rinka yi mana hidimominmu. Ban kula zancen nashi ba, wucewa kawa' nayi na kwanta a bayanshi. A warnan noman da Ado ya yi na wannan damunar ne na gane talaka dai ba karamar wahala yake sha ba a kasar nan duk abin da zai yi karfin shi kadai yake yi mishi bai da wani mataimaki ba dai na Ubangijinshi ba. An riga an sani sarai babu yanda za'ayi a hada noman wanda yayi amfani da karfi yayi da na wanda yayi amfani da hanyoyin noma irin na zamani wanda bai yiwuwa sai ana da wani abu a hannu. Amma an ki a yi wa manomanmu na asali taimakon da ya dace da su wanda za su sau su bunkasa aikin nomansu sai kullum ayi ta bayani a baki a gidajen Radiyo da Jaridu, amma wasu yan 137 tsirarun mutane suke tsare komai su amfana da shi a bira ne ba tare da ya kai ga manoman na asali ba. Kullum irin korafi da maganganun da nakeyi wa Ado kenan a duk lokacin da ya zauna yayi min bayanin mai dadin ji kan aikin da ake yi mishi a gonakin nashi in ganshi kuma garau babu wata alama ta wahalar da zata tayar da hankali a tare da shi. Hannu babu bororo balle kanta, bal;e aje ga jallin yin fason kafa ga ciwon baya da na kugu, gashi kuma ya tabbatar min da cewar noman nashi na bana zai nika na bara sau goma ko a fiye da haka. Sannan a hakan duk dan wani dama da ya samu na zama zaka gan shi yana tashe da laptop din shi bincike yake kara yi kan hanyoyin noma irin na zamani a kasashe daban-dabarn da suka ci gaba, wai ya kara koyo da sanin sabbin dabarun noma don ya kara samun sauki. A wannan damuwar ta bana sau biyu ina kaiwa gonakin Ado ziyara sabanin na bara da na ki zuwa saboda aikin ya wahalar min da mijina da yawa ya fitar min dashi daga hayyacinshi, don ma shi din namiji ne. A duk lokacin da na kaiwa gonakin nan ziyara 138 kuwa tsayawa nake yi in yi ta kallon yabanya, yanda ta mike fetal ta tafi tayi nisa cikin jeji ban iya hango karshenta. Gashi ta yi kore shar. Wani irin dadi ne yake kama ni wani irin sanyi ya sauka cikin zuciyata, in ji ba ni da wani sauran nauyi ko kunci da ya addabi zuciyata in ji babu abin da yafi dacewa da ni irin in kara tsarkake Ubangijina. In kara kadaita shi da bauta, in kara jin tsoronshi saboda ko daga kallon baiyanannun ayyukanshi na zahiri a kawai wadanda su ba sai mai hankali da ura ne kawai zai gansu ba. Misali halittar sama da kasa canzawar yanayi daga rani zuwa damuna, yanda dan Adam ke shuka kwaya guda daya ya fitar da daruruwa kasa guda daya ruwa iri daya ya fitar da nau'o'in tsirrai daban-daban ya ishe mu zamowa abin lura. Bin bayan Ado nayi can cikin gonar saboda hangenshi da nake yi yana ciccire kananan ciyayin da ke son fitowa da tsirran da bai son gani don in gaya mishi tunanin da ke damun zuciyata. A duk lokacin da na kalli yanayin sama ko yanayin shuka a lokacin da tayi shar a jeji in ji ko shima tashi zuciyar tana raya mishi irin wadannan al' amuran, 139 Ban san yanda aka yi ba, ban san ina na tsunduma wajen aikin ciccire mishi kananan ciyayin ba sai da na ji shi yana cewa "Ke Humaira ba fa abin da na kawo ki gonar nan kiyi kenan ba. Kawo ki kawai nayi ki ganta kiji dadi ki taya ni yi mata addu'a na rokon Ubangiji ya sanya mata albarka mai yawa." Na ce mishi amin Kawu. Taso ni yayi