*_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆_ _______ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 __________ .......Suna shiga cikin headquter ɗin Lawyers nashi na isowa shima. Sai dai kafin su ƙarasa gareshi an shige dashi wani ɗakin bincike. Table ne kawai da kujeru biyu masu facing juna. Sai da ya gama ƙarema ɗakin kallo fuskarsa a yamutse kafin yaja kujerar ya zauna. Yana zama cikin jami'an wani shigo, da girmamawa yake tambayarsa ko yana buƙatar wani abu kamar su tea haka. Ɗan jimm yay yana kallon ma'aikacin, sai kuma ya murmusa kaɗan alamar a'a. Fita Jam'i yayi, shi kuma ya jingina bayansa da kujerar sosai ya lumshe idanunsa kawai. Kusan mintuna fin ashirin sannan aka sake buɗe ƙofar. Bai motsa ba bai kuma buɗe idanunsa ba har jami'in ya kai zaune. Kaɗan ya ɗan buga table ɗin, sai dai a hakan ma Maash ɗin ƙin motsawa yayi. Sai da ya mula dan kansa sannan ya buɗe idanunsa ya zubama jami'in batare daya tashi ba. Ji Jami'in yay bazai iya jure kallon ba, sai ya kauda idanunsa cike da basarwa yana furta, “Sir bamu da isashen lokaci. Idan ba damuwa ka amsa mana wasu ƴan tambayoyi mana”.        “Jeka maganarka kai tsaye” Maash ya faɗa a daƙile.      Ran jami'in ne ya sosu, sai dai baice komai ba ya cigaba da faɗin, “Akwai containers ɗinka da suka tashi daga Lagos a shekaran jiya da dare zuwa ƙasar Ghana. An samu yara ƴammata a cikin ɗaya da muke da tabbacin safararsu aka shirya yi. Still dai a cikin container ɗin anyima yaran makwanci, a ƙasan shi mun samu kayan laifi”.        “Kamar......?” Maash ya faɗa cike da rainin hankali. Yanzu kam a fusace jami'in ya kallesa. Sai dai kuma bai iya cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Drivers ɗin sun tabbatar mana da cewar sun fito daga companyn ka ne”. Ya ƙare maganar da tura masa hotuna gabansa. Batare da Maash ya ɗauki hotunan ba ya zuba musu ido kawai. Kansa ya ɗan girgiza cike da rashin damuwa ya furta, “A staff ɗina bana tunanin nasan waɗan nan fuskokin”.        “Ba zamu tabbatar da hakan ba, dan zaka iya hiding nasu. Sai dai kuma su containers ɗin ai bazai yiwu kace ba naka bane ba”.        Shiru babu alamar Maash ɗin zai tanka, sai da ya mula dan kansa sannan ya saki ɗan gajeren murmushi da kai hannu ya shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Zamansa ya gyara da ƙyau gaba ɗaya hannayensa akan table ɗin ya zubama jami'in ido. “Mr Man kamar ya dace ka tuna kai jam'i ne ba alƙali ba. Damar samuwar amsar tambayoyinka kuwa zaka same su ne kaɗai a bakin lawyers ɗina”. Daga haka ya gyara zamansa ya sake lumshe idanunsa duka hannuwansa harɗe a ƙirjinsa.      Iya ɓacin rai Jam'in nan ya shiga. Dan haka ya miƙe a fusace ya fice abinsa. Murmushi Maash ya saki mai ɗan sauti batare da ya buɗe idanunsa ba.          Har yamma Lawyers na Maash na fafatawa a station ɗin, shi dai yana a inda aka kaisa har yanzu. Sai da lokacin Sallah yayi ya buƙaci yin alwala. Basu da damar hanashi. Abincin da Hayatu ya kawo masa kuwa ko kallonsa baiyi ba. Dan shi fa sam bawai cakwakiyar station ɗin ma bace damuwarsa. Hankalinsa ma gaba ɗaya baya a wajen.      Gab da magrib Baba prof... Ya iso, da ga airport kai tsaye shima station ɗin yayo, anan ya samu kusan duk ahalin gidan. Paah, Uncle Abdullahi, Hajiya Mammah, Maman Maleeka (Matar Uncle Abdullahi) sai Hayatu dake kai kawo tsakanin asibiti da aka kwantar da Samraah zuwa nan. Ko bayan isowar Baba prof.. ɗin shima ya kai awanni uku a station ɗin kafin su samu bell ɗin Maash ɗin bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri.          Ƙarfe tara da wasu mintuna aka fiddo Maash da ga ɗakin nan. Kallo ɗaya yay ma ahalin nasa ya ɗan kauda idanunsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a nutsensa har inda suke. Baba prof.. ne ya riƙosa ya rungume yana faman ambaton Alhamdullah. Shi dai Maash baice komai ba. Bayan ya sakesa kuma ya koma tattaɓashi da jera masa tambayoyi. “Kana jin yunwa? Akwai inda ke maka ciwo? Sun maka wani abu ne?.....”        “Grandpa! I'm not small boy now”.    Ya katse Baba prof.. ɗin cikin wata irin murya mai cike da rashin damuwa. Murmushi Baba prof.. yayi da kai hannu ya yamutsa masa sumar kansa kamar yanda yake masa a duk sanda suka haɗu. “Oh na manta Muhammad Awwab ɗina dutse na rimi ne baka fargaba sai ta ruwa.”          Dariya su Paah suka ɗan yi, kafin shima ya matso ya rungume Maash ɗin, hakama Uncle Abdullahi. Maman Malika ma tai masa barka. Ganin haka itama Hajiya Mammah ta bashi side hug. Shi dai komai bai cema kowa ba. Sai hankalinsa da ya ɗan maida ga lawyers ɗinsa da Hayatu dake fitowa. Cike da girmamawa suka shiga gaisheshi. Tare da jajanta abinda ya faru suma. Idanunsa ya lumshe kaɗan da sake buɗewa, suma ɗin dai batare da yace ma kowa komai ba ya motsa a hankali ya fara tafiya.      Suma duk ƙoƙarin ficewar sukayi, kowa da abinda ke a zuciyarsa. A motar da yazo da ita da safe ya shiga. Sai dai yanzu Hayatu ne a mazaunin driver. Har sun ɗauki hanyar gida a kasalance Maash da idanunsa ke rufe har a lokacin a hankali ya furta, “Hospital”.        Cikin girmamawa Hayatu ya amsa masa, tare da fita a cikin sauran motocin ya ɗauki hanyar asibiti. Sauran abokan tafiyar basu farga ba sai da akaje sauke Baba prof a gidansa. Da farko sun ɗauka ko gida su suka wuce saboda Maash ɗin ya huta, sai da drivern Baba prof ɗin ya sanar da inda yaga sunyi sannan ne a fusace Hajiya Mammah ta ce, “Eh lallai, al'amarin Awwab kullum sake gawurta yake wlhy. To amma kuma anya ba wani abun yaje aikatama yarinyar nan ko hana likitocin faɗa ba saboda ya rufe sirrinsa.”         Har cikin rai zancenta ya soki zuciyar Paah, sai dai baice komai ba. Baba Prof ne ya tambayi abinda ke faruwa? Har zagwaɗi Hajiya Mammah keyi wajen zayyane komai daya faru da safe har neman yarinyar da suka dinga yi da daddare. Wani yawu mai kauri Baba prof ya haɗiya idanunsa akan Paah da Uncle Abdullahi. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Wayarsa ya amsa a hannun drivern sa daya kwaso kaya zai kai ciki, dan duk abinda Hajiya Mammah ta faɗa ya laɓe yana jinta. Kai tsaye Baba prof ɗin wayar Hayatu yay kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga.       “Kuna ina?”.    Da ƴar in ina Hayatu ya ɗan kalla Maash dake ƙoƙarin fita a mota daya buɗe masa dan isowarsu ke nan. “Bab ba baba muna CLINIC”.      “Clinic! Yin me?”.    “Zamu duba mara lafiya ne”. Ƙittt Baba prof ya yanke kiran batare daya sake cewa komai ba. Cikin damuwa Hayatu ya dubi Maash ɗinya ce, “Baba Prof”.         Komai baice masa ba, sai ma ƙoƙarin raɓasa da yake yi zai wuce abinsa. Dole shima ya haɗiye abinda ke bakin nasa ya bisa.           ★★     Mama Balki na zaune a saman abin salla idar da shafa'i da wutirinta kenan akai knocking ɗin ƙofar. Miƙewa tai tana kallon agogo, azatonta ma Nurse ɗin data sakama Samraah ruwa ce ta dawo. Ruwan ta kalla taga ko rabi bai kai ba ma, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ƙofar ta nufa, sai dai kafin ta buɗe sai da ta tambaya waye?. Hayatu ne ya amsa mata da cewa, “Mama mune”.      Da sauri ta buɗe tana murmushi, tana ƙoƙarin bashi hanya ya shigo idonta ya sauka akan Maash. Wani irin washe baki tayi tana ambaton Alhamdullah. Da jerama UBANGIJI kirari. Ɗan lumshe idanunsa yayi tare da sakin gajeren murmushi ya shiga gaidata. Amsa masa tai tana ƙara godema ALLAH daya sa komai ya zama mai sauƙi.        Nan ma murmushin kawai ya saki baice komai ba, sai Hayatu ne ke tayata murnarta. Ƙarasa takawa yay a hankali zuwa gaban gadon idanunsa a kanta. Tana kwance samɓal idanunta a rufe alamar barci take. Fuskarta ta wani irin yin fayau da ita, sannan har yanzu idanunta a kumbure suke alamar taci kuka mai yawa. Lips ɗinta sun bushe tare da tsukewa waje guda sun ƙara pink sosai. Take wasu abubuwa suka shiga dawo masa game da ita. Cikin sauri ya kauda su tare da janye idanun nasa daga lips dinta, akan hannunta da aka saka ruwa ya sauke. Madaidaitan farcinanta dake da ɗan sauran jan lalle na biki kaɗan da bai gama fitaba yaja kusan mintuna biyu yana kallo, kafin ya maida ga ruwan da ake ƙara matan. Sai kuma ya janye gaba ɗaya ya matsa gaban side drawer dake a gefen gadon ya ɗauki file ɗin da aka ajiye ya fara dubawa. Juyowa yay da nufin yin magana sai ya ga ɗakin wayam, ashe Mama Balki da Hayatu sun fice. Kansa kawai ya girgiza yana ajiye file ɗin, sannan ya zagaya ta ɗayan side ɗin gadon inda hannunta ke free ya zauna kusa da ita jikinsa na gogar nata. Hannun nata ya kamo cikin nasa, ya zubama dan sauran lallen dake jikin faratan nata ido, abubuwa da yawa zuciyarsa ke tunano masa da suka shafi Ummie, mace ce mai tsananin son jan lalle, tunda ya santa kafin lalurarta lalle baya gama fita a hannunta take yin wani. Hakan ya sashi tashi da son lalle shima, lokacin yana ƙarami yakan saka mata rigima shima sai an masa. Takan ce masa maza basa lalli, amma ya tubure ya dinga bori ko yaje ya tsare Mama Balki ko mahaifiyar Hayatu akan dole su sai sun masan, dan a farkon ciwonta kafin komai ya damule har da kansa yake mata lallin a yatsun hannu saboda yasan tana so. Murmushi ne ya suɓuce masa da shi a karan kansa ya mance tsahon shekarun daya ɗauka baiyi irinsa ba. Sai kuma ya kai babban yatsarsa ya ɗauke guntun ƙwallar da suka taru masa a gefen ido kaɗan........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _______ .......Ɗan motsi Samraah tayi fuskarta a yamutse baki a taɓe kamar mai shirin sakin kuka. Idanu kawai ya zuba mata yana kallon yanda take laɓe bakin, ƙoƙarin motsa hannunta da tai ya sashi sakin wanda ya riƙe ya riƙe mata wancan gudun karta goce ruwan, sake yamutse fuskar tayi da ƙara tura baki.       “Cry. Cry”.     Ya faɗa a hankali saman lips ɗinsa yana kai ɗayan hannunsa a karo na farko kan fuskarta ya ɗan shafa gefen kumatun kaɗan. Idanunta ta shiga motsawa a hankali, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya. Cikin yanayin wadda barci bai saka ba ta ɗan zuba masa su, shima kallon nata yake...             Tar tar fuskarsa ta fara bayyana cikin idanun nawa sosai. Wani irin harbawa zuciyata tayi babu shiri na zabura. Sai dai jin an riƙeni yasa na kallesa a marairaice, batare dana san hawaye sun ɓalle min ba na fara roƙonsa cikin magiya. “Na roƙeka dan ALLAH kayi haƙuri ya Awwab, wlhy zan iya mutuwa bazan iya ba”.       