BAKAR AKIDA🏻 ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION GABATARWA_ :"DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN BAYINSA,SALATI MARAS ADADI GA SHUGABAN HALLITA MANZON RAHMA DA ALAYENSA BAKI DAYA." TSOKACHI: "WANNAN LITTAFI NA BAKAR AKIDA LABARI NE KIRKIRARRE KAGAGGE BANYI DOMIN WANI KO WATA BA." SADAUKARWA:"GAREKU MASOYA DANGINA DA ABOKAINA INA MAKU FATAN ALKHAIRI😍 Page 1/5 Bismillahir rahmanir rahim _____________________________ "Billahillazi!Salman kayi kadan ka auro salma ka kawo gidan nan a matsayin surukata!"Can dai inji su gada!"Ga yar arziki wacce ta gado shi tun kaka da kakanni kamar kai!Amma sai ka nacewa waccan mayyar yarinya yar gidan mayu masu shegen shiga ran tsiya!"Na rasa me ka gani ga salma wanda minal batada shi!"Ace karasa abin so sai wannan kodaddiyar yarinya yar matsiyata da kaf danginsu ba wanda ya taba mallakar keke bare babur!"To wallahi idan ni hjia mai gado ce na haife ka!Bazaka auri salma ba kaji na gaya maka!" Minal ce zabina kuma ita ce zaka aura tashi ba fashi kuma ka b'ace min da gani tun ban sassaba maka ba."Kar ka qara yimin zancen ta!" "Salman dake gurfane gaban mahaifiyarsa ne ya dago kansa idonsa jajir kmr barkono ya ce,Allah ya huci zuciarki Ammina in shaa Allah zan ga nayi kokarin hana zuciata abinda ta ke so zanbi umirniki(Umurnin Uwa)ya qarashe maganar cikin kunar rai!" "Hanyar waje Hjia mai gado ta nuna masa da hannunta cikin bacin rai ta ce Salman tashi ka tafi ko zan samu nutsuwa wato ni zaka fadawa har ynzu salmar ce aranka ba minal bako!?" get out!' "Very sorry Hajiya in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba!"Inji salman cikin ladabi!" "Tashi yayi sum-sum ya wuce yabar falon saboda yasan halin Hjiarsa sarai fagen iya masifa ta kwarai sosai!"Dakinsa ya nufa yana mai zubda hawaaye ciwon son salma ne ya addabe sa!" da kuma tsantsar tsanar minal ne dauke a qalbinsa!"A gaskiya shi kam bAzai iyA dAina son salma ba har karshen rayuwar sa!"Dan kuwa ita ce zabinsa ba minal ba marar kunya!"Ya rasa a ina wannan BAK'AR AK'IDA tasamo asali acikin afamly dinsu!"Da har suke cigaba da Assasata!."Fatan shi Allah yasa su gane gaskiya!" "Zaune ta ke a Dan madaidaicen tsakar gidansu mai kama da kango tana jika gari da suga domin Karin safe." "A gefen ta wata dattijuwa ce ke daka Tim tin tuuum in banda sautin karar turmi da tabarya ba abinda ke tashi,wurin!" "Wacce ke shan gari da sugan ce ta taso ta qaraso gurin da matar nan mai dakan ta ke." "Ta ce Inna kawo in idar da surfen kije ga naki gari can na rage maki."Kinga dakan nan baki ko iya yinsa sosai." "Matar wacce aka kira da inna ta ce kibarshi kawai salma wannan dakan sai ni naga ke gabaki daya kirarki ta fita daban da takowa agidan nan kamar yanaynki da jikinki basa jure wahala!" Wallahi ina tausayin ki salma!"Inna ta karashe maganar tana mai zubda hawayen da take gogewa da gefen zaninta." "Murmushi Wanda yafi kuka zafi Salma tayi tace,Haba Inna ki daina damuwa da halin rayuwar mu haka Allah ya so kuma hakan ya ke son ganinmu karfa ki manta kaf danginmu ba mai arziki kedai mu godewa Allah da yayi mana arzikin samun rai da lafiya masu arziki nawane adunia suna da dimbin dukia amma sun rasa rayukansu da lafiyarsu kinga basu da anfani Innata saboda haka Allah yai mana komai arayuwa.!"Kawo tabaryar jeki ki karya zan cigaba!" Inna miqawa salma tabaryar tayi tana mai tausayawa rayuwar 'yarta!"Wacce aka Haifa acikin talauci ta girma acikinsa fatan ta Allah ya sa ta mutu acikin arziki!"Saboda batason tasha wuya da azabar rayuwa da suka gani!" "Salma ko cigaba da dakan tayi da kyar take dakawa saboda ita sam bata iyawa karfin haline takeyi domin ta taimakawa innarta da tsufa ya tasowa sanadin talauci domin tuni tabarya ta tsotse mata kurciya takoma tsuhuwa Dan kuwa wannan ce kadai hanyar cin abincinsu wato surfe." " Zaune take ta daura kafa daya kan daya cikin shigar wasu mugwayen English wears wando da riga Kore, matsatsun gaske, acikin qayataccen falon ta da in ban da qamshi da sanyi A.C ba abinda ke tashi acikin sa," earpiece sanye a kunnenta tana sauraren waqoqin justin bieber." "Sai wani bin waqar takeyi tana lumshe ido,A gefe 'yan aikinta ne zaune suna kallon t.v a qasan kafet." "Falmata ta ce,ranki shi dade lokacin sallaah yayi muje muyi sallah!? "Mtwsssss ke wace irin jaaka ce bazaki bari idn kinje gidan ubanki ba, kiyi sallolinki ko sallah aka kawoki kimin ne?" "A ah falmata tace, cikin firgici!"Kiyi hakuri Anty minal!" "Okay!Meye aciki idan kin koma gida saiki kiyi gabadaya mana."Ni kaina ma nafison in hada uku ko hudun inyi at dsame time yafi sauqi ko ba hakaba."In ji Meenal "Hakane Anty!"Su ka amsa mata dukan su falmata da lami suna duban junan su." "Am lami je ki part din mum kice ina kiranta." "To Anty, Lami ta ce, ta wuce domin Isar da saqon uwar gijiyarta cikin sauri!" "Meenal jiyowa tayi wurin falmata tace,Ke jaaka awuni sallah nawa ma akeyi na manta nace Hudu uku ne ko?" "Cikin ladabi falmata ta ce,A'ah Anty,biyar ne awuni." "To ya akeyi Dan naga ke kin iya ita waccan banzar kmr jahilace!"(Lami) "Akwai Subhi ana raka'a biyu,Zuhr,Asr raka'a Hudu,sai magrib 3 da isha itama hudu akeyi Anty."In ji falmata cikin nutsuwa saboda ita tanada dama fagen ibadah." "Okay"Naji abin ashe da yawa nikam biyu nikeyi kowacce." "Toh!Falmata tace cikin mamaki azuciyrta duk da tasan cewa ita kanta bawani ilimi ne da ita ba Amman tasan ya zatayi sallah amma ita minal din kmr ba diyar musulmai ba koda yake baza tayi mamaki ba tunda ba a nigeria tayi rayuwarta ba duk a London tayi karatunta harta gama cikin yahudawa tasamo dunia kam amma komai bata sani ba ga me da lahirarta."Allah ya shirya tace azuciyarta." "Minal ko sai waqa takeyi tana shan shishaa tana rausayawa." BAKAR AKIDA👸🏻👸🏻👸🏻 ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITES ASSOCIATION Page 6/10 An karbou daga Abih hurarah(R.A) ya ce,"Manzo Allah_ _(SAW) ya ce, "Kashedin ku da zato domin shi zato zance ne na karya."_ _Bukhari da Muslim ne suka ruwaito._ ________________________________ ASALIN SU DR.SALMAN "Dr.Salman Tahir Galadima yaro ne matashi kyakkyawa wanda ya ke da shekaru 30 cip a dunia." "Yayi karatu a qasar India inda ya zama babban likita Wanda ayanzu hakan ya na aiki GENERAL HOSPITAL da ke garin ARGUNGU." "Mahaifinsa Alh Tahir galadima ya rasu tun yana qaramin yaro sunan mahaipiyrsa hajia Bilkisu(Mai gado) sai qañwarsa daya tal adunia wato Rukayya mai sunan kakar su mahaifiyar marigayi tahir wacce sukeyiwa alkunya da (Ilhaam)" "Salman ya samu so da kauna da duk wani gata awurin iyayen sa,Sai dai hkn baisa shi karya alqawarin da ya daukarwa mafinsa ba na zama yaron kirki kuma da nagari."Saboda mahaifinsu mutumen kirki ne kuma hamshaqen mai kudi Wanda yakeda katafaran gida anan G.R.A ARGUNGU ga shi mutum mai kyauta da ilimi ga taimako da tausayin mutane."Dukkan halayensa na kirki ba Wanda salman bai dauka ba akullum burin shi ya zarce ayyukan alheri da mahaifinsa yayi arayuwarsa." "Hajia bilkis(mai gado) macece mai son mulki da takama sam batason talaka ya rabeta saboda iyayenta da danginta masu arzikin gaske ne shiysa ita bata son mu'amula da marar shii."Kaf halayenta iri daya daya ne da yarta kuma autarta Ilhaam."Ta gado halayen hajiya mai gado har ta zauce." Shiyasa akullum salman ke kokarin tunatar da su wasiyyar Alh tahir tun kan yavar duniya da su ji tsoron Allah su daina wulaqanta mutane amma ina abin ya riga da ya zame masu jiki."Sai addu'ah." BARRISTER MINAL "Minal Maina Sadauki 'yarinya ce mai masifar kyau ga ta da jiki mai kyau sai dai tsabar rama da tayi mata yawa ke sa ta muni." "Minal 'yar qanwar hjia ce uwa daya uba daya, mama Zainab wacce ke auren Justice Maina sadauki da ke zaune a garin Argungu." "Barrister Meenal Maina tayi karatun low a london Wanda a yanzu hakan lawyer ce mai zaman kanta da ta ke aiki a high court Argungu."Tana da shekaru 26 a duniya,Sangartacciya ce ta gaske batada ilimin komai da ya danganci addini kasancewar basu wani Dade da dawowa gida Nigeria ba,"Dan tunda aka haifeta suna London har sai da ta kammala karatunta suka dawo."A Yanzu ne ake koya mata abubuwa da dama dangane da addini dan ko sallah bata iya ba!" kuma bata ma wani maida hankali sosai Dan tana ganin tafi karfin malamman na ta."Saboda minal batada kunya ga rashin ji da shigar banza Sam bata da kama da diyan musulmi tun kan halayenta da dabi'arta,suturarta,da maganarta na marasa tarbiya ne komai take so ko ta ga dama shi takeyi kasancewarta 'ya daya da Allah yabawa iyayenta kuma suna sonta sosai shiyasa takeyin duk abinda ranta ke so agidansu da garin Argungu baki daya." SALMA MAI WALDAH "Salma Abu sufyan (Mai waldah) yarinya ce Matashiya black beauty ce mai kyaun diri ga ta kamila mai hankali ga ilimin addini da mutunci tasan girma da mutucin manya." kasancewar da kyar ta samu ta kammala karatunta na sakandare dan ko basuda kudi ko kadan bare ta cigaba da karatunta duk da taso hakan amma ba hali!"Ba kowa ba ce,"Ba diyar kowa ba ce face bayin Allah da su ke zaune acikin tufin asirin Allah Sam gidansu salma baiyi kama da in da mutane ke rayuwa ba,tamkar wani kango haka yake kuma a hakan suke tafiyar da rayuwar su da sauran jama'ar gidan saboda lungu biyu ne da na babanta da kanin babanta da iyalensu duka Suna zaune acikin gidan su da ke garin Argungu a unguwar Allugu Wanda idan ba gidan 'yan walda ko surfe akace ba, bama za a gano gidansu salma ba a unguwar.saboda waldah gadon gidan su ne,wanda duk mazan gidan shi ne sana'ar su matan kuwa surfe ne aikin su." "Malam Abu Sufyan mai walda shi ne babanta sai Innarta Baraka ita kadai ce Allah ya qaddari ta tsaya acikin yaran da suke samu saboda inna baraka wabi takeyi da ta haihu bayan lokaci kadan yaran komawa(rasuwa)sukeyi."A hakan kowa ke tafiyarda rayuwarsa agidan mata suna dakau(Surfe) yara da manya wasu talla,maza ko suna fitaa faci da walda saboda, su ne sana'a ta gadon gidansu salma." "Watarana da salma tayi rashin lafiya ne sai innarta ta kaita asibiti sai Dr.salman ya duba salma sosai harda bata magani da yayi mata allura to irin yadda salma take kuka alokacin da yake mata alluran ne har yaji ta burgeshi daga nan ya sauke su gida kuma ya fara bibiyarta tun bata kula shi har tafara kula shi saboda yanda ya ke ba ta kulawa da tausayinsu tare da taimakonsu da yakeyi har dai soyayya mai karfi ta dunke atsakanin su."Ba yadda baban salma baiso ya raba salman da yarsa ba!" dan kuwa ruwa ba sa'an kwando ba ne" amma abin yaci tura domin salman baya jin kora da wulaqanci idan dai akan abinda yake so ne."A hankali tun salma bata nuna masa so har tafara saboda irin yanda ya ke nuna mata so da kulawa duk da alokacin tanada shekaru 20 ne aduniya amma tasan cewa salman ya ci akirashi da mai sonta na gaske Dan baya dubin yafi karfinsu kasancewarsu marasa hali." (So ne hana ganin laifi inji yn mgn lol) "Tun minal na yarinya qarama take son Yaya salman dinta,Dommin ada can baya gidansu take zama tana hutu,yana sonta tana sonsa irin na kurciyar nan to shi ne ita har xuwa girmanta bata daina ba tun iyayensu na daukar abin amatsayin kurciya har aka gano lalle son salman acikin jinin jiki minal ya ke."Hakan ne ya sa iyayensu mata suka shiga cikin zancen saboda masifar son da minal keyiwa salman." "Amma shi sam da ita da iyayensu basa gabansa kan maganar hadasu auren! saboda shi halaye da dabi'un minal basu yi masa dan kuwa batada kamun kai bare ilimi da tarbiya ga ta sangarta da rashin kunya da yayiwa rayuwarta katutu." "A rayuwar salman yana son mace mai tarbiya ilimi da alkunya ba watsatsiya kamar minal ba saboda yana son ya samawa yaran sa uwa tagari wacce zata kula da rayuwarsa da ta yaransa." BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 11/15 _"Duk abinda ka raina, shi wani ke so aduniya, yi kokari kayi amfani da damarka, domin daya ce, idan ta wuce bazata dawo ba,Zama mai dubin na kasanka da wanda ka fi, domin kallon Wanda ya fika komai Babbar kasada ce."_ NASIHA CE! "Inna Baraka ce zaune akan wata tsohowar tabarma da ta sha rana kuma ta ga duniya harta rarake!" ita da 'yartah Salma dubanta ta kai gareta ta ce"Salma a kullum ina maki fadan akan yawan tunanin nan da kikeyi!" "Ina kara horonki da ki debe soyayyar Salman azuciyarki!"Hanyar jirgi daban da ta mota!"Duk kin wani ki rame!"kina damar da kanki kin sani ko Salman na sonki uwarsa ba sonki takeyi ba!"Har nan gidan ta zo kwanakin baya ta zazzaga mana rashin mutunci!"Tayi mana kashedi kuma ta riga ta gina katanga atsakaninki da Salman!"Ba ke ba shi!" "Kinga ko salma dole ne ki hakura da salman ko kina so!"Ko ba ki so!"Masu kudin nan da kike gani auren kwarya tabi kwarya sukeyi bani gishiri in baka manja!"Kin ga ko gwara kowa ya tsaya inda Allah ya ajiye shi."Ki daure Mu mikawa Allah lamurran mu sai mu ga haske acikin su"Ni kaina ina jin zafi da tausayinki araina!" saboda nasan kin rasa mai sonki wanda baya dubin yafi karfinki Salman yaron kirki ne mai mutunci Wanda ya cancanci ayaba masa."Fatana Allah ya musanya maki da mafi alheri!" "Salma hawayen da ke zuba tun a lokacin da Inna tafara maganar har yanzu ne ta share a fuskarta azuciyarta ko zafi ne ke ta fita."Ta nisa tace "Inna na hakura kuma In shaa Allah zan cigaba da addu'a Allah ya musaya min da Alheri."Zanbi umurninki!"Daman tsautsayi ne irin na so nasan cewa salman Dan masu kudi ne yafi karfina!"Allah ya yaye min damuwata!" "Ameen,Salma hakan nike so kinji kiyi hakuri."Yanzu tashi muje mu fara surfen can!"Kar azo amsa ba mu karasa ba!" "To inna muje!"Allah yasa mudace" "Ameen."Wurin turmi da tabarya suka nufa dan karasa surfen su." *********** "Na Shiga uku mummy na rasa me na yiwa Yaya salman!"Ya tsaneni baya sona!"Baya kaunata!"Idan nakira shi wulaqanta ni yakeyi!"Baya kula dani da sonsa da nikeyi!"kamar ni ba jininsa bace qanwarsa kamar Ilhaam !"Mummy Ku aura min ya salman ko da sonsa zai zamo ajalina!"Mummy ko gawata ce ku kai agidansa domin cikar burina!"Son sa zai kashe ni!"Minal ta qarasa zancen cikin kuka da karaji!" "Mummy kara rungumo minal din tayi cikin jimami da bacin rai!"Ta ce"Kiyi hakuri minal aure tsakaninki da salman kamar anyi an gama!"Ki daina zancen mutuwa idan kin mutu ni da dadynki rayuwar mu taqare saboda son da muke maki bazamu jure rashinki ba!"Yanzun nan gidan Yaya mai gado zani na gaya mata!"Abinda salman ke maki da irin cin fuska da zarafinki da yakeyi yayi kadan ya wulakanta ki!"Dan kawai Allah ya jarabceki da sonsa!"To wallahi yau za'ayi ta takare!"share hawayenki bari kuka domin na marasa gata ne." "Mummie Har kinsa naji dadi da sanyi araina shiyasa nike sonki!"Idan kinje Ki nuna mata ranki ya baci saboda harke baya girmamawa kar kibar gidan har sai an tsayar da maganar auren mu!"Kuma wallahi cikin satin nan sai na nemo ko yar gidan uban waye yake wulakanta ni akan ta zan shirya komai domin wulaqanta ko wacece!" "Hakan yayi kyau minal!"Yanzu bari na wuce ki kira su lami su baki abinci ki ci ki koshi ki kwanta ki huta kinji Durlin." "Okay mum sai kin dawo ki gaisheta." "Zataji."Sai nadawo ko gobe idan mun hadu kinsan idan kina bacci ba a tashinki!" "To sai dai naji ki, adawo lafiya." "To mumy ta ce,"ta wuce abin ta." "Salman ne da abokinsA Jameel tsaye jingine da motarsa Bugati (Brown colour)a kofar gidan su Salma wanda akalla sunyi 20min a tsayen suna jiran fitowar salma." "A hankali da sanyin jiki ta ke tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki"Da sallama ta kara so wurinsu da hijab dinta har kasa."Cikin ladabi ta gaishe su." "Jameel ne ya amsa mata."Dan kuwa tuni salman ya Shiga duniyar tunani ba abinda yake son gani kamar salma da take tsaye agaban sa Kallonta yakeyi kamar madubi." "Sun dauki wani lokaci ita da jameel suna tattaunawa yana bata baki dangane da yanayin soyayyar su da salman da matsalolin da suke fuskanta." daga bisani bayanin irin son da salman ke mata yaqara jaddada mata."A karshe wuri yabasu domin waqa abakin mai ita tafi dadi." "Sun dauki mintuna kafin salma ya yiwa salma magana." "Ya ce salma kin daina so na yanzu!? kin daina kulawa da ni!"kin daina amsa kirana!"Meyasa!"Shin kinsan yadda hankalina ya tashi!"Na shiga tashin hankali mai yawa saboda duk wata kafar da zamu ga juna kin kulleta!"Ko yanzu nasan alfarma ce nasamu kika fito!"Me nayi maki ne?"Salman ya ce cikin kunar rai yana kallonta!" "Idon ta yacika taf da hawaye ta daga idonta ta dube shi kana ta ce,Salman ba kai min komai ba amma *BAK'AR* *AK'IDA* ce tayi komai arayuwar mu!"Ita ce ke kokarin gina Katangar karfe atsakanin mu!"Muyi hakuri ka nemi zabin iyayenka daidai kai!"Nima na samu iri na talaka na aura, kwarya tabi kwarya kowa ya tsaya in da Allah ya ajiye shi!"Ko yanzu Inna ce tabani umurnin in zo in gayamaka kabi zabin mahaifiyarka da umurnin ta domin tazo har nan tayi mana kasheki akanka dan haka nima iyayenah sun Gina Katanga atsakaninmu dole mu bar junanmu domin bin umurnin iyayenmu!"Ba domin ranmu yaso ba!"Kai hakuri Salman ka fita harkata....Kuka ne mai tsanani ya kufcewa Salma da gudunta ta shige gidan su ta rufe kofa." "Salman awurin da salma ta barshi ya durkushe yana kuka!"Da hanzari jameel ya zo wurin tare da taso shi zuwa cikin mota yana bashi hakuri duk da bai San dalilin kukan nasu ba!"Amma yasan tatsuniyar gizo bata wuce k'oki."Nan take suka bar unguwar." "Hello Nidal.."Kina jina? "Eh Minal ya kike?" "Lafiya qalaw, wani aiki nake so muyi da ke gobe kizou ina neman ki." "Okay,Sai nazo."Inji Nidal." "Nagode sai na ganki minal tace tare da kashe wayar."Wallahi na dauki alkawarin illata ko wace mayya ce!Ko wace sakarai!Banza!Kucakar da Yaya salman ke wulakantani akanta!"Ko 'yar gidan uban wace kasheta zanyi!"Sai dai nima akashe ni!"Lami ce ta katse zantukan da minal keyi azahiri kamar mahaukaciya ta ce,"Anty minal na gama wankin toilet din zan iya tafiya?" "Mari ta watsawa Lami tace,Har kin isa in sakaki aiki kizo kice min kin gama ni zaki nunawa lokacin wucewarki ya yi!? meye amfaninki?"Idan ba bauta ba?"To kisani ke baiwata ce bakida amfanin kanki sai nawa!" Kuma ki koma acan toilet din ki zauna har sai kinyi awa biyu ki fito."Mtwssss banza yar talakawa da basu da cikakken hankali!"Wuce kibani guri!"Ta fada tana huci!" "Lami da ke dafe da kuncinta kwallah na zuba a idonta tace ayi hakuri Anty!"Allah ya huci zuciyarki nagode!"juyawa tayi zuwa toilet din shiga tayi ta zauna ciki tare da rufo kofa domin bin umurnin minal!" "Wadda ko ba komai ta rage zafi da radadi takeji aranta!" tafara rage haushi da takaicinta akan lami da kaddara ta fadawa." (Ni kuma na ce Allah ya shirya minal da masu rayuwa kamar irinta ta Amin) BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 16/20 " _An karbou daga Abdullah d'an umar ,Yardar Allah ta tabbata agare su yace,"Manzon_ _Allah(SAW) ya ce,Kunya na daga cikin Imani."Bkhari da Muslim ne su ka ruwaito."