a gaba muka fito daga cikin gonar muka dawo in da ya ajiye babur dinshi da muka zo akai, cikin natsuwa ya kalle ni bayan ya burga mashin din. "Hau mu tafi mana." Na kalle shi na ce, "uh'uh yi gaba zan tako da kafa ba zan sake hawanshi kayi ta tsalle da ni a kan kunya ba." Cikin natsuwa da nuna kulawa ya ce "Ba kunyaa ba ce Humairah, hanyar ce babu kyan, na ce eh to jeka. Ya sauka daga kan mashin din ya shiga tura shi, ni kuma ina takawa da kafa muna tafiyar mnu muna hirarmu mai dadi. Mafi yawancin hirar kuma kan abin da ya shafe mu ne, haihuwata da ta matso, gonarshi da kuma aikinshi, kullum hirarmu bata wuce wadaunan abubuwan guda uku. Ranar Juma'a sha tara ga watan tara cikin damuna sosai a lokacin da manoma suke matukar 140 taka tsan-tsan da dan abinda yai saura a hannunsu saboda tuni karfinsu ya koma gona. Ita kuma gcnar bata fara bayar da komai ba, na haifi diyata ta mace lafiyayya, kana ganinta kasan ubanta manomi ne, taci ta koshi. Ado ya shigo gida cikin sauri a dalilin ya kwana a dakin zauren gidanne saboda zuwan da Sa'adatu tayi. Ina jin shi yana dariya yana tambayar Goggo Ayalle. Goggo wai yau ma an yi haihuwa a gidan nan ko? Tana taya shi dariyar tana fadin "An kara wata haihuwar. In ce ko dukansu ne suke shirin haihuwar ne Goggo." Goggo tayi dariya ta ce, to wa yasan musu ne? wacece kuma ta haihu yau? Goggo ta ce a'a ashe baka ji mnai baihuwar ba, ai Aisha ce." Dib naji Ado yayi, yayi shiru na lokaci mai tsawo yana sauraron bayanin da take yi, jarumar yarinya ita kadai ta haihu sai zuwa Kanwarta tayi ta tashe ni, hatta tsofaffin matannan da suka haihu basu haihu su kadai ba, sai da suka taso mu muka zo muka kwana muna zaune da su amma ita.. Ado ya katse ta ya ce to tsofaffin mata Goggo ba sun san zafi da mutuncin kansu ba, amma ita fa tana da hankali ne? Goggo ta rufe Ado da fada. 141 Wanne irin magania ne wannan? Yarinya tayi kokari ba za ka yaba mata ba, bata hutar da kai biyan kudin asibitin nan na zamani mai tsada ba? To ni dai ban gode mata ba Goggo in tayi ne don in yaba mata to ban yaba ba, ya juya ya bar ta tana tayi mishi fada ina jin shi yana kwalawa Sa'adatu kira, tayi maza ta fita ta tafi wurinshi. Aka gama min komai aka dawo dani dakin Goggo Ayalle wai a nan zan yi jegon, ina zama Sa'adatu ta sake shigowa rike da kwano, ga dabonon da Inna ta ce kar ki manta dashi. Na kalle ta nayi murmushi na ce ai kuwa in ban da kin tuna da na manta na karba ina ci ita kuma sai kallon yarinya take yi tana murmushin jin dadi. Ran Yaya ya 6aci, wai kin zauna kin haihu a gida baki ga nima fadan da yayi min ba akan wai ban je na gaya mishi ba. Na ce ai nima kukan yarinyar kawai naji, in kai mishi ita ya ganta? Na ce ke Sa'a, kin san nan gidan komai muka yi za a iya cewa ba muyi daidai ba, ta ce haka ne. naci dabinon sosai nasha ruwa kamar yanda Innan ta ce a gaya min, na gyara nayi kwanciyata. Kan ka ce meye wannan? Sai na ji ni garau kamar ba ni ce nayi wannan uban wahalar ba. Jimawa can Ado ya shigo dakin wurin ya nema 142 ya zauna suna gaisawa da Goggo cikin girmamawa irin wannan alheri ya same muka tashi kana fada? Ado ya ce kiyi hakuri Goggo raina ne ya baci ana jaruntaka da wahala