Ganin bashi da niyyar tanka min sai rikitattun idanunsa daya zuba min yasa na sake fashe masa kuka mai ɗan sauti. Kansa ya ɗan girgiza tare da sakin hannun nawa ya kuma janye wanda ke a fuskata sannan ya miƙe, kaɗan ya ranƙwafo ya kama bargon. Sake marairaice masa fuska nayi ganin yanda ya duƙo kaina sai yanayin ya sake min kama da na wancan lokacin, idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe cikin soft voice ya furata, “I will go now. calm your mind”. Ya ƙarasa lulluɓa min bargon har saman ƙirjina. Idanuna na lumshe sauran hawayen dake cikinsu na ƙarasa gangarowa. A bazata naji saukar lips ɗinsa saman goshina. Kafin na buɗe idanuna a firgice harya juya yabar wajen.      Ƙofar daya maida ya rufe na zubama idanu, a hankali bugun zuciyata na sauka. Shigowar Mama Balki ɗakin ya sani kauda kaina daga kallon ƙofar. Kaina tayo kanta tsaye tana faɗin, “Kin tashi Samraah?”.         Kaina na jinjina mata da ƙoƙarin kai hannu na share hawayena, zama tayi a gefena tana mai kamo hannuna cikin nata. Cike da lallashi da kulawa ta ce, “Kukan nan ya isa mana haka Samraah. Abinda ya faru dai ya riga ya faru ai. Sai fatan ALLAH ya baki lafiya. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, bana son ko a fuska ki nunama Alhaji ƙarami wani abu. Koba komai shi ɗin mijinki ne, kowace mace kuma da haka ta girma. Komai zai wuce kamar bai faruba. Naga ya fita kamar cikin damuwa, gaki ke kuma kina kuka. Dan ALLAH ki daure ya samu sassauci ko'a wajenki ne. Kinga yanzu daga police station ya fito tun safe amma ko gida baije ba sai da yazo nan domin dubaki. Alhaji ƙarami abin tausayine wlhy”.          Idanuna na buɗe a hankali ina kallonta, sai kuma na kai hannuna na sake share hawayen da suka gagara tsaya min. Cikin dasashjiyar muryata na ce, “Mama ni babu abinda nai masa fa. Kawai dai shi yasan mike damunsa. Mi yaje yi police station kuma?”.      “Nasan babu abinda kikayi masa Samraah. Amma nasan kukan nan da yaga kinayi ma ya isa ya sake ɗaga masa hankali. Ki daure ki daina kinji. Idan shima yaga kin kwantar da hankalinki zai fi samun nutsuwa wajen baki kulawar da duk kike buƙata. Sannan ya fuskanci abubuwan dake gabansa. Dan nasan akan batun nan naku wata sabuwar cakwakiyace kuma. Su suna kallo al'amarin da wata suffa daban, idan kuma baya gadama ba duk abinda zasu yi bazai sanar musu alaƙarku ba dan da kike ganinsa nan akwai taurin kai da kafiya. Bamu san abinda ya faru ba da safe folisawa suka cika mana gida wai sunzo kamashi” daga haka ta cigaba da lallashina har na sake komawa barci raina fal mamakin zancen kamashi da tace anyi, a yanda yake da kuɗi da power ɗin nan har jami'an tsaro zasu iya kamashi ashe?...          💦💢💦💢💦    “Ni nai sa'a da masoyi mai fara'a, shi ya fara sa shadda duk garinmu an shaida bai ɗaya. Ni na shirya, zana baka soyayya, koda ƴan baƙin ciki zasu haɗiyi zuciya. Ni na dace, na faɗa ko na dace, da sahibi imamullah mijin ƙwarai”.         Halime kenan, ke raira waƙarta cike da nishaɗi tana wanke-wanke a babban kitchen dake mallakin kowa da kowa. Wanke-wanke take na kwanikan da akaci abincin rana da tayi, yau kuma ne zata fita a aiki Mom ta amsa. Da farko aikinta take hankalin kwance sai dai shigowar Mom kitchen ɗin da abinda tai mata ya ƙona mata rai. Maimakon ta biyema Mom ɗin sai kawai ta shiga raira waƙa. Idan tayi wannan sai ta saki ta kama waccan harta kammala wanke-wanken. Kasa haƙuri Mom dake tare da mai-aikinta tana bata umarnin abincin dare da zata ɗora musu tayi. Cikin fusata ta shaƙo wuyan rigar Halime ta baya ta fusgota.        “K ƙaramar ƴar iska waƙe-waƙe ai bazai kai miki ba. Rama abinda nai miki ya kamata kiyi sai na san kin cika matsiyaciya”.      Idanu kawai Halime ta zuba mata, sai kuma tayi murmushi da kai hannu ta janye hannun Mom ɗin a jikinta. Ƙoƙarin juyawa take ta ƙarasa aikinta Mom ta sake ƙoƙarin damƙota cikin masifa da haushin shirun da tai matan, dan so take ta tanka mata akwai abinda zata saka mata a gashi. Wani shegen tsalle Halimen tayi gefe kai kace tayi gamo da wani bala'i ne. Hakan yasa mai aikin Mom da ita kanta Mom ɗin sai da suka zabura. Sai kawai tsabar wulaƙanci Halime ta fashe da dariya. Galala Mom da mai aikinta sukai suna mata kallon mamaki. Itako sai ta kallesu sai ta fashe da dariya, da tayi kamar zata tsagaita sai ta kallesu ta sake fashewa da dariyar. Wani irin tuƙuƙi zuciyar Mom ta shiga yi, tana yunƙurowa a fusace zata sake shaƙo Halimen sai kawai ta kauce mata tare da ɗaukar kayanta data tara a kwandon kife kaya tai ficewarta. Sai dai taje bakin ƙofa sannan ta ɗan dakata. Juyowa tai ta kalla Mom har lokacin fuskarta da sauran dariyar ta ce, “Ƴar baƙin ciki, so kike na biye miki muyi dambe dalin Imamu ya talauce saboda ke kin gama shan daɗin romin zabbi. To wallahi bashi yiwuwa nima sai na dandali arziƙin nan. Ɗan romon kifin nan dana kaji da ban samu naci a gidanmu ba sai na sha farina ya sake fitowa nayi ɓul yanda zanje ƴan tumaki ana ku matsa ga matar Alhaji Imamu nan ta iso haaaah”. Ta ƙare maganar da gatsine mata baki tana yin gaba abinta.        Kasa ko motsi Mom tayi, sai zuciyarta dake wani bala'in yunƙurowa. Wai itako yaya zatayi da mahaukaciyar yarinyar nan a gidan nan. Tayi bala'in, tayi fitinar, tayi boren, tana kan asirin amma duk a banza. Babu irin maganin da batai amfani da shi ba a kofar shiga ɗakinta da cikin abincin da Abba da Halime zasu ci amma ko gezau. Jiya har layun da teacher ya bata ta shiga har ɗakinta ta sanya a ƙarƙashin gado amma ko gezau, bayan kuma Umma ta tabbatar mata idan har ta saka layun yarinyar nan ta kwanta a gadon bazata kwana a gidan ba sai dai gidan Ubanta. Kuma komai dare sai ta koma garinsu a ƙafa. Haka ta kwana zaman saurare amma har gari ya waye babu ko dogon motsi daya faru a gidan. Sai ma da farar safiya Halimen ta tashi ta damesu da aiki da waƙe-waƙenta na iskanci kai kace ita ɗin jikar barmani choge ce ko shata.          A fusace itama ta bar kitchen ɗin tana dakama mai aikinta tsawa....          💢🌟💢🌟💢             Suna akan hanya nufar gida Hayatu ke bashi labarin rikicin da Ummie tayi yau a gida na neman Samraah. Har falon ƙasa ta sakko yau tana riƙe duk wanda ta gani ta bisa da kallo, sai kuma ta girgiza kai ta saki wanda ta kama ɗin ta tafi na gaba. Bayan ta gama bin kowa bata ga wadda take neman ba sai kuma ta zauna ta sanya kuka. Abin yayi matuƙar bama kowa mamaki. Nima na koma amso kayan da zasuyi amfani da shi ne na tadda wannan drama. Da ƙyar na lallaɓata bayan na ambata mata sunan Aunt sai ta shiga gyaɗa kanta alamar dai tabbacin ita ɗin take nema. Lallashinta nayi tare da tabbatar mata zanje na kirawo mata ita sannan ta yarda ta koma saman. Shine dana kai musu kayan na samu abinci na kai mata taci na bata magungunanta. Tana kammala ci sai barci. Koda na koma bayan magrib ɗin nan na samu har lokacin tana barcin. Yaya abin nan yamun daɗi, da'alama Ummie ta fara samun lafiya, tunda har take iya banbance mai ƙyautata mata. Lallai Aunty Samraah alkairi ce a rayuwarmu. Lallai akwai hikima a cikin sanadin shigowarta rayuwarmu”.          Kamar yanda Hayatu yayi tsammani baice komai ba. Sai dai a bazata badan kar ace yayi ƙarya ba sai yaga kamar yayi murmushi. Amma dai baya ce ba, tunda ba gani yay ƙuru-ƙuru ba kasancewar fuskarsa na gefe.      Shiru ya samu gidan da alama kowa ya kwanta, maimakon wucewa nasa sashen duk da yunwa da gajiyar dake addabarsa sai ya nufi sashen Ummie. Daki-daki yake bin ko'ina da kallon tsaff, gaba ɗaya sashen ya canja yanzu akoda yaushe cikin ƙamshi da tsafta yake. Duk da a yanzu falon farko ne kawai mai kujeru, amma sauran duk an kwashe komai tunda Samraah tayi magana. Duk da a ɗari-ɗari yake bai dakata ba sai da ya dangane da bedroom ɗin da a yanzu yafi samunta. Sassanyar ajiyar zuciya ga sauke yana mai jingina da bango da lunshe idanunsa sannan ya buɗe a kanta. Barci take har yanzu, sai kuloli masu ƙyau ata gefenta alamar abincine a ciki, yasan wanda Hayatun ne ya kawo, dan haka ya ƙarasa a hankali cikin takun sanyin jiki ya bubbuɗe kulolin. Lafiyayyen abincine da ko ba'a faɗa ba yasan Falak ce ta yisa duk da tana fama da kanta itama. Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzar da iska mai nauyi daga bakinsa. Sai kuma ya maida komai ya rufe ya koma bakin katifar ya zauna. Blanket ɗin data ɗan zazzame ya gyara mata, a hankali ya kai hannu ya gyara mata hularta da ita ta zame. Sosai ya zuba mata idanunsa da suka kaɗa sosai. Daka gani kasan kukan zuci yake yi. Ya jima zaune a ɗakin duk da uban barcin da yake ji har kusan gabannin asuba ciwon kai ya takura masa sosai sannan ya miƙe........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_**_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _______ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 _______ .......Tsaff sashen nasa yake an gyara komai tamkar koman bai faru ba. Yasan aikin Mama Balki ne wannan. Dan hatta bedsheet ɗin saman gadonsa da blanket an canja su da wani fari tass mai ƙyau da masifar laushi. Bathroom ya shiga, can ma ɗin dai an tsaftacesa. Sai kawai yayi wanka tare da ɗauro alwala ya fito. Sai da ya fara gabatar da shafa'i da wutri sannan ya kwanta dan barci sosai ke cin idanunsa ga ciwon kai da baya raba ɗayan biyu a dalilin zaman sashen Ummie da yayi ne. Dan lafiya lau suka shigo gidan sai gajiya dake damunsa. Yana kwanciya kuwa barci mai nauyi yayi awon gaba da shi...          Da asuba makarar da yayi ce ya sashi yin salla a ɗakinsa ya sake kwanciya. Barci ne mai nauyi ya ɗaukesa har ya manta ma safiya ce ba dare ba. Duk da kuwa shi da wahala kaga yana barcin safe ko rana. To inama yaga wannan lokacin kullum abubuwa sun ma kansa yawa. Idan har kagansa yini guda a gida yana hutawa lallai ba lafiya ba. Ko kuma akwai wani ƙwaƙwƙwaran dalili. Dan ko nan ta samu ya gudo dan ya huta baka rabashi da laptop ko tab a hannu yana harkokinsa.       Cikin barci sautin knocking ɗin ƙofa ya addabesa. Dole ya buɗe idanunsa yana mai karanto addu'a. Sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya miƙe zaune cike da takaicin wanda ke damun nasa. Agogo ya kalla goma da wasu mintuna na safe. Yaɗan furzar da iska kaɗan tare da zuro clean ƙafafunsa ƙasa. Nan ɗin ma sai da yaja wasu sakanni sannan ya ɗauki remote ya danna ƙofar ta buɗe kanta. Paah ne ya shigo, dan haka ya zuba masa ido kawai yana kallonsa. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa a hankali ya ce, “Good morning”.         Amsa masa Paah ɗin yay da, “Morning dear, ka tashi lafiya?”.       “Alhamdullah”.     “To masha ALLAH. Dama Baba ne yazo tun ɗazun, da yace kar a tashe ka harka tashi da kanka, sai kuma ga baƙi munyi da ga human right, wai sunzo ne akan case ɗin yarinyar nan. Bamu san wanene yaje ya sanar musu ba a gidan nan. Muhammad wai miya kaika aikata al'amarin nan? Bayan nasan wannan ba halinka bane ba. Baka aikata a waje ba sai a cikin gida, haba Muhammad da mahaifiyarka na cikin lafiyarta mi kake zato”.           Komai Maash bai ce ba har Paah ya gama maganarsa. Cikin ɓacin rai ya juya ya fita yana mai bashi umarnin fitowa yanzun nan ana jiransa kada ya ɓata musu lokaci. Da kallo kawai ya bishi na tsawon mintuna har biyu, kafin ya furzar da nannauyar iska ya miƙe. Bathroom ya nufa, bai wuce mintuna biyar ba ya fito. Ba tare daya canja pyjamas ɗin jikinsa ba ya zura bedroom slippers ɗinsa masu taushi farare tas kamar pyjamas ɗin nasa ya fito. Baiyi zaton a falonsa suke ba. Dan haka yay ɗan turus yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Gaba ɗaya manyan gidan ne sai baƙi fuska mata biyu da maza biyu. Ɗauke idanunsa yay cike da basarwa, a dakile ya furta, “Good morning”. Yana kaiwa cikin kujera da ke gefen Baba prof alamar shi aka barma wajen zaman dama. Duk da dai kowa ya samu nasa gurin kasancewar falon bawai kujeru bakwai bane ba kawai. Yanda ya tsuke bakinsa da ga gaisuwar farko kowa ya fahimci jam'i yayi. Kuma bazai sake wata ba. Harara Hajiya Mammah ta watsa masa. Hakama Hajiya ƙarama sai da ta ɗan cija lips. Maman Malika ce kawai tayi ɗan murmushi da faɗin, “Awwab babu dai wata matsala ko?”.        Kansa ya jinjina mata. Sai kuma a hankali ya ɗan motsa lips ɗinsa ya ce, “Alhamdullah Mamy”.      Da fara'a itama ta ce, “Alhamdullahi mun gode ALLAH. ALLAH kuma ya kiyaye gaba”.      Baba prof, Paah, Uncle Abdullahi suka amsa da amin. Duk da dai fuskokinsu babu walwala suma. Kallonsa Baba prof yayi kamar mai nazari, kafin ya masa nuni da baƙin fuskar yana faɗin, “Baƙine daga human right. Wai sun zo ne akan case ɗin yarinya da akai raping anan gidan. Sunyi-sunyi da ita tun jiya wai ta faɗa musu amma taƙi. Shiyyasa suka zo domin ganawa da kai, suna son a basu izinin yin bincike akan case ɗin”.        Shiru babu alamar Maash zai amsa kamar ba da shi Baba prof ɗin ke magana. Dan tun kallo ɗaya da yayma mutanen bai sake ba. A yanzu ɗin ma da yaji bayanin komai daga baba prof ɗin bai kallesun ba bai kuma tanka ba sai da ya mula dan kansa. Zamansa ya gyara cike da ƙasaita a wulaƙance ya kallesu a karo na biyu. Cike da gizagonsa ya furta, “Ko zan iya sanin mai kai report ɗin?”.         Kallon juna sukayi, sai kuma cikin ƙarfin hali namijin dake facing Maash ɗin ya furta, “Ranka ya daɗe wannan ai sirri ne bama buɗesa. Duk wanda ya kawo mana report akan wani case yana da cikakkiyar kariya a garemu tako wace fuska. Amma idan munyi kuskuren shigowa bada izini ba ayi mana afuwa. Muna akan aikinmu ne”.         Kamar bazai tanka ba dan har sai da kowa ya zuba masa ido a falon, sai kuma ya yunƙura ya miƙe yana faɗin, “Okay tunda har kuka fahimci hakan da kanku ina fatan zaku gane hanyar da kuka shigo. Dan bana buƙatar fitowa na sameku koda a gate ɗin gidan nan ne”. Daga haka yay wucewarsa cike da takunsa na izza.        Duk binsa sukai da kallo, sai da Baba prof ya katse yanayin cikin wayancewa ya saki murmushi da faɗin, “Kufa yi haƙuri, shima tun jiya ransa a ɓace yake da faruwar al'amarin. Wani dalili ne ma daya ɗan gitta yasa bai ɗauki mataki ba. Amma na tabbatar tunda har kuka zo nan da kansa zai nemeku idan ya huce. Maybe shigowar karan tsaye da kukayi mana ne ya tunzurashi. Amma in har komai ya dai-daita ni da kaina zan nemo ku in sha ALLAH”.      Badan sun gamsu da bayanin Baba prof ɗin ba suka miƙe. Sai dai sun tabbatar da yanda suka karanci tsagwaron rashin mutunci a fuskar Maash ɗin to lallai idan har ya dawo ya same sun komai zai iya faruwa. Har gate Baba prof yay musu rakkiya yana ƙara basu haƙuri. Sai da ya ga fitar motarsu sannan ya dawo. Zama suka sake yi jugum-jugum amma babu alamar Maash zai sake fitowa. Hajiya Mammah ce ta katse zaman shirun nasu da faɗin bara ta sake kiran Maash ɗin. Amma sai Baba prof ya dakatar fa ita akan ta barsa yana son yanzu shi yaje asibiti yaga yarinyar kafin su san ta hanyar da zasu ɓullo ma al'amarin. Sam bata so haka ba, sai dai ganin sauran duk sun bada goyon baya yasa ta yin shiru....        Maash kam daga falon hanyar da zata sadashi da sashen Ummie ya nufa. Ya samu sashen na sabon ƙamshi alamar an masa gyara. Sosai yayi mamakin waye kuma? Tunda yasan ita tana asibiti. Yana shiga yaci karo da mama Balki na shirin fitowa. Cikin kasa ɓoye mamakinsa ya ce, “Mama kece?”.      Murmushi tayi cike da kulawa ta ce, “Eh Alhaji ƙarami. Ai mutuniyar taka ce tun asuba data farka take ta roƙona nazo na duba mata Ummie, tasan maybe bata ci abinci ba. Harda kukanta. Dan haka ina yin sallar asuba gari yay haske nai shirin tahowa sai kuma ga Hayatu ma yaje kai abinci shine na biyosa ya kawoni. Gata nan har ma taci abinci tasha magani barci ya ɗauke ta. Sauri nake kuma na koma can asibitin yanzu dan zata iya ƙin shiga ruwan zafin dana bar mata itama”.             Idanunsa ya ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci ɗaya. Sai kuma a hankali da silent voice ɗin nan nasa ya furta, “ALLAH ya saka da alkairi Mama”.     “Amin Alhaji ƙarami ai yiwa kaine. Bismillah ka shiga, Bara naje Hayatu na jirana zai maida ni”.      Shiga yay ita kuma ta fice. Ya jima a ɗakin yana kallon Ummie har sai da kansa ya fara juya masa sannan ya fito. Da gaske sauƙi ya fara samuwa. Dan inda dane a yanda ya shigo ɗin nan komai barcin da take yi saita tashi kansa. Amma kalla jiya yafi zaman awa biyu amma harya fita bata ko motsa ba sai shine da ciwon kai ya addaba. Sashensa ya koma batare daya bi takan su Paah dake a falo ba. Yay wankansa ya shirya tsaff da shi. Bayan ya gama fesa turarurtukansa masu ƙamshi da tsada kala kusan biyar, shiyyasa ba'a gane ainahin turaren da yake amfani da shi yay zaman saka takalmi. Wayarsa da akai kira ɗazun bai ɗauka ba ya duba. MD ɗin companyn sa ne na Kano. Kiransa yay back, dan yasan akan maganar Musaddiq ne. Cike da girmamawa baturen mutumin ya gaishesa da ga can. Kafin ya ɗora masa bayani akan komai na Musaddiq ɗin ya kammala. Zuwa next week zai biyo jirgi zuwa nan Lagos daga nan sai ya wuce. Kamar yanda ya saba amsa wayarsa bata wuce ɗaya biyu koda zakuyi maganar awa ne ya amsa masa da “Okay” kawai ya yanke wayar. Daga haka ya ƙarasa shirinsa ya fito.     Hayatu da Tj kawai ya samu a falon suna jiransa. Bai zauna ba da ga tsayen ya amsa gaisuwarsu yana mai ɗan kallon agogon hannunsa mai shegen tsada da ƙyau. Sai kuma a hankali ya furta, “Let's go”. Duk miƙewa sukayi, yana gaba suna binsa a baya, sai ma Hayatu ne dake ɗan masa bayani daya shafesu dan akan kasuwanci ne har suka iso gaban motocin da aka gama shiryawa domin fitar tasa. A tare guards ɗinsa da sauran ma'aikatan gidan suka dinga kawo gaisuwa da jajanta abinda ya faru, tare da masa addu'ar kariya daga sharrin duk wani abun sharri. A karo na farko ya ɗan saki gajeren murmushi tare da haɗe hannuwansa a waje guda alamar ya gode. Kamar ko yaushe yana baya TJ na mazaunin driver Hayatu a gefensa. Sai motar guards ɗinsa guda biyu ata gaba da baya su suna tsakkiya.      Sam yawo da guards ɗin nan ba sonshi yake ba. Sai dai baida wani zaɓin daya wuce hakan saboda yanayin ƙasar tamu balle shi mai yawan maƙiya da masoya. Yasha tsallake tarko da aka shirya halaka rayuwarsa. Ana kusan ƙarshe ne da har ya samu harbi gab da shirin buɗe Companynsa na kano har aka harbesa, ALLAH dai ya taƙaita wahala harbin ya samesa a gefen kafaɗarsa ta hagu, daga nan ne Hayatu ya dage akan fitarsu da Guards ɗin.       Tsaiwar motocin ya sashi kauda tunanin ya ɗago, ganin asibiti ya sashi ɗan kallon Hayatu daya buɗe masa ƙofa. Murmushi Hayatun yayi yana duƙar da kai da sosa ƙeya. Komai baice masa ba face ɗan girgiza kansa kawai ya zuro ƙafafunsa ya fito. Ciki suka nufa batare da ya lura da motocin su Paah ba, amma shi Hayatu sarai ya gansu dan tsakanin isowar tasu da tasu ma ƴan mintuna ne.........✍️ To Masha ALLAH. Barkan mu da dawowa, ku tayani addu'ar dagewa na gama book ɗin nan kafin salla😀🥰 _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_ _______ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ____________ ......A ɓangaren su Paah kuwa isowarsu kenan asibitin suma. Ba kuma su san da su Maash a bayansu ba. Kai tsaye suka nufi cikin ɗakin bisa rakkiyar Mama Balki da sukai kira a waya. A tsorace cikin damuwa ta musu jagora dan bata san dami suka zo ba. Sai dai babu yanda zatayi dole tabi umarninsu. Sauƙin ma taga akwai Baba prof a tare da su. Sun shigo Samraah na zaune a kan gadon jingine da filo tana shan tea ɗin da Mama Balki ta haɗa mata a hankali. Fes take dan har tayi wanka saboda gashin ruwan zafi da Mama Balki tai mata bisa umarnin likitan. A hankali ta ɗago ta kallesu.         