_ _Allah ya sanya mu acikin bayinsa masu kunya Amin_ ." "To kin dai ji dalilin zuwana Yaya mai gado dole sai mun tashi tsaye akan lamarin yaran nan!"In ji Hajia Zainab(Maman minal)." "Ba komai mummyn Salman yadda kin ka ce haka za'ayi in ji Hajiya mai gado da ya ke hakan ta ke kiran Hajiya Zainab wato(Mummyn salman)" "Ki duba ki gani Yaya mai gado wallahi salman idan ba minal ta kira shi awaya ba!"Ba zai kirata ba ko kiran nasa ma tayi sai ya ga dama ya ke d'agawa."Ban da zagi!da cin mutunci ba abinda ya ke mata!"Kullum ce mata yakeyi marar tarbiyya! Batada mutunci da adduni!Mahaukaciya ma Ya ke kiranta."Yanzu a karshe ma ya ce kada ta qara kiran sa a waya!"Ta fita harkarsa saboda ya tsaneta.....!"Yanzu kenan harmu iyayenta yana nufin bamu mata tarbiyya ba!Ni kaina ya daina kirana baya son ganina!"Kamar ba salman nawa ba.......Kuka ne Hajiya Zainab ta saki na kissa tana mai juyarda kanta hannayenta aka tana kukah!" "Da sauri Hajiya mai gado ta taso daga kan kujerar da take zaune zuwa inda qanwarta ta ke zaune tana kuka!"Ta ce kiyi hakuri mumyn salman!"komai zai wuce idan har ni na haifi salman to bayada mata sai Minal!" "Dole ne inyi kuka!Yaya kibarni inyi kukana!Tunanin duniyar nan nakeyi da yaran zamani!ace ka haifi yaro yafi karfinka Yaya?"Yanzu ko ni kinka ba umurni zanbi!"Bare Salman!"Ni da ke uwa daya uba daya kuma sun bar duniya da dadewa ynzu ke ce uwa agareni!"Banda kowa banda komai sai ke!"Yaya mai gado kece komai nawa ke da iyalanki!"Amma yanzu ace ni da minal ne Salman ya daurawa kiyayya!"Me mukayiwa salman d'ana da nikeso kuma minal ke so da ya tsanemu?"Me zamu yi masa ya so mu!?"Ni dai tunda bai so abar maganar auren nan Yaya domin mu zauna lafiya!" "Wannan wane irin zance ne mumyn salman ai aure ba fashi!"Domin bazan. Zauna ina kallo salman ya auro wata bayan 'yatah Minal." "Bari kiji shi fa wacce ma yake son ba kowa bace ba diyar gidan uban kowa bace agari, 'Yar talakawa ce gaba da bayanta!" marar gata!"Idan kinje gidansu kamar juji!"Ita yarinyar sunanta salma da kaina naje har gidan naga yadda suke rayuwa kamar ba mutane ba!"Naci mutuncinsu tare ja musu kunne akan Salman, babu 'yarsu ba d'ana su nemi talaka ajinsu!"kuma na shaida musu cewa ashirye nake domin sauke musu kwando kwado na cin zarafin su matukar mayyar 'Yar su mai masifar shiga ran tsiya ba ta bar yarona ba!"Ke koni sai da nayi da gaske da ta shiga ran nawa Allah ne ya tsare ni!"Dan hakan Ba zan baiwa salman damar auren wannan yarinyar ba!" ki kwantarda hankalinki!"Na saka ranar auren minaal da salman nan da wata daya!." "Yaya mai gado kar kiyi masa dole mu dai bishi ahankali ranar da kin kasa kamar tayi kusa sosai!" "Ba komai Kedai kuje Ku fara shiri aure ba fashi!"Ni zanyiwa minal komai Wanda uwa zatayiwa 'yarta kuma nan zata dawo nice uwarta"Ki turota mufara shiri."Shi kuma dama ya kammala ginin da Abbansa ya fara masa alokacin yana Raye!"Yanzu kudin laife kawai zai bamu muje Dubai mu hado!"Ko kuwa ya kika gani?" "To Yaya hakan yayi Allah yasa shi ne Alheri ni bari nazo na wuce."Daddyn minal yaje sokoto yau zai dawo." "To Ameen, Ki gaishe shi Allah ya dawo da shi lafiya ki ce ina neman minal din." "In sha Allah zan turo ta Yaya nagode Allah yabarmu da zumuncinmu." "Ameen,Bari na kawo maki kayan turarukan da nasayo maki wurin Hajiya Uwany Yar Dubai." "To Yaya nagode sosai sannu da kokari." "Bayan Anty Zainab ta karba turarukan tayi godiya ta bar gidan zuciyarta cike da farin ciki ta isa gidanta."Matsuwa tayi safiya bata waye ba Dan ta gana da minal dinta!" "Tun lokacin da Jameel da salman suka bar kofar gidan su Salma."Direct gidan su Dr Jameel Jibril suka nufa a nan ne ya dinga ba shi hakuri!" "Salman ya ce " Jameel Ina so Ka fahimce ni,"Ina son salma so bana wasa ba!Kuma har na mutu bazan daina son Salma ba!"Da sonta da zan rayu kuma da shi zan mutu!"Jameel ina son minal amatsayinta na jini na kuma qanwata"Amma na tsani halayenta da dabi'unta!"Minal macece marar kunya batada tarbiya bare addini bugu da qari gata da shigar banzah!"Halayenta basu kama da na mata masu mutunci ba bata cancanci zama uwa tagari ba!"Ba tada Da kamun kai ko kadan!"Wannan ne dalili na da bazan iya auren minal din ahakan ba!"Hmnnnn "Allah Sarki rayuwa yau dan babana baya cikin duniya Hajiya ke son azabtarda ni da auren dole,akan kawai *BAK'AR AKIDA* da suka dauka kamar addini ko al'ada!! saboda kawai salma na diyar talakawa za ace bazan aureta ba Jameel!?"Salma Yarinya ce mai ladabi da biyayya ga sanin girman manyanta."Abinda ke burgeni da ita Addininta da tarbiyyarta kuma nasabarta mai kyau ce!"Dan kawai talauci ne yayi musu katutu arayuwa, kuma mai nema baya da fidda ran samu bamu san me zasu zama ba watarana!"Jameel shin meye aibun salma wanda kagani?" "Tanada aibu tunda Basu da arziki kuma kasan cewa awurin Hajiya shi ne babban aibu da abin kunya ka auri Yar qaramin gida!"Salman ina son kawai kabi umurninta ka auri zabinta kai hakuri da naka zabin kabi umurnin uwa."In ji Jameel cikin tausayin abokin nasa da duk ya rame ya fita hayyacinsa saboda damuwa." "Jameel na amince da zabin Hajiyata amma kuma na dauki alqawarin auren salma kul ba dade kul bajima na shiryawa fuskantar komai a rayuwata!"Idan dai kan salma ne!" "To abokina Allah ya baka Nasara ni kaina ina sonka da yarinyar saboda nutsuwarta kawai dai Hajiya da fushinta nike jin tsoro!"Amma Allah ya samuna hannu muci abinci muje hospital daga nan zan bika gidan in gaida Hajiya." "Ameen Jameel nagode kaci abincin ni komai bai min dadi ka gama mu wuce!" BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 26/30 _"An karbou daga Saubanah (R.A)Ya ce,Manzon Allah(SAW) Ya ce,"Hakika Allah ya la'anci mai bayar da Rashawa(Cin hanci)Da Wanda ke cin rashawa."_ _A'hmad ya ruwaito._ ________________________________ "Salman Zaune sai faman gumi yake hadawa duk da kasancewar sanyin A.c na dukan jikinsa!"Tun sanda Hajiya mai gado ta fara magana." "Kana ya ce to Hajiya Allah ya bani ikon kiyayewa!." "Kallon gefen ido Hajiya mai gado tayi masa sannan ta ce to Amin." "Dama abin da zan fada maka shi ne"Na saka ranar aurenka da diyata Minal nan zuwa karshen wannan watan."Ina son ka fara duk wani shiri da ango keyi alokacin aurensa!"Domin aure ne na 'yan dangi auren Yar gata minal."Komai da za ayi na al'ada zan sa su kawunka bala sukai gobe."Kai kuma ka turo min kudin da za'a hada lefe,gyaran amarya da sauran sabgogin da zamuyi da na abokanta!"Bana bukatar wasa acikin lamarin nan Salman !"Dan haka ka nutsu ayi komai yanda zai kayatar ."Kasan cewa wannan Hadi na Ku daga Allah ne tun minal na qarama ta ke qaunarka!"Ina laifin masoyinka kuma dan uwanka jininka!"Kaje ka sameta gobe kuyi shirinku daga nan ka daukota saboda zamu fara shiri ba time saura sati biyu!"Kana iya tafiya!"Sai da safe!" "Salman kam tun lokacin da Hajiya ta ambaci ranar aurensa da minal kansa ke juyawa ga faduwar gabansa ya tsananta!"Numfashinsa sai fita yakeyi sama-sama!" "Hawaye ne!Ke zuba a fuskarsa!"A Hankali ya kalleta yace Naji zancenki Hajiya na yadda da umurninki Allah yasa hakan ne Alheri!"Tashi yayi da niyyar fita daga falon." "Duk da jikinta yayi sanyi tausayin danta namiji tilo ya kamata!"Saboda tana son yaranta sosai kuma ta tsani bacin ransu!"Sai dai ce mashi tayi to Ameen Allah yai maka ALBARKA." "Ameen Hajiya,Salman ya ce,Ya wuce da Sauri!Ya bar wurin!" "Ajiyar zuciya Hajiya mai gado tayi da tunanin anya tayiwa rayuwar salman adalci!"Amma kuma a wani gefe dole ne ta tashi tsaye akan lamarin shi!"Dan batason ya kwaso mata suruka Yar talakawa wacce ko aurensa akayi ba zaiyi suna acikin garin Argungu ba, bare ya mamaye kebbi da kasar Nigeria baki daya!"Auren gata shi ne aure inda zakayi bajinta a nuna maka bajinta shi ne aure."Da tunanin hakan ta tashi tabar falon zuwa bedrum."Wayar Ilhaam ta kira ta shaida mata 10:00pm tayi bacci zatayi duk lokacin da ta gama fira da Dr.jameel ta shigo ta rufe falon nasu."Iklhaam ce mata tayi toh!"Tare da datse kiran." "Agogon Hannunsa ya duba ya ga lokaci na tafiya tashi yayi domin sallama da Babynsa ya ce,My Elhaam sai nadawo gobe kinga dare yayi nasan Hajiya ma kiranki ne tayi ko?" "Haba Doctor tun yanzu!"Ai Umma cewa tayi na rufe Part dinmu idan na shigo!"Ilhaam tace cikin shagwaba." "Ya ce kiyi hakuri kin San halin yayanmu(salman) yace da ten zan dinga tafiya ba komai gobe nan zamuyi lunch."sowrie muje in yi masa sallama." "Okay!"My Mutafi Allah ya kaimu,Rakiyarsa tayi har part din salman amma kofar arufe yayi knocking ba a bude ba, kofar Gam!"Wayarsa ya kira a kashe!"Dr.jameel ya dubi ilhaam yace anya lafiya salman yake?Ba dai fita yayi ba ga kuma motarsa na hango a parking place!" "Ilhaam tace mtwssss ka kyale shi mana!"my man nasan yana cikin part dinnan nasa Hajiya ce tabata masa rai!" fada tayi masa kan Yaya minal shi ne ya harzuqa ya rufe kan shi!"muje shi acciki!" "Haba My ilhaam meyasa kike taya Hajiya wurin tilistawa abokina auren wacce baya so!"yanzu Idan aka rabamu kina jin dadine!?"Shin kina da labarin ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani!"Wanda akan sa zai iya barin duniyar nan!"Meyasa ke bazaki tausaya masa ba!?"Idan nine ke cikin wannan halin na tsaka mai wuya zakiji dadi ilhaam!?" "Ta Yaya zanji dadi Baby!? Kaga mu bar zancen bana so kuma ai ni da kai mun dace, amma ita wacce Yaya salman din ke so sam basu dace ba!"Kasan ana son dace da juna!"Me ake da yar tsiya!"Ai matsiyaciya bata dace da zuri'armu ba!"Dan ruwa ba sa'an rariya ba ne!"Shi kuma Allah ya bashi lpia yana son asaramu akan so!"Ni muje har kasa naji ba dadi!"Da haka har suka isa wurin motarsa ya Shiga ya wuce mai gadi ya rufe gida,"Ilhaam part dinsu ta rufe ta fada dakinta domin shirin kwanciya bacci cike da tunanin nasihar da Dr jameel yayi mata akan rayuwar yayanta!"Da tausayinsa da kuma niyyar taimakonsa domin taga yasamu abin sonsa bacci ya dauke ta." "A hanya ma Dr.jameel na driving yana tunanin wane hali abokinsa ke ciki a gaskiya shi kam yayi tir!"Da wannan BAK'AR AK'IDA ta mutanen wannan zamani ace Dan masu kudi sai yar masu kudi hakan talaka sai dan talaka kwarya tabi kwarya!"Da hakan ya isa gidansu sashensa ya nufa texts din ban hakuri ya turawa Salman kana ya kwanta domin samun Hutu arayuwarsa." "Gefen salman ko yanda ya ga safe hakan yaga dare domin baiyi bacci ba akarshe nafiloli ya dinga yi domin samun sauki arayuwar sa!" "Salma ta gama shirinta tsaf!Dan tuni baba ya bata izini"Na tafiya qauyen su Inna Baraka domin ita tana son rayuwar dangin Innarta"Domin suna nuna mata so sosai."Da tunanin tafiyar ta zuwan qauyen felende ta kwanta bacci!" "Anty Zainab kuwa ta kosa safiya bata wayewa ba domin ta sanarwa minal abin farin ciki."Da murna da zancen ta kwanta bacci." BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 21/25 _An karbou daga Abdullah d'an Abbas (R.A)ya ce,"Annabi(SAW) ya ce,Yin kyauta ka koma tamkar kare ne da yakeyin amai daga baya ya lashe abinsa."Bukhari da Muslim suka ruwaito."_ *ALLAH ya sanya mu acikin bayin sa masu kyauta saboda shi Ameen.* "Hajiya mai gado ce,Zaune akan 3siter ta sha kwalliya sai kamshi takeyi kamar wacce zataje gasa,Da yake macece mai son kwalliya da shigar girma,Hankalinta na kan T.v da take kallon AREWA24 Inda ake shirin nan na HASKE MATAN AREWA da qawarta kuma abokiyar business dinta Hajiya Aisha Falke"Haka kawai jinin su ya hadou har suka zama aminan juna saboda tana yin matar sosai."(Ni kaina matar ina yinta over da dukkan matan Hasken saboda sun tsaya da Kansu sun jajirce agida da waje,Ya kamata mu kama Sana'a mata domin mu kasance Haske aduk in da mu ke.") "A gidan Hajiya mai gado Ilhaam ce ke ta waya da Dr.jameel abokin yayanta Salman kuma mijin da take burin aure da zarar ta kammala karatunta nan da 'yan watanni."In da yake sanarda ita suna zuwa yanxun nan shi da mutumen wato Salman." "Ilhaam tashi tayi ta shiga kichen an gama girki ta hada musu a daning." "Dakinta ta fada domin ta tsantsarawa Habibinta kwalliya."Dr jameel." "Dr.Salman ko sai faman mita yakema Dr.Jameel wai ya daina nunawa Ilhaam so da yawa hakan,Shi fa baison ilhaam qaramar yarinya ta raina shi akan jameel saboda bai son raini!" "Dr.Jameel dariya yayi kana yace haba dai nawan kai ka manta har kuka kakeyi akan wacce ko sa'an ilhaam din batayi ba!"Ai ko ba'ayi ba Ilhaam dina tana bawa salma, 2/3years na kwarai wallahi..." "Murmushi Salman yayi yace to Dan iska saura ka fadawa Ilhaam!"Kaga ita fa salma ta daban ce wani abu ban ma sanin ina yinsa akanta." "Hahaha ai kuwa zan fadawa Ilhaam yayanta mayen so ne taima dariya.."In ji Jameel cikin sigar zolaya" "Aiko da na karye mata kafa na buge mata baki!"Ka ga sai kazo jinya bayan ta daku." "Haba salman ai bazan fara ba!" mai da wukar wasa nikeyi yanzu dai ka daina matsawa abin kaunata Ilhaam nasan ka baka wasa!" "Kai yaran sai da hakan ayanzu nine matsayin Abbanmu dole in kula da tarbiyar ta shiyasa bana daga mata kafa da yanzu ta wuce saninka wayewar kawayenta tayi yawa sai da sa mata ido sosai jameel amma ina sonta matuka!"Kasan fa Yar gatan Umma da Abba ce Maryama(Sunan umman marigayi babanmu shiyasa muke kiranta da ILHAAM) "Wannan kuma gaskiya ne salman ana son hakan Allah ya bamu ikon kulawa da su." "Ameen suka ce dukan su a daidai lokacin da mai gadi ya wangale musu gate domin shiga cikin gidan." "Mummyn Minal ce zaune da Abbanta da ya dawo daga sokoto bayan ya ci abinci ya huta ne suke tattaunawa dangane da auren minal da salman da suka da d'ai suna marari,da burin gani." "Abban minal yayi matukar farinciki da ya samu labarin auren kuma ya bada goyon bayansa 100% akan zancen bugu da qari yasha alwashin shirya shagalin da ba'a tab'a yiwa 'Yar kowa ba a jihar Kebbi da kewayenta saboda zai ba naira kashi!." "Hajiya Zainab ta nuna jin dadin akan kudin da Abban minal zaiyi facaka da su Idan ransu ya gani"Tasha alwashin ko ita ba za a barta baya saboda dole ta fita kunyar qawayenta ta ayi hidima ta yadawa a mujallu,Dan tun kan shigarta da minal ta alfarma Zasuyi yadda ake yiwa sauran diyan manyan mutane masu hannu da shuni kamar minal." "Tun lokacin da salma ta dawo daga wurin su salman ta shiga daki tana rusa kuka!" "Babu abinda takewa kuka!Irin rashin masoyinta mai kyau da kyawawan hali,mai mutunci,tausayi da taimakon al'umma."Sannan ga son sa da kaunarsa da ke addabar rayuwarta!" "Da sallama Inna Baraka ta shigo dakin rike da kwanon pura a hannunta,Karasowatayi awurin da Salma take kwance ta tasheta furar ta miqa mata ta sha,sannan tace share hawayenki Salmana in shaa Allah,Sai kinga musanya ta alheri agurin ubangiji yana tare da mu kiyi hakuri ki kuma jure!" "Salma duban Inna Baraka tayi da rinanun idaniyanta da suka kumbura saboda kuka!" tace to inna nayi!"Daga yau na debe salman arayuwata!"Bazan