ne Goggo? Ba za ta fada a san bata da lafiya ba? Ta ce to tunda Ubangiji ya raba su lafiya ai sai muyi mishi godiya, yayi murmushi ya ce haka ne. Goggo taci gaba da yi mishi bayani ita haihuwa ai duk ta wuce yanda ake maganarta, gida da asibitin duk daya ne. Ubangiji ke yin ikonsa ayi ta lafiya. Yayi maza ya sake cewa haka ne Gogg0, mun gode mishi. Ta tashi ta dauko yarinyar nan wai zata ba shi ita kamar yanda ta saba kawo mishi sauran yaran da aka haifa kafin ita a gidan. Ya ce "A'a Goggo, ai zan ganta a hankali." Ta ce ai haba? Ai na dauka ba za ka yi kunya ba, ta maida ita ta ajiye ta fita saboda kiran da Baba ya yi mata. Yayi maza ya dawo bakin gadon yasa hannu ya dauko ta ya kare mata kallo ya tofe ta da addu'o'i ya maida ita yana kallona cikin murmushi. Wannan yarinyar ta fito a jikinki Humairah ba ki samu matsala ba ko? Ban kula shi ba, ya dan yi waiwaye don kar yayi maganar da wani zai ji shi 143 ganin ba kowa yasa shi matso da bakinshi kunnena ya fadi abinda yake nufin fadin. Kallonshi kawai nayi ba tare da na ce mishi komai ba, hidima sosai Ado yayi sai dai yaja ya tsaya kan bai yarda ayi taron suna ba, tunda sauran haihuwar ma duka ragunan suna kawai ya bayar aka yi ysnka sai sunan da babu taro mai yawa. Don haka nima ba zai yarda da gayya daga wani wuri ba, Sa'adatun da tazo ita kadai ta isa. Ni kam kuka nayi tayi, Goggo ma ta ce akan me kuwa zaka yi haka? Wadannan yan uwa nata ka ce ba za su sUnan 'yarsu ba? Ya ce to 'yarsu tazo cikin tsululun damina Goggo ba sai suyi hakuri ba, manomi yana hidima mai tsanani ne da damuna? Goggo tayi dariya ta ce, wannan shi ne iya shege. Ni kamn da hankalina ya tashi da hana yan uwana ziwa suna da Ado yayi sai da naji yana yi wa Innata bayanin cewar shi din ya riga ya shirya zuwana gida da zarar mun yada wanka, don haka kar ayi wahalar zuwan. Yanda Ado ya bada ragon suna guda daya a duk haihuwar gidan da aka yi haka nan a wannan sunan ma rago guda daya ya bayar da safe ranar suna Baba Tanimu ya fadi sunan da ya sanyawa 144 yarinyar Umahmah. Gaba daya kowa a gidan mamakin sunan yake yi, wasu ma tambaya suke yi ina Baba ya samo wannan sunan kuma? Sai da Baban ya shigo Goggo tayi mishi tambayar naji yana yi mata bayani. Sunan jikar Manzon Rahama ne, Goggo tayi maza ta ce, (S.A.W), rannan da naje wajen wa'azi naji ana tarihinta na ce to in aka yi wa Adamu haihuwar ya mace sunan da zan sanya kenan. Goggo tana dariyar farin ciki ta ce ai kuwa dai Mallam tunda suna ne mai daraja, ya ce haba don ma ba ki ji tarihin nata ba." Duk da nanata haihuwar tsululun damuna da Ado yayi tayi, hidima sosai yayi min. Mutane da yawa kuma sun zo, mafi yawanci matan abokanshi ne da kuma yan uwanshi, nawa yan uwanne kawai ba su zo ba, shi ne abin da ya dan rage min jin dadi. Amma duk da haka na yi wa sunan kwalliya ta burgewa da ban sha'awa. Lesuna masu tsada guda biyu da atamfofi super suma guda biyu gami da shaddojin gezna na asali suma guda biyu, dukkansu a dinke. Dinki kuma mai ban sha'awa ya kawo min gami da takalma da jakakkunansu designers, ki 145 zabi wadanda za ki yi amfani da su. Na daga ido na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi ya ya zaka kwashi