Sai da zucuyata ta motsa da ganin waɗanda banyi zato ba. Idanuna na maida na rissinar ina ƙoƙarin haɗiye mamakina da ƴar tsorata. Sai da suka gama zama a inda Mama Balki ta nuna musu sannan na gaishesu cikin muryata da sam bata fita saboda kukan da naci na kwana da yinin jiya. Wasu sun amsa wasu basu amsa ba. Ni kuma sai banji damuwar komai ba tunda nasan dama ba lallai duk su amsa ɗin ba. Kasa cigaba da shan tea ɗin nayi ban kuma ɗago na kalla kowa ba a cikinsu, suma kuma babu wanda ya sake yin magana. Dai-dai nan aka ɗan sake knocking ƙofar. Mama Balki ta zabura domin buɗewa. Jin yanda take jaddada kalmar sannunku da zuwa cikin jin daɗi ya sani ɗan ɗago idanuna na kalla ƙofar. Tamkar abin shiri sai karaf suka faɗa a cikin nasa. Wani irin ɗan jan nasan yayi yuuuu zai lumshe nai saurin fara ɗauke nawa da maida kaina na duƙar. Sai kuma naji duk zaman yama gundireni, ga wani bugawa da zuciyata keyi dan harga ALLAH ko ganinsa tsoronsa yake ƙara min, ni kaɗai nasan kalar masifar dana gani a daren shekaran jiya hannun mutumin nan, dan haka ko matsoraciya kika kirani a wannan gaɓar Bily ni bazan damu ba. Kofin tea ɗin na ajiye a side drawer ɗin gadon na zame a hankali na kwanta tare da lumshe idanuna. Ƙasa-ƙasa na tsinkayi wata muryar dattijo da kamar na taɓa jinta na masa magana. Banji amsar daya bashi ba kasancewar shi dama idan zai yi magana sai in yaso kowa ya jisa ne. Ya ringa yinta acan ƙasan maƙoshi kamar mai jin haushin mutane. Kaɗan nai ƙoƙarin buɗe idanuna dan ina son ganin mai muryar nan sai naga ya nufo inda nake gadan-gadan. Sai da zuciyata ta sake harbawa. Babu shiri na maida idanun nawa na lumshe. A bazata, matuƙar bazata naji alamun rankwafowar mutum da mayataccen ƙamshin turarensa da saukar numfashinsa akan fuskata. Ai babu shiri na ware idanuna. Shi ɗin ne kuwa, gaba ɗayansa yamun rumfa hannayensa duka biyu ajiye a saman gadon ta gefe da gefena. (Kambu! Anya mutumin nan nada kunya?) Na faɗa a zuciyata ina waro gaba ɗaya idanuna waje. Amma shi sai ya wani kaɗa min cat ɗin nasa da ɗage gira hankali kwance. Tuni ƙwalla sun cika min ido, cikin marairaicewa na shiga motsa lips ɗina zanyi magana. Sai kawai naji saukar yatsarsa a saman bakin nawa, idanunsa cikin nawa, cikin salon lumshe idanu da maida muryarsa low sosai ya ce, “Shiii!! Bana son surutu”.      Kunya takaici suka lulluɓeni a lokaci ɗaya. Gefe na kauda kaina tare da ture yatsansa daga saman lips ɗina, dan kalmar baya son surutun faifan taswirar daren shekaran jiya ta dawo min da shi fes. Hannun ya saka ya taro fuskar tawa ya maidota inda take. Baki na tura masa, ina son na hararesa amma shakkarsa da kwarjininsa sunyi masifar min ɗaurin goro, ga mayataccen ƙamshinsa dake tsarga min zuciya.         “Bakin nan yana buƙatar wani abu ne halan?” ya faɗa cikin soft voice yana ƙoƙarin maida yatsarsa a saman lips ɗin nawa. Hannu na na kai da sauri na rufe bakin ina zaro idanu, amma shi ko gezau zama ka iya rantsewa ba shine ke maganar ba. Hankalina sake tashi yayi na saci kallon inda ƴan gidansu suke. Duk suna nan a ɗakin har Mama Balki ma. Tamkar zan fasa ihu idanuna cike da ƙwalla na ce, “Duk suna kallonmu fa”.        Ƙoƙarin juyawa yay zai kallesu, ai bamma san na kai hannuna ba da sauri kan fuskar tasa na dawo da shi.    “What? kuma. Bakin ce na faɗa musu ne su fita kina son mijinki ya ɗanyi kissing ɗinki ba”. Ya faɗa cikin salon kashe ido da ɗan ɗage gira sama murya can ƙasa kamar mai raɗa yana ɗora hannunsa kan nawa da nake ƙoƙarin janyewa daga fuskar sa.            Harararsa na ɗan yi hawaye na cika min ido na ce, “ALLAH ya kiyaye ni yaushe na ce hakan? Kuma ni ba ƴar iska bace”.      “Oh really”. Ya faɗa cikin ɗage gira sama yana ɗan taɓe baki kaɗan da sake matso da fuskarsa daf da tawan. Wani irin bugawa zuciyata ta shiga yi da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirjina ta fito. A hankali na fara jin saukar iska da ƙamshin mouth freshener mai ƙamshin strawbarry. Luff nayi zuciyata na sauka a hankali daga bugawar da take da motse-motse a cikin ƙirjina, harda tura baki batare dana sani ba.         Ɗal ya ɗalle lips ɗin da yatsunsa murya can ƙasa ya furta “I'm not interested maida bakin”.     Cikin sauri na buɗe idanuna wani irin tuƙuƙi na turnuƙe min zuciya da takaicinsa. Dai-dai nan yake ɗagawa da ga duƙowan yana wani yin fuuuu da idanun nasa. Jinai kawai hawayen da nake riƙewa sun wani irin silalowa a hankali...        Maash kam da ya ɗago kallo ɗaya yayma kowa na ɗakin ya ɗauke kansa tamkar baiga irin kallon da duk suke masa ba na tsantsar mamaki da tu'ajjibi. A zafafe Hajiya Mammah ta yunƙura zatayi magana Baba prof ya girgiza mata kai alamar kar tace komai ba. Badan taso ba tai shiru, sai dai kallo ɗaya zaka mata ka fahimci yanda ta gama cika tai famm. Duk abinda ke faruwa hankalinsa na kansu ta wutsiyar ido, amma yay tamkar hankalin nasa akan file ɗinta daya ɗauka yake dubawa. Dai-dai nan likitar da ke dubata ta shigo ɗakin Nurse biye da ita. Ita ta fara gaishesu, dan duk inda akaga Family ɗinsu ana gurmamasu saboda Maash ɗin.        Sai da suka gama gaisawar sannan shi da bai ko kalleta ba ya ɗago shanyayun cat idanunsa ya ɗan kalleta, sai kuma ya kauda kansa cikin dakewar nan tasa ya mika mata takardar daya zare jiya a cikin file ɗin ya miƙa mata. Amsa tayi cikin mamaki, sai kuma ta kalla takardar. Ɗagowa tai cikin rashin damuwa, sai ma gani da take ai tayi abin arziƙi dan haka baki a washe ta ce, “Sir komai da ya kamata mun rubuta kamar yanda binciken mu ya bamu akan fyaɗen, dan a yanzu haka ma muna muku albishir ɗin samar da ƙwararriyar lawyer da zata tsaya mata akan case ɗin. Yau kuma zan kai report ɗin ma police dama izininku kawai nake jira kasancewar ita Hajiya tace ba huruminta bane sai kai yayanta kazo. Amma gaskiya sir ina ƙara bada shawaran kowa ya aikata irin wannan zalincin ga baiwar ALLAHr nan shima ya ɗanɗana kuɗarsa. Dan ALLAH ne kawai ya taƙaita al'amarin da zata ma iya kamuwa da matsalar yoyon fitsari. A yanzu haka ma dole tana buƙatar kulawa sosai saboda ɗinkin dake jikinta abin sam babu daɗi, dan ban taɓa ganin case ɗin fyaɗe na tsagwaron zalunci irin wannan ba. Banama jin mutum ɗaya ne ya aikata abi.....”          “Ina buƙatar sallama by now”.     Ya faɗa cikin katseta da yanayin da kowa ya kasa fassarawa daga garesa. Sororo likitar tayi tana kallonsa. Sai kuma ta ɗan marairaice fuska cikin nuna damuwa ta ce, “Sir ko akwai wani kuskure da mukayi ne anan ɗin? Wlhy duk kulawar da kake buƙata muna kan bata ita yanda ta kamata. Yanzu fa nake maka bayanin har lawyer ƙwararriya mun samar akan case ɗin”.         Komai baice ba, sai ma ɗauke kansa da yay cikin nuna ƙosawa da maganar tata. Da yaga bata da alamar fahimtar shirun yake buƙata sai kawai ya nufi gadon da Samraah take cikin takun ƙasaita da bajinta hannayensa duka zube a aljihu. Duk abinda ke faruwa ina jinsu, dan haka zuciyata ke wani irin gudu raina fal mamakinsa. Guy ɗin nan he is stubborn mutum wlhy. Rayuwarsa har mamaki take matuƙar bani, mutum kamar wani dutsi baka taɓa iya gane gabansa da bayansa. Cak ɗin da aka ɗagani ya dawo dani hayyacina, sosai na zazzaro idanuna waje cikin matuƙar mamaki da ruɗani, rawa lips ɗina suka kamayi. Da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi...miye haka kake yi?”.       Ko kallona bai yi ba, sai ma takawa daya fara a hankali babu wani alamar jin shi yayi ba dai-dai ba ya bi ta tsakkiyarsu ya fice. Nikam ai sai naji bazan iya jurewa ba kawai na cusa kaina cikin ƙirjinsa tare da saƙalo duka hannayena ta wuyansa na saki kukan da ban san dalilin yinsa ba........✍️ _Ehem ehem Yayanmu ikon ALLAH, na Samraah bada kanka a sare kace ma su baba prof ya faɗi🤣🤣🤣_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆_ .......Da sauri Hayatu dake tsaye daga bakin ƙofa yaja da baya kansa a ƙasa yana ƙoƙarin ƙumshe dariyar dake neman kufce masa. Isowarsa dai-dai saitinsa ya sashi haɗiye dariyar da ƙyar ya buɗe masa ƙofar da sauri yana ƙoƙarin matsawa.      “Kuzo da kayan”. Ya faɗa a hankali dai-dai yana ficewa gaba ɗaya daga ɗakin.          “A lallai Mu'azz ka haifoma kanka jaraba wlhy.”     Hajiya Mammah ta faɗa cikin tafa hannaye da riƙe haɓa. Babu wanda ya iya cewa da ita komai dan duk abin faɗar ya gudu musu a bakuna. Sai ma Baba prof ne daya motsa a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki yabi bayansa. Dole duk suma sauran duk suka motsa suka take masa baya. Sai da suka gama fita Hayatu ya ƙarasa gaban doctor ɗin. Kallon Mama Balki yay yayi murmushi. Itama sai ta murmusa tare da nufar kayayyakin su kawai ta shiga haɗawa. Doctor data gama shiga cikin ɓacin rai kallon Hayatu tayi zatai magana. Da sauri ya katseta da faɗin, “Doctor kiyi haƙuri kawai ki bada takardar sallamar nan. Dan wlhy boss da kike gani baya magana biyu. Tunda ya yanke hukunci ya yanku, ya kuma fiki sanin muhimmancin wannan patient ɗin taki”.       Cikin ɗan ɓacin rai ta ce, “Wane muhimmancin ta ya sani anan?. Ana gaya masa haɗarin da yarinya ke a ciki saboda zaluncin da akai mata yana nuna kamar ma baya fahimta. Ni ban taɓa sanin guy ɗin nan stubborn bane sai yau. Idan ma ɗakin ne bai masa ba way not yay magana sai a canja mata da wani”.     Murmushi kawai Hayatu yayi dan ya fahimci bafa zata fahimta ba. Itama sai ta fita rai a ɓace tana mita dan gani gake shima Hayatun neman raina mata hankali yake yi. Binta kuwa yayi bayan ya amshi kayan da Mama Balki ta haɗa suka fito tare. Yana zuwa office ɗin doctor ta miƙo masa takardar sallamar a harzuƙe. Komai baice mata ba ya ɗauka ya juya abinsa ya fito.           Samunsu yay suna shiga mota, dan shi gogan nasa ma har ya shige abinsa. Gaba ya buɗe ma mama Balki ta gefen sa ta zauna, shima yana ƙoƙarin shiga Baba prof ya ƙaraso wajen, umarni ya bama Mama Bilki kan ta fito ta koma motarsa, shi kuma ya shiga gaban ya zauna yana bama Hayatu umarnin suje *_KARAMCI HOSPITAL_* asibitin Hajiya ƙarama kenan. Amsawa Hayatu yay yana satar kallon Maash dake a baya tare da Samraah ta cikin mirror. Jingine kansa yake da kujera idanunsa a lumshe tamkar bai san mike faruwa ba. Shi kuma ya tabbatar duk yana jinsu. Kallo ɗaya yay ma Samraah dake kwance kanta a saman cinyar Maash ɗin itama idanunta a rufe ya ɗauke kansa yana ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya......         🌿❤️‍🔥🌿❤️‍🔥🌿      Hajiya Sakeena na kai ƙarshen bayaninta Mansoor ya fasa wata gigitacciyar ƙara da ɗaga Centre table ɗin gabansu ya wancakalar. Babu wanda bai firgita ba. Ƙafa yasa ya bugi table ɗin da masifar ƙarfi, badan takalmin dake a ƙafarsa ba babu abinda zai hanashi jin ciwo. Da sauri Attahir ya miƙe yana ƙoƙarin riƙo hannunsa da kiran sunansa. Amma sai shima yay wani irin wancakalar da shi gefe har sai da Attahir ɗin ya zube a kujera. Cikin zafin zuciya da basu taɓa sanin yana da ita ba ya nuna Hajiya Sakeena da Mamynsa da take wani irin kuka tamkar ranta zai fita. Cikin kaushin murya da rufewar idon da fushi ya haifar masa ya ce, “Na tsane ku. Ku biyun nan ba bana son sake ganinku a rayuwata har abada. Kuma yanda kuka zama sanadin rabani da ita kuma na barku har abada!!!!!!”