kara sonsa ko tuna shi arayuwata ba!"Ki tambaya min Baba idan zai barni zanje qauyen ku(Felande) inda Gwaggo Hassana in kwana biyu ko na samu nutsuwa.! "Naji Salma babu damuwa kuma zan sanarda shi ki fara shiri dan nasan Malam zai barki ki tafi!" "To inna zan fara nagode."In ji salma. "Allah shi miki ALBARKA ya albarkaci rayuwarki ya sa ki huta duniya da lahira salma." "Amin Innata, Nagode,Allah ya Baku aljanna kuma." "Ameen ya rabbi suka fada gabaki dayansu cikin jin dadin addu'ar." "Dr.Salman da Jameel suka shigo falon da sallama da fara'arta ta amsa musu saboda tana son yaranta sosai musamman Salman da take gani kamar marigayi babansa saboda kamarsu da halayensu iri daya ne." "Cikin ladabi suka gaisheta yayinda suke shirin zaunawa a 2sitr dukansu, ta amsa musu fuskarta asake." "Hajiya mai gado ta tambayi Dr.jameel ya gidan nasu" "Ya ce, mata lafiya lau." "Ihaam......" "Hajiya ta kira awaya tace tazo ta kawowa yayyenta abinci." "Cikin material red riga da siket da Dan qaramin gyale red Ikhram ta fito kayan sun amsheta sosai kuma sun kame jikinta da kyar take tafiya sai qamshin Arabian perfumes(Sadat,Taiba,Burhan,Oud) ke tashi ajikinta."A hankali ta qaraso wurin su ta gaishe su." "Dr.jameel ne ya amsa mata sai faman kallonta yakeyi saboda ba karya ta hadu." "Dr.Salman ko harara ya watsa mata saboda shidai ya tsani irin saka banzan kayan nan da takeyi."yace,ke lafiya kika zo kika wani tsaya mana hakan wuce zuwa saka Hijab!" "Cikin tsoro da fargaba!"Ta ce tou! daman Yaya salman abincinku ne!"Yana dining....!" "Okay,Jameel Bismillah muje muci abinci."Tashi sukayi dukan su zuwa dining place." "Baki Ikhram ta tunzura cike da takaicin yayanta salman!"Ta nufi wurin Hajiyar tace Umma kina jin wancan bagidajen wai nasa hijab kamar wata malamar allo!" "Tsaki Hajiya mai gado tayi tace,barni da shi bakisan takaicin da ya bani ba!"Ga shi daman shi nike jira yafi son ya ganki kamar bagidajiyar yarinyar da yake so!"Meye acikin hijab banda zafi!"Mtwsssa ki kyale shi!" "A'ah Umma kinsan da zarar yazo yaga ban sa ba zai min fada agaban abin so na!"Umma kinga yadda naje da hankalin da Dr.jameel na burge shi amma shi wancan yana son kwafsa mana!"In ji Ilhaam. "Bakomai Auta na(Ilhaam) zan hana shi takura miki in dai kan wannan shigar taki ne saboda nima kin burgeni gaskiya telan nan ya fidda ke sosai kamar wata balaraba zan Baki 5k kikaai masa goron dunkin nan." "Kai Ummana zaiji dadi jibi yayi min Wanda yafi wannan duk da na biyasa kudin aikinsa amma yaba kyauta tukuici nagode Umma." "Suna cikin firar ne su salman suka dawo bayan sun kammala Dinner dinsu." "Bayan sun zauna Hajiya tace ke Ihaaam ku kuma dayan falon keda Jameel zanyi magana da Yayanki." "Okay Umma,Ikharam tace cikin jin dadi suka bar wurin ita da Dr.jameel." "Salman yace Hajiya kina fa gani hijab nace tasaka kafin ta tafi, hakan zataje Kamar wata bamaguza!" "Kai dataka!"Kasan batada tarbiya da kamun kai shiyasa zataje hakan!"ka fita idona in rufe!"Nasha fada maka kadaina takurawa Auta!"Amma bakaji to bamaguzar ce!"Kuma hijab bazata sa ba!"Ni na hanata Dan ba ta'aziyya ko Islamiyya zataje ba!"Dan ba ku maza ke sawa ba!"kasan yadda yake da takura!"Naga dai ba bare agidan nan, daga Ni sai kai da kuma abokinka ne,Kuma kai da shi tun kuna yara kuke tare yasan kurciyar Ikhram duka, kuma aurenta zaiyi ka ko ga ai anzama daya!"To waye acikin mu Autanah zata sawa hijab!"Ka fita harkar 'yahtah na gaya maka!" "To Hajiya Ayi hakuri."Salman yace cikin ladabi." "Naji!Kasan dalilin tsayarda kai nan!" "A'ah Hajiya.........." "Magana zamuyi kuma umurninah ne ba shawara nike nema va bana bukatar comment dinka ko guda!!!!!........." BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ® PEN WRITERS ASSOCIATION Page 31/35 _Wannan page na Ku ne, Masoyan Nabeela Dikko Novels, ina ganin sak'on Ku abin da yawa shiyasa ba kowa nakewa reply ba, amma nagode sosai da kulawa, na samu tsaikon typing sanadin zazzabi da nayi na kwana biyu amma_ _Alhamdullilah na samu sauqi sosai na kuma gode da addu'oinku da fatan alherin Ku agareni, kusani ina tare da Ku,A duk inda Ku ke kuma kwarin gwuiwar da kuke bani shi ke kara sa ni ina sanbadou muku novels masu ma'ana,Ba na mai da hankali kan soyayya a novels dina manufar rubutuna nikeso ku gane Ku dauki darasi mai kyau acikinsa Nagode Nagode Allah ya bar zumunci Ameen._ ________________________________ "Misalin karfe sha biyu da rabi na rana "Minal ce zaune a katafaren falon ta ita da mummynta su na tattaunawa bayan mummy ta bata labarin yadda sukayi da Hajiya mai gado sarai." "Minal taji dadi ba kadan ba kuma ta nuna farin cikin ta tare da jinjinawa mummynta bisa ga kokarinta domin ganin ta samu farin cikin ranta wato Yaya salman." "Mummy kara kwantar mata da hankali tayi tare da alqawarta mata irin shagalin da za ayi alokacin auren na su." "Murnar minal ta qaro ta ce agaskiya mummy ina alfahari da samunku da nayi amatsayin iyayenah kuna so na matuka." "Babu komai Minal idan bamu so ki ba wa zamu so?Ke kadaice Allah yabamu amatsayin 'ya kinga dole muyi kaffa kaffa da rayuwarki bamuson abinda zai dameki bare ya bata rayuwarki ko menene Minal dina," "Okay mummy yanzu zamu fita ni da Nidal Nasir zan bi ta gidansu mu wuce." "Ina za ku tafi Minal naga baki cika fita da wuri ba idan ba office zakije ba?" "No mummy karki da mu idan muka dawo zakiji." "To Allah ya tsare ki gaida Umman minal din." "To mummy zan fada mata bye!"Minal tace tare da daukar keys din motarta da glass dinta ta wuce." "Hajiya Zainab ko tashi tayi tabar part din minal da tuni 'yan aikinta suka fara gyarawa ta wuce nata sashen cikin jin dadin ganin minal ta sake sosai." "Salma ta shirya tsaf acikin wata yar kodaddiyar atamafar ta super java orange da hijab dinta har qasa tayi kyau matuka"Kayanta ta ke cusawa acikin wata jikka(Gari yayi zafi)Babanta kawai ta ke jira suyi sallama ta wuce Filende."Inna Baraka ko sai faman sakon gaisuwa ta ke ba salma zuwa ga yan uwanta da dan tarkacen kayan yaji da tsintsiyar sharar daki tace akaiwa qannanta." "Da kwantancen da Akayiwa Nidal har suka karaso kofar gidan bayan tayi parking ne ta kalli Nidal fuskarta dauke da mamaki tace Anya Nidal bakiyi batan kai ba!"Kin ko gane gidan sosai nifa tunda muka shigo unguwar nan nake kwankwanton da gaske ne Danbasaja yayi miki aikin kwarai kar dai address din sa na karya ne dan kawai yaci kudin Mu ne."Minal ta fada cikin mamaki!" "Hmnnnn....kawata kenan wallahi Danbasaja bai min hakan duk iskancinsa yana tsoron nawa dan yasan banda mutunci zanyi masa wankin babban bargo nan ne dai gidan da mukasa shi aiki akai Minal !" "Mtwsssss nan ne gida ai ko mahaukata ba zasu iya rayuwa anan ba!"Ni kinga ki fara shiga daga ciki idan nan ne kiyi flash dina!"Bazan iya shiga wannan banzan gidan ba Kada ma mu dauki wata cuta aciki!"In ji minal cikin jin haushi!Da takaicin abnda take tunani!"Azuciyarta!" "Okay bara ni na Shiga din nagani ko nan ne ." Nidal tace ta fita motar ta zarce zuwa hanyar shiga cikin dan akulkin gidan." "Inna Baraka na cikin daka taji motsin mutum batare da ta dago kanta ba, tace haba salma ba dai har kin gaji da jiran Malam din ba kiyi hakuri tunda yace ki jirasa mana kila Ma wani dan abu ne zai saya yabaki ki qara ga tsaraba!" "Mtwssssss duk da gidan naku kamar na mahaukata hakan ashe har abubuwan da ke ciki suna da cutar hauka!Ba zanyi mamaki ba dan naji kina magana ke kadai dan na karanta tun akofar gidan naku "Nidal ta ce cikin gadara." "Inna Baraka tabarya ta fitar cikin turmin tace baiwar Allah daga ina cikin mamaki da tsoro?" "Ke malama kiyi min shiru ba wurin ki Nazo ba nan gidan su Salma sufyanu mai walda!?" "Eh!"Nan ne ni ce Innarta kar dai laifi tai miki?"Inna tace cikin sanyin murya saboda daga ganin shigar Nidal tasan batada mutunci dan kamar ba yar hausawa ba." "Fine good tsohowa ki kirata batayi min laifi ba magana kawai zanyi da ita in ji Nidal sannan ne ta dannawa qawarta minal kira ta ce ki shigo nan ne gidan nasu ta maida wayarta ajaka!" " Inna Baraka tace bari in kira maki salma, jikinta na tsuma ta fara kiran sunan Salma ." "Hankali salma ta amsa tare da kinkimo jakarta saboda taji magana awaje ta dauka Ko Baba ne ya dawo tafiyarta ta tashi."Sai dai me wata mai kama da kabila ta gani tsakar gidan tsaye!"A jiye Jakarta tayi a gefe." "A hankali ta qarasa wurin da Innarta ta ke tsaye ta ce Inna lafiya!?" "Lafiyar ce zata kawo mu wannan makararran gida a bahagon tunaninki na dabbobi ko ban tambaya nasan ke ce Salma!"Sannu 'Yar matsiyaci da matsiyaciya!"A Jere ta zubo wadannan magangannu kafin ta karaso!"Minal Kenan." "Haba malama ya zaki shigo mana gida ko sallama babu kuma cike da magana maras dadin ji bare sauraro!"In ji Salma cikin bacin rai tana kallon su!" "Dariya Minal tayi tare da karewa gidan kallo tace wannan ne gidan!?Aini wallahi na dauka ma gidan ajiye gawar mahaukata ne!"To bazamuyi sallamar ba bamu iyaba sai ki koya mana!" "Inna ta ce kuyi hakuri bayin Allah kunga bai kamata ku shigo har gidanmu ba sallama ba maganarki sannan kuce zaku ci zarafin mu shin daga ina kuke?Me ke tafe da Ku?" "Minal cire glass din idonta tayi ta kalli inna da salma da ke tsaye ta watsar sannan ta maida glass din mazauninsa tace Ashe dai tsohowar nan kina da sauran hankali da kinka iya tambaya wadda ta dace!" Sunana Minal ni ce Matar da Dr.Salman zai aura nan da sati biyu nazo in muku kashedi ke da yarki ance min Ku mayu ne idan kun kama Baku saki!"To kusani kurwar yayanah Salma tafi madacci daci!"Daga yau babu ke ba mijina idan ba haka wallahi zansa a batarda ke a duniya!"Kisani salma nafi karfinki haka ma Yaya salman yafi karfin 'Yar tsiya Ahlil kwakwaf irinki!"Kije ki nemi dan talakawa kamar ke ki Aura!"Ni minal nice zabin salman kuma ajinsa ba ke ba banza ballagaza!"Narasa me ya gani yake so in banda kaddara an magancesa daga talla watakil!" "Tabbas haka yake qawata inji Nidal sannan ta karasa wurin Salma ta dafata ta ce"Malama Salma wannan umurni muke baki ba shawara ba!"Wane karambani ya kaiki ga mannewa dan masu Arziki saboda kwadayin abin duniya!"Ki duba acikin fadin qasar nan tamu ta Nigeria gaba daya atarihin auren 'ya'yan mayan mutane duk auren bani gishiri in baka manja akeyi haka gefen talaka sai talaka to akanki kike son afara auren kunya da takaici!"Auren da ba za'a iya wani abun azo agani ba!"Gwara tun wuri ki kama gabanki kije can ki nemo mudi ko tanko ki aura dan Dr.Salman na Brr.Minal ne ita kadai idan ba haka ba daga ke har iyayenki zaku hadu da Bala'i da cin mutuncin da zai iya zama ajalinku.....!" "Hannu Salma tasa ta kabe hannun Nidal da ta aza a kafadarta cikin fushi ta ce Wallahi kunyi kadan kuma ta Allah ba taku ba!"Kusani kunyi kadan Ku shigo gidanmu kuyimana abinda kukaga dama!"Ni ban damu Salman ba ku ya dama da har zaku zo fada da rashin mutunci akan shi kuma shi ke bibiyata !"Shi ke so na!"Kuje Ku masa fada ya daina sona!"Sannan kisani ke Minal dukan da nayi maki yafi wanda zakiyi min har abada!"Ni zuciyata kika daka saboda ki gayamin magana mai zafi!"Amma ni rayuwarki na daka inda baki ganin ciwo bare ki magani!"Na lura son maso wani kikeyi to kisani sona da kaunata sun riga da sun zama jinin jikin Salman."Duk da kasan cewar ina diyar talakawa amma a hakan nayi tagomashi da farinjini awurin shi duk dukiyarsa yace yana sona!"kuma Ina da masoya ban taba maular masoyi ba bare tada harshe na akan shi, nagode Allah!"Kuma har gobe ina qara gode masa da baiyi min kwakwalwa irin ta jahilan dabbobi ba, da bazan iya bambance tsakanin Kaddara mai kyau da marar kyau ba, Alhamdulillah mu talakawa ne kuma muna alfahari da jarabawar ubangiji kuje diyan masu arziki da za'a saku kabari da arzikin Ku....!" "Taaataasss!!taas!Salma taji saukar marin da minal ta yi mata cikin fushi!"Har ta daga hannu ta rama tayi daidai shigowar Babnta sai ta fasa!" da sauri ya qaraso yace subhanallahi!"Baraka lafiya?Me salma tayi musu!?"Salma ban yadda ki daki kowa ba acikin su kiyi hakuri!" "Salma da ke dafe da kuncinta tana zubda hawaye ta ce toh Baba!" "Dariya sukayi suka tafa minal tace haba tsoho ai idan yarka ta tabani to da baki dayanku sai kun mutu agidan kaso dan ba wanda ya isa ya fito da Ku!" "Ke kuma kashedi zan miki na karshe kisani idan ina magana ba'a mayar min da martani ko martani masu zafi ki kiyaye ni, kuma ba ke ba mijina, banza! mai bin maza! 'Yar iska! matsiyaciyar banza!"Minal tacewa Salma." ta kalli Baba da Inna da ke zugum suna sauraren su tace nadawo kan ku"Tsoho da tsohuwa nasan......." "Da sAuri ya karaso wurin....Yaya Habu shin lafiya mukaji hayaniya na tashi inji kawu tare da su karime ko wanne lungu na gidan kowa ya fito yayi tsaye suna kallon minal da Nidal cikin shigar su ta rashin mutunci!" "Minal cigaba tayi da maganarta ina son kujawa yarku kunne tafita da harkar mijina Dr. Salman nasan kuna sane yafi karfinta amma saboda kwadayi da son abin duniya kunka kyaleta!" "Kawu Bala ya amshe maganar minal yace"Hakane wallahi sai da na fadawa yarinyar nan da Yaya habu ku fita harkar yaron nan mai kudi kun kace shi ke bin salma Ai ga irinta nan dama ance kwadayi mabudin wahala!Azo har gida aci mutuncin mu!""Dan Allah kuyi hakurii...!!!Dakata Bala suwa zaka ba hakuri wadan nan yara marasa tarbiyya da mutunci!"Kufita Ku bamu wuri marasa kirki yara!"Baba yace ranshi abace." " Jakarta ta bude bandir din kudi yan dari biyar ta dauko da batasan yawansu ba ta jefawa Kawu Bala cikin gadara da sauri ya capke kada sukai kasa," Tace goronka ne na fadin gaskiya kai kuma tsoho meye acikin gidan ko dai kango ma," ai wannan baikai darajar akira shi da gida ba!"Zamu tafi amma kasani yarka ce marar mutunci ba mu ba!"Mu tafi Nidal tsaki Sukayi suka wuce su ka bar gidan." Kawu Bala har yaso yabisu yacewa minal ya gode da wadannan dambun kudi da tabashi amma yana tsoron Yayansa saboda ya ga ranshi ya baci matuka!"saurin Barin wurin yayi kowa ya bishi saboda kudin da yasamu suma araba da su!" "Salma barin wurin tayi tana kuka!"Dan anci mutuncinta da na iyayenta amma ta dauki alkawarin sai ta ramaabinda Minal tayi mata tunda har Salman na sonta to aikinta da kudurinta zaizo da sauqi!" "Inna baraka ko kayan salma ta duka ta kwashe ta shiga cikin dakin tana share hawayenta!" "Baba ko Alwala yayi yabar gidan zuwa masallaci saboda aduk sanda ranshi ya baci can ne wurin zuwansa sai ya huce ya dawo gida!" BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ® PEN WRITERS ASSOCIATION Page 36/40 *"An karbou daga Abih sA'idul khuduriy (R.A)Ya ce,"Annabi Muh'd (SAW) ya ce"Hakika Mafi sharrin mutane,Masu mummunar masauki agurin Allah ranar Alkiyama sune wadanda mutane suka guje musu saboda yawan ayyukan su na Alfasha(Marasa kyau)."Bukhari ya ruwaito."