kudi masu yawa haka ka. saya min irin wadannan kayan? Bai kula ni ba sai kawai yasa hannu a aljihunshi ya ciro wata sarka da yan kunne mai kyau English Gold. Ya miko min ki shirya in ga kwalliyar taki kafin in fita don Kaduna nake son atfiya, kan maganar nan da nayi miki. Kar dai ki fasa yin addu'a ko kina zaune na gayawa Inna ma ta kara yi min addu'a na ce mishi to. Sa'adatu ta shigo itama tayi kwalliya mai kyau atamfar super ce a jikinta itama Adon ne ya bata don tayi fitar suna. Nayi kwalliya sosai na kuma yi matukar yin kyau, shaddar na fara sakawa saboda dinkinta yayi matukar daukan hankalina. Nayi dauri mai kyau na sanya sarka da yankunne, ga agogo da zobe tunda nazo Dabai ban taba kwalliya irin na ranar ba, mutanen da ban basu taba sanina cikin kwalliyar da ta dace da ni, tunda shima Ado kananan zannuwa yake saya min sai ko yau dinnan. Ina cikin gyaran daurina Goggo Ayalle sai kallona take yi tana fadin iko sai Ubangiji sai ga 146 Sa' adatu ta shigo Anti wai kizo ki nuna mishi in da linka din shi suke na kwatanta mata ta tafi ta dawo. To kije mana kawai ki bashi tunda ya ce sauri yake yi zai tafi, nabi maganar ta Goggo na nufi dakin nawa da na kwana bakwai ban shige shi ba, komai a kammale sai kanshi yake yi a tsakar dakin. Na samu Ado a tsaye shima yayi kwalliya rigar da ke jikin nashi sabuwa ce sai kamshi take yi. Yana ganina ya rage fara' arshi kai ke kam ko wayo baki dashi can zan biyo ki dakin Goggo in ga kwalliyar sunan naki? Ya sake kallona cikin wani yanayi na sakin fuska da murmushi alamar ya gamsu da abin da ya gani, ya ce wannan ita ce asalin Humairar da Inna ta bani ba wacce na kawo na ajiye a wannan dan tsukakken dakin ba. Nayi murmushi don in rama mishi wayan nashi ya ji dadi, sai na ce mishi ba fa Inna ce ta baka Humaira ba, Baba da Mama ne suka baka ita. Ya sake fadada murmushin shi tare da jawo ni jikinshi har dankwalin nawa ya fadi a kasa, kankame ni sosai yayi a jikinshi kafin ya ce minni Inna ce ta bani ke Aisha, ita ce tayi dalilin da ki ka sallama min kanki. Ita ce ta biyo mu Dabai da umarnin da take 147 bayarwa ne na samu nayi sa'ar samun zaman lafiya a gidana don haka ni a wurina ita ce ta ba ni ke. Muka yi sallama ya kama hanya ya tafi nima na dawo dakin Goggon in da ake sha'anin suna, Goggo sai bina da kallo take yi tana kokarin ganin idona, ko me take son gani oho? Suna da kwana biyu Ado ya dawo yana dawowan yaje ya sayo wani katon rago ya kawo gida aka yanka yasa aka soya ya zuba shi a cikin kwalla wacce itama sayota yayi ya hada da katon din minti na malta sweet. Da katon din cingam Bazooka 200 da goro dan takarda biyu da dabino mudu biyar da shadda yadi goma-goma, guda hudu da atamfofin super guda uku ya tashi Bala ya ce mishi yayi wa Sa'adatu rakiya zuwa gida gaba daya kayan ya ce a kaiwa Baba a gaya mishi shaddojin guda hudu. Shi daya Baba Yahya daya, Mallam Liman daya, Mallam Harisu ma daya, atamfofi kuwa Mama daya Innata daya, Zubaida ma daya, sauran kuwa akai mishi a gaya mishi na haifi Umahmah ga kayan suna nan a rabawa Jama'a. Sannan itama Sa'adatu yayi mata tata tsarabar. Kwanan Bala uku a can maimakon daya ko biyun da Adon ya ce mishi ya yi ya