.      Daga haka ya figi bag ɗinsa fuuuu zai fice. Ƙoƙarin miƙewa Attahir yay cikin ƙarfin hali yana kiran sunansa. Yayinda Mamy tai wani irin fashewa da kuka ta bisa da gudu ta riƙo rigarsa. Ko juyowa ma baiyi ba yasa hannu ya kaɓe natan tare da hankiɗata yay ficewarsa. Kafin ta miƙe tabi bayansa tuni yama fice a gidan ko mai kama da shi babu a compaund. Nan ɗin ma fita Attahir yay a guje, sai dai yana fitowa napep ɗin data ɗauki Mansoor na barin ƙofar gidan. Komawa yay cikin gida da gudu bawan ALLAH duk ya ruɗe. Dan key ɗin mota yake lalube amma ya gagara ganin ko guda ɗaya. Haka ya sake fitowa da gudu ya fita shima ya tare napep ya shiga suka bi bayan Mansoor. Amma ko mai kama da shi basu gani ba. Har airport yasa suka bishi a tunaninsa can zaiyi. Sai dai nan ɗin ma babu alamar Mansoor ɗin. Abinda bai sani ba kuma Mansoor bai je airport ba, dan ya fahimci abu na farko da zasu farayi kenan dan haka yaje ya kama hotel anan anguwarsu da yasan bazasu taɓa tunanin zai tsaya anan ba. Na kwana ɗaya ya kama, dan daga yau zuwa gobe yake son sake barin ƙasar nan. Sam bazai iya zama ba. Gara yayi nesa nesa can inda bazai sake ganin kowa ba a cikinsu har ƙarshen rayuwarsa...       Duk wannan budiri da ake Dad bai ko motsa ba. Yana zaune ne kawai kamar saƙago a falon. Ba haka Hajiya Sakeena taso ba. Taso ace tana gama bada labarin nan yanda Mansoor ya fusata shima Dad ya fusata ya dinga ɗirkar Mamy da jera mata kalmomin saki uku sannan yace ta bar masa gida. Amma ba komai, ko yanzu ma ai tasan ƙurar bawai ta ƙare bane ba. Dan ita shaidace akan zuciyar Dad tamkar akku kuturu yake. Kusan zuciyar tasa ce ma yau Mansoor ya kwatanta. Shi kansa shirun da yayi ta tabbatar zuciyar ce ta kume ƴan maza wayaga kutu-ban-ban. Haka ta fito babu tausayi babu imani ta tsallake Mom da nunfashi ke neman ƙwacewa tai ficewarta. Acewarta ai itama haka Mansoor ya tsallake tata ɗiyar ɗaya kwallin kwal a duniya ya tafi babu tausayi balle imani bayan ya gama zana mata kalaman saki uku da gasa mata magana iya son ransa...      Duk neman daya dace Attahir yayi ma Mansoor amma bai gansa ba. Dole ya haƙura cikin maɗaukakin tashin hankali ya koma gida ransa duk a dagule. Yana zuwa kuma ya iske Mamy a sume a farkon shiga falo. Tashi hankalinsa ya sake yi, dan ga Dad zaune tamkar saƙagon gunki zuciya ya kumesa tamkar shima ɗin ya suma. Baima san ya sunkuci Mamy yay waje ba cikin tashin hankali yana kwala kiran sunan drivernsu..... 🪴🪴🪴🪴🪴               *_KARAMCI HOSPITAL_* asibiti ne da zamu iya kiransa tsaka tsaki a girma. Dan bai kasance ƙaton gaske ba, bai kuma kasance ƙarami ba. A ɓangaren kayan aiki komai an wadatashi da shi. Duk da sunansa asibitin kuɗi ana aiki a cikinsa tamkar ƙyauta ne saboda sauƙi da sauƙaƙama al'umma. Hakan yasa mafi yawan talakawa suke saurin garzayowa jiyya da karɓar magani a cikinsa. Sai dai da yake komai nasu a tsare yake bazaka taɓa samunsa barkatai ba komansu a tsare yake.       Kamar dai yanzu daya kasance rana ta fara ɗagawa, tako ina tsaftace yake sai ma'aikata dake ɗan kai kawo. Sannan shiru yake babu wata hayaniya ko yawan kai-kawon mutane bayan ma'aikatan saboda dokarsu ce irin yanzu ba'a zuwa duba mara lafiya sai yamma daga huɗu zuwa shida. Koda motocin su Maash suka iso ma da farko securitys ɗin ƙin tashi sukayi su buɗe saboda dokarsu ce ba'a ganin mara lafiya da dare ko safiya zuwa kafin cikar huɗu ko kai wanene, sai da Hayatu yay kiran number Hajiya ƙarama sannan securitys ɗin suka tashi cikin rawar jiki suka wangale gate ɗin. Suna gama parking Tsaki Hajiya Mammah tayi tana mita harda zagin Hajiya Ƙarama lokacin da take fitowa. Babu dai wanda yace da ita komai.         Hajiya ƙarama da kanta ta fito tana musu barka da zuwa dan ita tunda safe tana anan asibiti batama san sunje duba Samraah ɗin ba, ana gama case ɗin human right ta baro gidan. Cikin girmamawa ta gaida Baba prof.. ya amsa mata tare da mata bayanin maido Samraah da sukai nan dan a cigaba da kulawa da ita duk da dai shi ba sunanta ya ambata ba ya dai ce yarinyar dake jiyya. Amma kuma yanata tunanin a ina yasan fuskar yarinyar ne tun ɗazun. Cike da girmamawa Hajiya ƙarama ta amsa musu. Tare da musu jagora har cikin manyan ɗakunan jiyyarsu na vip na ƙarshe a daraja. Kowa baiyi mamakin rashin biyosu da Maash yayi ba, dan sai da Baba prof ya koma da kansa ya masa umarnin bari a shiga da ita kasancewar tare ya tafi da nurses dake ɗauke da gadon ɗaukar mara lafiya. Amma mi, ammakinsu ma ko kallon inda Nurses ɗin suke baiyi ba yanzun ma ya sake ɗaukarta camak yay cikin asibitin. Da kallo kawai Baba prof ya bisa abubuwa da yawan gaske na masa kai-kawo. Dan a wannan gaɓar ya gama sarewa da al'amarin jikan nasa. Sai ma yake wasiwasi anya kuwa shine ya aikata fyaɗen nan kamar yanda Nafisa ta faɗa. Dan al'amarin akwai matuƙar ban al'ajabi a cikinsa da ma ban tsoro.       Acan daga ciki suma kansu kallonsa kawai suke kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa musamman ma Hajiya ƙarama da bata ga abubuwan daya faru a farko ba sai wannan ɗin. Dan baki ta hangame har sai da taji iska na kai mata har maƙoshi sannan ta iya haɗiyewa da ƙyar.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_ ......Baba prof da bai koma ciki ba Nurse ɗin nan ya aika yace a sanarma su Paah su fito yana jiransu. Babu jimawa kuwa sai gasu ɗaya bayan ɗaya. Hajiya Mammah da Mama Balki da Hayatu sai shi uban gayyar kawai aka bari. Dan haka Baba prof ya sake aika Uncle Abdullahi yace yay kiran Hajiya Mammah saboda sanin halinta shi kuma baya buƙatar jan wannan maganar a waje shiyyasa ma da Maash ɗin yace a bama yarinyar sallama bai tanka ba. Ya kumace a kawota nan ɗin ne tai jiyya dan yasan asirinsu zai kasance a rufe tunda dai Hajiya Ƙarama ta gida ce. Rai a ɓace Hajiya Mammah ta fito. Dan itafa gaba ɗaya an ɓata mata shirinta. Dan har magana ta gama da waccan likitar akan ta riƙe Samraah har sai nan da wasu ƴan kwanaki da za'a iya fahimtar da ciki ko babu. Idan akwai ta fallasa a gaban kowa, idan kuma babu zata biya ko nawa ne aima Samraah dashensa sai kowa ya gama sani sannan ta tafi plan na gaba da za'a zubar da cikin wajen zubarwar a kashe Samraah. Sai kuma gashi cikin abinda bai wuce awa guda ba shegen yaron nan daya zame mata masifa da bala'i ya hanama rayuwarta rawar gaban hantsi tun yana mitsitsinsa ya rushe komai. Suma waɗan nan ƴan human right ɗin sai taci abu takazansu dan sun mata aiki ba'a yanda tace musu ba. Idan kuma basuyi himmar ƙarasawa ba ALLAH sai sun biyata maƙudan kuɗinta...      A ɓangaren Maash kuwa bai bar asibitin ba sai da aka gama yima Samraah dukan abinda ya dace. Duba magungunanta da sake bincikata in and out. Sai dai kuma anan ɗin ma dai doctor ɗin data duba Samraah ɗin dan ba Hajiya ƙarama bace saboda ba faninta bane. Abinda ta fara bincike da tambaya shine reping ɗinta akayi ne?. Shiru Maash bai tanka ba, bai kuma da alamar tankawar. Dan haka Mama Balki ta girgiza mata kai alamar a'a.  Rasa abin cewa tayi, dan dukkan alamu na jikin Samraah ya tabbatar da anje mata babu tausayi. Amma tunda ita Mama Balki tace ba haka bane sai ta tambayi mijinta, acewarta tana son ganinsa taji dalilinsa na nuna irin wannan rashin tausayi akan yarinya ƙarama. Kasa sake cewa komai Mama Balki tayi, sai ɗan satar kallon Maash ɗin da take ta gefen ido. Shi kuma yay masifar haɗe girar sama data ƙasa dan haka doctor ta haɗiye maganganunta a cikin rai dole.        Ruwa tasa aka sakama Samraah dan tana buƙatarsa. Kasancewar akwai cannula ɗin wancan asibitin da ba'a cire ba sai hakan ya sauƙaƙa musu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa barcin ya fara ɗaukarta dan shi dama suke buƙata tayin. Kiran wayar da Paah ya addabesa da shi ya sashi miƙewa cikin ɗan ɓacin rai sai dai bai ce komai ba bai kuma ɗaga wayar ba. Ƙofa ya nufa abinsa batare da yayima ko Mama Balki sallama ba.      Dishi-dishi nake ɗan hangosa, cikin mayen barcin dake ɗaukata a hankali batare da tunanin zai ma jini ba na furta, “Dan ALLAH ka dinga duba min Ummie akai-akai da bata abinci da maganinta. Kace kuma ina gaishet....”    Cak ya tsaya daga yunƙurin fitar da yake yi, hannayensa duka a cikin aljihun wandon suit ɗin nasa. Tamkar mai ciwon wuya ya juyo da kansa a hankali ya zuba su a kanta. Idanunta masu cikar gashi dake a ɗan kumbure har yanzu a lumshe suke. Kallon kusan minti ɗaya yay mata ciff kafin ya motsa a hankali cikin tafiyar nan tasa tamkar baya so ya fice. Da kallo Mama Balki ta bisa, sai kuma ta saki murmushin da har haƙoranta suka bayyana. A hankali ta furta, “Humm Alhaji Ƙarami”. Sai kuma ta juya ta zubama Samraah da har ta fara sauke munshari idanun nata. Shigowar Hayatu ne ya katseta. Sallama yay mata dan yasan ba lallai yau ya samu damar sake shigowa asibitin ba tunda suna tare da boss. Gashi ma acan office jiransu ake sakamakon meeting da yasa Juliet ta tara na gaba ɗaya exco ɗin companynsa na cikin Lagos dama wajen Lagos masu alaƙa da abinda ya faru. Ya kuma tabbatar dole meeting ɗin zai jasu lokaci mai tsayi....             🌺🌺🌺🌺🌺      “Magana ta gaskiya sai kun kula Attahir. Kun fa san Hajiya nada hawan jini. Yanzu badan ALLAH ya taƙaita ba a wannan faɗuwar da tayi fa komai zai iya faruwa. Dan ɗayan biyu ne. Paralysis ko heart attack. Saboda a kwanakin nan bincikenmu ya nuna zuciyarta na samun matsi sosai da yawan damuwa. Dan haka dan ALLAH ku kula. Zamu riƙeta anan zuwa 2days, ga wannan sai kaje konan pharmacy na asibiti ka samo dan data farka za'a buƙacesu”.      Numfashi mai nauyi Attahir ya sauke tare da jinjina kansa. Kafin a hankali ya ɗaura da yima doctor ɗin godiya sannan ya miƙe. Tafiya kawai yake amma shi baima san a inda yake jefa ƙafa ba. Dan shi a karan kansa yana buƙatar gadon ne a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya kai kansa pharmacy ɗin cikin asibitin ya miƙa musu takardar da doctor ɗin ya bashi kawai. Koda pharmacist ɗin ya duba ya sanar masa kuɗin baima bi takansa ba ya zaro ATM ɗin sa a wallet kawai ya miƙa masa. Hakama da aka saka adadin kuɗin bai wani dubaba ya amsa ya saka pin ɗinsa. Ledar ya amsa ya koma ɗakin da aka kwantar da Mamy.     