* ________________________________ "A hanyar su ta komawa gida sai murna sukeyi suna shewa saboda sunyi abinda ransu ke so." "Nidal ta ce,"Kin san Allah minal magangannun da kika yiwa baban salma sun min zafi saboda haka kawai naji ya bani tausayi!" "Mtwsssss amma ke Nidal anyi sakarya shi talaka maras gata kuma uban makiyiyar ta wa!wadda na tsana aduniya zakice kin tausaya masa!"Kenan har salmar kina so kuma kina tausayi ko!? saboda naga so yana tare da tausayi!"Minal tace tana duban Nidal cikin tuhuma! tare da sauraren amsar da zata bata." "Haba!Qawata ta yaya zan so salma?Kawai a lokacin da kike musu madifa ne sai naga kamar bamu kyautawa iyayenta ba!Domin ba laifin su ba ne,Laifin na Salma ne!"Amma ya wuce ai mun musu horo mai shiga zuciya bazasu manta da mu ba kuma bazasu qara Shiga gonar mu ba!"Ko ba komai Barazanar mu zata hori kwadayin su." "Atou Ni har kinsa nafara jin haushin ki saboda na tsani salma da duk wani da zai so ta wallahi!" "Ni kinga ma abin haushi da takaici da yafi tsaya min arai bai wuce wancan bagidajen ba wato Yaya salman shi kuwa wace bacewar basirace zata sa shi ya so wannan kucakar dabbar yarinya da bata wuce ko sa'ar Suhaima ba (Qanwar Nidal) ni duk na raina ajin shi da miskilancinsa!"Abin ban takaici!"Da ban haushi wai akanta ma ne yake wulaqanta yake cin zarafina!"Na dauki alkawarin illatah banzan nan matukar bai fidda ita a rayuwar sa ba!"Sai naga bayanta, Nidal!"Qarashe maganar minal tayi muryarta na rawa yayinda ta qara gudun motarta saboda bacin rai!" "Kiyi hakuri qawata komai ya zo karshe ke da Salman mutu ka raba!"Ba wani banza dan banzah da zai raba ku!"Ai yar gata sai dan gata Tawan." "Murmushin jin dadi Minal tayi,Domin maganar Nidal tasa taji sanyi aranta da hakan suka cigaba da firar su a hanya suka tsaya *Marhabah Super market* suka sayi ice cream da sauran kayan makwalashe suka wuce abin su zuwa gida cikin jin dadi." "Salman ne zaune a office dinsa duk wunin ranar bai ayyana aikin komai ba, fa ce tunanin sahibar sa Salma, babu abinda yake kona masa zuciya, irin yadda Salma tai masa gatanga da gidan su."A hakan yayi zaune da dakon tunaninsa inda agefe ga patients na ta jiran sa amma ya ce anema musu wani doctor shi baya jin dadi da hakan yayi sallama da amininsa Dr.Jameel,"Shi kuma yayi haramar komawa gida har ya kama hanyar gidansu amma kasa jurewa yayi karya kwanar da zata sada shi da unguwar su Salma yayi domin bazai iya jure rashin ganin ta ba na tsawon mako biyu!." "Tsaye yake a kofar gidan,"Bayan ya aika yaro a sallamo masa ita a zuciyarsa yana fargaba kar dai tace bazata fito ba!"Yana cikin zancen zucin ne sai ga yaro ya dawo"Wai tace bazata zo ba kuma kayi hakuri ka koma inda ka fito"Yaron ya ce yabar wurin!"Subhanallah!"ya fadi afili me na miki salma da zaki yi min wannan danyen hukunci... !" "Ba salma kayiwa laifin ba Salman mahaifiyarka da matarka da dukkan danginka kayiwa laifi da kake neman dauko cuta ka kai acikin zuri'ar Ku!"Baba ne da tun fitar su minal da yaje masallaci bai dawo ba sai yanzu ya ba Salman amsa.!" "Kamar daga sama Salman yaji zancen Baba abin yazou masa wani iri!"A ladabce ya durkusa ya gaida Baba cikin nutsuwa da sanyin jiki ya koma irin kalar tausayi nan!" "Amsa masa Baba yayi kana ya ce"Ina fatan lafiya Salman saboda ina so ka fita hanyar 'yatah Salma kaje ka rike matar da zaka aura!"Ka bi umurnin mamanka ka cikawa danginka burin su domin *BAK'AR AK'IDAR* su bazata barsu ka auri wacce zuciyar ka ke so!"Domin haka bakai ba salma!" Kasan kafi karfin salma Mu talakawa ne ba masu arziki ba!"Kuma Salmata bazata iya zama acikin daula ba, saboda bata taso acikinta ba!"Abin da nikeso kaja motarka kabar mana kangon gidanmu yanzu matarka da qawarta suka zo har gidanmu sukaci mana zarafi bamuji bamu gani ba!"Tun farkon haduwarka da Salma na sanarda kai kafi karfin ta mu talakawa ne, ba mutane muke ba acikin duniyar masu arziki!"Dan haka ina maka fatan alheri kuma ina code maka abisa son diyata da kakeyi da zuciya daya batare da tsangwama da dubin *BAK'AR* *AK'IDA* irin ta ku masu hali ba!"Nasan kana da mutunci kuma ina ganin mutuncika da kimarka salman to ka rikesu dan Allah daga yau kar ka qara neman Salma!"Nagode ka iya tafiya."Baba yace wa salman da tuni duniyar sama ke masa yawo maganar Baba ta yamutsa masa kwakwalwa!" "Ganin Baba da gaske gida zai wuce abinsa ne yasa yayi saurin dawo hankalinsa ya durgusa kasa ya ce"Dan Allah Baba kayi hakuri kada ka hukunta ni akan abinda bani na aikata wallahi ni kaina na tsani *BAK'AR AK'IDA* nan tasu da batada asali da amfani na yarda samu da rashi duk na Allah ne kuma da talaka da mai kudi duk daya ne babu banbamci domin duk bayi ne na Allah!"Baba karku rabani da salma ina sonta tana sona kawai akan *BAK'AR AK'IDA*"Baba nasan Minal ce tazo tayi muku rashin mutunci kuma zan dauki mataki Dan Allah kuyi hakuri!"Salman ya ce yana zubda hawaye!." "Tausayinsa ya kama Baba tallafosa yayi ya tashi tsaye yace babu komai Salman mun yafe maka bakai mana laifi ba!"Kuma munyi hakuri zan fadawa Baraka da Salma nasan zasu hakura Allah shi maka Albarkah!" "Amin Baba nagode." "Babu komai ni zan shiga daga ciki." "Baba dan Allah kaimin alfarmar inga salma in bata hakuri!" "Ba yanzu ba!Salman nasan salma bazata Saurareka ba!dan nasan cewa ta tsani ganin Bacin ranmu!"Ga shi yau agabanta anci mutuncin mu kuma na hanata daukar duk wani mataki da taso dauka saboda gudun hayaniya!"Amma ka tafi zan fada mata!" "To Baba ina gaida su zan dawo idan an kwana biyu ta huce nafiso nabata hakuri da kaina!" "To Salman Baba yace,tare da murmushi saboda yagano lagon shi, Da kallon tausayi ya bi Salman da yayi wani zuruzuru kamar wanda ya kwanta ciwo" "Sallama sukayi Baba ya Shiga gida Salman ko ya wuce Direct gidansu Aunty Zainab ya wuce saboda ya hasala da minal amma yasan ta ina zaiyi maganin iskancinta da rashin mutunci!"Shi zata rainawa hankali!" "Hajiya Maigado ce zaune a bedrum dinta gefenta qawarta ce Hajiya Raliya zaune agefen gadon da aka cika da laces,super,materials da sauran kayan da zasu bukata na bukin saboda shiri ake yiwa Auren na musamman." "Hajiya Raliya cikin kulawa ta dubi qawarta tace,Yanzu Hajiya Bilki kina nufin duk tulin kayan nan masu tsadar gaske kin saye su kenan?" "Dariya tayi tace,sosai qawata wannan ma soman tabi ne sai munje Dubai."Karfa kin manta aure ne yan dangi yn gata wadanda suka gaji arziki kinga dole ne mu nunawa duniya naira ta zaunu."Har tana kuka da hawayenta!" "Lalle kice min zamu sha mamaki, kuma mu kan mu muje mukara shiri kan wanda mukeyi, saboda na lura auren nan na fito na fito ne,"To kenan dole ne mu kure adaka,ka da ayake mu afimu wanka mai cizo zan sauya wani sabon shiri"Hajiya Raliya tace cikin dariya da raha." "Murmushi wanda yafi kuka!Ciwo Hajiya mai gado tayi tace Bari Hajiya Raliya abu daya ne ke ci min tuwo a kwarya wanda idan na tuna sai naji farincikinah ya gushe!"Shi ne yaron nan da har yanzu yaqi yarda ya so minal!"A kan tilas ne zaiyi auren dan kawai na tashi tsaye ne akansa!" "B'ata fuska Hajiya Raliya tayi cikin mamaki ta ce wai shin kina nufin Har yanzu Salman bai ce yana son minal ba!?Kuma a hakan zaki xuba ido ya aureta!?To meye ribarki dan kinyiwa danki Auren dole!?Ina iliminki da tunaninki ina wayewarki Hajiya mai gado!?"Salman danki ne mai miki biyayya idan har kin kayi masa hakan baki masa adalci ba d'a ne abin alfahari ga kowa!" "Kiyi hakuri qawata nasan cewa Zainab qanwarki ce kuma jininki bazan iya bata alakar Ku ba kuma bada wata manufa zan fadi maganar nan ba sai domin ita ce gaskiya!" "Shakka banayi Zainab bazata yiwa yarta minal auren dole ba!"matukar salman ke son yartah, batason sa." To Da tuni an wuce warin,"Kisani yanzu farinciki ne take nemawa minal." kuma tana sane da cewa shi fa bayaso!"Aini aganina dukkansu 'ya'yanta ne, da babu son kai aciki da ta hanaki tilastawa Salman dan ganin an masa adalci a rayuwa!" "Shawarata ki so abinda danki ke so, ki kuma taya shi neman farin cikinsa!"Meye aibun ita wadda kinka taba fada min yana so kwanakin baya?" "Hajiya mai gado da jikinta yayi likis tace Batada aibu face talauci da yayi musu katutu a rayuwa!"Gaba da bayansu talakawa ne kinga idan nabari ya aurota sai aitayi damu a dangi ya zama na farko da ya fara auro bare (Talaka)Acikin zuri'armu kuma kinsan irin su ance abin biyarsu yakeyi har gidan aure!"Shi nike gujewa Salman kada ya auro mai farar kafa asamu abin yayatamu a dangi."👸🏻👸🏻 BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ® PEN WRITERS ASSOCIATION Page 41/45 " *Wannan page na ku ne Dangi na Dikkon Kebbi and Madawakin Kebbi Family's Allah ya sanyawa zuriya ALBARKA Ameen.* " _"3rd February 2019,Wannan ranar ta kasance daya daga cikin ranakun alfahari da bazan manta da ita ba a rayuwata Alhmdllh acikin matakai rayuwa na samu nasarar d'ane mataki na biyu Fatana Allah ya tabbatar mana da alheransa Amin Nagode 'yan uwa da Abokan arziki Allah ya sanyawa zuriya Albarka yabar mu tare Amin summa Ameen."_ 🤝🏻 ________________________________ "Amma a gaskiya Hajiya Mai gado kin bani mamaki yanzu akan wannan *BAK'AR AK'IDA* ne da batada asali bare tushe maras kan gado kike son takurawa rayuwar Salman."A wane hadisi ko aya aka hana mai arziki auren talaka!Tabbas talauci bai da dadi domin Annabi(SAW) ya ce mu nemi tsari daga talauci!" Amma kuma ba'a hana auren talaka ba!"Domin mutum ne kamar kowa!"Samu da rashi duk na Allah ne!"Ki gyara imanin ki Hajiya Bilkisu ki gane cewa Ko ke baki wuce komawa talakar ba jarrabawa ce ta ubangiji!"Ki bar salman ya auri wacce yake so."Saboda shi talauci ba'a gadonsa kuma arziki na Allah ne!"Inji Hajiya Raliya cikin yanayin damuwa." "To Hajiya naji zancen ki amma yanzu ta ina ma zan fara!"Yanzu ya zanyi da dangina da Minal!."Hajiya mai gado tace fuskarta dauke da danasani!" "Babu abinda za kiyi sai dai kiyi kokarin toshe kunnuwan ki daga sauraren zantukan mutane!"Sannan auren minal da salman yana nan daram matukar ba ita tace bazata iya zama da kishiya ba!"Domin kokari za'ayi a hade auren har na salma kinga sai ayi mai gaba daya ko ya kika gani?" "Nikam ina tsoron lamarin nan yadda zai zo!"Ina jin kunyar yarinyar nan salma da iyayenta saboda har gidansu naje ba kalar masifar da banyi musu ba!"Akan su fita harkar d'ana yanzu kuma inje amatsayin mai nema masa aure kinsan na tsani awulaqanta musamman a inda nafi karfi!" "Kada ki damu zamuje mu basu hakuri kuma nasan cewa suna da ilimi bazasu wulakanta mu ba!Kawai ki sa muna rana mutafi kuma kar ki sanarda kowa har salman din sai munga yadda lamarin zai kasance"Hajiya Raliya ta ce tare da haramar komawa gidanta." "Sallama sukayi da Hajiya Mai gado inda ta qara godewa qawarta ta bisa ga ankarar da ita da tayi!"A kan lamarin Salman." "Da sallama Dr.Salman ya shiga falon Aunty Zainab zaune ya sameta ya gaidata cikin ladabi tare da tambayar minal." "Amsawa Aunty zainab tayi cikin kulawa sannan tace to sun fita ita da qawarta minal tun dazu basu dawo ba." "Dr.Salman ya ce,okay Aunty zainab ba damuwa daman nazo ne dan ta bani list din abinda kawayenta ke bukata na dangane bukin nan ne kuma in dauketa saboda daman hajiya ta ce"In daukota." "To Salman idan tazo ni zan kawo maku minal da kai na Aunty zainab tace fuskarta dauke da murmushin jin dadi." "Yayi Aunty zainab ni zan wuce dan Allah ayi hakuri da duk abinda ya faru a baya Aunty!"Dr salman ya fada a yanayin damuwa!" "Bakomai yarona duk komai ya wuce Allah ya yafe mana ka gaishe min da yaya mai gado." "Zan gaya mata in shaa Allah Aunty sai na dawo."Salman ya ce"Ya wuce a zuciyar sa ko tausayin Aunty da Minal ma yakeyi!"Allah dai yasa ya samu nasarar abinda ya shirya da hakan yabar gidan yana tunanin mafita." "Assakamu Alaikum." "Amin malam sannu da dawowa."In ji Inna Baraka tare da shinfida masa tabarma kusa ga kofar dakin nasa."Suka zauna dukkan su." "Yawwa Baraka ya gida.?" "Lafiya lau malam ka dawo ka sameni ina ta masifa da yaron nan salmanu yanzu nan ya aiko yaro aimasa sallama da salma nace bazata ba!"Da yasan rashin kunyar da akai mana yau akanshi da bai zo ba wallahi!" "Baraka kenan!"Ai yanzun nan muka rabu da shi........" "Salma da ke kwance a uwar daki ta kashe kunnenta ne ta zabura ta tashi saboda taji me Baba zai ce cikin faduwar da fargaba ta tashi." kwanon fura da abinci ta Baba ta dauka ta fito waje ta ajeye masa tare da gaida shi."Tana kokarin komawa daki Baba yace "Salma dakata!"Magana zamuyi!" "To Baba salma tace tare da zaunawa akasa tana fuskantar su idanuwata sunyi jajur saboda kuka!"Ta dukar da kanta a kasa tana sauraren jawabin Baba." "Yanzun nan muka rabu da salman Wanda zuwa yayi kawai domin ya gaishe ya ganki kamar yadda ya saba!"Sai kuma ya sameni awaje nayi masa bayanin duk abinda ya faru dazu amma fa mai faduwa da sauraruwa dan barna batada dadi!"Kuma naga rayuwarsa ta baci da jin labarin nan ba yadda baiso ya shigo ya Baku hakuri ba!"Dai dai ni na hana shi!"Saboda nasan baku huce ba!"Ina son kuyi hakurri Ku yafe masa da zuciya daya!"Saboda yaron yana kirki kuma baida labarin sun zo dan haka abin ya wuce Allah ya sauwaqa ki shirya gobe ki wuce Felende Allah yayi miki wani zabin nagari kinji koh." "Kanta ta daga ahankali alamar"Eh" "Tace Inna,Baba dan Allah kuyi hakuri.....Dakata salma munyi hakuri babu komai bakida laifi agurin mu har shi salman din " *BAK'AR AK'IDA* ce irin tasu ta masu arziki!"Tashi je ki abinki Allah yayi maki ALBARKA." "Amin Baba Nagode."Salma ta ce tare da shigewa dakin tana jin dadi saboda ba shakka haqar ta tayi kusa cimma ruwa.!"Minal zata dandana kodar ta!"Da yardar Allah." "Inna Baraka ta dubi Malam cikin jin takaici "ta ce Malam gaskiya naso ace ka nunawa yaron nan bakaji dadin hakan ba!"Ai cin mutunci da zarafi ne!" "Ai shi ba mahaukaci bane Baraka zai fahimta mana kuma bacin ran sa da ya nuna yasa nagane baiji dadi ba shi kan shi!"Abar maganar ta wuce Allah ya yafe mana!" "Ameen."Malam,Inna Baraka tace tare da sauke ajiyar zuciya."Malam ko abincinsa ya fara ci."Suka cigaba da firar su ta duniya kamar komai bai faru ba." "Minal da Nidal ne suka kara so part din mummy cikin dariya da shewa." "Mummy ta ce kai amma kunyi sabani da yayanku yanzu ya fita." "Haba Mummy bagan shi ba me yazo yi ne?" "Wurin ki yazo mana."Na ce kun fita run dazu Baku dawo ba!" "Ayyah mummy ai mun dawo da dadewa abinci muka tsaya ci apart dina kuma ina dawowa nabawa garbati motana ya kai agyara min problem take bani kwana biyu!" "Ai bansan kuna ciki ba!"Da nace masa kuna nan saboda ba motar ki."Abinda yafi ma a canjawa miki mota yafi gaskiya!" "Nidal ta ce mummy yau munyi abinda ranmu ke so gidan su matsiyaciyar can Salma mukaje muka keta musu rigar mutunci munja musu kunnuwa kuma barazanar mu ta shige su sosai." "Aunty Zainab ta ce haba dai yan albarka wallahi kun kyauta min da bakuje ba da ni zanje in musu kashedi na karshe!" "Minal ta ce haba Momy aini zanyi maganin maitar su!"Mutane kamar almajirai!"Matsiyata da su!" "Nidal da minal cigaba sukayi da ba mummy labari irin rashin mutuncin da sukayi agidan su Salma." ."Mummy ko sai dadi takeji tare da yaba musu dan sun burgeta kuma hakan ne daidai da talaka mai karambani acewarta." ( _Ya kamata iyaye mu lura mu kula da tarbiyyar yaran mu idan sunyi ba daidai ba atsawatar musu kadamu zuba mana su ido sunayin abinda rayuwar su ke so Hattara iyaye!"👂🏼) BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 46/50 *Meyetti Kwirei Allah Suddo'on Asiiri Duniyaro i lahira Ameen* 😍😍😍 "Yau ta kama Assabar saura mako daya auren Dr salman da Minal tuni aka fara shiri haiqan na budurin auren a dayan bangaren kuwa Salma makon ta daya a qauyen su Innarta Felende." "Tuni soyayyarta da Dr.salman ta dawo sabuwa dan suna waya sosai kuma ya bata hakuri dangane da abinda su minal suka aikata musu!"Da hakan ta hakura kuma dangin innarta kowa ya yaba da salman irin yadda rayuwar shi ta ke kmr ba mai arziki ba saboda yana zuwa wurin salma din amma asace batare da sanin Hajiyarsa ba hakan ita ma salma inna da baba sam basu sani ba." "A hanyar su ta zuwan gidan ne qawarta ke mata jawabi da jan hankalinta tare da ba ta muhimman shawarwari masu amfani har su ka isa gidan basuyi mamaki ba saboda sun san yadda gidan ya ke."Fita sukayi a mota su shiga cikin gidan." "Assalamu Alaikum Salamu Alaikum matar ta fada akaro na biyu yayin da dayan ta fara daure fuska alamar rashin jin dadi!"An ki karba sallamar su!"Matar qara sallama tayi...." "Da sauri wata mata ta fito daga bayan gida ta ce"Amin wa alaikumus salam maraba da Ku!"Tabarma ta shinfida musu ku zauna ku hakuri ina kewayawa kuna shigowa!"Kamar ance ta dago kanta sukayi ido hudu da matar da in ba mantawa tayi ba ita ce wacce taci mutuncin su akan danta!"To me yakawo su gidanta?ko sun zo su kara cin zarafinta ne?A gaskiya yau kam bazata sabo ba!?Ta fada azuciyarta a fili ko ta ce Hajiya ina fatan lafiya. Saboda idan ba gizo idanuwa keyi ba naga kamar ke ce mahaifiyar salman nace dai lafiya ba wani abin magana diyatah ta koma jawo min ba!"Inna Baraka ta ce ma Hajiya Mai gado da tuni kunya ta fara rufeta ganin yadda inna har wurin zama ta ba su." "Murmushi Hajiya Raliya tayi kana tace ba abinda ya faru Maman salma mun zo ne mu baku hakuri Dan Allah ayi hakuri komai ya wuce shi ne Maman salman din tazo da kanta ta ba Ku hakuri." Inna Baraka ta ce babu komai amma Hajiya da ciwo kam kananan yara suzou har gida su ci mutuncin mu abin takaici har mahaifin yarinyar nan yaran nan basu ragawa ba!"Ni shi ne abinda ya bani haushi..." "Daga Hajiya mai gado har Raliya duban Inna sukayi da mamaki dan basu fahimce ta ba!" "Hajiya mai gado ta ce kuyi hakuri amma suwa ne suka zo nan gidan bayan ni!?" ''Inna ta ce"Ko minal sunanta da kawarta marar kunya ba abinda basu ce mana ba! A gidan nan duk kowa na gidan nan na tsaye agabansu kuma a kan salman ne wai ita ce wadda zai aura salma ta fita harkar shi ba dai barazanar da basuyi mana ba mu kuma ba ruwanmu mun barwa Allah lamurran mu ba dai mutum ba!" "Subhannallah! Hajiya Raliya ta ce tare da kallon Hajiya mai gado ta ma rasa ta ina ne zata fara!" "Ta ce Dan Allah Maman Salma ayi hakuri abawa Malam hakuri!" kin san dan yau!"Wallahi mu bamu ma san sun zo ba kuma za ai musu fada ai an zama daya mu da ku komai ya wuce duk sharrin shaidan ne.....!" "A'ah Hajiya mu da ku ba guda ba!"Ina talaka bawan Allah, ina mai kudi!"Kinga akwai bambanci kuma hanyar jirgi daban da ta mota !" Sannan *BAK'AR AK'IDA* irin ta ku ta manyan mutane ita kesa kuna ganin sam talaka bai dace da Ku ba! Ku nemi wulakanta shi!"Dan haka komai ya wuce Allah yabamu hakuri da juna ya hada kowa da rabon sa!"Salma zatayi aure amma talaka dan uwanta shi ma salman din ya zauna da Yar uwarsa jininsa yafi sauki kunga kwarya tabi kwarya kamar yadda *BAK'AR AK'IDAR* ku ta tanada!"Allah yayi mana mafita ta alheri." "Amin Hajiya Raliya ta ce yayinda Hajiya mai gado jiki yayi sanyi, ko ba komai Inna ta saka musu magana!" "Daman abinda muka zo yi shi ne ban hakuri da kuma Neman alfarma agurin Ku Maman Salma, Ga dai qawata nan Hajiya Bilkisu tayi nadama ta gane zabin danta shi ne farin cikinsa har ita kanta,To shi ne muka zo nemawa salman auren yarku salma kuma ashirye muke idan kun yarda a hade da na yar uwarsa minal ayi mai gabadaya."Hajiya Raliya tace cikin tausasa murya." "Inna ta ce Dan Allah Ku rufa mana asiri ina d'an ku mai arziki ina salma yar matsiyata!"Ai ko gari ya watse ba'a kwashe daidai ba!" kuma ni agaskiya bazan iya hada 'yahtah da minal ba saboda ba rayuwar su daya ba,"bata da fitina da son fada kuma bana son a wulaqanta min yarinya akan wata *BAK'AR AK'IDA!."