kuma dawo da 148 shatara ta arziki. Jego mai kyan nayi mai kuma dadin gaske na murje nayi gwanin sha'awa in ban da ina lissafin kwana kin tafiya ta gida ma ina jin da nafi haka morewa jegon nawa. Rannan Ado ya dawo gida daga Danja a lokacin nan kuwa kwanana arba'in ne har da uku. Yana shigowa dakin ya nemi wuri a bakin gadon da nake zaune ya kama kallon yarinyar da ke ta faman bacci. NI wannan yarinyar da wa tayi kama ne? nayi murmushi na ce wah yasan mata, wasu suce da ni, yayi maza ya galla min uban harara wadanda basu san ka ma iso ba ko? Nayi shiru naci gaba da abin da nake yi, to wai ni ba kin yi arba' in bane me kuma kike yi a naan dakin? Nayi murmushi na ce to ai ban gama wankan ba Goggo ta ce sai na kara. Wai wata biyu ba kwana daya zan yi zamu bar wankan yau ne gobe mu tafi gida. Ya tsuke fuska ya ce a'a ban yi miki wannan alkawarin ba, na dai ce in kin yi wata biyu za ku tafi amma ai ba daga nan dakin za ki tashi kiyi tafiyar ba. Nayi maza na ce ban gane ba, ya ce to kar ki gane, kina nufin haka zan yi ta zama? An gama 149 hakurin tsohon ciki an yi na zaman jego sai kuma in yi ta zama ina jiranki sai kin dawo daga tafiya? Ki gayawa Goggo za ki koma dakinki yau sai muyi ko kwana bakwai ne tare in yaso rana itayau ma kiyi tafiyarki, na sunkuyar da kaina kasa na ce ba zan iya ba. Ya ce to shi kenan ni zan koma duk ranar da ki ka gama wanka ki ka koma dakin naki sai in zo muyi kwana bakwai tare kafin ki tafi, in kuma naga raina ya 6aci da yawa ma sai in fasa tafiyar taka gaba daya. Da sauri na kalle shi "Me nayi maka?" Hawaye suka soma ganagarowa daga idanuna, saboda fargaba. Na matsa na matsu in je gida in ga Innata da Babana dama sauran dangi baki daya. To tun yaushe muke zaune ni da ke a haka Humaira? Sai kuma ace ba za ki tausaya min ba ai babu son kai a tsakanina da ke. Goggo ta shigo ta same ni ina kuka ta soma salati ina dalilin wadannan hawaye da suke zuba, kai Ado me kayi mata? Ban yi mata amai ba Goggo wai babu hali ne kawai ta ce ga yanda za' ayi in ce a'a. Ai kuwa dai ba zai yiwu ba. Goggo ta soma yi min fada bakin cikin Ado ya kama ni don haka ma 150 ban sake daga ido na kalle shi ba balle in san maganar da yake yi min. Kwana uku bayan nan ya sake baro Danja ya dawo gida ina ganinshi na tsuke fuskata, amma bai hana shi yin magana ba. Wurinki nazo saboda naje nayi wani sabon tunani. Wanda zai yi mana amfani dukanmu, ki rinka zuwa kina samuna adalci muna hira da daddare in su Goggo sunyi bacci. Na girgiza kai nuna alamar rashin yarda tare da fadin ba zan...tun kafin in karasa maganar tawa ya katse ni da wata irin rantsuwa na kuma san ba dabi'arshi ba ne yin hakan. To na rantse miki babu inda za ki in dai ba ki yarda da wannan ba gaba daya na fasa tafiyar ki zauna kawai tunda ni dama ba don ke na shiryata ba, don nna ce nasan yanzu haka tana son ganinki balle taji kin haihu. Zata zo ta gan ki taga abin da ki ka haifa amma duk da haka nasan in nayi waya na ce mata tayi hakuri wani uzurin ya hana ki zuwa, ai zata hakura tunda ita ba irin ki ba ce, ace mata baka da ikon sarrafata. Ba ka da halin ka ce mata ga yanda za'ayi ta ce maka to sai a'a? sannan a rinka yimaka karyar 151 ladabi