Har dare yay nisa babu Dad babu Mansoor. Babu kuma wanda ya kirashi koda sau ɗaya yaji yaya Mamyn take. Haka ya kwana cikin asibitin shi kaɗai, sai a washe gari bayan sallar asuba yana fitowa a massalaci fita yay a asibitin dan likita ya tabbatar masa Mamy zata iya kai sha ɗaya ma bata farka ba. Kai tsaye gidan ƙaninsa na ɓangaren Ummie ya nufa. Kakarsu mace ta rasu, sai tsoho mai ran ƙarfe da ya ragema Ummie kawai. Bai tsaya kwana-kwana ba ya zayyane masa komai dake faruwa. Sosai hankalin kakan nasa ya tashi, Attahiru na gabansa ya shiga bugama sauran ƴaƴansa waya duk yace suzo yana buƙatar ganinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa duk sai gasu, ALLAH ya taimaka ma abin ya haɗa da weekend. Sake saka Attahir yay ya maimaita duk abinda ya faɗa masa. Suma ransu yay matuƙar ɓaci da wannan hali na ƴar uwarsu. Tun tana budurwa sunyi matuƙar yaƙi na ganin ta ajiye waɗan nan banzan halayen amma a banza. Kullum shari'arta da miji bata wuce akan wannan halin na son kuɗi da ƙarya. Gashi nan dai sai da takai ta watsa farin cikin gidanta da kai wa matsayar da suka dinga guje mata sannan hankalinta ya kwanta. Itama autar tasu Sakeena zama da gurɓataccen miji ashe ya canja musu ita ta koma irinta. Ɗunguma sukai su duka harda tsoho zuwa asibiti suka dubata. Sunko samu ta farka, haka duk suka jajanta mata sama-sama. Gaba ɗaya kunya ta hanata iya kallon kowa a cikinsu musamman ma Attahiru. Nauyin yaron take ji, dan yanada matuƙar haƙuri da kawaici. Duk irin banbancin da take nunawa tsakaninsa da ɗan uwansa bai taɓa ɗauka ya sakama ransa balle har taga ɓacin ran hakan akan koda fuskarsa ce. Yau ga wanda take matuƙar nunama soyayyar ya tsallaketa ya wuce akan mace. Duk da dai tasan ita duk ta jawo komai, sosai take jin dana sani da nadamar ƙwaɗayayyar rayuwarta a yau.      Kwananta biyu a asibiti babu ko ƙyallin Dad. Tana son ta tambayi Attahir tana jin tsoron jin abinda bashi zuciyarta take son ji ɗin ba. Dan tana matuƙar so da ƙaunar mijinta. Hasalima kamanninsa da Mansoor ya ɗebo yasa take fifita soyayyarsa akan sauran yaranta. A ranar aka basu sallama. Tun da suka baro asibiti taga an ɗauki hanyar gidan babanta gabanta ke faman faɗuwa. Sai dai tsoro ya hanata tambaya har suka iso. Isowarsu babu jimawa suma su Amal suka iso. Dama suna Abuja gidan kawunsu ne. Sanda zasu wuce India su aka turasu can sai yau suke dawowa.      Anan ɗin ma babu wanda yace mata komai har tsawon kwan biyu, abu ya dameta amma itama tsoron jin abinda bashi take son ji ba ya hanata iya tambaya. Zuwan Sakina biyu gidan babu mai tankama wani ita da ita. Su duka sun ɗauki zafi da juna tamkar ba ƴan uwa ba jini ɗaya. Hasalima a baya sun fi shiri da juna matuƙa, dan rayuwar ƴammatanci gaba ɗaya Sakeenar a gidanta tayita ma..       Attahir dai yakan zo da safe kullum kafin ya wuce aiki ya gaisheta. Hakama idan ya tashi sai yazo nan ya gaisheta sannan yake wuce gida. Kamar wasa a haka kwanaki suka dinga tafiya tana a gidansu. Ga baba ma sama-sama yake amsa mata gaisuwa. Baya shiga sabgarta baya kuma bata damar shiga tashi har gata da watanni biyu cif a gida. Su Amal ma tuni suka tattara kayansu suka gudu gida. Dan sunce bazasu iya zama gidan Baba ba saboda gidansu komai najin daɗin rayuwa suna da shi. Nan ko duk da ƴaƴan baban maza sun tsaya akan al'amuransa shima kasancewar matarsa ba itace kakarsu ba abubuwa da yawa sai a hankali kawai. Ta kankane komai daga ita sai nata jikokin Mamy ma sai tayi da gaske wataran take samun abinci a gidan. Dan ma Attahir baya gajiya da kawo mata kayan shayi da ƴan kayan maƙulashe. Amma itama da tuni yunwa ta kai rayuwarta ƙasa kam.........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_ ........Tun fitarsu a ɗakin jiyyar yarinyar har barinsu asibitin akan idanunta ne. Numfashi ta sauke mai nauyi tare da ture ɗan kwalin kanta baya. Dauriya kawai take da danne abinda ke matuƙar cimata zuciya. Wayarta ta ɗauka a ɗan zafafe, tai ƴan danne-danne tare da kaiwa kunnenta. Ana ɗagawa daga can ta ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai kuma cikin ɗan farin ciki mai gauraye da sauran damuwa ta furta, “Sabon labari”.      Cike da zumuɗi daga can akace mata “Name fa Hajjaju masu Lagos da kayan cikinta.”          “Hummm Jannifer bar batun wasa Please. Yarinyar nan ce fa suka maido asibitin nan yanzu”.      “What! Kina nufin Samraah?”.   “Yess. Yanzu haka tana nan tare damu. Ban san miya faru ba suka maidota nan ɗin. Naga dai mutuniyarki a zafafe cikin matuƙar damuwa kuma. Yanzu kam na fara zargin akwai abinda take ƙullawa. Na kuma yi alkawarin sai na bincikosa a koma ina taje ta bizne shi”.        “Karki wani damu Hajjaju wannan duk mai sauƙi ne. Ko ni nan na isheta. Har mi akai akayi Alaja Nafee kuma. Matar da bata iya komai ba sai da shawaran banzan Madan Rubayya ɗin nan. Ni dai kawai yanzu shawaran da zan baki kawai kiyi ƙoƙarin ki kula da yarinyar nan da ƙyau, tunda dama tun farko kayanki ce. Kin zauna sakaci ne Alaja Nafee ta nema ƙwacewa. Banzama irinta da ta ƙare a ƙarƙashin guzumomi irin su Rubayya. Dan bana raba ɗayan biyu shakkar Rubayya ɗinne ya hanata taya yarinyar kafin ke, tunda itama ai mayyar ce. Saboda haka kiyi amfani da wannan damar akan ita yarinyar kiyita banka mata maganin da zai fidda mata sha'awar namiji gaba ɗaya a ranta, ina tabbatar miki da kanta zata kawo miki kanta tana kukan ki mora albarkacin jikinta. Haba Alaja Lawusa kamar baku bane Lagos ɗin. Ni fatana ma idan zakije honeymoon da ita aje dani koda a ƴar riƙon handbag ce”.      Dariya mai ƙayatarwa Hajiya ƙarama ta saki, tare da sake lume kanta a cikin kujera idanunta a lumshe tana siffanta cikakkiyar surar Samraah data jima tana birkita mata lissafinta. Dan tun randa Jannifer tayi kiranta ta sanar mata da zuwan yarinyar gidan matsayin gift da Mashi'a tai shirin kawoma Hajiya Babba dan ta kula da ita ta gama jin ƙaguwa da son ganin yarinyar. Saboda haka ta azalzali Paah suka dawo Nigeria washe gari badan ma sun kammala abinda ya kaisu ba. Koda suka iso tai ido biyu da Samraah sai da numfashina ya nema shiɗewa. Dan yarinyar irinsu ne ake kira da full option. Komai yaji yanda ya kamata. Sai dai kash abubuwa da dama sukai mata katanga da hakan, tayi ƙoƙarin riƙe kanta har zuwa sanda ta gama shiryawa sai kuma ga wannan abin ya faru da yay matuƙar ƙona mata rai, dan a yanzu haka ita kaɗai tasan irin kalar zafin yaron nan Awwab da take ji a rayuwarta. Wani irin kishi take ji tamkar ta kashe banza a wuce wajen dan son Samraah take na gaske. Har ma ta gama yankema kanta shawarar auran yarinyar zatayi ta ɗauketa daga Nigeria zuwa duk ƙasar da take so sai ta dinga kai mata ziyara....        “Alaja!”.    Jannifer ta katse mata tunani. Firgigit ta dawo hayyacinta tana mai sauke nannauyan numfashi. Cike da basarwa taja ɗan sirrin tsaki da faɗin, “Sorry Jannifer na tafi wata sabgar ne kuma.”      Dariya Jannifer ta ƙyalƙyale da shi daga can, cike da shaƙiyanci ta ce ko dai kin tafi tunanin kayan alatu ba”.     Murmushi Hajiya Ƙarama tayi tana mai cije lips ɗinta. Kafin a hankali ta ce, “Ke dai Jannifer sheɗaniya ce wlhy. Lallai da ace bakiyi ridda daga musulimci zuwa kiristanci ba da ba ƙaramar sheɗaniyar matar hausawa musulma akayi ba. Amma yanzu mun bar musu, dan inba ma wanda ya sani ba taya zai taɓa yarda kin haɗa iri da fulani. Humm ALLAH dai ya jiƙan General. Ya tafi yabar baya da ƙura. Maybe da za'a shawarcesa a dawo da shi duniya yaga Munirra ɗinsa yanda ta koma kamar bata taɓa haɗa jini da yan arewa da musulunci ba da dakansa zai kashe kansa ma wlhy”.         “Hummm Hajjaju kenan masu Lagos da jama'ar cikinsa. Ai duk nawa wasan yara ne. Idan kuna guri mu kuma wake ta tamu ƙananun ƙwari. Mufa a riddar kawai muka tsaya sai ɗan cinikin goron nan da muke kafawa a faifai da ɗan hutawar nan muna more ƙuruciya. Ku kuwa fa, idan akace ai tone-tone ai kema musulman sai sun gwammace riddar kikayi wlhy”.       “Uhhm to ya isa. Dan ke baki gajiya da zakuɗe-zakuɗe. Yanzu dai sai anjima idan na tashi zan zo gida na sameki mu ƙarasa. Dan zan ɗan shiga theater”.      “Hummm” kawai Jannifer tace daga can tare da yanke wayar tana dariya. Itama sai Hajiya ƙaramar tai dariyar kawai tana ƙoƙarin ajiye wayar, a dai-dai nan wani kiran ya sake shigo mata. Ido ta zubama number na tsawon lokaci, YALLAƁAI ɓaro-ɓaro ya fito. Mamaki ya sake kamata dan rabon da mai number yay kiranta ta jima sosai, dukan tara-tara ƙirjinta ya shiga hi har sai da wayar ta kusa yankewa ta dawo a hayyacinta. Da sauri ta ɗauka tana miƙewa ta nufi ƙofar office ɗin ta murza key cike da rashin gaskiya....       _🤔Hummm wai ina matan nan suka dosa ne?  Sannan waye yay kiran Hajiya Ƙarama kuma? Idan na fahimta dai Hajiya Ƙarama na waya da Madam ne a farko, matar data ɗakko Samraah daga Abuja zuwa Lagos. Tab ɗin babbar magana. Ashe ita ɗin musulma ce shine tai ridda. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Anya wannan duniya kuwa. ALLAH mun tuba badan halinmu ba😭🙏._       __________________    *_THREE DAYS LATER_*           Kwanaki uku kenan da faruwar komai. Sam Maash yaƙi yarda ya zauna da family ɗin nasa akan batun Samraah. Dan haka ran kowa a matuƙar ɓace yake. Amma shi ko'a jikinsa sai manna musu hauka kawai yake. Dan gaba ɗaya ma ya maida hankalinsa ne akan binciken yanda akai containers ɗin companyn sa suka ɗiba yara da wiwi saɓanin lodin kayan abinci. Dan suna shirin tunkarar Mr Paul ne da ƙarfinsu a court saboda sun shigar da ƙara ne kafin shi bisa shawarar lawyers ɗinsu.        Ta gefe kuma ga jikin Ummie da ya rikice. Ga kuma Samraah dake asibiti har yanzu ba'a sallamota ba itama, sai dai wata irin kulawa take samu ta musamman da tattali a wajen Hajiya ƙarama har Mama Balki ta fara shan jinin jikinta. Sai dai abinda Mama Balki bata sani ba ita kanta Samraah nazartar Hajiya ƙarama take sannu a hankali. Gefe kuma tana kaima ALLAH kukanta. Koda labari Mama Balki bata sanar mata da ciwon Ummie ba sai yau da Falak tai kiran wayar Mama Balkin, a lokacin ita kuma ta ɗan fita dan haka Samraah ta ɗaga. Har yanzu basu taɓa haɗuwa da Falak ba sai dai tana cin abincin gidanta kullum. Bata da lafiya ne tana fama da tsohon ciki shiyyasa bata zo tama dubata ba, sai dai sun gaisa ta waya har kusan sau uku. Yanzun ma sun gaisa cike da kulawa ma juna tamkar dama can sun san junan nasu, kafin Samraah ta sanar mata Mama ta ɗan fita ne, amma idan ta dawo zata faɗa mata sai ta ƙara kira.      