* "Ai kowacce acikinsu da gidan ta daban kuma hakuri dai za ayi adaina tuna baya,Salman da Salma hadin Allah ne ,"kar mu cutar da yaran mu tunda suna son junan su! Dama can rashin sanin illar wannan *BAK'AR AK'IDAR* ne ayanzu mun gane gaskiya *BAK'AR AK'IDA* nan ta auren bani gishiri in baka manja Bakomai bace kuma batada wani amfani bare nasaba!"Kuma Akida ce ta wadanda suka jahilci meye gishirin zaman duniya!"Da Allah a qara hakuri Maman salma yanzu an zama daya komai ya wuce adaina tuna baya"In ji Hajiya Raliya." "To ni ba zance komai ba sai dai idan Malam yazo zamuyi magana Inna ta ce atakaice." "To mun gode ina Yar tamu salma bamu ganta ba har zamu koma." "Dan Allah Ku tsaya ko ruwa baku sha ba fa,salma tayi tafiya taje garin mu sada zumunci." "A'ah ba komai mun gode in Shaa Allah gobe zan dawo in ji kome kun ka yanke shawara akai."In ji Hajiya Raliya. "Mun gode Hajiya mai gado tace,suka wuce yayinda inna tayi musu rakiya har zaure ta sannan ta koma daga ciki." "Dr Salman da abokinsa Dr.Jameel tsaye a bakin office dinsu tattaunawa sukeyi akan zancen auren sa anan yake fadawa Dr.jameel kudurinsa na auren salma a boye batare da Hajiya tasani ba saboda shi ita ya ke so ba minal ba."Kuma tuni ya gama shirin auren nasa abisa yarda da amincewar dangin babansa kuma ya samu nasarar saye kawun salma baban karime domin shi ne waliyyin salma ya ce zai tsaya masa ayi auren domun salma 'yarsa ce!" agefen dangin inna ma tuni suka yaba da hankalina kuma sunce sun bani salma ayi komai a felende na bukin, dAga baya a sanarwa iyayen mu su saka albarka tunda su *BAK'AR AK'IDA* irin tasu ta hana su fahimci halalcin auren mu da salma sai dai dinbim haramci da suke gani!"Dan haka kaji yadda muka shirya abin mu ni da salma kuma zanyi mata komai tun kan sutura har kayan daki." "Ina Neman alfarmar ka taimaka min ka rufe min asirin nan kamar yadda muka saba!"Ka taimaka min domin samun cikar burina Salma!"Ka kuma tayamu da addu ah domin samun Nasara."In ji Salman da ya kare maganar yana kalon Dr jameel." "Numfashi ya saki mai nauyi sannan yace tabbas wannan shi ake kira da gadar zare sai mai rabo zai fita "Ka ga laifin nan abokina har ni sai ya shafa bazan taba fita ba!"Shiyasa nikejin tsoro bana son rayuwar Hajiya ta baci akan mu!" Ba abinda zance Salman sai dai Allah yasa mudace yasa shi ne alheri saboda ina jin tsoron sabawa umurnin iyaye!"In ji Dr.Jameel."Fuskarsa dauke da damuwa!" "Ba abinda zai faru Jameel,kawai ka tayani addu'a dan babu fargaba!"A zuciyata hakan na nuna min zanyi Nasara!"kasan dukkan mu daga ni har salma iyayen mu na sonmu bazasu iya fushi damu na tsawon lokaci ba, zasu yafe mana." "Hmnnnn daga baya kenan."Inji jameel. "Da hakan dai suka Wuce zuwa parking place na hospital din motocin su suka shiga suka wuce kowa da abin da yake tunani a ran sa!" BAKAR AKIDA! 👸 ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 51/60 *"THE VIRTUE OF REMEMBERING ALLAH*:" _Allah the all mighty has said:"Therefore remember me,I will remember you,Be grateful to me and never show me Ingratitude."Al baqara 2:152."_ _And He said:"O you who believe, remember Allah with much remembrance. Al-ahzab 33:41."_ *Subhanallahi wabi hamdihi* *Alhamdulillahi Kaseeran* *Allahu Akbar kabeeran* ________________________________ "Ilham da Hajiya mai gado zaune a cikin katafaren red and black din falon gidan nasu."A lokacin ne Hajiya ke sanarda Ilham duk abinda ke faruwa." "Ilham ta ce"A gaskiya nima tuni na gane gaskiya na fara goyon bayan Yaya salman yanzu hakan ina zumunci da Yaya salma."Dan kuwa muna waya kuma gaskiya tana da kirki nima na goyi bayan abarshi ya auri zabinsa sai ya hada da naki zabin, kuma ina da tabbacin zai musu adalci!"Idan ma ansamu matsala Yaya minal ce kinsanta sarai ba tasan kimar mutane ba!"Kuma nayi faricikin amincewarki Ummana Allah ya qara maki lafiya."Ilham ta ce fuskarta a sake." "Hajiya ta numfasa domin duk zancen autar ta gaskiya ne!"Sai yanzu ta gane rayuwar salman da minal ba daya ba!"Sai dai kaddara ta riga fata!"Ta ce "Ba komai Ilhaam Allah yasa hakan ne alheri!" "Ameen Umma,yanzu kin sanarda Aunty Zainab din da minal?"Sun san da auren?" "Ban fada musu ba!"Ni ina jin abin ba dadi ne!"Kishiya ba dadi!"amma kuma rayuwar salman nike dubi yana bani tausayi!"Sannan iyayen salma har yanzun ba su sanarda Mu Ko sun amince sun yarda da auren duk da nasan Su na da fahimta!" "Umma akwai damuwa a tattare da shi Dan fa tun kwanaki Baby (Dr.jameel)ke sanar min Yaya salman ya kamu da matsanacin ciwon zuciya!" yanzu hakan an daura shi akan magani duk akan ciwon son salma!"Da auren dole da ake son yi masa!"Ya ce kada afada miki ne, ko ni Yaya baisan cewa jameel ya sanarda ni ba!"Dan haka umma hakuri zamuyi dukkan mu, tun da kowa ba wani so yakeyi ba, minal dai jinin mu ce dole mu so ta fiye da salma, kawai a aura masa burin ran sa kowa yasamu kwanciyar hankali shi yafi dacewa!"Inji ilham." "Hajiya mai gado ta ce ikon Allah yanzu shi baida lafiya ya boye min, abinda bai taba faruwa ba!"Duk kusancina da yarana ashe da kadan na rasa shi batare da nasan dalili ba sai dai inji labari a gari !" "Wallahi Umma Allah kadai ya tsare akan wata can *BAK'AR AK'IDA* ta banza da ba amfani bare tushe!"Da mun rasa magajin Abbana Yaya salman shi ne garkuwan mu kiyi hakuri Umma ya auri zabinsa ni kaina banaso hakuri kawai zamuyi dan samun farincikinsa.! "Ai bari kedai auta yanzu kam na gane gaskiya ashe talaka mutum ne,Mai hakuri da juriya,Duba fa duk rashin mutunci da cin zarafin da nayi musu akan salman, ashe minal da Nidal sunje sunyi musu ubansa har citta!"Amma matar nan bata wulaqanta Mu ba!"Sai yanzu na fahimci girman kai!Daukar kai! Da wulaqanci da fariya na ga wad'an su masu kudi kuma masu *BAK'AR AK'IDA* irin ta mu!"Allah ya yafe mana." "Ameen umma gaskiya bamu kyauta musu ba!"Da masu saurin fushi ne bama zasu saurare ku ba!"Yanzu Ni zanje na karbo dinkin nan namu na dinner idan telan ya qare Umma." "Kada kiyi yamma Auta!" "Okay,Umma bazan jima ba!" "Adawo lafiya Allah ya tsare min ke."Hajiya ta ce tare da shigewa bedrum." "Malam a duba mana kuma a yafe mana mun san munyi ba daidai ba!" Amma ayi hakuri abar yaran nan su samu kwanciyar hankali."Hajiya Raliya ta ce cikin sanyin murya." "Inna Baraka ta ce Hajiya da kin hakura domin shi malam idan ya hau yana da wuyar saukowa!"Saboda wallahi tun ranar da kuka zo na yi ta bashi baki amma fuuur!"Ya ce bazata sab'u ba!"Dan ya ce Yar sa bazata auri salman ana mata wulaqanci da cin fuska ba!"Kamar Yadda kinkaji ya fada miki da bakinsa!"Dan haka maganin kar ayi kada afara!" "Malam da ke gefen zaune yana jan carbin sa kallon Baraka da haj raliya kawai yakeyi domin shi ya qare magana idan sun gama cin kasuwar su zasu tashi a karshe!"Daga nan tashi yayi yama Haj Raliya sallama da ban hakuri kada taga kamar bai raga mata ba!"Ya wuce abinsa ya bar gidan zuwa majalisinsu na dattiban unguwa.' "Itama sallama tayi da inna Baraka ta bar gidan tare da shaida mata!"Za dawo jibi kuma zataje felende abisa kwatancen da inna tayi mata domin dauko salma aji ta bakinta idan ta amince dole ne Baba ya barta ta auri shi salman din!" "Inna Baraka tuni ta yarda da shawarar Hajiya Raliya domin tana da tabbas idan har ya lura salma har yanzun tana son salman zaiyi hakuri!"Duk da ta fahimci kamar salma ta bar salman din har abada ne!" "Bayan fitar Hajiya Raliya daga gidan inna cigaba tayi da surfenta." "Kawu Bala da matarsa Inna larai sai facaka sukeyi da kudi su karime har sababbin dinkuna akayi mata sai kuri ake acikin gida!" "Larai ta ce shin malam har yau kudin da Hajiya melal ta bakane basu kare ba naga namu da ka bamu sun kare da dadewa?" "Haba larai ana babbakar kura wa zai jiyo kaurin zomo."Ai salman ne ke bani kudi kuma yace min gidan sumunti zai gina min idan har na bashi auren salma." "Hararar takaici ta watsawa kawu Bala ta ce lalle malam zuciyarka ba ta kishin kanka ba ce ta yaya ga karime nan gida batada mai kudi ko daya a ma nemanta!"Muna nema bamu samu ba!"Zaka bari salma ta auri salman mai kudi!"Kuma kana gani tun bata aure shi babu abinda baya yimasu har mu kan mu!"Meyasa baka watse maganar auren ba!"Ko ka mayarda zancen kan karime ni wallahi na tsani tauraruwar salma domin idan ta hasko na fahimci ta karime disashewa takeyi mtsssssww!Yarinya kamar aljana!"Inna larai ta karashe maganar cikin takaici!" "Hahaha Larai ta malam Bala ikon Allah!"Ke meyasa tsabar son kanki rufe miki ido yakeyi ki kasa bude su ki gane waye gabanki nine naki bala fa larai kamar kin mantani da halina!" "Ai tun farko da yazo min da zancen salma ce masa nayi ya hakura da salma tunda yaya Habu bayaso ga karime nan zan bashi amma ya nuna min salma ya ke idan bai samu ba zai hakura da su dukan su!"Kinga ko gwara na amshi kudi na kada nayi asara na aura masa ita!"Nasan bazataji dadin zama da matarsa,uwarsa,da danginsa ba,Wuya da tsangwama zata hanata zama acikin su!"Dole ta baro gidan idan taji babu dadi ko!?" "Haba malan to ai mijinta na sonta kuma zai bata kudi kaga ko zamu sha kallo wurin su baraka!" "Meye amfanin kudi babu kwanciyar hankali larai!?Shi salman kullum zaune zaiyi gida yana kulawa da ita ne!?Ai dole ya fita aiki kedai ki yarda bazata ji dadin ba kuma kinsani komai ta ba su baraka da kason mu Dan Yaya habu zai bani nawa!"Ita wannan yarinyar karime nagane kashin tsiya ne da ita tayo mugun gado wallahi!" "Wurin ku kenan ta gado shi!?"Saboda nidai Allah yayi min arzikin ma nema masu kudi yan kasuwa karyarka tasa na aure ka ashe kaima duk jaar kanwar ce!"Wallahi Bala ka cuceni!" "Dakata larai rashin kunyarki ya tashi kinka dai cuci kanki da kwadayinki na banza kashin tsiya kuma naki ne karime ta gado!" dan ga salma nan tabiyo kashin arzikina tasamu mai kudi!"Aini da zarar nasamu gidan nan mai kashin arziki zan auro ku ruwa na canja kala!" "Mtwssss!!!Ai kin banza ai sai ka gina naka da arzikin Kanka ba da na wani ba!*Banzah!"Mai matacciyar zuciya!"Kuma gidanda za a ginawa Yaya Habu sai yafi naka komai saboda shi ada surukin ba kai ba!"Larai ta ce cikin hushi!" .."Babu komai aure kuma sai na karo matsiyaciya!"Bala ya ce ya wuce yabar gidan!" "Kai ne matsiyacin ba niba!"Dan bakinciki da hassada!"Da ko dan uwansa bai bari ba!" Ai zaka dawo wallahi!zaka sameni!"Mtwsss banda kaddarar aure me zanyi da kai ma karyaci!"Larai tace tare da zama tsakar gidan tana neman wanda zai tsakanota ta sauke masa Kwadon cin mutunci kamar yadda ta saba ta cika faam sai batsewa takeyi!" BAKAR AKIDA!?👸🏻 ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION_ ~Page 66/70~ " _Wannan Shafin naki ne Qanwata Qawata Aminiyata 'Yar uwa rabin jiki my twiny *NANA AYSHA AMEEN DIKKO Ina* yinki Over."_ 😍 ________________________________ "A zaune ta ke gefen katafaren bed din ta da misalin 9:pm na dare, cikin shigar bacci waya ce a hannunta tana magana cewa tayi..."Kai!Haba?Ki ce dai kin sha fama da Baban na salma!"Wallahi ni kaina sai addu'a nike tayi Allah ya sa ya amince!"Amma yanzu "Alhamdulillah a gaskiya naji dadin zancen nan Qawata," Nagode sosai da kokarin ki wallahi kin fidda dani daga cikin duhun jahilcin *BAK'AR AK'IDA*." Allah ya saka maki da alheri Hajiya Raliya,Kuma idan Salman ya dawo zan sanarda shi komai!" "Gaskiya sun fimu gaskiya saboda shi baban salma din da so yayi kada ayi auren domin yana ganin fa abinda akai musu! Akan talauci!"Amma Kada ki damu Hajiya Bilkis yanzu ya zama tarihi,"Sannan ai yiwa kai ne salman D'ana ne Kuma ki tuna aminchi ba wasa ba."Tun fa yarinta har ga shi mun tsufa,..."Sai dai Na zo goben nagode!"Inji Hajiya Raliya a dayan bangaren.cikin raha da jin dadi" "Allah sarki,Kuskure kam anyi shi," Hakane Wallahi...."kurciya dangin hauka har kin tuno min da baya...Hajiya" nagode nima Kwarai da gaske sai da safe." "Allah ya kai mu Hajiya Raliya ta ce tare da katse kiran bayan sun gama sallama da qawarta Hajiya mai gado." "Itama Hajiya mai gado tana gama waya ta kira layin Aunty zee (qanwarta)Ta ce gobe tazo tana son ganinta." "Cikin murna Aunty zee ta amsawa hajiya mai gado tare da bata tabbacin zatayi sammako gobe goben." saboda duk zaton ta akan sabgogin auren Minal da Salman ne." "Hajiya mai gado tana kashe wayar ta koma kan layin My son." "Bayan ya dauka ya gaidata." "Amsawa tayi,Kana Ta ce kasa me ni a bedrum idan ka dawo." "Owk Umma gani nan shigowa yanzun nan ma." "Kwance suke a makeken bed din kayataccen bedrum din."Ta ce Hello! Nidal ke din dai ashe banza ce wallahi!" yau nai ta Dubin ki shiru!"Ba ke ba labarin ki!"Meyasa zaki min hakan!?" "Mai da wukar qawata gobe zan zo in shaa Allah, Naso in shigo yau,"Ammi nayiwa rakiya unguwa."kuma na kira layinki baya zuwa!" "Okay ki gaishetah yanzu gobe ki zo da wuri kinga week din nan ya kamata mu kammala duk wani shiri na mu." "Hakane Minal amarsu sai nazo din Mrs Dr salman."Nidal tace tana dariya." "Minal tayi wani fari da ido kamar Nidal na gabanta ta ce kina da kyautar 5k gobe na baki qawata.." "Ooooh!Kai amma nagode Minal sai mun had'e." "Okay Bye Nidal Nagode Night!"Ta kashe wayarta ta ce "Allah ka nuna min an daure auren nan nawa next week." "Ameen Sisi na juilet uwar soyayya Ilham ta ce tana dariyar minal." "Pillow ta jefawa Ilham din ta ce kema mun kusa kai ki gidan Dr.jameel Majnun." "Dariya Ilham tayi tare da juyawa baya,a saman bed din tace to Sisinah Allah ya nuna mana dukanmu. (A zuciarta ko tausayin Minal takeyi saboda son ma so wani takeyi)" "Ameen my Sis." "Daga nan sukaci gaba da fira akarshe ilham waya ta dinga yi da jameel ita ma minal wayar habibinta salman ta kira suka gaisa saboda yanzu suna dan dasawa amma sai dai ita ce ke kiransa da wuya ya kirata!"daga nan mummie ta kira da Daddy suka gaisa kana ta koma online domin sada zumunchi." "Knocking! Knocking!! "Bismillah."Bude dakin yayi kana ya shigo cikin dakin da sallama" "Mummy Ina wuni,lafiya qlaw ya ka ci abinci?" "Eh, na ci." "To daman magana nike son muyi ni da kai."kuma ina son ka tattaro min hankalinka da tunaninka anan!"Abinda zan fada maka shi ne ranar assabar idan Allah ya kaimu za a daura aurenka da Minal da kuma yarinyar da kake so wato Salma........" "Cikin razana da tsoro ya ce Salma fa Hajiya..?"Fuskarsa dauke da mamaki."Da alamar tambaya?" "Eh,Hakane Salman na nemo maka auren salma kuma na yarda da amince ka aureta domin naga ita ce zabinka!"Kuma ita ce silar ciwon zuciyarka da kake boye min salman!"Ita ce kuma silar kafara yi min boye boye a dukkan lamarinka abinda bai taba faruwa ba atsakanin mu dan hakan naga ya dace ka sameta tun kan ni da ita muyi asarar rasa ka!"Amma kuma wani hanzari ba gudu ba!"Ina da sharadi daya!. "Kada kaga kasamu zabin ranka kace zaka wulaqanta minal!"Kasani 'yatah ce kuma jinina ce!"Bazan lamunce cutarta!cin zarafinta!"Kada ka kuskura in ji wani sabani atsakanin ku kayi kokarin daidaita adalci atsakanin su!"Fatana Allah ya Baku zaman lafiya!" "Ameen Umma nagode."Kuma in shaa Allah zanyi kokarin yin hakan!"Dan Allah Hajiya ki yafe min na rufe ki!"Kuma ni yanzu ina jin kunyar fada maki shirina.........!" "Dakata Salman duk abinda kakeyi dangane da aurenka da salma ina sane saboda tun kafin kaje wurin kawunka da maganar ni naje na same shi da zancen kuma duk abinda kakeyi ina sane domin d'ana Jameel yana sanarda ni."Idan kai boye min kakeyi!"Kavani mamaki wato kai Auren Sirri!"Batare da sani na ba!"Hmnnnnn Dan yau kenan."Kayi kuskuren farko karka soma kayi kwatankwacin sa!"Kaje Na yafe maka Allah shi maka albarka." "Ameen ummana nagode kuma nasan nayi wauta da kuskure kiyi hakuri dan Allah.. " Salman ya ce fuskarsa dauke da dinbim kunya da nadamar kuskuren da yayi."Ga mamakin iron yadda Hajiya mai gado ta canja nan take."Kara godewa mahaifiyarsa yayi."A kan abinda tayi masa na bazAta."Da hakurin da tayi da iyayen salma wanda batada shi saboda yasan ta sarai batason Jan rai!"Da hakan yayi sallama da cikin jin dadi ya wuce." "A part dinsa ma baiyi bacci ba sai da ya kira jameel yana masa tsiyar dan iskanci da neman wurin Shiga shi ne ya fadawa Hajiya da hakan dai har suka