da biyayya ta musu? A haka fa muke zaune ni da ke in kin yi min alherin kwana bakwai to sai kin yi dalilin 6acin raina na kwanakin da ban san adadinsu ba. Cikin zuciyata kalaman Inna suka fado min game da muhimmancin mijinka yasan alherinkato ni yaushe ne Ado zai san alherina da kokarina akan shi ya rike wannan yabon guda daya a mafi yawancin lokaci yakan yabe ni ne a daidai lokacin da abin yabon ya faru. Amnma 'yan mintoci kadan bayan nan da zan yi mishi wani kuskuren musamman ace kan abin da ya shafi kankanshi ne ba zai tuna kokarina na baya ba don haka naji hawaye sun fara zuba a idona a dalilin zuciyata ta kuntata na fara kukan kenan sai ga Goggo ta shigo. Ni fa naji abinda ya ishe ni wai ina dalilin wannan kuka ne na iya shege? Kai Adamu yayi maza ya ce na'am Goggo ta ce na roke ka ka yi wa yarinyar nan abinda take so. Ya ce mata to Goggo ya tashi ya fita ya bar mu ni da ita a dakin tana ta mita dama kin yi a hankali namiji ne in ki ka zauna ki ka yi jegonki na gaskiya ma ina ruwanki da shi yaushe za ki je kina daga ido kina kallonshi. 152 Balle ki san abinda yake ciki ranki yana baci a banza, taja tsaki ta wuce ta fita taje sanya mana ruwan wankan yamma. Mun kammala komai muna shirin kwanciya Goggo kam ma tuni take ta faman gyangyadi jira kawai take yi in gama baiwa Umahmah nono in mika mata ita suyi kwanciyarsu da tuni tayi barcinta, don tare suke kwana. Muna cikin haka sai ga Ado ya shigo, Goggo sai da safe ta ce mishi to sai da safe, ta amsa daidai ta karbi yarinyar sunyi kwanciyar su. Nan da nan ta soma minshari, ya mike tsaye yana kallona muke ko? Nayi kamar ban ji shi ba, na ce muke ko? Ko kina son yi min wulakanci ne? na mike tsaye na fita na nufi wurin namu gabana sai faduwa yake yi, shi kuma ya tsaya yana jawowa Goggo kofarta wacce dama ba sakata take sanya mata ba. Ina shiga dakin na shaki wani irin kamshi mai dadi ga kayaiyakin ciye-ciye iri-iri ya ajiye ga wasu dunkakkun zannuwan da ban san da su ba a gefe. Yana shigowa yayi murmushi, kici wani abu mana ga kuma dinkunanki nan ki duba, na ce uh'uh ai ba dadewa zan yi ba. Bai kalle ni ba ya ce min dama kin saki ranki 153 don ba zan yarda da wannan dari-darin ba kin gane? A kan dole na saki jikina da Ado na bar shi yayi abin da yaga dama, kuma wai maimakon yayi la'akari da halin da muke ciki na satan jiki muka yi na kawo mishi kaina bai damu be, bai yarda ya hakura dani ba sai wajen karfe biyu na dare. Ya rako ni na dawo dakin Goggo na hau gado na kwanta yayi min sai da safe yaja kofar ya koma wurinshi don yin wanka tunda ni kanm na riga nayi nawa. Na fara bacci kenan, Goggo ta tashen a dalilin yarinya ta tashi na karbeta na bata nono. Washegari da safe Ado ya shigo bayam munyi wanka daga ni har yarinyar Goggo tana wurin kosanta, zama yayi a bakin gadon yana wasa da kafar yarinyar dake faman shan nono. Zan fita amma ba zan dawo da wuri ba in na dawo zan zo in sanar da ke don ki zo ki same ni, na ce mishi kai...yayi maza ya katse ni da kin koyi ce min to don ki rinka sarun cikakken lada. Da daddaren kuwa sai da ya dawo ya zo yaja ni muke je. Washegari ma haka tun ina tsoro sai kuma na saki raina, rannan ina tare da shi mun yi matkar sakin jiki mun shagala cikin al'amuranmu. 