Daga can Falak tai murmushi da faɗin, “Okay ba damuwa ALLAH ya ƙara lafiya, dama zanji ko yaya jikin Ummie ne dan na kira Yaya Hayat ashe garin sauri yama bar phone ɗin a gida, gashi yanda ya fita a hargitse duk na kasa nutsuwa”.          Ɗan jimmm nayi zuciyata na bugawa da sauri-sauri jin ta ambaci Ummie, da ƙyar na iya tambayarta “Ummien Maash Mansion? Wani abu ne ya sameta?”.      Batare data fahimci kan tambayar ba cikin damuwa muryarta na rawa ta ce, “Eh ita, kin san kwana biyun nan jikin nata duk babu daɗi, to yau dai da alama ya tsananta ne dan shima Yaya Hayat a rikice ya fita TJ ya kirashi. Wlhy ina tausayawa Ummie, da ace inada wata babbar dama akan baiwar ALLAHr nan abinda zan farayi shine tsayawa akan samun lafiyarta, amma muna gani an hanamu taimakonta. Wanda keda ƙarfin yin hakan kuma an kulle masa tunani gaba ɗaya, dan wlhy da ace Yaya Awwab basu shiga tsakaninsa da lafiyar baiwar ALLAHr nan ba da kowama yaci ubansa, ai sun san shi ɗin ba kanwar lasa bane har Baba prof ɗin da Paah ba iya tankwarashi suke ba. Amma ba komai ALLAH yana nan, watarana sai labari”.        Tuni ma ni ba fahimtar zantukanta nake da ƙyau ba, rawa sosai jikina ke mun, ga hawaye suna bala'in gudu a saman fuskata. Ashe shiyyasa duk jiya bai zo asibitin ba, yau ma haka. Ko Hayatu mai ƙoƙarin zuwa sama da sau uku yana kawo musu abubuwa jiya sai dare ya shigo ya duba ta. Abinci ma TJ ne ke kawowa. Amma Maash tun daren shekaran jiya da zai tafi take cemasa ya dinga duba mata Ummie da bata abinci bai sake zuwa ba, harta ƙullacesa ma ita da, da tunanin ya gama cin moriyat ganga zai yada kwautrnta, ashe abinda ke faruwa kenan...       “Ya subahanallah Samraah! Wani abu ke miki ciwo ne? Ko tashi kikayi da ƙarfi kika fama ciwon?”.     Mama Balki ce mai maganar nan a rikice. Ɗagowa nayi ina kuka mai tsanani dan shashshekar da nake tasa har fisga numfashina keyi. Lallashina Mama Balki ta shiga yi tare da bani ruwa tace nasha. Da ƙyar na amsa nai maƙwarwa uku, jikinta ta jawoni ta rungume, hakan sai ya taimaka min wajen samun nutsuwa na fara sassauta kukan. Kaina na a saman cinyarta tana shafa gashina ta ce, “Samraah”.        Cikin dasashjiyar muryata na amsa mata da, “Na'am Mama”.    “Mike faruwa?”.   Da ƙyar na iya danne kukan dake taho min na ce, “Mama Ummie. Ashe bata da lafiya amma shine babu wanda ya sanar min”.      Iska ta ɗan furzar cikin damuwa. Kafin ta ce, “Waye ta faɗa miki?”.     “Falak”. Na bata amsa ina sharce hawaye.......✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_ *_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._ *_My account on TikTok_* https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1 *_Instagram_* I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv *_WhatsApp_* https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5 ___________ ......Kanta ta girgiza da faɗin, “Ni ban san sai yaushe bakin Falak zai iya dinga koyon shiru ba. Kiyi haƙuri an ɓoye miki ne saboda kema ga yanayin da kike ciki. Shekaran jiya ne Alhaji ƙarami ya shiga yana ƙoƙarin bata abinci shine fa kawai jikin ya rikice. Ta jimasa ciwo sosai a hannu da ƙyar aka iya fiddoshi a ɗakin, daga nan duk wanda ya shiga da duka take korosa, to yau kuma sai ta yanke jiki ta faɗi saboda kwana biyun nan bata ci bata sha rashin abinci jikinta yayi week. Amma ki kwantar da hankalinki zuwa yanzu sun ce Alhamdullah komai ya dai-daita. Dan Hayatu ma ya tabbatar min tana barci saboda drip ɗin da aketa ƙara mata.”       Duk da na ɗan ji nutsuwa sai da na sake sharce hawaye, ɗan shiru mukayi kafin a hankali nace, “Mama”.     Da kulawa ta amsa min da, “Na'am Samraah”.         “Mama a yanzu sai nake ganin kamar shi yafi dacewa ma abinda ke tare da shi ya rabu da shi kafin a samu nutsuwar yima Ummie magani. Duk da dai wani abu ya jima yana damuna. Yanzu duk kuɗinsa ace gidan nan babu cctv camaras tako ina?”.        “Tabbas gaskiya kika faɗa Samraah. Sai dai mun kwatanta hakan muma bai yiwu ba, a dalilin tsanar magani da Alhaji ƙarami yayi tun yana ƙaraminsa. Ko yaya ruwa ya surka wlhy bazai sha miki shi ba koda da kala ne. Shiyyasa yin maganinsa keda matuƙar wahala. Gashi kuma shi ba'a zaune yake ba waje ɗaya, duk yanda muka so fara bashi koda ruwan addu'a ne sai kiga abin ya zama shiririta. Ina da tabbacin kuma wanda ke wannan aikin kullum cikin sabuntashi suke bawai sun koma sun kwanta bane suma. Maganar camara kuwa ai Alhaji ƙarami yasha sakawa amma sai a wayi gari duk an ciresu. Har ɓoyayyar camara an saka a gidan nan amma kamar abin maita wlhy sai da aka cireta. Hakan na nufin koma su waye a biye suke, shiyyasa ma kikaga ina sake jin tsoron al'amarin gidan nan da mutanensa. Dan idan bana jikinka ba banga wanda zai dinga maka wannan bita da ƙullin ba a nesa da kai”.      Baki na buɗe zanyi magana sai naji kamar amalar motsin tsayawar mutum a ƙofa. Shiru nayi bance komai ba, sai kuma kamar ance na ɗaga ido na hango inuwa ta jikin window. Magana Mama zatayi na wayance ina mai zame kaina da ga cinyarta na ce, “Mama barci nake ji. Dan ALLAH idan Nurse ɗin nan tazo kice bana son allurar nan ni nama warke karki bari tamun”.         Kallon mamaki da naga Mama namun yasa nai mata nuni da window da ido. Tuni ta ɗauki haske kasancewar dama a ankare take. Itama sai ta wayance ta shiga ƴar dariya da faɗin, “Ja'ira ai allurar nan sai an kaita har ƙarshe, bari ma Hajiya tazo zance ta sake ƙara miki kwana biyu kiyi digir dake yanda zamu koma gida da ƙarfinki”.        Shagwaɓa na shiga mata da faɗin ni bana so. Itako tana dariya. Daga haka mukayi shiru. Kwanciya nayi zuciyata na faman kai-kawo. Tabbas lokaci yayi fa dazan dawo hankalina. Dan na fahimci in har shi bai fita a halin da suke sanyashi ba baiwar ALLAHr nan bazata taɓa samun ingantaccen lafiya ba. Domin sauƙi yana samuwa a gareta, sai dai yanayin kwan-gaba kwan-baya da ake fuskanta yasa al'amarin ke taɓarɓarewa. Idan kuwa har za'a iya hana cctv camaras zama lafiya to lallai waɗan nan mutanen ba ƙaramin shiri sukai ba. Suma kuma suna buƙatar a shirya musu yanda ya kamata. Dan dole wayo al'amarin yake buƙata da hikima kamar yanda suma suke komai ta cikin basira”. Wannan tunane-tunanen da hawayen da suka kasa barin idanuna ne suka haifar min da zazzaɓi mai zafi, gashi naƙi gayama Mama har bayan sallar isha'i. Dan da ƙyar ma nayi alwala saboda sanyin da nake ji. Ina idarwa na haye gado na kwanta tare da duƙunƙunewa cikin bargo. Sosai na gaji da zaman asibitin nan, fatana kawai ALLAH yasa yazo dan shine kawai zaisa a sallameni. Yan gidansu dai dama babu wanda ya sake zuwa sai Hajiya ƙarama da nake gani, ita kam kullum ne sai ma tazo sama da sau uku, sai daga baya na fahimci ai dan asibitinta ne shiyyasa itama muke yawan ganintan.....          🩸🌟🩸    Sosai damuwar halin da Ummie ke ciki a kwana biyun nan yasa bai sake waiwayen asibitin ba. Duk da kuwa wani sashe na hankalinsa na'a can ɗin. Sai dai rashin isashen lafiya shima dana lokaci ta sashi baiyi wani yinƙuri ba. Yau kuma zafi da ƙuncin da gidan ya masa matuƙa ya sashi ɗan kimtsawa bayan ya dawo sallar isha'i. Tun la'asar ya kora Hayatu gida dan haka shi kaɗaine a sashen sai Laalah da TJ dake leƙowa akai-akai duba shi shi da Shu'aibu amintaccen guard ɗinsa. Tsaff ya fito yana zuba mayataccen ƙamshin nan nasa tamkar ba dare ba. Tj da Shu'aibu na ganinsa suka miƙe da sauri, hakama sauran ma'aikatan gidan sai gaisuwa suke miƙawa. Hannu kawai yake ɗaga musu dan kwana biyun nan miskilawan ne a kusa. Da ga shi sai TJ da Shu'aibu sukai fitar dan hana sauran guards ɗin binsu yayi. Tj ke driving Shu'aibu a gefensa. Shi kuma yana baya zaune idanunsa akan wayarsa yana daƙila. Kicin-kicin fuskar nan take babu alamar ya taɓa sanin minene ma dariya.      Cike da girmamawa TJ ya ce, “Boss ina muka nufa?”.     Shiru bashi da niyyar amsawa. Sai da ya mula dan kansa ya furta, “Hospital”.      Cike da girmamawa TJ ɗin ya amsa masa tare da ɗaukar hanya. Har sun gota wani bakery yace TJ ɗin ya dakata. Tuna duk lokacin da zasu je asibitin tare da Hayatu sai ya sa an tsaya ya sayi wasu abubuwan ya sashi cewa a dakatan. Shima TJ ɗin tun bai furta ba ya fahimci abinda yake nufi tunda dai koda yaushe da shi ake zuwa asibitin shima. Fita yayi zuwa cikin bakery ɗin batare daya amshi wani kuɗi ba, dan boss ya wuce fiye da haka a wajensu ai. Bai wani jima ba ya fito ɗauke da ledoji masu ƙyau har guda uku. Booth ya buɗe ya sakasu sannan ya dawo cikin motar. Zuwa yanzu ba wayar yake daƙila ba kansa ya kwantar a jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Koda suka iso ma sai da ya ja kusan mintuna biyu tamkar mai nazarin ta yanda zai shiga cikin asibitin sannan ya fito. Yana gaba cikin takun nan nashi na ƙasaita da isa su TJ na biye da shi. Babu yawaitar mutane har ma ma'aikatan jefi-jefi ne. Ko kallon wanda suke a reseption ɗin kuwa baiyi ba yayi wucewarsa. Sai su TJ ne suka gaishesu. Suko suka bishi da kallo tamkar wasu tsoffin mayu. Sai faman washe bakuna suke yau gasu ga Maash, mutumin da yafi kuɗi wahalar gani a Nigeria. Dama wasu a abokan aikinsu sun sanar musu da zuwansa a kwana biyun nan, sai dai su basu taɓa cin karo da shi ba sai yau ɗin... Har yanzu duƙunƙune nake a cikin bargo ina rawar sanyi dan zazzaɓi nake ji sosai. Ga hawayen damuwa da halin da Ummie ke ciki sun kasa tsayawa a idanuna. Ita mama Balki ta ɗauka nayi barci ne, dan haka ta maida hankalinta a kallon tv tana sauraren wa'azin malam Ali isa fantami da aka saka a African tv3. Knocking ƙofa da akayi a hankali kamar abin dole ya sata rage ƙarar tvn, shiru kamar baza'a sake ba sai kuma aka ƙara. Miƙewa tayi zuwa jikin ƙofar tana tambayar waye? Jin ba'a amsa ba ta buɗe. Ni dai duk ina jinsu amma da yake har kaina na'a cikin bargo ba ganin komai nake ba.      