gama wayar tare da alkawarin gobe zasu hadu."Daga nan Salma ya kira ya labarta mata Hajiya ta yarda da zancen auren su." "Ta ce masa ai ita tuni tanada wannan labarin na dukkan avinda ya faru tun farko har karshe ta zayyano masa." "Fushi yayi ya kashe wayar bayan ya gama mata bambami akan ta dan ta rufe shi!"A karshe wayarsa ya kashe ya kwanta yana mamakin zurfin ciki irin na salma gimbiyar mata."Salma kwantawa tayi tana tunanin bahagon halin Salman dinta." *3:00pm* "To kin dai ji dalilin kiranki da nayi ke da minal domin in sanarda ku rubutaccen al'amarin da zai faru!"Kuma na amince ne saboda ai masa adalchi kuma lafiyarsa nake duba masa!"Ni kaina ba hakan naso ba Zainab!"Kin ga hajiya Raliya nan ita ce shaidata."Minal Kiyi hakuri ki yarda da wannan kaddarar kinji 'yahtah.......!" "Dakata hakan ya isa! Yaya mai gado!....sannan ta juya wurin minal da Nidal da sukayi mutuwar zaune cikin zuciya tace ku tashi mu tafi gida!" "Haba zainab meye haka daga magana.....dan Allah can ki min shiru nayi da ke!?ko na saka ki acikin lanari na!?Saboda tsabar munafunci mai shiga a tsakanin jini daya wallahi Raliya Yanzu nagane wannan duk Sharrin ki ne daman can kina bakin cikina ni da minal baki kaunar ganina da yayata mai gado lafiya to burinki ya cika kin rabamu!" "Zainab kina cikin hankalinki ita hajiya raliyar ce zakiyawa wannan rashin mutunci!"Inji Hajia mai gado cikin bacin rai!" "Eh na yarda!kuma na amince banda mutuncin meye aciki dan na cinye na tsohuwar banza...!"Munafuk....!" "TAtass taji saukar marin da hajiya mai gado ta watsawa zainab ta ce na gane ke baki da kirki kuma ba a maganar girma da arziki da ke!"Duk karamcin da nai maki da wannan zaki saka min zainab!"Meye kikeso ban miki ba!? ni zakiyiwa wulaqanci!"Meyasa kinka cikaa son kai!"Ki tuna tilastawa salman nayi sanadin hakan ya kamu da cutar ciwon zuciya!"Amma duk baki damu ba kanki da minal kawai kinka sani!"Baki damu da rayuwar shi ba!"Meyasa zainab!"Duk irin sonki da kaunarki da nikeyi baki gani!"Meye aibu dan ya hadasu duka ya aure su haram ne..." "Ba haram ba ne amma ni zainab uwar minal mai qaunarta na haram ta 'yata ta auri salman kuma bazan lamunce zaman ta da matsiyaciya yar mayu ba!" kuma ku fadawa salman ya kyauta!"Yaya mai gado mun gode!"Nidal kuzo mu wuce!" "Ilham cikin kukah!"Ta ce,Dan Allah Aunty zainab kuyi hakuri bamu taba jin tsakaninku ba!"Kada kiyi fushi kibari asamu masalaha!" "Ke dallah yimin shiru makira azuza duk shirin da kukayi ai kina sane kinka rufewa minal abin bakin ciki tana zaune da ku acikin gidanku amma kuna kulla mata gadar zare!"Ni bani wurin in wuce!" "Juyawa tayi cikin bacin rai ta ce dan uban ku kuzo muje!"Minal!!!!" "Nidal da ke kuka tana sharar hawaye tace muje minal ko!"tare da kamata domin ta tashi tsaye dan takoma kamar hoto." "Minal tuni bakinta ya rufe!" kukan ma ta neme shi ta rasa!"Bugun zuciyarta sai qara tsananta yakeyi!" komai ganinsa takeyi kamar a mafarki!"Tashi tsaye tayi suka fara tafiya hajiya zainab ta wuce gaba Nidal rike da hannun minal abayanta sai dai basuyi aune ba sai jin minal kawai sukayi tayi suuuuluuu sai qasa!"Ta fadi tuiii!"Tamkar matacciya tuni numfashin ta ya tsaya!" Da gudu Hajiya zainab ta dawo tanw fadin Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!!!!!!!" minal na Shiga uku Nidal ta mutu ne!"Cikin kuka take fadin maganarta jikinta na rawa!"Da gudun su suka karaso wurin suna cewa INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJU'UN!!!!"MINAL!!!!" BAKAR AKIDA! ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 71/75 _SADAUKARWA:" GA K'ASATA NIGERIA INA ROKON ALLAH DA SUNAYENSA TSARKAKAH DA YA SADAMU DA SHUWAGABANNI NAGARI MASU TSORON ALLAH WADANDA ZASU TAUSAYAWA MUTANEN K'ASATA ALLAH YA QARO ARZIKI DA CIGABA ACIKIN K'ASATA NIGERIA AMEEN, DA FATAN ANYI ZAB'E LAFIYA ALLAH YA SA A KAMMALA LAFIYA FATAN ALHERI JAMA'AR K'ASATA MAI GIRMA NIGERIA."🇳🇬_ ________________________________ "Kaga malam dan Allah ni ka wuce kabar kofar gidanmu tun kan nasa ai maka wulakanci!" "Ko kuwa ana so dole ne Dan ummaru!"tunda can kasan ni ba wani sonka nikeyi ba Zainu Dan gudun hijira nikeso!"Rashin sa ne saboda ya koma cikin sauran danginsa yasa nafara kula ka!"Yanzu kuma anyi walqiya gari ya haska na hasko rayuwAr tsaf nace banyi kuma bazan taba yi ba!"Wallahi bari kaji daga yau kar naqara ganinka kofar gidan nan kuma sunan karime ya fita daga bakin ka!"Bani ba kai...!"Dole mu rabu...!"Inji karime da ta riqe kugu sai masifa take zubawa saurayinta cikin bacin rai da rashin mutunci!" "Haba karime ban cancanci ki wulakanta ni hakan ba!"Ki sani ina sonki kuma ina kaunarki domin Allah!"na miki alqawarin zan maye maki gurbin Zainu Dan gudun Hijara....!" "Wallahi har ka mutu bazaka iyaba!" koh ba maye gurbin zainu ba?Ai yayi maka zarra!"Domin gari da madara suna da bambanci, kalar su ce dai iri daya amma dandano ba guda ba Dan ummaru!" yau ina kai ina Zainu jarumin maza!"Mtwssss shin wai kai ma idan ana babbakar giwa wama zai jiyo kaurin zomo!"Ai da iya takun mutum akan gane shi gwani ne!"Ni Dan Allah ka fice kabarni da bakin cikin da ke damuna....!" "Karime kisani shi arziki na Allah ne kuma wannan *BAK'AR* *AK'IDA* ce da kika daukarwa kanki!"Ki debeta acikin rayuwarki!"kice sai mai kudi zaki aura!? sai naga tufin asirinki shi ne kisamu talaka kamar ke domin ruwa ba sa'an kwandon ba ne!" "Ko zan auri talaka ba dai kai ba kwalin kifi a tabe ka asha karnin banza!"Dan bakada amfani bare mamora!"Kullum cikin harkar tsiya da talauci tun ana waje kwakwaf bare na aure ka,"Gaskiya ni bazan iya zaman hakuri ba!"Zaman gani ga sa'anni nah!" "Cikin kunar raiI!"Ya kalleta ya ce naji nagode karime cin fuskar yayi yawa!"Amma kisani shi arziki na Allah ne kuma da ace ina shi da nayi miki!" "Kana da shi!Dan ba ka rasa aikin yi ko sana'a ba!"Dan ummaru kace min zuciya ce tayin alherin ne a bakada ita!" ai ita kyauta tanada dadi ga kowa kuma sabo ne abin daga jini ne!"Zainu ma da ba dan garin nan ba, ya nemo yayi min sha tara na arziki da dukkan lalurorina wadanda saurayin kwarai ke yiwa budurwarsa balle kai."Ni alokacin sa komai ban rasa va!"Ba dan ya koma garin su maiduguri ba da banyi maraicin komai ba!"amma gashi nan yanzu banda komai ko powder nan neman gagarata takeyi abinda nafi karfi yana neman yafi karfina!"Gaskiya kayi gaba Allah ya raka taki gona lafiya nagode!"Karime ta cewa Dan ummaru ta juya ta shige zauren gidan su tayi tafiyarta cikin gida tana masifa da kumfar baki!" "Tsaye yake kamar ruwa sun cinyesa yana kallonta har ta shige cikin gidan da kyar yaja kafafuwan sa ya bar kofar gidan zuciyar cike da takaicin abinda karime tayi masa ya dauki alqawarin zuwa binnin Lagos domin neman na kansa yadda zai korewa bakinsa k'uda kuma ya huce takaicin wulakancin da karime tayi masa da haka har ya isa gidan su rai a bace!" "Wayyo! Allah na shiga uku minal kada ki mutu!!"Kinsan muna sonki ni da daddynki bamuda wata sai ke dan Allah ki tashi...!!!" "Da gudunta har tana tuntube da haki ta qaraso wurin hannunta rike da robar faro mai sanyi"Gurfanawa tayi tare da amsar minal a hannun zainab da Nidal da ke ta faman kukah!" "Kan minal din ta tallafo, ta aza a A jikinta!"tace Ilham ungo bude min ruwan!"Da saurinta ta bude ruwan tare da mikawa Hajiya mai gado da ke cikin tashin hankali!" "Ruwan ta dinga watsawa minal a fuska!"Hajiya Raliya ko sai faman fifita take yiwa minal da mayafinta cikin tashin hankali!" "Ilham banda kuka ba abinda takeyi!"Da kyar ta samu ta kira Dr.salman awaya ta Sanarda shi kaf abinda ke faruwa,"Cikin Sauri ya shaida mata suna zuwa yanzun nan....!" "Numfashi takeyi sama sama tare da Jan doguwar ajiyar zuciya!"Idonta da sukayi mata nauyi ta bude!" "Minal!Minal!!Minal!!!Ki tashi bazan iya rayuwa babu ke ba ina sonki my daughter!"Hajiya zainab tace kamar zautacciya tare da rungume minal din ajikinta tana zubda hawayen da kowa ke zubarwa a wurin!" "Minal cikin karajin kuka!"Ta ce mummie mutuwa zanyi matukar ba mafarki nikeyi ba!"Idan gaske ne maganar danaji dodon kunnena ya fadawa kwakwalwata da zuciyata!"Idan da gaske kunnuwa na keyi to babu shakka zuciyata zata Buga nan take!"Kuce min in farka daga mummunan mafarkin da nikeyi ba gaske bane!" "Saboda Ina son yaya salman son da ba'a taba yimasa ba a duniya!"Ashe sonsa ne ajalina!''Ban sani ba!" meyasa baya sona!?Meyasa ya tsane ni!?Mummie ku fada masa ni qanwarsa ce ni jininsa ce!Ni ce Minal din Aunty Zee dinsa!"Wallahi na tsani wannan salma sai nazama ajalinta.....!!!" "Subhannallah kiyi hakuri minal ki daina wadannan zantuka marasa dadi mana!"Inji Hajiya mai gado!"Cikin damuwa da tausayin minal." "Duk zantukan da takeyi Dr.salman da jameel suna tsaye a kofar falon suna saurarenta kamar yadda jama'ar falon ke saurarenta."Sai dai abu guda da ya tsaya masa rai! kuma ya kara jin yana haushinta da tsanarta Yakama shi duk da ta bashi tausayi shi ne"Kalmar na tsani wannan salma!"Sai nazama ajalinta!" "Da kyar yabawa zuciyarsa hakuri ya karasa wurin su ya gaida su cikin Sanyin murya Hajiya mai gado da Raliya suka amsa masa."Yayinda Aunty zainab ko kallo bai ishetah ba!"Nidal ko sai harara take watsa masa!" "Zubura tayi sanadin jin muryarsa ta karaso gareshi cikin kuka!" tace"Yaya salman wallahi ina sonka kaine rayuwata da farin cikinah idan narasa ka mutuwa zanyi matsanacin Sonka shi ya haifar da tsananin kishinka na tsani kishiya dan Allah ka fasa auren salma ka zauna tare da ni har abada!"Zan zame maka fiye da salma zan koma kalar macen da kake so zan daina duk wasu halayena da bakaso!!!"Kai min rai....! "Duk naji zantukanki minal amma har gobe ba'a canjawa tuwo suna!"Kamata yayi kifara jin tsoron Allah ki gyara halayenki domin Allah ba domin saboda ni ba!"Kiyi hakuri ki yarda da kaddararki Nima salma ita CE kaddarata bazan iya rayuwa babu ita ba!"matukar tana Raye!"Allah ya halatta min auren mace Hudu saboda me zaki haramta min minal!?Bakida dalili bakida hujja!""Son da kike min yasa nike sonki ko ba komai ke jinina ce, salma kuma rayuwatq ce!"Dukkan ku bazan iya rayuwa babu ku ba!"Ki daina zancen mutuwa kowa yanada lokacin sa!" kuma kishiya ba akanki aka fara ba!"Ko ban auri salma ba bazan zauna da mace daya ba dole nai miki kishiya minal!"Dan haka kiyi hakuri kinji!"Hawayenta yake share mata tare da bata ruwan sanyi ta sha!" "Aunty zainab ya kalla cikin sanyin murya yana bata hakuri amma firrrr...!!!"Tak'i ta sauraren shi saima ruwan masifa da takeyi masa tana ce masa macuci mayaudari sunci amanar zumunci!Kuma an fasa auren!" ba ita basu har abada!"A karshe Nidal da minal ta tasa agaba suka bar gidan!"Cikin matsiyacin gudu @360 suka iso gidan su dan tuni takira daddyn minal tace masa yadawo gida su hadu ba lafiya.!'" "Hajiya mai gado sam bata ji dadin abinda ya faru ba duk da kasancewar daman tasan halin qanwarta zainab da masifa domin tun can ita ce aqasa koyaushe tana lallabata dan kawai burinta azauna lafiya!"Amma yau ta kaita makura,"Hakuri Hajiya Raliya da Dr.jameel suke basu domin ganin an shawo kan matsalar Dr.salman kam ko ajikinsa tafi nono fari!"Gaba takai shi gobarar titi!"Abinci ma yasa ilham takawo musu su ci shi da Dr.jameel ." BAKAR AKIDA! ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION_ ~Page 76/80~ _*Wannan shafin kyauta ce zuwa gareka DR.ZAINUDDEEN JIBRIL(ZAIN)Ina miqa godiya ta mai tarin yawa, A bisa namijin kokarin ka domin ganin nayi tsaye kyam a duniyar marubuta,Ina maka Fatan alheri, Allah ya saka maka da mafifichin alheri ya sanyawa xuriya albarka Ameen, Gaba dai gaba dai Oga Zain*_ 👍🏼👍🏼👍🏼 ________________________________ "Da masifa ta shiga gidan nasu,Sashen su salma ta nufa domin tasan halin mamanta larai sarai!Da zarar ta gano Danummaru ne yazo wajenta to kashinta ya bushe!" "Da sauri ta isa dakin su,"inna baraka tasamu zaune tana gyaran shinkafar tuwo,Da sallama ta shiga tare da gaida Inna Baraka." "Yawwa karime kina lafiya?'' "Lafiya qlaw Inna,Salma na nan kuwa?'' "Eh,tana nan yanzu ta kewaya bayi ki zauna mana ko kasuwa za'aje ne?" "A'ah inna wurin salma dai nazo muyi zumunci."" "Atou karime kyale ku ne nayi ai,ace kuna gida daya amma baku biya junanku tunda akai fadan nan!Ki tuna ke ce babba ko ba'a yi ba kin baiwa salma shekara d'aya kin ko ga bai kamata ki biyewa qanwarki ba" "Inna wallahi ba haka bane kasuwa nike zuwa shiyasa ba na shigowa kuma muna gaisawa idan mun ka hadu domin nagane salma na da kirki da mutunci sharrin shaidan ne!" "To gaskiya ku gyara karime......" "Salma ce ta katse zancen su ta hanyar shigowa dakin da sallamarta" "Inna amsa mata tayi kana ta tashi ta fice daga dakin tana cewa yau dai yayarki ta kawo maki ziyara tunda ke baki shiga sashen su, ai idan abu ya wuce barinsa akeyi!"Inna Baraka tace tare da wucewa zuwa aikinta." "Salma da murmushi ta kalli karime ta ce"Sannu karime yau kece asashen namu?" "Ni ce Salma dan Allah kiyi hakuri sai yanzu na gane hassada ga mai rabo taki ce!"Wallahi ina sonki salma Innata ce ke ta kitsa min komai duk abinda nikeyi miki ita ke sakani!"Ko yanzu aboye ne na shigo inda kuke,"Amma yanzu nasan cewa "Karya fure takeyi bata 'ya'ya!"kiyi hakuri!Bamu kyauta muku ba ni da iyayena kuna zaune da mu da zuciya daya mu kuma muna jin haushinku!"Salma ki yafe mana"Kinji 'yar uwata!" "Hannunta ta kamo ta hade da nata, tace babu komai karime na yafe miki komai ya wuce duk abinda kike min ban taba kallonki da ko daya ba!Harma su inna da baba"Nasan Sharrin zuciya ne!" "Karime murmushi tayi jikinta asanyaye tare da jin kunyar salma ta ce nagode 'Yar uwata!" "Babanmu ya ce min aurenki za'ayi makon nan mai zuwa?" "Eh in shaa Allah karime,"Ki tayani addu'ah domin ni har yanzu ina jin tsoro da fargabar shiga gidan Dr.Salman saboda *BAK'AR AK'IDA* Irin ta danginsa kinsan sun tsani talaka ya rabe su!" "Babu abinda zai faru da ke Salma sai alheri da jin dadin rayuwa." Allah ya sanya alheri ina tayaki murna domin salman mutumen kirki ne, Allah ya sa ayida mu" "Ameen,Karime nagode Allah ya nuna mana naku!"Shin Ina Dan ummarunki ne?Ko yayi tafiya ne? na daina ganinsa!"" "Mtwssssa dan Allah ki daina min zancen sa!" Yanzun nan ma na koreshi! domin ni nagaji da gafara sa banga qaho ba!"Mutum kullum ta-tau kamar jijiya!"Nikam gaskiya nagaji bazan iya rayuwa da shi ba ahakan!"baya iya tabuka min komai!"Kinga fa ko irin... !" "Haba karime!"Salma tace tare da dakatar da ita!"Meye aibun shi!?Sai naga yana da mutunci kirki ilimi da addini!" "Aibun shi matsiyaci ne!"Salma.''Me akeyi da talauci ai ko mu da ke zaune acikinsa kullum muna addu'ar Allah ya fidda mu daga cuta ya bamu lafiya!"Ke kinyi arziki Allah yayi maki gyadar dogo saura ni da sauran!"Kin isa barkah shiyasa nazo in tayaki murnar barka da arziki salma!" "Menene na barkah kuma aciki Karime?"Dama ace kin min barka ne kan nasamu miji nagari zanyi aure in tufawa kaina asiri da nafi jin dadin hakan!"Amma ace barka kike min ta samun mai arziki!?Nikam wannan baya cikin tsarina!"Ya kamata Ki gane shi samu da rashi duk na Allah ne!"Yaushe kika koyi wannan *BAK'AR AK'IDA* ta banzah!"Kina yar talaka kice ke sai mai kudi kike so karime!?"To wallahi kinyi babban kuskure dan ba'ayiwa Allah wayo masani ne akan dukkan komai!"Kuma shi ne mai bayarda mulki da arziki ga wanda yaso!"Idan Allah ya tashi jarabtarki sai yabaki mai kudin karshe kisha wuya!"Ni kaina da kike gani wai zan auri salman wallahi Allah ne shaidata ni kudin shi baya agabana!Kuma naso ace a talauce zan aure shi daga baya muyi arziki atare nafi son hakan!"Kuma ko yanzu Allah na iya maida shi talaka kamar mu!"Dan haka kiji tsoron Allah ki so mai sonki da zuciya daya karime!"Salma tace fuskarta a daure cikin rashin jin dadin abinda karime tayiwa Dan ummaru!" "Cikin yanayin nadama ta dago kanta zuwa gareta tace na fahimceki salma Allah ya yafe min nasan nayi kuskure abaya kudi ne kawai agabana,Tare da rudi na innata,Hakika ta daurani akan tafarki marar kyau!" sai yanzu na gane da kika fargar da ni gaskiya!"Kuma in shaa Allahu zan nemo shi in bashi hakuri!"Amma salma duk da hakan Danummaru ya cika matse hannu sosai ya kamata ace dan mayukan nan su turare da sauran yan kayan nan na makwalashen kanti da naga ana kasowa abokaina nima yayi min inji dadi komai dai rashinsa yafi karfin su dan iya kudin ka iya shagalinka ne karfi baifi jiki ba!"Ai wannan ma wani abu ne!"saboda rayuwa ce da zamani yazo mana da ita salma!" "Hmnnnn karime kenan awani wurin kina da gaskiya amma ki qara yin hakuri watarana sai labari."Yanzu kiyi kokari ki bashi hakuri saboda baki kyauta ba kuma shawarata ita ce ki damu da wanda ya damu da ke!"Ki roki Allah ya hada arzikin ku." "To salma zanyi kokarin yin hakan nagode zan wuce kada inna ta nemeni, amma salma nifa kallonki nike tayi tun dazu naga sai wani sheqi kikeyi kinyi kyau hakan...kamar wata sabuwa