154 Gaskiyar magana ita ce daga ni har shi muna Son juna, muna son kasancewa tare da juna, nakan dai jawa Ado raine kawai in yi mishi yanga saboda kawaici da kuma jan aji irin namu na mata. Amma in ba haka ba kasancewa tare da shi yana sanya ni jin dadi, ya sanya ni farin ciki da nishadi, ya sanya ni in rinka ji da ganin tanfar bayan ni din to babu wata. Barin komai yake yi ya tarairaye ni ya gaya min kalmomi mnasu sanyaya rai da tofar da zuciya. Ya maida kanshi zama tanfar wani dan yaro ko wani mara yawo a gabana, bai kuma gajiya kullum muka shiga cikin irin wannan halin zai nanata kalmarshi guda daya da ya saba gaya min ita ce ke din matata ce Humnairah. Ke ce matata kar ki taba ganin nayi aure a wani lokaci kiyi tunanin zan mallaka mata kaina kamar yanda nake mallaka miki ko zan zauna in yi mata shagwaba da sakarci irin wanda nake yi miki. Muna cikin wannan halin ne kawai naji Goggo Ayalle tana kwala min kira a tsakar gida da iyakacin karfinta, a cikin kua wannan tsohon daren. A kidime fwarai nayi maza na bude baki da nufin amsawa don in hutar da ita wage bakin da take yi tuna yi min irin wannan kiran a cikin 155 wannan daren wanda nasan da wuya kwarai ace akwai wani cikin mutanen gidan nan da bai ji kiran da take yi min din ba, tunda dare ne, dare kuwa ba raina motsi yake yi ba. Ado ya yi maza ya dora tafin hannun shi akan bakin nawa ya rufe da iyakacin karfinsh1, don hana sautin maganar tawa fitowa sosai. Ganin hakan ya sanya ni kokarin kwatar kaina a hannunshi, tunda shi da kanshi ya ji kiran da ake yi min daga inda muke din kuma muna jin muryar Umahmah da ke ta faman canyara kuka. Amma hakan bai sanya shi ya hakura ba, sai da ya natsa don kan shi sannan ya kalie ni cikin wani yanayi da yafi kama da na tsananin gajiya. A hankali ya bude baki yana yi min magana, ke ba ki da wayo ai shiru za ki yi abin ki sai ta gaji ta koma daki sai kiyi fitowarki, na ce mishi to. Amma duk da haka jikina ya kai matuka wajen tsorata sai bari nake yi, ya zuba min ido yana kallona ke menene haka? Na fa zunubi muka yi ba ni mijinki ne ke matata ce. Na ce mishi uhun, ai ni babu abin da yafi damuna da tsayuwar min a rai irin bazuwar maganara cikin gidannan da yanda za'ayi ta yadata ana cancanzata, cikin sauri ya ce min ke kar ki 156 nemi ki maida mutane wadansu iri mana. Goggo Ayallen da girman shekarunta ne ki ke cewa za ta yada wannan maganar? Kina so ki ce ita din bata san girma da lalurar aure ba ne? nayi kamar in ce to ai a sanin girma da lalurar auren nata ne taja ta tsaya a tsakar gida a cikin tsohon daren nan ten wage balkinta tana kwalawa sunana kira tanfar wata yarinya yar Karama. Bayan kuma tasan karamin mnotsi ma dare bai raina shi ba, balle wannan ihun da ta rinka yi wanda ba mutanen da ke cikin gidan nan ne kadai za su jiwo ta ba, har makwabta sai sun ji. Sai kuma na ce uhun, bari dai ma kawai in kama bakina in yi shiru, kar in jawowa kaina wata magana tsakanina da shi a wannan lokacin da na san ba karamin abu zan fuskanta a cikin gida ba, in fadi wata magana ya ce na yi wa matar Baban shi rashin kunya. Rako ni yayi nayi wanka yana tsaye yana jiran