Murnar da naji tana yi da ambaton sunan Alhaji Ƙarami ya sanya gabana faɗuwa. Sai ko ga mayataccen ƙamshinsa ya gama isowa har cikin hancina. Wasu muryoyi biyu naji suna gaisheta da tambayarta mai jiki. Na gane muryar driver ɗinsa. Ɗayan ne dai ban gane waye ba amma nasan ba hayatu bane ba. Sai da naji alamun fitarsu da rufe ƙofa sannan shima naji muryarsa a daƙilen nan can ƙasa-ƙasa kamar abin dole yana gaida Mama. Ita ko da kulawa take amsa masa da tambayarsa jikinsa da kuma na Ummie. Nan ɗin ma da ƙyar ya amsa itama yana tambayarta ya mai jiki. Itako da fara'a ta ce masa, “A jiki da sauƙi sosai. Yau ne ma ta so birkicewa saboda samun labarin jikin Ummie daya motsa da tayi. Dan har bayan sallar magriba ɗin nan tana shartar hawaye sai da na ɗan mata nasiha sannan tai shiru, inaga shine ma dalilin kwanciyar da wuri sai kuma barci ya ɗauke ta. Banji yace komai ba, sai dai haka kawai na dinga jin kaifin idanunsa a jikina. Shiru ɗakin na kusan minti ɗaya sai kuma naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa. A zatonta shine ya fita, dan haka cike da shagwaɓa na janye bargon daga saman fuskata zanyi magana da Mama. Zuuuu naji jinina na falfala uban gudu ta cikin jijiyoyina tsabar shock ɗin cin karo da abinda nai zaton shi ya fita. Da sauri na kauda kaina na sake maida fuskata cikin bargon.         A bazata naji alamar an zauna a kusa da ni, Ji nai na sake daburcewa kamar zan fasa ihu, amma sai na dake tare da yin luff a cikin bargon ina addu'ar ALLAH yasa kada yace sai na buɗe kaina........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_* _(Itama nama ce)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_ _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒏𝒊𝒏𝒆_ ......Shiru ɗakin har na fara murna. Kusan mintuna uku muna a haka babu motsin komai sai naji yayi ɗan gyaran murya. Idanuna na sake rumtsewa da ƙarfi batare da na yarda na motsa ɗin ba dai. Sake yi yayi, nan ma naƙi na motsa, sai da yay ta uku sai kuma a hankali ya ɗaura da faɗin,       “Dama Ummie c....”     A zabure na yaye bargon gaba ɗayansa. Na ware dukan girman idanuna a kansa. Lips ɗina na rawa a marairaice na ce, “Ummie mi?”. Maimakon amsa min sai kafe cikin idanuna yayi da nasa cat eyes ɗin masu matuƙar girma da yalwar gashi. Wani irin tashi tsigar jikina tayi, sai kif-kif kawai nake faman yi da idanu. Sai faman kokawa nake da numfashina dake seizing.          “Stubborn girl”.     Nakasashiyar muryarsa ta daki cikin kunnena duk da kuwa cikin low voice yayi ta, badan ma idanuna na akansa ba babu yanda za'ai na jisa dan pinkish lips ɗinsa ne kawai suka motsa a hankali. Kamar wata sakarai na jujjuya masa kaina a hankali. Motsa lips ɗina dake ƴar rawa na shiga yi, da ƙyar na iya haɗa kalmar, “Mi ya sa mu Um mie?” a rarrabe ina rissinar da idanuna da suka ciko da hawaye. Dan duk yanda na ƙudirci masa tsiwa ko kallon cikin idanunsa nayi magana sai naji sam na gagara yin hakan. Mutum ne mai masifar kwar jini da cika wuri. ALLAH ya azurtashi da wani irin girma a gaban duk wanda ya tsaya koda ace ya fisa a shekaru da matsayi. Saukar tattausan tafin hannunasa saman fusakata ya sani sake ɗago idanu da sauri na kallesa. A cikin nashi cat idanun suka sake faɗawa. Kallon juna muke a wani irin yanayi har na tsawon shuɗewar wasu sakanni. Kafin a kasalance na motsa nawa dake tara ƙwallan da ban san na minene ba. Shi ko har a lokacin kallon nawa yake yi batare da ya ƙyafta ba, sai ma cikin wani irin soft voice and silent and slowly ya furta, “She is missing you, and she need you”.         “I miss her too”. Na faɗa nima a hankalin ƙwallar data cika min idanu na gangarowa. Idanunsa ya sake ɗan lumshewa tare da buɗewa a lokaci guda ya cigaba da kallona ina kuka sosai harda shashsheka. Shi bai lallasheni ba, bai kuma janye hannunsa dake a kan fuskata ba har yanzu. Tsawon mintuna biyu ina kukana, dan shirunsa sake tunzurani yake. A bazata matuƙar bazata cikin low voice ɗin sa ya furta,       “Samrh”.    Cak na tsaya da kukan da nake, tare da ɗago jiƙaƙƙun idanuna na kallesa. Kallon nawa shima yake da shanyayun nashi da suka canja launi zuwa golden an blue.         “Why are you crying?”.      Ya sake faɗa muryarsa na sake komawa can ƙasan maƙoshi. Samun kaina nayi da sake sakar masa sabon kukan. Tare da riƙo hannunsa dake akan fuskata na ƙan ƙame.       Idanunsa da suka gama canja launi kawai ya zuba mata. Sai Adams apple ɗinsa ne ke faman kaiwa da komawa a cikin maƙoshinsa. A hankali ya kai ɗayan hannunsa saman kafaɗarta, riƙota yayi tare da ɗagota gaba ɗayanta batare da ya janye hannun nasa data ƙanƙame ba sai da ya kaita gab da jikinsa sannan ya janye ya turata cikin jikin nashi gaba ɗayanta. Tsam ya rungumeta yana mai lumshe idanun nasa ƙam-ƙam shima saboda zafin da jikinta ya ɗauka duk da da akwai kaya a jikinsu su duka sai da ya bala'in ratsashi.          Ni kam jina a jikin nasa ya sakani sake fashewa da kuka. A hankali na fara ɗan dukan bayansa ina faɗin, “Why! Why? Why? Suke wahalar da rayuwarta? Mita musu da zafi haka? Da ga ganinta She is an innocent and strong woman. Basu barta haka ba, sun rabata da ku jininta da zata ji sanyi a wajen ku. Natsane su, wlhy na tsanesu. I promise my self sai na ɗaukar mata fansa koda zasu maidani fiye da yanda suka mata. Sai na sakasu gudun ceton rai da babu mafaka Ya Awwab. I promise....”      Kuka ya sake sarƙeta. Sai wani irin jan nunfashi take a sarƙe kamar mai ciwon asthma. Da sauri ya rabata da jikinsa, tare da kwantar da ita a kan cinyarsa. Sosai numfashin nata ke fisga, hannayensa ya saka duka biyu a kumatunta ya shiga ɗan bubbugawa da kiran sunanta.          “Samrh! Samrh! Please keep calm. I know you can, please calm down. Hundred percent I am with you.”       Ina da gaske ƙoƙarin ƙwacewa numfashin nata yake. Ai baima san ya figi bottle na ruwa dake a side drawer ba ya zuba a hannu ya shafa mata duk da kuwa tana numfashi, sai kuma yay saurin kai mata ruwa a baki amma bakin ya gama datsewa ruwan yaƙi shiga. Da sauri ya kai kan nasa bakin ya zuƙa, batare da wani tunani ba ya ranƙwafo kanta ya ɗaura lips ɗinsa a saman nata ya shiga juye mata ruwan tare da riƙe hancinta. Wani masifar jan nunfashi tayi ta baki sai gashi ta zuƙe ruwan gaba ɗaya. Hancin nata ya saki tare da janye bakinsa. Ita kuma ta fara tari sosai. Sake ɗagota yayi a hankali ya maidata jikinsa ya rungume suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sunfi mintuna uku a haka sai da ya tabbatar zuciyarta ya gama sauka sannan ya raba jikinsu ya kwantar da ita a gadon a hankali...            Kasa buɗe idanuna nayi, sai ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jajjere. Jin saukar abu mai taushi da ƙamshi a saman fuskarta ya sani buɗe idanuna a hankali. Shine ke goge min hawaye da farin handkerchief ɗinsa tass. Idanunsa ya saka cikin nawa har ya gama. Batare da ya janye handkerchief ɗin ba da ɗan yanayin lumshe idanu da buɗewa ya furta, “Miyasa fitina baya miki wuya? Samrh! Ba'a gaggawa a al'amarin maƙiyi, idan ba haka ba zai fika gudu ne wajen cimma manufa. Lokacin da zaka isa sai ka samu shi har ya gama ya juyo. Be a gentle okay”.      Sosai zantukan nasa suka shigeni tare da canja min wasu tunanina da yawa a kansa. Cikin suɓutar baki muryata a dusashe na furta, “Kana nufin kaima duk abinda ke faruwa kana sane?”.         A bazata naga ya wani ɗan taɓe gefen small pinkish lips ɗinsa da lumshe idanunsa sannan ya saki murmushi. Bily idan nace miki kaɗan ya rage zuciyata ta ɓaro akan murmushin nan nasa da salon da yayisa ki yarda da ni kawai. Badan yafi kowa iyawa bane, sai dan murmushi ya kasance ba ɗabi'arsa bace. Amma tabbas magana ta gaskiya murmushin ya ɗebeni iya ɗiba. Dan kaɗan ya rage na fallasa ɓoyayyen al'amarin da na jima ina binnewa a kansa.       (Kin sani a duhu mutuniyar, kodai kin jima kina son Maash ne?).      “Hummm Bily kenan abar dai zancen sai lokacin yinsa yayi”. Na faɗa cikin ƴar dariya.     (Lallai kam, to shike nan na bari muje zuwa labari).        Yanda yay murmushin har ban san na kafesa da mayataccen kallo ba.  Idanunsa ya ɗan waro min waje da ɗagesu alamar kallon fa?. Cikin sauri na kauda fuskata gaba ɗaya ina tura baki da faɗin, “Miye abin kallon ma anan”.        Bai tanka min ba, sai ma ɗan kauda kansa da yay gefe. Banyi zaton jin shirunsa a wannan gaɓar ba. Amma nima dai sai na basar kawai tare da ture hannunsa na janye sauran jikina dake a nasa tare da jan bargo na juya masa baya. Dan in banyi hakan ba akwai babbar matsala, dan komai zai iya fitowa saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri abinda ke can ƙasanta a ɓoye na azalzalota.        Shiru ban sake jin motsinsa ba. Ban kuma yarda na kallesa ba har fin mintuna biyar. Sai a lokacin naji motsin buɗe ƙofa, ɗan juyawa nai kaɗan. Sauka idanuna sukayi akan bayansa dai-dai yana ƙarasa ficewa da jan ƙofar ya rufe a hankali. Nima lumshe idanuna nayi ina sauke ajiyar zuciya. Sai kuma na sake dunƙule jikina a cikin bargon dan ji nake kamar zazzaɓin na ƙaruwar min ma. Mintuna bai fi huɗu da wasu sakanni ba aka sake buɗe ƙofar, idanun na sake buɗewa a hankali. Yanzun kam Mama Balki ne da Doctor sai shi a ƙarshen shigowa. Hannayensa duka biyu a cikin aljihun baƙin wandonsa. Idanun na maida kawai na rufe, dan nasan bai wuce akan zazzaɓin jikina yaje yayo min wannan gayyar ba.          🩸🌟🌟🌟🩸 A hankali take faman kaiwa da komawa a cikin ɗakin nata kai kace safa da marwa take ko motsa jiki. Sai dai sam ba haka bane. Abubuwane masu yawa ke matuƙar damunta da cizar mata zuciya. Dan tun zaman da sukai da Yallaɓai ɗazun da magrib ta gagara samun sukuni. Gaba ɗaya taji ta kasa komawa asibitin da taci burin komawa dan akwai wani baƙo da zatai mai muhimmanci. Maganganunta da Yallaɓai ne suka shiga dawo mata dalla-dalla tamkar a yanzu suke tattauna su....     “Yaushe yarinyar nan tazo aiki gidanku? Waye kuma ya kawota?”.           “Lokacin muna Dubai muma zuwa kawai mukai muka sameta anan. Amma ance Mashi'a ce ta kawota”.       “Mashi'a?!”.     “Yes ita fa. A cewarta kuma ta kawota ne as a birthday gift wa mahaukaciyar matar can. Tunda masu aikinta sun sake guduwa a lokacin babu mai kula da ita”.      “A ina ta ɗakkota?”.    Ɗan jimm tayi, sai kuma ta ce, “Gaskiya wannan ne ban sani ba”.        Kasa sake cewa komai yayi, sai ma kai-kawo daya shiga yi hannayensa goye a bayansa..........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*