ba ke ba?"Ko duk amarchin ne wallahi ba karya kin canja sai haske kikeyi kamar tauraruwa?"Karime ta ce harda shafa fuskar salma da ke walwalniya kamar madubi tayi (smooth)" "Murmushi tayi tare da duban karime ta ce baki rabo da abin dariya ki wani ce kamar bani ba,Nice dai salmarki...."To daman Hajiya Raliya qawar Maman salman ce ta kaini gidan wata Aminiyar su hamshaqiya kuma kwararriya Mai sayarda komai da ya shafi jiki wato Hajiya Amina Na'amore duka yau kwana na Hudu ne ina zuwa amma ni kaina naga canji wato ita aikinta yana kyau, sha yanzu magani yanzu ne" "Haba gaske dai kice naira ce kwance a fuskar ki."Ke kam kin fara komawa kalar masu kudi!"Yanzu nima ina so in gyara tawa fuskar ko zan haska ranar aurenki!"Zatayi min?" "Eh mana ai matar batada matsala!"Ga kayanta da sauki da rahusa, ga aiki kuma ko'ina tana tura kayanta, kedai bari gobe zamuje tare idan aka qare min sai tayi miki ni zan biya kudin naki" "Yawwa salma nagode."Bari inyi hanzari n shiga gida nabaro inna zata daura sanwa."Niema muje in taya Inna aiki ta fita da jimawa!"To muje sai gobe idan nazo!"To yayi Allah ya kai mu."In ji salma. "Amin karime tace Nagode Sannan tayi sallama da Inna Baraka ta wuce sashen su cikin jin dadi." "Bari kawai Abban minal yaya mai gado ta nuna min bani kowa!"Kuma bani bakin komai ni da 'yata a rayuwarta!"Duk fa abinda na labarta maka shi ne ya faru!"Babu abinda bata ce mana ba!"Akan salman ai d'a baifi d'a ba!"Saboda wata can talakar banza marar gata!"Za'a wulaqanta min minal!"Abinda bazai taba yuyuwa ba ne domin bazan dauki raini!"Ba awurin kowa wallahi!" "Numfasawa yayi bayan zurfin tunanin da yayi akan zantukan Hajiya zainab din."sannan ya ce"Naji kuma dukkan abinda ya faru!" Gaskiya abin ba dadi amma kisani yadda muke kare lafiyar Minal, haka itama kariyar lafiyar salman takeyi!"Ya kamata muyi musu uzuri zainab!Da salman da minal duk daya ne ya kamata abasu abinda suke so aimasu adalci!"Kada zuciya da saurin fushi yasa muyi da na sani...!" "Haba!Abban minal wane Dana sani kuma!? Ai ana yinsa ne idan ana tare!Kuma ni minal nasani kamar yadda itama da d'anta tafi damuwa!"Na riga na fada mata wallahi bani ba ita kuma minal bazata taba auren d'anta ba"Domin bazata taba zama da ' Yar matsiyatah amatsayin kishiyarta ba!"Dan haka dole ne a fasa zancen auren.....!" "Dakatah zainab...Bana son shirmen banza!"A fasa auren fa kinka ce!?To Saboda me!? Salman ne ya ce yafasa!?Ko ita minal din tace maki tafasa!?" "Ai Ko basu fada ba ni na fada!"saboda ance labarin zuciya a tambayi fuska na hango farinciki kwance a fuskar salman Kasan daman shi ba so yakeyi ba!"Kuma yanzu mahaifiyar sa ta goya masa baya!"Maganin kar ayi kar afara!"Dan haka muma zamu ba minal hakuri ta tsaya jiran mai sonta ba wanda ita ke son sa ba!"Yanzu haka da kyar ni da Nidal,muka samu ta kwanta bacci ko zata samu sassauci!" "Yanzu zainab meye zamu cewa mutanen da da muka gayyata!?Yanzu duk shirin mu ya zama na banza kenan!"A gaskiya dole ne mu samu mafita...........!" 🏻👸🏻 BAKAR AKIDA ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 81/85 _Dedicated to my little princess Mufeeda Ameenu😍 Allah ya nuna min ranar aurenki Amin._ ________________________________ "Gidan malam Abu Sufyan ne cike da jama'ar binni da na qauye." Ba kowa bane face Hajiya Raliya da jama'arta ta arziki da ta gayyato domin kawo kayan lefen salma saboda duk dangi Hajiya mai gado sunce su bazasu iya shiga wannan unguwa ta qauyawa talakawan da wasun su duk mayu ne!"A cewar su wai duk garin cin maganin arzikine talakawan ke komawa mayu!"Dalilin da yasa hajia Raliya ta nemo mutanen arziki suka kawo kayan da yawan su har baya faduwa babu kawai ce a ba'a saka aciki ba!"Dozin akwatuna biyu kalolin kayan sunfi dari su sarka jaka gyale da sauran su tamkar wani kanti har su gwala gwalai ba'a barsu abaya ba!"Kaya dai na arziki."Sai masha Allah." "Tarba ta arziki da mutunci dangin Inna baraka sukayiwa su Hajiya Raliya." "Yan uwan malam duk sun zou auren kowa sai murna yakeyi da farin ciki domin salma ta zama tauraruwa acikin yaransu ita kadai ce ta auri mai arziki kaf dangin su!"Domin haka ne sukaji dadi sosai komai an gudanar na al'ada wanda karfi bai fi jiki ba."Da hakan aka kammala komai su Hajiya Raliya su ka koma." "Yayin da karime da sauran sa'ointa ke ta kaiwa da komowa sai murna sukeyi suna duban kayan na arziki da basu da adadi."A gefe ko Baba larai sai faman cika takeyi tana batsewa tana hararen karime da bata ma san masarda innarta ke toyawa ba dan tuni ta kama salma ta rike gam.''Da dai larai ta fahimci karime bata kulata ficewa tayi daga sashen zuciyarta cike da bakinciki da takaicin wannan kayan da aka kawo ga karime sai wani rawar kai!"takeyi domin rashin sanin ciwon kai!"Amma zata dawo ta sameta sai ta ci mutuncinta.!" "Salma ko tun safe tabar gidan taje gidan wata qawarta Zara'u, Saboda kada masu kawo lefen su sameta." "Dr.Salman da jameel da sauran abokan su ne zaune amajalisa yayin da suke ta masa tsiya domin yaki ya amince suyi pre-wedding pics."Sam yaki ya amince saboda yace haram ne ba kyau kuma baya son ya tallata matan sa aduniya yana kishin su!"Da hakan dai suka gama cike ciken Wedding I.v din su suka wuce domin aiwatar da wasu lamurra nasu shi da jameel." "A gefen minal ko da lauje acikin nadi domin ita kam gaskiya tana son Dr.salman matuka amma *BAK'AR AK'IDA* ta tsanar talaka tayi mata tsirou a zuciya da take ganin bazata iya zama da salma a matsayin kishiyarta!"Ai wannan wulaqanci ne domin tafi karfin tayi kishi da 'yar talakawa!"Domin wannan babban ci baya ne agareta kuma abin kunya ne da fad'a familynsu." "Tana cikin tunanin ne taji sautin muryar daddynta da ke shigowa acikin falon nata "Da sauri ta tashi daga kwancen da take akan 3siter din tare da gaida daddynta." "Amsawa yayi tare da zaunawa akusa da ita ya ce my daughter ya jikin ki? "Da sauki daddy har ka dawo ya office!?" "Normal!"Dear."Ya bata amsa a takaice." "Duban royal stool din da ke gabansu cike da magungun nan ciwon zuciya da cup da robar ruwan faro da ke ajiye."sannan ya kalleta yace an baki magani duk ina ma'aikatan naki!? "Eh,Daddy su bani na sha ni ce na sallame su dan ban son damuwa sai gobe zasu dawo nafi so na zauna nikadai shiyasa!" "Haba!"Daughter ya kamata ki debe damuwa aranki kin ga idan har kina son salman aure babu fashi komai an shirya har I.v daurin aure an buga ni banga abin damuwa ba aciki!"Yarinyar nan gidanta daban naki daban kuma komai gidanki yafi NATA!"Ba akanki zata zauna ba Dear!"To meye abin tashin hankali aciki!?" "Haba Dady talaka ce fa matsiyaciya kaima Kasan duk dangin mu basa son talaka amma sai ace nikai ce za'a fara yiwa kishiya kuma talaka gaskiya nikam ina jin takaici da bakin cikin abin!? "Ina son kiyi hakuri minal wannan yana daga cikin kaddarar ki babu yadda zanyi da nayi wani abu salman yana da kirki kuma dole ne ayi masa adalci shima ya auri zabin shi matukar ba son kai zamu nuna ba!"Domin ke da shi duk abu daya ne kuma muna bukatar rayuwar kowa acikinku!"Kiyi hakuri kiyi watsi da *BAK'AR AK'IDA* irin ta mahaifiyarki kisani shi arziki na Allah ne kuma mai kudi da talaka duk daya ne agurin sa wannan shi ne mafita agareki idan ko kin fasa auren salman zan sanarda su mun hakura adaura aurensa da salma kawai Allah yabasu zaman lafiya." "Daddy wallahi ina sonsa ban fasa ba zanyi kokari naga na hakura!"Amma wallahi Daddy na tsani salma tsana mai tsanani!"Ta Shiga tsarin rayuwata ta bata ta dagargazani yadda banyi zato ba!"Minal ta ce tana kuka!" "Babu komai Dear ki hakuri kinji Allah yasa hakan ne alheri!"Inji Daddyn minal." "Ameen Daddy nagodeminal tace tana zubda hawaye!"Daddy ko kara lallabata yayi tare bata haske akan rayuwa sai da yaga ta gamsu sannan ya wuce zuwa sashen su."Minal koh ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tare da furzo iska mai zafi sannan ta kwanta domin ta dan samu sassaucin Bacin rata!"Ya ragu cikin hakan bacci barawo yayi awon gaba da ita!" "Hajiya mai gado zaune afalo tana sauraren jawabin da yan uwanta sukeyi domin auren! suna son ita da salman su janye yadda da auren salma ya auri minal kadai ita da a jininsa kuma 'yar masu kudi!" "Hajiya mai gado kallon su tayi sosai domin tuni ta gano zainab qanwarta ce ta turo su ayi mata taron dangi a hade mata kai!" "Ta ce nagode da shawarku da kuma korafin ku yan uwana kuma nagode sosai Allah yabar zumunci." "Amma kusani batun auren salman da salma ba fashi idan har zaku zo kusa ALBARKA kofata abude take!" "Yadda kuke son minal hakan nima nake kaunarta domin yata ce,Auren su kuma ahakan yazo dole ne mu karbe shi yadda yazo mana domin rubutaccen al amari ne daga Allah" "Salman ya shiga mugun hali saboda salma yana sonta tana son sa shin meye aibu dan an hade su dukansu har minal ya aura!?"Kun san cewa cinsu da shansu har sutura ba abinda zai gagare shi dan haka kuje gidan zainab ku tayata hidima saboda ni kunce bazaku xou auren tsiya ba salman zai auro muku bare talaka acikin ku ko!?"Ko da ku ko bada ku ba za'ayi harka aqare lafiya ai ni da nan gidan da gidan zainab duk dayane agurina!"Kusani duk abinda ke zuwa yana dawowa ina sane ido ne na zuba muku duk abinda kuke fada ina ji kuma kayan lefe an kai min su lafiya an dawo tunda abokaina suke kashe min kunya!"Ba ku dangina ba!" To nagode da irin sakayyar da ku kai min amatsayinku na jinina! Allah ya bamu lafiya!"Hajiya mai gado ta ce su ta tashi ta shige bedrum dinta tabar su zaune kamar ruwa ya cinye su sai wani fidda ido sukeyi.! ?🏻👸🏻 BAKAR AKIDA! ©TASKAR NABEELA DIKKO ®PEN WRITERS ASSOCIATION Page 86/90 _Dedicated to my SAHEEBA Rahmah m Sani Ina yinki 0ver Habibarty Allah ya qara damqon zumunchii yabarmu tare Qawalliyya Muna tare Iya wuya Nabeela Dikko taki ce Aminiyatah_ 😍 ________________________________ "Saudat ce ta dubi sa'adatu ta ce"A gaskiya yaya sa'adatu kamar bamu kyautawa yaya mai gado ba!"Kinga tayi fushi ta tashi ta barmu anan abinda bai taba faruwa ba!" "Ke dan Allah ku kyaleta daga fadan gaskiya!"Ya zamu bari gida naso sai akai kasuwa ko ma kasuwar ta talakawa me zata zama dan ta aurawa danta yar talaka!"Taya dunia zata kira sunanta har taji ta amsa!"Ni kunga kutashi mu tafi inji Hajiya sa'adatu cikin fushi!" "Hafsa ta ce hakane yaya mutafi ai wannan wulakanci ne dan kawai taga munzo gidan ta ai muma muna da gidajen mu!"Tai jira idan har mundawo!" "Saudat ta dubi yayyen nata cikin rashin jin dadin zantukan su!"Ta ce yanzu wucewa zamui bazamu je mu mata sallama ba!?"Daga nan mu bata hakuriya yaya hafsa!" "Ke sakarai!Marar zuciya kizo mu wuce!"Ko mu tafi abinmu!"Ke dan rashin sanin ciwon kai muzo gidanta tayi mana wankin babban bargo ta tafi tabarmu da gadin falonta! dan wulaqanci!"Kice zakije ki bata hakuri....!?To Allah ya kiyaye mu mun wuce kuje muje!" "Hanya suka kama dukkan su suka fice daga gidan!" ba dan ran saudat yaso ba tabi bayansu zuwa motar su!"A hanya ma sai zagin Hajiya mai gado sukeyi wai ta wulaqanta su akan yar talakawa!"Saudat wayarta,Ta ciro daga jekarta ta rubutawa Hajiya mai gado sakon ban hakuri tayi tare da nuna mata sun wuce saboda sunga kamar bataji dadi ba!"Bayan ta tura mata tayi tagumi tana sauraren yayyenta da ke zuba musamman yaya sa'adat dake driving har buga sitarin motar takeyi kan masifa!"Direct gidan Aunty zainab (Maman Minal ) "Suka nufa cikin fushi!"domin basuji dadin yadda yayar tasu tai masu ba!"Yadda sukeji da kansu da kudi!"Ace har an ci mutuncinsu."Ko sallama basuyi ba suka shiga falon, saudat da ke bayansu kadai ce ta shigo falon da sallama!" "Karime an sha kyau an fara fresh saboda Aikin Hajiya meena yana kyau."Salma amarya ba'a magana domin ta koma kamar balaraba haskenta ya fito fuskar sai kyalli take kamar madubi."Tayi kyau matuka."Acikin napep suke suna fira har da raha."Salma ta dubi karime ta ce"Shin karime ya zancen dan ummaru kin kira shi!?" "Karime tace"Na kirashi yafi akirga bai daukah ba!"A karshe kashe wayarsa yayi duka salma!"Jiya da yamma naga Indo kanwarsa na tambayeta shi...Hmnnnnn...kinsan me!? "A'ah sai kin fada!" "Wallahi indo wani kallon banza!"Tayi min cikin tsiwa ta ce mi wai yaje neman na kansa tunda har diyan gidan laaka da tab'o sun iya faden arziki!" "Salma ta ce haba! cikin tsoro! yanzu kina nufin indo ce tace miki hakan wacce naga kuna dasawa sosai!" "Sosai Salma, Indo koh!" Ni kaina abin yabani mamaki amma nasan cewa bai fadawa iyayensa abinda nai masa ba!"Daman Indo ce abokiyar shawararsa akwai aminci atsakanin!"Amma na bata hakuri kuma nace idan ya kirata ta fada masa nace yadawo zan aure shi, ko da baida ko taro!"Na amince domin nayi nadama!"Karime ta karashe zancen tana hawayen nadama!" "Salma ta ce"kiyi hakuri karime komai zai daidaita in shaa Allah."Yanzu yana ina ne!?" "To Indo ta ce min yaje lagos gurin nema tun daren ranar da nayi masa wulaqanci yabi hanya!" "To kiyi hakuri ni zan kira shi anjuma nasan zai saurareni ke kuma ki kiyaye Allah ya tabbatar mana da abinda yafi zama alheri."In ji salma cikin damuwa da tausayawa yar uwarta!" "Karime tace"Ameen nagode salma!" "Da hakan har suka kawo kofar gidan su."Bayan sun sauka sukai sai da safe da shi domin Dr.salman ya dauko musu hayarsa yana kai su gyaran jiki yana mayarda su." "Cikin gidan suka nufa da sallama......sai dai me Gud'ar da Inna lantana Qanwar su Baba,Ne tayi arba da su cikin murnar ganinsu...sai da suka tsorata daga Karime har salma!"Kana tafara kirari iri-iri da habaici wanda kowa yasan da Inna larai (Maman karime)Take wacce ke kunshe a sashenta tana hadiyar yawu da bakinciki dan sai aikace aikace mutane keyi gobe jumma'a ne auren salma."Cikin rashin jin dadin abinda akeyiwa Innarta tayi sallama da salma ta wuce sashen su!"Karime kenan wadda ke ganin duk bakin halayen Innarta ne ke jawo ana mata arashi!"Salma ko cigaba tayi da sabgogin gabanta da sauran yan uwanta da su ka zo aurenta." "Zaune suka sameta afalon duk abin duniya ya dameta!"Ko amsa sallamar tasu batayi ba!" "Da sauri Hajia sa'a ta isa wurinta ta zauna tace me yake faruwa Zainab!"Duk kin wani fame!"Tunanin me kikeyi!" "Cikin damuwa zainab ta kalle su dukansu da ke zaune a falon!"Tace basai na fada maku damuwata ba kun sani!" "Wai akan yaya mai gado da dan nata ne zaki kashe kaki ke da minal!?"To bari kiji wallahi idan bakuyi da kyau ba sai ciwon zuciya ya zama ajalinku!"Saboda duk abinda kukeyi da halinda zaku shiga ba ruwanta!"Mu ma nan da kinka ganmu daga gidan muka fito korar Kare taimana!" "Cikin mamaki da fidda ido da dukan kirji Hajia zainab tace Ke sa'adatu korar Kare fa kika ce!?Me kukayi mata!?Anya yaya mai gado matsiyatan nan sun barta akanta kuwa!?" "Yanzu Zee, mu yaya maigado zata duba tace muna munafuntanta!"Menene... kuma akarshe zata barmu afalonta zaune kamar shegu ina gaya miki ta shige bedrum ta rufe!"Domin kawai mun fada mata gaskiya kan auren yaran nan!"Ni badan kinkarani muje ba da bazan he ba saboda banaso ace na shiga cikin zancen nan !"Wallahi bakiji ba babu abinda bata fada ta inda take shiga bata nan take fita ba!" "Ni kaina nafara nazarin ba a banza suka barta ba!"Daga ita har salman din!"Idan ko haka ne sai mun tashi tsaye domin ganin an fidda su cikin wannan halin!" "Hakane Sa'adatu ni yanzu komai ya kwance min,Yanzu ace ni da yar uwata uwa da uba daya munyi kare jini biri jini!"Ku abin da sauki tunda ku tobasanmu ne!"Ni fa Har marina sai da tayi akan auren nan!"Shiyasa naso minal ta hakura amma son salman ya hanata ta barshi tare da goyon bayan mahaifinta!"Domin ya ce aure ba fashi sai anyi!" "To yanzu ita minal auren nan zatayi inji Hafsa cikin mamaki!"Tana duban Aunty zainab!" "Ya zanyi Hafsa tunda sun ce sunji sun gani zasu iyah! nikam nace ba ruwana da auren....!Haba Yaya zainab kuyi hakuri mana idan kince ba ruwanki da auren ai kamar kin zuba fetur ne awuta kina jiran ta tashi da rayuwar minal!" saboda bazata taba ganin haske a auren ba matukar babu yardar ki alamarin!"Dan Allah kiyi hakura ki saka musu ALBARKA.!"Inji saudat cikin sanyin murya.!" "Mtwsssssssss!!!"Hafsa ta ce kana ta dubi yaya Sa'adatu da zainab ta ce kunji wannan santobola!"To idan bata nunawa minal ranta ya baci ba ta ina zata gane kurenta ai gatane da yanci ake nema mata!"Ace kamar minal mai ji da kanta da ilimi da kudi zatayi rayuwa da kishiya ko banzar ma 'yar matsiyatw da batasan arziki ba!?" "Yaya Hafsa ina son ku ajiye wannan *BAK'AR AK'IDA* Kuma ku ajiyeta agefe saboda ba addini bace al'adace irin ta marasa ilimi ba dole sai anyi auren kwarya tabi kwarya ba kowa zabi nagari ya kamata ya nema awurin ubangiji sann.......!" "Dakata alaramiyya shehiya munji mu jahilai ne!"Kina ganin ke wata mai ilimin addini ce dan kawai kinga ke ce kinka taba sauke alqur'ani mai girma acikinmu!"Shi ne zaki taramu kina mana wa'azi ko said at.!"To Alhamdulilah dan