fitowata sannan ya tasa ni a gaba ya kai ni har kofar dakin Goggo Ayalle. Ya kalle ni cikin natsuwa da murya mai sanyi ya ce min shiga kiyı kwanciyarki na sake daga ido na kalle shi. Fuskata ta bayyanar da alamar tsoro yayin da 157 zuciyata ke ta faman harbawa da sauri ya sake kallona fuskarshi ta bayyanar da murmushi mai yawa daina jin tsoro Humairah. Ai ni mijinki ne ba wurin wani kika je ba kin amsa umarnina ne na kuma gode miki iyakar abinda Goggo zata yi in ma ranta ya baci ta ce ki koma dakinki gobe shi kenan, amma ba za ta je tana yáda wannan maganar ba. Ai ita babbs ce, in kuwa haka zata yi to ai ai yafi min na riga na gaji da wankan naki, lin gane? Na gyada kai nuna alamar eh, don ni kam ko bude bakin nawa in yi magana bana iyawa, saboda kaduwar da nake yi. To shiga mana, na kaile shi cikin natsuwa a hankali cikin muryar da tafi kama da rada na ce mishi, to jeka ka kwanta zan shiga. Ya ce uh'uh ai ba zan bar ki cikin daren nan a waje ba in haka yasa na tura kofar a hankali na shiga. Cikin sa'a gaba daya dakin a duhu yake nayi matukar jin dadin hakan don haka na lallaba a hankali na dale kan gadona, ina shirin kwanciya kenan sai kawai naga Goggo ta hasko ni da tochlight dinta. Ashe wai duk abin nan da ake yi duk da dadewar da nayi ban baro wurin Ado ba, duk da ita 158 yarinyar tuni ta hakura da kukan nata ta koma baccinta. Ita Goggo bata hakura ta kwanta ba, tana nann zaune dingir a tsakar dakinta bata ma yarda ta hau gado ba, don kar tayi gyan-gyadi da bacci zai dauke ta har in shiga bata sani ba. Don haka tayi zaman dirshan a tsakar daki tana Jiran sai taga zuwana wai ita nan a dole sai taga KWALUWAR DAKA'. "Ina ki ka fito? Ruwan me ke diga a jikinki? Jegon kenan? Dama damuwarki kenan yasa kika yi ta tasa yaron nan a gaba da koke-koke? Haba ni fa...kuka na soma yi wa Goggo kuka kuma mai tsanani, saboda tambayoyin nata sun yi min tsanani da yawa. Kukanki din banza da na woff? Ina...daga waje Ado yayi gyaran murya mai karfi, wai dai don Goggo tasan shi din bai yi nisa ba yana wurin ko zata yi hakuri ta bar maganar tata. Ban sani ba ko bata gane abinda gyaran muryar tashi ke nufi ba ne ya hana ta saurarawa ta ci gaba da fadin ina amfanin ace mace ita ce fitinanniya? Namiji bai damu ba sai kece... Uh'uh Goggo, uh'uh Goggo, abinda ya ci gaba da fadi kenan don kara yi wa.Goggo Ayalle 159 kashedin maganar tata, yayin da ni kuma gabana ke ta faman harbawa saboda tsoron kar ya ce zai tanka mata. Gaba daya fatana da burina bai wuce ya bar wwrin tsayuwar tashi yayi tafiyarshi wurinshi, ba Care da ya bude baki ya ce mata komai ba. Saboda nasan yin maganan nashi ba zai taba haifar mana da da mai ido ba, fin barin maganar da Goggon tayi shi ne ya hassalar da Ado har yayi dalilin da ya toro kanshi cikin dakin ya ce mata ba ita na ce Gogggo ni ne, ba ita ba ce kyale ta kawia ni ne. Abinda kawai naji Ado ya gayawa Goggo Ayalle kenan sai kawai naga ta fashe da kuka tare da salati mai tsananin karfi. Mu tafi littafi na hudu don jin yanda za'a kare tare suke'. Fatan alheri gare ku dukanku taku, Hafsat Chindo Sodangi (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) 24 ga watan uku 2013 07035586299 160