muma mun san wasu surori!"Wallahi idan na karajin bakinki acikin maganar mu sai ranki yayi mummunan baci!"Inji Hajiya sa'adatu cikin takaici!" "Ta kalli Yaya zainab tace kiyi hakuri kinsan iyayinta da nuna ita takwarai ce!" "Dan Alllah yaya kuyi hakuri dukan ku!"Inji saudat!" "Ba komai ya wuce malama sauda!"Inji hjia zainab." "Daga nan cigaba sukayi da tufka da warwara akan maganar da yadda zasu bullowa al'amarin Hajiya maigado,Minal,da salman da kuma Abban minal!." BAKAR AKIDA! © TASKAR NABEELA DIKKO ® PEN WRITERS ASSOCIATION Page 96/100 LAIFIN DADI KAREWA ALHAMDULILLAH! _WANNAN SHAFIN KYAUTA CE GAREKU_ 👌🏼 _'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI INA MUKU FATAN ALHERI_ _MASOYAN LITTAFAI NA BANSAN ME ZANCE DA KU BA A DALILIN SO DA KAUNA KUNA CIKIN ZUCIYATA KWANCE,NI DA KU SAI DAI FATAN ALHERI ALLAH YA BAR ZUMUNCHI MAI DOREWA ATSAKANIN MU AMIN,SO DA QAUNA NI DA KU YANZU AKA FARA, ANA TARE_ 🤝🏻 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 "A yau Jumma'a 22/2/2019 ne aka daura Auren Dr.salman Tahir Galadima da Barrister minal Maina akan sadaki naira dubu dari da hamsin." "Sai kuma na Malama Salma Abu Sufyan akan sadaki naira dubu hamshin."Daurin auren da aka gudanar a sheikh Abbakar gumi Mosque bayan an kammala sallar jumma'a, Auren na su ya samu halarta dinbim manyan mutane da yan boko, kama kan gwamnan Jihar Kebbi manyan yan siyasa har ma abokan marigayi Tahir da justice maina da Jama'ar kauyen su Malam Abu Sufyan da sauran yan uwa da abokan arziki sunzou sun kuma sanya albarka abin ya qayatar,Musamman Abokan Dr.salman na India da U.s duk sun zo,Da sauran likitocin da ke jahohin nigeria,Shi da abokinsa Dr.jameel sunyi kyau matuka domin shigar su irin daya ce,Bama za'a banbamce waye angon mace biyu acikinsu ba,Sai an cinka saboda sun hadu karshen haduwa acikin tsadaddar shigarsu ta alfarma."An kammala lafiya daga nan suka wuce grand fishing park da ke garin na Argungu domin cin abincin liyafar angwaye da aka shirya ta musamman." "Gefen Hajiya Mai gado sai dai San barkah domin alheri ne ke kwaranyo mata ta ko'ina."Gidanta ya cika maqil da abokan arziki da makota saboda Hajiya mai gado na kyautatawa makotanta."Abin dai ba'a cewa komai HAjiya Raliya uwar kirjin buki sai hadahadar fama da jama'a takeyi cikin shigA ta alfarma domin sunyi kyau matuka ita da Hajiya mai gado cikin shadda gizna kalar ruwan hoda da tasha pent work mai kyau,Gold masu tsada ne awuyan su hannu da kunne sai dai masha Allah Dan sun sha light make-up,Duk falon cike yake manyan mata yan kasuwa ma'aikatan gwamnati sai faman tande-tande abinci da abin sha kala-kala akeyi domin babu ce kawai babu agidan Hajiya Bilkis(Mai gado)."Wacce tuni ta manta da danginta da *BAK'AR* *AK'IDA* Ta hanasu halartar auren ko ba komai abokanta yau sun share mata hawaye!"Domin dimbin jama'ar da ke buki budiri a gidanta said dai ta ce"Alhamdulillah." "Gidan Malam Abu Sufyan mai walda ne cike tinjim da jama'ar binni da kauye sai kidin kwarya akeyi da gud'a mata na raqashewa."Karime ce tsakar fili da su luba da hure harma umaima sai kwasar rawa akeyi ana kakkaryawa cikin murna da farinciki yan uwa sai liqin goma ashirin sukeyi!." "Salma an sha make-up mai kyau cikin rantsattsen Material dinta maroon da silver head tasha adon sarka da yan kunne silver masu kyaun gaske takalminta Hill's da yar qaramar jakarta duk silver color."Fadan irin kyaun da salma tayi ma bazai fadou ba."Duk gidan sai faman qamshi yakeyi,"Inna baraka ma ta hade cikin swiss less dinta mai kyau kamar ba ita ba."Baba larai ko tana sashenta kunshe tana taunar bakin ciki kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu!"Duk da taso kange yaranta kar sutafi gurin amma INA!"Dukkan su sun wuce suna shan shagali ita kadai suka bari kamar mayya!" "Yan uwa da abokan arziki sunyi bajinta domin kuwa sun bayarda gudun muwarsu sun inna sun samu alherai da damage."Kowa ya CI ya sha anyi hani'an sai bararrajewa sukeyi cikin jin dadi." "Gidan Justice Maina cike yake da jama'a maza da mata."A sashensa manyan mutane abokansa da yan uwansa sai fira ake ana raha abinci da abin sha ne ajiye firjit a katafaren falon nasa sai taya shi murnar auren minal akeyi mashi kuma yanata godiya da nuna jin dadin sa." "Barrister minal maina ce zaune tsakar qawayenta ta sha kyau har ta gaji!"Da ganinta kasan cewa dalolin naira ne kwance ajikinta domin "ance ido mudu ne" ko da ba'a fada ba zai auna."Haka ma Nidal da Ilhaam sunyi kyau sosai da sauran abokan su duk sun zo."Sai ciye-ciyen kayan dadi sukeyi kafin time din dinner yayi da abokan Dr.salman suka shirya musu." "Hajiya Zainab Maina zaune cikin matan abokan mijnta da danginta su Sa'adatu hannatu hafsatu da sauda dai sauran yan uwa da abokan arziki."Sai faman hidima sukeyi cikin jin dadi yayinda Hajiya Zainab ke boye damuwarta kada mutane su fahimta domin akan dole ne ta aminta ba dan ranta ya so ba!" "Hakan dai ta faru akowane bangare shagalin buki buduri sukeyi." "Kawu Bala sai kwasar wasa wasar buki akeyi yana d'aga kwalbar fanta sama..."Bakinsa kamar zai tabo kunne kan dadi saboda ya samu kudi sosai wurin su Salman." "A gefen salman din ma sai san barkah domin abokan sa sai tsiya suke masa suna kiransa da mijin Mace biyu."Shirin sukeyi sosai domin zuwa daukar amaren aje dinner." *8:33 PM* "Salma ce gurfa ne agaban Babanta da inna suna yi mata huduba mai ratsa jiki da zuciya!"Ba abinda takeyi sai rera kuka!"Mai tsuma zuciyar mai sauraro!"Inna ce ta katse mata tunani!"Da ta ce kin ji duk abinda mukace da ke salma ina so ki rike su kuma ki Santa su azuciyarki kada ki dauki Munanan halaye da *BAKAR AKIDA* wadanda ba irin naki ba!"Kin ga dai salmanu yayi miki komai a rayuwa ba abinda bai saya miki ba agidanki duk da ba hakan mukaso ba,Amma ya hana muyi maki komai ,dan hakan kiyi biyayya Allah ya Baku zaman lafiya Ameen." "Baba ya ce yanzu kuje bala da larai suyi mata nasiha da gwagwanninta da iyayenta Kinji Baraka kuma zan tsaya abakin kofar gida no zan kai ki salma gidanki da kaina ba wani wuri na Bidi'a da zakije dan bazan aminta da ayimaki walima dazu da Yamma sannan yanzu ace zakije wurin kidi sam ba zai sabo ba!" "Inna Baraka ta ce"To Malam za ayi yadda kace tashi muje salma."Tallafota tayi tana share mata hawaye suka wuce!" "Sashen Kawu bala Gwaggo Hanne ta wuce da salma yayi mata huduba sosai"Daga nan ne tace to larai ga salma ta zo neman gafararki"A dakile tace Amara Allah ya raki taki gona ya yafe mana!"Larai tace tare da shigewa dakinta!"Kawu Bala yace ke hanne Ku tafi abinku Allah ya ba su zaman lafiya kubarni da ja'ira mai baqin hali!"Hanne tace to Yaya Habu mungode Allah ya nuna manager nasu karime."Ya ce,"To Amin Sai kun dawo."Tuni suka dauki haramar barin gidan bayan nasihohin da yan uwa da abokan arziki sukeyi ma salma." "Babu yadda abokan salman basuyi da babanta ba! amma fir yaqi!"Yace bazataje dinner ba dole suka hakura suka kai salma a Katafaren gidanta." "Gefen ango Dr.salman ko sai faman bude ido yake domin yaga ta ina zai ga sarauniyar mata salma zata fitou."Sai dai kash!Minal ya hango kamar wata queen da abokanta suna biye da sauran danginsu abayanta haka Hajiya mai gado da abokanta sun sha ado da gwalagwalai da gani ba sai an fada ba kasan cewa wannan Bukin na 'yan gata ne masu arziki ." "An gyara wurin ya sha kyau wato Dancing Arina Argungu,"Kujeru ne na alfarma aka ajiye,Domin zaman manyan mutane maza da mata kayan makulashe ne ajiye agaban su."A kan higher table ko zance bai faduwa domin wurin ya sha kyau da ado,"Dr.salman ne atsakiya gefen daman kujerar da aka tanada domin salma ne abokinsa Dr.jameel ya zauna gefen hagun shi minal ce zaune sai wani shan qamshi takeyi tana jin dadin labarin da suka samu akan salma bazata zo ba!" "Anyi dinner mai kyau wadda ta qayatar." makada da mawaqa sun baje kolin su anyi liki da naira dollars har Europe an mannawa ango da amarya, iyayensu sai barin kudi suke sun nuna bajinta sosai masu hoto sai aikinsu sukeyi yan mata ko sai selfie akeyi ana daurawa a whsup istagram fcbuk twnter,da sauran su tun kan kace kwabo auren Dr.salman da Barrister minal ya bazou a duniya kowa sai yaba auren yakeyi da koda irin dukiyar da aka kashe musu."Da hakan aka watse misalin 12am na dare."Hajiya mai gado tayi ma danta nasiha sosai da abokanta had minal duk an musu huduba ba sannan suka wuce a hanya yayi umurnin afara kai shi gidan salma."Sai dai abin yabawa minal mamaki kar dai ananufin salma ce uwargida!" "Kallon shi tayi sannan tace Yaya me zai hana ni ka saukeni agidana naga kai ka hana kowa ya biyomu domin dare yayi sosai kuma nafi salma shekaru ka ga ai nice babba a kanta!" "Salman ya kalleta ta gefen ido."Ya ce kiyi hakuri minal,"salma ta riga da ta shiga gabanki domin tayi kusan awa hudu agidana."Kuma amatsayin mata ta,"kinga ta rigaki shigowa gidana ita ce uwar gidana."Saboda haka kiyi biyayya kawai a zauna lafiya." "Hawayen da take kokarin maqalewa ne ke zuba a idonta kamar an bude famfo tace Yaya salman meyasa bazaka kai ni gidana ba!? sannan ka tafi gidanta!"Kasan cewa haka zakayi min ka hana kowa ya biyo bayan mu." "Bazan kai ki gidanki ba sai na tafi da ke gidan yayarki!"Inji salman."Cikin fushi tare da Daure fuskarsa!" "Da hakan suka isa gidan salma,Kowa da abinda yake tunani akai!"Sun sameta zaune afalonta tana share hawaye! Sunna t.v take ta kallon tun bayan tafiyar yan uwanta!"Da sukaji da jiran angwaye suka wuce!"Kamar daga sama tagansu tafe cikin tsoro!Ta miqe tsaye saidai ganinsu yasa taji sanyi gaida su tayi aladabce tare da tarbar su."Kallonta yayi daa tausayi Yace amaryata sannu da zaman kadaici kowa ya watse an barmunke ke daya!"Kiyi hakuri kinji tunaninki kawai nikeyi Bakomai mujina tace cikin sanyin murya!" "Daga nan nasiha yayi musu sosai tare da alqawarin yin adalci atsakanin su."Sannan ya ce minal ta tashi ya sauketa gidanta ya dawo!"Minal ta cika sosai irin yadda salman ya gyare gidan Salma kamar 'yar wani da wata."A karshe kuma ya bata muqamin zama uwar gidansa."Da hakan har ya sauketa agidanta tare da Jan kunneta sannan yabar gidan."Hakan ta kwanta cikin baqin ciki da bacin rai tare da alqawarin daukar mummunan mataki akan salma!" ________________________________ "Bayan watanni al'amurra sai tafiya sukeyi budi da haske sai qara shigowa yakeyi acikin rayuwar salman." "Hakan Rayuwar matansa normal sai dai babu zaman lafiya atsakanin su.Sam ko magana basayi bare biya juna dan minal tafi karfin salma acewarta!"Tuni Hajiya mai gado ta shirya da qanwarta da yan uwanta."Yayinda minal tana fita aikinta kudi na shigota ta ko ina tazama babbar mai kudi kuma sawon farko na manyan matan garin na ARGUNGU ana damawa da ita,"Aunty Zainab abin nema ya samu!"Sai baza rashin mutunci sukeyi ita da minal dinta." ita kuma salma tana business sai dai har yanzu babu abinda take fuskanta ga yan uwan mijinta sai zagi,da kyara,da gorin arxiki!" A kullum cikin kuka Take domin *BAKAR* *AKIDAR* su ta hana su yadda da ita kuma su zauna da zuciya daya ita minal kowa ke so!"Daga Maman salman da qanwarsa ilham sai shi kadai ne takejin dadi da sassauci tare da su!"Hakan ta cigaba da hakuri da taimakawa iyayenta." "Salman ya ginawa iyayen salma katafaren estate mai Babban get daya yayi kyau matuka gini kalar na qasashen waje ba zaka ga abin burgewa sai an shiga daga ciki tamkar aljannar duniya."Inna baraka da Malam an murje kurciya ta fito sunyi kyau sosai ashe daman talauci ne ya mayar da su tsofaffi!" .A cikin estate din duk yan uwan Malam ne suka dawo ciki da zama sai dai part din Iyayen salma yafi na kowa kyada tsaruwa akwai masu gadi masu baiwa flowers ruwa drivers yan aiki da sauran ma'aikata."Part dinKawu Kawu Bala ma ba laifi komai ya wadace su shi da matansa,Dan ya auri wata malamr islamiyya Ayshatou suna zaune lafiya da abokiyar zamanta"Tuni Larai tayi laushi ta gane hanya kuma ta tuba."Domin ta fahimci duk arzikin da suke ciki ayanzu albarkachin salma da iyayenta ne."Yanzu komai tana yiwa inna baraka cikin jin dadi."Karime ko tana gidan dan ummaru suna zaune cikin tufin asirin Allah. "Anyi shagali Auren Dr.jameel da Engr.Maryam(Ilhaam) da dadewa ta tare gidanta da haduwarsa ma bazai fadu ba da me unguwar lowcost Argungu,"Suna zaune lafiya da mijinta."Nidal qawar minal ma tayi aure a garin sakkwato."Tashin hankalin da minal da mahaifiyarta ke ciki bai wuce salma nata haihuwar yan biyu har sau biyu ta farko maza ne Muhammad,da mahmood,ta. biyu mata Nabeeha da Nabeela."Amma ita har yanzu ba amo ba labari!"Dalilin hakan yasa suka tilastawa Dr.salman da yayi iya kokarinsa domin ganin ya sama mata magani !"Amma basu gani sunce dole sai an fita waje anyiwa minal dashe!"Ta haihu!Saboda duk duniya ba wacce suka tsana irin salma da yaransa!"Dole salman ya amince shi Hajiya ba dan ransu ya so ba!"Aka fita da minal qasar India."Anyi aiki kuma an samu Nasara minal tasamu juna biyu sai wani kaudi da iyayi akeyi duk wani shiri anti."Saboda suna son ayi sunan da ba'a taba irinsa agidan Dr.salman ba." "Lokacin haihuwar minal yazo daya da salma inda ta haifi d'a namiji minal ko C.S akai mata inda tasamu baby girl."sai dai minal ko 'yartah bagani ba Allah yayi mata rasuwa!Saboda wuya da azaba da wahala!"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!!!Mutuwar minal!"Ta razana kowa duba ga irin shirin da sukayiwa sunan idan ta haihu!"Aunty Zainab da Hajiya mai gado da salman sunyi kukan rashin minal sosai da sauran dangi 'yan aikinta ma sunji ba dadi falmata da lami duk da bawani jin dadinta sukeyi ba amma kudin da suke samu ne abin bakin cikin su"Bayan sadakar arba'in yarinya taci sunan Zainab ana kiranta da (mimah)Shi kuma yaron salma yaci sunan Marigayi Taheer (Mu'allim)Sai dai mima na hannun Aunty Zainab tana bata madara."Ba yadda salman baiyi da ita ba dan abawa salma ta hada mimah da mu'allim ta dinga shayarda su amma tace sam ba za'a gurbata mata jinin jika da gubar talauci da tsiya ba!"Haka ya hakura ya barta hannun Aunty Zainab din, tare da nuna mata so da kauna da kulawa saboda yana jin tausayin marainiyar yarsa Mimah mai kama da mamanta minal!"Fatan shi kada ta biyo halayen mamanta duk da tuni ya yafe mata."Domin Sam minal batasan darajar aure ba!"Bata iya komai sai dai yan aikinta suyi!" *BAYAN WASU SHEKARU* "HAjiya salma ce zaune acikin hadadden gidan su da Ambr.Mahmood Salman ya Gina musu."Yanzu ta zama hamshakiya uwar manyan mutane masu ji da kudi."Domin Mahmud shi ne Ambassador na Nigeria, Muhammad ko comisioner of police, Sai Dr.Nabeela da Nabeeha ta zama International business woman."Duk Kansu sunyi aure an fara tara iyalai." "Mima da mu'allim suna saudiya suna karatun Islamic shar'ah low." A yanzu family *GALADIMA KO MAI WALDA* sune family da yayi sunan kudi ciki da wajen Nigeria saboda yawan kamfanoninsu,Gidajen sayarda man fetur, super market, da sauran ababen kasuwanci makarantu,Asibitoci,gidajen marayu Da sauransu."Malam Abu Sufyan mai walda An zama kakan alhazai da hajiyoyi duk shekara sai sunje Hajj da umrah kawu Bala naira ta zauna sai kasuwanci yakeyi shi da yaransa." "Hajiya Zainab taga iznah!"Da dadewa tagane gaskiya kuma tayi nadama akan *BAK'AR AKIDA!* Irin tasu ta banzah!Yanzu daga ita har mijinta basuda komai tunda yayi ritaya da jimawa kuma minal ta bar duniya asirin su yaso ya to no sai dai diyan salmar da suka tsana!A yau su ne suka tufa masu asiri suka tallafa masu ta hanyar dauke duk wasu lalurorin su da na sauran danginsu baki daya."Su saudat ancigaba sosai domin tana shiri da salma kwarai."Hakan Yaya Hafsa da sa'adatu an bi hanya angane gaskiya tuni suka nemi gafarar Hajiya mai gado da salma domin anyi laushi biye ake Ana cin arzikin salma da yaranta."Dama can BAKAR AKIDA CE ta rudesu ta bata masu tunani." "Yanzu kam duk masu tsanar salma akan tana 'Yar matsiyata sun tuba sun gane gaskiya kuma sun tabbatar samu da rashi duk na Allah ne, shi ke bayarwa alokacin da yaso ya kuma aminche!"Da talaka da mai arziki duk daya ne agurinsa!"Shi ke maida mai arziki talaka ya kuma mayar da talaka mai arziki."Dan ayanzu sun ga zahirin gaskiya."Hajiya Salma Dr.salman a yanzu batada matsala tana zaune da kowa lafiya Dama can batada problem da kowa tsakaninta da kowa alheri." "Ya kamata mutane masu irin wannan *BAKAR AKIDA* Su gane gaskiya akwai aure atsakanin mai kudi da talaka."Wani auren kwarya-tabi-kwarya ko bani-gishiri in baka manja ba alheri ba ne!"Da macen da namijin duk nagari masu nagarta yafi dacewa a aura."Masu nasaba mai kyau ilimi tarbiyya gaskiya da amana masu riko da addini."Kalubale gareku iyaye masu iron wannan Dabi'ar." "ALLAH YA SA MUGANE AMIN ,ALLAH YA SA MUTANE SU AMFANA DA HALAYE DA D'ABI'U MASU KYAU, ALLAH YA YAFE MIN KURAKUREN DA NAYI ACIKIN WANNAN RUBUTUN DA NA BAYYANE DA NA AIKATA , AMIN." *TAMAT BII HAMDILLAHI*